Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 18, 2015

WACE CE ITA? 29

adsense here WACE CEE ITA..?? 29
Na ABBA GANA
Farhaan duk da baiso yin maganaba saida yayi,
lool farahnax ki fita hanyar iffaat ya fiye miki,
banason kina biye mata yarinta Yana damunta
kuma bakisan ko waye itaba, tace WACE CE ITA
bayan house girl dinmu..! Nidai na fada miki ya
miqe ya fita iffaat ma tashi tayi taje dakinta,
tana zuwa tahau hada kaya, kawai ita dole ta
koma qauye ita ba zata iya zama a gurin da
tanaji tana gani a mata bata ramaba, sabida
haka gara qauyensu, suci uban juna da yan
qauyensu
*****
Ki bari sai an kusa sallah mana, aah hajiya
inason inyi azumi gidan mu, goggo ita kadaice a
gida, kamar tayi goggo aikin takeyi, bayanda
ba'ayi da itaba, amma iffaat ta rufe ido tace
gida take so dole suka haqura suka barta..
sun shirya mata goma na arziki akace farhaan
yakaita, baisan qauyen ba amma an mai
kwatance sai ya gane ita kuma dama da an isa
garinsu zata gane gidan su.
Suna kan hanyar komawa yake gaya mata zai
tafi karatu UK bazai dawoba sai bayan shekara
uku saidai ya riqa zuwa hutu, ita kam duk daya
a gurinta, Dan ta gaji da zaman birni ba abokai,
sun Isa qauyensu yara kuwa tun daga farkon
gari suke bin motar har aka shigo ainihin qauyen,
iffaat tace ya tsaya, yace mun kawone tace
kaidak ka tsaya, ya tdaya. leqowa kawai tayi ta
kallesu batama fitoba gabaki daya yarannan
suna ganin iffaat a mota suka watse, suna ihu
wallahi ippatu ce kozo mi gudu, bawanda ya
manta da ita, cox har yanzu su dije da rukayya
ana xuba iskanci son rai a gari...
Sun Isa gidan su ta tarar anyi ginin bulo an
gyara ko ina abin ya bata mamaki, farhaan har
ciki ya shigo goggo na ganin iffaah ta Hau salati,
da mamaki Dan batasan zatazo yauba koda
matar da ta dauketa tace mata qarshen wata
zata dawo kamin azumi kenan tayi sallah gida
sannan ta koma.
Aka fara shigowa da kayan abinci kala kala, ita
kanta iffaat batasan dasuba, sannan ga kayan
sallar da umma ta mata kala uku shima farhaan
ya dinka mata guda biyar ya qara biyu daga
baya, goggo ma an kawo mata atamfa guda biyu
baki yaqi rufuwa Dan murna....
Muje zuwa muji anya iffaat zata iya rayuwa a
qauye ko yaya?? adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *