Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, October 26, 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-11

adsense here rayuwar-fauziya.jpg

11RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (11) Cigaba 11.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Me Fa'iza
takeson sanar da ni? Meye ma'anar wannan
d'abi'a da Nuraddeen yake aikatawa ga matarsa?
La'anannun mutane 'yan LUWA'DI su aka sani
da wnnn d'abi'ar, Nuraddeen kamilin mutum mai
faran faran da jama'a? Ya ALLAH kasa ba wnnn
bace d'abi'arsa. Ban 6ata lkc ba nakira Mama
awaya nace Fa'iza takirani bata da lfy me aikinta
batanan tace don ALLAH inje in taimakamata,
hankalin Mama atashe ta amince inje indubata,
ban 6ata lkc ba nashirya natafi nabar Fadila
agida. Ina shiga falon na iske Hajara me aikinta
tana goge goge a falon, da gudu ta tsuguna
tagaisheni tare da yimin sannu da zuwa yarinyar
tana birgeni akwaita da ladabi, bayan mungaisa
nace ina Auntyn tace "tana d'aki akwance" kai
tsaye na wuce d'akin nasan Nuraddeen bayanan,
Ya Salam! Akwance nasameta tayi goho kamar
me azababbiyar lalurar basir, subahanallahi
Fa'iza abin har yakai haka? Ta d'ago da hanzari
agwaggwafe ta ri'keni tana zubar hawaye,
Fauziyya ina cikin wani mawuyacin hali banda
sa6awa Mahaliccina da nayi ga lalurar data
addabeni ga d'abi'ar da Nuraddeen yake akaitata
akaina da gangan aduk lkcn daya bu'kaci hakan,
idan nakasance cikin wnnn halin wllh Mutuwa
zany... Ta sake fashewa da kuka tare da wani
irin tsuguno jikin gado kamar me na'kuda,
hawaye naji yafara sintiri akumatuna na tausaya
mata matu'ka, na tsuguna na dafa bayanta nace
Fa'iza yasan kina cikin wnnn halin kuwa? Ta
gyad'a kai alamar eh, amma yake miki wannan
izayar don rashin imani km yagama yatsallake
yabarki awnnn halin, yazama dole afad'awa
Mama ba ita kad'ai ba harsu Abba Tijjani ('yan
uwan Abbanmu) idan bazai daina wnnn muguwar
dabi'ar ba to sud'au mataki akansa, cikin hanzari
tad'ago fuskarta wadda ta ji'ke sharkaf da
hawaye ramarta ta bayyana kamar wadda ta
jima tana cuta, tace " Fauziyya kitaimakeni karki
sanar da su, yayimin gargad'i idan nasanar da
kowa zaid'au mataki mai muni akaina don
ALLAH ki rufamin asiri, Fa'iza bamu da mafitar
data wuce wnnn koda auren za'a raba gwara
araba don wnnn cutartayi yawa ga tsagwaron
sa6o kuna aikatawa, da ace yaadena halin da
yake shikenan amma bashi da ranar dainawa
meye amfanin 6oyewa? Fauziyya inason mijina
idan narabu dashi zan shiga wani hali dayafi
wnnn muni, rabuwarmu awnnn lkc duniya zata
iya zargin komai akanmu, munemi wata mafitar
datafi wnnn sau'ki, na kalleta cikin takaici nace
yanzu Fa'iza har akwai ragowar SO ga wanda
yake cikin wnnn halin? Lallai baki da hankali
bakisan ciwon kanki ba, zakijawa kanki masifar
da zata gagareki zama lfy, ki ajiye SO kinemawa
kanki 'yanchi idan ba haka ba zai wula'kanta
miki rayuwa abanza yacuceki, ina iliminki ina
wayewarki? Dazaki zauna kina aikata sa6o da
cutar da kanki azahiri? Karki yarda zuciyarki ta
fifito umarnin Nuraddeen ko soyayyarsa akan na
mahaliccinki, har takaiki ga sa6a masa cikin sani
ki dulmiya kanki a halaka. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *