Friday, January 15, 2016
NA DAINA SO!! 41 & 42
NA DAINA SO! 41
Muhd-Abba~Gana
amma zata ji dadi kuwa idan aka ce yusuf mayaudarine? shin yusuf zai dawo? wata rana zai tuna da ita ya dawo? idan ya dawo zai nemi gafararta? idan ya nemi gafararta zata iya yafe masa kuwa? babban abin da yafi ci mata kawo a kwarya har yanzu tana son yusuf kuma tana ji a jikinta kamar ba zata iya daina son shi ba lalle so babbar cuta! kiyi hakuri mairamu na san cewa nayi laifi babba don Allah ki yafe min yusuf ne ya durkusa a gabana yana bata hakuri nima wannan al,amarin ba,a son raina ya faru ba har da hawaye a fuskarsa na yafe maka.........na yafe maka....tana mai kuka ta fadi hakan a daidai lokacin ta farka daga barci cikin talatainin dare sharkaf! jikinta ya jike da gumi takaici ya lillibeta bayan data tuna da mafarkin da tayi tana sa ran wata rana mafarkinta zai zama gaske tana sa ran kwananta ya kusa karewa WASHE GARI DA SAFE tana cikin wanka taji an kwala mata kira tsayawa tayi cak! muryar irin tasa ce.......a,a ba irin muryarsa bace
... muryarsa ce mana kiranta a ka kuma yi a karo na biyu daga can daki ake kiranta hakika muryar yusuf taji.
Muhd-Abb~Gana
www.abbagana.pun.bz
NA DAINA SO!42
Muhd-Abba~Gana
yusuf ya dawo! ya dawo bata hakuri bata damu da wanke kumfar da ke jikinta ba zani ta daura ta fito a guje daga bandaki ta nufi daki arba tayi da kabir tsaye a kofar falo lafiya ya tambaye ta a razane ya...ya..da..wo?? ta tambaye shi a rude sannan kafin yace wani abu taci gaba da magana yayin da numfashinta ke neman dukshewa daga jikinta kamar mai fama da ciwon asima na....na...na jiyo muryarsa ba muryarsa bace muryata ce inji kabir a guje mairamu ta karasa cikin daki don ta tabbatar ba kowa a dakin karo na farko da kabir yaji tsoron kada mairamu ta haukace a sanadiyyar cin amanar kauna a ranar bayan da mairamu ta idar da sallar la,asar lekawa tayi kofar gida a in da ta hangi yusuf tsaye yana yi mata murmushi na san dama zaka dawo kusan da karfi ta fadi hakan yayin da ta nufe shi a guje rungume shi tayi tana kuka ture ta yayi cira kai tayi ta kurawa fuskarsa ido sai a lokacin ta kula mutumin da ta rungume ba mijinta bane kuma ba mijin surayya bane sunansa kallamu kusan duk sa,ilin da mairamu ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yusuf a wasu lokuta yana bata hakuri yayin da a wani sa'in yake yi mata wulakanci iri daban-daban jefi-jefi surayya a mafarkin sau da yawa tana kyalkyala mata dariya.
Muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
Gaskiya kana kokari mallam abba allah ya kara basira
ReplyDelete