Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, December 2, 2021

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here

JASEENA COMPLETE HAUSA NOVEL

 [3/2, 5:44 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃 JASEENA🦃⚔ 2016

🐚Na Jeeddah jao🏵🐚

                          1⃣⏯5⃣


          Gudu yake kan wani farin doki mai kyaun gaske da ka ganshi kasan a rude yake ,wata mata ce a bayanshi ta ‘kank’ame shi sai zare ido take yi yayinda shi kuma sai ‘kara gudu yake ,da an hau tudu ko tsauni sai matar ta sa ‘kara ta rike ciki da hannu daya, da ‘kyar ya samu wani kogon dutse ya shige ga dukkan alamu Matar na’kuda take yi domin dauke take da juna , ‘karar dawakai da yaji sun tukaro inda kogon yake yasa ya toshe wa Matar baki da hannun shi ganin tana kuka duk jikinta yana b’ari ,mutanen suka gama dube -duben da zasuyi sai wani daga ciki yace “sun yi nisa sosai!! Mu koma kawai ,a lab’en da suke babu wanda ya motsa har mutanen suka tafi sannan ya cire hannun shi daga bakin Matar da tuni na’kuda ya zo mata gadan-gadan, Allah cikin ikonsa ya jiyo ‘karan ruwa daga d’ayan ‘bangaren kogon ya mayafin ta ya nufi hanyar da gudu ,kafin ya dawo ma har ta haifu Yar cikin Jini Kwance a ‘kasa itama uwar haka ,ruwan da ke jikin tsumman ya d’an matsa a fuskar ta ta dan farfado ,shi da kanshi ya gyara yarinyar ya mik’a mata. Murmushi take yi tana hamdala amma hawaye ne zafafa ke bin kuncin ta ,ta sumbaci yarinyar sannan ta rufe idonta hannunta ta sa ta damk’e hannun mutumin wanda da ka ganshi kaga sadauki, tana salati rai yai halinsa.

         🦂wani ‘kara mutumin ya saka wanda duk kogon sai da ya d’auka, ya kifa kai a cikin matar yana ta rusa kuka mai ban tausayi ,idanuwan shi suka rine kamar garwashi ya mik’e tsaye ya d’aga jinjirar sama cikin murya mai firgitarwa yace” masarautar KALAHARI !!! Sai na mayar muku jin dad’i da walwala !! Na lashi takobi!! da ikon Allah sai  JASEENA ta zamo ciwon ido ga azzalumi JALALUD-DEEN!!!!


         🐚 🐚🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🐚🐚

Asalin labarin


         Masarautar Kalahari babbar masarauta ce wanda ake sakota a matsayi na farko cikin jerin masarautu, mai kuma cike da tarihi, mayak’a da kuma kayan ma’adanai na ‘kasa kamar su lu’ulu’u , gwala-gwalai da sauransu. Sarki Hameed shine ke mulkin Wannan masarauta, mutum ne jarumi ,mai tausayin talakawa gashi da kwarjini. Hameed shine d’a na  biyu kuma na k’arshe gun mahaifin su ,ma’ana yana da wa mai suna JALALUD-DEEN ,wanda ya kasance baya son talakawa kuma shi duk abunda zai yi in dai don ya musguna ma talaka ne toh ya fi burgeshi, son zuciya gareshi , hakan ne yasa da aka tashi bada sarautar sai dattijawan gari suka zabi a bawa Yerima Hameed kasantuwar d’abiun sun daban ne kwata kwata JALALUD-DEEN bai chanchanta ya mulki Kalahari ba, a fuska JALALUD-DEEN ya nuna babu wani abu amma dai na ciki na ciki !!domin zuciyar sa tafarfasa takeyi kuma a nan ne ya k’udiri niyyar ganin bayan Hameed !!!


Jeeddah jao🏵

[3/3, 7:07 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵 Jeeddah ja’o🏵🐚


           6⃣⏭1⃣0⃣


Bayan an na’da Yerima Hameed a matsayin sarkin Kalahari sai Jalalud-deen ya fuskanci cewa matar sarki Hameed Sarauniya JASEENA tana dauke da juna biyu hakan ya tunzirashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko baccin kirki bayayi tsabar Kishi domin gani yake yi in har Hameed ya samu magaji to tabbas babu makawa ko ‘kamshin sarautar ma zai daina ji…………


    🏵cikin Sarauniya Jaseena yana wata tara ,haihuwa ko yau ko gobe ,tana zaune cikin dakinta mai cike da kayan ado da k’yal-k’yali sarki Hameed ya shigo ,mutum ne mai tsayin gaske ga haske kyakkyawa ne wanda ba sai na tsaya misalta shi ba haka ma Jaseena kasantuwar a kasar masar ya auro ta , zama yayi kusa da ita yana zolayan ta suna ta hira ,basu ankara ba sukaji ‘kara a waje ,a tare suka mik’e cikin firgici Jaseena ta rike Hameed ta ‘boye ta bayan shi jiki na rawa yayin da shi kuma ya zare takobin shi 🗡ya rik’e yana dube-dube don yaga ko waye zai shigo Kwatsam sukaji an banke k’ofa kamar daga sama mutanen suka yo kansu nan suka kaure da fad’a ,gashi mutanen fuskar su a rufe da kyar ya iya fisge mayafin d’aya daga cikin su ,abun da ya gani ya matuk’ar girgiza shi !!! Amintaccen shi na fada ne Zakar da wasu wanda ya tabbata fadawan shi ne ,da yaga sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi kaway ya figo Jaseena suka fita yayinda mutanen suka bi bayansu ganin Jaseena ta gaza yasa ya kwantar ta bayan wani k’aton tukunya yace yana zuwa ,cikin sand’a yake tafiya har ya isa gurin da dawakai suke ,fito kawai yayi wani kyakkyawan ingarma ya nufoshi fari ne fes ,ya shafa kan Dokin sannan ya haura shima ya nufi inda ya bar Jaseena,ya sameta yanda ya barta cikin ciwon na’kuda ,take ya umarci dokin da ya kwanta ,hakan yayi ma Jaseena daidai yanda zata samu sauk’in daidaitawa a saman dokin ,kafin su ankara sukaji harbi kibiyar ta chaki Jaseena ta gefen ciki ganin sun kusa far musu yasa ya fita a d’ari da dokin suma suka hau dawakai suka bi bayan su har suka samu suka shiga Wannan kogon dutsen……..


🦃🦃🦃🦃🦃     JASEENA.        🦃🦃🦃🦃🦃


        Hameed ya d’auki gawar Jaseena ya fito bakin kogon ya tsaya , kasantuwar bai taho da komai ba daga shi sai takobin shi haka ya dinga tono da Wannan takobi har rana ta fito yayi gumi ba na wasa ba hannuwan sa duk sun salube sun ya’yyanke har saida ya gama tono ya sallace ce sannan ya binne ya d’au takobin ya koma cikin kogon ya zauna ya k’urawa jaririyar ido ,tsananin tausayin ta ya kama shi kasantuwar ta zo duniya ne lokacin da uwarta take gangaren barin duniya ,gashi shi bashi da abincin da zai ciyar da ita gata kuma abar tausayi kasancewar ta bak’uwa a duniya ,ya d’aga hannayen sa biyu yace ” ya Allah ga baiwar ka ta zo duniya lokacin da zalunci ya mamaye al’umma Kowa burinshi yaga shine a gaba ,Allah na rok’eka ka raya ta kan tafarki madaidaiciya kuma ka bata ikon kare hak’k’kin duk wani wanda aka zalunta a gaban idon ta ,ya Allah ka kareta da ikon kariyar ka!!!

   🏵    Kukan Jaseena(sunan mahaifiyar ta ya maida mata) ne ya katse shi  ya je da sauri ya dauketa ya rasa ta inda zai fara domin kuka take na fitar hankali ,kamar ance d’aga kanka sama kawai ya hango wani haske ya hasko cikin kogon kuma ba daga asalin k’ofar da ya shiga ba ne, ya mik’e ya nufi gurin dokin shi ma ya bishi kasantuwar kogon makeken gaske ne …..,


     Abunda idon shi ya gane mishi yasa ya zaro idanuwa ya d’aga hannu yana godiya ga Allah .,……..,🦃


Jeeddah jao🏵

[3/3, 11:10 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔

🐚🏵Jeddah ja’o 1⃣1⃣⏭1⃣5⃣ Wata sabuwar duniya ce domin kogon nan zagaye yake da wani dutse wanda tsakiyar Wannan dutse ya kai girman rabin masarautar Kalahari gashi kuma jeji ne sosai mai yawan duhuwa ,kayan itatuwa kuwa babu kalar da babu ga ruwa yana gudana daga saman dutse tsuntsaye sai shawagi suke a gurin ,🕊🕊 , ‘kara da yaji ta wani 6angaren ya tabbatar masa akwai namun daji ciki kuma masu cike da had’ari🐅


        🦃ya ja dokin sa har inda ruwan yake hannun shi d’aya kuma rik’e da Jaseena. Ruwa ne mai kyaun gaske ,yanda yake gudana ma abin kallo ne a nan ya dauraye jikin Jaseena dokin shi ma ya sha..nan ne fa Hameed ya fara sabuwar rayuwa daga shi sai dokin shi Zabil da kuma Jaseena wanda mahaifin ta ya maida ruwan kwakwa abincin ta, shi kuma yakan kama kifi ya busar don ya samu abin ci ,ko kuma y’ay’an itatuwa..haka suka yi ta rayuwa a jejin………..🦁

        


        🦂bayan shekaru goma sha shida(16 yrs ltr)🦂


    Zaune yake a fadar sa, su waziri sai zuba fadanci ake , wasu maza wad’anda da ka gansu kasan cewa magidanta ne sanye cikin kayan da basu fi a k’ira su  da tsumma ba suka shigo fada gami da zube wa ‘kasa suna kwasar gaisuwa duk jikin su sai 6ari yake yi d’aya daga cikin su yace ” Allah ya baka nasara sarki !!! Mun kawo k’arar Yerima !! Ya takurawa y’ay’an mu ko diban ruwa basa iya fita saboda da ya gansu sai ya fasa tulun,shine  muk………….kafin ya k’arasa yaji sauk’ar mari Tas!!!! Hakan yasa ya mik’e a firgice yaji an sake kwarfe shi ta k’afa take ya zube ‘kasa warwas !! Sarki ya ja tsaki Mtsew!! Yace ” ni zaku dubi tsabar idona Ku zo min da zancen banza Wai kun kawo karar Yerima? Toh baku isa bah !! Wato har an fara sa mishi ido kenan ? Ina so ku sani ,Rizwan Jini ne na sarauta yana da ikon taka duk wanda ya so kuma babu mai tanka masa ” ya dubi sarkin yak’i yace ” me kuke jira ne Amjad?!!! Aje a rufe min su a kurkuku da kuma horo mai tsananani!! Da sauri sarkin yak’i Amjad ya kama hannayen su ta baya ya tisa ‘keyar su suka bar fada yayinda Jalalud-deen ya koma kan kujerar sa yana maida numfashi kamar wani damisa 🐅


           Sarkin yak’i Amjad yana fita da su yayi hanyar kurkuku dasu ,murya ‘kasa- ‘kasa yace sai dai ku yi hakuri da irin Wannan zalunci da ake muku ni na tabbatar cewa akwai ranar da zata zo idon Jalalud-deen sai ya raina fata kuma sai ya zama wulak’antace a idon jama’a!! Yayi d’an murmushin takaici dai dai lokacin sun iso mashigar kurkukun ya wuce chan ciki da su ,sun dad’e suna tafiya kafin su iso d’akin da za’a sa su ,ganin masu gadin na kallon sa ya sa ya hakad’a su ciki a fusace ,gami da rufo k’ofar ya juya idonsa cike da k’walla ya fice Daga kurkukun…..


🗡🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🗡


       Gudu take a kan dokin sanye da bak’in dogon wando mai fad’in gaske ta sama , ta ‘kasa kuma a tsuke,rigar jikinta na cikin dogon hannu ne da shi kuma sak’awa akayi da auduga na saman kuma da fata akayi shi bak’in mayafi ne rataye a kanta wanda har ya zagaye fuskar kamar wanda tasa nik’ab baka ganin komai sai girar ta ,idon ta da kuma saman zirin karan hancinta , takalmin k’afarta ma na fata ne ,ta rataya wata y’ar jaka a jikinta sai wani dan biri da ke zaune a kafad’ar ta yana ta fama da ayaba🐒…..


     ”  Hyaaaa!!!” Ta fada gami da bugan dokin ta baya ,yayin da shi kuma ya kara gudu. Sun dad’e suna tafiya kafin su isa mashigar garin tana isa ta sauk’a daga saman dokin ta kama linzamin suka ci gaba da tafiya basu zame ko ina ba sai kasuwar garin nan ta wuce gun wani mai saida ganyeyaki na magani ta mik’a masa jakar , ya karba ya Ciro kad’an daga ciki ya shinshina sannan yayi murmushi ,yace ” yayi kyau Jaseena !! Wannan na’a  na’a mai kyau ne !! Ya sa hannu cikin aljihun shi ya Ciro sulalla ya muk’a mata ta kar6a ta juya abunta ba tare da ta ce k’ala ba ……..


        Cikin kasuwar ta sake kutsa kai tana ganin yanda Kowa ke gudanar da alamuran sa cikin kwanciyar hankali ,kai tsaye ta nufi gun mai shinkafa ,ya auna mata ta kar6a kawai ta jiyo hayaniya bata ankara ba ta hango dawakai kusan biyar sun dumfaro inda suke ,da wasu matasa a kai sai 6arna suke ,guda daya daga cikin su ya sha ado da kaya irin na alfarma shi ya fi Kowa ma ta’adi a cikin su suna ta buge mutane ,suna zubar musu da kayayyaki ,ta gefen Jaseena suka wuce gami da banke wata mata mai juna  ta fad’i ‘kasa kayan marmari da ta siyo ma duk suka zube ,a fusace Jaseena ta dubi mai shinkafan tace “Wannan kuma su  waye haka kamar mahaukata ??!!! Mai shinkafa ya zaro ido yace ki rufa ma kanki asiri baiwar Allah!! Wannan shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !! Ta juya ta sake kallon hanyar da suka wuce tana wani irin murmushi na k’eta ” a ranta tace lallai yau kakarta ta yanke sak’a!!! Mai shinkafa ya ce ” amma baiwar Allah kina garin nan kice baki san Yerima Rizwan ba? Murmushi kawai tayi ta d’auki shinkafan ta sa a Jakarta ta juya ba tare da ta kalle shi ba balle ma ta bashi amsa ,ta nufi gun matar da ta fad’i kasa wanda duk an zagaye ta ana kallo kuma babu wanda ya ma je kusa da ita  don ya taimake ta…………….🦃


Jeeddah ja’o🏵

[3/3, 10:16 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔

🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚

       


         1⃣6⃣⏭2⃣0⃣


     Kutsawa tayi cikin taron mutanen da k’arfin hali ta samu ta shige inda matar take ta d’aga ta tana yi mata Sannu yayinda sauran mutanen suka watse daga gurin Kowa ya fara tattare 6arnar da akayi masa amma da ka gansu kasan a tsorace suke duk da Jaseena ta fuskanci hakan bai sa ta ko girgiza ba ta d’aura matar kan dokin ta sannan ta ja akalar dokin suna tafiya matar na mata kwatance har ta kaita gidan ta, ta kuma taimaka mata har cikin gida ,wanda ba girma gareshi ba amma sai tsafta ,wani gadon kara ne gefe guda ta hango ta ja matar har gurin ta zaunar da ita sannan ta tashi ta nufi d’ayan 6angaren gidan don nema wa matar ruwa, akayi sa’a ta samu ta d’ebo mata….

        Bayan ta tabbatar matar ta samu nutsuwa sai ta tashi zata fice ,hannun ta matar ta rik’e ta ce ” nagode baiwar Allah !! Amma yaya sunan ki ? Ta juyo da murmushi tace ” “Jaseena ” matar ta d’an jinjina kai ta ce ” amma ke bakya tsoro labari yaje kunnen Yerima Rizwan cewa kin taimaka wa wanda ya wulak’anta? Zai ce kin raina mar hankali ,sannan ya sa a miki horo mai tsanani ,kuma gashi ke yarinya ce bai kamata kina k’arama ki jefa kanki cikin had’ari ba !!! Murmushi kawai Jaseena ta sake yi tace ” Kar ki damu umma !! Ni ma ba kanwar lasa bace !!!in yana ji da sarauta nima ina ji da ita !!🗡 ke dai ki kula da kanki kuma ki daina fita ke kad’ai domin hakan ba k’aramin had’ari bane” tana kai Wannan ta juya ta fice gamida rufo k’ofar gidan ,matar ta bita da kallo ,a ranta tace ” yau naga mace mai kamar maza!! Yanzu har a masarautar Kalahari akwai macen da zata iya tsallake dokar Yerima ?? Ta girgiza kai ta koma ta kwanta.


  🐚 kasuwar ta k’ara komawa ta gama saye-sayen da zatayi sannan ta juya ta bar garin , da la’asar ta isa kogon su ta shige ta nufi inda tasan kullum mahaifan ta yake motsa jiki da yamma ,wani d’an fili ne ya zagaye da itatuwa a nan ya ke koyawa Jaseena dabarun yak’i ,da gudu ta nufi inda yake ta zari wani sanda suka fara fad’a cikin raha har suka gaji suka bari.


       


       🔥wuta suka hura tana taya shi gasa kifi sai zuba take yi don duk abunda ya faru a Kalahari sai da ta zayyano masa shi dai bai ce ‘kala ba ya ci gaba da gasa kifin ,ganin ba sauraron maganar ta yake ba ta mik’e ta nufi wata duhuwa mai siriryar hanya ,gaba kad’an ruwa ne ke sauk’a ta saman dutse birin ta wanda take k’ira da suna Zainu yana nan kan kafad’ar ta yayinda take Kutsawa cikin duhuwar 🌳 kukan damisa ta jiyo hakan ya sa ta wata Yar siriryar dariya ta kama wata reshe kamar biri tana lek’o inda taji kukan ,domin takan ji kukan ne tun tana Yar yarinya amma bata tab’a yin gaba da Wannan gurin ba kasantuwar daga Wannan dutsen mai ruwa babu wani guri a gaba balle ta ce ko daga chan ta jiyo k’ara. yau de ba Jaseena bace zata fita ,mahaifin ta Hameed ne zai fita duk da ranta bai so ba amma tasan bata isa hana shi fitan ba ,kamar kullum ya debi ganyeyaki a jaka ya ja Zabil suka fice …..tana cikin wasa da zainu su kama Wannan reshen su saki wancan Kwatsam ta sake jin Wannan kuka na damisa ,ai kuwa nan ta k’udiri niyyar sai ta gano duk inda Wannan ‘kara ke fitowa !!! Diro wa tayi daga saman bishiyan tabi hanyar da ta jiyo karan kamar kullum de bakin dutse take riskar kanta amma yau tace bazata juya ba sai taga menene a bayan ruwan da yake zuba kuma zata nemo inda Wannan damisa take


; Hawa tayi kan dutsen duk ruwa yana ta jik’a ta a hankali ta mika k’afan ta gaba taji dai ya zauna ai kuwa sai ta kutsa kai ,zainu kuwa tun da yaga ta shiga ruwa ya koma gefe yana kallon ta itama bata biya ta kanshi ba tai shigewarta………….


Wata Yar siriryar hanya ce a ciki sai duhun tsiya amma don rigima ta shige sai tafiya take ,har tayi tsakiya ta juya tana kallon hanyar da ta baro ,sai kuma ta tabe baki ta ci gaba da lulawa……………


Jeeddah jao

[3/4, 7:41 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


2⃣1⃣⏭2⃣5⃣


Ta kai ak’alla minti talatin tana tafiya wani wajen ma sai ta sunkuya don ta wuce amma bata fasa ba har sai da takai wata Yar k’aramar k’ofa wanda aka toshe bakin da Yar ciyawa tasa hannu ta ture ciyawar dayake rana ta kusa faduwa Hasken wanda yay ja ya dalle mata ido sai kakkarewa take da hannun ta ,cikin dabara ta fito daga ramin dutsen ta tsaya ta jikin dutsen tana bawa idonta abinci domin banda dajin da yake gurin tana hango wani gini mai tsayin gaske ga kyau ,da gani kasan masarauta ce amma gaba yake da dajin shima ta hango shi ne don tana saman dutsen ne ta hango amma akwai wata siriryar hanya da ta bi gurin. Daji ne mai kyau don har yafi na inda suke kyau, da gudu ta juya tana dariya ta koma kogon bata yi wata wata ba sai gida Zainu na ganin ta yai tsalle ya koma kafad’ar ta yay zaman shi ita kuwa ganin yadda tayi datti yasa yasa ta nufi inda take wanka gefen Wannan ruwan tai ta wanke jikin ta tana wasa da ruwa ,k’iran da babanta yay mata ne yasa ta fita da sauri ta nufi inda taji Muryan shi ,fuska a turnuk’e yace “ina kika je?!!!” Nan ta fara kame kame ya juya ya barta gurin bai kuma cewa qala ba….


Cikin sand’a ta nufi d’akin ta, gami da turo k’ofar shi kuwa Hameed sai da ya gama kaifa takobin shi sannan ya wuce d’aki. Cikin dare ya kasa bacci domin jikinshi na bashi akwai abunda zai faru ,duk zuciyar shi sai bugawa take ya rasa dalilin faruwar hakan ,ya d’auki takobin shi ya nufi d’akin Jaseena wanda itama ba baccin take ba ,tana ganin shi ta tashi ta zauna tace ” baba na mai ya sameka? Yaya na ganka cikin daren nan? Murmushi yayi sannan ya kama hannun ta ya d’aura takobin ta daga kai tana dubanshi bai daina murmushi ba har Lokacin yace ” Jaseena !! Ko ma me zai faru yau d’in nan ka……….. Kafin ya k’arasa yaji motsi a waje tuni ya ce Jaseena ta fita ta bayan d’akin amma ta ture Wai itama zata iya fad’a ai kuma bazata tafi ta bar shi ba ,ya gaura mata mari wanda tsabar ta rikice sai da taga wuta🔥 ya ce ” nace ki tafi !!! Cikin kuka ta zari jakar ta na fata ta rataya zainu na biye da ita ta fice ta kofar bayan shi kuma ya fita don ya duba me ke wakana. Sauk’ar itace yaji a kansa wanda hakan yasa shi k’ara da zubewa a ‘kasa sumamme , duk abun nan da ya faru a idon Jaseena ne domin la6e wa tayi tana ganin duk abunda ke faruwa duk mutanen ta ga fuskokin su kasancewar Hasken farin wata duk ya mamaye gurin suka jashi suka tafi da shi ,nan ta zube tana wassu zafafan hawaye na takaici, a ranta tace ” toh ya akayi suka gano inda baba ya 6oye? 🗡……,


🐚🕸🕸🕸🕸🕸  🕸🕸🕸🕸🕸🐚


Kafin kace wani abu har gari ya waye Jaseena na idar da sallah tana goge takobin da Hameed ya bata kawai taji takun mutane ,cikin sauri ta haye wata bishiya cikin duhuwa zainu ma ya bita , a hankali suke magana tana jin su ,”sarki yace a duba ko akwai Dan sa ko kuma d’iya domin da ciki a jikin matar sa ya baro Kalahari !! Jin haka yasa Jaseena ta diro ta yi hanyan Wannan kogon wanda ke bayan ruwa mai zuba ta shige Wannan ramin Wannan karon har da zainu a tare da ita tana dirowa ta d’auki Yar ciyawar ta maida shi gurbin da yake ta fara tafiya tana bin Wannan hanyar da ta gani sai kalle kalle take yi zainu kuwa an samu bishiyoyi ya hau wancan ya kama wancan. Har lokacin bata daina kuka ba ,don tsoro take yi Kar a kashe mahaifin ta.. Gurnani ta jiyo ta gefen hanyar kamar na zaki ai kuwa Kwatsam yayi tsalle ya tare gabanta 🦁 ta tsaya chak a gurin ta zubawa sarautar Allah ido , bata ankara ba taga wani kyakkyawan sadauki a gabanta ya tsugunna yana shafa kan zakin ,damtsen shi ma. Kad’ai abin kallo ne shi kanshi kamar zakin yake ga gashi har Ka fad’a wata Yar farmalam ce a jikin shi wanda gabanta a bud’e take ya rataya kwari da baka a bayanshi takalmin ‘kafar shi kuwa na fata ne , ya mik’e yana kallon Jaseena sannan ya k’arasa kusa da ita ,hawayen da ya gani a fuskar ta yasa ta bashi tausayi saidai ba tare da yace komai ba ya ciro k’ullin gurasa a jakar shi ya bata ,kamar yasan tana jin yunwa. Da sauri ta wafce ta nemi guri ta nad’e k’afa ta fara ci ,chan sai ta tuna da mahaifin ta, hawaye na zubo mata sai chusa gurasar take yi tsabar ta zuciya ,har ya shak’e ta ta fara tari kamar dama jira yake , matashin ya ciro wata Yar gora na fata ya mik’a mata ta kar6a sai bayan ta d’an nutsu sannan ta dubeshi tace ” nagode !!👏🏽 murmushi kawai yayi ya yi mata nuni da hannu ma’ana ta tashi su tafi , nan ne ta gane cewa baya magana kuma ba kurma bane yana ji sarai amma baya iya magana ,saidai akwai kyau kamar balarabe , ta tashi ta bi bayanshi suka ci gaba da tafiya har suka k’ure Wannan dajin ,abin da ya bata mamaki shine wani tafkeken kogi ne a gurin saidai daga bakin ruwan ma kafi ganin masarautar ,jirgin ruwa suka shiga mai tuk’in yan ta fama da tuk’in shi kuwa sai wasa da ruwan yake yi…..,…….🦃


Jeeddah ja’o🏵

[3/17, 11:35 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


2⃣6⃣⏭3⃣0⃣


Isarsu masarautar ,bai zame da su ko ina ba sai cikin hanyar fada ,yana gaba tana biye da shi cikin ranta tace ” yanzu har akwai masarautar da bawa zai dinga kutsa kai cikin fada ba tare da izini ba? ” bud’ewar wata k’atuwar k’ofa ne ya katse ta daga tunanin da take yi ,kai ya kutsa ba tare da fadawan sun Hane shi ba har ya k’arasa ya nemi guri ya zauna ……..🦃


Zubewa tayi itama tana kwasar gaisuwa kamar yadda yayi sannan ta gyara zama. Wani bak’in mutum ne wanda fuskar shi ba wani almuru don ko murmushi da yake yi kamar dole aka sa shi yake yi . ” yarima har an dawo ne!!? ” tambayar da sarkin yay masa kenan ,yayin da shi kuma saurayin ya gyad’a masa kai ,nan yaci gaba da yi masa kwatance da hannu irin na kurame ita dai Jaseena ta zuba musu ido cike da mamaki da kuma tambaya dake cikin zuciyar ta ” me yasa Yerima guda babu ko hadimai balle shiga ta alfarma?! ” don ita da tayi zaton bawa ne😄 gashi kuma kyakkyawan gaske amma mahaifin sai bak’i da muni 😂 ,ta d’an jinjina kai tace ” hala mahaifiyarsa ya biyo”

Maganar sarkin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga ” Yaya sunan ki baiwar Allah? ” shine abunda yayi karo da kunnen ta. A d’an rusune tace “Jaseena”. Sarkin ya d’an yi murmushi yace ” daga yau na baki masauk’i cikin masarauta ta domin Yerima Haidar ya sanar da ni cewa 6ata kikayi ,toh nan ya zama miki gida kina da iko ki shiga duk inda kike buk’ata a masarautar nan ! Tai ma sarki godiya sannan Haidar ya ja ta suka fice daga fadar ya mik’e da ita har wani hanya daban wanda ta yi nisa sosai da fada ga k’ofofi kala kala masu kyau da kwalliya ga fitilu masu haske abin ba’a cewa komai …..

Wani d’aki ya nuna mata ta sa hannu ta bud’e ta shiga da murmushin ta zainu na biye da ita ,shima murmushi yayi sannan ya juya ya fice daga wajen yayinda ta bishi da kallo kamar Yar k’auye.


🐚🐚🐚🏵  🏵🐚🐚🐚


Yau kwanan Jaseena uku a Wannan gari wanda ko ita kanta bata san sunan garin ba ,Haidar kuwa kusan kullum da safe sai ya lek’o don ya duba lafiyar ta ,haka take wuni ita kad’ai sai zainu yana d’ebe mata kewa kasantuwar Haidar bai cika dawowa da wuri ba in ya dawo ma sai gari ya waye yake duba su….” Yau kam sai na fita na zaga gari!!” Cewar Jaseena kenan tana ta faman gyara zaman dogon rigar da ta saka ,sai duba kanta take ta madubi don bata saba saka irin kayan nan ba ,ita kanta ya mata kyau ,sannan ta dauki mayafin wanda da shi da kwalin tata duk d’aya ta yafa a kanta ta nannand’e ta fice zainu na binta a baya kamar yadda ya saba , tana tafiya tana faman tattare riga don yadda yake Jan ‘kasa a haka har ta bar fada ,tana ta kalle kalle ta tsaya can ,ta ta6a wancan , tana cikin haka har tayi nisa da masarautar a can nesa ta hango wasu mata guda uku kowacce da tulu sun sha ado sai ture -turen juna suke a kan hanya suna ta raha……

Cikin sauri Jaseena ta k’arasa inda suke ,tana iskesu ta sa hannu ta ta6a kafad’ar daya daga cikin su duk suka juyo suka k’urawa Jaseena ido sai kuma suka bushe da dariya suna nuna ta da yatsa 👉🏾 hakan yay matuk’ar bawa Jaseena haushi ta yamutsa fuska tace ” toh me nayi kuke min dariya !!😠. A tare suka tsare kamar da gaske sannan suka sake bushe wa da dariya ,wata Yar siririya sosai tace ” ke kuma Wacece haka !? Ko rigar ma bata iya sak’awa ba Yar k’auye kawai!! Suka juya suka ci gaba da tafiya yayinda ita kuma Jaseena ta tsaya Kallonsu har suka shige ta daina hango su ma……………🦃


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/18, 9:58 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


3⃣1⃣⏭3⃣5⃣


Duk Wannan abun da ya faru Haidar na tsaye yana kallon ta ,shi ma kanshi ta bashi dariya kawai ya tsare ne,kwata – kwata rigar baibai ta saka shi bayan haka kuma gaba a baya ,duk da hakan da tayi yay matuk’ar yi mata kyau amma ba daidai bane shi yasa matan ke mata dariya….


🎗Nan ta nemi k’ark’ashin wata y’ar bishiya ta zauna tana ta 6ata rai harda d’an hawayen ta ,tace ” ai yanzu da baba ne bazai min dariya ba cewa zai yi yayi min kyau !! Toh ma miye laifin kayan nan tunda dai ba tsiraici na bari a fili ba!!!Mtsew!!!” Take ta zabura ta mik’e tace” Baba!!!”


🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸


Kwance yake cikin wani matsatsen d’aki mai duhun gaske duk ruwan datti ta nan yake biyo wa ,ya tashi ya mik’e tsaye sai kai kawo yake a d’akin yana cizon le6e ,duk tunanin shi ya koma kan y’ar sa Jaseena addua kawai yake yi Allah ya sa Kar su gano ta ,Allah yasa basu kamata ba duk da yasan k’arfin damtse na y’arsa da kuma wayo irin nata. ” HAMEED!!! K’iran da waziri Zakar yayi masa kenan , hakan ya sa shi juyawa cikin sauri fuskar shi a d’aure. ” kamar yadda muka kamoka kamun wulak’anci haka zamu kamo d’iyar ka da kake tak’ama mai k’arfi ce mu wulak’anta ku a bainar jama’a !!! Hhahhah !!!!! ” Zakar kenan yayi Wannan magana ,bai ankara ba yaji an shak’e wuyan shi har saida idanuwan shi suka fito kwala kwala ,ya kasa magana. Hameed kenan !! Yana cikin kurkuku ma amma k’arfi na nan !!💪🏼. Wasu masu gadin gurin su biyu ne suka tunkari inda suke da ‘kyar suka cire waziri daga rik’on da Hameed yay masa sukayi waje da shi ,yayinda shi kuwa gogan ya koma ya zauna yana maida numfashi 😤………….

👑.  👑

A tsayen da take tana tuna halin da mahaifin ta zai shiga a Kalahari taji durowar abu ta bayanta tuni ta zari wata y’ar wuk’ar ta ta juya zata kai hari ,hannu ya sa ya tare ,wuk’ar ta yanke shi a hannu. Tana juyawa taga ashe Haidar ne 🙄ta zare ido,a rikice ta cire gyalen da ta rufe

kanta ta raba gida biyu ta d’aure masa yankan da tayi sai bashi hak’uri take yi ,ga dukkan alamu bai ji zafin ciwon ba sai murmushi yake mata ,jiki a sanyaye ta nemi guri gefen bishiyar ta raka6e tana y’ar hawaye….

Wata murya mai dad’in gaske da ratsa zuciyar duk wani mai sauraro taji yace ” Jaseena!! Ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ,inaga lokaci yayi da zaki sanar da ni matsalar ki wata’kila na nema miki mafita ko in taimaka miki!! Kinga dukkan mu nan ko wanne yanada matsalolin da yake neman mafita amma 6oye su bazai amfane my da komai ba har lokaci ya k’ure mana !! A firgice ta juya tana neman inda akayi maganar amma ta rasa domin ta lura babu Kowa a gurin sai Haidar da har Lokacin murmushi kawai yake yi rik’e da hannun shi yana kallon ta da kuma mamakin yadda ta rikice tana neman wanda yayi magana………


Ta dawo gaban Haidar tana kallon cikin idon shi tace ” bakaji wani yayi magana ba ? Baka ga wanda yayi ba?” Murmushi ya sake yi sannan yace ” ni nayi miki magana Jaseena !!” Nan ta tabbatar tabbas shi ne yayi magana ,kafin ta ce komai ganin yadda ta saki baki kamar wawuya yasa ya fisge hannun ta yabi wata hanya da ita sai cikin wani daji dake gefe da gurin ,kan wani gungume ya nuna mata ta zauna ,yace ” eh nine nayi magana ! Kuma ke kad’ai ne kika san hakan ko sarki bai sani ba ,kuma ina so ki rik’e shi a zuciyar ki ,duk Lokacin da kike buk’ata muyi hira to kizo nan amma Kar ki kuskura wani yasan ina magana !” Kai kawai ta girgiza mishi cike da mamaki har lokacin ta kasa nutsuwa…,……….🦃


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/19, 12:16 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


3⃣6⃣⏭4⃣0⃣


“Dama kana magana ne?” Shine tambayar da ta fara fita daga bakin Jaseena. Haidar yayi wata Kyakkyawar dariya yace ,ina magana amma banda iyayena babu wani mahalukin da yasan hakan ko sarki Hasheem da kika gani bai sani ba ,duk da shine silar dawowa ta hakan !! Duk Wannan maganganu da yake yi babu abunda Jaseena ta fahimta duk ya dagula mata tunani , Ta mik’e tace in na fahimce ka ,kana so ka ce min kai ba d’an Wannan sarkin bane ? Kuma akwai abunda kake 6oye masa a matsayin sa na wanda ya yi rainon ka?

Wata dariya ya saki mai ban mamaki yace ” Jaseena duniyar tamu zagaye take da azzalumai masu bak’ak’en zuciya da son abun duniya !! Zan baki labari na da kuma dalilin da yasa na zama haka ,amma kafin na baki labari ina so ki min alk’awari babu wanda zai san ina magana a cikin masarautar nan ko da wasa ne! ” Jaseena ta furzar da iska daga bakinta tace ” inshaa Allah bazan bari Kowa ya san da Wannan zancen ba !! Sirrin ka zan killace shi kuma na bashi mazauni na musamman a zuciya ta !!” Murmushi yayi yace na gode !! Amma yanzu muje in nuna miki gari ,gobe zan sanar da ke tarihi na in Allah ya yarda ” Jaseena ta d’an 6ata rai tace” me yasa bazaka fad’a min yau ba? ” murmushi kawai yayi yace ” muje ” ya tashi ya mik’e ita ma tabi bayan shi har ta sa k’afa zata tafi sai tace ” kai ka je !! Ni zan gyara riga na, ba tare da ya tanka ba yayi tafiyarshi ita kuma ta juya rigan ta gyara tsaf sannan ta fito daga duhuwar da take …

Tsaye ta same shi a gefen Wannan bishiyar yana jiranta ” na gama mu tafi” shine maganar da ta ratsa kunnen sa ,ya juyo ya k’ura mata ido kamar ya had’iye yace ” muje” ya fara tafiya ta bi bayanshi sai fama da doguwar rigar takeyi duk ta mata nauyi ta tattare rigar har guwiwa hakan yasa ta bata sauri sai ta d’an ruga ma take iske Haidar duk da ya ga yadda take fama da rigar wanda hakan ya bashi dariya matuk’a amma ya kafse kamar bai san ma tana yi ba .


⚜kasuwar garin ya fara kai ta ,sai kalle kalle take yi ,Kwatsam ya bi da ita layin sayar da tsuntsaye ,su Jaseena an samu abun yi ,nan ta dinga bin keji keji tana ta dariya kamar pagal (mahaukaciya) shi dai haka yake a tsare sai tafiyar shi yake in taga yayi nisa sai ta sa gudu ta taro shi ,ga shegen surutu kamar aku ta sha gaban shi yana tafiya ita kuma tana tafiya da baya baya ,” kai nace ka d’an tsaya mana sai sauri kake yi ko baka ji na ne!! ? A garin ja da baya ta banke wata budurwa ta d’ebo kwai a kwando ta fad’i k’asa kwayayen suka fashe ,a gurin ta daskare ta kasa magana ,budurwar ta mik’e tana karkad’e jikinta yayinda Jaseena ta sunkuya tana kwashe mata wayanda basu fashe ba sai hak’uri take bata. Murmushi yarinyar tayi tace ” babu komai !! Ba kece wadda muka gani dazu zamuje deban ruwa ba?” Jaseena ta d’an d’aga kai alamar tunani tace “🤔 ” Eh nice !! Ina sauran guda biyun suke?” Yarinyar tayi murmushi tace suna can gida ni sunana Jauda , ke kuma fa?” Ni kuma Jaseena! Shine amsan da Jaseena ta bata .


Ta juya sai dube dube take yi bata ga Haidar ba murya can k’asa tace “toh shi Wannan ina ya tafi ne?!” Murmushi Jauda tayi tace ” tun yaushe ya tafi!! Kizo mana mu tafi tare zamu nuna miki cikin gari ni da yan uwa na !” Da ‘kyar Jaseena ta yarda ta bi ta suka tafi………….


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/21, 9:24 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


4⃣1⃣⏭4⃣5⃣


Suna tafiya tana mata hira har suka isa wani babban gida ,ginin mai tsayi ne sosai ga kyau kuma tare suka shiga kai tsaye hanyar d’akin girke -girke suka nufa yarinyar ta ajiye kwandon kwai din ,a d’ayan 6angaren kitchen din kuma wayannan yan matan nan ne da suka mata dariya tare da Jauda suna tsaye sun zuba musu ido ,d’ayar tace ” ke!! Benaxir fa ta dawo !!! Kika shigo da Wannan bakya tunanin zata iya 6ata miki rai in ta ganta ko??!” Murmushi Jauda tayi sannan tace ” babu komai Aisha ai zamu fita ta baya in Mun gama aiki !!” Aisha de bata sake tanka mata ba ,Jaseena tace ” Wacece Benaxir har kuke tsoron ta haka ? D’ayar da tun farko bata tanka mata ba tace ” Wannan bai shafe ki ba !!:roll:” a tare Jauda da Aisha suka daka mata tsawa gami da k’iran sunan ta Meenah!!! Wai ke me yasa bakya son mutane ne kin cika bak’in hali !!? ” Aisha ce ta k’arasa maganar……


Jaseena tayi murmushi tace ” ni zan koma ,nagode da kyautata wa da kuka yi min ” Aisha tace don Allah ki tsaya mana yanzu zamu gama aiki mu tafi fada ,yau akwai tseren doki a fada kuma Kowa zai halarci gurin domin fidda gwani a wajen sarrafa doki ,kuma fa har akwai fad’a da zaki ,kowacce shekara yarima Haidar ke gaba a duk fannin.!! Kinsan yarima Haidar da son mutane ! Ai shine ma sadaukin Wannan masarauta Kowa yana karrama shi ,ba kamar mahaifin shi sarki Hasheem ba ,bai d’auke shi a kan komai ba ,Kinsan Haidar abokin mu ne tun muna k’anana tare muka taso har yanzun nan da kika gani ,ko lokacin da muka miki dariya a hanya ma ai shi ya hana mu in ba haka ba da abun ya fi haka ,ko wacce a cikin mu na da labari mai ban tausayi tun yarintar mu kuma labari mai ban tausayi amma da Sannu zaki san komai amma kafin nan ko zaki iya bamu labarin rayuwar ki da yadda akayi kika tsinci kanki cikin Wannan masarauta ta Ramali?? ”

Nan Jaseena ta kwashe duk labarin rayuwar ta ta fad’a musu har yadda akayi ta fito daga dutsen da had’uwar ta da shi Haidar ,duk sun tausaya mata matuk’a , Jauda ta mik’e tsaye tace ” toh ai duk labarin d’aya ne duk fa akan mulki aka k’ask’anta mu kawai don an fi k’arfin magabatan mu toh yanzu zama zamuyi a dinga cin kashi a kan mu ne??!! Aisha ta mik’e tace ” inaaaa!! A’a Sam bazai yiwu ba dole mu kwace hak’k’kin mu da kan mu mu tashi muyi yak’i mu k’watar ma kammu y’anci!!! ” Jauda ta sa hannu tace ” wa yake tare da ni??” Duk suka d’aura hannayen su a kan nata gami da cewa “ni!!” Duk suka maida dubansu ga Meenah da ko motsawa bata yi ba ,ganin duk sun sa mata ido itama ta d’aura nata hannun” Jaseena ta rasa Wannan wane irin hali ne Meenah take da shi kwata kwata batada fara’a a fuskar ta. A tare suka watsa hannayen sama kowannen su yana murmushi irin na masu k’arfi a jika 💪🏼


💞🏵 Jaseena.  🏵💞


Guri ne babba na gaske amma mutane duk sun cika gurin an zagaye makeken filin wanda Hasken farin wata ya cika shi fal! Gurin da mutanen suke hawa hawa ne ga fitilu nan ta ko ina sun haska benen dake sama sosai shine inda sarki Hasheem ke zaune shi da wata Kyakkyawar mata tasha ado na zinare ,gefe d’aya kuma sarakuna ne da matan su wayanda suka zo suma da y’an wasan su ma’ana sadaukai na k’asar su don suma su fafata a cikin gasar ,akwai gefen sarki Hasheem wanda duk cikin guraren ya fi ko ina k’ayatuwa ,wani sarki ne bashi da haske sosai amma da ka ganshi kasan ya dama ya shanye a sarauta ,gefen shi wani kyakkyawan saurayi ne ya sha ado gwanin sha’awa fuskar shi babu almuru ga dukkan alamu d’an sarkin ne ,ga kuma wani ta bayansu a tsaye da alama sarkin yak’in su ne don sanye yake cikin kayan yak’i saidai ya manyanta sosai don dattijo ne….


Toh masu ku biyo ni a episode na gaba don jin wainar da zata toyu a Wannan fili na gasa ,ina godiya masu karatu love you all!!💞


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/23, 9:15 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵jeeddah ja’o🏵🐚


4⃣6⃣⏭5⃣0⃣


Haidar ne a kan doki suna Jere shi da wasu ,yayan sarakuna ,Jaseena da ke zaune a bene na farko kuma na k’asa ita da su Jauda kawai ta mik’e ba shiri ,su Aisha ma suka mike suna tambayar ta ko meyasa ta zabura haka? Fuskar ta babu almuru tace ” tabbas na san wancan !! Shine Rizwan d’an sarki Jalalud-deen !!! Me kuma yake yi anan ? Duk yadda akayi sarki Jalalud-deen ma yana nan !!” Aisha tace ” kice ba mu muka je neman su ba su da kansu sun kawo ‘kafar su inda ya dace!!” Duk suka bushe da dariya ,chan kuma sai Jaseena tace ” toh amma ai in an gama gasar yau gobe zasu tafi ko ?” A tsare Meenah tace ” sati biyu ake yi ana wasannin lallai muna da dama ” duk suka jinjina kai ,yayin da Jaseena tayi murmushi cikin ranta tace ” lallai Wannan Meenah d’in y’ar ganin dama ne !!.


Tun da aka fara tseren dawakai Haidar ne ke Jan ragamar Kwatsam sai dokin shi tayi wani irin ‘kara ta tik’a shi da k’asa ta yi gaba ,yarima Rizwan wa wuce shi yana masa wata muguwar dariya gami da cewa “Wannan karon kam baka isa ba!!! ” dokin Haidar da ya fita a guje ya zagayo ta inda su Jaseena ke zaune kawai se ta mik’e tayi tsalle ta fad’a kan dokin ” Hyaaaa!!! ” ta sa gudu ,ganin yadda ta kusa cimma Rizwan yasa sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye yana zare idanuwa.


Gudu suke daf da daf da ita yayinda Rizwan ya kasa mai da hankalin shi kan tseren ,abunka da mayen mata ,ya tsura mata ido ita kuwa ta sakar masa da wata hadaddiyar murmushi wanda ya sa sai da ya kusa tsaya wa. Sai da ta tabbatar ya gama rud’ewa kawai taja linzamin dokin ta kara gudu har ta tsallake Jan layin da aka zana ,ta zo na d’aya ,bak’in ciki ya sa Rizwan ya gagara k’arasawa yayin da idon Jalalud-deen suka rine tsabar haushi ace duk shirin da suka yi na ganin sun ci amma hakan bai yiwu ba?


Mutanen gari aka hau ihu ana Jaseena! Jaseena !! Jaseena!!! ,Wannan sunan da aka kira yasa sarki Jalalud-deen d’agowa cikin sauri yana kallon Jaseena !tabbas babu maraba tsakanin ta da mahaifiyar ta ,saidai a tunanin shi wata’kila idon shi ne ke mishi gizo sai yayi tsaki ya juya ya bar wajen ,yayinda Rizwan da sarkin yak’i Amjad suke taka mishi baya.


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/24, 7:40 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


5⃣1⃣⏭5⃣5⃣


Haidar kuwa murmushi kawai yayi ya nufo inda take ,kanshi a k’asa yace ” nagode jarumar mata!!! ” Wannan sanyin Muryar tashi ta sa Jaseena lumshe idanuwa tana murmushi ba tare da ta tanka masa ba,shi ma yadda yayi maganar ba wanda zai gane magana yake yi ..

🐚. Gurin duk an watse Kowa ya koma gida, daga Aisha ,Jauda, Jaseena sai Meenah da Haidar, suna ta hirar su cikin nishad’i Meenah ce kad’ai kamar bata gurin. Jauda tace “Jaseena mu zamu tafi dare na yi sosai Kar Benaxir ta rufe k’ofa Kinsan ba mutunci gareta ba! Nan suka yi sallama suka bar ta da Haidar. Ganin sun share mintina babu wanda ya tanka wa wani yasa Jaseena ta mik’e tana kad’e rigar ta tace ” sai da safe yarima ,idon shi cikin nata yayi mata wani murmushi ba tare da ya tanka ba ,ganin shiru yasa ta juya zata tafi…….

Mahaifina sarki Mahmoud shine mai mulkin Wannan masarautar mutum ne wanda bai yadda ya ci ya sha ba tare da ya tabbatar jama’ar k’asar nan sun wadatu ba kullum burin shi yaga na gefen shi cikin walwala koda shi zai rasa ,hakan ne yasa ya fita daban da sauran yan uwan shi wanda kuma sun kasance ba uwa d’aya suke ba domin shi d’aya mahaifiyar shi ta Haifa kuma halin shi ma babu mai irin sa kasantuwar ,kakan mu mata biyu gareshi…..


Da sauri Jaseena ta juyo ta dawo inda yake ta nemi guri ta zauna don ta jiye wa kunnen ta ……. Yerima Haidar yaci gaba da cewa ” duk mahaifina ne babba a ciki domin mahaifiyar sa itace ta fari daga baya ne zaliha (ta biyun ) ta haifi maza biyu Hasheem ,Hayatud-deen ,da kuma mace d’aya Saleemah. Duk cikin su ukun Saleemah kad’ai ke son baba na don sun shaqu sosai hakan ne yasa tun tana y’ar shekara goma ,mahaifiyar ta Zaliha ta bada ita aure a wani masarauta Wai shi Kalahari aka daura mata aure da d’an sarkin garin yarima Jalalud-deen , wanda hakan yasa bata ‘kara zuwa ko da ziyara nan masarautar ba,Domin shine hud’ubar da mahaifiyar tata tayi mata.


Jin haka yasa Jaseena ta mik’e a razane ta ce ” Kalahari?? Jalalud-deen?!! ” shima Haidar ya mik’e yace “eh! Kin san su ne? Nan ta kwashe labarin rayuwar ta ta fada masa yayinda ya cika da mamaki ” haka Allah yake abin shi!! Shine abunda Haidar ya iya cewa kenan ,ya dubi Jaseena yace “Kin ga yanzu dare yayi ,ki je ki kwanta ki huta gobe in shaa Allah zan sanar da ke dukkan labari na. A nan suka rabu da alkawarin zai sanar da Jaseena komai game da shi washegari……………..


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/25, 12:20 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


5⃣6⃣⏭6⃣0⃣


Tafiya take tana ta fama da y’ar doguwar rigar ta ,tazo wucewa ta gurin fada kenan taji kamar maganar mutane,ta d’an lek’a daya daga cikin tagogin fadar don taga su waye a fadar cikin Wannan dare. Tana lek’a wa idanuwan ta suka yi karo da sarki Jalalud-deen da kuma sarki Hasheem suna tsaye ,koda ta kasa kunne don tajiye wa kunnen ta abunda suke shiryawa……

” Ai Wannan ba komai bane ni a gurina domin a kan sarauta babu abunda bazan aikata ba !!! Ko yarima Haidar da ka gani ban barshi a Wannan masarautar ba saida na tabbatar cewa yana da nak’asa sannan kuma ban daukeshi a kan karon komai ba !!! Duk da ma de Y’ata Meenah bata k’auna ta Sam !! Amma Wannan karagar mulkin da ita ya dace ba Haidar ba!!!” Sarki Hasheem ne yayi Wannan maganar hannunshi rik’e da kofin zinare. Sarki Jalalud-deen ya mik’e yayi wata y’ar muguwar dariya yace ” lallai abokina baka da wayo !! Ai sai da wuta ake shan Zuma!!!domin dan hakin da ka raina shi zai tsone maka ido ,yaran yanzu da ka gani ,zamani ya chanja domin babu wata dabara da basu sani ba ,bar ganin shi da nakasa ,kaga fa yadda ya mamaye zukatan al’umma ! Abun yi kawai shi ne ka kawar da shi kwata kwata domin in baya nan tare da kai babu yadda za’ayi Meenah ta ‘ki kar6ar mulkin Ramali ,ka duba fa ka gani ,mace ce mai kwarjini ga jarumta bai kamaceta bama a ce Wai ta bar daular dake cikin wannan masarautar! Ni ina da shawara ,me zai hana a had’a su aure da d’an wajena Rizwan? Kaga zasu yi mulkin Ramali cikin kwanciyar hankali ,kasan ko d’ana Rizwan bashi da masaniya akan abubuwan da nayita tufkawa a masarautar Kalahari , don na lura yan da son gaskiya shi yasa na ci gaba da 6ata shi da sakalci don in har ya gano ni ba mai gaskiya bane ,Rizwan zai iya juya min baya kasan duk da ba Saleemah bace ta haife shi amma goyon ta ne shi yasa nayi duk yadda zan yi su daina ganawa da juna kullum!!” Duk suka bushe da dariya Hasheem yace ” baka da dama abokina!! Shikenan! Na amince da shawarar ka!! …..


Jaseena ta toshe baki da hannayen ta ,ganin fitowa zasuyi yasa ta ruga a guje ,bata ankara ba taji an fizgo hannun ta cikin wani d’aki an rufe k’ofar ,zata yi magana yasa hannu ya toshe bakin ta yace , “ki nutsu” tana juyawa tayi ido hud’u da Rizwan:oops: tace ” kai!!! Sake min hannu na !!! ” ta fisge hannunta daga rik’on da yayi mata ,ta bud’e baki zata ‘kara wata maganar ya ce ” naji duk abubuwan da suke shiryawa !! Kamar yadda kema kika ji su ‘ da na zaci ni ne asalin wanda ya cancanci sarautar k’asar Kalahari ashe ba sarauta ta bace ta wani ne ! Duk rashin mutunci da cin amanar da nake wa mutane ashe de duk a banza ne , duk kuri da gadara da mulki ashe ba ta mahaifina bane !!! Kaicho na wlhy nayi nadamar samun irin wannan uban ,wanda kawai son zuciya ya saka a gaba ,kuma yanzu na tabbatar ba sona yake ba don yana turanine cikin halaka !! Wani hawaye ne ya biyo kumatun Jaseena tace ” hakane yaya Rizwan amma ai babu komai akwai Allah!! Tana kai wannan ta fice tana goge hawaye ,tabar Rizwan yana tunanin dalilin k’iran shi da tayi da yaya Rizwan ; cikin ranshi kuwa sai tambayar kan shi yake ,dama akwai ranar da zata zo har zai zubar da kwalla da kuma jin tsananin tsanar mahaifin shi?


Da sassafe Jaseena ta shirya cikin irin shigar da ta saba ,ta fice don gari ko gama wayewa bai yi ba ,bata zame ko ina ba sai inda sukayi alk’awari zasu na had’uwa ita da Haidar ,amma abun da ya d’aure mata kai shine tun da taje tana masa magana ko kallon inda take bai yi ba ballantana ya amsa mata ,da gani kasan ranshi a 6ace ne. A fusace ya tashi zai bar gurin ta sha gabanshi da gudu tace ” Wai ni laifin me nai maka ne!?tun d’azu ina maka magana ka min shiru kamar da gunki nake magana alhali na tabbata kana ji na “! Bai saurareta ba ya bi ta gefenta zai wuce ta sake tare shi ,cikin tsawa yace ME KIKE YI JIYA A DAKIN RIZWAN!!! ” shiru tayi tana kallon shi ido da ido ta ce ” me kake nufi Haidar ? Me kuma zanyi a d’akin Rizwan ,chan ta juyo tace ,yaya Haidar !! Yaushe muka fara haka da kai? Me yasa bazaka fad’a min ba? Me yasa kake boye min ? ” Haidar yayi sauri ya tari bakin ta yace ” Jaseena ban fahimce ki ba ” tayi murmushi wanda yasa hawayen da ke idanuwan ta suka zubo ba shiri tace ” ka kasa fadamin kana sona ko” ka kasa kuma bawa zuciyar ka hak’uri har ta fara zuga ka,ka fara zargin abin da kake k’auna kuma sannan ka kasa daurewa! ” Haidar ya juyo yana kallon cikin idonta” yayinda ta juya zata bar gurin. Haidar yace ” na soki Jaseena kuma har abada zan soki ” ya durk’usa k’asa yace ” kiyi hak’uri ya ke Kyakkyawa ! Ki taimaka min da zuciyar ki domin tawa ta riga ta kufce min ! Ban kuma san yaushe zata dawo gareni ba don ta fita farautar abunda tafi mata komai soyuwa ne!”


🏵 Jeeddah ja’o🏵

[3/25, 10:45 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


6⃣1⃣⏭6⃣5⃣


Jaseena ta juyo idanuwan ta duk sun yi ja ,tace “Na baka !! Na baka ya Haidar!! Ka kula da ita domin taka ta riga ta iso inda zata tsaya da farautar kuma bani da tabbacin zata koma gareka !!” Haidar ya mik’e yace ” nagode kyakkyawa !! Jaseena tayi murmushi tace ” akwai maganar da nake son sanar da kai ne ” Haidar yace” ki fad’a mana ko ma menene. Ta kwashe duk abubuwan da ya faru a daren jiya ta sanar da shi har abunda yasa ta shiga d’akin Rizwan. Haidar ya sake bata hakuri ,sannan ta gyara zama ta ce ” baka k’arasa min labarin ka ba” ya d’an yi murmushi sannan ya ci gaba……..


🕸🐚🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🐚🕸


A lokacin ina da shekaru goma sha shida ne ,k’ anin babana wato Hasheem ya bi rud’in uwarsa na cewa Kar ya kuskura ya bar babana da rai don in har ya tsufa a kan karagar mulki nine zan gaje shi na zama sarki , don shi a cewar shi ni ba komai bane in ya kawar da mahaifina, da duk wani mai ji dani, kasantuwar kullum da safe muna fita daji ni da kakana yana nuna min nau’in ganyayyaki da amfanin su ,hakan yasa ya shirya mana gadar zare.

Mun yi Nisan kiwo nida kaka har bayan la’asar sannan muka iso gida ,muna shiga wasu mutane a kan dawakai su kuma suna fita ,ga gari duk ya turnuk’e da hayak’i ko da muka k’arasa cikin fada nan muka tarar da gawawwakin iyayena da kuma na k’annen k’ anin Hasheem Hayatud-deen , Hasheem ya kwanta a kansu sai kukan munafurci yake yi kamar da gaske ,a nan ne zuciyar kakana ya buga take rai yayi halinsa , bayan kwana uku da faruwar hakan ,kawu Hasheem ya na’da kanshi a matsayin sarkin Ramali ,duk dattijawan da basuyi Na’am da hukuncin da ya yanke ba sai ya sa aka kwashe su aka kai su masarautar Kalahari aka rufe ana basu horo mai tsanani ,daga cikin wadannan dattijawan sun had’a da mahaifan Aisha da kuma Jauda ,kamar yadda na fad’a miki Meenah itace d’iyar kawu Hasheem amma tun tana y’ar shekaru tara ne abun ya faru don duk sa’anni suke da Aisha da Jauda kinga kuma k’awaye ne hakan yasa ta baro fada ta zab’i zaman bauta a gidan Benaxir har ta girma ta kawo lokacin nan da kike gani….


Ni kuwa tun lokacin da abun ya faru na daina magana da Kowa da na gano hakan kawu Hasheem ya ke so sai na nuna mishi ma kwata kwata bana magana na daina yi ko da da wasa ,a haka shi da mabiya bayansa suka zata na riga na zama miskini. Kin ji yadda rayuwa ta ta kasance kullum cikin k’ask’anci amma ko a jikina domin na san dole ne wata rana sai gaskiya tayi halinta!!” Amma tunda haka abun yake toh mu zamu fara wargaza mishi rayuwar sa” Jaseena ta goge d’an hawayen fuskar ta sannan tace ” lallai ka shiga k’uncin rayuwa Haidar !! A nan ne Jaseena ta kwashe labarin ta ta bashi ta kuma sanar da shi ko wanene sarki Jalalud-deen. Sun dad’e suna shan hirar su ,kafin nan suka nufi gidan Benaxir don yin magana da su Jauda……….


🏵Jeeddah ja’o🏵

[3/27, 11:25 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


6⃣6⃣⏭7⃣0⃣


Sarkin yak’i Amjad ne zaune a gefen sarki Hameed hannun shi rik’e da na Hameed. Na ganta! Naga y’ar ka Jaseena ,tana cikin k’oshin lafiya ,kuma ga dukkan alamu tana cikin shiri,Hameed ya mik’e yana murmushi yace ” nasan ban haifi lalatacciya ba!! Kuma nasan dama tana nan tafe , amma ya maganan mayak’an da na ce ka tara ? Amjad yace ,komai an kammala shi kuma yanzu haka suna chan a kogon tare da y’an fursunan k’asar Ramali! Da sarki Hasheem ya sa Jalalud-deen ya d’aure shekaru kusan goma sha da suka wuce ” Hameed yayi murmushi yace ” da kyau sarkin yak’i!!! Aikin ka yana kyau ,Allah ya mana jagora!! Sarkin yak’i yace “Ameen”sannan ya mik’e ya fita………


Yau tun da safen nan Jaseena take motsa jiki tun bayan sun dawo daga gurin su Jauda Zabil kuwa ya samu Haidar ba kasafai yake waiwayar inda Jaseena take bama don in zai fita daji tare suke tafiya. Saidai yau Haidar bai je ko ina ba yana tare da k’anwar sa Meenah a cikin makeken lambun dake wannan masarautar suna ta hirar su duk da ma dai itama maganar kurmancin yake mata amma ta saba don ko ubanta Hasheem bai iya magana dashi sosai ba. A nan ya sanar da ita cewa yana soyayya da Jaseena, murmushi kawai tayi. Haka sukayi ta hira har kusan azahar, sannan ya tafi domin gudanar da ibada yayinda itama Meenah ta juya tabar wajen ,zata koma gidan Benaxir.


🏵🐚🏵🐚🏵🐚. Jaseena🐚🏵🐚🏵🐚🏵


Yau kwana na uku kenan ana ta bidirin gasa, Sam Sam Rizwan abun ma bai dameshi ba balle ma ya shiga ,hasalima cewa yayi babanshi ya chanja wanda zai yi wasan shi bazai iya ba ,babu yadda aka iya haka aka chanja shi da wani k’ak’k’arfa daga cikin mayak’an Kalahari. Jaseena kuwa tun ranar farkon nan bata sake shiga filin ba kullum tana daga chan baya ita da su Aisha amma fa ta lura cewa sarki Jalalud-deen hankalin shi bai kwanta da ita ba. Washegari da safe ta shira cikin dogon bujen wandonta bak’i da wata riga fara sannan ta rataya takobin ta da y’ar jakar ta ta fice daga fada ,fuskarta a rufe ta bar idanuwan ta a waje kamar wanda ta saka niqab , tafiya take cikin sauri kamar zata tashi sama, duk saurin ta sarki Hasheem yana tsaye ta sama a d’akin shi daga tagar d’akin yana kallon duk abunda ke faruwa ,tana fita Rizwan ma ya bi bayanta, ganin haka ne yasa sarki Hasheem shima ya rufa wani k’aton mayafi don Kar Fadawa su ganshi su ce zasu rakashi ya fice daga fada suna tafiya yana binsu duk yana jin abunda suke fad’a har suka shiga Inda Haidar yace za suna had’uwa ,ya lab’e bayan wani dan ice yana sauraron duk abunda suke fad’a…..


🏵Jeeddah ja’o🏵 BACCI😴😴😜

[3/30, 9:17 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


7⃣1⃣⏭7⃣5⃣


Haidar, Jaseena, Aisha, Jauda, Meenah, da Rizwan!!!! Duk na ji abubuwan da suke shiryawa !!! Don haka dole ne mu kawar da su tun kafin su cimma burinsu🙄. Sarki Jalalud-deen ya mik’e tsaye ya rasa me zai ce saboda ko kad’an baya son dansa ya shiga wannan alamari amma tunda ya nuna taurin kan shi a fili toh lallai ba makawa sai an hukunta shi.


Haidar yana sane da cewa sarki Hasheem yana wannan gurin shi yasa ko ‘kala bai ce ba a gurin ,sannan kuma yasa Jauda tayi karya akan shirye shiryen da sukayi ,sun yi akan sai an gama gasa zasu far musu amma ashe shirin Sam ba haka yake ba !!! Cikin dare k’afa duk ya d’auke suka shirya duk irin yadda Jaseena take shiganta ,suka shigo fada ,Jaseena akwai ilimin duk wani abu da ya shafi yayan itatuwa da ganyayyaki saboda haka ta shiga d’akin da sarki Hasheem yake ta zauna bakin makeken gadonsa tana wani muguwar dariya 🤓ta fito da had’in maganin da tayi sannan ta debi kad’an ta watsa a fuskar shi a take ya farka gami da yin wani atishawa ya sulale ya koma kan filow ,nan ta d’aure shi ga igiya tam sannan tayi fito a hankali ,Haidar ya shigo shi da Rizwan suka ciccibeshi suka yi waje. Haka ne ya faru da sarki Jalalud-deen ma ,suna fita basu zame ko ina ba se cikin wani tangamemen daki mai kama da keji suka tura su ciki ba komai bane ke gadin wajen illa damisa guda uku manya manya 🐅


Da dariya suka fito su Jauda suka d’aga Jaseena sama yayinda Haidar da Rizwan ke ta musu dariya, suka koma cikin gari ,kasantuwar inda suka je da nisa ,sai kusan asubah suka iso cikin Ramali ,wannan kurkukun kuma shine asalin kurkukun masarautar Ramali kafin sarki Hasheem ya hau mulki. Isarsu cikin gari basu zame ko ina ba sai fada ,Haidar yasa a tara masa duk jama’ar wannan masarautar su hallara a cikin fada ,kafin awa d’aya duk Kowa ya samu isowa ,Haidar yayi murmushi ya gyara murya sannan ya fara da cewa:

Al’ummar Ramali !!! Akwai wani d’an karamin labari da zan baku labari ne na mikiya kuma ina kyautata zaton daga jin wannan labarin zaku fahimci Inda na dosa!!” Cike da mamakin jin magana da sukaji yarima Haidar yayi suka amsa da ” muna sauraron ka yarima!”


🏵Jeeddah ja’o🏵

[4/3, 10:43 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


7⃣6⃣⏭8⃣0⃣


Ita mikiya wata tsuntsuwa ce wadda zata iya rayuwa har tsawan shekaru saba’in, amma domin kaiwa wannan Shekarun ,dole sai ta d’auki tsatsauran matakai,domin lokacin da takai shekaru arba’in dogin faracinan ta zasu zama basu da karfin neman ko kuma chafke abunda zasu samu a matsayin abinci,wannan dogon bakin ta mai kaifin zai kwanta (lank’washe ) fukafukan zasu zama tsofaffi, masu kauri kuma ga nauyi , wannan fukafukan masu kauri da nauyi ,zasu zama kamar a k’irjin shi suke hakan zai basu wuya wajen tashi sararin samaniya daga nan ne mikiya zata zama bata da wani zabi wanda ya wuce guda biyu kachal ✌🏾 ko ta MUTU ko kuma ta rayu cikin salo mai wuya na neman SAUYI! Hakan yana bukatar mikiyar ta tashi ne sama ta hau kan tsauni ,ta zauna cikin gidanta (nest) sannan sai Yayita buga wannan tsohon bakin nashi jikin dutse har sai ya fincike shi , sannan wannan mikiyar zata bari har sai sabon ya fito sannan sai ta fincike tsofaffin faracinan ta da shi ,lokacin kuma da wadannan faracinan suka fito ,sai ta fara fiffige tsofaffin fukafukan nata da shi wannan shine chanji da yafi ciwo zafi!! Toh daga nan ne wannan mikiyar take sake daukan sabuwar rayuwa ta sake yin wasu shekaru talatin din a gaba! ME YASA AKE buk’atar CHANJI??? Saboda a rayu kuma ayi zamantakewa!! Muma dole mu bi hanyar SAUYI!!! Amma ba kamar mikiya ba ,Muma dole mu sauya munanan d’abiun mu zuwa kyawawa da kuma abubuwan da muka aikata marasa kyau zuwa masu kyau ,mu zama masu koyi da abunda addini ya zo mana da shi!!

Saboda haka domin daukar hanya zuwa wannan SAUYI sai ku watsar da wadancan d’abiun domin samun sababbi ,duniyar da fadi take amma mu bita a Sannu! Ku bude ajiyayyan k’wak’walwar ku don ku Adana wannan ko zaku tashi da sabuwar rayuwa irin ta mikiya!!!……..


Kowa yayi shiru jiki a sanyaye ,fadar tayi dub kamar babu wata halitta a cikinta , wasu na hawaye amma hawaye ne na farin ciki cewa yau gaskiya ta dawo masarautar Ramali! Wani dattijo ya mik’e yace ” wannan haka yake yarima Haidar! Muna tare da kai ! Dattijawan gari suka na’da Haidar a matsayin sarkin Ramali , ganin yadda komai yazowa Haidar cikin sauk’i yasa Rizwan ya mak’ale mishi yace shi zai raka shi masarautar Kalahari don ya nemi gafarar mutane wata’kila in yasa baki za’a yafe masa shashanci da yayi ta aikata musu ba dare ba rana,nan suka sake sabon shiri dukan su tare da wasu mayak’a guda ashirin suka d’au hanyar Kalahari…………


🏵Jeeddah ja’o🏵

[4/7, 6:04 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


8⃣1⃣⏭8⃣5⃣


Kasantuwar ba hanyar da su Jalalud-deen suke bi don shiga k’asar Ramali zasu bi ba ko dawakai basu d’auka ba cikin sauki suka bi ta inda Jaseena ta fito suka shiga wannan ramin ruwan har ta kaisu ga asalin cikin kogon ,bayan sun gama dirko wa daga wannan dutsen ne suka tsaya karkade jiki su Jauda se kalle kalle ake yi basu ankara ba suka ga sojojin yak’i sun zagaye su kowanne hannu rik’e da mashi ,gashi kuma abun da ya basu mamaki duk babu saurayi cikin su don duk sun manyanta da gani kasan sun yi zamani, Jauda ce ta fara jefar da jakar da ta rik’e tana motsar k’walla ” baba!!! Abunda ta iya furta wa kenan ta nufi gurin d’aya daga cikin wad’anda suka zagaye su ta rungume tana kuka Aisha ma ta nufi gurin wani da ke tsaye yana kallonta sai hawaye ,Jaseena da ke kallon su tuni itama ta fara k’wallar saboda ta tuna nata mahaifin da bata ma san wanne hali yake ciki ba , Muryar sarki Haidar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, tana juyawa taga gurin babu Kowa daga shi sai ita ta fara juye juye fuskar ta cike da alamar tambaya?? Kafin ta furta komai Haidar yace ” ya ke ma’abociyar kyau da farin hali, kada ki damu Mun basu dama ne su gana da iyayen su domin kuwa sun yi kewar juna ” Murmushi Jaseena tayi sannan ta fara share hawayen da ke gangaro wa daga idanuwan ta ,Haidar ya matso kusa da ita yace ” ya isa haka Kar ki sake yi min asarar hawaye ! Kuma baba yana cikin k’oshin lafiya” Jaseena ta d’ago manyan idanuwan ta tace ” don Allah muje in ga baba na ,don hankali na bazai kwanta ba in ban sa shi a ido ba tana fad’in hakan hannunta guda kuma ta chafke wuyar rigar shi ,inda ta shak’e ya kalla sannan yayi Yar murmushi cikin murya irin na zolaya yace ” irin wannan chafka haka ,duk kin yamutsa min riga! Lallai kina so na sa a kulle min ke a kurkuku yanzungaske.😜 ” Hakan yayi matuk’ar bata dariya yadda ya ta6e fuska kamar da gaske. Ya ce Haba!! Ko ke fa ? Amma matar sarki guda gashi kuma jarumar mata amma tana hawaye kamar raguwa?” Dariya ta bushe da shi tace ” Aa ba wani nan ! Cewa zakayi jarumar mata da maza 😝 ai mazan ma saidai in basu nemi in sambad’e su ba 💪🏼”. Dariya sosai ta bawa Sarki Haidar har ya shagala ya nemi gurin zama yana kallonta, ita ko sai fama take da y’ay’an innibi🍇 ,yana kallon yadda karamin bakinta ke motsawa cikin nutsuwa ta lumshe idanuwa sai faman tauna take, yayi murmushi ya mik’e ya d’auki wani dan karamin dutse ya wulla mata ya samu damtsen ta ,tuni hankalin ta ya dawo daga duniyar da ta lula tace ” ya dai?* ya had’e rai yace ” kin barni babu hira sai faman tauna kike yi !! Ni na fa gaji ma kuzo mu tafi inda zamu je kafin dare yayi mana” chan sai suka lura ko ina yayi shiru cikin kogon


Cikin sand’a yake tafiya tana biye da shi ,haka suka gama dube duben su basuga Kowa ba a cikin kogon ,Jaseena tace ” toh ina suka tafi ne?” Haidar ya yi shiru na yan mintina sai yace” duk yadda akayi sun nufi Kalahari ne zo mu tafi!! ” ko da suka fito bakin kogon suka tsaya suna tunanin yadda za’a yi su tafi Kalahari babu doki kuma gashi da nisa suna so su tadda su Jauda. Har ta hak’ura ta jingina da jikin kogon kawai suka jiyo sautin doki ,tana juyowa ta hango zainu shi kad’ai ya dumfaro su ta juya ta dubi Haidar tace baba ne ya turo shi , na tabbata sun isa Kalahari!! ”


🏵 Jeeddah ja’o🏵

[4/7, 9:36 PM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeedah ja’o🏵🐚


8⃣6⃣⏭9⃣0⃣


Isarsu Kalahari basu zame ko ina ba sai cikin fada kamar wanda ake jiran isowar su mutane aka fara bude hanya don su samu su wuce ,Jaseena kam da ta hango baban ta taga yadda suke tafiya a hankali a saman dokin ,yasa ta dirko daga kan dokin ta ruga. Rungume mahaifin nata tayi tana kuka ,ya d’ago ta yana faman share mata hawaye ,zata yi magana kenan suka ji Hameed ya ja wani irin numfashi kamar an shak’e shi ,idon shi na hawaye ,tace ” baba!! Me ya sameka baba??” Kallo na biyu da zata masa ne ta ga abunda ya matuk’ar tada mata hankali ,mashi ne a wuyan shi ga kuma Jini yana malala kamar ruwa ,a take ta kurma ihu ta zube a k’asa jiki na b’ari ,da gudu Haidar ya iso inda suke ya rike Hameed yana hawaye , abunda ya iya furtawa shine ” ga Y’ata nan Amana ,Kar ku cutar da ita marainiya ce don Allah!! ” ya dan saki wani ‘kara gami da Kalmar shahada take ya mace a gurin ,wani irin ihu Jaseena tayi ta sulale daga zaunen da take ta fad’i sumammiya Haidar ya dubi su Jauda da ke faman zubar da k’walla yace ” ku kai Jaseena ciki ku tabbatar ta samu kulawa don Allah ! Suka yi kamar yadda ya umarce su.


Haidar yace sojojin yak’i su shiga su nemo koma waye yayi wannan Harbin a kawo masa shi. Ana cikin wannan alamari ne wani soja ya zo da gudu wujiga wujiga duk jikinshi yanka ,sai haki yake yana kiran sarki Haidar. Fadawa suka tare gurin shigowar amma ya umarce su da su barshi ya karaso domin daga ganin shi kasan akwai wata matsalar da ke tafe da shi. Kafin mutumin ya fara magana ,Haidar ya juya ya dubi su Rizwan yace ” a shirya gawar baba mu sallace shi Mu kaishi makwancin shi na gaskiya,” sannan ya juyo ya dubi mutumin yace ” bawan Allah me ya faru da kai haka? Wa ya aikata maka wannan taaddancin kuma daga ina kake?

Cikin rawar jiki mutumin yace ” Allah ya baka nasara daga Ramali nake ….” Ko da Haidar yaji an ambaci Ramali yasan tabbas babu lafiya gashi sarki Hameed ya rasu ,ga Jaseena Kwance babu maraba da matacciya dole su Jauda su kasance tare da ita , toh me ma yake faruwa ne haka?” Tambayar da yayi wa kanshi kenan gaba daya ya kasa tunanin abu daya, ya tura wasu Fadawa tare da mutumin su bashi taimakon gaggawa kuma a kula da shi”…….


Ana shirin sallatar Hameed ne Jaseena ta farka ,bata bi ta kan su Jauda ba ta furma a guje ko mayafi babu duk gashi a barbaje gashi duk ta zabga gumi gashin ya mammanne mata a fuska bata zame ko ina ba sai gaban gawar mahaifin ta cikin yanayi na tausayi ,bakinta karkarwa kamar mai jin sanyi , ta d’aga hannun ta mai karkarwa kamar zata yaye masa fuska sai kuma ta fasa ta dunkule hannun cikin kuka tace ” baba !! Ka tashi don Allah kar ka tafi !!! Abunda ta yi ta maimaita wa kenan hakan ya sake tada wa Haidar hankali don a tunanin su ta zauce ne ,yadda take yi din abin tsoro da kuma tausayi. ” Meenah ku koma da ita ciki don Allah ” shima yana kokarin danne kukan da ya so kufce mishi.


Bayan sun dawo daga janaiza Haidar bai zame ko ina ba sai cikin fada don ya nemi dakin da Jaseena ke Kwance ,ko da ya iso gurin shi da Rizwan basuga Kowa a d’akin ba ,babu Jauda ,Jaseena Aisha da kuma Meenah. Haidar ya fito a fusace ya dubi bafaden da ke bakin k’ofar yace ” ina suka tafi kuma ?” Bafaden yace ranka shi dad’e sun fita su hud’u amma fa naji kamar suna maganar Ramali ban sani ba ko Chan suka nufa……. Bai ma saurari k’arshen zancen ba ya juya suka nufi hanyar fita……………….🦃


🏵Jeeddah ja’o🏵

[4/8, 8:19 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


9⃣1⃣⏭9⃣5⃣


Gudu suke kamar zasu tashi sama ,Jaseena ce kan gaba sai faman k’walla take yi zuciyar ta na ta tafarfasa har suka isa masarautar Ramali ,shigan su ke da wuya suka ji ana ta rufe kofofin gurin wasu sojoji suka zagaye su kamar masu kama barayi ,babu wanda ya motsa a cikin su tabbas Jaseena ta lura cewa duk sojojin da ke zagaye da su kibiyar da ke kwari da bakan su iri d’aya ne da wanda aka harbi mahaifin ta ,ta tabbatar cewa wannan aikin Jalalud-deen ne ba Kowa ba ,abunda ya sake kulle musu kai shine yaya akayi suka fito daga wannan kurkukun? Jauda ma abunda take ta sak’a wa kenan………


Ko da Haidar ya fito waje ,yasa an tara mishi jama’ar garin manya da k’anana da kuma gagga gaggan sojojin yak’i wadanda ake ji da su suma sun hallara nan ne Yerima Rizwan ya rok’eksu yafiya kuma ya sanar da su cewa zai yi koyi ne da irin halin kawun shi marigayi sarki Hameed ya kuma yi rantsuwa da hakan ,Kowa ya ji dad’in wannan alamari saboda haka dattawan garin basuyi wata wata ba suka na’da shi sarkin Kalahari ,bai hau kan karagar mulki ba yace har sai yaje an yak’i azzaluman da suka kashe sarki Hameed kuma in har bai dawo da rai ba ,toh ya bawa Meenah wannan gadon mulkin domin ita tafi chanchanta ,amma idan har komai ya tafi daidai toh za’a hada masarautar Ramali da Kalahari su zama masarauta d’aya a k’ark’ashin mulkin sarakuna biyu wato sarki Haidar na Ramali da kuma sarki Rizwan na Kalahari ⚔


Jaseena bata wani tsaya 6ata lokaci ba ta zare takobin ta ta diro kasa suka fara fada su Jauda ma suka biye mata gurin ya kaure bakajin ‘karar komai sai na had’uwar karafuna kafin kace wani abu sun gama da sojojin suka tsaya a gurin sai haki kamar zakanya Jaseena ke yi ta mayar da takobin cikin rigar shi ,d’aga kanta da zata yi kawai ta hango munafukan guda biyu ,sarki Jalalud-deen rik’e da kan d’aya daga cikin damusar da ke gadin kurkukun ya d’aga sama yana kyalkyata dariya daga chan saman benen da yake yace ” me ya farune GIMBIYA JASEENA!? Ina fata ba karaya kika yi ba don in hakane wasan Sam bazai yi dadi ba ! In kin isa yadda na saka tsaro dinnan ki karaso kiga me zai faru! Amma ko da yake ina so inyi magana da ke ,kuma ke kadai don haka ke kadai nake so ki zo ki sameni babu makami kuma !!! Ya sake burgewa da wata muguwar dariyar. Jaseena da idanuwan ta sun kad’a sun yi jajir ta kau da kanta daga duban da take masa tace KAI !!!! MATSORACI!!! KAI NE KAKE TUNANIN TAKOBI KO BAKA SHINE ASALIN MAKAMI ,AMMA ASALIN MAKAMI A ZUCIYA YAKE!!!!” Ta zubar da makaman zata tafi su Jauda suka sha gabanta Aisha tace ” Jaseena ba zamu barki ki shiga ke kadai gurin wad’annan azzaluman ba gaskiya” Jaseena tayi murmushi tace Haba Aisha ,ai koda kashe ni zasuyi inshaa Allah zan shiga kuma zan d’auki fansa!!:evil: ta wafce hannun ta tayi ciki duk fadawan suka bita da kallo 🙄


Shiganta kenan su Haidar suka iso gurin ,garin ma shiru kamar babu Kowa , a nan ya iske su Jauda cikin matsananciyar damuwa , suka sanar dashi duk abunda ke faruwa hankalinshi ya tashi Rizwan yace ” yanzu meye abun yi ??¿

Jaseena kuwa da ta shiga kai tsaye fada ta nufa shiganta kenan taji an rufe k’ofa ta juya da sauri don taga wanene daga cikin su, Muryar shi ne ya fara ratsa kunnuwan ta tabbas sarkin yak’i Amjad ne:oops: ta waro ido waje tace ” kai ! Dama Kaine?!! Me kake yi a nan kuma?!!” Ya matso kusa da ita ya makureta a bango kamar me neman kasheta ,sai taji yana mik’a mata abu a hannun ta ,tayi amfani da tunanin ta taji ashe karamar wuk’a ce tayi wata k’aramar dariya yace ” godiya nake” shi kuma ya hankad’a ta gefe ta zube a ‘kasa su Jalalud-deen kuma basu san wainar da suka toya ba sai wani dariyar keta sukeyi. Jalalud-deen ya karaso inda take rik’e da irin kibiyar da aka harbi Hameed yace ” ban sani ba Jaseena ! Ko tayaya zan fara gamawa da ke ! Ko in sambad’e ki da wannan takobin ne kokuma wannan kibiyar wadda itace silar barin ubanki da uwarki duniya?? Ko kuma………… Kafin ya karasa ta buga masa wannan y’ar wuk’ar a daidai mak’ogoro kamar me bud’e madarar peak 😜 tuni ya durkusa kan gwiwar shi ,Jini na malala kamar ruwa, ta zare wuk’ar tace ,ba sai ka za6a ba🙄 take ya fadi ‘kasa ya gama shure shuren sa har ya margaya (Hmmmm duniya kenan budurwar wawa akan son abin duniya har ka kai kanka ga halaka!!) Ta juya ta dubi sarkin yak’i tace” ina Hasheem? ” ya nuna mata k’ofar fita yace ” ya fice tun tuni! Mu bishi!!!!! Jaseena tayi wata muguwar dariya tace Kar ka damu ,yayi gudun gara ne ya tadda zago don nasan yanzu haka jikina yana bani ZAKI NAH!(Haidar) ya riga ya iso 👣


Suka dunguma sukayi waje suma, ko da suka fita basu tarar da Hasheem a raye ba amma kuma kamar mutuwar kasko sukayi da Jauda😭 da gudu Jaseena ta yo kan Jauda da ke Kwance a gurin matacciya ta rungume ta ,kuka takeyi duk ta susuce su Meenah ma na durk’ushe a gaban su suna kukan. Haka ranar Jaseena ta kwana tana kukan zuci wanda yafi kuka ciwo😭……………


🏵Jeeddah ja’o🏵

[4/8, 10:20 AM] Jeeddah ja’o🏵: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016

🐚🏵Jeeddah ja’o🏵🐚


9⃣6⃣⏭1⃣0⃣0⃣


BAYAN SHEKARA D’AYA


Zaune yake kan kujerar mulkin sa yana magana da waziri Jabeer ,sarki Haidar ne cikin kaya na alfarma na sarauta sai hira sukeyi wanda har masu gadin ma suna saka baki , ana ta raha, chan waziri yace ” Allah ya baka nasara zan iya yafiya yanzu?” Haidar yayi murmushi yace me zai hana ? Ko so kake kayi tafiyar dare baka ga yamma ta kawo kai ba ? Waziri Jabeer yayi murmushi ya mik’e ya nufi hanyar fita.


Dank’o ne a hannun ta irin na Harbin tsuntsaye ta saita shi a kan kujerar ta sake masa daya a hannun shi ,ko girgiza bai yi ba ya basar ,har tayi sau uku ,sannan ya juya don ganin me aikata masa hakan. Had’a idon da zasuyi kuwa ta zaro manya manyan idanuwanta da suka sha ado da kwalli:oops: sannan ta tattare doguwar rigarta ta ruga a guje ta fice zuwa lambu , murmushi kawai yayi ya mik’e ya kwashi duwatsun da ta jefo mar ya fice ,bai ma san inda ta nufa ba shidai kawai yana ta kallon yadda mutane Kowa ke gudanar da alamuran shi cikin lumana wasu yara kyawawa sun kai biyar suka rugo da gudu suka rungume shi suna dariya ,sai d’aga su sama yake yi yana musu wasa wata tazo wucewa dauke da kwando cike mak’il da kayan marmari ya tsayar da ita ta kawo ma yaran ,sai tace ” Allah shi taimake ka Sarauniya JASEENA ke da buk’atar su ” murmushi yayi yace ” ki basu sai a kai mata wasu , tana ina ne itan?” Matar tace tana cikin lambu ” gami da mik’a masa kwandon ta wuce. Shi kuwa ya durk’usa gaban yaran ya ajiye musu kwandon yace ” bismillah! ” kowannen su ya d’eba shima suna ta Saka mishi a baki sai da yaga sai loda mar suke ya mik’e da sauri yace ” Yauwa maza ku cinye kafin na dawo ya wuce ya barsu suna ta fama ,ba ma mutane ba har dabbobi ma sun san akwai y’anci a Ramali:).


Lek’o ta yayi suna had’a ido ta ruga da gudu ya bi bayan ta sai fama take da doguwar riga hakan yasa ya cimmata ,ya d’aga dutsen data wurga masa kamar zai rama sai yaji daga waje wani mayak’i yace ” Allah ya baka nasara sarkin Kalahari Rizwan ne tafe da Sarauniya Meenah!!!! Jin hakan yasa ya sauk’e hannun shi yace ,a shirya tarbar su ,kuma a sanar da sarkin gida ” mayak’in yace toh ranka shi dad’e! ” sarki Haidar ya maida dubanshi ga Jaseena yace ,kin taki sa’a yau da sai na rama jifan da kika min!!” Ta rungume shi tana ta dariya tace ” kai dai kace kaji tsoro Kar na fille maka kai yanzun nan 😝 ” ya bushe da wata irin dariya yace ” ni din ? Toh ko za’a gwada karfi ne?” Ai ko bamu gwada ba kasan na fika k’arfi 💪🏼” ya sake bushewa da dariya yace ” karfin cin tuwo ba! Yanzu ma naga an taho da k’aton kwando cike mak’il da kayan marmari Wai naki ne 😜 ” Tuni ta had’e rai tace ” toh ai kasan ba ni kadai bace shi yasa 😒 ” ” Ohhhhh na gane !!! Kar kiyi ma d’ana sharri ,ke kad’ai kike cin kayanki ☺” ta bugi kirjin shi da hannun ta tace ” zan rama ai!!!” Ya kama hannunta suka fita suna tafe yana tsokanan ta………..


Haka dai rayuwar su ta kasance cikin farin ciki da kaunar juna ,ga gaskiya da rikon Amana ,sukan ziyarci junansu daga su har su Rizwan ,Aisha ta auri abokin Rizwan ne majeed aka kuma suka zauna a gidan Benaxir don yanzu kam bata nan dama ba gidan ta bane mallakin su Aisha ne ,majeed kuwa likita ne don babu wani magani da bai san amfanin shi da kuma yadda ake hadawa ba!! Saboda haka wannan babban gida ake kiranshi da gidan majeed likita!


Akwana a tashi yaran Jaseena biyu ,na farkon sunan mahaifin ta ne wato HAMEED na biyun kuma mace ce mai sunan JAUDA yara ne kyawawan gaske son Kowa !

Bangaren Meenah kuwa danta daya mai sunan mahaifin Haidar wato MAHMOUD! Aisha kuwa mace ta Haifa sunan ta Sameerah sunan kanwar majeed da ita ,gaba daya suna cikin farin ciki ,nutsuwa da kwanciyar hankali ,zalunci ya kau!!!!


🙏🏽ALHAMDULILLAH🙏🏽


Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah mai Kowa mai komai wanda ya kawo ni har izuwa wannan ranar da na kammala wannan takardan nawa mai suna JASEENA !!


Dama ance in kaki sharar masallaci zakayi ta kasuwa ,kuma abunda kashuka shi zaka girbe , masu iya magana sunce RABON KWAD’O BAYA HAWA SAMA!!!

Duk abunda Allah ya kaddara zaka samu tabbas babu makawa sai ka same shi ,amma in kasa son zuciya toh lallai zai zamto sanadiyyar zubar ruwan idanuwa a gareka 😭 Allah kasa mu dace AMEEN


ALL CREDITS GOES TO

MY BESTIES

– Rukayya Abdullahi Kakumi (Rukey kaxs)

– Aishat Muhammad (maman abd Shakur)

– Sufeeyah abdoul

– mah Nancy trbl

-my ‘kawas Zeetu and Zainab Ahmad…..

And Ameener esmael( maman Ilham)

GODIYA TA MUSAMMAN

AJAJIGEEE GROUP

ZINARE BOOKS

SADAU GROUP OF WRITERS !!!

AND OTHER MEMBERS OF JEEDDAH JAO 📚NOVELSTOPIA🏵

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *