Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 28

adsense here WACE CE ITA..?? 28
Na ABBA GANA
Qawa kuma Alhaji ya maimaita?, eh lokacinda
tazo tayi kwana hudu anan har na taba mata
kaya ta mareni, hajiya tace amma dakinki take
kwaniko?? Aah dakin farhaaah take kwana ai ba
ita kadai bace sunada yawa, yace min duk
qawayensa ne, yace wai anan wayewane,
sabida nace mai mu qauyenmu iskancine, umma
tace hardake yake kaiwa dakin nashi?? Aah
hajiya ni kullum dukana kawai yakeyi, nan dai
madam iffaat tayita bada labarinda
ba'atambayetaba, ganin duk sunyi shiru ransu a
bace yasa tasha jinin jikinta a ranta tace koda
yaya farhaan yace aboki mace gun namiji a birni
shine wayewa so ba komai bane, taci gaba da
kallonta sukam tuni sun bar gun sunje daki
domin tattauna xancen wayo farhaan Neman
mata yakeyi.!!! Ran umma yayi matuqar sosuwa,
saida tayi hawaye, Abba yayi ta bata haquri,
Da yamma farhaan ya dawo da farahnax coz
tunda suka dawo cikin yawo suke, umma ta
turkeshi da ba zata! Tace mai dazu baka nan
daya daga cikin budurenka tazo nemanka, ya
Sosa kai budurwa umma?? Eh inaga bakuyi
waya ka gaya mata iyayenka sun dawoba hala?
Ko kuma tana sane tazo ta nuna kantane ko
qawayenka zance a yanda kake cewa kai
wayayye, nan umma ta shiga yimai fada kamar
numfashinta zai dauke Dan takaici, iffaat ce taji
magana fada fada tafito taga abin mamaki ana
yiwa farhaaah fada, farahnax ta koreta, umma
tace ta tsaya, taja ta tsaya, ai ita ta fada mana
yarinya yar albarka, farahnax ta taso a fusace
tazo gun iffaat kinyi muna funci kinji dadi
munafuka kawai, iffaat tace haba daga fadan
gaskiya saikice nayi munafunci ai ba qarya
nayiba labari na baiwa umma kuma ni bansan
fada zata masaba, kee ina magana kina magana
sakarya kawai ta wanketa da mari, kamin ta
sauke hannu tuni iffaat ta aiko mata da nata
saqon Marin,umma tace that is very good iffat,
ta gane very good coz malamansu na
makarantar boko kamin a koresu yana cewa very
good, idan aka bada amsa yaji dadi kin min
daidai gobe sai ki qara dukanta, umma ta kalli
iffat tace duk ta dakeki ki rama ran farahnax ya
gama baci koba kamai ta girmi iffaat anxo ana
siyamata raini a gunta. fau zata wuce dakinta,
kowa yayi tsit a palon Abba yace ta dawo duk
Ku zauna har umma ta zauna, ya kalli farhaan
daya sunkuyar da kanshi a qasa tunda aka fara
zancen, abba ya kalli farahnax da tasha mari
umma nacewa good, ya kalli iffaat da tayi wani
rasha rasha da ita a qasa tana kallonsu, Abba
ya fara magana yace farko dai iffaat ba gulma
takawo manaba labari ta vamu kuma da ita
yarinyar batazoba da naxamu saniba, a yanda na
fahamci labarin itama farhaan ya gaya mata, har
take cewa a garinsu maiyin haka Dan iska shi
kuma yace anan wayewace kunga ita bata
daukeshi bad thing ba cox haka ya nuna mata,
ya juyo ya kalli farahnax millions time na gaya
miki ki daina saurin fushi, ke macece Aure zakiyi
ba abinda haka zai haifar miki nan gaba sai
nadama, iffat kin burgeni da kikayi jarumta irin
haka amma ki riqa haquri kuma ki kula da
Wanda ya girmeki, tace Tau Alhaji., ba ko wanne
mutum bane zai iya yanda kikayi, kai farhaan
bayan sallar maqreeb ka sameni a daki... Abba
ya tashi umma ta bishi, farahnax ta juyo gun
iffaat ke ni zaki Mara......?? adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *