Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, June 12, 2021

LAILAH-DIZHWAR COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
LAILAH-DIZHWAR COMPLETE HAUSA NOVEL

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*


*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_**(1)*__________ 


Ahankali motar take tafiya kamar ba'a san motsawar ta, motace kirar Rang rover,baka tasha tinted, sai faman kyalli take, haka take tafiya ahankali cikin Layin nasu da yake shimfide,gwanin ban Sha'awa, gidan su ya nufa dake cikin garin *Zamfara State*,Kauran namoda, cikin Yarima Quarters. 

   Katan gidan saurautarsu ya nufa, wanda tsananin girmansa yafi karfin a kirasa da Karamin gida saide Mansion.


Daidai kofar gidan ya tsaya batare da naga wani ko wata ta zo dan bude masa gate din bah, ya bude da kansa, cikin salo irin nasa ya saka hancin motar cikin gidan, wanda tun farkon shigansa, manyan ma'aikatan gidan da yan aiki suke mika masa gaisuwa duk da ba ganinsa suke bah,amma sanin babu me isar sah da kuma irin yanayin driving dinsa. 


Saida yayi tafiya me nisa ya isa ga parking space, saida ya dauki lokaci kafin ya gama parking Dinta. 


Bayan ya gama ya fito, Kafar sace ta fara fitowa sanye da takalmi  flip-flops, kafar nan tasa fara tasa da dogayan yatsu tasha gyara tamkar ta jariri. 

  Haka ya fito sanye da  3quarter, da riga baka me polo neck. 


Hannusa rike da waya kirar iPhoneX.


Dayan hannun kuma mukulin motar sane. 


Batare daya kalli duk wanda suke kawo masa gaisuwar bah ya daga wayarsa wanda take ringing, cikin gidan ya nufa yana takunsa cikin kasaita. 


Kai tsaye part dinsa ya nufa, wanda basaina tsaya ina gayar yanda aka tsara shi bah. 


Kayan jikinsa ya shiga cirewa bayan ya ajje wayar da kuma key din. 


ToiToilet ya shiga danyin wanka kasan cewar safiya ce. 


Ya jima cikin toilet din kafin ya fito yayi shiga cikin manyan kaya, wanda suka masa kyau suka kuma amshi kalar jikinsa.


Bayan ya gama shirinsa ya fito ya nufi Part din iyayansa. 


Koda shigarsa babban falon gidan babu kowa dan haka wata hanya ya nufa be jima yana tafiya bah, ya isa wani falon,  nan ya tarda Kuyangi zaune ko wacce da abunda takeyi. 


Be kula suba ya shige, suna gaidashi,  hannu kawai yake daga musu harya shiga cikin dakin. 


Nan da nan na ciki suka fita, yayin da wata mata wanda a kallah shikarunta sun kai 50,tana xaune taci uwar kwalliya ga lalle hannu da kafa jajir tayi shi,  kalar fatarta ba baka bace kuma ba fara bah amma da ganinta kasan tana jin dade, mikewa tayi zaune da murmushi a fuskarta har ana iya ganin hakorin makkah jah, cikin bakintah.


Zama yayi gefanta tare da fadin

_"Hajiya ina kwana? "_


_"Lafiya qlau *DIZHWAR*,harka fito bade kanon zaka tafi yanzu bah? "_


_"Eh wallahi Hajiya,bana san nayi delay shiyasa, nasan kuma Jafar baya san jira kuma nina dau alkawari"_


_"Hakane amma ko karyawa bakayi bah zaka fita bayan kasan bana san kana zama da yunwa"_


Kasancewar baya san bata mata rai ko jayayya da ita yasa shi fadin, 


_"Akira Asiya ta hada min breakfast ta kawomin dakin nan"_


_"Yawwah!, ko kai fah bara na kira tah"_


_____

 Bayan yan lokuta asiya ta shigo da trey babbah tare da duk abunda tasan  Yayan nata yana bukatah. 


Bayan ta gaida shi ta fara hada masa tana mika masa. 


Duk cikin gidan babu girkin wanda Dizhwar yake ci daga na asiya saina Mamanshi fulani, haka kuma bame shigar masa daki sai su biyu, sabo da Allah yayi masa kyankyami da tsafta, ko kadan baya san talakawa baya san nakasasshe, haka duk kuyangin gidan da masu aikin gidan babu ruwansa dasu. 


Bayan ta gama hada masa ya fara ci, suna hira da Hajiya harya gama, mikewa yayi tare da fadin

 _"Hajiya bara in yima su Mami sallama"_


Ba'a san ranta bah ta amsa da 

_"Saika dawo Allah ya kiyaye hanya"_


Ameen ya fada yana fita daga cikin dakin nata.


Kai tsaye bangaran mahaifiyar tasa ya nufa, koda ya isa kannansa ya tarda zaune tare da ita kan gado suna hira da dariya. 


Ganinsa yasa Asiya da Zakiyyah suka Fito daga dakin suna da da gaidashi. 


Zama yayi gefan gado yana fadin

 _"Wai dan Allah Mami Na gaya miki Ki daina zama da yaran nan, basu da aiki sai hira"_


Kallansa tayi tana fadin

 _"Ni Bana san iyayi, daga zuwanka zaka takura musu, basai anyi hutu bah suke zuwa, kaida yake baka gani ka kyale, bana san takura, babu wanda ya takuraka kaima baka isa ka takura kowa bah"_


Shiru yayi dan abun yana kona masa rai, mikewa yayi yana fadin

 _"Naje kano saina dawo"_


_"A dawo lafiya ta fada"_


Harya fita ganin ranta a bace ya dawo tare da zama kusa da ita yana fadin

_"Mami kiyi hakuri dan Allah, bana san kina fishi dani, kullum Cikin nunamin fishinki kike"_


Murmushi ta danyi kafin tace

 _"Kaima haka Zalika kullum cikin takurawa yarana kake"_


_"Toh na daina wallahi, aimin addua saina dawo"_


_"Allah ya dawo dakai lafiya"_


_"Ameen"_ ya fada yana Murmushin farin ciki. 


Kasan cewar me martaba yaje gaisuwa gidan wani amininsa yasa be je wajan sabah, cikin mota ya shiga ya nufi Airport.


🌸🌸

______


Misalin karfe 5pm, Ta fito daga wani katuwar plaza, hannuta rike da leda, ita da wata kawarta tana gefantah. _"Rauda pls dan rike kin kayan nan ina zuwa"_


Wanda aka kira da Rauda ta amsa tare da fadin

 _"Baki da aiki Kullum sai kinyi mantuwa bana san irin wannan"_


_"Pls kiyi hakuri mana, wayata fa na manta tana chaji"_


Amsar kayan tayi tare da fadin

 _"Allah ya kawo ranar da zaki daina wannan mantuwar taki"_


Murmushinta me kyau tayi tare da mika mata kayan ta koma ciki tana dariya. 


Tana nan tsaye harta karaso tana fadin, 

 _"Wallahi na manta ashe na sakata tana chaji kinga kuma na fito na barta"_


Ita de wanda aka kira da Rauda batayi magana bah ta mika mata kayan nata. 


Duk rigar plaza dince jikinsu Red an rubuta sunan plaza din a bayansu,da kuma wando na jeans ajikinsu, sai karamin hijab, sai suka dora dogayan riguna bakake a sama. 


Rauda da kuma Kawarta Lailah suka tare taxi suka nufi gida. 


_______

Kasancewar ba unguwarsu daya bah, saida aka fara sauke Rauda tukun aka nufi Gida da Lailah. 


Daida unguwarsu dake cikin Zamfara wato *Sabuwar kaura*, Daidai wani gida madaidaici, ana sauketa ta mika masa kudinsa tare da shiga cikin gidan. 


Tsakar gidan ba babbah bace haka kuma daki biyu ne aciki sai bandaki da kuma kitchen. 


Zaune take kan tabarma tana tankade gyari. 


Kasancewar Iyayan nata kuramene, yasa batajin Sallamar da tayi bah sai ganinta tayi. 


Murmushi tayi tare da ajje garin tana nuna mata da hannu alamun sannuda zuwa. 


Zama tayi kan tabarmar kusa da ita, tare da janyo laidar, data shigo da ita, ta dauko mayafi daga ciki tare da mika matah, tana nuna mata da hannuntah, 

 _"Mamana wannan siya miki nayi sabo da baki dashi, acikin albashina yau an bani, kingani"_

 Ta dauko sauran kudin tana nuna mata. 


Dadi taji, sai kuma ta nuna mata, 

_"Kudin haya kuma waye xai biya da kika kashe mana su"_


Hannunta ta kamo tana murmushi, 

 _"Mamana, ina sanku Sosai,duk abunda na samu Nakune, kuma zamu biya kudin haya, lafiya kiyi farin ciki"_

Tana nuna mata da hannunta yanda zata gane. 


Dadi Maman taji,  ta mike tare da dauko mata abinci, Tana ci tana yima maman hira suna Dariya.*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(2)*
__________*ASALI*Mahaifin Dizhwar wato sarkin Zamfara, Maimartaba,

*Alhaji Uthman Abdulsalam Shehu*

Cikin dan garin Zamfarane, yan asalin *Zurmi*


yana da ilimin bako da kuma na arabiya, su biyu iyayansu suka haifa shida yayarsa mace, kasancewar shi kadaine namiji shiyasa aka Bashi saurautar garin duk baya so, dan yafi so yayi rayuwarsa. 


Yakasance yana kaunar yayarsa kuma yana mata biyayyah kamar yanda ya kamata.


Tun lokacin kanfin yayi aure yaso Yayar sa *Bilkisu*, ta haihu dan ya barma yaran nata sauratar inya girma, amma har yayi aure Allah be bata haihuwa bah, ita kuma nan garin kano take Aure. 


Bayan Uthman yayi auran fari ya auri Matar sa wato Hajiya Khadija, wanda suke kiranta da hajiya Babba. 


Itama har suka shekara, Biyar bata haihuwa, ganin haka yasa hajiya Bilkisu jin tsoro ko atunaninta sune basa haihuwa. 


Shiyasa ta takurawa Uthman akan ya kara aure. Nan ya auro wata bafulatana yar kauyan su wato Zurmi, me suna *Sakina*,watan Sakina uku gidan sarki ta samu juna biyu,  murna wajan Hajiya Bilkisu ba'a magana, kasancewarta yarinya karama yasa take Kula da ita sosai,haka ta buro gidanta ta dawo Zamfara dan bawa Sakina kuwalawa ta musamman. 


Hajiya Khadijah kuwa bakin ciki kamar ya kashe tah, bata da aiki Kullum Sai Kuma,duk yanda zatayi dan ganin itama ta samu ciki ta kasa hakan ya sa ta shiga tashin hankali, duk tabi ta rame ta lalace kullum cuta. 


Iko. Na. Allah ashe itama Hajiya Bilkisu tana da ciki jikinta bata sani Bah.


Lokacin da cikin Sakina ya isa haihuwa, haka ta samu gata kamar a cinyeta, haka itama Bilkisu farin ciki ganin tana da juna biyu. 


Nan me martaba ya sanar musu cikin su duk wanda ya riga haihuwa to dansane sarki. 


Haka Kuwa akayi, Sakina ta fara haihuwar danta namiji, gaba daya saida gari ya dauka kowa cikin farin ciki,  sarki kuwa murna da shaagalin da aka sha bashi da adadi,  ranar suna yaro yaci *DIZHWAR (strong)*,


Bayan wata biyu da haihuwar Dizhwar Hajiya Bilkisu ta haihu itama, sai Allah ya bata Namji, ranar suna yaci Suna Jafar. 


_____

Lokacin da yara suka isa yaye, Hajiya khadija ta dauki Dizhwar tare dayin alkawarin ya zama dantah, nan kuwa Sakina ta barmata shi,  haka ya zauna awajanta tun daga yaye, ta nuna masa gata iya gata tamkar ita ta haifeshi,  har Dizhwar ya zamana baya yarda da kowa sai ita ita ce mamansa haka itama Sakina bata tafa fada masa bah duk da ba wajanta yake zuwa bah. 


_____

Bayan Hajiya Sakina ta yaye Dizhwar wanda suke Kira da yarima,da shekara uku tukun ta kuma haihu, amma wannan karan saita haifi mace, ita kuma aka saka mata Aisha, sunan kakarsu kenan ake kiranta da Humaira. 


Cikin ikon Allah bayan Humaira ta girma dan wajan shekararta bakwai, sai lokacin Allah ya bawa  Hajiya Hadiza rabu,  nam kuwa ta shiga murna da kuma farin ciki, haka tayi ta rainan cikin nata,da ciki ya isa haihuwa ta haifo yarta mace, duk da ba haka taso ba amma tayi farun ciki sosai, ranar suna yarinya taci Suna  Zakiyyah. 


Nan ta dauki san duniya ta dorawa Zakiyyah da Dizhwar tamkar yarantah,saide kama data babbantah. 


Tun daga lokacin bata kuma haihuwa bah, haka itama Sakina haka kuma itama sakina. 


Dama hajiya Bilkisu tun daga kan Jafar bata kara haihuwa bah. 


Zakiyyah ta fara dan tasawa, Maimartaba Uthman ya kuma yo amarya, yar gidan Abokinsa, nan kuwa yarinya tazo ta mallake gida, sauran matan saisu kwana biyu basuga me gida ba Amarya ta boyeahi,  sam! Sakina bata nuna damuwa bah, 

 Amma Hajiya babba wato Hadiza saida ta shiga ta fita ta raba kowa da mijin sai ita haka suke ta faman Wani kamar gasa da asiri tsakanin su biyu hajiya babbah da kuma Amarya. 


Ita kuwa Fulani ta koma. Kamar ba matar shi bah haka taci gaba da hakuri cikin gidan, in har zaizo. Wajanta saide a boye kasan cewar yana kaunarta kuma duk. Asirinsu be hanashi Zuwa wajan ta bah. 


Cikin wannan hali ta samu Juna biyu,  mamaKi duk ya kamasu, nan kowacce ta karama tawadarta ruwa, dan basa kunar fulani ganin ta fisu Komai,

  Tunda ta samu ciki Harta haihu,babu ruwansa da ita dan kusan tare suka haihu da Amarya, haka suke Zaune cikin gidan nan, Hajiya bilki ce take kaunarta ta share mata kukanta. 


Da yar ya saka ma yarinyarta suna Asiya, ita kuma yar Amarya taci suna Farida. 


Tun daga lokacin babu wanda ya kuma haihuwa cikin gidan. 


Sarki babu ruwansa da Sakina da kuma.

 Part dinta haka take Zaune, har yarna nan suka girma, koda aka tashi Bikin Humaira ita da Bilkisu suka mata komai Amma Shi babu hannunsa ciki.


Shikuwa Yarima yana kasar waje yana karantunsa, harya gama, ya dawo. 


Har wannan lokacin Hajiya sakina haka nan take zaune gidan sarki Amma babu ruwansa da ita. 


Shima Dizhwar besan Sakina bace babarshi bah saida Jafar ya gaya masa,dan ganin yanda ya tsanetah kuma ya rainata tah,  yayi nadama sosai. Haka ya dawo ya bata hakuri,  amma ko kadan Hajiya babba bataji dadi bah. 


Amarya samira kuwa duk duniya babu wanda take kauna kamar Dizhwar shikuwa ko wajan ta baya zuwa balle ta gansa, amma kullum Bata da aiki sai Lekensa da kuma. 

 Kalan  sah hotunan

Sameera babu ruwanta da Hajiya babbah hasalima. Babu wajan wanda take zuwa, sukuwa yaran sun hade kansu yan matan,Zakiya ce yayarsu kuma tana san Fulani, amma Farida ko part din Kowa bata zuwa kullum Tana wajan su. 


Allah yayi mata girman kai raini da kuma rashin kunya irin na mahaifiyarta, ga san yawo. Kullum cikin gantali yau tana can kasar gobe tana can, sai tara kwayan banza, ita kuma. Babarta kullum cikin fegen dan mijinta take, bata da buri daya huce ta kasance tare da Dizhwar, haka zalika ta kudiri Niyar duk wanda Dizhwar yake tare da ita saita kashe tah, shiyasa ta kaisa wajan boka babu wata mace da take burgesa a duniya gashi yana da farin jini amma. Babu wanda ta masa shi kansa yana mamankin hakan. 


Sukuma. Matan suna ganin kamar girman kansa da kuma. Ji da mulkinsa yasa yake. Musu hulakanci. 


Babu sunan daya tsana a. Kirasa kamar yarima dan baya san sarautar shima gani yake Kauyan cine da kuma bata lokaci. 


Shiya basa shiri da Abbansa, shi ko. Kadan ma. Baya san zaman garin, dade shine yake takurawa saiya gansa a gida. 


Babu wanda Dizhwar yake kauna sama da Jafar dan gidan Hajiya Bilkisu, yana kaunarsa yaro. Me hankali nutsuwa da kuma ilimi yana sansa. 


Haka. Shima me. Martaba yana kaunar Jafar, din, dande alkawarin daya dauka na dyk wanda aka haifa shine sarki amma da Jafar zai sa, yasan yayarsa bazata taba yarda bah. 


Ita kuma Hajiya babbah so take a hada jafar aure da Zakiyyah. 


Yayin da shikuma Jafar baya san ta ko kadan dan bata burgeshi. 


Wannan shine cikakken labarin Dizhwar.


🌸🌸


________

*LAILAH*Asalin iyayan lailah yan garin Zamfarane itama suna zaune acan wani kauye wajan hanyar fita daga garin.


Mahifinta muktar, shi kadai iyayansa suka haifa, ya kasance yana da lalurura ta rashin ji, amma in akayi magana da karfi yana ji, lokacin da ya taba fadawa rijiya yana yaro tun daga lokacin jinsa ya dauke gaba daya, kasancewar kauyene sosai basu dauki wani mataki bah yana ji yana gani ya rasa ji ko kadan. 


Haka yake rayuwarsa yayin da jama ke. Masa dariya suna kuma hulakantashi da masu zaginsa dan baya ji. 


Ganin haka yasa yabi wani abokinsa Rabi'u almajiranta cikin Gusau, 


Allah da ikonsa suna kara,suna yar Sana'a har Allah ya buda masa, yana, suna aiki,Suna samu har Rabi'u yayi aure, kasancewar Muktar yana da san yara shima yana san yin auran amma yasan babu me auransa haka, shiyasa ya hakura.


Suna nam zaune cikin gusau,suka samu wani aiki cin nan zamfara sai suka dawo na da zama, haka suke ta aikinsu har matar Rabi'u ta samu ciki, bayan ta haihune suka zo ganin gida da ita, nan kuwa Muktar ya hadu da Maimuna kurma, ita kuma tun da aka haifeta bata ji dama, gashi babu inda zaka kushe tah, kyakkyawar bafulatana, amma babu ji. 


Nan kuwa soyayyah ta kullu. 


Kasancewar itama wajan kishiryar babarta take babu uwa ba uba nan ta aurar da ita, haka. Nan babu wani abun arziki, haka tabiyo Muktar babu wani gata ya tafi da ita. 


Shikuwa yana san matar sah, haka. Suka zauna a wani daki daya a gidan Rabi'u, amma bata jin dadin zaman gidan sabo da ta koma me bauta ita takeyi komai a gidan gashi ta takura mata. 


Tana so ta gayawa mijinta amma in yana nan bata nuna mata wani takura, shiyasa yake kara girmama Tah. 


Suna nan har ogan Muktar ya bashi gida sabo da yana jin dadin aiki dashi rukan amana da kuma aiki tukuru,  ganin haka yasa Matar Rabi'u shiga damuwa dan za'a dauke mata yar aikin tata data maida tah. 


ita kuwa Maimunatu farin cikine ya cikata duk da ba fada zatayi bah. 


Bayan sun tashi, suka sake shimfida wata sabuwar rayuwa da soyayyarsu, dama tana da ciki sanda suka koma, basu jima da komawa bah ta haifi danta namiji, suka saka masa Aminu. 


suna kula dashi sosai gashi shiba kurma bane, suna ta murna amma basa jin yan gwarancinsa da yake saide suyi ta kallansa, gashi in yana kuka baji suke bah, haka suke zaman saide in yana kusa da ita, nan ya fara girma har yakan iya nuna hannu in iyayansu suna magana. 


Shekarar sa uku ta kuma haifar namiji, suka saka masa Ahmad,yamafi Aminu kyau sosai, shima lafiya qlau ba kurma, Bane,haka yana aiki yana samun kudi dan bashi da buri daya huce yaransa suyi karatu,dan yana sha'awar ganin mutun me,Ilimi,


bayan sun dan tasa sun shiga makaranta ta kuma haihu aka saka masa,Aliyu,shine yaso yaya su amma yana ji duk da haka, tun daga lokacin basu kuma haihuwa bah, nan suka tsaya dan nunawa yaransu kulawa sosai, babu ahunda suka rasa gata iya gata suna samu, dan Muktar makarantar kudi duk ya saka su arabi da buko.


kullum shine zai kaisu makaranta ya dauko su, gaba dayansu sun iya maganar kurame, amma abun yana damun aminu,  nan ya sanar da iyayena nasa akan Babansu ya daia kaisu makaranta yara suna tsokanarsu ama ce musu yaran kurame. 

Abun be musu dadi bah, haka suka daina kaisu saide shiyaja kannna sah. 


Muktar yana ta fadi tashi har yaran suka tasa suna karatu, bayan Aminu ya shiga Secondary, matsa ta fara kunnowa Muktar dan ya ragr samun kudi ba kamar da bah, amma haka ya. ki. nunawa kowa, aiki babu dare babu rana dan wani. zubin baya kwana a gida, gashi gidan da aka basu ba. kyauta bah, haka yaci gaba da aiki yana biya musu kudin makaranta, har Aminu ya gama secondary lokacin kargin Muktar ya fara raguwa sosai dan yana da ciwan siga. 


Duk da haka baya gajiyawa wajan aikin dan ya rufawa yaransa da kuma. Matarsa asiri dan yana ganin in suka zama wasu nan gaba sune zasuyi farin ciki. 


Nan abokin Aminu yayi masa hanya yake zuwa kasuwa kuma yana karatunsa, amma shi zuciyarsa ba irin ta maifinsa bace bashi da ra'ayin yin alheri,  ko. Iyayan basu da kufi ko babu abinci baya bada kudi saide in sun samu yaci, wani. Lokacin azumi suke dan abincin ya karu subawa yaran nasu suci. Cikin ikon Allah Muktar baya gajiyawa da abunda yake, saiga wata haihuwar Allah ya basu ya mace, ga kuma halin da suke ciki,  haka suka amsheta hanu bibiyu dama suna san yar budurwa, nan aka saka mata Lailah. 


ita kam. bata zo. lokacin jin dadi bah, shiyasa gatanna kamar yar tsana, tana da kyau dan tafi kowa kyau da haske daga yayyanta har iyayyantah. 


Nan itama ta kuma karuwa, kumai ya karu gashi,kudin makarnatr tah da kuma kaya da abinci,  ganin nauyin yayi mai yawa yasa ya Samu Aminu ya rokeshi dan ya taimaka ya dauki nauyin karatun Lailah tunda yarinya ce, kuma Yana da halin yin hakan, amma ya nuna bazai iya bah in aka takurashi zai bar gida.  


Nan suka hakura aka rabu dashi, nan suka camzawa sauran makaranta dan bazasu iya bah. Akwana atashi ba huya wajan Allah, kullum kaga muktar jiya iyau duk ya rame duk da karamin jiki garesa. 


Gaba daya yaransa sun gama karatu dan Lailah kanta ta kusan gama Secondary school tana Ss2 lokacin. 


Gana dayansu sun samu aiki,  danshi Yanzu Aminu babban Lawyer ne vikin garin Zamfara, dama ga yanda halinsa yake daya auri mata irinsa saita kara canza masa ra'ayi, baya san yan uwansa haka gidansu su baya zuwa har yaransa da kuma matarsa data tsani Iyayansa. 


Haka shima Ahmad soja ne ahikuma dama ba'a gida yake zama bah yana kaduna, saiya jima bezo bah inba uban bane ya neme su, sai suzo gidan matarsa su jima amma bazai zo gida bah, dan yaranshi biyu bama susan kakan subah dan ba'a zuwa dasu.


Aliyu shine beyi aure bah, amma baya Katsina yana Sakoto yana kara karatu, koda ya tashi zuwa gida, gidan Aminu yake zuwa baya sauka a gida, gaba faya sunyiwa iyayan nasu butulci. 


gaba daya gidan ya watse babu kowa sai Lailiha da iyayantah, ita kuwa duk duniya babu wanda take so sama dasu bata da buri daya huce tayi karatu ba saka iayyanta cikin farinciki ta jiya musu dadi. Bayan sun shiga Ss3 an fara batun exam, babu kudi gashi yayanta babu wanda bata da numbersa amma bata rokonsu babu ruwanta dasu sabo da basa kaunar ta ita da iyayansu. 


Kudin exam da Aka tara mata, baban ya kwanta cuta ta dauko tayi amfani dasu ba'a sanin su bah. 

bayan ya dagi ya wararke,yake ta faman murna atunainsa yaransa ne suka biya komai dan ina zasu samu kudi haka. 


nan Maimunatu ta sanar masa abunda Lailah tayi,kuka ya kama yana mata fada, 


Lailah in tana gida kurma take komawa dan bata magana saide tayi yanda suke saide in ta fita waje wajan kawanta. 


Nan ta nuna masa batasan komai bata san karatun ma, ita su take so, bata so ta rasasu, in ya mutu ina zata waye zai riketa ita da mamanta. 


Ba karamin tausayi ta basu ba shiyasa suke kaunarta kullum shiku mata Addu'ar samun ci gaba. 


Nan Baban ya shirya da kansa in ka gansa kamar almajiri kayansa, ya nufi wajan Aminu danya taimaia. mata ta zana jarabawar kar a rufe registration din. 


kwanna sa uku yana jera zuwa amma baya samun ganinsa, gashi duk nisan wajan haka ya ke zuwa a kasa dan ashi da kudin motah. 


Koda ya sameshi rana ta hudu zai tafi meeting Abuja. 


yana ganinsa cikin bacin rai ya karasa wajan wasa yana nuna masa, Mai yasa yazo!?,bazai sa yazo ba shi baya san ganinsa a kofar gidan sah, in yana bukatar abu ya kirashi yaje, nan ya nuna masa macin ransa, haka ya juya zai tafi, ya dauko dari biyar ya bashi ya hau mota, haka ya amsa ya nufo gidan a kafa duk ya gaji ga ciwon kafa, ya nunawa Maimunatu ya gaya mata abunda sukayi musu, kuka tasa tana mamaki irin halin yaransu ace sun haifesu da cikin su amma suke wulakantasu haka. 


Duk abunda ake lailah tana lafe tana jinsu dan haka,ta amshi dari biyar din nan ta ajje ta awajantah. 


Nan ta nufi makota gidan wani Alhaji me kudi, yaa da mata daya da kuma yara uku, Yaseer shine babba sai kuma kan nan sa mata guda biyu, Yasmin da yusra. 


Kasancewar me gidan dan bokone, shiyasa suke da karya da kuma iyaye, sun tsani Lailah musamman da sukaji Yaseer din yana santa, har mahaifiyar tasu bata santa, nan ta shiga ta rikesu dan ta dinga musu aiki zasu ara mata kudin jarabawar in tayi aiki zata biya su. 


amma Mommyn taki yarda dan haka, ta hakura har zata tafi sai kuma ta kirata tace zata ara mata amma bazata musu aiki ba, zata biyata kudin tah da zarar sun gama jarabawar tasu. 


Nan ta yarda tana murna da farinciki,  ta ara matan. 


Ita bata san Yaseer din amma yana kaunarta har zuwa yake duk sanda yake gari daye ba anna yake karatu bah yayi. musu alkairi, ya kuma kawo Mata tsaraba, shine yama sai mata waya itama da er ta amsa saida taga ran Maman ta ya bace. 


Nan ta ara ta biya, cikin ikon Allah sukayi jabarawa suka gama dan,bata da hanyar ci gaba da ajje result din tah, nan ta samu wani me katin unguwarsu yayi mata hanyar fara aiki a wani babban Plaza dake garin Zamfara, gkasancewar sunga tana da hankali da kuma tsafta, gata kyakkyawa suka dauke tah, duk wata 10k ake Biyan ta. 


Da wannan kudi take alfari sune komai. Nata, allah ya taimketa, ahakan take hiya bukar ta dasu,  nan da nan ta biya Mommy kudin ta harda na ruwa ta dora mata, itade ta biya tah, yan huka gidan da suke ciki take san ta siya, tana ta biya ahankali, saura 45k ta gama biya ya zama mallakinsu. 


Duk wannan abu da ake ciki babu ruwan su Aminu haslima sun manta da wani maganar Iyayansu da yar uwarsu. 

ita kuwa intintinta ta samu kudi ta yima iyayanta, sannan ta da kudirin hukanta yayanta kamar yanda suka mata, saita nyna musu basu da hankali, har yanzu tana rike da wannan dari biyar din, tana jiran ranar da Allah zai hada ta da Aminu saita hukantatshi da kudin nan, dan ita har duniya ta nade yai alkawarin bazata taba jusantar inda suke bama. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *​🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR* 🤴🏻🌼​

 *🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*

         *​​ZAINAB NASEER SARKI​​*

             *​_ (ZEENASEER😘)_​*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*VaWattpad@Zeenaseer01​​**​(3)​*
__________
*​​CIGABANA LABARI​​*


Bayan an kai Dizhwar airport jirgin kano ya nufo, dan inyazo kwana zasuyi sannan su koma Zamfara.


Cikin lokaci marar yawa suka iso kano, koda ya sauka a Aminu Kano international airport, tym din da jirgin su Jafar zai iso bashi da yawa,  zama yayi cikin daya gada cikin kujerun airport din yana jiransa yayin daya ciro wayarsa yana dubawa. 


Agogan hannusa ya duba tare da mikewa tsaye yayi wata hanya. 


Daida wani waje ya tsaya yana kallan agogan hannunsa, daga kan da zaiyi ya hango Jafar din ya nufosa yana murmushi. 


Dadi yaji tare da karasawa wajansa sukayi masabaha, kafin su rungume juna. 


_​"Mutumin gida fa ya amsheka wallahi kafi kyau yanzu"​_ 

 Jafar ya fada. 


Tsaki Dizhwar yayi tare da nufar hanyar fita daga wajan yana fadin

 ​"Ina wani dadi kullum. Mutun yana cikin takura, ni wallahi komawa zanyi kawai bana san bacin ran Abba ne"​


Shide Jafar babu abunda yace, haka suka karasa har inda motar take, kasan cewar Jafar bashi da girman kai kamar Dizhwar, nan yayi ta gaisawa da mutanan da suka zo tarbar su har mota uku,  sanin Dizhwar baya yarda wani driver ya tukasa aka bar musu mota daya da Key ciki,  shiga yayi, yayin da Jafar ya zauna gefan sah, ya jasu,shiru babu meyin magana cikin su. 


Gidan Hajiya Bilkisu suka nufa dake, GRA, koda isar su aka bude musu gate din suka shiga. 


Bayan Dizhwar yayi parking cikin gidan ya nufa,batare daya kula kowa bah,  dakinsa ya shiga yayi wanka ya canza kaya tukun ya fito ya nufi part din Umma, (hjy bilkisu) kenan. 


Tana xaune a falo, ganin Dizhwar yasa ta mike tsaye tana murmushi, ta taryoshi ya zauna kusa da ita tana fadin

  _​"Munyi waya da Sakina take cemin tun dazo ka taho, hala saida ka jira dan uwan naka kuka taho tare kenan?"​_


_​"Umma ai dama shi nazo tarba, shiyasa ban nufo nan kai tsaye bah, mun sameku lafiya?"_


_​"Lafiya qlau wlh, ina shi sarkin nawar yake kuzo kuyi lunch nasan kuna jin yiwa"​_


Dan kwantar da kansa yayi jikin kujerar ya lumshe ido tare da fadin

  _​"Wallahi kamar kin sani kuwa, dan nayi missing girkin ki, shi me Martaba baya yima mutane uzuri wallahi bani san zaman Kasar nan"​_


_​"Haba Dizhwar, kaida ake fatan ka zamu shigoba nan gaba kace aa, wallahi ka rage wanann rigimar taka gwarama ka saba da kasarka mahaifarka, bana san fitina"​_


Batare daya ce mata kala bah, yaci gana da danna wayarsa yana kara hade fuska. 


Yana nan zaune har Jafar ya fito, bayan sun gama gaisawa da mahaifiyar tasa abincin tayi musu serving da kanta, zama sukayi suna ci suna dan taba hira amma banda Dizhwar da yake ci yana danna waya. 


Ranar de babu inda suka je, dan anan suka kwana sai washe gari tukun Zasu huce Zamfara. ________

Lailah kuwa, yau tunda ta tashi da zazzabi ko aiki bata samu ta fita bah sai Rauda ta kira ta sanar ma. 


Tana kwance har yamma tayi babu inda taje, da er ta fito danyin wanka, tana tsaye a tsakar gida sanye da zani da hijab ajikinta, tana yima Mamanta magana, da hannu kamar yanda ta saba. 


Da Sallama Yaseer ya shigo cikin gidan. 


Amsa sallamar tayi batare data juya bah dan tabbas tasan shine shiyasa bata san ko gidansu ya dinga shigowa. 


Mama ce ta shiga mai magana da hannu tana dariya. 


har kasa ya durkusa ya gaida tah. 


itakam Laila wani haushine ya kamata. 


 Yaseer farine saurayi kyakkyawa ga san jama'a, fara'a da kuma kyauta, yana da tausayi musamman ga marar gata. 


Nan yasa aka kawo musu kayan abinci da kuma makulashe masu yawa. 


Nan mama ta shimfida mai tabarma ya zauna, shima kuwa harya iya maganar kuraman, yana ta tambayarta ya suke, ina kuma Baban yake. 

 Itade Takaicine ya isheta ta shige bandaki danyin wankanta, har kuka tayi dan bakin ciki, ita bata sanshi gashi yan uwansa da iyayansa basa sansu ita kuwa mezai sa ta hada zuri'a dasu, duk dan sabo da iyayanta kuramene. 


ta jima kafin ta fito, koda ta fito fuskar nan a hade ta shige daki,  shikuwa kansa yana kasa, yana san Laila ko makaranta ya tafi kullum cikin tunaninta yake yana san taimaka mata amma bata sanshi, hakan yasa take masa kurjina yake kuma tsoranta ma. Ta jima kusan awa saya tana saka kaya, kafin Maman ta saka ta ta fito. 


Zama tayi kan tabarmar tare da gaida shi. 


Cikin jin dadi da murmushi a fuskar sa ya amsa yana tambayarta ya bayan saduwa,

Shiru tayi masa, yayin da shima ya rasa abunda zaice mata. 


_​"Lailah kamata yayi iya dadewar da mukayi dake mun fahimci juna, na gaya miki ni sanki nake kuma auranki nake san nayi, kuma da kike maganar na mayar daku almajirai ina kawo muku sadaka, wallahi koda ace babu ke, ni zan iya taimakawa su Baba, amma bana san irin wannan fahimtar da kike yimin"​_

 ya fada yana me marairaice wa. Saida aka kusan mintina goma kafin itama tace dashi

 _​"Tun ba yauba na gaya maka, bana san ka dinga hada kaina dakai, ni bazan iya auran kaba sabo da danginka da kuma Yan gidanku basa kaunar talakawa, musamman iyayena da suke nakasassu, bana san sabawa iyayena, in har da gaske kana sona, toh ka daina duk abunda kake mana, kuma kabar shigowa gidan nan, dan hakan yana jamin matsala in kai baka sani bah"​_


Shiryu yayi yana ganin kamar abunda bazai yiyu kenan bah, 

gyara zamansa yayi cikin fuskar tausayi ya kaleta tare da fadin 

 ​  _"tabbas duk abunda kike so nima ashi nake so, kuma insha Allah dukkan abunda kikeso shi zanyi miki, inde hakan zai saki farin ciki na amince na yarda​_

_"Dan Allah nima inason wata alfarma guda daya a wwajanki, ko a sati sau ukune ki taimakamin ki dinga daga wayata, bakisan hali danake cikibah hala Lailah? "_


Shiru tayi dan wani Bakin ciki yake Kara mata. 


Haka yayi ta magana amma tayi banza ta kwale shi,  har ya gaji ya mike yasa takalminsa kamar yayi kuka yayi mata sallama, dan yanda yake ji ko Sallama be yima iyayan nata bah ya fice. 


Tsaki tayi ta shige daki, dan har taji cutar ta huce dan tsabar takaici. 


______

Haka Yaseer ya koma gida jikinsa duk babu dadi dan yanda yake ji ma kamar yayi hauka, ya rasa wani iri so yake yima Laila amma taki fahimta yana ganin kamar harda yarinta nan gaba zata gane hakan, amma bazai iya jurewa ya hakura da ita bah, zaici gaba da yima ta yanda take so har Allah yasa ta fara Sanshi. 


Cikin gida ya nufa, dan babu abunda yake Sha'awa yanzu illah ya gansa ya kwanta ya huta da wannan takaicin, in yayi bacci ko yaji dadi. 


   Dakinsa ya nufa kai tsaye dan ya kwanta din,

Ga mamakinsa yaga Saudat zaune kan kujera a falonsa tana jiransa. 


Kallo daya yayi mata ya nufi bedroom dinsa. 


*Saudat*

{Yar gidan yayan Daddyn suce ake san ayi mata auran zumunci dashi, yayin da shikuma baya kaunarta ko kadan} 


_"Yaya, tun dazu fa nake anan ina jiranka, ina ka tafi?"_

 Ko kallanta beyi bah ya shige dakin sa, tare da saka key,  

 dan yasan halinta, zata iya binsa ciki, dan bata da kunya. 

nan ta kubura baki, ta fita daga dakin kamar zatayi kuka. 


Falon Mummy ta nufa tana kuka, da shigarta ta samesu duk zaune suna kallo,nan suka hau tambayarta ko lafiya. 


_"Mommy ni wallahi nagaji da wannan wulankacin da yaya yake min, kamar ba mijin dazai auri ni bah, wallahi zan kira Baffana in gaya masa kawai a fasa auran"_


Ita kuwa ganin Saudat yar masu kudi, dan Mommy tana ganin inya rasa ta bazai samu wanda takai taba shiyasa  take san ayi ayi,ai auran. 


_"Kwantar da hankalinki, shi ya isa in gaya masa ga baunda nake so yace ba haka bah, barshi a mai uzuri zai iya yiyuwa ko dan ya gaji a hanya"_


Tsaki tayi ta mike ta koma cikin dakinta tana gunguni. 


Kanwar sace Salima tace da Mommy,

_"Wallahi Mommy babu wani gajiya, kinsan me akayi, dazu ladi ta fita tagansa ya shiga gidan su Laila, har abubuwa taga ana shiga dasu cikin gidan, kinga kuwa ai ba maganar gajiya"_


Cikin jin haushi Mommyn tace,

_"Ni nasan babu wani batun gajiya,kawai Yaseer so yake ya bani kunya shiyasa, yake wulakanta wannan yarinyar, kuma wallahi ita zai aura saide in bana numfashi"_


Sannan ta mike tabar dakin. 


______

Yaseer yana ji ana sallar ishsha'i amma kin fitowa yayi, dan kansa ciwoma yake. 


Wayar shice ta shiga Ringing, kamar bazai daga bah, sai kuma ya dauka dan besan me kiran bah. 


Ganin Number an rubuta Jafar, yasashi mekewa zaune tare da karawa akunne,

 _"Hello, Yaseer gani kofar gidan ku, nayi tunanin gwara nazo yau dan Gobe bani da tymne zan huce zurmi, nida Cousin dina muke ka fito pls"_


_"Ohk gani nan, ku shigo ciki mana akwai me gadi saiya bude muku gate din"_


Bayan ya kashe ya fito, tare da nufar wajan harabar motocin gidan. 


Lokacin daya fito,  sun gama gyara Parking din har sunma fito. 


Cike da murmushi a fuskarsa ya karasa yana mika musu hannu. 


Dizhwar de beyi magana bah, illah mika masa hannu da yayi suka gaisa dan baya san zuwa, Jafar ya takurashi. 


Da kansa ya musu Isu cikin falon bakin. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(4)*
__________
Bayan sun zauna, kara gaisawa sukayi, Yaseer ne ya kalli Jafar tare da 

 _"Malam banyi tunanin yau zaku shigo ba ai"_

 cewar Yaseer 


_"Wallahi nima haka, mai martabane, yace mu taho, bama mu dade da zuwa bah, na takura Dizhwar ya rakoni, cos in muka shiga rububi ba lallae na samu tym Nazo wajan ka bah"_

Jafar ya fada. 


_"Gaskiyane, kana hutawa abokina"_


Sun jima suna hira amma, Dizhwar baya furta ko kalla daya, yana ta faman abunda ya saba wato danna waya. 


Har suka gama hirar su, tukun sukayi sallama dan  tafiya. 


_______

Washe gari tunda safe, Mai marta ya hada kan Jafar da Dizhwar suka tafi kauyansu dayake duk karshan wata yakan je, duba garin nasu. 


Haka Dizhwar ya bisu badan yana so bah. 


________

Laila yau tunda safe aka shirya dan tafiya wajan aiki, bayan ta gama abunda Zatayi, fitowarta kenan,ta gamu da Ladi me aikin gidan su Yaseer.


Kallan ta tayi sama da kasa kafin tace 

_"Lafiya ladi, me kike anan wajan yanzu"_


_"Hajiya ce take kiran ki? "_


Kamar zata bita sai kuma tace

 _"Dan Allah ladi, kice mata kawai na tafi aiki,  dan wallahi in aka makara kora ake kuma wannan aikin na rasashi akwai matsala, ina dawo saina zo, yanzu haka ma Na fara lattin"_


Batare da Ladi tace komai bah, ta mufi hanyar gida, haka itama  Laila ta nufi titi dan hawa mota. 


______

Koda ladi ta koma, duk suna falo zaune, tace da Mommy, 


_"Hajiya naje gidan na tarar da ita, zata tafi aiki, amma tace dani kiyi hakuri inta dawo zata zo, yanzu sauri take_"


Shiru Mommy tayi yayin da Salima tayi carap!, tace, lallai ma wannan yarinyar bata da hankali,  harkice kina nemanta ta nuna miki aikinta yafi kiranki, wallahi saikin koya mata hankali.


Saudat ce tace da Mommy,

  _"wai wacece wannan da har take gaya muku irin wannan maganar? "_


Budar bakin Salima sai cewa tayi,

_"Hmm, ai nasan wallahi in kikaji ko wacece sai kin je har gida kin mata warning,  wata banza ce yar gidan kurame anan unguwar, wai yaya Yaseer  ya rasa da wanda zaiyi soyayyah sai ita har wani wulakanci take masa"_


Shiru Saudat tayi batayi magana bah ita kadai tasan abunda zatayi mata. 


______

Dizhwar kin kwana sukayi shida Jafar a Zurmi dan haka suka biyo Maimartaba suka dawo gida. 


Lokacin da suka dawo yamma tayi sosai, gashi suna jin yinwa, balle Dizhwar mesan coffee, gashi babu wanda ya iya hada masa sai Asiya kuma bata nan. 


_"Jafar wai nan garin kuwa babu wani gurin da zaka ce ka samu abinda zakaci kamar snacks haka da Coffee"_


_"Ahh!  Akwai mana meka maida mana garin namu ne, akwai *Madina plaza*, wajan yana da kyau sosai, ga ma bangaran Restaurant dinsu, sun iya abinci da kuma coffee, wajan babbane harda mall dinsa"_


Mikewa yayi tare da daukar key dinsa, 

_"Taso mana muje mu samu abunda zamuci ni bana cin girkin kowa gidan nan sai Asiya kuma bata nan, gashi bana san saka Mami aiki"_


Haka ya mike suka tafi tare, babu nisa sosai tskaninsu da wajan. 


Kai tsaye bakery dinsu suka nufa, koda zuwansu yayi parking, shiga sukayi suka zauna, basu jima bah, Rauda ta karaso wajan tare da fadin, 

 _"Barkanku da zuwa, me kuke bukata a kawo muku?"_


Jafar ne ya kalle tah, fuskarshi dauke da murmushi yace da ita,

_"Coffee muke bukata, 2cups da kuma chocolate cake"_


Nan take ta huce dan hado Musu,


_"Laila, ke kinga wasu hadaddu yau da suka zo siyan abinmu, wallahi kamar Yarima Dizhwar  din nan da ake fada"_


Laila dake zaune tana danna waya tace da ita, 

_"Dan Allah kiyi sauri ki gama, 9pm,takusa cika mu tafi"_


_"Toh in baki ki Kaimusu?,nikuma sai in kaima sauran mutanan da suke jira, dan Allah kinga har yanzu wanda zasu amshi Aikin ina tashi Basu Zo Bah."_


Ba san ranta bah ta amsa ta nufi wajan su, Ahankali ta karasa, ta shiga ajje musu duk Su biyu babu me Kallan ta, haka itama bata damu dasu bah,  bayan ta ajje cake din ta koma dan dauko Coffee din,  koda ta kusan kara sowa wajansa kamar an tunkuta ta fadi, gaba daya coffee din duk zafin sa ya zube masa a fuskar sah. 

da sauri ya mike tsaye har yana sakin wayar hannunsa ta fadi kasa, 


Wani irin kara ta saki dan taji zafin faduwar sosai. 


nan ya mike yana yarfe hannu, ko taba fuskar yaki yi,  Jafar ne yayi maza ya yi wajansa yana mai Sannu. 


Da sauri ta mike, tana rike kugu tace dashi, 

_"Dan Allah malam kayi hakuri wallahi ba'a sanina bane"_


Har sunyi hanyar fita, sai kuma ya juyo tare da karasowa wajan ta yana fadin, 

 _"Ko wasu irin mahaukatane, bakwa ganewa ne, bazaki iya tafiya a hankali bah, idiot kawai"_


duk da maganganun sun mata ciwo batayi Magana bah, sai. Hawaye da yake zubar mata. 


manyan ma aikata wajan ne suka kaita basu hakuri. 


wani daya daga cikin masu aikinne ya fara fadin

 _"ke meya kawoki nan, keda ba'a nan kike aiki bah, meyasa baku da tunanine, "_


itade Laila kasa magana tayi sabo da yanda take ji, Rauda kuwa kasa magana tayi dan gani take laifin tane. Haka ya fita daga wajan yana faman bala'i fuska na masa zafi. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(5)*
__________Tund suka fita daga wajan beyi magana bah har suka shiga mota.


Duk da zabin da yake ji, haka yayi driving din, sanin halinsa yasa Jafar be kuma yimai magana bah, har suka isa gidan. 


Koda yayi parking fita yayi batare daya cire key din bah, ya shige cikin gida. 


Toilet ya huce kai tsaye tare da tsayawa jikin mirro din wajan sink yana kallan fuskar tashi da tayi jajir, tsaki yayi tare da dauko ruwa me dumi ya wanke fuskar sabo da kamshin Coco da take. 


Wanka yayi tukun ya fito, riga da wando na bacci ya saka. 


Koda ya kwanta, kasa mantawa yayi da abun,  zaune ya mike yana tuna abunda ya faru, 

 Hanu yasa ya kuma shafa fuskar tasa yana faman bacin rai.


Haka ya koma ya kwanta badan yana jin bacci bah. _______

Ita kuwa Lailah ganin abunda ya faru hankalinta yayi mugun tashi, gashi manager sai faman fada yake musu kamar zai doke su, haka jikin su san yaye suka dawo gida. 


Koda ta shigo gidansu, an kawo wuta, dadi ta danji cikin ranta. 


Da Sallama ta shiga dan tariga ta saba duk da baji iyayan suke bah,


Ga mamakinta Saudat ta gani da kuma Salima tsaye kamar suna jiran awani abu dan jaraba da karfe 9pm. 


Ganinsu yasa duk da ranta babu dadi tayi Murmushin dole tare da fadin, 

 _"Sannunku, ya kuka tsaya ku shiga ciki mana"_


Salima batayi magana bah Saudat ce ta matso gaf da ita tare da kallanta sama da kasa, wani takaicine ya kamata ganin kamannin Lailah, dan ba haka tayi tunanin zata same ta bah. 


_"ke har kina tunanin, akwai abunda zaisa mu shigo wannan matsiyacin gidan inba warning  bah"_


Ganin babu kowa tsakar gidan yasa taji dadi dan da alama, Mama tayi bacci, dan Babansu sai 10pm yake shigowa gida. 


_"Dan Allah in wani abun nayi muku kuyi hakuri, amma ba kuzo har gida kuna neman fada bah"_


Wani bakin cikine ya kama Saudat, ta duro wata uwar ashariya tare da fadin. 

  _"Hahhhhh lallai baki da hankali,  atunanin ki nan gidane, kina rayuwa da dutsunan har kike tunanin ke bil adama ce, wallahi yarin kasheri nazo nayi miki, duk sanda na kuma ganin ki da Yaseer sai nasa an kulle ki,dan ruwa ba sa'an kwando bane"_


Mamakine yaso kama Lailah kamar tayi dariya, sai kuma ta ce da ita, 

 _"Wallahi har kin bani tsoro, nina zata wani abunne ma ya faru har kike faman fada haka, maganar yaseer shiya gani yana so, duk da yasan akwai wata a gida, dan haka ina ganin bani ya kamata kizo kima Warning bah, dade ana so  din shine, sabo da haka Umma ta gaida Aysha"_


Tana kaiwa nan ta shige daki ta barsu tsaye a tsakar gidan. 


Wani abune ya tsayawa  Saudat a huyanta, bakin ciki kamar ta rusa kuka haka take ji, dan ta tsani Lailah a rayuwarta. 


Batare data kula Salima bah tasa kafa ta fice daga gidan itama tana binta abaya. Ita kuwa, Laila bayan ta shiga daki, tsaki tayi tare da fadin, 

 _"in banda hauka ma irin naku, kowa ya gaya musu ina san wani Yaseer"_

 Tsaki tayi, taci gaba da abunda take. 


________

Yau tunda Safe Mai martaba ya tara gaba daya yan gidan kwansu da kwarkwata, harda Anty Humaira. 


Bayan an bude addu'a da taro, mai martaba ya fara bayani kamar haka. 


_"Na tarakune badan komai bah, sai dan in sanar muku da lokaci yana ja, kuma kullum muna dada tsufa kwanaki na raguwa,sabo da haka ina gaf dayin murabus, daga kan kujerata dumin bama wanda ya kamata"_


Gaba daya kowa yayi shiru yana jinsa, yayin da Anty Amarya idanta yana kan Dizhwar daya maida hankalinsa ga abunda mai martaba yake fada. 


_"Kasancewar gaba dayanku, kuna karkashina, kuma na isa na yanke hukunci a duk abunda naga dama, haka zalika, dukkan dukar dana kafa dole abita. 


Shiru duk sukayi babu wanda yayi magana, har Hajiya Bilki dake zaune kasancewar tazo dumin kiran da yayi mata. 


_"In baku mantaba, nayi wani alkawari tun kafin Yaran nan suzo duniya, wato Jafar da kuma Dizhwar, sabo da haka yanzu lokaci yazo dazan ciki wannan alkawarin dana dauka"_


Gaban Dizhwar ne yayi mugun faduwa, dan ko kadan baya kaunar abunda zai fito daga bakin Maimartaba. 


_"Kai Dizhwar, da Kai Jafar, da kuma Fareeda haka zalika har Zakiyya, nariga na gama magana, wata mai zuwa duk zan aurar daku"_


Gaba daya duk wanda aka anbato Sunan saida ya dago ya kalle shi. 


_"J afar, zan hada ka da Fareeda, kai kuma Dizhwar yar gidan *Abdulganiyu Governor*,mun yi magana da Mahaifinta, ke Kuma Zakiyya, zaki Auri Dan gidan *Alhaji Uthman Waziri*,"_


Gaba dayansu babu wanda yayi farin ciki da abunda Sarki ya fada. 


Dizhwar batare da ya furta komai bah, yayi shiru babu abunda zuciyar keyi sai bugawa da karfi. 


Fareeda kuwa, kuka ta kama tana fadin

_"Gaskiya Nide bana san wanann auran, aiba dole bane haka ake dan Allah Abba a canza magana wallahi bana sanshi"_


Kowa mamaki yake abunda take fada. 


Anty Amarya kuwa bata kowa take bah, itama hankalinta ba karamin tashi yayi ba jin Dizhwar zaiyi aure.   


Shiru babu wanda ya bata amsa, yayin da shima Jafar wani haushi ya kamasa, dan ko xa'a kashe shi bazai taba auran Fareeda bah, yarinyar data gama watsewa, shi baya santa, Kuma har abada dade ya aureta gwara ya mutu beyi aure bah. 


Tashi tayi tana kuka ta fita daga falon, yayin da babarta ta mike ta bita itama ranta a bace. Hajiya babba kallan me Martaba tayi tare da fadin , 


_"Gaskiya gaskiya wanann tsarin beyi ba, ba zai yiyuba wallahi, ai yanzu an waye ba'a auran dole, kabar yarinya ta zabiwanda take so gaskiya"_


Itama ta mike ta ja, Yarta suka fita daga cikin dakin, 


Kowa mikewa yayi yabar Falon, babu wanda aka bari sai Fulani. 


Itama tashi tayi zata tafi, ya kira sunan ta. 

Ahankali ta karaso wajansa tare da durkusa. _"Kema baki da abunda zaki fada ne?"_

  Cewarsa. 


Murmushi tayi tare da fadin,

 _"Babu saide ince Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lkcn lfy "_


Tana kaiwa na ta fice, dan ita ta manta raban data gansa.Asiya kuwa, tana Barin wajan taran daki ta nufa ta fashe da kuka, dan ita a duniya babu wanda take kauna kamar yaya Jafar, dan tana jin an bashi Farida taji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. 


Dizhwar kuwa mota yahau yabar gidan ko yaji dadi cikin ransa. _______

Kasancewar duk ranar litinan sai wajan 2pm, Laila take zuwa wajan aiki yasa bataje yau da huri ba, dan haka ta shirya dan kai Baba asibiti, haka yasa ta tafi har Mamanta. 


Bayan sunje sun dawo suna tafiya kafin su fito titi su samu mota,ita dasu sai faman Tafiya suke, 


Laila tace dasu

 _"bara ta shiyo kati tana zuwa, karsu je ko ina"_


Nan suka tsaya suna jiranta. 


Nan ta gangara ta tsaya wajan masu katin zata shiya, tana nan tsaye ana daukomata ,ta shiga sakawa. Dizhwar kuwa yana ta faman gudu a motar bunda be saba bah kenan,yafi yin hakan in ransa ya bace, daidai wajan da Kuraman suke, yaci wani wawan birki dan saura kadan yayi ciki dasu. 


Wani uban tsaki ya buga dan ganin ko ajikinsu, suna tsaye suna kalle kalle. 


Hakanne ya kona masa rai ya fito yana faman huci,  da sauri ya karaso wajan su tare da dauke Baba da mari,  nan ya kifa kasa ,

Shi kuma yana tsaye yana faman huci. 


Da sauri Mama ta karasa wajansa ta daga shi tsaye daga faduwar da yayi. 


_"Ko wasu irin dambobine, baku da hankaline, kuna ganin kun tsaya akan hanya, wallahi dana kadeku na kade banza babu abunda aka isa ayimin, banzaye matsiyata. 


Duk da basu san abunda yake fada bah, amma yanayin da suke kallan bakinsa da kuma yanda yake masifa sun san fada yake yi. 


Tun sanda ya kwadawa Baban mari ya fadi kasa, Laila tana tsaye tana kallo, bakin ciki da kuma mamaki lokaci daya suka hadar mata, nan da nan kwallah ta cika mata ido, sakin jikar hannuta tayi tana binsa da kallo, tabbas ta gane sa, kuma wallahi be daki banza bah. 


Da sauri kamar an koro ta ta karaso wajan tare da wanka masa mari har sau biyu, tana hawaye ta nunasa da yatsa tare da fadin, 

 _"Kaima mahaukacin inane kokuma wasu jakanne suka haifeka, baka da iyayene ko bakasan darajar subane, yanayinka da kuma yanayin rashin tar biyarka ya tarbatarmin da ba mamaki a tasha ka haife kah,wallahi duk fadin duniyar nan banga wanda zai hukanramin iyayena ba in rabu dashi ko uban waye kuwa, kuma wallahi wallahi sai Allah ya saka masu marin daka masa, ko kai baka yiam mutane uzurine, sudin kasan wata larura garesune, dahar zaka fito kana wani tinkawo kai gaka mai mota, uwar motar taka"_


Ta dauki wani katan dutse ta bugawa glass din gaba ya tarwatse,nan iyayan suka dauke mata jakar tata suka janyeta suka tafi. 


Shikuwa Dizhwar kasa tattacewa yayi a wata duniyar yake, shine kuwa kode wanine, anya kuwa ba mafarki bane, in kuwa mafarkine addu'a yake Allah ya dauki ransa kafin mafarkinsa ya zama gaske. 


Ga mamakinsa yaga hawaye yana zuba, wani bakin cikine ya kamasa ji yake kamar zuciyarsa zata tsaga kirjinsa ta fita tsabar bugawa. 


Batare daya taba motar tashi ba, haka ya dinga tafiya tamkar mahaukaci, har gida ya isa duk inda ya nufa binsa ake da kallo. 


Koda ya karasa gida, nan ma Mutane mamaki ya kamasu suka shiga binsa da ido. 


Jafar ne daya hangosa yayi saurin karaso wajansa yana duba jikinsa. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(6)*
__________
_"Lafiya, menene ya faru na ganka haka, abunda bansan ka da haka bah?"_

 Jafar ya fada yana kallan sah, 


Maimakon yamai magana koya basa amsa, sai ya huceshi kamar ma besan abunda yake fada bah.

Mamakine ya kama, Jafar, haka yayi tsaye yana kallan sah, har ya shige ciki. 


Dizhwar kai tsaye dakinsa ya nufa, be tsaya ko ina ba sai cikin toilet, shower kawai ya kunna ya tsaya cikin Jacuzzi, yana jin saukar ruwan a kansa. 


Yakai Awa daya ciki,shi kansa besan me yake bah. 


Haka ya fito a jike ya zauna kasa kan tiles wajan stairs din da zai sadashi da Dining area. 


Haka iska taita kada shi, har saida kayan jikinsa da sumar kansa ta bushe tamkar be shiga ruwa bah. 


Yana nan zaune, Jafar ya kuma turo dakin da Sallama, mamakine ya kuma kamashi ganin sa zaune ya dora hannunsa saman gwiwar kafarsa yana tunani. 


Karasowa yayi wajan yana kallansa, baki ya bude tare da fadin

_"Dizhwar kuka fa kake"_


Abunda ya kuma kona masa rai kenan yayi kukan kura tare da daukar kujera ya jefi glass din kofar kitchen dinsuhi, saida ta fashe, ya durkusa tare da kurma ihu, idanunan sunyi jajir, cikin wani irin karajin magana yake fadin

 _"Wallahi saina kasheta, saina nuna mata karfin mulkina, saina nuna mata asalin koni waye gaba daya danginta sai sun gane kuransu, saisun gwammace ba'a haifi ahalinsu cikin Zamfara bah, saina kashe duk wani me alaka da ita, saina rabata da farin ciki na har abada"_

  Jafar ganin abun yaki karewa, kuma ya tabbata mace ce tamai wani babban laifin, da sauri yayi ta maza ya kamashi ya zaunar yana kwantan masa sa hankali, dan baya san abun yayi nisa, haka yayi ta lallashin zuciyarsa yana controlling dinsa. 


Haka yayita masa har yaji ya daina wannan nishin da yake tukun, yana san jin menene ya faru amma baya san cukalo ciwan. 


Ganin ya samu saukin bacin ran yasa shi tashi ya fita daga dakin. 


Yana san yayi bacci ko yaji dadi amma ya kasa, yana rufe idansa zaiga saukar marin data masa. 


Mikewa yayi ya shiga toilet yayo alwala ya fita masallaci danyin sallar magriba. 


__________

Lailah kuwa haka iyayanta suka jata, tana ta faman kuka har suka je gida, 

  Ko bayan sun koma gida, kasa wani katabus tayi, babu abunda take tunawa duk bayan seconds sai saukar marin data gani fuskar Babanta. 


Wani bakin cikine ya kuma kamata, nan ta kuma fashewa da kuka. 


Koda dare yayi, kasa bacci tayi, ko kadan bata danasani ko tunanin abunda zai biyo baya akan abunda tayi masa,bata da burin daya huce su kara haduwa domin ta kuma masa sarar data fi wanda tayi masa yanzu, yanda ta dauki iyayanta babu abunda bazata iyabah inhar mutun ya shiga gonar su, ta tsara musu rayuwa batare da wani takura bah ta yanda babu ruwansu da kowa, hakan yasa ko yan uwanta baxata saurarawa ba in har suka taba mata iyayanta. ________

Washe gari haka Dizhwar ya tashi badan yayi bacci ba, wanka yayi ya shiga gaida iyayansa. 


Duk wanda yagansa yasan ya canza, koda an tambaya saiya ce bashi da lafiya. 


Yana zaune a garden din gidan, koya samu saukin bacin ran daya ke ji. 


Yaji karan tafiya, amma kin dagowa yayi dumin baya bukatar kowa shiyasa ya kuma wajan da babu wani.


Ahankali ta karaso wajan, sanye da goduwar riga ja, kasan cewar fatar jikinta farace tas!, sai kayan suka dauki jikin ta. 


Kujerar da take kallansa ta zauna, batare datayi mai magana bah, ta zaro wayarta tana dannawa tana cin chewgam .


_"Sannu Yarima"_


Hakan data fada yasa ya dogo da kansa tare da kallanta. 


Wani sanyi taji cikin ranta, tare da kara gyara zaman ta tana murmushi. 


_"In bazaka damuba inasan yin magana dakai"_


be kalletaba haka kuma be bata amsa bah, saida ta kara, maimaitah tambayar tata. 


Kamar bazaiyi magana bah ya kura mata ido har saida ta fara tsarguwa, kafin ya shafa sajansa, tukun yace da ita, 

 _"Ina jinki"_


Saita tsinki kanta da dabarbarcewa yanda ya tsareta da ido saitama rasa abunda zata ce dashi. 


_"Am dama in bazaka damuba, ina san inyi tafiyane, gashi inasan kaman rakiya"_


Still kallanta yake ko ido baya daukewa a kanta. 


Cikin zuciyarsa kuwa cewa yaye, 

 _"Lallai matar nan ta raina min hankali, kenan nine dan rakiyar tatah"_


Batare daya bata amsar taba, ya mike tare da barin wajan. 


bin bayansa tayi da kallo, rungume hannunta tayi a kirjinta tana murna, dan ko kadan kome Dizhwar yayi bata jin haushi dan gani take koma me yayi ya isane.

 Anty Amarya kenna, tana kaunar Dizhwar itade. Shikuwa Dizhwar batasan akwai abunda yake damunsa bah, bashi da burin daya huce su hadu da Yarinyar nan badan komai ba saidan daukar fansa. 


________

Laila yau bata da Niyar zuwa aiki ko kadan, har kusan 10am, tana kwance kan gado taki tashi ta karya ma, kanta ta daga sama tana kallan Ceiling dakin nasu,da duk yayi jirwayan ruwa da hujewa da beraye suka masa, wani takaicine ya kuma kamata, tsaki tayi tare da juyawa tana kallan kasa kuma. 


Wayar tace ta shiga kara, tana ji amma harta katse vata dauka bah.


Saida aka kara kiran nata tukun ta mika hannunta ta dauka ta kara akunne, tare da mikewa zaune, gashin kanta ya zuba bayanta da kuma gaba ya rufe mata fuska hannu tasa tayi gefe dashi tare da fadin, 

 _"Hello! "_


Daga dayan bangaran kuwa, Rauda ce take fadin, 

 _"Hello Lailah, yau bikizo aiki ba, inata nemanki kwangila ta samu, bayan abun duk zamu samu 10k, amma na saka sunaninki ciki, abunne yazo da gaggawa, kisan yar gidan sarkin nan Gimbiya Fareeda?"_


_"eh"_

 Lailah ta fada harda, gyada kanta. 


_"Itace take cika, shekara 22,yau shine zatayi celebrating birthday dinta, kuma Mune masu decorating da ordering na Abinci, Madina plaza ta gaiyata, shine aka ce za'a dauki mutun 20,cikin mu,yanzu haka mun ciki, bayan abunda Za'a biyamu, tace inde komai yayi zata bamu kudi masu yawa, manager yace kowa 10k za'a bashi,yanzu haka duk mun zo, ke kadai ake jira, karfe 12,zamu isa can din mune masu serving food"_


Batare da tayi murna ko wani murmushi ba bisa bayanin Rauda dan abunda yake damunta, 


_"Toh ganinan"_

 Shine abunda ta fada kenan ta kashe wayar ta mike. 


Gadan ta gyara sharp Sharp, ta gama ta yi wanka, batare data karya ba kota tsaya yima Mama bayani ta tafi. 


Lokacin data karasa suna kokarin shiga mota su tafi tayi saurin sauka, ta karasa ta shiga, kusa da Rauda ta zauna tana Maida numfashi. 


Kallanta, Rauda tayi tare da fadin, 

 _"Lailah ya naga kamar baki da lafiya"_


Lumshe ido tayi, dan yau ko makeup babu, farar Powder kawai ta shafa, sai pink lipstick, tasa riga da wandonta, da after-dree,data dora, tayi rolling mayafinta akanta dayasha gyara, ga abu gashinta da tayi acuci dashi. 


_"Sunnu, dana sani da bansa sunanin kibah"_


Murmushi ta danyi, ta dora kanta kan kafadar Rauda tana fadin, 

 _"Ba komai Rauda na gode, zan iya ahakan ma"_


Tun daga nan babu wanda ya kara magana, har suka iso gidan sarautar, kai tsaye Bangaran da aka tanada domin aikinsu aka nufa dasu. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(7)*
__________


Koda suka isa already duk ankai musu abunda zasu bakata, dan har wasu sun fara girkin.

Kana ganin yanayin Laila kasan tana cikin damuwa, aiki kawai takeyi babu wani walwala cikin fuskar tah. 


Sosai gurin da aka masa decorations din sun iya sosai, dan yasha kayan ado tamkar a india, ga flowers kala kala anyi ado da shi, kofar shiga wajan gaba daya anyi musu ado da purple na flowers. 


Duk abunda ya kamata suyi sun riga da sunyi kafin magriba. 


Ganin yamma tayi sosai, bayan sun idar da sallah, ta kalli Rauda dake gefanta tace da ita, 

 _"Wai har zuwa nawa zamubar nan wajan, ka idar aikinmu 9pm Muke tashi,in na huce hakan akwai matsala dan ban sanar dasu mama bah, gashi kuma maybe mu huce tym din"_


_"Gaskiya kema Laila aida kin gaya musu dole hankalinsu zai tashi tunda bakya huce hakan"_

 Rauda ta fada tana gyara mayafinta. 


Shiru Laila tayi dan bata da abunda zata ce. 


_______

Fareeda kuwa tana can tana ta faman shiri ita da kawayanta, anata faman kwalliya cikin daki. 


Anty Amaryace ta shigo dakin da yan matan suke, 

 _"Wow masha Allah yarannan kunyi kyau wallahi, dole duk wanda ya ganku ku tafi da hankalin sah, yarinyata so nake yau Wannan Faisal din in yazo ya kasa tafiya"_

  Anty Amarya ta fada tana faman iyayi, 


Gaba daya yan matan daki suka hau shewa da dariya dan suna san matar sabo da yar shafta ce ga bata jin kunya. 


Kamar yanda yarta taci uwr kwallahiya haka itama tayi kwalliya kamar ba ita ta haifeta bah. 


Sanin halin Fareeda na girman kai tasan babu wanda ta gaiyata acikin gidan ita kuwa, tana san Dizhwar yazo wjan wannan Party, dan haka da kanta ta mike ta nufi part dinsa. 


________

Zaune suke cikin falon, kowanne cikin kana nan kaya suna kallon ball, 

Suna hira. 


Tura dakin tayi ta shiga batare da tayi sallama bah. 


Jin turo kofar yasa suka kalli wajan dukkan su. 


Ganin me shigowa yasa Dizhwar dauke kai yaci gaba da kallan da yake yi. 


Karasowa tayi cikin takunta na daukar hankali ta zauna kan kujera tare da dora kafa daya kan daya. 


Shiru na tsawan lokaci babu wanda yayima wani magana. 


_"Dizhwar wajan ka nazo"_


Jin haka yasa Jafar tashi ya fita daga falon yana murmushi. 


Shiru Dizhwar be bata amsa bah,ganin bashi da alamar mata magana ta fara magana kamar haka. 


_"Kasan yaune ake birthday party na Fareeda, so nasan bata gaya muku ba, kasan cewar abubuwa sunyi mata yawa shine nazo da kaina domin na yi inviting dinka, pls ko 5mins ne kayi a wajan bayan ta yanka cake saika tafi"_


Ba kallanta yake bah, hankalinsa yana wajan Tv, hakan yasa tayi tunanin ko beji bah, 


Cigaba tayi da kallansah, tana ji kamar taje ta rungumeshi dan wani Magnet da yake fuzgarta, san Dizhwar yana kara shiga cikin zuciyar ta. 


Lumshe ido yayi ya bude ya sauke a kanta. 


Wani iri taji a jikinta ta runtse ido tana wani farin ciki cikin ranta. 


_"Bani da lokaci, zan bada gift a kawo mata"_


Ya mike yana shirin barin wajan, da sauri ta mike tare da rike hannunsa, ahankali ta karaso gabansa ta yanda suna iya shakar numfashin juna, tsayawa yayi yana shirin jin menene tagged dinta na gaba. 


_"pls Dizhwar kaine fa special Guest dinmu, ur d first person to received ur gift, karka min haka pls kazo dan Allah"_

  Yanda take masa saika dauka wata budurwar sace. 

Hakan da ta fada yasa, be kula taba ya shige ya barta anan. 


Ido ta rufe tare da fadin

 _"Ya Allah kasa yazo"_


______

Kwance kan sofa ya tarda Jafar zama yayi kusa da kafarsa tare da sa hannunsa biyu ya shafa sumar kansa. 


_"amma wannan matar bata da hankali wallahi"_


Mikewa Jafar yayi xaune tare da fadin, 

_"pls kabar fadin irin haka mana, matar mahaifinkace tamkar uwa take a wajan ka, pls karka bada mutane mana, kayi mata abunda take so"_


Kallansa yayi tare da yin tsaki, 


Dariya Jafar yayi yana fadin, 

 _"Abun kuma kaina zai dawo"_


Tashi yayi ya nufi bedroom dinsa yana fadin, 

 _"ka shirya sai muje, in kuma bazaka ba nima ba inda zani"_


Yasan halin Dizhwar in yace bazai je bah, shima haka zaice, kuma gashi tazo da kanta ta roka hakan yasa ya tashi shima dan yaje ya shirya. 


________

Karfe 8pm daidai, lokacin motoci kala kala suka fara shigowa cikin gidan, haka aka dinga  shiga kowa yana nuna gate pass dinsa, mata da maza kamar wajan saida motoci haka wajan ya koma, wajan parking daban aka ware musu. 


Haka wajan ya koma kamar rana tsabar fitilon da aka zuba, kowa ka gani wajan ya kure adakarsa babu wanda zaka ce be burgekaba ko kayansa busuyi kyau bah, yaran manyane wajan, daga gari gari haka suka zo harda wanda ba'a kasar suke bah, haka ga yan jarida da masu daukar hoto, ga masu video covering ,kai abun sai wanda ya gani ba karamin kyau wajan yayi ba. 

  

______

Gaba daya hankalin Laila yayi gida, dan ji take kamar ta matso da tym din ayi ayi a gama ko zataji dadi. 


Ga girman gidan da kuma wajan da aka kawo su, dan ji take ko za'a kasheta bata san ta hanyar da zata bi ta fita daga wajan ba.


Suna nan zaune kowa yana jiran yaji an fara kiransu, amma sai karfe 9pm daidai tukun aka bukace su. 


Nan suka shiga wajan dan za'a fara aikin, riga aka basu duk suka canza. 


Nan suka fara aikin serving jama'a, wasu suna cin abinci wasu suna rawa, kowa da abunda yakeyi,  ita kuwa Lailah kallan ikon Allah take ta faman yi, ga uba cake wanda ko yan wajan zasuci su koshi bazasu cinye shi bah, abun sai ya koma mata sabo, kamar yar kauye, cikin zuciyarta kuwa fadi take, 

 _"ikon Allah, kudi suna idan suke, Allah ka azurtamu"_


Komai yana tafiyar musu daidai kamar yanda suma can basu da wata matsala. 


Fareeda ce ita da wata kawarta, suke faman yawo a wajan, tasha wata farar riga kamar wedding gown, fara tas ga uban gashin doki data sha tamkar nata, tayi Makeup sai faman iyayi ake,inka ganta sai kace tayi shekara 30,amma yarinya ce karama. 


Waya ta kuma kira, da alama saurayinta take jira yazo wajan.


Can, sai gashi shima ya shigo cikin wajan, yasha Suit ash color, ga escort a bayansa kusan su biyar. 


Nan Mc ya fara koda shi, waje yahau tafi,  kasan cewar kowa yasan shi. 


Babban dan gidan Minister na kudi na Nigeria, kana ganinsa katan gardi tamkar Arne, farine dogon namiji me kira irin wanda ake kira da Giant, 


Babu annuri a fuskarsa, sai faman shan kunu yake, haka ya karaso ya nemi waje ya zauna, tana ganin yazo tayo wajansa tana murmushi. 

  Nan kawayanta sukayo wajansa aka hau musu hotuna. 


Daidai lokacin Dizhwar da Jafar suka shigo wajan, cikin shiga ta alfarma, nan yan mata sukayi wajansa shima, dan suna so suyi hoto dashi, watama sabo dashi tazo wajan. 


Cikin takunsa na kasaita, suka nemi waje suka zauna shida Jafar. 


Kowa wajan tana ji da mulki da kudi da kuma matsayi, babu wani namiji da zakaga ya mike yaje wajan wani sun gaisa. 


Haka anata abu, Anty Amarya taja Mc gefe, kome ta gaya masa, nima ban sani ba sai ganinsa nayi ya fito yana fadin. 


_"All our Friends, sisters and brothers, ur most welcome to ur dearest Sister's special day,once Again, So friends u have to put ur hands together for our Special guest,our King *Yarima Dizhwar*"_


Gaba daya waje yahau tafi, shikuwa Faisal da yayi kokarin mikewa komawa yayi ya zauna sabo da haushin da yaji, dan gaba daya ya zata shine, haka itama Fareeda mikewa tsayi tayi tana kallan jama'a dan haushin da take ji, kuma tasan babu wanda yayi wannan abun sai Babarta. 


Da sauri ta mike ta nufi wajan da uwar tata take. 


_"Haba Mum wannan wani irin abune, yanzu kinzo kin batamin shirina, menene na wani sa a kira Ya Dizhwar bayan kinsan ni ko inviting dinsan banyi bah, wannan ai cin mutuncine ki bari in birthday dinki ya tashi saiki nemoshi"_


Tana fadar haka tayi tsaki tabar wajan. 


Koda ta koma wajan, babu kowa Faisal da mutanan sa sun tafi,  wayar ta ta dauko da sauri ta shiga kiransa amma taji switch off , kamar tayi kuka,ta fita wajan da gudu amma bataga  kowa ba,  tsaki tayi ta koma dan ba huce haushinta kan su Dizhwar. 


Lokacin shi kuwa an kirayeshi dan bata gift din daya kawo mata,Anty Amarya sai faman farin ciki take. 


Tana tafiya kamar zata harde har sauri take ta karasa wajan,  fuskarta babu murmushi, tana kara sawa ta tsaya gaban sa, ya dauko gift din ya mika mata, kowa yana dauka. 


Amsatayi tare da cilla masa kayansa jikinsa.


_"Wanene ya baka ikon zuwa wajan nan, da har kake kokarin bani wani matsiyacin gift dinka"_


Abun ya bawa Dizhwar mamaki, be kalli kowa ba sai Jafar dake gefe, da sauri ya taso, yana kokarin jan Dizhwar daga wajan. 


Fareeda kuwa dagewa tayi ta dauke Jafar da mari tana fadin

 _"munafiki ai kaine kake zugashi"_


Bata gama Magana bah,Anty Amarya ta bata mari masu kyau har guda biyu, nan fa waje ya hargitse da fada. 

Su Laila suna gefe suna ganin ikon Allah. 


Nan Jafar ya fara janye Dizhwar daga cikin wajan da yake shirin ballah Fareeda. 


Yana jansa, har suka fita daga cikin Taron, tsaki yayi ya juya zai fita daga wajan, da sauri ya kuma, juyowa ganin Laila tsaye tana kallo.


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(8)*
__________


Da sauri ya nufi wajan yana, binta da kallo. 


Kafin yazo har sun fita waje, nan yaci gaba da binta har ya hangota a wajan.


Har ya kusan karasawa wajanta sai kuma ya fasa, 

  Ganin suna kokarin shiga mota, yasa yabi motar da kallo, da sauri har gudu yake ya nufi part dinsu, yana sauri ya shiga mota, ya fita waje ya tsaya yana jiran yaga fitowar motar tasu. 


Ya jima a waje tukun yaga an fito dasu, nan yabi motar duk inda tayi,  karfe 10:30pm motar tayi parking daidai Madina plaza, 

  Nan suka shiga fitowa, kasan cewar wajan da haske hakan yasa be rasa gane tabah.


Yana nesa dasu kadan cikin motar yana binta da kallo har suka yi sallama da kowa, suka nufi taxi ita da Rauda kamar yanda suka saba. 


Nan yayi ta bin Taxi din har aka sauke Rauda, har kofar gidan su Lailah saida Dizhwar yagani, sunayin parking, ya ga ta fito ta bashi kudin ta shiga gidan. 


Dariya yayi me karfi tare da shafa gemu, shi kadai yasan dalilinta. 


Nan yayi baya ya koma gida cike da murna da farin ciki cikin zuciyarsa. 


_______

Laila kuwa duk abunda ya faru babu wanda ta gane sai Dizhwar, mamakine ya kamata, kenan dama dan gidan sarkine shidin,  ganin hakan yasa tayi mugun tsorata jikinta yayi sanyi, yanda taje haka ta dawo babu wata walwala. 


Koda ta shigo gidan su Mama suna zaune ita da Abbansu akan tabarma kowa yayi gum!, suna jiran shigowar yar lelansu. 


Gani ta shigo yasa duk suka Mike suna haskata. 


Nan ta kalkalo dariya tayi, kama hannunsu ta zauna tana basu labari da kuma basu hakuri da bata sanar bah. 


Dadi sukaji nan kuma ka hau hira da dariya, amma cikin ranta kunshe yake da damuwa dan abunda idanta ya gane mata. 


Saida ta tabbata ta saka Su farin ciki tukun ta shiga daki,  zama tayi bakin gado tare da rufe idanta ta saka hannunta kan kirjinta tana jin yanda zuciyarta ke bugawa. 


Koda Maman ta shigo ta ganta haka da fata tayi, 

Da sauri ta bude idan ta wayance  tare da dora hannunta kan kirjin uwar tata tana jin yanda tata zuciyar take bugawa ba kamar tata bah.


Hannu ta nuna alamun menene yake faruwa? 


Itama girgiza mata kai tayi alamun babu komai.


Sai sannan taji dadi, ta fita daga dakin. 


Komawa tayi kan gadon ta kwanta tayi reran tare da sauke wani gwauran numfashi, ta rufe ido,a Haka bacci yayi awon gaba da ita. 


Batayi aune ba taji sallar asbah, da sauri ta tashi ta kunna fitilar, ta canza kaya ta fita danyin alwala. 


Banyan ta idar da sallah, ta koma ta kwanta, hijab din ta cire, kayan Baccine jikinta riga da wando masu laushi wanda suka sha jiki, ta daure gashinta a baya da ribbon sauran kuma ya zoba har kasan bayanta. 


Tunda ta koma baccin bata farka bah. 


_______

Koda gari ya waye sosai gari yayi haske dan 10am ta kusa, ganin Su Laila sun jima wajan aiki kuma har lokacin bata tashi ba yasa Mama bata tayar da ita bah. 


Tana cikin kitchen bayan ta gama hada koko ta zuba cikin flash. 


Jiyowar da zatayi taga kwalaye da kuma buhun shinkafa kusan uku, a tsakar gida, tsoro taji ta fito tana kalle kalle. 


Ganin mutane tayi anata shigo da abubuwa anki dainawa, ganin haka yasata shiga daki ta fito da mijin nata. 

Shima kawai bi yake da kallo, saida aka ciki tsakar gidan da abubuwa na daban daban. 


Bayan kamar min10,babu wanda ya kuma shigowa, Dizhwar yayi sallama. 


Ganinsa yasa suka kara hadewa waje daya suna kallansa da mamaki,  shigowa yayi ciki ya tsaya kusa dasu tare da durkusawa, 


_"Dan Allah kuyi hakuri nasan abunda nayi muku ban kyauta bah, wallahi ba laifina bane sharrin shaidan ne"_


Sukama ba jin abunda yake fada suke ba kallansa kawai suke. 


Jin kamar a mafarki ana magana yasa Laila mikewa da sauri ta fito waje. 


Mamakine ya kusan kasheta ganin abunda batayi tunaniba, bin komai take da kallo kafin ta kai idanta ga Dizhwar dake tsugunne gaban su Mamanta. 


Kasa magana tayi sai nunashi da tayi da hannu. 


Shima binta yayi da kallo,dan tinda yake be taba ganin yarinyar data burgeshi kamar ita bah. 


Takowa tayi ta karaso wajan iyayan nata ta tsaya, nan suka hau tabata suna mata magana, hannu ta daga musu alamun su dakata. 


Tsaye Dizhwar ya mike yana kallanta, kafin yace Mata, 

 _"Sannu yan mata, na jima ina neman gidanku domin na baki hakuri keda iyayanki bisa abunda nayi miki, nasan nayi kuskure amma bazan kara maimaita makamancin hakan ba, dan Allah kiyi hakuri suma na basu hakuri amma basu cemin komai bah"_

  Yana magana yana.

 Kallan ta. 


Jin haka yasata ajjiyar zuciya saita tsinci kanta da maida masa magana a hankali, 

 _"am, ba haka bane, iyayena basa ji,suna da matsala jine, kayi hakuri"_


Murmushi,yayi tare da fadin, 

 _"Ba komai kiyi kokarin musu magana yanda zasu gamsu na yi nadama, Sunana, Dizhwar, maybe kin taba jin sunnan ko makamanci haka, Dama abunda ya kawoni kenan, Nagode"_


Kasa magana tayi, harya fita daga cikin gidan. 


Daga ita har iyayan mutuwar tsaye sukayi babu me magana acikinsu. 


Sai bayan fitarsa, suka kama tambayarta, kasa masu bayanima tayi, tana bin abubuwan daya kowo musu tana mamaki.


Ranar batayi niyar zuwa Aiki ba, amma kodan taba Rauda labari saida ta shirya ta tafi. 


Zuciyarta fal da farin ciki da abun mamaki. 


_______

Shikuwa Dizhwar, dariya yayi kamar cikinsa yayi ciwo, sannan yaja motasa yabar kofar gidan, Amma yana mamakin ganin iyayan Laila kurame ita kuma tanaji gata kamar ba yar kasar ba, ga kyau ga gashi komai ta hada, murmushin ya kumayi. 


________

Koda ya dawo gida, kai tsaye part din su yanufa, amma kafin ya karasa yaga kiran Jafar, yana dagawa ya sanar masa yazo babban falo. 


Nan gabansa ya fadi yasan, sai babbar magana ake haduwa acan. 


Da sallama ya shiga kamar yanda yayi tsammanin ganin kowa da kowa zaune da alama shi kadai ake jira. 


Nan ya mika gaisuwarsa ga kowa tukun ya nutsu kamar yanda kowa yayi. 


Shiru babu me magana kafin daga bisani me Marta yace dasu. 


_"Kuna ganin yanzu abunda kukayi kun kyauta, kun nunawa duniya cewa bakwa zaune cikin zaman lafiya, wayema yasa ayi celebrating wannan birthday din acikin gidana, meyasa baku da mutunci, ni zaku tozarta a idan jama'a bayan kunsan babu abunda za'ai be fita vah"_,

 nan yayi ta fada ta inda ya shiga bata nan ya fita, bah. 


BAbu wanda yake magana kowa yayi shiru yana jinsa.


Bayan ya gama wannan ya dira da wani sabo. 


_"Wancan karan na zo muku da magana amma kowa ya gayamin Ra'ayinsa,to wallahi baku isaba, saide duk wanda beji maganata ba yabarmin gidana, kuma maganar aure dana fada babu fashi sai anyita wannan tilas ne, kuma nan da sati biyu za'ai komai dan haka in mutun yana da shirin da zaiyi gwara tun yanzu kuje ku fara na fada kuma bazan canza magana bah"_ 


Hajiya Babbace tace da shi, 

 _"Amma kasan wannan hukunci da ka yanke ba daidai Bane, mumafa muna da hakki akan yaran nan ba bamu dashi bah"_


Be mata magana bah,

 Anty Amarya ce tace, _"tunda ya riga ya yanke ai yakamata kowa yabi abunda ya fada, dan be kamata babba yana magana ana masa jayayyabah"_


_"ke kuma wa yasa dake bakar munafuka, meyasa  wacan karan kika nuna bakya so, har ina magana kina magana sabo da baki da tarbiya"_

 Hajiya Babba ta fada cikin fada. 


_"Na fada din, ke tarbiyar gareki, ai shima sama yake dake kika saka Masa baki, gakinan Katuwar bakar munafuka, wanda babu abunda ta sani sai Akuyanci"_


Nan hajiya babba ta mike tsaye, tana kokarin nufar wajan Ta. 


Da sauri Fulani ta mike tana fadin, 

 _"Haba hajiya kikayi haka girmanki zaki zubar, dan Allah ki rabu da ita"_


_"Dallah can matsa ki bani waje, ke dama an gama dake babu abunda zaki iya shiyasa kike fadar hakan ai"_


_"Ya isa ya isa haka, bana san hauka, kowa ya tashi ya fita yaban waje"_

 Cewar me martaba. 


_"wallahi zakisan dani kike wannan zancan"_

 Hajiya Babba ta fada tana jan Zakiyya suka fita. 


Itama Anty Amarya ranta a bace suka fita daga wajan. 


Babu wanda aka bari cikin falon sai Dizhwar dame martaba. 


_"Dan Allah Baba kadan karamin lokaci nifa bana san wannan yarinyar da kake fada"_


_"Dizhwar na gama magana, kuma bazaka maidani karamin mutun ba, sabo da haka in baka santa inka aureta ka saketa, kuma in bayan auranku, in yaso duk da wanda ka shirya saika kum aurowa ni ban hana ka ba kuma ka sani bayan auranka da wata biyu zanyi murabus sabo da haka ka shirya"_

 Yana kaiwa nan ya fita daga wajan. 


Zama Dizhwar yayi, yama rasa abunda yake masa dadi dan bashi da shirin yin duk abunda Baban nasa ya ambata. 


Kowa kam da bunda ya damesa dan ba shi kadai vane yake da matsa cikin gidan ba. 


______

Lailah tana isa wajan aiki, ta nufi wajan Rauda, nan ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar mata. 


Mamakine ya kama ta, 

 _"Lallai Lailah kin ciri tuta kode karya kike, wannan fa wanda yazo nan kika zuba masa coffee wanda muka gani jiya a gidan partyn nan"_


_"humm! In kina tantama kizo na kaiki kiga abun mamaki, ga abunda ya kawo mana nan, a ajje a gida"_


_"tabdijan, bama saina gani ba wallahi na yarda, amma saide in sanki yake yayi miki haka amma kina ganin wannan da kudinsa da komai har zai tsaya Yana wani baki hakuri"_


Daga kafada tayi tare da fadin, 

 _"waya sani,nide nayi mamaki"_


Shiru Rauda tayi tana jin jina abun acikin ranta. 


_______

Fareeda kuwa, kuka tahau yima Anty Amarya dan ita bazata Auri jafar ba saide tabar gidan yanda sarki ya fada, ita za'a yima dole, ita Faisal take so Kuma sun riga sun gama maganar aure dashi za'a mata wata maganar Jafar. 


Haka tayi ta bata hakuri amma kin hakura tayi, ta hada kayanta ta fita tabar gidan. 


Anty Amarya tsaye bakin window ta tsaya tana kallnta. 


_"hmm!, lallai akwai tashin hankali tunda kuwa, Fareeda tabar gida kowa sai ya kuka da kansa, mu zuba mu gani"_

  Abunda ta fada kenan. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(9)*


*Assalamu Alaikum*


  *Ina neman afuwa a gareku masoyana, abun alfaharina, kwana biyu nayi rashin lafiya ne, shiyasa bakwa ganin posting dina, ina fatan bakuyi fishi dani bah.*

   _~ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke~😍_

_________


Koda Laila ta dawo daga wajan aiki zowa tayi ta zauna tana kallan abunda Dizhwar ya kawo Musu, su Mama sunata murna.


_______


Yaseer kuwa tun ranar daya je wajan Laila ta sanar masa da abunda take so da kuma wanda bata so be kuma zuwa wajan ta ba dan baya san bacin ranta. 


Yau yana kwance cikin dakinsa, yaji Kiran Daddyn sa, wayar ya dauka ya sanar masa yana zuwa. 


Tashi yayi ya fita daga dakin ya hau sama dakin sa. 


Koda yaje Mommy ya gani zaune da Daddyn sai kuma Saudat, ko ba'a fada ba yasan ko maganar menene. 


Zama yayi kan carpet Bayan yayi musu sannu da gida. 


Daddyn ne ya kalle shi tare da fadin,

 _"Yaseer ina maganar da mukayi dakai akan yarinyar nan?"_


Shiru yayi ya kasa ya magana dan bema san abunda zaici masa bah. 


_"Magana fa nake maka kana jina"_


_"Dan Allah Daddy kayi hakuri kadan karamin lokaci"_


_"Bana san wani dogun bayani, zabin da muka maka shine baka so Kenan,yarinyar yar uwar kace, taya zaka ce baka santa?"_


Shiru yayi kafin yace, 

 _"Dad ni ban taba gaya mata bana santa bah"_


_"Toh in baka gaya mata bah, amma ai alamu sun nuna"_


_"Yaseer"_

Daddyn ya kuma kiran sunan sah. 


_"Naam"_


_"Meyasa kake san maidamu kananan yara? "_


Shiru babu amsa, Daddyn yaci gaba da magana. 


_"In har da gaske baka furta kalmar daka furta bah, toh ina so Kafin ka koma ayi auranku da Saudat  kafi da matar ka"_


Wani iri yaji kamar an kwada masa guduma a tsakiyar kansa


Shiru yayi dan bashi da bakin magana. 


_"Magana nake maka kayi shiru"_


_"Dan Allah Dad kadan dada min lokaci, ni akwai wanda nayima alkawarin aurene shiyasa"_


Kallansa suka tsaya sunayi har Saudat din. 


_"Wacece? "_


Tambayar data fito saga bakin Daddyn kenan. 


_"Daddy yar gidan malam Muktar kurma nake So Laila"_


Shiru Daddy yayi, Mommy ce ta fara badin, 


_"Wallahi baka isa ba, wannan yaran fa bashi da hankali, taya zaka auri wannan yarinyar da bata da gata, wallahi bazamu hada zuria da kurame bah, Allah ya kiyayye"_


_"Dakata mariya"_

Daddy ya fada yana kallan Yaseer da kansa yake a kasa. 


_"Yaseer da gaske kana san yarinyar kuma itama  tana sanka?"_


Da sauri ya dago da kansa jin tambayar da Daddyn yayi masa, Murmushi ya danyi,  tare da fadin, 

 _"Sosaima kuwa, Dad, dan Allah kaima karka ce bazan aureta bah"_


_"Shikenan, tashi kaje zanyi magana dakai nan da kwan biyu, zan samu mahaifin yarinyar nayi masa magana,inyaso kaima saika mata,tashi kaje"_


Wani dadine ya cika Zuciyarsa dan yama kasa boye farin cikin sa gaban iyayan nasa. 


Saudat kuwa fashewa tayi da kuka, yayin da Mommy tahau fada, bayan fitar Sa kenan, 


Daddy ya kalli Saudat tare da fadin, 

 _"Ki kwantar da hankalinki, karki samu damuwa kinji, in Allah yayi mijin kine shi zaki aure shi inde darai da lafiya"_


Haka ta mike tana kuka jikinta duk ya mutu, haka zalika, itama Mommy haka ya mike ya barta anan tana ta faman fada da masifa, kan Ya daurewa dansa gindi yana abinda yaga dama. 


_______


Bayan kwan biyu, Lailah ta kasa jurewa, bata da aiki sai tunanin Dizhwar, fatan ta Allah yasa santa yake har yayi mata wannan abu, dan tabbas ta rasa abunda yake damunta bata da aiki sai fegensa, haka yau da taje wajan aiki babu abunda ta tabuka sai tunaninsa, haka aka sauke ta daga taxi ta fito tana Mika masa kudinsa. 


Ganin wata hadaddiyar mota kofar gidansu yasata jin wani irin farin ciki da sauri ta shiga tana murna, ganin Dizhwar zaune kan tabarma yasa tayi turus!  Tana kallansa. 


Shima daga kansa yayi yana kallan nata, sai kuma ta tsinci kanta dajin kunya dan tasan ya gane tana murna da ganinsa. 


Wani arnan Murmushi ya sakar mata, tare da dauke kansa. 


Ahankali ta karaso wajansa, tama Kasa  kai jakar tata cikin daki, zama tayi tare da fadin, 

 _"Sannu da zuwa"_


_"Yawwah"_ 

ya fada yana kallan ta,


_"Na jima anan ina jiranki, haka aikin naki yake sai wannan time din kuke tashi, gaskiya bana san kina kaiwa haka a waje ga wanan hawala da kuke sha, ta zirga zirga"_


murmushi ta saki tana wasa da yan yatsun hannunta kanta a kasa.  


Leka fuskar tata yayi yana murmushi, 

 _"Nifa har yanzu ba'a gayamin sunan abokiyar fadan nawa bah"_


kunya taji harda rufe ido,  cikin sanyin murya ta furta, 

 _"Laila Muktar"_


_"Wow suna me dadi, kinga nan gaba kuma saiki koma, 

 _" *LAILAH-DIZHWAR* "_


Shiru tayi bata ce komai ba, dan tama rasa a wani, Stage take tsabar murna da kuma mamaki, tama kasa yarda dan sarkine cikin gidansu kan tsohuwar tabarma yana hira da ita, unbelievable!. 


_"Lailah kinyi shiru, ko na takura miki ne?"_


_"Aa"_


_"Toh kunya ta kike ji? "_


_"Aa"_


_"Meyasa bakya san yimin magana, nima fa haka nake bana san yin magana, amma sai na tsinci kaina ina miki Surutu haka"_


_"Nasani ai"_

Ta fada tare da kallansa. 


Yana dago kansa suka hada ido tayi maza ta sauke idanta kasa. 


_"me kika sani toh? "_


_"Nasan yayan sarki ko yayan masu kudi basa san yin magana da yawa"_


Murmushi yayi me sauti, sannan yace da ita, 

 _"Hm haka kika fahimta kenan?,_

 _toh Laila ba haka bane, ya danganta da yanayin mutun, kin gane, kema ai bakya san yin maganar tunda gashi ni harma na fiki yin maganar ke kuma yar gidan President ce?"_


Girgiza kai tayi, alamun aa. 


Agogon hannunsa ya duba tare da fadin, 

 _"Dare fa yanayi, karnaje a zaneni a gida bara na tashi na tafi"_

 Ya fada yana mekewa, takalmansa dama suna kafarsa, haka ya fita daga gidan, tana biye dashi a baya har bakin motarsa.


Bayan ya shiga ita kuma tana daga jikin glass din, 


Hasken wayarsa ya haska fuskarta,

murmushi yayi tare da fadin, 

 _"Zan tafi sai kuma in an dan kwana biyu, duk da nasan bazan iya jurewa rashin ganin wannan kyakyawar fuskar taki da kuma wannan muryar me dadi bah, kina da waya?"_


_"Eh"_


Tana fadar haka ya zira hannunsa gefe, ya miko mata wata waya, kirar *'Samsung X6 edge plus'*,amsa tayi tare da fadin,

 _"Wannan fa?"_


_"Ki riketa zan kiraki, bana san kowa ya kiraki ciki saini, kinji Lailah Lollipop"_


Bata iya magana ba, illah gyada masa kai kawai da tayi. 


Nan yayi mata sallama yaja motarsa yabar kofar gidan. 


Daida lokacin, Yaseer yake kokarin shiga gida, ganin Lailah a tsaye ga wani yabar wajanta yasa zuciyasa susa, abun be masa dadi ba hakan yasa itama ta tsaya tana kallansa, ciki yayi da motar yayin da itama ta shige gida ta kulle. 


Da gudu ta shiga daki, ta zauna tana kallan wayar, ko ba'a fada ba tasan wayar nada tsada, dadi taji sosai wayar tayi mata kyau, tana kunna screen din wayar taga pic dinsa, wani sanyi taji cikin ranta tare da shafawa tana murmushi. 


_"Ya Allah"_

 Ta fada dan gaba daya Dizhwar ya kwace mata zuciya, ta gama nisa cikin dunbin soyayyar sah. 


Da baya ta fada kan gadon ta kwanta tare da fadin, 

*_"LAILAH-DIZHWAR!"_*

 Sunan yayi mata dadi, kara dago wayar tayi ta kunna screen din tana kallan fuskarsa, da murmshinsa. 


Ganin bata da aiki sai Wannan,yasa ta mike zaune tare da ajje wayar ta shiga cire kayan jikin ta, wanka taje tayi, time din data dawo taga missed call,  

  Da sauri ta dauka ta zauna gefan gadan tasan shine ma ya kira, sai taji dama bata shiga wankan bah, tsaki tayi tana kokarina ajjewa  taji ya kuma Kira.


Da sauri ta shiga kkarin dagawa, karawa tayi a kunne har tana kokarin subucewa. 


Sallama tayi tare da yin shiru dan jin abunda zai biyo baya. 


_"Sarauniyar kyawawa na duniya gaba daya, ayimin hakuri na kasa jure rashin muryarki shiyasa kika ga na dameki da kira"_


_"Kayi hakuri, wallahi ina wanka ne Shiyasa ban daga bah"_


_"Ohk yayi"_


_"Kaje gida lafiya?"_


_"Lafiya qlau, wallahi na tafi cike da kewanki fa"_


Dadi taji ta yarda har ta kasa tsayiwa saida ta zauna. 


_"Lailah"_

 Ya fadi Sunan tah.


_"Wayyo!"_

 Ta fada cikin ranta dan jin yanda ya kirayi sunan nata kamar yafi kowa Iyawa. 


_"Zaki aureni?"_


Da sauri ta kashe wayar, 


_"Innalillahi wa'inna illaihir raji'un, wayyo wayyo wayyooooh! "_


Da gudu ta fito waje tayi tsalle ta koma daki tana ihu. 


Kasancewar Iyayanta kuramene duk bidiri datake basu sani ba. 


Komawa tayi ta dauki wayar tana dariya da ihu, 

 _"La'ilah! Dizhwar waye zaice baya sanka, wallahi ina sanka Wayyo Allah yasa da gaske yake ina sanshi wallahi"_

 Abunda Lailah ke fada da karfi kenan dan gani take kamar mafarki take. 


Kallan wayar take tayi tana jira Ya kuma Kira. 


Har 12am, amma Be kira ba haka ta kwanta badan tana jin baccin bah.


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(10)*
__________
Shikuwa Yaseer tunda ya shiga gida kasa sukuni yayi, har kara fitowa yayi ya duba wajan ko zai kuma ganinta amma bega kowa bah.


Cikin gida ya koma ya shiga daki, abun yana bashi mamaki, 

 Kenan bayan shi akwai wanda Laila take so shiyasa ta ki amsar soyayyar sah, haka yayita yawo cikin daki yana sake sake kala kala, daran ranar de beyi bacci bah. 


_______

Washe gari, ya kama lahadi, dan haka Lailah bata zuwa aiki duk ranar, 

   tana kwance cikin dakin tana jiran kiran Dizhwar, amma har lokacin be kira ta bah. 


Abbanta taga ya shigo daki ya nuna mata ta saka hijab, sunyi bako, tazo zasuyi magana. 


Mamaki ya kamata, dan ita duk a tunaninta Dizhwar ne, fuskata cike da murmushi da farin ciki, ta saka ta biyo bayan sah, a bunda ya bata mamaki ganin Daddyn Yaseer, 

  Da sauri ta durkusa tare da gaida shi. 


Cikin fara'a da walwala ya amsa mata tare da fadin. 


_"Kasancewar iyayanki kuramene, inaso zan yi magana daku,  bana san ki boye musu abu daya duk abunda na fada miki ki gaya musu"_


Kanta yana kasa ta amince da abunda ya fada mata. 


_"Lailah kina san Yaseer?"_


Shiru tayi tama rasa amsar da zata bashi, dan yanda tayi tunin Daddy zai kasance sai kuma taga ba haka bah, sai kuma ta kama jin kunya karta ce bata san danshi yaji babu dadi tunda harya tako yazo da kansa, amma tabbas tasan zata cuci kanta, haka zata hakura, duk wanda Allah yayi shine mijinta haka zata hakura ta aureshi. 


Cikin jin kunya tace dashi,

_"Eh"_


Kallanta yaci gaba dayi tare da fadin, 

 _"Yanzu ina ce miki, zakuyi aure dashi, kuna da kudin da zakuyi dukkan abunda ake bukata in za'a aurar da yarinya"_


Shiru tayi dan babu abunda ta dogara dashi sai aikin tah, 

 _"Aa Daddy, dama koda auran za'a saka, sai an saka mana da yawa sabo da babu kudi kuma bamu shirya hakan bah"_


Dariya yayi tare da fadin, 

 _"Ai koda an saka muku me yawan bazaku taba samun kudin bah, sabo da tsiya a gindinku take,in banda karfin hali ma, menene ya kaiki har zakiyi soyayya da wanda yake giwa a bangaran kudi, ke kuma ko Kiyashi vaki kai bah, kenan abunda aka fada gaskiyane, kun asirce Yaseer shiyasa kike juyashi yanda kika ga dama?"_

  

Jin haka yasa gaban Laila faduwa tayi maza ta dago tana kallan sah. 


Shikuwa Abba yana gefe yana kallansu, sabo da yanayin yanda Daddyn yake magana kamar ba baka yake fada bah. 


Kwallah ce ta cika idanta, kamar zata fashe da kuka haka take ji. 


_"Wallahi wallahi, inma ku dangin mayune, munfi karfinku, dan bazamu taba hada jini da matsiyata nakasasau irin ku bah, sabo da haka zan baki zabi daya cikin biyu, na farko koku hada kayanku da komai naku, kubar unguwar nan, ku tafi can inda bazaku hadu da Yaseer vah, ko kuma ni insa a dauke ku harsai bayan bikinsa da yarinyar danake so tukun a maidoku, na baku nan da kwana uku"_


Kukane yaci karfin Laila, kasancewar a cikin Hijab take yasa Abba be gani bah, tayi dana sanin abunda ta fada, sai ta tsinci kanta da tsanar kanta. 


Yana gama fadar haka ya mike ya tafi,batare daya yima Abban sallama bah. 


tana fita, ta mike da gudu ta shige toilet ta kulle ta fashe da kuka me karfi. 


Ganin haka yasa Abbanta mikewa da sauri yana buga kofa da karfi, alamun ta bude masa, Mama data fito taga abunda ke faruwa itama ta taya shi, haka sukaita bugawa, tana jin su amma saida tayi kuka me isarta tukun ta bude.


Binta sukayi da kallo suna, tambayarta abunda ya faru, idanta yayi jajir fuskata ta canza kama dukta kumbura. 


Nan suka tsareta saida tayi musu bayanin komai, 


Abban ne ya kama kuka, yana nuna hannayansu da Allah ya taimake su ya barsu dan su zauna ya rufa musu asiri. 


Itama kuka Laila take yi, dan tasan babu inda zasuje inba a titi zasu kwana va, gashi ta kusan siyan wannan gidan gaba daya. 


Dabara ce ta fado mata ta a saida gidan, sai ta biya wancan mutumin cikon kudinsa, sauran kuma saisu kama haya kafin Allah ya hore. 


Amma sai Abba yaki yarda yace lallai saide in su hadu suje su gayawa Aminu matsalar su, inyaso duk abunda ya yanke saisuma susan abinyi. 


Amma Lailah fir taki yarda akan abunda ya fada, haka shima ya kafe dole suka hakura suka shirya domin zuwa wajan nasa. 


_________

Koda suka isa, kasancewar me gadin gidan ya san Abba ya bude masa suna gaisawa, 


Abbane ya yima laila magana kanta tambayi me gadin ko Aminu yana ciki. 


Nan ta tambaya ya sanar musu da baya nan amma yana kan hanyar dawowa. 


Shiyayi musu rakiya har cikin gidan. 


Tunda Lailah take bata taba shiga gidan ko daya daga cikin su ba, nan Su Abba suka shiga kallan gidan suna mamaki wai nan gidan dansune, amma su gasu suna yawo suna neman gidan da zasu zauna, Mama kuka ta fara, amma bata bari kowa ya fahimci hakan ba. 


Nan suka rabe gefe daya, suka zauna, me gadinne ya shiga ya sanar wa da matar sa zuwansu. 


Nan ta sanar masa daya gaya musu su jira anan tukun yazo. 


Nan yazo ya gayawa Laila duk da bata ji dadi ba, ji take kamar ta fita daga cikin gidan. 


Abba da Mama suka zauna kan tiles suna jiransa, yayin da Laila take tsaye dan taki zama. 


Tunda suka tsaya anan kusan awa daya babu wanda yazo wajansu. 


Sai can tukun sai ga wata me aiki ta shigo tace dasu da su shiga ciki.


Wani katan falo aka shiga dasu, suka zauna kan carpet, yayin da basu jima da zama ba, Aminu ya fito ransa a bace dan beji dadin zuwan su bah,


Suna ganinsa suka fara dariya, farinciki amam banda Lailah. 


Zama yayi kan kujera tare da gaida su yanda suka saba da kurmanci. 


Kallan Laila yayi, tare da fadin, 

 _"Ke dake zanyi magana tunda su basa ji ni yanzu bana gane wannan abunda suke yi"_


Kai kawai ta iya gyada masa dan zata iya fashewa da kuka tsabar bakin ciki. 


_"Menene kuka zo gaba dayanku? "_

 Aminu ya tambayi Lailah. 


Kallan Abba tayi, yayin da yayi mata nuni, 

_"da ki gaya masa so muke ya sama mana inda zamu, zauna koya sama. mana gidan haya"_


Nan ta gaya masa. 


_"Gida kuma, ina gidan da kuke zaune, wannan be isheku bah, wani gida kuma kuke bukata?"_


_"Yaya wancan fa gidan haya ne kuma me gidan yana san amfani da abunsa shiyasa ya ce zai tashemu nan da kwana uku"_

  Laila ta fada tana kallansa. 


Shiru yayi kafin daga bisani,yace da ita, 

 _"Gaskiya yanzu hidima tayi min yawa, akwai bikin kanwar matata, da nake rukwanta ,nan da sati biyu, kuma ga hidimar gida, kuma nan gidan yayi mana kadan in nace zan zauna daku, zaku takurawa matata da kuma yarana, abunda nakeso dake yanzu shine, zan baki dubu biyar, inyaso saiku samu cuko wajan masu taimako, saiku hada ku kama ko daki daya ne, kafin nima in asamu kudi"_*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(11)*

__________
Aminu ya fada yana kallan Lailah.Shiru tayi tana jin sa, dan kadan ya hana ta hadiyi zuciya ta mutu tsabar bakin ciki.


_"Yanaji kinyi shiru, shawara na baku, ki gaya musu kiji me suka yanke hukunci"_


Mikewa tayi tsaye tare da nunawa su,Mama su tashi su tafi, kallansu tayi tana hawaye ta nuna musu da hannu kamar haka, 

 _"Nida ku, zamuyi magana ta fahimta, karku saka mana baki, komai zai zama daidai, zamu samu gida me kyau, kunji karku damu"_


_"Mungode Yaya kuma Allah da ya haliccemu bazai hana mu gurin zama ba, bama san kudin ka mungode"_


Tana fadar haka ta juya, tare da jan iyayan nata. 


_"Ga #500,ku hau mota naga sun tsufa da yawa karki basu wahalar tafiya a kafa"_


Jin abunda ya fada tasa bazata iya jurewa bah, ta juya a fusace, ta amshi kudin tare da Yayyagasu ta watsa masa sannan tace dashi, 

 _"Lokacin da zamu zo aiba kai ka bamu kudin ba, da har yanzu zaka bamu wata tsinanniyar dari biyar dinka, Wallahi kuji tsoran Allah, sai kunyi nadamar abunda kukeyi"_


Tana fadar haka ya wanka mata mari, da sauri Abba ya karaso tare da wanka masa shima marin,cikin zafin nama ya juya zai rama, ganin haka yasa Mama itama ta mareshi. 


Lokacin yayi daidai da fitowar matarsa da kuma yaransa guda biyu. 


_"Ni kike gayawa wanann maganar sabo da basu baki tarbiya me kyau bah"_


Lailah tana kuka tace dashi, 

 _"Anyi maka rashin kunyar, kai yanzu ba iyayanka kake dagawa hannu ba, zaka mara bah, wallahi na kuma fada saikun hulakanta, sai kun zama abun gudu,tsinannu wanda basu san darajar iyayansu bah"_


Jin haka yasa ta kuma tinzira Aminu, yayo kanta zai doketa, yatsa ta nuna masa tana hawaye , tare da fada masa, 

  _"Wallahi kasake ka tabani sai kayi nadama, saina maka sharrin da bazaka taba mantawa dani bah"_


_"ke meyasa baki da tarbiya"_

 Matar Aminun ta fada. 


Rasa abunda Lailah zatace da ita tayi, tayi kukan kura tare da shakar ta nan suka hau dambe, duk da yanda Laila take kamar Baby doll, amma tafi Nusaiba, karfi. 


Da yar Aminu ya raba su, su Mama suka ja Lailah, nan tayi ta zaginsu tana tsine musu har suka fita daga gidan. 


Bakin gate ta zube ta hau kuka tana bakin cikin abunda aka musu, gaba dayansu kuka suke, abun abun tausayi. 


Haka ta dawo lallashin iyayan nata, harta tare musu Taxi suka nufi gida, kowa ransa babu dadi. _____

Bayan tafiyarsu matar Aminu Nusaiba, ta fara kuka tana fadin, 

 _"Nagode ai kana sane ka bari kanwarka ta dakeni a gaban yaranka, Nagode"_ 

tana fadar haka ta mike, ta shige daki ya bita yana mata magana amma ta kulle kofa, komawa yayi ya zauna kan sofa yana bakin cikin zuwansu zasu tayar masa da hankalin gidansa. ________

Koda suka koma gida,kowa ransa babu dadi, tana kwance cikin daki ta rasa abunda yake mata dadi,  kiran Dizhwar ne ya fara shigowa wayar ta. 


kamar ta daga amma ta fasa, tunda yanzu gashi tace tana san dan da be kai Dizhwar ba, an janyo mata bala'i yanzu inta ce tana san Dizhwar killa danginsa kasheta zasuyi.


Da sauri ta janyo wayar dan bazata iya hakura ba, sabo da san da take masa, tana daga wayar ta fashe da kuka. 


Hankalinsane ya tashi jin tana kuka, ya rikice ya fara tambayarta abunda ya faru, nan da nan ya gaya mata yana nan zuwa. 


Bayan ya katse, wayar gefe ta tura ta taci gaba da goge Hawayanta jikinta duk yayi jajir, haka idanta. 


________

Bata jima da gama waya dashi ba, taga kiransa ya shigo yana kofar gida. 


Mikewa tayi, ta zira Hijab dinta ta fita daga cikin dakin, tana ganin motar tasa ta karasa ta bude tare da shiga ta kullo kofar. 


Kallo daya yayi mata yasan tana cikin damuwa. 


_"Princess Lafiya kike kuka, wanene ya taba ki, gaba daya kin daga min hankali"_


Jin haka yasa ta kuma fashewa da kukan ta juyo tana masa magana cikin kukan, 

 _"Bansan yaya zanyi ba da rayuwata ba, kasancewar halin da muke ciki da kuma larurar da Allah ya bawa iyayena, hakan yasa babu wanda yake kaunar mu, babu me san mu rabeshi koda jinin mune, yaya zamuyi yanzu,Dan Allah Dizhwar karka gujemu kaima, kaine kawai me kaunarmu, Allah ne gatanmu, kaine me taimakon mu, inka gujemu bansan yaya zanmuyi ba"_

 Ta kuma fashewa da wani saban kukan. 


Karo na farko daya fara jin tausayin wata ya mace a duniya bayan yan uwansa da mahaifiyarsa. 


_"Ki kwantar da hankalinki, koba dan soyayya ba, zan taimaka muku domin Allah, zan share muku hawayanku badan komai ba sai dan Allah"_


Dadi taji sosai cikin ranta, kuma kallan ta yayi tare da fadin, 

 _"Lailah kibar kuka mana, bakisan kukannan yana taba min zuciya bah, Inde *LAILAH-DIZHWAR* ce ta goge hawayanta"_


Dagowa tayi ta shiga gogewa, tana Murmushi, 


_"Ywwah, toh yanzu a gaya ma Dizhwar menene matsalar Lailar sah, kokuma ya hadiyi zuciya ya mutu"_


Da sauri ta juyo ta kalleshi da jajayan idanta, tare da fadin,

 _"Gidan da muke cikine aka tashemu, kuma ni aikin da nake ba wani bane da har zan iya kama Mana haya da kudin,  dashi muka dogara, abincin mu, rashin lafiya da sauransu"_


Sai Kuma tayi shiru, dan abun baya mata dadi, tasan da tayi karato kamar wanda su yaya Ahmad  sukayi, zata taimakawa iyayanta amma iya secondary ta tsaya itama din yau taje gobe babu kudin makaranta. 


_"Insha Allah duk wannan ba matsala bane, a wata unguwa ko gari ko kasa kike san asiya muku gida"_


Wani sanyi taji acikin ranta, ji take tamkar ta rungume Dizhwar tsabar farin ciki.


_"Ni bani da zabi dik inda Dizhwar ya zaba toh yayima Lailah"_


_"hhhh, toh yanzu kam kin yima Dizhwar wayo, amma next time, dole *LAILAH-DIZHWAR*,ta kasance special ce kuma  classic lady, ba kamar sauran Lailar jama'a take ba"_


Sun jima suna hira, saida ya tabbata babu wata damuwa cikin ranta tunkun yayi mata alkwarin gobe zaizo har gida ya dauketa ya kaita gidan daya siya musu. 


*Muje zuwa*😇


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(12)*
__________
Ko bayan Lailah ta koma gida, zuciyarta cike da farincikin, wannan alkawarin da Dizhwar yayi mata.


Tana shiga ta samu iyayanta ta sanar dasu,  da farko Mama kin yarda tayi, saida Lailah ta dage tukun dan itama bata san wulakanci. 


Haka kuwa akayi washe gari, bayan sallar azzhr, Dizhwar ya kira lailah ta fita. 


Bayan sun gaisa yayi mata albishir da Gida daya sama musu, murna kamar ta hadiye Dizhwar haka Lailah take ji. 


Cike da farin ciki,  ya gaya mata su shirya, zai aiko an jima a tafi dasu. 


Nan Lailah ta koma tana ta faman farin ciki ta hada duk abunda tasan zata bukata, haka suma iyayan, amma basu daukar kayan su na Katako bah, dan a tunanin su, aro ya basu zasu tafiyar Yaseer da Amaryar sah. 


Yamma nayi,  kuwa mota tayi parking kofar gida su, Lailah nan suka shiga aka tafi dasu saban gidansu da yake a, Unguwar Kaura. _________

Mamakine ya kama Su gaba daya ganin gidan da Dizhwar din ya saka a kaisu,  gidane har gida amma flat ne, yana da kyau iya kyau,ga wadatattun dakuna, sannan babu abunda suka rasa acikinsa, tun daga kan kayan furnitures har zuwa kayan abinci,  ba karamin mamaki Lailah tayi ba dan ko amafarki bata tunanin nan kusa zata rayu a gida irin wannan. 


Haka sukaita shiga suna fita daga daki zuwa daki, parlor daya ne sai bedroom har guda uku kowanne da toilet a cikinsa, sai kuma kitchen da dining area, haka zalika akwai, wajan parking space a harabar gidan da kuma wajan me gadi, sai wajan da aka yishi tamkar karamin garden flowers ne kala kala, gaskiya gidan yayi kyau sosai. 


Nan da nan kuwa suka raba dakuna, kowanne ya zabi guda daya, Lailah zama tayi cikin dakin ta, kan gado tana faman kallan ko ina a dakin, fadawa tayi kan gado tana maida numfashi, ga wani sanyi da yake shiga illahirin dukkan wata kofa dake jikin ta. 


Ta jima nan kwance idanuntah a lumshe, mikewa tayi ta shiga toilet dan yin wanka, bayan ta gama ta fito, cikin kayanta masu kyau data dauko ta zaba ta saka. 


Tayi kyau sosai gashin nan yasha gyara har gadan bayantah tukun,ta  zauna tana kallan kanta, bayan ta gama kalle kalle, fita tayi inda ta samu Abbanta da Kuma Mama zaune a falo suna hira. 


Ba karamin dadi taji ba ganinsu tare haka cikin nishadi, jingina jikinta tayi jikin bango tana kwallah,yau gashi Allah ya kashe ya basu, sanadinta suna cikin jin dadi, wanda dama burinta be huce ta kyautatama iyayanta bah. 


Wayar tace da tayi kara, yasa ta dawo tunanin da take, dubawa tayi tare da yin murmushi, mayafinta ta yafa ta fita. 


Yana cikin mota a zaune, tunda ta fito yake binta da kallo harta karaso wajansa. 


Cikin motar ta bude ta shiga, batare da yayi magana ba ta, rungumeshi tana kuka. 


Shikuwa kasa hanata yayi, illah bayanta daya fara shafawa yana lallashinta. 


_"Nagode,Nagode Dizhwar, ina sanka kamar yanda kaima kake sona kuma insha Allah bazan taba cin amanarka ba dan Allah nima kamin alkawarin har abada xaka kasance tare dani, bazaka karyamin zuciya bah, zan maka dukkan biyayyar da mace takewa mijin ta, karka saka in shiga wani hali wallahi ina sanka"_

 Ta karashe maganar tana kuka. 


Kara rungumetah yayi yana murmushi batare daya ce mata komai bah. 


________

Yau Yaseer yayi niyar komai Lailah zata mai saide tamai amma sai ta gaya masa waye wanda ya gansu tare da dadare. 


Koda yazo gidan ga mamakinsa yaji gidan a kulle. 


Hannu yasa ya taba kwadan tare da zaro wayarsa daga aljihu. 


Amma koda ya kira wayar tata bata shiga,da sauri ya kuma gwadawa amma still switch off, gaban sani yayi mugun faduwa. 


Nan yayita kira kamar wanda ya zauce dan bama ya sauraran maganar computer. 


Cikin zuciyarsa salati kawai yake, karde sun tashi daga gidan, ina Lailar sa ta tafi ta barsa. 


Nan hankalin Yaseer ya rashi, haka yayita tsayiwa anan gashi babu wanda zai tambaya. 


Haka ya hakura ya koma gida jikinsa duk a sanyaye. 


Yasan babu yanda zaiyi, gashi gobe ne ranar da Daddyn sa ya daukar masa. 


_________

Kasancewar biki ya matso shiyasa Aka shiga shirye shirye gidan Mai martaba,dan har Hjy Bilki ta dawo nan, 


Kasancewar Fareeda tabar gida yasa ran sarki ya bace dan haka ya yanke hukunci hada auran Jafar da Asiya. 


Shima Kasan yayi farin ciki da haka, domin koba komai suna dasawa da Asiya amma be sani ba ko ita tana da wanda take so. 

 Shine damuwarsa, Karta ki yarda. Ban garan Asiya kuwa babu wanda ya kaita farin ciki, sabo da dama faduwace tazo daidai da zama domin duk duniya babu wanda take so fiye da Jafar. _________

Yaune Ranar da za'a kai lefe, kuma ranar da Za'a kawo na gidan sarki,  dan haka falani ce tasa ayi abincin kala kala na taryar baki, daga na bangaran Hajiya Babbah harna wajan ta domin ita babu damuwa ko daya cikin ranta. 


Shikuwa Dizhwar da Jafar basu suka hada lefan su ba, gaba daya Hajiya Bilki ita ta hada musu,da kudin da Sarki ya bada. 


Kowanne akwati 24,da key din mota, haka aka hada musu gashi gaba daya babu kananan kaya harkar girma akayi. 


Dan gin Babban jafar yan kano suma ranar zasu zo, haka nan dangin Sarki suna nan mata zasu shirya suma dan kai na Dizhwar, yayin da can Family na Waziri zasu kawo na Zakiyya. 


_______

Bayan sallar azzhr, motoci suka fara shigowa cikin gidan sarki kala kala, anata faman buda, familyn Waziri ne suka iso dan kawo lefan Zakiyya, kai tsaye Part din Hajiya Babba aka nufa dasu, dama itama Nata dangin suna  nan cike da falon ta.

  Zakiyya kuwa banda kuka babu abunda takeyi dan itama bata sanshi. 


Da buda suka shiga, haka aka dinga shiga da akwatinan nan,mata Manya da yan mata ko wacce cikin shigar alfarma, duk suka nemi waje suka zauna. 


Tunda suka shigo babu wanda ya kulasu ko kuma ya kalle su, hakan yasa jikinsu ya fara sanyi. 


Nan suka zazzauna ga kuma Kayansu sun saka su Gaba,ganin babu wanda ya kulasu suke shirin kokarin tashi su tafi. 


Hajiya Babbace ta fito tare da fadin, 


_"Sannuku da zuwa, kwadayayyu dangin mayu, wato Kun dauko kafa da wasu ban zayan kayanku wanda basu kai sun kawo Ba har kuka cikawa mutane gida da ihu, sabo da wannan watsatstsun kayan dako kuyangata aka kawowa bazan yarda ta amsa bah"_

 Nan suka hau kalan kallo. 


Wata dattijuwa ce ta mike tare da fadin, 

 _"Haba hajiya, ai be kamata ki Gaya mana irin wannan bah, nan fah gidan sarauta ne, kuma ba haka aka san gidan sarauta bah, kamata yayi koda ke kina fishi damu,sai ki saka wasu su tarbemu kodan kar kubar abun fadi a bakin duniya"_


_"Dallah gafara can yimin shiru,  ita duniyar ta dade ba'a fade taba, in banda iskanci Ma da hulakanci taya za'ai Me Martaba ya hadani da wannan mahaukatan"_


_"Ke baiwar Allah dakata"_

 Kanwar wazirin ta fada tana bada rikon jakarta wanda itama kana ganinta babbace, dan zata kai 40da wani abu. 


_"Wallahi karya kike, mulki haukane, ko An gaya miki kowama irin kine jahili Marar ilimi dahar akan yarki zaki dinga gayawa mutane maganar banza, inba daban Mai martaba bama ya hada wannan zumunci ke Kin taba ganin wani ya tako Yazo Wajan ki, ke kin isama har azo Wajan ki, wallahi karyar ki, mune ya kamata muce danmu baya so, in kina takama damijinki Sarkine, toh Nima Mijina Sarkine, kuma babu abunda kuka isa ku Nuna mana,"_


juyawa tayi ta kalli wasu mata tare da fadin, 

 _"Ku kwaso Kayan nan mu tafi"_


Tana fadar haka ta nufi hanyar fita, da sauri Hajiya Babba tasa wasu manyan mata susha gaban ta. 


_"Haba yarinya, kin isa ki Shigo har cikin gidana ki zageni ki hulakantani gaban mutane kice zaki fita lafiya"_


Lokacinne yayi daidai da Shigowar Hajiya Bilki da Fulani da kuma mutanan su, dan tarbar an kawo lefan Zakiyyah tunda su har yanzu yan kano basu karaso ba. 


Ganin ana hayaniya, Fulani tayi saurin fadin, 

 _"Haba Hajiya Babba lafiya kuma kuke hayaniya haka, wannan fa ranar farin ciki ne, yarki Allah ya zabeta cikin mata masu tare yawa, ya bata miji ya rufa mata asiri zatayi aure, amma kuma azo a dosa hayaniya haka,gaskiya wannan ba girma bane, musamman ace a gidan sarauta ake irin wannan abun, gaskiya bayi bane?"_


Hajiya Babba tana jin haka, ta kara hasala tare da kallan wannan matan, 

 _"ku kamaso Ku saka su a kurkuku"_


nan fa aka hau danbe, ana fada, gaba daya waje ya hargitse da yan kawo lefe ana danbe sosai, harda su jini. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(13)*
__________
Ganin abu yaki karewa yasa Fulani ta shiga neman wayar Dizhwar, jin shiru be daga ba yasa ta fara kiran Jafar,


Zuwa wannan lokacin mutanan da suka samu rauni da kuma barnar da akayi a part din Hajiya Babba ta bace. 


Dan kar hukuma ta shigo cikin abun, aji kunya kamar gidan sarki ana wannan abu, yasa Fulani gayama Jafar halin da ake ciki,  nan da nan ya karaso part din. 


Zuwanshi tare da manyan masu tsoro na gidan, nan da nan duk aka tattara Bakin akayi part din Fulani dasu, yayin da aka saka Family Doctor dinsu tazo dan bawa wasu taimakon gaggawa, dan an zubar da jini ba kadan bah,

  Haka gaba daya kayan lefan da akwatinan duk saida aka wulakantasu. 


______

Bayan duk Jafar yayi kokarin ganin kowa ya samu kulawa daga wajan Hajiya Babba har zuwa masu kayan lefan tukun yasa me martaba a cikin wannan zance, 

 Jin abunda ya faru ba karamin bata masa rai yayi bah, sabo da haka nan da nan yasa aka tattara duk wanda abun ya faru. 


Bayan sun zauna kamar yanda ya bukata, nan Fulani tayi masa bayanin komai kamar yanda Kanwar Waziri ta sanar musu wato Hajiya Zainab. 


Shiru Sarki yayi yana naxarin abun, kafin daga bisani ya fara magana cikin fishi, da daga murya. 


_"Magana ta gaskiya Abunda Kikamin Khadija banji dadi bah, wannan yana nuna kamar ban isa da ke ba da kuma yara na, kin nuna wa duniya cewa gidan sarauta bashi da daraja, kin zubar mana da mutunci sabo da wata banzar manufataki, toh wallahi tallahi, koda xaki kashe kanki, Allah ya riga daya saka wannan yarinya itace matar sah, kuma aure babu fashi sai anyi shi, saide in ki bar gidan nan, kuma babu inda Zakije da Zakiyya,tunda har kika nunamin bani da iko akanta sai ke"_

 

Shiru Hajiya Babba tayi dan tasan laifin tane, kuma yanda ransa ya bace, ta tanka ba karamar matsala zata kunnowa kanta bah, sabo da haka bata ce uffan ba harya gama maganar sah. 


Sannan ya kara da bawa mutanan hakuri tare da sanar musu suje suci gaba da hidimar biki kamar anyi an gama nan da sati daya. 


Nan yasa aka musu sha tara ta azriki suka tafi. Wannan abu daya faru shine abunda ya kuma tunzura Hajiya Babba,Ranta yayi mugun baci ta yanda ta kudiri yin abubuwa masu yawa domin huce Takaicinta. 


______

Ita kuwa Samira, Anty Amarya kenan,dukkan abunda ya faru taji da kunan ta, haka zalika tayi mutukar farin ciki, domin dama burinta be huce ko wacce ta kasance cikin fishi Memartaba. 


________

Yaseer kuwa kamar yanda Daddynsa ya daukar masa lokaci, lokacin ya cika kuma ya bukaci ganinsa. 


Suna zaune kamar wancan lkcn, yanda ya tarda su. 


Bayan ya gaisa da iyayan nasa, ya nemi waje ya zauna, kansa a kasa zuciyarsa tana ta faman dukan tara tara sabo da yasan ba lallai yaji alkairi bah. 


_"Yaseer, yaune ranar da mukayi dakai zamu kara zama, wato naje na sami Mahaifin yarinyar nan kuma munyi magana dashi, amma ya nuna, akwai wanda ya riga ya bawa ita, sabo da haka ma suka nuna bazasu zauna nan bah, domin sun kusan tashi dama zasu koma kauyansu acan za'ai bikin"_


Duk da besan abunda zai fada ba, amma yasan da wuya hakan ta kasance, amma bashi da zabi Allah yasa hakan yafi alkhairi. 


_"Daddy naji na yarda zan auri Saudat din Allah yasa hakanne yafi alkhairi"_


Dadi sukaji gaba daya suka hada baki da Amin. 


Saudat kuwa murna kamar ta rungumi Yaseer gaban iyayan nasa, tashi yayi ya fita daga dakin badan yana farin ciki bah, tun a Stair hawaye suka fara zubo masa sabo da bakin ciki da kuma kunar da zuciyarsa take masa. 


Haka ya sauka a daddafe yana goge hawayan nasa harya shiga cikin dakinsa, yayin daya zauna kukan nasa saiya karu, babban namiji dashi amma sai gashi yana kuka shabe shabe harda hawaye, wayarsa ya janyo ya kuma kiran ta amma akashe, da karfi ya buga wayar da bango tare da hade hannayansa waje daya ya shafe a kansa yana me kukan takaici. 


________

Dizhwar kuwa kamar wasa bashi da aikin daya huce zuwa wajan Lailah, yanzu harya saba, kullum yana gidan, amma yaki yarda kowa yasan inda yake zuwa, ya hanata zuwa wajan aiki, kullum Suna tare ana shan soyayyah, gaba daya ya gama siye mata Zuciya, wanda a yanzu dayan biyu wajan Lailah in har ta rasa Dizhwar zata iya mutuwa kokuma ta haukace, haka shima ya nuna mata. 


Yauma yana gidan,suna harabar gidan a zaune kan kujera suna hira kamar yanda suka saba suna dariya. 


Jafar ne ya kira shi a waya bayan sun gama ya ajje wayar tare da kallan ta. 


Itama shi din take kallo tare da fadin, 

 _"Wai waye Jafar din nanne?"_


_"Kinasan sanin kowaye"_


Kai ta daga masa alamun eh, 


 _"Nan da One week zamuyi bikinsa zan gaiyaceki, ai nasan zaki zo ko? "_


Murmushin ta me daukar hankali tayi tare da fadin, 

 _"Zanzo mana, in har kana so Koda yakai nisan inane"_


_"Amma kwana zakiyi"_

 Ya fada yana kallanta, ta kasan ido. 


_"Ammm!, mezai hana hakan ma, in kana so"_


Dadi ya kuma ji tare da murmuyi, 

 _"Lailah Ina san nan bada jimawa ba ayi Bikinmu dake,amma ina ganin kamar su Abba bazasu yarda bah"_


Da sauri ta kalleshi, 

 _"Me zai hana, zasu yarda mana"_


Da sauri ta kara matsowa tare da fadin, 

 _"Kasan in basu yarda ba, kashe kaina fa zanyi"_


Shima da saurin ya kalle tah, tare da kamo hannuwanta biyu ya hade da nasa, 

 _"Bana san na rasa ki, koda wasa, Lailah, kece farin cikina, kece mace ta farko dana fara so a duniyar nan in kika barni yaya zanyi?"_


Binshi tayi da kallo na tsawan lokaci ,yayin da shima yake kallan nata,kowanne shi yasan abunda yake ji acikin zuciyarsa, da sauri ya Rungumetah, kamar itama Abunda take jira kenan,ta rikeshi sosai a jikinata. 


Sun jima a haka, kafin yadan janyeta daga jikinsa, kan kurjinsa ta kwanta tayi shiru idanta a rufe, hannunta ya kama guda daya ya hada da nashi yana murzawa, shiru na tsawan lokuta a haka, ita dashi kowanne yana Jin dumin dan uwansa, ji suke kamar karsu rabu, wayar shice ta shiga, Ringing, dauka yayi still tana jikinsa ya kara a kunne. 


Yana magana tana kallan bakinsa, Ahankali ta saka yatsanta tana shafa lips dinsa. 


Bayan ya gama wayar ne yace da ita,cikin wata irin murya wanda be taba mata ita vah, shi kansa besan yana da ita bah. 

  _"Zanje gida Ana nemana"_


Maimkon ta bashi amsa sai ta kuma shigewa jikinsa, tana dada lumshe ido. 


Jin haka yasa ya janyeta Ahankali tare da kallan fuskarta, suna kusa da juna sosai ta yanda hancinsu ya kusan haduwa, kamar acikin bakinta yake maganar, 

 _"Pls Lollipop, Memartabane yake nemana, zan dawo,ko kinaso Amin fada"_

 

Yana magana tana kallan bakinsa, itama kara kashe murya tayi ta kuma sakin jikinta tare da fadin, 

 _"Bana san kayi nisa dani, dan Allah zaka dawo kokuma sai gobe, ina sanka da Yawa Dizhwar"_

 Ta fada hawaye ya zuba ta gefan idanunta. 


Ahankali ya furta, 

 _"I know, I know"_

 Yana shafa gefan kuma tunta da hannunsa, bata yi aune ba ya manna mata kiss, sannan ya jinjinar da ita jikin kujerar, dan yaga duk jikinta ya mutu da er in zata iya Rakashi. 


Tana ganin ya fita daga wajan, wata ajjiyar zuciya ta ajje dan ita kadai tasan yanda take ji Acikin ranta. Mikewa tayi ta shiga gida jikinta duk a sanyayye. 


Shiga falon tayi da sallama, Mama ta gani tsaye ranta a bace tana kallan ta. 


Hannu ta wara amalun, Menene?.


Ranta a bace, ta gaya mata meyasa ta rungume Dizhwar. 


Gaban tane ya fadi tare da yin shiru tama rasa abunda zata fada. 


Kara matsowa tayi tare da dago da kanta ta shiga mata nuni da hunnu, 

 _"In kina yarda dashi, zai cuceki ya gudu ya barki"_


Da sauri ta rike hannun Mamar, tana girgixa kai, 

 _"har abada bazai barni ba, sabo da yana so na kuma aurena zaiyi"_


Shiru Mama tayi kafin ta kuma fada mata,

 _"Kibi a hankali sabo da banji dadi ba, kuma Allah yana fishi daku, bana san irin haka, in kika kara zamu Bar masa gidansa"_


Tana fadar haka ta juya ta tafi. 


Ita kuma Lailah binta tayi da kallo, dan bata san koma waye ya fadi Laifin Dizhwar dan hakan ita bata ga wani abu ba, sabo da yana santa in ma yayi mata wani abu ai duk cikin so ne, ita bazata taba rabuwa dashi ba koda yankan naman jikinta yake, balle nuna mata so yake zallar sah. 


Tuno da subbatar da yayi mata tayi, rufe ido tayi, tsigar jikinta ta tashi, da sauri ta shige daki tana farin ciki. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(14)*
__________


Yan kano sun iso lafiya, Nan suka kawo nasu kayan lefan harda abunda suka kakkara na al'ada.


Nan sukaci suka sha, cikin farinciki da kuma karamci, anan suka kwana dan sai washe gari zasu tafi, nan da sati kuma su dawo domin daukar Amarya dan Kano za'a kai Asiya. 


_______

Anty Amarya, yamma tanayi, ta shirya ita da Kuyanginta guda hudu, ta nufi part din Hajiya Babbah, koda isarta Mamakine ya kama Hajiya baba, 

  Falonta suka zauna, yayin data bawa kuyangin dama dasu basu waje, bayan sun zauna kowacce tana kallan kowacce, ta fara da fadin, 

 _"Nasan zakiyi mamakin gani na a part dinki, ba komai bane ya kawo Ni, illah ina so mu hada kai gaba dayan mu domin yanzu mun riga mun zama daya, hakan zai bawa mutane Sha'awa, sannan mu zama abun kwatance musamma a bikin nan da za'ai, domin kinga ni Babu Kowa a wajena dan nasan kinji Labarin Fareeda ta tafi, nayi miki alkawarin zan Zauna daku lafiya da kuma yaran har ayi biki a gama Lafiya"_


Kallanta kawai Hajiya Babba take dan Bata yarda da abunda take fada bah, da kamar zata mata wulakanci sai kuma tayi tunani tare dayin murmushi, tace da ita, 

 _"Babu komai Allah ya kara hada kanmu"_


Nan ta dan taba hira ta fice ta nufi part din Fulani itama ta sameta da wannan maganar, haka kuwa itama ta yarda. 


Cikin Farin ciki Anty Amarya ta koma part dinta domin ita kadai tasan abunda take hadawa. 


_______

Ana saura kwana biyar biki, dan Har yan gidan su Amaryar Dizhwar sun dawo gidan sarki dan aciki za'ai bikin gaba daya, part daba aka basu da masu Musu hidima har a gama biki.
Yayi daidai da saura sati guda  Bikin Yaseer da Saudat wanda yake ji tamkar ana mai Barazana da Rayuwar sah. 


_____

Yaune kamu, dan haka waje daban aka ware aka Masa Kwalliya, aka shirya shi, tamkar ba mutane bane suka hada bah, sai kwalli yake da kuma kamshi turarukan huta kala kala. 


Anty Amarya tun ranar da aka nuna mata Amaryar Dizhwar Hankalinta ya tashi domin tabbas tasan itama wannan yarinyar yar duniya ce, babu makasa saita kwace Dizhwar ko a hannun wa yake. 


Ita da kawayanta suka zo da kuma yan uwanta, gida ya koma tamkar wani wajan saida jama'a. 


Anty Amarya ita ta dauki Nauyin Shirya Shiryan Amare da wani gyaran su, amma Husna, Amaryar  Dizhwar tace babu inda zata itama zata iya shiryawa dan an raina musu hankali har wata tsohuwar kilakice zata wani dauki nauyin shirinsu, Asiya ce kawai ta yarda dan ita babu ruwanta. 


Haka itama Zakiyya bata yarda bah, saida Hajiya Babba ta lallabata. 


______

Dizhwar, shida Jafar suna zaune cikin dakinsu, Jafar yana sanar masa da Amaryarsa tazo fa, amma shi banza yayi da ita dan baya san ya bata masa rai. 


Ita kuwa Husna tunda tazo babu wanda take san ta gani inba Dizhwar bah, dan haka nan ta dinga tambayar part dinsa saida ta isa ranta yayi mata dadi. 


Ahankali ta shiga Knocking kofar, dakin.


Dizhwar dake waya da Lailah banza yayi, Jafar ne yayi magana. 


Nan ta turo Ahankali ta shigo, sanye take da Pakistan Yellow riga da wando sai karamin mayafi, tasha makeup kamar aljana, dan ita ba fara bace sosai, ga uban gashi dayasha gyara kamar Bororo. 


Shigowa tayi ta zauna, batare datayi sallama ba ko ta gaida Jafar. 


Binta kawai yayi da kallo danya santa Asin shi ta nuna masa ita. 


Wajan Dizhwar tayo kai tsaye ko ba'a fada mata ba tasan shine tunda taga pic dinsa wajan Abban ta. 


Zama tayi kusa dashi tana kallansa tare da fadin, 

 _"Habibee Dizhwar nayi fishi dakai dan naga ko nemana ma bakayi kamar ba matar ka bah"_


Banza yayi da ita yaci gaba da wayar sah, hakan ya sosa mata rai dan ta fara gane da mace yake waya, 


Ganin zata bata masa rai, yasa yayima Lailah Sallama tare da kallan ta,

 _"Wacece wannan? "_

 Ya fada yana nunata yana kallan Jafar. 


Murmushi yayi tare da fadin, 

Matar kace mana.


Wani haushine ya kamasa dan ko Yar kunyar nan bata da ita. 


Hakan yayi mugun bata mata rai, 


_"Amma wallahi baka da mutunci, nidin kake gayawa haka,lallai kayi babban kuskure dahar kake neman wulakantani"_


Duka su biyun kallan ta suke dan suna ganin abun kamar a film. 


Dariya Dizhwar ya kwashe da ita yana nunata. 


Da sauri ta mike tare da yin wajansa, har saida ta rutsashi a bango tare da fadin, 

 _"Dani kake zancan"_


Daidai lokacin Anty Amarya ta shigo dakin, ganin Husna jikin Dizhwar yasa ta sakin baki tana kallansu, bata san lokacin data furta, 

 _"ke meye haka baki da hankali Ne?"_


Juyowa tayi ta kalli, Anty Amary tare da kallan Dizhwar tukun ta sakeshi ta nufi inda take, zagayeta ta fara yi tana leken idanta tah. 


_"Ohoooo!, Antynmu karfa, ta kashe mata ido daya😉"_


Bata ce mata komai ba ta ci gaba da kallan ta. 


_"Hhhhhh, Allah de ya biya, kenan duk yan soyayyah ne acikin gidan"_

 Husna ta fada tana kallan Anty Amarya.


Kusa da kunnan ta ta matsa tare da fadin, 

 _"Ki fara sama Zuciyarki ruwan sanyi ko baki fada ba nagani cikin idanki, amma karki manta saura kwana, hudu ya zama Nawa,so better mind ur business"_

 Tana fadar haka ta juya ta yima Dizhwar signa ta fita daga dakin. 


Jafar ne yace, 

_"Tabdi jan!, Dizhwar akwai aiki a gaban ka"_


Ita de Anty Amarya kamar gunki, kasa jurewa tayi ta fita daga dakin ta kullo Kofar. 


Kallan juna suma Sukayi. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(15)*
__________
Bayan Husna ta fita daga part din su Dizhwar, wajansu ta nufa ranta a bace.


Koda isarta cikin daki da, Babbar yayarsu take, Anty Salima, kuka ta kama. 


Nan tahau tambayarta abunda aka mata, nan ta bude baki ta gaya mata abunda Dizhwar yayi mata harda karawa da karyarta. 


Kasancewa babu wanda besan danginsu bah, Sun kasance yan boko, babansu ma Yayi Ambassador, sun zauna da a America, in har ka aure family dinsu babu kai babu kara aure, haka zalika saika koma tamkar bawansu, mahaifinsu Abokin Mai martabane tun na yarinta, kwanan nan yayi hadiri ya rasu, shiyasa Sarki yake tausaya musu,tun Babansu yana dare yaso Sarkin ya Auri Salima amma abun be yiyu bah, shiyasa yanzu ya barwa Sarkin wasiya akan yana so ko bayan ransa ya hada aure da yan gidansa da nan, shiyasa Ya dage akan Dizhwar saiya auri Husna, duk yan gidansu mata Ne, susu biyar Amma dayace kawai tayi aure, duk sai sun gama karatu sun fara aiki ake aurar dasu, dan Ita Kanta Husnar ta kusan sa'a da Dizhwar din. 


Gaba daya da sauran yan uwansu suka tare gidan sarkin, yayin da mahaifiyarsu da take zaune can gida dan bata gama takaba bah. 


Bayan Husna ta gama yiwa Dizhwar din Karya, Anty Salima tahau masifa tare da fadin, 

 _"Mu zai yiya iskanci dan bamukai sunan saba har yake wani daga kai, zai gane shi yarone saimun koya masa hankali, ki kwantar da hakanlinki ayi bikin nan lafiya a gama lafiya kiga aiki da cikawa, kitashi a fara shiryaki, kinsa karfe 4:00pm za'a fara taran kamun"_.

_______

Ita kuwa Lailah tun ranar da Tabar Tsohuwar unguwarsu bata koma ba, dan haka yau Rauda ta kawo mata ziyara dan ganin ta dena zuwa aiki, zuwa saban gidansu. 


Nan ta shigo ta zauna a falo,  ta hado mata kayan kwalam da makulashe. 


Babu abunda Rauda take sai faman kallan irin daular dasu Lailah suka samu, yake kawai take dan cikin ranta bakin cikine yayi mata katutu. 


Nan Lailah ta zauna suka gaisa amma Rauda tsabar bakinciki tama kasa cin ko abu daya balle tasha ruwa. 


_"Rauda yaya wajan aiki, aini wallahi Dizhwar ne ya hana ni zuwa ko ina daga gida sai gida, saide in dashi zamu fita"_


Shiru kawai Rauda tayi tana jinta. 


_"kwana biyu ko kiranama bakyayi yanzu"_

 Lailah ta fada rana murmushi. 


Yake tayi tare da fadin, 

 _"Wallahi abubuwane sunyi min yawa, ai yanzu keya kamata kina kirana sabo da kin zama Madam"_


Dariya Lailah tayi,tare da fadin, 

 _"Bana san iskanci, kinsan kuwa kwanan nan, zan zama Madam din domin ina gab da shiga daga ciki"_


Da sauri Rauda ta dogo  kai tare da fadin, 

 _"Wai kina nufin dagaske auranki zaiyi"_


_"Hmmm kina wasa kenan,ai in gaya miki nidin bata wasa bace, wallahi gaba daya baki ga yanda Dizhwar ya haukace a kaina ba, barama kiga in gwada miki"_

 Wayarta ta janyo tare da kiransa, harta katse be daga bah. 


Kafin ta ajje ta kan kujera ya kira, nuna mata tayi, tare da dagawa tasa hands-free,  

 _"Hello"_

 Lailah ta fada cikin wani salo,

 Da saida Rauda ta hadiye wani kululun bakin ciki. 


_"Me Babyna take a wannan lokacin?"_


_"Wallahi ina kewarka sosai, har na kasa jurewa shiyasa na Kira ka"_


_"Ohh!, nima haka, am Busy ne amma ina so in shigo inga sanyin idaniyata, but karki damu soon, zamu zama always together"_


_"Yawwa masoyi, ina dan wani abu ina zuwa,love u bye"_


_"Ok, Love you too sweetheart"_


Sannan ta kashe, kallan Rauda tayi data saki baki tana kallan Lailar. 


_"Lallai Lailah, gaskiya Malamin da yake muku aiki ba sabo bane"_


_"Ban gane bah? "_

 Lailah ta fada tana kallan ta. 


_"Wai kina nufin, ba sunansa kuka kai bah"_


_"Bana san iskanci Rauda, sunansa aina kuma zankai, Allah ya rabani da bin bokaye, ai banga abun alfaharin ba ga soyayyar daba ta Allah da annabi bah, Allah ya tsareni, wallahi Allah ne kawai ya hada jini na da nashi, amma babu wani maganar kai Suna ko wani abu, haba karkibani kunya mana saikace ba musulma ba kike irin wannan maganar"_


Shiru Rauda tayi dan abun ya fara huce tunaninta, tabbas yakamata ta tashi tsaye dan bazai taba yiyuba, in har Tana raye, Dizhwar bazai taba auran Lailah bah.


_"Toh Lailah nide zan huce sai kuma in an kwana biyu"_

 Rauda ta fada tana kallan ta. 


_"Toh bara in dauko hijab dina sai in taka miki"_

 Ta fada tare da mikewa ta nufi dakinta. 


Rauda tana ganin haka tayi maza ta dauki wayar Lailah, ta dauki Number Dizhwar ta saka a tatah tare da maida mata ta ajje ta zauna tana jiran fitowar ta. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(16)*
__________

Ko bayan Anty Amarya ta fita daga part din Dizhwar, kai tsaye wajanta ta nufa, batare data kula kowa ba ta shiga daki, wani wawan ihu ta saki tare da fara bari da duk kayan dake kan bedside dinta, ta zauna idanta yana hawaye, duk kwalliyar tatah tayi wani iri.


Bayan tagama hawayanta, ta mike tare da bude wardrobe dinta, wani karamin kwalbar turare ta dauko, tare da kallanta, murmushi, tayi, tare da shiga toilet wanke fuskarta tayi ta fito ta gyara, sai faman yake take yiwa jama'a harta fice daga part dinta. 


______

Amare kuwa sai faman kwalliya ake ko wacce tayi shiga cikin kaya masu kyau da tsada sai faman kamshi suke, 

  Duk da Husna ta kasance ba fara ce sosai ba amma kana ganinta kasa wayayyace, haka zalika akwai ta da iyayi, ga gashi tubarkallah. 


An gama shirya ko ina, ko wacce Angonta kawai take jira domin su fita a huce wajan kamu dan tuni jama'a sun fara taruwa. 


______

Koda Anty Amarya ta isa part din Dizhwar, a kulle ta tarda shi, tsaki tayi ta tsaya tana tunanin inda yayi, ganinsu tayi sun Fito daga mota shida, Jafar, Jafar can cikin gida yayi yayin da Dizhwar ya nufo bangaransu, tana hangosa tayi maza ta boye dan bata san ya hangota. 


Bayan ya shiga tabi bayan sa itama ta shiga tare da kiran sunan sa, 


Da sauri ya juyo yana kallan ta, 

 _"Ywwah me martaba ne yake neman ka"_


Cike da mamaki yake kallanta, kamar zaiyi wani abu sai kuma ya fasa dan baya so ya karyatata, 


_"Muje"_

 Kawai ya fada yabi bayanta, ga mamakinsa sai yaga sun nufi lambun Baban nasu, amma be mata musu ba yasan yana yawan zama a wajan. 


Haka ta jashi har ciki, bayan ya shiga falon wajan ganin baya nan yasa ya bita da kallo, 


Beyi magana bah, ta shiga ciki bata jima bah, sai gata ta fito tare da fadin, 

 _"Ka shigo"_


Ba musu ya shiga wayarsa tana hannunsa. 


Yana shiga yaji wani kamshin turare ya bigi hancinsa take ya fara ganin wani iri jiwa yake ji kamar zai dauke sah, da sauri ta karaso wajanta tare da rungumeshi, jin yana kokarin faduwa yasa ya rike ta sosai, haka ta jashi har kan gado, ta shiga rabashi da kayan jikinsa tana murmushi, rigar ta cire masa, yayin da itama ta cire tatah, rungumeshi tayi tahau romancing dinsa iya yanda take so, bayan ta gama ta maida rigar ta tare da mikewa ta dauki Camera data saka tayi musu hotona, ta kunna taga duk gasu nan sun dauku, ta maida ta rufe ta bishi da kallo tare da durkusa ta dauki wayarsa data fadi ta fita daga dakin bayan ta saka masa key. 


Fita tayi tana Murmushi tare da fadin, 

 _"Husna zakisan dani kike, zamuga Dizhwar din da zaizo wajan Kamu"_


Haka ta koma cikin mutane akaci gaba da hidima da ita yayin data saka wayar Dizhwar cikin wardrobe dinta ta kulle dakin ta fita. 


_____

Tun bayan da Husna ta gama shirin ta ta shiga kiran Number Dizhwar amma yaki dauka, hakan yasa ta sanar da Anty Salima, ba wani jayayya ta nufi wajan Fulani dan sanar mata abunda Dizhwar din yake shirin musu. 


Nan ta basu hakuri tare da fara trying number tasa da kanta, amma shiru yaki dagawa hakan yasa ranta yayi mugun baci, tunda tasan yana sane zaiki dagawa tunda shima basan Husnar yake bah. 


Jafar ta shiga nema ko suna tare, amma koda ya dauka, sai yace da ita, shima nemansa yake, ga kayansa an kawo masa shima ya gama shiryawa, hakan yasa Gaban Fulani yadan buga. 


Wasa wasa lokaci yana ta tafiya ga dangin Husnah sun dame su.


Batayi kasa a gwiwa bah, taci gaba da trying number tasa. 


Anty Amarya kuwa tana zaune gaban Mudubi tana kwalliya taji wayar Dizhwar tana ta faman ringing, mikewa tayi ta dauka tana kallan missed calls da akayi masa dayawa, murmushi tayi ta ajje wayar tana kallan ta, 


Mami taga an saka tasan Fulani ce dan haka da sauri ta dauka ,batare da tayi magana bah. 


_"Dizhwar ka kyauta, tun dazu ina faman kiran ka amma kanajina kaki dagawa, bayan kasan jiranka sukeyi, Koso kake Babanku ya shigo maganar bayan kuma an gama komai,toh Wallahi duk inda kake kayi maza ka dawo gida ko ranka yayi mugun baci"_

  

Babu abunda Anty Amarya take sai dariya kasa kasa, jin Fulani ta gama yasata, kashe Murya tare da fadin, 

 _"Kiyi hakuri, yagajine shiyasa yake bacci amma inya tashi zansa ya kira ki"_

 Tana fadar haka ta kashe tana ihun dadi. 


Bin wayar Fulani tayi da kallo da sake sake kala kala cikin ranta, 

 _"Innalillahi wa'inna illaihir raji'un"_


  shine abunda take ta faman maimatawa kenan,da zuciyarta da take saka mata ko neman mata Dizhwar din yake dama. 


Hankalinta ba karamin tashi yayi ba kasa kiran Jafar din tayi haka ta kasa bawa kowa masar tambayar da yake mata ta ina Dizhwar din ya shiga. 


Fita tayi tabar wajan, dan ta samu saukin hayaniyar da akeyi ko kanta zai dawo dai dai. ________

Husna kuwa banda kuka babu abunda takeyi, hawaye shafe shafe. 


Duk ta bata kwalliyar tatah, Anty Salima da sauran yan uwanta sai hakuri suke bata, taje haka nan babu Angon. 


_"Wannan ma ai wulakancine, dama yasan haka zaiyi mana, shine zaisa mu gayyaci mutane ya ci mana mutunci, wallahi saimun nuna masa damu yake wannan abun, ya za'ai yayi mana irin wannan cin mutuncin"_

 Anty Salima take ta faman balbalin bala'i. 


Gaba daya yan Bangaran Amarya Husna kowa yayi jugun jugun duk an fara cire kwalliya tunda Amarya kanta itama ta lalata tatah. 


_"Husna ki tashi a gyara miki fuskar kar kuma yazo a kuma bata lokaci"_

 Wata kawarta ta fada. 


Dago kanta tayi tare da fadin, 

 _"Rabu dashi wallahi ko yazo babu inda kuma zani"_


Mikewa tayi kai tsaye ta nufi part din Fulani, koda taje babu mutane sosai duk sun tafi wajan kamun Asiya.


Nan suka shiga neman, Fulani yayin da ita bama ta wajan. 


Babu abunda suke a wajan sai faman habaici,da zage zagen abun da aka musu. 


Hajiya Bilki ce ta zo wajansu tare da fadin, 

 _"ku in baku da tarbiya anan za'a koya muku, in banda baku da mutunci kuzo kona mana fada kamar wasu kannanku ko sa'aninku,ku kiyayi kanku nan Gidan sarautane ba Club bah,  kuma fadan ku da zagin da kuke, shine zaisa Dizhwar din yazo? "_


Shiru sukayi babu me magana acikinsu, nan ta kira me martaba ta sanar masa. 


Shima kiran Dizhwar din yasa ayi amma tana ta Ringing ba'a dauka bah. 


Nan fa Husna ta zauna tana ta faman ihu, babu ji babu gani, kamar yarinya karama. 


Anty Amarya ce ta karaso wajan tana fadin, 

 _"Dan Allah kuyi hakuri ku lallasheta mana,tunda yaki dagawa kuyi hakuri mana, tunda wayar tana shiga in yana gani ai zai daga, kuma bakwa tunanin ko wata matsalar ce ta faru"_


_"Babu wata matsala data faru, ai Jafar yace tare suka shigo gida "_

Hajiya Bilki ta fada taba gyara zamanta. 


_"Innalillahi,Gaskiya shima ai ba'a irin haka, saiya dauka yace bazai zo wajan ba amma yana gani ana kiransa ai saiya dagawa mutane hankali "_


 Anty Amarya ta fada tare da mikewa, 

 _"Bara muje mu leka nasu Zakiyyah"_

 Ta fada tare da fita daga wajan tana murmushi. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(17)*
__________Haka ta ficewarta ta barsu ana mai da zance.


Ranar haka Husna tana ji tana gani sukayi zaman bakin ciki babu kamu, sai mutane aka bawa hakuri kowa ya tafi dan babu yanda basu yiba taje ita kadai ta kiya.


Anty Salima so tayima su hada nasu inasu su tafi gida amma Husna ta dage da babu inda zata dan ita tana san Dizhwar kuma duk abunsa saiya aureta. 


_______

Lailah ma haka tayi ta faman kiransa amma sai gajiya tayi dan be daga ba hakan yasa hankalinsa yayi mugun tashi. 


______

Bayan an tashi daga wajan party, saida Anty Amarya ta tabbata babu me ganinta takun, ta saka aka dauko Dizhwar din daga can aka kaisa dakinsa, tare da ajjemai wayarsa kusa da shi, yaci   gaba da baccinsa hankali kwance. 


Koda can dare yayi da Jafar ya dawo, cike da mamaki ya shiga bedroom din Dizhwar ya gansa kwance yana faman Bacci. 


Abun ya bashi mamaki, karasawa yayi ya shiga tattabashi yana tashin sa amma kamar gawa haka ya koma dan bama jinsa yake yi bah. 


Hakan yasa ya dauki wayarsa tare da duba dumbin missed da aka masa.


Zama yayi kusa dashi yana nazari, tabbas yasan Dizhwar akwai dalilin daya hana shi zuwa wajan nan amma sai ya tashi sai yaji koma Menene. 


______


Washe gari saida gari ya waye wajan 8am tukun ya fara motsi,ahankali ya tashi zaune kamar wanda aka masa duka duk jikinsa ya mutu, bude ido yayi ya kalli Jafar dake zaune kusa dashi. 


_"Sannu"_

 Jafar ya fada yana kallansa. 


_"Lafiyar ka kuwa, kode shaye shaye ka fara, Dizhwar ?"_


Binsa kawai yake da kallo, shima mamakin kansa yake duk da besan iya adadin time din daya bata ba yana Baccin bah. 


Batare da yayi magana ba ya shige toilet, bayan yayi wanka ya fito,  duk Jafar yana zaune yana kallansa ya gama shirinsa yayi sallah, tukun ya dauki wayarsa ya fara dubawa. 


Mamakine nan ma ya kamasa, yana san tuna abunda ya faru amma ya kasa, ya akai yayi bacci haka,shi kansa yasan ba'a sanin saba kuma gashi beje wajan Kamu din nan bah. 


Tsaki yayi ya maida wayar tashi cikin aljihunsa. 


______

Ita kuwa Fulani kusan kwana tayi batayi bacci ba, sabo da abunda Kunan ta ya jiye mata, 


Koda safiya tayi, kasa wani walwala tayi babu abunda take jira kamar shigowar Dizhwar gidan  nan. 


Kamar daga sama kuwa taji sallamar sah. 


Tana ganin ya shigo ta mike daga inda take ta karaso wajansa tare da marinsa har sau hudu, sannan tana kuka ta fara tambayarsa,

 _"Daga ina kake, ina kaje jiya?"_


Kasa magana yayi yana kallanta, ji yake kamar yayi kukan shima, 


Kwalar rigarsa ta rike tana masa magana. 


Nan da nan duk wanda suke Dakin suka fita, Humairah ce ta fara kokarin janya Fulani tana bata hakuri, 


Tureta tayi tare da komawa ta rikeshi tana fadin, 

 _"Baza ka gayamin ina kaje ba Dizhwar, dama abunda kake kenan shiyasa kaki yin aure tun tuni, dama abunda kake shiyasa bakasan zaman gidan nan, wallahi ban yafe maka bah"_


Asiya da Humairah ke bata hakuri suna rokonta datayi hakuri, yayin da Humaira ta jashi gefe tana masa magana. 


Ita kuwa Fulani kuka kawai take. 


Saida ta fita dashi daga inda Fulanin take, tukun ta zaunar dashi, bata mai magana ba, ta fita ta hado masa breakfast, tare da ajje masa tana kallansa.


_"Yaya gashinan ka karya tukun, Mami tana cikin bacin rai sosai, tun jiya kasa bacci tayi haka ko abinci bata cibah, munyi munyi ta gaya mana damuwarta amma taki, dan Allah karka koma wajanta ka bari saita huce"_

 Binta yayi da kallo yana san yin amgana amma ya kasa, hawaye kebin kumatunsa sabo da takaicin shi kansa besan abunda zai fada mata bah, gashi besan me take tunani bah. 


_"Yaya dan Allah kaima kayi shiru, haba sai kace ba Namiji bah, ka samu kasa wani abun acikinka mana"_


Cikin muryar kuka yace, 

 _"Humairah me nayima Mami, ni kaina bansa ya akayi ba, wallahi kawai tashi nayi na ganni cikin dakin mu, amma ko za'a kasheni bansan abunda ya faru bah"_


Jin haka yasa ta bishi da kallo, tasan bazai mata karya ba, toh dole cikin wannan lamari akwai abun dubawa, dan in ba haka ba saide in shaye shaye yake yi, amma ya za'ai ace mutun da ransa da lafiya yace besan ya akai yayi abu ba.


Mikewa tayi tsaye tare da fadin, 

 _"Kayi hakuri, ka saka wani abun a cikin ka, bara naje na dawo"_

 Tana fadar haka ta mike ta fita daga dakin.


______

Haduwa tayi da Jafar yana kokarin shiga dakin Fulanin. 


_"Lafiya kuwa meke faruwane wai"_

 Ya fada yana kallan humairah. 


Shiga dakin  sukayi,tare ya zama, Daga Mamin har Asiya kuka suke. 


_"Kekuma kukan me kikeyi? "_

 Jafar ya fada yana kallan Asiya. 


Kasa magana tayi, 

 _"Shagwababbiya tashi ki hadan abinci"_

 Ya fada yana zama, babu musu ta fita daga dakin tana goge hawayanta. 


Zama Humaira tayi tana kallan Jafar tare da fadin, 

 _"Wai ina Yaya yajene haka?"_


_"Wallahi Humairah ban sani bah, nasan tare dashi muka dawo daga wajan aski, toh amma koda muka shigo nasan be kara fita ba yana cikin gidan nan, amma abun mamaki anan shine, dana dawo bayan naci abinci danna shirya baya cikin dakin, amma dana dawo da daddare zan kwanta na gansa yana bacci, kuma wallahi ko sallar asbah beyiba sabo da wannan bacci saida gari ya waye"_


_"Amma abun da mamaki, kuma nasan baya shaye shaye"_

Humairah ta fada. 


_"Amma ai yana neman mata"_

 Fulani ta fada tana kallan Jafar. 


_"Neman mata kuma, Mami?, wallahi Dizhwar baya Neman mata"_


_"Karya zanyi maka kenan?,jiya dana kirasa macece ta daga, tasanar min da yana bacci"_


Shiru Jafar yayi yana nazari, 

 _"Amma abun da mamaki, Wallahi Mami ki yarda dani, Dizhwar baya neman mata, Wallahi kinji na rantse miki"_


_"Mami ki yarda mana nima abunda nayi tunani kenan,kode sharri aka masa"_

cewar Humairah 


_"Sharri kuma, wanene zaiyi masa wani sharri?, shide ya sani amma tabbas mace, ta daga min waya jiya dana kirasa"_


_"Toh Mami in ma wajan watan yaje, saide in a gidan nan take amma wallahi be fita daga gidan nan bah, ko masu gadi zaki tambaya"Jafar ya fada, yana kallanta. Shiru itama tayi dan abun itama ya daure mata kai, dande ance ba'a saidar mutun, amma tabbas taji muryar mace kuma tasan abunda take tunani Dizhwar bazai aikata bah, 

 _"Toh wace wannan?"_*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(18)*
__________


Ranar ne ya kama Dinner, sun so suyi a kano ko lagos amma Memartaba ya hana dole anan aka shirya komai.


Dizhwar yasan Mami tana fishi dashi sosai hakan yasa be koma wajan tabah, dakinsu ya koma dan abun ya fara bashi tsoro. 


Yana nan zaune Jafar ya shigo, shima be kuma masa maganar ba haka zalika shima yayi shiru, nan suka fara shirya yanda abun zai kasance, duk da baya son Husna, yana yin komai ne dan karsu Mami su kara jin haushinsa.


Nan Jafar yahau kiran friends dinsu domin ya sanar musu da batun Dinner, dan lokacin ma ya riga daya kure sosai. 


Harda Yaseer cikin wanda suka gaiyata. 


________

Shima Yaseer an fara hidimar bikinsa,amma ko kadan be gayawa wani abokinsa ba dan ko kadan da er in zai halarci wani party nasu can da suka hada. 


_______

Lailah ma yanda taga rana haka taga dare domin babu yanda ta iya, kuka kuwa tasha shi harta gode Allah, sabo da rashin Kiranta da Dizhwar yayi. 


Tana kwance kan gado kamar marar lafiya, haka Mama ta kawo Mata abinci amma kinci tayi, sabo da tunanin masoyi. 


Nan ta shiga kiransa, cikin sa'a kuwa tana katsewa ya kira shima. 


Batare datayi masa magana ba ta fara sakin saban kukan, dama yanda yasan Lailah da shagwabah yasan dole zatayi kuka. 


Sanin cewar kukan ta yana sashi yaji wani iri, duk da har yanzu ba wani shararran so yake mata ba, banda na yaudara da yake nuna mata. 


Saida tayi ta gama tukun yace da ita, 

  _"Kiyi hakuri pls nace miki ina cikin Busy na bikin Nan da muke"_


_"Amma dan Allah kana ganin kirana kaki dauka, wallahi jiya banyi bacci ba duk hankalina a tashe yake"_

 

_"Ayyah am sorry kinji yan mata na, ki kwanta kiyi bacci, an jima zamuyi waya"_

 Yana fadar haka ya kashe. 


Bin wayar tayi da kallo tare da saka ta a kirjinta ta rungume tana sauke ajjiyar zuciya, sai lokacin bacci ya dauke ta. 


______

Gurin party ya hadu iya haduwa, komai yayi kyau cikin tsari, yayin da Ko wace Amarya da irin Decoration da akayima Sit dinta ita da Angonta ta, abunde sai wanda ya gani duk da a waje daya za'ai komai. 


Tabbas yau ba karamin taro za'ai ba a garin Zamfara, domin an sanar a media, ana bikin yaran mayan, haka zalika baki daga waje waje suke zuwa domin wannan dinner ta daran yau, wanda zata kasance da misalin karfe 9pm zuwa 12am. 


Tun bayan la'asr aka bude gate, sabo da masu shige da fice, an saka manyan masu tsaro a wajan domin checking da kuma bada kyakkyawan tsoro ga jama'a. 


Gaba Daya Dizhwar yana cikin Busy dan har abokansa sun fara zuwa, 

Ko abinci beci ba daga shi har Jafar din. 


Jafar ne ya kira Humaira danta hada musu abinci, ta bada a kawo musu. 


Shikuwa Dizhwar Coffee kawai yasa Humaira ta hada masa. 


Bayan an gama hada Abincin su Jafar an kai musu, Shima Dizhwar din ta gama hada masa Coffee din, Zata bada akai masa, Anty Amarya ta shigo wajan tana fadin, 

 _"An kaiwa Angwaye abinci kuwa?"_

  kasancewa Humaira basa wani shiri da ita sosai kawai tace da ita. 


_"Eh an kai musu, Dizhwar kawai za'a kaima wannan Coffee din"_


Da sauri Anty Amarya ta amsa tare da fadin, bara a bada a kai masa, ta amsa tare da fita dashi waje. 


Humairah kuwa kasancewar bata waniyi tunanin wani abu ba taci gaba da harkokinta. 


Yayin da Anty Amarya ta bude, wani magani a takarda ta zuba kadan a ciki, harta juya zata bada akai, sai kuma tayi wani tunanin, ta karasa juye sauran maganin gaba daya aciki,  kyalkyalewa tayi da wata irin dariya kasancewar babu me kallan ta, ta hada magani ta juya ta bada akai masa.


Shikuwa dama jira yake, ga kuma yinwa da yake faman ji, ana kawowa, Tun daga bakin kofa ya fara sha, yana hira dasu Jafar harya shanye kayansa gaba daya, yayi masa dadi sosai kuma nan da nan cikinsa ya cika. 


______Koda yamma tayi, Lailah ta tashi tayi wanka tayi abunda xatayi, jin har tym din Dizhwar be kuma kiranta ba, yasa ta kuma neman number sah.


Yana ganin itace kuwa ya dauka, 

_"Babyna bade kin tashi daga baccin bah"_

 

_"Wallahi ban jima da tashi bah,ya hidiman bikin, ai har yanzu kaki ka gayyaceni"_


Shiru yayi dan baya san balloma kansa ruwa.


_"Hello"_

 Ta kuma magana. _"Kina so kizo ne?"__"Eh, sosai mana"_


_"Ok to ki shirya zan aiko mota ta daukeki, saiki shirya"_


Cike da murna da farinciki, Lailah ta amsa. 


Ko Bayan ya kashe wayar, 

yana so in tazo ya Wulakantattah kamar yanda ya tsara, amma ba haka yaso ba, yaga yarinyar in har yana tare da ita, toh dole zai iya kamuwa da santa shikuwa abunda baya fata kenan,dan bazai iya taba hada jini da talaka ba, musamman ita da take yar gidan Kurame. 


Wani haushin kansa ma yaji daya tuna irin zaman da sukayi shida ita. 


_______

Cike da Murna Lailah ta hau dubo kayan da zata saka, wani jan material ta gani wanda suka dinka ita da Rauda da sallah, wani me kyau dan Yadi Biyar dubu takwas, shita dauko tare da mayafinsa da talmin da suka siya, ta dauko fashion dan kunne tukun da abun hannu. 


Bayan ta gama hada duk abunda zatayi amfani dashi, kasancewar Mama har lokacin bata gama yarda da Dizhwar ba, ta sanar mata da Rauda ce ta gayyaceta biki dan in tace Dizhwar bazata yarda bah, 

 Abunda yasa ita kuma ta yarda sabo da taga Raudar tazo bada dadewa bah. 


Cike da murna da kuma farin ciki ta fara shiri tana kwalliya, dan tana so ace *LAILAH-DIZHWAR* tayi kyau. 


Nan ta saka material din ya zauna ajikinta yayi mata mugun kyau tamkar itama Amarya ce, nan ta feshe jikinta da turare me sanyin dadi. 


________

Su Dizhwar an gama kashe kala, an gama shiri kowa yayi kyau, nan aka iso da rantsantsun motoci suka jeru kowanne shida Amaryarsa, duk da cikin gidannne amma saida aka hau mota, nan kowa ya nufi part din da Amaryarsa take, har Dan gidan Waziri Umar Pharouk wanda zai auri Zakiyya. 


Nan Amare aka fara fitowa ana ta musu faman hotona haka ana ta zuba fure a hanyar da zasu fito din.


Dizhwar motarsu bata jima da tsayiwa bah, Husna ta shigo ciki, tare da kara matsawa jikinsa har wani kwantawa take tana musu selfie yayin da Ango aka Sha kunu ko murmushi bama yayi. 


Kara shigewa jikinsa tayi, nan take Maganin Anty Amarya ya fara aiki,Dizhwar ya tsinci kansa ame biye mata, dan yanda yake ji komai ma Zai iya faruwa. 


haka ya rungumeta har suka karasa, ko kadan beso suka sauka daga motar bah. 


Haka suka shiga cikin wajan, sai faman janta jikinsa yake, ita kuma Sai wani kara manne mai take, nan fa suka burge kowa, sai faman hotuna ake musu kamar sa cinye juna haka suke ji. 


Nan kowanne Ango da Amaryarsa suka Zauna a wajan zaman su. 


______

Dizhwar daya jima da aika mota gidansu Lailah, yama manta shab, dan gaba daya yanzu halin da ake ciki ya fita daga hayyacinsa. 


Yayin  da aka shigo Da Lailah cikin gidan sarautar nan, tana zaune bayan mota tana faman kallan irin motocin dake dankare cikin gidan, haka aka karasa da ita har kofar hall din. 


Ahankali cikin takunta najan hankali, ta shiga wajan tana faman taku daidai, saida taja hankalin mutane da yawa, dan gani ta ake kamar wata yar gidan manyan nan. 


Karasawa tayi can, tana kokarin zama, Ganin Amare guda uku da kuma Angwaye uku yasa kanta ya juye, dan ita bama ta gane Dizhwar din nata bah. 


Zama tayi nan aka cika mata gabanta da Abinci da Abinsha, ita kuwa lokacin babu abunda tafi bukata ta gani sama da Dizhwar, sai faman waige waige take, taga ta inda zata hangosa. 


Jin Mc yana fadin, 

 _"Yarima Dizhwar da Amarya Husna suma suna yima bakinsu barka da zuwa"_


Da sauri ta mike tana kara kurawa Angwayan ido, 

  Nan kuwa idanta suka sauka kan Dizhwar, kasa tsayiwar tayi dole ta nemo waje ta zauna tana me kura musu ido, yayin da Amaryarsa take masa magana yana murmushi. _"Innalillah,innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, ba gaskiya bane Lailah, ba gaskiy bane, Mafarki kike Lailah, Innalilahi !"_

 abunda take ta faman fada kenan zuciyarta tana mata wani irin Abu, da bata taba jin irinsa ba tunda take a duniya. 


Da sauri tayi kokarin mikewa dan fita waje ko zata shaki iska Me dadi dan iskar wajan tayi mata kadan, sabo da tashin hankali, amma ji tayi kafafunta kamar an daure su. 


Nan da nan idanta suka kada sukayi jajir dasu. 


Anty Amarya na zaune a gefanta itama, jikinta yana tsuma sabo da abunda ta bama Dizhwar itama shi tasha jira take kawai taga ya fita waje itama ta bishi dan ta biyama kanta bukata, dan tasan nan gaba kadan in har be kasance da mace ba zai iya mutuwa.*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(20)*


   


*Dedicated This page to all my Whatapp Fans, love you irin sosai sosai din nan, Allah ya bar zumunci Nagode sosai da irin soyayyar da kuke nuna min Nagode*😍
__________Cikin sauri ta shiga, tare da janyo Husna gefe, hular ta nun mata tare da fadin, 

 _"Wannan Hular Kamar ta Dizhwar"_


Amsa tayi tare da fadin,  _"itace mana"_


kamar ta nuna mata abun hannun, sai kuma tayi tunanin kar tajI kunya, aje watace ta yarda shi tunda bashi kadai yake bin hanyar bah. 


_"Amma ya akai, hularsa ta fadi kamar wanda bashi da hankali be sani bah"_


_"Toh kode da gasken bashi da lafiya, kuma ina ya tafi"_

 Husna ta fada. 


Wayarta ta amsa ta shiga kiransa amma harta gama ringing dinta be daga bah. 


_"Anty Salima barshi kawai koma menene maji da safe, sabo da dolansa ai yaje wajan daurin aure, babu damuwa"_


Tana fadar haka ta shige cikin jama'a, batare da ta nuna wata damuwa sosai bah. 


Binta Anty Salima tayi tana so ta tuno inda taga wannan abun hannun. 


_____

Haka aka sha shagali aka tashi daga wajan Party kowa cikin farin ciki amma Banda Amarya Husna, shima Jafar ya duba amma be gansa ba, amma be nuna damuwa ba tunda yasan ai yana nan saide in waje suka fita.

Itama haka Husnar duk jarabarta ta hakura, amma tasan koma ina ya tafi gobe ahine karahe, tuda za'a daura musu aure kuma dole yaje wajan daurin auran, in yaso in sukayi auran dolansa ya gaya mata ko ina yake zuwa. 


_______

Dizhwar kuwa saida yaji ya gamsu dari bisa dari babu wani sauran ciwo da yake ji, 

  Gefe ya koma ya kwanta yana maida numfashi, saida yayi kusan awa daya tukun hankalinsa ya dawo jikinsa. 


Da sauri ya mike zaune ganin inda yake, da sauri ya kalli gefansa, ganin Lailah yasa yayi saurin matsawa gefe. 


Ganin kamar bata numfashi bare motsi yasa yayi sauran matsowa ya shiga marin fuskarta Ahankali yana saka kunansa kan kirjinta amma shiru.


_"Innalillahi wa'inna illaihir raji'un, shikenan na kashe Lailah, ashe dama nine ajalin yarinyar nan shiyasa na gaiyaceta wajan nan"_

 Gaba daya hankalinsa ya gama tashi, haka yaci gaba da tashinta amma babu abunda yake motsi ajikinta, ga fyade da yayi mata, gaba daya daga shi har ita da kuma wajan ya bace da jini. 


Da sauri ya mike ya dauki wandansa duk da jinin da yake jiki ya saka, ya nemi kayanta ya saka mata,yanayi yana kuka dan yasan bashi da yanda zaiyi, gashi Anata sallah yama rasa yaya ziyi, gashi kayansa duk sun bace da jini balle ya fita. 


Haka ya dauka ya saka,Ahankali ya bude dakin ya leka ganin babu kowa yasa ya dawo ciki, jin yataka abu ya durkusa ya dauka ganin wayarsa yasa yayi saurin dauka, dubawa yayi yaga lokacin karfe 4:03am, cikin aljihunsa ya saka tare da daukar Lailah ya matsar da ita can gefe cikin kaya ya rufeta da bargunan wajan ya fita daga cikin sakin. 


Ahankali ya fita yana sauri harda gudu gudu ya nufi part dinsu, kana ganin yanda yake dube dube kasan bashi da gaskiya. 


Yana zuwa dakinsu ya bude tare da shiga falon, babu kowa dan haka da sauri ya nufi bedroom dinsa. 


Yana shiga yasa key ya kulle tare da cire kayan jikinsa ya shiga wanka, ya jima a bandakin kafin ya fito, alwala yayi, yayi sallah anan dan bama yasan fita daga Dakin. 


Bayan ya idarnne yaji wata irin kasala ta saukar masa, amma gaba daya hankainsa baya jikinsa, banda tunanin halin da yake cike ga kuma kisa da yayi. 


Mikewa yayi ya koma kan gadon ya lullube dan zazzabi yake ji ajikinsa. 


______

Koda gari ya waye, Jafar fitowa yayi daga dakinsa ya nufi wajan Dizhwar dan ko ya dawo. 


Yana shiga kuwa ya gansa kwance cikin bargo, da sauri ya karaso wajansa tare da budeshi ya taba shi. 


Zafi yaji sosai ajikinsa. 


_"Dizhwar"_

 Jafar ya kira sunan sa. 


Ahankali ya bude ido yana kallan Jafar din. 


Ganin yana rawar sanyi yasa yayi maza ya rufe shi tare da kiran dr. A wayarsa. 


Koda yazo ya auna shi magani ya bashi da kuma allura. 


Sannan ya samu bacci. 


Jafar yana nan yana faman kallansa ganin duk ya rame lokaci daya, zuwa yayi ya sanar ma da Mami abunda ya faru, nan da nan hankalinta ya tashi gaba daya gida ya dauka Dizhwar bashi da lafiya. 

Nan da nan part dinsu ya cika dan ganinsa. 


Husna kuwa kuka take dan ganin halin da ya shiga. 


Koda Anty Amarya taji labari bakin cikine ya kamata sabo da kasancewar da batayi dashi bah, itama abunda ya faru da shi itama ya faru da ita, dadde ita tana da yan iskanta waya kawai zata musu su ,suzo su biya mata bukatar tah,bakin cikinta shine da bata san dawa Lailah ya kasance bah, dan tabbas da be kusanci wata ba saiya mutu, dan haka bokanta ya gaya mata. 


______

Lokacin da ya farka, nan Jafar ya lalabashi danya shirya aje wajan daurin auran. 


Breakfast yayi dan yaji kafin jikinsa, bayan ya gama ci, gaba daya hankalinsa yana wajan gawar nan, fita yayi waje ya samu wani yaran sa,nan ya sanar masa da wata matsalace ta faru yana so, yaje cikin dakin, yayi masa kwatance, ya dauki gawar mace kuma ya dauke dukkan wata sheda yaje ya yarda ta acan nesa da gari batare da kowa ya san da hakan ba. 

  Nan kuwa yayi Naam da abunda ya gaya masan. 


_____

Bayan sun gama shirinsu cikin kayansu na alfarma suka nufi wajan daurin Auran anan masallacin gidan sarautar inda manyan mutane suka halarci wajan, dan babu masaka tsinke. 


Bayan an gama dukkan abunda Za'a yi, aka hada wata babbar walima. 


Amma duk abunda ake Dizhwar dauriya kawai yake dan bayajin dadi har lokacin. 


_______

Ita kuwa Lailah abunda aka saka wannan bawan shi yayi, ya dauketa ya nufi can hanyar Sokoto da ita ya yarda ta cikin wani daji, ya dawo gida ko ajikinsa, sannan yasa a gyara cikin dakin da Abun ya faru,

 Bayan ya dawo ne ya sanar da Dizhwar din aikin gama Ya gama, sai lokacin hankalimsa ya kwanta, sannan yayi masa alkawarin kudi masu yawa, sannan karya sake ya gayawa kowa. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(19)*
__________Zuwa lokacin babu abunda Lailah take banda kuka,


Duk inda yayi sai faman kallansa take, jira kawai take taga ya fita. 


Idannan yayi jajir dashi. Shikuwa Dizhwar zuwa lokacin ya fita daga haiyacinta, sai faman gumi yake, ga wata Mahaukaciyar Sha'awa wanda besan da akwai irin tabah.


Ahankali ya rada ma Husna wani abu a kunne, batare data bashi amsa bah, ya fita da sauri. 


Da Sauri Lailah ta mike haka itama Anty Amarya. 


Da gudu Lailah ta fita dan tasha gaban sah, yayin da Anty Amarya ta fara sauri, Jafar da Asiya suka iso wajan ta tare da me hoto, nan taji kamar zata mutu, sai faman kallan kofa take, haka suka hanata tafita ana ta hoto. 
Lokacin daya fita kofar wajan, yaji cikinsa ya kulle ya tsaya tare dafa bangon wajan, hular dake kansa ya cire tare da yardawa, 

  Karan takun mutun da yaji gabansa, yayi saurin dagowa, duk ya fita daga haiyacinsa. 


Ganin Lailah gabansa yasa ya bita da kallo, Ahankali ta jaraso tana kallansa tana hawaye. 


Saida tazo daf! da shi, tukun ta fara fadin, 


_"Amma ban taba tunanin zaka ci amanata haka bah, ashe dama aure zakayi amma shine ka shigo Rayuwata danka cuceni"_


Ahankali ya mike tare da nufo ta, 


Da sauri taja baya tare da fadin, 

 _"Karka sake ka matso kusa dani"_

 Tana magana tana nuna shi da yatsa tana kuka. 


_"Dan Allah Lailah ki tsaya ki saurareni kada kimin muguwar fahimta haka mana"_


_"Me zaka gaya min,  bayan gashi na gani ido da ido ba lbr aka bani bah, meyasa zaka min haka meyasa ka yaudareni"_

 Ta karasa maganar tare da durkushe kasa tana kuka. 


Batare daya mata magana bah, ya dauketa cak!. 


Da sauri ta bude ido tana ihu, tare da mai Masifa danya ajje ta, garin dukan bayansa abun hannunta ya fadi anan wajan. 


Cikin wani daki ya shiga da ita, inda ake ajje Carpet manya da kuma abubuwan shimfidu kala kala. 


Saida ya shiga ya kulle kofa tukun ya Ajjeta kasa. 


Da sauri taja baya tana fadin, 

 _"Meyasa zaka kawoni nan, nariga na gama gane ko kai waye, ka bani hanya in huce, Allah ya isa tsakanina da kai"_


Tana fadar haka ta nufo wajan zata bude kofar, da sauri yasha gaban ta tare da durkusawa kasa yana mata magana, 

  

_"Dan Allah Lailah kiyi hakuri, ki rufamin asiri wallahi ina cikin wani mahuyacin hali, da in baki taimakaminba zan iya mutuwa"_

 Yana tsugunne a kasan ta ya rike mata kafar ta. 


Idanta ta rintse, tana jin yanda wani mugun sansa yake Kara shiga dukkan illahir bargo da kuma tsoka na jikin tah. 


kamar ta juya ta ji damuwarsa amma tayi saurin fizge kafar ta. 


Ganin haka Dizhwar yaga zata bata masa lokaci gashi kuma jikinsa har ya fara yin weak, yasa ya janyota tare da hada ta da bango ya shiga kissing din tah, tun daga bakinta har huyanta da kirjinta, ga wani Mugun ruko da yayi mata, da karfin tsiya kamar wani Zaki ya fincike yar rigar da take jikinta. 


Hakan yasa Ahankali ya kara tashi babu abunda take banda ihu da kuka,nan da nan ta tuna abunda Mama ta gaya mata . 


Da sauri ta samu ta kwace jikinta ta koma can karshan dakin tana kare kirjinta da hannunta tana kuka tana kallansa. 


_"Dan Allah kayi hakuri, wallahi ni baka cuceni ba, dan Allah karka lalatamin Rayuwarta, wallahi nayi maka alkawarin bazama ka kara gani na bah, zan bar maka gidanka da kuma garin ku, Dan Allah Dizhwar"_

 Tana kuka tana magana harta kai kasa dan rokonsa. 


Shima Kara sowa yayi tare da durkusa a gabanta, da sauri ta kara makurewa jikin bango. 


_"Lailah ke nake kauna kece farin cikina, kece matata da koda yaushe nake mafarkin kasancewa dake, in kika barni cikin wannan halin wallahi mutuwa zanyi, karki min haka dan Allah Lailah"_

 Shima kukan yake kamar yanda itama takeyinsa. 


Babu bakin magana illah,Girgiza kai da takeyi, dan ganin yanda Dizhwar din ya koma kamar bashi ba. 


Cire rigarsa yayi, yayin data rufe idanta ta dan bata san ganinsa gaba daya. 


Da gudu ta mike zata fita, cafkota ya kumayi, tare da turata kan Carpets din, tare da Hawa kanta, yana kokarin cire wando. 


Wani ihu ta saki,kodan mutane zasuji su kawo mata agaji, amma babu wanda yasan tanayin, haka.

  gashi yanayin yanda ya danne ta, ko motsi bata iyawa saide ihun. 


Suna fada haka ta tattaro dan karfinta tana dukansa da yakushinsa, yanda zai rabu da ita, amma saida ya cire skirt din da pant din tukun ya fara kokarin aikata abunda zuciyarsa da duk illahirin jikinsa yake san yi. 


kuka kawai Lailah take tana rokonsa amma ko jinta baya yi, saida ya fara aikatawa tukun bakinta ya fara rage ihun sabo da ta fara fita daga haiyacinta, tun tana kallan fitilar dakin har duhu ya mamaye hasken Dakin. 


________

Ganin har lokacin Dizhwar be dawo ba yasa hankalin,

 Husna ya tashi, nan ta fara neme neme, Anty Salima ta sanar ma, nan itama ta shiga duba san. 


_"Bara na leka waje nagani ko yana can baki yayi"_

  sannan ta fita dan duba sa, amma ganin babu kowa a wajan yasa ta dawo ciki, kan hanyarta na shiga hall din, ta taka Abun Hannu, da sauri ta tsugunna dan dauka, Hular Dizhwar ta gani yarde a kasa. 

  Dauka ta yi, tana dubawa tare da komawa cikin Hall din.
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(21)*
__________

Kobayan an gama Walimar da Memartaba ya shirya, kowa gida ya nufa, yayin da Dizhwar yana zuwa, abinci aka kawo masa, sai bayan yaci ya koshi yasha magani ya kwanata.


_________

Mama kuwa tun bayan da Lailah ta tafi gashi time din anyi magriba, tashi tayi ta fita waje dan ganin bata dawo bah, 

  Kasancewar tasan gidan su Rauda ta tafi shiyasa bata wani damu sosai bah,


Abu kamar wasa har goma tayi shiru, kasa zaune tayi bare tsaye, Daidai lokacin Babansu ya dawo. 


Nan ta nuna masa ai Lailah bata nan har yanzu bata dawo bah,  dan haka shima fada ya kama yima Maman akanme zata bari ta fita duk da sunsan Lailah yarinyace me hankali bazasu zargeta bah. 


Shiru suka zauna ganin bata dawo ba har 11pm, hakan yasa Abban ya fita. 


Kai tsaye gidan su Rauda ya nufa, koda yaje gidan kulle da kwado babu kowa, wani gumine ya karyo masa. 


Yana kokarin tafiya saiga Rauda ta dawo.


Ganin shine yasa ta gaida shi, nan ya hau nuna mata Lailah bata zo bah. 


Haka itama ta maida masa, dan raban da taga Lailah ta jima dan ita yanzu daga wajan aiki take ba wajan biki bah. 


Batare da yace mata komai ba, ya tafi hankalinsa a mutukar tashe, gashi Lailah bata taba musu irin haka bah. 


Haka ya dawo gida duk jikinsa a sanyaye, tunda Mama taga ba Lailah ta fara kuka, nan ya zauna tare da sanar mata be gan ta bah, kuma ba gidan su Rauda taje bah. 


Kuka Mama ta fara tana nuna hannu alamun dama saida jikinta ya bata karya tayi mata. 


Nan de suka rasa abunyi, suka hakura zuwa wayewar gari, amma koda garin ya waye, duk da ba wani baccin kirki sukayi bah, 

  Safiya nayi Mama ta tashi Abban dole sai sunje wajan yan sanda sun sanar musu da batan yar tasu. 


Haka ya hakaru suka je,

  Suna zuwa kuwa suka samu wasu anan waje suka fara nuna masa magana da kurmanci, kasancewar be gane abunda suke nufi sosai bah, suka dauko musu biro da Paper dan su rubuta abunda ya kawo. Su. 


Nan suka zauna Abban ya rubuta yakai musu. 


Bayan sun gama karantawa, suka maido musu da amsar ko tana da saurayi. 


Nan suka rubuta tana dashi amma dan gidan sarkin Zamfara ne. 


Koda suka karanta abunda Abban ya kuma Rubutawa, kallan Juna sukayi, tare da fadin, 

 

_"Amma wannan mutanan basu da hankali, taya zasu ce mana dan sarki ne yake san yarsu, kode dan sarkin mahaukata"_

  Haka suka kora su daga police din suka fita suna Rokonsu amma babu wanda ya kula su. 


Mama zama tayi tana ta faman kuka, ganin abun yaki karewa yasa Abban,fada mata suje su Sami Aminu. 


Kallan sa kawai tayi, tare da goge hawayanta ta tashi tayi tafiyarta ta barsa anan dan koda Lailah mutuwa tayi bazata nemi daya daga cikin yaran nasu ba, balle kuma bata tayi tana sa ran insha Allah zata dawo gareta. 


________

Har yamma tayi anata faman shagali a gidan Sarki domin yaune za'a kai Amare gidan su. 


Gaba daya an gama shirya wa su Jafar Jirgin tafiyarsu. 


Asiya da yan kano suka fara shirin tafiya yayin da Asiya banda kuka babu abunda takeyi, haka itama Husna aka kaita part dinta da Memartaba ya tanadar musu, yayin da Zakiyyah ita Za'a dauketa a kaita gidan ta dake nan cikin garin Zamfara. Jama'a duk an fara watsewa amma Shi Jafar ya ringa ya fada ba ranar zai tafi ba sai washe gari sabo da Jikin Dizhwar. 


Sai wajan karfe 9pm tukun ko wacce aka tafi kaita, gidan shiru duk babu hayaniya duk an tafi kai amare. 


Sai dangin Husna kawai a part dinsu suna shagalinsu. 


________

Lailah kuwa tunda aka kaita wannan wajan aka yarda ta, bata san inda kanta yake ba cikin wannan dajin, tana kwance har zuwa lokacin kamar gawa ko ba numfashi balle Motsi. 


Gaba daya jikinta ya kumbura, gashin kanta duk ya hargitse ga uwar dauda da tayi, duk tayi baki in baka sanda ba da yanzu bazakace ita bace. 


_________


Bayan an kai Amare, dare Yayi wajan 11pm, har lokacin Dizhwar yana daki a kwance, babu zazzabin yanzu a jikinsa, illah Kasalar jikinsa.


Yana kwance akan sofa, shida Jafar, Anty Amarya ta turo kofar dakin nasa. 


Da sallama ta shigo, wata tana biye da bayan ta, sata tayi ta ajje babban tray din daya cika da flasks akansa, ajje shi tasa ayi sannan wacan din ta fita. 


Itama zama tayi tare da fadin, 

 _"Sunna da jiki Dizhwar "_


_"Ywwah"_

 ya fada Jafar yana gefansa.


_"Katashi ka dan daure kaci dan farfesun dana sa ayi maka saikasha magani ko kaji kwarin jikinka"_

  Ta fada tana kallansa. 


Shiru yayi dan baya bukatar komai, amma jin abunda ta fada yasa ya fara Sha'awarci jin ace Farfesune. 

  Amma sai yayi shiru be mata magana bah. 


Jin haka yasa tayi murmushi tunda taji yayi shiru tasan zaici,

 Dan haka mikewa tayi tare da kallan Jafar, 

 _"Pls Jafar kasa yaci ko kadanne, Allah ya sauwake"_

 Ta fada tare da fita. 


Jafar binta yayi da kallo danshi sam!, be yarda da ita bah. 


Tana fita Dizhwar din ya mike zaune tare da fadin, 

 _"Jafar dan zubomin inci dama ina san cin Abu medan yaji yaji"_


Anty Amarya dataki kulle kofa sosai dama dan taji abunda Za'a fada, murna ta kama dan ta saka maganin mallaka aciki, burinta Dizhwar yaci, yana ci kuwa ya dawo a tafin hannunta dan sai abunda tace masa shi zaiyi. 


Banza Jafar din yayi dashi, ganin haka yasa ya mike da kansa ya nufi abincin. 


Hannu yasa ya bude flask din. 


Wani irin kamshine ya daki gancinsa, hannu yasa zai Tun aciki ya fara ci dan baze iya jiran ayi serving dinsa bah. 


Turo kofar da Husna tayi yasa yayi saurin dauke hannunsa daga kai tare da mikewa tsaye. 


Binshi tayi da kallo, tare da kallan Jafar. 


Ganin kallan da takema Dizhwar din yasa, Jafar mikewa yabar wajan. 


Da sauri ta karaso tare da rungumeshi, suka koma kan kujera suka xauna. 


_"Hubby yaya jikin naka? "_

 Shiru yayi mata yana kallan tah. 


_"Baka kaunar matar kane, zaka zo na ka zauna bayan kasan wanna shine ranar mu ta farko ranar da ya kasance mu nunawa juna farin ciki da kuma sun da mukewa junan mu, amma shine zaka ki zuwa kayi zaman ka anan?"_

  Bece mata komai ba, illah kallanta da yake yi. 


_"Kidan zubomin wacan abun, inaso inci yinwa nake ji"_

 Daga shi tayi tare da nufar flask din,  tana budewa taji kamshin maganin, kasancewar suma masu harkanne yasa tayi saurin ganewa. 


Da sauri ta kalle shi tare da fadin, 

 _"Wanene ya kawo wanna abun? "_


_"Ki Zuba min magana ina ruwanki da wanda ya kawo ki kawo Min mana"_


_"Toh wallahi in baka fada min ko waye ya kawo maka ba, bazaka cishi bah"_


Shiru yayi mata yana kallan ta. 


Daukar tray din tayi tayi hanyar fita dashi. 


_"Husna ki maidomin mana meyasa baki da hankali ne"_


Bata kulashi ba sabo da ita tasan abunda ta gani Ta fita, 


Binta yayi da sauri suka fita wajan 12am, tana tafiya yana binta a baya. 


Anty Amarya dake kusa dasu, tana jiran DIZWARH ya gama ci ta kirashi, dan yau tana bukatar shi, ganin Husan ta shiga yasa gabanta ya fara faduwa dan tasan wannan jarabarbar bazata barshi ya ci abincibah. 


Kamar kuwa ta sani ta hangota da flask din tana faman sauri, shikuma yana binta a baya. 


Da sauri ta mike, da kamar bazata fita ba, sai kuma ta tuna irin kudin data kashe kan maganin da kuma tana da hadama gaba daya ta juye. 


Da sauri ta fita tare da tarar Husnar, a tunaninta bata san komai bah. 


_"Ke Husna meye haka baki da hankaline wai ke"_

 Ta fada tare da karasowa wajan. 


Dizhwar kuwa bata masa rai tayi, tsaki yayi ya kOma dan baxai iya jurewa binta haka bah. Gabanta ta tsaya suna kallan juna. 


_"Meyasa kike irin wannan, kefa bakuwa ce, nikuma uwar shice, zai iya sakinki kibar gidan nan, nikuma ina nan daram!, akan me nayi masa kirki zaki hana yaci, kuma ma sabo da baki da hankali da tarbiya kika biyo miji sai kace ba mace bah"_

 Anty Amarya ta fada ranta a bace. 


Tsayiwa Husna ta gyara tare da fadin, 

 _"Ashe ke babar shice, kina da sanin cewar yau in ubansa ya sakeki baza kibar gidan bah, har zakizo kina min wannan maganar, ko a tunaninki kece surukata, toni ko ita wanda ta haifeshin bata isa ta shiga tsakanina da mijina ba in rabu dashi, balle ke, ko an gaya miki bansan abunda kika zuba acikin abin cin bah, ninan da kika ganina karshece, a cikin tafin hannu na kike,da naga dama Sarkin zan aura gaba daya, amman ni Dizhwar nake so, ke bara ma kiji in gaya miki, tunda har muka kawar da mahaifinmu, toh duk wani dan iska ya kuka ga kashi sabo da haka"_

 Tana fadar haka ta saki flask din a kasa ya hude abincin duka ya rube a kasa. 


Bate cewa Anty Amarya komai ba ta nufi dakin Dizhwar din. 


Binta tayi da kallo tare dayin murmushi itama ta koma dakin ta. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(22)*
__________
Koda ta koma dakin nasu, ya kulle kofar, dan yasan zata dawo ta dameshi. 


Nan kuwa ta murda taji akulle, tayi ta faman knocking amma shiru harta gaji ta koma dakinta, ganin hadari ya hado alamun ruwa zai sauko.


_______

Can tsakiyar dare kuwa Ruwan sama ya sauko me karfi, aka sheke kamar da bakin kwarya. 


Duk wannan Ruwan da ake akan Lailah ya sauka, lokacinne ta dawo hayyacinta, Ahankali ta fara bude ido jin har lokacin ruwan yana zuba a kanta ga walkiya da akeyi. 


Tana san ta bude idon amma ruwa da yake sakkowaya ya hanata, tana ji tana gani dole saida ta hakura tukun Aka gama ruwa. 


Wani mugun sanyi takeji domin kayanta gaba daya sun jike da ruwa. 


Gashi ko motsin kirki bata iyawa, sabo da ciwan da jikinta yake mata. 


Hakan yasa ta fara zubar da hawaye, tana daga kwance. 


Kwata kwata tama rasa abunda ya faru da ita, domin ganinta cikin dokar daji, tunaninta yama kasa kawo mata tayayya har tazo nan wajan. 


Ahankali ta fara fadin, 

 _"Mama, mama,Abbana kuzo ku taimakamin wayyo Allah ni mutuwa nayi waya kawoni nan wajan?"_

 Surutai kala kala take a wajan sabo da rudani data shiga ga kanta daya juye, sai karkarwa take haka hakoran bakinta sai haduwa suke, ta rasa yanda zatayi da sanyin datake ji. 


Har gari ya fara haske kayan jikinta sun fara bushewa sabo da iskar da akeyi. 


Duk wannan sanyin a kanta ya kare, tana nan kwance rana ta fara fitowa. 


Ahankali ta haske inda take kwancan, hakanne yasa taji dadin wajan, harta fara daina jin sanyin. 


Karfin hali tayi ta fara kokarin motsawa. 


Amma jin radadi daga kasanta yasa ta kasa, ta koma tana kiran sunan Allah. 


Saida ta jima tana addu'a, tukun ta kara kokarin tashi tsaye, wani ihu ta saki tare da fashewa da kuka jin zafin da taji yafi na da. 


Kuka sosai take tana kiran taimako amma ganin babu me jin ta yasa ta fara jan Jiki a kasa tabi wata hanya wanda bata san inda zata kaita bah, tana yi tana kuka tana hutawa. ________

Koda gari ya waye wajan 10am, Jafar ya gama shirinsa na tafiya, fitowa yayi ya tarda Dizhwar zaune yana shan Coffee. 


_"Aa naga harka fito bade tafiya bah?"_


Kallansa yayi tare da fadin, 

_"an gaya maka nima irin kane, kawai nayi aure saina zauna ina kallanka, tafiya zanyi in yaso kaita zama kaida dakin, Amaryata rana jirana, sabo da Haka, Sokoto zani inna gama abunda zanyi, zan hau jirgi na tafi gida"_


_"Amma bazaka kara ko kwana daya ba"_


Kalansa kawai yayi dan bashi da amsar dazai bashi, fita yayi daga dakin yana murmushi. 


Cikin gida ya shiga ya karya tukun yayi musu sallama, sannan ya nufi wajan Memartaba. 


Saida ya jima tukun ya fito ya koma wajan Dizhwar. 


_"Toh kai zan huce, sabo da haka,ka kula da kanka kuma ka dinga addu'a sabo da kwana biyun nan duk an rasa kanka, nina huce,aci Amarci lafiya"_


Banza Dizhwar yayi masa, sai tasowa da yayi dan masa rakiya, cikin motar ya shiga dan yayi rana sosai. 


_"Allah ya kiyaye inka isa saika kira ni, ka gaida yan gidan, sai nima nazo"_


Kallansa Jafar yayi yana saka Sit-belt tare da fadin, 

 _"Haka zaka ce sai kunzo, yawwa nama manta ban yima Anty Husna sallama bah, in kaje saika gaya mata na huce, a kula Abokina"_

 Ya karasa maganar yana murmushi. 


Cin magani  Dizhwar yayi, tare da fadin, 

 _"Allah kiyaye sai munyi waya"_


Yana fadar hakaya juya ya nufi dakin nasu. 


Shikuwa Jafar girgiza kai yayi yana dariya tare dajan motar ya fita, masu aiki suna daga masa hannu harya fita Daga cikin gate din. 


Nan ya dauki hanyar Sokoto yana faman sauri. 


Wayar shice ya ga tana haske alamun kira na shigowa, ganin Asiya yasa yayi Murmushi tare dagawa. 


Yana tafiya suna waya, har yayi Nisa tukun ya kashe. 


Saida yahau kan Tatin Sokoto tukun ya ajje wayar yaci gaba da tukin.


________

Lailah tayi nisa sosai dan ta fara gajiya, kwanciya ta kumayi tana hutawa dan duk jikinta ciwo yake mata. 


Haka taci gaba da jan jikin dan ta kusan fitowa titi.


Tana ganin mota ta huce, ta fara kokarin daga hannu amma ta kasa, haka ta yi kokarin daga murya tayi ihu nan ma shiru, dole ta kuma daurewa danyin sauri ta fita. 


Ahankali tana fadin, 

 _"Wayyooooh Allah na"_

Tana matsawa harta fito titin gaba baya. 


Tun daga nesa, Jafar yake hango kamar mutun yana rarrafe ko jan jiki ne, ya kura ido, hakan yasa da ya danji tsoro kawai ya huce warsa. 


Ita kuwa ganin motar yasa ta daga hannu, dan lokacin duk karfinta ya kare. 


Ganin ya huceta yasa ta saddakar, ganin wajan dama tudu da gagarene, kawai ta saki jikinta, ta koma baya. 


Ta jikin mirro dinsa yake hango yanda ta koma, tsayawa yayi da motar tare da yin baya yana addu'a cikin zuciyarsa. 


Saida yazo daidai inda yake hangota tukun ya tsaya ya kashe motar tasa. 


Fitowa yayi tare da gangarawa wajan ta. 


Tana kwance a kasa, gashi a rufda ciki bama ya iya ganin fuskarta. 


Bismillah yayi tare da durkusawa ya jirkitatah. 


Zuciyarsa sai bugawa take dan yana da tsoro ba laifi. 


Hannu yasa ya gyara mata gashin kanta, ya kalli fuskarta da duk tayi dirty ga kuma Kumburi da tayi buga da kari ga ciwo. 


Hannunsa yakai wajan huyanta ko tana numfashi, nan yaga ta bude ido, Ahankali idanta ya cika da kwallah, tare da fadin, 

 

_"Wayyo Allah na, ciwo Nake Ji sosai, da ciwo Yaya, ciwo nake ji"_


Kasancewar Jafar akwai tausayi yasa,ya fara kwallah da kokarin daukarta hannunsa yana Karkarwa. 


Ahankali take magana wanda shi kansa besan abunda take fada bah. 


Daukarta yayi, lokacin daya dagota ya mike tsayi ta saki wani kara me karfi, dan ita kadai tasan yanda take ji. 


_"Ciwo nake ji, ina jin ciwo, ku taimakamin, ku ciremin, wayyo, wayyo AllahNa,Mama ta mama kizo ciwo nakeji"_

 Haka kawai take fada tana kuka har ya karasa da ita wajan motar tashi. 


Yayin da shima yake goge hawayan nashi idansa yayi jajir, dan ji yake kamar bazai iya driving din bah. 


A baya ya saka ta, tanata faman surutun nan. 


Shima shiga yayi hannunsa yana karkarwa ya fara tukin yayin daya juya zuwa Cikin garin Zamfarar. 


Haka yayi ta faman sauri dan baya san ta mutu. 


Nan da nan ya shigo cikin gari, kai tsaye babban asibitin kudi dake a garin ya nufa,kafin ya karasa ya kira likitansu dan jin ko yana nan, ya sanar masa gashinan  zuwa da patient kuma emergency ne. 


Kafin su iso har an turo ma'aikata dan daukarta. 


Yana isowa kuwa suka isa wajan tare da dukota, Jafar sai fadi yake,

 _"Kubi Ahankali tana jin ciwo"_


Nan ya bisu aka Nufi emergency da ita, yayin da dr. Ko tsayawa gaisawa basu yiba bayansu, danganin tana cikin neman taikon gaggawan kuwa. 


Zama yayi a wajan, tare da hada kansa da hannunsa,dan wayar sama cikin mota ya barta sabo da yayi mutukar rudewa. 


Sun jima a kanta ciki tukun, kafin Dr. Ya fito. 


Kiran Jafar din yayi, tare dashi suka shiga wajan da take. 


Tana kwance an saka mata karin ruwa da kuma jini, sun canza mata jaya duk inda yake da ciwo sun saka mata Magani,sun gyarata sosai, sun saka mata ruba a cikin hancinta. 


Ba karamin tausayi ta bawa Jafar ba ,kujera ya samu ya zauna kusa da ita yana kallanta. 


Hannunta yake kalla da take bude shi Ahankali, besan sanda ya hada shi da nata ba, wani irin sanyi yaji hannunta ya dauka, damke masa hannun tayi, idanta yana rufe amma kuka kawai takeyi.


Dr. Sai binta yake da kallo, shide yasan tunda yake be taba ganin ta cikin family dinsu ba kuma besn taba. 


Jafar Idansa yayi jajir yayi kuka ya kalli, Dr.cikin Rawar murya tare da fadin, 

 _"Dr. Yaya jikin nata, zata warke ko, ina san ta warke ta hadu da iyayanta, ko waye ya mata wannan cin mutuncin wallahi sai na daukar mata fansa, na dauketa tamkar yar uwata da muke ciki daya da ita, nayi alkawarin zan tsaya mata tamkar yayanta"_

 Ya karashe maganar yana kuka. 


Dr. Din shima tausayi ya bashi, ya dafa shi tare da fadin insha Allah zata samu sauki. 


Dagowa yayi tare da fadin, 

 _"Menene ya faru da itakan hakan?"_


Shima zama yayi tare da fadin, 

 _"Da farko anyi mata fyade, kuma da alama wanda yayi mata fyade yana cikin maye dan tabbas baya cikin haiyacinsa,dan saida aka mata dinki har biyu, sannan kamar an doketa ko kuma sanadiyar yarda tan da akayine daga waje me nisa yasa, jini ya kwanta a bayan ta saida,akayi aiki aka zuke shi, kuma tasha ruwa sosai, hakan yasa sanyi ya kamata, amma insha Allah komai zai daidaita"_


Kuka sosai haka Jafar yakeyi, saida yayi me isar sa tukun ya mike tare da fadin. 


_"Daga Naira daya zuwa millions dukkan abunda ya dace ayi mata ayi mata, zanje in nemi lawyer da yafi kowanne a garinnan inma ya kama zan nemo wani daga wajen gari, sai nabi mata hakkinta wallahi, inaso a bata private room, dan bana san a takura mata"_


yana fadar haka ya fita daga cikin dakin. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(23)*
__________

Koda Jafar yabar asibitin, motar shi ya  nufa, be zarce ko inaba sai wajan saida kaya, Boutique ya shiga ya siya mata kaya masu kyau, tare da takalma, sannan ya kuma ban garan kayan provision , da kuma kayan wanka, tukun ya koma ya bawa Dr. 


zama yayi tare da fada masa, 

 _"Dr. ni duk wannan abun da zanyi, zanyi dan Allah, sabo da haka bana san kowa yasan wannan magana, sannan koda bayan na tafi pls a taimaka inta farfado ta fadi inda iyayantah suke a nemosu, ina ganin in tana ganin wani nata kusa da ita Zata fi jin dadi.


Babu musu kuwa Dr.  Ya bashi amsa da 

 _"Insha Allah za'ayi yanda kake bukata, fatanmu Allah ya bata lafiya"_


_"Ameen Ameen Nagode sosai, sai munyi waya, sannan dan Allah dukkan abunda take bukata, ayi inyaso sai a sanar min koda kudine"_


_"Ba matsala"_

 ya fada tare da masa rakiya. Cike da tausayin Lailah haka Jafar ya shiga motarsa dan lokacinsa ya fara kurewa ya nufi Sokoto.


_______

Koda su Mama suka koma gida, sun kasa zaune sun kasa tsaye haka sukaita faman neman Lailah amma shiru har akayi la'asr babu ita. 


Hakan yasa ko abinci basu iya ci bah, duk inda ya dace suje domin nemanta sunje amma bata nan duk da ba yawo suke bah. 


Bayan sun dawo gida ne sun zauna shiru babu wanda yake yiwa wani magana. 


Abbane ya kalli mama tare da mata nuni da hannu kamar yanda suka saba maganar su. 


Shiru tayi tana kallansa, yana fada mata, 

 _"Ko kuma wannan dan gidan sarkin yasan inda take, tunda gashi shima be zoba kwana biyu? "_


Kallansa kawai tayi, dan itama abunda tayi tunani kenan,abunda yasa bata yi yinkurin fadin hakan ba sabo da Tana tsoran abunda zai biyo baya, karta yima dan manya sharri azo a kamata, da ace tana da kudi ko akwai wanda ya tsaya musu saita iya tarar aradu, toh amma abunne na zamanin nan sai kana dashi akeyi da kai.


_"Baya ma garin gaba daya, ka bar zancan shi kana san kaja mana bala'i"_

 Mama ta bashi amsa, tare da tashi tabar falon. 


________

Tun bayan dasu Abba suka baro gidan su Rauda suka sakata cikin tunanin, ina Lailah ta tafi ita kuwa har ake nemanta haka, dama ita tasan biri yayi kama da mutun, taya za'ai ace, wai Dizhwar kesan Lailah tsakani da Allah har ya gaya mata zai aureta ita kuma ta yarda sabo da bata da hankali, yayan sarakai da basa auran talaka, daga jinin sarauta sai kuma me Naira, dama tasan lalatata zaiyi ya rabu da ita. 


Ahankali ta janyo wayarta tare da duba number sa da tun ran nan ta dauka, amma kullum in tayi tunanin kira sai taji tsoran karya mata wulakanci, amma tunda yanzu taga dan harkane dole ta neme sa ko itama za'a dama da ita. 


Ahankali ta shiga duba kudin wayar tatah kartaje tana kiransa kudin su kare ya dauketa kamar harka. 


Nan kuwa ta duba akwai sauran bal 85:30.

  

Murmushi tayi tare da kiransa, gabanta sai faduwa yake amma haka ta daure ta na jiran ya daga ta ji abunda abunda zai fada. 
Shikuwa Dizhwar yau koda yayi wanka kin fita yayi dan baya san takura, haka zalika yaki jinin Husna ta shigo masa daki, gashi gaba daya yanzu tun abunda ya faru tsakaninsa da Lailah ya rasa sukuni duk da ba acikin haiyacinsa yake ba, hakan ya sa bashi da buri domin ya kuma samun hakan, cikin nutsuwa ko yaji dadi a ransa. 


Ganin wayarsa tana ringing yasa ya dauka yana ganin me kiran, dayaga bakuwar number kin dauka yayi, yaci gaba da kallansa. 


yana ji harta katse, aka kuma kira amma be daga bah, sa'a na uku tukun ya Daga. 


Koda ya daga beyi magana bah, haka Zalika itama Rauda tsoro da kuma bugun da zuciyarta take yasa ta kasa magana. 


tsawan mintina amma babu wanda yace kala, 

 Ganin ana ci mata kudi yasa ta fadin, 

 _"Assalamu Alaika yakai kyakyawan tauraro acikin taurari, kasaitaccan Jarumi cikin dimbin jarumai, da fatan ka yini cikin koshin lafiya da kuma farin ciki, ina maka fatan alkhairi a koda yaushe ka huta lafiya"_

  Tana fadar haka ta kashe, 


Rufe idanta tayi tare da Rungume wayar tana sauke ajjiyar zuciya dan bata san ta inda maganar tatah take fitowa bah. Shikuwa Dizhwar jin wanga batu, ya shiga da'irar tunani, dan tunda yake babu wanda ta taba kiransa ta gaya masa hakan sai wannan a karo na farko, abun mamakin ma anan shine aina ta samo wannan number tashi, babu wanda yake kiransa da ita daga Jafar sai Lailah. 


Hakan yasa ya dauki wayar da bin Number badan komai ba dan yasan wacece take masa magana haka. 


Koda ya kira ta shiga, tana fara ringing bata jin ma ba aka dauka tare dayin sallama. 


_"Ywwah, dama inasan in tambaya da Allah ko zan iya sanin me magana?"_


Murmushi me sauti tayi tare da fadin, 

 _"Tabbas mana, mezai hana a baima zuciyar kyakkyawa,ma'abocin Murmushi da kamala abunda take bukata, saida zai dan dauki lokaci kafin kasan hakan, domin gudun karta bata masa rai"_


Ajjiyar zuciya yayi tare da fadin, 

 _"Look!,ba wani abu nakeso ki gaya min ba face inasan ki gayamin inda kika samu wannan number?"_


Shiru Rauda tayi kafin daga bisani tace, 

 _"Nasan zakayi mamaki amma, ba abun mamaki bane tunda sauda yawa hakan ta faru musamman ga kawaye ko kuma ince abonkan tarayya, na dauka cikin wayar kawata ne dumin in dinga gaida kai, wato Lailah"_


Gaban sane yayi mugun faduwa jin an ambaci sunan Lailah. 


Jin yayi shiru be bata amsa ba yasa ta fara fadin, 

 _"Hello, hello! , ko kayi mamaki ne, dan Allah ka kwantar da hankali wallahi zanyi maka dukkan Abunda Lailah take maka koma fiye da hakan, ka taimaka kar ka ki amincewa dani Dizhwar"_


Banza yayi da ita ya kashe wayar, tare da mikewa ya nufi fridge dinsa tare da shan ruwa me sanyi tukun yaji dadi cikin ransa. 


Yana tsaye a wajan yana kokarin maidawa ya rufe, Husna ta turo kofar falon. 


Katan Hijab ne ajikinta, fuskata tasha uban makeup sai faman yanga take,  ahankali ta cire hijab din jikin nata, wani shegen skinny jeans ne a jikinta yayi mugun kamata sai riga iya jibiyarta, wanda gaba daya ana ganin saman kirjinta ya fito waje sosai, ta zubo da gashinta bayanta da kuma saman kafadunta. 


Shikuwa tsaye yayi yana kallan ta, dan yama kasa maida Ruwan cikin fridge din ya rufe. 


Ahankali ta taku, cikin takun jan hankali ta karaso wajansa  tare da rungumeshi, numfashin sane ya kusan daukewa dan dama kamar tasan yana bukatar hakan. 


Be hanata ba kuma be taba tabah, dagowa tayi ta kalli fuskarsa tare da shafa hannunsa har izuwa inda ruwan yake ta amsa tare da sakawa a fridge din ta kulle. 


Cikin muryar Shagwaba ta furta, 

 _"Hubby pls ka kaini Kan kujera in zauna kafata tana mun ciwo"_


Kallanta kawai yake dan ta bashi mamaki beyi tunanin haka Husnar take ba, dan ta tafi dashi sosai, ba musu ya dauketa tare da ajje ta kan daya daga cikin sofa wajan, shima ya xauna a gefan ta, ahankali ta matso tare da hawa kan ciyarsa kamar babyn da za'a shayar haka ya dauketa, sai faman masa magana take cikin Shagwaba. Yayin da suna cikin wannan yanayi Anty Amarya ta shigo dakin babu sallama, ba karamar girgixa tayi ba ganin Husna kan cinyar Dizhwar gashi shima yana kokarin biye mata harda shinshina huyanta ya rufe ido. 


Gyaran murya tayi, yayin da Dizhwar dinne ya iya dagowa ya kalle ta ita kuwa, Husna duk da taji shigowar Ta bata fasa abunda take bah. 


Da er ta iya fadin, 

 _"Ina san Magana  dakai Dizhwar "_


Kallan Husna yayi, ita kuwa bama shi take kallo bah. 


Shiru yayi mata be bata amsa ba illah kallanta da yake. 


_"Ke ki dagasa mana inasan magana dashi"_


Wani irin kallo Husna tayi mata tare da fadin, 

 _"Zance bakiga aikin lada muke ba, sabo da haka zaki iya bari, in ya gama diba sai kuyi, dan nasan maganar taki bata kai abunda yake samu anan bah"_


Kamar ta kurma ihu haka taji, dakewa kawai tayi tare da fadin, 

 _"Ke kin isa ki hana ni ganinsa kedin banza kedin hofi"_


Ahankali ta mike daga kansa bayan tayi kissing lips dinsa, sannan ta karaso gaban Anty Amarya tare da fadin, 

 _"Wallahi wallahi Samira kina shige min hanci da kufindine, duk ranar dana fyatoki ina ganin abun bazai mana kyau ba, in banda iskanci da wulakanci kinsan yanzu bashi kadai bane amma sai ina cikin wasa da mijina zakina zuwa kina saka mana ido, in yazo wajan naki ubanme zaiyi miki"_

 Ta fada cike da tsiwa da rashin kunya. 


Shikuwa Dizhwar da yana zaune an gama dashi baya a cewa ko uffan!. 


Hannu ta daga xata mareta, matsawa tayi tare da fadin, 

 _"Kul!  Kada ki sake kiyi wannan gangancin, wallahi kika bari hannunki ya tabani, saikin gammace kida da karatu, ki fitar mana daga daki inba haka ba naci miki mutunci dan Wallahi duk bala'inki nafiki"_


Rasa abunda Anty Amarya zatace tayi, illah tsaye da tayi tana juya maganganun dan sun mata ciwo matuka. 


_"Ni kike gayawa wannan maganar, zaki gane kuranki, zakisan da wanda kikeyi ba, banza karuwa"_


Dariya Husna ta kama harda rike ciki, ta juya tana fadin, 

 _"zan nuna miki kuwa ni cikakkiyar karuwace"_


Tana gama fadar haka, ta daga hanunta sama tare da fadin, 

 _"Hubby bacci nake ji ka kaini daki mana"_

 Kamar kuwa rabbot, haka ya dauketa suka shige daki aka bar Anty Amarya tana zara ido. 


Wani bakin cikine ya kamata wanda bata taba jin irin saba, tabbas tasan ba hakanan Husna tabar Dizhwar ba lallai itama yakamata ta tashi tsaye, kuma sai tayi maganinsu. 


Juyawa tayi ta fita daga dakin tana masifa ita kadai. *ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(24)*
__________

Dakinta Anty Amarya ta nufa, ranta ko kadan babu dadi sabo da abunda Husna tayi mata, ko kadan bata so Asirin Husna ya fara aiki har haka ba jikin Dizhwar taso ace natane ya fara. 


Yanzu tasan bata da wata manufa daya huce itama ta afka masa nata, amma yanzu ita da bata tare dashi tayaya, zatayi, saide in tayi ma Bokan bayani daya karkato mata da hankalinsa gareta in kuwa ba haka ba bata da wata manufa, ita de ko sau daya ne Dizhwar ya kasance da ita.


Dabara ce ta fado mata, babu abunda take bukata yanzu sama data bata ma Husna rai, tasan kuma tabbas abu daya ne zai iya bata mata rai, in har ta ganta tare da Dizhwar, Camera ta dauka tare da fita ta nufi part din Husnar. _______

Husna kuwa koda Dizhwar ya kaita dakin,  kin yarda tayi daya ci gaba da taba ta, dan kar abun yayi nisa sabo da akwai plan din da suke shiryawa ita da Anty Salima, dan haka haka ta lallabashi har suka fara bacci, tana ganin shima yayi baccin ta mike ta fito falon tare da zira hijab dinta ta fita daga dakin.
Part dinta ta koma, tare da yin wanka ta canza kaya, tana zaune bakin gadonta, Hadimanta suna mata gyaran gashi, ita kuma tana chat da wayar ta. 


Anty Amarya ce ta shiga har cikin bedroom dinta, ganin Anty Amarya yasa duk Suka fita waje. 


Husna batare data kalle tabah, ta nuna mata wajan zama. 


Bata xauna ba ta mika mata Camera da take hannunta, kallan Camerar tayi tare da kallan Anty Amarya.


Murmushin mugunta tayi mata tare da zama ta dora kafa daya kan daya, tana jiran Husna ta gani, ta ga halin da zata shiga ko Kuma yanda zatayi. 


Ajje wayar tayi a gefe tare da daukar Camerar, Ahankali ta shiga ganin Pics din da Anty Amarya ta dauka da Dizhwar a dakin garden data kaishi. 


Da Sauri Husna ta mike tsaye, gaba daya fuskarta da yanayin annurinta ya canza, kallan Anty Amarya tayi, fuskarta cike da damuwa. 


Kamar zatayi Kuka tace da ita, 

 _"Wayyo Allah na, wannan menene haka, garin yaya Dizhwar ya tsaya har hakan ta faru, dama ashe ba suna yake bah, bara na hada kayana nabar masa gidan sah, tunda dama Cin amanata ake, kuma Saina tuna muku asiri"_

 Ta karasa maganar tare da tsayawa gaban Anty Amarya, sannan ta saki fuskar ta tare da cilla mata Camerar ta. 


_"Haka kike so kiji na fada shine harda wani tasowa da nunamin kenna"_

 Husna ta fada tana kallan tah. 


_"Toh kin bata lokacin ki a banza, sabo da duk wanda ya fiki wallahi ya riga ya fika, ko An gaya miki Son da nake masa na Karya ne?"_


  _"Dukkan abunda kika sani game da Dizhwar nikuma Na dame ki, sabo da haka ki koma da baya sabo da wannan yakin ba naki Bane,tun lokacin da mahaifin Dizhwar ya shaida min cewar shine zai auran, toh gaba daya na maida hankalina kansa, dukkan wani Motsi nasa ya kasance tamkar a cikin tafin hannuna yake, kin nuna min kuma Naji babu dadi,amma ki sani nikuma full video garine na abunda kika masa tun daga lokacin da kika Kirashi har lokacin da kika maida shi daki, kin hana shi Yaje wajan kamun bikin mu, banji dadi bah, sannan kin hana shi ya tsaya wajan dinner kinyi kokarin biyan bukatarki dashi, shima, banji dadi bah, hakanyasa ya yima Lailah fyade kuma burinki ya cika, duk da nasan babu abunda kika sani game da haka, Sabo da haka abunda nake so dake,ki bace min daga daki, dan in har kika bari Na fara saka ido a kanki wallahi duniyar ma saita gagareki bama gidan nan bah"_


Cike da Al'ajabi Anty Amarya batare da tace komai ba ta fice daga dakin da Camerar ta a hannu. 


Tsaki Husna tayi tare da hayewa kan gadon ta janyo wayar ta. *Ta Yaya Husna tasan Batun Lailah?*


Kamar yanda ta fada, tun sanda Baban Dizhwar yayi mata alkwarin auransu, ta saka yara cikin masu aikin gidan dansu dinga kalle mata shige da ficansa da kuma dukkan abunda yakeyi, hakan yasa duk sanda zai fita saita sa an bishi a baya, anan ne ta gane yana zuwa wajan Lailah tun lokacin suna tsowan layinsu, hakan yasa hankalinta ya tashi ganin Dizhwar yana son Lailah, dan haka saita ci gaba da saka Ido akan duk wani motsin su. 


Ta nanne ta gano kawar Lailah wato Rauda, dan haka har gida tasa aka dauko mata Rauda ta zauna tare da ita, gaba daya ta gaya mata karya da gaskiya a tsakaninsu Wato Lailah Dizhwar din,  jin hakan yasa ta bata aiki akan ta dinga bugar cikinta tana gano Mata bayanai akan hakan. 


Ta nan ne ta gano irin son da Dizhwar din yake mata a ranar da taje gidan nasu, nan take kuwa ta sanar ma da Husna abunda yake gudana, dan hakanne yasa bataji dadi ba kuma ta kara dan marar hallakar da Lailah kota halin kaka. 


Sabo da haka taci gaba da bincike ba dare ba rana ta hanyar da zatabi Lailah tazo wajan bikinsu dan tasan ta hanyar Dizhwar ne kawai za'a iya hallakar da Lailah. 


Koda ta sami Dizhwar yana waya akan zai saka a dauko masa Lailah, saita riga shi da hakan, ta tura drivan ta daban, tun kafin na Dizhwar yaje nata ne ya fara zuwa, koda na Dizhwar yaje bata nan dan haka yai ta kiran Dizhwar danya sanar masa da bata fito ba. 

  Amma Dizhwar be daga wayar tashi bah. Bayan nan lokacin da Anty Amarya tasa a kaima Dizhwar Coffee din nan, akan idan Husna dan Yarinyar ta aka bawa ta kai masa,saida ta gama gane abunda ke ciki, tunda taga Anty Amarya zata bada akai dan bata yarda da ita ba, bata nuna damuwar taba domin ta riga da tasan dukkan abunda ta zuba aciki shiyasa tayi kokarin kara tayar masa da hankali dan abun yayi aiki. 


Tunda Lailah tazo wajan Party, Husna tana kallan duk wani motsi nata da kuma Anty Amarya, shiyasa bata hana su ba, tana sane taci gaba dayin abunda dole Dizhwar zai kuma rudewa. 


Ana cikin hakanne ta janyo shi wajan kunna ta tare da sanar masa da ya fita waje tana zuwa,

Ba musu kuwa ya fita,sabo da shi kadai yasan yanda yake ji a lkcn, tana ganin haka ta duba wajan Lailah ganin bata nan Farin ciki ya kamata ta tura su Jafar Wajan Anty Amarya danyin Hoto, batare da kowa yasan hakan ba, ita kadai take shirya abundata. 


Gaba daya dakunan dake wajan hall din tasa aka Kulle su sai guda daya kawai aka bar musu, nanne Inda Dizhwar din ya shiga,tasan bazai iya jurewa yabar wajan ba. 


Koda gari ya waye, tasan sanda Dizhwar yabar dakin dan haka da kanta ta kuma shiga dakin, nan ta tarda Lailah a kwance,  dariyar mugunta tayi mata, tana cikin hakanne taga ashe bata mutu ba tana kokarin farfadowa danta tashi,  ganin hakanne yasa ta dauki wani katan katako tayita buga mata a baya har saida taga ta daina motsi tukun ta yarda shi, hakan yasa duk jikin Lailah ya kumbura ga kuma duka da taci har jini ya kume mata. 


Bayan ta fita ne kuma, Dizhwar yasa aka kai gawar tata aka yarda, hakanne ya tabbatar mata da An yarda Lailah ta gama da babin ta saura kuma Taji da soyayyar Dizhwar da kuma Yin maganin Anty Amarya. 


Amma kuma bata sani ba, duk ta gama haukanta dan duk Kudin data bawa Rauda a banza domin itama tana shirin shigowa Rayuwar Dizhwar din, dan ko Kadan bata jin tsoran Husna, dan ta gama Sanin ko wacece ita, ko Kuma waninta, bata da buri daya huce Dizhwar din ya amince da ita, itama a dama ta itan. 


*Wannan kenan*
________

Bayan kwana biyu da wannan abun da yake faruwa, babu wanda yasan Halin da Lailah take ciki har yanzu, haka zalika suna bata kulawa sosai a asibitin domin burinsu be huce ta farka bah. 


______

Shima Jafar ko bayan ya koma gida, dama an riga da an kai Asiya part dinta cikin gidan nasu, hakan yasa ta nuna fishinta dan rashin zuwa da huri da beba, nan ya sanar mata da dukkan abunda ya faru, amma baya san ta sanar ma da kowa, itama ta tausayawa Yarinyar Sosai kuma tana mata addu'ar samun sauki. 


________

Yau tunda safe, Dr. Yana zuwa dakin Lailah ya nufa dan duba jikin nata, koda yaje idanta biyu ya sameta. 


Ahankali ya karasa kusa da ita tare da fadin, 

 _"Sannu kinji"_


Kallansa kawai take batare data masa magana bah, 


Haka ya shiga duba ta harya gama ya fita daga dakin. Kallan wajan kawai take dan tasan de asibiti ne, amma tunanin da take anan taya tazo asibiti kode ta haukace, daga ta farka ta ganta acan saita farka ta ganta acan, gashi duk inda ta farka babu wani wanda ta sani, kode a lahira take, shine tambayar da take gashi. Babu me Bata amsa. 


Dan karfin hali harso take ta mike zaune sabo da ta tabbatarwa kanta, amma taji ta kasa dan har lokacin tana jin ciwo bana wasa bah. 


Tana kokarin tashinne, wata Nurse ta turo kofar tare da shigowa ganin idan Lailah biyu yasata yin murmushi tare da fadin, 

 _"Sannu ya jikin naki"_

 

Sai lokacin ta danji dadi, ganin mace yar uwarta tana mata magana, 


Ahankali ta furta 

_"Da sauki"_


_"Allah ya kara sauki, ko kina san ki tashi xaune ne"_


Gyada mata kai tayi alamun eh. 


Ajje tray din hanunta tayi tare, da hada mata pillow a bayanta ta taimaka mata ta zauna. 


Binta kawai take da kallo, 


_"Ko zakici wani abunne? "_


Girgiza mata kai tayi dan bata san cin komai, sabo da har yanzu bata gama yarda da suba tukun. 


Sannu ta kara mata tare da fita daga Dakin bayan ta canza mata drip din. 


Cigaba tayi dabin jikinta da kallo, gaba daya ta rame sosai tayi fari kamar ba ita bah, har so take ta ganta a mudubi,  sai lokacin Abbanta da Ammi suka fado mata, daurewa tayi dan taba san yin kukan, amma bata san inda xata gansu ba gashi tana san ganinsu ko zata ji dadi. 


Ahankali ta kuma jingina da pillow, bayanta yana mata ciwon, idanta ta lumshe tana tuna abubuwa da dama. 


*LAILAH-DIZHWAR*,sunan na ya fado mata. 


Da sauri ta bude idanta tana kalle Kalle. 


_"Innalillahi wa'inna illaihir raji'un"_

 Take ta fada cikin zuciyarta dan bata san tuna wani abu me kama da wannan sunan dan tasan ta sanadiyar hakan ta shiga wannan bala'i, toh amma tasan ba ita kadai hakan ya shafa ba, shi ina Dizhwar din yake, ko shima bashi da lafiya, 


Hawayene ya fara zuba mata, 

Allah yasa shima besha irin wahalar data sha bah, sabo da tana tausaya masa, bata san wani mugun abun ya samu Dizhwar dinta,wajan kofar take kalla ko Allah zaisa wani ya shigo ta tambaye sa inda Aka kai Dizhwar din. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(25)*
__________
Tana nan zaune, tsawan lokaci har zaman ya fara mata rashin dadi. 


So take wani ya shigo, dan tana so ta tambayi wani dan gidansu ma amma babu wanda ya kara waiwayar inda take ma.


Jin an murda kofar yasa da sauri ta kalli kofar, Dr. Din daya shigo da farko ne ya shigo yanzu ma. 


Shiru tayi gashi tana san masa magana amma ta kasa. 


_"Sannu, ya kikejin yanayin jinkin naki yanzu?"_


Ahankali ta furta da sauki, dan zaman da tayi ta tuna dukkan abunda ya faru da ita tsakaninta da Dizhwar sai lokacin ta tabbata da bata da Laifi laifinsane da yayi mata fyade, to hakan yana nufin baya santa kenan tunda ya nemi ya lalata mata rayuwa ko kuwa hakan soyayyace, abunda ta kasa ganewa kenan. 


_"Zaki iya tashi ne "_


Girgixa kai tayi alamun aa, dan har lokacin tana Jin zafi daga kasan ta, kuma tasan bazata iya tafiya bah. 


_"Dan Allah aina nake ne? "_

 Ta fada tana kallansa, nan da nan idanta ya ciko da kwallah. 


_"Kinga, kar kiyi kuka ki kwantar da hankalinki, nan asibiti ne, kuma a garin Zamfara, kinji ki nutsu, dukkan abunda kike bukata ki fada za'a miki"_

 Dr. Ya fada cikin lallashi, dan shima yana tausayin Lailah. 


_"Menene sunanki?"_

 Ya kuma tambayarta. 


_"Lailah, Lailah Muktar shine sunana"_


_"Ywwah Lailah, sannu kijin, zaki samu sauki ki koma gidanku, yanzu bara azo a kawo miki kaya, sai ki tashi ki lallaba ki daure ki shiga toilet"_


Gyada kai tayi, kafin ta kuma dago da kanta,tana kallansa, 

 _"Ina Abbana da Mama suke?"_

  Itama ta tambayesa. 


ya uma tambayarta, 

_"Anan garin suke? "_


_"Eh"_

Ta fada tare da masa kwatancan gidan nasu. 


Yaji dadi sosai dan shima yana so yaga ta samu nutsuwa kuma hankalinta ya kwanta. 


_"Toh insha Allah yanzu zasu zo, kinji, ki kwantar da hankalinki"_


Naam tayi da maganganunsa, harya fita daga cikin dakin. 


Be jima da fita bah, saiga  matar dazu ta dawo cikin dakin. 


Batare da Lailah ta kalle tabah, kanta yana kasa taji shigowarta, gaban gadan ta tsaya tare da fadin. 


_"Sannu, Kozan iya jin sunan patient din tamu"_


Dan murmushi Lailah tayi me sauti tana goge idanta tare da fadin, 

 _"Sunana Lailah Muktar"_


_"Allah sarki Lailah, ni kuma sunana, Sister Zainab Ahmad, ki daukeni kamar kawarki, nice me kula dake, dukkan abunda kike bukata koda wani ya shigo ki ce kina nemana, yanzu zan hada miki ruwan wanka, danki gasa jikinki kiji dadi"_


Tunda Zainab ta fara magana babu abunda Lailah ta furta, tana jinta  amman kanta yana kasa. 


_"Toh Nagode"_

 Abunda Lailah ta fada kenan. 


Murmushi Zainab tayi tare da shiga toilet din, bata jima ba ta fito tare da cire mata drip din, sannan ta taimaka mata ahankali ta sauko daga kan gadon tana dingishi, cikin kayanta ta dauko mata Takalmi ta saka, ahankali take takawa tana rike Zainab din dan tana jin ciwo. 


Koda ta kaita toilet din, bata ji kunyar tabah, ta yarda da duk abunda zata mata, saida ta gasa ta sosai tukun ta taimaka mata tayi wanka tayi brush da alwala tukun ta fito da ita. 


Mai ta shafa mata, ta dauko mata kaya mararsa nauyi cikin kayanta, ita kawai kallanta take dan ita bata san daga ina duk wa'en nan abubuwa suke zuwa bah. 


Duk da ta fada sosai amma tayi kyau kamar ba ita bah, itama kuma taji dadin jikin nata. 


Zaunar da ita tayi kan kujera, ta hado mata tea tare da chips da Omelet,dadi taji dan cikinta ta dan fara jin yinwa. 


Da kanta ta riga ci, harta gama, Ita ta amshi kayan ta fita dasu tare da taimaka mata,Sallah tayi,tukun ta koma kan gadan ta maida mata drip din tukun ta fita daga dakin. 


Ajjiyar zuciya Lailah ta ajje dan ba karamin dadi taji bah. 


_______

Har zuwa wannan lokacin Mama ta kasa hakura da Lailah kamar itama tayi cuta dukta rame bata iya cin komai, koda Abba ya takurata amma bata ci, kullum Bata da aiki sai Kuka da addu'ar Allah bayyana mata Lailahr ta, domin duk ta fiye mata tarin mazan da ta haifa. 


Yauma koda ta tashi da safe, kamar yanda ta saba bata ci abinci bah,tana zaune de akan kujera dan ta rasa abunda yake mata dadi. 


Koda Abba ya fita ya ganta, zama yayi kusa da ita yana mata magana, amma kin kallansa tayi, dan tasan maganar tasa be huce ta tashi suje wajan Aminu ba ko a samu waya a kira Ahmad,ita kuma taki yarda dan data kirasu gwara kar a nemo Lailah.


ganin haka yasa shima ya fara masifa, binsa tayi da kallo yana nunai, 

 _"Ke kin fiya taurin kai, ace bazaki yarda a kira su bah, in basu ba muna da wasu ne, da zasu iya taimaka mana, kina batamin rai in har baki yarda ba, wallahi ni zan tafi ni kadai, tunda naga kamar baki damu da Lailah bah"_

 Yana yi da karfinsa yana nuna hannu alamun fada. 


Abunne ya kona mata rai, ta kama kuka, itama tana bashi amsa, 

 _"Ni baxani ba na gaya maka, inda sun damu damu zasu tafi su barmune kamar bamu muka haifesu bah, zance wajan zama ma rasawa mukayi, zakace in basu ba babu me taika mana, yanzu saika gaya min agidan wa muke acikinsu, wallahi nagaya maka bazanje wajan su bah, suje can zasu gani inde duniya ce, ni daman bani na haifesu bah"_

 ta karasa tana kuka tare da fita daga dakin da takalmanta a kafar ta. 


Shima Yasan basu kyautaba, kuma basu musu adalciba, abunda yaketa gudu gashi yau ta fara dana sani da haihuwarsu, duk da bayinta bane, tana hakuri bata taba nuna damuwarta game da abunda suke mata, amma yasan tabbas akan Lailah babu abunda bazata iya bah.


Fita tayi daga gidan tana goge hawaye, tana budewa taga mutun tsaye da alama bugawa yake, tsaye sukayi shida ita suna kallan juna, yana jiran yaji tayi magana amma shiru, amma ya lura da yanayin fuskarta da alama Kuka tayi. 


_"Sannu baiwar Allah, dan Allah dama tambaya nake ko nanne gidan su Lailah Muktar"_


Tunda ya fara maganar take bin bakinsa da kallo dan gane abunda zai fada, 


 Shikuma tsoro yaji yasa yake fadar maganar daki daki dan yaga kamar bata da hankali. 


Ganin bakinsa ya fadi, Lailah da kuma Muktar yasa ta nuna masa. 


_"Ita bata jin abunda yake fada, mijinta ma baya ji, amma taji kamar yana neman wani abu"_


Kallanta yayi, kamar yace mata sai anjima sai kuma ya biye mata kasancewar ya gane abunda take nufi ya nuna mata, suna da y'a budurwa. 


Da sauri ta gyda masa kai, alamun eh, ta girma kyakkyawa, amma babu ita. 


Shikuma ya zata ta mutu, saiya bata hakuri zai tafi, da sauri ta rugasa tare da nuna masa, ya rubuta mata a takarda wa yake nema. 


Saida ya kalleta sosai, ya tabbatar tana da lafiya, sannan ya dauko biro a gaban aljihunsa tare da memo karami, ya rubuta mata,

 _"Ina neman iyayan Lailah Muktar"_


Mika mata yayi, kasan cewar ta dan iya karatu,ta gane abunda ya rubuta, da sauri ta gyada masa kai tana nuna masa sune iyayanta, tana ina, ya tsaya, ta maza ta ruga ciki tare da janyo Mijinta tana nuna masa abunda ya rubuta a jiki, nan kuwa ya nunawa mutumin alamun sune iyayanta. 


Shima sun Bashi tausayi da dariya, ganin yanda suke kaunar yar tasu, zaisu yaga haduwarsu da ita, shin tabbas shine iyayan nata, maybe itama kuramance, ikon Allah, shi kadai yake magana cikin zuciyarsa. 


Nan kuwa ya nuna yana son kaisu wajan ta babu abunda Mama ta koma yi cikin gidan, Abbane ya kulle gidan dan ita tuni ta shige cikin mota. 


Koda ya gama abunda zaiyi shima shiga yayi, batare da sunsan inda aka nufa dasu ba sukayi shiru, abaya suna jiran ganin ikon Allah. 


Yayin da Mama babu abunda take sai godema Allah. 


______

Yaseer kuwa ansha biki da Saudat duk da kuwa baya so, bayan bikinsu da Kwana biyu ya koma Makaranta tare da matarsa duk da ba hakan yaso Bah, 


Ai lokacin hankalin Hajiya Mariya ya kwanta dan dama ita bata san tarairayar su da Lailah shiyasa tayi yanda zatayi ta takurashi ya auri Saudat dan yabar Lailah kuma anyi hankalinta ya kwanta yanzu kuma saisu rabu da su. 


__________

Daidai baban asibiti Motar tayi parking, bitowa sukayi nan ya jagorancesu har zuwa dakin likitan daya turasa ya dauko su. 


Koda yasa su tsaya daga waje yana zuwa. 


Zama sukayi suna kallan wajan, mama kuka ta fara tana nuna hannu , 

 _"Ni nasan Lailahta bazata yi abunda ba shikenan bah, nasan saide in hadari tayi shiyasa bata dawo Gida bah,Allah yasa abun beyi muni bah"_

 Shine bunda Mama take ta faman fadi. 


Koda ya shiga wajan likitan, sanar masa yayi an samo su, amma yasha wahala dan gaba dayansu kurame ne.


Mamakine ya Kama Dr. Din jin an fada masa iyayan Lailah kuramene. 


Koda ya fito ya gansu, hannu ya mikama Abba suka gaisa, sannan ya jasu dan suje wajan Lailah. 


Yana tafe suna binshi a baya. 


Ita kuwa tana kwance, dan bama tajin bacci kallan tv, take, amma inka kalle ta a nitse zakaga ba tv take kallo  ba, ta tafi duniyar tunani, tunanin ta kuwa be huce, tashin hankalin data fada bah. 


_"Yanzu ina su, Mama sukazo Mezata fada musu ya sameta,dan bata san susan anyi mata fyade, gashi taji ance wasu in aka musu fyade har ciki suke Samu, yanzu ita inta samu ciki shikenan haka za'a dinga cewa danta shege, gaskiya hakan ba soyayya bace da Dizhwar yayi mata, yaudarar ta yayi ya cuceta kuma, gashi yayi guduwarsa ya barta kuma babu yanda za'ai budurcinta ya dawo"_

 Abunda zuciyarta take ta faman fada mata kenan. 


Hawaye ke zuba, yayin da hankalinta yayi mugun tashi. 


Jin an turo kofa yasa tayi saurin juyowa tare dasa hannunta daya ta goge saman kumatunta. 


Ganin Dr. Ya shigo ga Abba da kuma Mama suna biye da shi yasa ta saurin kokarin tashi tana dariya hade da kuka. 


Da sauri Mama ta rungumetah itama tana kuka, hannunta daya tasa itama ta rungume Maman tana kuka yayin data kalli Abban nata shima yana tsaye kasa jurewa yayi shima saida ya matsa gareta tare da rungumetan yaji dadi. 


Dr. Da wannan mutumi dake tsaye tausayi suka basu tare da burgesu, yanda suke san yar tasu itama take sansu, da alama ita kadai suka haifa, abunda duk sukayi tunani kenan,wacan din juyawa yayi ya fita, dan dama abunda yake san gani kenan. 


Kofar Dr. Ya kulle tare da shigowa ciki yana kallansu. 


Saida suka gaji dan kansu suka saki juna. 


Mamace ta zauna gefan gadan tana shafa fuskar ta, tana kallan yanda lokacin kadan haka ta koma kamar wanda tayi jinyar shekara guda. 


Itama rike hannun nata tayi tana jin dadin ganinsu, idanta daya cika da ruwa ta daga tare da kallan Dr. 


_"Dr. Nagode da abunda kuka yimin Allah ya saka muku da alkhairi ya kuma biyaku da gidan aljanna, amma dan Allah ina rokanka da karka gayawa iyayena batun fyaden nan, nice komai tasu, na tabbata bazu taba jin dadin hakan bah, bana san na saka Su bakin ciki duk da nasan a tsautsayi abun ya faru, zan sanar musu da kaina dan Allah kayimin wannan taimakon"_

 Batare da ya mata magana ba ya nuna ya gamsu da maganar ta, yaji tausayinta matuka. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(26)*
__________

Fita yayi daga dakin batare daya musu magana bah. 


Kujera Abba ya janyo tare da zama, itama Lailah kokarin tashi zaune take.


Da sauri Mama ta mike tare da saka mata pillow a bayan ta, 

 Sanna ta taimaka mata ta tashin tare da zama, ajjiyar zuciya ta ajje tare da bin Maman tata da kallo. 


Komawa tayi ta zauna duk ita suke kallo. 


Mamace ta nuna mata da hannu, kamar yanda suka saba. 


_"Lailah kin tafi, kin samu a damuwa, munyi kuka, munyi yawa amma bamu ganki bah"_


Murmushin takaici tayi da kuma dana sanin abunda ta aikata din. 


Hannunta biyu tasa ta kama kunan ta tare da langwabe fuskarta alamun bada hakuri kenan. 


Ba komai suka nuna mata, sunji dadi sosai da suka ganta. 


Ita kanta tasan babu abunda suke bukata kamar suji abunda ya faru da ita din. 


Labarin karya ta shiga hadawa a zuci kafin ta fada musu.


Nan tahau musu bayani kamar yanda ta saba, 


_"Nayi miki karya, zanje wajan Rauda"_


Ta fada tana kallan Mama dan, tasan dole sunje gidan su Rauda. 


_"Banan naje bah, wajan aikinmu nake san inje, najima banje bah, amma nasan inna gaya miki, zaki ki yarda tunda Dizhwar ya hanani zuwa, saina shiga mota ashe mai motar bashi da gaskiya, yana so ya saceni"_


Duk su biyun suka tsorata tare da tsine masa cikin zuciya dan sunsan Lailah bazata musu karya ba shiysaa ta samu damar hada lbr. 


_"Muna tafiya, saiya watsomin wani abu, tun daga nan ban san me yake faruwa bah, sai na ganni anan"_


Mamakine duk ya kama su, dan sun tsora, bada ban Allah ya taimaka ba dasun rasa ta. 


Abbane ya tambayeta inda shi mutumin yake. 


_"Can hanyar Sokoto ya yardani, shine wannan likitan ya tsinceni"_


Mamaki da kuma dadi sukaji lokaci daya na abunda Dr. Yayi musu, gashi ya bata kulawa ta musamman. 


Abba ma yaji dadi sosai, Mama shafata tayi tana tambayar babu abunda ya sameta itama. 


_"Aa, kasancewar yardani da akayi, bayana da kuma kafata suna ciwo dan bana iya tafiya sai dingishi, sai kuma aiki da akayi a bayana, aka zuke jinin daya kwanta, shikenan"_ 

 Duk Lailah ta yimusu karya dan bata san dukkan abunda akayi mata ba, tayi hakanne danta kwaci kanta kuma sun yarda da hakan. 


Sai lokacin hankalin ta ya kwanta Sosai dan ba karamin dadi sukaji bah, ganin da sauki jikin nata har take iya tafiya. _________

Anty Amarya kuwa tun da farar safiya aka shirya ta fita dan zuwa wajan bukanta, cancikin wani kauye a Sokoto, dan inta tashi wannan tafiya tata, ita kadai take zuwa batare da dan rakiya bah, dan haka da safe ta tafi dan dama shine lokacin zuwanta. 


Dan haka lokacin data isa, babu kowa a wajan nasa, kasancewar duk sanda zata zo yasan da zuwan nata yayi mata iso zuwa cikin wajan nasa. 


Zama tayi tamai gaisuwa kamar yanda ta saba tare da fadin, 

 _"Boko abubuwa sunki yin gaba, kullum jiya iyau na rasa gane kan wannan abun"_


Dakatar da ita yayi tare da fadin, 

 _"Ba saida na gaya miki Komai kina binsa ahankali bah, amma ke Kina sauri da rawar jiki,wannan yarinya da aka Kawo muku, ba karamar hatsabibiya bace ita, kanta dole saikin tashi tsaye"_


Anty Amarya ta girgixa kai dan itama tasan akwai babban yaki agabanta. 


_"Ina jinka boka, na yarda dakai, kuma nasan bazaka gaji da bukata ta bah"_


_"Wannan haka yake,yanzu kina so a raba su, ya kasance yana karkashinki, sai abunda kika fada shine zaiyi, toh tabbas in har kikayi abunda na saka ki za'a samu nasara, kuma dole da kanki Zakiyi wannan abu, ba wani zaki saka bah"_


Gyada kanta tayi, tare da mika gaba daya hankalinta gareshi. 


_"Kamar yanda kika sani har yanzu mace daya ce duk duniya ta taba kusantar shi wannan yaro, kuma tana nan acikin garin Zamfara wato Lailah, sabo da haka, zaki samu fitsarin wannan yarinya na farar safiya kafin taci komai, zaki hada shi da naki, saiki hada masa lemo ko kuma wasu dabarunku na mata, da zakiyi, domin yasha wananwannan abu, mundin kikayi haka kin samu soyayyar sata har abada, sai abunda kikace yayi,amma fa da sharadi, karki sake ki bari Ya sadu da Matar tasa, dan inya sadu da ita gaba daya aikinki ya lalace. "_


Dadi taji sosai, sannan kuma ta kuma gyara zama. 


_"Abu na biyu kuma, shine nasan ki wulakanta Ita matar yaran, wannan yarinya gaskiya na gaya miki, tana tare da manyan aljannu, kuma yan gidansu tsafi sukeyi suma, dan haka dole akwai hadari dangane da aikinta, kuma Mundin aka sami sabani a wajan aikinta dayan biyune, koki haukace ko kuma ki rasa ranki"_


Gaban Anty Amarya ne ya fadi, dan har gumi ya fara zubo mata. 


_"Zakiyi in fada miki kokuma abarshi tukun"_


Shiru tayi tana tunani kafin tace, 

_"Ina ganin inde na samu Dizhwar din, ai dole abun zai dinga mata ciwo, kuma dama ni abunda nake bukata kenan,ina ganin abarshi gaskiya"_


Boka ne ya fashe da dariya tare da fadin, 

 _"Matsiyaciya baxata iyabah😂"_


Saikuma ta kuma da cewa, 

 _"Boka har tanzu fa, naga kamar tauraruwar Fulani tana haskawa a idan Sarki, kumani harga Allah na tsani matar nan, babu abunda Za'a iya mata tabar duniyar kokuma a saka ta wahala?"_


Shiru yayi kafin yayi zabure zaburansa tukun yace, 

 _"Za'a iya mana, zaki samu Hawainiya"_


_"Hawainiya?"_

 Ta maimata tana kallansa.


_"kwarai kuwa, hawainiya tare da jelar bunsuru, za'a binnesu da ranta a kofar dakin Memartaba,zatayita rashin lafiya da kuma Kuma wari, za'a rasa abunda yake damunta, in har wannan hawainiya ta mutu, toh itama mutuwa zatayi, sabo da haka, kema kinsan ladan aikina, bana amsar kudi"_


Murmushi tayi tare da fadin, 

 _"Ai babu matsala nide burina bukatata ta biya"_


Nan kuwa tahau cire kayan jikinta,dan biyama boka bukatarsa, yayin da nikuma Na barota ina fadin, 

 (Allah ya shirya).


_______

Husna tunda aka kawo ta bata taba zuwa ta gaida Memartaba ba, ko Kuma wani da yake cikin gidan nan bah, har ita kanta surukar tatah. 


Abunda yake bama Fulani,mamaki kenan,shi kansa Dizhwar din tunda akayi biki ko Inda take ya daina zuwa,dan haka ta shiga nemansa a waya amma shiru yaki dagawa. 


Abun yana bata mata rai, ga Asiya kanwarsa da shi kansa Jafar din da suke Nesa, kullum ta Allah sai sun kirata safe da dare dan jin lafiyar tah, ita kuwa bazata je wajan yarinya ba dan mata magana, inda yar gidan masu mutunci ce ai tasan abunda ya kamata tunda tana da iyayye, shikuma da yake sakarai, in ita bata zo ba ai shi ta haifeshi amma shima shiru, kullum Yana cikin daki kamar mace. 


Abun yana kona masa rai. 


Jafar ta kira danya kirasa, ya sanar masa da tana nemansa dan ita inta kira baya dagawa. 


Nan ya bata hakuri kuma ya shiga neman wayar Dizhwar din. ________

Yana dakin Husna dan yau ita ta kira sa, kuma yanzu ya rasa abunda yasa baya mata musu dukkan abunda take bukata shi yakeyi. 


Yana kwance kan gadonta, tana gefe tana masa hira, wayarsa ta fara Ringing, da sauri ta dauka ganin Jafar ke kira yasa ta kashe. 


Kallanta yayi tare da fadin, 

 _"meyasa kika kashe? "_


Maimakon ta bashi amsa, saita matso jikinsa tare da fadin, 

 _"Hubby bana san a dinga kiranka in muna tare, sabo da takura mana akeyi wallahi"_

 Ta karasa maganar da shigar shagwaba.


Be mata musu bah,illah komawa da yayi ya kwanta kan ciyar tah. 


Murmushi tayi tare da ajje masa wayar a kusa dashi. 


Wani Kiranne ya kuma Shigowa,harta katse daga shi har ita babu wanda ya daga, Murmushi kawai take dan yaji maganar tatah. 


Kiranne ya kuma Shigowa a karo na uku. 


Dauka yayi tare da mikewa zaune, dan ganin Jafar.


Yana dagawa batare da yace masa komai ba, Jafar din yahau fada. 


_"Gaskiyane, ka kyauta, ashe ba Mami ba kadai gaba daya ka daina daga wayar mutane toh da haka mana ba gwara ka Kashe wayar ba gaba daya kowama Ya huta"_


Shiru Dizhwar yayi dan yasan be kyauta bah.


_"Haba Dizhwar kai haka ake, Aure haukane, shikenan kuma daga ka samu mace saika manta da kowa har mahaifiyarka, kuna gida daya amma kaje ka gaida ta kake ganin abun ya gagara, in ita baza taba kai kaje mana, kuma harta kiraka amma kaki dauka, gaskiya wannan ba wayewa bace"_


Shiru yayi dan Jafar ya bata masa rai,ya wani Kirasa yana masa fada kamar wani Babansa ko Yayansa. 


Tsaki yayi tare da kashe wayar gaba daya ya cilla ta kan gado, mikewa yayi ganin Husna bata nan yasa ya fara dube dube, can ya hangota,jikin window tsaye. 


Dadi yaji cikin ransa, ya karasa gareta tare da rungumetah ta baya, ya zura kansa tsakanin huyanta da kafadunta. 


_"Fishi kike dani? "_


Banza tayi dashi, 

 _"Ki gayamin mana pls"_


Bata mai magana ba still, nan fa yaji ba dadi cikin ransa. 


Hannunsa yasa ya zagaye kugunta, tare da fada mata cikin kunne, 

 _"Dan Allah ayimin afuwa baxan kara bah, nayi alkawarin in har muna tare duk wanda ya kira bazan daga bah"_

 

Da sauri ta juyo tana murmushi tare da fadin, 

 _"Dagaske"_

Tana Murmushi. 


Kai ya gyada mata, yana maida mata Murmushin shima. 


Rungumeshi tayi, tare da jansa zuwa gadanta. 


_______

Hajiya Babba tun bayan tafiyar Zakiyya kullum ita kadai babu kowa a wajan ta hakan baya mata dadi, shiyasa ta shiga rokan kanwarta danta kawa yarta ta rike a wajanta ko zata ji dadi ta saba da Zakiyya, nan kuwa tasa a kawo mata yarinyar kanwar Tatah daga Kaduna. 


Tana zaune cikin falonta, abu yayi mata yawa, gashi Anty Amarya munafuka tun bayan biki ta dauke kafa, ga shi dama basa wani shiri da Fulani, sabo da haka abu ya hade mata,  

  Ita kuma yanzu burinta a duniya be huce taga ta raba kan Dizhwar da  Mahaifinsa ba, dan tabbas ya amshi Sarautar nan tasan dole Fulani tayi farin ciki, sabo da haka dole ta tashi tsaye dan ganin be samu sarautar bah, tama fi san yabar gidan gaba daya. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*

*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
*(27)*
__________


Kwanan Lailah biyar a asibiti tana samun kulawa sosai kuma kamar yanda ta bukata har yanzu Babu wanda yasan da batun mata fyade. 


Kullum da safe da yamma Sister Zainab zata zo ta dubata ta saka ta cikin abinci sannan ta gasata. 


Har saida ta saba dasu Abba dan Suna burgeta yanda suke nunawa Lailah so da kuma kulawa.


Yau Jafar ya sanar da Dr. Zai shigo garin dan suzo su duba ta, haka kuma zai mata magana dan ta sanar masa wanda yayi mata fyade domin ya daukar mata fansa. 


Haka kuwa akayi, shida Amaryarsa da kuma Hajiya Bilki suka shirya suka taho domin duk ya sanar musu da abunda Ya faru da kuma zuwan da zaiyi na duba tah. 


2:00pm,suka sauka a Sokoto, Mami ce ta sanya domin aje a dauko su, dan sun sanar mata da zuwan nasu.


Kasancewar motocin gidane, da huri suka iso cikin Xamfara kai tsaye gidan sarauta aka nufa dasu, 


Mami tayi shirin tarar autar ta, ana saukesu kuwa da guda ta shige cikin wajan nata, suna ta mata dariya masu yima Fulani hidima, Tana shiga kuwa ta ganta ta fada kanta tana murna. 


Binta tayi da kallo tana dariya ganin yanda ta kara kyau da kuma kiba kamar ba ita bah. 


Suna nan zaune su Jafar da Hajiya Bilki suka shigo. 


Zama suma sukayi aka hau gaisawa, kafin a cika musu gabansu da kayan ciye ciye da shaye shaye. 


Kafin daga nan, Jafar yace, 

 _"Mami Yaya Dizhwar din kuwa yana zuwa ko kuma har yanzu be canza bah? "_


Shiru tayi dan bata san amanta maganar sah, 


 _"ai bana tunanin zai canza halinsa, wannan hankali gareshi, ya maida mata kamar Allan sa, bazan mai magana bah, yaje wallahi dan bezo ya gaida ni ba baxai rageni da komai bah, kude Allah yayi muku Albarka"_


Ko kadan basuji dadin Abunda yakeyi bah, amma shi Jafar gani yake kamar ba laifinsa bane. 


_"Dan Allah Mami kiyi hakuri, ina ganin ba laifinsa bane, amma zan mai magana tunda gani Nazo ai"_


_"Karka masa, karka sake ka bata bakinka, har sai kamai magana bayan shine gaba dakai, zance shima yasan abunda ya kamata da wanda be kamata bah, amma ai yana zuwa ya gaida Baban sa, kodan bani da daraja tun tuni cikin idanunsa"_


_"Haba kekuwa fishi ba naki bane, ai irin wannan magana zaki zauna kuyi dashi ta fahimta, amma baxaki dinga fadar irin haka bah abunda ya faru da, aiya riga da ya huce yanzu, shima yasan ke wacece a wajan Sa"_

 Hajiya Bilki ta fada tana kallan ta dan itama san abun be mata dadi bah. 


_"Haba Yaya, tun yaushe ake abu daya, inda ya daukeni matsayin uwa baxai dinga min irin wannan ba ai, sai kace wata wanda ta tsare masa wani abu dama can baya kaunata, ni ko mutuwa nayi bana san yazo wajena ma"_

 Ta karashe maganar tana kuka. 


_"Dan Allah Mami kiyi hakuri, kiyi shiru dan Allah"_

 Asiya ta fada itama kamar zatayi kukan. 


Hajiya Bilki itama abun yana bata tsoro kuma tasan rabashi akayi da ita, in ba haka ba mutun da uwarsa ace baya kaunarta, 

 _"Menene na kuka, ki share hawayanki, addu'a Za'a dage a dunga masa, yana cikin wani hali wallahi, kibar masa kuka kina fadar irin wannan maganar, in rai ya bace ai hankali baya goshe bah"_


Itade Mami bata kara magana bah, hawayanta kawai take gogewa. 


Jafar daya kasa magana tun dazu, tashi yayi ya fita daga dakin, koda ya fito wajan me martaba ya nufa, cike da mamaki kuwa,  yaga Dizhwar din zaune a wajan sa. 


Da Sallama  ya shiga Falon nashi ya zauna suna gaisawa, sannan suka gaisa da Dizhwar din, daya amsa masa cikin fara'a kamar bashi ya kashe masa waya ran nan bah. 


Sun jima suna hira kafin su fito tare suna taba hira, kallansa Jafar yayi tare da fadin, 


_"Angon Husna, kaga yanda ka yi kiba kuwa, gasiya wannan Amaryar tana kula dakai, muje in gaidata mana"_


Dizhwar dariya kawai yake, dan yanzu yanda yake jin Husna cikin ransa, duk duniya babu ya ita. 


Tare suka shiga har falonsu, suka zauna. 


Dizhwar dinne ya shiga daki dan kiranta su gaisa da Jafar. 


Sun jima kafin su fito, tukun ta fito sanye da atamfa doguwar riga kanta babu dankwali, da waya a hannunta, tazo ta zauna, shima yana biye a bayansa


Kamar ba ita ba suka gaisa faran faran, har take tambayarsa Asiya. 


Shikansa yayi mamaki, 


Sun danyi barkwanci kafin ya mike yace da Dizhwar zaidan shiga gari, Adawo lafiya ce kawai ta hada ss dan ba shi da alamun masa rakiyar. 


Mamaki sosai Dizhwar yaba Jafar dan yanda suke be taba tunanin irin wannan yanayin ba a tsakaninsu. 


Koda ya fita be koma can ba, dan baya san kara ganin Kukan Mami. 


Koda ya shiga mota tunaninsa, sam be dace ace Husna bace matar Dizhwar dan sam Yarinyar bata da hankali, gashi kana ganinta idanta ya bude da yawa, babu abunda bazata iya bah Wannan,haka ya nufi asibitin yana tunanin mafita.


Parking yayi inda aka tanada domin yin hakan, shiga yayi kai tsaye Office din Dr. Ya nufa. 


Kwankwasawa yayi kafin ya shiga, da sallama ya bude ya shiga, yana hangosa ya mike yana murmushi suka hada hannu suka gaisa kafin ya zauna suna fuskantar juna. 


_"Kenan harkun karaso, yaya gida ya Amarya"_

 Dr. Ya fada yana Murmushi._"Lafiya qlau wallahi, ai tare muka zo garin tazo gaida su Memartabah, yaya me jiki kuma ya faman wahala da ita, kuna ta fama Allah ya biyaku"_

Jafar din ya fada. 


_"Jiki Alhmdullh yayi kyau dan yanzu ta warware ina tunanin zata iya tafiya gobema in Allah ya kaimu"_


Dadi jafar yaji tare da fadin, 

 _"Masha Allah ai haka ake so, Allah ya kara sauki"_


_"Ameen"_

Dr. Ya fada tare da mikewa yace da Jafar, 

_"Muje ka ganta, iyayanta ma suna nan ai"_


Ba musu kuwa yabi bayan Dr. Suka nufi dakin nasu. 
Da sallama suka shiga tare da kullo Kofar, 


Gaisawa sukayi da iyayan nata dan Dr. Yayi masa bayanin su tun acikin waya, kasan Cewar basu san ko Waye ba yasa basu masa godiya bah. 


Ahankali ta fito daga Toilet, sanye take da doguwar riga baka, tayi kyau harta danyi kiba, ta daura dankwali amma daga baya gashinta ya zubo har gadan bayan ta. 


Ganin Dr. Yasa ta karaso tare da gaida su. 


Binta Jafar yayi da kallo dan ta bashi mamaki Ganin yanda ta koma kamar ba ita bah. 


Dr.  Ne ya kalle ta tare da fadin, 

 _"Ga wanda ya tsunto mana ke ya bamu umarnin muyi muki dukkan abunda kike so, a takaicede komai da ika samu daga wajan sane"_


Dadi Lailah taji ta rasa da wani bakin Zata masa godiya domin ya gama Mata komai,


_"Nagode, Nagode Allah ya saka da alkhairi ya kara budi, Allah ya kareka daga dukkan wani mugun sharri ya saka maka da gidan aljanna  Nagode "_

 Ta karasa maganar tana kuka. 


Da sauri ya furta, 

 _"Menene na kuka, kefa kika Kirani da yaya, ko an fasa yayan kuma kike kuka, yayan kine fa yayi miki abun alkhairi Nagode da addu'ar amma bana san kuka, ki gogeshi ko kuma ince bana san addu'ar take"_


Murmushi take tana goge hawayan nata. 


Batare da tayi magana ba ta juyo tana nunawa su Mama shi da hannun,  shine wanda duk ya biya kudi ayi mata magani kuma ya kawota asibitin. 


Nan suma Suka hau masa godiya, duk da ba ganewa yake ba amma Lailah tana gaya masa abunda suke fada. 


Sunji dadi matuka kuma sunyi godiya marar iyaka da kuma addu'a. 


Bayan haka Jafar yace da ita,  


_"Ni Sunana Jafar duk da nasan Dr. Ya fada miki"_


_"aa ban fada mata ba, dama jira nayi kazo da kanka"_

 Dr. Ya fada yana dariya. 


Shima Dariyar yayi tare da fadin, 

_" toh Lailah, ni ya gaya min komai tare dake, Sunana Jafar, amma ni ba'a nan nake da zama Ba, ina zaune a kano da iyayena da kuma matata, ina zuwa nan sanadiyar yayan mahaifiyata, kuma kijin matata, wato Memartabah Sarkin Zamfara . 


Da sauri ta dago tana kallansa, a tsorace tare da fadin, 


_"Kaine Jafar"_


Kallan juna sukayi Shida dr. Kafin yace, 

 _"Dama kin sanni?"_


Kai kawai ta iya girgiza, kafin kuma ta fashe da kuka .


Duk. Kallan juna suka fara, haka suma su Mama. 


_"Lailah kukan me kikeyi?"_

Dr. Ya fada yana kallanta cikin damuwa. 


_"Kaine Jafar dan Uwan Dizhwar?"_


Nanma kallan juna suka kumayi tare da girgiza mata kai, 


Sannan tace, shine _"yasaka ka biya min wannan abunda kamin ko, ka gayamin gaskiya"_


_"Wallahi bashi yasani ba, ki mana bayani bamu gane ba, dama kinsan Dizhwar dinne? "_


Tana kuka tana fadin,

 _"Nasanshi mana, shine,shine wanda yamin fyade, shine wanda ya yaudareni"_

 Ta kuma fashewa da kuka. 


Gaba daya Mamaki da kuma abun al'ajabine ya kama su, dan gaba daya sun kasa fahimtar abunda take fada. 


Da er Dr. Ya lallabata, dan tayi musu bayani,  haka tana kuka har saida ta gaya kusu dukkan abunda ya faru tsakaninta da shi. 


Jafar mutuwar zaune yayi dan ya yarda da maganar Lailah, tunda shi kansa yaga alamun hakan da kuma gaskiyarta, domin tabbas ranar dinner nemansa sukayi suka rasa saida safe ya dawo, gashi abu kadan saika gansa yana waya kamar marar gaskiya. 


Bayan ta gama sanar masu, Jafar yace da ita, 


_"Kinga ki kwantar da hankalinki, insha Allah, a yayan da kika kirani haka zan zame miki yayan, zan tsaya miki akan dukkan wata matsala taki, na yarda da abunda kika fada kuma na miki alkawarin zan kwatar miki yancin ki mundin ina raye kede kawai ki bani hadin kai"_

 Kai kawai Lailah  take dagawa shikuwa likita shiru yayi yana jin abunda suke fada. 


_"Yanzu, ki kwantar da hankalin zan samo lawyer sannan zamuyi magaba da Memartabah duk yanda ya yanke hukunci saimu shiga kotu amma nayi miki alkawarin kwatar miki yancinki kamar yanda kike tamkar kanwa a gareni"_


Dadi Lailah taji sosai, dan yanzu zuciyarta ta gama tsanar Dizhwar, dan ko wani nayi mata maganarsa bata kauna, danya koya mata hankali kuma, Ya cuceta, yanzu ta gane Yaseer shine masoyinta na ainayi, shine me kaunarta tsakani da Allah,amma ta watsa masa kasa a ido. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄**_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(28)*
__________

Jafar ya jima cikin asibitin kafin yayi musu sallama ya tafi.

Daga shi har Dr. din ba karamin mamaki sukayi ba jin abunda Lailah ta fada, koda ya rakasa dukkan su babu me yima wani magana, Dr. Ne yayi dariya tare da fadin.


_"Kana ganin kuwa yarinyar na ba karya take masa ba danta bata sunan gidan ku ba, amma taya hakan zata faru shida Dizhwar yan mata ma basa gaban sa balle wannan yarinyar"_


Shima de abun yana bawa Jafar mamaki amma yasan dabarar da zaiyi dan gane gaskiyar magana,  

  Be bawa Dr.  Amsa bah ya fice daga asibitin. 


Koda ya koma gida danki nsu ya nufa cikin sa'a kuwa ya tarda Dizhwar din ya fito daga cikin daki. 


Zama yayi kan kujera tare da sauke Gauran Numfashi. 


Zuwa yayi shima ya zauna kusa da shi, tare da fadin

 _"Daga ina haka naga kamar ka Gaji sosai?"_

 Dizhwar ya fada yana kallansa. 


Shima juyowa yayi sukayi ido biyu tare da fadin, 

 _"Naje gidan gaisuwa ne, wata budurwar abokina ce ta mutu"_


_"Allah ya jikanta"_

Dizhwar ya fada. 


_"Wallahi kuwa, abunne abun tausayi, an ma kusa bikin su fah, kawai tsautsayi yasa ta fita da dare ta tafi unguwa wallahi sai gawar ta aka kawo, yaban tausayi baka ga yanda ya rame bah, nikuwa kaji sunan Budurwa tasa"_

 Jafar ya fada yana kallan Dizhwar, yanayin yanda yake yin kamar gaske, Shima Dizhwar din kallansa yake. 


_"Yawwah Lailah"_


Yana fadar haka, Dizhwar yayi saurin juyowa ya kalli Jafar din. 


Kana ganin fuskarsa kasan yasan ta dan yanda ta nuna abun mamaki. 


_"Kasan tane?"_


Jafar yayi masa tambayar. 


_"Aa, ah, haba aina zan santa kuma?,  kawai tabani tausayi nima"_

 Dizhwar ya fada tare da tashi ya fita daga cikin dakin. 


Binsa Jafar yayi da kallo, dan gaba daya ya gama ganosa, Murmshi yayi tare da tashi ya fita daga cikin dakin.


Kai tsaye wajan me Martabane ya nufa, cikin sa'a kuwa yana nan be fita bah, yana can cikin dakinsa na Garden. 


Babu kowa a wajansa, yana zaune yana shan iska. 


Da sallama Jafar ya shiga tare da samun saman carpet ya zauna. 


Kallansa Memartaban yayi tare da fadin, 

 _"Kadawo kenan? "_


_"Eh wallahi, Baba dama akwai wata magana da nake san muyi me Mahimmanci"_


Dagowa yayi daga kishingidan da yake tare da fadin, 

 _"Bismillah inajinka"_


Shiru yayi dan yana danjin kunya amma kuma inya ki sanar masa kamar yaci amana ne, ahankali yayi gyaran murya tare da fara fada masa abunda yake faruwa tun daga farko har karshe. 


Shiru yayi dan abun ya daure masa kai Kuma ya basa mamaki,


Gaba dayansu shiru sukayi babu wanda yake magana gurin yayi shiru Baka jin komai sai kukan tsintsaye. 


_"Yanzu yaya ake ciki, menene mafita?"_

 Memartabah ya tambaya yana kallan Jafar. 


_"Yanzu shi yayan yarinyar ya riga ya shigar da kara"_

Jafar ya fada masa dan jin abunda zai fada. 


Abun ya kara jinjinawa tukun yace da Jafar, 

 _"Gaskiya abunda Dizhwar yayi min be mana adalciba, kuma saina masa hukunci daidai da abunda yayi, tabbas in har aka bari aka shigar da kara zamu shiga cikin matsala, haka zalika sunan mu Zai baci,manyan mutanan da suke ganin mutuncina duk zasu dena gani, abunda nakeso dakai shine, ka basu hakuri, akan su janye karan In akai hakan sai a lallaba su, Shi Dizhwar din ya aureta kaga ai hakan yayi. 


Shiru Jafar yayi dan yasan da er in har Lailah zata yarda ta aure Dizhwar amma kuma Bashi da mafita dole ya gwada hakan. 


Jafar Naam yayi da shawarar da Sarki ya fada tare da mikewa ya bar wajan. 


_________

Koda Jafar yabar asbitin nan, abunne ya mutukar daurewa Dr. Kai dan haka waya ya dauka ya kira Dizhwar. 


Koda ya daga kaisawa sukayi, ya tambayeshi ya karfin jikinsa. 

  Bayan sun gama abunda zasuyi, Dr. Yace da Dizhwar, 

 _"Kasaan wata Yarinya Lailah?"_


Gaban Dizhwar ne ya fadi dan baya san kowa yasan wanann maganar, amma kuma karyace aa abun ya dagule masa, 

 _"eh nasanta"_

Ya bashi amsa. 


_"Toh wallahi kana cikin matsala, domin kuwa tana nan asibitina, a kwance, Jafar ya tsinceta ya kawota dan amata magani, har suna maganar shigar da kara akan abunda Kayi mata"_


Shiru Dizhwar yayi dan tashi ta kare, wani gumi ne ya keto masa dan tashin hankali.


_"Am Dr. Nagode da sanar min da kayi, zanzo asibitin in gani in itance"_


Sannan sukayi sallama. 


Dizhwar wani baki cikine ya kamsa, kenan shiyasa Jafar yake masa wannan tambayar ,tabbas dole ya kashe lailah, saiya koya mata hankali harshi zata tunawa asiri, da sauri ya shiga neman key din motarsa. 


Wayar shice tahau Ringing, kamar bazai daga ba ganin Sarki ke kiransa yasa ya daga. 


Batare da yayi magana ba ya daga dan jin abunda zai fada. 


_"Kai ko aina kake kayi maza maza ka dawo cikin gida nanina san ganin ka."_


Batare da Dizhwar yayi maganaba ya kashe wayar, kallan wayar yayi kamar zaiyi kuka, ya fita daga dakin. 


Part din Memartaba ya nufa amma began saba, masu aikinne suka gaya masa inda yake, haka ya nufi wajan nasa gaban ya sana faduwa.


Koda yaa isa, shiga yayi ya zauna, dan besan abunda zai sanar masa bah. 


Ganin Memartaba ya hade rai yasa ya fara jin tsoro, shiru babu wanda yake magana. 


_"Dizhwar, yanzu ka Kyauta abunda kayi mana kenan,kullum burina be huce ka Zamanto yaro na gari, amma koda yaushe kana cikin bani matsala, meyasa baka sona baka kaunar barin cikin mu, yanzu kaje kayiwa yarinyar mutane fyade, yaya kake san duniya ta kalli abun? "_


Innalillahi wa'inna illaihir raji'un, yasan Jafar ne ya gayama Me martaba wannan maganar.


_"Dan Allah kayi hakuri wallahi bada sani na hakan ta faru bah"_

Dizhwar ya fada kamar zaiyi kuka. 


_"Kamin shiru, ahaka zaka iya mulkar jama'a, da in baka masarautata gwara na mutu a kan kujerata ko kuma inbawa wani bare, kai baka cika adaliba har yanzu, kai mahaukacin inane, bana maka Aure bah, me kuma ya kaika wajan yaran waje, wallahi na yanke hukunci, nan da Kwana biyar zaka aure tah, kuma Wallahi wallahi Sai kayi nadamar abunda kayi"_


Hankalin sane ya tashi ya fara hada hannu yana rokonsa kamar me bara. 


Hannu ya daga masa tare da fadin, 

 _"Na gama magana in bazaka yi abunda nace ba, ka fitar min daga gida, can suje su shigar dakai kara, babuni babu kai"_


Memartaba yana gama fardar haka ya shige ciki.


Zuciyar Dizhwar banda tafasa babu abunda takeyi, shi kadai yasan yanda yake ji. Da sauri ya mike ya fita daga wajan, jikinsa har tsuma yake ya nufi Part din Mami yasan nanne kawai inda zaije ya tarda Jafar. 


Kana ganinsa kasan babu lafiya.


Suna zaune a Babban Falon Mami, gaba dayansu suna hira, babu Sallama ya shigo dakin yana ganin Jafar ya hau dukansa. 


Nan suka mike suna masa magana, Mami kuwa kuka takeyi, dan ganin zai kashe Jafar din. 


Asiya ma kukan take, Hajiya bilki ce tayi kokarin janye Jafar din daga jikinsa. 


_"Baku da hankaline, menene hakan kukeyi kamar kananan yara"_

 Ta fada tana kallan ko wanne cikinsu yana huci, ga jini da yake zuba daga bakin Jafar din. 


Mami ce ta nufo wajan tana duba jikin jafar din tare da taba jikinsa. 


_"Meka masa menene ya faru Jafar?"_


Jafar shima dabe kawo ga abunda yayi masan ba, neman amsa yakeyi. 


Juyowa Mamin tayi tare da dauke sa da mari, zaiyi magana ta kara masa wani marin. 


Kallanta yakeyi da hawaye a fuskarta, 

  _"meyasa kike marina kinsan abunda yayi min ne, kowa baya bani gasikiya, wannan munafikine kuma wallahi saika gane da wanda kake"_

 Nan ya dage yanata faman masifa. 


_"Mamice tace dashi, Fitar min daga dakina, banza marar kunya wanda besan darajar mutane bah har iyayansa"_


kallanta yayi zuciyarsa tana kara tafasa. 


_"Ko dukana zakayi nima da kake kallona, ta fada tana ture shi baya, tana kuka, wallahi baka da mutunci Dizhwar, ka dakeni nima sai insan ka cika futsararre"_


Hannu yasa ya turata baya shima yana huci, gaba daya mamakine ya kamsu, itama surrender tayi tana kallan sa, ga hawaye yayin da itama Asiya ta nufo wajansu tana kukan, 

 Wajan Dizhwar ta nufa, kafin ta karasa Mami tace da ita, 

 _"Inde kika kuma Masa magana ban yafe miki bah"_


_"Kaikuma fitar min daga daki, karka kuma Zuwa wajena koda bayan raina kazo inda nake ban yafe bah , kamar yanda koda yaushe kake sani kuka, insha Allah kaima sai kayiwa mace kuka, wallahi sai kayi nadama"_

  tana fadar haka ta shige dakinta


Kowa tsaye yayi a inda yake babu wanda yake magana, tsaki Dizhwar  din yayi tare da fadin, 

 _"Ina fita daga dakin mutuwa zanyi, inna kara shigowa nan wajan niba dan halak bane"_


Yana fadar haka ya juya zai fita, da gudu Jafar ya bishi yana fadin, 

 _"Dizhwar "_


Hajiya Bilki ce tace, inka kuma masa magana, 

 _"Allah ya isa ban yafe maka bah"_
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄**_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(29)*
__________
Cak!, Jafar ya tsaya ina bunda Mamanshi ta fada. 


Yana san yaje wajan Jafar din, dan gani yake kamar bashi da lafiya


Dan ba karamin mamaki yake basa ba in yaga yana irin wannan bun. 


itama Hajiya Bilki cikin dakin ta shige, Yayin da Jafar ya zauna kan kujera abun ya dameshi, dan be taba tunanin akwai ranar da hakan zata faru tsakaninsa da Dizhwar din bah, be damu da gefan bakinsa daya fashe bah. 


Ahankali Asiya ta karaso tare da bude karamin First aid kit data dauko bah, goge masa wajan tayi ta saka masa magani,


Dogowa yayi ya kalleta, yanda take hawaye, rungumetah yayi tare da fadin, 

 _"Kukan ya isa haka"_


Kamar ya kara zugata ta kuma fashewa da wanda yafi wancan, shima tausayi ta fashi, hawayanne ya zubo masa dan gaba dayansu tausayin Dizhwar din suke. 


_______

Koda ya fita dakinsa ya nufa ya shiga hada kayansa, saida ya tattara komai sannan yasa a dauke masa ya koma part din Husnar, amma tabbas bada ban me Martaba ba babu abunda zaisa ya zauna a cikin gidan nan, babu maganar wanda yake ji saita mai martabane. 


_______

Anty Amarya ko bayan data dawo gida, tunanin fara shirinta take, tukun kafin lokaci ya kure mata, ta shiga binciken wacece Lailah dan tabbas tana san burinta ya cika. 


Saida tasha hawala matuka tukun ta gano, amma ita kanta yanzu bata san inda take bah, shine kuma Abunda ya daure mata kai Kenan. 


Amma ganin kar tayi biyu babu bara ta fara da Fulani itama,sawa tayi a nemo mata hawainiya da kuma jelar Bunsuru kamar yanda Bokanta ya fada. 


________

Shikuwa dan abunda Dizhwar din yayi yaji kamar an kara masa kwarin gwiwa dan haka, ya nufi asibiti batare da sanin kowa bah haka batare da sanin dr.  Din bah, dan yazo Yayi ma Lailah maganar Abunda me Martaba yanke. 


Koda ya iso, babu kowa cikin dakin,  sai ita kadai dadi yaje yanda zasuyi maganar su a tsanake, dan so yake ayi komai kafin ya koma kano. 


Koda ta ganshi dadi taji sosai. 


Bayan sun gaisa yasanar mata da 

_"Ashe ba'a sallame kun bah?"_


_"Eh wallahi bansan  meyasa hakan ba, amma Insha Allah zuwa gobe kila zamu tafi"_


_"Lailah dama abunda ya kawoni magana nakeson muyi ta fahimta nida ke"_


Hankalinta ta maida kansa dan jin abunda zai fada din. 


_"Har ga Allah nayi kokarin taimaka muku, kuma har yanzu ma banyi kasa a gwiwa ba domin na gaya miki tamkar kanwa kike a wajena, dukkan wani abu dazai cutar dake bazan yishi ba. 


kaita gyada masa dan ta yarda dashi dari bisa dari. 


_"Naje na sanar da Memartabah dukkan abunda yake faruwa, kuma ya nuna rashin jin dadinsa game da hakan, amma ya nemi wata alfarma guda daya, Yana me rokon dan Allah a janye maganar Kara da za'a shigar tunda mutuncin gidansa da kuma iyalansa Za'a tabah, kamar yanda nasan kema baa muku adalci bah,amma ya nemi amafarki dan Allah kiyi hakuri, ki auri Dizhwar ko zaki zamo canji cikin rayuwarsa "_


Da Sauri Lailah ta kalleshi tare da fadin, 

 _"Dan Allah kabar wannan maganar, cuta an riga da an cucemu amma baxan taba iya auran Dizhwar bah, kayi hakuri kawai"_


kara matsowa Jafar yayi tare da fadin, 

 _"Dan Allah dan annabi Lailah bada ni bah dan darajar Ubangiji ki daure ki aureshi, dan Allah taimkona zakiyi dan Allah, wallahi matar daya aura gaba daya ta juya masa tunaninsa Yanzu ko mahaifiyarsa baya kauna"_


Shiru tayi tana jin abunda yake fada, wanda take ganin ko kasheta za'ai babu abunda zaisa ta auri Dizhwar duk kuwa da irin san da take masa.


_"Bazan iya jayayya dakai ko Kuma Iyayanku bah, an Cuceni, kuma abun be mana dadi ba, duk da har yanzu iyayanmu basu san abunda ya faru bah, bamuda kowa sai Allah, bamu da wani me tsaya mana, nice jin dadin iyayena ni nake musu komai, ko yaya aka samu matsala su aka cuta, soba da haka ina kaunar iyayena fiye da kowa, dan Allah ka janye magnar nan, bazan taba tona muku asiri ba kona aibata gidan ku bah, wallahi nayi rantsuwa da Allah babu wanda zai kuma jin abunda ya faru daga ku din nan da kuka sani, zanyi nisa da garin nan inda babu wanda zaiji labarina koya ganni"_


Shiru Jafar yayi, dan besan kuma ta inda za'a bullowa abun ba. 


_"Nagode da karamcin da kika nuna min Lailah, amma duk inda kike karki manta dani, kuma nayi alkawari kamar yanda nayi da, zan tsaya miki tamkar yayanki, zanyi miki dukkan abunda kike bukata dake da iyayanki, Nagode sosai, kuma in kuna Bukatar abu ko ina kikaje kimin magana"_


Hannu ya zura cikin aljihunsa ya dauko karamar wayarsa ya mika mata, 

 _"Gashi zan dinga nemaki ta wannan wayar, kuma zan dawo gobe insha Allah, insu Baba sun dawo a gaida su"_

 Yana fadar haka ya mike ya fice daga dakin. 
Koda ya fita tausayin sane ya kamata, kuka ta kama dan ganin yana rokonta abu amma taki masa, shida ya gama Mata komai ya ceci Rayuwarta, ya mata abunda ko wanda suke ciki daya bazasu taba mata bah, bazata taba mantawa da Jafar bah, kallan wayar tayi ta kuma fashewa da kukan. 


_______

Dizhwar kuwa, dare yayi bayan ya gama cin abincinsa, ya lallaba Husna ya fito daga cikin dakin, mota ya shiga ya bar gidan. 


Kai tsaye asibitin ya nufa, daya kira Dr. Ya riga da ya tafi gida, dan haka sanar masa yayi daya nemi Sister Zainab Ahmad, zata kaisa dakin da Lailah take. 


Babu musu kuwa ya nemeta, nan ta rakasa har dakin. 


Lokacin, Mama tamayi bacci, Lailah ce zaune kawai tana kallo, tana shan ice cream. 


Koda ta nuna masa dakin bata shiga ba,

Komawa tayi, shiga yayi tare da sallama, yayin da yaga wutar dakin a kashe, sai hasken tv, Murmushi yayi ganin tana kallan me shigowar, hasken tv ya haska kyakyawar fuskar tah, kunna fitilar yayi tare da kulle kofar, ya tsaya daga bakin kofar yana kallan ta. 


Da sauri ta saki ice cream din hannunta, ta mike tsaye tare da jan bedsheet din ta kare jikinta.


Murmushi ya kumayi tare da karasowa waja ta, zama yayi yana kallan Mama da take kan sofa tana bacci. 


Kasa magana tayi tana tsaye tana kallansa, shima kuma zama yayi yana kalla nata. 


_"Menene kike wani boye boye, bayan babu abunda ban ganinbah"_


Wani bakin cikine ya kuma kamata. 


Mikewa yayi tsaye tare da nufo inda take, hannu yasa ya shaketa jikin bango  yana fadin, 

 _"Duk yanda nayi domin ki fita daga rayuwarta amma bazaki fitaba kenan, Shine yanzu har kike hadani da iyayena da kuma yan uwana, kinsan wanene ni Kuwa, bakya kaunar Rayuwar ki kenan bakya san nakasassun iyayan ki kenna, wallahi in bakiyi nisa dani ba sai na rabai da rayuwarki"_

 Ya fada har lokacin hannusa yana Huyanta. 


Zuwa lokacin ta gama jigata, idanta duk ya firfito ga hawaye da take, yana sakinta ta durkusa tana tari. 


Saida ta gama ta dago indanta yayi jajir. 


Da zafinta ta kwada masa mari, 


_"Kai kana ganin abunda kayi kaci bulus kenan,wallahi karya kake kasan nida kai kar tasan kar ce, kaci wasan farko amma wanan karan baka isa kayi nasara bah, har kake tunanin yimin abunda Allah bemin ba, kai waye kaidin banxa kaidin hofi, wallahi ni macece, kasan zan iya wulakantama bade kaika wulakantani bah, kuma ka fitar min daga daki kokuma na maka Ihu, tsinanne matsiyace wanda besan darajar dan Adam bah"_


Kalanta yake yayin da itam take kallansa. 


Ahankali aka hau murda kofar za'a bude. 


Da sauri Lailah ta matsa jikinsa, binta yayi da kallo da kuma mamaki. 


Zainab ce ta shigo, ganin Lailah kusa da Dizhwar yasata yin murmushi. 


_"Sister shine fa mijin dazan aura, ya kika ganmu mun dace"_

 Ta fada tana kara rikema Dizhwar hannu. 


Dariya tayi tare da fadin, 

 _"Sosaima kuwa Allah ya sanya alkhairi"_


ta fada tare da ajje mata magani kan fridge, 

 _"Lailah gashinan karki manta kiyi bacci baki sha bah"_

 Ta ajje tare da fita.


kallan Dizhwar din tayi tare da matsawa baya, zaka iya fita ai. 


Gaba daya mamaki take bashi, ashe dama haka take yana ganinta da innocent face ashe itama kwaru wace. 


Ba musu kuwa ya fita, dan kara fara shirin da zai bi ya rabu da 'kaya. 
*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(30)*
__________

Cike da mamakin Lailah Dizhwar yaban asibitin nan, tare da kunar zuciya akan abunda tayi masa.


________

Bayan fitar Dizhwar Lailah zama tayi bakin gadan tana ajjiyar zuciya, dan tabbas cikin tsoro da Tarad dadin abunda zai biyo baya, tayi karfin halin yima Dizhwar din hakan, dan tasan any mistakes game over, shiyasa zata tattara inata inata tayi nisa dashi inda daga shi har Jafar din babu wanda zai kara jinsu. 


Ranar de kusan kwana tayi batayi bacci bah, ga kuma soyayyar Dizhwar din a gefe daya dan tasan ita kam, bazata taba daina sanshi ba saide in numfashi ta dena a doran kasa shine wannan tasan zata dena. 


_________

Koda safiya tayi, bata da burin daya huce Dr.  Ya shigo ya sallame su. 


Hakan yasa tayi tsuru tsuru tana jiransa, amma har kusan 10am amma bezo bah hakan yasa ta fara kosawa. 


_______

Shima Dizhwar tunda yaga Lailah jiya hankalinsa ya kasa kwanciya domin duk da yana tsanar ta, amma gefe daya ta tsaya masa cikin ransa, ko kadan ya kasa bacci abun yana damunsa, hakan yasa ya kuma tsanar kansa, tabbas yasan inba daina ganinta yayi ba bazai taba samun kwanciyar hankali bah. 


Gari kuwa yana wayewa ya dauki number dan kiran Dr. 


Koda suka gaisa, ya shiga tambayar Dizhwar ko lafiya yaga kiransa da wannan time din. 


_"Ko kana Asibitinne, ina san ganinka ne"_

 Dizhwar din ya fada. 


_"Wallahi bana nan, ina airport, akwai matsala ne? "_

 Dr. Din ya tambaya. 


_"Maganar gaskiya aiki nake san kayi min,  wanda dole saika yi hakuri da hakan, duk da nasan ba aikin ka bane"_


Shiru Dr. Yayi kafin daga bisani ya furta, 

 _"Ina jinka babu matsala"_


_"Lailah nakesan ka kashe"_

Dizhwar din ya fada masa.


_"Wata irin magana kake haka Dizhwar, kisan kaifa kake san nayi kenan? "_

Dr. Ya fada cike da rudewa.


_"Eh nasani mana shiyasa na gaya maka, in baza kaiyi bah, amsar me sauki ce, abu dayawa, sai in samu wani"_


Shiru Dr. Yayi dan yana mutukar jinjina abun. 


_"Shikenan babu matsala, yaushe kake San ayi hakan kuma a nawa?"_

  Dr. Ya tambaya, jikinsa a sanyaye. 


_"Yau nake bukata, kuma bana san kowa ya gane hakan, sannan maganar biyanka in ka dowa sai muyi magana, ko nawa kake bukata"_


Murmushi Dr. Yayi tare da fadin, 

 _"An gama ranka ya dade, Allah ya kara girma magajin sarki"_


Dizhwar kashe wayarsa yayi dan, sai yanzu hankalinsa yake shirin kwanciya. 


_______

Kasan cewar Dr.  Zaiyi tafiya hakan yasa, ya kira Sister Zainab tare da sanar mata inda wata allura take, akan ta dauko taje ta yima Lailah, babu musu kuwa ta yi biyayyah bisa abunda ya fada, taje ta dauki allura tare da nufar dakin da Lailah take,dama ya sanar da ita 12pm tanayi za'a sallamesu. 


Lailah zaune bayan ta fito daga wanka tana gyara jikinta harda kwalliya tana murnar tafiya gida, lokacin Mama tana cikin toilet. 


Da Sallama Zainab ta tura kofar tare da shiga. 


Ganinta yasa Lailah sakin Murmushi tare da fadin, 

 _"Ina kwana"_


Cikin fara'a itama tace da ita, 

 _"Lafiya qlau, yaya aiki?"_


_"Alhamdulillah,ya karfin jikin naki, koda yake da sauki ma tunda naga gashi nan harda Kwalliya"_


Dariya Lailah tayi, dan ba karamin farin ciki take bah dan zata tafi gida, ta gaji da zaman asibitin nan. 


_"Toh ga alurar karshe nan, za'ayi"_


Da sauri Lailah ta kalle ta tare da fadin, 

 _"Allurar Karshe kuma?, gaskiya tunda na samu sauki babu wata allura da za'a karamin"_

 Lailah ta fada tana hade rai. 


_"Aa, kar muyi haka dake Lailah, sabo da karin lafiyar kine, zakice baza a miki bah, nima nayi mamki dan nayi tunanin an gama sai kuma muka samu waya daga Dr.da sassafe akan ayi Miki ita kafin ku tafi"_

Sister Zainab ta fada. 


Shiru Lailah tayi dan bata kaunar allura a rayuwar tah, 

 _"Aina za'a min"_

 Ta fada tana turo baki gaba. 


Murmushi Zainab tayi tana kallan Lailah.

_"Bakya san alurar Lailah? "_

 Zainab ta fada tana matsowa wajan ta. 


Shiru Lailah tayi dan haushin da takeji. 


Ahankali ta dauko Audigar tana goge mata inda zata mata allurar. 


Bayan ta gama gogewa ta dauko zata soka mata, da sauri ta dan janye hannun tana rufe ido, hakan yasa allurar baduwa kasa ta fashe, dan Zainab bata rike ta sosai bah,gashi kuma syringe din bana roba bane kamar glass haka yake, ita kanta Zainab in za'a kasheta bata san allurar mecece wannan bah. 


Binta sukayi da kallo har wani kumfa take kafin kace me, gaba daya ta bushe kamar babu abunda ya zube a wajan, ga kan tiles din wajan yayi wani kal, kai da gani kasan allurar ba karama Bace. 


kallan Juna sukayi, 

 Zainab ce ta fara fadin, 

 _"Wayyo Allah Lailah yanzu yaya zancewa Dr., Kina ganin allurar kinsan tana da tsada gashi na fasa tah"_

 Gaba daya hankalinta ya tashi. 


_"Karki damu, Zance kinyimin, kema Saiki gaya masa hakan"_


Shiru Zainab tayi, dan tasan Dr. Da fada akan hakan zata iya rasa aikinta, amma bata da mafitar data huce ta fadi hakan. 


_"Nagode Lailah, Allah ya kara lafiya"_


_"Ameen Ameen Nagode nima, sai ki bani number ki dan mudinga waya"_


amsar Wayar Lailah tayi ta saka mata number sannan ta fita daga dakin, dan gaba daya bata ji dadin fashewar allurar bah._______

12pm daidai, Abba ya shigo asibitin bayan ya kira taxi tana tsaye a wajan asibitin, Mama da Lailah ne suka dauko wasu kayan a hannunsu dan tafiya dasu.


Har sun fito daga dakin, suka ga Abban ya nufo wajan su, koda ya hangosu saiya karaso yana murmushi yana fada musu ya samu taxi, tare da amsar kayan hannun Lailah. 


Nan Lailah tayi sallama da duk wanda zatayi, sannan suka fita daga cikin asibitin tana me murna da jin dadi, amma babban damuwar tata anan ina suka nufa dan tasan bazasu zauna wa Dizhwar acikin gidansa bah dan haka tamkar bara zana da rayuwarsu ake yi. 


Dan haka koda suka shiga cikin Taxi shiru tayi dan tunaninta be huce ta samu mafuta bah. 


______

Anty Amarya har zuwa yanzu bata samu wani saban bayani kan Lailah  bah, dan haka Kayan aiki na aikin Fulani ta riga da ta samu kuma a daran Yau take san gabatar da wannan aiki, dan tana ganin kamar bata da rabo Akan na Lailah, sabo da Dizhwar ya riga daya kwanta da Husna tasani, yanzu ita tashin hankalinta daya kartaje tayi wannan aiki akan idan Husna ko kuma ta mata video shine tsoran data ke ji. 


_______

Yaune Su Jafar zasu koma, kuma Hajiya bata san tafiyar dare, dan haka,amma shi kam yafi san harsai abunda Memartabah ya fada ya tabbata zai tafi batare daya sanar da kowa bah, Sai abun ya tabbata tukun dan yasan tabbas, Inhar Dizhwar ya auri Lailah bashi kadai zaiji dadi bah har Mami ita kanta sabo da dama babu wanda ya dace Da Dizhwar din sai Lailah,haka zai kuma daurewa ya kara gwadawa ko Zata yarda.


Saboda haka bayan ya karya, ya nemi uzuri wajan Hajiya akan bazai jima ba yanzu zai dawo. 


_______

Amma koda yazo Ashibitin Aka sanar dashi sun riga da sun tafi. 


Hakan yasa ya shiga neman wayar Lailah amma bata daga bah. 


_______

Koda suka isa gidan Dizhwar din fitowa sukayi da kayan su, bata san nunawa Su Abba komai amma bazata iya zama cikin gidan nan bah. 


Haka ta shiga jikinta duk wani iri kamar Dizhwar din zata gani acikin gidan. 


Haka kuwa ta shige dakinta, babu abunda ta fara sai binciken kudin da Dizhwar din yake bata da kuma wanda ta tattara na aikinta a baya. 


Nan ta duko harta hada 100k, ba karamin dadi taji bah, batare data sanar musu ba take san a kama masu haya, su koma tsohon gidan su dan dauko kayan su, ta samu wata dabarar ta sanar dasu Abba, dan su haka Allah ya tsara musu. 


______

Koda ta dauki wayar ta, ganin missed call yasa ta duba gashi Jafar ke kira amma bata san Koda kudi cikin wayr ba bare ta nemesa, gwadawa tayi, cikin sa'a kuwa ta shiga dan shi har ya hakurama yana shirin komawa gida yaga ta kira sa. 


Da sauri ya dauka tare da sallama. 


Amsa sallamar tayi tare da fadin, 

 _"Jafar kayi hakuri dan Allah, wallahi banga kiran naka bah, Sai yanzu"_


_"Ok babu damuwa ya kwarin jikin naki"_


_"Alhamdulillah naji sauki sosai wallahi"_


_"Nima yanzu nazo asibitin ashe kun tafi"_


_"eh"_

 Kawai tace dan tasan bata kyautabah tunda yace ta jirasa. 


_"Ki turan da address din gidan naku yanzu da Allah"_

 Yana fadar haka shima ya kashe wayar. 


Kallan wayar ta tsaya tana yi, nan ta shiga ta tura masa full yanda zai gane dan itama yanzu ta yarda da bukatarsa dari bisa dari tana ganin ta hakanne zata samu damar rama abunda aka mata. 


*ZEENASEER*

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

            🌷🌷🌷🌷🌷🌷

   *🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*

    *_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*

         *_ZAINAB NASEER SARKI_*

             *_ (ZEENASEER😘)_*

          🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄**_ViaWattpad@Zeenaseer01_**(31)*
__________
Kasan cewar yasan unguwar sosai yasa be dauke tsawan lokaci ba ya iso, dan bemayi tunanin gidan nan bane inda su Lailah suke zaune bah.


Waya yayi mata ya sanar mata da yana kofar gidan nasu.


Kallo kawai yake yaga ta inda zata bullo. 


Hijab din ta,ta saka tare da takalmi ta fito daga gidan, ganin ta fito daga gidan da beyi tsammani bah, mamaki ya kuma kamasa, sai yanzu ya kara yarda akan cewa Dizhwar yasanta ba tun yanzu bah, 

  Yana hango ta nufo motar yayi saurin fitowa, murmushi ta kumayi tare da gaida shi, tare suka shiga cikin gaidan, 


Kai tsaye inda Dizhwar yake zama in yazo ta nufa dashi. 


Zama yayi ,itama ta zauna gefansa, 


Shiru babu wanda yayi magana,ganin kamar da magana a bakinsa yasata fadin, 


_"Wanann gidan Dizhwar ne ya bamu shi akan ku zauna na dan lokaci,kuma nasan yanzu babu abunda zaisa muci gaba da zama acikinsa, na yanke hukuncin zan kama Mana haya kamar yanda muka saba muje mu zauna har zuwa ranar da Allah zai hore mana gidan mu na kanmu."_


Ta fada tana wasa da yatsun hannunta. 


Shiru Jafar yayi Batare da yayi magana bah, sai zuwa can tukun ya furta. 


_"Be kamata ku tashi ba, zaman haya bashi da dadi, wahala Kike san dorawa kanki Lailah kefa mace ce ba namiji bah"_


Murmushin takaici tayi tare da fadin, 

 _"Tun kafin nakai haka nake wahala, sabo da bamu da wanda zaiyi mana, ina aiki tukuru dumin na samu abunda zamuci, musha mu saka da kuma mahalli, ni nake biya mana kudin haya tun bayan na gama Secondary school dina,ina ma yanzuma dan nayi wahala ba wani sabon abu bane, zan kara samun wani aikin kamar wanda nayi a baya domin mu rufama kanmu asiri"_


Sosai Jafar yake tausaya mata, baya san yaga mata suna shan wahala, musamman yara kamar Lailah, amma tana burgesa sabo da hakan zaisa baza'a rainata bah ko kuma a mata wulakanci sabo da ta tashi ta nema, ga kuma uwa uba soyayyar da take yima iyayanta, da shi kansa hakan yana furgesa, duk da kasancewar ita take musu komai ga halin da suke ciki, amma be hana ta musu biyayya bah, sabanin wasu yaran da sun fara tara abin duniya zasu dinga yima iyayansu yanda suke su, su maidasu tamkar masu aiki ko kuma wasu yan maula,wasuma su gujesu. _"Hakane Lailah, kuma Gaskiya inajin dadin yanda kike da kokari da kuma jajir cewa wajan neman nakanki, amma mutuncinki shine aure, kamata yayi kiyi aure wallahi suma iyayyan naki zasuji dadi"_


Shiru kawai tayi dan bata san amsar da zata bashi bah. 

  Yanzu in tayi aure zata shiga damuwa ba karama bah. 


_"kinyi shiru, dan Allah nide akan maganar da mukayi jiya itace de yauma nazo da ita, zan iya durkusawa a gaban kima, dan Allah ki amince da Auran Dizhwar din mana"_


Shiru tayi, dan tabbas tana da burin yin hakan yanzu tunda ta canza shawara amma, Matsalar anan itace, ina zata kai iyayanta kuma basu taba jin dadin rashin ta bah, babu me gane abunda suke nufi sai ita, basu da wanda suka shaku dashi sama da ita, itace komai nasu inta tafi ta narsu wani hali zasu kasance. 


_"Kinyi shiru Lailah"_

Jafar ya fada yana kallantah. 


_"Shikenan Nayarda zan aure sa,amma nima ina san amun abu guda daya"_


Da sauri ya fada cikin kaguwa da kuma farin ciki, 

 _"Dole Za'a bama iyayena mahallin zama da kuma me kula dasu"_


_"Babu matsala wannan ba damuwa bane, kome kike da bukata zan miki shi wallahi, burina be huce ki aminceba kuma kinyi, nagode miki sosai ,saiki sanar da Abbanki, gobe Za'a zo neman auran naki wajansa"_


_"Allah ya kaimu, Nagode "_


_"Nine da Godiya Lailah,insha Allah bazaki taba tabewa ba, Allah ya hada kanku da Dizhwar, na tabbabata nan gaba zakuyi farin ciki da kuma alfahari da juna"_


Itade Lailah shiru tayi, haka suka gama abuda zasuyi yayi mata sallama cike da farin ciki ya tafi. 


________

Koda ta shiga gida ta sanar da mama, tayi farin ciki da hakan sosai dan dama itama burinta Allah ya bawa Lailah miji na gari,kuma ta tabbatar da soyayya ta gaskiya da Dizhwar din yake yiwa yar tasu sun san bazai wulakanta ta bah. 


________

Koda Jafar ya koma gida, Memartabah ya nema ya sanar masa da duk yanda ake ciki, 


Sarki yayi farinciki da yawa kuma yayi alkawarin hada Jafar da manya wanda zasu can gidan su Lailah gobe insha Allah kamar yanda Jafar din ya fada.


Shima Jafar din yayi farin ciki,  dan haka yana fita daga wajan sarki, nan ya fara kiran ma'aikata domin a fara gyaran wani part dan saka lailah, so yake a gyara mata shi a zuba mata kaya kamar yanda ko wata yar me gata ake mata. 

  Nan da yan kwanaki kadan za ai komai a gama, ko kafin a gama gyaran wajan nata ta zauna wajan Mami shide Jafar ya ganta cikin gidan.


Yanzu tunda yasan komai ya kammala yana da Guarantee da zai iya gayama Su Mami wannan maganar, kai tsaye can ya nufa. 


Komar kullum Suna cikin dakin Mami, Asiya tana jikin Mami akan gado, yayin da Hajiya tana zaune kan kujera sun gama shirinsu Jafar din kawai suke jira. Zama yayi, tare da fadin, 

 _"Hajiya har kun gama shirin kenan,toh ba yau zamu tafi ba kudan kara mana Sati daya domin akwai wabun da nakesan gamawa dan Allah, in kuma zaku tafi Muje ga motoci can a waje"_


Duk su ukun kallansa kawai suke dan suna san jin abunda yake san yi din. 


_"Menene kuma kake shirin yi kenan?"_

 Hajiya ta fada tana kallansa. 


_"Amarya"_

 Ya fada yana murmushi. 


Da sauri Asiya ta mike zaune tana kallansa. 


Dariya yayi tare da fadin, 

 _"Dama ina ta san zama nayi muku Bayani, toh tunda nazo ina busy sosai shiyasa, amma yanzu komai ya kankama, nan da kwana biyar Insha Allah zata tare"_


_"Kai bana san iskanci, kayi mana bayani yanda zamu gane"_

Hajiya ta fada. 


Dariya Mami tayi tare da fadin, 

 _"Jafar shakiyin yarone kai wallahi. 


Shima Dariyar yake, 

 _"Wallahi sabuwar Amarya a gidan nan, nan da kwana biyar ina fada muku"_


_"Munji sabuwar Amaryar wa? "_


Hajiya ta fada tana kallansa. 


_"Dizhwar"_


Jin abunda ya fada yasa gaba daya suka kalli juna, sannan suka maida kallansu gareshi. 


_"Dizhwar kuma?"_

Mami ta fada tana mamakin abun. 


_"Kwarai kuwa Dizhwar, Mami, kanwata na bashi,nima kwanan nan zan karo wata"_


gaba Dayan su mamaki suke dan har yanzu Jafar yana musu yaho da hankali. 


_"Ku nutsu kuji dukkan abunda ya faru, dama so nake sai komai ya daidaita sannan kuji."_


Nan ya fara basu labari tun daga farko har zuwa yanzu. 


Mamaki da Al'ajabi ya hana kowa magana acikinsu, dan abunda basu taba tunani ba kenan, Mami kuwa ba karamin farin ciki tayi ba da Jafar ya tsaya tsayin daka dan ganinsa sai anyi wannan auran,dan ya nuna musu Dizhwar din baso yake bah.


Cike da farin ciki Mami tace, 

 _"Ubangiji Allah yayi maka albarka Jafar, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, ya baku yara Nagari masu albarka, kayimin daidai, shi Atunaninsa yaci bulus kenan, ya lalata musu yarinya yayi auransa, sabo da tsabar bashi da mutunci harda zuwa da yarda tah yana kokarin yin kisan kai, kayimin daidai wallahi"_


Kallanta Hajiya Bilki tayi tare da fadin,.  


_"Fulani, meye abun daidai anan, shi haka yace yana santa, ubanwa yasa ta zo wajan nasa"_


_"Wallahi aa Yaya, dan tazo wajan biki,  bashi ya gaiyaceta bah, dan masoyinka ya gaiyaceka waje kaje laifine, shiya janyota kuma kina gani, shine ya takura ta, tunda inda da son ranta akayi da kanta zata koma gida amma kiji fa yanda akayi da ita"_

 Mami taji dadi ba karami bah.


Kallan Jafar tayi tare da fadin, 

 _"Yanzu an gama magana an samu masu gyaran?"_


Mami ta tambaya. 


_"Eh yanzu zasu je, wajan dama fa bashi da wani matsala dama komai sabone, kawai kaya tarkace za'a kwashe ayi saban fenti, sai furnitures da za'a saka"_


_"Masha Allah, ni nan zan mata komai, yarinya abun tausayi haka, zan yima Humaira magana kan furnitures dinta,insha Allah bazai dau lokaci ba"_


Dadi sosai Jafar yaji haka itama Asiya.


_"Amma Yaya saida nace maka zani na dubo ta kaki yarda,kayi tafiyarka"_


_"Menene na damuwa kuma, har gida fa zata zo yanzu ai ta zama Anty kuma"_

 Murmushi tayi. 


Hajiya Bilki itama taji dadi tana yima dan nata addu'a ko yaushe, amma a fili sai ta nuna rashin jin dadinta dan bata san a takura Dizhwar din. 


______

Dizhwar kuwa babu abunda yake jira sai saka mako daga wajan Dr.


Yana zaune cikin falon su,


Husna ce ta shigo tare da zama. 


_"Hubby tafiyar nafa gobe ne, kuma na gaya maka sati daya zanyi"_


Kallanta yayi tare da fadin,

_"Yanzu bikin kawa har sai kinje kinyi sati, nikuma fa"_

Dan bata rai tayi kadan tare da fadin, 

 _"Itama fa tazo min nawa kuma har aka gama tana nan, dan Allah ka barni naje"_


Shiru yayi yana danna waya, tashi tayi dan barin wajan alamun tayi zuciya, hannunta ya kamo, Murmushi tayi, 

 Janyo ta yayi ta fada jikinsa, ya shafa fuskarta tare da fadin, 

 _"Bawai ina hanaki bane, ina tunanin adadin kewarki da zanyi, shiyasa but am sorry,yanda kika ce haka za'ai"_


Dadi taji sosai, tare da kara shigewa jikin nasa. 


______

Dr. Kiran Zainab yayi dan jin ko tayi abunda ya saka ta domin yana bukatar kudi masu yawa wajan Dizhwar. 


Haka ta sanar masa kamar yanda sukayi da Lailah, kuma ya yarda dari bisa dari dan yasan tabbas inde anyi allurar nan ba makawa sunan mutun gawa. 


Cikin farin ciki ya turama Dizhwar text, dan sanar masa da komai ya kammala. 


*ZEENASEER*adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *