Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, January 28, 2021

SURUKATA CE SILA COMPLETE HAUSA ROMANTIC NOVELS WATTPAD

adsense here

SURUKATA CE SILA COMPLETE hausa romantic novels wattpad

 [19/12, 18:07] Hassan Atk: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 *SURUKATA CE SILA*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


*TRUE LIFE STORY*


BISSIMILLAHIRRAHMANIRRAHIM


BA MUYISHI DAN WANI KO WATA BA LABARINE DAYA FARU DA GASKE,DA WATA BAIWAR ALLAH,DAN HAKA IN KINCI KARO DA WANI ABU DAYAYI SHIGE DA RAYUWARKI ARASHINE.*BY**ZAHRA SURBAJO*


          *AND*


*HUMMY LUV**1-2*"wallahi baze yiwuba hakurina ya kare a gidannan,yarinya kamar mayya kin nace kin like aguri alhalin baki da amfani,wlh idan bakisa dana ya sakekiba sena kashe ki tunda ni kinsa yafi karfina kin mallakeshi"cewar wata mata dattijuwa,me kimanin shekaru hamsin aduniya,


Tsugunne take agabanta tana kuka,se digar ruwa take dan kayan jikinta gaba daya ya yi sharkaf da ruwa.


Bakinta na rawa sabida sanyi take fadin.


"inna don Allah kiyi hakuri,wlh ban mallake miki yaroba,kigafarceni,don Allah"


Wani wawan mari ta dauketa dashi wanda sabida zafinsa seda ta fadi kasa daga tsugunon da take.


ita ko tsohuwar cigaba tayi da masifa.


"Dan ubanki ni fes nake kallonki ke baki isa kimin kwarkwasa ba,da har zaki wani shake murya kina ban hakuri,Wallahi Jawahir na tsaneki natsani rayuwarki,duk sanda naganki kina numfashi ni nawa yi yake kamar ze tsaya,ina me shawartarki dakifita daga rayuwar dana tunkan nai miki illah"


Wayyo jawahir hannu tasa ta kama kafar innan,tana kuka me tsuma zuciya tana fadin.


"inna ki tausayawa zuciyoyin da basu san komai ba se kaunar junan su,don Allah karki rabani da Jabeer ina masa son dani kaina bansan adadinsaba,shima kuma yana sona,Daki rabani sa Jabeer ciwon sonshi da rashinshi ya kasheni na yarje ke ki kashenin da kanki,amman don Allah karki rusamin farincikina"ta karasa maganar cikin matsanancin kuka.


"Uban waye ya shaida miki ina son farincikinki jawahir?nifa kaunarkice banayi,sam bana sonki ki kyalemin dana,amman matukar baki amince da zancena ba wlh sena sabauta rayuwarki,mayya kawai me gadon maita"


Tana kaiwa nan azancanta ta hankadeta tabi takanta ta wuce tana ci gaba da masifarta.


Da kyar Jawahir ta mike daga inda ta yar da itan,jikinta duk ya baci da kwata haka ta nufi dakinta tana dingishi dan da dukkan alamu taimata targade akafa takatan da tayi.


Tana shiga dakinta Toilet ta shige,ta tube kayan,ta yi wanka,sukuma ta daurayesu da ruwa,dan ko sabulun da zata wankesu se taje gurin inna ta amso yanzu ko inna fushi take da ita tasan ko taje bazata bata ba.


Cikin uwar dakanta ta shiga inda ta dauko wata doguwar riga tasaka,bata tsaya shafa maiba tabi lafiyar gado,badan taji dadiba,sedan tayi kuka kamar yadda tasaba kullum kwanan duniya.


Bacin ranta na yau yafi na kullum,tunda yau ne Jabeer ke dawowa daga Abuja inda yake ayki,tayi kwalliyar tarbarshi gashi mahaifiyarshi ta bata mata su,tayi girki me dadi dominsa tazo ta shirya masa adaki mahaifiyarshi tasata ta kwaso ta kai dakinta dan kawai ta kuntatawa rayuwarta,


karshema jikata tayi da ruwan sanyi sabida tsabar keta,haka taci gaba da tunaninta tana kuka gamida tausayin kanta,


Tananan kwance ta jiyo karar mota,alamun Jabeer ya dawo,gabanta ne yayi wani mugun faduwa dan tasan dawowarshi daidai yake da karuwar tashin hankalin da take ciki.


Kan tayi wani yunkuri tuni ya shigo cikin gidan,se jiyowa tayi anata hayaniyar murnar dawowarshi,dan dama ya kwana biyu be dawoba.


Shiko jabeer ido kawai yake rabawa yaga ta inda Jawahir dinshi zata bullo amman shuru kakeji,karshema innarshi suka hada ido da ita ta shiga doka masa harara dole tasa yadauke idonsa daga kallin ƙoɗar dakin nasu.


Duk yadda yaso ya je yaga jawahir dinshi amman fafur mahaifiyarshi ta hana shi fita yana gurinta ta tsareshi da zance wanda beda kai bare kan gado.


Wasa wasa har karfe goma na dare jabeer na gurin Inna taki barinshi ya tafi,daga karshede kwanciya yayi adakin yafara baccin karya.


Ganin hakane yasa inna ta tada shi tace yatafi dakin matarsa,kar yay mata bacci a daki.


Ayko cike da farin ciki ya mike ze fice dauke da jakarshi,da sauri ra shaidashi.


Bayan ya tsayane,ta taso da kanta tazo,ta amshi jakar ta ajiye,sannan tasa hannu a aljihunsa ta cajeshi tsab ta cire kudin jikinshi,shide binta yake da kallo,kasa daurewa yayi yace.


"inna meye maanar hakan don Allah?"


Harara ta watsa masa gamida cewa.


"kai tafi can soko kawai wanda besan abinda yakeva,wato so kake na barka ka tafi dasu dakinta ta yasheka ko?"


dafe kanshi yaƴi alamar takaici yace.


"inna jawahir bata sata,kuma kinfi kowa sanin hakan,danme zesa to na gujeta da kudina?"


"ni ficemin da gani shasha namijin hotiho kawai,wato ira bata sata ni nakeyi kenan ko?"


"Ni bance haka ba,amman de gaskiya inna kidena yiwa jawahir haka dan in aka yiwa zainab bazakiji dadiba"


Afusace tayo kansa tana fadin.


"Jabeeru ka kitayenifa,wlgnatashi daukar mataki akanka bazaka ji dadiba,kodan kaga kai ina daga maka kafa shine har kasamu damar fadamin magana?kudine nace bazaka dasuba,inkaji zafi ka rufeni da duka"


"Allah ya baki hakuri"yace gamida ficewa daga dakin,ya nufi dakin gimbiyarsa.Allah sarki tana kwance tana kuka,dan ko kadan tagaza yin bacci kewar mijinta na damunta ta kosa tasashi a idonta,ko zataji dadi.


Da sallamarshi ya shigo dakin,ganin bata falone yasa ya shiga cikin dakin,akwance ya hangota kan gado ko baa fada masa yasan kuka takeyi,ji yayi zuciyarshi tai masa baki ranshi na kuna dan ba abinda ya tsana kamar ganin hawaye a idon jawahir.Takawa yayi a hankali ya hau kan gadon,dagota yayi gaba dayanta ya mannata da kirjinshi ya rungumeta.


Ayko fashe mishi tayi da kuka tana kara shigewa jikinshi,Rarrashinta yashiga yi yana shafa bayanta,dan ko bata faɗa masa ba yasan ita da inna ne.


Da kyar yasamu tayi shuru,tayi lub ajikinshi tana ajiyar zuciya,se alokacin yaji hankalinshi ya kwanta ganin ta dena kukan.


Dagowa tayi ta kafeshi da idanuwanta da suka rine sabida kuka,tace.


"Don Allah Hubby ka roki inna karta rabani da kai,wlh bazan iya rayuwa babu kaiba don Allah"ta karasa maganar cikin kuka.


 da sauri ya hade bakinshi da nata dan yasan in yabarta taci gaba da magana karshenta shima tasashi kukan.


Cikin salo da kwarewa yake tsotson bakinta,wanda hakan ya tilastawa jawahir yin shuru ta maida hankali gurin amsar sakon nashi.Muje zuwa.

[19/12, 18:07] Hassan Atk: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SURUKATA CE SILA*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


*BASED ON TRUE LIFE STORY*


   *BY*


*ZARAH SURBAJO*


       *AND*


*HUMY LUV**2-3*


Tun tana ajiyar zuciya  har ta sake gaba d'aya  suka Lula duniyar masoya, sai wajan share d'ayan dare suka dawo cikin hayyacin su ,Tashi jawahir tayi suka  shiga toilet  bayan sun fito Jabeer yaji cikin sa na kukan yunwa kallon jawahir  yayi sannan yace "happy  yunwa nake ji"zaroo ido Tayi  sai lokacin ta tuna bata bashi abinci ba 

,hawaye ya shiga  Xuba Mata,  ta Matso kusa dashi ta manna kanta a k'irjin sa tana magana  cikin muryar  kuka"hubby kayi hakuri abincin  ka na gurin Inna  na d'auka kaci acan gurin ta Kafin ka shigo""Hmm  Banci komai ba 

had'a min tea Mai Kauri nasha"kuka ta saki Wanda  yasa shi  rud'ewa "happy  what's  wrong with  you  again? su Zainab  sun kwashe komai ne?"kai ta d'aga masa alamar Eh!.


DafE Kansa yayi sannan hannu yace "OK don't  worry,mu kwanta dare yayi"a'a Bari naje d'akin Inna na d'auko maka" Yauwa ngd sosai happy" murmushi  tayi doguwar rigar tasa ta nufi d'akin Inna. Tayi sallama yafi biyar ba Amsa ba kawai  ta shiga ganin su Tayi suna barci ahankali  take tafiyar  har takai gurin Kular abinci tasa hannu Zata d'auka taji an rik'e  Mata hannu nan da nan ta Fara kuka tafi Inna tafara Yi Tana fad'in "Na shiga uku ban Lalace ba yau zan ga fitina, kaiiii tirrrr,kaambuu dama sata Kike min a d'aki idan bana nan? " 


Kai ta shiga  girgizawa tana hawaye "Inna abincin  jabeer nazo d'auka kiyi hakuri  Kibani yunwa yake ji""Eh! Lallai  kin rik'a wato ni Zaku rainawa hankali ke da mijinki  kud'in da na k'arba shine ya Turo ki Kizo ki sata dake ke kinfi Sanin yadda akeyi"Zatayi magana taji muryar  jabeer "jawahir hayaniyar me nake ji haka? "


Shiru ta Masa bata Ce komai ba kukan  da yaji Inna  keyi yasa shi  rud'ewa  ya k'ara  so kan Gado "Inna meya Faru?" "Jabeer  Zaku Samin ciwon zuciya kai da matar ka,shikenan wlh ta wanke ta baka Kasha," 


"kai yake girgiza Mata alamun Tayi Shiru amma ina sai masifa take Tana fad'in 


"Sbd na k'arbi kud'in  ka shine Zaka gaya mata, ita kuma ta kasa  barci  Saida ta biyo  cikin dare Dan ta sata, to Allah  ya Fiki munafuka sai rik'a  Yi Kamar Saliha,ta k'ara fashewa da kuka"


jabeer  dake tsugune ya Zauna Ya rasa abinda zaice ya dubi Jawahir  da ta had'a kai da gwiwa Tana kuka yace "happy  let's  go an sleep"


Inna Najin haka ta rik'e  baki Tana mamakin  jabeer "Allah  sarki jabeer Allah  ya baka lfy Dan wannan annami miyar ta gama dakai"


Jawaheer  Najin kalmar da inna Ta fad'a  Ta kai hannu Ta d'auki Kular abinci  ta fita jabeer


Yabi bayan ta,suna shiga d'aki ya rungume zaiyi  magana  ta sa hannu  Ta Rufe masa baki "shhhh Zauna kaci abincin ka Bakomai jarabawa Ce kowa da irin Tasa" 


"happy  kenan mu kwanta kawai muddin  naci cikina zai Lalace"hmmm kuma Fa hakane kar ka kumburamin ciki Kafin safiya" 


"haha zo Kiji" ya Jawo ta jikin shi suka kwanta  cikin Kunnin ya rad'a Mata.


"happy  I love  you  so deeply  don't  allow  anybody  to separate  us pls,bazan iya rayuwa babu ke ba"


"Hmmmmmmmm in-sha-Allah  but ina fargaban gobe" 


"Inna ko? "kiyi hakuri  tabbas  gobe akwai Tashin hankali"


"Bakomai  INSHA Allah,amma ni canzswar inna  yana bani mamaki  sosai"


"bake kad'ai ba har sister  Hauwa Ma ta fad'a  min haka,nikam Anya Inna  tace kuwa? ""Karka k'ara fad'in haka  kawai sona ne batayi Shiyasa  take maka haka"Zai k'ara  yum magana  ta Rufe masa baki  tayi addu'a Nan da nan barci  ya d'auke su.*Washe Gari* sai k'arfe  Tara suka Farka salati suka shiga yii ganin sun makara dayawa toilet  suka shiga  Alwala sukayi sannan  suka fito atare sukayi sallah  bayan sun gama  ta jawaheer  ta kalli jabeer fuskar Ta d'auke da murmushi  tace 


Barka da Safiya Mijina,ya gajiyan  hanyar? "Barka dai happy  ina fatan kanki bays miki  ciwo""Baaya yi bari  na had'a  mana breakfast"tsaya mu tafi tare na gaida Inna  daga nan

muje xuwa💃🏻


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

 *SURUKATA CE SILA*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


*BASED ON TRUE LIFE STORY*


*BY*


*ZAHRA SURBAJO*


*AND*


*HUMY LUV*


*Bilkisu U Hamza surbajo na gaisuwa Allah yabarmin ke ki jima ki karko,ina yinki irin sosai dinnan♥*


*Last page munyi mistake na numberring*


*5-6*


Har takai bakin kofa da sauri jabeer ya bita a baya ya kamo hannunta,yana fadin.


"happy ba jira irin wannan sauri haka"


Murmushi tayi gamida kokarin kwace hannunta daga nashi,amman fafur yaki sakar mata hannun,cike da fargaba tace.


"hubby pls ka sakarmin hannu kamin inna ta ganmu"


Ko ajikinshi haka yajata zuwa waje tana tirjewa,


Abinda ta guda shine ya afku,domin inna ce tsaye kofar dakinta ta kafesu dana mujiya,


Shi kanshi jabir ya tsorata da ganinta amman se ya maze,ita ko jawahir tuni fitsari ya cika marar ta sabida tsananin firgita.


Kwace hannunta tayi daga nashi ta matsa gefe da sauri


budar bakin inna se cewa tayi


"innalillahiwainnailaihirrajiun,yau ni ina zansaka rayuwata?yanzu jawahir karuwancin naki har yakai ki fito gabana ki nunamin,koda yake gado ay sedan gado barewa batai gudu danta yay rarrafeba"


Da sauri jabeer ya karasa gurin inna,yafara bata hakuri.


"Don Allah inna kiyi hakuri,wannan ba abun magana bane dan na rike mata hannu agabanki,dan haka don Allah kibar maganar"


"kai dallah tafican shanyayye kawai,ni zaka duba kace ka rike mata hannu,agidan ubanwa ka rike matan bayan uta ta ruko ka,to wlh baka isa ba dole sena dauki kwakkwaran mataki akanku"


Ita de jawahir sum sum tayi ta wuce inda ake girkin,inda ta tarar zainab ta dora ruwan zafi har yakusa tafasa,matsawa tayi kus da zainab din tana murmushi tace.


"Yi hakuri zainab yau mun makarane shiyasa nabarki ke kadai,don Allah kiyi hakuri"


A fusace zainab ta mike ta fara magana muryarta asama dan inna ta jiyo.


"ke dallah can juya kawai,dan ubanki har kin isa kuzo gabana kicemin wai innace bata barku kunyi bacci da wuriba,yanzu kuma ta tsaidaku da masifarta?wlh baki isaba ni nasan darajar mahaifiyata,wawiya mayya kawai"


Tsananin mamakin sharrin zainab ne ya hana jawahir koda motsine,baki kawai ta saki tana kallonta.


lokaci guda inna da Jabeer suka karaso gurin.


Jabeer na zuwa ya daga hannu ya wanke zainab da mari,beyi wata wataba ya rufeta da duka,badan komaiba sedan zagin matarsa da tayi tana kanwarsa wacce a girme ma jawahir din ta girmeta nesa ba kusa ba.


"wayyo na shiga uku mayya ta shigomin rayuwar da gashinan tasa ze nakasa yar uwarsa,Jabeeru ka sakarmin yarinya wlh ka kuma dukanta sena baka mamaki"


Kobi takan inna beyiba,dan so yake yau ya kotawa zainab hankali dan tana daya daga cikin masu haddasa fitina tsakanin inna da jawahir.


Da gudu jawahir taje gurinshi tana janshi,tana kuka tana fadin.


"hubby kayiwa girman Allah ka kyaleta don Allah kabarta wlh ni banji haushiba"tanayi tana janshi.


Tureta yayi ta fadi batare daya saniba,hakan yay dadidai da karasowar inna dauke da tukunyar tafasasshen ruwan zafi,bata jira komaiba ta juyewa jawahir tafasasshen ruwan zafin a kafa.


Wata razananniyar kara ta saki,wacce ta janyo hankalin jabeer gurinta,tiririn da yagani na tashi ajikinta da tukunyar da yagani a hannun inna shi tabbatar masa da abinda inna ta aykata.


Aguje yayi kan Jawahir,wacce zuwa lokacin sabida tsananin azaba tuni ta sume,Agigice ya dauketa ze fice da ita daga gidan,


Da suri inna tasha gabanshi gamida cewa.


"wlh kasake kafita da wnnan bakar kadarar daga gidannan ban yafemakaba"


Idonshi jawur yadubi inna yace afusace.


"Allah yace,ci da shanta da suturarta da gurin kwananta da lafiyarta duka nauyine daya rataya awuyana,wanda inbanyiba inada halin yin se wutarsa tacini,kuma yashaida mana,la daata li makalukina fi maasiyatil kaliki,dan haka inna zan fita da jawahir daga gidannan koda bada izininkiba inyaso kije kaaba ki tsinemin acan"


Yana kaiwa nan yas kai yafice dauke da uta rai ahannun Allah,motarshi ya nufa yasata aciki,yaja da gudu zuwa asibiti mafi kusa.


Ita ko inna baki bude tabusu da kallo,ganin yafitanne yas ranta yasake baci tasake dauka mummunar aniya akansu.


A asibitin kuwa sun anshesu da gaggawa unda sukayi nasrar farfadowarta,duk inda ta kone sukabi suka cire fatar gurin gamida wankewa,sukamata dressing din gurin,azaba iya azaba tashata se kuka take jabeer na tayata .


Gado aka bata a asibitin,inda jabeer ke jinyarta gar tsawon sati biyu,be taba zuwa gidan inna ba sede yaje gidan abokinshi yayi wanka acan yasa kayan abokin yayinda itakuma matar abokin ke zuwa mata da kayan da zata sa,kuma su suke kawo musu abinci.


Ranar da aka sallamesu ma dakyar take taka kafafunta,da taimakon Jabeer ta iya zuwa mota,yaja suka nufi gidan inna.


Suna zuwa Allah tataimakesu tana bacci dan haka da sauri suka shige dakinsu,sede sunyi shuka a idon makwarwa dan zainab tagansu da gudu taje ta shaidawa inna.


Ayko afusce inna ta nƴfo dakinsu,jabeer ya hangota d sauri yaje ya kulle kofar koda tazo tadunga bugawa yaki budewa,ayko nan tashiga laantar jawahir.


Itako tana dakin tan kuka tana tunanin sauyawar halayyar inna,koda was akace mata inna zatamata haka zata karyata,innan da da ko bacci vata iyayi inde ita batayi ba yau itace ke hanata bacci,inɓar da da inbata da lafiya cikin kuka take yau itace ke janyo mata ciwon fashew tayi da kuka tashiga tuno rayuwarsu acan baya.


FARKON LABARIN


Muje zuwa


🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*SURUKATA CE SILA*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀


*BASED ON TRUE LIFE STORY*


   *BY*


*ZARAH SURBAJO*


       *AND*


*HUMY LUV*


*Mzeeta,Ermeenart  Auta BK, wannan Shafin nakune ina yinku irin sosai  dinnan*❤


*6-7*


*Farkon Labari*


Jawaheer  'yace ga Alhaji Ja'afar ma'aikacin Wani company shine manager  agurin Mutum ne Mai son mutani yana da rufin asiri gidan sa d'an  Mai daidaici  Suna RAyuwar  su  cike da jin dadi da son juna shi da matar sa d

hajiya Rakiya suna zaman lfy Allah ya azurta su  da yara Guda bakwai jawad shine Farkon Dan su,Juhaifat, Junaid jawaheer,


jadwat,Jameelu,sai d'an  autar su Jabeer, inkiyar  gidan su shine *J-J house* Yawan cin su da wannan  sunan ake Kiran su,jawaheer ta kasance yarinya Mai farin jini Tun Tana y'ar k'aramar ta gata kyakkawa  Fara Ce Sol gata da jiki maikyau y'ar  Duma Dumaa, mutani na son ta Sabida  fara'ar ta gata  da son mutani saidai bata d'aukar wulakanci ko  kad'an Tana da son Tara, Mahaifin SU banufe ne suna zaaune a Zaria sabon Gari,sun Sami karatu sosai both  Arabic and English gaba d'ayan Suna zaune lafiya soyayya  tsakanin Momy da dad d'insu yaja baya Sanadiyyar  komawa da yayi Lagos  acan ya Auri wata yaroba,


Ya kan dawo gida every weekend daga baya Yakoma karshen  wata.


Haka suke Rayuwa   da d'adi ba d'adi Suna zaune  karatun su ya tsaya Sanadiyyar  rashin  school fees  hakan yasa Maman Yankee hukuncin Fara sana'a, Tana cikin wannan  tunanin  sukaji sallamar Dadyn  su  da gudu  jameelu da jabeer suka je masa Oyoyo,wani Abun mamaki shine Alhaji Ya marii jameelu  sbd ya taka shi rik'e  baki sukayi ganin sabon lamari agurin sa,hakan MA bai gama Basu mamaki Saida yace akwai general  meeting  yanzu a parlour ,


wannan  Rana Baza su ta a taba mantawa da shi ba, Suna zaune a parlour dukkan  su Harda Dadyn su ya dubi Jawad yace "Son tunda kun girma kai da Ja'afar  ina ganin Zaku iya rik'e  k'annen ku.


Ya dubi Mom yace"Rakiya na Kiyi hakuri  da abinda  zan  gaya miki Nima ba'ason Raina bane,na sauwak'e miki,ni Na tafi Dan sauri nake ana jirana,"Har yakai bakin k'ofar  gida ta bishi da gudu ta rik'e  masa k'afa "Alhaji  karkamin haka agaban Yarana dan Allah Ka gayamin laifina wlh zan gyara"


"kiyi hakuri  Rakiya baki min komai ba Baffa ne ya umarce ni  da cewa  idan nasan  bana sonki yanzu na sauwak'e miki Tun Kafin yayi fushi Dani Wai ina shiga Hakkin  ki dayawa"Yana kai karshe ya fita Tun daga wannan ranar suka Fara shiga Halin mairaici ga  mahaifin su a rayee amma  Suna maraicin UBA ,bayan watanni uku Hajiya  Rakiya  ta Yankee hukuncin  kafa shagoo tafara Saida  abinci ta kashewa yaranta mata xuwa makaranta  sbd ba kud'i,amma Mazan sun cigaba da xuwa.
Jawaheer  kullum  Tana tare da momynta a shagoo. ita ke kaiwa baki  abinci  saidai  baka taba ganin fuskar ta  a sake,kwakwata Zaka d'auka  bata  Tab'a yin Dariya  ba,wannan dalilin  Ya hana maza dayawa tunkaran ta da zancen soyayya  daga Cikin su kuwa Harda jabeer  Dan Kwakwata soyayyar jawaheer  na nimar hana sa aiki, Wataranar  laraba haka kawai  Jawaheer  taji Tana sha'awar yin kwalliya bayan Tayi wanka Tana 

Nufi Gaban mirror  Zaman dirshan Tayi Ta fara kashe lokaci  Tana tsala makeup  doguwar riga Tasa sannan  Ta rolling  gyalen akan ta,ta d'auko wata bakar eye 👓  tasa Ita kanta ranar tasan Ta hadu,hand pose  ta d'auka  pink da takalmi pink Tasa, sannan  Ta nufi parlour  Tace "Momy  how did I look"?"Woow J-J You look  gorgeously,   gsky Jawaheer  ba inda kika rage dadynki komai Nak'i sak ja'afar""Hmmmmmmmm haka Kaka yacemin jiya da natafi,Momy  mu tafi Na shirya"


"Yanzu kuwa Dan yau Friday  kinsan yawancin Masu dawowa gida weekend  daga Abuja Suna tsayawa suci abinci Kafin su shige""Yauwa ni kuwa Momy  ina yaron ki Dinnan Mai sunan d'an  Auta yana xuwa kuwa? "


"yama cemin yau zai shigo fride rice  yace na mishi mai hanta aciki zai kaiwa Innar sa"Hmmm ki bani nayi masa Mai d'adi"wato ni ban iya Mai d'adi  ba ko?"a'a ni na haka nake nufi backyard, "jawaheer  kenan"


Suna hira har suka fito Titi suka tare adaidaita ya kaisu shago,suna xuwa Jawaheer  ta Fara had'a  girki banda k'amshi ba abinda yakeyi Rashid murmushi  kawai take itadai gayen Yana burgeta Gashi ba ruwansa,ita k'adai take zancen cikin xuciyar ta har ta gama ta wanke hannun  ta sannan  Ta Nimi guri ta zauna Tana baza idoo ta ina zai shigo.kamar ance jawaheer  d'aga  idon ki ta hango wata Motar  k'irar  Lamborghini  Black  Tana shigowa  layin Shagon su*Masoyan mu bafa Afara komai Dan Lbrn  jawaheer labarine Mai rikitarwa tausayi  burgewa musamman RAyuwar  auren ta Matar aureee ku shirya Dan kuwa Surbajo  da Humyluv  sun shirya Kawo muku abubuwan  karuwa  cikin wannan  novel  din*mujee xuwaadsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *