Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, 3 February 2017

ASHE KAINE MIJINA? COMPLETE

adsense here ASHE KAINE MIJINA?1... Na HAUWA M. JABO... Ke nazia kiyi sauri ki tattaro kayanki kizo mu tafi yayanki yana jiranmu, ko walle mu tafi mu barki! ganinan zuwa inna! nazia ta baiwa inna amsa tana qoqarin fitowa daga tadinka da dan gunshin kayanta a hannu, da yar jakarta inna ta kalleta a hantare, kekam kinji haushi Kullum idan za'afita sai an barki, duk zumudin da kike ya zama na banza tunda har na rigaki shiryawa, nazia ta kwashe da dariya, wallahi inna kesan kayana sunada yawa shi yasa ban samu na fito da wuriba, ke dan Allah wuce ki bani guri ko in hantareki, mara kunya, dama haka kike kullum da baqar shiririta, ta qara kwashewa da daria, hadda gyagyataWa, duk wanda yaga nazia a gida idan ya ganta a waje zai dauka ba ita bace, yanda take daure fuska kamar bata taba murmushi ba, zaka dauka kamar ma bata taba dariyaba a rayuwarta,tafito da dan gudu gudu tana kallon ko ina idan basuyi Mantua ba ta kalle ko ina amma komai babu tafito tana murmushi, yayanta ya kalleta, ke wallahi kinci albarkacin inna da sai mu tafi mu barki kinfi kowa cewa a koma birni amma kuma kinfi kowa shiririta, mtsww yayi tsaki, na qyalqyale da dariya abina na fada jikinsa yi haquri yayana, yanzu ai gashinan na fito mu tafi ko, amma fa abu daya ya rage min, inna da yaya duk suka juyo suna kallon juna da mamaki, inna tace dama baki kammala ba Nazia??? aah inna na qare komai amma ai kince inje gidan....... ASHE KAINE MIJINA..? Na HAUWA M. JABO.... Amma ai kince inje gidan su abban fatin birni in musu ban kwana, Inna ta saka salati tana tafa hannu, dama nazia da nace kije ki musu sallama bakije kin musu sallama ba, yar duniyar ta qara kyalkyalewa da dariya, amma anyi shaqiyiyar yarinya inji inna, ta kawo min duka amma ina na kauce, na qara kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza, sai ta ishimutane da dariya sai kace mai tabin jinnu, yaya ya gama qufula, baice komai ba.!!! Na zabga a guje ina ta dariya, ina shiga dayar kwanar na daure fuska, kamar banice mai kyalkyala dariyannan ba, na gyara hijabina nashiga gidansu hafizun birni mamanshi tana ganina ta hau washe baki,tana min kirarin da ta saba amma ko ajikana nasha magani abina tace auta matar auta, badai tafiyar ceta tashiba, kamar banason magana na kebe baki nace, E, tace yar nan Allah ya kaiku ya lafiya gashi sameer baya nan da sai in ce ya baki number yayan naki nura idan kunje sai ku nemishi ku riqa qaisawa, bance mata komai ba, ta qare surutanta, nace zamu wuce su yaya hafizu suna jirana, tace to yar nan Allah ya miki albarka, ta bani kudi wai insha ruwa a hanya amma naqi in karba, nace ina fati take? Allah sarki bata dawo makaranta ba idan ta dawo xan fada mata kun tafi, xatayi kewa Wallahi xan wuce yarnan baxaki karbi kudin ba nagode hajiya, dama itama ta sanni da taurin kai aranta take cewa tauri da tauri sai qaqa.. ...... ASHE KAINE MIJINA..3 Na HAUWA M. JABO Sai qaqa, koda na qaraso na tarar da an kulle gidan mu kuma ba motar yaya ba labarinta!!! Tuni hanjin cikina suka shiga kadawa idona suka cika fall da hawaye sai kuka, yanzu su yaya da inna sun tafi barni, kuka Sosai nakeyi na zauna dirshan a qofar gidan mu na rufe ido ina kuka,maimakon in dan xagaya amma anan na dabe ina kuka, sai ji nayi ankwasheni da mari ta gefen fuskata ! Kutumar uba waye yake dukana duk da ina cikin qunci amma da bala'e na dago kai inga wane dan iska ne yake dukana!!! Daga kan da zanyi sai kawai naga yaya, fuskar nan a turnuqe kamar an aiko mishi mutuwa, wallahi idan baki tashi mun wuce ba zan babbalaki anan, mamaki da tsoro ya cikani, araina nace su tafi su barni sannan kuma yaxo yana dukana da zagi, araina na fara balaee na daure fuska, ashe nice banida kai mota gatachan gaban gidan mu kadan kwana sukayi suna jirana, da yake ni idan ina tafiya bana qage sai ban hango motar ba, na kuwa sha kunu na fuske abina, ya shiga gaba ina bin bayanshi saida muka isa jikin mota naja na tsaya, kamin kace kwabo inna ta wankeni da wani marin,ta buda baki xatayi magana na rigata nashiga uku, nace minayi muku kukeson ku kasheni,sai inna ta shige mota ta barni, naci gaba dan kunga ina zumudin zuwa birnin ne ake min wulaqanci...!! to Wallahi na fasa zuwa birnin banaso, bazanjeba asaukemin kayana...!! ba inda zanje, na qara fashewa da wani kuka.... yaya ko kallona baiyiba shima ya zagaya ya shiga mota ya kunna yana jiran in shiga amma ina taurin kai ya motsa, ko ajikina, yayi horn alamar in shiga amma ina sai ya fito ......, ASHE KAINE MIJINA..4  Na HAUWA M. JABO sai ya fito, kinsan Allah nazia idan baki wuce muka tafi ba zan babbalaki yanzu nan, ko kallonsa banyiba, na kauda kaina gefe, yaga da gaske nake yakaimin duka, ko in kauce na tsaya qiqam mugun halin ya mosta hakan ya qara bashi haushi, dama shima gwanine a gun xuciya amma dai bai kaini ba, ya fara dukana har na fadi yasa qafa yayi ball dani, hankakin Inna ya tashi tasan idan zai kasheni a gurinnan ba tashi zanyiba, kuma tunda nace bazan jeba ba tafiyar zanyiba, tazo ta janye yaya hafeez daga gareni, ba halin ta mishi fada yanda taga ya chanza har fuskarshi tayi jaa dan tsananin fushi ,da yake shi yaya hafeez fari ne Sosai ko kunya yaji sai kaga yayi ja, haka lokacin sanyi ma jaa yakeyi, uwa uba idan yayi fushi sai yayi jaa kamar bature haka yake, tayi gefe dashi ta daura hannunta akan kafadar shi ta dama, haba yaya!! Ya zaka biyewa nazia? Yarinyar da ba hankali ya ishetaba, kuma sam batasan ciwon kantaba, wuce ka shiga mota bari in daukota, yayi mini wani mugun kallo, rai a bace ya shiga mota yana huci "nima dai m. jabo da nake biye dasu ya bani tsoro dan nayi niyyar in gudu sai mun hadu birni amma dai nayi ta maxa na tsaya" inna tazo ta durqusa kusa dani, tace ba tafiya mukayiba kinsan haryar qaramace shine sai yayanki yace bari muyi kwana kamin kizo shi yasa baki hango muba kuma ke gashi bakya kallon hanya kina zuwa baki ganmu ba maimakon ki duba gefenki sai kawai kika nemi guri kika zauna kika fara kuka, abin ya bani haushi ne dan kada yayanki yace na goyi bayan ki shi yasa nima na dakeke amma nima raina baiso ba....!! haba autan inna kuka ba naki bane kinga kin bata wa yayanki lokaci kusan awa biyu fa muna jiran ki kuma ya gayamana yanada aiki kuma duk ke kika janyo araina ......, ASHE KAINE MIJINA..5  Na HAUWA M. JABO Araina naji dadi ko banza na bata masa Lokaci, amma kuma naji jiki, Lallai nice banida gaskiya sabida ina zuwa kawai banga motaba sai na zauna na fara kuka, kuma ni kaina nasan ba yanda za'ayi su tafi su barni, wauta ce take damuna ko qauyanci? na bude baki cike da yawu da jini na zubar da yawun gefen inna, inna da taga jini hankalinta ya qara tashi, maimakon in sassauto in lallaba in tashi mutafi sai na fuske, "kamar jabo tayi rashin kunya ta fuske" ina sheshe kar kuna bace inna ba inda zani na fasa tafiya,birnin banza, dan yaga inason inje birni ne shi isa yake min wulaqanci, yanxu kuma na fasa zuwa asaukemin kayana, ashe yaya yana jina, da qarfi ya fito motar ya bude bayan motar motar ya ciromin kayana ya jefini dasu kikaji jakar timmn akaina, tabbas wannan yafi dukan da yamin qonan rai, inna ta kalleshi, ta daure fuska, ashe bakada hankali? Mi kayi kenan? To sai ka fito min da nawa kayan nima ba zaniba, tunda abin naku rainin hankaline, hankalin yaya ya tashi, nima dai naji tsoro kuma naji kunya, ya durqusa inna.... kamin shiru ka fito min da kayana nace ba zaniba ko dolene,!! Narasa yanda zanyi akaina ake mishi fada kuma nice banida gaskiya ga uban taurin kai, ya juyo gurina nazia dan Allah kiyi haquri�� na sunkuyar dakai, banji dadin abinda na masa ba... Itama inna taga rashin dacewar hakan abu ya hade masa biyu ta miqe tsaye ke nazia tashi ki shiga mota kaima wuce mu tafi sumui sumui kamar munafuka na miqe zan dauki jakar kayana yaya ya karba inna tace sake mata kayanta ta dauka da kanta, Lallai ban kyautaba kuma duk ni na janyo amma...... ASHE KAINE MIJINA..6  Na HAUWA M. JABO Amma ya zanyi fuskewa kawai zan cigaba dayi yaya yashiga mota nima nashiga, nasani sarai idan akwai abinda ya tsana baifi ashiga bayan mota a barshi shi kadai a gaba ba, na kuwa fuske nabi Inna baya, ya kalleni irin kallon tausayi muka hada ido amma na fuske abina, na bude baya zan zauna, Inna tace nan kika saba zama?? Sumui sumui naje gaba na zauna, yaja mota sai sakwato birnin shehu, sokoto garin dan fodiyyo garin karamci qarin mutumci, garin dattako, garin kashe kunya, na jinjina muku sakwatawa, Allah ya barmu da qaunar ma'aiki.!! Tunda muka shigo nake raba ido sabida qarin yamin, Gaskiya qarin yanada kyau da tsabta, sai kalle kalle nake sabida tunda nake ban taba zuwa sokoto ba sai yau, rabona da sokoto tun ina shan nonon innata, haka kawai naji hawaye suna saukomin, Lallai ban kyautawa yayaba! Na mishi butulci Sosai, shine wanda Kullum burinsa ganin farin cikina! Shine Kullum burinsa farantawa mahaifiyata,! Muna qauye amma ba wanda zai kirani da ba qauya! Ba wanda zai rainani, a qauyen mu nice gwana, nice yar gayu, nice kowa yakeso, kuma duk albarkacin yayanane, yanzu haka da na shigo cikin birni duk yan matan da na riqa hangowa a mota, ba ko wacce na gani da irin tufafinaba, sai daidaiku, cox yaya yayi ta fadamin tufafin da yake min ai na manyan matane dinkin ma haka, tufafina masu tsada na yayan masu kudi amma shine zan yiwa butulci irin wannan gaskiya dole in........, ASHE KAINE MIJINA 7  Na HAUWA M. JABO Dole in bashi haquri, na dan faki ido na kalleshi, sai ya qara bani tausayi,matuqa narasa irin halina, tun bayan rasuwar mahaifin mu munsha wahalar duniya, wanda daga baya yaya yana karatu yana bin motar daukar kayan gwari irinsu ayaba da lemo da mangoro, duk dai wani fruits da ake yayi, haka zasu loda cikin mota idan sun isa gari sai su sauke, ana biyansu, kuma ahakan yake karatu yana wannan sana'ar har ya qare secondary anan mai gari ya dauki nauyinsa da yake mai qarin mu abokin marigayi babane, ya dauki nauyinsa yaje dan fodiyyo sok anan yayi dgr na farko yana kammalawa ya fara karantar wa a sokoto cement primary anan dai ya sami kudin shiga Sosai har ya ci gaba da karatunsa, duk albashinsa akan mu yake qarewa sabida yaya mutum ne mai zuciyan yi kuma yanada son fitarda kanshi dama wani nashi kunya shi isa tun yana qarami da yake dako kayan kwalliya ina dasu komai yana siyamin har na tasa nadan girma, kuma sam bashida qyashi duk abinda ya samu inna da naxia, Mu biyu muke a gurin mahaifin mu ni da yaya, mahaifin mu ma'aikacin prison ne yana gadi a sokoto prison a wani rikici da akayi a gidan yari aka harbeshi anan Allah ya karbi ranshi, tun daganan muka dawo qauyen mahaifiyata da zama tun ina shan nono ataqaice dai bansan mahaifinaba..... ASHE KAINE MIJINA 8 Na HAUWA M. JABO Bansan mahaifinaba sai yaya da inna stakanina da yaya shekara takwas ne, sabida inna tace har ta daina tunanin haihuwa sai ta sami cikina ta haifeni, yaya na matuqar sona kamar shine babana, bansan wahalar rayuwaba sam, Ki fito mun iso naji ya fada cikin sassanyar murya, tausayinsa ya qara kamani, ban san lokacin da na masa murmushiba, amma sam fuskar sa bata kaina, gidan da na gani ya tsoratani, wani fakacecen gidane, da gate yaya ya bude, muka shiga, naga ikon Allah araina nace a cikin wannan gidan zamu zauna, sabida ko a mafarki ban taba ganina a iran wannan gidan ba, gidane bangare biyu ban gare daya an kammala ginin dayan banqaren kuma ba'a kammalaba amma wanchan bangaren da ba'a kammalaba yafi banqaren mu girma, muka shiga, muna shiga na tabbatar da yaya yamin gatan da yake fadar zai mini, naga so da qaunar da yace zai nuna mini, tabbas nayi sa'ar dan uwa, wasu hawaye suka sake zubomin, yaya ya shigo da kayan mu, ya nuna min dakina komai a tsare hattana kayan make up an saka min toilet dina sai wanda ya gani dakin inna ma haka komai tsab an gyara, sai dayan dakin da ya nuna mana na baqi, ya nuna ma inna kitchen da kayan abinci da komai a ciki duk da tana daure masa fuska yana mata bayanin komai nima yamin bayanin komai amma yaqi bari mu hada ido yayi waya ya........., ASHE KAINE MIJINA 9 Na HAUWA M. JABO. Yayi waya yace aturo yaron sun iso, almajiri ya nema mana wanda zai riqa mana cefane da sauransu, ya baiwa inna kudi kamar yanda ya saba sai kawai yace sai anjima ya fita, nida inna mukayi jugum jugum sabon gida sabuwar rayuwa, Lallai yaya ya cika min alqawarina, sabida ya kawo ni birni kamar yanda kullum nake cewa inason akawoni birni gurin mijina, yau gani a birni a birnin ma sokoto birnin shehu, gari mai kyau kuma gida mai kyau, in kalli inna ina tsoron in mata magana naga ta daure fuska, sai na tashi nashige dakina, nayita kalle kalle, komai a tsare kuma tsab dai dai da buqatar duk wani dan birni, hotona dana yaya da inna munyi kyau Sosai anyi babban frame dinsa an kafa a dakina, nayi kyau a hoton yarinta na a fuska qarara amma bai hana kyauna fitowa ba, yar qaramar fuskata das da manyan idanuwana das dasu, hmmm gaskiya nayi kyau a hoton, na zauna jigum, sai na fara tunanin qawayena na qauye fatima yarin yayar nura ce duk qauyen mu ita kadai tamu tazo da ita sabida itama yar gayuce iyayenta suna birni amma ita tana qauye abinta, nura shine wanda tun da mahaifiyata ta sami cikina yace idan mace aka haifa matarshice, hak kuwa akayi tunda aka haifeni ya ke sona ana cemin matar nura, mamanshi takance dani auta matar auta, tun inada shekara uku, ya koma birni gurin yayanshi baban fatima qawata ban qara ganinsa ba har yanzu da nakeda shekera 14 a duniya...., ASHE KAINE MIJINA.10�� Na HAUWA M. JABO Shekara14 A duniya, tun ina cewa a kaini birni gurin mijina har na daina da na fara wayo na fahimci ba sona yake ba, lamarin qauye ne kawai, gashi kuwa mahaifina yace bai yarda in auri wani idan bashiba, kuma kowa ya san ni matar nura ce, amma nura sam bai damu da harkataba, bai damu daniba, ko.qauye yaje gurin mamarshi baya kwana ranar da yaje ranar yake dawowa ban taba qaninsaba sai dai yakan yomin tsaraba tuli tuli, nida fatima, da alama ma iyayen fatimar ne suke min siyayyar, sabida komai iri dayane nida ita, shi isa shima yayana komai iri daya yake mana da ita, Allah sarki fatima ko Yaushe xamu qara haduwa gashi tace xata bani address din qanwar ta idan naxo birni muyi qawance amma naxo tna skull ina cikin wannan tunanin sai naji kiran inna natashi naje, kizo ki hada mana abinci idan kin iya nidai kam ban iya aiki da gas cooker ba, nace nima ban iyaba, nadauki a shana naje gurin da ake wancan ginin na tattaro itace na hura wuta na mana girki, muka danne abinmu,har lokacin fuskar inna a daure take narasa yanda xanyi in bata haquri sai bayan maqreeb yaya ya dawo yashigo da ledodi,dayar ledar tablet ce da kuma wayoyo guda biyu, ya bani tab din ya hadamin da wayar, da sim itama inna ya bata wayar ya nuna min yanda ake kunnawa da kashewa da Sauran abubuwan duk dai fuskar shi ba yabo ba fallasa amma yaqi bari mu hada ido yace zancen skull dinki gobe zan kaiki makarantar da zakiyi karatu sai kiganta dama anyi komai kaiki kawai xa'ayi....... ASHE KAINE MIJINA 11 Na HAUWA M. JABO Xa'ayi, naji dadi Sosai a raina da jin zancen makaranta sabida har nakai jss3 nayi jlc kawai aka shigo da zancen birni, yaya ya juyo gun inna ya sassauta murya, ya fara baiwa inna haquri abinda ya faru dazu da safe, inna tace ba komai nima nan na Sami dama na bashi haqurin rashin ta idon da na masa, dan uwa rabin jiki aka yafi juna muka dawo kamar yanda muke ada, farin cikina ya qaru ganin cewa yaya na da innata sun daina fushi dani, duk mun saki jiki kamar ba'abinda ya faru da safe har na bama da yaya labarin yanda mukayi girki, yasha dariya, qarshe yace za'asamo wa inna wacce zata tayata zama da aikace aikace tunda ni makaran zan riqa zuwa, dagyar dai inna ta amince da mai tayata zama, mun shiga kitchen yaya ya nuna min yanda ake amfani da komai, mukaje bayi yanuna min yanda ake komai da komai, munyi hira Sosai dashi daga bisani ya wuce dakinsa nima nabi inna dakinta dan nasan bazan iya kwana ni kadaiba, naje muka fara hira nida inna ta, acikin hirarta dai ta hada da wa'azi, ta qara jan hankalina akan zafin rai irin nawa, taja kunnena akan yanzu nashigo wata sabuwar rayuwa mutane daban komai daban so dole sai na san yanda zan riqa hulda da mutane, kuma ta ja min kunne daga yin mugayen qawaye, da kama kai kada in riqa shishigi ga wayanda suka fi qarfina, in kama mutuncina insan cewa ni ba kowa bace, ta qare muka dauko waya na nuna mata iya abinda na gane nasan kuma zata qane, ni kuma nahau daddana tawa ina qara fahimtar abubuwa, haka dai har bacci mai nauyi ya daukeni nabar inna tana......... ASHE KAINE MIJINA  Na HAUWA M. JABO Nabar inna tana ta kallon wayarta,dama tunda asuba yaya yace in shirya zai wuce aiki yanason ya kaini skull,din mu ai ko dan kada amaimata dan gidan jiya tun asuba ban koma bacci ba, bayan mun qare break fast muka dauki hanyan makarantar da za'akaini, tun daga nesa na hango hadaddun motoci suna sauke yaransu, nasan cewa wannan skull din ta well to do ce, araina nace yaya ya kawoni gurin yayan masu kudi, tun bamu isa admn block ba na ba na fahimci wasu yara yan mata suna ta kallona suna dariya, araina nace ko dai sun gane cewa daga qauye nake, haka na fuske abina,sabida nasan banida munin da za'amin dariya, haka ni bana tafiya bazar bazar " kamar zainb khalifa princesszee" bare ince na kwafsa, to dai haka har muka iso admn block ina tunane tunane, matsalar farko dana fuskanta rashin iya speak da English , ina gane duk abinda ake fada amma bana iya bada amsa, shima dai da ni daqiqiyace da dan karatun qauye ba abinda xan iya yaya ya bada C. A dina daya karbo a qauyenmu, akamin interview dagyar dai suka aminta na zauna jss3 maimakon ss1 da zanje, shima jss3 din saida yaya ya dage dan jss1 sukaso su kaini tunda bana iya magana da English, admn off ya kira wana yarinya yace ta nunamin clss dinmu, ta kuwa nunamin nashiga nayi sallama da yaya, na wuce clss Lallai sabuwar rayuwa da mutane kala kala, abinda yafi bani haushi kallona da suke suna dariya na qare musu kallo kaf ba wacce takaini ko kyau bare ........ ASHE KAINE MIJINA.13 Na HAUWA M. JABO. Takaini kyau bare suce ni mummunace, Lokaci daya naji na tsanesu dukan su na tsani rayuwar birni ma, ina tsoron in musu magana akan dariyar da suke min in gudun su faramin turancin iskanci dan na kula ba wanda yake Hausa cikin su, haka na kama mutuncina, na zauna a clss din a quntace ba dadin rai har aka tashi break fast, sai yanzu na tuna yaya bai bani ko gwandalaba, Kuma gashi banzo da wayataba, haka dai na zauna idona sukayi rau rau, kamar zanyi kuka, ina zaune ni kadai wata yarinya tashigo ga dukkan alamu na girmeta, sister bissimillah ko, nidan bansan miye takeshaba dan yaya baitaba kawo mana irin abin ba, nayi murmushin dole, no na gode, tayi dariya ai wallahi saikinci, ta bani dariya yanayin rigimarta kamar fatimata ta qauye,kuma ga kama da sukayi da fatimar nace aah ina azumine da yake yau Monday da mizai hana in siyo nima inci, ta kwashe da dariya, nadauka ta gane qaryar dana sharamatane, ta kalleni kice dai qawar tawa malamace, araina nace yaushe na zama qawarki haduwar minti biyu, ta kalkeni sunan khadija, Muhammad, ana kirana da sista kd, amma fili na maimata sunanta sista kd, tace of course, ko sunan ba dadine, nayi murmushi araina nace kada ta faramin turancin banxa,Aah da dadi mana inason in zabi wanda zan kiraki dashine, tayi murmushi da yake ta cika baki da cake, ke ya sunanki, sunana nazia Muhammad, itama ta mimaita sunan, yadai, no kamar na tabajin sunan ne a wani guri amma na manta, nikuma araina nace nikam a gurin fatima ce naji sunan ki sista kd , nice to meat you, nace thanks, na kasa daurewa nace nihal dan Allah miyasa tunda naxo sukemin dariyane? Itama tayi dariya tace sabida kin....... ASHE KAINE MIJINA 14 Na HAUWA M. JABO. Sabida kin saka sababbin kaya baki musu iron ba, kinsan fa yanzu an waye an ci gaba, ba yanda za'ayi ka saka sababbin kaya baka musu iron ba, ana ganinka za'agane kuma sai a maka dariya, shi isa kikaga suna dariya, amma kada ki damu gobe idan zakizo sai koyi qoqari kiyi iron din uniform dinki kamin kizo, araina nace da yake su yan birni yan iskane ba dole suma mara iron dariya, a fili nayi murmushi, na kalli kayana na tabbatar da cewa da gani an san sababbine, sai na fuske, na basar da maganar, munanan har yara suka dawo break, malami ya shigo aka gaidashi anan yake tambayata ni baquwace nace eh, sauran yan clss sai dariya sukemin, araina nace wato rainin wayon hadda malamai akeyinsa, tun lokacin nayi marking din S/S master, hadda shi a yiwa students rainin wayo, haka dai har aka tashi makaranta zuciya ta cike da qunci da tsanar birni da mutanen birni, bayan an tashima saida naga tasku, sabida kowa anzo an daukeshi, wasu kuma skull bus take kaisu, ni kuwa bansan ko inaba bare inje kuma bansan kowaba, haka na zauna jikin gate har 3:30 sannan yaya yazo ya daukeni, sister ya karatun dai? Ya naga fuskarki ba annuri ko skull din bata miki ba,?? Na turo baki wallahi yaya ba skull din bace students dinne basuda kirki, hakafa duk inda na wuce sunamin dariya, wai banyi iron ba shima ya kalleni ya kwashe da dariya, au hadda kai yaya!?? to ke sister ai dole a miki dariya kin saka kaya haka kamar..... ASHE KAINE MIJINA 15 Na HAUWA M. JABO Kamar wata zainb khalife ba tsari ba komai, ban san lokacin da na qyalqyale da dariyaba, wallahi yaya ka raina zainb khalifa, kuma ita ganin kanta takeyi wayayyiya tunda ta zauna qasar waje,har ma yanda takejin da yaruka kala kala.... ki barta shirmen banza takeyi, ni haushi take bani, kinsan yanzu wani abokina takeso,? Na gyalgyale da dariya, wallahi yaya duk sai na gayawa gwagwo sharrin da kake yiwa yarta, ya harareni, kefa matsalar ki kenan yanzu sai kije ki fada,? Sosai kuwa sai in fada mata kana tsinar mata ya, to ai abokiyar wasan muce, gwago ba abinda zatayi, heheheee, Kullum da haka kake fakewa kana zagar mata ya. Da hirar zainb khalifa "presenceszee" muka iso gida, ina abincina yunwa nakeji, yaya yayi salati, sorry sister Wallahi sam na manta ban baki kudin break ba, mi kikaci,? Nayi mumushi.! Banci komai ba hasali ma da wata sis kadee ta min tayi cewa nayi azumi nakeyi, Yaya ya zagayo ya dafa kaina, kiyi haquri sister Allah namanta sam.! Laa yaya ba komai fa, ai nasan mantawa kayi idan ba mantuwa ba ba yanda zaka barni da yunwa, yauwa kici abinci ki huta anjima zamu je day to day shopping, idan kin kammala ki kirani...... ASHE KAINE MIJINA.16 Na HAUWA M.JABO Kammala ki kirani a waya sai muje ko, Ina qoqarin dura lomar a bakina nace mishi to yaya, ya wuce, nici gaba da chin abincina ina baiwa innata labarin rashin kirkin yan makarantamu, da kuma qawar da nayi sis khadee, da kuma tsinar da yaya ya riqa yiwa Zainb khalifa a mota, inna itama dariya tamun, ai sai na hada yayanki aure da zainb khalifa muga qarshe tsiya, na kyalkyale da dariya, wallahi kema kinsan inna zakisa kawai ya qara tsanartane, dama haushinta yakeji, Allah sarki zainb nifa bana ganin abinda yaya yake cewa tana dashi, kawai tanada dan Rawan kaine, inna tace nidai ba ruwana,nayi murmushi, muna chin abinci muna hira har na kammala, inna bari inje in danyi bacci, inna ki tayar dani 4:30 pls, to Allah yakaimu, Kamin biyar dagani har yaya mun gama shiryawa, har munshiga mota muka dauki hanya sai DAY TO DAY, gurin ya hadu Sosai, super market ne hade da restaurant da kuma park a gurin, nidai kam fuskewa nayi kada a gane sabon shigace ni,amma Lallai gurin ya burgeni matuqa na sha magani ga shigar da nayi nasan qaryar yan birni Su nunan dressing, ina tsosta minti na a hankali, irin nima yar birnin nan dan na kula birni yan rainin wayone Sai Su nemi Su min dariya wannan karon kuwa na shirya chin uban Su, "ni jabo araina nace kaji naziah da zuwa birni Sai xancen cin uba" ....... ASHE KAINE MIJINA 17  Na HAUWA M. JABO. Munshiga day to day, munyi shopping, kayan make up, ba qara kwasowa da turaruka kala kala da Su chocolate ba abinda bai siyamin ba, muna fitowa cikin ikon Allah na hadu da Sis khadee sunzo siyayyah,itada wani hand some guy, araina nace kar dai Saurayinta ne, dan yanayin yanda naga yana bata kulawa ko motsi tayi a kan idon sa sai kuma Suka burgeni, naziah wannan shine ammar shi xan aura Insha Allah, ta wani lumshe ido ta kalle shi, shi ko wawan Sai murmushi yake, tace wannan fa ko dai shine angon namu,tuni yaya ya daure fuska, na kalli yaya naga yasha magani no yayane fa....!! Ta dan sosa kai irin taji kunyar nan, ta gaida yaya na gaya ma yaya itace wacce ta min mutunci suka gaisa da yaya, yadan saki rai, mu dan kebe da ita ke mutuniyar ai na dauka wannan kamu kikayi guy haka har guy, uhummm kina tare da ammar dinki kina kallon wani, tayi dariya aike ba'a tsayawa guri daya ne, har na fara joules naga saurayinki xaifi my ammar, mita gani kuma tace kai ammar dina fa qarkene araina nace wannan yarinya da saurin sabo take, muka danyi tadi muka sha ice cream tare daga baya mukayi sallama muka wuce, muka dawo gida cike da farinciki..... Kwanaki sun shude, watanni sun haura shekaru sun jaa qaba, nida sis khadee mun zama daya, mun zama qawayen juna, fiye da tunanin mutum dan kuwa komin ta yayi kama dana fatima na, mun zama abinda muka zama a skull,amma nafita wayo, duk wani neman magana ni nake turata tanayi amma ita bata ganewa kuma bata ganeba, idan akazo in fuske a mata bulalarta, koda tace ni na turata ba wanda yake yarda sabida kowa yana min kallon waliyiya dan ba mai ganin koda murmushi na bayan ita... Duk wannan shaquwar tamu da nihal kusan shekara biyu amma tunda nake sau daya na taba zuwa gidansu, sabida yaya baya bari, hattana qawaye baya bari inayi barkatai, bare zancen samari, Nihal ta roqi yaya da kanta, akan ya barni inje gidansu, haka kuwa akayi yaya ya barni amma bazai kainiba sai dai in shiga motar kasuwa sabida yana da aiki sosai a office, ban damuba coz inason fita, na shirya tsab na musu tsaraba, na nemi motarda zata kaini unguwarsu, saida na fito na fuskanci garin akwai hadari sosai, na sami mota na shiga sai unguwarsu nihal, kofar rini...... ASHE KAINE MIJINA.18  Na HAUWA M. JABO. Unguwar su sis khadee kofar rini, ina isowa unguwar hadari ya fara tasowa tare da iska, duk wanda yasan hadarin Sokoto yasan yanda yake da iska mai hade da qasa a ciki, idona suka cika da qasa, har bana ganin gabana sosai, unguwar ba kowa, tayi shiru sai qarar itace da suke kadawa kakeji, kowa ya shige gidansa, iska akeyi sam bana ganin gabana, sai samun kaina nayi cikin qaton ramin kwata tsundum, Subahanallahi..... na fara swimming a kwata,mai uban wari ga kaina da ya bugu, haba ga ruwan sama an farayi kuma da qarfi, na tabbatar da idan ruwannan sukafi haka qarfi wucewa zasuyi dani, na tabbatarda kuma mutuwa ta tazo, dagyar Allah ya taimakeni na fito ramin nan, ruwa kamar da bakin gwarya, na fito amma na baro jakata jikin kwata, kuma gashi tace idan na iso in kirata, dan ban gane kwatancen da tamini ba gashi wayar na cikin jaka, jaka kuma na cikin kwata, sai qaqa....!! ga ciwon kai buguwar da nayi, nasan ba taxin da zata daukeni haka dame dame da kwata in bata mishi mota, nasan ko na sami mota banida ko kwandala, haka naja jiki na rabe jikin gate din wani gida, ina tsaye sai ga wata mota tazo music ne yake tashi sosai, saida suka iso kusa dani suka tsaya suka kwashe da dariya, nadago na kallesu, bance komai ba ba bakin musu tsiya, sukayi horn aka bude musu suka shiga gidan, araina nace dole in bar nan gurin Dan yaran gidannan da alama basuda kirki dagani yan iskane, na duba gabas da yamma ba mafaka sai nan, sai kawai na haqura har a qare ruwan kunyar duniya ta isheni, jikina duk kwata, ga ciwon kai ya tsananta har na kasa tsayuwa na tsuguna, ruwa yaqi zaqaitawa sai...... ASHE KAINE MIJINA 19  Na HAUWA M. JABO. Yaqi tsaqaitawa Sai na yanke shawarar bari in daure in dan shiga ruwannan idan kwatar jikina ta wanke, my be zan samun abin hawa, na miqe kenan kawai sai jiri ya kwasheni na fadi a gurin sumammiya, kaina ya qara bugun gate din gidan,kikaji gwall, maigadi ya fito ya ganni a hakan ya shiga ya kira matar sa aka taimaka masa ya shigo dani daga ciki, shida matarshi suka taimakamin har na farfado na dawo hayyacina, amma bana gane komai kuma ban san inda nake ba, matar ta ciremin kayan kwata ta daurayemin jikina ta saka min wasu tsummakaronta,ta bani dan paracetamol da panadol na kora, bayan kamar awa biyu na fara farfadowa, na gane inda nake, suka tambayeni sunana da komai na musu bayani, muna cikin magana najiyo muryar sis da wani namiji a waje Uncle wallahi tun kamin afara ruwa tacemin ta fito, gida, kuma batasan nan gidan ba, na kira wayanta yafi sau dubu baya shiga, kataimakeni dan allah uncle, kinsan Allah, wallahi ba inda zani gwanda ma ki haqura ki kama kanki ke idan ma kika qara min maganar wata anan sai na babbalaki.... Tabbas muryar nihal ce kuma ni take nema, nace ma matar maigadi, gurin waccan yarinyar nazo, tanajin haka tayi wuf ta tashi, ta qwala mata kira.. sis khadee.! Sis khade!! Ko ta waigo ta wuce abinta, sista khadi kizo ga nazia anan, ba shiri ta waigo ba shiri ina take rabi??..... ASHE KAINE MIJINA 20 Na HAUWA M. JABO Ina take rabi!!!??? Gatachan dakina, mi takeyi a dakin ki kuma da gudu ta qarasa, tana ganina ta rungumeni, duk da warin kwatar bai saki gashinaba, amma haka ta rungumeni tana kuka,kin bani wahala naziah, ta janyo hannuna muka shiga daga cikin gidansu, dagyar nake tafiya, ga sanyin da nakeji, mun shiga gidan kenan, bamu kai parlour ba naji murya daga baya ke ina kika samo wannan almajirar?? Sis khade dai kam ko waigowa batayiba bare ta bashi amsa,! Yaci gaba da magane, ke badake nakeba, wallahi idan nazo gurinnan sai na babballaki, haba uncle ba girmankabane wannan abin da kakeyi, da talaka da mai kudi duk Allah yayisu,kuma ai wannan naziah dina ce fa.!! Kece naxoon taki almajirace amma kuma akwai diri, dayake duk kayan sun manne min a jiki shape dina ya fito, najuyo na kallashe, fitsarar ta motsa na kalleshi daga sama har qasa na zubar, na hada da tsaki, sis khadee ta kalleni, haba nazia, qanin abbanmunefa, na fuske ko qanin abbankune ai baisan darajar mutaneba, koma miye ai uncle dinane, kamin ta rufe baki tuni naji saukar mari a fuskarta kamin in ga waye nima ya kwasheni da nawa marin guda biyu lafiyayyu, saida na gigice,Cowon kai ya qaru na bude ido naganshi gabana tsaye, kuuuut idan na barshi Lallai ya daki banxa, nima nasa hannu na kwasheshi da irin nashi marin guda biyu lafiyayyu....... ASHE KAINE MIJINA..21 Na HAUWA M. JABO. Mamaki ya kama sista khade, taga yanda na mari ganin mahaifinta, wanda yake ji da ita, kuma a gabanta a gidansu.!! Lallai koda uncle ne bahida gaskiya dole ta nuna ma naziah kuskurenta dan gaba...!! Sista khade ta kalli nazia tace, ke dama yar akuyace??? Wacce batasan darajar na gaba da itaba?? Wallahi da nasan ke butuluce da bazan taba qawance da yar qauye irinkiba.!! Mamakin duniya ya cika nazia dama haka sista khade take mara mutunci to ba gyaleta zanyiba, wata zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikaxo, sista khadee sai masifa takeyi, inda take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufe naziah uncle yayi Sokoko yana saqa Wulaqancin da xai mata, ni kuma ga mugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi inaji ga yunwa, na dunqule hannu nakaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na kamata da duka baki, sai jini, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon wai almajirace zata mishi wannan wulaqanci yana chi gaba da saqa sharrin da zai mata kuma yasa a ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya hanbare ni a wurgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun shogo na samu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin kwata gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga taxi, ina tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace ina zuwa na fada mishi unguwarmu tuni ya bude min nashiga........ ASHE KAINE MIJINA. 22 Na HAUWA M. JABO. ya bude min nashiga, ina shiga motar ban qara sanin inda nakeba, suma nayi mi nayi Allah masani, sai farkawa nayi na ganni a wani makeken gado an saka min ruwa, na bude ido a hankali, na jujjuyasu bansan inane nan ba, nayi qoqarin tashi amma nakasa tashi kaina yayi nauyi, naduba sai naga ashe ruwa ake qaramin, iya tunanina gidan su sista khadee ne tunda daga chan nafito, my be faduwa nayi aka maidani chan.! Kawai sai na daure fuska dan kuwa banason ganinsu. Banason taimakonsu, banason duk wani abu daya shafesu, ina kwance sai ga wani saurayi gajere fari ya shigo, ina ganinsa, na fara surutai, miyasa kuka maidani gidanku, miya dameku da lafiyata da ciwona?? Kumaidani gaidanmu banason ganinku ko kadan, haka nayita surutai ina qoqarin cire drop dinda aka sakamin sai naji ya riqe hannuna, na daga ido na kalleshi baice min komai ba saima bina da ido da yayi ina balaee na, naso in ci gaba sai kuma na fasa sabida kaina yayi nauyi Sosai ihun da nayi.. namaida kaina, na rufe idona, bacci mai nauyi ya qara daukeni banfarka ba sai tsakiyar dare, abin mamaki......... ASHE KAINE MIJINA.23 Na HAUWA M JABO. Abin mamaki gajerin qaton da na gani daxu shine na gani kwance a gefena yana sharar bacci abinshi, dayake qadon qatone Sosai, kuSan gadon ya cika dakin, har yasa ko gurin sallah babu, na tashi ina dube dube ga dukkan alama nan dakin mazane, amma sista khade ta cuceni maimakon ta kaini dakinta sai ta ijiyeni anan? Dakin uncle dinta Wallahi nida ita har abada ta xubar min da mutunci yanxu idan yaya da inna suka ji na kwana daki daya da qato mi xasu kalleni,.....!!?? N qare tunane tunane da bala'eena cikin xuciya, nayi niyyar in tayar dashi ya kaini gida amma kuma na fasa, na dago kaina na hango qofa biyu naje a hankali na murda daya najita gam a kulle na murda ta gefenta sai ta bude na leqa sai naga ashe toilet ne, ko nayi wanka bnida tufafin sakawa gwanda in haqura nayi fitsari nafito, raina duk a bace, ina dubawa naga ledar DAY TO DAY, kuma ledar ta clothes ce sai na buda ina dubawa naga tufafi da brush da duk abin buqatar mace hadda pad ko sista khadee dan uban tace mishi bana sallah ohon mata!!!?? Na dauki ledar na shiga bayi na kulle nayi wanka da yake kaina adaure yake, amma dai gashina anyi sama dashi hakan ya bani damar wanke gashina tsab, nayi wanka kamar ban taba wankaba, ga ruwan da zafi Sosai, duk sanyi da kasalar da suka rage naji sun tafi, nayi brush, amma yunwa ta addabeni, na saka kayan top ne da jeans, nafito kamar baniba, amma zuciyata cike da haushin su sista khadee, ina fitowa naji ana kiran sallah, na tuna inna tace kada inkai maqreeb....... ASHE KAINE MIJINA.24 Na HAUWA M. JABO. Kada inkai maqreeb, naje na tayarda wannan gajeren yana wani mutsuke ido, mlm ka tashi kaje ka kira sista khade akaini gidan mu ko a budemin qofa inje gida... na fada cike da qadara, wani kallo yakemin, kallon baisan alqiblar maganataba, kallon mi kike nufi??, ya tashi zaune, amma kya bari gari ya waye sannan akaiki gida ko,?? wane gari zan bari ya waye? Yace Bakiji ana sallar asuba bane??Asuba!?? Dama asubace ba maqreeb ba?? Kuka ya kubucemini ba tare da nasaniba, miyasa sista khadee tamun hakane? Miyasa zata bari ihar in kwana gidansu kuma ta ijiyeni a dakin uncle dinta?? Lallai khadija ba qawar kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na kalli mutumin nan,na rasa irin rashin kunyar da xan surfa mai, kawai, nace uncle to sista khadee ta gayawa inna da yaya ina gidansune??, sabida inna tace kada in kai maqreeb gashi har gari ya kusa wayewa?? Yayi kasake yana kallona, kayi magana mana uncle, yaji dadin sunan data kirashi dashi, har yana maimaitawa a fili uncle.!!! amma kuma shi wacce sista khadee ce take fada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sista khadee ba wannan rudaddiyar zata daga mishi hankali fiye da na yanxu, amma zai lallabata har gari ya waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki zauna in miki bayani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin ya fadi sunan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin umurninsa, na zauna girmn kai ba nawa bane na xauna.,........ ASHE KAINE MIJINA 25 Na HAUWA M. JABO. Na zauna, kiyi haquri zuwa wayewar gari zan gaya miki komai, kinji? na daga kai alamar shkenan ba komai, na zauna jigun, chan natuna banyi sallar ko azzahar bare magreeb gashi har an kira asuba, na miqe naje na dauro alwula nazo nayi sallolin da suka hau kaina bayan na kammala nayi sallar asuba nayi addu'a Allah ya fitar dani wannan qangi da sista khadee ta jefani, ya tsareni da sharrin uncle dinta,! Anan zaune bacci yayi awon gaba dani ban farkaba sai guraren tara na safee, ina farkawa na duba bashi ba labarinshi, na tashi na murda qofa najita kulle gam, ga BF nan an hadamini an ijiye mini, wasu zafafan hawaye suka gangaro a kumatuna Lallai sista khadee ta cika yar iska! Wato haka zata min ko? Ba wata mafita illa in danne abincina in barwa Allah ko na mutu in tafi ciki da nauyi.!! A bangaren iyayen nazia kuwa tunda inna taga an kira maqreeb bata dawo ba ta kira wayar nazia, tana ringing amma ba'adauka, tayi ta kira har ta qufula ta daina kira ta dauki alwashin idan ta dawo zata gane kurenta, shiru nazia har qarfe goma bata dawoba, sai hankalin inna ya fara tashi, ta dauki waya kena zata kira yaya hafeez sai gashi yazo, kasan fa har yanzu nazia bata dawo ba!??, haba dai,? Allah kuwa! Kuma nayita kiranta bansametaba, to baki kira qawar tataba? Eh ban kiraba, to bari in kirata. Saida ya kira sau uku ana hudu aka daga, batayi maganaba shi ya fara sallama aka amsa mishi sama sama, yanxu inna take gayam nazia har yanzu bata dawoba! Kuma tace gidan ku xataje kamar yanda kika roqa na amince ta tafi, tace Nazia kuma?? Ai batazo nan ba!! What???....... ASHE KAINE MIJINA.26 Na HAUWA M. JABO. What..!!!?? Eh batazo ba nace, ai kuwa tun safee tafito gida tace zatazo gidanku, kamar yanda kika buqata inna ta barta tazo, hmmm to kuwa banan tazoba, sai ku kira wayarta kuji ina yarku take.! Ban..... yaji ta katse waya bata ma saurari abinda zai ce mataba, ya juyo yayiwa inna bayanin abinda khadijar ta fada hankalinsu duk ya tashi, suka fito aka fara chigiya unguwa unguwa har kofar rini unguwar su sista khadee saida akaje nemanta, amma bata ba labarinta, gashi dare yayi, haka suka kwana zaune, ga wayarta na ringing amma ba'adauka guraren asuba ma wayar saita daina ringing hankali ya qara tashi, tunda asuba yaya ya koma police station aka kai hotonta ana cigiyarta, aka kai gidan tv gidan radio jarida duk aka baza ana nemanta, amma har guraren 12 na rana ba ko karenda yace ya ganta, Tana zaune ta tanqware gafafu, taji ana murda qofa, tuni ta miqe tsaye tana jiran shigowarsa, yana kunno kai dakin da sallamarsa da murmushin sister har kin..... sai saukar mari yaji a fuskarshi, kai mahaukacin inane da xaku kawo gidan maxa ku ijiye, idan ita khadijar yar iska ce to ni ba yar ita bace kuma ka gaggauta maidani gidn mu...!!! ya dago da sauri ya kalleta, ya daga hannu zai mareta kome ya tuna kawai ya sauke hannunsa,ya dunqule hannu rai bace ya mata wani kallo ya wurga ledar da ya shigo da ita ya ja qofa ya kulle ya tafi abinshi, sai tafara dana sanin hukuncin da ta mishi, tafara Allah wadai da zuciyarta,da kuma rashin kunya irin tata, miyasa ta mishi haka?? Lallai bata kyauta ba gashi ya tafi ya barta,jiya ta mare shi yauma ta mare Shi, itako haka xata qare da dukan maxa..!!!!? qeqe idonta ba kuka ba alamunsu ta miqe ta janyo ledar Abincine take away guda biyu komai dai guda biyu, da alama da nashi da nata dasu drink da ice cream duk a ciki, ta bude ta sa abincin gaba amma ta kasa chi tayi tagumi ta tashi tayi sallah azzahar tananan zaune har la'asar tayi sallah taga cikinta ya fara ihu, ta janyo abincin taci ta qoshi,a haka bacci yayi awon gaba da ita....... ASHE KAINE MIJINA..27 Na HAUWA M. JABO. Gaba da ita har dare yayi bashi ba labarinsa guraren sha biyu ta dauko abincin dazu, dayan da ya rage ta chinye, shiru shiru har bacci ya dauketa bata farka ba sai guraren biyar, bashi ba labarinsa, amma kuma ya ijiye mata ledar BF. hakadai wasa wasa har saida Nazia tayi kwana hudu a gidannan bata qara ganin saba, kuma kamar aljani sai tayi bacci yake kawo mata abinci abin yana daure mata kai, yau ta dauki alwashin bata ba barci, har kusan maqreeb ba'a kawo mata abinci ba, data gaji da jira sai ta dan gyangyada baccin da tashinta duka minti hudune amma har ya kawo abinci ya fice abnshi, tunani kala kala takeyi, ta fara tunanin ko ta daina cin abinci ne, wata xuciyar tace ki danne abinki ko kin mutu kije da nauyi.. Duk tayi wani iri da ita ammafa bata rameba ko kadan dan kuwa bata wasa da abinci saidai akwai alamar tashin hankali tare da ita, Iyaye anyi sanarwa har an gaji bata ba labarinta, anje gun malamai suna ta addu'a anata sauke qur'anai Allah ya bayyanata amma shiru.. sister khadee kuwa bata ma san cewa har yanzu ba'aga nazia ba, hankalinta kwance tana al amarrunta, ko a skull da andauko zancenta sai tabar gurin batason zancen, bata San xancen batanta akeyiba, su kuma sauran sun dauka haushin rashin qawane yakesa bata zama cikin mutane musamman da ake cewa garin zuwa gidansu ta bata.. Yaudai baxanyi bacci ba sai naga aljanin da ke ijiyemin abinci,baccin qarya nayi ya dauka nayi bacci ko minti uku ba'ayiba naji ana buda qofa a hankali bayan ya bude sai kuma ya tsaya kamar bayan minti daya sai aka turo qofa ina jin ya turo qofa nayi zubur na miqe dama akan dadduma nayi baccin gefen qofane........ ASHE KAINE MIJINA..28⃣ Na HAUWA M. JABO. Qofane, yana Shigowa na miqe dan Allah uncle kayi haquri.!!! da abinda na maka dan Allah ka kaini gida, aranshi yace dama batayi bacci ba??. Ya tsaya bakin qofa ya toge, ina tsoron in shigo ki mareni! Ko ki dakeni dan nakula bakida lafiya!! Naji xafin maganar amma na Shanye yaci gaba idan haukar taki baxata motsaba in shigo, kuuuuut dan na mareShi xaicemin mahau kaciya, na daqo na kalle shi namai kallon raini har na hada baqar maganar da xan yaba mai, kawai na sunkuyar dakai kayi haquri uncle..... Yashigo dakin ya zauna, ya kalleta ashe ganin da yake mata a camera ba haka bane duk ta firgice a camera kuwa yana ganinta kaman lafiya lau, Yana xama ta fara jero mai tambaya... Miyasa ka ijiye ni anan?? Mi kakeso in maka?? Baka tsoron Allah ne?? Ko kai ba musulmi bane?? Baka tunanin halinda iyayena zasu shiga?? Is ok.... ya katseta, da daga mata hannu kansa na kallon qefe, ta dago ta kalleshi, ki natsu kiji mi zan gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada kiyi magana sai na qare, kinajina? Eh naji!! Ya juyo ya kalleta tausayinta da yanda ta bashi amsa ya kamashi , lokaci daya sonta da sha'awar kusantarta ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi ta wani mishikyau, tufafin sa ne a jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da kai, ya miqe tsaye idan har ya kuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi niyar keta mata mutunci ladar mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye shi, ya miqe anjima zan miki bayani, zatayi magana, mi nace miki?? Ta tuna yace kada tayi magana, ta kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji tsoro, ya fita, mamaki ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi sallar tana nan zaune sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya zaune ya juya mata baya..... ASHE KAINE MIJINA??29 Na HAUWA M.JABO. Ya juya mata baya, yafara da cewa ranar assabar na dawo daga kasuwa sai naga kamar kina neman taxi, sai na tsaya in rage miki hanya dan unguwar nasan ba'acika samun taxiba, abinda ya bani mamaki yanda idonki ya rufe kika kasa banbance motana da taxi, dan ni ba dan taxi bane,har kina gayamin address dinki, bawai nagane bane nayi niyyar idan naje unguwar naku sai ki nuna mini guri in saukeki... bayan mun isa unguwarku na miki magana nace mun kawo naji shiru ina ta magana kikayi shiru nadauka gyaleni kikayi nayi magana har na gaji sai kawai najuya kan motana na wuce gida nakai saqon baba.... Mun kama hanyar gidana in dauko wani abu bayan na iso nan sai na qara miki magana shiru,ba motsi na tabaki naji bakya nunfashi, hankakina ya tashi matuqa, tsoro da fargabar idan kin mutu yaxanyi dake ya kamani..!!! a haka na daukokoki na kawo ki dakina batare da na bari kowa ya ganki ba, dama ni Dr ne, na miki treatment, na qara miki ruwa har zuwa lokacin da kika farfado kika fara xagina,to kinji ataqaice yanda akayi na samoki, ni banida alaqa da wata sister khadee hasalima ko sunan ban tabajiba, kuma xan gaya miki Gaskiyar magana sonki nakeyi,taji wani dummm... aranta tace idan dai xaka kaini gida mai sauqi ne, ya qara mata mata bayanin lahinda ya sami kanshi dazu na ganinta da yayi, kuma ya nuna mata cameran da yake ganinta idan zai kawo mata abinci dan bayason ganinta, tun ranar da ta mareshi kuma yayi alqawarin horata har na kwana bakwai yama yi nufin keta mata mutunchi Allahne ya kareta sai kuma Allah ya taimaketa, nan itama tabashi haquri rashin kunyar da ta mar da taimakon da ya mata, takuma hadamai da labarin abinda ya faru daga farko har qarshe, yayi mamakin irin zuciyanta da kuma yanda take iya dukan namiji, yaga marin da tayiwa unlce din sista khadee ne ya janyo mata haka, dadewar da tayi anan ma sanadin marin da ta mishine, yanxu dai kisharya inkaiki gurin inna.... ASHE KAINE MIJINA?? 30 Na HAUWA M. JABO.. Ki shirya inkaiki gurin inna, wani sanyi naji araina,nayi tsalle da ihu, inata dariya murna... "nima jabo na matsu inga yanda xata kaya gaba",tace ai ashirye nake, ya juyo ya kalleni karo na farko daya kalleni tunda ya shigo dakinnan, kin cire mini tufafina? Eh yanzu zan cire, shine kike cewa kin sharya? Murmushin da tayi ya qara daga mishi hankali, yasa kai idan kin shirya ina waje ki fito muje, yana fita na cire kayanshi na maida wayanda ya siyomin koda sunyi datti amma su na saka hakanan nafito na sameshi, abin mamaki gidan da nake qaton qaskene kuma part part ne ga mutane a ciki suna kai da kawo, a raina nace dana sani da na riqa dukan qofa tun Lokacin ai da xa'a jiyoni a bude min da yanzu na tsufa gida. Mun isa unguwar mu da misalin qarfe tara na yamma, na rangada sallama inna tana ganina ta fara salati Sai kawai ta fashe da kuka nima na fashe da kuka, tana kuka ina inayi tayi wa yaya waya ko minti biyar ba'ayiba ya iso, yana zuwa naje na rungumeshi ina kuka, araina nace ni ban rameba su suka rame, duk sai suka qara bani tausayi, nan aka fara tambayar ya akayi? Na koro musu bayani daga farko har qarshe, sun tausayamin kuma mamaki ya kama su, suka gayamin rashin mutuncin da sista khadee ta musu, anan dai wanda ya kawoni shima yayi bayani nashi, sai dai yayi qarya sabida ce musu yayi sai jiya da dare na farfado kuma yace tsoro yaji ganin lalacewar qasa kada yakaini gurin yan sanda ya janyo wa kanshi wani abin daban, to hakadai a ka jajantawa juna akayi waya qauye aka sanar dasu an ganni iyayen nura sunji dadi Sosai inna tace gobe sai ayi sadaka...... ASHE KAINE MIJINA?? 31 Na HAUWA M.JABO... Sai ayi sadaka tunda Allah ya mayar dani gida, yaya sai kallona yakeyi kamar wata baquwa na tashi naje na haye shi ina dariya sai naga uncle habeeb ya daure fuska na rasa dalili,anyi hira sosai inna tana bada labarin yanda yaya yayi shima yana bada labarin yanda tayi cikana kamar ya qulle dan dariya," nima jabo na dara��"munchi mun qoshi yaya yace sai na warware zan koma makaranta uncle habeeb dai ya qara gaba abinshi ya karbi number yy data inna..... Yy ya Siyo min siyomin sabuwar wayah da sabon sim, sabon gata da kulawa wajen inna da yaya ba'a magana, kusan kullum sai unle habeeb yazo gidan mu har dai ya shaqu da inna ya zama kamar dan gida tun da inna ta fahimci sona yakeyi kamin ma ya furta take bashi labarin nura kuma ta gaya mishi Lallai wasiyar mahaifinane in auri nura, baiji dadin rasani da yayiba hakan kuma baisa mun daina zumunci dashiba, amma ya rasa wani farin cikin sa, yan gidan su sun sammu muma munsansu har xumunci mukeyi....... Saida nayi wata biyu chur a gida sannan aka fara maganar komawata makaranta, yaya habeeb yace a chanzamin skull, haka kuwa akayi aka chanza skull, ban qara jin labarin sister khadee ba, Ranan munje bakin auren qanwar uncle habeeb nida inna muna dawowa a hanya mota tayi tsayinta na kunna na kunna taqi tashi munanan tsaye saiga wasu Guys sun wuce sai inna ta musu hannu har sun wuce Sosai sai suka dawo, da yake ina cikin motar ne, ki fito ga wasu yan samari nan na tsayar kinsan ba jin maganata zasuyiba, nafito suna zuwa suka fito motar su, sai dayan guyx din yace kace kamar kasan matar kuma kace tsohuwace, eh Wallahi kafa San yau tin safe nakejin faduwar gaba, qirjina sai dukan 3..3 yakeyi i don't know y!!! Yanxu ma Sai naji ya qaru, ita tsohuwar fa?? Share Ashe ba tsohuwa bace manyan kayace, suka kwashe da dariya, suna qoqarin tsallakowa, amma fa daga farko tsaHowar dana gani kamar na santa amma na manta inda nasan ta, any how tunda munzo mutaimaka musu kawai, inna dama tana ganin sun dawo ta ta shige mota abinta, abokin deen ya shiga motar yayi danne danne sai kawai motar ta tashi, tunda suka xo naji jikina ya chanxa na Kasa dago kai in kalle gefen da nakejin ana kallona, muje ko deen dayan abokin ya fada amma ina deen yayi Nisa,Na dago da gyar na kalle mai maganar nayi godiya zan zaga yace idan ba damuwa ki bamu number ki, murna kamar ta kashe deen, Lallai yayi dacen aboki da yake gane duk wata matsala tashi, na bashi number bada son raina ba dan kawai mutunchin da suka mana ne..... ASHE KAINE MIJINA?? 32 Na HAUWA M. JABO... Har ya juya xai tafi sai yaga bari dai yayi ta maxa yaji sunanta,.!! Ehem, am, inn, duk ya dabirce, dagyar ya iya furta kalma biyu M deen by name, what of u please?? , Na kalleshi a raina nace wannan kamar wani gaula daga kallon mutane kuma sai Kasa magana!! Nace bari in fada mar Sunan da inna tace babana yana kirana dashi, M hulwah, wawoo nice name, yamin wani murmushi bansan dalilin da yasa naji rass ba,nima na maida mai, owk hulwatiy sai kinjimu, yana murmushi yana sosa qeya kamar mara gaskiya, suka wuce nashiga mota inna tace da ace sun ganni ko taimakon ma bazasuyiba, na kyalkyale da daria wallahi inna akwi ki da zance akanme bazasu taimakamikiba,? To Sunga tsohuwa, Haka mukayi ta hira har muka isa gida, muna isa naji saqo a whtasapp, na duba naga sabuwar number kawai sai nayi blocking din number, dan Banason shirme, kuma nasan ban bama kowa number naba, sam na manta da na hadu da wani wai shi deen har na bashi number, sai da dare na kwanta bacci amma ina bacci yaqi zuwa, sai juyi nake, karo na farko a tarihin rayuwata da na taba tsayawa tunanin Wani namiji, sai karanto fuskarshi nake,murmushin da ya mun yake min gixo bacci yavqaura cemin, araina nace wallahi guy din ya hadu sosai, Nasami kaina da qara yin murmushi na janwo pillow na matse gamm!! lokaci daya na tuna an mini magana ta whatasapp my be ma shine nayi blocking dinsa ai kuwa dana chuchi kaina, na je neman phone din, na janyo ta qasan dadduma naga 8 miss call, na tabbatarda cewa shine, yayo sms hudu, na budeshi, Na duba number sai naga d Same number da aka kirani da ita aka mun magana ta whatasapp akamin sms, na bude nace salam, Kamar yana jira dama, ya fara surutuai... Haba hulwaty, ya zan kiraki kiki dauka kinsan kuwa abinda nakeji araina......??? ASHE KAINE MIJINA 33 Na HAUWA M.JABO Araina kuwa??? Hmmm! Let me call u, No ka barshi let us chat, Why my hulwah?? Coz dare yayi yanzu! Owk hulwaty, Hakadai yayi ta yimin kalaman soyayyah masu kashe jiki, duk abinda yaake fadar yana feeling nima ina feeling dinsa but ni na barwa chikinane dan banga amfanin yin haka ba tamkar na bada kainane ranar farko, sai hmmm, da owk da lol nake tura mishi, bai barni barni nayi bacci ba sai qarfe uku na dare ni kaina bansan lokacin yayiba, kuma banji bacciba, zan iya cewa nafada tarkon son deen, koda nasan cewa ni matar wani ce, abinda ya hanani kula samari kenan a rayuwata, amma wannan karon an sami akasi sabida dare daya deen ya sacemin zuciya, sonshi ya kamani,wanda nima jabo na hango hakan a fuskar naxoon inna.... Wasa wasa har na qare secondary skull, wanda yayi daidai da cikata shekara 18 kuma shekarar mu biyu tare da deen muna barza soyayyah dashi, amma ba wanda yasani a gidanmu, duk soyayyar da muke a waya mukeyinta ko kuma idan naje Shopping mu hadu mu hadu, amma ban taba gigin kawoshi gidan muba, dan nasan xanci ubanane gurin inna, yayi qorafi har ya gaji, amma ba abinda ya chanza, har cewa yake bana sonsa amma haka nake shanyewa.. Inaga ba wata halitta da ta tabason juna kamar yanda nida deen mukeson junan mu, kuma ayanda na fahimta deen dan duniya ne na qarke, yanason rayuwar duniya amma haduwar mu dashi komai yasha banban so dayawa abokinsa yakance dani, nayi jihadin da ko malm yakasa yin irinsa,..... ASHE KAINE MIJINA 3⃣4⃣ Na HAUWA M.JABO... Yakasa yin irinsa, na maida deen mutum, kamilalle nima na kula da haka, sabida deen yadaina wasu saka tufafi na mahaukata waishi swagger, wani Aski, duk ya daina, rashin kunya da Wulaqanta mutane duk ya ijiye su ya natsu Sosai, nima naji dadin haka... Waiiii, inna, yau Allah ya rabani da tashin asuba zuwa skull, na girma yanzu...�� Inna tayi dariya, ina fa ya rabaki dashi tunda idan kinyi aure dole ki tashi ki yiwa mijinki girki, kamin yaje aiki... Kamar ta dakamin guduma a qirji, na fuske inna ana aure ba miji?? Ba'ayi kam, to kingani ai sai na sami miji sannan zanyi aureko inna??, inna tace nuran fa?? Haba inna nura sona yakeyi??, nura damuwa yayi dani?? Ki duba fa shekaranmu uku hudu a garinnan bai taba kiranaba kuma kin tanbbatar da yana garinnan,hatta qauye idan yaje baya zuwa guna, sai kace mara gata haka xa'bashi ni kamar abar sadaka , ki kalla fa hadda ko batan da nayi sau daya yayi miki jaje, shima bayan Sati uku sannan ya kira, da ya damu dani da yazo ya dubani amma shiru ni gaskiya inna yanzu an daina wannan qauyanci auren hadi, auren qauye, nasan da ace baba yananan koshi bazai bari in aureshiba wallahi, yanzu fa ki duba inna ace t........ ke rufemin baki da shegen iyayin tsiyaa, ni zaki nunawa boko, wayewa taci ubanta! Wallahi ko kinqi ko kinso, sai kin auri nura, sabida marigayi yana cikin halin mutuwa saida ya jaddadamin kada in kuskura in raba aurennan matuqar ba shi nuran yace ya janyeba, to wallahi in gaya miki kinyi kadan kisa akalleni mutuniyar banzabaaa........!!! ASHE KAINE MIJINA??3⃣5⃣ Na HAUWA M.JABO... Banxaba gara ki rufawa kanki asiri ya fiye miki, dan ba chanxa wannan xancen xa'ayiba, na miqe traye ni wallahi inna banasonsa, de........ Taaaaaassss naji saukar mari kamin in bude idoin dawo hayyacina tuni inna ta miqe tsaye taci gaba da masifa,tunda nake ban taba ganin inna na rigima ba sai yau, ashe inna ma idan tayi fishi tana ja kamar dai yaya.... Wato shi yasa kikace sai kinje " unibarsit" to ba inda xaki boko ya qare, aure za'amiki cikin watannan, naga qarshen fitsara ta wuce ta barni danne da kumatu ina kuka.. Tabdijan...!! nifa a tunanina mutuwace kawai zata iya rabani da deen dina amma gashi lokaci daya, inna na neman ta tarwatsamin farin cikina,! tana neman ta jefani cikin qunci da baqin ciki da xullumi,! Wallahi da in rasa deen gwanda in rasa rayuwata, sabida shine rayuwata, ni kaina bansan irin son da nake masaba sai yanzu, sabida yanzune nakejin wata axaba araina, naji na shiga qunci, da damuwa!, inaji ina gani za'arabani da deen wallahi baxan yardaba, sam! Yaya yazo nakai kukana gareshi, dama shi yaya bayason nura sabida ya kula basona yakeba, amma ba abinda zaiyi illa ya bani haquri in bi umurnin mahaifana ni nazia ina zan saka kaina, na tashi sumai sumai na wuce daki naci gaba da kuka na ...... ASHE KAINE MIJINA 36⃣ Na HAUWA M.JABO.... Na wuce daki na kulle kaina ciki, na dauki waya na kira deen dina, ringing daya ya dauka, hello my hulwah.! Bansan Lokacin da wasu zafafan hawaye suka qanqarominva, tabbas saidai akasheni baxan iya rabuwa da deen ba, bazan iya rayuwa idan bashiba.! Hulwaty kinyi shiru, na kasa magana sai na kashe wayar ya kira sau uku a na hudu na daga, ina dauka na rushe masa da sabon kuka hankalinsa idan yayi dubu saida ya tashi na gaya masa aure za'amin a wannan watan, kukana ya qaru, yayi shiru, chan yafara magana muryarshi na rawa tana sassarqewa, damaa nasan ba sona kikeba,!! dama nasan yaudarata kike! Shi yasa kikaqi nunamin hatta gidanku.. tuntuni kinsan an miki miji miyasa kika koyamin qaunarki? Miyasa kika bari na shaqu dake? Miyasa kika bari saida nakai haka sannan zaki gaya min cewa an miki miji?? Kinsan kina da wanda zaki aura miyasa kika shigo rayuwata?? Kin cuceni hulwa! Zaki azabtar da zuciyar da ta mutu akanki! Wallahi tallahi bazan juri ganinki tare dawaniba a matsayin mijinki, idan kuwa har hakan ta kasance ina mai tabbatar miki zan iya rasa rayuwata! Baibarni nace komai ba ya kashe wayar, nayi kira har na gaji yaqi dagawa qarshe ya kashe wayar! Tabbas zan shiga tsaka mai wuya, wallahi bazan iya barinka na deen koda zan rasa rayuwata, kaine farin cikina! Kaine rayuwata! Kaine ganina! Wani sabon kuka yaci qarfinta, "tabbas hauwa jabo tayi gaskiya da tace so ya mayar da ita makauniya mahaukaciya kurma wawuya, mara bin umurni mara ra'ayin kanta'" sai yanzu nake fahimtar abinda take cewa! Namiqe a fusace na nufi qofa....... ASHE KAINE MIJINA?? 37⃣ Na HAUWA M.JABO... Na nufi qofa bana gani Sosai jiri jiri nake gani dama gani ba auki ba, amma haka na nufi dakin inna, da nakai bakin qofa kuma sai nayi turus, tabbas bazan iya bijirewa mahaifiyataba koda zan rasa raina, kuma bazan iya haqurin rashin deen dina ba! To ina mafita??? Babu...!! Ba abinda nake tunani illah ranarda za'a daura min auri da wani ba deen dina ba! Haka na juyo jiki ba qwari na dawo daki naci gaba da kuka, gashi kiran duniya nayiwa wayar deen dina amma a kashe,! Da wanne yakeson inji? Da baqin cikin auren wanda baya sona koda baqin cikin rabuwa dashi?? Haka nayi sati daya a daki banachin komai sai tea, kuma inna ko ta kaina batayiba, ga deen dina wayar shi a kulle, yau da safee ina zaune na hada kai da guiwa, kawai naji qarar wayata banyi niyyar dagawaba da naga baquwar number sai kuma na daure na daga, abokin deen yake shaida min deen ba lafiya yana asibiti yau kwana shida kenan hankalina ya gama tashi, na rarrafa naja mota sai asibiti ina shiga na hadu da tsohuwar qawata sista khadee itada ammar dinta tana mishi iyayi shi kuma yana biye da ita, tamin kallon mamaki, tanamason tamini magana amma ni banyi takantaba,dan hankalina baya tare dani kallo daya na mata na kauda kai Na shiga inda akacemin an kwantarda deen dina..ina zuwa naga ya rame yayi wani iri, na matsa kusa dashi kamar in fada jikinsa in nuna masa sonda nake masa da missing dinsa da nayi amma kuma ba hali, haka na daure nayi tsaye ina kallonsa ina kuka, qamshin turarena ne ya daki hanchin sa hakan. yasa ya bude idonsa yana ganina ya rufe idonsa ya juyan baya, Bashir bashir, yanxu ma Wallahi idan na bude ido ita nake gani, qamshinta nakeji, please ka kawo min hulwaty na..!!! Yanda yake magana yasa ta fashe da kuka, hakan yasa deen ya bude idonsa a hankali ya tabbatar da ba gixo take mar ba, sai kuma ya chanxa xance miya kawoki gurina....?? ASHE KAINE MIJINA.??38⃣ Na HAUWA M.JABO... Miya kawoki gurina?? Kinzo ki qarasaninie? Ki sani kin cuci rayuwata hulwa! Yana magana da gyar muryarsa na rawa,har ya Kasa magana haka ya saki kuka hihihi kamar qaramin yaro, na rufe masa baki da hannu... ina bashi haquri, duk da cewa nima kukan nake amma kamar nafishi qarfin hali, na samu na lallabashi, yayi shiru, na kwantar mishi da hankali da kalamai masu dadi abin mamaki cikin 30mnt har ya fara murmurewa a fuska saidai rama kam tananan a tare dashi, "ni jabo araina nace Lallai taku soyayyar daban take" na dade muna hira har yake bani labarin Nihal dinsa zata tafi karatu canada, koda bansan taba ina yawan jin sunanta a bakinsa, kuma dukkan alamu yanasonta sun shaqu sosai, yar yayansa ce, munyi hira Sosai nidashi duk mun sami walwala, kamar bamuba ban koma gidaba sai wajen 4PM nakoma gida, da yake inna ta fita harkata batasan nafitaba batasan nadawoba.....! Inna tayi mamakin ganina a palo yau tun bayan sati daya da suka wuce, har yaya na hira ina dariya, na ga alamar taji dadin haka Sosai amma bata bayyanaba amma ya bayyana a fuskarta, ina zaune muna hira sai ga uncle habeeb yana shigowa ya fara zolayata, amarya kinsha qamshi, raina ya sosu, wani baqin chiki ya tulloqoni kamar in mare shi, shima na kula da damu wa a fuskar shi, banji dadin sunan ba, sunan baima dace daniba, nayi yaqe, kinga yanda kika rame kuwa? yy Habeeb, ai inna tacemin tunda aka miki zancen aure Kika shiga halwa, kullm nazo bana ganinki, dazu yaya hafeez yake cemin angon ma naki yaje gurinsa dan suji yanda za'ayi ashe bashida lafiya zazzabi yakeyi kwana biyu, amma ance yau ya sami sauqi, Allah ya qara lfy, nace ameen araina nace Allah ya kashe dan banxa in auri deen dina..... ASHE KAINE MIJINA..??39⃣ Na HAUWA M.JABO. .. Nace ameen, inna tayi mamakin amin dinda nace, amma bata nunaba, haka mukayi hira Sosai da uncle habeeb ya debemin kewa Sosai.... An saka ranar aurena yau saura sati daya, zainab khalifa ta tare gidanmu tunda aka fara shirye shiryen biki, gaskiya tanada kirki zainb yaya ne kawai ya tsaneta gata yar gayu wayayyiya,duk wannan abin da akeyi zainb da abokin nura takeyin Su, dai dai da rana daya ango bai nemeniba, nima ban nemeshiba... Gaskiya dangin nura sun nuna mishi gata ta uwa da uba, musamman babban yayanshi da ya riqeshi, sabida komai na aure sun mini na gani na fada duk abinda ake yiwa yar gata an mini, fatima qawata ta qauye tazo, maimakon taje gidan Su Sai ta tare gidan mu da zama, zainab khalifa da fatima su suka rarraba katin gayyata da anko wa qawaye da abokan arziki, amma ni ba hannuna aciki ba wanda yasan abinda ke zuciyata sai Allah, duniya tamini zafi, na rasaa yanda zanyi da rayuwata, Saura kwana biyu a daura aurena, deen dina ya kirani yana kuka wiwiwi kamar qaramin yaro dama shi haka yake San garta tamai YAWA kamar jinjiri bayajin wuyar yin kuka, yana kuka yake gayamin wai za'amishi aure, shima yamin bayanin komai, inaga zafin kishin da naji deen baijishiba, na ci gaba da kukan da yafi na farko aka rasa gane kaina inna tace kar wanda ya kulani, deen dina yake tambayata ya zamuyi, nace mubi maganar iyayenmu yace shi bazai iya hada jiki da wata idan baniba, duk abinda ya fada nace nima haka.... Yakenan??? Qarke dai Munyi alqawarin dagani harshi, ba wanda zai kula wanda aka auramai kuma duk mun amince da hakan, zan kashe aurena kamar bayan wata hudu shi kuma zai saki matar da watahudu dai dai nan sai muyi auren mu, kuma ba wanda zai tuhumeni sabida dama ansan yanda auren yake..... ASHE KAINE MIJINA.?? 40 Na HAUWA M.JABO... Yanda auren yake, mun amince da hakan haka kuwa akayi, ranar assabar aka daura auren,. NAZIA &NURADDEEN. Aurenda ya sami halartar manyan qusoshin gwamnati da manyan yan siyasa da manyan malaman qasar nan duk abokan yayan nura ne da kuma abokan yayana, mutane kamar me, amma abin haushi ba ango ba labarinsa wajen daurin aure, abin yayiwa yayan nura zafi Sosai sai ya biqe da cewa ango ya tashi ya matsanancin ciwon ciki, kuma an riga an tara mutane shiyasa aka daura auren, yana bama mutane haquri akan rashin halartar ango... Ana shagali haka na sulale naje ban kwana da deen dina, a wani gida muka hadu dashi, anan ni kuka shi kuka,ba mai rarrashin wani, qaunar juna ta rufe mana ido zuciyoyin mu sai harbawa suke ya rungumoni, yana shafani yana rarrashina, sam na manta da an daura min aure, koda wannan shine karo na farko dana hada jiki da deen duk kuwa qaunar juna da mukeyi, nida deen qabaki daya mun fita hayyacinmu, nidai ban tabajin abinda nakejiba yanzu sabida shine karo na farko dana kusanci namiji, kuma namijin ma wanda nafi qauna arayuwata, in taqaita muku dai deen yayi nasarar kawar da budurcin hulwarsa, duk tsimin da ake dura mata,sai da ya Siga, kundai san sakwatawa da hade hade, wallahi haka deen yayi nasarar kawar mata da budurcinta, tun tana kuka, har ta daina kuka numfashinta ya riqa fita sama sama, sabida taji jiki, ga budurci kuma ga magungunan da aka kimsa mata cikin ma wasu idan sun shigo hannunta a shara take zubawa, amma ta hadu hadi, ke in taqaita muku saida deen yayi kusan awa daya da rabi akan nazia yana abu daya,Kuma ba wanda ya gaji cikin Su bare yayi qoqarin hana daya, ba wanda yana da aure, qarar wayarshine ya mayar dasu halinda suke ciki, abu na farko da yazo mishi shine yayi zina da matar aure.!!! Subahanallahi.... Bayan kowannensu ya dawo hayya cinsa sannan suka fuskanci illar laifinda suka aikata, tabbas basuda uzuri gurin Allah, kuma hukuncinsu dukansu kashine, A banqaren nazia kuwa zuciyarta cike da farin ciki, ganin cewa koda wanchan wawan mijin nata yayi nasara akanta ta biyawa zuciyarta buqatarta, lallai har yanzu akwai yarinta cikin nazia, ita sam bata hango illar laifinda tayiba, amma kuma ta kasa tashi, da gyar tasamu ta miqe da taimakon deen tana dingishi, batada time din wanka, haka ya dingisa ta dawo gida, dama bataje da wayaba, har tazo bakin gofa tace bakace qunshina yayi kyauba, yayi murmushin qarfin hali yace ai bani aka yiwabako, ranta ya sosu Sosai, batace komai ba ta dingisha ta tafi, gida, bawanda ya gane cewa amarya ta fita an dauka taron jama'ane ya boyeta, ta dawo dab da maqreeb zafin saduwar da sukayi ne yake damunta, ta wuce bayi tayi gashi da qyar, tayi wankan tsarki ta, tana bayi taji inna na nemanta, taje ta sameta inna ta mata nasiha mai ratsa jiki, saida tayi kuka, aka shiryata za'akaita gidan mijinta kamin nan aka kaita gidan yayan nura din, duk da cikin kuka take kuma fuskarta a kulle take bai hanata gane gidan ba Gidan su sister khadee ne tsohuwar qawarta da taso ta salwantar da rayuwarta ita da mugun uncle dinta amma ta ijiye akan cewa my be sun saida gidanne yayan nura ya siya, da yake bata shiga gidan ba, so bata san yanda gidan yake ba bare ta gane, kawai dai an yiwa gidan sabon fentine, sun shiga an mata nasiha maman nura da babasu da yayyenshi da matar yayanshi da duk danginsu suntofa albarkacin bakinsu, ana ta sakamini albaka ana dada cewa inyi haquri, aka kwasheni sai gidan mijina WASA SABON GIRKI, KU BIYO JIKANYAR JABBI YAR MUHAMMAD JABO KUSHA LABARI..,, ASHE KAINE MIJINA.?? 41 Na HAUWA M.JABO... Yanda auren yake, mun amince da hakan haka kuwa akayi, ranar assabar aka daura auren,. NAZIA &NURADDEEN. Aurenda ya sami halartar manyan qusoshin gwamnati da manyan yan siyasa da manyan malaman qasar nan duk abokan yayan nura ne da kuma abokan yayana, mutane kamar me, amma abin haushi ba ango ba labarinsa wajen daurin aure, abin yayiwa yayan nura zafi Sosai sai ya biqe da cewa ango ya tashi ya matsanancin ciwon ciki, kuma an riga an tara mutane shiyasa aka daura auren, yana bama mutane haquri akan rashin halartar ango... Ana shagali haka na sulale naje ban kwana da deen dina, a wani gida muka hadu dashi, anan ni kuka shi kuka,ba mai rarrashin wani, qaunar juna ta rufe mana ido zuciyoyin mu sai harbawa suke ya rungumoni, yana shafani yana rarrashina, sam na manta da an daura min aure, koda wannan shine karo na farko dana hada jiki da deen duk kuwa qaunar juna da mukeyi, nida deen qabaki daya mun fita hayyacinmu, nidai ban tabajin abinda nakejiba yanzu sabida shine karo na farko dana kusanci namiji, kuma namijin ma wanda nafi qauna arayuwata, in taqaita muku dai deen yayi nasarar kawar da budurcin hulwarsa, duk tsimin da ake dura mata,sai da ya Siga, kundai san sakwatawa da hade hade, wallahi haka deen yayi nasarar kawar mata da budurcinta, tun tana kuka, har ta daina kuka numfashinta ya riqa fita sama sama, sabida taji jiki, ga budurci kuma ga magungunan da aka kimsa mata cikin ma wasu idan sun shigo hannunta a shara take zubawa, amma ta hadu hadi, ke in taqaita muku saida deen yayi kusan awa daya da rabi akan nazia yana abu daya,Kuma ba wanda ya gaji cikin Su bare yayi qoqarin hana daya, ba wanda yana da aure, qarar wayarshine ya mayar dasu halinda suke ciki, abu na farko da yazo mishi shine yayi zina da matar aure.!!! Subahanallahi..... ASHE KAINE MIJINA. ??42⃣ Na HAUWA M. JABO.. Bayan sun mini nasihohi aka kwasheni sai gidan mijina, su zainab khalifa da fatima duk an kawo jiki ana jiran ango da abokan ango Suxo ko za'ayi sa'a asamu wanda zai taya, amma har gurren 12:30 na dare ba ango ba abokanshi haka suka gaji da jira suka tafi gida, suna cixon yatsa" nima jabo xee khalifa ta bani tausayi danaga kwalliyar data chaba�� " Naziah dai haka ta zauna jugum sunaa fita ta kulle daki, dan ta cika alqawarin deen dinta, Nayi bacci na, ga zafin da gabana yake min na wahalar da deen ya bani, cikin bacci nayi ta mafarkinsa...!! Ji nayi an bubbuqa mini qofa, in fito ashe har 11 na safee yayi, na fito wai zamuje walimar da akeyi bayan amarya da ango sunyi Xxxxxxxx.. na buqa gafa ni wallahi banida lafiya!! akayi sama da qasa in xo muje naqi zuwa suka gaji suka kyaleni, Bangaren nura kuwa yayanshi yayi rantsuwa idan har baije walimar nan ba sai yaci mutuncinsa, kuma bashi bashi har abada, dan ya zubar masa da mutunci iya zubarwa ranar daurin aure da baijeba, bama daurin aureba duk wani events da aka shirya nura bai halarci ko daya ba, haka dai ya shirya yaje walimar bada son ranshi ba wannan karon kuma ba amarya.. Walima tayi walima, an raba kayayyakin aure, gaskiya yayan nura mutumin kirkine kuma ya fitarda dan uwansa kunya, inaga walimar da akayi ba'ataba yin irinta ba duk sokoto, sabida komai need, anyi lafiya an qare lafiya an bar amarya da angonta da kuma halayensu...... ASHE KAINE MIJINA 43⃣ Na HAUWA M. JABO.. Nura ya siyo wa matarshi sabuwar waya kuma aciki yayi saving din numbersa da sunanshi, koda bashida number ta amma ya mata letter yace duk duk abinda take buqata ta mishi sms a wayan da ya aiko ya ijiye mata akan hanyar dakinta.. Bangaren nura dana nazia daban ne, batasan shigarshiba batasan fitarshiba, haka shima,m baisan chinta ba baisan shantaba, kullum yana manne da waya yana waya da abar qaunarshi hulwaty azeez dinsa,.itama dai haka, suna farantawa juna rayuwa da kuma jaddada alqawuran da suka yiwa juna na kada ta kuskura mijinta ya kusanceta ita kuma tace kada ya kusanci matarshi..... Haka rayuwar aure ta kasance, mata tun tana kulle qofarta har ta gane cewa mijin nan nata yafita qiyayyarta, sabida haka saim ta dan saki jiki ta rage zaman daki tana zama parlour tayi kallon ta tayi chatting dinta, a groups chat, dama mayyar chatting ce idan sun hadu da m jabo a group din kar mu shagala ayita wasa da dariya kamar dama sun san juna su suke debe mata kewa, idan ana zolayarta da zancen banana takanyi murmushi aranta tace da deen dina bai dandana min ba ina har in koma ga mahaliccina indai akan wannan mijin nawane bazan san komai akan banana ba... Gashi duk wani salon sarrafa namiji ta koyo shi sai dai ba mijin kuma bata buqatar sa a tunanin ta anyitane dan deen dinta.... SHE KAINE MIJINA 44⃣ Na HAUWA m. JABO Deen dinta, wasa wasa naziah tayi wata biyu gidan nura, kullum cikin liSsafi take, yanxu ya rage saura wata biyu ta kashe aurenta taje gurin abin qaunarta tanata shirya plane na yanda xata bullo ma abin ya sallameta cikin mutunci dan ta kula shima dan is ne.... Bayan wata biyu ne yayan nura ya shiya mana tafiya honey moon a turkey, Cyprus da India, nidai kam sai sms ya mini wai inje kaduna gobe amini passport in shirya driver zai kaini, araina nace kuma uwar me xa'ayi da passport har baxan je ba kuma Sai na tuna da yaya yace ko banyi dan kowa ba nayi dan yayan shi... munyi passport da komai, aka karbo mana visa da ticket da komai tafiya ta kankama na gama shirina koda ni ba son tafiyar nake yiba dan ina gudun achan ya sami sa'ata ya bata min shiri amma haka nayi biyayya ga karamcin da yayansa yake min yasa na amince.. Na fito parlour ina jira sai sms naji ya shigo "kije driver zai kaiki airport zanzo daga baya" araina nace tafi nono fari, na kira deen dina na gaya mishi zanyi tafiya yace shima zaiyi tafiya amma ya chanza bucking dinsa, naje airport driver ya bani dollars rapper daya nidai bansan ko nawa bane amma nasan suna da yawa, na saka jaka, har jirginmu ya kusa tashi baizo ba araina nace kardai ya wuce cikin jirgin ban ganshiba tunda ba saninsa nayiba, nayi hanxari na shiga jirgi, ko minti uku banyiba da zama ba sms ya shigo, Bazan sami damar zuwa yauba, idan kin isa let me know..!! haushi ya kamani, ya zai turani wata qasa ni kadai, amma van damuba sabida nafi buqatar haka... Na isa Cyprus lafiya, qasace ta arna ga tsadar rayuwa, dala 100 idan na fitar ko abincin kirki banaci in qoshi da ita, ni kadai nake holewata, na sayi sim C guda biyu daya a dayar wayata daya a tablet dina, na kira deen dina na fada mishi na iso lafiya, na kira iyayena na gaya musu na iso lafiya, layin da nake kiran deen daban wanda na kira gida daban, ban kira nura ba dan banida Lokacin sa, sati na daya a Cyprus deen dina ya baqunci qasar, tunda yazo muke tare dashi ya mayar dani kamar matarshi, gabaki daya na tare hotel dinda ya kama ina honey moon dina dashi mai makon mijina na sunna, sau dubu sai mun qare lalartamu deen yake kukan abinda ya aikata ni nake qarfafa mishi guiwa garin qarfafa guiwa ma sai na qara bashi kaina akoma ruwa nariqa na gama da rayuwar deen na Sangartashi da kaina, yanda baxai taba iya rayuwa da wata mace idan baniba..... Tir da halinki naziah ��������....., ASHE KAINE MIJINA 45 NA HAUWA M.JABO Bacci mai dadi da nauyi cike da mafarkin deen dina.. ban farkaba sai guraren 11 na tashi na kimtsa mukayi break fast, deen ya siyo min ticket daga abuja zuwa sokoto, shi kuma yace sai gobe zai dawo, bada son raina na rabu da deen dinaba amma ya xanyi dole in haqura, na isa gida cike da murna da farin ciki bana tunanin komai sai deen dina, inna taji dadin yanda ta ganni nayi qiba tubarkalla dani, qirjjina ya cicciko Sosai, nima na kula da hakan, musamman lokacinda na zo abuja deen dina yake cewa na qara kyau da ni'ima qirjina ya cicciko dai dai hannunsa, na dauka santina yakeyi ashe da gaskene, munsha hira da inna Sosai, sai guraren maqreeb yaya ya dawo muka gaisa dashi yaji dadin ganin yanda nayi kyau, autan inna waje ta karbeki, na kyalkyale da dariya, ai yaya waje ta hadune naijarmu ce sai a hankali..!! munyi hira sosai dasu, anan nakejin yaya wai zai auri Zainab khalifa, abin mamaki yarinyar da ya tsana kuma ya raina wai itace har yake ce mata honey a waya,Lallai soyayyah soyayyah ce, sai guraren 10 na dare sannan na koma gidana duk na gaji ga kaya niqi niqi dana niqo.. ina zuwa sai bacci ya kwasheni, ban farkaba sai kusan asuba, nayi sallah nashiga aikin gida ko ina na gyara duk yayi qura na aikatu amma kuma gidan sosai yayi kyau gidan na chanxa mai fasali.. guraren la'asar sms yashigo" GOBE KISHIRYA KIYI GIRKI SU YAYA XASUZO SU MIKI SANNU DA DAWOWA" mtwss shi wannan mutumin shirmensa yayi yawa.. Na Shirya musu girki kala kala, Cikin kayan da deen dina ya siyo min na fitar musu da tsaraba, sunxo sunji dadin ganina da sukayi na kula da matar yayan nura sai kallona take tana murmushi motsi kadan tace mini sannu, araina nace matar nan tana sona, naji dadin zuwan su, sun tafi sun barni da Kewa..... ASHE KAINE MIJINA.??46⃣ NA HAUWA M.JABO... Na isa Turkey... Ai nasan kin isa Turkey Ya karanta sms din yayi dariyar mugunta nura kenan... A Turkish naji dadin qasar duk da cewa ita ma akwai tsadar rayuwa amma tafi Cyprus arha.. sai da na shalle sati biyu anan, nayi kewar deen fiye da ko wane lokaci,kullum muna waya muna faranta ran juna, danma kar ya ga jarabata tayi yawa ya rainani da tuni nace ya biyoni Turkey, amma dole in kama kai, ko yanzu dai na more, "wawiya" Haka na qare zama Turkey na wuce India ba nura ba labarin sa nayi xaton xamu hadu koda sau daya ne amma ina... a indiya nayi wata daya cur dan qasar tafi su dadi da kuma sauqin rayuwa, duk kudina da suka rage a India na qarar dasu... a India ne na fara wani zazzabi zazzabi, amma dai ban baiwa zazzabin hadin kai ba dan kada ya rage min jin dadina, har yaren India na koya dan xaman da nayi, na hada tsarabata da wacce deen ya siya mun da wacce na siya na biya kudin kilo na dawo gida, a abuja na sauka, nayi waya gida na gaya musu na iso gida, ina mijin naki nayi dumm,ko baya kusa idan yaxo ki gaidashi, nace aah ai sai qarshen sati zai Dawo.... , sukace to Allah ya dawo dashi lafiya, nayi waya da deen dina na gaya mishi ina abuja yace in kama hotel in jirashi yazo, haka kuwa akayi na kama hotel, shima gobe ya iso, aranar kwana mukayi muna abu daya, deen ya nuna min yanda yayi missing dina nima na nuna mar munji dadin juna.....Tir daku.�� Har deen yake cewa Asia ta karbeki kalli yanda qirjinki ya cicciko, na rufe fuskata na fada qirjinsa, yayi murmushi yana shafani a hankali, tabbas da ba deen ban san yanda rayuwata zata kasanceba, banajin ko za'amutu zan baiwa nura kaina a matsayin mata, haka bacci ya daukeni bacci mai dadi da nauyi inata mafarkin deen dina.... ASHE KAINE MIJINA ???4⃣8⃣ Na HAUWA M. JABO, Barni da kewa.... A mota matar yayan nuru take ma yayan nuru gulma wai inada ciki, Kaga yaronnan mutumin banxa yana nuna ma mutane bai damu da naziah ba Ashe munafukin yana xagawa kaganta har da ciki, murna a gurin abban Fatima kamar me, kamar ma ba'ataba musu haihuwa ba, a hirar har an saka suna yaran da naziah xata haifa, idan macene sunan mamar nura idan kuma namijine sunan marigayi baban naziah, kunji mutane da iyayi..... Dan aikin da nayi na gaji Sosai na kwanta sai bacci, na tashi da wani irin xaxxabi da kasala na kula aikin da nayine ya haifar min dasu tunda da muna gun honey moon bana komai deen dina yake mun, a India ma nayi irin wannan xaxxabin Nasha panadol naji sauqi.... Nura ma ya dawo Sokoto munanan kamar yanda muke ba wani bayani har yau nakai wata uku da Kwana ashirin jikina ya bude, nayi qiba na gara kyau dani sai missing din deen dina nakeyi... Na dauko waya na kira deen muna hira nake gayamai fa lokaci yayi ya kitsa min abinda xan fada ma mijina ya sakeni nima yace min akwai wani abu da yake jira yana kammala shi xai sallami matar tashi kamin lokacin na kammala idda na sai muyi aure.... Suna kammala waya jikinta na rawa ta dauko dayar wayan da nura ya bani dama dashi take mai SMS. Bata taba kiran saba Shima bai taba kirantaba, Duk abinda deen dinta ya fada taga idan ta fadamai xai rainata my be ma yaqi sakinta sai kawai ta chanxa shawara ta tsara yanda xata mai haka kuwa akayi ta aika SMS tana jiran reply.... Abin mamaki ba musu ya aminta da buqatar ta na ya saketa amma da sharadin cewa sai nihal ta dawo ta ganta sannan xata tafi gidan su amma yanxu xai bata takarda tayi ran tsawa akan ta yarda..... ASHE KAINE MIJINA ?? 49⃣ Na HAUWA m. JABO. .. Itama ta amince da sharadin sa duk a SMS suke maganar, Nan take nura ya rubuta takardar saki ya ijiye ma naziah a hanyar dakinta, murna kamar ta kasheta yau xata kai ga burinta,ya deen dinta xaiji idan yaji ta karbo takardar saki,murna ba'a magana, kamar ta wuce gida amma sai tace bari dai ta cika alqawari kuma taga wannan nihal da akeji da ita,kowa xancenta yakeyi xata dawo karatu canada, kuma tace gidansu xata sauka... Naziah na Kwance tana yan tunane tunanenta, yanda aurenta da deen xai Kasan ce tunda yanxu ta xama baxawara, a bikin Su tayi kaxa tayi kaxa, a wannan tunanin ta gangaro wani tunani.. Sai yau nake tuna cewa fa... tunda nayi aure banyi al'adaba ko sau dayaba.. Sai yau nake tuna dan ciwon dane da yawan xaxxabin da nakeyi.. Yanxu nake fahimtar inajin cikin cikina kamar ana min motsi.. Sai yau na tuna duk kwanciyar da nake da deen dina a jikina yake xube min.....din bai taba amfani da condom ba!!! Lokaci daya hankalina ya tashi lallai ni lafiyayyace kuma komai xai iya faruwa dani, Kardai ciki nake dashi??? Wai ma idan nayi ciki ya xan kalli inna, gashi na kashe aurena rana ta farko da naziah ta fara nadamar abinda ta aikata gashi ta karbi takardar rabuwa da nuraya xatayi??? Ta Shiga kogin tunani Lallai mafita itace taje asibiti Dr ya dubata, ba shiri tadauki key Sai wani prvt hospital, ta fara yima Dr bayani abinda ya kawota, Bayan bincike bincike Dr ya gane cikine da ita Dr yaxo yana fada, ke kinsan kinada ciki amma bakixo aka dubaki ba sai yau, to lallai jaririnki yan...... Batamaji abinda Dr yace ba ta fadi sumammiya.... ASHE KAINE MIJINA ??50 NA HAUWA M. JABO.. Sumammiya, likitoci sukayo kaina aka samu ta farfado ta fara sun batu, Dr dan Allah kataimakeni Dr ka rufamin asiri ya xanyi da rayuwata...!! shi Dr yadauka taji abinda ya fada ne na cewa yaron cikinta na cikin matsala kuma cikin xai iya xubewa ko wane lokaci.. hakan yasa yake bata haquri da magana tare da alqawarin kasan cewa Dr ta har ta Sami sauqi, ya rubuta maganguna da allurai da kuma abincin da xata riqaci... Ta dawo gida cike da xullumi,da tunani, shin xata fara fadama deen labarin cikin da take dashi ne?? ko kuma ta fara da maganar sakin da aka matane,?? "Nima dai jabo sai kallonta nakeyi" tadai yanke shawaran Sanar dashi xancen cikin b4 sakin.... dama bata tafi phone dinta ba, Ta kira deen dinta, koda taxo ya kira har 8,ta kira He'll hulwatiy ya kike ina kika shiga inata kira baki dauka ba.?? Hello ko baki jinane?? har xai kashe sai yaji maganarta a hankali, Inajinka deen!!! Lafiyan ki kuwa?? Naje hospital ne...!! Subhanallahi hulwatiy mi yake damunki?? Waye bashi da lafiya?? Kimin bayani mana kinyi shiru... Na fara magaba ka katseni shi yasa nayi shiru..!! Sorry hulwatiy kinsan Banason abinda xai taba min lafiyar kine ko kadan, kece jina kece ganina.. kece duk wani buri na rayuwata...!!! Talk to me please m hulwatiy.!! Tayi ajiyar numfashi, Daxu Dr y dubani... Eh inajinki ci gaba, miyake damunki mi Dr yace?? Yace wai inada juna biyu... What..!!???? [9:13PM, 2/14/2015] ‪+98 939 488 1183‬: ASHE KAINE MIJINA ??..515⃣1⃣ NA HAUWA M. JABO.. WHAT...!!!!??????????? Eh yace ciki nake dashi, haba hulwatiy, Kidaina min irin wannan wasan mana!! Kamar ya Wasa Wallahi deen da gaske nakeyi. Hankalin deen ya tashi matuqa, ya Rasa abin cewa, Ok ki bari anjima xan kiraki yanxu inajin maganar wannan shasha shar tana zuwa kada taji mi muke fada!! Amma ai yau Monday deen daxu kace min kana office ne!!! Eh ina office inaga tanada buqatar kudine taxo gurina!! Amma kace min baka taba ganinta ba ya akayi har kake gane muryarta.?? Anya deen!!!! No kingane ai...... Sai taji sallamar mace a wayar kuma taji an kashe aranta tace ee naji muryar mace inaga ta biyo shine, sai bata gane komai, kuma bata taba tunanin yaudara a gurin deen ba. Da farko kuma har taji tsoro, Amma fa ita dole deen yaxo a xubar da cikin nan kamin tayi yun qurin barin gidan aurenta, aranta ta riqa saqe saqe har bacci ya dauketa A bangareen deen kuwa yanata saqe aran shi yanda xa'ayi da ckin nan, shikam bai San yanda xaiyi da itaba, kuma yasan illar xubar da ciki dan xata iya mutuwa, kuma dole Shi xaikaita hospital kuma shi xaiyi sign Lallai baxai iyaba...!! idan ta mutufa?? Miye mafita?? Mafita dayace kawai ka rabu da matar mutane kaje ka rungumi matarka!!! Idan nayi haka anya na mata adalci??? Lallai nayi kuskure nayi jahilci tarayya da matar aure, Haka ya qare tunanensa qarke ya yanke cewa xai rabu da ita kawai taSan yanda xatayi da cikin...... Kinji mugu dan iska kadan daga cikin halayen sheguuuu..�� bata farka ba sai guraren maqreeb, tasan ma deen ya kira, a gurguje tayi sallah bata qareba aka kira maqreeb tayi maqreeb tayi addu'a ta janyo waya.. Ta duba wayam ba miss call ko daya abin ya bata mamaki matuqa. Ta daure ta kira shi sai na uku ya dauka, Hello deen....ASHE KAINE MIJINA ?? 52. Na HAUWA M.JABO.. Hello deen, Hello...Kanajina kuwa? Eh inajinki.!! Ya naji kana magana fada fada.?? Waya tabamun kaine?? Kedai ki fadi abin da xaki fada kawai.!! Tayi shock dajin wannan maganar a bakin deen, wanda daidai da rana daya bai taba mata koda gaddama ba bare ya mata baqar magana.!! Tayi ajiyar xuciya, Allah ya baka haquri, dama maganar cikinnan ne nace ya xa'ayi dashi.?? Kuma dama inason in gayamaka na karbi takarda sakina..!! Deen yayi duuum jin wannan maganar ta hulwaty, Lallai maisha ta riqa tasha ba abinda yafi illa ya fatattaketa ta rabu dashi, amma ya mata adalci kuwa? Anya yiyiwa kanShi da son da yake mata adalci kuwa? Anya xai ma iya rayuwa ba hulwar sa, xaka iya mana dayan xuciyar ta bashi amsa.... Takeshi daga dogon tunanin da ya tafi, deen kayi shiru deen!! , Yanda ta fadi maganar da murya mai Sanyi sai ta qara bashi tausayi.!! No Inajinki ci gaba.. Ai na fadi duk abinda xan fada.! Kai nake jira... Dama ke duk abinda mukeyi dake kinSan bakiyi planing ba?? Dan ki xubar min da mutunci yasa kikayi tarayya dani? Akan me xaki bari ciki ya Shiga,?? Ta yaya xan aureki da ciki?? Sam bakiyi tunaniba kuma bakiyi naxariba, ni Muslimine baxan taba yin shirka gurin xubar da cikiba, Sabida haka kisan yanda xakiya da cikin ki, ki nemi mijinki kuyi Sulhu ya rufa miki asiri ba hannuna ac...... Deen kaine kuwa..!!? Ta Katse shi cike da mamakin abinda yake fitowa daga bakin deen mi yake Shirin faruwa da itane abin kamar a mafarki... Ki saurareni ya fada yana mai daqa murya.!! Daga yau Sai yau kada ki qara nemana..!! kadama ki qara nuna kinSanni.!! jahilar banxa wacce batada tunanin.... Bansan lokcin da wayar hannuna ta subucemin ba cikina ya fara juyawa na fadi qasa na fara rero kukan nadama... Tabbas na jahilace tana kuka tana surtai,banida ilimi gaskiyan ka deen ni jahilace ina matar aure namaida wani namijin mijina ina xankai haqqin aurene?? Kadan daga axabar da Allah xaimin kenan kamin inje qiyama inchi ubana... Chikinta yaci gaba da juyawa, sai ta fara xubar da jini, Ta tabbatar da idan har ciwo yakamata anan sai dai ta mutu ba wanda xaikaita asibiti, Ta rarrafa tun tana ganuwa taja mota sai hospital, kamin ta Isa ta jiqe sharkaf da jini, bayanta kamar ya bude.. Takasa qarasawa cikin sai kwasarta akayi akayi ciki da ita, Likitoci sukayo kanta, aka mata allurai.... Lokacinda ta farka taji ana qara mata ruwa, Dr yaxo yana mata sannu, Hajia naziah sai dai kiyi haquri munyi iya bakin qoqarinmu na ganin mun tsayar da xubar cikin amma abin yaci tura, qarke ma Sai mukaga idan mukayi wasa xaki iya rasa rayuwar ki, sai kawai muka miki allura cikin ya qarasa xubewa... Wata hamdala tayi hadi da jin dadi, lallai Allah ya rufa mata asiri da ya xubar da cikinnan..., Dr yace Yanxu xamu baki allurai da yan magunna kuma yakamata ki sanar da mai gidanki halin da ake ciki, kamin mu sallameki, No Dr maigidana baya gari kuma ni ba yar nan bace.! Tafada muryanta yana hadewa, Dr ya kalleta yace to shikenan xaki xauna anan har zuwa gobe ko jibi idan kin qara Samun lafiya Sai mu sallameki... Dr kayi haquri ka sallameni yanxu kaga banxo da phone dina ba kuma nasan mijina da iyayena xasuyi ta nemana hankakin Su xai tashi ataimaka min please Dr...!! Hajiya baxai yiWu ba, duk da kinada cikakkaiyar lafiya amma ya dace kidan qara samun rest.... ASHE KAINE MIJINA?? 5⃣3⃣ Na HAUWA M.JABO... Samu rest, duk yanda Dr yayi akan naziah ta bari har gobe idan taqara jin sauqu a sallameta ta tafi gida amma abin yaci tura, ta nace akan tunda tanada lafiyar ta gida xata tafi... Ya rubuta mata magunguna da kuma allurai , kuma yace tana buqatar hutu da natsuwa, yace mata mahaifarta ta sami matsala xata riqa zuwa ana dubata har ta Sami lafiya,kuma idan tayi wasa xata iya rasa haihuwa har abada, ya qara bata haquri akan Kasa war da yayi na ceton yaron dake cikinta kamar yanda ya mata alqawari anan dai ya qara mata bayanin cewa dama cikin xai xube dan ba daidai yakeba, haka ta dawo gida guraren 11 na safe, tanata saqe Saqe aranta har ta iso gida, Nidai banyi dacen rayuwa ba, na cutar da kaina na cutar da mijin aurena, nakasa kare darajar aurena, qarke ga yanda deen dina yamin, Lallai maxa ba abin amince wa bane, anya kuwa deen dinane yamin haka?? Dayan xuciyar ta ya bata Amsa Eh deen dinke malam naziah... Any how mun tashi 1__0, tasha alwashin sai ta rama abinda ya mata... "Kinji hauka ko ina xata Ganshi ta rama ohoooo" Ta iso gida ba qarfin jiki, ta Samu tayi wanka da ruwan dimi ta qasa jikinta Sosai tasha tea ta nemi guri ta kwanta, a baccin ma dai mafarkin deen ta riqayi, tana taShi ta tsine ma baccin da mafarkin gaba daya.. guraren qarfe hudu na yamma sms ya shigota, taji duuum nurane "JIBI NIHAL XATAXO KI GYARA MATA DAKINDA XATA SAUKA" .... Tayi duum ita kadama suxo Suga halinda take ciki su ganota, Hakanan ta lallaba taje dayan banqaren ta dan gyara sama sama, ta koma dakinta, dama naziah akwai xama daki "kamar jabo" Yauce ranar da nihal xata iso guraren 4:pm xata iso, Nura yasa an yo siyayyah abubuwa kala kala duk na tarbar nihal, Naziah aranta taji tana son gani wannan yarinyar da ake axarbarbabin zuwanta... kamin qarfe biyu ta kammala hada komai gida yayi fes dama fes yake girki kala kala ta hada duk na tarbon nihal, itama dai tadanyi wanka duk da yanayin yanda ta kode ta chanxa tayi wani iri da ita amma dai tayi kyau, abinka da kyakyawan mutum... ASHE KAINE MIJINA.?? 54⃣ Na HAUWA M. JABO.. Tana xaune parlour tana kallo har guraren biyar basu isoba,lokacin shan maganinta yayi ta shiga daki kenan taji qarar mota haka qirjinta ya riqa dukan uku uku, ko miye haka ohoo..!!, tanajin maganar Su sama sama, abinda yafi bata mamaki muryar wacce takeji kamar tasan muryar amma ta manta inda tasan muryar, Aunty..! Aunty..!! Auntyyyyyyy..!!! Ina kike gamu mun iso, muryar da taji kenan ana gwalla mata kira, Shikam nura yana ijiye nihal ya fita dan kada naziah ta kwafsamai gaban m nihal.... Na'am ina zuwa... naziah ta bada amsa a taqaice.. Ta fito qamshin da taji Lallai tasan qamshin, amma tasan hancin tane yake yaudararta... Tafito da Walwala abinda take gani gabanta yafi bata mamaki akan komai, ba kowa bace face tsahuwar qawarta da tafi tsana a rayuwar ta itada mugun uncle dinta wacce Sanadiyar su ta bata wato sista khadee, tuni ko wacce ta daure fuska naziah ta kalli s...khade a wula qance ina nihal take?? Nihal ta kalli naziah cike da mamaki da al'ajabi Lallai wannan naziah ce kuma itace matar uncle dina dama ance mata sunanta naziah...!! Kuuut yau ake yinta.. Ko wacce na kallon yar uwar ta, nihal cike da mamaki tace nicefa nihal din,naziah tace miya kawoki nan gidan, suna cikin magana kawai sai ga nura ya shigo... Nihal..!! Nihal...!! Ya Shigo da kaya niqi niqi a hannu yana kwalawa nihal kira.. Abinda ya gani shine ya bashi mamaki hade da daure kai, ledodin hannun sa duk suka xube, Jikin Sa na rawa hadi da sarqe war murya ta tashin hankali hadi da tsori ya kalleta murya na dancing, ke miyaa miyaa kawoku gidanaaa.!!?? kinxo dan ki tarwa tsamin iyali na hadi da jin dadina ko??, waima uban wa ya baki address din gidana...!!! Naziah ta gama raxana jin yace miya kawota gidan sa, idan dai nan gidan sane to Lallai mijintane!! Kuma shine uncle din sista khadee da yace mata almajira kuma ya mareta, shine mutun na farko data tsana a tarahin rayuwar ta.!! Shine sanadiyar batanta.!! Kuma shine mutumin da ta qara tsana second time a rayuwarta wanda yayi sanadin shiga tashin hankalinta..!! Jin tayi an katsata da wata irin tsawa ke hulwa badake nake magana ba?? Nura ya kalli nihal yace ke ina naziah ta shigane?? Nihal ta kallu uncle dinta cike da mamaki tace uncle wannan ma ai sunanta kenan fa naziah .. WHAT??? [11:00PM, 2/13/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA.?5⃣5⃣ Na hauwa m. jabo... What??? Eh uncle itama sunanta nazia.... itace qawata da nake baka labari lokacin, kuma itace wacce ta maka rashin kunya lokacin da taje gidan mu, No bashi nake neman saniba nihal.! wai itace matar tawa??? nihal da mamaki ta kalli uncle dinta.! tace kaman ya uncle dama bakasan matar taka ba??? yayi shiru yarasa abinda xai fada... ita nihal mamakinta shine wata hudu dayin auren baima tama sanin matar ba to ya akayi akace mata tayi ciki?? kuma uncle yace mata bai santaba baima taba ganintaba amma batayi tunanin abin yakai hakaba!!! nazia iya tunaninta ta gane cewa lallai wannan nura shine mijinta, kuma shine uncle din sis khadee, kuma shine deen dinda ya yaudareta yaci mata mutunci.... Dukansu sunyi churko churko kowa ya rasa abinda xai fada.!! nazia taji tsoro matuqa tayi tunanin kada su mata wulaqancin dayafi wanda deen ya mata da wanda wannan tsohuwar qawar tata ta mata, tajuya xata koma dakinta ta tattaro kayanta ta wuce gida tunda dama ya saketa.. tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki dama batada lafiya cikinta daya xube... tayi taku biyu uku kikajita lauuuuu... ta fadi "nima jabo bansan miya sa ta fadiba" duk sukayo kanta nura jikinsa na rawa yake bubbugata amma ko motsi batayiba hankalinsa ya tashi matuqa suka yayyafa mata ruwa amma inaaa shiru da sukaga xasu bata lokaci sai suka dauket sai asibiti.... a hanyar asibiti kamin a isa ta farfado taganta a mota tayi yunqurin miqewa xaune taji an dan daneta irin ta kwanta dinnan a jikin wani qamshin da takeji yana dukan hancintane ya tabbatar mata cewa tana tare da deen ne ta daqo dagyar tana dubawa taganta ashe jikin deenma take kwance... dukda rashin qarfin jikintanba bai hanata tashi a jikinsa da qarfiba hadi da dalla mai harara da wani uban tsakiba, ko ajikinsa shidai ta samu lafiya itada dan cikin da ke jikinta!!! "kunji wawa baima san cikin ya xubeba koni jabo da masu karatu munsan cikin ya xube ko baku saniba��??" kusaukeni anan.. !! ta fada a taqaice dan bata iya magana sosai. deen ya bude baki xaiyi magana... Nace a saukeni anan!! Wannan karo da gadara hadi da isa ta fada tare da tsiwa irin tata, komai ta fanjama fanjam... ta murda marfin motar wallahi idan baku tsaya ba xan sauka, kuma motar tana tafiya ne... deen ya tabbatar da xata aika yacema nihal ta tsaya tafita ta basu wuri... nazia tamai kallon banxa. dawa xa'abarka??? [11:23PM, 2/13/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA.?5⃣6⃣ Na hauwa m. jabo. Ya kalleta ya marairaice haba hul.... ta katseshi da sheeeeee....!!! yimin shiru munafuki macucu mayaudari lokaci daya ta kirashi da sunayen ta bude marfin motar da qarfi ta fita abinta... yafito yabita a baya har xata shiga taxi yaja ya tsaya yabita da kallo hadi da kallon cikinta lokaci daya Allah ya sakamar qaunar cikinta fiye da yanda yake tunani... nihal nason tayi magana amma kuma yanda taga ya daure fuska ya wani chanxa sai tayi shiru... chan kuma sun kama hanya tace uncle nifa bangane wannan abunba nakuba naga.. bakuma xaki ganeba... ya bata amsa a taqaice, ta kalleshi ta gefe, har xata qara magana ya katseta.. kuma banason inji wannan abinda ya faru gurin kowa...!! hmmmm..! nihal taci gaba da driving dinta, uncle ina xamu tafi yanxu.. gidana!! nanma amsar a taqaice ya bata.. To ai.. to ai me? look nihal kindameni da magana kibarni inji abinda nakeje pleaseeeeeeeee...! har suka isa bata qara mai maganaba... nazia direct gidan su ta wuce tana xuwa ta fada jikin innarta tana kuka, inna tana tambayarta abinda ya faru dagyar ta iya bude baki tace nurane ya sakeni .!!! Inna tasaka salati..! sakifa kikace!!! eh wallahi inna ya sakeni!! inna tana ganin abin kamar bada gaskeba ko kuma mafarki, to Ina takarda, nazia tadan taqaita kukan nata tace takarda tana gida namanta da ita, hankalin inna inyayi dubu ya tashi, inna ta kalleta rai a bace kinga yanda kika dawo lokaci daya kamar mai jego!!? qirjin nazia ya qara bugawa.. waima miya hadaku ne da har ya sakeki?? naci gaba da kukana ban bata amsaba inajinta tayi waya da yaya ta gaya mar abinda yake faruwa. bansan abinda yace mataba kawai sai naji tace to sai ka iso ta kashe wayar... taxo taxauna kusa dani, tayi tagumi chan kuma tace, Allah dai ya saukeki lafiya amma wallahi yaronan baiyi halin iyayensaba, amma dai bari muji miya hadaku kamin ince wani abu. !! Wani rasss naji dama inna tasan inada ciki kenan ?? to ya akayi suka gane inada ciki? yanxu idan ma nace baitaba kusantanaba ba yarda xasuyiba lallai da sake.... [11:31PM, 2/13/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA.?5⃣7⃣ na hauwa m. jabo. Lallai da sake dole insan yanda xan bulloma lamarin "xancen xuci takeyi" Allah nagode ma da ka xubar da cikinnan.. na tashi xan shiga dakin inna kenan, sai sallamar yaya mukaji yashigi kamar an turo shi yayi jaaa kamar qauta�� sai huci yake kamar wani kasa... wallahi inna tun farko nasan xa'ayi haka.!! nurr bayason nazia itama bata sonsa amma muka rufe ido muka ce sai anyi auren nan kuma na gaya miki haka tun farko yanxu ga wulaqancin da yayi mana nan yasokota dan ma cikarshi dan iska baitashi sakintaba saida ya mata ciki yanxu dan Allah inna abinda yayi ya kyauta kenan?? Ya mata adalci kenan?? yanxu ki..... inna ta katseshi kai wai wane irin mutunne kai bakasan miye ya hadasuba kawai xakaxo kana ma mutane rigimar banxa, Ai ka bari ta mana bayanin miye ya hadasu har ya saketa sannan ka fara rigama rigimamme kawai.! dan taxo tace yasaketa haka kawai ba fada ba komai xai saketa?? dukansu basason juna to katabbata akwai laifin kowanne su aciki kabari tayi bayani da bakinta, ta kuma nuna takardar sakin sai aji yanda xa'abullowa abin.. yaya yayi ajiyar xuciya ya nemi guri ya xauna, amma fuskar nan har yanxu a turnuqe, ya kalleni cike da tausayi kiyi haquri nazia kidaina kuka Allah xai saka miki idan ya yaudareki ina takardar sakin naki,?? Nazia ta bude baki dagyar muryanta duk ya dushe.. yana gidan! miyasa bakixo dashiba, mantawa nayi dashi. gobe xamuje ki dauko kayanki da kuma takardar Allah ya sakamiki!!, ana cewa ya natsu ashe da sauransa, ni da ganin idinsa nasan baida kirki mutum banxa ay dama nasan xaiyi fiye da haka....!! Inna ta kalleshi rai a bace waikai lafiyanka? waya gayamaka ana shiga tsakajin mata da miji.?? wallahi xasu baka kunya daga baya ana ma magana kamaida ni mutuniyar banxa...! ai inna duk ke kika janyo tun farko ni banso auren nan ba amma kika nace sai anyi sannan yanxu ga wulaqncinda yaI mata kina cewa abari sai anga takarda, kawai inna kisa mana ido dan ba qara bari xamuyi mu maimaita kuskuren farkoba dole in nemawa qanwata yanci dan anga bamuda uba..!! Karo na farko da yaya yaqi sauraren inna idan tana magana, haka idan tana magana ya maida mata amsa.. mamakin duniya yacika inna tasaki baki sululu tana kallonsa, Lallai baitaba mata hakaba, kawai bari ta barshi har ya sauko sannan su fahimci juna.... [11:38PM, 2/13/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA?5⃣8⃣ na hauwa m. jabo. har ya sauko sannan suyi magana su fahimci juna. ya tashi fauuuu... har yakai qofar fita ya juyo ke nazia xo muje, na kalli inna naga ta dauke mana kai na fuske abina nabi yaya ina dan dingishina. part din yaya muka wuce da yake an gyarashi tunda yaya ya kusa aure da zainb khalifa.! mukaje sashensa muka xauna a parlour yaya yaso yamin magana amma ganin fuskata yanda na harqitse yasa yaja bakinsa ya dinke, amma ransa a bace, ki shiga dakina ki kwanta ni xan kwana anan kamin gobe muga yanda xa'ayi.. ba musu na amince dan bayana kamar ya bude dan xafi gashi na jiqe sharaf da jini, ina buqatar xagayawa in kimtsa jikina... na tashi naje dakinsa.. direct bayi na wuce dan in gyara jikina saidai kuma ba pad sai da tissue nayi amfani na watsa ruwa na fito.. ina fitowa na nemi guri na baje. abinka da mara lafiya ga gajiya nandanan bacci yayi awon gaba dani... A bangarennura ko kuma muce deen, ya gama rudewa ya zare kamar wani dan gwaya.. dama hulwarsace matarsa?? dama itace a gidansa bai saniba?? yanxu tana dauke da cikinsa! waima ya xaman cikin yake shege ko mai uba.!?? dana ba shege bane! dana dan halal ne koda bada sanin junan mu muka sameshiba.! dayan bangaren xuciyarshi ya bashi amsa, ina qaunar dana fiye da raina! lokaci daya qirjinsa yayi wani mummunan bugawa daya tuna cewa ya saketa!! ya tuna wulaqancin da yamata. anya xata yafemin kuwa?? bangaren xuciyarshi ya bashi amsa da xata yafe masa tunda tana sonsa!! amma yana tunanin baxata taba yafe marba..... yafi yarda da cewa baxata yafemar ba. kuka ya saki kamar qaramin yaro ya durqushe qasa lallai na yaudari kaina na yaudari soyayyar da hulwaty ta nunamin... [12:08AM, 2/14/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA??5⃣9⃣ Na hauwa m. jabo.. ta nunamin, ya rasa yanda xai yi da rayuwarsa, xuciyansa kamar ta fito dan baqin ciki da damuwa babban burinsa ta isa gida lafiya..! waima da wane ido xai kalli iyayenta dama nashi iyaye iyayenta sun mai karamci tun tana jinjira ya nemi a bashi ita kuma aka bashi aka ijiyemasa ita tun lokacin har ta isa aure lallai ya xalunceta, koda baya sonta baidace ya mata abinda ya mataba, kodan karamcin da iyayen ta suka mai , mixaicewa iyayensa idan sukaji cewa ya saketa.!? yanxu yake tuna maman nihal ta taba cemar nazia nada cikii yana kallonsu wani iri har yake ce musu shi ko ganinta yayi baxai ganeta, ashe da gaske hulwarsa tana dauke da cikinsa..!! Lallai ya tsuke tunaninsa ya akayi bai ganetaba? ya akayi bai gane sunantaba..!? Ta taba gayamin sunanta nazia amma tace babanta yana kiranta da hulwa, so tafison sunan shi yasa bai gane sunanta na asali ba. ya tuna lokacinda xai siyamata ticket daga abuja xuwa sokoto yaga sunanta Nazia muhammad amma baiganetaba.! duk tunanin daya dauko baya kaiwa qarshensa, yaga ba yanda xa'ayi ya ganeta, amma hadda jahilci yayi mai yawa . yanxu yatuna ya kirata hulwarsa da jahila ashe nine jahilin nine daqiqin nine axxalumin yaci gaba da kuka hadda gunji kamar qaramin yaro.... nihal tana parlour tayi jigum tajiyo kamar ana kuka ta leqo taga lallai uncle dintane yake kuka..!! itakam ta rasa gane komai duk tunaninta bata samun amsa, lokacinda xata iso Mamanta tace kada ta riqa barin antin nata da aiki dan tanada juna biyi (ciki) lokacin da taxo uncle da aunty nazia sun nuna basu ma san juna ba.!! duk tunanin ta bata sami amsaba. taja ta tsaya qofar dakinsa. tana tsoron ta shiga dakin ya balbaleta da masifa gashi ya gargadeta.. ganin kukan da yake ya tsananta da wani gunji da yake yasa bata tsaya wata wataba ta fada dakin taje gunsa cikin tsoro, uncle miyake faruwa?? kamar baijitaba ta qara maimaita tambayar har saida ta tabashi da qarfi sannan ya dago ya kalleta yanda taga ya chanxa ya hargitse lokaci daya abin ya bata mamaki da tsoro.. kodai yanada aljanune?? ta kalleshi uncle mi yake faruwa ?? ya kasa magana amma dai ya daina kukan da yakeyi, ya dago ya kalleta abin tausayi dashi " koda ni jabo bancika jin tausayin maxaba dan basuda kirki amma yadan bani tausayi kadan��" ya bude baki nihal xaki timakeni???. Eh uncle xan taimakeka..!! kinyi alqawari!?? Eh nayi..! Duk wahala??? Eh.!! nihal talk tome ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali kimin alqawari idan kowa ya gujeni ke xaki tsaya tare dani xaki rufamin asiri..!!? Uncle na maka alqawari duk wuya duk wahala xan kasance tare dakai har qarshen rayuwata...!!! ___________________ kuyi haquri kun jini shiru wallahi nayi busy ne da yawa wannan ma a train na rubuto mukushi idan na dawo xan kammala. [1:07AM, 3/21/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 6⃣0⃣ Na hauwa m. Jabo. Har qarshen rayuwata. Yaji dadin alqawarin da nihal ta daukar masa yasan kuma akwai ta da jajircewa akan abinda takeso idan har ba wulaqanci a ciki. ta yarda dashi saidai tunaninsa daya ya xasu bullowa abin., ? Dolene ya gayawa nihal gaskiyar abinda ya faru anya zai iya kuwa? tabbas baxai iyaba zai tonawa kansu asirine kawai wannab sirrine tsakaninsu baidace kowa yajiba. zaidai san yanda zai bullowa abin. Nihal dai tana zaune tana kallon uncle dinta duk da ya daina kuka amma yana wani gunguni gunguni dukkan alamu dai ya zautu ta kira sunansa uncle ya dago ya kalleta, au kinanan? Ai Kina iya tafiya, tace to, ta tashi ta tafi cike da saqe saqe a ranta haka yaci gaba da tunane tunanensa yana kuka har barci yayi awon gaba dashi.. Bai farka ba sai guraren asuba ya tashi idonsa sunyi hulu hulu ba kyan gani. Maimakon yayi sallah sai ya wuce dakin hulwarsa yana shiga ya dauki turarenta yana shinshinawa hadi da hugging din kwalbar turaren yana kwalla kamar wani xararre ya tashi yana yan tabe tabe tabensa har yakai gun wayarta battery low ta mutu ya jona chaji komi yake nema oho ya dauko hand bag tinda yana lakube anan yayi karo da takardar sakinta da magungunab.! vai duba maganin kona miye ba tunda yasan tanada ciki xai xama maganin masu cikine. Aranshi Wato bata tafi da takardar ba "yama manta da cewa suma tayi a hanyar hosptl ta farfado tace a kaita gida" lokaci daya baqin cikinsa ya dawo farin ciki yayi wani murmushi bada bata lokaciba ya shiga bayinta ya yayyaga takardar yayi xuba a bayi yayi bayan gida akai�� ya kora rowa yayo alwula yaje yayi sallah... Allah kadai yasan abinda yake saqawa a ranshi har gari ya waye yana laximi akan Allah yasa ta yafe masa su dawo normal... Yaxo ya sami nihal ta hada mai break fast bai iya ci sosai ba yadan taba dai kawai duk dahaka nihal tayi mamakin sakewar da yayi akan jiya. Nan xarginta ya qara tabbata akan uncle dinta yanada jinnu dan su suke haka one time kuma kamar ba'ayiba Taso suyi magana sai kuma ta basar tunda jinnu ne baxai tuna komai ba....!! Naxia bata farka ba sai guraren 8 na safe duk jikinta ya qara ciwo sabida batasamu tasha maganiba, ta rarrafo taxo palo ta sami yayan ta bayanan tasan ba gurin aiki yaje ba dan sai 10 yake tafiya aiki?, tayi tunanin bari taje kitchen ta hada tea ta kora tana xuwa taga yayanta tana fere dankali abin ya bata dariya dan bata taba ganin yaya a kitchen ba. duk ya xubar da rabi garin ferewar aranta tace lallai zainb khalifa xatayi fama ko irin mata bataji dadiba miji ya tayata girki da dan ayuka yaya kam ba abinda xai tabuka. Ta kalleshi ta gaidashi ya amsa cike da fara'arsa hadi da tausayin yar marainiyar qanwarsa!!! kin tashi tace eh.! Ka kawo In qarasa yace aah ki barshi xan qarasa kina baquwar tawa sukayi dariya... AI yaya a wannan duk ka xubar da rabin dankalin yayi murmushi ina practice ne kamin maaadam taxo dariya ta kamani amma na fuske wato zainb khalifa ce maaadam. lallai rayuwa mai juyi da yanda yaya ya tsani xainb khalifa amma yanxu itace wacce yake burin ta xama uwar yayansa.... Kije ki shirya muje gidan wancan yaro ki dauko takardar sakinki da kayan buqatarki. No yaya muje a haka kayana duk suna chan gidan. Kije ki duba wardrobe dina zaki ga kaya ki xabi daya ki saka Naje dakin abin ya bani mamaki ganin kayan mata kamar wani qaramin store ta dauki wani dogon riga baqi ta saka duk da ta rame amma kayan su. Karbeta sosai. Koda ta fito harya qare hada musu break fast ta xauna suka ci lallai taji yunwa rabonta da abinci tun jiya da safee.!! Suka fito sukaje sashen inna suka gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa suka gaya mata zasuje gida nura in dauko takardar sakinna da kayana har sunkai bakin qofa inna tace ban yarda kuyi chin mutunci da kowaba yaya ya amsa da insha Allah..! Suka isa unguwar tunda suka isa unguwar qirjinta yake dukan uku uku har suka isa gidan suka iske gidan a bude suka shiga nihal "sis khadee" sukayi karo da ita a palo tana chatting fuskarta cike da fara'a da gani ita da ammar suke soyewa koda bansan still suna tareba. Tana ganin mu tayi shock xunbur ta miqe ta gaidamu cike da fargaba yaya ya amsa mata rai a sake direct dakina na wuce abu na farko danayi karo dashi yasa nasan an mini bincike dakin cike da qamshin turarena kamar anyi wanka dashi hand bag dina komai an juye a saman gado waya a chagi haka dai ta tattare kayanta na buqata amma ta nemi takardar sama da qasa bata ba labatinta.! wayarta ma dagyar ta ganta dan a chaji take ta fito a sanyaye tacewa yaya bataga letter dinba da kuma yanda ta sami dakin anan suka gane yayi bincike ne kuma shi yadauke takardar ran yaya ya baci matuqa ya kalli sista khadee ke ina nura?? Bakinta na rawa tace Yaje office ya dauko wasu takardu har suka gama xaman jira bai dawoba an kira wayar a kashe suka tafi gida sunje sun ma inna bayani tayi tagumi batace komai ba. Anan aka xauna ake tambayata da wane dalili ya sakeni yaya yake cewa kodai da nihal kuka sami sabani nace aah na rasa abinda xan fada....... [1:54AM, 3/21/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA6⃣1⃣ Na Hauwa m. Jabo. Na rasa abinda zan fada na sake fashewa da kuka, shikam yaya ya rasa abin fada sai kawai ya tashi ya fita abinshi nayi kukana, inna dai taga kukan bamai qarewa bane tazo tana rarrashina har nayi shiru. Guraren maqreeb yaya ya dawo ya sameni nadan saki jikina baicemin komaiba har zai fita inna ta kirashi ta tashi ta shige daki ya bita baya bansan mi suka tattaunaba naga sun fito abinsu. Ya qara wuta inna bata min magana nima bance musu komai ba har nayi Kwana biyu a gida. Ina duba wayata da yake na dan saki jikina kadan kuma na warware rashin lafiyarda nayi dan inashan magani akan kari. Ina karanta wani hausa novel a group din hauwa m jabo sai wata tace amata sending din wani pic ina dubawa kawai naci karo da hoton takardar sakina dana dauka zan nunawa deen lokacin dan inason inyi surprise dinsa.. sai yacimin mutunci yace bani bashi "dama na nuna mai tun lokacin zai gane tunda rubutunsane" sai naji maganar yaya da inna da guduna na fito na na nunawa yaya hoton takardar sakina yana dubawa baice komai ba ya ma inna bayanin takardar inna tace saina fadi dalilin sakina naga dai boye boye ba nawa bane sai kawai na bayyane musu komai na gaya musu bai taba kusanta naba yaya ya kalli inna inna ta kalli yaya cike da mamakin maganata sai inna tayi qarfin hali ke dan mijin ki ya sakeki kada ki maida mu mutanen banza, kinason kice cikin da kike dashi ina kika sameshi?? Ko kin dauka dan baki gaya mana kinada cikiba mu ba zamu ganeba ki chanza wata qaryar ba wannan ba.!!!! Inna ta karkade zaninta ta qara gaba ta barmu da yaya ya juyo ya kalleni yazo kusa dani ya zauna. Ya dafa kafadata nazia kiyi magana ki fadi gaskiyar abinda ya hadaki da mijinki wani ki mai sharri ko qire ko qage duk bai taso ba ki fadamin gaskiya kinji autar inna! Na fara rantse rantse akan ba abinda ya taba shiga tsakanin mu dashi iya abinda na fada shikenan ba wani ciki da nake dashi kawai dai nayi jikine hatta honey moon da mukaje kowa da ban ya tafi abinsha haka dai nayita tona asirin zaman mu amma ban fadi yanda muke dashiba.... Yaya kam ya gamsu dan bai sanni da qarya ba dama shi baiga ciki ba inna ta bashi labarin cikin wacce akace tanada tace ba haka bane miye nasu na qarya tawa. Ya shiga sukayi magana da inna ya fito ana maimaita maganar cike da jimami.... Zamu jirasu zuwa qarshen sati idan har danginsa basuce mana komai ba zamuje mu kwaso kayanki dan ba komawa zakiyi gidannan ba.. nura da nihal sun rasa yanda zasu bullowa lamarin nura daikam ya dawo kamar wani almajiri sai tarin qasun ba dayatara duk wanda yaganshi ada yaganshi yanxu yasan yana cikin wani hali, su kitsa su warware duk yanda zasu bijirowa iyayen zancen saki ba tare da tonon asirinsa ba a maida nazia sun kasa samun mafita nura ya rasa yanda zaiyi, ba wata mafita da yake da ita idan yace baitaba kusantar ba to cikin na uban waye waye?? Ga son duniya ya dauka ya gwallafawa cikin nan hawaye ne suke gangaro mai na nadamar abinda ya aikata nihal har ta saba da ganin kuka uncle dinta tuntana mai kallon mai jinnu har ta gane tsabar son da yake yiwa nazia ne da damuwar da yake ciki. A qarshe sun yanke shawarar kada su gayawa iyayensu ita nihal qarshen wannan satin zataje gidansu nazia suyi magana. "kaji wauta irinta yara wai nihal zataje biko" Nazia dai kam inna ta yarda ba tada ciki tunda bataga cikin ba yanxu kuma alamomi sun nuna haka tunda lokacin kullum idan sunyi waya da nura daga yace baya gida sai yace yana kan hanya sai yace tana bacci ko tana sallah hakadai bai taba baiwa nazia sun gaisaba kullum kwana kwana yake mata shima yaya ya yarda dan shima kusan haka ta faru ya kira nazia ina nura tace baya gida ya kira nura ya nazia yace tayi bacci bayan daidai likacin suka qare waya yayi tunanin wani abu saidai bainkawo komai a ransa ba haka dai kowa ya riqa fadin albarkacin bakinsa.. Nazia baqin cikin wulaqancin da deen ya mata yana damunta amma ba halin fada dan ita ta janyowa kanta sonsa ya rufe mata ido yanxu ga abinda ya mata tasha alwashin duk ya kuskura yazo gidansu sai tamai kaca kaca. Yau suka shirya kwaso kayanta da la'asar guraren biyu saI ga nihal a gidan inna dai kam bata ganeta ba tace gun nazia tazo. Inna ta kira mata nazia ta shige dakinta. Nazia ta fito da fara'a wa zata gani maqiyarta sista khadee. Nazia Ta wani daure fuska tasha magani ta zauna akan hannun kujera ta dora qafa daya akan daya tana girgizawa tana shan sweet..... sis khade ta gaisheta ta amsa da lfy a taqaice. Gunki nazo, aunty nazia idan zaiyiwu mu shiga daga ciki.. No.. Nan ma is ok nazia ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba. Ta hadiye yawu tayi qasa qasa da murya. Dama aunty akan maganar....... Ta dakatar da ita da hannu... Don't ever called me your aunty, am not & i will never be the one. I can hear you go ahead.! Ta qara kawar da kanta gefe.. Nihal Tayi ajiyar zuciya dama akan maganar uncle ne naxo dan Allah...... nanma ta qara katseta.. Shot your mouth up! you thinkless, do to most disgraced embrassemented matter you already done to me & your inrespective your mannerless, uncle do! But your came with another ovios alonatic thinking?. to let me tell you, kije ki fada ashawon uncle dinki idan ya isa yazo da kanshi ke banida lokacinki wawaye kawai, ran sis khade ya bala'en baci taji maganar har cikin ranta tasosu kuma taji haushin maganganun nazia amma ba yanda ta iya tazo gyara tayi barna.?? Ta dago ta kalli nazia taga yanda ta daure fuska tasha jinin jikinta ta rasa abin fada chan nazia ta juyo. Get out of this abode.! before I disgraced your personality now! Think less, stupid people haved to go and find an approach of manners & valuable of any mankind has wasing to you. Oya ga hanya ta nuna qofa get out.!! Ta fada da tsawa.! Sis khade ta gama qulewa tasan idan har taci gaba da zama faruwa naci ba nata bane mutuncinta yafi mata komai ta dauki jakarta ta fita kamin ta fita ta jiyo tsakin nazia think less kawai..! Nazia tasani sarai sis khade batason tsaki tasha fada da mutane a secondary skull akan tsaki dan kuwa da kamata tsaki gara ka waska mata mari... har ta tsaya sai kawai ta wuce rai a bace... Ta fada mota taja daqarfi tana fotowa gidan taja ta tsaya tana kwalla, lallai nazia taci mata mutunci da yake tasan weak point dinta shi yasa ta mata haka anya zata iya cika alqawarin da tayiwa uncle dinta kuwa da wuya dan bata daukar raini gun kowa wallahi. ta share kwallarta taci gaba da driving kamar zuciyarta ta fito dan baqin ciki ita zata cire hannunta dan tasan nazia da bala'en tsiwa komai zata iyayi.. Idan kuma ta juyawa uncle dinta baya wazai taimakeshi.?? Dayan xuciyarta tace wanda yasa ya saketa ya taimaketa.. [5:14PM, 4/2/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 6⃣3⃣ Na Hauwa M. Jabo. Sis khadee Tana tafe tana tunani yanda zatayi. qarshe ta yanke shawarar zame hannunta daga lamarin baki daya. ko banxa batasan abinda ya hadasu, ga rainin wsyo irin na nazia da bazata daukeshiba tayi tayi uncle ya fada mata abinda ya hadasu, saidai yace just help me nihal.!! a hakan zatayi helping dinsa batasan abinda ya hadasuba?? kawai zan koma gidane bana ganinsa ma bare ya bani tausayi...!! Da wannan tunanin ya isa gidansa koda taje ta tarar baya gidan ta tattara kayanta tayi gidan su, mamanta na ganinta taji tsoro kardai kun saida hali da matar uncle din naki?? Da yake ke nihal bakida hali ga zuciya kamar ta kasheki naga fuska duk a turbune... Sis khade tayi murmushi ta nemi guri ta zauna to umma yau baki chankaba, ta kwashe duk abinda idonta ya gano mata ta fada musu kuma lallai alamu sun nuna baima taba ganinta ba itama haka. Maman nihal tayi dariya.! kefa har yanxu yarinyace wata qila sabani ya hadasu amma mace hadda ciki kice basu taba ganin junaba. Nihal dai tayi qoqarin yiwa umna bayani har saida umma ta gamsu da dalilan da ta kawo mata dan kuwa taji har ya saketa da kuma ta fada mata da bakinsa ya fadi ya saketa din. amma kuma nihal din tace abinsa harda aljanu kam. Amma bari baban fati "abbansu nihal kenan" ya dawo muji yanda abin yake. Ran nazia yayi fari sol ko banxa ta gaya mata magana kuma tasan ranta zai sosu, taso taqi fita ta hadata da karen gidansu amma sai ta tafi. Ta shiga daki cike da farin ciki tasha maganinta ta shirya tana jiran yayanta. Bada jimawaba yazo suka je gidan mai gadi ya bude musu gidan suka tattara duk wani abu da sukasan nasune suka qara qaba.... Bayan isha saiga nura yazo gidan yana neman nihal yaga gida wayam!! Ba nihal ba kayan naxia abin ya bashi mamaki wato ya tura nihal gyara ta maibarna ko?? Zai kuwa chi ubanta.!! ( kaji wawa) yaje gun maigadi a firgice yana tambayarshi ya haka maigadi yamai bayani daga zuwan nihal har zuwan su nazia yana qarewa nura ya wankeshi da mari kaji taaasssssss!!! kuma yace sai ya dawo da kayan da suka diba dan bai bashi umurnin barin kowa ya dauki komai a gidan ba! ((kaji hauka ina ruwan maigadi ai sai yace sai ya dawo mai da matarsa bawai kayan matarsaba��)) Magadi yayi tsuru tsuru ya riqe kumce yana bada haquri nura ko saurarensa baiyiba yace yabar mai gidansa ya sallameshi ya wuce cikin gida a fusace. Dama su nura an iya kuka ya zauna tsakiyar palo ya fara kuka ba mai rarrashinsa cikin kuka ya jiyo magana sama sama koda ya duba sai yaga abban nihal tsaye yaxo gabansa yaja ya tsaya yamai kallon banxa ganin gidan ba kayan nazia ya qara tabbatar mai da cewa lallai ya saketa. Bai tausayawa halinda yaje cikiba ya haushi da masifa. Qarshe yace yadauka yazama mutum ashe har yanxu da sauransa! Sabida haka ya tattara kayansa ya bar wannan gidan dama albarkar nazia aka bashi wannan gidan nura ya tsananta kukansa basu barshi da baqin ciki rabuwa da mataraaba suna qara mai wani baqin ciki. Yayan nura yayi waya gida ya fadawa mamansu da babansu abinda yaronsu yayi itadai kam maman nura da taji abin kasa magana tayi dan tsananin bacin rai... nura baiyi halacciba sai kallo kallon suke itada mai gari "baban nura" maman nura tace a kira inna amma mai gari yace wannan mugun abin ya wuce waya saidai su tafi. da kanmu har gidan. tun da asuba iyayen nura suka baro qauye sukaxo birnin sokoto. Bayan sun dan huta suka kwashi jiki sukaje gidansu nazia bawai biko sukaje sunje bada haqurine. Koda Inna batasan zuwansuba ta musu tarba cikin mutunci da sakin fuska kamar ma ba abinda ya faru amma maman nura ta kasa koda hada ido da ita. Inna kam Sai neman ayi hirar bayan rabo takeyi amma duk sun kasa kunyar abinda dansu yayi ya ishesu. Chan dai maman nura ta fashe da kuka ta rungume inna tana bata haquri. Nura vai kyautaba! Baiyi halacciba.! Yaci amanar nazia.hakadai tayi ta sunbatu. inna nafadin babu komai har dai itama ta fashe..!! dan abin ya dade yana cinta inna kuka maman nura kuka dagyar dai mai gari ya samu ya rarrashesu sukayi shiru cike da kunya shima.....!! [5:22PM, 4/2/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 6⃣3⃣ Na Hauwa M. Jabo. Mai gari (mahaifin nura) yaci gaba da maga. dukan mu bamusan abinda ya faruba jiya ake gaya mana abinda ya faru, dan Allah kuyi haquri yaron ne basu da hankali kwata kwata, basu san halacci ba da nura yasan halacci da nura ko bayason nazia ai dan darajar halaccin da kuka masa yaci ace ya zauna da yarinyar nan, maigari dai yayi maganganu na ban haquri qarshe yake tambayar lafiyar nazia da lafiyar cikin ta. Inna ta musu bayanin da nazia tayi na cewa basu taba hada shinfidaba mamaki ya kama kowa ganin yanda ake fadar tanada ciki duk dangi sun sani amma yanxu ace ba ciki. Basu isa su qaryataba. Ana nan mai gari yaci gaba da cewa yanxu sai ayi haquri a maida auren inna batace komaiba sukayi ta bata baki har tace Allah yasa hakan yafi zama alkhairi ana haka saiga yaya hafez ya shigo shida zainb khalifa su zainb ana wani iyayi an sami saurayi dan gayu , suna zuwa suka ga baqi a gidan sama sama suka gaisa zainb ta wuce gun nazia, yaya ya zauna ayi dashi anan mai gari ya fadawa yaya buqatar su ta da amincewar inna akan maida auren. zunbur ya miqe. Baxata yiwuba.!! Akan me kuke playing dinmu? Ko dan kunga mahaifin mu ya rasu?? to nine gatan nazia kuma nice mahaifinta.!! idan har kukaga ta koma gidan wannan yaron to ita ta buqaci hakan. amma baxa'a qara wulaqantamin yar uwaba ya buga rigarsa zai fita. Inna ta miqe zata cimai mutunci akan rashin kunyar da take ganin yayi. mai gari ya takatar da ita yaje ya janyo hannun yaya hafez ya zaunar dashi. Hafizu bazamu taba tursasa nazai akan ta koma gidan nuru ba abinda kawai mukeso shine kada wannan zumunci namu ya lalace. idan har basu shirya kansuba zan turo Dr mustafa yaron qanina wataqila su daidaita kansu banason abinda zaisa zumuncin mu ya bace , maman nura bataji dadin hadin da mai gari yake shirin yiba tace insha Allah ma zasu daidaita kansu haka dai zaman ya kasance har guraren azzahar. Suka kwashi jiki sai gidan su sister khadee mai gari yasa aka kirawo masa nura bai bata lakociba yaxo ganin yanda ya zama lokaci daya abin ya basu mamaki da tausayi.!! Jikinsu yayi la'asar maman nura ta kalli autanta tama manta da aika aikar da yayi ta taso ta riqeshi tana tambayar lafitar shi. Ran yayan nura ya baci ganin yanda mamansu ta rude ganin halinda danta yake ciki ya daka mai tsawa hadi da cemai munafuki wallahi mama kuk kuke kulashi iskancine kawai.!! mama ta dalla ma abban nihal harara ta zaunar da shi. Palon yadau shiru chan mai gari ya fara yiwa nura bayanin abinda suka sani hankalin nura yayi mugun tashin dajin cewa tace basu taba hada shinfidaba, kuma batada ciki kenan ta zubar mai da ciki?? Cikin da ya daura ma son duniya.! Cikin da yake tunanin shine zai taimaka masa su gyara auren su. Ya saki wata irin qara saida kowa ya firgita a gurin yace......... [5:31PM, 4/2/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 6⃣4⃣ Na Hauwa M Jabo. wallahi ni ban saki nazai ba!! kuma qaryane tace bamu hada shinfidaba har cikina tana dashi wallahi.!!! kenan ta zubar mun da ciki?? Kowa yayi tsit.... sai kukan nura ke tashi a palon jikinsu yayi sanyi yayan nura yace dama nihal tace aljannu ne suka shafeka, inaga yafi kyau a bari sai yaji sauqi sannan ayi maganar. nura ya dallama yayan sa wata muguwar harara idonsa cike da hawaye sunyi jaa cike da fushi yace kaine mai aljannu baniba dama ka tsaneni baka sona daaga yau kai ba yayana bane..!! Duk palon saida kowa ya yayi dariya da maganar malam nura autan mamanshi... suka qara tabbatar da cewa yanada rashin lafiyar jinnu. dan kuwa ko musu bai taba hadasu da yayan saba kuma yana tsoronsa fiye da yanda yake tsoron iyayensa. Amma yana mai irin wayannan maganganu. kowa sai ya gasganta maganar abban nihal. Ya taso yaxo ya rungume qaninsa yana rarrashi cike da tausayi shi kuwa sai wani qace jikinsa yakeyi.!! Haka dai zaman ya qare ba wata natija. Da dare maman nura ta bi nura dakinsa suna magana ya qara jadda dama abinda ya fada farko cewa bai saki nazia ba idan ya saketa kuma ina takardar saki?? Nan fa duk da cewa tana mai kallon mara lafiya ta gasganta maganar sa. Bayan ta fito ta samesu a palo suna tattauna maganar akan a nemowa nura magani anan maman nura tace idan har da gaske ya saki nazia ina takardar sakin take?? yaka mata fa idan za'ayi abinnan ayi adalci bai yuwa ace autana ne kawai bashida gaskiya itama da laifinta. Sukayi shiru lallau yakamata ace ga takardar saki bawai kamar yan da inna ta musu bayaniba wai sakin a waya ne. Haka dai aka qare akan za'a nema mishi magani idan yaji sauqi sai a hadasu su biyu a aji gaskiyar maganar.! Haka kuwa akayi an kai nura gun mai ruquya aka danna mai maganguna da hayaqi kala kala. kamar gaske bayan kwana uku yadan da normal amma fa bai daina hararan yayansaba kuma baya gaidashi ba yace duk ya hadu da nihal sai ya kakkaryata dan gani yake zuwanta gidan su nazia yasa komai ya qara lalacewa bayan tace zata taima keshi..... [5:54PM, 4/2/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 6⃣5⃣ Na Hauwa M. Jabo. ********************* An shirya zama kowa yazo hadda su nihal an hallara. Aka fara maganar kowa ya fadi albarkacin bakinsa amma nura yaqi saukowa akan cewa ya saketa. Akayi sama akayi qasa amma yaqi yarda yace idan har da gaskene to ta kawo shaida a rubuce dan ba zasu yarda da waya ba, wannan zamanin komai ana iyayi. qarshe nazia taga ba nasara a gunta ta miqe taje daki ta dauko qur'ani tazo gabansa ta tsuguna ta miqa mai qur'anin tace idan har yayi rantsuwa da wannan qur'anin akan cewa bai saketa ba, zata koma gidansa yau dinnan.!! Nura ya rasa yanda zaiyi sai zufa ke keto masa.!! Chan dabara ta fado masa ya karbi qur'ani yace zaiyi rantsuwa amma itama tayi alqawarin cewa zatayi rantsuwa akan cewa basu taba hada shinfidaba kuma bata dauki cikinsa wata huduba. Qaqaqara qaqa.... Suka fara kallon kallo tsakaninsu palon yayi tsit ana sauraren wannan lamari nasu.! Nazia ta karbi qur'ani jiki a sanyaye tace kamin ka rantse ni zan rantse. ta riqe qur'ani hannu bibbiyu ta rufe ido tana hawaye... Tace Ni nazia muhammad na rantse da darajar wannan qur'anin!! A matsayina na matar nura ta sunna bai taba kusantana da sunan raya wannan sunnar aure ba daidai da second daya saidai ya......... tuni nura ya taso yarufe mata baki ganin zata fallasa sa dayan mugun aikin da suka aikata.! wanda baya fatar hakan ta kasance har qarshen rayuwarsa.!! Bayason Iyayensa susan halinda ake ciki. Tausayin nazia ya kama kowa yayan nura ya haushi da fada akan me xaka hanata fadar gaskiya? ? Ta tabbata kenan bakada gaskiya.!! kamaida mutane sha sha shai. Yayan nura yazo gaban nazia yace mata nazia ci gaba saidaime??? Nura baisan lokacinda ya juye bakiba da harshen farisanci da suka koya tare da nazia tun kamin suyi aureba yace mata (( nazia turo khuda asrari moro pakhsh nakun na bi khatiri man bi khatiri khuda.....)) ta dago ta kalleshi harga Allah ya bata tausayib yanda ya hargitse da kuma yanayjn sautinsa ko banza tana sonsa ta kalli yayan nura tace mai ba komai. Nura yayi ajiyan zuciya yayansa ya kalleshi ya rasa bakin magana tunda baisan mi yace mataba.!! (( nima hauwa jabo saida na tambaya aka fassaramin abinda yace kuma bazan fassara mukuba ��)) nihal ta taso taxo ta qarbi qur'ani itama tayi rantsuwa akan cewa lokacinda tana gidan uncle ya fada mata da bakinsa ya saki nazia yakai sau 50. Ta fadi yana yawan maimaita cewa ya yaudari nazia ta taimaka masa..... Mai gari yace kada ku maida qur'ani abin wasanku mana. Ya karbi qur'ani hannunun nihal ya koma ya zauna kowa yayi shiru ana jiran gogan naku nura mayaudari yayi magana amma kamar ruwa yacishi yayi tseeeeet.... [9:22PM, 4/6/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA?? 6⃣6⃣ Na Hauwa M. Jabo. Nura mayaudari yaqi magana kamar ruwa ya cishi yayi tseeeet.! Palo ya dauki shiru kusan minti uku ba wanda yayi magana ana sauraren nura mayaudari. Chan ya dago kai ya kalli hulwarsa yaga yanda take zaune a natse amma da gani a kwai damuwa tattare da ita tausayinta hadi da wani qaunarta da yakeji ya qara kamashi, ya tuna maganganunda ya fada mata lokacinda tace tana da ciki wato zafin maganar ne suka sakata ta zubar da cikinsa kenan? miye laifinta ma tunda shi yace ta zubar ba ruwansa.! Idonsa sun cika da kwalla ya sunkuyar da kai yace.... Baba lallai na saki nazia saki daya!! Lokacinda na saketa bansan cewa itace matar tawaba! Kuma ni dauke takardar sakin dana mata na yaga dana fahimci itace matar tawa, dan wallahi inason nazia baba fiye da yanda nakeson raina bazan iya ruyuwa ba itaba yana magana murya na sarqewa.! Maigari yace alhamdulillahi dama munason muji gaskiyar magana, kuma gashi kun fada da bakinku. amma cikin maganganunku akwai abubuwan da ban ganeba.! Kace lokacinda ka saketa bakasan itace matarkaba!! Kenan kasanta tun farko kenan?? Itama tace baku taba saduwa da sunan aureba saidai.... sai ka hanata qarasa magana wanda yake nuna kamar kunsan juna kamin aure ko makamancin haka Sai maganar ciki da kakeyi wanda kowa ya shaidi tanada ciki kuma akazo aka rasa cikin yanxu. Ka nuna baka taba saninta ba baka ma taba ganinta ba ya akayi kasan tanada ciki?? Hakan ya nuna akwai wani boyayyen lamari da mu bamu saniba yanada kyau muma a mana bayani.! Lokaci daya nazia da nura suka kalli juna kamar hadin baki sukace wallahi baba!!! sai dukansu sukayi shiru,, babu kom..... nan ma hada baki sukayi suka qara yin shiru nura ya qarasa maganar da cewa baba ba komai tsakaninmu baba! Maigari dai bai gamsu ba sauran mutane ma tambayar maigari ta sakasu cikin tunani yanda suka hada baki ma ya nuna rashin gaskiyarsu a bayyane, yaya nura yace tunda dai munji haqiqan abin shikenan wani bincike bai tasoba baba koma miye wannan tsakaninsu ne rashin kyautawa ne dai nura ya riga yayi muna dada bada haquri. inaga shikenan kawai. anan dai akayita bada haquri akan qara abinda nura yayi aka shigo da maganar komawar nazia, yayan nazia yace abarta ta huta daga baya ayi wannan zancen, nazia da qarfin hali tace ni na bazan koma gidansa ba na amince idan na qare idda xan zamu daidaita da Dr mustafa idan mun shiryasai muyi aure. Ke hulwaty..!!! Kinada hankali kuwa?? Kinsan abinda kike fada?? Da aurenki kina tunanin wani namiji ko?? Ta dalla mai harara da murguda baki aure kuma?? Ai yanzuu hulwa ta mai raboce haka suka fara musanyar magana sun ma manta akwai mutane tare dasu kowanne cike da kishi da bakin cikin rabuwa da dan uwansa!! Harga Allah naxia dan ta bata masa rai tace zata aminta da Dr mustafa bawai dan tanasonsaba. Dukansu abin ya basu dariya yayan nura yace shikenan ya isa! Nura ya kalli yayansa cikin kwalla yace yaya kanajin abinda take cewa ko?? Nura yama manta da baya ma yayan nashi magana!! Tausayin qaninsa ya kamashi yace kayi haquri ta bari zamuyi magana daga baya.! Haka dai abu ya qare, zaman baiwa nura dadiba idan ya tafi ina zai qara ganin hulwarsa. Kowa ya watse aka qara qaba.... ************************** Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yau wata shida abubuwa sun faru na baqin ciki da farin ciki nura ya zautu kamar bashiba ya dawo ustaz baya magana sosai abinci kadan yakeci ba wanda yake ganin walwalarshi yayi yayi akan hulwarsa ta haqura ammabina tqqi haqura. yayi kamun qafa gun yayanta sai yace ya nemeta su daidaita ta chanxa layi baya samunta. Jin dadinsa daya qin yuwar aurendu da Dr mustafa yanaga da mutuwa kawai zaiyi. Naxooo tun kan ta qare idda yayanta ya samo mata admtn a dan fodiyo ta fara karatun ta amma soyayyar mijinta tana mata yawo akai ta tabbata har abada ba zaata daina son deen ba saidai tana barwa cikintane tunda ba yanda zatayi.....! Kaji sona gaskiya. [9:35PM, 4/6/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA6⃣7⃣ Na Hauwa M. Jabo. ****************** Yau nazia ta fito lecture tare da sabuwar qawarta da tayi mai hankali da natsuwa Aysha ameen sokoto wacce haifaffiyar sokoto ce yarinyar nimw kaina jabo nq yaba da natsuwarta amma najma ake kiranta dashi yarinyar akwai ilimi kamar ana mata wahayi ga natsuwa da hankali, abinda yasa tasu taxo daya da nazia kenan duk da naxia akwai tsiwa amma tadan natsu yanxu.! Suna tafe suna tadi har suka kawo gurin cin abinci sunyi letti ba sakwara gashi ita sukeson ci sai sukace to su fita wajen makarantar su siyo a motar najma ameen aka tafi motar sukaje Dady smart anan suka yada zango sunyi sa'a akwai sakwara a gun suna ci suna tadi anan nazia take cewa taji qamshin wani turare mai tayar mata da hankali yanayinta yadan chanza amma ta fuske kada najma uwar wayo ta ganota.! sunci sun qoshi, suna dati sama sama daga sama taji muryar da ko cikin bacci ko mutuwa tayi ta dawo taji muryar zata ganeta rabonda ta ji muryar wata shida kenan. Muryar deen dinta ne yake kiranta hulwaty!!zunbur Ta miqe cike da mamaki ta kalleshi ya chanxa gaba daya. ya tara suma a fuska sai kuma ya mata kyau! chan ta tuna da chin mutuncin da ya mata ta daure fuska Malam lafiya ?? Kawani xo ka tsayawa mutane akai.? Najma kinsan shine? Gurinki yaxone? Najma ta kurba malt ta kada kai alamar aah. Ta watsamai kallo da dara daran idonta masu rudar dashi tace to malam sai anjimako. Yaja ya tsaya yana kallon ikon Allah hulwa ce take nuna cewa bata sanshiba! Da taga ya kafe kamar an dasa ice sai ta zargu tacewa najma suje. Suna kan hanya najma tana driving tace waye wannan mutumin na dazu?? Nima bansanshiba ta bata amsa a tsanake, Najma ta murmusa dama akwai wayo najma ko hanjin mutum tana gani! Amma acting dinki ya bayar dake naxoo, alamu sun nuna kunsan juna ! kuma kunyi kewar juna! kuma kunason juna! kuma kun tsani juna! kuma..... Is ok phycologist!@ ke haka kike kullum da fassara ni ko mai kama dashi ban taba ganiba sai yau najma ta qara murmusawa naxoo ki gaymin mana duk maganar da najma take bata kalli nazia ba tuqinta take hankali kwance, amma hajiya nazia hadda xufa dan kuwa ta rude tasan najma smart girl ce amma batayi xaton xata gane haka da sauriba. Sai ta basar da maganar. kai yaufa zamu shiga hannun Dr shu'aib kinsan bamuyi assignment dinsaba ko? Najma ta ganota sai ta shareta itama ta murmusa tace Eh yanxu muje muyi kamin mushiga lectr. ahaka har suka isa makaranta... Naxia kam duk ta rude ganin deen tsohon abu ya dawo mata sabo, ta samu dagyar aka tashi ranar batayi bacci ba dan tunani!... ********* Nura kuwa binsu yayi a hankali har yaga inda suka shiga. Tun daga ranar dan fodiyyo ta zamo mishi gida har ya gano department dinsu hulwarsa. Ranar nazia ta fito shago ta siyo musu malt najma na hall tana jiranta sai kawai tayi kichibic da nura. Tsoro ya cikata. Haba hulwa miye duniya karki manta deen dinkine masoyinki mijinki... Ta katseshi da daga hannu, ✋ That was then..! but now lost substances value & no regard before me.You are completely out of my mind, you are neither trusted nor reliable. Please find your way live me alone.!! Bata jira amsarshiba ta qara gaba abinta malt dinda batasha ba kenan zuciyanta tana quna amma taji dadin maganganun da ta danna mai ko banxa tasan ya yaji haushi.. Najma ta kasa gane kan nazia qarshe naxia tasa kuka dagyar najma ta rarrasheta.!! [1:59AM, 4/7/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA??6⃣8⃣ Na Hauwa M. Jabo. Bayan tayi shiru ne take tambayarta abinda ya faru anan nazia ta baiwa najma labarin komai amma bata fadi mugun aikin da suka aikataba.. Najma ta murmusa I know that. ! Na fahimci akwai wani abu tsakaninki da wannan guy din tun ranar. na barkine kawai dan naga bakyason maganar.! Amma miye aibi tunda yayi regret ku daida kanku mana?? Kinasonsa yana sonki mistk ba wanda ya wuce yinsa inaga kawai ki haqura nazooo ku maida aurenku. Ashe kin taba aure bansaniba.!! shine idan ana zancen banana kike fuskewa kinuna mana irin u don't now everything. Kai nazoo kin burgeni u are so smart more than me wallahi nazoo tadan dara batace komaiba.! Haka najma tayita rarrashinta tana bata haquri har tadan saki rai suka rabu akan zatayi tunanin akan shawar da najma ta bata, koda ta aminta saita walfa nura.. Nura kam yasha wulaqanci kala kala a gun nazia wanda sam baya damuwa burinsa ta amintace masa su maida aurensu. Tunda yaqara sakata a ido ya kasa sukuni da walwala kullum yana dan fodiyyo (( nidai jabo nace kawai ya nemi admtn makarantar ya fiye masa yawon hanya��)). Wannan karon ma nura ya tare nazia tare take da najma ya mata magana kamar yanda ya saba itama ta bashi amsa kamar kullum, ta nunashi da yatsa waike wane irin mutum ne?? And I won you not get to any of my bussinees any more.It also look like you don't have human conscious & moral values. Leaves for your own interest. Ta murguda baki ta wuce abinta. Ran najma ya bace ba kadan ba, kuma tasan duk randa nazooo taga nura tamai cin mutunci sai tayi kuka tana dana sani abinda ta aikata Najma ta kalli nura ya bala'en bata tausayi sai ta wuce su dukansu tabar nazai ita kadai tayi kukanta har ta qare ba mai rarrashi.... Ran nazia ya bace wato najma laifinta ma take gani abinda takema nurako duk zata raba jaha dasu. Gobe sai taqi xuwa makaranta wasa wasa nazia saida tayi sati daya batazo skull ba ba nuraba hatta najma hankalin su ya tashi nura yaga najma ya daure ya tambayeta tamai bayanin rashin xuwanta ya bata haquri akan kada tayi fushi da aminiyarta akanshi. yakamata ta kira taji lafiyarta tunda bata saba fashin xuwa makatantaba. ya karbi number najma akan xata sanar dashi lafiyar nazoo idan sunyi waya. Naxai kuwa ta sharawa inna qarya da yake inna ba yar boko bace tace sun sami dan hutune. Inna tahau ta zauna. Bayan tafiyar nura najma ta kira nazia amma taqi dauka takira yafi sau biyar amma shiru ba labari, bayan lecture ta wuce gidan su nazoo. A palo ta sameta nazia ta daure fuska najma ta kwashe da dariya taja hannunta tana kwacewa har dai suka shiga daki. Ta ijiye jaka taje ta gaida inna ta dawo ta bude fridge ta samu malt daya ta bude zatasha nazoo ta kwace daga bakinta ta harareta tace: dan uwanki nura bai siyo mikiba!!? Maganar ta baiwa najma dariya tace ya siyomin gata a jaka ba sanyine ta bude jaka ta fito da malt ta bude xatashi naxia taqara kwace wai baza'asha abin nura a gidansuba. Najma kam dariya Abin yake bata dagyar ta samu naxoo ta dan saki jiki sukayi nagana ta fahimtar juna. Ta bata shawara har cikin ranta taji dadin maganar suka shirya suka dawo kamar basune suke rigima ba nazia har tana tambayar najma da gaske shi ya siya mata malt tace wasa takeyi wallahi ita miye hadinta dashi a hanya ta siya suka tafa ta tafi.... najma ta kira nura tamai baya ni nazia lafitanta lau da sauran bayanai kuma tace zata taimaka masa. amma bata nuna mai cewa naxia ta haquraba tadaice yaci gaba da addu'a kuma yaci gaba da mata magana... ********** Kamar kullum sun fito lecture tace a bari ta samo musu dan cake da malt susha da yake nazia mayyar malt ce ta hadu da wani course mate dinta da yake mutuwar sonta mai suna ahmad. ahmad Allah ya jarabceshi da son nazoo amma daidai da rana daya bata taba bashi fuskaba sama sama duke gaisawa yauma sun dai gaisa sai suka jera tare har shagon suka dawo. A kan hanya ya bata labarin ban dariya ta kyalkyale da daria dago kanta da zatayi sai taga deen gabansu ya daure fuska kamar ance maigari ya mutu. Keeeeee waye wannan?? Ashe bakida hankali bansaniba?? Kina da aurena akanki kike tsayawa tare da samari?? Kin manta........ shot your mouth up.! Don't ever called me matarka.! Am not & I will never be the one! So yafi kyau kasan inda dare ya maka!! Ta watsamai harara. ahmad yace malam an rasa hanyar da za'a bullone sai aka fake da cewa matanace so sai a nemi wata hanya bawannan ba. Naxoo ba tasan lokacinda ta kamo hannun ahmad ba tace muje ko baby na.!! Tuni idon nura sun rufe ya wanke nazia da wani wawan mari. Ahmad ya daga hannu zai rama mata nura ya riqe mai hannu..... Boy! Don't make the mistake of bullying me...! And for your information, you made a great mistake the other time because she's married to me, any time I sight you talking with her, you'll rest behind the bars... Ya sakeshi da qarfi. [2:08AM, 4/7/2015] Auntie M. Jabo: A SHE KAINE MIJINA6⃣9⃣ Na hauwa m. Jabo Ya sake mai hannu da qarfi & ka bace min da gani! ahmad yaji tsoro, ya matsa baya sai na hadaka da security wallahi ya wuce yan surutai ya juyo gun nazia. kada kiga ina nibiyarki ki nemi wulaqantani gaban mutane.! Ke har kin isa ki rqee hannun namiji a gabana wannan ya....!! Ta kalleshi ido cike da hawaye murya na rawa ta rasa abin fada mai yaji haushi, duk fasaha ta bace mata. I definitely loved you before I know your dirty hidden color. Learn your lessons as appropriate.... I really hate you deen...!! Ta bi ta gefensa ta wuce ya rasa abin fada waima shi da yake neman sulhu mixai kaishi marinta?? Ya dungule hannu ya daki iska ya wuce abinshi. Abin mamaki nazia sai bata fadawa najma abinda ya faruba tunda tasan batada gaskiya kuma ta mata alqawarin xata daina wulaqanta nura.! Tana xuwa tace miya tsayar dake haka tace fada na tsaya kallo security sukazo garin gudu aka bigemin fuska. ayyah sannu.!! ************ Tun daga ranar nura bai qara xuwa makarantarsuba harkwana hudu.! Nazia tadamu tana kallon cewa abinda ta masa ne yasa yaqi dawowa gashi ba halin magana, Naxoo xamuje gidan uncle dina na karbo saqon umma please tunda bamuda lecture sai 4.. naxoo ta aminta sukaje, a hanya najma sai danne dannen waya take a mata sms itama tayi har suka isa gidan ba kowa maigadi ya gaidasu ya basu key suka shiga najma tace ta zauna ta kawo mata lemu. Ta kawo mata lemu ta shiga wani daki ta dauko wasu ledoji ta fita tace mata idan kun shirya ki mini waya inxo mu koma skull..!! Nazia ta miqe tsaye banganeba malama mi..... ta budebaki da mamaki miya kawo nura nan gidan?? Yasa key ya kulle qofar ya maida key aljihu ya matso kusa da ita tsoro da mamaki suka kamata wato set up ne suka mata ko?? Ta rasa bakin Magana sai ta nemi guri ta zauna. Nura ya matso kusa da ita ya tsuguna yana fuskantarta qamshin turarensa ya daga mata hankali amma ta fuske.... nura ya fara bata haquri akan marin da ya mata a skull gaban saurayinta, nifaba saurayina bane! Ok. Koma miye kiyi haquri ta kawar dakai. Nura ya shiga aikin rarrashin nazai yana magana yana kuka alamu sun nuna yayi dan dana sanin abinda ya aikata. Ita dama tuni ta yafemai kodan ganin halin da ya shiga, (( kaji mace idan dai tanason namiji tsakani da Allah wallahi komai ya mata zata haqure)) batace dashi komaiba ganin ya tsananta kukanshi ne sai taga rashin dacewar haka yana namiji yaxo yana mata kuka tace shikenan ya wuce!! Ya dago jajayen idinsa ya kalleta nazai kice kin yafemin mana!! karo nafarko da ya taba kiranta da nazai saidai hulwaty....!! [2:14AM, 4/7/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 7⃣0⃣ Na Hauwa M. Jabo. Ta kasa magana tausayinsa da tausayin kanta ya kamata ta tuna soyayar daya nuna mata amma lokaci daya ya wulaqantata har yana cemata yar iska!!! Batasan lokacinda ta fashe da kukaba ta dora kanta akan cinyoyinta tana rera kuka.! Hankalin nura yayi matuqar tashi ganin kukan hulwarsa baisan sanda ya rungumota jikinsa ba yana rarrashi tana shaqar qamshin turarensa hankalinta yana neman gushewa a jikinta batayi qoqarin kwace kantaba taci gaba da kukanta da sauti. tana kwance a jikinta shiko yana ta rarrashinta yana bata magana yana jadda damata ya karbi kuskurenshi bazai iya rayuwa idan bataba, tana kuka tayi qasa da murya daidai kunnensa tamai magana kamar rada, deen u betrayed my life! U really hurt and harm my life because my heart insisted & become mad in your love.!! It's not an exergration that i can't do with out you. I remain yours no shacking I sincerely love you.! Deen please kada ka qara barina please!! Ya qara matseta a jikinsa, ya rada mata a kunne Hulwaty..!! I can't leave you! You're my life, sight. I wholeheartedly love you. Your love is in my blood. me all my short comings, I will never repeat it again.! Ta qara lafewa a jikinsa batace komaiba taci gaba da kukanta yana shafata yana rarrashi nidai jabo na saki baki ina kallonsu abin yana bani mamaki wai har sun shirya! dama ance tsakanin mata da miji sai Allah, da nice da ba haka kam��... Sun fahimci junansu sun yafi junansu a hankili ta janye jikinta daga cikin nashi yace kin gaji dani ne tamai murmushin nan da yayi watanni bai ganiba ya shafa fuskarta daidai dimple dinta shima yayi murmushi. Suka share hawayen Junansu suka dan taba hira chan nazia tace: najma fa tana jiranmu, deen yace nifa har na manta da ita! Lallai deen duk taimakon da ta maka shine zaka manta da ita? Waima ya akayi kukayi wannan tunanin?? Ba ruwanki sirrine tsakaninmu.! Su rirri manya koda muka fito sai mukaga bashir da najma suna soyewa..( aruwar jabo najma da basheer suna burgeni da sunyi aure da saina rubutomuku labarinsu.) Sannunku fa, laaaa kinga ni har na manta da ku. U see.. da deen ma yace ya manta dake! Laa hulwa banda sharri fa yaushe nace na manta da najma, ai ni banida kamar najma a fadin duniyar nan. Duk muka kwashe da dariya.... Mun koma makaranta cike da farin ciki na baiwa najma labarin abinda ya faru tanajin dadi har tana cewa yaushe zamusha biki! ************ [2:27AM, 4/7/2015] Auntie M. Jabo: ASHE KAINE MIJINA 7⃣1⃣ NA HAUWA M JABO. ******** Wata sabuwar ssoyayyah akeyi tsakanin nura da nazia kamar ba abinda ya taba shiga tsakaninsu nima dai hauwa jabo suna burgeni kuma ina daukar darussa a love dinsu kamar su hadiye juna. Haka zaka gansu kamar wasu budurwa da saurayi, amma duk da haka naxia akwai abinda bata yi dan kawai tsare gida.! Nura yama mai gari magana akan sun daidaita da nazia zasu maida aurensu kowa yayi farin ciki da haka bada bata lokaciba aka maida aurensu nan ma anyi sabuwar bidi'a auren ssoyayyah...!! Daren ranar nura ya tuhumi nazia akan xubar mai da ciki da tayi kamin ta gane shine mijinta aranta tace ASHE KAIE MIJINA bansaniba.!! sabida haka yau sai ya tabbatar da cewa ya sami wani yaron. bata bashi amsaba dan tasan bata zubar da cikin ba tayi niyya sai Allah yayi nasa ikonn. sai bayan sati daya tace ya rakata asibiti yana mamakin mi ya sameta tace sudaije a sibiti takaishi gun Dr da ya dubata anan Dr yama nura bayanin cewa ba zubar da cikin akayiba zubewa yayi da kanshi sanadiyar damuwa da tashiga da kuma rashin lafiyar yaron kuma ya gaya musu dagyar ma idan xata qara samun ciki hankalin nura ya tashi dajin haka Dr ya kwantar mai da hankali da cewa akwai magungunan da takesha tana qarewa zata warke zata samu ciki. Haka kuwa akayi nazia tun daren farko data koma samu wani cikin. Soyayyah suke kamar su hade juna suna girmama juna.!! Sun shiryaa da sister khadee amaryar ammar, kamar basu ba haka qawancen su da najma sai abinda ya qaru dan nazia nason najma. dan itace sanadin maido mata da farin cikin ta, so tana mata fatan samun yaya bashir dinta. zainb khalifa kuwa uwar kuri da iyayi kullum tana min waya ya baby irin dai ana neman gindin zama gun nazia wai ita dangin miji.... *********** Naxaia da nuraddden kullum cikin farin ciki suke Cikin ikon Nazia ta haifi yayanta uku duk maza AHMAD HAMEED MAHMOUD. yayan abin son kowa kyawaonsu ma ya wuce misali nima jabo nayi kamen daya da yata dazan haifa idan nayi aure.. ummulkhairi qarin jini ma tayi kamun daya da yarta mai shan nono..... Tammat bi hamdillah. ----------------------- Ina godiya ga dinbin masoyana masu bibiyar books dina da masu kirana a waya da masu mini magana a whtassapp duk ina godiya da qauna da kuka nuna min nagode.... Duk da tsaikon da aka samu na rashin kammala littafin da wuri ina dada baku haquri.. kuma kuyi haquri da hausar tawa sai a slow. sai mun hadu a wani book nan gaba mai suna...........WACE CE ITA. Hauwa m. Jabo take muku fatan alkhairi kullum. Love u all . adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *