Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, March 22, 2017

Al'adun wasu

adsense here [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿1 Batul Mamman(Mrs)💖 Bismillahir Rahmanir Rahim Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu yara suka fara binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa baya rabo da yar tsarabar da zai kawo musu. Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu sakamakon zarton da ya fada kai har ya tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka ce hannun ya mutu dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. Da dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya mikawa yaran. Suna ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka hada ido da wani matashi a layin. Da sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade jikinsu. Baban yara barka da yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba Sani. Yanzu don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas so kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza kai. Kayi hakuri in Allah Ya yarda bazamu sake ba. Yayi murmushin takaici Allah Ya bada ikon denawa. Kuna ta batawa kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. Na tabbatar babu wanda zai so nan gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa. Sani ya dan yi murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin ya murde. Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta kuce gado ne. Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu. A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. Mal Bashir ya dauko naira dari ya mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan Baban Yara? Darin da ka bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi zata je karbo sakamakon jarabawarta. Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau daya banga fitowarta ba. Mal Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama. Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai ta tashi da gudu ta shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa. Ummanta ta soma fada ke lafiyarki kuwa. Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan. Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji sallamar ba. Takalmansa ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin sallama ta tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin jikinsa. Yace da Umma ta karbo sakamakon jarabawarta kuwa?Umma tana kwashe yakuwarta ta ce bana jin amma ga wasu takardu can akan taga wanda Hajara ta kawo mata dazu. Mal Bashir ya tashi ya dauko a sanyaye...ai tunda ta gudu yasan bana ma bata kitsa abin arziki a makaranta ba. Ai kuwa yana budewa yaga abin haushin da yasa rai da gani. Ta 48 tayi cikin su 52. Ransa ne ya sosu. Ya rasa yadda zaiyi da yarinyar nan. A fusace ya tashi ya tafi kofar bandakin. Zuhra me kike yi ne ya tambaya da daga murya. Daga ciki ta ce ehem ehem! Ya sake bugawa idan ba so kike na bude ki ba gara ki fito tun wuri. Zuhra ta gwammace ta yini a bandaki da ta fito ta sha fadan Baba. Ta sake cewa ehem..... ya ce bari na fita tunda mun koma wasan buya da ke. Sai da ta kara kusan minti biyar sannan ta fito duk ta hada gumi. Ta dubi Ummanta, wai yau da Baba ya kamani bansan....saukar rankwashi taji a tsakar kanta ta durkushe a kasa tare da rike kan ta soma kuka. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿2 Batul Mamman(Mrs)💖 Baban Yara yace idan baki rufe min baki ba sai na kara miki. Da kuka Zuhra ta mike tsaye tana turo baki ko saboda rankwashin nan ba dole na kasa kokari ba. Idan kana taba min mandula oblongata dina haukacewa zanyi nan gaba kadan. Baban Yara yace kece mandular ai. Nan kika fi kauri dama. Kin iya haddace 'yan kalmonin turanci kizo kina barazana dasu kamar wata wadda tasan abinda take yi. Zuhra dai kuka ta cigaba da yi har sai da Umma tayi mata tsawa. Wallahi idan kika tara min makota yau jikinki sai yayi tsami. Jin haka ta soma tsalle tana kara kukan. Baban Yara yace bari na dauko wayar chaja na yi miki mai dalili. Ai kamar anyi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan. Takardun jarabawarta da aka hada da report card din ya soma dubawa. Wasu har zero ta ci. Maths(lissafi) tace arbain da takwas, Arabic tace casa'in da hudu sai Hausa ta taci sabain da daya. Dama sune darrusan da suke dan taimakawa bata daukar ta karshe gaba daya. Sai ko rubutu da ta iya mai kyau idan ka gani zaka dauka na wata mai kokarin ne. Yana dubawa yana tsaki sai daga baya ya kula da yadda take rubuta suna. Kansa ya rinka girgizawa kawai don takaici. Ko shi da iyakarsa aji hudu a secondary ga shekaru sun mika amma yasan idan suka shiga aji shi da yar tasa sai yafi ta kokari. Zo nan ya yi mata tsawa. A hankali ta ja kafa ta je ta tsugunna a can gefe. Yanzu kin tabbatar duka takardun nan naki ne? Nawa ne Baba duba sunan da rubutun mana. Yace ai na duba. Wasu ki rubuta Zuhra Bashir wasu kuma Fatima Bashir don tsabar rainawa malamai hankali. Yana cigaba da dubawa yayi karo da wata. Takalminsa ya raruma ya kwada mata. Ya daga takardar yana nunawa Umma. Kinga wulakancin yar nan wai Fatima Basiru. Ya nuna kansa nine BASIRUN??? yadda yayi yasa ta soma dariya Umma tace Allah Zuhra zanci mutumcinki. Ana miki fada kina wa mutane dariya don shakiyanci. Zuhra ta kara matsawa gefe tana sharar hawaye to ba haka naji su Kawu Sabiu da Innar Ajingi suna kiranka ba. Baba ya cije lebe saboda takaici. Da kika ji sun fada ba sunan gida bane?. A nan wa kika taba ji ya kirani Basiru? Tace to yi hakuri wallahi daga yau na dena. Ki ma kara ya fada yana tattare takardun. Yana yi yana mita. Yarinya sau nawa ana miki repeating gashi kin kusa shekara ashirin. Amma kanki kamar kifi, nasan duk ajin kece mamansu ko. A'a Baba ga Hajara, ka manta ajinmu daya. Yace ina fa zan manta...an tara dakikai biyu a aji daya. Baku da aiki sai cin awara da wainar flawa. Zuhra da baki baya shiru tace to ba kai kake bani kudin ba. Umma tace kaga ka dena kula yarinyar nan sai jininka ya hau. Takardun ya miko mata jeki ki ajiye min a dakina. Ni ina ta kokarin hada kudi na biya miki kudin WAEC saboda kada a rufe amma naga kamar asara zanyi. Sau biyu kina qualifying din nan amma kin kasa hada credit uku. Zuhra tasan yadda babanta ya damu tayi karatu amma duk yadda ta dage a cewarta ko kadan bata ganewa. Zama tayi kusa dashi kaga Baba kawai ka kaini makarantar koyon sakar nan. Har na tambayo matar tace a wata biyu zata koya min sau uku a sati zani. Kuma a dubu shida. Ai kaga yafi sauki akan WAEC din. Ta nuna kanta ni da ka ganni bani da abinci a boko. Kan baya dauka yadda kasan an zuba dusa a kwakwalwar haka nake. Shi din ma ya kusa dariya sai ya dan dake. Tashi ki bani wuri ni. Ko damuwa ba kya yi yan ajinku zasu tafi makarantun gaba ke kina son koyon saka. Ta dan tura baki to ya zanyi Baba. Suma fa duk harkar ta koma satar amsa. Idan sakar ma bazata yiwu ba kawai kayi min aure ka huta. Shi da Umma a tare suka yo kanta suna mata fada. Da gudu ta tashi tayi hanyar waje tana dariya tare da jan mayafin Umma a igiya. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿3 Batul Mamman(Mrs)💖 Mal Bashir Ibrahim mutumin Ajingi ne ta jihar Kano. Su biyar ne maza a gidansu shine na biyu. Mahaifinsu manomi ne kuma yana kiwon shanu da tumaki. Da farko sun fara karatu har ya kai aji hudu a makarantar gaba da firamare sai babansu ya matsa akan basa samun lokacin taimaka masa a gona. Shi a son ransa duk su hakura da karatun. Ko kadan Bashir baiji dadin hakan ba, sai da ya hakura shi da wansa da mai bi masa suka koma gona. Sauran biyun suka cigaba. Akayi rashin saa autanma ya dena zuwa don shi yafi son kiwo. Wanda ya karasa kuma kan nasa kamar na Zuhra. Ba wani sakamakon kirki ya samu ba. A halin yanzu ma masinja ne a wani company. Mal Bashir ya dawo birni shima aikin kafinta a nan ya hadu da Atine yar kwanar Diso ya aura.sun jima basu sami haihuwa ba gashi yana da son 'ya'ya ,sai daga baya aka haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Mal Bashir kuma sunan Atine shiyasa suke kiranta Zuhra. Zuhra na fita gidansu Hajara ta nufa tana ta mita ta jawo mata fada a gida. Da sallama ta shiga sai dai babu kowa a tsakar gidan. Daga dakinsu Hajara ta ji an amsa ta shiga. Kwalliya Hajara take yi anyi wankan yamma tana shirin fita unguwa, mudubi ne a hannunta tana zana gira. Zuhra ta sakar mata dundu a baya...shegiya kin hada min zafi a gida kin zauna kwalliya. Hajara na sosa bayanta suka ji muryar mamanta. Ta shigo dakin haba Zuhra sau nawa za'a hanaki zagi ne? Zuhra ta sunkuyar da kai tana hararar Hajara. Mama tace idan na sake ji Allah da yayanku Lawal zan hadaki. An kwana biyu ba kiji bulala ba shiyasa kika dawo da yi mana zagi. Zuhra tace don Allah kiyi hakuri na dena daga yau In sha Allah. Mama tace da kin kyautawa kanki sannan ta fita. Hajara ta cigaba da kwalliya suna hira tace ke ni fa Sahabi ya dage sai nayi karatu. Yace zai rinka yi min lesson kafin a fara WAEC don har ya biya min kudin a wata makarantar. Zuhra tayi dariya zaiyi asarar kudi da lokaci kenan. Baki fada masa kina sahunmu bane? Bana son wulakanci wallahi tunda na fahimci yana son nayi karatu na soma dagewa. Wannan karon mutum shida na doke harda ke. Zuhra ta daga hannu alamar jinjina kaga su Fropesa Hajara kenan. Hala irin su Ligan dinnan zai nema miki. Kanwar Hajara da ke tsakar gida sai dariya ta leko ta taga...Yaya Zuhra kin fiye abin dariya. Wai Ligan...Legal ake cewa. Zuhra ta hade fuska tace in ba tsoro ba ki shigo dakin nan ki fada mana kiga yadda zanyi dake. Marar kunya kawai. Hajara ma dai dariyar take ta dauko dankwali zata daura. Sai da ta daura wani dakal dakal din mayafi karami. Ta daure shi da ribbons har biyu manya sannan tayi dauri. Daga karshen daurin ta zaro wani ribbon din mai gashi dogo daga jikinsa ta makala taga ya zauna sosai sannan ta tura shi a jaka. Duk abinda take idanun Zuhra kyam a kanta. Tace Hajara gashin doki kika koyi sawa? Da sauri Hajara ta toshe mata baki. To sarkin karadi kada ki fada da karfi sai na fita zan saka. Zuhra tace wallahi babu kyau kuma kema kin sani. Ga acuci kin dora wannan wari ma ya isheki. Hajara tace ke ba yau zan saka ba fa. Yanzu ma gidan Anti Faiza zani tayata aikin abincin da zasuyi a makotansu. za'ayi party ne a gidan. To gobe zansa idan zaa wurin party din. Zuhra tace happy bazday tuyu zasu yi? Oho nima ban sani ba. Tace dai yan gayu ne a gidan. Zuhra tace duk da haka bani gashin na kona ko na fadawa Mama. Da kyar Hajara ta bata ribbon din. Za ta fita Zuhra tace ke kamar kwailin kike ko, kinga fuskarki kuwa? Sai yanzu na lura. Hajara ta dora hannu a ka. So kike dai Mama taji tayi fada kike wani daga murya. Kuma bleaching ake cewa ba kwailing ba kalmar ko dadin ji babu. Tana murmuahi tace wani mai na samu mai dan kyau na gyaran fata. Kinsan tunda biki ya matso gara na shafa na dan washe. Zuhra dai tabe baki tayi...wallahi Hajara ki kiyaye sabon Allah. Ga acuci, ga bleaching ga karin gashi. Shi Sahabin zaki ha'inta da farin karya ko danginsa. Naga dai duk a unguwar nan kuka tashi to meye basu sani ba. Karasa hada jakar tafiyarta tayi tace to malama zuhra idan kin gama waazin ki zo ki rakani bakin titi. Kuma wallahi kika fadawa su Mama sai munyi fada. Zuhra tace mun dade bamuyi ba...ni akan irin wannan ba sai dai aji kanmu ba. Lokaci guda kika tsiri irin wadannan abubuwan kawai don zakiyi aure. Hajara tace to in kinji haushi kema ki fitar da miji mana. Ran Zuhra ya soso ta dan yi murmushi miji dai Allah ke bayarwa. Kuma da yardarSa idan na tashi aure sai na sami miji na gani na fada. Daga nan tayi tsaki ta fita Hajara na kiranta tana bata hakuri. A tsakar gida suka tarar da Mama tace har anyi fadan ne kajin Mama? Ku zo nan...suna harare hararen juna suka durkusa gaban Mama. Tace duk naji abinda kuke fada. Ke Hajara akan an fada miki gaskiya kike gayawa yar uwarki magana ko? Duk canjin halin da kika koya yan kwanakin nan ina lura dake. Shiru nayi so nake farin naki yafi haka yawa sannan nasa yayyanki maza suci ubanki a gidan nan. Zuhra ta kwalo ido....lah Mama kema zagin kike yi. Mama tace ban kuma ce kiyi ba, nima kuskure ne. Ta cigaba da yiwa Hajara fada kije gidan Yayar taku ki dawo zanyi maganin rawar kan nan naki. Ita ma ba kyaleki zata yi ba kin sani sarai. Idan na sake jin kuna fada kuma ni daku ne. Ki wuce ki rakata ta hau adaidaita tace da Zuhra. Sum sum suka tashi suka fita. Zuhra ke rike da jakar kayan amma har suka je titi ko tari basuyi wa juna ba. Sai da adaidaita sahun ya fara tafiya Hajara ta leko tana dagawa Zuhra hannu. Itama dagawa take tana tambayarta yaushe zaki dawo. Hajara tace sai yanzu zaki tambaya? Kwana goma zanyi.....Zuhra harda dan hawaye ta koma gida. Irin wannan fadan sun saba yin shi da Hajara. Sai dai suna sake haduwa zancen ya wuce kenan. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿4 Batul Mamman(Mrs)💖 Hajara na sallama gidan yayarta ta hadu da babban dan Anti Faiza Abba zaune a bakin kofar gida. Hannunsa ta gani a nade alamun gyaran karaya ko gocewar kashi. Yana ganinta ya rungumeta A dan tsorace tace Babana me ya sami hannunka? Yace fadowa nayi daga kan babur din Baba. Ba dai hatsari kukayi ba ko ta tambayeshi suna shiga cikin gidan. Yace a'a jiya ne da daddare na hau sai na fado. Anti Faiza na jin muryarsu ta fito tana mata sannu da zuwa. Tace kafin ki fara korafi jiya abin ya faru ni kuma bana son tadawa Mama hankali sai ya dan ji sauki. Hajara tace ba komai Allah Ya sauwake. Sauran yaran uku suka zo suna mata sannu da zuwa. Mai bin Abba ce ta kalli Hajara da kyau sai tace Anti Hajara kinga fuskarki tayi fari, kafarki kuma baka. Ko kema mai bleaching ce irin ta fim dinnan.... Gaban Hajara ya fadi, Anti Faiza ta bar raba kayan wanki da take yi tace bazaki make mata baki ba kina jin abinda take fada. Nabila ta ce Allah ki kalli kafarta da fuskarta ki gani. Anti Faiza ta taso zata kaiwa Nabila duka sai taga Hajara na jan siket dinta tana kara rufe kafa. Anti Faiza tace su fita tana mata wani kallo. Gaba daya cikin Hajara ya duri ruwa. Tun kafin ta tambayeta tace wallahi Mama tayi min fada dazu kuma bazan kara yi ba. Anti Faiza tace da kina hauka ne kika fara shafe shafe. Ta fizge jakar kayan Hajara ta zazzageta a wurin tana duba kayan tana fada. Hajara a hankali ta gode Allah da Zuhra ta karbi ribbon din mai gashi a jiki. Anti Faiza kuwa ta kare mata tas sannan tace ke da Zuhra kuke yi ko? Hajara tana matsar kwalla tace a'a ni kadai ce. Ba wani nan, abokin barawo ai barawo ne kuna tare wata rana zata koya ne. Ta fara laluben wayarta. Zan kira Umma ince a turo min ita ko zuwa asabar ne in ja muku kunne da babban baki. Ba don hannun Abba ba ai gidan zani na hada ku. Wato kun girma zaku nunawa duniya baku da mafadi. Ita dai Hajara sai bada hakuri take. Bayan kwana biyu Zuhra na zaune kan karamar kujera a kofar kitchen Umma na ciki tana duba miya da yar karamar fitilarta gwamnati ta gaza. Zuhra ta rike ciki ta fara waka. Dan kanzo Iya ko dan dago dago Iya yunwa bata da hankali Iya yunwa taci mutum tara Iya..... Umma tace Zuhra ko in miko miki kwano ne? Ta washe baki Umma kin gama girkin. Umma tace a'a wai da ki tafi makota bara. Baki Zuhra ta turo tana rike ciki ni shiyasa bana so kice zakiyi girki Umma musamman tuwo sai ki dade. Miyar nan tun kafin magariba kika dora gashi har an idar da isha. Umma tace ni kuma kinga bana son danyen girkin nan naku. Sai ayi tuwo da miya cikin rabin awa. Suna magana Baban Yara ya shigo. Zuhra tana matse ciki tana masa sannu da zuwa. So take yasa Umma ta kada miyar haka. Dariya yayi musu ya shige ciki. Ga mara juriyar yunwa , ga mai dadewa a girki. A falo suka zauna suna ci. Da yake ba wuta Zuhra kasa jira tayi nata tuwon ya huce tasa mafici tana fifitawa tana ci. Ta cika baki da tuwo tace Ummana kin iya girki sosai sai dadewa. Umma tace bazaki yaba min ba sai kin hada da mita. Wannan mijinki sai yayi da gaske wurin noma. Baba yace to dai kada ki takurawa babata. Ya fito da wata leda daga aljihunsa. Ya danne ta da dungulmin hannunsa sannan ya bude da dayan ya dauko gasashshiyar kaza. Umma tace yau dadi zamu ci BabanZuhra. Yace Ya'u ne ya siya shine ya debar min yace na kawowa Zuhra. Dadi ya kamata taje ta durkusa a gabansa. Cinya ya dauko mata da fikafiki biyu. Ta karba da murna ta koma wurin zamanta. Kamar ance ta daga kai ta hango hannuwan iyayenta a gefen kwano suna kokarin raba wuya su ci. Duk zumudin da take a lokacin wani daci taji a wuyanta. Hawaye ya sauko mata tayi saurin gogewa. Ta dan gutsiri naman kadan tace washhhh. Umma tace kin kone ko? Dama cin abinci kin kasa jira ya huce. Zuhra tace hakori na ne yake min ciwo daga nasa naman a baki. Baba yayi mata sannu. Ta tashi ta mayar da duka naman gashi ku cinye bakina zafi. Baba yace ki ajiye zuwa gobe mana. Idan ya lalace ai sai nayi kuka Baba. Ta dauki tuwon bari na kai kitchen bazan iya ci ba. Ta fice tana fifita baki. A bakin rariya ta tsuguna ta cinye tuwonta ta wanke baki. Umma tace ya naji shiru ko bakin ne. Tace a'a almajiri na nema a waje. Wuraren shadayan dare su Umma sun kwanta Zuhra ta lallabo ta fito falo. Tayi sa'a kuwa ledar naman tana nan kan dan tebur din da suka ajiye tare da jug din ruwa. Zuhra ta bude ledar a hankali ta sami yan kasusuwan da basu cinye ba duk ta tsotse don naman yayi mata dadi. Baba ya taso Umma suka tsaya ta yar kofar jikin tagar dakinsu suna kallonta. Hawaye Umma take sosai a hankali tace bar mana tayi muci. Baba yace muna tausayinta tana tausayinmu. Allah Ya albarkaci rayuwarki Fatima. Suka koma suka kwanta. Da safe Umma ta riga ta tashi. Ta fito suka gaisa ta dauko tsintsiya zata fara shara. Umma tace kamar na bar ledar naman nan a falo. Zuhra ta dan tsorata sai tace ai da asuba na dauke saboda beraye. Umma tayi murmushi kawai ta fita tsakar gida. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿5 Batul Mamman(Mrs)💖 Kafin karfe tara ta gama duk ayyukan da zata yi. Wanka tayi sannan tayi shirin islamiyya tunda asabar ne ana yin ta safe. Ta gama shirinta tsaf ta yiwa iyayenta sallama ta tafi. A darasi na uku Malama Rabia ta shigo. Ita kadai ce mace da ke koyarwa a islamiyar tana koya musu Nahawu. Zuhra jira tayi sai da aka kammala darasin gaba daya sannan tace tana da tambaya. Yan ajin har sun soma dariya sannin halinta. Wata tambayar idan tayi sai kaji kamar shirme. Ita kuwa sai ta dake, sai an bata amsa tace nasan ku ma kun karu. Malama Rabia tace ina jinki Fatima. Zuhra tace menene hukuncin macen da ke karin gashi ko bleaching a musulunci. Malama tayi dan murmushi ai hukuncinsu a bayyane yake, babu kyau. Zuhra tace ai nima nasan babu kyau ina nufin akwai wata aya ko hadisi da yayi nuni an hana ko kuwa fatawar malamai ce kawai. Malama Rabia tace to bari mu fara da maganar karin gashi tunda shi tabbas akwai ingantattun hadisai a Sahihul Bukhari da Sahihul Muslim da suka nuna anyi hani da yinsa. Manzon Allah SAW yana cewa Allah SWT Ya tsinewa mai karawa wata gashi da wadda tace a kara mata. Ki duba hadisi na 5934 a Bukhari da 2122 a Muslim. A wani hadisin kuwa, Asma'u bint Abubakar(RA) tace wata mata tazo wurin Annabi SAW tace masa ta aurar da yarta amma lalura tasa gashin kan yar ya zube. Shin zata iya saka mata gashi? Sai Annabi SAW yayi kashedi ga mai karin gashi da wadda aka karawa. Bukhari 5479, Muslim 3962. Malamai sun dauki karin gashi a matsayin yaudara sannan suka yi hani dashi. Akwai hadisin Mu'awiyya RA wanda yace Annabi SAW yace karin gashi yaudara ce. Sahihul Bukhari 3229. Ta koma ga sauran daliban gaba daya. Ku kanku a ma'aunin hankali kunsan cewa akwai ha'inci a karin gashi. Banda asarar kudi da kuma warin da yake yi a kan mai sawa. Sannan duk mai karin gashi bata taba rufe kanta gaba daya domin tayi ne don a gani. Asali ma a shekarun baya muna ganin mace da karin gashi mun san ba musulma bace. Sai gashi a hankali mun dauki al'adu da dabiun wasu muna yi. Allah Ya shirye mu baki daya. Sai tambayarki ta biyu akan masu shafa mai su canja kalar fatarsu daga baka ta koma fara. Wasu masu zalamar ma fararen ne suke kara kode fatarsu. To duk wannan yana cikin nau'in canja halitta wanda Allah Ya hana. Shaykh Ibn Uthaymeen yayi bayanin canja kalar fata na dindindin kamar bleaching a matsayin laifi kamar masu yin tatoo(zane da wuta ko abu mai kaifi a jiki) da kankare hakori ayi wushirya. Irin wadannan laifukan Annabi SAW ya sanar damu tsinuwar Allah ta tabbata ga masu yinsu. A bangaren lafiya kuwa munsan cewa babu wani nauin bleaching wanda bashi da illa ta kusa ko ta nesa. Wanda munsan Allah Ya hana mu cutar da kawunanmu. Ga zubar da mutumci da kimar mai yi a idon wadanda suke da hankali suke amfani dashi. Ga asarar kudi da sauran abubuwa marasa kyau. Allah Shine mafi sani daga kurakuran da muke aikatawa. Allah Yasa duk abinda zamuyi mu tsaya a iyakar da Yayi mana. Laifukanmu kuma Ya Yafe mana. Gabadaya ajin suka ce Amin. Jikin yan matan duk yayi sanyi saboda ba'a rasa masu dan shafe shafe da masu dora gashi ko da a jikin acuci ne irin na Hajara. Zuhra tayi godiya ga Malama Rabia sosai. Duk bayanan da tayi kuwa ta rubuce su a yar takarda wanda zata nunawa Hajara shaida. Ta so ace Hajarar na nan tayi tambayar. Daga kofar daki 'yan matan biyu suka ce Mama mun tafi. Ba tare da ta dago kanta daga laptop din gabanta ba tace Allah Ya kiyaye hanya ku gaishe su. Shiru taji ba amsa...tana dagowa taga sun tafi. A ranta tace na rasa saurin me yaran nan suke yi haka. Hajiya ta fito daga dakin Alhaji taji karar mota. Sauri tayi kada su tafi ta basu sako su siyo mata a hanya idan suna dawowa. Kayan da ta gani a jikin Adabiyya ne yasa ta kara sauri tana kwala musu kira. A tsorace Adabiyya mai shirin shiga mota ta juyo. Hamida tace shikenan mun gama yawo. Ko kadan ba haka suka so ba. Hajiya na dakin Alhaji suka ki zuwa yi mata sallama. Ita kuma Mama daga bakin kofa suka yi mata basu bari iyayen nasu sunga kayan jikinsu ba. Hajiya ta fito har wajen rai a bace tace duk su shigo ciki. Mama ta fito daga daki tace Hajiya lafiya? Kafin ta bata amsa yaran suka shigo. Ya Salam...Hamida? Adabiyya? Meye hakan kuma? Hajiya tace kema basu ce miki zasu tafi ba ko. Nima karar mota naji na fito da sauri ashe rabon idona ya gane min ne. Hamida yar shekara ashirin da biyu jeans ne a jikinta da top wadda ko rabin cinya bata rufe mata ba. Duk ta dameta sai tayi rolling da karamin mayafi. Adabiyya mai shekaru shatara kuwa skirt ne a jikinta amma itama ya matse har shatin pant dinta ake gani. Shima don tafi yayarta jiki ne ta saka. Sai riga matsatstsiya karama har da wata belt a samanta an kara tamketa. Da dan karamin mayafinta. Hajiya ta kalli yayansu Nura. Kai mahaukacin ina ne da kana ganin sun fito a haka kake shirin jan mota. Ku fada min gaskiya ina kuke shirin zuwa. A tare suka ce gidan Yaya. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿6 Batul Mamman (Mrs)💖 Mama tace ni na rasa gane me ake yi a gidan Yayan naku ne? Jiya kunje kun ce aiki zaku taya Izzatu yau ma kun ce aikin zaku kara yi. Ko packing suke yi ne zasu tashi bamu sani ba, ta zauna akan kujera kusa da Hajiya tace ni a iya lissafi na ma ai sai karshen August za'ayi birthday din Nana. Kuma ita ce ta rage anyi na yayyenta. Hajiya ta tabe baki kina ma kokarin rikewa. Sun mayar da birthday tamkar wata ibada. Duk shekara sai anyi sau uku a gidan. Allah Ya kyauta. Mama ta ce Nura fada min gaskiya me ake yi. Indai birthday ne an saba yi mun kuma hakura mun zuba ido. Tunda shima Hamzan bai ji maganar mu su dena ba ai matarsa bazata ji ba. Shiru yayi har sai da Hajiya ta daka masa tsawa...baka ji ana tambayarka ne? Adabiyya ta soma kuka dama ita akwai tsoro tace Hajiya party din wedding anniversary zasu yi na shekara goma da aure. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda su Mama ke fada. Hajiya ta mike tsaya tana magana a hankali...lalacewar Yayanku har ta kai nan? Allah Ya shirya. Daga nan dakin Alhaji ta koma ta cigaba da gyarawa. Mama ta dubi yaran. Yanzu don Allah waye ya ce ku saka irin kayan nan? Yaushe ma kuka siya? Adabiyya tace jiya da muka je ne Anti Izzatu tace kananan kaya zamu saka yau. Shine muka ce bamu da masu kyau. Sai ta kaimu wani kanti ta siya mana. Mama tace eh lallai yarinyar nan bata nemawa kanta zaman lafiya a gidan miji. Shirun da taga munayi don bama son zama iyaye masu sa ido a lamarin gidan 'ya'yansu ne. Amma wallahi idan na bullo mata ta bayan gida sai ta gane karyar rayuwar turai take yi. An gayyaci su Mariya? Hamida tace eh duk su biyun. Har Yaya Ibrahim ma an gayyace shi da Anti Umma. Mama tace suma duk kananan kayan aka ce su saka? Hamida tace bamu sani ba. Mu da kannenta tace mu saka dai jiya. Mama tace duk su je su canja kaya tana zuwa. Nura yace harda ni Mama? Ta harare shi ban sani ba. Dakin Alhaji ta shiga ta tarar da Hajiya a zaune a kan gado tana kuka. Mama tace haba Hajiya kukan iyaye ga 'ya'yansu bai taba zama alkhairi ba. Hajiya ta share hawaye da gefen dankwali. To ya zanyi Kaltume? Yaron nan ko kadan ban goyi bayan zuwansa Canada karatu ba amma Alhaji ya dage. Karshe yaje ya hadu da mata itama tashin can. Mama tace shekara hudu fa kawai suka yi da babanta yaje aiki. Hajiya tace to ai dai ta zauna ko. Gabadaya sun dauko wasu al'adu daban da namu. Wadanda basu dace da addinmu ba. Kina kallo duk shekara sai sunyi party nasu da na yaransu. Sati kusan uku da suka wuce ba ya kawo mana laces ba wai na Mother's day. Na Alhaji kuwa na Father's day ai kinga bamu taba gaya masa dalilin bayarwa ba kila da zaginsa zaiyi ma. Duk wata rana da turawa suke bawa mahimmanci Yaya da matarsa suna yi. Ko da ba kowanne muke gani ba amma munsan anayi. Su a dole rayuwar turawa sukeyi. Mama tace kiyi hakuri yanzu zan kira shi a waya yazo. Dole mu sake masa magana ko mu hadashi da Alhaji. Wannan karon sun wuce gona da iri tunda suna son batawa yaranmu tarbiya. Hajiya tace Allah Ya shirya mana. Amma don baki ji yadda raina ke baci ba idan su Khalifa na kirana Granny dinnan. Mama ta kwashe da dariya. Ai gara naki ma. Nida ake kira Grams fa. Yau da bamuyi boko ba ai da mun sha kunya tunda sai kiyi musu magana ma amma su amsa da turanci. A dole sai an bambanta su da 'ya'yan yan uwansu. Sani masinja ya dauki wayar landline din office dinsu da aka kira. Muryar mace yaji tace matar Hamza ce. Ji yayi tana kuka tace ya fada masa Junior ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Sani ya tashi da sauri sai ya tuna meeting din da suke yi mai mahimmanci ne. Har ya koma ya zauna ta sake kira a fada masa yanzu ya taho gida. Ta kira wayarsa a kashe. Dole Sani masinja ya shiga hall din da ake meeting din. Architect Hamza Nasir Hamza ya juyo a fusace yace meye haka Sani? Manyan baki gareshi turawa masu son hadin gwiwa da kamfaninsa na zane da ginin gidaje da hotels da sauran manyan gine gine. Sani masinja yace ranka ya dade uwargida ce ta bugo tace Jiniya ya fado daga kan kujera ya karye a hannu. Hamza ya tashi da sauri....what? Ya dubi bakinsa yace da turanci kuyi hakuri dana ne ya karye a hannu. Sun tausaya masa suka ce zasu dawo a karasa meeting din. Amma ya daure yasa hannu a takardar shaidar amincewarsa da sharudansu. A gaggauce ya karanta ba tare da ya fahimci kalma ko daya ba yasa hannu a duka biyun. Daya tasu dayar ta kamfaninsa. Sunji dadin amincewarsa sosai suka tashi. Yana ta sauri a hanya wayar Mama ta shigo. Ya dauka a gigice a zatonsa Izzatu ce. tace Yaya kana ina ne? Mama ke ce? ina hanyar zuwa gida. Tace to maza kazo ina son ganinka. Yace Mama Izzatu bata kiraku bane? Junior ne ya karye a hannu. Yana hango wani dan sanda ya nufo motarsa saboda yana amsa waya yana tuki da gudu yaja motar kafin a bada hannu har ya kusa karawa wani. Mutane suka bishi da zagi da bakaken maganganu. Mama ta dubi Hajiya tace bamu ga ta zama ba wai Junior ya karye a hannu. A tare suka fito daga dakin suka kiran Nura yazo ya kaisu gidan Yaya. Hamida tace Mama me ya faru? Junior ne ya karye a hannu. Yanzu yayanku yake fada min. Adabiyya tace ba gaske bane. Jiya ne Anti Izzatu tace bata san da yadda zata sa Yaya ya baro office da wuri ba. Partyn surprise take son yi masa. Bai san komai game dashi ba. Ana haka wata makociyarsu da aka bawa aikin meatpie ta shigo take cewa danta ne ya karye kuma ya kwana da zazzabi shiyasa bata aiko ta karbi kayan yin meatpie din ba. tana fita ne shine Anti tace ta sami idea din abinda zata fada masa. Hajiya ranta ya kara baci. Mama kuwa ashar ta dannawa Izzatu saboda yadda zuciyarta ke mata zafi. Ta kalli su Hamida duk sun saka material ne da mayafansu manya tace Nura ya kaisu amma ya fadawa Yaya tana son ganinsa komai dare. Sai bayan fitar bakin sakataran Hamza yana hada takardu ya duba wadda ya saka hannu a kai. Jikinsa ne ya fara rawa ya soma salati. Wani cikin yan office din yace menene. Inuwa Sakatare yace ai bana jin oga ya karanta takardar nan da kyau. Ta nuna ya amince ya karbi kudin da suka bashi saboda haka nan da wata shida duk ribar da aka samu tasu ce. Daga wani wata shidan kuma sai su rinka raba ribar gida uku. Su kaso biyu shi kuma daya. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿7 Batul Mamman(Mrs)💖 Alhaji Nasiru Hamza dan kasuwa ne mazaunin Kano amma asalin iyayensa mutanen Kumo ne na garin Gombe. Sana'ar siyar da shanu da tumaki ya fara wadda a hankali har ya fara fitar da fatar dabbobin kasashen waje yana sayarwa. Shiyasa ma aka fi saninsa da Nasiru maifata. Halima wadda suke kira Hajiya ya fara aure yar kanwar babansa. Sun fara zama a Kumo kafin kasuwancinsa ya bunkasa ya dawo Kano. Lokacin ta haifi danta na fari Hamza suke kiransa da Yaya. Suna zamansu lafiya da mijinta. Kuma suna yawan zuwa gida ganin iyayensu. Hamza na da shekara biyu ta haifi Ibrahim sai Mariya. Alh Nasiru ba karamin soyayya yake nunawa yaransa ba. Yana da amini kuma abokin kasuwanci Alh Sabiu. Kowa ya sansu tare hatta iyalinsu suna mutunta juna. Matan Alh Sabiu biyu. Kaltume ce uwargida sai Sahura. Kaltume bata taba haihuwa ba a shekarun da sukayi da mijinta. Tana dai karatu a lokacin. Ita kuwa Sahura 'ya'yanta shida. Da kamar gaske suke zaman lafiya. Sai daga baya Sahura ta rinka daukar zigar yan uwa da kawaye ta fara yiwa Kaltume habaici da gorin haihuwa. Tun bata kulawa har dai ta fadawa mijinsu akan ya yiwa Sahura magana sai cewa yayi ai ba matsayinsu daya ba. Idan taji haushi ta haihu mana. Da kadan kadan suka juya mata baya. A lokacin tayi shawara ta sanar da Halima halin da take ciki lokacin tana da ciki na hudu. Ita kuma sai ta fadawa mijinta. Ko kadan Alh Nasiru baiji dadin faruwar hakan ba. Ya zaunar da abokinsa yayi masa nasiha. Sai dai duk a banza. Wata rana Kaltume zata tafi makaranta ta shirya ta rufe dakinta sannan ta leka dakin Sahura tace ta fita. Tana dawowa da yamma ta tarar da Alh Sabiu da Sahura har da wasu makota a kofar dakinta. wasu samari ne suke kokarin balle kofar. Kaltume duk ta rude ta tambayi abinda ke faruwa. A madadin amsa sai mari da duka da Alh Sabiu ya rinka kai mata. Sahura na kuka tace muguwa saboda baki haihu ba shine zaka kashe min nawa 'ya'yan. Tunda kika fita nake neman Ihsan banganta ba. Sai dazu kawai naji kukanta a dakinki. Ba yadda banyi ba na kasa budewa, tun tana kuka har muka ji shiru. Ta cigaba da kuka ina jin ma ta mutu Alhaji. Shi kuwa sai dukan Kaltume yake har sai da aka bude dakin. A kwance suka tarar da Ihsan yar wata takwas. Sahura tace ai kawai ta mutu ko ta suma. Alhaji Sabiu ya cire babbar rigarsa yana ta dukan Kaltume. Babu mai hanashi har Allah Ya kawo Alh Nasiru. Yayi ta rokon abokinsa amma sam yaki dena dukanta. Alh Nasiru ganin babu yadda zaiyi ya ja hannunta. Sahura tace shikenan Alhaji dama tunda yake kare mata kwartonta ne. Ji yadda yake rike mata hannu a gabanka. Alh Sabiu yace ko Sahura, to ke Kaltume na sakeki saki uku in kin gama idda ki auri kwarton naki. Kai kuma Nasiru bani ba kai. Da haka abokan suka rabo. Ashe mukulli Sahura ta sata na Kaltume ta durawa yarta maganin bacci ta kaita dakin. Halima taji tausayin Kaltume sosai barin ma da aka rinka yadawa a gari abokin mijinta ne kwartonta. Gashi ya gujeta bayan aurenta ya mutu. shi kanshi sai da abin ya shafi kasuwancinsa. Sai da ta kai ko makaranta ta dena zuwa. Har yan uwanta wasu suna kyamarta. A wannan halin ne Halima ta bawa mijinta shawarar ya auri Kaltume domin ta tsira da mutumcinta. Da kyar Kaltume da Alh Nasiru suka yarda. Bayan anyi auren saboda Halima ta lura Kaltume na son 'ya'ya ta dauki Hamza da Mariya ta kayansu ta mayar dakin Kaltume. Wannan abu ya kara musu zaman lafiya sosai. Kaltume har kullum bata yiwa Halima kallon kishiya sai yar uwa. Haka suka zauna lafiya Halima ta haifi Jidda. Daga nan Kaltume ita ta sami ciki ta haifi Nura da Adabiyya. Sannan Halima ta haifi auta Hamida. Gidansu abin sha'awa saboda kan 'ya'yan a hade yake. Daga baya asirin Sahura ya tuno Alh Sabiu yaji tana bawa yarta labari. Har gida yazo bawa Kaltume hakuri domin ya gane bai kyauta ba. A yanzu ma dai komai ya sukurkuce musu shi da Sahura don yaran babu wani mai abin kirki gasu har su shadaya. Tun daga farkon layin gidansa yake hango motoci. Hankalin Hamza ya sake tashi sosai. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai yake fada. Shikenan Junior ya rasu.........jikinsa duk a mace yayi parking din motarsa daga can baya ya fito. Sai kawai ya kasa karasawa gidan. Kifa kansa yayi a saman motar. A wannan yanayin Ibrahim ya iso. Yana neman gurin parking don layin ya cika ya hango yayansa a tsaye ya kifa kai. Ibrahim ya fito da sauri da matarsa Ummahani da yaransu uku. Hannu yasa ya taba Hamza a kafada. Hakan yasa ya juyo da sauri. Muryarsa a raunane yace ashe kuma kunji. Ummahani tana gaishe shi yace mata shiga ciki Umma ai dukkanmu mukayi rashin. Ibrahim yace rashi kuma Yaya? Nifa tun jiya Izzatu tace muzo da yara yau. Nayi tunanin irin partyn da kuka saba ne na kawo su don kada ace ina raba zumunci. Amma wallahi barnar kudin naka tayi yawa. Hamza yace ina maganar party Ibrahim. Junior ne ya rasu. Baka ga mutane da yawa ba. Ummahani na kokarin bude gate Junior ya bude tare da wasu yaran. Sun sha sababbin kaya. Hamza ya kura masa ido sannan ya dubi Ibrahim. Ibrahim yace kai wa ya fada maka ya rasu? Hamza a rikice yace Izzatu tayi waya Office tace a fada min ya karye a hannu. To ina zuwa naga motoci nayi tunanin ya rasu ne. Ibrahim yayi tsaki cike da bacin rai yace Allah Ya kyauta ni na tafi. Zuciyarsa na kuna yaja motarsa yayi gaba. Ace babban mutum kamar Yaya dan shekara talatin da bakwai ya bari mace na karanta masa yadda zasuyi rayuwa. Kodayake ba laifinta bane. Tare suke yin komai. Daga nan Ibrahim gidansu ya tafi. A hankali Hamza ya tura karamar kofar gate din ya shiga. Kawai sai ji yayi mutanen wurin sun ce SURPRISE!!! farfajiyar gidan ya gani ya sha kwalliya an jera kujeru da tebura. Ga fitilu suna ta haskawa an kunna inji. Kida aka kunna yana tashi a hankali. Bai gama tantance abinda ke faruwa ba Izzatu taja hannunsa suka shige cikin gida. Muje ciki ka canja kaya. Suna shiga daki ta rungume shi. ....HAPPY ANNIVERSARY MY BABY. [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿8 Batul Mamman(Mrs)💖 Hamza ya yiwa Izzatu kallon rashin fahimta. Izzy me yake faruwa ne? Kince Junior ya karye but it seems lafiyarsa kalau. Fari tayi masa da ido irin yadda tasan yana kara dauke masa hankali, sai a lokacin ya kula da kayan jikinta. Wani irin yadi ne mai matukar santsi aka yi mata doguwar riga wadda ta dameta daga sama har gwiwa sannan ta bude sosai. Ga wani abu kalar takalminta da sarka anyi mata dauri. Tamkar wata amarya ta fito. Jikinta mai kyau ne ba kace ta haifi 'ya'ya uku ba. Tana lura da yadda yake binta da kallo tayi murmushi. Dama nayi ne kawai don ka dawo gida akan lokaci. Na gama komai na shirya mana anniversary dinmu na shekara goma. Ya shafi gefen fuskarta amma Izzy ba kya ganin abin ya danyi yawa. Ki ce dana ya karye kinsan zan tsorata. Kiss tayi masa a kumatu to yi hakuri daddyn Junior. Kaga ana jiranmu a waje. Tare suka fito rike da hannun juna. Sunyi matukar kyau sosai ga yaransu suma sun sha ado. Babban shekararsa biyar suna kiransa Khalifa mai sunan Alhaji Nasiru. Sai Junior mai shekara uku sunan baban Izzatu gareshi Sunusi sai kuma Nana(Halima) mai neman shekara ta biyu. Sunan Mama yaso saka mata sai dai Maman taki saboda Ibrahim da Mariya duk sunyi mata takwarori. Hajara tana ta binsu da ido duk inda suka yi ana ta gaisawa da daukar hotuna. Ga masu rabon abinci suna ta yi su ma. Tace kai Anti Faiza ina ma Zuhra tazo muci son ran mu. Ji kaji kamar su suke kiwonsu. muma dai Allah Ya bamu kudin nan muji dadin rayuwa mu rinka party duk shekara. Mariya tace ba amin ba kanwata. Anti Faiza da Hajara suka juya suna kallonta. Hajara tace kinji min mata da bakinciki. Faiza ta kai mata duka to shashasha baki san mutum ba zakiyi rashin kunya, yi hakuri baiwar Allah. Ko ba'a fada ba daga shigar Mariya an san tana da kudi. Murmushi Mariya tayi ba komai ke dai kiyi adduar arziki mai albarka ba na party ba. Daga nan ta tashi ta hada kan 'ya'yanta sukayi waje. Haka aka cigaba da taro har wurin karfe takwas na dare. Nura ne suna shirin tafiya dasu Adabiyya yazo ya fadawa Hamza sakon Mama kan cewa tana son ganinsa a yau. Sai bayan fitarsu ya duba agogonsa. Subhanallah ya fada da karfi tare da mikewa. Izzatu tace yaya akayi? Ya nuna mata lokaci. Kinga har lokacin isha yayi bamuyi magriba ba. Ta dan tura baki idan an watse ba sai muyi ba. Bana son a fara shiga ciki ne azo a bata min toilets. Hamza yace ni dai bani key please. Ta dan daure fuska Allah bazan bayar ba. Kana shiga mutane zasu fara bin bayanka. Ya girgiza kai yana murmushi Izzy baki da dama. Wani famfo ya zagaya a bayan gidan yayi alwala sannan ya fita masallaci. Duk lalacewar lamarinsa bai tashi da tarbiyar sakaci da sallah da gangan ba. Ana gyaran wurin jamaa sun watse sauran kadan Hamza ya fito zuwa gidansu. Izzatu ta bashi manyan kuloli cike da abinci, nama da snacks. Ga katon din juice da na ruwa ya kaiwa su Hajiya. Kula daya ya dauko maigadi ya biyoshi da sauran. Da sallama ya shiga babban falon. Mama da Hajiya ne a wurin sai Jidda da ta biyo su Nura tana jiran mijinta. Duk suka amsa sallamarsa sannan Mama tace maraba da Mungo Park. Turus Hamza yayi ya kasa furta gaisuwar da yake shirin yi musu. Hajiya tace Jidda tashi mu shiga ciki uwa da danta zasu gana. Dama zamanta a wurin ta kara tunzura mama da bayanin abinda ya faru a wurin partyn. Hamza yayi murmshi da wuya kaga fuskarsa a hade sai dai idan yana cikin tashin hankali. Mama nasan nayi laifi ko baki fada ba. Amma wallahi nima bani da masaniyar wannan party din. Surprising dina tayi nima. Mama tace ai naga alama. Zaka ce iyayenta basu da labari ne? Ka hado kuloli ka kawo wa mayunwatan iyayenka abinci ko. To duk ka kwashe abinka bama so. Yace Mama ita da kanta ta bani na taho dashi. Tace kaga ni ba wannan ke gabana ba kaji ko. Yanzu don Allah Yaya yaushe zaka san ka girma? Wace irin rayuwa ce kuka daukarwa kanku kai da iyalinka. Kanka aka fara zuwa kasar waje karatu ne da zaka dauko al'adun da ba naka ba kayi ado da su. Sau nawa muna yi maka fada ni da Hajiya akan birthday partyn da kuke wa yaranku duk shekara amma ka share. Irinsu valentine dinnan ma duk kuna yi ko? Shiru Hamza yayi don yau kam ya san ya batawa Mama rai. Tace ba tambayarka nake ba. Yace munayi. Ta cigaba da fada....duk wani dan iskan day da yahudu da nasara ke girmamawa kaima ka girmama. Ka iya kashe kudi mai tsoka ka shiryawa yara party kawai don suji dadi. Irin sadakar nan ta abinci ko kudi kuwa sai karshen ramadan. Baka tunanin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki yanzu. Alhamdulillah muna da rufin asiri ci, da sha da sutura babu wanda Alhaji baya saukewa amma ai ihsani yana da dadi ko. Ko kasan duk wata sai Ibrahim ya kawo buhun shinkafa gidannan sannan ya bamu dubu biyar biyar ni da Hajiya. Ya san ba kudin ko abincin muka rasa ba. Amma yana neman albarkar iyaye. Mariya da Jidda suma suna nasu kokarin da dan abinda sukeyi. Duk cikinsu kafi kowa morar Alhaji kuma ka fisu kudi amma daga kai sai iyalinka. Kawaici kawai mahaifinka yake maka irin na bafillatani amma ko kadan baya jindadi. Shin ka taba zama ka tambayeshi a halin da kamfaninsa yake ciki? Ko ka tambayi Hajiya me take bukata ko da ba na kudi bane? Hamza ya girgiza kai a hankali. Mama bata san cewa tana fadan ma hawaye take yi ba. Tace to girma ya kama babanku. Ibrahim lecturer ne amma daga wurin aikinsa yana zuwa kamfanin taya shi aiki. Nura yanzu yake ajin karshe a jamia amma tun yana level one yake zuwa. Hamza yayi mamaki wai Nura har ya kai level four yanzu sai dai bai nuna ba kada fadan ya karu. Ita kuwa Mama cigaba tayi da fadanta. Yan uwanku na Kumo makusanta. Ina nufin yan uwan Hajiya da na Alhaji kasan halin da suke ciki? Ko kasan a rage maaikatan banki harda kanin Hajiya. Hamza ya dago kai wanne? Tace Nafiu. Gashi yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha uku. Watansa kusan bakwai ba aiki. Akan Nafiu Hajiya ta soma kukan rashin taimakon da kake yi. Maganganun sun ratsa Hamza sosai. Ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci. Mama tace ni dai lahirarka nake duba maka Yaya. Rayuwarka nema take ta sauka daga turbar addini. Har yau ban manta yadda Izzatu tasha maganin hana haihuwa ba wai sai ta gama karatu. Allah ne ma Yaso kuna da rabon haihuwar daga baya. Ka tashi ka je ka bawa Hajiya hakuri ka tafi dare yayi. Hamza yayi godiya sosai tare da sake bata hakuri. Har ya kai bakin kofa tace Yaya....naam ya amsa. Nasan saura baifi sati biyu ba birthday din Nana. Kwana hudu kafin ranar ka dawo dasu nan. Wallahi ka sake celebrating birthday a gidanka zaka ga fushina sosai.. Allah Yayi muku albarka [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿10 Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra ta shigo layin gidan Anti Faiza sai ta hango mai tsamiyar biri yana turawa a baro. Tsallakawa tayi bangaren da yake zata siyo. Dama tana ta tunani yar tsarabar da zata kaiwa su Abba. Hamza da Izzatu suna mota suna hira tana fada masa Inuwa sakatare ya kira yaji ya jikin Junior fa. Dariya sukayi yace kin mayar dani makaryaci dai. Khalifa ne ya hauro daga baya ya dawo gaba ya zauna kusa da Izzatu. Ta juya ta harari maiaikinta. Ke Tala garin yaya kika bari ya taso har ya dawo nan. Oya Khalifa koma wurin zamanka. Ko kulata baiyi ba yace daddy ka kawo na tayaka driving. Hamza yace not today Khalifa kaga anyi ruwa jiya titin babu kyau. Kuma akwai mutane a nan. Khalifa yace ko sau daya ka bari na dana. Izzatu ta kama shi zata mayar bayan mota yasa ihu tare ta riko wuyan Hamza. Iyakar karfinsa yasa yana jan babansa. Garin ya cire hannun Khalifan ya dan dauke ido daga kan hanya. Tana tura ledar tsamiyar birin a jaka taga mota ta yo kanta. Hantar cikinta ta kada ta rasa ina zata yi ma. Gabadaya ta rude kafafunta sun kasa daukarta. Da kyar Hamza ya iya tsayar da motar bayan ya shigar da ita cikin wani ruwa da ya kwanta a gefen titi. Har fuska ruwan ya watso wa Zuhra sannan ta zame ta fadi a zaune cikin ruwan. Karshen bacin rai kam taji shi a lokacin. Musamman da ta hango mai tukin da yaro suke kicikici da sitiyarin motar. Da sauri Hamza ya tura Khalifa wanda yake ta kuka cinyar Izzatu ya sauke glass din motar yana duban Zuhra. Leko da kansa yayi zai bata hakuri sai dai akayi rashin sa'a kwalliyar fuskarta ta bashi dariya. Izzatu da Tala ma da suke cikin motar sai da suka yi saboda yadda lebenta ke daukar ido. Ita kuwa Zuhra haushi ya kara kamata. Hamza ya dan daure amma fuskarsa dauke da murmushi yace don Allah kiyi hakuri kinji. Yaro ne ya rike sitiyarin Allah Ya kiyaye ban tabaki ba dai ko? Zuhra ta tsuke baki ban sani ba...don tsabar wulakanci kayi min wanka da kwatami sannan ka wani kame a mota kana tambayar ko ka tabani. Hamza ya dan sha kunu jin abinda ta fada yace to naji kiyi hakuri don Allah. Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata dubu biyar. Gashi ki sayi sabulu. Ganin ya tayar da motar ta kama hannun gefen inda yake zaune ta soma masifa. Amma kai baka da mutumci wallahi...tana kallonsa tana kallon kudin. Kudinka me zasu min. Malam ka fito ka duba ko naji ciwo ka kaini asibiti. Izzatu ta dan leko kiyi hakuri kinji, kinga yaron da ya jawo, ta dungure Khalifa. Maganar Zuhra ta bawa Hamza haushi yace idan bazaki karbi kudin ba sauri nakeyi. Kin samu na tsaya zaki rinka yi kin rashin kunya. Zuhra tace anyi din, nace anyi din kuma Allah Ya isa abinda kayi min. Ka wani makale a mota kai mai kudi ko. Yadda take magana ya sake bawa Izzatu dariya. Haka kawai yarinyar ta burgeta. Hamza kuwa harararta yayi sannan cikin fushi ya fito daga motar. Tun kafin ya karaso tsoro ya cika mata zuciya. A gabanta ya tsaya ta daga kai ta kare masa kallo. Tabdijam...da kyar in kanta zai kai kafadarsa ma. Ta hadiyi yawu da kyar. Mutumin duk da bashi da kiba amma dai baya sahun masu rama, gashi da tsaho. Idanunta suka kawo ruwa don kallon da yake mata ba na wasa bane. Idan ya dake ta kuwa ya daki banza. Ya dan rage sautin muryarsa ke kinga nayi kama da sa'anki ne? Ta girgiza kai. Yace to ina baki hakuri sai ki rinka yimin rashin kunya. Izzatu ta dan bude kofa tace babyna ka taho mu tafi kawai. Zuhra ta zaro ido ta kara kallonsa....baby kuma? Katon gardi da kai a kiraka baby. Lallai an cuci kalmar nan al'quran. Ran Hamza ya sake baci ya daga hannu zai mareta. Tace kana tabani zanyi suman karya a wurin nan sai mazan can sun taru. Kuma in fada musu abinda kayi min. Daga kai yayi ya kalli kofar kantin da ta nuna yayi murmushi yace bismillah. Zuhra ta dan ja da baya da gaske nake fa...shima ya kara matsawa gabanta ai ban hanaki ba. Ta tabbatar dai ba wasa yake ba kawai sai tace Allah Ya isa da karfi ta kwasa da gudu. Binta yayi da ido sannan yayi tsaki. Idan ya sake ganin yarinyar nan sai jikinta ya gaya mata. Shi zata yiwa Allah Ya isa har sau biyu. Yayi kwafa ya shiga mota. Izzatu sai dariya take. Yarinyar kamar wata clown. Ita fa gani take tayi kwalliya karshe ko? Hamza yayi tsaki yanzu duk abinda ta fada min bai dameki ba Izzy sai ki rinka dariya. Tace ai abin naku ne da ban dariya. tayar da motar yayi don idanun Izzatu suna ga yarinyar da ke gudu ba maganar da yake ba. Tana kallo har Zuhra ta fada gidan Faiza.... [25/09 3:14 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿9 Batul Mamman(Mrs)💖 Tunani ne duk ya ishi Hamza har ya isa gida. Tabbas ko makaho yasan kasarmu tana cikin matsi a wannan yanayin da muke ciki. Sai fatan Allah Ya kawo mana sauki. Amma a haka duk shekara basa rasa dalilin yin taro a gidansu. Duk da hakan ba ra'ayinsa bane tun farko amma ya goyi bayan Izzatu akan duk abinda take yi. Dole ne kuma ya nuna mata kuskuren rayuwar da suka daukarwa kansu ko don inganta tarbiyar 'ya'yansu. Kila mutane suna ta zaginsa bai taba tunanin haka ba sai yau. A haka ya isa gida zuciyarsa duk ba dadi. Izzatu ta gama gyaran dakin yana ta kamshi ita kanta ta yi kyau sosai tace ya shiga yayi wanka. Inuwa Sakatare ya karanta takardun gabansa yafi a kirga. Yana son sanar da ogansa amma yana tunanin kada ya zama ya nuna rashin damuwa akan lalurar Junior. Daga karshe dai text ya tura masa wanda ke dauke da cikakken bayani dangane da yarjejeniyar dake tsakaninsu da turawan. Kusan minti goma ba reply sai kawai ya kira wayarsa. A lokacin Hamza na wanka. Izzatu na kallo har wayar ta tsinke aka sake kira har sau hudu. Tayi tsaki ta dauka. Bata son abinda zai bata romantic night din da ta tsara musu ita da mijinta. Gashi baya yarda da kashe waya komai dare. Inuwa ya gaisheta ya tambayi jikin Junior tayi dariya kawai tace da sauki. Yace na turowa Oga sako ne nake son tambayarsa ko ya gani. Izzatu tace yana wanka amma zan sanar dashi. Inuwa yayi godiya yace sai da safe. Har ta ajiye wayar ta dawo ta dauka. Tasan halin Hamza kafin ya kwanta sai ya duba sakonnin wayoyinsa mai bukatar reply ya tura. Ita kuwa daren yau na tunawa da ranar aurensu ne. Bata bukatar duk abinda zai dauke masa hankali. Duba sakonnin mail dinsa tayi duk ta bude su a matsayin an karanta haka ma na whatsapp. Text kuwa banda na Inuwa duk sauran na etisalat ne da mtn. Gabadaya ta hada ta goge harda na Inuwan saboda daga farkonsa taga an rubut RANKA YA DADE YA JIKIN JUNIOR......iya nan ta gani ta goge ta saka masa wayoyin a chaji. A tunaninta text din dubiya ne. Da ya fito ya duba wayar babu wani abu mai mahimmanci sai kawai suka yi shirin kwanciya.... Zuhra ta dawo daga islamiyya tana ta zumbura baki. Sallamar ma a ciki ciki tayi. Umma tace waya taba uwar masu gida? Jakarta ta jefar a kan tabarma ta cire hijabin ta kwanta. Umma yunwa nake ji kamar naci babu. Baba ya fito daga bandaki da buta a hannu yace Allah Ya rabamu da babu. Shine zaki wani kwanta kina turo baki. Ji don Allah kamar ba mace ba. Kin wani kwanta a kasa. Ji gaban rigarki ma kamar manja. Ya taba kitsonta da tsagar har ta bace don tsufa...yanzu kan nan yaushe rabonsa da ki wanke shi? Wai wa zan samu ya aureki a haka? Ba kwakwalwar karatu ga rashin jure yunwa. Gaki ba wani kyan azo a gani ba. Da nayi kudi ne ma sai a aureki ko don nauyin aljihuna. Zuhra ta soma shura kafafu Umma kinji Baba ko? Ai dai kai na biyo wallahi. Yace wa? Ni? Haba yarinya don kinzo na fara tsufane. Tambayi Ummanki lokacin da nake matashi yadda mata ke bina. Umma tana wanke shinkafa tana musu dariya. Zuhra tace har tafiyarmu iri daya fa. Baba yasa dariya ai kuwa da kinji kunya ace budurwa kamarki tana tafiyar maza. Maganin farinjini zan nema miki. Tunda karatun yaki sai ayi auren. Maganarsa ta sake tunzura Zuhra har ta soma hawaye tace Umma ina kama dake ko? Umma ta rike baki tace ta ina? Ni duk gidanmu babu mai kyau na. Ke kuma da Babanki kike kama. Kaga Sima yar gidan Malam Basiru. Dariya sosai suke yi mata tana ta kuka. Ta tashi ta shige daki. Baba yace kinga kin batawa uwata rai ko. Umma tace don na tayaka?. Amma maganar gaskiya rashin saurayin Zuhra na damuna. Maikifin bakin layi ne kawai yake zuwa kuma tace bata son shi. Baba yace nima abin na damuna. Bata son kula da tsaftar jikinta ne kuma da laifinki. Umma tace akan ta tsefe kanta har dukanta nayi. Lokaci na bata zuwa wani satin tana bacci zan sa mata almakashi kowa ya huta. Baba yace wallahi ban yarda ba. Da nayi saa ta gado irin gashinki mai dan tsaho kuma sai ki aske. Ba gidan Faiza zata ba bayan azahar...Umma tace can zata je. Baba yace to kice ta tafi da kaya ko biyu ne ta kwana. Kinsan halin Faiza ko taki ko taso sai tayi tsifar nan. Zuhra na jinsu daga daki ta leko ta taga na fasa zuwa gidan Anti Faizar. Umma tace kunfi kusa ai. Sai da ta gama cin abinci ta sha ruwa sannan ta dauko hijab ta saka da kullin kayanta a dankwali tace Umma zan tafi. Baba ya harareta a haka Zuhra... Islamiyya fa kika je ko wanka bakiyi ba ki ka saka kaya. Ji hijab din ko guga babu. Ke ko irin gayun mata baki iya ba. Ki dan saka kayanki a yar leda zaki kulle a dankwali. Yarinyar nan da a kauye muka tashi bana jin zaki taba wayewa. Gaskiya Umman Zuhra bakya kyauta min. Kin bar min yarinya ta zama borar karfi da yaji. Umma tace ai kana gidan kana ganin yadda nake fama da ita. Baba yace zo ki zauna kinji Fadimatu. Ta zauna bakin nan kamar ya zunguri kofa saboda yadda ta turo shi gaba. Yace yanzu don Allah idan ke namiji ce kika ga mace irinki zaki so ta? Tace eh to ya danganta da namijin. Baba yace ni bance sai mai kudi ba amma dai Zuhra a sami rufin asiri. Ke kadai fa Allah Ya bani dole na so ki da alkhairi. Dazu kina cin abinci lomarki har tafi tawa. Itama dariya maganar ta bata. Ta sunkuyar da kai. Baba yunwa naji sosai a lokacin. Yace to abinda zai faru nayi miki alkawarin waya mai kyau harda kemara indai zaki rinka tsafa. Alhamdulillah Zuhra tace da karfi tare da fadawa jikin Baba tana godiya. Yace dagani duk gidannan kinfi kowa nauyi saboda cin ki. Ta mike tsaye tana tsalle daga yau zaka ga canji Baba. A wurin ta cire hijab da dankwali ta kama zanin zata kwance Baba yace shiga daga ciki dai yana kawar da kai. Ta wuce da tsallenta kamar karamar yarinya. Baba yace da Umma kin kula da hannun rigar mamanta kuwa? Dandakuwa..... Umma tace Baban Zuhra ka fiye gane gane kaima. Allah Yasa canjin ya dore dai. Kusan minti goma sai gata ta fito da daurin kirji da gashinta buzu buzu. Ta dauko kwandon wankanta da yar robar shampoo ta wuce bakin rijiya ta debi ruwa bokiti biyu. Suna nan zaune ta fito bayan kusan rabin awa tayi wanka da wanke kai. Umma tace har kin danyi haske kuwa. Bata ce komai ba ta shige daki. Tasha wahalar taje kanta sosai saboda tsabar cikarsa. Ta shafa mai a ko ina ta raba biyu tayi kitso manya. Ta shafa mai a jikinta da body spray din da Baba ya siyo mata. Ba wani abu ke sawa bata amfani dasu ba, ita a tunaninta idan basu kare ba Baba zai ajiye kudinsa yayi wani abin dashi. Tana matukar tausayinsa saboda lalurar hannu da ta same shi. Sai da akayi laasar ta fito fes da ita. fuska tasha hoda da janbaki orange, har girarta ta gyara. Baba kuwa baki yaki rufuwa da ya ganta bayan ya dawo daga masallaci yace ko ke fa. Allah Yasa ayi gamon alheri a hanya. Umma tace iyayen zamani ba kunya. Dari biyu ya bata kudin mota tayi godiya ta fita. Tafiyar ma kokarin daidaita kafarta ta rinka yi kada Baba yace tayi ta maza. Sai da ta fita Umma tace ba naga ka siyo wayar ba. Yace eh kyaleta muga zuwa kwana biyu sai na bata. Ki rinka sa ido tana gyara kanta. Ga iya zuwa islamiyya daukar karatu amma bata damu da tsafta ba. [25/09 3:27 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿11 Batul Mamman(Mrs)💖 Su Anti Faiza sun sha dariya da Zuhra ta basu labarin dalilin shigowarta a guje. Anti Faiza tace lamarinki sai addua Zuhra. Yanzu meye na rashin kunya bayan an baki hakuri? Zuhra tace yana daga mota fa yake bani hakurin. Ni dariyar da suka yi min ita yafi bani haushi. Hajara tace to ba dole suyi ba kin kama fuska kinyi mata zane. Ji girarki kamar an miki fenti. Zuhra tace wai haka Anti? Yau baki ga yadda Baba yayi murna ba har alkawarin waya yayi min. Daga nan suka cigaba da hira. Anti Faiza ta sako zancen bleaching tana musu fada. Zuhra tace nima hanata nayi har malama Rabia na tambaya hukuncin mai yi. Ta zauna tayi musu bayanin yadda suka yi da malama. Anti Faiza tace ato ni dai nasan kuna tare naji tsoro kada ta koya miki hali kinsan ance zama da madaukin kanwa..... Bayan kwana biyu suna cin danmalele a falon Anti Faiza suka ji sallama. Zuhra ta kwaye zaninta har ana ganin cinyoyinta. Anti Faiza sai fada take mata basu ji sallamar ba. Abba ne ya amsa sai ga Izzatu ta shigo. Da yake Zuhra na fuskantar kofa tana shigowa suka hada ido. Sai da ta kware don tsoro sannan ta tashi da gudu ta shige daki. Anti Faiza cikin mamaki tace sannu da zuwa Maman Khalifa. Ganin Izzatu na kallon kofar dakin tana dariya tace wata kanwata ce mai shirmen tsiya. Izzatu tace ai mun taba haduwa. Ta baki labarin an kusa kadeta da mota shekaranjiya ko? Zuhra daga daki tana lasar hannunta da ya sha manja tace na gama yawo yau. A falo Anti Faiza tace ba dai Alh Hamza ta yiwa rashin kunya ba? Ke Zuhra fito. Izzatu tace ba kararta na kawo ba. Ni ta burgeni ne ma. Don baki ga idanunta ba da ya fito daga mota. Yadda kika san ta saki fitsari a wajen amma duk da haka bata dena magana ba. Anti Faiza tace ai indai Zuhra ce ta wuce nan. Sai ki fito ki bata hakuri ta kira Zuhra daga daki. A sanyaye ta fito ta gaishe da Izzatu sannan tace ku yi hakuri. Hajara tana gefe tana musu dariya. Izzatu tace ba damuwa. Ai ranar baki ga yadda yaji haushi ba. Har muka je muka dawo yana mita. Ni da zaki bini gidana ma ai da saka ku zanyi a gaba ina samun abin nishadi. Zuhra ta kalleta da mamaki. Yanzu nufinki baki ji haushin duk abinda na fada masa ba? Izzatu tace not at all. Zuhra dai bata gane dangantakar turancin da tambayarta ba, sai tace da nice wallahi fitowa zanyi daga motar in saita bakin mara kunya. Hajara ta dan taba Anti Faiza sannan ta kallo Zuhra alamun ayi mata magana. Izzatu ta ce ni bana son hayaniya nasan he will handle everything shiyasa na kyale ku. Maganar ta bawa Zuhra mamaki sosai. Ace wata tayiwa mijinki rashin kunya kice baki damu ba. Gaskiya ke a mata daban ce....anti Faiza tayi saurin toshe mata baki. To sarkin shirme ance abinda kika yi babu komai kin dage sai neman jawo magana kike. Maman Khalifa don Allah kiyi hakuri. Izzatu tayi dariya ke babu komai fa. Haka suka cigaba da hira Zuhra tana basu labarin Baba na son yi mata aure amma yace yafi son miji mai ilimi. Ni kuwa indai gida da abinci bani da damuwa. Hajara tace amma kika ki maikifi? Baki taba tsayawa gabansa bane shiyasa kike magana. Banda karni babu abinda yake. Anti Faiza tace wai kura ce zata ce da kare maye. Ke da ba kya minti uku kin gama wanka ai bai kamata ki guji dan uwanki kazami ba. Zuhra tace baki ji na fada miki Baba zai bani waya bane..ai daga yanzu zan rinka wanka sosai. Ita dai Izzatu har ranta shirmen Zuhra yana bata shaawa. Dalilinta kenan na zuwa gidan ranar don idan tana neman Faiza waya take yi mata. Kwana hudu Zuhra ta yi a gidan suka koma tare da Hajara. Baba ya bata dubu shida yace ta kaiwa mai koya mata sakar. Cikin dan kankanin lokaci ta fara kwarewa saboda abu ne da take so. Ga tsafta an dore da wanka. Kwalliyar ce dai har yanzu da sauki. Baba ya cika alkawari ya bata wayar. Ranar murna ba'a magana. Haka ta rinka shiga makota tana nuna musu. Mamansu Hajara ma tayi murna. Don duk makotansu sunfi shakuwa sosai tamkar yan uwa. Tecno ce second hand ya siya a wurin wani dan layinsu. Da yake suna ganin girman Baban Yara kamar yadda suke kiransa ba karamin sauki mai wayar yayi masa ba. Arch Hamza na zaune yana duba wasu takardu a office dinsa Inuwa sakatarensa yayi sallama ya shigo. Bayan sun gaisa yace ranka ya dade naji baka ce komai ba game da text da wayar da nayi maka. Hamza yace yi hakuri wasu abubuwan ne suka dauke min hankali. Izzatu ta fada min komai. Babu matsala nagode. Har kunya yake ji ace matarsa karya tayi. Inuwa yace ranka ya dade babu matsala? Hamza ya ajiye takardun ko dai akwai wani abu ne Inuwa? Shi a tunaninsa Inuwa ya gano Junior lafiya yake. A'a babu komai, dama wannan maganar ce kawai. Daga nan ya fita. Tunda Oga bai damu da yanayin contract din ba gara ya dena damun kansa kawai. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿12 Batul Mamman(Mrs)💖 Da daddare yana bacci yaji kamar ana taba shi. A tsorace ya tashi ya lalubi fitilar gefen gado. Zaune ya ganta ta dora pillow a cinyarta. Sweetheart ka tashi muyi magana game da birhtday din Nana. WHAT??? Shine abinda ya iya fada a hasale. Izzatu tace maganar birthday din Nana nace. Ya nuna mata agogo Izzy kinga time fa, uku saura na dare. Ta dan kwanta a jikinsa kullum ina son mu tsara komai baka dawowa gida da wuri. Jikinsa ya janye sannan yace saboda haka sai ki tasheni da tsakar dare? Haba Izzy! Tashin miji ayi magana a irin wannan lokacin ai sai a film. Indai maganar kirki ce ai ido biyu ake yinta. Ni naga irin haka is normal tsakanin couples. Idan abu na damun daya sai suyi discussing at night. Kasan kuwa na sake ganin yarinyar da kuka yi fada saboda ka watsa mata ruwa. Ashe kanwar Faiza ce. A wannan lokacin Hamza ji yayi tamkar ya saka ihu. Fuskarsa ko kadan babu annuri yace yanzu Izzy ki tasheni a tsohon daren nan saboda zancen birthday sannan ki ce kinga yarinyar nan? Did I ask you? Gobe meeting gareni da sassafe kuma na fada miki. amma sai kika zabi yanzu ki hanani bacci kuma ki bata min rai. Kallonsa kawai take yi....yau me ya sami baby dinta yake irin wannan fadan. Shi kuwa Hamza banda bacin ran gani yayi dama ta samu na bin umarnin Mama a soke maganar party. Yace ki manta da maganar wani party don an dena. Kina iya dafa abinci ki kawo a kai asibiti ko makarantar allo sadaka. Wannan karon ita ce nata ran ya baci. Wace irin magana kake yi ne? Yarinya duk na gama sa mata rai. Har kayan da zata saka ranar duk na gama siya. Hamza yace indai kaya ne ko gobe ma ki saka mata. Izzatu ta soma hawaye kada kayi min haka Hamza please. Yace meye na daga hankali, shekara biyu zata yi ai ba wayo gareta ba. Hawaye take sosai ya rungumeta yana rarrashi. Tace indai don na tasheka ne kayi hakuri amma kada kasa yan gidanmu suyi min dariya ko aga kamar baka da kudin ne. Bai san haka suka daukaki abin ba sai yanzu. Yace na gama magana Izzy no more parties. Ki duba a family dinku mai bukatar taimako sai mu bashi jari. Su Mama basa son abinda muke yi kuma nima na fahimci kuskurenmu. Ai ture shi tayi ta tashi tsaye. Dama nasan zugoka aka yi tunda ka fara magana. Na rasa meyasa 'yan gidanku basa sona. To wallahi sai anyi ko kana so ko baka so. Hamza yace ni kike fadawa haka Izzy? Yau daya don na hanaki abu shine zaki nuna min ban isa ba. Ba tare da ta bashi amsa ba ta fice daga dakin harda buga kofa. Kansa ya rike ya zauna a bakin gado. Lallai yayi sakaci da har abin ya kai haka. Dole ya nemi yadda zai gyara gidansa don a zauna lafiya. Cikinsa ne ya murda alamun yunwa. Yau kamar sauran alhamis Izzatu batayi girkin dare ba. McDonald's tayi musu order. Soyayyan dankali aka kawo musu da kaza harda Tala da maigadi. Ko kadan Hamza bai koshi ba sai dai an saba irin haka wanda tun kafin suyi aure yayi mata alkawarin ware rana daya a sati kada tayi girkin dare zasu rinka ci a waje ko ayi order a kawo musu gida. Tashi yayi ya bita dakinta sai dai a rufe yaji dole ya koma ya kwanta. Da kyar ya iya bacci saboda yunwa. Washegari saboda tana fushi bai sami breakfast ba. Da yayi magana tace ta dena girki sai ya janye maganar party. Shi kuma yace ta bashi atm card dinsa na wurinta maganar soke party babu fashi. Baram baram suka rabu. Har mamanta ta kira a waya ta fadawa tace kada ta damu idan bata da kudi ne zata turo kaninta ya kawo mata. Hamza gani yayi an cigaba da shirye shirye. An siyo katons din lemo da ruwa. Ga gifts duk an gama hadawa a wata jaka mai hoton Nana duk an ajiye a store. Ya sake wa Izzatu magana tace ai ba kudinsa bane. Maganar Mama ya sake bi ya kwashe yaran ya kaisu gidansu. Su Hajiya sunyi mamaki da farinciki ganin Hamza yaji maganarsu. Aka sa Ibrahim dasu Mariya suka kawo nasu yaran. Tuni su Khalifa suka saki jiki cikin yan uwansu. Idan suna Hausa sai ka rantse daga turai suka dawo. Kwatakwata basu iya sosai ba ,sai turanci. Nana kuwa dama bata iya magana sosai ba. Tunda suka zo ta likewa Adabiyya take kiranta Anti Adab. Izzatu tayi mamaki da ta dawo daga supermarket ta tarar yaran basa nan. Tala ce ta sanar da ita sun fita da daddynsu. Sai dai tasha takaici da ya dawo shi kadai yace a can zasu kwana. Tasan saboda maganar party ne. Tayi ta rokonsa da koke koke duk a banza. Har zaunar da ita yayi yana mata nasiha amma ta kafe. Shi kuwa yace indai zata iya zuwa gidansu ta dauko yaran shikenan. Bata san gatse ba ta tafi ana sauran kwana biyu sai dai ta tarar duk sun tafi Kumo. Babu kowa a gidan sai maigadi. Kuka kam ranar ba'a magana. Izzatu tayi fushi sosai da Hamza tare da alkawarin sai ta rama duk ranar da dama ta samu. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿14 Batul Mamman(Mrs)💖 Tala ta zazzaro idanu tana kallon Izzatu. Na rantse ba karya nake ba. Hajiya da Mama sai kallonsu suke yi. Tala na maida zance suka ji kukan Nana tana kiran Izzatu. Tare duk suka yi hanyar inda suka ga Tala ta fito. Hajiya ce a gaba. Sai da cikinta yayi mugun kadawa saboda abinda ta gani zaune akan po yana miko hannu alamar ta dauke shi. Na kusa dashi kuma mai siffar kwarangwal ya rugo da gudu zai rungumeta. Da kyar ta iya cewa Hasbunallahu wa ni'imal wakil sannan tayi baya kamar zata fadi. Mama tayi saurin tareta itama a tsorace har ta fara tunanin kada aljanun su rufe kofar gidan su hanasu fita. Tala tace kun gani ko Hajiya ai na fada muku. Nana dai tasowa tayi ta nufo su shima Junior haka. Khalifa da yake kwance a daki shima ya fito saboda hayaniyar da yaji. Mama ta karewa aljanun uku kallo tace Hajiya gidan Yaya ba lafiya. Izzatu ce karshen shigowa tana ganin abinda ya kidima surukanta ta kyalkyale da dariya harda hawaye, karshe sai da ta kai kasa. Hajiya da Mama sai kallon kallo a zatonsu ma ko aljanun sun taba ta. Sai da tayi mai isarta suna kallonta sannan tace Hajiya su Nana ne fa. Kaya ne na saka musu yau halloween. A gabansu ta cire musu fuskar kayan tana mai cigaba da dariya. Ransu Hajiya yayi matukar baci. Tala kuwa karasawa tayi gaban yaran tace Khalifa kaine tana tattaba musu jiki. Ta dago kai tace Hajiya ai kuwa su din ne. Mama ta dubi Izzatu, hallo...me kika ce? Izzatu tace halloween. 31st October ake yi. Lokacin da muna Canada muna yinsa sosai. Tsabar bacin rai Hajiya ta kasa magana ma. Karshen wulakanci da cin mutumci Izzatu tayi musu. Mama tace Hajiya ai sai mu tafi ko, don banga dalilin zamanmu ba. Su Junior suna ta binsu suna cewa zasu bi su. Cikinsu babu wadda ta iya kula yaran saboda yadda zukatansu ke kuna. Izzatu tace muje falo ku sha ruwa don ita bata dauki shirunsu a matsayin bacin rai ba. Sun kai bakin kofa zasu fita idon Mama ya kai kan wani mutum mutumi mai siffar mutum kafarsa ta akuya ga kaho har a saman hanci. Shima duk cikin kayan kwalliyar gidan ne na halloween. Cikin Mama har murdawa yayi, gabanta ya fadi don abin ya bata tsoro har kafarta ta goce ta fadi kasa. Hajiya tayi saurin durkusawa ta taimaka mata ta tashi. Junior da Khalifa ma suna ta cewa sannu Grams. Ita kuwa Izzatu wata dariyar ce ta subuce mata. A ranta tace ko ba komai ta rama abinda suka yi mata na sa Hamza ya hana su party. A fusace Hajiya ya dago kanta cikin zafin rai zata yiwa Izzatu magana Hamza yayi sallama. Ganin Mama na kokarin mikewa yayi saurin karasawa gabanta yana tambayar abinda ya faru. Dama zuciyar Hajiya a kusa take maimakon ta bashi amsa ta kwashe shi da mari. Falon a take yayi tsit Tala tayi saurin komawa dakin su Khalifa ta ga an mari ubangidanta. Falon yayi tsit Izzatu ta hadiye sauran dariyarta. Shi kuwa hannuwansa biyu yasa ya dafe kumatunsa ya dubi mahaifiyarsa a razane. Mama tace haba Hajiya ya zaki dauki hukunci kan wanda baiji ba bai gani ba. Murmushin takaici Hajiyan tayi tace tunda nake ban taba ganin wulakancin da yayi min ciwo irin wannan ba. HAMZA ka guji ranar da zanyi maka baki.....idanunsa sunyi jawur yana mamakin sunansa da ta fada da kuma dalilin bacin ranta. Yace da Izzatu me ya faru? Ta dan tabe baki babu komai. Don basu dade da zama ba suka tashi. Hajiya da Mama suka yi hanyar kofa yana ta basu hakuri da son jin abinda ya faru sunki sauraronsa. Har bakin mota ya biyo su. Sai da dreban ya tada motar sannan Hajiya tace wallahi in dai da raina da lafiyata Hamza bazan kara taka kafata nazo gidanka ba. Mama da yake tunanin zata bata hakuri ko kallon inda yake bata yi ba. Sai ma kwalla da yaga tayi saurin sharewa kafin motar ta fita daga harabar gidan. Da sauri ya shiga gidan yana kwalawa Izzatu kira. Ta fito hankali kwance tace sweetheart abinci zaka fara ci ko wanka. Izzy kina da hankali kuwa? Ya dubi su Junior kai ku koma dakinku. Sai da yaran suka tafi yace idan naki iyayen ne suka fita haka zaki musu? Ki fada min gaskiya me akayiwa su Hajiya. Izzatu tace ni ban sani ba. Suna ganin su Khalifa suka kama hanyar fita. A daidai can ne mama ta dan fadi. Hamza yace ta fadi? Ya karasa yaga gunki a wurin ya dago shi..meye wannan kuma? Izzatu tayi yar dariya na halloween ne. Ka tuna sanda akeyi a Canada? Akwai da yawa naso gama jerasu kafin ka dawo. Ya ce wane irin hoto kika turo min dazu? Ni abinda ya dawo dani kenan. Izzatu ta riko hannunsa zo mu zauna babyna. Ta kira yaran sai a lokacin ya kula da kayan jikinsu. Na nana yafi tada hankali ya mike a fusace izzy dont tell me haka su Mama suka ga yaran nan. Tace haka suka gansu mana. So what? Dafe kansa kawai yayi yana karanta Innalillahi a zuci. A hankali yace Izzy don Allah ki ajiye al'adun wasu a gefe mu zauna lafiya. Yadda Hajiya ta rantse ta bar zuwa gidana na miki rantsuwa da Allah idan kika sake dauko min wani abu da bai dace da dabiar musulmi ba sai na bata miki rai. Bacin rai wanda sai kinyi nadamar aurena. Iya nasihar da zanyi miki nayi nima na gane rashin kyautuwar abinda muka yi a baya. Kina zaune lafiya da iyayenki baki isa ki rabani da nawa ba. This....ya nuna ta da dan yatsa is my last warning. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿13 Batul Mamman(Mrs)💖 Fada sosai Hamza da Izzatu suka yi sai da kyar ya samu ya rarrasheta suka daidaita. Amma kudirin ramuwa yana nan a ranta, dama kawai take jira. Kusan wata biyu suna zamansu lafiya. Architect Hamza na kokari wurin cigaba da kulawa da iyalinsa. Su Hajiya ma yana wadata su da abubuwan bukata. Hatta kawunsa da aka kora aiki sai da ya aika masa da dubu dari. Hajiya taji dadi sosai har waya tayi masa abinda bata yi sai da dalili saboda dan fari ne tayi masa godiya. Wannan wayar tasa shi jindadi mara misaltuwa. Shiyasa ya cigaba da yin abinda zai kyautatawa iyayensa. Itama Mama taji dadi ya dauki shawararta don Izzatu bata nuna musu bacin ranta game da tafiyarsu Kumo da 'ya'yanta ba. Zuhra an gama koyon saka Baba ya kukuta ya siyo mata injin saka tsoho ne ma amma bai lalace ba. Tayi murna sosai shiyasa sakarta ta farko shi da ummanta ta fara sakawa rigunan sanyi masu kyau da kauri har uku uku. Duk da suna tsokanarta taki karatu amma sakar tayi kyau sosai. Umma ta bata shawarar duk lokacin da aka bata kudi ta sayi kulu tayi sakar ta ajiye kafin lokacin sanyi tunda ya kusa sai tq sayar. Wata rana Hamza ya fita zuwa gidansa da suke shirin komawa tun safe saboda aikin yazo karshe. Gida ne da ya tsara komai na ginin da kansa sannan kamfaninsa ke ginin. Izzatu tana kitchen yayarta dake aure a Alaska ta kirata a waya. Suna hira ne Izzatu ke tambayarta ina yaranta. Zeenatu tace sun fita da babansu siyan kayan da zasuyi amfani dasu na HALLOWEEN. Izzatu tace kai sis har kin tuna min lokacin da muke siyan namu da Daddy. Gaskiya ba karamin missing America nake yi ba. Zeenatu tace ba kinga dan fillo duk kin rude ba. To amma meyasa bakiyi a nan? Hmmm kinsan yan Nigeria da kauyanci kada ma yan kauye suji labari. Gidadancinsu yayi yawa...ko kin manta yadda muka yi da inlaws dina game da birthday din Nana? Zeenatu tayi dariya haba Juliet din Romeo duk soyayyar taku har zakiyi korafi. Ba haka bane sis, abin ya bani haushi sosai. Amma gaskiya zamuyi halloween this year. Ba don yana wani aiki ba ai da dole mu taho sai muyi celebrating tare. Zeenatu tace muma zamu taho nan da December a gida zamuyi new year. Bayan kwana biyu da wayarsu zancen halloween ya tsayawa Izzatu a rai. Lokacin da suna Canada da iyayenta suna celebrating tare sa sauran turawa. Nan da nan ta fara shirye shiryen yadda zasuyi nasu a gida. Hamza ta tambaya kudi don ya dena bata atm card dinsa. Tunda tace kaya zata siya bai hanata ba saboda rigimarsu ta party ta wuce. Washegari ta debi yara suka je manyan shopping malls din Kano da kyar ta sami abinda take so ta dawo rai a bace. Me zaayi da Nigeria abinda bai taka kara ya karya ba sai ka nema ka rasa. Washegari Khalifa ya tashi da zazzabi dama mura yake suka fita wannan siyayyar. Abu kamar wasa sai da suka kaishi asibiti da daddare, sai da safe aka sallamesu bayan an gama kara masa ruwa. Da suka dawo ne wurin karfe takwas ya kira Mama ya sanar da ita. Ranar ta dace da talatin da daya ga watan october wadda a irin wannan ranar ne turawa suke yin halloween. Izzatu bata fadawa Hamza ba domin bata dauki abin a cikin irin wadanda ya hana ba tunda ba gayyato mutane zata yi ba. Ita da 'ya'yanta zasuyi abinsu a gida. Bayan Hamza ya fita tasa Tala tayi musu wanka ta koma kitchen. Ita kuma ta dauko musu kayansu da ta siyo ta saka musu. Harda Khalifa mara lafiya. A ka'idar wannan rana ta halloween wadda take da sunaye da yawa harda Day of the Dead ana yin abubuwa masu yawa. Nasara mabiya addinin kirista suna celebrating wannan rana ne domin tunawa da matattunsu. Kamar waliyai, manyan masu bauta da shahidansu. Ana saka kaya na ban tsoro a ranar kamar riga mai alamun jini, fuskar shaidanu, yin shigar da baza'a gane mutum ba, tsorata mutane a gidajensu ko waje, zuwa wuraren ban tsoro kamar makabarta, tsohon kango ko gidan da babu mutane. Kai hatta horror films(fim na ban tsoro) ana gani a wannan ranar ko ka ziyarci malamin duba da sauran abubuwan firgici dai. Haka halloween yake ko kadan bashi da alaka da musulunci. Amma wani lokacin musulmai yan uwammu idan suka sami kansu cikin yahudu da nasara sai kawai su dauki al'adunsu suna ado dasu ba tare da sunsan ainihin dalilinsu na girmama ranar ba. Zama a kasar waje ba shine dalilin da zaisa mu dauki dabiar nasara wadanda suka bata da yahudu wadanda Allah ke fushi dasu ba. Allah Ya tsare mana imanimmu. Amin Izzatu ta sakawa Khalifa da Junior kayansu. Rigace mai dogon hannu da dogon wando duk sun dame musu jiki ga kuma fuska wadda aka fitarwa hudar idanu da wurin numfashi. Kayan bakake ne. Idan daga nesa ka hangosu zaka rantse kwarangwal ne saboda zanen kayan da yanayinsu. Bayan ta shiryasu ta daukesu hoto ta turawa Hamza a waya. Daga nan taje ta dauko na Nana. Su kuma jajaye ne harda safar hannu mai alamar farata zako zako. Fuskar(mask) kuwa kamar ta aljanu harda kaho biyu a sama. Nana tana ta dariya Izzatu ta gama shiryata ta daukota zasu fito falo sai Nana tace Mummy poo. Izzatu ta san halin Nana bata kashi a pampers duk yadda za'ayi da ita. Dole ta cire mata ta zame mata wandon ta dorata a po ta tafi kitchen duba girki don shabiyun rana ta wuce. Junior da Khalifa suna falonsu suna kallon cartoon. Tana kitchen taji sallamar su Mama. Da sauri ta fito tana musu sannu da zuwa. Duk su biyun rungume su tayi yadda ta saba. Hajiya sai dan yake take don wannan halin na Izzatu na bata kunya. Bayan sun zauna ta gaishesu Mama tace ina Khalifan? Ashe baiji dadi ba. Izzatu tace eh amma yau da sauki sosai. Zazzabi ne da mura. Hajiya tace to Allah Ya bashi lafiya. Mama tace kirawo shi mu ganshi. Dazu babansa yayi min waya da safe shine muka zo duba shi. Izzatu tace Tala ta dauko musu ruwa da lemo. Tala na tashi Nana ta fara ihun Mummy na gama da dan gwarancinta. Izzatu tace jeki kiyi mata tsarki bari na kawo musu. Tashi tayi tana kiran su Junior su zo ga su Hajita ta shige kitchen. Ba'a fi rabin minti da shigar Tala ciki ba ta fito falo tana ihu. Gabadaya jikinta rawa yake sosai tana kuka. Hajiya da Mama suka tashi a firgice suna tambayarta abinda ya faru. Cikin kuka tace mutanen boye sun bayyana. Mama tace su wa? Tala tace aljanun. Yau na gansu da idona ra'ayil aini har su biyu. Wallahi sai ga yarsu zaune akan po din Nana dayan kuma yana mata wasa. Na higa uku na lalace kwarankwatsa ko a kauyenmu ban taba gamo ba he yau. Izzatu ce ta fito da sauri daga kitchen tace ke Tala bana son rashin hankalin nan naki. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿15 Batul Mamman(Mrs)💖 Yana gama magana ya tashi yana kwalawa Tala kira. Da yake tana labe a bayan kofa da gudu ta fito jiki na rawa yace jeki ki cire musu kayan nan ki kawo min mota ina jiranki. To kawai tace ta kwasa da gudu tayi ciki. Izzatu ta kalleshi itama rai a bace kudi fa nasa na sayi kayan nan. Me zakayi dasu?. Ya dan daga gira daya Allah ko? Tunda kudin nawa ne babu ruwanki da abinda zanyi. A iya zamansu basu taba samun sabani kamar yadda suke yi yan watannin nan ba. Kirikiri iyayensa ke nuna mata kiyayya amma zata yi maganin abin. Ta yanke shawarar bazata taba bari maganganunsu suyi tasiri a ranta ba har ta dena rayuwarta yadda ta saba. Ita tasan iyayenta sun bata tarbiyya irin wadda ta dace kuma ga yayarta da mijinta suna zamansu lafiya sai ita kadai ce zasu takurawa. Horn Hamza ya rinka dannawa da karfi sai ga Tala kamar an jeho ta. Ta mika masa kayan. Har ya dan ja motar sai ya dawo ya sake kiranta. Ke fada min gaskiya me ya faru da su Hajiya suka zo dazu? Ai kamar jira take ta soma bayani dalla dalla. Dama banda tsoron da taji ba karamin mamakin Izzatu tayi ba da tayiwa surukanta dariya. Fuskar nan ta Hamza kamar bai taba dariya ba ya ja mota ya nufi gidan iyayensa. Hankalinsa a tashe ya gyara parking din motarsa saboda yaga alamun Alhaji na gida. Yana shiga falo Adabiyya da Hamida ya gani suna kuka. Gabansa ya fadi yace ku meye haka? Adabiyya ta taso ta rungumeshi tana cigaba da kukan. Dama duk ta fisu raguwar zuciya. Hamida tace Mama akeyiwa gyaran kafa. Me kika ce??? A razane yake maganar tace gocewar kashi ta samu. Matsar da Adabiyya yayi daga jikinsa ya shiga falon Alhaji. Mama ya gani zaune a kasa tayi gumi sosai Hajiya na rike da hannunta. Kafarta ta hagu daure da wani farin yadi. Gefe kuma mai dori ne durkushe gaban Alhaji zai karbi kudinsa. Mai dorin yace in Allah Ya yarda gobe da safe zan dawo na duba. Allah Ya kiyaye gaba. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka Hamza ya karaso cikin falon. Mama ce kawai ke kallonsa, ita Hajiya kawar da kai tayi gefe. Alhaji Nasiru ya hade fuska kana ganinsa kasan yana cike da bacin rai. Kusa da Mama Hamza yaje ya zauna ta riko hannunsa kawai sai ta soma kuka. Hajiya ta tashi zata bar falon Alhaji ya dakatar da ita. Hamza yace Alhaji barka da rana. Muryarsa har rawa take bata fita sosai. Alhaji yace Hamza.....toh fa yau duk su biyun sun kira shi da sunansa. Allah gani gareKa yace a zuci. Naam Alhaji. Alhaji yace dago kanka ka kalleni. Kasawa Hamza yayi. Alhaji yace ashe kana da sauran kunya. Dubi yadda iyayenka suke kuka saboda bacin ran da suka kwaso a gidanka. Yau Mamanka ce a zaune ana mata gyaran gocewar da tayi a gidanka matarka tayi mata dariya. Wace irin rayuwar aure kuke yi kai da iyalinka? Me kake son nunawa duniya game da tarbiyar da muka baka? Ba don tsarewa ta Allah bace duk kannenka koyi zasuyi da irin dabiun da ka kwaso a turai. Alhaji ya cigaba da cewa duk irin abinda kuke yi babu wanda ban sani ba amma na kawar da kai saboda iyayenka basu tunkareni da maganar ba. Na basu damar su ta iyaye mata su saita ka a hanya kuma nasan sunyi iya kokarinsu. Amma yau saboda abin yayi yawa Halimatu da kanta ta sanar dani abinda yarinyar nan tayi musu. Wulakanci na karshe Izzatu tayiwa iyalina amma bazan umarceka da rabuwa da ita ba. Sai dai ka sani wallahi nayi maka rantsuwa ranar da duk kuka sake aro daga munanan al'adun wasu har kunnena ya jiye min ko ido ya gani zanyi maka hukuncin da baka taba tsammani ba. Da sauri Hamza ya kalli mahaifinsa don Allah kuyi hakuri Alhaji. Nasan nayi kuskure tunda da goyon bayana komai ke faruwa. Amma in Sha Allah zan gyara kuma yanzu zan daukota tazo ta bada hakuri. Hajiya tayi saurin cewa ban yafe maka ba muddin kace mata tazo bada hakuri. Indai hankalinta da tarbiyarta basu nuna mata abinda ya kamata ba shikenan. Alhaji yace ina zaune kike irin wannan zancen Halimatu? Tace ayi hakuri. Hamza ya dubi Mama wadda kanta yake a kasa ki yafe min Mama don Allah. Abinda ya faru yau ko kadan bani da masaniya a kai. Alhaji yace halo me ma kuka ce sunan abin? Hajiya tace yo ni ina zan rike. Kamar ba kalmar turanci ba, yau na fara jinta ma. Hamza ya sake dukar da kai ko a da bama yin wannan ranar bansan dalilinta na yi ba yau. Alhaji yace dalilinta ya wuce ta tozarta min iyali ne? Ka tashi ka tafi Allah Ya kyauta. Hamza dai kin tashi yayi ya kara matsawa jikin Mama yana rokon ta yafe masa. Murmushi kawai tayi tace masa ka tashi ka tafi ba komai. Duk yadda yaso Mama taki tsawaita magana. Hajiya tace ka tashi ka bamu waje magana ta kare. Idan ka fita ka turo min Adabiyya da Hamida. Jiki ba kwari ya fita ya turo su. Hajiya tasa Adabiyya sake gyara gadon Mama , ita da Hamida suka kamata suka kaita daki. Zuwa dare su Ibrahim duk sun zo gidan da iyalansu. Kowa yayi bakin cikin jin abinda Izzatu tayi musamman dariyar. Ummahani matar Ibrahim tace ni Yaya tausayi yake bani. Jidda tace tausayin me? Ba fa auren hadi bane da kansa yaje ya kwaso mana ita. Mariya tace kuma dashi suke komai ba. Dama matsalar ka fara abu kenan. Sai kaso denawa mabiyanka suce basu san zance ba. Motoci hudu ne a gidan Yaya amma ko keke bai siyawa ko da Nura ba da yake karatu. Irin abinnan ka daukewa iyaye wani nauyi ko a jikinsa. Daga shi sai iyalinsa. 'Yan kwanakin baya ne ma naga abin ya dan canja. Mama dai tana daga kwance tace ku bar zancen nan haka. A haka sai da Mama tayi sati uku a kwance saboda banda gocewar tayi ta fama da zazzabi. Kullum safe, rana da dare Hamza sai yazo. Da daddaren ma da su Khalifa yake zuwa. Izzatu kuwa tunda baice tazo suje dubiya ba itama ta share. A ganinta yan uwansa ne bazata masa shisshigi ba. Wani lokacin ya hadu da kannensa wadanda suka hade masa kai. Daga gaisuwa basa kara yi masa wata maganar. Su Hajiya suna amsa masa gaisuwa amma suma daga nan magana ta kare. Rashin kula shi da Mama keyi duk yafi komai tada masa hankali. Bashi da aiki sai bada hakuri sai dai tace masa babu komai. A haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya har suka dan daidaita. Mama ce dai har yanzu bata yi masa kamar da. Shi kuwa bai kosa da yi mata siyayya ba kullum. Domin yanzu ya dauki irin abinda Ibrahim yake yi tun bayan yayi aure. Kullum sai yazo gidan ya gaishe da iyayensa ko da safe kafin yaje aiki ko bayan magariba. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿16 Batul Mamman(Mrs)💖 Wata asabar da safe Izzatu ta nemi izinin Hamza tana son zuwa Abuja tunda su Junior na hutun makaranta wurin iyayenta. Ya amince har ya bata dubu hamsin ko zata yi siyayya sannan ya cika mota da mai yasa dreba ya kaisu. Ashe new year celebration taje gani. Sauran shekarun duk tare suke yi da Hamza, ganin yadda lokaci guda ya canja mata yasa bata sanar dashi gaskiya ba. Da yaran ta tafi suka je kallo tare da kannenta. Bayan sati daya suka dawo gida. Zuhra ce take tafe da katuwar ghana must go shake da kayan sanyin da ta saka. Yanzu ta kware sosai don sanyin da ya wuce tayi ciniki sosai. Da yake farkon March ake gari ya soma zafi. Sai dai mijin Anti Faiza ya samar mata wata makarantar primary sun bata kwangilar sakar rigunan sanyin dalibai. Murna sosai su Baba suka yi. Ta gama na farko shine zata kai musu. A daidai wani lungu zata wuce bakin titi ta hango Anas da abokinsa Sani suna busa wiwi. Idonunta kyam a kansu, Anas ne ya fara hangota yayi saurin taba sani. Dukkansu kashe tabar suka yi suna murmushin yake. Fitowa suka yi daga lungun Sani yace kaga manyan yan mata. Zuhra ina zuwa haka da rana? Ta karkace kai tana kallonsu wai nan bagarar dani zakuyi. To nagani kuma sai na fada. Anas yace don Allah kada ki fadawa Baban yara. Kinga muje mu rakaki inda zakije ma. Sani ya karbi jakar zai daukar mata. Da sauri ya mayar ya ajiye...ke yanzu tun daga gida kika dauko jakar nan. Zuhra tace eh menene? Sani yace Anas dauki ka ji. Anas ma dagawa yayi ya mayar Zuhra haka kike da karfi. Wani murmushi ta saki da yasa duk munin kwalliyarta tayi kyau. Au ku da rainani kuke yi? Ai kada ku taba bari dambe ya hada mu don kasa zan kaiku. Sani yace ke dalla can wa ya fada miki maza na son mata karfafa. Ko ni naji nauyin jakar bare ke. Wallahi ina baki shawara idan kika yi aure ki nunawa mijinki ke raguwace. Sai yafi sonki. Amma yana ganin kin fara aje kwanji wata zai dauko a mayar dake maigadi. Zuhra ta sha kunu amma ka zage ni Sani, kai Anas kayi wa abokinka magana wallahi. Anas yayi dariya ai gaskiya ya fada miki. Daukar abu mai nauyi ai ba na yanmata bane. Fizgar jakar tayi ku bani kayana yan wulakanci. Kun tsayar dani kuna ci min fuska..kuma sai na fadi abinda naga kuna yi. Anas yace to yi hakuri. Yanzu ina kika nufa mu daukar miki kayan. Dayake dama ta gaji sosai tace bakin titi. Gidan yayar Hajara zani. Sani ne ya dauko jakar Anas yace yaushe ne bikin Hajara. Nan da sati biyu Zuhra ta bashi amsa. A bakin titin suka tarar mata adaidaita sahu. Anas ya mika masa dari biyu yace ya kaita har kofar gidan da zata je. Tayi musu godiya suka juya. A hanya Sani yace Baabaa yaushe zaka fadawa yarinyar nan kana sonta ne? Anas yace haba Sani. Zuhra tafi karfina. Sani yace Zuhran?yarinyar da ko kwalliya bata iya ba. Ko sakandare bata gama ba fa. Anas yace amma ai tana da tarbiya. Kuma sau nawa Baban yara na kama mu a wurin nan. Ai da kunya nace ina son yarsa. Sani ya bigi kafadar Anas to tun wuri gara ka sani ni zan mata magana. Dama don naga kamar ka rigani fara sonta shiyasa na kyale. Anas ya daure fuska kasan Allah bazan bari ka aureta ba. Zuhra sai mutumin kirki mai rufin asiri. Sani ya soma gudu bari kaga har gida zan sami mahaifinta. Da haka suka tafi suna dariya. Su Zuhra sun kawo kwanar layin gidan Anti Faiza wasu mata uku suka tsayar da mai adaidaitan. Suka yi ciniki yaji kudi yace Zuhra ta sauka. Rai a bace tace haba malam ba haka mukayi da kai ba. Jakar nan nauyi gareta kuma gidan yayi dan nisa daga bakin titi. Naira hamsin ya miko mata gashi ki nemi wani ya karasa da ke. Ba yadda zatayi dole ta fito tana kunkuni. Ta kalli matan sunsha ado da gani biki zasu je ta dan murguda baki...ku ma Allah Yasa ku hadu da wanda zai muku abinda kuka yi min. Dankwalinta ta ciro daga kanta ta gyara hijab din sannan tayi gammo da dankwalin. Tana kicikicin dora ghana must go din taji horn din mota a gefenta. matsawa tayi tana tunanin ko ta tare hanya ne. Horn din ta sake ji sai ta dan juyo taga ko da ita ake. Ba karamin mamaki tayi ba da taga matar mutumin nan mai fadan tsiya. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿 17 Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra ta washe baki tana murmushi tace ke ce? Izzatu itama murmushin take tace nice. Kingane ni ko? Zuhra ta gyara jakar kanta tace eh mana. To shigo na rage miki hanya Izzatu ta fada tana bude mata gaban motar. Allah Ya sani kayan da nauyi ba musu ta sauke tace ina zan saka jakar? Izzatu ta bude mata booth ta saka sannan ta dawo gaba ta zauna. Sai da ta zauna sannan ta gaishe da Izzatu. Sanyin AC yasa ta wani lumshe ido don har ta fara gumi. Izzatu ta ce gidan Faiza zaki je ko? Kai Zuhra ta daga don ji takeyi kamar tayi bacci. Ba karamin dadi take ji ba yadda sanyi ke busowa ta gaban motar. Ko da suka tsaya tace da mun saba dake cewa zanyi ki sake kunna min sanyin nan ko da na minti daya ne. Izzatu sai dariya tace ai mun saba idan kina so sai na kunna miki amma idan zaki bini gidana. Da sauri Zuhra ta bude kofa, wa ya aikeni naje na hadu da mijinki. Rufa min asiri. Tare suka shiga gidan tana jan jakar kayan Izzatu na binta a baya. Anti Faiza tayi mata godiyar taimakon Zuhra da tayi. Izzatu tace ai ba komai. Kanwar taki ce akwai ban dariya. Ta dauko wayarta daga jaka, dan bani number dinki sai mu rinka gaisawa. Anti Faiza tayi saurin rike hannun Zuhra da take kokarin duba numbarta a cikin wayarta don bata haddace numbar ba. Tana dan yake tace rabu da lamarin Zuhra damunki zata rinka yi da flashing. Zuhra ta zumburo baki haba Anti Faiza nima fa yanzu ba zaman banza nake ba. Da sana'a ta, dan kudin gaisawa dai ina dashi. Izzatu tana dariya tana kallon kayan da Anti Faiza ke dubawa. Daya ta dauka ta bude daga cikin ledarta tace amma sakar nan tayi kyau. A ina kuka siya? Zuhra tayi caraf tace ni nayi. Da gaske Izzatu ta tambaya. Anti Faiza tace eh sanaarta kenan. Izzatu na jin haka tace lallai sai ta karbi numbar Zuhra. Kizo muje gidana ki gwada su Nana sai kiyi musu. Zuhra tana ta zumudi ta bada number sannan ta amince zata je gidan Izzatu tunda ta tabbatar mijinta baya gida. Cikin daki Anti Faiza ta kira Zuhra. Naga kina ta rawar kai akan matar nan. Tunda nake da ita bata taba zuwa gidana ba sai kwanakin baya da suka kusa bige ki a mota. Daga ranar ban kara ganinta ba sai yau duk a dalilinki. Don Allah ki kama kanki nima ba wani sabawa mukayi ba. Aikin kayan flawa take bani tana biyana. Kuma kodayaushe ni nake zuwa gidanta. Zuhra tace to ko dai na fasa zuwa kawai. Nace ta kawo yaran nan. Anti Faiza tace ba haka nake nufi ba. Kije amma ki kula kinji ko. A hanyarsu ta zuwa gidan Izzatu tana ta yiwa Zuhra tambayoyi ita kuma ta dena yar fara'ar da take yi saboda maganar Anti Faiza. Izzatu duk ta damu don ita tsakani da Allah shirmen Zuhra na burgeta. Tace ko dai nayi miki wani Zuhra? Eh to ba wai wani abu kika yi ba, Anti Faiza ce tace na kama kaina a gabanki itama bata saba dake sosai ba. Izzatu tace kuma a sirri ta fada miki ko? Zuhra tace eh....au tayi saurin rufe baki. Kuma wai sai na fada miki. Kai amma banji dadi ba. Izzatu tace bazan taba nuna mata kin fada ba. It's going to be a secret. Zuhra tace uhmmm tana dan murmushi. Turancin yayi tsauri kuma gashi kamar na yan TV ba'a ganewa sosai. Shiyasa tayi shiru kawai. Gida ne mai kyau suka shiga sai dai ga kaya a kwaleye ko ta ina. A falon ma babu kujeru sai carpet kawai. Zuhra tana ta kalle kalle tace tashi kuke ko tarewa? Izzatu tace tashi zamuyi. Babyna ya gama gininsa. Zuhra ta rufe fuska da hijab tana dariya. Wai baby....Izzatu tace shine kike min dariya to ya kike kiran naki saurayin? Zuhra tace bani dashi amma ko na samu ni ban iya irin wannan abin ba. Kunya zanji wallahi. Izzatu tayi dariya sannan ta tashi ta kirawo yaranta daga dakinsu. Zuhra kallonsu kawai tayi tace ta gane yadda zata yi sakar. Suna tafiya tace 'ya'yanki kyawawa kema kyakkyawa. Ke kam kinji dadinki. Ga gidanku ma mai kyau. Yanzu idan kuka tashi wanda zaku koma ya kai girman wannan? Izzatu tace yafi wannan ma. Hira sosai suka yi har Zuhra ta fahimci Izzatu tana da kirki. Har kyautar turare tayi mata da zata tafi. Bayan ta koma gida ne take bawa su Umma labarin Izzatu da kyautar da tayi mata. Sunji dadi amma anyi mata fadan karbar turaren. A nata bangaren Izzatu ta bawa yayarta Zeenatu labarin Zuhra ta waya suna ta dariya. Zeenatu tace irinsu idan kika yi fooling dinsu bazasu gane da wuri ba. Izzatu tace kwarai kuwa. Ita da akayi sirri da ita shine ta fada min. Ina jin APRIL FOOL din shekarar nan da ita zanyi. Zeenatu tace ke da mijinki ya kafa miki doka. Mtsw rabo dashi wannan ai ba harkar kudi bace bazai damu ba. Ke ni har dashi ma zan hada ta fada tana dariya. Dama nace zan rama hanani party da yayi. Zeenatu tace zamu zo Kanon da su Mummy cikin next month kafin na koma Alaska. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿18 Batul Mamman(Mrs)💖 Bayan kwana biyu Izzatu ta gama tsara yadda zata bullowa Zuhra. Murmushi keta tayi don ta tabbatar ba karamin shan dariya zasuyi ba. Hamza ya dawo gida a gajiye 'yan kwanakin nan baya samun hutu sosai. Wani aiki ne ya sasu gaba, ga shirin tashi sunayi. Duk abin ya rincabe masa. Yana kwance necktie dinsa Izzatu ta shigo dakin ta rungume shi ta baya. Sannu da zuwa my darling. Murmushi yayi mata..kema sannu Izzy. Duk na barku da aiki ko. Ba komai, how was your day? Alhamdulillah ya bata amsa. Amma ina jin yunwa sosai. Me kika dafa mana yau? Ban fahimceka ba, ka manta yau thursday. Ga yara sun dawo daga school kowa yunwa muna ta jiranka. Naso kiranka na tuna maka a kawo na rana sai nayi bakuwa. Tun kafin ta gama magana ya rufe idanunsa saboda ransa da ya baci. Ba rashin girkin ne ya dame shi ba kamar yunwar yaran. A hankali ya kalleta Izzy ina ganin lokacin canja wannan tsarin yayi. Ga 'ya'ya Allah Ya bamu. Ki duba irin ayyukan da suke gabana kinsan dole na manta. Kuma su yaran ba kya jin tausayinsu ne. Ko indomie sai ki dafa musu. Ta harare shi wasa ma kake yi Hamza. Duk tsarin da muka yiwa rayuwarmu tun kafin aure yanzu a hankali kake soke komai. Don kawai kaga ina hakuri. Tana magana sai kuka ya kwace mata. Kada ka bari soyayyarmu ta ja baya saboda sabon ra'ayinka. Ni ba wannan Hamzan na aura ba. Wanda na aura ya damu da farincikina. Tausayi ta bashi ya rungumeta yana bata hakuri. A hankali yake magana. Izzy ya kamata mu fuskanci rayuwa a yadda take. Na daukar miki alqawura da dama ba tare da dogon tunani ba. Ba kullum ne zamu sami abinda muke so ba. Kinga saboda bana son tsegumi da kaina nake siyo mana abinci duk alhamis. Yau na gaji ga ayyuka. Ki daure ki rinka girkin ni kuma duk lokacin da nake da time sai na siyo a waje mu ci. Ta dago fuska sharbe da hawaye to naji amma sai ka amince ranar da zamu tare zamu danyi walima mutane su tayamu murna. Izzy na dauka mun rufe irin wadannan abubuwan. Tace walima nace ba party ba. Ko kida bazamu kunna ba I promise. To ba komai amma har yaushe zaki shirya wata walima. Tace ka bari sai nan da kwana tara mu koma. Jumaa ta sama kenan, mu sami albarkar Jumaa. Yayi dariya to naji amma please kafin nayi wanka abinci....tana tafiya tace Jumaa 1st April tayi kwafa. Su Zuhra ana ta shirye shiryen bikin Hajara zama ya gagare su. Kullum sai sun fita. Sune kasuwa ko wurin mai dinki. Ana saura kwana biyu kamu ta dawo daga raka Hajara saloon din unguwarsu taji Baba da Umma suna magana a tsakar gida. Allah Yasa Hajaran ta wuce gida. Baba ne yake cewa...ina farinciki da auren Hajara amma lamarin Zuhra na damuna. Duk samarin da ke zuwa sai kiga babu na aure. Bana son tayi ta zama a gida tunda ba karatu take yi ba. Umma tace haka ne, kuma abin ba zai dameta ba yanzu sai taga an kai Hajara dakinta. Amma da kake damuwa yarinyar nan ko shekara ashirin da daya bata cika ba. Baba yace to ai dai ta kusa. Shekaranjiya da naje Ajingi baki ji fadan da Inna tayi ba wai mun sa yarinya a gaba munki yi mata aure. Yaya Sabiu kuma sai cewa yayi ko Garzali ne na wajensa a hada su tunda shima yaki karatun. Zuhra tana daga soro ta dafe kirji....Yaya Garzali kuma? Allah Ya kiyaye. Mutum mai shegen ji da kai kamar wani mai mulki. Baba taji yace duk da ba kudi gareni ba bana fatan yarinyar nan ta auri mara ilimi irinta. Ba mai kudi nake jira ba amma ina mata fatan samun rufin asiri a rayuwarta. Umma tace Allah Yayi mana zabi nagari. Idan ta dawo sai kayi mata maganar Garzalin tunda a gaban Inna akayi ya kamata ta sani. Hawaye ne suka saukowa Zuhra ba tare da ta sani ba. Allah Sarki Baba da Umma. Sai yanzu take jin inama ta dan mayar da hankali a makaranta. Wayarta ta zaro daga yar jakarta ta bude sakonnin da yau kwana uku kenan kullum sai anyi mata safe da dare. Ta rasa ko waye yake mata wadannan sakonnin soyayya. Lokaci yayi da zata dena sharewa kila alkhairin da Baba ke jira ne ya tunkaro ta. Ta goge fuska ta shiga ciki. Jikin Umma ta fada tace wash Allah nagaji sosai. Umma ta ture ta to dagani kada ki karasa kashin tsufa. Zuhra ta tashi ta koma kusa da Baba. Tana dan daga gira tace in kwanta a jikinka Baban yara? Rankwashi ya kawo mata ta goce...yarinyar nan kin gama rainani. Wayarta ta mika masa Baba sirri nazo muyi. Umma tace ai sai dai idan na fita amma babu inda zani ayi a gabana. Shi kuma Baba yana murmushi yace to ko daki zamu shiga. Dariya kawai tayi ta bashi wayarta ta nuna masa sakonnin text da ake yi mata. Baba ya karanta yafi sau uku uku murmushinsa na fadada yace waye wannan? Zuhra tace nima ban san shi ba. Amma kaga a sakon karshe yace yana jiran amincewata ne ya gabatar da kansa wurinka. Da izininka zai fara zuwa. Duk dadi ya kama Baba sai murna yake. Umma tace kuyi min bayani mana. Baba yace saurayi muka yi. Umma tace kai Baban Zuhra akan yar nan ka iya rufe ido ka manta kai babanta ne. Yace to da 'yar wani kike so nayi. Kinga Zuhra ki tura masa da amsa mai dadi...banda shirme kinji ko sannan kice kin amince ya gabatar da kansa. Tunda yace yana aiki a wani kamfani ai kinga ko ba komai da dan iliminsa ko da na sakandare ne. Karfe tara na dare text ya sake shigowa wayar Zuhra. ** Kewarki ta dameni, ki amince na nuna miki soyayyata gareki** Wani juyi Zuhra ta rinka yi cike da tsananin jindadi. A yan kwanakin nan ta tsinci kanta da jiran text duk safiya da dare. Reply ta tura kamar yadda Baba ya bata shawara ** Na amince** Har Izzatu ta kwanta taji shigowar text. Hamza ya kai hannu zai dauki wayarsa tayi saurin dauka. Yace ni da wayata zaki min kwace? Tayi murmushi ta bude ta karanta. Dadi ne ya kamata. Hamza yace text din waye ne kike murmushi. Kamar yadda ta saba saurin gogewa tayi tace kyale tallan MTN ne. [25/09 3:38 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿19 Batul Mamman(Mrs)💖 Su Zuhra an fara biki. Sunyi kamu ranar laraba a wani fili nan cikin layinsu. Yan makarantarsu da yawa sun zo bikin. Wata cikinsu mai suna Ikilima ce tayiwa amarya kwalliya. Zuhra tana daura dankwalin ankonta Ikilima tace don Allah ki bari nayi miki kwalliya. Wannan fuskar taki duk kin bata ta. Tissue tasa ta goge fuskar Zuhra sannan tayi mata kwalliya. Nan kawayensu suka rinka cewa tayi kyau sosai. Washegari da babu abinda zasu yi amma an dan taru a gidansu Hajara. Yan mata kuma suna gidansu Zuhra. Tana zaune ana yi mata kitso wayarta tayi kara. Ta daga taga sunan Izzatu. Hankalinta ya dan tashi bata gama mata sakar yaranta ba. Hakuri ta soma bata tana daga wayar. Izzatu tace ba komai ai nasan kuna bikin kanwar Faiza. Ni magana daban na bugo muyi. Zuhra tace to ina ji. Izzatu tayi yar dariya, dama ranar da kika zo gidana kina fita kanina ya shigo kila ma kin ganshi. Zuhra ta dan yi tunani kai babu kowa a hanyar. Izzatu tayi saurin gyara zancen kada Zuhra ta gane. Cewa yayi ya ganki don yana shigowa tambayata yayi ko kina da aure. Nace a'a. Shine ya dame ni har na bashi numbarki. Ina tsammani ya kiraki ko yayi text. Daga daya bangaren Zuhra taji wata murya mai dadi ana cewa haba Izzatu na fada miki ban fara yi mata waya ba sai naga babanta. Zuciyarta har wani saurin bugawa tayi, ba dai mai yi mata text dinnan bane. Izzatu ta katse mata tunani yace sai gobe zai zo gidanku magana da babanki bayan magariba. To a ranar zamu tashi shine za'ayi walima a sabon gidan. Don Allah kizo in nuna miki shi. Ni a ganina gara ku fara haduwa kafin maganar taje ga iyaye. Kuma sunansa Hamza don yace bai fada miki ba ko. Lallai da gaske Izzatu take don jiya yayi mata text yace zai zo ranar Jumaa. A take taji tana jin kunyar Izzatu. Ashe ma dan gayu ne indai kanin Izzatu ne. Ji tayi ance Zuhra zaki iya zuwa din ko ma hadu a gida? Farinciki fal zuciyarta ta rike wayar tana murmushi. Wai ita ce saurayi ke mata magana irin haka. A hankali tace zanzo in sha Allah. Daga nan ta ajiye wayar. Izzatu ta kalli kaninta Walid tace gobe akwai show a gidan nan. Walid yace amma sis sai naji ba dadi kuma. Dungure masa kai tayi...to kill joy idan ka ga dama kada ma kazo. Ya gyara face cap dinsa da ta karkace wai da yaya kike daukar wayar Hamza ne bai sani ba? An gaya maka ni din ta wasa ce? Baya amfani da wayar sosai sai nace ya bani aronta don kada Zuhra tayi text ko waya yana office. Bayan an watse ne ta sanar da Umma yadda suka yi da su Izzatu. Umma tace ba komai amma idan kinje kada ki dade saboda lanchin din Hajara. Ku ne iyayen biki. Haba ai bazan dade ba Umma. Don tana ta rokona ne ma. Umma tace ba komai ki yi sauri dai. Daga nan fita tayi taje ta sanar da aminiyarta Hajara. Amma fa ban fadawa Umma zamu hadu dashi ba. Hajara tayi mata dundu tana dariya tace yarinya ta fara sanin soyayya. Tana dawowa gida ta tarar da Umma tana wanke wata farar shaddar Baba mai kyau. Zuhra tace gobe zashi daurin aure ne? Umma tace ba kince yaron nan Hamza zai zo gaishe shi ba, ai gara a ganshi da kwarjininsa shima. Wani dadi Zuhra taji tace to kawo na karasa wankin. Umma tace bari dauraya ta rage min. Biyun dare ta wuce sannan aka kawo wuta. Zuhra ta tashi tana magagin bacci dama jiran wutar take yi. Da sanda ta lallaba ta dauko kayan Baba daga shanya tazo ta goge masa. Itama cikin kayanta na bikin Hajara ta sake gogewa. Daya zata je gidan Izzatu walimar tarewa, dayan kuma sai da yamma idan Hamza yazo. Rigunan sanyin da ta karasa sakawa ta saka a leda ta gama shirinta tsaf. Shigen gyaran girar da kawarta tayi mata a kamun Hajara ta kokarta tayi. Sai dai tata tayi girma da baki da yawa. Leben nan yasha janbaki purple don ance mata shi ake yayi yanzu. Tayi daurin dankwalinta sannan ta kawo katon mayafi ta dora a kai. Umma ta yaba da kwalliyar tace idan kin kai mata kayan kada ki karbi kudi tunda kinga inda rabo kaninta zaki aura. Zuhra tayi dan murmushi tace to Umma. Ko daga nesa ka hangota za ka san tana cikin nishadi. A haka ta je gidan anti Faiza don tare zasu tafi. Anti Faiza tace naga alama dai Izzatu na ji dake. To dai muyi sauri kinga akwai sauran shiri a gabanmu. Ni ba don aikin meatpie dinta ba ai ba inda zani. Sai dai ta bani fiye da kudin aikin shiyasa na karba. Dreba Izzatu ta turo ya dauki su Zuhra saboda kulolin da Anti Faiza ta zuba meatpie har uku ne. Hamza ya gama magana da lauyansa an gama komai a takardun tsohon gidansa. Da daddare in Allah Ya yarda zai kaiwa Alhaji a bawa kaninsa Nura. Idan yaso in ya tashi aure sai a kara gyara gidan. Ya dan shafi kansa yasan yau iyayensa zasuyi farinciki da abinda yayi musamman Mama. Sakonnin email dinsa ya bude yana karantawa don yau bazai koma gida da wuri ba sai sun gama walimarsu. A firgice ya tashi yana kiran Inuwa sakatare. Inuwa ya shigo da sauri yana tambayar ko lafiya. Hamza ya nuna masa wani sako da aka turo daga Mr Peter wakilin turawan da suka hada gwiwa dashi. Gumi ke keto masa ko ta ina yace Inuwa mutanen nan sunsha kwaya ne da zasu ce wai suna yi min tuni akan basu ribar da muka samu a watannin nan shida gaba daya. Ya ture takardun tebur dinsa. Ni ban fahimce su ba kwata kwata ina aka taba kasuwanci haka.. Inuwa yace ranka ya dade ka manta a contract din ance ribar wata shidan farko tasu ce. Daga nan kuma sai ku rinka raba ribar kai da su. Hamza ya daka tsawa inji uban wa??? Inuwa ya zabura ya matsa gefe. Wata tsawar ya sake yi jeka ka dauko min copy din contract din. Inuwa jiki na bari ya bude wata drawer a cikin office din Hamza ya dauko masa. Karantawa yake yana maimaitawa. Ya dago idanunsa da suka yi ja yace Inuwa garin yaya nasa hannu a takardar nan? Inuwa ya tausayawa ogansa yace ranar da Junior ya karye ne. Nima bayan ka fita na sake karantawa shiyasa na turo maka da text a daren. Hamza yayi saurin dago kai. Text kuma? Eh text na sake maka bayanin contract din ko zaa gyara tun kafin abin yayi nisa. Kuma ka tabbatar min ka karanta. Don kace Hajiya ta sanar da kai na bugu waya ma. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Izzatu kin kasheni shine abinda Hamza ya iya fada a hankali. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿20 Batul Mamman(Mrs)💖 Lokacin da suka isa gidan cike yake da mutane tamkar ana biki. 'Yan gidansu Izzatu har da mamanta duk sun zo. Ga kawayenta da makota da wadanda ma ba'a sansu ba 'yan cin ta tsotse. Kannen Hamza kuwa Mariya ce kadai taje sai Ummahani matar Ibrahim. Su Hamida suna Kumo ita da Adabiyya da Nura. Gidan ya tsaru sosai kana gani kaga gidan babban architect. Sama da kasan ko'ina mutane hawa sukeyi ana kallon yadda aka kashewa gidan kudi. Zuhra sai rakube rakube take yi ita tazo gidan surukai. Anti Faiza tana mata dariya don Hajara ta tsegunta mata zancen kanin Izzatu. Izzatu na ganinsu sai murna tasa aka shigo da meatpie din aka hada shi cikin kayan rabo. Zuhra ta mika mata kayan sanyi tace bari na dauki miki kudinki. A kunyace Zuhra tace ta barshi. Tayi murmushi ta fita bari a kawo muku abinci. Hamza ta fita ta kira tana rokonsa yazo gida Mummynta tana son ganinsa. Muryarsa a dashe saboda tsananin bacin ran da yake ciki yace mata ya kusa karasowa gidan. Da sauri ta koma dakin da ta bar su Zuhra tace mata dan sake gyara fuskarki muje. Anti Faiza tace ina zaku ake magana bama ganewa? Izzatu tace sirri ne. Kawayenta na dakin kuwa sun gane suma dariya suke yi. Yan kayan kwalliyar jakarta ta dauko ta sake shafa hoda da janbaki. Fuskar nan ta fita daban da sauran jikinta saboda kyallin foundation. Tun a dakin kannen Izzatu da yayarta Zeenatu ke dariya kasa kasa. Ita kuwa uwar gayya ko a jikinta tace da Anti Faiza yanzu zata dawo su tafi. Mamaki Hamza yayi yadda gidan ya cika da mutane haka. Yadda yake ji idan Izzatu bata yi da gaske ba zai iya marinta. Sanadiyar bin al'adun wasu ta janyo masa asara mai girma. Ita ta tada masa hankali yasa hannu a takardar ba tare da yasan me yake yi ba. Kuma ta goge masa messages. Tsaki yayi ya shiga gidan ta baya. Wani karamin falon ya shiga shiga ya kirata a waya. Bata kawo komai a ranta ba jin yanayin muryarsa. Burinta kawai taga yadda zasu kwashe da Zuhra idan sun hadu. Its Zuhra zaman jiran da take yi a falo ya fara isarta don ma da mutane. Da sauri Izzatu tazo da tray a hannunta dauke da juice da soyayyan nama a karamin plate ta mika mata. Muje ku gaisa ku tafi Faiza duk ta damu. Zuhra ta dan gyara mayafi ta karbi tray din. Sai da suka je kofar falon duk taji kunya kamar kada ta shiga. Izzatu ta turata tare da komawa falo tana sanar da mutane su shirya dariya zata yiwa wata April Fool. Mariya na jin haka ta mike da sauri tace da Ummahani kila yarinyar nan ce. Na rasa abinda ke damun Izzatu. Bata kara magana ba suka ji karar fashewar tangaran. Lokacin da Zuhra ta shiga falon da sallamarta. Hamza ya taso a fusace yana cewa Izzy kinsan abinda kika jawo min yau? Zuhra tayi saurin daga kai suka hada ido, bata san lokacin da ta saki tray din ba. Mutumin nan da ya kusa marinta ta gani. Bakinta har rawa yake tana cewa yayi hakuri ta durkusa tana tsince sauran jug da kofin da ya fashe. Dama a harzuke yake yace me ya shigo dake falona? Waye ya bude miki? Duk ta kidime tace Anti Izzatu ce. Zuwa lokacin kofar falon ta cika da yan gidansu Izzatu har da ita. Sauran mutane ma jin ana daga murya suka zo kallo. Hamza yace ita Izzatun ce ta bude miki falona tace ki shigo. Zuhra tace eh. Hamza na daga murya yace ba kece mara kunyar yarinyar nan ba, wato sata kika zo yi. Da sauri ta girgiza kai tace a'a wurin Hamza nazo. Daga shi har Zuhra babu wanda hankalinsa ke bakin kofa bare su ga yadda mutane ke kallonsu. Yan gidansu Izzatu da suka san komai sune suke dariyar yadda jikin Zuhra ke rawa. Yace Hamza? To nine Hamzan ya akayi? Zuhra tace ba kai Hamzan ba. Kannin anti Izzatu ne yace yana sona shine yake min tes. Ita tace na zo nan yana jirana wallahi. Hamza ya runtse idanunsa yace idan na bude baki bace min a wurin nan ba sai na bata miki rai. A gigice ta juya ta hango Izzatu. Ta karasa gabanta tace yi hakuri na fasa miki kaya. Amma ni ban gane ba mijinki yace shine Hamza. To waye kanin naki? Wata irin dariya taji sun kwashe da ita suna cewa APRIL FOOL!!!. Ko da bata gane me suke nufi ba amma dariyarsu tayi mata ciwo sosai. Hawaye kawai take yi ko gani bata yi sosai yadda hawayen ke zubo mata tace Apre..me? Kanwar Izzatu ta sake cewa April Fool. Da wannan fuskar taki kike tunanin yin saurayi dan gayu. Ina ji kuna hirar da matar da kuka zo. Anti Faiza tace Izzatu wai me yake faruwa ne. Na zata kuskure kikayi da kika ce a nan kanin naki yake jiranta. Ba sai kiyi musu bayani ba. Da kyar Izzatu ta tsayar da dariyarta tace ni nake yin text din. Hamza kallon Izzatu yake yi tana dariya ita da yan uwanta. Sauran mutanen wurin kuwa kadan ne abin ya basu dariya. Sauran tausayin Zuhra suke yadda rashin sani yasa ta fuskanci wulakanci. Anti Faiza ta rungumo Zuhra wadda bata san inda take jefa kafafunta ba. Sautin dariyar da aka yi mata kawai take ji a kunnuwanta. Izzatu ta cigaba da cewa april fool nayi mata na rinka tura mata text din soyayya. Ta zata saurayi tayi har ta amince. Ta dafa kafadar Zuhra ta sake cewa april fool. Kada ki damu it was just for fun. Saukar mari taji mai kamar wuta a kumatunta kafin Hamza yace kowa ya fice masa daga gida. Mata suka tsaya kallonsa ya daka musu wata tsawa. Ba shiri suka fara bacewa. Izzatu na dafe da kumatu ta juya taga ba Hamza, Zuhra da Anti Faiza. Anti Faiza jan hannun Zuhra kawai take yi har suka fita daga gate din gidan. Ummahani ce tayi musu horn Mariya na gaban motar suka ce su shigo. Anti Faiza tace su tafi kawai. Mariya tace kiyi hakuri ku shigo kada a rinka kallonta kinga an fara fitowa.. Anti Faiza tana ta cewa su tsaya zasu sauka a hanya amma Ummahani taki tsayar da motar. Mariya tace ki kwantar da hankalinki zamu kaiki inda za'a bi muku hakkinku. Anti Faiza ta cije lebe tana kallon yadda Zuhra ke zubar da hawaye tace Allah zai isar mana ku ajiyemu kawai ba sai munje wurin yan sanda ba. Ummahani tace gidansu Hamza zan kaiku. Ni matar kaninsa ce, wannan kuma kanwarsa ce. Sai a lokacin Zuhra tace ku ajiye mu don Allah. Mariya ta juyo ta kalleta. Dole Zuhra ta baka tausayi. Wannan karon Izzatu ta wuce gona da iri. Kiyi hakuri mun kusa zuwa gidan. Anti Faiza tace kunga bama son wani wulakancin ku barmu kawai. Ummahani bata tsaya ba sai a cikin gidan don tayi saa an budewa Alh Nasiru gate zai fita kenan suka shigo. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿21 Batul Mamman(Mrs)💖 Ummahani na tsayar da motar Mariya ta fita da sauri ta tari Alhaji. Su Anti Faiza kuwa fita suka yi daga motar suka yi hanyar gate zasu fita. Muryar dattijo suka ji yace don Allah su tsaya. Kuka Zuhra ta cigaba tana jan hannun anti Faiza. Mariya ta zo gabansu tace don girman Allah ku tsaya. Ba yadda zasuyi dole suka biyo bayanta. Amma duk yadda aka yi Zuhra ta kafe bazata shiga cikin gidan ba. Kukan da take yi yasa Alh Nasiru yace Anti Faiza da ke mata fada ta kyaleta. Sai a lokacin Zuhra ta kalli dattijon. Ko ba'a fada ba tasan shine baban mijin Izzatu saboda sunyi kama. Da sauri ta durkusa har kasa tace ina wuni? Lafiya kalau ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Kallonta yake yadda take goge hawaye da majinar fuskarta da dankwalin kayanta. Sannan ta nade kanta da jikinta da katon mayafi. Suna nan tsaye Mama da Hajiya suka fito tare da Mariya. Hajiya tace yanzu Mariya ke fada min munyi baki kuma wai sunki shigowa. Anti Faiza da Zuhra suka gaishe su. Mama ta ce ya naga bakuwar na kuka Allah Yasa lafiya. Alhaji yace Mariya ta dan soma fada min. Ku daure mu shiga ciki. Mama ce tazo ta kama hannun Zuhra ta tayar da ita suka shiga cikin gidan ba don tana so ba. A falo suka zauna Zuhra da Anti Faiza suka rakube jikin kujera. Mariya ta bada labarin abinda idanunta suka gane mata a gidan Yaya. Mama da Hajiya sai salati suke. Ita kam Hajiya har kunya taji ace wai Hamza danta ne kuma na fari ma. Alhaji ya dubi su Zuhra yace ko zaku yi mana bayanin yadda abin ya samo asali. Nan Zuhra ta soma basu labari. Tana yi tana kuka. Su Ummahani sunji tausayinta sosai. Alhaji yayi murmushin bacin rai Mariya ku tashi ku kaisu gida. Sai ku gane mana gidan. In sha Allah anjima zamu zo gidan nayi magana da mahaifinki. Amma kafin nan don Allah kada ki sanar dasu komai. Zan gyara matsalar in sha Allah. Mama ta matsa kusa dasu ta rike hannun Zuhra ki yi hakuri kinji 'yata. In Allah Ya yarda Alhaji zai share miki hawaye kuma zai hukuntasu daidai da abinda suka yi miki. Zuhra ta gyada kai ni dama dariyar ce ta fi bani haushi. Anti Faiza tace to ba an baki hakuri ba. Tashi mu tafi. Bayan sun fita Mama tace Hajiya ya kika yi shiru? Hajiya tace hmmm to me zan ce? Kina kallo kullum lamarin gidan yaron nan kara lalacewa yake. Wai april fool sai kace wasu kasurguman kafirai. Na rasa yadda ake suke kwakulo duk wata al'adar banza suna dabbaka ta. Alhaji yace ku kyale ni dashi. Alkawari ne tsakaninmu akan idan haka ta sake faruwa zan hukunta shi.....wani murmushi kawai Alhaji Nasiru yayi. Sai na nunawa yaron nan nima ina riko da namu al'adun nagari. Izzatu ta rike kumatu ta soma kuka. Ita Hamza zai mara a gaban mutane. Sai a lokacin ta kula kowa ya watse sai yan gidansu da mamanta. Da sauri ta nufi wurinta zata rungumeta, sai taga maman tata ta matsa. Izzatu ta zaro ido meye ma'anar hakan. Raliya mahaifiyar su Izzatu ta kalli 'yarta fuskarta na nuna alamun rashin jindadi tace Izzatu that was extreme. Ban taba nuna damuwata ba idan kuna wasanku ke da yan uwanki. Kuma ni mutum ce da ta yarda a bar yaro ya sake yayi abinda ransa yake so. Amma ban yarda da cin zarafin wani don nishadi ba. Me yarinyar tayi miki haka da har zaki kirawota har gidanki ki mayar da ita laughing stock(abin dariya) a gaban mutane? Hawaye ne ya cigaba da sauka daga idanun Izzatu tace Mum har me nayi mata? Kawai ba'a fahimceni bane amma yi nayi don ayi dariya. Raliya tace kada ki manta yarinyar nan nan mutum ce kamar kowa. Ya zaki ji idan kika sa rai da abu kamar soyayya sai kawai ace miki wasa ne har a biki da dariya? ta dubi sauran 'ya'yanta ku tashi mu tafi. Laifinmu ne ni da Dad dinku da muka dora ku kan al'adun da basu dace da society dinmu ba. Gashi mun dawo Nigeria kina ta samun matsala da inlaws dinki. Izzatu na kallo duk suka fita jiki a sanyaye. Share hawayenta tayi ta hau sama. A hankali ta bude kofar dakin ta hango Hamza zaune a kan kujerar gaban madubi ya dafe kansa. Karasa shiga tayi ta tsaya a gabansa, ka kyauta Hamza. You slapped me for no reason. A yadda ya dago kansa sai da ta razana ta matsa baya da sauri. Gani take wani marin zai kai mata. Har wani huci taga yana yi saboda yadda ransa yake a bace. Izzy kinsan abinda kika yi kuwa? Ta dan sha kunu ita a dole bazata nuna masa ta yarda tayi laifi ba. Don kawai nayi april fool shikenan sai ya zama laifi. Har ka manta babu shekarar da bama yiwa juna. Last year kaya ka kawo min wai na fadar kashiya. Sai da na gama yarda nasha kukana sannan kace april fool. Shi inda ya dosa daban da abinda take fada. Saboda tashin hankalin da yake ciki ya manta da wani wasan april fool da tayi. Wannan last year ne, har kin manta nace mun dena duk irin wadannan abubuwan. Tace ban manta ba amma ai wannan ba na kudi bane. Ya rasa yadda zaiyi da ita. Kinga sami wuri ki zauna kin tsaya min a ka. Bakin gado ta zauna tana fuskantarsa. Izzatu ya kira sunanta..... naam. Kin taba goge min text da Inuwa ya turo ranar wedding anniversary dinmu? Dan tunani tayi tace eh, amma na karanta farkon sakon na kuma fada maka abinda nagani. Shine duk ka wani daure min fuska har da mari. To wallahi bazan hakura ba. Ta fadi maganar ne tana tashi. Bata ankara ba taji ya janyota iya karfinsa ya hadata da bango. Da sauri yake numfashi don ji yake kamar zuciyarsa zata iya bugawa. Idanunsa duk sun kankance. Sai a lokacin Izzatu ta ji tsoro tayi tunanin tambayarsa abinda ya same shi. Kafin tayi magana yace daga yau idan kika sake daukar min waya sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. A dalilin wayar karyar da kika yi kika ce Junior ya karye da deleting text dina da kika yi karayar arziki na iya samuna. Ga mamakinta hawaye ta ga ya zubo daga idanunsa, abinda bata taba gani ba. Nan da nan ta rikice, babyna ya zamuyi idan ka talauce? Zamu sami abincin da zamu ci ko sai Daddyna ya taimaka mana? Gashi kayi min alkawarin zaka canja min mota. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya ke nanatawa. Zancen ace ransa ya baci da maganarta ma bata lokaci ne. Izzatu dama baki da hankali??? Tace bangane ba. Ya daga murya ya soma fada... ina fada miki matsalata kina zancen canjin mota. To hell with canjin motar taki. Ya dauki kujerar gaban madubin yayi wurgi da ita. Wani irin bakinciki yake ji wanda yake tunanin idan ya taba Izzatu kila sai dai ta kwana a asibiti. Ba talauci ba ko me zai sameni tare zamu zauna. Kin jawo min tashin hankali kala kala kinga ina rabuwa dake shine yanzu zan fada miki halin da zamu iya fadawa kiyi zancen damuwarki ta banza. Gefe ta koma don gaba daya ta tsorata da Hamza. Mutum ne wanda da wuya kaga bacin ransa. A hankali ta soma matsowa kusa dashi zata bashi hakuri sai wayarsa tayi kara. Ita ma wayar ji yayi kamar ya kwadata da kasa sai yaga Alhaji ne yake kiransa. Yana dauka Alh Nasiru yace ana saukowa daga masallaci kazo ina nemanka. Sai kawai ya kashe wayar. Hamza ya rike wayar yana kallonta...Allah Yasa ba gulmar abinda ya faru dazu Mariya ta kai gida ba. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿22 Batul Mamman(Mrs)💖 Daga masallaci gidansu ya wuce ya baro Izzatu tana ta aikin kuka a gida. Lokaci daya duk ya birkice mata abinda bata saba gani ba. Allah Ya sa su Khalifa ta hadasu da Tala suna dakinta suna cin abinci duk wannan tashin hankalin da ake yi. Baiyi mamakin ganin motar Ibrahim ba don yasan kullum sai yazo gidan. Yana ta sallama yaji shiru ba'a amsa ba. Kande mai aikinsu ce ta fada masa suna dakin Alhaji. Sallama yayi ya shiga ya tarar dasu suna ta hira. A ransa yace babu wanda yasan matsalar da yake ciki. A lokacin da yake jindadi bai kyautatawa iyayensa yadda ya kamata ba saboda haka yanzu bashi da dalilin tada musu hankali ya fada musu halin da kamfaninsa zai iya shiga. Mama na ganinsa ta washe baki ta soma guda. Murmushin yake yayi yace Mama alkhairi muka samu ne? Kwarai kuwa Yaya in sha Allahu alkhairi zamu samu. Ya karasa ciki ya gaishe da iyayensa. Ibrahim ya miko masa hannu suka gaisa suna tambayar juna aiki da iyali. Bayan sun dan nutsu Alh Nasiru yace bayan magriba in Allah Ya yarda zamu je gidan surukan naka. Hamza ya kalli Ibrahim da alamar tambaya. Alh Nasiru yace da kai nake Yaya. Ni kuma Alhaji, wani abin ne ya faru? Mama ta katse shi cike take da murna tace babu komai. Rabon da ta sake masa sosai tun kafin ta karye a gidansa. Alhaji ya ce bani hankalinka nan Yaya. Duk aka yi shiru ana sauraronsa. Dazu Mariya da Ummahani sun zo gidan nan da yarinya tana ta kuka akan cin zarafin da kuka yi mata kai da matarka. Hamza yace wallahi Alhaji ban san da abin ba sai da naje gida. Yau har marin Izzatu nayi akan abinda tayi. Hajiya ta tabe baki sai kace kayi wani abin arziki. Ai ba laifinta bane ita kadai. Alhaji ya cigaba da magana...kasan akwai alkawarinmu na ka amince da duk hukuncin da zan dauka a kanka idan irin haka ta sake faruwa ko? Tuni Hamza ya gano inda Alhaji ya nufa..muryarsa har tana sarkewa yace don girman Allah Alhaji kada kace nema min auren yarinyar nan zaka yi. Kayi min wani hukuncin ba wannan ba. A rana daya abubuwa sai samunsa suke yi. Ba don kada ya nuna karayarsa ba babu abinda zai hana shi fashewa da kuka. Alhaji yayi yar dariya. Dadina da kai akwai hazaka gashi har ka gano inda na nufa. Kamar yadda kuka sawa yarinya rai cewa bayan magariba zaka je gaishe da mahaifinta to tare zamu ayi mai gaba daya. La'ila ha ilallah...Alhaji kayi hakuri. Idan kaga Hamza a lokacin shima sai ya baka tausayi. Yana cikin wannan matsalar ina shi ina aure. Auren ma da wannan kucakar yarinyar mara kunya. Muryar Alhaji ce ta katse masa tunani. Wallahi idan har kaki yarda da auren nan daya hukuncin da zan iya yanke maka shine na zare hannuna daga dukkan abinda ya shafeka. Babana ba fa kai kadai na haifa ba, kuma kaine na fari amma matsalar gidanka ta isheni. Sam ka kasa rike matarka. Hamza yayi shiru yana jinjina kalaman mahaifinsa. Can dabara ta fado masa yace Alhaji nayiwa Izzatu alkawarin bazan taba yi mata kishiya ba. Alhaji ya tashi yana cirw babbar rigarsa yace ashe auren zobe kuka yi bamu sani ba. To kada ka damu yanzu ma alkawarin naka bai tashi ba tunda ba kai ka nemi auren ba. Ita da kanta ta nema maka. Mu nan karashen aikin ta barmu dashi kawai. Ka tashi ka tafi gida ka saka manyan kaya don bazamu gidan surukai da kai a haka ba ka wani ci zanzaro. Ko kazar da kwai ya fashewa a ciki zata fi Hamza kuzari. Daga kafa yake kamar ba'a jikinsa take ba. Ko da ya koma gida dakinsa ya shiga ya rufe. Izzatu tayi bugun har ta gaji. Bai fito ba sai da aka kira magariba. Yayi wanka ya canja kaya. Ba don kuncin da zuciyarsa ke ciki ba sai ka zata sabon ango ne....kodayake ya kusa zama angon! Masallaci ya fara zuwa yayi sallah sannan ya wuce gida. Alhaji da Ibrahim ya gani a shirye suna jiransa. Mama har bakin mota ta rakosu tana musu fatan alheri. da ta shiga gida Hajiya tace wato duk gidannan kinfi kowa farinciki da wannan abin. Mama tayi dariya Hajiya bazan taba manta abinda Izzatu tayi mana ba. In Allah Ya yarda yanzu Yaya zai san yayi auren yar da ta dace da addini da al'adarsa. Yadda Ummahani ta kwatanta masa haka Ibrahim ya bi. Hamza yana gaba kamar ruwa ya cinye shi. Alhaji da Ibrahim sai hirarsu suke yi. Daga bakin layin suka ajiye motar Ibrahim yace daga nan na manta kwatancen, Yaya ya ma sunan yayartawa? Wata muguwar harara Hamza yayiwa Ibrahim kafin yace zanci.....Alhaji yayi gyaran murya don yasan karshenta zagi Hamzan zaiyi. Yau ya zama a lallaba auren zamani. Ibrahim dai dariya yayi sannan ya kira Ummahani ta tuna masa sunan. Da tambaya suka sami gidan domin ba wuyar ganewa. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿24 Batul Mamman(Mrs)💖 Wurin goma da rabi na safe kukan Nana ya tashi Izzatu daga bacci. Tana bude ido ta kalli agogo. Da sauri ta sauko daga kan gadon ta dauki Nana da ke kawo karar Junior ta tafi dakin Hamza. Abin mamaki a rufe taji dakin. Ta tsaya tana bugawa Khalifa yace Daddy ya fita. Ranta ne ya baci. Tunda suka yi aure ranaku kadan ne suka taba kwana daki daban shima sai da dalili mai karfi. Amma akan abinda bai kai ya kawo ba shine jiya yaki tashinta daga bacci ta koma dakinsa kuma yau harda kulle kofar daki. Kwafa tayi zai dawo ya sameta ne. Bayan tayi wanka ta sauko kasa. Tala ta gyara gidan tas kamar ba'ayi taro a cikinsa ba. Hatta su Khalifa duk tayi musu wanka. Da yake asabar ce babu makaranta. Sabon dakin wasansu suka tafi suna ta tsalle tsalle. Tala ce ta rugu da gudu ta kawowa Izzatu wayarta da ke ringing a daki. Bakuwar number ta gani ta dauka suka gaisa. Da jin gaisuwar kasan bata san da wa take magana ba. Mama tace Haj Kaltume ce daga gidan Alh Nasiru uban mijinki. Izzatu ta dan ji kunya tace yi hakuri Mama bangane ba. Mama tace ah ai babu komai idan kina da lokaci kizo nan gida Alhaji ya bayar da sako. Kafin Izzatu ta amsa Mama ta kashe wayarta. Duk da babu mutane sosai a office din saboda weekend ne amma can Hamza yaje. Tunani ne yayi masa yawa bai iya yin baccin kirki ba. Shawara daya ya yanke zai basu ribar kamar yadda suka bukata sannan zaiyi kokarin hada kudin da suka bashi ya biyasu. Yana wannan tunanin Izzatu ta kira shi tana sanar dashi kiran Mama. Yace taje shima zai je anjima kadan. Har zai ajiye wayar yaji tace sweetyna kayi hakuri da duk abinda nayi ba daidai ba. Sai yaji ta bashi tausayi. Basa iya dogon fushi da junansu. Babu komai Izzy, love you. Tace love you more. Dakin Mama ta wuce kai tsaye tunda ita ta kirata. Hamida tana gyaran wardrobe din Mama taji sallamar Izzatu. Wata sabon gani. Anti Izzatu dama kina nan, yaushe rabonki da gidan nan? Izzatu ta dan sunkuyar da kai. Ita kanta tasan tafi wata biyar rabonta da gidan iyayen mijinta. Ko da Mama ta karye kunya da tunanin basa sonta ya hanata zuwa. Kuma Hamza baice taje ba. Mama ta fito daga toilet tace Hamida bana son rashin kunya ko sa'arki ce da zaki zauna ki titsiyeta. Tashi ki fita magana zamuyi. Ki kawo mata dan abinda zata ci. Izzatu ta sami wuri ta zauna tace ki barshi a koshe nake. Hamida ta tabe baki tayi gaba. Mama ta dubeta, gabadaya Izzatu ta fice mata a rai. Mun sami labarin abinda kuka yiwa yar mutane jiya a gaban jama'a. Izzatu na jin haka tasan kila fada za'ayi mata tace Mama don Allah kuyi hakuri. Itama yarinyar zan kirata na bata hakuri. Maybe bata ji haushi ba saboda bata yi kama da mai daukar abu serious ba. Mama tace ga mahaukaciya ko, dole kice bata daukar abu serious. To sakamakon abinda kuka yi jiya Alhaji yaje neman aurenta wurin iyayenta. Izzatu ta zaro ido harda dafe kirji. Yanzu Alhaji Zuhra zai aura? Karamar yarinya ce fa da kadan zata girmi Hamida. Ikon Allah ai da Nura ya nemarwa aurenta. Mama ta tsaya kawai tana kallon Izzatu ranta na kara baci. Ba shi zai aureta ba mijinki ya nemawa aurenta kamar yadda kika fada mata. What? Tashi Izzatu tayi a gigice... Mama don Allah da gaske kike? Hajiya ce da ta shigo dakin a lokacin tace da kuna yar wasa ne da ita. Kan kace meye wannan Izzatu sai kuka. Ta durkusa gaban Hajiya don Allah ku bawa Alhaji hakuri wallahi bazan iya zama da kishiya ba. Bazan iya sharing mijina ba. Daga Mama har Hajiya kallonta suke yi tana kuka wiwi. Mama tace don baki da kunya Izzatu mu kike gayawa bazaki iya sharing miji ba. In sha Allah aure kamar anyi an gama. Tana kuka tace dama kirana kuka yi kuyi min wulakanci. KE IZZATU MEYE HAKA. Ta yi saurin juyawa wurin Hamza daya shigo dakin shima. Rungume shi tayi tana kuka. Kaji abinda suke cewa wai Zuhra za'a aura maka. Duk kunya ta kamashi yana kokarin tureta tana dada kankame shi. Ya daka mata tsawa sake ni mana... iyayen nawa kike cewa suna miki wulakanci? Ba kin iya kiranta ki fada mata Hamza na sonta ba. To zan aureta kinga bukatarki sai ta biya. Idanu sharbe da hawaye tace ni kake fadawa haka Hamza....sai kawai ta fice. Mama tayi murmushi sannan ta nuna masa kofa bita kada tayi wani wurin. Ya yi hanyar kofar Hajiya tace Alhaji yace na fada maka lallai kaje gidansu Zuhra yau ku daidaita. Tsayawa yayi kamar gunki yana kallon yadda su Hajiya ke nishadi saboda za'a kakaba masa auren da baya so. Bai ankara ba yaji tashin motar Izzatu. Da sauri yabi bayanta. Hajiya tace an dai ji jiki. Wallahi Alhaji yayi min daidai. Su Mama za'ayi surika, Allah Ya tabbatar da alkhairi. Mama tace Amin Hajiya tana fadada murmushinta. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿23 Batul Mamman(Mrs)💖 Yaron da ya rakasu gidan har soro ya shiga dasu sannan ya karasa ciki ya fadawa Baba yayi baki har su uku. Dama a shirye yake shi da baban su Anti Faiza ne a tsakar gidan suna jiran zuwan suriki. Basu san wainar da ake toyawa ba. Baba yayi wa yaron godiya yace da Umma ta dauko juice din nan da ya tanada domin bakon. Manyan kwalin happy hour ne guda biyu sai ruwan roba babba daya. Akan tray ta jera da cups hudu ya mika hannu zai karba babansu Anti Faiza da ake kira Malam yace haba Baban yara bari na dauka. Tabarmi biyu Baba ya dauko suka shigo soron. Da yake akwai wuta yana ganin bakin yadan ji faduwar gaba. Irin wadannan mutanen da gani masu arziki ne. Anya sa'anin auren Zuhra ne kuwa. Ibrahim yayi sauran karban tabarmin ya shimfida musu. Suka zazzauna suna gaisawa. Alh Nasiru ya sake dasu sosai suna ta barkwanci kamar sun dade da sanin juna. Idon Hamza kyar akan dungulmin hannun Baba. A ransa tunani yake Allah Yasa ba kuturu bane. Kodayake ya gama tsara yadda zaiyi ya gujewa auren nan. Alh Nasiru ne ya fara magana. Alhamdulillah tun kafin muyi abinda ya kawo mu kunyi mana tarba mai kyau. Wannan yasa naji dadi nasan yaron nan baiyi zaben tumun dare ba. Malam yace in sha Allahu. Ai Zuhra yarinya ce mai ladabi duk layin nan ko ince unguwar nan babu wanda bai san gidan Mal Bashir ba. Baban yara ake kiransa saboda dan kowa nasa ne. Bakin gwargwado kuma yayiwa tasa yar tarbiya. Alh Nasiru yace haka ake son duk uba nagari. Ni sunana Alh Nasiru Hamza amma anfi sani na da Maifata saboda sana'ar sayar da fata nake yi sannan yayi musu bayanin asalinsa. Ya nuna Hamza da Ibrahim duk ya gabatar dasu. Sai ya nuna Hamza shine mai neman auren Zuhra. Baba ya sake kallonsa yace nagodewa Allah. Dana Allah Yasa kai abokin rayuwa ne na kwarai ga Zuhra. Ita kadai Allah Ya bani kullum adduata ta sami miji nagari. Tun farkon lokacin da ka fara turo mata sako a waya babu abinda ta boye min. Ni kuma a lokacin na yaba da tarbiyarka nake ta addua. Allah Yasa ayi a saa. Kowa yace Amin. Baba yayi musu bayanin matsayin karatunta da sana'ar da take yi yanzu. Alh Nasiru yace duk babu komai. Zai sanar da yan uwansu na Kumo nan da sati biyu idan ya amince sai a kawo kudin aure ayi maganar sa rana don baya son a dauki lokaci. Hamza dai sai yake yakeyi zuciyarsa na zafi. Ya rasa ta ina zai fara kokarin tattaro rayuwarsa da ke neman rugujewa lokaci guda. Suna mota Alh Nasiru yace yanzu da bamu zo ba ai alhakin yarinyar nan kila har jikoki sai ya bika Yaya. Zuhra na dawowa Baba ya sanar da ita Hamza da mahaifinsa sun zo. A zahiri ta nuna musu farincikinta amma a tsorace take da abin. Gashi baban Hamza ya roketa ta rufa masa asiri kada ta fada a gida. Anti Faiza ma tace ko Hajara kada ta fadawa. Haka ta shiga daki ta kwanta tana jin iyayenta suna tattaunawa akan bikinta. Hamza bai sami komawa gida ba sai kusan shadayan dare. Dakin Izzatu ya shiga ya sameta a kwance tana bacci. Hmmm kina jindadinki ya fada kafin ya koma nasa dakin. Yunwa yake ji sosai don rabonsa da abinci tun safe amma baya sha'awar komai. Kitchen din kasa ya sauka ya tarar da kulolin abinci kala kala ga wasu ko budesu ba'ayi ba. Kitchen din tsamin abinci kawai yake yi. Duk da cewa ba'a gama taron ba ya watse amma anyi almubazzarancin abinci. Tea ya hada ya koma daki. Tunanin sa na farko yadda zai biya turawan nan kudinsu gaba daya ya fasa hadin gwiwar dasu. Kudaden kamfanin yanzu da yawa an fara ayyukan ginin dake gabansu. Daya a Jigawa ne dayan kuma a Abuja. Kowanne sai sunyi rabin aiki za'a biyasu gashi duk zasu ci kudi sosai. Nasa kudin kuma ya kashewa gidansa don komai sabo ne a gidan. A gefe daya kuma ga zancen auren yarinyar nan. Gashi iyayensa duk fushi suke yi dashi. Ji yayi kansa yana sarawa saboda tunanin da yayi masa yawa ya tashi ya dauro alwala yana ta nafilfili da adduar samun sauki akan dukkan matsalarsa. Mama ce zai iya fadawa matsalarsa ta bashi shawara to itama yanzu basa dasawa kamar da. Izzatu kuma damuwarta akan abinda ya shafeta ce kawai. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿25 Batul Mamman(Mrs)💖 Gidan kanwar Mamanta inda suka yi masauki Izzatu ta tafi. Ko rufe motar bata yi ba ta shiga cikin gidan tana ta rusa kuka. Ana ta tambayarta abinda ya faru taki bada amsa. Sai da kanwar Maman tasu tayi mata tsawa sannan tana shesshekar kuka tace Alhaji ne yace Hamza sai ya auri yarinyar da nayiwa April fool jiya. Anti Larai kanwar Raliya tace kai amma Allah Ya sakawa Alh Nasiru da alheri. Ni dama kinsan duk wannan shirmen naki ba zuwa nake yi ba saboda na rasa wace irin rayuwa kuke yi ke da mijinki. Tun jiya da aka bani labarin abinda kika yi raina ke kuna. Ta mayar da kallonta ga Raliya...Wallahi duk laifinku ne Yaya Raliya. Rayuwar turai ai ba hauka bane. Yara kusan shekara tara da dawowarku kasar nan amma sunki yarda su yar da al'adun da ba nasu ba. Yanzu wa gari ya waya. Raliya ta sunkuyar da kanta kasa. Tasan tabbas gaskiya kanwarta take fada. Ta kalli Izzatu da take ta kuka...sai ki rungumi kaddara tunda ke kika jawowa kanki. Ni bazan shiga zancen nan ba kuma daddynku ma zan fada masa babu ruwansa. Allah Ya baku zaman lafiya. Izzatu tace haba Mum haka ma zaki ce. Raliya tace to ai tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka. Daki Zeenatu ta Izzatu tana rarrashi. Kinga Izzatu kiyi hakuri yayi auren nan tunda dama yan gidansu basa kaunarki. Idan kika nuna bakya son auren suna iya sawa ya rabu dake. The way I see it wannan yarinyar bazata kai ko'ina a gidan ba zai saketa. Da haka tayi ta rarrashin Izzatu har ta hakura ta dauki wayar Hamza da yake ta kiranta ta fada masa inda take sannan ta kusa dawowa gida. Bayan ta koma ne suka yanke shawarar yaje gidan su Zuhra kamar yadda Alhaji ya bukata. Maganar auren tasa fushin da yake da Izzatu akan matsalar kamfaninsa ta ragu. Wani light blue din yadi ya saka da aka yiwa dinki mai kyau amma simple style ba ado da yawa. Yasa hula mai ruwan madara da light blue. Yayi kyau sosai don ma bai fiye sa manyan kaya ba. Ya sha turare sannan Izzatu ta daura masa links a hannun rigar da agogo. Yana saka takalmi tace cikin shagwaba ni gaskiya kayi kyau da yawa kamar kada ka fita. Murmushi yayi mata. Kada ki damu bazan dade ba. Da tambaya ya iso gidan domin zuwan su na dare ga ransa a bace ko kallon hanya baiyi ba. Yaro ya tura yayi masa sallama da Zuhra. Yaron na tafiya yabi bayansa ya tsaya a soron inda suka zauna da Baba. Yaron na sallama Zuhra ta amsa. Ita kadai ce a gidan Umma ana la'asar suka tafi kai garar Hajara. Baba ma ya fita tun safe bai dawo ba. Tana gaban murhu zata fara tuka tuwo. Da murmushinta tace Isuhu daga ina haka? Isuhu yace wani mutum ne a waje wai Hamza yace kizo. Wallahi baki ga yadda ya hadu ba Zuhra, motarsa ma abin kallo ce. Ga wani kamshi dan ubansu yana fitarwa. Tunda Isuhu ya fara magana gabanta ya fadi. Ba yadda za'ayi ta yarda da auren nan. Rokonsa kawai zata yi su fadawa iyayensu basa son auren. Ina ita ina wannan mutumim, ita tsoronsa take ji. Isuhu ta kalla kace masa ina zuwa tuwo zan tuka na kwashe. Babu kowa ne a gidan. Duk maganar da sukeyi Hamza na jinsu. Bashi da niyar dadewa a gidan saboda haka dan aiken nasa na fitowa naira hamsin ya bashi shi kuma yayi sallama ya dan shiga daga cikin tsakar gidan. Zuhra bata gama tantance sallamar waye ba taga mutum ya soma shigowa. Gashi ta zuba garin alkama ta fara tuka tuwon. Da sauri ta fara cewa kai dakata kada ka shigo mana. Wani tsohon zani ne a jikinta da koriyar t-shirt sai dankwalin zanin da ta daure kanta tamau dashi. Hamza bai kula ta ba ya shigo har tsakiyar tsakar gidan tana ta kokawa da dankwalinta tana son bude shi ta rufe jikinta. Wani irin kallo ya bita dashi mai wuyar fassara. Kinga yi aikinki ni ba zama nazo yi ba. Magana nake so muyi ina sauri ne. Fuskarta a turbune tace don kana sauri ko sallamarka ban amsa ba ka fado mana cikin gida. Kuma ko lullubi babu a jikina. Dan karamin tsaki yayi, kwantar da hankalinki baki da abinda zai daga min hankali don na ganki ba mayafi. Maganar ta bata haushi sai ta danne tace ina wuni? Kafin ya amsa ta cigaba da tuka tuwonta. Kallo ya bita dashi yadda take zaune gaban murhu zafin baya damunta. Bazaki bani wurin zama ba? Ko juyowa bata yi ba tace na dauka ba zama kazo yi ba. Can gefe ya sake matsawa saboda wutar ta fara hayaki. Ita kanta Zuhran yana damunta ta fara hawaye da majina. Tasa gefen dankwalinta ta goge fuskar ta cigaba da aiki. Da kyar ya hadiyi yawu saboda gabadaya kyankyaminta ne ya kamashi. Gara yayi abinda ya kawo shi ya fita kafin zuciyarsa ta fara tashi. Ji tayi yace Ke,wai baki da saurayi ne?....ta murguda baki duk da ta juya masa baya ni ba sunana ke ba. Kuma ina ruwanka da samarina. What ever taji ya fada da turanci. A ranta tace ban yafe ba idan ka zagen. Alhaji yace yana so na zo wurinki atleast sau uku kafin a kawo kudi. Za'a tambayeki kafin ranar idan kin amince da auren, ina so kice ba kya sona. Mun gama magana da Izzatu tace kina da saukin kai zaki amince. Izzatu da ya fada ya kara bata haushi. Ko kadan bata son sake jin sunan matar. Kinga ni bana sonki kuma idan kika aureni wahala zaki sha. A tsarina mace daya ta isheni. Tunda bana jin kina da saurayi akwai sakatare na Inuwa zanyi mishi tayinki. Idan ya amince kinga shikenan. Ko ba komai na taimaka miki. Kuma nayi alkawarin yi miki kayan daki idan kin tashi aure. Murmushi kawai Zuhra keyi ta gama tuka tuwon ta rufe tukunyar sannan ta gyara wutar. Wato mutumin nan ya raina mata hankali. Shi iyayensa su yabe shi ita kuma ace bata da kunya. Wai har cewa yake zaiyiwa wani tayinta. Ko na sati ne sai ta aure shi ta bata masa rai daga shi har masoyiyar tasa Izzatu. Da wannan shawarar ta dago kanta amma bata hada ido dashi ba. Tace shikenan abinda ya kawoka? Hamza yace eh ko kudi kike so zan iya biya kice ba kya sona kinji. Wannan karon tamkar mai magiya yake magana. hanyar dan karamin falonsu ta kama. Zanyi tunani a kan maganar, ka gaida gida. Shigewa tayi ta barshi nan a tsaye yana mamakin wai itama ta iya jan aji. Ya kada kansa ya fice daga gidan. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU🗿26 Batul Mamman(Mrs)💖 Washegari Hamza ya koma gidansu Zuhra. Soro ta fito ta same shi. Yau zama yayi yana lissafa mata irin mawuyacin halin da zata iya shiga muddin ta yarda aka yi auren. Kanta a kasa har ya gama bayaninsa ya juya ya tafi. A waje ya hadu da Baba yana dawowa gida. Yara ne sunfi goma suke biye dashi yana rarraba musu alawa. Hakan ya bawa Hamza sha'awa. Karasawa yayi suka gaisa da Baba cikin ladabi sannan ya tafi. Yau dai ya karewa hannun Baba kallo ya kula yankewa aka yi ba kuturta bace ta cinye yatsun. Saboda matsalar office dinsa sai bayan kwana biyu ya sake komawa. Umma tasa tayi kwalliya irin wadda ta saba yi tana ta yabon kyan tilon yarta. Zuhra tace don ma banyi wanka ba Umma ai da sai nafi haka kyau. Umma tace to sakarai sai kin fada da karfi yaji yasan cewa ke kazama ce ko. Bata rai tayi haba Umma ki dena ce min kazama. Baba yace na kile. Ai fa naga alama, to wuce ki tafi kin barshi yana jiranki. Tabarma ta dauka ta fita soron. Kamshin turarensa ya cika wurin. Yau suit ce a jikinsa ruwan toka. Zuhra ta gaishe shi ta sami wuri ta zauna don baya zama akan tabarmar. To yau nayi zuwa uku ina fata kina rike da dukkan abinda nake fada miki. Ya dan jima yana magana sannan ya lura ba saurarensa take ba. Shi ta kurawa ido....ke, keee, KE lafiyarki? Bata dawo hayyacinta ba sai da ya dan tafa hannuwansa a gaban fuskarta. Ajiyar zuciya tayi sannan tace yanzu don Allah kana iya numfashi? Ni bansan haka ake saka abinnan a zahiri ba sai yau. Waige ya fara yi don bai gane kan zancen ba. Tace neck tayil dinka nake nufi. Naga ya shake maka wuya kamar mai shirin rataye kansa. Yanayin maganarta yasa shi yin murmushi. Necktie ake cewa sannan bai shake ni ba. Amma dai baka sakewa ko? Dauri irin wannan akwai ganganci a cikinsa. Dole Izzatu tace yarinyar nan tana da shirme. Yace ni zan tafi ina tunanin jibi Alhaji zai zo. Ki kiyaye abinda na fada miki. Har ya juya sai ya dawo...by the way nayiwa Inuwa maganarki sai dai mun makara. An kusa kai kudin aurensa. Zuhra tace babu komai. Nagode.....yadda yaga kamar ta nutsu yasa ya kwantar da hankalinsa. Dubu goma ya dauko yan dari dari sababbi ya mika mata. Ga wannan ki rike. Nagode ta sake cewa sai kawai ta nade tabarmarta ta shige ciki. Mayar da kudinsa yayi aljihu yana mamaki da bata karba ba. Bayan Isha Baba ya kira Zuhra da Umma. Wani katon littafi ya dauko mai hotunan kayan daki irinsu gado, kujeru da kitchen cabinet masu tsada. Kunsan aikina ba wai ina yin kayan daki na masu kudi bane sosai. To amma na sami wani ya bani aron littafinsa nake son kwaikwayon duk wanda kika zaba zanyi kokari na kwatanta miki irinsa uwata. Atine gashi ki tayata zabe. Hawaye ne mai zafi ya saukowa Zuhra. Tabbas iyaye sun cancanci dukkan girmamawa daga 'ya'yansu. Allah Ka sakawa iyayenmu da alkhairi. Baba ne ya fara gani yace meye haka uwata ta kaina? Da yake Umma ma akwai rauni sai kawai suka hadu suna kuka maimakon ta rarrasheta. Baba ma dai ta maza yayi ya fara musu fadan su dena yi masa kuka. Burina Zuhra tayi aure ta sami mai kula da ita. Sai da shekaru suka zo mana muka haifeki dole nayi murna idan na sami wanda zai tayani kula da Fatima kyauta daga Allah. Zuhra fadawa tayi jikin Baba tana kuka. Ni bazanyi aure ba. Saurin tashe mata baki yayi...kul na sake jin irin haka. Aure ai shine rufin asirin kowa. Zaki yi aure cikin gidan mutumci kuma in Allah Ya yarda zaki kawo min jikoki su zo in basu labarin tabara irin ta babarsu. dariya ta rinka yi. Daga baya suka zabi gado da kujeru ita da Umma. Sai da ta kwanta ne a kan dan gadonta maganar Hamza ta rinka dawo mata. Tabbas da niyarta ta aureshi ta kuntata masa. Don duk zancen da yake mata jinsa kawai take yi. Sun dauketa wata gaula daga shi har matar tasa. To amma maganar Baba ta tsaya mata a rai. Duk shirmenta tana kaunar iyayenta kuma bata son bata musu suna. In Allah Ya yarda bazata wasta musu kasa a ido ba. Idan har baayi auren ba sai dai idan Hamza da bakinsa yace baya so. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿27 Batul Mamman(Mrs)💖 Bayan kwana biyu Umma ta sanar da Zuhra yau iyayen Hamza zasu zo. Mamansu Hajara ta shigo tayata aiki. Kaji hudu suka soya, Anti Faiza sarkin flour tayi musu cake, meatpie da doughnut. Zuhra ta wanke tsakar gidansu tas dama irin fasassun tiles dinnan ne. Nan da nan wurin ya hau sheki. Bayan ta gama aikin ta hau magiyar a barta taje gidan Hajara. Tunda akayi biki Baba ya kafa mata dokar sai tayi sati baya son yawon gulma. Anti Faiza tace ke da zasu ji ta bakinki ai bai kamata ki fita ba. Kannen Umma biyu suma suna ta zolayarta da matar kanin Baba. Sai bayan la'asar suka watse aka bar Maman Hajara da Umma. Baba ya shigo tare da Malam yace su bakin zasu shigo. Kaninsa da yake aikin masinja ma yazo tunda Alh Nasiru yace indai ta amince to a lokacin zasu bada kudi asa rana. Su Umma daki suka koma bayan an jerawa baki kayan motsa baki. Sai da suka gama barkwancinsu sannan Alh Nasiru ya bukaci ganin Zuhra domin yaji amsarta. Dan karamin falonsu ya shiga tare da Baba. Kanta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana mai yabon halayenta. Sannan ya tambayeta domin baya son matsa mata ta auri wanda bata so. Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai. Ganin haka ya mike suka koma tsakar gida. Ya dubi sauran jamaar wurin. Shirun budurwa alama ce ta amincewarta saboda haka idan duk kun amince ina so asa rana nan da sati hudu. Kowa yayi naam da hakan harda Baba. A take suka bada kudin aure dubu dari aka yi addua taro ya watse. Ranar murna a wurin Baba da Umma ba'a cewa komai. Kudin da aka bayar Baba yace zai ajiye mata zuwa lokacin biki. Kinga ko mijinki bai yarda ki cigaba da saka ba kina da dan abin hannunki. Sannan ku shirya karshen sati zamu je Ajingi. Nan Zuhra ta hau murna zata je wurin Inna. Yinin ranar Hamza suna ta meeting da maaikatansa akan yadda zasu samu su karasa biyan kudin da turawan ke binsu kamfanin ya dawo mallakin Hamza shi kadai. Ya sanar dasu dole su zage damtse ayi aiki sosai domin su fitar da kudin kafin watanni shidan da aka basu su cika. Suna fitowa gidansu ya tafi saboda amsa kiran Alhaji. Yasan zancen bazai wuce Zuhra taki amincewa ba ayi masa fadan bai yi abinda ya dace wurin jan raayinta ba. Mama bata gida lokacin da yaje sun fita da Nura. Da Hajiya suka gaisa kafin ya karasa wurin Alhaji. Fuskarsa a sake ya amsa gaisuwar Hamza sannan yace ya kamata ka fara shiri tunda sati hudu kawai aka sa rana. Idan baka son hadasu gida daya sai ka gyara mata tsohon gidanka. A dan daburce Hamza yace wa zan gyarawa? Alh Nasiru yayi murmushi amaryarka mana. Yadda gabansa ya fadi bai san lokacin da yace amincewa tayi??? Alhaji yace ba haka kaso ba ko. Ai nasani Babana. To sai ka dau hakuri yarinya tana neman albarkar iyaye. Hamza yace Alhaji nima ina nema. Don Allah a janye zancen nan. Ko Nura ka aurawa ita. Dariya Alhaji yayi shi kuwa Hamza kamar yayi kuka yace yarinya ce karama. Ya za'ayi na zauna da ita? Alhaji ya gyara zamansa. Kaga ba jan zance nake so muyi ba. Aure ne sai an daura in sha Allah. Ni ban dora maka nauyin komai ba sai sadaki. Tunda na fika son ayi auren na dauke maka duk wata hidima da zata taso. Rasa bakin magana yayi yana kallon mahaifinsa. Mama ce ta shigo tare da Nura da su Hamida suna rike da wasu jakunkuna masu kyau. Seti ne guda shida, tace Alhaji kaga wadanda muka samu. Sai ta kalli Hamza, a'a kaga babban dana angon Zuhra. Ta tura masa daya daga cikin jakankunan. Kaga wannan sunyi kyau? Yanayin fuskarsa bazai fasaltu ba yace Mama harda ke? Nice ma kan gaba ta bashi amsa. Uhm Alhaji gobe da safe zamu je da su Jidda kasuwar, kasan hada lefe akwai cin lokaci. Yana shan furarsa yace Allah Ya kaimu. Share Hamza suka yi tamkar baya wurin. Tunaninsa daya yadda zai fadawa Izzatu plan dinsu bai karbu ba. AL'ADUN WASU 🗿28 Batul Mamman(Mrs)💖 Abinda yaji tsoro ne ya faru. Izzatu tayi kuka har ta gaji. Rokon Hamza take yi ya rufa mata asiri kada yayi auren. Tun yana rarrashinta har ransa ya baci da tace duk gidansu babu mai kaunarta. A hasale yake kallonta ke har kina da bakin cewa ba'a sonki Izzy? You caused everything. Lokaci guda kin lalata farincikin gidan nan. Ganin ya soma fada yasa ta rungumeshi. Am sorry baby. Na yarda kayi auren amma bayan lokaci kadan sai mu nemi dalilin da zaisa ka saketa. Jinta kawai yayi. Shi da Alhaji ya kafa masa sharadin indai ba da dalilin da ya sabawa shariah ba bai yarda ya saki Zuhra ba. A bangaren su Zuhra kuwa shirye shirye ya kankama. Makota da abokan arziki kowa yana son gwada bajintarsa wurin bikin tilon yar baban yara. Gudunmawar kudi suka rinka bawa Mal Bashir sai da ya tashi da dubu dari biyu da talatin. Shi kanshi ba karamin mamakin wannan karramawa ta mutanen unguwarsu yayi ba. Anas da Sani ma ba'a barsu a baya ba domin kuwa gas cooker karami suka kawo. Baba yayi murna da godiya sosai. Haka Umma ta rinka shiga gida gida tana godiya itama. Zuhra taje gidan Hajara a nan suke nasu tsarin bikin duk da ba damunta yayi ba don tasan wahala zata sha kawai. Hajara tace wato Zuhra da gaske kike da kika ce idan kika tashi aure sai munyi mamaki. Gashi zaki auri dan gayu dan boko. Wallahi ki dage sosai tunda yana da mata. Zuhra tayi dariya wace irin dagewa kuma. Ai kawai indai zasu bani abinci naci na koshi to suje can su karata. Sahabi da yake daki ya fito ba shiri. Amma dai Zuhra wasa kike ko? Tace da akayi me fa? Maganar da kika fada yanzu nake nufi. Yaushe zaki ce abinci zaki je ci. Wuri ya samu ya zauna yana karanta mata yadda zata yi a gidan miji. Hajara sai dariya saboda Zuhra rufe kanta tayi da mayafi. Irin wannan bayani na Sahabi yafi karfinta. Shi kuwa ya dauketa kanwarsa ne tunda duk unguwarsu daya. An kawo lefe akwati shida da kit. Komai Alhaji ne ya siya. Makota da yan uwa suna ta san barka. Washegari Baba yayi shatar mota suka dauki kayan suka wuce Ajingi. Nan ma kowa yace Zuhra tayi goshi. Yan uwanta suka shiga hada mata abubuwan da zata gyara kanta. Yi kawai take don kada a gane auren da matsala. Cikin wannan lokacin ko text bai taba hada Hamza da Zuhra ba. Har Umma sai da tace naga kwana biyu shiru yaron nan. Zuhra tayi yake muna waya kullum Umma. Wani aiki ne yake son karasawa kafin bikin. Umma tace to Allah Ya bada saa. Alhaji ya sake tuntubar Hamza inda zai ajiye Zuhra. Takardun tsohon gidansa ya dauko ya mikawa Alhaji yace na riga na gama komai ya zama mallakin Nura. A sabon gidan akwai dakuna sai ta zauna a cikin daya. Alhaji yasa masa albarka sannan ya tura Mama ta gano dakin da za'a bawa Zuhra. Dakina ne babba a kasa da toilet a ciki. Mama tace sam amarya ma a sama zata zauna. Dakunan saman uku ne har an gama jera kayan su Khalifa a ciki. Bisa umarnin Alhaji dole aka dawo dasu kasa ba da son ran Izzatu ba aka sabonta fentin. Katon daki ne kamar na Izzatu da toilet. A ciki aka jerawa Zuhra gadonta daga wani gefe da yayi dan tudu. Dayan gefen kuma kujerunta da su tv. Mama tace kuma lallai ayi kitchen kabinet a daya daga cikin dakunan kasan saboda a raba musu kitchen. An fara biki cikin kwanciyar hankali. Baba yana ta yabon Hamza saboda yana yawan kiransa a waya su gaisa. Hakan yasa suka cigaba da tunanin komai lafiya tsakaninsa da Zuhra. Anti Faiza kuma ta sake ja mata kunne akan tayi shiru da bakinta. Sannan tayi mata nasiha akan kwalliya da tsafta. Ni girar nan da kike ja ce bana so Zuhra. A shagwabe tace nufinki bana yin kyau Anti Faiza. Kinsan ni gaskiya zan fada miki. Bata miki kyau don ba iyawa kika yi ba. Kuma babu ruwanki da Izzatu ki kama kanki kinji ko. Zuhra ta gyada kai. Kinga yadda iyayensa suka tsaya miki sosai. Ina so ki kyautata musu daidai gwargwado. Babu fitsara ba rashin kunya. Nagode Anti Faiza in sha Allah zan kiyaye. Anyi kamun Zuhra a unguwarsu washegari alhamis suka tafi Ajingi. Jumaa bayan masallaci aka daura auren Arch Hamza Nasir Hamza da Fatima Bashir Ajingi. Kai ka dauka auren yar wani maikudi ake yi saboda yadda mutane suka zo. Asabar da safe suka dawo kano aka fara shirin kai amarya. Jikin Zuhra a sanyaye tunda aka daura auren. Shikenan zata bar iyayenta ta zauna da mutumin da babu soyayya a tsakaninsu. Ba'a tashi kuka ba sai da motocin daukar amarya suka zo. Aka rasa yadda zaayi a raba Zuhra da Umma. Gabadayansu kuka suke yi tamkar sun rabo kenan. Baba ya shigo yana fadan sun bar mutane a waje. Sai dai Zuhra na rungumeshi ya soma hawaye. Daki yaja hannunta suka koma. Yana kuka yana mata nasiha....uwata ki rinka tsafta kinji ko, ki rike Allah da ManzonSa SAW komai zaizo miki da sauki. Ki rinka taimakon mijinki. Kuma banda katuwar loma a gaban miji. Murmushi tayi hade da kuka ta sake fadawa jikinsa. Baba wa zaku rinka gani a gidan nan idan na tafi? Umma ce ta bata amsa bayan ta fyace hanci cikin yaran Yaya Shafiu matarsa tace na dauki duk wadda nake so. Baba ya dauko wata leda ya damka mata. Ga wannan dubu hamsin ne. Cikin kudin da na samu ne. Zan ajiye miki sauran. Ki rinka amfani dashi. Allah Yayi miki albarka. Basu fito ba sai da Malam babansu Hajara yazo ya buga kofar. Haka suka tafi tana ta rusa kuka ita da Hajara. Anti Faiza tace gulmammu duk wadda bata son auren sai mu koma da ita. [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: ABIN DUHU 18_09_016 TIME 09_00pm NIGHT POST ki ke zaune da shi, me ya sanya tun farko ba ki sanar da ni hakan ba? Me ya sanya ki ke zaune da shi a matsayin mijin aure ba ki nemawar kan ki mafita ba? Karima ta sunkuyar da kanta hawaye suka fara zubowa daga idanuwanta ta sanya hannu ta goge fuskarta tana kada kai, kamar yanzu komai ya faru, itama haka ta .fara ji sanda ta fahimci waye Murtala. Ta kamo hannun Hasna ta riKe gam cikin hannunta tana magana. .‘ ' ‘ “Hasna na jima da sanin Murtala yana yin luwadi? “Kina nufin' ya gaya miki tun kafin ku yi aure kenan? Hasna ta kara tambayarta cikin tsoro da fargaba. Karima ta gyada kai “K0 daya bai gaya mini ba, ban ma taBa gano hakan ba, kamar yanda kika kasance da Abdul haka na kasance da Murtala, tun randa na fare haduwa da shi da Abdul na gansu, na kuma Saba da ganinsu tare, ban taBa kawo tabbatar duniya masu gaskiya kadan suka rage Duk maganar da Karima keyi bata damu Hasna ba, illah sanin dalilin da ya sanya ta ci gaba da zama da mijin nata bayan ta san abin da yake yi, yaya za ta ci gaba da zama da .mutumin da yake aikata irin wannan abin? Sune tambayoyin da ta ke yiwa kanta, hat ta kasa barin su cikinta ta bayyana su a fili. “Wai bayan kin san abin da Murtala ke aikatawa ke nan amman ba ki daukarwa kan ki mataki ba, ki ka ci gaba da zama da shi Anty Karima? Ta tambaya cikin jiran amsa cikin Kaguwa. Karima ta kalleta a yanzu jikinta ya fara yin sanyi da maganganun Hasna ta ci gaba da magana “Hasna dole ce ta sanya na haqura din bayan na yi duk abin da zan yi na ganin na jawo Murtala hanya amman hakata ta gaza cimma ruwa, daga qarshe ma sai na fuskanci zai iya rabuwa da kowa da komai akan ya rabu da wannan harkar hasna zata qara magana amman ta daga mata hannu ta hanyar dakatar da ita “Kafin ki zarge ni ki tsaya ki ji hujjata." Hasna ta yi kasaqe cikin yin shuru amman ranta abubuwa ne kala~kala suke sake, Karima ta mike tsam ta yi gaba ta nufl jikin wundo ta tsaya tana dan leqe waje kamar tana neman satar amsa anan, sannan ta waigo ta tsaya tana kallon Hasna wacce ke cike da qaguwa da damuwar jin abin da ta keson sanar da ita. Karima ta fara bayani “A lokacin da na hadu da Murtala mun fada soyayya mai karfi wacce tun da na ke a duniya ba a taBa yi mini irin ta ba, kasancewar na fito a hannun Kanin mahaifina ne ban san gatan iyaye ba, tun ina yarinya iyaye na suka mutu, qanin mahaifina ne ya dauke ni, gidan ‘ sa babban gida ne da kowa ke harkarsa kasancewar yana da kudi sai dai mu da ba mu da iyaye wato ‘ya’yan riKo na gidan muna cikin wani hali don ba mu da wata madogara, hatta makarantun da ‘ya’yan sa ke yi ba iri daya ne da namu ba, wani ' lokaci idan na ji haushin kawu na sai kuma tausayin sa ya dame ni a wani lokaci, domin ya hadu da fitinannun mata ne guda biyu, bayan tsananin kishi da ke tsakanin su muma ba su bar mu ba, don haka muka tashi a matsayin ‘ya’yan tsakar gida ni da wasu ‘ya’yan yayan baban mu da shi kuma ya tashi bashi dakarfi daga Karshe kuma ciwon ajali ya kwantar da shi.” “Duk da halin da muke ciki ba mu da matsala ta rashin ci k0 kuma _rashin sha, haka nan mun sami karatu mai kyau duk da makaratun da muke yi ba su kai kyan na ‘ya’yan gidan ba, amman da yake abin baiwa ne sai mu muka fisu KoKari, wannan ma ya Kara ja mana tsana wajan matan kawun mu. K0 bayan da muka kammala Sakandire muka wuce makarantun gaba da ita mun Kara ganin banbanci, domin ‘ya’yan gidan Kasashen waje suke tafiya karatu yayin da mu kuma muke yi anan, hakan ya sanya muka tashi da kokarin ganin mun tsaya da qafafuwanmu domin kwatar kan mu. Hatta gurin samun mazaje ma sun fi mu, domin sukan auri manyan gayu kasancewar suna haduwa akai su gurare na manya, mu kuma sai dai mu kare a irin mu, Haulat da Fadila sun girmemu sune manyan ‘ya’yan yayan baban mu da suka yi aure, mazajan su ba su da wata wadata, don haka k0 bayan sun yi auran ba su sami wata darajar arziqi ba sai ma qaskanci da ya Bullo.” Bayyyanar Murtala gareni lokacin ina gab da kammala karatun digirina ya tayar da hankulansu kwarai da gaske, domin ta kowanne Bangare Murtala ya hadu, mahaifinsa mai kudi ne, yayin da shi ma ya kasance mai kudi, ga shi kuma ya sami karatu mai zurifi domin sai da yayi karatunsa har zuwa matsayin Master a Kasar , bayan nan kuma dole skaya shi a sahun samari masu kyau dadada iyiyawannan abin yayayaahannundakali hannuna daga cikin sa’annina na gidan har suka yi kokarin kwace mini shi, ni kuma na nuna musu kwace goriba a hannun yaro ba abu ne me sauqi ba, Murtala ya nuna mini dukkan soyayyar duniya, sannan ya fitar da ni kunya, don tun kafin ya aure ni ya mallaka mini komai na sa, lokacin bikin mu hankali ya Kara tashi, ba a taBa yin bikin wata yarinya a gidan da ya kama kafar nawa gurin shirya fati da kayan lefe ba, dole suka Boye bakin cikin su suka sakar mini mara, gidan da aka kai ni ya Kara janyo mini martaba gurin ‘yan’uwana balle da zama na ya mika da Murtala, yanda yake kula da ni.” “Domin da yawa daga cikin ‘yan’uwana sunsha. ganin babu inda aurena da Murtala zai je, amman sai ya nuna musu ba hakan ba ne ba, ya barni na kammala karatuna har na je bautar qasa sannan muka fara tinanin haihuwa a shekararmu ta daya da rabi da aure, kullum shakuwar muda soyayyar mu karuwa ta ke yi, abu daya ya so kawo mana sabani shine yawan abokai, kullum gidan mu cikin abokan Murtala yake, kuma basa zama gurina sai bangarenshi shi da abokai su kuma raba dare suna hire, tun ina jin haushi har na hakura domin da na nuna masa ina son ya [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: rabu da abokansa sai ya nuna mini ba zai yuwu ba, tare na gansu, a wannan lokacin mun fuskanci babbar matsala ni da shi wacce ta tsorata ni Kwarai da gaske, domin na fuskanci zai iya rabuwa da ni akan abokansa ma gabadaya duk da irin kaunar da yake mini, don haka na samawa kai na lafiya, duk cikin abokan sa nafi kaunar Abdul, domin shine idan yazo kai tsaye Bangare na zai shigo ya zauna ayi hira aci abinci, koda Murtala ya buKaci su tafi Bangaransa ba ya yadda, don haka muka shaKu da shi, na ke kuma ganin mutuncin sa fiye da saura.” Ta yi doguwar ajiyaI zuciya cikin damuwa sannan ta Karasa ta zauna kusa da Hasna wacce ke kallonta cikin idonta, labarin ya fara shigarta amman ba za ta iya yanke hukunci ba dole sai ta ji Karshen labarin. Karima ta kara dafa cinyar Hasna ta na kallonta ta ci gaba da magana “watan da muka cika watanni goma sha tara da aure na yi katari na kuma yi mugun gamon da har yau bana fatan na kara yin irinsa.” Ta Kara yin shuru, wannan karon Hasna ta kasa yin shuru cikin Kaguwa ta ce “Irinabin da na gani kika gani ke ma k0? Karima ta daga mata kai “Haka ne, na tashi ranar bana jin dadi ina ta amai ga zazzaBi, Murtala yana gidan amman ya qule a bangaransa shi da wani abokinsa Dauda da na tsana a rayuwata, domin kallon da Dauda ke mini da irin kalamanasa ba su yi kama dana mutum mai mutunci ba, amman babu yanda zan yi da shi domin Murtala yana kaunarsa, ina son nace masa ya kai ni asibiti k0 kuma ya sanya direban gidan da yake yawaita aike ya kai ni, wannan dalilin ya sanya na nufi Bangaransa, yammace sakaliya ba wai dare ne yayi ba, na yi sa’a yau bai rufe Bangaran na shi ba, domin lokuta da dama na kan tarar a kulle ne sai na kwankwasa zai Bude da danayi korafi sai yace mini dole ne yayi haka saboda tsaro.” Na shiga falo ban gansu ba, hakan ya bani mamaki, amman ban kawo komai cikin rai naba sai na ratsa na nufl dakin baccinsa, anan na ci karo da mummunan abu domin Murtala mijina na gani da Dauda cikin haihuwar iyayansu suna aikata irin abin da muke aikatawa ni da shi a gadon mu, tsoro da fargaba ya kama ni har na kasa jurewa na sanya hannu bisa kaina fara ihu.” Hawaye ya fara gangarowa daga idon Karima ta sanya hannu ta goge, a ranta tana jin tamkar yanzu abin da ya faru ke faruwa, Hasna ta kasa bata hakuri ta barta ta yi kukan ta ta more domin itama ta dandani ciwon ta san azabarsa da zafinsa. Sai da Karima ta yi kuka mai isarta Hasna na kallonta sannan ta ci gaba da bayani “Ihun da na sanya shi ya firgitasu har ya fargar da su ina gurin, amman sai Murtala ya doka mini tsawa gami da fadin nabar dakin.” “Tsoro da rashin sanin abin yi ya sanya nabar dakin cikin gaggawa na nufi dakina, na yi ta kuka, sai bayan kusan awa guda sannan Murtala ya shigo dakina cikin sanyin jiki, ina ganinsa na far ihu da kururuwar yabar mini dakina, babu irin maganar da ban gaya masaba amman bai ce mini komai ba, daga qarshe ya fita ya bar mini dakin nawa, na ci gaba da kuka na, kwanaki biyu muna cikin halin doya da manja ni da shi, babu abin da ban saKa cikin rai na ba ga ciwo ina fama da shi, daga Karshe na tattara na tafi asibiti ba tare da na nemi izininsa ba, sanda na je asibitin aka tabbatar mini ina da ciki na wata uku, hankalina yayi matukar tashi da jin wannan labarin domin bansan ya yazan yi da cikin nan ba, haka na tattaro na dawo gida.” ‘Ko da na dawo gida na tarar da Murtala zaune a falo ya bini da kallo cike da fargaba, duk ya rame ya flta daga hayyacinsa shima, sai na ji tausayinsaya kama ni, amman ban kula shi ba na shige daki abuna, bayan tsahon lokaci Murtala ya biyo ni, ban kula shi ba ina kallonsa ina cikin bargo a kwance tun bayan da na sha magungunan da aka bani na dan ji sauKin jiki na, hanyoyin da zan samar wa kai na mafita kawai na kenema, Murtala ya jima a zaune sannan ya fara yi mini magana. “Kiyi haquri Karima, Allah ya sani matukar Kaunar da na ke miki ce ta sanya ni auran ki har kuma na kasa sanin ki, domin ban yi zaton zan iya aure ba kwata-kwata cikin rayuwata, sai dai ganin ki ya lalata mini komai.” “Ban ce masa komai ba yaci' gaba da maganar sa “Na san za ki yi ta tinanin inda na koyo wannan abin da kika ganni ina yi da Dauda, to wallahi a makarantar kwana aka fara lalata' ni, lokacin da aka kai ni ina junior akwai wani groups na siniyoyi wanda hatta malamai shakkarsu suke yi saboda taurin kansu, gasu ‘ya’yan masu hali, babu irin kalar Barnar da ba sa yi kama daga shaye~shey zuwa Kungiyar asiri tun lokacin abin bai gama bazuwa ba, babu kuma babu kalar yaren da babu a cikin su, akwai iyamurai, akwai yarabawa da hausawa da sauransu, kasancewar .Federal collage ce, tun da aka kai ni daya daga cikin ‘yan Group din nan Jonh ya sanya mini ido, sati guda da kai ni' ya shigo dakina yayi mini fyade, ina ihu da kururuwa ya toshe mini bakina, daga karshe suka tsorata ni da idan na gayawa wani sai sun kashe ni, har suka bani misali da yaran da ya mutu ranar da aka kawo ni wanda cikinsa ne kawai ya kumbura ya dinga aman jini, sai suka ce sune suka yi masa haka, saboda yace sai ya tona musu asiri, ina ji ina gani na kasa fadawa kowa, tun daga wannan lokacin kullum dare sai john ya yi mini wannan abin da ya saba mini, har aka shekara guda, tun yana mini bana so har na fara yadda da shi ta dadin rai, domin na riga na saba, a wannan lokacin suka bar makarantar bayan ya riga yagama lalata ni, amman kasancewar akwai irin su da suka maye gurbinsu wato ‘yan aji Biyar ya sanya wasu suka ci gaba da mu’amala da ni, tun daga wannan lokacin ya kasance idan ban yi wannan harka ba bana jin dadi, duk yanda zan yi na dai na na yi amman na kasa Karima, don Allah ki yi hakuri ki yafe mini.” “Na yi shuru cikin jinjina halin maganarsa,a qasan raina tausayin sa ne ya cika ni, amman a fili na kasa cewa komai, sai na tashi zaune na dube shi cikin Bacin rai nace masa, Murtala ina son ka amman bazan iya zama da kai da wannan halin naka ba, don haka gwara mu rabu, ga mamakina sai na ga [25/09 3:48 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿29 Batul Mamman(Mrs)💖 Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan gidan sunfi nata kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari sosai. Gida ya cika da yan kawo amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta. Duk da tasawa ranta bazata kula Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda. Adabiyya da Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara mata daki. Tashi tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin. Hajara tayi saurin mayar mata. "Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake shigowa fa." Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa dasu Umma." Tana magana idanunta suka cika da hawaye. Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa turare."to mu zamu tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena kukan su Umma haka. Irin haka sai yaga kamar auren dole aka yi muku. A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai da taji dakin tsit ta tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin turaren wutar da kanwar Umma ta hada mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga. Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a gidan shugaban kasa. Ta mika hannu sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da gudu zata fita don a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga ruwan ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata kunna sai taga bai sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa. Fita kawai tayi ta rufe toilet din. Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura. Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba. Wuri ta samu a tsakiyar gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita. Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin aure bai dawo gida ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da Tala tana ta gyara gidan. Ita kam dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama. Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko alamar zuwa baiyi ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a shake alamar taci kuka yaji tace "Waye?" Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi shiru don kanta. "Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa. "Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har yanzu tana bakin cikin canza musu daki da aka yi. Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita. Kansa ke ciwo kamar ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son tambayar Izzatu amma yasan idan bata da nutsuwa girki ma baya gabanta. Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana". Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka" Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda yadda kansa ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin yarinyar nan. Zan iya mutuwa saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa. Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci tace babu amma bari tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya dan zauna ya fada masa. Suka kwanta shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai abinda ke damunsa. [25/09 3:52 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿31 Batul Mamman(Mrs)💖 Sai karfe uku da rabi Tala ta kwankwasa mata kofa. Ko da ta bude abinci ne a plate an rufe da wani sai ruwa roba daya mai sanyi da cup. Godiya tayi mata ta karba. Gara a rinka kawo mata don ita bata jin zata iya jurar zama tare da mutanen da basa kaunarta su ci abinci. Dama tuni ta soma jin yunwa. Tana budewa taliya ce da miya sai coleslaw a gefe. Kare masa kallo tayi tana mamaki. Abin kuma harda rowar abinci? Abincin dan kukut a plate kamar zaa bawa Khalifa. Tas ta cinye ta sha ruwa rabin robar. In ba haka tayi ba tasan bazata koshi ba. Hamza tun bayan azahar suka fita da wani abokinsa. Gidansu Zuhra suka je yi musu ban gajiya. Su Umma sunji dadi sosai. Har ta cire kunyarta ta tambayeshi ya Zuhra ta kwana. Murmushi yayi sannan yace mata lafiya kalau. Tana gaishe su. Da zasu tafi Baba ya bawa Hamza wayar Zuhra. A jakar Hajara ta manta ta daren jiya. Juya wayar ya rinka yi, banda tsufa ta dade da fita yayi. Da daddare ma har daki aka biyota da abincin. Macaroni ce da vegetable soup. Sai dai Zuhra ta tsani macaroni. Duk yunwar da take ji dole ta hakura. Gudun kada aga kwadayinta ma ko naman dake cikin miyar bata ci ba ta dauki tray din ta sauka kasa dashi. Tana tafiya Hamza da Izzatu dake zaune a dinning table na binta da ido. Bata ko tanka musu ba ta wuce ta ajiye abincin a kitchen. Ta fito kenan Tala ta biyota da sauri. "Naga baki ci abincin ba" Dan murmushi tayi "na koshi ne". Tana wucewa idonta ya kai kan nasu abincin. Shinkafa suke ci, wato ita suka hada da macaroni. Hamza na lura da irin kallon da take musu har ta wuce. Wurin karfe goma da rabi Zuhra tana zaune tunani duk ya isheta gashi ta manta wayarta a gida. Ga uwa uba yunwa. Turo kofar taji anyi tayi saurin tashi zaune ta saka hijab. Daga ita sai daurin kirji saboda zafi ya dameta. Kafin ta rufe jikinta ya kula da daurin kirjin. Ba karamin tsanar sa yayi ba. Bai tsaya jan zance da ita ba yace.. " kina jindadin cin abincin ke kadai ko zaki rinka ci tare damu?" Tasan har ransa ba so yake taci dasu din ba." Zanci ni kadai" "Fine, sai ki rinka fada da wuri idan bazaki ci ba saboda a dena wasting. An kawo miki kin mayar batare da kin taba ba". Idan kika yi shiru zaki kwari kanki shine abinda zuciyarta ke raya mata. Ta dan rage murya "bana cin macaroni ne" "Macaroni kuma? Mtsw ke bana son karya." Turo baki tayi "ni ba karya nake ba. Abinda aka kawo min kenan." Dafa kansa yayi yadda yake idan yana cikin damuwa." Me yasa bakiyi magana ba. Anyway nasan shinkafar bata kare ba idan kina so kije ki ci." Tana kallo ya karaso cikin dakin ya kunna wani abu. Da yake tana setin AC din tuni ta fara jin iska. Yana gani tayi murmushi. Sannan tace. "Don Allah ina ka kunna? Jiya zafi ya isheni na zata da sankarau zan tashi da safe" Ta kusa sashi dariya sai ya gimtse. Idan ya sakar mata fuska zata yi tunanin ta sami karbuwa ne. Remote din AC din ya nuna mata sannan ya miko mata wayarta da chaja a cikin leda. Murna tayi sosai tayi masa godiya. Sai da ya kama hannun kofar ta sake magana tana sosa keya. "uhmmm" Ya tsaya yana kallonta "yes" ganin taki magana. "Dama, dama famfon bandakin ne naga kamar sun lalace." "Kin lalata su dai" ya fada yana shiga ciki. Ya duba duka komai lafiya kalau. Ya fito "wai ni abokin wasanki ne? Babu famfon da ya lalace" Bata ce komai ba tayi saurin shiga. Hannu ta tara a famfon sink da baho duk ruwa ya fito da kansa. Sai da ya tsorata ta duk da ta gani jiya. " ka gani ko, yau tun sallar asuba da shaya nake yin alwala." Wannan karon murmushi yayi. Sannan yayi mata bayanin yadda kan famfon yake. Tun kafin ya fita ta rinka bi tana tara hannu ruwa na zuba. Dariya take yi don abin ya burgeta. Yace to kada ki karar mana da ruwan gidan. Kunya taji tayi saurin cire hannunta ta fito. Shi kuwa tuni ya fice ya tafi nasa dakin. [25/09 3:52 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿30 Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra anji dadin bacci saboda gajiyar da ta tara ta biki. Ba ita ta farka ba sai bayan tara. A firgice ta tashi ganin hasken rana a dakinta. Ko sallar asuba batayi ba. Sai da ta shiga bandakin ta tuna da matsalarsa ta jiya. Gashi ta makara sallah. Banda bahon wanka daga gefe wata yar matakala ce mai karamin bene da yayi kasa akwai shower a wurin. Kunnawa tayi ruwa ya watso mata saboda yayi karfi. Da kyar ta iya rage karfin ruwan. Cire kayanta tayi ta koma tayi wanka tare da alwala. Tun kafin ta gama shiryawa cikinta ya soma kukan yunwa. Nan fa ake yinta. Zuhra bata jurar yunwa gashi tunda aka kawota ko motsi bataji a kofar dakin ba. Haka ta gama duk abinda zata yi ta sami wuri ta zauna. Tunanin iyayenta ne ya zo mata ta soma kuka. Izzatu da Tala sun gama hada komai na breakfast suka jera akan dinning table. Sama ta hau ta kira Hamza. Sanye yake da jallabiya light brown sai kamshi yake. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa da ta zama maabociyar damuwa yan watannin nan. Yaransa duk suka yi masa kiss a goshi kamar yadda suma iyayen suka saba yi musu. Sannan suka zauna Izzatu tayi serving dinsu. Lomar farko da zai kai bakinsa ta tuna masa da Zuhra da ke daki tun jiya ko lekata baiyi ba. Tsaki tayi ya tura kujerarsa ya tashi. "Baby what is wrong?" Izzatu ta tambaye shi itama tana mikewa tsaye. Sama ya kalla ya sake yin tsaki "zan kira yarinyar nan tazo taci abinci ne." A take Izzatu ta hade rai. "Ka bari Tala ta mika mata mana. Ai ba sai kaje dakinta ba." "Hakkinta ne na ciyar da ita" yana fadin haka ya hau saman. Ya kusa minti biyu kafin ya murda kofar ya shiga. Akwai kamshi dai saboda dakin amarya ne sai dai zafi sosai duk da tagar a bude take. Ko meyasa bata kunna AC ba oho. A tsaye take tana jera kayanta a wardrobe har ta kusa gamawa taji an taba kofar. Cikinta sai da ya bada sauti saboda tsoro. Ko da ya shigo duk rashin kunyar da taso yi masa sai ta fasa saboda yadda ya cika mata ido. Bata taba kare masa kallo ba sai yau. Da ace zaman lafiya suke yi da ta fada masa yadda yayi kyau. Shima ita yake kallo. Riga da skirt tasa na atampa fuskar nan tasha farar hoda. Kana ganinta ita daban fuskar ma daban. Ga hannun breziya ya fito ta kowane gefen hannun rigarta. Ya dan tabe baki....kai kuma irin taka jarabawar kenan Hamza. "Ke baki iya gaisuwa bane?" Saurin durkusawa tayi tare da jin kunya. "Ina kwana, an tashi lafiya"? Bai amsa ba ya juya"ki sauko muyi breakfast". Kafin ya kai kofa ta biyo bayan shi. Yunwa take ji sosai. Ace yau har shadaya saura bata ci abinci ba. Ita kanta tasan tayi abinda zaa jinjina mata. A baya ta rinka binsa har suka sauko. Izzatu ta kai karshe wurin bacin rai, sai kawai ta danne. Kujera ta samu kusa da yaran ta zauna tare da yin sallama. Khalifa ne kawai ya amsa. Ya kalli Mamansa. "Mummy wannan ma mai aiki ce?" Hamza ya ce masa yayi shiru kawai yaci abinci. Zuhra tana sane bata ji ya gyara masa yace ita ba mai aiki bace ko da bai kirata matarsa ba. Izzatu ko daga kai batayi ba bare ta bashi amsa. Itama Zuhra taki kallonta. Yadda take jin haushin Izzatu ko kallo bata isheta ba. A dalilinta tazo gidan nan da bata da wata kima a idon mazauna cikinsa. Muryar Hamza ce ta katse mata tunani. "Wai ba kya gaishe da mutane ne?" Ta dago fuska suka hada ido. "Na gaisheka a daki" Da kansa yayi mata alamar bata gaishe da Izzatu ba. Amma lallai ya rainata da yawa. Su basu ce 'ya'yansu su gaisheta ba sai ita zata gaishe da matarsa. Kamar bazata yi ba sai kuma tace "ina kwana" Maimakon ta amsa sai kawai ta tashi ta koma dakinta. Hamza ya bi bayanta. Yaran ma suka gama suka tashi. Suna tafiya Zuhra ta janyo flask ta bubbude sannan ta debi abinda zata ci ta hada tea. Sai da taci ta koshi sannan ta tashi daga dinning area din ta koma wurin yaran inda suke zaune suna kallo. Tambayarsu sunayensu tayi suka bata amsa. Junior yace "ke kuma ya sunanki?". Murmushi tayi "sunana Zuhra". Khalifa yace "nice name, will you be my friend?" Ido ta dan zaro "tohhh kun iya turanci tun yanzu..." da haka suka rinka hira da ita tana jansu da wasa. Hatta Nana mai kyuya ta yarda da Zuhra. Hamza ya dauko laptop zai fara aiki sai kuma ya rufe. "Izzy kirawo yarinyar nan, I need to talk to both of you" Wani irin kallo tayi masa. " sweety nice zani dakin Zuhra? Allah Ya kiyaye. Kuma ai bai kamata ta shigo mana bedroom ba. As far as am concerned ni ban dauketa matarka ba." "Gashi kuma na biya sadaki" yadda yayi maganar tasan har yanzu yana ganin laifinta a matsayin wadda ta jawo masa auren. Tana fitowa ta jiyo muryar Junior yana cewa Zuhra ta yi masa tatsuniya. Daga saman ta leka ta kirawo Khalifa. Shi ta fadawa ya rako Zuhra dakin daddysu yana jiranta. Rike da hannun Khalifa suka shiga dakin. Wata irin niima taji. Ita nata dakin sai zafi. Falo ne a farko sannan kofar dakin daga ciki. Wurin ya tsaru sosai ta tsaya tana kallo. Izzatu tace da Khalifa yaje wurinsu Junior. Babu wadda ta kula yar uwarta har Hamza ya fito. Kusa da Izzatu ya zauna. Ita Zuhra kasa ta zauna kan kafet saboda gudun kada ace tayi laifi. Gyara zamansa yayi fuskarsa ta nuna alamun ba wasa. Sannan ya soma magana "Kamar yadda kuka sani dukkaninku matana ne duk da cewa circumstances behind auren kowacce is different...... Zuhra anzo wurin...gabadaya jumlar karshe bata fahimta ba. .....bana son tashin hankali a gidan nan. Izzy kece babba ina so kija girmanki. Ke kuma ya juya ga Zuhra ki bata girmanta. Tun farko na gargadeki akan auren nan kika ki ji. So duk abinda kika gani sai kiyi hakuri. Sannan a yanzu baki da kitchen don sai an gyara miki daki a kasa. For now idan Izzy tayi girki zata baki. Saboda haka babu zancen rabon kwana sai an gama kitchen din." Ya kallesu duk su biyu. "Ko akwai mai magana?" Izzatu tana ta kumbure kumbure tace " ka fada mata ta fita harkar yarana". Bai ce mata komai ba yace da Zuhra tana iya tafiya. Tunda ya soma magana bata daga kai ba. Yayi tsammanin zata nuna bacin rai amma sai yaga tayi shiru. Kanta a kasa ta fita daga dakin ta koma nata. Tana rufe kofar ta suma kuka duk yadda taso daurewa ta kasa....ba son Hamza take ba amma babu macen da zata so a nuna mata ita ba komai bace a gaban kishiya. [25/09 3:52 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿32 Batul Mamman(Mrs)💖 Haka rayuwa ta kasancewa Zuhra a gidan Hamza. Kullum safe, rana da dare duk zaa kawo mata abincin marowata kamar yadda take kiransa. A kullum zata yi waya da iyayenta. Idan bata kira ba zasu kira ta. Idan aka tambayeta Hamza tace yana nan kalau. Bata taba tunanin fadin komai ba domin Anti Faiza tace zaman gidan miji yana bukatar sirri. Ko Hajara ta hanata ta sanarwa komai na dangane da gidan aurenta. Hamza dai yasan ana bata abinci saboda haka bai taba damuwa da sanin yawansa ba. Idan ta fito sauka da kwanunkan abinci suka hadu da Izzatu zata gaisheta a ciki ciki. Itama da kyar take amsawa. Don Hamza yayi mata fadan baya son gaba ne da ko kallon Zuhra bazata yi ba. Shi kuwa matsalar kamfaninsa tasa shi a gaba, bashi da lokacin gidansa sosai. Ranar alhamis da safe Tala ta kawo mata abinci kamar kullum. Tea ne a dan karamin cup irin mai saucer dinnan wanda kurba biyar zuwa shida zai kare. A plate din kuma sliced bread ne guda uku. Wani irin kallo Zuhra ta yiwa abincin. Ta dauki bread daya taji shi a bushe da tauri. Murmushin yake tayi... Tala yau kuma bushasshen brodi kike kawo min. Tala ta dawo ta dan durkusa gabanta amarya ai wannan tos ne. Tala zata yi sa'ar Izzatu ko ta girmeta da kadan. To...to me? Zuhra ta fada tana yamutsa fuska. Tala tace tos. A tosta ake sakawa sai kiga ya fito ta sama kamar an jeho shi. Har dan bota na shafa miki don kiji dadinsa. Zuhra ta gyada kai, naga alama. To nagode. Bayan fitar Tala tayi ta juya bread din a hannunta. Tunda tazo gidan breakfast dinta na farko ne kawai ta taba koshi. Kullum sai dai rage hanya, gashi bata taba ganin alamar za'a fara aikin nata kitchen din ba. Ba yadda ta iya a dole ta fara cin bread din. Kana ganin fuskarta kamar mai shan madaci. Ko rabi bata ci ba ta shanye tea din. Ta sake kai bread din bakinta Hamza yayi sallama ya shigo batare da ya jira ta amsa ba. Zaune take da tray a gabanta kanta babu dankwali. Doguwar riga ce a jikinta ta wani material. Dinkin dai yayi kyau sai dai wadda tasa kayan ce sai a hankali. Sunkuyar da kanta tayi kasa tace ina kwana? Bai amsa ba yana daura agogo a hanunsa ya dubi plate din gabanta. Ashe ma zaki iya ci. Dama naga toasted bread aka yi nayi tunanin baki saba ci ba a baki wani abincin. Zuhra tayi sauri ta tofar da na bakinta akan tray din. Wallahi bana iya ci, hakan ma dauriya ce kawai. Hamza ji yayi kamar ya amayar da abinda yaci. Wannan wace irin kazanta ce ta gama jika bread a bakinta ta dawo dashi. Fuskarsa na kallon gefe yace naga saura biyu da rabi ki cinye. Tashi tsaye tayi tana karkade hannuwanta...wallahi dama uku ne. Dan murmushi yayi...haka Izzatu take bata son ayi abinci da yawa, a cewarta zasu yi kiba suyi loosing shape. Farkon aurensu har rama ya rinka yi. Daga baya sai yake siyan biskit da cake a ajiye a office. Kyalesu zaiyi, kila idan Zuhra ta dan horo zata nemi komawa gidan iyayenta. Sai ya saketa cikin sauki. Ba tare da ya kalleta ba yace zansa a kawo miki wani abincin. Da ya juya zai tafi yaji tace adawo lafiya, Allah Ya kiyaye, Ya bada sa'a, Ya tsare kuma Ya kare dukkan sharri. Adduar tayi masa dadi yace Amin a hankali. Wannan adduar kullum Umma sai tayiwa Baba idan zai fita wurin sana'arsa. Tunda ya fita bata ga alamun abinci ba sai uku saura aka kawo na rana. Cikin kankanin lokaci ta tayar da abincin. Ta fito daga toilet kenan Tala ta shigo tace amarya kinyi baki. Shikenan anzo wurin.....kullum addua take yi kada tayi baki saboda bata san me zata basu ba, yau gashi wasu sun zo. Tunani ta soma yi lokaci guda idea ta zo mata. Kanta ta rike da hannu biyu ta rufe ido. Tala kaina ciwo yake min sosai kamar zai tsage. Tala tayi saurin karasawa ta riketa har bakin gadonta. Sannu amarya ko na karbo miki magani wurin Anti Izzatu? A'a Zuhra tayi saurin dakatar da ita. Nima ina da shi. Kice su hawo nan bazan iya saukowa ba. Tala duk tausayin Zuhra ya kamata tace ba komai amarya. Kafin ta fita Zuhra tace ki dan taimaka musu da ruwan sha don Allah. Tana fita Zuhra ta gyara kwanciya. Bata san ko su waye ba amma dai tasan gidan amare ana son a bawa baki dan abin kusa da baka. Ita kuma bata da komai, idan za'a bata ma karba zata yi. Ba jimawa yan uwansu na Ajingi suka shigo. Kirikiri Zuhra taki tashi tana ta langabewa ita mara lafiya. Da muguwar rawa gwamma kin tashi. Anti Faiza ce ta rako su. Suna ta mata tsiya ko har an fara laulayi ne na kwana biyar. Ita dai sai murmushi take yi a dole taji kunya. Tala ta kawo musu ruwa harda lemo a jug da kofona. Basu dade ba suka ce gobe zasu koma Ajingi. Tayi musu godiya ta rakasu har kofar daki. Sai da suka sauka kasa Anti Faiza ta dawo da sauri take tambayarta yaya zaman nata. Kuka Zuhra tasa mata ta sanar da ita ko abincin kirki ba'a bata. Anti Faiza tace kiyi hakuri gobe za'a kawo gararki. Akwai kudi ne a wurinki? Zuhra ta share hawayenta tace eh Baba ya bani. Duka ta debo ta bata Anti Faiza ta dauki dubu goma a ciki ta bata sauran. Zanje kasuwa gobe kafin azo kawo garar zan zo in sha Allah. Ta dafa kafadarta...ki kara hakuri kuma kada ki bari Izzatu ta san ba kya jindadin zaman. Daga ita har mijin nata so suke kiyi abinda zai sakeki. Kuma In sha Allah kinzo kenan, yadda iyayensa suka yi miki kokari kema ki dage nemawar kanki wurin zama a zuciyarsa. Zuhra ta tura baki ni me zanyi dashi Anti? Ai kawai idan ya gaji ya sakeni. Anti Faiza toshe mata baki tayi. To banza na sake jin zancen saki sai na fasa miki baki. Biskit ta dauko guda biyu a jakarta ta bawa Zuhra sannan ta sauka kasa suka tafi. Fitarsu ke da wuya Izzatu ta shigo tare da Tala. Zuhra tana kwance akan kujera ta gansu. Tashi tayi zaune tace lafiya cike da tsiwa. Fuskar Izzatu a daure tace ke kika ce Tala ta bawa bakinki ruwa da juice a jug dina? Zuhra ta kalli Tala tayi tsuru tsuru. Kiyi hakuri na zata mijinmu ne ya saya shiyasa nace ta taimaka ta kawo. Izzatu ta soma fada rai a bace...mijinmu fa kika ce? Yanzu Zuhra don baki da kunya sai ki hada baki da inlaws dina ki auri mijina kawai don kinga ina sakar miki fuska. To Tala mai aikina ce ni kadai kuma kada ki sake taba min kaya. Ignorant fool yadda kika zo haka zaki fita ki bar min gida. Zuhra tayi yar dariya ko na kwana daya ne Izzatu kin taba zama da kishiya a tarihin rayuwarki. Izzatu ta tsaya tana kallon Zuhra..dama bata da kunya? Kwafa tayi sannan ta fita tare da buga kofar da karfi. Tala ta dauki tray din Zuhra na bata hakuri tace babu komai. Ita sai mamakin wannan aure na ubangidanta take da yadda suke wulakanta amaryar. Zuhra tayi murmushi ko ba komai yau ta dan gasawa Izzatu magana taji dadi. Daren ranar ba'ayi girki ba ana jiran Hamza ya kawo abinci daga tantalizers. Da yake bai fito office da wuri ba abincinsu ya kare sai snacks ya siyo. Yana wanka Izzatu ta rabawa kowa banda Zuhra. Shima burger yaci ya kwanta a zatonsa an aikawa Zuhra nata. Tala tana son tambayar na amarya tana tsoro don ba karamin fada Izzatu tayi mata ba. Har shadaya da rabi babu abinci babu dalilinsa. Dole Zuhra ta karasa sauran biskit din da Anti Faiza ta bata ta shiga toilet ta sha ruwa sannan ta kwanta ciki na kukan yunwa. [25/09 3:52 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿34 Batul Mamman(Mrs)💖 Kafin Hamza ya dawo daga raka su Mama mota tayi saurin shigowa ta hayewarta sama tana murza hannunta wanda ya matse mata harda hawayenta. Tala tana kwashe trays din da aka yi amfani dasu Izzatu ta tsaya mata a ka. Nace Tala ko kin gaji da aikin ne? Ido ta zaro a'a Hajiya wani abin ne ya faru? harara Izzatu ta jefa mata. Jiya banyi miki magana akan yiwa bakin yarinyar nan amfani da kayana bane? Tala tace Allah Sarki ai naga harda maman Alhaji shiyasa na dauko musu. Kiyi hakuri. Izzatu tace ba mamansa bace kishiyarta ce. Kuma na karshe kenan da zaki taba min kaya da sunan karrama bakinta. Wallahi ranar zaki koma kauyenku. Daga nan ta juya ta koma kan kujera ta zauna tana huci. Yadda Mama da su Mariya suka ki amsa gaisuwarta ke damunta. Kwafa tayi inma suna rawar kafa ne sun koma bayan amarya zata bar gidan ne da wuri. Su basu san wasa bane ko abubuwan nishadi da har zasu ji haushin abinda tayiwa Zuhra asa mijinta aurenta. Tana ta karkada kafa tana mita a ranta Hamza ya shigo yayi hanyar sama. Da bibbiyu yake tsallake steps din. Murmushin mugunta tayi Allah Yasa daga nan ya saketa kowa ya huta. Zuhra na tsaye gefen kujera tana hawayen yadda hannunta ke zafi tace kuma Allah Ya isa na....dawa kike taji Hamza ya fada yana shigowa dakin. Duk da ta tsorata cike da tsiwa fuska duk hawaye da majina harda murguda baki tace da wanda ya tsargu. Baki Hamza ya saki lallai yarinyar nan bata da kunya. Shi saboda yadda yaki jinin raini shiyasa baya shiga sabgar autarsu Hamida. Itama tsiwa ce da ita.... Ke, dani kike? Share shi tayi ta cigaba da matsa hannu. Tsawa ya daka mata ke ba kya jina ne. Nace ni kike yiwa Allah Ya isa? Waige ta soma yi hagu da dama ita a dole bata san da wa yake ba. Ransa ya kara baci yayi kanta. Da gudu ta kara shigewa cikin dakin sai da ta kai jikin bango. Kafa yasa ya buga kofar da karfi daidai da bugawar zuciyarta. Sai rarraba idanu take. Wani irin kallo yake mata kafin ya sake cewa wai kina ji ina tambayarki kin kasa bani amsa saboda ki nuna min ban isa ba. Tsoro kam ta gama ji amma ta rantse bazata yi shiru ba tace au dama dani kake? Maganar ta sake sosa masa rai ya biyota har inda take tsaye jikinta ya soma rawa. Tana cigaba da hawaye tace to ai ke naji kace ni kuma da aka haifeni Baba saniya da rago ya yanka ya rada min suna Fatima. Dayake sunan Innarsa ne da kuma Ummana shine ake kirana Zuhra. Ta turo baki sai ka zabi daya a ciki ka dena ce min ke kamar wata...yan lips din nata ya kama da yatsunsa biyu. Taji zafi ta fara kokarin cire hannun nasa. Idan kika ki tsayawa tsinkesu zanyi sai naga na tsiwar . Idanunta duk sun firfito sai hawaye sharrr. Sai lokacin ya kare mata kallo. Ba wani tsahon kirki gareta kuma tana da jiki madaidaici. Kalar fatarta bata da haske sosai amma kuma ba baka zaa kirata ba. Akwaita da idanuwa masu kyau ga hancinta da baki duk yan madaidaita. Banda rashin iya kwalliya da itama zata shiga jerin matan da basu da muni. Hijabin jikinta ya kalla duk yasha hawaye da majina. Sai lokacin yaji kyankyami ya sakar mata lebe. Ta karkace baki ta sake cewa Allah zai saka min. Kan gadon ta haye zata zagaye shi ta gudu. Yasa hannu ya fizgota ta saki kara. Da karfi ya manna ta da bango ta runtse idanunta tana jira ya sake kama leben. Dalli taji masu zafi guda uku ta sake cewa Allah Ya....wani ya kara mata da yafi sauran zafi. Nan da nan ta soma kuka mai sauti. Irin kukan da idan ta fara a gida har makota sai sun leko an bata hakuri take denawa. Hamza huci kawai yake don bacin rai. Me zaisa Alhaji ya hadashi aure da wannan mara kunyar yarinyar. Gashi ta kafeshi da idanu kamar wani sa'anta. Yi min shiru ya fada da karfi. Tsaf ta hadiye kukanta. Ina so kisan cewa ba'a min rashin kunya. Sannan kika kara cewa Allah Ya isa sai na dirje miki baki. Kina jina? A hankali ta gyada kanta domin taji zafi a bakin da ya dalle. Good ya fada, me yasa baki fada min za'a kawo gara ba? Kuma a ina kika sami abinda zaki bawa bakin? A hankali tace Anti Faiza ce ta kawo. Ga gidan yunwa ko, shine abinda za'a bawa baki ma sai kin roka don ki jawo min magana ace bana kula dake. Hannu tasa ta rufe bakinta sannan tace nima bansan zasu zo ba sai jiya. Kuma ban ganka ba bare na fada maka. Ni duk abinda kuke yi min banji haushi ba sai....sai me ya tambaya da yaga ta kasa karasa maganar. Ba komai ta sunkuyar da kai. Zare mata ido yayi bazaki fada ba sai na kara dalle bakin. To ba kaine jiya kace zaka aiko min da abinci ba amma naji shiru. Da daddare ma kuka barni na kwana da yunwa. Wani iri yaji a jikinsa...kika kwana da yunwa??? Nufinki ba'a kawo miki abinci ba. Zaka ce baka sani bane.....auuuu, tayi saurin rufe kanta da hijab kada ya sake mata wani abin. Ga mamakinta shiru taji tana dago kai har ya bude kofa sai ya juyo. Da sauri ta sake rufe bakinta. Key din kitchen din ya jefo mata gashi nan zansa a hada miki gas cooker. Bai kula ba yayi tafiyarsa. Key kuwa a goshinta ya sameta ta soma tsalle tana ihu. Allah Ya isa ta fada a hankali. Kasa ya sauka ya sami Izzatu tana kallo. Tana ganinsa ta taso Baby....hannuwanta ya ture da take shirin taba shi. A wane dalili ne jiya baki bawa yarinyar nan abinci ba? Wani irin kallo ta masa Why do you care? Saboda matata ce hakkinta ne na ciyar da ita. Matarka fa kace Hamza? Har Zuhra takai matsayin da zata hada kai dani. Wallahi sai ka saketa a yau....wayarsa ce ta soma ringing. Yana dubawa yaga manajan bankin da ya tura Inuwa ne ya karbo kudi a cigaba da aikin ginin da suke yi. Izzatu sai fada take yana daga mata hannu tayi shiru taki. Mr Oscar ya gama tsorata tunda manajan yace bari ya kira Alh Hamza ya tabbatar ko shi ya aiko shi. Ya gama hango kansa a matsayin korarre daga aiki kila ma a rufe shi. Bayan sun gaisa manaja yace Alhaji dama na kira ne domin confirming ko kai kayi authorizing cheque na 10 million. Gefe Hamza ya dan matsa amma Izzatu har nan ta biyo ita wallahi ko ita ko Zuhra. Daidai sanda manaja yace ka turo Mr Oscar Hamza baiji ba amma tunda yasan ya turo Inuwa sakatare sai yace eh ya ajiye wayar. Ya juyo ransa ya gama baci Izzatu ki shiga hankalinki dani wallahi. For God's sake ya kike so nayi da rayuwata ne. Daga ke har yarinyar da kika yi sanadiyar zuwanta gidan nan bakwa gabana. Duk kin birkita min lissafi lokaci guda. Da kamfanin zanji ko masifarki? Come on get out of my way ya tureta ya fice don ya kusa makara masallaci. Mamaki ya kama Mr Oscar lokacin da manaja ya bada order a bashi kudin. A tsorace ya karba jiki na rawa yana ta tunanin kada ace ya dawo dasu. A daidai bakin gate suka hadu da Inuwa sakatare. Cikin Mr Oscar ya murda sosai ji yake kamar ya saki zawo don firgici. Inuwa yace Oscar kaima ashe kana banking a nan. Nima sauri nake kada su tashi kasan yau Friday Oga ya aiko ni. Kai kawai Oscar ya gyada yayi gaba yana kankame jakar kudin. Inuwa bai kawo komai ba ya shiga bankin. Shima wurin manaja aka kaishi saboda yawan kudin. Manaja yace kuma kaga yanzu wani maaikacin kamfaninku ya karbi the same amout na 10 million. Hala babban project ne a gabanku. Inuwa sakatare yace Oscar ma kudin kamfani ya karba? Manaja yace eh har da Oganku nayi confirming. Inuwa yayi mamaki dai amma sai ya karbi kudin ya tafi. A iya saninsa shi kadai Oga yake aika banki. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿33 Batul Mamman(Mrs)💖 Washegari Jumaa tun bakwai da rabi Hamza ya fita zuwa site din da suke wani gini. Dama a daren Izzatu ta kai masa karar Zuhra wai tayi mata rashin kunya. Da safe ta sake tuna masa yace idan ya dawo zaiyi maganin abin. Yau bakin shayi da bread aka kaiwa Zuhra a matsayin breakfast. Bata nuna damuwa ko kadan a fuskarta ba da Tala ta kai mata. Tasan Izzatu na neman suyi fada ne ita kuwa bazata biye mata ba. Bayan ta gama sha ta dauki kofin ta sauka kasa. Junior ne ya tareta a kofar kitchen din...Zuhra meyasa kika dena cin abinci tare damu? Shafa kansa tayi babu komai nafi son zama a daki ne. Hannunta ya rike to nima zan rinka zama a dakinki. Khalifa ya taho da sauri ayi hirar dashi suka hada ido da Izzatu. Ba shiri ya koma dakinsu don yasan ma'anar wannan kallon. Tsawa ta dakawa Junior tace ya bar wurin. Ya buga kafa a kasa ni Mummy ki kyale ni Zuhra is my new fiyend(friend). Karasowa tayi gabansu ta kalli yadda suka rike hannu. A sakar min hannun yaro ko. Zuhra ta durkusa a gaban Junior. Kaga tunda Mummy tace ka tafi to ka zama yaron kirki kaji. Watarana har goyaka zanyi,amma yanzu idan kana rashin kunya babu ruwana da kai. Murmushi yayi wanda ya kara fito da kammaninsa da Hamza. Pyomis(promise) ya fada yana tsalle. Dariya kawai tayi don bata gane abinda yake nufi ba. Ga mamakinta dage yayi ya mata kiss a goshi tunda durkushe take a gabansa. Izzatu ta fizgo shi tana fada. Muje nayi maka brush, ji yadda ka taba wannan kazantar da bakinka. Ta gallawa Zuhra harara, ita kuwa bata tanka mata ba har suka shige ciki. Mamaki take yadda dan karamin yaro ya iya iskanci a cewarta. Kiss ai sai marasa kunya..... Bata bar wurin ba Anti Faiza tayi sallama. Da sauri ta tarota ganinta da kaya niki niki. Kwalayen juice ne guda hudu, ruwa guda biyu da cake da biskit duk na kwali. Sai da suka gama hawa dasu Anti Faiza ta sake fita ta dauko wata katuwar kula da taimakon mai adaidaitan da ya kawota. Zuhra tace Anti Faiza wannan kayan fa? Bari na sallami mutumin nan ina zuwa. A falo ta jirata ta dawo. Sai da suka gaisa Anti Faiza tace kudin da na karba a wurinki dashi na siya. Kinga anjima zaa kawo gara sai ki bawa baki. Sauran ki ajiye kiyi amfani dasu. Ta nuna kular can kuma meatpie ne da spring rolls shima sai a basu. Da kuka Zuhra ta rungume Anti Faiza tana godiya. Hayaniya Izzatu ta soma ji ta fito falon. Mata ta gani wadanda bata sani ba zazzaune suna ta hira. Ana yan ciye ciye, yan uwan su Zuhra ne da wasu makotansu harda Maman su Anti Faiza. Basu jima ba sai ga su Mama , Mariya, Jidda da Ummahani matar Ibrahim. Cike da kunya Zuhra ta gaishe su. Mama tace duk kannenki ne kike durkusa musu. Tashi abinki kinji matar Yaya. Kunya sosai take ji yadda Mama ke janta a jiki kamar wata yarta. Su Umma sunyi matukar kokari kayan garar da suka hadawa Zuhra. Mama ta basu tukwici suka fara shirin tafiya saboda kada a rufe tituna tunda Jumaa ce. Izzatu komawa tayi daki ba tare da ta sauko sun gaisa ba ta dauki waya ta kira Hamza. Shi da accountant din kamfaninsa ne suke ta lissafin kudi. Duk yadda zaiyi su hada kudin nan kokari yake yi. Sau uku ta kira baya dauka saboda abinda yake yi. A na hudun ne ya dauka Izzy what is it? Honey ni bansan abinda akeyi ba a gidan nan amma ga su Mama da wasu matan da ban taba gani ba a cikin gidan nan. Kamar wata walima suke yi ko me oho. Ana ta ciye ciye dai a falon. Table din gabansa ya buga rai a bace. Ya rasa wani irin abu ke faruwa dashi. Wane irin taro ake yi a gidansa wanda bashi da masaniya a kai. Tunda Izzatu tace harda Mama gara ya kira yaji ko meye. Yayi ta trying din number dinta ba'a dauka. Suna can tasa ana ta shigo da kayan garar cikin falo. Ta tambayi Zuhra tace key din inda akace shine kitchen dinta baya wurinta. Jin shiru da yayi yasa ya hada kayansa yace da accountant din zaije gida ya dawo. Yana fita Mr Oscar ya fara hada takardun da yazo dasu wurin. Cheques ya gani har hudu na miliyan goma goma da Hamza yasa hannu. A take zuciyarsa ta soma rawa. Kamfanin nan na Hamza nema yake ya durkushe duk su rasa aiki. Gara ya taimaki kansa kawai. Guda daya ya dauka ya fita. Shima rufe nasa office din yayi sai banki. Hamza na zuwa gida ya tarar saura Anti Faiza dasu Mama. Duk sauran matan sun watse. Izzatu na ganin shigowarsa ta taga ta fito daga dakinta. Sai a lokacin ta gaishe da Mama. Ko kallonta bata yi ba ta cigaba da tambayar Hamza ya aiki. Baya jindadin yadda iyayensa basa shiri da Izzatu. Tace Mariya ya yara? Itama bata kulata ba. Ai nan Hamza ya soma fada akan me zata share matarsa. Jidda tace Yaya munfi awa daya a gidan nan bata fito ta gaishe da Mama ba sai yanzu. Kallon Maman yayi tace kaga ina key din kitchen din Zuhra a bude a zuba kayan nan a ciki. Sai a lokacin idanunsa suka kai kan kayan. Kamar ya tambayi ko na meye sai ya fasa yace yana daki bari na dauko. Mama tace yi zamanka mu danyi hira yanzu zan tafi. Zuhra jeki ki dauko....dibi dibi ta soma yi don bata san inda zata duba ba. Izzatu ta sha kunu , shi kuma ya dan wayance ki duba bedside drawer ta bangaren dama. A sanyaye ta hau saman. Ita da sau daya ta shiga falonsa ma bata gane inda yake nufi ba. Su Nana ne suka fito daga daki sai murna anga Grams. Shiru Zuhra bata dawo ba yayi dan murmushi Mama bari na bita. A falon ta tsaya kasa shiga dakin. Bata ankara ba taji ya shigo ya rufe kofar har sai da gabanta ya fadi. Hannunta ya ja cikin dakin ya matse shi iya karfinsa. A tsawace yace what the hell is happening a gidan nan? Jikinta a take ya soma bari ga hannu ya matse mata. Idanunta suka ciko da hawaye, ya sake yi mata tsawa nace me ake yi a gidan nan? Kayan garata aka kawo. Tana fada hawayen ya soma digowa. Ransa ya gama baci, kin fada min za'a kawo gara??? Tayi saurin girgiza kai. Snacks da nagani anci a falon daga ina aka samo su? Shiru tayi saboda yadda hannunta ke zugi. Baki da baki ne? Nan ma bata yi magana ba. Sakinta yayi ya dauko key din sannan ya nuna mata toilet maza kije ki wanke wannan hawayen munafurcin. Da gudu gudu ta tafi. Koda ta fito yana jiranta suka sauka tare. Mama tana murmushi tace daga dauko key sai ka shanya mu Yaya. Zuhra yake kallo abu ne ya shigar mata ido na tsaya wanke mata. Kowa sai sannu yake mata ana tambayarta ko ya fita. Budar bakinta kawai sai ta soma kuka. Mama ta tashi da sauri tana tambayarta me aka yi mata. Shima Hamzan tambayar da yake mata kenan a dan tsorace. Tana kukan tace idon ke zafi....Mama ta rungumeta Yaya kace yar tawa sarauniyar shagwaba ce. To sannu kinji Fadimatu ki dena kuka. Idan bai fita ba sai kuje asibiti Yaya. Kai kawai ya daga yana kallon Zuhra cike da tsoron kada ta fadi abinda yayi mata. Sai da aka shigar da komai kitchen din har Mama na fadan garin yaya ba'a fara aikin gyara wurin ba yace sai weekend mai aikin zai zo. Tare da Anti Faiza suka tafi suka ajiyeta a hanya. Zuciyar Mama tana mata wasi wasin dalilin kukan Zuhra. Bata sani ba ko idonta ne amma kamar ta rame ma. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿 35 Batul Mamman(Mrs)💖 Fadan da Hamza yayiwa Izzatu yasa ta kuka sosai bayan fitarsa. Kwana biyu a tsakani yana share lamarinta. Ranar monday ran kowa a bace suka rabu saboda sun kwana da fushi da juna. Ta dage sai ya saki Zuhra idan yana son zaman lafiya. Takaicinsa shine kamar bata san mahaifinsa yayi masa katanga da sakin Zuhran ba. Ita ba ruwanta ko Alhaji zaiyi fushi dashi ita dai bukatarta ta biya. Ko kulata baiyi ba ya fice abinsa. Saboda bacin rai wata jaka ta dauko tana kuka tana watsa kayanta a ciki. Sai da ta gama ta kira mahaifiyarta tana sanar da ita zata taho gida. Idan babu jirgi zata yi shatar mota. Da kyar Raliya ta samu Izzatu ta fada mata abinda ya faru. Tsaki Raliya tayi...ni bansan baki da hankali ba sai yau Izzatu. Yanzu sati daya da zuwan yarinyar har kin karaya? Duk ke kika jawowa kanki ai. Muryarta har ta dashe don kuka tace what do I do Mum? Bazan iya zama da wata mace a gidan nan a matsayin kishiya ba. Raliya tace calm down. Yanzu abinda nake so dake shine ki bude kunnuwanki kiji abinda zan fada miki........... A site din ginin Hamza ya hadu da Inuwa sakatare yace Inuwa hala baka sami zuwa bankin bane ranar Jumaa banji alert ba. Ikon Allah kuma naje ranka ya dade har ma na hadu da Oscar. Sakon yana cikin motata bari naje na dauko. Hamza ya dakatar dashi. Ka bari sai mun koma office. Zuhra tayi mamakin abincinta na rana yau. Duk da bashi da yawa sosai amma yafi abinda aka saba zuba mata. Da laasar ma Izzatu har shiga dakinta tayi tace mata zata je unguwa. A darare Zuhra tace Allah Ya kiyaye hanya. Bayan ta tafi Zuhra ta tashi taje inda Izzatu ta tsaya zuwa bakin kofa ta karanta Ayatul Kursiyy ta tofa a ko'ina. Irin wannan makircin na kishiyoyi ai mun saba jin labarinsa ta fada a fili tana dan dube dube ko an barbada mata wani abin. Kin gama yi min masifa yau kice min zaki fita kamar nice dan gatan mijin nan naki. Ga mamakinta da Izzatu ta dawo tare da yaranta suka sake zuwa dakin Zuhra tace ta dawo. Da dan murmushinta na tsoro tace sannu da zuwa. Zuciyarta ta gama bata akwai abinda ke shirin faruwa ko zai faru. Ranar Hamza bai sami dawowa gida ba sai wajen tara na dare. Gidansu ya biya Mama take tambayarsa yaushe zai kawo amarya. Dammm yaji a zuciyarsa, yanzu jira ake ya dauko wannan kazamar a mota. Cewa yayi weekend in Allah Ya yarda zai kawota. To ka biya da ita taga nata iyayen inji Hajiya. Lokacin da ya shiga gida falon tsit. Yasan su Khalifa sunyi bacci saboda makaranta. Dinning table ya kalla yaga an jere shi da kwanuka kamar ana jiran baki. Ko bi ta kai baiyi ba ya haye sama ya shige daki. Abinda ya kwana biyu bai gani bane Izzatu ta gyare dakin tas sai kamshi ko ta ina. Murmushi yayi yasan tana neman shiri kenan. Jakarsa da takalma ya ajiye yana cire safa ta fito daga toilet dinsa sanye da wata rigar bacci mai matukar kyau. Binta yayi da ido har ta karaso gabansa. Ba karamin kyau tayi ba tasha kwalliya. Safar ta karasa cire masa sannan ta rage masa kayan jikinsa. Bata ce komai ba shima baiyi magana ba. Toilet ta kaishi ta taimaka masa yayi wanka. Abinda ta dade bata yi ba tun kafin tayiwa Zuhra April fool. Sai da ta gama shirya shi suka je kasa ta bashi abinci da kanta. Da ta tabbatar ya koshi sai suka koma dakinsa durkusawa tayi a gabansa gwiwoyinta a kasa ta soma kuka. My sweetbaby nasan na bata maka rai da yawa a iya zaman da muka yi amma ina rokonka don Allah ka yafe min. Hannuwanta ya kama zai tayar da ita zaune taki tashi. Bazan tashi ba sai ka fada da bakinka ka yafe min. Na janyo maka auren da mu duka bamu shirya masa ba sannan itama yarinyar na dauki alhakinta. Kukanta har ransa yake ji. Tayar da ita tsaye yayi ya rungumeta yana rarrashi. Komai ya wuce Izzy tunda kin gane kuskurenki. Kissing dinta ya soma saboda shi kanshi ba karamin missing dinta yayi na. Wani dadi taji yana ratsata ta biye masa. Sun jima a haka kafin tace Hamza dear ina zuwa. Sai da tayi da gaske ya saketa ta fita. Dakin Zuhra taje, lokacin Zuhra tana waya da Hajara suna ta hira kamar bata da wata damuwa. Ganin Izzatu a bakin kofa yasa tayi saurin sallama da Hajara. Da fara'arta kamar Izzatun da ta fara sani tace kizo zamuyi magana a dakin Hamza. I hope ban takura miki ba? Zuhra kallonta take da mamaki ga wata irin riga da ta saka. A ranta tace wasu matan dai basu da kamun kai. Yanzu meye na shigo min daki tsirara. Mayafinta ta dauko ta yafa tabi bayanta. Suna zuwa Izzatu bata daukeshi komai ba ta fada jikin Hamza wanda yake sanye da wandon bacci kawai. Dorawa yayi daga inda suka tsaya. Zuhra tayi saurin runtse ido ta juya baya tace wayyo na shiga uku iskan...... Hamza na ganinta yayi saurin ture Izzatu tare da yi mata tsawa. Idan kika kuskura kika ce iskanci sai na dalle miki baki. Kina hauka ne zaki shigo mana daki babu sallama. Izzatu ta sake rike shi ni na kirawota baby. Rigarsa ya dauka ya saka gaba a baya saboda kunyar da yaji Zuhra ta ganshi a haka. Sabon raini zai shigo kenan. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿36 Batul Mamman(Mrs)💖 Bakin kofar Izzatu taje ta riko hannun Zuhra suka shigo cikin dakin. A gefen gado ta zaunar da ita, mugun kallon da Hamza ya watsa mata yasa tayi saurin zamewa kasa, dama a darare ta zauna. Wasu yan siraran hawaye Izzatu ta soma yi tace Zuhra don Allah ki yafeni. I played a cruel joke on you. Zuhra tace eyye...play kuma? Kawar da kai Hamza yayi yayi dan murmushi. Yana ganin da kyar idan Zuhra ta fahimci abinda Izzatu ta fada saboda yadda ta soma yaken karfi da yaji. Izzatu ta cigaba da magana, nasan ban kyauta ba amma don Allah ki yafe min. Babu komai Zuhra tace idanunta na cikowa da kwalla. Ta dai yafe amma bata jin zata taba manta irin dariyar da Izzatu tayi mata a gaban mutane. Tashi ma tayi zata koma nata dakin Izzatu ta dan taba Hamza, baka bata hakuri ba. Ni kuma??? A wani dalili? Dan marairaicewa Izzatu tayi, shi kuma yana kallon Zuhra da ta tsare shi da ido. Dena kallona ya fada yana harararta. Kanta ta sunkuyar dama tasan bazai bata hakurin ba. Izzatu dai da fara'arta tace ni na baki hakuri a madadinsa. Kai Zuhra ta gyada kawai, Izzatu tace to tunda kin hakura ina fata zaki amince ya SAKE ki. Ta juya ga Hamza, daga shi har Zuhra kallon mamaki suke mata. Zuhra tace dama abinda kike so kenan shine kika rinka yi min kirki dazu? Duk abin Izzatu sai da taji kunya. Hannuwan Zuhra ta rike, nasan kema auren nan dole ake yi miki kamar yadda aka yi mana. Ki amince ya sakeki ki koma gida ki auri miji daidai da ke wanda zai so ki. Nasan idan da bakinki kika fadawa Alhaji ke kika nemi sakin bazai ga laifin Sweetyna ba. Sai ta kalli Hamza ta kalli Zuhra duk tunani suke yi. Dan gyaran murya Hamza yayi duka suka mayar da hankulansu gareshi. Idan kin amince da sakin bazan sake ki yanzu ba sai nan da kamar wata shida ko shekara daya saboda Alhaji bazai taba yarda ke kika nema ba. Izzatu ta bata fuska habaaaa Hamza, wata shida is too long. Hankalinsa yana ga Zuhra yana karantar yanayinta saboda ta zurfafa a tunani. Zaman gidan nan ba nata bane saboda babu mai kaunarta. Itama kuma ba son mijin take ba, son kyautatawa iyayenta da nunawa Izzatu kurenta yasa tun farko ta amince. To yanzu idan aka saketa yaya Baba da Umma zasu ji? Waye zai yarda ya aureta idan aka ji aurenta ya mutu bayan wata shida. A sanyaye ta dago kanta suka hada ido da Hamza, saurin kawar da kanta tayi kamar ba itace mai tsare mutane da ido ba. Na yarda amma don Allah kada ku bata min suna idan anyi sakin saboda iyayena....hawaye ne suka zubo mata tayi saurin rufe fuskarta da mayafinta ta fita. Tana jiyo ihun murnar Izzatu ta sake danewa jikin Hamza. Shima duk jikinsa yayi sanyi don baiyi tunanin zata amince da wuri haka ba. Dole ya sami dalilin da zai fadawa iyayensu yadda baza'a ga laifin kowa cikinsu ba. Izzatu yaji tana kokarin cire masa riga yasa hannu biyu ya rike abarsa. Meye haka? Dazu kinzo kinyi hugging dina a gaban yarinya. To meye ta fada tana jan rigarsa. Ai tasan abinda yafi haka ma munayi. Tana dariya tace Baby we need to celebrate bari na samo mana juice mai sanyi da cups muyi toasting. Duk da wata shida is a long time amma ba komai. Fita ta sake yi ta barshi yana tunani. Kamata yayi ya yi murna da amincewar Zuhra sai dai a kasan zuciyarsa yasan abinda suke niyar yi bai kamata ba. Ba jimawa ta dawo da apple juice a wata roba mai kyau ta tsiyaya musu a glass cups. Hamza zai kai nashi baki ta rike hannun, I said lets toast ta kashe masa ido. Tare suka dan buga cups din suka yi yar kara. Izzatu tace TO FREEDOM. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿37 Batul Mamman(Mrs)💖 Kwanaki biyu a tsakani Zuhra na zaune a falo don yanzu Izzatu tace ta rinka zama tana sakewa. Hatta su Khalifa tana bari su zauna da ita. Wurin karfe biyar na yamma Hamza ya shigo maigadi ya biyo shi da ledoji. Kofar inda ya kamata ya zama kitchen din Zuhra yace ya ajiye masa. Su Junior da Izzatu suna ta yi masa sannu da zuwa Zuhra ta mayar da idanunta ga kallon tv. Ita yanzu da tasan matsayinta a gidan tana ganin yi masa sannu da zuwa kamar shishshigi ne. Shima a nasa bangaren bai kulata ba suka tafi dakinsa shi da Izzatu. Ba jimawa ya fito da shirt mara nauyi da dogon wando, da gani wanka yayi. Abinci ya zauna ci suna ta hira da Izzatu. Sai da ya gama ya tashi ya bude kitchen din Zuhra sannan yace ke zo. Da farko tayi niyar sharewa sai Izzatu tace mata jeki mana Zuhra kayan miya ya siyo miki. A hankali take tafiyar har sai da yaji haushi. Ya nuna mata kayan da hannu alamun ta dauko. Wato kace na dauka da bakinka ne kake ganin asara....Allah Ya sauwake ta fada a ranta. Dauka tayi gabadaya hudun ta shigar dasu kitchen din. Kallon mamakin da yayi mata yasa ta tuna maganarsu dasu Anas da suka ce mata maza basa son mata masu karfi. Sai kuma ta tunawa kanta ai Hamza ba mijin da zasu so juna bane. Kwalin gas cooker dinta ya farke ya sake fita. Bai dade ba ya shigo dauke da karamar cylinder. Daga can gefe ya ajiyeta sannan ya hada mata gas din. Ya koma kan fridge din shima dan madaidaici ya jona mata. Ita dai tana gefe tana binsa da ido. Sai da ya gama tsaf yace ga kayan miya nan da nama sai ki saka a fridge kada su lalace. Daga yau ki rinka dafa iya abincin da zaki ci. Idan akwai abinda babu a cikin kayanki sai ki fada a siyo. Tsananin farinciki da taji yasa ta washe baki da gaske kake don Allah....daure fuska yayi, na taba wasa dake ne? Nagode, nagode, nagode ta rinka fada tana bude ledojin. Ji tayi yace kuma ki kula kada ki bata wurin nan kinga tun asali ba kitchen bane. Ya nuna mata sink shi kadai zan iya sawa idan kin tafi sai a cire amma bazan miki wani kitchen kabinet ba. Duk da haka ma nagode ta fada cike da murna. Yau zata dafa abinci son ranta taci ta koshi. Hango kanta take da kwano ba ma plate ba shake da abinci. Wannan irin farinciki da take yi yasa shi jindadi. Ko ba komai yana ganin ya tsira daga laifin tauye mata hakki a ganinsa. Zuhra tana susar kai tace uhmmm....yes ya amsa don yasan akwai abinda take son fada. Dama...dama... gajiya yayi da inda indarta yace dama me? Uhmm nace shi gas din ya zan rinka kunnawa? Au dama baki iya kunnawa ba aka kawo ki dashi. Turo masa baki tayi to mu a gida ba da itace muke yi ba ko risho. Ganin ya daga hannu tasan a bakinta zai sauke shi tayi saurin ja da baya. Nufi na fa ban saba dashi ba amma cikin kayana akwai risho din sai na fito dashi. Hannu ya daga yana nunata, ki fito da me? Wallahi kada kuskura ki kunna min risho a wurin nan in ba so kike ki sake min sabon fenti ba. Kinji ko! Gyada kai ta rinka yi kamar kadangaruwa da taji ya fara daga murya. Sai kuma yace matso ki gani..kunnawa yayi sannan ya gwada ragewa da kashewa duk tana gani. Idan kin kasa ki kira Tala ta nuna miki don naga alama kin fita kauyanci. Ni ba yar kauye bace ta fada tana kara turo bakin nan nata. Biyota Hamza yayi zaiyi maganin rashin kunya ta juya da gudu. A bakin kofa suka ga Izzatu tana dariya. Ai tunda naji kana daga murya nasan kun fara fada shine nazo kallo. Ta kalli Zuhra bai dake ba ko...babu wanda ya bata amsa ta cigaba da dariyarta ta kama hannun Hamza suka fita. Tuwo Zuhra tayi niyar yi Izzatu tace kada tayi girki an riga anyi abincin dare da ita. Har ranta bata ji dadi ba amma haka ta daure taci abincin. Inuwa sakatare yana ta hada wasu files zai kaiwa Hamza saboda meeting din da zasu yi sai gashi ya fito daga office dinsa rike da waya da makullin mota. Inuwa yace ranka ya dade fita zaka yi ne? Akwai meeting fa biyu da rabi. Ba jimawa zanyi ba Inuwa in sha Allah. Zanje banki ne tun friday kaga yau alhamis banji alert ba na kudin da ka ciro. Inuwa yace to Allah Ya kiyaye adawo lafiya. Amma ranka ya dade yaushe Oscar yace zai dawo ne muna bukatar sa hannunsa a wasu takardu. Hamza yace nima duk na damu ko jikin mahaifiyar tasa ne sai dai ban same shi a waya ba. Bari nayi sauri na dawo sai muyi maganar dai. Koda ya fita jikin Inuwa sakatare yayi sanyi....Allah Yasa abinda zuciyarsa take kitsa masa ba gaskiya bane. Manyan architects yau da kanka a office dina. Manaja ke magana yana tashi tsaye suka gaisa da Hamza. Kowa fuskarsa dauke da murmushi suka tambayi juna iyali. Manaja yace sai kuma naji kayi aure ba labari. Kai Hamza ya dan sosa yana tunanin yadda zance ke yawo a gari..kayi hakuri abin ne yazo a gaggauce. Babu komai Allah Ya sanya alkhairi. Yanzu dai how can I help you? Tashi Hamza yayi kada ka damu shigowa nayi mu gaisa na riga na sanar dasu a costumer care alert ne bana ji tun last friday. Kuma har a atm da na cire kudi still banji ba. Manaja yayi dariya ai dole ka damu ku masu harka da manyan kudi. Suna magana text ya shigowa Hamza. Yayi murmushi dadina da bankin nan saurin gyara abu. Gashi har alerts din sun shigo. Yanayin fuskarsa ne ya soma canjawa a take. Manaja ya naga alert na an cire ten million har sau biyu a ranar friday din? Manaja ma dena murmushi yayi ai sau biyun ne Architect. Ka turo sakatare dinka sannan ga mamakina ka turo wani Mr..Mr....mtsw na manta sunan amma dai na kira nayi confirming a wurinka kafin a sakar masa kudin. Jiri ne ya soma dibar Hamza daga tsaye yayi saurin dafa tebur din manaja ya zauna. Da kyar ya iya cewa Mr Oscar? Eh shi kuwa manajan ya amsa. Ka tuna na kira na tambayeka kace eh kaine ka turo shi. Tabbas manaja ya kira amma a lokacin Izzatu ke faman daga murya tana masifa sai ya saki Zuhra baiji abinda manajan yace ba ya amsa masa. Wato shiyasa Oscar yace mamansa ba lafiya ya tafi garinsu gashi an kusa sati babu mai samunsa a waya. Allahumma ajirni fi musibati wa akhlufni khairan minha. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿38 Batul Mamman(Mrs)💖 A rikice manaja ya fara tambayar Hamza ko sunyi kuskure ne. Numfashin Hamza da kyar yake fita ya dago idanunsa da suka yi nauyi lokaci guda yace babu abinda kayi manaja. Matsalar daga bangarena ne. Sau biyu yana yunkurin tashi amma kafafunsa sun kasa daukarsa. Manajan sai bashi baki yake yana rokonsa ya zauna har zuciyarsa ta daidaita amma sam yaki zama. Ko da ya shiga mota rasa wurin zuwa yayi. Gidansa zai tafi ko office zai koma. Yafi rabin awa a motar kafin ya tayar ya dauki hanya. Lokacin da ya shiga gidan babu kowa sai Kande mai aikinsu. Da fara'arta ta tare shi tana masa sannu da zuwa. Jikinsa duk a sanyaye yake yace ina mutan gidan ne naji shiru. Nura yana daki su Adabiyya kuma sun tafi makatanta. Hajiya da Mama kuma sunje unguwa. To din ma da kyar ya iya fada sai ya tashi ya tafi dakin Hajiya. Babu abinda yake a lokacin kamar yaga mahaifiyasa. Yaji dadi a bude ta barshi kamar tasan zai zo. Gadonta ya nufa ya kwanta abinda ya dade baiyi ba. Yana rufe ido sai wasu zafafan hawaye suka sauko masa. Ji yake kamar komai nashi ya tsaya cak. Cheque din da Mr Oscar ya dauka hade da sauran da suke office dinsa idan an hada miliyan arbain kenan zai hada ya bawa su Mr Peter ya kawo karshen contract dinsu. A dalilin hada wannan kudin gabadaya maaikatansa suka amince da karban rabin albashinsu a wannan watan don kawai su tseratar da kamfanin. Yanzu gashi miliyan goma ta tafi a kudin bai san ta ina zai samu su ba. Ginin gidansa yaci kudi ba na wasa ba. Idan kuma ya tattara kudaden account dinsa tare da sayar da filayensa zai iya biyan kudin to amma rike iyalinsa zai zama da matsala domin kuwa akalla kafin kudin ayyukan da yake su fito zai dan dauki lokaci. Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi. Hajiya ta kira Mama ko sun taho daukarta daga tata unguwar Mama tace tun dazu nake kiranki ban samu ba. Gamu a garejin makanike ban je inda zani ba. Amma na fasa ana gamawa zamu biyo. Hajiya tace babu komai bari na bi adaidaita sahu kaina ke ciwo. To ki kira Nura mana yazo ya dauke ki. Hajiya tace babu komai shima yau da mura ya tashi. Sai kun dawo ni zan wuce gida. Tana gama wayar suka yi sallama da kawarta da taje dubawa ta fita ta hau adaidaita sahu. Gabanta yayi mummunan faduwa ganin mutum a kwance a kan gadonta. Alhaji yana Kumo kuma ko shine da wuya ya kwanta a dakinta. Nura kuma sai da ta leka dakinsa ta dubashi sannan ta taho nata. Babu inda baya rawa a jikinta ta ja kafa ta je gefen gadon inda zata ga fuskar mai baccin. Sai da ta dan ja baya saboda wanda bata taba tsammani ba ta gani. A tsorace tace Yaya....shima kansa ke masifar ciwo ya bude idanunsa da kyar. Hawaye ne bushe a fuskarshi Hajiya ta matsa ta taba shi. Bakinta har rawa yake saboda tsoron abinda zai ce tace Yaya me ya faru? Tashi yayi ya gyara rigarsa da ta yamutse sannan ya mayar da hularsa. Yana dan murmushi yace Hajiya babu komai. Zuwa nayi mu gaisa duk bakwa gidan. Bari na koma office sai anjima. Hannunsa ta rike. Itama hawayen take yi....haba Yaya duk duniya idan akwai wanda zaka boyewa damuwarka kasan banda ni ko. Bar ganin ban fiye shiga harkarka ba duk yanayin da ka shiga nakan gane na farinciki ne ko akasinsa. Dawowa yayi yasa mata kuka kamar karamin yaro. Kai bakace Hamza bane dan shekara talatin da takwas mijin Izzatu da Zuhra. Akan kujera ta zauna tana rike da hannunsa ya zauna a gabanta. Kansa ta dora akan cinyarta yayi kukansa mai isarsa. Rabonsa da yi mata irin kukan nan tun ranar da zai tafi Canada. Duk ranar da yayi irinsa to ba karamar damuwa yake ciki ba. Babu wanda yasan yana yi sai ita mahaifiyarsa. Cike da tausayawa irin ta uwa ta rinka shafa kansa har yayi shiru. Ko da ya dago kansa murmushi ne a fuskarsa yace Hajiya na dade banyi miki kuka ba ko. Yau ma sha'awarsa nayi shine na taso daga office. Bari na koma ana jirana meeting karfe biyu da rabi. Lokacin biyu saura kwata. Tunaninsa bai wuce yadda ya mori kudinsa ba lokacin da yake dasu shi kadai. Sai da matsala ta tashi zaizo ya tayarwa da mahaifiyarsa rai. Ya santa bata da magana sosai, ba lallai ko Alhaji ta fadawa amma zata shiga damuwa. Hajiya tace tunda baka son fada min damuwarka zan tayaka addua kamar kullum. Allah Ya kawo sauki cikin dukkan al'amuranka. Ka yawaita ambaton Allah hakan yana yaye damuwa da bacin rai, sannan kayi kokarin sauke hakkin wadanda ke kanka Allah Yayi maka albarka. Wani hawayen ne ya sauko masa yayi saurin gogewa. Amin Hajiya nagode. Tana kallo ya fita ta shiga toilet tayi alwala. Tasan da kansa zaizo ya fada mata matsalar amma abinda yafi dacewa yanzu tayi zata masa. Addua ta dukufa yi masa sannan ta saka dukkan kannensa da iyalansu. Waya yayiwa Inuwa meeting sai gobe baya jindadin jikinsa. Tunani ne fal a zuciyarsa. Sai yanzu yake tunawa cewa Allah SWT Ya na jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama. A irin rayuwar sakaci da addini da yayi ai dole watarana ya fuskanci irin wannan. Sai yanzu ya sake nadamar abubuwan da yayi a baya da wanda yake kanyi yanzu wato sake da hakkokin matarsa don a zahiri suna damunsa. Sonta kawai baya yi. Zaiyi kokarin kyautata alakarsa da Mahaliccinsa da sauran mutane. Itama Zuhra zaiyi kokari ya sake da ita zuwa lokacin da zai saketa. Tunda basa son juna rabuwar ce zata fi. ta yadda bazai cigaba da daukan hakkinta ba. Zai bari sai komai ya lafa masa a wurin aiki sai ya sanar da Alhaji zai saketa saboda gudun kada Allah Ya kamashi. A lokaci daya duk sai ya zama abin tausayi. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿39 Batul Mamman(Mrs)💖 Karo na biyar kenan da Zuhra ke dandana ruwan miyarta. Yawunta duk ya tsinke saboda yadda kamshin daddawa ke tashi. Nana na biye da ita a kitchen din har ta gama. Tuwon shinkafa tayi malmala biyar yadda zai isheta taci da rana, da daddare sannan ta sami na dumame da safe. Plate ta dauko mai dan fadi da zurfi ta saka malmalar da tafi kowacce girma da miyar kukarta duk a hade. Manshanu kadan ta zuba ta goya Nana a bayanta ba zani ta dauki plate din da hannu biyu ta tafi falo. Tana tafiya tana cewa Nana rike wuyana sosai fa. Ita kuwa Nana sai murna take tace toh. Sai da ta shimfida tabarma kusa ta dinning table sannan ta zauna cin tuwo. Loma take kaiwa kamar za'a kwace. Tana ci tana bawa Nana a baki. Sun kusa cin rabi Izzatu ta sauko...idanunta kan Zuhra tana bawa yarta tuwo a baki. Har da nan gudunta tayi saurin zuwa inda suke ta dauke Nana tana ta warin kuka da daddawa. Zuhra ya zaki bata abincinki ke da aka ce ki dafa naki ke kadai? Ni ban saba bata abinci da hannu ba kuma bama tuwo sosai saboda yayi mata nauyi. Bata nuna jin haushi ba tace kiyi hakuri ban sani ba. Ganin Izzatu tayi hanyar kitchen yasa Nana ihu tana cewa Mummy sauketa, sauketa abinci. Izzatu tace naji yunwa kike ji bari na wanke miki baki na zuba miki couscous. Bata ankara ba Nana ta galla mata cizo a kafada. Ba shiri ta sauketa tana sosa wurin. Ita kuwa da gudu ta koma gaban kwanon Zuhra. Hannu biyu tasa tana ci bata jira Zuhra ta bata ba. Sake komawa Izzatu tayi zata dauketa sai taji muryar Hamza yana sallama. Yana shigowa Zuhra ta kai wata shirgegiyar loma bakinta. Ido suka hada ai kuwa ta kware saboda kunya. Ji yayi nauyin zuciyarsa ya ragu saboda yadda yaga tana cin tuwon cike da nishadi. Izzatu tace sweety kaga rigimar Nana wai sai taci abincin Zuhra. To ki kyaleta mana ya fada tare da wucewa sama. Ita kanta Zuhra tayi mamakin amsarsa. Bayansa Izzatu tabi tana masa sannu da zuwa. Zuhra ji tayi jikinta yayi sanyi saboda yanayin da taga Hamza. Da gani yana cikin damuwa Allah Yasa ba wani laifin tayi masa ba. Plate din tuwo kuwa sai da suka sude shi tas ita da yarta Nana sannan aka tashi aka wanke hannu. Bayan yayi wanka Izzatu ke tambayarsa ya aiki. A hankali yake magana yace Alhamdulillah. Tana zaune akan kujera tana masa kallon tuhuma tace Hamza ko ka fara sonta ne? Bangane ba shima a zaunen yake don baya jin zai iya cin abinci. Banda damuwar da yake ciki hannun Zuhra yake hangowa miya na binsa ta gefe tana kai lomar tuwo. Yarinyar ta fiye kazanta. Izzatu ta dan sha kunu Zuhra nake nufi. Lokacin da ka shigo ita ka fara kallo kuma ka danyi murmushi. Izzatu kenan,yanzu baki bani komai nasa a baki ba kike tuhumata. To idan naso ta laifi ne? Matata ce fa. Sosai ta daure fuska bana so, Hamza bana son irin wannan wasan. Nan da wata shida zata koma gidan iyayenta mu cigaba da zamanmu yadda muka saba. Daga nan sai kuma ta soma murmushi baka ga yadda take cin abinci ba dazu. Baka ce dan bakin nan tana zai dauki abinda take tura masa ba. Idan ka fita yau pizza zaka siyo mana Baby a matsayin dinner. Ko sau daya bata damu da rashin walwalarsa ba. Hmmm kina bani mamaki Izzy...me kuma nayi Babyna? Murmushi take masa tana kashe ido. Fada mata ma bata lokaci ne don karshenta ta fadi abinda zai kara bata masa rai. Babu komai bari na dan kwanta kaina na ciwo. Tashi tayi to bari na kawo maka magani. Amma kafin nan ga wannan....ta dauko cards har kala hudu na biki. Ni duk matsalar Zuhra yasa na manta next week za'a fara bikin Mardiya cousin dina ta kaduna. Yar Uncle Jibril kanin Dad dinmu. Wai matar da miji ya fadawa yana ciwon kai kenan. Ga naka na daurin aure, ni a son raina ranar saturday na tafi kadunan saboda muna da shirye shirye a gabanmu. Kasan dani suka dogara tunda na zauna a Canada suna son ayi abin da tsari sosai. Kije Allah Ya kiyaye hanya ya fada a takaice....bargo yaja ya rufa har kansa. Bashi da kwarin yi mata fada ko fada mata abinda ya kamata. Sai da ta gama yi masa lissafin kudin da take bukata sannan ta dauko masa magani da ruwa. Sai la'asar ya tashi jikinsa ya danyi kwari sannan kan ya dena ciwo. Masallacin kusa da gidansa yaje yayi sallah ya dawo yaci abinci. Yana gama cin abincin ya dauki key din mota....Izzy ni zan fita ki fadawa yarinyar nan kada tayi abincin dare zan taho muku da pizza din in sha Allah. Duk maganar a sanyaye yake yinta, wani salihanci yake ji tunda Oscar ya dibga masa sata. Tace harda Zuhra kuma? Ba kayi mata siyayyar kayan abinci ba. Yace nasan nayi amma as long as tana gidan nan zanyi kokarin sauke nauyinta. Tabe baki Izzatu tayi to shikenan sai ka dawo. Har bakin mota ta rakashi ya tafi gidansu. Nan ya zauna suka sha hira da kannensa kamar bashi ba. Hajiya taji dadin ganin ya sake ba kamar dazu ba. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿41 Batul Mamman(Mrs)💖 Washegari meeting din gaggawa ya kira da dukkan maaikatansa. A nan yake sanar dasu abinda Mr Oscar yayi. Inuwa sakatare yace shi yayi mamaki da ya ganshi a banki amma tunda manaja yace da yardar Hamza aka saki kudin shiyasa bai tayar da zancen ba. Maaikatan suka tambayi Hamza garin yaya haka ta faru yace matsalace ta taso daga gida a lokacin. Yana kujerar tsakaya a conference room din yadda kowa zai iya ganinshi a katon zagayayyen table dinsu yace kada ku damu in sha Allah bazan bari kwazonku ya tashi a banza ba. Sauran cheques din ya nuna musu Allah Yasa na rarraba da guda daya ne Oscar ya dauka ba karamar matsala zamu shiga ba. In Allah Ya yarda zan san yadda nayi na fito da wata miliyan goman da zamu hada musu. Next zuwan Mr Peter kasar nan zamu hada musu kudinsu. Ayyukan gabanmu kuma kunga manyan projects ne. Ina rokon kuwa dage ayi ingantaccen aiki. Sannan ina neman afuwarku na kasancewata shugaba mai sakaci da aiki. Muryoyi ne suka rinka tashi suna fada masa babu komai. Wani yace yallabai irin haka shine yake sa bawa ya kara jajicewa da imani. Ba karamin dadi yaji ba da yadda suka yi masa uzuri. Bayan sun gama tattaunawa addua suka yi aka rufe taron. Shima sai ya sake samun kwarin gwiwa tare da yiwa kansa alkawarin bazai sake basu kunya ba. Kafin ya koma Izzatu ta gama hada duk kayan da zata bukata na tafiyar. Idan ta tafi sai lahadi ta sama zata dawo. Sannan ta sanar da Zuhra zatayi tafiya. Tala ma ta hada nata kayan dana yara. Suna zaune a falo daga Zuhra sai Izzatu tace idan mun tafi basai kinyi girki da Sweetyna ba. Zai rinka siyan abincinsa, da zaki yarda ma kawai ki tafi gidanku ki kwana biyu kafin na dawo. Zuhra tace a ranta lallai Izzatun nan ma, daga aure sai tafiya gida a kwana? Wannan ai sai mutane su gane lallai auren babu lafiya. Izzatu tace kinyi shiru ko ba kya son zuwa gida. Nasan dole zaki fi jindadi da sakewa a nan to amma....Zuhra taji haushin maganar tace ba haka bane, su Baba zasu yi tunanin ko akwai matsala. Kinga idan akayi sakin laifinsa zasu gani. Izzatu tayi dan tunani eh haka ne fa. To ki zauna amma ko da wasa kada ki shiga harkarsa nasan shima bazai shiga taki ba don ba sonki yake ba. Murmushi Zuhra tayi tana jin yadda Izzatu ke fada mata bakaken maganganu. Dubu dari Hamza ya bawa Izzatu kafin su kwanta. Tayi murna amma fuskarta ta nuna ba haka taso ba. Yana daga kwance yace ya akayi ne? Juya kudin take yi a hannu babu komai, nayi tunanin zaka karamin ne saboda yara. Ga Tala zan tafi da ita don ta kula dasu. Tashi yayi zaune ba shiri, da Tala zaki tafi amma baki fada min ba? Tunaninsa bai wuce zaman da zaiyi da Zuhra shi kadai ba na kwana takwas. Izzatu tace da bakinka kace ko unguwa zani na dade na rinka tafiya da ita. To zan sami karin kudin? No, yace tare da sake kwanciya. Bani dasu. Idan kin dawo akwai maganar da nake so muyi. Ta tashi ta saka kudin a jaka. Indai ba Zuhra ka fara so ba ko meye babu damuwa. Hamza ya girgiza kansa kawai ya kwanta, halin Izzatu sai ita. Wato gara duk abinda zai faru ya faru akan ta zauna da kishiya. Washegari da wuri suka shirya kafin goma duk kayansu suna mota. Suna gama breakfast dreban da yake kai su Khalifa makaranta ya iso. Tare zasu tafi ya dawo a motar haya ya barwa Izzatu motar. Idan sun tashi dawowa ya koma ya dauko su. Har bakin mota Zuhra ta rako su. Hamza ya rungume 'ya'yansa sannan suka wani manne da juna shi da Izzatu ana kiss a gaban mutane. Kunya duk ta ishe Zuhra. Ita kuwa Tala dama ta saba gani. Nan suka tsaya har motar ta fita maigadi ya rufe gate. Ajiyar zuciya Zuhra tayi tana tausayawa kanta yadda zata zauna ita kadai a gidan. Kasancewar Hamza ba tafiya zaiyi ba bai dameta ba tunda ba harkar juna suke shiga ba. Ciki ta koma zata tafi dakinta Hamza ya shigo yace ki shirya bayan azahar zamu fita. A sanyaye ta dan juyo gida zaka mayar dani? Na fada mata zan zauna a nan saboda kada a zargi wani abu a gida. Hamza yace Izzatu tace ki koma gida ne? Wai ita zai nunawa bai sani ba. Tace eh jiya ta fada min. Dan guntun tsaki yayi. Izzy ta fiye rigima itama. Ki shirya zamu je ki gaisa dasu Baba sannan muje gidanmu. Wani tsalle tayi da yasa ya matsa gefe kada ta bige shi. Alhamdulillah ta fada ta haye sama cike da murna. Wani lokacin sai ya ganta kamar mai hankali, idan abin ya motsa kuma ba kanta. Daga murya yayi yace idan na dawo daga masallaci baki shirya ba an fasa. A hankali tace zaka sha mamaki. Ai kuwa yasha mamakin domin yana dawowa daga masallacin ya ganta zaune kwam a falo ta gama shirinta. Tuna masa tayi da ranar da ya fara ganinta har ya kusa bigeta da mota. Duk zafin da ake a gari fuskarta sai kyallin foundation take. Tabi girarta da pink din jagira ta gyarata, da yake kayan jikinta akwai green sosai har mayafin haka ta saka green din eyeshadow. Sai yan labbanta da ta zanawa bakin lining sannan ta saka jan janbaki da ya fito sosai. Abin bai bashi dariya ba ma, wannan wace irin kwalliya ce. Mtswwww Da taji yayi tsaki ga wani kallo da yake binta dashi sai jikinta yayi sanyi. Shi dama bai ma gama shiri ba don jallabiyace a jikinsa. Muje yace da ita yana shirin hawa bene. A tsorace tace ina???? Sama ya nuna mata da hannu. Kawai gani yayi ta durkusa gwiwoyi a kasa idanunta sun ciko da hawaye don Allah kada mu fasa zuwa. Don Allah ka kaini naga Ummana da Babana. Yayi yar dariya au gorin iyaye zaki min? Girgiza kai tayi da sauri a'a Ummanmu da Babanmu nake nufi. Yace to naji tashi muje yana murmushi. Da gaske sama taga zai hau sai ta dan ja baya. Hannunta kawai ya kama ya ja ta suka hau saman tana ta tirjewa. Wani abu yaji ya soki zuciyarsa da ya kama mata hannu. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿40 Batul Mamman(Mrs)💖 Takwas da rabi a gida tayi masa ya shigo da ledar pizza har hudu manya. Ya riga ya kudurce a ransa daga yau siyayyar abincin alhamis ta kare sai lokaci lokaci kuma. Itama Izzatu zai bata kudi taje bikin ta dawo sannan ya sanar da ita halin da yake ciki tunda bata tambaya da kanta ba. Ita da yara suna ta murna da ya dawo ta karba ta rarraba. Yanka biyu ta sakawa Zuhra a plate Hamza yace ta kara mata daya saboda big size ce. Tala ta kirawo ta kaiwa Zuhra daki saboda tun bayan magriba bata sauko ba. Tala ta fito daga kitchen hannunta duk kumfa tana gogewa da tsumma. Hamza ya mika hannu bari na kai mata saman zani. Plate din ta mika masa tana tambayarsa a ina zai ci tasa yace ta kai masa falonsa yau baya son hayaniya. Zuhra na kwance akan doguwar kujerarta tana kallon wani film din Hausa na marigayi Rabilu Musa dan ibro tana ta dariya. Tun daga bakin kofar dakin Hamza yake jin dariyarta. Yarinyar nan bata da kamun kai ya fada a ransa. Ji yadda take dariya kamar ba mace ba. Sallama yayi ta tashi da gudu ta dora hijab a jikinta. Plate din kawai ya mika mata zai fita sai yaji tace ina wuni? Tunawa tayi dazu tana cin tuwo bata gaishe shi ba. Jiya kuwa dama basu hadu ba. Da ya juyo ya amsa sai yaga plate din take karewa kallo. Ta dan kalle shi....shi kuma wannan menene? Pizza ce, baki taba ganinta bane? Tace eh, Allah Yasa da dadi dai. Sai da yayi murmushi sannan yace ci ki ji mana. Yanka daya ta dauko gashi da girma ta dan lankwasa shi biyu ta tura a baki ta gutsiri rabi. Sai da Hamza yasa hannu a bakinsa don mamaki....tabdi! Ke bakinki zai iya yagewa idan kina katuwar loma haka. Dan gayun nan na mata ma baki iya ba. Wani irin dandano taji da bata taba ji ba. Abin dai bazata iya kwatantashi ba. Bata san lokacin da ta furzar da na cikin bakinta ba, wanda bai sauka a ko'ina ba sai kafar Hamza. Wayyo Allah, Wayyo Allah, Wayyo Allah shine abinda yake ta nanatawa ya dage kafar tare da kawar da kansa gefe. Idan ya kalli kafarsa yasan dole ne yayi amai. Kamar yayi kuka saboda da takaici. Yana girgiza kai yace ke kuwa me nayi miki zaki tofa min abin baki. A tsorace ta dago kai zata bashi hakuri. Sauran ya gani a gefen bakinta da habarta. Dan danne fushin da yake yi ne ya gagara ya daka mata tsawa....Goge bakinki mana. Da hijab dinta tayi saurin gogewa sannan ta sake cewa kayi hakuri, shi kuwa sake hade fuska yayi yana ta yatsina hanci....kai so disgusting yace yana rike hanci. Irin kallon bangane ba tayi masa sannan tace SO kuma? Ni yaushe kaji nace so? Ba cewa nayi ina sonka ba hakuri nake baka. A wane dalilin zan ce ina sonka? Mamaki ta bashi ya rasa daga ina taji kalmar. Sai daga baya ya tuna yace SO DISGUSTING. Dariya sosai abin ya bashi, yace anya kin taba shiga aji kuwa? Sosai ma kuwa, har SS3 na kai a sakandire. Tana magana ta durkusa zata goge masa na kafar tasa da hannunta. Saurin jan kafar yayi tare da yin tsaki...kazama da hannu kuma zaki goge, ni bani tissue. Eyye me kace? Ya sake maimaimatawa. Dan murmushi tayi na ta gane zancen. Toli fefa kake nufi, wallahi bani da ita. Jin kafarsa yake kamar ya yanke ta yace to dauko min ta toilet dinki da sauri. Ya dan kalli kafar....Oh God I hate this. Gani yayi bata tafi ba ya dan daga murya nace ki dauko ta toilet kin tsaya kina kallona. Baya ta dan sake matsawa na fada maka babu. Iko sai Allah, yanzu ko a toilet babu? To da me kike amfani. Dariya ya bata ji wata irin tambaya.... tace da tawul mana, ni bansan ana goge jiki da toli fefa ba. Jin bata fahimce shi ba ya kara bashi haushi. Ni ba cewa nayi a goge jiki ba. Shiru yayi saboda kunyar abinda zai fada. Da kyar yace kafin kiyi tsarki nake nufi. Kanta ta dan juyar a kunyace tace tsarki da toli fefa kuma kamar wata arniya. Yarinyar nan duka take so...kwafa yayi sannan yace ke a kazantarki idan kin gama abinda kike a toilet hannu kike sawa? Shi kam Izzatu ta cuce shi da tayi sanadin auren nan. Gaskiya ke kazama ce ta karshe ya fada yana toshe hanci. Hanyar toilet dinta yabi zai wanke kafarsa sai wata zuciyar ta hanashi. Karshenta yaga wani kayan kazantar. Da jan kafa ya fita daga dakin ya tafi nasa. Ya shiga toilet ya sakarwa kafar ruwa. Sai da yaga babu komai a kafar sannan yayi wanka ya fito. Ita kuma Zuhra gyara wurin da abin pizzar ya bata tayi ta sauka da sauran a plate. Izzatu ta kaiwa suna cin nasu dasu Khalifa tace bazan iya cin wannan abin ba. Izzatu tayi dariya dama shi ya dage sai ya baki. Tana karba ta bude plate din da ta saka masa nasa ta kara da sauran biyun na Zuhra. Tana kallo Zuhra ta wuce kitchen dinta ta dumama tuwo ta haye sama zata ci. A bakin bene suka hadu yace mhmmm haka kika iya, ki cika kwano da tuwo. Bata amsa ba ta bashi wuri ya sauka. Izzatu ta biyoshi falonsa da nasa abincin. Biyun saman wanda aka yi da naman kaza ya cinye yace ya koshi. Izzatu tace kuma kai na ajiyewa mai beef(naman saniya) din don nasan shi kafi so. Ruwa ya dauka a cup yana sha tace ashe rabonka ne mai chicken din da Zuhra ta dawo dashi wai bata.......kwarewa yayi sosai tun kafin ta gama maganar ya soma kakarin amai. Idanunsa har ja suka yi saboda wahala yace yanzu Izzy ragowar yarinyar nan kika bani. Tace to meye ai bata ci ba, hannu tasa tana shafa masa baya. Sannu kaji my darling shiyasa ba'a son magana idan an cin abinci. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿43 Batul Mamman(Mrs)💖 Har suka isa gidan babu wanda yayi magana a motar. Ficewarsa ma yayi daga motar ya shiga gidan ya barta. Kwafa tayi sannan ta fito da ledarta a hannu. Hanyar da yabi itama ta bi. Sai ta ganshi a bakin kofa yana tsaye...kinji yadda naji dazu da kika fita baki jirani ba. Bude baki tayi....lahhh wai haushi kaji. Sai kuma yaji haushin kansa meye zai biye mata harda ramawa. Gyaran murya yayu shi a dole a bawa. Shige muje ya nuna mata hanya. Dakin Mama suka fara zuwa bata ciki. A hanyarsu ta zuwa dakin Hajiya suka hadu da Adabiyya. Wani ihu ta saki tare da kankame Zuhra. Oyoyo Anti Zuhra....Hamida naji ita ma ta fito daga dakinsu suna ta ihun murna Zuhra na murmushi. Hamza yace lallai yaran nan. Kirikiri kun nuna min bakwa son uwar 'ya'yana. Hamida tace to Yaya ai itama ba sonmu take ba. Tana fada ta shige daki da gudu don tasan muguntar dallin bakin da yake mata. Adabiyya ta gaishe shi sannan taja hannun Zuhra suka tafi kitchen. Hajiya na dora ruwan tuwo suna hira da Mama. Adabiyya na shiga Hajiya tace wato don kada kuyi aiki kunce zakuyi karatun jarabawa sai gashi kun cika mana gida da ihu. Adabiyya tana dariya ta turo Zuhra da ke makale jikin kofa kinga bakuwar da muka yi. Mama ta taso itama tana mata sannu da zuwa. Kasa Zuhra tayi duk ta gaishesu. Ina Yayan naku Mama ta tambayi Adabiyya. Yana wajen dakinku. Fita Mama tayi tace Adabiyya kaita dakinku zata fi sakewa ki kai mata abinci. Idon Zuhra na kan Hajiya tana bare albasa zata hada ruwan miya. Gabanta ta karasa a kunyace tace Hajiya kawo na yanka miki. Itama Hajiyan ta rasa dalilin da yasa taji kunyar Zuhra kamar yanzu Yaya ya fara aure. Barshi kuje daki da Adabiyya idan na gama zanzo mu sake gaisawa. Adabiyya ta gama hada cup da lemo a tray tace zo muje Antinmu. Zuhra ta mika hannu don Allah Hajiya ki kawo na tayaki. Me zaki dafa nayi miki? Na iya girki fa. Hajiya tayi murmushi tana kallon Zuhra. Mayafinta ta cire ta jefa saman kofar kitchen din. Adabiyya tace don Allah kizo muje idan kika sha ruwa sai mu dawo. Ki tayani zama a nan kawai muyi girki. Ta karbi albasar Hajiya kije ki huta. Sosai Hajiya taji dadi sai dai kuma girkin saboda Alhaji da zai dawo daga Kumo yau take yi. Amma yadda Zuhra ta langabe mata kai yasa ta hakura ta fada mata tuwon semovita zata yi da miyar danyar kubewa wadda tuni Hamida ta gurza. Tana fita Adabiyya tace gaskiya ina taya Yaya murna yanzu yayi aure. Zuhra bata ce komai ba sai dariya tace ta bata roba zata yi rude. Sai ga Hamida da littafi a hannu tace ayi hirar da ita. Sunso sa mata hannu tace ita dai su tayata zama. Komai ta nema zasu nuna mata haka tayi tuwonta wanda ya tuku sosai yayi kauri. A leda ta kulle sannan ta bar ruwan miyar wajen awa daya yana dahuwa wutar kasa kasa yadda Umma ke yi. Hamida tace ita kamshi ya dameta a kada miyar yau tuwo zata ci ba indomie ba. Suna ta barkwancinsu har ta gama hada miyar kitchen din yana ta kamshi. Mama da Hamza suna daki suna hira. Da suka gama yace zai fita sai bayan sallar isha zai dawo. Dakin Hajiya taje tace mu leka yarinyar nan ko? Hajiya tace tana kitchen da yan uwanta wai ita zata yi tuwon. Farincikin Mama bazai misaltu ba tace Hajiya kinga ikon Allah ko. Kina ganin Zuhra kinsan yarinya ce mai tarbiya. Hajiyan ma murmushi take, sai wani koda surika kike a gabana ko kunya babu. Bari nawa dan Nura yayi aure kisha mamaki. Haka suka sha hirarsu gwanin sha'awa har suka ji shigowar motar Alhaji. Ana magariba Hamida ta zuba musu tuwon a katon faranti. Suna ci yan matan na zuba mata santi. Ita duk kunyarsu take ji ta kasa sakin jiki taci sosai. Bayan sun gama Mama tace su rakata falon Alhaji ta gaishe shi. Tuna ranar da ta fara zuwa gidan tayi kunya ta kamata ta rufa katon mayafinta ko fuskarta baa gani. Tana durkusawa ta gaisheshi ya fara miko mata rafar kudi dubu goma. Tayi saurin daga kanta yayi mata murmushi wannan tukwicin ciyar da dan tsoho ne. Itama murmushin tayi Hamida tace Alhaji mun tayata fa. Yayi dariya kin tayata hira dai. Daga shi har Hajiya da Mama duk sun mata karba mai kyau suna ta yabon iya girkinta. Wannan kuwa a wurin Ummanta ta koya. Da zasu koma dakinsu Adabiyya ta dauko turaren ta mika masa gashi inji Baba. Allah Sarki mal Bashir harda wata wahala banda 'ya da ya bani. Ina fata babu wata matsala dai tsakaninki da Yaya da Izzatu. Tace babu komai nagode. Ledar kayan da Umma ta bata ta bawa Adabiyya ta kaiwa su Mama. Tasha addua sosai a wurinsu. Da Hamza ya dawo falon Alhaji yaje. Suna hira ya bude food flask din yaga akwai sauran tuwo a ciki. plate din Alhajin ya jawo ya zuba yaci harda karawa. Alhaji yace Kaltume kiyiwa danki magana ya bar min na dumame. Hamza na dariya yace yau tuwon yayi dadi amma ba jagwalgwalon su Adabiyya bane ko. Mama tace me ka mayar min da 'ya'ya ne. Don kasan matarka ce ta dafa kake mana santi. Cak ya tsaya da shan miyar da yake da cokali yana kallon Mama. Hajiya tace yau kowa yasan sabon hannu yayi mana girki sai yabonta ake yi. To Hamza, ga abinci da dadi ga kyankyamin Zuhra da yake. Amma dole ya yaba mata don ba karya ta iya girki. Da zasu tafi Mama atampa Super Exclusive ta bata mai kyau, Hajiya kuma ta bata dubu biyar. Sai godiya take musu kamar ta ari baki. Su Adabiyya suka yi mata alkawarin zuwa su kwana biyu da weekend don duk cikin satin zasu gama jarabawa. Adabiyya na level two Hamida na level one a jamia. Hamza sai mamakinsu yake basa son zuwa gidansa a iya saninsa. Ba karamin dadi taji ba yadda suka karbeta a gidan. Suna isa gida ya rufe ko'ina yace mata sai da safe. Yana son yaba mata yadda ta kyautatawa iyayensa amma wata zuciyar ta hana shi. Abinda su Hajiya suka bata ta nuna masa yace to Allah Ya saka da alkhairi. Kema an fada min abinda kika kai musu nagode. Taji dadin godiyar tasa ta tafi dakinta zuciyarta fes. Da sassafe ta farka ta gyara wake ta bawa maigadi ya kai mata markade. Haka kawai taji kosai take son yi. Waken ba dayawa ta hada ba tunda nata ne ita kadai amma tayi yadda maigadin zai samu don tana ta tunanin me yaci jiya da rana da kuma dare. Tafi kowa sanin yunwa ba dadi. Kunu ta dama da tsamiya ta dan saka lemon tsami sannan ta soya musu kosan. A dan karamin jug din roba ta zubawa maigadi nasa kunun sannan ta sami wata robar ta zuba masa kosai da yaji. Nata kuma ta kwashe daga mai ra barshi ya tsane kafin ta kaiwa maigadin. Tana juyowa taga Hamza har sai da taji tsoro. Ya gama shirinsa zai tafi wurin aiki. Gaisheshi tayi tace zan mikawa maigadi abinci. Hanya ya bata ta wuce ya tsaya yana kallon kosan. Yana jin yunwa amma bazai ce tayi abinci dashi ba duk da jiya yaci kuma ya yaba. Kamar ya fita daga kitchen din sai ya dawo bari yaci yaji ko ta iya kosan. Izzatu bata yi tace abincin talakawa ne. Daya ya jefa a baki yaji dadi harda dan kurbar kununta dake cikin kofi. Gaskiya da dadi, a hankali ya dawo ya dan leka falon yaga bata taho ba. Da sauri yazo ya dauki wani harda saka yajin da ke wata yar roba ya kuma sawa a baki duk da akwai zafi sannan ya dauki biyu a hannu. Ko taunawa bai fara ba Zuhra ta dawo tayi mamakin ganinsa a kitchen din tace ashe baka tafi ba. A ransa yace me zaisa ta dawo yanzu. Gimtse baki yayi yace uhmm. Kallon rashin yarda tayi masa ko akwai abinda kake so? Uhmm uhmm ya amsa bakin nan a rufe. Ya rasa yadda zaiyi da kosan bakinsa. Daukar plate tayi ta juye kosan ta dauki kofin kunun tace to adawo lafiya ta fice ta barshi a tsaye. Sai a lokacin ya saki numfashi sannan ya sami damar tauna da hadiye kosan bakinsa. Ficewa yayi ya shiga mota ya cinye sauran biyun sannan ya goge hannu ta tissue. A mudubin motar ya kalli kansa....Hamza kaji jiki, satar kosai a cikin gidanka. Murmushi yayi ya ja motarsa. [25/09 3:56 pm] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿42 Batul Mamman(Mrs)💖 Iyakar karfinta tasa tana neman kwace hannunta amma rikon da yayi mata ba na wasa bane. A haka ya jata suka je dakinsa ya dauko kwalin tissue sannan suka koma nata dakin. Iyakar tsurewa Zuhra ta gama don bata san abinda zaiyi mata ba sai magiya take yayi hakuri. Yana jinta ya share, sai da suka zo gaban dressing mirror dinta ya jawo stool din ya zaunar da ita. Numfashinta har wani sama sama yake don fargaba. Har tausayi ta bashi sai ya dan sassauta murya tare da daidaita fuskarsa da tata har suna jin numfashin juna...ke, rufe idonki. Ji tayi kamar zuciyarta zata ballo kirjinta ta fito, ba dai hada bakin da ya gama da Izzatu zaiyi da ita ba. Ita ko a litattafan hausa idan tana karantawa ta tsani ace anyi kiss. Turawa dai marasa kunya suyi abinsu amma ita duk yar kazantarta kyankyamin haden bakin nan take yi. Kokarin tashi tayi ya rike kafadunta ya sake zaunar da ita. Kawai sai ta saka masa kuka...don Allah kada kaci amanar matarka. Kamar yau ne zata dawo kuyi abinku. Tissue yake zarowa daga kwali yace me zamuyi? Kanta a kasa tace sumba mana. Bai san lokacin da ya soma dariya ba. Kece sumbar ai....ya nuna bakinta Allah Ya kiyaye nayi kissing wannan dan bakin. Ina miki kallon saliha ashe kema idonki ya bude kinsan kiss. Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta don kunya yasa hannu ya sauke su. Rufe ido nace. Ba musu ta rufe...tissue ya ninke ya soma goge mata girarta. Yana yi yana kallon yadda ta bata rai harda turo baki. Bai bar abinda yake ba yana yi yana kallonta. Ya gama da girar ya koma saman idanunta da lips dinta. Takaici duk ya isheta kwalliyar rabin awa an goge mata ita. Hannunta ya sake kamawa ya kaita kofar toilet. Jeki kisa sabulu ki wanke fuskarki. A tsiwace tace bayan duk ka goge min kwalliyata. Daga hannu yayi zai dalle mata baki ta tafi da sauri. Ke dawo ki ajiye mayafin kada ya jike. Kamar bata ji me yace ba sai da ya maimaita da dan fada fada. A hankali ta warware shi. Idanunsa a kanta, dole ta rufe jiki da katon mayafi irin wannan matsatsiyar riga. Doguwar riga ce mai kyau duk ta fito da surar Zuhra. Ta wuyan rigar kirjinta ya dan fito. Tana daga hannu ta ajiye ya hango hammatarta......fal gashi. Saurin kawar da kansa yayi. Yaso shagala da kallon jikinta sai gashin da ya gani ya dawo dashi. Gaskiya lamarin Zuhra akwai gyara. A inda ta barshi ta dawo ta same shi yace ta sake zama a kan stool din. Wani lotion mai kamshi yasa kadan a hannunsa saboda zafin gari ya shafa mata a fuska. Daga shi har ita wani yanayi suka shiga yadda yake shafa mata fuskar. Bayan ya gama ya dauko hoda ya shafa mata. Sai ya duba lip gloss light brown ya sa mata a baki. Har abin taje gira yasa ya kwantar mata da gashin girar sosai. Ita kanta sai taga tafi dazu kyau duk da tana son saka janbaki da eyeshadow. Kallonsa take yadda ya iya sarrafa kayan kwalliyar mata. Da ya gama mikewa yayi yana dan sosa bayansa da ya kage saboda ya jima a duke. Hararta yayi saura kice min dan daudu, kuma ko kice kinyi kyau bare kuma godiya. Murmushi tayi tace nagode. Shareta yayi ganin ta fara dariyar shakiyanci bari naje na shirya ki canja kayan nan kafin na fito ki saka mai zani. Wata atampa mai adon pink da fari ta saka wrapper skirt da riga. Duk Hajara ke kai musu dinki kuma sunyi sa'ar tela. Pink din mayafi ta saka da farin takalmi da yar jaka fara mai kyau. Sake kallon kanta tayi a mudubi tayi murmushi. Mutumin min nan yana da kirki idan yaso. Amma banda wayon ya tabani meye zai goge min fuska da kansa. Tana zancen zuci taji wani kamshin turare mai dadi. Hamza ne sanye da yadi ruwan madara mara nauyi. Ya gyara fuskarsa ya rage gemu da gashin baki. Sai ya kara haske da yi mata kyau. Shima kallonta yayi ta canja kayan yace better...Zuhra tace best. Ta dan daga gira...nima fa na iya turancin nan. Good, better, best waye bai iya ba. Dariya ta bashi ita kuwa ko a jikinta tabi bayansa suka fita. Da kansa ya bude mata gaban motar ta zauna ya rufe. Yana tayar da motar ya kunna AC, ko minti biyar basu yi da fara tafiya ba ta soma gyangyadi. Dan bugun kujerarta yayi, kinji sanyin AC ko, to idan kika yi min bacci jefar dake zanyi a titi na huta. Gyara zamanta tayi tace amma dai wasa kake yi ko? Gabansa yake kallo ki yi baccin sai mu gani wasa ne ko gaske. Waje ta koma kallo. Da shirun ya isheta tace Allah Sarki su Nana suna hanya ko. Kaduna babu nisa sosai tun dazu suka isa ya bata amsa. Daga nan motar tayi tsit ko rediyo bai kunna ba. Motar na shiga layinsu Zuhra yara suka fara binsu ana ga Zuhran baban yara. Hannu bibbiyu ta rinka daga musu. Har su Anas da Sani kowa ta gani sai ta daga hannu. Haka kawai Hamza sai abin bai masa dadi ba. Tana dagawa Munkaila mai shagon kusa da gidansu hannu Hamza yace kika kara daga hannu sai na dalle miki baki. A islamiyya ba'a koya muku kamun kai bane. Turo baki tayi to kuma sai ka hanani zumunci da mutane. Rai a bace ya juyo sai dai ko motar bata jira ya kashe ba ta fice da gudu. Umma na kwance a falo taji an fado mata a jiki. Tana kokarin tashi Zuhra ta soma kuka. Umma tace to meye haka kuma. zuciyarta cike take da farincikin ganin yarta. Baba da ke daki fitowa yayi da jin muryar Zuhra. Shima makale shi tayi tana kuka. Umma tace wai kukan na meye ne? Hamza ne ya shigo dauke da manyan ledoji guda biyu yace kukan shagwaba take yi Umma. Baba ya tarbe shi, har kasa ya durkusa ya gaishesu tare da ajiye ledojin a gaban Baba. Umma tace kai kuwa baka gajiya da wahala. Duk zuwa sai kayi dawainiya. Dan sunkuyar da kansa yayi albarkarku muke nema Umma. Zuhra mamaki tayi wai dama yana zuwa gidansu. Kawai sai taji ya kara girma a idonta. Zata yi kokarin dena yi masa rashin kunya. Hira sosai suka yi da Baba ita kuma suka shige daki da Umma. Duk dadi ya kama Umma taga kamar Zuhra ta nutsu. Zuhra tace sai bayan hutu zaki dauko Safara'u ne? Umma tace eh ance sun kusa fara jarabawa. Zuhra tace yace daga nan gidansu zamu je. To me zaki kaiwa surukan naki? Sai a lokacin tayi tunani ya kamata ace ta kai wani abu tunda yana yiwa nata iyayen. Umma bata jirata ba ta fita kitchen. Kayan kamshi da kayan kadin da kanwarta ta aiko mata da yawa ta zuba a leda ta bata. Da zasu tafi bayan sunyi sallar laasar Baba ya bata wani turare mai kyau yace ta kaiwa Alh Nasiru. [26/09 9:00 am] Inna👬👫: AL'ADUN WASU 🗿47 Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta tana tsoron kada naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa Hamza ya dawo daga masallaci ya sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake. Amma yau gabadaya kunyarsa take ji da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan tafasa na soya kada ya lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar tafi ta jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya ta nuna damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta, hakan bai hanashi tuno surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi kamar ana kallonta ta dan juya suka hada ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi. Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da kaninfari. Ta soya kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza na son kwai da albasa. A karamin plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread daya ta bawa maigadi ya siyo musu jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa da kayan tea. Kasa shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne. Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan doguwar kujera ya zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga mura tayi masa kamu sosai. Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta ajiye masa tray din a gabansa sannan ta koma ta dauko flask din. Kallon kayan yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace uhmm dama nasa citta da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa duk babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka kirji. To nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya bata sosai bata yi masa musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen. Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da jajjagen kayan miya tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa, attaruhu, karas da koren wake. Harda grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake komawa falon ko ya gama cin abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita da maigadi ba saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata nikan shinkafa. Talle maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar Zuhra yace to Hajiya nagode. Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a kan kujera tana sha don bazata iya cin kwai zalla ba. Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai yaji babu dadi. Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota tana sha shi kadai. Shiga yayi yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai yarda ba ya duba dustbin dinta ina ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa yace bakya jina ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika bawa maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora abincin rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura da abinda take so domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya kama suka koma falo...meyasa baki fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da lafiya kuma zan iya jira. Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu ba yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta kasa sakewa . Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya baki lada, kin nuna damuwa da rashin lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi. Amma daga yau ki rinka fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta koma aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan shinkafar sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar da ya gyara mata ranar da suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta ma suka sha turare mai kamshi. [26/09 3:26 pm] Sahura: [17:23, 26/09/2016] ‪+234 813 652 9082‬: AL'ADUN WASU 🗿45‬ Batul Mamman(Mrs)💖 Amma yarinyar nan bata da hankali. Rai a bace ya tashi ya zaki min haka? Don me bakiyi shawara dani ba kika fadawa maigadi kamar zamansa kike yi? Ni gidana babu aljanu. Dariya take kasa kasa, daga abin arziki sai kayi min fada. A take ta kwabe fuska tana shirin yin kuka....sau biyu suka ci min abinci. Wannan wace sabuwar rigimar ce kuma ya fada a zuci. Sannan ya dan rage murya ni kada kiyi min kuka. Kamar yace yi kukan kuwa hawaye ya wanke mata fuska. Sai dai bai sani ba hawayen dariyar da takeyi ne ta wayance kamar kuka take. Rannan sunci min kosai a kitchen sannan a gabanka ma suka ci min tuwo. Subhanallah.....da gaske wai ta zata aljanu ne? Muryarsa da kyar take fita yace ke banda jaraba meye na kirga kosai har kika san anci miki. Kuma ya akayi kika san anci tuwonki a gabana? Zuhra na kukan karya tace ka manta da suka ci tuwon har suka saki cokalin a kasa. Kawar da kansa yayi gefe, ni banji ba bana son sharri. Da dankwalinta ta share idanunta tace kosan zai kai goma wanda suka ci. Hamza bai san lokacin da yace kiji tsoron Allah uku ne zuwa hudu kawai. Ai kuwa Zuhra ta kyalkyale da dariya sosai. Duk yadda yaso dakewa fuskarsa sai ta bawa mutum dariya. Har yayi hanyar fita ya fadawa maigadi kada a kira malam mai ruqiya sai kawai ya gano tsokanarsa take yi. Ya rufe bakinsa da hannunsa da ya tuna har adadin kosan da yaci ya fada mata. Yana juyowa suka hada ido Zuhra ta kwasa da gudu tayi sama. Binta yayi wato kin mayar dani abokin wasanki ko. Nine aljani me satar abinci.... bata jira ya iso ba ta shige daki ta rufo kofa. Duk yadda taso ta kasa murda key din ta rufe saboda tsoro gashi yana turo kofar. Karfinsu ma ba daya bane sai kawai ya tura kofar. Hanyar toilet tayi yayi murmushi kina shiga zan rufeki a dakin nan sai kin kwana biyu. Can gefen gado ta tafi babu wurin buya....gabanta na dukan uku uku taga ya biyota. Sai kawai ta zauna a wurin ta boye fuskarta a cikin cinyoyinta. A hankali ya tako yazo gabanta yana murmushi sannan shima ya zauna suna fuskantar juna. Zaman nasu yayi kusa da yawa saboda wurin yayi musu kadan. Da wata irin murya mai dadi yace dago kanki. Sake tura kan tayi cikin cinyoyinta zuciyarta na bugawa da karfi. Bata ankara ba taji yasa hannu biyu ya daga kan nata. Babu inda baya rawa a jikinta don tsoro...shi kuwa wani irin yanayi na daban ya tsinci kansa. Kukan gaske yaga tana yi sai ya soma dariya har sai da tayi mamaki. Yayi ajiyar zuciya, kin iya tsokana amma kina tsoron hukunci ko. Shiru tayi yau babu rashin kunya su kadai a gida. Duk laifinki ne baki taba yimin tayin abinci ba, baki damu da inda mijinki yake samun abinda zaici ba. Kunnenta yaji da kyau kuwa? Miji fa yace. Bata iya kallonsa ba tace kai kace na rinka dafa na iya cikina. Kuma itama kafin ta tafi tace kada nayi girki da kai. Hannunta ya kama suka tashi muje na hukunta ki. Sake yin alamar kuka tayi yace kinga ni na dena yarda da kukan naki na karya. Plates din ya dauka yace babu ruwa ne ko juice. Akwai ta amsa da mamakin me zaiyi. Ki dauko ki hado da wani spoon din. Falonsa ya shige da abincin. Sai a lokacin tayi ajiyar zuciya....wai amma ta tsorata. A tray ta dora jug cike da zobo mai sanyi da cup da kuma spoon din da yace ta dauko. Samunsa tayi a falonsa yana zaune a kasa yana cin abincin. Murmushin da tayi yayi masa kyau yace na dena satar abincin a bayan idonki. Gabansa ya nuna mata zauna muci. Dawa??? Ta kwalalo idanu tana kallonsa. Tashi yayi ya zaunar da ita. Punishment dinki kenan na tsokanata kici abinci tare dani. Idan baki ci ba kuma nayi bakinki zan dalle. Don Allah kayi....hannu ya daga mata. Kada ki bata bakinki ki bani hakuri. Daga yau har Izzy ta dawo zaki rinka yin abinci dani. Tace to amma ni bazanci da kai ba. Harara ya sakar mata. Don ma kin samu Hamza zaici abinci plate daya dake...kuma wallahi bana son kazanta. Idan zakiyi na dare zan zo inspection naga yadda kike girkin don nasan halinki. Ba yadda ta iya dole ta zauna suka ci. Sai dai bata iya sakin jiki ba don da ta diba zaice lomarta tayi girma ko kuma tayi kadan. Haka yayi ta mata har suka gama ta kwashe komai ya wanke. Zobon kuwa bayan ya shanye cewa yayi ta hada masa wani...zobo ma yana cikin abinba Izzy bata masa. Shima na masu karamin karfi ne. Da daddare tuwon semovita yace tayi da duk miyar da ta ga dama. Su Hamza an sami sake Izzy bata nan. Miyar kuka ta kada taji wake da nama. Bai iya boye mata santinsa ba. Sai da ta gyara kitchen din tsaf ta tafi dakinta. Wurin shadaya da rabi tana kallo aka dauke wuta. wayarta tayi saurin janyowa daga jikin chaja sai taga ashe bata yi chajin ba. Chajar bata shiga jikin socket din da kyau ba, ga wayar dama bata rikon chaji yanzu. A take ta fara jin tsoro ga zafi. Da bin bango ta janyo bargo daga gadonta da pillow tayi shimfida a gefen kofa. Bata son duhu ko kadan shiyasa take kwana da fitila a kunne ko ta kunna torch light din wayarta. Hamza na fesa bodyspray ya fito daga wanka aka dauke wuta. Wurin minti biyar baiji maigadi ya tayar da inji ba sai ya sauka. Maigadi yayi yayi injin yaki karbar wuta kuma akwai mai a ciki. Dama irin babban nan ne da yake daukar har AC da fridge. Sunyi iya kokarinsu abu yaci tura Hamza ya kira mutumin dake masa gyara yace ko zaizo da safe. Mutumin yace yana kauyensu yaje karbar kudin auren kanwarsa amma jibi zai dawo. Hakan baiyiwa Hamza dadi ba ya yanke shawarar neman wani washegari domin zafin gari sai ya hana mutum bacci. Dakinsa ya koma sai ya tuna da Zuhra yace bari ya doba ko tayi bacci. Tsoro yasa Zuhra ta dukunkune kanta cikin bargo duk zafin da akeyi. A hankali ya bude kofar dakin gudun kada ya tasheta idan baccin take yi. Dishi dishi take ganin inuwar mutum da yayi hanyar gadonta. A ranta tace shikenan barawo ya fado dakinta. Tashi tayi da sauri zata gudu ko da bin bango ne taje dakin Hamza taji anyi saurin rungumota ta baya. Sandarewa tayi a wurin don tsoro kamar ta saki futsari, gumi ya rinka tsatstsafo mata. Hamza bai ankara ba yaji ta kai masa naushi a ciki ta soma ihu...Wayyo Allah barawo. Duk da zafin cikin bakinta ya samu ya toshe da hannunsa ai kuwa ta gantsara masa cizo iya karfinta. [17:23, 26/09/2016] ‪+234 813 652 9082‬: AL'ADUN WASU 🗿46‬ Batul Mamman(Mrs)💖 Ba shiri ya saketa, yana yarfe hannu. sake bude baki tayi zata yi ihu a hankali yace ke nine....ajiyar zuciya tayi da karfi sannan tace da tsoratani kazo yi kake min sanda a daki? Kaima baka da fitila ne? Dukan da tayi masa ya kulle masa ciki gashi ta dame shi da surutu. Da waya na shigo karama bansan inda kika jefar min da ita ba. Yayi kokarin dukawa ya lalubi wayar yaji zafi a cikin....auchhhh. Zuhra tayi saurin matsawa kusa dashi menene ta tambaya a tsorace. A duhun ya harareta naushi na fa kikayi a ciki ga cizo sai kace wata yar dambe. Duk hanyar mugunta kin sani. A wahale take jin muryarsa na fita ta mika hannu tana sannu taji ta taba cikinsa....kamar wadda aka tsikara tayi saurin janye hannun tana cewa yi hakuri. Shima hakan yaji amma bai so ta dauke hannunta ba. Dakin yayi shiru na dan lokaci...Hamza ya kasa gane dalilin da yasa ko yaya jikinsa ya taba na Zuhra sai abin yayi affecting dinsa sosai. Dan gyaran murya yayi bazaki tayani neman wayar ba? Kamar jira take ta durkusa tana rarrafe tana shafa hannu a kasa. Abu taji ta taba tayi saurin janyowa ashe hannun Hamza ne shima yana duddubawa. Da yake da karfinta taja shi kuma baiyi tunanin hakan zai faru ba sai ya fada kanta. Bakon yanayi duka suka tsinci kansu a ciki. Kunya kamar Zuhra ta nutse a wurin, kamshi ne mai dadi yake fita daga jikin Hamza. Yana fadawa ya gane daurin kirji ne a jikinta...a hankali ya soma yi mata magana. Nifa bana son daurin kirji don Allah ki dena. Wai ita yake hadawa da Allah....saurin dawowa tayi hayyacinta ta fara kokarin ture shi. Yana ji ya sakar mata nauyinsa yana mata dariya.....wai kema kina son jin dumin mijinki shine kika janyoni. To saboda ina tausayinki bazan miki fada ba mu kwana a haka. Wayyo Allah, karshen kunya Zuhra ta gama ji. Har wata in'inar karfi da yaji ta fara. Al'Quran....Al'Quran ba...ba haka bane. Ko kadan bashi da niyar tashi don ya soma jindadin tsokanarta yace to yaya ne? Abinda kika ga munayi da Izzy kike so nayi miki? Wani karfi ne yazowa Zuhra ta dage ta ture shi. Tana ji yana dariya ita kuwa sauran kadan ta soma kuka. Bata dade da matsawa ba yaga wayar ya dauka ya kunna tare da soma haska dakin. Can bakin kofa ya ganta ta takure harda jan bargonta ta rufe jiki. Koda ya matso harda dan hawayenta. Kusa da ita ya koma me kuma nayi miki kike min kuka? Sai da ta dan matsa sannan tace ba kaine kace wai...wai...wai....kwafa tayi ta kasa karasa maganar. Dariya shagwabarta ke bashi, dazu fa aljani kika kirani banyi kuka ba sai kece mai arhar hawaye zaki min kuka daga wasa. Kin kallonsa tayi saboda kunyar ganinsa babu riga. Yace kinga fito daga bargon nan kisa rigar bacci bana son daurin kirji. Tana kumbura baki tace ni a haka zan kwana. Mikewa yayi to ya rage naki...wai ma kinyu wanka kuwa kafin ki kwanta. Tsami nake ji a dakin nan....dama zuciya na kusa ta fara kuka wallahi bana tsami. Yace to kinyi wankan..tsakaninki da Allah. Rufa tayi har ka sannan tace banyi ba. Rufe bakinta ke da wuya ya janye bargon gaba daya tana kuka ko kulata baiyi ba. Lokaci daya ya yankewa kansa shawarar abinda zaiyi ya taimaka mata kafin su rabu. Kan gadonta ya jefa bargon sannan ya shiga toilet dinta. Babu komai sai sabulun wanka da omon wanki da wanke toilet. Ficewa yayi ya barta a duhun baiyi magana ba. Ga tsoro tana ji ita kadai amma bata son binsa. Bayan kamar minti biyar ya dawo da wata fitila mai haske wadda tafi karamar wayar tasa. Shima a babbar bashi da chaji sosai. Wani abu ta gani a hannunsa kamar toothpaste tace ina da makilin fa. Wannan ba makilin bane yar kauye zo nan. Baya ta dan matsa tace yi hakuri. Fitilar ya ajiye a kan dressing mirror dinta sannan ya jawota ya zaunar da ita kamar ranar da yayi mata kwalliya. Duk ta tsargu da daurin kirjinta, shi kuwa ya saka kayan bacci marasa nauyi yanzu. Yana zaunar da ita ya kama hannunta duk da yadda yaji ya daga. Allah Sarki Zuhra sai hawaye...ashe dazu bata ga komai a kunyar da Hamza yake shirin bata ba. Kokarin sauke hannunta tayi ya sha kunu zan matseki idan baki tsaya ba. Kuma kinga mu kadai ne a gidan babu mai taimakonki. To me zaka yi min? Yace sa ido ki gani bana son surutu kuma ki hadiye kukan nan. A hankali take hawaye tana gani ya bude abinda ta zata makilin ne ya zuba a wani abu kamar cokali mai dan fadi ya soma shafa mata a hammata. Ji tayi kamar cakulkuli ta soma dariya....girgiza kai yayi kina da matsala, daga kuka sai dariya. Bata dena dariyar ba har ya gama yace ta bar hannunta a bude. Dayan hannun ya daga ya shafa a nan ma. Wurin minti biyu yana dube dubi a dakin har yaga inda ta ajiye turaruka da body spray din lefenta. Tace wai a haka zan zauna ne? Sai da ya dauko wurin kala biyar sannan ya dawo ya dauki yar robar da tisssue a hannunsa ya kwashe duka gashin. Zuhra ta wage baki ....lahhhh kaga gashin ya cire. Hamza murmushi kawai yayi..yar kauye bata san shaving cream ba. Fes ya share mata sannan ya mika mata shaving stick har uku. Shiga toilet kiyi shaving sannan kiyi wanka ina jiranki a nan. Ya Salam yau Hamza so yake ta tona rami ta boye kanta don kunya. Kasa shiru tayi tace can kasa wai yau kunya kake son sani ji? Bata san yaji ba yace yes idan baki wuce ba zanzo nayi miki da kaina. Fitilar ta dauka da sauri ta shige harda murda key. Murmushi Hamza yayi ya dan matsa kofar toilet din...kada ki fito sai kinyi wanka sau uku. Ki tabbatar jikinki ya fita sosai don zan duba. Idan baki fita ba na iya yiwa kazamai irinki wanka. Kuma kiyi brush sosai. QTo an hada Zuhra da aiki, sai da tayi amfani da duka shaving sticks din wurin gyara jikinta sannan ta shiga dirzar jiki. Allah Ya kiyaye ta bari yayi mata wanka. Sau biyar ma tayi harda goge kafa da abin kaushi duk da kafar tata bata da matsala. Brush da toothpaste kuwa sun san Hamza na dakin don sun sha aiki. Katon tawul tasa ta goge jikinta sai taji wani dadi da iska na shigarta. A hankali tace na gama. Yana kwance akan gadon nata yace to fito mana. Lallai ma a hakan? Rigar bacci yake duba mata amma sai yace to meye ya rage da zaki boye min. Shiru yaji bata fito ba ya dan kwankwasa, bude ga riga ki saka. Dan kadan ta bude kofar ta zura hannu. Wata rigar bacci ce mai kyau amma cotton mara nauyi ta wuce gwiwarta ma da karamin hannu. Yace ki goge jikinki sosai kafin ki saka. Dama ta goge ta saka ta yafa tawul din ta fito. A kan stool din yake zaune yace tunda yau akwai zafi sosai ba sai kin shafa mai ba. Har gabanta ya karasa ya cire mata tawul din sannan ya fesa mata body spray kala uku. Don Allah baki ji dadin jikinki ba yanzu ya tambayeta yana murmushi. Kanta a kasa tace naji...yace good, lesson one duk dare sai kinyi wanka kafin ki kwanta kinji ko. A hankali tace to. Wayarsa ya kunna yace to sai da safe ya fita ya bar mata fitilar. Gado ta haye tayi addu'o'in kwanciya sai dai baccin yaki zuwa. Duk abinda Hamza yayi mata tun shigowarsa ta rinka tunawa tana murmushi...... [17:24, 26/09/2016] ‪+234 813 652 9082‬: AL'ADUN WASU 🗿47‬ Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta tana tsoron kada naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa Hamza ya dawo daga masallaci ya sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake. Amma yau gabadaya kunyarsa take ji da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan tafasa na soya kada ya lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar tafi ta jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya ta nuna damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta, hakan bai hanashi tuno surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi kamar ana kallonta ta dan juya suka hada ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi. Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da kaninfari. Ta soya kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza na son kwai da albasa. A karamin plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread daya ta bawa maigadi ya siyo musu jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa da kayan tea. Kasa shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne. Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan doguwar kujera ya zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga mura tayi masa kamu sosai. Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta ajiye masa tray din a gabansa sannan ta koma ta dauko flask din. Kallon kayan yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace uhmm dama nasa citta da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa duk babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka kirji. To nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya bata sosai bata yi masa musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen. Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da jajjagen kayan miya tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa, attaruhu, karas da koren wake. Harda grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake komawa falon ko ya gama cin abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita da maigadi ba saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata nikan shinkafa. Talle maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar Zuhra yace to Hajiya nagode. Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a kan kujera tana sha don bazata iya cin kwai zalla ba. Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai yaji babu dadi. Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota tana sha shi kadai. Shiga yayi yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai yarda ba ya duba dustbin dinta ina ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa yace bakya jina ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika bawa maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora abincin rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura da abinda take so domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya kama suka koma falo...meyasa baki fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da lafiya kuma zan iya jira. Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu ba yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta kasa sakewa . Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya baki lada, kin nuna damuwa da rashin lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi. Amma daga yau ki rinka fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta koma aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan shinkafar sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar da ya gyara mata ranar da suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta ma suka sha turare mai kamshi. AL'ADUN WASU 🗿48 Batul Mamman(Mrs)💖 Hamza na falonsa ya gama waya da assistant director akan wasu ayyuka. Duk yayi musu bayanin yadda yake so ayi aikin da alkawarin idan yaji sauki anjima zai shiga office. Bayan ya gama Izzatu ya kira. Hira kadan suka yi ya gaisa da su Khalifa tace masa tana son wucewa Abuja idan an gama bikin. Dad dinta ne zai tafi Japan shine zata je yi masa sallama sai wata lahadin zata dawo. Ransa a bace yace Izzy ba haka muka yi dake ba. I need you here, bama ni da lafiya. Izzy tace kayi hakuri baby amma Dad zaiyi wata biyu kaga ya kamata naje muyi sallama. Idan yace bai amince bama yasan sai taje ko tasa mamanta ta kira shi a waya. Abin mamakin ma tsakaninsa da Allah rashin dawowar tata bai wani dameshi ba. Shi da baya iya nisa da ita...yace to su Khalifa kinsan zasuyi missing school da yawa ko. Eh zasu taho da Tala ranar lahadin amma da Nana zan tafi Abujan. Bye baby, love you. Dip ta ajiye wayar, rike tasa wayar yayi a hannu yana mamakin Izzatu. Ko sau daya bata yi masa sannu ba duk da muryarsa data canja ko bai fada ba za'a gane bashi da lafiya. Har tunani yake yi wai dama haka take masa ko yanzu ne dai saboda bikin da suke yi. Zuhra na saukowa aka kawo wuta. Tsabar murna yasa tayi ihu har sai da Hamza yaji. Da sauri ya fito yaga abinda ya sameta sai yaga tana ta juyi a falo tana kiran nepa, nepa.... baki ya rike yana kallon ikon Allah, sai kace wata karamar yarinya sai tsalle take yi. Riga da skirt ta saka na yadi mai laushi. Dinkin ya kamata tsam ta daura dankwalinta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi masa kyau. Gabadaya surar jikinta ta fito sai tuna masa daren jiya take. Sannu da aiki yar kauye ya fada yana tsaye a bakin koma. Da farko tsoro taji har zata gudu sai kuma ta tsaya ta fara neman wuyan hijab dinta ta saka. Jira yayi ta saka din sannan ya karasa gabanta ya kama kasan hijabin. Hannunta tasa tana neman kwacewa ya janyota gabadaya jikinsa. A take ta fara rawar jiki tana cewa kayi hakuri na dena tsallen. Sosai ya rungumeta yana kallon fuskarta ya cire mata hijab din cikin nutsuwa sannan ya saketa. Kirjinta ta fara kokarin rufewa yace ke jiki ba jiki ba kiyi ta wani rufewa. Haushi taji ta dan tura baki sai ta fara juyi a gabansa tace a hakan? Wallahi ina da jiki, kaga fa...dariyar da yake mata yana cewa juya na gani da kyau yan mata yasa ta bar abinda take yi ta soma kokarin kwatar hijab dinta. Hannunsa ya daga sama tace to na bar maka bari na dauko wani. Baifi taku biyu tayi ba ya jawota jikinsa. Hannuwansa na gaban kirjinta ya dan rage tsaho daidai da kunnenta...ki hakura da hijab din kinga akwai zafi. Kuma naga ashe kina da jikin da zan kalla. Yana magana taji yasa hannunsa a kafadarta yana mayar mata da hannuwan breziyarta da suka fito. Daga daren jiya zuwa yau Hamza yasa Zuhra tsananin jin kunya. Yadda ya rufe mata jiki gabadaya ta baya yasa ta kasa motsi. Zuciyarta ce kawai take bugawa da sauri. Tana wannan yanayin har ya saketa bata sani ba. Ganinsa kawai tayi a gabanta yana murmushin da yanzu take yawan gani tare dashi. Hada ido suka yi ta kawar da kanta, a hankali tace duk kasa ni jin kunya. Sai ka rinka wayon taba min jiki. Kuma dai kasan babu kyau. Ya daga gira kina matar tawa. Tace to ba sakina zaka yi ba. Tana fada ta wuce kitchen ta barshi a tsaye. Maganar Zuhra tasa ya shiga damuwa sosai. Dambun shinkafa ta hada mai rai da lafiya. Ta rinka yawo tsakanin falo da kitchen har abincin ya dahu. Daya da yan mintuna ta gama ta mikawa maigadi. Shi kam yana jindadin sauyin da ake samu na girki a gidan nan. Gashi harda ruwan sanyi tunda an kawo wuta. Na Hamza ma ta hada masa komai a tray ta shiga falonsa ta ajiye sai dai baya ciki. Yunwa take ji sosai domin yau tayi dauriya. Nata tayi niyar zuwa ta diba a kitchen sai taga wata kofa ta bude ashe da toilet a wurin. Tashi tayi zata gudu yace dawo ki zauna fita zanyi, da alama alwala yayi. Zan canja kaya naje office zaman gidan ya isheni. Ba komai ke damunsa ba sai maganar Zuhra ta saki. Ya rasa gane yana son zancen sakin nan yanzu ko kuwa. Da 'yar damuwa a fuskarta tace amma baka da lafiya, ka hakura mana. Yana jindadin yadda take kulawa dashi yace bazan dade ba in sha Allah. A gaban tray din ya tsuguna Me kika dafa mana ne...yar kazama ta iya girki. Tray din ta dauka tunda ni kazama ce ka nemi wani a waje. Yi hakuri ki kawo kinji, ai kinfi kowa tsafta a gidan nan. Bubbude flask din yayi yaga dambun shinkafa tayi da farfesun kaza. A take yawunsa ya tsinke. Wai me yake damunka ne Hamza da kaga abincin sai ka rude kamar wani mayunwaci. Kinsan abincin da Hajiya tafi so kenan dambu ko wane iri ne. Zuhra tace da gaske? tare da dauke flask din da ta zuba masa nasa. Bari naje na juye sauran ina ga zai kai cin mutum uku idan aka hada. Tana magana tana neman fita daga falon. Hamza yace ke dawo bangane me kike nufi ba? Ya daga kawo min abinci ko tasting banyi ba kin dauke. Buga kafa tayi irin ya ma zai ki ganewa...yanzu fa kace min Hajiya na son dambu. Zan hada da sauran sai ka kai mata. Bari nayi sauri ko taliya na dafa mana tunda kaima fita zaka yi. Tashi yayi da sauri ya kamo wuyan rigarta ta baya ya dawo da ita...haba yar kauye daga magana sai ki dauke abincin. Ya dan yi mata kalar tausayi, nima ina son ci don Allah ki ajiye. Zuhra ta dan harare shi to Hajiyan fa? Flask din ya soma ja itama tana ja. Da taga yafi karfinta sai tace to bari na zuba maka kadan sai ka kai mata sauran. Kaga duk duniya ga namiji bashi da abinda yakai mahaifiyarsa daraja. Kafin na tafi in sha Allah idan kana so kullum duk abinda take ci ka fada min sai na dafa mata. Ummana tace idan nayi aure na taya mijina neman aljanna ta hanyar kyautatawa iyayensa da sauran ayyukan kirki. Kaga yanzu kafin ka sake ni ko dan yaya sai nayi abinda tace ko? Sai kuma ta rufe baki da hannu daya...ka ganni ko? Umma cewa tayi ba fada maka zanyi ba sai dai ka gani a aikace. Don Allah kada kace na fada. A shagwabe take masa maganar wadda tayi matukar tasiri a ransa. Har wani dan dukan bakinta take yi ita a dole tayi laifi. Allah kadai Yasan farincikin da Hamza yaji a wannan lokacin. Yau shine da matar da take nuna damuwa akan mahaifiyarsa fiye dashi. A wannan lokacin gani yake Zuhra tafi masa kowace mace. Bai yarda sonta yake ba amma a shirye yake ya kyautata mata iya karfinsa...a hankali take samun masauki mai daraja a zuciyarsa. Ido ya zuba mata kawai yana kallonta. Ita kuwa kuwa tana kare maganarta tayi gaba da flask din ba tare da ya tareta ba. A dan plate ta zuba daidai yadda zaici ta hada sauran wuri daya. Takaici ma take bata sani da wuri ba ai da tayu mai yawa. Naman da ta soya ta diba ta zuba a kai saboda farfesun tayi shi da yaji tunda Hamza na mura. Tunda Zuhra ta fita yake ta kai kawo....ya tsani ta tayar da maganar sakin. Shigowarta tasa ya sami wuri ya zauna ta mika masa plate din. Jan hannunta yayi ya zaunar da ita a gabansa. Nasan kin fini jin yunwa ki ci ni ga nawa abincin ya nuna mata farfesun....cikinta har wani kullewa yake ta yi murmushi da gaske ka bar min. Hamza yace eh...plate din ta janyo gabanta ta soma ci da sauri. Ya kama hannunta lesson two yar kauye, ki dena cin abinci da sauri kuma banda katuwar loma. Ta danji kunya sai tace to yaya zanyi? Dan madaidaici ya diba a spoon din ya nuna mata. Tace dama Babana yace kada nayi loma a gabanka...Allah Yasa na iya denawa dai. Amma meye kake cewa lesson one da two? Kallonta yake ya rasa me yake ji game da ita so nake ki zama yar gayu kafin lokacin rabuwarmu, yadda zan dena kiranki yar kauye. Washe baki tayi da gaske don Allah? To ai da ka fada min da wuri yadda zan kiyaye duk abinda ka gyara min. Rabin abincin taci ta ture plate din ni na koshi. Hamza yace don nace ki rage loma? Yamutsa fuska tayi a'a cikina ne ya kulle tea zan sake sha. Sannu yayi mata sannan yaja plate din ya ci sauran tare da shan farfesun. Kamar kullum yau ma abincin Zuhra yayi dadi. A zuciyarta kuwa dadi taji ta bashi dambun saboda tana ganin irin kallon da yake yiwa abincin tunda ta soma ci. Yana gamawa ta hada masa wanda zai kaiwa Hajiya a wata yar jaka ta bashi. Yace to daga can zai biya office. Har ya isa gidansu ko na sakan daya bai dena tunanin Zuhran Baban yara ba. AL'ADUN WASU 🗿49 Batul Mamman(Mrs)💖 Da yake weekend ne a falo ya tarar da mutan gidan suna kallon wani shiri da akeyi a Sunna TV. Kannensa suka gaishe shi ys amsa da sakin fuska. Sannan ya gaishe da iyayensa. Mama tace Yaya yau ina office din? Zama ya fara yi sannan yace mura ke damuna amma tayi sauki. Yanzu ma can zan wuce, aiko ni aka yi wurin Hajiya. Hajiya tace ni kuma? Jakar hannunsa ya tura mata gabanta gashi inji Zuhra. Hajiya dai kunyar bude jakar tayi Mama tace kaga Yaya miko min nagani. Kowa a falon zuba ido yayi yaga abinda ke jakar sai ga Mama ta fito da food flask mai kyau. Tana budewa dambun shinkafa ne ke kamshi mai dadi. Muryarta a shake kamar tayi kuka tace Adabiyya, Nura, Hamida ku shiga ciki. Ba musu suka tashi suka barsu su uku a falon. Mama ta turawa Hajiya flask. Kinga abinda ke ciki kice wani abu. Murmushi Hajiya tayi nagani Mama amma me zance? Ga mamakinsa duka su biyun hawaye sukeyi. Hankalin Hamza yayi matukar tashi ya fara basu hakuri. Mama tace Yaya ko kasan tunda kayi aure abincin gidanka bai taba shigowa gidan nan ba sai yau. Kasan gidan iyayenka babu yunwa amma a tamu al'adar lokaci zuwa lokaci mace takan yi girki na marmari ko da da sallah ne ta aika gidan surukanta. Irin haka yana sa iyayen miji su so matar musamman idan tana da tarbiyya. Shima mijin indai yasan kimar iyayensa dole matar ta sake samun wuri a zuciyarsa. Hannuwansa ta kama gam ta rike...Yaya yanzu kayi aure, nasan zaka ga kamar muna kin Izzatu amma ko kai shaida ne akan bambancinsu da Zuhra. Kwalla ce ta cika masa ido shima ya basu labarin yadda akayi ya kawo dambun. Hajiya dai kasa rike kukanta tayi ta tashi ta bar falon. Ashe tana da rabon ganin Hamza ya auri macen da zata saka shi a hanya..Allah Yayi mata albarka. Ko ba'a fada ba tasan shima ba karamin dadi yaji ba. Tana tafiya Mama ta share hawayenta. Yaya ka rike Zuhra amana Alhaji bai maka zaben tumun dare ba. Idan ka cutar da 'yar mutane saboda dalilin da ya jawo aurenku Allah zai kamaka da hakkinta. Tana gama magana tace jirani ina zuwa. Kafin ta dawo Hamida tazo tace Yaya gobe bayan laasar zamu zo ni da Adabiyya muyi weekend. Yace to Allah Ya kaimu.....shikenan zasu zo su takura masa idan yana tare da Zuhra. Shima weekend din yake jira yini biyu a gida ba fita. Mama dakinta ta tafi ta dauko dubu sababbin dari dari ta bawa Hamza ya kaiwa Zuhra tukwici. Tunda yake bai taba tunanin irin haka na faranta zuciyar iyaye ba sai yau. A hankali yace God bless the day I met you Fatima. Allah Yayi miki albarka. Ko flask din bai jira ba ya fita ya tafi office. Duk aikin baya masa dadi so yake yaji muryar Zuhra tana masa shirmenta ko shagwaba. Har mamakin kansa yake, ga babban abin kunya bashi da numbar wayarta ma. A lokacin ya tuna wayar tata tana da matsala, bayan sun gama cinikin filayensa da wani dillali ya tashi. Beirut road ya wuce ya siyo wata sabuwar waya kirar Samsung mai kyau. Nasa tukwicin kenan na abinda Zuhra tayi masa yau. Daga nan ya biya wani shago yayi yar siyayya ya tafi gidansa. Yana ajiye mota ko gida bai shiga ba ya fita masallaci saboda a hanya yaji kira. Can ya zauna har aka yi sallar Isha sannan ya dawo ya shigo da kayan da ya siyo. Duhun da ya gani ya tuna masa bai nemi wani maigyaran injin ba gashi har dare yayi. Zuhra ce ta fado masa ita da ko wayar kirki bata da ita. Nemanta ya shiga yi daki daki baiji motsinta ba. Abin ya bashi mamaki ko bacci take yi ne? Yana hawa sama tana fitowa daga dakinsa da fitila a hannu daya, daya hannun kuma tsintsiya ce da abin kwasar shara. Har ajiyar zuciya yayi, ita ta fara magana tace sannu da zuwa. Murmushi yake yauwa yar kauye. Me kike yi da tsintsiya a duhun nan? Tsoro na rinka ji ni kadai sai kawai na fara shara da wankin bandaki. Amma dai ban bata maka rai ba da na shiga dakinka ko? Naga yanzu kana min kirki shine nace bari nima na gyara maka daki. Bai amsa mata ba sai da yazo gabanta...baki yi laifi ba yar kauye, nagode. Ki je kasa akwai kaya a falo ki kai kitchen dinki bari nayi wanka. Bai shiga dakin ba sai da ta saukq kasa. Dadi yaji sosai har da turaren wuta ta saka. Ta gyara gadon tayi shara. Toilet din ma ta wanke shi tas har boxers dinsa da vests da suke cikin wani abin zuba kayan wanki duk ta wanke amma bata shanya ba saboda wurin shanyar yayi mata tsaho. Sau uku take niyar wankewa sai ta fasa wai kada yace bata da kunya. Sai daga baya ne ta daure zuciyarta ta wanke su harda kawar da fitilar gefe ita bata kalla ba bare ace mata 'yar iska..... Ba jimawa ya sauko yace mata tayi girkin dare ne tace a'a amma zata dora yanzu. ki dafa mana indomie kawai akwai a cikin kayan da nazo dasu. Cikin 'yan mintuna ta gama ta kawo. A plates daban ta zuba musu. Maigadi kuwa dama ana magariba ta dafa masa taliya. Hamza na kallonta har ta zauna zata fara ci ya dauko nasa plate din ya dawo gabanta, tasa ya juye a cikin natan sannan ya soma ci batare da yace mata komai ba. Ido ta zuba masa ta kasa ci saboda tana gudun tsokanarsa. Ya dago kai suka hada ido....lesson three, yana da kyau mata da miji suci abinci tare. Yana kara musu shakuwa da son juna. Kyakkyawan murmushi tayi...Allah, to amma ba da kai ya kamata naci ba kada mu shaku gashi zamu rab....hannunsa yasa ya rufe mata baki ta daga ido tana kallonsa. Ki dena zancen rabuwarmu akwai sauran lokaci. Just eat. Babu abinda yaki jini yanzu kamar tayi zancen rabuwarsu, idan lokacin yayi sai asan abinyi amma for now so yake yayi enjoying moments dinsu tare. Sai da Zuhra ta gyara kitchen sannan tace masa sai da safe Allah Ya kara sauki. Lokacin aiki yake da laptop a gabansa. Suma yan nepa kamar sunsan injinsu ya lalace suke kim basu wuta sosai. Wanka ta dauki lokaci tayi don so take duk abinda ya koya mata ta rinka yi. Zafin yau da sauki akan na jiya shiyasa ta dan shafa mai kadan sannan ta shiga barnar bodyspray. Har humrarta da bata taba shafawa ba ta dauko kwalba daya mai kamshi ta rinka bin duk gabobinta tana shafawa. Rigar baccin da ta dauko yar karama mai siririn hannu har tafi ta jiya kankanta da rashin kauri. Wani dadi take ji ashe haka tsafta ke da dadi...gadonta ta haye ta ajiye fitilar a bedside drawer tayi kwanciyarta. Zafi baisa ta rufa ba amma ba bacci ma take ji ba. Tunani take ko me Hamza yake yi yanzu....... Kusan rabin awa kenan da yayi wanka ya gama shirin kwanciya sai dai ko alama babu bacci a idanunsa. Zuhra yake son gani amma yana kokarin hana zuciyarsa sabawa da son kasancewa tare da ita. Sakon kudin da Mama ta bashi ya tuna yana wallet dinsa ga wayar da ya siyo mata duk bai bata ba. Murmushi yayi ya tashi don ya sami dalilin zuwa dakinta. AL'ADUN WASU 🗿50 Batul Mamman(Mrs)💖 Zuhra na kwance tana 'yan tunane tunane taji ana bude kofar dakinta. Tasan babu kowa a gidan sai Hamza shiyasa tayi saurin kashe fitilar gefen gadon. Ba komai ne a ranta ba sai yar rigar jikinta. Wayar Hamza ce ta hasketa da sauri ta fara jan bargo ta rufe jikinta. Shima saurin yayi da ya lura da abinda take yi...me kike saurin boyewa ne haka 'yar kauye? Babu komai ta bashi amsa. Dan kashe wayar kada chajinka ya kare kaga babu wuta. Kashewar yayi amma ya zauna a kan gadon gefen bangarenta na dama. Kamshin turarensa maidadi ne yake tashi a wurin. Shiru baiyi magana ba Zuhra tace ko akwai abinda kake bukata ne? Sake gyara zama yayi sannan yace yanzu ke haka ake jinya? Kinfi kowa sanin bani da lafiya yau amma saboda kirki yayi miki yawa kika barni na kwana ni kadai. Yanzu idan wani abu ya same ni cikin dare fa. Zuhra ta dan muskuta gefe saboda ya danyi kusa da ita. Kayi hakuri amma ai mata da mijin gaske ne suke kwana daki daya. Hamza yace ni kuma gani kwarto ko??? Zuhra ta kwashe da dariya harda hawaye da kyar ta iya tsayar da dariyar tace kasan mun taba zuwa biki Ajingi a gidan da 'yan mata suka kwana kwarto ya fado mana. Nishadi yake kawai saboda yasa ta farinciki yace bai taba ki ba ko. Zuhra tace ina fa ai lokacin ni ban girma ba sosai amma har fitsari sai da nayi a wurin don tsoro. Kowa ya gudu ya barni ina ta salati. Sosai Hamza yake dariya. Amma an kamashi kafin ya gudu. Yaci duka sosai har hakorinsa daya ya cire. Hamza ya dan kwanto jikinsa akan gadon, to yanzu kin girma dai ko? Da dan murmshinta tace sosai ma. Kudin da Mama ta bashi ya mika mata a cikin duhun tayi godiya sannan yace nima akwai kyautar da zan baki amma sai an kawo wuta. Yau manatawa nayi da batun inji but hopefully da safe maigyaran zai zo. Allah Ya kaimu Zuhra tace, amma kaje ka kwanta kaga gobe zaka je aiki. Maimakon ya tashi sai taga ya gyara zama sosai don yanzu irin yadda bayanta ke jingine da pillow shima haka yayi. Kara matsawa tayi shima ya matso. Haka suka yi har ta kai karshen gadon. Ta dan turo baki wai sai ka rinka wayon tabani kuma kasan dai babu kyau. Yayi dan murmushi tare da shafa fuskarta. Miji ai ba sai yayi wayon taba matarsa ba, abinda kike boyewa nake son gani. Pillow tasa ta kare jikinta...ka rufa min asiri rigata yar karama ce. Hamza yace to na rufa, dan matso na tambayeki. Ba musu ta matso kadan domin a karshen gadon take. Wai baki san sunana bane? Ban taba ji kin fada ba. Sai dai kice yi kaza, ko kayi kaza. Alamar tana jan bargo yaji yasa hannu ya danne. Baki amsa min tambayata ba. Naga alama so kike na kwana a nan. Bari ki gani...kwanciyarsa yayi tare da dora kansa a cinyarta. Idanunta kamar su fito waje tace don Allah ka tashi. Gyara kwanciyarsa yayi naki din. Idan kina so na tashi ki bani amsa. Baki san sunana bane? Dadin kwanciyar yaji ga kamshi mai sanyaya rai da jikinta ke fitarwa. Ita kanta kawai fada take da tace ya tashin, duk da taji kunya amma hakan yayi mata dadi. Duk iya kokarinta na ta janye jikinta ta kasa, gashi rigar jikinta ta danyi sama. Rabin kansa a cinyarta yake babu riga a wurin. Shi kanshi Hamza bazai iya tantance yadda yake jin Zuhra a wannan lokacin ba. Gajiya tayi da yunkurin tashi tace nima baka fadan sunana sai dai kace ke ko yar kauye. Yace to yi hakuri kafin nayi bacci zan sama miki wani sunan. Ina amsata? Cike da shagwaba tace to ba sunayen naka bane masu yawa. Hmmmm lissafa min su ya fada yana lumshe idanu. To nasan sunanka na gaskiya sunan babban sahabin Annabi SAW ne kuma Kawunsa. Ta dan sunkuyu da kanta har yana jin dumin numfashinta a fuskarsa in fada bazaka ce nayi rashin kunya ba? Fadi....tace HAM-ZA. Yadda taja sunan yayi masa dadi har wani abu yaji tun daga kansa har kafarsa. Na biyu kuma a gida su Hamida na kiranka Yaya, su Khalifa suce Daddy, maigadi da Tala suce yallabai. Ita kuma Maman su Khalifa tace su Honey, Sweetheart....har wani kwafar muryar Izzatu take yi idan ta kasheta tana kiran Hamza. Abin dariya ya bashi yace kin iya gulma yarinyar nan, to su kenan kika sani? Zuhra tace ina fa...harda wani Babyna, shima a wata irin murya ta fada kamar rada. To idan kai baby ne jariran gaske kuma me za'a kira su. Da gaskenta take magana Hamza yace lallai da sauranki. Lesson four...maza suna son matansu su rinka kiransu da sunaye masu dadi kamar yadda suma matan suke so. Kuma idan miji ko mata ya kira dayan baby ai saboda a aure ana son mutum ya rike abokin rayuwarsa tamkar jariri. Kinga a aure ana son mace ta girmama mijinta kamar wanta sannan a bangaren soyayya da kulawa ta rike shi kamar baby dinta. Ta bashi abinci a baki, ta yanke masa farce, saka masa turare, cire masa kaya da saka masa, tayi masa wanka da shafa mai ko suyi tare......mun shiga uku !!! Zuhra ta katse shi harda dora hannu a ka. Ni kasa ni jin kunya ma, don Allah a bar zancen haka. yanzu harda wanka kuma duk girmansa. Ni dai gaskiya a'a wannan karatun ban dauka ba. Hamza yace amma kinsan ko a hadith daga Nana Aisha RA ta kasance suna wanka tare da Annabi SAW. Zuhra tace haka ne an fada a islamiyya...amma da kunya. Hamza yace indai kina son zamanku ya dore da miji dole ki rinka yi masa irin wannan da abinda yafi haka domin nuna kulawarki gareshi. Shiru tayi tana tunanin duk abubuwan da ya fada mata. A hankali tace Ya Hamza.....har ransa yaji dadin sunan....in sha Allah duk abinda ka koya min idan na sake aure zan gwada. Daga yau ka zama yayana saboda kana min kirki sosai .....tayi 'yar dariya wai, don Allah Ya Hamza hangoni ina yiwa kato wanka. Rufe idona zanyi don bazan iya kallonsa ba. Nagode da yadda kake bani shawarwari. Ko yau muka rabu bazan dena yi maka addua da fatan alkhairi ba. Ba ma jinta yake ba sosai. Ya hangotan tana yiwa katon wanka kuma ko kadan hoton da zuciyarsa ta nuna masa bai masa kyau ba. Ransa ne ma yayi matukar baci ya tashi ba shiri zai koma dakinsa. Meyasa zata kawo zancen wani suna tare? Ita kuwa bata kawo komai ba a ranta tace Ya Hamza sai da safe. Juyowar da yayi aka kawo wuta ta haske dakin gaba daya. Idanunsa a kan Zuhra suka sauka da yar rigarta. Numfashinsa sai da ya canja saboda yadda ya ganta a cikin rigar. Tayi masa kyau sosai. Maimakon ya fita makunnin fitilar dakin ya nema ya kashe tare da kunna AC. Zuhra duk kunya ta isheta ta shige cikin bargo harda rufa har kanta. Ji tayi ya dawo ya kwanta sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta kamar wani zai kwace ta, rabin jikinta duk a nasa jikin yake. Sai kokarin gudu take ya kara matse ta. A kunnenta ya rada mata " Good night Cutie, kuma ki dena yi min shure shure haka". Dena motsin tayi amma ta kasa sakewa. Wai yau ita Hamza ya rungume a jikinsa haka. Basu sake magana ba kowa da tunanin dake ransa har suka yi bacci makale da juna kamar ba Hamza da Zuhra ba. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *