Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, February 12, 2022

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here

MISBA COMPLETE HAUSA NOVEL

 👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI=================== GIDAN NOVELS ====================================BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM


PART ONE 


01


Yammaci ne mai cike da sanyi hade da ni'ima tare da kamshi irinna damina, dai dai wannan lokacin ta fito daga islamiiya iska na kada hijabinta tare da hura fuskarta yana ratsata.haka nan ta dinga jin soyayyarsa tana bin jikinta, tana ratsata,kewarsa taji tana shigarta.farida kenn matashiyar budurwa da bata wuce sha bakwai ba .

  Daga kai tayi ta kalli gate din gidansu data zo wucewa ,haka nan zuciyarta ta bata ta shiga gidan wanda yake makwabtaka da gidansu, haka nan gidan tamkar nasu gidan ne .

    Nan ta tura karamar kofar shiga gidan ta kutsa kai tana tafiya cikin nutsuwa ,zuciyarta na magana tana tunanin wacce dabara zatayai taga NURA ? Da wannan tunanin ta shiga falon gidan ,tayi sallama .

         Mama ce ta amsa mata tana daria ,tace Farida ce ? Yan mata ,an taso daga islamiyya ?

  Ta sunkuyar da kai tana dariya ,ita dai mama ranta nason farida ,yarinya me kunya da tarbiyya .

    Nan ta zauna bisa carpet ta gaida mama ,ta amsa da fara'arta tare da tambayarta karatu na islamiyya dana boko, ta amsa da Alhmdllh .nan tayi mata addu'a tare da fatan alkhairi .

    Tana nan baba ya shigo wanda hakan yasa mama mikewa dan daga tafia ya dawo.faridan ta gaisheshi tare da amsar kayan dake hannunshi tayi kitchen dashi, sannan tadawo ta gaisheshi tare da yimishi ya hanya, yana daria ya mika mata wata leda dake dauke da zannuwa guda biyu masu kyau da tsada , yace to kinga kin tarar da tsarabarki ,ki dauki daya ki bawa Aisha kanwarki daya .

  Tayi murmushi tace ,"nagode baba, Allah ya kara arziki"

Nan ya haura sama ,mama ta bishi .

  Wannan yabawa farida damar zuwa bangaren nura wanda suke kira da DEENI .

Nan ta kwankwasa kofar dakin shuru ,ta kwankwasa ya kai kamar sau uku shuru ba motsin kowa ,hakan yasa ta tura kofar dakin tare da yin salllama. Har yanzun shuru tamkar ba me rai a ciki,sai karar Ac da sanyinta ya ratsata tare da kamshin turaren deeni mai qamshi da dadin gaske .ta lumshe ido tana shaka ,tana jin sonsa a ranta..

  A hankali ta dunga ratsa dakin tana ganin yadda ya tsara dakin ,ta kwantar da kai tana murmushi a ranta tace, "shiyasa nake sonka deeni,daga yanayin yadda ka tsara dakinka ya nuna halayyarka da personality dinka a zahiri ,,wannan yasa banajin akwai namiji irinka a duniya, kai daban ne,kai nawa ne ,kai mallakina ne"

 Nan ta lumshe ido ,ta fada wata duniyar tunanin wadda daga ita se deeni a ciki ,wata rayuwa mafi dadi a cikin rayuwar duniya"

Ta jima a haka sannan ta ware idanu tana neman ina nuran yake ?tunaninta yabata ba ya dakin,, hakan na nufin baya gidan . Nan ta turo baki alamar bataji dadi ba .

Naso ganin deeni yau ,kuma sai ya fadi dalilin da yasa naji shuru kwana biyu ban sashi a idona ba ,sai ya biya pains din danaji a zuciyata na rashin ganinsa da tsada ""


   Har zata juya sai wani haske na daban ya dau hankalinta ,wannan ya tuno mata da study room dinshi dake manne da dakinshi ,nan ta nufi gurin da saurinta .nan ta hangoshi cikin tsakiyar takardu suna zube a gurin , yayin da ta hangoshi fuskarsa mai sauke mata duk wani jin dadi da nishadin a zuciyarta ....

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRICOPIED BY SUMAYYA SAAD(sumy luv❤)02


Cikin nutsuwa yana karatu ya mai da hankalinsa sosai kan littafin, duk wanda yaganshi yasan yana karanta wani abu mai matukar mahimmanci da motsa kwakwalw da tunani.

      Ta jima tana tsaye kansa amma ko alamarta be ji ba ,,sai data kalleshi iya san ranta sannan tayi mishi uzuri data tuno gagarumar jarrabawar da ke gabansa,,haka nan tasan naci ne kawai ba wai dan yansan karatun ba ne sai yayi dagaske yake iya fahimtar karatun, sabida wannan bashi ne ra'ayinsa ba ,ra'ayine na mahaifinsa ya bi don ya faranta masa rai..

     A yadda tasan deeni mutum ne wanda baya son karatu me tsanani ko me zafi ,,deeni yanason abubuwa masu sauki haka rayuwarsa da tunaninsa duk masu sauki ne ,duk da tafito daga gida da yake cike da mutane masu zafi ,mutane ne masu matsayi,,rayuwarsu me tsada ce,tunaninsu mai girma ne,yayin da shi kadai ya bambanta..

        Deeni masoyin abubuwa masu sauki ne ,farin cikinsa yanaga abubuwa masu sauki..

   Deeni masoyin tsuntsayene ,dabbobi da duk wani abu da bai da bakin magana. Abu uku ke tsananin sanyashi farin ciki a rayuwa ,karance karance game da rayuwar wasu mutane daban da bai sani ba ,mutum ne me son karatu da bincike sai swimming pool wanda yana matukar sashi nishadi ,sai zama cikin tsuntsaye da dabbobi yana karantarsu,yana fahimtarsu tare da connecting kansa da su,sai kuma soyayyar farida data zame masa wani haske a rayuwar. Don haka a study room dinsa cime yake da takardu kala kala tun daga kan na larabci ,hausa dana turanci,na tarihi dana addini. Sai kuma takardunsa na makaranta da suka zame masa dole badan son ranshi ba sai don mahaifinsa.

       Duk da farida tasanshi da son karance karance yadda hankalinsa ya tafi akan littafin har beji motsinta ba yabata mamaki,mutumin dake fahimtar tana guri tun kafin ta iso  inda yake shine yau ta iso har gabanshi amma be san tana gun ba ,hakan yasa ta sunkuya dan taga wani irin littafi ne haka daya dauke mishi hankali har fiye da ita ?nan idanunta suka hango mata abu daya data tsani gani ,suna daya data rsani gani ba dan ta tsani me sunan ba sai dan yadda wannan marubucin ya ke dauke hankalin masoyinta akanta,,duk kuwa yawan son dayake mata..Tayi tsaki tarw da fisge littafin ,bai ankara ba ta galla masa harara tarw da turo baki ,cikin tsiwa ta ce "SAUYIN SHAUKI ko? The change of emotions) shi ne abinda zakaje ka rubuta a exams din ko ? Na tsani marubucin nan l just hate wannan writer din,saboda kai na tsani wannan MISBAH din "

     Tayi wurgi da littafin ta fita tana mita ,ya mike da sauri ya bita hankalinsa tashe ya sosa ran farin cikin rayuwarsa.

"" haba farida na,,kinsan fa bani da kamarki a duniyar nan"

   Nan ta dalla masa harara,"ai naga alama ,shiyasa har nashigo nagama tsayiwata a dakin baka san inayi ba ,naga yawan son da kake mun . Wannan banzan liffafin MISBAH din yafini muhimmanci" 

  "Oh oh !!  Haba farida na ya kike hada kanki dawani writer daban,ai darajarki ya wuce haka a gurina ,ni fa i have nothing to do with MISBAH ,damuwata shi ne brains dinsa,da intelegent dinsa" hakan ya kara kular da ita tace "to ai sai kaje kayi soyayya da brains dinsa da labaransa ,kaje ka  rayuwa da labaransa,dama new version na littafinsa ya fito shi yasa kwana biyu ban ganka ba ,na zata karatun exams kake ashe kaba nan kana wai abun daban ,to nafasa soyayyar ma "

"Haba farida na ,ai bazan iya rayuwa ba ke ba ,kema kin sani kece macen kadai da deeni zai iya rayuwa da ita,kece kadai macen da zata iya jan ragamar rayuwata ,in ba farida ai ba deeni"

 Ta turo baki ,ni dai gaskia ban yarda ba farida ta fada"

  Farida kalle ni mana "ya fada cikin murya me kashe jijiyar jiki ,ba shiri ta juyo tana kallonshi. 

 Ya harde hannu tare da zuba mata idanunshi masu rikira zuciya da kwakwalwarta,yana mata murmushi me kwantar da hankali da dauka bacin rai.

Yace tama ki yarda dani farid,trust me you re d most important person in my life,kece macen da tafi komai muhimmancin a rayuwata,my love ,my wife, my friend .

    Tuni jikinta ya mutu,taji wani irin sonsa me karfi yana tsuma ta ,ta dinga jin tamkar ta rungume shi,ra zauna a jikinsa har abada.

   Ta kwantar da kai tana masa kallon kauna tace ,,"  deeni kamin alkawari as long as ina rayuwarka bazaka sake karanta littafin MISBAH ba ,komai koyarwarsa ,komai ilimin dake cikinsa ,saboda littattafan MISBAH sun zama kishiyoyina ,shi ne abu na farko dana taba gani yana kokarin janye hankalinka a gare ni. Deeni bana son ganin abinda zai janye hankalinka daga kaina.... 
Copied sumy luv ❤❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRICOPIED BY SUMAYYA SA'AD (sumy luv❤)


03


Kamar yadda kace baka da damuwa da MISBAH sai brains dinsa ,to nima bani da damuwa dashi,damuiwata shine deeni,in kuwa labaransa na dauke hankalin deeni a kai na ,to inada matsala da hakan ,don haka inada matsala da brain dinsa,da intellegent dinsa,i have a problem wit his stories"

     Ta dan fadada murmushinsa tare da fadin "" anyi an gama ,daga yau bani ba karanta littafin MISBAH ;nayi alkawari""

   Tayi daria har da tsallen farin ciki ta ce " shiyasa nake son deeni na ,he care for me yana jin maganata ya damu da farin ciki na ,,my deeni is d best""" 

 Dariya yake mata shina yace my farida is d best"ki tsaya a gabana in ta kallonki ina jin dadi . Haka kawai kin hanani jin dadi da sukuni ,kwana uku ban ganki ba ,meyasa kika ki zuwa ki ganni ? Kinsan baba kulle yakemun inmun fara jarrabawa ya hadani da wannan manya manyan takardun ina karantawa, bana ganewa,daga na bude littafin sai inga furkar farida tanamun murmushi,bana iya komai sai kallon fuskarki a littafin "tayi murmushi tace meyasa baka dirko ta window ba ? 

 Yace " so kike in karye a ce mijinki gurgu?

Tayi daria tace "to ina ruwansu ,inma gurgun ne ba mijina bane ? Deeni na ne ni daya " 

    Yace haka farida na ni daya ""

  Farida ta dubeshi taxe deeni yaushe zamuyi aure ? Ya kalleta ya ce ko yau Abbanki ya shirya aura minke zan aure ki "

Ta masa hararar wasa ta ce ina zaka ajiyeni baka da gida baka da aiki ? Ya ce,shine damuwarki ? Kalli girman dakin nan bazai ishemu ba ? Ya jawota ,"zo kiga yawan abincin da mama take samun kullum so uku so hudu a rana ,ko ke rumbu ce zaki koshi. Awani lokaci mama nasamun abinci fiye da kala hudu a rana ,wani lokaci ma bana ci ake fita dashi .

 Bari in fada miki ni mrs deeni NURADDEN dan gatan mama da baba ne auren gata zatamun dakina ya ishemu,abincina ya ishe mu ,balle ma inkin zo mama zata kara kara. Kayan sawa zan sai miki ko wanne ,inada kudi enough a account dina ,kullum baba samun yake bana kashesu . Zan iya kula da lafiyarki ,babban shine zan kula da farin cikin ki,kullum zan dunga saki daria ,har funny faces zan dunga miki in kina so .

   Zan so ki sosai my farida ,ki rayu a dakina ,gado na,wardrop dina,toilet dina ,komai na baki . Ni zan rayu a jikin kj" yana magana yana lumshe ido.

Murmushi tayi ,kinya tasa ta sunkuyar da kai. 

Ya kira sunanta yana mata murmushi,wannan tunanin da halayyar tasa yake kara haukata zuciyarta cikin soyayyarsa, itama murmshin take masa,ganun yana matsowa gareta yasa ta fara ja da baya ,tayi hanyar fita tana kallonsa,bataki tai ta kallon sa a haka ba. Sai dai ya zama dole tayi gidan dan an fara kiran sallar magriba,za'a nemeta a gida in anji shuru bata dawo ba . Haka tana tsoro kar mama ta leko su .

     Bata ankara ba kuwa taji tayi karo da abu,da sauri ta juyo tare da daga kai. Yaya SHAMSU ne yayan deeni ,ya kalleta .  

 Haba farida yi a hankali maba,bakya gani ne?" 

 "Yi hakuri yaya ai duk laifin deeni ne " ya zaro ido ,sharri zakk mun ? Yaya laifinta ne" girgiza kai ya yi tare da murmushi ,ya ce "Deeni da Farida sai Allah ,ba'a gane muku kuma ba'a shiga tsakaninku . Ni kan nayi masallaci ,maza kaima kayi harama ,kema ki shige ciki ayi sallah,in yaso kuyi soyayyar daga baya "

 Kunya tasa ta rufe fuska ,ta fita da gudu ko sallama da mama batayi ba, deeni yabita da kallo yana murmushi ,sonta na bin jikinsa . Ya Shamsu ya kalleshi yace wai wani irin so kake wa farida ne ?

"Yaya nima ban sani ba ,ni kaina na rasa wane irin so nake mata da yawansa "

 Girgiza kai shamsu ya yi ya wuce ya barshi a wurin ...

Cpied by sumy luv❤❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Wirtting by SA'ADATU WAZIRICOPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv ❤)05 


Gidansu farida cike yake da mata da maza da kuma matan aure uku,farida ta kasance yar amarya Alh Ahmad,wato mahaifinta,kuma ita kadai ce a gurin mahaifiyarta . Haka hankalin Haj A'i yafi zuwa dana mahaifiyar farida ,dan haka shkuwarsu da zumuncinsu yafi karfi da mahaifiyar farida Haj bilki akan sauran mata Alh Ahmad din. Haka nan burinta farida ta zamo surikarta saboda salihar yarinyace ,zata zamo mace ta gari kuwa uwa ta gari. Don haka sun dade suna tsara yadda zasu hada auren deeni da farida.

Duk wani dan yasan deeni to da farida ya sanshi,haka duk wanda yasan farida da deeni yasanta ,sun zana identity na juna . Ahalin yanzu deeni nada shekara ashirin da daya yayin da farida take shekara sha bakwai,tana aji shida na secondry, su kuma yan katsina ne. 

     Farida na shirin jarrabawar gama secondry ,,shi kuma deeni ya na shirin jarrabawar shiga aji biyu na jami'a.  Haka wannan lokacin zuciyoyinsu nada burin auren juna a wannan shekarar,sabida aladar gidansu farida be aurar dasu suna gana secondry sch ba cigaba se a gidan miji. Wannan ya karawa deeni karfin gwiwar yin karatu da naci domin mahaifinshi ya cika masa burinsa. Dabi'ar deeni na son karatu yasa shi cin karo da littafin MISBAH, wanda shahararren marubuci ne na harshen hausa dama turancin duka,,idan yayi littafi da turanci yakan fassarashi ta harshen hausa,wannan ya nuna cikakken bahaushe ne,,sai dai bayaga sunan sa da email din sa bawani abu da ya nuna shi din waye ko dan ina ne"" bawani tarihinsa ko wani abu game dashi,banda sunan labari da email address dinsa sai sunan sa,,ba information akansa sai na email address din sa dayake bayyane a zahiri,,amma kuma ya boye kansa.

  Yawancin labaransa ya kunshi irkicin da samari da yammata suke suntar kansu a lokacin tasowarsu da irin matsalolin da suke fuskanta ,sai kuma abinda suka shafi shauki emotions dinsa ,yadda kwakwalwa ke ban bamta da zuciya,,da yadda suke tafia tare kwarai.

Akwai ilimantarqa sosai a littatafansa ,daga rubutunsa zaka fahimci mutun ne me ilimi da sani,,da kuma bincike akan abinda yake rubutawa ,haka nan zaka san tubutu passion dinsa ne,wani abu ne dayake so kuma yake jin dadin rubutawa,hakan ya zama tamkar wani bangare na rayuwarsa,yana nuna hikima sosai a rubutunsa ,,ga bincike ta fuskar addini da boko, ga sanya irin matsalolin da mutane ke fuskanta . Hakan yakansa mutun yaki tamkar dashi yake,ko ya taba wata matsalarsa. 

     

Wannan yasa deeni yake ba karatunsa muhimmanci fiye da na sauran marubuta. 


     Abinda yakara jan hankalin wannan karan shine yadda marubucin yake fada wasu halayyar da kwatance tamkar irin nasa,marubucin na rubutu tamkar ya sanshi,da tunani irin nasa,da hobbies dinsa, da kalar soyayyarsa,irin yadda yakeson rayuwarsa ta fati,,da irin matsalolin da yake fuskanta a halin yanzu ,,da irin rayuwar auren da yakeso yayi da farida.........wannan kenan CIGABAN LABARI

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬writting by SA'ADATU WAZIRI COPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv❤)
04


 Nuradden da farida sun kasance makwabtan juna,gidajen su na kallan na juna ,haka nan akwai mutunci da zumunci me karfi a tsakanin gidajen,akwai abota a tsakanin iyayen deeni da na farida,,haka iyayensu mata wanda zaman unguwa daya ne kawai ya hada su,duk da yanayin rayuwarsu da dukiyarsu ya ban bamta,,wannan be hanasu abota da zumunci da juna ba.

         

     Mahaifin deeni mutum ne dan kasuwa ,mai dukiya. Rayuwar gidansa kuwa zamu iya cewa rayuwace ta yan bariki tsantsa,dayawa sukan masa lakabi da bakin bature ,saboda yanayin rayuwar sa .

      Matar sa daya hajia A'i da yaransu maza uku rak. Shamsudden shine babba, sai Nuruddeni da kaninshi lukmanudden wadan nan sune yara hajia A'i .su biyar dinnan su ke rayuwa a gidansu,sai ma'aikatansu,sai dai lokaci lokaci yan uwa na kawo musu ziyara..

 Alh Umar mahaifin deeni duk da turancinsa da bokon sa bashi da wani mugun hali, ko wani mugunta . Mutum ne me kirki da alkairi ga mutane,jamaar unguwa sunajin dadin zama dashi da mu'amalar sa da su . Shi dai kawai baya so a shigar masa rayuwa,ko wani shisshigi ta fannin gidansa ko iyalinsa. Haka mutum ne me yanke shawara akan abinda ya ma sa ta harkar gidansa ko iyalinsa,mutum ne ne ra'ayi da akidar tsiya.. bai shiga harkar rayuwar wasu haka nan beso a shiga nashi. Mutum ne da in ya yanke abu ba wanda ya isa ya canja mishi ra'ayi..

      Duk wani abun jin dadin rayuwa ya mallakawa iyalinshi,,matarsa da yaransa,,haka sauran dangi da iyayensa ya wadata su da duk wani abu da zasu bukata. Sai dai fa yaransa da matarsa shi ne me yanke musu hukunci,duk wani abu dazasuyi kamar ta fannin karatunsu,me zasu karanta ,a ina zasuyi karatun ,da sauran su...


   Shamsu babban danshi yasa shi ya karanta fannin kasuwanci domin taimaka masa wurin business dinsa,yana da shekara ashirin da bakwai a duniya ya kammala masters dinsa,yana aiki tare da mahaifinsa a kamfaninsu.

    Suna zaune cikin garin kaduna ,sai dai mutanen gombe ne ,,gaba dayan zuriarsu suna can gombe.

  Shamsu yayi karatunsa a waje ,sai nurudden da mahaifinsa ya ce medicine zaiyi duk da kuwa baya so,sai dai bai masa musu ba saboda sanin hali irin na mahaifinsa.

   Tun suna yan yara shine me yanke hukunci ,ko da abincin da zasuci ne ,hatta suturar da zasu sa shike yanke musu hukunci . Sai dai wannan shekararsa ta biyu ,amma abin ya gagara ,duk nacin sa ya kasa,har yanzu yana aji daya ,duk yan ajin su da suka fara tarw sun wuce sun barshi.

    Mahaifinsa yaso turashi waje kamar yadda yayiwa shamsu ,sai dai ranshi nason deeni da yawa da bazai iya nisa dashi ba. Cikin yauansa yafi kaunarsa,ba mahaifinshi kadai ba duk wanda ya zauna dashi sai yaji  ya shiga ransa,yana kaunar sa.haka nan Allah yamasa wannan baiwar. Halayyarsa da dabiunsa abin so ne da shaawa ga kowa,dan haka yasa duk tsananin Alh umar amma yana dagawa deeni kafa.. 

       Wannan karan deeni zai sake jarrabawa ta shiga aji biyu a ABU zaria,yayin da babanshi ya mishi alkawarin yi mishi duk abinda yakeso matukwar yaci jarrabawarsa. Haka nan deeni ya dage domin a zahiri ba abinda deeni yakeso kamar farida,,zai yi dukkan iyawarsa dan mahaifinshi ya bashi farida ,ya aura masa ita .

 Soyayyar farida da deeni da shakuwarsu ya samo asali,tun suna yara ,tare suka tashi suna girma,saboda zumuncin da iyayensu mata sukeyi.... Deeni ya girmewa farida da shekara hudu ,tun suna wasan yara har takai ga suka fara girma da abota,har ta juye soyayya da shakuwa me tsanani,,wanda mutum bazai gane wayafi son wani ba a cikinsu. Iyaye da yan uwansu duka ba wanda beson maganar soyayyarsu ba . Mahaifiyar deeni na matukar son farida sabida kaunar  da sukewa juna,da kuma irin tarbiyyarya da nutsuwarta . Ta fita daban da yan uwanta.

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI COPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv❤)06 


Tunda deeni yadawo daya masallaci bayan sallar isha ya zubawa wannan littafin na MISBAH ido,wanda faruda tayi wurgi dashi ,labarin ya taba zuciyar sa da tunaninsa,yanason sanin ya aka kare amma kuma alkwari yayi ,haka nan farida na gava da wannan labarin .

    Yasa hannu ya dauki littafin yasa shaida a inda ya tsaya ,ya rufe yana kallon littafin har yasa shi cikin wata karamar drower ya rufe ,yana tunanin kalmar nan ta sauyin SHAUKI anya kuwa ?change of emotions gaskia hakan bai yiwuwa ba,gashi shi yakan gasgata duk wani labaran MISBAH ,yana da yakinin duk wani abinda ya fada yana iya faruwa,infact yana ma faruwa gana gani ,to amma wannan karon yana da ja ,sabida bai taba yadda shauki yana canjawa ba ,musamman ma shauki irin nasa,shauki na gaske ,shaukin da ya jima yana gina shi gini me karfi da tushe ,rushe shi abune da bazai taba yiwuwa ba balle a akai ga canji ..

    Nan ya yi saurin canja tunani ya dakko littafin sa yana karantawa ,amma fa karatun babu abinda yake tunawa sai littafin . Tuni haushin kansa ya kama shi , ya ma zaayi ya bari haka ta faru dashi ,?

    Zuciyarsh yaji tana zafi ,,deeni akwai dan banzan zuciya,tuni yaji tana hawa. Rufe ido yayi yana addua cikin zuciyarshi,sannan yayi saurin mikewa yabar study room din ,ya nufi cikin dakinsa ya dakko laptop dinsa yana kallon hotunan farida yana murmushi,,wasu hotunan nata tun tana jairirya,wasu kuwa tana yarinya ,,wasu kuwa suna tare tun suna yara har zuwa girmansu..

    Waya ya dauko ya buga mata ta dauka tana murmushj tare da kashe murya tana mishi kalaman soyayyar da yake so,wanda suke kara haukata zuciyar sa da soyayyarta.

  Lumshe ido kawai yayi yanajin kaunarta na bin jikinsa,yana ratsawa tare da hango su suna gudanar da wata aurw ne tattare da tsananin so da kauna,,tarw da farin ciki mara iyaka.

   Bayan sun gama wayar ne ya tirawa MISBAH labarinsa kamar yadda ya saba ta email dinsa,yana yawan sharing feelings dinsa da kuma experience dinsa akan soyayyarsa da rayuwarsa ,da tarin tunaninsa da kuma hangensa, harma yayi challengn sabon labarin sa da ya rubutu na CHANGE OF EMOTIONS .


     Duk da MISBAH bai taba bashi amsar emails dinsa ba bai sa ya fasa rubuta masa ba ,,saboda yasan ba dole ne saya karanta ba,kuma in ya karanta din ma ba dole ne yabashi amsa ba. Irin su misbah dole za suyi jin kai da miskilanci,duk littattafansa yana nuna illar girman kai,,don kuwa Allah ke bada daukakar da mutum zai yi takama dashi,in yaga dana zai iya kwacewa darw daya,wanda a wannan lokacin muamalarshi da mutane zai iya taimakonsa,sai Allah sai dai yasan akwai mutane dayawa da suke da bambanci a rubutunsu.

    Rashin amsar da misbah baya bashi be damshi ko ya bashi mamaki ba ,saboda dama ya zaci haka daga gareshi. Yasha masa tambayoyi amma shuru ,dan haka ma wannan karan yana gama tura masa email din ma ya rufe . Da da jyar yasamu karatun ya fara shiga yana fahimta kadan kadan har bacci ya dauke shi ..


Deen matashin saurayi ne dogo ba baki,kyakkyawan gaske . Ba kyanshi zai sa kasoshi ba se halayyarshi ,yana da shiga zuciya . Matashi ne da yake da kula da addininsa sosai,ya yarda cewa Allah zai taimakeshi a rayuwa,zai cika masa burinsa na samun mace saliha,kamila ta gari...

    

Bayan bautar ubangiji da biyayya ma iyaye deeni bashi da wani buri da wuce yayi aure ,rayuwar cikin aurw da yadda ya tsara zai yi shi,rayuwa ce me cike da soyayya da kuma ibada irin wadda annabin mu (SAW )ya yi da matansa,dan haka kullum adduarshi Allah ya cika masa wannan burin nasa tarw da farida.

Duk wani abu dayake fata da so da tunani a mace to farida na da shi,ga kuma soyayyar da sukewa juna mai tsanani wanda wannan shi zai taimaka su gina rayuwar auren da suke da buri. Saboda idan akwai so da kauna ana iya jure dukkan wani tsanani da jarrabawar rayuwa.

  Duk da karancin shekaru irin na deeni shi da auren nan yakeso,bashi da wani dogon buri illa ya kara girma yayi dogon karatu da kudi,ya mallaki abin duniya kafin yayi aure,saboda a fadinsa rayuwar sa ba a hannunsa take ba ,bai so ta Allah ta kasance akansa batare da ya cika burinsa ba .

Haka nan ta bangaren farida ,tunda tayi wayo,ta girma tasan kanta ,to deeni shine abokinta ,kuma masoyinta ,bata sauraron wani namjij balle ta bashi fuskar soyayya. Asali ma dai tun kafin wani ya tunkareta labarin ta da shakuwar su da deeni zai riske shi.

Gata mace me kyau da tsari ,ga tarbiyya ,abin so da sha'awa ga kowanne namijj,sai di fa nan gani nan bari ,saboda ita jinta take tamtar matar deeni,bambancin ta da matar aure kadan ne a cewarta.saboda a tunaninta tsayawa da ma ta yi magana da wani namiji tamkar tayi cin amana ne ga deeni ...


Wannan kenan🤔

 

 

Copied by sumayya sa'ad

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI 


COPIED BY SUMAYYA SA'AD(sumy luv❤)07


Kwani tashi deeni ya tattara ya koma zaria,suka fara jarrabawa. Haka nan ra bangarwn farida ma suka fara jarrabawar kammala secondry,hakan yasa sukayi besa da juna . Haka nan yawan mu'amalar su ya ragu sabida karatu da kuma karancin lokaci,sai dai duk da haka rana bata fitowa ta fadi batarw da sunyi magana da juna ba na tsawon lokaci tare da mafarkin tsara rayuwarsu tare..

     Deeni ya rigata gama jarrabawa dan haka ya tattaro ya dawo gida tare da shiri da tsare tsaren yadda aurensu zai kasance .yana karati sannan wani lokacin yana zuwa gidansu farida suna karatun tare ,,yana koya mata abinda bata gane ba . Haka nan yana matsawa mahaifiyarsa akan tafara yiwa mahaifinsa maganar auren sa da farida .

     Takanyi murmushi tace karka damu mahaifinka zai yi kama komai ,,farin  cikinka shine namu duka "

  Hakan yasa hankalinsa kwanciya tare da alkawarin dagewa yayi duk abinda mahaifinsa yakeso,donya faranta masa ko da zaiyi abin da ransa bai so,don ya yadda farin cikin mahaifinsa shi ne samun nutsuwar sa da kwanciyar hanklainsa 

  

* * **************

Farida !farida!!farida !!! Taji muryar kaninta na kwala mata kira.

 Hararsa tayi ,"meye ne ?

 Tana kwance kan gado rungume da hoton deeni,yayin da take magana dashi ta waya,kuma ko minti goma basuyi cikakke da rabuwa ba . Ba abinda ta tsana irin tana magana dashi a katse ta .

      Ganin harar datayi masa yasa kanin nata me suna yusuf shima ya turo baki . 

    "Meye kikke hararata ? Ai nima Abba ne ya aiko ni in kiraki ,in ba zaki zo ba sai inje in fada masa kina waya baki da lokacin amsa kiransa;""

A'a'a ,zo yusuf,tsaya,yi hakuri bazan sake harararka ba ,kace masa ina zuwa""

Harararta yayi yace kinci sa"a da kinga sharri :"

 Nan ya fice ,ita kuma ta mike da sauri ,ta bangarwn deeni a waya kuma yanata tsokanarta.

  "Kicewa Abba kina biyayya wa mijinki ne ,kina faranta masa rai ,kina masa hira me dadi ,yana jin miryarki me dadi yana ratsa masa jikinsa,kina samun lada,""

""Eh sosai zan fada masa,in yazo mun fada sai in tattaro har da kai ya hada-" 

"Bakomai ya bata amsa"

"Ai dama dadi da wuya munyi alkawarin rabashi ni dake "

 Tayk murmushi zan dauki wuyar ka dau dadin .

"A'a ni zan dauki wuyae ke ki dau dadin " ni dai a'a . Ta fada xikin muryar shagwaba .

 Kin gankk ko ? Kin fara kashemun jiki da shagwabar kin nan ko ? Yanzu tunaninki sai ya fitine ni ya hanani sakat "

Tayi daria , ai haka nake so ,tunani na ni kadai ya fitini zuciyarka ""

     Farida ! 

 Ta sake jin murtar mahaifiyarta ,da sauri ta katse wayar ta fita da gudu ,ta ce 

Gani nan zuwa umma ,ina bayj ne ." To maza kiyi ki fito Abbanku nasan magana dake tun dazu " to umma " 

Nan fa tayk falon nashi zuciyarta cike da tunanin kiran me yake mata haka?

 Ganin sauran yayunta mata yasa gabanta faduwa ,dole akwai maganar da Abba zai mata .

   Nan ta nemi guri ra zauna ta gaishe shi tare da fadin "Abba gani "

 Ya kalleta yace naki ra yan uwanki nayi musu maganar aure ,kamar yadda kika san aladar gidan nan kuna gama sexondry nake auren ku .  To Alhamdullilah ,lokaci yayj yan uwanki kowacce ta fada mun zabinta ,kuma nace su turo iyayensu ,sannan zanyi bincike in mun dai daita sai aure,don haka kema nakeso ki fadamun zabinki ,in baki dashi to sai ni in zabar miki ."

   Kanta sunkuye zuciyarta taji tana harbawa ,ga Abba yasa mata ido alamar ita yake saurare . Bata dago kai ba ta ce ."Abba Deeni ne mukayi maganar aure dashi ""

 Dama dai hakan ya zaci ji ,,sai dai saboda sanin su tare da kuma mahaifiyarta ta fada masa,sai dai yana son jin hakan daga bakinta . Ya gyara zama ya kalleta ya ce " deeni dan gidan makwabcin mu ko ?"

 Ta amsa da eh "

"Yace to kamar yadda na fadawa yan uwanki ,kema ki fada masa ya turo mahaifinsa inhar aurwnki zai yi da gaske ,yaro ne da aka haifeshi a ido na nasan iyayensa,nasan halayyar sa,don haka bani da bukatar bincike akansa illa maganar aure. Ku tashi kuje dama maganar kenn""

  Nan suma mike duka suka fita.Farida ta tsinci kanta cikin wani yanayi dabata taba shiga ba ,,ta rasa wani irin abu takeji a zuciyarta da jikinta ? Fargaba ne ? Farin ciki ne ? Doki ne ko tunanin aurwn ne ? Ta rasa me takeji ,sai dai tabbas jikinta ya mutu murus.

Jiki ba kwari ta dau waya ta latsa sunan deeni ta sa a kunne, sai dai wayar tayi ringing har ta gaji ba amsa.


A dai dai wannan lokacin deeni na zaune gaban mahaifinsa eansa bace yana masa  fada saboda sake faduwa jarrabawar sa da yayi wannan karon . Ya jima baiga mahaifinshi cikin bacin rai haka ba,shi dai kansa sunkuye yana bashi hakuri,saboda shima baiji dadin hakan ba .

     ""  Baba kayo hakuri ,nayi iya kokarin iyakacin iyawata amma har yanzj Allah bai sa na kai ga masara ba "" 

Wannan kake kira kokri " baban ya fada a fusace.

   " ai mai kokari ba ya gazawa,kar ka dauka zamu shirya muddin kana wasa da karatu,in har baka min yadda nakeso ba kar ka zata zan taba maka yadda kake so ""

 Nan ya mike ya fita ya barshi a wurn .

Hankalinsa ya tashi matuka ,haka ran sa ya mummunan baci ,yaji wanj irinzuciya da bacin rai na taso masa. Rufe ido yayi yana addu'a saboda samun saukin abinda yakeji. .

Wai har yaushe za su dunga samun rashin fahimta da mahaifinsa ? Sam ya kasa fahimtar sa ;ya kasa ganin kokarinsa. Ya makale a aji biyu ya kasa gaba ya kasa baya ,tabbas in ya sake faduwa korar sa za'ayi.

Zuciyar sa da kwakwalwarsa suka cushe da tunani iri iri ,ya rase meke masa dadi  .

Mahaifiyarsa ce ta shigo tana bashi baki da lallashi tarw da kalamai masu kwantar da hankali har ya samu zuciyarsa tayi sanyi kadan ,,sannan ya mata godia ya samu ya mike ya shiga ciki . A nan yaci karo da tarin kiran farida a wayarshi,bai bata lokaci ba ya kirata ta dauka cikin muryar shagwaba tace "

      " nayi fushi "

". Afuwan my dear ".   Ya fada cikin mueyar lallashi.

"". Deeni meke damunka naji muryarka kana cikin damuwa?

 "Akwai farida ,yau ma kamar kullum ban sami nasara a jarrabawata ba ,banji dadi ba ,haka na batawa baba rai , dukkan wani tsammani na yanaga jarrabawata""

  Murya kasa kasa tacw nina banji dadi ba deeni ,,wannan karon naji ciwon abun diue da kai da Baba " 

""Farida kalamanki sun razana ni ,yau ce rana ta farko danaga kin nuna damuwarki akan rashin nasarata , na zata kin fahimce ni ,kinsan matsala ta na rashin fahimtar karatun da nake amma duk da haka ina dagiya don ganin na cimma burin baba da kuma burin kasancewarmu tare da ke "" na sani deeni " ta bashi amsa .

Murya kasa kasa tace "kamun rashin fahimta nima,na nuna damuwata ne badan gazawarka ba ,sai dan son kasancewarmu tare ,tunda da bakin ka kace idan ka ci wannan jarrabawar babanku yayi alkwarin maka duk abinda ka nema ko kake bukata ,tabbas da ka samu nasara da yazo dai dai lokacin da muke da neman biyan bukata .......

 

 Bye 

 

Copied sumayya sa'ad❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRU GOMBECOPIED BY SUMAYYA SA'AD❤❤

09


 Muryar deeni sukaji tsaye daga kofa.

  Ya karaso cikin falon hankalinsa a tashe. In akwai abinda take dagawa deeni hankali be wuce ace zai rasa farida ba ,ya durkusa a gaban mahaifinsa idanunsa jawur ,hanakalinsa baya jikinsa,,ya ce ,

"Baba addini be hanani aure ba ,hasali ma ya halattamun yin aure a wannan lokacin. Baba addini bece dan bakaci jarabawar makarantar duniya ta boko karkayi aure ba ,,addini bece dole sai kanada gida da mota da abun duniya sannan kayi aure ba . Baba ka fadamun hujja da addini ba da abin duniya ba . 

   " ina zaka ajiye matar?

"Dame zaka ciyar da matar?:

   Mahaifinsa ya jefa masa tambaya fuskarsa a daure,saboda koda wasa bai shirya yiwa deeni aure a yanzu ba .

Baba inada mahaifina wanda yake da arzikin da zai iya rikeni nida mata ta,har zuwa lokacin da zan gina kaina incigaba da rike kaina da matata har da iyayena da kuma sauran 'yan uwana. Baba ba zama zanyi kaita ciyar dani kana rike ni ba ,zan tashi in nema ,zanyi karatu,komai zanyi dan in kafa kaina . Baba ka taimaka mun matsayinka na mahaifina ka dafa mun .

 Baba ni dan gatan ka ne ,na roke ka don Allah kayimun wannan gatan ka auramun farida, baba idan na rasa farida na rasa komai,baba farida macece ta gari,yarinya ce kamila ,ga nutsuwa da addini,macece danake yiwa yayana kwadayin samun uwa kamar ta.

 Na jima ina gina soyayyata da rayuwata da zanyi da farida,baba banj da wata rayuwa in har ka rusa min wannan rayuwar na rasa ta............

      Tausayinsa ya kama hajia don haka itama tasa baki tana taya deeni rokonsa. 

     Alhaji yaji ransa na baci ,,sai dai deeni yayi abinda zai yi ,amma bai isa yace zaiyi aure yanzu ba ,hasali ma ya dauki abin nasa a yarinta ,dan haka ya mike yabar musu falon ransa a bace batare da yace musu kala ba . Sai dai hakan ya tabbatar musu dacewa bai yiwa deeni abinda yakeso ba ,lokuta da dama daga yanayinsa suke gane eh ko a'a dinsa.

Hakan ya kara rikita deeni ,yabishi yana rokinsa.


  Ransa na matukar kaunar deeni ,,komai zai iya masa amma fa banda maganar aure yana dan karaminsa. Bashida wani dalilin da zai sa yaki aurawa deeni farida,sai don kawai ba yanzu bane lokacin da yakamata  deeni yayi aure ba . Don haka ya dauka kai garesu yayi tafiarsa.

       Bangarensa ya nufa batare da damuwa da halin da deeni yake ciki ba,dan yasan yarinta ce ke damunsa,rashin sanin ciwon kansa ne yasa yake cewa zaiyi aure yanzu.

   Deeni yakasancwe cikin halin dimuwa da tashin hankali,lokaci guda yaji duniyar tana juye mishi sama da kasa ,rayuwa ba farida wani abune da bai taba tunani ba ,don haka da sake .

Ganinsa cikin tashin hankali yasa mama itama hamkalinta ya matukar tashi,ta hau lallashi da bashi baki cewa zata cigaba da lallaba mahaifinsa har ya amince. Da kyar tasamu ya saurareta ,sabida idonsa ya rufe ,bai san ma me yake fadi ba .

Yace ,, ba wanda ya isa ya hanani auren farida ,ko mahaifinsa bai yadda ba shi zai aureta a haka". 


A wannan dare deeni yayi kwanan tashin hankali da bakin ciki tare da tsoron rasa farida a rayuwar sa,a duk lokacin da yatuna zai iya rasa farida idan har nahaifinsa bai amince masa ba sai yaji ya tsinci kansa cikin gigita da dimauta. Haka ya kwana abin a ransa,ya kuma tashi dashi ,yayin da hajia ta kwana magana daya da mahaifinsa tana nuna masa  tsakanin deeni da farida in an raba su ba karamin illata rayuwar su za'ayi ba.amma fir Alhaji ya kafe ba wanda ya isa ya canja mishi ra'ayi.

 Washe gari a haka suka tashi gidan cikin rashin kwanciyar hankali ......Sumy luv❤❤❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE 


COPIED BY SUMAYYA SA'AD❤❤08


Deeni ,abba na yamana maganar aure yau,kariga da kasan hakain abba,muna gama secondry sch yake aurar damu,kuma kasan tsattsauran raayi irin nasa,ba mai canja masa,wannan akidar gidanmi ne ,ni ban isa incanja ba . Kuma deeni kasan kaine rayuwata,baza iya ko tunanin rayiwa da wani da namiji ba ,inba deeni ba . Abba yace katuro,in baba yaki fa ?

     " bazai ki ba farida ,saboda baba naso na,kuma zan nuna masa idan bayason rasa kai na to ya auramun farida "

     Tuni muryarshi ta canja ,"Farida kimun alkawari duk runtsi bazaki rabu dani ba ki auri wani ba. Farida bansan ya zan rayu bake ba ." 

  " Deeni nima ba zan iya rayuwa dawani ba in ba kai ba ,,nutsuwata da lafiata sai in ina tare da kai deeni" 

Cikin muryar damuwa yace ,farida muna tare duk rintsi bazamu rabu ba ,zan fadawa abba zai zo nema mun aurenki gurin abbanki"

     " kayimun alkawari deeni?? Nayi miki alkawari farida " ya bata amsa. 


  Nan sukaita bawa juna kwarin gwiwa tare da kaunar juna,,sannan sukayi sallama.


     Wannnan tsoron dashi deeni yake kwana yake tashi ,wato tsoron rasa farida. Yana firgitashi sosai,sabida sanin halin mahaifinshi dana farida,dukkansu suna tafia ne akan ra'ayinsu da tsarinsu,ba wanda ya isa ya canja musu ,,sai dai yakan danji sanyi idan ya tuna irin soyayyar da mahaifinsa ke masa,zai iya aura masa farida don farin cikin sa.sannan a tunaninsa daga shi har farida basu da wani dogo buri,,dakinshi zai ishesu rayuwa kafin su kai ga inda zasu.


Suna gama waya bai bata lokaci ba ya nufi dakin mahaifiyar sa,kai tsaye ya labarta mata abinda ake ciki. Kansa sunkuye gaban ta yana sauraron amsar ta,yayin da ita kuma tayi jugum tana juya maganar a ranta.


 Tabbas tasaan abu ne me wuyar gaske,sai dai kuma tasan irin tarin soyayyar farida da deenikarfin soyayyarsu ya wuce a rabasu,,ya wuce tsattsauran ra'ayi da akida irinta iyayensu ,dole ne daya zai sakko ko mahaifinsa ko nata,raba deeni da farida sai Allah .


      ""Mama""deeni ya katse mata tunani.

Ya kalketa,tunanin me kike ? Ko akwai matsala ne ? 

Tayi masa murmushi tarw da girgiza Kai , ta ce .

  """ Bawani matsala insha Allah ,anjima idan ya shigo zanyk masa maganar ,karka damu "

 Ya sake kallonta cikin fuskar damuwa ya ce ;;

" mama ba ' a samj matsala ba ko ?

 Tayi masa daria ,deeni kenan ,baza'a samu ba insha Allah ,komai zai tafi dai dai .ba kai kadai keson farida ba,nima ina sonta "

   Murmushi yayi ya sunkuyar da kai,, ya fiya zuciyarahi cike da murna.

 Tun fitarsa mama tashiga cikin damuwa da maganar zuci,tasan dole akwai rigima tsakanin deeni da mahaifinsa. Nan tacigaba da addua Allah ya kawo abun cikin sauki.

 Daga deeni har mahaifiyarsa sun kasance cikin zulumi da tunanin me zai faru ? 

Jin dawowar mahaifin nasa yasa yaji bugun zuciyar sa ya karu ,ya dunga safa da marwa a tsakar dakinsa. Baiyi yunkurin fita ba ,yana jira har sai an bukaci yaje.

    Yadda deeni yake cikin tunani da fargaba haka farida ma ta kasance ,tana sauraron wayar deeni .

  Bayan Ahj umar wato mahaifin deeni ya gama duk wani abu daya saba na al'adar sa in ya dawo,yana zaune a falonsa haj A'i ta same shi da maganar deeni . 

"Alhaji magana zamuyi" ta fada tana kallon sa ,hakan yasa ya juyo ya maida kallonsa gare ta tare da tattaro hankalin sa akanta yace """  wace irin magana kuwa "? Ta gyara zama tacw ,,nu kabata sanin soyayyar deeni da farida kuwa,,''??

Ya kalleta ban gane ba ,deeni da farida?

 "".  Ta girgiza kai " kwarai......

Nan ta bashi labarin soyayyarsu,da shakuwarsu, takara da cewa .

"Yanzu lokaci yayi da mahaifin farida yakeson ya aurar da ita tarw da yan uwanta,kamar yadda kasani shi mahaifinsu yaranshi na gama secondry sch yake aurar dasu ,farida kuwa bata da wani saurayain da yawuce deeni ,,dan haka tayi masa magana ya fito,ya tura iyayensa a san da maganar neman aurenta ,shi ne ya min magana ya ce in fada maka""

Alhaji ya kallwra cike da mamaki ,ya ce .

Haba hajia ,ya kikemun irin wannan maganar kamar wata karanar  yarinya ? Insu yara ne kema sai ki zama yarinyae ki biye musu ? Yaron da karatu ma ba inda yaje ? Yaron da baisan ciwon kanshi ba shine zaa nemar masa aure? Dan uwansa ma yaushe akayi maganar airen sa wanda ya girme da komai balle shi ? Da maganar shamsu ma kika min sai na saurareki amma DEENI ?ai ko ina da yarinya bazan aurawa kamar deeni ba ,yaron da yaki karatu,ya kasa nai da hankali akan rayuwar sa, yasan me yakeyi,ahekarun deeni nawa wai kike maganar auren sa? Shekarunsa ishirin da daya,yaro ne dabai san ciwon kansa ba balle har a dora masa na wata .

" baba addini ya hana dan shekara ishirin da daya aure ????

Muryar deeni sukaji tsaya daga kofa...................
Copied by sumy luv❤❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE


COPIED BY SUMAYYA SA'AD❤❤
10Tunda sassafe farida ta bugawa deeni waya,daga jin muryarsa tasan ba lafia ba ,hankalinta yai mummunan tashi,kawai sai ta fashe mishi da kuka ,muryarta na rawa tace .

    ""Deeni ya zamuyi ? Dama abinda nake tsoro kenn kullum ,kasan babanka ba zai yarda ba ,haka abbana ba mai canja masa ra'ayi,bazai taba bari na in zauna injiraka ba ,hada ni aure zaiyi da koma waye ""

" cikin muryar rauni da matujar tashin hanklai yace 

   ""Saurareni farida, baki da wani miji sai in Nsha Allah,Allah ne ya hadamu ba mai rabamu . Inma baba yaki nizanje in sami yayana babana,Bappah na zaj daura mana aure ,ba dai abbanki zai aura min ke ba ?

 Abbanki zai aura min ke ,in har nabturo waliyyi na zai daura mana aure . Anjima kadan ,zan fita,zan wuce gombe ,zan je in sami bappah na ,kafin in wuce inason ganinki,ki fito kofar gida mu hadu"

 Nan ra amsa masa da toh,ta ajiye wayar .

 Bai bata lokaci ba yayi wanka ya kimtsa,ko breakfast bai tsaya yi ba ,ya cewa mama shi ya fita. Ko kallon mahaifinsa baiyi ba balle ya gaishe shi.

Tsawa ya daka masa tare da kiran sunansa.

  Cak deenin ya tsaya ,sai dai ko juyowa bai yi ba balle ya yi niyyar zuwa inda yake.

    Alhaji yace ,ban haifi dan da gari zai yawaye yana kallona ya wuce bai gaisheni ba,baka isa ba ." 

Jin hakan yasa deeni ya juyo ya kalleshi fuska ba walwala ya ce .

      " Ina kwana ? Da fatan ka wayi gari lafia ""?

 Bai saurari amsar mahaifin nasa ba yasakai ya fita ,mahaifin nashi ya bishi da kallo. Baiyi mamakin hakan ba,sabida yasan halin deeni ,sai dai fa duk abinda zaiyi yi dan baazaiyi aure yanzu ba da  bai san ciwon kansa ba ,yayi haukansa ya gama .

   

""Ina kaunarka dana ,,shiyasa nake son yiwa rayuwarka gata kafin in kai ga maka aure,,sai na maidaka mutum sosai,,mace kowa zaka sani kowacce iri kakeso a rayuwa " 

          Mahaifiyar deeni ce ta shigo tare da matsowa inda yake , ta tsake masa tunanin da fadin "

     Alhaji bazaka sake duva maganata ba kuwa ? 

       Ka auna irin soyayyar da rayan nan suke yiwa juna , karfa ka illata rayuwarsu sabida wani dalili naka na daban . Sannan yarinuar nan ya kakeso tayi ? Dukkna tsawon rayuwarta bata da wani wanda take saurara in ba deeni ba ,kanaso ace deeni ya yaudareta ya rabata dawasu mazan kuma shi be aure ta ba ? 

     Ya dago udo ya kalleta yace ,

 In bazaki gaji da maganar nan ba ,to nima bazan gaji da fada miki a'a ba ,sabida bazan biye miki inbata rayuwar dana ba . Inshi bashi da hankali yakamata ace ke kina dashi .

   " Alhaji a duba yarinyar nan,ita kuma meye laifinta a ciki don taso danmu,jininmu ,sai mu hukuntata akanshi ? So kake mahaifinta ya hadata da duk wanda ya samu ? Farida kamar diyarmu ce,bazamuso ta shiga gidan wani can da bata san halinsa ba ..""

      " wannan ne damuwarki ?

   ," duka"" ta amsa  masa .

" Saboda deeni yanason yarinyar nan fiye da tunaninka ,haka ba jima da saka burin farida tazama surikata ,uwar jikoki na . Na tabbatar da zanyi alfahati da ita ,duk inda akeson mace ta gari ,yarinyar nan ta kai ""

   "".  To shikenn naji ,karki damu indai wannan ne damuwarki ""

     Ta kalleshi cukin murna sa doki tace ,,kana nufin ka amince ?   

    " ki saurara ,ki sa ido kiga hukuncin da zanyj ,,ba zan bata rayuwar kowa ba "

 Yana gama fadi ya mike ya nufi dining table ,ta bishi da kallo tana nazarin kalamansa.

     Kawarai hakan ya mata dadi ,saboda akwai alamun nasara . Da murna ta mike ta bishi tana murmushi ba tare da takara ce mishi komai ba ,sai kokarin masa hidima . 


      Denni na fita kai tsaye ya wuce gidansu farida ,a kofar gida suka hadu dukkansu hankalinsu a tashe ,,farida idanunta jawur tana ta zabgar kuka tamkar wadda akace iyayenta syn rasu. Hakan ya mummunan daga hankalin deeni ,soyayyarta ya dinga ji yana ratsa shi,yaji tankar ya jawota jikinsa ya rumgumeta ,sai dai bashi da ikon yin hakan ,don hakan sai yayi abinda yasan zai iya ya hau lallashinta tare da bata karfin gwiwa cewa ba gudu ba ja da baya yana tare da ita ,alkawarin da ya mata na aure ba fashi ,yana tare da ita.

 Ta kalleshi idanu jawur sun kimbura ,ta ce 

     ""Deeni ina zan saka raina in na rasa ka ?

  " ya zanyi rayuwar da batare da Deeni ba ?yaya zan soma rayuwa da wanj namiji a rayuwa matsayin miji ba Deeni ba ??

 Nan yayi saurin rufe mata baki ,idanunsa suka kada,ya dinga jin wani irin zafi da radadi a zuciyarsa.

   " karki kara furta haka farida ,karki sake ambatun rayuwa da wani namiji a rayuwarki. Kinajin zan iya numfashi in ganki kina rayuwa da wani ? Farida duk runtsi,duk wuya ,duk dadi ,munabtare da junan mu. Ni ne mijinki abokin rayuwarki,in Allah ya yarda zan mutu in na budi ido naga kin auri wani namiji """

 Hawayene ya gangaro mishi na tausayin kansu duka .Sumy luv❤❤

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECOPIED BY SUMAYYA SA'AD❤❤
11


Deeni ,farida ,ku ne da sassafe haka? Lafia kike ta kuka inata magana tun dazu baku.ma san ina gurin ba ?


 A tare suka mai da kallonsu kansa,shamsu ne yayan deeni. Tuni deeni ya fada jikinsa yana kuka.

     " ya shamsu kaji abin da Abba ya mun ko? Wai bazan auri farida ba ,ya shamsu kasan irin son da nakewa farida,ta yaya zan iya rayuwa babu ita ? 

 Itama faridan tayashi tayi tana kukan tace .

 " ya shamsu ka taimakemu ,bazan iya auren wani namiji ba sai deeni,ya shamsu zan mutu inba deeni ,"

   Kawai ta durkushe har kasa ta rushe musu da wani irin kuka deeni na tayata . Gaba daya suka zamewa shamsu hoto,ya bude baki yana kallonsu,yana mamaki duk da yasan irin soyayyar datake tsakaninsu ganin su cikin wannan tashin hankalin ya bashi mamaki tare da tausaya musu.

   " yi hakuri farida " ya fada cikin muryar lallashi.

      "" ba mai rabaki da deeni insha Allah ,zan taimaka muku , dake da deeni duk kanne na ne ,share hawayenki,mike muyi magaana." 

      Haya ya dunga sharewa deeni hawayenshi ,yana lallashinsu duka har suka dab fara samun nutsuwa ,anan ya tambayi deeni ya bashi labarin yadda sukayi da mahaifinsu,farida ma ta fada mishi yadda tayi da nata mahaifin ,ta kare zancen da kuka tana cewa "

    Ya shamsu in deeni bai fito ba wlh Abba auramun duk wanda yakeso zaiyi,ni kuma ya shamsu deeni nake so " ta fashe da kuka .

        " ya isa farida,naji "

   Ya fada cikin muryar lallashi da tausayawa , a ransa yace ,"soyayya me zafi ta kama zuciyar yan  yara."


     Ya tausaya musu kwarai,musamman a wannan shekarun irin na su da dukkansu ba mai tunani dai dai,,haka nan duk yadda zaa musu bazasu taba fahimta ba ,sabida sun haifi soyayyarsu tun suna yara suka tashi da ita ,sukayi ta rainonta ,don haka ravasu da juna ba karamin tashin hankali bane a gare su. Don haka ya kudiri aniyar taimaka musu,sabida a halin yanzu bazasu taba fahimta ba ,abu daya zasu fahimta a aura musu juna,kafin haka ya faru kuwa sai iyayensu sun canja ra'ayinsu ,ko dai baba ya hakura yayiwa deeni aure yanzu,ko kuwa Abban farida ya hakura tabar farida har deeni ya gama karatunshi. Sai dai fa wannan abin yafi komai wahala,don kuwa in duk duniya da abinda ke cikinta zasu taru basu isa su canjawa iyayensu ra'ayi ba.

        A nan ya shamsudden suka yanke shawara da deeni da farida. Cewa zasuje can Gombe su sami Bappan su suyi mishi bayani ,haka zai nemi wani yayanta ya rakashi katsina itama su sami wani yayan mahaifinta wanda in abbanta yaki amincewa shi sai ya daura mata aure da deeni,shima deeni se kanin mahaifinshi ya masa waliyyi, in yaso wurin zama gida da komai zai dauki nauyinsu akansa. 


Nan take murna ta cika zuciyar deeni da farida,har ma suka haskowa juna murmushi,suna yiwa shamsuddenen godiya .

   Kwarai yaji dadin ganinsu cikun farin ciki ,saboda shi dai daga deeni har farida kannen sa ne . 

    Bayan sun sami butsuwar ne ya tambayeta ko Abbanra ya tashi ? Don dana baba ne ya aikeshi ya  ce ya fada masa yau da yamma inbaya komai yana so su hadu,akwai maganar da zasuyi .

   Nab deeni da farida suka kalli juna jikinsu yayi sanyi,deeni ya ce " maganar rabamu zasuyi ko ?

 Shamsu yace kwantar da hankalinka ,in ma magnar zasuyi ai mun samo mafita ko ? Kasan ko baba beji maganar bappa ba amma dai bappah zai saurare mu ,kuma ya daura maka aure ko ? 

    Farida ma tace ,Abban mu dai najin maganar Bappan mu,amma fa zai yi wuya ya canja masa ra'ayi , sai dai nima zai iya daura min aure "

    Shamsu yace to kun gani ,karku damu,kuyi murmushi"

    Nan suka masa murmushi duka,shima ya musu sannan ya shige ciki ya barsu a gurin a tsaye.

         Deeni ya kalli farida yace, " Nsha Allah sai na mallake ki masoyiyata ,matsayin matata ta sunnah". 

Allah ya tabbatar mana deeni,tafada tana kallon sa.

         Yace , farida in yaya shamsu ya fito zamu wuce,inaso ki tuna ki sani ,duk wuya duk rintsi muna tare,farida ke tawa ce kimun alkawari."" 

       "" ni taka ce har abada ,ni amanarka ce""

    ""Farida nima naki ne har abada ""

   " Mu tafi " muryar shamsu sukaji ya fito. 

     Nan ya dinga zolayar farida yana cewa.

 " mata zankadediyar zan masa a Gombe ,sai ku zama ku biyu ;" 

     Ai kuwa bai ankara ba ya ga tasa masa kuka ,ba shiri ya hau lallashi har ya samu tayi shuru. Yana jinjina soyayyar da suke yiwa juna . Nan ya shige ciki ya fadawa baba sakonsa ,sannan ya ciro motar sa suka kama hanyar Gombe ,farida na tsaye tana kallon su har suka bace .

Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE


Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤
12


Dab da magriba Alh.Umar ,wato mahaifin deeni ya dawo daga office dinsa,kai tsaye ya wuce gudansu farida,ya samu mahaifinta a falon sa ,suka gaisa ,suka hau tattaunawa akan kasuwanci sannan matsalolin kasarmu da muke ciki na yau da kullum har aka kira magriba,sukayi alwala suka nufi masallaci tare.

      Abinci da komai tare sukaci a gidan Alh. Ahmad,wato mahaifin farida. Suna nan tare har bayan isha'i,sukayi sallah suna hira har Alh. Umar ya yi masa maganar da ainihin ta kawoshi. Sun jima suna tattaunawa akan maganar wanda ya dauke su tsawon lokaci,har kusan karfe goma na dare ,sannan suka kai ga matsaya ,suka yanke hukunci, da alama kuwa dukkan su sun amnince da hukuncin da suka yanke.

       Goma da rabj sukayi sallama ya nufi gida wanda ya yi dai dai da lokacin da su deeni suka dawo daga gombe.

        Alhji yayi mamakin ganinsu a wannan lokacin. 

      " shamsu ,deeni, daga ina haka "? 

      Deeni bai saurareshi ba ya kama hanyar shiga cikin gida,ya daka masa tsaqa. 

   " Wai bada ku nake magana bane zaka kama hanya ka shiga ciki?

      Bai saurare shi ba ya cigaba da tafiya,hakan yasa Alhaji shan gabansa ya ce,,,,

    "" kai saurara ,gidana kake ,magana nake maka,wa zaka gwadawa danyen kai ? Me kake ji dashi ne ? Kana tsaye a gidan nawa.............""

 Deeni ya katse shi ,ya ce, " ina tsaye a gidan mahaifina ne ,bandmga kuma wanda ya isa ya hanani shuga gidan nahaifina ba ,randa na shiga gidan mahaifinka sai ka kore ni ;;""

 "" Deeni !!! Shamsu ya daka masa tsawa .

  "" Bakada hankaki ne ? Baban kake yiwa wannan maganar? Ban fa sanka da rashin da' a da kadabi ba , meye ya haifae da wannan rashin da'ar ? 

   Mahaifin nasu ya kalle shi ,"dakata shamsu,kyale ni dashi ," ya kalle deeni ya yi murmushi tare da shafa kansa ya ce , 

"" kayi gaskia dana ,nan gudan mahaifinka ne ,ba wanda ya isa ya hanaka shiga ko da kuwa mahaifin ne da kansa. Ina alfahari da hakan,da fatan kai ma zaka yi kokarin tsayawa kan kafafuwanka ka samu naka gidan na kanka ka ajiyeqa naka yaran yadda watarana zasuyi alfahari da cewa nan gidan ubansu ne ,don kuwa kai zan iya kyale k saboda kace nan gidan ubanka ne,kuma ba yadda na iya da kai tunda ni nakawo ka duniya. Amma kasani bazan bar dan ko yarka a gidana ba ,sabida kai ka kawosu duniya ,dan haka kayi kokarin nema musu muhalli kafin suzo,in ba haka ba karkayi kuka dani duj randa ba kori naka yaran a gidana na bar nawa dan,tunda gidan ubansa ne ..?

      Nan deeni ya dinga jin zuciyarshi kamar wuta ,ransa bace ya shige ciki ba tare da ya sake tankawa ba . Ya fahimci sarai me mahaifin nasu ke nufi.

        Alhajin ya bishi da ido yana masa daria ,zuciyarsa cike da tsananin kaunar sa. Sannan ya mai da hankalinsa kan shamsu,ya kalleshi yace .

   " In shi yaro ne kai babba ne a kansa,ka dunga kula dashi kana bashi shawara me kyau,ka dai na biye masa. Karku manta ku ya'ya na ne ,ni mahaifinku ne "

   Yana gama fadi ya juya ya yafi batare da ya saurari me zai ce ba ,nan shamsu ya wuce daki yana nazarin maganganun mahaifinsa tare da juya su a kwakwalwarsa.

      Bayan fitar Alh. Umar daga daga gidansu farida bai jira sai da safe ba ya nufi bangaren su farida don yana da bukatar yin magana da ita a wannan daren. Ga mamakin sa kuwa ,da ya buga kofar bangarensu ita tazo ta bude masa kofa,ya lura tana cikin damuwa wanda shi ya hanata baccin ma.

      Hannunta ya ja har zuwa falonshi ya zaunar da ita suna fuskantar juna ,idonta jawur ,fuskarta cike da tashin hankali. Tausayin 'yarsa da kaunarta ya shige shi,tana cikin rudani a lokacin da take da shekaru masu rauni.

      " farida "" ya kira sunanta.

    Ta dago kai ta kalle shi.

 Menene damuwarki ?=

  Menene matsalarki ? Ni mahaifinki ne ,zan miki duk wani abu da kikeso a rayuwa muddin ba cutarwa ne a gareki ba ""

    Hawaye ne kawai ya fara zubo mata,don haka ya kyaleta da maganar tambaya,ya ce ,,,,

   "" share hawayenki,ki kwantar da hankalinki,ki kuma sani duk wani abu da zan miki ,ko wani hukunci da zan yanke akanki ba cutarwa ba ne a gareki. 

 Dazu mahaifin deeni yazo gidan nan,wato Alh umar,"

    Kanta a sunkuye ,sai a lokacin ta dago kai ta kalleshi ,ya ce;;;

      " ya dafa mun duk abinda ke faruwa,kinsan irin mutuncin da dangantaka me karfi da ke tsakaninmu ,duk da bamu da wata dangantaka ta jini sai nakwabtaka . Sai dai fa mun dauki wannan makwabtakar da matukar muhimmancin gaske fiye da komai,ko dan uwana na jini bamu da kusanci da su kamar Alh umar . Mun daukaki juna ,kuma mun rike juna da mutunci da amanar makwavtaka. Don haka mun yanke hukuncin daura auren yaranmu ,dansa da ke 'yata ,ina fata ba zaki ban kunya ba ,za ki ban hadin kai ki min biyayya.............

Sumy luv😍😍😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤13 Wani irin farin ciki taji ya lullubeta ,bata san lokacin da tasaki dariya ba tana fadin.

     " Nagode Abba "

    Kafin ma yace wani abu tayi ciki da gudu tana tsananin murna.

   Binta ya yu da kallo yana murmushi tare dabkadankai.

       Tana shiga daki ,ta fada kan gado ta zari wayarta tana kiran deeni,amma layinsa yaki shiga ,ta kira har a gaji hakan ya tabbatar mata wayar sa na kashe. Amma duk da haka bata hakura ba ,haka ta dinga danna wayar har bacci ya dauke ta.     Deeni kuwa a wannan dare kwana yayi yana safa da marwa,kansa ya dauki zafi,yana tunanin yadda bappansa zai kaya da babansa,in yaji zai daura masa aure. To amma duk da haka Bappansu ya tabbatar musu da in har baba yaki yarda shi zai shige masa gaba a al'amarin aurensa. Saboda Bappan sa mutum ne me addini da sanin ilimin sanin yakamata,duk zafin mahaifinsa ba zai hana shi fadar gaskia ba da yin abinda ya kamata.

    " farida insha Allah sai na mallake ki matsayin mata,sai kin zama abokiyar rayuwata,uwar 'ya'yana ,soyayyar sa mukwyiwa juna ba zai tafi a banza ba ,burinmu da mafarkin mu bzai rushe ba "b

       Da wannan tunanin a ransa da zuciyarsa har asuba .

   Bayan dawowarsa daga masallaci ne ya dauko wayarsa , anan ya lura ashe ma tana kashe ne. Nan yayi saurin kunnata ,don yana son jin muryar farida kafin kowa,muryarta na bashi nutsuqa da duk wani gwarin gwiwa. Dan haka ya danna sunanta,shiga daya kuwa yaji ta dauka da sauri tana haki,tamkar wacce tayu gudu. 

    "" farida lafia kuwa ? Ya fada a firgice.

   "" haba deeni "" 

Ta fada cikin muryar haki da sauke ajiyar zuciya, ra cigaba.

  ,"" me yasa ka boye min gaskia baka fada mun ba tsawon dare ,ka sa na kwana cikin tunani da dokin wayewar gari ?

     Farida me kike fadi?  Me na boye miki ?

 Ban fahimta ba "

   ' deeni ashe baba da Abba sun amince su daura mana aure ?"

      "WHAT " ya fada da karfi .

" me kike nufi ? Wa ya fada miki ? Ina kikaji ? 

   A jere ya mata wadannan tambayoyin .

 "Hey deeni relax,kana nufin baka sani ba ? 

  " Ni ban san komai ba ,ba wanda ya fadamun .

    Farida tace ,to nida jiya da daddare abba ya kirani ya fadamun ,yace jiya babanku yazo sunyi magana,kuma sun yanke hukuncin daura mana aure " ALHAMDULILLAH " 

Ya fada da karfi tare da ajiyar zuciya ,ya ce .

   _" farida wannan albishir din naki wani irin tukuici kike so na baki ? Da yardar ubangiji farida zata zamo mallaki na,uwar 'ya'yana ?

 Ban san ma wacce irin murna da farin cikin zan nunawa abba ba,ya gama min komai a duniya farida ina zuwa ........"

  

     Nan ya kashe wayar ya nufi falon babansa da gudun sa ,zuciyarsa cike da tsananin farin ciki da jin dadi mara misaltuwa. Ya same shi zaune a terrance na falon sa,hannunsa rike da jarida yana karantawa yana shan tea. Da Murnar sa ya iso yana daria tare da  fadin .

   ""Baba ina kwana ? Baba dama na san kana so na ,ba zaka so gani na cikin damuwa ba ,you re d best father in d world nagode baba ,Allah ya kara girma da daukaka. Baba na maka alkawari  i"ll  do my best to prove myself,,zan yi karatu ,in tsaya da kafafuna ,zanyi duk wani abinda kakeso ,daga yau bani da wani buri ko mafarki sai na faranta maka ya babana.

     Na gode da wannan gata da ka min na aura min abinda nakeso ,ka tsareni daga fadawa sharri iri iri,kamin babban gata ,ka min abinda kowani uba mai hali zai yiwa dansa. Allah ya. Kara arziki ,Allah ya barni da kai ya babana,nagode".

     Kawai sai ya rungumeshi ,abin da bai taba masa ba da girmansa.

 Wani irin sanyi da farin ciku yaji a zuciyar sa,tabbas yana matukar kaunar dansa Deeni fiye da komai ,ganinsa haka a jikinsa tamkar yadda yake masa tun yana dan karaminsa yawanci da yake yaro in ya masa wani abu da yake so,irin wannan rungumar yake masa,yana nuna masa yaji dadi soaai da abinda ya masa.

     Tuni shauki ya dibesa ,har yaji hawaye sun cika masa ido. Shima ya dada rungumar sa tare da sa hannu yana shafa bayansa,ya ce.

   'Naji dadin ganinka haka Deeni,wannan farin cikin da jin dadin da na jima inason ganinsa a fuskar ka ban ganshi ba sai yanzu ,nayi missing din wancan deenin nawa da wannan moment din a kokarina na gyara ka in sa ka a hanyar da naga ya dace da kai, kazama mutum mai daraja da kima anan muka samu sabani ,muka yi nesa da juna ,muka zama tamkae bakin juna,"" 

    Ya dada manna shi a jikinsa tare da fadin . 

   "" Bari inyi enjoying wnnan moment din don ban san yaushe zan sake samun wannnan kauna da kulawa daga gareka ba haka deeni """ 

    A zuciyar sa yake wannnan maganar ,sai  dai a zahiri lumshe ido kawai ya yi yana jin kaunar dan nasa cikin farin ciki.

    Muryar deeni ya jawo hankalin mama da ya shamsu da lukman zuwa inda suke ,suka tsaya suna kallon su. Mama ce ta ga abin ba na karewa bane tace . 

    " Deeni lafia ko ? 

  Nan ya saki baban da sauri ya nufe ta, " Mama "


 Ya kalli ya shamsu ,ya kamo hannunsa yace ,,

  " kaji baba ya amince zai aura min farida ,mama ku tayani godia wurin baba,ban san irin godiar da zan masa ba sai addu'a"" 

  Dukkansu murna suke suna dariar ganinsa cikin farin ciki.

 "" Deeni abinda zai sa ahi farin ciki ba wani abu ne wuya bane ,san shi bai dau duniyar da zafi ba,,,"" mama ta fada a ranta .

"" Dama nasan mahaifinka zai gane cewa abinda yake hanga maka da rayiwar da yake son maka ba shi ne a gabanka ba,farin cikinka yana ga abubuwa masu sauki,rayuwa mai sauki.Allah ya tabbatar da wannan farin cikin a rayuwarka ";;

    Ya koma gaban mahaifin nasa tare da zama a daya kujerar dake gefen sa,ya jawo hannunsa ya hada da nasa ya manna,ya ce ,,

    " Baba me kakeso in maka a rayuwa ??

 Mahaifin ya kalle shi ya yi murmushi , ya ce.

     ". Karatu nakeso kayi Deeni ,zaka iya barin kasar nan karatu,ba zaka dawo ba sai ka gama ????????????


   🤔🤔ANYA BABU LAUJE CIKIN NAKI KUWA A WANNAN TAFIYAR


SHIN A RA'AYI IRIN NA IYAYENSU DEENI ZASU IYA SAKKOWA CIKIN SAUKI HAKA DAMA ?? 


KUBIYO MU DANJIN ME AKE CIKI 


SUMY LUV😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Wrirting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

 


Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤ 14 Shuru yayi na tsawon lokaci,yana kallon sa ,sannan ya ce.

     " Baba ban fahimta ba ""

 Ya yi murmushi ya ce ," zan fahimtar da kai ,ba dai farida kakeso ba ?? 

Ya girgiza masa kai da ,Ehh " 

"" kanason farida ,inaso kayi karatu,tunda kuwa ba sama maka farida kai kuma zaka cika min burina na ganka a cikakken likita ko ? Ya girgiza masa kai alamar eh . Yace " to nayi magana da mahaifin farida ya amince zai bar farida ta jiraka,kaje kayi karatunka ka dawo tunda har nasa baki yasan da gaske nake. Sai dai duk da haka zabi biyu na bashi ; ko ya amince sai ka dawo ,ko kuma a daura auren karshen wata baka nan jar se kadawo ta tare,da kanshi ya yanke shawarar se ka dawo din,saboda ba yadda za'ayi ka tafi da ita wata kasa kana karatau ita kuma tana zaune haka a kasar da bata san kowa ba ,haka karatinka nason nutsuwa da mai da hankali,ba gadda za'ayi ka raba hankalinka ya zama baka bata lokaci ba,haka baka bawa karatun ka lokaci ba,kaga za'ayi biyu babu.

     Don haka ya amince mana na tsawon shekara biyar din nan ,dan mutinci na da kuma zumuncin da ke tsakaninmu da kuma soyayyar da ke tsakaninka da faridan. Amma yace idan ya wuce ahekara biyar din nan bazai kara maka ko kwana daya akai ba ,don haka ya rage naka kayi kokari kagama karayunka na likita a cikin wadannan shekarun ka dawo ka aureta ,ko ka tsaya wasa kayi ta komawa baya wannan damar ta kubuce maka.."

     Y kalli mahaifin nasa ya ce ,,"Abba na.maka alkawarin zan yi dukkan iya kokarina da iyawata ,ba zan yi wasa ba ,zan dage inyi karatuna in gama a cikin shekarun nan insha Allah . Ina fatan in cin ma manufata; in cika burinka da nawa ,ba zanyi wasa da damar da Abban farida da kai ku ka vanj ba ,da fatan zaku taya ni da addu'a kusa min albarka ,Allah ya taimake ni ""

       "Zamuyi maka Deeni insha Allah ,Allah ya saka maka da mafificin alkhairi ,Allah ya baka abinda ya fi maka alkairi albarkacin wannan biyayya da kai min "" 

    ""Ameen baba ""

     Ya amsa yana godiya ,sannan ya kalli mahaifiyarsa yace ,,,

"Mama ina bukatar addu'arki,ya shamsu kaima kasani a addua. Sannan mama na baku amanar farida ,da kula da ita kafin in dawo""

     Tayi murmushi," zan maka addua deeni,,sannan farida "yata ce,zamu kula da ita insha Allah ""

     Nagode mama

  Ya fada yana murmushi,ya fita jikinsa a mace sabida tafiyar ya bar farida ba abu ne me sauki ba ,sai dai zai dage ya yi abinda zai sa ya samu farida ,ya mallaketa na har abada.       Wata guda da maganar Alh umar ya yi ta shige da fitar samawa deeni addmission gurbin karatun likita a America,ya taki sa'a suna daukan sabbin dalibai,dan haka ya shiga ya fita sai da yaga ya samawa deeni gurbin kaeatu a florida medical collage .

     

   A wannan lokacin kafin tafiar deeni kullum suna tare da farida,,baiyi wasa da wadannan kwanakin ba gurin kasancewa da farida,ko a gidansu ko a gidansu faridan,don kuwa haka suke shiga gidajen juna kai tsaya kamar nasu,haka irin so da kauna da tarairaya da mahaifiyar Deeni ke nunawa farida ko mahaifiyarta sai haka,son da mahaifiyae deeni kee masa ya shafi farida,haka mahaifan farida keji da Deeni sosai.

 

  Ranar da deeni zai tafi tun sassafe farida taje gidansu ta tayashi shirya kayan ssa,duk inda deeni yayi idanun farida na kansa,ya lura da hakan amma sai yai kokarin kau da kai saboda kar tayi kuka ,,amma daga karshe sai tayi abinda bai so din,ya matso gabanya yana mirmushi tare da ciro wayar sa ya ce ,,

      "" saki fuska ki daina daure ahi in dauke ki hoto in dinga kallonki ina yuna ranar da na tafi na bar farida "" 

       Kara kumburo kumatu tayi saura dis tasa kuka,haka ya dunga daukarta hoto , ya ce .

   "" To na kumburarrun fuska da kumatun sun ishe ni haka,ayi min murmushi kuma in gani. Ki tuna duk randa kika sake ganin deeni to ranar zai zama angonki ,me gidanki,,wannann kadai be isheki murmushi ba ;;? 

    Nan da nan tasaki murmushi ,bai bata lokacin daukar ta hoto ba . Ya yi saurin matsowa kusa da ita ya dauke su tare suna yiwa juna murmushi,wanda daga karshe mirmushin ya koma kuka.

        Farida tasa kuka da karfinta,,"" yanzu deeni bazan sake ganinka ba se bayan shekara biyar? Ya zan rayu na tsawan wannan lokacin ? Deeni bazan iya jure rashinka na tsawon wannan lokacin ba ,,ni dai karka tafi ka barni,ka tsaya a daura mana aure ka tafi dani,"

     Kuka take sosai wanda kukanta da yanayinta ya mugun karyawa Deeni zuciya,yaji kamarbya zubar mata da hawaye,tausayinta da tsananin soyayyarta ya dinga ratsa shi . Ranar ta farko kenan dayaji yason ya rumgumeta a jikinsa domin ya lallasheta. 

     Son ta mai karfi da wani irin shaukinta yaji yana fisgarsa,ya yi nufin rungumar ta din ,amma sai ya dinga jin zuciyar sa na bugawa da karfi,ta hana shi ,tsananin tsoron yin hakan ya shige shi,tsoron Allah ya shige shi. Shin in ya taba ta suka kai ga aikata abinda bai kamata ba fa ? 


    "A'uzubillahi minasshaidanjrrajim " 

  Abinda ya dunga maimaitawa kenan.

Gaba daya ya rude ,ya rasa abin yi ,ga sonta ,ha tausayinta,ga tunanin tafia ya barta. Dabara ce ta fado masa,ya jawo hijabinta da take sake dashi,ya fisgeta har dakin mama,ya kaita gaban mama ya ce . To mama kinganta zata hana danki tafia ko ? Ta sani a gaba tamun kuka ,fada mata manyan 'yan mata da suka isa aure ba sa kuka kamar na 'yan yara"....


Sumy luv😍😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤
15Ai kuwa kamar ya ce ta kara kukan ta kara fashewa da kuka.

     Ta ce " To wata baturiya ma zan samo can in aura"

    Nan ta dalla masa harara hawaye na zuba ta ce ,,

   Mama kin ganshi ko ?

Mama ta jayota jikinta,"Rabu da shi kinji,duk baturiyar da zai je ya samo bazata kai rabin farida ba ,zai yi ya gama ne ya dawo ya nemeki,duk randa ya dawo ki masa yanga son ranki,ki kyale shi ki sami wani mijin .

   Duk da wasa mama take amma sai da yanayinsa ya canja,ya canja fuska duk da yana kokarin murmushi,juyawa yayi ya nufi ciki.

   Farida tasan halin kayanta,don haka ta bi bayansa ta ce .

  '" Ai duk duniya ba wanda ya kai deeni na a wurina,indai ba deeni ba sai dai in hakura da aure"

  Jin hakan yasa ya tsaya tare da juyowa ya kalleta tare da sakar mata murmushi,yace.

   " shi yasa nake sonki farida na,kin san yadda zaki kawo murmushi fuskata,kin san yadda zaki kula dani. Ina da yakinin in na aureki zan kasance ciikin farin ciki tarw da ke. Farida inasonki,ina kaunarki ke daya,ki kirw wannan a ranki gada ke ba wata."

       Tayi masa murmushi itama,ta ce," Deeni na ka rike wannan a ranka ,daga kai bawani a zuciyar farida ,na ma alkawarin kaina da ajiyar kaina da zuciyata,zan tsarw maka amanar kaina."

Nan suka zubawa juna ido suna yiwa juna murmushi na tsawon lokaci,sannan deeeni ya yi ciki,ita kuma ta wuce gida da niyyar sai yazo tafia tazo su kaishi airport.


    Sai dai deeni bai bari hakan ya faru ba,wannan sallamar da sukayi shine ban kwanan da yayi mata,saboda yasan inta rakashi airport bazasu iya jure rabuwa da juna ba .

        Jirgin deeni karfe biyu ne,amma sai yace mata karfe shida ne ,saboda baiso ta rakashi.

     Lokacin tafiyar su ,har gidan su ya shiga ya yiwa iyayen farida sallama,sai dai basu san lokacin zai tafi ba . Nan suka masa addu'a tare da fatan alkhairi da kuma Allah ya kiyaye masa hanya. Lokacin nan farida na ciki tana ta kokarin faman neman kayan da zata sa ta yiwa deeni gayu ya yanga lokacin da zata rakashi,a wannan lokacin ma har deeni sun kama hanyar airport har da mahaifin faridan.


     Tunda suka dau hanya yake basu amanar farida,tare da kara jaddada musu irin son da yake mata,da kuma irin dagewar da zaiyi ya yi karatu. Nan mahaifinsa ya kara masa tuni da ko hutu bazai zo ba ,shi da nigeria sai ya gama karatu.

       Ya kalli mahaifin nasa yace," nasanj baba,ba zan dawo ba sai na cimma manufata da burinka da yardar Allah.," 

       Mama da shamsudden tarw da kaninsa. Lukman da mahaifin farida suka masa rakiya wanda mahaifin sa kuma tare zasu tafi sai ya kaishi sannan ya dawo .

  

    Bayan sun isa zasu shiga jirgi kafin ya kalli mama yace,

" in farida taji na tafi zatayi kuka,ki lallasheta sosai kinji mama ?

  " To deeni ,zan lallasheta,sai dai kai kuma wa zai lallashe ka?

    Idanunsa suka kada sukayi ja ,ya yi saurin kai da kai ya ce,ba komai zan lallashi kaina"

     Shamsuddeen yayi saurin rungumarsa yana lallashi har da lukman a masu bashi hakuri,dakyar ya iya danne zuciyarsa ya juya ya tafi. Har ya bar ganinsu yana kara maimaita musu ,mama,shamsu,lukman ku kula min da farida ,na baku amanar farida.Mama tayi karfin hali kamar zatayi kuka tace .

   Mun rike amana deeni,Allah ya kai ka lafia,ya kare ka"

     Ameen" ya amsa,sannan ya shige suka tafi. 

     Su mama basu bar filin jirgin ba har sai da suka ga tashin jirginsu sannan suka kama hanyar gida,dukkan su jikinsu a mace,zuciyar su cike da kewar deeni.


    Suna isowa kofar gida kuwa sukaci karo da farida ra hada kai da gwiwa tana ta zabga kuka,,tun daga wannan lokacin mama tasoma aikinta na lallashi. Ta ja hannunta suka shiga ciki,ta dinga lallashinta tarw da kalamai masu dadi da kwabtar da rai,ta nuna mata deeni ya yi haka ne saboda kada ya ganta ya karaya ya kasa tafiya.

 ""  farida kiyi masa addua tare da kara masa karfin gwiwa har ya samu nasarar yin abinda ya kai shi ya dawo lafiya kuyi aurenku kinji ko ?

   Ta girgiza mata kai ,. Naji mama ,na gode,zan jure in Allah ya yarda.

Yawwa farida ,shiyasa nake sonki,akwai biyayya da jin maganar na gaba da ke. Allah ga miki albarka.

    Ameen mama" . Ta fada murya a sanyaye. Ta mike tayiwa mama sallama ta nufi gida zuciyarta cike da tsananinson deeni,da kuma kewar sa. Ita dai bataki ta dawo gidan da zama ba tayi ta zama a dakin deeni tana kallon inda yake rayuwar sa tana jin dadi ,sai dai ba halin yin hakan sai dai ta dinga zuwa,ya zama dole tayi hakuri da rashin Deeni......

Sabo shi akewa kuka,inba so kuma baza'a yo ba ,,ma'anar so a zuciya ku rike amana ku kau da zan ba..... ...😍😍😍😍😍Byee 


Sumy luv😍❤😍❤😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting bySA'ADATU WAZIRI GOMBE=================== GIDAN NOVELS ====================================
17 Washegari bayan sun gama breakfast ,Alh. Umar tare da shamsu da likman duk sunyi shirin fita office yayin da lukman makaranta zai tafi.

       Alhaji ya kalli shamsu dake shirin mikewa yace ,

    " ka zauna ina da maganar da nakeso muyi da kai da mahaifiyarka ,kai kuma lukman kaje driver ya ajiyeka a makaranta"" 

     Nan ya mmike ya fita ,yayi da shamsu ya bar dining table din ya nufi tsakiyar falon kamar yadda yaga mahaifinsa yayi yana tunanin to wacce magana Alhaji zai yi da shi haka?

   Mama ta iso cikin falon ta zauna a kujerar da ke kallon tashi , tace .

   " *Alhaji muna sauraronka ,wace magana ce haka?

  Ya gyara zama yace,inaso ku saurare ni da kyau da kunne basira,kwanakin baya kafin deeni ya tafi karatu munyi wani shirri ni da mahaifin farida. Maganar gaskia bamu shirya maganar auren deeni da farida ba  ,sai shamsuddeen da farida ,haka kuwa bazai yiwu ba har sai deeni ya tafi karatu ya bar kasar nan,fatiyarsa kuwa abu ne mai wuya in ba har yaji za a aura masa farida ba.

      Maganar gaskia mahaifin farida bai yarda da barin 'yarsa tayi jiran shekaru biyar ba,ni kuma ban yarda da aurawa deeni mace ba tare da ya gama karatu ya mallaki hankalin kansa,yasan ciwon kansa ba daga farida har deeni soyayyar yarinta ce ke damun su,dukkan su basu san ciwon kansu ba ,ba yadda za'ayi mu hadasu aure da deeni .


   Sai dai maganar ta mana amfani , na sami deeni ya nutsu yana karatu,kafin shekara biyar din nan zai shiga ruwan hankalinsa,ya nutsu ,zai mance farida idan yaji dan uwansa ya aureta ya fara sabuwar rayuwa. Itama kafin nan zata gane shamsu shi ne wabda ya dace da ita.

    Babban dalilin kulla wannan aure shi ne ,na farko dacewar farida da shamsu,tana dai dai lokacin aurw shima haka. Sannan Nuraddeen ya bata mata lokaci ,tun tana karama bata bawa wani saurayi dama ba sai deeni,ba zan so yanzu da ta tashi aure ya zama tamkar deeni ya yaudar ta ba. Yanzu bata da wanj,haka bazan so kuma nahaifinta ya aurar da ita ga wani wanda bai dace da ita ba ,wanda bazai bata kulawar da jindadin da ya dace da ita ba . 

     Farida tamkar diyar cikina na dauke ta ,shiyasa zan damka amabarta ga dana wanda na yadda dashi ,na amince masa. Inada tabbacin shamsuddeen zai bata suk wata kulawa da kauna matsayin mijinta. Sannan burina da naki zai cika na ganin farida ta zama surukar mu,zamu hada jini da zuri'a dasu ,zata haifa mana yan jikoki. Da Shamsuddeen da Nuraddeen duk abu daya ne a wurin mu,don haka mun yanke hukunci a watan sha biyu za muyi auren su december ,sai ku soma shiri." 

     Yana gama fadi ya mike zai fita,,hajia tayi saurin mikewa cikin girgiza da firgitar jin maganganunsa hade da mamaki,yayin da shamsuddeen kansa na sunkuye,maganar mahaifinshi ta mugun kadashi da bashi tsoro. A kullum yana yiwa mahaifinshi abinda yake so,amma wannan karan zasuyi tsiya irin wadda basu taba yiba ,don kuwa ba zai taba aurwn macen da kaninsa,jininsa,dan uwansa ke ciwon so ba.

        Hajiya ta sha gabansa,ta tsare shi da ido ,ta ce

     " wacce irin magana kake ne me kama da ta yara? Ba na tsammanin deeni da farida yara ne ,sai dai kai da mahaifin farida ne tunaninku irin na yara. Kuna nufin kuce min kun yaudari yaran ku kenn? Kun yiqa yaranku karya kuna iyayensu ? Kana son fada mun zaku wargaza rayuwar yaranku da hannun ku ? 

    Na yarda na amince ina son farida matsayin sirika ,haka kuma babu bambanci tsakain shamsu da nuraddeen a wurinmu. Sai dai fa inaso kasani akwai bambanci tsakanin deeni da shamsudden a wajen farida . Zuciyarta da ruhinta gaba daya deeni suke so,deeni suke muradi.

Wannan maganar da ka kawo bata wasa bace,kanason haddasa gaba tsakanin yaranka ,ka dauki abinda daya take matukar so kabawa daya? Shamsu yace kamaka yanason farida ne ko ita faridan ta fada maka zata amincd ta auri shamsu ? Kasan ko yawan soyayyar da ke tsakanin farida da deeni?

        Wannan ba damuwa ta bace " ya fada cikin daga murya d bacin rai,ya ce 

   " karki zara maganganunki zasu canja min niyyata da ra'ayi na,ba shawararki nake nema ba ,ina fada muku ne dake da danki ku soma shirye shiryen biki,banason sake jin wani raayi naki ko na wani musu akan maganar nan "" ya kalle shamsu da kansa yake sunkuye , ya kira sunansa. 

   " Kai shamsudden ,dago kai ka kalleni nan " yayi saurin dago kai cikun tashin hankali da kuma tsorata da yanayin mahaifin nasa, yace .

Na maka zabin mat matsayina na mahaifinka ,ina fata ba zaka bani kunya ba idan har na isa da kai,kuma na taba maka wani alfarma a duniya a matsayina na uban da ya kawo ka duniya,to ina so kayi biyayya ga maganata ka auri farida, ka rike ta hannu bibbiyu da amana . Ni nan mahaifinka nina baka amanar farida kanaji na ? In kuma kana ja to inji "

 Ya sunkuyar da kai muryarsa na kyarma yace ,,naji baba ,na amince,na maka biyayya,bani da ja ,"

     Mahaifin nasa yayi murmushi , ya ce naji dadi ,Allah ya maka albarka ,Allah yasa ka gama da duniya lafia,Allah yasa 'ya'yanka su maka biyayya kamar yadda ka mun ""

    Ya kalli mama cikin bacin rai ,ya ce.

 Saura wani yayi garajwn sanar da deeni abinda ke faruwa,ko ma waye ne zai fuskanci mummunan fushi daga gare ni""

   Yana gama fada ya juya ya fita,ya bar mama da shamsu cikin balain tashin hankali.

    Haka kai yayi da gwiwa tamkar wani karamin yaro yana kuka ,hankalinsa ya mummunan tashi . Dum yadda ya kai ga kin aurwn masoyiyyar dan uwansa bai isa ya ki bin umarnin mahaifinsa ba,bashi da karfin gwiwar kin yiwa mahaifinsa biyayya ,ya zama dole ya bi umarnin mahaifin sa kamar yadda ya ke masa tun yana dan kankaninsa. 

    Mama ta tsinci kanta cikin rashin hankali da kaduwar da itama tana bukatar mai lallashinta balle ta lallashi shamsu.

       Sai dai shamsu ya kas jurewa har sai da ya matsa gabanta yana kuka yana fadin .

      Mama ki taimake ni kiyiwa baba magana ,ya za ayi in auri farida yarinyar dana shaida soyayyarsu da kanina da nake matukar so ? Tun suna yara ni na san irin soyayyar sa sukewa juna ,mama ya za ayi in jefa kannena biyu cikin tashin hankali da bakin cikin rabuwa da juna? Ya za ayi in raba su ta hanyar auren farida ? Mama da wane ido zan kalli Deeni? 

   Kasa magana tayi saboda bata da abinda zata iya fada masa illa ta taya shi kuka ,hawaye taji yana gudu a fuskarta,tausayin yaran nata duka biyub ya kamata.shin mahaifin su bashi da zuciya ne da bai tausayinsu ? Ko baya hangk cewa zai hada gaba da fitina a tsakanin yaransa? 

     Da kyar ta iya budar baki tana lallashin sa tare da bashi hakuri cewa basu da yadda suka iya ,saboda mahaifinsu yafi karfin su duka .

      " ka dage da addu'a in haka shi ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar ,in kima ba alkairi Allah ya warwre shi.

     Mama ina alkairi a auren cin amana ? Mama kin tuma har deeni ya shiga jirgi yana bani amanar farida ? Mama yaya deeni zai dauke ni in yaji na ci amana na auri macen da take rayuwar sa,farin ckin sa,koman sa ? 

 Tayi murmishin karfin hali tace, kar ka damu ,Allah na nan ,kayi kokarin mai da al'amarin ka gare shi,haka nan deeni ya san halin mahaifinku,zai fahimci ba kayi auren ne da niyyar cin amana ba .

     Shamsu ,yana da kyau ka  kwantar da hankalinka ,kasawa kanka aurwn farida ko baka so,ka tursasawa kanka da zuciyarka,saboda tun da mahaifinka ya lashi takobi sai ka auri farida to ba makawa si ka aureta ,sai wani ikon Allah,,""

Nan ta shige ciki ta barshi a wurin a durkushe ,abin duniya ya masa zafi. Daga karshe ya mike ya koma dakinsa,office din da bai fita ba kenn. Ranar mahaifinsa ya masa wannan uzurin ,don yasan halin da ya tsinci kansa . Ya bashi dama yaji da kansa da zuciyar sa.

    Haka mama ta koma daki hankalinta tashe ,idonta rufe tana addu'a da fatan kar wanan abu ya zama sanadin wargaza kan 'ya'yanta ,yayin da tausayin farida da deeni ya cika mata zuciya . Tabbass zasu fuskanci tashin hankali,sai dai zata taya su da addu'a Allah ya basu juriya......


    


Shin farida zata amince da wannan sabon al'amarin ?? 

 

Yaya deeni zaiji idan ya riski wannan bakin labarin ??

  

 Ga masu binmu sai ku biyomu a wannan lambar 08029350366  dan jin ra'ayoyinku ,,kofarmu a bude take ...  

 

Cigaban labari kuma yanaga yawan ra'ayoyinku ,domin shine zai tabbatar da kuna binmu da gaske kamar yadda kuka fada..mun gode Sumy luv😍😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


 Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤16Sati guda da tafiyar Deeni komai ya mike masa,ya gane yadda wurin yake. Gida guda mahaifinsa ya sama masa kusa da makaranta,bai samu wata matsala ba ya fuskanci abinda ya kawo shi,ya hau karatu gadan-gadan . Ganin ya mike yasa mahaifinsa ya yi sallama da shi ya dawo gida nigeria don fuskantar nasa ayyukan.

 

    Ya dawo hankalinsa kwance,bashi da wata matsala ganin deeni ya mike kuma da gaske yake,wannan ya matukar bashi kwanciyar hankali.


    Duk da Deeni yana matukar kewar farida,amma ya daure bai mata waya ba saboda gudun mai da hannun agogo baya,a duk lokacin da zai ji muryarta dukkan wani kokarinsa zai iya komawa baya,hankalinsa zai tashi yaji yanason komawa ya ganta. Don haka ya daure,ya hora zuciyarsa da rashinta na tsawon lokaci ,sannan ya kirata.

        Da farko ta nuna masa fushinta na kyaleta da ya yi ba waya da kuma tafia ba yayi ba tare da ya bari ta masa rakiya ba . Sai da ya jira ta gama mitar sannan ya ja dogon numfashi ya ce.

    "" farida na,farida matar Deeni . Kinsan deeni da irin son da yake miki ,trust me inada da dalilina na yin haka"" 

     " Na sanj Deeni "

Ta fada murya kasa kasa,ta kara da cewa.

    " ina kewar ka ne kawai Deeni,kasan na saba da kai da soyyyarka ,Deeni ba dadi da baka nan "

          Yi hakuri farida,zai zama tarihi"

Ya canja zancen ta hanyar zolayarta da cewa,

    Nasan duk randa kikazo America kika ga dogon gini rudewa za kiyi ,saboda farida ta yar kauye ce "

   "" Ta turo baki tamkar yana ganinta ,ta ce. 

     "" kai da bamu ga ka rude ba ,saboda kaima dan kauyen ne ai" 


      Yace oho dai ,ni dai yanzu na zama dan birni na barki" 

    Dariya sukayi duka,sun jima suna hira suna bawa juna labarin yanayin da suka shiga da kuma halin da suke ciki. Ya bata labarin yadda yake matukar jin dadin karatun sa a yanzu,,yake kuma ganewa,saboda yadsa aka saukaka musu shi,sabanin yadda yake a nigeria. 

   Itama ta bashi labarin makarantar high islam da mahaifinta yasa ta koma,saboda yaki barinta tashiga university sai dai tana karuwa sosai ta fuskar addini a wannan makarantar ,tana kuma ganewa ,tana jin dadin karatun addini. 

     Sunyi sallama da juna ,suna yiwa juna addu'a da fatan alkairi,zuciyoyin su cike da jin dadi da farin cikin magana da juna 


Wasa gaske deeni ya mike da karatu har ya saba da rashin farida ,yana kiranta wani lokaci sau daya a wata ,saboda dagewa da yayi ya fuskanci karatun dake gabansa,soyayyar farida na kara masa karfin gwiwa. Haka itama farida kullum suka yi waya sai ta karfafa masa gwiwa da kara jaddada masa soyayyar da take masa . 

      Itama haka tayi sabo da ba sa waya da deeni sosai sai lokaci lokaci,kuma ta fahimci dalilin sa don haka tayi masa uzuri ta fuskanci nata karatun tare da musu addu'a.  *      *       *      *      *


 Zaune yake a falo shi daya yana kallon labarun karfe tara ,Alh umar kenan ya mai da hankalinsa gaba daya kan jin abinda ke faruwa a kasar tamu, lokacin Alh Ahmad ya masa sallama ya shigo falon. 

       Ya mike da sauri yana dariya ya tare shi saboda muhimmancin da yake dashi  a wurinsa,yana matukar girmama shi,da kuma dangantakar su ta makwabtaka. 

         Nan ya nuna masa wurin zama tare da sawa a kawo masa abin sha. Suka sake sabuwar gaisawa,suka dan taba hirarsu data shafi kasuwanci da kuma kasar gaba daya. Tare suma kalli labaran suna sharhi akai.

     Bayan sun gama Alh Ahmad ya kalle shi ya ce .  


 "" ya labarin deeni kuwa ? Duk da dai muna waya da shi amma mun kwana biyu bamuyi waya ba ,yana lafia ko ?

    Alhaji yayi murmushi yace ,lafia kalau,ya maida hankali yana karatu yadda ya kamata. Ina kara maka godia bisa taimako da hadin kai da ka bani ""

     Alh.Ahmad ya yi daria ya ce ,"Ai deeni ya dana ne,kamar yadda ku ka riki farida kamar 'yarku haka nima na riki deeni""

       Ya kara kallon sa da kyau yace,,"yanzu ma maganar yaran nan ce ta kawo ni,kan maganar da mukayi kwanaki ,kaga tsahon wata tara kenab da tafiar deeni,komai ya mike masa ya soma fuskantar karatunsa da gaske,haka nutsuwa tana kara shigar sa,din haka inaga lokaci yayi da zamu fito mu bayyanawa yaran nan da iyayensu mata manufar mu da kuma dalilinmu ,kaga watan sha biyu nakeson auren yaran nan ,kuma har da farida ciki,kaga yanzun wata biyu ya saura ,gara mu sanar dasu su shiryawa maganar auren tun wuri;""

       Alh. Umar ya sauke ajiyar zuciya ,yace. 

   " kayi gaskia tamkar ka shiga cikin zuciyata ne,inada shirin maka maganar sai ka rigani ,inaga yanzu abinda za'ayi ,ka kira farida da mahaifiyarta kayi musu bayani,haka nima nan zan kira nawa iyalin nayi musu magana. Abinda nakeso da kai shi ne,mu tabbatar musu da maganar da muke fada UMARNI ne muke basu ,maganar mu doka ce a gare su ,dole su bita ba wai ra'ayin su muke nema ba. In munyi haka zai zo mana da sauki,amma in muku nuna ra'ayinsu muke nema zai sa mu sami matsala ,zai zamana tamkar mun vasu damar kin bin abinda muke so ne "

Alh Ahmad yayi dariya,yace,,kayi gaskia ,maganarka abin dubawa ce. Inaga gobe in Allah y kaimu zan kirasu muyi maganar,zaka ji yadda mukayi da su"

      Alh. Umar ya amsa da,nima in Allah ya yarda goben zanyi magana dasu,sai mu duba ranar da ta dace mu tsayar da ranar biki"

     " To shikenn ,Allah ya kaimu goben " 

     Da wannan. Maganar suka yi sallama ,tare da yiwa juna sai da safe akan zasu hadu washe gari bayan tashi daga harkokin su da yamma za su hadu..........SHIN IYAYEN SU SUN YARDA ZAA AURAWA DEENI FARIDA NE KAFIN YA DAWO ????


 WANI IRIN FARIN CIKI DEENI ZAI YI IDAN YA SAMU LABARIN AN DAURA AURENSHI DA FARIDA? 

             MUJE ZUWA 😜😜😜


.

sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE


Cpoied by SUMAYYA SA'AD❤❤ 
18Kamr yadda ta kasance da su shamsu haka ta faru tsakanin farida da mahaifinra da mahaifiyarta. Tunda ya fara musu bayanin manufar sa bai kai ga karasawa ba ma farida ta mike ta tare shi da fadin .

    "Abba ba zan taba airen wani namiji a duniya ba inba deeni ba ,nayiwa deeni alkawarin kaona da zuciyata,zuciyata deeni take matukar so,don haka Abba kabar wannan maganar ta yaudara. So kike inci amanar deeni ? Kuma Abba bazan iya rayuwa da wani ba in ba deenni ba ,Abba ka taimakeni ,gara min mutiwa ta daa rasa deeni" 

      Mikewa yayi ya sharara mata mari sai data ga taurari.

   " yarinyar banza mara kunya" ya fada yana huci. 

   ". Ke har kin isa kiyi jayayya dani ? Yaushe kika koyi rashin kunya ? Kin san me kike fada kuwa ? Har kina fadan mutuwa da iliminki da hankalinki ,kin san meye mutuwa da har kike ikirarin gara miki mutuwa ? Me aka miki me zafi a duniyar nan haka ? Kuma ko me ya miki zafi babban sabo ne kice kin gwammaci mutuwa . Miji dai nike da hakkin zaba miki shi ko ? Ba ke ba ,don haka na zaba miki shamsu ,inkin isa  in na daira miki aure da shi ki ki zama a gidansa ,sai in san ke cikakkiyar mara kunya ce "

        Ta durkusa har kasa tana kuka ,baba kayi hakuri don Allah kar ka rabani da masoyi na deeni,Abba deeni shi ne rayuwata ,ban taba tunanin wani a matsayin mijina in ba deeni ba,Abba ba zan iya biyayyar aure ga kowanne namiji ba sai Deeni "

    Ki daina bata yawun bakin fa, shamsu dai kin aurwshi kin gama "

      Ta miki , Abba bazan auri shamsu ba sai dai ka kashe ni "

 Ya kalleta cikin bacin rai ,ya ce

   Baki isa ba ,idan kinason zama a gidan nan matsayin diyata ,idan kinaso mahaifiyarki ya cigana da zaman aure a gidan nan kar ki sake musu dani akan maganar auren ki da shamsu""

     Maganarshi ta karshe ya mugun girgizata ,tabbas bazataso auren uwarta ya kare akanta ba . Ya kalleta,kina da zabi ,ko naki auren ko na uwarki,ina saurarwnki"

  Cikin tsananin kuka da bakin ciki tace ,Abba na amince ba don inaso ba ,sai don umma," 

     Ro banason sake jin komai ko wani musu akan maganar nan,munyi mun gama . Haka ko da wasa ban yarda idan kunyi waya da deeni ki sanar masa ba ,balle ya dawo ya daga mana hankali. Sai ki soma shirye shiryen biki" 

  Ya kalli mahaifiyarta da ta bude baki tana sauraron su cikin tsananin mamaki ,ta rasa abin fadi. Tabbas namiji halinshi sai shi . 

     Yace ,ki rubuto mun duk abinda ku ke bukata na bikin farida za'a siyo shi,cikin december za'ayi auren "

       Yana gama fadi ya juya ya fita ba tarw da ya saurarwsu ba,haka farida ta zauna a wajen ta sa hannu akai tana ta rusar ihu tamkar wacce aka cirewa ido ko ta easa uwarta ko ubanta. 

       Mahaifiyarta dai bata da yadda zatayi sai lallashi da nasiha ,sai dai tabbas dole ta taya 'yar ta kukan rashin babban masoyinta . Sannan karin tashin hankalin ma wai ta auri dan uwansa? 

     Nan ta rungumo ta a jiki tana lallashi ,tana mata addu'a.

    'Farida Allah zabi mafi alkairi"" tana fadi tana hawaye ,basu ankara ba sukaga jama'ar gidan duk sun cika falon kowa na tambayar meya faru ? Duk wanda yaji abinda ya faru sai ya tausayawa farida gami da juyayin wannan alamari,saboda kowa yasan karfin soyayyar dake tsakanin Deeni da Farida. 

   Haka farida ta wuni kuka ,ba ci ba sha,bakin ciki da takaici ya cika mata zuciya,tsananin kewar deeni da kaunarsa taji yana ratsa ta. Hankalinta ya mummunan tashi ,taji kwakwalqarta na juyawa tabdinga jin kamar zata yi hauka saboda kwakwalwarta ta kasa amince mata da hukuncin da mahaifinta ua yanke akanta,ta dawo tamkar wata mai jinni. 

          Ta mike da gudu ko dan kwali babu akanta ta nufi gidansu deeni,kai tsaye ta wuce dakin shamsu tana kwala masa kira.

    ". Ya shamsu"" ya shamsu ka taimake ni " 

     Ta sameshi ya kasa tsaye ya kasa zaune yanata zagaya dakin ,shima abin duniya ya masa zafi. Bai ankara ba ya ganta a dakinsa ba zata tamkar an jehota ,ta sunkuya ta kama kafafunsa. 

  

     Ya shamsu ka taimake ni kace baka sona,kace ba zaka aure ni ba . Yaya shamsu kaima ka sani ko ? Kasan deeni nake so,kasan ba zan iya rayuwa da wani namiji ba in ba deeni ba . Ya shamsu ina son Deeni ,ka taimake ni ya shamsu ,bazan iya aurenka ba "" 

Kaka take tana ta surutai kamar mahaukaciya ,sai da shamsu ya rikota suka fuskanci juna.    Kiyi hakuri farida ,an fada miki ba dole akayi min ba ne kamar yadda aka miki ? Bani da yadda zanyi sai dai bin umarnin mahaifina,bani da yadda na iya,ya zame min dole zan ci amanar dan uwana . 

          Deeni ya bani amanr kula da ke kafin ya dawo,zai dawo ya samu naci amanarsa ,na auri macen da yake matukar so. Farida ba abu ne me sauki ba a gareni,duk kuka da rokona da zakiyi bani da ikon canja ra'ayin mahaifina ,yadda bazaki iya kin bin umarnin mahaifinki ba haka ba zan iya kin bin umarnin mahaifi na ba ;""

   Ta fashe da kuka, to ya kakeso nayi? 

 Kasan dai deeni nakeso ,Deeni ne rayuwata,please ka taimake ni ya shamsu ka taimake ni.

Mama ce taji hayaniyarta ,ta fito ta zo ta janyeta, yayin da shamsu ya lumshe ido hawayen bacin rai na zuba masa,yana jin kukanta na ratsa kunnuwansa,yana kuntata masa zuciya 

.....

 Kuyi hakuri bacci yazo yasin 😀😀Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting bySA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤    Salam !!yan uwa ayi mun afuwa na rashin posting two days🙏🏼🙏🀊

􏁫uma sannan naga sakonninku,kuma naji dadi sosai Allah ya bar zumunci

 Ameen ..

 


19


 A daki mama tayi ta lallashi amma inaaa!! Farida kuma take ,bata ji bata gani,bata saurare,daga karshe ta tashi ta tafi dakin deeni,ta hau bisa gadonsa tana shakar kamshinsa,tana kuka tana fada masa irin tsananin son da take masa.

    Farida taba gushe ba a gurin har sai data shide ta suma a wajen,mama da shamsu sukayi asibiti da ita a rude. Da kyar likita ya samu ta karfado,,sai dai zazzabi mai zafi ya lullubeta,haka nan bata nar kukan da take ba har sai da akayi mata allurar bacci,bacci me nauyin gaske ya dauke ta . 

        Mama ta zuba mata ido tana kallonta,tana matukar tausaya mata tare da mata addu'a a ranta ,tana maganar zuci.

    " Yarinya karama ta hadu da kaddarar da ta kasa jurewa,ta kasa tawakkali,haka nan mahaifanta sun kasa ganewa."" 

     Nan ta mike don zuwa tayiwa mahaifiyar farida waya ,,nan shamsu ya zauna ya zura mata ido,sai ya daina jin tausayin kansa se farida..  halin da ta shiga ya firgita shi,ya san suna matukar son juna da Deeni amma bai zaci farida na haukan son deeni haka ba. Shin taya zai rayu da macen da take matukar haukan son wani bata ji bata gani ? Taya zai iya rike amanar da mahaifinsa ya damka masa bayaan cin amanar dan uwansa da ya yi ? 

     Yana cikin wannan hali mahaifiyar farida da yan uwanta suka shigo,hakan yasa ya fita .

     Kowa dai bashi da ikon mata wani abu sai addu'a har kusan magriba ,mahaifansu maza sukazo. Tabbas sun tausaya mata,amma hakan bai sa dayansu yaji yana da niyyar canja ra'ayi ba.

      Har faridan ta farka tana kuka tana rokon mahaifinta,amma sai ya kau da kai gareta,yace,intaga bata auri shamsu ba to dayan su ba ya numfashi ne ko ita ko shi mahaifinta,ko kuma shi shamsu din . Yana gama fadi ya fice abinsa. 

     Daga nana farida tasawa kanta dangana,sai dai ita tasan tabbas mutuwa zatayi in tta auri wani da ba Deeni ba ,don haka ta soma shirin bankwana da duniya tana jiran ta Allah ta kasance akanta.


   *  * * * * * * * * * *


    Tun lokaci da aka kulla maganar auren shamsu da farida duk iyayen su suka hau shirye shiryeb biki ,duk wanda yaji magnar aurwnsu sai yayi mamaki saboda kowa dai yasan farida da Deeni take soyayya ba da yayansa ba . 

    Tuni Alh umar ya siyawa shamsu da farida tsalelen gida na gani na fada,ba abinda bai sa musu ba na zamanj mai tsadar gaske.

Hatta kayam daki bai bukaci Alh Ahmad da yayi ba,b dakin da bai sa kaya a ciki ba ,duk wani kayan l

Kyalw kyale an sakwa farida da shamsu.

   Ganin kara da kawaici da Alh umar ya masa yasa shima ya ce to ya bar wani maganar hada kayan aure ,haka nan shi ya dauki nauyin biya masa kudin sadaki. Alh umar baiki tayi sa ba ,saboda a fadinta shamsu dansa ne.

     Ansa bikinsu a juma'ar farki na watan karshe.


    Ranar da Deeni ya bugowa mama  waya gaba xaya rudewa tayi har ya so ya fahimci akwai matsala ,amma sai ta nuna masa ba komai,tana fama da hayaniya ne ana shirin auren yayun farida wani satin ,sannann shamsu ma zai yi aure.

     Ihu yasa mata na murna da mamaki ,ya ce 

    Mama ya shamsu zaiyi aure ? Mama kinsan ban taba ganin ya shmsu da budurwa ba sai kace me tsoron mata,amma nayi mamaki . A ina matar da zai aura take ? Unguwar mu ? 

     Mama tayi masa dariar da bata kai zuci ba ,tace. 

       Deeni kenan ,wannan tambayoyi haka,ro koma dai yana nema ko baya nema ya samu ,yarinyar unguwarmu take ," 

        Ayya mama,ina farida? Tna zuwa kuwa ? Kinsan nayi ta neman wayar ta a kashe,haka layin ummanta ma baya shiga ,ina jin dai hidimar bikin suke mama,yanzu da ina nan da har dani za a hada da auren yayun ta da yaya shamsu ayi,amma ba komai mu namu mu biyu zaayi mana special one ....

     Tuni mama taji t rude ,ganin shamsu ya shigo tayi saurin mika mishi wayar. 

    Ga dan uwanka nan kuyi magana ""

  Jiki ba kwari shamsu ya karbi wayar yayi da mama ta koma gefe tana hawaye,tsananin taisayin danta ya ratsa ta ,tana tunanin ranar da deeni zai samu labarin  auren farida shamsu da halin da zai shiga ,bacin rai da tashin hankalin da zai shiga ne babban fargabarta . Tasan halin Deeni da zuciyar sa,in ta kule shi ba me kyau bane ......

   Oh Allah !!! Kayi mana maganin abinda ba zamu iya yiwa kanmu ba ""

 Tunda shamsu ya karbi wayar Deeni ke ta masa surutu yana zolayar sa,yana masa tsiya amma yayi tsit kamae ruwa ya ci shi. Deeni na tambayar sa yarinya da zai aura yar wanj gida ce? Kuma meye sunanta? 

  Tuni yaji kansa ya sara,tambayar tayi masa kunci , y rasa inda zai sa kansa.ya hau masa kame kame,yayin da deeni ya dauka zafin kan aure ne ya debe shi,don hka ya kyale shi,nan ya kawo masa zancen da yafi kowanne kunci.

    Ina amanata da na baka ,farida ? Ina fata kana kulamun da ita ,ya take ,a wane hali take ? Kullum sonta da shi nake kwana ina tashi  ,bani da burin da ya wuce in gama karatu in dawo in auri farida............

       Kafin ya kai ga ida maganar sa shamsu ya yi saurin katse wayar tare da kashewa ,saboda ba zai iya jurewa ba . Dum kunyar deeni ta ishe shi hauahin kansa da tsanar kansa ya kama shi , bai san yaushe ya sa kuka ba.............    


Nace wai dan ma ba ido da ido suke magana da deenj ba kenn🤔ASUBA TA GARI YAN UWASUMY LUV😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤20


Kwanci tashi ba wuya,bikin su farida ya matso,an gama shirin komai ,'yan uwa da abokan arziki sun gama cika gidagen duka biyu cike yake da jama'a. 

     Duk wanda ya kalli fuskar shamsu da farida yasan suna cikin dmuwa da tashin hankali,kowa kuwa yasan dalili ,don haka dai aka dinga binsu da fatan alkhairi.

    Ana gobe daurin auren da safe mahaifin farida yayi kiranta falo,fuskarta a kode kuma a kumbure saboda kullum tana cikin kika. Nan ya sata a gaba yana mata nasiha.me ratsa jiki sosai tare da fada da kuma gargadi na taji tsoron Allah tayi biyayya ga mijinta,ta rungumi kaddarata hannu bibbiyu.

   Tana kuka tayi masa godia ,tare da alkawarin zata yi masa biyayya,ya rungumi kaddara ,ta saduuda,Allah ya bata ikin jurewa.

     Yaji dadi kalamanta sosai ,ya sa mata albarka sannan ya ce mata Deeni ya kira shi yana son magana da ita saboda duk wayar da zai saneta ya kora a rufe.

    " Inaso in ya kiraki ki nutsu ki amsa,kar ki nuna masa komai . Sannan karki fada masa abin da bai sani ba ,kar kiyi yadda zai zargeki. Ki tuna taratu yake yi ,idan yaji wani abu yana iya barin karatun ya dawo,kuma ya samu an daura miki aure,yazo aita rigima dashi ,zhi ya rasa ki kuma zai rasa karatun ,kinga ya yi biyu babu kenn. Ni na tabbar in kina son deeni ba zaki so hka ya faru da shi ba ".

   Nan ya mika mata wayar," zai iya kira a kowanne lokaci"". 

    Gabanta na tsnkewa ta karba tana tunanin me zata ce masa ? Ya zata yi ta fara magana da deni ? 

   Tana cikin wannnan tunanin kuwa ya bugo ,nan ta zurawa wayar ido da lambobin nasa tana kallo,idonta ya ciko da hawaye ,da kyar ta iya hadiye kukanta ta dauki wyar .

       Murya kasa kasa tayi sallama,nan Abba ya mike ya bar falon,don ya basu wuri suyi magana.

     Farida na!!!. Deeni ya fada cikin muryar shauki . 

    Farida I missed u so much,nayi rashinki sosai wayarki da ta umma sam ba a samu,na san dai hidimar biki ne ko ?

Lumshe ido tayi tna jin muryarsa hade da soyayyarsa mai karfi suna ratsa ta .

    "Darida kinyi shuru ,kina jina kuwa ?

   Ina jinka deeni,ina sauraron daddadar muryar da nayi matukar kewa ne. Deeni kunnuwa na sun jima suna son jin wannan muryar,kasan mun jima bamu yi waya ba ,wayarka ba a kira ,sai dai kai ka kira,in kuwa an kira ma za a ji baya shiga." 

    Jikinsa ne taji yayi sanyi,ya rasa dalili muryarta duk ya kashe masa jikj. 

    _" Farida kiyi hakuri ,ki kuma dada hakuri akan wanda kikeyi ,kinga yanzun mun gama jarrabawa har na samu nasarar shiga aji biyu ,kinga kuwa na fito da result me kyau irin wanda ban taba ba . Inasha Allah kamar yau ne zan gama in dawo "". 

    "Nayi murna matuka deeni,Allah ya baka saa ,Allah ya taimake ka. Ina nan ina maka addu'a.

    " na gode farida,shi yasa nake sonki,nake kuma jin kamar duk duniya zai yi wuya a samu mace kamar ki. Ya shirin biki? Naji har da ya shamsu ma zai yi biki,ranar muna magana da shi su mama wayar ya yanke ,da na sake kira kuma bai shiga ba. Ya ce mun a unguwarmu rake ko ? Kin san wacce yarinya ce ?

  Nan da nan ta rude ,ta dabarbar ce ,ta rasa inda zata sa kanta ,baki na bari ta ce.

 Ban sani ba ".

   Tayi saurin cewa ,baka tambayeni karatu na ba""

    Haka ne fa faridana ,in na dawo zaki hada matsayi biyu ai ,mata da kuma malamata,don kuwa darasi zan dunga dauka a gurinki. Tabbas farida inna aureki nayi sa'ar mace ,'ya'yana sai sun min godia da sama musu uwa ta gari.

   Kuka me karfi taji yazo mata,tayi karfin halin cewa ,

Deeni umma na kirana ,zan  mata qani aikin,sai mun sake waya""

   To farida na ,ya amsa .

Kullum kina tuna inasonki ,kullum sonki karuwa yake ,ina nan na rike miki amanar kaina kamar yadda kika rike mun amanar kanki".

    Ba shiri ta kashe wayar ta kwanta a wurin tayi kukanta ta koshi,ta tuno gove inAllah ya kai mu war haka ta zama mallakin shamsu ,ta rasa deeni har abada.

    Bayan ta fita ta mikawa Abba wayar sa ta nufi gidansu deeni ,kai tsaye ta  wuce dakinsa domin yin bankwana da shi da memories dinsa. Haka ta dinga bi tana tsincs duk wani hotunanta,wasikunta da duk wani tarkacenta da zai tuno masa da ita. Duk wani gift data taba bashi sai da ta tattara . Sai dai tana da tabbacin ba za ta rasa wasu a wurin sa ba,yayin da ta dakko nata gaba daya da ya taba bata ta dawo da su. Duk randa ya dawo yaga haka yasan ehh sun rabu har abada,taci amanar kaunarsu da soyayyar da suje wa juna ,bata rike alkawari ba.

     ""KAYI HAKURI DEENI "

Nan tayi kuka tayi kuka har ta gode Allah,yayin da take kallon dakin tamkar yana ciki,tana ganin duk wanj shiga da fita nasu da suka raba yi a dakin,fadan su,wasan su,dariyar su da kukansu . Ta tuno da zolaya tare da tsokana irin na Deeni ,sai da tay murmushi.

   Ba shiri ta dinga tuno irin ran da ya dinga daukar ta hoto ranar da zai tafi. Bata da yadda ta iya sai hkuri da abinda ya fi kardinta.

   Nan ta share hawayenta ta fita,t ja kofar.

Tuni taji zuciyarta ta bushe ,hawayen idanunta ma sun bushe ,bata da sauran abinda zai kara daga mata hnkli ko sa ta kuka ko daria ,ko wani farin ciki tunda ta riga ta rasa DEENI ........Hmmmmmm.....Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤Naji dadin yadda wasu suka fahimci cewa wani baya taba auren matar wani,haka nan wata bata taba haifar dan wata ,,yayinda wasu suke ganin anyiwa Deeni rashin adalci ,,tabbas dan jin dadi kam dole deeni bazai ji dadi ba amma ku duba exactly abinda ke faruwa mana ,wlh nawa ne suke shan soyayya kuma yazama na wadda akayi dashi ba dashi ake murarta ba ......

     Gareki MARIAM HASHIM naji dadi yadda kika fi kowa fahimta😍😍i am really appreciated, tnks 
21 


Washe gari bayan an sauko daga masallacin juma'a aka daura auren Shamsuddeen da farida,dubban jama'a ne suka shaida ,kasancewar daurin auren dana yan uwanta yasa jama'a sukayi yawa,aka cika,manya da kananan ,talakawa da masu kudin duka wannan ranar unguwar ba masaka tsinke,cike take da jama'a 'yan daurin aure,'yan uwa da abokan arziki.


     Bayan daurin aure mahaifansu maza suka shirya gagarumar walima wanka aka gayyaci manya manyan malaman sunnah ,suka zo suka gabatar da wa'azi me tsoratarwa da kuma shiga jiki game da aure. Daga shamsu har farida sun sha jinin jikinsu ,wa'azin ya shige su,suka kara tabbatarwa da fa aure ibada ne ba son rai ko zuciya ba,haka nan aikin ibada zasuyi . In kuwa aka samu akasin haka za su iya fadawa ga halaka,ya zame  musu dole su ji tsoron Allah ,suyi aikin auren don Allah don tsoron sa da kuma kwadayin samun rahamar sa. Anan dukkuansu suka kara sakankancewa,suka saduda,suka rungumi kaddara.

  Da yamma lis aka tashi daga walimar ,jama'a suka watse ,wanda suke nesa kuwa suka koma cikin gidajen da suka zo,sai washegari su tafi ,saboda su Abba dai sunce ba wani sauran taro ko bidi'a ,wannan daurin aire da walima ya isa.


   Bayan sallar isha'i Abba da kansa ya raka sauran 'ya'yansa gidajensu,yayin da farida take karshe kasancewarta kusa,nan ya kira farida ta kara jan kunnenta da taji tsorob Allah,kada ta kuskura ra biyewa wani son zuciyarta tace zatayiwa mijinta wani eashun kunya ko saba masa,din kuwa aljannatar na karkashun kafar sa,don haka ta bi a hankali tayi masa biyayya ,ta manta baya. Ya kara sa mata albaek na biyayyar da tayi masa,tare da mata alkawarin cewa zai mata duk abinda take so a duniya muddin bai fi karfinsa ba . 

    Bayan angama iyauenta mata ma suka bita da tasu kalar nasihohin,sannan Abban da kansa ya rike hannunta tare da kishiyar mahaifiyarta suka kawo ta har gidansu deeni. 

        Falon baba sukayi da ita,inda mama da Baban tare da shamsu da kuma wasu 'yan uwan suke jiran zuwan su,nan kuwa suka mike suka tarbe su cikin murna da farin ciki,inda mama ta jawo hannun farida dake ta rusar kuka tace.

  " Bari ni dai in amshi 'yata da ke ta rusa kuka,an rabaki da mama bayan kina tare da daya maman naki ,me zai dame ki?

 Nan suka yi daria duka,amma ban da farida da shamsu. Nan dai akayi gaishe gaishe tare da barkwanci ,yayin da aka gabatar musi da abinci da sha ana hira. Sannan Abba ya bada amanar farida ga Alh umar da mama da kuma shamsu.

         Sun karba hannu biyu tare da nishi alkawarin farida ba zata taba fuskantar wata matsala ko damuwa ba ,zasu riketa tamkae yar cikinsu . Haka shamsu ma yayi alkawarin riketa amana da kula da ita ,tare da yin hakuri da duk wani abu dazata masa.

   Abba yaji dadin maganar sa kwarrai ,nan aka ta saka musu albarka ,yayin da suka hadu duka suka yi musu nasiha sannan suka kara jaddadawa juna yanzu zumunci ya kullu,an zama yan uwan juna . 


  Bayan tafiarsu baba yasa shamsu a gaba yana gargadin sa da ya rike farida hannu bibbiyu ,ko da wasa kada ya musguba mata . Anan shamsu ya masa alkawarin rikera da gaskia .

     Mama kuwa alfarma ta nema abarta tayi rikon farida na tsawon sati biyu a wurinta kafin su tafi gidansu da shamsu.

     Baba yace wannan tsakaninki da ita da mijinta ,in sun amincen to,in kuwa ba su amince b babu dole,.."

   Nan farida tayi saurin mannuwa a jikin mama tace ,"na amince" 

   Mama tayi murmushi tace ,"yawwa yar mama "

      Shamsu ya kalle su yana daria ,ya ce 

    Nima na amince"

    Baban shima ya kallesu yace ," To nima na amince ."

     Nan suka sa daria duka,sun jima suna hira a wajen kafin suyi sallama. Shamsu ya nufi dakinsa na gidan ,baba ya yi bangarensa,mama ta ja farida suka yi nasu bangarwn. Ta sa mata ruwan zafi tayi wanka saboda tasan tana tattare da gajiya ,ta bata gashasshiyar kaza mai zafi tare da tea me zafi. Bata so haka ta sa ta ci sosai,sannan ta ce to maza ta haye gado ta shige bargo tayi bacci don ta samu hutu.

  Bata musa mata ba saboda ita dai farida ko ummanta bata sakewa da ita kamar yadda take sakewa da mama tun tana kankanuwa.


      Washegari kuwa 'yan biki suka watse kowa ya kama gabansa,gida ya saura daga mama sai farida ,shamsu,lukman da masu aiki. A wannan lokacin mama ta samu damar yiwa farida gyara ba musammana wanda ta san mahaifiyarta bata samu damar mata wannan ba ,sboda wai kunya da kuma ba wani shakuwa tsakanin su. Dan haka mama ta daukarwa kanta nauyin farida da kula da ita.

   

    A hankalin ta dinga mata nasiha akan aure,da kuma tadda rayuwar aure take. Ra dinga fahimtar da ita abubuwa da yawa wanda bata sani ba ,ta wani bangaren tana shiga da ita kicin tana koya mata girke girke kala-kala saboda ita mama Allah ya bata baiwar iya girki. Ba anan tsaya ba,hatta kwalliya da iya dressing kamar ba dattijiwa ba ,,sai da ra koya mata tana nuna mata wani...... 

  


Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE=================== GIDAN NOVELS ====================================22 Wani lokacin haka zata ta dinga mata fada da nasiha akan ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,idan ta nuna halayya na kin amincewa hakan ya nuna bata yarda da abinda Allah ya bata ba,don haka ta hore ta da tayi hakuri ,tayi juriya ta saka soyayyar shamsu a zuciyarta,saboda shine mijinta yanzu,don haka ba karamin zunubi bane ta mayar da tunanin wani namiji da sunan so balle har taji sha'awar sa. Ya zame mata dole ta danne son zuciyarta,ta fi karfin zuciyaeta ta rungumi abinda Allah ya bata hannu bibbiyu ,ta gode masa.

    Nan ta girgiza kai tare da fadin , naji mama,nagode ,insha Allah zanyi duk yadda kika ce.."

     Mama tace ,"Akwai wani aiki a gabanki ,nasan bakya son shaamsu,haka shima baya sonki,amma fa yanzu ya zame miki dole ki so shi,kuma dole ki ja hankalinsa ya so ki a matsayin ki na matarsa. Yana da kyau ki kama zuciyarsa,ki jefa soyayyar ki a zuciyar sa kafin ku kai ga fara zaman aure.

   Sunkuyar da kai tayi kinyar mama ta kama ta ,hakan yasa mama ta mike tace. 

   To zan fita amma ga kaya nan ki ahirya kiyi kwalliya ki fito ,shamsu na falo yana jiranki ,na hada muku dinner zakuyi tare.

   " To mama "

 Ta amsa murya kasa-kasa .

Bayan fitar mama ta mike ta kalli kayan,,wani jan material ne mai kyau da tsadar gaske ,sai kamshi yake. Ta sa a jikinta,doguwae riga ce mai sharpe ,dinkin ya kamaa jikinta tamkar don ita akayi material din ,fatarta mai haske tayi matukar karbar kayan.

Nan ta tsaya tana kallon kanta a mudubi,ta tuno yadda take bata lokaci da tana kwalliya don ta burge Deeni,amma in ya zo sai dai ya yi ta mata daria da gwalo yana cewa bata yi kyau ba . Da kanshi yake tayata ta gyara yana koya mata yadda zata yj kwalliya,in yaga ya kalleta ya mata murmushi yacs,,

  ". Kinyk kyau mrs Nuruddeen duk duniyar nan ba macen xa ta kai matata farida kyau a wurina_

   Ta kanyi murmushi ta boye fuska ,amma yau da ikon Alkah tana kwalliya don ta burge wani ba deeni ba,wani namijin da bata taba noticing dinsa ba a matsayin namiji ,bata taba kula da shi ko ta bashi muhimmanci ba ,asali ma ita yaya shamsu tamkar bako ne a gareta ,shi ne yau ya zamo mijinta. Lallai Allah shi ya barwa kansa sanin abinda ya lullube .

     Tana cikin wannan tunanin mama ta dawo ta ce.

    "Har yanzu farida,ina ji dai sai na sa miki hannu . Farida sarkin tunani ,na ce miki ki rage tunani amma ba kya ji ko ?

      Murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kai. Ta ce ' kinyi kyau kuwa,kayan sun karbe ki. Bari in miki daurin tunda naga ke bakya son yi.."" 

   Nan kuwa ta ajiyeta ta mata daurin da ya kara fito da kyan fuskarta,ta taimaka mata wurin sa dan kunne da abin wuya da dai sauran kayan karau. Ta bata takalmin da ya dace da kayan ,sannan ta fesa mata turare mai kamshin da dadin gaske.

     Ta ce ,yauwa ,yanzu 'yata ta fito a amarya sak,sai gun ango ko ?

   Kanta sunkuye tayi saurin rufe fuska.

     Mana tace to na rafi tunda kunyata akeji ,amma fa ina fita ki fita ,kinga tun dazu yana jiranki.."

" To mama " ta amsa murya a kasa.

  Bayan ta fita itama ta bi bayanta ,tana tafiya cikin nutsuwa da hankali tamkar mai tsoron kasar ko taisayinta.

   Tun kafin ta iso turarenta ya rigata isowa,hakan yasa ya dago kai a zatonsa ta iso falon. Hango ta yayi tana tahowa ,ta zuba kyau,tana wani taku tamkar wacce take filin gasar sarauniyar kyau. Yarintarta da cikarta ,budurcinta ya bayyana a zahiri,nan ya tsinci kansa da kallonta ya kasa kau da kai daga garera . Sai sheki take tana kamshi,bai ankara ba har ta iiso dab da shi. Nan yayi saurin kau da kai.

   Ta ja kujerar dake kallon sa ta zauna itama ta kasa dago ido ta kalle shi,kanta a sunkuye ta ce . 

   Yaya shamsu ina wuni?

  Muryarta me dadi da sanyi ta daki dodon kunnensa ,yaji ya taba zuciyarsa.

   Ya amsa," lafia farida ,ya kike? Ya fada cikin kau da kai .

   Ta amsa kai sunkuye ,"lafia "

 Mama ta shigo tace ,To ko waye ake kawar wa da kai da sunkuyar da kai ban sani ba. Shamsu ,farida halal dinka ce fa,farida shamsu mijinki ne,kina da damar kallonsa ko mene abin sunkuyar da kai ban sanj ba . Ni zan wuce bangaren babanku,ki tashi ki zubawa mijinki abinci, kuma ina so ku saki jiki da juna kuyi hira," 

    To mama" suka amsa a tare.

  Bayan fitar mama farida ta kasa daga kai,yayin da shamsu ya yi karfin halin dago kai yana kallonta kanta sunkuye tana wasa da yan yatsunta.

  Nan y yi kokarin kawar da shirun ta hanyar cewa. 

 Tunda bazaki zuba min abincin ba bari ni in zuba miki,"

   Nan ya bude kular abincin fried liver with potatos ne,ya zuba mata ta hade da juice ya mika mata . 

    Ta dan kau da kai ," Da ka barshi  zan diba da kaina " 

  Ya yi murmushi yace,"Naki ba barshi".

  Ya fada cikin muryar tsokana da kwaikqayonta ,hakan yasa t dago kai ta kalleshi. Gabanta ne yayi mummunan faduwa saboda yadda ya yi sai taga ya bala"in yi mata kama da Deeni,yadda yake murmushin sa da yadda yake zolayarta. Bata san yaushe ta saki murmushi ba ,murmushin da yasa shamsu yaji ya tsaaya masa a zuciya,ya tsinci kansa da kasa dage idanunsa daga gareta har sai da ya ga ta dago. 

 Ya yi saurin mikewa," Ni zan wuce naga dare yayi "

   Cikin sanyin murya tace,ya shamsu kaci abincin mana,kar ka kwanta da yunwa"=

 Ya tsinci kansa da kasa musa mata. 

  Sun ci abinci tare ,sai dai sunyi zaman kurame,dukkansu sun kasa sakeqa da juna yayin da suke kallon juna a sace,,har mama ta dawo ta same su a haka. Ita ta zauna a wurin ta kau da shirun tana kokarin jansu da hira tare da sa su yin magana da juna . Da Shamsu ya zo tafiya mama ta sa farida tayi masa rakiya har kofar dakinsa da ke gidan ,suka yiwa juna murmushi tare da fadin " sai da safe " ta juya.

  Shamsu ya bita da kallo yana jinjina takunta da yaba halittar da bai taba mai da hankali ya lura ba,yayin da farida taji hankalinta ya tashi da ta hango kofar dakin Deeni wanda suka kallo juna da na shamsu . Ta sawa kofar dakin ido,hawaye suka zubo mata,soyayyar sa da kewar sa taji yana ratsa ta.

     Shamsu ya tsinci kanshi da zuwa inda take,ya lura da yanayin da take ciki idonta lumshe hawaye na zuba ,bai san yaushe ya jawota jikinsa ba ya mannata da jikinsa gami da shafarta yana lallashi.

     " kiyi hakuri farida ,nasan ba abu ne mai sauki ba ,sai dai tuna baya ba abinda zai baki sai bacin rai."

   Nan ta fashe masa da kuka ,ya zanyi ya shamsu? Ya zanyi da soyayyar Deeni da ke cina yana azalzalar zuciyata? Ya shamsu ina son Deeni ,ina cikin tsananin kewar sa. Ina son kasan cewa da Deeni"

     Nan ta dada kankame shi tana kuka,tun yana lallaahi har ya daina ,ahi kadai yansan me yakeji a jiki da zuciyarsa.

   Tabbas abinda bai so ba abin da bai zata ko ya tsammani bane ya faru da shi,wato ya tsinci kansa da jin kishin dan uwansa,hakan yana nufin soyayyar farida ta shiga zuciyarsa kenn ? Ya ci amanar dan uwansa da tushe ,ya bari zuciyar sa ta kamu da son farida lokaci guda.

    Addu'a ya dinga yi a zuciyarsa,tare da kokarin sharewa farida hawaye.ya ja hannunta ya kaita har kofar dakin mama tare da kara bata baki,har sai da ya ga ta saki ranta tayi murmushi tare da masa godiya.

       Ta shige ciki ta samu mama suka dan yi hira kadan sannan tayi shirin bacci. Duk yawanci hirar tasu ta kare ne a nasiha da misalai da mama ke bata game da yanayin irin  mata da t ahiga ne ..............


     


Gaskia yau nayi typing da yawa 😡😡se kuma ankwana biyu😜😜Sumy luv😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA"AD❤❤24 Kwanci tashi ba wuya a gurin ubangiji,sai ga ciki ya bayyana jikin farida,iyaye da 'yan uwa kowa ya yi mirna musamman iyayensu maza da mta. Suna shan addua da albarka a kowanne kwanann duniya.

 

   Shamsu dai kamar zai cinye farida,da yanada iko da numfashi ma sai ya mata. Baya bari tayi komai , ya bata kulaqa ta musamman tare da kokarin ganin kullum tana xikin farin ciki . Kullum ana kan binciken lafiaeta data baby.


      Tun daga wannan lokacin mama ta kara tsinkewa da al'amarin auren farida da shamsu,ta kara tabbatarwa aurensu wani hukunci ne na ubangiji,rabon shamsu ne a jikin farida bana Deeni ba,wani baya haifar dan wani,haka wani baya auren matar wanj


       Nan ta kara dukufa da yiwa deeni addu'a. Allah ya bashi ikon hakuri da juriya,ya kuma kawo masa nasa rabon ta wani wurin.


     Farida ta haifo danta santalele namiji mai matukar kama da shamsu,tamkar an tsaga kara. Nan zuciya ta cika da murna ,iyayensu sunyi matukar murnar samun zuri'a da akayi tsakaninsu . Wannan ya kara karfin zumuncin su da kara tabbatarwa sun zama daya.


      Farida da baby sun sha kaya da gata kala-kala. Sun zama abin so a dangi,kowa son su yake da sha'awar su.


     Shamsu ya fadawa iyayensa cewa ya yiwa yaro huduba da sunan kaninsa deeni,wato NURADDEEN . Sun yi murna kwarai,musammaman mahaifin deeni da mama.

     Tabbas deeni ya cancanci haka daga gare su,saboda dukkan su masoyan Deeni ne,daga shamsu har farida,haka nan shi masoyin su ne.


   Alh Umar ne ya bugawa deeni waya ya yi masa albishir da zuwan baby da kuma takwara da aka masa ,wato mai suna da shamsu ya masa.

  Kwarai Deeni ya ji dadi yayi murna soaai har ya cewa babansa zai zo in sunyi hutu,sai dai mahaifin nasa ya taka masa birki,ya nuna masa zuwa gida zai mai da masa hannun agogo baya ,ya daure dai ya karasa,sauran sa shekara biyu ya gama ,in yaso zuwa ya sayo wa mai sunan sa duk irin abinda yakeso.

Ba don yaso ba haka ya hakura ,ta wani bangaren yana ganin gaskiyar mahaifinsa ne. Tabbas inya dawo gida yaga farida sake tafiya ya barta zai yi wuya,don haka hakurin dai shi yafi masa.

   Haka rayuwa ta cigaba da tafiya musu,shamsu da farida da dansu Deeni karami,suna rayuwa tare da rainon dansu cikin so da kukawa da juna ,tare da kulawa da juna ,tare da mahaifansu,yayin da deeni ya dage ya ci gaba da karatun sa.* *        * *       * *     * *       * *


Tunda ya sauka kasar sa nigeria yake cike da farin ciki da wani irin dokin zuwa ya ga yan uwansa,lumshe ido yayi yana shakar iskar kasar sa mai albarka,kasar mama da baba,kasar masoyiyar sa farida.

     Sanye yake da red t.shirt hade da blue jeans ,idanunsa boye cikin fararen glass ,ya yi wani irin haske da kyau ,saboda samun hutu da canjin yanayi da ya samu.fuskar sa kunshe da murmushi,kana ganinsa kaga wanda yake cike da farin ciki.

    

    Hayar taxi yayi a nan cikin airport din,ya sa kayansa a boot sai gida.

      A cikin taxi din Deeni yana ta sake sake tare da tunanin shin wa zai fara zuwa ya gani?masoyiyarsa farida ko kuma iyayensa ko yaya shamsu da matar sa? Yaba son basu surprise ne shi yasa ko baba bai fadiwa yana zuwa ba ,yafi so sai dai su ganshi kawai,mahaifinsa ya zata sai wani watan zai gama ya dawo.

    Ya yi murmushi,"Farida zata ganni bazata,zanga ni da ita wa zai fi farin ciki da ganin dan uwansa?

   Yana wannan sake saken har suka iso cikin unguwarsu,a nan ya tsaya yana tunanin ina zai fara shiga gidnsu ko na su farida ,ko kuma gidan ya shamsu..............??


To masu karatu ku bawa deeni shawarar inda zai fara shiga........

 Sai munji shawararku wadda zan bawa deeni😜😜😜😜😜Sumy luv😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤23 


A wannan sati biyu mama tayi dukkan iyawarta da dagewarta akan Shamsu da farida,taga sun saki jiki da juna ,da kokarin nuna musu su rungumi kaddara suyi ibadar aure,su manta komai. In sunyi haka tabbas basu yiwa Allah butulci ba ,kumansun yarda da kaddara kamar yadda ake so kowane musulmi na kwarai ya yi. In sun haka kuwa Allah zai sa albarka a rayuwar su,ya daga darajar su a duniya da lahira. 

       Da irin wannan maganganun na mama yasa suka saki zuciyar su,musamman ma dai farida ta riga ta saduda,ta daura damarar manta baya,ta kuma cusa soyayyar mijinta da Allah ya kaddara mata a zuciyar sa.

        A satin biyin ta koyi abubuwa da yawa ,don haka tayiwa mama godiya sosai,dami da mata alkawarin zama mace ta gari,saliha ga Shamsu,zata yi kokarin kawo farin ciki da kwanciyar hankali tare da nutsuwa a rayuwar Shamsu ,ta riga da ta amince,ta karbe shi matsayin mijinta. 

  Wannan magaba tayiwa mama dadi matuka da zancen farida ,tayi ta saka mata albarka.

    

Shamsu shima bai yi kasa agwiwa ba ya kara jaddadawa mama rikon da zai yiwa farida bisa gaskiya da amana da kuma soyayya.

   Mama tayi ta sa musu albarka ,ta raka su har mota tare da hadawa farida guzuri iri-iri.


  Farida taji kewar mama sosai ,saboda shakuwa da sukayi a yan wadannan kwanakin da sukayi tare.

   Kauna da soyayya tare da kulawa da shamsu ya dinga nunawa farida. Ya tabbatar mata da soyyayr ta na tare dashi ,don haka itama ta saki jikinta da shi,ta mika wuya gareshi. Da kanta ta kai kanta garw shi har dakinsa,mutuncin mama kadai da girmanta da take gani ya isa ya hnata cutar da shamsu.

   Ta lura yana sonta da bukatarta ,amma ya kau da kai,bai taba nuna mata hakan ba ,don haka da kanta ta yanke shawarar mika kanta da rayuwarta gaba daya ga mijinta. Bazata iya raba kanta da son Deeni ba ,amma zata iya raba kanta da tunaninsa ta cusa na mijinta a zuciyarta.

     Wanka tayi fes ta feshe jikinta da kamshi ,tare da saka sexy dress ,ita kanta ta yaba kanta,ta zurawa kanta ido a mudubi .

   " Yau ce ranar da zan ci gaba da rayuwata,ranar da zan mallakawa wani kaina,zuciyata da gangar jikina,wani ba deeni ba. 

   Ina fata zaka yafe mun ,ka manta dani a rayuwarka Deeni,na yankewa kaina hukuncin rungumar aurena da mijina hannu bibbiyu don nemar yardar Allah.

       Da wannan tunanin ta nufi dakinsa,tayi sallama ,yana zaune bisa gado sanye da kayan bacci,hannunsa rike da ipad yana danne dannen sa alamar wani aiki na office yake yi.

     Sallamarta yasa shi daga kai yare da amsawa,ganinta a yanayin da bai zata ba yasa shi kasa karasa sallamar. Ya yi saurin kau da kai zuciyar sa na bugawa,tuni ya ji ya rude musamman da ya jita dab da shi.

Hannu tasa ta karbi ipad din ta ajiye a gefe ,ta dare bisa cinyarsa tare da jawo shi jikinta ta rungume shi . Nan ya bata hadin kai ,shima ya kara mannata a jikinshi sosai yana shakar kamshi tare sauke wani irin ajiyar zuciya yana jin tsananin son ta da sha'awarta suna shigar sa.

  Cikin muryar rada idon sa a rufe yana manne a jikinta yace...

  Farida kin amince dani,ba kya tunanin dee.....

    "" shhhhhh" 

Ta fadi gami da saurin rufe masa baki tace ,,

   Karkace komai,na mika rayuwata da kaina ga mijina wanda shamsu shine mijina,gaskiyar rayuwata. Ni matarka ce,kanada hakki da damar yin duk abinda kake son yi dani,buri na a yanzun kawai in kyautata maka . Ina neman yardarka ,saboda Allah ya yarda dani.

   Nan ya dunga sauke ajiyar zuciya ,shi kadai yasan me yakeji a zuciyar sa da jikinsa.

  Bai bata lokaci ba ya dada cusuwa a jikinta ,tuni suka manta komai suka fada wata duniya. Farida ta mallakawa mijinta shamsu kanta ,, yayin da shimanya mallaka kansa da komai nasa ,yana mai sa.mata albarka gami da alfahari da ita .

  Tuni suka rungumi auren su suka rike hannu bibbiyu,suna kula da juna tare da tarairayar juna,suka bude sabon shafi na rayuwar su,iyaye na sa musu albarka.

Ba wanda ya kai mama farin ciki da kuma fargaba ,a kullum Deeni ya yi waya sai shamsu da farida sun tsinci kansu cikin sabon  tashin hankali . Sai dai a kwana a tashi har sun saba da hakan ,don kuwa mahaifin deeni ya hana ko da wasa a fada masa gaskia ..

  Lokacin da karatu yayi wa deeni yawa ma yana dadewa bai yi wayar ba.mahaifinsa yana yawan ziyarar sa,yana ganin yadda ya cigaba sosai a karatunsa,ya yi nisa kuma tana kokari sosai ,ya kwantr da hankalinsa,,saboda ko da wasa bai san me ke faruwa ba. Kullum da burin auren farida yake kwana yake tashi........

   Bye 


Mu kwan lahia jama'a
Sumy luv 😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBECopied by SUMAYYA SA'AD❤❤
25


  Can dai deeni ya yanke hukuncin zuwa gidan dan uwansa ,ya cewa direba ya juya. Dama ya riga yasan gidan da mahaifinsu ya bawa shamsu,don haka ya yanke hukuncin wucewa gidan shamsu ya ga mai sunansa Deeni da dan uwansa,ya yi masa murnar aure,ya ga kalar matar da yayansa ya aura...😭


    Yana daria ya fito hannunsa dauke da akwati wanda cike yake da kayan sawa da kayan wasa na mai sunansa Deeni karami. Nan ya cewa mai taxi din ya jirashi zai shiga ciki ya amso masa kudinsa. Nan ya yi ciki ya bar sauran kayansa a motar.

       Tura gate din gidan ya yi yana jan akwatin da ke hannunsa,yana ratsa tsakiyar gidan,yana kallin ginin da cikin gidan yana murmushi. A ransa yana fadin,kwannan shima zai mallaki nasa gidan tare da farida.

     "Anya kuwa in na auri farida ina da wani sauran buri kuwa a rayuwa?

  Yana cikin wannan tunanun yaci karo da security na gidan wanda dama ya shiga ciki kai wani sako ne ,ganin Deeni yasa shi washe baki yana dariya saboda dama tsohon mai gadinsu ne Alh ya bawa shamsu shi yana masu gadi.

     Nan ya karbi akwatin tare d a bude masa kofar falo,anan ya ci karo da Deeni karami a tsakiyar falon ,an baza masa toys yana wasa .

   Da sauri ya isa gare shi yana dariya,yasa hannu ya daga shi, Deeni kuwa kamar ya sanshi ya wangale baki yana dariya.

      Deeni yana zura masa ido yana kallon irin kamar da yake yi da shamsu,son yaron da kaunar sa yaji ya shiga zuciyar sa,nan ya dinga masa wasa yana cilla  sama shi kuma yana daria.

      Nana ya bude akwatin ya ciro masa sabbin toys din da ya siyo masabya bashi,anan wurin deeni ya zauna yana ta wasa da Deeni. Shi dai megadi ya tafi ya barsu don Deeni ya hana ya musu magana ,ya ce suprise zai basu.


     Tsawon minti goma yana da Deeni har ya soma mamakin me yasa yaji tsit ba wanda ya fito duba Deeni karami shi daya? 

Nan ya daga shi ya nufi falon ciki yana fadin...

 " zanci tarar iyayenka ,sun barka kai kadai na tsawon lokaci ba wanda ya leko ka,kar ka damu ga uncle Deeni ta dawo ,zai dauke ka ya tafi da kai su kuma suyi ta zaman su a ciki...."""

   Deenibdai sai dariya yake masa tare da fadin mommy ko daddy.

  Ya ce "uncle zaka ce,uncle Deeni "

  Nana ya yi kokarin kwaikwayon sa ya fada cikin maganar yara 'yan koyo. Shekararsa biyu amma ba baki sosai,sai girma da yayi kamar dan shekara uku.yaro ne lafiyayye mai ki da karfi. Da alama ya samj kyakkyawan raino da kula daga iyayensa.

    " Salamu Alaikum ,mutanen gidan suna nan kuwa ko sai na tafi muku da yaro za ku fito?

 Deeni ya fada yana kokarin kutsawa cikin daya falon tare da daga labule.

 Wani abu idonsa ya gane masa me kama da mafarki ko almara,,wani abu da kwakwalwa ko hankalinsa ba zai iya dauka ba.

    Farida ya hango kwance jikin shamsu ,shi kuma ya rungumota yana ta kokarin massaging kanta,yana matsa mata kai alamar yana mata ciwo ,tana ta zuba shagwaba.

   " Daddy kaina zai tsage,daddyyn deeni inajin murda;;""

     Yi hakuri mommyn Deeni,zai bari,kwanta ina ci gaba da matsa miki tunda kin sha magani zaki samu bacci yanzu,kiyi shiru kar ciwon kan ya karu"

 " Daddy deeni fa ?  Ta fada cikin shagwaba da kuma ciwo .

  Yana can yana wasa ,ki samu bacci zan fita da shi in kaishi gun mama tunda ka kya jin dadi. Wannan babyn namu dai da yazo yanzu yana wahalar min da farida na,sai mun masa bulala in yazo.

  Tayi murmshi ta ce , Ya shamsu macw zamu haifa mai sunan mama,kaga kuwa ba a yiwa mama bulala ba,in kuwa ka mata sai hannunka ya nade" 

    Dariya sukayi duka,sam basu kula da Deeni da ke tsaye a kansu ba,wabda tsananin firgita da kaduqa da abinda ya gani sai da ya saki deeni ya sha kasa ,bai ma san yayi hakan na. Gaba daya hankalin sa ya bar jikin sa,baya hayyacin sa.

    Ihun deeni ya jawo hankalinsu ,shamsu ya mike a firgice gabansa ya mummunan faduwa,yayin da farida ta ji wani irin hajijiya ,sabon zazzabi ya lullubeta ,tsananin firgita da ganin Deeni bata san lokacin da taji mararta ta juya ba ,wani azabar ciwo taji ya kamata,tuni jini ya soma bin kafarta yna gudu ,alama ne na cewa cikin jikinta wanda bai wuce wata biyu ba ya bare saboda tsabar tsorota da tashin hankali data shiga. Haka nan shamsu duk kokarinsa ya kasa ko da motsi a wurin ,kansa sunkuye ya kasa hada ido da Deeni,ya kasa ko da motsawa balle yaje ya daga deeni dake ta kwala ihu a wurin 

   Farida dai dakyar ta samu ta zauna bisa kujerar da suke da sabida hajijiya da wani abu da taji yana yawo a tsakiyar kanta ,ki ciwon marar ma bata lura da shi ba sai dai tabbas tasan abu na bin kafarta wanda bat san menene ba.

  Tsawon minti biyar suna cikin wannan halin,duk wani farin ciku da murnar da jin dadin da ya dawo da shi nigeria sai da ya neme shi ya rasa,kunci ,bakin ciki ,takaici, da bacin rai ya maye gurbin su.

  Halin da ya gansu ya ganar da shi dukkan abinda yake faruw ,ya fahimci cin amana da. yaudarar da farida da shamsu suka masa.wani abu da bai taba zata ba balle tsammanj ,ko a mafarki ko. A tunaninsa bai taba giftawa ba.

   Wani abu yaji ya tokare shi a zuciyarsa,haka ya dinga jin wani azabar radadi a kansa,wani irin azabar ciwo da bai taba jin makamancin sa ba . Amma duk da halin da yake ciki sai ya sa hannu ya dauki Deeni ya nufi gabansu ya mika musu shi,sai dai dukkansu ba wanda ya iua motsawa balle ya sa hannu ya karbe shi. Hakan yasa ya ajjye shi. Akan cinyar farida ya juya ya fita.

   Yana shirin barin falon ya ci karo da su umma tare da baba ,da kuma Abba da umma ,wato mahaifiyar farida.

    Ashe Alh Umar ya yi waya can America aka ce masa ai tun tuni Deeni ya taho nigeria,tun daga nan hankalin sa ya tashi ya aina tsawon lokacin da aka ce masa ya taho yasan tabbas ya iso,haaka nan tunda bai je gida ba ko gidansu farida ,to tabbas yasan gidan shamsu zai nufa. Ranar da suke gudun zuwanta ne dai ta zo.

     Tunda mama ta sami labari hankalinta yai mummunan tashi,Alh ya tattaro su duka don su yiwa Deeni bayani,su fahimtar da shi ,wanda a zatonsu zai fahimta,(hmmmm atunaninsu akwai wani bayani da deeni zai fahimta ne🤔),to amma mama tasan dama za'a rina.....

   Mama na ganinsa da yanayin da ya shiga hankalinta ya kara tashi,ta jawo shi ta rike gam tana fadin .

Deeni addu'a zaka yi kaji,ka dinga maimaita hasbunallahu wa niimal wakil,ko la'ilaha illah anta subhanaka inn kunti minazzalimin""

     Gaba daya kansu suka yi kowa da irin abinda yake fada masa ,da irin bayanin da suke masa . Sai dai deeni ya dawo kamar zararre,tamkar mara hankali,kallon su kawai yake bakinsa na motsi amma baya ma jin me suke fadi balle ya gane.

     Ya kalli mahaifiyarsa yace,,Mama kinada kudi ki bani in biya me mota lr da ya kawo ni ?

    Deeni na biya shi,har mun sa ya sauke maka kaya ya sa a motar mu,zo mutafi gida""

    Deeni ya kalleta,"Mama farida ,jini na zuba a jikinta ku kaita asibiti"

    Sai a lokacin suka mai da hankalin su kanta,umma ce da mama sukayi kanta,suka dagota hankalinsu a tashe suna salati,sukai mota da ita. Tare da Abba suka tafi,yayin da baba ya tsaya tare da shamsu da deeni,ya jawo su duka.

    Bayani ya fara da nasiha ,da kuma fadin ba laifin shamsu da farida bane ,su suka yi hadin nn saboda wani dalili nasu,su kuma suka musu biyayya.

     Bana son ji Baba ,duk wani abu da zaka fadamin ko wani dalili bana son ji,ka rike dalilinka,duk abinda zaka fada ba zai cire min ciwon da nakeji yanzu a zuciyata ba.  Kasan me nakeji Baba ? Da kasani da baka tsaya yi mun wani magana ba ...

   Baba ka sama mun magani ,ciwon da nakeji a kwalkwata da zuciyata yanzu za su iya kashe ni,Baba yanzu ina jurewa amma anjima ba zan iya jurewa ba. Baba zai kashe ni ka kaini asibiti ko ka min addu"a ,kamin duk abinda zaka iya mun ko zan samu saukin ciwon da nakeji .....     

      Kai Babana nw ,ME SONA ,me yanke dukkan wani hukunci na rayuwa saboda ka kawo ni duniya ,ka bani ci da sha, ka kula da lafiyata da karatuna ,ya zamar min dole in maka biyayya.

   Nayi biyayya baba da abinda kayi ,sai dai baba ka taimake ni wannan abinda nakeji baba ban taba jn irinsa ba,baba bana ganinka sosai ,duhu na rufe mun ido,ina jin duniyar na zagawa dani ....

     Kama kansa yayi da karfi,basu ankara ba sai ganinsa sukayi ya fadi ,ya zube kasa a sumeeee.............

     

       😭😭😭😭😭😭😭😭


Allah ya bamu alkairi jama'a ,,dan wlh nima hannu na rawa yake kar ayo biyu,,ga deeni a sumee nima wayata karta fadi......
Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤


ASSALAMU ALAIKUM 


Yan uwa!! Mata ce ta cewa mijinta ya saketa,shi kuma yaki ,hakan yasa ta dakko wuya wai idan be saketa ba zata kashe kanta.

  Shi kuma ganin haka yasashi sakinta. SHIN YAYA HUKUNCIN WANNAN SAKIN DA YAMATA ? TA SAKU KO BATA SAKU BA 🤔🤔?

    Sai naji daga gareku....nagode
27Wasa gaske al'amarin Deeni ya tsananta,wani lokaci ka ganshi lafiya wani lokaci ya haukace musu,gana daya baya hayyacinsa,bai san me yake yi ba,hankalin iyayensa da masoyansa ya kai kokuluwar tashi. Daga karshe Alh ya fita dashi kasar india ,anan aka ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar sa,saboda abin yamatukar raba masa kwakwalwa,kwakwalwarsa ta kasa dauka da jurewa wannan damuwar.


    Ana duba lafiarsa a asibiti kuma ana masa rokon Allah,tare da sauke masa Alkur'ank ,da haka da taimakon ubangiji Deeni ua soma dawowa hayyacin sa. Sai ya zamana ya daina surutu tunda suka dawo gida,ba ya kula kowa ,baya cewa kowa komai. Kullum yana zaune a dakinsa,baya fita sai dai wani ya tafi masallaci ya dawo. In an kai masa abinci wani lokaci zai ci ,wani lokaci kuma haka abincin zai kwana wani ya tarar da wani.

   

      Lokaci guda rayuwar Deeni ta canja ,ya yi baki,ya rame ,kuma baya aikin komai sai kwanciya da zaman gida. Ya dawo rayuwar sa sam bata da wani manufa.


    A duk lokacin da Deeni zai kwanta bacci,to yakan rufo ido ya hango shi da farida,lokacin da hoton farida da shamsu zai bayyana a fuskar sa yakan yi saurin bude ido wanda a nan za su rine suyi ja,yaji kansa ya fara sarawa ,ya kama kai da kirji . Wani lokaci sai dai a shigo a same shi a sume. 


    Halin da Deeni ya shiga ya daga hankalin kowa a zuri'ar su,musamman iyayensa da kuma shamsu da farida. Wani lokacin mahaifin sa sai ya zubar da hawaye saboda bakin cikin halin da dansa ya shiga. Rayuwarsa ta dawo useless bata sa wani amfani ,ya yi da na sani tare da jin bakin cikin abinda ya yi.

     Kulum yana binciken asibiti ko masu maganin gida da za su dawo da shi dai dai,sai dai abu guda yake ji kullum,shi ne abin ya mugun taba masa kwakwalwa da zucya,wanda fitar sa a wannan hali sai a hankali . Sai dai dayawa masu magani ko likitoci na bashi shawarar cewa ya canja masu wuri,wato ko dai ba ya bar garin ko kasar ,ko dai wani wurin da zai nesanta deeni da rayuwar da yayi ta baya.


   Wannan yasa Alh Umar ya tattara nasa ya nasa da kasuwancinsa ya raba su biyu ya koma lagos ,ya yin da ya barwa Shamsu sauran kasuwancin sa a kaduna .


Alh Umar ya tattara iyalinsa,wato hajia A'i da Deenj da lukman suka koma garin lagos ,ya bar Arewa gaba daya. Saboda ya san Deeni yana da sha'awar zama a garin ,sannan yana ga zai ji dadin tafiyar da kasuwancin sa. Haka Deeni zai samu kyakkyawan canjin yanayi ,yayin da ya bar Shamsu da Farida a kaduna. 

     

    Tabbas Alh.Ahmad ya yi bakin cikin rabuwa da abokinsa,makwabcinsa,wanda yake kamar dan uwansa Alh. Umar . Ya daukar masa manar dansa da kuma hakkin kula da shi da kasuwancin da ya bar masa,da ya dinga kokarin sa ido inda yaga ya karkace ya yi masa gyara.

     Farida da mama sun rabu cikin kuma tare da bakin cikin rabuwa da juna.***      ***     ***    ****      **


    ""ALHAJI ! ALHAJI   !!

Haj. A'i ta shigo falonsa tana kwada masa kira .

    Ya kalleta a firgice ," lafiya cikin daren nan ?

Ta mika masa wani farin takarda ,ya kalleta cike da mamaki.

   "Menene wannan ?

   Tace ,Address ne na samu,inda zamu kai Deeni,yanzu na kasa bacci na kunna tv kenan naga suna tallen wurin nan. Na lura masu matsala irinta Deeni sun samu waraka..""

  Ya kalleta ransa bace ,ya ce,"Dana ba mahauci bane ,kuma ba dan shaye shaye bane da za a kaishi REHABILITATION CENTER 

   Cikin nuna damuwa Haji. A'i tace. Alhaji ka duba ka bincika ,wannan wurin ba mahaukata ko 'yan shaye-shaye bane,kafin in baka sai da nayi bincike naji komai akan su. Abinda yafi jan hankalina gare su ahi ne,sun hada da Addini da kuma magungunan musulunci . Deeni yana bukatar taimako na Addini da na asibiti duka,wanda duk sun hada.

       Dakyar ta samu ta shawo kansa ya yarda zai binciko,in ya masa yadda hankalin sa zai dauka to zai yi tunanin tura Deeni wurin.....
Gaya nan ayi breakfast😜😜😜


Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
=================== GIDAN NOVELS ====================================26Alh Umar ya mugun rudewa ,rabon sa da ya zubar da hawaye har ya manta,amma a wannan lokacin sai da ya zubar da hawaye,hankalin sa ya mugun tashi.ya tsorata da lamarin Deeni,haka shamsu duk jikinsa ya mutu,ya rasa me ke masa dadi,ga halin da Deeni ke ciki ,ga na farida.

       Tare suka nufi asibiti dashi,in da faridan take nan suka je,sai dai ita an dace an shawo kan alamarin ,sai dai tayi barin cikin har an mata wankin ciki tare da bata magunguna da allurai.

     Tana kwance tana hawaye ,mama rungume da ita tana bata baki da nuna mata ta ci gaba da dauriya da cijewa kamar yadda tayi a baya,,zai wuce.

   Umma rike da Deeni karami tana kallonsu,ta kasa fadin komai sai tsabar tausayin 'yarta da ya kamata,ta ahiga halin tsaka mai wuya.

    Nan ta matsa itama tayi mata nata nasihar ,sannan ta ce zata wuce gida da Deeni,sannan zata shirya musu abinda za su ci ta aiko asibitin. Mama kuwa tacw zata zauna da ita.


    A nan ta samu damar kwaniciya a cinyar mama tayi kukanta sosai,mama bata hanata ba sai dai bata fasa lallashi da bata baki ba.

     Suna cikin wanann halun shamsu ya iso yana rude ,mama ta kalle shi tace,,,,

 Ka dauki abin nan a hankali,komai ta yi zafi magninsa Allah."

     "Mama Deeni yana kwance a emergency tun dazu muna can likitoci a kansa sai yanzu muka samu ya farfado,"

   Hawaye ne ya gangaro masa,ya ce,"Mama Deeni yana cikin wani hali wanda mu ne dalili." 

    Da sauri mama ta mike ba tare da ta karasa jin me yake fadi ba ta fita wurinsa,Shamsu ya matsa gaban farid yana fadin . "Ban baki kulawa ba lokacin da kike bukata,saboda Deeni yana bukatar kulawata fiye sa ke. Farida ban kaea sanin cewa bamu kyautawa Deenj ba sai yau da naga halin da yake ciki ,halin da ya shiga yana cikin tsanani da firgita tare da zafin zuciya da kwakwalwa""

     Ta fashe da kuka ,"Ya shamsu ba abinda zai samu Deeni ko? Ya shamsu munci amana.."

   Ta fada a lokaxin da ta kara fashewa da kuka .

  'Ya Shamsu ba zan iya fuskantar Deenj ba har abada,fatana Allah ya bashi lafia,yasa kuma ya manta sa ni da wannan cin amana da muka masa."

     " Ba mao sauki banw farida ,tabbas bamu kyauta masa ba ,har ga Allah bamu kyautawa Deeni ba "

  Nan suka lallashi juna ,daga karshe Shamsu ya kama ta suka nufi gurin Deeni a emergency.

      Tana hango shj ko daga nesa ne,hango shi tayi yana kwance idonsa biyu sai dai ya kau da kai hawaye kawai ke zuba masa,ransa a mugun bace,hankalinsa a tashe.

     Tausayinsa da tsohuwar soyayyar sa taji sun taso mata suna tsuma zuciyarta,tayi saurin dafe kirji tana hawaye,ta lura ya kara girma da haske hade da wani irin kyau duk da yana cikin tashin hankali.

    Ta lumshw ido tana jin wani abu mai ciwo da radadi yna ratsata.

    "Ka yafe min Deeni na ci amanar kauna ,sam ko kadan ban yi fighting wa soyayyar mu ba,nayi saurin mika wuya . Na cika makiyarka da nayi sanadin jefa ka a cikin wannan halin,nasa ka dandani wannan zafin zuciyar. Allah ya baka wacce ta fini,ni kam ban dace da kai da rayuwar ka ba da soyayyarka,tunda can ma kila shiyasa Allah ya rabaka danj. Na tabbatar Allah zai baka wacce tafi dacewa da kai,sai dai ka sani Deeni ba zan daina sonka ba ,hae abada soyayyar ka zata kasance a cikin karkashin zuciyata. Sai dai zan danne ta in ci gaba da rayuwa ta da mijina gami da faranta masa iyakar iyawa ta..""


    Muryar mama ce ta katse mata maganar zucin da take yi,ta mai da hankalinta kansu.

    Mama ke masa magana cikin kwantar da murya,tana shafar kansa kamar karamin yaro tace,,"" Deeni kayi hakuri ,bani da abinda zan iya baka sai hakuri ,ba wani bayani ko kokarin kare kanmu da zan maka. Magana guda ce ,mun maka laifi duk da muna manya kai kana karami ,amma min maka laifi,mun zalunce ka,kayi hakuri ka yake mana,kar kayi fushi damu."

       Deeni yayi murmishin kardin hali yace,"Fushi "" ? Da wa zanyi fushi ? Kima ni waye da zan yafe muku ? Ku iyayen mu ne,kuna da damar yin yadda ku ka so. Da mahaifin farida zanyi fushi don ya zabawa 'yarsa miji ? Ai bani da hujja.

    Da farida zanyi fushi ,masoyiyata ,wacce ta min alkawarin soyayyarta da kanta ,wacce tun muna yan kanana muke wa juna son da bamu san irinsa ba ? Ko da yayana da na bawa amanar masoyiyata ,wanda yasan duk wani sirri da tarihin son da nake wa farida ? Ko da nahaifina da ya yaudare ni ya min karya? Ko da mutumin da na dauke shi tamkar mahaifina yace min ya mun alkawarin bani yarsa har inje in dawo ? Ko da mamana mahaifiyata da ta boye min gaskiyar magana? 

   Mama da wa zanyi fushi a cikinku ? Kuma meye riba ta in nayi fushi da ku ? Abinda ya faru zai canja ne ? 

    Ya mike cikin zabura da zafin zuciya ,ya ce.

     "Damuwata shine yadda zan share wannan mummunan al'amarin daga kwakwalwata da zuciyata ..""

   Ya kalli likita dake tsaye a kansa tare da mahaifansa ,ya ce

    " Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala likiminka ya kai inda za'a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka  bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..""

   Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar ak samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.

     Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.

   Mama tana kuka tana tofa masa addu'a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani..............
Hmmmmmmmmmm😭😭
Sumy luv😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬Writting buSAADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤28 Ruwan sama ake tsugawa sosai ruwa irin na lagos,wanda idan ya fara sai anga tsawarsa. Iska ce me hade da feshin ruwa ya shigo ta windo ya wanke mata fuska,hakan yasa tayi saurin bude ido hade da addu'a. 

    Ta mike ta nufi jikin window din ta lumshe ido tana shakar daddadar iskar da ke dukan fuskarta tana jin yana ratsa ta ,yanayin da tfi so fiye da kowanne yanayi kenn.tuni taji zuciyarta tayi mata fari,ta tsinci kanta cikin wani nishadi.


    Karar door bell ne da aka danna ya ja hankalinta zuwa kofa,Doctor Bahijja kenan tayi saurin zarar hijabinta ta nufi kofar falon , a nan mai gadi ke fada mata suna da baki da ke son ganinsu,sunje cikin asibiti aka ce basu iso ba ,shi ne suka biyo su gida,sun ce wai yana da matukar muhimmanci suga likita.

   Tayi mirmuahin da tasaba wanda kullm yana makale a fuskarta ,ta ce

 " Kaisu falon baki,kace su jira ko ?

     To madam

Ya amsa tare da juyawa ,duka cikin harshen turanci suke maganar..

    Nan ta juya ta nufi dakin barcinsu,kai tsaye ta same shi har yanzu bacci yake duk da iska mai sanyi da ke ratsa dakin ,yana ratsa fuskar shi bai sa shi farkawa ba .

      A hankali ta sa hannu tana jan bargon da yake lullube tana murmushi ,amma sai ta ga ya dunkule guri guda ya ci gaba da baccin sa tamkar wani baby.

    Ta kalli kyaykkyawar fuskar sa me kunshe da annuri da lafiya ,tare da kwanciyar hankali . Soyayyar sa taji ya kara tasiri a zuciyarta ,cikin muryar shagwaba tace.

   ""Please my dear" ka tashi mna,kana da baki "

   Bai saurareta ba sai kokarin jawota jikinsa da yayi yana narke mata a jiki,ya cigaba da kwanciyarsa a jikin ta,yana jin sonta na karawa baccin nasa dadi.

    Girgiza kai tayi tana murmushita kwace jikinta tare da sa hannu tana jan hancinsa,tana wasa da shi .

     My dear please ka tashi ka duba time fa karfe sha daya na safe ,baccin ya isa haka. Ba don ruwan sama ba da fa ka fita tun karfe takwas."

   Cikin muryar bacci ya ce,"shiyasa nake son damuna ,yana bani hutu ,ina samun nutsuwa da Bahijja na,amma ina!! Wannan likitar ba zata bar wannan likitan ya huta ba.

    In barka ka huta daga baya kace me yasa ban tashe ka ba ? Ka fa tuna me kace mun "

  ," Komai bacci me dadi da nake ki tashe ni ko da kamshin jikinki" 

 Rungumota ya sake yi ya cigaba da kwanciyar shi"

 Bata kulashi ba ta mike ta nufi gadon Muhammad da taji alamar ya tashi yana ta ciccilla kafa yana wasa tare da surutai irin na yara. Yana ganinta kuwa ya wangale baki yana mata daria,yana sanye da body suit dinsa masu kyan gaske da ban sha'awa .(hmm, kaga dan likitoci ,😀)kaunar dan nata taji ya kara shiga zuciyarta ,dariyar da yake mata ya sa taji kaunar danta har cikin zuciyarta tare da godewa Allah da ya azurta ta da kyakkyawa kuma lafiyayyen da son kowa.( dama ahalin likita na cuta ne 😜😜ciwon ma tsoran gidan likita yake)

   Tasa hannu ta daga shi,yaro ne da bai wuce wata shida ba ,ta rungumo shi a jikin ta ,ta ce. 

    Ni dai na kasa tashin Abbanka ,amma ni da kai zamu tashe shi tare.

   Nan taje ta ajiye shi a kansa,nan da nan ya wangale baki har da tsalle saboda ya ga abokin wasansa. Nan ya hau sukuwa a kansa yana jansa tare da masa yaren su na yara ,dolensa ya bude ido yace.

   " Ta nan mommyn ka ta bullo ko ? Ta hada ni dambe da kai,to bari in mike muyi.

  Nana ya tashi ya biyeshi suna wasa yana cilla shi sama ,shi kuwa yana ta dariya,itama ta taya su. Sannan ta barsu ta nufi toilet don shirya masa bayi ,ya yi wanka . Tazo ta barki Muhammad ta kai shi gurin baba Andi,dattijuwa me kula da shi in bata nan. Sannan ta dawo ta taimaka masa ya yi wanka,ya shirya kusan komai ita ta masa,hatta turare ita ta fesa masa ,gyaran fuska da komai ,sannan ta kalleshi ta ce . 

    Perfect!!! Mijina is d best" Ya jawota jikinsa yace,"A'a mama ta is d best ,,ina sonki Bahijja na,ina son ki sosan gaske ,musamman in kina sakaltani ,ina jina kamar dab baby. Zan iya yin tiyata inyi allura in bada magani in duba mara lafia,amma ba zan iya kula da kaina ba,ko daurawa kaina tied bazan ita ba balle shafar mai ko sa kaya. Ko siyen sutura nawa ban iyawa saboda Bahijja na ta bata ni,ban iya komai nawa.

   Allah ya bar mun ke Bahijja na,Allah ya miki albakrka ,Allah ya hadani da ke har a gidan aljannah"

     " Ameen my dear""

 Ta fada a lokacin da take kokari. Kwanciya a jikinshi,idon ta a lumshe ,ta ce.

   Wa zan sakalta in bata in ba mijina ba ? Kai ne first baby na,babyna na farko kafin Muhammad,kaine zuciyata, kaine rayuwata,kaine mutumin da bazan taba gajiya da masa hidima ba har iya karshen tmrayuwata. You are my world nd my happiness duk wani abu a duniya bayan Addini na to komai ya biyo bayan kai da Muhammad ,bani da kamar ku.

   Aure na da rayuwarsa gaba daya na daukeshi ibada ne,sai nayi dace da samun soyayya da kwanciyar hankali da duk wani abu da mace zata bukata a rayuwa . Na gide Mislihu ,Allah ya saka ma da gidan Aljanna. Duk wani abu da nake maka ban yi rabin wanda kake min ba ."

     Yayi murmushi ,A duk lokacin da na kalle ki da Muhammad da kuma asibitina,yadda kike taimako na ,kika fahimce ni,yadda kika yi spporting dina sai naji tamkar Allah ya biya mun dukkan wani bukata ta na rayuwa,sai fatan Allah ya hadani da ke har a Aljannah. Ina alfahari da ke Bahijja."

   Tayi murmushi ,Nima ina alfahari da kai Mislihu.."

   Nan ta ja shi zuwa dining area kamar kullum kamar yadda suka saba,ta tabbatar ya ci ya sha abinda ya kamata ,sannan ta raka shi har kofar ya fita wurin bakin sa. Sun rabu cikin soyayya da kaunar juna kamar yadda suka saba.

       Dr Mislihu ya samu bakinsa a falo Alh. Umar ne da amininsa Alh. Tahir suka zo da maganr Deeni . Nan ya nemi jin abinda ke damun sa ? Me ya faru dashi ? Dan yana son ganin medical report dinsa wanda ya tabbatar musu da sai in yaji case din irin wanda suke maganin matsalar sa ne ,to zai karbe shi. 

Alh. Tahir ya masa bayanin komai sannan suka yi alkawarin kawo miahi medical report dinsa washegari. Da wannan suka rabu akan za su hadu washe gari a cikin asibiti......... . To nan muka kawo karshen wannan kashi.....

   Sai kuma ku tara a nan gaba ,wanda zamuci gaba ranar monday in Allah ya kaimu..domin gobe sunday ranar hutu nace 😎😎😎

    

Nagode ,taku har kullum,,,

👩🏻‍🔬👩🏻‍🔬MISBAH👩🏻‍🔬👩🏻‍🔬writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
=================== GIDAN NOVELS ====================================30Bahijja mace ce abarbso ga kowa balle mijinta.  Macece da tasan hakkin mutane da basu hakkin su, tare da tsananin kulawa da nuna damuwa ga mijinta. Tasan yadda zata kula da kanta da kuma mijinta da duk wanda yake tare da ita ko yake karkashinta, don haka ma'aikatan su ke matukar jin dadin aiki da ita. 

   Komai tsananin abu ta iya mai dashi mai sauki, mace ce mai so da kuma kokarin aika gudunmawarta ga alumma, a duk lokacin da ta samu wata yar dama komai kankantar ta tana amfani da ita don tura sakonta ga al'umma a 

fili ko a boye, a zahiri ko a badini.  A duk lokacin da taso tura sakon da bata so a santa ko a san ita ce, to takan yi amfani da sunan MISBAH, wato ta hada sunanta da na mijinta, farkon sunanta da farkon sunansa. 

Shikansa Dr Muslihu bai jima da gane wacece MISBAH ba. Saboda bata fada masa ba, a fadinta tace ba tayi dan a santa ba, sai dan bukatarta ta biya, ta tura sakon da takeso turawa kuma ya isa. Wanda ladanta gun Allah takeso ba mutum ba. 

Wannan halaiyar tata shike karawa mijinta sonta,  yake gani kamar ba irinta  a duniya. Bahijja baice ta hada komai ba dan 'yar'adam take (She is not 100%) amma halayenta masu kyau da niyyarta sun maidata 100% da har ba'a kula da sauran illolin nata. 

Bahijja (MISBAH), macecemai aiki da niyya, mace mai akida da ka'ida,  mai yin abinda tace da abinda tayi niyya. Intai alkawari zata cika, in kuwa tayi magana gaskiya ce zata fito daga bakinta. Bayan aikint babu inda take samun matukar nishadi da jin dadi kamar ta tsinci kanta a gaban (computer) tana bincike ko ta fada duniyar rubutu, tana aika sakon zuciyart da iliminta da iya fahimtarta ga al'umma. 

Tana kula da bangaren mata a asibitinsu, shi kuma bangaren maza. Suna kula da damuwar juna da farin cikin juna, suna bawa juna lokaci da kula, suna tsananin farin ciki a duniyarsu. 

Lokacin da ta cika shekara goma da aure Allah ya azurtasu da haihuwar da namiji mai kama da Bahijja, yayin da ya biyo mahaifinsa ta hanyar halittarsa. Farin cikinsu ya karu,  suka yiwa Allah godiya. 

Bahijja ta rungumi danta da mijinta wanda suke sune duniyarta da farin cikinta gaba daya. 

Bahijja ta sami dukkan abinda takeso, saidai ta inda tayi rashin sa'a ta bangaren dangin mijinta, wani lokaci uwar mijinta da 'yan'uwansa zasu zo har gida su zageta suci mutuncinta gaban ma'aikatanta. Suna tunanin ta mallake Muslihu, gata tsintacciyar mage bata da asali. Ba irin cin mutuncin da basa mata, amma bata taba nunawa Muslihu ba balle ta fada masa, har ya gane da kansa, saidai bai nuna mata ba tunda ya lura bata so ya sani balle har ya nemi fad da 'yan'uwansa akanta. Dan haka yai yadda takeso, bai musu maganar ba balle su sami rashin fahimta. 


Bayan son Bahijja yana mugun ganin girmanta da darajarta, wani lokacin yakan rasa mai zai mata dan ya nuna mata jin dadinsa da farin cikinsa da soyayyarsa gareta, kome yai mata sai yaga yayi kadan, dan haka yake ronkon Allah ya bata farin ciki da kwanciyar hankali duniya da lahira. Allah ya daukakaa,  ya daukaka darajarta a duniya da lahira,  Allah ya bata Aljanna.

    A halin yanzu Bahijja na hutu tunda ta haihu ba ta koma aiki ba,saboda Mislihu ya hanata,ya ce sai ta huta nabtsawon shekara guda.

     Bata musa ba tayi yadda yake so. Sai dai fa Bahijja Bahijja ce ,bata san zaman banza ba,don hka ta bawa jikinta hutu amma kwakwalwarta kullum tana cikn rubuce - rubuce ,daga na turanci har hausa,daga na addini har na zamani.

     Wani lokaci (poem )take rubutawa daga na hausa har na turanci,wani lokaci kuma ta zauna tana koyon abinda bata iya ba matsayinta na mace,kamar girke girke ,iya kwalliya ,(dressing) da sauransu. Don Bahujja kam tana da mugun rauni a wurin, wani lokaci takan fi sati bata shafa ko (powder )a fuskarta ba ,balle jan baki da sauransu.a

       Wani lokaci Mislihu ke zama yana mata kwalliyar,har gyaran gashi. Wani lokaci yakan tsokane ta,ya ce sai ya auro wacce ta iya kwalliya da gayu.

   Ta kanyi murmushi tace,"Wa ya hana ka ? Ni duk abinda kake so ina maraba da shi." 

   Yakan jawota jikinsa ya tallafi kanta,ya ce.

   Ga abinda nake so, wannan halayyar,wannan (personality ) din ba kwalliyar fyska ba . Ina miki fata da addu'ar ki zauna a yadda kike kar ki taba canjawa. Ina son wannan Bahijja kullum kwanan duniya ina da da sonta."

   Takan rungume shi tace,"Ina sonka Mislihu na ,ka kasance dani har karshen rayuwata."

  Yakan amsa mata da,"Insha Allah ."


     Asibitin su Bahijja Alh. Umar ya yanke hukuncin kawo Deeni,saboda yadda ya buncika yaga ingancin asibitin ,da tasirin da yayi sosai a cikin al'umma ,da kyakkyawan shaidar da suka samu.

    Shi kanshi yadda ya ga tsarin asibitin da ayyukan su sai ya ji sun burge shi, har ma ya yiwa dansa Deeni sha'awar bude irinsa in Allah ya bashi lafiya.

    

   Kamar yadda sukayi alkawari,washegari Alh. Umar ya kawo wa Doctor Mislihu (report)din Deeni na duk wani asibiti da suka taba zuwa,daga gida Nigeria har na waje. A nan Doctor Mislihu ya bashi kwana uku cewa zai neme shi bayan ya karanta (report) dinsa.

       Tunda ya karbi ( report din bai samu zama ya karanta ba ,saboda ayyuka da suka masa yawa,kuma gashi kwana ukun da ya basu saura kwana daya,don haka ya yanke hukuncin dawo da su gida ta duba ,duk da baya hada lokacin iyalin da na kowa don haka baya dauko aiki ya kawo shi gida,haka itama Misbah. Wannan dama ka'ida ne a gida basu da lokacin komai sai na kansu,sai dai ko in baya gida ita takan yi wasu ayyukan ,in ta gama da ayyukan gida . Lokaci na farko kenn da Doctor Mislihu ya taho da aiki gida........Pls ayi mun hakuri na rashin posting din jiya ,,,wlh gaba daya service dina ne ya dauke ......Nsha Allah yau sai kun gaji da karatuSumy luv 😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬
Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE.

Copied by SUMAYYA SAAD❤❤31Ya dawo gida a gajiye ,Misbah tayi masa abinda ya kamata,suka yi hirarsu irinta ma'aurata masu matukar son juna.

   Can ta jiyo Muhammad yanata rigima a gurin baba Andi,hakan yasa ta fice wurinsu,lokacin Doctor Mislihu ya samu damar dauko (report ) din Deeni yana karantawa yana bin (history) na ciwon nasa da matsalar sa.

   Ya yi nisa sosai wanda har Bahijja ta shigo kusan sau ukku amma baiji shiguwarya ba,ita kanta tayi mamaki,abinda bai taba yi ba. Yawanci ma in yana da aiki yakan je (office ) dinsa ya zauna koman dare,amma baya dawowa da shi.

     Shigowar da ta sake yi na hudu ne ta samu bacci ya kwashe shi da takardun a gabansa. Murmushi tayi ganin yadda ya karya wuya kamar wani karamin yaro yana bacci.

     Bayan ta kwantar da Muhammad a gadonsa ta zo ta gyara masa kwanciya tare da lullube shi,nan kuwa ta ga ya kara gyra kwanciya ya jawota jikinsa yana fadin,,,"Na gode Bahijja,Allah ya miki albarka.

     Murmushi tayi ta kara manna shi a jikinta yadda zai ji dadin baccin ,har itama baccin ya fara daukarya. Nan ta farka ta zame jikina a hankali sannan ta tattara takarsun tare da canja kaya ta sa na bacci,har zata kwanta sai kuma wannan file din yaja hankalinta,wanne irin muhimmanci yake da shi haka yasa Doctor dawowa da shi gida ?

  Nan ta bude ta fara bi a hankali tana karantawa ,kamar wasa gaske ta tsunduma cikin karatun ,tana kokarin fahimtar case dinsa. 

    Tuni taji zuciyarya ta karaya ,ta tausaya ,duk da ba ainihin tarihinsa taji ba amma (report ) dinsa ya nuna ya kamu daa ciwon (emotional disorder)tabbas yana bukatar taimako,yana bukatar (couseling )musamman ta fuskar Addini .sannan yana bukatar a nuna masa reality gaskiyar rayuwa ta canja masa,saboda tsawon shekarun da ya dauka a cikin wannan yanayi amma ba canjj,ya rayu cikin bakin ciki,bacin rai. Wanda wannan ba karamin ciwo bane kwarai.

   Ta so tasa kanta cikin (case) din don jin me ya jawo masa wannan (emotional pains ) din ? Amma tayi shiru ta yarda da mijinta fiye da kowanne likita,fiye da ita kanta ,ta tabbatar zai taimaka masa . Nan ta tattara ta rufe ta ajiye file din gefe guda,yayin da ta kwanta da tunanin abin a ranta. 


Washe gari da safe bai fada mata ba,ita kuma bata tambayeshi ba,ta tabbatar in yana bukatar taimakobta zai fada mata.


Kamar yadda suka yi alkawari a washegari  ya nemi su ,wanda yayi dai dai da kwanakin da ya basu,anan doctor ya basu form su cike ,sannan wata takarda wadda take cike da sharudan asibitin kafin su karbi mutum,da kuma in sun karbe shi. Idan sun amince da sharudan su to su sa hannu su kawo shi,in kuma basu amince ba to kar ma su dawo.

      Tun a wurin Alh. Umar ya karanta duk da halayyar da Doctor Mislihub ya nuna musu ya yi kama da gadara,amma ba yadda ya iya sai ya bi dokar don ya lura ba maganar alfarma wa kowa a bisa dokar su da akidarsu. Bashi da zabi saboda yanada bukatar taimakonsu,ya yarda da sahihancin su da gaskiyar su,hka akwai tsaro na sosai .dole ya amince da dokar su.

    Doka mafi tsauri a cikin dokokinsu shi ne ba a dauke mara lafiya har sai in. Su suka sallame shi bayan ya warke,haka nn basu da wani sauran iko ko isa akan mara lafia da suka kawo,basu da ikon wani yanke hukunci akansa.


    Alh. Umar ya so yaja baya ,sai dai a lokacin da ya rufe ido ya tuno halin da Deeni yake ,sai yaji hankalinsa ya tashi,tsananin tausayinsa ya ratsa shi,soyayyar dansa da tausayinsa yasa shi zub da hawaye tare da dora laifin halin da dansa ya shiga akansa. Haka nan zuciyar ya amince da wannan asibitin, yana da tsammanin Deeni zai samu lafiya a wurin. Don haka wannan ya bashi karfin gwiwar sa hannu,ya yi cike - ciken da duk ya kamata tare da karbar (sliip) don biyan kudin jinyar Deeni. Sun rabu akan washegari zasu kawo shi...


Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬
Writting by SAADATU WAZIRI GOMBE 
Copied by SUMAYYA SAAD❤❤
32


 

  A hankali ya turo kofar dakin nasa tankar mai jin tsoron kofar,zuciyarsa na tsinkewa saboda tunanin wane hali zai samu dan nasa ? Tsawon sati guda kenn bai leka shi ba,saboda gudun wani hali zai same shi.

      Kamar kullum ya same shi makure a lungu guda tamkar mai jin tsoron kar azo a kama shi,fuskar sa daure tamau ba alamar fara'a tare dashi. In bai manta ba kayan da ya barshi da shi wancan satin har yanzu sune a jikinsa. Tuni idanunsa suka kada suka yi jawur.

   Deeni da na sani da tsafta da son gayu komai fes-fes ba ma jikinsa ba,dakinsa ,kayansa komai fes-fes suke,kuma cikin tsari. Amma yau rayuwa ce ta mai da Deeni haka kuma ni ne sanadi"".

    Ya yi haske amma ya fada,yayi wata irin rama mara kyau ,hasken da ya yima albarkacin zama wuri daya da take yi ne,da kuma yanayi irin na lagos. Tunda suka zo garin ko kofar gida bai fita ba ,yana nan a dakinsa da aka ware masa.

    Mama bata fasa masa addu'a ba da nema masa sauki, da mafita a wurin ubangiji.

    Deeni "" mahaifin nasa ya kira sunansa.

Juyowa ya yi suka yi ido biyu,tuni kuwa ya kara daure fuska tamau,idanunsa suka juye alamar bacin rai ya bayyana karara a fuskar sa ,ya yi saurin dauke kai.

   Mahaifin nasa ya fahimci har yanzun yana cikin fushi dashi ,ya matso dashi.

   Kayi hakuri Deeni,na maka laifi ,zan yi iya dukkan kokarina inga na  gyara kuskuren da nayi,Deeni kar ka hukuntani ta hanyar tsanantawa kanka da bata rayuwarka a banza,Deeni wanne farin ciki ka tsinta a irin wannan ratuwar da kake ? 

   Deeni nasan ba zaka so ba kuma ba zaka yarda ba,dai dai zan fada maka ina son kaika inda raguwarka zata dai daita,wanda bayan nan na maka alkawarin ba zan sake maka shisshigi a rayuwarka ba,zan baka dama kayi rayuwar ka yadda kake so kuma yadda kaga dama. Ina so ka shirya mu tafi don Allah...""

    Jin kalamansa  da yayi na karshe ne ya juyo ya kalle shi,ya ce.

    " Kai mahaifina ne ,ba sai ka rokeni ba zan maka biyayya . Ina kake so inje ? Zan je zan je amma karka taba zaton wai don kaina ne sai don kanka,kamar yadda ka dauko mana tun farko ka sabar mana ,bamu da zabi sai naka,to yanzu ma haka ne. Saboda ni kan yanzu a rayuwa ba abinda ya saura zaka min ,baka da abinda zaka iya sake min ko bani ya sani farin ciki,ba abinda zaka min ya goge min bakin cikin da bacin ran da ke cikin kwakwalwats da zuciyata .

   Wanann abinda kuka hadu kuka mun va zai taba barina naji wani dadi ba a ratuwata ba,ba yadda za'ayi in samu wani farin ciki ko kankani bayan cin amana da rashin kauna da kuntata mini da yaudarar da iyayena da dan uwana da wacce... .........

Maganar ta sarke ,numfashinsa ya dinga fita sama sama,vai ankara ba sai ganinsa yayi ya fadi ya suma . Cikin tashin hankali da damuwa sukayi asibiti da shi,asibitin da bai shiga yana cikun hankalinsa ba sai a sume.

    Dokar farko ta fara aiki akan su,wato su ajiye shi su tafi su barshi ,kuma ba zasu sake waiwayar sa ba sai bayan wata shida wanda in ya samu wannan wata shidan zasu iya zuwa bayan wata daddaya.

   Haka haji. A'i da Alh. Umar suka tafi suka bar dansu cikin mawuyacin hali da ciwk ,mama tayi kuka har ta gode Allah ,yayin da Alh. Umar bai yi ba,sai dai abinda yake ji a zuciyar sa yafi kuka ciwo.     Doctor Mislihu ne tsaye kan Deeni tare da sauran likitoci da ke aiki a karkashinsa,da sauran ma'aikatan asibitin suna iya dukkan kokarinsu don ganin ya farfado.sai dai fa abin ya ci tura,va irin dabarar da basuyi ba hakan yasa ya nemi taimakon gaggawa dafa sauran 'yan uwansa wadanda suke manyansa ne ta hanyar wayar sadarwa.

    Tabbas duk kokarin ka da kwarewar ka wataran sai aikinka ya kunyata ka,kwarewa da dai dai sai Allah,Dr. Mislihu bai kasa va kuma bai yi kasa a gwiwa ba ya ci gaba da ba da himmar sa da kokarin sa,bai ji dar ko tsoro ba,sai dai abin ya matukar daure masa kai,saboda shi yasan ya sha fuskantar masu ciwo irin na Deeni.

     Da taimakon Allah yana addu'a tare da yakini a zuciyar sa ya samu deeni ya farfado da wani bakon yanayi,yana cikin tsananin ciwo da rudani,idanunsa sunyi jawur ,hawaye kawai ke zubaa ba kakkautawa,haka nan ya rike kansa gam alamar yana jin azabar ciwo,abin har ya kaishi ga yana doka kansa jikin karfen gadon da yake kwance.

   An masa allurar da ya kamata ayi masa ya samu nutsuwa kadan,da kyar suma samu bacci ya dauke shi. Baccin da yakamata yayi na wuni guda kafin ya farka,amma awa biyu zuwa uku kawai allurar take masa aiki ,haka magani ba ya aiki a jikinsa.


A wannan dare Doctor Mislihu ya koma a gajiye tare da wannan damuwar a tare da shi. Bahijja na ganin sa tasan ba lafiya ba,ta riga da tasan yanayin aikin nasu ,akwai gajiyarwa ,sabida jikinka da kwakwalwarka da zuciyar ka duk sai sun jigata,sun wahala.

  Ta shirya masa ruwa yayi wanka,bayan ya fito tayi kokarin sauke masa gaijyar sa da (tension ) dinsa ta hanyar masa matsa a gabban jikinsa da kansa,tana (massaging )cikin nutsuwa yadda zaiji dadinsa,kuma ya yi masa aiki.

           Yaji dadin hakan kwarai,ya jawo hannu ta.

   Na gode Bahijja ,naji dadi sosai, naji dadin wannan abinda kike min don ya bani nutsuwa tare da sauke min wani (tension)din . Tayi murmushi tare da shafa shi,ta ce ." Burina kenan inga na rage maka damuwa,naga yau kana cikin zafi ,bari in kawo maka abincinka daki.

Nan ta fita ta dawo hannunta dauke da babban (tray ) ta shirya masa duk wani abinda zai bukata. (Coffe) mai zafi ta fara bashi sannan ta zuba masa abincin wanda kadan ya ci shima don ta matsa masa ne,kafin ma ta ce wani abu aka masa waya ya nufi asibitin a rude..

   Wannan al'amarin ya daurewa Bahijja kai,"" To shin meke faruwa ne ?

 Nan ta buga waya asibitin don jin meke faruwa? A nan aka bata labarin sabon mara lafiya da aka kawo wanda ya ta da hankalin oga.

 Haka ta dunga kawai da kawowa har ya dawo ,ta tare shi da tambayoyi amma bai amsa mata ba ya nuna ta kyale shi akwai binciken da zai yi ,in ya gama zai sanar da ita.

    Wannan abu ya daure mata kai ,sam bata jin dadin ganinsa haka. Ya dawo kullum yana cikin karatu da bincike saboda matsalar Deeni ta zame masa sabo,ya zama kamar (challenge) ne a tare dashi..

      Abokinsa Doctor yasir ya nemo wanda suka yi karatu tare ,kuma sunyi aiki tare a dashi lokacin da suke ( teaching hospital) wanda shi bayan bude asibitin su ne suka rabu. Sai dai dama lokaci lokaci sukan hada kai suyi karatu.

     Dr. Yasir kamar aboki ne a gare shi,kuma abokin aikinsa,don haka ya roki alfarmar ya zo su binciki case din deeni tare.

      Da farko ya so yasa Bahijja ciki,sai dai baya sob wahalar da ita,sannan tana cikin hutu ne,gara ta zauna ta bawa muhammad kyakkaywar kulawar da yake bukata. Kuna yasan Bahijja sarai da daukan zafi,tana iya watsar da komai ta tsunduma kanta ciki,don haka ya yanke shawarar ya yi aikinsa da kansa.


    Wata guda suna bawa Deeni(treatment) amma ba wani cigaba ,babbar damuwar sa yana cikin ciwo balle har a samu nutsuwar da za a sai ta hankalinsa da tunaninsa,balle har a san matsayin da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ciki. wannan abu ya mummunan daga hankalin Doctor Mislihu da sa shi cikin damuwa,duk maganin da ya bashi baya aiki dai dai a jikinsa yadda ya kamata yayi. 

   Gaba daya y rasa nutuwa da kwanciyar hankali,kullum bashi nan bashi can neman yadda za a samu waraka ,haka ya dauki (case)din deeni da zafi tamkar na wani dan uwansa na jini,ya ci alwashin sai inda karfinsa ya kare.

 Ya dawo ba ya bawa kowanne mara lafiya kulawa kamar yadda yake bawa Deeni,tausayin sa da kaunar sa ya shiga ransa,musamman in yaga yadda wataran Deeni ke zura masa ido yana kallon sa tamtar mai kokarin fada masa wani abu,tamkar yana ce masa ka ""ka taimake ni,"" tamkar dukkan tsammaninsa na kansa. Haka wani lokaci hawaye zai yi ta zuba masa,lokaci guda kuma ya kuma rikecewa.

     

   Abin na Deeni gaba-gaba yake,don haka Doctor yasir ya bashi wata shawara akan abinda zasu masa,amma fa sam ya ki yarda ,yaki amincewa ,saboda yana ga akwai garaje ciki,sannan ciwon Deeni bai kao har hakan ba. Amma a hankali Doctor yasir ya dinga nuna masa dukkan wani (treatment) da zasu mada sun masa,amma baya (respondng) wannan shi ne option da ya rage dashi.

   Ya tuna ya yiwa kansa alkawarin yin duk abinda zai yi don ya taimaki shi ,haka iyayen yaron na da dukkan wani tsammaninsu akan shi. Da kyar Dr. Yasir ya shawo kansa ya amince...........Barkanku da rana jama'a

Sai ayi wa deeni addu'a za'a yi masa theatre Allah yasa a dace  😭😭

Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬
Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by. SUMAYYA SA'AD❤❤
33 Nan ya hau shirye-shirye ,yasa lokaci da rana,ya gama amimcews kansa amma duk da hakan sai yaji zuciyarsa na fada masa ya nemi shawarar matarsa,ya sanar da ita,ko ba komai rana da ilimi akan cuwon Deeni sosai kamar yadda yake da shi. Da wannan tunanin ya dauki waya ya bugawa Bahijja.

     "Bahijja"

   "Yes my dear,kana hanya ne na jira ka shuru,hope dai lafia."

  Ya yi mata murmushi tamkar tana kallinsa,ya ce 

   "Lafiya Bahijja ,wani aiki ne yasha kaina da na gama zan taho. Dama ra'ayinki nake son ji akan wani abu da zan yiwa patient dina."

 Tayi masa daria tace ,"Zan yi farin ciki da baka shawara mai kyau ,na lura kana cikin damuwa akan wannan mara lafiyar ,kar ka damu nasan ko me zaka yi ( you re the best on it).

 Yace,"Duk da haka dai ina neman kwarin gwiwar a wurin ki."

  Ta ce,"To ina jinka,mene ne matsalar ka?

   A hankali ya labarta mata case din Deeni da yadda yayi ta fama da shi.

   Ta dan yi dogon shuru tana tunanin ai indai wanda ta karanta file dinsa ne case dinsa ba haka bane,abinda reporrt dinsa ya ce daban abinds kuma Doctor ya fada mata yanzu da irin treatment din da suke masa daban .

    "Bahijja " 

  Muryarsa ta katse mata tunani.

   Kina jina kuwa?

  " Eh ina ji"

  Ta fada cikin muryar damuwa,sannan ta ce.

  To yanzu wane shawara ka yanke? Me kake ganin zaka masa?

   "Shawarar da muka yanke yanzu ni da Doctor Yasir shine,zamu masa (E.C.T)

      ""WHAT!!!!!!!!

 Ta fada da karfi cikin zare ido tamkar yana ganinta,hankalinta ya tashi.

   Ta ce please Doctor kar kuyi masa,kasan dangers na wannan therapy din" 

 "Bai kai stage din da za a masa haka ba.

    " Da hankalinka,da tunaninka?

  "Me kike nufi? Kina so kice bani da hankali ko ban san me nake yi ba ? Laifina ne ba naki ba da na fada miki ,dama na lura komai ke kina son nuna kin fi kowa sani."

   Tayi kasa da murya ,Kayi hakuri my dear ba haka nake nufi ba,nasan kai fini ,kasan komai ,amma ina so ka fahimci danger din dake cikinsa ne,kar muyi wasa ko garaje da rayuwar wasu. Ka tuna amana da yarda yasa iyaye da 'yan uwa ke kawo mana marasa lafiya,kasan yadda (electro convulsive therapy )yake,idan ya yi (seizing ) kwakwalwar sa gaba daya fa?

  A tunanina baya bukatar wannan,ina gain (right medication) da (couseling ) ya ishe shi ya dawo dai dai ,wato maganin da ya dace.

   Maganganunta yasa shi kasala ,ya ce.

   Na bugo ne ki bani kwarin gwiwa ba kisa na karaya ba,ni kike yiwa maganar (right medication)?Don baki ganshi a gabanki bane da irin kokarin da nayi akansa da ba zaki fara fada min haka ba. "

 Doctor duty na ne in tsaida ka,please na rokeka kar kayi,ka sake tunani.

   Kashe wayar yayi ya kyaleta cikin rudani tana ta buga wayar tana ihun kar yayi amma bai dauki wayar ba ma. Hankalinta ya matukar tashi,ba shiri ta dauki hijab ta nufi cikin asibitin da sauri.

   Sai dai kafin ta zo Doctor yasir yayi nasara akansa na cewa.

    Kasan halin mata da tsoro ,da gajeriyar kwakwalwa ."

   Ya amince amma maganar Bahijja da dalilan da ta bashi na yawo akansa,don kuwa yasan matarsa Bahijja bata cikin mata masu tsoto ko gajeriyar kwakwalwa amma da yake ya riga da ya yanke hukuncin sai ya yi din . Don haka kafin Bahijja ma ta iso dun riga da sun yiwa Deeni abinda suka yi niyya.

   Yana kwance a wurin kamar gawa,dukkan gabobin jikinsa sun amsa,duk jikinsa ya sassake ,bawan Allah shi kadai yasan wahalar da yasha. Gashi jikin Deeni jiki ne da bai saba da wahala ba,bai ma santa ba gaba daya don haka abin ya fi wahalar dashi fiye da yadda ya kamata. Tuni ya manta kansa da duniyar da yake ciki.

     A lokacin da Doctor Bahijja ta shigo zama tayi ta kama kai tana kuka .

   Doctor me yasa kayi haka ? WHY!!!!!!

  Tuni ya harzuka ,"Me kike nufi da (why)? Ban san me nake yi bane ? Me kike so kiyi (proving) da kika shigo kina min tsawa gaban abokan aikina da ma'aikatana ? Me kike ji da shi ? Wa ya baki izinin fitowa ki zo ?

     " Doctor (please )."

  Ta fada cikin kwantar da kai .

  ( This is not you)wannan ba kai bane,ba haka na sanka ba ,kai mutum ne me taka tsan tsan da rayuwan alumma. Wannan ciwon nasa da ya zamo maka sabo ba firgita ka ya kamata yayi ba,ko kuma wani abin cews sai naga ya warke ko ta halin kaka kar a ce na gaza .

   Ka tuna asalin purpose dinmu shi ne mu taimaki mutane ba mu wahalar da su ba ,ba muyi wasa da rayukansu ba. Yaushe tunaninka ya kauce,ya canja ? Yau ina cikin bakin ciki da na kasa tsai da ka,na kasa hana ka yin abinda ba dai dai ba,sai addu'ar Allah ya tashi kafadar wannan bawan Allah.

 Bai kulata ba sai sa kai da yayi ya fita cikin bacin rai,yayin da sauran suka rufa masa baya.............

Shin wai wani irin aiki doctor mislihu yayiwa deeni ,,wanda har ya sa shi hatsaniya da matarshi...  🤔🤔

Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬
Writting by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤Bismillahirrahmanurrahim

    RABBANAGFIRLI WAL-WALIDAYYA WALIL MU'UMININA YAUMA YAKUMUL HISAB............AMEEN YA ALLAH.😭😭Allah yasa mu dace duniya da laira..34


 Ta mai da hankalinta kan Deeni ,taje tayi dukkan iya kokarinta domin ta samu ya dawo hayyacinsa,ya farfado kafin ya yi nisa. Sai data dauki tsawon awa uku akansa kafin ta samu ya bude ido sannan ya sake rufewa,numfashinsa ya daidaita. Sannan ta dan samu kwanciyar hankali da nutsuwa kadan,ta koma gida hankalinta a tashe ,tayi ta fama da Doctor Mislihu .

   

   Fada yake mata ta inda ya shiga bata nan yake fita ba,ta lura yana cikin tsoro da tashin hankali ,sai dai yana kaucewa hakan da fada.

   Bata ce masa kala ba sai rungumar sa da tayi sosai a jikinta,ta riga da ta fahimci (fears) dinsa da tashin hankalin daya shiga. 

      Kwantar da hankalinka ,insha Allah komai zai dai dai ta ,baa abinda zai faru (he will be fine) . Kuskure  be kowa yana yi a rayuwa ,sai dai muyi kokarin kare faruwar haka a gaba. Bamu da damar yin wasa da rayuwa wasu.

   "Bahijja ban san me ke faruwa ba,na kasa gane komai. Nasan cewa duk wani (treatment) da nake masa  dai dai ne ,sai dai ban san me yasa ba ya (responding) ba,kuma ban yi niyyar wasa da rayuwar sa ba har zuci,ina son taikamakon sa ne. Ina ganun wahalar da yake sha,ina jinsa kamar dan uwana,sannan inason raikamakon mahaifinsa shi yasa duk abinda zanyi ya kare na dauki wannan (option )din. Ban yi tunanun komai ba ,sai dai nasan wanann a cikin (shock treatment ) wannan (is the most safest and effective).

     Na sani my dear ,amma wannan ciwon sa(disorder) din da yake da shi ba na wannan treatment din ba ne. A ganina kun yiwa abin gaggawa ,kuma naga kamar baku yi shi dai dai ba,dole akwai wani kuskure a wani wurin ( something wrong somewhere ). Wa ya baka wannan ( idear ).?

     " Doctor yasir ;;" ya fada kai tsaye .

   Ta dafe kai cikin takaici ,ta ce. Haba doctor !!

    " Har yaushe ka fara amfani da basirar wasu maimakon taka?

   Kin san mutumin nan likita ne dan uwana ,meye a ciki in munyi (studying case ) na mara lafiya,munyi (sharing idea)?

    " Baa laifi bane,amma abin akwai daure kai"

  A wanann dare daga Dr. Mislihu har dr. Bahijja ba wanda ya runtsa ,suna tunani tare da juya al'amarin a cikin ransu wanda Dr. Muslihu ya kasa jurewa gari ya waye,a daren ya fita domin zuwa ya sake ganin Deeni.


     Ga mamakin sa yana kofar shiga dakin yaji muryar Doctor yasir da wasu ma'aikatansa guda hudu wanda amintattun ma'aikaransa ne,yaji dr. Yasir yana raba musu kudi na aikin da suka masa. Ba farko sunyi ta canja duk wani magani da allurai da ya ce su kawo a dinga bawa Deeni. Wanda wannan yasa jikin Deeni ya kara rikicewa maimakon samun sauki. Saboda yana so ya batawa dr. Misilhu suna don ya jima yana jin haushin cigaban da ya samu ya barshi. Abu na biyu shi ya so Alh. Umar ya damkawa Deeni a asibitin su saboda ya ci kudinsa sosai ,amma sai Alh. Umar ya ci mutuncinsa ya ki. Tun daga lokacin ya dau lwashin sai ya dau fansa,kuma ya batawa doctor mislihu suna. Don haka ya bawa ma'aikatansa cin hanci.

    

  Da farko kun ki,amma ganin yawan kudin da ya saye imaninsu suka manta amana da yarda dake tsakaninsu da mai asibitin. Ya ce kuma in aiki ya yi zai kara musu .


    Lokacin da Dr. Mislihu ya gama jin abinda suke fadi ya ciro wayar sa ya kira (police) sannan ya kira Bahijja yana fada mata. 

  "Doctor yasir ya ci amanata ,Bahijja gaskiyarki ne,akwai abinda ua faru wanda ban fahimata ba sai yanzu".

Yana cikin magana da ita ya jiyo motsin su zasu tafi,ya yi saitin banki kofar ,bai bata lokaci ba ya cakuno wuyan rigarsa tare da shakar masa wuya yana zaginsa.

    "Yau sai na kashe ka ,maci amana. Ku kuma sai nasa an kulle ku,kun ci amanar yarda,kunyi wasa da rayuwar wani sabida abin duniya."

   Ganin yadda ya haukace musu Dr. Yasir ya ce.  

    Yaa zama dole muyi maganinsa kafin ya fallasa mu"

   Tuni suka hadu akansa,hayaniyar su ya ta da Deeni ,ya yin da yakr ganunsu hazo-hazo ,duk da baya magana da Dr.mislihu ya saba da shi da dawainiyar da yake masa. Sannan da ikon Allah da taimakon da misbah tayi masa ya masa amfani ,ya dawo hayyacinsa.

  Gani yadda suka toshe bakin dr. Mislihu suna dukansa tare da kokarin toshe masa hanci yasa ya mike ya nufi inda wani bell yake wanda alama ne na danger in an danna,ya yi sauri domin dannawa ,anan daya ya hango shi,ya yi kansa suna ta kokawa,yayin da dr. Yasir ya dauko wani almakashi ya soma cakawa Dr. Mislihu tuni jini ta wanke wurin . Yana kokarin guduwa ya ceci kansa ko ta halin kaka,yasan in Dr .mislihu ya kubuta to asirinsu zai tonu.

   Deeni bai san yaushe ya bude baki a firgice yana ihu bmtare da neman taimako ba,yana fadin .

   "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!

   Nan sukayo saurin toshe masa baki da hanci har sukaga ya dai na nunfashi. Za su fita kenan sai ga 'yan sanda sun iso,kafin su gudu kuwa aka cafke su,yayin da akayi kokarin daukan doctor mislihu zuwa emergency tare da deeni......


    Lokacin Bahijja ta iso a rude tamkar mahaukaciya ,ganin mislihu cikin jini ya bala'in firgita ta da razanata. Tashin hankali ne wanda bata taba fuskantar irinsa ba,duk kuwa karfin hali da karfib zuciya irin nata a wannan rana sai da ta karaya ,hankalinta ya nemi barin jikinta.

  Tayi kan dr. Mislihu jikinta na bari,ta rasa ma me zata mishi? Ta rude sai kiran sunansa take tana salati.

    Tare akayi wani asibiti da su da wasu yan sanda dob basu taimakon gaggawa ,likitoci sunyi kokarin tsai da jinin dake zuba a jikinsa wanda a wuyansa suka caka masa da gefen ciki amma jinin bai tsaya ba,haka aka dinga masa kari wani ni fita wani na shiga. Suna iya dukkan kokarinsu akanshi.

   Bahijja dai alwala tayi ta zo ta fara sallah,daga karshe ta hau addu'a saboda ta rasa nutsuwar yin sallar.

    Wani likita ne ya zo ya kirata mijinta ya ce yana son ganinta. Jiki a sanyaye ta isa dakin tana kuka kamar ranta zai fita,ya kalleta cikin galabaita da kyar ya iya bude baki.

  Kar kiyi kuka Bahijja ,ko yanzu ko bayan raina ,kituna yanzu nauyin asibiti da sauran al'umma da ke cikinsa na kanki,ki tuna mafarkin mu ne da burin mu wannan asibitin. Sai dai ki kula kar abinda ya faru dani ya faru da ke,mutum yana nan yana rayur sa bai damu da wani ba ashe makiya suna nan sun sa masa ido suna neman yadda za su cutar da shi.

  K tuna nauyin asibiti da Muhammad na kanki,sannan in bani da rabon haduwa da mama in ta zo kun hadu kice ta yafe mun ""

      Bahijja dai kuka take kamar zata hallaka ,ga tsoro da fargabar rasa mijinta ,ga maganar sa mai kama da bankwana,ga azabar ciwon da ta ganshi a ciki.

  " Dole ne in maka kuka my dear,dole kuma in yiwa kaina kuka . Mutanen nan sun cuce mu,sun rusa mana 'yar karamar duniyar mu da muke farin ciki a cikinta .."

    " Sun cuci kansu dai Bahijja ,ki tuna kece me lallashin wasu da ( couseling ) dinsu in sun shiga hali makamancin wannan ,yau rana tazo da zaki yiwa kanki wanann tatan.

   Bahijja kada ki karaya kima fi yadda na sanki da,kiyi addu'a Allah na tare da ke ,kada ki taba jin ke kadai ce a duniya. Ki tuna duniya taki ce da mutanen arzikin da suke cikinta ,duk wani Musulmi dan uwanki ne .

    Abu na karshe Bahijja,wannan. Bawan Allah da ya shiga rudanin rashin lafia da karin ruda masa jiki da kwakwalwa da ya samu ta sanadina ,ina fata zaki taimaka masa ya warke da iyakar iyawarki . Ina fata zaki gyara kuskuren da nayi."

      Tayi karfin halin share hawayen da ke zuba mata tare da yi masa murmushi , tace,,

In sha Allah my dear zan taimaka masa har kaima ka samu lafiya mu taimaka masa tare,mu cigaba da kula da asibitin mu da Muhammad,a duniyarmu zamu sake ginata tare da kai insha Allah." 

    Duk da yana cikin ciwo sai da yayi mata murmushi alamar gamsuwa da maganarta. Nan ta kwantar da kai a gefen pillown dake jike da jini,tana rike da hannunsa,ita kadai tasan irin radadin da zuciyarta ke mata ,tana masa addu'ar fatan samun sauki da lafiya.hawaye na gudu a idonta ba kakkautawa,tana tunanin duniyarta ta zo karshe a duk lokacin da ta rasa doctor Mislihu .

  ** Ya Allah nasan baka barin wani don wani,ya Allah ka bani karfin imani da karfin zuciyar daukan duk wani ikon ka da aiwatar akan mu"

   Da irin wadannan addu'o'in a zuciyarta bacci ya debe ta bata sani ba ................Hmmmmmmm.

Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE 


Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤Please kuyi hakuri na rashin jina jiya ,,bikn aminiyata ake shiyasa na mnta daku😎😎😎
35


 Da irin wadannan addu'o'in Bahijja a zuciyarta bacci ya debe ta bata sani ba,sai farkawa tayi taji hayaniya akanta. Sauran likitocin asibitin ne suke bata hakuri mijinta kam ta Allah ta kasance akansa,ya bar duniya. 

   Jin abin ta dinga yi ba zata,kamar mafarki. Wani jiri taji yana dibanta tana salati tana kallonsa tamkar mai bacci.

   Wayyo duniya,duk wanda ya dauke ki da zafi tabbas yana cikin masu asara. Jiya tana yare da mijinta ,abokin rayuwarta,gatanta a duk duniya ,amma yau baya duniyar.

   Hawaye na zuba ta ce,Allah ya jikanka Doctor ,Allah ya maka rahma,ya yafe maka kurakuranka,yasa ayyukanka na alkhairi su bika" .

    Bahijja tayi kuka tayi kuka har taji ba dadi. Kafin a yiwa Doctor wanka da sutura 'yan uwansa suka iso daga kano ,mahaifiyarsa da danginta tare da dangin mahaifin sa tare dasu akai masa sutura aka kaishi gidansa na gaskiya,yayin da mahaifiyarsa ta yafe masa tare da binsa da addu'a.


Gidan Bahijja suka dawo aka yi ta karbar gaisuwa ,yayin da maganar rasuwar ta baza ko ina,saboda Doctor mislihu yaui suna kwarai ,haka yana da jama'a . Ya yi suna ba don yana kudi ba sai dan kwarewarsa ta wurin aikinsa da sunan da yayi saboda asibitin su.


 Kwana uku aka yi ana karbar gaisuwa ,mahaifiyar sa tace su za su tattara su koma kano,don ita har yanzu ba wai tana son Bahijja ba ne ,asali ma ta dauka nauyin mutuwar danta akanta saboda ta ce ita ta sa shi zama a lagos yaki komawa can gida kano,ya guje su. Tunda tayi sanadin sa to zasu kwace danshi su tafi da shi ta dinga ganin jikanta. Kuma ta ce ko da wasa Bahijja kar tayi tunanin cewa zata zo ko da ganinsa balle daukar sa.

  Anan fa ciwon yayiwa Bahijja bibbiyu,hankalinta ya mummunan tashi. Ta yaya za a rabata da Muhammad da bai fi wata takwas a duniya ba ??


Ba irin rokon da bata yi musu ba har ta musu alkawarin kawo shi idan ta yaye shi,amma fur mahaifiyar mislihu ta ki. Haka ta tattara shi suka koma kano yana kuka Bahijja na kuka suka rabu.


    ****        ****       *****


A wannan lokaci Bahijja tayi dan karamin hauka ,ko dai ta dinga jin muryar Doctor ,ko kukan Muhammad. Zuciyarta tayi rauni sosai,kullum tana cikin kuka,bata iya kulla komai. Daga karshe ita ke tashi ta share hawayenta,tayi karfin halin lallashin kanta.

    Ta so ta bi iyayen Mislihu kano ,sai dai kuma ta tsai da kanta,ko me za su mata ba zata taba fada da su ko shari'a dasu ba albarkacin dansu da take so take ganin girma da darajarsa fiye da kowane namiji a duniya. Don haka ta sawa kanta hakuri,kamar yadda ta jure rashin mijinta shima dan nata zata jure rashin sa,in da rabon haduwarsu kuma da rai da lafiya to Allah zai hada su wata rana.


Haka Bahijja ta hau takaba ,kullum kwana take tana zubar da hawaye tana yiwa mijitan da danta addu'a tare da fatan Allah ya kara mata hakuri da juriya. 

   Daga ita se Baba Andi a gidan wacce take mata rainon Muhammad,kasancewar kyautatawa da take mata ta dauketa kamar uwarta,yasa itama ta zauna tare da ita tana mata hidima tare da bata shawarwari da bata baki da lallashi. Tana matukar tausaya mata.


   Bahijja ta kasance bata  da kawa ko wata 'yar uwa ko wata da suke da kussanci na sosai,saboda a RAYUWAR BAHIJJA ba (space) na kawaye ,wato ba fili ko lokacin yin kawance a rayiwarta,saboda ayyukanta da rabuce-rubucenta. Mijinta da danta sune kawayenta,sune rayuwarta.

Don haka yanzu rayuwa tayi mata wahalar gaske wanda daga rubutun har aikin sai da suka gagareta,damuwa da yawan tunani suka sako ta a gaba,ta rasa inda zata sa ranta taji dadi . Tuni ta kma ga Allah ,kullum tana cikin karatun Alkur'ani da addu'o'i tare da yawan istigfari don neman waraka daga halin da ta shiga..


   Wani lokacin takan rufe ido ta dinga tuno da kalaman Doctor wanda suke kara mata karfin gwiwa ,taji tana son mikewa tayi wani abu me amfani da rayuwarta bayan kuka da bacin rai.

 Da haka a cikin wannan halin da yanayin ta gama takabar,sai dai duk da hakan ba tayi yunkurin fita fara wani aiki ba....

Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤

36 


Bayan rasuwar Mislihu Alh. Umay ya samu labari don haka ya zo ya dauki Deeni bayan ya farfado ya samu sauki na jiki amma fa kwakwalwarsa tamkar ya farka da sabon abu ,kullum yana cikin firgita da yin wasu abubuwa tamkar yana tsorace.

    Haka mahaifinsa yasa ana yi masa addua su ma suna masa ,har ya dan samu sauki,amma kam har yanzu da matsala . Yayin da kotu ta yankewa Dr. Yasir da sauran ma'aikatan asibitin hukuncin daurin rai da rai. Allah ka tsare mu da son zuciya..     Asibitin ya tsaya na dan wani lokaci saboda abunda ya faru da gidan da asibitin duk sun shia gado ,sai dai dama asibitin nasu ne su biyu da shi,sannan itama tana da gadonsa. A takaice dai wurin ya dawo nata da danta Muhammad ,wanda tayi alkawarin kula masa da shi ta damka masa kayansa wataran in tana da rai. Don haka ta shirya komai a rubuce saboda mutuwa ta kuma nemi lawyer na musulunci da Alkali suka zama shaida.


   Watanni shida da rasuwar Doctor Mislihu bayan gama takabarta ta hau shirye-shiryen yadda zata farfado da asibitin yafara aiki,ya dawo kamar da,a niyyarta ma har yafida,saboda tsaro da tantance ma'aikata sai yafi nada.

   Bahijja kenan mace mai kamar maza,haka ta dage tana ta shige da fita ba zama ,tana neman taimako da yadda zaayi komai ya farfado ,wanda gudun tunani da bacin rai yasa ta dage da zama(busy) yau bata nan gobe bata can har sai da ta tabbatar komai ya dai daita mata kamar yadda takeso ,komai ya farfado ya soma aiki,sannan ta samu nutsuwa kadan.


A kullum ta zauna maganar Deeni ke fado mata,da sakon da amanar taimakonsa da mijinta ya damka mata.

   "Ya zama dole in nemo shi inji ya ya kare ? Sannan in sake duba (case) dinsa inga wane irin (treatment) ya kamata a masa."

   Bata bata lokaci ba ta fara binciken file din Deeni wanda ta riga da dama tasan wannan case din,sai kari akan (wrong treatment ) din da aka yi ta masa.

    Nan ta bincika address dinsa,sannan ta sake zuwa asibitin da aka kwantar dashi tare da Doctor ta sake bincike akan treatment dinsa ,sannan ta sake tabbatar da address dinsa. Daga nan ta daura damarar niyyar taimakon sa har sai inda karfinta ya kare,in ta tabbatar ya samu lafia zata samu kwanciyar hankali ,burinta da na mijinta ya cika,daga nan zata ci gaba da cika burin mijinta da nata har ta Allah ta kasan ce akanta,idan kuwa Muhammad ya girmata damka masa dukiyarsa,ta ci gaba da masa addu'a da shi da mahaifinsa. Wannan shi ne burin Doctor Bahijja da kuma kudurinta ,bayan shi ba komai a zuciyarta da tuaninta ,daga aikinta sai rubuce rubucenta.....    Hmmmmm ,,Doctor MISBAH KENAN Please kuyi hakuri aiki ne yamun yawa 🙏🏼🙏🏼🙏🏼
SUMY LUV 😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by.  SA'ADATU WAZIRI GOMBE


Copied by. SUMAYYA SA'AD❤❤ 37Haj. A'i na zaune a falo ita daya tayi nisa sosai a tunani,tana tuna yadda rayuwarsu take da da ta yanzu,lokaci guda rayuwarsu ta canja ,sun baro yankin su cikin 'yan uwa da abokan arziki,inda suka saba da rayuwarsu da komai ,sunyi nesa da dansu da 'yan jikokinta guda biyu da duk da suna zuwa lokaci-lokaci,ga rayuwar Deeni ta canja gaba daya . Duk kokarin da suke yi akan Deeni ba wani canji,yadda Deeni yake rayuwa yana matukar kona mata rai. Lukman ne take dan gani taji dama- dama,shima tunda ya kammmala katarunsa na jami'a kullum yana tare da mahaifinsa wurin harkar kasuwancin sa,rayuwar su na cike da kewa da wani walwala.

     Mai musu aiki ce ta katse mata tunanin,'"Hajiya kna da bakuwa".

  ""Wacece haka ? Daga ina take ?

  Gata nan ." Ta bata amsa,sannan ta juya.

  Bahijja tayi sallama tare da karasowa cikin falon, Hajiya ta amsa tana mata maraba tare da mta kallon rashin sani.

Bayan sun gaisa Bahijja ta kalleta,ta ce.

"Nasan zaki yi mamakin ganina,saboda baki sanni ba. Sunana Doctor Bahijja ,ni likita ce a asibitin da aka kai Deeni kwanakin baya,asibitin doctor Mislihu . Ni matarsa ce da muke aiki tare ,bayan rasuwarsa ni na ci gaba da kula da asibitin.

   Kafin ya rasu burinsa ne ya ga ya taimaki Deeni,sai dai burin nasa bai kai ga cika ba ta Allah ta kasance akan sa. Ina fatan cika masa wannan burin don haka nake son taimakon Deeni da dukkan kokarina har dai naga ya samu lafiya.

   Bama bukatar taimakon ki""""".

  Sukaji muryar Alh. Kamar daga sama .

 Dukkansu suka mai da kallon su kan Alhaji,ya ci gaba da fada.

   "Yau ce rana ta karshe da zaki sake tako gidan nan ,kowa yasan irin yadda ku ka kara dagula rayuwar Deeni,ku ka yi wasa da lafiyar sa. Ku godewa Allah da banyi kararku ba.

  Cikin sadda kai da girmamawa Bahijja ta ce.

   "Alhaji dukkan mu ba wanda yaso abinda ya faru,kuma bamu yi haka da ganganba sai don wata kaddara da ta fada mana. Burin mu ne daga ni har marigayi maigidana mu ga muna taimakon mutane,haka taimakon danka yana daya daga cikin burin,don haka nake me rokon ka da ka kara bamu dama ,insha Allah zamu yi kokarin mu akan danka ya samu lafiya.

   Alhaji dai ya dage Bahijja ma ta dage da kyar da kyar ta sha kansa ya yarda ,sai dai ta dinga zuwa duba shi har gida . Bata musa masa ba saboda tana son taimaka masa,don tasan an musu laifi ,sannan zata karasa abinda mijinta ya fara kamar yadda ya UMARCE ta.

Hajiya ce tayi mata jagora har zuwa bangaren Deeni,ta nuna mata kofar dakinsa. Nan ta cewa  hajiya ta koma ita zata shiga. Hajiya bata musa mata ba ta juya,ita dai addu'ar ta Allah ya bawa danta lafiya.

    Tura kofar dakin tayi wanda yake mamaye da duhu,duk da rana ce amma ya rife ko ina kif. Yanayin garin kuma dama inba a kunna wuta ko bude windo ba babu ta inda haske zai shigo. Hakan yasa ta kara bude kofar don taga haske,nan ma ta hango window din dakin.

    Kai tsaye ta nufi window din ta sa hannu ta zuge labulen tare da bude (windows) din daki duka ,tuni haske da wani irin iska mai sanyi ya dinga ratso dakin,nan ta maida kallonta gare shi ,yana zaune tsakiyar gado kamar kullum ya hade kai da gwiwa yana kife wuri daya.

   Cikin nutsuwa ta matso gare shi ta tsaya tana kallon sa tare da nazarin halin da yake ciki . Kamshin turarenta tare da iska mai sanyi ne suka soma ziyartar sa,wannan ya dawo da shi daga wata duniya da ya fada.


     Assalamu Alaikum Nuraddeen ". Ta fada cikin sassanyar murya.

    Jin murya da bakon yanayi yasa shi dago kai suka hada ido,tayi masa murmushi ,shi dai kallonta yake. 

     Ta sake kiran sunansa,"Nuraddeen ,na maka sallama baka amsa ba,kasan kuwa shaidanun mutane ne kawai ba sa amsa sallama ? Kai kuma nasan ba ka daya daga cikin su,kai salihi ne,bawan Allah(you re a gentleman) nasan nan gaba in na shigo zaka amsa sallamata. Ni sunana Doctor Bahijja,amma zaka iya kirana da Bahijja . Ni sabuwar kawarka ce,abokiyar ka,naji baka da aboki haka kake rayuwa kai daya,nima bani da kawa don haka na cewa hajia me zai hana mu zama abokan juna ni da kai,? Ka fadamun damuwarka ,in fada maka nawa,mu bawa juna shawara. Ina  fata zaka amshi abota ta ?

     Kallonta yake fuskarsa daure,sannan da alamar mamakin ganinta duk da yana jinta amma bai kulata ba ,daga karshe ma ya kau da kai daga gareta saboda Allah Allah yake ta fita ta bashi wuri,saboda ba abinda yafi kauna irin ya zauna shi daya ya fada wata duniya daban wacce take da bambanci da wacce mutane ke rayuwa.

    Ganin ya juya kai yasa ta sake zagayawa ta fuskance shi,ta ce.

     " Hakan na nufin baka amince da abota ta ba? Duk da baka amince da ni ba ni dai ba zan fasa zama abokiyarka ba,saboda Niraddeen shj kadai ne abokin da nake so nayi a duniya,saboda daga ji da ganin Nuradden (is special) .

   Zan fara aikina daga yanzu kafin ka amince,shawara ta farko ka dunfa barin ( freash air ) yana ratsowa cikin dakinka,zai baka (good company) kuma zai kara maka lafiya ( it will keep u healthy nd cheer you up).

    Na biyu,ni bana abota da kazamai,wannan dakin da kake zaune cikin kura ga kayanka a zube (,toilet )dinka datti,kai baka gyara ba,sannan ka hana a gyara maka. To in kanaso mu zama abokai sai ka koyi tsabta,kasan mu likitoci bama shiri da kazamai,din haka ka tuna kai abokin likita ne." Tana maganar tana tattara dakin.

  Ba shiri ya dazo kai yana kallonta,da ta ishe shi,yaji ranshi ya baci,ya mike a zuciye ya fisgi hijab dinta,yaja ta har kofar ya cillar ,fuska murtuk yace.

  "" Waye abokin ki ? Bana son kowa,bana bukatar kowa arayuwata ,bana son kowa,ina so in rayu ni kadai,in kika sake zuwa nda nake zan kashe ki. 

     Bata yu mamaki ba ,dama ta zaci haka daga gare shi...

    Murmushi ta masa,tace," Shi yasa nake  son ka zama abokna,zan dawo gobe in Allah ya kaimu sai ka fada min damuwarka (and yes ) bana so in dawo in same ka da kazanta,ka tabbatar da kayi wanka."

   Rufe kofar ya yi da kardi ,ta jima tana tsaye tana kallon kofar,yayin da kwakwalwarta ta shiga zarya tana tunanin ta hanyar da zata bullo masa har taja ra'ayinsa. 

    Alama ta farko ta nuna mata yana cikin fushi da zafi ,na biyu kuma kamar yana cikin wani fargaba. Na uku ,alama ya nuna ya yanke kauna daga dukkan wani farin ciki da rayuwar duniya. Wannan ya nuna rauninsa akan addini a zahiri.

    Ta jima tana nazari kafin ta juya ta samu Hajiya tana kaiwa da kawowa alamar jiran fitowar ta kenn,tana ganinta kuwa ta nufi wurinta da sauri. " 

   ""Likita yaya kika ganshi :?

   Bahijja tace,"kwantar da hankalinki Hajiya ,zauna zan miki bayani"".


   Ta ce,"Insha Allah Deeni zai samu lafiya,zai samu sauki. Sai dai sai na danyi fama da shi,saboda na lura mutum ne me zafin zuciya da zafin rai,sannan yana tattare da wani fishi da bacin rai a tare dashi...

     Sannan akwai wani (memories)* a kwakwalwar sa da yake son shafe su,ya mance da su. Yana so ya shafe wani bangare na rayuwar sa a baya wanda suke masa ciwon gaske. A kokarinsa na wannan yasa kwakwalwarsa ta kamu da ciwo ,rashin lafiya. Ba wai hauka yayi ba,kamar yadda Kai, ko zuciya ,ko ciki suke yyiwa mutum ciwo a jikinsa, haka kwakwalwa ma tana ciwo wanda dole sai ya sha magani zai samu waraka da yardar Allah. Sannan kuma ya kaucewa wannan tunanin.

   Na biyu ,matsayinsa na musulmi ya samu rauni,na uku, na lura yana da matsala da duk wata dangantaka a duniya wanda ya jawo yasa ya tsani kowacce irin dangantaka ,har yasa baya kaunar kulla dangantaka kowacce iri ce da kowa ,yafi so yayi ta rayuwa shi daya.

    Don haka Hajiya deeni na bukatar taimako kwarai wanda zan yi iya kokarin nayi,sai dai ba mai sauki bane. Mutum ne mai taurin kai da zafin zuciya ,tankwara shi ko juya shi abu ne mai wahala. Ina son jin tarihin deeni kakaf da ainihin shigar sa wannan halin ,saboda in san ta ina zan soma bi in taimaka masa..

    Hajiya ta ja dogon numfashi ta kalleta ido cike da tsammani ,tace.

 "Zan fada miki komai,tabbas Deeni danmu ne amma bamu kyauta masa ba ,bamu masa adalci ba. Zan baki dukkan wani hadin kai da kike nema domin inga dana cikin walwala............


Please nagaji wlh ,,kuyi hakuri se da safe............Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤
38Deeni mutum ne wanda yake (full of life)kullum yana cikin dariya da zolaya gami da kyautatawa kowa,duk da yana fmda zafin rai yana da zuciya da fushi da kuma ra'ayi amma yana wuyar gaske ka fahimci haka,saboda kullum yana cikin wasa da dariya.

    Duk wani abu da deeni yake so mu ba shi muke so masa ba,don haka muka sa shi yin abinda muke so musamman mahaifinsa ya danne abinda yake so yana yin abinda muke so saboda biyayya. Sun sha samun sabani da mahaifinsaakan abu da yawa ,amma daga karshe zai hakura yayi abinda mahaifinsa ke so.

  Deeni bashi da rauni a addini,asali ma sanin addini yasa shi yi mana biyayya duk da mun fi ba da karfinmu ga neman ilimin duniya shi da kanss ya dage da neman lahira,don haka anan mu muke da rauni ba shi ba.

  Ya yi amfani da iya ilimun da ya nemawa kansa na addini ,yana kokarin neman ilimin ne kuma muka raba masa hankali tare ds daga masa hankali akan karatun jami'a ,din haka ya qatsar ya koma bokon.

  Raunin Deeni guda daya ne a rayuwa FARIDA."

  Sai a lokacin Dr. Bahijja ta ce wani abu tunda ta fara magana ,ta ce.

"Farida ?""

   Mama ta girgiza kai ,tacd ,"kwarai farida,in akwai abinda Deeni yake so a rayuwa da muradi a rayuwarsa to farida ce. Dukkan ZURI'AR mu ba wanda bai san da haka ba,tun yana yaro har ya girma ya mallaki hankalin kansa,abinda yake so daya ne Farida,ita ce rauninsa..........


     A hankali Hajiya ta labarta komai tun daga farko har karshen abinda ya faru.

   Bahijja taji jikinta ya yi sanyi,ta matukar tausaya masa sosan gaske.

    "Allah sarki bawan Allah." Ta fada tana kallon mama .

   " Tabbas ba ku kyauta masa ba ,mahaifansa ,dan uwansa da masoyiyyarsa,tabbas wannan cin amana ne mai girma,dole ya ji dukkan wata dangantaka ta fita ransa.

  Tabbas ya yi kokari ma da ya tsaya a haka,Deeni jarumi ne,na jinjna masa,kuma  Nsha Allah zan taimaka masa ya fito daga cikin wannan kejin ya zo yayi rayuwar sa kamar kowa.

  Kila da mutuwa farida tayi,zai iya daukar kaddara ya jure, da farida ce masa tayi Deeni bana sonka wani zan aura zai jure ya hakura,amma wannan abinda ku ka masa ya masa ciwo wanda ciwon da cin amanar shi yafi zama a zuciya da kwakwalwar sa fiye da Farida.

  Yana jin cewa iyayensa basa son sa,ba sa kaunar sa,sun ci amanar sa. To in iyauenka za suki ka su ci amanarka zaka dinga jin to kai ina zaka shiga ? Ya zaka yi da rayuwarka ?

   Abinda ciwo matuka,zaka iya jure tsana da kiyayyar kowa amma ban da mahaifanka,saboda mahaifanka ,'yan uwanka su ne kai,su ne rayuwarka.

    Abinda Deeni yakeji, ciwon da ke cikin cikinsa da ni daku duk ba zamu iya sani ko fahimta ba sai shi sai Allahnsa. Ina fata Allah Ubangiji ya bashi lafiya,ya bani iko da taimakon iya taimaka masa,ya cire masa wannann ciwon da ke zuciyar sa."


      Ta mike ,'Ni zan wuce ,zan dawo gobe in Allah ya kaimu . Sannan zan ci gaba da bincike akansa daga gare ku,da fatan zaku bani hadin kaii""

  Mama dake sharar kwalla ta ce,"insha Allah za muyi duk abinda ya kamata ,mun gode "

   Nan sukayi sallama ta tafi.


   Alhaji dake tsaye yana jinsu hankalinsa ya matukar tashi,tsananinnadama ya kara shigarsa,tausayin dansa ya kama shi. Ya iso falon hankalinsa a tashe ,ya kalli hajiya.

   " Ki yafe mun abinda na miki ,abinda na yiwa danmu ban kara fahimtar illar da na yiwa yara na ba sai yanzu.

   Hajiya tsayawa tayi tana kallonsa,don kuwa a tsawon shekarun da sukayi na aure bai taba budar baki ya bata hakuri ba komai girman laifin da ya mata,haka bai taba nadama akan wani abu daya zartar don ra'ayinsa ba ....


   *****       *****     *****

 

  Washegari karfe sha daya ta nufo gidan,bayan ta gama zagaye marasa lafiya a asibiti.

  Kamar yadda ta same shi jiya haka ta sake samun sa a yau,hannunta rike da tray.

   " Asslamu Alaikum  Nuraddin"

 Dago kai yayi ya kallera ya watsar,ta kalle shi ta girgiza kai..

   *Ka.manta me nafada maka jiya? Ka dinga bude (window) ,kaga yau ka kara min aiki,dole in dinga zuwa bude maka (window ) tunda ina son abokina ya shaki iskar duniya.""

  Nan ta zage komai kamar jiya ,sannan ta zo ta hada (coffee) ta mika masa. Ko kallonta bai yi ba balle ya karba,ya dage kai...

  Bata hakura ba ,"kayi kokarin sha (I'am a very good coffee marker ).oh na gane ,ko sai na sa maka a baki ne ?

  Nan tayi kokarin kai cup din bakinsa,ya yi saurin doke hannunta sai da cup din ya fadi kan tiles ya kashe har ruwan coffee din ya dan kona ta.

   ""Auchhhh!!! Tayi kara.

  '"" In ba zaka sha ba meye na bigewa ? Kaga yanzu ka kona ni, ( u re such a bad friend ) ""

  Har yanzu bai kulata ba,nan ta hau tattara glass di. Da ya fashe,bata ankara ba kuwa ya yanke ta. Ga mamakinta ta ga ya mike ya dauko (first aid box ) yayi dressing wurin ..

 Ra jima tana kallonsa tana mamaki ,saboda bata zaci hakab ba.

 Ya kalleta fuska a murtuke ," Wai me kike so ne gare ni ? Na ce miki bana son ganin kowa a inda nake,bana bukatar wata DANGANTAKA !!!!

  ya fada cikin tsawa da huci..

   Kinji ciwo saboda ni,ban so,don haka kar ki sake kuskuren zuwa inda nake.""

  Da karfi ya fisgeta zai yi waje da ita ,sai yaji kansa yana wanj irin sarawa ,yana masa azabar ciwo . Nan ya saketa ya rike kai yana nishin azaba tamkar mai shirin barin duniyar....

  Hankalinta ya tashi ,tayi saurin ciro wasu allurai guda uku a cikin jakarta tayi masa a hannu,ta taimaka masa zuwa gado ya kwanta,bacci mai karfin gaske ya dauke shi. Ta jima tana zaune tana kallon sa cikin damuwa da tausayawa,sannan ta mike ta karasa abinda take yi a dakin ,sannan ta fita.


   Haka Bahijja ta kasance kullum sai ta zo gidan du Deeni duk da baya son hakan,baya kulata,haka zata yi ta masa surutu tana masa hira,har ya soma sabawa da hakan.wataran cikin dabara zata dinga jefa masa magani cikin (juice) ko abinci.

   Ganin har yanzu bata samu yadda take so ba tsawon qata uku amma Deeni ba shi da niyyar canjawa,don haka tayi niyyar sake canja salo,ta cewa hajiya tana son zuwa har kaduna gidansu Deeni inda ya zauna da inda ya yi rayuwa ,sannan tana son ganin farida don mata wasu tambayoyi akan deeni.

    Hajiya tace,'Da zai yiwu da na rakaki,to amma ba inda zan iya rafita in bar Deeni,don haka zan yi waya in sanar da su Shamsu zuwanki,zan baki cikakken (address) ba zaki fuskanci matsala ba insha Allah ".

 Ta mike ,"Na gode Hajiya da yarda da kuma hadin kai da kike bani."

   Hajiya tayi murmushi tace ," Nice da godiya,ba abinda zan miki sai addua,Allah ya ska miki da lakhairi"".

  Sn rabu akan zata yi kwana biyu kafin ta dawo...


  ****        *****        ****


 Kwance yake yana ta juye-juye a gado ,ya rasa me ke masa dadi,tun dazu yake sauraron zuwanta amma shuru. Ya riga ya saba da tana zuwa kullum dai dai wannan lokacin,amma yau har yamma shuru..

  Nan ya mike ya zuge labulen dakin kamar yadda ta saba masa,nan ya dinga kaiwa da komowa . Can ya bude kofar dakin ya fita abinda ya jima bai yi ba tunda ya dawo daga asibitin yana nan a cikin dakinsa.

   Hajiya na tare da Alhaki a falon kawai sukaga Deeni bazata yana leke-leke ,a tare suka mike cikin mamaki ...

    " DEENI" 

Suka kira sunansa a tare.

 Ya kalli Hajiya yace ,"Mama ba wadda ta zo gidan nan yau?"

  Kallon sa take da mamaki ,ta jima sosai rabon da taji Deeni ya kirata balle.magana,kuka zatayi ko dariya? Ta rasa.

   Bai bata amsa ba ya koma ciki ya tuea kofa ya kwanta,kwanciyar da yaji bata masa dadi ba ,ya mike ya nufi bakin window ya tsaya yana kallon motoci dake wucewa bisa titi..........Se anjima jama'a 


Taku har kullum...Sumy luv 😍😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by  SAADATU WAZIRI GOMBE 

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤
ASTAGHFIRULLAH WA'ATUBU ILAIK

   Allah kayafe mana kura-kuranmu,,,,Ameen 

    

 

39


 Zaune take a falo tana jiran isowar masu gidan,yayin da take kallon yadda aka tsara ginin gidan da yadda aka tsara falon.

   Farida ta iso tare da 'yan yaranta guda biyu suna ta tsalle-tsalle Deeni karami da Aisha,ta tarbi Bahijja cikin fara'a ,itama ta amsa tana daria ,suka gaisa.

   Deeni karami ne ya gaisheta,ta amsa tare da jawo su tana musu wasa da dariya ,tana tambayarsu makaranta suna bata amsa.

     Farida ce tace,to maza a je ciki ayi wasa a barni zanyi magana da Aunty ko?

  Nan sukayi ciki sannan ta maida kallon ta ga Bahijja tace,

   "Hajiya tamun bayanin zaki zo,sai dai bata fada mana ko mene ne ba "

   Bahujja tayi murmushi tace," Abu me muhimmanci ke tafe dani,sunana Doctor Bahijja,kamar yadda na fada miki ni likitar Deeni ce.

  Jin sunan Deeni yasa fatida taji zuciyarta ta tsinke,hankalinta ya tashi. Nan da nan Bahijja tayi mata murmushi.

   Keantar da hankalinki,ba wani abu me wahala yake tafe dani ba,illa iyaka inaso ki tainake ni in taimaki Deeni. Inaga wannan shi ne iya abinda zaki iya masa ki taimake shi shima yaci gaba da rayuwa kamar yadda kika ci gaba da naki rayuwar.."

Kanta sunkuye jiki ba kwari tace,"A shirye nake da in baki ko wani irin taimako ,zanyi farun ciki in har akwai taimakon da zan iya wa Deeni."

   Bahijja tace ,"Naji dadin hakan ,ina so ne ki fada min komai akan Deeni ,ina nufin ,halayyarsa,me yake so ? Meye baya so ? Banda wanda nasani ,a ganina kece mutum mafi kusa da Deeni,wacce tasan kananan abubuwa akansa wanda wasu ba za su sani ba. Komai ina son sani,me yafi sashi farin ciki,? Ya yake rayuwar sa? Kamar ( hobbies ) dinsa ,wane abinci yafi so ? Wanne yanayi yafi so? Me yafi sa shi nishadi da farin ciki ?

   Farida tayi shuru ta fada duniyar tunani ,rufe ido tayi tana tuno komai a game da shi,tana tuno wasu yanayi da suka yi tare a da.

   Ta bude ido jikinta a sanyaye tace,tashi mu shiga ciki"

   Nan ta ja ta sama zuwa bangaren da Deeni yake ,ta bude mata dakinsa,ta kunna wuta haske ya bayyana ,ta ce.

   Ga dakin Deeni wanda ya shirya shi da hannunsa,ina ga ganin wannan ko ban fadi ba zai fahimtar dake ko wanene Deeni.

   Bahijja tayi murmushi tace,"Kwarai ddakinsa ta bayyana shi a zahiri,daga (study room) dinsa na fahimci Deeni mutum ne me son karance-karance."

   Farida tayi dariya,"Kwarai yana son karance-karance da binciken takardu tin daga kan na Addini har na boko.

   Deeni ma'abocin ilimi ne ,ma'abocin soyayya. Yana samun farin ciki a kananan abubuwa,mutum ne me son zama cikin dabbobi,tsuntsaye da son kiwon su.

    Deeni yana son (spat) yana son (swimming),yana matukar son MISBAH da labaransa"

   Ras! Ras!!  Ras!!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ta maimata 

   **MISBAH**

  Ta tambaya cikin mamaki.

  Farida ta girgiza mata kai ,'Kwarai MISBAH (the author )wannan marubuci Deeni yana sonsa da labaransa. (Ideologies ) dinsa suna matukar burge Deeni,a kullum in munyi fada da Deeni to akan littafin MISHAB ne ,har na dauki littattafansa kishiyoyina saboda ba abinda ke dauke hankalinsa daga gareni sai takardun MISBAH.

  Tana maganar tana bude mata wani drowar dake cike da takardun MISHAB,gaba daya ba wanda bashi da shi,daga na hausa har na turanci,daga na labari har na addini.

  Shuru tayi tana jnjina soyayyar da yakewa takardunta,ko ita bata da wasu copies na takardunta sai dai original dake cikin computer dinta.....

   Lafiya Doctor ??;

   Farida ta katse mata tunani.

   Ta girgiza kai,,"Ba komai""

  Farida taci gaba ,"Deeni yana son rayuwa mai sauki,haka nan yana son ganin ya taimaki marasa karfi. Deeni bai dauki rayuwa da zafi ba""

   Magode kwarai da wannan bayanai naki da hadin kai da kika bani."

  Farida ta kalleta ,(please ) likita ki taimake shi""

   Bahijja ta girgiza kai,"Nsha Allah.

   Bahijja bata bar gidansu farida ba wanda ainihin cikin gidan su Deeni suka dawo tunda zuka koma lagos,sai da ta sa Bahijja taci abinci tayi wanda da sallah sannan suka rabu.

   Bahijja ta gama abinda take a garin kaduna ,washegari ta hau jirgi ta koma lagos,tare da sake sabon shiri wa yadda zata tafiyar da Deeni.


       Asslamu Alaikum"

  Ta fada lokacin da take kutsa kai cikin dakin .

Yana tsaye bakin window bai juyo ba,ta karasa dab da shi.

 " Deeni sallama nake "

  Nan ya juyo ya kalleta a yatsine ya watsar , sannan ya amsa ciki -ciki .

 Tayi murmushi,yau ce rana ta farki da ya amsa sallamarra.

  Tayi murmushi ,a ranta tace,"Wanann akwai son nunawa mutane isa."

  Gado ya nufa ya kwanta,ya juya mata baya. Ta matsa kusa da gadon.

  Deeni abokina ba gaisuwa ? Ko fishi kake dani ne ? Sorry "

 Ta kama kunne,"Na tafi na bar abokina ,to ai ba laifina ba ne,in na zo baka kula ni,baka jinm maganata,ba ka taya ni aiki,shi yasa na dai na zuwa. Ina zaune yau a gida sai mind dina ya dinga fada mun Deeni abokina yana missing dina ,kuma gashi na zo ka juya mun baya..""

   Duk surutun nab da takeyi bai ce mata kala bahar ta gaji ta kyale shi,can ta canja salo. 

    Naji labarin abokina ma'abocin son karance-karance ne,ko zaka iya fada min waye (favourite author ) dinka?

  Har yanzun bai kulata ba,nan ta mike ta bar inda yake ta zauna kan kujerar dakr dakin,ta jawo jakar data zo da shi tafara ciro littattafan da ke ciki tans dubawa,har yanzun ya juya mata baya. Waya ta dauko tayi kamar tana magana.

    '"Naga kun samin sabbin littattafai har wanda bana karantawa,wa ya ce kusa min littafin MISHAB? Ni bana son karanta labarinsa,yabi ya ishe mu da labaran rikicin rayuwa ,duk labaransa na bakin ciki shi kullum sai wahalar da mutane ,kullum yana hada mutane da matsaloli.

In soyayya ce ma yayi ta wahalar da su,mutm ba zai samu wanda yakeso ba." Tana maganar tana satar kallonsa.

   Gani tayi ya juyo ya mai da hankalin sa kanta gaba daya,ganin ya mai da hankalinsa gareta tasa ta ajiye wayar ta juyo da sauri suka hada ido,ya yi saurin kau da kai.

  Tayi dariya ta mike ta matso kusa da shi hannunta rike da littafin .

  "Kasan labaran marubucin nan kuwa ?

  Ya dago idanunsa ya tsareta dasu,"kar ki sake""

   Ya fada yana kallonta har ta so ta rikice,akwai wani abu a muryar sa mai sa a saurare shi,kuma ayi yadda yake so. Zai iya controlling mutum da muryar sa kawai wanda za mu iya cewa baiwa ne da Allah ya yiwa Deeni.....

  Tayi saurin cire idanunta cikin nasa,tace.

  " Kar in dake me ? 

    *Zangin (best author ) dina MISHAB . Dazu kin tambayame ni waye beat writer na,to MISBAH NE"

   Ta dan yi murmushi tace,"Ai ba zaginsa nayi ba,gaskia na fada"

  Ba gaskiya bane,me kika sani akan rubutun MISBHA ?

  "Fadamun ina son sani."

 Haka nan yaji yana son biye mata,yace.

  "Ba zan fadi ba sai dai in kina so mu zama abokai kamar yadda kika nema ki dauko sabon littafin da kika ce ya yi sabo ki karanta mun,saboda yanzu ina da ciwon kai ba zan iya karatun ba. Kinga kema in kin karanta za kiji wani darasi ne dabirin (logic )hikimar da ke cikin rubutun sa."

  Tayi murmushi,"Me zai hana ? Zan karanta maka ,amma ba don mu zama abokai ba,,saboda na riga na zama abokiyarka tun tuni. Sharadin karanta maka labarin MISBAH shi ne,zaka dinga jin maganata,zaka dinga fada min damuwarka,sannan zaka yarda in dinga duba lafiyar ka"""

   Lafiya ta ? Ya tambaya yana kallonta.

   "Ban fada maka abokiyarka Bahijja likita bace? Kuma na lura abokina baya cikin koshin lafiya,kamar ciwon kanka,inka bani hadin kai cikin kankanin lokaci zamu yi maganin sa. Sannan kana fada min damuwarka in baka shawara ,kaga riba biyu ,yi sauri ka amince ,yi sauri ka yarda..."""

   Kallonta yake yana mamakin ta,ita ko wace iri ce ? Bata fushi bata gajiya da magana,duk da baya kukata ba ta gajiya da duj halin da ya nuna mata,gashi har ta koya masa ya saba da ita da halayyarta.

  Zura masa ido tayi tana kallon sa,'Ina sauraron amsar ka""

    Bai bata masa ba sai jan pillow da tayi ya hadasu waje daya yayi matashi dasu,ya dago kansa tare da dora kafs daya kan daya. Ya kalleta yace.

   "Ina jin ki"

  Tayi murmushi,'inason (style ) dinka da (attitude ) dinka ""

  Tayi saurin ciro wani card da biro a jakarta.

   ".  Samin hannu mana (autograph)in zama mutum ta farko saboda nan gaba in ka fita kana yiwa 'yan mata wannan halin zasu haukaxe akan ka,kasan "yan mata na son namiji mai aji (classic tall ,handsome) sannan ga (attitude);yana musu jun kai yana shan kamshi,maganaa ma tsada take masa,yanzu zan zo ince in suna son zuwa kusa da kai to su zo ta wajena,saboda ni abokiyarka ce,ta hannun damarka,har (Autograph )dinka ina dashi. A lokacin ni zan zaba maka irin matar da ta dace da (personality ) dinka ,wacce za ku dace,zata haifa maka (cute cute little angels)"

   Tsayawa yayi yana kallonta kamar wata t.v,yana mamakin ra.

  Cikin tsawa da daga murya yace ,"Zaki karanta ne ko a'a ? Na rasa wane irin tunani ne dake"

   Ta harare shi,kai ,karfa kaga na ce ni abokiyarka ce ka nemi ka raina ni,ni yayarka ce,na girmeka (at least respect my age) ka daina min tsawa "" 

     Juya mata baya yayi ya kyaleta,dariya ma ta bashi,ya hau murmushi shi daya...........
RAF.   RAF.    RAF 

👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼

A tafawa MISBAHA ,tasa deeni murmushi wanda ya rasa shi tsawon shekaru har ya fidda tsammani da kuma yin sa...

Sumy luv 😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤
40


Juya mata baya yayi ya kyaleta, dariyq ma ta bashi, ya hau murmushi shi daya. 

Lekashi tayi tace, "laa ! murmushi nake gani a fuskarka ? Amma shan kamshin nan yafi maka kyau, gaskiya zaka daina murmushi kar ya bata maka kwatancen ka na (Mr. Attitude).

Karamin pillow dake gabansa ya dauka ya wurgeta dashi, tai saurin cafkewa tana dariya tace:  "to tsokanar ya isa lokacin karatu yayi". Nan ta dauko wasu littattafanta ta fara karanta masa. Ya juyo ya kalleta, "sabon littafin MISBAH".

Nan tahau 'yan kame-kame tana zare ido, ka bari wannan sai gobe, bari in fara maka da wani.  Ban so, ya fada kai tsaye sai kin fara wannan. Sai tace naji (Mr. attitude). 

Nan ta dauko wani littafin da tayi BALLE ta karanta masa, don haka kawai ta juya masa baya ta fara kirkiro masa sabon labari a lokacin, saboda duk littafin da zata karanta masa nata ya sani, kuma ba yadda za'ayi ta karanta masa labarun wasu tace nata ne, don haka tai dabarar kirkira ta hada masa labari a lokacin. 

A hankali yaji labarin na ratsa shi yana taba zuciyarsa, yaji yana sashi nishadi, baisan yaushe ya juyo ba ya samata ido, dukda ta bashi baya, ya lumshe ido yana sauraronta. Dr. bahijja na ta kokarin hada labari kiran Sallah ya katsesu, tayi godiya ga Allah ta juya ta kalleshi. Lokacin Sallah yayi. Ya bude ido kinyi alkawarin ci gaba ? Ta girgiza kai, amma bayan ka dawo daga masallaci. 

Mikewa yayi ya fita daga dakin ya nufi masallaci, sabanin da da yake sallah a daki. 

Fitar sa ya bata damar gyara gadon, da kade kurar da take gadon, ta tattara dakin sannan ta fita ciki tayibdakin am don yin sallah.  

   Mama tasa aka kai masa abincinsa dakinsa, yayin d suka zaunanda Bahijja sunanhira wanda duk ya kare akan rashin lafiyar Deeni ne da irin canjin da aka samu sosai a tare da shi. 

  Deeni ya dunga kaiwa da kawowa cik8n dakinyqnq jiran dawowar Bahijja a haka ta same shi. 

  " kaci abincin kuwa ?  

"sai kin karasa mun'"

Ta nade hannu, sai ka ci abinci"

  " Banzan ci ba.. "

  "Nima bazan karasa ba " 

Nan ta bude abincin ta zuba nasa ta mika masa, karba yayi da karfi yana ci. 

  "Bi a hankali, karka kware, bakasan cewa akwai (manners)  na cin abinci ba ma ?  " 

"Ban sani ba mana na, sai kin fada mun".

Ta girgiza kai,"za dai ka iya kirana yayarka amma banda mamanka".

  Murmushi yayi ya girgiza kai, ya kyaleta har ya gama cin abincin ya mika mata. 

   Tayi daria, (good boy) ,"Karbi magani kasha"

   Bai musa mata ba saboda burinsa taci gaba masa da labarin da ya tsaya masa a rai, yayinda Bahijja ke tunanin ta ina zata fara karasa masa ?  Haka dai ta zauna tana hado labarin tana jan ransa har bacci mai karfi ya fizge shi alamarmaganu da yasha ya fara aiki ,ta kimtsa dakin ta tattara jakarta (box)  din maganunsa ta adana waje guda, tazo fita ta tsaya tana kallonsa. 

"Ina tayaka murna da sabon canji da ka soma samu a rayuwarka, na fahimci kai mutum ne mai kirkin gaske da saukin kai duk da zafin zuciyarka".

Sau da dama Bahijja kan debewa kanta kewa ta hanyar hidimar Dini da asibiti wanda ta lura suna taimakon juna ne ta sami abuda ke debe mata kewa, ta mance damuwarta da kuncin da take tsintar kanta na dan wani lokaci, yayin da inta koma gida da dare ne komai ya zam a mata sabo, soyayyar mujinta da danta ya dawo mata sabo. 

A haka kullum Bahijja ke yi da Dini, har timetable na karatu ta sa musu, in sukayi karatu na addini kamar Alqur'ani da sauran takardu, sai tai ta kokarin hada masa labarin da take kirkira, daga nan sai shawarawri ya biyo baya. Cikin dabara da hikima da kwarewa irin nata ta ringa masa (brain therapy), tana bashi addu'o'i da magani na asibiti da Islamic medicine kamar su habbtis sauda da zaitun da makamantan su,  tana bashi shawarwari masu amfani da misali kalakala. 

Haka nan cikin dabara ta dinga dangana labarin da take masa na kirkira da labarin rayuwar sa, a hankali ta dinga saita tunaninsa har ya soma manta damuwarsa da bacin ransa. Ya tsinci kansa da rungumara sabuwar rayuwar da ya tsinci kansa, wacce yake jin dadinta. Kana ganinsa za kaga alamar sauki atre dashi, saidai a duk lokacin da yaga mahaifinsa ko yaji sunan dan'uwansa Shamsu yakan tsinci kansa cikin bakin ciki da damuwa.


  Kamar kullum yau da ta shigo ta samu yayi kaca-kaca da jakar takardunta da suke karatu yana ta bincike..

   " Meye haka Deeni? Me kake nema?

  "Naji sauki ne nake neman littafin da kike karanta mun na MISBAH in karanta,meye sunan labarin ma ?

   Ras !! Taji gabanta ya fadi.

  Ya tsare ta da ido,"Ina littafin ?

  Tayi saurin kau da kai ,xBan sani ba,don kawai kana neman littafu sai ka wargaza mun kaya? To sai ka tattara."

     "Bazan tattara ba." Ya bata amsa kai tsaye. 

  Ba zan tattara ba ,kuma sai kin bani littafin nan."

 In naki fa ?

 'In kinki yau bazaki fita a dakin nan ba".

    Hannu yasa ya daddanna (password) din kofar.

   "Ba zaki fita ba sai kin bani"

  *Deeni ""Ta fada cikin zare ido.

   "Baka da hankali ne ?

"Bani dashi "

"Please ka bude "

" In kina son tafiya ki bani.

  Ya juyo ya kalleta ,"Kar ki damu ba abinda zan miki ,ni kanunki ne."

  Nan ya dare gado ya hau ya juya mata baya tana ta masa masifa amma bai sairareta ba.

Nan tayi ta kokarin daddanna numbers din tana kokarin canka,yace.

   In kika yi sau uku ba dai dai ba to ko ansa na dai dai din ma bazai bude ba,kinga zama daram ni dake (my sweet)yaya." Ya fada cikun zolaya.

  Nan ta hau masa magiya har yamma ,tace masa ta tafi da littafin gida ta manta ,gibe zata kawo masa.

  Nan ma bai kulata ba ,nan fa ta hau lallaba shi tana lallashi,duk wannan bai yi aiki ba.

   Ta ce,"Deeni in na tafi fa ba zan sake zuwa ba,ka manta sharadin mu zaka dinga jin magana ta ??"

   Ya juyo ya kalleta,"Maganar ki wanne ne banji ba ? Na sha magani,na ci abinci irin wanda kike so,na sa kaya irin wanda kike so,na saurari shawarwarinki ,kullum muna karatu tare sannan yanzu mu abokai ne ,surutun da banayi kinsa na fara magana ,tun banaso har na fara so,menene baki sani nayi ba Doctor Bahijja...........Oops Abokiyata Bahijja?

   Ta daka masa harara ,"Akwai abinda ya saura baka yi ba,shi ne kunce abotar mu,daga yau na daina abotar ,kuma ta window zan fita kaje ka nemi wata abokiyar ta karanta maka labarun ,don ba zan baka littafin ba ,kuma ko ina zaka shiga ba zaka samu ba.""

   "Me yasa?

  Ya bata amsa,,"saboda ke ce MISBAH da zaki hana ni ko kuma zaki boye mun labarin. Sannan batun neman wata abokiyar bazan iya ba,saboda ko bakomai a tare da ke akwai muryar da take taba min zuciya in kina karanta min labarin, don kuwa ko shi MISBAH da ya rubuta labarin in yaji yadda kike karantata shi da dukkan (feelins) dinki da (emotions )dinki zai ji kamar ba shi ua rubuta ba.

   Sannan batun fita ta window kuwa Bismillah,iyakaci kugunki da kafarki daya ta karye,iyaka ta in sai miki ayaba da lemo"".

  Harara ta galla masa,ta kuwa nufi window gadan-gadan zata fita ,ya yi saurin fisgota fa rigarta.

  Ta daure fuska ,"Ka kyale ni""

  Zuwa yayi ya bide mata kofar ,"Fita,kin kira kanki da abokiyata amma ba zaki iya daukar wasa da nake miki ba.""

    " Eh bana son irin wanan wasan. ""

  Nan ta sa kai ta fice ,ya lura ranta ya baci,sam baiji dadi ba.


   Kwana uku Bahijja bata zo ba,Deenj ya rasa me ke masa dadi? Ya samu sabuwar rayuwa tare da ita da (company) dinta.

      Hankalin sa ya matukar tashi da rashin ganin Bahijja ,ya kasa hakuri har sai da ya tamvayi mama ina ne gidansu ne ? A wanne asibiti take aiki ?

  Mama ta kalle shi,Deeni kenan yanzu duk zuwan da Bahijja yake gidan nan baka taba tambayarta ita wacece ko daga ina take ba ?

    "Mama ki ban amsa." 

""Nima ban sani ba ,sai na bincika. Zan tambayi mahaifinka""

  Ranshi ya baci,ya juya ya koma ciki. Wanan ya bata damar yowa Bahijja waya ta fada mata halin da yake ciku.

    Bahijja tace,""Mama ina ga lokaci yayi da Deeni zai soma zuwa asibiti yana shiga cikin ajin da muke musu (lecture da ba da shawarwari,ya kamata ya fara shiga mutane. Munyi mai wuyar,kiris ya ragewa Deeni. Kafin ya samu waraka sai ya dai na  kebe kansa a gefe......

Wannan kenan Sumy luv ce dai har kullum😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE


Copied by SUMAYYA  SA'AD❤❤Assalamu Alaikum 

   Gaskiya ina matukar jin dadin yadda jama'a da dama ke binmu da nuna jin dadin wannan labari,hade da qara min kwarin gwiwa,da addu'o'i da nake samu,duk da wasu sun san cewa bani na rubuta ainahin labarin ba..........👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼

42Bahijja tayi kokarin janye kanta daga gidansu Deenj saboda tana gani lokaci yayi da zata janye daga gareshi,yanzu ya sona dawowa hayyacin sa. Abu kalilan ne ya rage masa yawan nasiha da masa tuni akai-akai, don haka ta bada shawarar in yana zuwa daukan darasi a (couselin center ) dinsu zai mike.

    

   Mama ta same shi a daki ta mika masa (address)din su Bahijja,ta lura yana cikin damuwar rashin zuwanta,tabbas Bahijja tayi tasiri a rayuwar Deeni.

     

   Tunda ya karbi (address) din yake tunanin yaje ko a'a ? Haka zuciyar sa da kwakwalwarsa suka dunga tun zura shi da ya je.

    Washegari ya shirya ya fita,tunda ya shiga wurin kwakwalwar sa ta dinga tunano masa da abunda ya faru. Hankalinsa yaji yana tashi, yaji kamar ya koma,ya tsaya shi dai bai shiga ba shi bai fita ba.

  Wani ma'aikacin wurin ne ya masa magana.

   "Malam wa kake nema ? Ba a tsayawa a nan,ko shiga ko fita"".

    Deeni ya kalle shi ya mika masa hannu suka gaisa,sannan yace.

  "Ina tambayar Doctor Bahijja ne ""

  Mutumin ya kalle shi yace,"Madam tana can bangaren koyarwa ,tana cikin aiki amma ka jira in ta gama zan mata magana,in kuma kana sauri sai ka dawo gobe da wuri kafin ta fara aiki.

  Deeni yace ,"In ba zaka damu ba ka raka ni zuwa inda take sai in jirata a can"".

 Tare suka jera da mutumin zuwa ciki,suna fatiya yana kalle-kallen yadda wurin yake,da irin jama'ar da ke zarya a wurin.


    (Hall) ne dan madaidaici cike da majinyata kuma dalibai,Bahijja tsaye gaban su tana ta bayani,tana ilmantar da su tare da wayar musu da kai,su kuma suna mata tambayoyi tana basu amsa,yayin da ta dinga binsu daddaya tana tambayarsu matsalolinsu suna fada mata tare dsmusu misalai da mutane daban-daban. Wani lokaci takan koma tarihin Annabawa,Sahabbai da manyan bayin Allah da irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwa. Don haka ba wani bakin ciki ko bacin rai da zai saka tsayawa da rayuwarka bayan kana da Allah da addini,kuma Allah ya baka yadda zakayi in ka koma ga Alkur'anj ,sannan zaka ga kai baka da matsala ma kan tasu ko na wasu.

    Allah ya mana kyautar rai da lafiya ne don mu bauta masa,don samun rabo duniya da lahira,ba zamu samu wannan babban rabon ba sai mun kula da kanmu da lafiyarmu,sannan muji dadin kyautata idar mu.

   Nan ta basu addu'o'in da za suyi na cikin Hisnul muslim,wanda yake cike da azkar din da Annabin mu yayi,kuma ya yi umarni da a yishi.


   Deeni ya harde hannu a kirji yana tsaye ya kwanyar da kai yana jin ta da saurarenta,maganganunta na ratsa shi. Hikimar ta na iya zance da iya fahimtar da mutane ya burge shi,iliminta da fahimtar ta yasa shi jin wani sauyi.

  Ya zura mata ido yana kallonta yana murmushi,wai da wa wannan likitar ke masa kama ? Yanayinta,koyarwarta,hikimarta akwai inda ya sansu.

  Kamar da wasa ta juyo sukayi ido biyu,ta hango shi tsaye gabanta. Nan ta dage kai kamar bata ganshi ba.

  Murmushi yayi ya kutsa kai ajin ,ya wuce kai tsaye gabanta ya kama kunne.

    "Sorry"

   Bata kula shi ba,ya juya ya kalli ajin ,"Sannun ku 'yan uwana dalibai majinyata,wannan. Malamar ta ku kuma likitar ku nima malamata ce kuma likita ta,na mata laifi na zo bata hakuri kuma nima daga yau zan fara zuwa ajinku,ku tayi ni bawa malama hakuri na dawo dan uwanku kuma abokin ku."""

   Nan suka hada baki suka ce,,'''muna maraba da sabon abokin mu..""

  Suka kalleta ,"Malama kiyi hakuri.."

  Nan suka sake hada baki suna ta bata hakuri har sai da ta amsa ta hakura,Deeni ya kafa mata ido yana mata dariyar zolaya. Bata kula shi ba har suka tashi ya bita har (office)a nan ya sata gaba yana ta mata naci tayi hakuri.

  " Ba zan kyaleki ba kamarnyadda baki kyale ni ba kwanakin baya,kiji ya fitinar take ? Gara ma ki hakura mu shirya."

  Ta kalle shi ba alamar wasa,ta ce.

    "Mr . Deeni ,nan ba gida bane,wurin aikina ne inda ma'aikata na ke ganin girma na da girmamani ,don haka ban son wasa. In har zaka ginga zuwa daukan darasi to ba wasa,muna da (discipline)da dokokin da zaka kiyaye. Ba latti,ba fashi,kuma ba yin yadda kake so..""

   Dauke kai yayi ya bata fuska,"Bana son (classes) din naki.""

   Ganin yadda ya juya ya murtuke ,lokaci daya kamanninsa suka canja ya  firgita ta,ta mike . 

     ""(Please )mana Deeni ,ka saurare ni"

Damuwa ta bayyana karara a fuskarta.

  Nan kuwa ya kwashe mata da dariya yana tsokanar ta.

    "Na firgita wata .""

      "Deeniii """""

Ta fada tana zare ido.

   " Kai ki,zan kama ka ne .

   Dariya yayi yabfita yana fadin," Gobe karfe tara na safe (i will be here )ba latti ba karya doka,ba fashi.

   Nan ta bishi da kallo taba dariya,har ya tafi ya dawo.

    "Zan sami littafin nan ki sunan littafin ??""

 Juyawa tayi bata kulashi ba ,ta rufe kofar office din. Don haka Deeni ya dage da zuwa kullum ba fashi,haka kullun yana mata nacin labarin nan ko sunan sa,amma bata saurare shi ba,va irin nacin da bai yi ba har ya hakura. Har (internet )ya shiga yana (searching)sabbin littafan  MISBAH amma bai samu ba,tun na karshe da ya sani da ba sunan wani sabo a cikin list din littattafansa.

    Abun yana matukar daure masa kai,duk nacinsa da kokarinsa ya kasa samun ko mutum daya da yace ya samu sabon littafinsa.

    Haka Deeni ya samu sabuwar rayuwa tare da sabbin mutane da suke tare da Doctor Bahijja,killum takan musu darasi tayi musu tambayoyi,duk wanda ya ci takan fita da su yawo zaga gari,da zuwa ziyarar wuraren tarihi na ilimi. Duk wanda ya warke gaba daya a sallame shi 

  Anan Deeni ya dunga taimaka mata da wasu ayyukan kasancewarsa likita,duk da kwarewar sa da karatun da bai kai nata ba zama da ita yau da gobe yasa ya fara sabawa da koyon aiki sosai ,daga dalibi ya bige da (praticing)da (training).

    Bahijja takan yi mamakin kokari da nuna kware na Deeni gashi da saurin fahimtar aiki,tabbas da ya jima yana aiki da karo karatu da ba karamin taimako zai yi ba ...


  A kwana a tashi Deeni ya ya warware ,shakuwa da sabo yana karuwa tsakanin sa da Bahijja ,zukan wuni tare a asibiti suna aiki tare.

  Sai dai har yanzu Deeni  bai taba fada mata damuwarsa ba wanda ke cinsa,abinda iyayensa da farida suka masa ya kasa mantaws da wannan cin amanar,haka kullum gudun haduwa da su yake,gudun maganarsu yake ko jin labarinsu. Wanda Bahijja kuma ta dage sai ya fuskanci abin ya wuce ya huya,sai dai duk kokarinta ya kauce....

   

   Bai taba tambayarta ta tarihinta ba ,haka bai taba fada mata nasa ba,a haka suke zaune ,haka nan har yanzu bai fasa binciko labarin MISBAHA ba......... 


Yaseen ya nagaji zan je hutun sati🤔🤔bayana ya rike😡😡


Sumy luv😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA

 SA'AD❤❤❤
Assalamu Alaikum

Masha Allah!!! Bisa ga hutun zango da muka dauka ,yau Allah ya dawo damu...Nagode da kulawarku a gareni ,Allah ya kara zumunci. Masu cewa ko lafia aka jini shuru ,,,wlh lafia lau sai dai Dan Adam da baa rasa shi da wasu yan hidimomi nashi na daban ... 

      Sannan dan Allah ina fatan baza'a kuma samun miskila kamar yadda aka samu a baya ba ,,wannan abu nina sa kaina pls nd pls abarni murabu lafia da kowa kamar yadda aka fara tun farko....

 

    Ina godia ga big Aunty Allah ya barmun ke bisa ga jajircewarki wajen ganin nacigaba da wannan rubutu(Aunty zee )maman nawal❤❤❤❤love u wujiga wujiga😘😘😘😄😄

42Wata safiya Bahijja da Deeni bayan sunyi aiki sun gama da marasa lafia,suna zaune a (free time )dinsu ,Bahijja ta kalleshi .

    ''Deeni, me yasa ka ke gudun mahaifinka ? Me yasa baza fuskanci gaskia ba da abinda ya faru ? Abinda ya faru ya wuce,kayi hakuri ka yafewa dan uwanka,wannan kaddara ce,bashi da laifi . Farida taci gaba da rayuwa,tana rayuwarta da mijinta da yaranta,me yasa zaka yi ta kuntatawa kanka ? 

   Idanunsa ne suka kada sukayi jaa,ranshi ya mummunan baci,duk da haka bata fasa maganar ba. 

    Deeni (you have to let go of ur past )ba zai yiwu ka rike su a zuciyarka ba kana wahalar da kanka,please ka yafe musu....

   Nan kuwa taga ya haukace mata yana zazzafa mata bala'i....

    Bazan yafe ba,saboda me zan yafe ? In ma na yafe nusu kina nufin zan iya mantawa da abinda suka mun in zauna lafia da su ? Ko na yafe musu bani ba su,bana son jin maganar su a ratuwata,na tsane su,zan iya kisa idan na ganus gabana...

    Ta kalleshi cikin fuskar damuwa ta tsiyaya masa ruwa mai sanyi a cup ta mika masa,tace..

   Please Deeni zauna... Ya zauna amma bai karbi ruwan ba 

   Saurare ni Deeni,in har ka dauke wannan zafin a ranka ba zaka iya yafe musu ba ,ko tsana ne ko so je ka sake shi a ranka,ka fiddashi a zuciyarka akansu. Ganun su ko maganarsu dole ne ,dan uwanka ne uwa daya uba daya,zumunci dole kayi,Allah ne ya ce kayi.. Gaba ma ba zakayi da musulmi dan uwanka ba balle dan uwa na jini.

     Farida kuwa akwai lokacin da kyakkyawar dangantaka ta hada ku,yamzu kuwa matar yayanka ce,dole ka yarda da wannan....

    Mahaifinka kuwa in kayi fada da shi baka da riba ,duk kai zaka sha wuya kaita wahalar da kanka...

  Kayi hakuri Deeni,Allah zai baka ladan hakurin da kayi,ya kuma baka sakamako mai kyau a duniya da lahira....

   Tana maganar kamar zata zubar da hawaye....

    ""kamar kani kake a gareni ,ba zan so ganin kanina cikin wannan halin ba... 

   Tsura mata ido yayi yana kallonta,maganarta na ratsa shi,haka nan ya dinga jin maganganunta na masa tasiri a zuciyar sa ,yaji zuciyar sa ta sauka ,tayi sanyi..

   Ya dauki ruwan sanyin yasha ,ya kalleta ya mata murmushi tare da mika mata tissue.

    "" Gashi ,share hawayen da ke shirin zubo miki,kar su zubo in miki tsiya nan gaba.......

   Murmushi tayi ta amsa,"Deeni ba zaka canja ba,tashi yau kaine best student koyarwar da na maka ya shiga kwakwalwarka da zuciyarka,don haka yau da kai zamuje outing..

  Yayi daria ,"yau ta ina rana ta fito Abokiyata DoctorBahijja zata fita dani yawo ?? 

    Murmushi tayi bata kulashi ba ,taje ta dauko mota ya shiga suka fita...

  Kai tsaye suka wuce asibitin gwamnati na garin suka dinga bi tana nuna masa marasa lafiya,wasu gasu nan kwance cikin azabar ciwo ba lafiya wasu ga ciwo ba kudin magani,wasu na son yin ibada da sauran ayyuka ba lafiya. Abin tausayi kala-kala da ya fara sa jikin Deeni mutuwa,daga nan suka wuce sauran asibiti na masu kudi su kuma ga kudin ga komai amma lafiya da saukin Allah bai nufa ba...

  Daga nan suka zarce gidan marayu,marasa galihu ,masu neman taimako basu da kowa bansu da komai sai Allah, sai abinda gwamnati taga dama ta san musu,suna watse basu da mai tallafa musu,ba uwa ,ba uba da zasu lallashe su,basubda wanda suka damu da su da rayuwarsu. Anan Deeni ya ga abun tausayi sai da ya zubar da kwalla...

    A mota duk jikinsa yayi sanyi ,Bahijja ta kalle shi tace,

   "" Yaya bakin cikinka da dacin ranka yake da na wadannan bayin Allah ?  Baka ganin ni'imar da Allah ya maka,kana da lafita da karfinka da gatanka da iyayen da suka damu da kai...

   Anta baka ganin matsayin iyaye ya kai suyi mana yadda suke so ko da bata mana rai ne suna da hakki??  Deeni rayuwar nan tayi kadan mutsaya muna bata lokacin mu akan wani bacin rai ko tsana,gaba ko wata kiyayya...

  Ka godewa Allah da ni'imomin da ya maka,in ya jarrabe ka sai kayi kokarin ka ci jarrabawar . Ka yarda da kaddara,ka saki ranka kayi hakuri Allah yana tare da masu hakuri(innallaha ma'assabirin😭)...

    Yayi murmushi idon shi jawur,hawaye ya gangaro masa,ya ce.

  "Nagode Bahijja ,tabbas kin cika abokiya tagari,likitan da tasan hakkin patient dinta,sannan ke mutumiyar kirki ce,Allah ya miki sakayya da abinda kika mun. A yau kinsa naji wani kunci da nauyi ya bar zuciyata ,duk wani fushi da kiyayya da nake ji a raina  ya tafi .......

  Tabbas nayi nadamar bata lokacina da nayi,sai dai insha Allah zan gyara gaba ,daga yau,daga yanzun nan Deeni ya zama sabon mutum wanda ba ya rike da kowa  a zuciyar sa,ba ya fushi da kowa. Ina jin zuciyata fara , zanyi kokarin gyara rayuwata da tsakanina da iyayena da 'yan uwa na...

    

Yau ce rana ta farko da nakeji da son fuskantar yaya Shamsu da Farida ba tare da wani bacin rai ko tsanar su ba, na yarda na amince haka Allah ya hukunta mun. Na gode Bahijja ...

     Lumshe ido tayi hawaye na gangara wanda bata san yaushe suka zo ba ,tana fadin..Alhamdulillah "".. A ranta..ya tsura mata ido yana kallonta,kamar wata bakuwa ko sabon halitta,kaunarta yaji ta shiga ransa,haka yana bata wani girma na musamman.   Ta mike,"Yau ranar farin ciki ce garemu da ni da kai,sai godiyar Allah .yanzu saura guri guda zan kaika,ina fatan zaka ji dadin zuwa wurin ""

  " Me zai hana ?" ya bata amsa ..

  ""Musamman inda ke a wurin..

  murmushi tayi ta girgiza masa kai suka tafi..

   wani tafkeken farm house ta kaishi  na (lagos state government )ba abinda babu ciki,kaji ne,dabbobi ne ,shuke-shuke ne,tsuntsaye ne,kala kala a wurin ..

     Wani farin ciki da jin dadi ta gani ya bayyana a fuskarsa,ya dinga ratsa cikin gonar yana bin kan dabbobin dabtsutsayen yana shuke-shuken dake wurin sun matukar burge shi, bai san lokacin da ya fara dariya shi daya ba. Irin abin da yake so yaga ya yi,ya kafa a rayuwar sa. Ga bishiyoyi,ga shuke-shuken 'ya'yan itace kala daban -daban ...

   lumshe ido yayi ya ware hannun yana shakar iskar wurin yana jin yana ratsa shi,yana jin wani irin tsananin dadi a ransa irin wanda ya jima bai ji ba.

   Zuwa tayi gabansa ta harde hannu tana kallonsa tana murmushi,tana jin dadin yadda ta ga tayi sanadin kawo farin ciki a rayuwar sa. Nan ta dinga jin wani irin farin ciki a ranta ,wannan dama shi je burinta a rayuwa ta ga tana sanya dariya da farin ciki a rayuwar mutane ,anan take samun nata farin cikin da nutsuwa da jin karfin gwiwar cigaba da rayuwa....... sry nasan zaku iya samun mistake ko typng erro ,,wlh typing din dare nayi kuma ban kuma bi nayi editing ba kawai nayi posting,,wlh nagaji ne kuma burina kawai nima inga yau nasaku farin cikii  (kamar dr da patient dinta😛😛)

 Tnks 

Sumy luv😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE
Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤
43


Kamshin turarenta yaji iska ta debo yana sauka kan fuskar sa yana shaka yana ratsa jiki da zuciyarsa,yana shiga yana ratsa shi. Soyayyar tace mai zafi da sanyi tare da dadin gaske yaji yana shiga yana kama zuciyarsa da dukkan ilahirin jikinsa yana ratsa shi tare da saukar masa ds wani irin farin ciki da ni'ima mai dadin gaske.....

    "Alhamdullah",Allah na gode maka."

  Ya bude ido yaci karo da fuskarta tana masa murmushi,shima ya hau mata murmushin  Suka kyalkyale da daria duka,tace. "Wow! In kayi dariya kana cikin farin ciki (u rilly look great)"".

     Ya kalleta,"(thanks to u )Bahijja."

  Ta girgiza kai,"Mun godewa Allah,don haka Mr. Deeni daga yau kasan inda ka kama,kasan inda kasa gaba,(u belong here)...... Ta nuna masa gonar.

  Ba gidan magani da allura ba,duk da likita kake amma kafi kyau da dacewa da nan gidan gonar,inda farin cikinka,jin dadinka da passion dinka yake,to me zaka jira? Ko ka nemi aiki anan ko kayi kokarin bude naka,duk wanda kakeso zaka iya""...

    Yayi dariya," Na gode da shawararki ,tabbas a nan passion dina yake ,(thank u so much)Bahijja . Daga yau din nan na miki alkawarin bude sabon rayuwa ,kuma zan fara yin wani abu me ma'ana da rayuwata insha Allah.

    Amma ina so ki min wani alkawari, ki zama abokiyata mai ban shawara ,yayata kuma mai guiding dina...""

   Tayi murmushi ,"Insha Allah ,Allah ya yi mana jagora duka".

   Ameen "Ya amsa tare da fadin .

   ""Sannan zaki bani littafin nan na MISBAH ,kuma zaki zama ABOKIYAR RAYUWATA...""""

    Ta dalla masa harara ,"Abokiyar rayuwarka kadai? Ka manta har ABOKIYAR MUTUWARKA ma zan zama .."

   Ya yi dariya ,"yauwa my Bahijja'"..

  Wucewa tayi ta fita ta wuce mota ,har ta saba da halinsa na zolaya. Ya bita har ya shiga suka tafi yana zolayarta.

  Har gida ta kaishi ta ajiyeshi,ba yadda bai yi ba ta shiga ta ki,ta ce ya gaida hajiya. Anan ya karbi numbern wayarta sukayi sallama.


   Kai tsaya ya wuce falon mahaifinsa,anan ya same su duka har lukman kaninsa,yana dariya ya gaishe su. Kallo daya zaka masa kasan yana cike da tsantsar farin ciki.

    Ya zauna kusa da mahaifinsa tare da kwantar da kansa a cinyarsa. 

   "Baba ka yafe mun"

Alhaji Umar ya dinga ji da ganin Deeni kamar a mafarki,sai da hawayen farin ciki ya zubo masa bayan shekara takwas zuwa tara Deeni ya fito daga kejin da ya shiga...

   Mahaifinsa ya kalleshi,Deeni Alhamdulillah ,tsantsar farin cikin da nake ciki bnsan iyakarsa ba. Nima ka yafe mun.

   Mama dai ta kasa jurewa sai da tayi kuka,farin ciki da jin dadin da suka tsinci kansu a ciki,sai godiyar Allah. A nan Deeni ya tabbatar musu da ba zai taba sake daga musu hankali ba.

   "Zan yi biyayya a gare ku insha Allah"".

  Alhaji ya kalleshi,ya ce,"Allah ya maka albarka Deeni,nima na muku alkawari dukkan ku 'ya'yana ba zan sake shiga rayuwarku ba,kowa yayi abinda yakeso duk da nasan nayi latti duk kun gama karatu..

""Baiyi latti ba Baba ."Deeni ya katsae shi.

  Ko a yanzu zaka iya yin abinda nake so,ina fatan zaka taimake ni kasa mun albarka."

   Insha Allah Deeni sai inda karfina ya kare..""

   Yace,"Wannan yarinya likita Bahijja Allah ya mata albarka ..

   Mama ta kalli  Deeni ,"Zaka kaini jar gida insa mata albarka.

   Yayi dariya ,"To mama ko yanzu ma in kin shirya".

  Tayi dariya ,*ba yanzu ba sai gobe " 

  Alhaji yace,"Nma ba za a barni a baya ba""
Washegari bayan sallar isha Deeni ya tuka su zuwa asibiti wanda anan gidan Bahijja yake,suka yi tambaya don kuwa Deeni bai taba zuwa gidanta ba.

   Sun samu baba andi ta ce bari ta shiga ciki ta mata magana,anan Deeni ya mike yana zagaye falon nata dabyadda ta tsara shi yana murmushi yana jin sonta na kara tasiri a zuciyarsa,soyayyar Bahijja na shigarsa yare da saka masa wani irin tsananin farin ciki da jin dadi.

   Yana tafiya yana zagaye wurin har ya hango gurin da ta kebe mai kama da (libry)anan ya hango hotunanta da mijinta da danta suna rumgume da juna,ya zurawa hoton ido yana tuno Dr. Mislihu . Sai a lokacin ya fahimci mijinta ne.

    Wani dan madaidaicin (diary)ya gani da biro a hade alamar bata jima da yin rubutu ciki ba,haka zuciyarsa ta dinga azalzalarsa ya bude ,yana kwadayin sanin komai game da Bahijja. Nan ya yi karfin halin budewa duk da yasan hakan ba dai dai bane.

     Abu na farko da ya fara gani yaji zuciyarsa tayi mummunan tsinkewa shi ne,(To my dearest wife MISBAH).

    ""MISBAH ? Ya maimaita a ransa ..

  Bai bata lokaci ba yaci gana da karantawa,sai lokacin ya lura da diary din da marigayi mijunta ya rubuta mata ne,yana fada mata irin muhimmancinta da soyayyar da yake mata gami da yabonta na ayyukan kwarai da take,yana mata addu'a gami da sa mata albarka.

  Nan ya rufe ido yana kokarin tuno inda yake ganinta da diary din nan mai kama da littafi,da lokacin da take zuwa gidansu wurinsa,da kuma asibiti,in tana zaune bata da komai takan dauko littafin tana karantawa ...

    Sannan wannan shine littafin da ta rike da sunan tana karanta masa sabon littafin MISBAH.

    "Wato Bahijja ita ce MISBAH"". Ya maimata.

    'Author din da nake so tun ba yau ba ,Author din da na hada (special bond ) da ita tun lokacin da na fara karatun littafin ta a rayuwata,Bahijja abokiyata wacce take yanzu masoyiyata ita ce MISBAH na da na jima ina so ina kauna?  Wow ! Bahijja na ita ce MISBAH na ..""

   Kaunarta yaji yana dada tsuma shi,yana ratsa shi..

    

   **Ke din daban ce special ce tunda har kika iya min dabara ,ni kika mayar marar wayo ? Ni kika fooling,wato dama wannan labarin kirkirankika yi a lokacin shi yada na nemi lityafin nan sama da kasa na rasa,ashe dama yana boye ne a cikin kwakwalwarki. (I love ur smartness)ina sonki Bahijja 'yar Baiwa,MISBAH na . Sai yanzu na fahimci labarin rayuwata da kikela yi kokarin hada min naji yana shiga ta,naji labarin ya tsaya mun a rai . Na so inji karshen sa ko zan samu in warware nawa matsalat..""

   Ya yi murmushi yana kallon hotonta ,""labarin da kika fara ni zan karasa miki,ba ni kika fooling ba ?  Jiya kiga yadda zan fooling dinki...""

    Nan ya yi ta ganin takardunta a wurin daban-daban da irin article din da tayi ta rubutawa.


   MISBAH na 'yar baiwa ce ,Nsha Allah zan zama ABOKIN RAYUWAR ki da MUTUWARKI kamar yadda kika fada,zaki ga yadda zan kawo farin ciki da canji a rayuwarki" 

   Ya yi murmushi ya ce,""Yayata Bahijja,Abokiyata,masoyiyata MISBAH .""

    Nan yasa hannu ya dauki littattafan da yake so,sannan ya dawo gun su mama ya samu Baba Andi ta gabatar musu da abin motsa baki,yasa hannu ya dauki apple yana ci yana lumshe ido ,yana jin kamshin Bahijja ko ta ina a gidan .

    Baba Andi tace,"kuyi hakuri na samu ta fara sallah ne .""

     Mama tayi murmushi ,""Bakomai"

  bata rufe baki ba kuwa Bahijja ta fito da fara'arta lullube da hijab,tunda ta shigo falon idonsa ke binta,ya zurawa fuskarta ido me cike da kamala da annuri ,murmushin dake kan fuskarta ya kara haska fuskarta ,yaga ta masa wani irin kyau da kwarjini......

    Wani irin SO me karfi yaji yana shigar sa,Son da bai taba tsammanin akwai irinsa ba ,ashe da wasa yake ba so ba,MISBAH ita ce so,ita ce SHAUKI. kallonta na kara masa son rayuwa,yana kara masa tsammani ,yana sa shi wani irin farin ciki da nishadi............
he's inlove again 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 
🤔🤔🤔🤔amma anya kuwa Deeni baya zurfafawa dayawa a soyayya ?? 

     

Shin Bahijja zata karbi Deeni kaninta a matsayin masoyi ???


wani hali Deeni zai kasance idan Bahijja taki amincewa a karo na biyu???


 sai munji ra'ayoyinku...
taku har kullum......
SUMY LUV😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

=================== GIDAN NOVELS ====================================44
Yadda Deeni yaga tana gaisawa da su Mama da Baba suna ta hira cikin kaunar juna da kulawa ya kara masa jin dadi da nutsuwa,haka yake burin ganin matarsa da iyayen..

    Bahijja ta mai (a kallonta kansa,ta lura ya tafi wata duniya. Biron dake hannunta ta jefa masa tana dariya ,ta ce.

    '"Abokina Deeni,wacce duniyar aka tafi??

    Yayi mata murmushi,ya ce,"Duniyar abokiyata Bahijja,gidanki ya mun kyau ,ya birgeni ,musamman (libry)dinki,cike yake da irin littattafan da nake so""

     Ta zaro ido tana kallon sa,"Kaji min yaro ,daga zuwa gidan mutane har kasan hanyar (libry)dinsu ?? 

  Ya yi mata muryar tsokana ,yace,"Ba gidan mutane bane ,gidan Abokiyata fa Bahijja ne. Sannan kin manta lokacin da kike zuwa nawa dakin kina mun yadda kike so ? Yanzu lokaci na ne."""

       Tace,"" Gidanku gidanmu ne ,ko mama? 

   Mama ta girgiza kai,"kwarai """.

    Ta kalli Deeni tana masa gwalo,ta ce.

"Gidana kuwa gidana ne ni daya,Baba Andi daga yau in yazo kar ki bude masa kofa ..""Baba Andi tayi dariya tace,"Ni na isa in shiga tsakanin yaya da kaninta ?? Deeeni yayi dariya,ya ce ,"Yawwa Baba Andi, daga yau kin zama babbar abokiyata,zan shigo inyi yadda nake so gidan yayata..""

   Bahijja tace,"In kuwa kayiwa yayarka barna zaka sha bulala."

     Dariya sukayi duka har da Alhaji,Mama ta kalleta tace.

   "  Allah ya miki albarka 'yar nan "

   Ameen Maama."ta fada kanta sunkuye.

  Tace,"kuyi ta mna addu'a mama,kuna sa mana albarka,insha Allahu Allah zai taimake mu..

   Deeni ya kalleta yana dariyar tsokana,zuciyarsa cike da sonta ,yace.

   "Allah ya miki Albarka 'yar nan ......

   Ta hararebshi ,"Mama kinga yaron nan ya raina ni." 

    Alhaji ya kalleta yana murmushi ,ya ce .

 Zan baki bulala ki dinga zane shi."

 Suka yi dariya duka,tace,'Yauwa Baba,gara in fara zane shi don naga girman jikinsa na yaudararsa...

   Deeni yace,"To wata ma tayi girman jijin mana 

   Mama tace,"Deeni naga alama nima zan fara maka bulalar.."

   Nan suka yi ta dariya suna hira har wurin karfe tara sukayi niyyar tafiya,Bahijja ta raka su har mota. Ta lura da wani irin mayataccen kallo da Deeni yake mata,haka ta ganshi cikin tsananin farin ciki. Sai dai bata zurfafa tunani ba ta kau da abin a ranta amma ta rasa me yasa kallon yake yawan fado mata rai(💃🏻💃🏻💃🏻)...*****        *****        ****


Deeni da iyayensa suka ziyarci su Shamsu tare da sauran dangi,Shamsu da Farida kam sunsha mamakin ganin yadda Deeni ya ware har abinci ya zauna suka ci tare da shi da Faridan da yaransu ana wasa da dariya..

   Tun Farida najin wani iri ,tana takura har ta ware tana kallonsa tana mamakin ganinsa haka. Ya kuma nuna mata shi dan duniya ne ,ya dinga janta da hira,"Aunty Farida kaza ,Aunty kaza akayi." Tun bata da niyyar sakewa har ta sake..

   Deeni kuwa har cikin ransa ya gama da farida da tunaninta ko soyayyarta,a halin yanzu duniyarsa,farin cikinsa da shaukinsa yana ga Bahijja.

    'yan uwa da abokan arziki kowa ya yi murna da sabon canjin da aka samu daga Deeni. Farida ta masa murna sosai ,amma sai ta tsinci kanta a cikin wani bakon yanayi na rasa soyayyar Deeni da tayi,sai a lokacin ta kara fahimtar abinda yayi,addu'a tai tayi har ta samu saukin abin. Saboda ita har yanzu cikin kasan zuciyarta akwaii Deeni a binne ,sai dai zata ci gaba da jurewa da kuma rungumar rayuwarta da mijinta da 'ya'yanta ,ba zata taba tono shi ba.


  

  A cikun wannan lokacin Deeni da mahaifinsa suka yi ta shiga da fita da buge bugen neman makeken fili a kusa da asibitin Bahijja don ann ya cewa mahaifinsa yake so ya yi gidan gonarshi. Shi dai bai tambayeshi dalili ba,ya biye masa don yanzu duk abinda Deeni ke so shi ake masa,da sauri ma kuwa. Shakuwa da soyayya ta musamman ta shiga tsakaninsa da mahaifinsa,gaba daya Deeni ya dawo sabon mutum..

   

    Abinka da masu gidan rana ,lokaci kankani aka gama ginawa Deeni gidan gonar sa,aka daukar masa ma'aikata masu taimaka masa da komai. Duk wani abinda yake bukata an sa masa ciki,a hankali wurin ya dinga habaka yana yiwa Deeni yadda yake so..


   Irin farin ciki da jin dadin da ya tsinci kansa a wannan lokaci ba a magana ,yayin da ya sako Bahijja gaba da nasa salon tsokanar wanda ya samo. Wata number ya samu yana tura mata text message.


   Tana zaune office dinta tana karance karance taji wayarta tayi kara alamar shigowar sako,ta dauka ta bude. Gabanta ne ya ba da rass!!

    "MISBAH""

Shine abinda taga an rubuta.

  Tayi bala'in rudewa saboda duk duniya mutum daya ne yasan ita ce MISBAH ,wanda yanzu baya duniyar.

   Kafin ta gama fita daga wannan rikicin ta sake ganin an turo mata wani.

     (I knw u re my MISBAH).

Mikewa tayi tana sake maimaita sakon a ranta,mamaki ya bayyana karara a duskarta,nan tayi saurin mai da amsa.

    "Waye kai?(wrong number)

  ya bata amsa da ,"In wrong number ne me yasa kika tambayeni ? 

   Nan tayi saurin kiran layin,amma sai taji a kashe ,tayi shuru tana tunanin duk wanda yayi abin nan yasan yadda take tunani,yasan zata kira ,to waye ne ? Ko da wasa bata taba kawo Deeni a zuciyarta ba,asali na ta kasa kawo kowa a ranta. Haka tayi aikin wurin da abin a ranta.

    Tana sallama gidanta kuwa wani sakon ya shigo.

   "Allah ya hice gajiyarki my MISBAH ""

Yanzun abin ya fara taba mata rai ,wa ce ko wane dan rainin wayon ne ? 

 Tayi tsaki ,zata wuce ciki taji muryarsa. 

"Haba madam Bahijja ,wucewa haka ba kya duba gabanki ? Tun dazu nazo ina jiranki,awa na guda na samu Baba Andi itama har ta gaji ta tashi,amma ni ban gaji da jiranki ba. Haba abokiyata."

   Bahijja ta harare shi,"Gama cin abincin ka sha ruwa maza kaje gida kayi wanka ka kwanta kayi bacci,kana da aiki gobe..""

     Ya yi saurin mikewa ya sha gabanta ,"Wa kike cewa yaro ? Wai an fada miki shekara talatin wasa ne ? 

  " Matsa ni kaban wuri,talatin din  har wata kayan gabas ce ? Akai na dai talatin dinka na komai bane.." 

    Har ta soma tafiya ya sake shan gabanta ya harde hannu tare da shan mur ,ya kafa mata idanunsa.

    ' Waye yaro ? 

   Muryarsa da irin kallon da yake mata duk suka rikitata ,ta rasa me yasa take jin shakkar sa. Nan dai ta dake ,murya na rawa ta ce.

   ""Way...  ...waye kake zarewa ido ? Wa zaka bawa tsoro ? Ni da waye a wurin ? 

 cikin muryar rada mai kashe jiki yace,"Yayata Bahijja da abokiyata Bahijja ,ita nake bawa tsoro ,kuma naga ta tsorata...

   Gaba daya ta rikice ,taji jikinta na bari,da kyar ta iya daga kafa tayi ciki da sauri . Ya bita da kallon kauna yana murmushi,can ya jiyo muryarta tana cewa.. 

    " Ka fita ka kira baba Andi ta rufe mana kofa,kuma karka sake zuwa mana gida da dare""

  ""  zan zo ko yaushe nakeso,kuma in kin isa ki fito ki fuskance ni ki hana ni.

  nan ta leko da kai ta ce,"Na fuskance ka,sai me ? 

 " ki kalli cikin idona in kin isa" "Naki din "ta fada tare da rufe kofar da karfi tasa key.

    ""Wannan yaro ya zame min damuwa gurin aiki da gida duk bai kyale ni ba,sai na hada shi da mama".

  Tana cikin wanann mitar wani sako ya sake shigowa ....

  " Ki tabbatar kin ci abunci kafin ki kwanta,karki kwana da yunwa MISBAH NA.

SUMY LUV😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE 

Copied by SUMAYYA SA'AD❤❤

     Kuyi hakuri da  abinda kuka samu,wlh nayi typing me yawa da safe ban san ya akayi ba akamun deletn....wlh saura kadan nayi kuka ,sabida yafi na koyaushe yawa..

    


45 

     Tsaki Bahijja tayi ta kashe wayarta takwanta a wurin ko kayan jikinta bata cire ba ta kwanta a kasa zuciyarta cike da tunani kala kala musamman na wanann sakonni dake shigo mata.

   Can ta kau da tunanin ta soma tunanin yadda Deeni ya saki jiki da ita sosai,tayi zaton in ya warke a yadda ta sanshi da attitude zai fita harkarta ne amma sai wani sabon shakuwa ma da kara kusanci da ita yayi,lokaci guda sun zame mata kamar 'yan uwa shi da mahaifansa da 'yan uwansa. Tabba da haka kowani mara lafiya yake mata da duk kusan rabin kasar nan sun zama yan uwanta. Shi dai Deeni daban yake,mutumin kirki ne,mutumin kwarai.

    Dariya tayi da ta tuna halayyarsa da yadda yake yawan nasara akanta.

   Deeni kanina ,ina son sweet nature dinsa.

   Ta yiwa kanta murmushi ,sannan tasa hannu ta dakko hoton Doctor Mislihu da danta kana kallo tana jin tsananin kewarsu.

   "Allah ya jikanka,ya maka rahama masoyina. Muhammad dana Allah ya maka albarka ,ya albarkaci rayuwarka. Allah ya kare min kai a duk inda kake..

   Hawaye ne ta dinga gangaro mata,ta tsinci kanta cikin kewa kamar yadda ta saba kowani dare,da hakan bacci ya dauke ta.

 

     Haka Deeni yasa Bahijja a gaba da tura sako,ya hanata sakat. Wani lokacin sai ya zo gabanta sai ya tura mata,nan da nan zai ga ta rikice tayi wurgi da wayar har ya zamana tana shakkar kunna wayar,a dole take amfani da layin saboda shi ne layin da aka santa dashi ,ana iya nemanta.

   Haushi ya kamata ,ga matsalar me matsa mata da text da bata san waye ba ,ga Deeni kusan sati guda bata ganshi ba ,ta masa waya bai dauka ba ,kuma bai kirata ba. Ta kira mama ta tabbatar mata lafiyar sa lau,aiki ne ya masa yawa.

   Tsaki tayi ta kasa kulla komai,can ta yanke hukuncin leka shi a ma'aikarsa ,tunda ta shiga ta hango shi yana aiki bai zauna ba yana ta faman kaiwa da kawowa da ma'aikatansa,ya leka wannan fannin ya leka wancan . Can ra ga ya hau tractor yana zaga cikin farm din nasa,ta sa masa ido tana kallonsa tana murmushi..

   Nan take ta rsinci kanta cikin nishadi,tana jin dadin ganinsa haka tana matukar sha'awar halinsa,wasa da dariya da maaikatansa gami da mutunta su,haka tsakaninsa da dabbobi,kaji da sauran tsuntsaye tamkar abokan sa.

   Harde hannu tayi tana kallonsa kamar t.v. can ta ga wata yarinya matashiya ta zo tana kiran sa,ganinta yasa ya sauko daga kan tractor din ya zo yana kallonta yana daeiya suna magana,haka ya bata muhimmanci sosai. Haka kawai taji ranta ya baci,ta kasa ci gaba da jure kallonsu.

    Har ta juya zata tafi sai taji muryarsa,''Har abokiyar tawa zata tafi bamu gaisa ba?

   Ta kau da kai ,"Dole ne in gaisa da kai ?

   Gaisuwa ba dole bace amma ganina dole ne "

    Ta harare shi ,"Ta yaya ya zama dole?

    Tabbas nasan tunda har kika zo gidan gonata ba kinzo yawan shan iska bame"

 " Kwarai ". Ta bashi amsa.

   "kaji nazo gani da dabbobi."

   To ai baki gansu ba zaki tafi.

  " Na fasa "

  Ta fada a hasale tana kallon yarinyar alamar tana tsaye tana jiransa ne.

   " kaje kaji da bakuwarka "

  Ya yi murmushi ,kar ki damu da bakuwa ta,wannan special ce ba rabuwa za muyi yanzu ba,gara in gama da ke yanzu in koma.

    "Yanzu ma ka gama dani,sai ka tafi.

 "Bashi yiwuwa kizo ki tafi baki shiga office kinsha ruwa ba"

   Ba shi nazo sha ba""ta bashi amsa.

"Na sani amma za kisha "

  Dura mun zaka yi ?

"A'a da hannunki""

" wai me kakeji da shi? Ta fada a hasale. "Ban ji ds komai sai gidan  gona ta da special bakuwata" 

   Hawaye ta ji ya ciko mata ido,jikinta yayisanyi tace,

Deeni sati guds ba waya ba ziyara? Na kira baka dauka ba ,ko special bakuwar ce ta hana ka ? 

  Yayi mata murmushin dake fadar mata da gaba ,yace

   Ki yi hakuri aiki ne ya mun yawa da lokaci.

   Deeni ba zaka iya samun lokaci komai kankantar sa ba mu gaisa?

   Tana maganar saura kiris tayi kuka glhar ya lura da hakn yayi saurin kau da kai don ya bata damar zubar da hawayen.

   Ya ce,MEYE DANGANTAKARMU? Bahijja kina naki duniyar ina tawa ,kina farin ciki da aikinki ina yi da nawa,idan halin haduwa ya zo sai mu hadu. Yanzu ba da bane,dukkan mu muna da abinyi,saboda me zamu dinga bata lokacin mu ?

   " Haka me ".Ta fada murya kasa kasa .

Kayi hakuri,sai anjima.

   Tajuya jiki ba kwari da kyar take iya daga kafarta .

     "Bahijja"

Ya kirata amma bata juyo ba valle ta tsaya. Ya so ya bita amma sai ya fasa ,ya nemi wuri ya zauna ya fada wata duniyar tunaninta yana jin wani irin shauki mai karkin gaske game da ita yana ratsa shi,idonshi ya kada yayi ja yayin da gugiwar kaunarta ta dinga tashi a zuciyar sa...Sumy luv 😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE


Copied by  SUMAYYA SA'AD❤❤ 

46Bahijja ta koma office amma ta kasa zaune da tsayee,gaba daya ta kasa samun nutsuwar yin aiki,dole haka ta tattara ta koma goda. Nan ma tayi kokarin yin rubuce rubucen ta amma hakan ya gagara...

     Duniyar internet ta shiga ko zata samu abin bincikawa shima ta kasa,nan ta dauko liyyafi amma karatun ya gagara,ranta yayi mummunan baci,ta rasa me ke mata fadi...

  Wannan shi ne lokaci na farko da haka ya faru da ita a tarihin rayuwarta,damuwa da bacin rai komai yawan sa da karfinsa ba ya hanata sukuni har ta kasa yin komai,ta kasa jin dadin komai a rayuwarta. Haka ta kasance har yamma lis ita daya a gida,don baba andi ma bata nan taje gai da  yan uwanta zata yi kwana biyu..

     Kicin ya shiga amma ta rasa abinyi,ta fitofalon. Tana nn tsaye ta hango kanta tsaye a gaban tafkeken madubin dake manne a bangon falon.

    A hankali ta matsa tana kallon kanta da yanayin ta,gaba daya ta canja,ta birkice,ba nutsiwa ko kadan a tare da ita.

    " Meye haka Bahijja ?

Ta tambayi kanta.

"Me ke damunki ? Me ya hanaki sukuni? 

  Can karkashin zuciyarta tasan amsar ,amma sai ta ki amincewa wanda ita kanta tasan kin amincewa abinda kasan ba gaskia bane yana matukar wahalar da zuciya tare da ruhi da jikin mutum gaba daya.

    Idanunta suka kada sukayi ja,tausayin kanta ya kamata. A hankali ta sa hannu ta zame gyalen da ta daure kanta dashi,ta baza gashin kanta tana shafa fuskarta da gashin ta,idanunta suka kada sukayi jajawur,ta tsinci kanta cikintsananin kewa . Sai a wannan lokacin ta tuna cewa eh ita mace ce fa mai rauni,abinda ta manta da shi duka yau ta tuna,tana bukatar a kula da ita ,tana bukatar soyayya ,tana bukatar wani ya sota,ya kuta da ita,ya kawo karshen wannan emptiness din a rayuwarta.

    Bata ankara ba sai hawaye taji yana zubo mata da karfin gaske,har bakinta na bari. Ta sa hannu duka biyu ta rufe fuska tana kuka .

   Ya sake kallon kanta ,"Bahijja ya kike ? Ya kamanninki kaye ? Ke kyakkyawa ce ko mummuna ?

   "Ya kamannina yake ban taba sani ba,kullum dai mijina ya kan kalle ni ya yabani da kyauna,amma ni ban taba tsayawa na kula ba""

   Shin me yasa nake son kula da kamannina na yau? Shin wa zai fada min ya nake? Ya kamannina suke? 

   ""Bahijja u re a beautiful woman,""""

     Taji muryar Deeni tsaye a bayanta.

   Ras !!!Gabanta ya fadi,tuni tayi wani mugun rudewa,tayi saurin jan gyalen ta lullubu,ta kasa ce masa komai.

    ""Gidanki ne amma zan miki tayin gurin zama""

    Ta rasa me yasa yake iya  controlling dinta,bata iya musa mishi ko tayi niyya duk kuwa zafinta da jin ta isa.

     Wuri ta nema a kujersr falon ta zauna,ta kau da kai.

    Ya matsa gabanta ya kafa mata ido,"Bahijja meye damuwarki?

    ""Me yasa zan fada maka damuwata? 

  "Hakan na nufin cewa akwai damuwar kenan ? Ina son sani...""

   Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai.

   "Bahijja ""ya sake kiran sunanta.

    A duk lokacin da ya kira sunanta tana jin wani abu me sanyi da dadi yana ratsa ta har cikin zuciyarta da kwakwalwarta,yana kashe mata jiki.

  Lumshe ido tayi tana jin wani abu me karfi game dashi..

    Ya cigaba ,"Bahijja ninda ke duk muna cikin kuncin zuciya da shauki,bambanci shi ne kawai naki ya fito nawa kuma na boye shi a zuciyata,saboda bana son bayyana shi har sai na fahimci meye a zuciyarki.

      Kuncin da kika shiga yanzu ni na shige shi na tsawon lokaci,ni kadai nasan ta yaya na rayu da wannan shaukin ..""

  Wayar sa ya ciro ya daddanna a gabanta ,yayin da tana ji nata wayar yayi kara. Shi ya dauka ya mika mata,gaba daya jikinta ba kwari maganganunsa kawai ke mata yawo a jiki dabjijiyarta,da kyar ta iya karba ta bude sakon tana karantawa,ya sa mata ido yana karanta mata abinda sakon yace.

   " I love you MISBAH"

  Bugun zuciyarta taji ya tsananta ,ya sake maimaitawa yana kallon cikin idonta.

   "Ina son ki MISBAH " 

  Nan tayi saurin sunkuyar da kai ,gaba daya taji ta rufe ,ta susuce,bakinta na bari,ta rasa abin fadi,ta kasa zaune da tsaye ,gashi ya tsareta da ido.

   "" Na san abokiyata itace MISBAHna tun randa  na fara zuwa gidan nan , na miki abinda kika koya mun ne na kirkirar sabon labarin MISBAH a lokacin,tunda kin kasa karasawa ni zan ci gaba ,sauran sai mu karasa tare. Ina fatan za ki bani hadin kai mu karasa tare .

      Bahijja ina matukar sonki,so na hakika,zan kawo farin ciki ratuwarki,zan kula da ke,zan shagwabaki ,dukkan damuwarki zai zama nawa,zan dauki nauyin sa ki farin ciki a rayuwa...

    Nasan nayi soyayya mai zafi a baya ,sai dai ina so ki sani dangantaka ta da kaunata da ke ya jima sosai,tun kafin in san ke wace . Na jima da kaunarki tun kafin in san ke mace ce ko namiji,ta hanyar rubutunki.

  Bayan haduwa ta dake,kin taimake ni na manta da abin da ya faru a baya,wanda soyayyarki ce ta mantar dani. Yanayin rayuwarki abar so ce,abar koyi ne,sannan kin fahimtar dani abubuwa da yawa da baiwarki,wanda karo na biyu na sake fadawa sonki ba don komai ba sai wannan halayyar taki  wanda ita na jima ina mafarki da burin gani a wurin mata ta (how u cope ur loneliness)ya birgeni ,ta kara min ganin ganin girmanki ,sannan lokaci guda na zo na fahimci MISBAH na ita ce Bahijja na ,sai abin ya min bibbiyu.

    Halayyyar Misbah da Bahijja shi ya haukata zuciyata da sonta har na manta da na taba wata soyayya a rayuwata,duk abinda Misbah tayi yana burge ni,yana min dadi,musamman zuciyarta da boye kanta da tayi wa duniyata watsa iliminta da baiwarta ga alumma suna amfana.

   Bayan nan Misbah kina da kyan da ya shiga zuciyata ya zauna,murmushinki,muryarki mai dadin sauraro,wannan bakin dake min mita da surutu kullum,wannan idanun masu kashe min jiki ko kirarki ,iya takunki ko nutsuwarki me hanani sukuni.

      Bahijja ina sonki ,kina sona ?? 

    Gaba data ya gama tsuma da kalaman sa,ya kashe mata dukkan gabban jikinta ,sonshi ne mai tsananin gaske take jin yana huda dukkan ilahirin jikinta. Da kyar ta iya bude baki murya kasa kasa tace.

 "  Kasan me kake fadi kuwa ?  Ni na ce maka ina sonka? 

   Ya karya kai yana kokarin su hada ido amma taki ,yace.

     "Ba ke kika ce ba,ni naga haka,ni naji a jikina ,lokacin da hankalinki ya tashi da na daina zuwa wurinki na daina daukar wayarki,lokacin da hankalinki ya tashi da kika ganni da ma'aikaciyata. Wannan abin shi ne so Bahijja ,wannan feelings din da muke ji shi je so. Ko ki so ko ki qi mun riga da mun shirya duniyarmu nida ke tun tuni,mun tsara rayuwar mu ba tare da mun fahimci haka ba sai yanzu. Ina fada miki gaskiyar da kin kini sani ne ...""

     Ta mike da sauri,"karka manta kai kanina ne,har yanzu ni yayarka ce,wacce na taba aure har ma na haifi yaro. Kai saurayi ne,dan gata ne,dan asali ne. Kar ka manta ni marainiya ce da bani da asali.

   "" Martabarki da darajarki ya wuce haka,ke abar so ce Bahijja,ina son sani wanne ne daya kike magana akai,sona ne bakya yi ko kuma wannan bayanan zai hana ki aure na ? Uwa ta gari nake nemawa 'ya'yana na gani a tare da ke,mace saliha nake nema na gani a tare da ke ,don haks ki bar wannan zancen..

     Ni ne me aurenki ba mutanen duniya ba,ni zan zauna da ke na miki alkawarin soyayyarki ba zata canja ba,haka zan cigaba da daraja ki da mutunta ki. Ke abu ce mai matukar muhimmanci da daraja a wuri na,kin wuce wasa""

    Bata furta komai ba duk da alamar maganganunsansun ratsa ta,wucewa tayi library dinta hankalinta a tashe ta rasa inda zata sa kanta da soyayyar Deeni da ke azalzalar zuciya da ruhinta. Ta dauko wannan diary din da kullum ta rsinci kanta cikin kewa da rudani yake bata kwanciyar hankali in ta bide ta karanta,twyi ta kokarin budewa page by page amma ta kasa karanta komai,sai hawaye da ya cika mata idanu . Bata ganin komai haka ta dinga bide shi da sauri da sauri.

   Ya biyota ya sa hannu ya karbi diary din.

 ""Duk da abu ne mai muhimmanci a gareki Bahijja ni yana kona min zuciya ,ina kishi da shi,kishin gaske da ba na wasa ba nake yi da diary dinki.

   Kiyi hakuri ina jin wani tashin hankali,Bahijja ina tare da tsoron rasa ki,duk da una da tabbacin kina sona,ina tsoran kar wannan diary din da dalilan da kika kirkiro dazu marasa tushe su sa na rasa ki..

     Bahijja da can na yi hakuri amma yanzu ban san ta yaya zan fara wanann hakuri ba ,saboda abinda nakeji yanzu da can ban ji rabinsa ba . 

    Bahijja ni masoyinki me,me yasa zaki hana ruhinki abinda yake bege? Me yasa za ki cutar da mu ki kuntatawa zuciuar mu?

    Muryarta na rawa tana kuka ,ta ce.

    " Deeni saboda ina tsoro. Ina fargaba da tsoron son da nake maka,so ne mai yawan gaske ,son da yafi karfina,son da ya tilasta mini mika wuya ga soyayyarka,so mai radadi da ciwon gaske. Ina tsoro Deeni idan duniya ta raba ni da kai fa ? Ba zan iya wata rayuwar jin dadi ko sukuni ba tare da kai ba . Ina tsoron idan na bata makafa na ki aurenka saboda wasu dalilai da nake ganin zasu iya hana mu kasancewa tare ? Deeni shekaru uku na baka kai saurayi ne,ni bazawara ce,iyauenka ma ba zasu amince ba,nima in nayi haka ban maka adalci ba . Budurwa ya kamata ka nema ka aura ku more rayuwarku tare ""

     ""Bana son budurwar,ke nake so. Bahijja ke nake so ,ko shekara nawa kika bani ke nake so ki zama abokiyar rayuwata. Iyayena ba ruwansu da aurena,wacce nake so ita zan aura,kuma zanyi alfahari da auren mace irinki."

  " Deeni ina tsoro"

   Ta fada cikin murya dishasshiya.

    Ina tsoro Deeni,so na kake ko kuma ina cire maka keawar Farida ne ? Ina tsoron wataran kaji kana bukatar auren budurwa i dont want to rubish myself wato bam son wulakanta kaina,bana so ka aureni saboda ka rasa Farida ne ".. 

  "Ba haka bane Bahijja ,ke kika ja hannuna kika sa ni mancewa da Farida da soyayyarta"

    "Wanann gaskia ne,amma soyayyar da nake miki na faara ta ne lokacun da soyayyar Farida ta kare a zuciyata,ki yarda dani ba Farisa a zuciyata ko kadan..

    Farida matar wani ce,uwar wasu ce,na shafeta a babin rayuwata,SHAUKI NA YA SAUYA tun tuni,idan kika rabu dani akan haka ba ki min adalci ba,kuma zaki kuntata rayuwata,kyautar da kika mun na farin ciki a rayuwata za ki kwace shi. In kika yi haka za ki kuntata mana duka..

    Ki tuna kece me fadakar da mutane akan wanann matsalar,yanzu kuma da yazo kanki sai ki nemi kauce masa ? Bahijja ina sonki,kina sona? 

   Girgiza masa kai tayi alamar eh hawaye na zuba,ta kwantar da kai tana kallonsa tana jin sonshi kamar zai hallaka ta,wani so da bata taba sanin akwai irinsa ba. ..

     Ra ce,"Ina sonka Deeni so na sosai,ina kishinka,ba zan jure ba nan gaba in ka auro wata,saboda wani na kasu ko gazawa a tare da ni,Deeni bakin ciki zai kasheni a wannan ranar.."

    Durkusawa yayi a gabanta yace ...

   ""zan miki alkawari yau,ina kin yarda dani?

    Ta girgiza masa kai.


   "Na baki kyautar kaina ke kadai,ba zan taba auren wata wai don saboda una bukatar budurwa ko don kina bazawara ba,idan na same ki MISBAH bana bukatar wata mace..""

    Ya jawo diary din,"Gashi a rubuce ,ni Deeni mallakin Bahijja ne ita daya kawai👌🏼👌🏼👌🏼👌🏼👌🏼👌🏼..................Gaskia yau na rubutu,,sai bayan sati daya nida kuma yin posting😒😒😒ina jin wata ce tamun baki ,na dingi rubutu kamar an aiko ni wlh....


SUMY LUV😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Written by SA'ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by  SUMAYYA SA'AD❤❤
47


Kallon shi take tana jin wani nutsuwa a ranta,yadda dai Deeni ta amince masa tasan mutum ne da yake yin abinda yace,haka soyayyar sa ba karya ba yaudara,mutum ne mai gaskia da nagarta.

   Tayi masa murmushi ,"Deeni ,ba sai ka rubuta ba,na yarda da kai,nima wanann halayyar taka ita taja hankalina gareka har na saki jiki da kai muka shaku. Sai dai nima zan rubuta maka na amince maka Deeni ka auri ko wacce irin mace a duniya in kana so,amma banda mutum daya FARIDA wacce nasan ka daina sonta,kuma matar aire ce. Amma ita ce mave daya da nake kishi a duniya,nake jin zafin kishinta a raina ,saboda nasan irin soyayyar da ka mata ba na wasa bane. Idan kuwa kaddara yasa ka aureta to duk hukuncin da na yanke zaka amince da shi.."

   Ya yi murmushi,"Bahijja na haramtawa kai farida tun lokacin da ta zama matar wani,ba ciwon sonta na yiwa jinya ba sai ciwon Cin amanar da suka min. Amma duk da haka don ki samu kwanciyar hankali na amince.

  Tayi masa murmushi me cike da kauna tana masa kallon so ,ta ce,

   Deeni komai kake so matarka ta maka zan maka shi a rayuwa duk dadinsa ko wuyar sa ""

     " Ina da yakini akan haka Bahijja,kuma nima zan miki duk wani abu da mijin kwarai ,uba na gari ga 'ya'yanki MISBAHna,Abokiyata,matata."

    Dariya sukayi duka,sun jima suna hira sannan sukai sallama da kyar kamar ba zasu rabu ba.

 

     Soyayya mai tsafta da tsananin shakuwa ya kullu tsakanin Deeni da MISBAH,dukkan su suna son juna sosai so mai ban mamaki,dukkunsu kowa na aikin sa,sai dai wanann bai hana su bawa juna lokaci daga gidan gonar Deeni zuwa asibitin Misbah ba,nisan sa bai wuce tafiyar kafa ba.

    Haka wata rana Deeni zai bat abinda yake ya je wurin Misbah yana kallonta daga nesa ko da bata sani ba baya gajiya da kallon ta,haka kullum sonta karuwa yake a ransa. Tana masa wani irin kwarjini,ya dinga jin sonta yana tsuma shi,yana godewa Allah da ya hada shi da MISBAH ,yana godiya da wannan shauki nata da yaje ji,fatansa da burinsa Allah ya bashi 'ya kamar MISBAH...... 


    Ta bangaren Bahijja lokaci gida Deeni ya canja rayuwarta,ba ta taba zato ko tsammanizata tsinci kanta a wannan sabuwar rayuwar ba. Wani lokaci inta tuna irin soyayyar da take yiwa Deeni hankalinta na tashi saboda nata tsoron kar wani ya shiga tsakaninta da Deeni,don kuwa tasan tabbas bazata iya rayuwa ba Deeni ba. Don haka kullum tasa goshinta a kasa tayi sujjada sai ta roki Allah da ya mallaka mata Deeni matsayin abokin rayuwa ,ya mallaka mata deeni da zuciyar sa.


     Zaune take a office dinta idonta rufe ta tafi wani duniya tana hango rayuwar da za suyi da Deeni,tana jin son shi na tsuma ta. A lokacin ya shigo ya harde hannu a kirji yana kallonta yana murmushi,yana jin wani irin dadi a ransa.

     Kamshin turaren sa mai karfi da dadin gaske ya dawo da ita hayyacinta,ta bude ido ta ci karo da fuskar sa yana mata wannan murmushin nasa da take so fiye da komai a rayuwa...

   Itama murmushin ta masa ta zuba masa nata many manyan idanun ,ta ce...

   "Har sakon zuciyar nawa ya isa gare ka ? 

Ya fadada murmushinsa,yace ,"Wannan idanu suna kasheni da yawa ,suna tsumani ,suna gigita ni."

    Nan ta sake lumshe masa su ta kuma bude su,sai da wani abu yaji ya tsirke shi har tsakar kanshi,yaji wani irin tsananin kaunarta da sha'awarta mai karfi yana shigarsa. Zai yi magana yaji muryarsa na shakewa,da kyar ya iya furta maganar...

     Bahijja lokaci yayi da zamuci moriyar soyayyarmu,Bahijja ina bukatarki kusa dani,ba zan iya jure yin nesa da ke ba. Ina zaune yanzu fitinar sonki ya hana ni sakat ,na rasa sukuni ,na rasa inda zan sa kaina ..

    Mayiwa baba. Waya nace masa Baba zan yi aure ,ya ce in kawo duk mayar da nakr so a duniya zai aura min ita,na ce masa na samu mata,na samu uwar 'ya'yana ,Doctor Bahijja,Abokiyata kuma likita ta. Ya taya ni murna ,ya min alkwarin mallaka myn abinda nake so ko menene shi indai bai fi karfinsa ba.

  Na ce masa bana son komai sai Bahijja 'yarsa ce,shi babanta ne,'yarsa nake so ya aura min. Na masa alkawarin rike masa ita da amana,don haka yau mamanki da babanki zasu tambayeki wa kikeso? Ina fata zaki fito musu da gwaninki..

       Kalamansa sun ratsata,kuma sun mata dadin gaske,wanda bata san yaishe ta fara hawaye ba. Tun tana 'yar karama take buri da sha'awar ta ga soyayyar uwa da uba,ta ga kauna da gata daga iyaye kamar kwacce yarinya ,amma ta san wannan burin nata ba zai taba cika ba. Muslihu ya so ya cika mata wannan burin ,sai dai hakan bai samu ba...

    Bata san yaushe ta kifa kanta bisa hannayensa ba tana kuka..

    "" Deeni ka gama min komai a rayuwa"""

    ""Burina kenan Bahijja in faranta miki,inga na cika kowanne irin buri naki karami ko babba,duk da ke din ba mai buri bace."

      ""Burina guda in mallaki Deeni da zuciyarsa "

    Yayi mata murmushi,"Burinki ya cika my dear,ina jin dadin yadda kike sona Bahijja ,yadda kike nuna damuwarki da kulawarki a gareni.. Ina bukatar wannan har karshen rayuwarta..""

   " kasamu Deeni,soyayyata da kulawata naka ne"

    Yayi murmushi ,"Nagode ,anjima Mama zata zo ta tafi da diyarta gida don mata shirye-shiryen aure,saura kadan Abokiyata ta zama amaryata..""

    Murmushi tayi tare da boye fuska saboda kinya ,musamman da ta ga irin kallon da yake mata.......  ****        ****      ****


 Da yamma Mama ta zo ta tafi da Bahijja tare da Baba Andi can gidansu Deeni,duk da tana jin wani iri da nauyin Mama amma ta daure sabodaDeeni..

    Mama ta lura da haka,don haka tayi kokarin kawar mata da nauyin da take ji,ta ce.

      "Bahijja ke diyata ce,soyayyar da kike wa Deeni shima yake miki ya sani sonki da kaunarki kamar 'yata. Ina godiya ga Allah da ya kawo ki rayuwar Deeni,don haka saki jikinki nan gidanku ne,zan miki duk wani abinda uwa zata yiwa diyarta ko shakar haka kar kiyi..""

   Alhaji ya shigo yana jinsu ,shima ya matso ya ce.

   Haka zan miki duk abinda amahifi zai yiwa 'yarsa Nsha Allah""   

    "" Na gode Baba "

     Ta fada kai sunkuye yayin da taji hawaye na kokarin ciko idonta,wani feelings ne da bata taba jin irinsa ba,wani irin farin ciki na daban taji yana ratsa ta.. 

     Allah abin godiya ,Allah mai kyauta da kari,ya bata miji da iyaye lokacin da bata zata ba balle tsammami....

      Alhaji ya zauna gefen Mama ,ya ce,"Bahijja wane lokaci kika ga ya dace mu tsaida ranar aurenku?

    Kanta sunkuye tace,"Baba ai ku iyayena ne,duk ranar da kuka ga ya dace ku ka tsayar dai dai ne.." Alhaji yace ,"To Allah ya miki albarka,ina so zan hada airen ku tare da lukman ,shima ya samu matar sa,sai mu hada muyi nan da sati biyu masu zuwa. In mun hada ku mun hutar da 'yan uwa masu zuwa daga nesa sau biyu,tunda mun shirya sai mu hada""

     To Baba ,tafada kai sunkuye.

   "To Allah ya miki albarka."

  Nan ya mike ya fice,mama ta kalleta ta ce, 

   "To diyata zata zama amarya sai an bawa asibiti hutu ko saboda a bawa jiki hutu da nutsuwa""

    Tsananin kunya yasa Bahijja kife kai,Mama na dariya ta ce.

   "Na fada miki ni mahaifiyarki ce.."

   Deeni dake tsaye yana kallon su ya tsinci kansa cikin wani irin tsananin farin ciki da jin dadi ,son mahaifan sa da kaunatsu yaji yana kara kardi a zuciyarsa.

     ""Zan mallaki Misbah na nan da sati biyu Nsha Allah."


A sati biyun nan mama tayi hayar masu gyaran amarya na musamman suka sa Bahijja gaba da gyara baji ba gani..

    Mama ta fahimci nauyinta da Bahijja ke ji,wanann yasa ta damkata a hannun masu gyara da kuma aminiyarta Haj. Amina da tazo bikin da kanwarta...

   Ya zame mata dole tayiwa matar Deeni gyara,Deeni gudan zuciyarta ne,zata iya komai don farin vikinsa,tunda Bahijja ce farin cikin Deeni ba zata yi wasa da ita ba...

   Lokaci guda Bahijja ta canja,rayi wani irin kyau da haske me ban mamaki ,ta dawo tamkar wata Balarabita,duk inda ta wulga sai kaga tamkar anyi walkiya saboda tsabar haske da kyau da daukar ido da take ...

    Deeni ya kasa daga ido akanta duk inda tabi yana binta da idanunsa,yana jin alfahari da samun mace irinta. Tabbas Bahijja ta ishe shi har iya karshen rayuwarsa,bashi da bukatar wata mace ......


    Ana saira kwana uku biki 'yan uwa da abokan arziki suka cika gidan wanda musamman Alhaji ya tura ticket na jirgi wa mutanen gombe da kaduna don zuwa bikin dan gatansa. 

     Daya bangaren na gidan aka warewa baki,yayin da bangaren su Hajiya sai aminiyarta da kanwarta tare da su farida da mahaifiuarta.

    Dakin Deeni shi ua koma dakin Bahijja shi kuma ya koma gidansa na farm house sai dai kullum yana makale tsakanin idonsa kan Bahijja ,bai iya jure rashinta ko na kankanin lokaci...

     Bahijja ta kasa gasgatawa kanta sabuwar duniyar da ta tsinci kanta,gata da kauna da take gani gun mahaifiyar Deeni da 'yan uwansa kadai ya isheta farin ciki,ballantaan kuma uwa uba Deeni..

 

      Bayan sallar juma'a jama'a  da dama suka shaida daurin aurwn Deeni da Bahijja ,aure yayi albarka,dumbin jama'a ne suka cika a daurin auren. Bayan nasu aka daura na lukman da Amaryarsa Abida,duk a masallacin juma'ar unguwarsu aka daura...

  Bayan daurin aure Mama ta shirya walima ta musamman ,abinci ba irin kalar da babu tun daga gargajiya har turawa. Wajen ya tsaru soaai,an gayyaci malamai mata masana da kuma 'yan uwa da kowa in ya ci abinci ya tofa albarkacin bakinsa.....
Ina kuke FANS din Dr Deeni Da Dr Bahijja 🗣🗣🗣🗣ranar da kuketa jira yau gata ta zo.......   


SUMY LUV😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬

Written by  SA'ADATU WAZIRI GOMBE

Copied by  SUMAYYA SA'AD❤❤
48Haka a wajen Alhaji ya shirya nasa da maza abokai da yan uwa a waje,kowa ya ga Deeni wannan rana yasan yana cikin tsananin farin ciki. Wannan ya kara kayatar da kyan fuskar sa.

     

   Cikin gida a daki Bahijja  ta sha kwalliya da gayu sosai,duk da shiga mai sauki tayi,doguwar riga mai tsadar gaske ta sa wanda Mama tayi mata order daga Dubai. Blue ce ammata kwalliya mai sauki da fararen duwatsu,ya matukar karbar fatarta mai haske ,haka ya dad fito da kwalliya fuskarta. Ta tufke gashinta baki mai tsayi da sheki tare da lulluba gyalen rigar ,ta sa cover shoe masu tsadar gaske da ya yis shige da irin dressing dinta,ta sa bracelet mai saukin kwalliya tare da zobuna guda biyu wanda suka yi matukar kayatar da dogayen yatsunta.

    Bahijja macece doguwa mai kyakkyawar kira,shigar da tayi tai matukar kyau da bata taba ganin tayi ba ,sai kamshi take.

    Mama ta shigo ta ganta ita kanta tayi bala'in mata kyau,ta dinga ganin duk yawan taron nan ba kamar surukarta Bahijja ,tabbas ta amsa sunanta matar Deeni.

      Tayi murmushi,"Tabbas diyata tayi kyau"

   Tace,"Bari inje zan turo wacce zata zo ku tafi tare wurin walimar,duk an gama taruwa"" 

   Ita dai Bahijja kanta sunkuye har mama ta fita,shuru taji gidan yayi alamar duk an fits wurin walima. Tana nan zaune shiru zuciyarta cike da tunani kala kala taji motsin shogowa. Kamshin turarensa ya tabbatar mata da Deeni ne ya shigo dakin,nan tayi saurin daga kai suka yi ido biyu,yana mata wannan  murmushin..

   Ya zuba mata idanu,itama ta kasa dauke idonta a kansa,yayi mata kyau sosai. Sanye yake da blue shadda kalar nata kayan ya sha aiki,shigar ta matukar masa kyau. Hular da ya kafa a kansa ta kara fiddo da kyan fuskarsa,gashin kansa kwance irin na fulani sak,ga sajen da ya karawa fuskarsa kwarjini da annuri...

     Ji tayi tamkar ta je ta fada kirjinsa ta kwanta,amma sai ta kasa saboda kunya duk da yana mijinta. Shi yasa hannu ya jawo hannunta yana wasa da 'yan yatsunta,tsigar jikinta taji tana tashi tana jin sonsa da shaukinsa yana ratsa jijiyoyinta,yana bin jikinta.

       " Haba MISBAH na ,ya zaki kawar min da fuska,amaryata ki tuna fa ke halal dina ce yanzu,baki san irin jin dadi da tsananin farin ciki da fuskarki ke sauke mini bane da baki kawar da kai gare ni ba . A yau sai naji soyayyarki ta zama sabuwa ,ta zama danya sharaf a zuciyata. Toho gareni,please Bahijja ko zan samu nutsuwa.."

   A hankali cikin nutsuwa ta matso gare shi ya jawota jikinsa tare da bata kyakkyawar runguma,tuni ta bace a cikin jikinsa,suna manne da juna tare da jin irin son juna da sha'awar juna..

      Cikin muryar rada yake mata wasu irin kalaman soyayya masu ta da hankali da tsuma zuciya da ruhinta.

     Nagode Bahijja da soyayyarki,wannan shi ne (the most beatiful moment of my life)..

   Rufe ido tayi jin kalaman sa na ratsa ruhinta,tana shakar kamshin sonta tare da fadin.."Deeni ina sonka ,kai nawa ne ni daya,mallakina ni daya.."

    Haka ne Bahijja ni naki ne ke daya kamar yadda kike ke tawa ce ni daya,bana taba hada ki da kowacce mace a duniya,haka ba zan taba hada soyayyarki da kowa ba""

     Sun jima a cikin wannan halin na tsananin shauku da son juna..

     

    A hankali ta turo kofat tayi sallama amma shuru,hakan yasa ta kutsa kai,Farida kenn..

    Gabanta yayi mummunan faduwa ,ya dinga bugawa da karfi ganin Deeni da Bahijja a hakan ya mummunan daga hankalinta.

      Wani irin masifaffen kishi taji yana turniketa,masifaffen kyan da ta ga sunyi da Deeni da Bahijja ya razana ta tamkar dama an halicce su don juna ne. Tsohuwar soyayyar sa taji ta taso mata ta kasa gani da jure soyayyar  da taga Deeni yana yiwa Bahijja wanda ita duk tsananin soyayyar da suka yi a baya ta dinga gani kamar wancan soyayyar wasa ce..

      ''Ya za'ayi Deeni yaso wata mace a duniya fiye da ita?  Ya za ayi Deeni ya ci amanar kauna? (Readers kuji fa karfin ) Na zata Deeni zai yi aure ne ba don soyayya ba sai don raya sunnah kamar yadda nayi,ya za'ayi Deeni yaso wata fiye da ni ? Har yau ban taba son wani fiye da shi ba ,duk da nayi aure na zama uwa amma soyayyarsa bai taba barin zuciyata ba ko na second daya. Ya zanyi in rayu da wannan bakun ciki da bacin ran da na gani yanzu. ???(To jama'a farida na tambaya)....

   Nan ta sake daga kai ta kalle su,har yanzu suna wata duniyar . Ta kalli kanta ta kalli Bahijja sai taga ta mata nisa,ta mata fintinkau nesa ba kusa ba...

   ""Shin ni ya akayi na kasa hada Deeni da kowanne irin namiji a duniya ?  Tabbas saboda Allah bai taba hadani da namijin da ya kaishi bane,yayin da Allah ya hada Deeni da macen da ta fini."

   Kau da kai tayi taji hawaye na zuba mata,tsananin kishi da son Deeni taji yana shigarta,ta macen da abinda ya kawota,ta mance da cewa ita matar wani ce,uwar wasu ce....

   Karar wayarta ce ta dawo da su hayyacinsu duka,nan tayi saurin share hawayen yayin da Deeni da Bahijja suka ganta bazata a gabansu..

     Ras !!! Bahijja taji gabanta ya fadi,ita ma din kishin farida taji ya shigeta,har yau in ta tuno irin soyayyar da Deeni da Farida sukayi sai taji hankalinta ya tashi...


     Deeni ganin Farida a gabansa bazata tana kallonsa tamkar ta hadiyeshi yasa ya ji ya shiga dan rudani,musamman da ya san yadda Bahijja take da kishin Farida a zuciyarta,duk da ya sha nuna mata cewa Farida ba ta gabansa yanzu,amma ta kasa fahimta. Sam ko kadan babu ita a ransa,amma ya rasa dalilin da yasa yaji ya wani irin rudewa a wannan lokacin...

     Bahijja na kallon irin rudewar da yayi yasa taji ranta ya mummunan baci,hankalinta ya tashi .

     Dukkan su idon su ya rufe da wani irin kishi,musamman irin kallon da Bahijja ta ga Farida na yiwa Deeni. Yayin da Farida ta dinga jin kishin irin kallon da Deeni ke yiwa Bahijja...

    Nan faridan ta daure,tayi dariyar yake ,ta ce....

      ""Ango da Amarya ,ina tayaku murna,Allah ya bada zaman lafiya.."

    Bahijja bata iya ta amsa ba,sai Deeni ne ya amsa a takaicw,yasa kai ya fita..

    Farida ta kalli Bahijja tace,"Amarya,Mama tace in fito da kee ana jiranki wurin walima""

    Girgiza kai tayi dakyar ta cije tayi dariyar yake,ta fito suka jera tare..


     Tunda ta fito idon kowa ya koma kanta ta fito ta haska wajen gaba daya kowa sai albarkacin bakinsa yake fadi,Mama kanta ta kasa hakuri ,ta taso da fara'arta ta zo ta kama hannun Bahijja ta jata gun zamanta. Wannan ya kara bakanta ran Farida,har agun mama ma Bahijja ta ture gwamnatin ta ...

     Wani hawayen bakin ciki taji yana zubo mata ,wurin walimar da bata zauna ba kenan,ta juya ta koma ciki,har aka tashi daga walimae bata dawo ba....


         Ranar lahadi jamaar biki kowa ya watse ,yayin da ranar lukman ya tare da amaryar sa a gidansa da mahaifin su ya bashi,yayin da Shamsuddeen ya koma saboda aikin da ya bari a kamfaninsu na kaduna. Farida kuwa da yake ana hutu da yaara za su zauna su yiwa mama hutu...

    Mama ta shiryawa Bahijja da Deeni kayansu,siyayyar da ta musu na kayan sawa da sauran su ta sa a mota ta tura tare da baba andi taje ta shirya musu.... 


    Gidan yayi tsit ba kowa daga Farida da yaranta,sai Deeni da Bahijja wanda suma suna shirin tafiya nasu gidan....


   Alhaji ne ya kira Deeni da Bahijja falo suka same shi yana zaune shi da mama ,nan suka nemi wuri suka zauna.

     Alhaji yayi musu nasiha da fada sosai tarw da musu fatan alkhairi haka mama ta kara damka musu amanar juna tare da musu nasiha da cewa siyi hakuri da juna,zo mu zauna zo mu saba..

     Alhaji ya mika masa key na gida.

ya yi murmushi ,"Nagode Baba,mallaka min Bahijja da kayi matsayin nata ta kadai ya ishe ni babbar kyauta. Ka mata waliyyanci,ka zama mahaifinta,yayin da Bappah ya min waliyyanci. Na gode da amanar yarka da ka bani Baba,ina da gidana nallakina na godan gona wanda ka taimaka min na kafa shi,haka Bahijja tana da gida,zamu zauna a duk wanda muke so. A  halin yanzu rayuwar mu soyayyarmu ,ayyukanmu,gidajen mu da dukiyoyinmu suna hake ne. Baba,Mama,mun gode ,kuyi ta mana addu'a,muma zamuyi ta muku.."

     Dariya sukayi yayin da yace,"Allah ya muku albarka Deeni"

  ""'Ameen  """.

    Suka amsa a tare ,sannan sukayi sallama da su mama ta raka su har bakin mota ita da Bahijja kamar ba zasu rabu ba.

    Wannan soyayya da shakuwa na Bahijja da Mama ba karamin dagawa Farida hankali yake ba,sai tana ji kamar ta zama ita bata da mihimmanci..

    Tabbas daga Farida har Bahijja suna fama da kishin juna da ke tsananin cin su a zuciya..

    Kai tsaye suka wuce gidan Deeni ,wanda ya ra tsara musu shi sosai,kana shiga gidan zaka fahimci gida ne na masu ilimi daga bokin har addini...

 

    Tun a mota Deeni ya lura da Bahijja bata magana,duk kokarin da yayi don ya takaleta amma bata kula shi ha,shima sai ya nuna mata halinsa,ya dage kai ya kyaleta..

   Addu'a tayi sannan ta sa kafarta a gidan ,wani irin kamshi taji yana tashi mai kwantar da zuciya.. Ta lumshe ido tana shaka,nan take taji hankalinta na kwanciya ,fushin nan da take taji yana sauka. A hankali ta dinga bi tana zaga gidan ,Deeni ya bita danido zuciyarsa cike da sonta da sha'awar ta.

    Ko ina ta gama zagawa yana biye da ita,ta dawo falo ta zauna,nan ya jawo kujera ya zauna a gabanta yana kokarin su hada ido amma taki. Ya yi murmushi ,yace..

    Haka kawai Amarya taji bata son sakar min fuska a daren mu na farko a gidan mu ?

   Zuba mata ido ya yi yaji kamar yanzu ma ya fara sonta..

   Ina sonki Bahijja soyayyar da ban san irinta ba,komai kika yi a rayuwa sai inga ya miki kyau. Wannan kamshin da ake sha min ma sai naga ya miki kyau,kin kara burgeni"".

    Nan ya sauko yasa kanshi bisa cinyoyinta ,ya jawo hannayenta kansa.

     MISBAH na meye ya dame ki ?

   Ta kwantar da kanta akan nasa suna manne da juna ,ta ce.

    (My dear nice house)".

   Ya yi murmushi ,yace. Na tabbatar u will be a good home maker?" 

   Nsha Allah"Ta amsa.

  "Deeni ina sonka"

    Ta fada tamkar meyin rada a kunnen sa,yana jin muryarta na ratsa shi,yana jin tsigar jikinsa na tashi ,tsantsar sha'awarta cike fal zuciyar sa.

    ""Bahijja ki kasance dani har abada karki kyale ni,ki cika min gida da irinki da alnarkar ki,ki cika min gida da yaranki,zaki sani farin ciki sosan gaske""..

   "" Komai kake so zan maka Deeni,,Allah ya bani yaran da zan cika masu. Nima ina addu'ar Allah ya bani irin Deeni,Allah ya bani ikon sanya ka farin ciki da kyautata maka,Allah ya bani juriya akan ka Deeni..

   Ina maka wani so Deeni,gashi dai ka zama nawa amma zuciyata na cike da tsoro da fargaba."  

      "" Kar kiyi fargaba Bahijja,ni naki ne ""

   Bai ankara ba sai jin hawaye na zuba masa yayi Saurin dago ta hankalinsa a tashe..

    My deae mene ne ??

 Idonta jawur ta kalle shi,"ko zaka iya fassara min rudewar da kayi lokacin da kaga Farida ??? Na mene ne ??  Don kaji tsoro masoyiyarka ta gannu a manne da juna ko kuma ka rude ne saboda ka ga tsohuwar masoyiyarka ???Tofaa!!!! Ango kaka-kara   kaka.........

SUMY LUV😍😍😍😍

👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬MISBAH👩🏽‍🔬👩🏽‍🔬


Written by  SA'ADATU WAZIRI GOMBE

=================== GIDAN NOVELS ====================================

 Assalamu Alaikum

    Yan uwa a wannan page din nake tunanin zan kammala littafin nan part 2 wato kashi na biyu insha Allah...

Wanda kuma a nan nake tunanin dakatawa zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.......

    Idan da me korafi nasan dayawa sunada contact dina,,,so se yayi pinging dina.....tnks 

    
49
Zura mata ido yayi cike da mamaki,"Haba Bahijja,ban zaci haka daga gareki ba,wannan halin na zace shi ne daga halin wata me kasa da shekarunki, (me matured)" 

    Ranta taji ya mummunan baci,ta ce.

   I will not be ,me kake nufi? Me yasa kake avoiding tambayata ? Ka fada min wane irin rudewa kayi don kaga Farida. ??

      Ranshi yaji ya baci,amma sai ya daure ya ce.

     Ke kinga ya dace mu zauna muna bata lokacinmu a irin wannan lokacin akan wannan maganar marabtushe ko kan gado ? Me ya kawo maganar Farida tsakanin mu a yanzu ? 

    "Akwai abinda ya kawo,ka ban amsa,me yasa mijina zai rude don yaga tsohiwar budurwarsa ?

    For God sake!!Farida matar wani ce,uwar wasu ce,saboda mene ne zaki ta da min rigima yanzu ? Har sau nawa zan fada miki cewa bana son farida,na manta da farida. In ada baya can na so farida laifina ne da za ki dinga daga min hankali akan farida? Haba Bajijja ,a yau zamu fara sabuwar rayuwa,ya zaki bari wani dalili mara tushe ya nemi kawo mana matsala ?

   To naji ya ishe ni haka, kiji kiyi tunanin duk yadda ki ka ga dama ,na ganta na rude sai yaya ?""

     Cikin zafin rai da bacin rai yake maganar wanda ya kara tunzura Bahijja,ya kona mata zuciya. Ta fashe da kuka ta nufi daki ta rufe ....

    Bai yi yunkurin binta ba don shima yana cikin zafi,ya zurawa abubuwan da ya shigo musu dashi na ci da sha  ,duk ta daga musu hankali har ya ji bashi da sauran sha'awar cin wani abu.

    Kukanta yaji yana matukar daga masa hankali,ga sonta dake kara ruruwa a cikin zuciyarsa,amma zafin zuciya ya hana ya bita dakin balle yayi lallashi. Haka  ya dinga kaiwa da kawowa cikin dare,ya rasa me ke masa dadi,haka suka kwana baran-baran a darwnnsu na farki..

    

   Ankira sallar asuba yayi alwala ya murda kofar dakinta,ga mamakinsa bata sa key ba ya sameta zaune kan sallaya. Bai ce mata komai ba ya fice zuwa masallaci,ya dawo ya nufi nasa dakin ,duk da ya kwanta ba bacci kirki amma haka baccin ya gagare shi..

     Karfe takwas na safe ya fito falo,anan suka yi kicibis sanye da hijabinta...

   ""Ina kwana?"" Ta fafa tare da kau da kai 

   Bai amsa mata ba ya sha gabanta ,tayi saurin kaucewa ta kama hanyar fita..

   "Ina zakije ? Ya fada cikin daga mirya.

    Gidana zan tafi".ta bashi amsa a takaice.

   Da izinin wa ? Da yardar wa ? Karki manta baki da gidan da ya wuce wannan,sannan fita a gidan nan ba da izinina ba,kar ki sake wanann kuskuren....

    Ya fada cikin tsare gida ,fuskar sa ba alamar wasa,ya juya..

    Wani iein bacin rai da takaici taji ya turnike ta,ta juya ta nufi kicin ranta bace ta dinga kaiwa da kawowa ,gata ba gwana ba wurin girki,da kyar ta samu ta hada masa patatos da source tare da yanka fruit da fresh juice da kuma ruwan tea a flask tare da sauran kayan tea ta jera kan dining table..


    Yayin da Deeni yake kaiwa da kawowa ,sam baiji dadin yadda ya mata ba,to amma yana da matukar muhimmanci tasan cewa shi mijinta ne,aure sukayi ,ba zata yi yadda take so ba. Haka nan zafin zuciya da jin kai ya hana shi zuwa ya lallasheta,don shi gani yake bai mata laifi ba..

    Bahijja na shiga daki ta fashe da kuka,nan ta dauko diary din nan cikin jakarta ta rungume tana kuka...

    Hankalinsa ya kasa kwanciya har sai da ya bita dakin ganunta rungume da diary din tana kuka sosai ya taba zuciyarsa. Abu biyu ne suka hadu masa,tsananun sonta da tausayinta da kuma wani zafin kishi,saboda yasan me ke cikin wannan diary din .

   Nan ya daure ya isa gareta ya jawota jikinsa,nan ta hau kokawar kwace jikinta amma bata yi nasara ba. Ya rufeta ruf kan faffadan kirjinta,ga turarensa mai hade da kamshin sin sa da ke ratsa ta ,yana kashe mata jiki,kawai ta fashe masa da kuka..

  ( I'm sorry my dear)nayi laifi kiyi hakuri..

  Ya fada cikin murya mai taushi da lallashi. 

   Bahijja hawayenki da kukan ki yana daga min hankali fiye da komai,kin san yadda nake matukar jinki a raina ,kin san yadda jiki da euhina tare da zuciyata suke tsananin sonki ,please Bahijja kar ki daga mana hankali daga ni har ke.

Ba mai samun farin ciki a kan wannan halayya taki na kishi (I'm sorry l hurt you).

      Bahijja da ina da ikon share baya da na share,amma bani da wannan ikon,abinda zan iya shi ne yanzu-yanzu kuwa da nan gaba duk kece.

   Bahijja ina so kamar yadda kika taimaka min na manta baya na cigaba da rayuwata ina so ki taimaka ki bani hadin kai ,mu shirya rayuwarmu mai cike dab tsabtatacciyar soyayya da fahimta tare da kula da farin cikin juna...

     Ina so ki sani kina da matukar muhimmanci a rayuwata,please dont make me hurt you again.."

   Ta fashe da kuka,"Deeni na gaza ban san mw yasa na kasa jurewa ba,ban san me yasa nake jin tsananin kishin Farida ba ,duk da na sani matar aure ce,matar dan uwanka ne,uwace. Deeni ka taimake ni,zan iya jure komai anma banda wannan.."

    Ta dago dara-daran idanuwanta wanda sukenrine,suka dawo ja,hawaye na zuba wanda yanayinta ba karamin tsuma shi yayi ba,ta ce ,

    ""Deeni kasan ina sonka ko? Ina sinka sosai "" Ya girgiza mata kai yana jun tamkar ya hadiyeta don so ,ya ce.

    Nima ina sonki Bahijja kin san haka kuma. Ina sonki"

   Ta kankameshi ,"Nasani Deeni ,"please ka kula dani..

   "Zan kula da ke Bahijja na,bari ma in fara daga yanzu."

   Nan yasa baki yana lasar hawayenta tare da bin fuskarta,kan idanunta zuwa wuyanta yana sumbata. Haka ya dinga bin jikinta.

      Wani irin abu taji yana zaga jikunta har zuwa tsakar kanta,yayin da ta dinga jin wannan kuncin yana barin zuciyarta,sai tsananin so da shaukinsa,taji zuciyarta ta wanke tas. Nan ta biye masa itama ta ramawa kura aniyarta..

   Sun jima manne da juna sannan ta zame jikinta a hankali ta nufi bayi don shirya masa ruwan wanka,yayin da Deeni ke kwance idonsa jawur,hankalinsa tashe.. (Deeni dai ba wanka yakeda bukata ba🙈🙈🙈🙈🙈🙈sry anty zee karkice banda kunya)..


   Kwarai ya so kasancewa tare da ita yau,sai dai kasancewar Bahijja na farko ya zamana a wuri na daban lokaci na daban.......

   Karfe goma mama ta turo musu da break fast kala-kala,sannan tayi waya suka gaisa ta kara da cewa su shirya jirgin su zuwa kasa mai tsarki,wato saudia. Karfe sha biyu ne wanda ta biya musu suje suyi Umra su kara yiwa Allah godia tare da yin addu'o'i,sannan daga nan in suna so su wuce duk kasar da suke so su zaga duniya har na wata guda ,sannan su dawo.


*****     *****     ***** 


A kasa mai tsarki Deeni da Bahijja suka san sirrin juna,suka zama abu guda,,suka barji gumin juna. Kwarai sun more rayuwar su yadda ya kamata ....

    Bayan sun gabatar da idabar su ta Umrah tare da yin addu'o'in su,nan suka ci gaba da gudanar da ibadar su na aure ,sun manta duk wani damuwa da bacin rai da tashin hankali da suka taba fuskanta a rayuwa ,suka bude sabon rayuwa mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali tare da yiwa juna alkawarin kula da juna farin cikin juna da kuma kasancewa da juna har abada Nsha Allah...

      

    Bahijja na da kyau na daukar hankali,kyau mai sa nutsuwa da kwanciyar hankali ga wanda ya mallake ta,yasan sirrin ta,ya dandani zumar ta. Don haka Deeni ya tabbar shi din mai sa'a ne da ya mallaki mace kamar ta...

    Duk inda ake son mace Bahijja ta kai ta kawo,sai dai abinda yake kara jan hankalin sa gareta da kara masa sonta shi ne halayyar ta,hikimar ta da baiwarta. Yadda take kula da shi,take sarrafa shi da rayuwar sa,irin soyayyar da take masa,take kuma nuna masa,ga wata girmamawa ta musamman . Duk da kasancewar ta girme masa amma bata taba nuna masa raini ba,asali ma in ba an fadi ba babu mai cewa ta girme masa,saboda bala'in dacewa da sukayi da juna ...

    Halayyar su ta zo daya,tunaninsu yazo daya,duk abinda daya keji dabshi daya naji da shi. Don haka suke yawan hakuri da juna ,in data ya hau daya na dannewa,sun zauna sun tsara yadda za su gabatar da rayuwarsu cikin soyayya da saukin rayuwa..

     

   Bayan sunyi sati biyu suka bar saudia zuwa Dubai,sun zaga kasashe uku zuwa hudu suna yawon shakatawa da more rayuwar su. Sunyi wani irin sabo da kara shakuwa da juna sosai sosai..

      Sun kasance cikin farin ciki marar misaltuwa ,watansu guda suka tattaro suka dawo gida Nigeria..

      A nan suka tarar da mummunan labari da kuma mummunan tashin hankali na rasuwar Shamsuddeen tare da mahaifin Farida...

     Satin su biyu da tafiya hatsarin ya faru da su a cikin garin kaduna,mahaifin Farida ya je duba Shamsu a ma'aikatar su don ganin ya yake da yadda ayyukan suke tafiya,dama ya saba kai masa irin wannan ziyarar . Anan Shamsu ya bar motarsa a office ya biyo Alhaji Ahmad don dawowa gida tare ,a hamyar su ta dawowa tsautsayi da karar kwana suka hadu da doguwa ta taho ba birki ta hade motoci da yawa tayi barna wasu sunji rauni wasu sun rasa rayukansu ciki har da Shamsuddeen da Alhaji Ahmad wato mahaifin Farida.

    Cikin tashin hankali da damuwa Deeni da Bahijja suka nufi kaduna inda ake zaman makoki....


   Muje ga littafi na uku...DANDANO DAGA LITTAFI NAGABA

 

    kanta sunkuye gaban su ya ce,"Mama ina jinki ""

  Hajia ta kalli Bahijja ta ce,""Bahijja kin tabbar kin amince ina sonki kamar yadda nake son Deeni ko ? Kin dauke ni mahaifiyarki ?

   Bahijja ta girgiza kai,ta ce,"Kwarai Mama,tsakanina da ku sai addu'a ,bani da iyaye amma kun maye gurbin su,tsakanina da ku sai addu'a"

     Mama tayi murmushi ta ce,Alhmadulillah,kamar yadda na rike ki 'yata haka ba riki farida,ina neman alfarmarki bamu hadin kai mu hada auren Deeni da Farida.......🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀🙆🏻‍♀SHIN WANNAN MUTUWAR TA SHAMSU FARIDA AKAYIWA KO BAHIJJA ???????

    SAI NA JIKU

  TAKU HAR KULLUM 


=================== GIDAN NOVELS ====================================

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *