Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, April 22, 2021

WATA UWAR Complete Hausa Novel

adsense here

 

WATA UWAR Complete Hausa Novel


👵🏻    WATA UWAR   👵🏻

    BY HAERMEEBRAERH

Ina mai miqa godiya da Allah da yaban iko nai nufin fara wannan novel mai sunan 👵🏻WATA UWAR👵🏻, sakamakon wani labari da aka sanar dani dazu da safe, wanda nima shaida ce abubuwa da dama sun faru akan ido na. Naso barin shi a raina amma duba da cewar akwai wadanda ke min magana akan na fara novel, ina ganin ba zan iya ba,😱 yau nayi tinani nima ina son na bada gudummawa ta ta wannan fanni.😎 Allah yasa yanda na fara lfy na gama lfy, Allah yasa kuma kuso shi ya amfanar da mu baki daya.❤

Page 1:

A guge ta fito daga dakin tana kuka, sakamakon dukan da innar ta ta biyo ta da shi, kamar ba ita ce ta haife ta ba , duka ne ta ke mata da wata qatuwar muciya, wanda in da sabo ta saba, amma da yake na yau yafi na kullum shi ya haddasa mata gigicewa, kuka take tana " dan Allah inna kiyi hakuri bani bace hinde ce tai fitsarin ta tace nice ya kamata ki gane vani nake yi ba inna" " sharri kenan kk nufin auta ta zata miki ko?" Inna ba haka nake nufi ba ki duba ni ki gani ki duba ta ita tai fitsarin ta" lallai baki daku ba ne ina fada kina magana ra ra ra ra kamar redion da bata da makashi" ta zaburo tayo kanta tana fadin shegiyar yarinya baqa, ni anya ba canjan ke akai ba a asibitin binni? Saida nace kar a kaini haihuwa birni aka dage sai an kaini ga haihuwar hannun likita bokan turai me ta jawo min haihuwar asara haihuwa ba riba" inna dan Allah ki daina fadan haka Allah ne ke halittan kowa shine yasan arziqin kowa ya zai kasance ba wanda ya san ya rayuwar shi xata kasan ce" tana yi tana kuka kamar ranta zai fice a jikin ta idon ta yai jawur doqon hancin ta sai majina yake fiddawa ta wahala, da dan qaramin bakin ta da ya dade da bushewa, tana tsayen taji an kwado mata bokitin qarfe a gaban ta " gashi nan dan uban ki maza ki tafi ki dakko ruwa ki fara aikin gaban ki dan banga amfanin ki ba da ya wuce aikatau ke dai, tinda nasan ko gaba ba wani mashinshinin kirki zaki ba saidai kiga auta na farar mace alkyabbar mata tana abun arziqi amma banda ke, kin tashi ko saina sheme ki" ta wurga mata takalmin qafarta, ta dau bokitin kenan ta juyo" tace inna da kin bari nai sallah sai na je nai aikin dan Allah" iyeeee ina ga abinda zaki kina ga abinda kk so yo ke ko sallar ma kikai ai nasan ba wata me kyau zaki ba, dan haka ba karbuwa zatai ba, maza kije ki abinda na saka ki inyaso kinyi sallar" ta saka takalman ta ta kama hanyar soron gidan su kenan baban ta ya shigo daga masallaci, tana hada ido da shi ta kauda kanta qasa ya wuce ta wuce dan ya zama sallamamme a  gidan bai da katabus innar Hinde ta gama da shi sai yanda tace a gidan akeyi, dan kuwa baya aikin komai dai noma, itan ma ba wani abun kirki yake tabukawa ba, ita ke ci da gidan amma dik da babun shi yana qoqari in ya samu a ci mai dadi a gidan ya faranta masu, topa a lokacin ne zakuga fara'ar innar hinde ba qaqqautawa ranar har mijina zata ce mai amma, a yi wanka a ranar dan wanka ba wai yana cikin tsare2n ta bane ita in kunga wankan ta topa zata biki shima ba kowanne ba, sai wanda ta so.


     Dawowar ta kenan daga debo ruwan Hinde ta fito da buta da niyyar diban ruwan tana sane ta tankade ta yanda bokitin zai zuba a jikin ta yana ko xuba ta sa ihuuu " wayyoooo Allah na inna ta kashe ni da asubar nan ta kwaran ruwan sanyi wai saita rama dukan da aka mata akaina" tana gunjin kuka dan mamaki Nasreen bude baki kawai tai tana matuqar mamakin wannan qanwar tata da tabawa aqalla shekara uku take hada sharri inta girma ya zata koma? Da gudu ko ta fito tana salati tana kumawa " ashe dama kallon danaga kina mata da ina dikan ki na zamu hadu ne?" Lallai kuwa yau me rabani da ke sai Allah" ai tana jin haka ta diba waje da gudu dan tasan yau sai an kusa kaita binni asibiti inna ta kamata.
Wasa take da tsinke a hannun ta ya karyo kwana yana isowa ya ganta yai burki ya iso inda take" ya yammata ta Ado bada kanki a sare in kinje gida kice na amshe abuna, me ya faru kuma yau na ganki anan da sassafe?" Bata daga kanta ba ta bashi amsa da " ba komai nidai ka tafi karka jamin magana dan Allah Ado" " haba abar son Ado kema kinsan ba wadda nake so data wuce ki dik karkarar nan irin wahalar da kk sha yasa na maki tayin guduwa lagos amma kin qi, ko kiban dama na fede wa waccan shegiyar qanwar taki fuska naga ta taqama dafarin da suke fan ba abinda ta fiki" da hanxari ta daga kanya ta kalle shi da idun ta masu haske da suka koma ja tace "Aa Ado ni dai na hane ka da irin wadannan maganganun dan basu da amfani dika" to shikenan yanzu fadan yau me ke faruwa ko zan iya taimakawa?" Ruea xaka debon anan " ta miqa mai bokitin ya karba kan minti biyar ya dawo ya bata ya zauna yana jiran ta juye ya qaro a haka suka gama cika gidan tas.......


👵🏻   WATA UWAR   👵🏻

    BY HAERMEEBRAERHPage 2:Tana gamawa ne ta dawo wajen shi ta mai godiya da taimakon ta da yake ta koma ciki ta dakko buta ta debi ruwa ta zaga tai alwala ta koma soro ta dau dankwalin ta ta yafa ta fara sallah ta kai ruku'u kenan raji an dima mata dundu a baya saida ta gantsare dagowar nan da zatai taga qanwar ta Hinde kan tai magana ta durqusa ta fashe da kuka mai tsanani tana kiran inna aiko sai gata a guje zani a hannu " me nake ji kamar an fasa kabewa " tana shidewa ta qarya take fadin " inna Nasreen zata kashe ni zata gama da ni inna duban baya na zan wuce kawai ta diman dundu" jikin Nasreen har rawa yake ta zube a kan guiwowin ta tana kallon qanwar tata tana hawaye daga baya hawayen ya tsaya cak ta kalle ta tace "Hinde me na maki ne? Me kk so dani ne? Ko kin manta ni yar uwar kice ta jini? Uwar mu daya uban mu daya amma kk min abinda kk man ? Burin ki kullum ki hadani da Innar mu" kan ta rufe baki jitai an bige mata bakin ya fashe sai jini ke zuba inna kenan " dan uban ki baki ga me kk mata ba ne ko nace me kk mana duk gidannan wa kk gani baqi kuma mai kyau kamar ki daban kk duk zuri'ar mu ba mai kamar ki" kan ta rufe baki sukaji daga bayan su ance " to in haka ne kenan ba ita za a tambaya ba ko?" Da masifa ta juyo sakamakon gane mai maganar da tai " to uban wa za a tambaya kenan?" Hmmmm Innar Hinde kenan kece fa uwar ta ai ko kinga ba wanda ya dace a tambaye shi dawa take kama in ba ke ba, haba kin bi kinsa yarin ya a gaba sallar ma tinda ku bakui ba kun hana ta" a kufule ta katse shi " sannu sallahu baban ta sallah aaaa nace sannu sallau baban ta sallah banga damar barin ta sallah ba sai ta gama man komai in ba haka ba daga kai har ita yau baku da abinci" a take ya dakko dari biyar ya wurga ma yar tashi wato Nasreen yace "ga shi nan kije ki siyo dik abinda kk son kari da shi yau" habaaaamana ai tini innar Hinde aka koma kusa da shi "habaaa mijin Tabawa mijina abin alfahari na ai yau kam a gidannan kaine sarki sai abinda kace shi za ai" yai murmushi dan yasan yau daga yanzu zuwa dare zai samu kan innar Hinde har a dan raba shi a daki.

Yana fita ta amshe kufin hannun ta ta bi shi ita kuma ta samu damar yin sallar ta tau addu'o'in ta musamman akan halin da take ciki na Allah ya kawo mata mafita ya daidaita ta da yar uwar ta da mahaifiyar ta.
Sannan ta tashi ta dakko kwanikan wanke wanke tana hadawa waje daya tai shara tas ta wanke bandaki tai wanke2 tai wanka dan ita kome za ai mata ba za a hana ta wanka da wanke baki da gishiri da gawayi ba shiyasa kullum cikin tsafta zaka ganta. Data gama ne ta dau hanyar zuwa gidan qawar ta yar mai kudin garin Barira......


👵🏻    WATA UWAR.  👵🏻

     BY HAERMEEBRAERH


Page 3:


Da sallamar ta ta shiga ta tadda innar Barira na shara ta hanxarta xuwa karbar tsitsiyar amma innar Barira ta hana ta anan ta gaida ta ta tambayi aminiyar ta shaida mata tana daki a kwance aiko rai bace tai dakin nata. Daka mata duka tai a duwais din ta irin na (Roumie mutan sahara😂😜) da hanxari ta miqe taga waye dan dai tasan ba innar ta bace saidai ko wannan...... kan ta qarasa tinanin ta suka hada ido, da murnar ta ta sakko ita kuma ta hade fuska, " yanzu Barira abinda kikai kin kyauta kenan? Inna na can na shara kina nan kina shara bacci hankali kwance, yaushe zaki hankali ne? " Aa malama karki matsa min daga shigowa yo kk san ni aikin da nai kan ki zo? Nafa gyra dakina nai wanka ko baki da ido ne? Ta murguda baki ta haye gado abinta Nasreen tai murmushi ta xauna gefen ta tace qawata ina mai maki nasiha da ki dinga taimakawa taki mahaifiyar kinga ke bata takura maki kamar tawa innar duk da nasan tawa innar harda zugar qanwata ki duba ki gani yanzu shekarata sha biyar ba a daina duka na ba a qauyen nan namu ai na isa aure shekara mai zuwa a dau ki da amma kullum kamar jaka haka nake " wasu hawaye masu xafi suka sakko mata anan qawar ta ta share mata ta rungume ta tana buga bayan ta da sigar rarra shi itama nata idon ya cika da hawaye tace " Nasreen hakuri xaki tayi inshaa Allah watarana sai labari kuma dama akwai abinda nake son na fada maki dan dai innata ma tana da niyyar shiga gidan ku anjima, daxu baba ya shigo yace mana zamu koma birni nan da kwana biyu ya samu aiki a can zamu garin Lagos na kasa zuwa na fada maki ne yasa na kwanta ina tinani bacci ya dauke" nam da nan hankalin Nasreen ya tashi ta tsanan ta kukan ta tace "to ni yanzu in kuka tafu ya zan? Wa zai dinga sharen hawayena a duk sanda na kawo kukana? Wa zai..... bata qarasa ba ta fita da gudu tana kuka. 

         Itama Barira binta tai amma inaaa ta wuce bata san ma wace kwanar tai ba can bayan garin taje ta zauna qasan wata bishiya taita kuka tana tambayar kanta " anya Innar Hinde ita ta haife ta ? Wace irin uwa ce ita ? Taga iyaye kala2 amma bata taba ganin irin tata ba WATA UWAR kome ya samu yarta itama saita jishi a jikin ta amma tata uwar ko a jikin ta ta share hawayen ta, ta daga hannu sama tana ma Allah kirari da riqon shi ya kawo mata mafita karta wulaqanta a wannan qauye take tinanin Ado ya fadi mata akan maganar su da suke yi kullum.......

👵🏻    WATA UWAR   👵🏻 

     BY HAERMEEBRAERH
Page 4:

 Kamar wadda aka mintsina haka ta tashi ta fara tafiya ganin rana na neman bacewa tana xaune hankalin ta ba qaramin tashi yai ba data tina gida, nan take baqinciki ya bayyana a fuskarta, da tana da hali da iko da ta samu WATA UWAR  a matsayin mahaifiya ta canja ta ta, ta goge hawayen idon ta," kaga ta Ado bada kan ki a sare in kinje gida kice na amshi abuna" hmmm Ado daga ina haka kamar anyi halin" hhhhhh ba wani da yawa bane Tawan kawai na dan sha na daidaita haxo ne kin gane" hmmm Ado kenan bari kaga na isa gida dan yau nasan saidai nai kwanan soro rabona da gida tin 12 na rana" tab ke ko ina kk tsaya bayan kin san Halin wannan shegiyar uwar taki" a fusace ta dago ta kalle shi saida yaji hankalin shi ya tashi" kiyi hakuri Nasreen da ina da iko saina canja maki WATA UWAR kema ki dandana dadin mahaifiya domin duk iskanci na innata na so na amma taki bata da burin daya wuce ta lalata ki daga gidan ku nake yanzu naje neman ki ban same ki ba, naga Innar Hinde muka gaisa nace mata kina nan? Budar bakin ta cewa tai " ni na namtsu naji ta fara amai a gidannan ko mun baka ita dika ka qarasa dan wallahi baxata ci gaba da zama da mu ba" a firgice Nasreen ta kalle shi tace " da gaske innata ce tace maka haka?" Ya daga mata kai jikin shi a sanyaye ya qara da cewa" ni dama sallama na zo na miki zan wuce lagos ne anjima da yamma, zamu binni mu kwana mu wuce" Allah sarki Ado in ka tafi sai yaushe kuma" hmmm Nasreen kenan saikace wani damuwa kikai da ni bayan ko dan ina son ka dinnan baki taba fadan ba" Ado ai kaima kasan ba soyayya tsakanin mu da da akwai da tini ka sani yar makarantar nan kaqi sam bayan kana da dama mu da muke so sai an bushi iska ake barin mu zuwa amma kai kaqi zama mutumin kirki" Nasreen watarana sai labari gashi mun iso gida ki shiga kan a gammu ace daga yawon ta zubar kk bayan ni ko hannu ba a taba bari na dan riqe ba ma naji dadi" hmmm to saduwar alkairi"

 


Tai wuf ta shige soro tana leqe ta dade a haka taji an tankada ta ciki ta fadi qasa juyawar nan da zatai taga Hinde ansha kwalliya irin ta qauye " Hinde meye haka sai kinji man ciwo?" Hhhhh ciwo indai ciwo ne ki kwantar da hankalin ki yar uwa ai sai na ji maki ciwon zahiri da badini zaki tabbatar da ni Hinde bana qaunar ki sam" Hinde me nai maki ne" wannan karon ta miqe tana fuskantar yar uwar ta ta" me kikai min fa kk tambaya ? Ki duba ki gani a garinnan kaf samari ke suke hari, qawaye ke suke hari, manyan gari da an ganki an hau maki addua ana sa maki albarka ni ko sai tsinuwa da shegen baqin jini" haba yar uwa karki manta malamin islamiyyar mu me ya ce kowacce rai da arziqin ta take zuwa ba wanda zai ci arziqin wani bakisan baiwar da Allah ya miki ba kk sawa tawa ido kuma ma me nake da shi da baki da shi? Ai sai dai ma ki fini" ke uwar tsara zance wallahi na kusa maganin ki kin kusa guduwa da qafar ki ki bar gidannan indai ni ce" ta bangaje ta ta shige gida me tace ma inna oho sai Allah sai gata a zabure ta yo soron da gudu tana xuwa ita kuma ta hada kai da guiwa tana kuka sai saukar duka tashi ko ta ina tana fadin" sallamammiya ina yake kwarton naki kun gama lalube2n naku kenan shine kika zauna harda dukar min yarinya dan ta shigo ta katse ku" ta daga kai ta kalli Hinde dake kukan qarya tana mata gwalo tace inna mari fa wannan qaton ya sakar min da hannun shi kamar katako" Innar Hinde tace zo ki rama a kanta shegiya baqa mai baqar aniya" kan ta gama mamaki da komai taji saukar mari kamar hannun qato amma ko a jikin ta abinda yar uwar ta da mahaifiyar ta ke mata yafi komai damun ta, saida sukai mai isar su suka tafi ta wurgo mata tabarma tace saidai ki kwana anan.

Baban Hinde duk yana saurar komai amma yau yana son ya dan labe a dakin Innar Hinde yasa yana jin su yai shiru dan kudin hannun shi baifi dari biyu ba 200 in ya matsa sai a hana shi abun duniya yau. Tana shiga daki ya matso kusa da ita dik da yau an samu wanka amma bakinnan wani wari yake kamar an bude shaddar gidan haya, tana daga hannu da niyyar rungume shi bayan ya miqa mata dari biyun hannun shi saida nunfashin shi ya kusa daukewa domin a wajen shi Nasreen ta gaji tsafta, amma ya zaiyi haka ya fara shafata a yi yan wasanni ita dai inaaa kawai so take taji ya fara bata darussa a wuce wajen dan har gargadi take mai" lokaci ne da kai Baban Hinde in kace tsotse2n nan zaka tsaya lokacin ka ya cika tashi zan nai kwanciyata nai bacci " ai ko baida zabin da ya wuce ya shiga badan rai da kwadayi ba da ba yanda za ai ya ce anan yake sauke buqatar shi waje kamar yana shiga masai dan wari da doyi kaiiiii Innar Hinde ta zame mana qaddara mummuna nida Yata........


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻

          BY HAERMEEBRAERH

Page 5:

Yana samu ya gama biyan buqatar shi ya tashi ya koma gefe yana hango da ace Innar Hinde na gyara ai da ba qaramin morewa zai ba tinda ba laifi komai yaji matsalar shi daya qazantar dake damun ta , tsaki yaja a lokacin da yaji tana wani irin munshari mai mugun qarfi ya miqa hannu da niyyar tashin ta akan taje tai wankan tsarki kan ta kwanta baccin sai ya tina kwanaki yanda suka qare maza ya janye hannun shi, bai shirya karbawa iyayen shi xagi ba da darennan, tashi yai taje yai wanka yai alwala ya hau sallaya ya na ta salloli bayan ya idar ne ya hau addua akan Allah ya shiryi matar shi ta zama macen kirki uwa ta gari wadda za ai kwatancen alkairi da ita, yana idarwa ya shafa ya koma gefen ta ya kwanta nan bacci yai gaba da shi.
Nasreen na kwance a soro duk sauron dunya ya gama cin kasuwa a kanta ya amshi kudin shi yai gaba, tai kuka har ta dena ta zubama bango ido a kan idon ta Baban Hinde ya wuce, yana komawa taga itama ya kamata ai ta tashi ta yi sallah ko ta roqi Allah sauyin rayuwa a tashi tai ta dauro alwala ta hau sallah bayan ta idar ta hau karanta surori daga alqur'ani gwargwadon wadan da malam sule ke koyar da su a islamiyya tana idarwa tai ta addua akan neman sauyin rayuwa, a haka bacci yai gaba da ita.

"Tashi baqa mai baqar aniya Inna na kiran ki" tana yi tana kada qugu su da masifa ba sa barin ta safe sai rana tayi su dora🙄 miqewa tai jiki ba qwari tai dakin Innar, tana kwance shame2 kamar gawa bata ko farka ba tana shiga Hinde ta hankada ta ta fada kan innar aiko ta bude ido da bakin ta mai mugun wari ta fara hamma tana miqa kula da Nasreen ne ya katse mata miqar ta dura ashar" dan uban ki me kk kallo? Me kk zo yi da asubannan ( kunji wai asuba rana gatso2 dan batai sallah ba shikenan kawai ya zamar mata asuba) saiga Hinde ta shigo ta je kusa da innar ta ta zauna sai cewa tai" hmmm ai Inna baki sani ba na dade a bayan ta ina kallon ta tana leqo ki tana ta kallon ki tana matse qafa dan ina kyautata tsammanin nan ta kwana tana leqa ku keda Baba komai akan idon ta akai har lokacin da kike wani irin kuka ba abinda bata ji ba sai gani nai ta dau buta taje tai wanka ta dawo tai sallah tai karatu" mamakin duniya ya cikawa Nasreen ciki babban mamakin ta bai wuce ya akai yar shekara 12 tasan ya ake in an gama xxx na biyu ashe idon ta biyu kenan duk taga komai labe take ma iyayen nasu wannan wace irin yarinya ce? Tafi tajiyo daga sama ana salati sai kuma duka ko ta ina wanda in da warin da ke fita daga jikin Innar aka barta ai an gama mata hukunci. Tsayawa tai innar taita duka da kyar Baban Hinde ya karbe ta wuya kam ta shata ba  ta wasa ba duk inda Hinde tai binta kawai take da ido.
Yaune ta yanke hukuncin tinkarar mahaifin ta ta tambaye shi wacece mahaifiyar ta. Zaune hake akan sallaya a daki ta shiga innar hinde tana bayi tai sallama ta xauna a gefen shi tace "Barka da rana Baba" amsawa yai cike da tausayawa dan ko ina tabon duka ne jikin ta da fara ce ba a san ya zata koma ba. Baba dama zuwa nai na tambaye ka dan girman Allah ka fadan gaskiya wacece mahaifiyata ko a ina take nai alqawarin zuwa na nemo ta, in ko mutuwa tai la fadan dangin ta na koma wajen su da xama in ba haka ba ina tsoron randa zaku nemen ku rasa" ta qarasa cikin matsanancin kuka hankalin malam Lawan tashi yai dayaji maganar barin gida, matsoea yai kusa da ita yana kama hannun ta zai magan kenan yaji ihuuuu a tsakar gida leqawar nan da zai yaga Hinde da Innar ta suna kururuwa wai" jama'a kuxo ku kawo mana dauki ga kwarton cikin gida uba na neman yarsa" kuka take tana qarawa malam kao ya riqe yana karanta kome yaxo bakin shi Nasreen kuwa faduwa tai a qasa sumamma. Malam ne yai kanta ya yayyafa maya ruwa ta farka tana kuka mai tsanani ba wanda ta kalla sai Hinde dan tana kyautata zaton cewa ita ta hada wannan sharrin. 

Tinda ta miqe kan mutane su iso malam ya miqa mata kudin hannun shi dika yace mata ya amince da yawun shi ta canja mazauni dan ba abinda yafi wannan muni ace an maka sharri da mahaifin ka tana kuka ta saka takalmi ta dau mayafi ta fice tana kallon uwar tata da yar uwar ta tana kuka har tai gaba ta dawo ta tsaya a gaban inna tace mata" inna na gode da dawainiyar haihuwata da kikai da kula dani har girmana tinda inda kin so da kin halakani kan kowa ya kula amma ina mai tabbatar maki cewa akwai hisabi tsakanin da da uwa Allah ya yafe maki karna dawo maki da abu dayan biyu ko abinda kullum kk man baki akai ko kuma arziqin da kk kam gori akai" ke kuma Hinde ga gidannan xan bar maki ki ci gaba da kawo ma inna kudin da take so ta hanyar da kk ga dama amma ki sani watarana sai labari kuma ki bi duniya a sannu" ta sa kai ta fice tabar inna na fadin " sallamammiya yo in banda ke da kinbj shawarar qanwar ki ni kullum in dari biyar xata na rabamu da ke banda matsala da baqin ku tinda kina da kyau amma yarinya sai tarin samari ba ko fus ki gaba in kinje kin samo kinna aiko mana" Nasreen rasa ina zata tai nan take ta hango machine ta tsayar tace ya kaita tasha........


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻 

      BY HAERMEEBRAEHAisha Aliyyu Garkuwa 

Zahs Surbi yel

Mrs J moon 

Cute one

Mrs Habnour

Maman Sadeeq 

Sawwama Qawwama

Mero Tsokana😂 

Roumie 

And many more........

Wannan page din da dikka sauran da zasu zo gaba naku ne. Ina son ku kamar yanda kuke so na tsakani da Allah ana tare❤  Matan Gidan Tabital Fullaku gaba daya Haermyn Hamma na son ku❤

Page 6:
Tashiga tasha da tinani kala2 da ya cushe mata a zuciya, da farko dai ina ta nufa yanzu? Wa take dashi a duniya da zata dosa bayan uwar da ta haifeta ta mata sharrin da har ta mutu bazai goge mata a zuciya ba? "Ya ilahi ka taimaka min" abinda bakin ta ke furtawa kenan. " kano, kano,kano" da sauri ta fada motar dan bata da wani tinani da zatai again tana shiga mutum uku kawai aka qara mota ta fara tafiya hankalin Nasreen a tashe yake dan bata taba hawa mota ba abin tsoro yake bata in ba ikon Allah ba ya za ai wannan qarfen ya motsa🤔 , tinanin ta ya qare ne a lokacin da barcin ramuwa yai gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da suka isa anan me motar ke rambayar ta kudi dan an tashe ta yafi sau nawa taqi bude ido ma bare taji shine dalilin bari saida suka iso ya karbi kudin shi, waige2 take ta faman yi bayan sun sauka a tashar unguwa uku anan ta hango masallaci ta isa tai alwala ta koma gefe ta saka dankwalin ta ta fara sallah ta idar kenan tana tinanin ina ta nufa kuma daga nan ? Taji wasu samari biyu suna magana" sani yanzu kana ganin mu wuce lagos din yau kawai tinda ga mota a arha zamu shiga dubu daya da dari biyar fa kawai zamu bashi har can saidai kawai a bayan motar zamu xauna shine matsalar duk sanyin hanya akan mu" Ah me zai hana me ya rage kawai mu bi shi yafi mana sauqi" nan take Barira ta fado mata arai, matsawa tai kusa da su tai masu sallama suka amsa " bayin Allah naji kuna zancen tafiya lagos ne dan Allah yaushe motar zata tashi? Kuma ana tafiya da mata?" Dariya suka fara sannan daya yace "baiwar Allah ai ba a hana maza ko mata tafiya ina kk son zuwa?" Tace " lagos nake son zuwa nima" kinada 2500? Kuma sai 6pm zamu tashi" tace ina da su ta kunce zani ta dakko masu yace to amma zamu fada maki gaskiya 1500 ne kudin mu zamu raba sauran" tace."ba komai" anan take suka isa wajen mai mota suka hada kudi suka bashi nan ta zauna sai hamma take taga mai awara ta siya bayan taci ta sha ruwa, 6pm nayi suka tashi tin ana tafiya tana an kusa har wani yaji haushi yace " malama sai fa an kwana dan haka in kinada abin yi kan mu isa ki fara kawai dan rage dare" ya koma ya kwanta nan ta koma gefe ta takure take dabara ta fado mata ta fara karanto al'qur'ani mai girma domin kuwa ko a qauye duk da muguntar Innar hinde takan je makaranta ajinta 2 a secodary a qur'ani kuwa ta sauke a hadda izunta 19 nan ta fara rera karatu da muryar ta mai dadin sauraro a take yan tafiyar ta kowa hankalin shi yayo kanta nutsuwa na shigar su , a haka har bacci yai gaba da ita.Isar su Lagos da safe ne ya bata damar bude ido a hankali ta duva ko ina sai jamaa kala2 take gani kawai ta sakko a hankali wadanda ta taho da su ne wani a cikin su yazo ya kawo mta abin da zata ci da ruwa yana mai girmama ta har ya bata mamaki dan ba a haka suka taho ba, anan yake tambayar ta wajen wa zata tace mai " wajen Barira zani yar malam Bashari na qauyen mu na Langyam" bai san sanda dariya ta kwace mai ba yace" baiwar Allah anan zaki nemi wata da wannan kwatancen tace " eh haka aka san su da shi a can gida" yaga zata bata mai lokaci yace muje na kaiki wani waje kan a samu wadan da kk nema yana dariya............


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻

     BY HAERMEEBRAERH


Page 7: 
Sun samu taxi da ta kaisu wata unguwa mai cike da qabilar hausawa ko ta ina yan kazo nazo mai suna Apapa, a gefen qarqashin gada rumfar Hajiya Asabe mai abinci take macece mai mugun son abin duniya ko ta halin qaqa ita dai kawai taga kudi haka zalika akan cimma burin ta ba irin hakurin da ba zatai ba da canja fuska dan dai kawai a fahimce ta ta isar da saqon ta na son zuciya ta fece, a haka Sani ya iso da Nasreen wajen ta tana hakimce ta ci kwalliya kota ina tana hura hanci, ya kwashi gaisuwa yana mata kirarin su na yan duniya tana murmushin isa da qasaita, ta daga kai ta kai duban ta gefen shi tace "Sani duniya wannan kuma hajar fa?"  Kyafta mata ido yai akan suje ciki tako tashi ta bishi tana juya mazaunan ta tana taqama ita dai Nasreen baiwar Allah sai ido take bazawa tana kallon yanda mata keta kai kawo suna wasannin banza da maza, da sauri ta kauda kanta da ta hango wani matashi na mata kallon kurilla.ta juya bayan ta ta rufe idon ta.


"Hajiya wannan yarinyar da kk gani a mota muka hadu, daga dikkan alamu kuma bata san ma gun wa ta zo ba, bayan haka in kin kula da ita bazata wuce shekara sha biyar zuwa sha shida ba, sannan koda zamui qoqarin sata a network sai munyi babban aiki sai mun bullo mata ta hanyar ta wato mu nuna mata muma na Allah ne, dan dan zamana da ita na fuskanci yarinyar akwai tsoron Allah ga ilimin addini" Dariya Hajiya Asabe tai tana kada ido da hannaye irin na yan duniya " yo wannan ai mai sauqi ne dan kuwa wannan yarinyar ta kile gidaje da motoci sai na zaba ba" Hhhhhh Hajiya baqa ce  fa" hmmmm Sani kenan meye a cikin farin ne da baqa bata da shi to kasani duk wata baqar mace tana da wani sinadarai da fara bata da shi mai banbancewa sai wanda ya same su su dika ( ba baqa bace ni ehe kar a ce na bi bayan kalar mu lols) " Anyways nidai gata na kawo komai ake ciki ina jin dumus innaji shiru ansan halina ehe" Kana tsorata ni ne Sani ko me kk nufi da hakan?" Aa hajiya ni na isa" yana magana yayin da yake kunna sigari yana kada qafa ya kada kai yai waje. Hangota da yai maza ya kashe hayaqin ya nufeta ya mata sallama ta amsa daidai fitowar Hajiya kenan, "Sannu baiwar Allah, sani yamin bayanin komai dan haka karki damu zan sa cigiya a nemo maki yan uwan ki inshaa Allahu nan kusa amma sai kinyi hakuri Lagos nada girma bamu san inda suka sauka ba balle ace dan haka zaki iya daukan lokaci mai tsaho damu, hakan nne yasa muka yanke shawara ko zaki iya fara tayani koda wanke2 ne ina biyan ki sannan kina da wajen kwana a gidana da abinci zan riqe ki kamar yata, dan baka san wa zai mori wani ba a rayuwa sai Allah" tinda ta fara magana Nasreen kanta ke qasa bata ce komai ba saoda ta kai aya sannan tace" Nagode Hajiya Allah ya qara girma, ina son nai sallah gashi lokaci nata wucewa"anan hajiyar tasa aka nunama Nasreen inda zata iya yin sallah a wajen tai sallah taci abinci tasha ruwa sai bacci mai dadi yai gaba da ita.Da wajen qarfe takwas na dare ta farka taga manyan motoci na zuwa suna diban yammatan nan suna tafiya da su, sai hajiyar tace mata ai suna kaisu gidajen kwana ne Nasreen a lokacin hankalin ta ya kwanta ta kalli y

Hajiyan tace " amma ni dai hajiya nafi son na kwana wajen ki dan Allah " hajiya tace laaa karki damu yata ai nima bazan so ki nesa dani ba tare zamu tafi yanzu ma motar mu nuke jira mu tafi" ana haka wata mota ta iso hajiya ta miqe ta kama hannun Nasreen suka shige sai gida. Isar su keda wuya ta nuna ma Nasreen wani daki mai kyau da gado da komai daidai buqatar mace mai son gyara da tsafta da bandaki a ciki, hajiya nuna mata komai daya dace ta sani tai ta mata saida safe ta juya ta fita...........


👵🏻   WATA UWAR.  👵🏻    

   BY HAERMEEBRAERH

 Maman Manal

Aunty Rumaisa

Gaisuwa mai yawa gare ku ANA MUGUN TARE❤
Page 8:

       Fitar Hajiya Asabe keda wuya Nasreen ta samu kanta da hayewa sabon gadon da aka bata akace nata ne, tai juyi ta kuma, tai murmush, ta gode ma Allah da ya hadata da Hajiya Asabe a matsayin wadda xata taimaka mata. Wanka ta farayi sannan tai alwala tai sallar isha'i ta taba karatun ta sannan tai shirin bacci taji ana buga qofa, zuwa tai ta bude ta koma baya sai Hajiya ta shigo dauke da wata rigar bacci mai kyau kalar pink, " karbi wannan ki sa dan baza kiji dadin bacci da wannan kayan da kkai tafiya da su ba" ta amsa tana qara godiya da adduoi masu dad'ad'a rai, murmushi hajiya tai, tace " to saka rigar na gani in ta maki gobe muje a siyo maki wasu" a take ta je bandaki ta gwada amma ta kasa dawowa dakin sakamakon ganin yanda rigar tabi shape din ta ta kwanta, tana cikin tinani taji an bude qofar Hajiya tace " haba 'yata ai ni uwace kuma dan kinsa wannan ai ba wani abu bane baki gani a TV yan gayu yanda suke saka kaya qanana kuma su fita cikin mutane kowa ya dinga yabawa?" Anan ne ta tina in taje gidan su Barira suna gani a TV, ta daga mata kai alamun "eh" Tace " yauwa kinga in kina son cin ribar zama a wannan garin dole ki fara yin shiga irin tasu, saboda in ba haka ba fada zai iya tashi ya ritsa da ke a kashe ki, amma in kina saka kaya irin nasu ba mai kula ki" ai dajin maganar kisa idon Nasreen ya qara girma , tai wani abin tausayi tace " nidai Hajiya to ko a kidin da zan na maki aiki ki taimaka ki siyo min nima" tana share zufar dake karyo mata, Hajiya tai murmushin samun nasara a tashin farko tace ki kwanta ki bacci ki huta xamui maganar gobe, ta ja mata qofa ta fita dan gulma harda ce mata " kardai ki manta ki addua kan ki bacci" tace to Hajiya mu kwana lfy" tai addua taja bargo tana tinanin gida bacci mai dadi yai gaba da ita.


"Kin gama shiryawa ko" cewar Hajiya Asabe dake fitowa daga dakin ta, ta kalli Nasreen da ta maida kayan ta masu dauda tace " eh na gama Hajiya Ina kwana" " lfy qalaou, ya baqunta?" Tana murmushi ta amsa da " lfy qalaou" to muje ko in yaso in mun dawo munbi shago muci abinci.    
Sun sai kayayyaki kala2, takalma,turaruka, mayuka kala2 masu gyara fata daidai kalar ta, shampoo da dai duk abinda zata buqata, a kayan ta babu wasu manyan kaya sosai sai wasu jalbab guda biyar da hijabs biyar amma sauran duk qanana ne matsattsu da na bacci. Sun isa shago a wahale aka kawo masu abinci suka ci suka qoshi, "Nasreen ya kamata mu koma gida, akwai abubuwan da ya kamata a fara koya maki, saboda zaman Lagos dole sai da su, in dai kina son ki tsira da rayuwar ki, dan ko yan uwan ki da zaki wajen su, suma nasan in suna son zaman ki zasu koyar da ke"  Nasreen zuwa tai ta durqusa idon ta na zubda hawaye ta ce" Hajiya banda bakin gode maki, kin min abinda tinda nake ba wanda ya taba min, kin zame man uwa, in Allah ya yarda kuwa kome kk so zan miki, indai zaki tiqe amanata" Take Hajiya tai murmushi na samun nasara again Tace habaaaa Nasreen tashi meye haka? Ai yiwa kaine, d'a da dukiya ba a masu mugunta, baka san wa zai mora ba, dan haka karkiji komai kome kk so ki sanar da ni kan ki tsaye kinji" ta daga kai tana goge mata hawayen fuskar ta ta jata suka nufi gida.

Suna isa..........


👵🏻   WATA UWAR    👵🏻


    BY HAERMEEBRAERH
Page 9: Suna isa Hajiya Asabe ta sa Nasreen a gaba ta kaita toilet, tai mata wanka tin tanaqi tana nuna jin kunya, Hajiya tace " Ni fa  a matsayin Uwa nak gare ki dan haka ki saki jikin ki na koya maki al'adar garin nan, kar wata matsala ta taso  ki ji ban kyauta miki ba, tinda ban koya maki ba" sannan ta samu nutsuwa ta sake sosai. Anan ne Hajiya ta nuna mata yanda ake shaving hammata, HQ, da qafa,da hannaye, ta nuna mata ya ake asalin yin brush yanda zata wanke cikin harshen ta da lungu da saqo na haqori da ko ina na cikin bakin ta, ta koya mata yanda zata wanke kunne har cikin shi ba tare da ruwa ya shiga ba, ta wanke mata gashin ta tas da Shampoo masu qamshi, ga yankan farce ta mata kai in aka nuna maka hoton Nasreen din qauye da wannan cewa zakai qarya ne wata ce ba ita bace, ta dau haske da wani annuri ke fita kawai fatar nan tasha gyara sai santsi take. "Zo ki kalli kan ki ko xaki gane min wannan budurwar " tana fada tana murmushin hango Nira a jikin 'yar mutane 🙄 Nasreen daskarewa ne kawai batai ba ga wata irin riga da Hajiya ta bata ta saka mai kalar red ta matse ta daga sama mai siraran hannu daga qugu ta sake ta gaba cinyoyin ta a waje ta baya ta kai bayan guiwar ta, kannan ya sha gyara wani ya zubo ta gaba, sauran ta baya ga make up ta sha, (koni dana leqa na kalleta na ga kyau na zaci Qawwama ce lols😜) kunya da dadi ne suka kama ta, ta rufe fuska tana murmushi, " Hajiya na gode sosai Allah ya saka maki da gidan Aljanna, amma Hajiya wannan a gida zan dinga sawa ko bazan fita da su ba ko?" Kwarai da gaske ai ke musulma ce, duk da irin su zakina sawa, amma wadan da suka fi wannan mutunci, dan kinga in ba haka kk anan ba aka gano riqon addinin ki kashe ki za sui kawai, su basa son musulmai"  da ta ji an ce mutuwar nan ita fa   an gama da ita kawai, yanzu za ta fara rarraba ido , tace" ba komai Hajiya Allah ya kare mu, ai Allah na amfani da zuciya ne" Hajiya tace "wannan haka yake 'Yata. A haka dai Nasreen ta wanke kwalliya tai alwala Hajiya kamar ta shaqe ta ganin bata lokacin da tai tana mata amma yar banzar yarinya ta goge ta,  ta ce a juri zuwa rafi dai...

Sai da sukai sati biyu ana koya mata kwalliya, tafiya, magana, da kallo, wasu girke2n zamani, da duk dai abinda ya dace ace mace mai aji ta san su ta iya, kafin wata uku Nasreen ta kware a duk wadannan abubuwan, wani fanfon karuwanci duk Hajiya ta fara sa mata a qidar saidai duk abinnan baya hanata sallah da karatun qur'anin ta. A kwana a tashi lokaci ya ja sosai Nasreen ta manta da wani tinanin neman su Barira da iyayen ta shekara biyu kenan tana wajen hajiya amma har a wannan lokacin Hajiyar renon ta take so take sai ta samu wanda a tashin farko zai bata damman kudade, kan ta miqa mai Nasreen Aji dan yanzu tsabar ajin ta da iya gaye da turanci, kai da komai ma in tana magana zaka ce rada take, wannan dalilin ne yasa suke kiran ta da Nasreen Aji. A lokuta da dama takan tina gida saitai murmushi tace "Inna ga fata da adduar ki na aiki, dan ko hajiya bata hadani da kowa ba by now i know what she meant, and i am going to give her d suprice of her life."


Sun shiga wani hadadden super market ne suka hadu da shi, wankan tarwada ne shi mai tsayin burgewa jikin shi madaidaici wanda kowacce mace zata so ace ta samu miji kamar shi, ma'ana son kowa qin wanda ta rasa, baida irin kyaun nann da da an ganshi za a ce ga kyakkyawa amma a tsari da dressing da cikar zati ba a magana🤐. Kallon ta yake da yana yin takun ta komai ya mishi, sannu a hankali ya matsa kusa da ita, dan ko kula da Hajiya bai ba, yai mata magana cikin isa ta samarin da suka yarda da kansu," hi" daga kai tai ta kalle shi take taji wani sabon yanayi a tattare da ita, tini ta manta Nasreen Aji ta amsa" hey" kafin yai magana "Hajiya ta ce Nasreen in kin gama ya kamata mu tafi" hmmmm Hajiya Asabe Duniya kenan, kula da tai wannan Yaron akwai manyan fa ( Farare bugun ABJ) shine dalilun da yasa take son su fara da shi and after all dan Nasreen tai loosing mashi komai ba matsala he worth it, dama daidai shi suke nema a fara da shi. " Eh na gama Hajiyata " sunan da Nasreen ke kiran ta kenan yanzu ( dan iyayi🙄)  kama hannun ta tai suka fara tafiya, binsu yai dan baiga ta zama ba...........

    


Tanx alot for reading my novel, i did not espect to c so many of u liking it, to alhamdu lilLAAH all i want is for u guys to read and understand kuma ai aiki da abinda aka ji din, dan Allah kar wata ta zaci na fara novel ko dan a karanta ai nishadi ne, no dis is not my aim, my aim is duk wadda ta karanta a shafi daya tai qoqari ta koyi wani darasi tai aiki da shi shin buri na komai qanqantar abu indai me kyau ne kar a raina amfanin da zai. And for ur information my novel is base on true life story amma dole a kwai abubuwan da sai an qara kar wata taji yanda bai mata ba taji haushi, wadda taji haushi ina me neman afuwar ta da yafiyat ta. Na gode sosai da kulawa ba kadan ba ban tsammani ba. Love u all


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻

      

BY

 HAERMEEBRAERH

Page 10:


Sun kai qofa ne yai gyaran murya ya kira sunan ta da wata irin murya mai sace zuciyar wadda akai domin ta"  Nasreeen"  tsayawa tai cak, ta kasa motsawa ko ina, a hankali ya qarasa gabanta, yana mai neman su hada ido da ita amma ta saukar da kai qasa, sakamakon yanayin daya jefata ciki, musrmushi yai na na ganin tarkon shi na neman kama kurciya, a hankali ta dago ta kalle shi, ta amsa da " Na'am ? " Sunan ki yai kama da ke suna mai dadi a tare da yarinya mai sanyi da Aji"  hmmmm maza kenan zuma kuke ga zaqi ga harbi" tana magana ne cikin wani irin salo da ya rikita mai tsayuwar shi saida ya jingina da motat dake gefen su, sai lanqwasa ake tana fari da ido tana lankwasa harshe, miqa maya complimentary card din shi yai sannan yace" ban yarda na tafi ba saina saka digits din ki a waya ta dan nasan ku mata akwai jan aji ni kuwa bazan iya jira yau ban zo inda kk ba" nan take ta fado mai tai gaba tana wani irin takun,da ni kaina sai da na tsorata da anya Nasreen ce kuwa🤔
Sun isa gida kenan hajiya na qara koyar da ita salon yanda zata jawo shi a jiki,su tatse shi kamar toothpast. "Hajiya ta ki daina damuwa, Nasreen Aji kk magana da ita ba Nasreen yar qauyen Langyam ba"  tare sika bushe da dariya. Kiran sallah akai,ta tashi taje tai alwala tai sallah, tai karatin ta na duk bayan sallar farilla data saba, bayan tai azkar din kowacce sallah da akeyi, Nasreen bata manta da sallar ta ba,balle karatun ta,dan a haka ma qoqarin ci gaba da haddar ta take,duk bayan asuba. Ta idar ta shiga wanka,ta dade tana gyara jikin ta, ko ta ina musamman bakin ta ( warin baki ga mace bala'i ne mu kula kar muna magana oga na ja baya muji haushi muce ko dan kiss dinnan ma baya som mana ba laifin shi bane namu ne ba mai son wari koda kuwa shi yana yi) fitowa tai ta ga wayar ta nata faman neman agaji, bata daga ba saida ta gama shafa mai daya dauketa kusan 8mnts , ta samu tirare kala2 ta saka a duk inda ya dace kamar, hammata, wuya,bayan kunne, cibiyar ta , bayan ta, da matsematsin hannu da cinyoyin ta, sannan ta bi dukka jikin da humra mai kyau da qamshi, ta shafe ko ina har fuska, kan ta gama komai dama ta wurga kaninfarin ta daya a baki tana ta tsotsa, ta dakko wani riga iyakarta guiwa mai kalar pink ta saka qasan rigar a bide yake fadi ne da ita sosai,  ta sama kuma a matse yake da wani net shara2, sai aka yiwa daidai inda boobs dinta yake shafi da dark pink color material , wanda yai shape kamar bra ,ta gyara gashin ta daya sha wanki da qamshi, ta mai da shi tsakiya ta daure,ta dakko takalmin ta kalar kayan ta flat ta saka. Wayar ta ta gama dialing no data kirata kan ta fara connecting kira ya sake shigowa, saida ta kusa katsewa ta daga, " lallai da baki daga ba inajin daga nan sai asibiti dan bazan qara moruwa ba" wata irin siririyar dariya ta saki mai cike da kissa wadda ta haddasa mai kasala tai, " bazaka je asibiti ba saidai zaka iya zuwa gidan mu yanzu dannima na matsu na qara kallon kyakkyawar fuskar ka" Really?" Itake kalmar daya furta, " Amma kin min laifi" ya fada da shagwaba, " name? Har yanzu baki damu da sanin suna na ba" hhhhhh lallai ne, kamanta kenan ka ban katin ka?" Oh yeh na tina" cike da murmushi, ok Dr Naseer Uamar Tafeeda sai na ganka" kit ta kashe wayar ta barshi da mamakin yanda tafi kowa iya furta sunan shi a duniya.
Wanka yai ya gyara jikin shi, in ba zuqa maku zan ba ma sai nace ya fi ta iya gyaran jiki a matsayin shi na namiji, duk abinda tai ya ninka nata, yana kammalawa ya fito, cikin wata baqar riga mai dogon hannu da baqin wando, da wuya ya canja wata kalar kayan saidai ya qara da fari shigar shi kenan ko a inner wears ma nashi fari da baqi ne, yana fitowa hadaddiyar motar shi ya nufa sai kwatancen da ta turo mai ta waya ya bi.


Yana isowa palo aka mai iso, ya samu daya daga kujerun gidan masu kyau ya zauna yana kada qafa. Wani irin qamshi ne ya daki hancin shi ya ruda shi gaba daya ya maida hankalin shi zuwa qofa, isowarta keda wuya ya miqe tare da bude hannu qarasawa tai ta mai wata iriyar rungumar da yaji kamar zai fadi, amma ita ta basar a zuwan gaisuwa ne kawai hakan ta koma nesa da kujerar da yake ta zauna ta barshi a qame baki bude😮 " Have a seat pls".....


..


HOOOOO NASREEN KAMAR WATA RENON XINNEE........😂😂😜


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻


      BY HAERMEEBRAERH

Page 11: 
Zama yai yana qoqarin daidaita nutsuwar shi, amma dik da haka saida Nasreen ta gane ya fara shiga tarkon ta, murmushi ta mai mai ratsa zuciya tace " so what next?" Tana daga gira guda daya, miqa hannun shi yai da nufin ta isa gareshi, ba musu ta miqe cike da yanga da taku irin na yan duniya ta isa ta zauna a gefen shi ta raba jikin ta a nashi sosai, ajiyar zuciya yai ya fara magana" Nasreen a gaskiya duk wanda ya ganki ba zai so ki wuce shi ba tare da ya so kasancewa da ke ba, amma abun mamaki adress din da kk ban tin daga shi jikina yai sanyi, meye dalilin ki na zama gidan karuwai?" Murmushi ta sake yi ta kalle shi ido cikin ido ba ko kunya tace" Naseer kenan to ai kaima kasan ba yanda za ai wadda ba karuwa ba ta zauna a gidan karuwai ko?" Dan razana ce ta bayyana a fuskar shi amma ya dake " wannan haka yake, kenan kinaaa nufinnnn keeeee..?" Hhhhhhhh kwarai da gaske, saidai ni akwai bambanci, ni ban taba wannan al'amarin ba ba kuma na son na fara da wanda ya girmen sosai kamar ace irin tsoffin banzan nan masu bin 'ya'yan mutane da matan mutane sun killace nasu a gida da tsattsauran tsaro, nafi son saurayi kamar ka, dalilin amince maka da nai kenan" take kishi mai tsanani ya bayyana a fuskar shi ya dan janye jikin shi yace" kenan kina nufin in na fara yi da ke zaki koma kici gaba da bin qadangarun bariki babba da yaro, talaka da mai kudi, qazami da mai tsafta, sannan nima in zo in hadu dasu na sauke buqatata?" 😡" come down will u? Ba nufina kenan ba in zaka iya daukan nauyi na da bqatu na ni mai iya zama dakai kai daya ne me ka rasa, after all ai buqatar maje hajji sallah" anan ya samu nutsuwa ta shige shi, tqttaunawa sukai tayi yanda komai zai kasance, yanda zasu tafi da rayuwar su sannan kullum nawa zaina bata da dai duk abinda suke ganin ya dace sui da rayuwar su. Kafin ya tafi a ranar ma saida yai wasanni da ita sosai ba kadan ba ya sha mamakin yanda ya tabbatar da eh budurwa ce da gasken, ita kuma tai mamakin dama ashe haka ake ji a wannan abun🤔 lallai tana jira taji nan gaba me zai faru. Sunyi sallama ya bata 30k ya tafi tana daga mai hannu. " Hajiya ta duba ki gani" " me muka samu " qirgawa tai taga 30k tai tsaki, ta fara magana cikin fada da fushin daya tsorata Nasreen " ke wannan yarinyar wace irin shashasha ce ke ta ya ma za ai yazo yai wannan uwar jimawar ya baki wannan dan kudin, duk latsa jikin naki da yai ya qare a wannan sanin kanki ne mayukan da kk amfani da su kan a kaiga turare sunfi kudin wannan, ke da zaki fara mana da dubu daruruwa to bari kiji tun wuri ki nuna mai kuren shi a waya kan yace zai sake dawowa ya mana harkar qaranta" to hajiya kiyi hakuri " idon ta taf hawaye " zo 'yata raina ne ya baci amma ki kiyaye darajar ki nake son dagawa bana son ki fara karuwanci da qaramin kudi qaramar karuwa zaki zama kamar na shagon saida abinci na, so nake ki zama profesional karuwa ke ki zama international karuwa, wadda koda govenor ne zai iya daukan ki, dan haka ke zaki nuna masu ke me tsada ce,sunan ki na Aji ya biki" daga kai kawai take kamar qadangaruwa tana sauraron wannan baiwar Allah.
A kwana a tashi Nasreen ta zama kwararra a fannin karuwanci, ta fara tarayyar karuwancin ta ne da Naseer inda ya dinga binta a hankali har ya cimma burinsu ya samu nutsuwa da ita, dadin da ya samu da gamsuwa bai taba jin shi wajen manyan mata da yammatan da yai hulda da su ba hakan ne yasa yai mata kyautar wani katafaren gida a Oni Reke, bayan sun kai wata biyu tare ya mallaka mata wata katuwar jeep black, saiga Nasreen ana riqe manyan wayoyi, da manyan kudi Naseer ya tsaya mata. Abu na biyu data bata rayuwar ta da shi shine, SHAYE SHAYE, ta fara da busa sigari sai gata tana shan wiwi da sauran kayan mayen da ni bam ma san sunan su ba sam☹ abu daya na burgewa a wajen Nasreen shine rashin wasa da ibada wanda ko me za sui in zai kai ya shiga lokacin sallah fa to sai an jinkirta shi, da dama qawayen ta na bariki da Hajiyar ta da Naseer kan mata dariya suce "duk watsewar da kk kina tsammanin Allah zai amsa sallar ki ne ?" Takan basu amsa da " koma dai me muka dole mu riqe identity din mu mu musulmai ne kuma karuwanci ba dawwama za mui ba muna sa rai da rahamar Allah ai" sai su bushe mata da dariya Naseer ya sha son ya shammace ta da salon shi da bata iya jure mai amma inaaa baya nasara akan wannan. Wannan kenan.   

      QAUYEN LANGYAM

Zaune take gaban kayan kwalliya tana ta rangada kwalliya tana murmushi, sakamakon tunawa da tai yanda Nasreen ta fita tasan tana can tana wulaqanta, sai kuma ta kwashe da dariya ita daya, " lafiya Auta keda wa?" Innar Hinde kenan, " hmmmm inna tinawa nai yau Dan liti yace zai ban dari bakwai innaje shagon shi 700 ( sokuwa a dari ba kwai take rabama gayu jikin ta har take murna) " a hayyeeeeeeeee Allah nawa, kai jama'a kice kwanan nan zan fara riqe dari biyar biyar din kaina kullum?" Hhhhh sosai ma Inna duk abinda aka ban ko da dari shida ne ke biyar zaki ci " ta fada tana wre idanu🙄. Kofa wanka ba tai ba amma an lafta mai a jikin an sha kwalliya ba tsaftar ciki balle ta waje su kansu gayun qauyen kamar kai amai ka kalle su amma a haka ake lalacewar ba ko kyankyami🙄 . Baban hinde ne yai magana" Innar Hinde ki kiyayi Allah, baki da magana sai ta kudi kedai ba zaki tsaya ki gyara kanki da gidan ki ba ki min biyayya ki ba yayan ki tarbiyya sai yawon tazubar kk sa a gaba kk koyawa yayan ki habaa?" Ehhhhhh lallai ne, aaaaa nace lallai ne ya kamata ka min wa a zi, tinda in ban fita nida yarinyar nan mun nemo na abincin mu ba bamu kake, ko na wankin da wanke2 da gyara gidan ba saida kudi ake yin su ba?" Aa Innar Hinde, nan nan gidan malam Kalla sun fimu babu amma gidan shi gwanin sha'awa matar shi tsaf yayan shi maza da mata 8 amma kowanne tsaf ga qana'a da tawakkali da son juna kuma wannan aikin na mahaifiyar su ne dan dai shi in aka bi tashi gidan ba zai haka ba, amma ni na kan qoqarta yi maki abubuwan da kan a samu mai irin su karkarar nan za a dade duk baki gani me yasa ne haka dan Allah? Mu zauna mu rufawa juna a siri kinji mata ta " hahaiiiiiii cassssss malam yaufa ko limamin garin nan aka baka sai yarinyar nan ta fita ta karbon darinnan bakwai dan kaji, ka adana wa'azin ka akan yarka in ta dawo daga yawon abinda ka koya matan" tare suka sa dariya ita da hinde yana jin haka ya bar wajen, dama haka suke masa in ya ce zai masu fada.


"Subhanallahi me nake ji ne a toilet dinnan ne Nasreen?"😱😱.........


👵🏻     WATA UWAR   👵🏻

  

     BY HAERMEEBRAERH


Page 12:  

          A wahale ta fito sanye da pant yellow mai ratsin fari da vest fara mai ratsin yellow, tana kama gini ta iso gado ta kwanta, da sauru Hajiya Asabe ta isa wajen ta tana " 'Yar nan lfy meke damun ki? Na shiga uku ni Asabe me nake gani ha?" Cike da tashin hankali take maganar ta matso ta dudduba ta ta na ta tambayar ta kamar likita, tana gama jin amsoshin ta, ta miqe tsaye cike damuwa, " Yau mun shiga uku to yaushe ma muka fara tara abin duniyar da har zamui baqon cinyewa da shi? Inaaaaa ba zai yu ba sam wallahi dole asan abin yi wannan cikin zubar dashi zamuje ayi tin lafin Naseer ya san da zaman shi ya guje ki" Hankalin Nasreen ya tashi sakamakon kalmar ciki da taji Hajiya Asabe ta ambata, bakinta har rawa yake wajen furta " ci...ciiiiki fa Hajiyata ?a jikin wa ?" A jikin ki Nasreen ba yau na fara aje yan bariki a wajena ba, dan haka alamomin cikine kaf dake" na shiga uku ni Nasreen, ina zan sa kaina, Innar Hinde kinga abinda kk jawo man ko, bakin ki bai zamo alkairi a gareni ba, kullum mugun fata kk man, ga abinda bakin Uwa ya jawo man" tana yi tana kuka sosai mai ban tausayi, Hajiya zama tai tajawo ta jikin ta, tana lallashi, "kiyi hakuri kinji 'yata ki sauqaqawa kanki wannan cikin zubda shi za ai, kuma........." ba wanda ya isa ya zubar min da gudan jini, duk da ba a samar da shi ta hanyar halal ba, dik wadda tai yunqurin zubar min da d'a ko 'ya kotuce zata raba mu da shi, bani da kowa sai uwata a duniya kowa nawa ya rasu mahaifiyata kadai ta ragen, Allah ya ban wannan ba zan qi shi ba, amma akwai maganar da nake son fada maki Nasreen" daga idanuj ta da suka koma jawur tai tana kallon Naseer da ya shigo bayan ya gama jin duk abinda ke faruwa, " in kin amince ni Naseer ina son na aure ki bayan kin haihu na kaima Hajiyata abinda kk haifa ta gani, nasan in Allah ya yarda baza ta qi ba, amma sai kin amince" zuciyar ta ce tai sanyi akan quncin da ta shiga da, Hajiya ko tafi kowa baqin ciki da wannan labarin amma ta danne bata nuna ba, to in yarinyar nan ta tafi wanan gidan kadai tasan wataqila da motar zata tsira da shi amma in tana nan filayen da ta sissiya da kudin datake samu wajen ta ai ta gine su, aranta take wannan tinanin, " Allah to ya raba lfy" fita tai ta barsu yana lallashin ta, wni irin kyau yaga ta mai da ba zai iya jurewa ba saida ya san ya yai yaja ra'ayin ta suka watse.        Akwana atashi asarar mai rai Nasreen ciki ya kai watan haihuwar shi, shigowarta kenan daga kasuwa ta siyo kayayyakin da duk suka kamata, daga qafar nan da zatai ta shiga daki taji bazata iya ba, nan danan naquda mai tsanani ta kama ta gashi ba kowa a gidan Hajiya na wajen abinci tana ganin ya suke tafi da wajen dan tin zuwan Nasreen ta daina zuwa likafa taci gaba. A daddafe ta samu ta isa bakin mota tai kasada ta hau sai asibitin da take awo, nurses ne suka zo suka shiga da ita, tin shigowar ta ta hango ta daga nesa..............


👵🏻     WATA UWAR     👵🏻

   

    BY HAERMEEBRAERHPinkyn Cute One Allah ya bar qauna soyayyar ku da ban ce Allah baku miji daya asha bidiri😂😂😂😂😂😂😂😂😂 kar naji yarinya tace ba Ameen ba kuma😎 😂😜😜😜


Page 13: "Wannan kamar Nasreen Inna!" Cewar Barira kenan da take gefen motar ta ita da Innar ta, " Aiko dai dan inma ba ita bace kamar to tai yawa, amma ya akai naga wannan kamar tana da ciki haihuwa tazo? And ki duba kayan jikin ta ba ko mayafi, anya itace kuwa?" Inna mu je ciki amsar na can ba zamu gane komai anan ba kar suje inda bamu sani ba" da hanzari suka bi bayan su, suna isa daidai an shiga da ita dakin haihuwa kenan da ganin ta Barira ta qara tabbar ma Innar ta wannan Nasreen ce tabbas, amma ya akai haka ? Meke faruwa? Damun kwakwalwar ta tai da tinani har daga baya ta girgiza kanta ta daga kafada alamar bari ta fito sunji komai. Nurses ne ke magana akan "to ya zamu san yan uwanta ita daya fa tazo sai dai ko ta wayar ta" cewar wata siririya sosai qugunnan kamar an daurawa tabarya zani Sak Cutie dai😜💃🏻

Barira ce ta matsa kusa tace "mune yan uwan ta me ya ke faruwa " ta haihunne" Eh ta haihu, ta samu namiji, muna buqatar kayan ta ne da za a canja masu ita da babyn" k ba damuwa in ba matsala muna son muje mu dawo tukunna dan bamu zo da su ba"K No p, amma kui sauri pls" da hanzari Barira taje ta siyo duk abinda za a biqata ta kawo masu, karba sukai sukaje suka shiryata da komai, taje office din Doctor bayan ya kirata ya mata bayani akan zasu iya sallamar ta tinda ta haihu lfy ba matsala, biyan kudin komai tai suka je dakin da aka kwantar da ita. Sallama sukai suka shiga ido hudu sukai da juna, Nasreen waroo manyan idanun ta tai kamar zasu fadi irin na Pinky tace " Ba....Bariiiraaa, Barira kece ko mafarki nak?" Nice Nasreen ba mafarki bane" qoqarin tashi take amma ta hana ta ta zauna kusa da ita suna mai kallon juna, ganin Innar Barira ne ya sa Nasreen saukar da idon ta qasa cikin jin matsananciyar kunyar ta da kunyar aminiyar ta ta, nan take hawaye ya fara zuba a idanun ta, wayar ta ce ta katse ma Barira tambayoyin ta, miqa mata wayar tai ita kuma ta karba cike da kasala" Hello Baby kina ina ne naje gida baki nan na hana ki fita a condition din ki so kk ki haihu a hanya ko ki bari na zo na kaiki duk inda zaki mana amma bakijin magana ta ko?" Kayi hakuri Daddy gani a asibiti ma na haihu dazu ina dawowa naqudar ta kama ni na taho nan na haihu lafiya" Cikin wata irin murna da ta ba Nasreen mamaki dan shegen akewa wannan murnar🤔 ya amsa da " Nasreen my baby da gaske i am nw a Dad? With excitement yake maganar kamar ya huda wayar ya ganshi gaban su , kashe wayar tai karya fasa mata kunne ta tura mai Address din asibitin ta aje wayar.Labarin komai ta basu kafin ya iso, Innar Barira kuka tai tayi ita da Bariran sun tausaya mata amma kuma sunji tsananin baqincikin salwantar da bata rayuwar ta da tai gashi harda rabon dan shege, Barira ce tace "amma Nasreen kin ban mamaki har xaki iya zama ki aikata wannan mumminan abun saboda kawai Innar ki ta miki sharri da yar uwar ki" ba haka bane qawata wannan abun na dauke shi a matsayain qaddarar rayuwa ta ne tinda kowa da tashi, and in kin kula anyi amfani da rashin sani na ne aka fara koyar dani abunda banda ra'ayi da dabara Hajiya ta samin son karuwanci dan haka ni yanzu saina yi kudi na fara aikawa inna taji dadin su kamar yanda take so" kan tai magana aka bude qofa, cikin hanzari ya iso gareta ko kula da mutanen wajen bai ba ya rungume ta yana mata kiss ko ta ina ya samu yana surutan yi mata godiyar sama mai d'a da tai Innar Barira ce taja hannun ta sukai waje bakin Barira bude tana mamakin wannan abu. Suna tsaye sukaga sun fito shi riqe da kyakkyawan yaron su a hannu , ita kuma tana maqale a qugun shi, wajen su Barira suka nufa Inda ya gaida su dan Nasreen ta bashi labarin su, ya masu godiyar komai likita ya sanat da shi sun biya kudin komai yace masu zai biya su in sun koma harda qari dan sun taimaka mashi yaita godiya saida Innar Barira ta katse shi da " Yaro wannan da kake gani 'Yata ce haihuwar tane kawai ban ba dan haka ba godiya a tsakanin mu" nan yace masu shi zai wuce da Nasreen wajen hajiyar shi ne dan haka su su bashi Address din su zasu neme su, Barira ce ta basu Address da no wayar su sukai sallama suna masu kewar juna.


Suna shiga gidan Nasreen baki bude dan tin daga waje dama take mamakin kyau irin na gidan, masu aiki ne suka zo da sauri daya ta kama Nasreen daya ta bude qofar shiga cikin palon gidan suka sa kai, Wata Hamshaqiyar mace ce a kujera ta dora qafa daya kan daya, ana ta latsa waya☹ ganin danta ne ya sa ta miqe cike da fara'a ta tarbe shi amma ganin shi da wata ga jariri ya bata mamaki sosai, duk da haka farincikin ta bai gushe ba, amsar yaron tai tana kallo, wani irin faduwar gaba ne ya sameta, hankalin ta yai mummunan tashi ganin yaron dake hannun ta, ta daga kai ta kalle shi," Wannan dan waye Naseer?" Mum ki taimaka wa wannan baiwar Allahn mana yanzunnan ta haihu tana buqatar kulawa kafin bayanin komai, bata wa dan nata musu kamar wani Uban ta take bin umarnin shi haka ta kama ta suka shiga, ta hada mata ruwan zafi sosai ta kaita toilet ta gyara jariri ta sa mai kayan shi da suka zo da su sabbi, bayan ta fito wanka ne daure da towel, Mum ta bata wasu daga cikin kayan ta ta saka dan Da kadan ta fita qiba tinda Nasreen ba dai diri ba, ta fito sak me jego da ita looking take away😘 fitowa sukai ta kaita palo aka kawo mata abinci da Tea mai zafi da kauri ta sha sosai kuwa dan tunda ta haihu take jin wata muguwar yunwa, bayan kowa ya nutsu ne Mum ta leqa dakin Naseer, kwance ta hango shi ya tallabe haba yana kallon waje daya, zama tai kusa da shi ta dafa shi tace" Son me ke faruwa ne kamin bayani naji wacece waccan? Dan waye kuma?" Mum Dana ne ita kuma budurwa ta ce" cikin tsananin firgita ta miqe tsaye "Dan kaaaaaa ??????.....👀👀👀👀

 "


👵🏻     WATA UWAR     👵🏻


    BY HAERMEEBRAERHPage 14: Baya ta fara ja tana girgiza kai, tana hawaye , dan tasan in ya matso kusa da ita ba abinda zai hana ta sallama mai kanta, hade hannayen ta tai duka biyun waje daya da alamar roqo," dan Allah ka rufa mana asiri ni da dan ka ka fita in Mum taji labarin ka shigo dakin nan which zata ji din dan sai an fada mata, barina gidannan ya zo" kiyi hakuri Nasreen na kasa jurewa ne, yau watan mu shida rabon mu da juna, hakurina ya kare nai ya qoqarina" daidai nan ya iso gareta, hannun shi ya sa ya janyo ta gare shi a hanzarce kamar dai (mero tsokana ta ga masa 😂😜 ) a hanzarce yake aika mata da saqonnin shi masu wuyar fassara, tana jin bakin shi anata komai ya kwace mata sun manta a ina suke, wane hukunci ne zai biyo bayan su, suna tsaka da jiyar da junan su dadin da suka dade basu samu ba aka banko qofar da qarfin gaske, wanda yai sanadiyyar firgitar su dika, jiki na rawa Naseer ya sakko daga kan ta kai a qasa, Mum idon ta kamar gurjiya dan girma, ta shiga mummunan tashin hankali daya sa saida ta jingida na bango na kusan minti 3, kannan Nasreen ta suturta jikin ta ta dakko yaron ta dake bacci zata raba Mum ta wuce, dan ko ba a gaya mata ba tasan zaman ta yazo qarshe, shaqe mata wuya Mum tai tana zare ido tana masifa" jarababbiya wato fitar da nai saida kk san yanda kikai kija jawo ra'ayin shi kanki ko? An dade ba a yi ba shine dan jaraba kk sa yazo wajen ki ko? To fitar tawa ma minti nawa ne? Na gode maki Saude da kk sanar da ni da wuri duk da na makara zuwana, amma van makara ba wajen aika wannan lahira,dan yau, sai dai,ko ni,ko ke,  a hanzarce ya isa gaban ta ya kwace ta da kyar yana kuka " Mum kiwa Allah ki auran Nasreen, karki cutar da rayuwa ta dan Allah"😭 "Nasreen zo ki wuce ki bat gidannan yanzunnan kan na budi ido na qara ganin ki" bude jakar ta tai ta debo kudi masu tarin yawa ta bude jakar ta ta zuba mata ta hankada ta waje ta rife qofar, miqewa yai da gudu zai fita waje ya bita Mum ta daka mai wata gigitacciyar tsawa, qamewa yai a wajen jiki na rawa, a fusace ta matso inda yake ta wanka mashi wasu marika masu zafi guda uku, ta nuna shi da yatsa" Naseer indai ni Habee nice na haife ka, kuma ka sa qafa kabi yarinyar nan ko yanzu ko a gaba kai ko a hanya ka gansu ka nuna ka san su to bani ba kai na yafe ka nonona da kasha ban yafe maka ba ka nemi WATA UWAR amma ba ni ba, duk iya alfarma na maka banga dalilin bin wannan karuwar ba na fada maka" ta sa kai tai dakin ta ta bar shi nan kwance kamar xai mutu dan baqin ciki, dirqushewa yai yana kuka mai ban tausayi yana "shikenan ni kuma rayuwata ta halaka, na shiga uku Nasreen na rasaki har abada, ki yafe man , ki kula mana da dan mu" haka yaita sambatu har yai baccin wuya. Mum ce ta fito ta ganshi a wajen tausayin shi ne ya kama ta mai tsanani amma haka ta wucewar ta, ta dakko wayar ta" Hajiya Bilki akan maganar da muka fara dazu ne ni bana son auren ya wuce wata daya komai da komai nake son mu kawo a gama akan lokaci" To shikenan Hajiya ba damuwa data dawo daga Adamawa za ai komai dan dama Naseer shine burin ta a kullum shine dai baya kulawa" to na gode Allah ya bar zaman tare ya qara mana zumunci".
Ta fita gidan tana kuka sosai Taxi ta tsayar sai gidan su na da, dan dama Hajiya Asabe na sane d komai da ya ke faruwa kawai dai Nasreen taqi yarda da abubuwan da Hajiyar ke fada mata ne, na ta bat gidan ta dawo su dora daga inda suka tsaya. Kuka take sosai tana cewa" dana sani na bi maganar ki hajiyata da duk wannan wulaqancin bam fuskance shi ba" ganin mahaifiyar shi na kuka ne yasa Naufal kuka shima, Nono ta fara bashi tana rarrashin shi suka isa , daidai nan hajiya ta fito daga mota itama da alama unguwa ta fito.Bayan jajantawa da komai, daga ranar Hajiya Asabe ta fara gyara Nasreen sosai ta maidata hadaddiyar mace, kyau kam ba a magana, irin cika da kyau da Nasreen tai ba a magana , a haka ne Hajiya ta samo mata mai reno ta aje Naufal ta dora daga inda ta tsaya masu kudi kuwa manyan qusoshin gwamnati ne ke zuwa wajen ta, hajiya nada wannan connection din har waje saida Nasreen ta fara fita  akan harkar karuwanci, duk abinnan da ake Naufal ya kai shekara biyu lokacin bai san meke faruwa ba, domin in zata hadu da danta cikin shigar mutunci take zuwa tai wasa da shi tai mai komai, ya saba da ita sosai in bata nan ta dawo yaita murna, tsaraba ba irin wadda bata kawi mai, ana haka ne ta yanke shawarar aika wasu kudade masu yawa gida, ta kuma yanke shawarar zuwa ne da kanta ba aike ba.😱

       QAUYEN LANGYM

Hinde ce take miqawa inna dari biyar duk ranta bace, "ke inna yau fa iya abinda na samu kenan kuma ba sisin da zaki ban yanzu?" Tab ai ko sisi ba zan baki ba, naga in haka ne kin tsira da jin dadin da kikai a can yawon naki ni ba saina tsira da dari biyar din ba?" Allah gobe ba zan kawo maki ko........, sallamar Nasreen ce ta sa dukkan su suka miqe suna zaro ido, " wana ke gani kamar Nasreen ?" Cewar Inna kenan" Inna nice Karuwar yar ki ce ta dawo tare da jikan ki, Hinde bismillah mana ki iso ki dauki dan ki mana ga kaya bako taimakawa? Tana yi tana murmushi, Baban Hinde ne ya shigo riqe da ciyawa a hannu , da gudu Nasreen ta qarasa ta karbi ciyawar ta sauke masa tana masa sannu, baki bude yake kallon ta da kayan jikin ta da suka matse ta yan kanti riga da skirt , "wace wannan kamar Nasreen?" Baba nice

Muje ciki" ciki suka shiga inda Innar hinde da Hinde suke baki sake. Bayan sun zauna ne Nasreen ta kwashe komai ta gaya wa mahaifin ta ta ce "Yanzu ma kwana biyu kawai zan na koma akwai inda zamu da wani Alhaji zuwa Ingland  damu dan yi sati biyu yasa nace bari na zo a gaisa an dade ba a hadu ba" Baban Hinde kuka ya fara yana" Haba Nasreen yanzu tarbiyyar dana maki kenan ? Ina hankalin ki yake? ina tinanin ki ya tafi?" Kuka take son yi saboda jin da take bata kyauta wa rayuwar ta ba da mahaifin ta amma ta danne, " come on Baba meye na kukan, haka fa Innar Hinde take son ganina kuma yanzu gani ba shikenan ba " Innar Hinde ce ta matso for d first time tai magana" 'Yannan rayuwa fa saida kudi ni kuma naga alamar wu a tattare da kw dan haka ki abinda kk so ba mai takura miki a gidannan, Hinde ce ta matsa tace wallahi kuwa, da ace kinbi shawara tin da ai da kin dade da sanin dadin kudi, ni yanzu so nake nima ki kaini nai kudi irin naki dan Allah kiyi dan zumunci ba dan halina ba" dariya sosai Nasreen take yi" Lallai hinde baki da hankali a birni wa zai ma zauna kusa dake balle ya neme ki? Ai ke sai mazan qauye" tana fada tana miqewa tsohom dakin su, a daidai gaban Innar su ta tsaya ta budw jakar ta ta dakko kudi yan dubu2 ta aje mata a gaban ta kimanin dubu dari biyu, Inna hauka ne kawai ba tai ba ranar dan murna, sai ga kirari ana zabgawa Nasreen a haka ta ba baban ta wayar Hannu da kudin da Mum ta bata, ta mai bayanin wannan kudin ga yanda ta same su dan haka da Allah ya karba ya ja jari, kafin ta tafi saida ta bude masu account a qauyen gaban su ta damqa ATM hannun wani maqocin su mai shago, tsohon saurayin ta ne shima yana da hankali yaso auren ta matuqa amma Inna ta qeqasa qasa tace baida arziqi, a haka ta bar qauyen Inna na sa mata albarka Baba na mata nasihar taji tsoron Allab ta gyara rayuwar ta,  Hinde kam in banda baqin ciki daya qaru mata ba abinda ya qaru a ranta.

Ta koma Lagos lfy, inda sukai tafiya da Alhajin ta har suka dawo. 

A wata yamma sakaliya ne ta hadu da su........


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻


    BY HAERMEEBRAERH


Na'ima Tabital❤

Salma qanwa ❤Tabital 

Duk na gaida ku kyauta ANA MUGUN TARE❤

Page 15:Ta fito dauke da Naufal a kafadar ta, zata bude mota suka qaraso, dayan ne yabi ta bayan ta ya sa mata bindiga a qugun ta, dayan ya shiga mazaunin driver ya zauna ya miqa mata hannu, yana nufin ta bashi key, shigar da su motar sukai suka bata wuta, a can bayan gari suka shiga wani dakin katako, dauke yake da katifa, shiro, ledar daki, dadai tarkacen da ba a rasa ba, SANI kenan, suna isa suka tura ta cikin dakin suka zauna, " Sani meke faruwa ne naga ka kawo ni nan? Kar ka cutar da ni bayan alkairan da kk samu a sanadina" Alkairai???? Alkairai fa kk ce Nasreen ? Wanne alkairai baya ga cin mutunci da Hajiya ta min d korar kare? Sannan ki budi baki ki kira hakan alkairi? To bari kiji in ba baki san meke faruwa ba ki sani, a kwanakin baya naje shago wajen Hajiya Asabe akan nima adan dinga ban wani abu, duba da ni na kawo ki wannan garin, amma Hajiya ta ci mun mutunci tamin tas, tace i should do my wost in ina so but she cant give me a penny, raina ya baci ba kadan ba, tin a lokacin na qudiri dauke ki amma na kasa ganin kina dauke da ciki, bayan kin haihu na rasa ki, sai shekaran jiya na nan ku ke da wani mai kudi, daga nan na fara bibiyar ki, in da kk ganni ma bacen kikai na je gidan da niyyar na ga ina kk, na hango Hajiya da wasu da muka saba sayar wa da gidaje da dikkab alama gidan da kuke ciki zata siyar, hakan ne yasa na biyo bayan ki na sanar dake dan ki koma ki san abin yi, amma a gaskiya a yanda na ganki ba zan iya bari ki kufcen nima ban mora ba," yana yi yana lashe lebe, yana binta da wani shu'umin kallo da shi da abokin nashi suka tafa, "innalillahi wa inna ilaihirraji'un, kana nufin yanzu ta siyar da gidan da komai nawa a ciki? Kenan jiya bamkwana mukai da ita hirar da mukai mai tsaho? Ban taba zato ba, ban taba tinanin haka Hajiyata zatai min ba,😭yanda na dauke ta kamar uwa" hhhhhh a barikin? Anyway banga laifin ki ba coz ke din ba wani kinsan gari bane har yau, zonan dan baba zamu dan ari uwar ka na dan awanni kaji" ya amshi Naufal ya ba abokin, ta miqe tsaye da hanzari zata karbe dan ta, kan ta isa har ya fice, Naufal nata kuka itama tana kuka tana " kaiwa Allah karka cutar da ni da dana Sani ka tai maka ka kyale ni naje na amso dukiyata mai tarin yawa dana tara karna wulaqanta" hhhhhh wulaqanci na nawa kuma maza nawa kk bari suka wulaqanta ki da sunan karuwanci? Kawai bude nima na dana kamar sauran, matsalar daya ni ba biya zan ba kyauta za a ban, kuka ne mai tsanani da nadama mai yawa suka taru mata, wannan wanne irin wulaqantacciyar rayuwa ta zabawa kan? Gashi yau ana son a mata abinda ba ita take so ba, a take tinanin Naseer ya fado mata, wani sabon kuka ta saki mai ban tausayi, amma inaaa Sani ba ruwan,matsowa yai kus da ita bakinnan sai mugun wari yake, toshe hancin ta tai ga uban warin zufa da yake hannun shi wani irin baqin datti, a haka ya sa ka mata a fuska yana share mata hawaye ya sa dayan ya cire mata punnytail din da tai d gashin kanta, ja ta farayi da baya har ta kai qarshen katakon da yake a matsayin katanga, duqawa take qoqarin yi, amma ya riqe ta ya hade bakin su waje daya, wani irin amai ne ya taso mata da bata shiry ba, kafin yai komai ta zubo shi mai mugun yawa a jikin shi tana maida nunfashi d kyar,ashar ya saki ya wanka mata mari mai zafin gaske, ni zaki wa amai a jiki dan........ to ki tabbata kin gyara wajennan kuma yanzu ba sai najima ba saina dana ki nima kamar kowa yar......... kuka take tana roqon shi ya kyale ta amma inaaa, take dabara ta fado mata tinda abinnan dama yi take da kowa ma amma qazamai irin Sani ne bata taba harka da su ba," naji zakai komai kk so da ni nima zan taimaka maka ma, amma wallahi in bakai wanka ka wanke baki ba bazaka taba samun yanda kk so a wajna ba amai zanta yi" hhhhhhj indai wannan ne karki damu fita yai tana nan ta gyara wajen tana rakube tana kuka, tin tana jiyo kukan Naufal har ta daina ji, alamun yai bacci oho🤷🏻‍♀ bude qofar yai ya shigo ashe dai kyakkyawa ne qazanta ce ta maidashi wani iri, yana yaqe haqora ya qaraso, a haka dai saida yai abinda zuciyar shi ke raya mai da ita, abu kamar wasa ya aje ta ita da dan ta har na wata biyu, tin yana kawo musu abinci har ya zamana baya kawo wa ya fara wulaqanta ta ta kode ta jeme kamar ba ita ba dama baqa ce sai ta qara duhu sosai, ga rama da tayi, gashinnan da ke shan gyara inaaa tini sai da ruwa take wanke.shi, dan ma mai tsafta ce da haka.zatana xama inda Hinde ce😜  a haka si Sani sika dauke qafa, suka daina zuwa.Wata rana tana bacci.goshin asuba taji hayaniyar wasu samari, qoqari suke su shogo, dan sin dade suna noticing din ta a unguwar, sunyi2 su bude qofa abu ya gagara, jin hakan ne yasa ta tsorata ba kadan ba, Allah Allah take gari ya waye ta canja mazauni, a haka suka gaji suka tafi suna zasu dawo ne, suna tafiya ta miqe ta saba Naufal a baya ta tattara sauran komatsan ta ta qara gaba tafiya take batasan ina ma take tafiyar ba, har taje wani waje kamar tasha, anan taji suna lodin arewa, tinani take na gwara ta koma arewa da zama akan nan sai ta mutu da danta ma ba wanda ya sani amma acan tasan da yardar Allah bazata na kwana da yinwa haka ba ko aikatau zatai amma alqawari daya data dauka ta gama.karuwanci, tina hakan ne yasa ta goge hawayen dake zubo mata masu mugun zafi da quna ta nufi wajen driver ta mai bayanin ga inda take son zuwa amma bata da kudi ya taimaka mata dakko ta akai aka kawota nan ita da danta bata san kowa ba, a haka dai ya tausaya ya ce ta jira motar ta cika su wuce


Tafiya mai nisan gaske sukai kafin su iso garin kebbi a nan Jega aka sauke ta suka qara gaba jinta a arewa sai yasa mata wani kwanciyar hankali, gefen wata mai abinci ta je tai mata sallama ta fada mata yunwa take ji ita da danta dan Allah ta bata abinci suci zata mata wanke2, kamar zata kore su amma ta tausaya ta bata shinkafa ce da miya ba ko nama haka sukaci suka sha ruwan da ake tarawa dan ko arziqin na yar ledar ba a basu ba, tana gamawa kuwa mayat ta loda mata uban wanke2 mai tarin yawa, ga mamakin ta sai taga Nasreen na murmushi " baiwar Allah hankalin ki bai tashi da ganin wannan uban wanke2 ba?" Hmmm Hajiya ai ni taimaka min kikai domin wannan dan ragiwar na su inna tattara zamu samu na dare da dana wataqila ma harda na safe" tana magana tana maida wani hawaye dake son zubo mata, cikin tsananin tausayawa matat tace mata muje gidana yar uwa zan baki aikatau amma zakina min shara da wanke2 ne a gida zanna biyan ki dubu 3k a wata inkin yarda akwai daki da bandaki a tsakar gida zaki koma can da zama bazan hana ki yin kowacce sana'a ba in kina so" zubewa tai a qasa tana godiya cikin kuka mai ban tausayi Hajiyar daga ta tai.Bayan sun tashi gida suka nufa, daki da komai ta nuna mata kamar yanda ta alqawar ta mata godiya mai yawa Nasreen ta qara yi ta shiga ta aje kayan su ta fito ta dan tattara gidan nan danan ya dau haske tana gama wa ta shiga wanka daidai nan mijin Hajiyar ya dawo dan kasuwa ne shi kuma, ganin Nasreen ne yasa shi hade fuska sosai kamar wanda akai wa saqon mutuwa..........


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻

 

   BY HAERMEEBRAERH


Page 16: Bude labule yai" kaltume! Kaltume ! Kaltume ! "Na'am Alhaji, sannu da dawowa, irin wannan kira hk? Mi yaffaru halan?" Shiga palon yai mai dake da kujeru masu kyau da TV plasma sai dan abubuwan da ba a rasa ba, kadaran kada han, gidan masu rufin asiri, " wace ta waccan niggani tsakar gida naga kuma qaramin yaro?"kai amma wallah ka ban tsoro, na zaci wani abu na yassame ka can kassuwa wallah🙄 " Shin baki amsamin tambaya ta na?" Me aikatau ta niddako, ayyukan gidan ga na yi min yawa Alhaji, shi nassa na dakko ta ta zanka taimaka min, sai ina bata 3k a wata, ko mi kaggani? Wallahi tausayin ta na yakkamin nace ta tahowa nan din, don Allah mu taimaka mata Alhajina" magana take tana wani rangwada tana matsawa kusa da shi, cire mai hula tai ta fara shafa sanaqon kan shi, take fara'a ta bayyana a fuskar shi yace " to shi kenan yanda kk so ai haka nan za ayi, debo min ruwa nan na sha da abinci wallahi yunwa nika ji" tashi tai tana kada qugu tana rausaya , shiko bude baki yai kamar wawa yana kallon ta yana hadiye yawu, dan Alhajin ba qaramin mayen mata bane, duk qoqarin ta na ganin ta kiyeye mai buqatun shi dake kanta, hakan bai hana shi shegen son mata ba, baya raina haram a mata shi, ba dan yawan son matan shi ba da dukiyar shi ta fi haka yawa, dawowa tai tana kada qirji, da shigar ta mai burgewa, ta durgusa ta aje mai a gaban shi babban faranti ne dauke da abinci da ruwa na wanke hannu da na sha, zuba mai tuwon alkama da miyar kubewa danya da yaji tantaqwashi, ga jus din lemon zaqi da tsami da danyar citta da abarba da tai masa yaji kayan kamshi da sugar, zubawa take tana mai wani salon daukar hankali" Hajiya do Allah dai ki bari na isuwa cin abincin ga lahiya kar ya maqale min ga maqoshi" hhhhhhhhh Alhajina kenan, me nai kuma 😉"  ta qarasa da yar shagwaba" hmmmm kaltume kenan bari na isuwa ki ga wani abu" dariya sukai a tare ta zauna kusa da shi tana mai firfita, tana lumshe ido. Bayan ya gama ne taja shi zuwa toilet ta mai wanka tsaf ta saka mai toothpast a brush ta miqa mai itama ta juya tana son tai wankan" Aa ba za ai haka ba nima yanda kk wanke ni nima saina wanke ke, ke kadai ta kason ladan?" Dariya tai mai daukan hankalin shi ta miqa mai soson, wanka yai mata tas suka fito, goge mai jiki tai ta feshe shi da turaruka masu qamshi, dayake garin akwai zafi sosai, ba ta damu da shafa mai ba , mai ta miqa mai ya fara shafa mata cikin salon shi mai rikita ta, tindaga nan salon su ya sauya, ina ganin haka nace to Mero yar sa ido muo waje😂 har an baza ido ana son aga kwakwaf😂😂😜 .Washe gari da safe kan ya tashi ta farka tai wanka ta yi kwalliya tashiga kitchen ta fara hada abin karyawa, fitowar ta ya bata mamakin ganin Nasreen har ta wanke kwanukan jiya ta gyara tsakar gidan ta wanke bandaki, cike da mamaki tace" eh lallai in a tafe kake wani a hanyar ya kwan" gaisawa sukai Naseern ta tambaye ta ko da abinda za a dafa Hajiyar murmushi tai ta sanar da ita wannan abincin mijin ta ne sai in zatai na siyarwa ta taya ta, daki ta koma ta shirya wanka, wanka taima Naufal itama tayi suka koma ciki, komai akan idon alhaji ya faru dan fitar Hajiyan kenan qarar bude qofa ya tashe shi yana hango su ta windo, ganin yanda mazaunan Nasreen ke motsawa a zanin ta ne ya daga hankalin shi" wannan da gani nan gaba ta murmure za ai kaya😋 motsin qofa ne yasa shi fadawa toilet Hajiya ce ta shigo dauke da doya da kwai da taiwa suya mai ban sha'awa tai souce mai yankakken nama qanana a ciki ta dafa masu Tea daya sha kayan qamshi ta shigo ajewa tai ta leqa bandaki ta qarasa taya shi wankan suka fito ta shirya shi dan daya yagama zai wuce kasuwa, bayan sun gama ne kan ya fita Hajiyar na rungume a gefen jikin shi ta dawo gabam shi ta saqale hannayen ta a wuyan shi tana kallon idon shi tana murmushi" Alhajina Allah ya bada kassuwa mai albarka, Allah shu kare mun kai, ka dawo lahiya Alhajina" yana amsawa shi kuma da Ameen, bakin ta ta kai nashi ta dade tana mai kiss sannan ta janye jikin ta tayo gaba ya biyo ta a baya, qofar dakin Naseeren ta tsaya, tai sallama , fitowa tai cikib shiri ita da danta, duqawa tai kai a qasa "Alhaji ina kwana" " lafiya qalaou" yana amsawa yana wani kauda kan munafurci yana hade gira, " to naji duk bayani daga wajen Hajiya ta fadi man komai ina fata xaki abin da yakkawo ki gidan ga lahiya, bana son kuma naji wani abu mara dadi daga wajen ki, dan wanda zai taba min mata to shina fuskantar fushi na ko, ke jiya" daga kai tai ta amsa da " Na gode Allah ya saka maku da alkairi, in Allah ya yarda ba abinda zai faru mara dad'i" kallon Hajiya yai yace " tau ni sai na dawo" yana mata murmushi, itama murmushi tai "ka dawo lahiya Alhaji na.Haka rayuwar su ta kasance, kullum kaga Alhaji zata zakai duniya baya kallon wata mace sai tashi, ita kuma Hajiya bata da burin da ya wuce faranta mishi , Nasreen ko aikin ta take cikin kwanciyar hnkali, ga wata qiba mai kyau data fara, ko ina ya fara dawowa daidai a jikin ta, abu daya ke damun ta ALHAJI, dan yasha nuna mata wasu alamu da ta fara jin tsoron shi, misali: akwai ranar da Hajiyan nawajen saida abinci ya dawo gidan ya tadda Nasreen tana duqe tana share inda Naufal yaci abinci sai ji tai an dakar mata duwais ta baya dagowar nan da zatai kawai suka hada ido ta ja baya da sauri" Subhanallahi meye haka Alhaji?" Au ai na zaci Hajiya ce ashe kece" yana wani shu'umin murmushi, " haba Alhaji ya zaka ce haka bayan kasan ba utan bace?" To ke yanzu yarinya dan na mori jikin ki ma mene a ciki ba fa sani za tai ba" subhanallahi haba Alhaji kamar yanda hajiya ta ban labari da kun samu haihuwa da kana da kamar ni, ai ni 'ya ce a wajen ka, kuma Hajiya na iya qoqarin ta akan ka" ganin da yai lokacin dawowar matar shi yayi e ya sa kai zai fita, " in kka bari mata ta taji labarin nan zaman ki yazo qarshe kuma ba yarda zatai da ke ba in kin kiyaye kin tsira" ya fice ya barta cikin matsananciyar damuwa, "oh ni Nasreen ya zanyi?.......


👵🏻      WATA UWAR    👵🏻

   

BY 

HAERMEEBRAERH

    Masoya novel dinnan na WATA UWA amin afuwa yesterday i was so busy ne yasa ban yi typing ba, dan Allah wanda suka ji haushi har ake sa min red face ayi min choli😂ayi hamfuli inshaa Allah daga yau har sai na gama ban tsaya ba. Tanx for d love and care.❤

Page 17:  


Tinanin ta ne ya katse bayan sallamar Hajiya da tai, ta dawo daga wajen sana'ar ta, amsawa Nasreen tai ta tashi da hanzari, ta fara karbar kayan hannun ta, tana sauke ma yaran da suke taya ta kwaso kaya su ajiye, "Sannu da dawowa Hajiya, ya kasuwa?" Alhamdu lilLAAH Nasreen, yau da zazzabi mai zafi na dawo gaba daya jikina ciwo yake bana jin dadi ko kadan" Subhanallahi, Hajiya muje ki watsa ruwa sai ki ci abinci ki sha magani, Shifakillah Hajiya" Ameen na gode Nasreen, a gaskiya ina jin dadin yanda kk tafi da al'amuran ki cikin nutsuwa ga hankali, zan so sanin labarin ki" Murmushi Nasreen tai tace," Hajiya kenan labari na ba komai cikin shi ban da abin haushi da dana sani, amma ki gama komai sai na baki labari na inshaa Allahu" shiga ciki sukai ta taimaka wa hajiya ta gama komai ta kwanta a palo, anan Nasreen ta bata labarin ta da komai, Hajiya ta tausaya  mata amma ta mata fada sosai na wautar da ta aikata, dan dalilan ta bai kai ja ta fara karuwanci ba sam, wa'azi sosai Hajiyar ta mata wanda ya ratsa zuciyar ta yasa mata jin tsoron Allah sabo a ko ina na jikin ta, kuka take mai cike da nadama da dana sani, Hajiya nuna mata tai ya kamata ta je taga mahaifan ta tanemi gafarar musamman mahaifiyar ta, ta kuma nuna mata abubuwan da ta dora su akai ita da qanwar ta ba mai kyau bane, Share hawayen ta tai, tai mata godiya, ashe duk abinnan da suke fada akan kunnen Alhaji ne😱fita tazo yi taji ta bige mutum,tai maza tai baya tana kallon hanya, Alhaji ta gani yana mata wani mayunwacin murmushi, amma yana daga labulen ya bata rai ya shiga da sallama, fita take qoqarin yi Hajiya ta dakatar da ita," Dan Allah Nasreen debon abincin Alhaji, kin dai ga yanda nake hada mai ko?" Eh Hajiya" fita tai a hanzarce ta kawo, daidai nan Alhajin ya dora ta akan cinyar shi yana wasa da gabibin jikin ta wai tinda ba ta da lfy bari ya mata tausa yasan harda gajiya, bakin shi a wuyan ta yana kissing yana taba qirjin ta da hannun shi daya dayan kuma ya saqalo ta qugun ta, Shigowar Nasreen ne ya sa Hajiya ke son sauka amma ya hana , yana ci gaba yana bin Nasreen da wani shu'umin kallon da yasa tai saurin dauke kanta ta fice, zuciyar ta bugawa take da sauri sosai kamar zata fasa qirjin ta ta fito," Ya ilahi wannan wanne irin karuwan namiji ne haka?😱 anya zamana zai ci gaba anan kuwa? Inna bar nan na bar gidan aminci, ka taimake ni ka barni na zauna cikin rufin asiri" tana fada hawaye na bin fiskar ta, a haka ta zame ta tsugunna ta ci gaba da zubda hawayen rashin sanin abin yi, jitai wani dan qaramin hannu na share mata hawayen kuma ya rungume ta duk da bai iya ritsa jikin ta dika , rungume shi tai sosai a jikin ta itama, kuka mai dan sauti ta fara tinawa da uban shi da tai, ko ya yake? Ko yayi auren? Allahul musta'an, tashi tai ta dauki danta ta koma gefen katifa tana jijjiga shi yai bacci, kiran sallah akai ta miqe taje tai alwala tai sallar isha'i tai adduoin ta, tqi karatun Qur'ani, ta kwanta a gefen katifar ko hijabi bata cire ba, dan tana son tai wankan kwanciya da ya zama dabi'ar ta ko tayi da magrib in xata kwanta sai ta sake, a haka bacci ya dauke ta bata farka ba sai qarfe 11pm, sa hanzari ta miqe ta daura zani ta sa hijab da take wanka da shi ta dau kayan wanka ta fita ta shiga wanka kenan ta saka sabulu a fuska taji kamar an shigo, tsoro ne ya kama ta sosai, kan tai qoqarin wankewa an janye robar wankan gefe, lalibe ta fara, qara ta bude baki zata saki ya saka nashi bakin a nata, kamar mayunwacin zaki haka ya dinga laliben jikin ta kuka take sosai amma ya hana ta bude bakin tayi ajiyo ta, dabara ce ta fado mata, harshen shi ta kama ta cixa da qarfi kan ya janye ta kama leben shima ta kafa mai cizo sosai saida taji alamun jini ta saki, wani wawan mari ya sakar mata ya hada ta da bango, qoqari yake ko ta halin qaqa sai ya cimma burin shi akan ta, wannan dalilin ne yasa kan ya fito ya kunna karatu ya ware volume yanda Hajiya na bacci bazata ji ba, kuka Nasreen take amma ba mai taimkon ta, addua ta fara sosai akan Allah karya bashi sa'a, yana gab da zai karya mata alqawarin ta na daina kusantar kowanne namiji in ba mijin ta ba aka turo qofar, 😱😱😱 Hajiya ya gani a gaban shi tana kuka sosai, bata kula shi ba tai wajen Nasreen dake kuka ta kama hannun ta suka fita a lokacin ne ta kula ma idon ta da kumfa, daura mata zani ta fara sannan ta wanke mata fuska taja ta sukai dakin ta ta rufe qofar, zama tai a qasa tana kuka sosai mai ban tausayi, dukan su ba mai ba wani hakuri saida sukai mai isar su, Hajiya ce ta fara magana" ta shi nai zan fitsari naga ban gan shi ba, sai nai zaton ko ya je waje dakko wani abu ne dan banji motsin shi toilet ba, fitsari na nai na kwanta naji shirun yai yawa bai dawo ba shine na fito ina fitowa naji kamar kuka a toilet kuma naji qarar Alhajin😭 ina bude qofa na ga abinda ke faruwa" ta qarasa cikin matsanancin kuka" ka cutar da ni Alhaji, kacu amanar qaunar da nake maka, qawayena da yan unguwa na ban labarin halin ka na neman mata na kauda kai, na toshe kunne na saboda na zauna lfy, saboda kar na yarda bayan ban taba gani ba, shine dalilin da yasa ban bari nabi ta qawaye na ba na mun girma da zuba soyayya irin ta yara, ba dan komai ba sai dan na kare ka daga fadawa sharrin zina, amma dik da haka ban iya ba" da qarfi take maganar, yana waje hawayen nadama na bin fuskar shi tin da yake ba ta taba kama shi ba, bqi taba jin kunya da tsanar zina ba irin na yau, yayi nadama mara iyaka, amma yasan halin matar shi in tai fuahi da abu, shiyasa ma take kauda kai sosai dan karta sa a ranta ta tsane shi, ya san rabuwa za sui kawai, tina hakan ne ya sa hankalin shi ya tashi ya fara buga qofa yana" Hajiy ki min rai ki hakuri kowanne hukunci ne ki min amma karki rabu da ni mutuwa zan na rasa ki"😭 kukaya ke kamar yaron da aka hana chocolate🙄 Hajiya kallon Nasreen tai tace tashi ki je ki hada kayan ki gobe da safe zan baki dubu 10k ki je gidan iyayen ki nima zamana a nan ya qare.

Washe gari da safe komai ta hada na kayan ta da danta data runquma a baya dan taji dadin tafiya, Hajiya ce ta fito fuska tai mata jawur dan kuka, ta muqa mata kudin itana cikin shiri, a hanzarce ya taso a inda ya kwana a gefen dakin ya durqusa gaban Nasreen yana mai bata hakuri, tace " bani zaka ba hakuri ba, danni daga yau bazaka sake ganina ba, Hajiya zaka nema ta yafe maka,Hajiya ki hakuri ki sassauta wajen yanke mai hukunci, domin kema in bashi bazaki iya rayuwa ba, fatana wannan abuj ya zama hanyar shiryuwar ka, kamar yanda Allah ya shiryar dani" hanya ta dauka zata fita............


👵🏻     WATA UWAR.   👵🏻

  


 BY  

HAERMEEBRAERH  
Page 18:
   QAUYEN LANGYM
     Nasreen ta isa qaunyen su lfy, kafin ta shiga gidan su saida ta dade a qofar gidan tana jiyo mitar Innar Hinde, akan kudin abincin dare da ba zai isa ba," to dai kaji na fada maka sai dai inna dafa mu muci kai ka hakura, ace mutum ba zai fita ya nema ba kamar yanda sauran maza keyi, sai mun samo ka dinga bude baki ana baka kana amshewa" Innar Hinde wata rana sai labari, babu wani mai arziqi da yae dawwama da arziqi haka ba wani talaka da yake dawwama da taluci? Kowa kk gani da rayuwar da Allah ya tsara masa" hahaiiiiii casssss an iya wa'azin babu ba a iya na nemowa ba, kaini bani wuri na wuce" ina Hinde taje da magaribar nan kina kallo ta fice" taje wajen saurayin ta da yai mata alqawarin in ya qasa tsire gashin farko nata ne" yanzu rayuwa zatayu a haka kuwa?" Sai kuma kayi" sa kai tai ta bar wajen ta shiga madafi. " Assalamu alaikum" sallamar ta ce ta sa Baban.hinde fitowa cikin hanzari 

Kamar a tare suka fito da Inmar Hinde, " Aa mutanen Lagas ke kk tafe da maraicen nan? Sannu da zuwa bismilla shigo lale maraba" tana yi tana kallon jikin ta, kallo take mata na to wannan karon ke da zamu ga kinfi da arziqi, me nake gani kuma haka? Shiga tai ta durqusa gaban mahaifin ta ta gaida shi ya amsa ta gaida Innar su ta amsa, miqewa tai ta aje Naufal ta tafi bandaki, ta fito kenan tai alwala ta kama Naufal ta sa shi yai fitsari yai alwalar shi da ya koya wajen Mummyn shi ya biyo bayan ta, a yanzu ya kai shekara uku, daki suka je ta tada sallah ta rama sallolin ta dika, ta jira isha'i , ta idar ne taji an daga labulen an shigo, " mutanen birni ko dan kudi a hannun ku mu samu na dora abincin dare" tana wani dariya kamar wawuya haqoran nan kamar ta ci dorawa , miqewa tai taje kusa da handbag din ta, ta bude ta miqa maya dubu daya, kallon kudin tai ba yabo ba fallasa, ta sa kai tai waje wani shegen tuwo ta debo mata wani baqiqqirin, aka kawo mata, wato wannan tuwon kudin ta ne ko me? Hmmmm.  "Inna ga kinga tsinke uku ya ban" wani burki taci kamar mota a gaban Nasreen da ta dawo tsakar gida ta sa tabarma ita da Naufal, " mutanen birni yaushe a gari inji maqi baqo" Nasreen murmushi tai tace oh Hinde ana nan da halin ashe ke baza ki ma kan ki fada ba, ki duba kiga rayuwar nan yanda ake mutuwa, ga cututtukan zamani da ake dauka ta hanyar saduwa barkatai, ke baki nutsu a matsayin ki na mace kin koyi abubuwan da macen aure ya kamata a ganta da su a same ta da su a gidan aure, sai dai ki ta yawo maqota shaguna, a haka kk so watarana ki aure? Wace irin rayuwa kk son kiyi anan gaba?" Hahaiiiii casssss dakata min limamiyar gidan karuwan Lagos daga zuwana? Daga tambayar yaushe kk zo? To ahir din ki da matsawa rayuwa ta, har kina da bakin magana? Tinda nake yawo na kinji ance na yi ciki bare na haihu? Ni yawona bai nisa ba gaban iyaye nake yin shi, ban kuma nemi ubana ba kan na bar gida ehe" tana kaiwa nan Inna ta bushe da dariya tana kama baki" kaiii yar nan kin san ta kan tsiya" Baban Hinde ne da ya gama jin komai ya leqo ya kira Nasreen, ta shi tai ta isa ita da yaron ta, suna zuwa ta durqusa gaban shi idon ta a bushe ko digon hawaye babu, saboda zuciyar ta ta gama bushe wa ta kuka akan su, " da farko dai duk da ban san me ya dawo da ke ba amma naji matuqar dadin fahimta da nai kin aje harkar karuwanci kin ringumi rayuwar da Allah ya amince da ita, sannan jna maki fatan alkairi da qara maki nasiha akan kiji tsoron Allah, ki qara tsare mutuncin ki, Allah ya miki albarka,ya kawo maki miji na gari"Ameen Baba" anan ne hawaye suka taru a idon ta tasa yatsan ta ta share ace" Baba so nake inna dan kwana biyu zan dan dinga koda wanki ne na tara kudi ina son na koma Lagos na nemo Baban Naufal a qalla yasan inda muke da zama saboda yanayin rayuwa yaron nan wataran zai so ganin shi ban san ina zan same shi ba, gwanda tin da wuri na nemo inda yake" kuka ne ya kwace mata duk son dauriyar da take amma ya gagara, tinda ta rabu da Naseer kullum da son shi take kwana take ta shi, bata jin zata iya auren wani in ba shi ba, hawaye ta share, sallama taiwa Baban ta kafin su fito Naufal yayi bacci, gware sukai sa su Inna komai akan kunnen su, (yan labe kenan, yin labe a abinda ba ai niyyar kaji ba haramunne) to su Inna su wane haram ne basu aikatawa?🤔 sai abinda ba a rasa ba, kada kai tai tace " Allah ya kyauta" tai daki ta barsu suna qusqus" 


Washe gari tashi tai ta gyara gidan tai komai, ta dama koko , ta debo ruwa, sannan ta fita shagon maqocin su data damqawa ATM tai, sallama tai masa, ta sanar da shi ta dawo, dakko mata yai ya bata a hannun ta tai godiya mai tarin yawa ta miqa mai dari biyar ta fito, dan achaba ta dauka ya kaita can inda ake cire kudi farawa tai da gwada cire dubu biyar taga ta cire, wani dadi ne ya kamata ta qara cire wa" Alhamdu lilLAAHI" a haka ta cire dubu sha biyar ta dawo gida cike da murna, kayan da ta dan tsaya ta siyo masu ta aje a kitchen ta je qofar dakin Baban Hinde tai sallama" Baban Hinde amsawa yai ya fito bayani ta mai da komai, sannan ta qara da cewa" ina ganin wata juma'ar zan tafi tinda na ji ance Ado ya zo sai mu tafi tare, in yaso daga nan zan nemo Baban Yaronnan dana ganshi zan dawo" To Allah ya nuna mana, ya kuma sa. Ki dace in kinje" Ameen Baba" miqa mai dubu uku tai, ya karba yana mai sa mata albarka, aiko sai ganin Innar Hinde sukai ta dire a tsakiyar su, miqawa Nasreen hannu tai tana kada qugu" lallai yarinyar nan ashe uba yafi uwa? Ina zaune ina ganin kina mai barin dubunnai kin hadani da wasu kaya kin wuto nan to ahir din ki da baki na, maza2 naji hannuna ya cika da kudi nima" miqa mata dubu biyu tai tai daki abinta, ledar data shigo da ita ta hannun ta ta budewa Yaron ta a gaba nama ne gasasshe ta tura mai yaci, ci ya fara kamar wani mayunwaci( ko dake mayunwacin ne ma ina yake samun hakan?) Sai da ya ci kamar yanka biyar ya dakko ya sa mata a baki, murmushi tai idon ta taf kwalla tace Naufal ke nan ka tina dani na gode amma so nake kaci in ka qoshi sai naci sauran, ni na ci dazu" girgiza kai yai ya miqa mata a baki, daga lokacin wani tinani ya shige ta, yaron nan fa bai taba qoqarta yin magana ba fa daga kuka sai dariya meke damun shi ne ko dai kuma ne😱 tashin hankali taji ya shige ta da ta tina hakan, "Naufal! Naufal!!Naufal!! baya amsawa saidai ya kalle ta ya qara matsawa kusa da ita " ka amsa min in kana jin me nake fada ko baka iya magana ne, girgiza kai yayi yana murmushi, kuka ta fashe da shi ta rungume shi tana "kai min magana dana  rashin maganar ka is killing me, pls say something, anything my bby"" Daddy".....

👵🏻    WATA UWAR    👵🏻


     BY HAERMEEBRAERH

Masoya novel din nan na WATA UWA ina fatan zaku gafarce ni na dan samu rashin lfy ne yasa kuka ji ni shiru. Na gode sosai da kulawa da adduoin ku Allah ya barmu tare. Love u all❤

Page 19:

     A hanxarce ta dago shi daga kafadar ta tana kallon shi ido taf hawaye " Naufal dear me ka ce? Cikin doki da zaquwa take tambayar shi, dan bata taba zato ko tsammanin hirar da takan mishi na mahaifin shi yana ma saurarar ta ba sai.yau, "Daddy" " Daddyn ka kk son gani Naufal?" Daga mata kai yayi ya kwanta a jikin ta, qara rungume shi tai tana kuka sosai tana cewa" nima ina tsananin son ganin shi Naufal Mum ta raba mu da masoyin mu, ta nesanta mu da shi, da bai aikata kuskuren da ya aikata ba na kuma biye mashi, da tini muna tare, koda kuwa yayi wani auren, bazamu ravu ba, zamu dinga ganin juna" kuka tai sosai har bacci ya dauke ta, cikin dare ta farka ta aje Naufal ta shiga ta watsa ruwa tai alwala ta hau abin sallah taita sallolin nafila bayan ta idar ne tai addua sosai ta shafa, ta nemar wa kanta sauqin samun Naseer in ta koma lagos.


Yau alhamis da yamma ne ta fita neman Ado, can ta same shi tare da abokan shi, suna shan abubuwan da suka zama masu kamar farilla, yana hango ta ya taso," ashe da gaske ne?" Aka ce wai me?" Aka ce wai kina gari kin dawo" Ado kenan na dawo, amma yanzu ma gobe nake son komawa, amma zan ji dadin tafiyar in aka ce kaima zaka koma din a goben, ba damuwa in ba zaka samu komawa gobe ba,saidai ba haka na so ba"hhhhh to ai faduwa ce ta zo daidai da zaunawa don kuwa yanzu ma sallama nake wa guys dina, gobe zan koma motar asuba zan bi, kinga kawai sai ki shirya ko" kaiiii amma naji dadi sosai, Allah kuma ya nuna mana" to sai mun hadu goben" gida ta tafi ta sanar da Baban Hinde yanda sukai da Ado, addu'ar samun nasara ya mata, da nasihohi masu ratsa jiki wanda yasa taji ko mai rintsi komai wuya bazata iya wulanqanta kanta ba kamar yanda tai a baya, godiya ta mai sosai sannan ta sanar da shi ba zata tafi da Naufal ba dan in taje da shi suna iya amsar shi su barta ta dawo ba dan ba uban, amma in ta tafi ita daya dole zai so ganin dan shi kuma zai biyo ta yaga mazaunin ta ko dan gaba, Baban Hinde yai na'am da shawarar ta, sai dai a qasan ran shi yana tausayin yaron in ta tafi ta bar shi a hannun wadannan mugayen ya zata kasance da shi, itama tinanin dake zuciyar ta kenan amma ta dake, a ranta tace Naufal ka yafe min zan je nemo mana yancin mu ne da gata, wahalar da zaka sha ta lokaci ne inshaa Allahu, a haka ta goge idon ta tai ma babanta sallama ta shiga ciki.  Zaune suke ana maida yanda akai da rana ta shiga, tai sallama suka amsa dari biyar ta ba Hinde tace ta siyo masu tsire aiko kamar zata kwata haka ta fizge ta fita da gudu kamar balama, girgiza kai Nasreen tai cikin takaici ta dawo da kallon ta wajen Innar su, kora mata bayani tai akan tafiyar ta da kuma barin Naufal da take son yi, " kan uban can, akan me zaki ta fi ki bar mana shi anan? In ji da ci da uban ki da qanwar ki ko inji da ci da kaina?" Can kuma tai qasa da murya tana murmushi" to me zai hana ma na riqe jikana musamman un uwar shi zata na aiko mana da kayan masarufi?" Murmushin takaici Nasreen tai dan Innar Hinde bata san neman uban Naufal ne zai maida ta can ba, a zaton ta karuwancin zata koma," Inna karki damu yanzu ma zanbar miki dubu uku a hannun ki inna je naga yanda abubuwa suka kaance zan dinga aiko kudi ta wajen me shago kamar da" shewa Innar ta tayi tana mata kirari tana sa mata albarka, hawayen baqinciki ne ke bin kuncin ta masu zafi tana fadin " oh ni Nasreen ban dacen uwa ba, wannan wace irin uwa ce? In zan kashe mutum na kawo mata kudi ba ruwan ta, amma in abun alkairi zan sau dubu ba zata samin albarkar ta ba, da WATA UWAR ce ta gane ma yar ta na bin maza ai sai ta kusa kashe ta, amma tawa Uwar hankalin ta kwance ita ke sani hanya ma" kukan da ya kusa kwace mata ne yasa ta tashi da hanzari ta tafi dakin su, akan shimfidar su ta fada ta na kuka mara sauti, yaron ta tajawo jikin ta ta rungume tana mai kiss, tana kuka tana mai addu'o'in tsari, tana mai magana kamar yana a farke" Naufal ka yafe min, nasan abinda zan ban kyauta ma rayuwar ka ba tin farko ma dana samar da kai ta hanyar zina, sannan gashi yanzu zan tafi na barka, a inda ba qaunar ka suke ba iya soyayyar su da kai iya abinda zan mallaka a hannun su ne, wanda inna ta fi ban san ya rayuwata zata kasance ba, shin zanyi nasarar ganin Daddyn ka ko ba zan gan shi ba? Allahul musta'an" kuka take sosai har yaron ya fara motsawa sannan ta rage sautin muryar ta, daga kai yai ya kalle ta cikin barci ya qara rungume ta ya kwanta kuka mara sauti ne ya qara kama ta ta rungume shi sosai, har a suba idon ta biyu a hankali ta zame shi daga jikin ta ta mai kiss a goshi da kumatun shi, kamar ba zata bar shi ba ta fito da kayan ta a hannu ta kwankwasa wa su Innar ta qofa, fitowa tai tana hamma, da mugun warinnaj na bakin ta, da sauri Nasreen ta kauda kai ta ja baya, duqusawa tai ta gaida ta sannan ta fara mata sallama, kauda kai Innar hinde tai tana kada qugu ta miqa mata hannu" ai ni sallamar ki shine naji kudi a hannuna shine nasan kina sallama, wani na yafe ki ko karna yafe ki duk bai taso ba" kada kai Nasreen tai da takaici ta bude jaka ta miqa mata kudin, Baban Hinde ne ya fito sukai sallama ya raka ta har tasha, amana ya damqawa Ado ita sannan ya koma gida.Sunyi tafiyar kwana daya da wuni daya cur a hanya dab sai jusab 10 dare suka isa garin lagos      suna zuwa suka hau mota tace so take a kaita Apapa can wajen Hajiya Asabe dan koma meye data je inda bata sani ba gwanda ta je inda ta san halin su, van kwana sukai da Ado ya bata lambar wayar shi a jikin kwali ta sa a jaka, ya kama hanyar shi ta kama ta ta, ta isa wajen Hajiya Asabe ta tarar suna qoqarin tafiya gida kenan, ganin Nasreen ne yasa Hajiya Asave kusan kifewa, Zata gudu ciki ne yasa  Nasreen ta dakatar da ita tace" Hajiya karki damu ni ban zo dan na tambaye komai nawa va nazo ne dan ki taimakan da wajen kwana da aikatau har na gama abinda zan a garinnan na koma, dan ni yanzu ko kin dawon da komai bar miki zan bazan ci ko sisi ba nq haram" yawu ta hadiye ta na zare ido fuskar data sha hoda duk ta jiqe da gumi ta sa kukan munafurci ta rungume ta" 'Yata Nasreen muje gida na baki labarin abinda ya samen bayan na cuce ki na saida maki da komai" kama hannun ta tai suka shiga Taxi suka nufi wata unguwa coconut suna isa Nasreen taga wani gida mara kyan gani da qazanta wai nan zasu shiga nan ne gidan Hajiyar yanzu, dama tun  a wajen saida abincin ta kula komai ya ja baya, suna isa ta sallami mai Taxi suka bude wani dakin katako suka shiga daga katifa dai leda da sauran tarkace, zama sukai a qasa Hajiya ta fara bata labari..........


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻


    BY HAERMEEBRAERHPage 20:


       " A gaskiya million 5 zan siyar maku da wannan gidan, wannan in kun kula ai ba irin wancan vane, kuma in ba baqin ciki zaku min bama ai ba ku kuke siya va, ku je ku gayama Yallaban ga akan yanda na ce" " Hajiya ke nan karfa ki manta akwai filaye uku da kk ce zaki hade ki siyar kina nufin duk suma a million 1 din zaki bassu?" Kwarai kuwa kunsan da yaya na sane su ne? Wahala na sha kafin na same su, dan haka dole na siyar yan da kudi na za su fito " k ba damuwa, yanzu abun da za ai ki kawo takardun komai har da na motocin kawai ki sa hannu a jiki mu kai masa in yaso yanda dai aka saba kin jimu da kudaden kin, daga nan sai a fiddamu koya baba?" Tafawa sukai a tare suka bushe da dariya, jiki na rawa ta tattaro komai ta basu suka tafi," Hajiya aita hakuri ko da kin dan ji shiru zamu neme ki sabo da kin san yanayin kasuwancin namu ba ke kadai bace zamu tattara na wasu mukai inda za a siya, yanzu mu mun wuce sai kin ji mu" A ba damuwa wannan harka ai an zama daya" ba matsala Hajiya an zama daya" fita sukai suka hau abin hawan su suka bar wajen suna dariyar da ban gane wacce iri bace sai yanzu, ashe dariya ce ta sata ta saci sata😭, zan gansu yau ne?gobe ne? Ga shi har yau shiru basu ba labarin su ban da wajen kwana sai shagon abinci a hankali da na dan samu wasu kudin na kama hayar nan din shima kuma kudina ya kusa qarewa ga wajen abincin duk ya ja baya, Nasreen ki yafe min, tin da na fara harkar nan na sha cin kudin mutane ta hanyar da na ci naki amma ba abinda ya taba samuna sai a wannan lokacin , ba komai ne ya jawo ba sai yarda amanar ki da kk ban da nai saboda kowacce karuwa tasan ba amana amma ke kin ban amanar kanki tin fari kuma na tozarta amanar taki wannan daliline ya jawon wannan qasqancin nasan" kuka take sosai tana share hanci da gefen zani Nasreen ce ta matsa kusa da ita tace" Hajiya kar ki damu kan ki komai ya wuce a waje na , kudinnan duk dama na haram ne yanzu ni akwai abinda nake son na kammala kan na koma gida zan fara yin wasu ayyukan na qarfi na samu abin da zanna ci da kuma wasu buqatun inshaa Allah, bazan qara komawa gidan jiya ba dan ni ko shagon ki ba na jin zan iya yin aiki a wajen saboda gudun faruwar wani abun, na gode kuma da kk bani wajen kwana" Habaaaa Yarnan in da hali ma ai gida zan sama maki mai kyau wajennan zaman shi ai sai mu da muka saba da gararamba dama, tin da unguwaa ce cike da yan kazo na zo" a haka sukai ta tattaunawa har gari ya waye. 


Nasreen ce ta fara tashi tai sallah, ta fara gyara dan dakin nasu, sannan ta fita lokacin garin bai gama waye wa ba, tafiya take tana shiga gefen unguwar in da taga wasu gidaje masu dan kyau ta fara shiga tana neman wankau, dan shi take ganin zata iya yi ta samu abinci tinda su ta can wanki da dan tsada riga da wando #50, a haka sai da ta zaga gida wajen shida, sannan ta samu a na bakwai din nan fa ta fara tiqar wanki kamar wata jakar aiki, tana yi tana goge zufar sake karyo mata na rashin sabo da wankin, a haka ta gama wankin tas, kudin ta aka qirga ya kai dari 600, durqusawa tai tana ta godiya" i beg oga if u get another one even if na tomorrow i go come back do am" No me i no get oo but make i ask my sister for u" shiga yai ta tambayi qanwar shi tace ta dawo goben, godiya tai ta koma gida, a hanya ta sai Garri da sugar da gyada sai ruwan sha, da wannan Garrin ta karya a lokacin wajen qarfe 12pm yayi tana sha tana tuno Naufal, wasu hawaye ta goge masu zafi" Allah kai ne ka tsara min rayuwata kai ne masanin abinda ka boye a cikin ta Allah duk rintsi kar ka barni na koma karuwanci ka bani juriya da hakuri, Allah ka cikan buri na na ganin Naseer".


Rayuwar Nasreen haka ta kasance in ba tai wankau ba ba zata ci abinci ba a ranar, sannan ba zata nunawa Hajiya bata ci abincin ba, haka zata tashi ta ci gaba da yawon ta, ana haka ne wata ranar larava da sassafe ta fita wata unguwa dake maqotaka da tasu tafiya take a qafa, ga yunwa ga wahalar nisan tafiyar da tasha, ga shi rabon ta da abinci tin washe garin ranar da safe, duk ta fita hayyacin ta hankalin ta baya jikin ta, ga tinanin halin da yaron ta ke ciki dan tabbas tasan ya fara fuskantar wuaqancin mahaifiyar ta da qanwar ta, tinda kudin wajen su tasan ya qare, ba tai aune ba sai ji tai an yi sama da ita da mota, gefen titi motar ta watsa ta, a guje mai motar ya gudu bai tsaya ba, mutane sun cika wajen ana ta kallon ta, masu Yarabanci nayi, masu turanci nayi, Ibo, Da sauran yaruka, wata hadaddiyar mota ce tsaya a wajen sakamakon tare mata hanya da akai zata wuce, ganin cincirindon mutane ne ya sa ta fitowa daga motar ta na son ganin me ya mutane suka cika haka maqil? duvawa tai taga kamar almajira ce a kwance,qarasawa tai da nufin taimaka mata saboda ganin koma dai mene ne musulma ce da dikkan alama kuma ba datti a jikin ta sai dai kayan sun kode kuma bahaushiya ce, dan haka kodan wannan dalilai zata taimaka. Dago ta tai da niyyar daukan ta sai dai wa zata gani............


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻    BY HAERMEEBRAERH

Surayyah Tabital 

This page is for u😊 ANA TARE❤


Page 21:  "Subhanallahi, Nasreen? Tabbas wannan ita ce, to garin ya haka ta faru, why is she looking very poor like this?"  Pls come and help me carry her" ta cema wata a kusa da ita, kamata sukai suka sa a mota basu tsaya a ko ina ba sai a gida, kafin ta isa taima Naseer waya, ta tabbatar yana gida, bude masu gate me gadi yayi suka shiga. 

Kira ta kwala ma Naseer ya fito fuskar nan gaba daya ba walwala a tattare da shi, ya zo ya tsaya a gaban ta qiqam kamar wani soja,

"Naseer kama min ita mu shiga ka duba ta kaga meke damun ta" bata rai yai sosai yana kumbura" ya zan na kama wannan matar na shiga da ita ta taka da qafarta mana dole sai na daga ta zata tash" cikin tsananin jin ciwon da Nasreen ta ke hakan bai hana ta dago kai ta kalle su ba gaba daya, dan ta gasgata kunnuwan ta, hada udanun su ke da wuya Naseer ya zaburo da sauri ya dago ta a hanzarce yai hanyar shiga cikin gidan, gaba daya ya rude hankalin shi na neman barin jikin shi dan tsananin mamakin anya itace kuwa🤔  tambayar Mum ya fara" Mum ina kk gamin farin cikina? ina kk samo man priceless jewel dina? Me ya same ta naga ba kwari jikin ta kuma duk qasa? "Naseer ka dakko kayan aikin ka ka duba ta ta samu hatsari ne ka gani ko akwai buguwa ko wani abu" da sauri ya miqe yana yi yana juyo wa kamar wani zai dauke ta kan ya dawo, a hanzarce ya shiga duba ta tsaf ya ga ba wani abu daya same ta sai kurjewa da tai a hannu yai dressing wajen ya kira mai aiki da aka kawo mata abinci amma a hada mata da Tea mai kauri da zafi,kawo mata akai aiko kamar wadda ta shekara dari bata ga kwano ba ta hau shan abinci da ci Naseer ne cikin hawaye ya riqe hannun ta ya dakko Tea din ya sa mata a baki yace ta fara sha cikin ya warware sannan ta karba tas ta gama da shi, ta koma kan abincin Mum cikin tsananin tausayin ta ta fara goge kwallan idon ta" Allah kadai yasan irin wahalar da yarinyar nan ta sha" wani kallo Naseer ya bita da shi da yasa jikin ta yai sanyi ta kauda kai, bayan ta gama ne Mum ta kai ta dakin da aka taba saukar ta tai wanka ta bata wasu riga da skirt purple ta saka sun mata kyau sosai, sai dai gaba daya ta sauya kamar ba Nasreen mai Aji ba." Nasreen ina mai neman yafiyar ku ke da Naufal, ban maku adalci ba, ban kyauta wa rayuwar ku ba, na cuce ku na cuci kaina kuma, gashi abinda nai dan na sawa dana farin ciki abun ya zama na baqin ciki, na mai aure dan na raba shinda karuwa, sai ga karuwa a cikin gidana 😭 "tana fada tana zubda hawaye Naseer kam gaba daya jijiyoyin kashi sun miqe idon shi yai jawur." Bayan tafiyar ki ne, Mum ta auran yar qawar ta Hajiya Bilki wato Siyama, Siyama a ido ka ganta ba zaka ce mata ko kallon wani namiji ma da ba muharramin ta ba bata taba ba, amma daga ciki gaba daya maza sun gama mata illa ko ta ina, Mum ba ta da masaniya da hakan amma mahaifiyar yarinyar da yarin yar sun san halin da take aikatawa, tsabae iya taku ne kawai, a haka akai aure aka kawon Siyama wadda Hajiya Bilki ta kaita asibiti aka mata aiki a gaban ta dan ta koma budurwa bayan kayan mata da tai ta dura mata, dan kawai a cuce ni😡 a haka aka kawon ita, amma dake ta riga ta saba da maza kuma dama ta dade tana sha'awa ta, bayan mun kammala duk wata sunna da ya kamata ango da amarya su gabatar ne na haye gado xan bacci na, dan duk da gargadin da Mum ta min ai bata ce dile sai na kusance ta ba, ina kwance ina hawaye sabida tuna ku danake , ko a wane hali kuke? Ko ya rayuwar ku ta kasance bayan kun fita daga gidannan? Kawai naji wani qamshi mai dadi na ratsa dakin, amma ban juya ba na dake to be honest zan so ganin daga ina wannan ni'imtaccen qamshin ke zuwa, daga nan naji motsi alamar an hawo gadon a hankali, sai gani nai an kashe fitila sai bedside lamp ce a kunne, kwantawa tai a gefena ta ratayo hannun ta daga bayana zuwa ciki na kanta a kusa da kunne na tana man wani salon da ya birkita ni, in baki manta ba tinda na fara sanin ki na yanke hulda da duk wata mace, har kk haihu Mum ta hana mu ganin juna ta kuma hana mu aure, kuma ni mutum ne mabuqaci sosai, ta haka tai nasara har muka muji amarcin mu, sai bayan komai ya lafa ne na gano ba budurwa bace rainan hankali tai kawai, sannan na fuskanci akwai ciki a tattare da ita daga alamar saman niples din ta dana gani da yaba yin ta dai dika ja masu ciki ne, shiru nai ban ce komai ba, na tsarkake jikina tana wani yauqi wai ita a zaton ta ban gane ba tana jira na taimaka mata na dau sallaya na fara salla ina karatu bayan na idar da sallah" haba Nass Haka zaka barni ko dan irin tattalina dinnan ba zakai ba? Wato kaci moriyar ganga ko?" Wani kallo na wurga mata daya sa ta sakko da qafarta tai toilet ta gyara jikin ta da shege qarin gashin ta ta fito, koma wa tai ta kwanta ta na bacci. Kamar kasa🙄 da safe bata roba nai nasata a gaba nace tai fitsari ta ban jiki na rawa tana ita fa lfyr ta qalaou , zata min musu na kwada mata wani marin da saida ta ban tausayi, da gudu ta amsa tai toilet tagama ta miqon, fita nai asibiti na, na duba komai na tabbatar tana dauke da ciki na dawo zuwa nai palo na tsaya na kwada mata kira"Siyama ! Siyama ! Da gudu ta fiti jiki na rawa fuskar ta da tasha mai tai jawur Mum ! Da qarfi na kira ta sai gata daga kitchen ta fito," lfy irin wannan kira haka" To taho kiga yar Limamin garin Lagos dauke da cikin wata biyu da sati daya, a daren farko, ita ta fara neman mijin ta, Mun ga matar da kk kori karuwar da ta tuba zata auri mazinacin danki su bar sabon Allah su raya sunnar Annabin rahama dauke d ciki ta na mena ango a daren farko, Nayarda Nasreen ta fito karuwanci ne amma nine namiji na farko dana fara sanin ta a cikakkiyar budurwa, sannan ko da ta dauki karuwanci a matsayin sana'a hankalin ta ya tashi a lokacin da na zo kusantar ta, Mum😭😭 kin cutar da d'an ki, kin cutar da jikan ki, kin cutar da baiwar Allahn da take neman ta samu mafaka a wajen mu, da mun taimaka mata mun rungumi dan mu, mun yi ta istigifari, da Allah ya mana rahama, ya yafe mana, amma ki duba ku ga wannan irin abu an gudu ba a tsira ba" kuka nake sosai a lokacin ina tina ki, ina a ina zan gan ki? Ina wannan halin ne naji an riqe qafata ana kuka" Naseer ka yafen ina son ka, bazan iya rayuwa ba kai ba, a da zan naji zan iya hakura da kai kafin auren mu, amma a tsakanin daren jiya da yau bazan iya rayuwa ba kai ba , ka yafen inna haihu mu maida wa uban dan dan shi, sai mu ci gaba da rayuwar mu" wani wawan maruka muka kai mata a tare ni da Mum, dai dai shigowar Hajiya Bilkisu kenan, a guje ta iso tana " na ga abinda ya ishen, kashen yar zakui kuka sa min ita a gaba?" Hankade ta Siyama tai tana kuka sosai" Umma kin cucen, kin sa yanzu dole rayuwata ta zo qarshe, dan Naseer ba zai ci gaba da zama da ni a haka ba, kince an kwantarda cikin ashe ba wani kwanatr wa, ga shinan ya gane, na tsane ki Umma da ke gwanda min WATA UWAR sau dubu" tana kaiwa nan ta tashi da gudu tai daki ta fada kan gadon ta tana kuka sosai, banko qofar yai ya daka mata duka a cinya, taso munafuka ga takardar ki nan na sake ki saki uku 1 2 3, maza zo ki wuce da shegiyar uwar ki gida tasowa tai tana layi zata fadi nai ficewa tai kan na kai da fita naji faduwar ta timmm! A qasa gaba nai abuna na turo Umman ta nace su fice kan na dawo a hannu ta daga ta suka fita jini na zuba mta, ban qara jin labarin su ba, dan ko Mum na son fadan bana yarda ta qarasa, tun daga ranar na bazama neman ki, ba inda ban duba ba har gidan su wannan qawar taki Barira sai da naje tsammanina ko kan mu karbi Number din su da address ke sun fada maki, Barira ta shiga tashin hankali jin labarin dana bata, tayu kuka sosai ita da mahaifiyar ta suma sika min alqawarin duba ki amma bamu same ki ba, Mum ma ba a barta a baya ba wajen neman ku,wannan shine a binda ya faru bayan rabuwar mu , ki yafen Nasreen"

Bude baki tai...

........


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻


    BY HAERMEEBRAERH
Aunty Ummu Sokoto😘

Baba Larens😘

Sis Rammalek 😘

Ina ji da ku sosai.  ANA MUGUN TARE❤Page 22:
" Naseer bakai min komai ba da zan riqe ka, ko dikkan ku ma, Mum uwa ce tana qoqarin kare danta ne da zuri'ar da za a samar masa, ta manta cewa shima in wasu iyayen kirkin sukaji halayen shi a bayan bazasu so su bashi yar su ba, shikenan dai yanzu komai ya wuce, ni ba komai ne dama ya kawo ni nan garin ba illa na neme ka, na baka address din in da muke kaje kaga danka, sabida rashin ka yai affecting rayuwar shi fiye da yanda ban tsammata ba, Naufal bai taba magana ba😭sannan kuma randa na damu da rashin maganar tashi sunan ka ya fara kira a duniya,"Daddy" shine abinda Naufal ya fara fada, hakan ne yasa naji dole na zo neman ka, ba zan iya zuwa da shi ba coz ban san irin wahalar da zan sha ba, kar muzo muna jigata ni da shi, ya sa na bar shi a gida can, wajen mahaifiyata" anan ta tsaya da bayanin ta, matsawa kusa da ita yai ya riqe hannun ta yana kallon ta cikin ido ya furta " I missed u so much Nasreen, nai missing dib ku Ke da Naufal, kullum ta Allah sai nai kukan rashin ku, ko a fili ko zahiri ban damuwa da wazai ga hawaye na, u mean so much to me dat i can't just forget what we had, u ar d only gurl i ever love and will forever love Nasreen, dan Allah Nasreen ki auren ko zuciyata ta huta da azabtuwar da nake" da hanzari ta dago ta kalli inda Mum take, tsoro duk ya cika fuskar ta, wani welcoming smile ta samu Mum na mata, sannan ne ta fuskanci wannan karon Mum ba zata ja da wannan al'amarin ba, sunkuyar da kanta tai a hankali hawayen farin ciki na bin kuncin ta, da bayan hannu tasa ta goge, kan ta goge daya Naseer ya riga hannun ta, sai dora wa tai a kan na shin, murmushi sukai a tare ta rufe idon ta tana giggling, Mum ce tai gyaran murya tace " yanzu dai na kula wannan love birds din sun manta da ni gaba daya ni kuma yaushe za a dakko mun nawa mijin kenan?" Tana fada tana karya wuya kamar mai shirin musu shagwaba, dariya suka sa dika.Yamma na yi sosai Nasreen tana kusa da Naseer suna hira , daga kai tai ta kalle shi tace" Abban Naufal ni fa ina ganin ta kamata yau ka maida ni gidan su Barira na kwana a can sabida bai kamata na ci gaba da zama anan ba, in yaso ka dinga zuwa can zance" ta qarasa zancen tana dariya, qura mata ido yai yace " Tab lallai kina son nima na kwashe kayana na koma can da zama kenan, ai ba zai taba yuwa ki tafi ki bar ni ba yammata" yana wani kashe mata ido, matsowa yai sosai kusa da ita har suna jin numfashin juna idon su cikin na juna hannun su na maqale da na juna, wani irin yana yi ne ke ziyar tar dikkan nin su, da sauri Nasreen tai breaking feelings din da zare hannayen ta, miqe tace bari na shiga nai wa Mum bayani nasan dama kai bazaka yarda va, saurin riqe hannun ta yai ya jawo ta jikin shi, da sauri ta kwace kanta ta dan hade fuska" Naseer dole ne mui fighting feelings din mu mui facing reality in ba so kk Naufal ya sake qani ba nan kusa, which we all don't want dat to happen again, wannan dalilin ne yasa nake son mu nesanta zaman mu kusa da juna zai leading din mu mu koma wa aikin baya, kaga kenan memakon mu hattawa kan mu juna muna qara nesanta kan mu da juna ne, in dan tani ne Naseer i want to be with u right now, i want to stay in ur arms to feel u so close, amma dole mui hakuri mu jira lokaci, lokaci ba abinda bai bari ba, in lokaci yayi komai da kk so har da wanda ba kai tsammani bama i will give it all to u, i am ur Naseer and u ar mine, i am totally and utterly head over heels in love with u" tana kaiwa nan Naseer ya gama daskarewa a tsaye gaba daya ba laka a jikin shi kan yai wani yunquri har ta vacewa ganin shi, murmushi yai mai cike da sauti, qara ya dan saki yai tsalle yai juyi, sannan ya bi bayan ta. A palo ya tadda su suna hira ita da Mum ta gama sanar da ita qudirin ta, Mum ta amince akab zata koma din.   QAUYEN LANGYM

"Jar uban can, lallai yau kai dan Lagos zaka ci uban ka bayerabe, Uban wa yace ka zo na aje koko ka shanye ? Iye? Ko ba da kai nake ba ne?" Wani wawan mari ta sauke mai kamar ta mari sa'ar ta, a gigice ya tashi zai fito da gudu ta sa qafa ta kwarfo shi ya kufo ta gaba, nan da nan kuwa bakin shi ya hau jini, wani irin kuka yake a shide tin da yake Mummyn shi ba ta taba dukan shi ba, tsawa ta daka mai ganin fitsarin dake zubowa ta qasan shi" Dan uwar ka gantalalliya anan ake fitsari? Kai in fa ina maka magana kana amsa min " tana yi tana jijjiga shi da qarfi, " ke Hinde ! Baki da hankali ashe wai da wa nake jin kina wannan surutan da doke2n ne ina bayi?" Da wa zan in ba wannan dan Yarbawan ba🙄😚" " iko sai Allah Naufal kai, zo nan" kasa tashi yai, Baban hinde ne ya qarasa ya daga shi baki fashe ga fitsari a wando fuskar nan tai dagaje2 da koko, kama hannun shi yai ya je ya cire mai kaya, ya mai wanka, ya dawo da shi daki yana ta bashi hakuri ya sa mai kaya suka fita, wajen mai shago yaje ya tambaya har yau ba waya, ba wani saqo daga wajen Naufal? Ya tabbatar mai da va komai shiru, nera gomar aljihun shi ya dakko ya miqa mai a bashi biscuit ya karba ya ba Naufal suka koma gida, " ai da ina nan dana barar da su dika har kakan nashi , sallamammu ta aje dan ta tafi ba ko aike, tin ina lissafin kwanan wata har na manta" sannu tijararriya, ni kk cewa zaki hada mu ki barar ko? To bari kiji na fada maki ki kiyaye ni dan gab nake da na sake ki na kore ku ke da wannan yar ta ki na qara wani auren, dan nasan sana sake ki Allah zai duben ya horen nai wani auren, na dauki iya abinda zan iya na qasqanci a wajen ki, iyaka dai nasan ni na nuna kwadayin abin hannun ki har wulaqanci ya shiga tsakanin mu to daga yau na yanke, azabar da kukewa yaronnan ta isa haka, zan tsaya mai har uwar shi ta dawo, ke kuma in ga qafar ki ta qara fita nan da can kiga yanda zan dake kin bar gidannan kenan kuma uwar ki ma kin ja mata dan sakin ta zan" dafe qirji Innar hinde tai tinda ya fara magana" to malam...........


👵🏻     WATA UWAR    👵🏻

 


  

    By HAERMEEBRAERH
Sisters masu cewa suna na akwai wahalar fada😂 naga masu tambayar na da yawa, 

Hamida+ Ibrahim= Hamibrah, Haermeebraerh kuma dan iyayi nai wa rubutun hope yanzu zai dai na baku wuya😂😂 

Page 23: 

"Malam kayi hakuri duk abinda ka lissafa ba zasu faru ba" ( ni haermeebraerh nace hahaiiiiii casssss bari ba shegiya bace da uban ta ashe😂)   saiga Innar Hinde har wani sinne kai ake qasa, Hinde ana son ai rashin mutunci baki ya mutu, haka ya wuce ya bar su. Da dare Innar Hinde ta shigo dakin jiki daqa2 da datti, bayan akan idon ta Baban hinde yai wanka yaiwa Naufal wanka, ya sa yai bacci ya kwantar da shi, ya dawo dakin su ya kwanta, amma ita yarkace2 da ita zata tafi ta kwanta mai haka, ai daya buga mata wata uwar tsawa a gigice ta juya taga waye yake maganar, dan tinanin ta aljanu ne suka shigo masu ta bango, waige2 take tayi" Ba dake nake magana b😡 Nace ki wuce kije ki wanka, kin daina kwana min kamar wata mahaukaciyar da ta shekara tana ciwon hauka" dubawa tai da gaske Baban Hinde ne, jikin ta yai mugun sanyi ta dau hanyar fita ya dakatar da ita da cewa" ki tabbatar kin wanke bakin ki tas kin aske gashin jikin ki mai doyinnan kk dawon nan haka saidai ki kwana a tsakar gida yau" amsawa tai da " to me gida" tana fita Baban Hinde yaji wata dariya ta zo mai" ashe haka iko yake a gida na ke wasa da dama ta? Dan Allah ji yanda take wani noqewa kamar wata mutuniyar kirki, Ya Allah kasa addua ta ce ta daidaituwar iyalina da shiriyar su ne ta fara karbuwa Allah ka sani ina son iyalina ina son mata ta, amma baqaqen halaye da qazantar ta na nesanta mu, Allah ka daidai ta mun zuri'ata" yana sauke hannu ne yaji alamun fitowar ta ta shiga madafi, toka ta diba da gawayi da gishiri ta hau wanke bakinnan tayi ta gama tas ta shigo" dauki wankakken zanin ki ku goge kan da kk wanke kafin ya fara mana warin da ya saba, ga dan guntun tirare na can a yar kwalbar durin nan ki shafa"magana yake fuska a daure amma dariya ce fal cikin shi da tausayin ta, dan ko bacci ne cike a idon ta( to an kau da wari da tsami, qofofin gashi sun samu sararin iska, baki ya huta da gumus🙊) tana gama shiryawa ta haye gado, matsowa Baban Hinde yai ya fara sarrafa ta, ba saiga Innar Hinde ta gigice ba, fadi take" Malam na cuci kaina, 😭 ashe haka yan tsotse2n da nake ma masifa suke da dad'i nake bala'i? Malam meyasa da bakai min ba da bala'i?" Dariya ce ta kwace ma Baban Hinde wannan karon yace" To yanzu laifi na kk gani? Da ai ban da wannan ikon zaki fara fada kamar ki hadiye ni, ki na kira min lokaci garen" ni dai daga yau ba zan qara ba ka yafe" to ya wuce in dai zakina gyara jikin ki kuwa yan tsote2n nan kullum sabon salo zan na maki, dan haka share hawayen ki daina kuka, sai abu na gaba, ina so na roqi arziqi ki kula da yaronnan, ki daina mai halayen da kk masa, kiji tsoron Allah akan 'ya'yan ki amanace Allah ya bamu, ba wayon mu bane ya bamu su, ganin damar Allah ne, dan haka ku dage da musu addua, nayi sakaci tin fari da na aure ki, na kula wajen tarbiyya kina da rauni van bada mahimmancin gyara maki ba, dan haqqina ne, sai da abun ya kai yafi qarfi na banda yanda zan dake, har gashi abun ya taba yaran mu" Malam ka yafen😭😭 da yardar Allah komai ya wuce bazaka qara jin wani abu mara dadi daga wajena ba" a haka malam ya qara lalubo ta ya ci gaba da aika mata da saqonnin da yasa ta fara mai koke2 zata tara mai maqota ya rufe bakin ta da nashi🙊

Washe gari da asuva suka tashi sukai wanka sukai alwala suka fara sallah, sun idar Baban Hinde ya ce ta zauna ya fara koya mata karatun muhammadiyya dan tana buqatar shi, shiko ilimi baya tsufa, ba kuma a jin kunyar shi, bayan sun gama ne ta tashi tai hanyar dakin Hinde tai daidai a shimfidar ta, tana asararren baccin ta, duka ta dasa mata ta ce " tashi kije ki alwala ki zo ki sallah shashanci ya qare a gidannan, maza kafin ranki ya baci" tana zumbura baki tana qunquni tai waje, ita kuma tai madafi, haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya Naufal na samub kulawa ba laifi, amma a wajen Hinde sai ta ga idon iyayen ta take jan shi a jiki, har ya gane ta, dan in basa nan shima baya zuwa wajen ta.Ta gama shiryawa tsaf ta fito, a mota ta same shi, lokacin magrib ta kawo kai sosai, da alwalar su suka fita( Note: yana da matuqar mahimmanci mu koyi yin alwala in zamu fita musamman alokacin magariba mu koyawa yaran mu hakan ko gidan qawaye suka je su kai yamma su fito da alwala, sabida a lokacin aljanu ke yawon su) suna hanya kowa da abinda ke saqawa a ranshi, daga baya Nasreen ta aje tinanin komai ta gyara zama ta rufe ido tana ta tasbihi har suka isa, sakkowa tai ya fito ya tsaya" sai yaushe kuma My priceless jewel?" Duk sanda kk son zuwa My Handsome" hhhhhh lallai baki da dama ni dinne Handsome" hmmmm ni a wajena da duk abinda yafi hakan ma zan kira ka da shi, amma gudun kar a ce na zaqe ne yasa na tsaya a hakan" jiyai kanshi ya wani fasu, a ranshi kuwa fada yake " in ban gaggauta auren yarinyar nan ba ina gab da susucewa" kiran magrib ne ya katse su yace " ni na tafi sai gobe, zan dan tsaya nai sallah a bakin qofar gidan naga masjid a wajen" k no p love, na gode sosai Allah ya bani kai" dariya yai sosai sannan ya amsa ya tafi cike da jin dadi da nishadi.

Ta shiga ciki ta tadda Barira na alwala a pampo, daidai ta idar kenan, da gudu ta taho ta rungume ta, tna murna," Inna ! Inna ! Inna ! Da sauri ta fito taga wannan kiran na meye.........


👵🏻    WATA UWAR     👵🏻


    BY HAERMEEBRAERH

Rouqy Zuma ( yar mitsila😂😜) this page is for u, Allah ya sa ki kamo ni😂Page 24:

" Allah mai iko Nasreen ke nake gani ko ido na ne?" Inna ni ce " tana dariyar cin dadin ganin su, daki suka shiga sukai sallah, sannan suka shiga hirar yaushe gamo, ranar kusan kwana zaune sukai, Nasreen ta sha nasiha sosai wajen Innar Barira da Barirar kanta, anan take sanin an saka ranar auren bikin Barira wanda ya qarato nan da sati biyu. A tare Inna ke masu gyaran amare, dan a cewar ta, waya sani ko itama ayi lokaci daya? Kwana biyu tsakani Nasreen bata ji daga Naseer ba, tin tana jurewa har ta zo tana zancen da Barira, hakuri ta bata ta kwantar mata da hankali.

A bangaren Naseer kuwa so yake ya gyara kanshi dan rabon da yai aski mai kyau ya manta, zuwa yai ya gyara kan shi sosai, gyaran da ko da Mum ta gan shi sai da  ta bude baki tana kallon shi, rungume ta yai ya dora kan shi a kafadar ta " Mum ya kk ga yaron ki? Kina ganin yanzu ko yar shugaban qasa nace ina so zata so ni? Ya kk ganin Nasreen dina zatai in ta ganni?" Naseer stop feeling nervous , she is in love with u anyway she will never reject u, she is urs, her heart, soul, and body belongs to u son" wani dadi ne ya kama shi ya mata kiss a kumatun ta na hagu ya fita da sauri2 gudu2" Mum sai na dawo na tafi wajen Priceless jewel dina" mota ya fada, ya fita da gudu yana murmushi mai sauti, hango irin farin cikin da zata shiga in ta ganshi ne kawai ke qara ma fuskar shi annuri, a wani butique ya tsaya ya sai mata kaya harda na subhalallah, takalma da jakkuna ma bai barsu ba saida ya diba,kashe kudi yai kamar ba a so,  a wani shagunan cusmetics ya tsaya ya sai dangin kayan kwalliya da turaruka masu tsada da qamshi, bayan ya kammala da nan wani fancy super market ya shiga, ya lodar mata fevorite chocolates din ta, sannan ya dau hanyar gidan nasu, a lokacin tsakanin magrib da isha'i ne, yana isa ana kiran sallah a masallacin qofar gidan shiga yai akai sallah da shi domin da alwalar shi yake yawo, ana idarwa ya fito yana neman izinin shiga gidan a wajen mai gadin su. A ban garen Nasreen kuwa ba walwala a tattare da ita, daka ganta kasan tana cikin damuwa, hada ido sukai da Barira tai mata murmushin yaqe, Barira tashi tai ta zauna kusa da ita tace " haba sister, ki kwantar da hankalin ki dan Allah Naseer naki ne ke daya, ina kyautata zaton akwai kwakkwaran abun da ya riqe shi bai zo ba, dan haka na san duk inda yake kina ran shi, kuma yanzu haka kar ki mamakin yazo" tana fada tana dukan kafadar ta da ta ta, murmushi ne ya kwace wa Nasreen tace" lallai da ban san kyautar da zan maki ba in ya zo yau, ban san irin murnar da zan ba ni Nasreen" wasu hawayen missing din Naseer ne ke fitowa daga idon ta, hannu Barira tasa ta goge mata tace" to malama da kk kuka yanzu in aka ce ki fito yazo gashi kin bata yar kwalliyar taki ta yamma sai kije mai fuska a bace da hawaye?" Saurin gogewa tai ta tashi kamar wadda aka sanar wa cewar ya zo ta hau gyara fuska, wata doguwar riga ce a jikin ta kalar golden da ratsin silver, mai dogon hannu, ta kama ta ta sama, ta bude daga wajen qugun ta, kan ta ba dan kwali sai ponytaile da tai da dogon gashin ta baqi, ya sha gyara sai qamshi yake, Nasreen kenan Allah ya yi ta da son gyara, ko da ba su da shi tana da tsafta balle kuma ga samu yanzu? Ai gyara ba kama hannun qazamar mace😜

Komawa tai ta kwanta bayan ta gama juya jikin ta a madubin dakin nasu, ta limshe ido, tinani take duk wannan kyaun da tai da dan anjima zata cire kayan, ta maida na bacci, dan guntsun tsaki ta saki ta dad'a gyara kwanciya," Assalamu alaikum" muryar Baban Barira kenan, " Nasreen ! Nasreen ! Kafin yai na ukun ta fito sanye da dankwalin rigar a kanta, durgusawa tai," Sannu da dawowa Baba" kanta a qasa take maganar, " Yauwa diyar albarka, Naseer din ku dai yau gashi can a waje, dan na kula wannan rashin fara'ar da bama samu kwana biyu har da rashin shi" kunya ce mai tsanani da dadi suka kama ta ta tashi da gudu tai dakin su, gado ta fada tana tsalle kamar wata yarinya, can ta sakko ta kama hannun Barira tana juya ta suna rawa, Tambayar ta take me ya faru? Amma ba baki sai dariya kawai take, kai bakin ta tai kumatun ta na dama ta mata kiss , sannan ta sake ta ta je gaban madubi ta dau tirarukan su ta hau fesawa, toilet ta koma ta fesa mouth freshner, fitowa tai ta qara powder da lipstick sannan ta zo gaba Barira," ya kk ganni yar uwa komai yaji? Zan iya zuwa wajen mai ni din yanzu? Sister Naseer is here" ta fada tare da rungume Barira itama murn ta fara, sannan tace maza ki fita kina bata mai lokaci, golden takalmin ta ta dakko mai tsini, saka fita tai tana taku daya daya, a palo ta tadda shi yana tsaye hannun shi ya goya su a baya, yana fuskantar windo da hanzari ta je , zata rungume shi ta baya, tinanin haramcin hakan ya tsaida ta, taja ta tsugunna a wajen, qamshin d yaji ne ya sa shi juyowa da hanzari, ganin ta duqe ne yasa shi durqusawa shima, hawaye ya gani suna bin fuskar ta kamar an bude pampo," My Priceless jewel, ki daina kuka, daga idon ki ki kalli masoyin ki, wanda ya susuce a kwanakin da bai gan ki ba, ina fatan zaki yafe min rashin zuwa na da kuma jina da baki ba" daga kai tai suka qurama juna ido a hankali take kallon shi ta tsaida idon ta akan gemun shi da yasha gyara da sajen shi, murmushi sukai wa juna sannan tace" na yafe maka, amma da ka sake ka qara kwana baka zo ba yau hukuncin da zan maka ba kadan bane" dariya sukai a tare ya nuna mata kujera akan su zauna zama sukai suna kallon juna, kowa da abinda ke saqawa a ranshi, Naseer ne yai breaking shirun su " a gaskiya ni dai ina zuwa gida zan sanar da Mum gobe a yi maganar zuwa can garin ku a tambayar man auren ki, kuma bana son ya wuce nan da sati biyu, dan Allahu shahid ba zan iya jure mu wuce hakan ba" murmushi tai idon ta cike da hawayen jin dadi tace" Kai Handsome yanzu ba zaka dan iya bari mui kamar wata biyu ba haka" miqewa yai tsaye a razane yana mata kallon anya kanki daya kuwa? Dariya ta hadiye, tace" mene ne kuma irin wannan kallo kamar yau ka fara gani na" tana yi tana turo bakin ta gaba da shagwaba, idon ta tana kifta shi in a sexy way, qara rikicewa yai yace" yanzu Nasreen in ba mugunta ba ji fa yanda kk sani a gaba kk man sannan ki ce wai a bari bikin mu ya kai wasu watanni, haba babe, ai saiki sa nai zaton baki so na yanzu kuma" kamo hannun shi tai for d first time tun zuwan shi ta zaunar da shi a mazaunin shi sannan ta saki hannun, " ka kwantar da hankalin ka, ni Nasreen ta Naseer ce har abadan, idan gobe kk son a mana aure zan fika murna, fatana Allah ya sanya mana albarka a ciki" jiyai kamar ya rungume ta dan farin ciki, amma ya basar, 😎 sallama akai sannan suka ji shiru ba a shigo ba Nasreen ce ta amsa sannan Barira ta shigo, dauke da faranti a hannun ta, an jera jug din da aka hada kunun aya da mai zobo sai kuma jofuna biy, gaida Naseer tai tana ma Nasreen sherin damuwar da ta shiga na rashin shi, dukan wasa ta kai mata da pillo, ita kuma ta fita tana dariya. Sun gama hira ne ta tashi raka shi, a bakin mota ya miqa hannu ya dakko wani kwali ya miqa mata" Sweery ga wannan ki riqe dan na kula ba waya a hannun ki yanzu dana zo qofar gidan nan ne na tina sai na koma na siyo maki, komai na ciki da digits dina" godiya ta hau yi kamar ba zata daina ba, hannun shi ya sa a kan leben ta " shshhhhhhh, sai kace wadda na ba wa shagon saida wayar dika? Naseer kenan yaba kyauta godiya, godiya tana da da di ga wanda akai wa koda yafi qaruna dukiya, in aka gode mai bayan yai abin kirki yana sa ya ji dadi sosai, dadi ne ya qara lullube shi" nimq na gode to dear da soyayyar ki a gare ni" Sallama sukai, ta tafi, ya bi bayan ta da kallo, murmushi yai" kamar ba yarinyar da tazo bata fi sha bakwai ba ji yanzu yanda ta cika ta zama budurwa sosai, Allah ka mallaka min Nasreen" kayan ya diba ya kira wasu yara a bakin gidan sukai ta shiga da su, ya basu kudi, ya tafi cikin farin ciki sosai.

Washe gari Mum ta samu limamin da yai mai wakilcin auren shi na farko magana, akan zuwan su qauyen Langyam da ke a garin kano, sanar da ita yai ba damuwa, amma su mai hakuri zuwa gobe Naseer ne ya matsa kusa da shi" Dan girman Allah malam mu tafi yau, gani nake kamar za a kwacen ita" idon shi yai jawur kamar zai kuka, murmushi malam liman yai yace to Naseer amma bari naje na gabatar da wani uzuri in na gama kafin shabiyi sai mu wuce in ban gama ba mu bari zuwa gobe, " Malam Liman kana da passport dan Allah muje kano a yau komai dare, in yaso gobe mu isa qauyen nasu"dariya Mum da Malam sukai Lallai Naseer ka fada tarkon so mai tsanani Allah ya tabbatar muku da alkairi" AMEEN" tashi yai yaje ya fara hada kayan shi tsaf, ya sanar da Nasreen ta waya akan ta shirya zai zo yanzu ya dakko ta zasu tafi kano, tambayar ta yai passport din ta, ta shaida mashi ya na wajen ta amma sai ta duba, yace ta hanzarta dai yau yake so su tafi, sallama sukai ta sanar da Inmar Barira da Baban ta addua da fatan alkairi suka mata, Barira ta je suka fara hada kayan su, kudin da Naseer ya hada mata a kayn da yakwo mata jiya ne tace suje super market, tai siyayyar tsaraba, musamman ga dear Naufal......👵🏻     WATA UWAR    👵🏻

    

   BY HAERMEEBRAERH

I am once again sorry, readers ban da ra'ayin bude group din kaina tin fil azal gaskiya, har yanzu ma haka, amma zan qoqarin inna kammala dika na dinga turawa group daya bayan daya, in yaso masu nema ta PC sai su na bi, wayata na riqewa in ina tura abu mai yawa, amin afuwa. THANK U FOR D LOVE ANA TARE❤

Page 25: 
Zuwa sukai suka sai mai kayayyaki, musamman na sakawa, da takalma, sai abun wasa na yara dai haka, sannan tai ma Innar su da Baban Hinde da Hinden tsarabar kayan sawa da turare, sai yan kayan kwalama, da suka dawo duk ta samu babban akwati ta zuba, bata jima da dawowa ba 11:35am sukaji sallamar Baban Barira yana ta fito ga Naseer ya zo, sallama ta musu tare da godiya mai tarin yawa sannan suka tafi, gaida Malam Liman tai sannan ta Kalli Naseer da ke zaune a gefen ta da wani salon dauke mai hankali, " Ina kwana my Handsome" tana wani kifta ido 🙄 amsawa yake son yi amma saida ya hadiye wani yawu sannan ya amsa da" lfy qalaou, and how is my baby doing?" I am  gud Alhamdu lilLAAH" murmushi sukai a tare . Sun isa airport lfy jirgin su ya daga zuwa lagos tafiya ce mai cike da nishadi sukai da zaquwa ta qare su isa ayi ta ta qare, Naseer ta matsu su isa yaji an bashi Nasreen din shi, at d thought of that,gaba daya sai yaji kamar ya bude ido ya gan shi a qauyen Langyam" calm down will u? Ko dake u have every right to be nervous dan wataqila Baban Hinde ya bama abokin shi ni, tinda kasan second hand ce ni" ta fada tana teasing din shi, wani irin bata rai taga yayi a hankali ta saki dariya mara sauti" ni dai karka zane ni da wannan manyan idanun naka, wasa nake" better" abinda ya furta kenan ya ja ya lumshe ido, sanar da su akai sun kusa sauka a garin kano, wata murna ce ta kama su dika. Sun isa lfy inda suka sauka a hotel suka ci abinci suka shiya sannan suka kama hanyar qauyen langyam goshin Magrib kenan.

  QAUYEN LANGYAM

Innar Hinde na hango ta fito wankan yamma, ta samu bakin nan tana ta dirza kamar an aiko ta, tin kwanaki da malam ya mata dandanen tsotse2 ta dage da tsafta, gaba daya ta sauya, ita da Hinden haske da kyaun su ya fito, dan dama kyawawa ne daidai su, qazanta ce ta mai da su wani rodi2, Nasreen ce kawai baqa a gidan," hhhhhhhh Inna wallahi sai kinje kin jima kan ki ciwo, ji yanda kk dake kina dirzar baki kamar kina wanke bayan tukun😂" in ji Hinde tana fada tana faman dariya kamar zararriya" hmmmm yarinya me kk sani in ban da shirme ni na san dalilin wankin baki na ai, kiyi dariyar ki ki gama" Baban Hinde ne ya shigo tare da sallama, Naufal ne ya tashi da gudu ya rungume shi yana dariyar jin dadi, Baban Hinde daga shi yai bayan ya aje ledojin Hannun shi," Ke Hinde zo nan ki dau wannan ki gyara mana zuwa anjima kowa ya gama shiryawa mu hadu a dan motsa baki" amsawa tai ta tashi fakam2, dan duk da ta fara tsafta har yanzu wautar na nan, wanka ya shiga ya fito, wanke bakin shi ya qarasa sannan yai alwalar Isha'i, ya shiga daki ya tadda Innar hinde an sha gaye ana ta zuba qamshi da turaren su dan duri da yake siyo masu a masallacin juma'a" Kaiiiii mata ta kinga yanda kikai kyau kuwa, sai kk koma kamar wata budurwa, kin tinan farkon gani na da ke, ranar da kk sacen zuciya, naji duniya ba wata sai ke" wata iriyar dariya ta sake ta jin dadi, kanta kamar ya cika dakin dan girma " Malam irin wannan washi haka? Kar kasa nai kaifi da yawa fa, in kyau ne ai ba kamar ka kaf garin nan, tin daga yarin ta har iyanzu" to shi kenan kin rama dai kawai, amma ni dai ai gaskiya na fada" nima gaskiyar na fada ai" yana yi yana shiryawa, daidai ya gama kuma ana kiran sallar isha'i, sallama ya mata akan za shi sallah, adduar dawowa lfy ta mai itama ta fara ta ta, kama hannun Naufal yai suka fita Shima ya samu arziqin wanka, Hinde ce ta mishi, tana yi tana mitar ita fa ta gaji da bauta, ko yaushe uwar dan Lagos zata dawo oho, an kawo musu jikan yarbawa an aje an koma, ko yanzu jikan wane yare zasu samu kuma oho🤷🏻‍♀. 

Mota ya gani a qofar gidan bayan sun iso daga Masjid, tsayawa ya danyi yana nazarin mutanen da yake hangowa suna fitowa, Naufal ne ya cirw hannun shi ya diba da gudu, " Mummy" wata runguma ta mai kamar za a kwace shi, tana hawayen farincikim ganin danta fes da shi, gaba daya tsoro da fargabar ta sun kau, Baban Hinde ne ya iso bakin shi a washe, sai fararen haqoran shi kk hangowa, miqa masu hannu yai suka gaisa, Naseer ya wani noqe ya durqusa ya na kwasar gaisuwa, dariya Nasreen tai ta shiga ciki, sallama tai Hinde ta fito da gudu daga daki, dai dai Innar su ma ta fito, a tare suka furta"Nasreen"

"Na'am" cike da murna dan da dikkan alamu Innar ta ta sauya dabi'a saidai daga Hinde ne kawai ta samu kallon ban damu da keba🙄 Sallama Vaban Hinde yai sannan ya sanar da su za a shigo, shiga sukai Ciki Innar Hinde ta dakko tabarma ta shimfida tana " lale maraba da baqin lagos" Naseer kai a qasa, haka suka zauna aka fara gaishe gaishe, da gabar ta da kai" wannan da dukkan alamu shine surukin nawa Baban Naufal ko?" Baban hinde ya fada yana murmushi, " Hakane malam" inji Liman, shi kuma qara noqewa yai,Naufal na jin haka ya taso da a hankali, ya tsaya gaban shi , ya kalle shi, sannan ya ce "DADDY?" Naseer idon shi ne ya cika da kwalla ya daga kai, ya kama hannun shi ya jawo shi jikin shi, a take Naufal ya rungume shi kamar zai qara tafiya ne ya bar su, kowa a wajen jikin shi ne yai sanyi, Hinde kanta sai da taji tausayin su, Innar Hinde ce ta iso da faranti a hannu yanke da kayan marmarin da Baban Hinde ya shigo da su dazu, ta aje Nasreen kuma ta taho da ruwa a kwanon sha, Nan take Nasreen ta fita taje ta aiki yaro ya siyo mata balangu da gurasa na dubu uku aka kawo ta debar wa su Malam da Naseer , sannan ta debar ma Inna sa Baba , sai nata da Hinde da Naufal kuma, fafir Naufal ya qi yarda ya bar baban shi ya ma ko sha ruwa ne ta dadin rai, ya qanqame shi sosai ta wuya, tashi Nasreen tai taje ta gyara masu Malam Liman dakin soro tai shimfida ta sanar da su, bayan an gama gaisawa ne da komai, Baban Hinde ya masu jagora akan sai da safe zai kira yayan shi da qanain shi ai maganar saka ranar auren nasu, sallama sukai ma Inna suka tafu makwancin su.


Da sassafe Nasreen ta tashi ta hada abin kari mai dadi, dubawa tai ba wasu kayan abincin kirki a qauyen da zai masu dadi dabara ce ta fadi mata kawai ta samu naman jiya da bata ci ba ta dan tafasa da albasa da maggi sannan ta yanka qana2 , sai ta ba Hinde kudi ta siyo flour d kwai, hade su tai tai qulli da su ta saka maggi da dan citta da kaninfarin da ta daka sai tafarnuwa, ta saka da man gyada ta fara soyawa tana wainar flour, ba sai ga qamshi mai dadi na tashi a gidan ba, Hinde ce ta matso kusa" yanzu dan Allah waya koya maki wannan irin girki mai sa mutum ya qoshi tin kan ya sa a baki? Ji yanda qamshi ke tashi ta ko ina?" Dariya tai sosai kan ta amsa ta" Hinde shi girki ba wai dole sai an koyawa mace ba, yana da kyau ace kowacce mata ta san yanda zata sarrafa kayan abinci kala2, tanda in iya flour dinnan mijin ta ya aje mata a gida ba zata damu ba, zasui ta cin girki kala2 na flour din je kawai ba tare da sun gundira da flour din ba, ina fatan kin gane" daga kai tai kamar wawiya yawunta sai tsinkewa yake🤤 bayan ta gama ne ta daga ruwan shayin da yasha kayan qamshi ta jera komai ta je daki ta shirya, sannan ta fito ta miqawa su Naseer, ta same shi yana kan sallaya har lokacin, gaida shi tai, ta gaida malam ta futo, bayan ta sanar da su ruwan wanka will be ready in sun gama
Baban Hinde ne ya shigo da wasu dattijai su biyu, Malam Bala da Malam sale kenan, wan shi da kuma qanin shi, sun tattauna sun fahimci juna, inda Malam Liman ya sanar da su suna son a saka ranar aure nan da kwana takwas, sabida yai daidai dana Barira, inda zasu daura aure a nan, dan iyayen Barira ma nan zasu zo ai daurin aure, sai a tafi da su can Lagos din, sun miqa kudin na gani ina so da sadaki da komai da ake buqata, Naseer ya basu hakuri akan lefe sai sun koma, inda Baban Hinde ya nuna mai ai ba ibada bane, dan haka karya damu. Abincin da Nasreen ta dafa masu mai dadi suka ci, sannan sukai sallama suka tafi, su kuma su Naseer sunyi zasu koma Kano a ranar su tafi Lagos daga nan sai ana gobe daurin aure su dawo. 


" Priceless dan Allah kar ki na zama ba caji, dan ba zan jure zama ban jin muryar ki akai akai pls" fari tai da ido tace" nima ba zan iya jure rashin muryar ka ba koda na yini daya ne, saidai zaka na min uzuri kasan nan qauye ne, ba koda yaushe ake samun wuta ba, amma zan iya bakin qoqari na, ka kular min da kan ka kaji" ta qarasa cike da shagwaba, murmushi yai yace" zaki bayani ne dalla dalla, ki ta ja min rai randa na kama ki a hannu na sai kin yi larabci( 😂 irin  Minaleen Hamma Haidaer😂) dariya sukai a tare sannan ya miqa mata wata envelop ya shiga mota, godiya tai ta yi tana daga masu hannu, gaba daya jin shi yake kamar a akurkin kaji, motar duk qarafa , daga tasha aka kira masu ita qofar gidan.

Bayan tafiyar su ne ta dakko akwatin ta, ta fiddo ma kowa tsarabar shi, anan ne Hinde taga ruwan abin arziqi, sai ga kuka," yar uwata ki yafe ni, tabbas kin min nisa, wannan shine fassarar hassada ga mai rabo taki, na maki hassadar da duk zan miki amma gaba kawai kk yi, ban tsane ki dan komai ba sai dan fina komai da kk yi a koda yaushe, gashi yanzu auren ki ma za ai ni ina zaune ko mashinshinin kirki bani da shi" kuka take sosai tana sharce majina da gefen riga, " Haba yar uwata ki daina kukan haka ya isa, bam taba riqar ki da komai ba, fatana Allah ya mana gafarar laifikan mu duka, ya qara hada kan mu" magan ganun da suke dik a kunnen Inna da Baba, Baba ne ya kai hannu ya sharewa Innar Hinde hawayen ta ya jata sukai daki.


Rama bata qarya sai dai uwar diya........

.

👵🏻      WATA UWAR.   👵🏻


    BY HAERMEEBRAERH

Page 26:


Yau ne washe garin ranar daurin auren su Naseer da Nasreen Barira da Umar, sun iso qauyen langyam tin da yamma, wannan xuwan a mota suka yi shi, gaba daya jikin Barira yai ciwo, sakamakon shi Umar ba wani mai qarfi bane sosai, da zasu iya tahowa a jirgi, hakanne yasa suka taho da jama'ar shi gaba daya ta mota, Naseer ma da tashi jama'ar abokan da Malam Liman wakilin shi, gidan su Nasreen da Naseer ya sa akaiwa gyara sosai tare da qarin dakuna uku, dan gidan ba dai fili ba, a tsohon gidan su Barira amare suka koma, inda suka zo da mai qunshi da gyaran jiki daga can ta fara masu da gyarab jiki zuwa qunshi," wallahi haishina da garinnan ko saloon babu yanzu dole sai mun koma zani saloon, ke kin samu me makon ki gyara zaki wani ce tinda ban ba bazaki ba kema🙄" eh ban yi sai mun koma😚" harara wasa Nasreen ta mata tace" amma ai baki qi karbar kayan gyaran da Inna tai ta baki ba, da sai ki qi sai na koma" dukan wasa Barira ta kai mata tace" ai wannan gyaran ciki ne, wannan kuwa na fili ne, ke wa yasan me kikai ta banka"dariya qawayen su suka saka, ko nace qawayej Barira dan ita Nasreen ko a da bata da qawaye anan balle a Lagos , qawar ta daya Barira(Bally sunan iyayin da takan fada mata kenan).


Naseer na can daya ga mata zai fara baza ido ko zai hango Nasreen dan ko dakin da aka sauke su ya qi shiga, wai tinda ana ce bata ciki, karta wuce bai gan ta ba, Umar dariya ya dinga mishi yana tsokanar shi, amma hakan bai sa ya hakura ba" kai ai dake kana tare da taka amaryar kace na shiga ciki mana" a bu wasa2 har yamma, ga wayar ta bata shiga, yana tsaye ne yaga Hinde zata wuce, magana ya mata, ta juyo tana wani fari ita ga budurwar qauye" dan Allah ina Nasreen ne, in kin san inda take ki wa Allah ki kaini na ganta, bqzan iya jurewa har dare bam gan ta ba ki taimaka" wani fari ta qara yi tace" ikon Allah, ai ni ban gane ka ba ma, gaba daya ka qara kyau, dama maza suna yin gyaran jiki in aure yazo? hmmmm taho na je na kai ka inda take" tafiya suke tana ta zuba shi ko hankalin shi yayi gaba , suna zuwa daidai gidan ta nuna mai zata juya" ki taimaka ki kirawon ita mana ai kinyi mai wuyar ko" tabdi jam na shiga su din ga min kallon yar qauye? Duk fa yan binni ne a ciki? Ai na ma mai wuyar dana nuna maka gidan"hannu yasa a aljihu ya dakko kudi ya miqa mata," dan Allah ki taimakan" hahaiiiiiii cassssss dannan ina ma ace lokacin Hinde na mai idon cin nera ka bata kudinnan ai da har hannun ka sai na kusa tsinkewa wajen karba, amma ka makara Adda Nasreen ta mun wa'azi akan karbar kudi kuma na dauka, dan haka ka barshi zani dan zumunci, da son yar uwata da kake" sa kai tai kamar balama, balam balam ta shige, xaune ta gansu sun wanke qunshi kenan ta zauna, " ina wunin ku, Adda Nasreen ga Abban Naufal a waje yana jiran ki"Wa ni tsallen murna tai ta dakko hijab ta saka, tanaa sauri zata fita taji an riqe hijab din ta baya, tsayawa tai ta juyo taga wace," yo yanzu in da ni ce nai wannan abun ace yar qauye ban da aji , ke yar birnin ma gashi sai bari kk akan saurayi, ni da nice sai na ja aji kan na fita😚" gaba tai ta bar su suna dariya sosai" Hinde hooo" Nasreen ce ta dan gyara sannan ta fita a hankali tana taku daidai."Hayyakallah ya Hubby" Hayyakillah ya Habibty" murmushi mai cike da kewar juna sukai wa juna, iso ta mai zuwa soron gidan suka bude dakin soron, ta shiga ta dakko tabarma, sannan ta koma ta dakko ruwa da abinci, shigowa tai sannan suka zauna, firfita take mai da maficin hannun ta sakamakon zufar da taga yana yi,"My handsome ka ci abinci, da ganin ka ka dade rabon ka da abinci" lallai kin san mijin ki tin kan a daura auren ma, amma kin san bazan taba iya cin abinci ba in ban gan ki ba" murmushin jin dadi tai sannan ta bude ta fara bashi a baki, karba yai shima yana bata har suka gama, zai magana kenan sai suka ji kiran sallah, shiru sukai suka din ga bin kiran sallah bayan an fada suma su fada, da suka gama sukai adduar da aka sunnan ta yi bayan kiran sallah sanan sukai salatin Annabi, a tare suka daga hannu sama suna roqon Allah yafiyar zunuban su, sannan, sukai adduar samun zaman lfyr su da arziqi mai yawa,( Allah na karbar adduar da aka yi bayan kiran sallah , in mutum yayi kamar yanda su Naseer sukai) tashi sukai sukai alwala, Naseer ne ya jasu sallah dan ba zai iya komawa gidan su Nasreen ba,kuma masallacin na ta can ne, gaba daya hankalin shi na kan neman inda Nasreen din shi take, Sallah ya jasu suka ci gaba da hira, har qarfe 9:45pm sannan yabi yaran da suka kawo masu abinci suka koma. 

Yaune ranar daurin auren su Nasreen, can na hango su sun sha kwalliyar da aka dinga zuwa kallon su a qauyen saboda wani kyau da sukai, dinkin wani material suka saka red head din Yellow, ba qaramin kyau sukai ba, yanda shape din rigar yabi jikin su abin kallo ne da cece kuce a qauyen, wasu suna sun burge, inda wasu suke gani basu burge ba suna yawo cirara, whatever 🙄 sn dai yi kyau musamman Nasreen coz ta fi Bally shape sosai. An daura auren su akan sadaki dubu hamsin hamsin, Naseer harda hawayen dadi saboda gani yake a yanzu ba wanda ya isa ya raba shi da abar son shi, sai Allah, Nasreen ko kuka take kamar me Naufal  ganin tana kuka ne yasa shi rungume ta yana kuka shima, " ni dai ki daina wannan kukan karki sa min yaro yai rashin lfy, wannan ai kukan dadi ne kk yi, shi ko bai san name bane zakisa yaga kamar wani abune ya same ki" cewar Hinde da ta sha kwalliya, aikin wata qawar Bally ce dan a cewar ta in hinde ta waye ba qaramar Babe za ai ba a wajen😂, Nasreen ce ta share hawayen ta ta miqe ta kama hannun shi ta kai shi wajen Innar su tai gaba, Inna ce ta kama shi ta kai shi daki ta debo mai abinci ta aje mai tana lallashin shi.


An gama duk wani bikin da zasu gudanar a nan qauyen sannan suka rankaya sukai Lagos, wannan karon amare da angwaye sai wasu qawye na kusa da abokan ango na kusa ne suka tafi ta jirgi, sauran kuma a mota suka koma, isar su ke da wuya kaya kawai suka canja suka tafi wajen dinner, a wani hamshaqin Hotel suka gabatar da dinnar party din, ya qayatar matuqa anci ansha, sannan angwaye kowa ya kama hannun amaryar shi ana rawa a haka suka fita da ga wajen, kowa yai mota da matar shi sukai hanyar gidajen su , kafin su rabu ne Bally ta je da gudu ta rungume Nasreen suka hau kukan rabuwa, a kunne Bally ke fadawa Nasreen" Sister i am scared , bana son a barmu mu biyu tsoro nake ji sosai" jikin tq sai rawa yake," It will be awsome i promise, dont be scared, nasan umar akwai tausayi he will treat u like a princess, kin san lallaba su ake, haka zai lallaba ki, just promise me in ya neme ki ba zaki qi ba, kin san hakan haramun ne, he is now ur husband" I promise i iwll give him what ever he ask for" dats my gurl, i love u" i love u too sis" da kansu suka rabu, kowa ta koma kusa da mijin ta, bude masu qofa sukai suka shiga inda sauran abokai da qawaye sun firfito sukai ta daga masu hannu.


Bally da angon ta sun isa gida lfy, inda Nasreen da Naseer sun isa gidan su Lfy, ya riga ta fitowa ya bude mata mota, tana fiddo qafafun ta ya daga ta cak in a bridal style yai ciki da ita ta kwantar da kanta a qirjin shi, daki suka nufa............


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻   BY HAERMEEBRAERH

Page 27:A kan gado ya aje ta, yana mai tsanan ta kallon ta inda ita ma cikin ranta tana son ta daga kai ta kalli fuskar shi, amma a yau kunya take ji sosai, take tinanin da ya fado mata, wato aure daban, karuwanci daban, ajiyar zuciya rai mai qarfin da ya dawo da Naseer daga duniyar tinanin da ya shiga, domin shima tinanin da ke ranshi kenan, duk wata soyayya in ba da aure ba ragaggiya ce, ba ai komai a cikin ta ba, jiyake a yanzu haka daya same ta yana kallon ta a gaban shi, tana a matsayin mallakin shi, wanda komai zai mata na alkairi da jin dadin ta lada zai samu, hannu ya kai fuskar ta ya bude mayafin da ta rufe fuska da shi bayan ya aje ta," haba priceless jewel, yau ai ba ranar rufe fuska bane ko, rana ce ta nuna ma juna yanda muke son juna, rana ce ta nuna ma juna we belong to each other" tini hawayen dadin kalaman shi sun fara bin kyakkyawar fuskar ta, hannu ya sa yana share mata su, daga idanun ta masu haske tai tana kallon shi, inda gashin idon ta masu tsaho suka daga har suna tabo girar ta, kallon da take mai ne ya sa ya miqe da hanzari ya zauna kusa da ita, jawo ta yai kusa da shi yace " priceless tell me, tell me whatever it is dat u want to say pls, ina kwadayin jin abinda ke cikin zuciyar ki pls" ya fada yana mai riqe wrist din ta tare da hada goshin su waje daya,kallon shi tai cikin ido tace" abinda znce ko nake fada a zuciyata shine, Ya Allah na gode maka daka mallaka min Handsome di na, abin so na, wanda nake jin in bashi ba zan iya rayuwa ba, Ya Allah na gode maka da ka tsamar damu daga cikin masu tsananin sabo a gare ka ka tsarkake mu ka mallaka mana juna ta hanyar aure, Ya Rahman ka tausaya mana da tausayawar ka ka yafe mana zunuban mu da muka aikata a baya, ka bamu zaman lfy, ka kiyaye mu daga dikkan sharri, Allah ka bani ikon kyautata ma mijina a zaman mu na bashi dikka n soyayya da kulawa ta" shassheqar kukan angon nata taji wanda ita ta dade da jiqa fuskar ta da hawaye mai tarin yawa, kamo ta yai gaba daya ya rungume ta yana furta"Ameen ya Allah, Ameen ya rahman, Ameen da'iman" sai da sukai kuka mai yawa ba mai lallashin wani, suka gaji, dan kan su suka tsagaita, a nan ne ya tashi tsaye ya daga ta, ya ja hannun ta zuwa toilet din su mai kyaun gaske da ya sha kanay alatu a ciki, alwala ya fara ya sa tai alwala, kauda kai yaga tayi tana murmushi, ba shiri ya fara zaro ido " me kk nifi? Ki taimaken kar ki fadan baki sallah coz i dont even know how to sleep at peace today" dariya ce sosai ta kama ta, tace ni ba haka zan fada ba, duk ka bi ka wani rude🙄, ni dai kawai ka fita tukunna kafin nai alwalar akwai abinda zan yi ne shiyasa" ( Dan Nasreen tana da masaniyar cewa tabbas aka idar da duk abinda zasui sai ba barin ta zai tai watsa ruwa ba ita ko bazata iya bacci ba saita watsa ruwa dan rabon ta da wanka tin a hotel, ga rawa da suka sha duk sunyi zufa, bata qaunar angon ta yaji wani yanayi mara dadi a tattare da ita musamman a yau, da tasan sun dade basu hadu ba) kada kai yai ya fita ya ja mata qofa, wanka tai first tai brush ta qara gyara duk inda ya kamata a jikin ta sannan tai alwala, ta fito da kayan jikin ta, 

Ko da ta fito bata ga kowa ba da alama ya tafi dakin shi kenan, wajen d Innar Bally ta sanar da ita kayan ta suna ke ta dakko abubuwam da zata buqata, ta koma toilet ta saka wasu kayan bacci, bby pink ce rigar, iyakarta guiwar ta hannun siriri sosai shape din ta ya fito sosai a jiki ta qasan rigar silk ne ta sama kuma net ne, sai ta daura zani akai ta saka hijab ta fito, tai wajen tiratikan ta ta fesa kamar ba zata daina ba, tana juyowa yana bude qofar, murmushi sukai sannan ya zo da sallaya biyu, ya shimfida masu, sallah ya ja su sikai, raka a biyu, sannn ya matsa kusa da ita ya dora hannun shi a kanta, ya fara karanto adduar da aka wajabtawa angwaye suyi a daren farko ma iyalan su


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻

   


    BY   HAERMEEBRAEH

Haermeebraerh na godiya mara iyaka ga dukkan masoya wannan novel na WATA UWAR ina mana fatan alkairi a duk in da muke, Allah ya amfanar damu da abinda ke ciki na fadakarwa. LOVE U ALL ANA TARE😉❤
Page 28:
Innar Bally na cewa," Innar Hinde dama saqo ne daga wajen wadan can yaran, su Naseer, Nasreen ta dame shi da son ganin Naufal, shine yace in tambaye ku ko zaku iya basu shi, ya koma can da zama, dan yanzu ya shekara biyar kinga , bai kamata ace kamar shi a ta can birni yana zaune a gida ba makaranta ba, dan haka suka ce, in zan koma gobe na taimaka na wuce da su, dan sunce a ara masu Hinde taje taga yanda birni take itama" murmushi Innar Hinde tai tace " wannan dai dabara suka min su kwashen yaran gaba daya, sai dai sun yi tinani da suka ce a tafi harda Hinde, dan a yanzu yanda take son Naufal da ba ita, wallahi sai ta daga mana hankali dika" dariya suka sa, da jin haka Hinde jiki na rawa ta bazama daki, hada kayan su ta fara masu datti ta fito da su, ta je ta debo ruwa ta hau wanki😂, ( da dane aka ce Hinde tai wanki ai sai an tara yan kallo😂 amma da ta ji birni ba wanda ya sata) wanki tai tas, dan kayan ba yawa dama, tana shanya ne Innar Bally ta fito, ganin tana wanki bata dauka ta ma ji me ake magana akai ba, sai dai ganin fara'a a fuskar ta yasa take tinanin "Oh su Hinde anyi hankali ansan ai wa baqi fara'a unlike b4 ta hau bata rai kamar ta daki mutum" " ai dawowar Nasreen na qarshen nan ba qaramin gyara yarinyar nan yai ba, Allah ya qara shiryar da mu dika" Ameen" suka fada a tare, sallama sukai ta tafi gida, da daddare ba wanda ya sani, Hinde ta gama hada kayanta kaf dana Naufal a jaka, bayan Malam ya dawo ne, yayi wanka, ya gyara jikin shi tsaf ya ci abinci ne, Inna na gefen shi da mafici a hannu, tana mai firfita, tace" Baban Hinde , dama yarannan ne ke son a basu Naufal, kuma inda hali Hinde ta bisu taga wajen zaman yar uwar ta" murmushi yai" dama na san za a rina, dan yanda na kula suna son yaron nan, ba zasu iya rufa wata biyar ba shi ba, gashi wata uku kawai har sunyo aike, yaran zamani kenan" murmushi sukai, Innace ta kwala Hinde kira a lokacin Naufal yao bacci, amsawa tai ta fito ta tsugunna a gefen Baban ta, gaida shi tai, ya mata tambaya akan karatun ta, bayan ta gama bashi amsa ne yake sanar da ita tafiyar tasu a gobe da bayan asuba, fadada murmushin ta tai,"Allah ya kaimu Baba" sallamar ta sukai suna dariyar murnar da take, a wani bangaren Baban ta na godiya ga Allah daya shirya mai iyalan shi, Inna ya kalla yaga yanda take cike da farin ciki, hannun shi ya sa ya shafi gefen fuskar ta yana murmushi shima" kinga ko yanda fuskar ki ke haskawa a cikin farin watan nan? Na kasa gane to iya hasken ki ne ko kuma na dan sammi ki nawa ne?" Yana fada da yanayi zolaya, matsawa tai jikin shi tace" Malam kenan baka rabo da tsikana, ai kaima kasan na fika haske zama dani ne yasa ka qara hasken" dariya suka sa a tare, suna cike da so da qaunar junan su.

Da asuba Hinde har tai sallah, tai wanka, ta daura ruwan zafi yana gama yi tai ma Naufal, fadi take"  Dan yarabawa gobe iwar haka muna garin su Oduduwa yacin, zakaje kaga yan uwan ka masu kwale, dabaje kasan me zan fara koya? "Girgiza kai yai alamar Aa" yarbanc zan koya, dana dawo ba raini wajen su karime, dan na musi shar wallahi" dariya suka sa ita da shi suka tafa, a haka suka gama shiri dan jakar su tin jiya ta make ta da kaya, Sallamar Innar Bally ne ta dawo da su daga sallamar da take da iyayen ta, Malam ya mata nasiha sosai da ta sa ta kuka da hawaye ba kadan ba, tare da tsantsar nadamar qiyayyar da ta nunawa yar uwar ta a baya gashi tana neman tsufa a gida ba aure. Tasha suka je suka hau motar kano daga kano sai lago shine ur eyes, Idon Hinde kamar zai fadiqasa, hango manyan gine2 da tai da dogaye da tai sai da ya sata kuka,tana share majina da mayafin ta tace" Yanzu inna dan a wahalar da magina shine akai wannan dororon gidan? Ina laifin mai tsahon irin naku, kowa ya huta, duk fa tsayin mutum bai isa ya kai tsahon ginin nan ba, da kudin da zasu bannatar na wajen tsawaita katangar haka, ai da wasu ginin akai a gefe, 😤🤧 share majina ta sake yi, fuska tai mata jawur, daga Innar bally har naufal mai qananan shekaru saida sukai dariyar wautar Hinde" zaki fahimci wannan ginin ne Hinde in lokaci yayi" Sun isa gidan InnarBally lfy, da wajen isha'i gaba daya jikin su yai tsami tafiya kamar za a bar qasa, cewar Hinde kenan, qauyanci kan ranar ya amsa sunan shi wajen Hinde, komai sai da aka nuna mata musamman bandaki, a matse ta shiga, amma ta rasa inda zata hau shadda injita da fada, fitowa tai da gudu tana riqe baya da gaba, irin na masu jin bayan gid, Innar ta tarar da Baban Bally a palo, ko ta kan shi bata bi ba, kuka ta sa" Ni dai dan Allah tinda na kasa gane komai a gidannan ki nuna min ko wata yar duhuwa ce na shiga nai ba haya, a matse nake, na rasa  shaddar" kuka take sosai,hankali a tashe, Inna ce ta tashi tana dariya ta kaita ta nuna mata yanda za tai da komai ta fito, bayan ta gama ne kamar yanda aka nuna mata, ta tsaya mamaki, lallai sha'anin bature sai dai ai kurum🤔
Washe gari ne Naufal ya fara kuka tun asuba, yana kiran Mummyn shi da Daddyn shi, dan shi dai a sanin shi wajen su aka kawo su amma baiga ko daya ba, hakuri Hinde ke bashi, tin tana iyawa har ta fara sharce kwalla da majina, dan yanzu yanda take son yaron ko kukan shi bata son ji, Inna ce ta same su a haka, take tambaya " lfy? Naga kuna kuka?" So yake yaje wajen iyayen shi shine yake kuka tun goshin subahi, ni kuma na gaji da lallashin shi, yaqi shiru" to kui hakuri bari gari ya waye aiwa Naseer waya yazo ya dauke ku" murna suka fara a tare Naufal ya daga hannu alamun su tafa, tafawa sukai yana dariya" Yau zanga Mummyna da Daddy" zabura sukai jin murya mai taushi da dadin sauraro ta qaramin yaro, "Inna kinji me naji kuwa? Ko gidan ku akwai makarai ne" zaro👀 suke kamar ace ar su gudu, Naufal ne yai magana yace "Nine fa" bayan ya kama hannun Hinde, ihu Hinde tasa tana murna sosai harda hawayen farin ciki, ta tabbatar yaron nan rashin iyayen shi a hade waje daya ne yai affecting din rayuwar shi dik.da qanqantar shekarun shi, Innar Bally ce ta fita a hanzarce taiwa Baban magana ta sanar da shi komai,cikin hamdala ya daga waya ya sanar da Naseer sannan ya fada mashi suzo su dau ke su yanzu,  ba a jima sosai ba like awa daya da yan mintuna su ka ji tsayuwar mota a waje, da hanzari Naufal ya leqa window, hango Daddyn shi yai yana bude daya bangaren motar, ai da gudu ya fita, daidai mummyn shi ta fito daga motar, rungume ta yai ta daga shi sama, ta qara rungume shi" Naufal honey me kace dazu kan mu zo?" Mummy ina son ganin ku ke da Daddy, shine nake ta ma Hinde kuka" yana fada yana dariya wani irin farinciki ne mara misaltuwa a tattare da iyayen shi, da su Hinde da suka fito harda jakar su, " Ya Allah na gode maka da ka sa yaron nan bai zamo daga masu nakasa ba, Allah ka yafe mana" Naseer ne ya ringume su duka yana buga bayan ta da alamun rarrashi, Baban Bally ne ya ce " to alhamdu lilLAAHi naji matuqar farin ciki nima dan a yanda naji labari baya magana, amma yanzu gashi Allah ya bashi iko yana magana cikin murya mai dadin sauraro, wato kai dama rowa kk mana sai da ka zo kaga amaryata ka fara magana dan ka siye zuciyar ta ko"  dariya mai dadi Naufal yai yana riqe da wuyan Mummyn shi.Sun isa gida, cike da farin ciki, bangaren su Mum suka nufa, In da suka iske ta ta hada abincin karyawa mai yawa, tana ganin su ta taho cike da fara'a, Naufal ta miqawa hannu  ya je wajen ta, gaishe ta yai, tai maza ta kalli iyayen shi" ba kince man baya magana ba?" Hawayen farin ciki Nasreen ta goge tace" Mum ashe Naufal na gane komai da ake, yana fahimtar komai, wataqila da zuciyar shi yake hira? Da ace Allah bai bamu ikon gyara rayuwar mu ba da yaron nan zai iya samun ciwon zuciya, ko ya kurumce da gaske din" Oh thank God he is all okey" cewar Mum Hinde ce ke magana a zuciya" ikona wajen lillahi ko me ta fada oho na ga suna gyada kai kamar qadangaru sai Allah" jitai ance to bismillah Nasreen kaita dakin ki na da" kama hannun ta Nasreen tai ta nuna mata dakin da yanda ake amfani da komai, gudun kar taje tai masu qauyanci dan ba sanin kan abubuwan tai ba" wannan gidan yafu rikitarwa akan nasu Innar Bally" dariya Nasreen tai," to in kk shiga bangare na sai kin kama baki, yafi na Mun rikitarwa" kai habaaa, anya kuwa yan binni na cikakkiyat sallah kuwa, dan ba yanda za ai a kwanta a wannan gadon da asubar fari a tina sallah" Nasreen dariya take sosai, ta kama hannun ta suka fito palo a dinning room suka isko su Mum, zama suma sukai a kan kujerun dake zagate da table din" serve ur self pls" Mum ta fada tana muemushi , Nasreen ne ta bude wani flask da bata san meye a ciki ba ma, budewar da za tai yai daidai da thowar amai da taji...........


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻


    BY HAERMEEBRAERHPage 29: 


Amai ta shiga toilet din dake cikin palon tai sosai kamar xata amayar da hanjin ta, gaba daya Naseer hankalin shi ya gama tashi kamar ba Dr. Ba , dan ko hint bai dauka ba😜 Mum ce ta ma cike da fara'a da jin dadi ta je inda Naseer ya riqo Nasreen din suna dawowa palo, akan kujera ya aje ta, yana faman jera mata sannu, wani irin tausayi ta bashi amai daya duk ido ya fada tai firi2 kamar Buzuwa😜😂(in ji kince wani abu kum😎) Mum ce tace" Sannu Sweetheart, tin yaushe na samu sabon mai gida ko kishiya ba ko labari?" A dan firgice suka juyo, Naseer ne ya shafa kan shi yana murmushi, gaba daya sai yanzu ya fuskanta, Nasreen ko dan kunya saka kanta tai tsakiyar cinyoyin ta tana dariya qasa2, dafa bayan ta Mum tai " don't be shy, come on tell me?" Mum wallahi nima ban sani ba amma ni tinda aka kawo ni banyi al'ada ba, ban kawo komai ba game da hakan" Sujjada suka ga Naseer yayi ta godiya ga Allah, bayan ya dago ke ya matsa kusa Nasreen kamar zai shiga ciki su gana da bbyn🙄 riqe fuskar ta yai da dikkan hannyen shi biyu ya hada goshin su, ya rasa kalmar da zai magana da ita," Priceless, u ar indeed my priceless jewel, u give me all the happiness in dis world dat i could ever ask for, may Allah reward u, Allah ya miki albarka, domin bam ma san iyakar adduar da zan iya miki ba, amma albarka ta qunshi komai, domin ko a islam ba adduar da tafi a ce maka Allah ya albarkace ka, to ina roqon Allah daya albarkace ki, ya sauke ki lfy, kenan yanzu bbyn mu zai yi wata uku ko biyu da wasu satika?" Murmushi tai tace"Ameen mijina and maybe wata biyun da wasu satikan ko" qarasar da bakin shi yai nata yana kissing yaji an kwade qeyar shi ta baya,"Ouch !really  Mum, do u have to do that now?" Yeh i think o have to , for a wake up to u guys🙄 " ko bakuga yanda kuka saka Hinde ta koma bane, juyawa sukai suka gan ta ta takure a bayan labule, wai ita sun bata kunya a dole, dariya ce ta kwace masu, gaba dayan palon, Naufal ne ya zauna a gefen mahaifan nashi yace" Daddy Mummy Allah ya yi muku albarka" Dariya sukai sosai wato yaji me aka fada game da albarka kenan, rungume shi sukai suka hada baki " Naufal Dear/Honey Allah ya maka albarka da dukkan yara" Ameen" Naufal da Mum suka amsa" kin iya futowa daga labulen ko kici gaba da tsayuwa mu kuma mu cinye kajin kan ki fito" da gudu ta fito" to ni dai ba na qi kaji ba ko a gidan surukai ne( waya ga surbajo taga nama a gidan surukai😂) atoh, amma gaba in zakui wannan tsotsen2 kuna yi a daka ku biyu ba wanda ya gani" dariya kowa yake yi a wajen, Nasreen qin komawa tai wajen dan qamshin farfesun Kajin da taji gaba daya dawo mata yake bata son qara shaqa, "My Dear what do u want for breakfirst pls, coz ba zai yu ki zauna da yunwa ba kin sani ko" Mum ni dan wake nake so sai kuma wainar flour  mai manja, da yajin da aka sa ma Garlic da thyme please" Ok karki damu just give me a minuts yanzu zan kammala na kawo maki inshaa Allah" da hanzari tai kitchen, su Hinde ana can ana ma kaza dalla2, wani cin chips da fork gaba daya bata gan shi ba hannu take dannawa a plate kawai ta na sawa a baki, Naufal sai dariya yake," Inna Hinde dan ku na kallon kina cin abinci haka, kinga sai dariya yake miki" Yo a yaya yake son naci, in dai dariya ce gaka ga ta yaro" Naseer ne yai tashi dariyar yace "tsaya fa kiga ya zaki yi" Nuna mata yanda ake xin abinci a table yayi, ita kuma tana dauke duk wani salo da ya nuna mata" kinga in kina cin abinci haka zaki samu miji dan birni wanda ya fini kyau da komai, amma in ba haka kowa ya ga yanda kk cin abinci da tafi da magana cewa zai kaiiiii saita waye na je wajen ta" Naufal dariya ya saki sosai data sa Hinde quluwa" Haaaaaa yaro kai dariya yanzu gobe na baka mamaki kai da tsohon ka, in haka ne naga matar taka ma Mun,(Mum)ta fita gayu, dan haka ni wajen Mun zani ta koyan nafi wayewar da kyau" Aaa fa malama yanzu za a ji kanmu dake, waya ce maki Mum ta fi matata gayu? Taya zaki hada sabon jini da tsohon jini" ya fada yana maqe murya yana kai kanshi kusa da ita kar Mum taji, jiyai an sake make qeyar shi a karo na biyu,"Muuuummm" Yesssss, wato nice tsohon jinin ko, to ai da nake tsohon jinin ga shi nan Hinde ta fada maka nafi matar ka gayu" can bangaren Nasreen kuwa shiru kk ji dan hannu ta danna a kwanon itama ta bude qafafu ta baje a qasa ta hau dan waken da ci ta kuma koma kan wainar, haka tai tayi har ta kammala, daidai suma sun gama kenan, wanke hannu sukai gaba daya suka zauna hirat duniya.


Bayan wata uku, wata kyakkyawar farar yarinya na gani tana tajewa wata black beauty kwantaccen gashin ta kai, tana yi tana shafawa a hankali suna hira"Adda nasreen ni dai gaskiya ku kaini gidan Adda Bally i really want to see her plssss" cike da shagwaba Hindatu ke maganar,(Dan daga ranar nan ta dage ba wasa, Mum kuwa ta yi iya qoqarin ta da hakuri da juriya, ta koya ma hinde gayu bata mata hausa sam, tin tana hirme yanzu ba abinda bata ji a turanci, saidai wajen yi ne takan dan kwafsa, ga girki kala2 da Mum ta koya mata, tabbas ta koyi abubuwa sosai, lesson teacher aka dakko maya ita da Naufal ga kuma malamin islamiyya na musamman, tsoron Allah da tawadi'u ya shiga Hinde sosai kusan kullum sai ta ba Nasreen hakuri, inda ita kuma tai alqawarin ta qara bata hakuri Ado zata aura mata, daga ranar ta daina ) " to ki bari yayan ki ya dawo sai ki fada masa wataqila nima innaga ina iyawa na biku" Yeeeeeh U ar d best Adda" rungume ta tai ta tura kanta gefe ta dakko wayar ta, danna digits din Adda Bally ta hau yi tana sanar da ita zasu zo da daddare, Nasreen kama baki tai tana tinani a ranta wannan da sauran ta, in Naseer yace ba yau ba fa? Ta bada fake promise kenan. Kshe wayar tai ta juyo, " Hinde yanuzu in Abban Naufal yace ba yanzu ba fa?"😡 " ni Adda bana son sunan nan pls meye kuma wani Hinde dan Allah ko so kk halina na da ya bini😙 ni gaskiya a dena ce man wata Hinde, in baza a ce Hindatou ba ace Auntyn Naufal ko ace min Ke zaifi sauqi😙" hannu Nasreen ta hade alamar ban hakuri tana dariya Naseer da Naufal na tsaye sun na dariya qasa2 dan har suka shigo basu ji su ba, " "Aunty Hinde au Aunty Hindatou" cewar Naseer kenan, buga qafa ta fara ta wuce shi " ga wajen ku nan ku in zaku kori mutum sai kuita neman dalili" tafiya bangaren Mum tai tana ta cika kamar wadda akai ma wani abun" Hindatou dear me ya faru ne wannan long face haka? " Mum ba su Adda da yaya bane, wai sai wani kirana Hinde suke, bayan sun san bana so, kuma Malam Anwar ya hana yace in daina bari ana kirana haka nan" ta turo baki gaba kamar Roumie tayi fushi😂😜Mum dariya take sosai tace " Ohhhhhh ga inda zancen yake nan mana , kice kawai Malam Anwar ne baya so shiyasa bana so nima" da gudu Hinde tai daki tana dariyar kunya( Malamin Islamiyyar su kenan, sun fara soyayya da hinde  a sati biyu da fara zuwan shi rayuwar hinde ba abinda bai sani ba ta sanar da shi, a hakan yaji yana son auren ta coz shima has his past, so ya nuna mata kawai su yafi juna su riqe juna da amana, inda ta amince da hakan yanzu haka an sa musu rana bayan wata takwas za ai auren su) dariya Mum tai ta miqe tai daki itama.

Sun shirya sunyi fes da su gwanin sha'awa suka nufi gidan Bally inda Naseer ke tuqa su, sun yi tafiyar rabin awa kan nan suka tsaya a qofar wani gida madaidaici mai kyau, shiga sukai bayan Umar ya fito ya masu iso ciki, Bally ce itama da dan cikin ta a gaba tayi kyau hasken ta ya fito sosai ga kuma na ciki, Nasreen ce tace" Maman biyu ana nan na ta turawa" dariya suka sa "Aa wallah na bar maki biyun dayan ma wallahi tsoro nake ji ni" Kaiiiii Adda Bally kar ki sa ta dinga ganin mu ragwaye pls k dage ki haiifo biyunnan kawai" cewar Hinde kenan " Rufan asirisweet qanwa, ba zan iya biyu ba gaskiya" Naseer ne ya amshe" kinga kuwa Priceless zata iya zata baku mamaki kuwa" murmushi tai tace" Allah ya bamu masu albarka, Handsome" shafa gefen fuskar ta yai yai kissing hannun ta" to love birds taso muje mui sallar isha'i" dariya sukai dika Naufal ne ya zauna kusa da Bally yana shafa cikin ta" My Naufal ka matsu a haifo maka budurwar nan naga alama" dariya yai yana sosa kai wai shi yaji kunya🙄( yaran zamani masu zamammiyar qeya wai ya san budurwa🙄)" Yar uwa ina son mui wata magana mai matuqar mahimmanci kafin su dawo shawara nake son ki bani dan Allah wallahi akwai matsalolin da ke damuna sosai, na rasa yanda zan , dan koda baki zo ba nai niyyar na zo da kaina.............


👵🏻    WATA UWAR    👵🏻


   

   BY HAERMEEBRAERH
Page 30: 


" Ba komai ke damuna ba sis sai matsalar da nake fuskanta a wajen Umar, kafin auren mu ke shaida ce yanda yake man kalama soyayya, yake nuna min matuqar kulawa, amma yanzu gaba daya abun ba haka bane, ya canja sosai, duk da ina hango tsantsar siyayya ta a wajen shi, sai ma qaruwa da tai ba raguwa ba, amma duk wata kulawa da yau promising me are all lies, ba wani abu da yau keeping da ya wuce satika uku da auren mu, kin ga da farko dai, in mun zo auratayya gaba daya baya tsayawa mu danyi wasanni, dan kar na zo ni i am not ready yazo yana bari na da wahala, inaaa kawai shi da ya matsu zai zo kawai ya fada min da ya gama ya tashi ya barni duk kuka da zan sai yace to shi ya zaiyyi? Sannan kinga in ban da lfy irin ya damu dinnan ya nuna min kulawa a'a kawai sai yai ta harko kin shi bai damuwa, dana ji sauqi kuma ya dora da buqatun shi😭 kuma kinga wallahi in nai laifi ya dinga fada kamar bai sanni ba haka zai ci min mutunci tas ya gama, sai daga baya ya zo yana wani.ban hakuri musamman in yana son kusanta ta,ke abubuwan da yake min suna da yawa na rasa yanda zan bullo mai😭😭"  a gaskiya ban ji dadin jin wadannan abubuwan ba domin kamar ba zai yi ba, amma kin san me zaki? Na farko stop especting too much from him, espectation  hurts, musamman in akai disappointing din ka , ur heart will break, sannan game da baya wasanni sai dai kawai ya fara kusantar ki, wannan laifin ki na gani, dan me zaki bar shi ya shiga jikin ki ba tare da kin tabbatar kin mai wasannin da zai tada taki sha'awar ba da jikin shi shima zai ji dadin hakan in kk mai yau kk mai gobe ko baya so a hankali zai fara so dan yaji dadin wasan, in kk ji u ar good to go, sai ki bashi dama ku more wa rayuwar auren ku, dan haka ta nan laifin ki yafi yawa, ina son ki gyara pls sis, abu na gaba kuma na rashin lfy, wasu mazan ba sa son raki duk da an san baki da lfy ki zama mai juriya wani nishe2 ki ta ihu bai ba in azaba tai yawa zaki iya yin kuka amma ba wanda zai sa.miji ya ji haushin ki ba, in yaga haka zai san kina cikin azaba amma juriya kk ta haka sai ya tausaya maki kiga yana nan nan da ke, sai in kin yi hakan ne bai kula da ke still, in kk ji sauqi randa kuke raha kk tabbatar ranshi ba zai baci ba da duk maganar da kk gaya masa to saiki fada masa ki ce Wane me yasa kk man kaza in ban da lfy? In ya gaya maki dalili in kina da laifi saiki gyara in babu sai ki qara da wallahi sai in ga kamar baka sona ne saboda masoyi yana jin ciwon da dan uwan shi ke ciki, zai iya baki hakuri ku daidaita kuma ya daina amma in bai baki hakuri ba ya daina nan ma yayi, in ma bai daina ba sai ki dau matakin qarshe, kauda kai, domin ta yu haka yake, kuma hakan na samo nasaba ne daga tatbiyyar shi tin fil azal, sannan da daga wane gida ya fito, sai ki cire a ran ki kina so mijin ki yana baki kulawa , dan ba halin shi bane, a kwai wani abu Bally da ma'aurata ya kamata su sani shine, ita rayuwar aure dole miji da mata su koyi tattauna dukkan matsalar su a tare, ba tare da fada ko yin fushi ba, in kuna haka sai ku shekara dari ba wanda ya ji kan ku, a ce tinda ake ba a taba jin kan su ba , ba dan baku fada ba sai dan kun fahimci juna, ni kin ga ni da Abban Naufal in mun samu sabani, komai dare in mun gama abun da zamui zamu tttauna damuwar mu , kowa ya ba kowa hakuri, shikenan ya wuce, dan haka ki zauna ki gyara rayuwar gidan ki kan lokaci ya qure maki, ina maki fatan alkairi yar uwa da mu dika" hawayen ta ta share ta rungume ta tana murmushi," na gode yar uwata da ban sanar da ke ba da ina jin baqin ciki ya sa min hawan jini" ta fada tana dariya, sallama akai aka leqo "in kun gama hirar ta mu sai ku fito ku bamu abinci yuwa muke ji"😱🙊 dama sun ji kome muke fada? Ban ji shigowar su ba yau na shiga uku na" in ji Nasreen da ta rude ta kasa fita daga dakin" itama Bally ta ji ba dadi amma wani sashen na ranta taji dadi. Sauraran ta da Umar yayi wataqila ya gyara, aiko suna fita ya kamo hannun ta ya rungume ta ta baya ya dora kan shi akafadar ta ya hade hannayen su yana bata hakuri sannan yai mata alqawarin komai zai wuce shima abun na damun shi amma ya kasa gyarawa, amma hirar nan tasu ta sa yaji dole ya gyara ma, musamman da itan tana iya qoqarin ta akan shi, hawayen dadi ne ya gangaro mata daidai lokacin daya juyo da ita yana goge mata kiss ya mata a goshi ya na shafa fuskar ta, gyaran murya Hinde tai tace" Oh ni Hindatou wai ba dama ka sa qafa gidan masu aure sun dinga shinshime shinshine kenan , dan Allah ji yanda Ya Umar ke shinshine mata fuska🤔" dariya suka sa gaba daya har da Naufal " Aunty Hindatou ke kuma in dai kk gani sai kin yi magana" dukan wasa ta kai masa ya fada jikin ta ta rungume shu suka ci gaba da dariya, abincin dare suka ci tuwon farar shinkafa miyat wake da busasshen kifi, da drinks da tai na pineapple da ta zuba kayan qamshi da sugar,( hadi ne mai kyau ga mata harda mazan ma yana sa qamshi daga baki har HQ🙊) sun gama cike da nishadi suka koma gida.Yau tin safe Nasreen take jin jikin ta ba dadi sosai, daurewa kawai take Hinde kuma ta zata yana nan dan haka ma tin da safen bata shiga ba, Naseer bai da niyyar fita saboda weekend ne, (sunday) aya aka mai an kawo mara lfyr da suna da buqatar shi, ya fita tin 7:15am har azahar, tin tana daure wa har ta fara safa da marwa, ta kai ta kawo Naufal ne ya shigo daga wajen Mum, ya shigo shirin islamiyya, ganin Mummyn shi yai tana ta wahala, da gudu ya fita, karo yai da mutum, yana daga kai yaga Daddyn shi ai rungune shi yai yana kuka ya nuna mai hanyar shiga palo," Naufal calm down and talk to ur Daddy" Mummy na" kalmar da ya iya fada kenan Naseer ya dauke shi suka shiga da gudu, yana isa yagan ta a durqushe tana nishi mai wahalarwa, daidai nan suka ji kukan jaririya, Naufal ta aje ya ce ya je ya kira mum ya zauna wajen Aunty Hindatou, kafin Mum ta shigo Nasreen ta qara haifar wata jaririyar, jikin Naseer banda rawa ba abinda yake, daga yaran yai ya yanke cibi,sannan ya taimaka mata mahaifa ta fado, aje yaran yai daidai Mum ta shigo kenan, ta kama bakin ta🙊🙊😭😭😭 ga hawaye ga murmushi, she is speechless, qarasowa tai da sauri ta dauki yaran shi kuma yai toilet da Nasreen, ruwa mai zafi ya saka mata ta shiga ta kwanta a ciki tana ta maida nunfashi tana godiya ga Allah sannan ga mamaki fal cikin ta wai yara biyu ta haifa, ita da take zaton Bally ce zata haifi biyu, iko sai Allah, hure mata ido yai ya kamo hanun ta daya adduoin alkairi ba irin wanda bai mata ba har saida yaga tana hawayen farin ciki sannan ya tsiyaye ruwan ya sa mata wani shima mai zafi, saida ya sa mata sau uku sannaj ya saka mata daidai wanka, wankan ya fara mata yana kallon cikin ta kamar ba yanzunnan ta gama haihuwa ba yanda yai, tabbas ya daga amma ba za a ce wai irin tai qaton timbi ba, sai hips din ta da cinyoyin ta da suka qara girma ga girjin ta kamar ai magana su amsa, kallon ta yake yana hadiye yawu" Hey man dont even look me like dat u have no chance here u know dat, dont u?" Hhhhhhh kai babe ni kawai ina yava yanda Allah ya miki kyaun jiki ne kawai Allah yasa yaran mu sui kama da ke" Ameen amma ni nafi son wata tai kama da kai wata tai kama da ni" wowww Allah yasa" daidai ya dakko ta sun fito kenan, shiryata yai suka koma palo, Mum ta gyara yara sunyi fess " Addana sannu da qoqari Allah ya raya mana su akan sunna, ya albarkace su"Ameen Sweery" Mummy kin samo min qanne, na gode Allah ya baki lada mai yawa, Mum tace mata ne dika" Ameen Yaya Naufal dina Allah ya muku albarka dikan k, Mum i am hungry, i want something liquid please" Eh na sa Haulat ta dafa maki farfesun naman rago, da kunun gyada, in kina son na kaji ma nasa duk tayi inna kaine ma haka, ki bari nan da minti kadan zata kawo maki" Tea Naseer ya shigo da shi a hannu ya zauna kusa da ita ya kafa mata a baki, da sauri ta kama ta hau sha, tana shanyewa mum ta miqa mqta yaran," to suma a basu na su abincin" karbar su tai tana ma Allah tasbihi, daidai nan Naseer ya kawo dabino da zamzam inda ya miqawa Nasreen ta tauna ta sa musu sai tandewa suke dan bakinnan yai jawur gwanin shaawa bayan sun cinye ta sa musu ruwan zamzam din a baki suka shanye sannan ta sa musu nonon suka ko hau sha kamar jira suke, dan zafi saida tai kwalla ta rufe ido yanda suke sha kamar wasu manya, ankali ta bude idon ta tana kallon su ,lallai Allah mai halitta, nida uban yaran dika baqaqe amma yaran mu kamar yaran turawa, wannan misali ne akan Innar Hinde dan muddin ta gan su sai an sake sabon kuka da nemab gafara, tinda itama Nasreen duk dangin su farare ne ita daya ce baqa,hawaye ne suka bi fuskar ta, Naseer ne ya karbe su ya msusu huduba ya masu adduoi.


Hinde har ta yi waya ta sanar da mutane haihuwar, ai ko sai ga Innar Bally........

👵🏻    WATA UWAR    👵🏻


     BY HAERMEEBRAERH
Page 31:
Innar Bally bata iso ba sai goshin Asr, tana shigowa ta tadda kowa ya saka yaran a gaba sai kallo ake, kowa da abinda ya ke furtawa, domin kuwa yaran sun debo kyau irin na Innar Hinde, komai da komai, saidai su suna da beuaty point a qasan habar su, da akuma alamun za sui hushirya( irin tawa😎lols) ba abinda ta ke furtawa sai" Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen" ta fada ta kuma sai kuma tace" Sannu Nasreen dina" dariyar Hinde ce ta sa ta sassauta kallon t ga yaran ta na kallon ta " Inna Hooo, gaba daya kin kasa ma ko kallon yayan ki, sai kallon kishiyoyi, to wallahi ku shirya ke da Innar Hinde, dan kuwa su Baba suka ga wadannan halitta haka, kwanan zaure zasu fara saka ku" dariya kowa yake a wajen " to ai ni ba zan ga laifin su ba don an aje mu an dau wasannan tsalan yaran ki fa duba ki gani fisabillahi a zuri'a kaf an taba irin wannan haihuwar?" Dariya wajen ya qara dauka, ga sasshen naman da ta zo mata da shi shi ta dakko, ta miqo mata ya sha kayan qamshi da dan wasu hade2n irin na sirrin Innar Bally😜, ci ta fara tana lunshe ido ga gashin harda wani ruwa2 a ciki," A gaskiya ni ba zamu yar da ba ko Naufal? Ya muna zaune sai kwanuka ake miqa mata ita daya🙄" hhhhhhhh in kin ji haushi kema nan da wata goma sha biyu ki haihu zaki ga kwanuka kala2 a gaban ki" rufe fuska tai ta tashi zata gudu dan bata dauka amsar da za a bata ba kenan, kuma ko za a batan ba ta zaci Abban Naufal bane zai fada, ban garen Mum ta gudu, kwanta wa tai tana tinanin baya, "Oh ni Hinde, duba matar da na sa wa qahon zuqa da tsana, da qiyayya yanda Allah ya daukaka ta? Sannan ya sa gani ni ma a sana din ta na samu daukaka, ko shiryar da ni da Allah yayi ai ba qaramin arziqi bane, ga shi harda mijin aure na samu duk irin lalacewar da nai a baya, kaiiiiii amma wallahi qauye ba tai ba da kuma rashin samun tayayyar UWA, da a ca WATA UWAT gareni ba Innar Hinde ba mai hankali da nutsuwa da duk raba ma qazaman qauye budurcina da darajata da nai a baya da ban ba, a yanzu na fuskanci mutuncin mace da qimar ta shine nesanta kanta daga fadawa sharrin zina, Allah kaine ka tsara mana komai kuma yake ta fiya da izinin ka, Allah mun gode maka da ka canja mana rayuwar mu daga mummuna zuwa kyakkyaw, Allah ka barmu na ka duk lalacewar zamani" hawayen daya taru a idon ta ta rufe suka sakko fuskar ta, ji tai ana share mata su, daga kai tai taga Naufal ne, kusa da ita ya qara matsawa, janshi tai ta rungume, ta ci gaba da matse kwalla" Naufal kai yaro ne, amma yaro mai hankali da fahimta, ina sane da cewar a yanzu da shekarun ka suka kai bakwai zuwa takwas ka fuskanci abubuwan da suke faruwa a rayuwar ka, ka yafe min dik abin da na maka a baya kaji dana, ka yafewa Innar Hinde itama, sannan ka sa Allah a rayuwar ka a komai za kai, ka na neman zabin Allah a dikkan abinda ka saka a gaba, to Allah zai tina da kai a lokacin da kk cikin qunci" rungume ta ya sake yi yace"Aunty Hindatou na yafe maki, ki kwantar da hankalin ku kema ki samo min qanwa, amma ni bana son fara fa" hhhhh Naufal hooo" Aunty Malam ya zo, yana waje tin dazu kina nan kina kuka😃" biyo shi tai suka fata zagaye dakin suna dariya, taje toilet bayan ya fice ta wanke fuska ta zo gaban madubi ta gyara fuskar ta ta fice sin sha hirar su ta masoya yai mata barka, bayan ya tafi ne ta koma bamgaren su Nasreen ta tarar Innar Bally na mata wanka, tana ta raki" Oh ikon Allah, to dayan biyu ne wannan rakin, wataqila kin fi son wankan Abban Naufal, ko kuma dazu bai sa maki ruwan zafi da yawa bane" Ina ruwan ki, Allah ya kaimu naki zaki bayani ne ni da kaina zan maki" Nasreen ce ta fada bayan ta tro qofa ta fito, bakinnan ta turo shi gaba, ido ya kumbura alaman tai kuka, tana zama sai gyangyadi, dariya Hinde tai ganin hakan, Innar Bally komawa tai dakin da bbies din  suke, ta wanke su tas suna kuka suna komai, kafin ta gama musu suma sai bacci, Naseer ne ya gyara Nasreen ya shiyata, ya gyara mata kwanciya, a dakin yaran Innar Bally ta kwana Hinde tai bangaren su.

Kafin suna da kwana biyu Bally ta haihu ta haifi yarta kyakkyawa itama black beauty, kowa ya ganya sai ya tanka, yarinyar qatuwa kamar ni na haife ta, 😂 Bayan sati biyu,  anyi suna an gama komai, yaran Nasreen sunci sunan NI'IMA & NAEEMA, yarinyar Bally ta ci sunan NAWWARA, Naufal gidan ya tare, kullum yana kusa da bby ko tana hannun shi, kowa yazo sai ya tsokane shi,saidai yai ta dariya. Su Innar Hinde ba su zo ba, a cewar ta da wane ido zata kalli Yaran bayan irin abubuwan da tai ma uwar su, Baban Hinde yayi2, taqi, amma Hinde tace in bikin ta yazo bata zo ba, ba zata ji dadi ba, ta fada tana kukan haushin qaramin dalilin da zai hana ta zuwa ganin jikokin da Allah ya bata, ta wani bangaren kuma tana ganin har yanzu da sauran Innar Innar Hinde a wajen kula su.


Kwanci tashi a sarar me rai, yara sunyi bulbul, da su ga wayo, watan su hudu2, yayi daidai da yau saura wata biyu bikin Hinde da Malam din ta, shirye2 sike ba kama hannun yaro gyara ba irin wanda ba sa yiwa Hinde,daga kan Mum, Bally, da kuma Nasreen, ba wanda ya zauna wajen gyarata, saida ta koma tai wani irin kyau, na ban mamaki, kullum da irin abincin da take ci duk dan gyaran jikin ta.
  QAUYEN LANGYAM


" A gaskiya Innar Hinde baki da dalilin qin zuwa wannan auren, domin in baki je ba kina nunawa yarannan halayyar ki ta da na nan ne fa, ki duba ki gani, lokacin da yarinyar nan tana tsalle2n bin samari shago ke kika bata qwarin guiwa, sannan lokacin da Nasreen ta zo da Naufal baki nuna damuwar ki ba musamman da ta baki kudade a hannun ki, sai yanzu sa suka samu abu ta hanyar halal lokacin ne zaki ce wai ke ba zaki je ba kina jin nauyin su? Wanne irin gwari ne wannan?" Kuka take tana share majina" ni malam ba wai naqi bane, gaba daya kunya nake ji na qara hada ido da su a mazaunin su,ganin irin rayuwar dana sa su a ciki a baya, da wanne idon zan kalli yaron nan Naufal, ni nai sanadin da aka haife shi ba ta hanyar halak ba" ki daina sa wannan a ranki, dik abinda ya faru kuma ya wuce ya wuce kenan, fatan mu mu nemi gafarar wanda mukaiwa laifi ko Allah zai yafe mana muma, sannan mu maida hankalin mu wajen gyara gaba da ci gaba da istigfari" kwantar da kanta tai a inyar shi ya shiga shafa kanta, tana sauke ajiyar zuciya" to yaushe zamu tafi?" yanzu kinga sauran wata daya da wasu satika bari zamui sai irin sauran sati daya dinnan sai mu tafi ke ko ana sauran kwana biyu ko daya dan kar ki zama baki sake ba, bana son duk abinda zai sa kiji kin damu" na gode mijina, zanfi son mu je sairan kwana biyu din" Allah ya kaimu to da rai da lfy" Ameen" a haka suka bar maganar. A kullum Hinde da Nasreen abun qara damun su yake ganin kwanaki na qaratowa ba Innar su ba Baban su, Naseer da malam din Hinde kullum basu gajiyawa da kwantar da hankalin su, da basu baki akan zasu zo ne.
Yau sauran kwana biyu bikin su Hinde, can na hango Innar Hinde tana ta zare ido a tasha bayan saukar su a mota a cikin garin Lagos, motat Baban Bally ce ta tsaya a gaban su, bayan ya fito yana fara'a ya miqawa Baban Hinde Hannu suka gaisa," kai jama'a wannan gari da shi da cikin garin kano a kwai alummar rasulu, badan wancan yaron da ka gani ba, da ko wayar ma ni ban san ya zan da ita ba, tinda muna gida saidai a kira mu" dariya Baban Bally yai yace "tabbas Malam kaima ba zaka koma ba sai ka koyi duk wadannan abubuwan har da wasu ma" mota suka shiga suka hau titi, suna isa a qofar gate din gidan suka tadda Innar Bally tana jiran su, da sauri ta bude wa Innar Hinde motar ta kama hannun ta cike da murna" sannun ku da zuwa ikko ikon Allah, cunkus dakin tsimma" yauwa Innar Barira, ni dai wannan gari tafiha haka kamar za a fita daga qasar, da na san haka ne da ban zo ba sai na shirya" dariya sukai daidai lokacin da suka shiga palon gidan, abinci suka ci sukai wanka, dakin da aka nuna masu nan suka shiga, kwanciya sikai su huta, dan Innar Hinde sai wani shagwaban ta gaji take( kuji man tsohuwa fa🤔lols) tausa ya mata nan da nan ta hau baccin gajiya, murmushi yai a ranshi ya furta" da tin fari haka kk me zai sa mu cikin damuwa da tashin hankalin da muka fuskanta a baya".Su Nasreen sun san da zuwan iyayen su, inda farinciki mara iyaka ya mamaye su, Hinde ta so taje ta gansu amma su Bally suka ce ba inda zata, ta hakura har su zo, ba zasu zo sina mata gyata tana yawo a rana ba, a cewar ta to zata da dare, sa kyar suka barta, taje da dare amma a ranar zata dawo saboda gobe za a fara biki, sun kwana suna hira ita da Innar ta, hakuri ko ta ba Hinde har saida ta hana ta bata hakurin, ta mata nasihohin da saida ta ba Hinde mamaki, dama tasan wadannan abubuwan? Wajen qarfe tara na dare ta tafi cike da kewar dama tare zasu kwana.
An yi taron yini da rana inda, qawayen Mum ne yawanci, sai abokan arziqin Innar Bally, su suka halar ta anci an sha, zuwa  Asr aka daura auren su, aure kamar auren bazawara ba budurwa ba, hakan sai da ya dami Hinden sosai, daga bayada kanta ta sanar da kanta dalilin kasancewar auren ta ba armashi duk yanda yan uwanta suka so hakan ta kasance kuwa, ba komai bane illa bata rayuwar ta da tai a baya, hawayen ta ta share tace" Allah na gode maka da hakan ma domin kuwa ba kowa ke samun irin nawa ba ma" An kai amarya gidan ta dake can kusa da unguwar su Bally, amarya dai kun san ba wata wahala da zata sha, dan ta saba da gayun qauye, saidai ta wahalar da ango,😜 sun sha amarcin su sosai kamar ba zasu hakura su barwa gobe ba, ga gyara dama da tasha, tashi tai lokacin qarfe hudu ta yi goshin Subh, sukai wankan tsarki suka fito a tare, sannan suka duqufa sallolin nawafil, tare da adduar godiya ga Allah da kuma neman gafarar shi akan laifukan su na baya.
Wani matashin saurayi na gano da ba zai wuce shekara sha takwas ba ya biyo wasu yara masu matuqar kama da juna, suna gudu suna dariya shi kuma ya bata rai, bayan Mummyn su suka maqale suna mai kwalo, " wai kai Naufal yaushe zaka girma ne? Dubi dan abin kunya yanda kk bin qannen ka da gudu, me suka maka yau kuma?" Mummy kinga yanda yarannan suka shiga dakina suka hau gado suka tsaya a tsaye suna man rawa? Bayan kunna min laptop da sukai ina aiki akai ko saving rubutuna ba sui ba fa?" Ya fada yana maida numfashi" a gaskiya ba ku kyauta ba My Cuties, Yayan ku kunsan baya matsa maku amma ku kun sa shi a gaba, ba kyau fa, kar yazo ya dawo yan dukan ku bayan ku kuka jawa kan ku, kun kqi shi maqura" fitowa sukai daga bayan ta suka nufe shi, suka kwanta a jikin shi, "we ar sorry sweet broth" daga su yai ya rungume, ya ce "its k, amma kar ku sake,in kuna min rashin ji, My Nawwara will not be happy,kumq b azatai qawance da ku ba" hakuri suka hada baki suna bashi, wai kar ya fda mata plsss, dariya Mummyn su take sosai, da jin wannan maganar ta naufal.Cikin dare Nasreen na kwance a jikin Naseer yace " a gaskiya Mummyn twins ya kamata a sama masu qani ko qanwa kin huta da yawa fa" murmushi tai tace" hmmmmm not a bad idea, i will love that too"ta shi tai zaune  suka fiskanci juna, gyaran murya yai yace mata, " Nasreen" daga kai tai ta kalle shi dan rabon daya kira ta da sunan nan ya jima, and d way his face looks ta san akwai wata magana mai mahimmanci da zai mata.........


👵🏻    WATA UWAR   👵🏻      BY HAERMEEBRAEHPage 32:


 


" Da farko dai ina son nai maki godiya ta musamman" tashi yai ya dakko wasu takardu," na gode sosai a kan dukkan alkairan ki a gare ni, musamman na mai da ni mutum da ki kai cikakke, ta dalilin ki na bar neman matan banza, ta dalilin ki na nutsu na san ko ni waye, nasan ya kamata na kama daraja da mutunci na, sannan ke ce kk zama uwar 'ya'yan da nake alfahari nawa ne, har Naufal bana jin haushin samuwar shi, sai dai kullum ya zamar min wani tini na cewar ni mai babban zunubi ne a wajen Allah da bai kamata na shagala da duniya ba, wannan dalilin ne yasa na gina mana masallatai da makarantu da ni da ke, domin ko mutuwa mukai muna saka ran rahamar Allah a gare mu , sannan mu dage da aikin alkairi domin cewar Annabin rahama da yai na" kyawawan aiki na tafiyar da munana" kin ga in muka dage da yin kyakkyawa Allah zai dube mu da rahamar sa inshaa Allah" Nasreen kuka take sosai na jin qaunar mijin ta da kuma qara dasa mata tsoron Allah da yake yi a zuciyar ta, " ki dai na kuka my love ba ina fada maki wadannan abubuwan bane dan na tada hankalin ki, lakin sai dai dan mu ci gaba da shimfida rayuwar mu akan sunnar Annabin rahama, dan haka nasan kin san cewa Naufal ba zai gadi komai daga dukiha ta ba, wannan karatun a wajen ki na same shi malamata😊, so ni da Mum mun yanke shawarar mallaka mai wasu mahimman filaye da kamfani guda biyu na atampopi, daya a England yake daya anan gida Nigeria ne, sannan akwai gidaje guda biyu manya da Mum ta mai kyautar shi, ina fatan ki zama shaida a matsayin ki na mahaifiyar shi, a duk randa ya gama University a ranar zan damqa mai komai da ya mallaka ta hanyar halal na wajen mu, in mun mutu ba su a gado, dan na sanar da Lauya na da duk wanda ya kamat, infact malam Liman ma yasan da hakan" cikin kuka da farinciki Nasreen ta fara magana" Abban Naufal nice zan maka godiya, soyayyar ka ta tsamo ni daga fadawa halaka, ta sa na gane karuwanci ba abin yi bane abin kyama ne, sannan soyayyar ka ta sa na fuskanci kome iyayae zasu maka hakuri zai tadda rabo musamman UWA, soyayyar ka ta sa na zama mai yafiya, domin daga randa na koma gida na aje Naufal na fito neman ka naji na yafe ma 'yar uwa ta dukkan abin da ta min da mahaifiyata, naji zan iya dawwama a halayyar su in dai zan gan ka ko sau daya ne, sannan gashi ka zama babban alkairi a rayuwa ta, ka ban farin cikin 'Ya'ya kyawawa, ga ni ka aje ni cikin hutu da jin dadi, ga soyayyar nan ta ka da baka gajiya da nuna man ko a gaban waye, what would i ever ask for? Sai dai nace Alhamdu lilLAAH sannan na qara da astagafurullahi a kulli zanbin ya rahman, ina mai godiya da Allah ya ban kai a matsayin miji ubam yayana, kuma ina taya Naufal godiya Allah ya qara budi mai yawa mai albarka" aje takardun yai ya rungume ta yana shafa bayan ta da sigar lallashi, daga haka salon Naseer mai mantar da Nasreen dukkan wani quncin ta ya fara aiki, sarrafata yake kamar yaro da abin wasan shi, a ranar jin su suke kamar wasu amare, sun sha soyayyar da suka dade ba su gudanar da ita ba, gaba dayan su ji suke bazasu taba iya mantawa da wannan rana ba, domin kuwa ganin ta suke mai matuqar mahimmanci,"Ya Allah ka taimake ni kasa na dasa yan uku anan yau" ya fada yana shafa cikin ta, dukan wasa ta kaiwa hannun shi tace" tab ai ko da sai dai kai ka dau cikin yan biyun ni na riqe dayan😙" dariya sosai Naseer yake ya dagota ya dora kan cikin shi yana kallon yanda da gaske ta turo baki gaba tana wani narkewa( ni ko nace soyayya ruwan zuma😉).

Bayan shakara daya da wata Uku, Hinde na hango Malam din ta ya riqo ta ya sata a motar da Nasreen ce ta mallaka masu saboda zirga2, asibiti zasu da dikkan alamu dan wannan qaton cikin haihuwar gida ba zata yu masu ba. Kuka take tana qarawa" Wayyo Innata ki yafe min ni kam mutuwa zan yau, Baban Hinde ka yafen rashin jin maganar ka da taurin kai da na din ga maka a baya, wayyo bayana marata zata balle, Husby ka taimaka min kar na mutu bam qara neman yafiyar Adda Nasreen da Naufal ba" saiga angon Hinde na matse yar kwalla" ba zaki mutu ba My Lady, zaki rayu ke da ya ko dan zaki haifa mana , kuma duk sun yafe maki, ko kin manta kullum kuka hadu sai kin nemi gafara, kuma sai sun yafe maki? Ki kwantat da hankalin ki ki ta addua, inshaa Allahu kome ki ka riqa a wannan stage Allah zai amsa maki dikkan buqatun ki" kukan ta tsagaita ta hau adduar Allahumma la sahla illa ma ja'al tahu sahla...... har zuwa qarshe daga nan ta kamo Allahu Allahu Allahu rabbee la ushrika bihi shai'an wa hussami'ul aleem, kai adduoi dai taf bakin Hinde dai ga su nan yau, ba kalar wadda bata yi har da ta shiga bandaki sai da ta zayyano, sun isa lfy an kuma karbi haihuwar ta in da ta haifi Namiji, bayan ta haihu ne aka kira mijin ta ya miqa kayan haihuwa kan su Nasreen su iso an gama gyara komai an miqo masu jariri, inda na ga Nasreen dauke da cikin da ba zai wuce wata shida ba, zuwa bakwai, An gama komai aka sallame su zuwa gida Nasreen ce zatai ma Hinde wanka zo ku ga kokawa,ita fa sam ba za a jibge ta da ganye ba, kuma in towel ne sai dai a bata tai da kanta, miqa mata Nasreen tai ba musu ta sa hannu zata dauka, data zunduma wani uban ihu saida mijin ya leqo yana Adda Nasreen lfy dai ko, hannu ta daga alamar leqo ka gani ba ruwana, kuka ya ga Hinde nayi dan shagwaba ta na ganin shi ta qara fasa kuka, " Nashiga uku wai ruwan zafin dole ne? Banaji ance in aka hada wa mutum shayi mai kauri da manyan kaji da wasu kayan dadin sun isa ba? " dariya mijin nata da Nasreen suke sosai Naufal na palo yana jiran ta fito ya tsokane ta dariya shima yake va iyaka, Innar Bally ce tace ma Nasreen ta tafu ta barsu kan ta qarasa ta itama tana fama dana ta jikin, tafiya tai tana dariyar wautar Hinde, " eh tabbas akwai ma wani ganye da yare suke amfani da shi mai suna EFIRI. Ko a ce mai ILERU amma ileru a okene ne suke kiran shi haka, mai jego ana mata miya cike da nama da ganyen da gyada ko egusi taci, yana gyara jiki sosai duk wani qaton tumbi da jini ya maqale duk ficewa yake, da damar su ma basa wankan jego iya ganyen suke ci, amma dole ke a hada maki biyun dan muma al'adar mu ne wankan jego kin qara da al'adar wasun, Hinde jan zance tai tayi ruwa na sanyi sannan aka mata wankan suka fito, ta turo baki gaba kamar a jawo shi, " Aunty Hindatou ai shi ruwan zafi ba wani abu bane dan an sa ya tafasa kamar sau uku an miki wanka da shi, ko so kk su Karime qawar ki ta qauye ta fiki dauriya ne" filon kusa da ita ta dauke ta maka mai " to dan ta fini ta nan wajen ruwan zafi ai ba damuwa tin da dai na fita wayewa na fita kilewa ai shikenan dama kalar ruwan zafin ce ita"ranar kam an sha dariya a gidan Hinde. Bayan kwana bakwai yaro yaci suna Na'eem, sosai suke ji da yaron nan kyakkyawa sai manyan ido, ga Hinde da tsoro daya fara bude su yana zaro harshe irin na neman Nono zata miqawa uban da sauri tana " ce mai dan Allah ba sai ya tsorata ni ba zan bashi aboncin shi, ai na shi ne dama ba na wani ba" sosai mijin ke dariya yace" to in banda abinki My Lady ga ki ga shi sai an aika dan saqo?" .
Yaune Su Hinde da Nasreen suka shirya tafiya qauye ganin gida, sun shirya har da Mum zata ganin gidan surukai, kuma a satin da ya wuce ne suka angwance ita da Malam Liman da kyar bayan Nasreen da Naseer sun sha fama, daga qarshe Naufal ne yaci nasarar shawo kanta ta amince, shiyasa ma Malam Liman ke kiran shi da Wakili. Sun isa qauyen Langyam da yamma lis inda suka tarar da gidan su Hinde qal, kamar ba nan ba, ya sha ginin zamani, mai matuqar kyau, ga wani babban masallaci a kusa da gidan,  shiga sukai gidan me bangare hudu kowanne da daki daya, bandaki, da babban palo, daya Mum da Malam liman aka sauka a ciki dayan kuma Hinde da mijin ta, daya Nasreen da Naseer dan na musamman dama ya gina masu in sun zo da yara nasu ne kawai mai daki biyu, sai wajen su Inna mai hade da babban kitchen da danning, a babban palon gidan aka hadu dika bayan isha'i an ci an sha, an yi gaishe2, Baban Hinde ne riqe da dan gidan Hinde twins na gefe da gefen shi, sai Naufal wajen qafar shi, inda Nasreen da Naseer ke zaune a one seater mai fadin da zata ci mutum biyu, ya na riqe da ita ta dora hannu kan cikin ya zagayo qugun ta da nashi hannun, Hinde da mijin ta na tasu kujerar, sai malam Liman da Mum ana ta aikawa juna kallon love(lols😉) Ita kuma Inna ta shigo dauke da babban Faranti cike da kayan marmari, ta aje a center table, ta koma kusa da mijin ta ta zauna, ta sha ado ba ka ce ita ta haifi Su Nasreen ba, Baban Hinde ne tai gyaran murya, sannan ya fara da" Assalamu alaikum" waalaikumussalam " kowa ya amsa harda masu tsamin baki," Da farko dai ina mai miqa godiya ta ga Allah mai kowa mai komai daya nuna mana wannan rana, mai cike da dinbin tarihi, domin wannan rana ce ta farko da dukkan mu muka taru anan, don sada zumunci, na gode maku a matsayin ku na kasancewa zuria ta gaba daya, kuma ina mai godewa allah daya amsa addua ta, a kullum ganin halin da zuria ta ta shiga a baya, ya sa ba dare ba rana nake adduar Allah ya shiryan ku, to ga shiriya da albarka ta same mu baki daya, ina fatan kowa iyanzu ya fuskanci kuskuren shi, ya kuma dau damarar gyara da neman gafarar Allah, nasihata gare ku iyaye mata da maza, ku so yayan ku, kar ku nuna banbanci, ba yanda za ai ka haifi yaya ka so su duk so daya, dole akwai wanda ka fi so, amma ana son ka batwa zuciyar ka, karka nuna masu, ka ba su tarbiyya iyakar iyawar ka, ku ilmantar da su? Addini da zamani, ku maida su qawaye abokai , domin su sake da ku kuji damuwae su suji taku, ku san qawayen su su waye da abokan su, ku na masu nasiha lokacu zuwa lokaci ku guji munana zato akan su, ku guji zargin su akan wani abun da baku tabbatar va, ku guji tsangwama da aibata su" in taqaice maku masu karatu ranar Baban Hinde har da Malam Liman ya sa hawaye, dimin ya wa'azantar da su ba kadan ba, ya nuna masu rayuwa da yanda take, daga qatshe kowa ya qara neman yafiyar kowa, tambaya Na'eema ta watsowa Mummyn su" Mummy yaushe zaki haihu" kallon jama'ar wajen Nasreen tai ta shafa kant cikin kunya tace nan ba da jimawa ba sweery" to Mum meye sunan Baby in kin haihu?" Hmmmmmm to wannan kuma ki tambayi yayan ku" wajen shi ta nifa da gudu amma kan taje Ni'ima ta riga ta" Yaya yi sauri ka fadan sunan pls" dariya wajen ya dauka " sunan baby in mace ce Hameeda, in na miji ne Abdul Hameed" yeeeehhhhhhh na riga ta ji" aiko zagaye palon suka hau yi tana bata yarda ba ita saita biya ta jin da ta riga ta, dariya kowa yake cike da farinciki da nishadi.

ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN 

INA MIQA GODIYA TA GA DIMBIN MASOYAN WANNAN NOVEL AGAIN NA GODE DA QAUNA DA KUMA KULAWA BAN ZATA BA , BAN TABA ZATON NOVEL DINNAN ZAI MASOYA HAKA BA AMMA GODIYA TA TABBATA GA ALLAH , INA FATAN ABINDA MUKAJI NA DAIDAI MUI AMFANI DA SHI SABANIN HAKA MU GUJE MASA, INA RIQON ALLA DAYA GAFARTA MIN DA KU BAKI DAYA YA KUNA BANI LADA A INDA NAI SAIDAI YA MIN AFUWA A INDA NAI KUSKURE. INA QAUNAR KU DOMIN ALLAH INA FATAN KUMA DIMIN SHI KUKE QAUNATA BA DAN HINDE KO INNAR TA BA😂 

Ga masu tambayar novel tindaga farko kuma pages dan Allah sui hakuri ba zai samu ba wayata na riqewa in ina tura pages wallahi, amma inshaa Allahu zan mai da shi docment nan ba da jimawa ba inshaa Allahu. Tanx for d love, me love u too❤

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *