
🍃ETRAT🍃 Complete
By Hauwa jabo 08:06 No comments
[5/16, 1:10 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 1&2
Na Hauwa M Jabo
Zaune nake a kan daya daga cikin manya-
manyan kujerun da suka mamaye falona, wanda
dagani kasan cewa gidan akwai ni'ima da hutu
mara iyaka a cikinsa, ga wadata ta kowane
fanni amma kana dubin mai gidan, wato ni zaka
fuskanchi cewa ina cikin matsananciyar
damuwa...
Tunani nakeyi wane irin haline nasamu kaina
a ciki? wanda nikaina nakasa gane bakin zaren
abun!! nidai sunana ETRAT, mahaifina yanada
hali dai-dai gwargwado tayanda zamu rufawa
kanmu asiri.
Inada k'ani guda daya Hammad, da yar
autarmu Iffat, atak'aice nice firs born a
gidanmu, nayi karatu daga prmry har zuwa
secndy, bayan na kammala secondry, nanfa
mahaifina yace dole aure zaimun, araina
nakance naga yanda ake aure ba miji.
Allah yayi min kira ta halitta, wacce duk
namijin da ya kalleni nasan sai ya maimaita, ni
ba doguwaba kuma ba gajeraba, inada
matsakaicin tsawo gani yar duma duma dani,
inada hips sosai wanda har asibiti naje inason
su bani magani su rage girma, akace ba magani
saidai ayimin aiki arage su, ana zaune k'alau ina
naga kud'in ragiyar hips?
Tun daga nan ban k'ara zuwa asibiti zancen
ragiyar hips ba, kirjina cike fam, kamar an
girkasu gasu lukuta-lukuta, inada ido manya
manya wayanda idan ka kalleka sai ka kauce,
dan wai sexy ne injisu, wasu na cewa kamar
nayi sha haka nake yi da idanuwana, abin
yazamomin kamar al'ada lumshesun da nakeyi,
amma ana cewa wai dagangan nakeyi, hancina
dai dai ni, kai nidai badan kar inyi saboba, da
sai nace ni dai na cika goman da ake cewa
mutum dan tarane, sabida banida rangwame ko
daya a halittar jikina, fagen gashi kuwa, nikaina
bansan inda nayi gadon gashiba, sabida mamata
da babana dukansu hausawan sokotone gaba da
baya, haka Allah ya halicceni da gashi bak'i silk
ga tsawo ga shegi ni farace amma ba irin
mugun farinnan ba ataqaice dai wllhy inada kew
sosai, wata baiwa da Allah yamun itace kwata-
kwata bana warin zufa, kuma idan nasaka turare
ajikina ko bashida tsada zakiga yadade ajikina
bai bi iskaba, wanda hakan yakesaka bana saka
turare sosai .
Sai kiji ana
"wane turare kika saka haka Eetrat??" basusan
cewa jikinane keda wannan baiwarba, kuma gani
da wata irin mahaukaciyar tsafta, ga
k'yank'yami da yake damuna, idan guri bashida
tsafta komi tsaftar abinchin sa, bazan iya chiba,
ni kuma haka allah yayini....
Arayuwa na tsani samari, burina in auri tsoho
mai shekaru masu yawa, atunanina yafi sanin
darajar mace, bantaba kawo zancen saurayi
arayuwataba, wanda har nakai shekara 18 amma
ba wani dattijo dayazo neman aurena, duk
samarine, hakan yakan bani haushi da takaici
narasa miyasa wayanda nakeso basa sona, sai
wani sarkin nachi waishi Mahbuob, shinefa yake
biye dani baya barin kowa magana dani kuma
shi bayamun magana, atunaninsa zansoshi
baisan ni sai dattijo ba, nifa ko sa'ar babane
ashirye nake da na aureshi.
Mahbuob matashine dan kimanin shekara 29,
Wanda ya kammala karatunsa, mahaifinsa
yasamamasa aiki a airport, duk sati sai yazo
gidansu gun iyayensa, ya gaidasu haka zaizo
gun babana suyita tadi, har sai ya ganni sannan
yatafi gidansu.
Bai taba furtamin yanasonaba, kuma
baigayawa mahaifinaba, amma duk unguwarmu
kowa yasan cewa yanasona, wasu har matar
Mahbuob suke cemin, ni kuma ko a jikina, dan
nikam ko za'a mutu sai dattijo wanda yasan
darajar mace......
🍃ETRAT 🍃3-4
Na Hauwa M. Jabo
Idan Mahbuub yazo, sai ya rabawa yaran
unguwar kud, da kayan kwadayi, yace musu duk
wanda sukaga ya min magana to sugayamishi,
haka kuwa sukeyi, suna kai masa rahoton duk
wani motsina, idan aka gaya masa wani yamin
magana, zai nemi mutumin yamishi magana da
lalama, yace yayi hak'uri wannan matarsace,
yadaina yi mata magana, idan kuwa yagamaka
bakajiba aka k'ara gayamasa kazo, to zai saka
yaransa suyita jifanshi sai ya daina kulani,
hakan yasa samarin gabaki daya suka daina
zuwa gurina, nadawo banida kowa ba tsoho ba
yaro, kuma shi Mahbuub din yak'i fitowa yayi
maganar aurena..
Ranar wata assabar Mahbuub yazo gurin
baba suna tad'i kamar yadda suka saba duk sati
idan yazo hutu gida, yakanzo gurin baba, yauma
haka nikuma nadawo daga islamiya kenan ina
shiga gida sai Mahbuub yamike yace'
"ni zan tafi baba"
ashe duk yazo haka yakeyi, ina dawowa daga
islamiya daya ganni sai yatashi yak'ara gaba,
sai kuwa baba yace mishi
"zauna inada magana dakai"
ya zauna baba yace mishi
"Wai miyasa Eetrat na dawowa daga
makaranta, duk muhimmanchin maganar da
muke, sai ka katseta, katashi katafi?? ko itace
agogonka??"
Mahbuub ya sosa k'eyya azuciyarsa yace ashe
har anganoshi!!
"Aa'aa baba, kawai ina tunanin yarane sun
dawo gida, zaka shiga gida kuyi tadi da iyalinka,
shiyasa, wai kar na shiga hak'k'in ka dana
iyalinka,"
sai baba yace,
"Idan dai wannan ne to kayi zamanka bana
shiga gida sai dab da magrib idan zanyi alwalal
sallar magrib"
yace
"to baba"
suna tsaka da tadi sai aka kira baba awaya
yadan tashi yakoma gefe yana magana,
Mahbuub haka yazauna sai ga iffat qanwata
aguje an biyota, Eetrat ce ta biyota, wai ta yaga
mata littafine ai kuwa iffat tayi jikin Mahbuub,
Eetrat tabita Mahbuub ya riqe hannun Eetrat
yana bata haquri, haka yaji wani yarr a jikinsa,
sai lokacin Eetrat ta tuna cewa ba dan kwali
akanta balle takalmi, kuma kayan jikintama sai
ahankali, nan take kunya takamata, tajuya zata
shiga gida aikuwa yak'i sakin hannunta, tajoyo
ta mashi kallon na huqura zan shiga gidane.
Tawani lumshe ido, bashiri ya saketa sabida
yanda tayi da ido ya firgitashi ,nan fa baba
yadawo yana tambayar lafiya, iffat zatayi
magana kenan sai Mahbuub yace taje gida, shi
yagayawa baba abinda ya faru baba yay dariya
yace,
"Ai haka iffat take da tsokana kamar me,
Eetrat, din ma takusa aure naga wazata
tsokana..!"
ba shiri Mahbuub ya mik'e tsaye yace
"WHAT!!!???"
Baba yace
"lafiya kamar nagaymaka mutuwa"
Sai lokacin mahbuub yadawo hayyachinsa yaga
ashe har tsaye ya tashi, tuni kunya takamashi,
ammfa idonshi sunyi tsuru-tsuru (kamar Jabo
batada kud'i)
baba yaso yagane cewa Mahbuub, Eetrat
yakeso, amma baice komaiba, tunda yayi kusan
shekara yana zuwa guri na baitaba gayamun
ba, nandai baba yakawar da zancen azuciyansa,
har aka fara kiran sallaar Magreeb, suka nufi
masallaci dan gabatarda farali, amma fa
hankalin mahbuub kwata kwata baya tare
dashi.....zan chi gaba
🍃ETRAT 🍃5&6
Na Hauwa M. Jabo
Yana sallah amma kwata -kwata hankalinsa
baya tare dashi, dan kuwa da ace shi kadai yake
sallan sai yayi demuwa fiye da goma, ba abinda
yake mishi yawo akai sai lafazinda baba ya
gayamasa ai "ETRAT TAKUSA AURE" nan
yatuna da hannunta da yakama wani laushine
dashi kaman auduga ga wani k'amshin turare
dayaji tanayi wanda baitaba jin irin
saba, idan na aureta na more gaskiya ina sonta,
kai yau zan gayamata abinda ke zuciyana, haka
yayita saqe-saqe a sallah nan take yace
astaqfirullah..!!! miyasa baituna da wayannan
abubuwaba sai yanzu, take yatuna ashe sallah
akeyi yayi istiqfari yadawo hayyachinsa, yayita
jiran liman yace allahu akbar yadago, daga
sujada yaji shiru, ashe anqare sallah yanachan
yana tunani, da ya gaji sai ya dago kai, koda ya
duba sai yaga wasu har sun watse daga
masallaci, yaduba yaga baba na lazimi kunyar
duniya ta isheshi baisan lokacinda aka qare
sallah ba, yanata tunani yadai san anyi raka'ar
farko dashi sauran kuwa sai Allah.
ya sallame yaje gun baba yace mishi zai tafi
gida baba yace
"bakada lafiya ne"
yace
" lafiya na k'alau baba"
"To amma naga lokaci daya ka chanza"
yace "lafiyata lau baba idan nayi sallah haka
nake "(kaji bawan Allah) bayan kuwa firgichin jin
za'ayiwa Etrat aurene, baba ya yarda da abinda
yace sukayi sallama yatafi gida...
Etrat kuwa kunya ta isheta yau namiji
yaganta ba hijabi, har ya rik'emata hannu wanda
tun tana karama take zunbula hijabi, har data
girma, sabida mazaunanta dasuke motsawa da
kansu idan tana tafiya sai tak'ara saba saka
hijabin har yazamo mata al'ada, yau shine namiji
yaganta har ya riqke mata hannu kuma tarasa
dalili idan ta tuna sai tayi murmushi maimakon
ta tsaneshi, baba yashigo gida sai taji tanason
taji labarin Mahbuub agurinsa, amma kunya
takeji, wata zuciya nacewa tambaya wata
nacewa aah haka har sukaje chin abinchi dare,
sai ga Hammad yashigo yace
" baba wai Mahbuub yana magana"
mamaki ya cikawa baba ciki yanzu fa suka rabu
ko yayi mantuwane? haka dai da waswasi ya
fita ita kuwa Eetrat ji take kamar ta lek'a
taganshi tadawo, karo na farko arayuwanta
dataji cewa zata iya auren yaro idan dai
Mahbuub ne, dan ya burgeta....
"Lafiya dai Mahbuub?" .
firgigit yadawo yace
"lafiya lau naje gidane wai sun dauka bazan
dawoba, shine basu ijiyemin abinchiba, shine
nazo nan kamin achinye inchi na iffat, sai Eetrat
tadafa mata wani."
Baba yay murmushi yace to bismillah shigo..
babana dduk yanda kake dashi baya kawoka
cikin gida, iyakachinku gofar gida, ko zaure
amma Mahbuub dan gatan baba har cikin falon
baba, dama duk tare muke chin abinchi dadare,
anachi ana tadi bansan cewa yashigoba da sai
na zunbula hijabi, amma ina saida nakawo
tsakiyar falo naganshi suna chin abinchi da baba
da iffat, dama naje kawo ruwa ne lokacin da ya
shigo, kunya takamani gani dagani sai wata riga
mai kamar bes sai wani shot nika, na rasa
yanda zanyi bazan iya komawa ba, natsaya chus
sai Hammad yace
"Aunty kishogo mana."
kamar an mini allura na zabura sai nawayance
nace
"Yau baqo mukayi?"
iffat tace
"Eeh, yaya Mahbuub ne"
nashigo na zauna, bai dago kai ya kalleniba
sannu kawai yacemin haka yasa na sake nachi
abinchina, amma inata sake sake araina, nace
dama karya yakeyi yakoramin samari amma
gashi ko kallo ban isheshiba, kuma yaqi cewa
yana sona, lokaci daya naji na tsaneshi kaman
da..
Dago idon da zanyi in harareshi sai kawai
muka hada ido, sai naga yay murmushi bansan
lokachinda nima nay murmushiba, nakawar da
kai take naji na k'oshi .....zanchi mana gaba
type wahala wllhy
[5/16, 1:28 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃 ETRAT 🍃 7&8
Na Hauwa M. Jabo
Namike tsam zan tashi, mama tace
"ina zaki?" nace
"nagoshi "
zatayi magana nayi mata wani iri da ido..
Ta tabe bakii batace komaiba, ina tashi shima
yaji ya k'oshi haka dai dan kar agane ya rink'a
tusawa, har suka kare, yayi godiya yakara gaba,
yaso ya fadi abinda ke zuciyarshi, amma sai ya
kasa ya haqura yatafi, ita kuwa Eetrat duk
kunya ta isheta namiji yaganta wit out hijab...!
Tun da safee sukaji sallamar bak'uwa ikon
Allah!!!
"Yau maman Ameer kece a gari!!!"
haka tace
"wllhy nice"
"Saukan yaushe?"
tace yau satinsu biyu da da dawowa
" kishigo daga chiki mana"
murna gurin mama ba'a magana yau babbar
aminiyarta ta dawo,
"Bari inje in hada miki abin karyawa"
maman Ameer tashiga d'aki,
Maman iffat ne ta hada mata break fast dai dai
aljihunsu, sunachi suna tadi maman Ameer
k'awar Maman iffat ne sosai, wanda tun suna
yan mata tare suke, da suka girma kowa tay
aure ta kama gabanta, amma suna zumunchi
sosai sai wannan tafiyar da sukayi Lebanon
basu dawoba sai bayan shekara 7, sunyi missing
din juna ba kadan ba, suna ta tadi bayan rabo
nannefa maman Ameer tace
"Ina Eetrat da hammad" .
"Wallahy duk suna barchi ne, Kinsan yau
Sunday ba skull," batamasan iffat ba wacce
bata nan mama ta haifeta, sunsha labari sosai,
chan saiga Eetrat ta taso daga bacci guraren
qarfe goma na safee,
Bayan tayi brush ta wanke fuska, taje zata
gaida mamarta, ta tarar da bak'uuwa, ta dan
ganeta, ta gaidata, suka gaisa bayan ta fita
mamaki ya kamata, wannan Etrat ce ta girma
haka koda nabarta shekaranta goma sha daya
fa, mama tay dariya duniya kenan gatanan sai
aure, nan maman Ameer ta gyara zama tace
"An tsayar mata da miji ne"
mama tacee
" aah"
nan maman Ameer ta kwashe da dariya suka
tafa, tace
"wllhy haka na riqa jin inzo giddannan akwai
alkhairi, kamar Ana korani, haka na rik'a ji,
shiyasa na danno sammako, ashe etrat rabon
Ameer ce.." .
batasan randa ta rangada gudaba dan murna,
muka shigo da gudu muma muji, Mama ta
hararemu muka koma, Maman Ameer ta kirani
nazo taqara kallona sama da qasa ta qara
rangada guda, tace
"Anyi angama kuma wllhy tayi"
ni bangane komaiba Mama tace
"Jeki ki hada muku abin karyawa"
natafi chike da mamaki mama da maman Ameer
suka kitse magana akan za'a hadani aure da
Ameer Hussein, tuni baba ya amince sabida
yasan iyayen sa suna da kirki sosai, kuma yasan
barewa bazatayi gudu d'anta yayi rarrafeba..
Da maman ameer zata fi tace muzo muyi
hoton tarihi aka dauki hotuna kala kala tanata
murna nidai ba ace mun komai ba, kuma ban
kuma tambayaba amma naga kowa cike da
murna da farin ciki, bama kamar maman Ameer
ba duk inda nayi idonta akaina, suka rabu da
mama chike da shauqin junansu.
babansu Ameer Hussain mai kudin gaskene
sosai, wanda yake sana'ar saida gwalagwalai a
Beirut babban city na qasar Lebanon, Ameer
hussain shi kadai yake agurin iyayenshi,
mamanshi saida ta haifi yara guda 8 bayan
Ameer Hussein duk suna rasuwa sai ameer
hussaini ya rayu, kuma shine babba, yasamu
tarbiya sosai agurin iyayensa wanda aga bansu
ya tashi sai dai kash ameer Hussein ......zan chi
gaba idan nay sallah☺☺
[5/16, 2:22 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 9&10
Na Hauwa M. Jabo
Kash Ameer Hussein mushkiline har na bala'ee,
wanda ko magana idan yayi zaki iya lissafa
haruffa nawa ne amaganar tashi, fuskarshi
adaure take, baya shiga harkar kowa sai ta
gabanshi, kai ko dariya bayayi sai murmushi,
shima wa iyayensa yakeyi awajee baya ko
murmushin, duk wanda yayiwa murmushi to
yagodewa allah..
Tun yanada shekara 8 aka kaishi qasar Cyprus
karatu inda kowa yasan k'asar akwai tsadar
rayuwa, sabida kasar da sunsan yanda zasuyi ko
numfashi idan kayi sai ka biya su, haka komai
tsada a qasar ammafa qasar kaje kagani ta
hadu sosai wllhy...
Anan ya girma gurin wani abokon babanshi,
yayi prmry yayi secondary har yashiga AUM
babbar jamiar gasar ce, anan yayi karatun shi
har yayi mastered dinshi, dayake allah yayishi
mai hazak'a sai yayi saurin kammala
karuntunshi yana da shekara 31...
Ameer Hussein ba abinda yatsana arayuwarshi
kamar mace, bai taba daukar mace a matsayin
Abu mai darajaba, Sam batada daraja, haka yake
ganinsu kamar bayi, sai yazamo kwata-kwata
bayason mace ko abokiya mace baitaba yiba
balle yayi tunanin aure, ikon Allah Ameer
Hussain dai ya tsani mata wllhy....
Shidai kawai karatu, skull mate, course mate,
musulmai, da arna farare da bak'ak'a, son nuna
mishi k'auna, amma baitaba amincewa da ko
dayaba, karkuyi tunanin ko mace ta taba yimasa
wani abu aah..!! Wanda yasa ya tsani mata, ko
d'aya, kawai ya tsani matane arayuwansa. h
Haka ya k'are karatunsa ya dawo gun
iyayensa, Lebanon yay shekara biyu dasu achan,
har suka dawo gida Nigeria sokoto.
Ameer Hussein kullum bashida aiki sai danne
danbe da Ipad d'insa, wacce inajin tafi mace
muhimmanchi agurinsa, shidai haka rayuwarsa
take kuma baya shiga harkar kowa kuma
bayason ashiga tashi...
Sai dai matsalanshi daya akwai k'azanta da
take damunsa, bawai ta tufafiba aah. ta gurin
zama idan kahadu dashi ahanya yana k'amshi
bazakayi tunanin zai kwana a inda yake
kwanaba, dan hargisti da yamutsewar gurin
wannan akan wannan wancan akan wannan..
tofa kunji tsabtar tsula inji ba sakwakwace.....
** ** ** ** ** ** ** ** ** ** **
Maman ameer tadawo gida cike da farin ciki da
murnar tayiwa Ameer d'inta mata, tasamu alhaji
labbo mahaifin Ameer tagayamasa, yaji dad'i
sosai musamman dayaji cewa yarinyar yar gidan
wayee, kuma dama bayason yar boko wacce
tayi zurfi da karatu yafison yar daidai wacce
zata iya hak'uri da Ameer hussein,
Maman Ameer tanuna masa hotunan da suka
dauka tare da Eetrat, nanfa alhaji labbo yaqara
jin dadi da samun suruka kyakyawa kamar
Eetrat. murna agurinsu ba'a magana,
yinin ranar gaba daya magana daya akeyi, ya
auren zai kasance, suna jiran sarkin mishkilan
duniya yazo sugayamishi suji abinda zaice,
sunsan sai sunyi dagyar amma kuma zai amince
duk da hakan.
Bayan sallar esha sukaji karar matarshi
yadawo daga office yana tafe yana danna iPad
a hannu har yana karo da fridge a fallo sannan
yadaga kai yay murmushi...(laaaaa dama maza
sunada dimple ne??) Ammafa wllhy Ameer
hussain hadadden guy ne ta kowane janibi
babanshi sak ya biyo, saidai shi black ne amma
yanada haske kamar irin black American dinnan
haka yake.
Gashinshi Wanda ya kwanta lub akanshi,
haka gashin yake ko ina ajikinshi musamman a
qirjinsa gashida faffadan qirji atak'aice dai
Ameer Hussein yakai iya inda namiji yake kaiwa
sai dai mishkilanchinsa yayi yawa.....
"Sannu umma sannu abbah" haka yagaida
iyayensa yana murmushi yazo yayi musu kiss a
fuska al ada dai ta turawa, zai wuce daki Alhaji
abbanshi ya kirashi yadawo ya zauna, ananfa
abbah yafara yi mishi maganar aure ya bushe da
dariya budan bakiin da zaiyi sai yace.....
🍃ETRAT🍃 11-14
Na Hauwa M. Jabo
"Wallahi abba kuna bani dariya da mamaki, ni
mizanyi da mace???"
ya wani ya tsina fuska irin maganar da ake
mishi sam batada muhimmanchi a gurinsa..
abba yaci gaba da magana,
"nidai dan Allah bamuce kaje ka nemo
mataba ga wannan yarinyar mamanka ta nema
maka, sai ka aureta,"
Abbah dai yayi iya k'ok'arrinshi na fahimtar da
Ameer amma yak'i fahimtuwa, nanfa Umma ta
daka mishi tsawa tuni ya natsu, ba shiri Ameer
hussain ya amince, nanfa suka fara murna
Umma taso yaga pic din Eetrat amma ina
yak'ara gaba abinshi, Umma takamoshi ta
rungumeshi tana saka masa albarka tana
murna........
Mahbuub daren nan kasa bacchi yayi dagyar
yasamu yayi bacci gashi gobe sunada buki a
famly d'insu kuma dole yazamana yananan
sabida haka bazai samu yazo gidansu Eetrat ba
haka yayi juyayinsa, Monday yakoma aikinsa
yamatsu sati ya zaqayo a yazo kawai ya
gabatarda kansa a gurin Eetrat....
Nimq kuwa daren haka nayi tafama da tunani na
rasa miyake damuna nida nake bacci qarfe 9 na
dare yau gani har kusan asuba ko gezau, kuma
narasa gane mi ya hanani bacci, dak'yar
nasamu nayi baccin sai mafarkin Mahbuub,
anan nagane cewa fa guy din ya shiga rainane
amma ba yanda zanayi tunda baya sona, fadawa
duniya kawai yayi.
D safee naso nayi tadinsa a gida sai mukayi
bak'uwa Maman Ameer wacce tasa namanta da
Mahbuub,
koda yake ni bansan zancen Ameer Hussein ba
kwata-kwata tunda bawanda yagayamin su biyu
sukayi shawaransu basu gayaminba....
Nidai araina nagane cewa inason Mahbuub
amma kuma ina jin tsoron yanda naga yazo
gidammu ko kallona baiyiba, kuma ya bazawa
duniya cewa yana sona ni banga so annanba,
naga kullum Umma da mama sai sunyi waya
idan tana wayar sai ta koremu karmuji mitake
cewa, dai dai da rana daya bankawo cewa
maganar aurena sukeyiba, nikuwa gashi sai
begen Mahbuub nake a zuciyana....
Ranar assabar kamar kullum Mahbuub yazo gun
baba sun fara firarsu da suka saba baba yadauki
mahbuub abokin shawaranshi sabida yanada
hankali sosan gaske suna magana sai baba yace
mishi
"Mahbuub inason muyi wata magana nae"
yaji dadi yadauka baba ya gane yanason Eetrat
ne yasosa qeya yace
" inaji baba!,"
" dama maganar auren qanwarkane ya
matso..." "Ina zuwa baba wace qanwar tawa?"
baba yay murmushi yace
"Eetrat mana"
" ETRAT baba?" kikaji.....
Kikaji shiru lokaci daya,
Mahbuub ya fashe da kuka baba yana lafiya
mahbuub?? yay shiru yasake fashewa da kuka
baba yarasa gane miyake faruwa sai tambaya
yake amma ba amsa sai yanzu Mahbuub yagane
kuskurensa na k'in furtawa Etrat kalmarr SO...
sai kawai duniya ya fadawa maimakon wacce
yakeson yagayamata amma yak'i fada, wauta
yayi? ko hauka? ko ma miye Dai yayi danasanin
aikata wannan wautar.
baba yana tambayar sa nanne dai Mahbuub
ya fayyacewa baba abinda ke cikin zuciyarsa...
Baba yay shiru ko ba komai Mahbuub yanada
kirki kuma iyayensa masu mutunchine ,amma
kuma yaza'ay ya warware Alk'awarin da yayi,
gashi har ankusa saka rana, baba ya tausayawa
Mahbuub, amma ba yanda ya iya,
Ya dubi Mahbuub yace
"Miyasa baka fadaba Mahbuub?"
yace
"sabida ba matana bane, da Etrat matanane
da tun lokachinda nake fama da sonta na
furtamata amma sai na ijiye abun araina wannda
yanzu nagane hikimar Allah ta rashi furtawan..."
haka dai Mahbuub yatafi da jimamin rashin
samun biyan buk'atarsa, amma fa yanason Etrat
sosai, kuma yana kishi da duk mijin da zai
aureta.. baba yashiga gida yafadawa Mama
abinda yafaru, Mama tayi jimami sosai, kuma ta
tausayamasa ana maganar sai na shigo naji
abinda suke fada bance komaiba, amma banji
zancen wai an mini wani mijinba, na dauka Baba
yabi ra'ayinane na sai tsoho, amma kuma baba
baisan inason mahbuub ba ??gaskiya nidai da
anmishi magana ace ya turo haka naita sak'e-
sak'e araina, har suka tafi suka barni, bansan
sun tafiba..... ashe so yakan hana bacci zancen
da na rik'a yi
Kenan a zuciyanta, amma fa naji haushin
hukunchinda Baba yayanke batareda ya
tambayeniba, haka na hak'ura amma fa abun na
rain.......
Ameer Hussein har ya manta da zancen wata
yarinya wacce ko sunanta baisaniba, kuma
bayama son yasan sunanta, Umma ce tashigo
da fara'arta tasamu Ameer yanata game a iPad
d'insa, Umma taje kusa dashi tazauna yay
murmushi
" sannu umma.!"
tace yauwa tay shiru chan tafara magana
"dama zancen Etrat ne, shine muka yanke
shawaran gobe lahadi da k'arfe goma na safee
zamuje kagaida iyayen rarinyar, kai kuma sai Ku
gaisa da yarinyar."
baice komaiba kuma baidago kai ya kalletaba
tace
"kanaji na kuwa?"
yace
"Eh Umma Allah yakaimu, goben"
tayi mamakin amsar dayabata, amma sai
tashare tasaka mishi albarka tak'ara gaba, yaci
gaba da danna iPad d'insa, Umma takira Mama
tagayamata gobe zasuzo harda Ameer, Mama
tay murna sosai tagayawa Baba aka fara shirye
shirye, nidai kawai ancemini zasuyi bak'i amma
bansan gurinaza'azoba, andai kawo mani
sababbin d'inki wani material less ne ,akayi dinki
mai kew wanda dagani zai kamani sai wata
qaramar sarqa mai kew nidau sai kallonsu
kakeyi......bari in fito wanka zan chi gaba☺
[5/16, 3:09 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 15-16
Na Hauwa M. Jabo
Kallonsu nakeyi abun bai bani mamakiba sai da
naji cewa wai harda Abban Ameer za'azo, to
amma miye had'in zuwan abban ameer da bani
sababbin dinki??
Haka dai na gaji da sak'e- sak'ena araina,
kuma ban sami amsaba....
anyi aiki sosai wanda aka share gidan ko ina
aka yi girki kala-kala nidai pizza kawai hada
musu,da kuma shawarma drink wanda akeyi da
shinkafa, kwakwa,da madara yanda na had'a shi,
Bayan na jik'a farar shinkafa, sai kuma na d'ora
daya akan wuta, ta dahu kamar tuwo, na
sauketa ta hada da jikak'k'iyar shinkafar da kwa-
kwa, na markad'e, na tace, na samu sugar da
madara na saka, aka saka a fridge, gaskiya yay
dadi sosai nima nasani,
mun kammala duk wani abu na tarbar bak'i
bak'inmu kawai muke jira......
"Wai ina Ameer yake ne"
inji abba, Umma
" yana ciki yana shiryawa"
"OK mudan jirasi kinsan mutumin naki
mishkiline,"
shiru kakejii har sukai minti goma zaune abba
yace
"bari indubasa ingayamasa yay sauri"
bude qofan keda wuya sukaga ameer kwance
yana shara bacci abin ya bashi mamaki sosai
yaje gun Umma
" dama baki gaya masa cewa karfe goma
zamu tafiba.?
tace
"Wallahy nagayamasa"
Abba yace
"To ai kuwa yana chan yana bacci abinshi,"
Umma ta fusata da sauri ta miqe Abba yace
"dakata malama lallabashi zakiyi sai yayi fushi
muje muga yanda bamaso a gun.!"
haka sukaje suka tasheshi cikin kulawa da wayo
irin na manya aka lallabashi ya tashi dayaga ran
mahaifansa ya bachi kawai hak'uri kawai sukayi
suka share, sai yayi sauri shima ya fara shiri.
kwata kwata Ameer yamanta da zancen zuwa
gurin wata mata, aransa yay dariya (wai mata!)
a tsanake ya shirya dan kar ya k'ara bata musu
rai, abinda ya tsana kenan arayuwarsa ganin
bachin ran mahaifansa abinda ya burgesu shine
tufafinsa yasa na k'asarsa Nigeria, wanda
rabonshi dasu tun sallar layya ai kuwa yafito tas
dashi ya kafa hula yafesa turare yay kew abinshi
ya dauki bakandamiyarshi wato iPad,
Yafito cikin minti ashirin yak'ara basu hakuri,
sunata mamaki, ko ya sauko ne, shi yay driving
din mota har suka isa kofar rini unguwar mu.....
Nayi wanka nasaka kayanda aka kawomin, dama
ni ba ma'abociyar kwalliya bace amma kayan
sun fitar dani sosai, ga qaramar sarqan nan da
na saka haka dai nafito kaman wata amarya,
mazau nan nan nawa kuwa sun fito tsab
atakaice dai nayi kew sosai nikaina naji haka
ajikina.....
Misalin qarfe 11 da rabi bak'inmu suka iso,
Umma tashigo ciki su Abba da Ameer suka
wuce sashen Abba, nanfa su Umma da Mama
suka fara tad'i abinsu, ni kuma na fita na basu
guri, zuwa 12 akace afito aci abinci, nanfa aka
kwasa akayi fallon Baba, aka bajee chan-chan
na hango Ameer Hussein zaune amma kanshi
ak'asa yana abinda yasaba da iPad d'insa,
nidama bansanshi so banyi k'ok'arin gaisheshi
ba, fuskar shi na gefe mu kuma muna waccan
barayin Ameer baici komaiba sai pizzan dana
had'a, da kuma shawarma drink, koda
bansanshiba naji dad'in abinchina daya chi,
kuma su kadai yachi aka k'are chin abinchi
ayanda ya mik'e bai waigoba kawai gaba ya
k'ara bandamu dasanin ko wayeba..na kashe
kwanukan naje na kanke, mukaje sallah, na idar
da sallah kenan ina lazimina dana saba sai
kawai ga Iffat,
"wai Auntie kije inji Mama"
natashi naje tace insaka powder fuskana yayi
wani iri na k'ara goga powder a fuskata nazo
kije fallon abbanku kina da bak'o inji Mama.
ETRAT 17&18
Nace
"bak'o Mama?"
tace
"Eh kije yana jiranki"
abin yabani mamaki ni ba saurayiba balle inyi
tunanin ko yazo gurina ne, araina nace ko
tsohon da nake nemane nasamu araina nace
tab.!! Haka naje pallon babana.
Ntarar da mutum zaune yana danna iPad, ko
game yakeyi oho nay sallama ya amsamin
batare da ya dago kai ya dubeniba, na kuwa sha
hijabina abina, nazauna a dayar kujeran gefen
sa daga yamma, yanda nazauna haka nake
zaune kusan awa daya bai dago ya kalleniba
haushi yakamani sosai wai wannan shine baqon
nawa ko kuma yaya?? har zan mishi magana, sai
kawai guntuwar sarautar mu ta mata ta motsa,
kawai sai na share shi, ai kuwa haka muka
share awa uku bai dago kai ya kalleniba ni kuma
ban mishi maganaba sai danne danne yake da
ipad, can sai ga Iffat a guje ta fada jikinshi,
"Yaya Ameer wai akawo maka wani abu
zakachi?"
nan natuna dako ruwa ban bashiba ko shiyasa
yak'o yimin magana? yay murmushi yace
"Ya sunanki ?"
tace
"Iffat shunana"
yaja kumatunta yana murmushi, nanne naga
ikon Allah, dama maza suna da dimple ne sai
yau nagani, yace ki kawo min ruwa idan akwai
sauran pizza akawo min,
ta tafi dagudu ya bita da murmushi ahakan ya
sake duk'ar da kansa ya chi gaba da aikinsa,
aka kawo masa pizza wacce na ijiyewa kainace
sabida ban chiba, kuma na wahala gurin
girkawa, haka ya chinye ta tass.
ko mai bai rageba naso inchi pizzar nan amma
wannan sarkin shurun ya chinye, na hak'ura dan
dole, yana chinyewa naga ya mik'e ya wuce
abinshi, ko sallama babu amma wannan mutum
anya gurina yazo kuwa...? oho.
nidai naje cikin gida nachi gaba da shirye shiyen
abinchin dare haka dai bakinmu suka kammala
abinda zasuyi akayi bankwana naji ana cewa 20
ga may din yayi, nace mi za ayi 20 may kuma,?
nace koma miye yau dai 12 may ne zamu gani
har suka tafi wanda akace bak'onane bai daga
kai ya kalleniba.
Nafito daga kitchen naji mama tana cema
Baba
"Anya niko aurennan baiyi kusaba 20 ga
wannan watan, fa? ba fa wani shiri da muka yi
ita kanta yarinyar bamu saniba ko tana sonshi.?"
sai Abba yace
"nasan Etrat zata soshi kincemunfa awansu
sama da uku suna magana, idan kuwa bata
sonshi bazasu shafe awa uku.suna maganaba!!"
tabbbbbb........
[5/16, 3:40 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 19-20
Na Hauwa M. Jabo
Lallai abinda najiyo gaskiyane aure za'amun
tabbb...!! da wannan mishkilin mutum wanda ko
gaisuwa bai iyaba za'ahadani aure, naja baya
nakoma d'aki na fashe da kuka, ni wllhy bana
son wannan mutumin gara Mahbuub sau dubu
akanshi, nifa gaskiya bana sonshi, dayar
zuciyar ai kya bari har amiki maganar aure
sannan ki ce bakya sonsa idan aka ganki kina
kuka mi zakice? wato labal kikayi kikaji sirrin
iyayenki ko? nan take nay shuru kar asirina ya
tonu haka naje nakwanta....
Da safeee natashi bayan nayi break fast baba
ya ce yanada magana dani, nan gabana yafadi
nasan cewa maganarce, haka jiki ba k'wari naje
pallon Baba natararda Mama agun fuskanta a
sake, nazauna gefen Baba yay murmushi yace
"Etrat matar tsoho... "
sai naji kunya narufe fuskana da hannuwana
Baba yay gyaran murya yace
"dama dai maganar aurenkine ya matso,
shine kuma mu munriga mun badake agurin
yaron gidan alhaji labbo wato Ameer Hussein
wanda kuka tattauna dashi jiya da yamma kuma
ga dukkan alamu kun aminta da juna sabida
mamarki tace kun kusa awa uku kuna magana
wanda ya tabbatar mana da cewa kuna k'aunar
juna, saidai jin ta bakinki ma yanada
muhimmanchi"
nanfa zuciyata bak'i k'irin araina nace wllhy
Mahbuub nakeso ba wannan Ameer ba shirun da
nayi naji Mama tana cewa..
"nagaya maka ta amince kawai sai ki fara
sanar da qawayenki 20 may auren"
araina nace nashiga uku bansan yanda zanyi da
rayuwataba baba yace inje Allah yayi min
albarka, jiki ba kwari na tashi naje daki sai sake
sake nake, wai zanyi aure nan da sati daya
Lallai ma, ahaka har bacci yay awon gaba dani
harda mafarkin Mahbuub zaune acikin wani
k'aramin dak'i yanata dariya nace mishi lafiya
sai kawai ya rungumeni, nan take nafarka natina
malamin islamiyan mu yace ,idan kay mafarkin
kuka dariyane dariya kuma kuka, nace duk
yanda akayi Mahbuub yana cikin wani hali nay
mishi addua naci gaba da baccina.......
Wasa wasa yaune daurin aurena inda tundaga
kan wurin sarki, har bakin kofar rini anan
unguwarmu mutanene ta ko ina, gaskiya naga
jama'a rabon da naga taron jama'a irin haka tun
auren ruqayyah da basasa shekara nawa da
suka wuce sai aurena, ko ina zancen aurena
ake yau andaura auren AMEER HUSSEIN &
ETRAT
Allah yasanya alkhairi ni kuwa duk wani tsimi da
ake yiwa yarinya idan zatayi aure anmini shi,
wanda kun dai san sokoto sarai basai na
gayamukuba, yamma tayi aka daukeni aka kaini
gidan mijina da yake nan GRA bayan kowa ya
watse ba ango ba abokan ango chan sai naji an
murda qofa.........
ETRAT 21&22
Aka murza k'ofan sai Naji maganar maza amma
wani yare suke, sai naji sun kwashe da dariya
sai dayan yace
"Inaga fa nanne" suka k'ara murda k'ofa suka
shigo su bakwaine harshi cikon na takwas hudu
fararen fata hudu kuma bak'ak'e yan uwanmu,
fuskata na chikin hijab nace araina dama yasan
zaizo shine ya bari saida qawayena suka ,tafi
nay tsaki araina... suka fara surutansu wani da
yare wani da English haka dai suka gama shi
dama bakandamiyarshice a hannunsa wato
iPad.. yana abinda ya saba sun k'are surutansu
suka kawo abinda sukazo dashi suka tashi yay
musu rakiya naji lokacinda ya rufe k'ofa amma
sai kuma banji tsoronda akace anajiba aranar
farko ko miyasa oho? ban kara ganinsaba har
bacci yay awon gaba dani.
Tofa gidan aure na nake yanzu gidan k'aton
gaske sabida zai kai rabin kilo mtr ko wane bari
hadda lanbune a gidan ga swimming pool agidan
k'aton gaske ne, falon wani irin babba dashi,
dakuna gasunan sunkai guda 10 kala kala abin
dai sai wanda yagani, bazan iya tsayawa
lissafawaba nidai ganinan aciki.
Yau nake ganin ango gobe nake ganinsa shiru,
nikuma ko za'a kasheni bansan haryar
dakinsaba.
nafito falo nafara yan lek'e lek'ena har na
hango kitchen, nanfa nashiga na hada break fast
amma ba ango ba labarinsa, saida na hada
kwana sha daya sai dai inji k'arar mota da safe
dakuma da yamma inji dawowar mota, amma
bana sakashi a idona tun ina damuwa har na
daina damuwa,
Wata rana guraren 12 naji k'arae mota abin ya
bani mamaki ya akai yadawo da wuri haka, koda
bana ganinsa, amma nakan rage tsoro idan Naji
cewa akwai mutum a gidan, sai kawai naji
motsin mutane, na fito waje, na daga kai naga
Umma da Abba da wata mata, nay musu sannu
da zuwa na kawo musu abinchi, sabida kullum
sai nay girki dashi na dare da narana, sai dai in
baiwa masu gadi sabida ba chi yakeyiba yau
kuwa iyayensa suka chinye abinchin.
Hakadai mukay ta tad'i dasu har yamma,
wannan matar zata koya min motane har in iya,
naji dadi sosai dadi ya bani key din motar
sabuwa ta zamani naji dadi ranar kamar me.
hakadai muka hira dasu suka tafi.
An bani waya, an kuma bani numbr sa idan
inason abu nakan yi masa sms amma bai taba
reply ba sai da nayi wata biyu aginnanan ban
saka Ameer Hussain a idonaba, wannan wane
irin aurene?? Ba miji nayi dana sanin aurensa
inason fita sai dai ingayawa mamansa
tagayamasa bantaba gigin fadawa kowa halinda
nake cikiba ranar wata laraba natashi nayi duk
abinda ya dace, niba miji ba sai kwalliya dan
banida bambanchi da hauwa jabo.
Nafito sai kawai nabi wata hanya wacce
bantama bintaba, acikin gidana sai kuwa ga
tarin key's a sakale a wani guri, nadauka na fara
bud'e bud'e in bud'e wannan in bud'e wanchan,
dakunane atsare duk sunyi k'ura ko ba komai
tsabta tana da kew na gogesu na yini aiki
aranar, nagama kenan sai naga wani labule ina
dagawa sainaga...
[5/16, 4:27 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 23&24
Na Hauwa M. Jabo
Sainaga wani falo a hargitse, wanda ga dukkan
alamu akwai mutun aciki, sai dai yanzu bayanan
haka na gyara fallon na share tas komai nai
arranging d'insa, yadawo kamar sauran dakuna,
sauran kuwa nace sai gobe dan nagaji na kulle
dakunanan na dawo sassana, nayi wanka na
saka wasu kaya gasunan dai, na fito tas tas
dani sai dai ba miji, bayan nadanyi bacci sai
naji motsin mutum abayana nay balaeen tsorata
watana biyu da kwana hudu bantaba ganinsa ba
sai yau, hasalima bamu taba hada ido dashiba
sai yau, fuskarsa a daure yafara min balaee
" keee !!! Waya aikeki dakina?? Wayace kitabin
kaya?? Ke mahaukacciyar inace???"
Tofa ranar farko da na fara hada ido da mijina
wanda nake zamansa wata biyu da kwanaki...
shima da masifa yafara min magana, Inna lillahi
wa inna ilaihi rajiun., haka kawai nace araina sai
naga ya juya har yakai k'ofa yadawo ya wani
jawomin gashin kaina wanda yasa nayi wata irin
k'ara, sabida zafin danaji yamun magana da ido
alamar idan kika k'ara sai naci ubanki ya
wurgani nafada akan hannun kujera wanda naji
zafi sosai bansan lokacinda hawaye suka
zubominba, nay kukan dana sanin aikin dana
aikata, waya aikeki, ke dadi miji hajiyan zabta,
haka zuciyata ta mai mai tamin, gobema kik'ara!
Nanfa wasu hawaye masu radadi suka
zubomin, dan nikam nayi rashin sa'ar miji,
arayuwa anya wannan yasan da zamana adunuyi
ma kuwa?? Wannan kamar baisan miye aureba,
haka nayi jinya ta kwana biyu har na warke,
ranar haka najishi shida abokansa, da matar
daya daga cikin abokan nasa sunata magana a
fallo suna dariya ni kuwa ina bacci ihunsu ya
tayar dani daga bacci, ina fitowa mukai ido biyu
dashi abin mamaki say yay murmushi, wanda
bantaba ganin irinsaba arayuwata, araina nace
amma fa mijina ya had'u, sai dai ba kyan hali
yace mun...
"keee!! ga k'awanan namiki matar abokinace
zata riga zuwa gidannan, sai kema kije gidanta,"
sai matar tace,
"Bamaso ai kayi mai wuyar tunda ka kawoni
gidanta, mu zamu shirya kammu,"
Dayan abokin yace min,
"Hajiya amarya ana hutuwa, tin dazu mukazo
yace kuna bacci bazai tayar dake ba." Nai
Murmushi kawai.
daga nanfa bai k'ara cewa komai ba,
Nan mukaita labari da ita matar mai kirki da
ita, khadija ana ce mata sista khadee.
Na musu girki hadda Ameer Hussein ya bud'e
ciki ya kwasa shima, munyi sabo da ita sosai
har tana zolayata wai bawani bayani shine fa
araina nace tabbb.!! ni ko mijin banagani balle
zancen ciki haka dai muka rabu mukai musanyar
numbr, gobe sai naga mijina yazo da safee ina
break fast yazauna shima yaci abinda na girka,
ya bani mamaki sosai jiya da bak'i sukazo dgyar
yaci abincin, yana farawa kuwa sai naga duk
yafi dukansu chi, yauma gashi yazo yana chin
abinchina, abin ya burgeni koda baya ko daga
kai ya kalleni, mun kwashe wata daya kullum
gida yake chin abinchi, sai ranar da gangan naki
girgi, da rana wanda yadawo don chin abinchi,
tun bakin k'ofa ya hango table din wayam, ya
lek'a kicin yaga wayam, sai yazauna fallo sabida
yana balaeen jin yunwa, kuma yanzu baya iya
chin abinchin ko ina sai na gida, nafito kena sai
nagansa zaune ko kallonsa banyiba, na wuce
kitchen nahada tea mai kauri nazo d'ayar
kujerar nazauna, yana kallon wani film da wani
yare ,wanda bansan mi suke cewaba.
Haka nazauna ina kallo nima, ina kurba tea na
a hankali lokachi daya wani haushina ya
kamashi.. ya zanzo gabanshi in zauna ina chin
abinchi shi ko tea din inkawo mishi mana ya
wane kalleni a wulak'ance, ya karbi kofin da tea
aciki ya fasamun akai ya fashe akaina, sai jini
nafashe da kuka ko kallona baiyiba, ina mik'ewa
tsaye santsin tys din ya hade da tean da ya
zube nafadi acikin glass dinda ya mutu tuni ya
shige min jiki na gara ihu ba mai taimako sai
Allah.....
By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
07039625239
🍃ETRAT🍃 25&26
Haka na mik'e da gyar naje toilet na wanke
jikina, inata kuka, naso in kira sister khadee
ingayamata halinda nasamu kaina ko akwai
shawarar da zata bani, sai kuma na fasa sai
naga wannan sirrinane nida shu'umin mijina,
haka na hakura ban gayawa kowaba, kwanana
uku in jinya, wanda ko falo bana fitowa, tea
kawai nakesha bantaba shiga tashin hankali irin
na yan kwanakinnan ba, duk jikina ciwo yake, ni
duk abinda zaimun ya daina dukana kawai...
ina zaune a falo lokachin na chika wata biyar
chur a gidansa, amma ba wani kulawa, nida
babu duk daya, na zaune afalona wanda kana
gani kasan ina gidan hutu da niima, amma
zuciyana chike take da bakin chiki da takaici,
akai akai nakanje gidanmu da gidansu , na gaida
iyayenmu, kuma su Abba suna sakashi yaje
gidanmu kuma yana zuwa sosai..
wannan zuwan kuwa da iffat akazo bansan
miyasaba yakeson Iffat ba, har yana wasa da
ita, ina chikin wannan dogon tunanin na tarihina
sai kawai naji
"ana Auntie'..!!"
nayi firgit nadawo hayyacina na je da gudu na
rungumeta ina jin dadi ina dariya, shi kuwa
ogan dama yanzu nima na waye nasan dawa
nake rayuwa, banda harara ba abinda ke hadani
dashi, naja k'anwata muka shige chiki naji dad'in
zuwan Iffat ko banza itace abokiyar fadana
agida, yar shekara takwas sai wayon tsiya.
Ranar nayiwa iffat wanka, nima na shiga inyo
wankan, kamin in fito na tarar ta bata duk jikinta
da kwalliyan hauka, saman ido bakinta ko ina ta
bata tana ganina tasan dukanta zanyi, tayi waje
da gudu ni kuwa dama nasaba binta da gudu ko
gida gata idan tana gudu baka iya kamota, sai
dai in fadi, amma bana daina binta.
Haka ma yau tafita aguje na bita tana fita
tayi karo da Ameer ta wani dadumeshi
"wayyo yaya Auntie zata dakeni...!!" tashige
chikin rigarsa, ni kuwa wai saina kamota naje da
k'arfina, hannu daya yasaka ya rik'enmin
hannuwa biyu, yacewa iffat ta gudu dakinsa
yana murmushi, dama daga wanka nake dagini
sai towel, ai kuwa tuni towel ya zame yafadi
k'asa, dagani sai pant, kawai gani haka
agabanshi, sai naga ya sakeni ya tsuramin ido
kunya tahanani duk'awa indauki towel dina, na
duk'ar da kaina gasa ina jiran ya tafi in dauki,
abina amma shiru kakeji, nidai bansan
miyakeyiba, hasalima ni tsanarsa nayi, mun kai
minti biyu a haka, sai naji dariyar Iffat tana kiran
yaya kazo na boye, sai kawai naga ya duk'a ya
dauko towel dina da sauri yana daura min, abin
ya dauremin kai matuk'a, amma duk da haka
ban daga kai na kalleshiba dan kunya da takaici.
Sai da na tabbatar da yabar gun sannan
nashige d'aki da gudu iya kunya, yau naji kunya
da takaichi, wannan ja'irar yarinyar ta janyo min.
Ina zaune bakin gado sai ga Iffat da Ameer
sunzo, sau d'aya na hada ido dashi na kawar
dan kunya, kuma nakasa karanto abinda ke cikin
idonsa..
yace
" Auntie kiyi hak'uri bazamu sakeba"
nakasa yimasa magana, nay shiru da bakina
yak'ara maimaitawa
" Auntie kiyi hak'uri kinga har wanka munsake
ko iffat?? "
Iffat tacee
" eeh kuma ba zan sakeba"
haka yak'are surutunsa shida iffatu, bance musu
komaiba yazauna ya shafamata mai, yasaka
mata tufafi suka fita abinsu ,basu dawoba sai
bayan sallar esha, dama duk dare suna fita,
suje yawo ni kuma ina gida ina gadi, sun dawo
abin mamaki yau harda ni aka yiwa siyyah, wai
ta lefin da Iffat tayi ne, nidai banchiba, gari
yawaye ta chinye abinta. Haka dai Iffat tay sati
biyu agidana,
Har ta koma gida, amma tun daga narar da
towel d'ina ya fadi gabam Ameer, ban k'ara bari
muka hada ido dashiba, shiko sai wani son yimin
magana yake,
ko miye dalili ohooo..!
Yana dakinshi yarasa mi yake mishi yawo akai,
wai miye mace??
miyasa da yaga halittar jikin wannan yarinyar
yaji shok ajikinsa???
miyasa yakeson sake ganinta ayanda yaganta??
Tambayoyinda suke masa yawo a kai kenan,
lokaci daya yasamu amsa adayan bangaren
zuciyarsa, mace dai wata halittace mara daraja,
kuma baiwa, kamar yanda ka dauketa ada,
kanason ganinta ne kawai dan tak'ara bata
maka rai, kawai k'ara nisantarta, tambaya ta
uku kuma sai yay shiru, sabida bakadamu da
mace ba, shiyasa kake son kaganta ayanda
kaganta..
Wannan lokaci dole in dauki mataki akanki karki
kawo min chikas a rayuwa
[5/16, 4:45 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 27&28
Na Hauwa M. Jabo.
Ya rasa mi yake masa dad'i,
Tuni ya fita falo ya zauna gashi baya magana
sabida mishkilanchi irin nasa,
Bansan cewa yana gidan ba na fito da kayan
bacci, gashi zuciya ta gama zugashi, yawani
dalla min harara keee!!
dama ke yake kirana, sabida ina kyautata
zaton baisan sunana ba, na waigo mukai ido
hudu sai ya kawar dakansa, ya mik'e tsaye ya
finchiko mun gashina da qarfin balaee wandaa
da kyar nake iya, nunfashi.. yacemun
"Nanfa gidan musulmaine sabida haka kar in
qara ganinki da wayannan kayan na arna, kinji
abinda nafada"
kinji fa fadan rashin dalili irin nasu Ameer,
Yaci gaba,
"oda yake mata haka kuke kamar dabbobi,"
ya turani da k'arfi na fadi tsakiyar d'aki, inda
bakina ya daki tys din falon, goshina ma haka
nanda nan bakina ya kumbura shafatain dina
sukayi manya manya, goshi kuwa tuni yay wani
jaaaa ina kuka ina dana sanin aurensa, wata
kusan shida kullum azabar yau daban ta gobe
daban, to wllhy nagaji nan nay tunanin gayawa
sists khadee, sai kuma na fasa na tuna wannan
sirrinane nace ko inkai kararsa gidansu? nan
ma naga ba sauk'i, haka daai nay ta sak'a da
war warewa..
To shi wannan mutumni so yake kullum in
saka hijabi hala??? Nandai ba maza suke
shigowaba balle inche kishi yake, nasan wannan
bazai taba kishinaba sabida sam ba k'aunata
yakeyiba. nay kuka idona sukai hulu hulu ga baki
ya kunbura ga goshi ya fashe nayi ta kuka har
na godewa Allah.
Naci gaba da addu'a sai yanzu nakejin cewa
Wllhy da Mahbuub na aura bazan taba irin
wannan wulaqantaba.
Ankawoni gidan mutum mishkili wanda baisan
darajar dan adam ba..
Tabbas Ameer baya cikin mazaje na gari, haka
naji na tsaneshi muguwar tsana, kuma ashirye
nake da yabani takardar saki na in k'ara gaba,
sabida na tsaneshi amma kuma ya za'ay ya
sakeni shine maganar???
Ba amsa haka dai na hukura
bayan kwana biyar na warke sumul kamar
baniba, sai dai ko kodan bana fitowa daga
dakina, namaida tea da Indomie abinchina anan
daki nake girkawa ina chinyewa, bana fita wajee
bare in chi karo da mugun mutum mai bak'ar
ziciya, ina kwanche adaki naji alamar tafiya,
daga kan da zanyi sai naganshi fuska babu
rahma, tun bai k'araso gunaba na fashe da
kuka, ya finciko hannuna iya k'arfinsa, yace
"baki da maraba da baiwa, so dole kina
yimin girki inachi..."
Tofa kinji wata sabuwa... nikuwa yanda
natsaneshi ko zai mutu wllhy bazan masa
girkiba...
"kina jina??"
nadaure fuska na share hawayena nace masa,
"wllhy ko zaka kasheni bazan maka girki
kachiba..! sai dai yunwa ta kasheka"
ya kawo min naushi a baki, sai kuma yayi sa'a
ya sameni, ya fasa min baki, haka ya wurgani
akan mirror, tuni ya fashe duk kayan kwalliyar
sukayo kaina, nan danan nayi sabbabin raunuka,
wanda dole sai naje asibiti inata kuka nafito falo
kenan sai nay karo da Umma mahai fiyar Ameer
ETRAT!!! Miya sameki??? Nafada jikinta ina kuka
wllhy umma..........
[5/16, 5:00 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 29&30
Na Hauwa M. Jabo
"Wllhy Umma na fito wanka sai kawai jiri ya
kwasheni, sai na fada kan madubi ,"
"amma ai da ban mamaki yarnan, ya kikayi
kika fada ajikin madubi kamar an wurgaki, kalli
bakinka fa"
gabana yafadi RAS..!! araina nace mugun
dankune kuwa ya wurgani..
nay take nace
"Aaah Umma faduwa nayi"
muka isa asibiti nanfa aka sakamin bndg ajiki ta
ko ina da naji ciwo, bamu wuce gidaba gidansu
muka wuce, anan umma ta fahinchi akwai wani
abu tsakaninmu, amma kuma ni nak'i fad'in ko
daya, aka gaji aka barni, na warke sumul amma
banason komawa gidan azaba..
Haka yazo ya daukeni na koma kurkukuna,
narame nay bak'i bakomai sai ido narasa miyake
mun dadi ranar haka kawai naji natsani kaina
kamar in kashe kaina, ga wani ciwon kai da
yake damuna, atak'aice dai banjin dadin jikina,
haka nay wanka nasaka wani riga da wando
wanda yay balaeen fitar da surar jikina, naje
kitchen ina hada abinchi sabida nagaji da chin
indomiee, kuma yanzu ashirye nake idan
yatabani zan tabashi, ina aiki dai ba lafiya haka
na tsaya ahankali ina aiki amma banajin dadin
jikina ashe mugun mutumin yazo yazauna yana
kallona ta baya, yau yakasa danna iPad d'insa,
sai tambayoyinsa suke masa yawo akai yana
k'aryata amsar da dayan bangaren zuciyarshi ke
bashi, sai yanzu ya tuna da wani abokinsa ya ce
masa Ameer duk lokacinda kafara son wata
mace zaka gane cewa mace ba baiwa bace
baiwa ce... kuma ni'imace...
mace tanada wasu ni'imomi masu yawan gaske
wanda Allah yay musu acikin jikinsu, Allah yace
su halittace mai sanya natsuwa tsakanin mu,
dayawa abokinshi yakan gaya mishi siffofin
mata masu niima, wayanda duk yagansu a jikin
wannan yarinyar ya elaheee...!!!
Yama sunanta!? dayan zuciyarsa ta
tambayeshi babu amsa Lallai bai san sunanta ba
ikon Allah...
Miyasa nazauna ina kallonta!?
dayan zuciyarsa tace sabida matarkace.
Matana...!!!? To mizan mata!? insota kenan!? sai
dayan zuciyar tace masa ai dan kana sontane
kadamu da ita JALLAL KHALEQ....!! Anya nine
kuwa!? sosai kaine AMEER HUSSEIN!!! A'ah
abin da yakasa ganewa shine miyasa yakejin
k'irjinsa na dukan uku uku idan bai gantaba!???
Miyasa yake damuwa da alamuranta!???
Miyasa yake son k'ara ganinta a yanda yaganta
ranar da towel dinta yafadi!??
Kai tambayoyi sun mishi yawa miyasa.......??????
K'arrar faduwar abu yaji tarrrr.. da kuma tar
watsewar plate yana zuwa sai ya ganta kwance
kaman ta mutu inna lillahi wa inna ilaihi
rajiuun...!!!!
[5/16, 9:46 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
[5/16, 6:40 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 31&32
Na Hauwa M. Jabo
Yana k'arasa wa, Anan yaganta sumammayi,
rana ta farko da mace ta bashi tausayi, yarasa
mizai mata, kawai ya dagata chak yakaita mota,
suka nufi asibiti aka bata gado, nan likita yace
masa damuwane yay mata yawa, da kuma
k'aranchin jini da yake damunta, anan fa yace
azo adibi jininsa asaka mata.
Ikon Allah wai Ameer ne zai bada jininsa ga
MACE??
Abin mamaki kuma abin alajabi, wanda shi
kansa baisai dalililn da yasa yake yin abinda
yake shirin yiba, Dr yazo Ameer ya bada jininsa
aka auna da nata, duk O+ ne, yayi dai dai da
natan, haka kuwa yakwanta aka dibi leda biyu
aka dura mata, aka saka mata ruwa leda daya,
sannan ta farfad'o aka samu ta dawo
hayyacinta, tana bud'e ido tayi salati, sai ta
fashe da kuka Dr yazo yan tambayar lafiya??
"Ni ku sallameni wllhy gida nakeso" nan Dr
yace tabari mijinta yazo yay signing za'a
asallameta, tace itakam batada miji ita kadai
take, akace yayanta to, namma tace aa sai ga
Ameer yashigo yana zuwa naga ya daure fuska
yacewa Dr. lafiya??waishi kishi tofa!! nima jabo
da nake kawo muku rahoto abin ya bani dariya
wai Ameer Hussein ne yake KISHIN MACEE...
Dr. yace
"No ba wani abu bane sir, tace a
sallametane, nace ta bari mijinta yazo wai
batada miji"
Ameer yacewa Dr
"Ok kaje ina zuwa"
yana zuwa ya wani doro min hannu akan
goshina, yace
"bakida zazzabi sannu!"
Ya sauke hannun sa,
haka naji hannunsa kamar ya d'aura min wani
garwashin wuta, dan zafi nagara jin tsanarsa
araina, sai likita ya lek'o yace
"Ameer Hussein baka gayamana sunan matar
takaba, zamu cika form ne"
nanfa kunyar duniya ta isheshi ya wani juyo ya
kalleni, na banka masa harara, wanda yasa ya
saukar da kansa k'asa, yabi likitan bansan yanda
suka yiba ya dawo, yace in tashi mutafi nanfa
nace ni gidan ubana zanje, kuma bazan shiga
motarshiba, nan ma wani sabon rikici haka dai
naga kamar yawace aganmu a asibiti muna
saida hali nan dai na daure na shiga motarsa na
zauna baya yanayi yana kallona ni kuwa banda
harara ba abinda ke hadani dashi.
Muka isa gida nasauka mota na shige dakina na
kulle.
Yakawo min magani anan yaji k'ofa gam, yau
ake yinta, sai yanzu tambayoyinsa da yasaba yi
suka rik'a dawo masa, tuni ya kawar da
tambayoyin yaje yadauko key ya bude k'ofar,
yata ya shigo tawani dalla masa harara, ikon
allah koni jabo abin ya bani mamaki kunsan mi
nagani?? HAWAYE a fuskar Ameer Hussein,
wanda saida na girgiza hmmm aranta tace
munafuki kuka kakeyi sabida ban mutuba ko,
Ameer Hussein ya matso daf da ita ya riqe
hannunta taso ta k'wace, amma takaasa haka
tabar mishi hannuwa ya fashe da kuka kamar
jaririn yaro yace mata....
🍃ETRAT 🍃 33&34
"Dan Allah.....!!!"
sai kuma yay shiru nanma yachi gaba da
kukanshi mai tsima zuciya, amma kuma koda
gwayan zarra ban tausayawa kukanshiba, hasali
ma wani sabon tsananshi ne ke dada mamaye
zuciyana.
Ahankali naji kukan nashi ba mai k'arewa
bane na sabule hannuwana nakoma falo, yayi
kukansa mai isarshi, sannan ya tashi ya tafi
d'akinsa, ai kuwa yaje daki tambayoyishi suka
kara zo mishi kamar dai yanda yasaba duk
tmbayar ta tazo sai ya bata amsa negative mai
makon da da duk positive ne, ya natsu sosai
yanason yagane miyasa yakejin abinda yakeji,
Lallai son yarinyarnan ya kamani, tashin
hankali..!! dama haka so yake? kodai
sha'awace? sabida abokinsa yagayamasa akwai
so akwai kuma sha'awa, tabbas son yarinyar
nan nakeyi, ya akayi haka? ohoo.. Mi yasa to
yake sonta???
Tabbas sonta yakeyi ai kuwa zaisha wahala
sabida ya riga ya b'ata aikinsa, sai yanzu ya
tuna wata shida chur da aurensu dai dai da rana
daya baitaba kyautata mataba,
toma wai miyasa nadamu da yarinnyar nan?
tabbas SONTA nake kamar yanda daya bangare
na zuciyar sa yabashi amsa cikin gaggawa,
tabbas duk wasu alamu da abokinsa yake
gayamasa naso da kauna yana jinsu ajikinsa,
shidai har yanzu yakasa gasgaska abinda
yakeji..
Duk yanda yay da zuciyanshi na k'iyayyar
mace ta dawo masa yakasa, saima wani tausayi
had'i da nadama akan abinda ya aikata yakeyi,
haka yayta tunaninsa har garin Allah ya waye
bai samu yay bacciba ko kadan..
Nii kuwa tunda nabaro mishi d'aki nadawo falo
tsanarsa ce takemun yawo azuciyana, haka
kawai naji inason ganin Mahbuub masoyina na
gaskiya. dayan zuciyana yacemun ki daina
tunanin wani namiji, har yanzu fa matarsa kike,
tuni nashare zancen Mahbuub araina nantake
bacci yay awon gaba da ni, da mafarkai kala-
kala dama ba sallah nakeyiba sai nay baccina
tazarce har safee.
Fitowan da zay yaje dakinta sai yaganta falo
kwance tana bacci, zuciyansa ta raya mishi yaje
gurinta haka kuwa yaje gunta tana ta bacci
abinta yatsaya yana kallonta, aransa yace Lallai
matanma suna suka tara, towai ma miyasa
natsani mace??? Alhalin duk wani jin dadi da
hutu yana tare da ita, nan take yaji yanason
taba pink d'in labbanta ko a hankali ta d'an
juya, haka ya baiwa rigarta damar dagewa
kadan, wanda yasa saman k'irjinta ya bayyana
lokaci daya yaji kwata kwata ya chanja yashiga
wani hali wanda tunda mahaifiyarsa ta haifeshi
bai taba jin irinsa sai kawai........
[5/16, 6:57 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃35&36
Na Hauwa M. Jabo
Yaji bari yay hugn d'inta, nanma yakasa, yariga
ya rude yarasa tantance miyakeji ajikinsa wanda
ga dukkan alamu sha'awace ta motsa, nan dai
yakai hannunsa ya rik'e hannunta amamakin sa
sai kawai yaji tarik'e hannunsa gam, har tana
murmushi wanda ya bashi damar kai dayan
hannunsa yana zagayawaa akan labbanta nan
ma ga mamakinsa yaga tai murmushi, shima yai
murmushi aransa yace ta hak'ura tayafemin
kenan..
Kai gaskiya yarinyar nan tanada kirki, dama
mata haka suke da rahama.?
baisan kuwa ita mafarki takeyiba, wai ta auri
Mahbuub suna soyayyah...!! lokaci daya na
bud'e idonna cike da jindadi sai kawai naga
mutum agabanna ya rik'e mini hannu, wani
sabon tsanarshi naji ya kamani, na kwace
hannuna, na tashi zaune, na dalla masa harara,
ya duk'ar da kansa sabida kunya, Lallai dole yaji
kunya idan yasanta, sabida ya musgunamata,
bance dashi komaiba nabi ta gefensa na wuce,
naje nayi brush nayi wanka tafito tas, ga
mamakina sai naji k'amshin abinchi, koda na fito
sai naga Ameer yana hada break fast sai
k'amshi ke tashi, abin ya dauremin kai azatona,
ko ruwan zafi baisan yanda ake dafawaba,
amma gashi sai k'amshi ke tashi, naso inshiga
kitchen in hada nawa brk fast d'in, sai kuma
naji bazan iya jerawa dashi guri dayaba, kawai
bari idan yafito sai inshiga in had'a, ina zaune
ina kallo na yana fitowa nikuma natashi nashiga
kitchen sai yacemin
"kee...."
sabida har yanzu baisan sunanaba
"kefanahadawa break fast..! sabida Dr yace
kina hutawa,"
ko kallonsa ban yiba haka nashiga kitchen
nafara hada abin karyawana yana tsaye yana
kallona har nak'are nazauna inachi yana kallona
duk sai naji wani iri, naso intashi sai kawai naji
bari inshare karma yaga nadamu dashi, har na
chinye naje kitchen nay wanke wanke nadawo
nachi gaba da kallona, shi kuwa yananan zaune
sai bina yake da ido, duk inda nayi yana biye
dani da ido, ranar ko ruwa banga yashaba, haka
ya yini yadan bani tausayi kadan ammafa
tsanarsa tana nan cikin raina, wajen qarfe goma
naga gabaki daya kalanshi yachanza ya rame
yayi wani zuru zuru dashi, yabani tausayi sai nay
dabara nazo da kayan tea na ijeye akan table
dinda yake gabanshi wai ina nufin yasha amma
ni bazan cemasa yashaba, kawai ni nahada
nawane nasha ko motsi baiyiba yabani tausayi
sosai dan kuwa har yarame ko azumi mutum
yay yana buda baki, amma gashi har shadayan
dare yayi baichi komaiba, nakasa cemaca
yatashi yasha haka natashi nashiga daki nay
kwanciyata, har bacci yay awon gaba dani
dasafee anan natarar dashi kwance yana bacci
nadubeshi yay balaeen bani tausayi sabida
nasan baichi komaiba, but ya zanyi in bashi
abinchi sabida ko bakomai musulumi ne dan
uwana....
(Hmmmmm... wallahi mata akwaimu da
tausayi) sabida lokaci daya zuciyata ta karaya
bawai dan Ina sonsa ba, aah kawai dai nasan
baichi abinchi ba, anan nafara tunanin yazanyi
nace yachi abinchi, shiru kusan minti biyar sai
natafi kitchen na fara hada masa break fast
wanda zai rik'e masa chiki sosai, nan danan na
hada abinchi kala kala nazo na ajiye narasa
yanda zanyi intayar dashi sai na daure naje ta
duk'a kenan na dago hannu zata tabashi sai ya
tashi mukayi ido biyu ...
[5/16, 10:44 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 37&38
Na Hauwa M. Jabo
Ya bude ido kunya ta kamata lokachi daya
tarasa yanda zatayi, sai Allah yakai idonta akan
phone d'inta, sai tawayance ta'dauki wayanta ta
k'ara gaba, shi kuwa ya d'auka dama wayan
zata d'auka, yatashi tsaye sai jikinsa yafara bari
bashiri yadawo yazauna, yunwa yakeji sosai ga
kuma abinchi agabanshi yatashi dagyar yana
dafa garu, yaje yay brush yadawo, sabida shi ko
ganintan da yakeyi yanasa ya k'oshi yazo ya
zauna yasan abinchi banashibane, saboda tace
ko zai mutu bazatay masa girkiba, haka yazauna
abin duniya duk yabi ya dameshi sai saqe saqe
yakeyi.
Tana chin abinchinta sai sukay ido hudu yay
balaeen bata tausayee sai tace masa
"bisimillah"
ba musu ba kunya yazo yafarachi, har suka
k'are, yay godiya ko kallonsa batayiba, dama
tausayani irin nata.
Tun daga ranar dai tana girki dashi, sai dai
yana shan wulak'anchi da kallon banza da
harara, kai duk abinda zai fusatashi tanayi
amma shi ko ajikinsa.
Kumma haka yana chin abinchinta kullum..
Aka samu sati d'aya, taga kamar neman shiri
yakeyi, ita kuma hanyar rabuwa dashi take
nema, sai ta dauki matakin daina zama falo
aikuwa haka yafi komi azaba agurinsa, sabida
zai iya hak'urin rashin abinchi, amma bazai iya
hak'urin da rashin ganintaba, ya sameta ya ya
gaya mata bazai iya haqurin rashin ganintaba ta
gaya masa magana mai zafi saida yayi jaaa dan
kishin da yaji lokacinda tay maganar Mahbuub...
Tun daga ranar bata fitowa saidai ta dugyre
masa abinci ta wuce abunta, yanda ta ijiye
abinchi haka take tarar dashi baichiba, sai kuma
abun yana damunta, kwana biyu da fara
boyewarta, ranar sai ta fito falo dan tun safee
bataji mostinsaba, koda tazo taganshi akwance
kaman yay bacci, har lokacin sallah azzahar
yay bai tashiba, bata kuma tayar dashiba,
lokacin la'asar ma shiru kakeji, abin yabata
mamaki sabida tasan yana balaeen kula da
sallah, da duk wani abu da yashafi addininsa.
Akayi Magreeb shima shiru ba sallah ba
zancen chin abinchi, tarasa yanda zatayi tatayar
dashi abinda ya daure mata kai shine, kwanciya
ko motsi bayyiba ballantana ya juya, sai kawai
tayanke hukunchin tayar dashi yay sallah tazo
takira sunansa ahankali, taji shiru, tak'ara
kiransa haka ma shiru, sai ta dan bubbugashi
nan ma shiru nan da nan sai taji matsananchin
tsoro ta bubbugashi da sauri ina fa baya mosti
nan danan ta girgizashi iya qarfinta amma shiru
ta kwantsa ihu ba wanda zai jita agidan datake
kuma bata iya daukarsa tuni tafita aguje bako
takalmi ta kira mai gadi sukazo sukaga baya
motsi, haka akaishi asibiti tay balaeen rudewa
haka suka isa asibiti aka bashi gado likita ya
dubashi iya dubawansa amma lallai bashida
rai.... tuni tasanar da iyayensu duk sun hallara
lokaci daya tafita hayyachinta dayan bangaren
zuciyarta yace mata idan ya mutu sai ki auri
Mahbuub masoyinki kinga kun rabu lafiya..
dak'arfi tace
"NOOOOOOOOO.......!!!"
Wanda duk akayo kanta, lafiya? tak'ara fashewa
da kuka, sabida tasan duk abinda yasameshi
itace sabida ya taba gayamata cewa.....
"Duk abinda zaki mini ko horo da yunya,
harara, idan ma zaki iya kadakeni zan iya jurewa
amma bazan iya jure rashin ganinkiba, sabida
ganinki yafiye mini chin abinchi, kece abinchin
ruhina, kuma wllhy gaskiya nake gaya miki,
bazan iya chin abinchiba matsawar bansakaki a
idonava, kinfi komai muhimmanchi agurina,"
a lokacin na dalla mishi harara da kuma tsaki
nace mishi
"Sai dai kamutu kuwa bazaka ganniba idan
ka mutu sai na auri masoyina Mahbuub......."
tak'ara fasheawa da kuka tabbas nice, sabida
yagayamin amma bankiyayeba kamar
mahaukaciya tafara surutai tana nina jawo..!
wllhy nice..! ku yafeeni wllhy nice..!! Duk abinda
ya sameshi nice. Sunrasa gane mi take nufi
tabbas tashiga rudani sabida yanzu ta tuna
kwananshi uku baici abinchiba tabbas ita tace
sillar duk abinda ya sameshi dai dai nan Dr
yafito yace musu sai dai kuyi
haquri Allah yayi masa cikawa haka kikaji ta lau
tafadi nan koda rai ko mutuwa........
[5/17, 7:00 PM] Auntie M. Jabonation✍🏾:
🍃ETRAT🍃 39&40
Na Hauwa M. Jabo
Umma mahaifiyar Ameer, tayo kaina tana kuka
tana,
"Shikenan ya mutu..!! shikadai Allah yabani
aduniya, kuma kin kasheshi," nanfa Umma ta ci
gaba da rera wani matsanancin kuka, ta rud'e
gaba d'aya.
"Shikenan narasa dan'a, dama shikadai
Allah ya rayamin, Ashe rabon ni zan kasheshi da
kaina ne, nida nai masa aure kuma nasan
bayason mace a rayuwarsa, yar nan har yasaka
miki doka miyasa kika taka dokar.? kince kece?
ya kikay kika kasheshe kitashi kiyi magana...!!"
Amma nima lokacin na riga na suma, dak'yar
aka janye Umma daga jikina wanda ga dukkan
alamu ta samu tabuwar hankali, aka kaini d'aki
dagyar na farfado daga dogon suman da nayi,
ina bud'e ido nace
"ina yaya As meer?"
kowa sai kallona yake natashi zaune nafara ihu,
sai an kaini gun yaya Ameer, nanfa akarasa
yanda za'ay dani, aka yiwa Dr. magana akan ya
nunamin gawar Ameer Hussein, yace sai nayi
shiru, haka nai shiru, aka saka min wasu kaya
nabi bayan Dr. naganshi kwance tunda nake
bantaba ganin gawaba sai yau, gawar ma ta
mijina, wanda nice sanadiyar mutuwar shi, na
daure nay shiru dama Dr. yace mini idan nay
kuka zan fita, tuni na natsu naje gunsa na tsaya
Ina kallon sa, na bud'e fuskarsa da aka rufe da
wani mayafi green, na kalleshi rana ta farko da
naji sonsa ya shiga raina, amma ba amfani
tunda na kasheshi..! na kama hannunsa ahankali
na rik'e gam, amma abin mamaki ba sanyi
ajikinsa, wanda a islamiyanmu ance mana gawa
tanada sanyi idan ta dauki d'an lokaci, amma shi
sai zafi naji ajikinsa, na kallesa Lallai nay asara
koba komai zaman aure yafi zaman zawarchi,
amma yazanyi tunda na riga na kasheshi, lokaci
daya wasu zafafan hawaye suka saukomin da
natuna da sista khadee yanda take soyayyah
damijinta wanda nay alk'awarin duk lokacinda
muka shirya sai namishi soyayyah wacce tafi
wacce sista khadee takeyi da angonta, amma
ina mijina ya zama gawa, wasu zafafan hawaye
suka sauka a idona ahankali na janye mayafin
da aka rufe masa jiki yanada singlet ikon Allah
arayuwa inason miji mai gashin k'irji gashi
nasamu amma nakasheshi..!! Ahankali na dora
kaina akan k'irjinsa ina zubar da hawaye, amma
ba sauti, na k'ara matse hannunsa iya k'arfina,
nayi minti biyar ahaka sai naji kamar zuciyarsa
tana bugawa kadan kadan nay balaeen tsorata
da naji ya motsa hannunsa dana rik'e, dama
gawa na motsi..?? Idan ma kasheni zaiyi to
yakasheni in huta... sai naga likitochi sun shigo
aguje ashe har sungani a dakinsu ceawa yana
nunfashi tuni aka kada ni waje, amma kuma sai
naji kukana ya tsaya kawai son ganinsa nakeyi.
Umma dai tanachan ba lafiya anmata allurar
barchi, nan dai na zauna ina tunaninsa lallai na
cutar dakai Ameer, koda kai ka koyamin
tsanarka, kai ka koyamin ki'yayyar ka.
Dr. Ne yafito yace mungode Allah ranshi
yadawo, dama dogon suma ne sai dai jikinsa
yayi wk sosai, so sai ankula dashi anan nay
hamdala, angayawa kowa Ameer ya dawo amma
kuma baya iya magana sai dai motsi da kai da
yakeyi.
Bayan kwana d'aya aka bamu izinin zuwa
ganinsa, munshiga mu biyar iyayensa da nawa
iyayen da kuma ni muna zuwa duk yay ma kowa
murmushi amma ni ko kallona baiyiba, nanda
nan nasha jinin jikina, duk naji natsani kaina sai
ya buda baki kaman zaiyi magana ina dago kai
naga ya tsuramun idoo ko gyabtasu bayayi, har
sai da na tsargu sai naji ance. ET...! ETR...!!
ETRAT...!!! Tabbas Ameer ne ya kirani wanda
bantabajin yakira sunanaba sai yau.....
🍃ETRAT🍃41&42
Nazo da sauri zan matso gunsa sai naga Umma
tatareni, tace
"bazaki zo kashemin d'aba tunda Allah yasa
bai mutuba ak'ara gaba da mugayen halaye...!!
Ki fita ki bace mun dagani"
haka naji maganar kamar saukar aradu
yadago hannu irin inje gunsa, amma umma ta
hana naja na tsaya sai kuma kuka ya
subuchemin haka na juya na fita bansan ina zan
nufaba gidan ubana zanje? ko gidan mijina?
Haka naita saka a raina tabbas nasan yanzu
ina son Ameer sosai, wanda nima bansan yanda
nakejin abun arainaba, sai su Hauwa Jabo da
suka san dadin soyayyah da zafinta, haka dai na
yanke shawarar tafiya gidan mijina idan ma
yasakenine sai maje gidan mu, haka kuwa na
wuce cike da bak'in ciki.
Iyayena suna gun amma basu cemata
komaiba, tunda basusan miyake faruwaba, saima
hak'uri da suke bata.
K'awata sista khadee tazo duba Ameer
asibiti wanda bata tarar daniba, taje gida
tanamun fada yazan bar mijina indawo gida
nanuna mata cewa nazo daukar kayan mune
nan dai nasamu narabu da uwar iyayi sista
khadee..
hardai ameer yay kwana uku banje na dubashi
ba Amma zuciyata tana Chan tare dasu.
Acan kuwa ya matsa shi sai an kirani,
Umma kuwa ta hana yace shiko sai an
sallameshi.
Haka aka salleshi yanata jin dad'i ga
mamakinsa sai yaga an wuce dashi gidansu, ba
gidansaba, yaso yay magana sai yay shiru suna
isa gida su mama sukayi Allah yak'ara lafiya
suka tafi gida, Umma kuwa nan tafara balaee
wllhy sai ya sakeni,
Ya tambayi dalilin hakan Umma tace sabida
tanason takashe min kai...
Yai murmushi nan yagayamata abinda yafaru
tun farkon auren mu har zuwa yau,
Umma tay shiru , lallai tayi saurin son yanke
hukunchi batare da binchikeba, bayan annabi ya
umurcemu da kada Ku rik'a yanke hukunci da
gaggawa ba tare da bincike ba, tay danasanin
abinda ta aykata sosai, wanda har kuka saida
tayi, sabida giyar son kai data kwasheta, kuma
Lallai Etrat tayi hak'urin zama da Ameer, wanda
ba yarinyar da zata iyayin irinsa batare da ta
fallasashiba, nan dai tai mishi fada sosai kuma
tace sai tarabasu idan baiyi hankaliba, suka tafi
dashi da ita chan gidansa, suka tarar dani a falo
na zauna naci uban tagumi, daganina kasan ina
cikin tashin hankali, naji tsoron ganin Umma,
amma kuma naji dad'in ganin mijina wanda ya
warke sai dai akwai rama kadan tare dashi nan
muka gaisa da Umma a tsorace, itama tagane
hakan, nan dai Umma tay ta bani hak'uri akan
abinda tamun a asibiti, kuma tace
" Ameer yafadamin duk chutarki da yayi
Ai da ki da kin masa fiye dahaka Wllhy, Amma
yanzu kina free, idan zaki zauna dashi to
shikenan, idan kuma bakyaso wllhy zan saka ya
sakeki sabida cutar tayi yawa idan kuma zaki
iya zama dashi to zabi nakine."
tabbb nan naga Ameer Hussein yana gumi
tabbas inason mijina, amma ina tsoron halin
maza nay shiru nan dai Umma takatse min
tunani tace ke muke jira nace Umma gaskiya.....
🍃ETRAT🍃 43&44
Gaskiya..... sai kuma nace
"Umma ba komai na hak'ura zan iya zama
dashi" hawaye ne suke mini zuba a idona narasa
mi yake damuna kawai inason hada ido da
mijina amma nakasa haka dai Umma tay mishi
fada agabana sosai kuma tasaka mishi sharudda
masu yawa nima tay min nasiha sosai sannan
tatashi ta tafi.....
kikaji guri tsit kamar bama gurin kusan minti
biyar chan dai naga shirun yay yawa nace masa
"ya jiki?"
Yace
"da sauk'i"
Koda na d'ago idona sai naga yana zubarda
hawaye, hankalina yatashi sosai amma sai na
dake "ETRAT....!!!"
Wllhy saida naji tsigar jikina tatashi sabida yanda
ya kira sunan, kuma dama ban taba jin ya fadi
sunanaba sai asibiti, sai kuma yau.
Mamakin inda yasan sunana nake, sai yace
mun "kina mamakin inda nasan sunankine? a
katin auren mu na duba anan naga sunanki"
nan dai yana hawaye yana bani hak'uri akan
abinda yamun nan da nan naji na hak'ura koba
komai yanzu inason mijina...
Amma nakasa magana, yau ga namiji yana
mun kuka koda yasha mun kuka, naji dad'in
haka, nakasa magana yasake kiran sunana,.
Wallhy idan ya kira sunana daga kaina
har zuwa k'afafuwana nakeji, na daga kai na
kalleshi nace
" ba komai komai ya wuce nima ka yafemin
abubuwan da namaka"
sai hawaye ikon Allah mata da miji kenan haka
ya matso kusa dani ya kamoni ya rungumeni har
inajin dukan girjinsa yana gogemin hawaye yana
yana rarrashina kaman wata jinjira har nay
shiru....
A bangaren Ameer kuwa wani yanayi yasamu
kansa aciki wanda baisan ko miyeba, tunda bai
taba rungume wata ya mace arayuwar sa ba,
gaskiya mata abinso ne yana ta tunaninsa kala
kala.....
Tay garfin hali tace masa yaje yay wanka suchi
abinchi, yayi wanka yafito tass dashi, suka hada
ido sukay murmushi dukansu lokaci daya...
sukachi abinchi suka zauna suna kallo, shikam
ita yake kallo ita kuma satar kallonsa takeyi har
11 na dare
hmmmm nidai jabo sai murna nake naga sun
shirya nasan zaay bayanin.....
Amma sai ameer ya bani mamaki yace ETRAT
kije ki kwanta dare yayi ta tashi tayi dakinta
shima yay dakinsa...
Sun bani haushi sosai yau kwanansu 10 dai
dai,da daidaita kansu, amma haryanzu ba wani
labari dukansu sun saki jiki da junansu wanda
har wasa naga suna yi amma ba dayan bayanin.
Amma dukansu basa bacci dadare kowa tunanin
daya yakeyi sai da safee suke fitowa falo suyi
bacci tare da junansu...
Watansu 7 chif da aure ba wani bayani, nikuma
hauwa jabo na gaji ina ganin haka zan barsu in
kammala amma sai k'awata Zainb khalifa tace
inyi hak'uri nachi gaba da binsu har muga
mizasu haifa.....
🍃ETRAT🍃 45$46
Ai kuwa haka nachi gaba da binsu kamar mayya,
kullum suna manne da juna sunajin dumin
junansu, amma basa yin wani abu bayan
kwanciya akan jikin juna abun yana burgeni
yanda suke kula da junansu, yauma kamar
kullum munchi abinchi sai yadan fita wajee,
yana fita nashiga wanka ina fitowa daga wanka
sai gashi ya dawo, wai yafasa fita yadauka nay
bacci shiyasa yashigo dakina, sabida sab maya
shigowa dakina, haka nayi karo dashi sai naji
kunya, amma sai na bayar ya kuwa budemin
hannuwa irin inzo, ni kuma da sauri nafada
ajikinsa yamaida hannuwansa ya refe ya
rungumeni ya matseni sosai, wanda saida naji
zafi a girjina, sabida baitaba rungumeni kamar
yauba, sai nayi k'ak'arin raba jikina da nasa,
amma sai yak'ra matseni a kunne ya radamin
cewa
"karkiji tsoro ETRAT NI K'AUNARKI NAKEYI,
SONKI NAKEYI, WANDA AJININ JIKINA YAKE
BAWAI SHA'AWARKI NAKEYIBA .....
Ki kwantar da hankalininki amma tabbas ina
matuk'ar son ganin yaro ko yarinya wacce zaki
haifamin."
Bance masa komaiba, na k'ara lafewa, mun
dade atsaye sai ya janye jikinsa yamun kiss
yace inshirya yana jirana a falo, naso ya chi
gaba damun waiwayin da yakemun, amma kuma
sai yace inje in shirya, haka naje nasaka tufafina
nazo mukayi labari yanda muka saba, har
lokacin bacci yayi, mukayi sai da safee naje
dakina, na cire kayan jikina wata rigar bacci na,
nasan mijina yanason kusantana, kawai yana
ganin kamar bana sone shiyasa yake dan
kaucewa ,amma yau angama haka natashi na
rasa miyake mun dad'i, ya zan bullowa al'amari
tabbas inason in kwana da mijina, kodan na
faranta mishi, amma bansan yanda zan yiba, ina
zaune sai na tuna da indo matar dan sarki yanda
ta jawo yarima gurinta, nace ko haka zanyi ? sai
kuma nace aah bazanyiba, nan dai na yanke
shawarar bari in hak'ura kawai inyi baccina har
ranar da Allah zai sa ya kawo kansa, ina
kwantawa sai naji an turo k'ofa, Ameer ne a
tsaye yay mun murmushi sai yacemun yau naje
nakwanta sai nariga jin tsoro, araina nace lallai
ma namiji da tsoro, nay murmushi nace to zomu
kwanta anan, yakuwa shigo araina nace gara ma
da banjebaa gashi yazo da kansa, yamatso
yatsaya yana kallona sai yanzu na tuna kayan
da nasaka banga laifinsaba, nandanan sai naji
kunya ya kwanta nima nazo na kwanta yace in
matso muyi labari, da yake na sama kwanciya
kusa dashi ban ji komai ba, nakuwa matso abina
muna ta hira ta soyayyah, bansan yanda akay
hannuna yakai saman k'irjinsa ba, nidai inason
gashin k'irji a gun namiji, gashi na samu agun
mijina, muna hira hannuna na kai kawo a gurin a
hankali wanda sai naji dukan k'irjinsa ya chanza,
yanzu yana bugawa sosai fat!.. fat!!!. sai na
janye hannuna ahankali, yayi shiru nace
"Saida safe"
Nak'arara shigewa ajikinsa, sosai nanfa naji
abu yasha banban dan kuwa gabaki daya Ameer
ya rude, kawai naji yana neman wuce gona da
iri, ni Jabo da ganin gwagwaf nafito da gudu ai
kuwa ina dawowa zainb khalifa ta maidani wai
sai nagano musu yanda aka k'are nanfa nakoma
amma nayi latti sabida sun riga sun gama
abinda zasuyi sai kukan Etrat nakeji, shikuwa
Ameer yanata aikin rarrashi, nan dai na tabbatar
da komai ya wakana, lallai Etrat taji jiki sosai,
dan kuwa Ameer Hussein dai dai da rana daya
bai taba kusantar wata maceca arayuwarshi, sai
matarshi ta sunna nan dai yayi jinyar Etrat har
ta warke kwana biyu nanfa yanemi amaimaita
batak'i ba sabida tasan ba kew hana mai house
abinshi, amma dai tana jin tsoro sosai, haka dai
tabashi hadin kai har Etrat tasaba nan sun saki
jiki da juna, tunda ya gane dawar garin kusan
dai kullum ne, tun abin yana damun etrat har ya
daina damunta, itama tadaina damuwa,
soyayyah suke da k'aunar juna suna kula da
junansu sosai....
"MATA akwai ni'ima ba halittar da takai mace
daraja aduniya cewar Ameer Hussein......."
Sista khade tazo gurina muna tadi wai taga na
chanza k'irjina ya fito, nandai tace tana ganin
nakamu, nikam banida wani ciki haka kuwa
akayi nakamu wata uku bansaniba.
Murna agun Ameer ba'a magana, lokachin
haihuwa yayi na haifi yarona lafiyayye aka saka
masa Aliyu ...
Ranar yaya Ameer yadawo yaganni da hijabi
"lafiya kike zama da hijabi kamar wata
malama?"
nace
"kasan nan gidan musulmaine ba gidan
arnaba."
nanfa yatuna da dukan da yayimin na rashin
dalili wai nazauna a gida ba tufafi kamar gidan
arna, nan yaji kunya yayo kaina nagudu nafadi
akan gado,
"Ai baki saniba lokacin kin fara sauyamin
tunaninane, shiyasa nace miki hakan"
Haka suka chi gaba da rayuwar gwanin ban
sha'awa,
Sun shirya zuwa yawo, sukaje Cyprus daga nan
sukaje Turkey gaskiya k'asar ta burgeni sosai
sabida ba ruwan kowa da kowa daganan suka
wuce mashhad, suka kawowa Hauwa jabo ziyara
inda suka tarar da ita abin tausayi, sabida dai
itama Ga dukkan alamu ta nuna tanason tayi
Aure amma kuma karatu takeyi muna mata fatar
alkhairi.......
TAMMAT BI HAMDILLAHI.
SAI KUNJINI A LITTAFI NA GABA MAI SUNA
"AURE KO ZAMAN GIDA"
DAGA TAKU HAUWA M. JABO....
Shin Ana Bukatan Blog ko website Kamar wannan kodai kamar Shafin
Duniyan Fasaha, za'a iya samu a kan farashi mai rahusa daga Babban kanfanin
Be With Me Technology Yola, Wayanda suka kware wajen
Website Design da kuma hada Mahajar Waya. Za'a iya tuntubansu
anan ko a wannan layin +2349039016969
Get Professional
Website Design For your business Today
Here. You can also visit our
Tech Blog for more awesome Information.