adsense here

akan hanyar asibiti nida qawata zeenah khalifa
zamuje duba wata maqociyarmu da batada
lafiya,Muna shiga asibiti mukayi karo da wata mata
da yara guda biyu a hannunta zenah khalifa tayi
sokoko tana kallonta.Ke zeenah khalifa kinji haushi
ki kalli maza ki kalli mata.! Banason wulaqanci
hauwa jabo.! Mikike nufi da inkalli mata in kalli
maza? kamar wata bunsura..!!! Na kwashe dadariya
nace yanzu dai yimin bayani mi kika hango.?? Ta
kwashe da dariya kibari kawai,Hauwa jabo matar
nan ta hadu billahillazi..Da ace ba baqa bace sai ince
wllhy ba indiyace keni muje muyi qawance da ita,Ke
zainab muna fama da talaucinmu zamuje gurin
masu kudi.? Bazanje a wulaqantaniba gaskiya,Ke
Hauwa jabo wllhy kin cika tsoro,Idan bazakiba bari
inje ingabatarda kaina,Ta kwace wayata taje tana
kuri. Bansan yanda sukayiba naga har sunyi
musanyar number suna yiwa juna murmushi wani
namiji yazo naga yana mata magana tay murmushi
ya rungumeta hannunsa dayan hannunsa riqe da
handbag dinta ya mata kiss a kumatu ina tsaye ina
kallo araina nace dama matan nigeria suna
soyayyah haka? In shot sun burgeni kuma inason
inji tarihinsu da inda suka iya soyayyah irinta Iranian
saboda Iranian ne kawai zakiga sundaukarwa
matansu jaka su rungume jariri kuma su rungume
matar kamar wani zai kwace musu.. !Zainb ta dawo
sai murna takeyi ina tsaye,Sai wangale baki takeyi
zainab,Amma fa matar ta haduko H jabo? uhun ba
laifi!, Ke Wllhy kincika matsala,! Nidai muje, Zamu
shiga kenan sai gasu sun fito suna dagawa zainab
hannu sai wangale baki take har yar wushiryarta da
dan dimple dinda take kuri dashi ya fito araina nace
zainb ansamu aikin yi, Munshiga mun duba mara
lafiya munfito muka wuce city plaza muka dan sayi
ice cream muka samu keke npn sai gida.....
Eshqi mano too... tuye qalbam mimune....zandagi
batu behtare..... Ringtone din zainb kenan kuma
gashi tashiga wanka naga anrubuta sister zainb
araina nace waye kuma sister zainb... hello, hello
namesake, nasissim adaya banqaren naji dafada
cike da dariya... Araina nace wannan yar turkiyace
ni jabo ba Turkish na iyaba hakadai na amsa mata
nasissim eyem ebit ta kwashe da dariya.. Araina
nace zatace ban iyaba na kwabsa, Sai tace ni ban
iya wannan da kika fadaba nima nay dariya, Tace
yaushe zaku zo gidana da sauri nace gobe zamuzo
ba matsala, Eh kuzo ta fada cike da shauqi, Ta bani
address dinta na rubuta zeenah khalifa na fitowa
nace namesake dinki takira tace gobe muzo...
ihuuuuuuhw.!! Wani ihu tayi tanajin dadi nima naji
dadi ko banxa inason muje inyo gulma...
Tun safe kinsan yau zamuje unguwa ko? Unguwa
kuma.? Lallai wllhy jabo kinji dadinki kin manta
zamuje gidan namesake dina.!!?? Au natuna qarfe
nawa ma zamuje.?? 12 mukace mata. Kk.. mun isa
gidanta wani qaton gidane da shuke shuke ya rufe
ko ina nace anya nanne zainb karmuje a cire mana
kai, Eh nanne mana muka danna bell maigadi yabude
mana yace su zainb ko mukace eh kushigo, Araina
nace har angayawa maigadi zamuzo Lallai anaji
damu..
Munsameta tsakiyar gida tana ganinmu tazo ta
rungume mu...... muje zuwa muji yanda hauwa jabo
zatayo mana gulma agurin zainab......
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥••••••••
•••••••PART 2••••••••••••••••••
…Munci munsha mun hole anan na fahinci zainab
tanada balaeen saurin sabo kuma akwai tsiwa da
wasan rainin hankali, Nandanan muka saba da ita
amma naga tafi maida hankali gurina ko dan taga
nafi hankaline ohoo..?
Watannmu uku da sanin zainab duk ansanmu a
gidanta tana zuwa gidanmu sosai,Ranar munje
gidanta, Nan nanemi ta bamu labarinta daga farko
tayi gardama daga baya mitayi tunani ta amince
naso inyi shishigi intambayeta amma sunyi rayuwa
a iran ko amma sai nafasa nace bari in barta kawai
maji daga baya...
Tun safee nazo inji gulma nikadai nazo saboda
nasan idan nazo da zeenah khalifa to labarin
bazaimun dadiba, Nayi sa'a tagama aikinta gaskiya
zainab tanada kazar kazar batada son jiki ko kadan,
Takawomin fresh milk nashanye, Ta gyara zama ta
fara bani labari kamar haka.........
Sunana zainab Abdullahi mahaifiyata gurin hai
huwata Allah yamata cikawa, Mahaifina mutum ne
mara kulawa sosai, Sam bai damu da tarbiyarmu ba
baidamu da chin muba bai damu da shanmuba,
Gamu mu mu shida ne a gidan ni kadai nake agun
mamata data rasu sauran biyar din duk yayan
kishiyar mamanmune maza uku mata biyu,Agurin
kishiyar mamata na girma, kishiyar mamata
mutumce wacce batayi dan Allah idan kikayi mata
zata miki idan baki mataba to bazatayi mikiba,Amma
bata cutar da kai sai ka cutar da ita, Tana dauramin
tallan kayan miya ranar da nasiyar to zamuji dadi
idan kuwa yayi kwantai to bamu ba abinci sam
saboda da dan ribar da take samune take bamu
abincin safe dana rana, Nadare kuwa baba yake
bayarwa, Bata ta6a dukanaba kuma bata cika yimin
fadaba amma tanacin uban yayanta sosai nice
babba agidan, Banta6a sanin hanyar makarantar
bokoba balle ta addini har nakai shekara goma sha
daya bana karatu sai yawon talla, Ina sha'awar boko
sosai inada wata qawa wacce muke yawon talla
tare da ita amina s bawa, Ita tana dan boko ta bani
littafinta daya tafara koyamin A B C D.... Ina ganewa
sosai saboda inada hazaqa duk ranarda muka saida
kayan miya da wuri to ranar zamu zauna muyi boko
wasa wasa har nafi amina iya karatu sai tafara jin
haushi saboda musun da nake mata akan wannan
haka yake tace a'a ba haka yakeba, Haka yake
tadaina koyamin komai ataqaice duk wata takardar
qosai ta unguwarmu idan nagani sai nakaranta na
iya hada kalmomin english inkaranta amma bansan
ma'anarsuba ke intaqaita miki jabo duk wani karatun
indai karantawane ina iyayi da rubutawa.....
Akwai wata rana na fito tallan wara saboda yanzu
nadaina tallan kayan miya wara nake talla yafi
kasuwa ina tafiya naga wata qatuwar mota baqa
baka ganin waye aciki,Anyi parking dinta a gefen
hanya, Kusan wata daya Kullum sainaga motarnan
wani yaro yace wai mai motan yace ki kawo wara
na kalli motan lokacin iya tunanina nasan mai
Wannan qatuwar mota bazai ci waraba, Nace
bazanje, Shegiya matsiyaciya arziki yana kiranki
kina gudu kar kije miya dameni wannan mutumin
duka yake siya yace kikai masallaci....
kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 3
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥••••••••
••••••PART 3••••••••••
…Abinda yasa naqi zuwa kuwa kiranshi maman
jamila (kishiyar maman mu) tace koda ban saida
tallan da ta dauramin ba kada in kuskura wani ya
bani kudi yamun juye ko in bishi gida duk ranarda
nayi haka sai ta yankani,Kuma zata riqa dukana
kamar yanda take dukansu jamila (yayanta
kenan )Ashe su jamila juye suke ana ta6a lalubarsu
shiyasa take chin ubansu.. naceto, Zo karakani muje
tare har yace bazai jeba sai kuma yace kawo
inkaimuki na bashi ya kai ya dawo yace waranki na
dari shida da talatinne ga kudin kikai wa almajirai
waran. Yace min ko ki saida rabi kikaiwa almajirai
rabi ki boye sauran kudin. Har na yarda da
shawaransa sai kawai naga idan maman jamila
tagane zataci ubana tace ina nake samun kudi,
Nakoma gida da wuri akace ya akayi nadawo da
wuri nayi bayani tace kar dai in kuskura in shiga
motarsa kuma duk abinda ya bani kar inci, Nace to,
Tun daga ranar idan nafito talla nan zan tarar da
motar mutuminnan nan kuma zan barta, Banta6a
zuwa jikin motanba sai na jira audu abokin tallana
yazo yakai asaye abani kudi...
Yanzu babana ya chanza yana bamu kulawa sosai
kuma ya sakamu islamiya dukanmu, Inada qoqari
sosai amma su jamila sai a hankali cikin shekara
daya na sauke qur'ani nashiga bangaren
hadda,Namma banyi qasa a guywaba wata tara na
haddace qur'ani da tajwid da komai, Nice tafarko
atarihin makarantarmu da ta haddace qur'ani cikin
wata tara dama tun lokacinda nake karatu kamin in
iya na haddace shiyasa da nazo sai yamin sauqi
nandanan na haddace, Akayi gagarumin bukin yaye
dalibai hadda shugaban makarantarmu yazo nay
karatu da muryar nan tawa nasamu kyaututuka
sosai agurin malamanmu da manyan baqi, Yanzu na
daina talla saboda baba yana iya bakin qoqarinsa
yachanza sosai yanzu baya barinmu da tsumma
kamar da mun wadata sosai, Ranar nadawo daga
islamiya baba yace inzo naje gunsa sai yacemun
wai aure zai nida ko nono banida za'ayimin aure gani
da qaramin jiki saboda ta dade da fara nono amma ni
yar qwaila dani, Bance komaiba nace to, ko kinada
wanda kikeso nace a'ah, Aka sa ranar aurena aka
dauramin aure da mijin da banta6a ganiba bansan
ko waye shiba…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 4
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥°°°°°°°°°°°
°PART 4°°°°°°°°°
…Iya tunanina aurena da wani dan mashukurin mai
kudi rana daya akayi shi dan jama'ar da suka taru
sunfi qarfin suzo aurena amma daga qarshe
mungane gurin auren nawa sukazo,Har bayan
daurin aurena ina gidanmuban tareba, Bana fita ko
ina, Sai taya maman jamila aiki, Ke in gayamaki jabo
wllhy saida nayi shekara biyar agidanmu ba miji ba
labarinsa kuma ba zancen tarewa, Har na balaga,
Ba miji inason inyi magana amma kunya ta hanani
yin magana duk qannena mata jamila da hafsatu an
musu aure jamila da wani har ta haihu da wani ciki
ajikinta hafsatu kuma da cikinta tsoho, Nigani agida
farko abin baya damuna kuma sam ban fuskantar
tsangwama agurin maman jamila, Yanzu na girma
nasan miye aure saboda ina zuwa wata islamiya
dadare ta matan aure a unguwarmu, Inajin
abubuwan da ake koya mana mata da wuri suke
zuwa dan suyi ta tadi, Mijina kaza mijina kaza nidai
bana ce musu komai, Abin duniya ya isheni nayanke
shawarar zan yiwa baba magana sai dai kuma
kunya nakeji nace ko infara yiwa maman jamila
maganane inji abinda zatace, Haka kuwa akayi, Ina
biya mata karatun qur'ani bayan munqare muna hira
saina cemata wai maman jamila waye mijina..? Naji
kamar bata jini ba namaimata tambayar, Ta d'ago
ido ta kalleni tace mun kitambayi babanki, Nayi shiru,
Ban qara cewa komaiba, Munqare karatu da ita na
shige daki, Sai tunani kala kala nakeyi gaskiya
inason sanin miye matsayina matar aure ko
bazawara? Zaman aure nake ko zaman gida?
Shekara biyar ba miji ba labarinsa sai wani niqab da
baba yasani sakawa tunda aka dauramin aure, Yan
kwanakinnan nashiga damuwa sosai sai nake
tunanin ko dan banida uwane aka yimin haka, Lallai
maraici hadarine, Nashiga rera kuka mara sauti nayi
wata biyu Kullum sai nayi kuka duk wata walwala ta
gushe mini banida aiki sai tunani da damuwa nashiga
tsaka mai wuya narame, Na kode, Nayi baqi, Duk
wata halitta ta jikina saida ta chanza.. Na yi alwashin
zanyiwa babana magana, Bayan yadawo daga
kasuwa nace inada magana dashi yace to naje
gurinsa, Inson inyi magana sai muryata ta fara rawa
bansan lokacinda kuka ya subucemin ba nayi kuka
sosai baba ya rasa gane kaina gashi ba kowa
agidan saini nima dan banje islamiya bane, Daqyar
nasamu nayi shiru amma nakasa tambayarsa, Can
baba yace nasan zaki damu ace shekara biyar da
watanni da daura miki aure amma bakisan mijinkiba.!
kuma baki tare Gidankiba ba ,Amma kiyi haquri
nasan banmiki adalciba, Nafarko ban baki damar
zabar mijin da ranki yakesoba ban tambayi
ra'ayinkiba inji shin kina sonsa ko yaya,! Bakisan
wayeba bakisan komai akansaba hasalima bakisan
wayeshiba ban barki kinyi karatun bokoba, Sannan
shekara biyar dai dai da rana daya bakimin magana
ba Allah yayi miki albarka kuma mijinki wannan
shekarar zai dawo insha Allah, Idan ya dawo tare
gidanki tashi kije ki kwanta Allah yayi miki albarka,
Koba komai raina yayi sanyi najin cewa mijina zai
dawo wannan shekaran dan wllhy na gaji da zama
da igiyar aure akaina…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 5
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥••••••••
•••••PART 5•••••••••
…Na rogi alfarmar baba ya barni in riqa zuwa wata
yar makaranta da ake lesson anan qasa da gidanmu
baba ya amince, Kuma yace inci gaba da kare
mutuncina, Nafara zuwa lesson abubuwa da yawa
nasan sunansu amma bansan ma'anarsuba malamin
da yaga inada hazaqa sosai sai ya bani kyautar wani
littafi sunayen abubuwa da hotonsu cikin sati daya
na haddace su duka dama nasan sunayen abubuwan
kawai bansan sunayensubane sai yanzu, Ahankali
nafara iya magana da english cikin wata biyu..
Hauwa jabo ko kin gaji mu bari sai gobe nace a'ah
muci gaba kawai, Tayi murmushi taci gaba.... Ranar
nadawo daga lesson dina tun zauren gidanmu naji
wani qamshin turare mai rudarwa qamshi sosai naji
wata sassanyar murya ana wani yare bansan mi
suke cewaba a lokacin (to namifahmi hamun juri k to
hamsari man hasti uwn ham hamsari mani to
modare bachem hasti, chira mutawajji nisti ) adaidai
lokacin nabi gefensa na wuce fuskansa na kallon
yamma so baisan nashigoba na shigo tsakar gida
natararda baba fuskarsa cike da fara'a nima nayi
murmushi nace baba miya faru naganku kuna jin
dadi yace ABDUL AZEEZ ne yadawo.Waye kuma
abdul azeez baba? mijinkine, mijina? Eh Sai ban
sake cewa komaiba yayiwa su baba sayayah sosai
ina tsaye ina kallonsu, Na wuce dakina nan natarar
da kaya niqi niqi naci dana sha dana shafawa tufafi
kala kala turaruka kala kala na kira maman jamila na
nuna mata tatayani buda wasu naji dadin kayan
koba komai nasan wanda yasiyo kayan mai kudine,
Wasu kayan irin na qasar wajene bana nigeria bane
hadda waya a cikin kayana (LG G Flex) wayan ta
hadu iya haduwa sai wani envelope nagane
wasiqace naqi budawa saida maman jamila ta fita ....
Hello my wife
Sai kuma number sa daya rubuta a qasa banta6a
ganin letter irin wannan ba, Naji dadi koba komai
nasan cewa inada miji, Tun safee baba ya kirani
yace in kunna wayan da aka bani na kuwa kunna ko
minti hudu ba'ayiba kira yashigo naga ansaka AZEEZ
nidai bansan ko wayeba na dauki wayan nayi
sallama ingayamiki jabo bai amsaba saida nayi
sallama biyar ba amsa nayta danne danne har na
gane yanda ake kashewa karo na biyu ya sake kira
na dauka namma ba magana nasake kashewa karo
na na uku naqi dauka har ta qare ringing ya turo sms
(I luv d way u r talk,ur voice is agreeable ) Kwana
shida da dawowar azeez aka fara shirye shiryen
tarewana anyi min duk abubuwan da suka kamata
maman jamila ta gyarani iya qoqarinta, Aka kaini
gidan mijina in taqaitamiki labari, H jabo saida nayi
wata shida cur agidan nan bansaka Abdul azeez a
idonaba komai na gidan ya wadata ba abinda nake
nema, Duk sati za'a kawo min cefane da kudi ko
zan buqata kuma aka bani mota da driver duk inda
nakeson zuwa akaini, Ingayamiki jabo saida na
gwammace zama gida da zaman gidan aure,
Rayuwa ta sauya bana zuwa ko ina sai gida zubi
zubi tun inajin tsoro har nadaina jin tsoro nabarwa
Allah komai, Nayi magana da malaminmu mai mana
lesson akan yasamomin wanda zai riqa zuwa gida
yana mini lesson, Yasamomin wata mata tana
koyamin dan science da wasu subject na seconds
skul naba kaina wahala sosai wajen ganin na iya
karatun science Kullum ina duba internet ina daukar
lecture a internet malamar har mamakin basirana
takeyi dan kuwa har tamun hanya inje in zana waec
idan naci zata nemamin admission a university
dinsu, Sai da na zana waec naci ina zancen zuwa
kenan sai ga saqo daga mijina inje za'amun
international passport, Wata mata takaini
immigration office akamin passport aka kar6o min
ticket da visa na barin qasa..…
Kukasance tare dani a AURE KO XAMAN GIDA part
♥♥♥AURE KO ZAMAN
GIDA♥♥♥★★★★★★PART 6★★★★★…Wai
ashe jabo duk zaman da nakeyi. Abdul azeez baya
nigeria gabaki daya yana iran abinshi, Ni ya zan bar
wata qasa ni kadai alhalin ban banta6a zuwa koda
airport ba, Haka nayi kuka nayi bankwana da yan
uwana dan bantabm6a tunanin zan dawoba nashiga
mota sai kaduna, Ina ganin jirgi jikina ya mutu na
tabbatarda bazanyi raiba matsawar na hau wannan
gangaramar, Wasu zafafan hawaye suka zubomin
tunda nashiga jirgi nake kuka har muka isa Lagos,
Daga lagos zamuyi fly 6:30 har aka gama shiga jirgi
ban saniba saida wata mata tamun magana sannan
nagane cewa jirginmu saura 7mnt ya tashi
tataimakamin nasamu nashiga jirgi ina shiga idon
kowa akaina har ina tuntu6e nazauna ga fitsari inaji
ina tsoron tashi, Da ya matseni haka nan na lalla6a
naje nayi amma ba ruwan tsarki naga zan batawa
kaina lokaci nasaka tissue na goge na fito, A
daddafe muka isa Beirut a Lebanon kenan, Na sake
shiga wani jirgi sai emirate dubai kenan, Nasha kallo
a dubai qasar ta burgeni sosan gaske a dubai
nasamu transit 18 hrs wllhy haka na zauna a airport
ga yunwa kamar zata kasheni na daddafa naje naci
wani abinci $50 bangane komaiba ba dadi sai dan
banzan tsami nayita amai sai zazza6i anan bacci
yayi awon gaba dani ban farkaba sai 9:12 kuma 8:30
zamuyi fly ataqaice nayi missing din fly naci kuka
har na gode Allah naje gun ma'aikatan gun namusu
bayani sukace jirgina ya wuce sai na sake sabon
bucking suka min komai da komai, Ina nan zaune
abin tausayi sai ga wata mata da mijinta zasuje iran
kuma hausawa ai kamar ansakani aljanna haka naji
nadan gaya musu yanda akayi nayi missing din fly
sukaita dariya nima saina wayance nayi dariya
amma nasan sungane ni dibgaggiyar local ce ni, Dan
kuwa kina ganina kinsan sai a slow ko a shigata,
Sun taimakamin mun isa iran nanma nayi wani
qauyanci dan kuwa anbani number akace idan na iso
airport din tehran inyi waya sai kawai nabaiwa
maman nargees kudi nace ta siyamin ticket nabisu
garinsu mashhad saida muka isa maman nargess
tasiyomin sim card nasaka nakira numbar da aka
bani, Nayi sallama aka amsa da wata sassanyar
murna mai ratsa jiki dajin muryar nagane cewa
antsorata ana tunanin na6atane kina ina yanzu,?
Airport kisamu wani mutum cikin ma'aikatan gurin
inyi magana dashi nasamu wani mutum na bashi
yagayawa. Abdul azeez cewa ina mashhad, Yaji
haushi sosai kaman in kar6i wayaya kashe nakira
ba'adauka qarshe ya kashe wayanshi natsorata
sosai naje gun wani mutumi shi ba England ba sai
surutu daga wata gasa nake (az kuzo omadid ) Ni ba
gane yarensu nakeba su kuma ba wani gwagwaran
turanci ba haka dai nasamu har ya gane me nake
nufi ya siyamin wani ticket daga mashhad zuwa
tehran inkoma inda nafito yamun komai mutanen
gasar iran akwai tsoron Allah tare dasu ga kuma
amana natashi nakoma tehran ina isa nasake
kiranshi naji wayan akashe can naji wayan yayi
ringing na dauka kina ina? Nadawo airport dinda na
sauka daga farko yayi shiru ina hello naji shiru sai
na kashe wayan ashe wai ya biyonine ni kuma
nakoma garin haka na qama zama a airport ga
qasar da wani mahaukacin sanyi wayata ta mutu
nasamu wani mutum ya nuna min masallaci nayi
sallolin da ake bina nasaka chaji sai bacci da gurin
akwai dumi ban farkaba sai asuba shima yanwa ta
tayar dani ina duba wayana naga 38 miss call. Banji
haushiba nayi sallah asuba na tashi na nemi gurin
chin abinci ina chin abinci naji ance min ke.!!…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 7
♣♣♣AURE KO ZAMAN GIDA♣♣♣::::::::
:::::::::::PART 7::::::::::::::::
…Ban waigibo hasalima banjishiba saboda na tafi
duniyar tunani, zainab ce.??
Na waigo sai naga wani kyakyawan mutum dogo fari
tareda yan sanda guda biyu, Sukayi yare sai naga
sun juya suntafi, Ina dago kaina ya kwasheni da
wani wawan mari saida na fadi qasa, Anan nace
Lallai ma mutuminnan dan iskane ya aureni ya
ajiyeni gidan ubana shekara biyar, Sannan yakawoni
gidansa wata tara, Ba kulawa, Yaturoni daga qasa
zuwa qasa ni kadai saida na hau mutuwa(jirgi) sau
shida sannan inyi kwana hudu ina garari qasa da
qasa inzo ya rasa mizai sakamin dashi sai mari
gashi banida lafiya , za'ayi ta kuwa dan wllhy sai ya
sakeni yanzu kuma ya maidani gidan ubana nagaji
da Wannan bala'een tun banida wayo nake hadiyar
baqin cikin sa har yanzu na tashi na dauki wayata
naja kujera na zauna, Bai min maganaba yaja hand
lgt dina ya tafi yana jiran in biyoshi nayi banza dashi,
Shiru sai da yakai gate din fita yaga bani ya dawo,
Na daura kaina akan table din gurin ina kuka yazo
ya ta6ani ban motsaba ya girgizani ya matso kusa
dani yace kizo muje gida, Wani dum naji, Araina nace
dan yasan muryarsa tanada dadine shiyasa baya
magana, Ashe duk abinda mukeyi a police din gurin
suna kallonmu a cameran dakinsu yazauna bai sake
maganaba sai ga yan sanda sunzo suka ja shi gefe
suka tattauna suka dawo police yacemin (he is ur
husband?) Araina nace inaga mutanen wannan qasar
basu iya turanciba sai yarensu, Nace masa (no he is
nt my husband ) Ya zare ido ya kalleni da idonsa,
Nasaukar da nawa idon, Suka sakeyin yare police ya
qara tambayata mijinkine nace musu a'ah, Suka
jamu mukaje wani daki suka fara masa question wai
idan matarsace ina certificate din auren mu? Nan
yayi turus baisan nigeria basa wani certificate ba
nan nafahinci bayason magana sosai duk yarasa
mezai musu, Suka kar6i passport dina sukaga
sunana da sunansa suka kar6i passport dina da
nashi sukace mutafi kamin suyi bincike,Intashi muje
na sake fashewa da kuka, Yayi bala'een daure fuska
yayi musu yare sosai sai ya miqa min hannu na kalli
yanda ya daure fuska na saduda na miqa masa
yamatse sosai ya jawo jikinsa ya rungumeni na
natsu sosai ban ji komai a rungumar da yamunba
saboda ina masa kallon azzalumine kuma ga
tsoronsa da ya kamani sai qamshin turarensa da
yake dukan hanchina, Mukaje yatari taxi muka shiga
munyi tafiya sosai sannan muka isa inda zamuje
muna isa ya bani key yace ga gidanki nan. Tofa…
Kukasance tare danu a AURE KO ZAMAN GIDA part
8
♦♦♦AURE KO ZAMAN GIDA♦♦♦°°°°°°°°°
°PART 8°°°°°°°°°°
Miyake nufi da ga gidananan yana nufin ya tafi
kenan wani sabon kuka nafarayi ga sanyi inaji harna
tashin hankali amma ba yanda zanyi naduba gabas
da yamma ba wani mutum na lalla6a na bude gidan
nashiga gidan qaramine zaman mutum daya na
zauna nayi kuka har na gode Allah ga sanyi kamar
me saboda anyi snow sosai gashi ni bansan yanda
ake kunna heater room ba danaga zan mutu da
sanyi natare kitchen da zama, Wato ya raboni da
iyayena yakawoninan dan yaudara garama nigeria
ina ganin iyayena idan naso ganinsu amma yanzu
idan naso ganinsu sai na kashe over half million
sannan zangansu, Lallai ina cikin tashin hankali
mara iyaaka, Satina uku bansakashi a idonaba
narame nadaina chin abinchi ranar naji hayaniya
ashe maqociyatace mijinta ya rasu naje sunata kuka
sun bani tausayi talakawane ba laifi yar budurwar
yarta tana gane English kadan kadan shima idan ta
kwa6a sai cikin mutum yayi ciwo kan dariya,
Ahankali nasaba dasu sosai suna koyamin yare
kadan cikin sati biyu nafara fahimta Abdul azeez
kullum sai yamun sms ya nake amma bana bashi
amsa wai ashe akwai camera a gidan wacce duk
wani motsina yana gani a gidanshi shiyasa
yashareni watana uku bansakashi a idoba na yanke
hukuncin komawa gidan su makwabciyarmu da
zama tunda yanzu nasaba dasu sosai kuma batada
yaro namiji a yaranta mata biyune. Na kashe wutar
gidan gaba daya na tafi abina yare kam alhamdu
lillah nagama iyashi tsab, Nagayawa mai kawomin
kayan abinci idan ya kawo min kayan abinci nan
gidan zai kawowa komai nawa nan nake yinsa
arayuwa kwata kwata namanta da abdul azeez
hankalina kwance nakashe banzar wayar da
yakemin sms, Ashe yayi tafiyane shima shiyasa bayi
gane bana gidanba yaje Turkey wani aiki na wata
daya yadawo ya kunna cameransa yaga wayam
basa aiki anma kasheshe gaba daya yayi forwarding
din karsheb zamanta gidan yaga tana hada kaya da
komai dakomai ta kashe wuta yaji tsoron ko ta gudu
ya tuna passport dinta na hannunsa hankalinsa yayi
bala'een tashi bashiri ya dawo gida qofa a gargame
nan ya zauna ya fara danasanin abinda ya aikata
tabbas bai yiwa zainab adalciba koda yasan shi
yayiwa matarsa alqawarin bazai kula wata maceba
matsawar tana raye, Zainab itace za6insa tun tana
yar shekara 9 yanemi aurenta aka bashi ita, Itace
za6insa, Ita yakeso, Dan yanasonta ya aureta, Ya
auretane dan kar wani ya gwace masa ita yasata
zaman kulli shekara hudu ya ajiyeta gidansa a naija
wata tara ya kawota qasar da batada kowa batasan
kowaba ya tafi ya barta yana ganin halinda take ciki
amma dan kar ya batawa matarsa uwar yayansa rai
yaqi za6insa wacce sonta yake neman kasheshi,
Yamanta itama zata haifamasa yarane, Yanzu ina
zai sameta..? Ina zuwa zainab kina nufin Abdul
azeez mijinki yanada wata mata?? Kibari kawai wllhy
mata harda yaro daya inna lillahi wa inna ilaihi
rajiun... Hauwa jabo muje muyi sallah mudawo in
qarasa miki.…
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part 9
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥°°°°°°°°°°
°PART 9°°°°°°°°
Jikina a mace nayi sallah dan abin ya dauremin kai
jin cewa azeez yanada mata harda yaro, Muci abinci
sai muci gaba ko jabo nace ai ina azumi ta kwashe
da dariya, kinmanta kinsha fresh milk dazu nima
abin ya bani dariya dan kawai insha labari nace ina
azumi tamana girki indomie mukaci a gurguje taci
gaba da bani labari...
In gayamiki jabo kamar ance fito dan ba inda nake
zuwa sai wani park na bayan gidana shima mutane
suka fara damuna suna cemin (siya pust)Baqar fata
kenan nadaina zuwa ina gida abina ina fitowa
naganshi zaune dirshan cikin sanyi yana kuka wllhy
jabo ko kwaya zarra banji ya bani tausayiba
hasalima wani tsanarsa da nayi duk lokacin bansan
yanada mataba, Ina kallonsa miyaji sai naga ya daga
kai da qarfi ya kalloni hadi da wata irin kyakyawar
aziyar zuciya, Ya miqe tsaye ya bude qofar gidan ya
shiga kai tsaye na koma inda nake har magriba ban
shigo gunsaba nama manta dashi inachan gurin
makwabtana yar tsohuwa dai tagane akwai wani
abu (chi shod dokhtaram?) Miyake faruwa yata
( hech) ba komai (pas chira shoharat omada wali to
khushhal na shodi ?)To miyasa mijinki yazo bakiyi
murnaba(Hech momon alan miram pishash)Ba
komai mama yanzu zanje gurinsa(Affarein dokhtari
khub zud baro guna dore az rahi dur omade
istiqbalash ham na karde)Da kyau yata yi sauri kije,
Bazaiji dadiba ace yadawo daga tafiya amma kinqi
kije tarbarsa, (Boshe momon)To mama. Na fito sumi
sumi na shigo a parlour naganshi zaune yayi wujiga
wujiga dashi ya kalleni ina shigowa ya miqe tsaye
naja natsaya na dauka zai kwasheni da wani marine
kamar yanda yayimin a airport, Amma sai naga
sa6anin haka, Durqusawa yayi gabana yana kuka
kaman qaramin yaro yana bani haquri ya cutar dani
yayita surutansa har yagama bance masa komaiba,
Yatashi yagoge fuskarsa wai inshirya zai maidani
wurin aikinsa nanfa aka fara sabuwar rigima dan
bazan yarda yakaini wani sabon guri ya ajiyeniba
alhalin bansan kowa agurinba, Nan nashiga rera
kuka yazo yana lallashina amma naqiyin shiru, Yayi
yayi naqiyin shiru sai shima ya zauna ya fara kuka
lokacin abin ya bani mamaki ace kamarsa yana
kuka sai ya bani tausayi ahankali na daina kukan
natashi na bashi guri intaqaita miki jabo saida yayi
nasarar barin wannan gidan dani...
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
10
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥<×><×><×
>PART 10<×><×><×>
Nayi kewar maman sumayyah maqociyata sosai
amma yana iya sai haquri, Zamana dasu na waye
sosai kuma nayi clean coz sumayya yarta yar
duniyace irin shigar datake agida da yanda take
hulda da mutane nima na koya dama nima ba
bayaba gurin shed'ana lokacin idan kika ganni sai
kince nayi karatu ne wata university jabo....
Mun isa gidan da zamu zauna, Gida qaton gaske
yanada part biyu a dayan gefe muka wuce da
kayana gidan yaci uban gidan da na zauna sau dubu,
A parlour na zauna fuskata a daure yaqare gyara
komai ya siyomin pizza inajin yunwa dole naci, Yazo
yazauna yaci gaba da bani haquri har ya gaba ban
ce mishi komaiba, Ina kwance ina game da wayata
najiyo hayaniya awaje kuma ga dukkan alamu da
hausa ake fadan hayiniyar tayi yawa kamar ma
gidana ake yinta ina fitowa nayi karo da wata mata
yar lukuta da ita dan takaiki jabo an, Ina zuwa abdul
azeez yachanza yare yakoma farsi yace (turu khuda
ba zabani khudamun juluyesh harf nazan namikhom
alan bi fahme)Dan Allah karkiyi magana da hausa
dan banason yanzu ta gane abinda muke ciki, Matar
itama da yaren tace (khub agyar nami khod bi fahme
y kari kun)Idan bakason ta gane kasan yanda zakayi
dani, Sukayi ta magan ganu da yare inajinsu basusan
adaqe nake kallonsuba dan duk inajin abinda suke
fadaba gashi batama iya yaren ba, Abin yabani
dariya sosai yanda take cewa sai ya maidani inda
yadau koni ita bazata zauna daniba, Araina nace
nima bari in ta6a nawa iskanci dana koya agurin
sumayyah, Na matso kusa dashi na rige hannunsa
yanda koda yayi qoqarin kwacewa bazai iyaba nace
masa eshqam (my dear ) Wannan matar da ka samo
tazo tana mana haushi agida kaman karyafa?? Ta
juyo da qarfi da daga hannu ta wankeni da wani
wawan mari, Kaji tassss itama ya wanketa da mari
nima na wanketa da mari sai tayi sololo tana
kallonmu dan gaskiya ta mata yawa nima nasan nayi
jarumta jabo, Dan matar agirme ta girmeni takai
34yrs fa nasaka hannuna na damana rungumeshi ta
baya na kwanta a qirjinsa, Nace mata duk iskanchin
da zakiyi karki kuskura kice zaki dagawa mijina
hankali najawoshi shiko solon sai ya biyoni nashiga
daki na kullu qofa ni na barta a parlour tana zage
zage ta fasa abunda zata iya fasawa ta gaji ta tafi,
Ingayamiki jabo tunda nashiga daki na wuce bayi na
kulle kaina shiru har yakirani na kunna ruwa yaji
qaran ruwa yasan dai cewa inajinsa yayi jira yayi
buga gofa har ya gaji nayi banza dashi, Kinsan
wannan matar wai matarsace ashe dama yayi aure
har sunada yaro, Ke wllhy jabo haka nasamu kaina
ina bala'een kishi da matarsa dukda nasan cewa
banasonsa, Amma matar ta bani haushi, Nayi kuka
har na nagaji, Nidai bansan bala'een da yake biye
daniba niba uwaba dasai ingayamata haka nayi ta
fama da baqin cikin kishiya amma duk da haka
tsorona take dan duk bala'een da zatayi bata zuwa
kusa dani saidai tayi nesa dani, Ataqaice ingayamiki
hauwa jabo, Matarnan maza takebi ke hatta yaron da
ta haifa ba na azeez bane kuma duk ni na ganesu,
Yanda akayi kuwa shine....
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
11
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA♥♥♥<<•>•<•>
•>>PART 11<<•>•<•>>
… Ina gaya miki jabo kullum idan abdul azeez ya fita
sai tayi wata baquwa da qaton hijabinta kinsan
Iranian akwai saka hijabi kaman larabawa to haka
baquwarta take zuwa kullum, Kuma sai mijinta ya
fita ranar ina wajen swimming pool ina kallon ruwa
sai kawai naji maganar namiji amma da farsi suke
magana tana cemishi.... Kaima kasan ina sonka
kuma nafisonka akan Wannan mutumin wllhy abu
kadan nake jira in kama gabana dan nagaji da zama
dashi,Nidai duk wuya duk dadi karki manta dani
kinsan idan baki bazan iya rayuwa ba, Duk wannan
maganar da yaren farsi sukeyi, Basusan inajinsuba,
Abinda yasa ban gara tantacewaba kuwa shi yaren
farsi bashida mace ba namiji suna zuwa tace mishi
karyayi magana ga yar iskar yarinyar nan sukayi
dariya a hankali suka wuce kinga zargi bashida
kyau jabo, So banyi saurin zarginsuba duk da haka
amma abin ya dauremin kai matuqa dan kuwa
muryan namiji sosai naji, Bayan kwana biyu yaqara
zuwa ita kuma tadan fita sai nace masa batanan
yayi kaman bayajin hausa inata magana ba amsa sai
kawai namishi na kurame najawo hannunsa nashigo
dashi sassana na zaunar dashi a parlour har
tadawo, Tunda muka shigo parlour na yake bina da
kallo duk inda nayi, Naji tsoro sosai dan kallon da
yakemin kallon da saurayi yakema budurwarsane,
Nashare kar yagane, Ya miqe tsaye yamin alamar
zai tafi inda nayarda namijine takalminsa dana gani
number 46 nasan ba qafar maccen da zata saka
wannan takalmin nakwashe dadariya nashe da
shigiyar qafa taki kamar ta masu kwasan kashi,
Yajuyo ya kalleni rai abace amma baicemin komaiba
na sake cewa kinsaka hijabi kin rufe rabin fuskarki
kamar munafuka daganin yanda yakeyi nasan
yanajin abinda nake cewa amma ba halin yamin
magana asirinsa ya tono naqara cewa tsawo kamar
palwaya nace duk mijin da ya aureki yayi asara
mace kamar namiji ga munin bala'een dagani kin
hada dangi da bare bare wannan uban muni haka kai
amma duk yayi qawance dake yaji haushi itama
maryam din asara ne yasa tayi qawance dake,
Wannan magan ganun da nake masa inayine dan
kawai yayi magana inji shin namijine ko mace amma
yaqi yayi saima daure fuska da nayi muka kawo
kofar shiga gidan ta nace mishi (khuda hafee) Sai
anjima yanda nafada irin nayan koyo kar yayi
tunanin na iya yaren, Yamin murmushi ya daga
hannu araina nace kinga gardin banza wllhy wannan
namijine kuma saina tona musu asiri abin duniya ya
isheni sai wata dabara tazomin kamin suzo lambu
suyi hira sai insaka wayata agurin inyi recording din
abinda suke cewa hausa da farsi duk ina ganewa
ranarda nasami abinda nakeso kuwa ranarda sukayi
maganar cewa shi ya gaji gaskiya zai sace mustafa
(sunan yaronta kenan) Dan yana buqatar dansa
agidansa tanata faman roqon ya rufamata asiri har
taqare hada dukiyarta sugudu tare sun saka ranar
da zasu gudu nikuma nashirya tona musu asiri
karkiyi tunani cewa wani abu yana shiga tsakanina
da Abdul azeez aah ba komai tsakaninmu dashi sai
sallama, Sai sannu da zuwa, Ranar da safee natashi
yana fitowa nace masa inada magana dashi yau
misalin qarfe biyu na rana yazo gida kuma banason
idan zaizo yagayawa uwar yayansa zaizo kawai
idan lokacinda nakeson ganinsa yayi zan kirasa
yakuwa amince yanajin dadi, Yadauka wani abune
kwarton maryam yana zuwa, Da kamar awa daya
nakira Abdul azeez nace yazo da sauri kuma kar
yazo da motarsa…………
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
AURE KO ZAMAN GIDA
*PART 13
Na Hauwa M Jabo.
Tunda muka iso nake tunanin yanda zan bullowa
plane in mishi magana amma nakasa saboda banga
fuskaba sai nayanke shawarar bari in toneshi ingani
haushi zaiji idan yaji haushi sai inbashi haquri haka
kuwa akayi bayan sallar isha yana zaune kamar
wani gunki nazo ina kur6ar tea ahankali nace masa
kana tunani uwar yayanka maryam ne...!??? Ya
waigo ya kalleni cike da mamaki da al'ajabi nasake
maimaita abinda nace naqara da cewa ko in samo
maka pic dintane ka kalla ko kaji sanyi,? Namiqe
tsaye nace ko kawai kabita qiyama ku soye acan
zaifi kazo nan kana tunaninta ko ka kar6o yaronka
agurin kwarton matarka nasan shi yake damunka.!,
Na kama hanyar dakina naji an kamoni ta baya da
qarfi wllhy jabo saida cup din da yake hannuna ya
fadi, Kinsanni akwai iskanci amma akwai tsoro, Ya
jawoni daf dashi ya d'ago kaina da qarfi yana
kallona har inajin nunfashinsa yana dukan fuskata
yace wllhy wllhy Wllhy..!!! Idan kika qara yimin
maganar maryam da mustafa sai kingane baki da
wayo a gidannan ya dallamin wata muguwar harara
sannan ya sakeni, Nace nasan zaka iya kasheni ma
tunda na rabaka da uwar yayanka da danka da kake
tunanin ita kadai zata iya haifa maka yaya, A fusace
na fadi maganar ashe mutumin yagane kishi nakeyi,
Sai yayi murmushi kawai yaje yazauna, Nasha jinin
jikina na wuce daki sumuy sumuy kamar munafuka,
Bayan kamar awa uku sai gashi yashigo dakina naji
tsoro sosai, Yazo daf dani yazauna ya sunkuyar
dakanshi yacemin zaki'iya zama dani zainab.?
Araina nace miya kawo wannan tambayar? Kinyi
shiru ina tambayarki zaki iya zama dani ko yaya??
Nanma ba amsa ba, Ya d'ago kai ya dubeni yace,
Zainab arayuwarki na cutar dake fiye da tunanin duk
wani makhluqi, Zainab banta6a son wata ya maceba
sai akanki, Tun kina yar shekara tara na nemi
mahaifinki ya bani aurenki kuma ya amince inda na
fara ganinki kinje wani gida kina talla sai wasu yara
suka qwace miki cinikin da kikayi duka suka gudu
kina kuka na hadu dake natambayeki kikamin
bayanin yanda akayi na biya kudin nakuma rakaki
har qofar gidanku idan zaki iya tunawa, Wllhy tun
lokacin Allah ya dasamin sonki azuciyana nagayawa
babanki yace yamun alqawari zai bani ke da yake
lokacin ina boarding school nakoma makaranta duk
abokaina sun san sunanki har naqare karatu naje
university ina university Kullum sai inzo da mota inyi
parking inda kuke tsayawa talla inyi ta kallonki har ki
saida waranki har nazo nafara sayen waran ina
cewa kiyi sadaka amma darana daya baki ganni ba
bakiga fuskataba lokacinda naga kinfara tasawa nayi
tsoron kar wani ya kwaceminke nayi magana da
iyayena dagyar suka amince kuma nagayamusu
yanda nashirya za'a dauramin aure dakene dan kar
wani ya gwacemin ke nacewa babanki ki riqa saka
hijab hadda niqab kuma duk suka amince da hakan
akan zanje wani.....
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
14
AURE KO ZAMAN GIDA 14
Na Hauwa M. Jabo
…Course idan nadawo saiki tare Kullum kina raina
amma nayiwa iyayena alqawarin saina qare karatu
zanyi maganarki, A iran na hadu da maryam
maryam tanunamin qauna ta gaskiya tun kafin muyi
aure muke harka da ita kuma banta6a ganinta da
alamar cewa tanada saurayiba nandanan nayi
maganar aurenta ba musu aka amince dan dad dinta
abokin dad dinane sosai, Ban ta6a son maryam ba
saidai sha'awar ta da nakeyi saboda ta iya duk wata
kissa da mace zatayi taja hankalin namiji matuqar
yanada lafiya, Tanada abubuwan da nakeso ajikin
mace wato nonuwa Kullum su suke rudani ajikin
maryam sam ba ita nakesoba, Ta haifi Mustafa Allah
ya dauramin son yaronnan har nake ganin idan
bashi bazan iya rayuwa ba inason mustafa sosai
lokackin nasami kaina kamar baniba, Sam ban damu
dakeba sam ban damu da inji labarinkiba kullum
daga maryam sai yaronta mustafa nima ina
mamakin kaina sosai da yanda na cutar dake bayan
aurenki na auri maryam amma maryam bata
qaunarki mustafa yayi wani ciwo aka kaishi asibiti
Dr yace damuwar mahaifiyarsa ce ta shafeshi kuma
idan bamuyi hankaliba zan iya rasa mustafa nan
dana hankalina ya tashi na rude ina tambayarta
miyake damunta nan tace ita sai na sakeke nagaya
mata bazan iyaba dataga ba nasara sai tace in mata
alqawarin bazan kula dakeba matsawar tana da
rayuwa Wannan ne na amince dashi dan gudun
6acin ranta ya shafi mustafa nadaina kulaki. Tun
daganan nadaina kulaki duk dan mustafa yasamu
lafiya amma ina shan azabar rashinki sosai sai
gashi wacce na cutar na wulaqanta itace tazo ta
fitarda rayuwata daga hadari ta ceceni zainab
kiyafeni pls wllhy nayi danasanin abinda na aikata
muki Kullum damuwar hakan ke sakani damuwa
inasonki sosai zainab amma na cutar dake ya fashe
da kuka mai ban tausayi wllhy hauwa jabo bansan
lokacinda na rungumeshi ba ta baya ina
rarrashinsaba lokacin na gama wayewa duk wani
makirci na mata na iyashi duk a tv na iyasu wani
channel (muharati zandagi) Rayuwar aurecekawai
da zama da iyayen miji ake koyarwa, Duk wani
rarrashin miji da tsokano mishi sha'awa na iyasu a
lokacin, Na juyo dashi na lashe masa hawayensa na
daura hannuna akansa cike da mur mushi nace
masa duk abinda kamun na yafemaka nima ka
yafemin tun daga ranar muka shirya da abudl azeez,
Kinji tarihin rayuwata hauwa jabo, Hmmmmmmmm..
Kinyi mantuwa zainab bamu qareba baki gayamin
first night dinki ba, hahaha ke hauwa jabo miye naki
aciki tarihinane kuma na baki, Kiyi haquri ki qarasa
min kinsan zee khalifa idan na bata labarin
bawannan bayanin bazataji dadinsaba, Dan nasan
tafison nan da ko ina, hahahaha, Owk zan fadamiki
ne saboda namesake dina amma bari muyi sallah ko
jabo...?
Kukasance tare dani a AURE KO ZAMAN GIDA part
15
♥♥♥AURE KO ZAMAN GIDA 15
Na Hauwa M. Jabo
…Bayan mun qare sallah mukaci abinci taci gaba da
bani labari,
Ingayamiki jabo ranar tare muka kwana da abdul
amma ba abinda yamun, Mun kwana biyu da
shiryawa ranar na uku ina bacci sai na farka ashe
mutumin naki idonsa biyuu daganandai aka raya sunnai
Tun taga ranar muka shirya da mijina sai
Kinga yanda muke rayuwa dashi gwanin ban
shi'awa yana bani muhimmanci fiye da tunaninki
jabo, Duk wata al'ada ta Iranian ita yake mun dan
kuwa duk inda zamuje shi yake daukarmin jaka shi
yake daukan beby kuma yana riqe da hannuna,
Wllhy hauwa jabo nikaina banason yanda yakemun
kinga nan Nigeria idan akaga mijinki yana miki
hidima sai ace kin mallakeshi yazama mijin hajiya
alhalin ba haka bane so da soyayyah ne ya haifar da
haka, To ina kika iya Turkish?? Kai hauwa jabo
akwai son labari to honeymoon mukajeyi Turkey
achan na iya tukish, Gaskiya labarinki yamun dadi
sosai zainb, Muna zaune sai ga mijin yashigo inaga
baisan cewa akwai baqi agidanba taje da gudu ta
rungumeshi yafara kissing din bakinta ina kallo
hannunsa na murza basawanta ahankali bashiri nayi
gyaran murya, Sai yasauke hannunsa akan
basawanta ya juyo yace baquwa mukayi nace eh
sannu dai jabo nace yauwa, Zainab tace nabata
labarin wahallada ka banine kaida uwar yayanka
taga ya lumshe ido yace yazanyi son maryam dina
ya rufemin ido banaji bana gani sai ita a really miss
u my mery.!! Tuni naga ta chanza fuska na
tabbatarda kishine yake damunta tajuya zata tafi
yabi banyanta da gudu yana dariya nakai 30mnt ni
hauwa jabo ina jiran sufito amma shiru sun mayar
dani kwalin taba nadauki yar wayata naqara gaba
amma naji haushi sun manta dani Lallai yau naga
aya, Inama ace nice..
Laifin dadi qarewa Hauwa Muhammad jabo take muku sai wata rana sai mun hadu a sabon littafi mai suna qarin jini,
adsense 2 here