Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, February 3, 2017

WACE CE ITA..?? COMPLETE

adsense here [3:43AM, 4/25/2015] .: WAC CE ITA..?? 1 1⃣ Na Hauwa M. Jabo Kiyi sauri ki sauko maigadi ya kusa zuwafa, Daga saman icen wata siriyiyar yarinya kamar bulala da qarfi tace mangoro nawa na tsinko? Daga gefen wata yar lukutar yarinya tace guda 8 ne Amma uku basu nunaba. Yarinyar da take saman ice tace yauwa.. haka naga ta diro kaman biri daga saman iccen ni jabo da naje gano muke WACE CE ITA? saida na firgita mace haka ba tsoro na kalli bishiyar naga tsawonta abinda yafi bani mamaki ya akayi ta hau bishiyar ba tsani.? Kamin in waigo sai kawai na hangota saman dayan bishiyar har ta Dane bishiyar, ta fara tsunko gwaiba tana wurgowa qasa qawayenta suna cabewa, da gani wayannan yaran taqdiraine waima ya take hawan bishiyar ba tsani?? Yau sai na kakkaryaku Dan ubanninku! Matsiyata..!! Muryar wani dan tsoho naji da alama shine mai gadin wurin Iffatu sauko baba shehu.!! baba Shehu!! Haka suke fada suna ihu, Timmm naji Abu siririyar yarinyar ta fado na tsorata Dan na dauka ta karye Amma inaaaa tana fadowa qasa ta dauki dayar gwaibar ta basu daukaba ta filfila har ta wucesu koda ta iso bakin qofar gonar taga baba Shehu ya kulle qofa tashin hankali..... Kunsan baba Shehu ya kulle qofa dole zamu tsallaka ne kamin yazo, tana fada jikinsu na rawa, ke dijee kulllum ke kike bamu matsala wallahi bazaki qara biyomuba gashi ke baki iya gudu sabida shegun duwawun nan naki. Mtswwww... Kuzo mubi ta chan ginin yafi gajarta. Suka kwasa a guje suka samu suka tsallakar da dije da yake ita rukayya irin ippatu CE ba auki da kanta ta tsallaka duk da haka sai da iffatu ta taimakamata. Juyowan da ippatu zatayo ta hango baba shehu da gudunsa ya kusa kawowa gurinta, ya wurgo mata sandarshi amma bai sametaba, da yake gurgune sai ta yanka a guje kamar fanka fil fil da ita, gurin ginin yafi tsawo dama, na yanda ta iya baba Shehu zai iya kamata, tana nisa dashi,taja baya sosai tazo a guje sai kawai ta dane ginin saida ta hau ta waigo tayiwa baba shehu gwalooo sannan ta dira a qasa...... WACE CE ITA..?? 22⃣ Na Hauwa M. Jabo Tana dirowq dijee rukayya kozo nan ta basu umurni. Sukazo ina mangurona da gwaibata ? Taki ko tamu inji dijee, ta wani harereta itama dijee ta harereta ta jajayen idonta gasu qanana itadai rukayya batace dasu komaiba tayi tsaye dama sune hatsabiban dije da ippatu. Ippatu ta rufe ido cikin tsiwa, abani kayana kamin in lissafa uku. Ta fara lissafi daya biyu uku itadai rukayya ta miqaa mata kayanta dijee ko ta sakasu a Dan kwali ta gulle taci damara da Dan kwalin. Bude idon ippatu ta kwashe dije da mari dama sun saba. Suka fara danbe aka tima dije a qasa dama batada qarfi sai rashin kunya, dagyar rukayya ta rabasu Amma duk manguron da gwaibar sun turmuje a qasa sai guda biyu da gwaiba hudu suka rage. Ko wannen su na fitarda numfashi daddaya. Amma fa dije anji ji jiki kusan kullum sai sunyi dambe da dijee Dan dukansu basuda kunya kuma basuda haqurin juna gashi basu iya rabuwa da juna.! Gamon jini da hali ita rukayya batada fada biye take dasu kamar raqumi da akala duk yanda akayi da ita chan takeyi. Ippatu ta baiwa rukayya mangoro daya gwaiba daya ta riqe mangoro daya gwaiba uku kaji adalci irin na ippatu dije kuwa tahau tsini Dan bata bata komaiba. Ta daure fuska muninta ya qara fitowa, Sunkama hanya ana gaba da juna kowacce tabi hanyarta ippatu na tafe tana shan magoro da gwaibarta, Bala'eeeee wallahi ga bello mai kifi chan, inji rukayya, Habawa baima hangosuba Amma tuni sun yanki ticket suka fara gudu ba tsayawa basu tsayaba saida suka daina hangoshi suka fara dariya. Kamar basune sukayi danbeba har sun shirya. Ippatu tana dariya tace dijee kin tuna faduwar da bello mai kifi yayi suka qara kwashewa da dariya suka tafa ai ranar saida ya bani tausayi habadai, wallahi baibani tausayiba kifinsa bala'en tsada sai shegen dadi inji dijee, Dan yaga ana saye yake yiwa mutane yanga. Shegiyarda sukamai saida ya qare suyar kifi ya jera akan tire zaije talla kawai sukayo tsokana aka biyosu suka zo a guje suka barar mai da kifi kuma sukabi takai suka wuce ko waigowa basuyiba shiko bello mai kifi dan jaraba maimakon ya tsaya kwashe Dan kifinsa sai kawai ya biyosu a guje, garin binsu ya fadi a qasa ya huge bakinsa, sukam tuni suka bace mai ko mai lafiya baya iya kamasu idan suna gudu bare bello mai kifi daya tsufa. Dan ko dijee bai mangalar duwawu idan ta saki qafa ba dama bare rukayya mai kamar bulala, Nidai Jabo bantaba ganin gyauyawa kuma Yan iskan yara, marasa kunya ga tsokana da rashin tsoro irin wayannan yaranba dije da ippatu ba, Dan ita rukayya yar kallo ce sai zugasu da takeyi idan sun samo su sammata ko ta musu gadi suyi abinda zasuyi. Suna dariya suna tafawa abinsu har suka iso gida sai lokacin ippatu ta tuna da aikenta akayi sayen daddawa da manja, ko shakka babu ta xubar da kudin, ta kwance Dan kwalinta data daure kudin amma ina tuni sun fadi, zakuwa tashi qaniyarta idan ta koma ba daddawar nan da manja ga uban shiririritan da tayi.. Maimakon ta shiga gida sai kawai ta kama hanya tana tafe tana tunanin yanda zatayi da saqon googo, kicibis taci karo da wasu yara suna fada ta tsaya kallo suma aikensu akayi sai taga sun yarda kidi naira ashirin da biyar ta dauke ta qulle a habar zaninta. Yau wace rana ippatu taga fada bata tsaya sayen fadanba da walakin. Taje ta siyo manjanta na goma daddawan biyar ta siyo kan kifi na biyar tana tafe tanaci har taje ta dawo suna fada fadan yanzu kuma na an sace kudin dayane ta kyalkyale da dariya iron ta mugunta ta wuce abinta..... WACE CE ITA..?? 3 3⃣ Na Hauwa M. Jabo. Ta wuce abinta koda taje gida ta rasa yanda zatayi ta shiga Gidan ta fara labe labe. Ubanme kikeyi anan ??muryar babanta taji ya mata tsawa saida hanjin cikinta suka juya duk duniya babanta kawai take tsoro ta fara kame kame, bakomai baba sannu da zuwa. To wuce gida munafukar banza ya tasa qeyarta suka shiga. Malam ina ka tsintomin ippatu? wallahi tun qarfe biyu na aiketa Dan nasan halinta batadawoba sai yanxu, kaga har na qare tuwo! Dan ubanki ina kikaje? Ta fashe da kuka wallahi baba sai bayan la'asar ta aikeni ko minti uku banyiba na dawo. LA ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi... Ihhatu "haka take kiranta Dan bata iya sunan ba" kina nufin qarya zan miki? Kinma saba bani kayana ta qwace manjanta da daddawarta, baba ya juyo ya kalleta ina kika samu kifi sai qarnin kifi kikeyi. Ta fuske kamar gaske gidan su kulu mai daddawa suka sammini.! Na dauka kin qara tsokano bello mai kifine. Aah wallahi baba.!! Idan ta tashi zama ta Allah sai ki rantse da Allah ba ita bace take taqdiranci a hanyaba kamar wata waliyiya har ma dai gaban babanta..... ********************* Ippatu yarinyace yar kimanin shekara 11 duk yanda zan muku bayanin ta idan dai ba ta muku taqdiranci nata kungani da idonkuba ba zaku gane WACE CE ITA ba, Sabida batada kunya, batada tsoro ba tada ladabi ba tada mantuwa ba yafiya haka take wata hargitsatsiyar yarinya da ita. Gata qazama taqin qarawa, batasan tsabtaba ko kadan haka batasan wankaba bare wanki farace Amma yanxu tafi zainb khalifa baqi, haqoranta Dan rashin wankewa har sunyi tsatsa daga sama, daga qasa kuwa kamar an kwaba laka an shafa mata idonta kuwa gasu Manya Manya Amma sunyi jaa kamar na sister khade qafar nan kuwa duk tayi wani iri Allah ne ya tsareta qafar bata Faso da tuni ta farfashe Dan su dijee tuni qafafunsu sun yayyage da Faso, bata yawo da takalmi, a cewarta takalmi basa barinta gudu. Mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tanada shekara 6 tanada yayye guda biyu maza duk mamansu daya, suna gurin mamansu, itama babansu yaje gun mamar ne akan dai ta bashi yayanshi, ta hana, dazai dawo ippatu ta maqalemasa ya dauketa ba da son ran mamarba, tana zaune gun kishiyar mamanta gwagwo rabi, gwagwo batason ippatu ko kadan ita kuwa ippatu ba abinda ya dameta harkar gabanta take bata damu da asotaba kuma gwagwo rabi duk abinda zata mata saita rama cox bata mantuwa bata yafiya.! Shiyasa hankalinta kwance bata tsoron kowa duk qauyensu sai babanta kuma bata ragawa kowa duk qauyen nan. An sakata makarantar boko har uku ana korota sabida uban yara da takeci, a makarantar allo ma Dan yana maqocinsune da tini ya korota ippatu kenan.... WACE CE ITA..?? 4 4⃣ Na Hauwa M. Jabo ************ Ta dauki allo na tafi makaranta, gwaggo ko kallonta batayiba Dan tasan ba makaranta zatajeba wacce batason makaranta zata fita tun qarfe biyu, za'a gurin jarabadai, allonta har rubutun ya goge dan tsabar rashin zuwa makaranta da takeyi tana fita taje bayan qyaure ta boye allon ta sa mai bata tsayaba sai gidan su dijee da yake dijee da rukayya gida daya suke dagyar suka samu suka sulalo suka fito. Suna tafe suna tadi duk yaran garin har Manya tsoronsu suke dan basu bar kowaba, idan babbane ya daki daya taron dangi sukemai ko suyita jifarsa da duwatsu, basu tsaya ko inaba sai rafi suna zuwa suka tube dagasu sai qajeren wando rukayya dai ta fara girgar dangi dija ma ya kunmo kai Amma basu kunyar kowa suka fada ruwa sukayi iyo sosai kaman kifaye sun iya ruwa kaman me suna ruwa suka hango baba shehu mai gadi shima ya hangosu sunsan kamin su fito ya iso sai dijee tace kar mu gudu idan yashigo kamamu mu bashi ruwa mu danneshi a ruwa.! Sun haqamai gadan zare, Baba shehu dayazo sai yaqi shiga kaman yasan abinda suka fada, ya kame guri daya kamar bai gansuba, sukayi jira har suka gaji Amma yaqi tafiya sai kawai suka yi shawara akan su nutse su tafi chan nesa dashi su fito. Suka nutse a ruwa, baka ganin tafiyarsu, saida sukayi tafiya mai nisa sannan suka fito suka lallabo suka zagayo suka saka tufafin su suka nufi gona satar mangoro shiko baba shehu yanachan yana jiran fitowarsu daga nutsewar da sukayi yaji shiru sai abin ya bashi tsoro kardai ya kashe yayan mutane!!! Tuni ya fada ruwan ya shiga lalube Amma basu ba labarin su chan ya hangosu suna gudu sun ciko zaninsu da mangoro da gwaiba yau hadda lemu da basu cika diva ba sun debo. Tsoro ya kama baba maigadi daganan baba shehu mai gadi ya sallama cewa ba mutane bane aljanun dajine ko Yan ruwa suke addabarshi, dole ya nemo tsari karsu hallakashi. Da sauri ya fito ruwan saida sukaxo Dan kusa dashi suka kwashe da dariya sannan suka mai gwalo suka gudu. Kaji hatsabibai.... ***** Tun daga ranar baba maigadi bai qara binsuba, hasali ko kallonsu baiyayi idan suna abinsu, da suka gane ya saka musu Idone sai suka maida abin Sana'a kullum zasuje su debo sai suje su wanke suje talla da sukaga basa ciniki sabida baqin halinsu sai suka riqa daurawa rukayya tallar rukayya kuwa akwai farin jinin talla, talla ta karbeta nan danan suke saidawa gurin rabon kudi suyita bala'e da danbe. Ba ranar da basa fada kuma aranar suke shiryawa,..... [4:50PM, 4/26/2015] .: CHI GABA.... WACE CE ITA..?? 5 Na Hauwa M. Jabo ******************** Yauma kamar kullum yan matan uku dije ippatu da rukayya suna tafe suna labari suna shewa da dariya da gani dai kasan basu da kamun kai bare uwa uba tarbiya, laaaaaaaa dije kalli malan garba da ya dakemu ranar.! suka waiga gaba dayansu suka kalleshi, ippatu tayi tsaki share shi mugun banza, dijee ta kalli ippatu bazamu share shi ba,yakamata mu rama, mi zamu masa mu rama kalli fa har yanxu tabon bulalanshi, ta nuna hannunta, kawai mu ramako ? Eh mu rama, Suka fara shawara sharrin da zasuyiwa Dan saurayin malamin makarantar allonsu, yayo wankansa na juma'a zashi masallaci sallar juma'a baima kula dasuba. har sun hada sharrin da zasuyi tunda nanne hanyar sa kamin ya dawo daga masallaci, sun nemi toka ta murhu sukaje Gidan da ake daka taba gari irin wannan da tsofafi suke sakawa a qasan lebonsu, suka siyo ta ashirin suka siyo garin barkono na goma suka hada guri daya suka ijiye suka samo bokoti daya suka debo ruwan kwata mai shegen wari suka je suka samo kashin shahu sabo suka kwaba da kwatar nan suka labe gefen hanya, ippatu ta dane bishiya kamar biranya, da bokitin kwatar ta da suka dama da ruwan kashi, malam garba na bullowa shida dije ta watso mai garin tokar daidai fuskarshi, da suka yiwa hadi ita, ita kuma ippatu ta watsomai ruwan kwatar daga saman bishiya, daga kansa har qasa ta diro gasa suka waske, idon malami sun cika da yaji ya sai ihu yake yana Neman dauki,yana murxawa ga ruwan wari a saman kanshi kamin mutane suji ihunsa tuni sun gudu gidajensu. Kuma ba Wanda ya gansu Amma sabida hatsabibancinsu duk Wanda ya sami labari sai yace hatman aikinsu ne sun koma gida duk ranar ba Wanda ya fita cikinsu, wayanda tun safe idan sun fita gantali basa dawowa sai guraren yamma shima Dan sunsan idan sunyi dare akwai samarin da zasu hallakasune shiyasa duk la'anarsu da dibar albarkarsu basa fita gida da dare. Ina ippatu? tana daki, Malam lafiya kashigo a hargitse?? Inafa lafiya yarinya tana son tasa xaman qauye nan ya gagareni.. Ke ippatu.!! Na'am baba, zonan mara kunya yarinya, ku ne kuka jiqe Malam garba da ruwan kwata kuma kuka zuba masa barkono a Ido ko?? LA ilaha illallahu Muhammad rasullullahi wallahi tana taba hannu tana salati kaman gaske, wallahi baba ka tambayi gwagwo yau duk ban fita koda zaureba, Dan banida lafiya, ko goggo,?? to ubanwa zai masa wannan ta'addancin idan bakuba gashichan ido sai Allah, kuma yace bazai barwa Allah ba. Salamu alaikum. Daga waje sukaji sallama koda baba ya fito saiga yan sanda biyu an kamo dije da rukayya akazo a tafi dani, ina kuka ina kiran baba, amma saida yan sanda suka tafi damu police station.. ************ Kun Dade kuna addabar mutane a garinnan, ba makhluqin da bai kawo qararkuba a qauyennan, kun zama annoba jaraba a gari to zamu kulleku har sai likita ya tabbatar mana da samun idon malam garba, DPO yake wannan bayani wasu ippatu, iyayensu sunyi sunyi abasu belin su amma sunqi badasu aka kullesu suna kuka suna basu bane! DPO yasa an musu Dan karen duka tunda ba wata sheida da take tabbatar da cewa su suka aikata wannan laifin, kawai sanin hali yasa aka tsaresu, sunji wuya matuqa, amma dukda haka sunqi fada gaskiyane, rukayya ta gaji ta tona asiri tace sune dije da ippatu duk wahalar da suka sha sun qi aminta hasalima sun qaryata rukayya ne, Dpo dayaga ba nasara kuma likita yace malam garba ya samu sauqin idon sai aka sakesu, aka musu kashedi mai tsanani, sunyi wujiga wujiga dasu, tun suna police station suka fara shirya sharrin da zasu yiwa dpo insun fito kaji hatsabibai dpo ne next target dinsu....... WACE CE ITA..??6 Na Hauwa M. Jabo ********* Bayan sun fito da sati biyu sundan yi lafiya dan iyayensu sun manna musu mari a qafafu basa zuwa ko ina hatta makarantar allo, gari ya samu lafiya two days, bayan sati biyu kamar sun shiryu sun zama na kirki, aka kwance musu marinda aka saka musu, ranar da suka hadu da juna suka fara dariya suna bada labarin yanda iyayensu suka musu, bayan sun qare labari suka fara shirrin yanda zasu yiwa Dpo su dau fansar dukanda yasa aka musu da marinda ya riqa tsinka musu lokacin, bayan iyayen su ba Wanda ya taba marinsu saishi.!! Sun shirya zuwa har gidanshi su fasa mai glss din akwalar motarsa. Amma basusan yanda zasuyiba, sun gargadi rukayya akan idan ta kuskura ta qara tona musu asiri basu ba ita ta amince, matsalar su daya kada a ganesu, sun yanke shawarar fita da dare Amma suna tsoron samarin garin. Yauwaaaaaa ina yan matannan da muke tsokana masu saka baqiin Abu da hijabi su kulle fuskarsu?? Eh nagane inji dijee naji ana ce musu wani Abu namanta sunan, yauwa mu samo irin wannan abin da suke sakawa mu rufe fuskar mu sai a dauka sune zasu makaranta sai muje mu fashe mu dawo, kaji hatsabibai marasa tsoro.!! Suka saka dariya sun sami wani tuggu da zasu qulla, Matsalar su daya basu da niqab din nan dijee akwai gyallen tatan gasara na Maman su zata dauko sai su yagashi suyi niqab tunda gyallen baqine haka kuwa akayi, suka tare yar makaranta ita ta dauka dukanta zasuyi, sai taga kawai sun karbi niqab dinta suna kalloyanda yake, suka sa allura suka hada irinsa, kaji shegun yara... da dare suka fita sai unguwar su dpo suka shiga har chikin gidansa batareda shakkun komaiba, da qarafunansu da suka samo gun kanikawa, suka ma glss din motar tamas tamas, da yake dpo yana gurin aiki, matarshi tana islamiyya yarane kawai suke Gidan wataqil suna bacci sukayi operation din ranar har suka gudu ba Wanda ya gansu,har suka iso gida!! Labari ya chika qari, ya yadu a kowa yace da dai da rana ne da sai muce su ihhatu da dijee ne, Amma yanzu duk qauyen an yarda basu bane barayine kawai suka masa wannan karen aikin... uku bala'e kenan!! suna nasara aduk aikinda sukasa gaba koda zasusha wahalane.. ******************* Yauda gobe ba wuya a gurin Allah abubuwa da yawa sun faru a dan qaramin qauyen nan ciki kuwa harda rasuwar mahaifin ippatu sanadiyar hatsarin mota, yajee birni siyo kayan shagonsa anan babbar mota ta bi saman motar su Allah yayi mai cikawa.! Su ippatu an Dan natsu kadan an rasa mahaifi, mahaifiya kuma dama batasan duniyar da takeba coz ba rabuwar allah sukayi da babantaba duk sharrin goggone, tunda tayi wayo bayan babanta ya kwatota a hannun mahaifiyarta bata qara saka mahaifiyarta a idoba haka ma yayyenta.. Tun farko farko zaman haquri goggo takeyi da ippatu, bare yanxu da ba mahaifin ippatu, sabida haka ta yanke shawarar miqata birni wanke wanke ko ta moreta.... [4:50PM, 4/26/2015] .: WACE CE ITA..?? 7 Na Hauwa M. Jabo Tashin hankali ni kaina Jabo na tausaya wayanda zasu dauki ippatu aiki gidansu kamin su korota nasan zataci ubansu.! Goggo kullum gori take mata har ta fara girgar dangi a gida, amma ba mashinshini bare a aurar da ita. Wazai kwasar ma kanshi jaraba. ippatu da yar birni ce da sai anyi haddadiyar mace dan komai Allah ya bata sak mamanta ta dauko fulani gaba da baya sai ta hada da da duhun babanta sai tayi Dan duhu farinta mai haske ne da duhu gata qirar kalangu ga gashinan kamar yakasheta amma ba gyara idan akayi kitson sallah qarama sai babbar sallah ake tsefeshi, tayi baqi Dan na tabbatar da tafi zainb khalifa baqi sabida tsabar rashin wanka, qafafu duk sun jeme haqora sunyi tsatsa da wata laka laka a ciki idonnan sunyi ja duk jikinta tabone sabida fadowa saman bishiya da akeyi a jijji ciwo, ko saman Garu da ake dirowa ko a na gudu a fadi a ji ciwo haka dai take masha Allah..... ********* Goggo tayi magana da altine akan tanason a kai ippatu birni aiki amma inaaaaaa altine taqi aminta Dan tasan halin ippatu sama da qasa, gaba da baya, altine taqi yarda har goggo ta gaji da zuwa gidanta neman alfarma ta haqura, ranar goggo taje suna maqotansu taga wata mata daga birni tana maganar a nemo mata yar aiki yarinya qarama mai qoqari da kuzari goggo batace komaiba, Dan tasan idan ma tayi magana anan mutane zasu fadi mugun halin ippatu. Saida aka watse matar na fita goggo ta faki ido ta bi bayanta, tajata gida tace tanada ya amma batason kowa yasan zata kaita aikine zatace takaita gun yar uwartane goggo tace yarinyar marainiyace, tanason ta dan riqa samun abinda zasu chi su rufawa kansu asiri, Amma batason kowa ya sani, hakadai goggo yayita tsara matar, ana haka saiga ippatu an dawo daga kogi tun safe dataje sai yanxu tayi shudi daya, Koda matar taga ippatu taga uban bokitin data dauko saman kanta chike da ruwa ta tabbatar da cewa ippatu Nada kuzari, kamar gaske ippatu ta gaida matar ta wuce abinta matar kuwa ta amince da ganin ippatu kuma tace baxata fadawa kowaba. Matar da yake gidan biki tayi sanarwar anata kawo mata yara yan mata amma Duk wacce aka aiko sai tace musu ai ta samu bata fadawa kowa cewa ippatu CE ta samuba har ta koma birni,.!! Bayan kusa sati uku da magana matar tazo ta tafi da ippatu birni ta mata dinki kala biyu Dan kar taje Gidan daga shigarta a koresu , aka hada da yan kayan sallarta. Ippatu tayi kukan rabuwa da qauyensu Dan batason zuwa aikin da za'akaita sun rabu da dijee da rukayya sunata kuka sai birni...... WACE CE ITA..?? 8 Na Hauwa M. Jabo ******************* Bayan sun isa birni matar da nikaina Jabo bansan sunantaba takaita gidanta, tasa tayi wanka ta saka kayan da ta dinka mata, suka kwashi hanya takaita gidan da zatayi aiki, ippatu tunda ta shigo birnin sokoto take qauyanci ganin sabuwar duniya ya hanata kula da fadan da matar take mata bare ta mata rashin kunya, data shigo gidan Alhaji Habib nan kallo ya koma sama, gidane da idan na tsaya muku bayaninsa zan bata lokacine, duk unguwar ba gidan da yakaishi girma, ga lambu a gidan shuke shuke manyan itatuwa swimming pool ne, gurin ijiye motoci ga abubuwa nan kala kala, ataqaice dai Gidan dai ya hadu, ippatu tana shiga palon santsin tayis ya kwasheta ta xube qasa tiiiiim..!! Wata Yar budurwa da matar gidan suka saka dariya, taji haushin dariyar da aka mata ta daure fuska abinta, badan yau tazoba da sai ta tsula musu rashin mutunci su har sun isa su mata dariya.!!? Matar data kawota ta riqa hannunta suka qarasa palon suka zauna, sanyin ac tuni ya fara shigarta ta fara rawar dari sai qarar haqoranta kikeji kakaf. kakaf, alhaji yace a kashe ac din baquwarsu tanajin sanyi.! haba Abba wallahi zafi akeyifa wani Dan saurayi ya fada yana yatsina fuska alamar zafi! Alhajin dakanshi yatashi ya kashe ac ya dawo ya xauna. Wacce ta kawoni ta fara musu bayanina kamar yanda goggo ta mata bayani, taji qaryarda goggo ta zuba tayi yawa ta kasa haquri Dan ita ba'aqarya gabanta, tayi charb ta chabke ta fara zuba, goggo ba itace mahaifiyataba mahaifiyata sun rabu da mahaifina tun ina qarama mahaifina ya rasu shekara kusan biyu da suka wuce kum..... Keeee, keep quiet mana ya fada yana mata kallon wulaqanci, chikin tsawa ya fadi maganar ta gane keep quiet dan lokacinda tana boko kamin a korota Malaminsu yana yawan fadar haka idan ana surutu kuma daya fada sai kowa yayi shiru, shima malaminsu da qarfi yake fada kamar yanda wannan ya fada, ta dallamai harara hadi da yimai kallon banxa ta zubar. Kaiiiii abba u see? Kaga yanda take kallona kuwa,? Farhaan yakamata ka riqa haquri mana, da zuwan baquwa zaka tsaneta haka, kada ka manta da ita zaka zauna.. farhaan ya juyar da kai gefe gaskiya dady bana tunanin xan iya zama da wannan, kalletafa!! wata kyakyawar dattijuwa ta kalleshi wallahi kayi kadan wannan itace ta qarshe ba chanji. Duk maganar. da suke da englsh suke yinta, Ya bata fuska ya tashi yabar musu guri yar qanwarshima ta bi bayanshi suna gunagunai da turanci, Matar data kawoni ta basu haquri tace kuma kada in qara magana, ganin maganata kamar itace ta haifarda rigima sai nayi shiru bawai dan raina yasoba, taci gaba da musu bayani inajin tana qarya amma ba halin magana...... Mujeee zuwa muji yanda iffat za'azauna a gidan aiki, da wannan hali nata......M jabo [4:00PM, 4/27/2015] .: WAYE ITA..?? 10 Na Hauwa M. Jabo. Ta kalleshi in tafi?? Yayi banza da ita, ta qara tambayar sa yayi mata banxa, ta kama hanya zata tafi ya daka mata tsawa, ki dawo ki tsaya nan, taja ta tsaya kusan 30mnt tana tsaye, ta gaji zata zauna ya hanata Idan kika zauna sai na kakkaryaki, tayi tsaki, ta kauda kai, ya qare abinda yakeyi ina miki magana zakice baki dauka dake nakeba ko?? To waye a dakin da zanyi magana dashi? Ta kalleshi a wulaqance da chan dakake maganar dawa kakeyi?? sau nawa ina ganinka kana daura hannu a kunne kanata magana ko kuma kayi yare kana dariya, wani lokaci ai wata waya kake sakawa a kunnenka kayita magana kai kadai duk da uban wa kake magana? Kaga yanzuma na dauka da ubanda kake magana farko dashi kakeyi yanxu . Zunbur ya miqe yayi niyyar mammaketa sai ya tuna da abinda ummanshi ta fada mai "ban amince ka daki yar mutaneba marainiyace duk abin da ta maka kamin waya zan mata magana" sai ya koma ya zauna ya dun qule hannu itako tana tsaye ta riqe kunkuminta kamar mai jiran danbe, ya kalleta wata mummuna qazama da ita, ya rasa abinda zai fada mata ta gane WACE CE ITA. ya harareta yaja dogon tsaki, to ki zauna, ta zauna ya maimata bayanin da ya mata da dazu, shima dai iskancine yazai ijiye baqauya kamar wannan yana mata English to amma ai da yayi na farko ta gane, ya akayi ta gane? Koma yane ya rage nata.. Yace Inada abokai mata da maxa, kuma ko wanne yana zuwa nan gidan suna kwana wasu suna wata daya wasu suna sati biyu idan sunzo suma duk abinda kike min suma zaki musu hadda girki idan suna buqata zaki musu. Ni ban iya girkibafa Malam.! Gidanku basu koya miki girkiba ? Eh basu koyamin ba, ta fada cike da tsiwa,sai yayi banxa da ita ya fahimci yarinta na damunta amma zai gyarata a hankali, ya nuna mata WACE CE ITA a gidannan, OK ya rage naki, haka zaki girka musu in sun buqata, tayi banza dashi Dan tunda take bata taba yiwa goggo girkiba cox batama zauna gidaba bare tasan yanda ake girka abinci. Ko girkin murhu bata iyaba bare na gas, ya qara jaddada mata abinda umma tace bata ba fita waje, ba wasa da masu gadi, ba ruwanta da kowa aikinta kawai. za'ayi shegiya kuwa.! Yaqare fada mata abinda zai fada mata ta tashi ta shige dakinta. Tunda tazo gidan a Leda take kashi sai ta saka bola idan yayi yawa ta fitar dashi sabida duk dube dubenta bataga masai a gidan ba, shi yasa dakinta yake wari Dan bata damu da gyara komaiba, gurinda kawai akace ta gyara dakin farhaan take gyarawa.... [4:00PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 11 Na Hauwa M. Jabo ******** Ranar farko da farhaan yayi baqo wani abokinsa da sukayi karatu a UK. Tare sunyi missing din juna, farhaan yanata addu'a kada wannan kucakar ta fito ta kwafsa mishi Dan ya lura kanta rawa yakeyi ba kadanba, suna tsaka da gaisawa sai gata ta fito. Kamar an korota daga daki, Ku tashi zan goge nan gurin! Ta fada ba tareda ta kallesuba, Tafara share palon, meene kebakiga inada baqo bane,? maza ki bacemin da gani har ta fara shara tajiyo tsawan da ya daka mata ta miqe tsaye, tana yatsina fuska kai bakasan lokacin aiki na bane da zaka kwaso tarkacen abokanka kazo dasu Ku hanani aiki..! Habawa Ya wanke ta da mari tashin hankali..! ta dauki bokitinta na ruwan dattin data goge sauran guraren dasu, ta watsawa abokinsaA fuska, tunda shine silar adaketa, ta matsa daga nesa tana jiran hukuncin da za'amata da Wanda itama zatayi Dan bata yafiya, dukansu sun rasa abinyi abokinsa ya fara bala'e ya zaka zauna da mahaukaciya farhaaah, bakasan hadarin hakabane? Wannan wata rana zata iya kasheka wallahi, tana shigowa palon nagane batada hankali, Kaine Mara hankali baniba tana zazzare ido kamar lecturer ya titsiye jabo a clss bata iya karatuba, farhaan zaije gunta abokinsa yariqe hannunsa, cool down my man. Akwai banbanci tsakanin mai hankali da mahaukaci nasan da tanada hankali bazata taba yimin hakaba, muje daga ciki inyi wanka in chanja kaya kawai. Baqin ciki ya hana farhaan magana ya rasa yanda zaiyi, Dole ya nuna mata WACE CE ITA a gidannan. Abokinsa yaja hannunsa suka wuce daki ita kuwa hajiyar tachi gaba da aikinta.((Allah ya tsaremu da aikin jahili da baqauye.)) ta gyara gunda ta jiqe da ruwa kamar bata zubarba, aikin ma fa yinsa kawai takeyi amma ba abinda ta iya bayi ruwa kawai take sakawa ta dauraye duk da cewa umma ta nuna mata wasu abunuwan, gadonsa kuwa sai Wanda ya gani da yake shima gwanine gun shiririta haka yake kwanciya akan gadonsa shi warine kawai bayaso. Bayan abokinsa ya tafi ya kwala mata kira ta fito ya nunata da yatsa wallahi yau sai kin bar gidannan Dan ba gidan ubanki bane, ko in hallakaki matsayaciya kawai, tofaaa ran ta ya baci ta tsani a zagi babanta ta kebe baki, ai bani nakawo kaina gidan na ubankaba, ubanka ya kawoni sai ka bari idan ubanka ya dawo sai ya maidani gidan ubana kamar yanda ya daukoni, ta fada cike da gadara da rashin tsoro. Sai ya saki baki yana kallonta ta juya ta koma dakinta ya bita da kallo, Ita kanta tasan zata iya gayawa farhaaah ko wace irin magana amma bata taba kawo ta kulla masa sharri ko daya a zuciyantaba, haka kawai yake bata tausayi kajifa.. Maamanshi ya kira, umma wallahi yau sai na babbala wannan qazamar yarinyar batada amfanin komai, umma dai nata bashi haquri dan tasan zai rina, nan ya kwashe duk abinda ya faru ya gayawa umma ita kanta umma ta jinjina wa wannan yarinyar da Karen aikinta. amma bata nunawa dantaba ta bashi haquri da kuma yimai kashedin ya fita hanyarta Kuma kada ya qara sa mata hannu, tace yakaiwa iffaaat waya, waye iffaaat umma?? Itayarinyar mana, baimasan sunantaba sai yau, kullum da yake kullum da keee yake kiranta ya kwala mata kira ta fito ya bata waya yaga dai batasan wayaba bata Masan yanda ake amfani da wayarba sai kawai ya sa speaker, taji ana kiran sunanta a ciki, farko ta dauka radio ne yake magana sai taji ana kiran sunanta habawa.... Ta wugar da wayar Da gudu ta koma daki jikinta na rawa abin ya bashi dariya sosai, sai ya bita dakin yana shiga wani qarni da wari ya tarbeshi ya kasa numfashi ya dawo Palo ya qara kiranta dagyar tafito, ni kaina Jabo abin ya bani mamaki Dan kuwa iffaaat ko lokacinda aka kaisu police station bataji tsoronda taji yanxuba Ashe Akwai abinda take tsoro....... Mujeee zuwa muji ta'addancin da zatamai kamin tafara........ [4:00PM, 4/27/2015] .: WAYE ITA..?? 9 Na Hauwa M. Jabo Wacce ta kawoni Ta qare bayananta na qarya dana gaskiya da goggo ta kitsa mata.... Kyakyawar matar tace Allah ya bamu ikon riqeta yar marainiya da ita, dama yaron mune muka nemowa mai aiki, duk wacce aka kawo sai su sami sabani dashi kusan mai aiki 13 ana kawowa suna samun sabani, shine yanxu yace asamo mai qaramar yarinya tunda aikin nashi bashida yawa yace bayason Yar cikin qari sabida sauran daga qazamai sai barayi sai yan iska sai marasa kunya da sauransu, shi kuma baya iya zama dasu amma wannan yarinyar ni tamini sosai, ammafa sai ta zama mai haquri Dan farhaan akwai fadin rai da fushin bala'e sai kina haquri kinji yan mata? Ta amsa da to kamar da gaske, ya sunanki da sauri nace ippatu. Matar ta maimaita iffaah suna mai dadi! Sai naji tafi kowa iya sunana yanda ta fada ta wani juya baki, "kunsan bahaushe baya banbanta "P""F" duk daya yake kiransu" Maman farhan ta mini nasiha ta kira yarta farahnax amma shiru bataxob, dakanta tace muje in nuna mini dakinki da zaki zauna, tashin hankali koni Jabo dakin ya burgeni bare wata yar qauye irin iffaaah... An gaya mata aikin da zatanayi, zata gyaramai dakinsa tattara mai kaya takai ma mai wanki ya wanke, ta wanke bayi, ita zata riqa tashinsa da safe yaje skull. Hummm iffaat kam sarkin bacci wa zata iya tayarwa daga bacci, Naji matar gidan ta burgeni cox batada gyama kuma ba wulaqanci haka mai gidan amma su hatsabiban yayan yan wulaqanci ne tasan ma korarta zaiyi Dan bazai iya zama da itaba. ******** Kwanan hajiya Fati hudu da iffaaat anyi sa'a ba wanda ya tsokaneta bare ta rama, yau zasu bar naija su koma UK da yarsu farahnax, akabar farhan da iffaaat a gidan. Da gani jininsu ko kadan bai haduba amma ba yanda ya iya mamarshi harda rantsuwa akan cewa bazai chanza taba, dole yayi haquri koda na shekara dayane, ya fahimchi yarinyar batada kunya dole ya saitata.!! Bayan tafiyar su hajiya ya dawo daga rakiyansu da yayi a airport ya shigo gidan, Keeee come here, taxo gabanshi tamai qiqam kamar ice ta tsaya, Oyaaaa get seat tazauna bawai ta gane mi ya fada bane kawai a makarantar boko kamin a korota taji maliminsu na cewa seat down ta gane cewa acikin biyun daya na nufin zamame tunda yana fada kowa yake xaunawa, haka yana cewa come here sai taga anje gun malami. sai itama tayi hakan, akayi Sa'a ta gane farhaan ya dauka tanajin English ganin ya mata Dan biyu ta gane sai ya fara bayani Hausa da turanci saida yayi yayi yace have u get me.? Yaga ko motsi batayiba, ya qara tambaya shiru kakeji yagane aikin banxa yayi, keee ya daka mata tsawa. Kina jina?? eh inaji. to mi nace?? Ta harareshi mi kace kuwa? Duk maganar da nayi bakiji abinda naceba. Ta tabe baki ai ban dauka dani kakeba to da uban wa nake, zanci ubanki fa.! ta miqe zunbur ta nunashi da yatsa kada ka qara zagar min baba sabida ya rasu idan ka qara zagin babana zan rama masa kaji na fada maka. Ta murguda baki ta maka mai harara... Farhaan kam gaskiya tamai yawa ya tsaya yana kallon baqauya tazo tanamai rashin kunya har gida wai kuma Yar aikinsa, anya kuwa tasan WACE CE ITA anan gidan? ba shakka batasan WACE CE ITA ba nine xan Sanar da ita WACE CE ITA a gidannan, baice mata komaiba yaci gaba da kallonsa..... [4:52PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 12 Na Hauwa M. Jabo Ta samu guri ta rakube nesa dashi, ya daure fuska ki karba umma zatayi magana dake, ina ummar? Magana take kuka kuka Ya zanyi magana da ita? Ki karba nace jiki na rawa duk ta rude ta karbi waya, ki daura a kunne takuwa danna waya a kunne,tayi mutuwar tsaye, Tana tsoron kar ta jata, wayar ma a juye ta daurata sai ya shareta, to kiyi magana, kamin tayi magana sai taji an sake kiran sunanta har zata wurgar da wayar sai kawai ta daure ta amsa, jiki na rawa, sundan gaisa, nan dai umma ta mata magana akan ta daina yiwa yayanta rashin kunya duk abinda yakeso ta mishi, ta amsa da to zata daina, amma hajiya kice ya daina dukana,!! gaban abokansa yake dukana kamar jakar gidansu, duka.!? Eh, kuma kullum saiya zagi margayi babana bayan na fada mishi babana ya rasu yadaina, amma kullum saiya zageni, kwallata ta cika mata ido batason a zagi babant ko kadan. umma taji haushi sosai ta bata haquri tace zatamai magana,daganan tadan bata labari har tana dariya, tama manta da tsoronda takeji,, haushi ya kama farhaan ya kira amata fada, ta bige dakai qaranshi, har tanata dariya, tana dariya shiko ya qura mata I do yana kallon haqoranta da sukayi wani tsatsa, ta qare ta kawo mai tana dariya ya kalleta ke wai laka kikeci hala,kinga yanda haqoranki sukayi tsatsa kuwa? Ta harareshi, ba laka naciba kashi nakecii, tayi tsaki ta wuce dakinta, ya bita da ido cike da takaicinta to waima miye amfanin kiran umma da nayi? Gashi ba abinda ya chanza! Kalli ko second goma ba'ayiba ta qara yimin rashin kunya, shima yayi tsaki lallai an hadashi da qaddara kuma umma tace sai ta dawo za'achanzamai ita, nanda shekara daya kenan lallai zaici uban yarinyar nan kuwa, dole ya nuna mata WACE CE ITA, a duniya ya rasa horon da zaimata taji haushi ko zata Dan natsu, ya kira kukunsu yace daga yau kada ya qara yin girki da ita, okay sir, ****** Da yamma mutuniyar taku ta tashi daga bacci ta nufi kitchen taga wayam ba abinci da Rana ma batachi komaiba yanxuma bataci komaiba, tana tsaye saiga farhaan ya shigo, abincin sa a shirye kamar yanda aka saba hadamai amma ba nata ta kalleshi fuska a yatsine, Ina abincina? Nine mai miki girki? Ko ni nasaba girka miki? Karki manta kema yar aikinace so ki kula kisan abinda kikeyi a gidannan ya bone. Ta kalleshi rai a bace to dan ina Yar aikinka sai akayi mine? Sai kada in nemi abincinda zanci? Ta kalleshi Ni yanxu mixanchi ? Yana kai spoon a baki ya tauna ba tare daya kalletaba Kici halinki ko ki girka da kanki idan kin matsu,.! Tofa yau za'aqure iffaaat yan mata...... [5:00PM, 4/27/2015] .: WACE CE ITA..?? 13 Na Hauwa M. Jabo Ta kalli kitchen din ko za'akasheta ba abinda zata iyayi a bayan buda fridge ba abinda ta iya, kuma ga wasu abubuwa kamar fridge akai taga ana girki. Za'ayi shegiya kuwa.ta kalleshi taga yana kai loma hankalinsa kwance., tayi tunanin ko ta barar mai da abincin da yake ci a jikinsa sai kuma ya bata tausayi, kawai saita rakube saida ya kammala Wanda ya rage shi tacinye.... **** Tafiya ta kama farhaan zuwa Lagos, ya tafi satinsa daya baidawoba. tun ranar da ya tafi batachin abinci saidai tabuda fridge duk abinda taga nacine ta dauko ta chinye, cikenta ya lallace kullum tana hanyar bayi, to anachin abinda ba'asaba Chiba wasu kuma ba bisa Qa'ida ake cinsuba duk wani abu da tagani mai Dan gishiri gishiri da zaqi zaqi ta gama dashi. Kaihar saida ta qare chiye chiyen takai batada abincin da zatachi yau. kwananta biyu bataci komaiba yunwa na Neman ta hallakata.. tunda tazo gidan bata taba koda fita wajen Palonba daga daki sai Palo sai kitchen, batamasan qofar da ake fitaba... Aranta taji ta fita haka ta biyo hanya tabi nan ta leqa chan har tayi karo da qofar fita, ta baya ta fita, Habawa, tayi murmushi taga S pool aranta tace wato gidan nan hadda qaramin kogi sukeda, ta waiga ta hango lanbu komai yaji fruit duk sun nuna wasu sun fado a qasa Habawa tayi ciki da sauri taci ayaba son ranta saida ta qoshi, sannan ta kwance Dan kwalinta tayo guxuri ta fito har zata wuce taga yanda ruwan nan sukayi sky colour sai suka bata sha'a ta tu6e ta fada tayi wanka sosai gata gwanar iya ruwa, gashi,an Dade ba'ahaduba ta Dade a ruwan sannan ta fito, dama tunda umman su farhaan ta tafi batayi wankaba kwana goma kenan, ta fito cike da nishadi an samu banxa, dagyar ta gane hangar komawa daki taje ta chanxa tufafi tunda wayannan sun jiqe, tana zaune Palo a qasa ta miqe qafafu ta saka fruits dinta tsakiyar qafafu, tanashan mangoro abin sai Wanda ya gani,taji qamshin turare hadi da dariya koda ta duba farhaan da wata mata yar gayu da qananan jaya a jikinta tasha attach fuskannan tasha fenti bakinnan yaji janbaki, ta rurungumo farhaan, tana mai shagwaba suna ta dariya, sun bata haushi haka kawai, ta miqe da dariyanta tagaishesu a tunaninta matarsace, matar ta mata kallon tsana da gyama ta kalleta a wulaqance ta zubar, hooney miya kawo almajirai a gidannan bayan kace min ba kowa dagakai sai masu aiki biyu. Wai itama mai aikinace, .matar ta wani jaa da baya honey wannan din?? Aiko hanyar databi bana son nabi tana magana ayangace tana wani rungumoshi, ran iffaaat ya bace tuni tasha magani aranta tace Dan an samu an gaishesu suke yiwa mutane wulaqanci ba matar shi bace ko uwarshice tamin iskanci zanci zan rama, taja wani dogon tsaki,ta murguda baki ta wucesu, hooney kana kallo mai aikin gidanku abinda ta mini...?? [2:48PM, 4/28/2015] .: WACE CEE ITA..?? 14 Na Hauwa M.Jabo Kiyi haquri tanada matsalar gwagwalwane, ta wani zare ido kana nufin mahaukaciya kake rayuwa,?? Haba Hoooney wannan ai gangancine ta fada da qarfi, har saida iffat tajiyota, ta waigo ta zare ido gasu masha Allah idonta, ido cikin ido tace; waye mahaukaciya?? Rufee ta rungume farhaan da qarfi kiyi haquri badake nakeba, rufee dai taji tsoro, hankalinta ya tashi qarshe taqi zama gidan tace sai dai ya kaita hotel Dan bazata zauna da mahaukaciyaba ta hallakata.! Haka dai rufee ta hana farhaan zama gida duk gajiyar daya kwaso saida yakaita hotol, kuma ta hanashi dawowa kar mahaukaciya tamai illa sai gobe da dare ya lallabata ya dawo gida, iffaaat dai fruits dinta takeci dare da rana amma taji jiki ba kadan ba har ta chanxa kala, kullum tana hanyar bayi tana gudawa. Dan ma Allah yasa ba irin zainb khalifa bace mai shegen ci da ba haka ba.. ******** Yana isowa ta fashe mai da kuka wallahi saika maidani gida!! angayamaka banida gata zata ijiyeni ba abinci wallahi saika maidani gidanmu ta riqe mai gefen riga tana kuka, anyi arziki bataci kwalarshibama. sai yanxu ya kula da ta Dan chanza kamar ta tame ta qara duhu ya tuna da cewa ya hana abata abinci.! Girjinsane ya buga to me takeci tsawon kwana 9?? Ya kalleta sai kuka take sai ta bashi dariya kuma, Ashe kawai abinda zaisaa wannan shu'umar kuka, yaji dadi aransa ko banxa ya rage baqin cikin ta kuma dama Dan ya bata wahala ya mata hakan.. Sorry iffaaahh, na manta dana hana abaki abinci, to mi kikeci kullum,?? bansaniba ta fada a yatsine wato kai ka yahana a bani abinci, wallahi Dana sani da ban mai kukaba duk a zuci take maganar.!! Kiyi haquri kinji, tana kallo ya kira kukunsa yace a riqa girki da ita,tace bazanciba gida zaka maidani, bai kulataba ya wuce abinsa. Bayan kwana biyar farhaan ya sallami rufee, Kwana na shida yazo da wata matar, Itama yar gayuce irin rufee saidai wannan tafi kyau, koda suka shigo iffat na goge Palo, yarinyar ta kalleta ke kawo min ruwa mai sanyi.! Ta fada a gajiye tafada kan kujera ta zauna iffat ko kamar batajitaba, aranta tace dama matansa biyu yaro dashi sai mata, baijira amsar iffat ba Dan yasan halinta sarai batada kirki, yanda ya gaji bazai iya fita nemawa ramsy hotel ba, ya dauko mata ruwan ya kawo mata kixo mushiga daga ciki kinga ana aiki anan ka shiga idan na huta zan shigo ta fada alalace, Ya wuce yabarta tana danna waya amma ranshi baiso barintaba, kee mai aiki idan kin gama kizo ki matsamin qafafuwana.... [3:00PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA.?? 15. Na Hauwa M Jabo Nan ma Tayi banxa da ita har ta qare aikinta, tana neman ficewa palon, ta kalli iffat kizo ki danna min hadda bayana kiyi min a hankali Na gaji sosai, tana magana a wahalce irin ta gaji dinnan, iffat nan ma ko ta mata banza ta fara waqar ta badi ba rai soyayyar jigon rayuwa da amana...... kusan kullum sai iffaat ta yi wannan waqar Dan tana bala'en Sonta kuma baiti biyu ta iya tun aqauyensu, ramcy taji shiru, ke kodai kurmace ke? Kurmane kuma zaiyi waqa,! Kee Ana magana kinyi banza da mutane, iffaat Tamata kallon wulaqanci, shi mijin naki yace miki aikina kenan danne dannen matansa?? Aikina biyune zuwa uku hajiya batace in ma matansa tausaba.! ta miqe zaune Ke marar kunyar yarinya, kina kallon mutane kamar kina kallon kashi, wai ma Waye matar tasa? Zan miki display a gidannan kuwa, iffat kam bata ko kalletaba taja tsaki ta wuce dakinta, ramcy a fusace ta tashi taje dakin farhaan, har ya fara bacci ihunta ya tayar dashi, ya zaku ijiye mai aiki Mara kunya a cikin gida yarinya har tana mini tsaki.! Yadanja tsaki ya rasa abinda zaice, aransa yace ki godewa Allah data tsaya akan tsaki, bayason ta fahamci koshi iffat ba ragawa takeyiba, cool down baby ba girman ki bane kina fada da mai aiki in kin kula yarinyace, xata qara magana ya janyota ya rungemeta.... nidai jabo danaga abin zaifi qarfina sai kawai na bar musu daki nayo waje. Guraren maqreeb suka farka daga bacci suka fito yunwa ta addabesu ya nema musu snack suci, ramcy tace indomie take so tachi, kuku kuma bayanan, to miye amfanin wannan yarinyar? Basai ta girkamin ba, no ki barshi xan girkamiki farhaan ya fada yana miqewa Dan yasan iffaat zubar mai da mutunci zatayi, ramcy dataga dai da gaske zai mata girkinne sai tace ta fasa amma zuciyarta fall da tunanin miye amfanin yar aikin, suna zaune suna hiransu suna dariya iffaat ta taso tazo gabansu ta wuce, wani warin datti ya daki hancin ramcy tace; kai amma wannan yatinya na wari! Ta toshe hanci, iffat ta waigo taceni nake wari? Farhaan yace ke ki matsa ki baiwa mutane guri,an fada kina wari qaryane bakya warin? Shima kallon banxa ya mata yaci gaba da hiranshi, ran iffat ya baci matuqa, ba'ataba fada mata hakaba wai tana wari sai yau, ko qauye su dijee da rukayya ne ake cewa suna wari ba wanda ya taba CE mata tana wari ta wuce fauuuuuh kamar guguwa ta tasooo, tana zuwa daki ta fara tunanin abinda zatama matar farhaan ta rama, cox taji haushin abinda ta fada mata, itaf ta dauka matarshice, batasan matan banxa bane, tayi wata dariya mugunta an samu idea ta miqe tsaye taje kitchen ta dauko man gyada, tayi zaune duk ta gogo gurin da ba carpet dashi tayis sai maiqo yake yaji oil sosai, cox ta taba zubarda man gyada a kitchen tafadi har sau biyu sai ta gane cewa yana fadar da mutum, ita kanta da tsantseni take tafiya har takai wani guri ta zauna, ba'ajimaba kuwa saiga ramcy an fito da kayan bacci kamar tsirara, tana fitowa daki tana yatsine yatsine, sai wayanta tayi qara juyawanda zatayi ta dauko wayan, kikajita teeeeem ramcy anfadi qasa ansha qasa, ta fadi saman hannunta tayi wata qara, iffat ta gyalgyale da dariya, tazo kanta tana kallonta tana dariya, ramcy kuwa sai kuka takeyi tace da bana wari Dana taimakeki Amma ina tsoron in saka miki warina ....... [3:43PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 16 Na Hauwa M. Jabo Maimakon ta dagata din amma ina sai dariya takeyi, ramcy sai kuka take tana ki taimakeni iffaat taci gaba da wa qarta ta badi barai, tayi sauri ta goge duk gunda ta saka mai,ramcy nata kiranta ta taimakamata amma iffaat kamar ma batajiba, hankalinta kwance, ramcy ta rarrafa taja jiki ta dauko wayanta ta kira farhaan ta gayamai faduwan da tayi da dariyar da house girl dinsa tamata ba'ajimaba saiga farhaan da Dr. Sunzo Dr. ya duba ramcy akace hannunta da qafarta sun targade, farhaan yaje dakin iffaat batanan yaje ko ina batanan kamar daga sama ya ganta ta chiko dan kwali da fruit lambu taje kenan, tana qarasowa ya wanketa da mari.!saida abinda ta debo ya watse, Ke dan ubanki Mara tarbiyar inace ke?? Mace ta fadi Dan bakida tausayi idan baki taimaketa kin dagataba ai bakya mata dariyaba, Dan Kinga ina gyaleki a gidannan kike abinda kikaga dama, karfa ki manta ke ba kowa bace illa yar aiki, kuma wallahi zan riqa chin ubankine, wawuya Mara tarbiya.!! Ya fada a hasale ya wuce daki gun ramcy, ranshi a bace yaci gaba da rarrashinta... ran mata ya bace ga duka ga zagin chin mutunci, ta fashe da kuka, ta fito harabar gida ta rakube wani guri tasa kanta a cikin chinya ta fara kuka, kuka take sosai cox ranta ya bala'en baci ba'ataba samun nasara akantaba irin wannan wato duk dabarar da zatayi dan ta rama abin da ya mata ta sai taji yana bata tausayi bazata iyaba, shegiyar matar ya kamata ta qara yiwa wani sharrin, haka taci gaba da kuka har farhaan ya fito zaikai ramcy asibiti ya sameta anan ya zabga mata harara ya wuce abinshi, har sukaje suka dawo tana kuka sai ta bashi tausayi yaje ya ijiye ramcy ya dawo, kewai mi kikeyi anan,? ki tashi ki shiga ciki kinzo kina ma mutane kuka, tayi banza dashi yayi yayi tun yana fada fada har ya dawo rarrashinta, har ya gaji taqi daina kuka kuma taqi tashi, ya gaji ya koma chikin gida, iffat dai ta gaji da kuka tayi bacci anan, har gari ya waye guraren 9 farhaan zaije skull yaganta anan kwance ya rasa yanda zaiyi da ita sai kawai ya dauketa a hankali yakaita Palo saman kujera ya shinfidar, ita kuma ramcy tana Palo zaune saman keken guragun da aka bata, tamai kallon tuhuma waye ka dauko, sheeeeeeee, ya dora yatsansa akan lebensa yace kada tashi, banganeba yar aikice kake dauka, yace batada lafiya, jiya sabida abinda na mata akan ki waje ta kwana. Ramcy tace then so what Dan ta kwana a waje, ya bata amsa da then so keep quiet kada ta tashi nace! Tamai kallon tuhuma farhaan ka gaya min WACE CE ITA?? [3:44PM, 4/28/2015] .: WACE CE ITA..?? 17 Na Hauwa M.Jabo Ya kalli ramcy kallon bangane mi kike nufiba, ya tambayeta WACE CE ITA?? Eh wace ce e ita.!! Wace ce ita kuwa bayan house girl dina, yayi guntun tsaki, ki kula kada ki tayar da ita bacci ba tada lfy, ya bata amsa ya fita abinshi, house girl ce hadda wani daukota,aranta tace yanda tasan farhaan da gyangyami ba yanda za'ayi ya kula wannan qazamiyar yarinya, yarinyar da ko qirqar danki yanxu takeyinsa. Ta gungura kekenta ta koma dakin farhan. Farkawan iffaat keda wuya taganta a saman kujera itada tayi bacci a waje taja tsaki ko wane aljanine ya daukota ya kawota nan oho? taje lanbu abinta ta nemi abinda zai qosar da ita taci ta haye wata qatuwar bishiyan mangoro mai sanyi bata dadeba ta fara gyangyadi da taga zata fado sai ta daura Dan kwalinta tayi yanda bazata fadoba. Farhaan yayi baqo kuma bayason yaga ramcy dan ba kowa yasa yana neman mataba, sai kawai ya janyoshi lanbu dama wasu takardune zasu cika tare, kusan awa uku sunanan suna aiki. bayan sun qare suna tadi suna dariya, sai kawai sukaga abu kaman ruwa saman kan baqo amma ruwan yellow ne har dai ruwan suka jiqe takardun da suka cija gabaki daya, takardun da da suka sha wahala kamin su sami signed su chika, sun miqe lokaci daya suna kallon sama cike da mamaki da tsoro coz sun gane ba ruwa bane fitsarine hadda diminsa... farhaan ne ya hangota tana sharar barchi, wato fitsarin kwance takeyi, yaja tsaki kunya da takaici suka isheshi kawai yaja abokin sa zo muje ciki, abokin yace minene?? wallahi wani hatsabibin MONKEY muke dashi, shine ya mana fitsari Dan Allah kayi haquri muje ciki kayi wanka ka chanza kaya, sai kuma ya tuna ramcy tana ciki bayason ya gantane shi yasa yama kawoshi nan ga wannan sakaran abinda ta musu, yaqara jan wani tsaki, ya zaiyi dole tasa ya bude mai dayan sashen gidan yayi wanka yadauko mai kayan sa ya saka, abokinsa yanata dariya abin ya bashi dariya matuqa yace farhaan wannan monkey da gani Dan iskane, farhaan ya murmusa ai hatsabibancinsa yafi wannan, ta ciki na ciki bayan ya sallami baqo yazo lanbu yaci qaniyarta sai kawai yayi karo da ita gefen bishiya tana wasa da qasa, abinda ya gani ya bashi tsoro matuqa idonta sunyi suntum kamar jabo tayi kuka.! Tana ganin sa ta kauda kai sai ya yazo gurinta, ya tsuguna umma tana gaisheki tace kiyi haquri zaginda ake miki,kinji tace in baki waya kuyi magana, cox yasan duk abinda za'amata taji haushi baikai a zagi margayin babantaba, yayi ta mata surutuai ko motsi batayiba bare ta bashi amsa har ya gaji ya tafi. Da yamma ta shiga gidan tasan farhaan bayanan sai ramcy zaune a Yar kekenta ta guragu tana cin Apple tana ganin iffaat tasha mur ta toshe hanci, iffaat saida taxo daidai ita ta wanketa da lafiyayyen mari, ta tureta saman kujera ta fadi, ta take qafar da aka daure ta murza sosai, koda batada nauyi saida ramcy ta saki wata qara Dan azabar da taji, ya kalleta irin kallon nan nata na wulaqanci, idan mijin naki ya dawo kice ya kasheni, ta koma lanbu abinta. Farhaan ya dawo ya tararda ramcy a qasa tana kuka ya tambayeta tace ba komai gida kawai takeson ya maidata tana tsoron ta fada yaqara daku iffaat idan yafita ta kasheta haka ya maida ramcy gida.... su iffaat sarkin gaba tun daga ranar bata qara yiwa farhan maganaba ta daina aikin da takeyi, burinta kawai a maidata gida, amma ina ba hali, Ranar tana zaune a sabon dakinta wato lambu cox yanxu kullum tana gun dare da rana ko tsoro bataji, dama tsoro bashida muhalli a zuciyar iffaat tana zaune ta hango wata qofa, koda taje ta daga an sa sakata an kulle ta bude sakatar tana budewa qofa ta wangale saiga ta taganta waje,.... [10:15PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 18 Na Hauwa M. Jabo Dama an hana mai gadi ya barta ta fita, itama an hanata zuwa gurinsa ba gunda take zuwa daga aiki sai aiki... Sai yau cikin ikon Allah gata waje, Ta kalli gidan da tafito kallon sosai, gidane na gani na fada, kusan duk unguwar ba gidan dayakaishi tsari da girma, tayi yan kalle kallenta, ta samu guri ta zauna anan taga yan mata nakai da komowa ko wacce kayan jikinta abin kallone fuska duk fenti ta kalli yanda suke tafiya kamar basason taqa qasa, aranta tace lallai birni birnine bata taba ganin yan birniba saiyau. Amma ita iya sanin ta karuwai ne basa yawo da gyale, amma taga wayannan manya dasu amma basa saka gyale kodai karuwanne?, haka dai aranta tayi ta saqe saqe har guraren yamma sannan ta koma cikin gida.! Tana shiga taga farhaan da wata mata, aranta tace matansa uku kenan, lallai suna qoqari, Bata takansuba dama bayi tazo, wucesu tayi ta fita abin ta bawanda ta ko kalla balls gaisuwa, budurwar ta kalli farhaan waye wannan?? Yace watace,! to WACE CE ITA?? Mai aikice, amma batada ladabi shine kota gaida mutane, look hafsa! ba ruwanki da masu aikiin gidan mu please, ke kullum kikaxo sai kin kawo Qatar masu aiki haba, Bawai komai bane illah bayason rigimar iffaat yanxu sai ta zubar mai da mutunci, ya qara da cewa kuma ma kurmace bata iya magana Dan ki fita hanyarta, tace Allah sarki, Yaja budurwarsa ya wuce daki da ita, kwanan hafsa biyu a gidan. ranar iffat ta dawo daga kallon mutanen unguwa da takeyi da yake tun lokacin ta daina mai magana tadaina yini gida hatta aikin ta dainayi, ta fado ba sallama, sai hafsa ta kalleta a yamutse ke Dan kina kurma baki iya ishara da hannuba Ko uyayenki basu koya miki gaisuwa bane? Kai Allah wadaran halinki, ran iffaat ya baci amma guduwarta data korota tafi mata tsayawa masifa Ta kalleta kawai ta mata tsaki ta wuce bayi abinta, Dan abinda takeji ya matseta!! ta qare ta fito tana waqarta ta badi ba rai soyayyah jigon rayuwa......., nan ma hafsa ta qara magana, wallahi sai na sa farhaan ya koreki duk masu aikin gidannan suna gaisheni amma bandake Mara kunya kawai, waike kurmako?? da ganin idonki nasan ba kurma kikeba iskancini kawai kurmace ke waqa .dama farhaaan duk masu aikin da yake mafi yawa yan matanshi suke sa yana korarsu, wasu kuma baqin halinsu kesa ya koresu, iffaat har zata tankata nan ma sai ta mata kallon banxa tayi tsaki ta wuce abinta. hafsa kamar an tsikareta dama idan kayi masifa akayi banza dakai yafi haushi, ta janyo iffaat ta wanketa da mari.... [10:22PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 19 Na Hauwa M. Jabo Habawa!! iffaat bata dubu girmar matarba Dan kobata kaiba zata kai 25yrs ita kuwa yanxu take Shiga14, itama ta wanketa da wawan mari daidai shigowar farhaan, kee iffaat lafiyanki? hafsa ta riqe kumatu tana mamaki, yau yar aiki take dukanta, tasan tafi qarfinta Dan ubanta mashhurin mai kudine itama kawai tanason farhaan ne take biyoshi har gida amma tafi qarfinsa, yana zuwa daidai ita hasale a ya wanketa da mari biyu masu kyau saida ta fadi, ya nunata da yatsa, ina Dada jaddadamiki ke ba kowa bace illa mai aikina kuma bazan maidaki gidankuba anan zaki ci gaba da zama, kinamin bauta, idan kikayi ba daidaiba am always ready na babbalaki,dama sabida umma nake raga miki so naga ba amfanin haka, qara in nuna miki ni waye, stupid girl kawai ya, rungume hafsa yana bata haquri, hafsa ranta yayi fari Sol Dan yayi hukuncin da ya mata dadi, ta kuwa narke a jikinsa farhaan mai farin jinin yan mata. Ta miqe tsaye taja ta toge ta rasa abinda zatayi ta rage haushi kuma ta bashi haushi ya sallameta amma ina kwakwalwanta baya aiki ko kadan hasalima tausayinsa takeji, *** Tafita daga gidan taje waje kallon yan mata, wata yarinya da take yawan gani tana wucewa yarinyar ta shiga ranta har takeji ina mazata yi qawance da ita, wata zuciyar tace a haka zatayi qawance dake kina duqun duqun, ta kalli jikinta ta tuna tafi wata daya a gidannan amma duka wankanta uku, kamar yan makarantar su jabo basa wanka daga frdy sai frdy.. Ta kalli kanta aranta ta fara imagine irin gasunan tare da yarinyar suna driving a mota Habawa ta gyalgyale da dariya hadda buga qafa a qasa, har ta manta da an mammareta ita kadai kamar zararriya, lallai idan har tayi qawance da yarinyar chan Yar baqa ta qare qawance a duniya, tana nan zaune taji kamar maganar farhaan saida hanjin cikinta suka juya dan kuwa shine, lallai kamin ta ruga ta shiga gida zai iya hangota, kamar monkey dinda ya kirata haka ta Dane bishiyar da take zaune gurinta farhaan yazo daidai bishiyar ya zatsa yana danna waya..... [10:29PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 20 Na Hauwa M. Jabo Yaci gaba da wayansa saida ya qare kamar zai daga kai ya ganta amma hankalinsa na gun budurwar da yake tsarawa a waya, bata gane mi yake cewaba Dan da English yake magana, ya wuce kamar da second 30 ta sauko ta shiga gidan da sauri ta kulle qofar lanbu taje gurin zamanta tana addu'a da Allah yasa bai gantaba, idan ya ganta tunda yace bazai maidata gidaba ya zatayi, zai kulle qofarne ya hanata fita ko ina gashi tanason tayi qawance da yar baqar yarinyar da take gani tana wucewa. Tana nan zaune Tana Zane a qasa ya kwala mata kira taje ta turbude fuska, yace taje hafsa na kiranta, batamai musuba ta wuce shima yayi mamaki sosai yanda ya wasketa da mari batace komaiba, aransa yace kodai ya fara nasarar natsar da itane, hafsa a Palo zaune, wai ta dan qasa mata qafafuwanta da ruwan xafi, ( inaga ta kusa fara period ne coz yan chinar skull dinmu haka sukeyi kuma zakiga sun Dan sami sauqin ciwon cikin) na watsa mata harara, banganeba, tamin bayani shiko gogan yana tsaye ya rungume hannuwansa, nikaina jabo nayi mamakin iffaat data amince da aikin, ta zauna ta riqa juya ruwan turinisu suna dukan qasar qafar hafsa har suka huce ta zubar ta dauko wasu ta mata daqowar da hafsa zataye ta hanbare iffaat ta fadi xaune ruwan suka zube a jikinta duk ta jiqe amma ruwan ba wani zafi sosai, farhaan ya kallesu baice musu komai ba, yaci gaba da kallon ball dinsa, karo na uku ta dauko ruwan zafin da gangan iffaat ta juye matasu a qafafu, hafsa ta tsallara ihu, iffaat ta miqe tsaye da qarfi tayi gefe farhaan yazo da sauri yana duba qafar ba abinda tayi a Zahiri amma tana zugi daga ciki iffaat tayi tsaye tana jiran hukuncin da farhaan zai yanke mata da sauri ya kira Dr. hafsa sai aikin kukatakeyi, yana rungume da ita tanata ihun, yace iffaahh. Ta watsomai idonta da gani tadan tsorata ya akayi haka?? Ta fuske kamar da gaske, naje zan juye ruwan sai kawai tasa qafa zata shureni saita shure ruwan suka juye mata a qafa, harga Allah ya yarda cox yaga yanda ta shureta karo na farko, ya jinjina kai, duk da baiji dadiba amma yasan iffaat batada laifi,...... Dr yazo ya dubata ya bata magunguna, tace zata koma gida kada yar aikinsa ta kasheta, baiji dadiba cox duk cikin yan matanshi hafsace kawai take iya jure jarabarshi, cox ita sonshi takeyi so duk wahalan da zai bata tana jurewa sauran kuma, kudi kawai sukeso, Yakaita gida, ya dawo bai kula iffaat ba ya wuce dakinsa sai yanxu ya kula dakin yayi kacha kacha ya kwala mata kira, ke zaman me kike a gidannan?? Kalli dakina kalli toilet dina! Miye amfanin kine?? [10:33PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 21 Na Hauwa M. Jabo Dole kiyi aikinda aka kawoki kiyi idan har kinason amaidaki gida, so zabi ya rage naki, ko kiyi aiki a maidaki gida ko kuma kiyi ta zama anan har qarshen rayuwarki. taga gara tayi aikin ya maidata gida. *********************** Yau watan iffaat biyar a gidansu farhaan inda sabo yaci ace ya saba da halinta ya kawo budurensa daidai har 8 suna chin uban juna Ita dasu, kuma ko wacce sai tayi nasarar daukar fansar abinda suka mata ta hanya kala kala, kuma farhaaah Sam baya ganewa, ita Har yau ta kasa gane cewa ba matansa bane matan banxa ne da taga sunfi hudu sai kawai aranta tace auri saki yakeyi, irin na wani alhajin qauyensu da akace auri saki yakeyi, kullum sukaje Gidansa kallon TV sai suga sabuwar mata a gidan akace auri saki yakeyi, anan ta gane halinsu daya da farhaan... ********* Yau dai iffaat an tashi ba lafiya zazzabi yake damunta da wani gwauron ciwon ciki, har bacci ya dauketa tsakar bacci ciwon ya tayar da ita taji danshi danshi a qasanta dubanwa da zatayi sai taga jini Habawa ta fashe da kuka koda ta tashi ya mata kache kace a jiki Ashe ya Dade da zuwa bata kulaba, tayi Sa'a farhaan yana palo yana kallon ball ta fito a hargitse tana kuka, ta nuna mai jininta fa na xuba, ya kalleta habo kikeyi? aah ta gun fitsarinane, kunya ta kamashi, shi wace irin yarinyace umma ta sashi dole zama da ita wai mai aiki gashi ta zame mai jaraba, yayi tsaki yana kall ball dinsa za'a katseshi, to kije daki zan siyo miki magani yanzu, yama Dr waya akawo mai pad da maganin ciwon cikin na mata bada jimawa ba Dr ya kawo mai, ya kirata amma ba amsa ya gaji yayi banxa da ita, sai da ya qare kallon ball dinsa ya miqe tsaye sai maganin ya fadi sannan ya tuna da wata iffaat ba lafiya yaje dakinta da yake yana mura baiji qarnin da dakin yakeyiba, koda yajee ya ganta ta dunqule a qasa sai juyi takeyi, duk jikinta ya baci, ya rasa yanda zaiyi idan ya dauketa zata bata mai jiki ya waya da Dr waya shiru bai daukaba, ya tsaya gabanta ganin numfashinta na hawa da sauka kamar zata mutu yaji tsoron tamutu a gida da zamo mai aiki, yaqara yima Dr. dinsu waya yace mai normal ne na farkone ya bata maganin da ya kawo zata warke kada ya damu, ya dagata chak ya yakaita bayinsa ya wanke mata jiki ya rasa yanda zai chire mata tufafi tunda duk sun jiqe yaje dakinta ba kayan da zai saka mata duk saman gadonta suke kuma duk ta batasu da jini, yaje dakin farahnax qanwarshi ya memo wata jallabiya baqa yazo ya rufe idonsa Dan kada ya ganta ya chanxa mata kayan jikinta ya.... [10:38PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 22 Na Hauwa M. Jabo Ya bata magani dagyar tasha ta amaryar ya qara bata wani, yace ta daure ta saka wannan abin pad tace bata iyaba, ya kalli bayan ledar yaga yanda ake sakawa ya hada mata ya bata ta saka, pant ma a kayan farahnax ya daukoshi, yace ta kwanta dakinsa dakinta ya harqitse tunda batada lafiya, tanashan magani tuni tayi bacci, Bata farkaba sai bayan la'asar tafito Palo tana dingishi zata tafi dakinsa ya kirata zonan, ya jikin ta amsa a kasalance, naji sauqi da gani hajiya iffaat anji jiki Dan har idonta sun fada, tayi wani iri da ita, ya kir Dr. ya miqa mata waya Dr ya mata bayanin yanda xatayi komai kuma kada ta damu duk mace mai lafiya tana wannan abin sabida haka ta godewa Allah ya fada mata zata iyayin kwana bakwai tana xubarwa, likita jinina bazai qareba?? No wannan ba jini bane ciwone yake fita idan bai fitaba idan kinyi Aure bazaki haihuba ko bakyason haihuwa?? inaso mana, him wayaga iffaat da ciki, yadai mata bayanin komai sukayi sallama, ta bashi wayarsa, ta wuce daki koda taje duk an tattara kayanta gabi daya da zanin gado duk babu, an saka wani, sai yanzu ta tuna yanda tayi kacha kacha da ko ina... Iffaat saida tayi kwana biyar sannan ta kammala, farhaan ne yasa aka kai mata kayanta wanki. Wannan ciwon shine mafarin fara shirin iffaat da farhaaah.. Tunda ta fara ciwo sai yau ta fita waje kamar yanda ta saba, tana zaune sai ga black girl dinnan ta wuce qamshinta ya doki hanchinta aranta tace anyi yar gayu anan gurin, ta qare kalle kallenta ta shiga cikin gida bayan ta koma gida tana dakinta zaune tunaninta daya ya zata zama yar gayu irin na yar baqar yarinyar nan, taje bayi ta kalli madubi, sosai ta bude haqoranta taga yanda sukayi laka laka a qasa ga wata tsatsa da sukayi tofa bata wankewa fiye da haka ma sai tayi, batasan yanda zatayi dasuba suyi haske irin na tsohuwar matar farhaan ramcyba, cox ramcy akwai wushirya kuma da fararen haqora Tass dasu, tayi tsaki ta qara gaba... Ranar ta fito Palo, karo na farko da ta taba tsayawa kallon TV tunda tazo gidan nan sabida farhaan kullum ball yake kallo itako batason ball a rayuwarta, tafison indiya an qare ball ne Anje talla sai kawai ga tallar signal, mouth Clean ne mai kyau, taga yanda ake wanke baki sai ta tuna ta tabaa ganin farhaan yana wankewa har ta tsaya kallonsa, taje bayin dakin ta nemi mouth clean din koda ta duba sai taga exactly irin Wanda aka nuna a TV ne, tayi murmushi Ashe haqoranta zasuyi fari irin na matar Tv ta Dan barashi a brush tana wankewa yana jini duk da ya mata xafi ta daure cox tanason ta zama yar gayu irin na yar baqa sunanda ta sanyawa yarinyar kenan, iffaat dai haka tajuri yi brush kullum ko nace duk lokacin da abin ya motsa sai tayi cox....... [10:45PM, 4/29/2015] .: WACE CE ITA..?? 23 Na Hauwa M. Jabo Cox a rana sai tayi brush Sau biyar ba'ayi kwana sati day ba suka fara cire wannan lakar, kuma tsatsar ta fara bacewa, Ranar tana zaune tana charafke sai ga farhaan, dama bata gaidashi idan yazo ya zauna yace yau kuma TV ake kallo da charafke, ta juyo ta kalleshi tayi dariya, tace eh so nake in zama yar gayu irin na matan Tv ya kalleta sosai sai yau ya kula tana da wushirya,idan ba idonsa suke masa gixo ba yaga haqoranta sun cire wannan laka lakar na da,. Yace gashi kuwa su Umma zasu dawo anan zasuyi azumi, Dan murna batasan lokacinda ta tashi tsayeba Ashe nayi kusa tafiya gida,? Naga su dije da rukayya da goggo, tanata dariya, lallai gaskiya ya hango, haqoranta sunyi haske, kinga idan kin tafi kin huta dani ko, ta kyalktale da dariya saida kumatunta ya lotsa, ai zama da mugu irinka sai An shirya kamaci arzikin ina tausayinka, shi yasa duk matanka suke guduwa duk matar daka aura sai ta gudu, kalli fa cikin wata biyar saida kayi Aure 8 lallai yarinyar nan batada wayo,! ita ta dauka duk matanane kena, hahaha nine mugu iffaat?? babba ma kuwa. Ta fada ba tareda shakkar komaiba bakya kunyar fadamin haka a gabana? lallai kin girma, ta kalleshi ta tabe baki, ai gaskiya na fada, nima yanzu zan shirya suna dawowa sai in tafi gidako? Taci gaba to yanxu kai zaka mini dunkin sallah ko hajiya?? Yagyara zama ni xan miki ai ni kike yiwa aiki ko? Eh Kaine maigiana, ta juyo tana fuskantarshi kasan wani abu,?? Saikin fada, naga aminar baba sule idan ta dawo aikibirnib sai ta dawo da kayan gayu, tufafi sabbi qanzon shinkafa sabulai, abubuwa dai da yawa na birni, ni ina zan samu?? yayi murmushi dama tanada surutu haka? Yace kema da kina min aiki da kyau da duk zan siya miki abubuwan da kika lissafa hadda qari ma zan miki, amma ke bayan tsiwa da rashin kunya da zubar min da mutunci ba abinda kika iya LA ilaha illallahu, yanzu duk aikinda na maka haka zakace? kallifa baka taba dukana na ramaba, au da ramawa kikeyi? Taaaab wallahi a qauyen mu komi girman qato idan ya dakemu sai mun rama, kai hadda shugaban yan sandan garinmu ya dakemu mukaje gidan sa da dare muka fasa mai mota, ya fito da I do da gaske kikeye?? Ta qara gyalgyalewa da dariya sai tamai kyau, wallahi da gaske nakeyi, kicemi ke yar ta'addace...! [11:13PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 24 Na Hauwa M. Jabo Nan ma dariya tayi ai baka sannibane, ta fara bashi labarin ta'addancin da takeyi a qauye, ya jinjina mata sosai kuma ta bala'en burgeshi Dan yanason yaga mace mai kamar maza, anan ya gane duk abinda yan matansa suke fada akanta gaskiya ne, Abinda yaxo mishi gona hafsa da tayi da ruwan zafi yace Kena da gangan kika xubawa hafsa ruwan zafi? Ta kalleshi ta kanne mai ido ai muguwace, kuma ita tafara xubamin ruwan kana kallo bakace komaiba, sannan akanta kamin mari biyu ita ma tamin daya shiyasa duk cikin matanka nafi tsanarta, kuma da gangan na zuba mata ruwan,? Ke yanxu data qonefa?? Aaaaaaaa miya dameni badai na rama ba!! Ya kalleta da kyau yarinyace sosai kuma lallai batada wayo ko kadan ga shegen surutu... To yanxu dai ki riqa aiki da kyau zan siya miki duk abinda kikace waccan qawar taki tana tafiya dashi qauye idan zaki tafi gida, yatashi ya wuce dakinsa, yabarta tanata zuba, aranshi yace lallai da yana kula yarinyar nan da ta debe mishi kewar qanwarshi farahnax Dan ya kula akwaita da shegen surutu ga saurin sabo saidai sabon baya hana tama mutum rashin kirki Dan yaji yanda take danbe da qawarta dijeee !!! Kamar kullum bayan fitar farhaan taje S pool tayi wanka da yake shi yake debe mata kewar kogin garinsu, tayi wanka abinta ta qare tabi ta lanbu taci abinda xataci ta fita doguwar rigar da farhaan ya bata lokacinda batada lafiya ta saka sai ta mata kyau sosai, tana zaune tana wasa da qasa sai ga yar baqarta tazo tayi kwalliya baqinta sai kyalli yake tayi kyau tsab tsab da ita da takalminta masu tsokane duniya, ba abinda yake burgeta irin yanda take wani Dan tuntu saman kanta ( acucu maza take nufi) yana burgeta matuqa amma batasan yanda zatayishiba ta qare zamanta, ta koma gida da tunanin yanda zatayi wannan abin na saman kan yar baqarta, tayi tunanin Idan ma gashintane zaiyi irin na Yar baqa, tinda gashinta yanada tsawo sosai tunda tazo gidan da kitso bata tsefeshiba. [11:23PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 25 Na Hauwa M. Jabo Tashiga dakinta ta zauna ta tsefe amma saida tayi kuka dan zafi kuma gashi ba kibiya duk ya harhade ko gida kullum sai tayi kuka idan ana mata tsifa, yauma saida tayi taje ta wanke da man da taga anyi hoton qashi jiki haka datti ta riqa zuba kamar an kwaba qasa, haka tayi ta xubarda daddi har yayi fess dashi kamar bana iffaat ba, matsalar daya ba tada mataji kuma ba tasan yanda zatayi irin na yar baqaba, sai ta fito Palo tana goge gashin farhaan ya kalli gashinta aransa dama tanada gashi haka, ya zauna yace dama kinada gashi shine baki kyarawa, tace wallahi parhuun zafi yake min.! Ya kalleta tanata kiciniya da gashi yace ya sunana? Tace Parhuun mana haka naji kowa yana fada, ya kwashe da dariya saida yayi kwalla wai PURHUUN yarinya katki bata min suna sai nanatawa yake PURHUUN lallai wato kusan shima bata iyaba gaskiya anyi baqauya anan yace to ba haka bane farhaan ne, ta dago kai tace Parhan, yace aah farhaan, parha, ke kalli bakina, kice far, tace, par, kalli ki haqoranki akan lebenki zaki Dora sai kice far, takuwa yi tace far yayi dariya yauwa kinyi daidai, sunana farhaan,ta fada daidai tace Dan gayu ko sunan ka sai ka koyamin. Ta bashi dariya wai Dan gayu, so funny, tace to yanxu gayamin yanda ake wannan abin a saman kai yayi sama sosai, yace ni ban iyabafa banmasan mi kike nufina, LA ilaha illallahu, ta to saki gashin ta toshe baki babba na qarya, wallahi ko wasu a matanka kamin ka sakesu nagansu dashi kace baka sanshiba, yayi dariya lallai yarinyar nan case ce, ni nake qarya?? Waima waya gaya miki matanane?? Ta zunburo ta kama gashinta ita burinta a mata irin na yar baqa ta hanya,tace to miye naka? Abokainane ko ban fada miki inada abokai mataba, ta saki gashin kanta ta qara rufe baki da hannu, shine kake tabasu? Hmmm!! Ta tabe baki Mudai garinmu duk namiji mai taba mata Dan iskane, ko wasa bamayi da maza duk iskancine garinmu, kaga da garinmu kake da nace maka Dan iska, keeeee, nine dan iska,?? ta zaro ido ai ban fadaba. nace da garin mu kake.. aranshi yace ko inane wannan iskancine, yace to a birni wayewace ba iskancineba, ya fuske ya miqe zai fita, baka gayamin yanda akeyiba, sai na dawo zan gaya miki... A hanyarshi ta dawowa yayi karo da wata tayi acucu maza sai ya tuna da alqawarin da yayi,ya siyo mata ribbon manya da mataji da man kai ya kawo mata.. Tanatajin dadi zata yi irin na Yar baqa, ba'anan kizo ke saqarba bata iya sakawaba ta kuwa fara hadashi da Allah, ya koya mata shi ba iyawa yayiba, yana mamakin yanda take mai kamar wani sa'arta yanaga ta mance WACE CE ITA.!! Yayi tsaki ke kada ki dameni kinji, na siyo miki kuma ni zan saka miki? duk ma yan matanshi basuda gashi irin nata duk qarine sukeyi, ya zauna yaci gaba da kallon ball dinsa, dama iffaat akwai naci akan abinda takeso. tazo tana hadashi da Allah tana mai shagwaba abin ya burgeshi.. Yayi tsaki aranshi yace yarinyar ta fara rainani, ta kuwa miqamai gashi ta zauna ya rasa yanda zaiyi to ki taje mana ta fara tajewa tana gwalla Dan duk ya sarqe tanayi yana shafa mata mai har ya taju yayi kyau gashin yana gyalli abinka da gashin fulwni sai Wanda ya gani,ya karbi gashin ya kasa tattarshi yace ta tattara da kanta ya nuna mata yanda zatayi ta tattara, to aike basai kin saka irin nasuba tunda gashinki yana da tsayi sosai, Allah ko? eh mana, haka ya taimaka mata tayi parking dinsa kuma yayi irin yanda take so, yanxu kasan mi nakeso? Yace Aah, akwai wasu kaya da ake sakawa sai ayi wannan abin sai ayi kyau a zama yan gayu idan xantafi gida zaka siyomin? nama taba ganin abokiyarka da irin su! Ke ni ban ganesuba, kuma ki sani duk suna cikin kayan sallanki, eh na yaddda ta amsa tana zagwadii.... [11:30PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 26 Na Hauwa M.Jabo Bayan ya dawo, ita duk wautarta yau zai siyo mata kayan taga wayam hannunsa ba komai, laaa farhaaah Yaushe zaka siyomin kayan gayuna? irin na abokanka,? Ya harereta bakida kunyako kina kiran sunana. Ko bangirmekiba. yi haquri Mixance makato? ta fada irin ta matsu dinnan taji zancen kayan gayu, look ki bari zan siyo miki kawai kamin ki tafi gida, yayi niyar yaje da ita a aunata gun mai dinki amma ina yana tsoron ta kwafsa mai wannan hargitsatsaiyar wataqilama taje ta nemo magana, to kawai tace mai amma ranta baiyi dadiba ta wuce daki ta zauna, ta fara tunaninta na zama gayu irin na Yar baqa iffaat yanxu batada buri irin taga ta zama Yar gayu, Niko inason ganin iffaat da gayu, aranta tace gayufa dole saida wanka, taaaab yanxu kullum sai tayi wanka kenan.?? idan ba wanka ba gayu, ta tashi ranar farko data ji tayi wanka Dan ra'ayin kanta, ta fada wanka tayi wanka da ruwan zafi ta wanke dattin wafafuwanta sabida bata yawo da takalmi ko lanmu haka take tafiya ba takalmi tana wankewa ta tuna da qafafun hafsa lokacinda tasata gashi, sumul sumul qafar yan gayu ba kaushi, ta wanke iya yanda zata iya, ta fito ta saka yan tsumma karonta.. Tayi bacci anan tayi mafarkin ta zama Yar gayu, tayi qawance da Yar baqarta, ta farka ta fito Palo cin abinci bata dadeba sai gashi ya kawo mata kaya English Wear ne, ya nuna mata wayannan kayan kike nufi?? Sauran nakai dinki duk na sallah ne amma, Ta kallesu a tsorace ita a qauyensu idan mace ta saka wando za'ace mata yar iskane so bazata sakaba, data fada mai yayi dariya sosai wato qauye bala'ee ne, qauyanci masifa, yace ki riqa saka wannan a gida idan zaki fita saiki saka wayanda bana yan iskaba. OK bari in saka ka gani, anan yaga zata cire kayan jikinta no ki shiga daga ciki mana, ta kwashi kayan ta shiga daki da gudu ta saka wandon yafito da ita ainihin ita sai Wanda ya gani mazaunan suka fito hips din ma ya fito, da yake dukiyar fulanin yanxu take fitowa yayi dan tudu kadan sai head dinsa ake gani ya fito saman rigar, ta fito da gudu tana dariya na fara xama yar gayuko? farhaaah ya kalleta tashin hankali, Ashe babyn nan ta hadu a ransa ya fada, dukda cewa ba daidai ta saka kayan ba amma sun mata kyau, kalli nayi kyau, sosai kin ganki kuwa, tace kamar ba yar aikiba ko, yace sosai kuwa, tana ta dariya ta janyo gashinta da yake ta cire riboon garin saka tufafi wai dole sai yayi mata yanda akeyi dinnan, no ki bari in miki hoton tarihi kuma na turawa umma taga yarinyarta ta fara zama gayu, nan ya sa tayi wannan tayi wannan idan tayi wani style sai yakai zauna Dan dariya, qarshe yace to tazo ya dauketa ita dashi ba tare da damuwaba ta kwanta a qirjinsa ya daukesu photo tana dariya duka dimple dinta sun lotsa gwanin ban sh'awa, kawai daga kan da zasuyi sukaga hafsa kamar daga sama, ta kalli kayan jikin iffaat ta watsa mata harara, ta riqe kunkumi wai farhan na tambayeka waye wannan yarinyar?? kawai fada min gaskiya, ya kalleta kallon bangane mi kike nufiba, sau nawa ina fata miki WACE CE ITA! Amma kina min magana wai iri, hafsa ranta ya gama baci iffaat kuwa dama batayi ta kantaba, murnar kayanta takeyi batama gane hafsarba yana juyowa tace Yaya farhaaah yaushe zaka kawo min kayan sallah? Ya kalleta ita ba abinda ya dameta sai su umma sun dawo, Kamin ya juyo hafsa ta fita Yabi bayan hafsa, itakam ta dauki kayanta ta je dakinta, Kamin ta tada mota yasha gabanta yace mai gadi ya kulle gate, hafsa kuwa anriga anyi fushi, ya bude motar ya janyota jikinsa, ya rungumeta yana shafata a hankali, miye na fushi, hafsa?? Ni kawai ka fada min WACE CE ITA please!! [11:45PM, 4/30/2015] .: WACE CE ITA..?? 27 Na Hauwa M. Jabo Wallahi na gaya miki WACE CE ITA, ba kowa bace illa house girl dina, house girl take saka English Wear?? house girl kake rungumewa kana photo da ita?? Haba farhaaah kada ka mayar dani qaramar yarinya mana! no hafsa wallahi ba haka bane kin gane yarinyar batada wayo ko kadan kuma zata tafi gauyensune da umma ta dawo shine na siyo mata tufafi, kuma wallahi kinji na rantse umma tace in siya mata duk abinda take so, tunda ta kusa tafiya, kiyi haquri wallahi ba komai tsakanina da ita, mi zanyi da mai aikina, haba aiba class dina bane, yarinyace fa qarama ya kanne mata ido, ai dama ka gware a sweet mouth, yayi kissing din gefen fuskarta, muje daga ciki tana jikinsa har suka shigo, dakinsa suka wuce nan dai yachi gaba da rarrashi har mai afkuwa ta afku, nidai jabo idan zasuyi labewa nake sai sun kammala inshigo ciki, Allah ya shirya mana zuri'a kwanan hafsa biyu a gidan amma farhaan bai bari sun hadu da iffaat ba Dan a labarin data bashi ya gane ba qaramar yar ta'adda bace kuma bata mantuwa bare yafiya, daukar fansa gunta wajibine.. ********** Ayau ne su umma zasu dawo farhaaah Dan dole ya karbo mata tufafin da ya dinka mata atamfa biyu les uku, yace ta saka idan su umma sunzo ya bata turaruka da sure duk ta riqa sakawa, da yamma su umma da abbansu da farahnax suka iso farhaan ya rungume farahnax suna tafe suna tadi, da guduna naje gunta ina hajiya sannu da zuwa ta kalleni, iye yarinyar hajiya an girma an qara kyau haskene kawai bakiyiba har yanzu, ina zatayi haske tunda bata wanka, ta gaida Alhajin nasu ta gaida farahnax kaman batajiba ta qara gaisheta, da dalla mata harara, kin ishi mutane, haba naji mana, farhan ya kwashe da dariya, yace sister ba sauqi ai iffaat akwai naci tun xuwan iffat jininsu bai hadu dana farahnax ba, ta tabe baki, tajoyo gun hajiya tafara surutu batama bari su hutaba saida farahnax ta daka mata tsawa sannan ta natsu, Sumi sumi ta wuce dakinta bata qara fitowaba sai gobe da safe shima hajiya ta kirata tazo aci abinci, farahnax tana bacci lokacin da sai taga tsiya, ***** Bayan kwana hudu da dawowarsu, suna zaune hajiya da Alhaji suna kallo, saiga daya daga cikin yan matan farhaan tazo, tana zuwa taga iyayensa saita wayance tace kuskuren gida tayi, tana fita iffaat tacema hajiya wallahi qarya takeyifa hajiya qawar farhaan ce nan ma take kwana har dukana ta tabayi TOFA ZATA TONA ASIRIN FARHAAN MUJE ZUWA ...... [12:58AM, 5/1/2015] .: WACE CE ITA..?? 28 Na Hauwa M. Jabo Qawa kuma Alhaji ya maimaita?, eh lokacinda tazo tayi kwana hudu anan har na taba mata kaya ta mareni, hajiya tace amma dakinki take kwaniko?? Aah dakin farhaaah take kwana ai ba ita kadai bace sunada yawa, yace min duk qawayensa ne, yace wai anan wayewane, sabida nace mai mu qauyenmu iskancine, umma tace hardake yake kaiwa dakin nashi?? Aah hajiya ni kullum dukana kawai yakeyi, nan dai madam iffaat tayita bada labarinda ba'atambayetaba, ganin duk sunyi shiru ransu a bace yasa tasha jinin jikinta a ranta tace koda yaya farhaan yace aboki mace gun namiji a birni shine wayewa so ba komai bane, taci gaba da kallonta sukam tuni sun bar gun sunje daki domin tattauna xancen wayo farhaan Neman mata yakeyi.!!! Ran umma yayi matuqar sosuwa, saida tayi hawaye, Abba yayi ta bata haquri, Da yamma farhaan ya dawo da farahnax coz tunda suka dawo cikin yawo suke, umma ta turkeshi da ba zata! Tace mai dazu baka nan daya daga cikin budurenka tazo nemanka, ya Sosa kai budurwa umma?? Eh inaga bakuyi waya ka gaya mata iyayenka sun dawoba hala? Ko kuma tana sane tazo ta nuna kantane ko qawayenka zance a yanda kake cewa kai wayayye, nan umma ta shiga yimai fada kamar numfashinta zai dauke Dan takaici, iffaat ce taji magana fada fada tafito taga abin mamaki ana yiwa farhaaah fada, farahnax ta koreta, umma tace ta tsaya, taja ta tsaya, ai ita ta fada mana yarinya yar albarka, farahnax ta taso a fusace tazo gun iffaat kinyi muna funci kinji dadi munafuka kawai, iffaat tace haba daga fadan gaskiya saikice nayi munafunci ai ba qarya nayiba labari na baiwa umma kuma ni bansan fada zata masaba, kee ina magana kina magana sakarya kawai ta wanketa da mari, kamin ta sauke hannu tuni iffaat ta aiko mata da nata saqon Marin,umma tace that is very good iffat, ta gane very good coz malamansu na makarantar boko kamin a koresu yana cewa very good, idan aka bada amsa yaji dadi kin min daidai gobe sai ki qara dukanta, umma ta kalli iffat tace duk ta dakeki ki rama ran farahnax ya gama baci koba kamai ta girmi iffaat anxo ana siyamata raini a gunta. fau zata wuce dakinta, kowa yayi tsit a palon Abba yace ta dawo duk Ku zauna har umma ta zauna, ya kalli farhaan daya sunkuyar da kanshi a qasa tunda aka fara zancen, abba ya kalli farahnax da tasha mari umma nacewa good, ya kalli iffaat da tayi wani rasha rasha da ita a qasa tana kallonsu, Abba ya fara magana yace farko dai iffaat ba gulma takawo manaba labari ta vamu kuma da ita yarinyar batazoba da naxamu saniba, a yanda na fahamci labarin itama farhaan ya gaya mata, har take cewa a garinsu maiyin haka Dan iska shi kuma yace anan wayewace kunga ita bata daukeshi bad thing ba cox haka ya nuna mata, ya juyo ya kalli farahnax millions time na gaya miki ki daina saurin fushi, ke macece Aure zakiyi ba abinda haka zai haifar miki nan gaba sai nadama, iffat kin burgeni da kikayi jarumta irin haka amma ki riqa haquri kuma ki kula da Wanda ya girmeki, tace Tau Alhaji., ba ko wanne mutum bane zai iya yanda kikayi, kai farhaan bayan sallar maqreeb ka sameni a daki... Abba ya tashi umma ta bishi, farahnax ta juyo gun iffaat ke ni zaki Mara......?? [6:05PM, 5/2/2015] .: WACE CEE ITA..?? 29 Na Hauwa M. Jabo.. Farhaan duk da baiso yin maganaba saida yayi, lool farahnax ki fita hanyar iffaat ya fiye miki, banason kina biye mata yarinta Yana damunta kuma bakisan ko waye itaba, tace WACE CE ITA bayan house girl dinmu..! Nidai na fada miki ya miqe ya fita iffaat ma tashi tayi taje dakinta, tana zuwa tahau hada kaya, kawai ita dole ta koma qauye ita ba zata iya zama a gurin da tanaji tana gani a mata bata ramaba, sabida haka gara qauyensu, suci uban juna da yan qauyensu ******* Ki bari sai an kusa sallah mana, aah hajiya inason inyi azumi gidan mu, goggo ita kadaice a gida, kamar tayi goggo aikin takeyi, bayanda ba'ayi da itaba, amma iffaat ta rufe ido tace gida take so dole suka haqura suka barta.. sun shirya mata goma na arziki akace farhaan yakaita, baisan qauyen ba amma an mai kwatance sai ya gane ita kuma dama da an isa garinsu zata gane gidan su. Suna kan hanyar komawa yake gaya mata zai tafi karatu UK bazai dawoba sai bayan shekara uku saidai ya riqa zuwa hutu, ita kam duk daya a gurinta, Dan ta gaji da zaman birni ba abokai, sun Isa qauyensu yara kuwa tun daga farkon gari suke bin motar har aka shigo ainihin qauyen, iffaat tace ya tsaya, yace mun kawone tace kaidak ka tsaya, ya tdaya. leqowa kawai tayi ta kallesu batama fitoba gabaki daya yarannan suna ganin iffaat a mota suka watse, suna ihu wallahi ippatu ce kozo mi gudu, bawanda ya manta da ita, cox har yanzu su dije da rukayya ana xuba iskanci son rai a gari... Sun Isa gidan su ta tarar anyi ginin bulo an gyara ko ina abin ya bata mamaki, farhaan har ciki ya shigo goggo na ganin iffaah ta Hau salati, da mamaki Dan batasan zatazo yauba koda matar da ta dauketa tace mata qarshen wata zata dawo kamin azumi kenan tayi sallah gida sannan ta koma. Aka fara shigowa da kayan abinci kala kala, ita kanta iffaat batasan dasuba, sannan ga kayan sallar da umma ta mata kala uku shima farhaan ya dinka mata guda biyar ya qara biyu daga baya, goggo ma an kawo mata atamfa guda biyu baki yaqi rufuwa Dan murna.... Muje zuwa muji anya iffaat zata iya rayuwa a qauye ko yaya?? [6:11PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 30 Na Hauwa M. Jabo ************* Kamin kace kobo duk qauye ya dauka da dawowar iffaat chikin mota mai kamar jirgin sama. Ko ina sukasan jirgin sama oho!?? kowa zuwa yake mata sannu, wasu kuwa gulma ake zuwayi, bawanda yasan aiki tajeyi birni sabida goggo bata fadawa kowaba duk wanda ya tambayeta sai tace ai tana birni gun qanwarta, Su dijee an tafi biki chan nesa dasu, basu ji labarin dawowar iffaat ba sai da la'asar bayan sun dawo, suka zo ganin iffat, ganin ta ya sasu farin ciki koda batayi wani haskeba amma tadan chanza suka fara baiwa juna labari, iffaat natajin haushi anyi shegiya da yawa bata, cox dijee tayi hatsabibanci bayan tafiyar iffaat, tayi wata qawa ummulkhairi wacce itama hatsabibiyar gaskece, bata wasa hakadai take yanda suke, itama iffaat ta basu labarin ta'addancin da tayi barni, amma bata fadi cewa qawayen farhaaan bane, sunsha dariya matuqa, anyi kewar juna, A tunanina iffaat zata bar abinda takeyi a qauye koba komai anje birni kuma ta fara Dan wayewa tanason ta zama Yar gayu, Ashe ni jabo bangane bane, iffaat iskanci da la'ana sai abinda ya qaru, bare yanxu da suka zama su hudu, ni kaina ina tausayawa iyayen yaran, kowa kuka yake dasu a qauye sun gagari kowa ga iffaat an dawo. ****** Iffaat take tambayar goggo ya akayi aka gyara gidansu, goggo ta bata labarin cewa ai yayantane dake birni sukazo ganinta suka tarar batanan kuma suka tarar da babanku ya rasu, to su suka gyara gidan suka bata wata takarda wai duk lokacinda kika dawo ki nemesu, zasuzo su ganki, sun kawo min alkhairi kala kala daga birni, ainikan naci arzikin yayan kishiya, Wannan karon Goggo bata tsangwmawa iffaat kaman daba, shi yasa suke zaman lafiya, ba ruwanta da harkarta itama haka, Ranar suna hira da goggo take cewa Wai ihhatu a birni bakiyi saurayiba, ta zare ido ta dafe qirji saurayi goggo!!! nida ko fitabanayi, nan iffaat ta gayawa goggo aikinta goggo taji tsoro, Allah yasa dai baya biyoki da dare, daga ke saishi a gida ba koea. iffaat tace taaab nida ko shiri bama bamayi, nan ta fadawa goggo ta'addancin da tayi,goggo bataji dadiba koda dama tasan za'ayi haka, nan goggo tadan fahimtar da iffaat yakamata ta gane ta girma yanxu tadaina shirme da shiririta, kina ganin idan kikaci gaba da haka zaki sami mijin Aure,?? a qauyen nan fa ba yarinyar da ta tabayin jini a gida, taji raaaas ta tuna itama tayi sau daya a birni amma bataabaiwa goggo labariba, ******* Maganganun goggo sun dan ratsa iffaat har ta fadawa qawayenta su daina tsokana ko su rasa mijin Aure duk da cewa basu dainaba amma sun rage kwarai saidak idan an musu suna ramawa, haka kuwa akayi sunyi sauqi sosai, har takai suna gaida mutane a hanya, amma fa idan ka tabasu zakaga bala'ee da masifa..... [6:17PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 31 Na Hauwa M.Jabo Rayuwa tana tafiya ayanda aka sameta, Tun bayan komawar iffat qauye takejin garin baya mata dadi amma bata gane komaiba sai take dauka kamar sabon da tayi da mutane birnine suma birni sunyi kewar iffaaat sundan saba da ganinta da tsiwarta idan sun tuna sai suyita dariya, idan ma farahnax tana magana akan rashin kirkin da iffaat ta mata sai su nuna mata ai itace batada gaskiya, akan me zata daketa,kusan duk bayan iftaar idan suka zauna sai anyi labarin iffaat tun farahnax bataso har abin itama ya riqa bata dariya kuma yana burgeta, duk Wanda yaji shaqiyanchin iffaat sai ta burgeshi, umma dai ta kula farhaan yaji dadin zama da iffaat, ranar bayan buda baki umma take cewa inaga bayan sallah mu tura azo mana da iffaat, naga duk kowa yaji dadin zama da ita, tunda yanxuma kaga bazamu komaba kai kadai zaki tafi ka kammala karatunka , koya kuka gani, eh umma duk sun amince, Iffaat ma zaman qauyen baya mata dadi matuqa kuma tanajin dadin harka da qawayenta saidai mafi yawan lokaci takanji tayi kewar umma, duk ta zauna takanyi labarinsu, amma bata bada labarin farhaaah, ************************* Yauda gobe ba wuya a gurin Allah, Ramadan ya qare anyi sallah lafiya su iffaat yan mata sai gantali akeyi a gari, ba mijin aure, ba mashinshini, abin yana damun iyayensu bama dijee ba da take yar lukuta ga manyan duwawun da suke biye da ita, gasuda tsini idan tana tafiya sai ta Dan duqe cox suna mata nauyi nima Jabo Dana ganta na dauka turosu takeyi, ita rukayya dama kamar bulala take, iffaat kuwa hips ne kawai take dashi mazaunanta basuda tudu irin na dijee dijee a gida tsini ake cema dijeee sabida tsinin maxaunnan ga gafafuwan nan nata kamar doya, qirar maxa takeda Allah ne kawai yayita mace... Akwai wani mai tura kura yana saida ruwa duk qauyennan shi kadai yake saida ruwan masu dadi, yakan sakawa ruwanshi alim idan sukayi kyau sai ya fita saidawa yazo neman auten dijee kuma an bashi, shima kasada yayi dan duk qauyen nan bai samu mataba sabida tsananin muninsa sai yazo neman Dije iyayenta suna Neman kai da ita tuni suka sallama, rukayya kuwa wani Dan uwanta za'a hadata dashi, su ippatu daikam ba Kowa har yanxu. Bayan sallah da sati biyu.... Ranar iffaat da qawayenta sunje yawo sun dawo sukaga mota mai kyau iffaat tasa aranta kamar tasan motar amma ta manta ina tasan motar, tana sanye da atamfarta ta sallah da yake yanxu gayu sukeyi an daina yawo ba takalmi duk sun iya acuchi maxa ataqaice duk qauyen ba Wanda yakaisu gayu da iskanci, motar ta tsaya gabansu farhaan taga ya fito daga motar, ai da gudu taje ta rungume shi, ba tareda damuwaba tanata dariya, su umma suka fito ai batasan dasuba tasaki farhaan taje gun umma ataqaice dai taji dadin ganinsu matuqa, farhaan rungumeshin da tayi yaji qamshin sure din daya bata yace kullum ta riqa gogawa Rexona na aloe vera ne kuma long lasting protection ne yace lallai yarinya ta waye harda saka turare.... [6:24PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 32 Na Hauwa M. Jabo Sun qarasa gidansu iffaat goggo tagansu ba zata duk da batasansuba amma ta gane farhan goggo harda tuntube Dan tsabar rudewa, baki kuwa har kunne tasan cewa zata samu alkhairi zuwansu, ta musu shinfida aka kawo musu fura sabuwa aka siyo nono aka xuba a cikin furar sun kwashi damu lafiyayye farahnax hadda santi da yake goggo ba qazama bace su iffaat ne dai ragajabul, mutane sai zuwa kallon su akeyi, iffaat dai bata gaida farahnax ba, ke ko kallon gefenta batayiba, iffaat tace wa farhaan yazo ta kaishi yaga gari, yakuwa biyota sun zaga garin tana nuna mai guraren da tayi hatsabibanci sunata dariya ko ina kallonsu akeyi wasu suna gulma ana cewa ta lalace, har yanzu ba miji amma ba halin magana yanxu mutum yaji ba daidaiba ba Wanda zai iya tunkararta da zancen rashin miji, dasu dijee aka zaga garin duk gunda ya masa kyau sai ya tsaya ya dauki photo har sukaje bakin ruwa, suka shiga kwale kwale yayi hotuna sosai, qarshe yayi photo da iffaat bakin ruwa, hotunan sunyi kyau sosai iffaat tayi haske yanxu cox kullum sai sunyi wanka tanason ta zama yar gayuuu.... Bayan sun dawo gida umma tace miyasa bamu tafi da farahnax ba, iffaat tayi sauri tace au dama tare akazo da ita?? Ni banma gantaba sai yanxu. Taci gaba umma kinsan farahnax ta tsaneni har na baro birni batamin magana, shiyasa nima na fita harkarta, kowa sharhin nata ya bashi dariya. duk suka kwashe da dariya, nan dai aka shiryasu sundaina fada, Su umma suna son a basu iffaat taci gaba da musu aiki, koda ba aiki takeyiba yanxu kamar yarsu take Dan Allah yasakawa umma qaunar yarinyar, dama ga iffaat akwai shiga rai, ran iffaat baiso tafiyaba amma idan ta tuna abinda goggo tace mata sai taji gara ma tabar garin wataqila birni ta samu miji tayi Aure, Sun tafi akan nanda sati daya za'a aiko a tafi da iffaat Sun ma goggo alkhairi sai washe baki takeyi, itakam yayan kishiya sun mata rana, koda bata haihuba ta moresu. **** Bayan Sati daya akaxo daukar iffaat ta buga qafa a qasa akan ita sam baxatajeba sai anyi bikin qawayenta dijee da rukayya, goggo tasata daki, ta mata huduba, Yanxu idan kika zauna har bikin su wallahi gulmarki kawai zasu riqayi ace har qawayenki sunyi Aure ke bakiyiba kinga ba dadi haka, gara kije birni abin ki, ki raqayin gayu kamar yar yarinyar nan danaga sunxo da ita har ki sami miji Dan gayu irinki kiyi aurenki a birni, idan kuma zama zakiyi bakin mutane yakamaki to shike nan. Maganar goggo ta shigeta , gara birni da qauye, ta hada kayanta taje tayi sallama da su dijee ransu baisoba tana babbar qawa ayi bikinsu batanan amma ba yanda ta iya itama taso ayi da ita, amma goggo ta hore mata kunne...... [6:46PM, 5/2/2015] .: WACE CE ITA..?? 33 Na Hauwa M. Jabo Iffaat an dawo birni system dinda Dana yanxu ba daya bane cox yanzu aikinta yafi Nada sauqi yanxu dakin farahnax take gyarawa Dana umma... Ranar iffaat ta qare aiki tana zaune ita kadai a Palo umma da Abba duk sun tafi aiki farahnax ta tafi skull taji sallamar mace ta amsa tashigo, wa zata gani yar baqarta, wacce take kwaikwayon gayu a gurinta, batasan lokacinda ta miqe tsayeba ta washe mata baki ta gaisheta a mutunce kamar ba itaba, yar baqa ta amsa tana mamakin waye wannan mai fara'a haka, duk da har yanxu da sauran qauyancinta batayi kama da house girl ba, ta zauna tana tambayar farahnax, tace ai ta tafi makaranta, amma ta kusa dawowa, suna zaune ta kawo mata ruwa da abin tabawa iffaat sai satar kallonta take, aranta tace ita ba wata kyakyawa bace sai iya gayu, Allah ya nuna mata ranarda zata zama Yar gayu irin wannan. Tana chikin tunani saiga farhaan ya fito, tana hangoshi sai naga ta sa hannu a jaka ta dauko turare ta qara fesewa a hankali ta mayar da sauri, batasan na gantaba, ta gyara zama tana wani murmushi. Farhaaah ya Iso, Tana wani kashe murya, yanda tamin magana daban yanda tamai daban wato akwai banbanci tsakanin mace da namiji ko duk chikin gayunne,?? Yaya farhaan kayi wuyar gani, ya dan sosa qeya abubuwan ne sai a slow zainb, ya kike yasu hajiya? Lfya lau tana wani maqe murya, araina nace dama sunanta zainab dama sai ita ance duk zainb haka suke da rawan kai da kurin banxa.. yanda take masa duk sonda nake mata sai naji lokaci daya na tsaneta, ta bani haushi, narasa dalilin da yasa raina ya baci.!! Kodai dan ta cika kurine yasa haka oho, hira suke dashi tasaki jiki tana fari da ido tana kashe murya tana Neman gindin zama, Ihuuun farahnax naje zainb khalifa kece gidan mu haka? Kai I miss much wallahi tunda kikazo bangankiba ina kika shigane? Wallahi karatunne kinsan sai a hankali,! hahaha hadda Ku gifted karatu na Baku wahala, chaiii dariss God oooooo, farahnax akwaiki da zolaya,sukasa dariya tajata suka wuce daki... Bayan sun wuce farhaaah ya juyo kaina yan mata yar gidan umma, har yanxu ba'a iya gayun bane, na harareshi na zubar Dan duk na tsaneshi duk haushi yake bani daya biyewa wannan zainb din, ya min kallon banganeba Mina miki kuma? namai kallon ya rage naka ni tashi na wuce dakina, na barshi yana mamakin mi ya faaru yarinya kamar hawainiya lokaci daya sai ta sauya, bayan da safee sun gaisa koma miye ya rage nata. ****************** Farhaaah yaune zai wuce Canada karatunsa, ana tadin rabuwa naji yana cewa yakamata asaka yarinyar chan makaranta, umma tace itama tayi wannan tunani Dan ranar taga yanda take sallah ban iya komaiba hatta alwula ma bata iyaba Kowa ya aminta da shawarar farhaaah na Sanya iffaat boko .. Farhaaah dai ya baqunci Canada yabar iyayensa da kewa. Muje zuwa muji yanda su iffaat za'a fara karatun boko idan ta waye ya style din zai koma.!!! [9:55PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 34 Na Hauwa M.Jabo ************** Tun ranarda farhaaah yabar naija gidan yake yiwa iffaat duhu da girma tin bata baiwa abin muhimmanci, amma tana damuwa matuqa yanxu har taji abin yana neman ya gagareta, haka takejin zuciyanta na wani bugawa duk lokacinda ta tunoshi, idan aka kira sunanshi sai taji kamar zuciyanta tafito waje, ta rasa gane yanayinda takejin ita ba wayoba bare ta gane cewa ta kamu. A duniya iyayen farhaan sunada kirki kuma sun mata halacci a rayuwarta a matsayinta na yar aiki amma sun mayar da ita kamar yarsu An nema mata mai lesson, haka an sakata makaranta tana zuwa, haka tana zuwa gun malamin hadda da farahnax suna karatu tare, gata da saurin fahimta so gun lessen da yawa ake mata karatun, Duk karatunnan da take lokaci daya idan ta tuna farhaaah sai taji ta manta komai hatta takan manta WACE CE ITA, In short rayuwa a gidan bata mata dadi ko kadan, umma tasha tambayarta mi yake damunta amma saita fuske tace ba komai idan aka matsa sai tace ta tuna babantane!! Sau tari zuciyanta takan mata qunci taji batason jin komai sai taje lanbu ta haye bishiya tayi kuka son ranta, ba Wanda yake jinta a gurin, idan ta qare ta dawo gida idan ma idonta sun nuna takance bacci tayi, ******** An Sami Hutun makaranta anan farahnax tasa rigima sai an tafi Canada gun Yaya farhaaah, da yake ita iffaat karatunta a baibai yake shi yasa takeshan wahala a gun lesson yanxu haka ko Hutu batada sabida anason a mata jumping to jss3 hakan yasa karatun ya danqaremata. Sun shirya tafiya canada Abba ya kaita gidan wani abokinsa Ajiya har su dawo daga Canada din. Kuma yace yarsace, gidan sunada mutunci abinda ya bani mamaki shine nan ne gidan su Yar baqa wato zainb khalifa sun mutuntani coz Basusan gaskiyar Wace ce ni ba, Dan zaman da nayi gun zainb khalifa na koyo abubuwa ba kadan ba gata very friendly saidai tacika rawar kai da jiji dakai sai qaryar yaruka kala kala, gashi malama iffaat yanxuma take koyon turanci bare wani yare, Dan sati ukun da nayi da yake zainb akwai surutu sai na rage jin zafinda da nakeji idan na tuna farhaaah, Allah mai iko tanason tayi tadin farhaan da yar baqarta idan ta tuna WACE CE ITA sai taja bakinta ta dinke,Dan ta kula kamar Yar baqa bunsurace Kowa so takeyi. Satin su umma uku suka dawo, sun mini tsaraba kamar nice yarsu, ba abin da yafi bugeni kamar kayan da farhaan yace a kawomin, da body spray na Rexona da sure, idan naji qamshinsu yakansa na riqa wani tunanin da ni kaina bana gane mi nake ciki .. [10:02PM, 5/4/2015] .: WACE E ITA..?? 35 Na Hauwa M. Jabo A cikin kayan da Yaya Farhaan ya siyomin hadda waya wai mu riqa gaisawa, ranar da aka bata kayan Dan murna ko bacci takasa yi, kuma wannan abinda takeyi bata gane komai, ** wayar ni ban iya komaiba hasalima nidai saidai na gaisa dashii in miqa musu, tawa wayar kullum tana qasan pillow karatu ya sakata gaba, ga abinda ta daukarwa kanta tunene tunanene... farahnax ta koya min yanda ake amfani da waya, ta kira min yaya farhaaah munyi waya dashi, Wanda tunda ya tafi saudaya muka gaisa shima ina fara magana ta tsinke, Mun gaisa sosai yanayi yana jefomin English ina ganewa amma bana iya bashi amsa, har yan kudin dake cikin suka qare abinka da international call.. Bayan kaman kwana hudu ranar na dawo lesson ina danne danne a wayar kawai tayi karo da maganar da sukayi da Yaya farhaan, zan iya CE muku duk yinin ranar abinda ta saurara kenan, ta rasa mi yasa komai nashi burgeta yakeyi, bama kamar idan taji dariyarshiba, itama saita dara haka take zama ta miqe gafafu tayita saurare tana dariya, wannan voice yasata walwala ranar farahnax taso ta gane sai kawai ta daina saurare dan bata iya delete ba, Sai yanzu ta gane mi wannan takardar da goggo ta bata tace yayyenta sunce ta kira take nufi, Ta nemota a cikin kayanta ta saka amma wayar tata ba kudi, ta je gun farahnax tace ta kira mata wannan number, farahnax kuwa chatting takeyi bazata iya bata wayantaba sai ta saka mata recharge card na 1,500 ta saka mata number tace ta kira, ta koma dakinta haka tayi ta kira ba tareda tasan kiran yana shigaba saida ta bar miss call 47... Ameen bayan ya dawo yaga miss call da yawa sai ya kira, Tayi sallama, ya amsa yadauka mamarshi ne Dan kusan muryarsu iri dayane, mama lafiya kira haka ?? sai tace ba Maman shi bane ya tabbatar da wrong number ne sai kawai yace wrong number ya kashe, bai tsaya yaji abinda zataceba, Itama dataga haka sai bata qara kiran number ba, *************** Kwanaki sun tafi iffaah ta waye iya wayewa kamar ba Yar aikiba, wani lokaci Idan sunfita tareda farahnax bazaka ganetaba cox tafi farahnax kyau nesa ba kusa ba, saidai har yanxu qauyancinta da yake nuturally ne sai bai saketaba tana taba abinta, gata bakinta baya shiru duk abinda ta gani saita tambaya gata a waye a dressing amma a aikace har yanxu da saura... shekara ta zagayo iffat zata koma qauyensu Dan sallah da azumi achan kamar yanda sukayi alqawari run farko,ta rasa gane dalilin da yasa ranta bayason komawa qauye kodan zancen goggo ne da take cewa za'a saka mata ido a qauye tayi zamanta birni! ko kuwa rabuwa da iyayen farhaan da, ko mahaifiyarsa ta kalla sai taji sanyi sabida tsabar kamarsu da farhaaah..... [10:05PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 36 Na Hauwa M. Jabo ************** Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa da da iyayen farhaaan.. Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da takeyi. Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba, hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah, sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa rashin gane takamammen abinda yake damunta. Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce. Hello Ta amsa tanajin dadi Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi bala'en bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye, na rashin dalili ta yi shiru. Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa duk lokacinda take tunanin yaya farhan take shiga wani hali?? Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba?? Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ?? Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi?? Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko daya. Tayi wani tsaki Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi fiffike taje ta Ganshi, Amma ba halin yin haka, Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada labari har yanxu ba tasan miye soba.. [10:11PM, 5/4/2015] .: WACE CE ITA..?? 37 Na Hauwa M.Jabo *********** Kwanaki sunja gaba har anyi sallah qarama, iffaat zata koma gidan aikinta a birni, tun lokacin da farhaaah yazo batayi waya dashiba jifa jifa tana kiran su umma ta gaidasu, kuma farahnax tana turo mata recharging wayanta. Ta shirya tsab sai birni, Su umma sunyi murnar zuwanta matuqa ko banza umma nasonta Dan akwai bada labarin ban dariya kamar me shi yasa daga umma har Abba zaune sukeyi tana basu labari suna kwasar dariya. Wannan karo an samu chanxi iffaat ta dawo amma ba komai tsakaninta dasu, musamman umman farhaan kunyar su takeji! Da kuwa zaune take tasasu gaba tana basu labari suna dariya, gashi kullum tanada sabon labarin da zata bayar, bata maimaici amma yanxu Dogon motsi bata iyayi gabansu, Ashe akwai abinda zai iya chanza wannan hatsabibiyar yarinya,?? Hmmm sai soyayyah.. soyayyar da ita kanta batasan tanayiba, Kai amma ni jabo na jinjinama duk soyayyar da tayi tasirin chanxa wannan yarinya koda ta qara wayewa yanxu... ******* Iffaat miyasa tunda kika dawo kika daina bamu labari?? ta sunne kai qasa tayi murmushi ba komai hajiya! Nidai wannan zuwa hutu baiyimin ba yarinya duk ta susuce sai rama takeyi? Ko wani Abu ya faru bakyason fada mana?? Laaa hajiya bakomai Abba yace ki kyaleta kinsan fa ta qara girma hankali yana shigarta, duk aka saka dariya, Farahnax ce ta shigo tare da wata yarinya kyakyawa zatakai 24yrs kyakyawace sosai, tana shigowa tace kinganta, yarinyar mai amsa sunan suhailah ta gaida su umma da abba a kunyace, ta kalleni cikin fara'a tace Ashe ma qaramace sosai gata kyakyawa kuwa saidai tafini kyau da kike cewa munyi kama., umma tace ai kuwa nima sai yanxu naga wannan kama da kuke cewa sunyi, saidai yata iffaat tafi kyau, sukayi dariya gaba daya iffaat ta gaisheda suhailah umma tace kuje daki mana, suka wuce umma tace na bisu mama na tashi na bisu, anan farahnax take baiwa Suhaila labarina sunata dariya, sai nadan saki jiki dasu dama wani lokaci zaman kadaicine ke haifar mata da damuwa bata saniba.. Suna tsaka da hira wayar Suhaila tayi qara, ta dauka tana kashe murya, duk da cewa da English suke maganar hakan bai hanani fahimtar dawa take maganaba kuma mi suke fadaba, farahnax tana bani labari amma hankalina Sam baya tare da ita qirjintane ke dukan uku uku wani baqin ciki Mara dalili takeji Wanda ya haifar mata da rashin natsuwa lokaci daya, Daidai nan kunnenta ya jiyo mata maganar da takasa tantance sanadiyar rudewarta sai ganinta tayi a asibiti....! [12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 38 Na Hauwa M. Jabo Tana bude ido taga Su umma sun zagayeta Yar budurwar na zaune gefenta itada farahnax, sai nan ta tuna da abinda kunnuwanta suka jiyo mata, LAAA KINGA NA MANTA IFFO BANGAYA MIKIBA, KINA QAUYE AKA YIWA YAYA FARHAAN BAIKO DA SUHAILA..!!!! Hawaye ne suka wanke mata fuska shaaaaar, idan bata mantaba Wannan maganar itace qarshe maganar da taji sai yanxu da ta farka ta ganta a asibiti, ta motsa hannu taji yayi nauyi ta qurawa Suhaila ido mi yasa taji tana Sonta aranta?? Amma sai take ganin kamar ba sontane takeyiba tsanarta takeyi,?? Tanajin Suhaila har cikin ranta amma kuma tsanarta tayi yawa a zuciyanta. tana tsaka da tunani umma ta dafataa ta mata sannu, ta kalli umma tace hajiya miya faru?? Ya akayi mukazo asibiti? Umma ta bata amsa da kin samu sauqi dai ko? suna haka sai ga nurse tazo ta dubata aka tabbatarda yanxu ba abinda yake damunta, illaa kawai ta rage tunani.... Ta tashi zaune anan farahnax ta bata labari muna tadi dake nake gaya miki an yiwa Yaya farhaan baiko da Suhaila sai kawai naga kin danne kai kina juyawa kika miqe tsaye sai kuma naga kin kika fadi sumammaiya, Suhaila ta katse wayar mukayo kanki muka kira umma taxo aka saka miki ruwa amma ko motsi daga qarshe sai Abba yace a kawoki asibiti, farahnax tace miyake damunki iffo?? Tunda kika dawo gida kika chanja ko su sukace miki ki riqa yi mana haka? Wallahi iffo banajin dadin ganin ki a haka, Dan zaman da mukayi na Saba da tsokanarki da labaranki Masu dadi, shiyasa ma na kawo Suhaila itama ki bata labarai sai Kuma haka ta faru, please ki saki jiki damu ke Yar uwarmuce kinji.!? Aranta tace da nasan abinda yake damuna Dana fada kodan samun natsuwar xuciyata.. Ta kallesu tayi murmushi ba komaifa, sai tayi shiru hawaye suka gangaromata,umma ta matso Ku bar min yarinta ta qarajin sauqi sannan Ku fara mata jarida. Dukansu suka saka dariya har iffaat din saida tadan murmusa. Saida ta kwana daya da yini sannan aka sallamesu. ** sun koma gida umma da farahnax suka sa iffaat gaba sai ta fadi abinda yake damunta. Amma ta murje ido tace bakomai koda yake ba komai din tunda ita kanta batasan abinda yake damunta ba, nifa tinda ta dawo Hutu banga dariyarta sau ukuba, umma tace nimadai banganiba umma ranar abbanku yace a kirata ta bashi labari amma tazo ba wani labari, Iffaat!! Na'am hajiya! Ki mana magana zama damune kike gajiya dashi ko kuma wani yake quntata miki ko kuma wani Abu yake faruwa a qauye?? Kawai sai ta fashe da kuka, kuka mai tsuma zuciya, ita kanta batasan sanadin kukanba, sukayita rarrashi har tayi shiru, ki fada mana minene idan mune mu gyara muryan ta a dishe tace wallahi Baku bane hajiya, nima wallahi bansan abinda yake damunaba haka kawai idan ina zaune sainaji raina ya baci ko kuma na riqajin inason wani Abu amma bansan ko miyeba qunci yamin yawa hajiya ta qara fashewa da wani kuka, sukayi chirko chirko, chan iffaat tace mamarta takeso ..... [12:04AM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 39 Na Hauwa M. Jabo Umma ta nunfasa tace idan wannan ne damuwarki karki damu xamu nemo miki mamarki duk inda take, ta danyi shiru amma jifa jifa takan zubarda hawaye, bayan kwana biyu, muna zaune palo nidai kamar hoto ko nace gunki kawai cika wuri nakeyi. Suhaila ce ta shigo ina ganinta naji qirjina ya wani buga, da Leda a hannu, tana murmushi ta gaida umma tace nazo dubiyar mara lafiyane suka saka dariya ai ga tanan taji sauqi, ta zauna tamin ya jiki, na amsa mata inata kallonta har tadan tsargu, suhaila tace iffaat wallahi kinyi kama da qanwar babanmu sosai saidai tafiki haske amma hatta gashinki irin natane ke ko murmushinku iri daya tafiyarku ma iridayace ke hatta maganarku iri dayane ke komai naku iri daya, duk aka saka dariya har iffaat din ganin yanda Suhaila ta jajirce da bayani, sai kun sami lokaci kixo muje gidan mu ki ganta a gurinta nake zaune, iffat ta amsa da insha Allah.... ***** Iffaat dai bata gane karatu yanxu, gashi an mata nisa sosai abubuwan da bata yisuba a lesson take samu a namatasu, karatun ma haushi yake bata yanxu, zaman gidan ya gundureta, idan har aka zauna Idan ba hirar farhaan akeyiba bata taba samun sukuni a rayuwarta, wutar sonsa kullum Dada ruruwa take a zuciyarta amma har yanzu bata gane cewa she is fall in love ba... Yar baqa qawarta tayi tambayarta har ta gaji sai tace ba komai, to batasan mi yake damunta ba bare ta fada, Zaman birni ya gagare iffaat, kusan kullum saita xubar da hawaye wace irin rayuwace wannan?! ta matsa musu akan ita sai ta koma gurin iyayenta ta gaji da zama anan, aka buga sama da qasa amma taqi amincewa har suka gayawa abba, Ranar yasa aka kirata ya tambayeta ko ana mata wani abinne tace ba abinda ake mata, iffaat bamu daukeki a matsayin Yar aikiba a matsayin Yar cikinmu muka daukeki wannan dalilin yasa har muka damuwa da damuwarki, muka sakaki makaranta Dan kema ki sami gata da yanci irin Wanda ko wacce yarinya take samu a gidan mahaifinta, iffaat kamar jiran abba take ta fara kuka kamar ranta zai fita, Abba nagode da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da alkhairi, abba wallahi ni kaina bansan abinda yake damunaba rayuwata bata min dadi ba abinda yake burgeni a duniya komai haushi yake bani, banason naci gaba da wannan hali na damuwa kuma na sakaku akan shakkun kanku, wallahi kun min komai a rayuwa kuma na gode, wata qila Idan na koma qauyenmu tunda nasan yayyena suna zuwa nemana wataqil Idan nagan su in sami sassauci. Amma Dan Allah Abba Ku mayar dani gida taci gaba da kukanta...... Tofa muje zuwa muji anya zata iya rayuwar qauye? Yama za'ayi ta gane cewa soyayyah ce take damunta...??! [11:44PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 40 Na Hauwa M.Jabo Abba Ku taimakamin ku mayar dani gidan mu, jikin kowa yayi sanyi yanda take kuka kamar ranta zai fita ta basu tausayi koni Jabo ta matuqar bani tausayi Dan saida nayimata qwalla, tabbas So bala'eeee ne, yana zautar da mutum ya rasa mi yake masa dadi yama rasa gane kansa,! zaiyi loosing din control dinsa ne gaba daya, ko manya ya suke fafatawa da soyayya bare yarinya Yar shekara 15 irin iffaat da har Yanxu batada wani wayo bare har ta gane wane hali take ciki.... Abba yace To ki daina kuka iffaat za'akaiki gida dama Dan kada ya zama mune muke shiga haqqinki ba tare da mun saniba amma tunda kince bakomai kin zabi hakan shikenan, dukansu basu ji dadin tafiyar da iffaat zatayiba, amma ba yanda suka iya dole su saka mata ido, farahnax ma ta sameta a dakinta tana kwance bayan ta hada kayan ta, yanxu iffo tafiya zakiyi ki barmu?? Muka miki dan Allah da har bakya iya zama damu?? Ta kalleta tace sister wallahi ba haka bane bakumin komaiba, kawai rainane baya min dadi kuma bansan dalilin hakanba, kuyi haquri Dan Allah, anan dai sukayi hirar qarshe, koda iffo taqi sakin jikinta... sun mata goma na arziki suka bata kudi masu yawa sannan akasa driver yakaita har qofar gidansu. Shikenan iffaat ta baro gidansu farhaan..... ******** Iffaat a qauyen su, Ashe yanzu bala'en yake bata saniba, yanzu take qara shiga damuwa yanzu take gane cewa ganin iyayen farhaaan rahamane gareta, amma kuma still bata gano hakanba, ganin su da takeyi yana raqe mata qunci matuqa, ta sukukuce kamar ba itaba kai duk Wanda yaga iffaat sai yayi mamakinta bata magana, Yar gayu kam da take burin zama ta Riga ta zama, saidai so silent yanzu take yanxu. goggo har tana tsoro kardai ba abin kunya tayo aka korota birnin ba!! ******* Watan iffat biyu a qauye ba walwala kullum fuskar nan a turnuqe kamar ta dijee dama dijee haka take ba sakin fuska su iffaat ne masu dariya, yanzu kam iffaat ta zama Yar baqin rai fiye da dijee.. Ranar iffaat ta tashi da ciwon cikinta har Yanxu goggo batasan ta fara period ba tasha magani ciwon ya fada mata tana zaune cikin runfar qofar dakinta da Dan tsinke a hannunta tana tsane a qasa taji sallama ta amsa batareda ta dago kaiba tsul goggo ta fito daki tana washe baki na dago kai na kalleshi, ke ihhatu bakiga yayanki yaxoba, koda na Dade ban ganshiba hakan bai hanani ganeshiba Yaya nane! Taje gunsa na fada jikinsa tna kuka shima dai yayi gwalla, suka zauna saman tabarma, Yaya Ameen yake cewa goggo kinsan kuwa ba nan nakeda niyyar zuwa ba sai naga na biyo ta kusa danan nace bari na shigo qauyen namu in gaisheki, Ashe rabon naga Yar mamane kullum zancenki take mana, nayi murmushin jin dadi Dan uwa Rabin jiki ciwon cikinta tuni ya ware sai murna takeyi tana xubar da yan hawayen murna.. Nan take Ya kira Mama ya gayamata ai gani ya sameni yanxu mama murna kamar ta kasheta yau taji autanta munyi magana ta ita inatajin dadi, Anan aka kitse akan gobe Yaya zaizo ya fafi dani daidai nan na Dan shirya, goggo ranta baisoba don iffaat ce rufin asirinta gata ba da bare jika..... [11:48PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA 41 Na Hauwa M. Jabo Tun da safee iffaat ta shirya kayan da take buqata sai rawar jiki takeyi duk da har yanxu zuciyanta a qunci take hakan bai hanata zagwadin ganin mahaifiyarta ba, goggo ta sakata taje tayi ban kwana da mutanen , taje tayi bankwana dasu, wasu nata mamakin natsuwarta kowa na fadin albarkacin bakinsa, taje gidan qawayenta dijee da tsohon ciki abin sai Wanda ya gani, tana tsaka da ban kwana akace mata yayan ta yazo zasu wuce, a gurguje tayi sallama ta dawo gida... Ranar goggo tayi kuka kamar ranta zai fita tana ganin kamar hanyar samunta duk ta to she kenan... ta manta samu da rashi na Allah ne.... **************** Guraren 6 na yamma suka Isa zaria birnin zazzau amma iffaat anyi bacci a mota so bata gane garinba, direct unguwarsu aka wuce da ita gyallesu, iffaat sun tararda mama tana ta gyare gyare tarbon autarta, tana ganina taxo ta rungumeni tana yan hawaye, nima hawayen nakeyi Yaya Ameen kuwa yanata dariya, yace mama murnace haka harda kuka haba miye aciki Dan ba iffaah tunda nida Yaya Ali mumanan, dama kullum ta damesu da zancen iffaah autarta, mama ta harareshi ai kowa matsayinsa daban, taja autarta suka wuce daki suna marmarin ganin juna, a takaqaice zuwan iffaat yayimusu dadi babban yayan su mai suna Yaya Ali shine babba kuma Allah ya azzurtashi matuqa tun bayan rabuwar mamansu iffaat da babansu ta dawo birni gurin yayanta dama chan su yayyen iffaat gurin yayan mamansu suke suna karatu so basuyi zaman qauye ba iffaat ce kawai gurin mamar kuma da suka rabu da baban sai ya kwace ta da qarfi da yaji... Yaya Ali Allah ya azzurtashi sosai bayan business da yakeyi tareda qanin mamanshi yana aikin Kaduna in short dai suna shanawa wannan gidan ma da suke ciki shiya Gina ma mamashi... Iffaat ta kalli gidanda suke ciki aranta tace wannaan gidan kenan gadansune zatayi duk abinda take so bawanda zai hanata rayuwa sabuwa jin dadi sabo komai sabo saidai batasan bazata iya chanza kuntacciyar xuciyartaba.... Lol. [11:57PM, 5/5/2015] .: WACE CE ITA..?? 42 Na Hauwa M. Jabo Rayuwa gidan mahaifiyarta Yana mata dadi matuqa tana samun gata ta kowane fanni, Sai yanxu ta gane cewa wannan garin garinsu farhaaah ne, koda ko za'a kasheta bazata bata gane gidan su farhaaan din amma dai ta gane makarantarda aka sakata da tana gidansu farhaaan nan guraren PZ ne. Yanxu kuma Hall Mark international school aka sakata kuma duk gurare dayane... mama ta samo mata mai lesson Yana mata a gida, islamiya ma tana zuwa anan unguwarsu ta gyallesu, saidai a tunanin iffaat xuwa gidansu gun mahaifiyarta zai sa ta daina damu wa batasan ba anan gixo yake saqaba ita zuciya kawai burinta takai ga wannan abin da takeso idan ba hakaba kuwa ba zaman lfya.. ***** Wata rana maman iffaat take tambayarta lfy bata walwala? Tace ba komai mama. Mama tace kodai bakyajin dadin zama damune? Laaaa mama wallahi ba haka bane nafison nan da ko ina har gidansu..... Sai kuma tayi shiru sai mama tace har gidansu waye?? Ba kowa mama, hmmmmm. nidai da yawa mama nakanji banajin dadine saina riqajin kamar inason wani abu Amma bansan ko miyeba haka zan kasance chikin damuwa.... iffaat tama mama bayanin abinda takeji, tace wani abin mama sai idan na tuna yaran gidan da nayi aiki,! Sai nayi tajin raina yana wani iri, kawai mama shine ba wani abubw kuma inaga kamar sabone ko mama, mama tayi murmushi tace Eh inaga sabon ne kawai. mamadai ta gano cewa iffaat wani take so amma itama mamar bata fahimci ko wayeba Kuma iffaat din har yanxu batada wayon da zata san cewa ta fada tarkon soyayyar farhaaan ne, mama da ta fahimci halin da yarta take ciki sai ta dada janta jiki ko zata mantar da ita wannan mugun ciwo da yake addabarta.. Sau da yawa idan iffaat ta shiga daki ta fara tunane tunane sai taga kamar ba ita bace.. taci kuka taci kuka har ta godewa Allah.... *** Wata rana iffaat bayan ta fito a class sai ga wasu yan samari sun wuceta tana jikin class suka fara mata hy yan mata ji mana,! iffaat kamar bata jisuba, sukayi iskancinsu suka gaji suka wuce bata ko daga kai ta kallesuba, har sukaje suka dawo suka qara mata tayi banxa dasu.... Bayan sun wuce tana zaune sai ta fara tunanin iskanchin da aka mata ta gyale, anya nice iffaat kuwa? Wacce Ko ba'akasa dani nakan siya, nakan sayi fada da kudina bare a tsokaneni, waima wayannan yaran zasu min iskanci na gyalesu tayi tsaki kamar an tsira mata allura, ta tashi ta fito tsakiyar makaranta don nemansu, fitanta keda wuya tayi karo da malamai suna kora a koma class juyawanda zatayi head boy dinsu ya fara tsula mata bulala tayi class a guje amma taji bulalar ba kadan ba taso ta bisu ta musu nata rashin kunya aka koreta, ko minti 10 ba'ayiba ta manta da abin ta koma tunaninta da baida natija ,..... [12:11AM, 5/6/2015] .: WACE CE ITA..??43 Na Hauwa M.Jabo ********* Wata rana Suna hira da mama take bata labarin tanada ya, yarinyar yayanta ne lokacinda babanki ya kwaceki to lokacin aka bani ita, to ina take mama? Tana Qatar karatu takeyi wannan shekarar zata kammala data qare sai a mata aure,! iffaat tayi dariya da shewa Ashe dai mama mun kusa shan biki, kinsan kuwa inason biki a rayuwata, lokacinda muna qauye kullum sai naje biki ko ba'a gayyaceniba kuma ni bandamu da su bani abinciba kawai mukanje muyi tsokana, idan za'a kai amarya da dare mu sami allura muyita tsikarawa matane ko Ku muyiwa yayansu da suka Goya suyita kuka sai mu boye, mama Dan tsabar dariya saida ta kai kwance, tashajin ana cewa iffaat ta gagari Kowa a qauye amma ba tasan abin yakai hakaba, nidai jabo araina nace to iffaat kan tayi hatsabibancin da yafi wannanma!! Yanxu kinga mama biki namu sai yanda mukayi ko, mama cikin dariya tace eh, da yake har baiko ma an mata ai. Habawa? Ashe munada biki duk suka saka dariya... iffaat tanatason ta tambayi mama hoton yar tata amma Sam ta manta har ta kusa dawowa! *** Ranar da Yar mama zata dawo gidan mu yasha gyara anyi girke girke kala kala, guraren qarfe 2pm ta sauka Kaduna daga chan aka daukota aka kawo ta Zaria da yake an barni gida, isowarsu keda wuya, wazan gani a matsayin yar uwata?? Suhaila matar da akayiwa farhaaah baiko da ita, wani rass taji ni kaina jabo sai da naji bugun zuciyarta kuma na tabbatarda kuma Masu karatu kunjiyo kobakujiba???? Suhaila tana ganina tahau dariya tana tambayata farahnax, cox ita achan tasañi, tace iffo surprise dina kukayi haka? So happy wallahi ina farahnax din? Itakam iffaat tsaye tayi tana mamaki abinda take gani, wato Suhaila itace yarinyarda aka baiwa mamanta kuma itace matar farhaaah! Sai yanxu ta gane kamar da akace sunyi da Suhaila, Ashe jini dayane, sai yanxu ta gane dalilin da yasa takejin Suhaila cikin ranta amma kuma miyasa take tsanar ta?? Suhaila sai washe baki take tana tambayarta farahnax, mama tace keewai waya gaya miki tasan farahnax? Ke dadi miji dadi dangin miji!! Laaa mama wallahi gidansu fa nake ganinta farko, itace wacce nace miki akwai wata cousin din farhaan mai ban dariya kuma kunyi kama kin tuna mama? Eh na tuna to itace, nifarko ma na dauka aiki take a gidan sai ranan umman farhaan tace ba Yar aiki bace yartace, anan dai na fayyace musu komai mama da Suhaila suka gane cewa gidan su farhaan goggo ta kawoni aiki, mama taji dadin yanda umma ta kula dani har tana cewa suruka ta gari...... Nida Suhaila mun dinke mun zama kamar abokai dukda ta girmeni nesa ba kusaba cox lokacin ina 16 ita kuma tana 24 ne, duk iyayen farhaan sun ganeni sunata jin dadi, mama kuwa hadda zuwa godiya yanda aka kula da yarta har umma tana cewa a qara bata ita... **** Bansan miyasa nake tsanar Suhaila ba nakan kwatanta boyewa araina amma duk ranarda naji sunyi waya da farhaaah to kuwa duk yanda zanyi sai nasan yanda zanyi muyi fada da Suhaila da yake ita ba mai kulawa da qananan abubuwa bace so bata kulawa dani Sam. Banxa takeyi dani kamar ba da ita nake yiba, nayita gabata har na gaji na sauko. Mama ta kula kamar na tsaneta amma ita kanta bata gano dilin hakan ba, Ranar mama ta kirani take tambaya ta miyake faruwa tsakanina da Yar uwata nafara kame kame, ba komai, mamadai tayi ta min wayo har na fara magana wallahi mama nikaina bansan dalilin da yasa mafiyawan lokuta nake jin na tsanetaba haka kawai take bani haushi kuma wallahi mama banajin dadin abubuwan da nake mata ta fashe da kuka, mama ta rarrasheta, taso ta gano sirrin amma aranta tace bari saita qara gwadata. Tofa MUJE ZUWA MUJI IRIN GWJIN DA MAMA ZATAMA IFFAAT... DA KUMA WANE IRIN MATAKI ZATA DAUKA AKAN HAKA, ZATA IYA ADALCI KO KUWA SON KAI ZATAYI TSAKSNIN YARTA DA YAR RIQONTA?? [11:13PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??44 Na Hauwa M.Jabo ****** Ranar da farhaaah yazo Nigeria goben aranar aka hada mai tarba ta musamman a gidan su iffaat, duk da cewa bata iya komaiba kuma har yanxu bata taba shiga kitchen da sunan girkiba amma ta nemo hutunan girki a internet, an hada kayan komai da komai ana jiran Yy farhaan, tayi kwalliyar da itakaitaa bansan ta iyataba kuma batasan dalilin da yasa tayitaba, Suhaila ta tsaya tana kallonta kinganki kuwa wallahi kamar wata amarya, please kimin irin kwalliyanki, ta kuwa xauna gaban iffaat nidai jabo nace su iffaat Masu haye hayen bishiya sune ake kwalliya haka, ai yanxu kam taci uban Yar baqa zainb khalifa da iya kwalliya iffaat ta dara tace kina nufin kwalliyata tafi taki kyau? Sosai ma kuwa nidai kimin tun basu qarasoba haka iffaat ta tsinci kanta da gyashin yiwa yayar tata irin kwalliyarta, ta nemi dalilin yin hakan ba dalili, Suhaila har ta gaji da bibiyarta akan ta mata irin kwalliyar ta iffaat ta nace akan bata iyaba itama Sa'a tayi tama kanta....... Guraren la'asar saigasu farhaan da farahnax sun iso gidan ita Kuma tana dakin Yayanta tana hada wasu kaya kamin baqin su Iso, dariyar farahnax taji tana tambayar ina iffaat take, ta hango farhaan, wani raaas taji zuciyata ta shiga harbawa kuma batasan daliliba, farhaan guy ne lafiyayye duk yanda namiji yake cikakke mai lafiya to farhaah yana cikinsu dogo ne mai jiki daidai shi yanada faffadan qirji haka yanada sajee a fuskarshi wanda ya kwanta yayi luf a fuskarshi, yana zuwa naga yy Suhaila taje ta fada jikinsa ya rungumeta, iffat taji wani dum dum dum...!!! wasu emergency hawayene suka bulbulo daga fuskata, lokaci daya taji ta qara tsanar Suhaila da farhaan, kee mi kikeyi anan ga baqi chan tun dazu naji suna kwala miki kira,? Ta waigo ba tare da tasan ko wayeba, idonta sun Riga sun rufe, ta watsamai harara, miya dameka da abin da nakeyi anan.!? Sokoko yayi yana mamaki, iffaat kinsan wa yake magana kuwa?? Tace a gadare nasani Yaya ameen ne yake magana, kaiiii iffaat too lallai bakida kunya, Ta kalleshi ido cike da hawaye tana kuka tace Kaine bakada kunya, ni inada kunya Kaine kaine Yaya, ta fada jikinsa tana dukan qirjinsa sai jin yayi tayi deef tayi tana Neman faduwa qasa, kamin kace kobo ta sumaaa..... [11:20PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 45 Na Hauwa M.Jabo Ya riqeta ya dagota yana jijjigata yana kiran sunan ta, amma iffatu ko motsi haka ya dauketa chak dama ba wani aukine da itaba, yakaita dakinsa yaci gaba da jijjigata yana fadin sunan ta, farahnax yaji tana kiran iffaat iffaat kina ina?? Ya xuba mata ruwa shiru,Yayi sauri ya tura qofa yayiwa mama waya bata daukaba tana chan suna gaisawa da suruki, ya dakko ruwa a fridge ya qara zuba mata yarinya still ko motsi yaga kamin yaje ya kira mama zata iya mutuwa, tuni ya fara hawaye yana kiran sunanta yana jijjigata, Muryar mama yaji, Aminu naga ka kirani lafiya? Nidai kuje Ku gaisa fa yaron chan mai Neman qanwarku Suhaila, mama kizo iffaat ba lafiya, Subhanallahi.!! Miya sameta ta shigo da takalmi a qafa taga yarta kwance kamar gawa ta fara jijjigata, taqara watsa mata duka ruwann dake cikin robar swan din, iffaat tayi wani gwauro numfashi ta bude Ido kadan ta kalli yayanta ta kalli mamanta ta fashe da kuka, mama ta rungumeta tana rarrashinta, wai ya akayi haka aminu miya sameta?? Wallahi mama kawai naga ta tsaya jikin window tana kallon su farhaaah da sukazo shine na tambayeta miya faru,.................. Yayi bayanin komai umma ta kalleta taga ta rufe ido lallai xatonta ya zama gaskiya, tayi jeeem amma ba halin magana wannan tashin hankali har ina.!? Suna zaune jugun jugun dasu saiga Suhaila ta shigo, iffaat wai ina kika shiga tun dazu sunata nemanki Yy farhaan kuwa ya kawo miki....... Ai bata qarasa zancen ma taga su mama an xuba uban tagumi ta kallesu mama miya sami sister na?? Hankalinta ya tashi, mama batace komai. iffaat kuwa sai ma qara runtse ido tayi wasu hawayen suka ci gaba da sauko mata, tsanar ta takeji a ranta Yaya Ameen zai fara mata bayani mama ta katseshi. Kije ki sallami baqinki ki dawo mama wallahi ba zan iya komaiba sister na acikin wannan halin mama miya faru da ita,? bakomai bane kune kullum cikin saka takalmi masu tsini garin rawar kai ta fadi kanta yadan daki jikin qofa shine kawaifa, Ta dafe qirji Allah sarki sister sannu kinji bara na kirawosu anan suxo su dubaki ta miqe tana sauri Iffat da qarfin hali tace kada ki kirasu banason ganinsu bana so, mama tayi sauri ta toshe matabaki, Batasan lokacinda ta fada hakan ba lallai iffaat soyayya tana wujijjigata, suhaila ta waigo mi tace mama?? Cewa tayi kada ki kirasu, Nima ina ganin ki barsu kada hankalinsu ya tashi,... [11:25PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??46 Na Hauwa M. Jabo To mama mixance dasu?? Yy amin yace kice na aiketa har yanxu bata dawoba, ta tafi cike da baqin cikin da jimamin faduwar Yar uwarta Allah sarki Suhaila akwai sanyin hali. Bayan ta tafi yaya yake tambayar mama miyasa baki fada mata gaskiya ba?? To sai kawai nace tana kallon su sai ta suma ai kaga dole aji tabakinta kamin ayanke hukunci,ya jinjina kai hakane, anan suka zauna har saida su farhaan suka tafi, Suhaila taxo ta fada musu sun tafi, su tashi su koma cikin gida. Iffaat tace ita batason chikin gida dakin yayanta zata zauna, dama iffaat da naci sukayi sukayi Amma inaaa ko bude Ido batayiba bare ta tankasu suka gaji suka barta, har sunkai bakin qofa, Suhaila ta dawo. Suhaila tace Iffaat na kawo miki kayan da Yy farhaan ya siyo miki?? Ta daka mata tsawa da bataso. saida su mama suka jiyo kuma duk abinnan da akeyi idonta a rufe suke taqi budesu, tana budewa hawaye ne zasu fito.. ******** Bayan faruwar haka da yan kwanaki iffaat yanda take jin ta tsani Suhaila ba dalili yana matuqar damunta, duk abinda takeyi idan Suhaila ta saka hannu sai ta tsani wannan abin tabarshi kenan har abada, idan kuwa ta saka bakinta sai ta gwaleta gaban ko waye, ranar maman Suhaila hajiya kulu taxo gidan yini dan yinin da tayi ta fahimci yanda iffaat ke yiwa Suhaila sai ranta baiyi dadiba har take tambayar Suhaila tana kuwa jin dadi bayan xuwan iffaat?? tace lfy lau idan kikaga tana haka to wani ya bata mata rai a skull sai ta sauke akaina, maman Suhaila tayi dariya tace kice iffatun dai har yanxu hukumace kenan suka dara gabaki dayansu... ***** Ranar iffaat tana zaune gindin bishiya a makaranta tana shan malt da snack sai taji wasu yan mata suna tadi akan soyayya ta kuwa kashe kunne, dayar take bada labarin cewa tanason yaron qanin baban ta amma batasan yanda zata bullowa abinba tana bayanin duk abinda takeji a ranta game dashi dayar ma tana fadar nata keni Zumar abinda yafi bani haushi baimasan inayi, Zibraheeem tace kar kuwa kisake ya sani Dan raini ne zai shiga tsakaninku. Iffat sai taji d same da abin da takeji suma shi sukeji, ta juyo ta kallesu sun girmeta duka ta musu sallama, please tambaya ce dani, naji kuna wata magana, yanxu kuna nufin duk maijin wayannan abubawan da kuka fada shine me,?? dayar tace its mean ya fada tarkon soyayya!! ta kallesu, kuna nufin nima na fadane? Toni wa nakeso?? Suka kalli juna suka kwashe da dariya, mu muka San Wanda kikeso, dayar tace Wanda kikejin haka akanshi shi kikeso!! Ta zare Ido kuna nufin YAYA FARHAAAH NAKESO?? suka kalleta sukayi tsaki ke baquwace yarinya dayar tayi dariya tace kinji suna mai dadi daji gayen zai hadu, daji akwai zafi a gunsa har naji inasonsa !! Iffaat ta juyo a fusace keeee ta wanketa da mari..... [11:28PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??47 Na Hauwa M. Jabo Yan matan gaba daya suka miqe tsaye, dayar ta gefe ta kwasheta da mari itama dayar taci kwalarta suka mata lilis,duk sun buge mata fuska, suna tsaka da dukanta saiga baba sajeen yana kora kamin yazo sun gudu bai tsaya duba halinda iffaat take cikiba kawai yaganta kamar tsugune yahau zuba mata bulala tun tana kuka har tayi shiru. Ke wace irin mai taurin kaice? Maza ki tashi ki wuce class bai tsaya kulataba ya hango wasu yara biyu ya bisu a guje suka tsere, iffaat dai an mata lilis baki sai jini yake yaji duka gun yan mata gashi baba sajeen ya qara mata wani, tana nan gurin taji ana cewa still tanananfa, kixo mu dubata, nidai baxanjeba ke kije , habadai sabida kefa na daketa kuma kice bazakijeba, please kixo muje, sukazo gurin iffaat sai kuka ganta tana xubar da jinin baki da hanci duk hijabinta ya lalace, nidai jabo abin har mamaki ya bani wai iffaat ce take daukar xilla yau!! Rayuwa juyi juyi....!!! Suka dagota suka tallabota hannu biyu dayar ta ruga ta siyo pure water Leda daya sukaxo iffaat bata iya koda magana, suka wanke mata jikinta suka qaro ruwa suka wanke mata hijabinta da duk gun da jini ya bata, dayar take gulma a hankali tace kalli gashinta! Dayar tace ummm nagani, suka kalli iffaat wacce ta bige mata bakince ta fara bata haquri, sai dayar ma tac ci gaba da bata haquri batace dasu komai ba, hasali ita batajin zafin dukanda aka mata illa xafin Cewar da akayi Yy farhaaan takeso.! Sunata bata haquri ita kuwa tanata tunaninta.! Wai yaza'ayi taso saurayin yayaryta? Yaza'ayi taso Wanda nake kallo a matsayin yayantaa? Lokaci daya ta tuna da rashin kamun kansa shegen Neman mata, ta tuna duk wani iskanci nata yasanshi, shine yafi kowa sanin WACE CE ITA, har abada baxai karbi soyayyar taba, idan ma zai karba yazatayi da yayarta Suhaila, anya ma gaskiya suka gaya mata da sukace sonshi takeyi,??? [11:32PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 48 Na Hauwa M. Jabo Tayi ajiyar xuciya Ta juyo ta kallesu sunyi cirko cirko dasu, da kunburarren bakinta take musu magana, kiyi haquri Dan Allah wallahi bansan lokacinda na daki qawarkiba, sukace ba komai kema kiyi haquri, nan dai suka yafi juna suka qulla qawance da ita da alqawarin zasu taimakamata da duk abinda sukasan zasu iya. Haka suka zauna Kowa shiru har aka tashi makaranta.. *** iffaat na zuwa gida mama ta fara tambayar ta lafiya kike kunbura haka kamar jabo tayi kuka?? Wallahi mama anyo korane, zasu shiga class tayi karo da wata frnd dinta sai kuma ta fadi qasa shine bakinta ya kunbura, Subhanallahi. Kinga yanda kika kunbura kuwa? Allah ya tsare gaba ta amsa da amin ta wuce dakinta. Bayan ta shiga daki ta cire uniform, ta zauna ta fara tunanin abinda yan matannan suka fada tabbas kuwa idan har abinda suka fada shine kaji kanason mutum to wallahi tanason Yaya farhaaan, aiki jaa wanda zai zama mijin yayarta takeso?? Dole ta dauki mataki wa zuciyarta.! Tayi murmushi Kai amma so shegene shine ya hanata sukuni shekara da shekaru! Amma so ya wanketa! Waima miyasa bata ganeba? Tayi tsaki ni ko zan mutu zan auri Yy farhaan ne gashi da shegen son mata! Duk maganar da takeyi aranta takeyinta amma Sam zuciyarta bata aminta da ko kalma daya tataba, kawai tana fadane amma tasan yanda takeji da gudu idan yace yana so zata amince,... Hmmmm dole zuciya taso Yy farhaan ta saba dashi, yy farhaan duk inda namiji mai lfy zai shiga yana shiga haka tayita karanto siffarsa da maganar sa da tafiyarsa da murmushinsa tana murmushi, lallai ta yarda tanasonsa but miye mafita??? Dole ne ta ijiye sonsa taci gaba da danneshi har Allah ya bata mijinta tayi aure?? Anya zata iya kuwa?? Zaki iya mana dayar zuciyarta ta bata amsa aiki ja gabanta.. Suhaila ce ta shigo tana waya ta gane da farhaan take wayar kuma taji yanayinda ta saba ji amma ta basar..... [11:37PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 49 Na Hauwa M. Jabo Ta juyo suka hada ido Subhanallahi sister miya sameki? Tambayawa kawai tayi batayi tunanin samun amsa ba, Dan tasan halin mutuniyarta, cox jiyama da dare ma kamin su kwanta bacci sun sayar da hali.. Ta miqe zaune Ki bari kawai Yy Suhaila..... ta bata labarin abinda yanda ta baiwa mama labari, Eyyah kinji yy farhaan yaba miki sannu Allah ya kiyaye gaba, sai kuma taji sanyi aranta, nagode bani mu gaisa, ta karba tana karba ya fara mata tsiya anya faduwa kikayi ba tsokana kikayiba aka miki duka? Tasa dariya. Laaa wallahi aah faduwa nayi, koda naga yanzu kin natsu kamar bakeba,amma kinfi kyau da qiriniyafa, tayi dariya sai mu samo miki miji mu aurar dake kowa ya huta, kar kuma mu samo ki kashe Dan mutane da rigima, da yake Suhaila tanajinta itama tayi dariya, Yy Suhaila karbi wayar ki kinji tsiyar da yy farhaan yake min ko !? Ta bata waya chike da nishadi, Ta shiga bayi ta kalli kanta a madubi taga yanda ta kunbura kamar rukayyah qawarta ta qauye Dan haka fuskanta take kamar fulawa ta kwana ta tashi, tayi wanka ta fito, tanata Jan Suhaila da hira itadai Suhaila abin mamaki yake bata, cox tun dawowarta ba ranar da basa saida hali har ta saba, idan basuyi da safeba tasan kamin a kwanta sai anyi, dama ita bamai kulawa bace, haka bata baiwa Abu muhimmanci...! ********* Tun daga wannan ranar iffaat ta daina fada da Suhaila idan taga tana wayarta sai ta tashi ta fice gun mama ko ta danna eir ps dinta tana sauraro waqoqinta. Ataqaice dai sun daina fada da juna, bata kula da ita idan tana abinda tasan zai bata mata rai, Iffaat itada qawayenta. skull mate dinta zainb Ibrahim da zainb Umar da ita iffaat Habeeb, da yake sunan baban farhaan take amfani dashi tun lokacinda ya sakata makaranta har yanxu. Zan iya ce muku ZZ sun ninka su dijee iskanci da rashin kunya kowa yasansu a makarantar kuma anqi korarsu sai suka hadu da iffaat Habawa sai abin ya qaru dama iffaat ba bayaba soyayya ce ta dangwasheta amma yanxu kam ta gano bakin zaren so bonewa takeyi bata baiwa abin muhimmanci Sam duk da tana jin zafi cikin ranta... [11:43PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..?? 50 Na Hauwa M. Jabo Suna zaune gindin bishiya sun fito break aka fara kora ko ajikinsu tadinsu suke yi suna baiwa iffaat shawara kada ta yarda ta nuna tanason farhaan harma yanda suke gida daya da wacce zai aura, daga sama suka ji bulala akansu Malam tunde ne zibraheem ta tashi ta riqe bulalarshi, haba sir miyasa kullum sai ka riqa dukanmu Dan muna kunyar Kane kawai muka sharewa but gaskiya ya isa haka.! Ta fuske, ki sakarmin bulala Mara kunya, sai nayi maganinku a skull dinnan, duk da English suke zancen nan. Da hausa zumar tace saidai muyi maganin juna bayajin hausa so baiji mi sukace ba, yadai qyalesu ya wuce gaba abinsa, iffaat tace malamin nan Dan rainin wayo ne, suka kama hanya ko wacce ta kama hanyar clss dinsu da yake duk yara sun shiga clss sai su gagararru. Koda iffaat taje clss malami ya shiga kuma Malam jocob ne baya wasa ko kadan,economic master, ta fuske yace from ware? Tace daga gidanku da hausa ta fada duk clss suka saka dariya, Habawa yaji haushi ya gane zagin sa tayi ya fara zuba mata bulala taji zafi tuni tayi cikin sa tana duka ta kamashi da kokowa clss ya dau ihu ana buga table, saida sukaci uban juna kawai ta saki jiki ta fadi wai ita mai aljannu so aljanun sun tashi, dama su ZZ sun gaya mata cewa tayi iskancinta idan ta qare ta fadi kawai ita batasan tayiba, Kaji iskanci... Haka dai akasha oga jocob a banxa gashi ta wawwaskamai mari ta karyamai glass.. Tofa iffaat hatsabibanci ya dawo. Akaje gun principal tace ita sam batasan tayiba sharri ake mata, haka a ka rufe case akasha oga jecon a banxa. Wata rana suna zaune suna tadinsu kowa ya tafi class saisu kawai saiga principal ta biyo hanyar duk yara suna clss amma su suna nan zaune kamin ta qaraso iffatu tuni ta haye bishiya, principal taga hawanta amma bata San kowayeba, iffaat kuwa tayi tsanda a hankali ta hau rufin classes din kamar mage taje qarshen rufin ta diro qasa, koda taje class ta tarar malimi ya shiga yana note ta lallaba ta shiga ba tare da ya gantaba tayi sauri ta dauko note book ta fara rubutu. Tana fara rubutu saiga principal tare da ZZ akaxo nemanta, malamin mu yace lallai koda ya shigo ina clss din, students dinda suka ganni sukace yanxu Na shigo malamin yaji haushi kuna nufin kunfini ganine ko qarya nakeyi? ya za'ayi mutum ya shigo clss banganshiba..... [11:50PM, 5/7/2015] .: WACE CE ITA..??51 Na Hauwa M.Jabo Duk sukayi tseet principal taja su ZZ aka Basu punishment mai tsanani dama ansha kawo qararsu gaskiya sunji jiki ba kadan ba ga duka ga uban aikinda aka sakasu, duk sun kamawa iffaat mutunci sunqi mata magana, aka tashi suka kama hanyarsu itama tayi banxa dasu. Gobe sukazo nan ma gaba sukeyi sun shirya mata sharri da zataci duka amma bata saniba tazo ta musu magana sukayi banza da ita har ta juya sai Zumar tace ke banza ce wallahi, jiya shine kika gudu kika barmu, mufa duk wani hanyar dojewa mun koya miki amma ke baki koya mana komaiba kalli Dan Allah jiya yanda aka lallasamu, ta nuna mata hannunta dayasha bulaloli. iffaat tayi dariya son ranta sannan ta Basu haquri suka fara tambayar ta ya akayi daga saman bishiya ta wuce clss? Harda baba sajeen aka saka yahau bishiya amma baki ba labarin ki tayi dariya sosai lallai bakusan iffaatu Yar mamaba nan ta Basu details yanda tayi sunata mamaki lallai wannan yarinyar mayyace, kuma hartashiga class malamin bai gantaba...... Sun shirya mata sharri ZZ kenan sun hada mata gadar zare sukace sujee baya, sunje baya kuma an hana xuwa wajen da yake iffat bata taba zuwa gurin ba, kuma batasan an hana zuwa gurinba suka turata sukace suna zuwa, har ta shiga sai kawai ta hango bishiyar mangoro ya nuna tayi murmushi haba Ashe dadi suka turota tasha tuni ta haye bishiya ta fara tsinko mango tana saman bishiya kawai sai taji maganar su da wani malami wallahi tananan kullum nan take zuwa mun gaya mata an hana zuwa tace ba ruwanta. yanxu ma mungaya mata zamu fada muku tace sai dai a kasheta, kaji mugayen qawaye.... Iffaat tanajin haka tayi tsanda daga saman bishiyar tahau garu ta dira a toilet, ta barsu a gurin, taje da gudu ta kira principal tace tana bayi taji maganar mata da maxa a bayan skull principal taje da sajeen koda akaje aka gansu duk sun cire hijabi suna Neman ta wai ko ta hau bishiya coz ta gaya musu ta iya hawa bishiya ko wace irikuwa. jikinsu ya fara rawa ganin principal tana zuwa ta fara yiwa Malaminda yake tare dasu fada mi yaxo yi da yayan mutane anan bayan an hana zuwa anan tasa aka tafi da su ZZ office.. iffaat tayi wata dariya ta musu gwalo aranta tace wallahi saidai Ku wahala duk case dn dana shiga a duniya zan iya fitardakaina yanxu ya rage naku ta kakkabe hunnu ta qara gaba..... Muje zuwa. [11:13AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 52 Na Hauwa M.Jabo Anje dasu office ana tuhumarsu da aikata lalata, Dan yan iska kawai suke zuwa gurin kuma duk Wanda aka kama gurin qa'idace korarsa za'ayi da sukaga lallai korarsu za'ayi suka fara kuka suka fadi gaskiya principal abin ya bata dariya tace a kira iffaat aka kirata akace ta fadi gaskiya ko a hadasu a koresu ta fuske tace gaskiyar kenan yanda ZZ suke kuka sai suka bata tausayi, sai kuma ta tuna da ita aka kama korarta za'ayi imani dai ya shigeta ta fadi gaskiya... abin ya ba kowa dariya wato ko junansu basu bariba sharri suka mata tafisu zama yar duniya ta rama, nan dai aka shirya su aka musu fada akace suje class tun a hanya iffaat take musu dariya tana maimaita abinda ya faru tun suna daurewa har suka fara dariya lallai iffaat taci jinjina duk abinda takeyi Allah yana taimakonta...... Akwai lokacin da iffaat tayi zazabi aka bata maganin mura da maganin bacci to maganin yana Jakarta ne, sai kawai ranar tayi lettin shiga clss to malamin akwai shegen gayu da jiji da kai kawai ta karbi permission tace xataje bayi da gyar ya barta ta fita taje ta siyo drink ta bude ta saka maganin baccin har guda shida a ciki ta girgiza ta kulle ta baiwa wata students tace ta kaiwa malaminsu tace inji anti funke. Aka kawo masa yana mamakin funke zata kawo mai drink yace bari yayi sauri ya shanye kar azo ace ba nashi bane, ya zuge banxa ko minti biyu ba'ayi ya buge da bacci iffaat sukayi iskanci a clss sir na bacci sannan ta daukeshi hoto a wayarta ta bayan kowa ya qare aka tayar dashi bacci ya fara na yan giya tamai video, yanata sunbatu yana fadin ya akayine baby??wallahi saida aka kwasheshi ranar cox ya kasa ko bude idonsa.. Goben ranar aka saka bincike amma ba Wanda ya gano anti iffaat... Kai iffaat manyan duniya. Kuma haka tayita tura video da hoton nasa gashi malamin Dan gayu da jiji dakai tuni ta zubar mai da clss a gurin yan matansa da sauran students, yanxu sunansa ya koma ya akayine?? Cox lokacin da aka tayar dashi bacci sai ya fara fadar ya akayine baby yana layi.... Wasa wasa iffaat Iffaat an kai Ss2 su ZZ kuwa ana final year sun yi hatsabibanci bana wasa ba har andaina kulasa kuma iffaat ce leader dinsu....... [11:21AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 53 Na Hauwa M. Jabo ******* An saka ranar auren Yy farhaan da Yy Suhaila 20/5 daidai da ranar brdy din Hauwa jabo. Tunda aka saka ranar auren iffaat sukuni ya qara kubce mata saidai ta fuske takeyi tayi harka amma tana azabtuwa matuqa, ta fadawa ZZ suka bata shawara taci gaba da haquri kawai.. Lokaci sai matsowa yakeyi ita dai mama ta rasa gane sirrin zuciyar iffaat farko ta gano cewa tanason farhaan ne musamman lokacin da ta suma, nan zatoñta ya zama gaskiya, sai kuma yanxu komai ya tsaya mata yanda iffaat ta chanxa gaba daya duk wani Abu da take da wa suhaila batayinsa yanxu, hakan yana basu mamaki sai kawai suce ta qara girmane.... An fara shirye shiryen biki su iffaat da farahnax sune qirjin biki dama farahnax ta hada auren, shi farhaan irin ya nuna yanason suhaila irin soyayyar shan minti sai kawai farahnax taje ta fadawa su umma, kuma Suhaila ce keson farhaan sosai shi ba wani sonta yakeba, amma ganin iyayensa sunshige gaba yasa ya sallama ko banxa Suhaila kyakyawace kuma tana daga cikin matan da yake so dalilin da yasa ya amince da ita kenan. amma bai taba sontaba daidai da rana daya.. hasalima mafi yawar da sukeyi ita take kiran shi kuma ita Suhailar tasan ba wani sonta yakeyiba haka take son kayanta. Allah sarki Suhaila tana bala'en burgeni cox ba ruwanta abinda na fahimta farhaan ya sace zuciyar Suhaila da iffaat ne amma iffaat ta barwa Allah tasan ba yanda za'ayi ya aureta bayan ma ya rainta gata qanwar matarshi... haka dai akayi komai cikin jin dadi auren ya qayatar anyi komai cikin jin dadi da arxiki naira taci ubanta... An kai amarya dakin mijinta, Hmmm Daren dai iffaat ba'ayi bacci ba gaskiya na jinjinawa iffaat matuqa cox tayi jarrumta ba kadan ba nidai jabo idan nice wallahi sai nayi ciwo, Ashe Banida labari hadda iffaat anyi zazzabin daurewa kawai takeyi, ta bani tausayi matuqa kowa sai yace gajiya ce da kuma kewar Yar uwarta har mama Dan yanxu mama ta gane ba komai zatonta ba gaskiya bane,..... [11:27AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..??54 Na Hauwa M. Jabo Suhaila anachan ana barsar amarci da angonta... Iffaat kuwa ananan ana fama da axaba gwanin ban tausayi.... ko wata Biyu ba'ayi farhaan ya fara chanza wa ya gama da ita kenan, ya koma Neman matanshi duk qoqarin Suhaila na kyautata mishi ta ko wace hanya duk abinda tasan zaiji dadi tana masashi iya qarfinta kuma qaryane yace bata gamsar dashi cox a dare daya sai yayi round biyu haka take haqura duk da tana jin jikii burinta ta faranta masa, amma abanza takeyi su farhaan kam ba hali.. dama mai hali baya barin halinsa abin dai ba dadin ji sau tari takan qyanqyasawa iffaat amma tace kada ta fadawa mama..... Ranar Suhaila ta kama farhaan yana waya da wata akan zasu hadu wani guri, ranta ya baci ta mai magana kuma tace sai ya fada mata ina zaije sannan ta barshi ya fita... Habawa kamar jiranta yake ya wani taso mata kamar ya cinyeta hadda su gori wai albarkar qanwarsa takeci ita tasa ya aureta, ba itace choice dinsaba inda yake shiga banan yake fitaba, maganganun farhaan sun qona Suhaila matuqa ta shige daki tana kuka...! Allah sarki Suhaila.!! Kamar daga sama saiga iffaat yan mata dama iffaat bata cika xuwa Gidan ba cox abinda take gani ranta yana quna, idan dai kaga tazo Gidan to aikota akayi, yanxuma wani tsimine aka kawo mata daga sokoto shine akace ta kawo mata aka aiko iffaat... tin tsakar gida take kiran yy Suhaila har tashigo palo bata nan, tashiga daki taganta tana kuka hankalinta ya tashi tayi ta tambaya amma taqi fada mata dagyar ta fada mata Ashe yana bakin qofa yana jinta tana qare fada ya shigo a fusace.. Kin gayawa uwata sai ta kasheni ko ta hanani yin abunda naga dama wawuya kawai.! Ashe bazaki iya rufawa mijinki asiriba..?? yayi tsaki ya koma Palo tofa masu sayen fada da kudin su bare an sami dalili,ta miqe tsaye ta tsallake Suhaila ta fito Palo... Taxo gaban sa ta riqe kunkumi amma wallahi Yaya farhaan ka bani mamaki, ashe har yanxu kana wannan mugun halin naka?? Koda ba abin mamaki bane hali zanen dutse. Ta nunashi da hannu abin kunya namiji kamilalle a fuska amma xuciya ta shedan tirr da hali irin naka, koda ba komai bane wayewace!!! Amma Allah wadaran wayewa irin taka wacce akeyinta da Neman mata ni wall...... Kamin ta qare farhaan ya miqe ya kwashe ta da mari kuuut..... [11:32AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 55 Na Hauwa M. Jabo kaiiii..! Ya na sauke hannu itama ta wanke shi da nata Marin, kamar daga sama saiga Suhaila taga an mari mijinta tuni ta wanke iffaat da mari tofa iffaat ansha mari ta daga kai ta kalli yayarta taga yanda tayi wani iri haushi ya qara kamata, dama ita iffaat duk bala'en da takewa farhann da biyune ga kishin abin da ya aikata ga baqin cikin rashin samunsa. Yayar ta fara mata masifa, bata cewa yayar komaiba taci gaba da yimai masifa da fitsara yayar tanata cewa ta bari tana rufe mata baki Amma inaaa saida takai aya ta zazzagemasa kwandon rashin mutunci Suhaila abin ya qara kwabe mata baqin ciki kamar ta hade rai ta mutu, ta qare tamai tsaki ta murguda baki ta juyo gun yayar ke kuma ki zauna yana qunsa miki baqin ciki kina shiga daki kina kuka kamar wata doluwa.! ta kama hanyar fita Suhaila ta bita tanason tace kada ta fadawa mama farhaan ya daka mata tsawa akan ta dawo, ta rasa yanda zatayi, taxo gabansa ta tsuguna tana bashi haquri abin mamaki yace ba komai ya wuce laifin sane shima dama baiji dadin abinda ya fada mataba nan dai suka shirya hmmm mata da miji sai Allah hardai suka aikata aikin lada nan take, farhaaan yasan bala'en iffaat yafi nashi nesa ba kusaba cox shi yasan WACE CE ITA baisan miyasa yake shakkartaba.!! Ta isa gida a fusace amma kuma saita tsinci kanta da kasa fadar abinda ya faru, ta rufa masa asiri chaiiii soyayya bala'ece nan ma qarya ta xubawa mama tace wasu samarine suka bata haushi. mama tace nidai zanso naga mijinki kullum cikin korar samari waike yarinya, tayi murmushi ta wuce dakinta,. Tana shiga ta kulle qofa ta fara kuka tayi nadamar dukan farhaan koba komai ya girmeta kuma gashi mijin yayarta haka kuma masoyinta ta tsinewa kanta yafi sau dubu amma ita kanta batasan lokacinda ta aikata hakan ba.!! Farhaan kuwa duk ya damu yayi nadamar abinda ya aikata qarshe yasa Suhaila ta kira iffaat tana bata haquri itama ta bata haquri tana ce mata ga yy farhaan zaiyi magana da ita ta kashe wayar farhaan yace ta kyaleta amma ya damu matuqa... [11:38AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 56 Na Hauwa M. Jabo Su ZZ an qare skull an bar su Iffaat yan mata anata gwagwatawa Da students, dama ko ita kadai tana abinda taga dama.... Cikin ikon Allah iffaat ana shirye shirye kammala secndry skull any qara hankali amma fa har yanxu tana jinyar soyayyar farhaan a zuciyarta, ba Wanda yasani sai qawayenta ZZ.... ****** Wata Ranar Suhaila taje sokoto bikin dangin mamarta kusan sati biyu tayi bata gari, ana gobe zata dawo tace wa iffaat taje ta gyara mata gidanta tasan yayi qura ba kowa aciki tunda tasan farhaan aikin banxa ne ba abinda yake iya tabukawa kuma idan ta dawo ma ba wani abin kirki zata iyaba gata da tsohon ciki kwata 7 , dagyar iffaat ta aminta shima saida aka hada da mama sannan ta aminta. mama batasan sirrin ba iffaat tun lokacin da abin nan ya faru bata qara zuwa Gidan Suhaila ba sai wani zuwa da sukayi duba Suhaila itada mama, sai kuma yau... Waike Dan Allah idan bakiyimata wa zaki yiwa?? yarinyar tana qaunarki ta damu dake amma ke kina Neman ki yanke zumunci mama dai haka tayi fadanta dole tasa iffaat ta tafi Gidan.. Hmmmm Su farhaan ba'asan da zuwan iffaat gidanba, kuma yasan sai gobe matar shi zata dawo hankalinsa kwance shida karuwarsa... iffaat tazo ta gyara ko ina na Gidan har ta kammala Basu saniba suna chan ciki. haka kawai taji tanason shiga dakin farhaan ta gyara kuma batasan yana gidanba. Takama hanyar dakinsa Ta buda qofar tajita abude sai ta tsaya ta qara budewa Sanyin Ac da qamshin turarensa ya daki hancinta ta lumshe Ido ta dauke numfashi hadi da wani ajiyar zuciya ta tura kai dakin tana bude ido sai taga mace kwance tana sharar bacci daga ita sai wasu tsinannun kayan bacci, numfashin tane ya tsaya chak..!! tama rasa mi zata mata ta gane ta tsab hafsa ce tsohuwar budurwar farhaan, ta tsaya waige waige ta hango Yar yawo gefen fridge ta Ciro ta zo zata fara zabga mata sai ta tuna duka ana bacci bashida xafi sosai, ta bude fridge ta samo ruwa ta juyesu a jug taje ta yaye bargon da ta rufa ciki da qarfi, hafsa ta juya cikin shagwaba tace dear kabarni zuwa anjima mana.!! tace kinci ubanki keda dear. ta watsa mata ruwan da qarfi a fuska, hafsa ta wani zabura da qarfi tana miqewa zaune iffaat ta kwashe banxa da mari saida ta koma kwance tuni hafsa ta gigice, iffat kuwa batayi qasa a guiwa ba tafara zuba mata bulala hafsa tana ihu, ta mata lilis chan farhaan ya fito bayi da gudu yayi turus da ganin madam iffaat..... [11:41AM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 57 Na Hauwa M. Jabo Bata tsaya ba taci gaba da chin uban hafsa farhaan ya kasa aikata komai kunya ta isheshe dagyar hafsa ta samu ta miqe tayi bayan farhaan da gudu tana kuka, tabbas hafsa ta gane iffaat Dan kuwa itace ta qona mata qafa shekara wajen Shida da suka wuce, iffaat ji take kamar ta hada da farhaan din ta musu lilis amma bazata iya dukan farhaan ba, tsanar sa ta rufe mata ido ta tausayawa yayarta da take tareda fasiqi irin sa tagodewa Allah da bata aureshiba, da saidai suyi kashin kai a gidan Dan bazata dauki wannan iskancinba ta dakawa hafsa tsawa tabar gidannan hafsa ta kasa fitowa bayan farhaan ta qara mata tsawa wallahi idan naxo sai na kakkaryaki, inbanda hafsa batada gaskiya ai ko qanwar hafsa iffaat bazata iya fada da itaba bare hafsa mai Shekara wajen 30, zata kakkarya iffaat. amma tunda batada gaskiya dole ta boye farhaan kuwa ya rungume hannuwa yana kallon ikon Allah kunya ta isheshi da nadamar abinda ya aikata, tayi cikin hafsa da qarfi hafsa ta riqe farhaan da qarfi wani baqin cikine ya qara tasomata yanda taga tana rungume farhaan ta baya uhum su kishi manya tayi cikinta da qarfi ta janyo gashin da tayi qara da qarfi ta wurgata a kan fridge farhaan ya dakawa iffaat tsawa akan miye haka ta juyo tamai kallo keep quiet ina zuwa gunka kaima..!!! tama hafsa gargadi kamin ta lissafa biyar tabar gidannan hafsa dagyar ta miqe ta kwashi kayanta a hannu taji jiki tana gudu tana tunanin wai wannan WACE CE ITA?? House girl ce haka kyakyawa kuma ta mata haka gaban farhaan. Anya kuwa?? Bayan ta kori hafsa ta juyo ta kalli farhaan ido cikin ido tana tunanin balbala masa masifa ji take kamar zuciyarta ta fito Dan baqin ciki aranta tace wai ita kenan inaga matarsa da sukasan juna idan taga haka sai hade rai ta mutu.! Ya dago ido ya mata wani kallo ta mayataccun sexy eyes dinsa tuni ta manta abinda takeson ta masa sai ya bata tausayi tayi tsaki..... Har zata fita dakin sai kuma ta daure ta dawo ta gyara ko ina ta tattara sauran kayan hafsa data bari ta miqa masa tace ga kanan tsohuwar karuwarka nan idan ka bita ka kai mata.. ta juyo kenan ya janyo mata gashi da qarfin bala'ee saida tayi wata qara.... [12:12PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 58 Na Hauwa M.Jabo Ta sa hannu tana qoqarin kwacewa amma ta kasa ya qara janyota da qarfi saigata saman qirjinsa, ta daga kai tuni idonta sun cika da kwalla Dan tsabar azabar da takeji, da qarfin hali, tace, so bansan kacika wayayyeba sai ka aikata abinda kake da niyyar aikata wa aikana.!! yanxu ya gane manufarta tuni ya saketa yayi tsaki ya fada bayi ya kulle kansa cike da baqin ciki da nadama, a duniya ba wacce ya raina kamar iffaat amma itace take gwadamai axaba, iffaat kuwa tana samu ya saketa ta fita da sauri ta wuce gida tana zuwa ta fada dakinta ta kulle tana kukan takaicin rayuwa da mutum irin Yy farhaan ta daga kai taga hoton Yaya Suhaila da Yy farhaan sun rungume juna suna dariya tayi tsaki,ta tashi ta cireshi ta saka a drawer ta dawo taci gaba da tunaninta har barawo bacci ya dauketa, bayan ta tashi taje gun mama.. Ah ah yaushe kika dawo? Tayi murmushi wallahi tun dazu na dawo nasan kina bacci lokacin shi yasa banma zo natayar dakeba, okay suka yi tadi mama tana tanbayarta ta gyara Gidan dakyau kuwa? Dan tasan son jiki ya mata yawa Laaa mama kin manta nayi aikatau suka saka dariya gaba daya, Yaya Ameen ne yazo da Yaya Ali suka zauna akayi tadin dasu suna cikin magana Yy Suhaila ta kira... Sister sorry na sakaki aiki da yawa,!laa kinji dai Yy Suhaila wane aiki kuma idan ban mikiba mawa xan yiwa, ta fara godiya, wallahi idan kinamin godiya zan kashe wayata, to nabari yi haquri, kin tarar da farhaan a gida?? Wallahi Naso nace idan yananan ki masa Dan girki, Tseeeet tayi kamar ruwa ya cita qirjinta yake bugawa, lokaci daya ta tuna abinda ya faru tausayi Yy Suhaila ya kama ta Amma bazata iya fada mataba, hello kinajina kuwa sister? Tayi xumbur ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi.. Inaji Yy Suhaila, to ki bawa mama wayar na miqawa mama ta tashi tsaye, Yaya Ali ya kamo hannunta.. bayan sun qare yace wani abokinane yakeson ta kinma sanshi Nurane mama tace nikam ko sunansa banaso bare shi na tsani wannan yaron akwai shegen rawar kai, iffaat tace wallahi nima mama na tsani Nura kamar me nima dai jabo ba abarni a bayaba gun tsanar sunan Nura mugu. Duk aka saka dariya kowa ya tsani Nura Allah sarki har ya bani tausayi...... ** Goben ranar tinda safe Suhaila tayi waya da iffat ta gaya mata sun kamo hanya Guraren qarfe 11 iffat na zaune da mama dasu yaya da yake yau Saturday, wayar iffat tayi qara laaaa yy Suhaila hatman sun iso, hello Yy Suhaila kuna ina? Kun kawo hala? Taji namiji yace ke sister din Suhailar ce ?? Tace Eh kai waye? Sorry Dr ne daga Chika, yayar Ki sun sami accident Allah ya mata cikawa driver kuwa gashinan kwance ya kakkarye? Iffaat wata irin qara ta saka ta fadi sumammiyaaa.... [12:18PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA..?? 59 Na Hauwa M. Jabo Mama tayo kanta tana tambayar lafiya amma ina iffaat ta riqa ta suma, Yy Ali ne ya dauki wayan ya kira number Yy Suhaila, Dr. Ya masa bayanin da ya yiwa iffaat yace babbar motace ta shiga gabansu suka yanka daji anan motar ta wuntsila rai yayi halinsa Yaya Ali ma dashi da qarfin halinsa sai da yayi kuka, ya yiwa mama bayani tuni gida ya rude da koke koke Yy Ali yayiwa baban Suhaila waya ya fada Masu abinda yake faruwa kamin kace kwabo labarin rasuwar Suhaila ya baje family namu kowa yaji mutuwar Suhaila cox Suhaila mutunce mai mutunci ga haquri da kawaici, bata shiga harkar da ba nataba kai mutuwa tana dauke nagari. farhaan kam da ya samu labari mutuwar tsaye yayi bai samu damar maganaba saida yaga gawar Suhaila, sannan ya fara kuka kamar qaramin yaro kamar wani zararre, lallai ta tafi tana binsa basussuka cox bayajin tayi wata biyu yana kyautata mata kullum cikin muzguna mata yake, su farahnax kam haka ta dawo kamar mahaukaciya, mutuwar ta ratsa kowa a gidannan musamman iffaat da farhaan da maman Suhaila.!!! Iffat koda ta farfado har an kai Yy Suhaila makwancinta wayyo Allah, mutuwa mai raba da da mahaifi miji da mata Yaya fa qanwa aboki da aboki. Mutuwa tayi yankan qauna a wannan family... cikinta ma anciroshi da ranshi amma da yake wata7 ne kwana biyu yayi yabi uwar shi, cikin da farhaan yayi burin ta zubar tun tana amarya zan iya cewa ma bayason cikin. Sauda yawa Suhaila tana kiran iffaat qanwarta ta fada mata abinda farhaan yake mata amma tace kada ta fadawa kowa, kuma bata taba fadaba Mutuwar Suhaila yasa iffaat ta qara tsanar farhaan gani take kamar shiya kashemata Yar uwa! amma fa still sonsa yana cikin zuciyarta, hmmm soyayya manya..! ***** Arba'en din Suhaila yayi daidai da fara jarabawar su iffaat mutuwar Suhaila tadan natsar da ita kadan dama iffaat ta iya matsuwaa idan Abu ya faru da ita! sunyi neco da waec lfy sai jiran saka mako, xubi xubi iffaat tana zuwa gidansu farahnax ta gaida mamarshi da farahnax din da kuma qawarta Yar baqa zainb khalifa, Ranar tana zaune dakinta taji sallamar farhaan, da yake Gidan idan aka shigo dakinsu yana daga gefe ne sai dakin mama, tanaji ta gane tayi banxa dashi. Sunyi hira da mama, tanaji yana tambayar ina iffaat tace tana daki, Har ta manta da wani farhaan yazo gidan. Chan taji sallamar sa a dakina, Dan amsa sallama wajibine da nasan iffat ba zata amsa maiba, taci gaba da aikinta, ya zauna ya fara sun batunsa, yaga ba nasara, yace iffaat....... [12:21PM, 5/9/2015] .: WACE CE ITA.?? 60 Na Hauwa M.Jabo Iffaat miyasa kike min hakane? Koba komai ni Dan uwankine tun kamin mu hadu da margayiya, kuma naxo na auri yayarki, kina tunanin kodan wannan ai bai dace ki riqa min wani gani ganiba, ki tuna kin min laifinda ya dace na hukuntaki amma na gyaleke na yafee miki..! Anti masifa madam iffaat ta watsa mai kallon banza hadi da wata uwar harara! Laifin me na maka oga? Wato ma ni na maka laifi ko?? Ka manta chin mutuncin da kake yiwa Yar uwata? Kamanta wulaqancin da kake mata?? Ka manta yaudarar da kake mata?? Sannan duk ka shuresu kaxo kana cewa ni na maka laifi?? Ta daga kai tayi karo da hotonta ita da Suhaila sun rungume juna suna dariya. Hawaye ne suka wanke mata fuska tayi missing din Yar uwarta abar sonta, farhaan ya kamo hannun iffaat yana zaune iffaat Dan Allah ki yafemin! Nasan ban kyautawa Suhaila ba ko kadan, wallahi sai yanxu nake ganin irin rashin kyautatawar Dana mata idan kika yafemin tamkar itace ta yafemin ta kasa kwace hannunta daya riqe batace komaiba.! Tayi ajiyar zuciya ta karbe hannunta, ta zauna har ya qare surutansa batace masa komaiba, wallahi iffaat ina tsananin son Suhaila, ji tayi ya daba mata wani gwaho a zuci har saida ya gane. Nasan baxaki yardaba amma gaskiyane na fada miki, ya gaji ya tashi Ya qara wuta.. ***** Iffaat yan mata result ya fito ana kiciniyar shigarta jami'a ta sami damar shiga cikin nasara an bata course dinda takeso kuma. Dai dai lokacin auren farahnax ya matso sai shirye shirye suke qawayen amarya, komai itace gaba itada Yar baqa sai iyayi suke, anyi auren farahnax lafiya ankai amarya Gidan mijinta da ke abuja, iffaat dai kam kullum sai tayi sabon saurayi amma ko kallo Basu ishetaba karatun ta ta saka gaba.! Ranar umma tayi rashin lfy sunje dubata itada mama da maman suhaila, umma ke tambaya ta yaushe zatay aure? Ko sai ta samo mini mai saida ruwa irin na dijee, akasa dariya kunya ta kamani na tashi na shige lanbu don demo abincina na da na barsu su nan..... KU BIYOMU DON JIN ABINDA IYAYEN WAYANNAN YARAN ZASU TATTAUNA AKAI, jiya banyi posting ba wallahi network yamin tsiya nayi nayi fcbk dina ya bude yaqi buduwa kuyi haquri.!!! [10:49PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..??61 Na Hauwa M.Jabo Suna tsaka da labarin su saiga farhaan ya shigo ya gaida surukansa yama ummanshi ya jiki ya shige dakin abbansa, Bayan ya wuce ne maman Suhaila take cewa Allah sarki yaronnan har yanxu bai nemi mataba? Umma tace kedai bari gashinan Bansan mi yake jiraba, niko ga shawara, mizai hana a hada farhaan da iffaat aure. Mama tayi dariya kai hajiya kulu ina kika taba ganin rigima da rigima sun hadu duk sukasa dariya umma tace lallai kam Dan farhaan da iffaat basa zama guri daya. Mama tace koda yake shi aure daban ne wata qila sai kiga sun zauna lfy. Gaskiyar magana dukansu sunyi na'am da shawarar hajiya kulu maman Suhaila sun tsaya akan zasu shawarci mazajensu suji, Suna zaune suna tadi saiga iffaat da ta ciki kyale da su mangoro da gwaiba umma tace um um mai hali baya barin halinsa..! duk suka saka dariya, taje ta wanko ta kawo musu suka farasha, dama ita qa'idarta idan zatasha mangoro saita mulmulashi yayi laushi yayi ruwa sannan tasha. Ta kuwa miqe qafafu ta saka basket dinda ta saka kayan a ciki ta fara shan mangoronta tana zaune saiga farhaan ya shigo ya kalleta, xaman da tayi ya bashi dariya ya tuna mai da lokacin da take qarama sai yaji bari ya tsokaneta komai ta fanjama fanjam.!! Wai umma wannan Yar taki ba university take xuwaba? Umma tace eh chan take kaga yata an zama yan mata ko..!! Inafa yan mata har yanxu bata wayeba! Kalli Dan Allah yanda take shan mangoro kamar wata Yar ruga,! ruwan mangoromangoro suna bin hannu, ya kwashe da dariya hadda buga qafa ya gama quleta ya kalli umma anya kuwa zata sami miji a haka?? Umma tace ka sakawa yata ido dayawafa miji kam sai ta xaba Dan ma bakaga yanda ake layiba dukansu suka dara nima dai jabo na dara kuma Masu karatu sai Ku dara.!! Iffaat tace umma ki barshi, ta dago ta kalleshi ido cikin ido tace mijina sai ka Ganshi wayayye na gaske ba irin wayewarkaba, ba Wanda yagane habaicin da ta masa sai shi damu Masu karatu. Yadan Sosa kai yayi murmushi qarfin hali mama bari na tafi tunda kun hanani mangoro, umma tace sai kace wacce da debo ta sammaka, yace waa ai wannan tafi dijee rowa.! da zai fita ya hada da gefen chinyarta ya take saida tayi qara ta jefeshi da qallon mangoro...... [10:57PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 62 Na Hauwa M. Jabo Mama tace Waike iffaatu bakida kunya ko, miye na jifanshi da kwallon mangoro? umma tace rabudamin da ya, wallahi shiya tsokaneta ina kallonsa ya taketa, Dan ya taketa sai ta jefe shi, karki sa mata baki Dan Allah ke iffaat tashi ki shiga ciki. Bayan ta wuce umma tace kin ganiko,? Haka suke kamar tom & Jerry, hajiya kulu tace ai aure daban yake alkhairin sa zamu nema kawai,... *** Hajiya kulu na komawa gida ta sami mijinta mahaifin Suhaila tamai xancen ai tuni ya amince abbah ma da umma ta masa magana ya amince 100% mama ma haka tayi shawara da su Yaya Ameen akan wannan auren kowa ya aminta yanxu ya rage aji ta bakin gogayen... Abba da umma suka kira farhaan aka fara masa maganar Dan tsananin rudu da tsoro saida ya manta yana gaban iyayensa, atafau farhaan yace aah miye dalilinsa yace kawai matsayin farahnax ya dauketa, shi bazai iya auren taba tun ana lallashi har Abba ya yanke dole ya aureta ko bayaso, kana tunanin zamu aura maka macen da zakayi kuka da ita? Duk cikin mu ka fimu sanin WACE CE ITA! cox ka zauna da ita tun tana Yar mitsiyayarta, Farhaan dai kawai yajisune amma Sam bai amin taba, Itama madam iffaat an mata maganar farko dariya ta saka musu irin ga zancen nan Mara kan gado. Da taga dai da gaske akeyi kawai saita saka musu kuka! Aka buga Sama da qasa tace bazata auri mijin yayartaba... Abba Suhaila ne yace sun Riga sun yanke magana ba chanji ba mijin yayartaba ko waye shi zata aura.. Nikam jabo abin mamaki ya bani yanda iffaat tayi jinyar son farhaan tun batada wayo amma yanxu ga dama ta samu tace batasosa! Uhum kuma ga dukan alamu da gaske takeyi, ta daga ba nasara taci gaba da kuka ta wuce dakinta, Yaya Ameen ne yabi Yar qanwarsa yana lallashi, Haba iffaat miye aibin farhaan? Kina gani wallahi guy ne gashinatsatse ga kamala, wallahi yanzu dagyar ki sami namijin na kirki kamarsa baya shaye shaye baya Neman mata. ta dago kai da sauri ta kalleshi amma sai ta kasa fadar cewa yana Neman mata, kowa ya shedeshi ke kanki shedace akan haka! Sabida kinyi rayuwa dashi, iffaat dai batace komai ba har Yy Ameen ya qare rarrashinta ya tashi ya fito! Ta miqe wallahi da na auri farhaan gara na shiga duniya.... [10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?? 63 Na Hauwa M.Jabo Tun daga ranar ta kamawa su mama mutunci ta daina musu magana tadaina chin abinci ba ruwanta dasu ita dole fushi, anyi sati biyu da maganar sai ranar taji su yy da mama suna maganar, ana maganar daurin aure kuuut saidai wata ba itaba, ta miqe tsaye ta riqe kunkumi ta fara shawara da zuciyarta yanxu ita iffaat har sun isa su mata auren dole? Waima...! Idan ta saka musu ido zasu aurar da itane, su Basu damu da damuwartaba, abinda ya fado mata kawai ta gudu, kai guduwa ba jarumta bace, duk macen da za'ayiwa auren dole ta gudu ba jaruma bace,so bataso ta gudu a ganinta ba jaruma bace duk wani tunani sai taga bai dace da itaba, nidai jabo zaune nayi ina kallonta ina jiran muga abinda zata aikata, amma ga dukkan alamu ba wani Abu da ya rage gwagwalwarta bata aiki, sai fashewa tayi da kuka.. Yanda ta tsani halin Yy farhaan ko sonsa zai kasheta bazata aureshiba, tanada mahaukacin kishi Tayita tuna yan matan farhaan din da yanda yake musu ta runtse ido da qarfi ta daki madubi tace Nooooooooooo, ta na kuka tana dukan madubin duk ya yayyanke mata hannu, ashe su mama sun jiyo mama ko a jikinta, Yy amin ne yaxo gunta da sauri ya riqe hannunta duk ya yayyanke, ya yiqeta ya kalleta yaga yanda ta rame tana juyowa ta fada jikinsa tana kuka, tana cewa Yaya ka taimakeni wallahi banason sa Yy Ku aura min wani not Yy farhaan, yace to shikenan kiyi shiru zamuyi magana da mama, dagyar ya samu tayi shiru ya dauko first aid yadan gyara mata hannun ta ta ta yayyanke, ya jata da hira har tadan saki jiki, qarshe yace tazo su fita yawoooooo... [10:58PM, 5/11/2015] .: WACE CE ITA..?64 Na Hauwa M. Jabo No ka tafi Yaya ni baxanjeba ya rarrasheta har ta amince suka shirya suka fita. Sunje wani park ne suna shan ice cream, hakan ya faranta mata rai matuqa suna sha suna tadi a hankali yy amin yake nuna mata illar abinda takeson tayi, suna tsaka da magana tana yan kalle kalle charab ta hango wani abu wacce ta hango ba shakka itace ba qarya budurwar farhaan ce ramcy, tayi murmushi su ramcy ananan da yake Yy baisan taba tana kallon ta har ta shige ba'ayi minti goma sai kuma ta hango farhaan, wani rasss taji ko shakka babu tare suke da farhaan amma da yake shi mai wayone a hankali yake takunsa, wai farhaan wane irin jarababben mutum ne? Tayi tsaki, yy amin yace miya faru kuma? Ta kalleshi idonta sun kada sunyi jaa ba komai! Ya ba komai, ta dago mai idonta da har sun zama qanana tace ba komai yy, sukaci gaba da tadinsu amma Sam bata tare da yy amin tanachan tana tunanin farhaan, kusan 30mnt Basu fitoba ta kasa haquri ta miqe tsaye, ina zaki kuma? Y tace ina zuwa yaya ya kalleta, yanxu zan dawo Yy, ta wuce da sauri ta shiga Ashe cikin gurin hotel ne ta fara dubawa duk ta zagaye gurin bata gansuba, sai taje gun reception ta tambayi farhaan mutumin yace mata yanada baquwa wani rass taji, tace ai na na sani shi yace nazo na karbi saqo yayanane, ya kalleta sosai sai ya gaya mata number dakinsa wani dumm dummm dummmm takeji, ana mata zagaye a zuciya ta isa gofar dakin tayi jimm ta daure ta bubbuga saida ta buga uku sannan aka bude, ramcy ce ta bude qofar iffaat ji tayi kamar ta shaqeta ta mutu ramcy bata gane iffaat ba Sam.! ta watsa mata harara, tace lfy iffaat ta daure tace yy farhaan yace naxo na karbi saqo na kaiwa umma, tanajin haka sai ta saki fuska, okay bari na kirashi, ta kwala mai kira yazo yana zuwa ya ganta......... Tofa. [11:19PM, 5/12/2015] .: WACE CE ITA..?? 65 Na Hauwa M. Jabo hankalinsa ne ya tashi! Ya rude yama rasa mizaice mata, itama haka wato wani tashin hankalin sai mutum yama rasa mi zaiyi, ta kalleshi tayi murmushin qarfin hali tace sannu Yy farhaan.!! Kamin ya bata amsa hawaye ne suka zubo mata batasan dalilin zuwansuba, gaskiya hawayennan sun kwafsa mata taso tayi chin mutunci cikin ruwan sanyi amma ina kuka ya kwafsa mata, bazai yiwuba chin mutunci ana kuka baiyiba, da sauri ta bar gurin tana juya kenan sai ga yy amin yaxo nemanta, lafiya kike kuka? Tace Ta hadu da wata qawartace shine take bati labarin mutuwar mijinta ......... Eyyah Allah yajiqanshi ina take? Tace sun wuce, farhaan yana jinsu kuma yaji abinda tace, yayi tunanin zata tona masa asiri amma ina bata fadaba, Suka kama hanya idon iffaat Sam bata gani gabanta hawayene suke rally a fuskarta.! ta kasa jurewa sai wani Abu takeji yana taso mata,ta rasa gane kanta, Yy amin yana gefenta yanata bata labari amma taqi bari su hada fuska kuma taqi cemar komai, har suka isa suka zauna!! Waike har yanxu kukan kikeyi? Ta dago kai ta kalleshi, wallahi Yaya ta bani tausayine tana matuqar son mijinta amma mutuwa ta rabasu, sai na tuna da yy Suhaila... yace Eyyah sai haquri Allah yajiqanta ya Dan qara lallashinta har tayi shiru amma zuciyanta cike da tunani.! Har suka dawo gida tunani takeyi. Shiko farhaan yana ganin sun bulle ya kori ramcy tana tambayar lafiya ya daka mata tsawa akan ta bace mai da gani, ta tattara yan kayanta ta wuce, ya fada kogin tunani,! Baisan miyasa wannan yarinya takeda bala'en tasiri rayuwarsaba, duk abinda yake a boye yake yinsa, amma kuma bawai yana damuwane da kada a Ganshi ba amma yana jin haushi idan iffaat ta Ganshi..! Gashi tun tana qarama tasanshi da wannan hali,amma har yanxu baidainaba, yasan yana fama da sonta kuma tun tana qarama yakejin haka yaqi qasqanta hakan ne, ya yakamata fa ya daina. Kai wannan mitsitsiyar yarinyar tama isa ta hanashi abinda yakeso!? Amma miyasa take yawan kamashi? Yaja tsaki ya juya ya miqe tsaye yana zagaye dakin. Chan ya daki iska yace auren ta kawai zan aminta dashi shine zaiyi maganinta, shima ya huta da azabar rashinta. haka dai ya qare yan tunane tunanensa cike da damuwa. Iffaat kuwa ana isa gida ta fada daki ta kulle ta fara sana'ar tata yanda take kishin farhaan tasan wata rana kisan kai zatayi, gara kawai ta nemawa kanta zama lafiya ta aureshi, ba wata hanya da takeda da ta wuce ta amince masa kamin baqin cikin sa ya kasheta ko banxa zata rage azabar rashin ganinsa da take fama da ita, haka har bacci ya dauketa, Yy amin ne ya tayar da ita daga bacci, ya kawo mata pizza tayi murmushi Yy amin ne kawai yake rarrashinta idan tana fushi mama kam ko kallo bata ishetaba itama haka.... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 67 Na Hauwa M.Jabo 20/5 idan ban mantaba yayi daidai da ranar daurin auren yy Suhaila kuma shine ranar brdy dina ni Hauwa Jabo wannan ranar itace rana mafi girma da daraja a idon iffaat wannan ranar ita ta chanxa ta daga jerin yan mata zuwa matar aure a wannan ranar ne ta taka matsayi na Chika da kamala, Farhaaan kuwa jinsa yake gashinan dai ya rasa abinda yake damunsa tsorone ko kuma murna ko baqin ciki gashinan dai kamar ba angoba.. Ba wani shagali da akayi, Dan zance muku iffaat har ranar dauren auren ta saida ta sulale taje makaranta wayanda sukasan da zancen auren suna ta mamaki irin ga serious student dinnan, basusan dawar garinba, ai kuwa tana dawowa tasha fada gun mama haka dai aka qare taro akan gobe za'akai amarya gashi Kuma amarya gobe ma tanada test gashi ance sai ta fadawa ogan zata iya fita, sai kawai haqura tayi, ankai amarya gurin su umma suka mata nasiha, nidai tunda nake ban taba ganin amaryarda ana mata nasiha tana kallon mutaneba sai iffaat ba Dan sunkuyar dakai ba komai haka umma na mata nasiha ido cikin ido tana kallon ta har abin ya baiwa umma dariya amma ta fuske Abba ma yayi har ya bata kudi yace ko zata buqaci wani Abu. Daganan aka kwashi amarya aka kaita Gidan mijinta PURHUUN... Abokan ango sun rako ango yan matan amaryar da suke nan su black one ZZ da najma da meena slow sune suka sayi baki idon amarya tar akansu Allah ne kawai ya dinke bakinta batayi maganaba Dan kuwa taso tayi magana, an sayi baki kowa ya kama gabansa amarya ta tashi ta cire kayan jikinta dama sun dameta kuma gata da jin zafi kamar me, ta saka wasu kayan tana danna waya saiga farhaan ya shigo ta kalleshi shima ya kalleta ta mishi kyau itama ya mata kyau uhuuuuum ya zauna gefen madubi. Iffaat ya kira sunanta koni nan Jabo saida na jiyo bugawar zuciyarta, ta dago ta kalleshi, Ya fara yan maganan ganun da ake yiwa amarya sannan ya qara jadda mata cewa yanxu da da ba dayaba akwai haqqinsa akanta itama haka yana cikin mata nasiha sai yaga ta dauki waya hello tana dariya, shiru yayi yana kallonta tana rai nashi yana maganaba tana waya tsaki yaja ya kwanta abinshi ta qare wayarta itama ta kwanta nayita jira ko za'ayi wani Abu amma har na gaji ba wani bayani na fito abina..... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??66 Na Hauwa M.Jabo Taci pizzar sosai suna dan labari sama sama chan ya sako zancen auren ta da farhaan irin dai yana son ta amince ya nuna mata illar fushin iyaye akan yayansu, jiki a sanyaye tace mishi ta amince, Dan murna baisan lokacinda ya tashi yayi rawaba ya juya itama abin ya bata dariya nima Jabo abin ya bani dariya, yana ta saka mata albarka, yaje jikinsa na rawa ya gayawa mama da Yy Ali sun ji dadi ko ba komai sun yanke shawarar idan taqi aminta za'a bar auren.. *************** Magana ta kowane ban qare ta kan kama iyayen sai murna suke sunata shirye shirye, amma amaren kam ko a jikinsu, ana saura kwana biyu daurin aure saiga goggo da dijee da rukayya sunzo, koda sukazo iffaat tana skull Dan ita wannan shirye shirye bai hanata zuwa makarantaba, Koda ta dawo bakin qofar dakinta taga wasu takalmi Masu kama da kito amma dai na matane, ta shiga dakin saiga su dijee anyi arshe arshe tsakayar daki da yayanta biyu rukayya ko yarta daya da ciki ta kallesu ta kwashe da dariya harda durqusawa qasa Dan dariya, tayi dariya saida ciknta yayi ciwo suko sun tsaya kallon ikon Allah ta dago ta qara kallonsu nan ma ta kwashe da dariya dijee tace ke bamusun iskanci Dan kin zama Yar birni zaki ijiyemu kina mana dariya kamar Kinga tutu...!! ta harareta ta zauna da kyau tana dariyar tace wallahi mamaki nakeyi wai dijee da Yara har biyu! Ta qara saka dariya dijee ma sai ta dara, ta kalli yayan tace amma dai dijee kina dukansu ko? Rukayya tayi charab ta chabke tace ai yanzu duk bala'en dije akansune Dan har danbe tanayi da uwayen yara akansu, dijee tace ke rukayya banason sharri da zuwa ko gaisawa ba'ayiba zaki fara mini sharri, nan dai qawayen suka yini suna tadi suna dariya duk da qauyanci su bai sa ta gyamacesuba tunda itama chan aka fito sun cire mata kewa matuqa kuma bata bari suka gane cewa auren nata sai a hankali bane.... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 70 Na Hauwa M.Jabo Taje ta zauna sai ta kasa chin abinchin don an hanata fita kuma sai a hanata xuwa skull... Wasa wasa iffaat na Neman wata daya Gidan farhaan baya kulata itama bata kulashi amma rashin xamansa gida na damunta ko ina yake zuwa Allah masani kuma bata gane takunsa, Ranar tana zaune dabara ta fado mata yanda zata gane ina yake tafiya, bayan ya dawo gantalinsa na dare ya kwanta bacci, dama batayi bacciba tana jiransa ya dawo ya ijiye wayansa tana tabbatarda yayi bacci ta dauki wayansa ta shige bayi ta kulle ta danna power off screen din yayi duhu ta duba da kyau sahun hannunsa ya yake zana pattern dinsa bataci wuyaba tana zagaya yanda taga sahun hannunsa yabi tayi sa'ar bude wayar pattern dinsa ba wahala ma, tana budewa ta fara aiki, farko saida ta budamai Google account sannan taje play store tayi downloading din latitude tamai register dama tana dashi ta dauko wayanta tayi sending request ta karba shikenan ta gama da wannan duk inda yake matuqar data dinsa a kunne take zata Ganshi baya buqatar GPS latitude din, ta shiga SMS bata sami komaiba taje contact ba wani number da bata yarda dashiba harda searching na sunayen yan matansa data sani amma babu ta duba logs nan ma babu da qanqaro WhatsApp a kulle yake kuma da pin number kawai zai bude bata wahalda kanta ba taje gallery ba wasu hotuna daga nashi sai iyayensa sai kuma na margayiya Suhaila, gasunan sunfi 100 wani qololon baqin ciki da kishi ya taso mata ganin hotunan da Wanda suke tare da Wanda rake ita kadai amma ba nata ko daya kamar ta goge amma kawai saita fasa har zata fita sai taga wani folder ta shiga akwai wani aciki ko wanne an rubuta empty haka tayita dannawa saida ta wuce folder 14 sannan takai gunda aka rubuta Mrs PURHUUN, ta shiga ciki hotunan tane aciki daga kan wayanda ya mata lokacinda ta fara koyon gayu gun Yar baqa Dana zuwa qauyen da yayi wasu ma ya saka su a cikin frame mai heart wasu kuma itada Suhaila ne amma an gutsure Suhaila ko farahnax wasu ma batasan ya dauketa suba irin tana zaune dinnan tana shirme ko kuma tana surutunta tun kamin ta qare wayewa gasunan dai kala kala, mamaki da jin dadi suka mamaye mata zuciya ganin ya damu da ita hatta hotunanta a wayar, sai wani video da ta gani rawar da suka tabayine itada farahnax a daki sukayi video ko ina ya samu ohoooo tana tsaka da kallo taji yana qwanqwasa bayi tsoro da tashin hankaline suka baibayeta..... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 69 Na Hauwa M. Jabo Tace Idan da kana dukana ada yanxu akwai banbanci wata qila ada ina gyalewa ko kuma ina ramawa to ka sani yanxu akwai banbanci, ni matar aurece inada yanci kuma nasan yancina so ka kiyaye hannunka daga Taba matar aure.! Ta sake mai hannu da qarfi Ta wuce abinta ya bita da kallon Mamaki hadida zargin abinda ya kawota yi anan ya akayi tasan yana nan ya daki iska baima jira karuwarshiba ya fito da qarfi koda ya fito bata ba labarinta ya shiga mota gudu yake kamar ya ya hira sama koda ya isa gida bata isoba yayi kusan 30mnt sannan ta iso da ledojin abinci a hannu.! Tana zuwa ya daka mata tsawa ina taje? Ta kalleshi dukda taji tsoro amma bonewa tayi, ta danqaramar uwar harara, kamar ma bada ita yakeba, tana Neman guri ta zauna ya fincikota ke badake nake maganaba, ta kalleshi ido cikin ido tace mai inda yaje chan taje? Mi kikaje yi achan nanma ta bashi amsa abinda kajeyi achan shi najeyi.? Idonsa suka kada sukayi jaaa sun firfito waje iffaat kinsan abinda kike fada ya qara fincikota ya mannata a garu kinada auren nawa zakije gurinnan ? Ko kin manta ke matar aurece. Taji tsoro iya tsoro amma ta daure ta bashi amsa ta kalleshi idonta cikin nasa tace, au auren akan mace kadai yake kenan kaima ai kanada auren nawa kaje gurin nan ko kaman ta kanada aurenane akanka? Idan kuma akwai banbanci tsakanin mu let me know. Yanda idan ka'aikata badaidaiba za'a maka hukunci haka nima za'amini so miye banbanci?? Wani baqin cikin kishi ya turnuqeshi. Muryansa na rawa yace iffaat tell me the Truth mi kikajeyi a gurin nan ? Ya bata tausayi yanda ya sassauto, nace abinda kajeyi shi najeyi. Sakinta yayi ya fuskanceta dakyau iffaat mi kakajeyi a gurinnan Har kika ganni? Tace abinci naje siya, Ya manna mata arniyar harara, daga yau na soke baki ba fita sayen abinci idan dai ba makaranta zakijeba baki ba fita, abincin kuma ki shiga ki girka da kanki!! Tsaki tayi ta wuce shi, Farhaan ya tsargu matuqa yauda ta kamashi da wata ai bai isa ya shigo gidannan ba.. [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 68 Na Hauwa M. Jabo Gari ya waye ma amaren farhaan yana jiran amai breakfast amma shiru har 12 yunwa ta isheshi ya duba ko ina ba alamar girki sai hayaniyar mutane, Yakama hanya ya fita abinsha bai dawoba sai guraren daya na dare bata damuba cox yan ganin amarya da qawayenta sunanan sunyi girki sun debe mata kewa, bayan sun tafi sannan ta fara tunanin ina yaje!? Daya na dare ya dawo daya shigo tamai kallon tuhuma tana Palo bai kula da itaba ya wuce dakinta, Koda ta shiga ya shiga wanka ta zauna bakin gado har ya fito ta kalleshi yana goge kai alamar wankan xxxxxx yayi. Ta fuskanceshi da kyau, tace ina kaje yau? Gurin abokaina ya bata amsa yana chire doguwar rigar dake jikinsa dagashi sai towel bata taba ganinsa hakaba sai yau tsoro yakamata ta tashi ta koma palo, ranar dai batayi bacciba zuciyarta cike da tuhume tuhume, sai guraren asuba bacci yayi awon gaba da ita bata farkaba sai guraren 12 Subhanallahi yau tayi lettin lecture dole taje ta nemo abinci ta tashi ta fita direvan bayanan an ma fita da motar da ake kaita skull da ita tayi tsaki tafito ta taka sosai sannan ta sami mai adaidaita sahu ya dauketa koda taje Al nasiha restaurant abincinda takeso ya qare aka mata kwatancen wani guri inda zata sami abincin ta qara tsayawa chan saiga mai adaidata sahu ta tsayar dashi suka tafi sun isa gurin tace ya jirata ta fito tana zaune tana jiran a hada mata abincin taji ance farhaan, wani rass taji mace ce ta kira Sunansa ta juyo ta kalleta ga dukkan alamu tasan ta amma ta manta ina tasanta Dan kamar ta qara fari yanxu, ta kashe kunne taji tace Tana xuwa yanxu. Iffaat tace ina xataje oho? Tana fita tabi bayanta Tana kallo ta tsallaka titi sai taga ta shiga wata villa a gun, tayi tsaki, ta dawo abinta ta karbi abinchinta ta shiga adaidata sunxo daidai villa taga motar da ake kaita makaranta.... Jiki na rawa ta tsayarda mai adaidaitan tace Tana xuwa qirjinta kamar ya fito Dan tsananin tashin hankali wata zuciya tana kije wata na fadin kada kije, haka ta shiga gurin taje gun Masu coffee ta nuna musu hoton farhaan mutumin ya gaya mata dakin da yake zama kullum, taje dakin da qarfin guiwa za'ayi kashin kai wallahi! Ta bubbuga farhaan ya taso ya bude mata, tsaye yayi yana mamakin mi tazo yi anan gurin ya kalleta mi kikeyi anan ta watsa mai harara abinda kakeyi shi nakeyi ta shiga dakin ta duba ko ina ba mace, tazo ta kalleshi karuwar taka bata Iso bane?? Keeee waike bakida hankaline?? Mutum bai isa ya fito shaqatawa ba sai ace yaje gun karuwai wall....... Sheeee ta katseshi da Dora hannu a lebenta... da kunnena naji kana waya da karuwarka kana taxo ka iso tazo kuyi iskancin da kuka sabako?? Ya daga hannu zai wanka Mata mari tuni ta riqe hannunsa,... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??71 Na Hauwa M. Jabo Ta sadaqar kawai har zata danna power Off ta kulle wayar sai ta tsaya tayi clear din duk abinda ta bude tabar wayanda ta gani ta danna power off ta bude bayin, Tana jiran ya fara masifa akan me zata Taba mai waya amma taga ya shiga bayin baima kalleta ba tana ganin haka tayi sauri ta ijiye masa kayan sa tana ijiye wa ko hannu bata daukeba alarm ya fara bugawa na sallar asuba. Allah yasota da ya buga Tana bayi ai da asirinta ya gama tonuwa, tayi murmushi yana fitowa itama ta shiga tayi alwula tayi sallah...... ********** Aiki ya sami iffatu duk yinin ranar Tana biye dashi a latitude duk inda yaje Tana biye dashi haka tayita saka mai ido har kwana uku ta gano gurin da yake xuwa kullum ta gano gunda yake yawon dare, hatta gurinda yake parking din motarsa ta gane so zata fara aiwatarda aikinta akansa. Farkon abinda ta farayi ta Riga ta gano gunda yake parking kuma tasan lokacinda yake xuwa gurin, saida ta tabbatarda yana office ta kira driver tace yakai motarta gurin ya ijiye tamai kwatance ya kuwa je ya ijiye farhaan an qare aiki akazo gantali tashin hankali abinda ya fada kenan lokacinda ya hango motar ta, ko miya kawo wannan yarinyar anan gurin?? Ya fara tunanin ko tazo nemansane ya tafi akan tazo nemansa ne kawai, bai tsaya bata lokacinsanaa jikinsa na rawa yabar gurin bayan ta duba taga yaje sai kuma taga ya bar gurin ya nufi hanyar nasiha restaurant Tana ganin haka Tama driver dinsu magana akan yaje da sauri ya dauko motar bayan ya ijiye motar a gida dama tayi kwalliya kamar wata amarya, yana dawowa ya ganta kuma, ya kalleta kwalliyan ta ya sakashi zargi,! To Ina taje miye na kwalliya ma! Cox bata taba masa irin wannnan kwalliyar ba, Yanason Ya mata magana amma yana tsoro, yasan zatace shima mi yajeyi a chan? Ko kuma tace ina ya ganta? Tinda bai gantaba gara ya bari har y kamata da kanshi, haka ya zauna yana tafarfasa har yayi bacci Dan baqin ciki ranar ko fitar dare baiyiba.. Goben ranar sai baije gurin ba daga office ya dawo gida kuma idan ya dawo saiya ganta gida zaune ba inda tajee har kwana uku ranar na hudu yaje gurin tana ganin haka ta tura driver yaje yayi parking din motarta daga kan hanya hanya ta yanda dole dole yaga motar tazo tayi kwalliya abinta ta kame bayan ya fito hotel din yaga motarta, mamaki ya kamashi, tana kallon duk wani moving dinsa a latitude yana yawo hakan ya tabbatar mata da nemanta yakeyi a gurin tayi murmushi ya fito wajen gurin yayin parking yana jiran ta fito kusan awa daya yana jiran ta tafito amma bata ba labari, ya gaji. ya riqa ya tabbatar da cewa nan gurin tazo yaja mota Kamar wani mahaukaci..... [7:50AM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 72 Na Hauwa M. Jabo Tana ganin yabar gurin dama driver yana gurin tamai waya tace yayi sauri ya dawo da mota gida yayi gudu sosai farhaan kam traffic ya tsare shi a hanya ga uban go slow ya biyo ta PZ shi kuwa driver ta by pass yabi kamin farhaan ya kawo tudun wada tuni an dawo da motar gida yana shigowa gida yaga motar, yana huci Kamar kasa tana zaune a Palo ta saka fura gaba tanasha yana xuwa yasa qafa yayi ball da furar gaba daya ya finciko gashin kanta ya wurgata saman kujera, yazo Dai dai da ita zai kasheta da mari ta wani riqe hannunsa da qarfi, tayi tsaye saman kujerar wallahi idan ka mareni ba mijina bane ko waye kai sai na rama... A fusace yace ke Dan ubanki ubanwa kike yiwa kwalliya kina kina fita? Ta watsa mai harara tace ubanda ya chanchanchi na yiwa kwalliya shi nake yiwa.! Ya daki iska ya juya yana huci iffaat ni kike yiwa rashin kunya?? mi kike zuwayi a Zaria hotel? Mi kikiye achan?? tsaki ta masa ta diro daga kujerar ta kama hanyar dakinta ya biyo ta kinsan Allah wallahi idan bakiyi magana zan iya kashe ki iffaat wallahi xan sallantar da ruwuyarki..!! tashin hankali lallai farhaan yafi iffaat kishi hadda zancen kisa ta bala'en jin tsoro ta juyo ta kalleshi taga yanda yayi wani iri dashi, tayi sauri tabi gefensa ta fita bata tsaya ko inaba sai Gidan su farhaan tana zuwa ta fada jikin umma tana kuka... Akayita tambaya amma ba amsa umma ta kira farhaan tace maxa yaxo tana Neman sa ya kuwa zo, umma ta fara tambayar sa mi ya mata haka duk ta firgice shiru yayi ya kasa magana umma ta dakamai tsawa ya mata bayanin komai tsaki tayi, rudadden banxa wai kai mi yake damunka ne? Ko kunya bakajiba Dan Allah kace ka ga mota amma baka gantaba kuma ka dawo ka tarar da ita gida, haba wane irin shirme ne wannan umma wallahi har kwalliya fa takeyi.! Umma tace to mace a Gidan mijinta batayi kwalliya idan batayi kwalliya ba mi kake son tayi kaji shiriritar banxa, kai waya gaya maka haka ake kishi da hauka, ka bari sai ka tabbatar sannan ka yanke hukuncin waima kai uban me kakeyi a Zaria hotel? Da har kaje kayita ganinta? Ya Sosa kai iffaat data narke jikin umma ta dago ido ta saci kallonsa ya duqar dakai, yace umma baqi nake saukewa a gurin. Tayi tsaki wallahi ka shiga taitayinka. kada ka qara daga mata hankali da haukarka kaji na gaya maka sannan duk abinda kakeyi ka bari sai ka tabbatar sannan ka yanke hukunci farhaan kam ya rasa bakin magana umma ba fahimtar sa zatayiba tonon asiri ne ma zai yiwa kansa idan yace zaiyi ma umma bayani har ta gamsu,!! akace ta tashi ta bishi ta sa kuka ita bazatajeba dole umma tace ya tafi gobe ya dawo ya tafi da ita, Na gaya muku iffaat fa taji tsoro matuqa taji zai kaita lakhira... Dole ta chanxa wata hanya... Muje zuwa muji hanyar da zata komawa. [9:32PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??73 Na Hauwa M. Jabo Farhaan kuwa zaune ya kwana yana ta tunane tunane, kamar ya hade rai ya mutu Dan baqin ciki... Ya janyo wayarsa ta bude hotunan ta yana kallo tabbas yasan yana son iffaat babban abinda yake damunsa idan ya tuna WACE CE ITA.. Yar aikinsace fa wannan gani da yake mata har kullum shi yakesa baya darajata, amma yasan yanasonta babban dalilin da yasa ya qara aminta da auren Suhaila Dan sunyi kama da iffaat ne, hakadai yayita mulmula saman gado kamar an xuba lemu a paranti sai zagayawa yakeyi yana juyi wata zuciya tace idan ma Yar aikinkace ai matarkace yanxu yakamata ka bata haqqinta na matarka, ko ka sami sauqi, chaiiiiii. qarshe ya tafi akan iffaat bazata taba aikata hakanba amma xaiyi magana da driver dinta yaji gaskiyar magana,. Hmmmm nidai jabo Bantaba tunanin farhaan yana son iffaat hakaba ba sai yau Ashe shima ya kamu bamuda story, Haka gadon ya masa fadi yasaba da kwanciya tare da ita koda ba abinda sukeyi amma yana jin qamshin jikinta, yanajin dadi amma yau babu... Tunda qarfe 8 yaje daukota umma tace sai ya dawo office sannan yazo ya dauketa.. Yinin Ranar dai bai gane komaiba gashinan sai a hankali, har ya taso ya dawo office yazo umma tamusu fada musamman shi, sannan suka tafi, iffaat dai taji tsoro fa yanda ya mata ya firgitata ba kadanba, amma bata nuna masaba So ta yanke shawarar bazata qara kai motar ta gurinba...!! Iffat Kura ga tsoro ga ban tsoro.!! ****** Farhaan ma haka bai qara xuwa Zaria hotel ba. Bayan yayi bincike ya gano shirinta dariya kawai yayi, lallai wannan yarinya akwai rigima.. Yanxu ta saka masa ido sosai a latitude tana yawan ganin yana zuwa wani guri so abinda ta farayi shine ta sami mai adaidata sahu ta biyashi tace kawai ya bishi na kwana biyu yaga mi yakeyi a gurin ai kuwa an kawo mata labari wata yarinya yake dauka gurin tasa aka duba mata gidansu yarinyar da komai nata, ta riqa ta shirya abinda zata mata ta kiyaye lokacinda yake sauketa ya wuce. ta sami almajirai su biyar tace aiki zasu mata farhaan na sauketa ta riqa ta tare hanyar tasa yaran suka tareta har ta fara xaginsu iffaat taxo ta wanketa da mari tace wayannan almajiran sun fiki daraja Yar iska yarinyar.! mamaki ya cikata hakadai iffaat tace ta shiga wani kongon gida zasuyi aiki, ta turje sai tasa almajiran nan suka durata cikin kongon gidan taso tayi taurin kai sai taga batada mafita illa miqa wuya, bayan sun shiga iffaat ta zauna saman wani bulo tabata almakashi tace ta yanke gashin kanka ta fara gaddama iffaat ta qara waske banxa da mari saida bakinta ya fashe da jini ba shiri yarinyar ta karba ta aske iya yanda zata aiya iffaat tace bai mataba haka tasa reza ta mata tall kobo almajiran sai dariya suke nima jabo dai na dara cox mace ba gashi batayiba!! bayan ta mata gwandal tace saura Abu biyu kuma, matar ta fara kuka tana tataimaketa iffat tace ta rufawa kanta asiri ta bari suyi aikinsu idan ba hakaba zata qara mata wani punishment,mata kuwa sai kuka take tana roqon iffaat tayi haquri amma iffaat ko kallonta batayiba tasa almajiranta suka danne mata ita ta mata bille guda biyu a fuska sannan ta fito da bulalarta ta zaneta saida ita kanta ta gaji da dukan nata sannan ta barta tace idan an tambayeki wa ya miki haka kice iffaat ce ko kice Mrs PURHUUN..... ta fita tabarta nan tana kuka..... [9:38PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 74 Na Hauwa M.Jabo Yarinyar taji jiki matuqa sai kuka takeyi, babban baqin cikinta billen data mata cox gashi zai fito nan gaba amma bille bazai baceba har abada ta fara tunanin WACE CE ITA?? Mrs PURHUUN kuma?? waima da wane dalili ta mata haka?? Ta gaji ta rarrafa taje gidansu tana kuka..! Ran iffat yayi sanyi farhaan na dawowa ta kalleshi ta kwashe da dariya ya juyo ya kalleta yace lafiya? Ta wani daga ido alamar dawa kake? Yace hmmm yasan tabbas akwai abinda takema dariya, sai daibai bazai kulataba. Iffaat haka ta riqa bin farhaan a latitude saida tama yan matanshi shida aski hadda su ramcy ko ina hafsa take ohoo taso ta aske hafsa ta mata bille.... ******* Ranar sun fito lecture ta hadu da wata tsohuwar qawarta Aisha armiya'u mada. Sun Dan yi skull tare da ita tanason iffat sosai bayan sun gaisa take bata labarin tayi aure tanata tayata murna hardai tace zataje gidanta bayan lecture sunje gida akan hanya ta siya mata abinci Dan iffaat har yau bata iya girkiba hasalima bata taba girkiba saidai dafa tea, hatta kunna gas har yau bata iyaba.... Bayan sun qare chin abinci suna tadi saiga farhaan ya shigo, armiya'u ta gaidashi ya amsa iffat kam ko motsi tadai kalleshi kawai, bayan ya wuce ta kalleta tace iffaat wannan ne mijinki? Tace eh kinsan shine? Tace Eh nasanshi, iffaat aranta tace wallahi zan miki bille kuwa. Ina kika sanshi? No tunda dadewa sunyi soyayyah da wata cousin dina but Allah bai qaddari aurensuba, iffaat tace eyyah aure nufin Allah ne.! Eh hakane har an bar zancen amma iffaat sarkin kishi abin yana cinta. Chan tace ya sunan cousin din taki? Tace hafsa, amma sun rabu yanda tace min wai yasa house girl dinsa ta mata wulaqanci abin dai ba dadin ji wallahi... Nidai nace ko baka son mace ai ba haka ya dace kayi Dan ka rabu da itaba.... Ka gaya mata bazaka auretaba sai a zauna lafiya iffaat tayi murmushi wato abinda ta mata ya rabasu da farhaan lallai aikinta yayi kyau.. A munafunce tace Allah sarki kinsan mazan yanxu sai a hankali , tanason ta sami information a gurinta, Kuma ai farhaan ya damu da ita har ya bani labarinta, armiya'u najin an fadi haka sai ta saki jiki dama tana tsoron tayi siririn baha ya zamana batasan da zancen ba..... [9:45PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 75 Na Hauwa M.jabo Armiya'u tace Wallahi kuwa hafsa taso farhaan kamar rayuwarta ta bashi kanta sabida tana gannin kamar zai aureta, kai ai hafsa tayi jinyar rabuwa da farhaan, iffaat ta gyara zama tace ai yace min tanada jarumta sosai, armiya'u tace uhum Ashe dai kinsan komai kena,? nama daina jin tsoron fada, iffaat tace eh duk ya fadamin yace har matarsa ta farko tananan yana tare da ita yace har gida yake kawota.! armiya'u ta gyara zama za'ayi gulma ai iffaat in gaya miki yanda hafsa ta bani labari mijinki akwai tsananin buqata kuma yanason jarumta matuqa gurin harka, idan kika kiyaye haka wallahi zaki sameshi a hannu shiyasa ma hafsa ta daga tuta duk cikin yan matanshi yafi ji da ita, idan kika kiyaye sai yanda kikayi dashi.! Iffaat dai duk da qunan da zuciyanta keyi bai hanata saurareba, wai har wata tasan asirin mijinta Allah wadaran halin farhaan, Kinga mijin ki Dan gayu ne, so wallahi sai kin kasa kin tsare yanda yan mata sukayi yawa idan ma Allah ya tsareki bai miki kishiyaba to zai nemi mata a waje amma idan kika gyara kanki kin gama komai Dan maganin matannan kinasha kwalliya duk ki riqayi kissa da kisinsina ki zama first class gaki da gashi kiyi yanda kikasan mijinki zai ji dadi, Dan girkinnan duk ki xama kece kan gaba, wallahi nasan yan matan da suke son mijinki ba adadi kuma duk sun fiki girma da wayo, ko wacce tasan yanda zata sace zuciyar namiji so ki zama very careful iffaat kam ta sassauto da kishi tana sauraren jawabin qawarta Aysha armiya'u mada lallai ita tasan inda duniya ta Nufa kuma itace qawa ta gari.... Armiya'u tace ki duba yanxu ina kallo mijinki ya shigo baki gaisheshiba kuma ko ruwa baki kaimasaba bare abinci, iffaat tayi murmushi batace komai ba Armiya'u dai ta baiwa iffaat darasi kuma ya shigeta matsalar batasan yanda zata fara bane, bayan sunyi sallama ta tafi saiga farhaan ya fito a daki dama jiran tafiyarta yake yaxo yayi tsaye yana kallonta wannan yarinya akwai kwarjini sau da yawa idan ta masa Abu ya tunkareta sai ya kasa..yaga idan ma masifa zai mata aikin banxa zaiyi don ba jin masifar takeyiba so gara ya mata magana cikin ruwan sanyi.... Ya kira sunan ta tana kwance ta dago ta kalleshi, ki tashi zaune batace komaiba ta miqe zaune yace ki ijiye waya, zamuyi magana kafada inajinka kawai. Ya kira sunanta, Iffaat tace na'am ki ijiye waya, sai ya bata tausayi ta ijiye waya ta fuskanceshi dakyau yace iffaat abinda kikayi kina ganin kin kyauta? Ta xaro ido mi nayi kuma? Kin fini sani, aah Malam kada amin sharri ina zaune lafiya mi nayi?? mi kika yiwa yaran mutane? Ta bone kuwa wayanni yara kuma ?? Yace abokan aikina! Uhum yy kenan abokan aikinka kuma? Ya za'ayi nasan abokan aikinka? Iffaat wannan serious issue ne, miyasa kika aikata hakan?? Nifa yaya ban gane mi kake fadaba kamin dalla dalla kawai, yaga zagaye zagaye ba nashi bane yace yaran da kika yiwa aski da bille Kuma kika dakesu....!! [9:59PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??76 Na Hauwa M. Jabo Au kace min karuwanka koda yake suma abokan aikine tunda dasu ake iskancin no no no na manta wayewace, ko ba wayewa bace?! ranshi ya baci, sai ya share yaci gaba da magana kinsan kuwa kan haka wata har qara ta shigar kotu dagayar na rufe case dinnan,? iffaat tayi dariya hadda kwalla, wallahi da ka bari an tafi dani kawai kaga sai kaji dadin kawo su har cikin gida kamar yanda ka saba,! shiru yayi aransa yace wannan duk abinda aka fada tanada amsa, shikam gara kawai ya nemi shiri gunta koya sami sassauci dama laifin sane dabai nuna mata shi wayeba da yanxu rawar ta chanxa amma soon zata shigo hannu.. chan yace iffaat kinsan kuwa ina tsananin sonki? Kinsan tun yaushe nake fama da sonki cikin rayuwata? Please iffaat kidaina wahala min da zuciya... Wani sanyi taji a ranta inaga tinda tazo duniya bata taba jin kalma mai dadi kamar wannan ba, amma bata nunaba Sam, iffaat ki tausayawa rayuwa wallahi wasu abubuwan duk rashin ki yake sa ina aikatasu...¡! Ta kalleshi ta watsa mai harara Malam Dan kawai yan matanka sun gudu shine zaka lallabo gurina ka min wayo ko? To kayi letti bazakasamu hakanba, No iffaat ni ba sai na sami komai a wajenkiba just kawai ki amince dani maisonkine, mudaina rigima nagaji. wallahi ina axabtuwa da rashinki, guntun tsaki taja, ta koma ta kwanta ta dauki wayanta ta danna recoding duk abinda yake fada tana dauka har ya qare batace dashi komaiba, ya qare yazo kusa da ita tayi sauri ta kashe ya dafa kafadarta ta watsomai ido miye haka wai? Ta bani dariya miji ya taba mata tana miye haka!? Yace ba komai yakai hannunsa akan gashinta ya shafa yace kizo na gyara miki gashin ki! Kallonsa kawai tayi yanda ya chanza ya bata tsoro ta yinqura zata tashi ya danneta ta koma kwance ta kalleshi wai mi kakesone Malam? Ya kawo bakinsa daidai da kunnenta ya mata rada saida tsikar jikinta ta tashi yace ke nakeso iffaat, tace Banganeba! ina nufi matata nakeso! Tofa yau akeyinta gata kwance duk ya dabai bayeta, yana zauna qasa hmmm kawai tace bata ce komaiba tana jinsa yana Dan mata wai waye a qirji alamar yanason ya aika hannunsa ciki, Yya farhaan ina zuwa bari nayi fitsari. Ya gane guduwa takeson tayi sai yace muje na rakaki,! Burinta dai ta tashi zaune ya daga mata ta tashi zaune muje mana. Ta harareshi nama fasa xuwa. Murmushi yayi yace idan kina tsiwa kinfi kyau.! aransa yace sai kin shigo hannunna yarinya ya miqe ya shiga daki, Iffaat kam dadine yake Neman ya hallakata dama Ashe yanasonta? Da tasani ta tambayeshi tun yaushe yakesonta tayi murmushi ta shafa gashinta, ta tuna shine mutum na farko daya fara gyara mata gashinta! Ta qara murmusawa ta tashi tayi sallah... Goben ranar farhaan ya ya fitowa office wata budurwarsa ta kirashi tace su hadu wani guri kamar bazai jeba sai kawai ya wuce gurin iffaat kuma tana sukul bayan ta fito lecture sai ta duba latitude dinta taga farhan yananan kusa da skull dinsu, har ta qara shiga lecture ta fito bai motsa daga gunba tayi refreshing still yana gun tayi zooming sosai taga gurin a qafa ta tattaka koda taje ta qara refreshing taga itama tana gurin nisansu Kadan ne, koda ta daga kai sai ga motarsa da wata mota,! Tayi tsaye ta rasa yanda zatayi, ta duba ba kowa a gurin, sai mai gadi, tanuna ma mai gadin gurin hotonsa tace yaga wannan yace eh yana ciki.! tayi shiru ya zata shiga gurin aka nuna mata dakin tana kallon dakin amma ta kasa qarasawa sai ta fito Dan tasan baqin ciki kawai zata gani idan ma taje din tana hanyar dawowa sai taga police station tayi murmushi wallahi yau farhaan sai ka kwana a Gidan yayan sanda direct gurin su taje........ Muje zuwaa [10:07PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 77 Na Hauwa M. Jabo Ta je gurin yansanda ta sami babban su tace tanason yan sanda hudu ya tambayeta dalili batasan abinda xataceba tace wanine yake bata mata qanwa kuma ta rabasu sunqi rabuwa shine takeson akama- matasu duka biyu taga kamar baxasu bataba tana dubawa sai taga gun cirar kudi anyi Sa'a ATM yana cikin jaka ta chiro kudi tazo ta miqewa Dan sandan jiki na rawa ya karba ya bata kwalawa hudu tace kuma kada abada belinsu karma a bari suyi magana taje tanuna musu gun tayi sauri ta dawo skull, policawa kuwa sun cika aikinsu suka kama farhaan da budurwarsa dama iffaat tace kada a sakeshi kuma kada a sauraresu dukansu sai taxo gobe zata karbesu kuma kada a bari yayi magana da kowa!! farhaan kam Dan baqin ciki har kuka yakeyi mi yake faruwa dashine tunda yake ba'ataba kamasahiba sai yau an wulaqantashi ba kadanba.. tsanar bariki ta shige mai zuciya yayi nadama, yayi yayi abari yayi magana amma ina sunqi kulashi tunanin sa daya iffaat yanda zata kwana ita kadai..! Uhum, itakam hankalinta kwance tanajin dadi koba komai tamai rashin kunya da safe ta chaba ado na gani na fada ta saka kayanda ita kanta tasan tayi da saka glss dinta ta wuce skull bayan ta fito lecture taje gurin yansanda, tace yazo beline, aka fito da farhaan da matar tace a maida matar sai an qare case din farhaan aka maida matar wata jaka da ita sai jalkuna, yana ganinta ya rude ya ma rasa abinda zai fada kamar gaske tace ma yansanda Dan Allah a bata belin sa mijintane bazai sakeba ayi haquri.!! ya kalleta cike da mamaki iffaat waya gaya miki inanan? haka kawai ya samu damar ce mata..! tace naji a jikina kaje abinda ka saba an kamaka.! Ta kalleshi but so happy wallahi Allah ya qara maganin irinku kenan masu bata yayan mutane.. Sosa kai yayi, police din yace kai kanada wannan baby mixakayi da waccan ashawon kalleta haddadiya da ita kunya ta rufe shi da haushin dansanda ina ruwanshi da matarsa.. ta cika takardu aka saki farhaan sun fito ita dashi ta kalleshi ta nunashi da hannu, kalleka Dan Allah namiji har namiji amma ba halin kirki.! Tir da hali irin naka, idonta suka ciko da kwalla amma da yake ta saka glass sai baxai ganiba nayi nadamar kasan cewa tare dakai a matsayin matarka. Kullum cikin tunanin kana ina mi kakeyi!!? kallonta yake tamai kyau iffaat baby ce shima yasani kullum qara cika takeyi tana wani fresh murmushi yayi ya janyota jikinsa ya rungume yana bata haquri, tayi tayi ta kwace kanta amma ta kasa sai ta barwa Allah....... Dagyar Tasamu ya saketa hawaye ta gani a idonsa tausayi ya bata, ta bude mai mota ya shiga itama ta shiga taja suka tafi,mamaki yake ya akayi ta iya mota? Waya koya mata? waima waya gaya mata yana gurin baiso ta saniba Sam har suka Isa gida bata kalleshi ba tana tauna chewing gum a hankali suna Isa gida kuma sai yaga motarsa...... [10:14PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 78 Na Hauwa M. Jabo Ya kalleta chike da mamaki yaga batama kula da mamakinsaba sai shima ya basar.! sun shiga gida ta kawo mai abinci abinda bai taba samuba tunda ya aureta yasan ba ita ta girkaba amma duk da haka yaji dadi ya zauna yaci yana chi tace, nasan police station ba abincin kirki shi yasa na kawo maka wannam, lokaci daya har ya hargitse, tayi dariyarta ta mugunta ya dago ya kalleta tace kaima ka dandana kwana Gidan yan sanda ko? Ta qara yin dariya tace dadi ko?? Baice mata komaiba ina tambaya.! ya kalleta wai ya akayi kikasan ina chan ? Tayi murmushin mugunta tace sabida ni na saka a kamaka..! Ya zare ido Kamar ya? Tace Kamar haka.! Please kimin bayani ya akayi kikasan ina gurin? Wallahi Nina tura a kamamin kai, kuma yanxu na fara duk lokacinda na ganka da wata mace wallahi saina kulleka. Mamaki yakeyi dukda cewa yasan iffaat fiye da hakama zata iyayi amma ta bashi mamaki, miyasa duk motsinsa akan idonta,? Ya akayi kikasan gunda nake zuwa? Tace sabida ina iffaat, baice komaiba aransa yace Ko ta saka a riqa bibiyarshine? Kallonta kawai yayi Dan gaskiya tamai yawa,!! yana zaune wayanshi tayi qara ya daga abbanshine ya gaisheshi anan abba yake gayamai zai aikeshi Thailand, kuma ya tafi da matarsa, bayan ya qare waya ya mata bayani ido bude tace baxataba karatunta zai sami matsala kuma tafiya har wata biyu ko uku, yaso ya tafi da ita wataqila ma achan su shirya amma taqi. Farhaan yama Abba bayanin abinda ta masa bayani Abba yace ba komai... Tunda tun cikin Daren yabar gida yaje Kaduna yana shirye shiryen tafiya, mai sami kansaba har ya tafi, Farhaan dai an tafi Thailand yabar iffaat ita kadai a gida an kawo mata wacce zata tayata zama kamin mijinta ya dawo... Tunda matar maman nargees tazo ta kula iffaat abincin take siyo musu, tanason tayi magana amma dai tana tsorooo ace tayi shishigi..... [10:19PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 79 NA Hauwa M.Jabo Kusan sati daya da tafiyar farhaan amma still siyo abinci take ta kula iffaat akwai saurin sabo kuma batada matsala amma kuma batason shishigi, ranar suna zaune sai matar tace yau nayi mafarkin Dan wanke, iffaat tace Allah ko! Ki bari anjima idan na fita sai na siyo miki, matar tace aah gara dai mu girka kayan mu ko mi kika gani, iffaat tace gaskiya ban iyaba, sai na koya miki ko bakyaso tace tanaso, anan iffaat tabata labarin cewa tunda take bata taba girkiba, matar nata mamaki ace mace bata iya girkiba, haka dai matar ta dage ta koyama iffaat girki kunna gas yanda akeyin komai tace akwai books na girki ta siya, tace mata, wallahi girki shine mace duk kyanki da yanga idan baki iya girkiba baki cikaba bakida daraja a gurin miji, matar dai ta kula iffaat gayun banxane bata iya komaiba, a labari iffaat take fadamata cewa ai idan taga mijinta yana magana da wata ubanta takeci ta mata aski da bille matar tayi dariya sosai wai bille, tace to aike iffatu ba haka akeyiba baki kyautatawa miinkiba ya za'ayi yaqi Neman mata, kina gani maxan yanxu ko kin kyauta tasu ya kuke qarewa bare baka kyautata musu, wallahi kiyi hankali ki San ciwon kanki ki fara dafe mijinki sosai sannan idan kin Ganshi da wata sai kisan abinda zaki mata, amma haka kawai baxaki hanashi abinda yakesoba ke baki biya mai buqatansaba ki hanashi ya nema!! Ai in gaya miki kina zaune saidai kiga kishiya, ta dafe qirji kishiya!!? Sosai kuwa kishiya, Allah ya rabani da kishiya, Yan zu maman Nargees ya zanyi,? Ya zakiyi kuwa illa ki koyi girki ki iya kwalliya koda naga kwalliya ke ajin farkoce ki iya shagawaba idan yana gida ki manne masa duk motsinsa akan idonki, iffaat ta kwashe da dariya.! Miye abin dariya? Tace ba komai, haka dai tayita gaya ma iffat abubuwan ta bata sirrikun mallakar miji wani abin iffaat tayita dariya tana mamaki, bayan ta tashi taje ta kwanta a nan ta fara tunanin maganganun da ake fada mata gaskiyane dole ta fara saba masa da kanta sannan taje chin uban na waje.... [10:30PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..??80 Na Hauwa M. Jabo To amma ai ba laifinta bane? Shine bai nemetaba! Wata zuciyar tace yaga fuska bare ya nemeki? Aike ya dace ki kwatanta kiga yanda zai dawo hannunki, wata zuciyar tace kawai ya rainakine yana jiran kikai kanki ya qare dake,! Tayi tsaki. Miye mafita idan bata mantaba Aysha armiya'u mada ma haka tace mata farahnax ma da taxo haka tace mata a skull ma idan suna tadi zancen kenan daya kyautatawa miji, ga lada ga la'ada. Tayi murmushi ta janyo wayarta ta dauko hoton farhaan tana kallo tana zooming batasan lokacinda tayi kissing din bakinsaba tayi jimm gatada miji har miji amma manemin mata! Lallai ta bala'e bazata wani gyarashiba ya kamata ta dandana masa Zumar ta sannan ta kasa ta tsare idan ta kama ta raka anan ne idan yaqi dainawa taci gaba da chin ubansu.. 100% ta aminta da haka so tana jiran dawowar farhaan ne taga yanda zata fara, kunya takeji anya zata iya? Taya zata fara!? da shedana da wasa zata cusa kanta, har komai ya daidaita, ta lashe lebenta tayi murmushi ta rungume pillow Allah ya shirya min kai Yy farhaan.. Haka dai madam iffaat tayita tunani har bacci ya dauke ta,... ************* suna waya akai akai amma dai ba wani chanxi data nuna mai, shikam hadda cemata yake yayi missing dinta takanso tace bawani Dan tasan yana tare da yan matansa amma kuma sai ta share... kwanci tashi har farhaan yayi wata daya a qasar iffaat kuwa lokacin ta gama iya girki nikaina jabo idan tayi girki badan kada aga kwadayinaba wallahi dasai naci, amma ba hali, girkinta haka yake qamshi kamar me maman nargess hatta yanda ake tafiya gaban oga saida ta koya mata da yanda ake shagwaba a narke jikin miji duk ta koya mata cox practice sukeyi maman Nargees ce iffaat iffaat ce farhaan sai tace ta fita waje tana shigowa maman Nargees taje ta rungume ta tana mata wani Abu iffaat Dan dariya har hawaye takeyi, anya zata iya yin haka kuwa?? Maman Nargees kuwa sai qarfafata takeyi, har dai taji zata iya, ga iffaat gwana gashi dama ba auki zatayi dadin kakkarya jiki.... Daidai wannan lokacin farahnax ta haihu ta sullubo yarta kyakyawa kamarsu daya da farhaan idan kaga Yar kace ta farhaan ce Dan kamar har ta baci da iffaat ta tura mai hoton baby ya gani yace da babyn Suhaila ta rayu da itama yasan kamar shi zata dauko iffaat dai batace dashi komaiba, yace amma insha Allah ina dawowa zan samo wata zaki tayani nemowa, tayi kamar bata gane mi yake nufiba, tace eh mana duk inda ake siyowa kaima ka siyo yayi murmushi ya basar Da maganar.... [10:33PM, 5/13/2015] .: WACE CE ITA..?? 81 Na Hauwa M. Jabo Anyi suna lafiya ansha shagali taga yanda ake soyayyah gurin farahnax ranarda mijinta yaxo tana wani mai shagaba tana narkewa abin dariya yake bata, kuma gaban kowa zata mai haka saidai a bata guri badai ita ta basu guriba abinsu yana burgeta, farahnax takance niko sister iffo zanso naga ranarda zaki daina halin ki, takanyi murmushi baatace mata komai. duk abinda sukeyi tana recoding a kanta kuma shima yana shiga cikin list dinta zata ma farhaan dinta fiye da wannan idan ya dawo... Duk kudinda abba yake xuba mata da wayanda farhaan yabar mata taje ta siyo arnar nyte dasu ta siyo English wr masu zafi ita kanta tasan dole ya girgixa idan ya gansu gashi yana sonta dole kuwa yayi sha'awarta.. Nidai sai kallo nake wai iffaat ce take tanadin kayan da za'a sakawa miji, batada matsala gurin kwalliya ta iya kayanta tana biye da group chat duk abinda akace yana saka ni'ima saitaci tasha, duk wannan tanadin na PURHUUN dinta ne, Ranar tana zaune a Palo ta qare gyara gunba yatsunta sunyi kyau abinta, tayi zaune tsakayar daki saman center carpet tana kallo taji tsayuwar mota ta dauka maman Nargees ce Dan taje siyyah kasuwa kuma kayan sunada yawa da zata siyo, ko motsi batayiba taci gaba da kallonta daga bayan ta taji mutum ya Dora wuyansa akan kafadarta ta wani zabura da qarfi amma qamshinsa ya bayyana mata wayeshi! farhaan ne batasan lokacin da maqalqaleshiba tana dariya yayi surprised dinta ba kadanba mutumin da akace zaiyi wata biyu koma fiye amma yau kwana 48 ya dawo, farhaan kam murna yakeyi yauga iffaat dinsa a jikinsa kuma da ra'ayin kanta, ta sakeshi ta riqe kunkumi tana dariya tace, wai Kaine naka gani ko kuwa mafarki nakeji, yace sosai nine farhaan na dawo na gaji da rashinki kusa dani koda kuwa kasheni zakiyi gara ina ganinki tayi dariya na Isa na kashe yayan farahnax, yayi dariya dhima ya janyota jikinsa uhum su farhaan an sami yanda akeso.... [11:34PM, 5/14/2015] .: WACE CE ITA..??82 Na Hauwa M Jabo. Ya jata kujera Suka zauna tace Bantaba tunanin zaka dawo yanxuba shine ko waya kaqi gaya min ai da sai ko girkine a maka, mamakine ya cikashi shikam gara da yayi tafiyar nan tayi missing dinsa, hadda su girki,! ana wani mai murmushi shida idan yaga dariyar ta to tabbas tamai mugunta ne take dariya....!! . mai gadi ya fara shigowa da kaya niqi niqi yana ijiye wa gefen qofa, ya rungumota sosai jikinsa, Abu daya ta manta bata tambaya ba idan miji ya dawo sai yasha ruwa sannan zaiyi wanka yaci abin ci ko kuma sai yayi wanka sannan yaci abinci, ta rasa yanda zatayi kamar taje kitchen ta ma maman Nargees waya ta tambayeta sai tace bari kawai ta masa yanda ta iya, ruwa ta kawo masa da drink ta zuba masa yace hannunsa ya gaji saidai ta bashi a baki, dariya tayi ni ban Iya baiwa ko yara abinciba bare manya, yace ai nima yarone a gurin ki ko bakyaso,? murmushi tayi aranta tace shima yaxo da nasa kwandon iskanci, tace inaso mana,! Yace to ki baiwa babyn ki ruwa ta kuwa taso ta tsuguna gabansa ta bashi ya kwankwade yace a qaro ta qara mai ya kwankwade yace a qaro tace aah ya Isa,yayi murmushi idan dai ke zaki bani xan tasha har sai na shanye duka,murmushi kawai tayi batace komaiba, tace muje kayi wanka, yace iyeeeee duk ni kadai gaskiya dole duk sati na riqa yin tafiya tunda idan na dawo gata ake min, ta waigo ta Dan qaramai harara ta murguda baki, saida ya tuna da ita a yanda take da tamai gata gwanar murguda baki,tuni yayi tsitt kamar ruwa ya cishi, suka shiga bayin zata fito yace kixo muyi wankan tare mana tace ni nayi daxu kai kayi yace to kixo ki wankemin bayana hannuna baya kaiwa, kallon sa kawai tayi ta wuce abinta duk shekarunda kayi kana wanka wa yake wanke maka bayanka! Shikam murna da dadi ya ma rasa abinda zaiyi dan murna, iffaat ta rasa mi zatayi girki zata masa ko kwalliya zata tsaya tayi, sai kawai ta Yanke shawarar girki, ta shiga ta duba duk wani abinci idan tace tayi shi zata bata lokaci sai kawai tayi sauri ta hadamai danbunb cos cos da busashen kifi yaji ganye, duk Wanda Yaji qamshin girkin to zaisan cewa abincin ma zaiyi dadi dambun cos cos dan taga yafi sauri dama farhaan idan ya shiga wanka sai mutum ya manta da cewa ya shiga, taxo gaban madubi ta Dan goga powder ta gyara fuskar batayi kwalliya ba kada ya rainata da xuwa yaga ta fara shafe shafe, taje ta Dora mai abincin akan table ta dauko mai wasu kaya da taga idan yana gida yake sakawa..... Muje zuwa muji shin kulawar iffaat zata sa farhaan ya chanxa ko kuwa halinsa dai!! Idan bai chanxaba wane mataki anti iffaat zata daika,? Ya soyayyah zata guda tsakaninsu!? KU BIYO YAR MUTAN JABO KUSHA LABARI.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??83 Na Hauwa M. Jabo Yana fitowa wanka ya saka tufafin data ijiye masa ya feshe jikinsa da turare yadauki waya ya kira abba ya gaya masa ya iso anjima zaizo ya kawo mai report din komai, Abba yace ya bari sai gobe idan ya qara hutuwa,ya kira mama da umma da hajiya kulu duk ya gaishesu ya gaya musu ya iso, iffaat ce ta shigo tace Au har ka fito? Ya kanne ido yana Neman janyota jikinsa yace nayi missing dinkine Dan shiga bayin da nayi shi yasa nayi saurin fitowa, bata bari ya kamataba ta zille, tayi murmushi, tace sai tsara zance, nidai muje kaci abin ci tana gaba yana Binta baya sun Isa Palo ta zasu fara chin abinci farhaan yasa rigima shi dole sai ta bashi a baki idan ba hakaba bazaiciba, aranta tace anya xan juri Wannan shiriritar kuwa? Mutum da girmansa yana Wannan Abu, yaji shirun yayi yawa yace bari naje na kwanta, ta kalleshi da dara daran idonta abincin fa? Ba kinqi bani abakiba, yanda yayi ya bala'en burgeta kuma sai taji wani sonsa ya ninku a zuciyanta Allah ya shirya min kai mijina!, tace to bari na baka ya kuwa gyara zama tafara bashi duk taje saka mai loma sai rabi ya shiga rabi ya xube hakadai taga chi da chokali shirititane ta ijiye tafara bashi da hannu nan ma da gangan ya riqa chijeta wai ya dauka kifine, suna tsaka da wannan drama saiga maman Nargees ta dawo, ta wangale baki taji dadi ba kadanba, ga dawowar farhaan ga kuma abinda tagani wai iffaat tana baiwa farhaan abinci a baki, hmmm. Ta gaidashi, iffaat nason ta daina bashi shi kuwa sai haaaaa yake mata baki yake irin na yara, haka dai ta bashi sama sama. sun gaisa yake mata godiyar xaman da tayi da iffaat tace ba komai yiwa Kaine. Ta wuce kitchen ta jera kayan data siyo ta wanke kayan da iffaat tayi aiki dasu tsab sannan ta fito koda ta fito sun tashi gurin duk yayi abinci tayi murmushi tace sai kace an baiwa jinjiri abinci, ta share tsab, ta gyare.! Iffaat bayan sun qare chin abinci farhaan yasa wata rigimar wai wallahi bayan sa kamar ya bude Dan gajiya, taxo ta masa tausa, tace bakyau ana qare chin abinci a kwanta Dolensa yayita zagayawa a daki har yaji ya gaji kuma ya hanata tafiya bayan ya qare ya kwanta bacci.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA.. ??84 Na Hauwa M.Jabo Bayan ya kwantane Ya nace saita mai tausa gata bata iya tausaba haka dai tayi ta dannawa tun yana wash wash har dai baccin gaskiya ya kwashe shi, tana tabbatar da yayi bacci ta janyo bargo ta lullubeshi, ta zauna akan madubi tana kallonsa, tana tunani, Dama ana cewa namiji daidai yake da jinjiri idan kana mai abinda yakeso to ka gama dashi, saidai ita kam nata mijin mayen mutane Allah dai ya shirya matashi hakadai tayi ta tunani... chan ta tuna da maman Nargees tayi sauri taje Palo koda taje ta hada kayanta bayan ta gyara palon, iffaat ta kalleta Dan Allah kiyi haquri wallahi na manta kin dawo! Ya naga kin hada kaya ina xuwa?? Zani gida mana aikina ya qare gashi tun ba'aje ko inaba har an fara mantawa dani, iffaat tayi dariya tace wallahi ba komai mukeyibafa ! nace wani Abu kukeyi? Naji dadi sosai wallahi nan dai maman Nargees ta qara bata wasu shawarwari sannan tace duk da haka ta riqa ja masa aji ba komai bane jiki na rawa zata masaba, tayi dariya taso ta bari farhaan ya tashi ya sauketa amma tace ya gaji kuma ta hanata itama ta kaita wai idan ya tashi bata ba zaiji dadiba, uhummm maman Nargees dai ta gyara aure sosai ta tafi... Bayan maman Nargees ta tafi iffaat kayan da aka shigo daso ta musu muhalli bata budeba Dan tasan bata aikesaba!! Ta gaji Dan aikinda tayi ta zauna tanata tunanin yanda xuwan farhaan ya chanza ta tayi murmushi tasan dai har yanxu bazata iya bari suyi wani abubua Dan tsabar kishi irin nata, bari tayi wanka har zata shiga bayi sai tace bare taje S.P ta dauko Yar figaggiyar rigar wankanta ta saka taje ta fara wanka,. Ashe farhaan ya tashi yana kallonta ta window yana murmushi yanda take wasa da ruwa kamar kifi, Yaji bari yaxo shima ayi dashi tana cikin ruwan kawai jin tayi mutum ya fado ciki da yake tafi shi iyawa shi farkon ruwan yake tsayawa ita ko har gurin xurfin take tafiya.. [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 85 Na Hauwa M. Jabo. Tana ganin yazo kusa da ita kunya ta kamata Dan kayan sai a hankali komai na jikinta suna nunawa gasu irin masu hade da wandone, yayi qoqarin kamata amma yana xuwa kusa da ita ta gudu ya kuwa biyota sai ji yayi kamar ana jansa tuni ya nemi nutsewa a ruwan tana mai dariya sai taga da gaske yakeyi yanda yake dukan ruwa, ba shiri tama manta da wani kayan jikinta da boyon da takeyi kada ya ganta tayi sauri ta rungume shi ta janyoshi bakin ruwa farhaan duk ruwan dayasha bai hanashi jin laushin fatar jikinta ba jikinsu ya hadu sun kawo bakin ruwa amma farhaan da iskanci yayi lamo a jikinta yaji fresh fata ba irin ta gardawan yan matansa ba, ta kalleshi ta jijjigashi ya bude ido a hankali tace mai sannu ko? Ya harareta ya murguda baki yanda yake murguda baki ya bata dariya ta kuwa dara, yace dariya ma kike min ko bayan kin wahaladda ni, tace to ai Kaine kasan baka iyaba ka biyoni, ya qara narkewa a jikinta to yanxu ka fita waje kamin nazo yace ba inda zaije saima ta koya masa yanda takeyi, tayi tayi amma ya nace ba inda zaije sai ta koyamai yanda ya maqalqaleta ne ba yafi damunta tace to sakeni sai muje! Yace wayo zaki min ki gudu tace zan koya maka amma ba yanxuba yace shiko idan har bazata koya mai yanxu baisaidai su kwana chikin ruwa, Tace to, ya maqalqaleta har suka kai gurin sannan ya saketa, ta fara nuna mai farhaan kam kallonta yakeyi ba kallon abinda take koya masaba.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 86 Na Hauwa M. Jabo. Data gane kallonta yake tace a bari sai gobe yace ai bai gwada ya ganiba ko ya iyaba, ta riqoshi tana nuna mai ya bata wahala ba kadanba amma fa shima yasha ruwa.... Hmmm , soyayyah cikin ruwa dadi wallahi, tana Neman fita ya kamo gashinta saida tayi qara tana waigowa ta zabgamai cizo shima saida yayi qara tace ka tsani gashinnan nawa kodan ina aske na yan matankane kakejin haushin nawa.!? ya tun karo ta da qarfi tuni tayi wani super a ruwa ta gudu yasan idan ma ya bita wasu ruwan zaisha sai ya gyaleta, ko banxa tayi tsokana bare ta sami abin fada, yana kallon ta ta fita ruwan ya qurawa halittarta ido iffaat akwai chinya, ga uban hips dinnan ta take juyashi kamar me yayi murmushi ya lashe lebe aransa yace Allah yayita bani sa'arki, har ta wuce ta juyo taga yana kallonta tasan dama zai kalla yanda ta saka wannan kayan haka tamai bye tayi sauri ta wuce ya Dade a ruwa yana tunani sannan ya fito ya shiga gida koda yaje ta shiga kitchen daura abinchin dare, yaje ya saka tufafi ya biyo ta kitchen ya rungumeta ta baya, yayi kissing din wuyanta. Tace Dan Allah kaje ka kalli ball dinka gashichan an fara. Yace au korana ma kikeyi ko?? Ta baxan tafiba, tace yi haquri mana, yace kibar girkin anjima sai mu fita muci tace itakam ba inda zata chin abinci. Haka yayita damunta kuma ya qi sakinta, saida yaga ta daure fuska ya kama kanshi, ya dan samu tana sake mai idan ta daure mai ai ya shiga uku yace tayi sauri ta qare yana jiran ta, Ayanda iffaat takeda saurin aiki yana burgeni cikin lokaci kadan zatayi aiki ta qare dama tasan farhaan akwai chin amala kamar Dan yarbawa cox lokacin da tana mai aiki kusan kullum sai anmai amala, ita kuma lokacin komai aka bata chi take dukda bata gane abincin amma haka take chinyiewa, to itama amala ta hada mai da miyan agusi yaji kayan ciki yana qamshin attarugu da carry ta hada mai fruit salad ta kawo ta ijiye... Uhummm su farhaan fa za'a fara dandana dadin aure... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??87 Na Hauwa M. Jabo. Bayan ta qare girki ta ta fito yanata mata sannu murmushi kawai tayi, ta shiga bayi ta watsa ruwa tayo alwula sannan ta fito shima yayi alwula ya tafi masallaci ta zauna saida ta qare kwalliyarta tsab sannan tayi sallah, nima ta burgeni Allah ya qaro min yawan gashi nasamu na kuri irin iffaat... Ta fito tsab da ita taje Palo farhaan ya dawo kenan ya ware hannu irin taje dinnan ta murguda masa baki abin ya bashi dariya ita iffaat komai sai ta murguda baki... Akaxo chin abinci nanma yace baxai iyaciba itama tace bazata iya Chiba tofa sai Yaya wai sai dai ya bata ta bashi haka sukayi kuwa wannan karon bata batamai tufafi sosai ba, Dan tana kallon yanda yake bata sai itama tana yin hakanan suna chi yana bata labarin Thailand har suka kammala suka tashi suka Dan zaga palon Dan abincin ya fada musu, bayan sun qare iffaat ta zauna farhaan yaje ya bude kayan da ya siyo abinda yafi bata dariya hadda kayan baby kuma bana babyn farahnax bane wai na babyn da zasu haifane nan da wata Tara a yanda yace murmushi kawai tayi ta tattara kayan ta saka a wardrobe ta dawo ta zauna, yayi miqa kixo muje ki kwanta mana, ta yatsina fuska kaje kawai zanzo, habadai kizo muje kin gaji, tayi fari da ido kaje mana idan naji bacci zanxo, ya dawo ya zauna ni bazan kwanta idan bakiba... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 88 Na Hauwa M. Jabo. Okay.! zauna muyi kallo ya zauna suna kallo har guraren 1 na dare iffaat idonta gyam akan TV ko motsi yanayi yana satar kallonta amma batada niyyar tashi, ya fara gyangyadi, ya karbi remote ya kashe dole sai sunje sun kwanta, iffaat kuwa ta fuske tace yaje xatazo yaga dai batada niyyar tashi sai ya wuce yace yana jirinta tace mai OK, iffaat dai anan ta gyangyade sai bacci da asuba farhaan ne yaxo ya tayar da ita bacci yana Dan shashafata har ta bude ido tamai murmushi ta tashi taje tayi alwula tayi sallah ta dawo Palo zata kwanta farhaan yasha gabanta yace idan dai dannine ki kwantar da hankalin ba abinda xan miki murmushi kawai tayi ta rabashi ta wuce, taje taci gaba da baccin ta qarfe 9 ta tashi ta hada mai breakfast ta shirya a D table ta dawo tayi kwanciyarta sai goma ta tashi da yake ba lecture ta Dan dima abincin a taje taganshi yana sharar bacci wanka ta shiga ta fito ta dandasa kwalliya ta saka wasu arnan kaya cikin kayan da tasiyo ita kanta tasan tayi ta fesa turare taxo kusa dashi ta shafa kumatunsa a hankali ya bude ido ya kalleta tamai murmushi ya janyo ta jikinsa sosai yayi kissing dinta a kumatu, tadan goce ka tashi muje kayi wanka, yayi miqa hadi da salatin annabi ya miqe yaje wanka bayan ya fito tazo tayashi goge jiki da shafa mai, daxai chanxa kaya sai ta miqe xata fita ya janyo ta ina xakije,? ta Sosa kai xan dauko abune a Palo yayi murmushi aranshi yace mata da mijinta amma tana guduwa. Ya saketa bata dawo ba saida ta tabbatar da ya saka kayan sannan ta shigo..... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 89 Na Hauwa M.Jabo Ta kalleshi ta riqe kunkumi iyeee kaganka kuwa.!? Kayi kyau kamar sabon ango, ya kalleta ya kanne ido yace ai angonne ko kinmanta har yau baisha maiba,! Ta gane mi yake nufi sai ta basar da zancen muje kayi breakfast kaje ka gaida su Abba da umma, yace to my princess, sun zauna ta kawo breakfast nan ma yasa rigima har yanxu bai warwareba sai ta bashi a baki, haka ta riq biye mai tana bashi yana chi idan ya cijeta tace sai ta rama haka zata samu wani guri shima ta chije shi har suka kammala, ta rakashi har mota ta dawo ta tattara kayan gudu gudu cox tanada lecture 12 gashi 11:30 ya wuce ta qare ta wuce skull. ********* Zaman iffaat da farhaan dai xan iya cewa lafiya lau duk wani kula dashi tanayi ba abinda za' nuna mata tun daga kwalliya har girki da tattalin miji saidai har yau taqi bada hadin kai farhaan yayi yayi amma taqi.. Ranar dai ya tirketa tana baccin rana a daki yaxo ya dabai bayeta ya fara yan shafe shafensa chan ta farka ta bude ido ta kalleshi tace miye haka?? Yace mata sunnace haka, tace sunna kuma? Yace eh bakisan annabi yace duk Wanda ya aikata Wannan sunnatawaba daidai yake da Wanda yayi jihadi ya kashe arna dububa. Ta kalleshi ta kyalkyale da dariya har saida tayi kwalla, sannan tace Yy farhaan watana hudu gidannan watanka uku muna kwana daki daya gado daya bargo daya bakasan da a kashe arna ba sai yanxu farhaan kam ya fara nisa ba wani jinta yakeba tuni tasa qarfi ta tureshi gefe ta miqe zaune ta kalleshi rai a bace wallahi kada ka qara kuskura kace zaka kusanceni! Ya kalleta ido sun wani Kada haba iffaat mi yasa kike min hakane? So kike na koma abin farko da nakeyi? Wannan kuma ya rage naka ko yanxu waya sani ko ana lallabawa dubunka ce bata cikaba na kamaku, ko kuma anji tsoron cell shiyasa ake kama kai amma dai badan iffaat ba kuma ba Dan tsoron Allah ba.!. Ta wuce Palo ya zauna saman gado yayi tsaki wannan yarinya mayaudariyace wallahi, ta koramin yan mata kuma ta hanani kanta kuma gata kamar aljana duk abinda nakeyi tana gani, yayi tsaki yadan kwanta akan gadon qafafunsa suna qasa ya dafe kai miye abinyi?? Da gaskiyar ta Dan tsoron cell naqi Neman matana amma yakamata na bari Dan Allah badan kowaba. Yayi ajiyar numfashi... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 90 Na Hauwa M.Jabo Ya biyo ta Palo tana sauraren waqarda kusan kullum saita saurareta koda waqar hausa bata burgeshi amma har ya haddace wannan wai kuma baiti dayane yakejin tana maimaitawa kullum shine na badi ba rai soyayyah jigon rayuwa ana cewa " itadai soyayyah maiyi bai samun sauqi, a jini take yawo wasu gunsu tana hanin aiki, na shiga cikinta ta xafar tamkar doki, na shaida sone mahadi gun rayuwa"ya kalleta yayi murmushi iffaat sarkin rigima normal xatamai duk abinda yakeso amma da xaran ya buqaceta sai taqi, ya zauna kusa ida ya daura kanshi akan chinyoyinta yana wasa da jelar gashinta, yace yakamata amin tafsirin wannan baitin waqar kullum shine a bakinki tun kina qarama nakejin kina yinsa, tace kace dai tun ina Yar aikinka nakeyinsa, tayi murmushi, nidai jabo da zasu ce na musu tafseer din wannan baitocin waqar da zanyi page 100 dashi amma basu bani damaba, iffaat ya kira sunanta ta kalleshi mi yasa kike guduna? Tace gudu kuma? Yace eh mana, tayi murmushi tace Sabida lokacin auren mu ba'ayi su dinner, su party su lunching ba wani Abu da akayi kaga kuwa kamar ba'ayi aurenbane ya miqe zaune yanxu kinason ayine? Tace eh ayi, shine matsalarki?? Eh to yanxu dai shine na farko, yayi murmushi wallahi duk abinda kikeso xa'amiki ya miqe zaune ya shiga dakinsa ya kira abokinsa wannan da iffaat tayi wa fitsari farhaan yace monkey din gidansune, yamai bayanin komai kuma yana son ayi komai cikin satinnan.. Bayan kwana biyu farhaan ya kawo mata IV yace ta rabawa qawayenta taji dadi sosai ta shiga rabo, duk Wanda ya tambayeta ba tayi aureba sai tace na jin dadin aurene wannan. tayi qayyar mutane farhaan ma haka su umma dai kam saidai su saka musu ido Dan sunga abin nasu wasane farahnax taxo su ZZ duk an hallaro Yar baqa ma haka hatta su dijee da rukayya ba'abarsu a bayaba..... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 91 Na Hauwa M. Jabo Abin sai Wanda ya gani, farhaan har tausayi yake bani wai wannan kudin da ya kashe duk Dan cika umurnin Mrs purhuuun ne, anyi komai cikin jin dadi da kwanciyar hankali su mama kam sai fada sukeyi wannan bidi'a haka aure na Neman shekara amma sai yanxu ake wani qaqale qaqale iffaat kam taji dadin komai d farhaan ya mata hatta kayan aure saida ya mata sabbi akwatuna kamar dai sabuwar amarya koda ai sabuwarce tunda har yanxu, wane yare da sukecewa ((dast na khurde )) budurwar kenan wacce batasan mazaba, An sallami kowa cikin aminci inda amarya da ango suka dawo gidansu farhaan kam hadda shan maganin qara qarfi irin yau za'a suburbudi iffaat... mutuniyar kuwa ko a jikinta Dan tasan batada tsarki, su farhaan anxo ana lalabe lalabe iffaat ta dakatar dashi ta hanyar gayamai batada tsarki kuma ta gaji ya barta tayi bacci, ga injin dinsa ya riga yadau zafi, farhaan Dan takaici ya rasa abinda zaiyi sai daukar key yayi ya fita yaje kozai samu gunda xaiyi aiki yanda yayi tsingau dinnan, iffaat ta gane ina ya nufa amma Sam bata kulashiba. farhaan bayan ya tafine yaje kuma yakasa Neman matan banxar, haka ya samu daki ya kwanta yanata juyi har bacci ya daukeshi bai farkaba sai guraren 3 Subhanallahi, ya tashi da sauri ya dawo gida koda yaxo ya tarar da iffaat zaune tana kallo abin ya bashi mamaki kallon iffaat cikin dare.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??92 Na Hauwa M. Jabo Yana shigowa ko kallonsa batayiba, duk kunya ta kamashi, gashi ma abinda yajeyi ya kasa aikatashi ya Dan Sosa kai yace bakiyi bacci ba!? Tace nayi faarkawa nayi yanxu, yaga kamar batayi fushiba sai ya matso kusa da ita zai zauna tayi xunbur ta tashi kada ka kuskura ka matso kusa dani tamai kallon raini kamar taga wani kashi, Ta kalleshi ai shi mai hali baya barin halinsa tunda ka saba da Neman mata wallahi ba abinda zaisa ka daina, ya xa'ayi na iya bacci bayan na auri miji manemin mata, ido cikin ido ta kalleshi tace farhaan nayi Dana sanin aurenka, nayi baqin cikin kasan cewa tare dakai, babban abin godiya ga Allah shine ba'abinda ya shiga tsakaninmu, bare ayi xancen hada zuri'a na tabbatar da yarana sai sunyi baqin ciki da samin uba mazinaci irinka.!! Amma yanxu kaga Hankali kwance zan nemi wani miji nayi aurena kuma wallahi saina fadawa umma halin da kake ciki.. Farhaan zuciya tayi xafi waishi take gayawa zata nemi miji tayi aure, yaso ya mammaketa amma sai ta wuce shi nan ya zauna yana Allah wadaran halinsa yayi tsaki yafi sau dubu ya kasa shiga dakin har bacci ya saceshi, iffaat kam ko dar bata ga bacciba gari ya waye kamar kada tamai breakfast Amma ta daure ta hada mai taxo tasa qafa ta shureshi ya tashi, ta kalleshi a wulaqance tace to aje ayi wanka a tsarkake jiki ayi sallah, a karya aje gun Neman wasu matan, aranshi yace wai dan wulaqanci da qafa xata tayar dashi yaji bala'en haushi Dan kuwa da atayar dashi da qafa gara a gyaleshi, kuma ga magan ganun banxa tana gayamai ya kalleta waike waya gaya miki Neman mata naje?! Cikin isa da tsabar rasjin kunya Tace sabida ba namijin kirkin da xai bar gidansa 12 na dare ya dawo 3 sannan yace ba gun banxa yake zuwaba, bare kaida akasan halinka na Neman mata.... Farhaan dai ya kasa magana yayi wanka ko karyawa yakasa yi ya Dan saba tana bashi a baki yau kam yasan koxai mutu bazata bashi abakiba, Haka ya dawo office guraren yamma ta qare girki tayi kwalliyarta kamar ba itaba. .. [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??93 Na Hauwa M. Jabo Tamai sannu da zuwa, ya amsa bayan ta juya ya kalleta mace kamar hawainiya sai chanxa wa takeyi, yaje yayi wanka. ta kawo mai abinci Dana safe Dana rana na yamma ma Dan ba yanxu yakeciba da sai ta hado mai dashi kuma duk sai ya cinyeshi, ta ijiye tace yaci wai ya qoshi, tamai kallon banxa kasan Allah wallahi sai kacishi, ya kalleta yanda ta hade fuska hakadai yayita durawa yana qarewa yaje yayita amai ko sannu bata cemaiba yana fitowa tace Allah yasa dai matan basu maka cikiba!! dagachin abinci sai amai ta bashi dariya sosai wai ciki, ya nemi guri ya zauna, bai tankataba haka dai iffaat take da farhaan kullum cikin yi masa habaici take, da rana taci uban kwalliya da dare ta saka arnan kayan bacci ta kuma fuske abinta, ranar da ya qara nemanta tace sai yaje asibiti an duba shi idan bashida rashin lafiya, farhaan kam ya shiga uku kullum cikin baqin cikin yarinyar nan yake, lallai yanxune yake sanin haqiqanin WACE CE ITA... dama hausawa sunce Dan hakin daka raina shi yake tsole maka ido, ai kuwa ga iffaat tana wanashi Son ranta, farko yace bazaije asibiti ba daga baya da yaga jan ran nata yayi yawa sai tsingau yakeyi haka ya daure yaje aka dubashi, lafiya lau yake ya kawo mata result tana kwance da kayanta na daukar allhaki ta tashi zaune ta duba taga lafiyanshi lau tace saura Abu daya kuma yace bayason yaji ko miye wallahi sai ta bashi haqqinsa, iffaat taga da gaske yakeyi idonsa sunyi jaa sai xuba masifa yakeyi hankalinta ya tashi tasan ba hanyar guduwa amma ta fuske ta nuna kamar bataji tsoroba farhaan kam matseta yayi ya cire mata kaya duka cizo duk yasha amma ina saida yayi nasarar kawar da budurcinta Allah sarki iffaat ta bani tausayi..... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..??94 kuka take tamkar ranta zai fita, Yaxo yana lallashinta yana bata haquri ya samu ya mata wanka da gashin jiki yayi toweling dinta ya kawota daki gaskiya taji jiki ba kadan ba bakinnan nata haka ya mutu murus kamar ba itaba, ba'ajima ba sai xaxxabi, farhaan shi kanshi yasan bai mata dakyauba yama manta sabon shigace an saba da masu wakeken abu shiga daya kamar an kada guga a rijiya, wannan kam a tame take fam shima da gyar ya samu shiga, ko Suhaila ma kusan haka take but na iffaat yayi yawa, Ya kira Dr. su yamai bayani ya kawo mai yan magunguna ya tayar da ita ya bata taqisha yayi yayi amma taqisha sai rawar dari take ga xafinda takeji a gurin, itakam ji take kamar ma ya yageta, farhaan dai anyi jinyar iffaat bata mai magana Sam, ko kallonsa ma batayi idan yaxo rufe idonta takeyi yaxo yayita surutansa ya gaji ba amsa... Kwananta uku a kwance ko lecture bata xuwa, ranar na hudu ta tafi skull, bayan sun fito lecture ta hadu da armiya'u suna tadi armiya'u dai kullum maganarta daya a kyautatawa miji a sha Abu Dan qara ni'ima, iffaat ta kalleta, ke kullum xance daya abinda ko dadi babu! Armiya'u ta kalleta tayi murmushi yarinya baki maida hankalinki bane abinda kawai zance miki wallahi so sweat, iffaat kam bazata iya fadar cewa sai yanxu ta shigo system ba sai ta basar da maganar... Ta dawo gida taga farhaan zaune batako kalleshiba ta wuce daki tayi wanka ta fito taje tayi girki, ta kawo mai yace dauke abinki baxanciba kamar bataji mi yake fada ba ta kama hanya ta wuce abinta janyota yayi da qarfi nace ki dauke baxanciba, kallon mamaki tamai taga yanda ya daure fuska aranta tace ai tunda ka biya buqatarka shikenan banida daraja. har zatayi magana kuma sai ta fasa da duqa zata dauki abincin farhaan ya janyota wato daukewa zakiyi ko? Bazaki tambayeni dalilin yin hakaba,? Haba iffaat miyasa kike min hakane? kuka ya kubce masa iffaat miyasa kike min hakane eeeh ? Kullum kina azabtarda zuciyarda ta damfaru da qaunarki, Dan kawai Kinga na damu dake matseta yayi sosai jikinsa itama dai hawayen suke xuba a idonta, ta fara magana tana kuka basai na kawo mukuba kawai akan Neman matanshine shi kuma yace tuni ya daina koda bata aminta 100% ba amma taji ta gamsu.... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA..?? 95A Na Hauwa M. Jabo Hmmmm. Wai har sun shirya an yafi juna sunci abincin tare... Wata sabuwar soyayyah ce a Gidan ma'auratan gwanin bansha'awa suna kula da junansu yanda yakamata. Yanxune iffaat take fahimtar abinda armiya'u ta taba gayamata na cewa farhaan bamuqacine na gaske lallai hakane kullum dai yajishi ciki uhummm. Abin ba'a cewa komai. Iffaat ta cika alqawari takai goggo makka kuma ta dauko qawayenta na qauye dije da rukayya an baiwa mazajensu lebaranci a companyn su farhaan suna shanawa suma ga dukkan alamu suma su waye su xama yan gayu, amma bana tunanin dijee zata waye Dan har yanxu tana nan sai a hankali.. Bayan shekara 7 Koda naxo naga iffaat da yara uku mamaki ya kamani naso naga iffaat da ciki amma ina banganiba sai yayanta na gani.. Mace daya namiji biyu Macen taci sunan Suhaila sai maxan dayan sunan mahaifin iffaat mahmoud dayan sunan mahaifin farhaan habeeb. Farhaan ya zama kamilallen mutum kamar bashiba, iffaat kam har yanxu saidai idan ba'asamu damaba.. Dan Ko yau da naje muku gidan, saman bishiya na ganta tana tsinkowa tana wurgowa qasa yaranta suna cabewa sunata jin dadi, farhaan ya shigo ya duba bata yasan ina taje ya girgixa kai, yaje ya kirata tana ganinsa ta diro saman bishiya saida naji tsoro na dauka ta karye sai na tuna fiye da wannan ma tayi.. taje ta rungume shi tanamai oyoyo yace bawai na hanaki hawa saman bishiya ba, ta kanne ido tace waya iya raba monkey da hawa bishiya dariya yayi ya tuna lokacinda tayi mai fitsari saman bishiya yace monkey ne, Suhaila ce ta shigo itada habeeb cox shi Mahmoud jinjirene, Suhaila da wayo tace Abba mu anti amarya mukeso.! gidansu hameed na uncle Ali an musu anti amarya kullum sai yace mana mu bamuda anti amarua, muma munason anti.... iffaat tace kiji yarinya da gulma xanci gidanku yanxu, ba anti amyaba anti ango bace min da gani, sakarya kawai...!! Suhaila ta wuce tana gunguni, Farhaan kam dariya yakeyi sosai, iffaat ta kalleshi miye haka.?? Daga jin anyi xancen amarya sai wani washe baki kakeyi... [8:07PM, 5/17/2015] .: WACE CE ITA.. ??95B Na Hauwa M.jabo To amaryaf taxo ina daidai da ita, yadan muskuta dama akwai wata yarinya Dana gani ta kwanta min arai inaga xan kawoma su Yy Suhaila ita tunda tanason anti amarya, Yy Suhaila suke kiran Yar tasu da ita. iffaat hararanshi tayi tace wallahi baka isaba, yayi dariya yace kefa kika ce taxo kina daidai da ita,! Ta fuske tace eh ta murguda baki, farhaan yayi dariya ya tashi ya shige, har yakai qofar bayi bari nayi wanka xan kawo miki ita ki ganta.. Iffaat kam taji ba daidaiba, harya fara wanka ta kasa haqura ya fito ta bishi bayi Yy farhaan waida gaske kakeyi? Yayi dariya sosai sannan yace eh mana ya wanke ko ina xai dauraye jiki ta kashe fanfo ta fara bala'e wallahi baxai yiwuba, ai wannan sharrine, yace aah kinji yarinya ke kinxama chuss dole na dauko sabuwa a Leda na bare ta kenifa sai nayi mace hudu Dan ki sani, kii kunna min ruwana mana, ta fara kuka, wallahi sai ta gayawa umma yace umma ai xataso a kawo mata sabuwar suruka ta haifo mata jikoki, ba kece kin daina mini wankaba ai dole na nemo mai mini wanka Dan ni Dan lelene, cikin kuka tace xan riqa maka wanka wallahi, yace to ki fara yanxu, ta kuwa kunna ruwa tamai wanka Tass suka fito ta shirya shi sai yan hawaye takeyi, abin yabana bashi dariya ba kadan ba, tana zaune saiga Yy Suhaila ta shigo iffaat tace ke get out masu tsokane tsokane kawai, yarinya tayi tsaye bata gane dawan gariba, farhaan yace Yy Suhaila kuje wasa kinji yarinyar anti amarya tace yeeeeeeeee ta tafi da gudu, farhaan yaga yanda iffaat ta hade fuska ta miqe da qarfi zata fara yankomai bala'e ya janyo ta ta fado jikinsa haba Yar gidan umma ni na Isa na qara aure yanda nake da mace kamar ki ai kin wuce 1 of 4 ke ta dabance kullum sweat kike qarawa, ya fara kissing dinta, tace bayan kace min chuss yace wallahi wasa nake miki kinfi komai daraja a gurina kece sanadin shiryuwata kuma kin haifomin Yaya masu kyau masu kama dake, ta qara shigewa jikin sa tana mai nata salon nidai sai na fito na basu guri suci soyayyah kar na makance,.... TAMMAT BI HAMDILLAH.... Qarshe wannan littafin kenan Ina godiya ga dinbin masoya da suke bibiyar ta a wannan Dan qaramin littafi na WACE CE ITA.. ina godiya ga masu bani shawara da Masu mini gyara hadda masu zagi ban barku a bayaba ina godiya matuqa Allah ya saka da alkhairi, Nasan hausar tawa sai a hankali kuna qoqari gurin karantawa... Naso littafin yafi haka, akwai abubuwan da naso na saka wayanda zasu qara nishadantar daku amma kuma inaa exam ta matso kusa... Ayi haquri da wannan sai mun hadu wani book mai suna........... nagode sosai Don shawara ko gyara ga number ta +98936 594 4638 Banda tambayar wane guri nake please... HAUWA MUHAMMAD JABO take muku fatan alkhairi. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *