Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, February 3, 2017

Bakin kishi complete

adsense here
Bakin Kishi 1 Posted by ANaM Dorayi on 08:16 AM, 29-May-15 Farko Ta sunkuyar da kanta da sauri kana ta sa tafukan hannunta ta rufe idanunta, "Allah da gaske ka ke Alhaji?". Ta bukata da muryar kunya. "Allah da gaske na ke Zainab...Ni fa mallakar ki ce kawai hutu da kwanciyar hankalina a yanzu. Wai ki na tunanin idan ban mallake ki ba, zan iya ci gaba da kyakkyawar rayuwa? Kin ko yarda da son da nake miki?" Ta yi gaggawar girgiza kai, "Wallahi ba haka ba ne Alhaji." Ta fada da saurin baki, a lokaci guda kuma ta na mai ci gaba da girgiza kan. "Wallahi Alhaji na san ka na so na, kuma na yarda da sonka gare ni, kamar yadda na ke fada maka kullum ne, abu guda kawai na ke jin tsoro a tattare da aurenka...". "Dakata Zainab". Ya katse ta ya na mai daga ma ta hannu, "Ni fa sam-sam ba na kaunar ki rika dawo da hannun agogo baya. Ya kamata zuwa yanzu a ce kin gamsu da abubuwan da na jima da fada miki. Don Allah ki saki ranki, ki manta da wannan...shin wai akwai wanda ya isa ya hana ikon Allah yiwu wa? Ko kuma idan Allah ya tabbatar da ke a matsayin matata duk dunutar nan akwai wanda ya isa ya hana? Wannan abu da ba kanta farau ba." Ya yi kasa-kasa da murya, "Don Allah ki sa tsintsiya ki share wannan daga ranki...komai na Allah ne". "Haka ne". Zainab ta ce da nisawa, "To Allah ya taimake mu, Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi gare mu." "Amin". Alhaji ya amsa a takaice, kana ya ce, "Amma fa addu'arki ba ta cika ba." Ta daga kai ta dube shi fuskarta kunshe da alamar tambaya. "Mene ne saura a cikin addu'ata?" Ta bukata. "Sai kin biya zan fada miki." Cewar Alhaji. "Nawa ka ke so a ba ka?" Ta ce da dariya. Ya nuna ta dan yatsa, "Zainab na ke so a ba ni". Ta yi dariya bayan ta sunkuyar da kai, "Ai dama Zainab taka ce, tunda babu wani a zuciyarta sai Alhaji Basiru. Nemi wani abin daban, wannan ka samu." ya yi dariya, "To ai shi kenan...dama ni Zainab ce burina, tunda kuwa tawa ce ai shi kenan an biya ni. A cikin addu'arki kin manta ba ki ce Allah ya kara mana dankon soyayya da kaunar juna ba." Ta kasa dago kai ta dube shi don kunya, "Ai wannan addu'a ita ce a ruhina Zainab kowace rana, a kwance, a zaune, a tsaye ko a tafiye, babu abin da Zainab ke yi sama da wannan addu'ar". Ya ji dadin abin da ta ce don haka sai da ya yi wata yar takaitacciyar dariya kafin ya ce, "Na gode kwarai zainab, kuma ina yi wa Zuciyarki albishir da cewa, ni ma haka na ke, kowace rana, ko yaushe, a cikin kowane lokaci da ke na ke motsi a cikin zuciyata. Babbam fata nashi ne, Allah ya tabbatar da kyakkyawan kudirinmu, a wayi gari a zahiri kin zama mallakata, ba a bafini ba." "Amin". Ta amsa a zuci. A zahiri kuma murmushin jin dadi kawai ta yi. "Ya na ji kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Ya ce ya na yi ma ta wani irin kallo. "Na fada fa a zuciyata." Ta ce har lokacin kanta a duke. "To ai ni ban ji ba". "Yanzu ya ya ka ke so a yi?" Ta bukata. "Ina so Zainab ta dago kanta, ta kalle ni ta kuma amsa mini da, amin". Ya ce idanunsa a kanta. Ta dago ta kalle shi. Da sauri sai ta kuma mayar da kanta ta dukar, "Ni ba zan iya kallon ka na fada ba." "To ya ki ke so a yi?" Ya bukata. "A yafe mini na fada a haka." Ta ce da muryar kunya. Ya yi murmushi, "An yafe, fada a hakan". "Amin". Ta fada da wata irin tattausar murya. "Amin me?" Ya dawo da hannun agogo baya. "Amin, Allah ya kara mana kaunar junanmu ko?" Ta ce da karfin hali. "Au tambaya ma ki ke?" Ta girgiza kai da sauri. Su ka fashe da dariya lokaci guda. *** Alhaji Basiru ya yi murmushi a karo na farko tun tsawon kusan mintuna talatin da su ka shafe su na musayar yawu da maidakinsa Hajiya Rukayya. "Ba ki fahimce ni ba Hajiya... Wallahi a cikin wannan al'amari ba na nufin tozarci ko cin zarafi a gare ki, kuma ko da wasa ba..." Dole ka ce haka." ta katse shi murya na rawa, "Dole ka ce ban fahimce ka ba Alhaji...ya za a yi ka fahimta na fahimta, ai abin sai ya yi yawa?" Ta tsahirta ta na kokarin daidaita numfashinta da ke ynkurin dauke wa. Hakan shi ya haifar da shirun wucin gadi a tangamemen falon. Yau kusan watanni biyu kenan da Alhaji Basiru ya fara fuskantar wannan matsala a wajen uwargidan tasa. Koda ya ke ba ya raba daya biyu ya san dalilin da ya jawo hakan, bai wuce shawartar ta da ya yi ba akan zai kara aure. A kalla shekarunsu uku su na zaune, zama na lafiya da kwanciyar hankali, har da arzikin yaya biyu mata (yan tagwaye), amma tun da ya shawarce ta kan karin auren, kwanciyar hankali ta karanta a gare su. Alhaji Basiru ya numfasa bayan dan gajeren tunani da ya yi. Kamar koda yaushe kokarinsa daya ne, duk lokacin da su ka yi irin wannan sa'insa, ya gamsar da ita ta amince da halaccin kara auren nasa. Da sanyin murya ya soma da kiran sunanta. Ba ta ko daga kai ta kalle shi ba balle ta amsa. Hakan bai dame shi ba. Ya ci gaba, "Gaskiya ban taba tsammanin za ki bijire wa wannan abu da na zo miki da shi ba, musamman ma da na yi la'akari da cewa, addinin musulunci ne ya ba ni damar yin wannan abu, kin kuwa san shi kadai ne addini a wajen mahaliccinmu. Kada fa ki manta Allah madaukakin sarki, a cikin Alkur'ni mai girma cewa ya yi, "Ku auri bibbiyu, uku-uku, hurhudu, idan ba za ku iya adalci ba ku auri daya..." To kin ga anan ina da kwakkwarar hujja ta kara aure, tunda kuwa insha Allahu zan iya yin adalci a tsakanin..." "Ka ga saurara Alhaji". Ta kuma katse shi a karo na biyu, sai dai wannan lokacin cikin karaji ta yi maganar, kuma muryarta na kunshe da alamun tsiwa sabanin maganganun da ta yi a baya. Lokaci guda kuma ta mike daga kan tattausar kujerar alfarmar da ke cikin jerin kujerun da su ka gewaye falon. Da muryar tsiwa ta ci gaba da cewa, "Dole ka yi min wa'azi yanzu tunda ka na bukatar aure, Na- mamajo! Ai a lokacin da ka ke matsiyacinka tsumma gaba tsumma baya ba ka tarka ba, sai yanzu da mu ka gama shan wahalarmu, ka ga ka yi arziki za ka je ka auro wata banzar-bazara wadda ba ta san halin da mu ka shiga ba, ta zo ta ci bulus! To, ba zai yiwu ba, wallahi ba zai taba yiwu wa ba, ka ma sake tunani tun dare bai yi ma ka ba...domin kuwa na sha alwashin matukar ina motsi a doron kasa kuma ina cikin gidan nan, babu yadda za a yi wata shashasha ta zo ta samu gindin zama balle har ta mike kafa". Ta tsahirta ta na duban sa, duba mai cike da raini. Na-mamajo. Ita ce kalmar da ta fi sauran bata wa Alhaji Basiru rai a duk tarin masifar da ta yi masa, domin ya san mayen mata, shi ne abin da kalmar ke nufi. Sai dai kuma duk da hakan, ko kusa ko alama ba zai iya yi ma ta komai ba koda ran nasa zai tafasa ya kone ne saboda abin da ta yi masa, don kuwa shi dai Allah ya jarrabe shi da tsananin son ta, ga shi ya ki jinin rabuwa da ita. Aure dai zai kara ne saboda umarnin Mahalicci da kuma son da ya ji ya na yi wa wadda zai auro. Amma a nata bangaren ba ta la'akari da hakan, shi ya sa duk kalmar da ta fado bakinta ba ruwanta da ta tauna kawai za ta yaba ma sa ita, ita kuma a tunanin ta hakan ne kadai zai sa ta yi nasarar dakushe yunkurinsa na kara auren. Sai dai abin da ba ta sani ba shi ne, duk da irin son da ya ke ma ta, ya kuduri aniyar babu abin da zai hana shi kara auren ko ana ha-maza-ha- mata. Ya numfasa da karfi bayan tsawon lokaci da ya dauka ya na tunanin irin soyayyar da su ka tafka da matar tasa kafin wannan lokacin. Ita kuwa ta na tsaye a kansa kerere kamar falwaya. "Ki kwantar da hankalinki Hajiya". Ya ce bayan ya daga kai ya dube ta, "Zauna, na ga har zuwa yanzu ba ki gamsu da..." sauran maganar ta makale a fatar bakinsa ganin ta juya ta nufi kofar da za ta fitar da ita daga falon. Ya bi ta da kallo cikin damuwa kamar mai kirga takun sahunta har ta fice daga falon. *** Kamar kowace safiya, yau ma ita kadai ce zaune cikin dakin nata, ta yi tagumi ta na sake-saken hanyar da za ta bi don ganin bayan kishiyar tata, abin da ya zame ma ta wajibi a kowace safiya tsawon shekaru ukun da amaryar mijin nata ta tare. Fadi-tashi, kujiba-kujiba da buge-buge babu irin wanda ba ta yi ba don hana auren amma abin ya faskara, aka zo aka yi auren, yanzu kuma ga amaryar kullum kara samun gindin zama ta ke yi a gidan. Sau da yawa takaici da bakin ciki su kan lullubeta ta idan ta tuna da rashin goyon bayan da mahaifinta ya nuna tun farkon al'amarin, sa'ar da ta je ma sa da batun za a yi ma ta kishiya. "Kada ki kuskura na sake ganin kafarki a gidan nan matukar akan wannan maganar ce, mutuniyar banza. Idan kuwa ki ka ki zan saba miki". Maganar da mahaifinta ya gaya mata akan lamarin ta bijiro ma ta a zuciya, ta ji kamar an harbo wani mashin bakin ciki ne ya soki zuciyar. Duk da dai a wancan lokacin mahaifiyarta ta yi wa mahaifin nata martani da cewa, "Haba Malam, gaskiya bai kamata ka ki goyon bayan yarka ba akan wata can". A fage guda kuma, alwashi da alkawarin da ta sha dauka na ba wadda za ta shigo gidan muddin ta na raye, shi ya ke dada daga mata hankali. "Lallai ya dace na dauki matakin gaggawa akan yar iskar nan". Ta tsinci kanta tana mai fada a fili, wanda kuma shi ne abin da ta saba duk lokacin da ta yi irin wannan tunani. "Tabbas lokaci ya yi da ya kamata na san duk yadda zan yi na ga babu ita a gidan nan, ko don na cika alkawa..." Sallamar da aka yi a bakin kofar dakin ta katse furucin nata. "A'a, ah! Baraka...yaushe a gari in ji maki bako. Saukar yaushe? Ta ce cikin fara'a bayan ta kawar da alamun tunani da damuwar da ke kan fuskarta, sannan da gaggawa ta mike ta tari yar siriyar matar da ke kokarin shigo wa dakin. "Oh! Hajiya Rukayya ashe rai zai ga rai". Siririyar matar da ke amsa sunan Baraka ta ce ta na duban tsarin dakin cikin mamaki. Hakika ta san cewa shekaru da dama da su ka wuce dakin ba haka ya ke ba, duk abubuwan da ta sani na daga cikin abin da aka kawo wa kawar tata a sa'ar da ta na amarya babu a ciki yanzu. Kai idan banda ta na tsoron kada ta yi karya ma da sai ta ce hatta kusoshin da aka kafe labulen dakin ba wandada su ka kawo Hajiya Rukayya da su ba ne. Koda ya ke tunanin nata bai zurfafa ba, da ta tuna da labarin shaharar da aka ce mijin nata ya yi.Yau rabonta da su hadu da Hajiya Rukayya tun ranar da ta tare a gidan mijin nata lokacin ya na talakansa. Tun daga wannan rana ba su sake haduwa ba, sai a yanzu saboda tashin da su Barakar su ka yi su ka koma jihar jigawa. "Wayyo Allah makashin kakana". Baraka ta ce daidai lokacin da ta zauna a daya daga cikin manya-manyan kujerun laushin da ke cikin dakin. Hajiya Rukayya da Baraka su ka gaisa cikin fara'a da murnar haduwa da juna. "Cewa na yi bari na zo na gaida ke tunda ke Allah ya yi miki arziki kin manta da mu". Baraka ta ce ta nayatsine fuska. "Uhm! Ke dai bari". Hajiya Rukayya ta ce ta naduban Baraka ido cikin ido. "Ba wani batun arziki, gari ne kawai ya dagule mana...ke dai bari na kawo miki ruwa ki tsotsa". Ta mike ta nufi wata karamar na'urar sanyaya ruwa da ke durkushe can gefe guda. Baraka ta bi ta da harara. "Ban gane gari ya dagule mu ku ba? Mutumin da ke cikin daula irin wannan ya ce gari ya dagule masa? To, mu kuma mu ce me?" Ta daga kanta zuwa saman dakin ta naduban kyakkyawar fanka ruwan zuma da ke makale ta nata faman aiki abin ta. Hajiya Rukayya ta yi wani motsattsen murmushi lokacin da ta dawo gare ta dauke da kwalin tataccen lemon zaki hade da karamin kofi, "Fara jika makogoron..." "Ina fa zan iya jika makogorona ban ji cikakken abin da ke damun aminiyar ba." Baraka ta katse ta bayan ta dawo da dubanta gare ta, "Hajiya wanda ke cikin daula irin ku jin irin wadannan kalamai ai ba karamin tashin hankali ba ne..." "Uhm! Ke dai bari Baraka." Hajiya Rukayya ta shiga cewa bayan ta koma wajenta ta zauna, "Wadannan kyale-kyalen ba su ne ba, al'amarin ya fi karfin su Ni yanzu duk a banza na ke ganin su...ke ni Wallahi da zaman su cikin halin da na ke ciki, gwanda zamana cikin halin da mu ke ciki farkon aurena da Alhaji". Baraka ta yi tagumi hannu bibbiyu bayan ta mayar da hankalinta sosai ga Hajiya Rukayya, "To, ni ban gane abin da ki ke nufi ba. Yanzu ki na nufin ki ce mijinki ba ya iya gamsar da ke ne ko ya ya?" Ta yi shiru cikin saurare da mamaki. "Duk ba haka zancen ya ke ba Baraka, na ga har zuwa yanzu ba ki fahimta ba. Ba ki da labarin an yi mini kishiya?" "Laa....ila...ha...illallahu".Baraka ta yi doguwar hailala ta natafa hannu, "Kishiya? Kishiya fa ki ka ce? A garin ya ya haka ta faru?" "Ke dai bari Baraka, Kishiya na gaya mi ki har da danta daya yanzu a gidan nan". Hajiya Rukayya ta fada ta na gyara daurin dankwalinta, ganin ta gamu da irin mutanen da ta ke son gamu wa da su (Wadanda za su taya ta alhini da nuna rashin jin dadinsu ga halin da ta ke ciki). "Ba shakka!" Baraka ta ce ta nagyada kai, "Ke kuma ki na zaune ki na kallo?" Ta yi shiru bayan ta dubi kasa, "To ya ya na iya da wannan shegen naci na Alhaji". Ta ce ta natabe baki. "Ba ki ga irin wutar da na hura masa ba kafin a yi auren, amma da ya ke Na-mamajo ne duk a banza, sai ya mayar da komai ba komai ba...". "To na ji, yanzu wane mataki ki ka dauka? Ko ki na nufin an fi karfin ki?" Baraka ta katse ta. Hajiya Rukayya ta numfasa, "To, kusan haka din ne Baraka, kin san al'amarin ne..." "Kin ga saurara!" Baraka ta sake katse ta, "Ba wani al'amarin, kawai sakacin ki ne...kya hura masa wutar murhu ki ce kin hura masa wuta? Ai wutar gidan burodi za ki hura masa ki gani idan zai kai labari. Bayan haka ga hanyoyi nan burjuk da za ki dauki mataki kin tsaya ki na cewa al'amarin ne... To tsaya ki na fadin al'amarin ne har ta kuma haihuwar wani da namijin, kin ga shi kenan kin fi ta shan wuyar miji, ita kuma ta fi ki more shi, tunda ke duk yayanki mata ne, kinko san a gado duk namiji daya rabon mata biyu gare shi. Wannan ai shi ne kura da shan bugu, Gardi da karbar kudi. Idan da ni ce ke da tuni ba a yi an gama da shegiya ba...duk malaman garin nan?" "Uhm!" Baraka kenan". Hajiya Rukayya ta fada da nisawa, "ke ce ki ke ganin a zaune na ke, ban da tsananin azaba da masifa da na ke yi mata da baki na, amma kin gan ta nan shegiya, zama daram a gidan nan sai ka ce ba ita na ke yi wa ba." Baraka ta saki wani dan murmushi iya fatar baki, "Wannan magana taki da ban mamaki ta ke...wai kin bi duk malaman garin nan. Uhm! Kin dai bi iya wadanda ki ka sani. To, wai tsaya, mahaifanki ba sa taimaka miki?" Hajiya Rukayya ta yi dariyar takaici "Ke ma dai da bata bakinki ki ke, sanin kanki ne ba zan samu goyon bayan Baba ba, ga shi kuma shi ne tsayayye akan gidan. Kin san shi irin mutanen nan ne ma su halin mutan da, bai damu da abin duniya ba. Babu yadda Umma ba ta yi ba wajen ganar da shi, amma daga karshe ba ki ga fadan da ya yi min ba lokacin da na matsa akan abin, kamar ya hada mu ni da Umma ya daka, wai shi ba mutumin banza ba ne." Baraka ta jinjina kai kana ta yi shiru na dan lokaci, "Lallai ki na cikin wahala Rukayya idan har ki ka biyo halin mahaifin nan naki, Wallahi ba abin da za ki tsinana, sai ki zo duniya a banza ki koma a wofi" Ta tsagaita ya naduban Hajiya Rukayya, jin ba ta da shirin cewa wani abu ya sa ta ci gaba "Yanzu a ina ki ka tsaya, ko kuma wacce shawarar ki ka yanke? Hajiya Rukayya ta saki wani guntun murmushi na jin dadin damuwar da Baraka ta nuna, kana ta ce, "Wannan shi ne abin da ki ka zo ki ka same ni ina yi Baraka, kin san tun da ta shigo gidan nan ban samu zama da sukuni ba, kullum kulle-kullen ganin bayanta na ke yi." Ta rage amon muryarta kamar mai tunanin wani zai iya jin abin da za ta fada, "Ni fa yanzu kuma na fi tsanar dan nan nata saboda abin da ki ka hango mini na game da gado don dai kawai ban san yadda zan yi na kawar da shi ba ne..." "Ba ki dai nemi shawara ba." Baraka ta katse ta, "Ai da kin nemi shawara da tuni kin gama da su ma duka ba shi kadai ba. Nawa su ke Allah na tuba?" "To, a wajen wa ki ke tsamanin zan sami sawarar?" "Hajiya Rukayya ta ce a marairaice, "Dama ke kadai ce abokiyar shawarar tawa tun muna yara, sai kuma furera, ita kuma yanzu babu Naira a gabanta, idan na kai mata wannan shawarar cewa za ta yi na bi duniya a sannu, duniya ba wajen zama ba ce. Kin riga kin san halinta dai tun a makaranta, mutuniyar da ko Alli ka dauka a lokacin za ta fara maka wa'azi Allah ya ce, Annabi ya ce. Wannan dalili ya sa na rufe kofar shawara da kowa na ke gaban kaina, ke kuma kin yi nisa da mu." Baraka ta yi jigum ta na sauraron ta kamar mai tunanin wani abin kirki har Hajiya Rukayya ta tsahirta. Ta nisa, "To kin ga kwantar da hankalinki yau dai zance ya kare tunda na zo...wa ta ke da suna kishiyar taki?" "Zainab". Hajiya Rukayya ta fada da saurin baki. "To, ina so ki ji a ranki Tuni Zainab ta bar gidan nan." Baraka ta ce ta na zare idanu. "Me ya sa ki ka ce haka?" Hajiya Rukayya ta tambaya. Ta yi wani kwakkwaran numfashi kana ta ce, "Ina da wani mutum ne sha yanzu magani yanzu, aikinsa kamar yankan wuka ya ke. Saboda haka idan kin shirya, ki na da wasu yan kudade a kasa, ki zo kawai mu je ki ga aiki da cikawa." Hajiya Rukayya ta nisa cikin mamaki. A tunaninta yadda ta sha wahalar bin malamai kamar ba za a samu wani wanda zai iya biya mata bukatarta ba. "Kar ki yi shakka kwalliya...wallahi wannan mutumin da zan kai ki wajensa ba dama ne" Baraka ta ce ganin ta yi shiru cikin tunani. "Allah Ta-hannun damar". Hajiya Rukayya ta ce bayan ta dan saki ranta. "Au! Ke naki ma wasa ne. Ai idan kin shirya kuma akwai kudi kamar yadda na fada miki, an yi an gama jinyar mayya. Saboda kwarewarsa fa har kirari ake masa da Mai-gobe-da-nisa. Tab! Ai wannan ya yi nisa, ya ci dubu sai ceto." Hajiya Rukayya ta kuma nisawa cikin jin dadi, "yanzu ki na nufin za a samu biyan bukata idan an je?" Ta kuma jinjina abin. Baraka ta dan bata rai, "Don Allah kar ki sa raina ya baci, ni ce fa na fada miki. Ko ba ki yarda da ni ba ne?" Har yanzu akwai kokwanto a fuskarta saboda tunanin irin wahalar da ta sha, amma ba ta samu biyan bukata. Amma don ganin ran Baraka ya soma baci sai ta yi ta maza ta saduda, ta mika wuya, "Yanzu ke ce abar ji, Akuyar daure, mara yanci." "Kin ci abinci Baraka." hajiya Rukayya ta ce ta nadariya, "kuma kar ki damu, ni ma na kusa samun yanci tunda yanzu na hau hanya, kin san kuwa sannu ba ta hana zuwa...saboda haka ki sa mana rana kawai, babu wani abu." Baraka ta cira kai ta naduban kyakkyawan rufin dakin da aka yi matukar kawata shi, alamun ta na tunani, "Me zai hana mu je gobe idan ki na da hali, tunda ni jibi zan koma." Ba ta yi tunanin komai ba ta amsa, "Allah ya kai mu goben lafiya. Amma fa kin san ba na son a fara ta kanta, na fi son a fara ta kan wannan shegen dan, musamman ma illar rayuwarsa da ki ka fito mini da ita." "Wannan kuma ya rage naki sabuwar amarya a dakin miji...gobe idan mun je kya ma sa bayani. Ni zan koma." Ta mike tsaye a hankali. "Tun yanzu?" Hajiya Rukayya ta ce da ita cikin daga murya. "Wallahi akwai gurare da dama da na ke so na kai ziyara kafin na koma jibin, sai dai goben kawai kya ganni." "To, Allah ya nuna mana" Hajiya Rukayya ta ce bayan ita ma ta mike tsaye, "Mu je na taka miki." To, a daidai lokacin ne Zainab ta daga labulen dakin ta shigo gami da sallama, shigowar da ta zamar mata da-na-sani. "Wa'alaikis sa..." Yunkurin amsawar da Baraka ta yi ya gaza kai gaci saboda zungurarta da Hajiya Rukayya ta yi gami da cewa, "Ke ita ce fa!" Baraka ta fahimci wadda ta ke nufi, don haka sai ta mayar da dubanta ga Zainab, a tsanake ta shiga yi mata duban Raini da wulakaci, kamar yadda ta ga Hajiya Rukayyar ta galla mata wata uwar harara. Ita kuwa a nata bangaren maimakon ta damu, sai ta saki wani matsakaicin murmushi, "Yaya bakuwa mu ka yi ne?" "Bakuwa? Ina ruwanki da bakuwa? Ta ki ko tawa? Haijaya Rukayya ta ce fuska a yatsine kamar yakuwar da ta sha matsa. Zainab ta yi kasake ta nakallon su cikin kunya. "Da ke na ke! Bakuwarki ce ko tawa?" Ta kuma fada da tsawa. Zainab ta nisa kana ta kuma yin murmushin karfin hali cikin son mayar da abin wasa ta ce, "Tawa ce mana tunda ta ki..." "Ke rufe mana baki sarkin iya magana, wa za ki yi wa wayo." hajiya Rukayya ta kuma katse ta, "Ki ji mu da yarinya?" Ta juya ga Baraka wadda tunda al'marin ya fara babu abin da ta ke yi sai hararar Zainab din, "A to! Ni ban ma san ta ba, amma kin ji saboda kalen dangi wani bakuwarta ce...ko ta ya ya na zama bakuwarta?" "Oho!" Cewar Hajiya Rukayya, "Wa ya san ma ta, kin gan ta nan kullum haka ta ke shisshige mini wai ita kanwa..." "Kanwarki? A gidan uban wa?" Baraka ta katse ta, "Dama an taba kanwa da abokiyar gaba?" "Ke ma dai kya fada". Hajiya Rukayya ta fada bayan ta mayar da dubanta ga Zainab wadda har yanzu ke tsaye, kai sunkuye, cikin tsananin jin kunya. "Ke!" Ta daka mata tsawa, "Wai mene ne ya kawo ki daki na?" Zainab ta cira kai a hankali ta dube ta, "Ba komai, dama abinci ne na kammala na zo don na sanar da ke". "Abinci?" Baraka ta cafe ta naduban Hajiya Rukayya, "Abinci fa ta ce? Har abinci ki ke yarda ku ci tare? Haba Gaskiya mana ki ka kasa fitar da ita daga gidan. Ai ta riga ta cinye ki...kai lallai ma Rukayya nan da wauta ki ke. Idan banda abinki, wa ke cin abinci da kishiya, wadda idan aka ba ta wuka aka ce ta yanka ki, a guje za ta aikata." Hajiya Rukayya ta girgiza kai, a lokaci guda kuma ta daga hannu, "Kin ga ni fa ba tare mu ke ci ba. Ina ni ina cin abinci da wannan." Ta nuna Zainab, "Ta dai gama ne, ta zo ta sanar da ni kawai. Yo da na ci abinci da wannan ba gara na mutu da yunwa ba." Zainab ta dago kanta da ke duke da nufin ta ce wani abu, sai baraka ta yi mata tsawa, "Ke malama! Ba ma bukatar maganarki, maza-maza ki fice ki ba mu waje tunda nan ba dakinki ba ne." Ba ta kuma wani yunkuri ba, ta juya jiki a sanyaye, zuciyarta cike da nadamar shigowarta dakin. Hajiya Rukayya da Baraka su ka fashe da dariya har da tafawa. "Shegiya kadan ma ta gani." Baraka ta ce, "Yadda na tilasta ma ta ta fita daga dakin nan, haka za ta fita daga gidan nan ko da ba ta so." Suka kuma kwashewa da dariya, kana su ka rungume juna. *** Wata dalleliyar mota kirar KIA picanto shudiya, ta cusa kai cikin tafkekiyar harabar makeken gidan bayan bude babbar kofar da maigadi ya yi. Kai tsaye direban motar ya wuce da ita cikin babbar rumfar kwanon da aka tanada musamman don ajiyar motoci, sannan cikin sauri ya fito ba tare da ya kashe motar ba, ya bude kofar motar ta baya. Alhaji Basiru, baki, kakkaura mai matsakaicin tsawo ya fito kallo daya za ka yi masa ka lakanci ya na da fara'a sosai duk da wadatattun kumatun da ya ke da su. "Sannu da zuwa Alhaji." Dattijo da ya bude mu su kofa ne ya fada bayan ya isa gare su. "Yauwa, sannu malam Bukar." Alhaji Basiru ya amsa, kana kai tsaye ya nufi kayatacciyar kofar da za ta sada shi da cikin gidan, zuciyarsa cike da zulumin abin da zai tarar a gidan, wanda ya zame masa sabo tun lokacin da ya kara aure. Ya daga labulen babban falon shakatawar gami da sallama. Zainab kyakkyawar fara da ke zaune kan daya daga cikin tausasan kujerun da ke kewaye da falon ta amsa sallamar da tuni ta gane muryar da ta yi ta. Cikin fara'a ta mike ta tare shi, ta karbi karamar jakar da ke rike a hannunsa. "Sannu da zuwa Alhaji." Ta ce. "Yauwa, sannu amarya. Yau ke kadai ce a falon? Ina yayar taki?" Ya amsa gami da tambaya. "Ta na ciki wallahi, dazun nan ta shiga." Ta ba shi amsa. Ya nufi daya daga cikin kujerun ya zauna. "Bari na kawo ma abin da za ka sanyaya makoshinka maigida." Ta ce da fara'a bayan ta ajiyr jakar a gefensa. Cikin nutsuwa ta mike ta nufi doguwar na'urar sanyaya ruwa da ke ajiye a can gefe guda, hakan shi ya yi daidai da lokacin da Hajiya Rukayya ta daga labulen falon ta shigo ba tare da sallama ba. "Sannu da zuwa." Ta ce da kyar kamar mai ciwon baki. "Yauwa. Sannu uwargida, kwanciya ki ka yi ne?" Alhaji Basiru ya amsa tare da yi ma ta tambaya cikin rashin damuwa da hade fuskar da ya ga ta yi. "Wane ne ya ce ma kwanciya na yi?" Tambayar kenan da ta fito daga bakinta. Alhaji Basiru ya yi murmushi, "Uwargida kenan...mene ne na zafi cikin wannan tambayar? Gani na yi idonki kamar da alamun barci." Ta yi wani takaitaccen tsaki, "Ni ba barci na ke yi ba, idan ma fada ma aka yi, wanda ya fada ya zama babban makaryaci." "To, ai shi kenan." Ya ce da ajiyar zuciya. Idan da sabo dai ya saba. Wannan wata al'ada ce da ya san ta dauka, ta mayar da karamar magana babba, duk don kar a zauna lafiya. Da yalwataccen murmushi ya dubi Zainab, wadda ke kokarin darkusawa gabansa, hannunta na dama rike da doguwar robar sassanyan tataccen lemon zaki, karamin kofi rike a hannunta na hagu. "Yauwa, a gaishe ki amarya. Na gode." ya fada bayan ya karba. Ta mike cikin jin kunyar abin da ya fada, ta koma kan kujerar da ke kusa da Hajiya Rukayya ta zauna, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Sannu Hajiya, har kin fi..." "Wane irin sannu...ciwo na ke yi?" ta katse Zainab da daga marya, sannan ta shiga jifan ta da wata uwar harara. Maganar ba ta yiwa Alhaji Basiru dadi ba, don haka yace, "Haba Uwargida, wai me ya sa ba..." "Ka ga malam, babu ruwanka a cikin wannan maganar." Shi ma ta katse shi, sannan ta ci gaba da cewa "Ai dama kai ka ke daure mata gindi, idan banda daurin gindin da ta ke samu a wajenka, ya ma za a yi wannan yar matsiyatan ta dora wa Hauwa'u sharri, wai ta yaga ma ta littafi, alhali wannan dan banzan yaron nata ne marar jin magana kamar barawo ya yaga kuma ma wani rainin hankali, na yi magana yarinyar nan ta rufe idanu ta yi min rashin mutunci a gidan nan, zagi ta uwa ta uba..kai in banda ruwa ya daki babban zakara, wannan yarinya ta isa ta ja da manyan mata, yarinyar da na tabbatar a haihuwar kaji na haife ta sau babu iyaka.." Ta dan sarara kadan, sannan ta ci gaba da cewa, "Ko da ya ke ba na mamaki don shi matsiyaci idan ya samu dama babu abin da ba zai iya.." "Ke saurara Hajiya! Zainab ta katse ta cikin fushi tuni fuskarta ta sauya. Da kaushin murya ta ci gaba da cewa "Ina so fa ki sani duk abin da ki ke mini kyale ki na ke yi saboda gudun ka ce-na ce da kuma darajar wanda mu ke aure, amma ba don tsoron ki ba. Kar ki ga ina kauda kaina akan wasu abubuwa ki yi tsammanin ban san abin da.." "Zainab" Alhaji Basiru ya katse ta ta hanyar kiran sunanta. Da girgiza kai ya ce, "kar na kara jin bakinki" Ranta ya yi mutukar baci, amma duk da haka sai ta shiga tausasar zuciyarta don bin umarnin mijin nata Ita kuwa Hajiya Rukayya sai ta mike tsaye ta natafa hannu ta nafadin "Ka kyale ta mana ta gani idan da yau sai na dandaka ki a gidan nan, don ina da tabbacin ko daga barci na tashi na fi karfin ki." Da wannan maganganu ta fice daga falon. Bayan fitar ta sun dauki tsawon lokaci babu wanda ya ce da wani komai. Alhaji Basiru mamaki ne ke damun sa da tunanin, yaushe za a kawo karshen wannan abin da ke faruwa a gidansa. Da ya ke ya san mai laifin sai ya numfasa a hankali, ya dubi Zainab, "Ki kara hakuri akan wanda ki ke yi da, komai na duniya watarana tarihi ne." Haka ya ci gaba da tausar ta saboda ko da yaushe dai kokarinsa ya daidaita tsakaninsu, don ba ya son rabuwa da kowaccen su, kamar yadda zuciyarsa ke ba shi shawara wasu lokutan ya kawo karshen matsalar ta hanyar saki. Amma idan ya tuna illar sa a addinance sai ya danne zuciyar tasa ya lallashe su. Lokacin da ya tabbatar ya gama tausar zuciyar zainab, sai ya mike ya bi bayan Hajiya Rukayya da nufin ita ma ya tausashe ta don a samu zaman lafiya. Amma ko da ya shiga dakin ya na yi mata magana sai ta yi kamar ba da ita ya ke ba. Don ya tabbatar ma ba za ta saurare shi ba sai ta shiga rera wasu wakoki na habaici gare shi. A daidai lokacin da wannan ke faruwa, acan bakin kofar gidan ma wani abu ne ke faruwa tsakanin malam Bukar maigadi da wasu bakin turawa da su ka zo wajen Alhaji Basiru. Turawan biyu yan asalin kasar Ingila ne, wanda a nan fiye da rabin harkokin Alhaji Basirun su ke. Kuma su ba sa jin Hausa, yayin da shi kuma Malam Bukar ba ya jin Turanci. Tsawon lokaci su ka kwashe suna musayar yawun da ba shi da amfani, don kuwa babu wanda ya fahimci dan uwansa, saboda rashin gane abin da kowa ke cewa. Baseer, shi ne abiin da turawan ke iya furtawa na daga sunan Alhaji Basiru. "Na ce mu ku a nan gidan kaf Babu Baseer, sai dai Alhaji Basiru kun ki yarda ko? To shi kenan sai ku yi ta yi, idan kun gaji da tsayuwa kwa tafi." Malam Bukar ya ce a kufule ganin suna kokarin cusgunawa daddadan gyangyadin da su ka zo su ka same shi ya na yi. Turawan biyu su ka kuma duban junan su cikin rashin fahimtar abin da ya ke nufi wanda kuma shi ne abin da su ke yi duk sa'ar da ya yi maganar. "Have you understand what he is saying?" Daya baturen ya ce da dayan. Wanda aka tambaya ya girgiza kai, alamun bai gane ba. Baturen da ya yi tambayar ya kuma duban malam Bukar fuska cike da alamun damuwa, ya kuma maimaita bukatarsu gare shi. "To, ai kuma sai ku yi tunda ni dai na yi mu ku bayanin babu wani Baseer a nan kun ki yarda. Yanzu kuma ga shi na ji ka tsiro da wani sabon abu kamar ka na ambatar Talle ko mene ne? Sai ku yi ta yi, dama ai mu na samun labarinku, ba ku da aikin yi sai shariri ta..mutanen da ke kula da lafiyar Beraye don sun tambayi abin da babu har wani abin mamaki ne? Ya na gama gadar haka ya rufe idanunsa kana ya langwabar da kansa a kan majinginar kwantacciyar kujerar mai kama da gado, wadda aka yi ta da icen makara ya ci gaba da gyangyadi abinsa. Turawan su ka kuma duban junansu cikin damuwa kana su ka kuma kallon malam Bukar wanda tuni ya fara layi irin na ma su gyangyadi. Wanda ke yi ma sa tambayar ne ya tuno wata dabara. A hankali ya mika hannu ya taba kafadar malam Bukar. Firgigit! Ya tashi sauran kiris ya hantsilo daga kan kujerar. Daga bisani ransa ya kara baci da ya ga cewa har yanzu turawan nan ne da ya tsana da gani su ka tashe shi. Ya mike cikin fushi da zummar kai duka gare su amma saboda labarin da ya taba samu a kauyensu tun ya na saurayi cewa, wai fararen fata jikinsu kamar nunanniyar Gwanda ya ke saboda rashin kwari, idan baki ya kuskura ya doke su mutuwa su ke yi domin wai jini ne zai fito daga jikin nasu, su kuma ba sa kaunar su ga jini a jikinsu, wai saboda haka sai yi fushi su mutu. Tunanin hakan ne ya sa shi sauya abin da ya yi nufi a farko na kai mu su duka, zuwa fadin, "Kai wai ku diyan gidan uban wane ne da za ku dame ni? Na ce mu ku ba mu da wanda ku ke fadi a gidan nan kun ki yarda. To, wai me ku ke nufi ne don buhun ubanku?" Turawan ba su damu da fadan nasa ba, don dama ba sa jin abin da ya ke fada. Don haka kawai sai dayan Baturen ya daga hannuwansa biyu kamar yadda ya yi nufi, ya fara yi wa malam Bukar zance irin na kurame da su. To, a sannan ne malam Bukar ya fara fahimtar su. Bayan dan lokaci da ya dauka ya na duban Baturen sai ya fahimce shi. Take shi ma ya sauya zuwa hakan. Cikin kankanin lokaci su ka fahimci juna duk da ba yarensu daya ba. A cikin tattaunawar tasu ne, Malam Bukar ya tambaye su, abin da ya sa ba su buga masa waya ba. Su ka sanar da shi sun nema ba su samu ba. Da fara'a ya sanar da su, su yi jiransa ya je ya sanar da Alhajin zuwan nasu. *** Tabbas Malam Bahaushe ya yi kyakyawan tunani da ya ce, " Sa kai ya fi bauta ciwo" Hakika haka abin ya ke, don wannan karin maganar ya yi tasiri akan Hajiya Rukayya wacce sau da yawa ta kan gagara tashi sallar Asuba ko da kuwa an tashe ta. Amma ga samun sauyi sai ga shi yau ta tashi tun kafin kiran sallar farko, saboda bukatar kanta. Bayan ta yi sallar Asuba, a gurguje ta shiga wanka, cikin mintinan da ba su fi a kirga da yatsun hannu ba ta fito, kana a gaggauce ta sanya kayanta ta fito fes da ita. Ta isa ga wani tafkeken madubi da ke kafe a jikin bango wanda a shi ne take yin kwalliya a duk sa'ar da ta yi wanka. Ta kare wa kanta kallo tsaf a cikin madubin kana ta yi murmushi. "To, yanzu me ya rage mini?" Ta tambayi kanta a fili ta cikin madubin, kamar mai neman shawarar siffarta da ta bayyana akan madubin. "Abu uku ne kawai ya rage miki." Zuciyarta ta kissima ma ta. Ta fadada murmushinta lokacin da zuciyar tata ta ci gaba da jero ma ta abubuwan da ya kamata ta samu. "Kudi da neman yardar Alhaji, da kuma jiran zuwan Baraka" Yanzu su ne abubuwan da su ke gabanta Shakka babu ya zama dole ta nemi yardar Alhaji Basiru a wannan karon, ba wai don ta nashayin zai iya hana ta fita ba, a'a, saboda ta nason ta fita da mota da kanta don gudun kar asirinta ya tonu idan sun fita da direba. Ta riga ta san duk abin da take so Alhaji Basiru zai ba ta, ko don a zauna lafiya. Amma fa banda barin ta ta ja mota. Haka dabi'arsa ta ke, ba ya barin iyalansa su ja mota da kansu sai dai duk inda za su a kai su. A tunaninsa, abin kunya ne a ce mai kudi kamar sa ya bar matansa su na jan mota da kansu. Tunda kuwa ta san da haka, lallai akwai bukatar ta lallashe shi ta kowace irin hanya don ya bar ta ta fita ba tare da direba ba. Al'amarin kudi kuwa da sauki-sauki, don ta natunanin wadanda ke hannunta ma za su iya isar ta, duk da ya kamata ta nemi kari. Sai kuma jiran Baraka, wanda ya zama dole don ita ce idon garin. Ta kuma yin murmushi cikin madubin a karo na biyu, ta namai yabawa da kyakkyawan tunanin da ta yi. A hankali ta juya, ta bawa mudubin baya kana ta fara duban gefe da gefen dakin a tsanake kamar mai tsammanin ganin wani a dakin bayan ita. Ba wani abu ta ke tunani ba kawai ta na fasalta adadin yan gaisuwa da zaman makokin da dakin zai dauka ne. Lokacin da ta isa dakin Alhaji Basiru a kishingide ta same shi a kan doguwar kujerar da ke cikin kujerun da ke dakin. Sau biyu ta yi sallama amma bai dago ba balle ya amsa. Ba wai bai ji sallamar ba ne, amsawar ce kawai ta gagara saboda hankalinsa ya tafi duniyar tunani, kuma ba wani abu ya ke tunani ba da ya wuce matsaloli na rigingimun da ke faruwa a tsakanin iyalan nasa, da kuma hanyar da zai bi ya warware su. Wannan shi ne tunaninsa a kullum. Sai dai baya ga wannan, yau akwai wani, tunanin gayyatar da aka yi masa zuwa kasar ingila a game da harkokin kasuwancinsa, wanda shi ne dalilin zuwan turawan nan biyu wajen sa. Abinda ya fi tunani a yanzu shi ne, ya ya iyalansa za su kasance idan ya yi tafiyar da ya ke so ya yi a jibi. Ya na nan ma ya aka kare? Wannan shi ne ya sa a yanzu da Hajiya Rukayya ta shigo cikin dakin ya gaza amsa ma ta sallamar har sai da ta je kusa da shi ta dafa shi. Ya cira kansa a hankali ya dube ta. Bai ce komai ba ya kuma mayar da kan. "Alhaji lafiya kuwa?" Ta tambaya da alamun mamaki a fuskarta. Ya nisa, kana ya kuma cira kai ya dube ta, "E, to, lafiyar kenan." ya ce daidai lokacin da ya ke yunkurin sauyawa daga kishingidar zuwa zama. "Haba Alhaji, to mene ne abin yin dogon tunani irin wannan bayan ka ce lafiya?" Ta ce bayan ta samu waje ta zauna kusa da shi. "Dogo ne tunanin nawa? Ya bukata ya na sababben murmushinsa don gudun bacin ranta. Don tun bayan karin aurensa, duk lokacin da za su yi wata magana sai sun saba. "Dogo ne mana..sau nawa na yi sallama ba ka amsa ba?" Ta fada a marairaice. Mamaki ne ya fi bayyana a fuskarsa fiye da komai, don rabonsa da ya ji sassanyar muryarta tun kafin ya tuntube ta da maganar karin aurensa. Ya kuma yin murmushi "Ina jin ki, kawai dai na.." "Au! Ashe ka na ji na ma ka kyale ni? Ta katse shi da tambaya ta naharararsa, harara ta wasa. "Ba haka na ke nufi ba, ki bari na karasa mana." ya ce cikin murya mai cike da mamakin irin hirar da ke gudana tsakaninsu. Ya kura ma ta idanu cikin kokarinsa na gano wani abu tare da ita. Ta dukar da kai kasa bayan ta fahimci abin da ya ke nufi. A zahiri har a badini ba ta bukatar ya gane yaudarar da ta ke kokarin shirya masa, don ta samu damar fita da mota ba tare da direba ba. Sama da dakika talatin ba ta dago ba. Shi kuwa bai daina kallon ta ba, zuciyarsa sai dawurwura ta ke tsakanin yarda da rashin hakan, a dan abin da ya nazarta a tare da ita. "Ai kawai ka godewa Allah, da alama ya shirye ta ne ta zo ta nemi afuwa ga abin da ta yi maka a baya. Idan ba haka ba, me zai kawo ta dakinka da sassafe kuma har ta rika yi maka magana a tausashe?" Wani sashe na zuciyarsa ya ambata. "Kai haba, ina! Ba wani nan, kai dai kawai akwai wani abin daban." Wani sashen ya karyata na farko. To, ko ma mene ne dai a yanzu ya na bukatar ya sani, kuma lokaci ya yi da ya kamata ya yi amfani da wannan damar wajen shawo kanta don su samu zaman lafiya da amaryarta. "Hajiya ya na ga kin dukar da kai kasa kamar mai dinkin hula?" ya bukata cikin raha. "Dole na yi haka Alhaji tunda na zo takanas gare ka ka ce ka na ji na ka kyale ni." Ta amsa ta na duban sa, a wannan karon ta kara kwantar da muryarta fiye da baya. Ya kuma fadada murmushinsa na mamaki da jin dadin ganin irin damuwar da ta ke nunawa, wai don ya ce ya na jin sallamarta ya kyale. Take sai ya ji kamar duk duniya babu wanda ya fi shi jin dadi. Don a rayuwarsa babu abin da ya fi so irin ya ga ya na zaune kalau da iyalansa. "Ba ki fahimce ni ba. Cewa na yi na dan sha'afa cikin tunani ne...amma ai ina jin ki." "To, share ni ka yi kenan?" Ta sake bukata ta nayi mai fari da idanu. "A'a." ya ambata da sauri. "To mene ne?" Ta ce ta nadariya, a wannan karon sai da fararen hakoranta su ka bayyana a fili, wanda hakan shi ma ya sa shi darawa. "Yau kuma sai ina? Na ga kin yi kwalliya kamar wata sabuwar amarya." Ya sauya hirar bayan sun dakata da dariyar. Ta harare shi, "Wa ya sani ko amaryarce?" Ya yi mamakin abin da ta ce abin da bai taba tsammani zai zama amsar tambayarsa ba. Ya riga ya san idan da abu guda da ta tsana a rayuwarta bai wuce amaryarta Zainab ba. To, amma jin sabanin abin da ya yi tsammani sai ya yi sauri ya ce, "Ni dai na san wannan shiga ba banza ba, akwai wajen zuwa ko?" Ta langwabar da kai akan majinginar kujerar kana ta kuma fari da fararen idanunta, wadanda sau da yawa ta san fari da su kan yi tasiri wajen jan hankalinsa. Sannan da sababbiyar murayarta ta yaudara ta ce, "Alhaji, ina so na je unguwa ne idan an jima." "Har ina kenan?" Ya bukata bayan ya dauke kansa daga kallon ta zuwa sakalallen hotonsa da ke kafe jikin bango, jin abin da bai taba tsammanin shi ya kawo ta ba. Abin da ya riga ya sani ne, ta sha fita zuwa unguwa ba tare da saninsa ba. To, amma yanzu me ya sa ta zo tambayar sa. Sai dai bai bari ta gane abin da ke cikin ransa ba, ya ci gaba da tambayar ta. "In ce dai babu nisa ko?" "Babu nisa sosai...wata gaisuwa na ke son zuwa." "Gaisuwa?" A wannan karon ya dawo da dubansa gare ta. Ta gyada kai, "Wallahi kuwa." "Allah sarki." Ya ce ya na sosa kai, "Wane ne ya rasu?" "Wallahi dan gidan wata aminiyata ce ya rasu daren jiya, da sassafen nan aka sanar da ni." Ita da kanta sai da ta ji wani iri abu banbarakwai a bakinta saboda mamakin karyar da ta shirga cikin kankanin lokaci. Ya nisa cikin tausayawa ya ce, "Allah ya ji kan rai, ya gafarta masa...mu kuma ya kayuta namu zuwan." "Amin-amin" Ta amsa kai tsaye kamar gaske. "Wannan ai babu damuwa Hajiya." Ya ci gaba, "Idan kin gama shiryawa kawai direba ya kai ki..." "A'a Alhaji". Ta katse shi, "Babu bukatar mu tafi da direba a wannan tafiyar don kuwa ni da kawata da mu ka jima ba mu hadu ba za mu je, kuma tuntuni ma na riga na yi mata bayanin ni zan ja motar." Ta dan yi shiru ta natunanin yadda za ta dire karyar da ta shiryo. Ta ci gaba a wannan karon da rawar baki, "Har gardama fa mu ka yi, ta naban iya ba, ina cewa na iya! Ka na so ta yi mini...dariya ne ko kuwa ya ya?" "A'a Hajiya ba na kaunar haka. Abin da ki ka riga ki ka sani ne Tunda Allah ya zurta ni na ji ba na kaunar iyalina su ja mota, don ni na dauki hakan abin kunya a gare ni. Kuma koya mu ku mota ma da na sa aka yi, ai ba don ku dinga ja ba ne, saboda kawai bacin rana." ya tsagaita ya na daidaita numfashinsa, a halin yanzu kuma ya hade fuskarsa sabanin baya. Hajiya Rukayya ta dukar da kai jin dogon jawabin da ya yi na kin amincewa, wanda da ma ta yi zaton samun sa. "Da alama idan ki ka saki za ki yi wa kanki sakiyar da babu ruwa, Muddin ki ka bari Alhaji ya ce lallai direba ne zai kai ki babu yadda za a yi asirinki ya rufu. Ki san duk yadda za ki yi a matsayinki na ya mace ki shawo kansa. "wani sashe a zuciyarta ya rada mata. Ta cira kanta a hankali ta dube shi. Da raunin murya ta ce, "Haba Alhaji." A hankali sai ta matsa kusa da shi sosai, wanda har ya na iya jin hucin numfashinta a gefen fuskarsa, "Mene ne abin jin kunya don mun ja mota da kanmu? Ai ni kuwa ina ganin babu kasawa ga hakan. Kuma ma idan ka na tunanin kasawa ne, wa zai kula har ya gane cewa ni ce ke jan mota?" Ya girgiza kai, "Gaskiya Hajiya ni ba na son abin..." "Kai don Allah Alhaji". Ta katse shi bayan ta kara matsawa kamar za ta shige jikinsa. Ta kara sauke muryarta kasa sosai kamar mai rada, "Alhaji don Allah ka amince...yau daya dai." Ta dan hade fuska, da shagwaba ta ci gaba, "Gaskiya idan ba ka amince ba raina zai iya baci, kuma za mu bata." Duk da ta yi wata yar malalaciyar dariya a karshen maganar tata wadda ke nuna da wasa ta ke abin da ta fada, hakan bai hana shi shiga fargaba ba. Haka kawai sai ya ji gabansa na faduwa, a sannu kuma sai ya ji zuciyarsa ta soma amincewa da bukatar ta. Fahimtar ta da hakan ne ya sa ta furta a hankali, "Alhaji ka amince?" gyada kai kawai ya yi ba tare da ya furta komai ba. "To, ai kai kawai ka gyada mini ba ka ce komai ba." Ta jefa shagwaba cikin muryarta, "Ka yarda na je?" Ya kuma gyada kai, kana a hankali ya ce, "Na yarda ki je." Ta mayar da kanta ta jingina jikin majiginar kujerar saboda dadin da ya mamaye zuciyarta. A hankali ta shiga furta, "Na gode, Alhaji, Allah ya kara dankon soyayya tsakaninmu." Wannan kalma ta kara tsunduma Alhaji Basiru cikin tsananin mamaki. *** Tun sa'ar da su ka kama hanyar zuwa gidan malamin tsibbun Hajiya Rukayya ke jin dadi ta nata washe hakora kamar wadda akawa wani babban Albishir, saboda tunaninta na ganin cewa yau ne za ta kawo karshen abin da ya tsokane mata idanu. Kuma ya ke damunta wato kishiyarta da danta mujahid. Koda yake a yanzu hankalinta ya fi karkata ga mujahid din, ta fi so ta ga babu shi kafin mahaifiyarsa musamman mada Baraka ta haska ma ta illarsa, na cewa ya na da gadon mace biyu. Ta dubi Baraka da ke zaune gefenta na dama gaban motar, daidai lokacin da ta fada wani kwazazzabo, "Baraka ni fa na fara ji a jiki na bukata ta biya, Ba ki ji yadda zuciyata ke tumbatse da farin ciki ba." "Ahaf! Wannan ma kadan kika ji, sai ma bukata ta biya tukunna." Baraka ta ce ta natabe baki, "Don ma kin ce dan kawai ki ke so a kawar, da da uwar ai da farin ciki naki ya fi haka." "ke dai yi shiru tawa". Hajiya Rukayya ta ce gami da dora yatsanta a baki "Ina so mu yi a hankali ne idan yanzu mu ka ce za mu yi mai gaba daya, ba makawa sai na shiga zargi da tuhuma kuma zai yi wuya na kubuta, amma idan mu ka dauke su daya bayan daya, sai ki ji shiru kamar an shuka dusa, babu wani dan iska da zai kalle ni, balle har ya zarge ni." "E to, ke ma kin yi tunani. "Baraka ta ce sannan ta daga yatsanta manuni, ta yi wa Hajiya Rukayya nuni da wata yar karkatacciyar bishiya da ke gabansu kadan, "Idan kin isa ga bishiyar can sai ki tsaya, mun iso gidan." Hajiya Rukayya ta gyada kai ba tare da ta ce komai ba, sannan ta ce, "Da ma yanzu na ke shirin tambayar ki ganin cewa muna nisa cikin wannan uban daji." Ta daka mata harara, "Ke kuwa akwai ki da tsoro Rukayya. Ina wani daji a nan? Ai yanzu babu dajin, ba ki ga har gidaje sun fara yawaita a cikin sa ba. Tab! Da a ce yan shekarun baya ne ki ka zo, da ba za ki kira wajen da daji ba yanzu." "Allah kawar?" Hajiya Rukayya ta ce da mamaki lokaci guda kuma ta na kara nazarin dajin. Dajin ya na da fadi da tsawo, sannan akwai yar duhuwa duk da cewa dai akwai yan gidaje tsilla- tsilla. "Ina, ai yanzu ina dajin ya ke." Baraka ta ce cikin murmushi bayan sun mayar da murafen motar sun rufe. Ta dubi Hajiya Rukayya ta yi kasa-kasa da murya, cikin rada-rada ta ce, "Sai ki yi shiri, kuma ki iya bakinki, ki san abin da za ki ce don nan mun zo wurin da ba a shiririta." "To, an gama...kar ki ji komai." Hajiya Rukayya ta amsa a tsorace, ita ma cikin rada bayan ta dafe kirjinta, alamun tsoro karara a fuskarta. A lokaci guda kuma ga rashin mamakinta sai ta ji zuciyarta ta soma harbawa, domin ita tun da ta ke ba ta taba ganin daji irin wannan ba a fili, sai dai ko a akwatin talabijin. Cikin fargabar da matsananciyar bugun zuciya ta dafawa Baraka baya su ka nufi dan durkushasshen gidan. Kadan ya rage fitsari ya kufce ma ta sa'ar da ta taka wasu busassun ganyaryaki su ka bada wani amo. Turus su ka ja su ka tsaya cak kamar dawakan da aka ja wa linzami. Da sauri su ka fara waige- waige kamar barayi sakamakon tsawar da su ka ji an yi mu su kamar daga sama yayin da su ka shiga gidan. "Ku tsaya nan, kar ku kuskura ku kuma takawa, idan ba haka ba fuskokinku za su koma keya, mutanen banza!" muryar da har yanzu su ka kasa ganin mai ita ta ci gaba da gargadin su. Tsananin tsoro da fargaba ya sa su ka soma tsuma kamar wadanda ake kada wa gangi. Nan da nan dakakkiyar zuciyar da Baraka ke tunkaho da ita ta bi ruwa. Karar sukuwar dokin da su ka ji daga bayansu ya sa su juyawa lokaci guda, kana da gagawa su ka tsuguna sakamakon ziyarar da wani kakkarfan haske ya yi w idanunsu. Sannu a hankali sai su ka fara ganin wata irin halitta a gabansu, wadda ba za su iya tantance wa zuciyarsu fasalinta ba. Abu guda da su ka fi lura da shi sosai ga halittar shi ne, ta fi kama da dodon da su ka sha ji a tatsuniya fiye da komai. Halittar ta fashe da wata irin shaidaniyar dariya, a hankali-a hankali kuma sai ta soma sauya kama, babu jimawa sai ta dawo siffar mutum sosai. Mutumin da ya maye gurbin halittar baki ne kato, sanye a jikinsa wasu bakaken kaya ne masu ratsin ja. Ya kuma fashewa da dariya tsawon lokaci, sannan ya soma da duban su ya na hura hancinsa mai kama da begila. Kusan minti guda ya yi ya na duban su, daga bisani ya ce da wata budaddiyar murya, "Kai mutanen banza. Shagalallu, bukatar da ku ka zo mini da ita mai sauki ce, ba kuma na bukatar ku sanar da ni komai game da al'amarin domin tuni dan marayan aljanu ya kawo min labarinku." Ya yi shiru ya na wani gurnani mai ban tsoro. Su ka yi ajiyar zuciya lokaci guda kamar wadanda aka watsa wa sassanyan ruwa, cikin mamaki su ka fara satar kallon junan su. "Lallai matsalar ki." Ya nuna Hajiya Rukayya, "Bai wuce ta kishiyarki da danta ba, me ki ke so a yi mu su?" Da tsawa ya bukata. Tsawon lokaci su ka dauka ba su amsa ba saboda tsananin tsoro. Sai daga bisani Baraka ta zura hannu a sace ta zunguri Hajiya Rukayya, cikin rada ta ce, "Ki fada masa abin da ya kawo mu." Ba ta yi gardama ba. Take ta sanar da shi bukatarta ta son a fara kawar ma ta da mujahid. Bokan ya tuntsure da dariya, kana ya yi wata irin kakkarfar ajiyar zuciya, "Tabbas kin zo da al'amari mafi sauki a gare ni, kuma karamin abu wanda ba ni ya kamata na yi shi ba saboda saukin sa, duk da cewa dai ke mai wahala ne a gare ki matukar ki ka kuskure wa abin da zan umarce ki." ya saurara ya na zare idanu. Hajiya Rukayya ta dafe kirji jin abin da ya ce. "Hajiya". Ya dawo da hankalinta gare shi cikin murya mai tsoratarwa. "Dole ki yi taka-tsan-tsan da abin da zan gaya miki tun kafin na sanar da ke, domin ko ya ya ki ka kurkure na hango miki nadama a rayuwarki." Ya yi shiru kana ya ci gaba da dariya. Su kuwa babu abin da su ke yi sai kyarma. "Hajiya" ya kuma kiran sunanta, wannan karon muryar ta fi ta baya tsoratar wa, "Matso nan na sanar da ke." Ya miko ma ta hannunsa. Ta juya da sauri ta dubi Baraka a tsorace. Kafin ta ce wani abu Baraka ta ce, "Ki matsa mana, kar ki fa bata ma sa lokaci." Ita ma a tsorace ta yi maganar. Take ta ji wani abu mai kama da kwallon kafa ya taso daga cikinta zuwa wuyanta. Ba don ta yarda Baraka na kaunar ta ba, da sai ta ce ba ta da babbar makiyiya irin ta, don a iya tunaninta babu wanda zai ce ta matsa kusa da wannan Boka sai makiyinta. Babu yadda ta iya, haka ta matsa kusa da Bokan a hankali kamar wadda ke rabar wuta. Wani wari ne ya fara dukan hancinta daidai lokacin da ya miko dogon bakinsa fa kunnenta. Duk da cewa abin da ya ke fada wani abu ne da ta jima ta na neman sa, hakan bai hana ta jin kamar za ta amayar da kayan cikinta ba, saboda tsananin warin bakinsa "Rike wannan!" Ya ce da kaushin muryarsa bayan ya gama yi mata radar. *** Da alama tafkeken ruwan saman da aka kusan kwana ana tafkawa a daren na jiya, kamar da bakin kwarya, shi ya haifar da wadatacciyar iska, iskar da ke kadawa fil-fil-fil babu alamar tsagaitawa. Iskar za ta fi gamsar da mutum idan har aka yi sa'a ya yi wanka, kamar yadda wasu su ke hasashe. To amma kuma ga mamakin wasu tsiraru daga cikin mutanen da ke mantawa da kudurar Ubangiji Madaukaki, korafi da mamakin ruwan su ka rika yi su na cewa, wai kasa ta tsotse makekan ruwan da aka maka. Hakan ya haifar da rabuwa a tsakanin su, yayin da wasun su ke cewa, meyiwa kasar ta tsotse ruwan ne saboda jimawa da aka yi ba a samu ruwan ba. To, ko ma dai mene ne, Allah shi ne ya saukar da ruwan, kuma shi ya kaddara kasar ta tsotse shi kasancewar sa Mai yin yadda ya so. A daidai wannan lokaci da iskar ke ci gaba da filfilwa, direba Lukman, direban gidan Alhaji Basiru na daya daga cikin mutanen da ke jin dadin ta, duk kuwa da cewa kwance ya ke a daki abinsa ya na ta sake-saken abin da ka je ya zo. Sannu a hankali ya yi mika akan figaggiyar katifarsa mai kama da takkaken silifas, sannan ya yi salati ta cikin iskar hammar da ke fita daga bakinsa. Daga kwance ya langwabar da kansa gefe guda, ya kai dubansa ga fuskar agogon da ke makalr a jikin bango. Ya yi tsaki ganin har zuwa lokacin takwas ba ta yi ba. Ya kuma dauke kansa a hankali daga duban agogon zuwa ga rufin dakin kamar mai kidayar hudojin da ke jikin kwanon, lokaci guda kuma tunani da mamakin kiran da Hajiya Rukayya ta yi masa a yammacin jiya su ka lullube masa zuciya. "Lukman na kira ka ne saboda na shaida maka cewa gobe ba na so ka zo kai yara makaranta..ni zan kai su. Sai dai ina so ya zama kai za ka dawo da su. Amma fa ka sani hakan ba ya na nufin kullum ba ne, daga gobe shi kenan" Maganar da Hajiya Rukayya ta fada masa a jiyan ta ci gaba da kewaya zuciyarsa. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 2 Posted by ANaM Dorayi on 08:18 AM, 29-May-15 "To, mene ne dalilin Hajiya na yin haka?" Tambayar da ya ke yi wa kansa kenan a duk sa'ar da ya tuno da maganar, to amma har zuwa yanzu ya rasa samun amsa. A hankali ya dogara hannunsa biyu ya tashi zaune a karo na farko tun lokacin da ya kwanta bayan ya dawo daga sallar Asuba. Abu guda da ya fi amincewa da shi a zuciyarsa shi ne, ba banza Hajiya Rukayya ta shirya hakan ba. To idan kuwa hakan ne babu shakka ya kwadaita da ya san dalili. "To, a ina zan san dalilin?" Wannan karon da sauri ya furta kuma a fili. Nan da nan sai ya fara zargin kansa da yin Allah wadai, da ya kasa tambayar ta dalili a jiyan. "Gaskiya na yi sakaci, tun a jiya ya kamata na tambaye ta dalilin ta na..." Tunaninsa ya katse da ya tuno da abin arzikin da ta yi masa a jiyan. Ya laluba aljihun gaban rigarsa da sauri kamar mai yin rige-rige da wani. Har yanzu kudin na nan. "Ga wannan ka karya kumallo da safe a maimakon wanda ka ke yi anan." ya tuna abin da ta ce da shi lokacin da ta miko masa kudin. "Har dubu daya Hajiya?" Ya tuna abin da ya ce da ita lokacin da ya karba ya kirga. Abin da ya riga ya sani ne tun farkon daukarsa aiki a gidan, kyautar Hajiya Rukayya ba ta wuce Naira Hamsin, a ta yi yawa dari. "Kai gaskiya da walakin." ya kara furtawa a fili ya na duban kudin. Bayan tsawon lokaci ya na duban su ya mayar aljihu, sannan ya kuma komawa ya kwanta ya na fadin, "Bari na jira lokacin da ta ba ni ya cika na ga abin da ya samu a gidan." Ya ja tsohon mayafinsa mai kama da matacin koko ya rufa. A can cikin zuciyarsa ya na Allah-Allah karfe daya ta yi. Da kyar da curewa guri guda kamar kunkuru mayafin ya ishe shi. *** Karfe takwas daidai agogon da ke makale jikin bango cikin makeken falon ya saki wani daddadan kara, karan da ya ja hankalin Zainab da yaran guda uku da ke cikin falon zuwa fare shi. Yaran ba wasu ba ne, Mujahid ne danta da Hauwa'u da Sailuba, 'yayan Hajiya Rukayya. Yanzu kasan sa'a guda kenan su ka share su na zaman jiran zuwan direba Lukman, don ya kai su makaranta, amma shiru ka ke ji kamar an aika bawa garinsu. Wannan al'amarin ya fi cusa zainab cikin damuwa. Al'adarta idan ta yi wa Mujahid wanka, ba ta iya yin komai sai ta ga Lukman ya zo ya tafi da su makaranta, wasu ranakun ma kafin ta gama shirya shi ya ke zuwa, amma sabanin kullum yau ga shi ta gama kammala masa komai, sama da sa'a guda bai zo ba. "To, mene ne ya hana shi zuwa?" Abin da ta ke yawan tambayar kanta kenan, amma ta kasa gane dalilin. Abu guda dai da ta fi yarda da shi shi ne, koma dai mene ne ya hana direban zuwa to ya na da karfi. Cikin wannan hali na damuwa da Zainab ke ciki Hajiya Rukayya ta shigo falon da sauri kamar wadda aka biyo a guje. "Me ya faru har yanzu ba ku tafi makaranta ba?" Wannan ita ce maganar da ta fara fita daga bakinta a maimakon sallama. "Wallahi har yanzu direban ne bai zo ba, ga shi kuma har sun yi latti." Zainab ta amsa ma ta cikin girmamawa, duk da cewa ba ita ta tambaya ba. "To, ina ruwanki? Ke na tambaya ko kuwa ya ya, Zakakura?" Zainab ta kada kai, "Allah ya huci zuciyarki, da ma gani na yi kin yi tambaya kuma duk cikin su babu wanda ya amsa, shi ya sa." Hajiya Rukayya ta kuma doka ma ta harara, "Sannu mai baki, su kuma 'yayan nawa ina ki ka kai min bakin nasu? Ko ki na so ki danganta min da wannan dolon yaron naki, wawa marar baki?" Ta juya ta naduban Mujahid a wulakance. Zainab ta cira kai ta dube ta, makale a fatar bakinta wani dan murmushi ne da Hausawa ke yiwa lakabi da yake, "To, don Allah ki yi hakuri, na ji na yi miki laifi, amma surutun ya isa haka..." "Bai isa ba!" Ta katse ta, "Na ce bai isa ba!" Ta tattara hankalinta gare ta, kana ta dora hannu a kirju, "Ni ki ke cewa surutun ya isa haka? Ni ce ma mai surutu?" Shiru ba amsa daga Zainab. Hajiya ta kwashe wata irin dariya da ta tuno da shirinta da ke a kasa, "Babu komai, kin susa dainawa." Ta ce a ranta. A fili kuma sai ta ce, "Na ga alama wuyanki ya yi kauri yarinyar nan." Ta tsagaita da dariya ta shiga gyada kai, "Amma ba komai, ci gaba za ki kwashi kashinki a hannu nan ba da jimawa ba." Ta juya ga yaran, "Ku tashi mu tafi ni na kai ku. Shi kuma Lukman idan ya zo ya fada mini dalilin kin zuwan nasa." Hauwa'u da Sailuba su ka mike kamar ba sa so, fuskokinsu cike da damuwa. Duk da cewa kananan yara ne da ba su haura shekaru tara- tara ba kasancewarsu an haife su yan biyu, su na matukar nuna damuwa da abin da mahaifiyarsu ke yi wa Zainba din, wasu lokutan ma har hakuri su ke bawa Zainab din idan mahaifiyarsu rufe ta da fada. Su ka rufa ma ta baya. Daf da za su fice daga falon ne ta juyo ta dubi Mujahid da har yanzu ke zaune kusa da mahaifiyarsa, "Kai kuma algungumi ba za taso mu tafi ba, ka makale a jikin uwarka ka na duban mutane dai-dai?" lokacin da suka shiga makarantar tuni dalibai sun jima da shiga azuzuwa, wasu ma har sun fara kara tu, amma duk da haka bai hana Hajiya Rukayya tsayawa wani dan madaidaicin shagon sayar da kayan tsotse-tsotse da lashe-lashen dake cikin makarantar ba. "Hajiya Na manta ban tambaye ki guda nawa ba". A wannan karon kafin ya dafa motar ya fada. Ta yi murmushi, "Ba mu biskit din guda uku, alewar kuma guda biyu." Ya so ya ce ma ta ta yi kuskuren fadar alewa biyu a maimakon uku ganin yaran su uku ne, amma sai ya kyale, sai da ya je ya kawo, sannan ya yi ma ta abin da ya kira wo da tuni, "Hajiya kin manta kin ce alewa biyu na ga yaran su uku..." "Ka ga saurara." Ta katse shi, "Ban ce ma na manta ba, kai dai nawa ne kudinka?" Bai ji haushi sosai ba don ya san shi ne ya yi shisshigi. "Naira dari da hamshin." ya amsa daidai lokacin da ya mika ma ta. "Ungo." ta miko masa sabuwar Naira dari biyu ko kari babu bayan ta karba. Sannan ta juya ga yaran da ke zaune bayan motar ta fara raba mu su. Duk da cewa saurayin ya sa hannu a aljihu ya na kokarin dauko ma ta canji, hakan bai hana shi jifan tsuntsu biyu da dutse guda ba, don kuwa da wutsiyar idonsa ya na kallon yadda ta ke rabon, ya san dai dole daya zai rasa, kuma za a bukaci ya kawo. A kan Mujahid alewar ta kare bayan ta gama raba mu su biskit din. Mujahid ya dube ta, ya dubi yan uwansa ganin alewar da ta kare shi bai samu ba, alamun damuwa gauraye da na kuka su ka bayyana a fuskarsa. "Yi hakuri Mujahid, kai bari na ba ka taka alewar mai dadi, ka ji." Ta ce ta nayin wani irin murmushi, sannan ta bude. 'yar karamar jakarta da ke ajiye gaban mota, ta dauko alewar, "Rike, da kyau, kar ka kuskura ka ba kowa. Kowa ya sha tasa. Kun ji ko?" Ta gargade su. Su ka gyada kawunansu cikin gamsuwa kuma hakan ne ya sa saurayin ya dauke kansa cikin fitar da rai cewa zai sake samun ciniki. "Ga canjinki Hajiya." Ya ce bayan ya gama kirgawa. "jeka ka rike" Ta ce da shi cikin kosawa, kana ta ja motar ta yi gaba. Saurayin ya bi motar da kallo sannan ya kece da dariya a fili ya ce "Kai kudi ma dai ba su da kama...dubi wannan mummunar mata haka kamar an sassako cikin wannan zundumemiyar mota. *** Sau daya kawai ya latsa hon din motar babbar kofar gidan ta bude. Cikin hanzari direba Lukman ya shige da motar cikin yalwatacciyar farfajiyar. Ba yanzu ya soma hanzarin ba, tun lokacin da ya bar gida ya nufi makaranta da zummar dauko yaran ya ke ta hanzari shi ya sa yanzu da ya danna hon din sau daya ya ga kofar ta bude ya ji dadi a ransa, har ma zuci ya shiga yabawa kulawar Malam Bukar akan aikinsa, duk kuwa da cewa wani lokacin sai ya yi hon sau fiye da goma bai bude ba ya na cen ya na ta gyangyadinsa. Kamar yadda ya saba, cikin sauri ya karbi jakunkunan da ke hannun su Hauwa'u bayan ya mayar da murafen motar ya rufe. Kai tsaye ya wuce cikin gidan, yaran su ka rufa masa baya. Duk wannan sauri da ya ke yi, ya na yin sa ne don kyautata zatonsa na samun bakon abu, musamman saboda hana shi zuwa gidan da Hajiyya Rukayya ta yi a safiyar yau. Hanzarinsa ne ya ragu lokacin da su ka yi daf da falon ya ji ana hira da shewa a ciki. Sallama ya fara kafin ya daga labulen. "Wa'alaikas salam." Muryar matan biyu ta amsa sallamar daga cikin falon. Zainab ce da wata kawarta da ta kawo ma ta ziyara, mai suna Barista Hannatu Muhmud. Barista Hannatu kawar Zainab ce tun su na makaratar sakandire. Sun shaku da juna matuka, har ya zamto duk inda su ka nufa za ka ji ana ce mu su yan biyu. Amma a lokacin da su ka gama sakandire sai su ka samu rabuwar ra'ayi. Ita Zainab ta sauya darasin karantunta ta wuce kai tsaye ga fannin koyon bada kariya ga al'uma, wato lauya. To amma wani abin mamaki dan sha'awa ga kawayen biyu, wannan rabuwar ra'ayi ba ta shafi kawance da son junansu ba. Duk da haka sai su ka ci gaba da ziyartar juna akai-akai, har kawo yanzu da kowannen su ya gama karatunsa kuma ya ke cin moriyar karatun. Haduwar wadannan kawaye ta na zama abin sha'awa, don da kyar su ke iya rabuwa saboda son juna. Yau ma tun karfe goma na safe Hannatun ta zo, kuma kamar yadda ta saba sai karfe biyar ko fiye da haka ta ke barin gidan. Shi ya sa yanzu da direba Lukman ya zo ya yi mu su sallama su ka ji kamar ya shiga rayuwarsu, don duk sa'ar da su ka hadu ba sa kaunar wani abu ya katse mu su hirarsu. Suka daubi kofar shigowa falon bayan sun amsa sallamar. Lukman ya daga labule ya shigo. Mamaki ne ya fi rinjayar komai a fuskar Zainab bayan ta gane Lukman ne ya dauko yaran daga makaranta. Shi ma alamun mamaki sun bayyana a fuskarsa sai dai shi nasa bai yi tasiri ba saboda sanin cewa dole ne ko wane ne zai yi mamaki musamman ma idan ka yi la'akari da cewa ba shi ne ya kai yaran makaranta da safe ba, kai hasali ma bai zo gidan ba tun safe. Bai samu damar magana ba har Zainab ta ce, "Lukman daga ina?" Tambayar ba ta ba shi mamaki ba. "Daga makaranta na ke na je na dauko su ne." ya amsa kai tsaye bayan ya tsuguna. Mamakin ta ne ya karu. Ta dubi Hannatu da zummar ta yi magana, amma kafin ta yi sai ta riga ta da cewa, "Lafiya na ga ki na mamaki don ya je ya dauko su daga makaranta, ba aikinsa ba ne?" "Aikinsa ne, amma..." "Amma me?" Hannatu ta katse ta. "Amma gani na yi cewa ba shi ya kai su ba, kuma ma bai zo gidan ba yau kwata-kwata!" Zainab ta amsa lokaci guda kuma ta mayar da duban ta ga Lukman din. Hannatu ba ta fahimci abin da ta ke nufi ba, don haka ba ta sake yin magana ba, maimakon hakan ma sai ta ci gaba da sauraron su. "Lukman me ya sa yau ba ka zo ba?" Tambayar ta so ta rikita shi, amma koda ya tuno da gargadi da kuma kudin da Hajiya Rukayya ta ba shi sai ya ji ya dan nutsu. "Ba ni da Lafiya Hajiya...mu..mura ce ke damu na Hajiya..dauriya ce kawai irin tawa ta sa na fi...fito." ya amsa a marairaice murya na rawai. Nan da nan alamun mamakin su ka yi kaura da ga fuskar Zainab yayin da na tausayi su ka maye gurbin, jin abin da Lukman ya ce. Ta girgiza kai cikin tausayi sannan murya a tausashe ta ce, "Allah ya saukake Lukman, sannu ka ji?" "Amin." Ya amsa lokaci guda kuma ya shafi kudin da ke aljihunsa wanda Hajiya Rukayya ta ba shi, a cikin zuciyarsa ya ce, "Yanzu har na yi aikin Naira dubu? Kai lallai wannan auki da sauki ya ke, da a ce zan rika samun irin sa tsawon wata shida ai da na bar aiki na koma ni ma na kwanta na dinga yi wa kudin cin kadan har su kare, na san dai kafin lokacin zan yi kaurin wuya da kumatu da kuma tumbi kamar na mai gidana." *** Sabanin kowace tana da Alhaji Basiru ya saba dawowa gida karfe shida na yamma, yau sai ga shi ya dawo tun karfe hudu, meyiwa hakan na da alaka da shirye-shiryen tafiyar da zai yi zuwa kasar Ingila. Kuma kamar yadda ya saba dawowa shi kadai, yau su uku ne, shi da kaninsa wanda su ke uwa daya uba daya da ke da zama a garin Katsina mai suna Alhaji Sambo da kuma wani abokin harkarsa kuma amininsa Alhaji Gali. Aminan biyu su ka samu a falon (Zainab da Hannatu) har zuwa yanzu su na zaune su na hira. "Sannun ku da zuwa." Zainab da Hannatu su ka fada lokaci guda cikin sakin fuska da walwala, bayan sun amsa sallamar magidantan uku. Doguwar gaisuwa su ka yi kafin daga bisani falon ya yi shiru. Alhaji Sambo shi ya kau da shirun da tambayar Zainab. "Hajiya Zainab amarya, ina uwargidan ne?" Ga ta nan tafe." Muryar Hajiya Rukayya ta ratso falon kamar daga sama, wanda hakan ne ya ja hankalinsu zuwa kofar shigowa falon daidai lokacin da ta dago labulen falon ta shigo. "Yar halak! Yanzun ann na ke tambayar ki." Alhaji Sambo ya ci gaba ya na duban ta cikin fara'a. "Ni ma ai ina jin ka, shi ya sa na amsa ma." Ta ce ta na yin wani dan asirtaccen murmushi, kamar ba ta so. "Ai daman na dauka kin fita ne ba tare da kin tambaye ni ba na dau mataki idan kin dawo." Ya kuma cewa cikin dariyar tasa, sai dai wannan karon ba shi kadai ba, kusan dukkannin su babu wanda bai dara ba, idan ka dauke ita Hajiya Rukayya da ta turbune fuska. Wannan wani wasa ne da Alhaji Sambo ya saba yi wa Hajiya Rukayya, wasan da ake wa lakabi da na kanin miji. Hajiya Rukayya ta samu daya daga cikin jerin kujerun da ke gewaye da falon ta zauna, sannan su ka gaisa cikin fara'a da sakin fuska. Ko shakka babu sakin fuskarta na da alaka da ganin bakin biyu, don kuwa idan da akwai abin da ya fi wuta zafi, zuciyar Hajiya Rukayya ta fi shi zafi a wannan rana ganin cewa duk abin da ta shirya akan Mujahid ya dawo daga makaranta lafiya. Ranta ya kuma kuna sa'ar da ta ji muryar Maigidanta ta ratsa dodon kunnenta da cewa, "Hajiya na zama mu ka zo yi ba abinci kawai mu ka zo ci kafin mu wuce, kin san karfe biyar jirginmu zai tashi." Duk da cewa muryarsa a kwancw ya yi maganar hakan bai hana jin kamar ta ce masa ba za ta kawo ba domin gani ta ke, raini ne a ce ta tashi ta kawo abinci bayan ga Zainab da ke matsayin kanwarta. Haka dai ta daure ta danne fushinta, ta tashi ta nufi kicin ta nakunkuni, shi ma kuma wannan duk ganin idanun bakin ne. Kamar wadanda ke jiran fitar ta, yaran uku su ka shigo falon a guje, Mujahid a gaba, Hauwa'u da Sailuba biye da shi. Turus! Hauwa'u da Sailuba su ka ja su ka tsaya kamar wadanda aka kira sunansu daga baya, wannan kuwa ya biyo bayan ganin mahaifinsu da su ka yi babu zato babu tsammani. Shi kuwa Mujahid bai tsaya ba har sai da ya dangana da mahaifin nasu, ya fada kan cinyarsa ya na dariya. "Kai, ua ya lafiya? Mene ne kuke bin sa a guje haka?" Alhaji Sambo ya fada. "Ba shi ne ya ce wai ya girme mu ba." Hauwa'u ta amsa da wata shagwababbiyar murya. Gaba daya su ka bushe da dariya. "To, mene ne don ya ce ya girme ku? Banda abin ku wa ya ke son girma?" A wannan karon Barista Hannatu ce ta yi maganar cikin ragowar dariyae da su ke yi. "To, ai karya ya ke yi...mun fa girme shi Wallahi." Sailuba ce ta fada ita ma cikin shagwaba ta na hararar Mujahid din. "To, ai shi kenan. Ku yi hakuri kun girme shi." Alhaji Basiru ya ce ya na shafa kan Mujahid da har yanzu ke kwance kan cinyarsa. Ya ci gaba, "Zan yi tafiya amma idan zan dawo karami kawai zan sayo wa kayan dadi, kun yar..." "E, na yarda ni ne karami, ni za a sayo wa" Mujahid ya katse shi ya na tafa hannu. "A'a, mu ba mu yarda ba" Su ma su ka fada. Da wannan kace-nacen su ka cika falon. "To, ku dakata, ya isa haka." ya dakatar da su "Kowa za a sayo masa...da me da me ku ke so?" "Ni ne zan fara Baba." Mujahid ya yi sauri ya fada bayan ya yi zumbur ya mike daga kwanciyar da ya yi. "To fadi." Ya ba shi izini da gaggawa don gudun kar su Hauwa'u su ce ba su yarda ba. Yanzu kusan falon ya yi shiru kowa yana sauraron abin da mujahid din zai ce ya na so. "Ina son a sayo min jirgi da mota, uhm...uhm da Bindiga da kuma kambos..." Gaba daya su ka kuma tintsire wa da dariya. "Babbar magana." Alhaji Basiru yace "mujahid sakon naka babba ne." ya juya ga su Hauwa'u, "Ku kuma fa me za a sayo mu ku?" Sailuba ce ta fara cewa, "Ni Dan kunne da Sarka da kwabashu (Cover Shoe) na ke so." Ba ta samu sabani da Hauwa'u ba, domin ita ma abin da ta lissafo kenan, sai dai karin abu guda akan na Sailubar, shi ne Alewa mai zaki, wanda kuma lokaci guda shi ne abin da ya tuna wa Mujahid alewarsa ra safe da Hajiya Rukayya ta saya mu su a makaranta. Nan da nan ya tuna, bai samu damar shanye tasa ba wancan lokacin saboda shiga aji da ya yi ya tarar ana karatu malaminsu ya hana shi sha, ya ce ya sa a aljihu. Allah da ikonsa kuma ya manta da ita sai yanzu da sakon Hauwa'u ya tuna masa. "Lah! Baba ni ma ina da Alewata wadda Momi babba ta ba ni da safe a makaranta." Bai saurare shi ba don a lokacin hankalinsa ya tafi ga Barista Hannatu da ta ce za ta tafi gida. "Tun yanzu za ki tafi Hannatu?" Alhaji Basiru ya ce ya na duban ta, "Ba za ki bari sai an jima ba?" Ta yi dariya lokacin da ta ke yunkurin mike wa, "Babu komai Alhaji, ai na dan jima anan, sai dai kuma an kwana bi..." Mujahid ne ya katse ta da kukan da ya soma ganin ba a saurari abin da ya ke fada ba. "Kai! Wai mene ne haka?" Alhaji Basiru ya tambaye shi da tsawa. "Alewata za a dauko min." ya amsa cikin kuka. "Ta na ina?" Bukata daga Alhaji Basiru. "Ta na cikin aljihun wandon makarantana." ya amsa ya na murtsuke idanu bayan ya tsagaita da kukan. "Zainab don Allah je ki dauko masa kar yua dame mu." Umarni daga Alhaji Basiru. Zainab ta mike, "Ina zuwa Hannatu, idan ban dauko masa alewar nan ba ba zai bar mutane su ji kumai ba." Cikin sauri ta shige dakin nata da ke manne jikin falon don gudun kar ta bata wa Hannatu lokaci. Jim kadan ta fito alewar rike a hannunta. To amma wani abin mamaki wanda ita kanta ta rasa sanin dalilinsa shi ne, tun daga lokacin da ta mike da zummar dauko Alewar sai ta ji zuciyarta ta na bugawa kamar za ta faso kirjinta ta fito, kuma har zuwa yanzu da ta shigo falon gaban nata bai daina faduwa ba. Tun kafin ta isa gare shi, Mujahid ya tafi da sauri ya karbi alewar, sannan ya koma wajen mahaifin nasa. "Baba ka ga alewar!" ya ce ya na nuna masa. "Na gani Mujahid, amma za ka sanwa su Hauwa'u ko?" Ya girgiza kai, "Ba zan ba su ba." "Kannan naka?" A wannan karon aminin Alhaji Basirun ne ya yi magana, wato Alhaji Gali. "Ni dai ba kannena ba ne." Mujahid ya ce ya na kumbura baki. "To shi kenan rabu da shi, idan na je na dawo ba zan kawo masa jirgi da mota ba." Cewar Alhaji Basiru. Alhaji Basiru mutum ne mai son hada kan 'yayansa a koda yaushe. Shi ya sa idan daya daga cikin su ya zo da wani abu matukar sauran ba su da shi, to sai ya ba su. A yanzu ma haka ce ta kansance don sai da ya lallabi Mujahid ya ba shi alewar. "Yauwa Mujahid, ka ga idan na je na dawo sai na sayo ma wata." yace bayan ya karbi alewar. "Bari na raba mu ku ko?" Mujahid da fuskarsa ke a turbune ya gyada kai cikin rashin son rai. Alhaji Basiru ya bare alewar sannan ya sa hakori ya fasa ta gida uku. "Fara zaba Mujahid." Ya ce bayan ya zube ta a tafin hannunsa. Mujahid ya dubi kason alewar cikin rainuwa da ruwan ido, ya sa hannu ya dauki daya. A hankali sai kuka ya kufce masa. Ba wani abu ne ya sa shi kukan ba, sai dariyar da Hauwa'u da Sailubar su ka shiga yi masa bayan sun dauki nasu kason. Ya dube su daidai lokacin da su ka sa alewar a baki su na yi masa gwalo. Da tsananin fushi ya dubi tasa alewar sai ya fashe da kuka, a lokaci guda kuma ya yi jifa da ita kai tsaye ya fice daga falon a guje ya nufi inda Hajiya Rukayya ta ke (Kitchen). Barista Hannatu ta mike, "Lallai Mujahid akwai rigima..Ni zan tafi." Zainab ma ta mike. "To, Hannatu a sauka lafiya, sai an kwana biyu ko?" Alhaji Basiru ya mike. "A gaida gida." Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka ambata. Momi...momi, Baba..ya kwace mini Alewa...ta". Wannan shi ne abin da Mujahid ya rika ambata cikin kukan nasa har ya isa gare ta. Ba ta fahimci abin da ya ke nufi ba saboda haka ne ma ta daka masa tsawa gami da kai masa hannu da zummar mangare shi. Maimakon damuwa da abin da ta yi masa sai ya ci gaba da cewa cikin kukan nasa, baya ya dan matsa baya, "Ba Baba ba ne ya kwace min...A...Alewata da ki..ka ba ni a makaranta...ya ba su Hau...Hauwa'u.." Sai yanzu ta fahimci abin da ya ke fada, ta kuma gane. A firgice ta saki kwanon abincin da ke rike a hannunta, abincin ya tarwatse a farfajiyar dakin girkin. "Kar ku sha alewar nan ba ta da kyau...kar ku sha alewar nan ba ta da kyau...kar ku sha!" Wannan shi ne abin da ke fita daga bakinta cikin daga murya da kuruwa, kuma shi ne abin da ya katse sallamar da kawayen biyu ke yi (Zainab da Barista Hannatu) Wadanda ke tsaye a bakin kofar falon. Cikin kin jinin rabuwa da juna kamar yadda su ka saba. Tafiyar ruwa ta so ta yi da su ba don sun ba ta hanya ba. Shakka babu ta tsorata su ganin shigarta falon kamar kibiya. To, amma duk wannan mai sauki ne, tsoron nasu ya fi bayyana karara lokacin da su ka rufa mata baya zuwa cikin falon su ka iske, Sailuba da Hauwa'u da Alhaji Basiru kwance a kasa su na murkususu! Turus su ka yi su dukansu sa'ar da kwayar idanunsu ta nuna mu su mummunan abin da ke faruwa a falon, abin da ya haifar da wasu irin alamu na rikitarwa da kaduwa lokaci guda a fuskokinsu, musamman ma Hajiya Rukayya da abin ya yi ma ta yawa, ga 'yaya ga miji, su na ta faman juye-juye da kakarin neman taimako. A ka ta dora hannuwanta biyu ta kwalla wani irin ihu mai garwaye da kuka. Lokaci guda ta nufe su, ta dire gwaiwoyinta biyu akan kilishin da ke shimfide a falon, ta tallafo kan Sailuba, ta girgiza ta, kana da sauri ta mayar da ita ta tallafo Hauwa'u ta girgiza, a yanzu sun daina motsi, jikinsu ya saki kamar matattu. Take ta kuma kurma wani uban ihu cure da wani kuka mai tsuma zuciya. "Wayyo Allahna... 'yan biyu sun mutu." Wannan ya sa Zainab ita ma da ke tsaye tare da kawarta cikin rashin sanin abin yi ta isa ga Hajiya Rukayya da ke kokarin faduwa ta dafe ta. Ba ta da abin fada shi ya sa ta kasa cewa komai, a lokaci guda kuma hawaye ya fara tsattsafowa daga idanunta ganin yara biyu da ke kwance ko motsa wa ba sa yi, bugu da kari ga mijinta na juye-juye cikin wani irin nishi na ban tausayi. Dabara ce ta fado ma ta, shi ya sa ita ma Barista Hannatu duk da cewa ta nacikin rikita ta motsa zuwa inda Zainab ke rike da Hajiya Rukayya. Ta duka da sauri ta tallafi Hajiya Rukayyar, "Sake ta Zainb, je ki kira likitanku a waya mana." Ba ta yi gardama ba kawai sai ta sakarwa Hannatu ita, ta nufi kan wayar sadarwar da ke ajiye kan matsakaicin teburin da ke durkushe can gefe guda. cikin hanzari ta soma lallatsa lambobin da su ne ta san za su sada ta da likita Idris. "Hello!" Ta ambata tun kafin ta gama daidaita zaman wayar a kunnenta. "Likita ne." Ta ci gaba. "Don Allah ka yi maza-maza ka zo." Ta juya kallonta ga maigidanta Alhaji Basiru jin ya ja wani dogon numfashi. "Likita ka yi sauri don Allah, alhaji ne da 'yan biyu su ka kamu..." Aka katse ta daga can bangaren ta hanyar ajiye wayar da likitan ya yi. Ita ma ta ajiye, maimakon ta dawo gare su sai ta nufi dakinta a guje, meyiwa akwai abin da ta tuno. Da sauri-sauri, gudu-gudu Zainab ta kuma shigowa falon hannunta na dama rike da 'yar karamar na'urar da likitoci ke rataya wa a wuya. Wajen maigidanta ta fara nufa. Da gaggawa ta balle maballen wuyan rigarsa ta dora na'urar a kirjinsa bayan ta sakala a kunnuwanta. To, a daidai lokacin ne Likita Idris ya shigo falon da sauri, hannunsa rike da irin karamar jakar nan tasu ta likitoci. Mamaki ne shi ma ya fara bayyana a fuskarsa ganin abin da bai yi tsammani ba, Alhaji Basiru kwance ya na nannauyan nishi. "Subhanallahi." Ya ce. Har ya nufi Alhajin amma ganin Zainab na yin iya bakin kokarinta, ya sa ya sauya nufin nasa ya nufi su Sailuba da ko motsi ba sa yi. Koda Hajiyya Rukayya ta kyalla idanu ta ga Likita sai ta yi zumbur ta kwace daga hannun Hannatu, ta mike ta tare shi ta nacewa, "Likita don Allah taimake ni, wadannan 'yayan sun mutu...wayyooo!" kukan ya hana ta ci gaba. Cikin hanzari Likita ya dire yar jakarsa a kasa, shi ma dai da yar na'urar da ke rataye a wuyansa ya soma. Falon ya yi tsit sai nishin kukan Hajiya Rukayya sakamakon zubawa Zainab da likita Idris idanu da aka yi akan gwaje-gwajen da su ke yi. Jim kadan likita Idris ya nisa, kana ya cira kai ya dubi su Alhaji Sambo da ke cikin wani mugun ya nayi, "Wannan ya na da kyau mu tafi da su asibiti da gaggawa domin..." "To, mu je mana likita?" Kusan mutum uku ne su ka katse shi (Ahaji Sambo da Alhaji Gali da Hajiya Rukayya). Ba su bata lokaci ba bayan umarnin likitan. Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka tallafi Alhaji Basiru a kafadarsu, su ka nufi waje da shi. Shi kuwa likita Idris ya sungumi Hauwa'u, Barista Hannatu ta sabi Sailuba Hajiya Rukayya ta sabi jakar likita ita da Zainab su ka dafa mu su baya har zuwa 'yar farfajiyar da aka 'kirkira don ajiyar motoci. Suna isa asibiti su ka zarce bangaren da ke da alhakin bayar da tallafin gaggawa A&E (Accident and Emergency). Sun amsa sunansu, domin ba tare da jinkiri ba su ka fara aiwatar da tallafin nasu na gaggawa akan Alhaji Basiru da 'yan biyu. Bayan wasu 'yan gwaje-gwaje sai wata kakkaurar likita fara, gajera, mai yalwar kumatu ta bayar da umarnin a shigar da su wani daki. Amma a duk cikin tawagar da su ka taho babu wanda aka bari ya shiga. Hakan ne ya sa su ka koma gefe su ka yi cirko-cirko su na jiran sakamako. A CAN GIDA *** Bayan fitar su da a kalla rabin sa'a Baraka ta isa gidan a kudurinta na jin sakamakon abin da su ka kulla. A bude ta samu babbar kofar shiga gidan, wanda hakan ne ya sa ta kunna kai ciki ba tare da jinkiri ba. Ta ja ta tsaya ganin mujahid na ta rusa kuka, mai gadi Bukar na ta rarrashin sa. Ga mamakinta sai ta ji gabanta ya yi mummunar faduwa. Ta taka a hankali ta isa gare su. "Assalamu alaikum." Ta ce a sanyaye. "Wa'alaikis salam". Maigadi Bukar ya amsa, ya cira kai ya dube ta. "Sannu Baba." Ta kuma cewa a sanyaye. "Yauwa ke ma Sannu." ya maida hankalinsa gare ta saboda sassauta kukan da Mujahid ya yi. Ta yi murmushin karfin hali, "Lafiya dai ya ke kuka?" ya dubi Mujahid din da ke zaune kusa da shi akan dogon bencin, "E to! Ba lafiya ba." "Mene ne ya faru?" Ta bukata wannan karon a 'kagauce. "Yan uwansa ne da kuma Alhaji ba su da lafiya." "Su wa kenan?" Ta dafe kirji. "Yan biyu mana, Hauwa'u da Sailuba." Gabanta ya kara faduwa, "Me ya same su?" "Abin da ban sani ba kenan. Ni ma ina zaune a nan na ga an fito da su za a kai su asibiti." Ba ta ga ta jira ba, akwai bukatar ta san dalili. Ta matsa ta dafa kan Mujahid, ta rankwafa, "Mujahid me ya same su?" Cikin ragowar shisshikar kukan da ya ke yi ya ce, "Ba...alewa ta su ka kwace min...ba, shi ne..." Ta saki kansa da sauri wanda hakan ne ya hana shi karasawa. Alamun razana su ka bayyana a fuskarta, take ta ji cikinta ya juya gami da bayar da wani amo kululululuuu, sai kuma ta ji kamar ta saki gudawa, cikin ta yan maza ta ce, "Yanzu su na asibitin?" "Eh". Maigadi Bukar ya amsa ma ta kai tsaye. "Wanne kenan?" Ta kuma bukata. "Ai ina jin ba za su wuce asibitin nan na dogon gida ba" "Har Hajiya Raukayyar?" "Dukan su!" Ba ta sake komawa ta kansu ba ta juya, "Sai an jimanku." Ta nufi babbar kofar da sauri da sauri kamar za ta fadi. Idan ka dubi saurin da ta ke yi sai ka rantse da Allah asibitin ta nufa. Ko kusa ba haka ba ne, ita Allah-Allah ta ke yi ta isa gidan da ta sauka domin tattare kayanta ta nufi tashar mota, don tuni ta kudurce ta kuma gaskata kwanan Kano a yau ya gagare ta, yau a kauyensu za ta kwana. To sai dai abin da ba ta sani ba shi ne; Ko da birnin Sin za ta koma bincike zai tuso keyarta zuwa Kano. *** Sa'a guda su ka share su na zaune su na jira amma shiru ba labari, hakan ne ya kara jefa zulumi a zukatansu, musamman Hajiya Rukayya da ta riga ta san makasudin faruwar abin da kuma irin hadarinsa. Duk ta rude ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta yi nan, ta yi can, ta na yi ta na sumbatu. Abu guda ta ke nanatawa. "Oooh! Wayyo Allahna, yau na shiga uku na lalace...shi kenan mutuwa za su yi. Wayyo ni kaina. Baraka ya haka?" duk da cewa a rikice ta ke yin maganar, babban abin mamaki da tambaya cikin abin da ta ke ambata, me ya sa ta ke cewa shi kenan sun mutu? Kuma wace ce Baraka? Wadannan tambayoyi guda biyu su na yin matukar tasiri a zukatan, Alhaji Sambo, Alhaji Gali da kuma Barista Hannatu, sai kuma yan tsirarun mutanen da ke zaune a wajen su na cikin jiran na su majinyatan da su ka kawo. A cikin wannan hali ne kofar dakin ta bude, likitoci guda biyu su ka fito. Likita Idris ne da wannan kakkaurar Likitar wadda ke amsa Dokta Safina A. Bashir. Cikin hanzari da kaguwa dukan su su ka tunkari likitocin don jin halin da ake ciki. "Ya ya likita...ya aka yi?" "Ya ya su ke?" "A wane hali su ke?" "Me ya faru da su?" Ba za ka iya tantance wadanda su ka furta wadannan kalamai ba a cikin su, da ya ke kusan a tare su ka furta. Bai ba su amsa ba sai kawai wani farin kyalle da ya zaro daga aljihunsa ya tsane gumin da ke tsattsafo wa daga goshinsa. Alama kawai ya yi mu su da hannu su biyo shi. Su ka bi shi kuwa duuu kamar kura har zuwa ofishinsa. Kai tsaye likita Idris ya wuce ga kujerarsa da ta sa wani madaidaicin teburin da ke dauke da tulin takardu. Alhaji Gali da Alhaji Sambo su ka zauna a kujerun biyu da ke gefe da gefen madaidaicin teburin. Barista Hannatu da Zainab da Hajiya Rukayya su ka zauna a kan wata kujerar laushi da ke ajiye gefe guda. Likita Safina kuwa wucwe wa ta yi kusa da likita Idris ta tsaya. Bai bari shiru ta ratsa tsakanin zaman nasu ba, likita Idris ya fara da cewa," ko da ya ke mun bar zane tun ran gini saboda dalilai na rikicewa, ma'ana ba mu tambaye ku abin da su ka ci ya kawo mu su wannan matsalar ba tun a lokacin da na isa gidan dazu. To, amma duk da haka zan so sanin hakan yanzu, me su ka ci haka?" Shiru ba wanda ya amsa tsawon dakiku goma, kowannensu na kokarin tuno abin da ya san sun ci, musamman ma Zainab da Barista Hannatu da su ka kasance a waje yayin Faruwar al'amarin. Amma ita fa Hajiya Rukayya ko shakka babu ta san abin da su ka sha. Ta san alewa su ka sha, to sai dai ita ma abin da ta ke tunani shi ne, shin wai maigidanta shima Alewar ya sha? Alhaji Sambo ne ya kawar da shirun wucin gadin da ya fara ratsa tsakaninsu, bayan ya tuno abin da a iya saninsa shi ne abin da ya gani sun sha a gabansa. "Am...likita ni dai Alewa ce kawai na ga sun sha. Amma fa shi Alhaji ban da shi domin shi kawai dai ya raba Alewar ne da hakorinsa." "Alewa?" Likita Idris ya maimaita cikin mamaki. "Eh, Alewa." Alhaji Sambo ya tabbatar. "Wacce irin Alewa?" "Alewa dai da ka sani". Likita Idris ya nisa, "To, tabbas wannan Alewar akwai wata guba a cikinta, gubar da ke saurin kashe Dan Adam. A ina aka samu wannan Alewa?" "A'a, mu dai ba mu sani ba, yaron nan mujahid ne da ya ce ya na da Alewa da aka saya masa a makaranta da safe. Ganin zai yi rikici sai Alhaji ya sa mahaifiyarsa ta je ta dauko masa...ka ji yadda aka samu Alewar? Dasss! Kirjin Hajiya Rukayya ya buga. Yau shi kenan asirinta ya tonu. Da wanne za ta ji? Rashin lafiyar 'yayanta da maigidanta ko fallasa. Nan da nan sai ya nayi na nadama ya fara kore na damuwar da ke fuskarta. "Wace ce ta dauko Alewar?" Likita ya bukata. "Ni ce Likita". Zainab ta amsa kai tsaye "A ina ki ka saya masa ita?" "A'a, ba ni na saya masa ba...ina jin Hajiya ce ta saya masa lokacin da ta kai su makaranta, tunda..." "Wacce Hajiya...Ni?!" Hajiya Rukayya ta yi zumbur ta mike tsaye gami da dafe kirji. Babu shakka yanzu ne ya kamata ta kare kanta domin idan wannan damar ta wuce ta, to fa babu wata da za ta yi amfani da ita don yiwa kanta garkuwa. "Sam! Ni ba ni ba shi wannan shegiyar Alewar ba." Ta ci gaba cikin tsagalgalewa, "Ki nemi wanda ya ba shi tun dare bai yi miki ba. Ni da ba na ma falon ki ka dauko..." "Kin ga saurara Hajiya, Zauna." A wannan karon likita Safina ce ta katse ta, kana ta ci gaba, "Shi dai wannan al'amari koma dai ya ya ke wannan alewar ce ta zama sanadiyar mutuwar yan biyu da kuma sa Alhaji cikin halin kaka-na-ka-yi, halin mutuwa ko yau ko gobe..." Maganar likita Safina ta katse ganin dukkansu sun mike a firgice. "La'ilaha illalLahu". Hajiya Rukayya ta fada cikin daga murya, "Wayyo Allah...na ga ta kaina yau." yanzu ne ya kamata ta yi amfani da abin da zuciyarta ta kitsa mata. Nan da nan ta juya cikin rufewar idanu ta cakumi wuyan Zainab, cikin kukan ta ci gaba da cewa, "Ke munafuka, wallahi yau sai kin sanar da ni inda ki ka samu wannan Alewar ki ka kashe min 'yaya na da mijina, sai kin fada min...sai kin fada min!" Ta na yi ta na jijjiga ta. Barista Hannatu da Likita Safina su ka zaburo su ka rike hannun Hajiya Rukayya da ta shake wuyan Zainab. Da gumi da sidin goshi su ka bambare hannun. "Ni wallahi yau ba zan yarda ba...wallahi ba zan taba yarda ba, shegiya, tsinanniya, da ma ki na jin haushin yayan nan..." Ta kuma fashewa da kuka. Likita Idris ya mike daga kan kujerarsa, "kin ga Safina, ku je waje da ita." ya yi Umarni. Likita Safina da Barista Hannatu su ka janye Hajiya Rukayya su ka fice daga ofishin su na bata hakuri. Zainab kuwa tuni jikinta ya yi likis tana tsaye dafe da wuyanta ta na wani irin dan tari, da alama shakar da Hajiya Rukayya ta yi mata ta kai matuka saboda idanunta sun kada sun yi jajur. Yanzu ofishin ya yi shiru kamar ruwa ya shanye su, meyiwa maganganun da Hajiya Rukayya ta yi ne sunyi tasiri a zukatansu Don kuwa tuni wasu daga cikinsu sun shiga zargin Zainab din a matsayin ita ta sa guba a cikin muguwar Alewar. Likita idris ya nisa cikin rashin sanin abinyi, Hakika shi ma yan surutan da Hajiya Rukayyar ta yi yasa zuciyarsa ta fi karkata ga darasin da ke nuni da cewa Zainab ce ta samar da wannan Alewa, kuma yana zargin tayi haka ne ga hajiya Rukayya domin ta hallaka ta da yayanta. Ya dubi Zainab a sanyaye yace "Hajiya Zainab". ya nuna mata gun zama. Zainab ta zauna a sanyaye hannunta rike da wuyanta. "Alhaji". Likita Sambo ya ambata ya na duban su Alhaji Sambo da su ke zaune cikin mutuwar jiki. Su ka cira kai a hankali su ka dube shi. Babu wanda ya samu amsawa. "Ko da ya ke". Likita ya ci gaba, "Zainab ku ya kamata na tambaya." Ta cira kai a hankali ta dube shi. "Tsakani da Allah Zainab a ina kika samu wannan Alewar. Ki daure ki sanar da mu sai mu je har gurin domin daukar mataki ga mai sayarwar. Ta yiwu ke ba ki san mai guba ba ce." Zainab ta sa mayafinta ta goge hawayen da ke faman bulbulowa daga idanunta. Abin gwanin ban tausayi, ta soma magana, "Likita, na rantse da Allah ba ni na saya masa wannan Alewar ba, hasali ma ni ban san da ita ba sai a lokacin da aka ce na dauko. Wallahi...walla..." kukan da ta soma ya ci karfinta ya hana ta karasawa. "Kin ga malama saurara, babu wani kukan munafurci da za ki yi mana, kawai ki sanar da mu inda ki ka samu wannan guda." Alhaji Sambo ya ce da ita a kufule kuma cikin tsawa, don tuni shi ya sakankance a zuciyarsa cewa ita ce ta samar da Alewar, idan ba haka ba ai Hajiya Rukayya ba za ta sayo abin da zai kashe ma ta ya ya ba. "Kawai abin da ya dace ki sanar da mu kenan amma ba rantse-rantse da kukan munafurci ba." Shi ma Alhaji Gali ya dora cikin fushi. Zainab ta ji kamar gini ya ruguzo ma ta a ka, jiri mai tsananin gaske ya afka ma ta sakamakon wadannan maganganun da ta ji daga bakin mutanen da ba ta taba tsammanin za su zarge ta ba. Nan da nan sai ta ji wata marainiyar murya daga can cikin Zuciyarta da ke iya sa mai sauraro kuka ta fara ambatar, "Wayyo Allahna, yau ya zan yi da kaina. Ubangiji ka kawo mini dauki cikin wannan al'amari." Likita Idris ya kuma nisawa. Yanzu kuma hankalinsa ya fara rabuwa tsakanin yarda da rashin ta da cewa Zainab ce ta samar da Alewar, a dan nazarin da ya yi wa fuskarta a yanzu. "Hajiya." Ya kuma kiran sunanta. Ta dago kai ta dubeshi, har yanzu ofishin juya ma ta ya ke yi. "Yanzu ke kin tabbatar ba ke ki ka samar da wannan Ale..." "Ka ga likita saurara! Ai sam babu bukatar ta tabbatar tunda na fuskanci ba ta da shirin fadar gaskiya. Mu da aka yi komai a gabanmu?" Alhaji Sambo ya katse shi kana a na huci ya ci gaba, "Ka rabu da ita kawai Likita, idan mu ta ki sanar da mu ai ta sanar da hukuma ko?" Ya mike tsaye, "Tashi mu je Alhaji Gali." Alhaji Gali ya mike. Har sun kai ga bakin kofar fita daga ofishin, Alhaji Sambo ya juyo, "Za mu je ga jami'an tsaro Likita, don Allah ku ba Alhaji Kyakkyawar kulawa, yanzu za mu dawo." *** Karfe Bakwai saura minti biyar su ka isa babbar Hedikwatar yan sanda kamar yadda agogon da ke like a gaban motar ya nunawa kwayoyin idanun magidantan biyu (Alhaji Sambo da Alhaji Gali) wadanda su ka zo don kawo karar Zainab a matsayin matar da ta aikata kisan kai. Bayan samar wa motar kyakkyawan matsuguni cikin yalwatacciyar harabar ginin Hedikwatar, su ka bude motar su ka fito, a lokaci guda su ka mayar da murafen su ka rufe. Kallo daya za ka yi wa fuskokinsu ka tabbatar akwai gagarumar matsala da ke damun su. Kamar kurame su ka dubi junansu ba tare da sun yi magana ba, su ka tunkari wata yar majalisa da wasu yan sanda biyar su ka kafa, su na hira, meyiwa su na yi wa juna murnar busharar da shugaban kasa ya yi mu su ne akan karin albashi. Sa'ar da su ka isa ga yan sandan su ka yi mu su sallama duk sai su ka juyo gami da amsawa. "Sannun ku." Cewar Alhaji Gali. "Yauwa, Alhaji ya gari?" Cewar biyu daga cikin yansandan. "Ma su gidana don Allah mu na neman ofishin bincike ne game da kisan kai." "Ofishin ASP Haladu kenan ko?" Daya daga cikin yansandan ya bukata ga yan uwansa. "Eh, nan ne." Yan sandan su ka tabbatar ma sa. "Ya na cikin gidan nan kuwa? Anya bai fita ba?" Dan sandan ya bukata bayan ya dubi fuskar agogon da ke daure a hannunsa, "Yanzu fa karfe bakwai saura minti uku." "Kai ya na nan bai fita ba, ba ga motarsa can ba." Daya daga cikin yan sandan ya amsawa dan uwansa bayan ya kai dubansa ga tsiraran motocin da su ka sage a harabar. "Eh, kwarai bai fita ba." Dan sandan ya amsa, "Ku zo mu je mu je na raka ku." ya ce da su Alhaji Gali. Ya juya su ka ki shi a baya, su ka ratsa ta tsakanin wasu yan furanni da aka jera gefe da gefen yar siririyar hanyar da za ta sada mutum da makeken benen. Daraf-Daraf su ka haye, su ka nufi wani lungu. A can kuryar lungun ofishin ya ke. Manne a bango jikin wani katako da ke saman kofar ofishin kadan, an rubuta cikin manyan haruffa "HOMICIDE" kasancewar a bude su ka same shi ba su yi jinkiri wajen kunna kai ciki ba. Faffadan ofis ne kuma ciki da falo. A zaune su ka iske wani Dan sanda mai mukamin sajen (Igiya Uku) ya sanya dan madaidaicin tebur a gaba ya na ta faman rubuce-rubuce. "Wa'alaikumus salam." sajen Sani ya amsa sallamar mutanen uku bayan ya cira kai daga rubutun zuwa duban su. "Ah! Auwal ya aka yi?" ya mika wa kofur Auwal hannu. (Dan sandan da ya rako su alhaji sambo) . Su ma su Alhaji Gali su ka mika masa Hannu, su ka gaisa. "Don Allah ko mai gida na ciki?" Cewar kofur Auwal. "Ya na nan" Sajen Sani ya amsa kai tsaye. "Yauwa, dama wadannan bayin Allah ne ke son ganinsa" sajen Sani ya dubi agogon da ke daure a hannunsa. "Kai karfe bakwai fa yanzu, kai ma ka san ganin maigida ba zai yi wuya a yanzu. Sa'a aka yi fa yau mu na son kawo karshen wani bincikenmu akan wani kes (Case) da za a shiga kotu gobe, idan banda haka ai karfe uku mu ke tashi" "Gaskiya da farko ni ma na dauka kun tashi" cewar kofur Auwal. Ya juya ga su Alhaji Gali "Alhaji Me zai hana gobe ku dawo da wuri ku gan shi, kun ga yanzu dare ya kawo kai.." "Don Allah yallabai a taimaka mana mu gana da shi yanzu, wani gagarumin al'amari ne..wata mata ce ta kashe yayan kishiyarta biyu da kuma jefa mijinta cikin gagarumin hadari. Don Allah a taimaka kar kafin goben ta gudu" Alhaji Sambo ya ce a sanyaye cikin muryar roko. Idannun yansandan ne su ka kara girma (alamun mamaki da tsoro) Hakika babban kes ne, ya kamata su bi diddiginsa. Sajen Sani ya rufe littafin da ya ke rubuta a ciki ya mike tsaye da gaggawa, "Ina zuwa" ya ce kana ya nufi kofar da ke like cikin ofishin nasa wadda kuma ita za ta sada shi da maigidan nasa ASP Haladu. Ya turo kofar ya rufe bayan ya shiga. Ya kame ga mutumin da ke zaune kan wata babbatar kujerar laushi, damfareren teburin da ke take da takardu durkushe a gabansa. "Sani ya ya?" ASP Haladu ya bukata. Ya saki jikinsa daga kamewar da ya yi, "Yallabai wasu ne dauke da wani muhimmin kes, su ke son ganin ka" "Yanzu abin da na ke so da ku." ya mayar da dubansa gare su, "Ku tashi maza ku koma asibitin, ku tattara kawunanku gaba daya ku hallara a gidan, don nan da karfe takwas zuwa tara za mu zo domin yin bincike." Ya dubi agogon da ke rataye jikin bangon ofishinsa, "Kun ga yanzu bakwai har da kwata." "To yallabai." su ka amsa kusan a tare." "Har fa gawar yaran mu ke so a mayar gidan. Ku yi maza don Allah." ya rufe littafin da ke gabansa. "An gama yallabai." Su ka kuma ambata, kana su ka nufi kofar fita. Su na fita ya janyo wayar sadarwar da ke dare a kan teburin ya soma laluban lambobi cikin sauri. *** Tunda Motar yansandan da ke dauke da yansanda hudu ta shiga faffadar unguwar, Sifeto Habibu da ke zaune a kujerar gaban motar ya ke ta rarraba idanu cikin fatan ganin lamabar da aka ba shi wadda aka ce ita ce lambar gidan Alhaji Basiru. Abinka da unguwar masu hannu da shuni, shiru babu motsin komai sai haushin karnuka da ke tashi lokaci-lokaci. "Tsaya mun zo gidan." ya ce ya na duban Direban bayan ganin lambar da maigidansa ASP Haladu ya ba shi sakale jikin kofar gidan da su ke kokarin giftawa. "No 20 B KNS." ya kuma ambatar lambar a fili, ya na duban wadda ya rubuta jikin wani dan littafi da ke rike a hannunsa, a lokaci guda kuma ya na duban wadda ke makale jikin kofar. Tabbas yanzu ya yarda gidan ne, don haka sai ya umarci Direban da ya gyara tsayuwar motar a gaba da gidan kadan. Ba gaba dayansu ne ba ne sanye da kayan aiki a jikinsu. Su ka mayar da murafen motar su ka rufe. Sifeto Habibu ya jagorance su har bakin makekiyar kofar. Sau daya kawai ya kwankwasa kofar, jim kadan sai su ka ga ta bude. Ba su yi mamakin hakan ba don sun san an san da zuwansu. Maigadi Bukar ne ya bude kofar. "Sannunku da zuwa." Ya ce da alamun mamaki a fuskarsa. Meyiwa saboda ganin su da ya yi ba yadda ya zata ba, cikin fararen kaya, "Ince dai ko kune jami'an tsaron". "Eh, mune Baba". Daya daga cikin su ya bashi amsa a takaice. "Bari nayi muku jagora zuwa ciki". "To, Baba." Sifeto Habibu ya amsa. Har maigadi Bukar ya shiga gaba da zummar su bi shi zuwa ciki, sai Sifeto Habibu ya ce, "Baba kafin mu shiga ciki ina so na yi ma wasu yan tambayoyi a matsayinka na maigadin wannan gida." Maigadi Bukar ya tsaya, "To, Dan nan, Allah ya sa na sani." Sifeto ya yi murmushi, "Ai sanannen abu ne a gare ka domin kuwa adadin shekarun da ka kwashe kana aiki a wannan gida na ke so mu sani." "E to! Ku san ni ne maigadi na farko tun gina gidan." "kusan ne, ko kuma kai ne?" Sifeto Habibu ya nemi tabbaci. "To, ni ne". "To Baba da ya ke kai ne maigadi tun farko, ko ka san wani abu game da Alhaji da matansa?" Shiru tsawon dakiku bai amsa ba, can ya nisa, "Yallabai ka san tsakanin miji da mata sai Allah, gaskiya ni kullum ina nan bakin kofa, zai yi wuya na san abin da ke gudana a ciki, sai dai kawai na san kirki da rashin kirkin kowacce a cikin matan. Idan shi ka tambaye ni zan iya fada ma. Tunda mai kyauta da mai rowa ma Allah Bai yi su daidai ba." Kusan dukansu sai da su ka yi murmushi. "Banda wannan Baba." Sifeto Habibu ya ce, "To, bayan kai akwai wani ma'aikaci a gidan?" "Eh, kwarai kuwa, akwai abokin aiki na amma shi ya jima da rasuwa, don yau..." ya cira kai sama alamar tunani, "Ina ga zai kai shekaru kamar bakwai da rasuwa." A wannan karon kusan ya ba duk yan sandan haushi, musamman Sifeto Habibu da shi ya ke tambayoyi. "Banda wanda ya rasu Baba. Bayan wannan ba wanda ya ke aiki a gidan ko da ba irin naka ba?" "Eh, lallai akwai Lukman, amma shi Direba ne." Sifeto ya gyada kai, "Ko ya na nan yanzu?" "A'ah ba ya nan, don shi rabonsa da gidan nan tun da rana da ya dauko yara daga makaranta, kuma shi da ma haka al'adarsa ta ke, idan ya kai yara makaranta ya koma da rana ya dauko su to aikinsa ya kare sai kuma gobe. Shi ya sa ko dazu ma da za a kai su Alhaji asibiti sai wata Bakuwar Hajiya Karama (Zainab ya ke nufi) da kuma kanin Alhaji ne su ka ja motocin" Sifeto Habibu ya nisa gami da gyada kai alamar gamsuwa, "Wato yanzu kai kana nufin shi Lukman ba ya nan abin ya faru?" "Sosai" In ji maigadi Bukar. "To Baba na ji kuma kawar Hajiya Karama, wace ce Hajiya Karama?" "Amaryar Alhaji Kenan" Ya amsa cikin dariya, "Ita a ke cewa Hajiya Karama, amma ni kadai na ke fada mata saboda la'akarina na ga cewa ita ta zo gidan daga baya" "To, ita wannan kawa ta Hajiya Karama ko.." "Ba fa sunanta Hajiya Karama ba, ni kadai na ke fada mata. Sunanta Zainab" Maigadi Bukar ya katse Sifeto Habibu. Sifeto Habibu ya yi dariya, "To, ita kawar ta Zainab ya sunanta?" "In ga?" Ya yi jim, "Sunanta Hannatu" "Kar dai ka gaji Baba, kasan aikin da mu ka zo yi kenan, ko za ka iya tuno tsawon lokacin da ita Hannatun ta dauka a cikin gidan, ma'ana tun yaushe ta zo, kuma yaushe ta fita?" "A'a dama ita al'adarta tunda na san ta, idan ta zo tun safe ba ta barin gidan nan sai yamma likis. To yau din ma ina zaune anan daidai lokacin da ta saba tafiya sai na ga sun fito gaba daya cikin halin rikita. To! Ka ji." Kusan gaba daya duk wanda ya kasance a falon yayin da al'amarin ya faru dazu, ya na cikin falon yanzu idan ka duke Barista Hannatu da kafin su Alhaji Sambo su koma asibitin ta tafi gida, sai kuma Hajiya Rukayya da ke can dakinta a kwance kasancewar ciwo da ta ce kanta na yi. Bayan yan gaishe-gaishe da jajantawa da yan sandan su ka yi ga mutanen da su ka iske a falon sai jagoran tafiyar, Sifeto Habaibu ya bukaci ganin gawarwakin su Hauwa'u. Ba tare da bata lokaci ba, Alhaji Sambo da Alhaji Gali su ka kai yan sandan wani daki da ke like cikin falon inda anan ne su ka shimfidar da gawarwakin. Lillibe da farin kyalle su ka iske su. Sifeto Habibu ya isa gare su ya duka a hankali ya yaye kyallen iya fuskokinsu. Idanunsu duk a rufe su ke. A hankali ya mayar ya rufe kana ya mike ya dubi jama'ar tasa. "Doctor Nasir." Ya kira sunan daya daga cikin su. "Na'am yallabai." wani dan dogo ya amsa. "Ina so ka yi mana kyakkyawan bincike akan wadannan." ya nuna gawarwakin, "Mu za mu koma falon." "An gama yallabai." ya ware daga cikin yan uwansa ya nufi gawarwakin, daidai lokacin da su Sifeto Habibu da sauran yan sandan su ka fice daga dakin zuwa falon. Har yanzu Zainab da ke zaune kan daya daga cikin kujerun falon na nan, ta zabga tagumi, hawaye sai kwaranya ya ke daga idanunta, danta Mujahid zaune kusa da ita, shi ma ya na kuka, meyiwa saboda ya ga ta nayi. Bayan sun kuma zama sai Sifeto Habibu ya dubi Alhaji Sambo, "Alhaji da ya ke kai ne kanin maigidan nan uwa daya uba daya, ko za ka iya sanar da mu iya adadin yan uwansa bayan kai?" ya girgiza kai, "Babu yallabai, mu biyu ne kawai a wajen iyayenmu." "To, su iyayen naku su na nan a raye?" "A'a, sun jima da rasuwa, don ni ban ma san su ba, tun ina karami su ka yi hadarin mota su ka rasu." Sifeto Habibu ya gyada kai, "To, bayan wannan ko ka san wani mutum da su ke muhimmiyar alaka da shi." "Su na da yawa, ga daya ma kusa da ni. Shi ne ma babba daga cikin aminansa." Ya nuna Alhaji Gali. Shi kuwa ya yi dan Murmushi. Sifeto ya kalle shi, "Alhaji kasancewarka aminin Alhaji fiye da kowa cikin aminansa, bai taba sanar da kai cewa akwai wani abu da ke damun sa ba, kafin wannan abin ya faru da shi?" ya girgiza kai, "Bai taba ba, sai dai kawai matsaloli na gida da ya ke yawan kawo min, ina nufin game da iyalansa." "Matansa kenan?" Bukata daga Sifeto Habibu. "Eh." Amsa daga Alhaji Gali. "Kamar wace irin matsala ya ke yawan kawo ma game da su?" "Rashin zaman Lafiya a tsakaninsu." "Kamar ya ya?" Sifeto ya bukata bayan ya ware hannuwa. Sai da ya yi gyaran murya domin bai yi tsammanin Sifeto zai nemi sanin irin matsalar ba. "Kamar yawan rikici da su ke..." "Na gane wannan." Sifeto Ya katse shi, "Game da me su ke yin rikicin?" Alhaji Gali ya dubi Zainab, "Kamar ita amarya da ta ke shan tsangwama da matsi daga uwar gidan..." "wato dai ka na so ka ce uwar gidan ce ke haifar da matsalar." "Eh, haka ne." Sifeto ya gyada kai bayan ya dubi dan sandan da ke ta faman rubuce-rubuce. Ya mayar da dubansa ga Zainab da har yanzu ke ta faman zubar da hawaye. Ba wani abu ne ya sa ta cikin wannan ya nayin ba sai sharrin da aka kulla mata, ita a rayuwar duniya ba abin da ta tsana irin a ce ta yi abin da ba ta yi ba. "Wannan wacce ce daga ciki?" Sifeto ya nuna Zainab. "Ita ce Zainab, amaryar kenan". Alhaji Sambo ya amsa. "Sannu amarya." sifeto Habibu ya ce da ita, "Ya mu ka kara ji da hakuri." "Hakuri sai Ma'aiki." Ta amsa da kyar cikin muryar kuka. "Hajiya, mu ma'aikata ne kamar yadad ki ka sani, mun zo ne domin warware wannan dambarwa musamman ma ga ke da ake zargi a matsayin matar da ta aikata kisan kai..." Zainab ta girgiza kai, "Wallahi Yallabai ba ni ba ce hasalima ni ban san da wata Alewa ba sai da aka umarce ni na dauko." Ta fashe da kuka. "Ya isa Hajiya." Sifeto Habibu ya dakatar da ita ganin kukan na kokarin tsawaita, "Ba kuka za ki yi ba. Abin da kawai na ke so ki gane shi ne, hukuma ba ta yankewa mai laifi hukunci har sai ta yi bincike ta tabbatar da laifinsa. To daga nan kuma sai ta hukunta shi daidai da abin da doka ta shimfida." ya tsagaita, kana ya ci gaba ganin ta sassauta da kukan, "Hajiya kin ce ba ki san da wannan Alewar ba a farko har sai lokacin da aka umarce ki da ki dauko ko? Ta gyada kai. "To, wane ne ya umarce ki ki dauko?" "Alhaji ne." "Alhaji? Maigidanku kenan?" "Eh." "To shi ya aka yi ya san da Alewar?" ta yi shiru na dan lokaci kana ta ce, "Shi ma bai san da ita ba sai bayan da mujahid ya ce ya na da ita a aljihun wandonsa na makaranta." "Wto ya tabbata ke ki ka je da hannunki ki ka dauko Alewar ki ka kawo ko?" "E, ni na dauko." "Ya gyada kai," To, wane ne Mujahid." "Ga shi." Ta dafa kan Mujahid da ke zune kusa da ita shi ne dan naki?" "shi ne." Ta tabbatar. "Zo Mujahid." Sifeto ya ce ya na dubansa gami da mika masa hannu. "Tashi ka je". Zainab ta ce da shi ganuin ya na dubanta. Mujahid ya mike idanunsa fal da kwalla ya nufi Sifeto, tun kafin ya kai gare shi ya mika hannu ya rike shi. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 3 Posted by ANaM Dorayi on 08:22 AM, 29-May-15 "Yaro kai ne Mujahid?" "Uhm!" ya amsa a ciki gami da gyada kai, a lokaci guda kuma ya na waiwayen mahaifiyarsa. "Wace ce mamanka?" ya nuna Zainab. "Ka na makaranta?" "E, ina yi." A wannan karon ya bude baki. "A wacce makaranta ka ke?" "Sasif Model School". "Ajinka nawa?" "A Naziru tu (Nursery 2) na ke." Mujahid ya amsa. Lallai yanzu ya tabbatar mujahid ya na da wayo. To amma ya na so ya tabbatar saboda tambayar da ya ke son yi masa sai mai wayo sosai ne zai iya amsawa. "Ka iya turanci?" Ya bukata bayan ya saki murmushi. Ya gyada kai, "E, na iya". "Idan na yi maka tambaya za ka iya mayar min?" ya gayda kai ba tare da ya yi magana ba. "How old are you?" (Shekarunka nawa). "I am five years old." (Shekaruna biyar). Kusan ba wanda bai ba sha'awa ba, saboda yadda ya amsa turanci ba tare da rawar baki ba. Yanzu Sifeto Habibu ya samu tabbacin Mujahid na da wayo sosai, hakan ne ya ba shi damar shiga yi wa Mujahid tambayoyi kai tsaye, "Mujahid wane ne ya saya maka Alewa?" "Momi babba ce." "Wace ce Momi babba...wannan?" ya nuna Zainab. "A'a." Mujahid ya ce da girgiza kai, "Daya Momin." "Waccekenan?" "Momin yan biyu." Sifeto ya gyada kai, ya gane wadda Mujahid ya ke nufi, "To, a ina ta saya ma?" "A makaranta." "Yaushe?" "Un...un, gobe da safe." "Gobe da safe? Ko dai yau da safe?" Sifeto Habibu ya gyara masa. Ya san shirme ne na yaro. Kuma ya kwana da sanin cewa ba kowane yaro ne ke iya rike lissafin raneku ba. "Eh, yau da safe ne." Mujahid ya gyara. "A wajen Habu mai shago, na makarantarmu." "Ka tabbatar?" ya gyada kai. Sifeto Habibu ya juya ga su Alhaji Sambo, "Alhaji ina ita uwargidan ta ke, ko ta na asibitin?" "A'a, ta na cikin daki, ba ta jin dadi ne." "Assha! Allah ya sawake. A wane daki ta ke?" "Ta na dakinta, zo mu je." Alhaji Sambo ya gayya ce su bayan ya mike tsaye. Yan sandan su ka mike su ka dafa masa baya, su ka bar Alhaji Gali da Zainab da Mujahid a falon. Sa'ar da su ka isa dakin Hajiya Rukayya kwance su ka same ta kan gado ta na ta faman barci, amma na karya. Kafin shigowarsu idanunta biyu, amma jin motsinsu na nufo wa dakin ya sa ta rufe idanun nata kamar mai barci. A nata tunanin wannan wata hikima ce da za ta kubutar da ita daga tuhumar yansandan, don gudun kar a gane ita ce sanadin afkuwar aika- aikar. Su ka dan tsaya a kanta, tsayuwa ta yan dakiku. Bayan kiran da Alhaji Sambo ya yi mata a kalla sau biyar, shiru babu ko motsi, sai Sifeto Habibu ya ce, "Kyale ta Alhaji mu koma falon." Babu wanda ya yi magana su ka juya su ka fice daga dakin. Su na shigowa su ka iske Doctor Nasir zaune ya na jiran su. "Ya ya Doctor, me ka gano?" Cewar Sifeto Habibu. Doctor Nasir ya mike tsaye, "Yallabai binciken da na yi na samu akwai guba mai hadarin gaske a jikin Alewar da su ka sha, wanda gubar na iya kashe mutum nan take. Idan kuma wasu halittu ne ba mutum ba, ba sai sun kai ga sha ba, ko shakar ta su ka yi za su iya mutuwa." Sifeto Habibu ya jinjina kai, "Yanzu dai ka gama kenan?" "E, na gama." Sifeto ya juya ga su Alhaji Sambo, "To, Alhaji a yanzu mun kammala wannan a matsayin rukuni na farko kafin mu dawo na biyu. Kuma kamar yadda doka ta tanada, za mu tafi da ita amaryar har zuwa lokacin da za mu kammala bincikenmu mu mika abin kotu." Zainab ta cira kai da sauri ta dube shi, "Yallabai me na yi?" "Ana zargin ke ce da hannunki ki ka dauko alewar da ta kashe wadannan yara." Kasa magana ta yi, kawai ta kifa kai ta shiga yin wani kuka na takaici, kukan da ka iya sa mai dakakkiyar zuciya taya ta. Amma duk wannan bai hana jami'an tsaron tafiya da ita ba, har da Mujahid ganin ya ki yarda a tafi da ita a bar shi. *** Kamar yadda ya zame masa sabo zuwa gidan karfe bakwai na safe domin kai yara makaranta, yau ma haka ne. To amma sabanin lokutan baya, yau ya riski mummunan labari da bai taba tsammani ba koda a mafarke-mafarken da ya sha yi a daren jiya. Tun da dai ya iso gidan ya ke zaune wajen maigadi Bukar wanda ya labarta masa faruwar mummunan abin, sai ya ji duk jikinsa ya mutu. Ya cire tagumin da ya zabga hannu bibbiyu bayan ya nisa, ya dubi maigadin, "Wato yanzu kenan kana so ka ce yan sandan sun gane cewa Zainab ce ta aikata laifin?" "Ba ni ne na ke son na ce ba, hakan ne. To idan ma ba haka ba, me ya sa su ka tafi da ita?" Lukman ya jinjina kai, yayin da shi kuma Bukar ya ci gaba da cewa. "Kai lallai mugu ba shi da kama. Kaga dai matar nan idan bangaren sakin fuska ne, kyauta da alheri ba kamar ita, ashe ashe... Shi ya sa fa wasu suke cewa mai shiru-shiru mugu ne, ko ni yanzu da na auri ami shiru-shiru gwanda mai suru..." "Ba haka ba ne!" Lukman ya katse shi "Ni ina da jan akan wannan al'amari, domin tabbas na san Zainab ba zata aikata wannan danyen aikin ba." "Uhm, uhm, Lukman.. Ka ga! Ka kiyayi kanka da shisshigi cikin wannan magana domin kuwa abin ya dangana da hukuma, idan aka ji kana fadar haka kai ma za ta iya shafarka." (Ayimin afuwa narasa kusan phragrap daya) Ta yi shiru na dan lokaci, kana ta ce "Lukman- Lukman na ji ka ce ka yi laifi da ka zo yau ko?" "Cewa na yi, na yi ko ban yi ba?" ya gyara ma ta. "To ba ka yi ba, ai dama kwana daya mu ka yi ko?" "Eh." Ya gyada kai. Falon ya yi shiru na dan lokaci. "Lukman ina bukatar wani taimakone gare ka kamar yadda ka yi min na baya..." A bazata ya ji maganar, har sai da ya dan zabura. Ya kalle ta a bukace da son jin taimakon, "Hajiya kamar na me fa?" Maimakon ta fada masa, sai ta ce, "Lukman a wancan karon nawa na ba ka?" "Du...bu daya." Ya amsa cikin rawar baki a tunaninsa cewa za ta yi ya biya ta. "Yau na shigangada, ina zan samu dubu daya." Ya ce a ransa. "To, a wannan karon aikin da zan sa ka ya rubanya na baya a kudi sau goma, kuma mafi sauki wajen aiwatarwa akan na baya. Ka ga kudin zai kai dubu goma kenan." "Dubu goma Hajiya?" Bai san sa'ar da ya ambaci hakan ba. A iya rayuwarsa yau shekaru arba'in da daya kenan bai taba rike naira dubu goma tasa ba. Koda ya ke ba anan ya fara aikin tuki ba, ya fara ne a gidan wani attajiri A.A. Boza. A wancan lokacin ya dai sha ganin makudan kudi, ya ma sha raka Alhajin banki karbo miliyoyi, amma duk wannan ba ta sa ya taba rike dubu goma a matsayin mallakar sa ba, har zuwa sa'ar da ya bar gidan ya dawo nan. "Eh, dubu goma Lukman, ka na ja ne?" Ta tabbatar ma sa gami da bukata. Ta ci gaba jin ya yi shiru "Me ka gani? Kawai idan za ka iya ka amsa min, sai na baka rabin kudinka tun yanzu ka ga zarar ka kammala sai ka karbi rabin." "To..to Haji..ya ya wanne irin aiki ne wan...nan? Ke ba ki fada...min ba har yan...zu." Ya ce bakinsa na rawa. "Ba wani aiki ba ne magana ce kawai ta fatar baki." "Idanunsa suka kara girma (alamar mamaki). Ya za a ce daga maganar baki mutum ya sami dubu goma? "Shekara nawa dubunnai daga cikin al'umma ke dauka su na aikin karfin musamman a wannan kasa tamu da mutum ke dama da talauci amma su ke gaza mallakar dubu goma?" a zuciyarsa ya fada. "Ya ka ce?" Ta dawo da hankalinsa gare ta. "Hajiya ina tunanin wacce irin magana ce mutum zai fada da baki kawai ya sami Naira dubu goma? Ta kyalkyale da dariyar karfin hali har da kyakya cewa. "Ka ga kuma magana ce mai sauki wajen fada, kwatankwacin gyada kai ko girgizawa ga mutum yayin da ya ke amsa tambayoyi, abin bukata kawai, za ka iya?" "Ka ce za ka iya dubu goma ba wasa ba ce." Wani sashe a zuciyarsa ya rada masa. Kai tsaye kuma ya ci gaba da lissafa ma sa abin da zai yi da dubu gomar, ciki har da auren dalleliyar bazawara sauta ga wawa. "Eh..zan iya." Ya amsa kai tsaye. Ta dan kau da murmushin da ke kan lebbanta. "Ka san duk abin da ya faru a gidan nan ko?" Ya jinjina kai. "Na sani Hajiya." "To a takaice dai yan sanda jiya sun zo sun yi bincike amma ni ba su bincike ni ba saboda ba ni da lafiya amma kowane lokaci daga yanzu su na iya zuwa kuma dama wanda su ka rage ba a yiwa tambayoyin ba mu biyu ne, ni da kai." Ya yi zumbur ya mike tsaye cikin firgici, "To ni me na yi?" Ya bukata cikin saurin baki. A rayuwarsa duk barikin da ya yi ya na karami ba abin da ya fi tsoro irin yansanda, duk da kasancewarsa gwani kuma shugaban zuke-zuke da caca a kauyensu wancan lokacin. Ta bi shi da kallo cikin mamaki, kana ta bushe da dariyar karfin hali ganin har ya fara hada gumi duk da na'uarar sanyaya daki da ke iya bakin kokarinta a karamin falon. "Zauna mana to, sarkin tsoro ina za ka?" Ya yi ajiyar zuciya "Ai Hajiya abin ne na ji ya na kokarin fin karfi..." "To zauna ka fada mana!" Ta ce da daga murya. Ya zauna a hankali. "To mene ne ke kokarin fin karfinka?" Ta bukata. Ya share gumin da ya soma taruwa a goshinsa. "Hajiya ni kin san duk wani abu in dai da yan sanda a ciki tsoronsa na ke." "Ka na namijin?" Ta rike baki. "To shi namiji karfe ne bai san wuya ba?" ya ce ya na zaro idanu. "Ai idan ki ka lura ma ko karfe idan ya sha wuya ya na sarrafuwa." Hajiya Rukayya ta yakune fuska, "To ka ga kwantar da hankalinka, in dai ina raye ba kai ba wahala, ka na ji ko?" Ya dube ta ya dan yi dariya "Allah Hajiya?!" "Af, ka dauki abin wasa, kawai ka yarda ka karbi wanan garabasar kar ka zama mai gudun rabo." ta dan kwantar masa da hankali. "To na ji Hajiya, wacce irin magana ce?" Ta mike tsaye, "Ina zuwa" Ta fice daga falon, ta bar shi zaune a nan ya na ta sake-saken zuci. Jim kadan ta dawo, kudi rike a hannunta yan naira hamsin-hamsin bandir guda. Ta na zuwa daidai shi ta jefa masa a kan cinyarsa. "Ga su nan naira dubu biyar ne, kafin ka kammala na cika ma sauran" numfashinsa ne ya ji kamar zai dauke da ya dubi kudin. Nan da nan ya dauka ya fara jujjuyasu. Sababbi ne kal-kal. Ya nayin kallon da ya ke musu na maita sun isa su tabbatar da a shirye ya ke ya aikata duk abin da aka umurce shi, tuni ya manta da cewa ya zo ne ya ji dalilin da ya sa Hajiyar ta hana shi zuwa gidan shekaran jiya da kuma kyautar dubu dayan da ta yi masa. "Hajiya yanzu ke na ke jira.. Wacce magana ce?" Ta yi murmushi ganin cikin dan kankanin lokaci ta gama shawo kan Lukman da maasu gidan rana (kudi). san kalmar a'a?" Ta bukata bayan ta tsayar da dubanta gare shi. Tambayar ta ba shi dariya, "Haba Hajiya ai ko yaron da aka yaye yanzu ya san wannan kalma. Ita wannan kalma ai ta na amfani ne yawanci don nuna ba haka abu ya ke ba, na ki ko rashin sani ga wani abu, kai har..." "Yauwa dan gari da kai ake zance". Ta katse shi, "To abin da na ke so ka yi kenan a duk sa'ar da yansandan su ka riske ka don yi ma tambayoyi, ma'ana duk abin da ka sani sai ka nuna ba ka sani ba, abin da ba ka sani ba shi ma daman ba ka sani ba." "Af, lallai aikin mai sauki ne" ya ce a ransa kana ya bushe da dariya "Wannan ne kawai aikin Hajiya?" "Eh mana" Ta amsa ta na tabe baki. "Yanzu daga wannan na ci dubu goma?" "Kwarai kuwa." Ta tabbatar masa. Ya kuma duban dubu biyar din da ke hannunsa, sannan ya mike tsaye ya sa a aljihun wandonsa, ya koma ya zauna. "To sha kuruminki Hajiya an gama, yaushe za su zo?" "Kowanne lokaci daga yanzu, kai dai ka kasance cikin shiri" ya kuma mikewa "To ina iya zuwa gida na adana kudin nan na dawo?" Ta kalle shi "Ka na iya zuwa amma ka dawo da wuri" Har bakin kofar ta rako shi da amon muryarta ta na jaddada masa bukatarta, shi kuma ya na dafe da kudin ya na tabbatar ma ta da kada ta ji komai. *** Kamar yadda abin ya ke a zukatan wadanda ya shafa, ita ma Barista Hannatu haka ya ke a zuciyarta domin tun a jiyan da abin ya faru bayan ta koma gida ta kasa runtsawa, babu komai cunkushe a zuciyarta sai mamaki da tunanin faruwar al'amarin. Har kawo yanzu karfe bakwai da rabi da ta shirya ta ke kokarin tafiya asibitin, tunanin ya gaza yankewa. To amma fa har zuwa yanzu zuciyarta ta ki ta amince da cewa kawarta ce ta aikata laifin. Shi ya sa yanzu ma da take tsaye gaban dogon mudubin bayan fitowa daga wanka take gaggawar ta tafi asibitin domin bin diddigin abin don sanin gaskiya, a matsayinta na mai bayar da kariya (Lawyer) Bayan fitowarta da nufin tafiya asibitin sai ta yi tunanin tafiya gidan su Zainab domin sanar da mahaifanta. Shakka babu ta san rikicewar da kawar tata tayi zai yi wuya ta sanar da mahaifan nata. Sa'ar da ta isa gidan ba ta iske mahaifin Zainab ba don tuni ya tafi kasuwa. Ko da ta sanar da Mahaifiyar Zainab da wani yayan Zainab din da ta samu a gidan sai su ka rikice, su ka rasa yadda za su yi. Daga karshe da kyar Barista Hannatu ta rarrashe su ta nuna musu idan Allah ya so komai zai daidaita. Bayan ta bar gidan kai tsaye ta wuce asibitin. Ko da ta isa sai ta iske labarin cewa ai tun jiya kawarta ta ke hannun hukumar binciken laifuffuka (Yansanda) sai ta ga ba ta ga ta zama ba. Nan da nan ta bar asibitin ta tunkari hedikwatar yansandan. Ba a wannan karon ne ta taba zuwa hedikwatar ba, wannan shi ne karo na uku, domin a baya ta zo kusan karo biyu don yin wasu bincike game da wasu kesa-kesai (Cases), da ta kare, don haka ba bakuwa ba ce a wajen. Kai tsaye bayan ta isa ta wuce ofishin ASP Haladu domin saninta na cewa shi ne ofishin da ke da alhakin wannan matsalar. Ta kuwa yi sa'a ba ta samu cunkuson jama'a ba kamar yadda ta sha samu a baya. Bayan dan jira na abin da ba a rasaba aka yi ma ta umarni da ta shiga. A nutse cikin dankareriyar kujerarsa ta same shi, shi ne dai da ta sani. Shi ma bai manta ta ba. Bayan sun ida gaisuwa, ya ce, "Barista-Barista, yau ke ce da kanki?" Ta yi yar dariya "Ni ce Wallahi yallabai" "Ina ce dai kes (Case) ki ka biyo?" Ta gyada kai kawai ba tare da ta yi magana ba. "Yauwa ni na san dai ganin ku ba banza ba, akwai magana" ya ce shima ya na dariya "Wane kes ki ka biyo?" "Yallabai na biyo kes din wata kawata ce Zainab wadda aka kawo ta nan jiya" Alamun dariyar da ke kan fuskarsa su ka sauya zuwa na mamaki. "wacce Zainab ce kawarki? Wadda ake zargin ta aikata kisan kai? Menene hadin ki da ita?" Barista Hannatu ta yi dan murmushin karfin hali "Yallabai ina da ja ne game da zargin da ake mata, domin kuwa na san zai yi wuya ta aikata, tun da kuwa na san halayenta ciki da waje, tun muna firamare (Primary) muke tare" ASP Haladu ya nisa "Wato yanzu dai ki na so ki nuna min cewar sanin da ki ka yi ma ta tun daga firamare zai iya hana ta aikata laifin da ake zarginta ko? Ko mutum idan ya na karami idan ya girma halayensa ba sa sauyawa?" Ta girgiza kai "Ba haka nake nufi ba" "To ya kike nufi?" A wannan karon ya na dariya ya bukata. "Ina nufin a yadda abin ya faru akwai dimbin mamaki ace wadda ake zargi ce ta aikata" "Wato yanzu dai ki na da ta cewa kenan?" ya bukata har yanzu ya na dariya. "Shi ne ma dalilin da ya sa na zo?" "Ki na nufin za ki iya ba ta kariya ne?" A yanzu ya tattara hankalinsa gare ta kamar mai kokarin gane wani abu a tare da ita. "Eh, kariya na ke so na ba ta da kuma bi ma ta kadin sharrin da a ka yi ma ta na bata suna, yanzu ina so a mika batun kotu ne?" ASP Haladu ya fashe da dariya, kana ya ce bayan ya sassauta. "Na san ki na da kokari sosai wajen tsayawa a kotu don ganin kin baiwa wanda ki tsayawa kariya. Amma wannan karon na san ko da ni mu ka tsaya a kotu sai na kada ke, duk da ba aikina bane. Barista Hannatu ta dan biyewa dariyar da ya ke yi ciki karfin hali. "Ba ka fahimci abin da nake nufi ba shi ya sa, saboda haka kawai ka kyale ni. Ina kan bakata ta ba ta kariya kuma yallabai yanzu ina son ganinta." Ta sauya hirar. Ya yi jim na dan lokaci sannan ya ce "Barista da dai kin jinkirta zuwa lokacin da za mu karasa bincike tun da yanzu mun yi nisa, domin yanzu ma akwai wadanda na tura can gidan don su kuma samo mana wani abu." Ta nisa "Yanzu ba za a bar nu na ganta ba kenan?" Ya yi shiru ya na tunani, ya san idan ya hana ta ganin Zainab din a matsayin wadda zata ba kariya bai kyauta ba, dadin dadawa ba shi da zabi don haka sai ya ce. "To yanzu ki ke son ganin ta ko kuwa ya ya?" Ta yi yar dariyar karfin hali (domin duk abin da ta ke hankalinta ya na ga tunanin Zainab din, da halin da take ciki). "Eh! Yallabai yanzu mana." Barista Hannatu ta ce. *** Idan ka kwatanta fitar Lukman da shigowar yan sanda gidan du-du-du bai dara rabin sa'a ba. Su ma a zaune a falon su ka iske Hajiya Rukayyar tare da yan zaman makokin, sa'ar da maigadi Bukar ya yi musu jagora. Bayan sun gaisa tare da yi ma ta gaisuwa, sai Sifeto Habibu ya shiga yin abin da shi ne ya kawo su, ba kama kafar yaro. "Hajiya zan so dayan biyu cikin wadannan abubuwan." ya dan yi shiru sannan ya ci gaba, "Ko dai mu kebe a wani waje ba wannan ba, ko kuma a dan ba mu waje." (Ya na nufin yan zaman makokin su fita daga falon. "A'a,mu ne dai ya kamata mu ba ku waje..." Wata mata da ta yi matukar kama da Hajiya Rukayya ta fada da saurin baki. Kana ta mike ta ce da sauran matan, "Ku taso mu koma ciki kafin su gama." Babu wadda ta musa, sauran matan su ka mike jiki a sanyaye su ka rufa ma ta baya, kai tsayae su ka fice daga falon. Sifeto Habibu ya numfasa, "Hajiya tun a jiya mu ka so mu ji ta bakinki game da wannan al'amari, amma sai ya kasance ba ki ji dadi ba shi ya sa mu ka jinkirta zuwa yau. To amma a binciken da mu ka yi mun samu labarin cewa ke ce ki ka sayawa yaran ita waccan alewa da ta zama silar rayuwar yayanki... Ya ya abin ya ke?" Ta zunkuda kafada gami da girgiza kai." Yallabai ni ba ni na saya musu irin wannan alewar ba. Ni alewar da na saya musu ma... Ai ba jiya ba ne yau fa kusan mako guda kenan, kuma ace ba a sha ba sai a jiya?" Sifeto Habibu ya girgiza kai "Hajiya Wannan fa an ce a jiya ne sa'ar da ki ka kai su makaranta..." "A'a ni jiya da na kai su makaranta ban saya musu komai ba. Ni dana kai su a makare, yaushe zan tsaya na saya musu alewa?" Ta fada ta nadaga hannu. "Yanzu dai ke alewar da ki ka saya musu an kai mako guda kenan?" "Sosai kuwa, domin jiya mako guda daidai." Ya jinjina kai "To Hajiya na ji kin ce jiya kin kai su makaranta da kanki. Me ya sa? Ko dama ke ce ki ke kai su? Ba ku da direba ne?" Tambayoyin sun yi ma ta yawa don har taso ta rikice sai da ta dau dakiku a kalla goma kafin ta ce "Direba ne ke kai su, amma ai ranar makara ya yi..." "Bai zo akan lokaci ba kenan?" Ta gyada kai "Kwarai domin har na dawo bai zo ba. "To bayan ya dawo ya sanar da ke dalilin makararsa? Ta gyada kai "Eh, bai tashi da koshin lafiya ba ne." Sifeto ya gyada kai a lokaci guda da nisawa. "To bari na koma da ke baya Hajiya, a wancan lokacin da ki ka saya musu alewar tsawon sati da ya shude, a ina ki ka saya musu? Itama a hanyar makarantar ne?" Ta girgiza kai "A'a. Shi lokacin mun fita unguwa ne kawai". "To wacce iri ki ka saya musu?" "Ah!" Ta bude baki cikin mamakin karya "Alewa da ka sani Alewa ai Alewa ce." "Haka ne amma ai kowacce da sunanta ko?" "Eh, tabbas amma ni yanzu ba zan iya rike sunan ba domin ban kula ba." Ya nisa da karfi "To yanzu Hajiya, ina za mu ga matukin gidan nan, ma'ana direba." Da ta yi niyar ta ce musu yanzu ya fita sai ta yi tunanin kar su gano abin da su ka shirya. Sai ta sauya da cewa Bai zo ba amma kuna nan za ku gan shi." Ta na rufe baki su ka ji sallama a bakin kofar shigowa falon. "Yauwa ka ga dan halak ma, ga shi nan". Hajiya Rukayya ta ce ta naduban Lukman da ya daga labulen falon ya shigo. Gabansa ya fara faduwa ganin yan sanda uku zaune kowanne da gishin baki kamar jelar tsuntsu, habarsu aske tas kamar bayan kasko. "Kai sakarai kar ka nuna tsoronka tun yanzu mana, aikin naira dubu goma fa za ka yi kuma har an ba ka dubu biyar." Wani sashe a zuciyarsa ya tunatar da shi. Ya nufi daya daga cikin kujerun ya zauna. "Sannun ku da zuwa." "Yauwa sannu." Sifeto Habibu ya juya ga Hajiya Rukayya. "Hajiya don Allah dan ba mu wuri mana." Ta yi murmushi "To". Ta mike tsaye ita ma ta fice daga falon, sashikan zuciyarta na ta fadar ra'ayoyinsu game da hakan. Wasu na cewa "Shi kenan asirinki ya tonu." yayin da wasu kuma ke cewa "Kar ki yi wata fargaba, Lukman ba zai bayar da kafa ba. Meyen kudi ne fa!" Ganin ta fice Sifeto Habibu ya tattara hankalinsa ga Lukman. Cikin duba na kwarewa ya ce. "Malam Lukman kai ne direban gidan nan ko?" ya gyada kai gami da cewa "Ni ne yallabai" "Kai kadai ne direban ko da wani?" "A'a, ni kadai ne yallabai, ba wani". "To me ya sa jiya ba ka zo ka kai su ba?" Tambayar ta yi ma sa bazata hakan ne ma ya sa ya amsa cikin rawar baki. "Eh, ba ni...da la...lafiya, yallabai...mura ce ke damu...na, shi ya sa ban...ban zo ba.." Sifeto Habibu ya jinjina kai, "Wannan shi ne kawai ya hana ka zuwa." "Yallabai shi ne." "To waye ya je ya dauko su, ma'ana bayan an tashe su?" "Ni ne?" Ya dafa kirjinsa. "Lokacin murar taka ta warke ne?" "A'a, na dai samu sauki." Sifeto Habibu ya shafi dumbujejen gashin bakinsa cikin kokarinsa na son sauya hirar. "Lukman sa'ar da ka dauko yaran nan ko ka ga wani abu a tare da su. Abin nufi a hannunsu wanda ya danganci na sha?" Ya girgiza kai "A'a gaskiya ban ga komai ba." Yanzu ya dan nutsu "Sai dai ko jukukkunansu." "Ban da wannan Lukman. Mun gode." "Yallabai ni ne da godiya." Cewar Lukman. Ya mike ya fice daga falon saboda umarnin Sifeto Habibu na sa shi ya kirawo ma sa Hajiyar. Ba a jima ba su ka dawo tare. Sifeto Habibu ya dube ta bayan ta zauna. "Hajiya yanzu za mu tafi domin mu tattara duk abin da mu ka samu, in ya so daga yanzu zuwa daren yau za ki ji daga gare mu. "Mun gode". "Mu ne da godiya."Hajiya Rukayya ta ce. Su ka mike su ka nufi kofar ficewa, har sun kai ga kofar Sifeto Habibu ya waigo. "Ko da ya ke Hajiya." Ya fara takowa zuwa ciki "Za mu iya cewa yanzu mun kammala bincikenmu. Abin da ya kamata ki sani shi ne, za mu kai ku kotu domin warware wannan matsala a can." Ya taya ya na duban ta sa'ar da ya kai ga tsakiyar falon "Zan so na ba ki shawara idan ki na da lauya ki sanar da shi domin za mu yi komai daga yau zuwa kwana shida mu ga an kira ku." Gabanta ne ya fara bugawa kafin ta yi fari da kwayar idanunta, cikin karfin hali ta ce. "To...to..yallabai..za a sanar da shi." Sifeto Habibu ya juya ya nufi kofar inda yan uwansa ke tsaye su na jiransa, su ka fice. Hajiya Rukayya da Lukman su ka numfasa, numfasawa me nauyi bayan fitar yan sandan. "Yau na shiga uku Lukman, wai ka ji kotu za a kai mu." Hajiya Rukayya ta fada hannunta a dafe da kirjinta. Lukman da ke zaune can gefe ya zuba tagumi ya cira kai ya dube ta. Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa ganin Hajiya Rukayya ta rikice, "Hajiya mene ne na damuwa cikin wannan al'amari? Ke da kike da gaskiya kuma aka cuceki. Me ye cuta? Aka kashe miki yaya har biyu. Haba! Wannan ai kamata ya yi ki fi kowa farin ciki kuma..." "Ba haka bane Lukman ka san fa kotu da bin diddigi." "Ammaai daga karshe gaskiya ce take nasara ko?" Das! Sai da gabanta ya fadi kafin ta ce. "Eh, ha...ka ne, amma ni da an yafe.." "Waye zai yafe Hajiya ai ko ke kin yafe yan sandan nan ba za su yafe ba. Saboda haka kawai ki saki jikinki a karbo miki hakkinki." Ta nisa kana ta sa hannu ta share gumin da ya soma jika ma ta goshi. A lokaci guda kuma sai ta fara tunanin zuwan Baraka kawarta sa'ar da ta isketa a daki zaune har kawo sa'ar da su ka dawo daga gidan boka. Ta na tafe har lokacin da Mujahid ya iske ta a dakin girki ya sanar da ita farkon faruwar mummunan ala'amarin, kawo lokacin da likita ya ce sun mutu zuwa yanzu da yan sandan su ka gama bincike su ka ce wai za su mika kotu daga nan zuwa kwana shida. Nan da nan zuciyarta ta shiga hadawa da tantance riba da rashinta a cikin al'amarin. Cikin kankanin lokaci sai ta gano cewa babu wata riba da aka samu ko alama, domin kuwa na farko Wanda fa su ka yi domin shi (Dan kishiyarta Mujahid) na nan da ransa yanzu haka. Na biyu yayan ta biyu duka sun mutu, su na da gado kuwa? Tun da an ce shi Alhaji Basiru da sauran numfashinsa. Abu na uku wanda kuma shi ne uwa uba wai za aje kotu, gurin da ta tabbatar idan ta shiga asirinta ya gama tonuwa, daga ya tonu kuma ba ita ba sauran rayuwa domin ta san zai yi wuya ta tsira. Nan da nan sai ta ji zuciyarta ta shiga kogin nadama da dana-sani, a fage daya kuma da zargi gami da la'antar matar da ta sa ta a wannan tafarki, Baraka. Ta kuma nisawa da karfi a karo na biyu, take sai ta ji kwalla ta soma kwararowa daga idanunta. Lukman da bai san me take tunani ba sai ya ji ya kagauta ta gama abin da ta ke yi shi ta cika masa sauran kudinsa ya yi tafiyarsa domin ya yi alkawari a zuciyarsa gari na wayewa zai yiwa kasuwar kantin kwari tsinke domin samo yan atamfofin da zai ganganda ya aika gidan yar bazawararsa Bintoto, shi fa aure ya ke so. Shi ya sa ya kasa bata dama ta ci gaba da tunanin ya ce. "Hajiya, ni ina ga kawai ki yi hakuri ki dake kotu za ta kwatar miki hakki. Yanzu abu guda da nake ganin ya dace ki yi kawai ki nemi lauya.." sai yanzu ta ji magana domin ko babu komai dai bata da wani zabi da ya wuce ta binciko lauya da zai tsaya ma ta, don haka da Lukman ya tabo wannan bangaren sai ta cira kai ta dube shi. Murya a shake ta ce "Lukman a ina kake ganin zan samu lauyan... Ka san fa ni ban san yadda zan yi ba." Ya ji dadi ya ji ta bude baki ta yi magana domin ya san in dai za ta ci gaba da magana da shi to sauran kudin sa ma za su fito. Ya sosa kansa "Hajiya ai wannan mai sauki ne, ko anan unguwarmu ma akwai wani da na sani..shi ma lauya ne." Ta ji dadin hakan da ya fada. Ta sa gefen gyalenta ta goge hawayen dake zuba daga idanunta. "Lukman! Kana nufin anan unguwar ku akwai lauya?" Ya gyda kai "Kwarai kuwa Hajiya makwabcinmu ne ma." "To yanzu ya za a yi mu gana?" Ya sunkuyar da kansa cikin yunkurinsa na son tuno lokacin da ya san Barista Garba Shehu ke zama a gida. Ya cira kai ya dube ya bayan ya tuno, "Hajiya na kan yawan ganinsa a gida da yamma...kai, ko yau ma idan aka yi sa'a za a iya samunsa bayan La'asar." Ta numfasa cikin gamsuwa "To yanzu nan zan ce ya zo ko ni ya kamata na neme..." "A'a Hajiya ai zai fi kyautatuwa ki neme shi." Ya katse ta. "Shi wanda ka ke nema a wajensa ai samunsa ya dace ka je ka yi." "Haka ne!" Ta ambata ta na gyada kai, "To yanzu yau din ya dace mu je mu gan shi ko?" "Kwarai kuwa ai da safiya ake kama fara." "To shi kenan". Ta mike tsaye "Idan anyi sallar la'asar ka zo ka kai ni wajensa, kuma ina zuwa". Ta nufi wata ko far dake manne cikin tafkeken falon. Ya so ya ce ma ta dubu biyar dinsa, amma ganin tana sauri kuma ta ce masa ta na zuwa sai ya kyaleta. Ba ta jima ba ta fito ta iso daidai kansa ta mika masa. "Ga cikon kudin ka Lukman. Dan Allah kar ka bata lokaci hudun na yi ka zo mu je." "An gama Hajiya." Ya ambata sa'ar da ya damki kudin, tamkar mai kamun fara. "Da zarar lokaci ya yi za ki ganni". Ya mike "Ko yanzu ma idan na koma gida da zarar kin gan ni na dawo to fa ya na nan sai kawai ki shirya mu je." "Yauwa Lukman don Allah ka kokarta". "To" Har ya je bakin kofa da kudin a hannu sai ya tuna take ya tsaya kamar an kira sunansa daga baya, ya cusa kudin a aljihunsa ya yin da zuciyarsa ke cewa. "Lallai komai taurin ruwa in an jefa dutse sai ya lume a ciki. Ka duba tsumulmula irin ta Hajiya amma da yake Allah ya kwata min. Gashi zan yi arziki ta dalilinta..." Da haka ya fice daga falon." *** SABANIN dazu da ta bar ofishin ASP ba kowa ta je ta ga kawarta, yanzu ofishin akwai mutane a ciki. Wannan ne ya sa ta samu waje ta zauna a falon ofishin ta najiran su fito ta shiga, zaman da ya ci gaba da tariyo ma ta faruwar dagulallan al'amarin garai-garai kamar a allon sinima. Shakka babu kallo daya za ka yi ma ta tabbatar cewa ta na cikin halin matsananciyar damuwar da ke bukatar tallafin gaggawa, jifa-jifa abin da kawarta ta ke yawan ambata ne yayin da ta je wajen ta yanzu, ke fadowa cikin zuciyarta. -Wallahi summa tallahi Hannatu ban san komai game da wannan alewa ba har sa'ar dana dauko ta na kawo...ba ni na samar da alewar ba...wallahi ba ni na samar da ita ba." Kuka ne ke biyo baya, kukan da ke sa zuciya kuka. Ta numfasa kamar dai yadda ta ke yi duk lokacin da ta tuno wannan kalami mai karya zuciya, wanda a wani sashen zuciyarta kuma shi ne ke sawa ta kara jin kwarin guiwa akan kudirinta na kare ta da kwato ta daga wannan kangi. To a daidai lokacin da ta numfasan ne mutanen da ke cikin ofishin (wanda su take jira su fito ta shiga ciki) su ka fito. Da gaggawa ta mike ta cusa kai cikin ofishin. "A'a...! Barista har kin dawo?" Tun kafin ta gama mayar da kofa ASP ya ce hakan, ya na duban ta cikin bayyanar da wani malalacin murmushi. Ita ma ta mayar masa da murmushin bayan ta rufe kofar, sai dai babu bambanci da irin wanda ya yi mata, "Eh, yallabai na dawo" Ta ce a sanyaye. "Sannu da zuwa...Bismillah.." Ya ba ta umarnin zama. "Yallabai na je na gan ta." Ta ce bayan ta zauna. "To amma ina neman wata alfarma." Ya tsayar da idanunsa ga kallon ta bayan ya dan tsuke fuskarsa. "Wace alfarma kuma ki ke nema bayan wadda ki ka nema ta, a kai ku kotu?" Ta nisa, "Ban da wannan yallabai don ita dama ba alfarma ba ce, tunda kuwa wajibi ne ku kai kotu ko da ban nema ba, sabo..." "To na ji yanzu wace alfarmar ki ke nema?" Ya katse ta, a kagauce gami da tambaya don kuwa ya san gaskiya ne abin da ta fada ko ba ta nema ba tilas a kai maganar kotu. Ta dan yi murmushi, "Haba yallabai mene ne na harzuka, sai ka ce wadda na ce ka sake ta?" Ya mayar da bayansa ga majinginar kujerar ya jingina, "To ai ke ce na ji ki na so ki yi min tsari kamar wadda aka hau kotu". "O.k, dama su lauyoyi tsari suke yi?" Ta ce bayan ta kada kai gefe. "Kin ga ni ban ce ba." ya daga hannu, "Kar ki kai ni gaba." Su ka yi dariya tare. "Don Allah wace bukata ce, fadi, don ina da aiki mai yawan gaske a gabana, kin ga bayan fitarki ma an kawo min rahoton wani bincike da aka yi dazu a can gidan, ina so a hada shi a shigar kotu. Idan so samu ne a ce Litinin kun hallara a kotun." Ta sunkuyar da kai, jim kadan ta dago ta dube shi, "Yallabai akwai halin a bayar da belinta kafin zuwa kotun?" Ya girgiza kai, "No! No!! No!! This is non bailable offence Hannatu (a!a!!a!!! Wannan ba laifin da ake ba da beli ba ne Hannatu) Abu guda kawai da zai sa a sake ta shi ne, a yi shari'a a tabbatar ba ta da laifi. Idan ta wanku daga abin da ake zargin ta, to sai kotu ta sake ta". Barista Hannatu ta kuma dukar da kai. Ba ta da ta cewa, domin ta san hukuncin kenan. Daga karshe haka ta hakura ta baro hedkwatar yan sandan da zummar zuwa ta fara bincike akan dan abin da ta tattara da wanda ta samu a bakin Mujahid kafin ranar Litinin, duk da cewa ta yi-ta yi ya bi ta ya ki yarda. *** Karfe hudu da kwata na yamma Lukman direba ya daidaita tsayuwar motar kirar "KIA" a kofar gidan lauya mai zaman kansa Barista Garba shehu, kwararre, gogagge kuma fitaccen lauyan da lauyoyi ke shayin karawa dashi. Cikin sauri ya fito bayan ya kashe motar, ya budewa Hajiya Rukayya kofa. Sannu a hankali kamar mai cikin wata tara ta fito. Ya mayar da murfin a hankali ya rufe. "Hajiya, nan ne gidan!" Ya yi ma ta nuni da dan madidaicin gidan mai dauke da farin fenti, da su ke tsaye gabansa. Gidan ba ya cikin sahun gidajen kece raini idan har za a tsunduma shi cikin jerin gidajen ma su hannu da shuni. To amma duk da haka shi ma ba laifi don ko ba komai dai shafe ya ke da sabon fentin farar kasa. "To yanzu ya za a yi mu tabbatar ya na ciki?" Hajiya Rukayya ce ta bukata. Lukman ya yi yan waige-waigenshi, "Kin ga wani lokaci fa, a nan kofar gida ma za ki gan shi, amma..." Wani yaro ya hango shi ya sa maganar tasa ta katse. "Kai! Zo mana!" Ya ce da yaron bayan ya yafito shi da hannu. Bai yi gardama ba ya tunkaro su. "Hajiya bari mu tura yaron nan ya kira shi." Ya ce bayan yaron ya iso gare su. Ba ta yi magana ba, gyada kai kawai ta yi. "Kai don Allah shiga nan gidan kace ana sallama da barista.." "Nan gidan?" yaron ya bukata ya na mai nuna gidan da yatsansa. "Eh, nan". Bai sake magana ba ya nufi gidan ya shiga, jim kadan ya fito. "Wai an ce ya na zuwa." Tun kafin ya iso wajen su ya fada. "Yauwa yaro, mun gode ka ji?" Lukman ya ce kana ya dubi Hajiya Rukayya, "Hajiya mu tsallaka daga kan dakalin ko?" Suka tsallaka. Daidai lokacin ne Barista Garba Shehu ya fito. Fari ne, ya na da yar kiba amma ba can ba, haka zalika shi ba dogo ba kuma shi ba gajere ba. Ya na da yawan fara'a daidai gwargwado. "A'a, Lukman kai ne kake sallama." Abin da ya fara fita daga bakinsa kenan. "Barista Garba Shehu!" Lukman ya ce gami da daga hannu cikin jinjina. Barista ya mika masa hannu su ka gaisa, kana ya duba Hajiya Rukayya da ke faman kallonsa tun sa'ar da ya fito, ya ce, Hajiya ina wuni?" Ta dan saki fuskarta kadan "Lafiya lau, ya gari, ya aiki?" "Lafiya Sumul Hajiya" ya amsa. "To madalla, sannu!" "yauwa sannu." Lukman ya dubi Barista bayan sun ida gaisuwar, "Barista wajen ka mu ka zo takanas ta kano." "Ni ko?" ya yi murmushi. "Kwarai kuwa." Ya gyada kai. "To ai ina ga zai fi kyautatuwa mu shiga daga ciki ko?" "Duk yadda ka ce." A wannan karon Hajiya Rukayya ce ta fada ta na murmushi. "Ina ga zai fi kyau...ku zo mu shiga daga ciki." Barista ya ce, sannan ya juya su ka dafa masa baya kamar jelar dawisu har cikin madaidaicin dakinsa. Dakin ba laifi kwarai da gaske. Daga kasa ya na shimfide da wani shudin kafet mai taushin gaske, ga wata tattausar katifa wadda a ka sa daga kusurwar yamma maso arewacin falon. Daga gabas maso kudancin falon kuwa wani dan teburi ne da ke daure da akwatin talabijin mai launi da bidiyo da kuma katuwar radiyo, rikoda. Daga samansu kadan an fasa bangon an zuro na'urar sanyaya ko dumama daki (Air Condition) duk ilahirin jikin bango kuwa zagaye ya ke da labule, hakan zai iya hana gane launin fentin da bangon ke dauke da shi. Sakale a sama wata kyakkyawar fanka ce ke ta faman aiki abin ta ba kakkautawa. Bayan sun zazzauna su ka kuma gaisawa. "Barista wasu yan matsaloli ne ke tafe damu." Lukman ya soma, "Shi ya sa ka ji na ce ma wajenka mu ka zo takanas." Barista ya gyada kai cikin saurare. "Ko da ya ke..." Lukman ya ci gaba bayan ya juya ga Hajiya Rukayya, "...wannan ita ce Hajiya Rukayya matar maigidana Alhaji Basiru, kuma ita ce ta kasance cikin wannan matsala. To da aka ce ana neman lauya, shi ne na shaida ma ta cewa akwai ka, saboda haka na yi ma ta jagora zuwa gare ka." Barista ya gyada kai cikin gamsuwa, "Wannan gaskiya ne. Hajiya wace irin matsala ce wannan?" Hajiya ta dube shi, cikin maraireta ta kwashe labarin abin da ya faru kaf na karya ta sheda masa. Barista ya jinjina kai bayan ta kawo karshe. Lallai ko shakka babu da alama shi ma abin ya ba shi mamaki. Domin sai da ya jima kansa a duke kana ya dago a hankali, "Hajiya sannu kin ji, Allah ya ji kansu ya kuma gafarta mu su." "Amin...!" Lukman ya amsa. Hajiya Rukayya kuwa tuni ta soma kuka. "Ki yi hakuri Hajiya, ki kwantar da hankalinki da yardar Allah zan tsaya tsayin daka akan wannan al'amari don ganin kin samu hakkinki." Ya dan tsahirta kana ya ci gaba, "Yanzu ina kanin mijin naki, da abokinsa?" Ta sa mayafi ta tsane hawayen dake zuba daga idanunta, cikin muryar kuka ta ce, "Suna can, asibi...ti, su na kula da Alhajin. "Wanne asibitin kenan?" Ya kuma bukata. "Asibitin lafiya jari." "Ok, a nan suke?" "Umn." ta gyada kai. "Shi kuma likitan da ya zo lokacin faruwara abin fa?" "Shi ma..acan ya ke". "Wato ita dai yanzu amaryar ta ki ta na tsare ko?" "Eh!" Ta amsa. "To mu na godiya Barista." Lukman ya ce sa'ar da su ka mike da zummar tafiya. Har bakin motar su ya raka su, su ka tashe ta su ka tafi. Hajiya na farin ciki ganin zata samu kariya a wani bangaren kuma ta na mamakin kankanta da karancin shekarun na lauyan da zai tsaya mata. *** A kokarin ta na ganin ta kubutar da kawarta daga cikin matsalar. Washe gari bayan ta gama kintsawa ta yi karin kumallo, ta fita ta nufi gidan Alhaji Basiru da zummar son ganawa da Lukman, a matsayin mutum na farko da ta ke son ta fara bincika. Lokacin da ta isa gidan, ta yi matukar sa'a da ta same shi zaune cikin harabar gidan, shi da maigadi Bukar. A gajarce su ka gaisa, kana Barista Hannatu ta bukata, "Don Allah ko Hajiya na ciki kuwa?" "A'a! Ba ta nan." Lukman ne ya amsa mata, "Ai ta na asibiti, tun dazu na kai ta." Hannatu ta gyada kai, "Ko kai ne Lukman?" Ta bukata ta na duban sa. "Eh, ba shakka ni ne." Ya tabbatar ya na jinjina kai. Ta yi ajiyar zuciya, "Ka ga kuwa ina son ganin ka." "Ni ko?" Ya dafa kirji. "Kwarai kuwa." Ta amsa masa. "Na taso kenan?" "Zan so hakan". Ta ce a takaice. Ya dubi Maigadi Bukar da ke taunar goro abinsa, "Malam Bukar ina zuwa" ya mike su ka dan kebe can gefe gindin wata kyakkyawar shukar fulawa mai yado. Ka sa jurewa ya yi bayan sun tsaya, kafin ta yi magana, yace, "Hajiya, na ce dai ko lafiya?" Ta tsaida kallon ta gare shi ta na murmushi, "Lukman ka gane ni ko?" "Sosai ma kuwa. Ba ke ce Hannatu Kawar amarya ba?" "Lallai kuwa, ko ka san abin da ya kawo ni?" "A'a, ina zan sani ba ki fada ba, ni da ba Allah- musuru ba?" Ya ce da wata irin tattausar murya. "Kana da gaskiya, na zo ne na yi ma ka wasu yan tambayoyi, a matsayinna na lauyar da za ta ba amaryar maigidanku kariya. Ka san za a kai su kotu ko?" Ya hadiyi yawu da kyar, "E...na..sani." Ya amsa cikin in-ina. Wannan ya biyo bayan kin jinin tambaya da ya yi a daidai wannan dan rukunin saboda ya san komai na iya faruwa tun da shi ma mai laifi ne. Kai! Idan ma ban da ya na tunanin idan aka je kotu Hajiya Rukayya ta yi nasara zai iya samun wani alkhairi daga gare ta, ai da tuni ya tsere kauyensy, (Gamadidi). Kafin ta kuma magana ya ce, "Me ki ke so ki tambaye ni?" Ta yi kasa-kasa da muryarta, "Dalilin rashin zuwanka kai yara makaranta shekaran jiya, na ke so na ji." Ya yi atishawa "Ai na jima ina amsa wannan tambayar. Ba ni da lafiya ne." "To ya a ka yi da rana kuma lokacin tashi ka je ka dauko su. Ka samu sauki ne?" "Na ji dama-dama lokacin." ya amsa da gyada kai. "Idan ka tashi daga aiki, abin nufi bayan ka dauko yara daga makaranta, kana tafiya da mota gida ne?" "A'a ya girgiza kai, "Ba na tafiya da ita duk a nan su ke kwana." "To a wannan rana ya aka yi ka tafi da mota gida. Ko ka san da ma za ka tashi da rashin lafiya? Kuma da rana za ka warke, shi ya sa ka tanade ta don kawai ka wuce daga can?" Tambayar ta kwarzanar masa zuciya don take launin fuskarsa ya sauya. Shiru ya yi cikin gaza amsawa. "Ya na ji ka yi shiru, ko ba amsa?" ya girgiza kai "Ba haka bane..." "To ya ya ne?" "Shi ne abin da nake so na tuno." Ta yi murmushi. "Ko na ba ka lokaci ka tuna?" "Da dai zai fi." Ba haka ya so ya ce ba, dole ce kawai ta sa shi fadar hakan da gudun tonawa Hajiya Rukayya asiri. Ta kuma yin murmushi, "To bari na baka dogon lokaci don ka tuna. Ni zan tafi." Ta motsa sahunta, ta yi taku biyu. Ya dube ta, "Sai yaushe kenan?" "Sai mun kuma haduwa." Ta bar shi nan tsaye ta nufi maigadi Bukar da tuni ya soma sana'ar tasa gyangyadi. "To Baba ni zan koma." Ta ce a tausashe. Ya cira kai firgit ya dube ta, "Uhum, yar Baba a sauka lafiya." Da a lokacin za a tambaye shi da wa ya yi magana, ba zai iya fada ba saboda gyangyadi da ya ci karfinsa. Bayan barinta gidan ba ta zame ko ina ba sai asibiti. Likita Idris shi ne na biyu cikin jerin mutanen da ta ke son ganawa da su, koda ya ke shi ba kamar sauran ba, wani taimako ta ke bukata daga gare shi. Ta taki sa'a kuwa, shi kadai ta iske a ofishin nasa ya na ta faman aikace-aikace. "Likita ya mai jikin?" Abin da ta fara fada kenan bayan sun gaisa. "Jiki da sauki Hannatu, ai koda yaushe ya na samun rangwame." "To, Allah ya kara sauki" "Ameen-ameen." Shiru ne ya dan gifta tsakaninsu. "Likita na zo ne don neman wani taimako gare ka, koda ya ke ya na da matukar fa'ida na sanar da kai matsayina cikin wannan al'amari bayan na amintaka ta da Zainab." Ta bude jakarta ta dauko wani kati na shaidar aiki (I.D Card) ta mika ma sa. Bai yi magana ba ya karba. Ya yi nazarinsa a hankali tun daga gaba har zuwa baya. Yanzu ya gane matsayin nata. Ya nisa, "Ga shi Hannatu." Ya mika ma ta. Ta sa hannu ta karba kana ta ci gaba da cewa, "Likita ina so na ba Zainab kariya a game da wannan badakala, shi ya sa na soma bibiyar al'amarin." "Wannan haka ya ke." Likita Idris ya ce ya na gyada kai, "To na ji kin ce ki na neman taimako, na mene ne?" Ta kura masa idanu, "Likita, idan dai har da yiwuwar hakan ina so ka ba ni sakamakon da ka samu na wannan guba a rubuce." Bai yi tsammanin shi ne taimakon da za ta nema ba. Ya yi murmushi, "Barista wannan ai mai sauki ne, bari na ga?" Ya jawo dan abin adana takardu da ke makale jikin teburinsa, ya dauko wani fayal kana ya mayar ya rufe, kai tsaye ya bude fayal din ya fara bincike. A hankali ya zaro wata takarda a ciki, ya yi dan nazarinta. "Barista wannan shi ne sakamakon." Ya mika ma ta. Ta sa hannu ta karba ita ma ta yi nazarinta. Ta cira kai ta dube shi, "Likita ya za a yi na samu kwafin wannan takarda?" "Kamar yaushe ki ke so?" "Ko yanzu ma." Ya nisa, "To za ki iya jira na na rubuta miki wata?" "Me zai hana?" Ya mika hannu ya karbi takardar, kana ya dauko wata takardar cikin gaggawa ya soma rubutawa. Bai dau lokaci mai tsawo ba ya kammala, ya mika ma ta. Ta karba, "Na gode likita." Bayan ta dan dudduba ta mike tsaye, "Ni zan tafi." Shi ma ya mike, "To barista, godiya na ke." "Ni ce da godiya." Ta ce ta na murmushi. Har ta kai ga bakin kofar ficewa daga ofishin sai ta juyo, ta dubi Likita Idris wanda tuni ya zauna, "Likita Alhaji Sambo da Alhaji Gali fa, ko su ke jinyar Alhajin?" Ya gyada kai, "Su ne, kuma su na nan don dazu na shiga wajen na gan su." Ta kama hannun kofar ta murda, "A daki na nawa su ke?" "Daki mai lamba na ashirin da daya." Ta gyada kai, "Na gode." kana ta bude kofar ta fice, ta nufi dakin da likitan ya sanar da ita da zummar ganawa da Alhazan biyu, mutane na uku cikin rukunan mutanen da ra ke son ganawa da su. Lokacin da ta isa ga dakin ta tura kofar ta shiga, su na zaune su uku, Alhaji Gali, Alhaji Sambo da Hajiya Rukayya, a kan kujera. Shi kuma Alhaji Basiru kwance ya na barci, robar karin ruwa makale a hannunsa. Salla ta yi mu su. Da kyar su ka amsa kamar an yi musu dole musamman ma Hajiya Rukayya da ke kallon Hannatun a wulakance. Ba ta damu da abin da su ka yi mata ba ko kadan, maimakon hakan ma sai ta ce, "Sannunku Hajiya! Ya me jikin?" "Jiki da sauki". Alhazan biyu ne su ka amsa, don ita Hajiya Rukayya ma dauke kanta ta yi gefe guda. Ta isa ga wata kujera daidai lokacin da take cewa, "Allah ya kara sauki." "Ameen." Su ka kuma amsawa. Ta zauna a hankali ita ma ta yi shiru kamar yadda su ka yi, tsawon dakiku talatin su na a haka. Can ta nisa ta dubi Alhazan "To! Ni zan koma, Allah ya ba shi lafiya." "Ameen". Su ka amsa. Ta mike a hankali ta kuma mayar da dubanta gare su, "Alhaji don Allah ina da bukatar tattaunawa da ku." kafin su yi magana. Hajiya Rukayya ta kalle ta da sauri, "Kamar ya ya ki na son ganin su su na zaman jinya? Idan wata magana ce ki yi anan mana." Ta yi murmushi, "Hajiya ba wani lokaci za a dauka ba. Ga ni na yi bai kamata mu yi a nan ba saboda mara lafiyar." Ta daka ma ta harara, "To ba za su..." "Ya isa Hajiya." Alhaji Gali ya dakatar da ita, "Bari mu je." ya taba Alhaji Sambo, "Tashi mu je." Su ka mike. Hannatu ta dubi Hajiya Rukayya, "To Hajiya sai an jima, Allah ya sauwake". Ta muguda baki, "Amin idan da gaske ki ke." Barista Hannatu ta juya su ka bi ta a baya zuwa waje. Wani dan benci su ka samu bayan sun fito farfajiyar asibitin. "Bismillah ga wajen zama!" Ta nuna musu dogon bencin. Bayan sun zazzauna, ta gabatar mu su da kanta a matsayin lauyar da za ta ba kawarta Zainab Kariya. Sun yi mamaki...ba su yi mamaki ba. Mamakin da su ka yi shi ne, ya za a yi Hannatu ta ba matar da a ka tabbatar da ita ta bayar da wannan guba kariya..ta wace hanya? Rashin mamakin kuwa shi ne. Dole ne ta yi hakan musamman da su ka duba cewa kawarta ce. "Ina so na yi muku wadansu Yan tambayoyi ne." Ta ci gaba bayan sun fahimci ko ita wace ce. "A game da me fa?" Alhaji Sambo ne ya bukata. "A game da abin da ya faru shekaran jiya, kasancewar ku na cikin falon abin ya faru." "To mece ce tambayarki?" Ya kuma cewa, a hasale ya ke maganar. Ta shafi goshinta "Alhaji a matsayinku na wadanda mu ka bari a falon, bayan fitar mu, ya a ka yi su Alhaji su ka kasance cikin halin da mu ka dawo mu ka riske su?" Alhaji Gali ya dube ta, "Su yaran kawai gani mu ka yi sun fadi, kuma Alhaji da farko cewa ya yi cikinsa ya na ciwo, kamar wasa shi ma sai ya fado daga kan kujera, duk kuma a kusan lokaci guda." "Daga nan kuma sai a ka yi ya ya?" Ta ce ta na kallon su ido cikin ido. "Daga nan sai mu ka jiyo Ihun Hajiya Rukayya, sannan kuma sai mu ka ga sun shigo falon." Barista Hannatu ta shafi kuncinta, "Don Allah ko za ku iya tuna abin da Hajiya Rukayyar ke ambata cikin ihun nata?" Shiru su ka yi na dan lokaci kana Alhaji Sambo ya ce, "Kwarai na tuna." "Me ta ke cewa?" "Cewa ta ke kar ku sha alewar nan, alewar ba ta da kyau." "Me ya sa ta ce hakan, daman ta san ba ta da kyau ne, ko kuwa?" Shiru su ka kuma yi su ma su na tunanin abin a zuciyarsu. "Haka ne fa! Ya aka yi ta san alewar ba ta da kyau." Zuciyar Alhaji Sambo ce ke juyayin abin. Lallai akwai alamar tambaya anan. Ganin sun yi shiru babu amsa, sai Hannatu ta ce, "To idan wannan ma ba komai ba ne, ko za ku iya tuna abin da Hajiyar ke fada cikin surutunta na jiya yayin da mu ke zaune muna jiran fitowar likita?" Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Bakin Kishi 4 Posted by ANaM Dorayi on 11:16 AM, 29-May-15 su na da yawa Hannatu wanne daga ciki?" "Ba ku ji ta naambatar Baraka cikin sambatunta ba?" "Lallai mun ji." su ka amsa a tare bayan sun tuna. "To wace ce Baraka da har Hajiya Rukayya ke cewa, Baraka ya haka?" Basu da amsa kuma shi ma lallai sun tabbatar abin tambaya ne. "Ba mu san ta ba Hannatu." Alhaji Sambo ya ce a sanyaye, yanzu kusan duk jikinsu ya yi sanyi kuma hakika su na son wadannan amsoshin, to sai dai duk wannan kafin su hada ido da Hajiya Rukayya ne, tuni za su manta. Barista Hannatu ta nisa, "To shi kenan na yi matukar godiya da wannan lokaci da ku ka ba ni, ni zan koma." Ta mike, su ma su ka yi godiya su ka koma ciki cike da raba daya biyu a zukatansu. Bayan ta bar asibitin, ba ta zame ko ina ba sai ofishinta na musamman da ke kan titin Gwarzo domin tattara abubuwan da ta samu, da ya ke sha biyun rana ta yi, idan ya so daga bisani idan yamma ta yi sai ta tafi ga mutun na karshe a cikin bincikenta, wanda ke sayar da kayan lashe- lashe a makarantar su Mujahid. Bayan an yi sallar La'asar ta bar ofishin ta nufi makarantar, sai dai ta yi matukar takaici da aka shaida ma ta saurayin Habu mai kanti ya yi tafiya, kuma ba zai dawo ba sai gobe. Haka ta hakura ta baro makarantar ba tare da ta sami komai ba. ZAMAN KOTU NA FARKO Arewa majistiri, Babbar kotu ce da ke da fadi da tsayin gaske. A bisa kiyasi kotun ta na daukar a kalla mutane dari da hamsin. Amma a yau take ta ke da yan kallo, haraba da wajen ta, babu masaka tsinke. Misalin karfe tara daidai babbar bakar motar yansandan (Irin wadda ake daukar yan fashi) ta shiga farfajiyar farko da aka tanada don ajiye motoci. Tsayawarta ke da wuya wasu dandazon jama'ar da su ka makara da shiga kotun su ka zubawa motar idanu. Bayan kashe ta, yan sandan dake ciki su ka fito da Zainab da ke daure da ankwa a hannu daga bayan motar, kai tsaye su ka shige da ita cikin kotun, da kyar da turereniya, saboda tasowa da jama'ar su ka yi cikin hargowa, wasu na la'antar ta da tsinuwa, wasu kuma na zagin ta gami da Allah wadai. Su kuwa lauyoyi tuni sun hallara a sababben dakinsu tun kafin isowar yan sandan. Rabin sa'a da zuwan yansandan mai shari'a Mukhtar kano ya iso, kai tsaye shima ya shige cikin dakin da aka kebe masa kafin shigowa dakin shari'a. Jim kadan lauyoyin su ka shigo cikin kotun, su ka zazzauna a kebabben wajensu. Barista Hannatu, lauyar da ta shigo dakin shari'ar yau don kare kawarta, fara ce kyakkyawar gaske, ta na sanye da irin bakaken kayansu da su ka yi matukar yi mata kyau. Ta na rike da takarda, farin gilashi dane a fuskarta. Sai dai kuma babu fara'a a tare da fuskar tata, meyiwa saboda ta san ita ce ke da karancin magoya baya a cikin kotun, musamman da ta yi la'akari da yadda aka rika sanar da shari'ar a kafafen yada labarai na cewa, ana zargin kawarta da laifin kashe yayan kishiyarta har da yunkurin kashe mijinta. Mintuna biyar su ka rage karfe goma ta cika, mai shari'ar ya shigo cikin dakin shari'ar. Wannan ya sa jama'ar dake dakin gaba daya su ka mike cikin mutuntawa. Mai shari'a ya dan rankwafa cikin girmamawa ga jama'ar, su ma su ka rankwafa cikin karamci kana ya zauna, su ma su ka zauna. A yanzu dakin shari'ar tsit ya ke kamar babu kowa, don son jama'a na jin me zai biyo baya. Koda aka tabbatar kowa ya nutsu, sai me karnto shari'ar Furoskito Nura Salihu ya gabatar da shari'ar da za a yi kamar haka: "A yau litinin ashirin ga watan goma sha biyu shekara ta dubu biyu da uku (20/12/2003) za mu saurari shari'ar Hajiya Zainab Iliyasu Umar a kan zargin da ake yi ma ta na kisan yayan kishiyarta guda biyu, wato Hajiya Rukayya da kuma yunkuri ko saka mijinta a halin kaka-ni-kayi, wanda har zuwa yanzu ya na kwance rai a hannun Allah." Bayan kammalawarsa sai hayaniya ta kunno kai tsakanin jama'ar kowa na fadr albarkacin bakinsa cikin tsana da kyamar Zainab. Idan ka dauke mahaifin Zainab, Malam Iliyasu Umar da Iyalansa, babu wanda ba ya surutu a dakin shari'ar. "Kamar yadda mai gabatarwa ya gabatar." Mai shari'a ya soma, bayan ya tsawatar an yi shiru, "Yanzu ba tare da bata lokaci ba, za mu saurari karar daga bakin jami'in tsaron da ya shigo da ita, wato Sufeto Habibu." Wani dogon Dan sanda ke zaune a gaba-gaba ya mike, hannunsa rike da wasu takardu, ya nufi mumbarin da masu amsa tambaya ke hawa, ya hau. Bayan an rantsar da shi, ya soma gabatar da karar cikin daga murya. "Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, da ya ba mu dama da ikon kammala wannan bincike, akan wannan mummunan laifi na aikata kisan kai, ta sigar yaudara, wanda Zainab Iliyas ta yi ga yayan kishiyarta Hajiya Rukayya. "Ya mai shari'a wannan al'amari ya faru ne a yammacin ranar lahadi sha biyu ga watan biyu na wannan shekarar. "Kamar yadda sakamakon bincike ya nuna akan wadda ake zargin (Zainab) ta samar da wata Alewa ne mai guba, da ita ce ta kai yaran ga mutuwa. "Hujjojin da ke hannunmu zuwa karshen wannan bincike namu, wadanda da su mu ka dogara wajen shigo da wannan kara su ne;- (Dan Allah kuyimin afuwa nangun ya yanke) "Zan fara da gabatarwa da shari'a kaina". Ta ci gaba, "Sunana Barista Hannatu, lauya mai zaman kanta. Na dauki wannan bangaren ne na ba wadda ake zargi kariya kasancewar har zuwa yanzu babu wata kwakkwarar hujja ta zahiri da ke nuna cewa, Zainab ita ta samar da wannan alewar. Sannan ina kira ga shari'a da ta yi duba da cewa, duk fa abin da a ka ce zargi a ke yi, bai tabbata ba kenan, akwai bukatar samun tabbaci tun kafin a shigo nan. Don haka ina fatan kotu ba za ta damu da duk wadannan abubuwa ba tunda an nuna ba a bincika an tabbatar ba. Idan kuwa haka ne akwai bukatar shari'a ta yi kyakkyawan duba ga ingantattun hujjojin da za a gabatar ma ta domin tserewa da gudun afkawa ga dorawa mara laifi, laifi. Na gode!" Ta koma ta zauna. Duk da cewa wannan jawabin nata kusan bai gamsar da kowa ba, da alama shi mai shari'a ya gamsu. Za ka gane haka ne ta hanyar gyada kai da ya yi, ya kuma duka ya yi yan rubuce-rubuce. A hankali ya dago ya dubi Barista Garba Shehu, "Shari'a ta baka dama ka fara gabatar da shaidunka yanzu." Garba ya mike ya fara takawa a hankali. "Da ya ke shari'a ta amince zan fara gabatar da mutane biyu a matsayin shaidar farko, amma daya bayan daya. Mutanen kuwa su ne, Alhaji Sambo kanin maigidan wadannan mata, uwa daya uba daya, da kuma Alhaji Gali babban aminin mijin wadannan mata. Amma da ya ke na ce daidai da dai-dai, za mu soma da kanin magidancin." Alhaji Sambo da ke sanye da manyan kaya (Malum-malum) ya mike ya nufi mumbarin shaida, ya shiga ya tsaya, aka rantsar da shi. Garba ya isa gare shi, "Ko za ka iya tabbatarwa da shari'a matsayinka ga Alhaji Basiru, mai gidan wadannan matan?" "Kwarai kuwa!" Ya ce ya na gyada kai. "To za mu so hakan." "Ni dai uwarmu daya, ubanmu daya." Ya fada a takaice. Garba ya gyada kai "Da kyau! Kasancewarka ka na daga cikin mutanen da su ka tsinci kansu cikin wannan falo yayin faruwar wannan al'amarin, ko za ka iya sanar da mu yadda abin ya faru?" "Tabbas zan iya". Ta ke ya zayyanewa kotu duk yadda a ka yi har zuwa sa'ar da su ka dunguma asibiti. Garba ya nisa cikin gamsuwa "muna godiya." Har ya yunkura da zummar sauka daga kan mumbarin shaidar sai ya ga mai shari'a ya juya ga Hannatu, "Ko ki na da bukatar tambaya?" Ta gyada kai kana ta mike, ta nufi mumbari. Bayan ta isa ta ce, "A matsayinka na wanda ya ke cikin falon abin ya faru ko za ka iya sanar da mu wanda Zainab ta dankawa wannan alewa sa'ar da ta shigo falon?" Ya gyada kai "Lallai kuwa". "To wane ne?" "Mujahid ta ba." "Mujahid dan wane ne?" Ta bukata. "Dan ta ne." ya amsa. "Kenan mutum zai iya daukar gubar mutuwa ya ba dan da ya haifa a cikinsa, musamman ma uwa da danta...?" "Malama saurara!" Garba ya mike, "Ya mai shari'a ina so kotu ta lura da cewa, wannan tambaya da aka shigar yanzu ta sauka daga kan asalin turbar da mu ke don kuwa me tambayar ta tambayi abin da ke cikin zuciya ne, kuma shi sanin gaibu sai dai Allah, Lallai ya dace a duba, wannan abin tsawatarwa ne." Mai shari'a Muktar Kano ya dubi Hannatu gami da tsawatar ma ta, da kar ta kuma irin wannan tambayar. "Na daina ranka ya dade." Hannatu ta ce kana ta kuma mayar da dubanta ga Alhaji Sambo. "Alhaji a lokacin da wannan al'amari ya faru an ce Hajiya Rukayya ta na waje, haka ne?" "A'a tana kicin dai." Ya gyara ma ta. Ta gyada kai "Ma'ana dai ba ta falon ko?" "Yaron nan mujahid ne ya fita da kukansa ya je ya sanar ma ta. Shi ne ta taho a guje." Ta gyada kai, "A lokacin ta taho ta namagana, ko za ka iya tuna abin da take fada...?" "Ya mai shari'a." Garba ya yi caraf ya cafe, "Kamar yadda na sanar yanzu, wajibi ne kotu ta dauki tsauraran matakai kan irin wadannan tambayoyin domin kauracewa afkawa rudani." Mai shari'a ya dubi Garba ya ce, "Ina so ka fahimta cewa, ba kowace irin tambaya ce ta sabawa doka ba, irin wannan tambayar akan hanya ta ke, don haka kai ma ka kiyaye." Barista Garba ya koma ya zauna cikin damuwa ganin mai shari'ar ya ba Hannatu damar ci gaba. Hannatu ta ci gaba, "To Alhaji za ka iya tuna abin da ta ke fada sa'ar da ta nufo falon?" Sai da ya yi dum na dan lokaci kana ya ce, "Na tuno." "Me ta ke cewa?" "Cewa ta ke, Alhaji kar ku sha alewar nan, alewar nan ba ta da kyau!" Hannatu ta juya ga mai shari'a, ta ce, "Ya mai shari'a lallai babu shakka ina so kotu ta lura ta gano wasu sirrika daga cikin maganar baiwar Allahn nan, don babu yadda za a yi kaza ta san hanyar rafi, abin nufi babu yadda za a yi Hajiya Rukayya da ba ta san komai a kan wannan alewa ba, ta yi wannan furuci. Na gode!" Ta koma wajen zamanta ta zauna. Garba ya mike "Shaida na gaba da za mu kira wo kamar yadda mu ka ce, shi ne aminin Alhaji Basiru wato Alhaji Gali." Alhaji Gali ya hau mumbarin shaidar, bayan Alhaji Sambo ya sauka. Garba ya isa gare shi. "Zan so kai ma ka sanar da shari'a matsayinka ga Alhaji Basiru, wato mai gidan wadannan matan." "Sunana Alhaji Gali." Ya soma da gabatar da sunansa. "Kuma ni babban amini ne ga Alhaji Basiru." "Ko kai ma ka na cikin wadanda su ka riski kawunansu a cikin wannan falop sa'ar da abin ya faru." Ya gyada kai "Hakika!" "To me za ka ce mana game da faruwar wannan abu?" Ya gyada kai, kana ya soma zayya na abin da ya faru. Ba su sami sabani ba, kusan abu guda su ka fada shi da Alhaji Sambo. Bayan ya kammala sai Garba ya yi masa wasu tambayoyi guda biyu, kamar haka. "Wato dai ya tabbata Zainab ta dauko wannan alewa kenan?" "Kuma a dakinta?" "Babu ko shakka!" "To madalla mun gode." Garba ya koma wajen zamansa ya zauna. Ganin ba ta taso ba ya sa mai shari'a Muktar Yakub ya juya gare ta "Ki na da tambaya ne?" Hannatu ta girgiza kai, "Babu yallabai!" Yar hayaniya aka yi kadan, me yiwa ta samo asali ne da tunanin mutanen na fara ganin gazawar Hannatun. Garba Ya mike, ya ce "Shaida na gaba da za mu gabatar wanda ya zama shi ne mutum na farko da ya halarci wannan gida bayan faruwar al'amarin shi ne Likita Idris, wanda kuma dama can likitan gidan ne." Likita Idris ya fito, dan kakkaura ne haka fari, mai sakakkiyar fuska. Garba ya ce, "Likita zan so ka warware min zare da abawa game da matsayinka a wannan gida, da kuma tsawon lokacin da ka dauka ka na yi musu aiki." Ya gyara murya, "Kamar dai yadda ya ke, a gaskiya ni likita ne na musamman a wannan gida, kuma tsawon shekaru goma kenan." Garba ya gyada kai "Da kyau! Wato duk abin da ya faru na game da rashin lafiya a gidan kai a ke nemo wa kenan?" "Haka ne." "To sa'ar da wannan abu ya faru aka gayyato ka, a ya ya ka riski abin?" Sai da ya yi dan jim kana ya ce, "Ni dai lokacin da na shiga falon yayin faruwar abin, na riski ita uwargidan wato Hajiya Rukayya durkushe gaban yayanta biyu, sai kuma Zainab, amaryar kenan, durkushe a gaban mijinta, Alhaji Sambo wato kanin Alhajin kenan da kuma aminin Alhajin wato Alhaji Gali tsaye a kanta. Ganin hakan ni sai na nufi gun Hajiya Rukayyar don ba ta tallafi." "To ita Zainab din me ta ke yi ga Alhajin?" "Ta nagwagwgada shi ne da irin abin gwajinmu na likitoci." "Hakan ya nuna ita ma likita ce kenan?" "Kwarai kuwa likita ce." Garba ya juya ga mai shari'a ya ce, "Ya mai shari'a idan har shari'a za ta tsaya ta fuskanci inda wadannan jawaban su ka sa gaba, lallai za mu ga cewa akwai wata makarkashiya cikin wannan al'amari wanda ya afku a ba-zato, wanda za mu ga kiri-kiri Zainab ba ta damu da yayan kishiyarta ba, ta mijinta ta ke, wanda wannan kadai ya isa ya sa a fahimci cewa akwai manufa ta son kisan gilla ga wadannan yara." Ya yi godiya ya koma ya zauna. Hannatu ta tako zuwa ga mumbarin da likita ke kai. Ta dube shi, "Likita ko za ka iya sanar da mu yadda aka yi ka sami labarin faruwar wannan al'amari?" "Eh! An sanar da ni ne ta waya." "Wane ne ya sanar da kai?" "Amarya ce". "Wace ce amarya?" "Zainab." "Wadda a ke zargi kenan?" "Eh!" ya amsa ta hanyar gyada kai. "Ita ce ta yi ma waya, ta ce da kai me?" "Ta ce don Allah na yi gaggawa na zo." Ta nisa kana ta juya ga mai shari'a, "Ya mai shari'a, idan mu ka yi la'akari da wannan za mu fahimci cewa, babu yadda za a yi matar da ta yi shirin aikata wannan abu da ake zarginta da shi yanzu, ta yi tunanin sanar da kafar da za ta bayar da taimakon gaggawa, don hakan na nuna cewa a na son ceto rayukan wadannan yara, musamman idan mu ka duba cewa ita ma likita ce zata iya ba mijinta shi kadai kariya, idan har zargin da a ke ya tabbata..." Tun kafin ta karasa hayaniya ta soma fitowa jifa- jifa, da alama jama'ar sun fahimci abin da Hannatun ta ke nufi, kuma har wasunsu ma sun fara shiga cikin tunanin abin. Bayan mai shari'a ya tsawatar sai aka yi shiru. Bayan saukar likita Idris daga kan mumbarin shaidar, sai Garba ya mike, sai dai mikewar tasa ta yanzu ba kamar ta baya ba. "Kafin na kira shaida na gaba ina so na yi amfani da wannan dama domin kira ga kotu da ta rika dubawa ta nakuma bijirewa irin wadannan sakarkarun tambayoyi da aka gabatar yanzu ko don tsafta ce wannan shari'a." Ya dan yi shiru kana ya ci gaba "Shaida na gaba da na ke son gabatarwa shi ne jami'in bincike a kan kisan kai, wanda kuma shi ne ya bi diddigin wannan al'amari, wato Sifeto Habibu Hudu Darazo." Sufeto Habibu ya mike ya shiga mumbarin shaida ya tsaya. Garba Ya dube shi, "A matsayinka na mutumin da wannan al'amari ke hannunka ta fuskar bincike, ko za ka iya sanar da shari'a sakamakon da kuka tattara?" Daki-daki Sifeto Habibu ya yi bayanin game da sakamakon bincikensu da kuma irin shaidun da su ka samu har zuwa lokacin da su ka miko karar ga kotu. Garba ya yi masa godiya, ya koma wajensa ya zauna. Hannatu ta mike ta nufi mumbari shaidar da Sifeton ke tsaye, "Sifeto zan so na san lokacin da ku ka isa gidan, abin nufi karfe nawa?" "Karfe takwas mu ka ce za mu isa gidan, amma saboda wani dan tsaiko da mu ka samu takwas din ta dan gota." "Yallabai kenan, saba lokacin bai sa kun samu matsala ba wajen ganawa da duk wanda ya dace, tunda watakila idan su ka ga lokacin ya gota za su iya fidda rai da zuwanku?" Sifeto ya yi murmushi, "Ba mu sami wannan matsalar ba, sai dai..." Ya dan yi shiru gami da dukar da kansa alamar tunani. "Sai dai me?" Hannatu ta bukata ganin shirun nasa na yunkurinsa tsawaita. Ya dube ta, "Sai dai uwar gida da ba mu sami damar ganawa da ita ba." "Uwargida? Hajiya Rukayya kenan?" "Eh, ita." Ya gyada kai. "To me ya hana damar ganawar da ita?" "Saboda ta yi barci lokacin..." "Barci?" Ta nanata cikin mamaki. Ba ita kadai ba ma kusan kowa a kotun sai da fuskarsa ta sauya, har da shi mai shari'ar. Ta juya ga mai shari'ar, "Ya mai shari'a lallai wannan gagarumin al'amari ne, ko na ce gagarumin sakaci ne da ya bar baya da kura, wanda kuma kacokan zai iya sauya dukkan sakamakon da jami'an su ka samu, domin kuwa wadda su ka bari din ita ce ta farko da ya dace a ce an gana da ita kuma ma abin tambaya ne a ce wai matar da ta rasa yayanta biyu ta sami damar barci. Don haka ina kira ga shari'a da ta shata layi a karkashin wannan babban kuskure don gudun kar a yi tsallen-badake a cikin wannan shari'a. Na gode." Ta koma ta zauna. A wannan karon ma sai da mai shari'a ya tsawatar saboda hayaniya da ta sopma karfi. Bayan an sarara ne mai shari'a ya dubi Garba ganin bai taso ba. "Garba ko shaidun sun kare ne?" Ya mike "A'a ba su kare ba, yallabai. Yanzu zan gabatar da shaida ta gaba wadda koken ta ne mu ke dubawa a yanzu, kuma matar da a ka ci amanarta wato Hajiya Rukayya." Hajiya Rukayyar ta fito ta hau mumbari. Garba ya dube ta, "Hajiya Zan so na ji ko lokacin faruwar wannan al'amari, ki na cikin falon?" T girgiza kai "Ba na ciki" "To ke me ki ka sani kenan dangane da al'amarin?" "Ranka ya dade, ni ban san komai ba, kawai dai ina cikin dakin girki sai na ga dan wajen amaryar tawa ya zo ya na sanar da ni cewa wai ga..." Shisshikar kuka ce ta hana ta karasawa. "Sannu Hajiya Ki yi hakuri...kar ki yi kuka." Garba ya shiga ba ta hakuri. Bayan ta sassauta, sai ya juya ya koma ya zauna. Hannatu ta mike, "Da farko in jajenta miki wannan rashi, Hajiya Allah ya ji kansu." "Amin." Ta amsa da kyar. "Hajiya sa'ar da aka sanar da ke cewa ga abin da ke faruwa, abin nufi lokacin da Mujahid ya kai miki kara cewa an kwace masa alewarsa. Me ya sa ki ka nufo falon a rikice?" Fuskarta ce ta sauya lokaci guda. Ba ta yi tsammanin wannan ta nacikin tambayar da za a yi mata ba. Shiru ta yi na yan dakiku. "Ba ki ce komai ba...ko kin taho ki kwatarwa Mujahid din alewar ne..." "Eh...e...ha...ka ne.." Ta ce cikin in ina ta nagyada kai, gami da kifkifta idanu. Hannatu ta yi murmushi, "To kuma me ya sa ki ka taho ki na ambatar cewa kar su sha wannan alewa ba ta da kyau?" Yanzu ma shiru ta yi cikin rarraba idanu. Tsawon dakiku goma ba ta yi magana ba, hakan ne ya jawo hayaninya a cikin kotun. Hayaniyar da jama'ar ke yi ta nuna mamakinsu ga faruwar wannan al'amari. Bayan kotun ta yi shiru ta hanyar tsawatarwa daga mai shari'a Mukhtar, sai Garba ya mike jiki a sanyaye. "Ya mai shari'a ba zan taba amincewa da wannan soki-burutsun tambayioyi ba. Sannan ina kira ga shari'a da ta bada umarnin a sassautawa wannan mata domin a halin yanzu ta na fama da tunanin makokin yayanta don gudun kar a tilasta ta ta amsa abin da ba ta yi ba." ya koma ya zauna. Mai shari'a ya dube shi, "Kotu ba za ta iya amsa wannan kira naka ba domin kuwa ya nayin mai amsar tambayar, ya nayi ne da ke da rufa-rufa a ciki, saboda haka akwai bukatar a kwalkwaleshi tas domin ketare zalunci a cikin wannan shari'a." Ya juya ga Hannatu ya ba ta umarnin ta ci gaba. Hannatu ta kuma murmushi bayan ta dubi Hajiya "Hajiya ba ki fadi dalilin da ya sa ki ka ambaci waccan kalmar ba, ko daman kin san da alewar?" "A'a...ban...san..da ita ba...kawai dai..." Ta kasa karasawa, ta juya kallonta ga Barista Garba da tuni kansa ya fara daukar zafi. "Kawai me?" Hannatu ta dawo da hankalinta gare ta. Yanzu duk idanun da ke kotun kallon ta su ke cikin mamaki. "Hajiya ya kamata ki amsa wannan tambaya domin ki na batawa shari'a lokaci". Mai shari'a Mukhtar ne ya fada. Ta yi ajiyar zuciya "Saboda alewar ba saya aka yi ba." Idanun da yawa daga cikin mutanen ne su ka kara girma don mamaki. "kamar ya ya ba saya aka yi ba, mu na so ki fayya ce ma na. "Ba...ba ni ce na sa..ya ba.. Wata...kawata...ce Baraka...ko da ya ke na saya mu...musu alewa a makaranta...uhn...uhn..." Ta kasa ci gaba. Hayaniya ta kaure a kotun kamar kasuwa, wasu har mikewa su ka yi don mamaki. Bayan an tsawatar Barista Hannatu ta dubi Hajiaya Rukayya ta ce, "Hajiya, yanzu dai ya tabbata ke ce ki ka samar da wannan alewa kenan?" Ba ta yi magana ba. Hannatu ta juya ga alkali, "Ya mai shari'a kamar yadda na sanar tun a farko, cewa wannan shari'a tabbatattun shaida ne kadai ke da muhimmanci wajen gano gaskiyar wannan al'amari, to wannan haka ya ke, domin kuwa idan mu ka duba a yanzu bisa wannan tabbatarwa da wannan mata ta yi da bakin..." "Ba zan taba amincewa da wannan ba." Garba ya mike, "Ya mai shri'a babu wata hujja a yanzu da za ta tabbatar da a bin da Hannatu ta ke shirin fada domin kuwa tun farko sai da na ja hankalin shari'a a kan ta tsawatar da a sassauta wajen yiwa wannan mata tsauraran tambayoyi don gudun kar a tilasta ta fadi abin da ba ta yi ba, kamar yadda a ka yi mata yanzu. Sannan daga karshe ina rokon shari'a da ta daga gabatar da wannan kara saboda dalilanmu na son binciko wasu kwararan hujjojin da za su tabbatar da gaskiyarmu, kuma kafin lokacin wannan baiwar Allah ta dan huce." Mai shari'a ya dubi Hannatu da ke ta faman murmushi ya ce, "Mene ne ra'ayinki dangane da rokonsa, ki na da ja?" "E, to ranka ya dade tun da har an samu tsaiko da dalilin gazawa daga abokin karawar tawa, zan iya amincewa, amma akwai wata alfarma da na ke bukata shari'a ta yi min. Lallai ya zama wajibi shari'a ta nemo wannan mata Baraka da Hajiya Rukayya ta ambata ta hanyar tuhumar ita Hajiyar, don kuwa ba yanzu ba ne ta fara ambatar sunanta, ta soma ambatar sunan matar ne tun sa'ar da su ke a asibiti, saboda haka babu ko tantama nemo matar gagarumin abu ne da ya ke da matukar amfani." Mai shari'a ya dukar da kansa ya yi yan rubuce- rubuce, kana ya dago, "Mun ji wannan kira naki Hannatu kuma lallai za mu aikata. Sannan mun daga wannan zama zuwa ranar Alhamis ashirin da hudu kennan ga wannan watan, a matsayin ranar da za mu ci gaba da sauraron wannan shari'a. Da wannan kotun ta tashi. 'yan sanda su ka kuma tusa keyar Zainab zuwa cikin bakar motar su ka tafi da ita, yayin da dokacin jama'ar da su ka sami sauyin ra'ayi daga zargin na zainab su ka bi motar da kallo suna cewa, "Allah Sarki, baiwar Allah, Allah ya kubutar da ke." *** Kashe gari da safe Hannatu ta nufi makarantar "Sasif da burin samun dan saurayi mai shagon sayar da kayan tsotse-tsotse, Habu mai shago. Tafiyar tata kuwa ta yi nasara, domin lokacin da ta isa makarantar dan saurayin na zaune cikin sa rai da ganin wanda zai zo ya yi masa ciniki, don haka ta na tsayawa a karamar motarta kirar Toyota Starlet, ya zubawa motar idanu. Lokacin da Hannatu ta kashe motar ta turo kofar ta fito, sai ya yi wata nannauyar ajiyar zuciya, kana ya ce, "Kai, ka ga wata tsaleliya, tsada! Allah ya yi halitta a nan. Tsantsari!" Amma ko da ya fuskanci ta nufo shi sai ya yi sauri ya dauke kansa daga kallon ta a kokarina na kare mutuncinsa, don ba zai taba mantawa ba, akwai wata yarinya kyakkyawa da ya taba kallo ta tambaye shi "Mene ne ya ke kallon ta?" "Assalamu alaika." Hannatu ta yi masa sallama sa'ar da ta isa gare shi. "Wa'alaikis salam!" Habu mai kanti ya dawo da hankalinsa gare ta, "Sannu da zuwa." "Yauwa sannun ka, ya gari?" "lafiya sumul, ya hutu?" Ta yi yar dariya, "Malam, hutu ai sai ku." "Hajiya wane mu?" "Ba sunana Hajiya ba, sunana Hannatu." Yayi dariya "Ai idan na ce Hajiya ban yi laifi ba." Su ka yi yar dariya su dukansu. "Malam don Allah wata bukata ce ta..." "Ba sunana Malam ba, sunana Habu mai kanti kuma ki na iya kirana da "Harka". Ta yi murmushi "To Habu mai kanti kuma Harka, ina da bukatar yin wata magana da kai." "Ni?" Ya bukata cikin mamaki. "Kwarai, kai" "To Bismillah, wace magana ce?" "Dan samar mana abin zama mana?" Ta ce ta na duban sa. Ya waiga "Ga wani benci can mu karasa gare shi." Ya nuna wani benci da ke ajiye can gefen gindin wata bishiya. Su ka nufi bencin fuskar dan saurayin cike da mamaki. A lokaci guda kuma zuciyarsa na ta saka masa cewa. "Lallai ka yi sa'a ka sami kyakkyawa, idan ta ce ta na son ka kar ka kuskura ka yi sanya don auren irin wadannan na da ribobi. Ka ga na farko dai ko ba komai fuskarta da kirar jikinta ta shiga taro ce. Na biyu kuma daga duk inda ta fito yar mai abin hannunsa ce, ka ga shi kenan ka sami auren jari." Bayan sun isa ga bencin sun zauna sai Hannatu ta shiga gabatar ma sa da kanta, sannan daga baya sai ta shiga tambayarsa, "Habu don Allah ko za ka iya tuna adadin mutanen da su ka zo sayayya kantinka daga makon da ya wuce zuwa yau din nan? Misali daga ranar Litinin sha biyu ga watan sha biyun nan har zuwa yau?" "Eh...gaskiya ba zan iya tunawa ba, amma da ya ke ina rubuta duk abin da na sayar ba mamaki na gane." "To idan ka rubuta abin da ka sayar kana rubuta sunan wanda ka sayarwa ne?" "A'a" "To, ya za a yi ka gane?" "Wani lokaci idan na dauko littafin ina dubawa, zuciyata na kokarin tuna min kamannin mutumin da ya yi sayayyar, in dai ba lokaci guda mutane daban-daban su ka zo ba." Taq gyada kai "To yanzu za ka iya dauko littafin kenan?" "Me zai hana." Ya mike ya nufi kantin nasa. Ta bi shi da kallo har sa'ar da ya shiga cikin kantin ya dauko littafin, da sauri ya kuma nufowa wajenta, "Kin ga littafin." Ya mika ma ta bayan ya zauna. Ta kuma mayar ma sa, "To bude ka duba mana, a ranar sha biyu ga wannan watan su wane ne su ka zo su ka yi sayayya?" Ya karba ya fara budewa. Da ya zo shafin ya tsaya, "Kin ga mutum biyar ne kawai su ka yi siyayyar a ranar, da ya ke ban jima ba na rufe saboda tafiya da zan yi a ranar." Ta dan leka ta dubi littafin, "To za ka iya tuna mutanen?" "Da wa-da wa kenan?" Ta bukata a kagauce. "Kin ga dai wannan Naira hamsin din malami ne a nan makarantar, malam Ibrahim Mu'azzam ya sayi sabulu guda biyu GIV, wannan kuma Naira dari da Naira sha biyar din wata mata ce da ta kawo yara cikin wata mota Lexus, ta sayawa yaran alewa da biskit, wanan su ne kawai zan iya tunawa." Hannatu ta dube shi ido da ido, "Matar da ka ce ta zo da yara ya ya take?" "Su uku ne, mata biyu namiji daya. Abin da ya sa na tuna hakan, bana mantawa, biskit uku ta saya alewa biyu har na tuna ma ta cewa alewa uku ya kamata ta saya amma sai ta ce dai biyu zan kawo ma ta. To bayan na kawo ne da ta raba alewar yaron namijin bai samu ba, har zai yi ma ta kuka sai ta bude yar jakarta ta dauko ma sa wata alewar." Hannatu ta nisa bayan ya ida. Shakka babu yanzu ta sami abin da take so kuma ta nada tabbacin Hajiya Rukayya ce, saura da me? Ta dube shi "Habu za ka iya tuna kalar biskit din da alewar da ta saya?" "Sosai, ai ga sunan a rubuce, alewar "NANY" ce, shi kuma biskit din "Shortcake' ne". Ta gyada kai "Na gode, Habu yanzu saura taimakon da na ce za ka yi min." ya dube ta, "Fadi ina jin ki." "So na ke dan Allah ranar Alhamis ka halarci kotu dan bada wadannan shaidu domin..." Ya daga ma ta hannu. "Wace kotu ce?" "Arewa majistiri" Ya yi dariya, "Kin ce da ke za a tsaya ko?" "Kwarai kuwa." "To kar ki damu, idan Allah ya so zan zo to sai dai ni ma da bukatata gare ki bayan kammala shari'ar." Ya ce ya na dariya. Ta kalle shi, bayan ta mike tsaye "Mece ce bukatar taka?" "Wallahi kaunarki nake yi, yar kyakkyawa." Zuciyarsa ce ta fada. Amma a fili sai ya ce, "Ki dai bari sai ranar." "To Allah ya kai mu," Ta ce. Ya taka ma ta, su na hira har gindin motarta. Ta bude ta shiga, ta tashe ta, ta tuka ta bar makarantar cikin murna da ganin cewa kawarta za ta kubuta daga zargin da a ke yi ma ta. Shi kuwa dan saurayi Habu mai kanti ya bi motar da kallo yana ta murna ya sami budurwa kyakkyawa. ZAMAN KOTU NA BIYU A yau ma kotin ta arewa tak ta ke taf da jama'a, kusan ta fi zamanta na farko ma cika. Meyiwa hakan na da alaka da bazuwar da shari'ar ta yi ta hanyar mutanen da su ka halarci zamanta a karo na farko. Lokacin da lauyoyin su ka shigo kotun sai jama'a su ka shiga nuna su wasu da zunde, musamman ma Barista Hannatu da su ke ganin ta nuna bajinta a zaman farko. Kafin Barista Hannatu ta zauna sai da ta dubi jama'ar, ta dubi bangaren da Zainab ta ke ta yi ma ta murmushi ita ma Zainab da ke dauke cikin sarka ta mayar mata da murmushin da kyar, kana Hannatu ta zauna. Zamanta ke da wuya sai ta hango cikin jama'ar ana dago ma ta hannu, ko da ta lura da kyau sai ta ga ashe Habu mai kanti ne. Ta daga masa hannu ita ma cikin fara'a don ta yi matukar jin dadin ganin sa. Shi kuma ganin ta dago masa hannu sai ya yi ajiyar zuciya kana ya ce, cikin zuciyarsa. "Kai, Allah fa ya yi hallita a nan. Ni idan wannan tsaleliyar za ta amince ta aure ni, ai zan iya amincewa a tsire min idanuwana duka na daina ganin komai, tunda ina tare da kyakkyawa karshen kyau." Da misalin karfe goma da yan dakiku mai shari'a Mukhtar Kano ya shigo cikin dakin shari'ar. Kamar yadda ya ke, jama'a duk su ka mike cikin girmamawa. Bayan mai shari'a ya yi rankwafawar da ya saba cikin girmama jama'ar, sai suma su ka rankwafa a girmame, ya zauna kan kujerarsa kana kowa ya zauna. Kotun ta yi tsit. Bayan kotun ta samu nutsuwa, mai gabatar da shari'a Furoskito Nura Salihu ya mike hannunsa rike da takardu. "Yau ranar Alhamis ashirin da uku ga watan sha biyu, ita ce ranar da Shari'a ta ajiye don ci gaba da sauraron wannan kara, wadda ake tuhumar Zainab Ilyas amaryar Alhaji Basiru da yiwa yayan kishiyarta kisan gilla". Ya rankwafa girmamawa ka na ya kuma tsawatarwar da mai shari'a Mukhtar Kano ya yi, sai ya dubi Hannatu, "Kafin mu mika damar ci gaba da gabatar da shaidu ga Barista Garba ko ki na da wani abin da za ki ce?" Hannatu ta girgiza kai "Babu Yallabai. Sai dai ina so na yi tambaya ga shari'a ko ta samo wannan mata, Baraka?" Mai shari'a ya gyada kai "Kwarai an samo ta, shi kenan?" Ya bukata. "Ranka ya dade, shi kenan." Hannatu ta ce Mai shari'a ya dubi Garba "Bismillah". Garba ya mike, "Zan so na yi amfani da wannan dama, na yi kira ga shari'a kafin na ci gaba da gabatar da kwararan shaidun nawa. Babu shakka ya dace akwai kuma soyuwar a ce shari'a ta gane cewa, ba kowane dan Adam ne ke iya magana ko amsa tambaya cikin jama'a ba ba tare da ya yi rawar baki ba. Don haka ina kira ga shari'a da kar ta yi la'akari da gaza amsa tambayar da shaidun da zan gabatar za su.." "Ina da ja!" Hannatu ta mike "Ya zama wajibi na kalubalanci wannan sharhi da Garba ya yi. Ya mai shari'a babu yadda za a yi gumi ya karyowa mai gaskiya a cikin ruwa. Abin da nake nufi shi ne, ba zai taba yiwuwa a ce mutumin da ke da gaskiya ya gaza amsa tambayar da za a yi ma sa ko ya yi rawar baki yayin amsa tambaya ba, matukar ba haka halittarsa ta ke ba. "Don haka ina kira ga shari'a da ta yi watsi da wannan kira don babu wata fa'ida a cikinsa." Ta koma ta zauna. Garba ya yi murmushin karfin hali, "Shaida na farko da nake so na gabatar a yau shi ne direban gidan Alhaji Basirun, wato Lukman." Lukman ya fito ya hau mumbarin shaida. Garba ya dube shi "Lukman kai ne direban gidan Alhaji Basiru ko?" "Haka ne." Ya amsa. "Kai yara da dauko su ne kawai aikinka a gidan?" Ya gyada kai "Haka ne." "A ranar litinin sha biyu ga wata kai ka dauko yara daga makaranta?" "Eh, ni ne." "Shin ko ka ga wani abu a tare da yaran sa'ar da ka je daukop su a makarantar, abin nufi na dangane da ci ko sha?" "A'a." Ya girgiza kai. "Kuma ba su fada maka cewa akwai makamancin wannan abu tare da su ba, har sa'ar da ka kai su gida?" Ya girgiza kai, "Ba su fada ba." Garba ya yi ma sa godiya ya koma nya zauna. Hannatu ta mike "Lukman zan so na san wanda ya kai wannan yaran makaranta a wannan rana". Sai da ya dan jinkirta kadan, kafin ya ce wace Hajiya kenan?" "Hajiya ce." "Hajiya Rukayya." "Daman ita ta ke kai su?" "A'a... " ya girgiza kai, "Ni ne ke kai su". "To, menene ya sa ta kai su a wannan rana?" "Saboda bani da lafiya." Ya amsa kai tsaye. "To, ba ka da lafiya, wa ya je ya dauko su da rana?" "Ni...ne?" "Hakan na nufin ka samu sauki kenan?" "Eh." ya amsa da kyar gami da gyada kai. "Dangane da gurbin kwanan motocin gidan zan so na ji, dukkansu su na kwana gida ne ko akwai ma su kwana a wajenka?" "A'a, duk a gidan su ke kwana, babu mai kwana a wajena." Sai bayan ya amsa ne ya gane cewa ya yi kuskure, domin irin tambayar da ta yi ma sa ya kasa amsawa, ita ta ke shirin yi ma sa yanzu. "To, idan haka ne me ya sa a wannan rana ka tafi da mota gida? Ko daman ka san za ka yi rashin lafiya, kuma da rana za ka samu sauki?" Lukman ya hadiyi yawu da kyar, "Motar ta kwana wajena ne saboda..." ya yi shiru ya na kifkkifta idanu, kamar kwado. "Saboda me?" Hannatu ta dawo da hankalisa gare ta. Ya na rawar baki ya ce, "Saboda Hajiya ce ta ce na tafi da ita." "Wace Hajiyar?" "Hajiya Rukayya." Ba shi da zabi ya zama wajibi ya fada. Idanun Hajiya Rukayya su ka dada girma, ta dafe krji, alamun fargaba da mamaki. Ta mike tsaye "Wace Hajiyar, Ni?" Ta ambata cikin karaji, wanda hakan shi ya ja hankulan daukacin mutanen dake kotun zuwa gare ta. Ta juya kallonta ga mai shari'a. Ta soma rantse- rantse, "Alkali! Na rantse da Allah...wallahi karya ya ke yi min. Ni ban fada ma sa ya ta..." Buga gudamar da mai shari'a Mukhtar ya yi ne ta katse ta, tare da guna-gunin da jama'a su ka soma. "Zauna Hajiya!" Mai shari'a ya yi ma ta tsawa, "Kar ki kuma magana in dai ba tambayar ki a ka yi ba. Idan ba haka ba za ki fuskanci fushin shari'a." Ya gargade ta. Jama'a su ka kuma mayar da hankalinsu ga Hannatu da Lukman don jin mafadar wannan abu da ya soma ba su mamaki, ganin mai shari'a ya umarce ta da ta ci gaba da yin tambayoyinta. "Saki jikin ka malam Lukman, ko za ka sanar da mu dalilin da ya sa a wannan rana ita Hajiyar ta ce ka tafi da motar gida?" Ya girgiza kai, "A'a, wallahi ni ma ban san dalili ba. Ni ma na yi matukar mamaki,tunda tun da na soma tuki a gidan hakan ba ta taba faruwa ba." Da alama ya amsa kiran na Hannatu, na ya saki jikinsa tunda yanzu murya ba ta rawa. Kuma ko washe gari ba ka tambaye ta ba?" Ya girgiza kai, "Gaskiya ban tambaye ta ba saboda..." Ya yi shiru. "Saboda me?" "Saboda ta ba ni kudi. A yanzu ya kudiri aniyar fadar gaskiya, don haka ba ya fargabar duk abin da zai biyo baya. Mamaki ne ya kara bayyana a fuskokin jama'ar, kana hayaniya ta biyo baya. Mai shari'a ya tsawatar. Bayan an yi shiru, Hannatu ta ci gaba, "Kenan ya tabbata a wannan lokaci akwai abin da ta ke kullawa, wanda daga bisani shi ya yi sanadiyar ya yanta ko?" "Kin ga saurara Hannatu." Garba ya katse ta a fusace, "Ya mai shari'a ba zan taba amincewa da irin wannan tursasawa ba. Don kuwa ta nakokarin wanda ta ke yi wa tambayar ya tabbatar ma ta da abin da bai sani ba. Lallai wannan ya kauce layin da mu ke kai, ya dace a tsawatar ma ta." Mai shari'a ya tsawatar ga Hannatu. Ta yi godiya, sannan ta koma wajen zamanta, fuskarta cike da annuri, musamman ma ganin yadda ta fuskanci kan yan kallo ya fara wayewa. Garba ya ce, "Zan gabatar da shaida na gaba kuma na karshe, wanda kuma nake matukar fatan ganin cewa daga kansa kotu za ta fahimci gaskiya, ta kuma yanke hukunci ga wannan mata mara amana. Wannan mutum shi ne mai gadin gidan Alhajin." Duk da cewa jikinsa a sanyaye ya ke yanzu, a muryarsa ya na kokari domin ba ta sanyaya ba. Maigadi Bukar ya hau mumbarin shaida. Garba ya dube shi, "Malam Bukar mene ne aikinka a wannan gida?" "Gadi nake yi." Ya amsa kai tsaye. "Kullum kai ne a bakin kofar kenan?" "E, kwarai." "A ranar da wannan al'amari ya faru ko ka ga Hajiya Rukayya ta fita da mota, abin nufi ta tafi kai yara makaranta?" Ya girgiza kai "Gaskiya ban gani ba...ai bama ita ce ke kai yara makarantata ba." Garba ya gyada kai "Na gode." ya juya ga mai shari'a" (Matsala akasamu anan wacca badan itaba datini nagama littafin,amma saidai nanemi afuwa dan batawarwaru bakidayaba) "Abu na farko da za mu lura da shi shi ne, hana Lukman direba zuwa kai yaran makaranta da kuma mallaka masa mota ta kwana a hannunsa da zummar idan rana ta yi ya je ya dauko yaran, bugu da kari da kudin da ta ba shi. "Abu na biyu kuma hikimar aiken maigadi don kar ya ga sa'ar da ta fita zuwa kai yara makaranta. Abu na karshe, alewa biyu da ta saya wajen Habu mai kanti, a maimakon uku wanda hakan ya nuna kiri-kiri ta tanadi waccan muguwar alewa kamar yadda shi Habu ya ce ya ga ma sa'ar da ta dauko alewar daga jakarta. Kuma idan mu ka lura da bawon wannan alewa mai guba ya bambanta da wadda Hajiyar ta saya." Hannatu ta gabatar da bawon alewar ga mai shari'a kowa ya tabbatar ba iri daya ba ne da wanda Hajiya Rukayya ta saya a wajen Habu. Bayan an tabbatar ta ci gaba, "Daga karshe ina kira ga shari'a da ta kula da wadannan dalilai da su ka kama Hajiya Rukayya da yunkurin kashe dan kishiyarta wanda daga bisani reshe ya juye da mujiya." Hannatu ta koma ta zauna. Bayan yan rubuce-rubuce da mai shari'a ya yi sai ya juya kallonsa ga Barista Garba. "Ko kana da abin cewa?" Ya girgiza kai a sanyaye, "Babu ranka ya dade." Har yanzu akwai guna-gunin jama'a. Hannatu ta mike, "Ya mai shari'a zan so shari'a ta ba ni dama na kirawo mace ta karshe wadda na ke son na yiwa yan tambayoyi, wato Baraka." Baraka ta hau mumbarin shaida ta tsaya. Kallo daya za ka yi ma ta ka tabbatar ce gaba daya a tsorace ta ke, kamar ace arr! Ta tsere. Sai rarraba idanu take. Wannan ya nayi na Baraka ya yi matukar yi wa Hannatu dadi, domin ta san dai ko ba Komai Barakar ba za ta wahalar ba. Hannatu ta dube ta, "Baraka mene ne tsakaninku da Hajiya Rukayya?" "Kawatace." Ta amsa a takaice. "Tsawon wane lokaci?" "Tun muna kanana" "Tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu ku na tare?" "E, muna tare a zuciya, amma mun dade ba mu hadu ba." Kai tsaye kuma a takaice ta ke ba ta amsar. "Me ya sa?" "Saboda mun tashi mun kma jigawa, tsawon shekaru." "Kun jima ba ku ga juna ba sai a yan makonni biyu da su ka shude, haka ne?" "Eh, haka ne." "Mene ne ya kawo ki?" "Ziyara na kawo gurin irinsu kawayena, da kuma sauran yan uwa." "Wato daga can ki ka taho ma ta da alewar me guba da ta hallaka yayanta..." "Wannan tambayar ba ta dace ba." Garba ya katse ta bayan ya mike tsaye da hanzari. Sannan ya juya ga mai shari'a, "Ya mai shari'a, ya kamata fa a lura, Hannatu na amfani da wasu irin tambayoyi da ba sa kan la..." "Ya isa Garba." Mai shari' ya katse shi, "Tambayoyinta su na kan layi." Ya juya gare ta, "Ki na iya ci gaba Hannatu." Hannatu ta yi murmushi sannan ta kuma maimaita tambayar ga Baraka, "Wato daga can ki ka taho mata da alewar me guba da ta hallaka yayanta..." "Ni!" Ta katse Hannatu, "Wallahi bani ba ce." Ta dubi bigiren da Hajiya Rukayya ta ke "Hajiya ke ce ki ka ce ni na kawo miki wannan alewar?" A rikice ta kuma mayar da dubanta ga Hannatu "Wallahi tallahi ba ni na bata da hannuna ba. Ni dai na san na raka..." Ta yi shiru saboda wani abu da ya shiga zuciyarta. "Kin san kin raka ta ina?" Hannatu ta bukata da sauri. Idan ba ta fada ba ta san ita za ta kwana a ciki. Bakinta na rawa ta ce, "Na san ni na...ra...ka ta ta karbo...alewar..." Wani sabon ya nayi ne ya bayyana a fuskokin daukacin ma su zaman shaidar, ciki har da mai shari'ar. Yanzu idanunsu gaba daya ya na kan Barakar. "A ina ku ka karbo alewar?" Ta soma kuka, "A wajen wani babban boka." shi kenan ta bayyana. Hayaniya ta kuma kaurewa a wannan karon shi kansa mai shari'ar kasa tsawatarwa ya yi akan kari saboda mamaki. Sai da aka samu tsawon lokaci kana da kyar ya dakatar da hayaniyar. Hannatu ta dubi mai shari'a, "A yanzu babu bukatar na tsawaita jawabi domin gaskiya ta bayyana, sai dai kira biyu da zan yi ga shari'a shi ne, lallai ya wajaba ta hukunta Hajiya Rukayya da kawarta Baraka hukunci mai tsauri don gudun kada irin wannan ta kuma faruwa a gaba, donin zamansu cikin jama'a haka sakaka hadari ne. Haka nan kuma tilas ne shari'a ta hukunta duk wanda ya ke da sa hannu cikin wannan shiri don ya zama a gaba ya kiyaye don samun kyautuwar al'umma. Kira na biyu, ina neman shari'a da ta tirsasa Hajiya Rukayya ta biya Zainab diyar kudi Naira Miliyan daya, don yunkurin bata ma ta suna da ta yi ta hanyar makala ma ta abin da ba ita ta yi ba...bugu da kari da zaman da ta sa ta yi na tsawon kwanaki a gidan horo. Daga karshe ina addu'a ga duk matar da ta ke tare da kishiya, Allah ya kiyaye ta kar a kulla ma ta sharin da zai kai ta cikin wahalar da Zainab ta shiga, kwana goma sha daya a 'Women Detention Centre' ma'ana "Gidan horo na mata" Kusan gaba daya kotun aka tallafawa addu'ar Hannatu da "Amin". Ta yi godiya ta koma ta zauna. A yanzu dai Barista Garba ya yi shiru cikin tunani da jimami gami da nadamar tsayawar da ya yi wa Hajiya Rukayya kasancewar ta ba shi abin a rufe. Ya yi tagumi hannu bibbiyu ya na jiran jin hukuncin da mai shari'a zai yanke. Hajiya Rukayya da Baraka da duk yan uwanta kuwa babu abin da su ke yi sai kuka. Ba tare da tsawaitawa ba ya yi bayani game da duk hojjoji da shaidun da lauyoyin biyu su ka gabatar. Bayan ya kammala sai ya fara bayar da sakamako shari'ar kamar haka:- "...Bisa dogaro ga duk wadannan hojjoji da shaidu da aka gabatar, shari'a ta tankade tsaf, kuma daga karshe ta wanke wadda a ke zargi, wato Zainab, ta kuma sake ta, bisa dogaro da doka mai lamba 103, sashe na 119, sakin layi na biyu, cikin baka. Kana ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga Hajiya Rukayya bisa laifin da ta aikata na zama silar kashe yayanta biyu...Da kuma biyan Naira miliyan daya ga Zainab kamar yadda lauyarta ta bukata, bisa dogaro da doka ta 99, sashe na 121. Sakin layi na uku..." Ihun da Hajiya Rukayya ta kurma ne ya katse mai shari'ar, lokaci guda kuma ta sulale ta fadi kasa sumammiya. Bayan yan sanda sun yi waje da ita bisa umarnin alkali, sai ya ci gaba, "Haka kuma Shari'a ta yanke hukuncin daurin shekaru goma ga Baraka ba tare da tara ba, bisa laifin hada kai don yunkurin aikata kisan kai. Shi kuwa Lukman, kotu ya yanke ma sa hukuncin daurin shekara guda bisa karbar cin hanci, amma shi zai iya biyan tara ta Naira dubi hamsin...Wadannan kuma mun yi duba ne ga doka mai lamba 69, sashe na 173, sakin layi na farko, cikin baka." Da wannan mu ka kawo karshen wannan shari'a." Ya rufe littafinsa ya mike. Duk jama'a su ka mike. Ita ma Baraka da Lukman su na kurma uban kuka, har da kururuwa, yan sanda su ka yi awon gaba da su. BAYAN MAKO GUDA DA SHARI'A Karfe tara na safiya wannan rana ta Alhamis a ka sallamo Alhaji Basiru daga asibiti. Murna a wajen Zainab ba a cewa komai. Koda isowarsa gida jama'a su ka rika zuwa su na yi ma sa jaje gami da ta'aziyyar rashin yayansa. Bayan komai ya natsa, sahun jama'a ya dauke daga zuwa yin jaje da gaisuwa, da karfe hudu na yammacin wannan rana sai Alhaji Basiru ya gayyaci matarsa dakinsa saboda wani zama da za su yi, zaman da ya kira shi da zaman shawara. Da godiya ga Allah (S.W.T.) ya soma, bisa ketarar da shi da ya yi daga wannan mummunan hadari, kana ya ci gaba da cewa, "Zainab a farko, bayan godiya ga Mai duka, ina mika jinjina gare ki bisa namijin kokarin da ki ka yi wajen jure duk abin da Hajiya ta ke mi ki. Lallai kin isa jinjina, ya kuma dace da ma ga kowace mace ta rike abubuwa hudu wadanda su ne ki ka rike har ki ka kai wannan matsayi. Allah ya saka mi ki da alkhairi." "Amin." Ta amsa murya a sanyaye. Shiru na dan lokaci babu wanda ya yi magana. Zainab ta cira kai ta dubi Alhaji Basiru bayan ta nisa, "Alhaji." Ta kira sunan a nutse. Ya dago kai ya dube ta, "Na'am amarya." Ta dukar da kai cikin jin kunya ta ce, "Alhaji har yanzu ban fita daga amarci ba? Shekaru nawa..." "Har yanzu ba ki bar matsayin wannan suna ba tunda ban yi wani auren ba, bayan naki." Su ka yi dariya gaba daya. "Me ki ke so ki ce ne?" Ya tambaya bayan sun tsagaita da dariyar. Ta yi murmushi, "Alhaji ina son sanin abubuwa guda hudun nan da ka ce ya dace kowace mace ta rike." Shi ma ya yi murmushi, "Ai ke kin rike su shi ya sa har yanzu ki ke zaune daraf a mukamin da babu kamar ke a cikin zuciyata. Kuma duk macen ma da ta rike su to babu shakka za ta zama sarauniya a cikin zuciyar mijinta. Sai ta fi komai soyuwa a zuciyarsa. Kai! Har ya ji cewa ma zai iya bayar da ransa saboda ita." Zainab ta numfasa, "Maigida ai ka san kogi bai ki dadi ba. Ina so ka kara sanar da ni su don na kara kankame su, don Wallahi ba na son abin da zai bata ma ka rai ko kadan." Ta sunkuyar da kai kasa. Alhaji Basiru ya nisa, "Kina da gaskiya amaryata." ya daga yan yatsunsa hudu, "Wadannan abubuwa guda hudu su ne; Hakuri da Biyayya da juriya da kuma Gaskiya. Kin ga dai Hakuri shi ne, kawar da kai da sanya dangana ga abin da aka yi ma ko da ya bata ma ka rai. Juriya kuma ita ce, ci gaba da jajirce wa a kan abin da ka ke yi mai kyau komai tsangwama, Biyayya kuwa, bi da yarda da abin da aka san bai saba wa Allah ba, don farantawa miji rai. Gaskiya kuma, tsaya wa a kan abin da ka san an yi ba tare da kaucewa ba, da kuma yarda da abin da aka sanar da kai na game da kuskure don gyara, komai dacinsa. Don akwai Hadisi na Manzon Allah (S.A.W) da ke bayani game da, ba wani abu ne girman kai sai kin gaskiya" Zainab ta jinjina kai ganin ya dan tsahirta ya na duban ta. "Kin ga duk macen da tare wadannan abubuwa." Ya ci gaba, "To, babu shakka ta tsira." "Wannan gaskiya ne Alhaji. To amma ni ban ji ka tabo bangaren..." Ta yi shiru. "Bangaren me?" Ya bukata. "Bangaren su kwalliya, tsafta da kyale-kyale, kissa don jan hankalin maigida ba, wanda wannan ma na san su na daga cikin abin da ke kara dankon auratayya." "Ya gyada kai, "Kwarai kuwa Zainab, amma duk wadannan da ki ka lissafo su na karkashin abu na uku da na lissafo, wato 'Biyayya', don sai da ita ne za a yi duk wadannan abubuwa don faranta wa maigoda rai." Ita ma ta gyada kai, "Gaskiya ne wannan maigida." "Ki na da tambaya cikin wadannan abubuwa kafin na je ga shawarar da na ce mi ki za mu yi?" Ta girgiza kai, "Babu maigida. Na gane su sosai, kuma da izinin Allah zan dage don ganin na rike wadannan abubuwa da ya kamata a kira su da Garkuwar Aure." Ya yi murmushi, "Haka ne. Abu na gaba da na ke son na gaya mi ki wanda na ce shawara ne, shi ne ina so zan sauwake wa Hajiya." Ta dafe kirji, "Haba Alhaji, yanzu..." "Saurara!" Ya katse ta, "Idan ban sake ta ba ya ki ke so na yi da ita bayan ta na karkashin hukuncin daurin rai da rai? Ki na ganin aurena da ita zai yiwu ina nan ta na can? Kuma ko ba wannan ki na tunanin zan iya zama da ita?" Zainab ta sauke hannunta jiki a sanyaye, babu yadda za ta iya. "Ya na ji kin yi shiru?" Alhaji Basiru ya bukata ganin shirun nata na kokarin tsawaita. Ta nisa, "Babu koma Alhaji...tausaya ma ka kawai na ke yi da kuma ita Hajiyar". Ya yi murmushin karfin hali, "Ni mene ne dalilin tausaya min din?" Ta sunkuyar da kanta cikin kunya, "Saboda bukatarka ta zama da mata biyu." Ya girgiza kai kana ya yi wani dan guntun murmushi, "Babu komai amarya, kar ki damu, ke ma kin wadace ni." Ta dan harare shi cikin wasa, "Gaskiya kar ka kuma ce min amarya." Ya girgiza kai, "Ina! Ai ba zan iya daina wa ba." Ta gyada kai a takaice, da muryar wasa ta ce, "Lallai idan ba ka daina ba zan dau mataki." Ya fashe da dariya, "Ai ba za ki iya ba. Kuma ma wane mataki za ki dauka?" "Uhm! Ya wuce na cije ka?" "Cizo?" Ya bukata, "Ni kuma nawa hakoran fa? Ba sai na rama ba?" Ta daga kai su ka hada idanu. Abin da ta gani cikin idanunsa ya sa ta ce, "Bari na cije ka din ka rama." Ta yunkura ta kama hannunsa ta sa hakora. "Wayyo Allana!" Ya ce da yar daga murya. Ta sake shi da sauri, ta mike ta yi waje a guje. Bai tsaya wata-wata ba, ya mike ya bi ta da gudu. Dakinta ta nufa ta na dariya. Shi ma dariyar ya ke Da haka su ka shige dakin. KARSHE MUHAMMAD LAWAL BARISTA. Zaharaddeenn Shomar Whtapp

Shin Ana Bukatan Blog ko website Kamar wannan kodai kamar Shafin Duniyan Fasaha, za'a iya samu a kan farashi mai rahusa daga Babban kanfanin Be With Me Technology Yola, Wayanda suka kware wajen Website Design da kuma hada Mahajar Waya. Za'a iya tuntubansu anan ko a wannan layin +2349039016969

Get Professional Website Design For your business Today Here. You can also visit our Tech Blog for more awesome Information. 
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *