Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 10 February 2016

BANA KAUNARKA!!! 21

adsense here bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

21


Muhd Abba Gana


gargadi:ban yarda wani ya cire koh ya kara wani abuba
--------------------------------------------

Yaya ai na share maka ya kalli dakin cike da takaici ko tsarar da tai bata kwashe va a kofar dakin ta barta sannan dakin buzu buzu faruq yace ayya kadan daga cikin aikin mahida,Al'amin ai tayi maka mai kyau ni dana sata gaba daya karkashi gado ta tura min sharar ka ganta nan bbu abin da ta iya sai kallo sai soyayya Al'amin ya hau salati da kin san baki iya ba kice min to kanwar kanwarki ta fiki iya abin duniya,mahida kuka ta saka ai kun san tuni ya ba kuka sani al'amin dan haushin bai karasa magana ba lallai ya shiga tattare sharar.
kwalliya nayi sosai na shirya cikkin wani ratsatten less,leshin ya amshe ni nayi kyau ainun na rataya jakata na sa karamin hijabi dakin dubai anty na tafi to wahida ki gaida mom amma fa kar ki kwana to anty a wacce mota zanje? ta mike ta dauko min mullin nace la! anty motar yaya shahid umh ni dai tsoro nake kin san motarsa da sunansa kar inje aka mani,antu tai ta dariya bbu me kama ki kallo daya za,ai miki a san ke kanwarsa ce,bbu me kamaki na juya na salube kai gaskiya notar akwai kyau, mota ce wadda ta amsa sunanta rantsattsiya kirar zamani gaban motar kawai zaki kalla kinsan waye me motar da manyan baki aka rubuta BOM BOY sai dana gama karewa motar kallo sannan na bude na shiga wayyo sanyi da kanshin me motar yaso rudata na shiga lumshe ido kwance nai cikin luntsumemiyar kujerar motar jina soma gyangyadi nai kirgil hoton me motar dake jiyawa gaban motar na zubawa ido yana murmushi yayi kyau ainun hannu nasa na shafi a fuskarsa tare da fadin i love you so much yayana,wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu,ashe duk abinnan da nakeyi bom boy na bayan motar yana kallona,ohi sam ban sani ba koda na hau titi nayi mamakin irin yadda mutane da dama suka dinga daga min hannu kasancewar glass din motar mai duhu ne bbu wanda ya ganni gaskiya kan naje gida na kara tabbatarwa shahid mutumin kirki ne mai jama'a.
ina fitowa mai gadi yace sannu da zuwa yauwa baba tsoho ya gida? lafiya lau ina shiga sister ta fito da gudu muka rungume juna dakin Abba muka karasa abba sannu,yauwa sister wahida abba ina kwana? lafiya lau wahida,ya kika baro yar uwar tawa tana nan lafita ta mace in gaishe ku muna amsawa da sauri na mike da gudu nai dakin yaya faruq hello yayana na fada jikinsa ya dago fuskata sister amma kin dawo kenan? la! anty wata in dawo anya anty ba zata bar man keba,umh ai nafi son can saboda me? can sunfi sona basa dukuna da sauri na fita hello ya amin hello ya amin dina na dawo na rungume yayana yace yaushe kika zo sister yanzu nazo amma kin zo kenan munyi kewarki,
Abbagana hausa novels @ facebook.www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *