Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 9 March 2017

AKAN SELFIE! COMPLETE.

adsense here [1/6, 7:56 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 1⃣. Tsaye take a bakin wani lambu, wanda yasha kayan marmari, ga wasu grass carpet dake kusa da gun. Misalta inda take tsaye wani irin aikine. Kyakyawar yarinya ce ta karshe ga gashin nn har gadon baya, wayan dake hannunta ta d'auka ta d'agata sama. Ta d'agata sama kenan ta hangi wani tsaye a bayanta. Cikin tsawa ta fara cewa "Kai dallah malam matsa daga chan kada ka fitomin a selfie". Yarinyar dake maganar wadda tasha farar shadda tare da aiki jah, dinkin dogowar rigane ya kamata sosai. Mutumin dake tsaye ya kyal_kyale da daria yace "kai su ameera kin cika iya yi, ynxn nan kika biya kud'i hr naira d'ari biyar dan kiyi pic a wajen nan. Kika aro kayan nan gurin halima amma duk da kinsan nasan komai sai kinmin yanga"? A hankli ameera ta d'an yamutsie fuskanta tare da tunzorou bakinta " Dallah naji! kai kuma mai bakin parrot kawai, oya dubie gabanka". Daria yayi tukkuna ya gyad'a kai ya wuce abinshi. Yayinda ameera ta karkace kugu tare da tsuke bakinta ta d'aga wayanta sama k'iran Samsung galaxy ta fara salfo kanta tare da chanza salo zuwa mazauninta. Tana kammalawa ta hau Facebook ta fara posting ba'a d'au minti 3 ba aka tara mata comments kusan hamsin tare da like d'in daya kai d'ari. Murmushi tai yayin da tagan guy d'inta mai suna al'amin yana yaba pic d'in da duk kusan halittan jikinta ana ganinshi... ©Kausar Luv💞 [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 2⃣. Idanunta ta daga masu kama dana mage ta kara sakin wani murmushi, tare da saka kafafunta ta fita a gidan, a hnkli take takawa har takai titi ta samu keke napep ta hau shigarta keda wuya tace "Malam geto area xamyujie" ba jira yaja motan dayake dan garine har unguwar y sauketa, tana sauka ta ciro kudi naira 100 ta bashi. Ta kama hanya zuwa gida, hanya ta mika santal tana tafiya, yayinda jama'ar unguwar sea kallonta sukeyi. Ita kuwa ko a jikinta, a hka har ta karasa cikin gidansu, wnda yake daki 2 ne a ciki, sai kitchen a gefen left side, wnda yake na kwano sai toilet a chan kuryan gidan. Shigarta keda wuya tai sallama, baaba rahane dake zaune a bakin kopar ta amsa sallaman tare da kiran sunanta "Ameeratu nikam yaushe zaki deana karya ne"? Kisani karya batada amfani ko kadan" dubie ynda kika fitoh kaman wata diyar arna" kai kawea Ameera ta gyada tace "Baaba rahane kenan" ina zuwa, da sauri ta shiga dayan dakin, wanda yake yar katifa ce kawea a ciki ta cire kayan jikinta ta dau wani zane da riga t_shirt ta saka tare da dan kwali ta fito tsakar gidan ta samu guri ta zauna kusa da baaba rahane. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 4⃣. Hka kuwa akayi washe gari, da misalin karfey 12pm, Ameera da halima suka kama hanya zuwa gurin bilal. Bilal ya kasance mutum ne mai shirya gurin haduwa, kaman gurin buki hka, to yanada gidah mai dan girma hka, gidan yana da kyau sosai. Suna isa kuwa dayake ya sansu basu samu wata matsala ba, sukayi masa bayanin komai, yce ba damuwa zai shirya. Cike da farin ciki da murna suka kamo hanya wanda kowacce a cikinsu ta dame jikinta cikin wasu kana nan kaya da dan karamin gyale, kaman diyan arna. Das_das suke takawa har suka kawo dea2 wani yaro mai kyau hka, kasancewar ameerah akuyta da son yara, ta matsa kusa dashi yaron da akalla zaiyi shekara 6 zuwa 7. Rage tsayenta tai dea2 nashi tace "Oh boy muyi selfie ko"? Ta daga wayan sama kenan yaron ya fara kucce2 alaman baya so. Halima dake gefe sai daria takeyi mata, inda Ameera tasha mur tare dayiwa wnnn yaron magana "Kai dallah ka bari mu dau selfie" yaron ya fashe da kuka, hakn ysa mutumin dake bayanshi yake magana da wani wnda mota ta kare shi ya matso, cike da tsawa ya bude bakinshi yace "Ke lpy menene kinayi hka"? A hnkli ta dago idanunta ganin mutum da tai da kayan sojoji, gashi ko alaman daria babu a fuskanshi yasa ta danyi murmushi, cikin rawar murya tace "Daman.. Damn... Daman mi? "Dama inaso mu danyi pics nida shi" Sojan dake tsaye yayi gyaran murya yace "I see! So kana so ka daukemin yaro ko"? Kanta yayi gadan2 Inda ammera ta ranta cikin na kare, gudu takeyi sosai har sai da ta bar titin, halima dama na ganin hka tai kaman ba tare suke ba. Ameera na kai titi kajie kincha! Sunyi karo da dan machine inda tafadie kasa tumus! Nikam kausar daria nai abina sosai, tukkuna n taimakawa ameera ta mike tsaye ta samu mai mota tai gidah. Shigarta keda wuya Baaba rahane tace "Lpy"? Yar nn mai ya faru dake? Ameerah ta dan yamutse fuska inda kafanta duk ta gurjie tace "Baaba rahane AKAN SELFIE MANA" baaba rahane tai daria sosai tace lallai kam akan selfie. Ynxn yaushe zaki kawo shi sbon saurayin naki gida"? "Chabb Allah ya kyauta baaba a wnnn gidan? Hajiyata gobe zamu hadu amma ba'a nan ba" baaba rahane tai shiru na dan wani lokaci tukunna tace "Ameera ki tsare mutuncin kanki, kisani cewan kefa wta rana xaki zama MATAR WANI! UWAR WANI! SIRIKAR WANI! kisani cewan wnnn abun da Allah y yi maki darajane ki kareta. Ameerah tai dan guntun Murmushi tace "baaba kenan na world fa, to ma mai nakeyi ne? Idan kika hango abunda wasu sukeyi wlh ni muminace bisah dasu. Baaba rahane a fusace tace "Shiyasa bamu tuba ga Allah! Muddin kana kallon abunda wani ke aikatawa sai kace gwara kai, tofa bazaka taba chanzawa ba. Allah ya shiryaki ameerah. Murmushi tai tace "amin" Allah ya kaimu gobe.. ©Kausar Luv💞 [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 3⃣. Iska mai dadi take kada jikinta, wnda ya sanyata nishadi da shiga cikin yanayi mai dadin gske. Karan wayanta ne ya katsie mata nishadin da takejie, murmushi tai ta dauka tare dayin sallama ganin bakuwan number. Dga chan cikin wayan tajie wata murya mai dadin sauraro ana kiran (meeeera) "Na'am" ta amsa a takaice. Bayan sun gaisa, sai mutumin daya kira wayan yace "Baby na tura maki pics dn fatan sunyi kyau" a hnkli tace au "Misbah ne"? Yace "eh nine, amma pls yaushe zamu hadu"? Meerah ta danyi murmushin kissa tace "Ko gobe xamu iya haduwa" Misbah yace "sai kinjini amma ba gobe ba gskya sai jibie, dan ina nan abuja amma zan dawo gobe kinga jibie sai nazo ko"? Ameera tace "Ba damuwa" sukayi sallama tare da kashe wayan. Baaba rahane ta duba tace "Wlh inna nayi sabon kamu, Allah yasa wnnn shine mijina" bara in kaiwa halima kayanta kapin ta aiko" da sauri ta runtuma daki ta dauko mayafinta ta fita kasancewar da gidansu danasu halima babu nisa" Hka ta fada a gidan da sauri, tana kiran kawata halima wlh nayi sabon kamu, halima tai shewa "Shegiya kawata wlh bakida dama" nn fa suka daura wta chapter akan inda zasu hadu, tare dayin estimating kudin da zea kama. Nan take akayi total kudi ya kama dubu 5. Ido Ameera tabi halima dashi "Ke banza a ina zansamu dubu 5 kuma"? Halima tai daria ta tafa "manta kawea hajiyata wnnn daga ganinshi ba karamin kwaro bane, kinsan Bilal ai, to shi xai mana lamuni har na kwana 2, kinga idan yxo ya bada kudin sai a biyashi. Hka kuwa suka ajiye mgna akan zasu tafie gobe gidan bilal. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 5⃣. Washe gari! Tunda safe Ameera ta fara shirye2 itada halima, har kaya sun aro masu tsada, a chan bangaren bilal kuwa shima ya tashi ya fara shirya masu gidan. Karfeyh 12pm, ameera ta dira a gidan bilal, cikin wata dogowar riga mai karamin hannu, daga saman rigan akuy kwalliya da golden stones, kasan rigan ya bude, tai rolling farin gyale, ta saaka takalminta da dan kunne fari da jakarta fara, ilahirin rabin kirjinta duk a bude yake, kamshi kawea take zubawa, koda ta isa bilal ya kammala shirya masu komai kaman ynda suka bukata, ameerah sai daria da murna takeyi, yau zatagan misbah. Ba'afi minti 30 da zuwanga ba kuwa sai ga kiran wayan misbah a wayanta, cikin hanzari ta dauka tare da cewa "Hello"! A cikin muryanta mai dadin sauraro. Misbah yace "A ina zanganki"? Nan take tayi masa bayanin inda zai zo. kasancewar yana a motane sai ya dau hanya, duk direction din da take bashi shi yake bi har ya karaso dea2 layin. A nn ya tsya ya kuma kiranta a waya. Ganin kiran data kara yine ya bata tabbacin cewen gafa misbah nan ya iso, da sauri ta bude jakanta ta dauko madubi ta kara duba fuskanta, ta shafa powder, ta Kara fesah turare gaba daya dakin ya dau kamshi, tukkuna ta dau wayanta, ta fara wata tafiya tana kada jikinta ko ina har ta fitah, kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce, kowa yana gidansa babu ruwan wani da wani, yasah ta kara jin kwarin guiwa, a hnkli ta isah bakin layin wnda babu wata tazara da gidan gidan bilal.. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 6⃣. Wayanta ta dauka ta kirashi, yayin dashi kuma ya hangota ta cikin glass din motanshi wnda yake tin_tied. A hnkli ya saukar da glass din ya fara duban ameerah tundaga sama har kasa, wani irin abu yji ya ziyarci zuciyanshi, amma sea ya danne ya saki wani irin murmushi yace "Ameerah"? Kai ta daga tare dayin murmushi, ta kama hnya zuwa motanshi, kai tsaye ta bude gidan gaba ta shiga ta samu guri ta zaunah, tai masa alama dasu jie, babu gardma ya rufe glass din ya kama hnya har suka karasa a kopan gidan, yayi horn mai gadi ya bude gate, inda misbah ya shiga da motanshi, yayi parking, suka fitoh su 2, ameerah tai masa jagora har cikin falon gidan suka zaunah akan kujera ta zaman mutum 3. Murmushi tai masa inda ta tashi tana rangwada ta nupie kitchen, shi kuwa mishbah dakin yabi da Kallo, ba'a dau wasu mintina ba sai gata tadawo da manyan farantai a hannunta, wnda suke dauke da kayan ciye2 iri2 a kai, ta dire ta koma ta dauko wani faranti ta dire tukkuna ta matsa daf dashi, har jikinta naso ya goge nashi ta fara magana tare da kashi mashi idanu. Misbah yayi gyaran murya, yace "Am sunana Mishbah dan Madami" Ameerah tai Mlmurmushi tace "Sunana ameerah sadiq" zea kara wata magana tace "ya isa hka ga wannan" ta bude golden ledan dake kan dayan farantin, kaxa ce a ciki gasasshiya ta dauko cinya zata bashi a baki yce "Ina azumi baby" amma zanso ki fadamin tarihin rayuwanki saboda a gaskya nida aure nakesonki" Ameerah tai dan gyaran murya a cikin ranta take cewa "Waiyyo! Allah gwanin baiwa nice nan zan aure wnnn mai kyau hka gashi da dukiya, ai nida talauci munyi hannun riga kenan" Nn take ameerah ta fara bashi bayani akan cewan itafa diyan Alh Sadik ne, this n that ta kwashe karya da gskya ta fadamsa, sai da ta kammala misbah yayi dan guntun murmushi yace "Ameera kinganni nan bana son karya ko kadan" sbd hka kada kimin karya. Ya tashi tsaye ya ciro kudi a aljihunshi yan dubu2 rafa 1 ya ajiye mata akan tebur ya fice, yana mai mamakin rayuwa irinta ameerah, dan shi ya dauka ba haka zea sameta bah, yana matuqar sonta amma yaga alaman kanta na rawa. Da wnnn tunanin ya isah gida, ita kuwa ameerah fita tai ta shiga dayan dakin, yanda sukayi ta baiwa bilal kudinshi ta kwashe sauran kayan ta kama hanya zuwa gida... [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 7⃣. Isarta gida keda wuya kuwa, bata tsaya ko inaba sea gidansu halima, ta shaidawa halima komai, halima tai shiru na dan mintuna kadan tukkuna tace "Bkomai zamuyi tunani akai amma ya zakiyi aure ynxn hajiyata"? Ki bari ki kammala shanawa mana (KUNGA ILLAR KAWAR BANZA). Halima ta cigaba da cewa "Ynxn ina nawa kasun"? Ameera ta ciro dubu 2 ta bata ta kama hnya zuwa gidah" tana isa Baaba rahane dke zaune kan tabarma ta tada kai ta dubieta tace "Allah ya shiryaki ameerah" (KUNGA RIBAR SAMUN MAGABATA NAGARI) wlh kiji tsoron Allah! Nidea addu'ahta a kullum itace Allah ya shiryaki" Ameera ta lumshe idanunta tace "Amin baaba" Wacece Ameera"? Ameerah Sadiq ne ainahin cikakken sunanta, su yan ainahin garin adamawa ne, a cikin yola, tsantsar fulani ne irin na daji din nn masu kiwon shanu, a cikin ruga suke, inda suke rayuwa mai inganci da kuma jin dadi, tare da mahaipinta Sadik da mahaipiyarta Salma. Rayuwa sukeyi dea2 hali, babu tsangwama babu wani takura, wata rana lokacin Ameera na yar shekara 6 baraye suka dira a rugar tasu, suka yi masu fashe, sanadiyar hka yasa sukayou birni a garin kano, kasancewar baaba rahane a nn take, kuma itace mahaipiyar baban ameera. Domin samun dan wani abu, amma kash! Akan hanyansu ta zuwa sukayi hatsari, suka rasu su duka, ameerah ce kawea ta tsira a cikinsu. Nn aka duba kayan jikinsu akagan address din gidansu baaba rahane aka kaita a chan. Baaba rahane itace ta rainie ameerah, tasata a mkrnta duk da ba wani karfie ne da itaba amma ta kula da ameera sosai. Ynxn hka ameera nada shekara 20 a duniya cib. Wnnn kenan... ©Kausar Luv💞 [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 8⃣. Da misalin karfe 4pm, Ameera jikinta duk yayi sanyi, tana xaune akan tabarma, halima ta shigo ko sallama babu, kusa da Ameera ta xauna ta dubeta wnda ameera ta riga ta fada a cikin duniyar tunanin dabama tasan haliman ta shigo ba. Halima ta bangajieta tace "Ke Yar iska lpy"? Ameera ta dubeta ta nisa tace "halima rayuwan nan fa damukeyi batada kyau, hakika batada kyau" ameera ta rike hannun halima ta fuskanceta tace "Halima ina tsoron abunda zan barwa bayana" halima tai tsakie ta cika hannunta daga jikin na ameera tace "Dallah banza kawea, ke wlh bari kijie duniya ce fa, ko kin deana tarihi zea nuna cewa kinyi, ko kin tuba mutane zasu rika kiranki da wnnn sunan, koda kuwa bayan shekara nawane, sbd hka kima bar wnnn zancen, bariki ynxn muka farashi kuma sai mun kaishi karshe" ameerah tai shiru na dan lokaci tukunna tace "ina bayanki" jirani inyi wnka mu fitah, ana tambayana pics kuma kinsan banda sabbi" halima tace "yauwa Yar gari shiyasa nake sonki wlh" (ILLAR TARAIYYA DA ABOKIN BANZA KENAN). Hka kuwa akayi ameerah ta fitoh a shirye, cikin wata riga da sket, pink in color, kayan duk sun matseta sosai har komai na jikinta ana ganinshi, kallo daya mutum zayyi mata yji wani abu a ranshi suka kama hanya suka fita, kai tsaye wani guri suka nupa, inda ake sabon gine2 masu kyau, wasu an kammala babu kowa a ciki sai masu gadi. A kopar wani gida, mai kyau suka tsaya, mai gadi suka tarar, ameerah tai masa sallama ta ciro dari 2 ta bashi tace "Dan Allah inaso xan danyi pics a gidan nn" mai gadin yace "babu damuwa amma kuyi sauri dan mai gidan ya kusa dawowa" gdya sukayi suka shiga aka fara daukan SELFIE. Tana cikin daukan selfie wani mutum na a bayanta har ta kammala bata lura ba. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 9⃣. Juyawan da xatyi suka hada ido, ya sakar mata wani irin lallausan murmushi, Ido ta zaro a fili, tsoro duk ya kamata, abunda ya bata mamaki sai taga mutumin yana daira, da sauri taja hannun halima suka bar gidan zuwa gidansu halima. Ajiyan zuciya ta sauke ta kallie halima tace "yau kam da AKAN SELFIE za'a dakemu". Halima tace "Ai dea mun kubuta" ba'a jimaba akayi kiran maghrib ba, ameera tai alawala tai sallah ta dawo ta zaunah ta bude pictures din data dauko ta fara dubawa, sunyi kyau sosai, amma abun mamaki sai ga mutumin nn ya fito a cikin pics din nn, dubawn da xatayi sai ta hango KUFATU ba kafafu. Nikam kausar tsoro najie nace "Hannefa usman dubamin ameera ko tai gamo da aljani ne AKAN SELFIE. Da sauri ta maida wayan ta Kefe kasa, ta murza idanunta ta kara dauko wayan ta duba, tagan again ga kufatu din nn, halima!!! Ameera ta hau kiran halima dake zaune a dakin, halima tace "yane wea"? Ko magana ameera ta kasa sea dai ta nuna mata wayan, halima ta xabura ta mike zaune, tace "Maza2 goge pics din nn" da sauri ta danna masu delete ta goge. Tare suka sauke ajiyan zuciya tukkuna ameerah ta fita ta zarce gidansu. Washe gari! Ameera na tashi daga bacci taga bakon abu a dakinta, ita dea tasan ta kwnta akan katifa to mai ya kawota kan gado"? Da sauri ta dau wayanta ta duba abun mamaki sea tagan pics din nn da tai deleting, hawaye ta farayi sosai tana kiran Allah!. Da sauri ta fita wajie sbd tsoro abun mamaki kuma tagan gidansu, hannun baaaba rahane ta janyou zuwa dakinta, ta nuna mata gadon, ita kuwa baaba rahane bata ganin gado katifa kawea take gani, datagakan hkn kawea sea ta fita ta bar ameera a dakin. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 10 Waiyyo! Na shiga 3! Yau mai nake gani hka"? Da sauri tai hanyar fita dakin abun mamaki kopar takie barinta fitah, nn take ameerah tajie juwa na dibanta, tana shirin faduwa kasah, nn ta fara karantu adduoi'h su ayyatul kursiyyu da dai sauransu, nn tke ta fara jin murya ana kiran sunanta, duk inda ta waiga bata ganin mai kiranta, gashin kanta datajie an taba, yasa ta waiga ta baya, nn ma wayam bbu mutum, ta cigaba da addu'ah (ADDU'AH MAKAMIN MUMINI) a kowanne hqli muka kasance kada muyi wasa da addu'ah. Wani ya baiyyana a gabanta da suffan mutane, hakn yasa ta kara firgita, cikin sanyin murya ya bude baki yce "N aljanine kuma ina sonki zan aureki, ni facebook friend dinki ne, kina burgeni, kina bani Sha'awa sbd duk photon nan da kike dorawa kina bude jikinki, musamman ma kirjinki, gaki da kyau, ga gashi, ameerah zaki aureni ko"? Ido ta kafeshi dashi, sirrrr! Sai ga ameera na fitsari a cikin wando tana kuka marar sauti sbd ta matukar razana. Tambayanta y karayi, wnnn karon ta dake zuciya, jiki na rawa na bari, tace "a.. A... A... A ina ka taba ganin anyi aure tsakanin mutum da aljan"? Budar bakinshi yace "Anayi mana, har haihuwa anayi ma kuwa, ni nn da kike gani yar adam 3 na aura, duk da suna auren wani namjin daban amma ni mijinsu ne, nakan hanasu tarawa da mazansu, su tsanesu, sujie basa son ko ganinsu, kinsan mai yasa"? Ameera ta girgizah kai, yayin da idanunta suka cika da hawaye fal. Inda aljanin yacigaba da cewa sbd "Sun kasance suna fitar da tsiraicinsu a fili, shiga toilet babu dan kwalli, babu addu'ah, Kwantawa bacci babu addu'ah, hkan yasa muke samun shiga jikinsu ta cikin sauki. Amma kinga masuyin Azkar to bama shiga jikinsu, Allah yana basu kariya.. Bit! Ya bace ya bullah ta bayanta, ameera na juyawa suka hada ido ta fadie kasa ta sulale sumammiya... Waiyyo aljani�������� AKAN SELFIE. SANADIN SELFIE SELFIE KO INA.... KOWA SELFIE...�� ©Kausar Luv.. [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 1⃣1⃣. Ta jima kwance a hka, tukkuna baaba rahane ta iso dakin, tare da kwanon towu a hannuta wnda ta dumama. Ganin Ameerah da tai kwance a kasa, yasa tai saurin ajiye kwanon tai maza ta karasa kusa da ita, ta dau kanta ta dora akan cinyanta tana kiran "Ameera"!!! Shiru babu amsa, fita tai a waje ta samu ruwa ta dawo dakin ta yayyafawa ameera a fuska, firgigit ameera ta farka tare da rungume baaba rahane tana kiran baaba rahane! Waiyyo aljani! Na shiga 3! Baaba rahane ya rungumeta sosai tare da bubbuga mata bayanta kadan2, tace "Ameerah ya akayi hakan? Ameera cikin muryan kuka ta hau baiwa baaba rahane labarin ynda abun ya faru, shiru baaba rahane tai tukkuna tace "AKAN SELFIE, duk hkn ya faru" "Ameerah mai nake fadamaki akan ki daraja jikinki, duk wani namiji daya gama ganin tsiraicinki to bazea aureki ba, ko yace zayyi tofa dadin bakine, itafa mace da kike gani Allah ya bata daraja mai girma, kmn hka, Allah ya bata daraja tazama DIYA! UWA! MATA! Da sauransu, wadda take itace ke haihuwan kowanne jinsi a cikin "ya yan Adam. Kinga addu'ah to ki kamata ameerah, ki killace jikinki. Ameerah ta fashe da kuka sosai tace "Wlh hkne baaba ngd sosai, in shaa Allah zan gyara. Allah yasa ameera Allah ya shiryaki, ameerah ta amsa da amin... [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 1⃣2⃣. A hka dea ameera tai wnnn wuni guda zungur tana ISTIGFAR! Tare dayin addu'ah, littafin HISNUl MUSLIM ta dauko tana azkar, duk wani kaya nata mai fidda tsiraici ta daukeshi ta zubar dashi, ta koma kaman ynda ake bukatan kowacce mace ta gari ta kasance. Hakika kowanne mutum da Allah ya hallita ya bashi karamci, babu wnda ya halitta dan iska ko dan banza sai wanda yasa kanshi, duk da kowanne dan Adam nada tashi kaddara. Ya Allah ka shiryamu akan tafarki madaidaici amin.. Karfey 12am, ameerah na zaune akan katifa tana nazarin abunda ke faruwa da rayuwanta. Kwatsam sai taji murya, ana kiran sunanta AMEERAH!!.. Addu'ah ta kamo a bakinta, yayin da wannan aljanin ya baiyyana a gabanta, addu'ah ta komayi. Aljanin daya dira gabanta da suffan mutum ya zauna kusa da ita yace "Ameerah! Allah yana jinmu, yana ganinmu yana kuma jin kukan mu. Ki kasance kina addu'ah, ynzn kam da kika kama addu'ah banda halin iya cutar dake. Bit ya bace, yyin da ameera ta sauke wata nauyayyan ajiyan zuciya. Ta kwanta kan katifanta tare dayin addu'ah, sai bacci. Washe gari! Ameera tai shirya tai wnka cikin riga da zane na atamfa, ta saka hijab dinta, simple make up tai, ni kaina kausar ta burgeni sbd yau na kara tabbatar da kyaun ameera na ainahi. Baaba rahane ta gaisar, baaba rahane tai murmushi ta amsa tare da cewa "Allah abun gdya, hakika Allah shine ke fitar da rayayye a cikin matacce ya kuma fitar da matacce daga cikin rayayye".... [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: ����AKAN SELFIE���� By Kausar M Hassan Page 1⃣3⃣. Ameera ta danyi murmushi tace "Baaba zanjie gidansu halima" baaba rahane tace "Sai kin dawo" A hnkli halima ta tashi ta kama hanyarta ta zuwa gidansu halima, amma koda ta isa bata nn, hkn yasa ta fito tare da tunanin inda zata tafie, tana cikin tafiya sea ta hango wnnn sojan, ameera ta tsorata lokacin datagan lallai shima ya ganeta kuma ita yake Kallo, jaa da baya2 ya sumayi shima sojan yana binta a baya, gudu ta sumayi iya karfinta bata ankara ba tajie ta fada a kan wani, da sauri ta waiga baya, suna hada ido ya sakar mata wani irin lallausan murmushi, da baya taja tana kokarin kaucewa, Mishbah yayi murmushi yace "Hajiya Ameerah, barka da wayewar safiya ya kyakyawan duniya" Murmushi ameera tai tukkuna ta danyi tsaye tana kallonshi sbd ta tuna karyar da tayi masa. Misbah murmushi yayi yace "Ameera ki deana boye2 pls, nasan komai na kuma yi bincike akanki sosai, ni mai sonki ne kuma mai kaunarki dan Allah, ni aurenki nakeo nayi idan har zaki iya aurena. Ameera ta nisa tace "Allah ya zabamana abunda ya zama mafi alkhairi a rayuwanmu amin.. Sojan daya kawo dea2 inda suke yyi daria yace "Oya let's do selfie ya dauko wayanshi yayi masu selfie sukayi wasa da daria tukkuna ya wuce. Su ameera kuwa hanya suka kama har suka karasa zuwa gida. Bayan sati 2. Shaquwa mai tsanani ta shiga tsakanin Misbah da Ameera, misbah yana kara mata haske akan yanda mace zata kasance ta gari. Komai nasu tsaf_tsaf abun ban sha'awa. Hka wasu satukan suka wuce, kauna da soyyayya na kara shiga a cikin zuciyoyin ameera da mishbah, inda itama halima Allah ya shiryata. Misbah ya aiko aka biya sadaki, aka kawo komai na auren aka kuma saa ranar auren watan gobe mai shigowa... Woo! Allah ya kaimu wnnn aure zamu dau selfie��, su misbah da ameera a angwance.... ©Kausar Luv�� [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 1⃣4⃣. Rana bata karya sea dai uwar diya taji dadi😝, Allah ya kaimu ranar wannan buki na Ameera da Misbah, inda akayi buki bada wata bidi'ah ba, walima kawea akayi, mu kam muna gefe, su rumah sune gaba2 gurin daukan selfie, jama'a gurin wnnn bukin kowa selfie yake dauka, amarya tayi kyau sosai su haleematu sune manyan kawayen amarya, abunda dai yayi kyau sosai, akayiwa amarya huduba aka kuma kaita dakin mijinta dake chann cikin manyan unguwanen masu kudin kano. A Chan gidanma ba'a barsu a baya, waya kawea ake dauka a dagata sama a karkace a tsuke baki, wasu kuma da selfie stick, chan na hango yan group dina na Facebook suma sunyiwa ameera kara tare da yan group din Deejah, naidaria nai nace lallai harkar ta manyan gayu ce. Hka dea aka barou amarya a dakin mijinta misalin karfe 9, bayan ango y shigo cikin shiga ta fararen kaya, ga wani kamshi na tashi a jikinshi mai dadi, tare da leda a hannunshi a yyinda ameera ke zaune akan gado, ta kudundune da hijabinta, murmushi yayi ya dafa kanta tare da yimata addu'ah tashi sukayi, suka daura alwala sukayi sallah raka'ah 2 suka godewa Allah, bayan sunyi hka misbah yayi murmushi yace ""Ameera gimbiyar mata ba sai na tsaya bata lokacinmu ba akan yimaki bayanin menene aure ba, fatana Allah ya bamu zaman lpy, ameera tace "amin" ya bude ledan dayazo dashi su naman kajiene da sauran abubuwa a ciki, a hankali ya dauko yana bata a baki tana ci kadan2 shima yana cin nashi, a hka har suka ci da dan yawa, suka shaa ruwa, misbah ya rage kayan jikinshi ya dauke ameerah ya dorata kan gado ya maida wutar dakin ya kashe. Bayan sati 2. A hka dea rayuwan ameera ta cigaba da kasancewa cikin jin dadi zaune suke akan dogowan kujera, inda ameera ta dora kanta akan cinyar misbah shi kuwa yana shafa gashin kanta kadan2, a cikin zuciyan ameera take cewa "Hakika babu rayuwan da takai ta aure dadi, aure shine hijab da kuma mutunci na kowacce ya mace, hijab sutura ne, jikinmmu kuma al'aura ne, hka kuma mu abun sone ga kowa, ya Allah ka kara bani zaman lpy nida mija amin" Chan misbah yaji shirun yayi yawa ya hura mata iska a kunne "Hey lpy kuwa"? "Em lpy lau" Murmushi yayi "Allah yasa" daria tai kadan tukkuna tace "Love2" da gudu ta tashi tai kitchen shima yabita yana daria.😄😍 [1/6, 7:59 PM] Kausar Luv💞: 📸📹AKAN SELFIE📸📹 By Kausar M Hassan Page 1⃣5⃣. Hka dea suka cigaba da rayuwa, yau fada gobe a shirya sbd kowacce rayuwa a hka take tafiya, Baaba rahane ta huta ita kam harda mai aiki aka dauko mata, aka gyara mata gidanta yayi kyau, yayinda ameera ta koma makarantar islamiyya da kuma boko. Hka dea rayuwan ta cigaba da tafiya, har Allah ya kaimu shekara daya da auren ameera da misbah, inda ta samu haihuwa ta haifie yaro wanda yaci sunan Abubakar Sadik suna kiranshi da Aman. A ranar wannan buki an chashe an kuma zuba selfie📸. Kasancewar a gidanta ta haihu, bata koma gidan baaba rahane ba. BAYAN KWANA 40! Suna zaune a daki suna hutawa, ga aman a gefensu sea kalle2 yakeyi, su kuwa sai wasu sakkoni suke aikawa junansu. Misbah aka kira a waya ya tashi ya dauka, yayinda ameera ta dauko wayanta tare da aman a gefenta ta fara daukan selfie, chann cikin camera din ta hango kaho, da sauri ta waiga, misbah tagani ya kyalkyale da daria yace "AKAN SELFIE". Itama din daria tai, yyin da misbah ya matso ya rungumesu dukansu yana shinshinar kamshin jikinsu mai ddi, wayanshi ya dauko yayi masu selfie, sukayi daria sosai cikin so da kaunar junah. ALHAMDULILLAH!!!!!!!!!!!!!!!! A nan wannan labarin na AKAN SELFIE yazo karshe, fatan yan uwa munsamu darasi mai yawa a cikin wannan labari... +2347067465637.. Comments only... Sadaukarwa Novel din nan takie ce AMEERA (Mss Ameera) Takie tafi ta kowa SWT UMMI AYSHA, kinfi karfin kawa a gurina, sbd kin zama yar uwata, ina gaisheki sosai. Amarya ga mai hula... Kawata Aisha Muhammad (Maman shakur😘) , just loved it when u smile dear... Yar mutan zaria.. GODIYATA GA YAN GROUP NA: KAUSAR LUV NOVELS(FB) DEEJAH ABDUL NOVELS(FB) AYSHA YA'A KURA NOVELS (FB). DUNIYAR MAKARANTA 1&2 MIEMIE BIE NOVELS "YAN UWANA MARUBUTA IRINSU Phertymah (Pherty) Haleematu lawal bala(Sardy) Fido sodangi Futhalkhair Khairat up Munay Miemie Bie Rumah Zynv Rumah Da sauransu, Duk Na gaisheku.. Masoyana ina gdya gareku sosai, domin kuwa kune ni, masu karatun novels dina ina yimaku fatan alkhairi... Sai kunjini a sabon littafina In shaa Allah mai suna HAUWA_JIDDA. xuwa bayan sallah... Happpy Ramadan in advance. Allahumma baligna Ramadan amin... ©Kausar Luv💞 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *