Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 2 February 2017

NAWAFF COMPLETE

adsense here

☆☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINK'AI, ya ALLAH kabani ikon fad'ar abinda zai amfani al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar da al'ummarka. Assalamu alaikum, gaisuwa da fatan alkairi, inamai farin cikin sake had'uwa daku asabon littafina mai suna NAWAFF, ALLAH yasa ya amfanar damu baki d'aya. Amin ­čÖĆ­čĆ╗. Page­čĹë­čĆ╗1&2 Yau antashi da tsananin zafi, saka makon ranar data kwalle­čî×, mutane kowa yana neman mafaka, a karkashin rumfa ko bishiya. Ga k'arar ababen hawa data cika birnin na kano, dukda katafaren gosulo d'in daya cinkushe titin, dayawa mutanen dake cikin moto cin sun gala baita, da tsananin zafin ranar. Amma wannan bai hana 'yan tallah daf dalaba suna yayata tallar ababen sana'ar su, musamman masu tallar ruwa, saboda yanayin zafin mutane suna buk'atar ruwa mai sanyi. Nakai dubana bisa wata farar mota mai k'yawun gsk, wadda daka mata kallo d'aya kasan mai ita yagama wada tuwa. Wata k'yak'yk'yawar yarinya nagani kwance a bayan motar, farace saidai farinta bamai haskeba sosai, tanada kala irinna 'yan itopia, tanada dogon hanci da manyan idanuwa, kwance take abayan motar tana nazarin littafi. Agaba kuma direbane, tad'ago kai tareda fad'in balarabe kaga abinda nake jiye mana ko?, shiyyasa nace kar mu biyo ta nan, gashi har ina neman makara, kuma inada lectures yanzu wlhy. Balarabe ya ce, "kiyi hak'uri hajiya, wlhy banyi zaton zamu sami wannan cinkoson ba. Ta d'anyi k'aramin tsaki tana fad'i ni wlhy saima karasa abinda yake haddasa irin wannan cinkoson a garin kano?, batareda ta saurari sharhin da balarabe yake mataba ta bud'e motar ta fice. Tafito dai2 sanda wata jar mota 'yar k'arama ta tsaya saitin ta, ahankali aka zage gilashin motar zuwa k'asa, wani had'ad'd'en saurayi ya bayyana, saikuma wani danake tunanin abokinsane. K'yak'yk'yawan saurayinnan ne matuk'in motar, kallo d'aya zaka masa ka gano yana cikin farin ciki, dan sai kad'a kai yake da alama wak'a yakeji, kuma wak'ar tana masa dad'i. Ya d'akko kwalin hollanddia yana sha ahankali yana cigaba da kad'a kai, harda had'e yatsun hannunsa biyu yana bugawa. Karku d'auka wannan k'yak'yk'yawar yarinyar shitake kallo, A'a ko kad'an hankalinta baya kansa. Jitai wani abu yadaki k'irjinta, da sauri ta kalli jikinta. Hummm kunsan miye kuwa??. Ba wani abu bane illa kwalin hollanddia da gay d'innan yake sha, takuma bin jikinta da kallo, dan ganin yanda yogot d'in yay mata kaca2 da bak'ar jallabiyar dake jikinta, ta maida kallonta ga motar dan ganin wane wawane yay mata wannan aikin??. Saitaga mutum yana kallonta yana tuntsirar dariya harda dukan sitiyari, d'ayan saurayin dake gefensa ya d'ago yana kallonsa, ya ce, "kai malam lafiyarka kuwa?, kanata dariya kai kad'ai kamar wani shafar aljanu. Cikin dariya ya nuna masa yasmeen dake tsaye tamkar gunki tana kallon ikon ALLAH, tana mamakin wannan wane irin shashashan mutum ne, yayi mata abu amma yana nunata yana dariya. Mas'ud ya ce, "amma kaidai d'an iskane NAWAFF, yazaka b'atama yarinya jiki, kakuma rink'a yimata dariya??. Kasan kuwa wacece wannan kalli nomber motar data fito fa. NAWAFF ya gallama Mas'ud harara yana fad'in aii bani nace tazo ta tsaya anan ba tana yima muta ne iyayi ko?, dazakace nawani kalli nomber mota, to saimi idan na kalla. Duk abunda suke fad'i Yasmeen tana jinsu, dan haka sai zuciyarta tak'ara tunzura, cikin fasifa ta k'arasa gurin motarsu. Ta ce, "kai wawa wanda baisan darajar mutaneba, shin kobaka ga b'arnar dakayi bane??. Cikin fushi NAWAFF ya kalleta ya ce, "waye wawan??. Itama cikin tsiwa ta ce, "masa kai mana!!!, ko wawan yayi maka kad'an saina had'a da mahaukaci, dan naga kanada k'aramar kwakwalwa. Afusace yabud'e mota yafito, ya wanka mata mari, jikake wani tasss. Dayawan hankalin mutane yadawo gurin musamman 'yan tallah. Ta dafe kunci tana kallonsa, sai kuma ta d'aga hannu itama zata wanka masa mari. Da sauri ya rik'e hannun ya murd'e, ta ce, "kai karamin d'an iska ka sakar mini hannu, hannu yad'aga zai k'ara marinta mas'ud yay saurin shiga tsakkiyarsu, ya ce, "haba NAWAFF yazaka mata laifi sannan ka daketa??. Cikin masifa ya ce, "dalla malam nibakaga raahin kunyar datake minbane?, ko kai kurmane?. Mutane sai kallonsu sukeyi. Mas'ud ya ce, "haba NAWAFF kasan dai fuskarka sananniyace dammi zaka aikata haka?, yanzu sakaji 'yan jarida suna yayataka aduniya kadai sani sarai. NAWAFF yaja tsaki, karsu fasa gayawa duniya abinda nayi kajiko, kodan kar afad'ama duniya saina zauna yarinya k'arama tayimin rashin kunya. Ya juyo gareta ­čĹë­čĆ╗ke kuma ki rubuta ki ajiye saina nuna miki ni­čĹł­čĆ╗ nafi mahaukaci hauka. Yasmeen taja tsaki ta ce, "wlhy nikuma saina nuna maka nike maganin dukkan wani mahaukaci komai haukansa. Aifa yasake harzuk'owa zai mareta, mas'ud dake tsakkiyarsu ya kare, wai ku miye hakane? dan ALLAH, waishin bakwa ganin kallon da'ake mukune??, gashi kun tarema mutane hanya. Sai asannan NAWAFF ya lura gabansu babu kowa, duk tarin gosulo d'innan ya b'ace, saidai mutanen dake bayansu, sunata danna musu hon. Balarabe da tund'azu yake bama Yasmeen hak'uri, amma tak'i saurarensa, ya ce, "kiyi hak'uri Hajiya kizo mutafi kinga kin makara. Harara ta watsa masa sannan taja tsaki, mas'ud ya ce, "plz kiyi hak'uri dan ALLAH kinga a titi muke. Juyawa tayi ga motarsu dan ganin kawai kallon da'ake musu, amma tad'auki alk'awarin duk ranar data sake had'uwa da gay d'innan saita nuna masa shi k'aramin d'an iskane wlhy.......................✍­čĆ╗ Tusk'ashi masu karatu, komi zai faru?, shin waye NAWAFF??? Miyasa 'yan jarida zasu iya yayatashi???? Wacece Yasmeen?? Kuma 'yar wacece??, kubiyoni danjin amsoshi tambayoyinku.... Taku har kullum BILKISA IBRAHIM (Bily) ( Mrs Abdus'salam) Ku kasance dani!!!!!!­čĹł­čĆ╗ Zaizo gareku nanbada dad'ewaba......­čśś­čśśluv u oll ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× [1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄżNAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× page­čĹë­čĆ╗3 Ta ce, "da direba maidani gida. Cikin tsoro ya ce, "to hajiya makarantar fa??. Cikin masifa ta ce, "gida nace ka maidani ba dogon bayani na tambayeka ba, kajiko. Ya ce, "yi hak'uri hajiya ALLAH ya huci zuciyarki. Bata tanka masaba domin zuciyarta sai tafarfasa take, babu abinda take tunowa sai abinda gay d'innan yay mata. Tun kafin yayi fakin tayi waje, da gudu tashiga gida. Humm kunsan abinda yaba ni mamaki??, gidan da yarinyar tashiga daka gani gidan talakawane, bazaka tab'a tunanin yarinyar da motar 'yan gidan bane,, tokomadai miye agaba zamu sani. Tashige falon tana kuka. Wata dattiyuwar mace tana zaune a matsakaicin falon, farace tas maik'yau, suna kama da yarinyar, daka ganta kasan ma haifiyarta ce. Tafad'a jikinta tana kuka, cikin hanzari dattijuwar ta rungume d'iyar tata tana fad'in yasmeen injidai lafiya?, bakije makarantar bane??. Cikin kuka ta ce, "umma bamun tafiba shine gosulo ya rik'emu. Umma ta ce, "to mikikema kuka? Ko gosulo d'in?, ta girgiza kai alamar A'a. To minene?, umma ta tambaya. Ta share hawaye bawani ne ya mareniba, mari kuma? Miki kai masa?, tana kuka tana bama umma labarin abinda yafaru. Umma tashiga lallashinta tana bata hakuri, babanta yashigo da sallama, dan tunda suka shingo yagansu, yatsaya tambayar balarabene abinda yafaru. Yashafa kan yesmeen ya ce, "karki damu mamana ALLAH yana tareda masu hak'uri, dan haka kiyi hakuri watarana sai labari. Ahankali tad'ago manyan idanunta wad'anda sukayi jajur saboda kuka, ta ce, "karka damu abba kabarni dashi dakaina zan rama, wlhy abba saiya raina kansa, dan na daina zama ana rainamu, dan kawai muna talakawa saikowa ya ce, zai rainamu, abba aii babu maraya sai rago. A'a mamana kibarsa kawai kinji, abbanta yafad'a yana shafa kanta. Shuru tayi batace komai ba, dan tasan bazata iya hak'ura ba. Umma ta ce, "mudai idan tamune ki hak'ura, yasmeen bana son tsiwar nan taki, idan kikayi hak'uri sai ALLAH ya saka miki, ki barmu muji da damuwarmu. Shuru tayi batace komai ba, sai hawaye da idanunta ke zubarwa, cikin raunin murya ta ce, "kuyi hak'uri iyayena shima ALLAH zaimana maganin sa, ina ji ajikina bazai tab'a nasara akanmuba insha ALLAH. Abba ya share hawaye yana fad'in to ALLAH ya amsa addu'ar ki mamana. Sukace amin itada umma. D'akinta ta shige, iyayenta suka bita da kallon tausayi, umma taja ajiyar zuciya mai k'arfi, ta ce, "lallai yasmeen kina ganin taskun rayuwa iri2, ALLAH dai yakawo mana k'arshen abunnan. Abba ya ce, "amin. Yasmeen tana shiga d'aki wayarta tahau wringing jiki a sanyaye ta d'auka, saidai fuskarta ta nuna alamun tsoro, murya na rawa ta ce, "Assalamu alaika. Bansan mi akace a d'ayan b'angaren ba, amma naga idanun yasmeen suna zubar da hawaye, saikuma ta ajiye wayar tafad'a saman gado tana kuka, duk da bansan ainahin damuwar yasmeen ba amma tabani tausayi kwarai da gsk, cikin sanyin jiki nabaro gidan nima. Ab'an garen su NAWAFF kuwa, sai mas'ud ne ya tuk'a motar, dan NAWAFF ya kasa saboda b'acin rai, tunda ya zauna akujerar gefen direba ya lumshe idanunsa masu haske, bai sake cewa uffan ba. Mas'ud yanufi hanyar gida dasu dan yasan ran 'yan maza ya b'aci, kosunje inda sukayi niyyar zuwa NAWAFF bazaya sakeba, saboda yana cikin b'acin rai. K'ofar wani matsaikai cin gida mas'ud yay hon, da sauri mai gadi yabud'e get d'in, mas'ud ya danna hancin motar zuwa ciki. Ba laifi gidan yanada d'an k'yau kuma daga ciki babbane, NAWAFF ya fito yanufi cikin gidan, kai tsaye gidan ya shiga, amma babu kowa a falon, fitowa yayi yanufi b'an garensa wanda baikai girman inda yafara shigaba. Ya fad'a saman doguwar kujera ya lumshe idanu, mas'ud yashigo ya bishi da kallo kawai. NAWAFF ya mik'e yashige bedroom d'insa, bayi yafad'a batareda ya cire kayan jikinsaba ya sakarma kansa shawa, yakai tsawon minti goma ahaka, sannan ya cire kayan jikinsa yay wanka yafito. Jalla biya kawai ya zura ya dawo falon, mas'ud na kwance a kan kujera mai zaman mutum biyu, ida nunsa nasaman tv yana kallon. NAWAFF yafito yazauna batare da yayima mas'ud maganaba. Mas'ud yad'ago yana kallonsa, dan shima yasan bazai tanka masa d'inba, yako bushe da dariya yana kallon NAWAFF. Nawaff ya d'ago yana hararar sa, yaja tsaki, tareda d'aga goran ruwa ya kwankwad'a, har sannan mas'ud yana kunshe dariya. Cikin masifa Nawaff ya ce, "dallah malam wai miye hakane??, zaka wani tasa mutane gaba kana musu dariya. Mas'ud ya ce, "kajimin mutum, ina ruwanka da dariyata, ko kaji na ambaci sunan kane?? Ammafa wlhy d'an uwa kun dace da yarinyar nan gsky. Wata uwar harara ya yasakar masa, batareda ya tanka masaba ya mik'e ya fice. Mas'ud yacigaba da dariyarsa, kamar wani mahaukaci................✍­čĆ╗ Ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turomin sakwannin taya murnan kammala book d'in NI DA AMINIYATA ngd ALLAH yabar k'auna­čśś❤❣­čĹł­čĆ╗ Kuyi hak'ura daga nan zuwa wani lokaci, zaku cigaba da samun page 1 ne kullum arana, kawai, kafin komai ya daidaita ngd. ­čĺ×bily­čĺ× ­čĺ×­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ×­čĺ×­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL­čśś­čśś­čśś­čśś­čĺ×­čĺ× ©2016 [1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄżNAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗4 Yasmeen tafito sanye cikin jan les, d'ikin riga da siket, ta nad'e kanta da d'auri mai k'yau sai zabga uban k'amshi take, ga farin mayafi da farin takalmi, abin sai wanda yagani. Mahaifiyarta ta bita da kallo, ta ce, "kai yasmeen d'in abba kinyi k'yau, kamar kece amaryar. Hannu tasaka ta rufe fuska­čÖł ta ce, "kai umma. Umma tayi dariya ta ce, "to nabari, yanzu ke dawa zaki tafi, koda yaseer zakuje. Yasmeen ta turo baki gaba, ta ce, "ALLAH umma bazanje dashiba, kina ganin jiya abinda yay min aii. Yaseer dake zaune yana cin abinci ya ce, "nima ba zuwa zanyiba, dan haka maida wuk'ar, ni nan dakike gani kallon kwallo zani. Yasmeen ta harareshi, aii kallon kwallo kawai ka'iya, mara aikinyi. Yaseer ya tab'e baki, ke kuma zuwa biki kawai kika iya, ni wlhy nak'agara abba ya aurar dake abar mini filin ma. Yasmeen ta kai masa duka, ya kauce yana dariya, cikin shagwab'a ta ce, "umma kin gansa ko?, umma tayi dariya, ta ce, "nikam babu ruwana, tunda kekika zauna yaseer ya rainaki, wanima saiyace shine yayanki aii. Yaseer ya ce, "to umma ba'ita ta tsaya shagwab'a ba, shiyyasa akecewa nine yayanta, yafad'a yana mata ­čśť. Yasmeen tabishi zata daka, suka fara zagaye falon, umma te ce, "kinga mamana k'yaleshi, zokiyi tafiyarki, kinga karkije ki fad'i da wannan takalmin mai tsinin tsiya. Yasmeen ta tsaya tana turo baki, yayinda yaseer yake tsaye bakin k'ofa yana dariya, ta harareshi, habawa yaro wlhy zan dawo nasameka, saika gayama aya zak'inta. Yaseer ya ce, "saidai mu fad'ama ayar tare, yana gama fad'a ya fice. Itama dai sallama tayima umma, ta ce, "zataje su tafi da ameena, umma ta ce, "to hakanma yayi, amma kudawo da wuri. Yasmeen ta ce, "to umma za'a kiyaye. Tana fita gidan su Ameena ta shiga, gsky gidansu ameena yafi nasu yasmeen k'yau sosai, a get suka had'u, ameena ta ce, "yauwa garama haka, dama bana son nashiga mu b'ata lokaci. Yasmeen batace komaiba taja hannun ameena suka shiga mota balarabe yaja. Wani had'ad'en guri aka kaisu, bazan fad'i gurinba dan karsu teema suce zasu itada deexerh­čśť, wajen yayi matuk'ar had'uwa, anshirya komai, yanda yakamata, yasmeen ta ciro waya a jakarta takira wata no. Ana d'auka ta ce, "Asmy ALLAH ke 'yar is... ce, kince babu African time amma gashi waje babu kowa. Daga can akace sorry my dear gamunan, wlhy laifin Safwan ne shida abokansa, wai sun tsaya jiran babban aboki, kuma har yanzu bai isoba, amma gamu nan zuwa. Yasmeen tayi d'an tsaki ta ce, "inji dai ba d'an iskan jiya bane daya shanyamu. Amaryar ta ce, "wlhy shine. Yasmeen taja tsaki, tswww, sai kuma akace dole saidashi za'ayi komai, cikin haushi ta kashe wayar batare da tajira amsar Asmy ba. Ameena ta ce, wai mitace miki??, yasmeen ta yatsine fuska, wai d'an iskan jiya suka tsaya jira, saikace wani d'an gwal, kina ganin yanda ya shanyamu jiya, daga k'arshe dan rainin hankali saiya aiko mana direba....... Yasmeen bata rufe bakiba motocin su Asmy suka fara shigowa. Bayan tsayawar su mutane suka fara fitowa, kowa yana neman wajen zama, saida kowa ya zauna sannan yasmeen ta je tafito da Amarya, ango ma yafito, 'yammatan amarya da abokan ango suka take musu baya har inda aka tanadar musu. Sai kujeru biyu a gefe wanda babbar k'awar amarya zata zauna, da babban abokin ango. Yasmeen ta zauna kusada asmy amarya suna magana kus2, yayinda aka fara gabatar da abinda yatara mutane. Zuwa can mai gabatarwa ya fara wasa babban abokin ango da aka dad'e ana jira, gaba d'aya hankalin mutane yakoma kan had'ad'd'iyar motar data tsaya kalar jaa da ratsin fari, gsky motar ta d'auki hankalin mutane, sai dai banda yasmeen, da waya ta d'auki hankalin ta. Tunda yafito ake ihun fad'in sai modeebbo! Sai modeebbo!!. Shikam hannu kawai yake d'aga musu yana murmushi, har wajen zamansa aka rakashi wato kusada ango. Bayan anyi shiru, akayima babban abokin ango barka da zuwa, ya k'ara d'agawa mutane hannu yana murmushi. Ango ya ce, "mutumina ina ka mak'alene haka, tuni kai ake jira, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, "ayimin afuwa my friend wlhy matsaya jiran mas'ud ne, baima dawoba hakanan na hak'ura na taho. Ongo yay murmushi ya ce, "anyi maka modeebbo, sukai murmushi tareda yin musabaha. Yasmeen koda tagama wayar bata damu kanta da son ganin waye babban abokin angonba, dan haushinsa takeji sabida b'ata musu lokacin dayayi jiya. Mai gabatarwa yafara kwala kiran sunan yasmeen Abubakar habeeb, tazo ana gayyatarta. Yasmeen ta dad'e zaune bata motsaba saida Asmy ta ce, "plz dear kitashi mana, yasmeen ta ce, "ALLAH kunya nakeji dear. Asmy ta harareta lallai dear awajen aurena kike jin kunya. Aka cigaba da yayata sunan yasmeen dole ta mik'e tsam tanufi inda aka tanada. Ya mik'a mata abin magana­čÄĄ, tareda fad'in munaso ki gabatar mana da kanki, dakuma tarihin amarya. Jiki a sanyaye ta karb'a, ­čÄĄ­čĹę­čĆ╗duk ta takura saboda kallon da mutane suke mata, ta d'auki hankalin yawancin gays d'in wajen, ahankali tafara magana, cikin murya mai zak'i, aii wasu saida wutar kansu ta d'auke, harda babban abokin ango (modeebbo) yak'agara yaga fuskar mamallakiyar muryar nan. ta fad'i sunanta da alak'arta da amarya, bayan tagama aka shiga yimata tafi. mai gabatarwa ya ce, "itace zata gayyato babban abokin ango zuwa wannan waje. Batare da musuba takarb'a takardar tafara kiran NAWAFF SA'ED MODEEBBO. Takira yakai sau biyar amma bai ko motsaba daga inda yake, tajuyo dan ganin wai waye wannan d'an rainin wayon abokin angon. Karaf idanunsu suka had'u a k'ar kashin inuwa d'aya, zumbur NAWAFF yamik'e tsaye. Yasmeen ta ce, "taf tsuntsu daga sama gasashe, azuciyarta take maganar. shima dai NAWAFF raya abinda zai faru yakeyi dan yasan dole sukwashi 'yan kallo, amma yasan maganin ta..........................✍­čĆ╗ Hahahha yauda budiri tsakanin YASMEEN DA NAWAFF.­čśé­čśé­čśé­čśé­čśť ­čĺ×Bily­čĺ× ­čĺ×­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ×­čĺ×­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL­čśś­čśś­čśś­čśś­čĺ×­čĺ× ©2016 [1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Assalamu alaikum. Alhmdllh 'yan uwana kamar yanda nafad'a muku natsaya da rubutu sabida wani dalili. To Alhmdllh yanzu komai ya dai daita, in farincikin kasancewa daku­čśś­čśś­čśé. Page­čĹë­čĆ╗5 .....Nawaff ya tsuke fuska, itama yasmeen ta tsuke tata fuskar. Yak'araso gareta cikin wani taku na isa da tak'ama, wajen yayi tsit ana kallonsu, yayinda masu hotuna suketa haskasu. Yak'araso daf da ita, tamkar zai shige jikinta, tayi saurin ja baya, ya had'a yatsunsa biyu yana bugawa, yay k'asa da murya yanda ita kad'ai zata iya jinsa, ya ce, "wlhy kika yimini hauka awajennan saina aikata miki abunda 'yan jaridu da mujallu zasu buga a safiyar gobe juma'a. Dukda tsoro mai tsanani yashigi yasmeen wannan bai hana ta hararar saba, ta rik'e k'ugi cikin tsiwa ta ce, "kai baka isa kasa 'yan jarida yad'aniba, kuma ALLAH shizaimin tsari da sharrinka. Nawaff modeebbo yad'an d'ago yana kallon yanda hankalin mutane yadawo kansu, saiya saki murmushi na basarwa. Gaba d'aya gurin yad'auki sowa da fad'in sun dace da juna. Nawaff yaja tsaki tareda fad'in shashashu kawai, ta ina na dace da wannan mai kama da aljanar. Yasmeen ce kawai taji furicinsa saikuma mai gabatarwa dayake kusada su tsaye. Yasmeen tai murmushin takaici ta ce, "ai basu bane shashashun kaine babban shash............kafin tarufe baki ya damk'o hannunta ya murd'a da k'arfi, wani tsananin zafi yaratsata har kwakwalwa, ALLAH yasota fitilar gurun Blue ce tana kuma kunnawa ta kashe, dan haka ba kowa yaga muguntar da Nawaff yake mataba. Zafin ya ratsata sosai, afusace ta watsa masa mari, da sauri yasaketa yana murza kumatu, itama takoma kusada amarya da sauri ta zauna tana haki. Nawaff yad'ago da sauri danjin andafa shi, mas'ud yagani tsaye. Mas'ud ya ce, "plz my bro's ka share kawai, karka bari wani yagane wani abu dake faruwa. Nawaff ya kalli mas'ud da idanunsa dasukayi jaa, ya ce, "wlhy Mas'ud saina yima yarinyarnan abinda zatayi dana sani arayuwarta, kamar yanda ka buk'ata zan barta ammafa had'uwarmu tagaba batada k'yau ko kad'an, kuma ka rubuta ka ajiye. Yana gama fad'a yakoma mazauninsa dake kusada ango, mas'ud ne ya wakilcesa, wajan fad'ar duk abinda ake buk'ata. Asmy ta ce, "yasmeen wai miye had'inki da modeebbo??, yasmeen ta share hawayen fuskarta, ta ce, "karki damu zan sanar miki, amma ba yanzuba. To shikenan asmy tafad'a, tacigaba da lallashin yasmeen, yasmeen ta ce, "Asmy kiyi hak'uri zan tafi gida, dan kaina yana mini ciwo. Asmy ta ce, "babu damuwa dear kije gobe ma had'u, ngd da k'ok'arinki. Yasmeen ta mik'e tana neman Ameena, bayan ta ganta suka fice, duk abinda take Nawaff yana kallonta, suna fita yarufa musu baya, shima mas'ud binsu yayi. Yasmeen tana k'ok'arin neman balarabe saitaji an fisgota ta baya, tajuyo da sauri, gabanta yafad'i rass dan ganin NAWAFF, Ya had'e fuska kamar bashiba, yasmeen ta ce, "lfy konaci bashinkane??. Nawaff ya damk'i gashin yasmeen data d'aure abaya, ya murd'e da karfi, tako kwalla k'ara, saidai babu maijinta saboda hayaniyar wajen tayi yawa, gakuma kid'a yana tashi, gashi a tsakankanin motoci suke. Cikin sark'ewar murya ya ce, "nikika mara ko??, to wlhy ki rubuta ki ajiye, wannan marin saiya zama FANSAR BUDURCINKI, NA MELODY , saikinyi dana sanin aikata hakan agareni, ya hankad'ata tadaki motar bayanta. mas'ud dake bayansu yabi NAWAFF da kallon mamaki, shin miyake nufi da marin datayi masa saiya zama FANSAR BUDURCINTA!!!!????. Da sauri yarufa masa baya, yayinda ameena ta k'araso takama yasmeen dake kwasar kuka, hannunta kawai taja batareda tace mata komaiba, mota suka shiga bala yajasu suka tafi. Ahanyama yasmeen sai kuka take, dan furicin NAWAFF yayi matuk'ar gigitata, ya dawomata da tunanin rayuwarta ta baya, lallai itakam tana cikin tarkunan maza azzalumai, shiyyasa takema maza KALLON KITSE na @UT@R H@JIYA@",, shin wai ita haka rayuwarta zata k'are, kowane NAMIJI burinsa yarabata da Abu mafi muhimmanci ARAYUWAR ta, miyasa haka???, mina musu???, miyasa suke son su rabani da mutuncina???, ta fad'a tana wani irin kuka mai ban tausayi,, Ameena da balarabe duk tausayin yasmeen ya cika musu zuciya, dan afili take maganar batareda ta saniba. Ameena ta rungumeta tana lallashi, dahaka suka k'arasa gida..........................✍­čĆ╗ © 2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL­čśś­čśś­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄżNAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗6 ........Nawaff kuwa tafiyarsa yayi yabar mas'ud, mas'ud bai damuba dan dama batare suka zoba, komawa yayi wajen taron dan baikama ta ace suduka sun tafi ba. NAWAFF kwance afalonsa dayaji kayan more rayuwa iri2 yana kwance saman doguwar kujera idanunsa lumshe, tamkar maiyin barci, amma idanunsa biyu, yana cikin tsananin b'acin raine kawai, tunani yake mizaima yarinyar nan ya huce haushinsa, dan ya tsaneta, hangota kawai yake lokacin data maresa, yakai hannu yashafa fuskarsa. Yay kwafa, wlhy sai yarinyarnan ta raina kanta inhar yana numfashi. Kofa aka kwankwasa, ya ce, "kowaye ya shigo. Wata 'yar aikin gidansu ce, d'auke da tiren kayan marmari, ta d'ora asaman tebirin dake tsakiyar falon, tad'an jawo tebir d'in gaban kujerar da Nawaff yake kwance. Watama tashigo da kuloli, ta d'ora inda 'yar uwarta ta d'ora, sannan suka duk'a suna kai gaisuwa wajen oga Nawaff!!. Hannu kawai ya d'aga musu sannan yay musu nuni dasu tafi. Da sauri suka wuce dan sunsan halinsa baya son wargi. D'aya acikinsu ta ce, "wlhy talatu yaya Nawaff yana burgeni, dama zaice yana sona!, Talatu ta rik'e baki, lallai ladidi yau na tabbatar bakida hankali, garama tu wuri ki fidda wannan tunanin a ranki, tun kafin wanima agidannan yajiki, in banda wuce gona da iri, yazaki had'a kanki da wannan had'ad'd'en mutumin, mai ilimi da kud'i, ga k'yau, wanda duniya tasan da zamansa. Ladidi tayi dariya kujimin wannan talatun, to kika San abinda ALLAH zaiyi ne??. Talatu ta ce, "A'a. Tunda suka fita baiko motsaba bare yaga abinda suka kawo masa, wayarsa tashiga k'ara cikin sauti mai dad'i, idonsa arufe ya mik'a hannu ya d'auka, ahankali ya bud'e idanu dan ganin wake kiransa, momcy yaga ansaka. Wayar ta k'atse aka sake kira. Cikin ladabi ya ce, "momcy barka da dare. Daga can ta ce, "barka dai, wai lfy banga kashigoba?, kuma ance mini kadawo. Wlhy babu komai momcy ina d'akine, nagajine shiyyasa kika ga ban shigoba, inaso nayi barcine da wuri, dan gobe d'aurin auren SAFWAN, banaso nak'i zuwa gashi kuma na safene. Okey to shikenan, dama nazata ko bakada lfy ne??. A'a lfyta k'alau momcy na!!. To shikenan saida safe. ALLAH yakaimu my sweet mom!!!!. Saida takashe sannan ya kashe. Number mas'ud yakira, batareda yayi sallamaba ya ce, "waikai malam kana inane??. Gani nanma shigowa gidan mas'ud yafad'a. Kashe wayar yayi batareda ya ce, "komaiba. Mas'ud yaturo k'ofan yashigo da sallama, bai saurari amsaba, dan yasan bazai samuba, saboda mutumin yau cikin fushi yake. Kujera yanema ya zauna, tareda fad'in gani neman mi kake mini??. Nawaff yatashi zaune, yad'an tsurama mas'ud idanu, bayan kamar minti d'aya ya ce, "bro's plz inaso ka taimaka mini??. Mas'ud ya ce, "to wane irin taimako kenan??. NAWAFF yad'an cije leb'ensa na kasa, ya ce, "na nemo yarinyar nan, inaso nasan ita wacece?, 'yar kuma wacece?. Dan wlhy idan banyimata rashin mutunciba zuciyata zata iya fashewa, ALLAH na tsaneta, kuma saina koya mata hankali, daga kaina bazata sake rashin kunyaba, ko kuskurwn marin wani. Mas'ud yay masa kallon tsaf dan ganin yanda yafita hayyacinsa yau d'aya. Yaja numfashi, Nawaff! Yakamata kadawo hayyacinka, karka manta kaifa kafara tsokanar yarinyarnan, kamareta, kayimata dariya. To dankuma yau tarama saikaji haushi, yakamata ku tsaida fad'annan haka tunda kowa yayima kowa, sannan ka janye k'udirinka na d'azu, dakace marin data yimaka shine zai zama fansar budurcinta, Nawaff bansanka da irin wannan halinba, kar ka aikata abinda zaizo ya dami kowa, wannan ba hanyar bullewa bace, kai dama soyayya kuka koma dan wlhy kun dace da juna sosai. Harara Nawaff ya watsama mas'ud, wadda dama tun d'azu ita yake masa bai ganiba. Ya ce, "ALLAH kuwa mas'ud yau dawanine yafad'a mini maganar nan wlhy dasai na bubbugeshi, amma............. yay kwafa kaiwai batareda ya karasaba. Mas'ud yay murmushi ya ce, "amma mi....?, ka karasa fad'a mana, to konima zaka bibbigeni ne?, ka huce haushinka!!,. Tsaki NAWAFF yayi yatashi zaibar falon, mas'ud ya tuntsure da dariya, tareda fad'in sakai a wahala kenan,, duk wanda dai yaga wannan fad'an naku yasan na masoyane­čśť. Har Nawaff yakai k'ofa yadawo ya ce, "kai dallah malam sauraramin!, mixanso a jikin wannan faratun yarinyar mai kama da aljana, kai dana so wannan yarinyar gara naso 'yar k'auye wlhy. Dariya mas'ud yake tuntsurawa harda hawaye, cikin dariya ya ce, "aii kaima faratunne Nawaff, koka manta?, amma mudai 'yan kallone mijin faratu, mas'ud yafad'a cikin tsokana­čśť. NAWAFF ya kula mas'ud yana neman maidashi wani sakaraine, dan haka yashige bedroom yay kwanciyarsa. Dak'yar mas'ud ya lallab'ashi yafito sukaci abinci. WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???????, kubiyoni danjin wannan amsar­čśť. ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL­čśś­čśś­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗7 ......WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???. ALHAJI sa'eed umar modeebbo shine mahaifinsa, babban alak'aline mai gsky da rik'on amana, bashida tsoro Ko kad'an, yakan yanke maka hukunci dai2 da abinda ka aikata, duk kud'inka ko mulkinka bazaisa ka kub'uta ahannunsa ba, sai dai gskyr ka ta kub"utar dakai. Kaifi d'ayane shi, idan ya ce, e, "baya cewa A'a. Alhaji sa'eed bafulatanine irin na daji, dan k'yak'yk'yawane abin so dagani, d'an asalin garin safana ne dake k'aramar hukumar caranchi, safanar ma acikin wani k'yauye suke cikin rugar jauro, amma yanzu yana zaune a kano. Matarsa d'aya hajiya ummul'khairi, balarabiya ce cikakkiya, k'yak'yk'yawar mace, mai hak'uri da ilimin addini, ga son mutane. A Egypt ya aurota lokacin yana d'alibin ilimi a jami'ar AL'AZHAR, soyayya sukayi har ALLAH ya mallaka masa ita amatsayin mata. Momcy Nawaff tafara haifa daga shi ta dad'e bata sakeba, sai bayan shekara bakwai ta haifi Abdallah, sai auta Anwar, Nawaff k'yak'yawane fari amma ba tas ba, ya biyo momcy sosai, dan shikad'aine yake tsananin kama da ita, kana ganinsa kasan itace ta haifesa, sai dai ita tafishi fari. Momcy tanada hak'uri batada hayaniya ko kad'an, amma Nawaff yanada zafi, indai wajen haline papa yabiyo Alhaji sa'eed kenan, Nawaff baya son raini ga son girman tsiya da miskilanci, gakuma ilimi, dan yanada sani wajen addini sosai, shima yanada son mutane. Nawaff yana son k'annensa sosai, duk abinda sukeso yana musu, shiyyasa suma suke sonsa da girmamasa. Nawaff tun yana primary yakeson kwallo har yashiga secondary, lokancin dayake a secondary sukanje gasar kwallo zuwa wasu makarantun, cikin ikon ALLAH sai sun ciyo kuma Nawaff ne mai zira musu kwallon. Bayan ya kammala secondary saboda k'aunarsa da kwallo papa, wato mahaifinsa ya nemi shawarar momcy domin kai Nawaff wata makaranta da ake kira School Academic domin k'ara samun ilimi a fannin kwallon k'afa. Fatan alkairi momcy tayi masa tareda addu'ar samun nasara arayuwa. Babu dad'ewa aka kaisa wannan makaranta ta (School Academic dake jihar kwara) iyaye da 'yan uwa suka bishi da addu'ar samun nasara, aiko ansami nasarar, dan addu'ar iyaye babbar katanga ce. In tak'aicemuku dai, Nawaff bai rufa shekara biyu ba yasamu nasarar shiga jerin wad'anda (NAJERIA's Foodboll Asocion NFF) suka gayyata zuwa abuja dan yin screening nazuwa kwallon kasa da kasa, na 'yan kasa da shekara 17, (under 17 play engle of Najeria ). Awannan screening ansha gwagwar maya, har ALLAH yabawa Nawaff nasarar fitowa d'aya daga cikin wad'anda aka zab'a, harda muk'amin capten na k'ungiyar kwallon kafar Najeria wato ta (under 17). Shigarsa (under 17) ta bashi damar wawuro nasarori da dama, dan sun ciyo kofin duniya na wannan lokaci, yasamu damar zurama Najeriya kwallo 9, wannan yasa yazama (here Gold scores )na wannan gasa, har aka bashi k'yautar, ( Golden but) wannan nasace tajawo hankalin manyan club club na duniya kansa. Samun wannan nasara yasaka family nasa cikin farinciki, yayinda shugaban k'asa na wannan lokacin ya shirya musu liyafar cin abinci tareda shi, da k'yautittikan ban girma. Bayan dawowarsa daga kwallon k'asa da k'asa wani (club na F,C 20)dake k'asar HOLLAND yasami damar d'aukarsa. ya rattab'a hannu✍­čĆ╗ da k'ungiyar na tsawon shekara 5, shigarsa wannan club ya k'ara fito da kwazonsa, yasamu nasarrar buga musu kwallaye masu yawan gsk. Awannan lokacin duniyar masana kwallon k'afa suka saka idanu k'ur akan Nawaff, manyan club club suka fara jawarcinsa. Daga k'arshe wani club mai fad'a aji yasamu nasarar sayen NAWAFF. To ayanzu haka dai girma da cigaba yazo masa, yasamu nasarar tsintar kansa a cikin club d'in (Barcelona F,C )dake k'asar Spain, wannanne ya tabbatar dashi zama babban d'an kwallon k"afa, wanda duniya tasani take kuma alfahari dashi, musamman ma k'asarsa NAJERIA. yanzu haka yazo hutun k'arshen shekarane da sukan samu, kwanansa d'aya dazuwa suka had'u da Yasmeen, har ya takaleta. Wannan shine tarihin NAWAFF SA'EED MODEEBBO atak'aice....................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗8 & 9 .....Mas'ud d'an abokin papa ne Alhaji khasim, tare sukayi karatu da papa a Egypt shima masanine ab'angaren ilimin addini danshi har isalamiyya gareshi. NAWAFF da MAS'UD tare suka tashi tun suna k'anana, bayan sun gama secondary ne kowa yakama inda yafi wayau, Nawaff yatafi makarsantar koyon kwallo, Mas'ud yatafi kasar INDIA domin k'aro ilimi a fannin Likitanci. Yanzu haka shi cikakken Likitane, a babban asibitin Aminu kano, Nawaff bashida wani aboki wanda ya wuce mas'ud, haka shima Mas'ud. Sun shak'u da juna matuk"a suna kuma k'aunar juna, saidai halinsu ya babbanta, domin mas'ud mutumne mai sanyi da hak'uri, amma Nawaff yanada fad'a, kuma baya son hayaniya. Basa shaye2 bare neman mata, hasalima shi Nawaff baya dariya gaban mata, dan ya ce, "yawan yima mace dariya yakan sa ta rainaka. Hummm kunji son girma, naga yannda za'ayi yayi aure tunda baya son mata su rainashi­čśĆ. A'ban garen yasmeen kuwa tunda suka shiga gida take kuka, umma bata tanbayeta abinda yafaruba, saidai tanata lallashinta, yaseer yashigo hannunsa rik'e da leda, yazauna kusada umma yana turo baki. Umma ta ce, "kaikuma lafiya??, ya nuna mata yasmeen data d'ora kanta saman cinyar umma, waishi adole kishi, ya ce, "ALLAH umma wanima saiya d'auka itace auta!. Umma tayi masa da'kuwa tana fad'in kaci gidanku bakaga halin datake ciki bane. Yaseer yad'an le'ka fuskar yasmeen saiyaga hawaye, yad'an zaro­čś│idanu yana fad'i sister miya faru dake??, tad'ago tana kallonsa saikuma ta fashe da kuka, da sauri yadawo kusada ita yana share mata hawaye, ya ce, "haba auntyna yakamata ki daina saka damuwa azuciyarki haka nan, ki manta da komai na rayuwa, idan kuma wannan d'an iskanne yake saka ki kuka kiyi ha'kuri ALLAH zai mana maganinsa, kuma insha ALLAHU abinda yake burin bazai ta'ba kasan cewaba, kullum muna miki addu'oin samun nasara a rayuwa, yafad'a shima yana hawaye. Da sauri yasmeen tatashi ta rungimeshi suka cigaba da kuka, sun bama umma tausayi, dan haka itama ta share nata hawayen, saida sukayi kuka mai isarsu, daga baya sukayi shiru. WAI WACECE YASMEEN????. FATIMA shine cikakken sunanata, malam Yakubu shine mahaifinta, su 'yan asalin kasar Nijar ne, awani gari kwangwalan, kwangwalan yana nan kusada jihar katsina, dan za'a iya cewa a boda suke. Kharima itace mahaifiyarsu wato umma, malam yakubu makiyayi ne a garin kwangwalan mutumne mai tsananin hak'uri, 'yan uwansa basa sonsa, kasancewarsu 'yan ubane, shi kad'ai mahaifiyarsa ta hafa a gidansu. Yaransa biyu Fatima sunan mamansa aka saka mata, shiyyasa suke kiranta da yasmeen, saikuma ABUBAKAR shima dai sunan baban umma ne, shiyyasa suke kiransa da yaseer. Yasmeen da yaseer k'yawawane, dan sunada kala irinta asalin buzaye. Yasmeen tun tana yarinya takeda farin jini, kowa sonta yake, dan haka dangin babanta suka tsaneta laifin babanta ya shafeta. Lokacin da yasmeen takai shekara 12 sai dangi suka matsa akan ayi mata aure, zuwa sannan yasmeen tanada wanda takeso wani sule, tana sonsa sosai shima haka, dan haka lokacin da'akace za'ayimata aure saitayi murna. Amma saidai kash, dangin mahaifinta sunce sun za'ba mata miji, d'an wan babanta wato Tanimu, yasmeen sam bata son Tanimu dan d'an iskane kowa yasani kuma, amma babu yanda zatayi. Aka saka biki wata hud'u, amma amarya bata so, dahaka biki yarage saura sati d'aya. Ana saura kwana hud'u d'aurin aure Tanimu yazo gun yasmeen, abin yabata mamaki dan bai ta'ba zuwa wajentaba tunda aka saka musu rana. Da'kyar umma ta lalla'bata ta fita, ko sallama bata yimasaba bare gaisuwa, yasaki baki yana zuba mata surutan banza, wai idan sunyi aure randa aka kaita zaiyi kaza zaiyi kaza. Yasmeen taji yana d'akko mata zancen daya fi karfin tunaninta, dan haka takama hanyar gida zata tafi, da sauri Tanimu ya dam'ko yasmeen, ya matse abango. Yasmeen tafara ihu dan ganin abubuwan daya ke mata, kafin mutane su kawo mata d'auki ya turmushe ta ak'asa, lokacin da mutane suka zo yana saman yasmeen amma baiyi mata komai ba, sai rigarta daya yaga, nanfa mutane suka shiga jibgarsa dan dama haushinsa akeji. Kafin safiya labari ya baje garin kwangwalan wai Tanimu yayima yasmeen fad'e a daren jiya. Duk gari ya d'auka cewa an lalata yasmeen, dan hakama fita ta gagareta, dan babu wanda zai yarda da ba haka bane, aranar kuma dangin mahaifinta sukace sun warware maganar auren, wai yasmeen 'yar iskace tana neman maza. Abu kullum k'ara gaba yake, harta kai umma da baba basuda ikon fita sai ayita zind'ensu, harda yaseer dabai san komai ba, idan yafita sai ayita tsan gwamarsa, itako yasmeen ma aibatada ikon fita ko k'ofar gida. Ahaka aka kulla wata 7 amma komai bai canja ba, kuma babu mai zuwa wajen yasmeen, sule ma iyayensa sun hanashi. Bak'in ciki da damuwa suka ishi baba, dama akwai wani Alhaji dayake zuwa sayen dabbobi a wajensa, shi d'an Najeria ne a jihar kano. Baba baiyi k'asa aguywa ba wajan sanarma Alhaji halin dasuke ciki,, Alhaji buba ya tausaya musu sosai, dan haka ya ce, "su baba su shirya yatafi dasu Najeria. Babu musu suka yarda, batareda kowa yasaniba suka baro kwangwalan, koda Alhaji buba yakawo su gidansa sai hajiya jummai ta nuna musu tsangwama, ta ce, "saidai baba yarink'a musu gadi dama mai gadinsu yagudu saboda wahala. Baba bai musaba yakar'bi tayinta, baba yana gadi umma tana taya hajiyar wasu 'yan ayyukan gida. Alhaji buba yanada wani yaro mara jin magana, sunansa Fasal, shikad'ai ya haifa dan haka ake nuna masa gata na tsiya, tunda faisal ya 'kayalla idanu yaga Yasmeen ya kafa mata k'ahon zuk'a. Yasmeen bata manta da abinda yafaruba a garinsu dan haka take baya2 da faisal, duk abinda yake faruwa hajiya jummai tana kula, tasan kuma halin d'anta yanzu saiya 'bata yarinyar mutane, dan haka ta tsawatar masa. Alhaji buba yasaka su yasmeen makaranta , ahankali k'yawun yasmeen yafara fitowa, zawa sannan faisal yakai 'kololuwar sha'awar yasmeen, awata ranar lahadine, yad'auki hanyar cimma burinsa, yasaka yasmeen ta gyara masa d'aki, daga haka ya rutseta a d'aki, ihu takwala wanda yasa hajiya jummai isowa da gudu d'akin faisal, saita tarar yana shirin aikata ta'asa, ta daka masa tsawa sanna ta 'ban'bare yasmeen dak'yar. Babu wani mataki da 'aka d'auka, dan ko fad'a basuyima faisal ba, dan haka hankalin umma da baba yatashi, suka fara tsanar zaman gidan, dan indai aka cigaba da tafiya haka wataran faisal saiya lalata musu yarinya. Da alhaji buba yaga hankalinsu yatashi saiya ce, "yana nemawa faisal auren yasmeen idan yadawo daga karatu america za'ayi biki, inko har basu aminceba to zasu barmasa gida, indan suka amince to zai siya musu gidan dazasu zauna ya nemawa baba aikinyi yabar gadi, zaikuma d'auki nauyin karatun yasmeen da faisal harzuwa inda suke buk'ata. Da farko basu aminceba dan sunsan faisal bashida tarbiya, amma dasukaga babu sarki sai ALLAH saisuka amince. Aka saka rana da komai, faisal yatafi america karo karatu, badan yasoba, dan yaso saiya mallaki yasmeen kafin yatafi, bawani so yake mataba sha'awarta kawai yakeyi, daya sami biyan buk'ata zai watsar da banxa­čśö. Bayan komai ya kankama alhaji buba yacika al'kawarin duk daya d'auka yasiyama baba gida madaidaici, yakuma d'auki nauyin karatun su yasmeen, yanzu haka yasmeen tana karatu a (FCE KANO ) yaseer yana shekararsa ta k'arshe a secondary, idan yasmeen zata makaranta ko anguwa kaita akeyi, dan an d'akko mata direba na musamman wato balarabe, duk motar dayaso yake d'aukowa a gidan su faisal yakai yasmeen makaran ta daduk inda take buk'ata. Sutura kuwa mai tsadar gsk su alhaji suke sayama yasmeen, haka kayan kwalliya, hajiya jummai tana k'ok'ari wajen sayama yasmeen, waya mai tsada yasmeen take ri'kewa, wata sa'in agidan take weekend, sunayin waya da faisal, saidai hirar tasa duk takan kasance batsa, abun yana damun yasmeen amma babu yanda zatayi. Yanzu haka saura wata 5 faisal ya kammala karatunsa, yana dawowa kuma za'asha biki, saidai yasmeen da iyayenta duk basa son wannan aure, kullum addu'arsu ALLAH yakawo sanadin da auren zai rushe, wannan shine tarihin yasmeen....................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗10 ......Yau takama d'aurin aure amma yasmeen batada niyyar zuwa, umma tayi mata maga ta ce, "bazata jeba sai anjima. Shima dai Nawaff ya halarci taron d'aurin auren daganan yakama gabansa, dan shi mutumne dabaya son yawan hayaniya, gashi da mutane sun ganshi bazasu bari ya huta ba. 3:30pm Yasmeen kwance a falo tana kallon film, umma tafito daga d'akin abba, ta zauna kusada yasmeen. Yasmeen ta d'ago tana kallonta, umma ta ce, "mamana yau bazaki wajen bikin asma'u d'in ba??, yasmeen ta ce, "gsky umma bazan jeba bana jin dad'i, amma idan naga zuwa anjima naji sauk'i sai naje. To shikenan ALLAH ya sauwak'e. Amin yasmeen tafad'a tana kallon tv, lfyr yasmeen k'alau, batason zuwa wajenne su had'u da Nawaff, tana tsoron karya aikata mugun nufinsa akanta, jadabaya ga rago ­čÉĆkuwa aiba tsoron fad'a bane, inji masu iya magana. Badan ALLAH Nawaff yay shirin zuwa wajen walimar ba, yajene kawai domin yasmeen, amma saidai kash ita batajeba, tunda yaje yake baza idanu, amma komai kama da ita bai ganiba. Duk abinda yake mus'ad yana kallonsa, dukda yasan Nawaff bazai aikata abinda yafad'a akan yasmeen ba, amma yayi matuk'ar farin ciki da bata zo wajenba. Bayan antashi daga walimar su Nawaff sukai saurin guduwa, saboda mutane, amota mas'ud ya ce, "bro's waimi kake nema d'azu kaketa lek'e2. Nawaff yad'an ja hancinsa tareda kwantawa sosai ajikin kujera yana kallon titi, daga bisani yadawo da kallonsa wajen mas'ud dake tuk'i, ya ce, mara kunyar yarinyar nan nake nema, amma ban gantaba, inaga tsoro yahanata zuwa. Mas'ud yay murmushi, hankalinsa na bisa titi, ya ce, "aii masu iya magana suna cewa hanyar lafiya abita da shekara, nikaina naji dad'i dabata zoba. Nawaff ya harari mas'ud, kai malam mikake nufine?? wai ko dai son k'abar nan kakeyi??. Mas'ud yay dariya yana fad'in A'a alhaji maida wuk'ar niba sonta nakeyiba, kada kishi yasa ka b'arar dani. Banza Nawaff yay masa, dan yasan halin Mas'ud sarai yanzu saiyayita jan wannan maganar har momcy taji. Dahaka suka k'arasa gida, kai tsaye b'an garen momcy suka nufa, afalo suka iskesu itada papa da Abdallah. Nawaff yazauna kusada k'afar papa yana kwasar gaisuwa, shima mas'ud ya gaisheshi, suka gaida momcy, Abdallah ya gaishesu. Papa ya ce, " 'yan samari daga ina haka??. Nawaff yad'an sosa sumarsa ya ce, "papa daga wajen bikin Safwan muke. Papa ya ce, "masha ALLAH, ALLAH yasanya alkairi, kuma aii yakamata kufito da matan auren ko??, da sauri Nawaff yad'ago yana fad'in papa aurefa kace??. Papa ya ce, "o, ashe kajini modeebbo!!. Nawaff ya ce, "papa 27year's fa. Momcy ta ce, "toshi wannan dakukaje bikin ba abokinku bane, amma gashi yayi, kudai nakula daga kai har Mas'ud bakwa sonyin aure, ko sokuke saikun tsufa??. Barsu ummul'khairi, aimun yanke magana da Alhaji, nanda k'arshen shekara idan har basu kawo matan aureba, tomu zamu nema musu. Nawaff ya ce, "papa saikace mata. Papa yakama kunnensa, yana fad'in toku zauna kukagani, sadaka zamu badaku. Abdallah ya tunysure da dariya. Nawaff ya harareshi yana mazurai, kai wa kakema dariya??, mas'ud ya ce, "bro's barshi zaizo ya samemune. Momcy tayi dariya A'a karku huce akan d'ana, tunda bashi ya ce, "ayi sadaka dakuba. Papa ya ce, "barshi ai shima hardashi. Abdallah ya zaro idanu, papa nikuma asuwa wai kare da gudun layya, 'yan 27year's basuyiba, bare ni d'an 20years papa kwanan fa nashiga jami'a. Nawaff ya daka masa tsawa, kai dallah kaima mutane shiru, kabi ka ishi mutane da shegen surutu. Abdallah ya zunb'uro baki gaba yana gunguni, amma Nawaff bayajinsa, Dan yasan idan yajisa, hummm. Saida sukaci abinci sanan suka tafi b'an garen Nawaff. Mas'ud ya ce, "kai malam kahuta wlhy karigaya ka kama matarka ahannu, babu rabon ayi sadaka dakai. Nawaff ya ce, "agidan ubanwa nasamu matar, ALLAH mas'ud kaifa d'an iskane. Mas'ud ya tun tsure da dariya, kazauna kallon ruwa wlhy kwad'o yamaka k'afa, kanaji kana gani za'ayi sadaka dakai. Nawaff yaja tsaki tareda kwanciya saman kujera, ya lumshe idanu. Duk surutun da mas'ud yakeyi yana jinsa amma yay kunnen uwar shegu dashi................✍­čĆ╗ ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's ­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗11 ....koda daddare yasmeen k'in zuwa kai amarya tayi, ta langyare akan batada lafiya, ta kashe wayarta kuma dan kar akirata. Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Nawaf yagama hutunsa ya tattara ya tafi kasar Spain domin cigaba da biga kwallo. Har ya taho bai k'ara had'uwa da yaesmeen ba, hasalima yamanta da ita, yacigaba da harkokinsa kamar yanda yasaba. Itakam yasmeen bata manta dashiba, ko makaranta zata takan fita cikin d'ar2, kullum addu'ar ta kada ALLAH ya had'ata da Nawaff ko da amafarki. Dahaka dai aka shere wata uku bataji d'uriyarsa ba, ahan kali tafara sakin jikinta. Yau agajiye tadawo daga school ta shigo falon tana jan k'afa kamar kazarda kwai ya fashewa aciki, yaseer ne kawai afalon yana cin abinci, idanunsa nakan TV ko k'yaftawa bayayi. Yasmeen tadaki kujerar dayake zaune dan taga alama baisan tashigoba, yajuyo da sauri yana kallonta. Yasmeen ta harareshi kaidai ALLAH ya shiryaka, shikenan indai kana kallon kwallo sai a rasa hankalinka gaba d'aya. Yaseer yay dariya, sorry my aunty ALLAH bansan kin shigoba, kinsan yau mutumina yake buga kwallo bana son komai ya katseni wlhy. Yasmeen ta tab'e baki, waye kuma mutuminka??, ata k'aice ya ce, "modeebbo mana, gaban yasmeen yafad'i ras danjin sunan wanda yazame mata baraxana arayuwarta ta yanzu, ta ce, "waye kuma modeebbo??. Idonsa na kan tv ya ce, "kalli tv zan nuna miki shi, shine number 10. Yasmeen taja flet d'in abincin dayakeci gabanta, ta hauci, saidai itama hankalinta yana kan tv d'in, wani uban ihu yaseer yatashi ya kwala tareda fad'in ­čŚúgoooooooooooooo⚽!!!!!!!!!. Yasmeen tai saurin rufe kunnenta danjin zai fashe saboda k'arar da yaseer ya kwala­čÖë, cikin kara ta ce, "dalla malam karka fasamini dodon kunne. Ya zauna yana dariya tareda ­čĹŹ­čĆ╗,yana fad'in sai modeebbo, kana wuta my gay. Sai asannan idanun yasmeen suka kai kan Nawaff tamik'e da sauri tana fad'in yaseer kana nufin wannan gay d'in, ta nuna Nawaf da aka nuno ya durkusa akasa yad'aga hannunsa samma yawani wage baki da alama shima ihun yakeyi dan murna, wasu 'yan kwallo sukazo suka rungumeshi suna ihu. Yaseer ya ce, "shine sistona, tauraro kenan mai haskawa a duniyar kwallo, yanzu su duniya take yayi dason gani, hala kin sanshine kika mik'e zumbur. Yasmeen taja ajiyar zuciya ta ce, "natab'a ganinsa dai, da sauri yaseer ya ce, "dan ALLAH dgsk kikeyi??. Yasmeen ta tab'e baki, ta ce, "kaji yaro natab'a yimaka k'aryane??, awajen bikin Asma'u natab'a ganinsa, dama d'an kwallone??. Yaseer yagyara zama Taf sisto idan kinji ana fad'in mai laya kiyayi mai zamani to modeebbo kenan!!, ai duk ranar dana had'u da bawan ALLAH nan to sainayi sadaka. Yasmeen ta tunysure da dariya, amma kaidai d'an wahalane wlhy, tafad'a tana mik'ewa. Yaseer ya ce, "kedai tafi dan bazaki tab'a ganewaba. Nawaff zaune ad'akinsa akasar Spain, yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya, hannunsa rik'e da remote, yana neman tasha, wayarsa dake gefensa tayi wringing yakai hannu yad'auka. Saida yad'an murmusa sannan ya ce, "Hello my gay ykk? Daga can mas'ud ya ce, "ina lafiya my bro's, naga wasa d'azu yayi k'yau, ammafa kayi k'ok'ari, acinkin minti biyu na farko fa ka jefa mana kwallo a raga, ina alfahari dakai my bro's. Nawaf yay sassanyan murmushi tamkar yana gaban mas'ud, ya ce, "nagode d'an uwana, kana k'ara mini karfin gwuywa a rayuwa. Karka damu bro's, dama Anwar ne ya ce, "nakira masa kai, tun d'azu yake nemanka bai samuba, yanaso yayi maka murnar nasarar dakuka samu. Nawaf ya ce, "ayya my little bro's banishi. Anwar yakarb'a wayan cikin 'yar muryarsa ya ce, "yaya congratulation!!, Tnx my boy, ykk??. Ina lafiya yaya, momcy ma ta kalli wasanka na d'azu. Woow nice, kace ina gaisheta kajiko??. To yaya bye­čľÉ­čĆ╗. Okey bye autan momcy. Mas'ud yakarb'i wayan suka cigaba da tattaunawa, mas'ud ya ce, "to shikenan bari nabarka haka, amma gsky kayi k'ok'ari nanda 2month d'in kazo, indai kanada dama, ko kwana uku kayi ma ya isa. Okey I will try, my bro's Okey ALLAH yakaimu lokacin. Sukayi sallama kowa ya kashe wayar. Nawaf ya kwantar da kansa ajikin kujerar tareda lumshe idanu..................✍­čĆ╗ ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗12 ....Zan iya cemuku biki yanata matsowa, dan shirye2 akeyi na garari agidan Alhaji buba, gidansu faisal kenan, shirin biki suke na d'an gata, dukda shi yana America abinsa, amma duk shirin da'akeyi da saninisa. Yau tunda safe hajiya jumai tasa balarabe yakawo mata yasmeen gida. Tunda balarabe yazo da sak'on kiran yasmeen ta had'e girar sama da k'asa­čśë, harga ALLAH bata son zuwa. Umma ta ce, "wai yasmeen banaji balarabe ya ce, "hajiya na nemankiba??. Yasmeen ta matso ­čśóhawayen datake matsewa tun d'azu, ta shagwab'e murya umma dan ALLAH kibarsu nikam babu inda zanje. Dak'uwa­čľÉ­čĆ╗ umma tayimata, kinci gidanku, hajiya ba mamarki bace ba, za kitashi kije kosaina Ci k'aniyarki, ko kin manta nanda wata d'aya kin zama surukarta. Yasmeen tafashe dakuka, umma yanzu nan har fata kikemini nazama matar d'anta­čśş??. Umma tayi murmushi mai ciwo, wanda ya nuna ainahin damuwarta, ta kamo hannun yasmeen tayi, ta zaunar da'ita gefenta tana shere mata hawaye, kinga mamana bar kuka, ba fata nake miki ba, amma yakama ta kisa a zuciyarki hajiya uwace awajenki, kuma bamusan abinda ALLAH ya shiryaba nan gaba, karki manta da irin hidima da d'awainiyar dasuke damu, komi muka zama a Najeria sune sila. Umma aii badan ALLAH sukayi manaba, sunyine domin d'an iskan d'ansu. Umma ta harareta banace karna sake jiba wai. Jiki asanyaye yasmeen ta tashi, to umma na daina. Bawata kwalliya tayiba kaya kawai ta canja ta k'ara turare ta fito. Umma ta ce, "adawo lafiya d'iyar kwarai. Amin kawai yasmeen ta ce, "dan idan tayi magana mai tsawo kuka zai iya zuwa mata, tasan umma ma tana cikin damuwa, tana dannewane kawai saboda ita. A k'ofar gida suka had'u da yaseer yadawo daga islamiyya, ya ce, "sisto sai ina haka??, ta ce, "anguwa zanje. Shiyyasa bakije islamiyyaba??, malam Dawud yanata nemanki!!. Yasmeen ta zaro idanu da gsk kakeyi yaseer??, ALLAH karkiji wasa, dan aunty Amina ta ce, "ya karb'i hadda yau. Yasmeen ta ce, "naga banu, bari nadawo naje wajen Aminar. To saikin dawo, yaseer yafad'a yana nufar gida. Tunda suka tafi take sharar kwalla, balarabe yana kallonta, harga ALLAH yana tausayama yarinyarnan, duk da bata tab'a fad'a masa damuwarta ba, amma ya fahimci bata son maigidansa, inama yanada hanyar taimaka mata wajen rushewar wannan auren K'ADDARA ko BIYAYYAR (book d'ina danafi k'yauna❤ ), amma zai gwada sa'arsa yagani. Dahaka suka isa gidan, mai gadi ya bud'e musu get, balarabe yasamu guri yay parking. Da sand'a yasmeen tashiga falon tamkar wata muna fuka, tai turus dan ganin samari guda uku zaune suna kallo, ta gaishesu sannan ta shige bedroom d'in Hajiya jummai dan babu inda bata shiga a gidan. Tunda ta tafi suka bita da kallo tamkar goyon mayu, saida tashige suka kalli juna, d'aya ya ce, "kai gays badai wannan beautyn ce sakarannan zai auraba. D'aya ya ce, "mudai tsaya mugani. Suna nan zaune yasmeen ta fito itada hajiya jummai, suka zauna, sai asannan yasmeen talura da kwallo suke kallo, tashiga baza idanu dan son ganin mugun nan ko yananan. Cikin sa'a kuwa aka hasko fuskarsa, yana tsaye zai buga kallon jikinsa sanye da jan JC sunyimasa k'yau, a bayan rigar anrubuta Modeebbo, kasa ansak 10, ya take kwallo da k'afarsa, da'alamadai penerrity zai buga, dan naga kowa tsaye yana kallonsa, yasaki wani murmushi maikama dana mugunta, sanna ya harba kwallon⚽, cikin sa'a tashige cikin ragar, gurin ya kaure da ihu, yayinda sauran 'yan kwallon suka d'agashi sama suna ihu, sumadai samarin saida suka furta ­čŚúgooooooo. D'aya acikin samarin ya ce, "kai gay d'innan lucky nefa wlhy, kaga yacimana kwallon nan. Hajiya ta ce, "umm kullum kudai bakuda aiki sai kallon kwallo da wak'a, ni bari na shige ciki, ga yasmeen d'innan. Yasmeen ga abokan mijinki nan, tare suke karatu a america su sun kammalane shiyyasa, sunzo ku gaisane. Yasmeen ta ce, "to momy. Hajiya jimmai ta shige, sai asannan yasmeen tad'an kallesu, saitaga ai ita suke kallo suma tai k'asa da kai tana fad'in sannunku da zuwa. Suka amsa da yauwa 'yammatanmu ykk?, ya Najeria??. Cikin jin kunya ta ce, "lfy lao kuma ykk, ya turai??. Suka amsa da lfy lao, d'aya ya ce, "sunan izziddin, wannan kuma hisham, wannan kuma hashim, mu abokan angonkine kodayake baki tanbayemu ya yakeba??. Yasmeen tayi murmushi mai ciwo ta ce, "karku damu ai nasan yana lfy, d'ayan data kula yafi kowa surutu iziddin kenan, ya ce, "duk da haka yakamata a tanmbayemu. Cikin kosawa ta ce, "to ya yake??. Sukace yana lfy ya ce, "agaidaki dak'au. Ta ce, "ina amsawa ngd. Nan dai sukayita zuba mata surutu, harda wanda bata tambayesuba, tanaso tatafi dan tagaji, amma bataso suga kamar ta wulak'antasu. Saida suka gaji dan kansu, konace saida suka gama kallon kwallon sannan sukai musu sallama suka tafi. Bayan tafiyarsu yasmeen ta ce, "mom nima bari nawuce magriba tayi. Hajiya ta ce, "aii nazata anan zaki kwana. Yasmeen tad'an sosa gefen wuyanta tana fad'in A'a mom, zanje gida nayi karatu dan gobe inada test a school. Okey to ALLAH ya taimaka d'iyata. Amin yasmeen tafad'a. Babudai wata matsala ko??, hajiya ta tambaya?, yasmeen ta d'aga kai alamr babu, to shikenan ina balaraben yazo ya kwashe miki kayannan dasuka kawo miki. Lah mom to kema d'iba mana. A'a d'iyata ke suka kawo mawa, dan haka jeki da abinki. Har wajen mota hajiya jummai tarakata, dan har zuciyarta tana k'aunar yasmeen, tamafi d'annata sonta. Ana sallar magriba yasmeen tashiga gida, balarabe ya tayata d'aukar kayan suka shiga, sallah tafara k'ok'arinyi dan kar lokacinta ya shige. Abangaren samarin nan kuwa tunda suka fita suke santin k'yawu irin na yasmeen, ixiddin ya ce, "hisham gafa hanya mai sauk'i ta d'aukar fansa, dan maida murtani ga abokin dambe ba laifi bane. Hashim ya ce, "gsk yarka iziddin, hisham yakamata ka rama abinda faisal yayi maka, dan wannan itace dama ta k'arshe dazaka iya samu, karka bari ta k'ub'uce maka. Kuma tabbas idan muka aikata, munyi jihadi, dan na lura yarinyar kamilace, bata dace da d'an iska irin faisal ba. Hisham ya dafa kafad'un abokan nasa, ya ce, "karku damu abokaina, kudai kusaka idanu kusha kallo, amma tabbas gsky kuka fad'a yasmeen kamilallaiyar mace ce, inhar ta airi faisal d'an giya manemin mata tofa tabbas ta cutu. Dan haka ku biyoni domin kallon wasan, kud'auka nine zanyi wining, faisal zai samu game over, yafad'a yana wata dariyar mugunta. Na ce, "tofa ana wata ga wata, to bamusan waye keda nasaraba saimunyi bulayiiiiiiiii........................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗13 .....A yaune aka kawo gagarumin lefen yasmeen, gsky su hajiya jummai sun taka rawar gani, dakaga lefen zakasan anyishine domin d'an gata. Tunda lefen ya iso yasmeen tashige d'aki tana kwasar kuka, dukkan mutan gidan idan ka kallesu zaka gano basa cikin walwala, saidai suna iya bakin k'ok'arinsu wajen yin fara'a koda iya ta hak'orice. Bayan masu kawo lefe sun tafi umma ta shiga d'akin yasmeen dan tasan tana cikin damuwa, cikin bargo ta tarar da ita kuwa tanata rawar sanyi da'alama bata cikin k'oshin lafiya. Cikin hanzari umma ta k'arasa gareta ta yaye bargo, wani irin zafi taji ajikin yasmeen ga rawar sanyi. Ba ab'ata lokaciba wajen kaita asibiti taga likita, da haka aka cigaba da hidimar biki, wanda gidansu faisalne kawai suke farinciki. A yaune kuma faisal ya diro k'asarsa ta haihu, iya yensa sunyi farinciki da ganinsa, babu abinda ya canja arayuwarsa sai lalacewa daya k'ara yi, saidai zamu iyacewa ya k'ara girma da wayewa mara amfani. Bayan ya huta da yamma ya aiki balarabe wai yaje ya d'akko masa yasmeen, lamarin yabama balarabe mamaki, ya za'ayi ace budurwa ce zatazo gidan saurayi???, haka dai yaja mota yatafi yana waswasi. Yaro yasamu ya aika saboda gidan yau akwai mata dayawa, anata hada2r biki. Yasmeen tafito dan taga wake kiranta, daka ganta zaka gano matsananciyar damuwar dake tare da ita. Takarasa wajen balarabe suka gaisa, ta ce, "balarabe wayake nemana. Ya ce, "dama ogane ya ce, "nazo nad'aukeki. kad'aukeni kuma??, to kakaini ina??. Wai na kaiki gidansu yanacan yana jiranki. Wata uwar harara ta sakarma balarabe kamar shine da laifin, ta ce, "kaje kasanar masa na ce, "bazan zoba, tana gama fad'a tashige gida. Balarabe baiga laifintaba dan hakan datayi shine dai2, ta burgeshi wlhy. Amma dayaje saiya cema faisal ya je bata gida, wai sunfita da k'awayenta. Hannu kawai yad'agama balarabe dan gsky yaso yasmeen tazo, wayarsa ya d'auka yakira wata number, ana d'agawa ya ce, "su had'u agidan daya nuna mata d'azu. Tashi yayi ya shirya ya d'auki makullin mota ya fice, kai tsaye gidanshi yanufa inda za'akai yasmeen, babu k'arya gidan ya had'u, anzuba komai amarya kawai ake jira, anan ya tarar da wata kod'ad'iyar mace wadda bilicin yayma k'awanya. ­čśölamarin yayi matuk'ar b'ata mini rai, lallai yasmeen taga takanta, dan nakula faisal bunsurune, inagama yasa ad'akko masa yasmeen d'inne dan ya........hummm shege d'an iska. Tun afalo suka fara k'auce hanya, bak'in cikine yasani nabaro gidan dan bazan iya ganiba. Haka biki yacigaba da gudana, yasmeen dai tak'i yarda faisal ya ganta, yabi duk hanyoyin dazai ganta amma ta rufe masa k'ofa, daga k'arshe abin ya b'ata masa rai ya tattarata ya watsar, dan yasan nanda wani d'an lokaci zata kasance agidansa dole, kuma duk wulak'ancin datake masa saiya rama. NAWAFF a yaune Nawaff ya sauka Najeria saboda kwallo dazasu bugama Najeria, wanda yakasance na Africa, kuma Najeria itace mai masaukin bak'i. Mas'ud da Abdallah da Anwar ne sukaje tarbosa, sunyi farin cikin ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu. Mas'ud ya ce bro's kudai ba'a ganinku saida dalili, turai ta kwace mana kai gaba d'aya. Nawaf yay dariya, su sun isa su kwace ni ahannunku, kawaidai nad'an lokacine, amma ni nakune. Abdallah ya ce, "yaya watanka 6 fa kenan da barin k'asarnan, yanzuma badan zakuyi wasannan ba dabazamu gankaba fa sai hutun k'arshen shekara. Nawaf yay murmushi kawai batarda ya ce komaiba. sunata hirarsu har suka isa gida, momcy ta tarbi Nawaf cikin farinciki, Nawaf ya narke murya cikin shagwab'a ya ce, "momcy nayi missing naku wlhy, ina papa ko yana wajen aiki ne??. Yana can momcy tafad'a, amma nasan yana hanyar dawowa, yakamata kadaina shagwab'a haka nan modeebbo, kagirma fa. Su Anwar suka tuntsure da dariya, ya wurga musu harara, sannan yadawo da kallonsa wajen momcy ya ce, "momcy ni ban wani girmaba. Momcy ta shafa kansa tana dariya, ta ce, "ina mas'ud wai?, Nawaf ya ce, "ya koma asibiti, dan yace yanada aiki sosai. ALLAH sarki Mas'ud sarkin k'ok'ari kenan. momcy tafad'a. Nawaf ya mik'e momcyna barinaje nayi wanka jikina duk yayi tsami, to abincin fa?, mom sainayi wanka sannan, yanzu zan dawo, dan nayi missing d'in girkinki. Momcy tayi dariya to aii yau zakaci kamore. YASMEEN. rana bata k'arya inji masu iya magana, yaudai aka d'aura auren faisal da yasmeen, d'aurin auren yatara manyan mutane masu fad'a aji ak'asarnan, saka makon babansa sanannen mutumne, kuma d'an siyasa. Sai dai abinda yabani mamaki duk d'unbin taron jama'ar nan babu ango awajen. Ana cikin shafa addu'ar k'atshe saiga faisal tamkar mahaukaci dagashi sai wando iya guywa da riga mara hannu, kutsa kai yake kawai cikin jama'a, har ya isa gabn liman, ya tsaya k'erere­čĹ»yana wurga idanunsa dasukayi jajur. Alhaji buba yamik"e da sauri yana tambayar d'an nasa lafiya???. Faisal ya yamutse fuska ta reda fad'in abba and'aura aurennan kuwa??. Alhaji buba ya ce, "emana faisal and'aura yanzu kazama ango.........hannu yad'aga wa mahaifinsa ya ce, "to abba awarwareshi yanzunnan. ­čś│Alhaji buba yazaro idanu faisal kamarya a warware??, cikin k'araji faisal ya ce, "kamar yanda aka d'aura narantse da sarkin dake busamin numfashi bazan zauna da karuwaba, dan haka sai an warware shi. Gaba d'aya gurin yayi tsit ana kallon sarautar ubangiji. ­čÄĄabin maganar dake hannun liman faisal ya kwace, yajuya yana kallon mutane, ya ce, "kamar yanda kuka shaida and'aura auren faisal da yasmeen, to haka nakeso ku shaida faisal ya saki yasmeen saki uku!!!!!!!!!!!!!!!!!. Gaba d'aya wajen akad'au "INNALILAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN....................✍­čĆ╗ Hummm nikaina dabana son wanga aure, saida na girgiza domin jin furicin faisal!!!. ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ× LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗14 .....Cikin b'acin rai Alhaji buba ya wankama faisal mari, faisal yadafe kumatu yana kallon baban nasa, mahaifin yasmeen kuwa fad'uwa yayi, dukda baya son auren abin yay masa matuk'ar ciwo. Gurin ya rud'e da surutai, kowa yana fad'ar albarkacin bakinsa, zuwa sannan an yayyafama abban yasmeen ruwa ya farfad'o, ya fashe da kuka yana fad'in yanzunan irin cin mutuncin daza ayimin kenan saboda anganni talaka, banida komai bani da kowa. Wani dattijo naga ya mik'e tareda dafa Abban yasmeen, ya ce, "kanada kowa malam, kuma ka kwantar da hankalinka, indai ka amince zan d'aurama d'ana aure da d'iyarka yanzunnan. Abba yabi dattijon da kallo, gsky ne dattijon mutumne mai kamala da dattako, yatabbata bazayayi dana sani da tayinsaba. Liman ya ce, "malam ka amince na tabbata bazaka tab'a dana sanin hakanba, Alhaji sa'eed mutumin kirkine, yakuma bama d'ansa cikkiyar tarbiya. Abban yasmeen ya ce, "shikenan nabashi!!, ALLAH yasa haka yafi alkairi. Liman da dattijo suka amsa da amin. Har mutane sun fara tafiya akayi sanarwa adawo za'a sake d'aura aure, mutane kam sun amsa kira, dandanan gurin yay tsit aka nutsu ana jiran mizaije yadawo. Nantake dattijo ya ajiye sadaki dubu hamsin, nakasa kunne naji dawa aka d"aura amma hayaniyar mata dake cikin gida yahanani, dole na hak'ura. Bayan angama d'aurin aure komai ya natsa, zuwa sannan labari yashiga cikin gida, dafarko umma taji bak'inciki, amma da'aka sanar da ita k'arshen al'amarin saitaji farinciki mara musali, nutsuwa da annashuwa suka bayyana saman fuskarta. Ammafa nakasa gano muku amarya bare nasan halin datake ciki. GIDANSU NAWAFF. papa yashiga gidan fuskarsa cikeda fara'a, momcy ta taryeshi, bayan yasha ruwa ta ce, "Alhaji lfy dai naganka cikin farinciki haka??. Papa yay murmushi har wushiryarsa ta bayyana, ya ce, "ummul'khairi ina cikin farinciki yau, kuma kema idan kikaji nasan zaki tayani farin ciki, kamar yanda nagaya miki zanje d'aurin aure to daga can nake, bud'e kunnanki kisha labari. Momcy tayi dariya tareda fad'in ina sauraraenka Alhaji. Papa yagyara zama tareda zayyane mata abinda yafaru, yad'ora da fad'in wlhy mutumin yabani tausayi, dan idan nine akayima haka, to idan na suma bazan far fad'oba. Dan haka atake agurin nabiya sadaki aka maida d'aurin auren akan MODEEBBO!!!!. momcy tad'an zaro idanu, Alhaji modeebbofa kace??, papa ya gimtse fuska ya ce, "ashe kin jini!!. Ta ce, "amma kana ganin baza'a samu matsala a wajen modeebbo ba??, papa ya kwantar da kansa ajikin kujera, ya ce, "aii bana fata na haifi d'an dazai bijirema umarnina, ko mas'ud nace na d'aurama aurennan dole ya amince bare NAWAF. momcy ta ce, "kayi hak'uri Alhaji bahaka nake nufiba wlhy, ina farin ciki da umarninka, ALLAH kuma yasanya alkairi, wlhy tun kafin naga yarinyar ma tashiga raina, kuma ina k'aunarta tamkar yanda nakeson su modeebbo. Papa yay murmushi yana tashi zaune, yakama hannun momcy yana murzawa, ngd ummul'khairi, ngd da had'in kan dakika bani, inaso ki taimaka mini wajen fahimtar da modeebbo. Momcy ta zare hannunta daga nashi tana fad'in Alhaji kar yarannan su shigo su gammu. Murmushi papa yayi batareda ya ce, "komaiba, waya ya d'auka yana kiran Nawaf!. Nawaf yana kwance ad'akinsa yanaso yay barci, dan yau zaitafi abuja da yamma, ya mik'a hannunsa yana laluben wayarsa datake wringing, da sauri yamik'e zaune dan ganin papane yake kiransa. Cikin ladabi ya ce, "papa barka da rana, barka kadai papa yafad'a, ya ce, "kana inane??, cikin ladabi ya ce, "ina d'akina papa!. To kazo kasameni. To Nawaf yafad'a tareda mik'ewa yafito domin amsa kiran papa. Afalon momcy ya tarar dashi, ya rissina ya gaishesu, suka amsa, papa ya ce, "Modeebbo miye matsayina a wajenka?. Cikin matuk'ar mamaki Nawaf yad'ago yana kallon mahaifan nasa, ya daure ya ce, "papa kai mahaifinane, wanda banida kamarsa aduk fad'in duniya. Papa ya jin jina kai, tareda cewa masha ALLAH, to modeebbo amatsayina na mahaifinka na zartar da umarni akanka yanzunnan, nan papa ya labratawa Nawaf duk abinda ya faru. Atsorace Nawaf yake kallon papa yayinda zufa keta ambaliya adukkan sassan jikinsa, ya daure cikin rawar murya ya ce, "papa aurefa kace??. Papa ya ce, "kwarai aure nace modeebbo, kuma ina fata amatsayina na mahaifinka zaka yimini biyaya, zaka kuma karb'i k'yautar da ubangiji yay maka da hannu biyu, natsuwarka nake buk'ata da farin cikinka, bana son wannan lamarin yatab'a rayuwarka bare kasamu matsala akan abinda kazoyi Najeria. Nandai sukaita lallashinsa, dayi masa wa'azi mai shiga jiki. Jiki a sanyaye Nawaf ya tashi yanufi d'akinsa, koda yashiga d'aki saiya zube afalo yana zabga zufa yadafe kai yana jujjuyashi, gsky yabani tausayi matuk'a. Ahaka mas'ud yazo yasameshi, arikice yake tambayarsa lafiaya, amma Nawaf yakasa magana, da hannu yaymasa nuni daya basa ruwa, ruwa mas'ud yabashi, tunda yakafa kai saida ya shanyeshi tas. Mas'ud dai kallonsa yakeyi cikin matuk'ar mamaki, saida suka d'uki tsawon minti goma ahaka, sannan Nawaf ya daure yabama mas'ud labarin abinda yafaru, mas'ud yay murmushi cikin tsokana ya ce, "haba mutumina kace kai yau angone, shiyyasa naji kana k'amshin angwanci. Harara Nawaff ya watsa masa tareda jan k'aramin tsaki. Mas'ud yay dariya ya ce, "ALLAH yasanya alkairi bro's, amma ka kwantar da hankalinka iyayenmu bazasuyi abinda zai cutar damuba, nima bari nazo nafara neman aure kafin ayi sadaka dani!, tunda anfara ta kanka. Duka Nawaf yakaima mas'ud, mas'ud ya kauce yana dariya. Nan yayta tsokanarsa har Nawaf yad'an saki jikinsa. AMARYA YASMEEN zuwa yanzu labari yaje kunnan yasmeen, tayi farin ciki da faruwar hakan, saidai tana fargaba kuma da sabon mijin nata wanda batasan koshi waye ba, wannan dalilinne yasakata kuka, wai ba'a rabu da bukarba an haifi habu, karin maganar ta hausawa. Umma da abba sunata lallashinta da mata nasiha. Amma gaba d'aya jikinta ya d'ume da zazzab'i mai zafi, dan danan tafar rawar sanyi, har hak'oranta suna had'uwa waje d'aya. Asibiti aka tafi da'ita cikin hanzari. FAISAL. A gidansu faisal kuwa tunda labari yaje kunnan hajiya jummai ta yanke jiki tafad'i, saida aka yayyafa mata ruwa ta kawo numfashi, da kuka ta farka, lallai d'anta yayi ganganci, ya kumayi asara wadda tanada tabbacin bazai samu madadintaba. Sukansu danginta dana Alhaji buba sai masifa sukeyi, suna fad'in aii laifinsune dan sune suka sangarta faisal d'in, shiyyasa baya ganin kowa da daraja a cikin family d'in. Faisal kam ko ajikinsa, dan aganinsa hakan shine dai2, amma daga lokacin daya ci karo da sak'on wata takarda sai komai ya canja, ya daddage ya tsala ihu yana kiran yashiga uku!!. Dafarko babu wanda ya kulashi, amma da akaga ihun nasa bana k'arewa bane sai aka fara kawo masa agaji, wani k'anin Alhaji buba ne yad'auki takardar yana karantawa, shikansa arazane yake duba takardar. Dangi suka shiga tambayar lafiya??. Ya ce, "inafa lafiya, lallai faisal kayima kanka, maganin mutumin dabaya bincike bare ganin girman manya a harkokinsa, kuma ka d'auka abinda ka shuka shine kake girba. Sakina k'anwar hajiya jummai ta kwace takardar tafara karan tawa kowa yanaji. Assalamu alaika babban yaro!! lallai kacika dak'ik'i mara tunani, kodayake ALLAH ne ya kwaci yarinyar kirki daga hannun fasik'i, wanda bai d'auki sab'on ALLAH komaiba. Na taya yasmeen murnar barin hannunka. Faisal ban rama kashi goma daga cikin abinda ka aikata minba, ­čśşkaine kayi sanadin lalacewar 'yar uwata, ka lalata mata rayuwa ka koya mata fasik'anci, ALLAH ya isa tsakanina dakai faisal. Kuma yasmeen ba karuwa bace, ita tsarkakrkiyace, kamilar mace, dama kun tursasatane itada mahaifanta akan ta aureka. To yanzu ALLAH ya bata miji nagari, mai k'yawawan halaye, d'an babban gida. Amma naso ace nine na auri yasmeen, kodan zuciyarka tabuga, sakari shasha. Sako daga abokinka mai sonka da k'aunarka HISHAM AHMAD KT! !!!!!!!!!!!. Talek'o ta koma­čść­čść­čśť­čśť. Gaba d'aya dangi suka d'auki sallalami, tareda ALLAH wadai da halin faisal. Wasuma ALLAH yakara suke cewa. Faisal kam sulalewa yayi a k'asa saboda bak'in ciki, dahanzari suka yayeshi zuwa asibiti.................✍­čĆ╗ Lallaikam yau anayin rikita2 a Najeria­čśť ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× ©2016 [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗15 ....A asibiti kam al'amura sun dai2ta a b'angaren yasmeen, ansaka mata k'arin ruwa tanata barcinta. Sai yamma lik'is ta farka, dak'ar tasha tee aka bata magunguna, takai dubanta ga Abba dake tsaye jingine da bango, saitaga har yad'an rame, ya ce, "mamana sannu kinji!. Kai ta d'aga tana hawaye, umma tashiga sharemata hawayen tana rarrashi, yaseer yazo yazauna kusada ita, shikanshi duk yayi wani iri, cikin sanyin murya ya ce, "kiyi hak'uri aunty kibar kuka, na tabbata hakan alkairine agaremu, tunda ALLAH ya ku'btar dake daga hannun wannan d'an iskan!. Yasmeen ta share hawaye, ta ce, "yaseer gskyarka, na! kub'ta daga hannun faisal, saidai bansan hannun wa? kuma na fad'aba, ta'kare maganar cikin kuka mai tsuma zuciya. Abba yakaraso ya zauna d'ayan gefenta, hannunta yakamo yarik'e, yay d'an murmushin dauriya, karki damu mamana insha ALLAHU mijinki na yanzu mutumin kirkine, kuma nasan zakiyi alfahari dashi watarana. Duk da nima banganshiba, amma yanayin mahaifinsa da kamalarsa yanuna d'an nasama mutumin kirkine, kiyiwa mijinki 'kya'ky'kyawan zato kinji!!. Yasmeen tad'aga kai tana share hawaye, ahaka likita yashigo ya samesu, ya k'ara duba jikinta, yaga komai normal, babu 'bata lokaci ya sallameta, suka tattara suka nufi guda. Wannan kenan. A'bangaren Nawaf kuwa yana cikin damuwa shima, shikam dayasan abinda zai tarar kenan a Najeria dabazaiyi fatan zuwaba, yafitar da huci mai zafin gaske daga bakinsa tareda cije le'bensa na kasa. Talatu taiyi sallam a 'kofar d'aki, banza yay mata bai amsaba bare yabata ixinin shigowa, takai minti biyar atsaye, jin ba'a amsataba yasa tadannakai cikin d'akin atunaninta baya nan. Saida gabanta yafad'i yayin datayi tozali dashi azaune, jikinta yana 'bari ta ajiye abinda takawo masa, ta rissina tana gaisheshi!. Maimakon ya amsa mata saiyaja tsaki tareda watsa mata harara, dasauri tatashi tafito tana rawar jiki. Kafa yasa ya ture kular, ALLAH yasama abincin bai zubeba, wayarsa tafara neman agaji, kallo d'aya yaymata ya d'auke kai, takatse aka sake kira, nanma yay burus, shikuwa maikiran sarkin naci saiya cigaba da kira. A'kufule Nawaf yad'auki wayar , amma yayi shiru ya'kiyin magana. Daga can akace modeebbo wai sai yaushe zaka shigo?, karka manta munyi dakai! zakataho yau da 'karfe 4, amma gashi har 5 tayi. Nawaf yaja siririn tsaki, ya ce, "saika bari kaga gari ya waye banzoba sannan kayimin 'korafi. Daga can akace to shikenan, amma yakamata kayi 'ko'kari kasandai kanada matu'kar muhimmanci a wasannan!!. Banza Nawaf yay masa, saima ya kashe wayar gabad'aya, yana bala'i, kabi ka isheni da surutun tsiya, bakusan abinda yadamu mutumba zaka wani dameni da kira, ku damuwarku kawai kuka sani, yaja tsaki tareda kwanciya ya lumshe idanu. Ahaka mas'ud yashigo ya sameshi, yad'an girgiza kai ta reda ta'ba Nawaf. Ahankali ya bud'e idanu yana kallon mas'ud. Mas'ud ya ce, "haba bro's yanaga baka shiryaba ne, kasanfa ka makara ma. Nawaf ya yatsine fuska yana yima mas'ud kallon gefe, har ya bud'e baki zaiyi magana saikuma yayi shiru. Azuciyar mas'ud ya ce, "yau kuma miskilancin ya motsa kenan?, ganin Nawaf ba amsa zai bashiba yasa yanufi bedroom d'insa, kaya ya had'├áma Nawaf tsaf sannan ya fito. Kan hannun kujerar da Nawaf yake kwance yazauna, cikin sigar lallashi ya ce, "kayi ha'kuri my bro's, ka d'auki hakan amtsayi 'kaddararka, kasan kanada matu'kar muhimmanci a wajen wasannan. Inaso kacire duk wata damuwa ka ajiyeta gefe, ka kar'bi 'kautar da ALLAH yabaka, aure alkairine, kuma nasan wataran zakayi alfahari dashi, idan papa yaga kana cikin damuwa zai d'auka bakabi umarninsaba, ka daure ka kauda komai kaji!!. Nawaf ya d'ago manyan idanunsa dasukayi jajir ya ce, "mas'ud ina cikin damuwa wlhy, karka manta aurefa papa ya d'auramini batareda nasan yarinyarba, bansan halintaba batasan nawaba, bata sanniba. yo wai tayayama zamu kasance amatsayin ma aurata?, kokad'an banida niyyar yin aure yanzu kaima kasani, amma papa ya kama 'ka'kaba mini, wlhy idan zaka kasheni bansan yanda zan zauna da macebama ni!!. Murmushi mas'ud yayi, kaga d'an uwa kwantar da hankalinka, indai yanda zaka zauna da itane damuwarka to zan koya maka, yafad'a cikin tsokana. Harara Nawaf yasakar masa, aii kaga matsalarka kai bakomai kake d'uka serious ba. Mas'ud yay dariya kaiwai batareda ya ce, "komaiba. Nawaf ya mi'ke yanufi bedroom d'insa, bayi ya shiga yasakarma kansa tsawa­čÜ┐, (nakula indai yana cikin damuwa yanaso yasakarma kansa ruwa­čÜ┐, komiye sirrin hakan??. ) yakai tsawon minti goma ahaka, daga baya yay wankan sosai yafito. Yaudai ba'ayi wani gayuba sosai, danko sumarsa mai gyaraba yafito, amma yayi 'kyau ba laifi. Mas'ud dake zaune yana cin abinci ya ce, "yauwa kokaifa, yanzu sauranka abinci, kaci saimu wuce. Yatsine fuska yayi tamkar wata mace, ya ce, "babu wani abinci dazanci malam, dan konaci bazaiyi amfani ajikina ba. Mas'ud ya ce, dadai kadaure kaci. Hanyar waje yanufa yana fad'in kasameni a wajensu momcy. Mas'ud yay murmushi, wataran yakan rasa Nawaf wane irin mutumne?, yasan duk duniya babu wanda yakaisa sanin halin Nawaf bayan iya yensa, amma shi kansa wata sa'in lamarinsa yana d'aure masa kai, mutimne miskili, masifaffe, saidai bayason yawan hayaniya, ba kowa yake ganin dariyarsaba, bakuma harkar kowa yake shigaba, wannan yasa wasu suke masa kallon mutum mai wula'kanci kuma ba haka bane. Saika zauna dashi zakaga yanada su'kin kai da son mutane. Nawaf yana zaune gaban papa sunata yimasa nasiha shida momcy. Papa ya ce, "yau dadaddare zamuje nida Alhaji khasim gidansu matar taka, abinda shawara tabayar zakaji a waya, saimuji lokacin daya dace ayi biki, kaima yakamata ace kaje kafin kawuce. Nawaf yad'ago da sauri, ya ce, "papa ayimin afuwa saina dawo, wlhy na makara sosai saikirana koc d'in yakeyi tun d'azu, amma nayi al'kawari idan nadawo zanje. To shikenan papa yafad'a, ALLAH yabaku nasara, amma zan kar'bi number ta na turo maka, dan kakirata ku gaisa. To kawai Nawaf yafad'a. Sun masa nasiha sosai, sannan suka tafi shida Mas'ud da Abdallah da Anwar, dan suma zasuje su kalli wasa. Tunda suka tafi Nawaf ya jingina da kujera ya lumshe idanu, shi kad'ai yasan damuwar dayake ciki. Mas'ud dasu Anwar ne kawai suketa hirarsu. A kaduna suka tsaya sukayi sallar magriba da isha'i, dan gudu sosai mas'ud yakeyi ahanya. Karfe 8:30pm suka isa cikin birnin abuja, mas'ud ya ce, "bari mufara kaika sanna mu nemi masauki ko??. Nawaf ya ce, "A'a kumuje ku fara neman masukin sannan. Hotel suka nufa, suka kama d'aki biyu, Abdallah da Anwar d'aya, mas'ud d'aya, bayan sun kammala komai suka d'auki Nawaf zuwa (trening cam)masukin 'yan wasa. Tunda suka shigo get d'in ake d'aga musu hannu, sauran 'yan wasa sukazo suka tarbesa sunamai farincikin ganinsa, shima dai dole ya daure ya kauda damuwarsa zuwa gefe yana amsa musu gaisuwarsu. Bayan komai yalafa su mas'ud suka nufi masaukinsu, sukabar Nawaf cikin takwarorinsa 'yan wasa. FAISAL faisal kam yanacan likitoci sun rufu akansa, hajiya jummai sai kuka takeyi, bata son tilon d'anta ya ku'bce mata, shikad'ai ta mallaka a duniya batada kamarsa. Alhaji buba kuwa sai safa da marwa yakeyi, yakasa zune yakasa tsaye. Haka dangi sunyi jugum jugum, taron biki yazama taron jimami, dayanzu anacan ana cashewa, amma ango yaja musu zaman tagumi a asibiti. To shimadai likitoci sunyi nasarar farfad'o dashi, amma anhana kowa shiga wajensa, dan ba'aso ayi masa hayaniya..................✍­čĆ╗ ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× ©2016 [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗16 .....da daddare su papa suka isa gidansu yasmeen, tarba akayimusu ta mutinci, har cikin falon abba aka kaisu, aka kawo musu ruwa da abinda ya sauwa'ka, bayan an gama gaishe2 suka shiga tattauna abinda ya kawosu. Alhaji khasim ya ce, "munzone muyi muku godiya da 'kyautar dakuka bamu batarda kunsan ko su waye muba, ALLAH ya d'orar da wannan zuminci yakuma basu zaman lafiya. Abba ya ce, "ai mune da gidiya, domin kun kauda mana wata damuwa dataso ruguzamu alokaci d"aya, mungode ALLAH ya'kara dan'kon zumunci. Gaba d'aya aka amsa da amin. Anan abba yabadua cikakken tarinsa, bai 'boye musu komaiba, har baro garin kwangwalan dasukayi. Suma sun bashi nasu tarihin batareda sun 'boye komaiba. Daganan suka tattauna akan biki sainan da 'karshen shekara zuwa sannan yasmeen takammala NCE d'inta. Abba yaje yakira yasmeen da yaseer sukazo suka gaisheda su, abba ya ce, "ga d'iyar takunan, papa ya ce, "d'iyata zonan kusadani!, akunyace yasmeen taje kusada 'kafafunsa ta tsugunna. Papa ya ce, "masha ALLAHU, ALLAH yaymuku albarka kinji, yasaukar da alkairi akan wannan had'in namu. Suka ce, "amin. Nanadai akayi mata nasihohi, akan takula dakanta, tasan yanzu ita matar aurece akwai banbaci tsakanin da, da yanzu. Papa ya kar'bi number d'inta, yabata ta Nawaf da tashi da momcy da mas'ud da Abdallah da Anwar, yay mata bayani akan matsayinsu, ya ce, "kuma ta saurari kiran kowannanensu. Sukai mata alkairi sannan suka tafi, suna mai yabon zuri'ar yasmeen. Lallai sun yaba da tarbiyyar muta nen gidan. Tunda suka tafi yasmeen tayi shiru tana tunani, indai yanda iyayen mijin nata suke haka mijin yake lalai ta more, dan taga dattako da kamala a tattare da iyayensa. To hakama abba da umma sunyi farinciki da samun suriki nagari. Yaseer ya ce, "gsky aunty kin more, ALLAH yasa haka mijinki yake 'kya'ky'kawa kamar abbansa. Yasmeen ta harareshi, kaifa nakula bakada kai wlhy, ni tashi kabani guri kazo ka cikani da surutu. Yaseer yay dariya, sisto plz ki kirashi mana tunda naga an baki number d'insa. Caja d'in wayarta ta d'akko tana fad'in kasan ALLAH idan baka tashiba zan zula maka ajiki. Yaseer yatashi yana fad'in A'a wlhy bara natashi, idan kika zulamin wanga caja ai sainayi jinya. FAISAL Alhmdllh jikin faisal yana sau'ki, saidai uban sambatu dayake zubama mutane, babu abinda yake kira sai sunan yasmeen, shi sai yanzuma yasan yana sonta, yawan surutun dayakeyine yasa ake masa allurar barci. Da mutum yazo dubashi zaifara ro'konsa ya kawo masa yasmeen, dan ALLAH karsu bari ya rasata, wlhy yana sonta, dan ALLAH aje asaka wanda ya auri yasmeen ya sakar masa ita, shikad'aine ya dace ya zauna daita. Hajiya jummai ta matse hawaye tana fad'in Faisal ina saura, kayima kanka aii, nasan babu wani namiji dazai auri yarinya kamar yasmeen ya saketa, duk abinda namiji yake bu'kata awajen mace yasmeen ta had'asu, Tarbiya, ilimi, addini, nasaba, 'kyau. Duk ta had'a. Danhaka ka d'auki 'kaddara kawai Faisal. Faisal ya 'kan'kame Hajiya jummai yana kuka, da sakin sambatun daya saba. Dole likita yazo yay masa allurar barci, sanna. Azuciyata na ce, "aii dama duk wanda ya taka rawar­čĺâwani, yarasa filin taka tasa. ABUJA. 6/7/2012 8:30PM Abuja international stadium cike take da'kam da matasa maza da mata, kai harda yara da dattijai na 'kasashe daban2, dake Nahiyar Africa, harma da 'kasashen turai, domin kallon (Netion cup ). Yau Najeria da ghana zasu buga, babu abinda kakeji sai hayaniya irinta al'adar kwallo. Su Nawaf suka shigo cikin fili suna d'agama jama'a hannu, yayinda suma jama'ar suke d'agamusu hannu saboda 'kauna ko birgesu da 'yan wasan sukeyi. Bayan addu'a da taken Najeria da 'yan wasa suka gabatar, suma 'yan wasan ghan sunyi nasu. Sai aka fara 'ko'karin fara wasa, wasa kowannen su yakeyi cikin 'kwarewa. Can na hango Nawaf sanye da JC mai ruwan tutar Najeria, sunyimasa 'kyau matu'ka, saidai fuskarsa babu walwala, dan buga kwallon yake kamar bayaso⚽­čÜ­čĆ╝. Gab daza'a tafi hutun rabin lokaci ghana tasmu nasarar zira kwallo 1, nanfa mutanen ghana suka hau ihu da sowa. And'an fara wasa aka hura, domin tafiya hutun rabin lokaci, saidai 'yan Najeria sun d'an fara shiga damuwa. Dan haka koc d'in Najeria yaja Nawaf gefe, yana tambayarsa ko bashida lfy ne??. Nawaf ya ce, "lfyr sa 'kalao. Nan dai koc yashiga ro'konsu akan su dage, karyazama tun a kolfayin(colfine) su nuna gazawarsu. Bayan andawo hutun rabin lokaci, aka d'ora wasa, nanma dai ghana sunfi nuna 'kwazo akan Najeria. Kad'an ya hana Ghana cin kwallo ta biyu. To daga nanne fa Nawaf ya dage, minti 15 da dawowarsu ya zira kwallo a raga, karkaso kaga murna wajen 'yan Najeria. Zan iya cemuku harda Yaseer da yasmeen amasu murna, dukda basosai yasmeen take kallon wasanba, amma dayake suna tare afalo itada yaseer sai take d'an kallo. Ammafa har yanzu batasan Nawaf shine mijin nataba. Abba yafito yana fad'an ihun da yaseer ya kwala musu. Yaseer ya ce, "abba kayi ha'kuri wlhy modeebbo ne yaci mana kwallo. Abba ya ce, "to basai ayi murnar ahankaliba, amma irin wannan ihu haka. ⚽kwallo taci gaba da tafiya yanda ya kamata, dan yanzu Najeria sun dage, suma ghana sun dage, dan haka wasan ya d'auki zafi kowa yana so yazira kwallo tabiyu. Saura minti 4 atashi Najeria takuma zura kwallo da taimakon Nawaf wani d'an kwallon Najeria ya zura, woyyo ALLAH karkuso kuga murna, koda yake kuma masu karatu na hangoku kuna murna. Daganan najeria tafara jan 'kafa domin acinye lokacin abanza, aka 'kara minti7, shima dai ashiririta aka cinyeshi, Najeria sai fitar da kwallo suke, suna langyare, harda tsayawa akayi canjin 'yan wasa. Ahaka dai aka tashi 2-1 Najeria-2 & ghana-1 Wasa yayi 'kyau Najeria sai murna sukeyi. Yaseer ya ce, "sisto dan ALLAH yakiga gay d'innan, jiba kiga yanda yake gara kwallo cikin kwarewa. Yasmeen tad'an ta'be baki, kaini wannan mugun baya wani birgeni, kai yake burgewa. Yaseer ya ce, "sisto muguntar mi yay miki??. Sai asannan ta tuna yaseer bai san komai daya faru tsaka ninta da Nawaf bafa. Ta ce, "sai yayimin wani abu zan kirashi mugu, kaga saida safe ni nagaji. Yaseer ya murgud'a mata baki ya mi'ke shima ya shige d'akinsa.................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗17 ......Yasmeen zaune ta rabga uban tagumi, gaba d'aya tayi kewar school, tanaso takoma makaranta amma batasan yanda zata fiskanci abba da zancrnba, ta fesar da huci mai zafi tareda dafe kanta datakeji yana sara mata. Waya tajawo ta kira yaseer, kana ina?, naji tafad'a, bansan miya cemataba daga can nagadai ta ajiye wayar kawai. Babu dad'ewa yaseer yashigo da sallama, ta amsa batareda ta tashi daga kwanciyar datayiba, ya zauna abakin gadon yana fad'in gani auntyna!. Yasmeen ta ce, "yaseer shawara nakeso miyi. To wace irin shwara kenan?, yaseer sonake na koma makaranta amma ina tsoron tambayar abba!, ya kake gani za'a ayine??. Shiru yaseer yayi yana ­čĄönazarin mafita, zuwa can ya ce, "ai inaga kibari kawai nafara yimasa magana saimuji amsar dazai bayar koya kika gani?. Eh yayi kakawo shawara mai 'kyau d'an uwa, yasmeen ta juya tana kallon wayarta datake wringing saidai batasan number d'in ba. Jiki a sanyaye ta d'auka saidai tayi shiru. Daga can akace salamu aliki!. Wa'alaikassalam yasmeen ta amasa. Amaryarmu ykk??, ta ce, "lfy lao, ta d'ora da fad'in dan ALLAH wanene??. Mas'ud yay sasanyar dariya, ya ce, "sunana mas'ud khasim, d'an uwan mijinki kuma abokinsa. ta ce, "ALLAH sarki, sannu!. Ya ce, "yauwa kema sannunki amarya, dama zan fad'a mikine ki saurari zuwanmu yau da yamma. Muryar yasmeen na rawa ta ce, "saina ganku. Ya ce, "to nagode, sai anjima. Yaseer daya tsura mata idanu tun d'azu ya ce, "sisto keda wa??, ta had'iye wani yawu sannan ta ce, "wanine wai mas'ud!. Mas'ud kuma?, yaseer ya maimaita sunan, ya ce, "sisto kodai abokin mijinki da aka baki number shi jiya. Yasmeen ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba. Murmushi yaseer yasaki, ya ce, "tomiya farune?? Ko zasuzone??, nanama kai ta kad'a masa alamar eh. Yaseer yami'ke yana fad'in bari nasanarma umma to. Da sauri yasmeen ta ce, "malam ban saka kaba, ko saurarenta bayyiba ya fice, yanaji tana kwala masa kira amma yay mata banza. 'Dakin umma yanufa, tana zaune tana linke kaya, ya zauna kusada ita. Umma ta ce, "autana lafiya dai ko??, yaseer yay murmushi yana fad'in lafiya lao umma, dama aunty ce zatayi ba'ki shine na ce, "bari nasanar miki, dan kinsan itadai ba fad'a zatayiba. Umma ta ce, "gsky ne d'an albarka, amma wad'anne irin ba'kine??, mijinta ne zaizo. Umma tayi murmushi ta ce, "madallah, ALLAH yakawoshi lafiya, sai azo ashirya musu kayan tarba kenan. Abuja (Trening cam). Nawaf zaune bisa kujera agefen fili, yana zaune yana hutawa bayan sun gama trening shida sauran 'yan wasa, zaune yake amma ya kwantar da bayansa a jikin kujerar, hannunsa ri'ke da waya, da'alama yana chatting ne, dan naga saifaman murmushi yakeyi. ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake wringing, cikin murmushi ya ce, "shegen sama sai yanzu katuna dani. Mas'ud ya ce, "A'a dama kana raina, banaso na takura makane ko kana uzuri. Ayya Nawaf yafad'a, kunje gida lafiya??, lafiya lao mukazo wlhy. Zaka shigo yaune?, ito gani dai, idan na samu dama zan zo, idan kuma banzoba zan kalla anan insha ALLAHU. wane uzuri gareka dazai hanaka zuwa kallon wasanmu na yau??. Hhhh, zanje ganin amaryane. Amarya kuma?, a ina??. Hhhh lallai mutumina kana sha'aninka, to zanje ganin amryarkane, dansu papa sunce yakama naje kafin kadawo. Tsaki Nawaf yaja, tareda gyara zama. Tomiye najan tsakin, ko bakaso naje saika dawone?. Kaga malam idan zaka kabar tsayani, idan kaje kabar tunawa dani, ALLAH idan wannan maganar tasa ka kirani to zan kashe wayata, inada aikinyi. Mas'ud ya ce, "to kashe mana, idan kakashe sai akace maka zanji haushi...... Kafin mas'ud yarufe baki Nawaf yakashe wayar d'if,, dariya sosai mas'ud yakeyi, saida yayi mai isarsa sannan yami'ke yana fad'in wannan man d'in wlhy d'an yawane.. 4:30pm Karfe hud'u da rabi direba ya sauke su mas'ud a 'kofar gidansu yasmeen, dayake shi yakawosu papa ranar, dan haka papa ya ce, "yakawo su mas'ud gidan. Wayarta mas'ud yakira ya ce, "munzo amarya. Yasmeen ta ce, "to, gaba d'aya batada walwala, daka ganta zaka san tana cikin damuwa, ita azatonta harda mijin nata aka zo, dan haka gabanta yafara dukan tara2. Yaseer ta turo ya kaisu falon abba, Abdallah ya ce, "lallai indai kaine 'kanin antyn mu, to kuwa yayanmu ya more. Dariya kawai yaseer yayi ya ce, "musu yana zuwa. Babu dad'ewa yacika musu gaba da kayan ciye2, saida yagama kawo komai sannan yasmeen tashigo falon 'kirjinta yana dukan uku uku. Kujera ta samu nesa dasu ta zauna, sanye take cikin ba'kar atamfa riga da sket, ta yafa farin mayafi har saman kai. Suduka kallonta sukeyi, ta ce, "ina yininku??, mas'ud ne kawai ya amsa, Anwar yataso yadawo gefenta, ya ce, "aunty aiimu 'kannenki ne, muzamu gaisheki, ina yini, kad'an ta d'ago tana kallon Anwar saida gaban ta yafad'i domin ganin yayi mata kama da wani data tab'a sani. Ta amsa tana murmushin ya'ke, Abdallah ma yadawo d'ayan gefenta ya gaisheta, nanma ta amsa masa cikin murmushi. Mas'ud ya ce, "amaryarmu!!. Na'am ta amsa tareda d'ago kai tana kallon mas'ud, suduka sukaima juna kallon mamaki, kardai ace wanan ne mijin nawa yasmeen tafad'a a zuciyarta. Saida kama tatuna daya kirata ya ce, "shi abokin mijintane, toko ina mijinki oho? ? Mas'ud ya ce, "dama kece amaryar tamu, lalali nayi matu'kar farin ciki da faruwar hakan ALLAH ya sanya alkairi. Ita dai yasmeen ta kasa furta komai, amma idanunta sun cika da kwalla, dan batasan waye zai kasance mijintaba, tunda gashi har abokinsa yazo shi yakasa zuwa. Kamar mas'ud yasan tunanin datakeyi, ya ce, "megidanki yana neman afuwarki, shima ya nan zuwa nan bada dad'waba, dan yanzu haka yana abuja, amma nanda nextweek zaizo insha ALLAH. 'Dan murmushi yasmeen tayi tareda fad'in babu damuwa ALLAH yakaimu. Sukace amin dai. Nan Abdallah da Anwar suka shiga zuba mata surutu, har saida mas'ud ya ce, "su tashi su tafi. Bayan sun shiga sun gaida su umma sannan suka tafi. Ji sukayi kamar karsu tafi, dan matar yayan nasu ta burgesu, gata 'kya'ky'kawa, ko amota hirarta sukayi tayi har suka isa gida. Nanma sukaita bama momcy labarin surukarta, da karramasu da akayi musu agidansu yasmeen. Momcy taji dad'i sosai, itama ta 'kagara taga surukar tata. Yaseer yataya yasmeen kwashe manyan ledoji dasuka kawo cike da sayayya ta birgewa. Lamarin yabama yasmeen mamaki, amma taji har azuciyarta zata iya zama da mas'ud amatsayin miji, inhar dashine mijin nata, dan alamunsa suna nuna mutumne mai ha'kuri. Yau ko abincin dare bata ciba tana d'aki kwance abinta. Abba ya ce, "aje akira masa ita, koda yaseer yashiga d'akin saitayi kamar tana barci. Yaseer yadawo ya ce, "barci takeyi.. Bayan fitar yaseer babu dad'ewa wayarta tahau wringing, tayi kamar bazata d'aukaba, saida takusa tsinkewa sannan ta d'auka ta kara akunnenta. Amma daga can an'ki yin magana, ta daure tayi sallama, nanma akayi mata shiru, a'kufule ta ce, "wai dan ALLAH wanene??. Cikin gadara taji ance, zaki baya fad'ar kansa, saidai risinawar namun daji ta bayyanar da matsayinsa. Yasmeen ta ce, "huuuum saidai kayi rashin sa'a ni mutum ce ba dabba ba. Tana kaiwa nana taja tsaki ta kashe. To shima dagacan tsaki Nawaf yaja, yana wani yatsine, fuska, shifa dama papane ya takura masa akan saiya kirata, shine zata wani kashe masa waya, lalaima yarinyar nan zanyi maganinki kwarai da gsk. Juyawa yayi wajen 'yan uwansa 'yan wasa dan dama wasa zasu fara, yakirata kafin lokaci yacika. 9:00pm Yauma dai Abuja international stadium cike take da 'yan kallon wasa. Yau Najeria zasu buga da kamaru. Bayan shigowarsu Nawaf cikin fili, sukayi addu'oi da sauran abinda yadace, aka fara wasa. Yaukam wasan yana tafiya dai dai, dan 'yan Najeria suna nuna kwazo, cikin kwarewa suke gara kwallon, yayinda 'yan bayan fage suketa zugasu da ihu. Har d'aki yaseer yaje yataso yasmeen wai tazo ta kalli kwallo, hararasa tayi takoma ta kwanta, dan tana cike da haushin rainin hankalin da'aka yimata yanzu a waya. Dayaga zata b'ata masa lokaci saiya fito kawai dan ya kalli wasansa. ⚽har aka tafi hutun rabin lokaci, babu wad'anda suka zura kwallo. Dan haka da'aka dawo kowa yayta 'ko'karin akan son yaga yazura kwallon, amma har lokaci yarage saura minti10 babu abinda ya canja. Ana saura minti1 atashi Nawaf yasami nasarar antayawa Najeria kwallo a raga⚽­čśâ­čśÇ­čśś☺­čĹŹ­čĆ╗­čľÉ­čĆ╗nantake 'yan Najeria suka hau ihun murna gurin ya kwaure da hayaniya. Da'kar aka lafa, bayan 'kara minti 7 da akayi. Acikin minti na 5ne kamaru suka so zira kwallo⚽amma golan Najeria ya cireta. Antashi 1-0 Najeria tanada 1 & kamaru 0 Can na hango Nawaf yad'aga gorar ruwa yana kwan kwad'a, yayinda suke tafawa da hannu d'aya da sauran 'yanwasa, kowa yazo akad'an tafa saiya wuce, wasu kuma sai an d'an rungumi juna. 'Yan kallo kuma sunata d'aga ­čç│­čçČNajeria suna wa'ka. Yayinda muta nene kamaru kowa fuska ahad'e­čśč­čÖé­čśĺ­čś×­čśť­čśť. ....................✍­čĆ╗ © 2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×LUV U OLL MY FAN's­čĺ× [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗18 BAYAN KWANA BIYU Najeria suka buga wasa da gini, sai dai wanan wasa baiyima Najiria dad'iba, dan antashi 1-1 amma yau ba Nawaf ya zura mana kwalloba. Dana kalli Nawaf d'inma sainaga baya cikin walwala, na ce, "yau miskilanci 'yan mazan ya motsa. KANO faisal ma an sallamesa saidai har yanzu yana zuba sambatunsa, duk ya rame yayi ba'ki, sai ro'kon iyayensa yake akan subarshi yaje gidansu yasmeen, 'kila idan yabata ha'kuri ta ha'kura tadawo gareshi. Tun iyayen na d'aukar lamarin nasa wasa har suka koma tausayinsa, idan yana surutai hajiya jummai har kuka takeyi masa, gabad'aya sun rasa kansa, bayada wani zance saina yasmeen. Hajiya jummai ta ce, "Alhaji kodai zuwa zamuyi mu ro'ki iyayen yasmeen ne?, 'kila su tausayamana su warware wancan auren, subama faisal. Alhaji buba yay shiru yana nazarin maganarta, zuwa can ya ce, "kina ganin hakan zata faru?, kuma idan sun yarda shi wanda ya auri yasmeen d'in zai amince??. Hajiya jummai ta ce, "to Alhaji saimu gwada, kuma ko biyansa yakeso muyi ai sai mu biyasa ko nawane, indai zai saki yasmeen faisal ya aura, karmuzo d'anmu ya susuce akan abinda baifi 'karfin saba. Na ce, "hummm aikodai wannan tafi 'karfinsa, dan ba kowacce mace kud'i ke iya sayaba. KIRA mu mata munada al'adar cewa sai mun auri mai kud'i, kuma hakan ba daidai bane, kedai amatsayinki na d'iya mace kamata yayi kiyi addu'a ALLAH yabaki miji nagari mai 'kaunarki da gsky. Wlhy masu kud'innan damuke hari ba kowane yadamu da fita ha'k'kin iyalinsaba. Musamman ma mazan hausawa, idan suna samun kud'i sunfi maida hankalinsu ga neman kud'in fiyeda 'ya'yansu da matansu. Wani saiya had'a wata uku zuwa hud'u baya 'kasar, yabar matar cikin damuwa da kewa, shikuma yanacan tareda karuwai a hotel, to dan ALLAH miye ribar auren irin wanan mai kud'in. Idan baki kai zuciya nesaba saiki fara bin mazan waje da aurenki, ALLAH ya kiyayemu. Idan kuwa kika auri talakannan daba kiso, duk inda yafita zuwa yamma yadawo, zai kula dake zai kula da 'ya'yanku, UBANGIJI ALLAH yasa mu gane amin. Yasmeen kuwa tana cikin damuwa, tanaso ta koma makaranta amma abba ya ce, "tabari mijinta yazo ta gaya masa, tayi kukan harta gaji dan tanaso takoma makaranta gashi anata wuceta a lectures. Yau suna zaune afalo harda umma da abba, sunata hirar gida, abba yana cewa lokaci kad'an yarage suje kwangwalan dansuga dangi dangi su gansu, yaseer yanata murna, amma yasmeen ko motsi batayiba. Abba ya ce, "mamana lafiya dai??, tai firgigit tana fad'in lafiya lao abba, ya ce, "inafa lafiya munata magana amma ba'kya tare damu, zonan mamana naji damuwarki kinji. Jiki a sanyaye yasmeen ta tashi taje kusada 'kafafun abba ta zauna, yadafa kanta yana fad'in mike damunki? fad'amin!. Saida ta matso hawaye sanan ta ce, "abba makaranta ta. Tofa, abba ya fad'a, yanzunan dama saboda bokonnan kika takuri kanki, to aii na ce, "ki bari mijinki yazo saikuyi magana. Babansa yakirani d'azu ya ce, "gobe zasuzo insha ALLAHU, dama baya nanane shiyyasa bai zoba. Cikin sigar lallashi ya ce, "kiyi ha'kuri kinji mamana, ki d'auki duk abinda ya sameki amtsayi 'kaddara. Yasmeen ta d'aga kai tana hawaye,. Abba ya ce, "yauwa mamana ALLAH yay muku albarka kunji, ya tsare mana ku. Umma da yaseer sukace amin. Daga nan yasmeen tad'an saki jikinta tana d'an saka baki a hirar tasu, amma ba sosaiba. NAWAFF yau da yamma Nawaf ya iso kano, zaid'an kwana biyu ya koma abuja, kafin aci gaba da wasa. Sunyi murnan ganinsa, momcy ta shafa kansa cikin hausarta dabata gama nuna ba ta ce, "my dear duk ka rame wlhy, mike damunka haka??. Nawaf yad'an cije leb'ensa na 'kasa ya ce, "momcy wanan auren da papa yay min mana, ALLAH bazan 6oye mikiba bana son aurenan momcy, ya'karasa fad'a cikin raunin murya. Momcy ta kwanto dashi gefen kafad'arta ta ce, "kayi ha'kuri Abbuna ina ji ajikina wanan auren Alkairine a gareka, kuma yanda su Abdallah suke bani labarin matar taka da gidan data fito duk masu mutuncine, da tarbiyya. Banaso akan aurennan kabari sa6ani yashiga tsaka ninka da papan ku, ka danne zuciyarka ka koyi son matarka tunkafin tadawo hannunka. Zanta tayaku da addu'a insha ALLAHU, itama ALLAH yacusa mata sonka kaji, dukda nasa modeebbona abin sone ga kowacce mace, babu macen dazata gansa ta ce, "bataso, momcy ta 'karashe maganar da tsokana. ­čÖłhannu yasa ya rufe idanunsa don kunya. Momcy tayi dariya, ato idan kuma bakaso mutafi saudia kaza6a cikin dangi, gama ummuhabeba nan kullum damuwarta tana kanka, kaga sai kawai musha biki. Nawaf ya zaro idanu­čś│ ya ce, "momcy yi shiru kar papa yaji, danni bana ra'ayin zama da mata biyu, kuma ma bana son ummuhabeeba tacika 'kyau dayawa nikuma bana son macen data cika 'kyau gsky. Tofa, momcy tafad'a, wanan kuma wani sabon idea ne na rashin son auren 'kya'ky'kyawar mace??. Nawaf yay murmushi har fararen ha'koransa suka fito, ya ce, "A'a my sweet mom ra'ayina ne nidai!!!.... Abdallah ya shigo da sallama, Nawaf ya ce, "ka amso mini?, eh yaya na amso, na kaimaka d'akinka banyi zaton kana nanba aii. Okey babu damuwa, amma yau miya hanaka zuwa islamiyya ne??, Abdallah yad'an sosai gefen wuyansa yagyara zama zai shararo 'karya.......Nawaf ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu­čľÉ­čĆ╗kaga basai kafad'aba, dan nasa 'karya zakamin. Momcy ta ce, "aii dama jira nake kadawo na sanar maka kwata2 Abdallah baya son zuwa islamiyya, danshi bai biyo halinkaba, tun kana shekara sha biyar ka sauke ALKUR'ANI, amma Abdallah har yanzu baikai ko izufi 50 ba nakula Anwar ma yakusa kamosa. Harara Nawaf ya watsa masa, ya ce, "wato kai nakula kaine mara ji d'in gidanan ko?, wlhy ka maida hankalinka kajiko, ku a tunaninku karatun boko shine wayewa ko??, amma ai baka ta6a fashin makarantar bokoba ko??. Kun manta karatun bokon iyakarsa nan duniys, karatun islamiyyar dabaku basa muhimman cinba shine zai zame mana tudun dafawa awata rana mai cike da rud'ani. Wlhy daga yau nasake jin bakaje islamiyyaba sai ranka yayi matu'kar 6aci, tashi kabani waje sakarai kawai. ­čÜ­čĆ╝sum sum Abdallah yatashi yashige d'akinsa yana zum6ura baki. WASHE GARI Tunda wuri umma da ameena suke hidimar had'a abubuwan tarbar ba'ki amma banda yasmeen data shige d'aki wai batada lfy. Dan haka umma taje ta nemo Ameena 'kawar yasmeen d'in dan ta tayata. Yasmeen kuwa tana d'aki cikin fargaba da damuwa, wai yau zataga mijinta, ko zaizo mata da mutuncine?, kokuma sa6anin hakan??. Har zuwa azahar tana d'aki tana kullawa da kwancewa, dakuma fad'uwar gaba. a wannan lokacin kuwa Nawaf yanacan anci kwalliya cikin 'kananun kaya, ya fito shida mas'ud sai zabga 'kamshi suke, 6an garen su momcy suka nufa, afalo suka iske momcy da papa dasu Anwar. Papa ya ce, "kunyi 'kyau sai dai modeebbo koma ka canjo kaya wad'anan basu yiba. Nawaf yabi jikinsa da kallo, papa miye aibun wad'anan kayan yafad'a cikin shagwa6a. Papa ya ce, "aibunsu dasuka kasance 'kananun kaya, kai bakaga shigar da d'an uwanka yayi ba mas'ud. Gidan surukai zakujefa, kuma yau zasu fara ganinka, sai kaiwai suganka da 'kananun kaya kamar d'an yahudawa, maza kaje ka canjo shadda ina nan ina jiranka, dan kuna 'kara 6ata lokaci. Badan Nawaf yasoba yakoma ya sako farar shadda 'kal d'inkin zamani, harda saka hula, kai yayi 'kau wlhy, saiya fito asalin balarabensa, dan dakaga Nawaf dole ka kirashi ci kakken balarabe. Nawaf dogone sosai yanafa jikin 'karfi sabida training dayakeyi, yana da suffa irinta kosashshen xaki, daga sama 'ka'k'karfane sosai cikinsa ad'ame tamkar baya cin abinci, farine amma ba tas ba, kalar fatarsa irinta larabawace jaa kenan zamuce, yanada suma mai yawan gske mai kuma laushi d 'kalli dukda tanashan gyara da mayuka masu tsada, yanada d'an saje wanda ya tsaya iya kumatinsa dai dai kunne, ida nunsa masu 'kyau da haske ga girar ido zara zara, kai komaidai yaji d'ammmmm. Papa yay murmushi yauwa ko kaifa modeebbo, yanzu kaga shine mutuntawa, sai kuje banaso naji wani abinda zai 6ata mini rai, kuma ku sayi wani abu akai mata kar aje hannu rabbana, ku gashe mana dasu. Mas'ud ne kawai ya amsa. Abdallah ya ce, "yaya dan ALLAH zanje. Harara Nawaf ya watsa masa wadda tasakashi saurin rufe baki. Sukuma suka fice. Papa ya ce, "huum d'an yanzu saka barsa da halinsa kawai. Amota mas'ud ya ce, "mutumina baka ta6a kwalliya irin ta yauba wlhy, gashi yau ranar shan mamakice. Nawaf ya ce, "wane irin mamaki kuma bro's??, wani murmushi mas'ud yayi, ya ce, "sai munje zaka gani!". Baki Nawaf yad'an ta6e yana fad'in ni babu wani abin mamaki dazan gani malam. Mas'ud ya tuntsure da dariya , banza Nawaf yay masa. Sun isa 'kofar gidansu yasmeen, mas'ud ya ce, "ka kirata kace mun iso mana. Harara Nawaf ya sakar masa, ya ce, "lallai ashe zamu kwana anan kuwa, indai har saina kirata ne. Girgixa kai kawai mas'ud yayi yad'akko wayarsa ya kira yaseer ya ce, "yaseer gamu munzo. Yaseer ya ce, "to yaya ku shigo falon Abba. Mas'ud ya kalli Nawaf bayan ya gama wayar, ya ce, "to saika fito ance mu shiga, baki Nawaf ya ta6e ya bud'e motar yafito. Cikin gidan suka danna kai, har zuwa 'kofar falon abba dake harabar gidan ta baya, babu yanda za ayi kaga masu gidan dan 'kofar falonsu tana can cikin lungu, Tunda suka shigo 'kamshin turare falon da abinci yake dukan hancinsu, suka zazzauna. Babu dad'ewa yaseer ya shigo da sallam suka amsa, ­čś│idanu ya zaro waje dan mamaki, ya 'kara murza idaninsa, yagadai kwarai dgsk modeebbo ne, ya ce, "yaya mas'ud dan ALLAH dgske ida nuna sukeyi??. Murmushi mas'ud yayi dan yagane me yaseer yake nufi, ya ce, "gsky suka nuna maka yaseer, modebbone dai daga kasani yana gara mana kwallo a afili. Nawaf yay murmushi shima ya ce, "zonan 'kanina!, jiki a sanyaye yaseer ya 'karasa wajensa, hannunsa yakama ya zaunar dashi kusadashi, kasannine??, yaseer yay dariya, aiko shekaran jiya saidanaga wasanka, wlhy narasa irin murnar dazanyi danna burge kaina, amma ALLAH ngd maka daka nuna min wanda nake 'kauna ido da ido. Nawaf yaji dad'i sosai, danhaka ya rungume yaseer shima. mas'ud ya ce, "yaseer sisto d'inkafa?. Yaseer yami'ke yana fad'in kuyi ha'kuri farinciki ne ya mantar dani bari na kirata!!. Mas'ud ya ce, "to karka gaya mata abinda kagani fa. Cikin dariya yaseer ya ce, "bazan fad'aba ALLAH. yasmeen zaune afalo tana jiran yaseer yazo yakirata, tayi 'kyau cikin les green ta d'ora farin mayafi dukda ba kwalliya tayiba amma tayi bala'in 'kyau. Muskarsa cike da fara'a ya ce, "sisto kije suna jiranki, bai jira amsartaba yashige d'akin umma domin kai mata rahoton farin ciki. Jiki a sanyaye ta tashi tanufi falon, tad'an dad'e a 'kofar falon 'kirjinta yana dukan tara2, daga 'karshe tayi kundun bala tashiga da sallama, cikin siririyar muryarta. Mas'ud ne kawai ya amsa, dan Nawaf yana wayane. Ta zauna suka gaisa da mas'ud yabata ha'kuri akan kwana biyu basu zoba, tayi d'an mumushi tana fad'in babu damuwa aii. Mas'ud sai dariyar mugunta ya ke k'asa2, ya'kagara yaga yanda za'a had'u. To nimadai 'yar rahoto abinda nake jira kenan. Bayan Nawaf yagama waya ya juwyo yana kallon mas'ud, mas'ud ya ce, "lafiya dai ko??. Harar sa Nawaf yayi ya ce, "ban saniba. Mas'ud ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "Amarya ga angonki na kawo miki yau dai. Kan yasmeen a'kasa ta ce, "ina yini?, Lafiya. kawai Nawaf yafad'a yana wani yatsine fuska. Yasmeen ta mi'ke domin ta basu ko ruwane dan takula ko bud'e abincin basu yiba. Ta 'karaso kanta a'kasa, shi Nawaf ma waya yake latsawa, gabansu ta dur'kusa ta tsiyaya lemon kwakwa ta mi'kawa mas'ud. Ta zuba wani ta mi'kawa Nawaf dake latsa waya abinsa. Mas'ud ya ce, "malam ana baka abufa, ayatsine Nawaf yad'ago zaiyi magana, saiya daskare a gurin. Cikin in ina ya ce, "kai ba dai ke ba ce..... Itama cikin tsoro take kallonsa, sudukansu 'kirjinsu yana bugawa da tsananin 'karfi, hannun yasmeen sai rawa yake, gashi takasa ajiye lemon. Shima Nawaf cikin rawar hannu da baki yake nuna yasmeen­čĹë­čĆ╗­čĹę­čĆ╗amma yakasa cigaba da furta komai. Shiko mas'ud sai dariya yakeyi yana tafa hannaye­čść­čśť.....................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×Luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:55 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗19 ....Lokaci d'aya suka mi'ke kowa yana kallon kowa, idan kagansu saika d'auka kallon soyayya sukema juna, yasmeen ce tafara janye idanunta tana zubar da hawaye, saikuma tad'ago da sauri tana kallonsa. Nawaf yagyara tsayuwarsa tareda 'kara d'aure fuska ya ce, "lallai yarinya dama kece papa ya 'ka'kaba mini, tofa ina mai baki shawara 'yammata tun wuri ki hanzarta fad'a musu su warware wanan auren ankuwa ba hakaba wlhy zaki gwammace kid'a da karatu, ya 'kare fad'a yana huci, kamar wanda yake afilin danbe. Cikin tsiwa yasmeen ta harareshi ga hawaye share2 a fuska, ta ce, "ai basai nasha wahalar sanar dasuba malam, wannan damar tana hannunka, idan kaso nanda minti d'aya saika datse igiyar da aka d'auramini ta 'kaddara dakai, tsowww... taja tsaki. Wani 'kududun ba'kin ciki ya tokare ma'koshin Nawaf, wlhy badan yanajin tsoron fushin mahaifansaba da agurinnan zai saki yarinyarnan, ya had'iye wani mugun yawu jikake 'kudddd. Idanunsa sun kad'a sunyi jajur,, yasmeen ta ce, "aikin banza ashema kai matsoracine??..........kafin tarufe baki ya dam'ki hannunta na dama ya murd'e tabaya, tako kware baki zatayi ihu dan azaba, da sauri yasa d'ayan hannunsa ya toshe mata baki, saida ya tabbatar hannun ya murd'u sanan ya saketa yana dariyar mugunta, ya ce, "nida ke za'a tantance matsoraci. Yasmeen ta durkushe tana zubar da hawaye, jitake kamar hannunta baya jikinta, kwatakwata takasa d'agashi. Mus'ud yale'ko dan yaga wainar da ake toyawa tunda yasan ba shiri sukeyiba.dan tund'azu yafita yabarsu su biyu kawai. Da sauri ya'karaso ganin yasmeen tsugunne tana rusar kuka, a hanxarce ya ce, "Nawaf!! mikayi matane??. Banza Nawaf yay masa ya koma saman kujera ya zauna yana shan lemon kwakwarsa wanda yayi masa dad'i. Ran mas'ud ya6aci sosai ya ce, "waikai Nawaf wane irin mugun mutumne yau kuma mizakace tayi maka??. Nawaf ya yatsine fuska, katanbayeta abinda taimin sai nikuma nagaya maka abinda nayi mata, kawani d'ora mini laifi ni kad'ai, tsowwww ya 'karashe maganar da tsaki. Mas'ud ya ce, "kiyi hakuri yasmeen ALLAH zai saka miki,, yasmeen tad'ago jajayen ida nunta ta ce, "karka damu mas'ud nima dakaina zan rama, dan wlhy bana barin bashi, karya d'auka dan yayi mini wanan muguntar zan barsa, shima ya saurari ranar ramuwa.. Tana kaiwanan ta mi'ke zata tafi, mas'ud ya ce, "plz karki tafi ki dawo, kinga su umma bazasuji dad'iba. Batayi musuba tadawo ta zauna dan tana ganin darajar mas'ud. Nawaf kam ko kallo basu isheshiba, yanata danne2 awaya hankalinsa kwance, yana kora lemon kwakwa. Na ce, ji 'kafin hali azo gidanku a cuceka. Afalon umma kuwa faisal ne da hajiya jummai da alhaji buba, zuwansu kenan suma, umma bata nuna musu komaiba ta tarbesu da mutunci, harda ruwa ta zauna suka gaisa sanan ta ce, "gashi kunzo malam baya nan amma yana hanya, dama jiya yake magana akan akwatuna, ya ce, "azo akai muku kafin ku biyo. Hajiya jummai tayi dariya, A'a mu ba kar6ar akwatuna muka zoba, munzo mu baku ha'kuri akan abinda yafarune, wlhy makircin wani abokin faisal ne, shikuma babu bincike yaje ya aikata wanan aika aikar, amma wlhy tunda aka gane makircine hankalinsa ya tashi, nan dai hajiya jummai ta labartawa umma komai daya faru. Umma ta ce, "ALLAH sarki ai bamu saniba damunzo mun dubashi, ALLAH yasa kaffarane faisal. faisal ya ce, "amin umma, yafad'a yana wani sissinkuyar dakai 'kasa, adole shi mai kunya. Hajiya jummai ta ce, "nibanga 'yar tawaba. Umma ta ce, "tana nan wlhy, tayi ba'kine, ALLAH sarki d'iyar albarka. Alhaji buba yaga hajiya jummai tanata wani kewaye2 takasa furta komai, sai kawai ya wage baki yashiga bayanai. Maman yaseer dama abinda yakawomu shine dan ALLAH ayi ha'kuri da abinda yafaru baya, tunda faisal yayi nadama ayi ha'ku amayar masa matarsa, munyi muku al'kawari hakan bazai sake faruwaba. Cikin mamaki umma take kallonsu, ta ce, "alhaji ai yasmeen yanzu tanada aure, ko baku saniba??. Hajiya jummai ta kar6e, munsani mmn yaseer, abinda dama mukeso muce shine dan ALLAH abama wancan mijin ha'kuri sai a war ware adawoma da faisal matarsa..... Da sauri yaseer ya shige falon abba, batareda yaji furicin ummaba, kai tsaye wajen Nawaf yanufa, yayinda mas'ud da yasmeen suke d'an ta6a hira. Akunne yaseer ya gwargwad'ama Nawaf abinda yajiyo. Idanu naga Nawaf yazaro ya ce 'kanina da gsk, yaseer ya kad'a kai tareda fad'in sunama falon umma,, kafad'ar yaseer Nawaf yadafa ya ce, "karka damu bazamu barima Mafita ba ka kwantar da hankalinka, yaseer ya ce, "to bara naje naji yanzu mi ake tattaunawa. To Nawaf ya cema yaseer. Maganar ta girgiza Nawaff, amma shi atunaninsa yasmeen tana son failal ne, yazata makircinne da gsk. Dan haka yake ganin ai bama saiya saketaba yasamu hanyar yima yasmeen abinda yaso kenan. Awajen su umma kuwa, umma ta ce, "musu to wanan ba maganarta bace sai abba yadawo zasuyi shawara. Alhaji buba ya ce, "to bari suje suna saurarensu idan sunyi shawarar. Umma ta ce, "to mungode ku gaida gida. Har ga ALLAH faisal yaso ganin yasmeen amma babu dama, danko mai kama da'ita bai ganiba,, jiki a sanyaye yatashi yabisu hajiya jummai yanata raba idanu dan son ganin yasmeen­čśť­čśť. Tafiyarsu babu dad'ewa abba yadawo, bayan ya huta yasha ruwa yashiga suka gaisa da su Nawaf, har 'kasa suka tsugunna suka gaidashi, Nawaf sai wani sisinkuyar dakai yakeyi. Yasmeen ta ce, "munafinci banza, wlhy indai nice zaka gane kurenka. Sun d'an dad'e suna hira da abba, daga nan umma tashigo suka gaisa, su duka sun yaba da hankalin surikin nasu, gashi 'kya'ky'kyawa laillai d'iyarsu ta more saidai subita da fatan alkairi, dan auren miji nagari bababar ribace. Sai gab da magriba suka tafi, abba yamatsa saita yimusu rakiya. A 'kofar gida mas'ud ya ce, "yasmeen yakamata nima ki samar min mata a anguwarnan gsky. Yasmeen tad'anyi murmushi, ai indai wannan ne takwana gidan sau'ki, nabaka ameena. Ya ce, "woow!! Kice harna samu?, yasmeen ta ce, insha ALLAH. to yakamata afara yimini kamfen daga yau. Nawaf yaja tsaki yana fad'in malam nifa kana 6ata mini lokaci kaji, tsaki mas'ud yaja, ya ce, "matsalarka ce kuma wannan, d'an rainin wayo kodan kaga ka kama taka a hannu, to nima tawa nake nema. Baki Nawaf ya ta6e ya ce, "kaine mata ke gabanka aii. Maganar tayi mugun 6atawa yasmeen rai, dan haka taja wani dogon tsaki tana fad'in wandama ya ce, "basa gabansa munafinci ne kawai... Da sauri Nawaf ya ce, "ke waye munafikin??, saida ta murgud'a baki­čśĆsanan ta ce, "damai aikatawa nake. Nawaf yay wata 'yar dariya, yarinya kin taimaki kanki dakika kauce, wlhy dasai na ida 6alla wananan hannun mai kamada sillen kara. Masha ALLAH yasmeen tafad'a tana murgud'a masa baki, ta ce, "basai kazo ka 6allaba, kuma dakai ake zaka kashe nine???. tana ganin Nawaf ya biyota ta tsillara da gudu cikin gida. Nawaf ya ce, "'karamar 'yar marakunya daki tsaya mana kiga hauka. Mas'ud ya ce, "wlhy tunda nake ban ta6a kallon film mai dad'in kamar nakuba, gsky kuna wuta alhaji. Harara Nawaf yasakar masa, ya ce, "kaifa d'an iskane wlhy mas'ud ya ce, "iskan cin menayi maka malam??. Nawaf ya ce, "wai mas'ud ya akayi haka, kodai kaine kayi wanan had'in yama za'ayi wanan yarinyar tazama matata, aii da sake. Babu wani sake malam aii ka d'auka an wuce gurin kawai, domin wannan wata hikima ce daga cikin hikimomin ubangiji. Wai mikayi mata d'azu naga tana kuka??, ko har an fara soye wane??. Duka Nawaf ya d'akama mas'ud ya ce, "a 'konewa aka fara ba soyewa ba, rashin kunya tamin na hukuntata. Hhhhh kaidai wlhy mugune nakula. Koda yake wasan yana 'kyau dan nasan saita rama. Lallai kam kokuma ta rame ba, dan wlhy yanzu ta ce, "zatamin hauka wahala zatasha ba 'karamaba, garama ka bata shawara ta kiyayeni. Hhhhh kadaiji dashi malam, dahaka suka 'karasa wani masallaci domin yin sallahr magriba. Yasmeen kuwa da gudi tashiga gida, a falo suka had'u da umma ta ce, "k irin wannan gudu haka lafiya?. Gefen wuyanta ta sosa ta ce, "babu komai umma. Girgiza kai kawai umma tayi tashige d'aki domin yin sallah. Itama yasmeen d'aki ta shige ta kwanta domin tana fashin sallah, dan danan tashiga duniyar tunani, lallai saita dage tunda har ALLAH ya 'kaddara mata zaman aure da wanan d'an haya'ki, saidai kuma tayi farin cikin rabuwada faisal d'an is......takumayi ba'kin cikin kasancewa da Nawaf d'an kwallo­čÄż, wai itace matar d'an kwallo kai lamarin tamkar almara wlhy, gsky bata moreba dan ita kwallo bata burgeta bare mai yinta, amma gashi ALLAH ya jarabceta da auren d'an kwallon. Ta kalli hannunta da har yanzu ciwo yakemata ta ce, "mugu ALLAH yasaka mini, kuma wlhy ka rubuta ka ajiye saina rama, 'kilama yayi mani targad'e azzalumin. Haka tai ta tuna abinda yafaru d'azu tamkar a mafarki. FAISAL faisal kuwa koda suka tafi saiya sakama iyayenasa kuka, hajiya jummai ta hau rarrashinsa haba faisal d'in dady kayi ha'kuri, kobakaga 'ko'karin da mukeyi akanka bane, ka d'auka yasmeen tama rigada tadawo hannunka nan bada dad'ewa ba. Alhaji buba ya ce, "bana son ganin kukanka my son dan ALLAH kabari indai yasmeen ce dan kai aka halicceta kaji. Kai kawai yad'aga yana share hawaye. Wlhy ni dariyama yabani­čść­čśť. BAYAN KWANA BIYU. yasmeen tasake yima abba maganar makarantar ta, abba ya ce, "banace ki fad'ama mijinki idan yazoba. Ta ce, "abba ai na manta ban fad'a masaba. Aii wanan mai sau'kine tashi kije ki fad'a masa ta waya yanzu, idan ya yarda saiki fara zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Jiki asanyaye yasmeen ta mi'ke, ita yanzu idan ta kirashi mizatace masa, 'kilama yay mata wula 'kancin daya saba mata, itako wlhy ba 'kyaleshi zatayiba. Tadad'e tana kullawa da kwancewa, daga baya ta d'auki wayar tafara kiransa cikin fad'uwar gaba, har wayar ta tsinke bai d'aukaba. Ta kai dubanta akan agogo 'karfe 9:56pm, wata zuciya ta ce, "ki 'kara kira, maso d'an tsuntsu aishi ke binshi da jifa. Ta sake kira har sau biyu bai d'agaba, jiki asanyaye tazame ta kwanta tana hawaye, shike nan an hanata zuwa makaranta tanaji tana gani. ^^^^^^^^^^^^^^^^ Alokacin da yasmeen take kiran Nawaf yana wanka, yanajin wayar tana wringing, gashi yana dad'ewa awajen wanka, saida yagama komai na al'adar rayuwarsa kamar shafa'i da wutiri, karatun alkur'ani, (dan duk dare saiya karanta littafi amai tsarki,) san shayi☕, sannan ya haye gado ya kwanta, wayoyinsa yajawo, yafara duba missed calls, ya kira wad'anda suke da muhimmanci sanan, wayar da yasmeen takira itace 'karshe, 3missed call yagani saidai kuma ba'kuwar number ce, shikuma baya kiran ba'kuwar number. Harya kwanta sai kuma zuciyarsa ta kwad'aita masa yakira, dan baisan dalilin dayasa mai number yay masa 3missedcall ba. Lokacin har yasmeen tagama kukanta tayi barci, dayake barcin baiyi nisaba saitaji phone d'inta na wringing, sanda ta d'auka harta kusa tsinkewama. Cikin muryar barci ta ce, "assalamu alaikum. saida yaja ajiyar zuciya wadda shi kansa basan yayiba, ya ce, "wa'alaikissalam wacece??. Tuni yasmeen ta watstsake domin jin muryar Nawaf, dan da farko bata duba number da aka kirata dashiba, ta tashi zaune, cikin rawar murya ta ce, "yasmeen ce!!. Yad'an ta b'e baki dan tunda tayi sallama yagane muryarta, ya ce, "ban ganekiba, kinga kimin bayani yanda zan gane banason inda2, inba hakaba zan kashe wayata. Saidata murgud'a baki ­čśĆtamkar tana gabansa, ta ce, "toni wane bayani zan maka tunda nafad'i sunana baka ganeba, ni dama sonake na koma makaranta kuma abba ya ce, "saina sanar maka shiyyasama nakiraka, inba hakaba mizaisa nakiraka, ta 'kare maganar cikin mugud'a baki. Tamkar yaganta ya ce, "mara kunyar banza, to ban aminceba inkuma kikaje ban saniba ALLAH ya isa, d'if ya yanke wayar. Wasu hawaye suka zubo mata masu zafi, zuciyarta taita zugata akan takirashi ta ro'keshi 'kila yabarta. Haka ta daure ta kirashi, yay buris da wayar, saida ta sake kira sanan ya d'auka, wani lallausan murmushi yasaki na mugunta kafin yad'aga, yana d'agawa ya ce, "k nifa kin dameni barci zanyi. Ta matse hawaye ta ce, "plz dan ALLAH kabarni, kaga zamu fara EXAM ne kwanan. Saida yagyara kwanciya sanan ya ce, "toni ina ruwana, nidai nace ALLAH ya isa ko, kuma zan kira abba na ce, "na hanaki, dan haka karki sake kirana zanyi barcine, bata ankaraba ya kashe wayar. Dariya yashiga tuntsurawa harda hawaye, yarinya baki sanni bane, inada hanyoyin maga ninki wlhy, yafad'a yana kwanciya. Itako yasmeen kuka tashiga rerawa kamar uwarta ta mutu, saida tayi mai isarta sanan tayi shiru, har barci ya kwasheta.. Na ce, "yasmeen asuba tagari..................✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Ina mi'ko d'unbin gaisuwa ga masoyana, nagode kuna 'karamin 'karfin guywa gsky, ngd ALLAH yabar zuminci. Luv u oll­čśś­čśś­čśś!!!!!!. Acigaba da gashi­čĹî­čĆ╗!!!!!!!!!!. ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×Luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗20 ....da safe sukuku yasmeen ta tashi batada wata walwala, umma tana kula da'ita amma batace mata komai ba. Yaseer yagama shirin makaranta yafito bayansa goye da schoolbag, ya ce, "sisto wai mike damunki ne??. Yasmeen tad'an yatsine fuska ta ce, "ba komai bro's. Ya ce, "to bazakije makarantarba ne?, naji kince yau zaki koma kuma. Kwalla suka cikama yasmeen idanu ta ce, bazanjeba na fasa. Kin fasa kamar yaya??. Zamewa tayi takwanta saman kujera batareda tace masa komaiba. Dole ya 'kyaleta ya fita danshima yaga yana neman makara. Umma tafito daga kichin tasamu yasmeen kwance tana hawaye, kusada ita ta zauna ta ce, "wai yasmeen mike damunkine??, ko bakida lafiya ne??. Yasmeen ta bud'e ido tana kallon umma, ta ce, "kaina yake ciwo tunjiya umma!. Umma ta ce, "o, ni kharima!! shine kuma bazaki fad'aba saidai kuka?, shidai d'an fari duk inda yake saiya nuna halinsa, to kitashi akwai magani ad'akin abbanku ki d'akko kisha. Jiki a sanyaye ta tashi taje ta d'akko maganin, koda tadawo sai ta tarar umma bata falon danhaka saita wuce d'akinta. Bayan madubi ta watsa maganin tana fad'in umma wannan bashi bane maganin ciwona, maganin ciwona yana hannun wancan mugun, ta 'karashe maganar da hawaye masu zafi. Na ce, "ALLAH sarki yasmeen yazakiyi aure kenan. ------------------------------------ A6angaren Nawaf kuwa ko ajikinsa, yanzu hakama yana kwance a d'akin momcy bisa gado yanata barcinsa hankali kwance, dan tun asuba dayaje gaishesu ya kwanta. Dama wata sa'in yakanyi barci a d'akin momcy. Momcy ta kalli agogo 'karfe 9:30am ta ce, "modebbo yakamata katashi hakanan, gaban gadon ta 'karasa tana tashinsa, yad'an bud'e ido yana kallonta, saikuma ya maida ya lumshe. Ta ce, "Abbuna yakamata katashi hakanan kaga rana tayi, tafad'a tana jan baban yatsan kafarsa. Ahankali yatashi yana murza ido, ya ce, "momcy har 'karfe nawa nakai ina barci yau?, ta ce, "kalli agogo kagani mana, koda ya kalla saiya zaro idanu waje, ya ce, "kai ashe nadad'e ina barci, yaufa ko motsa jiki ban fitaba. Momcy ta ce, "hala kadad'e bakayi barciba jiya. Yad'anja tsaki, mara kunyar yarinyar nan ce ta hanani barci da da wuri. Yarinya kuma? a ina kenan?, momcy ta tambaya tana yatsine fuska, Nawaf yad'an sosa gefen wuyansa yana fad'in yasmeen fa momcy. Murmushi momcy ta saki ta ce, "o, ai nazata watace kuma. Mi'kewa yayi yana murmushi yanufi 6angarensa. Wanka yashiga yayi yafito yashiga shafa can, dangwala can, yagara jikinsa tsaf, yad'ora 'kananun kaya ba'kin wando da green d'in riga mai 'karamin hannu, yakawo ba'kar rigar sanyi mara hannu ya d'ora, yasaki hular abaya, yad'anja zif d'in sama kad'an amma baikai 'kirjinsaba, yayi 'kau sosai gsky, yafito yanata zabga 'kamshi. Gefen momcy ya koma, tana kichin suna aiki itadasu talatu, suka russun suka gaisheshi, sai satar kallonsa sukeyi, dan ita ladidi a haukanta har yanzu son Nawaf takeyi. Momcy ta ce, "modebbona sai ina kuma, yashafa sumar kansa data sha gyara, ya ce, "momcy wajen mas'ud zanje. Ta ce, "to break fa??, ya ce, "uhmm!!! Kumafa inajin yunwa gsky, bari nayi break sanan. Momcy ta ce, "to ladidi jeki had'a masa.....da sauri ya ce, "no, my sweet mom, tabarsa zanyi dakaina kawai, yafad'a yana yatsine baki, dan ganin ladidin awani hargitse, kuma momcy tana 'ko'kari wajen kula dasu da saimusu sutturu masu daraja, amma a banza. Shiyyasa bakomai Nawaf yakeso asakasu suyi masaba. danning yanufa yazauna abinci kad'an yaci yami'ke, lokacin momcy ta fito, ya ce, "mata yawuce. Ta ce, "adawo lafiya babban mutum. Nawaf yafita yana murmushi yanaso momcy ta ce, "masa abbu! ko babban mutum!, dayake sunan mahaifinta aka saka masa, shiyyasa papa yasaka masa modebbo saboda yana yima momcy kara. Kai tsaye gidansu mas'ud yanufa, dukda yasan yana asibiti yanzu, wajen mami yashiga tana zaune afalo tana break dan yaran duk suntafi school, ta ce, "oyoyo my son!. Nawaf yazauna yana murmushi, yarissina yana gaida mami, ta amsa cikin fara'a, ta ce, "ina amarya?, saida yay 'kasa da kai yana wani sosa gefen wuya ya ce, "tana nan lafiya mami. Ta ce, "masha ALLAH agaishe mini da'ita, amma yakamata akawo mana ita mugani kafin ka koma, dukda muma zamuje muyima iyayenta godiya, dan ba kowane zaiyi kasadar bada d'ansa batareda yasan wanda yabamawaba. Nawaf ya ce, "karki damu mami za'a kawota insha ALLAHU. To ALLAH ya yarda. Amin Nawaf yafad'a yana mi'kewa, ya ce, "mami bari na iske mas'ud a asibiti. To shikenan ALLAH ya tsare shima aii yau bai dad'e da fitaba dan ya makara. Nawaf ya fara tafiya yana fad'in ALLAH sarki, to bari na 'karasa. To Modeebbo nagode ALLAH yayi muku albarka kaji. Amin yafad'a yana fita. Asibiti ya nufa wajen mas'ud, lokacin dayaje Nawaf yana duba marasa lafiya. Guri yasamu yazauna mutane sai kallonsa sukeyi, dan wasu sun riga sun sansa a magiji­čĹë­čĆ╗­čľą, saidai suna kokwanton shine koba shibane. Ga Nawaf baya son kallo dan haka sai yaji dukya takura, mota yatashi ya koma ya zauna, yad'an dad'e zaune amota yanata chattinga a awaya. Wata wayarsa tahau wringing, banza yay da wayar yaci gaba da chatting d'insa, saida aka 'kara kira sanan ya d'auka. Marakunya yaga ansaka, dan haka yay save d'in sunan yasmeen, saida ya ta6e baki sanan yad'aga, amma baiyi maganaba. Yasmeen ta ce, "assalamu alaika, muryarta can 'kasa tafad'a kamar mai mura. Sanin muhimmancin sallama yasa ya amsa. Sukayi shiru suduka harna tsawon minti2, ita a tunanintama yakashe saitaji ya ce, "dan wula'kanci kinsan bakida abin fad'a kika kirani!!. Cikin rawar murya ta ce, "plz dan ALLAH kabarni naje school d'innan wlhy idan kahanani zan cutu, kaga nayi asarar shekara d'aya da wata hud'u danayi ina zuwa kenan abaya. Plx duk abinda zakamin karka had'a da maganar karatuna. Banza yay mata kamar bazai tankaba, saikuma ya ce, "K!" Nifa ba'a sakani nayi abu dole, nafison idan na ce, "banason abu a 'kaleni, aii karatu ba dole bane ko?, duk kinbi kin wani dameni, kodai so kike kifita zuwa gidan tsohon mijinki daya sakeki ne??, yaja tsaki yana fad'in matsalar auren bazawara kenan!!!. Yasmeen ta rintse idanu dan jin yakirata bazawara, maganar tadaki zuciyarta sosai, wasu hawaye sukabi kumatunta, tayi shiru batarda ta 'kara firta komai ba. Shimadai shiru yayi baisake cewa komaiba, daga 'karshema saiya ajiye wayar batareda ya kasheba, kuma yana kallo itama bata kasheba. Daga baya yasmeen ta yanke wayar tana cigaba da kuka, ahaka ameena tashigo ta sameta, cikin mamaki take kallonta. Yasmeen ta ce, "ki zauna mana kika tsaya, Ameena ta ce, "ina naga tazama kina kuka, waike bazaki yarda da 'kaddaraba ne??, yasmeen ta share hawaye ta ce, "Ameena bazaki ganeba ne. To ganar dani Ameena tafad'a tana zama akusada yasmeen,, yasmeen ta gayama ameena yanda sukai da Nawaf tun jiya dasukazo, da kiran datayimasa da daddare, dakuma na yanzu, ta ce, "Ameena waini zai kira bazawara!!. Ameena ta ce, "kekam kinada abin haushi wlhy, to miye nawani kiransa saikace wadda take karatu aljanna, dammi bazaki share karatunba, idan kinada rabo nan gaba saikiyi, kuma ni banga abinyin kuka danya ce miki bazawara!!, aii kowa yasan keba bazawarar baceba ko??. To ki kwantar da hankalinki, dolefa kema saikin nuna masa baki damu dashiba sanan zaisan darajarki. Saidaifa 'kawata na tayaki murna, dan gay d'in handsome ne wlhy, saima yana gara kwallo a fili, gashi daga gani zaiyi soyayya. Harara yasmeen ta galla mata, ta ce, "kin ganki ko zaki fara­čśĺ. Ameena tayi dariya sorry my dear!, ammafa gsky nafad'a. Yasmeen ta ce, "Ameena yanzu kenan nayi wahalar banza a school. Bakiyiba wlhy tunda kin 'karu da wasu abubuwan,, kuma na tabbata zai barki kicigaba yana dai latsakine kamar yanda yasaba. Aiko saidai ya latsa kansa!, dan insha ALLAHU bazan sake yimasa maganarba. Hakan shine daidai 'yar uwa, nandai sukayita hira abinsu, Ameena tana 'kara koya mata dabaru. ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, To shima dai Nawaf bayan wasu 'yan lokuta tashi yayi yashige office d'in mas'ud batareda muta ne sun gama ganin mas'ud d'inba. Mas'ud yay murmushi, angon yasmeen kaine kake tafe. Harararsa Nawaf yayi ya ce, "kaifa sai ahankali, kulum saikaita abu kamar wanan 'katon kan naka baya kawo maka wuta. Dariya mas'ud yayi ya ce, "nida kai za'a tantance wanda kansa baya kawo wuta. Firij Nawaf ya bud'e yad'akko gwangwanin Moltina yazauna yanasha. Saida mas'ud ya gama sallamar mutane sanan ya juyo gareshi. Nawaf ya ce, "likita bokan turai, dama haka mata suke safa da marwa a office naka. Mas'ud ya ce, "tomiye aciki?, baneman lafiya sukazoba?. Nawaf ya ce, "sunzo neman lafiya kukuma kuna kallesu ko?, ALLAH likitoci ma 'yan duniyane!!!. Hhhhh ku kuma 'yan kwallo 'yan lahira, malam kada kayi mana mummunar fassara kaji. Nawaf ya ce, "babu wani fassara alhaji, nikam gsky bazan bari 'katon banza yaduba mini mataba. Hhhhh mutumina har kafara kishi kenan?, lallai na yasmeen bada kanka asare kaje gida kace ya fad'i. Tsaki Nawaf yaja ya ce, "banza kawai wanda ba'a maganar arzi'ki dashi, ni kagama katuna min wai jiya da daddare saiga marakunyar nan takirani. Mas'ud yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, kai malam dgsk?, to mitace maka??. Nawaf ya ce, "magulmaci harda wani tasowa kai kaji gulma. To ai kaine magul macin tunda kaine ka kawo maganar, plz bani nasha bana son jan rai. Nawaf ya ta6e baki yashiga bama mas'ud labarin jiya, harda kiran data masa yanzu amota. Ido mas'ud yazaro, kai amma bakada kirki, dammi ka ce, "mata bazawara??. Nafad'a ba bazawarar ba ce?, A'a malam yasmeen ba bazawar bace, tunda ba a kaita gidan mijiba, anan aka d'aura yasaki aka baka. Nawaf ya kur6i moltina yana fad'in malam babu wani kwaskwarima daza kamin na yarda. Ai dama basai ka yardaba, d'an rainin hankali kawai. Yakamata yauma kashirya da yamma muje, ko da daddare. Dawa zaka?, Nawaf yafad'a. Dakai mana, ba matarka bace. Tsaki Nawaf yaja ashe zaku dad'e banjeba kuwa, jiyanma dan papa ya takura mini ne wlhy. Hhhhh malam wataran bama zansan ka lalla6a kajeba. Kai dallah saikace wani mara gsky. Dariya mas'ud yaytayi masa, ya ce, "malam inzaka fito fili ka fito kafad'a kana son yarinya, zaka wani zauna kana kauce2. Banza Nawaf yay masa ya d'au wayarsa yana dan danne............✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Kuyi ha'kuri yaudai babu yawa, 'yan nefa suna tamana iskanci da wuta. ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ× ❤luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗21 & 22 ......yau tun farar safiya faisal yazo gidansu yasmeen, tana tana shara a tsakar gida yashigo, zumbur tami'ke tana fitar da numfashi cikin sar'kewa, saikace wadda tayi gudun fanfala'ke. A silo ya 'karaso gareta, hannu yakai da zummar ta6ata, ta kauce da sauri tana harara sa, cikin masifa ta ce, "kai malam bakada hankaline??. Murmushin takaici faisal yayi, ya ce, "indai akan sonkine to banida hankali yasmeen. Ya dur'kusa agabanta tamkar uwarshi, hawaye nata zirara bisa kumatunsa, cikin raunin murya ya ce, "yasmeen plz ki taimakeni ki dawo gareni, nine kawai nake miki soyayyar gsky, wlhy abinda kikaga yafaru sharrin shaid'an ne, da makircin hisham. Ta6e baki yasmeen tayi, ta ce, "kaga banida matsala da wannan, kuma ina mai gargad'inka daga yau karka sake koda kuskuren ta6ani, kai kanka kasan ada ban amince ka ta6a jikinaba bare yanzu danakeda aure.... Da sauri abba yafito domin jin hayaniyar tayi yawa, turus yayi domin tozali da faisal tsugunne a gaban yasmeen. Abba ya 'karaso yana tambayar lafiya dai ko??. Suduka suka dawo da kallonsu gareshi, yasmeen tafara zubar da hawaye tana nuna faisal, shima dai faisal d'in kuka yake, ya mi'ke ahankali yaje wajen abba, dur'kushewa yayi agabansa ya kama 'kafafunsa yari'ke yana gunjin kuka. Hannu biyu abba yasa ya d'agoshi, haba faisal babba dakai ka zauna kana kuka?, miya faru kake kukane??. Hannu faisal yasaka ya share hawayen fuskarsa, yashiga zayyano kalaman nadama daban ha'kuri ga abba, da ro'konsa akan yabashi yasmeen a karo nabiyu zai gyara halinsa. Abba ya ce, "kayi ha'kuri faisal yanzu banida iko akan yasmeen, mijinta shike da iko da'ita, kayi ha'kuri ALLAH zai babaka wadda ya fita insha ALLAH. faisal ya langa6e kai yana hawaye, itama yasmeen hawayen takeyi dan jitake tana wani son faisal d'in yanzu. Ahaka yaseer da umma suka fito suka samesu, yaseer ya ta6e baki danshi faisal baya bashi tausayi ko kad'an. Itama umma lalashi da nasiha takeyima Faisal, amma faisal ba gane yaren nasu yakeyiba, danshi burinshi kawai abashi yasmeen, itace kad'ai nasihar dazatayi masa tasiri. Babu dad'ewa saiga hajiya jummai da dadyn faisal. Suma saisuka kama hawayen dan suna tausayin d'ansu, abba ya ce, "yakamata suje ciki dan wajen akwai sanyi. Bayan sun zazzauna afalo, su alhaji buba sukacigaba da ro'kon abba akan yabama faisal yasmeen a karo na biyu. Abba ya ce, "bansan irin bayanin dazan muku ku fahimceniba, amma yakamata ku gane igiyar auren yasmeen ba'a hannuna takeba, bakuma yanda za'ayi nakira yaronnan na tsareshi akan yasaki yasmeen, kofa na aikata hakan tofa auren bai sakuba tunda ni ba mahaifinsa bane. Kuyi ha'kuri muci gaba da yima faisal addu'ar fatan alkairi.... Afusace alhaji buba yami'ke yana masifa, kai malam yazaka zauna kana jamana rai akan abinda baifi 'karfinmuba, harzaka wanice bayanda zakayi kasaka yaron yasaki yasmeen, shin wai bakada tausayine, baka ganin halin da d'ana d'aya tilo yashigane??, kodan kuna ganin 'yarku tanada 'kyaune??.... Abba ya 'katse Alhaji buba ta hanyar d'aga masa hannu­čľÉ­čĆ╗, kaga karka gaya mini magana, ai bani na ce, "faisal ya saki yasmeen bako??, ko kai ka manta da wula'kantani dayayi acikin taron jama'a ba yasaki tawa d'iyar ba!, sannan wanda kake magana na saka yasaketa shine ya share mana hawayenmu!!, to kuma saboda son zuciya saina sakashi yasaki yasmeen saboda faisal ya aureta???.. Hajiya jummai ta ce, "dan ALLAH kuyi ha'kuri, agaban yarafa muke, da'kyar suka lafa da hayaniyar dasukeyi. Alhaji buba ya ce, "kutashi mu tafi, kuma inaso kasaka a zuciyarka ka mallaki yasmeen ka gama, yana gama fad'a yaja hannun faisal da hajiya jummai sukayi waje. Kuka yasmeen tafasa ta zube afalo tana birgima, umma tasa hannu ta d'agota tana lallashi, abba ya ce, "mamana kiyi shurinki, babu abinda suka isa suyi miki, kuma nanda sati uku insha ALLAHU kina d'akin mijinki. Ni ban ta6a ganin jahilan mutane irinsu alhaji buba ba, in banda jahilci yazakuce wani yasaki matarsa d'anku ya aura, bayan kuma shine yafara tozartamu agaban mutane yasiki yarinyar atake agurin da'aka d'aura musu aure. Umma ta ce, "babu wani jahilci malam son cuciyane kawai yake damunsu, 'kila atunaninsu mu bamu san darajar 'yarba ko???. To aiko zanyi maganin son zuciyarsu kwananan. Yaseer kuwa d'aki yashige yashiga kiran number d'in Nawaf, saidai yayi masa kira yakai biyar bai d'aukaba, dan haka ya ha'kura yay shirin makaranta yatafi. ________________________ Alokacin da yaseer yake kiran Nawaf baya kusada wayoyinsa, yana wajen motsa jiki dayake fita akowace safiyar duniya, inhar yana 9ja. Sai wajen 'karfe 8:00am yashigo gidan jikinsa sanye da farin JC, gajeren wando da 'karamar riga mara hannu, 'kabarsa sanye da takalmin 'yan kwallo, dad'an gudunsa yashigo gidan, yasaka robar ruwan dake hannunsa cikin bola, key yasa yabud'e d'akinsa ya shige. Saida yasha ruwa sosai sannan yazauna yana zufa ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe idanu, yakai minti5 ahaka daga bisani ya cire takalman 'kafarsa ya ajiye. Bedroom d'insa yashiga, yacire kayan ya jefa cikin wani dogon kwando, ya bud'e wata 'yar durowa dake kusada bayi (bathroom) tawul ne aciki kala2, yad'akko kalar yellow ya d'aura daga 'kugu zuwa guywa. Wanka yashiga, ammafa ya dad'e, dan nikam harna fara gajiya ma da jira, ya kai tsawon minti50 sannan yafito, d'aure da tawul d'insa, hannunsa ri'ke da 'karami fari yana goge sumarsa. Zama yayi yashiga tsara ado, na ce, "kai gay d'inana d'an kwalisa ne gsky. Kwalliyarma yakai tsawon lokaci yana tsarata saikace mace lol, daga 'karshe yafito sanye cikin 'kananun kaya ya d'ora tafkekiyar rigar sanyi jaa mai 'kyalli saboda yanayin sanyin garin, sai zabga 'kamshi yakeyi. Zama yayi yay break, sanan ya jawo phones d'insa, ya kira wad'anda suka kirashi baya nan, haryazo kan number d'in yaseer, kira yashiga yi amma ba'a d'agaba, yasake kira, harta kusa katsewa aka d'aga. Mai makon yaji muryar yaseer sai yajita yasmeen, cikin muryarta mai za'ki ta ce, "mai wayar baya nan!. Nawaf ya ce, "ina yaje??. Ita bata gane Nawaf bane, ta ce, "yaje school, amma idan yadawo za'a sanar masa. Daya kula bata ganeshiba saiyayi niyyar zolayarta, ya ce, "toke wacece?. Saida taja numfashi sanan ta ce, "yayarsace. Saida yad'an ta6e baki sanan ya ce, "hummm kodai 'kanwarsa, dan dagajin muryarki "k, yarinya 'karamace. Cikin 'kufula yasmeen ta ce, "kai malam sai anjima, kabi duk ishii mutane da surutu, d'if ta kashe wayar. Dariya sosai Nawaf yayi, ya ce, "kai yarinyarnan 'yar bala'ice wlhy, dawata muryarta kamar ta gyare. Yashiga kwaywayon muryarta yana dariya, tamkar mai kallon film ko wa'ka. --------------''''''--------------------- Da yamma abba ya kira papa awaya yay masa bayanin komai, game da abinda yafaru da safe, maganar ta bama papa mamaki saikace a wasan kwaikwayo, kasaki mace kadawo kana hauka wai kana sonta. Papa ya ce, "karya damu zuwa gobe zaizo suyi magana, yasmeen ta tare kawai agindasa, ta 'karasa karatun a d'akinta. Papa yaji dad'in hakan, yakuma yi farin ciki, koda yagayama umma itama murna taitayi dan wanan shine kawai maganin son zuciya irin na alhaji buba da d'ansu. Yasmeen kuwa batayi murna da hakanba, dan itafa har yanzu zuciyarta bata wani saisaita mata zama da Nawaf ba, tana masa kallon mugune mara mutunci, darashin girmama d'an adam. To yasmeen koma dai miye?, lokacine zai nuna wannan. Da yamma ta saci jiki tashige gidansu Ameena, umma tana d'aki bata saniba, tazata yasmeen d'in tana d'akine, tunda tasaba yini a d'aki, bare yau ana sanyi a garin. Yasmeen kam tana can sunata hirarsu itada ameena da bello yayan Ameena. Saida taga ana kiran wayarta sannan ta mi'ke zaram, number yaseer tagani, tad'aga da sauri tana fad'in bro's yaya dai??. Ya ce, "kina ina?, anata nemanki. Yasmeen ta gwalalo idanu waje tana fad'in naga ta kaina ganinan zuwa. Ameena ta ce, "kije kisha fad'an umma, dan satar fita kikayi, kuma akwai zunubi Hararta yasmeen tayi tafice da sauri batareda tabama Ameena amasaba. A 'kofar gida tayi turus, dan ganin Nawaf jingine a jikin mota, kansa a 'kasa yana danna waya, yana sanye cikin shadda milk, d'inkin iya guywarsa, yayi 'kyau sosai sai 'kamshin tutare yakeyi, yaseer yana gefensa tsaye. Jiki a sanyaye ta 'karasa wajensu. Yaseer ya ce, "sisto wai dama kina nan gidan tund'azu??. Kai kawai ta d'aga batare da tayi magana ba, ta ce, "miyasa kuka tsaya nan??. Yaya ne ya ce, "mu tsaya muga inda zaki fito. Yasmeen ta kai dubanta ga Nawaf wanda tunda tazo ko d'ago kai baiyi ya kalletaba, yanata danna wayarsa kamarma baisan dawata yasmeen a wajenba. Saida tad'an turo baki sanan ta ce, "to kumuje mana, Nawaf ko motsi baiyiba dan haka yasmeen tayi gaba abinta. A falo ta iske umma, umma ta hauta da fad'a, itadai yasmeen fad'i take umma kiyi ja'kuri ALLAH gidan ne naji shiru shiyyasa na fita. Tsaki umma taja ta ce, "aii yayi miki 'kyau tun d'azu mijinki yazo yake jiranki, kinacan inda ba a aikekiba. Shiru yasmeen tayi dan tasan batada gsky. D'an abinda umma tahad'a yasmeen ta d'auka tanufi falon abba, azaune ta tadda Nawaf yana kallo, ita a zatontama har yanzu bai shigoba. Ta dire tiren a gabansa sanan ta koma nesa dashi ta zauna. Suduka kowa ya share kowa, dan Nawaf har yanzu ko kallonta baiyiba, itama saita shareshi taci gaba da harkarta. Sunkai tsawon minti30 ahaka, yasmeen ta daure ta ce, "nikan gsky inada abinyi dan haka zan 'kara gaba. Harara ya watsa mata batareda yayi maganaba, ya d'auki remote ya 'kara 'karan tv dan bayaso umma taji hayaniyarsu, tsam ya mi'ke yanufo inda take zaune. Atu naninta zama zaiyi, dan haka tashiga matsawa tana 'kan'kame jiki. Tsaki Nawaf yayi ya'karasa gabanta, gashinta ya dam'ko ya matse da 'karfi, gaba d'aya jijiyoyin kan yasmeen suka fito, tasaki wani walallen kuka tana 'ko'karin ri'ke hannunsa, gashi ya toshe mata baki da hankacif. Ya zare mata fararen ida nunsa masu girma, ya ce, "wayace kifita?? Yasmeen babu damar yin rashin kunya, saidai hawaye dake fita daga idanunta, ya saki gashin yana fad'in gobe idan kin tashi ki kuma fita bada izininaba, kiga abinda zan miki, baki ta murgud'a masa ta ce, "mugu ALLAH saiya saka mini. Hannu yakai zai kama hannunta ta kauce da sauri, yaja gefe danya kamata saita fad'a jikinsa, mai makon ya ri'keta saiya kama d'an yatsanta, tako daddage ta galla masa cizo a d'ayan hannunsa. Da sauri ya saki hannunta yana yarfe nasa hannun, abinka da fari gurin har yayi jajur, ga shatin ha'koranta awajen rad'a2. Nawaf ya rintse ido yana murza wajen, dariya sosai yasmeen takeyi, ta ce, "kaji idan da dad'i kaima. Ya bud'e ido yana cije le6ensa na 'kasa, har yanzu wajen zafi yake yi masa, ya ce, "ni kika ciza ko??. Baki ta murgud'a­čśĆ masa, gobema idan ka 'kara gwada mini mugunta saina yimaka wanda yafi wanan, mugu kawai. Wani murmuahi Nawaf yasaki mai kamada ya'ke­čśťya ce, "banza kuriya­čÉů, wlhy idan na kamaki zaki gane kuranki. ­čśťgwalo yasmeen tayi masa ta ce, "saidai mu gane kurenmu wlhy. Kwafa yayi ya ce, "yarodai baisan wutaba saiya taka. Nunata yayi­čĹë­čĆ╗­čĹę­čĆ╗yana fad'in kuma wlhy kifad'ama wannan jahilin daya sakeki aka 'ka'kaba mini, daga yau nasake jin yazo gidanna saina sa an 6atar dashi, dagashi har jahilin ubansa, idan kunne yaji jiki ya tsira. Kemad'in bance karki 'ki fitaba, saidai idan kika cigaba da karya dokata zaki cigaba da shan ba'kar wahala ne, danni ba sa'anki bane. Yana kaiwa nan ya fice dama har anfara kiraye2 sallar magriba. Dariya tasaka harda tafa hannaye, ta ce, aii dai kasha cizo azzalumi kawai, aii wlhy na daina 'kyaleka kana sakar min kwanjinka a banza, idan kafi karfina aibakafi karfin cizoba, zakayita shan cizone harsai hannunka yakoma da zanen ha'korana ko ina. _______________________ D'aki tanufa tayi sallar magriba, tana nan zaune tana karatun alkur'ani har akayi sallar isha'i. Bata fitoba dan tasan umma tana ciki da ita, saida tabari yaseer yadawo sanan tafito, ganin baya falo yasa tanufi d'akinsa. Saman gado ta tarar dashi ya bud'e waya 'katuwa akwalinta yanata kallo yana murna, NAWAF ne ya sayamasa. Yasmeen ta murtike fuska, cikin masifa ta ce, "yaseer yaushe kazama munafiki, kai har ka fifita bare akan ni 'yar uwarka??. Ubanwaye yasaka gayama wancan mugun faisal yazo gidanan da safe??. Yaseer ya had'e fuska, kai kaji sisto d'innan koda ban fad'aba ma aii abba ya fad'ama abbansa, kuma nasan zai gaya masa, zaki wanizo kina zagina, yafad'a yana turo baki gaba. Tsawa yasmeen ta daka masa dallah malam rufe min baki, munafiki kawai, wanda bai iya ri'ke sirrin gudansuba, saboda an kawo maka waya kazauna kasaki baki kana zuba gulma da tsigudidi. Wlhy daga yau nakuma jin maka manciyar wanan maganar saina daka ka agidanna, idan kaji 'karya ka 'kara, sakarai kawai, tayi waje. Yaseer yabita da kallo yana murgud'a baki, an fad'a d'in, kumani ba magulmaci bane. Kinason mutum kina wani kauce2, ai tuni na harbo jirginki­čśťooooh, yafad'a yana dariya. Nawaf kam cikin haushi yaje gida, koda yayi sallar magriba da isha'i bai nemi mas'ud ba, dan yanada aikin yamma shiyyasa basuje tareba. D'aki yadawo yay kwanciyarsa, kad'a2 saiya kalli inda yasmeen ta cijeshi, wajen yayi jajur. Yasaki murmushin mugunta, wlhy yarinya sakinyi dana sanin cizonan dakikamin, mara kunyar banza kawai, yay kwafa yana gyara kwanciya. Ahaka mas'ud yazo ya sameshi, ya zauna yana fad'in angon yasmeen kabarota lfy??. Banza Nawaf yay masa. Mas'ud yay murmuahi oh baza'a amsa miniba angon yasmeen??. Cikin masifa Nawaf ya ce, "kasan ALLAH mas'ud ka daina had'ani da wanan yarinyar inkuwa ba hakaba zamu sami matsalane. To miye dan munsami maysalar alhaji???, wata ran basai mu shiryaba. Nawaf yatashi zaune yana fad'in wlhy mas'ud saina koyama yarinyar nan hankali kwanannan. Hummm mitayi maka dazaka koya mata hankali. Hannunsa ya nuna masa ya ce, "kalla ka gani waini yarinyarnan ta ciza. Mas'ud yatuntsire da dariya, kai saikace wata kura??. Ai tafi kura Nawaf yafad'a yana gyara zama, nan yabama mas'ud labarin abinda ya had'asu. Mas'ud ya ce, "Ah wanan laifinkane alhaji, aiba haka ake hukunta mutumba idan yayi laifi. Tsaki Nawaf yaja ya ce, "wanan kuma matsalar kace.........................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× page­čĹë­čĆ╗23 & 24 ......WASHE GARI...su papa sukazo shida 'kaninsa dayazo daga katsina, dakuma Abban mas'ud, bayan angama gaishe2 suka shiga tattauna abinda yakawosu. An 'kar'kare magana za'ayi shagalin biki nanda sati hud'u masu zuwa, (1monch )sananan su Nawaf sun gama wasan kofin africa kenan, kafin yakoma Spain sai asha shagalin biki kawai. ­čĺâ­čĺâ­čĺâ­čĺâkai zamu shabiki, kowaya yashirya masu karatu­čśť. Bayan an 'kar'kare magana yasmeen tashigo ta gaidasu, 'kanin papa ya yaba kam da tarbiyyar yasmeen , yanada tabbacin Nawaf yayi dace!!!!!!!. ------------------------------------- Yau dai gaba d'aya family d'in suna falon papa, Nawaf yana kwance a kujera mai zaman mutum biyu, Anwar yana saitin kansa ri'ke da littafin larabci, Nawaf yana koya masa, Abdallah kam hankalinsa yana kan tv dan shi dama d'an a hutane. Papa da momcy suna gefe zaune papa yana nazarin wasu manya2 littatafai shida momcy, da alama bincike yakeyi akan wata shari'ar, momcy tana tayashi, tunda itama mai ilimince­čĹŹ­čĆ╗. Nawaf ya ce, "Abdallah tashi kakawo mini ☕lifton. Abdallah yad'an turo baki gaba, yaya dan ALLAH bari ad'an wuce nan. Harararsa Nawaf yayi, ya ce, "to uncle Abdallah bari najiraka, da sauri Abdallah yatashi dan yasan gatse yay masa, yana kuskurewa saiyasha mari abanza, dan Nawaf akwai saurin hawa kamar filawa­čśťlol. Momcy ta ce, "ya ALLAH kashirya mini Abdallah. Sukace amin. Papa ya ce, "aii Abdallah shike bama kowa ciwon kai agidannan. Abdallah yashigo d'auke da butar shayi mai 'kalli da 'karamin kofi da cokali, agaban Nawaf ya dire batare da yayai maganaba. Girgiza kai kawai Nawaf yayi yad'auka yazuba yana sha, ya ce, "yaro nafika zafin kai. Papa ya ce, "yau modebbo yaushane zaka koma abuja??. Papa gobe idan ALLAH ya kaimu da yamma. Okey ALLAH yakaimu, aii momcy tamaka bayani akan tarewar matarka ko??, Nawaf yad'an rage fara'a, eh tagayamin, amma papa dan ALLAH abari saina koma Spain idan mun gama (KAKAR WASANNI), nadawo tunda muna samun hutu awanan lokacin saita tare!!. Kagafa ko inda za'a ajiyeta babu, amma zuwa sanan an kammala ginina!!. Agidan Nawaf yake gini tacan baya, saboda papa yanada burin zama da iyalin guru ─Ćaya yasa yasayi filin dake ha─Će da nasa yazagayeshi kowa ya girma cikin 'ya'yan saiya gina 6angarensa. Toshi Nawaf ya─Ćan fara ginin ya watsar, gashi koma aure yaro yanzu. Girgiza kai papa yayi, ban yardaba Modebbo, kafin katafi za'ta tare, 6angarenka za'a gyara muku yanzu saiku fara zama anan, anjima ka cire dukkan abinda kakeso daga 6angarenka kadawo dasu ─Ćakin kusada nawa, dan za'a gyara 6angarenka asake komai naciki insha ALLAH. idan kazo wanan hutun saika tafi da matarka kawai, munriga mun gama yanke magana, yanzu hakama 'yan katsina sunsan komai, kuma yau dasafe nakira 'yan saudia na sanar musu, nextweek ma (MAHER da ZAID) zasuzo, 'kannanen momcy ne. Shiru Nawaf yayi dan zucuyarsa sai tafarfasa take, yanzu sai kawai abokansa suzo suga wanan 'yar yarinyar ya aura, gata mara kunya, kuma 6angarensa bedroom ─Ćayane, kenan papa yana nufin a bedroom ─Ćaya zasu zauna kenan???...... Momcy ta katse masa tunani da fad'in yakamata ka sanar da abokanka, tunda yazu zamanine mai sau'ki komai zaka iya yi ta hanyar SOCIAL MEDIA. Nawaf ya ce, "to momcy zanyi 'ko'kari nida mas'ud, amma sainake ganin abun kamar babu shiri??. Miye rashin shiri anan modebbo, acikin wata d'aya mu zamu shirya komai, shiyyasa na ce, "su maher suzo!. Su Alhaji buba ba muta nen kirki bane, zasu iya aikata duk abinda tu naninsu yabasu. Momcy ta ce, "gsky ne Alhaji. Su Anwar suka shiga tsallen murna, za'ayi biki agidansu, shi dama Anwar bai ta6a ganin anyi taro agindansuba tunda shine auta, gara Abdallah yaga taron sunan Anwar d'in. _________________________ Ita madai yasmeen wanan labarin ya iso mata, saidai suna hanya d'aya da ango itama batayi murnaba, saima kuka data zauna tanayi, umma ta ce, "hawayen gareki dayawa yarinya, ke komai akayi sai kuka saikace hanyar ruwa, haka zakije gidan mijin dayayi miki abu ki hau kuka??, A─╣LAH yabaki sa'a. Abba shidai lallashinta yakeyi, yayinda yaseer keta kwasar dariya danshi farinciki fal cikinsa. Da yamma Nawaf da mas'ud sukazo, fuskar ango da amarya babu walwala, bayan ta gaishesu mas'ud kawai ya amsa mata, ya ce, "Amarya ina 'kyauta ta??. Yasmeen tayi d'an murmushi, ta ce, "bari nakira maka ita, tana son tashi tana tsoron Nawaf ita kuma bazata tambayeshiba wlhy, kamar daga sama sai sukaji sallamar Ameena, yasmeen ta ce, " 'yar halak. Ameena ta zauna tana fa─Ćin to miya faru??. Tunda tashigo mas'ud ya yaba, kuma insha ALLAH yasamu matar aure kenan, Ameena ta gaishesu, amamakin yasmeen saitaga Nawaf ya amsa harda murmushi, ya ce, "Ameena zaki auri tuzurin abokina kuwa???. Harararsa mas'ud yayi ya ce, "kai malam waye tuzurun???. Cikin dariya Nawaf ya ce, "kai mana, aii itama tasan kai tuzurune 27years babu aure fa. Mas'ud ya ce, "ashe kaima tuzurinne??, yasmeen kinji tuzuru kika aura!!. Haka sukayita tsokanar juna, kuma anan aka kulla 'kya'ky'kyawar ala'ka tsakanin amina da mas'ud. Ficewa sukayi suka bar Nawaf da yasmeen a falon, suma suka tafi domin yin tasu hirar. Nawaf ya mirtike fuska, ya ce, "k kice su papa su tsaida maganar bikinnan dasuke shirin yi!!. Yasmeen ta yaysine fuska, "kai miya hanaka ka fad'a musu naga kaine Namiji. Harara Nawaf ya sakar mata, sai akace miki ni mara kunya ne irinki!!!. Baki yasmeen ta ta6e tace ashe.... Yay saurin cewa ashe mi???. ­čśĆta murgu─Ća baki tana fa─Ćin sainaji zafin ma'kara. twoow tsaki Nawaf yayi yana fad'in yarinya ki ajiye rashin kunyarki a gefe dan wlhy yanzu wahala zakisha bata wasaba. Yau ba shirmenki ya kawoniba dan inada abinyi, gobe zan koma abuja, duk abinda kike bu'kata ki sanarma mas'ud. Hummm kaidai kasha cizo malam, yasmeen tafa─Ća a zuciyarta. Saida ya'kara mirtike fuska sanan ya ce, "ki koma makarantarki idan kina ra'ayi. Cikin murna yasmeen ta ce, "dgsk??, harararta yayi ya ce, "k bana son shirme kinji. Baki ta murgu─Ća­čśĆ masa, ya ce, "dawa kike???, ta ri'ke 'kugu­čĹ»da wanda ya tsargu mana. Nawaf yay murmushi danshi dariya ma tabashi, yakula ta rainashi da yawa, amma zai koya mata hankali kwanan nan, ya ce, "habawa yarinya wataran ko ance kiyi mini rashin kunya bazakiyi ba wlhy. Kud'i ya ajiye mata 'yan dubu2 ─Ćauri biyu, ya mi'ke, karki ─Ćauka dan bananan ko dannance ki koma makaranta ki ─Ćauka kinsamu hanyar yawo, nasaka masu kulamin da shigarki da fitarki, idan naji wani abu sa6anin dokar dana kafa, tofa kiyi kuka da kanki, yana gama fa─Ća ya fice. Harara yasmeen tarakashi da ita tana fa─Ćin sai an karya dokar taka, tunda ba dokar ALLAH ba ce, "mutun ya rin'ka abu saikace wani ubana. Tashiga kwaykwayon maganarsa yanda yakeyi a─úadarence. __________ABUJA________ Bayan kammala (colfine second round) da akayi, Najeria ta tashi da maki 7. To ayau kuma zasu buga da Egypt, (colfine cotter pineal) wasan daf da 'karshe ke nan. Wasa yayima 9ja da─Ći, dan antashi 1-0, 9ja 1 & Egypt 0 Karkuga murna wajen 'yan 9ja. 2days later. (Seme pineal) wasan kusada 'karshe, 9ja da South Afirica, wanan kuma ankai ruwa rana, dan sai ana saura minti2 atashi, cosee!, wani ─Ćan wasan 9ja yay wani fasin da Nawaf yasamu damar antayawa 9ja kwallon cikin ragar south Africa, guri yaru─Će da ihu Najeria sai murna mukeyi. Dukkanin wasanan yasmeen ta kalla, dukda bawani burgeta yakeyiba, amma takanji tana sha'awar kalla, da antashi zakaga yaseer yakirashi yana masa murna, takan ta6e baki ta ce, "ma yaseer uban 'yan shishshigi kawai, ─Ćan san asani. Oho dai yaseer yafa─Ća, kema san asani ─Ćin yasa kike kallon kwallon yanzu tunda da ba'ka kallo da. Duka ta kaimasa ya kauce, cikin shagwa6a ta ce, "umma kinga yaseer ko yana tsokanata. Umma ta ce, "kunfi kusa, kubar sakani ashirmenku kunji. Yaseer yatashi yafice yana mata gwallo­čśť. Kwafa tayi ta ce, "zaka dawo ka sameni yaro. Yaune za'a buga wasan 'karshe, yaukam stadium d'in abuja babu masaya tsinke, dan yau harda shugaban 'kasar NAJERIA shima yazo. Bayan gama addu'a da abinda yadace,Najeria da Algeria suka fara buga wasa, kowa iya 'ko'karinsa yake a wasanan, dan haka har aka tashi hutun rabin lokaci babu wanda ya zira kwallo. Bayan andawoma gwagwar maya aka cigaba dayi, amma ina komai bai canjaba, tun ana saran wani zai ci har aka fitar da rai, lokaci yacika aka'ara, shima ya shu─Će babu wanda yaci, dole saidai ayi (peneritty). *Algeria ⚽tafara zirama 9ja *Najeria ⚽ sai 9ja itama ta zira *Algeria ⚽ *Najeria ⚽ *Algeria ⚽ *Najeria ⚽ *Algeria ❌9ja tazubar *Najeria ⚽ *Algeria ⚽ *Najeria ⚽Nawaf ya zira mana ta 'karshe. Dukkan filin da sassan gidajen kwallo dake Najeria suka d'au ihu na murn, bakin kowa abu─Će, shugaban 'kasa yayi murna sosai. Duk da kwallo bata burge yasmeen to yau tayi murna sosai, sai murmushi takeyi dan da─Ći. Na ce, "humm yasmeen kodai???????. Bayan shugaban 'kasa ya karramasu kowa yanufi inda yafi wayo, (club club nasu kenan) Shidai Nawaf kano yataho..................✍­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗25 & 26 ....To shima dai mas'ud a6angarensa komai ya dai2ta, har ankawo ku─Ći dan anaso ayi bikin tareda na Nawaf, yasmeen tayi farinciki sosai da faruwar haka, bare ameena amarya, ai tafi kowa farinci, dan tana son mas'ud sosai. Yau kuma aka kawo lefensu su duka akwatuna bakwai2, komai iri ─Ćaya, wanan aikin papa ne, dan shida momcy suka ha─Ćo lefen. Wannan shi ake Kiran lefen 'yan gata, mutanen anguwa da dangi duk sun yaba. Filin jirgin na kano cike yake da matasa domin tarbar NAWAF!!. ­čŤČjirgi yafara shawagi neman muhallin sauka, bayan tsayawarsa fasinjoji suka fara fitowa, Nawaf shine na 6, ahankali yake sakkowa kamar bayaso, jikinsa sanye da 'kananun kaya, ya ─Ćora 'katuwar rigar sanyi fara, ya saki hular a baya, sai tashin 'kamshi yakeyi, yagoyo jar jakka abayansa wadda aka rubuta (Adidas)na ce, "kai gay ─Ćinnan handsome ne gsky. Da gudu anwar yaje ya rungumesa, shima cikin farinciki ya rungume shi, yana fa─Ćin i missing u autan momcy. Missing u too yayana. Gaba ─Ćaya 'yan uwa da abokan arzi'ki suka taso gareshi, 'yan jarida kuwa sai 'kutsa kai sukeyi domin samo bayanai. Da'kyar suka barshi yashiga mota mas'ud yaja suka nufi gida, anata ─Ćaga masa hannu shima yana ─Ćagawa. Abdallah ya ce, "yaya dabamu samu mun gudoba dasai yamma zamu baro filin jirginnan. Nawaf ya ce, "gsky ne brother shiyyasa naso na sauka da daddare. Mas'ud yay dariya ai koda daddaren ne sai mutane sun jiraka tunda anuna a labarai zaka sauka kano yau, aii ko randa kazo daga Spain mutane basu taru hakaba??. Abdallah ya ce, "to ba sunga ya cimusu kwalloba yau, suka tuntsure da dariya su duka. Anwar ya ce, "nifa wani tsareni yayi saina bashi number yaya, na ce, "masa banida waya kuma ban ri'ke number ba. Mas'ud ya ce, "hummm autan momcy sarkin wayo. A babban tsakar gidan sukai Parking, Nawaf yasha mamaki dan ganin dangi cike da gida, 'yan katsina da saudia, duk sunzo, dangi sai rungumeshi ake ana murna, musamman 'yan saudia dansu dama al'adarsuce. Family falo suka nifa inda sauran dangi suke harda kakarsu Nawaf ta wajen uwa tanan darai hajja humaira kenan. Hajja humaira ta ringume Nawaf tana farin cikin ganinsa, ta ce Masha ALLAH mai gida ka 'kara 'kyau da girma, kodai an canja mini kaine??, Nawaf yay dariya A'a hajjana ba a canja miki niba ninedai maigidanki na 'karfen!!!. Gaba ─Ćaya akasaka dariya, ta ce, "kamanta damu ko Nawaf!!?, da sauri ya 'kara rungume hajja ya ce, "ni na isa na manta daku, uwargida sarautar mata, hajja nayi missing ─Ćinki sosai. Hajja ta ce, "─Ćan nema kai dai bazaki hausarba bare larabcin?, turawa sun 6ata mana ka!!. Nawaf yay murmushi yabi dukkan iyaye da kakannin yana gaishesu, har 'yan katsina. Ya ce, "ni banga sauran sisters ─Ćina ba??, kobasu zoba??. Tab wazai 'kizuwa bikin ka (Abi)yaya kenan, kowa yazo, sauran suna gidan amaryarka, muma yanzu za'a kaimu, wai a al'adar hausawa yaune ('kunshi)to zamuje mu ganine!!. Nawaf yay murmushi, lallai kam idan kun gani saiku koya koh??, dariya ameera tayi ta ce, "to Abi!!. Duk da larabci suke maganar, ina fassara mukune yanda zaku gane­čśťlol. D'akin kusada papa ya shiga inda ya maida kayansa kafin yatafi, yay wanka, yaci abinci, kwanciya yayi domin ya─Ćan huta. Sai wayarsa ta hau wringing, mas'ud ne yake kiransa, ya ce, "─Ćan uwa ya akayine??, ya ce, "tambayata ma kakeyi?? To kafito muje wajen kamu. Nawaf ya yatsine fuska, miye kuma kamu??, dariya mas'ud yayi ya ce, "idan munje zaka gani, kai malam nidai hajja haka ta ce, "mini sai gobe. Dariya mas'ud yayi ya ce, "nima wasa nake maka, bari nabarka kayi barci ka huta, sai mun ha─Ću anjima. Okey bye­čľÉ­čĆ╗Nawaf yafa─Ća yana ─Ćaga masa hannu kamar yana ganinsa. ____________________________ A 6angaren yasmeen kuwa suna gidan su ameena anan ake zaman 'kunshi, gidan cike yake da 'kawayensu da dangin Nawaf larabawa da 'yan katsina, muta nen saudia dai basa jin hausa saidai turanci, dan haka gurin yazama dandalin turanci, tunda duk sunaji. Wata mai 'kunshi aka ─Ćakko tanama amare yasmeen da Ameena ta iya sosai, saikuma wasu su biyu sunayima 'kawayen amre suma kam gwanayene, yasmeen bata cikin walwala, amma bataso dangin Nawaf su gane dan haka ta saki jiki anata hira, Ameena ce kawai take gane damuwarta. suma sai jida ita sukeyi, wata budurwace dai yasmeen takula batada walwala, tunda sukazoma tanemi guri ─Ćaya ta zauna ita ka─Ćai, (ummu habeeba ce) tana mutuwar son Nawaf, ita ce Nawaf ya ce, "ta cika 'kyau, kuma gsky ya fa─Ća dan tafi sauran 'yammatan 'kyau gsky. Sai dare aka maidasu gidansu Nawaf,, Nawaf yana zaune a harabar gidan tareda sauran samarin 'yan uwansa na katsina dana saudia, anata hira da raha. Moto ci suka fara sauke 'yammatan, wajansu suka nufo suna mai farin cikin ganin Nawaf, gaisuwa aka shiga yi irinta al'adar larabawa, ummu habeeba kam saita tokare agefe ta'ki zuwa, Nawaf yana ganinta ya shareta, saida ga baya kuma ya mi'ke ya nufeta. Tana sanye cikin ba'kar jallabiya ta na─Će kanta da ─Ćankwalin kamar yanda larabawa keyi. Ya tsaya yana kallonta, ta harareshi nagode abi tafa─Ća tana turo baki gaba. Yay ─Ćan murmushi minayi miki kike yimini godiya??, tai far da idanu, ta ce, "kaima kasani. Yay murmushi har fararen ha'koransa suka bayyana, yasan inda ta dosa amma saiya basar, ya ce, "kinga koma mikike ganin nayi miki to ki share ki tayani murnar aurena kamar yanda kikayi niyya tun farko, wananne zuwanki 9ja na farko ko??. Bataso aka daina waccan maganarba amma yazatayi tunda ya nuna bayaso, ta ce, "eh shine na farko, ahaka dai sukaita hirarsu, cikin harshen larabci. _______________________KAMU. Yau takama kamu, kamu kuwa za'ayi irin na saudia ne, a harabar gidansu ameena za'ayi saboda yafi girma, an 'kawata gurin da kwalliya mai tsari, an baza 'katuwar darduma inda amarya da ango zasu zauna, agefe kuma an jere fararen kujeru inda sauran mutane zasu zauna. Hajja ce tazo da kanta ta ro'ki su umma akan abarasu suma suyi al'adarsu ta larabawa a wajen kamu, su umma sukace babu damuwa suma sunada iko akan komai aii. Wajen 'karfe 4:00pm na yamma aka gama shirya amarya cikin ba'kar doguwar riga ba'ka mai ─Ćan karen 'kyau, gashinta yasha gyara an ─Ćaureshi abaya wanda bai saniba saiya ─Ćauka itama balarabiyar ce, dan NAFISAR KADUNA ce ta tsara mata kwalliya wadda amaren zamani suke yayi. Kowa ya hallara sai amarya datake falo tana jiran isowar ango, dan tare akeso su fito. Bayan kamar minti10 ango ya iso da tawagar abokansa, kowa ya zauna inda ya dace, aka raka ango inda zai ─Ćakko amaryarsa. Kai kawai ya tura cikin falon batarda yayi sallamaba, tana zaune akujera hankalinta yana kan waya tana game. Ai gogan naku yana tsaye ya daskare dan ganin tsarin hallita irinta ubangiji, gsky koba komai yayi dacen mata 'kya'ky'kyawa rashin kunyartane kawai matsalarsa. Jitai kamar alamar mutum yana kallonta, ta ─Ćago da sauri, Nawaf tagani tsaye kamar gunki yayi masifar 'kyau cikin kayan larabawa wando da riga farare, anyi musu kwalliya da golden ─Ćin zare, sumarsa tasha gyara daka gansa kaga cikakken balarabe. Saida ta murgu─Ća masa baki­čśĆta ce, "malam lafiya??, katasani gaba kana kallo, mi naci naka??. Hararar ta yayi ya ce, "ki ajiye makaman rashin kunyarki har zuwa nanda kwana uku, domin yanzu ina kan bin umarnin iyayenane, bazanyi abinda zai 6ata musu rai ba agaban ─Ćumbin jama'ar dasuka tara. Yay wani murmushin mugunta, ya─Ćora da fa─Ćin amma nanda kwana uku, ko ance ki kalleni kimin rashin kunya wlhy baza kiyiba, dan zanyi maganinki 'karamar mara kunya kawai. Ta bu─Će baki domin mayar masa da amsa sai aka turo 'kofar.....wata 'kanwar momcy ce Fateema, ta ce, "Abbuna ku ajiye wannan soyayyar taku sai nan da kwana uku dan yanzu mutane suna jiranku. Nawaf ya─Ćan sosa gefen wuyansa ya ce, "sorry Abla(aunty kenan) muna zuwa. Ya juyo ya harari yasmeen sanan ya 'karasa wajenta, hannunta yakama, jikin yasmeen yay wani yarrrrrrr, shimadai gogan naku saida sassan jikinsa suka amsa, Abla fateema ta gyarawa yasmeen ─Ćankwalinta tabaya, sannan ta rufe mata fuska da wani jan gyale. Nawaf ya ce, "Abla ai bata gani, idan ta fa─Ći fa??. Abla tayi dariya kai ka bari tafa─Ći bayan kaine ─Ćan jagora. Ya ce, "hakane idanma kin amince na ─Ćauketa gaba ─Ćaya naje na dire awajan. Abla fateema ta tuntsure da dariya ta ce, "babu ruwana. Yasmeen ta ce, "azuciyarta mugu saika nemi wadda zaka ─Ćauka amma baniba. Catake a zuciya take magana bata san afili takeyiba dan Nawaf yana jinta, amma Abla bataji tunda da hausa take maganar kuma ahankali. Bayan sun fito gurin ya ─Ćauki tafi, wajen kujerar da'aka tanadar musu mai ─Ćan fa─Ći sukaje suka zauna, saidai sun matsu juna sosai, yasmeen sai takurewa takeyi. Agaban kujera aka shimmfi─Ća dardumar daza ayi kamu. Ba6ata lokaci akayi addu'a ga ma'aurata, har yanzu fuskar yasmeen a rufe take. Nawaf tya ce, "malama nifa kin matseni. Dariya bin yabama yasmeen dan haka tayi murmushi, ta ce, "kanka akeji wai mahaukaci ya fa─Ća ruwa. Nawaf yay murmushi mai sauti, kema za'aji kankine yarinya, dan ─Ćazu ina jinki. Idan kagansu saika ─Ćauka hirar arzi'ki sukeyi. Bayan angama addua aka fara shirin kamu, ango da amarya suka sakko 'kasa kan dardumar, suna fuskantar juna fuskar yasmeen arufe. Wani ha─Ća─Ć─Ćen kwando aka ajiye agefensu wanda yake cike da turarurruka kala2 masu tsada da 'kamshi, abla ta su'ko tanama Nawaf magana acikin kunne da larabci, wanan yasa yasmeen bataji abinda suke fa─Ćaba, yay murmushi tareda jan kwandon gabansu. Saida akasaka wa'ka wadda akayima ngo da amarya amna da larabci, sannan aka bama ango umarni yashiga cikin gyalen da'aka rufe fuskar yasmeen dashi. Ya yaye ahankali ya rufa akansa, yazama su biyune aciki. Kan yasmeen na 'kasa Nawaf ya ce, "ina fata dai al'adarmu ta 'kayatar dake, ta─Ćan ─Ćago ta kalleshi ganin ya kafeta da idanu yasa ta maida kanta 'kasa da sauri. Turare ─Ćaya aka mi'ko masa yashiga fesama yasmeen, harda mugunta saida ya 'karar da turaren duka ajikinta, saboda 'karamar kwalba ce, fitinannen 'kamshin ya gauraye wajen. Ya yaye mayafin daga fuskokinsu, gaba ─Ćaya gurin aka saka tafi, daganan kowa yataso saiya ─Ćauka a kwandon yazo ya─Ćan fesa musu, saida kowa ya fesa sanan aka rufe taro da addu'a kowa ya kama gabansa. ____________________________ Yau aka ─Ćaura auren mas'ud da Ameena, ALLAH yasanya alakairi mas'ud. Da yamma aka tafi bababan filin kwallo na kano anan za'a buga wasan biki, wanda (KANO PILLAS SUKA SHIRYA DOMIN KARRAMA ANGO) an tsara wasanne 6angaren ango da amarya, abokansa 'yan kwallo dasukazo daga 'kasashe daban2 da 'yan kano filas, 'kuria aka yi idan ka ─Ćauki 6angaren ango kona amarya to suzaka bugawa. Wasankuwa ya 'kayatar dan har a labari aka nuna, antashi 8 da 5, ango 5 &amarya 8. ------------------------------------------ Da daddare aka shirya kai amare ─Ćakinsu anan naga kuka, yasmeen kuka take kamar ranta zai fita, sai nasiha da lallashinta akeyi, hakama ameena. Da 'kyar aka 6an6are yasmeen daga jikin umma, tanata kuka dafa─Ćin bazatajeba itafa tafasa aueren, amma ina, tuni aka dannata amota, sai gidan ango. An mi'ka Amin gidansu mas'ud yasmeen kuma gidan su Nawaf, a ─Ćakin momcy. Bayan kamar minti30 aka shiryasu zuwa wajen gagarumar dina da abokan Nawaf suka shirya, amma sun ha─Će harda mas'ud, ammafa wajen ya 'kayatu sosai. Amare sunsha shiri cikin rigunan aure, yasmeen sai masifa takeyi, wai rigar arna, Nawaf yana jinta yay mata banza. Komai ya 'kayar agurin, amma wajen bada cake Nawaf saida ya ciji hannun yasmeen, tai wata 'yar 'kara, wadda tasa muta nen gurin ihun dariya a zatonsu duk cikin soyayyane­čśťlol. Sai shabiyu aka tashi, idanun yasmeen cike da barci, suka fiffito tana tanga─Ći, ga wani dogon takalmi data saka, tako goce zata fa─Ći da sauri Nawaf ya tarbota ta fa─Ćo jikinsa, sai kawai ta lumshe idanu dan barci takeji. Girgizata yayi da 'karfi, ke dallah malam tashi karki karya mini hannu, inko ba hakaba zan sakeki ki fa─Ći 'kasa ALLAH. yasmeen batasan yana yibama, Kausar ta ce abi! ka ─Ćauketa kawai wlhy barci takeyi tagaji dayawa ne. Bayaso danginsa su gane komai gameda auren, dan haka ya sa6eta kawai sai ─Ćakin momcy, ALLAH ya taimakesa ma 'yammatan ne a 6an garen momcy, kuma babu wadda yake jin kunya acikinsu. Ruwa ya ─Ćauka a saman madubi da wata tasha tarage, yazuba ahannusa ya shafa afuskar yasmeen, tako kawo numfashi. Ahankali ta bu─Će idanu tana kallonsa, ya ce, "ke kitashi kicire wanan rigar, sanan ki kwanta yana gama fa─Ća yafice, da'kyar ya iya tashi tacire, ta koma ta kwanta................✍­čĆ╗ Na ce, "asuba tagari yasmeen. ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗27 & 28 ......Washe gari akayi walima, dakuma wa'azi wanda manyan malamai suka gabatar. Masha ALLAH wanda akayi dansu sun 'karu sosai, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a. Kowaya kama gabansa, musamman ma abokan Nawaf dasukazo daga 'kasashe daban2, karfe 2:30pm na rana jirginsu ya ─Ćaga, cikin 'yan katsinama wasu sun tafi mazansu da matansu, sai 'yan ka─Ćan aka bari. 'Yan saudia ne dai sai gobe wasu zasu tafi. 8:30pm Da daddare aka shirya yasmeen tsaf, dan za'a maida ita 6angaren Nawaf, wata 'kanwar papa tashigo tana fa─Ćin amarya tashi akaiki ─Ćakin ki ko??. Yasmeen ta marairaice fuska kamar zatayi kuka, ta ce, "inna dan ALLAH abarni anan, yafi da─Ći ga abokan hira. Murmushi tayi, ta ce, " 'yanan idan anbarki anan ─Ćakinki kumafa, da angoki, mukuma dakike gani nanda jibi bazakiga kowaba fa?, dan haka tashi muje kinji 'yar albarka. Badan yasmeen tasoba ta tashi suka rakata, wooow!! Lallai an gyara 6angaren Nawaf sosai an sake masa fenti, sannan komai na 6angaren an sake, tundaga kujeru labulaye tv kayan gado, komai ansake, dama papa cayayi karsu abba suyi komai, amma duk dahaka saida umma tasayi kayan kichin masu yawa, aka kawo, gakuma wanda momcy tasaya, kichin ─Ćin kam aii ya 'kayatu da 'kyau. Tana kuka suka tafi suka barta bayan an kaita bedroom ─Ćin Nawaf, wanda shi ka─Ćaine a6angaren nasu. Falo ne babba sai bedroom, kichin da sito, dakuma wani 'karamin ─Ćaki agefe wanda Nawaf yacika da kayan motsa jiki, sai kuma wani ─Ćan fili awaje wanda aka 'kawata da kujeru masu 'kyau domin hutawa, komai yayi awajen kuma komai naciki 6angare lemon green ne. Yasmeen tana zaune a tsakkiyar gado inda su inna suka barta, kuka taketa yi, na ce, "dama aike gwanace wajen iya kuka. Har 'karfe goma Nawaf bai shigoba ta mi'ke ta cire kayanta ta canja da marasa nauyi, gadon ta haye batareda wani tunaniba ta kwanta abinta, dan danan barci yay awon gaba da ita. Nawaf kam yana ─Ćakin daya koma harma ya kwanta, momcy tazo kawoma papa lifton sai taga wuta a kunne, ta ce, "oh ni modebbo akunne yabar wutar ─Ćakinnan, tura 'kofar tayi tashiga da nufin kashe wutar, turus tayi dan ganin Nawaf bisa gado yayi ─Ćai2 yana barci. Kai ta girgiza ta 'karasa gaban gado tafara kiran modebbo! Modebbo!!. Nawaf ya bu─Će idanu ahankali yana kallon momcy. Ta ce, "mikakeyi anan???. Ya ce, "momcy kamar ya??. Hararar sa tayi, ta ce, "shine kabaro matarka ita ka─Ćai kazo nan ka kwanta, maza katashi kafin raina ya 6aci kawuce ─Ćakin matarka. Baki ya bu─Će zaiyi magana........da sauri momcy ta ─Ćaga masa hannu­čľÉ­čĆ╗kaga bana son jin komai, katashi kawai ka tafi. Bayanda zaiyi dole ya mi'ke wayoyinsa kawai ya ─Ćauka, dan tunda rana momcy tasa Anwar yamaida masa kayansa 6angarensa, yafice yana turo baki gaba. Momcy ta bishi da kallo tana girgiza kai. Nawaf yashigo ya rufe ko'ina mai makon yatafi ─Ćaki saiya kwanta saman kujera doguwa. Can dare Nawaf yakasa barci dan bai saba kwanciya ahakaba, sai tsaki yakeyi yana juyi, ga kujerar ledace. Ya sakko 'kasa saman kafet ya kwanta aii saiyaji tamkar ana tsira masa allurai, yatashi zaune ya rabga uban tagumi kamar wanda uwarsa ta mutu, ga barci yana cin idanunsa. Tashi yay yanufi ─Ćakin, ahankali ya tura 'kofar, amamakinsa saiya jita abu─Će, baiyi zaton hakaba. Yasmeen tana kwance ─Ćai2 dan barci ya saceta, ga gajiyar biki, yanda ta kwanta saida ya ta6a zuciyar Nawaf. Ya kauda kai daga kallonta tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, asanyaye ya zauna saman kujerar dake ─Ćaki, yakai minti biyar ahaka, sannan ya tashi yanufi bayi, shawa­čÜ┐ yasakarma kansa, na ce, "ai dama ka saba. Yada─Će ruwa yana ji'kashi, wanda 'karar ruwan tasa yasmeen farkawa atsorace, tana nan zaune yafito jikinsa ─Ćaure da farin tawul, hannunsa ri'ke da 'karami yana tsane sumar kansa. Kallo ─Ćaya tai masa ta kauda kai, shima haka, durowar gefen gadon ya bu─Će ya─Ćakko wasu magunguna ya watsa abaki ya kora ruwa, gefen gadon ya zauna yana fa─Ćin ya salam!!. Ahankali yasmeen ta sauka daga gadon ta koma saman kujera ta kwanta. Yakai minti5 azaune kafin yatashi yahau shirin barci. Yabi yasmeen dake kwance saman kujera da kallo, ahankali yafurta kin taimaki kanki yarinya, gadonsa ya haye yay kwanciyarsa harda jan bargo. Yasmeen tana kallonsa ta─Ćan ta6e baki, itama ta maida kanta ta kwanta, babu da─Ćewa barci yay gaba da ita. WASHE GARI da safe yasmeen ta tashi ta gyara ─Ćakin tsaf ta wake bayi sannan tayi wanka, dan Nawaf tundaga sallar asuba bai dawo ─Ćakin ba, yana ─Ćakin motsa jiki. Gayu ta ─Ćauka cikin atamfa siket da riga tayi 'kyau sosai, bawata kwalliya tayiba fauda kawai tashafa. Ta le'ko falo azatonta Nawaf yana nan, saitaga babu kowa ta fito ta lalle'ka ko ina, komai ya burge ta, tagama zagayawa tazo tashare falon duk da bawani datti yayiba, amma ta─Ćan 'kara gyarawa. Har waje ta fito ta gyara tsaf, alokacin Nawaf yafito daga ─Ćakin motsa jiki yashiga bedroom, wanka kawai yashiga yada─Će sosai kafin yafito, bayan fitowarsa ya shirya. Yasmeen tana zaune afalo tayi shiru tana tunani. 'Karar takunsa yasata juyyo da sauri, Nawaf tagani cikin shadda orange color, ─Ćinkin zamani yayi masa 'kau sosai, amma fuskarsa babu walwala. Ta ─Ćauke kanta daga kallonsa, dan ganin gurinta ya nufo. Cikin takun 'kasaita ya 'karaso gareta dan i├▒a ganin yau sarautarce ta motsa, ya ce, "k ki tashi muje mu gaida mutane. Banza tayi masa. Hannu yasa ya fincikota "k 'karamar mara kunya har kin isa ina miki magana kimin banza. Ta ce, "anyi maka ka ─Ćauki mataki mana, ta murgu─Ća masa baki­čśĆ. Shi dariyama tabashi, amma saiya gimtse, ya ce, "zanyi maganinki ki bani lokaci. Tayi wata dariyar rainin hankali, aii ba saina baka lokaciba yanxu yadace ka─Ćauki mataki. Ya zaro wayarsa dake wringing momcy ce, cikin girmamawa ya ce, "momcy ina kwana??. Daga can ta ce, "lafiya lao abbuna kun tashi lafiya. Ya ce, "lafiya lao my momcy, ta ce, "ina ─Ćiyar tawa bata mugaisa. Ya ce, "momcy ai yanzu zamuzo gaisheku ma. A'a modebbo karka wahalarmin da ─Ćiya kabarta ta huta. Haba dai momcy yazamu zauna bamu gaida su hajjaba, bawani wahalar da ita daza ayi. To shikenan bata mu gaisa. To, juyowa yayi domin yabata wayar, saiyaga bata nan, bin bayanta yayi zuwa bedroom, batareda yayi mata maganaba ya manna mata wayar kawai a kunne. Tabu─Će baki zatayi magana saitaji maganar momcy tana fa─Ćin ─Ćiyata kin tashi lafiya??. Cikin girmamawa ta zamo daga kujera ta ce, "momy ina kwana??, lafiya lao ─Ćiyata ya ba'kunta. Ta ce, "lafiya lao. Masha ALLAH momcy ta fa─Ća, ta ─Ćora dafa ─Ćin babu wata matsala dai ko??. Eh babu komai momy. To shikenan gasu talatu nan zasuzo su─Ćan gyara miki inda aka 6ata kinji. Lah momy ai bama sai sunzoba nariga na gyara. Kai ─Ćiyata damme??, daga yau karki 'kara wahalar da kanki akan aiki, akwai masu yi kinji. Ta ce, "to momy ngd ALLAH ya'kara girma. Momcy ta ce, "amin ALLAH yay muku albarka. Ta ce, "amin. Nawaf yaji da─Ćin yanda yasmeen ta girmama mahaifiyarsa, amma sai ya kanne dan yasan matar tasa 'yar haya'kice. jallabiya ya ─Ćakko ya cilla mata, gashi nan kisaka mu tafi. Kai ta─Ćago daniyar yimasa rashin kunya, amma saitaga ya tsare gida kamar bai ta6a dariyaba, bata ta6a jin shakkar yimasa rashin kunyaba irin yau, ─Ćauka tayi tana zum6ura baki tanufi bayi ta canja, tayi mata matu'kar 'kyau dan rigar ta ha─Ću, shi kansa saida ya yaba amma bai nuna mataba, ya ce, "muje, yafa─Ća yana nuna hanya­čĹë­čĆ╗. Batayi musuba suka tafi, 6angaren papa suka fara zuwa yayi farincikin ganinsu, yasmeen ta zube tana kwasar gaisuwa wajen surikin nata, shima Nawaf yakai tashi gaisuwar, papa yay musu nasiha mai shiga jiki. Daga nan wajen momcy sukaje suka gaisheta, itamadai nasihar tayi musu. Sai 6angaren dasu hajja suke, cikin farinciki hajja ta rungume yasmeen itako sai kunya takeji. Nawaf kuwa tsakkiyar kakanninsa yaje ya zauna yana gaishesu cikin harshen larabci, suka shiga tambayarsa ya amarya. Ya ce, "gata nan lafiya lau. Ta─Ćan yi 'ko'kari wajen gaishesu da larabci, saboda islamiyya datake zuwa, daga nan sai Nawaf yakoma yimusu tafinta, idan sunyi magana da larabci ya fassara mata, idan tayi da hausa ya fassara musu, Nawaf sai dariya yake mata wai bata iyalarabci ba. Momcy ta ce, "rabu dashi yasmeen kema zaki iya indai larabcine. Yasmeen ta ce, "momy sainama fishi iyawa insha ALLAHU. Nawaf ya harareta wazakifi iyawar??, Ta ce, "kaimana. Haka dai sukaita hirarasu, saida hajja ta ce, "su tashi suje 6angarensu. Tun ahanya aka fara fa─Ća, na ce, "kai ALLAH ya shirya wa─Ćannan gays ─Ćin. Talatu da ladidi suka shigo da kayan break suka jere a dinning, sanan suka tafi. Nawaf yatashi yanufi dinning batareda yabi takan yasmeen ba, abincinsa yaci ya 'koshi kunsandai 'yan kwallo sun iya ci­čśť. Yasmeen tana zaune a falo ko kallo bai ishetaba, saida yagama yafita sanan taje taci nata, ta gyara wajen. Falo tadawo ta ─Ćauki wayarta tahau chatting dan tarage ka─Ćaici, dama kallo bai cika damun yasmeen ba. `````````````````````````````````` Sai bayan sallar la'asar Nawaf yashigo gidan lokacin tasake wanka cikin sket da riga na shadda tayi 'kyau, tana bedroom bayan ta idar da sallar la'asar, zaune ta ke kawai tunani fal zuciyarta. 'Karar bu─Će 'kofa yasata juyowa da sauri tana kallonsa, kallo ─Ćaya yay mata ya ─Ćauke kai, itama kanta ta maida gefe, tana ganin yafara cire kaya tatashi ta fice, yarakata da harara. Tana nan zaune afalo saiga 'yammatan danginsa na saudia, suka zauna ana hira harda ummu habeba, yau tasaki jiki anayin hirar da'ita. Suna nan zaune Nawaf yafito sanye da 'kananun kaya sai zabga 'kamshi yakeki, kan hannun kujerar da yasmeen take zaune ya zauna, suka shiga gaidashi, daga nan aka ─Ćora da hira, ummu habeba sai kallonsa takeyi, ita dai tana 'kaunar Nawaf, amma gashi ya zagaye yayi aurensa ya barta, kwata2 ta kula ma shi nunawa yake baisan tana sonshiba. Sai gab da magriba suka tafi 6angaren momcy. Shikuma Nawaf yatafi sallahr magriba masallaci. ____________________________ Yau jirgin muta nen sudia ya ─Ćaga, hajja kawai aka bari zatayi ─Ćan kwana biyu sanan ta tafi, da'kyar tayarda ta zauna. Yau gidan shiru babu kowa saisu ka─Ćai. Nawaf yadawo daga motsa jiki ya zube afalo saman doguwar kujera yana fa─Ćin wash ALLAH na nagaji yawa yau. Yasmeen tafito hannunta ─Ćauke da kofin kunun gya─Ća dan tana sonsa sosai, tundaga lokacin da Nawaf ya ce, "bayasan 'yan aiki awajensu idan bazatayiba tabarshi. Momcy ta ce, "bata yardaba yasmeen ─Ćin nawa take daza a sakar mata aiki, dayaga momcy ta dage saiya ce, "to saidai ita ta rin'ka musu girki, dan bazaici girkin 'yan aikiba. Momcy ta ce, "wanan mai sau'kine, yasmeen kiringa yimuku girki tunda ku biyune kafin yatafi, dan tuni mijinki baya cin abincin 'yan aiki. Yasmeen ta ce, "to momy hakanma yayi, nima nafiso nayi da kaina. Yabita da kallo danganin shigar dake jikinta, wandone iya guywa da 'karamar riga mara nauyi, rigar ta fallasa asirin jikinta sosai, kanta yasha gyara sai wal'kiya yakeyi. Tasan babu wanda zai shigo musu shiyyasa tayi wannan shigar, dan Tun agida yasmeen tanaso shigar 'kananun kaya damma wataran umma tana hanata ne. Ta wuce kamar bata ganshiba. Ya ce, "k zonan!, banza taiyi masa tunda ba "k aka ra─Ća mataba agidansu, bedroom tashige abinta. Nawaf ya ha─Ćiye wani mugun yawu jikake 'kuttttt, gaba ─Ćaya ta rikita masa lissafi ya rintse ido ya furzar da huci mai zafi, ya ce, "wai sai yaushe za'a kai 'karshene??, wata zuciyar sa ta ce, "randa ka shirya kwatar ha'k'kinka dan kasan indai dan itace ayita zama ahaka. Yay wani murmushin mugunta, afili ya ce, "aii ko ankusa zuwa 'karshen, ya mi'ke yanufi bedroom domin yin wanka. Koda ya shiga ─Ćakin baibi takantaba yashige wanka abinsa, ita kuma tadawo falo tana fa─Ćin ─Ćan rainin wayo ai wlhy yanzu na daina zama kana raina mini hankali, idan zaka shekara kiran "k! Bazan amsaba tunda bashi iyayena suka ra─Ća mini ba. Tana nan zaune yafito shima cikin 'kananun kaya, kusada ita ya zauna, bata ko kalli inda yakeba taci gaba da shan kununta. Gashin kanta yaja aiko ta kwala 'kara, yasa ─Ćayan hannunsa ya rufe mata baki, tasaki kofin hannunta saboda zafi, ya ce, "k wacce irin mara kunyace ne?, kinaji ina kiranki ─Ćazu kikai mini banza, ni tsarankine??. Cikin kuka ta ce, "kai kasani nidai kasakeni mugu kawai. Birkiceta yayi ya haye saman cikinta, tafara mutsu2n kwacewa. Amma takasa saboda yafi 'karfinta, ALLAH Yabata sa'a ta gallah masa cizo. Da sauri yasaketa danjin wani azababben zafi, mari ya kaimata ta kauce da gudu ta shige bedroom ta rufe, ya take mata baya­čĆâ­čĆ╗­čĆâ­čĆ╗........... ✍­čĆ╗ © 2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗29 & 30 .....kafin ya 'karasa ta kulle 'kofar yashiga bugawa da 'karfi amma yasmeen tai masa banza, saida yaga batada niyyar bu─Ćewa sannan ya ha'kura, falo yadawo ya zauna zuciyarsa cike da haushi, daga baya yatashi ya fice. Yasmeen ta─Ćan le'ko ta wata 'yar 'kofa ganin baya nan yasa ta bu─Će 'kofar ahankali tafito. Hijjab tasaka tanufi 6angaren momcy, tanata addu'a a zuciyarta ALLAH yasa bacan Nawaf yajeba. Da sallama tashiga falon, hajja da Anwar ne kawai zaune, tasaki ajiyar zuciya, gurinsu ta 'karasa hajja tanata mata murmushi, ta tsugunna har 'kasa ta gaisheta, Anwar ya ce, "aunty mu dama yanzu zanje 6angarenki hira. Kai Anwar banyardaba kullum haka kake fa─Ća amma komai kama dakai ban ganiba. Anwar yay dariya, A'a aunty kinafa ganin mai kama dani baga yaya nan ba, dariya sosai sukeyi harda hajja, momcy tashigo itama tana waya, bayan ta kammala ta ce, "A'a ─Ćiyata kece kika zomana, cikin jin kunya yasmeen ta gaisheda momcy. Momcy ta amsa cikin fara'a, tana mai 'kara jin 'kaunar yasmeen har cikin zuciyarta, itako saiwani sissinne kai take dan kunya, hajja sai tsokanarta takeyi, Abdallah yashigo shima aka fara hirar dashi. Anwar yabata wayarsa tana kallon hotunan biki wanda ya─Ćauka, tayi mamakin irin 'kyawun datayi, gashi wasu wuraren tana murmushi, wanda batasan lokacin datayiba, wani hoto ya─Ćauki hankalinta awajen dinner, tatuna fa─Ća sukeyi da Nawaf awanan lokacin shine ya harareta ta rama, amma idan kagani saika ─Ćauka kallon soyayya sukema juna, Anwar ya ce, "kai aunty nakula pic ─Ćinnan yayi miki 'kyau sosai, nima duk nafi sonsa wlhy. Abdallah yataso domin yagani shima, bayan kujerar yakoma yana kallo ta bayansu. Nawaf yashigo da sallama saida gaban yasmeen yafa─Ći, amamakinta saitaji ya ce, "dama kinanan inata nemanki, wani iri yasmeen taji aranta gashi yawani tsareta da mayun idanunsa masu hasken tsiya, ta daure ta ce, "yi ha'kuri bansan zaka dawoba yanzu, jinai 'kai─Ćaici zai dameni shiyyasa nataho nan. Okey to nima bari nazauna ayi hirar dani, ya zauna kusada hajja, hajja ta ce, "o, sai yanzu ka tuna dani. Nawaf yay dariya to dama na'isa na manta dake!. Momcy ta ce, "aii daga yanzu indai yafita kiringa tahowa nan saboda ka─Ćaici babu da─Ći. Yasmeen ta ce, "to momy. Nawaf yafaki idonsu ya harareta, ita kuma ta murgu─Ća masa baki, ya nuna kansa wai shi­čĹë­čĆ╗­čĹ«­čĆ╝!, ta ka─Ća kai alamar eh., le6enasa na 'kasa ya cije, itakuma ta maida kanta ga kallon pictures. Haushi kamar ya kashe Nawaf, amma babu damar ─Ćaukar mataki, dole yasaki jiki suna hira da hajja da momcy, dansu hankalinsu yana kan waya. Saida aka kira sallar azhur suka tashi, masallaci suka tafi shidasu Abdallah, yasmeen kuma tanufi 6angarensu. Wanka tafara shiga sanan tayi sallah, agurguje ta shirya tafito da nufin tasake guduwa 6angarensu momcy, sai sukayi kici6is da Nawaf a'kofa, kallon kallo aka tsaya yi, kowa ya ─Ćaure fuska. Tsaki Nawaf yayi tareda jan hannunta zuwa cikin falon, cikin tsiwa ta ce, "malam kasakeni, banza yay mata yacigaba da janta, saman kujera mai zaman mutum ─Ćaya ya hanka─Ćata, damma kujerar da laushi shiyyasa bataji zafi ba, ya─Ćora 'kafarsa ─Ćaya saman kujerar ya tsareta da idanu. Ta kauda kai daga kallonsa, dan ita idanunsa tsoro suke bata, haskensu yayi yawa, sunkai minti2 ahaka, sanan ya ce, "wai ke na tambayeki ni sa'ankine??, banza tamasa kamar batajiba, yacigaba da fa─Ćin ─Ćazu harda wani fa─Ćin aibansan zaka dawoba ne shiyyasa nafito, dan ka─Ćaici yaymin yawa, yafa─Ća yana kwaikwayon muryarta. abin yabama yasmeen dariya amma saita gimtse, ta ce, "oho dai naga kaine kafara, kaga kenan a wajenka na koya, agabansu hajja kayita wani kakkafi waikai mai gida, sai andawo nan kafara mazurai, ta 'kare maganar da murgu─Ća baki­čśĆ . Nawaf ya ce, "niko?" Cikin tsiwa ta ce, "eh kai─Ćin saime". yasaka yatsansa ─Ćaya ya ─Ćago ha6arta, ta rintse ida nunta, yaja tsaki yana fa─Ćin ke nifa nafiki miskilanci!. Sai asanan ta bu─Će idanu, dukda zuciyarta tana dukan uku2 saboda tsoro wannan bai hanata sake murgu─Ća masa bakiba. Ya ce, "ni dai ko??. ta ce, eh, ni kadameni da tambaya? ?". Kafin ta rufe baki yasa yatsunsa biyu ya kama la66anta ya matse da 'karfin tsiya, yasmeen tashiga tsungunin hannunsa tana hawaye­čśş, amma mugun ya'ki yasaki, gashi sai murzasu yatsun nasa yakeyi dan mugunta akan bakinta, saida yayi mai isarsa sanan yasaki, zuwa sanan la66an yasmeen sun kunbura, sunzama 'katun2n, yasaki yana dariyar mugunta. Yasmeen sai hawaye suke zirara a fuskarta, tana shafa la66anta, har yanzu 'kafarsa tana saman kujerar, ya ce, "yammata za'a sake mini rashin kunyarne??, hararar sa tayi ga hawaye fal fuska. Nawaf ya tuntsure da dariya, yasmeen tai sagade tana kallonsa, batayi zaton yana dariya hakaba, saida yayi mai isarsa sanan ya sauke 'kafarsa yanufi bedroom yana cigaba da dariyar. Yasmeen ta kifa kanta saman hannun kujera tana kuka, ahaka barci yay gaba da ita. Saida yay wanka ya shirya tsaf yafito cikin manyan kaya, wani farin yadine shara2 yay masa 'kyau sosai harda ─Ćora ba'kar hula wanda gays ─Ćin yanzu suke yayi, ya kai kallonsa ga yasmeen dake barci a takure saman kujera, murmushi yasaki yana fa─Ćin yarinya tayi barcin wuya. Har yakai 'kofa kuma yadawo, ─Ćaukarta yayi tsak yakaita bedroom, a saman gado ya kwantar da'ita, yana kallon la66anta dasuka kummbura yana murmushi, ahankali yajuya ya fice. Saida yashiga 6angaren momcy yafito sanan yashiga mota yafice, yana bani mamaki yanda yakeson mota mai ba'kin gilas, kobayaso idan yafita agansane oho??. A'kofar gidan su mas'ud yatsaya, ya ─Ćauki wayarsa yakirashi, malam kafito muwuce ko??, kai haba dan baka da kirki saikace bazaka zo ka gaida Ameena ba??. Kai mutumina ALLAH inajin kunyar zuwa haka. Tsaki mas'ud yayi aikai kajika, dan ALLAH kashigo ku gaisa saimu wuce, yakashe wayar. Dole Nawaf yafito yashiga gidan, da sallama yashiga falon, suka amasa. Mas'ud yashiga tsokanarsa kaga angon yasmeen, wanan irin 'kyau haka malam, lallai amarcin ya kar6eka. Nawaf ya zauna yana hararar sa, mas'ud kaifa ─Ćan iskane wlhy, nazata idan kayi aure zaka canja, amma kananan yanda kake, saima 'karawa dakayi. Kafin mas'ud yay magana Ameena tashigo hannunta ─Ćauke da tire. Nawaf ya ce, "amarsu ta ango!, sai dai baki more angoba, dariya tayi tana zuba masa lemo, bayan tagama ta gaisheshi ya amasa, ta ce, "ina 'kawata??. Tana gida nabarota lfy, ta ce, "na gaidaki!. Ameena ta ce, "ina amasawa. Ka─Ćan yasha lemon ya mi'ke kai malam tashi mije yamma tanayi. Mas'ud ya mi'ke yana fa─Ćin gsky ne, saida ya sumbaci goshin ameena sanan ya fito, Nawaf yana kallonsu shiyyasa yayo gaba, dan yasan mas'ud ba kunyarsa zaijiba. Amota mas'ud ya ce, "mutumina aure da da─Ći wlhy, yanasaka nisha─Ći da farinciki, musaman idan kasamu matar data iya tattalinka. Nawaf ya ta6e baki, kai Alhaji kai yayima da─Ći, nidai bandani!, dan ni takurani akayi, dana 6ararraje nika─Ćai a─Ćakina amma yanzufa??, ankawo mini wanan mara kunyar duk ta takurani. Dariya mas'ud yayi, haba malam fa─Ći gsky dai, kowa yaganka yasan ka 'kara 'kyau, zaka wani dozani, 'kilama mun samu baby. Nawaf ya ce, "kai mutumina ammafa ka iya tsiya ka ce, "har resold yafito??. Kai ─Ćan rainin hankali ka gama wani kauce2n ka kafa─Ći gsky, aii dakai nake!!. Tofa, Nawaf yafa─Ća yana 'kara dafe sitiyari, to indai nine wlhy kama fidda rai, bawai tonon asiriba, ko makwancima ni bamu ta6a ha─Ćawaba wlhy. Idanu mas'ud yazaro, kai amma dai kai garane wlhy. Oho kama fa─Ćamin abinda yafi gara mana, kai kanka kasan ba son yarinyar nan nakeba, kai nama ta 'kaice maka zance, kullum saimunyi fa─Ća. Dariya sosai mas'ud yayi, ya ce, "lallaikam zaku barine, koda yake shima fa─Ćan duk acikin soyayyane. Tsaki Nawaf yayi daganan yay masa banza. ________________________________ a6angaren yasmeen kuwa sai la'asar ta farka, tayi mamaki data ganta akan gado, itadai tasan ba'a nan ta kwantaba, zata iya cewama tundaga randa aka kawota batasake hawa gadon nanba da niyyar kwanciya, saidai kawai ta gyara masa. Bayan tagama mamkinta ta sakko, wajen madubi taje tana kallon fuskarta, la66anta sunyi fushi sosai, ta ce, "ALLAH yasaka mini mugu kawai, tunda nake arayuwata banta6a ganin mugun mutum irin Nawaf ba, ruwa zafi taje ta ─Ćebo a kichin, awani ─Ćan bokiti, tazo tazauna gaban mudubi, tasaka wani hankacif ─Ćinsa ta gasa bakinta,, dukda zafin datakeji haka tadaure tana hawaye ta gasa, saida taji ruwan ya huce sanan ta ha'kura, tashiga wanka. Tafito tayi sallar la'asar, ta shirya tsaf cikin doguwar jalla biya ba'ka, mai duwatsu. Falo tafito taci abincin, da momcy ta aiko musu, dama har yanzu bata fara abincin ranaba, saidai na safe, da daddarema ba girki sukeyiba, dan kowane daren duniya kayan fruit ne abincin Nawaf, suka─Ćai yakesha sai shayi na 'ka'ida, wanda saiyasha sau goma arana batareda ya isheshiba­čśť. Ta kammala cin abincinta tadawo falo, yasmeen bata cika damuwa da kalloba, idan itace sai ayi sati ba'a kalli tv ba, dan haka tai kwanciyarta saman kujera tana game a waya. Yaseer ya kirata awaya, ta─Ćaga cikin fara'a tana fa─Ćin ─Ćan 'kanina nayi missing ─Ćinka wlhy. Ya ce, "nima haka sisto na, ykk?, ya gida?. Ta ce, "komai lafiya Alhmdllh, ka'ki kazo ko??. Karki damu zanzo, school ce ke hanani wani motsi wlhy, amma zuwa weekend zaki ganni. To ALLAH ya kaimu lfy, yasu ummana da abba??, suma duk suna lafiya wlhy, aii yanzu su yaya Nawaf suka tafi, tun ─Ćazu suke anan. Yasmeen taishiru azuciyarta ta ce, "mugu, wato bayan yagama mini mugunta ashe gidanmu yaje, ta─Ćan murmusa koba komai taji ─Ća─Ći...........yaseer ya ce, "hello sisto kina jina kuwa??. Saida tayi ajiyar zuciya sanan ta ce, "ina jinka, ka ce, "tun─Ćazu yake anan??, eh, shida yaya mas'ud sukazo, bakiga alherin daya kawo manaba wlhy, ki 'kara yimana godiya, gsky aunty kin more miji.. Hummm to uban 'yan surutu anji, yaseer yay dariya, kai sistona daga fa─Ćar gsky, ina aunty amina??, tana gidanta itama nima bamu ha─Ćuba. Kai aunty gida biyune fa tsakaninku. To yaseer basai anbar mutum zuwaba?, ya ce, "hakane kuma. Sun da─Će suna hira, ta ce, "ka gaishemin da umma, itama zan kirata mu gaisa insha ALLAH, dan jiya mun gaisa da abba. To shikenan zataji insha ALLAHU, saina zo. Okey to saikazo. Shiru tayi tana tunanin mijin nata, tana mamkinsa, agaban mutane yakan nuna yana sonta, amma idan su ka─Ćaine sai muguntar tsiya. Anwar yashigo da gudu yana fa─Ćin aunty kina ina??, yasmeen ta tsshi zaune, ganinan Anwar, ya mi'ka mata kofi, yayinda Abdallah ma yashigo da gudu, yatsaya yana hakki yana hararar Anwar. Yasmeen tayi dariya tana tambayarsu miya faru, Anwar ya tuntsure da dariya, yaya ne ya ha─Ća askirim na ─Ćebo miki, shine yabiyoni zai kwace. Yasmeen ta ce, "kai Abdallah ALLAH yashiryaka wlhy, nixaka yima rowa. Ya 'karaso yana fa─Ćin ALLAH aunty dama nayi niyyar kawo miki, banfa gama ha─Ćawaba ya ─Ćebo, kuma dafarko bake yay niyyar kawomawa ba, kansa ya ─Ćebar mawa. Anwar yay dariya kaidai yaya fa─Ći gsky. Dagudu Abdallah yabiyoshi suka fara zagaye falon, yasmeen tana tun tsura musu dariya. Nawaf yashigo da sallama, bashiri suka nutsu, kowa yana hakki, yasmeen ce kawai taketa dariyarta. Nawaf yatsaya yana kallonsu kawai, yayin da yakejin kamar kar yasmeen ta daina dariyar dan tayi 'kyau da dariyar. Su Anwar suka ra6a ta bayansa suka fice, sum2­čÜ­čĆ╝­čÜ­čĆ╝kafin akai musu masga. Bayan fitarsu Nawaf yay tsaki yashige bedroom, babu da─Ćewa yafito sanye da jallabiya, ko kallon yasmeen baiyiba ya fice. Tabishi da kallo tana ta6e baki. Koda yadawo sallah wajen papa yawuce dan amsa kiransa, ya rissina ya gaisheshi. Papa ya amsa yana fa─Ćin zauna sosai mana. Nawaf ya zauna. Papa ya ce, "dama inaso na sanar makane ka shirya kaida matarka kuje safana, ku gaishe da jama'a damusu godiyar hidima. Da sauri Nawaf ya ce, "papa safana fa ka ce??. Eh, safana na ce, yakamata ka kaita tasan tushenka, tasan kaiba ─Ćankowa bane, talakane kamarta, baka fita da komaiba, wannan 'katon gidan datake gani da taimakon ALLAH aka ginashi, shima saida aka ─Ĺauki shekaru ba'a gamaba, dan har aka haifeka ban gama ginin nan ba, kuma haka mahaifiyarka ta zauna dani, duk da ita tafito daga wata 'kasa, kuma gidan arzi'ki. Nawaf ya ce, "to shikenan papa zamuje, amma aranar zamu dawo??, kai papa ya girgiza, ya ce, "A'a, kwana uku zakuyi ku zaga dangi ko'ina, kushiga ko'ina da ina. Nawaf ya ce, to shikenan zamuje nextweek, dan inaso 'karshen watanan na koma Spain!!. To ALLAH yakaimu lafiya, saikayi 'ko'karin shrya muku tafiyar, ALLAH yay muku albarka, yabaku zuria ta gari. A la66ansa ya ce, "amin. Sun─Ćan da─Će suna hira, saida papa ya ce, "yatashi ya je wajen matarsa, anbarta ita ka─Ćai. Akunyace Nawaf yami'ke yafice. Papa yabishi da kallo yana murmushi. Saida yaje wajen hajja yay mata saidai safe sanan yatafi 6angarensu. Afalo ya iske yasmeen tana kallon hausa film, ya ─Ćauki remote ya canja, wai shi bazai kalli wannan shashancinba, yasmeen ta turo baki gaba, a zuciyarta ta ce, "bagara hausa film ba wataran suna fa─Ćakarwa, akan 'yan kwallo da rashin aikinyi yay musu yawa...........Nawaf ya katse mata tunani da fa─Ćin "k ina shayina☕??. Banza tayi masa, tayi kamar batajishiba, ya mi'ke, da sauri ta tashi tsaye itama, tanufi kichin da gudu. Dariya ta su6cewa Nawaf, ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "kai matsoracima baiji da─Ćin kansaba wlhy. Babu da─Ćewa ta dire masa shayi agaban sa, tana wani zuzzun6ura baki gaba, ta ajiye zata wuce, ya ce, "k dawo nan, ta tsaya cak ita bata tafiba, kuma bata dawoba. Cikin fa─Ća ya ce, "wai badake nakeba??, saida ta murgi─Ća baki sanan ta juyyo, tazo ta tsaya akansa, ya watsa mata harara, wlhy yarinya kishiga hankalinki dani, inba hakaba kin rin'ka shan wahala kenan. Ta yatsine fuska sanan ta ce, "wlhy saidai musha wahala, kabar ganin ─Ćazu ka kumbura mini le6e na 'kyaleka, zan ramane. Ya tashi zaune daga kwanciyar dayayi, yasa hannu ya fisgota ta fa─Ćo jikinsa, runtse idanu tayi kam, tana rawar jiki, ya matseta kam ajikinsa, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, wata mahaukaciyar sumba yake mata, ga le6enta bai gama warkewaba, dan har yanzu yana mata zafi, amma dan muginta irinta Nawaf sai yaha─Će bakinta da nasa sai murza yakeyi. Itako hawaye kaiwai take zubowa, tana tsunguninsa da hannunta ─Ćaya, amma ko'a jikinsa, dan ya'ki sakinta. Saida yaga taji jiki sannan yasaketa, tana hawaye, tama kasa tashi daga jikinsa. Ya lumshe idanunsa dasukai jajir, yamaida kansa jikin kujera yana fitarda numfashi. Ahankali ta tashi daga jikinsa ta shige bedroom, saman gado tafa─Ća tana kuka, saida tayi mai isarta sanan ta shiga bayi taiyi wanka, tafito tayi shafa'i da wutiri, tana nan zaune yashigo ─Ćakin tai 'kasa da kai kamar bata ganshiba. Shima bai kalletaba yashiga cire kayan jikinsa, tashi tayi ta haye kujera takwanta. Yashiga wanka shima, yafito yagama komai na al'adar rayuwarsa, shafa'i da wutiri, karatun alkir'ani, sanan yaje kichin dakansa yasake dafa wani shayin dan wancan ya huce. Falo yay zamansa saida dare yayi sosai yashigo, sanan yasmeen ta da─Će dayin barci akan kujera. Kallo ─Ćaya yay mata ya ─Ćauke kai, ya hau gado yakwanta. Na ce, "mu kwana lafiya, nima wajen nawa handsome ─Ćin nataho­čśś. ________________________________ WASHE GARI. lokacin dana iso 'yan aiki harsun gama gyarama yasmeen 6angarenta, tagama ha─Ća break a falo na tarar da Nawaf yana break na ce, "tofa yau ba'a ra'ayin dinning ─Ćin??. Yasmeen ta fito daga ─Ćaki, hannunta ─Ćauke da littatafai, ko kallon inda Nawaf ya ke batayiba, ta zauna saman kujera tana karatun ta, ya─Ćago yana kallonta, wani abu yana ta6a zuciyarsa, amma yanaji har aransa bazaiyi fatan yafitowarsa filiba. Yasmeen taji ajikinta ana kallonta, ta ─Ćago tana kallon inda Nawaf yake, ta murgu─Ća masa baki­čśĆ. Ya 'kara ─Ćaure fuska, "k dawa kike??, ta ce, "da wanda ya tsargu mana. Ya ce, "toni na ysargu. Ta ce, "matsalarkace. Ya ce, "kema yanzu zata zama taki!". Aii tana ganin ya mi'ke ta tashi ta fallah da gudu zuwa waje, dama shiyyasa ta zauna kusada 'kofa. Nawaf yay kwafa zaki dawo ki sameni aii, matsoraciyar banza kawai­čśť.....................✍­čĆ╗ Assalamu alikum Masoya littafin NAWAFF kwana biyu kunji Shiru hakan tafarune sakamakon rashin lafiya danayi, amma yanzu komai normal, ngd da 'kyaunarku gareni, luv u oll❤❤❤­čśś [1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗31 & 32 .....koda yasmeen tafita zamanta tayi a waje, tanajin motsin fitowar Nawaf ta samu wani lungu ta 6uya, 6angaren momcy yanufa tasan zaije gaishesune, ─Ćaki takoma ta ─Ćakko hijjab itama, tana shirin shiga yana fitowa, tamatsa masa ya wuce batareda kowa ya kalli ─Ćan uwansaba, yasmeen ta ta6e baki tareda shigewa. Shima mota yashiga ya bar gidan. Yasmeen zamanta tayi a 6angaren momcy har azuhur, sanan tadawo nasu 6angaren, har sanan Nawaf bai dawoba, tayi sallah ta sake wanka, falo tadawo ta zauna zuciyarta cike da tunani, yau kwana uku ke nan kullum sai faisal ya kirata, amma bata ─Ćagawa, gsky tana fargabar Nawaf yagani, da sauri ta ─Ćago domin jin sallamar ameena.. Taje ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, Ameena ta ce, "kai yasmeen irin wannan 'kyawu haka, miye sirrin??. Yasmeen ta ajiye kayan hannunta tana hararar Ameena, 'yar duniya abinma harda zagi, aii kobaki fa─Ćaba kowa yaganki yasan kina jin da─Ći, kodai oga mas'ud yayi ajiyane??. Dariya Ameena tayi tareda shan lemon da yasmeen ta kawo mata, ta ce, "kin rama kenan??. Dariya sukayi suduka. Yasmeen ta ce, " 'yar uwa inatason shigowa wajenki amma ina tsoron na tambaya a hanani, ya amarci??. Ameena tayi far da idanu ta ce, "amarci muna ci kam, kamar yanda nasan kuma kuna shan naku. Yasmeen tayi murmushin takaici, ta ce, "k ni babu wani amarcin dana keci saima shan wahala, amma ba wannan bane mafi girman damuwata amina!. Ameena ta gyara zama, yasmeen miye damuwarki???, humm amina faisal ne damuwata. Ameena ta 6ata fuska tana hararar yasmeen, "k yasmeen kiji tsoron ALLAH wai da baki so faisal ba sai yanzu dakike agidan mijinki, karfa ki manta mijinki yafi faisal komai wlhy 'kyau aji ilimi wayewa, dan iskanci da shaye2 bashi bane wayewa. Yasmeen ta kamo hannun Ameena ta matse anata, Ameena ki saurareni nakai 'karahen zancena mana, kema kinsan bazan ta6a son faisal ba arayuwata, baki bari nafa─Ći abinda ke raina bane. Abinda yasa kikaji na ce, "miki faisal ne damuwata shine, yau tsawon kwana uku kenan kulum sai faisal ya kirani, gashi yay ta turomin sakwanni, shiyyasa ma kwana biyu na daina chatting kwata2. Ameena ina tsoron mugun nan ya gane, na tabbata bazai ta6a fahimtata ba. Ameena ta ce, "tofa, ba ance tun randa faisal yazo gidanku da safennanba washe gari yabar 'kasar??, nimadai haka naji, amma fa number dayake kirana da ita ta 9ja ce. Ameena taja numfashi, ta bu─Će baki da nufin yin magana.......sai Nawaf da mas'ud sukai sallama, dole suka katse hirar tasu. Su Nawaf suka zauna, mas'ud ya ce, "tunda ku kun'ki zuwa mu gashi yau munzo mu kwashe ladan. Yasmeen da Nawaf sukayi dariya, yasmeen ta ce, "ayi ha'kuri muma zamuzo, Nawaf ya ce, "kinga ishirunki, ranar aii saida naje gidan, shiko tunda aka gama biki bai zoba, saboda santin amarci, ranar har momcy daida ta tambayeshi. Mas'ud ya zaro ido kai da gsk kakeyi. Nawaf yay dariya yana fa─Ćin eh mana. Nandai sukaita hirarsu, har la'asar, mas'ud ya ce, "Ameena ta tashi su tafi, dole tabi umarnin mijinta, amma badan tasoba, dan tanaso su 'kare maganar da suka fara da yasmeen. To itama yasmeen ─Ćin taso hakan amma bayanda zatayi. Har get ta rakasu sanan ta dawo dan harda Nawaf suka fita, tunda lokacin sallah yayi. _________________________________ haka rayuwa taci gaba da tafiya, yau da gobe sai ALLAH, Nawaf yanata shirya musu tafiya katsina, amma dan rainin hankali bai sanar da yasmeen ba, tagadai yanata sayo abubuwa yana ajiyewa, itako ko kallo bai ishetaba bare ta tambaya. Dan yanzu ba sosai suke shiga harkar juna ba. Yau su duka suna falo amma babu wanda yadamu da abinda ─Ćan uwansa yakeyi, yasmeen tana zaune akasa ta shinmi─Ća farin hankici ta ─Ćora 'kafarta akai tana yanke farce. Nawaf kuma yana kwance saman doguwar kujera yana kallon kwallo. Wayar yasmeen tashiga 6urari, takai dubanta ga wayar faisal ne, cikin rashin gsky ta kalli Nawaf, idanunsa suna kan tv amma hankalinsa yana kanta, ta gefen ido yake kallonta. Ta kauda ido daga kallonsa alokacin wayar ta tsinke, cigaba tayi da yanke 'kumbarta. Aka 'kara kiran wayar nanma harta tsinke bata motsaba, shikuma kuma yaci gaba da kira, saida yakira sau 6 ana bakwaine yasmeen takai hannu zata ─Ćauka, da sauri Nawaf ya kawo hannu shima da nufin ─Ćauka, saiya dafe hannun yasmeen. Suka ─Ćago lokaci ─Ćaya suna kallon juna, har wayar ta tsinke basu saniba, kallo sukema juna mai cike da 'kauna, Nawaf yafara janye idanunsa saboda sake kiran wayar da akayi. Yasmeen ta sake danne wayar sosai da hannunta, cikin zafin nama Nawaf ya cire hannunta, ya tsaida kallonsa ga mai kiran wayar FAISAL!!!!, ya maimaita sunan ahankali, ─Ćaukar wayar yayi ya koma saman kujera. Yayinda yasmeen tayi mutuwar zaune, kiran faisal yayi, jikin faisal yana 6ari ya ─Ćaga azatonsa yasmeen ce, NAWAF yay shiru batareda yayi maganaba. Faisal ya ce, "my luv plz kizo gareni, idan ba hakaba zan iya mutuwa, ina nan kwance tsawon satu uku babu lafiya, ki taimaka kizo na ganki my luv!!!.... Nawaf ya rintse idanunsa, danjin 'katon banza yana kiran matarsa my luv!!, wata razananniyar tsawa ya dakawa faisal. Kaiiiiiiiiiii!!!, wawa jaki jahili, wlhy ka sake kiran matata my luv saina kasheka dan ubanka, kai wane irin jakine zaka rin'ka kiran matar aure jahilin banza!!!!, wlhy daga yau yazama na 'karshe dazaka sake kiranta, inko ba hakaba zakayi dana sani kaida jahilan iyayen ka, yana gama fa─Ća ya yanke wayar. Kwala wayar yayi da bango aiko ta ta rarratse, yatashi yanufi wayar kamar wani mayun wacin zaki, yasmeen ta rintse idanunta azotonta wajenta yanufo saitaga ya wuceta. Yasa 'kafa ya take waya ya 'kara takata, sannan ya bu─Će ya cire sim cart ─Ćin ya karya shi, itadai yasmeen sai jikinta yake 6ari. Yana gamawa ya dawo kanta ta rungume jikinta tana kuka, gashin kanta ya dam'ke ahannunsa ya fisga da 'karfi, tari'ke hannunsa tana kuka, idanunsa sunyi jajur saboda 6acin rai. Cikin muryarsa tamakar zaiyi kuka ya ce, "ya ce, "kin cuceni kina gidana kina soyayya da wani, ke wacce iri jahila ce???. Cikin 6acin rai yasmeen ta ce, "ka daina ce mini jahila, danni ban aikata abinda kake zargina dashiba???, dan haka ka sakar mini gashi. Yakuma mur─Će gashin tareda wanka mata mari, cikin 'karaji ya ce, "idan ba haka bane uban mi yasa yake kiranki, ubanmiye a tsakaninki dashi, wlhy zan iya kasheki shima na kasheki, sannan na kashe kaina. Yasmeen ta fashe da kuka, tana fa─Ćin ka kasheni ALLAH yasani gsky na fa─Ća maka. Ahankali ya saki gashinta yana cije baki, yakoma 'kasa ya zauna da6as kamar ─Ćan bori, kai ya dafe yana jujjuyawa, yashiga hargitsa sumar kansa tamkar mai ciwon hauka. Yasmeen ta tsura masa idanu tana hawaye, ga tsoro fal cikinta dan ganin yanda Nawaf keta jujjuya kai kamar ─Ćan kwaya. Sunkai awa biyu ahaka kowa yana jinyar kansa, daga baya Nawaf ya shige bedroom, kaitsaye bathroom ya wuce, shawa ya sakarma kansa, batareda yacire kayan jikinsaba, yakai minti30 ahaka, saidaga baya yay wanka ya fito, shiryawa yay cikin 'kananun kaya, ya fito. Har yanzu yasmeen tana gurin daya barta tana kuka, ko kallon inda take baiyiba ya fice. Ahankali ta tashi taje tayi wanka itama, tayi sallah ta kwanta, wani wahalallen zazza6i ya rufeta, gado ta haye ta kwanta tana rawar sanyi. Har dare Nawaf bai dawoba zuwa sanan yasmeen ta gama gala baita, duk abunnan da yake faruwa Nawaf yana 6an garen momcy yana hirarsa, dan yarage 6acin rai. Momcy ta ce, "wai ina ─Ćiyata??? modebbo, Nawaf ya ce, "tanaca karatu takeyi shiyyasa kikaga bata zoba. Okey aii nazata ko batada lafiya, A'a lafiyarta 'kalau. Sai 'karfe tara yakoma 6angarensu, bedroom ya wuce ya kai kallonsa ga yasmeen dake saman gado 'kudun dune a bargo, ya ─Ĺaukr kansa daga kallonta, cigaba yayi dayin harkokinsa, yagama komai na al'adar rayuwarsa. Yay tsaye abakin gadon yana fa─Ćin ke wai mikike nufi da kwanciya a gado, kinsandai bazan kwanta saman kujeraba ko??. Jin tayi banza dashi yasa kai hannunsa ya yaye bargon, wani hucin zafi ya dakeshi, yay sagare yana kallonta, zama yayi abakin gadon yakai hannu ahankali saman wuyanta, idanunsa ya runtse tareda fitar da huci mai zafi. Baisan sanda yakai hannu yana shafa gashintaba ahankali, ta bu─Će ido tana kallonsa, da sauri ta tashi zaune tana jujjuya ido. Ya gimtse fuska yana fa─Ćin mike damunki, cikin rawar murya ta ce, "zazza6i. Mi'kewa yayi batareda yayi magana ba, ya bu─Će durowar gefen gadon ya ─Ćakko magani harya mi'ka mata saikuma ya janye hannunsa yana fa─Ćin kunci abinci??. Ta girgiza kai alamar A'a, maganin ya mayar ya fita, babu da─Ćewa yadawo hannunsa ─Ćauke da kofin shayi, ya mi'ka mata, yatsine fuska tayi tana fa─Ćin nifa na'koshi. Batareda yayi magana ba ya zauna kusada ita, yaja filo yajingina mata ajikin gado, kamata yayi ya jinginata da filon, itadai sai kallon ikon ALLAH takeyi, kofin yasaka mata abaki, dole ta bu─Će bakin ta kur6a, haka yayta bata tana sha, amma babu magana tamkar wasu kurame. Saida tasha rabi sanan ta ce, "na'koshi, harararta yayi ya ce, "kar6a bana son yawan magana. Kar6a tacigaba dayi harta shanye tas, sanan ya ─Ćako maganin yabata, ta yatsine fuska kamar zatayi kuka dan bata son magani. Ya 'kara ─Ćaure fuska, "k ni ki kar6a kona tashi na kwanta dan barci nakeji, tana hawaye ta kar6a ta shanye tana rintse idanu. Tana gama sha tafara yun 'kurin amai, da sauri ya rungumota zuwa jikinsa yana shafa bayanta kamar wata jaririya, saida aman ya lafa sanan ya ─Ćagota yana fa─Ćin kin daina jin aman ko??. Kai ta ka─Ća masa. Ya gyara mata kwanciya ya lullu6eta da bargon, dandanan barci yay gaba da ita, shikuma yakoma saman kujera ya kwanta, aiko yada─Će baiyi barciba. Nima na lalla6o na firo­čÜ­čĆ╝. _________________________________ da asuba tunda yafita bai dawoba sai wajen 'karfe 7:30am tare suka shigo da mas'ud, zuwa sanan masu aiki sun gama gyara gidan tsaf, ita kuma tana kichin tana ha─Ća break. Yashiga bedroom bata nan ya fito yana fa─Ćar kaga yarinyarnan ko yanzu haka tana wajen su momcy. Mas'ud ya ce, "A'a, kadai duba kichin naji kamar motsi. Nawaf yanufi kichin batareda yayi magana ba, bakin 'kofa ya tsaya yana kallonta saidai fuskarsa babu walwala, da sauri ta juyo danjin tamkar mutum abayanta. Karaf suka ha─Ća ido da Nawaf ta kauda kai daga kallonsa, ya ce, "keda bakida lafiya miye nawaniyin girki. Kanta a'kasa ta ce, "aii naji sau'ki. Ya ─Ćan ta6e baki, wannan ba hujja bace, ki sauke abinda kika ─Ćora kizo ga mas'ud yazo zai dubaki, yana gama fa─Ća yafice. Ta sauke abinda ta ─Ćora dama ya nuna, falo tafito, ta gaida mas'ud, ya amsa tareda tambayarta ya jikin??, ta ce, "da sau'ki. Tambayoyi yay mata tana bashi amsa yana rubutawa, bayan ya gama ya ce, "bari naje zuwa anjima zan kawo miki magunguna, ta ce, "to, ka gaishemini da Ameenar, yafita yana fa─Ćin zataji. Kichin ta koma bayan fitarsu, dan tare suka fita da Nawaf. Mas'ud ya kalli Nawaf ya ce, "mutumina gsky yasmeen tana cikin damuwa, dan damuwarce ta haddasa mata zazza6in. Nawaf ya ce, "badole damuwa tasa ta zazza6iba tunda gangar jikinta ce a gidana zuciyarta tana wajen tsohon mijinta. Cikin mamaki Mas'ud ya ce, "ban ganeba, Nawaf ya zayyana masa duk abinda ya faru jiya. Mas'ud ya ce, "bawai ban yarda bane, amma yakamata ka sake yin bincike, danni amina tabani labarin komai. Nawaf yay shiru baice komaiba, mas'ud ya ce, "bari nawuce saina dawo. Sanda Nawaf yadawo yasmeen tana wanka, ya zauna saman kujera yana jiran fitowarta, ta da─Će abakin 'kofa tana tunanin yanda zata fito da tawul, kamar ance Nawaf ya juyo suka ha─Ća ido da yasmeen da sauri ta koma cikin bayin. ─Äan 'karami tsaki Nawaf yayi, tareda mi'kewa yanufi hanyar bayin, ahankali ya ce, "kifito ki shirya ni na koma falo, ki kuma shirya kayanki kala hu─Ću dan zamuje anguwa, yana gama fa─Ća yafice. Saida taji batajin motsinsa gaba ─Ćaya sanan ta fito, agurguje ta shirya dan bataso yazo ya ritsata. Saida ya daidaici tagama sanan ya shigo, ya ce, "kin ha─Ća kayan dana ce??, ta ce, "A'a, bayi yashige batareda ya sake maganaba. 'Karamin akwatinta ta ─Ćakko ta ha─Ća kaya biyar da duk abinda zata bu'kata, tai sauri ta koma falo, ta─Ćanyi break kafin ya fito. Shima daya fito saiya shirya kayansa a ─Ćan akwatinsa irin na maza, falo yafito ya isketa ya zauna yaci abinci, tana zaune a gefe tana kallonsa. Yagama tsaf yami'ke, ya ce, "tashi muje muyima su momcy sallama. Yasmeen ta ce, "azuciyarta wai wanan wace irin tafiya ce babu shiri???, na ce, "yasmeen yazakiyi, mulkin kenan aii. Sallama sukaiyima su momcy, anan takejin garin da zasuje, kafin Nawaf yagama tattaunawa da papa yasmeen tadawo ta gyagygyara abinda ya dace, sanana su talatu suka kaimata akwatinan wajen mota, saida suka jira mas'ud yakawo mata magungunan ta sanan, suka tafi su momcy suna ─Ćaga musu hannu. _________________________________ tunda suka fara tafiya babu wanda ya tankama wani, saida suka kusa fita kano sanan ya tsaya gidan mai, aka cika musu tankin mota taf, ya shigo suka ─Ćauki hanya bayan yayi addu'oi, itadai nata ameen. Gudu Nawaf yashiga shararawa kamar zai tashi sama, cikin awa ─Ćaya da rabi suka isa tsanyawa, fitsari ya 'kullema yasmeen mara amma takasa gayama Nawaf, saida suka ─Ćauki hanyar katsina sanan Nawaf ya kalli Yasmeen, cikin ─Ćaure fuska ya ce, "waike motse2n mi kikeyine haka??. Tayi 'kasa da kai tana fa─Ćin babu komai, ya ─Ćauke kansa ya maida bisa titi, ahaka suka isa safana, harta fara murna sunzo, saitaga ya ─Ćauki wata hanyar kuma, tun suna bin birji mai 'kyau har suka koma mai ramuka, yasmeen tagadai tafiyar bamai 'karewa ba ce, harta fara zargin kodai sayar da ita Nawaf zaiyi, ga azababben fitsari yana cinta, haka ta daure, suka wuce wani 'karamin 'kauye tazata nanne, amma saitaga sun wuce, saida suka wuce 'kananun 'kauyuka uku, sanan sukaje wani 'kyauye amma babban garine shi saidai shima 'kyauyene sosai. Tunda suka shigo garin yara ke binsu abaya suna fa─Ćin ga mota ga mota. Yasmeen ta ce, "tofa. Nawaf yanajinta yay mata banza. A'kofar wani gida suka tsaya, amma shi shafe yake da suminti, dukda ginin 'kasane, Nawaf yabu─Ĺe mota yafito batareda yayima yasmeen maganaba. Itama saita bu─Će ta fito, ya danna kai cikin gidan tabi bayansa. Suna shiga gidan aka taresu da murna, dan har yara sunkai labarin zuwansu, yasmeen ta ce, "ma wata 'yar buduwa dan ALLAH ina bayi yake 'kanwata, yarinyar ta ce, zona rakaki. Buta ta ─Ćakko ta rakata, cikin hanzari yasmeen tashige, babu da─Ćewa ta fito suka koma inda aka shimfi─Ća musu tabarma, a 6angaren wata 'yar tsohuwa. Sai asanan yasmeen ta lura da muta nen gidan suna kama dasu Nawaf musamman ma Abdallah dan shi yake kama da papa sosai.......................✍­čĆ╗ Kuyi ha'kuri yau babu yawa, ina busy ne. ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśś ­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗33 & 34 .....Gidan babbaban gidane, wanda za'a iya kira family house, saidai 6angare2 ne, wannan yasa yasmeen tagaza tattance adadin yawan muta nan gidan, dan danan aka cika musu gaba da nau'in kwanikan fura kala2. Gaishe2 aka fara da tambayar juna bayan rabuwa, amma sukan ha─Ća da fulatanci, wanda Nawaf shima yana yarawa, lamarin yabama yasmeen mamaki, bata ta6a tunanin yanajin fulatanciba. Nawaf ya ce, "wai inasu baffa??, 'yar tsohuwa mai ran 'karfe ta ce, "suna gona, wasu kuma suna kasuwa. Ayya ALLAH yadawo mana dasu lafiya, amin saura suka fa─Ća, bayan wani ─Ćan lokaci kowa yafita yabarsu dansu ─Ćan sha furar kafin a kammala abinci. Ita dai yasmeen bin kowa take da kallo, dan bata sansuba, tagadai wasu awajen bikinta, wasu kuma bata gane suba. Nawaf ya juyo yana kallonta, ya ce, "wannan ita ce, hajiya iya kakarmu kenan, kowa ya mutu yabarta, ya'karashe maganar da tsokana. Hajiya iya tayi masa da'kuwa, Nawafa kaci gidanku, kenan sokake na mutu. Nawaf da yasmeen suka tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "nikam ba sunan Nawafa ba, shiyyasa saboda ke bana son zuwa garin nan. Aii dama ba zuwa kakeyiba, sa'idune kawai da umma (momcy)suke zuwa, saisu Abdu, amma kai basai ka ha─Ća shekara biyu bamu gankaba. Nawaf ya tsaya da dariya ya ce, "bahaka bane hajiya iya, ni─Ćin nan dakike gani nafi kowa son garinnan, kawaidai yanayin sana'a tace haka, amma kiyi ha 'kuri tunda yanzu nayi amarya zan runga zuwa ganin uwargida sosai. Yakamata kam, dan babu abinda yafi zumunci da─Ći, shiyyasa nakeson sa'idu fiye da kowa acikin 'ya'yan gidanan, tafa─Ća tana bubbu─Će kwanukan da matan gidan suka tara, ko ina furace da tasha damu da nono mai 'kyau, hajiya iya ta ri'ke baki, to su wa─Ćanan ina suke nufin zakukai wanan uwar hura haka sakace masu cikin zani. Nawaf ya ce, "karki damu duk zamu iya shanyewa kinsanni da son fura. Tami'ke da 'yar sandarta tana fa─Ćin to saiku bada himma, kishiya kisha dayawa ─Ćanyar fata bata fashewa. A'a hajiya iya, sokike cikin matata ya fashe, nazama naki ke ka─Ćai. Hajiya iya tafita tana fa─Ćin ─Ćan nema mizanyi da ─Ćan ta maula. Bayan fitarta yasmeen ta ce, wai kana nufin wannan itace ta haifi papa?. Nawaf ya girgiza kai, wanan kishiyar kakarmu ce, duk yawan matan nan dakike gani daga matan 'ya'yanta sai na jikokinta, kakarmu papa kawai ta haifa, ALLAH yay mata rasuwa tuni itada kakanmu. ALLAH sarki yasmeen tafa─Ća, ALLAH yagafarta musu sukuma. A la66ansa ya amsa da ameen. Yami'ke yana fa─Ćin bari naje nayi sallah lokaci yayi. Yafice yasmeen tana binsa da kallo. Bayan dawowarsa sukaci abinci, zuwa sanan mazan gidan sun fara dawowa, kowa yagansu saiyayi farin ciki da zuwansu, dan sunsan yau sun warke. Zuwa dare Nawaf ya dam'kawa kowa tsarabarsa, sai murna da godiya sukeyi, har makwafta suma an kakkai musu. Nawaf yana 'kofar gida cikin danginsa anata hira da wasa da dariya, dan koka─Ćan baya 'kyamarsu, yanason danginsa sosai, ya kira musu papa a waya sukasha hira, sai wajen karfe tara suka shigo kowa yanufi ─Ćakin matarsa. Yasmeen ma harta fara barci a ─Ćakin hajiya iya, Nawaf yashigo da sallama hajiya iya dake gyangya─Ći ta bu─Će ido, Nawafa ina kashiga kabar yarinya ita ka─Ćai ga gajiya ga ba'kunta, baywar ALLAH harma ta fara barci anan. Nawaf ya ce, "hajiya iya aii anan zata kwana dama, miyasa bataje wajensu kuluwa tayi hiraba?, A'a ni ce, "na hanata dan naga tagaji wannan garin naku mai nisan tsiya. To shike nan ni bari naje na kwanta, sai da safe. Kaga dawo ka tada ita, saitafi sakewa acan, anan aii takura zatayi, dan yaran su hanne fitsarin kwance sukeyi, kuma anan suke kwana, dan haka tada ita kuje can, itama zatafi jin da─Ći aii. Batare da ya ce, "komai ba, yashiga kiran yasmeen! Yasmeen!!, ahankali ta bu─Će adanunta, danji take lamarin kamar amafarki, yauce rana tafarko dataji ya kira cikakken sunanta, amma "k shine sunan dayake kiran ta dashi, koyace mara kunya. Ya ce, "tashi mana, tami'ke tana murza idanu, hajiya iya ta ce, "bita ahankali mana, saida safenku, nasa salmanu yakai muku kayanku tun ─Ćazu. Nawaf ya ce, "to saida safe, yay gaba yasmeen tabishi abaya tana tanga─Ći, ahanya tayi karo da bishshiya dalbejiya, Nawaf ya ri'ke hannunta yana fa─Ćin waike idan kina barci saiki zama tamkar 'yar kwaya??. Itadai batace masa komaiba saima 'kara matse hannunsa datayi cikin nata. Wani 6angare suka shiga agefe da alama shine 6angaren papa, idan kuma sunzo nan suke sauka. ─Äaki ─Ćaya yanufa, wanda aka kunnawa fitilar kwai, 'katuwar katiface a─Ćakin, dan haka suna shiga yasmeen ta kwace hannunta ta kwanta, dan barci takeji sosai. Nawaf ya girgiza kai, yana fa─Ćin yarinya kamar 'yar kwaya?, ya canja kayansa zuwa na barci, "k kitashi ki cire wa─Ćannan kayan mana!. Yasmeen ta gyara kwanciyarta dan ALLAH kabarni ALLAH na gaji barci nakeji, tsaki yayi ya ce, "dallah ca akayi kitashi ki cire wa─Ćan nan kayan, yasmeen ta tashi tana murza idanu, ya hawo katifar ya kwanta, yana mita, zaki wani ishi mutane da fa─Ćin kin gaji to waye bai gajiba?, nida nakawo mu nan bance nagajiba saike!!. Banza tayi masa, tasaka hannu ta kashe fitilar kwan dakeci. Nawaf ya ce, "wane irin iskanci?, ne wanan zaki kashema mutane fitila?, saida ta murgu─Ća baki kamar yana ganinta, ta ce, "to kaya zan cire. Tsaki yaja yakoma ya kwanta, aikin banza ubanmiye abin kallo ajikinki dazaki wani rainama mutane wayo, ya 'kare maganar da kwafa, kyaaaaaak!!! Yasmeen ta ce, "oho dai nidai baza kayi daniba agidan mutane, shiru yayi kamar bai jiba. Tagama shiryawa tai tsaye tana tunanin inda zata kwanta, dan bazata ha─Ća makwanci da 'katoba, ta ce, "kabani bargon na shinfi─Ća a'kasa na kwanta. Ya ce, "zoki kwata mana. Shiru tayi bata tankaba, azatonsa ta kwanta a'kasane, ya─Ćauki wayarsa ya kunna fitila, saiya ganta gefensa tsaye jingine da bango, ya ta6e baki yakashe fitilar ya juya mata baya. Ta saka hannu da niyyar yaye bargon, caraf ya dam'ke hannunta, ya mir─Će, ta kwalla 'kara, ya fincikota ta fa─Ćo jikinsa. Ya ce, "ni wai sa'ankine??. Tai masa shiru tana hawaye, fitilar wayarsa yasake kunnawa, ya haske mata idanu, ta rintse idanunta kam. Ya ce, "matsoraciyar banza, nizaki yayema bargo, ta ce, "nifa ba ─Ćauka zanyiba, ya ce, "to mizakiya. To kasakeni basai na gaya makaba., ya ce, fa─Ći ahaka mana. ALLAH zan cijeka idan baka sakar mini hannuba,, hhhh yaro man kaza, ki cijeni mana, aii kinsan halina sarai. Shiru tayi masa, gata ajikinsa ga hannunta amur─Će, damma yau bai mur─Ćeba sosai, ganin bashida niyyar sakinta saikawai ta maida kanta saman 'kirjinsa ta kwanta, dan barci takeji. Nawaf ya lumshe idanu tareda sakin sassanyar ajiyar zuciya, yasmeen tana jinsa. Ahankali ya janyeta daga jikinsa, dan yanda yakejinsa ─Ćinnan zai iya aikata mata aika2 wlhy. Kwanciyarta yagyara tacigaba da barci abinta. Ya haska fuskarta yana murmushi, wanda shi kansa baisan na miyeba, dahaka barci yay awon gaba dashi shima. WASHE GARI da safe hayaniyar yara ta tada ita, tunda tayi sallar asuba takoma barci, shima Nawaf tundaga sallah bai dawoba, ta tashi ta share wajen, sai asanan taga tsarin wajen, yanada girma babu laifi, akwai ciki da falo sai ─Ćakuna ─Ćai2 guda uku, sai kichin da bayi, ginine dai irinna 'kauye, amma shafe yake da sumunti kamar ko ina agidan. Tayi wanka ta shirya tsaf cikin les tayi 'kyau. Tana shirin fita Nawaf yashigo ya bita da kallo yana fa─Ćin sai ina??, ta ya tsine fuska, zanje nagaida su hajiya iya ne!, ya ce, "to sarkin zumu─Ći, aidai 'kya jira na dawo ko??, itadai batace masa komaiba. Ya shiga ciki batareda yasake tanka mataba, dole ta biyoshi, amma sai tayi zamanta awaje, tana nan zaune yafito dagashi sai tawul, da sauri ta kauda kai, shima saiya ta6e baki yawuce. Koda yafito baibi takantaba yashiga yashirya tsaf cikin 'kananun kaya, harda jibga rigar sanyi mai'kyau dan garin ana─Ćan sanyi, yafito batareda yayi maganaba ya nufi hanyar fita, itama saita mi'ke ta take masa baya. 6angaren baffa sunusi suka fara zuwa, bayan sun gaishesu ya ce, "nanane 6angaren baffa sunusu, shida iyalinsa, shine yake bima papa. Sanan sai 6angaren baffa lurwanu, sai 6angaren baffa ─Äahiru, sai 6angaren baffa haruna. Sanan yakaita wajen 'ya'yansu kowa da matarsa, daganan suka koma wajen hajiya iya. Suka gaisheta, ta ce, "aiida yanzu zanzo na tasoku, sukayi dariya suna fa─Ćin aigamu mun tashi, nan yaran suka fara shishshigowa, yasmeen tana tambayar sunayensu. Nawaf ya ce, "ashe zaki gaji, dan koni bansan yawan adadin yaran gidannan ba wlhy. Saida suka karya sannan Nawaf ya ce, "zasuje su gaida dangi, daga nan har wasu 'yan 'kyauyika dake kusa zasuje. Zaikai yasmeen taga dangi. Hajiya iya ta ce, "tozata iya kuwa, dan kasan mota bata shiga. Ya ce, "karki damu hajiya, itama aii ba'kyauyarce zata iya. Yasmeen ta harareshi, shima ya rama. Cikin gari suka fara zagawa gidajen dangi, duk inda sukayi sai kallonsu akeyi,, garin ya burge yasmeen, ta ce, "kai garinku ya ha─Ću gsky, wlhy kamar karna tafi. Murmushi Nawaf yayi batareda ya ce, "komaiba. Bayan sun gama zaga gari, Nawaf ya 'kar6i mashin ─Ćin salmanu ya ce, "yasmeen tahau. Tsyawa tayi tana kallonsa, ya ce, "k nifa kina 6ata min lokaci, cikin marairaicewa ta ce, "wlhy tsoro nakeji, kaje ka kadani abanza. Nawaf ya─Ćan murmusa, 'yar rainin hankali mikika maidani??, yarinya ni tausayinki naji dan wlhy kafin mu dawo kin galabaita, kuma sonake muje ko ina yau, dan gobe zamu koma safana, dan haka idan kinga zaki hau ki hau. Jiki a sanyaye ta kama mashin zata hau saida ta rirri'keshi sanan ta iya hawa, ya tada mashin suka tafi. Aikuwa da gskyar Nawaf, tabbas da a'kafa sukazo dataji jiki, ammafa atsorace take bisa mashin ─Ćin, bata san lokacin datasaka hannunta biyu tai masa zobeba, ta kwantar da kanta abayansa. Ahaka suka isa wani 'kauye, Nawaf yatsaya awani 'kofar gida na jar 'kasa,, ya ce, "to ba'kauya sauka, kinbi kin wani 'kan'kameni, kinsa sai kallonmu akeyi. Ta sakeshi ta sakko tana fa─Ćin, wlhy suyita kallo, ai babu wanda yasanni, da asara gara gidadanci. Yakafe mashin ─Ćin yana dariya, to ke idan kin fa─Ći wayayi asarar. Ta ce, mutane dayawa kuma harda kai aciki wlhy. Kai haba ALLAH yakiyaye, ni aii narabu da 'kayama". Tsaki yasmeen tayi, ta ce, "aikai kafi 'kayarma. Gaba yayi yana fa─Ćin idan mun koma gida zaki maimaita. Suka shiga gidan da sallama, wata dattijuwa ta ─Ćago tana amsawa da fara'arta, ta ce, "wanake gani kamar Nawaf, Nawaf yay 'yar dariya nine kuwa inna, kai lale daku, sannu dazuwa kinji ─Ćiyata. Yasmeen ta amsa da 'yauwa, inna ta kwala kiran dijengala!!, wadda aka kira dijangala ta amsa tana le'kowa. Inna ta ce, "kawo tabarma maza. To tafa─Ća tana komawa cikin ─Ćakin, sabuwar tabarma dijangala tazo ta shinfi─Ća, tana fa─Ćin yaya na birni sannu da zuwa. Nawaf ya ce, "yauwa dijengala ya garin??, ta ce, "gashinan 'kalau, ta ce, "sannu amaryar yaya, yasmeen ma ta amsa tana murmushi, bayan tagama suka zauna, aka shiga gaishe2, da tambayar juna bayan rabuwa. Dijangala ta kawo musu ruwa, itadai yaameen sai kallonsu takeyi, dan ganin yanda suketa zabga sururutu, misamman ma dijangala, dan ita adole son Nawaf takeyi, shiyyasama ta'ki aure, tun abin yana burge yasmeen haryakoma bata haushi. Babu kunya dijangala ta ce, "yaya na birni nimafa nagaji da zaman nan gsky, Nawaf ya ce, "tokiyi aure mana, baga su sa'a nan ba harsun haihu, kuma kin girmesu. Tai far da idanu, to ai kasan kainake jira ko??, wata bazawarar dariya Nawaf yayi, ya ce, "yarinya kin ─Ćakko dala babu gammo, bakiga matata tafiki 'kyauba, kuma ni mijin ta cene. Dijangala ta rage fara'a, dan tada─Će tana nunama Nawaf tana sonsa, amma saiya maida abin wasa, dayake abokan wasa suke. Nawaf ya katse mata tunani dafa─Ćin inna kinji wani ─Ćigimi wajen dijangala, ko inani ina auren baiwata?. Inna habi ta ce, "aii komai na ALLAH ne, (WAYASAN GOBE??,) Nawaf ya ─Ćan ta6e baki dan yasan itama innar duk jirgi ─Ćaya ya kwasosu da 'yar tata, ya ce, "sai ALLAH, amma yakama ku aurar da dijangala kafin tarasa miji a 'kauyenana wlhy. Dijangala ta ─Ćaure fuska tamau kamar zatayi kuka, agaban matarsa yake gaya mata haka saboda wula'kanci. Itama ran inna habi ya 6aci, jitake kamar ta doke Nawaf, dan itama tana fata dijangala ta auri Nawaf kodansu 'kara hutawa. Nawaf ya kalli yasmeen data cika tayi fam kamar zata fashe saboda kishi, shi dariyama ta bashi, amma saiya gimtse ya ce, " 'yammata tashi muje munada sauran gurin zuwa. Yasmeen tami'ke tana zuzzun6ura baki, sukayi musu sallama suka fito, bayan Nawaf ya ajiye musu ku─Ći da tsaraba. Amma ko godiya basu yimasaba, shima bai damuba, dan hakan yafi sau'ki, inashi ina wannan kucakar yarinyar mai kamada 'yar bori. Koda suka fito yasmeen sai wani shan 'kamshi takeyi, Nawaf ya ce, "yammata tunkan nayi auren har kin fara nuna kishi??. Yasmeen ta murgu─Ća baki­čśĆtana harararsa­čÖäta ce, "ALLAH ya kiyaye, miye abin kishi awurinka, ai abinda kakeso kakeyima kishi. Dariya Nawaf yayi yana fa─Ćin aii kuma kin makaro yarinya, fuskarki ta nuna sirrin zuciyarki, dan haka babu abinda zaki fa─Ća na yarda. Tsaki yasmeen tayi tana fa─Ćin matsalarkace dai. Yahau mashin ─Ćin yana fa─Ćin kokuma takiba, kina ba'kinciki nasamu amarya, aiko saidai ki fashe nanda wata shekarar za'a sha biki. Banza tayi masa ta haye mashin─Ćin tana hawaye. Yanajin shashshekar kukanta, yayi murmushi kawai, azuciyarsa ya ce, "yarinya ta kamu. Haka sukaita zagaya dangi har yamma, sanan suka koma gida, a─Ćakain hajiya iya suka yada zango, ta ce, "sannunku, kishiya kinsha yawo ko?, yasmeen tayi dariya tana fa─Ćin ai da─Ći, naga gari. Hajiya iya ta ce, "yayi 'kyau. Bayan magriba ta tafi 6angaren su kuluwa matar basiru, dayake duk sa annintane, saidai kowaccensu tanada yara uku zuwa hu─Ću, idan ka gansu saika ─Ćauka sun haifeta, yasmeen ta ce, "azuciyarta dayanzu nima haka nakoma a kwangwalan, kai ALLAH na gode maka. Hira tazauna sunayi, suna labarin bikinta da 'kauyancin dasukayi awajen anata tuntsura dariya, firera matar salmanu ta ce, "aini da akaje wajen dakuka saka wa─Ćan nan rigunan kamar aljanu, da hasken wajen ya haskani saina ru─Će nashiga ─Ćimuwa, saida basira ta taimaka mini. Gaba ─Ćaya suka kwashe da riya, hira sukeyi sosai har wajen 'karfe tara, mazajensu suka fara shigowa gida, yasmeen tami'ke tana fa─Ćin bari naje na kwanta nima, wlhy duk nagaji. Tana tashi ta kwalla 'kara, ta zube awajen, cikin tashin hankali suka shiga tambayarta lafiya??. Ta ce, "wani abu ya cijeni a'kafa, wayyo ALLAHna, da sauri sha'aibu mijin barira ya haska, zuwa sanan Nawaf ya 'karaso waje danjin 'karar yasmeen. 'Katuwar kunama suka gani ba'ki'k'kirin, ta tada bindi sama­čŽé, sha'aibu ya ─Ćauketa da hannunsa, ya kashe, Nawaf ya'karaso wajen yasmeen daketa zabga zufa. Ya ─Ćagota zuwa jikinsa, ta ce, "modebbo ka taimakeni tafiya takemin, sai asanan kuluwa tai saurin cire ─Ćankwalinta ta ─Ćaura mata a'kafar. Nawaf ya rungumota zuwa jikinsa yana share mata zufar, yana fa─Ćin sannu kinji yi ha'kuri, salmanu yazo yasaka mata magani, sai sannu suke mata, aka zuba wani aruwa aka bata tasha, dandanan zufar ta 'karu, salmanu ya ce, "yaya ka ─Ćauketa kujecan zata fa─Ći insha ALLAHUi. Nawaf ya ce, "to, cak ya ─Ćauki yasmeen zuwa 6angarensu, suka rakasu da ALLAH ya kiyaye gaba. Saman katifa ya direta tanata zufa, ya ce, "sannu". Ta ka─Ća kai tana hawaye. Ya ce, "haryanzu tana miki yawon??, tace ba sosaiba amma. insha ALLAHU zata daina gaba ─Ćaya, bari acire miki wa─Ćanan kayan kinga kinata zufa, batareda yajira amsartaba, yakama zip ─Ćin ya sauke zuwa 'kasa, yasmeen ta rintse ido tana huci, yakama bra ─Ćinta xai cire, da sauri tajuyo tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, amma ya─Ćan ─Ćaure fuske, ya ce, "kafiya??". Cikin rawar murya ta ce, "plz kabarsa kawai, ya ta6e baki yana fa─Ćin keni bana son iyayi, bakida lafiyarma saikin jawo munyi, ko ba'kya ganin zufar dakikeyine??,. Ta ce, "to kafita zan cire da kaina nidai. Tsaki yayi saidai idan bazaki cireba kuwa, dan wlhy babu inda zanje. Ta ce, "to maidamini zip ─Ćin rigata, tunda ni yaronkine ba, yafa─Ća yana kwanciya. Hijjabi ta jawo tasaka, sanan ta cire rigar, taja zaninta zuwa sama, yana kallonta tana ta zufa, ya ta6e baki, daga nan ya ─Ćauki wayarsa yana danne2nsa, sai wajen karfe goma kunamar ta fa─Ći, yasmeen ta mi'ke waizata tayi wanka. Nawaf yashiga tuntsura mata dariyar mugunta, cikin jin haushi ta ce, "malam lafiyarka kuwa??, Nawaf yacigaba da dariyarsa batareda ya kulataba, harta kai 'kofa zata fita, ya ce, "wlhy kije kiji'ka tadawo sabuwa, kezakai sha wahalarki ke ka─Ćai, danni ficewata zanyi nabar miki ─Ćakin wlhy. Ita sai yanzuma tatuna idan kunama ta harbeka ba'a saka ruwa, tadawo bakin katifar ta zauna ta rabga tagumi. Nawaf yacigaba da dariyarsa ta rainin hankali, itadai banza taimasa ta'ki kulasa. Yafara fa─Ćin modebbo ka taimakeni tafiya takemin. Tagane kwaykwayon muryarta yakeyi, dan haka ta harareshi tana murgu─Ća baki, ya ce, "yarinya ashe zaki sake shan wata wahalar wlhy. Ta ce, "wlhy saidai musha, dan ba 'kyaleka zanyiba, yatashi daga kwanciyar dayayi, ya ce, "sake murgu─Ća wannan bakin maikama da na tsintsaye kigani. Saida tazamo daga katifar sanan ta murgu─Ća­čśĆ. Tami'ke da sauri, zata gudu, taku ─Ćaya yayi ya dam'kota, yamaidata saman katifar, saman cikinta yahaye, yakama fuskarta da hannu biyu, ya ha─Će bakinsa da nata yashiga kissing ─Ćinta. Itako sai mutsu2 take nason ta kwace amma takasa, gashi ya danne mata ciki, saida yayi mai isarsa sanan yasaketa yana maida numfashi, tabirkice zuwa rubda ciki tana kuka, tana tofar da yawu, 'kazami kawai, zakawani ta bani yawunka inasha, sai ALLAH yasaka mini wlhy. Kusada ita yakwanta, yadafa bayanta, 'yammata gobema ki 'kara yimini murgu─Ća baki ki gani, saina miki abinda yafi haka, ya 'kare maganar yana dukan bayanta. Ta mirgina 'kasa tana cigaba da goge baki da hijjab, Nawaf kuma yana mata sassanyar dariya, yajuya ya kwanta yana murmushi wanda shi kansa baisan na miyeba, a hankali yafurta 'yar rigima. Saida taga yayi barci sanan tadawo saman katifar, takwanta agefe nesa dashi kamar yanda tayi jiya. Washe gari tunda safe saddiqu ya wankema Nawaf motarsa, zuwa 'karfe goma suka baro 'kauyen cike da kewar muta nan garin, masu kirki da karrama ba'ko, yasmeen harda hawaye. Suma 'kyauyen sun tafi sun barsu da kewarsu. A safana suka yada zango, gidan wani abokin papa, nanma sun zaga dangi, ananma yasmeen taga 'yammatan dasukaje bikinta dayawa, sunyi farincikin ganinta itama haka. Anan batare suka kwana da Nawaf ba, a─Ćakin matar abokin papa ta kwana, shikuma ─Ćakin ba'ki. Washe gari suka ha─Ća inasu2 suka garzayo kano, cikeda uwar tsaraba, yasmeen takali Nawaf daketa wani ─Ćaure fuska, ta ta6e baki tana fa─Ćin mutum tamkar mai aljanu, yanzu zaka gansa yana dariya, yanzu zai ─Ćaure fuska kamar rundunar sojoji, har suka iso kano basa wata hirar arzi'ki, saidai ita dake tambayarsa sunayen garin dasuke wucewa, ada'kile yake bata amasa, itama daga baya saita kulle bakinta gam. Dahaka suka iso kano, cikin farinciki su momcy suka taresu, momcy ta ce, "─Ćiyata kinyi ba'ki wlhy, yasmeen tai murmushi tana sissine kai, hajja ta ce, "Nakuwa ha─Ća muku abinci mai da─Ći na tarba, dan haka saiku shirya ci. Nawaf ya ce, "kai hajja da kanki, amma kinyi 'kokari. Ta ce, "nayi kewarkune shiyyasa. Nawaf ya ce, "to mungode miki hajjarmu abin alfaharinmu. Yasmeen ta ce, "momy wai ina su Anwar???, suna islamiyya fateema, amma nasan suna hanyar dawowa, dan tun safe ake shirye2 dawowarku. Yasmeen tayi murmushi tana fa─Ćin ALLAH yadawo dasu lafiya...................✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Nagode da sakwanin gaisuwarku gareni, harma wa─Ćanda basu sami damaba,,,,, happy juma'at khareeeeem! !!! Luv u oll­čśś­čśś­čśś­čśś❤❤ ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśś­čĺ× [1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗35 & 36 ......Tunda suka dawo basa shiga harkar juna, sun koma zaman doya da manja, gaisuwa ce kawai ke shiga tsakaninsu, saikuwa girki da yasmeen zatayi, yazo shikuma babu kunya yaci. Abin yana bama yasmeen mamaki, idan ta tuna abinda Nawaf yarin'ka yimata a safana, takai dubanta ga 'katon hoton Nawaf dake falon, yana sanye cikin jan jc yayi 'kyau sosai, afili ta ce, "mutun 'kya'ky'kyawa a waje, amma azuciyarsa yafi maciji mugunta, ta gallama hoton harara. Nikam danake gefe na tuntsure da dariya, dan tabani dariye, kome hoto yay mata??. ☆ ☆ ☆ ☆ Ayaune kuma hajja zata lula saudia, fuskar kowa ka kalla a gidan babu walwala, amma babu yanda zasuyi, haka sukai gayya suka rakata airport Anwar sai kuka yake wai saiya bita, papa ya ce, "yabari ayi hutu saiya tafi, hakadai suka dawo gida kowa yana zum6ura baki. Yasmeen ma dabata da─Će da sanintaba saida taji babu da─Ći, dan hajja tsohuwace mai shiga rai, ga kirki da son mutane, lallai anan momcy ta kwaso 'kyawawan halaye, to saimuce hajja ALLAH ya kiyaye hanya. Tunda suka dawo daga 'kauye yasmeen batada cikakkiyar lafiya tana 6oyewane kawai, amma yau dole ta kwanta, shi oga Nawaf ma bai saniba, dan yanata hidimar komawarsa Spain. Saida momcy taga har la'asar yasmeen bata shigo wajensu ba sannan, tafara tunanin ko lafiya, ta mi'ke ta nufi 6angarensu, babu kowa a falon saidai an gyarashi tsaf yanata 'kamshi, kai tsaye bedroom tawuce, da sauri ta 'karasa bakin gadon domin ganin yasmeen a 'kudundune cikin bargo. Momcy ta zauna agefen gadon ta─Ćan ─Ćaga bargon tana fa─Ćin ─Ćiyata kina lafiya kuwa?....ta 'karashe maganar a ahankali, danjin zafin zazza6i a jikin yasmeen. Dan danan momcy ta ru─Će tashiga tambayar yasmeen tun yaushene batada lafiya?, yasmeen ta bu─Će ido da 'kyar, ta ce, "momy tunda daddarene. Cikin damuwa momy ta ce, "amma shine baki fa─Ćaba?, ina modebbo??. Yasmeen ta ce, "yafita tunda safe. A'a, baisan bakida lafiyaba ne??, yasmeen ta daga kai alamar eh. Waya momcy ta ─Ćauka takira Nawaf, modebbo kana inane??, Nawaf ya ce, "ganinan zuwa gida ma. To saika iso momcy tafa─Ća. Abinci mai sau'ki momcy tasaka su talatu su dafoma yasmeen, ta taimaka mata tayi brosh da wanka dantaji da─Ćin jikinta, tana fitowa Nawaf yana shigowa, tayi tsaye kamar gunki shima tsayen yake yana 'kare mata kallo, dan suka─Ćaine a ─Ćakin, momcy tana falo. Da sauri yasmeen taja hijjabin sallarta ta kudundune aciki, baki Nawaf ya ta6e yana wani yatsine fuska. Itakuma tawuce ta zauna bakin gado, momcy tashigo da sallam tareda talatu. Sai asannan Nawaf yazauna akan kujera, momcy ma ta zauna talatu kuma ta ajiye abinda takawo ta fice, momcy ta ce, "─Ćiyata saboda mi baki gayama mijinki bakida lafiyaba?, dan ya ce, "mini shima bai saniba. Saida yasmeen ta kalli Nawaf sannan ta ce, "banaso hankalinsa ya tashine. A'a wanan ba hujja bace, yaza ayi ki zauna da ciwo saboda kar hankalin mijinki yatashi, daga yau karki sake kinji ko?, yasmeen ta ce, "to momy insha ALLAHU baza'a sakeba. Nawaf ya ce, "momcy bari na kira mas'ud yadubata, dan naga bai fitaba. To, yakamata kuwa. Momcy dakanta ta bata abincin taci, sai yatsine fuska takeyi, ahaka su Nawaf suka shigo suka isketa, mas'ud yay mata sannu, tana gama cin abinci ta tashi da gudu ta nufi bayi, amai ta ringa zazzagawa kamar hanjin cikinta zasu fita, momcy tabiyo bayanta dasauri, ta taimaka mata hartagama tagyaramata jikinta, sanan suka dawo ─Ćaki. Su Nawaf suka shiga yimata sannu, ahankali take amsawa, tahau gadon ta kwanta, momcy ta ce, "mas'ud ai inagama wanan ciwon na yasmeen baya bu'katar gwaji. Mas'ud ya ce, "momcy saboda mi??, momcy tayi murmushi tana shafa kan yasmeen ahankali, ta ce, "mas'ud inaga lokaci yayi dazamuga yara suna tsalle2 agidan nan. Nawaf da mas'ud suka kalli juna cikin zaro idanu. Mas'ud yadaure ya ce, "dukda haka dai momcy barina dubata, saimuga maganin daya dace abata. Momcy ta ce, "to zoka dubata, ta tashi takoma kusada Nawaf daya shiga cikin waswasi da fa─Ćuwar gaba, momcy tadafa shi ya ─Ćago da sauri yana kallonta, saikuma yamaida da kai 'kasa da sauri, momcy tayi dariya tana fa─Ćin modebbo yaukuma kunyata akeji??, ai wanan abin farincikine. Nawaf ya daure ya ce, "momcy bafa ciki garetaba, ciwone kaiwai nake gani. Mas'ud ya katse musu hanzari da fa─Ćin bari naje nayi text daga nan asamo mata maganin daya dace. Nawaf ya mi'ke yana fa─Ćin muje tare, momcy tabisu da kallo tana murmushi. Suna fita mas'ud ya tuntsure da dariyar mugunta, Nawaf yabishi da kallon mamaki, kai wai lafiya?, ko ciwon haukane yasameka yanzunnan?. Cikin dariya mas'ud ya ce, "mutumina aikaine lamarin naka yay kama da abin dariya, wai yaushe akaje wajenne??, har saka mako yafito?. Nawaf ya yatsine fuska yana fa─Ćin ban ganeba?. Mas'ud ya ha─Ćiye dariyarsa, ya dafa kafa─Ćar Nawaf yana fa─Ćin abinda nake nufi ai afili yake malam. Nawaf ya ta6e baki, kai nifa abinda kuke zargi daga kai har mom ba haka bane, babu wani ciki da yarinyarnan take dashi. Mas'ud ya ce, "ban ganeba kai kana nufin yasmeen batada ciki, harara Nawaf ya sakarma mas'ud, to ana shan cikin aruwane dazakace wani baka ganeba, kainifa wlhy babu abinda yashiga tsakanina da yarinyarnan. Taf ─Ćijan inji mata, mas'ud yafa─Ća, to malam momcyfa jika suke so, dan nakula tana cikin farin ciki, amma gsky wannan ba dabara bace, idan kai zaka iya jurewa ai ita kana shiga ha'k'kinta ko??. Tsaki Nawaf yayi, yana fa─Ćin matsalarta ce, nibabu wani ha'k'kinta dake kaina malam kaji. Dariya mas'ud yayi, humm Nawaf kenan, akwai lokacin dazai zo, kazo neman shawarar hakan agurina, kuma wlhy tanada ha'k'ki a wajenka, kaima kasani sairai, saidai katake sanin,. Hhhhhh ashe shekarun dayawa kuwa, Nawaf yafa─Ća. Dahakadai suka 'karasa asibitin, bayan sunyi duk abinda yadace suka dawo gida da magunguna, amma dai text yanuna ba ciki bane. Koda suka gayama momcy saitace, babu komai shima cikin yana zuwa insha ALLAHU. tunda yasmeen tasha magani take barci, bata farkaba sai cikin dare, tajuya taga Nawaf agefenta kwance yana kwasar barci, ta lumshe ido ahankali ta sake bu─Ćewa, sakkowa tayi tashiga bayi tayi wanka dan jikinta duk ciwo yakeyi. Jin motsin ruwa yasa Nawaf farkawa shima, ya laluba gefensa saiyaji babu yasmeen yatashi yanufi bathroom ─Ćin, ahankali ya tura 'kofar saiyaji ta a bu─Će, yako tura kai cikin bayin batareda neman iziniba. Dasauri yasmeen tajuyo danjin motsi, ta kwalla 'kara dan ganin Nawaf tsaye yana kallonta, ta rarumi tawul ta 'kudundune jikinta. Da sauri Nawaf ya'karaso gabanta yana fa─Ćin "k dallah karki taramin mutane. Da'karfi ta ce, "to kafita mana, miye haka zaka wani shigo mini ina wanka. Tsaki Nawaf yayi ya ce, "ubammi zan kalla ajikinki, aikin banza kawai, yafa─Ća yana ficewa. Yasmeen tazauna jagwaf tana maida numfashi da'kyar, ta runtse idanu gam tana hawaye. A6angaren Nawaf madai hakan take, jagwaf yafa─Ća saman gadon yana fitar da huci mai zafin gaske. Yasmeen tada─Će bata fitoba, saida ta daidaici Nawaf yayi barci sannan tafito, ta saka riga mai ─Ćan kauri ta kwanta saman kujera. Nawaf yana kallonta, yaja Numfashi ahankali, gsky shikam yana bu'katar matarsa, amma yarasa hanyar dazaibi yacika burinsa, dawanan tunanin barci yakwasheshi ___________________________________ haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri, Nawaf yanata shirin komawa Spain. Yauma yana wajen papa suna tattaunawa, papa ya ce, "yanzu idan katafi sai yaushe??. Nawaf yay 'kasa da kai yana fa─Ćin papa da'an gama kakar wasanni insha ALLAHU zamuzo hutu. To shikenan, ammafa idan kadawo da matarka zaka koma, dan bai daceba ace kana can matarka tana nanba, tunda kana da─Ćewa baka 'kasar. Kan Nawaf a'kasa ya ce, "to shikenan papa, ALLAH yakaimu lokacin. Papa ya ce, "amin. Daganan Momcy tashigo itama suka cigaba da tattaunawa, sun da─Će suna hira saida papa ya ce, "yatashi yaje wajen matarsa, Nawaf yami'ke badan yasoba yatafi. A falo ya isketa tana waya da umma tana hawaye, ya zauna kujerar dake kallonta jiki a sanyaye, itako bama tasan ya shigoba, tacigaba da wayarta, umma wlhy iya gsky ta nake gaya miki, nikam nagaji wlhy. Tai shiru zuwa wani lokaci, tasaka hannu tana share hawaye, ta ce, "to shikenan umma nagode sosai, to ALLAH yakaimu. Sai asanan takula da Nawaf, ta kauda kai daga kallonsa. Nawaf ya ce, "k dawa kikeyin waya?, kuma wayace ki ─Ćaukarmin wayata kiyi kira?. Banza tayi masa kamar batajiba, tamaida kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, haushi ya tokare ma'koshin Nawaf, jiyake kamar ya doketa agurin, dan bayason kuka musamman kukan mace, yami'ke cikin haushin rashin amsa masa maganarsa datayi, kujerar datake zaune yadawo, yasa hannu ya─Ćago fuskarta. "K!!! Wai wane irin iskancine zaki zauna kinama mutane kuka, kamar wadda akaima wani abu, kuma kinaji ina tambayarki amma kikayimini banza. Cikin rawar murya ta ce, "tomi kakeso nace maka?, aidai kasan babu wanda zankira a wayarka sai 'yan gidanmu ko, kuma aiga wayarnan ka─Ćauka kakira number dana kira saikaji waye??. Kuma wayarka dake fa─Ćin wayace na ─Ćauka, kai wayace ka fasa mini tawa wayar??. Nawaf ya zazzaro idanu yana fa─Ćin "k!! Wlhy ki kiyayeni, kar 'kuruciyar ki tajaki ki ─Ćakko mini zancen wani 'kato anan, dan wlhy zan iya zaneki!!!. Yasmeen ta tsorata da Nawaf sosai, amma bataso ta nuna masa tana jin tsoronsa, dan zai samu lagontane. Itama ta zazzaro nata idanun, ta ce, "aikai kajika, sai ba'kin kishin tsiya, wlhy kayi wasa sai zuciyarka ta tarwatse abanza, nikam an cuceni wlhy da aka ha─Ćani aure da kai, shiyyasa bazan ta6a sonkaba kuwa har......... Kafin ta rufe baki ya matse bakinta da 'karfi, yasa ─Ćayan hannunsa ya matse gashinta, ya ce, "k!! karki ─Ćauka kishi nake akanki, karki ─Ćauka nima zan soki, dana soki gara naso dijangala, domin koba komai 'yar uwatace, inada wa─Ćanda suka fiki komai dayawa yarinya, ki kalli ummu habiba, yarinya 'kya'ky'yawa jinin larabawa, mai ilimin addini dana boko, akwai irinsu dayawa dasukeson na kasance mijinsu, tundaga turawa har ba'ka'ken fata, dan haka ki daina ─Ćaukar kanki "k wata tsiyace awajena. Ya fisga gashin sanan ya hanka─Ćata ta bigi kujera, yabuga yatsun hannunsa biyu yana fa─Ćin "k ba komai bace, face 'yar aiki, mai jiran tsammani, ki ─Ćauka darajar iyayenace tasa nake zaune dake, kuma ina ganin mutuncin iyayenki, domin muta nen kirkine, amma daba hakaba hummmmm ya 'karashe zancen acikinsa. Yasaki bakinta yashige bedroom, sai asannan tasamu damar yin kuka, takoyi kuka mai isarta harta koma bani tausayi. Ranar afalo ta kwana,. Washegari Nawaf tunda yafita daga gidan bai dawoba sai dare. Afalo ya isketa zaune ko kallo bai ishetaba shima ─Ćin haka, yay wucewarsa bedroom. Tsaki yasmeen taja tana fa─Ćin mugu kawai mai ba'kin hali, koda yashiga ─Ćakin kayansa yashiga ha─Ćawa dan gobe zai ─Ćage zuwa Spain, amma bai sanarma yasmeen ba. Yagama ha─Ća komai sannan ya kwanta yana tunanin yanda zaiyi da yasmeen dan shidai bazai sanar mata zai tafi gobe ba, kuma bayaso papa ko momcy suji cewar bai sanar mataba. Yajawo ledar daya shigo da ita, yaciro wata ha─Ća─Ć─Ćiyar waya akwali, yabu─Ćeta ya'kare mata kallo, sannan ya ─Ćakko biro da takarda yafara rubutu­čôŁyagama ya ninke yasaka acikin wayar ya ajiye yay kwanciyarsa. Saikuma wata dabara ta fa─Ćo masa, ya─Ćauki waya yana surutu kamar yanayi dawanine, harfalo yafito yana fa─Ćin karka damu insha ALLAH gobe zan iso Spain, zan biyo jirgin 'karfe bakwai nasafe da ixinin ALLAH. okey babu damuwa nagode zataji saina iso. Yasmeen tanajinsa, sai abin yabata mamaki, wai kana tareda mijinka amma yagagara sanar dakai zai tafi, wanan wace irin rayuwace, wasu hawaye suka wanke mata fuska, shikuwa tuni yakoma bedroom abinsa. Haka takwana rabi barci rabi tunani, aiko dasafe ta makara, sanda ta tashi 7:30am tadiro dasauri daga kujera tanufi bedroom wayam tagani Nawaf yatafi, hawaye suka shiga yimata ambaliya a fuska, jiki asanyaye tayi alwala tayi sallar asubahi. Tana zaune saman sallaya momcy tashigo, yasmeen ta─Ćago da sauri tazata Nawaf ne saitaga momcy, batasan sanda sabon kuka yazo mataba. Momcy tazauna ta rungumota zuwa jikinta tana lallashi, yihakuri barkuka, shiyyasa mijinki ya ce, "kar'a tadaki daga barci, dan tunjiya kike kuka, to kiyi ha'kuri aiba da─Ćewa zaiyiba zai dawo, kuma idan yadawo tare zaku koma kinji. Azuciyar yasmeen ta ce, "wato 'karyar daya shirya muku kenan?, ba komai zanyi maganin shi dakaina agidannan, komai yanada lokaci, nasan nima nawa lokacin yana zuwa. Nan momcy tayita lallashinta, daga 'karshe ta ce, "idan kinajin tsoro kishirya kayanki, ki koma ─Ćakina, idan yadawo saiki komi nan kinji, idan kuma ba'kyajin tsoro tokiyi zamanki anan ─Ćin. Da sauri yasmeen ta ce, "momy zanbiki can. Toshikenan tashi ki shirya kayanki kinji, bari na turo miki Anwar yatayaki ─Ćauka, ta ce, "to. Ta shirya duk kayan dazata iya bu'kata, sai asanan taga ledar daya ajiye, yarubuta nakine idan kina bu'kata. Kai kawai ta girgiza ta─Ćauki ledar tasaka cikin kayanta, Anwar da Abdallah sukazo suka tayata ─Ćaukar kayan, suka kashe duk wani kayan wuta na wajen, suka rurrufe ko ina. Tundaga ranar takoma ─Ćakin momcy da zama, tanajin da─Ćin zaman, saidai tunani Nawaf da kewarsa duk sun addabeta, har takanyi mamakin kanta, yanda tadamu da mutumin dabai damu da itaba, wanda bazaman lafiya sukeyiba sanda yana nan, taja 'karamin tsakai tareda gyara kwanciyarta, 'kilama shi yamanta dawata halitta yasmeen. Tasan Nawaf bazai ta6a sontaba sai wani abu ga ALLAH, wanan kuma ikonsane, yakan aikata duk yanda ya so, alokacin daya so. ________《》__________ To shimadai Nawaf hakan take agareshi, tunda yasauka 'kasar Spain bashida wani sukuni, tunanin yasmeen duk yacika masa zuciya da ruhi, bashida aiki sai tunaninta, yakanyi dariya idan yatuna wani fa─Ćan nasu, yayi waya da kowa nagidan amma banda ita, yatambayi Anwar ya ce, "baiga ta ha─Ća wayar daya saya mataba. Yana matu'kar bu'katar yin magana da'ita amma yarasa hanyar dazaibi. Ya lumshe manyan idanunsa masu haske, ya maida kansa jikin luntsume miyar kujerar dake falonsa yakwantar, tabbas yasan yafa─Ća tarkon son yarinyarnan, kuma yalura ita bata 'kaunarsa, haushinsama takeji, saboda har yanzu soyayyar tsohon mijinta tana tareda ita. Ya'karashe maganar kamar xaiyi kuka, yashiga girgiza kai yana fa─Ćin A'a FATEEMA ZARAH karkimin haka, nine kawai yadace ki so, domin dani kika dace, jiki yana rawa ya─Ćauki ─Ćaya daga cikin wayoyinsa yashiga kiran Anwar, harta tsinke ba'a ─Ćaukaba, yatuna yanzu yana islamiyya wajen karatun dare. Yamaida akalar kiran zuwa Abdallah shikuma tashi akashe, yayi tsaki, saikuma yakira momcy, bugu ─Ćaya biyu ta ─Ćauka, bayan sun gaisa yatambayi lafiyar kowa. Ta amsa dakowa yana nan lafiya, ya ce, "masha ALLAHU haka akeso, yanaso ya ce, "tabama yaameen amma yanajin kunya, dan haka sukayi shiru suduka, momcy takatse shirun da fa─Ćin Abdallah ya ce, "yau da daddare zakuyi wasa ko??. Eh momcy insha ALLAHU, sai a tayamu da addu'a. Babu damuwa kullum ita muke muku ALLAH yabada sa'a. Amin momcyna ngd, bari nabarki haka ki gaida min dasu. To sai anjima zasuji. Yasmeen tana zaune tana jinsu, abin ya sosa zuciyarta, tunda yatafi bai nemetaba, amma kullum yana kiran iyayensa da 'kannensa, ─Ĺazu datayi waya da yaseer a wayar Anwar yake gaya mata babu da─Ćewa yayi waya da yaya Nawaf, amma ita banda ita, wasu 'yan kwalla suka taru mata agefen idonta, tai saurin sharewa kafin momcy tagani. Su Anwar suka dawo daga islamiyya, suka zauna suka cigaba dahira, dukda ita yasmeen firar bawani da─Ći takemataba, danma anasako Nawaf a firarne da tuni taje ta kwanta. Suna nan zaune har aka fara kallon wasan su Nawaf ─Ćin, ta─Ćanji sanyi data ganshi, tunda wasan Life ne ake nunawa, sai wani murmushi takeyi najin da─Ći, ana haka su Nawaf sukaci kwallo kuma shine ya zura kwallon. Su Anwar suka shiga murna da tsalle, itamadai ta─Ćanyi murnan, damma ganin momcy awajen ta─Ćan kanne saboda kunya. Haka rayuwa yacigaba da tafiya yauda gobe sai ALLAH, yau watan Nawaf ─Ćaya datafiya, kuma har yanzu basu ta6a gaisawa da yasmeen ba, ga kowannensu yana cikin muradin son jin muryar ─Ćan uwansa, amma hakan ya gagara, suduka suna cikin begen juna, garama yasmeen tana ganinsa yayin dasuke wasa, takan─Ćan rage damuwa. ________________________________ ____ yauma tana kwance a─Ćakin momcy abin duniya duk yadameta, saitaji wayar Abdallah dake gefenta tana wringing, takai hannu ta─Ćauka saida gabanta yafa─Ći dataga ansa yaya Nawaf, ta rintse ido tabu─Će, har wayar ta'katse, yasake kira itama ta katse, ana ukunne ta ce, "bari ta─Ćaga. Jiki a sanyaye ta ─Ćaga wayar, muryarsa ta daki dodon kunnenta, tarintse idanu, cikin fa─Ća ya ce, "kai wane irin iskancine anata kiranka ka'ki ─Ćagawaya??, ubammi kakeyi??. Yasmeen tayi shiru takasa magana dan tsoro, shikuma jin anyi shiru yacigaba da bala'insa, ahaka Abdallah yashigo, da sauri ta mi'ka masa wayar....................................✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Kuyi ha'kuri masoyana, kunjini shiru ko??, wlhy har yanzu banida lafiyane, saida nakwanta asibiti kwana biyu. Ngd sosai. Luv u oll❤❤❤­čśś ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśś­čĺ× [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗37 & 38 ......Abdallah yakara wayar akunnensa tareda fa─Ćin Abi!!. Nawaf ya daka masa tsawa kai!! Dallah yimin shiru mana, sai yanzu kaga damar yimini magana. Cikin rawar murya Abdallah ya ce, "Abi kayi ha'kuri wlhy bana kusada wayar, aunty ce ta─Ćaga. Nawaf yaja tsaki wace aunty??. Aunty yasmeen mana, wayana tana hannunta ne, yanzu nashigo shine tabani. Nawaf yaja wani gwauron numfashi ya ce, "tana ina??. Da sauri Abdallah yajuya inda yasmeen take zaune amma saiyaga wayam ta tashi ya ce, "Abi ta tashi, bari na duba kotana falo. Ya duba falo batanan har waje. Ya ce, "Abi wlhy ta 6uya yauma. Shiru Nawaf yayi danji yake kamar zuciyarsa zata fashe, ya kula da gayya yasmeen take 6uya aduk lokacin dayace abata waya, ya yanke wayar batareda yasake cewa komaiba dan haushi.. Abdallah ya girgiza kai, yana mamakin hali irin na Abi!, shi daban yake da sauran mutane, yata6e baki tareda jefa wayar saman gadon momcy yafice. Yasmeen tabu─Će Bayi tafito, dak wanda ya kalleta yasan tasha kuka, tafa─Ća saman gado tana share hawe, lokaci yayi dazata nemawa kanta mafita, dukma yanda za'ayi saita cire son Nawaf azuciyarta, bazata bari sonshi yacigaba dayin tasiri azuciyar taba, takuma fashewa da kuka tana dukan 'kirjinta, cikin kuka take fa─Ćin saika fita! saika fita!! saika fita!!! Daga zuciyata bazan yi dakon son wanda baya 'kaunataba, dolene na canja kaina kota halin 'ka'ka Tacigaba da kukanta. Nagirgiza kai kawai nafito. Nawaf kam dafe kai yayi dan ba'kin ciki, yashiga share zufar dake kwararo masa adukkan sassan jikinsa, dukda AC dake aiki acikin ─Ćakin, ya 6alle murfin gorar yashiga kwan kwa─Ća, saida ya shanye duka sannan yamaida kai ya kwanta yana fitar da huci, kamar wanda yafito daga filin danbe. Ya─Ćanja tsaki waishi ya akayima ya fa─Ća tarkon son wannan yarinyar?, dayasan inda son yake datuni yacireshi ya yarda ya huta, yana zaman zamansa amma yanzu ansakashi cikin wani yanayi, ya huro huci mai zafi daga bakinsa, wayarsa yajawo yashiga bincikar ma'ajiya hotuna. Hotunan bikinsu yashagala da kallo, duk inda yasmeen take a hoton ta 'kayatar, takuma bada ma'ana, ya sumbaci wani hoto datayi masa 'kyau sosai, gawani 'kayataccen murmushi data saki a hoton, kamar kakirata ta amsa, ya lumshe idanu ahankali yana murmushi, tareda rungume wayar a 'kirjinsa tsam, jiyake kamar ya rungume yasmeen. Na ce, "lallai su Nawaf modebbo an fa─Ća tarkon SO!!!!!!.­čśť _______________________________ Haka rayuwar take tafiya, kowannensu yana dakon soyayyar ─Ćan uwansa, amma batareda sun sanar da junansuba. Dan har yanzu yasmeen bata amince sunyi waya da Nawaf ba, dukda yana tsananin bu'katar hakan, yabi duk wata hanyar dazasuyi magana da juna amma yasmeen ta tosheta, hanya ─Ćaya tarage masa itace momcy, itakuma yanajin kunyar tunkarar ta, yana gudun kuma kar allura ta tono garma. Yau yasmeen antashi da murnar zuwa gida, tanata farinciki zataga ummarta da abba, mas'ud ne ya kaisu itada Ameena, bayan momcy ta ha─Ća mata shatara ta arzi'ki takaima su umma. Mas'ud yanayin parking ta shilla da gudu cikin gida, Ameena da mas'ud suka tuntsure da dariya. Da gudu tashiga kuwa, ta rungume yaseer dake zaune afalo, suka shiga ihun murna su biyu, umma tafito daga ─Ćaki danjin ihunsu, da sauri yasmeen ta saki yaseer tanufi umma ta rungume ta. Umma ta ce, "nikam karki karyani yasmeen, yasmeen tasaki umma tana turo baki gaba, kai umma bakiyi kewataba ma kenan??, umma tayi dariya, haba ni na isa badole nayi kewar mamana ba, taja hannunta suka zauna. Yasmeen ta ce, "umma ina abba??, abbanku yafita amma zuwa anjima ka─Ćan zai dawo. Bayan mas'ud yashiga sun gaisa da iyayen Ameena saiya shigo nan suka gaisa da umma, zuwa sannanma abba yadawo, daga nan saiya tafi akan anjima zai dawo ya ─Ćaukesu. Anan suka wuni suna mai jin da─Ćin kasancewar su cikin 'yan uwansu, anan yasmeen takeji ashe Nawaf dazai tafi saida yazo yay musu sallama, kuma yana kiransu su gaisa, musamman ma abba da yaseer, dan ita umma tanajin kunyarsa sosai, wato itace yaraina, yamaida sakarai, baya 'kaunarta, itama zata nuna masa baya gabanta bai dametaba, duk a zuciyarta take maganar. Sai dare mas'ud yadawo ya ─Ćaukesu, yasmeen harda kuka, saida abba yay ta lallashinta sanan, amota su ameena sunata mata dariya, itadai shiru tayi musu, mas'ud yakira Nawaf yasanar masa. Nawaf bayaso ya nunama mas'ud yafara son yasmeen danzai takura masa da tsokana, dan haka ya ce, "matsalarta ce, dama tasamu akace taje zata wani yima mutane kuka, kaika zauna take maka kuka a mota. Mas'ud ya ce, "kai malam niba abinda nakiraka kaminba kenan, sai anjima, ─Ćif yakashe wayar. Nawaf ya rintse idanu, jiyake kamar mas'ud ya kwala masa 'karfe akai, yadafe kai tamkar zaiyi kuka, wai miya hanashi cewa ma abama yasmeen wayar, koba komai aida yaji muryarta, yasan zai rage wani ra─Ća─Ćin, shika─Ćai yasan yanda zuciyarsa take azalzalarsa a kan son yasmeen, amma ita bata damu dashiba, dolene ya─Ćauki matakin goge soyayyar yasmeen a zuciyarsa tunkafin zuciyarsa tabuga abanza a word. . Su yasmeen Suka isa gida, saida suka rakata har falon momcy sanan, bayan sun gaisa da momcy suka koma gida ita kuma yasmeen tazauna suka hau hira dasu Anwar. _________________________________ yau tunda suka tashi su Abdallah suke ─Ćokin ganin wasan su Nawaf dazasuyi, dansunce wasan mai zafine, 'kiri2 Anwar ya'ki zuwa islamiyya saboda ya kalli wasan, Abdallah sai tsokanarsa yake, wai yau su ustaz an ajiye ustazanci saboda kallon kwallo. Anwar yay tsaki ALLAH kaga abi kabari, inba hakaba zan ha─Ćaka da papa wlhy, dakaine yanzu saikace zaka 6ata mini rai kuma, ya 'kare maganar yana turo baki gaba. Yasmeen ta ce, "barsa kaji auta, ai akwai ranar ramuwa tana zuwa. Momcy tafito daga ─Ćaki tana fa─Ćin miya faru kuma??, Anwar yagaya mata abinda Abdallah yafa─Ća, ta ce, "to ya isa haka, amma Auta yanzu nan sabofa wasannan ka'ki zuwa islamiyya ko???.. ALLAH A'a momcy, yau 'kari za'a mana kuma na iya wajen shiyyasa, momcy tazauna tana fa─Ćin to shikenan aii. Babu da─Ćewa aka fara wasa, falon yayi tsit, kowa idonsa yana kan tv, yasmeen wani da─Ći takeji a zuciyarta dan ganin Nawaf, koba komai tarage ra─Ća─Ćin dake damun zuciyarta na son wanda bai damu da itaba. Wasa yayi wasa, anata gwagwarmaya da juna dan kowa gwanine, har akaje hutun rabin lokaci babu wanda yaci. Bayan andawo babu da─Ćewa ASINAL ta zirama su Nawaf kwallo, wannan yasa suka dage suma da bada 'kaimi, to suma su Nawaf sun zurama Asinal kwallo ─Ćaya a raga, ana gab da tashi Nawaf ya 'kara zirama Asinal kwallo araga, cikin jin haushin kwallon dasukacisu wani ─Ćan wasan asinal ya ta─Će 'kafar Nawaf yafa─Ći. Bisa tsautsayi wani yataka kafarsa da wannan mugun takalmin na 'yan kwallo. Wata irin 'kara Nawaf yasaki, wadda tai daidai da wadda yasmeen tasaki afalon. Da sauri momcy tari'ke yasmeen, su Anwar ma kuka sukeyi dan duk wanda yagani yasan Nawaf yaji takawarnan ajikinsa. Masu taimakon gaggawa suka rufu akansa, daga bayama ─Ćaukesa akayi daga cikin filin gaba ─Ćaya. Awannan lokacin hankalin duk wani masoyinsa atashe yake, musamman ma mutanen 9ja da saudia, harda sauran 'kasashen duniya, dan duk wanda yake abinda duniya zata sansa dolene yasamu ─Ćunbin masoya aduniya dakuma ma'kiya. Nima kaina saida nayi masa kuka, dan yana cikin jin jiki. Arikice papa yashigo gidan dan shima yakalli wasan a office. Wasu takardu ya─Ćiba yafita yana mai bama iyalin nasa ha'kuri, airport yanufa wajen wani abokinsa, domin nema musu biza shida iyalinsa. To dayake babban mutumne kuma mai alfarma, sai aka samu babu 6ata lokaci, zuwa gobe jirginsu zai ─Ćaga. Yadawo gida ya sanar dasu halin da'ake ciki, dan haka momcy da yasmeen suka fara shiri, sune zasu fara yin gaba, sukuma su Abdallah zasu taho abaya suma. Ranar haka gidan aka wuni sukuku kamar anyi mutuwa. A6angaren Nawaf kuwa karaya yasamu a'kafa, yanacan kwance rijif cikin ciwo, amma zuwa yanzu an gyara karayar, harma yasamu barci. Washe gari suka lula zuwa Spain domin ganin halin da Nawaf yake ciki. Momcy da papa da yasmeen kenan. Abdallah da Anwar da mas'ud zasuzo daga baya sukuma. Bayan sun sauka a masauki sun huta, dukda bawani hutawama sukayi sosaiba saboda hankalinsu yana wajensa. Wani abokinsa ne yazo yay musu jagora zuwa asibitin, yasmeen sai zare ido akeyi ana kalle2 tun ajirgi, sun isa ha─Ća─Ć─Ćen asibitin na alfarma kuma 'kayatacce, wanda 'yan kwallone kawai sukeda dangantaka dashi. Bayan kamar minti shabiyar aka basu izinin shiga wajen Nawaf. Tunda akace sushiga jikin yasmeen yay sanyi, papa ne yafara shiga sannan momcy, Nawaf dake kwance yafara murmushin 'karfin hali dan ganin iyayensa, yasmeen ma tashigo jiki asanyaye, saidai ta la6e abayan momcy. Ya yun'kura zai tashi amma saiya kasa, ya ─Ćan runtse idanu tareda cije le6e danjin zafi, da sauri papa yamaida shi kwance yana fa─Ćin A'a modebbo yi kwanciyarka kaji. Nawaf yakuma murmusawa yana fa─Ćin momcy sannunku dazuwa, momcy tayi murmushi itama ta ce, "yauwa abbuna kaine da sannu yajikin??, ya ce, "Alhmdllh momcy, ina sauran 'kanni na suke??, Momcy ta ce, "suna gida amma zasuzo nan gaba suma insha ALLAHU, tajuya dan bataji motsin yasmeen ba, saita ganta abayanta ta raku6e, momcy takamo hannunta tana fa─Ćin ─Ćiyata 6oyewa kikayi??, da sauri Nawaf ya─Ćago idanu suka ha─Ća ido da yasmeen, tai saurin yin 'kasa da kai. Ta─Ćan rissaina tana gaisheshi da tambayar jikinsa??, ya ce, "da sau'ki, jiyake ciwon nasa ya warke tunda yaga TAURARUWARSA, ya lumshe manyan idanunsa wani sanyi yana kwarar azuciyarsa, shikam saiyace gara da yaji ciwonnan, koba komai tasanadin ciwon yaga yasmeen. Momcy da papa suka zauna saman kujeru biyu dake ─Ćakin, papa ya ce, "fatima zauna kema, yanuna ma yasmeen gefen gadaon da Nawaf yake kwance. Cikin jin kunya ta zauna ka─Ćan kamar tana kusada wuta. Hira suka shiga yi da tambayar yanda akayi abin yafaru, dukda duk sun gani, amma yasmeen bata cewa komai, sai wasa datakeyi da yatsun hannunta. Sun da─Će suna hira daga baya papa da momcy suka mi'ke sukace yasmeen tazauna anan suna zuwa yanzu zasu dawo. Bayan fitarsu ─Ćankin yay tsit babu wanda yake motsi acikinsu, sai Nawaf daya tsirama yasmeen idanu kamar zai cinyeta ─Ćanya, ahankali yasmeen ta yun'kura zata tashi, da sauri Nawaf ya dam'ke hannunta, ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo, kallon ido cikin ido sukema juna, yasmeen tafara janye nata idanu. Ahankali Nawaf yafirta 'yammata babu maganane??, yasmeen ta ce, "bana gaishekaba. Ya ─Ćan murmusa to ina zakije dakike 'ko'karin tashi??, ta─Ćan motsa hannunta daya ri'ke, murya 'kasa2 ta ce, "zan koma kan kujerane. Hummm to idan su papa suka dawofa?, shiru tayi bata amsaba, ya matsa hannunta yana murzawa ahankali, gaba ─Ćaya tsigar jikinta tashi takeyi, tana mamakin wannan wane irin kuma sabon salone Nawaf yazo dashi, cikin rawar murya ta ce, "plz kasakar min hannu karsu mom su dawo su gammu ahaka. To miye idansun gammu, kinsan babu abinda zasuce aii,, eh, amma da kunya dai,, babu wani kunya malama yafa─Ća Yana yun'kurawa zai tashi saikuma yay sauri dafe gado yana fa─Ćin wash ALLAHNA!!. da sauri yasmeen ta ce, "yayadai??", ya yatsine fuska yana fa─Ćin wlhy mantawa nakeyi inada ciwo, ga 'kafar zafi idan na motsata. Yasmeen ta ce, "ayya sannu, cikin muryar tausayi take maganar. Kai ya girgiza mata alamar yauwa, ya ce, "zansha ruwa. Tajuyo tana kallonsa, ta ce, "ruwa kuma??, ya ce, "eh",. ruwan dake gefen gadon ta ─Ćakko ta bu─Će murfin tami'ka masa, ya harareta to dawane hannun kikeso nasha kenan??, ta turo baki gaba ta ce, "toda wayake baka?, kuma aii hannunka lafiya lau yake ko?. Ya ce, "Ahmad ne yake bani mana, shima ─Ćan kwallone abokinsane ─Ćan kasar saudiyyane, haifaffen amerika, ta ce, "to kakirashi mana yacigaba da aikinsa. Nawaf ya ha─Će fuska yana kallonta, ya ce, "mikike nufi?, "k bazaki iya yimini ba??. Tayi shiru, ya ce, "okey bari momcy tadawo ita saitayi mini aii, kinsan babu yanda za'ayi uwa tabar ─Ćanta ayashe. Yasmeen tai kwalkwal da idanu kamar zatayi kuka, ta ce, "ainidai ban fa─Ćaba ko??, ya ta6e baki yana fa─Ćin ai basai kin fa─Ćaba malama, yanayinki ya nuna. Bayanda zatayi dole ta mi'ke taunifi saitin kansa, tami'ka masa ruwan, ya ce, "kinsandai babu yanda za'ayi nasha ruwa akwance ko? Saikin taimaka mini na tashi, koki ─Ćago kaina, yasmeen ta ce, "azuciyarta kaikam kacika matsala wlhy. Dole ta tallafo kansa, tasaka masa ruwan yasha ka─Ćan yajanye baki, ta ce, "dama shan ruwan gulmane. Ya ce, "nine magulmacin kenan??, yafa─Ća yana hararta. Ta ce, "nidai aiibance kaiba. Haba yarinya duk wanda yay zagi akasuwa aii yasan dawanda yake barganina akwance ina dai2 dake wlhy . Kafin tayi magana su momcy suka dawo. Nawaf ya ce, "papa ina kukaje??. Munje wajen manyankune kozasu bamu kai mu koma Najeria tare, to papa misukace maku??, hummm basu aminceba, wai baikamata su ─Ćora mana nauyiba, dansuke da alhakin kulawa dakai, kuma anna zakafi saurin warkewa tunda sunada isasun kayan aiki, ingantattu kuma. To papa kubarsu suyi aikinsu dama nasan dawuya su amince gsky. Papa ya ce, "babu damuwa ai muna nan tareda kai insha ALLAHU, dama maman kace tadage akan mutafi dakai. Nawaf yamaida kallonsa ga momcy, ya ce, "sorry my momcy karki damu insha ALLAHU anan ma suna bani kulawa sosai, kuma zan koma daidai insha ALLAH. to shikenan modebbo ALLAH ya amince mana. Amin suka amsa harda yasmeen. Papa ya ce, "to bari mu koma masuki dan suna nuna mana lokacin ziyarku ya 'kare saikuma gobe, ALLAH ya'kara lafiya. Amin suka amsa gaba ─Ćaya, kafin su momcy su mi'ke tuni yasmeen tafice abinta. Nawaf ya bita da kallo yana cije le6e, azuciyarsa ya ce, "yarinya dole ki soni!!!. Tunda suka tafi saiyaji ─Ćakin babu da─Ći, baigaji da kallon 'kya'ky'kyawar fuskar yasmeen ba, amma babu yanda zaiyi. Likita yashigo ya dubashi, saima yaymasa allurar barci danya samu hutawa. Suma su yasmeen masauki suka koma, yasmeen ─Ćakinta ita ka─Ćai, papa da momcy kuma ─Ćaya suma. Tagama komai na al'adar rayuwarta ta kwanta, amma sai tunanin Nawaf yadawo mata, ta tuna yanda yau yake mata magana cikin taushin murya, babu fa─Ća bare nuna jin haushi, ta kalli hannunta daya ri'ke, hannun ta sumbata tana murmushi, talumshe idanu tareda furta i luv u my Nawaf...., tai saurin rufe bakinta­čÖŐtana girgiza kai. Na ce, "yasmeen ina saura kuma, sirrin 6oye yafito fili. Haka tayita juye juye dan takasa barci, daga 'karshema saita mi'ke tashiga bayi tayo alwala, tazo tayita nafil fili, tana ro'kon ALLAH yabama mijinta lafiya da dukkan muslmi al'umar ANNABI......................✍­čĆ╗ Asalamu alaikum 'Yan uwa kuyita ha'kuri danifa,karku ─Ćauka ina muku jan raine, A'a kunsan ance lafiya uwar jiki babu mai fushi dake, ina bu'kar addu'arku... Luv u oll­čśś­čśś­čśŹ­čśŹ © 2016 ­čĺ×Bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśś­čĺ× [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺ× Page­čĹë­čĆ╗39 & 40 ....da 'kyar ta tashi tai sallah da asuba, ta kuma komawa barci, sai 'karfe goma ta tashi na safe, shima saida momcy ta tada ita, ta tashi tayi wanka tayi shirinta cikin doguwa riga ba'ka, ta na─Će kanta da farin gyale, tayi 'kyau sosai, ko abincin da'aka kawo mata bata tsaya ciba tafito dan su momcy suna jiranta. Ta tsugunna har 'kasa ta gaishesu, cikin fara'a suka amsa, har papa na tsokanarta da fa─Ćin, gara muje da wuri kafin mijinki yafa kiran wayoyinmu, yasmeen tayi ─Ćan murmushi cikin jin kunya. Momcy takama hannunta ta mi'kar da ita. Ahmad ne yazo ya ─Ćaukesu, momcy da papa suna baya yasmeen kuma agaba kusada Ahmad. Asibitin cike yake da 'yan kwallo, Ahmad ya ce, "sunzo duba marasa lafiyane, su papa suka nemi guri suka zauna, Ahmad ya ce, "yasmeen mushiga ke saiki gaisa da abokanmu, suma suga matar modebbo ko??, momcy ta ce, "eh yakamata hakan, tashi kuje yasmeen. Yasmeen tami'ke tana fa─Ćin to momy, Ahmad da yasmeen suka nufi ─Ćakin da Nawaf yake kwance, cike yake da abokansu, wasu azaune wasu atsaye, yasmeen tayi tsaye takasa shiga saboda kunya, Ahmad ya ce, "shigo mana. Yasmeen tashigo kanta a'kasa, sukam sai kallonta sukeyi, yau dai Nawaf azaune yake, yajingina da filo a bayansa, kuma kumburin 'kafar da sau'ki, ya mi'kama yasmeen hannu alamar wai tazo, ta no'ke kafa─Ća, alamar A'a. Yay murmushi yana fa─Ćin to zoki zauna nan, dan kinga nan duk abokainane, karsu ─Ćauka 'kanwatace ba matataba. Yasmeen ta'karasa ta zauna kusada 'kafafunsa, yakamo hannunta ya rumtse anasa, sannan ya maida kansa ga abokan nasa dasuketa kallon yasmeen, ya ce, "friend ga matana, sunanta fateema xarah. Cikin harshen turanci yake maganar, sukace wow!! Beautiful Sannu dazuwa. Itama cikin harshen turancin ta gaidasu, suka shiga mi'ka mata hannu wai su gaisa, Nawaf ya girgiza kai tareda sake ru'ko ─Ĺanyan hannun nata, ya ce, "koda wasa karma ki fara, amma da hausa yafa─Ća. Wani bature acikinsu ya ce, modebbo miyasa zaka hanata, aii gaisuwa zamuyi ko??, ya girgiza kai yana fa─Ćin no ita bata gaisuwa da maza, saidai zaku iya gaisawa da baki. Sai ko─Ćata sukeyi, wani harda fa─Ćin wai zaizo 9ja abashi mata. Na ce, "aiko yazo yaza6a a group ─Ćina duk wadda tayi masa nabasa, kai ni harma na za6ar masa, ku kawo kunnanku nagaya muku,, nabashi kai­čÖŐ............baridai nayi shiru, kar wasu suce ban za6esuba­čśť. Bayan sun gama gaisawa suka fice, har yanzu Nawaf yana ri'ke da hannun yasmeen yana murzawa ahankali, ta ce, "plz ka sakeni su momcy suna zuwafa, yaja numfashi, to sarkin tsoro, kedai ba'a ta6a jikinki ko?, kodayake ba'kya bu'katar hakanne?, tazare hannunta ─Ćaya daga nasa tana ta6e baki. Ahankali ya ce, "kina nandai baki canjaba ko?, ta ce, "kaima ai baka canjaba,. Ya ce, "ko??, ta─Ćan murgu─Ća baki, tana fa─Ćin kaima kasani aii. Ya ce, "nasan mi?? Ta gyara zamanta tana fa─Ćin kasan baka canjaba ─Ćinba. Fatar hannunta yakama yamir─Će. Tari'ke hannunsa kam, wayyo ALLAH da zafi fa??. Yay 'yar dariya aii dama dankiji zafin nayi, yafa─Ća ahankali. Ta ce, " mutum yana hannun ALLAH amma bai daina muguntaba, wawura yakaimata tai saurin kaucewa ta ce, "aikuma kayi na 'karshe malam. Momcy da papa suka shigo, yasmeen ta fisge hannunta tana gyara zama, su momcy suka zauna suna mai yaba yanda jikin Nawaf yay 'kyau. Papa ya ce, "masha ALLAHU lallai jiki yayi 'kyau modebbo, yau harda zama. Nawaf ya ce, wlhy kuwa papa harma ji nake zan iya taka 'kafar, papa yay dariya, A'a modebbo wannan da sauran lokaci aii. Alhmdllh momcy tafa─Ća, aii haka muke fata muma muga ka taka, dama su Anwar sun damemu dakira, wai ykk??, Ayya 'yan 'kannina nayi missing nasu nima, su kwantar da hankalinsu, ina samun sau'ki, bari Ahmad yazo ya kwaso mini wayoyina, nasan mutane sunata nemana. Papa ya ce, "yakamata ka kunna kuwa, kodan gaisawa da 'yan uwa da abokan arxi'ki, dukda muma sunata kiranmu, kaga kuma bakoda yaushe muke tare da kaiba, indan kuwa ka kunna kowa zai dunga samunka, aduk lokacin daya kira. Nawaf ya ce, "to papa bari muga yazo saiya ─Ćakkomin. Nan dai sukaita 'yar hirarsu, suna yaba 'ko'karin Ahmad. Nawaf ya shagwa6e fuska wai yunwa yakeji, momcy tayi dariya itada papa, kai modebbo shagwa6a kuma??, kafa girma abbunmu. Nawaf yay ─Ćan murmushi yana fa─Ćin papa aini idan ina gabanku jina nake yaro 'karami wlhy. Nanma dariya sukayi, momcy ta ce, "to matarka tabaka abincin ko?, yasmeen tai saurin kallon Nawaf saiya ─Ćaga mata gira, ita kuma ta murgu─Ća masa baki, ya nuna kansa alamar wai shi. Su momcy suna kallonsu, yasmeen ta ha─Ća abinci ta matso kusada shi tana wani zuzzun6ura baki. Ta ─Ćiba a cokali ta mi'ka masa, saida ya harareta sannan ya kar6a, ya─Ćan kalli gefen dasu momcy suke yaga hankalinsu baya kansu, suma hirarsu sukeyi, yay 'kasa da murya yanda bazasujiba ya ce, "ki ajiye rashin kunuarki yarinya, dan wannan karan inada hanyoyin maganinki dayawa. Yasmeen ta ta6e baki ta ce, "aii nasaba jin wanan, hannunta yakamo ya sumbata, saida ta─Ćan girgiza dan sumbar tashigeta, Nawaf yay saurin ri'ke filet ─Ćin dake hannunta ya ce, " 'yammata harda wannan??. Yasmeen tai 'kasa da idanu dan yauce rana tafarko dataji tana jin kunyar Nawaf,, cikin shagwa6a ya ce, " momcy kinga ta daina bani abincin ko??. Yasmeen tazaro ido­čś│itama cikin tata shagwa6ar ta ce, "mom ALLAH ina bashi shine baya ci, dama babu wata yunwa dayakeji, su momcy dariyama suka basu, dan haka suduka sukayi murmushi, papa ya ce, "to yanzu mu yazamu gane mai gsky??. Nawaf ya harareta ALLAH papa nine mai gsky, yasmeen ta ce, "bawani nice mai gsky, Nawaf ya ce, "to nidai yunwa nakeji dan haka kibani abinci, filet ─Ćin hannunsa ta kar6a tana hararar sa, yasaki murmushin mugunta. Haka Nawaf yacigaba da jinyar jikinsa, Alhmdllh kuma jikin yana 'kyau, saidai tundaga ranar yasmeen take baya2 dashi, dan takula yana neman yarin'ka bata kunya agaban su papa. Amma soyayyarsa kullum 'kara ruruwa take azuciyarta, to shima dai hakane jiyake kamar ya ha─Ćiye matar tasa, amma jin kai yahashi fa─Ća mata yana sonta, dan haka kullum take ganin kamar tana dakon son wanda baya sontane. Shima Nawaf yanama soyayyar dayakema yasmeen kallon son maso wani, danshi atunaninsa har yanzu yasmeen tana son tsohon mijintane, baisan bata ta6a son faisalba ko a bayaba, bare yanzu. A yaune su mas'ud suka iso shida Anwar da Abdallah, Nawaf yayi matu'kar farin cikin zuwansu, haka suma sunyi farincikin ganin yafara samun lafiya, dan zamu iya cewa saura ka─Ćan, yausu anan suka wuni yasmeen ma no'kewa tayi ta'ki zuwa wai kanta yana ciwo. Suma a hotel ─Ćin dasu yasmeen suke anan aka musu masuki, da daddare suka ha─Ću akasha hirar 9ja, saidai papa ya ce, "kowa yaje yakwanta sanan. Nawaf yakira Anwar ya ce, "yakaima yasmeen wayar, tana 'ko'karin kwanciya taji an buga 'kofar, saida ta le'ka taga Anwarne sanan ta bu─Će, Anwar lafiya dai ko??, ya mi'ka mata wayar yana fa─Ćin yayane ya ce, "nakawo miki wayar, yana bata yajuya yana fa─Ćin mu kwana lafiya. Ta maida 'kofar asanyaye tarufe ta ce, "to ALLAH yakaimu, saman gado tafa─Ća ta kwanta, tayi addu'ar barci dan Nawaf bai kiraba ita kuma wlhy bazata kirashiba. Ta kammala addau'ar ta lumshe idanu amma badan barciba, dan tana bu'katar jin muryar Nawaf, kamar daga sama wayar tafara 'kara alamar kira, tayi Burus da wayar harta tsinke, yasake kira, saida yakira sau uku, nanma ta'ki ─Ćauka, sai ana hu─Ću ta ─Ćauka zuwa sanan Nawaf yacika fam da haushi. Ta ─Ćauka kuma tayi shiru, shima shiru yayi sai huci yake kamar yana gabanta, cikin masifa ya ce, "waike wace irin "'yar rainin wayoce, dan wula 'kanci tun─Ćazu nake kiran wayarnan kika 'ki ─Ćauka kuma nasan kina kallonta. Yasmeen ta ta ta6e baki, tayi shiru kuma, wannan yasa Nawaf 'kara hawa sama, yacigaba da masifa, "k wlhy kishiga hankalinki dani, karkiga ina kwance a gadon asibiti kice zaki raina mini wayo, kinsanni kinsan halina, kodan kinga ina kulaki shine zaki min hauka, daga yanzu idan kinga na sake shiga harkarki kiyimini abinda kika ga dama, tsowww yaja tsaki tareda yanke wayar. Yasmeen ta dafe kai tana hawaye, wai ita miyasama ta 6atama Nawaf rai, miyasa bata ─Ćagaba tun akiran farko, gashinan wajen jan aji ta 6ata komai, itada take fata tajawo hankalinsa gareta, gashi nan ta na 'ko'karin nisantasu da juna, sai kawai tahau kuka. Na ce, "tofa kaga wani ─Ćigimi, wai dukan sauro da 'kota. Shikam Nawaf wurgi yayi da wayar ta fashe, yamaida kansa ya kwanta yana hargitsa sumarsa, zuciyarsa cike da ba'kin ciki, yarasa wane irrin 'kiyayya yasmeen take masa haka, wace irin tsana take masa wai, ya rintse idununsa yana fitar da huci, dolene ya─Ćauki mataki akan yarinyarnan, yakamata yafita harkarta gaba ─Ćaya, dan yakula 'yar kulawar dayake bata ta kwana biyunnan ce takeson jawo masa raini a wajenta. Zai tureta daga zuciyarsa yacigaba da harkokinsa, inyaso yamutu da sonta azuciyarsa mana, ahaka doctor yazo yasameshi. Bayan ya─Ćan dubashi ya ce, "yana bu'katar ya kwanta yahuta, dan haka allurar barci zai masa. Nawaf ya ce, "A'a baya so. Doctor ya ce, "aii tazama dole, babu 6ata lokaci ya zurku─Ća masa, barci kuwa yay awon gaba dashi. To itamadai yasmeen barcin ne ya saceta bayan tagama koke kokenta. _________________________________ a yau aka fara koyama Nawaf tafiya, yana ri'ke da sanda guda biyu likitoci guda biyu suna gabansa saikuma wasu ma'aikatan abayansa, a harabar asibitin suke, dan haka su yasmeen suna gefe suna kallo. Nawaf sai matse idanu yakeyi yana dogara sanduna, ga zufa daketa tsatstsafo masa, sun─Ćanyi nisa da tafiya, aka kar6e sanda ─Ćaya, to dagananfa Nawaf ya 'kara shan wahala, zufa kuwa aii kamar ana kwara masa ruwa. Yasmeen tai 'kasa da akai tana hawaye, suma su Anwar haka, aka 'kara kar6e ─Ćayar sandar, yafara tafiya da 'kafafunsa, daganan jikinsa yafara rawa, dauriyarsa ta 'kare, hawaye suka fara ambaliya a fiskar Nawaf, gsky koni yabani tausayi, gashi mugaye likitocinnan sun'ki cewa ya zauna. Tun yana daurewa yana ─Ćaga 'kafar har yakoma janta, daga bayama saiya fa─Ći, daga nan suka ─Ćaukesa aka maidashi ─Ćakin dayake, zuwa sanan yafita hayyacinsa. Momcy ta rungume yasmeen tana rarrashi, dukda itama hawayen takeyi. Harzuwa dare an hana kowa ganinsa, sai ha'kura sukayi suka koma masauki. Washe garima dasukaje basu ganshiba, sai lokacin da aka fito dashi domin motsa jiki, yaukam yamafi jiya shan wahala, saboda 'kafar tayi tsami jiya, haka suka kwasheshi suka maida. To ayau rana ta uku sai ya kasance da sau'ki, dan yau baisha wahalarba, dakansama ya koma ─Ćaki. haka rayuwar tacigaba da tafiya, Nawaf yana samun sau'ki, kuma kullum ana fita dashi dan motsa jiki safe da yamma, saidai yafita harkar yasmeen gaba ─Ćaya, ko zuwa sukayi dubashi daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu, saima 'yar harara da murgu─Ća baki, amma kowa yana ma'kale da son ─Ćan uwansa, babu wanda yafahimci halin dasuke ciki sai mas'ud, dan basayi gaban su papa, da su Abdallah, amma gaban mas'ud yin abunsu sukeyi. To yaudai an sallami Nawaf, gidan dayake zaune suka nufa, ya ha─Ća duk abinda zai bu'kata suka koma hotel ─Ćin inda su momcy suke. Papa ya ce, "akai masa kayansa inda matarsa take, gaban yasmeen yashiga fa─Ćuwa, miyasa baza'a kama masa ─Ćakiba, kosu zauna da mas'ud, itako batason su kasance ─Ĺaki ─Ĺaya da Nawaf, bare yanzu daya tsaneta, ta lura ko ganinta baya sonyi, amma babu yanda zatayi tunda umarnin papa ne. Nawaf ya mi'ke yana dogara sanda yanufi ─Ćakin yasmeen yana fa─Ćin bari naje nayi wanka saida safenku, kowa ya ce, "ALLAH yakaimu, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije saida safe. Badan tasoba ta mi'ke dan cika umarnin momcy. Ta tura 'kofar tashiga jiki a sanyaye kamar wadda kwai yafashemawa aciki, Nawaf yana zaune bakin gado yana cire kaya, kallo ─Ćaya yasmeen tayi masa ta kawauda kai. Shiko aii ko kallon inda take bayyiba, tayi tsaye a tsakkiyar ─Ćakin tana wasa da yatsun hannunta. Ya mi'ke yanufo inda take dagashi sai ─Ćaurin guntun tawul, ahankali takeja baya azatonta wajenta yataho, daya matso saita matsa, yamatso ta matsa, haka sukaitayi har zuwa jikin 'kofa, ta rintse idanu dan sunje 'karshe, ta manne da 'kofa sosai ga idanunta a runtse, ya'karasa takowa ahankali gurinta yakai jikinsa kusada ita kamar zai ringumeta fuskarnan murtuk ya tsare gida...........................✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Nagode da sakwannin gaisawa da addu'ar samun lafiya dakuketa ─Ćawai niyar turomini, harma dama su kirana, , Nagode kwarai da 'kaunarku gareni, nima ina 'kaunarku a duk inda kuke, ALLAH ya barmu tare, ya bar mana zuminci­čśŹ­čśŹ­čśś­čśś­čĺô­čĺô­čĺÜ­čĺť­čĺľluv u oll!!!!!!!!!!!!!!­čĹî­čĆ╗­čĹî­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśŹ­čĺ× [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗41 & 42 .....Yasmeen ta ─Ćauke numfashi, sai 'kirjinta ke dukan tara2, ga jikinta yana rawa, tamaba Nawaf dariya kwarai da gsk, amma saiya gimtse. Ka─Ćan yara6u da jikinta, yakai hannu bisa key ─Ćin dake 'kofar ya kulle. Tanaji yana sakama 'kofa key sai rawar jikinta ta 'karu, tazame 'kasa ta zauna da6as, ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta, tana ambatar sunan ALLAH. Ya bita da kallo bayan yagama kulle 'kofar, kai ya girgiza yan ta6e baki, kamar wanda yaga wani abin daba'a so. Bayi yashige domin yin wanka abinsa. Bayan wasu 'yan mintina taji motsin ruwa, amma tsoro yahanata tashi daga wajen, tama kasa ─Ćago kanta, itafa har yanzu ta zata Nawaf yana awajen tsaye­čśť. Shima yana wanka yana murmushi, ashema yarinyar nan matsoraciya ce?, to ita da mitake tunanin zan mata ne?, yay wata 'yar dariya, ashedai ana tsoron iya iya inji 'yar mayya, yarinya kamar farar kura, ga tsoro ga jan fa─Ća, dahaka yagama wankan yana zancen zuci, yafito Abin yabashi mamaki daya ganta a inda yabarta, kuma kanta a6oye har yanzu, ya murmusa yana dogara 'yar sandarsa, abakin gado yazauna yana cije le6e dan har yanzu 'kafar tana ─Ćan masa zafi, tunda bata gama sakiba gaba ─Ćaya, ya shafa mai tareda shirin barci, harkokinsa yaketayi batareda ya'karabi takan yasmeen ba, yagama shirinsa tsaf, ya ha─Ća shayi yasha da magungunan sa. Saida ya kwanta sannan ya ce, "k anan zaki kwana ne??, tayi shiru babu amsa, yay tsaki waike ba'kya jina ne?, yay maganar cikin tsawa. Da sauri yasmeen ta ─Ćago tana kallonsa baiwar ALLAH ashe barci takeyi ahaka, ya ce, "bazaki tashi a 'kofar nanba nane??. Yanda yay maganar yana zaro idanu gashi ya ha─Će girar sama data 'kasa, saitaji bazata iya maida masaba, dan Nawaf yanada kwarjini, idan ya ha─Će fiska ko kai waye dole kaji tsoronsa, ta mi'ke jiki na rawa ta shige bathroom. Nawaf ya girgiza kai yana lumshe fararen idanunsa, gaba ─Ĺaya kansa a kulle yake, yakamata yanemi shawarar mas'ud, amma kuma bayaso kowa yasan sirrinsa, to kenan zai cigaba da zama da damuwa azuciyarsa, gashi wadda yakeyi dan ita batasan yana yibama, yafitar da huci maizafi daga bakinsa,, lallai lokaci yayi dazai gwada karfinsa yacije le6ensa na 'kasa, yakai hannu bisa 'kafarsa mai ciwo yana girgiza kai, afili ya furta akwai sauran lokaci!!!­čĹî­čĆ╗. Tada─Će a bayin zaune dan babu abinda takeyi, saima duniyar tunani data lula, ta manta da inda take zaune. Nawaf sarkin saurin jin haushi har ya sha'ka, ya mi'ke yana masafa, yaja sandarsa zuwa 'kofar bayin, da 'karfi ya buga 'kofar bathroom ─Ćin, "k wai wane irin iskancine wannan?, mikikeyi a cikin bathroom ─Ćin??. Yasmeen ta ce, "wankafa nakeyi. Yaja tsaki yana fa─Ćin A'a iyo kikeyi 'karewar wanka, wlhy idan baki baki fitoba saina 6alle 'kofarnan, kuma jikinki saiya gaya miki. Ta murgu─Ća baki kamar tana gabansa, a zuciyarta ta ce, "wlhy idanma wani abu kake 'kullawa to kama kwance sa, dan ALLAH bazai ta6a baka sa'a a kainaba, mugu kawai, amma afili sai ta ce, "aii dai ganinan fitowa ko. Kwafa Nawaf yayi yakoma kan gadon yakwanta yana jan 'kafa, yana mamakin miskilanci irin na yasmeen. Na ce, " kunji wani 'karfin hali, tomiye na damuwa da fitowarta, kuma shi ya manta da nasa miskilancinne??,­čśĆ Yakai kusan minti goma da kwanciya sannan yasmeen ta bu─Će 'kofar ta fito, babu wani alamar wanka datayi, zuwa sanan Nawaf ya da─Će dayin barci, saboda magungunan daya sha. Ta bishi da harara tana 'kun'kunai, saman kujera ta zauna, ta tsurama 'kya'ky'kyawar fuskarsa idanu, barci yake amma tamkar yana murmushi, ko afili bazakaga fuskarsa hakaba, lalle tayarda mijinta handsome ne, kuma Gentle man ne, domin komai nasa mai ajine, tafiyarsa, maganarsa, bare idan yana 'kayataccen murmushinsa mai kashe zuciyar 'yammata. Yanada kwarjini na musamman wanda dole ma'abota tarayya dashi su girmamashi, gashi da tausayi da son jama'a, tunda take tareda shi bata ta6a ganin ya wula'kanta waniba dukda ─Ćaukaka da ALLAH ya bashi, jarumi wanda duniya tasani, kuma take alfahari dashi, tunda yasamu ciwonnan gidan radio da tv mujallu da jaridu suketa yayatama duniya, yanzu ta'kara tabbatarwa Nawaf sananne ne a duniya, yakan girmama masoyansa, gashida 'kyauta, yakan taimakawa na 'kasa dashi bashida rowa ko ka─Ćan, tasaki wani lallausan murmushi yayinda taga fuskar Nawaf ma tana bayyana murmushin. Yajuya kwanciyarsa zuwa ─Ćayan 6angaren. Tazame ta kwanta saman kujerar dan ganin ya 6oyema ganinta, babu da─Ćewa barci yay awon gaba da'ita. Na ce, "mukwana lafiya. Da asuba yarigata tashi kona ce, "tare suka tashi, badai ta nuna ta farka bane, tana kallonsa yami'ke yana dogara sandarsa zuwa bayi, alwala yayo yafito, ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya fara, ya ─Ćauki abun sallah ya shinfi─Ća, saida taga ya kabbara sallah sannan ta tashi ahankali itama tayo alwalar, abayansa ta kabbara tata sallar. Bayan sun idar kowa ya zauna yana addu'a, Nawaf yajuyo da zummar tada yasmeen tayi sallah, sai kuma yaganta abayansa, ya ─Ćauke kai tamkar bai gantaba, itama tayi burus dashi kamar batasan da zaman wani ─Ćan adam a wajenba. Ya tashi ahankali yana dogara sandarsa, yafice batareda yabi takanta ba, murmushi yasmeen tayi tatashi ta haye gado ta kwanta abinta. Shikam wajan motsa jiki yanufa dake a hotel ─Ćin. Yasmeen tasha barcinta sosai, dan Nawaf bai dawoba, yanacan wajen motsa jiki, har saida ma'aikaciya tashigo, yasmeen ta fito waje dan bata damar gyara ─Ćakin, saida tagama sannan tadawo tashiga wanka. Tafito ta shirya tsaf cikin siket da riga na golden brown ─Ćin material, ta na─Ća ─Ćaurin ─Ćankwali mai tsari, dukda bawata kwalliya tayiba tayi 'kyau sosai, tana fesa turare Nawaf yashigo sai hura hanci yakeyi daka gansa kasan yagaji matu'ka. Momcy tashigo itama, da sauri yasmeen ta tsugunna tana gaisheta, momcy ta amsa cikin fara'a, ta ─Ćora da fa─Ćin ─Ćiyata, ga mijinki nan nakula yagaji matu'ka, daga wajen motsa jiki yake, kisamu ruwa mai zafi ki gasa masa jikinsa danya samu ─Ćan'karfi kinji. Yasmeen ta─Ćaga kai atsorace kuma cikin kunya, momcy tadafa kan Nawaf tana masa sannu, ya amsa yana ─Ćan murmushi, karki damu momcyna komai zai dawo normal insha ALLAH, wannan motsa jikin shine zai taimaka mini sosai. Momcy ta ce, "to shikenan abu na ALLAH ya'kara lafiya kaji, amin my dear mom, momcy ta ce, "bari naje, ─Ćiyata agasa 'kafarnan sosai, dan ya ce, "jiya da daddare ba'ayiba. Yasmeen ta ce, "to mom. Momcy tafice taja musu ─Ćakin. Yasmeen tana tsaye inda momcy tabarta ko motsawa batayiba, shikuma Nawaf yana zaune a kujera yana mata kallo kasa2, tayi masa 'kyau sosai yau, kayan sun dace da jikinta, jiyyake tamkar yaje ya rungumeta. Ya─Ćan gyara zamansa yana fa─Ćin wash ALLAHNA!!. da sauri yasmeen ta─Ćago tana kallonsa, ya ha─Će fuska kamar bashiba, ya ce, "kije ki ha─Ća ruwan mana. Ta ─Ćan hararesa kafin tawuce bayi, ta ha─Ća ruwa mai zafi sosai, wanda nakula harda mugunta, dan da alama zaiyi zafi sosai. Tafito tana goge hannu da 'karamin tawul, kallo ─Ćaya tamasa ta ce, "na ha─Ća, ya kalleta yana ta6e baki to dakika ha─Ća sai akayi yaya?, itama bakin ta ta6e sanan ta ce, "idan kana bu'kata saikaje kayi wankan. Yami'ke yana kwafa, gabanta yaje ya tsaya kerere, ta ce, "lafiya?, ya ce, "ita takawo haka, hannunta yaja kawai suka nufi hanyar bayi, ta ce, "wai miye haka ne??. Bai tanka mataba har saida sukaje cikin bathroom ─Ćin sannan ya ce, "bakiji mi momcy tace mikiba kenan??, catayi ki gasa mini jiki. Yasmeen ta zaro idanu waje, tokai saika amince nagasa maka jiki ─Ćin??, yay wani bazawarin murmushi yana fa─Ćin toke ba matata bace, miye aciki??. Yasmeen tajuya zata fice tana fa─Ćin nikam bada niba wlhy. Da sauri ya dam'ke hannunta, "k momcy kika raina kenan??. Yasmeen ta ce, "kata6a ganin mutum ya raina mahaifiyarsa, kodawasa bazan raina mahaifiyataba aii. Nawaf yaji da─Ćin furicinta, yaka─Ća manyan idanunsa cikin muryarsa mai da─Ći, ya ce, "to saiki cika umarninta aii ko, yasmeen ta girgiza kai, kaima kasan bazai yuwuba 'kato dakai ka tu..............saikuma tayi shiru. ya matsa hannunta daya ri'ke da 'karfi, nine 'katon???, jin zai murmushe mata kashin hannu abanza ta girgiza kai, nifa badakai nakeba, ya ce, "dawa kike to???. Tuni tafara hawaye, kasakar mini hannu to zan fa─Ća. Bayason ganin kukanta dan haka yasaketa, amma yakoma 'kofar bayin ya tsaya, babu damar guduwa kenan. Ta ce, "plz kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba, inajin kunya. Hummm dama kinada kunya 'yammata??, yasmeen ta harareshi A'a banida ita, ya murmusa ke dai bakinki baya mutuwa ko??, ta murgu─Ća baki­čśĆ, ya ce, "yayi 'kyau 'yammata, yafa─Ća yana nufota, ita kuma taja baya har suka kai 'karshen bango. Yay wata dariya yarinya ai anzo wajen kuma, ta manne da jikin bango tana mazurai. Ahankali ya'karasa gareta, har suna jin numfashin juna, ta runtse idanu kam kamar wadda taga ba'kin aljani, yadafe bango da hannayensa biyu, itakuma tana tsakkiya har jikinta yana gogar nasa, yakai fukarsa jikin wuyanta yana shinshina. Ta kauda kai gefe tana fa─Ćin wai miye haka??, yacigaba da shinshinar wuyanta batareda ya tankataba, tasa hannu tana ture fuskarsa. Cikin sar'kewar murya ya ce, zanyi maganinki ne 'yammata, dan na kula kin rainani dayawan gsk, ya ─Ćago yana kollonta, sai kauda fuska takeyi harda 'yan kwallanta, itadai aduniya ta tsani namiji yazo kusada ita, tun abinda yaso faruwa da ita a kwangwalan da wanda Faisal yaso aikata mata yasa takasa mancewa har yanzu, wasu hawaye masu zafi suka zubo akumatunta. Nawaf yasa yatsu biyo yadawo da fuskarta tana kallon tasa, sukaima juna kallon ido cikin ido, tai saurin lumshe nata idanun dan ganin yanda nasa suka canja launi zuwa jaa, ya tsura mata idanunsa masu kalar jaa ayanzu, ahankali yakai bakinsa kan nata, shima ya lumshe nasa idanu. Yasmeen tashiga turesa tana kuka, ganin zata iya sakawa yafa─Ći saboda 'kafarsa babu kwari, saiyasaka hannuwansa biyu yakamo kumatunta ya ri'ke sosai atafin hannunsa. Sumbatarta yake kamar zaicire mata la66a, duk duka da mintsini datake masa baisa yasaketa ba, saida yayi mai isarsa ya saketa dan kansa yana fitar da numfashi, dagudu tafito ALLAH yasota bai rufe 'kofar bayinba. Shikuma yay saurin zaunawa danjin zai fa─Ći, yadafe kai yana jijjuyawa, yada─Će ahaka, daga bisani yasakarma kansa ruwa, yakai tsawon minti20 ahaka, saida yaji ya dai daita sannan yaha─Ća ruwa mai zafi yashiga ciki, dan wanda yasmeen ta ha─Ća ya huce. Yay lamo aciki idanunsa alumshe ruwan yana shiga dukkan sassan jikinsa musamman ma 'kafarsa mai ciwo, yada─Će ahaka sannan yay wankan sabulu yafito yana goge sumar kansa da 'karamin tawul. Abakin gado ya tarar da yasmeen zaune ta rabga uban tagumi fuska sha6e2 da hawaye, da'alama tana duniyar tunani. Ya zauna yana fa─Ćin "k!, shiru tayi masa, yadaka mata tsawa "k!!! Ba'kya jina?. Afirgice ta kalleshi, ya ha─Će fuska kamar bashiba, cikin fa─Ća ya ce, "nabaki minti3 kije yanzunnan ki wanke fukarki, tun kafin nayi miki abinda yafi na ─Ćazu, 'yar rainin hankali idan momcy tashigofa basai ta zata wani abu nayi mikiba. Itadai yasmeen ta mi'ke taje ta wanko fuska, dan bataso ya ce, "zai rin'ka mata irin haka, zata tsaneshine, duk wanda zai nuna yana son jikinta tofa yana zama ma'kiyintane. Tafito tana wani rarra6ewa ajikin bango, ya ce, "maza ki shafa fauda a fuskarki kamar ─Ćazu, jiki yana 6ari tayi abinda yace, ta gyara ─Ćaurin ─Ćan kwalinta. Fuska a─Ćaure ya ce, "kizo ki shafa mini mai, ta bishi da kallo tana mazurai, ta daure ta ce, "bafa hannunka bane mai ciwon?, cikin rawar murya tafa─Ća. Idanunsa alumshe ya ce, "nasani, koban isa nasakaki aiki bane??. Ta ce, "ni ba haka nake nufiba, amma....... Yay saurin katseta da fa─Ćin amma mi???, tai shiru tana shirin yin kuka, yay sauri fa─Ćin karki yarda wa─Ćan nan hawayen su zubo, idan kuma ba hakaba zan aikata miki abinda ba'kya so,, kuma kiyi maza kizo ki shafa mini mai idan ba hakaba hummmmyim ya 'kare maganar dayin kwafa. Da sauri tazo ta zauna gefensa, ta ─Ćibi mai ahannunta tana murzawa, amma takasa shafa masa, sai mulmulashi take ahannu, yagaji da mi'ka mata hannu ya bu─Će idanunsa dasuke lumshe akanta. Tai 'kasa da idanunta, ya ce, "kin za6i komai yafaru kenan........? kafin yarufe baki ta kama hannun tafara shafa masa mai, ya lumshe idanu yana murmushi jiyake kamar tana masa susa, tagama ya mi'ka mata ─Ćayan hannun, dahaka dai aka gama shafa man, ya ce, "saura kaya. Ta marairaice fuska tana fa─Ćin dan ALLAH kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba ka tausaya mini. Yami'ke yana murmushi bataredaya tanka mataba, cikin 'kananun kaya yashirya, yagama ya ─Ćauki waya yay musu odar abinda zasuci, itadai tana zaune tana kallonsa. Babu da─Ćewa aka kwankwasa 'kofar yabada izinin shigowa, mai kawo abincine, ya ajiye yafita. Ya ─Ćauki nasa ya tura mata nata gabanta yana fa─Ćin minti20 nabaki kiyi maza kici abincin nan, daga nan ya hau cin nasa batareda ya sake bi takantaba. Itama saitaja abincin taci, dan dama yunwa takeji, kusan tare suka gama, ya ─Ćauki magungunan sa yasha, yana gamawa yatashi yadawo kujerar datake zaune, kusada ita yazauna, itakuma ta─Ćan matse jikinta kamar tana jinsanyi. Ya─Ćan murmusa tareda zamewa ya kwanta ya─Ćora kansa bisa cinyarta yana fa─Ćin matsoraciya kawai, ya lumshe idanunsa tamkar zaiyi marci. Aka kwankwasa 'kofar yasmeen tayi shiru kamar batajiba, Nawaf ya ce, "kowaye yashigo. Abdallah da mas'ud da Anwar ne, suka shigo da sallama, yasmeen tashiga ture kan Nawaf, amma ko motsi baiyiba, suka zauna mas'ud ya ce, "a lallai mara lafiya ansamu harda so............, da sauri Nawaf ya bu─Će ido yana harararsa, kaifa mas'ud ─Ćan iskane wlhy zaka fara ko??, mas'ud yay dariya to nabari bro's. Su Anwar suka gaisheshi da tambayar yajiki??, ya ce, "musu da sau'ki, suka gaisa da yasmeen, itadai duk kunya ta isheta amma Nawaf ko ajikinsa, hirarsa yaketa zubawa. Ana haka momcy da papa suka shigo, azatonta Nawaf zai tashi, amma saitaga ya 'kara gyara kwanciyama, yasmeen ta rissina tana gaishesu, Nawaf ma ya gaishesu, suka tanbayeshi ya 'karfin jikin ya ce, "da sau'ki, Papa ya ce, "to ALLAH ya'kara afuwa, mu bari muje wani wuri saimun dawo.. Suka ce, "to adawo lafiya", Anwar ya ce, "papa dan ALLAH zanje. Papa ya ce, "A'a kabari zuwa jibi zamuje tareda ku, saimun dawo, suka fice. Abdallah yashiga tuntsura dariyar mugunta, Anwar ya fashe da kukan shagwa6a, yana fa─Ćin yaya kagansa ko. Nawaf yadakama Abdallah tsawa dallah malam yima mutane shiru, ubanmiye abin dariya anan, Abdallah ya tsaya da dariyar yan toshe baki, wayar mas'ud tayi wringing yami'ke yana fa─Ćin ina zuwa. Nawaf ya ce, "malam babu wani kana zuwa kace kawai katafi soyayya. Mas'ud ya fice yana dariya, aii dai ba haramun zanyiba, kuma na fika, Nawaf ya murmusa azuciyarsa ya ce, "nima ina hanya, afili kuma sauya kalli yasmeen, suka ha─Ća ido, tayi saurin janye idanunta daga kallonsa. Shima saiya kauda fuska yana murmushi. Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, jikin Nawaf yana sau'ki yanda yakamata, sannan agefe ga son yasmeen yana ─Ćauwainiya dashi, saidai yakasa furta mata, dukda kwayar idanunsa da aiyukansa suna 'ko'karin fallasa asirin zuciyar tasa. Mas'ud ne kawai ya fahimci halin dayake ciki, amma shima bai nuna masaba tunda bai fito fili ya sanar masaba. Itakuma yasmeen dayakeyi dan ita takasa fahimtar ainahin gskyar sa, saboda kallon maza datakeyi abai bai, saka makon hare2 dasuka kawoma rayuwarta abaya, sai take kallon kowane namiji da irin wannan sigar yake kallon mace, dukda itama tana fama da dakon soyayyar tasa azuciyarta, amma ita takan gwada 'ko'kari, konace jarumtar 6oyewa, wannan yasa gwarzon nata yakasa fahimtarta yake mata kallon kitse afannin san maso wani, (wato yana sonta tana son faisal) wannan yasa yake kasa fallasa sirrin zuciyar tasa saboda tu'ku'kin ba'kin cikin kishi dakanyi ─Ćawauniya dashi aduk lokacin da kwarin gwuywar fa─Ća matan ya iso kwakwalwarsa. Shai─Ćan yakan kawo masa taswurar bazata amshi soyayyarsaba, dan tanada wanda takeso, 'kaddarace kawai tarabasu, shikuma ta ha─Ćasu. Aduk lokacin da shai─Ćan yagama masa wannan karatun yakanji baya son ganin yasmeen akusadashi, shikansa yakanji haushin kansa yanda yabari sonta da 'kaunarta suka yimasa kamun kaxar kuku, shikam ya yarda ALLAH ne ya yanka masa kazar wahala, shiyyasa yaketa faman figarta, gashi kuma gashinta yagaza 'karewa, yarintse ido yana fitar da huci mai zafi daga bakinsa. A haka yasmeen tafito daga bayi tasamesa. Tabishi da kallon mamaki, wannan irin huci haka kamar wanda yake filin gwada 'kwanji. Yajuwyo yana kallonta shima, ta─Ćan kauda idonta daga kansa, cikin sar'kewar murya ya ce, "lafiya dai?", yasmeen ta ce, "'kalau mika gani??, ya girgiza kai yana fa─Ćin babu komai. Ta juya tana linke kayansa daya cire yabajesu akan gadon, wayarsa dake bisa dirowar gefen gadon tahau kara alamar kira, ta ─Ćauka tanufi inda yake ta mi'ka masa, ya ce, "waye?, batareda ya kar6aba. Ta kalli fuskar wayar sannan ta kalleshi ta ce, "number ce babu suna,, ya─Ćan ─Ćaga kafa─Ća shikenan kowaye bazan ─Ćaukaba. Cikin mamaki yasmeen ta ce, "saboda mi??, ya─Ćan tsura mata idanu, ya ce, "saboda bana ─Ćaga ba'kuwar number, kuma wanan layin nawa kowa zai iya samunsa, dan shine number gama gari,, yasmeen ta ta6e baki, to kasan bazaka rin'ka ─Ćagawaba miyasa karin'ka bada number??. Nawaf ya─Ćan zaro ido waje tofa 'yar jarida akaina zaki fara aikin nakine??, A'a ALLAH yabaka ha'kuri malam niba fa─Ća nake nemaba. Nawaf ya murmusa, ainima ba fa─Ćan nake nemaba, ni dan ALLAH ma zokimin tausa. Tausa kuma?, aiini idan zaka saka bindiga akaina bansan yanda aikeyin tausaba. Nawaf ya ce, "hummyimm aiko dole ki koya, dan ni mutumne maison idan yagaji amin tausa, ya 'kare maganar yana wani kanne ido ─Ćaya, yasmeen ta kauda kai tana ta6e baki, ta ce, "dan kuma kanaso sai akace dole nice zan maka. Yay wata sassanyar dariya yana fa─Ćin, yarinyarnan nakula har yanzu 'kuruciya tana damunki wlhy, amma karki damu, nakusa kaiki makarantar hankali, kuma nine malamin.......bai gama rufe bakiba aka 'kara kiran wayar. Yasmeen ta ce, "babu 'kyau wula'kanta mutanedai. Yay murmushi nima ba wula'kantasu nakeyiba, inada hujjar 'kin ─Ćagawa, duk inda mutum yaga wannan no ─Ćin ya ─Ćauka to yaga dokokin dana kafa, na ce, "kafin ka kirani ka tabbatar katuro mini sa'kon dazan gamsu dakai, idan naso zan iya kirankama da kaina, amma haka kawai daga kirana da number saina kama ─Ćagawa, bakisan mu sanannu anada hanyoyin cutar damuba iri2, karki manta bakowa yake sonmu dan ALLAH ba. Yasmeen ta ─Ćan jinjina kai tana ta ce, "hakane kuma, amma kabari ni na─Ćaga wanan. Da sauri ya harareta, ya ce, "wlhy koda wasa karki fara, angaya miki kowane shara ya isa yaji muryan matata ne, ALLAH kobanan kika aikata saina gane, kuma zan miki kwakwkwaran hukunci. Yanda yake maganar cikin fa─Ća sai abin yabama yasmeen mamaki, a zuciyarta ta ce, "badai kishina yafarayiba??, ta tuna randa ya sha'keta akan faisal, da fasa mata waya dayayi, wata zuciya ta ce, "babu wani kishi yana kare martabar igiyoyin aurensane kawai. Ahankali tajuya tacigaba da aikinta,, yabita da manyan idanunsa farare tas, ji yake zuciyarsa tana ambaliya akogin 'kaunarta wadda shi kansa baisan lokacin daya afkaba, ya lumshe idanunsa ahankali. Bayan kwana hu─Ću. Suka fara shirin komawa Najeria harda Nawaf, dan ya─Ćauki hutu domin yin jiyya, daganan zai zarce da hutun 'karshen shekara,, suka shirya tsaf, Nawaf da Mas'ud suka shiga gari sukayo tsaraba, Nawaf ya ce, "malam wai lafiya naga tsarabarka ta 'kare akayan baby?. Mas'ud yay murmushi, ya ce, "malam aika kusa zama dadyne. Nawaf yazaro ido waje bro's dgsk kakeyi??, mas'ud ya sakeyin dariya, hakane wlhy bakai kana mana rowaba konace kana mana ba'kin cikin ganin baby,, Nawaf ya ce, "kai nayi farinciki ALLAH ya inganta mana, amma ni babu wani rowar baby danake muku dasauran lokacine kawai. Mas'ud ya ce, "shikenan muna nan muna jiran lokacin, amma gsky muna bu'katar baby, dan haka ku ajiye wani girman kanku ku bamu. Nawaf yakaima mas'ud duka, oh munema zamu baku babyn ba ALLAH ba??. A'a ALLAH ne zai bamu amma fa da taimakonku, Nawaf ya ce, "to saika bari saina 'kara aure,, hhhhhh su aure manya, malam tuni nafara harbo jirginka, saiya fa─Ćo zan maida yanda akayi, shiru Nawaf yayi dan yasan halin mas'ud sarai. 'Kananun kaya ya─Ćebo sosai, wanda duk azuciyarsa na yasmeen ne, dan ita ka─Ćai yay ma tsaraba, yabama su Abdallah ku─Ći suyi tasu, hakama su momcy, saikuma 'kannen mas'ud daya siyomawa, daga nan suka dawo hotel ─Ćin, ya tarar har yasmeen tagama ha─Ća musu komai nasu. 'Karfe bakwai na dare jirginsu yataso zuwa 9ja✈................✍­čĆ╗ Assalamu alaikum Ina muku barka da sabuwar shekara, amma ina kira gareku 'yan uwana akan mu gyara wani abu, damuke aikatawa a tsarin rayuwarmu. Idan ban mantaba munshiga shikarar musulunci wata biyu daya wuce baya, amma banga mutane suna posting sosai akan farin cikin shigarmu sabuwar shekaraba,, wasuma basu san munshigaba,, amma abin haushi da ba'kin ciki kowa yasan anshiga sabuwar shekarar 2017, harma yana 'ko'karin yin posting ─Ćin taya murna. 'Yan uwana mu gyara, muringa girmama addininmu da aldarmu, mudaina fifita addinin wasu akan namu, dansu basu damu da abinda muke cikiba, koda sun sani sukan nuna basu fahimtaba,, tofa lokaci yayi dazamu fara gane karatun kurma wlhy,, ALLAH yasa mugane amin.. ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś­čĺô [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗43 & 44 .....Sun iso 9ja cikin ─Ćokin son ganin 'kasarsu ta haihuwa, musamman ma Nawaf daya ─Ćan da─Će baya nan, da'kyar suka samu ku6towa daga hannun 'yan jarida afilin jirgin, bayan Nawaf yayiwa masoyansa godiya da irin kulawa dasuka nuna masa, yayi 'yan bayanai na gamsarwa ga masoyansa. A family falo suka baje kowa yana maida numfashin gajiya, aka kawo musu lafiyayyen abinci daga gidansu mas'ud, kowa yaci ya 'koshi. Nawaf ya ce, "momcy nifa barci nakeji wlhy. Momcy ta ce, "to mai sunan manya kujira papanku ya sakko, dan yay muku tanadin wani abu dazai sakaku farin ciki,, Nawaf yay murmushi, ALLAH sarki my sweet papa, to muna jiransa. Babu da─Ćewa papa ya sakko cikin jallabiya fara, momcy ta ce, "kamar kasan jiranka kuwa akeyi,, murmushi papa yayi ya ce, "to gani miya faru?, momcy ta nuna masa Nawaf, wai barci yakeji, papa yay dariya to kutashi muje, amma saikun ─Ćaure fuskarku, momcy ta ce, "gsky ne Alhaji. Nawaf da yasmeen suka ─Ćaure idonsu da hankici momcy takama hannun Yasmeen, papa yakama na Nawaf, su Abdallah suka take musu baya. Woow!! Nafa─Ća danganin inda suka dosa. Anwar yabu─Će 'kofa suka shiga, saida sukaje tsakkiyar falon san nan papa ya ce, "subu─Će idonsu, kowa yazaro ido ­čś│­čś│dan mamaki, cikin farin ciki Nawaf ya rungume papa yana sambatun farinciki, sai dariya suke masa. 6angaren da Nawaf yafara ginawane ya daina, papa ya 'karasa ginin aka zubama wajen kaya masu 'kyau da tsari, abin sai wanda yagani komai zam2, papa ya ce, "to kowa ya za6i bedroom ─Ćin dayakeso, Nawaf ya ce, "papa ni zan fara za6a. A'a modebbo yasmeen ce 'karama ita zata fara za6a, yasmeen tafakaici idonsu papa tayima Nawaf gwalo, ya ─Ćaure fuska tamau yana harararta, momcy ta ce, "za6i kinji ─Ćiyata, tako nuna wanda Nawaf yakeso acikin zuciyarsa, da sauri Nawaf ya ce, "tab yarinya wlhy nima shinakeso. A'a modibbo kayi ha'kuri kaci girma kaifa babbane, kuma aii ─Ćakin mai gida a ciki akesonshi, dan haka kaine zaka ─Ćauki na ciki, Nawaf yay wani murmushin mugunta ya ce, "na amince papa. To ALLAH yay muku albarka kunji, suka dawo falo akayi addu'oi sannan su papa suka tafi nasu waje. Bayan fitarsu yasmeen ta tashi tayi shigewarta ─Ćakin data za6a batareda tabi takan Nawaf ba, yabita da kallo yana murmushin mugunta, takai minti goma da shiga sannan yabi bayanta, har yaje 'kofar ─Ćakin saikuma ya fasa ya wuce ─Ćayan ─Ćaki, wanka yashiga . Itama yasmeen wanka tayi, tana fitowa ta zira kaya ajikinta marasa nauyi ta haye gado, harta kwanta saikuma ta tashi ta sakko 'kofar ta sakama key tabar key ─Ćin aciki, dan tanada tabbacin wannan mugun zai i ya biyo bayanta tunda tabashi haushi, dan tunda tace tana son ─Ćakin nan ya canja fuska yana harararta, ta haye gadon tana wata 'yar dariya, babu da─Ćewa barci yay gaba da ita. Shima dai Nawaf bayan yafito kwanciya yayi domin yin barci, amma saiya kasa, tunanin yasmeen yazo ya kanaynayeshi abubuwa dayawa yake kissimawa a cikin zuciyarsa, yanzun kam gsky bazai iya ─Ĺaga mata 'kafaba, yariga yashirya. komai tafanjama fanjam, shima yana bu'katar ─Ćan─Ćana za'kin rayuwar aure, yanason sanin banbancin da da yanzu, to amma tawace hanya zaibi domin mallakar wadda yada─Će yana muradi da bege??, taya zai fahimtar da yasmeen cewa ya fara 'kaunarta tun lokaci mai tsawo daya wuce?, to anyama zata fahimcesa??, idan ta fahimcesa zata amshi uzurinsa??, waishinma zata soshi??, ko har yanzu tana ma'kale da son tsohon mijintane??, yaja wani dogon tsaki, ko a mafarki bayason tuna anta6a ─Ćaurama yasmeen aure dawani kafinshi, yakaima iska naushi yana huro hanci tamkar mai shirin danbe. Zumbur yami'ke yanufi ─Ćakin da yasmeen take, yata6a 'kofar amma saiyaji gam ankulle, mtsowwwww yaja tsaki yakoma inda yafito, babu da─Ćewa shima barci ya ─Ćaukeshi. Basu farkaba sai da'aka kira sallah, yasmeen ta tashi tayo alwala, tanajin motsin fitar Nawaf, koda yadawo saiya shiga gidansu mas'ud, mami ta ce, "A'a Modebbo dakanka, muna shirin shiga anjima, nazata kunacan kuna barcin gajiya, Nawaf yay murmushi yarisina yana gaida mami, ta amsa cikin fara'a da tambayarsa yajiki??, ya ce, "jiki Alhmdllh ka─Ćan yarage aii. Masha ALLAHU aii haka akeso, sun─Ćan da─Će suna hira, 'kannen mas'ud sukazo suka gaisheshi dayi masa yajiki, cikin fara'a yake amsa musu,da tambayarsu ya karatu? , daga baya yanufi 6angaren mas'ud. A falo ya iskesu anata zuba soyayya, Nawaf ya ce, "ALLAH yashiryaka malam, kana nan kana soyayya shiyyasa muna sauka kagudo ko?. Mas'ud yay dariya yana fa─Ćin yaranka Alhaji?, Nawaf ya ce, "fari 'kal, yazauna suna gaisawa da Ameena, Nawaf ya ce, "ashe munsami 'karuwa to ALLAH ya inganta mana, Ameena ta ce, "amin tana murmushi, taje takawo masa lemo, saita koma bedroom takwanta tabasu waje. Nawaf ya ce, "mutumina kaikam sai ahankali, ahankalinma sai sannu mas'ud yafa─Ća yana hararar Nawaf,, ya─Ćora dafa─Ćin ina yasmeen??, Nawaf ya ta6e baki tana gida mana kozan rin'ka yawo da'itane. Dariya mas'ud yayi, to idan kayi yawon da'ita haramunne, aii yakamata ma kuzo tare yanzu. mtsowwwww!!!! Nawaf yaja tsaki Kaifa idan ana maganar arzi'ki saika rin'ka kawoma mutane ta tsiya,, hummmmyimm!!! Maganar yasmeen ─Ćince tatsiya?, malam idanzaka fito fili kafa─Ća kafito, wlhy tuni nagano ka kamu da son yasmeen, dan idanunka sun fallasa sirrin zuciyarka. Lah mas'ud sharri kuma ka koma yima mutane da sa ido??. Babu wani sharri alhaji gsky ce, idan kuma bakasan kakamu da sontaba to yanzu na fassara maka ba'kin. Nawaf ya ku6i lemo yana murmushi, saida ya ajiye kofin sannan ya ce, "amma kaidai mayene!, kace dama ido kasaka mini bansaniba. Hhhh aiba saina sha wahalar saka maka idoba, gaba ─Ćaya sassan jikinka sun tonaka, kallon dakakema yarinyarnan kawai ya'isa agane ka kamu da sonta. Humm kadaiji dashi, nikaga tafiyata, dama su mami nazo gaidawa daganin Ameena, dan haka mukwana lafiya. mas'ud ya tuntsure da dariya, to angon yasmeen, mu dai muna jiran baby a daren yau. Banza Nawaf yay masa yafice abinsa. Afalo yatarar da yasmeen dasu talatu tana nuna musu suna gyarawa, dansuma yau suka dawo daga hutun dasuje tunda gidan babu kowa. Da sauri suka rissina suna gaisheshi, sau ─Ćaya ya amsa ya ─Ćauke kai, ─Ćakin yasmeen yashiga, cikin haushi yasmeen ta take masa baya. Kwance ta tarar dashi akan gado yayi filo da hannayensa, idanunsa a lumshe kafafunsa kuma suna zube a'kasa yana ─Ćan motsasu, ta tsaya cak ajikin 'kofa tana kallonsa, 'kafarsa fes2 kamar baya takata a'kasa, bakowacce 'kafa bace abin kallo, amma idan kaga ta Nawaf dolene ka kalla, taci gaba da kallon sassan jikinsa ─Ćaya bayan ─Ćaya. Kamar daga sama taji ya ce, "mikike kallo ajikina??, da sauri ta kauda kai gefe, itafa azatonta idonsa arufe suke baya ganinta, ta ─Ćan ta6e baki tomiye abin kallo ajikin naka???. Ya bu─Će ido ka─Ĺan yana kallonta 'kasa2, tai 'kasa da idanunta dan bazata juri kallon nasaba, ya kauda kai daga kallonta, yasan yana tashi zata fice da gudu, tunda matsoraciyace, gakuma su talatu a falo. Yatashi zaune yajingina da jikin gadon yana latsa waya, ta ce, "wai miya kawoka ─Ćakina ma??, batareda ya kalletaba ya ce, "nan nakeson zama kozaki hananine??, bazan hanakaba amma zan ha─Ćaka da momcy dan nina fara za6ar nan. Murmushi yayi har fararen ha'koransa suka bayyana, yasmeen ta tsura masa idanu kamar zata cinyeshi, baita6a murmushin daya 'kawata 'kyawunsaba irin yau, jitayi 'kyaunarsa ta'kara ninkuwa azuciyarta. Maganarshi ta katse mata tunanin ta, "k zokiga wannan kokinsan miye, batayi tunanin komai ba tanufi inda yake dan tana cikin shau'kin so, kamar gsk ya mi'ko mata wayar, tami'ka hannu da zummar amsa, saiya dam"ke hannunta caraf, yafisgota ta fa─Ćo saman gadon, ya─Ćan kishingi─Ća agefenta it kuma tana a rigingine, idanunsa na kallon fuskarta . Cikin tsiwa ta ce, "malam wai miye hakane??, ya ce, "tambayeni mana?, ta ce, "aii tambayar taka nakeyi?, ya ce, "'kara tambayata. Takula abin nasa rainin hankaline, danhaka saitayi shiru, yasaka yatsansa yana zagayawa akan la66anta, ya ce, "wakikema gwalo ─Ćazu??, ta ture hannunsa tana fa─Ćin banason abinda kakeminfa, wannan aiba yibane. Ya ce, "hummyimmm! Bahaka kikesoba shiyyasa kika za6i muha─Ća ─Ćaki??, ta harareshi malam ni karkamin sharri ─Ćakinka daban nawa daban ta 'kare maganar da murgu─Ća baki­čśĆ. Oh!!, laifi uku kenan??, ta yun'kura zata tashi ya maida ita, yasa 'kafa ya danne 'kafafunta, 'yammata aii bakida ikon tashi anan, saikin gayamin ni sa'ankine??. Yasmeen ta ta6e baki, ALLAH idan baka sakeniba saina tara maka mutane, dan ihu zan maka wlhy. Nawaf ya tuntsure da dariya, yarodai man kaza, yarinyarnan har yanzu 'kuruciya tana damunki, "k atunaninki idan kinyi ihu wani zai jiki?, ki tuna tazarar dake tsakaninmu dasu momcy, tokoma sunjiki ai babu mai kawo miki ─Ćauki yarinya. Kaidai kasani, waikai babu abinda ka'iya arayuwarka sai mugunta ne??. Ya ce, "woow!! Kinaso na nuna miki abubuwan dana iyane bayan mugunta kenan?, yasa hannu ─Ćaya ya tallabo fuskarta, yamatso datashi harsunajin fitar numfashin juna, idanuwansu suka ha─Ću a 'kar'kashin inuwa ─Ćaya, yasmeen tafara kauda nata idanun, dan jitake kamar wani abu yanafita daga idanunsa zuwa nata. Ya─Ćan murmusa kinyarda ba mugunta kawai na iyaba, tayi shiru kamar batajishiba, ahankali ya ce, "bari na'kara nuna miki danki tabbatar, tabu─Će baki zatayi magana, ya ha─Će bakinsa da nata. Na ce, "humm bari kuga nayi nan, ­čĆâ­čĆ╗falo nadawo nabasu waje, bayan 'yan mintina ka─Ćan nakoma, zuwa sannan ya barta amma sai kuka takeyi, shikuma yayi shiru yana kallonta, tamkar yau ya fara ganinta, yakama hannunta ya rumtse anasa, har yanzu kina akan bakanki???.. Harararsa tayi da manyan idanunta wa─Ćanda suka so rikita masa lissafi, amma saiya dake, ya ha─Će fuska kamar bai ta6a dariyaba, ya ce, "nakula kinada tsiwa sosai xarah amma ina nan zan sauke miki ita, karki ─Ćauka nagama yimiki garga─Ćine, Wannan nayimikine akan laifin gwalon ─Ćazu, saura na ─Ćaki, ya'kare maganar dajan karan hancinta ya matsa da 'karfi, tari'ke hannunsa da 'kafi dan zafi. Yasaki hancin yana dariya, danganin yanda hancin yay jajur, yasauka daga gadon yana fa─Ćin sai gani na biyu fancy face!!. Yasmeen tabishi da kallon mamaki waye kuma fancy face??, wata zuciyar ta ce, "k mana., yasmeen tasaki murmushi tana maimaita sunan ahankali fancy face!! Ta lumshe ido tana murmushi, kardai ace mafarkintane yafara zama gsky, shin dgsk Nawaf yafara sontane??, tajawo filo ta rungume jitake kamar shita rungume, tuni ta manta da zafin hanci, sai maimaita sunan takeyi tana murmushi, gsky sunan yay mata da─Ći fancy face!!!!. Nawaf yafa─Ća kan gado yana murmushi, yakai hannunsa saman la66ansa yashafa, idan yana kissing ─Ćin yasmeen takan dukeshi da mintsini amma yau batayi masa hakaba, saidai hawaye datakeyi, to mikenan??, kota fara sonsane?, lallai dayafi kowa sa'a arayuwa, dayace, "shikam ya─Ćara sauran maza sa'a, da samun 'kya'ky'kyawar yarinya nitsatstsiya, yajawo filo yarungume tsam a 'kirjinsa,, ahankali ya ce, "I LUV U MY FATEEMA XARAH!!!!!!!­čś│ Woow!!! anzo wajen­čĺâ­čĺâkowa yakamu­čść­čśť. Haka kowa yayta sambatu da begen ─Ćan uwansa a─Ćaki, sallama a─Ćaki Nawaf yayita baifita ko'inaba, garama yasmeen tafito falo, bayan salkar isha'i, su talatu suka kawo musu abincin dare kona ce, "kayan marmari dakuma shayin Nawaf nafama, saikuma ─Ćan abinda ba'a rasaba, suna cikin jerawa Nawaf yafito daga ─Ćaki, dagashi sai wando iya gwuywa da 'karamar riga tashan iska, hannunsa ri'ke da wayoyinsa, suka rissana suna gaisheshi, ya amsa yana zama kujerar dake kallon yasmeen. Suna gamawa suka fice, yatashi yaje yakunna tv sannan yadawo yazauna hannunsa ri'ke da remote, idonsa yana kan tv ya ce, "azo abani shayi. Yasmeen tayi burus dashi kamar batajiba. Yadaka mata tsawa ALLAH kikiyayeni, dan iskanci kinaji ina miki magana amma kike shareni, yasmeen ta─Ćago tana kallonsa, ta tsorata da tsawar amma tadake, ta ce, "naga baka ambaci sunaba nasani koda bango kakeyin magana. Tab─Ćii yafa─Ća azuciyarsa, yama kasa cemata komai, saidai daka kalleshi kasan ransa ya 6aci sosai, itama ganin haka saita mi'ke tanufi kichin, kofi ta ─Ćakko tazauna tana ha─Ća masa shayin, tagama ta ajiye agabansa batareda tayi maganaba, binta kawai yayi da kallon shima dan yakasa magana. Maimakon yasha shayin kamar yanda ya saba, saikawai yaja tiren kayan marmarin yafara sha, yanasha yana kallo, itamadai idonta yana kan tv'n, wayarsa tashiga 'kara ya ─Ćauka, yana waya yana kallo ga kayan marmari agefe yana ─Ćorawa, da larabci yake maganar shiyyasa yasmeen bata fahimtar abinda yake fa─Ća ba, yakanyi dariyadai lokaci2, dakuma ambatar sunan ummuhabiba. Wani takaici ya turni'ke zuciyar yasmeen, tacika tayi fam da kishi, jitake kamar 'kirjinta zai fito waje, taji ya ce, "i ­čĺôu too my dear sis..... Da sauri ta mi'ke tana huci tashige ─Ćakinta, yabita da kallo yana gyara zama, yasaki murmushi yacigaba da wayarsa. Araina na ce, "haka zaku 'kare, kowa girmankai yana ─Ćawai niya dashi. Kan gado ta fa─Ća tana kuka harda dukan kanta,, shikam gogan ko'a jikinsa wayarsa yaketa zubawa shida ummu habeeba, saida tagaji dan kanta takashe sannan yatashi yanufi ─Ćakinsa, yasmeen tami'ke da haushi tanufo falon dashirin kota kwana, dan ta shirya suyi duk wacce zasuyi da Nawaf, to kuma saitaga falo wayam, sai ma falon a hargitse da kwanika, tazauna tahau cin abincin dan yunwa takeji sosai, ahankali Nawaf yazo ya wuceta yashige ─Ćakinta batareda tagansaba. Tagama ta gyara falon takashe komai sannan tanufi ─Ćaki, saida tagama sawa 'kofar key sannan ta ankara da Nawaf kwance bisa gado barci ya ─Ćaukesa, tayi tunanin takoma, saikuma taga tana ta6a 'kofar zai iya farkawa wannan mai kunnen macijin. Ahankali taja bargon zuwa 'kasa, ya─Ćan motsa, da sauri ta du'ke dankar yaganta, yagyara kwanciyarsa yacigaba da barcinsa. Ajikin gadon ta shimfi─Ća bargo, ta manne da gadon yanda bazai gantaba, ta kwanta ahankali, babu da─Ćewa barci yay awon gaba da'ita. Barci yay barci Nawaf yanata mirgina2 akan gado shi ka─Ćai, har yaiso bakin gado sosai kuma gefen da yasmeen take kwance, ya 'kara juyawa da zummar gyara kwanciya saigashi yafa─Ćo tim akan yasmeen dake rigingine,, afirgice ta farka, shima ya bu─Će ido, suka 'kurama juna ido cikin mamaki suke duban juna, amma kallon soyayya, kowanne kwayar idonsa na nuna tsantsar son ─Ćan uwansa, Nawaf yay ─Ćan murmushi, dama sabodani kika kwanta nan ko??, to gani ALLAH ya nuna mini ke. Yasmeen ta ce, "mizaisa na 6oye saboda kai??, yashiga shafata yana fa─Ćin dalilan dayawa fancy face!, dandanan tsoro yashigi yasmeen dan tunda suke baita6a yimata irin hakaba, yakandaiyi kissing ─Ćinta,, kafin ta ankara yafara wuce gona da iri, tafara kuka tana bashi ha'kuri, cikin sar'kewar murya ya ce, "fancy face! aii yaukuma kinzo hannu babu ─Ĺaga 'kafa, gara mu goga rainin dake tsakaninmu, 'kila daga nan zaki fara girmamani. Ta 'kara fashewa da kuka, kayi ha'kuri wlhy bazan sakeba, bazan sakeyimaka abinda baka soba, plz for giveme, wlhy ina fashin sallah kaji na rantse maka. Yanda take magana arikice saiya ─Ćauka tsorone yasakata fa─Ća, ya ce, "ban yardaba, ba─Ćazu kinji sallaba?,, wlhy Azuhur kawai nayi, saikuma yazo. aiko kafiri yaga halaka yana musulunta, danhaka ban yarda dakeba, wlhy da gsk nakeyi yaya!! narantse maka, ya ce, "to saina gani zan yarda 'kanwata, yafa─Ća cikin zolaya. Yashiga 'ko'karin tura hannu, aisai numfashinta ya ─Ćauke, saboda tsoro, babu abinda take tunawa saiwasu ranaku biyu abaya wanda suka kasance a mabanbanta lokaci, jin yarinyar mutane zata some masa saya ─Ćagata, hakan yayi dai2 dakiran sallar asubahi.tfmt m a ­čĺâkola ain [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ­čĹç­čĆ╗kunga ciban nan. Haka yayi daidai dakiran sallar asubahi, yamirgina gefe yana maida numfashi, itakuma tajuya tana kuka, jikinta sai tsuma yakeyi, jitake kamar ta tsaga 'kasa ta 6oye, yami'ke ahankali yafice, ─Ćakinsa yanufa yana cije le6e, yawuce bayi yasakarma kansa ruwa tamkar wanda yay dau─Ćar shekara guda, saida yaji ankira sallar shiga masallaci sannan yay wanka yafito, A─Ćaki yayi sallar danjin cikinsa ya kulle tamau. itama yana fita tami'ke tasakama 'kofar key tana kuka, tazame ajikin 'kofar tana kuka mai tsuma rai,, na ce, "saikace wadda akace umma ta mutu, bayanma bai miki komaiba­čśí. Har aka idar da sallar asuba tana awajen, saidaga baya tazame takwanta barci yay awon gaba da ita. Shima daya idar da sallar saiya kwanta awajen dan baya jin da─Ćin jikinsa, koda gari yawaye suka tashi, babu wanda yakula kowa, ita yasmeen tana tsoransane yanzu, shikuma yanajin haushinta, haka suka kullah kwana biyu suna 'yar wasan 6uya, amma Nawaf shi bashida lafiya, tun yana jurewa harya kira momcy awaya danjin zai halaka abanza, arikice momcy da umman yasmeen suka iso 6angaren nasu, dan tazo duba Nawaf ne itada ya seer, ─Ćakinsa sukanufa kai tsaye, suka tarar dashi ri'ke da ciki yanata mirgina2. Suka 'karasa da sauri suna tambayar lafiya??. Batareda ya iya furta komaiba ya nuna musu cikinsa, waya momcy ta ─Ćauka takira mas'ud, cikin 'yan mintina ya iso gidan,, bai tsaya neman ba'asiba yashiga duba Nawaf, yarage murya yanda momcy da umma baxasujiba, ya ce, "bro's kaga abinda kajawoma kanka ko??, kanada matarka amma kasaka kanka a wannan halin??, Nawaf yari'ke hannun mas'ud ahankali ya ce, "plz karka gayama su momcy kaga harda umman yasmeen. Mas'ud ya fisge hannunsa yana harararsa, dallah malam sakarmin hannu saina fa─Ća ─Ćin. Momcy ta ce, "mas'ud mike damunsa, mas'ud yay 'kasa da kai yana sosa gefen wuyansa saikuma yakalli Nawaf daketa ro'konsa wai karya fa─Ća. Momcy ta dakama modebbo tsawa ta ce, "saiya fa─Ća ─Ćin, mas'ud fa─Ćamana, Nawaf ya ce, "mom plz dan ALLAH basai ya fa─Ćaba kiyi ha'kuri,, harararsa ta yi ta ce, "bazaka yima mutane shiruba ko??, mas'ud ya ce, "momcy yasan bashida gsky shiyasa, dama yana bu'katar matarsane amma girmankai ya hanashi su zauna su dai2ta saboda wani dalilinasu mara tushe, to gashinan haryajama kansa ciwo saboda bazai iya daurewaba. Momcy tazaro ido, mas'ud kana nufin yasmeen da modebbo basa zaman lafiya??, mas'ud ya ce, "hakane mom. Momcy ta ce, "to miya ha─Ćasu??, mas'ud yami'kama Nawaf magani yana fa─Ćin mom bari yasha magani sannan. Nawaf yakar6i maganin yasha yana hararar mas'ud, babu da─Ćewa barci yay awon gaba dashi, mas'ud yazauna ya zayyanema su momcy duk abinda yake faruwa tundaga ha─Ćuwar su tafarko. Umma ta ce, "aiishi baya da laifi, laifin yasmeen ne wannan, A'a wlhy karkice haka laifinsane tunda shine yafara tsokanarta, kuma dan mugunta yamareta. Umma ta ce, "to wayace tayi masa rashin kunya??, waini tanama ina?, momcy tarakota har ─Ćakin yasmeen, tana kwance duk ta canja kamanni saboda tsoro da kewar rashin ganin mijinta, ta mi'ke zumbur tana kallon umma,, wani lafiyayyen mari umma tabata , tashiga zazzaga mata fa─Ća, bata ta6a ganin 6acin ran ummaba irinyau, momcy tashigo tana bata ha'kuri. Umma ta ce, "kibar bani ha'kuri hajiya yasmeen batajin magana ko ka─Ćan, tsiwarta tayi yawa wlhy. Kuma tashirya taje tabashi ha'kuri inkuwa bahaka ban yafe mataba, umma tana gama fa─Ća tafice. Yasmeen tadur'kusa tana kuka tana bama momcy ha'kuri, momcy ta rungumeta tana lallashi damata nasiha, saidataga hankalinta yakwanta sannan fice wajensu umma. Can ma momcy lallashin umma tayitayi harta sakko daga fushin datayi, suka─Ćanyi hira, sai bayan sallar axuhur suka tafi, yaseer yanatajin haushi baiga sisto ─Ćinsaba da yaya Nawaf, momcy ta ce, "yayi ha'kuri zata turo a ─Ćaukesa yayi weekend anan. Yasmeen ta tashi tayi wanka ta shirya tsaf kamar yanda umma ta shawarceta, dan kafin su tafi tasake shigowa, tayimata nasihohi, tagama gyara kanta tayi 'yar kwalliya ta feshe jikinta da turare, jiki a sanyaye tanufi ─Ćakin Nawaf, bayanda zatayi dole taje tunda al'kawari ta ─Ćaukarma umma zatayi duk abinda ta sakata. Ta tura 'kofar tashiga, yana zaune kan abin sallah ya gama rama sallolin da'ake binsa bayan yayi wanka, ko inda take bai kallaba, tawuce tana gyara masa gado, bayan ta gama ta kalleshi, yagama addu'ar yana zaunene kawai. Taje gabansa ta tsugunna ta ce, "dan ALLAH kayi ha'kuri bazan sakeba. Baiko kalletaba yami'ke yakoma saman gadon ya kwanta dan baya jin 'karfin jikinsa amma babu inda ke masa ciwo. Zuciya ta turnu'koma yasmeen danganin wula'kancin dayake mata danyaga tana bashi ha'kuri,, harta nufi 'kofa zata fita, saikuma ta tuna da batun umma, bataso iyayenta suyi fushi da ita. Duk abinda take yana kallonta yana mamakin taurin kai irinna yasmeen, tazo bakin gadon ta tsaya tana fa─Ćin kanacin albarkacin iyayenmune kawai, shiyyasa nake baka ha'kuri, amma wlhy dako zamu mutu ahaka bazan baka ha'kuri ba. Hannu yasa ya fincikota ta fa─Ćo jikinsa, dukda jikinsa babu 'karfi amma yafi 'karfinta,, birkiceta yayi yana fa─Ćin waike wacce irin mara kunyar yarinyace??, kodan kinga ina ─Ćaga miki 'kafa shiyyasa kike neman kawo mini rainine??. Yasa hannu yajamata la66a tasaki 'kara, ya ce, "banza matsoraciya yau ─Ćinnan zan kawo 'karshen rashin kunyarki, yasa hannu ya yaga ba'kar doguwar rigar dake jikinta....................✍­čĆ╗ ­čĹç­čĆ╗ ­čść­čść­čś│­čś│­čśť­čśťmuha─Ću gobe idan ALLAH yakaimu. Kuyi ha'kuri yarane sukaimin sending batareda nagama typing ba. Ina 'kaunarku aduk inda kuke fan's ─Ćina, kamar yanda kuke 'ko'karin bibiyata,, ALLAH yabarmu tare, kuna 'karamin 'karfin gwuywa­čĺő­čĺő­čĺő­čĺő ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś­čĺô [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗45 & 46 .....Bayyanar surar yasmeen afili ta ru─Ća Nawaf, yana mamakin dama haka yarinyar nan take?, cikin kuka ta ce, "wlhy idan baka ─Ćaga niba zan cijeka. Humm ki cijeni mana, koma kiyi abinda yafi cizo idan kinada dama. Ta bu─Će baki zatayi magana ya tura harshensa cikin bakinta, da zafi2 yake sarrafata, tamkar Namijin zaki yaga abinci, to abinka da farin shiga,­čśť­čÖł. Sai dukansa take tana mintsini amma ina wanda yay nisa bayajin kira. Sum sum sum­čÜ­čĆ╝nafito falo dan karna wuce gona da iri. Saidai komai yalafa sannan na koma. ALLAH sarki yasmeen tabani tausayi, tayi lamo ko motsi bata iya yi, sai hawaye dasuke zirara a idanunta, Nawaf dake kwance agefenta yatashi ahankali ya zauna, kanta ya ─Ćago ya ─Ćora saman cinyarsa yana share mata hawaye. Cikin taushin murya ya ce, "ALLAH yay miki albarka fancy face ─Ćina, lallai ke abin alfaharina ce, kinzama wata tsoka mai daraja ajikina, yakamo hannunta ya sumbata, yakuma share mata hawayen da har yanzu suke kwarara daga idanunta, yay ─Ćan murmushi, fateema xarah matar kwarai abin koyi da alfahari, nikam ayau nafi kowa sa'a. Ahankali ya kwantar da kanta saman filo, yaja bargo ya lullu6eta sabida sanyin AC, yatashi yashiga wanka, yana fa─Ćin fancy face ina zuwa kinji 'yar albarka. Momcy takalli agogon dake falon papa 'karfe 5:48pm takalli papa tana fa─Ćin Alhaji bari naje naduba ko modebbo yatashi??. Papa ya ce, "dama kin 'kyaleshi tunda shiya jama kansa, danni ko sannu bazata ha─Ćani dashiba. Momcy tayi murmushi to Alhaji yaya zamuyi, aii hannunka baya ru6ewa ka yanke kayar, injiku hausawa. Papa yay dariya lallaikam, amma kema aii kinzama bahaushiyar. Momcy tayi dariya to yazanyi tunda ka maidani bahaushiyar,,, hhhh kin amince kenan??, eh na amince,, to kije kidubashi, amma ba kince matarsa tana taredashiba??, hakane? ? tana wajensa, aifa─Ća sosai ummanta tayi mata, shima jira nake yatashi yasha nasa fa─Ćan. Gskyr kine kuwa dolene mu zaunar dasu muyi musu nasiha dansu rungumi juna kamar kowanne irin ma'aurata. Momcy ta ce, "toshikenan Alhaji ina zuwa, to kiyi masa sannu. Momcy tashigo ─Ćakin da sallama lokacin Nawaf yana wanka, da sauri ta'karaso gaban gadon dan ganin yasmeen 'kudundune abargo, ga shashshekar kuka tanayi ahankali, momcy tazauna bakin gadon tana tambayar ─Ćiyata lafiyarki kuwa??. Yasmeen ta─Ćago idanunta dasukayi jajur saboda kuka, tana kallon momcy, dasauri Nawaf yabu─Će 'kofa yafito, jikinsa sanye da farar rigar wanka. Momcy ta─Ćago tana kallonsa, ta ce, "modebbo miya faruda yasmeen??, Nawaf ya─Ćan sosa gefen wuyansa yana wani sadda kai 'kasa, cikin in ina ya ce, "babu komai momcy kawaidai...........saikuma yayi shiru. Momcy ta girgiza kai kawai dan ganin alamomin rashin gsky sun bayyana tareda Nawaf, ta maida kallonta ga yasmeen dataketa kuka har yanzu, ga kunyar momy datakeji. Momcy ta ce, "sannu kinji ─Ćiyata, yanzu zaki iya tashi??, yasmeen tai saurin ka─Ća kai Alamar eh. Okey to inazuwa, momcy tami'ke tara6a ta gefen Nawaf tashiga bayi. Da sauri Nawaf ya 'karasa wajen wardrobe ─Ćinsa yabu─Će wani akwati riga mai─Ćan kauri ya─Ćakko yanufo gadon, hawowa yayi saman gadon ya ─Ćagoda yasmeen zaune, taisaurin ri'keshi tana fa─Ćin wayyo zafi, ya rungumota zuwa jikinsa ya ce, "sorry my dear bari nasaka miki riga kinga momcy tana nanko. Yasaka mata kayan cikin hanzari, tana rungume ajikinsa momcy tafito tana fa─Ćin yauwa yasmeen daure kitashi kinji.... yasmeen tayin'kura zata tashi daga jikinsa, tai saurin cije le6e tana fitarda huci da'kyar. Momcy tari'keta da sauri tana fa─Ćin sannu kinji, Nawaf ya ce, "momcy konazo na ─Ćauketane??, harararsa momcy tayi suka shige bathroom ─Ćin. Nawaf yasaki wani murmushi tareda fa─Ćawa saman gadon zuciyarsa fal farinciki da nisha─Ći,, afili yafurta yaudai an wuce wajan, yafa─Ća yana shafa gemunsa na gayu. Momcy tafito fuska a─Ćaure ta ce, "kaje ka taimaka mata tayi wankan, Nawaf yashi zaune da sauri, kansa na 'kasa ya ce, "to mom batayarda kin taimaka mataba ne??, momcy ta harareshi tana fa─Ćin ai ita tanada kunya bakamar kaiba, tana fa─Ća tafice daga bedroom ─Ćin. Nawaf yami'ke zuwa bathroom ─Ćin, yasmeen dake tsaye tana cire kaya, tayi saurin 'kudundune jikinta waje ─Ćaya, yay ─Ćan murmushi yana ta6e baki, ya'karasa wajenta yana fa─Ćin oh, xarah na, ai ta6oye ye ta'kare kuma, zokiga nayi miki maganin kukan nan. Cak ya─Ćauketa yasaka acikin rawan da momcy ta ha─Ća, yasmeen ta ri'keshi tana kukan shagwa6a, yashiga shafa kanta yana lallashi cikin hikima da lalla6a yagasa mata jikinta, itakuma tana zuba masa shagwa6a, ya ce, "kin iya wankan tsarki ko??. Cikin gatse ta ce, "ban iyaba,, shikam bai fahimci gatse take masaba, dan haka yashiga koya mata, yana─Ćota a tawul yakawo ─Ćaki. KIRA......hum akwai wasu mutane dasuke fa─Ćar adaren farko ba'a shan wahala,, ban 'karyatasuba bankuma yarda dasuba,, saidai inaso natuna musu cewa dukkan macen data ri'ke martabarta zuwa gidan miji tofa dolene tafuskanci wannan ranar, kuma tabbas wannan wahalar dasuke 'karyatawa saitashata. Nibanga laifin marubutaba dasuke tsoratar damu akan daren farko, hakan abune mai'kyau, kuma wa─Ćanda basuda aure zasuso tattalin nasu budurcin harzuwa wannan rana, domin kwa─Ćayi samun tagomashin albarka da darajar wannan rana, amma ina kira agareku kudaina ─Ćaukar dole sai anmallaka muku wata 'kyauta a washegarin wannan ranar, suma kuma mazajenmu suzama masu daraja dukkan macen dasuka samu acikakkiyar mace. Amma akwai dalilan dasuke sawa mace tarasa budurcinta koda bata hanyar zinaba. ☆1 ─Ćaukar abu mainauyi yakansamu rasa budurcinmu, amma bazai hana mace taji zafiba koda ka─Ćanne awannan rana, domin itace rana tafarko data fara sanin ─Ća namiji. ­čÖł. ☆2 hanya tabiyu itace yawan tsallaka abu, ko hawa bishiya, gudu, ko yawan tsalle2, dakuma horo da akebama yara amakaranta, kamarsu tsallen kwa─Ćo, gwale2 da makaman tansu. tokam wa─Ćan nan hanyoyin sukansa mace ta rasa yanar budurcinta. ☆3 saikuma hanya ta uku,, wa'iyazubillah, ita ce hanyar ma─Ćugo, tabas mata sukan rasa budurcinsu ta wannan hanyar, miji bazai ganki da darajaba, gakuma ─Ćunbin zunubi awajen ubangiji,, wasuma basa sha'awar yin aure saboda she─Ćanci da bushewar zuciya sun kanainayesu. Ya ALLAH ka tserar damu,, kakuma ganardamu, katsaremana kakanninmu da iyayenmu da yayyanemu da 'kawayenmu da 'kannenmu, da 'yayanmu daga fa─Ćawa halaka,, ALLAH yashirya masuyi, damasu sha'awar aikatawa ya ALLAH ka tausasa zukatansu. Amma mata yakamata mucigaba da gane muhimmancin budurci da tasirinsa acikin rayuwar aurenmu, ALLAH yabama 'yan baya ikon kai nasu budurcin suma inda yadace, ameen­čÖĆ­čĆ╗­čĹŹ­čĆ╗. Nawaf ya canja kayansa zuwa jallabiya, sannan yafito domin ─Ćakkoma yasmeen wata rigar danyin sallar magriba. Afalo yay arba da momcy, tadawo hannunta ─Ćauke da shayi da magunguna, tawuce batareda ta kalli inda Nawaf yakeba, shima baice komaiba yawuce ─Ćakin yasmeen, saidai jikinsa asanyaye, bayaso yaga momcy ko papa suna fushi dashi, ya'karasa ─Ćakin ya─Ćako ma yasmeen wata doguwar rigar, sanda yadawo momcy tana bama yasmeen shayi ALLAH yasoshima da rigar wanka ajikinta. Ya ajiye kayan saman gadon yana kallon yasmeen 'kasa2, ahankali ta ce, "mom na'koshi, lalla6ata momcy tayi ta─Ćan 'kara sannan taba magani tasha ta kwanta. Momcy tami'ke tafice tana harar Nawaf dayake zaune bakin gado ya rabga uban tagumi. Bayan fitarta yatashi yakoma kusada yasmeen, ya zame 'karamin tawul ─Ćin data nanna─Će kanta dashi dan sumarta ta tsane,, ya wargaza gashin akan filo yana fa─Ćin kibarsa haka yasha iska. Ya tsuggunno ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, "naje masallaci saina dawo. Tana jinsa duk abinda yakeyi amma ko motsi batayiba, bayan fitarsa tayi murmushi tareda zirarar da hawaye,, tabbas batayi ba'kincin abinda Nawaf yaymataba saidai tasha wala, dan Nawaf damugunta yazo mata kokuma gaggawa, amma hakan bazai sa taji haushinsaba kota tsanesa, saima take ganin yanzune zai sota da 'kyaunarta harma da ganin girmanta, tatuna irin sambatu da addu'oin daya ringa zubo mata, yafa─Ća mata ita ka─Ćaice abin sonsa, kuma yada─Će yana 'kaunarta, shin da gskne kokuwa dan baya cikin hankalinsane??. To komadai miye lokaci zai nuna, kuma tana sauraren zuwan lokacin, amma tabbas itakam takamu da son mijinta mai tsanani, musamman ma yau daya sake kusanta kansa da ita, haka tayita zancen zuci har barci ya kwasheta. Nawaf daya dawo daga sallah saiya wuce wajan momcy danya bata ha'kuri, A─Ćakinta yasameta tana lazumi, yazauna kusada ita yana wani sissinkuyar da kai. Momcy ta shafa addu'ar tana fa─Ćin kai kuma lafiya??, Nawaf ya'kara 'kasa da kai yana fa─Ćin sorry momcy, dan ALLAH kiyi ha'kuri da duk laifin dakike ganin nayi miki, na ─Ćauki laifina kuma insha ALLAHU zan gyara, bakuma zan sakeba, insha ALLAHU yanzu zamu zauna lafiya nida yasmeen harma mu sakaku farin ciki, dan ALLAH karkuyi fushi dani plz. Momcy taja ajiyar zuciya, amma kasandai abbuna baka 'kyautaba ko??, kasan wannan ba halin kwarai bane, matarka tanada hakki akanka, kaima kasani, kuma ka girmeta ka fita hankali, dammi zaka biye mata ku aikata abinda bai daceba, yasmeen yarinyace mai hankali da nutsuwa, kowa ya zauna da'ita saiya sota. Hakane momcy, nima ─Ćin ko ada─Ćin ina 'kaunarta sharrin shai─Ćanne kawai, amma insha ALLAHU baza'a sakeba. To shikenan ALLAH yabaku zaman lafiya yakuma baku zuriya tagari. Nawaf ya amsa akan la66ansa da ameen, nandai momcy tayi masa nasihohi, sannan yami'ke ya ce, "momcy papa fa??, yana ─Ćakinsa momcy tafa─Ća, kaje ku gaisa mana,, A'a momcy barsa sai gobe idan ALLAH yakaimu, yau nasan inada laifi awajensa, gashi nabar Yasmeen ita ka─Ćai. Momcy tayi murmushi ta ce, "to saida safe, idan ta tashi kace inamata sannu. To my dear mom zataji yafa─Ća yana fita. Afalonsa ya isake Abdallah da Anwar wai sunzo dubashi, ya zauna suka gaisa, da tambayarsa ya jiki??, ya ce, "da sau'ki sosai, Anwar ya ce, "abi wai ina abla??. Tana ─Ćaki tana barci, barci kuma yaya?, tun yanzu ko itama batada lafiyarne??, Nawaf ya girgiza kai yana hararar Abdallah, sai ba'ada lafiya ake kwanciyar wuri, kunga saida safe kutashi ku tafi.. Anwar ya shagwa6e fuska kai abi hirafa mukazo muku, kuma saika koremu. A'a niba kirarku nakeba, kuje gobe idan ALLAH yakaimu kwazo hirar nima zuwa zanyi na kwanta, badan sunsoba suka mi'ke kowa yana zum'bura baki. Nawaf yarufe 'kofar yakashe komai yanufi ─Ćakinsa,, wani irin farincikine ke ─Ćawainiya dashi, ya 'karasa kangadon ya zauna kusada fuskar yasmeen, ya tsura mata fararen idanunsa tanata barcinta hankali kwance, ahankali numfashinta yake fita, ta cure waje ─Ćaya kamar ─Ća acikin uwarsa. Nawaf yay murmushi yana shafa sumar kanta, data bazu akan filo har saman fuskarta, yasaka ─Ćanyatsa ─Ćaya ya janye wasu gashi dasuka rufe mata fuska, ahankali yafurta ALLAH yay miki albarka yabarmu tare har abada, ALLAH yabamu 'ya'ya masu 'kyawawan halayenki, yadu'ka ya sumbaci goshinta, tasaki wani lallausan murmushi tamkar idonta biyu. Shima murmushin yasaki, yami'ke yacanja kayansa zuwa nabarci bayan yagama zuba sambatunsa, da zazzagawa yasmeen kalamn 'kauna batareda tasaniba. Gadon yahawo ya cire mata bargon sannan ya canja mata rigar wankan zuwa ta barci, yay musu addu'a tareda rungume matarsa suka lula duniyar barci. Da asuba tarigashi tashi, dan haka ta sulale zuwa ─Ćakinta, acan tayi sallah takoma barci harda kulle 'kofa. Fitarta babu da─Ćewa Nawaf yatashi, ya laluba bata nan, saiya mi'ke yana murmushi, shima alwala yayi yafice masallaci, koda yadawo saiya nufi ─Ćakin yasmeen, amma 'kofar arufe, ─Ćakainsa ya wuce yakwanta shima...............✍­čĆ╗ Kuyi ha'kuri yaudai babu yawa ina busy ne. ©2017 ­čĺŚbilyn Abdul­čĺŚ ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺŚluv u oll my fan's­čśś­čĺŚ [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗47 & 48 .....Sai wajen sha─Ćaya suka tashi, dan zan iya cewa kusan lokaci ─Ćaya suka tashi, yasmeen jinta take wani fayau kamar isaka zata ─Ćauketa, yanzuma saida ta'kara shiga ruwan zafi, tagasa jikinta tayi wanka, bawata kwalliya tayiba fauda kawai tashafa sama2 sai kwalli, tasaka siket da riga na atanfa, tana son fita gaidasu momcy amma tanajin kunya, bakuma taso ta ha─Ću da Nawaf, takoma bakin gado ta zauna shiru, maganganu takeji 'kasa2 afalo, tami'ke ahankali tafito, dai dai nan Nawaf shima yafito sanye cikin farar shadda ─Ćinkin zamani, kallo ─Ćaya tayi masa ta ─Ćauke kai, su ladidi suka rissana suna gaishesu, kusan atare suka amsa. Yasmeen ta ce, "sannunku da 'ko'kari ladidi harkun gyara waje haka??, talatu ta ce, "ai tun ─Ćazuma mukayi hajiya yanzuma abincine momy tasamu mu kawo muku. ayya to sannunku da 'ko'kari kunji, ALLAH yabiyaku ya baku miji nagari. Sukace ameen suna dariya, dan sunajin da─Ćin addu'arta. Bayan fitarsu tawuce kichin batareda ta kalli ko'inda Nawaf yake zauneba, binta yayi da kallo harta shige, tafiyarta ta canja, gsky tabashi tausayi, shima saidaga baya yagane yayi 6arna baikuma tausayamata ba, to asannan idanunsa yarufe baya tana komai, harta fito yana zancen zuci. Shayi taha─Ća masa da sauran kayan break ─Ćin, tazo gabansa ta ajiye saman tebir─Ćin tsakkiyar falon, dan tasan baya cin abinci a dinning, tagama jerewa takoma gefe tazauna da kofin shayi ahannunta batareda tayi masa maganaba. Shikuma sai binta yake da kallo kamar yau ya fara ganinta, ahankali ya furta xarah!, wani zuuuuuuu yasmeen taji acikin kanta, bakowa yake kiranta da ainahin sunantaba fateema barema xarah, saitaji sunan wani iri kamar banataba kokuma wani (SABON AL'AMARI) sabon littafina mai zuwa insha ALLAHU. Jin tayi shiru yakuma fa─Ćin xarah!!, wannan karon har tsigar jikinta saida ta tashi, dan saida yaja sunan, ta ─Ćago manyan idanunta tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, ta kauda idonta daga kallonsa ta ce, "ina saurarenka. Ya gyara zamansa har yanzu idonsa yana kanta, ya ce, "zonan kiji mana, batareda ta kalleshiba ta ce, "kafa─Ća ahaka mana aii inajinka, yakai hannu yana shafa gemunsa tareda kwantar da bayansa jikin kujera, ya ce, "plz kizo kici abinci". Saida ta kalli kofin shayin dake hannunta sannan ta ce, "bagashi ina shaba. Shayi aiba abinci bane xarah, ana shanshine kawai dan hanji ya warware, saida ta─Ćan ta6e baki sannan ta ce, "karka damu nikam ya isheni, tasowa yayi yanufo inda take danyaga magana bazata yimasaba, ya zauna kusada ita sosai, saita matsa, ya ce, "tofa fancy face guduna kikeyi kuma??. Ta ha─Ćiye shayin data kur6a sannan ta ce, "ai mugu abin gudune, ya─Ćan zaro ido nine mugun??, tami'ke tsaye tana fa─Ćin kaima shaidane aii, nikam saidai nabawa wasu labarin muguntarka, tana gama fa─Ća tashige bedroom tarufe. Yabita da kallo yana murmushi lallai yarinya kina nufin ba'azo 'karsheba kenan?? Aii dolene kiyi ha'kuri dan nariga nayi winning game ─Ćin, kekuma kinada game over, result kaiwai nake jira, kujerar daya taso yakoma yahau cin abincinsa. Bayan ya kammla ya gyara wajen, yanason zuwa gaida su momcy yana tsoron ha─Ćuwarsa da papa, yasan momcy tanada saurin fushi amma tanada saurin sauka, amma papa sai a hankali, yanzu yana zuwa zai hau kansa da fa─Ća ALLAH ne kawai zai kwacesa, kamar daga sama yaji sallamar mas'ud, ya amsa yana fa─Ćin bismillah dama gunka zani ─Ćan ha─Ći, mas'ud dake shigowa ya ce, "─Ćan ha─Ći ko ─Ćan fa─Ćar gsky, Ameena ma ta shigo, Nawaf ya ce, "ALLAH yasoka harda Ameena dasai ka yabawa aya za'kinta. Mas'ud da ameena suka zauna suna dariya, mas'ud ya ce, "malam mika isa kamin nidai gsky nafa─Ća aii, babu wani gsky malam kazo kawai kayimin ha─Ći awajen su momcy, yanzu haka tsoron zuwa gaida papa nakeyi. Hhhhh gay kace kotu zaka shiga babu lauya kawai,, Nawaf suka gama gaisawa da ameena sannan ya ce, "aiko maga takaddama babu, suka tuntsire da dariya su duka. Yasmeen tabu─Će ─Ćaki tafito danjin an ambaci sunan Ameena, cikin farin ciki ta rungume Ameena saidai fuskarta tana nuna kamar batajin da─Ći, Ameena ta ce, "yar uwa ykk, lfy lou 'yar uwa ya 'karfin jikinki??, Alhmdllh, aini sainaga kema kamar bakida lafiya?, saida ta kalli Nawaf sannan ta ce, " 'kalau nake sister mikika ganine??, ba komai nagankine fayau. Mas'ud yakali Nawaf kallon tuhuma, da ido yay masa magana wai lafiya, Nawaf ya datsa hannunsa saman ─Ćayan tafin hannunsa Alamar yagama aiki, ido mas'ud yazaro ya ce, "kai haba??. Nawaf yay wata 'yar dariya yana fa─Ćin angaya maka nina wasane, am winning wlhy. Yasmeen duk tana kallon zancen kurman dasukeyi, dan haka suna ha─Ća ido da Nawaf ta harareshi, yay ─Ćan murmushi yana shafa sumar kansa, tami'ke takawo musu ruwa da lemu, saida tagama basu sannan takama hannun Ameena suka shige bedroom, mas'ud ya ce, "za'ayi gulmarmu ne??, Ameena tajuyo tana fa─Ćin idan kunsan kunyi abin gulmar ba. Nawaf ya─Ćago daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, mutumina kaima kasani zata gumtsa matane kawai, mas'ud yay dariya amma kaimafa ─Ćan iskane, tokaida bakada lafiyama ina kaga 'karfi. To sarkin 'yanson gulma ina ruwanka, nida wajenkama zani samo mata magani saikuma naga momcy tabata wani, amma kamarfa bai mata aikiba, naga tana tafiya bayanda tasaba ba. Kai ─Ćan duniya kana nufin har momcy tasani?,, kabari kawai nima wlhy banso hakanba, amma tazo ta ritsani.. Hhhhh lallai kacika mara kunya kuwa Alhaji,, Nawaf ya harareshi, nida kai a tantance mara kunya, jiyafa inajinka sama2 kana koro rashin kunya,, hhhh aini akan aikina nake ehe. Ummmm lallai kam su aiki manya.... Suma su yasmeen ana 'kuryar ─Ćaki itada tata aminiyar, Ameena ta ce, "yasmeen mike damunkine wai??, yasmeen tayi kwalkwal da idanu tana shirin yin kuka, cikin rawar murya ta ce, "Ameena mugunnan yasameni abanza batareda yafara sonaba kamar yanda muka shirya dake. Ameena tazaro idanu kai sis... garin yaya hakan tafarune?, yasmeen tafa─Ća mata yanda sukayi da umma jiya, ta─Ćora dafa─Ćin dagafa bashi ha'kuri yay min fa─Će, dan nidai fa─Će zan kira wannan wlhy. Ameena tayi dariya A'a babu wani fa─Će, mutum da matarsa sai ace yayi fa─Će, kice 'yar uwa angirma,, yasmeen ta harareta kin ganki ko zaki fara. Ameena tadafata tana dariya yiha'kuri amarsu, haba shiyyasa naga Nawaf yanata fara'a ga 'kyallin angwanci yanayi. Harrarta yasmeen tasakeyi, tana kaimata duka da filo, itakuma Ameena tana tuntsura dariya dabata ha'kuri, tari'ke filon tana sassauta dariyarta, kinga yi ha'kuri na daina, yanzudai ya ake cikine??. Yasmeen ta ce, "ai saina garashi nima, dan bazai shani abanzaba, duk muguntar dayayimin saina rama,, A'a yasmeen kawai kishare, kinga ko ada kema kina masa rashin kunya, kinga kenan kowa yana ta6a kowa, kawai ki ringumi mijinki ku zauna lafiya, fatanmu yanzu kuma muga sakamako kawai, kayan harka na nan zan aiko haleematu takawo miki. Cikin rashin fahimta yasmeen ta ce, "miye kuma kayan harka??, saida ameena tayi 'yar dariya sannan ta zayyane mata komai, tab ALLAH yakiyaye yasmeen tafa─Ća, ni nasha wani abu, kina ganin ba'kar wahalar danasha hannun mugunnan jiya, ke kobansha wahalaba babu abinda zansha inma gaya miki gsky, kawai saina zauna nayita ─Ćirkar magani batareda ciwoba, 'katon banza yayta shan romo yana raina mini hankali ko,, aii badan wannan nazo duniyaba 'yammata. Oh oh yarinya zaki shane, ina zaune zakizomin da zancen, idan ALLAH yabaki fitinannen miji irin mas'ud wlhy dole kisha, kuma ina nan dake zaki bani labarine. Baki yasmeen ta ta6e ke nifa bazan zauna yamaidani wata kasar takawarsaba,, dan haka kima daina saran zan sakko wataran. ­čśé'yammata kenan mudai 'yan kallone, yasmeen ta ce, "uhmmmm keni mubar wannan zance kitso najeson yi yaza'ayine?, wake miki kitso?. Uhmmmm wata yarinyace a 'kasan layinnan, idan kin shirya sainasa su halimatu su kawo miki ita, to shikenan amma kinsan halimatu bata zuwa gidannan saboda momcy ko??. Hhhh ke bar 'yar iska amma ai batajin kunyar yin zancen Abdallah gaban mami ko?. A'a shima ai hakan take, ko agaban papa labarin masoyiyarsa yake, ranar inaji modebbo yana masa masifa wai bashida kunya. Tofa kaji manya su kunyar garesu?, 'k wai kema modebbon kike cemasane??, yasmeen ta ta6e baki keni duk sunan dayazo min nasa fa─Ća nakeyi wlhy, A 'yammata yakama acanja masa suna. Yasmeen ta ce, "k bayanzuba saiya jigatu sannan, dan idan nabarsa haka yaga lagona. Hummm yarinya kidaibi ahankali, mazan nan sunada hanyoyin maganinmu kala2, danhaka atafi a slowly.. Suka tuntsure da dariya harda tafawa. Nawaf yaturo 'kofar yashigo da sallama, Ameena ce kawai ta amsa masa, ya ce, "masu hira bari muje masallaci, kuma kutashi kuyi sallah. Ameena ta ce, "to, saikun dawo, harya kai 'kofa saikuma yadawo, yadu'ko ya sumbaci kumatun yasmeen, dasauri ta─Ćago tana kallonsa saiya ─Ćaga mata gira yana murmushi ya fice. Ameena tayi dariya tana fa─Ćin soyayya ruwan zuma, 'yar uwa kibada kai kaiwai bori ya hau, tunda kuduka kun kamu, harararta yasmeen tayi tashige bayi domin yo alwala. Ameena taci gaba da dariyarta tana fa─Ćin anaso ana kaiwa kasuwa. Bayan sun idar da sallah suka dawo falo, abincin dasu talatu suka kawo yasmeen ta jera musu akan daining. Suma su Nawaf bayan sun dawo daga sallah wajensu momcy sukaje suka gaishesu, zuciyar Nawaf tanata dukan uku2, amma abin mamaki papa baimasa fa─Ćanba, yasan saboda suna tareda mas'udne shiyyasa ya 'kyaleshi. Yasmeen ta kalli Ameena, wlhy 'yar uwa inason zuwa gaidasu momcy amma inajin kunya, wannan gay ─Ćin dukshi yaja min wlhy, saitaji Nawaf ya ce, "zomuje narakaki tunda nine naja miki. Dasauri suka juyo inda maganar tasa take, ashe tun ─Ĺazu sun shugo suna tsayene kawai suna kallonsu yasmeen. Su mas'ud suka 'karaso suka zauna, yasmeen ta zuba musu abincin amma ta'ki yadda su ha─Ća ido da Nawaf, ta turama kowa gabansa, ita kuma tazuba ─Ćan ka─Ćan, Nawaf ya kalleta xarah wannan abincin fa??, ta ce, "kamar yaya??, yajawo kujerarsa kusada ita batareda yayi maganaba, yabu─Će kulan abincin ya 'kara mata, da sauri ta ce, "wazaici wannan abincin??. Ke mana, ko kina nufin zancigaba da barinki da yunwa? Tun jiya rabonki dacin abincifa, gama magani nan mas'ud yakawo miki, idan kin gama saiki she. , ta shagwa6e fuska nifa lafiyata 'kalau, Nawaf ya murmusa nima nasan lafiyarki 'kalau fancy face, saidai yanada 'kyau kisha maganin dan tafiyarki tadawo dai2... ya 'kare maganar ahankali yandasu Ameena bazasujiba. Ya ─Ćauki cokalin ya ─Ćibi abinci yakai bakinta, ta kauda kai gefe tana fa─Ćin kabari zanci dakaina, A'a ban yardaba, ta ce, "ALLAH zanci dakaina. To naji kar6i wannan saina barki kici dakanki ─Ćin, bataso suyita ja'inja agabansu mas'ud shiyyasa ta kar6a, yawani kashe mata ido ─Ćaya wanda har murmushi yanemi su6uce mata amma saita dake, haka taita tura abincin badan yana mata da─Ćiba, su Nawaf suna hirarsu amma ita tayi shiru abinta, bayan sun kammla suka dawo falo suna hirarsu. Sai bayan la'asar su ameena suka tafi gida, dan mas'ud yanada aikin dare yau, tunda suka tafi yasmeen taje wajensu momcy tayi zamanta dukda ─Ćunbin kunyar momcy datakeji, shima Nawaf bai dawoba sai bayan isha'i, shima 6angarensu momcy yanufa acan ya tararda yasmeen suna hira itadasu Anwar. Ya zauna suka gaisa da momcy, su Anwar suka gaisheshi, sunanan zaune shi yana latsa waya sukuma suna hira, soyake su tafi kafin papa ya ritsashi amma yarasa yanda zaima yasmeen maga, yana zancen zuci sai sukaji sallamar papa. Yashigo falon kowa ya rissina yana gaisheshi, ya amsa yana zama, momcy takawo masa ruwa yasha, yami'ke yana fa─Ćin modebbo zonan, jikin Nawaf asanyaye yabi papa ─Ćakinsa, afalo suka yada zango, yasmeen yazauna 'kasa papa yana saman kujera. Papa ya ce, "modebbo dama abinda kake aikatawa kenan ban saniba??, Nawaf ya─Ćago fararen idanuwansa yana kallon papa, cikin raunin murya ya ce, "papa miya faru??, cikin fa─Ća papa ya ce, "o, bakasanma miya faruba ko??, papa yashiga yimasa fa─Ća tamkar zai dakesa, ta inda yake shiga batanan yake fitaba, saida yaymasa tatas sannan ya ce, "ni tashi kabani waje mutumin banza. Nawaf ya ce, "kayi ha'kuri papa na amsa laifina amma insha ALLAHU hakan bazata sake faruwaba, kuma mun daidaita itama nabata ha'kuri. Papa ya ce, "wannan kuma kaika sani, idan kabari ta su6uce maka aikaika jiwo baniba, tashi kabani guri nace. Nawaf yami'ke yafito dama yasan papa bazai saurareshiba a yau saiya huce. Yafito falo wajensu yasmeen fuskarsa babu walwala ya ce, "yasmeen tashi mutafi,, ta ─Ćaure fuska katafi ni anan zan kwanafa,, shuru yay yana kallonta, yazata momcy zata mata magana amma saiyaji tayi shiru bata samusu bakiba, ya daure ya ce, "bangane anan zaki kwanaba?, gidankifa?, yasmeen tayi kwalkwal da ido kamar zatayi kuka ta ce, "nidai anan zan kwana kawai. Jiki asanyaye yafice batareda ya'kara maganaba bare ya ce musu "saida safe", itako mom 'kala batace musuba, daga 'karshema saita tashi ta tafi ─Ćakin papa. Nawaf yafa─Ća saman gado yana maida numfashi, yakula mitin aka ha─Ća saboda shi kenan,, zaikuwa basu mamaki, zai nunawa yasmeen shima bai damu da itaba. Itako tayi kwanciyarta acan abinta, shikam haka yayta zarya tsakanin falo da bedroom, yazata daga baya momcy zata saka yasmeen ta taho, amma shiru kamar an aiki bawa garinsu, daga 'karshe yaha'kura yakwanta. Haka sukaita 'yar wasan 6uya shida yasmeen har tsawon kwana hu─Ću, tayi zamanta a ─Ćakin momcy, kotana falo dataji sallamarsa saita koma ─Ćaki ta kulle, tun Nawaf yana ─Ćaukar abin wasa har yafara bashi haushi, yakoma bashi tsoro, dan akowace da'ki'ka son yasmeen 'karuwa yake azuciyarsa, gashi kuma ta hanashi damar dazai nuna mata ainahin gsky sa, momcy kuma tayi kunnen uwar shegu dasu, ta'ki tayima yasmeen magana ko ka─Ćan, dukda tana kallon zaman doya da manjan dasukeyi, amma saita maida kanta makauniya. Itama yasmeen a 6angarenta tana jigatuwa da horon datakemusu dan harda kanta take horawa, kewar Nawaf dukta gallabi zuciyarta, idan yashigo haka zatayita le 'kensa ta kafar makulli, dukta rame akwana hu─Ću, sai wani fari datayi fauu. Amma haka zata cigaba da daurewa har komai ya daidaita. Yau dawuri mutan gidan suka kwanta sakamakon gajiya dasukayi, dansunje wani biki, kowa yana ─Ćakinsa kwance wasuma harsunyi barci irinsu yasmeen, Nawaf kam yanacan yakasa rintsawa, ya bu─Će wardrobe ya ─Ćakko kayan daya cire, wani mukulli ya─Ćakko acikin aljuhun rigarsa yakallesa yay murmushi, tirare ya 'kara fesama jikinsa, yasaka silifas yafice bayan yakashe komai. Ahankali yatura 'kofa yashiga 6angaren momcy ta 'kofar baya, yashgo ta kichin dan ba'a kulleta dama. Falon babu kowa anma kashe fitilar, dagaji kasan kowa yayi barci, Nawaf yay murmushin mugunta, yasaka key ─Ćin yabu─Će ─Ćakin momcy, yamaida yakulle ahankali, fitilar ─Ćakin akashe take, danhaka yataka ahankali zuwa bakin gadon, wayarsa ya danna ya haska yasmeen dake kwance ta 6ararraje tana sharar barci agadon momcy, yasaki wani 'kayataccen murmushi, ya─Ćaga bargon ahankali yashige, tareda rungume yasmeen zuwa jikinsa. Afirgice tafarka, tako bu─Će baki zatayi ihu, Nawaf yay saurin toshe mata baki da hannunsa ─Ćaya, cikin kunnenta ya ce, "k karki taramin mutane ninefa...................✍­čĆ╗ Tofa 'ka'karaka 'ka'ka, kudai biyoni kawai­čśâ­čĹî­čĆ╗ ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś ­čĺô [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺö Page­čĹë­čĆ╗49 & 50 .....Iya 'karfinta ta tureshi, tana fa─Ćin bangane kaineba?, miya kawoka nan??. Nawaf ya kunna fitilar dake saman durowar gefen gado haske ya gauraye ─Ćakin, ya maida kallonsa ga yasmeen data koma can nesa dashi, ya─Ćan murmusa sannan yamatso kusada ita, ta ce, "wai miye haka?, zakazo katasheni ina barcina. Ya kamo hannunta ya rumtse anasa, batayi yun'kurin hanashiba dan tayi kewarsa itama, cikin taushin murya ya ce, "fancy face kinso ki tashine kawai, kuma mutum da matarsa ace miyasa yazo wajenta??. Yasmeen ta ta6e baki to amma kasan bai daceba ko?, a ─Ćakin mom mukefa, shima bakin yata6e yana fa─Ćin ainasan a ─Ćakin mom ─Ćin muke bake kika kawomuba, ni kinga zuwa nayima kimin tausa wlhy jikina sai ciwo yake wannan bikin da papa yakwashemu mukaje. Yasmeen ta─Ćan zaro idanu lafiyarka kuwa malam??, tafa─Ća tana fisge hannunta daga nasa,, yakuma kamo hannun yana wani 'kasa2 da idanu, lafiyarce takawo haka xarah, idan ba keba wazance yay mini tausa?. Yasmeen tazame takwanta, saida taja bargo sannan ta ce, "nima ─Ćin bayimaka zanyiba kaini bamma iya wata tausaba, idan ka fita karufo mini ─Ćakin, ta kwantar da kanta saman filo. Okey karki damu 'yammata, tashi yay kamar gsk ya kashe fitila, ya─Ćaga bargon yashigo, da sauri yasmeen ta yun'kura zata tashi, yay saurin ri'kota ya matse a 'kirjinsa, tafara 'ko'karin kwacewa amma takasa. Yasaki sassanyar dariya acikin kunnenta, yasmeen ta rin'ka ture fuskarsa, ya kamo hannun ya ri'ke, yana fa─Ćin haba xarah na, kina nufin haka zan cigaba da rayuwa ni ka─Ĺai, duk wannan 'kamshin dakike zubawa ni bazan sha'kesaba naji da─Ći. Ninefa modibbonki mai sonki da 'kaunarki, i luv u my zarah, kece farincikin Nawaf modebbo.........dasauri yasmeen ta katseshi bayan wani da─Ći da farinciki sun gauraye dukan sassan jikinta, ta ce, "humm malam karka cikani da surutu kana yaudarar kankane kawai, kada kayi tunanin zaka iya wasa da hankalina mana.......da sauri yarufe mata baki da lallausan hannunsa, karki damu, bata baki kawai ake bayyana so ba akwai hanyoyi dayawa, yashiga aika mata sakwanni, itakuma tana tureshi tana masifa, dayaga zata dameshi da hayaniya harma wani yaji saiya ha─Će bakinsa da nata. ­čĆâ­čĆ╗dagudu nafito­čśť Humm su Nawaf manyan 'yan duniya, koda ya daidaita saiya shiga lallashinta da fa─Ća mata kalamai masu da─Ći, ya'kara jaddada mata iri son dayake mata, yasmeen sai hawayen da─Ći take zubarwa, jitake tamkar ta rungumeshi taha─Ća masa harda 'kyautar kiss to amma bazata nuna masa tama yarda dashiba, ta tureshi ta mirgina gefe tana cije la66a dan itafa yauma tanajin ─Ćan zafi, tashige bayi, shikuma yana binta da kallo yana murmushi, ahankali ya lumshe fararen idanunsa masu yalwar gashi, afili ya furta 'yammata ka─Ćan yarage kizo hannu, shima saiya sakko yanufi bayin. Yamur─Ća kofar ahankali yashiga, dasauri yasmeen tabu─Će ido tana kallon 'kofar, tami'ke zummbur tana 'kudundune jikinta, cikin rawar murya ta ce, "wai miye hakane??, yafara zame kayan jikinsa batareda ya tanka mataba, taisaurin dur'kusawa tarufe idonta da hannayenta. Yagama cire kayansa ya'karaso inda take, ruwa ya ─Ćiba yazuba mata, ta─Ćago da sauri zata yimasa kwakwazo yasa hannu yarufe bakin, "k wai lafiyarki kuwa??, darenefa kuma su papa zasu iya jinki ki kula mana. Harara ta watsa masa tana zum6ura baki, ya murmusa kai xarah kina 'kyau da harara plz kicigaba karki daina, shiru taimasa, shikuma yafara 'ko'karin yimata wanka, tanata kauce2 dahaka aka gama wankan suka fito, badan tasoba tayarda suka kwanta gado ─Ćaya babu da─Ćewa barci yay gaba dasu. Da Asuba koda yasmeen ta tashi saitaga babu Nawaf, tajawo filon daya kwanta ta rungume tsam a'kirjinta tana murmushi, afili ta ce, "sarkin wayo, wato danayi barci saika gudu ko??, karka damu lokaci yana zuwa dazan baka kulawa ta musamman wadda zakayi alfahari dani ina sonka mijina, abinda kaiminne yasa nakasa fahimtarka, nazata nika─Ćaice nake dakon soyayyarka ashe kaima ka kamu, ta lumshe ido tana murmushi, saidatiji ana 'ko'karin shiga sallah sannan ta tashi. Shikam Nawaf tunda yaga tayi barci ya lalla6a yafice dan bayaso su momcy su gansa da safe, musamman ma papa dayake fita sallar asuba dawuri kuma hardasu Anwar. Tunda suka tashi yau momcy take bin yasmeen da kallon mamaki, dan duk wanda yaganta yasan tana cikin farinciki, sai wata walwala takeyi, suna cikin yin break Nawaf yashigo, ya rissina yana gaida momcy sannan ya haye saman tebir ─Ćin shima, su Anwar suka gaisheshi, yasmeen ma ta gaisheshi, ya ce, "k wai bazaki bani abinci bane??, yasmeen tafara zuba masa tana zum6ura baki,, suna ha─Ća ido ya kannemata ido ─Ćaya, da sauri ta kauda kai. Nawaf ya ce, "momcy papa fa?, momcy ta ce, "yafita aiki modebbo,, da wuri haka momcy?, eh wai yanada aikine kuma shari'ar mai zafice yace,, tofa ALLAH ya yayyafa mata ruwan sanyi, yakamatama papa ya huta kahanan yayi ritaya kawai. Gsky ne wlhy abi, Abdallah yafa─Ća, momcy ta ce, "to saiku tayashi da addu'ar fatan alkairi, sukace to momcy ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi. Suka cigaba dacin abincinsu, duk ─Ćagowar da yasmeen zatayi sai sun ha─Ća ido da Nawaf, momcy tana kallonsu, azuciyarta ta ce, "kwadai gama gulmarku yara, nidai babu abinda zance muku. Dahaka suka gama cin abinci, Nawaf ya ce, "zaije wajen mas'ud, momcy ta ce, "to adawo lafiya. Fitarsa babu da─Ćewa halimatu tazo itada mai kitso, tunda suka shigo taketa kasa da kai, momcy ta ce, "ohni ─Ćiyata Abdallah yaraba mana zuminci, yanzu bakison zuwa gidannan ko??, ta tsugunna tana gaida momcy kai a'kasa, yasmeen ta ce, "momcy barta kwanannan zamu yayibota tadawo gidanma ganmba ─Ĺaya, inaga haka za'ayi yasmeen. Itadai halimatu sai murmushi take kai asunkuye, Abdallah yana gefe ya tsura mata idanu, ta ce, "aunty gamai kitsonnan aunty ameena ta ce, "nakawo miki ita. To 'kanwata ngd, amma yau anan zaki wuni koh?, da sauri ta girgiza kai tana murmushi, momcy ta ce, "aiko yau agidannan zaki wuni, yasmeen kuje 6angarenku ai dole ta sake dai acan, yasmeen ta ce, "to momy. Tashi sukai zuwa 6angarensu yasmeen bayanda halimatu zatayi dole ta amence zata wuni, suna tafiya Abdallah ya faki idon momcy yatake musu baya. Momcy ta ce, "oni ALLAH ya shirya minkai Abdallah. Na ce, "ameeeeeen. Yasmeen tazauna gaban mai kitso tana fa─Ćin manya za'ayi saratu. Halimatu ta ce, "kai aunty wannan gashin naki ai bazaiyi manyan kitsoba, wai miyasa masu gashi basusan 'kananun 'kitsone, aigara ki barsa atsefe ma. Yasmeen tashafa gashinta, wlhy nagaji dazama dashi haka, dole kullum saika gyara, azuciyarta ta ce, "ga wannan fitinatun yanasani ji'ka kai kusan kullum. Saratu ta ce, "to wanne iri za'ayi, eh yimini shikku banason yasauka abayana zai ringa damuna, shikku kam dana ─Ćaure shikenan, okey to bari mugani. Abdallah yashigo da sallama, suka amsa masa suduka, yasmeen ta ─Ćora da fa─Ćin to bita zaizai harka taho. Abdallah ya zauna yana dariya kai aunty keda kanki, koda yakema ai wajenku na koya keda yaya, dan soyayyarku abin koyi ce, ─Ĺazufa ina kallonsa yana...........yasmeen ta zaro idanu yana mi??, habawa kabada himma yajika wlhy. Abdallah ya ri'ke baki, tab danaga ta kaina, dan saiyayi kamar ya cinyeni. Dariya suka saka suduka, halimatu ta ce, "dama ya ha─Ća maka da duka aii........ta 'kare maganar da rufe baki­čÖŐ, Abdallah yakoma kusada ita yazauna haba my luv ke kinyarda azaneni, yasmeen ta ce, "harma tabada gudummawar bulala kuwa.......ta kare maganar ahankali dan shigowar Nawaf. Ya watsama Abdallah harara, Abdallah yay kasa da kai yana fa─Ćin kai malam kana soyewarka nikam baxaka hananiba nima, azuciya yake maganar, halimatu kuma da saratu mai kitso suka fara gaisheshi, ya amsa yana shiga bedroom. Itadai yasmeen batace 'kalaba saima ta maida hankalinta wajen kallon hotuna awayar Abdallah daya ─Ćakko jiya awajen biki. Abdallah ya mi'ke yana fa─Ćin aunty bani wayata na kama gabana, idan boss yafita saina dawo. Yakar6a yafice, sukuma suna dariya, yesmeen ta ce, "ALLAH yasa yajika. Suna cikin dariya Nawaf yale'ko yana kwala kiran Abdallah!!, yasmeen ta ce, "yafitafa tun ─Ćazu, baice komaiba yakoma cikin ─Ćakin, kwanciyarsa yayi yahau barci. Sukuma suna kitso suna hirarsu da dariya, ammafa kitson yana bada ma'ana, dan yarinyar ta"iya sosai. Sai wajen 'karfe ─Ćaya Nawaf yafito cikin 'kananun kaya yasake wani wankan, shikansa kitson ya bala'in burgeshi amma saiya basar saboda basu ka─Ćai bane, ya─Ćan kalli yasmeen ya ce, "kutashi kuyi sallah tukunna lokaci yayi, nima nawuce masallaci. To adawo lafiya yasmeen tafa─Ća, su halimatuma sukace haka Nawaf ya ce, "halimatu kinaso kema Abdallah yamaidake mara kunya kamar shi ko??, kan halimatu a'kasa ta ce, "A'a yaya. To miyasa kike biye masa, ko kinaso yahure miki kunne ki'ki karatu kamarshi??, nanma kai tagirgiza,, to indai bakiso hakan tafaru kidaina biye masa, kibari harsai kin kammala karatunki kinji ko!!, to yaya insha ALLAH ngd sosai, yafice yana fa─Ćin karki damu saina dawo. Bayan fitarsa yasmeen ta ce, "oh ke halimatu tamkar zaki iya, halimatu tayi dariya, zan iya mana aunty, nima saida na ce, "masa mudaina nunawa harsai mun kammala karatunmu, shine ya ce, "wai dazafi zafi ake dukan 'karfe. Yasmeen tayi dariya, iko dai da gskyr sa, bagashi yanzu kowa yasaniba, tafa─Ća tana tashi, bayan sunyi sallah suka dawo kan aikinsu, su ladidi suka kawo musu abincin rana. Sukaci suka 'koshi sannan aka koma aiki, sai wajen karfe uku aka gama, suka koma 6angaren momcy, alkairi mai yawa momcy tayima saratu mai kitso sannan ta tafi, halimatu kuwa sai dare. Bayan sallar magriba momcy take cewa idan ALLAH yakaimu gobe zasuje abuja wajen wata 'kawarta, kuma harda su Abdallah. Yasmeen ta ce, "mom nima zanje,, momcy ta ce, "to ki tambayi mijinki idan ya yarda saimu tafi kwana ─Ćayane xamuyi, yasmeen tayi shiru dan tana tunanin yanda za'ayi ta tambayeshi, momcy ta ce, "indai baki gaya masaba tom ke ka─Ćai zamu bari agidannan, zumbur yasmee ta mi'ke tanufi 6angarensu, momcy tayi murmushi kawai. Afalo ta iske Nawaf saman doguwar kujera kwance, hannunsa ri'ke da remote yana canja tashoshi, tayi tsaye abakin 'kofa tana kallonsa, yana ganinta ta gefen ido shima amma yay shiru kamar bai gantaba, takai tsawon minti bakwai awajen, Nawaf ya─Ćago ido yana kallonta, ahankali ya furta 'karaso mana. Tayi shiru kamar bazata zoba, sai kuma ta tako ahankali zuwa kusadashi, tayi yin'kurin zama a 'kasa, Nawaf yari'ko hannunta da sauri, no karki zauna a'kasa fancy face, tashi yayi zaune yajawota saman cinyarsa. Ta─Ćan ─Ćaga ido tana kallonsa da niyyar yin maga, ya watsa mata wani kallo dayasakata yin shiru, ta─Ćan lumshe idanunta ta bu─Će. Ya zame ─Ćankwalin kanta yana fa─Ćin woow!!! Xarah na, amma kitsonnan yayi miki 'kyau, yazame ribom─Ćin data ─Ćaure kitson dashi, kitson ya watsu ahannunsa, yakama jelar yana wasa da'ita, cikin kunnenta ya ce, "dolene nabiya mai kitsonnan na musamman. Yasmeen ta─Ćan ta6e baki, yakai hannu yana shafa la66anta kinsanfa banason ta6 e baki ko??, ko kinaso mukoma 'yar gidan jiyane?. Yasmeen tayi shiru dan ita tana neman hanyar dazata tanbayeshi zuwa abujane. Ya─Ćan girgizata ka─Ćan, ta─Ćago da sauri tana kallonsa, ya sumbaci goshinta yana fa─Ćin miye matsalar fancy face!, yasmeen ta lumshe idanu, idan nagaya maka zakamin maganinta, ya─Ćanyi jim sannan ya ce, "indai batafi 'karfinaba zanyi. Ta gyara zama ajikinsa tareda kwantar dakanta saman kirjinsa ahankali ya lumshe idanu tareda kara rungumota sosai,, ta ce, "dan ALLAH kabarni nabisu momcy abuja gobe idan ALLAH yakaimu. Da sauri Nawaf yabu─Će idanu, shifa azatonsa zata bashi hakurine tace kuma tana sonsa, amma saiyaji sa6anin haka, yayi shiru kamar baijitaba, ta─Ćan ─Ćago idanu tana kallonsa, suka tsurama juna idanu. Kallon juna suke cikeda so da 'kauna, ahankali Nawaf yafirta i luv u xarah, i luv u so very much ya rungumeta tsam a'kirjinsa yana hawaye,, cikin kunnenta ya ce, "plz & plz xarah, dan ALLAH kisoni, ki manta da abinda yafaru baya, mu ─Ćauka munyi kuskure, wlhy zarah ina tsananin 'kaunarki, tun farko kena fara so, tun aranda nafa ganinki akan titi cikin gosilo naji nakamu da 'kaunarki, nima kisoni xarah karkice ba'kya sona, idan kika furta haka akwai matsala. Ahankali yasmeen ta─Ćago tasaka hannuwanta tana sharema Nawaf hawaye, itama kukan takeyi, dan haka shima yasa hannu yana share mata nata, ta lumshe ido sanan ta ce, i luv u too my man!! nima ina 'kaunarka wlhy mijina, dama kaine nake kokwanton hakan daga gareka, plz kaci gaba da 'kaunata harmu koma ga ALLAH. Nawaf daketa faman murmushi yay saurin ha─Će bakinsa da nata, wata zazzafar sumba yake bata, itama saita bada kai bori yahau­čĹë­čĆ╗­čśť­čśťlol............✍­čĆ╗ ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś ­čĺô [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗51 & 52 .......Daga sumba aka koma soyayya, na ce, "wannan lamari bana kallo bane, bari nayi nanan. Saida komai yay dai2 nadawo falon, yasmeen sai 6oye fuska take wai ita kunya, yayinda Nawaf yake ri'ke da hannunta yana mata dariya, cikin shagwa6a ta ce, "ALLAH idan baka bariba zan ha─Ćaka da momcy, ­čÖŐyarufe baki yana fa─Ćin nabari, "k yanzu kina fa─Ćama momcy aizata 'kara baki mafakane, sorry na daina,, yasmeen tayi murmushi mafaka kuma kamar wata 'yar gudun hijira??. Nawaf ya ─Ćora kansa saman cinyarta yana dariya, eh mana gudun hijira kikayi harna kwana shidda,, amma ALLAH ya koromini ke. Hhhh malam aii yanzu zan koma inda nafito, tab zance kenan, ai yarinya kinzo kenan, keda ─Ćakin momcy saidai gaisuwa, ta waro ido habadai daga zuwa tambayar anguwa. Eh mana itama momcy zataji da─Ćin hakan, dama tayi miki wayone ta turoki kawai. Yasmeen tayi murmushi, toya maganar tafiyar zanje?, saida ya sumbaci tafin hannunta sannan ya ce, "kibarsu suyi tafiyarsu mukuma musha soyayyarmu ko??, ta─Ćan zum6uro baki gaba kai dan ALLAH kabarni ALLAH inason zuwa fa. Yatashi zaune, kinga kibarsu su tafi, mukuma dasun dawo saimu lula saudia muyo hutunmu acan ko babyna, yafa─Ća yana jan hancinta. Ta ce, "ALLAH kaima ka iya wayo, babu wani wayo fancy face gasky nafa─Ća, kinga tashi muje muyu wanka. Tare sukayi wankan, sannan sukayi sallar isha'i, bayan sun idar ta ce, "bari natafi saida safe, da sauri ya ri'keta "k 'yammata babufa inda zaki, ina bu'katar jin ─Ćumin matata, da lallausar fatarta ha─Ćeda sha'kar kamshin jikinta mai da─Ći, ta ce, "ALLAH inajin kunyar momcy, ─Ćaukarta yayi cak ya ─Ćora kan gado, babu wata kunya xarah na, zoki bama mijinki ─Ćumin jikinki, babu yanda zatayi dole ta ha'kura ta kwana anan, yaudai Nawaf ya zazzage mata sirrin zuciyarsa, harsukayi barci bai daina fidda sirrikan sonta dake kwance a zuciyarsaba, dan haka barci yay gaba dasu cikin farin ciki, irin wanda basu ta6a gamo dashiba.lol­čśť Da asuba ma suna idar da sallah suka koma gado, Nawaf yafara al'amura, cikin shagwa6a yasmeen ta ce, "plz kabarmu muyi barci, ya hura mata iska akunne, babu wani barci 'yammata, ta ce, "to mikakeso ayine?, ya ce, "kinfini sani, ta─Ćan lankwashe murya ALLAH saboda barci kaina har wani ─Ćan ciwo yake, da sauri ya rungumeta ayya sorry fancy face to muyi barci ki huta, ALLAH yay miki albarka kinji, yasmeen tayi murmushi tana fa─Ćin ameen, bayanta yayta shafawa da hura mata iska a kunnenta, babu da─Ćewa barci yay gaba da ita, Nawaf ya tsura ma face nata idanu, komai na yasmeen mai 'kyaune, dukda yafita fari amma tanada haske mai 'kayatarwa, yasa ─Ćan yatsansa yana zagayawa akan la66anta masu kalar pink, ya ALLAH kabarni da abar 'kyaunata ya firta ahankali, tareda rungumeta tsam shima barcin yay gaba dashi. Basu farkaba saida momcy ta kira wayar Nawaf, kusan atare suka tashi, jallabiya kawai yasaka, itakuma tasaka hijjab suka fito, a harabar gidan suka iskesu tsaytsaye, Nawaf ya ce, "momcy kuce harkun shiryama??. Momcy ta ce, "ehmana gashima zamu wuce tunda ka hana matarka zuwa, ya─Ćan sosa gefen wuyansa yana fa─Ćin ba haka bane momcy muma zamuje insha ALLAHU koba yauba. Momcy tayi murmushi to shikenan, mu bari muyi harama, sai jibi zamu dawo tareda papanku tunda yana can, gasu talatunan, lokaci2 yasmeen kiringa le'kowa kiga halin dasuke ciki kinji ko??, yasmeen ta ce, "to momy, ALLAH yatsare mana ku, yadawo mana daku lafiya. Amin momcy tafa─Ća tana shiga mota, su Anwar suka ─Ćaga musu hannu, suma suna ─Ĺaga musu harsuka fice daga get ─Ćin. Nawaf yajuyo wajen yasmeen yana murmushi, fancy face kozaki bisune?, yasmeen ta harareshi kafa─Ći haka tunda sun tafi, cak ya─Ćauketa suka nufi wajensu yana mata dariya, to bari na goge laifina, itama dariyar takeyi ta ce, "saidai ka goyani, ya direta 'kasa yana fa─Ćin wannan mai sau'kine, ya tsugunna ta haye, yami'ke yana dariya, amma kisani wannan goyon yanada tukuycifa. Ta ─Ćora kanta gefen kafa─Ćarsa, kai haba wane tukuyci kuma?, karka manta kayine dan lallashifa. Nawaf yay dariya yana tura 'kofar falonsu da 'kafa hakane kuma my xarah, saman gado ya sauketa yana wani fa─Ćin wash, kai ammafa kincika nauyi, a ido gaki siririya amma fa sai nauyin tsiya. Yasmeen ta zuro 'kafafunta tana dariya, haba my man abumma harda tsiya kuma, yari'ko hannunta babu wata tsiya sai gsky, ina zuwa haka??, tayi far da idanu zanje kichin nemawa habibina abinci ko. Ya kanne mata ido ─Ćaya tareda­čĹŹ­čĆ╗mata, ta sauka tana dariya. Tare suka ha─Ća break ─Ćin suka gyara ─Ćakinsu, su talatu suka gyara musu sauran guraren tsaf, dan danan gidan ya gauraye da 'kamshin turare gana dadda─Ćan abincin dasuka girka,, yaukam babu kunya tare sukai wanka kowa yay ma ─Ćan uwansa, suka fito kowa ya shirya, cikin 'kananun kaya,, Nawaf yabama yasmeen wasu fitunanun kaya cikin tsarabar dayay mata, daga Spain, ta ce, "woow!! Ammafa sun ha─Ću my man, ya ce, "da gsk??, ta kanne masa ido ─Ćaya tana fa─Ćin wlhy kuwa, ya ce, "ashe na iya za6e?, ta ce, "sosaima, aina kasiyo kayannan??, A Spain mana lokacin dakukaje jinyata, ta ce, "humm kace lokacin anajin haushina, amma harda tsaraba. Yay dariya kema aii sannan kinamin tashen rashin kunya, saidai ina ma'kale da sonki ko a sannan, yaja hannunta zomuje muyi break inajin yunwa. Ta ce, "wai yaushe kafara sonane??. Karki damu idan mungama zan baki labari. Suna cin abinci yana mata santi, itako tana 'kyal'kyata masa dariya da saka masa waugi, ya ce, "wai miki ─Ćaukeni?, kina zaton santi nake??, cikin dariya ta ce, "fa─Ći da wai ka 'kara da wayyo, kaima kasan santi kakeyi Alhaji, yay dariya, to idanma santin nakeyi toga akan abu biyu nakeyi. Yasmeen ta tsaya da dariyar datakeyi, to dami2 kenan??. Ya nunata fancy face ─Ćina mana da abincin fancy face, tayi dariya tana wani far da idanu to nagode abin 'kaunata. Ya lumshe idanu yana fa─Ćin i luv u fancy face,, ta ce, "luv u too my habibi. Hakadai sukaci abincin yana bata tana bashi harsuka 'koshi, suka dawo falo suka baje. Yasmeen ta ce, "to fa─Ća mini yaushe ka fara sona, saida ya kwanto da kansa saman cinyarta suna kallon idanun juna, tasa hannu cikin yalwatacciyar sumarsa tana masa susa, yafara lumshe idanu yana gyara kwanciya, cikin murya mai cike da shau'kin so ya ce, "idan na ce, "miki tun randa muka fara ha─Ćuwa harna jefa miki kwalin yogot ─Ĺin holladia zakisha mamaki. Ta ce, haba dai ban yardaba, ya murmusa, wato sanda muka iso cikin gosulo ─Ćin saina fara yima mas'ud Masifa akan miyasa ya ce, "mu biyo wannan titin bayan yasan yana ha─Ća gosulo. Shuru yay min saboda yana amsa waya, haushin hakan yasa na ─Ćauki yogot ─Ćin inasha, ─Ćagowar dazanyi sainayi tozali da 'kya'ky'kyawar yarinya tsaye tana hange2, wani shokin ne yaja kwakwalwata, kinyi bala'in tafiya da imanina saidai bansan yanda zan nuna miki hakanba banason kuma na fa─Ćama mas'ud nayi tsuntuwa, dan munsha tsokanar juna konace gardama akan soyayya shirmece kawai,, yakan cemini baka gamu da wadda tayi maka bane, nikuma na ce, "ai kona gamu bazanyiba, haka kullum muke akan gardama ─Ćaya, tokuma kwatsam ranar saigaki. Nasan idan har mukabar wajen bammiki maganaba ba lallai bazamusake ha─Ćuwa ba, tunda garin kano ba 'karamin gari bane, ina cikin sa'ka da kwancewa saidabara ta fa─Ćo mini, wani abokina yata6a fa─Ćamin daga fa─Ća suka fara da matarsa (prince salman mijin salma kenan, a novel ─Ćin ayusher muh'd NIDA PRINCE), to dana tuna haka sainace nima bari nagwada sa'ata, kawai sai kwakwalwata ta kawo mini wuta akan na jefeki da kwalin yogot ─Ćin nasan dole ki tanka,, bayan na jefeki sai abin yay matu'kar bani dariya yanda kika tsorata, to Kekuma saikikaji haushi harkika cemini w..............dasauri yasmeen ta rufe bakinsa dan ALLAH karka maimaita my man plzzzzzzzzzz!!. Yay murmushi to shikenan nabari, to bayan munyi fa─Ća agurin mas'ud yarabamu kowa yatafi, damukazo gida saina matsawa mas'ud akan yatayani nemanki amma saiya'ki, nashiga ru─Ćani alokacin dan banaso na rasaki gsky, ana cikin haka sai muka ha─Ću abinkin safwan ranar naji da─Ći mara musali, amma bai hanani takalarki fa─Ćaba, harma na ce, "marin dakikaimin zai zama fansar budurcinki,, hummm nafa─Ćane kawai danki tsorata, dan duk kamilar mace bata burin arabata da budurcinta bata hanyar aureba. To tundaga ranar ban sake jin labarinkiba, sabodake washe gari naje wajen walimar amma ke bakijeba,, yasmeen ta ce, "tsorone ya hanani, Nawaf yay dariya tareda jan hancinta ya ce, "matsoraciya kenan. To daga nanfa narasa hanyar dazan ganki,, sai ina gab da komawa Spain naganki keda ameena awani wajen hutawa, na ma'kale inda bazaku ganniba nashiga bin bayanku ayayin dazaku tafi gida, harsaida naga inda balarabe ya tsaya da mota, abin yabani mamaki danaga gidanku dakuma motar da aka ajiyeki, sai kawai najuya nakoma. Kwana biyu da faruwar haka nasa aka yimini bincike akanki, amma mas'ud bai saniba, babu abinda aka 6oyemin har tsakaninku dasu faisal, akwai abokina yana karatu a school ─Ćin su faisal a america, shinasa yaymin bincike akan faisal. Anan nagane cewa ─Ćan iskane manemin mata, harma ya lalata 'kanwar wani abokinsa dasuke zaune acan tare hisham kenan, amma baisaniba. Nine nasaka abokina ya gayama hisham, muka kuma kulla yazo Najeria domin yaga yarinyar da faisal zai aura yagano mana idan tana sonsa, dama suna gab da kammala karatunsu dan haka suna gamawa sukazo, idan baki mantaba aranda sukazo saida suka kalli wani wasanmu agidan, sunkuma rin'ka miki surutu marassa ma'an, hhhh duk sunayine dasu harbo jirginki. To bayan sunzo sun fa─Ća mana sai muka shirya yanda zamu rabaku, abinda muka turama faisal awaya baikai yazargekiba amma dayake jakine kuma badan ALLAH yake sonkiba saiya hau yazauna, har an ─Ćaura aurenku yaje yasakeki. Saidai kinsan wani abin mamaki??. Yasmeen ta girgiza kai. Nawaf yay dariya, wlhy bansan papa yaje ─Ćaurin aurenkiba bammasan angayyaceshiba, papa mutumne mai tausayi da kishin ─Ćan uwansa muslmi, hankalinsane yatashi yayinda faisal ya ce, "yasakeki abba ya yanke jiki yafa─Ći, shine kawai ya ce a─Ćaura auren da ─Ćansa. Bayan yadawo gida yakirani ya zayyana mini, hankalina yatashi danni zuciyata ke takeso, nagama shan wahalar rabaki da faisal da nufin bayan kamar wata ─Ćaya hankalinki ya kwanta sainaje na bayyana miki ina sonki, amma ga papa yayomini wata 6aran6arama, hankalina yatashi sosai nakuma shiga ru─Ćani, harna kasa ta6uka komai awasan danazo bugawa kasata. Kinsan abinda yasani farinciki?, yasmeen tagirgiza kai,, ya ka─Ćakai, randa mas'ud yakawoni gidanku ya ce, "nanne gidansu matata, nashiga ru─Ćani da farinciki da zumu─Ćin san ganin matar tawa, dan atarihinki da aka bani yanuna ku biyu aka haifa agidan,, hummm wayyo da─Ći abin farinciki wanda bazan ta6a mantawa dashiba shine lokacin danayi tozali dake naji kamar natashi nayita rawa amma saina dake dan banason kugane keda mas'ud. Yasmeen ta ri'ke baki "o, kai habibina amma shine harda mini mugunta aranar,, dama duk kaine kashirya wa─Ćannan abubuwan, amma danazo gidanka kake nuna kai bama kasona, tafa─Ća tana turo baki gaba. Yatashi zaune yana 'yar dariya, sorry xarah na, kemace dai kika kasa fahimtata, yakamata ki gane wani lokacin nakan kasa control ─Ćin kaina, harnakan fito da sirrin zuyata fili. Yasmeen tayi dariya aini ina ─Ćaukar hakan kawai amatsayi wani abu daban. Nawaf yay murmushi wlhy sonkine kawai yake ─Ćawainiya dani, aduk lokacin danayimiki abu nakan dawo inajin tausayinki, to amma babu yanda zanyi, gashi kekuma bakinki baya mutuwa, kin iya tsiwa, yafa─Ća yana ─Ćan buga bakin da yatsunsa biyu. Yasmeen ta rungumeshi tana fa─Ćin ammafa ka iya basaja bata wasaba, shima rungumeta yayi tsam yana sassanyar dariya a kunnenta to a yafemin bazan sakeba. Ta─Ćago tana kallonsa tana murmushi ta ce, "i luv u habibina, yasake rungumeta shima ya ce, "luv u too my xarah. Haka suka cinye kwana biyunnan cikin soyayya da faranta ran juna, sun manta da kowa da komai, idonsu yarufe sunata zuba soyayya, dabama juna kulawa, Nawaf baya zuwa ko'ina, sallah ce kawai take fiddashi, abin sai wanda yagani, a yau kuma su momcy suka dawo..........✍­čĆ╗­čśť ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś ­čĺô [1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗53 & 54 ....Su momcy sunyi farincikin ganin yanda ─Ćannasu da matarsa suka daidaita kansu, ga abinci mairai da lafiya an shirya musu, papa sai saka musu albarka sukeyi, dayi musu fatan alkairi arayuwa. Bayan anci an'koshi an─Ćan gaggaisa sukace bari su barsu su huta,, momcy ta ce, "aikuma yakamata kuje ku huta musammam ma ─Ćiyata datasha girki, sannu kinji ─Ćiyar albarka, yasmeen ta amsa da ameen cikin jin kunya, sukai musu sallama sannan suka nufi 6angarensu. Suna fita Nawaf ya harareta, "k fancy face ALLAH ya shiryamin ke wlhy. Ameen habibina, amma minayi???, ya─Ćan buga kutunta da yatsansa ─Ćaya, shine ko kice tare mukayi girkinnan momcy sai tausayinki takeji bandani. Dariya sosai yasmeen takeyi dan yanda yay maganar yabata dariya, cikin dariya ta ce, "o, my man kafara kishi dani kenan??, okey hakama zakice ko??, karki damu zan rama, yafa─Ća yana shigewa cikin falon. Itama shiga tayi tana dariya, ta fa─Ća saman jikinsa tana cigaba da dariyarta, ya tsura mata fararen idanunsa, idan tana dariya 'kyau take 'karawa, yakanji kamar ya ha─Ĺiyeta, yasumbaci goshinta my xarah dariya tana miki 'kyau, ALLAH yasa ki haifa mana 'ya'ya masu fara'ar nan taki. Yasmeen ta tura kanta cikin 'kirjinsa wai ita kunya, yashafa kanta yana murmushi my xarah aii kunya adon mace, ALLAH yayi miki albarka, tana kwance a'kirjinsa tana sha'kar dadda─Ćan 'kamshinsa ta ce, "ameen yayana. Yay dariya tareda ─Ćago kanta suna kallon juna, ya ce, "kinsan mikika tuna mini dakikace yayan nan??, yasmeen ta ce, "A'a, ya murmusa, ranar dana ritsaki a─Ćakin can mana, randa kika 6uya nafa─Ćo akanki kuma, kai fance face kekam matsoraciya ce wlhy,, ranarfa saidakikayi kamar zaki suma ya 'kare maganar da dariya, da tsokana yayana dan ALLAH kayi ha'kuri wlhy ina fashin sallah.... Filo yasmeen ta─Ćauka tana ─Ćan dukansa da masa kukan shagwa6a, shikuma yana dariya yana karewa da hannu. Ta tashi tashige bedroom tana turo baki gaba, shima binta yayi yana dariya, saman gado tafa─Ća tana kukan shagwa6a, yaja filo ya─Ćan daki bayanta dashi, aisaita mi'ke itama ta─Ćauki nata, sukayitama juna duka da filo, shi yana dariya ita tana shagwa6a, duk sunbi sun hargitse gadon, sun baje fililukan wasuma sun fa─Ća 'kasa, yajawota yarungume tsam ajikinsa, sorry teema na nabari bazan sakeba. Ta ce, "ai saina fa─Ćaka da momcy eh­čśĺ, ya kwanta tareda kwantar da'ita saman 'kirjinsa, kinga 'yar gidana yi ha'kuri bazan 'karaba, yanzu kina fa─Ćawa momcy ai cazatayi kikoma ─Ćakinta nikuma aii naga banu kenan ko?. Ta─Ćago ido tana kallonsa ta ce, "basai kazama gwauroba, tafa─Ća tana murmushi. Ummyimm 1/1 kenan 'yammata kin rama ko?, ta ─Ćaga gira tana dariya, ya ce, "yayi 'kyau, yafa─Ća yana mirginata, danaga za'a fara soyewa sainayo waje, dannaga wanga gay sai ahankali shi kullum..........um babu ruwana­čÖŐ. Ina nan zaune afalo suka fito, sun sake wanka kowa ya─Ćauki gayu, namaga alamar fita zasuyi, nima sainayo waje, Nawaf ya kulle 'kofar sannan suka nufi 6angarensu momcy, suka sanar musu zasuje gidansu mas'ud ne,, to adawo lafiya momcy tafa─Ća. Saida suka fara gaisheda mami sannan abbansu mas'ud ma yana gida, shima suka gaisheshi yay musu nasiha da wa'azi, sun ─Ćan da─Će awajen kafin su nufi 6angaren mas'ud. Duk suna falo zaune ameena tana 'kasa ta baje 'kafafu dan cikinta yayi girma ankusa juyo mana baby, mas'ud kuma yana zaune kusada ita yana matsa mata 'kafafunta dasuka─Ćanyi fushi,, cikin tsokana yasmeen tashigo tana fa─Ćin mai ciki uhum ganinan tafe, Nawaf da mas'ud suka tuntutsure da dariya yayinda ameena take hararar yasmeen,, habawa yarinya kema aigashinan ajikinki kwana nawane maye yaci amarya. Yasmeen tazauna tana fa─Ćin sannu mayya, inba mayyaba wazai hango kanada ciki??, Ameena ta ce, "ai alamomi sun fallasaki, yasmeen tabi jikinta da kallo tana ta6e baki ke 'yar fata 'kyayi ki barni, mudai kiyi maza ki juyo mana babynmu ko ya ya habibina?, Nawaf ya ce, "gsky ki fancy face. Mas'ud da Ameena suka kalli juna suna murmushi, harsuna ha─Ća baki wajen fa─Ćin tofa haka akayi??, Nawaf ya ce, "haka akayi mi??, A'a basai mun fa─Ćaba Alhaji abar kaza cikin gashinta. Nawaf yay dariya kajidashi dai magulmaci, A'a bro's aikaine babban magulmacin kaida kace..........koda yakedai bari nayi shiru kawai,, A'a kafa─Ća karta kasheka mana,, A'a arufe rufau kawai. Sukai dariya gaba ─Ćaya sannan suka gaisa da tambayar Ameena ya jiki??, ta ce, "Alhmdllh, ai nakusa barwa matarka, Nawaf yakalli yasmeen to ALLAH yakaimu lokacin, sukace ameen. Ameena ta ce, "dan ALLAH yasmeen ki ─Ćakko muku abinsha mana,, yasmeen ta ce, "oni kazo ba'kunta asaka aiki, mas'ud ya ce, "ba babyn ku bane yaja mana, duk yabi yahanamu mu shana ko my honey??, Ameena ta ce, "wlhy kuwa gsky ka. Nawaf yay dariya toku juyo mana abinmu mana, basaikuje kuyita shanawarkuba, aii muna gab kuwa mas'ud yafa─Ća yana kunna tv. Yasmeen tadawo da abinsha, nan suka zauna sunata hira da tsokanar juna, daga baya ameena taja yasmeen ─Ćaki, Nawaf ya ce, "o, mata kun iya gulma, kudai baza'a ta6a zama daku waje ─Ćayaba. Yasmeen tajuyo tayi masa gwalo, ya ce, "niko?, tashige tana fa─Ćin eh,, okey zan kamaki aii yarinya, zaki banbantamin. Mas'ud yay dariya wai mutumina yaushe aka koma haka?, Nawaf ya ce, "kamar yaya??, harararsa mas'ud yayi kaifa ka iya waskewa wlhy, Nawaf yay dariya yana shafa kai, yashiga bama mas'ud labari, sunayi suna dariya da tafawa. A─Ćakima aminai biyu sun 'kulle sunata hira akan abinda yashafesu, yasmeen ta ce, "yauwa ameena yamaganar kayan dakikai min kwanaki??. Ameena ta tuntsure da dariya 'yammata keda kikace bazaki nemaba??, yasmeen ta ce, "hum kibari kawai fitinar Nawaf dole saina shirya mata, plz kidaina mini dariya mana, ameena ta tsagaita da dariya, to nabari sistona yanzu abinda za'ayi littafin zan baki kawai kiringa ha─Ćawa da kanki, danni nafi gane naha─Ća abu dakaina, bawai da ankawo nahau shaba alhalin bansan daga inda yakeba. Hakane amma suna cutarwane??, kai, eh mana, akwai masu cutarwa, wasufa bakasan inda aka ha─Ćasuba, kinga kuwa ai za'a iya samun matsala. Gskyar ki, to amma aina zan samu kayan ha─Ćin idan kin bani littafin?, babu damuwa yawanci kayan itatuwane, barema ALLAH yabaki miji mayen kayan marmari, zakiringa samu koda yaushe, sukansu kayan marmarin idan kinasha komai zai zama dai2 kuma zam2, okey to shikenan kibama hanan takawomin littafin dan yanzu babu damar nace zan tafi dashi. Ameena tayi dariya kina tsoron boss yagani kenan???, hhhh babu wani tsoro ina kare martabatane kawai, suka tafa suna dariya. Sai bayan isha'i suka koma gidansu, a 6angarensu momcy suka yada zango, saida akasha hira sannan suka wuce 6angarensu, Nawaf yafa─Ća saman gado yana fa─Ćin wash ALLAH na nagaji my xarah. Yasmeen ta ce, "to yakakeso ayine??, ya ce, "amin wanka dan ALLAH yafa─Ća cikin shagwa6a, yasmeen ta zauna kusadashi tajawo kansa ta─Ćora saman cinyarta, ta ce, "kafa girma habibina amma kake shagwa6a,, ya kamo hannunta yasumbata yana murmushi, fancy face gara nayi kafin yara su zo su kwace mini fadata. Yasmeen ta du'ko ta sumbaci goshinsa, suka tsurama juna idanu cikin murya mai cikeda so da 'kauna ta ce, "bazasu kwace maka fadaba, dan kaina fara sani kafinsu,, yarungumeta kansa yacusa jikin cikinta, to shikenan fancy face ALLAH yakawo masu albarka, ina addu'ar kafin mu tafi Spain kin kamu. Yasmeen ta zaro ido waje, kai habibina nifa bazan bikaba ina nan tareda su momcy. da sauri yatashi zaune yana kallonta, yakamo hannunta, kina nufin zaki barni natafi ni ka─Ćai, xarah??, danayi ha'kurin rashinki akusa dani amma fa yanzu bazan iyaba wlhy, ina kikeson naringa kai matsalolina, ko kinaso mijinki yafara aikata abinda baiyiba yana saurayi??, plz & plz karki bari su momcy suji wannan maganar, wlhy zasu goya miki bayane. Ya jawota jikinsa cikin taushin murya yafirta ina sonki dayawa fateema, amma ke naga kamar har yanzu baki amintaba, kokuwa ba'kya sona.............da sauri yasmeen ta rufe masa baki, plzzzzz karka fa─Ća wlhy nima inasonka fiyema da yanda kake sona, nima bazan iya rayuwa babu kaiba kaji na rantse maka, da sauri ya rungumeta tsam suna fidda numfashi ahankali, saida zuciyoyinsu sukai sanyi sannan suka ─Ćago suna kallon juna suna murmushi, tafara cire masa ma6allin rigarsa tana fa─Ćin tashi muje muyi wankan nafara jin barci. Tare sukayi wankan sukai shirin barci sai gado, nima na tattaro inawa2 nayo gida. Haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri, komai yana tafiya yanda akeso, su Nawaf suna shan soyayya, koda yaushe suna manne da juna idonsu yarufe gaban kowa soyewa sukeyi, suna 'kyautatawa juna, kowa burinsa yafarantawa ─Ćan uwansa rai. Yasmeen takan shirya musu girki mai da─Ći da gamsarwa, suci susha abinsu, tana ma mijinta biyayya duk abinda ya bu'kata tana masa cikin hanzari babu nuna fushi bare ta ce, "tagaji,, aduk lokacin dayazo mata da bu'katarsa takanyi 'ko'karin taimaka masa dan yasamu nutsuwa, kullum sukan kasance cikin farinciki da 'kaunar juna. Shima Nawaf baya ba'kin cikin 'kyautata mata da 'karfinsa da lokacinsa aljihunsa dakuma farincikinsa,, nakula aurene mai cike da farinciki da 'kaunar juna. A yaune kuma Ameena ta haihu ─Ćiyarta mace, su yasmeen ana cikin farinciki, kamar su suka haihu, kullum tana gidan suna kar6ar barka sune amarori 'kirjin biki­čśť. Kullum a can take wuni, sai dare take dawowa gida, yau kam agajiye tadawo gida Nawaf yana kichin yana ha─Ća shayi, tashigo da sallama ta fa─Ća saman kujera tana kiran wash ALLAH na, Nawaf yafito daga kichin hannunsa ─Ćauke da kofin shayi ya ce, oyoyo my xarah kin dawo??, ta─Ćago ido agajiye tana kallonsa ta ce, "eh ammafa yau nagaji dayawa, ya'karaso ya zauna kusada ita, kofin shayin ya ajiye saman tabir ─Ćin gabansu, ya rungumota zuwa jikinsa ayya sorry my dear karki damu ai hidimar babyn muce, ta shafa kirjinsa tana murmushi hakane my handsome. Shima yay murmushi, nima kwana biyunnan duk an barni cikin ka─Ćaici, ga bu'katun sunyi mini yawa, kullum aka dawo sai ace angaji, yasmeen tayi dariya haba habibi yanzufa kagama fa─Ćar cewa hidimar babyn muce. Ya marairaice murya hakane fancy face, amma itama babynmu tana bu'katar sabon 'kani, atausaya mini plzzzzzz, yasmeen ta murmusa tana masa gwalo, ya ce, "niko??. Ta ce, "eh tareda 'kokarin tashi, yay saurin matseta ajikinsa yana bata 'kayatattun sumba ako ina na sassan jikinta...................✍­čĆ╗ Kuyi hakuri yanzu ina typing ka─Ćan, inada uzurine. ;luv u oll­čśś❤ kuna 'karamin karfin guywa ngd sosai. . ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś­čĺô [1/12, 9:10 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗55 & 56 .......A kwana atashi babu wuya gurin ubangiji, yaune sunan baby kuma taci sunan nana khadija, ubangiji ALLAH yaraya mana dukkan 'ya'yan da aka haifa ya albarkacesu. Su yasmeen ansha shagali, kuma tanun bajinta itada habibinta, sunyima baby alkairi maiyawa harda iyeyen baby, mas'ud har yarasa bakin magana, yasan shida Nawaf sunruga sunzama 'yan uwa na jini, tamkar yanda mahaifansu suke tare, babu abinda suke iya 6oyema juna, ALLAH kuma ya dubesu ya azurtasu da mata 'kawen juna, masu kula dasu dason farincikinsu. Nawaf yayi hidimar da ko mas'ud bayi rabintaba awajen shagalin sunan,, duk da yasan Nawaf yafishi samun ku─Ći, dan gsky 'yan kwallo suna samun ku─Ći sosai, to amma ba kowa bane zai bigi jiki yayi maka hidimar ku─Ći a irin wannan lokaci da kowa ya─Ćauki rayuwa dagashi sai 'ya'yansa. To mudai saimuce ALLAH ya sassaka da alkairi, yakuma maida kowa gida lafiya. Bayan kwana biyu da gama suna suka shirya tafiya saudia, amma harda su momcy da kowa da kowa,, papa ne kawai sai sun kusa dawo zaije su dawo tare. Nawaf dake kwance yana kallon yasmeen tana ha─Ća musu kaya, ta ─Ćakko manyan kaya wajen kala shidda zata zuba masa a akwatinsa,, ya ce, "fancy face wa─Ćan nan kayanfa, waye zai sakasu??, ta ce, "kai mana!!. Yatashi zaune yana fa─Ćin tab fancy face kina gani anan ma basakawa nakeba sai papa yayi magana bare acan,, tacigaba da zuba kayan tana fa─Ćin nikam ina son naga kasaka manyan kaya ba 'karamin 'kyau suke makaba, abinda manyan kayan nakama marabarsu da 'kananun ka─Ćan ne, tunda ─Ćinkunan sun cika fitat kamar wani mace. Ya koma ya kwanta yana dariya, toni ahakamma ina sakawane kawai dan suna takurani wlhy,, hummm zamani yazo damuka ─Ćauki Al'adar wasu muka yafama kammu, bayan kowa yasan kayan yarensa sunfiyimasa 'kyau. to nidai yanzu ni akema fa─Ća kenan?, tokiyi ha'kuri kwananna zan koma saka manyan kaya sosai tunda kina so kinji. Yasmeen tayi murmushi aiko danafi kowa jin da─Ći, dan wlhy manyan kaya suna maka bala'in 'kyau, saidaifa kaine kake haskasu, ta'kare maganar da ─Ćaga gira. Ya saki wani lallausan murmushi kina cikin aikina fancy face,, kinrigada kin gama mallakeni, nakula kofa aure na 'kara amarya baxata samu farincikina sosaiba. Dan danan yasmeen ta canja fuska, tamkar zata fasa ihu,, tabama Nawaf dariya amma saiya daure ya gimtse, ya ce, "yayadai naga kin 6ata rai, shiru tayi masa tana rufe akwatinsa dan tagama ha─Ća kayan, ta saukeshi 'kasa tana hawaye,, Nawaf ya mi'ke ya sakko dan yasan shirun datayi ta sha'kane. Rungumota yayi tabaya dan ta juya masa baya, ya le'ko fuskarta saiyaga hawaye share2, cak ya ─Ćauketa zuwa gado, ya kwantar da ita, shima yana gefenta,, yasa hannu yana share mata hawayen cikin kunnenta ya ce, "kinga nifa da wasa nake miki, plz kidaina bari hawaye suna 6ata mini 'kya'ky'kyawar fuskarnan tawa ni ka─Ćai,, ta harareshi tana fa─Ćin maza ai dama kun iya da─Ćin baki. Ya ce, "woow!! Ni na isa nayima fancy face ─Ćina da─Ćin baki, wlhy iya gsky ta nake gaya miki, kina kula dani, duk sanda nazo da bu'katata kina 'ko'karin biya mini, kina sakani farinciki, ba'kya barina da yunwa,, to idan na 'karo aure ita kuma mixata min??, bayan my xarah tana yimini komai,, ya sumbaci bakinta sorry dear kimin murmushi mana kozanji da─Ći. Yasmeen ta sake hararar sa, saiya rungumeta yana dariya, kinga bari na canja hanyar lallashin tunda sunada yawa, da sauri ta ce, "nikam naha'kura habibina,, ya─Ćago fuskarta suna kallon juna ya ce, "ban yardaba,, ta ce, "to mizan maka ka yarda na ha'kura,, ya lashe la66ansa, tayi murmushi dan tasan abinda yake nufi, ta ce, "to rufe idonka, yarufe yana fa─Ćin sarkin kunya. Saida ta 'karema 'kya'ky'kyawar fuskarsa kallo, sannan takai bakinta kan nasa, wasu zafafan kissis take bashi, wanda shi kansa baisan zata iyaba, dan tamaso tafishi shi dayake malamin nata, da'kyar ta janye bakinta ta tashi tana dariya 'kasa2, dan ganin yanda jikinsa yay lakwas. Shikuma sai binta yake da idanunsa dasukayi jaa, gaba ─Ćaya jikinsa yayi laushi, cikin dariya ta ce, "yakamata mutafi fa tunda kace bazaka barni na wuni acanba,, ALLAH inata zumu─Ćin son ganin umma da abba da yaseer. Nawaf ya lumshe idanu tareda fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ahankali ya furta to zokiji wani abu mana,, ta ce, "tab aina gane wayonka Alhaji, katashi kawai kayi wanka mu wuce kaga ni tun─Ćazu nayi nawa,, ya─Ćan cije le6e yana murmushin mugunta, ya ce, "to zomiyi wata shawara,, yanda ya─Ćan ha─Će rai saita ─Ćauka shawarar gsky ce, tanufi bakin gado ta zauna, ya ce, "karaso mana, A'a daga nanma ya isa..... kafin ta rufe baki yayi ciki da ita, na ce, "sai anjimanku,, dan naga soyayya za'a sha.. Ina zaune a waje suka fito Nawaf cikin manyan kaya hardasu hula, yasmeen kuma ta saka atamfa zani da riga ta ─Ćora farin gyale, sunyi 'kyau sunata zabga 'kamshi abinsu, bayan sunyima su momcy sallama suka fito hardasu Abdallah za'aje, itada shi suna gaba su Abdallah suna baya. Yana cikin tu'ki saiya kamo hannunta, da sauri ta janye, ya─Ćan kalleta, da ido ta nuna masa su Anwar,, ya ─Ćan murmusa yana maida kansa saman titi, babu da─Ćewa suka isa gidan. Da gudu yasmeen ta shige, da umma ta fara karo, tako rungumeta tana tsallen murna, umma ta ce, "ohni yasmeen wai sai yaushe hankali zai zomikine??, ta saketa tana turo baki gaba kai umma murnar ganinkufa nakeyi!!, to sannu da zuwa, yana ganki ke ka─Ćai bayan kince tare kuke da mijin naki, lah umma suna 'kofar gida hardasu Anwar ma. Oh ni ALLAH ya shiryaki mamana shine kika barosu awaje, yaseer!!! umma ta kwala masa kira,, yafito da sauri yana amsawa, ganin yasmeen zaune saiya rungumeta suna murna,, umma ta ce, "kaje kashigo dasu Abdullahi........ Bai bari umma ta 'karasaba yayi waje da gudu, acanma rungume juna sukayi da Anwar dan sunzama abokai tuni, ya gaida Abdallah da Nawaf, Nawaf ya ce, "o, yaseer kaima kayi girma wannan tsawo haka, yanzu wanda bai saniba saiyace ka girmi fancy face ─Ćina. Dariya sukayi sosai yayinda yaseer yay musu jagora zuwa falon abba, yaja hannun Anwar suka fice,, dayake ansan da zuwansu an shirya musu abubuwan ciye2 afalon,, Abdallah ya hau cin abinsa dan dama abinci zaici Nawaf ya azalzalesa yafito. Nawaf ya ce, "ALLAH ya shiryaka Abdallah kaidai acicine ko??, Abdallah yay murmushi abii wlhy yunwa nakeji, kumafa ni gidannan kamar gidanmu nake ─Ćaukarsa, duk abindazan iya yi aginamu zan iyayi anan, munzama ─Ćaya da ablah aii.. Nawaf yay murmushi danjin da─Ćin maganar ─Ćan 'kaninsa, ya ce, "hakane my dear bro's. Babu da─Ćewa abba yadawo yazauna sukasha hirarsu dayake mutumne mai sau'kin kai, ga son jama'a. Umma maidai ta daure yau ta ajiye kunya ansha hira da ita,, yasmeen sai shagwa6a take zubama abba,, ya ce, "mamana har yanzu ba asan an girmaba ko??, ta shgwa6e fuska abba nafa da─Će ban gankuba, kuma nasan yaseer yana nan yana ta6ara. Yaseer ya ce, "oh kina kishi danine aunty??, to aii yanzu lokacinane, ninake shanawa. Su Nawaf suka saka dariya, Anwar ya ce, "yaseer aii nima addu'a nake abii shima yayi aure abarni ni ka─Ćai nasha shagwa6ata,, Abdallah ya hararesa ─Ćan ba'kin ciki aiba yanzuba saina 'kara hutawa,, gaba ─Ćaya suka saka dariya, duk sanda Nawaf da yasmeen suka ha─Ća ido saiya ─Ćaga mata gira, ita kuma tayi murmushi, hakadai sukasha hirarsu,, Nawaf ya ce, "yaseer yay 'ko'karin kar6o takardunsa zai nema musu makaranta shida Anwar a kasar Rasha, yaseer akaita murna da godiya, suma su umma sun masa godiya, suka ajiye musu alkairi maiyawa suka taho, yasmeen harda ─Ćan kwallanta, tabama Nawaf tausayi,, amma sai ha'kuri duk macen duniya haka ta gada, bishiya agidanku, inuwa a gidan wasu. Bayan sundawo gida sun gama duk abinda yake al'adar rayuwarsu suka kwanta dan dare mahuta bawa,, yasmeen tana kwance agefen hannun Nawaf ta ce, "shine zaka nemawa su yaseer makaranta amma ni ka lalata mini tawa ko??. Yashafa kanta yana murmushi to kina kishi da yaseer kenan dgsk??, babu wani kishi, to miye inba kishiba??, ke aii kingama karatunki,, keda kike cikin babbar makaranta mai cike da aikin lada. Ta 'kara gyara kwanciyar ta tareda rungumeshi, hakane habibina amma wlhy inason karatu sosai,, yajuyo ya rungumeta sosai karki damu my xarah zakicigaba da karatunki, harma saikince kin haji dan kanki, aikine kawai banyarda dashiba,, damun koma Spain zan nema miki makaranta. Ta 'kan'kameshi sosai tana murna, ta ce, "wlhy ni dama bana karatu dan na samu aiki, inasondai kawai nazama mai ilimi,, saura karatun islamiyya, kai yaka mata kazama malamina mijina. Yay murmushi waya gayamiki inada kwarewa anan?,, tab ai momcy tabani labainka tun kana yaro, da 'kiriniyar dakayi, ta ce, "min kai Anwar yagado shiyyasa ga yaronnan akwai ilimin addini, kumama kafishi,, dan haka kawai kabada kai.. Ya ce, "shikenan tunda momcy ta fallasa ni insha ALLAHU zamu fara karki damu. Sunata 'yar hirarsu 'kasa2 har suka fara jin barci, sukayi addu'a suka lula duniyar barci. Washe gari jirginsu ya ─Ćaga zuwa 'kasa mai tsarki,, tarba akai musu ta mutunci, 'yan uwa cike da gida sunzo tararsu, aginda hajja tsohuwa mai ran 'karfe suka sauka, yasmeen sai ware ido take yau gata a saudia, kasar da aka haifi (mafificin halitta ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA) (TSIRA DA AMINCI SU 'KARA TABBATA GA SHUGABAN TALIKAI, MAI CETONMU AWATA RANA MAI CIKE DA HARGITSI DA RU─ÄANI,, ALLAH yasa muna cikin wa─Ćanda zai ceta, ameeeeen.) Lallai yasmeen ta yarda su momcy 'yan gatane, dan family nasu sunada ku─Ći da ala'ka mai 'karfi tsakaninsu da masarautar saudia,, abinci har rasa wanda zataci tayi, Nawaf sai dariya yake mata wai kartayi 'kauyanci,, itadai shiru tayi masa dan momcy da hajja suna kare mata,, bayan sunci sun 'koshi an gaggaisa da dangi, suka tafi dansu barsu su huta. Abin yabama yasmeen mamaki dataga an ha─Ćasu ─Ćaki ─Ćaya da Nawaf, itakam gsky tanajin kunya,, takira Abdallah ta ce, "yaje yasanar da momcy dan ALLAH araba musu ─Ćaki, dariya Abdallah yayi, ya ce, "Ablah aiko bazasu raba muku ─Ćakiba, dan momcy ma idan sukazo itada papa wlhy ─Ćaki ─Ćaya suke zama. Idanma na fa─Ća momcy koroni zatayi, kiyi ha'kuri kawai kuyi zaman ku, dan shima Abii ba yarda zaiyiba,, yasmeen ta ce, "ALLAH inajin kunya Abdallah, Abdallah ya fice yana mata dariya. Bai da─Će da fitaba Nawaf yashigo ita harma ta kwanta sannan,, ya shigo yana fa─Ćin sorry fancy face nabarki ke ka─Ćaiko, ina wajensu isma'il muna shan hirar zuminci, bayi yashige yay wanka dan azatonsa tayi barci ne.. Bayan ya fito yay shirin barci sannan tayi barcin gsky, sai kawai ya rungume matarsa suka hau barci. Da asuba tunda yatafi sallah bai dawoba, ta nanan zaune tana laximi saiga wata 'yar yarinya takawo mata dabino guda bakwai, ta ce, "taci, yarinyar ta burge yasmeen, ta zaunar da ita saman cinyarta tana tambayar ya sunanta, yarinya ta ce, sunanta fateema,, woow!! Yasmeen tafa─Ća, sunanmu ─Ćaya kenan ko, yarinya ta ─Ćaga kai,, duk suna magarne da turanci saikuma larabci ─Ćai2 da yasmeen take sakawa wanda ta iya. Suna nan zaune Nawaf yashigo dagudu fateema taje ta tarosa ya ─Ćauketa ya─Ćaga sama, suna dariya, yazau bakin gadon yana yana tambayarta tasan yasmeen tace eh, nan sukaita hira shida ita da larabci, yasmeen ta ce, "o ni yar yarinya 'karama ta iya larabcun. Nawaf yay dariya kajifa xarah da wani zance, to itada yarenta , ke sanda kina 'karama baki iya hausaba, da yaren buzaye??. Yasmeen ta ce, "na'iya mana, sukai dariya gaba ─Ćaya, ya ce, "fateema jeki amso min dabino nima, tako 'ki'kira da gudu amso dabino, Nawaf yasakko kusada yasmeen ya─Ćan kwantar da kansa a bayanta, cikin taushin murya yace nifa da matsala nazo, yasmeen ta ce, "matsala kuma wace iri??, yay mata zobe da hannayensa cikin kunne ya gwar gwa─Ća mata suna cikin yin dariya fateema tadawo da dabino, da sauri yasaki yasmeen yana ─Ćan sosa kai, tazo ta haye cinyarsa tana bashi dabinon abaki,, yasmeen ta ce, "kaganka kuwa kuna kama kamar kaika haifeta. Yay murmushi mai 'kayatarwa yana shafa kan fateema ya ce, "karki damu nima tawa tana nan zuwa,, yasmeen tai 'kasa dakai tana murmushi,, ta ce, "─Ćiyar waye??, Nawaf ya ce, "─Ćiyar uncle zaid ce, tunda mamansu tarasu wajen haihuwar 'kanin fateema aka kawosu nan wajen hajja. Ayya ALLAH yagafarta musu, wlhy harta bani tausayi, su nawane??, su ukune, akwai Nawaf mai sunana, sai muh'd Ariff, sai fateema Wanda tarasu wajen haihuwarsa shima yarasu,, ALLAH sairki ALLAH yaji'kansu. ameen fancy face. nansukaita hirarsu harsaida hajja ta aiko su fito suyi break sannan. Bayan sun kammala break suka ─Ćau gayu, Nawaf yatafi zagawa da yasmeen gidajen dangi, gidansu ummuhabeeba ne na farko, antarbesu da mutunci, ummuhabeeba sai rawar kai ake anga masoyi, yayinda yasmeen ta cika tayi fam, Nawaf ne kawai ya gane halin datake ciki, dayaga zata fashe saiyace ta tashi su tafi,, ummuhabeeba kuma ta ce, "zata bisu itama tayo ziyara, tofa. Koda suka fito yasmeen saita shige baya, Nawaf ya ce, "k miye haka??, banza tayi masa bata amsaba,, itako ummuhabeeba ko a kwalar rigarta ta bu─Će gaban mota tashige abinta,, da hausa Nawaf ya ce, "fancy face wai miye haka kikeyi??, baki ta murgu─Ća masa­čśĆbatareda ta tankaba. Ummuhabeeba ta ce, "my luv muje mana, wani haushi ya'kara turni'ke zuciyar yasmeen, wai agabanta akecema mijin ta my luv,, Nawaf yana kallonta tana hawaye ta madubu,, kai kawai ya girgiza dan baisan miya dace yayiba. Ummuhabeeba ta ce,, A'a yanaga kana nufar ka'aba­čĽődamune?, muda zamu ziyara,, batareda ya kalletaba ya ce,, "aidama can zamuje nida fancy face, mungama ziyara sai kuma gobe idan ALLAH yakaimu. Ummuhabeeba taji haushi ta 'kara maimaita sunan wai fancy face, wani ─Ćan 'karamin tsaki taja wanda Nawaf ne kawai yaji, itafa tabiyosune dan azatonta dangi zasu zaga tana kuma bu'katar dangi su tabbatar da soyayya takeyi da Nawaf, tasan dolene asakashi ya aureta. Amma shine dan wula'kanci yayo masallaci dasu. Yasamu guri ya tsaida motar, suduka suka fito fuska babu walwala, Nawaf ya ce, "lokacinma sallah yayi, saimushiga muyi sallah idan mun fito saina zagaya dake kiga guraren tarihi ko fancy face??,, bataso tabashi kunya agaban ummuhabeeba dan haka tayi far da idanu ta ce, "hakane habibina,, ummuhabeeba tayi gefe dakanta zuciyarta tana zafi,, yayinda yasmeen ta harari Nawaf,, yay mirmushi yana mata jinjin­čśâ­čĹŹ­čĆ╗. Haka suka shiga sukayi sallar la'asar,, bayan sunfito yashiga nuna mata wajajen tarihi hannunsa yana ri'ke da nata,, daga baya ummuhabeeba ta ce, "tagaji ya maidata gida. Ya kalli agigon hannunsa yana murmushi, aii inaga mu bari muyi sallar magriba kawai dan ta gabato, zata iya riskarmu a hanya. Badan tasoba dole ta ha'kura sukayi sallar magriba accikin masallacin­čĽősannan ya maidata gida suma suka koma inda suka fito, yasmeen tanata wani zuzun6ura baki, ita adole kishi ya motsa.....................✍­čĆ╗ ©2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś­čĺô [1/12, 9:11 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄż NAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗57 & 58 .......Nawaf yanaso yay dariya amma saiya gimtse, idonsa na kan titi ya ce, "matar NAWAF SA'EED MODEBBO ya yadai??. Yasmeen taimasa banza kamar bata jishiba, yay murmushi tareda kamo hannunta ─Ćaya ya rumtse anasa, yana tu'ki da ─Ćaya, ya─Ćan kalleta ka─Ćan yanda taketa zum6uro baki saida ya dara,, ya ce, "waishin yazanyi da shagwa6ar fancy face ne yayinda yarana sukazo duniya??, sai asannan ta kalleshi ta murgu─Ća masa baki, ya sake murmusawa dan yaganta ta madubi, antuna baya kenan yafa─Ća yana shiga kwanar dazata sadashi dagindansu hajja. Ta zame hannunta daga nasa tana cewa kadaiji dashi na ummuhabeeba,, tofa harkin sadakar dani fancy face, lallai kinason ummuhabeeba wannan irin 'kyauta da rana tsaka, aiiko muna sauka zan kirata na sanar mata kin barmatani tasamu miji a sanga. Yasmeen fa ta sha'ka da yawa danhaka tayi tsit, yanayin parking tafice batareda ta jirashiba, a'katon falon gidan ta tarar da ahalin gidan harma da ba'ki wa─Ćanda bata saniba,, tunda tashigo suke murmushi damata sannu da zuwa, itama saita daure take murmushin ya'ke, amma tuni momcy ta harbo jirginta, ta gaisheda kowa dake falon, wa─Ćanda ta girma suka gaisheta, hajja ta mi'ka mata hannu alamar tataho wajenta, kusada ita taje ta zauna sai asannan Nawaf yashigo yana cilla makullin mota sama yana ca6ewa, kai kai lallai ashe yau munada manyan ba'ki, wa─Ćanda yakecema manyan ba'ki suka shiga dariya suna fa─Ćin kainedai babban ba'ko, shekararka nawa rabonka da saudia, shima ─Ćayan gefen hajja yaje ya zauna suka sakata tsakki shida yasmeen, ya ce, "ablah kibari kawai wallahi sana'ar nan tamu itake hanamu wani motshi, amma waccan shekarar nazo saidai kwanana biyu naduba hajja na tsere, ya madina?. Ta ce, "madina lafiya lau, ya amarya tunda bansamu zuwa bikiba sannan jawad yana fama da rashin lafiya muna kwance a asibiti, ayya ablah karki damu aisu ummulkhairi sunje shima ya wadatar, su jawad suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya karatunsu, sukace lfy law, yamaida kallonsa ga jawad ya ce, "zo na ganka my boy, jawad yazo suka gaisa lallai kayi girma sai aure ko? , gaba ─Ćaya falon suka saka dari, ablah ta ce, "aure kam, Anwar fa ya girmi jawad jikinne kawai ALLAH yabashi haka. Koh ablah?, amma yanzu sai ace shine babba, ga Anwar ─Ćan 'karami,, gsky kam, shima yanzu yagama tsokanarsa aii. Ablah tacanja maganarta zuwa larabci danda da turanci sukeyi, ta ce, "Nawaf wannan matar taka kamar ba 'yar Najeria ba?, Nawaf ya kalli yasmeen ya ce, "ablah saboda mi kikace haka??, Ablah tayi dariya naganta 'kya'ky'kyawane,, lallai Ablah kin samemu mu 'yan Najeria bamuda 'kyaune?? Kunada 'kyau mana amma dai ku ba'ka'kene, inkuwa 'yar Najeria ce ka iya za6e, nanma dariya sukayi, banda yasmeen dabatasan misuke cewaba, Nawaf ya ce, "kai ablah ammafa kin samemu mungode,, saidai yakamata ki shirya kije Najeria kigammu muma akwai kala. Ta maida maganar zuwa turanci, Karka damu zanzo Najeria da bikin Abdallah insha ALLAHU. tab─Ći bikin Abdallah kuma?, kice da sauran lokaci kenan??, kai haba wane sauran lokaci?, aii kamar yaune,, ablah yanzufa yake shekara ta biyu a school, yaushe aka gama aka samu aiki, yarinyarma dayakeso ko secondary bata gamaba. Hajja ta ce, "aiko Abdallah aure yakeso kaida kadage kanata kwaso masa shekaru, kallifa yanda yake ha─Će fuska yaji kace da sauran lokaci. Abdallah yay saurin cewa hajja karkisa yanzu abii ya hau kaina fa, momcy tai masa dakuwa kaci gidanku ai gsky hajja ta fa─Ća nima ina kallonka. Dayaga za'a tasoshi gaba saiya tashi ya shige ─Ĺaki yana kunkune, lallai abii kaika kama matarka ahannu kunata shan soyayya saini zaka ringa lodamin shekaru, wlhy halimatu tana gama secondary aure zamuyi, dannikam aure nakeso. Na ce, "da gsky ka Abdallah wlhy kayi aurenka kaima kasha soyayya­čśť. Afaloma hirarsu suketa sha, dayake da turanci akeyin hirar yasmeen tanajinsu saidai bata saka musu baki, iyakarta daria ko murmushi, dahaka aka kira sallar isha'i mazan suka fita masallaci sukuma matan sukayi agida, bayan sun dawo akaci abinci sannan su Ablah suka tafi gindan iyayenta dayake anan suka sauka. Momcy ta kalli yasmeen datayi shiru cikin kujera ta ce, "─Ćiyata zonan, yasmeen ta tashi ta nufi wajen momcy, harzata zauna 'kasa momcy ta ce, "A'a takamota ta zauna kusada ita, tajawo kan yasmeen gefen kafa─Ćarta tana shafa bayanta ─Ćiyata miyake damunki?, yasmeen ta ce, "momy babu komai. Momcy ta saka hannunta gefen wuyan yasmeen ta ce, "bakijin da─Ĺi yasmeen tun jiya ina kula dake bakisan fa─Ćane kawai komuje asibitine??, A'a momy bama sai munjeba, to fa─Ćamin mike damunki??, mom jikina ne kawai yakeyimin nauyi sai kuma wani lokacin ina─Ćan ganin jiri, amma banajin zazza6i, saidai jikin yayi ─Ćumi kawai. Momcy ta shafa kanta amma shine baki fa─Ćaba ─Ćiyata, kuma mijinkima bai saniba ko?, eh yasmeen tafa─Ća,, humm ─Ćiyata zurfin ciki ko??, ALLAH mom niban ─Ćauki abin serious ba shiyyasa., aiko wannan serious ne ─Ćiyata, gobe idan ALLAH ya kaimu ummuhabeeba saitazo ta dubaki kinji, dam gaban yasmeen ya fa─Ći, badai wacan maikama da aljanarba ko tafa─Ća a zuciyarta. Nawaf dake gefe yana kallonsu ya ce, "momcy waimi ake tattaunawane haka?, sai kus2 kukeyi babu maiji. Tofa kaji wani sa ido ina ruwanka ko ka aikata wani abune dakake tsoron kar'afa─Ćane??, Nawaf ya murmusa A'a A'a, nikam ban aikata komaiba, amma momcy wannan irin sirri haka miyasa ba'aso muji??, aiba saikunjiba shiyyasa, to shikenan idan tayi tsami maji, nikungama bari naje na kwanta, inaso mu fita da wuri gobe idan ALLAH yakaimu gara muyi ziyarar nan mugama kafin wuri ya 'kure. Yay musu sallama ya shige ─Ćaki, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije ki kwanta kinji ALLAH ya'kara sau'ki, tami'ke tana fa─Ćin ameen mom, itama sallamar tai musu ta shige, yayinda suma kowa ya mi'ke yanufi makwanci, dama Abdallah yana ─Ćaki suna waya da halimatunsa. Yasmeen ta maida 'kofar tarufe, Nawaf dake zaune bakin gado yana tu6e kaya yajuyo yana kallonta ta ─Ćauke kai daga kallonsa,, murmushi yayi yatashi yashige bayi danyin wanka,, yaudai ba'a da─Ćeba aka fito, yana fitowa itama tashiga, sanda ta fito yana shafa'i da wutiri, itama saitayi harama dan dama batayiba. Bayan sun idar yazauna shan shayi itakuma ta haye gado tana mitar mutum kullun saiya sha shayi yake iya barci saikace wata kwaya, koni dana gada bana shansa haka,(karku manta yasmeen buzayene ), koda yake shima yagada awajen momcy. Tana nan tana sa'kawa da kwancewa Nawaf yagama ya hawo gadon yakwanta, shiru tayi kamar tayi barci, ya rungumota zuwa jikinsa yana fa─Ćin yarinya kokinyi barci saikin tashi, danyau bazan iya ha'kuriba, duk abinda yake mata tanajinsa tayi shiru. Dayaga haka saiya ─Ćauki wayarsa ya haska mata fuska, dole ta─Ćan 'kyafta idanu sabida haske, yay dariya, oh da wasan 6urun2 akeyimini to aii na harbo jirginki, hannu tasa ta─Ćan tureshi tana fa─Ćin dakazo kana 'yar murya bagara kabiya sadaki a─Ćaura muku aureba gobe kaida mai kama da aljana. Tabashi dariya sosai wai mai kama da aljana wato ummuhabeeba kenan,, cikin dariya ya ce, "A'a fancy face karfa ki fa─Ća abakin mala'iku, surubuta gobe ya tabbata, dama ─Ćazu kince kin barmata ni. Ta gallah masa harara tamkar yana ganinta, ta ce, "kaidai kasani. Yasake rungumota yana fa─Ćin kema zaki sanine, tunda zaki koma raba dai2 ─Ćina da wata. Haushine ya 'kara turnu'ke zuciyar yasmeen saikawai tafara kwalla,, jiyayi laima tana bin 'kirjinsa da sauri ya haska danyasan 'kila kuka takeyi, ilai kuwa shitakeyi, yashiga share mata haba matana uwargidana kuma amaryata dagake aii babu 'kari, itafa mai kamada aljanar nan amatsayin 'kanwa na ─Ćauketa, dan haka batada wani fili azuciyar habibinki, duk kinbi ki mamaye ko'ina, 'ya'yana kawai kika barma fili, plz banaso kibari kishi ya 6ata min ranki a banza, Nawaf nakine ke ka─Ćai fancy face, ya 'kare maganar da sumbatar bakinta, daganandai ya cigaba da kwantar mata da hankali ta hanyar daya dace. Washe gari momcy ta aika Abdallah ya ─Ĺakko ummuhabeeba danta duba yasmeen, sama2 suka gaisa kowa kishi yana cin zuciyarsa, Nawaf yay dariya wato sudai mata basuda wata damuwa saita kishi. Toshi wannan 'kaddara tasa ya ha─Ćasu aiyaga takansa. Ummuhabeeba tanama yasmeen tanbayoyi cikin wani yanayi, itama tana bata amsa cikin jin haushi, tun a tanbayoyin datake mata da amsar datake bata tagano yasmeen ciki gareta, amma tsabar kishi bazai barta tafa─Ća musu yasmeen nada cikiba, saita ce, "zataje asibiti tadawo. Momcy ta ce, "babu wani magani dazaki bata yanzu ummuhabeeba?, dan na kula batajin da─Ćin jikinta, karki damu momcy yanzu zandawo insha ALLAHU da maganin zan dawo, to shikenan saikin dawo. Ta kalli Nawaf abii zoka kaini muje mudawo plzzz, saida ya─Ćan harareta sannan ya ce, "dawaya kawokine?,, ta shagwa6e fuska ALLAH mijin Ablah hidaya ne ya saukeni, toga key kije kidawo, ta zaro ido waje­čś│ kamanta nanba 'kasarku bane, kasanfa mata basa tu'ki a saudia........ Momcy ta 'katsemusu zancen da fa─Ćin kaje ka kaita mana modeebo, kaga yasmeen batajin da─Ćin jikinta, zaku zauna gaddamar dakuka saba, saida yakalli yasmeen dake kwance ta ha─Će rai kamar zatayi kuka, ta harareshi, ya ─Ćauke kai yana fa─Ćin to momcy. Suna fita ummuhabeeba ta kamo hannunsa, da sauri ya kwace yana harararta, ta ce, "sorry bazan sakeba, batareda ya ce, "komaiba ya bu─Će motar yashige, itama saita bu─Će ta shiga, tanaso tayi masa maganar aurensu amma tanajin tsoro dan ganin yanda ya ha─Će rai kamar bashiba. Har cikin asibitin ya kaita, tafito tana fa─Ćin kazo muje ciki mana, kai ya girgiza mata, A'a jeki fito ina nan ina jiranki,, asanyaye ta ce, "to, taso yashiga dan 'kawayenta su ganshi, suna shan labarinsa sosai awajenta. Bayan tafiyarta ya kwantar da kujera ya kwanta, tuni tagama abinda takeyi amma tayi zamanta suna hira da 'kawayenta kamar babu wanda ke jiranta,, Nawaf yagaji da jira yafito, yasan matarsa tana bu'katar magani danyabaro jikinta da zazza6i, cikin asibitin yanufa, office ─Ćinta yafara zuwa amma arufe, wanine yake gaya masa aii yau bata aiki tana hutu sai dare, ya ce, "ai tare sukazo,, mutum ya ce, "to inaga tana wajen 'kawayenta zomuje na rakaka 6angarensu, acan kuwa ya sameta tana ganinsa tafara wani kame2n binciken takardu,, ya 'karaso yana fa─Ćin ummuhabeeba wai har yanzu?,, ta mi'ke tana fa─Ćin abii yanzu na kammalane. 'Kawayena ga abiina na 9ja sunansa Nawaf,, suka mi'ke suna fa─Ćin woow!! Nice guy, dama sun sansa a hotuna datake nuna musu, suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya aiki. Bayan sun gaggasa yayo waje, itakuma taimusu sigina da ido itama tafito tana dariya suma sunayi. Amota ta tarar dashi, harya tada, tashigo tana fa─Ćin albishirinka abii, batareda ya kalletaba ya ce, "goro, saida ta─Ćan cije le6e ta ce, "matarka tanada ciki wata biyu, da sauri ya tsaida motar yana kallonta, ya ce, "da gsk kikeyi ko wasa?, ta ce, "wlhy da gsk, aii baisan sanda ya rungumeta yana murna ALHAMDULILLAH yaketa fa─Ći, yayinda itakuma ta kwanta luf ajikinsa, da sauri ya tureta yana fa─Ćin wa'iyazubillah, ALLAH ka nisantamu daga sharrin shai─Ĺan. Shiru kawai ummu habiba tayi dan batada amsar bashi, haka suka 'karasa gida batareda ya kula dukkan maganganun datake masaba, yana zuwa ya rungume yasmeen babu ko kunyarsu momcy da hajja, ya ce, "fancy face albishirinki, da sauri ta tureshi dan kunyarsu momcy sai asannan ya kula dasu ya saketa da sauri yana sosa kai, yay 'kasa da kai yana fa─Ćin sorry mom & hajja. Momcy ta ce, "kaidai kasani mara kunyar banza, to Albishir─Ćin mi zakai mata??, ya sosa kai ummuhabeeba fa─Ća musu kawai. Ummuhabeeba dake tsaye kamar gunki tun ─Ćazu, ta mi'kama momcy result ─Ćin, momcy ta amsa tana dubawa, cikin murmushi ta mi'kawa hajja itama, hajja ta rungume yasmeen tana murna suka shiga mi'ka addu'oin alkairi ga cikin dabai wuce wata biyuba, kowa yana cikin farinciki da murna bare uban ginsamin Nawaf, momcy tabata shayi dakanta ta sha dayake ALLAH yasa cikin bamai saka ami bane, tanashan magunguna ta 6ingire barci abinta. Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, yasmeen tana samun kulawa wajen mijinta da iyayensa, yana zagayawa da ita ko'ina guraren tarihi da gidajen dangi, sunje har kabarin fiyayyen halitta (ANNABI MUHAMMAD ,,,S A W), Tanajin da─Ćin rayuwar saudia, kusan kullum saitayi waya dasu yaseer da ameena tanajin labarin 9ja, satinsu uku papa yazo, shima yay sati ─Ćaya sannan suka tarkato komatsansu zuwa 9ja, yasmeen tayi wani shegen 'kyau kunsan mai yaron ciki akwai bada kala, har wata 'yar 'kiba tayi, sun dawo 9ja suna kewar mutanen saudia,, su mas'ud ne sukazo tarbarsu. Tun afilin jirgi ameena take mata tsiya wai kodai ta kamu?, dan taga tayi wani 'kyau na musamman, yasmeen ta harareta kedai kika sani 'yarsa ido,, to shima mas'ud ba'a barsa abayaba wajen tambaya, kusan amsa ─Ćaya Nawaf yabashi data yasmeen, mas'ud ya ce, "mutumina karka fa─Ća ainariga na gane kasandai ni likitane, Nawaf ya ce, "to sannu likita, ya fa─Ća yana ─Ćaga nanah dake hannunsa, ya ce, "Ameena mikike bama babyn mu tayi girma da 'kyau haka cikin wata ─Ćaya??. Ameena tayi dariya, babu abinda akebata, sai abincinta,, kai amma ─Ćiyata 'yar baiwace, wlhy kuwa habibina yasmeen dake baya kusada ameena ta tafa─Ća. Hakadai akacigaba da gungurawa cikin yasmeen yana fitowa, sati biyu masu zuwa kuma zasu cane 'kasar Spain, saidaifa papa kamar yana shirin hana tafiya da yasmeen ya ce, "idan ta haihu tataho daga baya. Saidai nakula maganar bata shigi Nawaf ba sosai,, dan kamar baima yardaba, toko yaya za'ayi kenan kudai biyoni kawai. Suma su yaseer da Anwar wannan satin suka ─Ćaga zuwa 'kasar Rasha domin fara karatu a6angaren likitanci. To abokan juna saimuce ALLAH ya taimaka, yasa adawo asa'a.......................✍­čĆ╗ © 2017 ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ­čĺôMrs Abdus'salam­čĺô ­čĺôluv u oll my fan's­čśś­čĺô [1/12, 9:11 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆ ­čÄżNAWAFF ­čÄż ☆☆☆☆☆☆☆ NA BILKISA IBRAHIM­čĺô Page­čĹë­čĆ╗59 & 60 ......Nawaf zaune a falo saman doguwar kujera, yasmeen tana kwance tayi matashi da cinyarsa, sunata 'yar hirarsu, yashafa cikinta yana fa─Ćin babyna saura wata biyar yazo duniya insha ALLAHU, yasmeen tayi dariya kai habibina wai har kafara lissafi. Musrmushi yayi yana shafa kanta, lallaima fancy face ─Ćina, kinsan kuwa yanda na 'kagara naga babyna aduniya, shiyyasa da papa ya ce, "baxaki biniba na rikice, mutum da matarsa ayita nuna masa fin 'karfi. Yasmeen tayi dariya aiyanzuma bakada tabbacin xan bika ─Ćin, ya─Ćanja la66anta, ta ri'ke hannunsa tana fa─Ćin da zafifa habibina. Ya murmusa ai dama zafin nakeso kaji, ke yanzu kina fata natafi nabarki ke ka─Ćai?, duk fa─Ćin gadonnanfa ke ka─Ćai zaki ringa kwana, ke ka─Ćai kuma zaki ringa zama gidannan. Kai haba ai kana tafiya 6angaren momcy zan koma kamar wancen karan, harararta yayi waike dan ALLAH da gsk kikeyi?, ya 'kare maganar da ha─Će fuska. Yasmeen tayi murmushi tana shafa fuskarsa, A'a nifa wasa nake maka, ina zan iya farinciki babu habibina a gefena, insha ALLAHU 'kafarka 'kafata sai Spain, du'kowa yayi ya sumbaci goshinta, yanzu naji magana 'yammatana, yanda bakomai kike iya ci ─Ćinnan ba natafi na barki ai hankalina zai rabu gida biyu, gashi muna komawa akwai manyan wasanni dazamuyi kinga kuwa ni bazan iya ta6uka komaiba. A'a habibina kaifa jarumine wanda duniya takeson gani a filin kwallo, kanaso yaronka ko yarinya suzo duniya suji kakoma rago saboda rainon cikinsu??. Ya saki wani lallausan murmushi, my zarah ke dabance acikin mata, kin iya magana mai taushi da da─Ći ga mijinki, da sauran maza zasuyi sa'a irin tawa da har abada wani bazaiyi tunanin sake aureba, ina alfahari dake amatsayin mata 'kawa 'yar uwa. Yasmeen ta tashi zaune tana murmushi ta kama hannuwan Nawaf ta rimtse anata, cikin murya mai cike da kissa, ta ce, "nice nayi sa'a mijina, dan tabbas nafi sauran mata sa'a,, da samun miji kamili mai ilimi da tsoron ALLAH, wanda yake tattalin iyalinsa da sauke dukkan nauyin daya rataya awuyansa, nika─Ćai nasan sirrikan dake tattare da mijina, wanda baki bazai iya furtawaba saboda kar wasu matan suyi sha'awar ya kasance minijinsu koda amafarkine......, da sauri ya rungumeta yana murmushi, my xarah aikinriga da kin mallakeni nazama ra'kumi da akala, babu wata mace dazata sha gabanki awajena komai 'kyawunta, Nawaf na fateema xarah ne ita ka─Ćai, ina 'kaunarki sosai fancy face, ina ro'kon ALLAH ya kasheni da 'kaunarki, kinriga kin zama wata tsoka mai muhimmanci daga sassan jikina, nidake mun wuce hanta da jini,, suka 'kara matse juna kowannensu yana zubar da hawayen da─Ći, yasmeen ta─Ćago tana kallonsa, ta ce, "habibina nima ina 'kaunarka har bansan yanda zan fassara irin 'kaunar danake makaba, dan sunyima bakina nauyi, Nawaf ya kamo fuskarta ya ha─Će bakinsa da nata, soyayya mai tsafta da tsada suke nunawa juna, dan ballagaxar mace bata samun irinta­čśí. Nima fitowa nayi nabasu waje­čĆâ­čĆ╗­čĆâ­čĆ╗. Da hakadai suka fara shirin tafiya Spain wanda da 'kyar papa ya yarda atafi da yasmeen amma da shara─Ćin idan cikinta yakai wata takwas zai dawo da ita gida ta haihu, da sauri ya amince kuwa. Suka fara shirin tafiya,, ya kaita gidansu ta wuni acan tayi musu sallama, gidansu mas'ud ma yini tayi, ranar juma'a suka ─Ćage cike da kewar mutanen 9ja, suma sun barsu da kewarsu, dan tunda suka tafi gidan kamar anyi mituwa kowa yayi sukuku, har papa daba zama yake sosai dasuba shima sai yaji gidan yay masa wani iri. Ya ce, "ummulkhairi kinga daga tafiyar yarannan yau har gidan yazama wani iri gashi babu auta, dagamu sai Abdallah sarkin rashinji, momcy tayi dariya wlhy Alhaji har wani zazza6i nakeji fa, Abdallah ma saida yasha magani yana ─Ćaki kwance, shiyyasa akace sabo akewa kuka ba mutuwaba, balle yasmeen yarinyace mai shiga rai sosai. Papa ya ce, "gsky ne yarinyar tanada ha'kuri gatada girmama nagaba da ita,, wlhy danma ba zaman gida kakeyiba shiyyasa, amma modebbo ya dace da mace tagari mai addini kam. Papa yay dariya aidama haka ALLAH ya ke, sai yabaka abinda bakaso yazama alkairi arayuwarka, idan na tuna randa na sanarma modebbo auren yarinyarnan tamkar zai kwala min ihu koya hau bori, saiya bani dariya randa nace baxai tafi da ita Spain ba tamkar zai min kukafa, momcy ta tuntsure da dariya, itama ─Ćin yasmeen kalar marasa lafiya tazama, shiyyasa nace kawai kabarsu su tafi, cikin yana shiga wata takwas idanma bai kawotaba ni zanje na ─Ćakkota ne aii. To ALLAH ya kaimu lokaci, yakuma sauketa lafiya,, ameen momcy tafa─Ća. Sumadai ALLAH ya saukesu lafiya, suna zuwa barcin gajiya yasmeen tashiga yi, gashi dama jikinta babu 'karfi, Nawaf kam fita yayi dan yanada abubuwan yi masu yawa. Tada─Će tana barci, saida ta warware a gajiyar data kwaso sannan ta mi'ke da addu'a abakinta, wanka tashiga tayi a ha─Ća─Ćan bathroom ─Ćin, azuciyarta ta ce, "kaga masuyi dan ALLAH, wannan bathroom haka ai ─Ćakin watane a 9ja, tagama wankanta tafito tayi shiri cikin 'kananun kaya, tana cikin fesa turare Nawaf yashigo rungumeta yayi tabaya suna kallon kansu amadubi, ya ─Ćora hannunsa saman cikinta yana shafawa, my baby kabaro 'kasarka zuwa wata 'kasa wadda ta ri'ke maka dadyn ka ko?, yasmeen tayi dariya, to dadyn nasa yabarta mana, gefen wuyanta ya sumbata yana fa─Ćin inhar momy ta amince anjima ma saimu ─Ćauki hanyar 9ja. Hannu tasa tana shafo fuskarsa sunama juna murmushi ta madubi, ta ce, "A'a ban aminceba muyi zaman mu, Nawaf yatashi tsaye yana dariya to zomuje kici abinci babyna yanajin yunwa. Falo suka koma dakansa yabata abincin taci sosai kuwa, ta ce, "lallai andace, tashi ─Ćaya kikaci abincin nan batareda kin kusheshiba balle yatsina fuska. Yasmeen tayi dariya nifa wlhy bammasan ina yatsina fuskaba idan banason abinci, okey bari sai ankawo wanda bai mikiba idan kinayi zan ─Ćauki hotonki, kace terere zakami kenan?, babu wani tarere Nawaf yafa─Ća yana gyara wajen. Haka rayuwarsu ta Spain tacigaba da tafiya cikin soyayya da jin da─Ći, suna bama juna kulawa, cikin yasmeen yanata girma, yakan fita yawo da ita taga gari idan yasamu lokaci, idan zasuje wata 'kasar buga wasa da'kyar suke rabuwa idan kuma tafiyar ta wuce kwana biyu to tare suke tafiya. Komai yana tafiya musu yanda sukeso, suna waya da 'yan 9ja sosai, dakuma su yaseer, kosu ha─Ću a yanar gizo, yasmeen tayi 'kyau abinta tayi 6ul2 ga cikin yayi mata 'kyau, mijinta yana kula da ita dabata farinciki, dan mace mai ciki tana bu'katar kasancewa cikin farinci. To yanzu cikin yemeen yashiga wata na takwas, momcy fa tafara damun Nawaf da zuwan yasmeen gida, kwata2 bayaso yasmeen ─Ćin tatafi saboda shi bashida damar zuwa 9ja yanzu amma yazaiyi, dole ya ─Ćauki uzuri na kwana ─Ćaya yakawota 9ja ya juya. Su momcy sunyi farincikin ganinta, sosai nannama kulawa aka shiga bata ta musamman a─Ćaki momcy take zaune, tunda cikinta yashiga watan haihuwa momcy tadawo kwana ─Ćakin dan kar haihuwa ta risketa batareda an saniba. Awata safiya litinin yasmeen ta tashi da na'kuda babu 6ata lokaci momcy ta kwasheta zuwa asibiti, kar6arsu akayi cikin gaggawa dan haihuwarce gadan2, Alhmdllh yasmeen ta zullu'ko 'katon ─Ćanta maikama da ubansa namiji, karkuso kuga murna wajen wannan family, Abdallah yafara kiran Nawaf yasanar masa, tsalle yaytayi namurna gashi zasu shuga wasa alokacin, wannan farincikin ne yasashi nuna bajinta awajen wasan, saida ya zura kwallo sau uku, wannan lamari yayima koch nasu da─Ći ba ka─Ćanba. Tuni hotunan baby boy sun cika masa waya, kowa sai turo masa yake takafa sada zumunta, yaro ─Ćan gatan dangi, zuwa yamma aka sallamesu dan komai normal, sundawo gida yayinda 'yan uwa da abokan arzi'ki suketa tururuwa wajen ganin ba'kon duniya, tsaf aka shirya yaro cikin kayan sanyi masu 'kyau da laushi, yasmeen ma tashirya tsaf tagyara jikinta, bayan taci ta'koshi ta haye gadon momcy. Tana kwanciya wayarta tahau 6urari, cikin murmushi ta ─Ćauka, cikin kissa ta ce, "ALLAH yabarni da baban baby,, Nawaf yasaki wani lallausan murmushi kamar yana gabanta, ameen dear fancy face, ina fata dai kina cikin 'koshin lafiya, keda sweet babyna ?, yasmeen tayi murmushi lafiya lao muke habibina, ykk kaima??, ya ce, "nima Alhamdllh, sannu da aiki fancy face nagodema ALLAH kema kuma nagode miki da kika haifomin 'katon ─Ćana zuwa duniya,, yasmeen tayi dariya, kai habibina kaida baka gansaba ya akayi kasan 'katone??, yayi dariya lallai fancy face ai inagama narigaki ganinsa, aituni Abdallah da mas'ud suka samba─Ćo mini pic nasa, insha ALLAHU duk yanda zanyi sainayi nazo 9ja nextweek, to shikenan habibina ALLAH yakawo mana kai lafiya. Amin xarah na yanzu ina babyna samin naji numfashinsa mana, hhhh ai yana falo wajensu momcy nikuma ina ─Ćaki kwance,, ya marairaice murya to kije falon mana, ido tazaro lah habibina sokake ace banida kunya babu ruwana wlhy. Yay dariya to sarkin kunya yizaman ki kar ace bakida kunya, amma ki─Ćau al'kawari da an maidoshi kiyimin vedeo ─Ćinsa ki turomin, karka damu na─Ćau al'kawari, daganan hirarsu suka cigaba dazubawa cikin so da 'kauna, sun da─Će suna hira, sannan suka kashe, ana kawo baby ─Ćakin kuwa tacika al'kawari tayi video ta tura masa, tsalle yaytayi yana kallo saikace wani 'karamin yaro, ranar abinda yakwana yi kenan, haka yayta kallo yana maimaitawa. Haka rayuwar take gudu da sauri, yasmeen tana ta jego, hargashi gobe suna, aranar kuma Nawaf ya iso 9ja, dangi sunyi farincikin ganinsa, shima yayi farincikin ganinisu, yarungume ─Ćansa yana maijin 'kaunarsa jiyake kamar yatsaga jikinsa yasakashi, ranar ahanununsa baby ya wuni, da daddarema saida momcy ta koreshi waida nan zai kwana wajen yasmeen. Washe gari akayi suna yaro yaci sunan MUHAMMAD ubangiji ALLAH yaraya muhammad amin, bayyana muku yanda sunan yakasance 6ata lokacine amma nabawa kowa dama ya kiyasta azuciyarsa, shagali akayi bana wasaba, hardasu hajja 'yan saudiyya,, lallai munra'kashe mun kwalle ranar­čĺâ­čĺâ­čĺâ­čĺâ­čĺâkai harma 6arararrajewa mukayi, lol­čśť. Bayan sati ─Ćaya dagama suna Nawaf yakoma, yabar su yasmeen suna jego abinsu. Sunyi arba'in yayinda yaro yayi 6ul2 abin sha'awa, nisainajima kamar subani­čśś­čśťlol, su yasmeen an zagaya dangi ko 'ina, kowa yana sambarka da wannan yaro. Bayan wata uku. Nawaf yadawo gida hutun 'karshen shekara, tarairayar yaronsa yake sosai, damma wani lokacin su momcy suna masa fin 'karfi saisu kwaceshi ya wuni awajensu shan nono kawai yakesa akawoshi wajen yasmeen, idan papa yana gida shima saiya kwace saikaga kowa yana zum6ura baki, dan kowa yanason ─Ćauka, amma dole ya ha'kura tunda papa ya amsa, na ce, "kaga ─Ćan dangi yanashan tarairaya,, hakadai rayuwa taci gaba da tafiya MD yana girma da 'kara wayo, dole su Nawaf suka barma su momcy, suka koma nunama juna soyayya da fatan suma ALLAH yabasu wani. BAYAN WASU SHEKARU. gidansu Nawaf nayima tsinke, nayi sa'a kuwa suna 9ja, Nawaf anzama manya hakama yasmeen anzama manyan mata, ga 'yan yaransu abin sha'awa, bayan Muh'd sun haifi ummul'khairi mai sunan momcy, suna kiranta ummu, sai sa'eed papa kenan shikuma abbu, idan kaga yaran kamar ka sacesu, ─Ćas2, shi dama muh'd sun barma su momcy komai nashi acan yake. Anyi bikin Abdallah da halimatu 'kanwar mas'ud, naga harda ma 'katon ciki, na ce, "su Abdallah an huta kenan­čśťlol. Suma su Anwar da yaseer sun kammala karatu sundawo, sun zama cikakkun likitoci magada mas'ud kenan, abokan juna daba'a jin kansu, sumadai nakula aure sukeso­čśť 6angaren su umma ma komai dai2 kaji dattijan arzi'ki, hakama su mas'ud suma yanzu sunada yara hu─Ću abinsu gwanin sha'awa. muh'd yafito daga ─Ćakin Nawaf yana kuka, Nawaf dake falo yanama ummu homework ya ce, "yaya! lafiya dai??. Muh'd yafa─Ća jikin Nawaf yana kuka, yasmeen tafito hannunta ri'ke da bulala tana ─Ćaukeda abbu a─Ćayan hannun, tanufo muh'd, Nawaf ya'kara rungumeshi yana fa─Ćin sorry ummy miya faru??. Ta nuna masa goshin abbu dayayi fushi ta ce, "dan ALLAH kalla kagani habibina jibi yanda ya fasama yarona kai dan mugunta, yasan bazai iya ─Ćaukarsaba miyasa ya ─Ćaukesa??. Nawaf yajawo abbu dake kuka, ya─Ćorashi saman cinyarsa yana fa─Ćin yaya ya akayi haka tafaru,, muh'd ya ce, "dady ALLAH ban ganiba, fa─Ćuwa yayi dakansa ALLAH bani bane, yasmeen takai masa duka, da sauri Nawaf ya kare yana fa─Ćin kiyi ha'kuri tunda ya ce, "bai ganiba kinsan dai bazai cuceshi da ganganba, ai abbunema yacika nauyi. ALLAH bakasan muguntar muh'd bane, nibammasan miya kawoshi wajen nanba, bama momcy ta ce, "anguwa zasujeba shine yataho jan magana nan??. To yi ha'kuri dai bazai sakeba, yasmeen tashige ─Ćaki tana mita. Shikuma yashiga lallashin abbu haryay barci, shima muh'd yay shiru, ummu ta ce, "dady nima inajin barci,, A'a ummu na kigama homework ─Ćin sannan kinga gobe monday kunada school yaya zoka cigaba da koya mata na kwantar da abbuna kaji. Muh'd ya ce, "to, kusada ita yakoma ya zauna, Nawaf saida yaga muh'd yana koya mata dai2 sannan ya sumbaci kumatunsu yanufi ─Ćaki dan kwantarda abbu, yasan muh'd akwai 'ko'kari amma sai rashinji, babu abinda yabaro daga halayen Abdallah, shiyyasama yanzu yakoma kamanninsa gaba ─Ćaya. Nawaf ya kwantar da abbu tsakkiyar gado sannan yanufi yasmeen dake tsaye tana gyara masa kaya a wardrobe, ya rungumeta tabaya yana fa─Ćin sorry ummy bazamu sakeba,, yasmeen ta ce, "kuma sake mana jikinku yayi tsami ne aii, dan ALLAH jibi yanda aka samini yaro baccin wahala. To mudai ayi ha'kuri mukace, tajuyo suna fuskantar juna, kowa yanama ─Ćan uwansa murmushi, Nawaf ya ce, "i luv u my xarah,, itama murmushin tayi ta ce, "luv u too habibina, suka rungume juna tsam suna gayama juna kalamai masu da─Ći da gar─Ĺi, kowa yana farincikin kasancewa da ─Ćan uwansa. Tonima dai ina farincikin kasan cewa daku har abada. TAMMAT BI HAMDULLAH. Takucedai BILKISA IBRAHIM. (Mrs Abdus'salam) Nagode masoyana aduk inda kuke, nagode da 'ko'karin bibiyata dakukeyi,, ALLAH yabarmu tare, ina 'kaunarku kamar yanda kuke 'kaunata da zumu─Ćin karanta abinda yafito daga kwakwalwata.❤❤❤❤❤❤kucigaba da kasancewa dani a sabbabin books ─Ćina masu zuwa gareku insha ALLAHU nan bada da─Ćewaba.. Kusanar dani kuskure ko gyara daya dace nayi a novels ─Ćina, idan kunyi haka shine zan tabbatar da kuna 'kaunata, domin nima 'yar adamce azija. Kunnuna min 'kauna mai yawa kuma nagode sosai,, baxan iya lissafokuba saboda yawan dakuke dashi,, amma ina godiya gareku da group admins naku, nagode nagode nagode,, luv u oll❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤­čĺö­čĺö­čśś­čśś. Muha─Ću asabon littafina mai zuwa KUKAN KURCIYA........, shima zaizo muku da sabon salo mai 'kayatarwa dakuma fa─Ćakarwa,, zaizo gareku nan bada da─Ćewaba insha ALLAHU. CIGIYA dan ALLAH ina neman book's ─Ćina guda uku. RASHIN SANI auren 'KADDARA ko BI YAYA 'KANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA. dan ALLAH duk wanda yay dacen katari dasu yatura min ta wannan number 09093044460. ALLAH yasa adace­čśé­čĹî­čĆ╗ TAKU HAR KULLUM BILKISA IBRAHIM ­čĺôbilyn Abdul­čĺô ©2017 ­čĺôluv u, luv u, luv u, luv u, luv u oll­čĺő­čĺő­čĺő­čľÉ­čĆ╗­čśé­čśé­čĺô Saikunjini­čśé­čśé­čśé­čĹî­čĆ╗ ©2016 ­čĺ×bilyn Abdul­čĺ× ­čĺ×Mrs Abdus'salam­čĺ× ­čĺ×luv u oll my fan's­čśś­čĺ×

Shin Ana Bukatan Blog ko website Kamar wannan kodai kamar Shafin Duniyan Fasaha, za'a iya samu a kan farashi mai rahusa daga Babban kanfanin Be With Me Technology Yola, Wayanda suka kware wajen Website Design da kuma hada Mahajar Waya. Za'a iya tuntubansu anan ko a wannan layin +2349039016969

Get Professional Website Design For your business Today Here. You can also visit our Tech Blog for more awesome Information. 
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *