adsense here
novels
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [2:30pm],[2/12/2015]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
Gargadi gareku barayin basira duk wanda yayimin editing din novel koya sauya sunan,Ban yafe ba.
1⃣to5⃣
Kwance take kan makeken gadonta tayi daidai da kafafunta sai chatting data duqufa take,gashi sai faman murmushi take,jifa jifa kuma takan tuntsire da daria,hakan ya tabbatar da cewa tanajin dadin chatting din datake yi.
Al'adan Nasrin kenan inhar tana chatting da NY.
Ta maida hankalinta gaba daya ga wayan har batasan lokacin da mum tashigo dakin ba ji kawai tayi an fizge wayar a hannunta ay kuwa ba shiri ta juyo,sai duk kunya ta kamata,cewar mum,haba nasrin tuntuni kitashi ki yanka vegetables dinnan kinqi,kin shigo daki kin boye abinki sai faman hira mara amfani kike,bari Naufal yadawo xansashi kawai ya kwace wayar kowa ya huta,ay kuwa caraf nasrin tace haba mum pls kar muyi haka kinsan fa inayin duk aikin da kike sani fa sannan naga veggies din ba yanxu xaayi amfani dashi ba shiyasa banyi himman yi ba amma kiyi hkr xan tashi yanxu nayi,dan Allah kar kisa yaya naufal ya kwacemin waya pls mum,haba sweety ta I love u mum😘.Abin ma baiwa mum daria yayi tace to naji uwar iya magana da dadin baki wuce muje,Nasrin ta tashi tabi mum yayinda take godewa Allah a xuciyarta da baza asa yaya naufal ya kwace wayanta ba domin tasan tsaf xai iya.
Suna aikinsu a kitchen gwanin shaawa suna hirarsu yayinda mum ke tambayarta nasrin niko kinsan da irin mutanen da kike chatting kuwa?kinsan duniya ta baci yanxu,ta waya zaa iya batamiki tarbiya,abaki maita,asaki a abubuwa da dama,shin kinsan sharrin dake tafe da abubuwan nasara kuwa,uhmmm nasrin haryanxu ke yarinya ce,ki nutsu ki kula ki kiyaye ki yawaita addua tunda kin maidawa kanki chatting din yazama kmr ibadah,murya a sanyaye nasrin tace naji nagode sosai mum,insha Allah xan kiyaye Allah kara girma,mum tayi murmushi ta amsa da Amin.
*************
Asalin sunanta Nasrin Nazir Yunus,Ya' ta uku gun Alh Nazir da Hajia Nazifa,Naufal Shine babban dansu mai binsa kuma Nawas,sai Nasrin,Nabil sai auta Najwa,Asalinsu yan garin kano ne,amma a jos suke da xama a dogon dutse,Alh Nazir yanada kudi ba laifi,saidai duk da wannan bai bar ya'yansa sun tashi cikin rashin kwaba ko tarbiya ba,yaransa sun tashi cikin tarbiya da kaunar juna.
Naufal shekarunsa biyu kenan da gama karatu harya fara aiki,duk da yanada burin komawa yayi phd dinsa,Nawas kuwa yana final yr a Cambridge university dake london,yayinda nasrin ke final yr a secondary,nabil na jss3 auta najwa na primary 5.......wannan kenan.
Aman jini take tayi ba qaqqautawa saidai tayi mai isarta sannan ta daina,ta galabaita matuqa yanayinta duk ya sauya,hawayi daya nabin daya kamar famfo,Tayi wanke bakinta yayinda tayi flushing jinin,cikin muryar kuka me cike da damuwa nasrin ke cewa Aisha ya kikeso inyi da raina pls kibar bani hkr,nasan son NY ne xai kasheni,gashi bazan iya sanar mishi ba,Aisha in all indication ciwon xuciya na gab da kamani,tun yaushe nake DAKON SON NY?yaqi ya fahimta,lallai so ciwo ne,son maso wani.....bata karasa magana ba tare ya sarqeta sai amai kamar ranta zai fita.
Firgit ta farka daga mafarkin data kirashi mummuna,duk ta jike da zufa,tuni ta fara karanto addu'oi,ta dade a zaune tana addua tukun daga bisani ta koma ta kwanta cikeda mamakin mafarkinta duk da dai tasan tanason NY,fatanta Allah yasa yanajin me takeji game dashi.
Wai ma waye NY dinnan ne?????
Kubiyoni don sanin waye wannan handsome guy din😜dajin darasin da novel din ya kunsa....
Gareka na sadaukar da book dinnan yayana kuma aminina Nasir(Abu farhan)a duk inda kake ina maka fatan alkhairi.
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [12:23pm],[26/12/2015]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
1⃣1⃣to1⃣5⃣
Bayan an tashi daga school ne Nazira tace xata bi Nasrin gida domin ta nuna mata pic din NY,nan da nan nasrin ta hade girar sama data kasa,keee😳😳har saida nazira ta tsorata,meye hadinki dashi,kar kiga kina kawata idan har sunan NY bai fita bakinki ba to wlh kisani kawancen mu na dab da xuwa karshe👀👀ido nazira ta gwalalo a zuciyarta kuwa cewa take"gaskiya wannan NY ga dukkan alamu first class ne,bayan duk big guys dakeson kula nasrin bata kulasu amma wannan yasamu miqamin da ba wanda yasamu,dole nasan waye NY,inya min inmiki kwace inkin san wata bakisan wata ba"a fili kuwa nazira yaqe tayi😀tace kawata abin bai kai haka ba,Allah barku tare,Nasrin ta tabe baki😏tace dadai yafi miki,bro dinmu yaxo daukan mu sai gobe✋🏼
Da suka isa gida ma nasrin daki tayi ta kwanta bacci yayi awon gaba da ita,karar wayanta ne ya farkar da ita ta kalli agogo biyar da rabi😳lallai tasha bacci,a hasale ta daga wayan domin mai kiran bawani dasawa suke da ita ba tunda ta fahimci manufarsa a kanta,"hello yaya nasim barka da yamma",ay kuwa caraf ya amsa"barka dai sweet sis,na missing wannan baby voice dinki,hope duk kuna lfy,😏😏a daqile ta amsa lfy lau,yayita xuba ita dai sai cewa eh ko aa,ahaka tace mai xata kitchen ta taya mum aiki tun dawowarta school take daki,yayi mata sallama badon yaso ba.Ta jingina da pillow yayinda tafara tunano abubuwan rayuwa na ban mamaki da tausayi da dai sauransu,lallai Allah,Alhakim ne,duba yadda nasim ke sonta ita ma takeson wani,lallai wannan shine SON MASO WANI(littafin my khairat,luv u)ni kuma ummu arif nace koshin wahala ba😜.
😢😢hawaye ne yafara bin kuncinta,Ya Allah kasa na cinye wannan jarrabawar,Haqiqa so dafi ne😭😭😭(koni jidda na tausayawa nasrin)tana fama da DAKON SO(littafin kausar luv).
A haka Nabil yazo yasameta,yace adda nasrin mummy nakira,lallai kinsha bacci,har hajiyan su ya nasim taxo ta tafi😳nasrin tace da gsky yace wlh kuwa,tace tashi muje,da gudunta ta isa parlor gun mum,tagaisheta,mum ta amsa fuska a sake,tace ya naga kmr kinyi kuka,nasrin tayi yaqe wanda yafi kuka ciwo tace mum fa daga barci natashi shiyasa kikaga idona sunyi ja,mum wai hajyan su ya nasim tazo?mum tace eh,Nasrin ta kumace meya kawo ta???
Mum ta watsa mata harara tace shaqeni in fada miki,😞nasrin tace Allah baki hkr,ta tashi tai kitchen abinta ta hado tea ta haye sama abinta.
Asalin sunansa Nasim Aminu,mahaifinsa Alh Aminu abokin baban nasrin ne sosai tare suka taso,zumuncin su yaci gaba
Hakan yasa matansu da ya'yansu ma suka kulla abota,Sunan babar nasim Hjya Amina,Nasim shine dansu na biyu,yanada sis Nasima,sai twins dinsu Amir da Amira,sai Auta Amna.
Presently yana masters dinsa a mahatma gandhi university dake ghana inda ya karanci cardiology,tun nasrin na karama yake sonta amma yaqi furta mata shi anashi ganin abu ne mai sauqi,Nasim bafa sauqi inji ummu arif😜
***************
Lokaci na tafiya, soyayyar NY na karuwa kowanne rana a cikin xuciyar nasrin,yayinda kawancensu yaja baya da nazira domin nazira kishin nasrin take akan NY duk da batasan waye shiba(wahala girl)
A bangaren nasim ma hakan take,kullum son nasrin karuwa yake a ranson yayinda yake gani daya sanar da dad dinsa komai xaixo da sauqi,Ita kuwa Aisha saida tasan yadda ta janyo nasrin ajiki domin hakikanin gaskiya itake sonta tsakani da Allah ba nazira ba,inda suke gudanar da kawacensu mai ciki da amana da so da kaunar juna😊.
Lokuta da dama NY yakan tambayi nasrin yaushe xatayi aure,amsarta koyaushe daya ce"KAI NAKE JIRA"(littafin humaida)
Amma shi gani yake wasa take mishi,baisan cewa hakikanin gaskiyarta take fada mishi ba,
😢 kwalla ne kebin kuncinta yayinda ta tuno haduwarsu ta fari da NY,Ranar da baza ta taba mance taba,Tai murmushi tace ya Allah kaciremin son NY a zuciyata na huta(nima ummu arif nace ya Allah yaciremin son tuwo a zuciyata in huta😜),ta share kwallah yayinda ta nufi bandaki don gabatar da alwalar isha'i,nima ummu arif Ina biye da ita nace nasrin pls yaushe zaki fadama waye NY????Juyowan da zatayi naga hawaye ya wanke fuskarta ba shiri nabar dakin don nasan na fama mata inda yake mata ciwo,To wai waye NY dinnan ne😏😏
Masu karatu kucigaba da biyoni😊
Taku a koyaushe
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [4:34pm],[14/12/2015]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
5⃣to1⃣0⃣
Washe gari ya kama saturday ne,ba skul nasrin tun bayan datai sallan asubah ko karatun ma data saba yi batayi ba takoma bacci ba ita ta tashi ba sai wajen 10:00 na safe,ta tashi tayi wanka tasauko kasa.
Mummy tagani ita kadai a parlour sai kuma hayaniyan su najwa data jiwo a dadin yaya naufal,ta durkusa tagaishe da mum dinta sannan ta nufi dakin yaya naufal shima tagaidashi yayinda su najwa ma suka gaisheta,ta amsa cikin sakin fuska,caraf najwa tace Aunty Nasrin kinata bacci har Abba yayi tafiya,yace inkin tashi a gaisheki inya isa xai kiraki,tace ina yaje,Nabil yace kano yaje tace to Allah ya kaisa lfy ya kiyaye hanya dukkansu suka amsa da Amin,sannan ta nufi kitchen taje ta hado breakfast.
Takoma falo tazauna tafara cin abincinta yayinda mummy hankalinta ke kan tv tana kallon tashar MANARA TV,yadda ake baiwa nakasassu kafafu da hannaye,Nasrin ma shidin tafara kallo,tace umma gaskiya Shiekh Abdullahi Bala Lau yana taimakawa Al'ummar musulmai dayawa Allah dada taimakonsu yasa da niyya me kyau sukeyi,jiifa wai harda Christian da shia ma,Mummy tayi murmushi tace nasrin ay amfani ilimin da kudi kenan Allah yaqara musu himma da budi yasaka musu da mafificin alkhairi,nasrin ta amsa da Amin(nima jidda nace AMIN)
Nasrin bayan tagama breakfast duk da dai bawani abinci kirki taci ba tashi tayi takoma daki tafada gado,yayinda tunani biyu suka addabi xuciyarta,Nafarko shine meyasa Taga Aisha a mafarkinta alhali Nazira ce babbar kawarta,asalima bawani magana da Aishan suke ba,Na biyu kuwa shin dagaske ne son NY shi xai kaita ga halaka,in hakane gara tun wuri tasan abin yi.
Can kuma ta tuna ay mafarki ba gaskiya bane,ta tabe baki😏
Tace komadai meye Allah yasa alkhairi ne.
Yinin ranar tayishi ne a daki har mummy ta fahimci tana cikin damuwa,Ta tambayeta tace kanta ke ciwo ta bata magani tasha tai mata fatan samun sauqi.
Da dare
Wayanta ta dauko ta kunna domin yinin ranar qin kunnata tayi,Ay kuwa saqon farko daya fara shigowa wayanta bai wuce na NY ba take taji wani farin ciki at same time baqin ciki,sai hawaye ta goge yayinda tafara karanta message din:
"Slm N-square,me yayi zafi yau najiki shiru,kodai sub ya karene,dama naji ance bashi kike ci kiyi sub din😂to wai dolene chatting din😜inafata kin yini lfy,NY"
Tazauna akan gado tayi dariya ma'ishiya kafin ta bude sauran text din,Tagama budewa tas sannan tai murmushi tace waima mexance da NY ne,saita fara replying kamar haka
"Wkslm,na yini lfya NY,inafata kaima haka,Ay ni in takaice maka sim dina special sim ne,bansa kudi banyin sub,amma haka nake kira da surfing net nonstop,nikadai akayiwa irinshi😎
Ay sub saiku😀"
Tana sending mishi tayi saa yana online ay kuwa sai yayi replying
"Hhhhhhhhhhhhhh
Sannu Zubaida👉🏽😂"
Itama tai replying
"Yawwa Zubairu😏,ya yau?"
haka dai hirar tasu ta cigaba cikin wasa da dariya,Nasrin dai ta tabbata son NY take domin duk sanda take chatting dashi,hatta magana bataso ayimata,saita tsinci kanta cikin nishadi da annashuwa,Anya zata iya rayuwa ba NY kuwa???(ni jidda nace tabbas xakiyi,tunda ba tare kukazo duniya ba😏)
Wannan kenan..
Yau takama monday,Nasrin da wuri suka shirya bayan tayi waya da abbanta takuma turawa NY monday text(monday text😳ni ummu arif nace aiki yaganki yarinya)Sukai sallama da mummy yayinda Yaya naufal ya debesu ya ajiye kowa a makarantarsa shima ya wuce gun aikinsa.
Bayan anfito break ne nasrin ta kira kawarta nazira gefe ta labarta mata mafarkinta,tabe baki nazira tayi tace nasrin Who's this NY please,murmushi nasrin tayi wanda yake kara fiddo da kyawunta sannan tace Nazira I doubt if the combination of 26 alphabet can explain NY,cikeda da mamakin nasrin naxira tace uhmmmm abin naki babba ne,amma zanso in ga wannan NY din daya samu babban matsayi a xuciyarki ko kuwa ma ince a rayuwarki,for the second tym nazira takara cewa nasrin please who's NY,murmushi nasrin takuma yi tace yarinya zancen kikeso(wai anci da Abu farhan ya iyali😜)kinga tashi mu tafi class an ringing bell,Suka tashi suka nufi class duk da dai ba haka nazira taso ba,nima ummu arif nabisu a baya nace Nasrin pls Who's NY,juyowa tayi ta watsamin wani kallo,ay ba shiri nasha jinin jikina,kafa a sanyaye nabar wurin😞
Waye NY???????
Gaskiya sai masu karatu sun biyani xan fadi waye NY,ku gafa daga tmbya taimin kallon raini,xandai bita a hankali harsai munji waye NY😜
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [2:24pm],[13/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
2⃣1⃣to2⃣5⃣
Washe baki Nasim yayi,ban dade da zuwa ba,nazo daxu baku nan shine nadawo,nabil yace kina bacci,nace kada ya tadaki,inkin tashi ma gaisa.
Kakalo wani murmushin dole tayi tace likita bokan turai,hope ka dawo lfy,Allah yasa angama a saa,Ya amsa da Amin cikeda jin dadin maganganunta.
Haka suka cigaba da hiran da mum da naufal,jifa jifa dai nasrin takansa baki,Bayan sun dawo daga sallan isha'i ne xasu je dinning cin abinci,nasrin tayi sama keee,cewar yaya naufal ina zaki😡tace watsa ruwa xanyi,mum tace bawani nan,xuwa dai xatayi tayi hira da maso wani,dam nasim yaji gabansa ya fadi,ita kuwa da gudu tayi daki..
Naufal ne yadawo table din ya zauna yace mum make things obvious to me,Mum ta numfasa tace Naufal ina matuqar tausayawa nasrin,domin da dadewa ta fada son wanda baison tana sonshi ba,ta dade
Tana dakon sonsa,maimakon abin yayi baya sai gaba yake,saidai bata taba sanin nasan halin datake ciki ba,amma ina tayata da addua.
Naufal a sanyaye yace mum waye wannan wanda takeso?shiko nasim mutuwar xaune yayi,ji yayi abincin yadawo mishi kmr magani,Mum tace ba kowa bane illah Nasir,Wanda yake xuwa dinnan,har ku gaisa tace frnd dinta ne,Naufal yace tabbas nagane shi,Nasir na burgeni mum bana fada miki ba,gashi ga dukkan alamu yasamu tarbiya,Allah sarki sis,SON MASO WANI KOSHIN WAHALA,Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi,Mum ta amsa da Amin Nasim ko cewa yayi bro tashi karakani gate natafi kaina na ciwo I need to rest,Mum tace nasim abincin fa,yace mum wlh nakoshi,kwanciya kawai nakeson yi,tace Allah ya sawaqe kagaida hajiyanka,yace to a hasale,naufal ya rakashi yaja mota sai gida.
Dukkansu basu lura da halin da yake
ciki ba,saidai sunyi mamakin tafiyansa.
************
Nasrin result yafito sai murna take,tana dada godewa Allah,ta hada walima a gida ta gayyaci yan'uwa da abokan arziki ciki harda NY.
A filin gidansu akasa canopy da chairs akayi decoration,wurin yafito yayi kyau sosai,Dashike Saturday ne ba aiki har abokan yaya naufal dana dad saida sukazo.
Taro yayi taro,wuri yayi kyau,ga abinci nan iri iri,uwar taro kawai ake jira,
can sai gata tafito sanye cikin doguwar riga kirar dubai yellow ce mai adon ja da baki ajiki saita nade kanta da bakin kashka mai adon yellow ajiki,tasa takalmin vinci da wata yar ubansun purse baqi,tayi simply make up tayi kyau matuqa,tana fitowa wurin aka hau tafi ahaka taje ta dinga gaisar d abokan abba dana yaya naufal da kuma kawayen mum da sauran yan'uwa.
Kafin taje tasamu wurin da aka tanadarmata ta zauna,kusa da ita wani sit dinne anyi shimfidar alfarma kmr nata,bakowa ta tanadarwa gurin ba illah NY domin yace da ita yana hanya.
Nan aka fara walima,Mlm sani shine yazo yafara yayi wa'azi mai ratsa jiki mai taken duniya budurwar wawa,sannan mlm khadija tazo tayi nata da dai sauran mallamai,gaskiya kowa ya qaru sosai,sannan jama'ar gurin sunyiwa nasrin da iyayenta addua sosai,Bayan nan ak fara ciye ciye da shan abubuwan sha,daidai lokacin ne NY yaceda nasrin gashi a bakin gate dinsu,ay kuwa cikeda da zumudin son ganin NY tanemo Nabil tace yaje ya taho da NY,yace lah adda nasrin dama zaizo,nandai yaje shigowa dashi yayinda MC yace kowa ya nutsu domin babban bakon Nasrin xai shigo wanda yataso tun daga wani gari xuwa nan don ya tayata murna,Yana shigowa tareda nabil kowa yayi kabbara yayinda murmushin fuskan NY ya fadada,Nabil yakaisa yagai da abbansu da frnds dinsa sannan yaje yagaida mum da frnds dinta,su yaya naufal da frnds nashi sukazo suka gaisa,yagaida sauran yan'uwa sannan nabil yakaisa mazauninsa tun kafin ya iso ya hangi nasrin azaune ta fadada murmushinta,sai yaga tayimishi kyau da kwarjini,ita ko jitayi kamar taje ta rungumeshi,yayi wani kyau da fresh ga sajensa ya kwanta luf,har yaje yazauna nasrin ta tafi wata duniyar tunani,saida ya matso daf da ita ya hura mata iska saitayi firgit,yar jos tunanin me kikeyine,kinga nafi gayun jos kyau koh😜tasa dariya,tace waima wayace kasa irin kayana yellow shirt,black trousers,watch shoes,answer me😏budan bakin NY yace yanxu nake shirin kiran nabil in akwai boutique nearby ya rakani in sauya kaya,dukkansu suka kwashe da dariya,tace NY baka da dama,nan suka gaisa tamishi godiyan halartar walimanta,NY gaskiya kacika alkawari,ngd kwarai matuqa,yayi murmushi yace haba nassy bby wat are frnds for,common let's cheer up,Nan aka kawo musu abinci iri iri,sukaci suka sha yayinda suketa tsokanar juna,Inka gansu xaka rantse masoya ne,(what a perfect match inji ummu arif👌)yan'uwa da abokan arziki duk sun xaci masoyane sai xuwa suke suna yimusu hoto,wasu suce perfect match,wasu suce romeo and Juliet da dai sauransu,NY dai bai kawo komai cikin ransa ba.
Aka gama cin abinci aka yi pics aka baiwa nasrin kyauta mai yawa,NY ma baa barshi baya ba yayimata kyautar wani sarka da dan'kunne na gold da wani Qur'ani izu sittin da wasu littafai dasuka shafi mata,taji dadi matuqa,iyayenta ma haka.
Nandai NY ya rufe taro da addua,kowa yafara haramar tfya gida ciki ko hardashi,yayi sallama da iyayenta da yan'uwa,har bakin motarsa kirar 4matic ta rakashi,NY ngd sosai,words can't express my gratitude to you,am most appreciative,Allah bar xumunci,yadda kaxo lfy Allah ya maidaka gida lfy,Thanks alot,yayi murmushi yace mrs godia nike da godia,irin karramani da kukayi,nagode ko nassy bby,sai munyi waya,ya daga mata hannu yaja motanshi yayi gaba,ta dade a tsaye tana murmushi kafin tayi cikin gida,shigarta keda wuya saiga cousins dinta sun taho a guje Nasrin kardai shine angonmu,kallonsu take cikeda murmushi yayinda hawaye ya wanke mata fuska😭 sun fama mata inda yake mata ciwo,tashi tayi a guje tayi cikin gida ta haye sama sai dakinta ta murda key,Hasbunallahu wa ni'imal wakin kawai taketa fada,daga bisani ta daga hannu sama cikin shashekar kuka tace Ya Allah ka ciremin son NY a zuciyata na huta.
Ta goge hawayenta taje tabude kofa domin knocking ya dameta,Aisha ce da wata cousin dinta,a tare sukace nasrin pls waye NY????
Tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo,tace ummu arif naganki a labe shigo kuji waye NY,ay da gudu na karaso nazauna,yayinda nasrin tafara da NY........
Kucigaba da bin Jikar nayaya,Mrs Abdul,don jin waye NY???
Ummu Arif💞💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [12:44pm],[28/12/2015]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMIMIN KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
1⃣6⃣to2⃣0⃣
Nasrin exams ya matso har sun fara practical,saboda haka duk wani damuwa tayi kokarin watsi dashi domin tasamu damar yin karatu saboda burinta bai wuce ace tayiwa waec da neco one sit ba,saidai duk watsi datayi da damuwoyinta NY na nan daram a ranta,wannan addua kawai takeyi.
Gashi ya karfafa mata gwiwa sosai don yanaso taci wannan jarabawar,domin duk sanda yashaida mata zaiyi jarabawa adduar datake mishi ko kannensa iyakaci,shiyasa shima baiyi kasa a gwiwa ba wajen yimata addua,domin data fadamishi xata fara exams nasiha da adduar dayayi mata ko yayanta naufal iyaka,kullum saita karanta text dinnan don dadinsa da takeji ga abinda ya rubuto mata nan kmr haka
"Nasrin ina mai matukar tayaki murna don ganinki a wannan matsayi,domin akwai dubu masu so sukai wannan matsayi har su rubuta SSCE amma ba dama,wasu sun fara sunada burin gamawa Allah ya karbi ransu,Wasu basuda halin biya,wasu iyayen naso amma ya'yan sunqi su maida hankali da dai sauran jarrabawa makamanta haka,kinga ko dole kiyi murna muma masoyanki mu tayaki,Sannan kada ki sanya rauni cikin xuciyarki ko wani tsoro ko fargaba kidauka cewa yadda kike rubuta normal exams haka xaki rubuta wannan ma,kuma ki dada addua kan yadda kikeyi,Abune na mai saa,Ina miki fatan farawa lfy da gamawa lfy,Allah yasa ku fito da kyakkyawan sakamako ba sakewa,Allah ya sakawa iyayenku danamu baki daya da gidan Al-jannah..
Bst of luck,NY"
NY ya sake samun matsayi babba a xuciyar nasrin.Ahaka dai har suka fara exams suka gama,Alhamdulillah,sunyi lfy sun gama lfy,Saidai nasrin tace sai sakamako yafito zatayi walima,yan iyayin ajinsu kuwa tuni an shirya walima,ita ko ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,Adduarta kullum Allah yasa suga Alkhairi.
***********
A yaune Nasim Aminu ya diro naija domin ya kammala karatunsa cikeda doki dason ganin nasrin,Direba na dauko sa daga airport yace ya wuce dashi gidansu naufal,yayi rashin saa nasrin ta tafi islamiya naufal baya nan,yagaida hjya ya wuce gida rai duk abace,yana isa dayaga mum dinsa yadda take haba haba dashi saiduk bacin ran yatafi,suka sha hira yaushe gamo,daga bisani ya tashi ya tafi side dinsa wanda angyara mishi tunkan yadawo,yaje yayi wanka sai bacci....wannan kenan...
Nasrin nashigowa gida daki ta nufa,ta kunna wayanta tanaso ta fadama NY cewa tagama exams lfy,domin tunda tafara exams yanayin chatting dinsu yaja baya domin yanaso ta nutsu tayi karatu,cikin saa kuwa taganshi online💃🏻murna kamar me a gunta,
Nan tace mishi
"Slm Ma'abocin tsokana da barkwanci"
Ay kuwa nan yagani yayi murmushi sannan yayi mata reply kmr haka
"Wkslm mallamar tsokana da barkwanci ay koyi muke daku😜"
Dariya tayi sosai tukun ta kara cema
"Zaka fara koh😞,ay ngd,kamantani kwatata"
Dariyar shima yayi tukun yace
"Haba nassy baby na isa na manta dake,nabarkine kiyi karatun exams,kun gama ne???"
"Tace eh mun gama tun last week,muna jiran sakamako,hope kana lfy ka buya abinka,ko kudinka sun zo ne😜 "
Yace
"Hhhhhh kudi tukunna dai,ina lfy wlh,hope kema haka,gskya ina miki murna sosai na kammala exams dinki,Allah yasa kuga alkhairi,Nasrin inaso indan miki wani tuni,kinga ke mace ce,kuma iya gata iyayenki sun baki,saboda haka kada kisanya burin yin wani karatun boko mai tsayi,darajar ya'mace gidan mijinta,don haka inhar iyayenki sunyi miki maganar aure ki amince ki fidda mijin aure don samun kwanciyar hankalinki da nasu domin aure bai hana karatu muddin mijinki xai amince kicigaba,inma karatun suka miki maganar kicigaba,ki fara,sai kiyi aurenki kina cikin yi,amma kada kice saikin gama zakiyi aure,sannan kicigaba da xuwa islamiyarki domin ilimi addinini sau dubu yafi ilimin boko musamman gake diya mace,wacce wataran xaki xama maiyiwa ya'ya tarbiya,don haka ki dage gun neman ilimin addini shine abin ado ba boko ba,boko nan duniyane kawai,amma na addini na lahira ne,Sannan ki xamana mai cigaba da yiwa iyayenki biyayya,domin sun cancanci komai a gunki,infact u can even sacrifice your happiness for theirs as a good child,Iyayen sunsha gaban komai,pls ki nutsu kada ki biyewa kawayen xamani,duk da dai nasanki da wayau😜
Daga karshe ina miki fatan alkhairi a ko yaushe kmr yadda kikemin,Nasrin me cin bashi tayi sub😂😂😜"
Lokacin da nasrin tagama karantawa saida tayi kwallah,ji take kmr tace NY kai nakeso,amma takasa ta share hawayenta tayimai reply kmr haka
"Bansan iyakar godiyar dazanma ba NY,gaskiya kacika
🌹Aminin kwarai🌹
Nagode sosai,Allah ya saka da alkhairi,Fatan dakaimin,inaima fiye dashi,Ngd,Ngd,Ngd,Allah bar xumunci,Zanje nataya mum aiki a kitchen,ltr"
Murmushi yayi daya karanta yace Nasrin sarkin godia
"Nassy beb meye na godia,wat are frnds for,common karki damu,ki godewa Allah,agaida mum,ltr"
Haka dai nasrin ta kashe data d tasauka a whatsapo cikeda kewar NY,badon taso ba saidan inta cigaba da hira dashi a yadda takeji a tym dinnan xata iya fallasa sirrin xuciyarta gareshi.
Jiki a sanyaye ta tashi ta gangara parlour,amme wazata gani😳😳😳
NASIM,saukar yaushe ta furta a sanyaye....
Kubiyo jikar Nayaya don jin ya zata kaya😜
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [12:28pm],[18/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
3⃣6⃣to4⃣0⃣
A bangaren nasim kuwa,shirun da yayi bawai ya hakura da maganar nasrin bane,saidai mugun nufin daya kudirta yimata abisa bin gurbatacciyar shawarar abokinsa Bahar.
Hajiya ta bashi hkr acewarta wani hanin ga Allah baiwa ne,Domin bataso babansa yaji maganar nan because xai iya batawa da amininsa akan wannan maganar,amma me???
Nasim tuban muxuru yayi jira yake kawai Dad dinsa ya dawo ayita ta kare..
Wannan kenan
A yaune gidansu nasrin suka tashi da murna da farinciki kasancewar Nawas ya kammala karatunsa yau xai diro Nigeria yayinda Abba da naufal suka tafi Kaduna daukosa.
Mum dasu nasrin kuwa ana kitchen anata shirya abincin saukar Nawas,Nasrin ta xage domin tafi shaquwa da nawas akan naufal,nawas nasonta matuqa,shiyasa itama take sonsa,saidai tana baqin ciki saura kwana uku ta tafi skul.
Karfe biyar daidai na yamma su Abba sukay iso,suko su mum tun 4 suka kammala komai,gida sai qamshi yake,kowa yayi ado kmr masu xuwa biki😜Nasrin tayi ado cikin riga da wando pink da black,ta gyara gashinta tasa band pink,sai tayi kyau tafito kmr yar larabawa.
Ay kuwa tanajin horn itane tafara fita a guje,Tun kan naufal yayi parking nawas shima yafito ya taho gun yar kanwarsa abin kaunarsa,ya rungumeta qam kmr wani xai kwaceta,saiga su najwa da nabil ma,duk suka rungumeshi suna murna,nawas saida yayi kukan farinciki yace"indeed no place like home😊"
Nan suka shiga cikin gida,Abba yace su nasrin yau an mance abba,nasrin tai murmushi😊tace Abba kenan xancen kakeso.taje tahadama nawas ruwan wanka,tafito mishi da kaya mara nauyi sannan tafita taje suka shirya abinci bayan sunyi sallan isha'i.
Nawas nafitowa daga wanka yaga kayanshi already anfito mishi dasu,ga dressing mirror dinshi anshirya komai yayi murmushi yace lil sis I love you😘.
Kowa yafito ya hallara a Parlour domin yauma baa dining xaa ciba a tsakar parlour aka baje komai,Nasrin na maqe da nawas acewarta shixai bata abinci a baki yadda yake mata da,Abba yace Nasrin wai bakisan kin girma bane,tace Abba jst for today,nawas ma dariya yayi yace mudai kar a samana ido,Ahaka yadinga ba nasrin abincin abaki shima yanaci har suka koshi,naufal koh ya qula matuqa,yace da nawas tadai kusa tafya skul bare ka sangartar da ita irin da😏
Nawas qala baice mishi ba,mum na hira da Abba,shiko naufal da najwa da nabil suketa hirarsu,nasrin kuwa da nawas,sai kusan 11 suka watse a parlour nasrin ma bacci tayi,nawas ne yakaita dakinta ya shafeta da addua shima yayi nashi dakin.
Washegari sai ten ya tashi,yayi wanka yashirya yayi breakfast,yace su nasrin su shirya ashiga gari dashike Saturday ne,ay bada jimawa ba suka shirya sukaiwa umma sallama suka fita abinsu,nasrin ce a gaba sai najwa da nabil a baya yayinda dukkan su sukai dressing cikin milk and Brown,sunyi kyau abinsu,musamman nawas domin duk gidan shida nasrin sunfi kyau.
Yawo dai sunsha shi,sunje recreational centers iri iri,banda gidajen abokan nawas,sukai shopping sai sukayo gida ana kirayen kirayen magrib.
Ay kuwa sunayin dinner sai bacci dukkansu.
Washegari sunday Ranar da nasrin xata tafi makaranta,dama tuni mum tashirya mata komai,ta tashi jiki duk a sanyaye,tayi wanka tayi breakfast sama sama tashirya cikin wata doguwan riga casandra,tayi kyau duk da batai makeup ba,Su yaya naufal suka sa kayanta cikin mota yayinda idanunta suka kawo ruwa,taje tayiwa mum sallama bayan tasha kuka har saida tasanya mum kwallah,mum tayi mata nasiha sosai tafito nabil da najwa suka yo kanta da gudu suna kuka,ta rungumesu itama kukan take,dakyar naufal ya cirota daga jikinsu yasata a mota,suka ja suka tafi.
Naufal ke tuqin,dad na gefe nawas da nasrin na baya,nawas nata aikin lallashi,har mutuniyar tai bacci.
Cikin dan baccin ne datayi ne tai mafarkin NY yanata mata murmushi,itama murmushin takeyi mishi,ya matso daf da ita yace nasrin yau xan sanar miki abinda kika dade kinaso kiji daga gareni NASRIN ina......
Firgit ta mike,nawas ya riketa yace lil sis lfy,tai mishi murmushi tace eh lfy lau,A xuciyarta ko dadi taji gameda mafarkin nan ko kuwa me,itada tasan duk da ta nesanta kanta daga NY,tasan cewa sonshi na nan daram a xuciyarta,Shin NY zai iya zama nata,wata zuciyar tace eh nasrin,ay baa yanke kauna da rahamar Allah,Nasrin ta numfasa tace wato soyayya halittace,Ya Allah kazaba min abinda yafi alkhairi gareni,saiji tayi duk yan motan sunce amin,ashe xancen xuci yafito fili,Saitayi lamo kamar mai bacci
Sadness is
.
.
.
When the person you love,love someone else💔😢
Shin son NY na barin nasrin,me nasim yake shirin mata,kodai suna aure da NY,don jin yadda xaa kaya,kucigaba dabin jikar NAYAYA,Mrs Abdul 😊
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [9:52pm],[19/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🀼 Na,
Hauwa Hassan Nayaya
4⃣6⃣to5⃣0⃣
Zeenat ce cikin wata irin banxar dressing batada da maraba da irin ya'yan christian dinnan,nasrin mamaki ne ya kamata sosai,xeenat ina xaki a daren nan???cewar nasrin
Wlh wani birthday din friend din Zaks zani,karki kulle kofa,inkin gama ki kwanta,nina wuce bye✋🏼
Nasrin sake baki tayi takasa cewa uffan,lallai xeenat tana cikin rudin duniya Allah ya shiryata da masu hali irin nata.
Shirya komai dazata bukata wurin xuwa skul gobe tayi,Tai Addua ta kwanta cikeda kewar yan gidansu da tsantar son NY.
************
Nasrin batasan yaushe xeenat ta dawo ba,ita dai ta tashi sallan Asuba taganta,Bayan tai sallah tai Karatu da Azkar,kitchen tashiga tahada breakfast tafito tai wanka,sannan tazauna taci abincinta ta koshi tayi dressing cikin wata jar doguwan riga hade da mayafinta tadau jakarta ta fita.
Tafita kome ta tuna kuma ta koma taje ta tashi xeenert,da kyar ta tashi domin daren jiya tasha syrup shiyasa ta makara,Nasrin sallama kawai ta mata tayi cikin makaranta.
Tana isa bakin lecture hall din saida ta tsaya tayi addua takuma godewa Allah da lecturer din bai iso ba,Ay kuwa tana shiga bayan tazauna saigashi duk da dai a tsarge take bisa ga kallon da students din ke mata,amma kuma saita basar tacigaba da sauraron lectures abinta.
Yinin dai sunyi shine a gajiye from one lecture hall to another,kasancewarsu na sabbin dalibai dole su gaji.Sai 4 suka kammala lectures din ranar,Agajiye ta isa hostel ta bude daki kasancewar xeenat bata nan, tea kawai tasha sai bacci.
Bata tashiba sai 7,da gudu tasauko tayi toilet tai alwala tayi sallah tana kan sallayan aka kira isha'i tayi tukun ta tashi ta nufi kitchen ta daura indomie ta nufi toilet again don yin wanka.
Tafito taci abinci tayi waya dasu Abba sannan tayi bitan karatun ta,11 nayi ta kwashe books din tahau gado tai addua sai bacci har lokacin ba xeenat ba alamanta.
***************
Ahaka nasrin tacigaba da rayuwarta cikin jami'a,duk nacin yarinya hakuri take domin nasrin taki ba Kowa fuska shiyasa batada qawa,inbanda xeenat da Daki ya hadasu gashi tana iya kokarinta na nunawa xinat cewa rayuwar data dauko ba mai billewa bace,amma xinat turn deaf ears to all that nasrin is saying to her,amma duk da haka bata gaji ba tana cigaba fatanta kullum Allah ya shiryata.
Kullum sai tayi waya da mahaifanta da yan'uwanta,NY kuwa yazo sau biyu kawo mata xiyara,xuwansa na biyun ne yayi mata sallama xai tafi kasar waje don yin wani two year course,Nasrin tayi mishi fatan alkhairi da farawa lfy da gamawa lfy,Allah kuma ya kikaye hanya.
So tun sanda ma yatafi sau daya kawai sukai waya because yanxu bata chatting saita koma jos,ita nesantar ta ma dayayi yamata dadi,Amma duk da haka son NY na nan daram xuciyar nasrin😢💔
A haka nasrin harta shafe shekaru biyu a skul tashiga na uku.
In anyi hutu brothers dinta ke xuwa daukota sumaida ta,Nasrin an waye😜in xata koma skul ba kuka😭da wasa da dariya😀take barin gida.
Bangaren Nasim kuwa ya zauna ya zurfafa tunani,inhar ya cutar da nasrin Allah bazai barsa haka ba gashi xai bata zumuncin iyayensu dasuka dade sunayi,bayaga haka gashi da sisters mata,sakayyar nasrin xata iya sauka kansu ko daya daga cikinsu😞
Da wannan tunanin nasim ya janye duk wani abu daya kudirta yiwa nasrin,sannan yayi alkawari bazai sanar da dad kan maganar ba,zai hakura Allah ya bashi mafiyinta👏🏼(ko kaifa nasim inji jidda)👍🏼
Nasrin ce xaune a daki tagama assignment kenan xata tashi ta daura girki saiga xinat tashigo a buge,ita tarasa xinat wata irin diya ce asalima batasan me take karanta ba.ta tabe baki😏tace Allah ya shiryata ta taimaka mata tahau gado sai bacci.
Exam yazo nasrin karatu take ba kakkautawa,cikin ikon Allah tafara a saa tagama a saa,Nawas yazo ya dauketa randa sukai hutu,Murna agun nasrin kmr me domin almost four month kenan rabonta da gida.
Suna isa cikin jos saiga kiran NY cikeda xumudin sonjin muryarsa ta daga ji tayi yace slm,nassy bby gani a bakin hostel dinku kifito😳😳😳
Da gaske kake NY ceawr nasrin,,,,,,,,,
Ina fata masu karatu suna jin dadin karatu,kucigaba da saurarona,taku a koyaushe Jikar NAYAYA,Mrs Abdul.
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [9:41pm],[13/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
2⃣6⃣to3⃣0⃣
Asalin sunansa Nasir Yahya,haifaffan dan garin kaduna ne,shine da na farko a wurin mahaifansa,shiyasa suke matuqar sonsa,yanada kanne maza da mata,Bangaren tarbiya kuwa,koni daba gari daya muke ba na jinjinawa mahaifansa ballantana ace gari daya muke,indai tarbiya ne kam👌Allah yasakawa mahaifansa da gidan Al-jannah,domin hakikanin gaskiya yasamu tarbiya ba kadan ba.
Bangaren ilimin addini kuwa sai sam barka👌Domin NY mahaddacin Qur'ani ne da wasu littafan addini da dama,anma har yanxu nema yake,as it was said"learning never end"Bangaren bokon ma baa barshi baya ba wooo domin hes a smart philosopher,shiyasa yake matuqar so da girmama mahaifansa,domin sunyi mai dukkan gata.
Bangaren hali kuwa,A iya sanina dashi baida wani hali mara kyau,Chocolate colour ne shi,baida tsayi sosai,yanada dara daran idanu sannan ga saje daya kwanta luf gefen fuskarshi,bakinshi da hancinsa👌baida kiba sosai inyayi dariya gefen kumatunshi ya lotsa hakan na matuqar karamishi kyau,yadai hadu kmr jar fure🌹,ma'abocin wasa da dariya ne,zai fadama gskya komin dacinta,zai baka shawara ta gari,zai jaki da wasa da dariya don rage miki damuwa,inkina cikinta,uhmmmmm sisters to cut this long story short the combination of 26 alphabet can't explain NY😊😊😊
Nasrin ta goge hawayen fuskanta tace haduwata dashi nafari ko ince ranar dana fara ganinsa. .....
Tsaye nake a bakin titin tudun wada lokacin gabannin magriba narasa keke napep ga wani baqin hadari,hankalina yatashi matuqa,ga wayana ba charge bare in kira gida yaya naufal yazo yadaukeni,ina tsaya inata tunanin yadda xanyi har bansan sanda mota ta tsaya a gabana ba.
Ji kawai nayi ana yam'mata lift ne,Na leko nace aa mlm ngd,har yayi gaba anfara yayyafi sai gashi yadawo,yace sister pls kishiga i mean u no harm,I just wanna help,ga ruwa gaki mace wurinnan is not safe,kishiga kidaina jan aji karya tsinke,Nayi murmushi nashiga yaja muka tafi,saida yazo terminus yace ina muka nufa nace dogon dutse yace to madam shiru shiru,murmushi nayi nace kaikuma ogan surutu ba😃
Yace am Nasir Yahya,ni dan kd ne jiya naxo jos gobe xan koma,nasrin tayi mamaki kwarai dataga yasan jos din😏 tace am Nasrin Nazir,ni yar jos ce,amma dai kana zuwa jos sosai ne,yace well gskya saita kama,tace ok nice meeting you,yace same..
Nayi tamishi nuni har kofan gate dinmu yayi parking,kafin na fita saida yamin nasiha,amatsayina na diya mace nadaina kaiwa dare a waje its a risk,nace mai sam bankaiwa dare yauma dai kaddara ne kawai,namai godiya muka exchanging phone numbers,na mishi fatan alkhairi nashige gida.
Mafarin friendship dinan kenan da NY wanda daga baya kyawawan dabi'unsa,halinsa suka sa kawacenmu ya rikide min yazama tsantsar so,uhmmm son maso wani koshin wahala,To su ummu arif,nana,aisha yaudai a sararamin a tayani da addua tunda kunsan waye NY😊😢
Jiki a sanyaye muka amsa da eh,kowa yayimata adduar alkhairi muka fita muka barta don xata gabatar da sallah..
Yan walima duk sun watse har an gyara gida,yayi shiru kmr baayi taro dazu ba,Nasrin ko ana nan ana bacci bayan ta kira NY tamai ya hanya dafatan isa lfy😞
Bata tashiba sai bayan magrib,ba shiri tayi toilet tayi wanka da alwala tafito tai sallah sannan tadan murxa cream tazira wata doguwan riga ta sauko kasa,da gudu ta isa gun Abba ta rungumesa harda bashi peck a cheek,nanta fara kwararo mishi godiya,yace nasrin its enough,Allah kara ilimi,tace amin.
Abba yayi gyaran murya yace nasrin inaso in tambayeki ki fadamin gaskiya,wanda yazo gunki dazu meye alakarki dashi,a sanyaye tace abba abokina ne,yace good ina kika sanshi,nanta labarta mishi haduwarsu ta fari,yace mata tashi kije,dama ya zata soyayya ce tsakaninsu yace ya turo magabatansa ya mata aurenta kowa ya huta domin shine darajarta tunda yasan bata da tsayayye domin bata sauraransu.Amma yanxu kawai abin daya dade yana saqawa ransa shi xai faru wato ya hadata da NASIM😳😳😳
Tab nasim,anya nasrin xata amince kuwa,muje xuwa..
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [10:49pm],[13/1/2015]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
3⃣1⃣to3⃣5⃣
NY bai isa gida ba sai 7:00,Yaje yayi parking yafito ya bude baya saiga kaya lodi😳ya bude yaga souvenirs ne na nasrin,yayi murmushi yace nasrin harda wani wahala,nan yakira kannensa suka shigar dashi parlour,yana shiga ya baje a parlor yace hajia sannu da gida nasameki lfy,tace lfy lau Nasir ya hanya,yace Alhamdll,Hajia tace saika kirata kace mata ka sauka lfy,nan take ya ciro wayarshi ya dialing number dinta ringing biyu ta dauka,yace nasrin gani ga hajiyata,tace alhamdll,sannu da hanya,ina kara godiya,yace don't mention,shine harda wani samin souvenirs koh,tace ay ni bakai nabawa nasu hjya ne,yace hhhh hakane koh to shikenan,tace agaishesu sosai,yace zasuji ngd,saida safe,tace mukwana lfya ahuta gjya.
Yace hjya tana gaisheku tace muna amsawa,yace hjya wlh iyayenta masu mutunci,kinga karramani da akayi kuwa,abin sai godiya,hajiya tai murmushi tace ay hakan nada dadi,yace hjya ga souvenirs ni xanje nai wanka nabi gado saida safe,tace to nasir akwana lfy ahuta gjya,yace ngd hjya,ya nufi side dinshi.
Washegari kuwa Abba ne ya tarasu nasrin a parlour,ita,mum,naufal,yayi gyaran murya ya bude taro da addua sannan daga bisani yace nasrin inaso in hadaki aurene da Nasim,NA...SI..M nan take ta sume,mummy da naufal suka yo kanta,abba kasa komai yayi don mamaki,aka yayyafa mata ruwa ta farfado tanata surutai ni bansan nasim,aurensa kmr rabani da raina ne,wlh xan mutu kafin auren,saida naufal yayita mata addua kafin nutsuwarta ta dawo mata,amma hawaye bai tsaya ba,Abba yace nasrin baki sonshi ne,takasa cewa uffan,yace tashi kije,ta tashi tana tangadi domin jiri ke dibarta naufal ne ya riketa har daki,Abba yace hajiya inaga asa mata admission tafara karatu har Allah yakawo mata wanda takeso,hajiya tace Allah zaba mafi alkhairi ta tashi ta shiga kitchen,dad yayi hakanne domin baison yayi mata auren dole ko auren biyayya,tunda auren dole ba kyau a musulunci,yafiso tayi auren so da kauna,ya numfasa yace Allah zaba mafi alkhairi...
Nasrin taji dadi da Abba yafasa aurenta da nasim,ta sawa ranta salama cewan NY ba nata bane,kullum kokarin cireshi arai take tana adduar Allah yabata wanda yafishi saida tasan"first love never dies"
Alhamdulillah ansamata admission a Kaduna state university inda aka bata gynecology,bataso yin karatu a kd ba amma ba yadda ta iya,Tafara shirin tafiya kd,garin masoyi💔😢 dama baya nisa.
Nima jidda ku rakani garin masoyina saudiya ne😜😜
Muje xuwa....
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [10:58pm],[19/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
5⃣1⃣to5⃣5⃣
NY yayi murmushi yace kinji yar'kauye,wlh da gaske nake,A sanyaye tace NY ngd da kulawa Allah bar xumunci,Am sorry to say yanxu muka shigo cikin jos
Yace serious,tace wlh serious,yace ok no probs,hope kun isa lfy,barin wuce gida,Ahuta gjya my rgrds to all at home,tace lfy lau,ngd sosai,my rgrds too,bye....
NY yaja motanshi yayi gida,dama ya kawo mata tsarabarta ne domin two weeks kenan da dawowansa ya kammala course din dayaje yi yadawo gida Nigeria.
Nasrin sai duk taji ba dadi da tasan da xuwan NY ay data daga tafiyanta domin tanason ganinshi sosai don ta dade bata ganshi ba amma ba yadda taso haka Allah ya nufa....Dasuka isa gida ma mummy batanan anyi haihuwa a makotansu tashiga,tea kawai tasha tai sallah da wanka sai bacci.
Ba ita ta tashiba sai gabannin maghriba tasauko parlour ta hangi nawas a zaune ay da gudu taje ta rungumeshi💃🏻💃🏻💃🏻
Yace aa lonely sis yaushe a jos,tace kajishi kmr bakasan da zuwana ba,dariya yayi yace sis kin rame,tace uhmmmm bro kenan boko ba wasa ba fa dole na rame,na missing dinka fa hope kana lfy,yace lfy lau,nan sukayita hira abinsu cikin jindadi da annashuwa.
Ahaka mummy tadawo ita da naufal suka taddasu suna hira budan bakin naufal cewa yayi yau zaa kwana ana hira kenan,nawas yace fada da ihu ka kara da wayyo,nan shima yazauna aka cigaba da hiran dashi...
Nasrin tace bro naufal yaushe xamusha biki ne,yace yarinya very soon nasamo wata yar india,ita da nawas dariya kawai suka dinga yimishi😂😂😂 saida sukayi mai isarsu tukun sukace yaya naufal angon yar india,duk dai kyanta bata fimu ba nida nasrin,tabe baki naufal yayi😏yace kwadai ji dashi nabar muku parlon😏.
Ahaka Nasrin tagama hutunta nawas yamaidata makaranta cikeda kewar yan'uwanta.....
Zaman Nasrin da zeenat dai abin bawani dadi,acewar xinat nasrin na takuramata da Allah yace Annabi yace,tun daga wannan lokacin bata kuma ce mata uffan ba saidai suna gaisawa,sannan nasrin na mata adduar shiriya...
Wata ranar jumma'a nasrin ta fito daga hostel xataje kasuwa,ta tare keke napep tahau.suna cikin tfya daidai wani roundabout wani babban mutum yazo zai tsallaka tsausayi wanda baa sa mishi rana wata mota ta bugeshi,tana bugeshi tayi gaba a guje don kar a kama mai tukin.Mutumin yanata xubar da jini amma yan gurin ba wanda yayi yunkurin kaisa asibiti sundai xo wurin sun tsatsaya,Nasrin hawaye nazuba a idonta ta nufi gurin,tace su matsa yayan baban tane,xata kaishi asibiti kowa yabar wurin,ba shiri munafukan suka bar wurin🚶🏻🚶🏻ana haka saiga police sunxo nasrin tai hamdala suka sashi motansa nasrin ta figi motar sai asibiti suka bita a baya.
Suna shiga asibiti dashike akwai police sai aka karbesa akayi ciki dashi,nasrin tasamu wuri tai parking motan hankalinta a tashe ta shiga ciki,taje tana takai kawo a bakin kofan dakin dayake😭😭hawaye nata bin kuncinta,jitake kmr Abbanta ne yayi accident dinnan,tana nan tsaye saiga wani doctor yafito yace madam ke kika kawo patient dinnan,tace eh nice,yace alhamdulillah mun dressing wound din yasamu bacci but yana bukatar jini domin yazubar da jini dayawa.
Batare da wani tunanin ba nasrin tace doctor aduba nawa in xaiyi a diba a karamishi,takareshe maganar tana hawaye,doctor yace kiyi hkr madam,he'll be fine,muje a gwada jini koh,ya wuce tabishi a baya sukai hanyar lab......
Waye wannan patient din?
Shin Ana karamishi jinin nasrin kuwa?
Allah sarki nasrin duk tayi taimakon nan ne domin Allah,domin indai tausayi da taimako ne ita dai sam barka👌,
uhmmmm kucigaba da bin jikar NAYAYA,don jin cigaban
🌹AMININ KWARAI🌹
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [7:54pm],[18/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Nasrin tunda tayi lamo a cinyar nawas bacci ma nauyi yayi gaba da ita,dama daren jiya batai wani bacci ba tunani iri iri sun addabi xuciyarta.
Sai 1suka isa kaduna,suka tsaya gidan wani abokin dad dake unguwar dosa,zasuyi sallah suci abinci sai su kaita makaranta suma su dau hanya kar dare yayi musu a hanya.....
Nasriiiiin kitashi mun iso,ahankali ta bude ido ta kalli yayan nata bro har mun iso,yace yess har su dad sun shiga kitashi mushiga,gidan friend dinshi ne xamuyi sallah muci abinci sai mu kaiki skul.
Amma bro nawas shine koka tasheni muyi hira koh😏
Uhmmm in all indication jiya lil sis bakiyi bacci ba so dats y na barki ki rama na jiya.Tafito ya kulle motan,yace sis before we enter please could u jst tell me in a brief who's NASIR??
😳😳😳tears,meyayi xafi lil sis,I didn't mean to hurt u,am sorry koh,but its not normal sis daga magana sai kuka,something is hidden somewhere,ya share mata hawayenta cikeda mamaki,Nasrin tayi😊tace bro nawas NASIR is a friend,uhmmm its a long story,wani lokaci we would talk about it...
Ok sis ina miki fatan alkhairi.......Tace yaya nawas duk cikin yan'uwa kafi sona nima nafi sonka,I can sacrifice my happiness for your own,I can risk my life to save yours,Thanks alot,I will always count on you my special brother😘
Nawas har cikin ranshi yaji dadin maganganun nasrin,afili kuwa murmushi yayi wanda ke kara mishi kyau yace sweet sis yaushe kika iya magana haka😜Ashe ni dan lele ne,Ngd sosai sis,I luv u much more😘
Mushiga karsu abba sujimu shiru tayi gaba yabiita abaya yayinda tausayinta matuqa ya kamashi domin yaga son Nasir tsantsa cikin idon nasrin,saidai yasan taimako daya dazai yi mata shine Addu'a.
Bayan sunyi sallah sunci Abinci sukai sallama da friend din dadi da iyalansa sai makarantsr su nasrin.
Basu dade ba suka isa,sukaje suka kammals mata komai tukun suka rakata hostel,su yaya naufal suka shigar mata da kayanta,ba laifi wurin yayi su biyu a dakin kowacce da bed dinta da wardrobe,sai toilet da kitchen👌
Nasrin dai tana mota tanata cin uban kuka,Abba ne ya leko yace nasrin maza ki bude kunne kiji ni....
NASRIN a iya sanina dukkanin tarbiyar da akeso iyaye nagari su baiwa diyarsu mun baki,Sannan ki daina kuka ki maida hankalinki ga abin da kikazo yi,almost everyone had gone through dis stage abd now here we're,don haka ki mance batun kuka.
Nasrin kina wani wuri da zaki rayuwa ne cikin tsantsar tsoron Allah da tausayin mahaifanki,domin bakida me saki bame hanaki,Saidai kisani Allah na kallon,don haka kiji tsoronsa ki tausaya mana ki rike mutuncin da darajar ki na diya mace,Banda shakku kan halayenki nasrin amma bansan wasu mutane zaki fara mu'amala dasu,don haka ki yawaita neman tsari daga sharrin xuciya domin bata da kashi sai nama"a wani hadisi akace idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru,haka zalika idan ta baci,dukkan jiki ya baci"kinga koh neman tsari daga baccinta dolene,Nasrin ki nutsu kiyi karatu domin shi ya kawo hakanne kadai farin cikinmu,banda indecent dressing,banda hulda da kawayen banxa,banda yiwa mlmai tsiwa,kiyi xaman mutunci da amana da kowa,kiyi amfani da iliminki na addinin da kike dashi don inganta zamanki a wurin nan,a karshe una miki datan alkhairi,Allah yasa ki fara lfy ki gama lfy,yabada abinda akazo nema ya kade fitina.
Tunda Abba yafara magana nasrin tayi shiru tana sauraronsa,bayan ya gama tafara kwararo mishi godiya yayinda kwalla yafara bin kuncinta,yaya naufal da yaya nawas baa barsu baya ba saida sukayi mata nasu nasiha,ta musu godia tai sallama da Abba da naufal yayinda nawas ya rike mata hannu xai mata rakiya ixuwa dakinta.
Har cikin dakin ya kaita yabata muhimman takardun da zata bukata da kuma atm dinta sannan sukai sallama har saida tasashi kwalla,a sanyaye yafito yaje yasamu su Abba suka dauki hanyar jos,nasrin na kallon motansu ta window har saida ta bace mata tukun takoma kan gado tazauna tayi tagumi.
Tayi xurfin tunani har batason sanda room mate dinta ta shigo ba jitayi kawai an hura mata iska a fuska firgit tayi tadawo hayyacinta,Wata yar budurwa tagani tasha ado cikin wasu matsatsun riga da wando tasa band a kanta,yarinyar dai ba laifi tana dadan kyau sai wani saurayi a bayanta,fari ne kawai ya gyarashi.
Tace da Nasrin ga dukkan alama kinsha kuka,parent dinki basu dade da tfya ba I guess,nasrin ta gyada kanta alamar eh,tace sai hkr,Anyway am ZEENATU ZUBAIR ur room mate sauka na kenan,xaki iya kirana da Zeebby ko ZeeZaks,meet my hubby Zaks.
Nasrin wacce tunda zenat tafara magana tacika da mamaki ta gaishe da zaks din ya amsa fuska ba yabo ba fallasa,tai murmushi tace am NASRIN NAZIR
Woow nyc name cewar xeenat,nyc meeting u,nasrin tace same,Zeenat taiwa saurayinta rakiya tadawo,Nasrin baki bazai rufu xeenat ina iyayenki?saurayi yakawoki skul,xeenat ta tabe baki😏suna nan,kawai shi nakeso ya kawoni,Nasrim tace fine.
Tare suka tashi kowa ta gyara kayanta,sannan suka shiga siluka gyara kitchen,nasrin ta wanke toilet tai wanka tafito tahada corn flakes tasha,tukun tai sallan isha'i,,,,,,,,Ta fito da wayarta ta kura mata ido kmr maison gano wani abu ajikin wayar,yau kusan wata uku kenan rabonta da kunna waya☎tun bayan walimarta da sati daya data kashe wayarta bata kuma daukota sai yau.
Ta kunna wayar ta dialing number nawas ringing daya yayi ya picking,Hello lonely sis,shine kikaki kunna waya don kina fushi damu ko kiji ya muka isa koh,
Murmushi tayi tace bro wato har sabon suna kasamin wai"lonely sis koh😞 "
Ngd,kamanta wayan ya jima akashe yanxu na kunna nadan shirya kayane nai dan gyare gyare hope kun isa lfy,
Yace yeah lfy lau jst missing u sainaji gidan so empty,😊murmushi ta kuma tace bani su Abba,nan ta gaisa da kowa na gidan harda mum,suka kara mata nasiha daga bisani sukai mata sallama badon taso ba.
Nan tafara ganin messages nata shigowa,wai tunkan ma ta bude whatsapp rabin messages din ma na NY saina skul frnds da Nasim.
Messages din NY kawai ta bude,taji dadi matuqa sosai domin NY na sonta matsayinta na friend nashi,wani text dinshi nema yabata daria sannan yayimata dadi
"Nasrin kinsan halin dana shiga kuwa najinki shiru,ay sai inyi tunanin ba lfy ba,No call no text,nothing nothing,wayanki a kashe for more than a Month,haba nassy bby,haka ake aminta gskya banji dadi ba,ohhh kodai kinsai da wayar ne kinsha gullisuwa😜,Pls duk sanda kika kunna wayarki give me a call hope shirun alkhairi ne,in kuma naji shirun is 3much xaki ganni a jos,NY"
Nasrin ta dade tana karanta text din,sannan ta dialing mumbern shi ringing biyu yayi taji ya picking
NASRIN:Salamu alaika Aminin nasrin
NY:😏ay nayi fushi,haba nasrin meye duniyar haka ake aminta???kin kyauta,nasan matsayina agunki,ya kike ya mutan gida?
Duk sai nasrin taji ba dadi,lallai NY ya damu da ita,tunda tasan yanada gskya,tabbas hakikanin gaskya yake fada mata
NASRIN:👏🏼 ayimin afuwa,nasan nai laifi but kaji uxuri na wayana na nema narasa,gashi ban hadda number din ka ba,sai shekaran jiwa waccen ina hada kayan skul naganta,amma ban manta kana raina,mutanen gida kowa lfy,ina kd nazo karatu a KASU yau su Abba suka kawoni,ina fata kaima kana lfy da muten gida,
NY:uxuri rejected😜kowa lfy nima lfy,Eyye yarinya anxama yar jami'a,Allah ya taimaka ya kade fitina Insha Allah a weekend zanxo
Nandai suka shafe kusan awa suna hiran yaushe gamu,daga baya sukai sallama baa san ran nasrin ba,,,,, ,
Juyowan da nasrin tayi wa zata gani😳😳😳😳
Kuci gaba dabina masoyana don jin ya zaman nasrin da xeenat zai kasance,taku a kullum Mrs Abdul.
Ummu Arif💞
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [11:45pm],[21/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
5⃣6⃣to6⃣0⃣
Bayan likita yagama gwaje gwajensa ya tabbatarwa da nasrin cewan zaa iya sawa patient din jininta,batare da wani fargaba ba nasrin tahau gado takwanta tace mishi bismillah,Ba musu doctor yafara diban jininta.
Tana nan kwance tanata tunanin irin halin da wannan bawan Allah ke ciki,can saiga likitan yashigo yazo ya xare syringe din da alluran yace tadan kwanta tukun yadau jinin ya fita.
Yaje yasamishi yayinda yagyara mishi kwanciya yana sa ran inhar ya farka komai xaixo da sauqi.
Nasrin na kwance,can ta dubi agogo taga biyar saura,ay kuwa taji hankalinta ya tashi,Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun kawai take furtawa,yanxu ya zatayi tasan yan'uwan wannan bawan Allah ga dare nayi ba abin takwana ba inya tashi ya sanar da ita gidansu😞
Tana dai kwance tanata saqa da warwara can kawai saita tuno da motan wannan bawan Allah,ay ba shiri ta tashi tadauki jakarta ta bude ta fiddo da key din ta nufi waje yayinda jiri ke dibarta tana isa wajen motan ta bude ta fara dube dube cikin saa kuwa taga wayanshi tadauka,taga 2 missed call"Hajiya"nan da nan ta dialing number din ringing daya biyu aka picking.
Assalamu alaikum,Nasrin a sanyaye tace wa'alaikissalam,sai kuma taji ance Alhaji,sai tadanyi jim tace bashi bane,sai aka kuma ce to ina yake???cikin murya me kama dana kuka ta labartawa hjya abinda daya faru tafada mata asibitin dasuke,Innalillahi wa inna ilaihirrajiun shine abinda hjya taketa furtawa,tace ma nasrin gasunan xuwa yanxu ta ending call din.
Nasrin ta rufe motan takoma ciki rike da wayan a hannunta taje dakin da patient din yake tazauna daga waje dashike kofan na rufe,kuma private ward tace akaishi,da kudin dazata kasuwa duk ta biya kudin asibitin beside wannan baima dameta ba burinta kawai Allah bashi lfy.
Tana nan zaune sai taji wayan na ringing,ta duba taga hajiya ta picking,sai taji muryar wani daban sai yace kifito kiyi mana jagora,sai nasrin tace pls kayi hkr jiri nake ji amma barin ma kwatance inkun shigo baida wuyan ganewa,Kee dallah malama so muke muga halin da Abbanmu ke ciki tsabar isa baxama kifito ba,nan take nasrin taji rai ya soma baci,batare da tace dashi komai ba tayimai kwatance ta kashe wayan.
Jim kadan sai gasu sun shigo su kusan goma suna isowa gurinta wani dan matashi yazo ya fixge wayan Abba a hannunta ya fara zazzaga mata rashin mutunci,wato don ba mahaifinki bane shine baki damu da kixo kimana jagora ba shine baza ki iya wallahi saina.........kafin ya kareshe me xaice yaji ta bayansa ance haba dan saurayi karka xama BUTULU mana,a zancen da kakene nagane wannan yarinya batada alaka da wanda takawo asibiti,wallahil azim nazaci mahaifinta ne domin sanda takawoshi hankalinta bai jikinta,kuma ce makan datayi tanajin jiri,jininta aka diba aka samishi,because ya zubar da jini munxaci mahaifinta ne muka fadamata yana bukatar jini ba fargaba bakomai tace a diba nata,da munsan ba mahaifinta bane da bamu yi wannan danyen aikin ba,dan saurayi stop judging a book by its cover in baka godewa yarinyar nan ba ay bai kamata ka zage ta bata,nandai likitan ya sanar dasu komai,yayinda jikinsu yayi sanyi suka jinjinawa nasrin wanda idonta keta ZUBAR HAWAYE,musamman saurayin wanda naji sun kirashi da suna HYDAR yaje har gabanta yace tayi hakuri da sauran yan'uwan patient din sukayimata godiya sosai lallai kin cika yar halak cewar kanin patient din wanda naji sun kirada Alh MAHEER,godiya dai nasrin tashata,nan suka dunguma xuwa dakin inda suka tarar da Abbansu yanata sharar barci dama akafa ne yaji ciwo sai gefen hannu,an dressing duka,likita yace insun ganshi su fito kada su tadashi nanda wasu hours ma zai tashi dakansa,duk suka fito,lokacin anata kirayen kirayen maghriba,Nasrin taje tai musu sallama tace zata tafi insha Allah gobe zata zo dubashi,
Hajiya tace yar albarka ya sunanki?ahankali tace NASRIN,tace wacce unguwa kike??nan nasrin ta zayyano mata komai gameda ita,tace kasuwa xata daga skul ,ahanya taci karo da wannan tsautsayi,Hajiya ta kuma jinjina mata tace lallai kincika ya' dama haka akeso dukkanin musulmi ya kasance mai taimako,mungode sosai nasrin,sai ki bamu account numbern ki da phone number in Alhaji yatashi akiraki yamiki godiya,kudi kuma zansa haidar ya tura miki,murmushi nasrin tayi ta karanto mata phone number dinta amma account number fir taqi bayarwa acewarta wannan tayine don Allah,sukayi sukayi taqi badawa,sukai ta mata godiya duk sai sukaji ta burgesu matuqa,Lallai Nasrin kin tarbiyantu cewar wata agefe danaji sun kirata da PHERTY,
Nasrin dai qala batace ba hajya tasa hydar ya maidata makaranta,bayan tai musu alkawarin xuwa duba Abba gobe,har bakin mota sisters din hydar suka rakata tasha godiya kam,yaja motar suka tafi sai KASU.....
Kucigaba da sauraron
jikar NAYAYA,Mrs Abdul
Ummu Arif💞
📚✏Excellent Writers📚✏
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [6:45am],[22/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
6⃣1⃣to6⃣5⃣
Hydar har cikin school yakaita,tafito tamishi godiya yayinda yace ay suke da godiya Dan Allah ta dada hkr kan abin dayayi mata,murmushi😊tayi tace bakomai yawuce sai anjima,tanufi hostel dinsu shikuma yaja mota yayi gaba cikeda dana sanin abinda yayi mata.
Nasrin tayi mamaki ganin kofarsu a bude domin tasan xeenat bata dawowa at this time amma tana kutsa kanta cikin dakin wani karni ne yafara bugen hancinta mexata gani😳😳xeenat kwance a kasa cikin jini,bayaga haka ta bata dakin.a tsorace nasrin ta karasa ta ajiye jakanta taje ga xeenat ta dago ta saitaga ta bude ido,ahankali tace Nasrin pls help me pls👏🏼
Nasrin ta taimaka mata suka shiga toilet tahada ruwa me xafi tace mata tagasa jikinta sannan tayi wanka,tafito parlon ta gyarashi tsaf ta fesa freshner daidai lokacin xeenat tafito daure da towel taje tahaye gado,nasrin ta kalleta cikeda takaici ta nufi kitchen taje ta dafa musu jollof din couscous🍲ta hado tea mai kauri☕ ta dire a kasa tace zeenat sauko kici abinci,xinat jiki ba kwari haka tasauko suka fara cin abinci,saida suka gama cin abincin nasrin takwashe plates din takai kitchen tadawo tazauna face to face da zeenat yar kyakkyawan fuskan tannan kamar ba ma'abociya fara'a ba.
Tace zeenat kifadamin meya sameki?
Sannan bansan karya😡😡
Ke nake sauraro👂🏽
Zeenat tai mamaki yadda nasrin take mata magana,amma saita dake itama takuma kudirta fadamata gaskiya,tunda ba tsonta take ba(zinat yar gari)
A sanyaye zinat tace nasrin abortion pills nasha,so sai abun yazomin da gardama but Alhamdulillah yafita dama 1month ne,kinji abinda ya sameni,ngd da taimako,,,,,,
Nasrin wacce tunda zinat tafara magana tayi mutuwar xaune batasan sadda kwallah yafara bin kuncinta ba,kaico dama da mazinaciya take zaune,yanxu wani kallo jama'a zasu mata,lallai xinat ta cuceta😞😢
Ta goge hawayenta tadago tace zinat yanxu kina tunanin rayuwa me billewa kikeyi,uhmmm kinbi ZAMANI koh,iyayenki sun biya miki kudin makaranta kinxo kina bariki,shin xasuji dadi yayinda sukaji ankiraki da YAR BARIKI,wannan ay MUGUWAR SAKAYYA kikayi musu,meya kaiki??SON XUCIYA??
Uhmm xeenat kenan hala kinmanta cewa ABINDA KA SHUKA shi kake girbewa,,,,,
ZEENAT bude kunnenki kijini👂🏽👂🏽👂🏽👂🏽
Kinsan me kika aikata kuwa,ZINA😢
Shin kinsan babba ce cikin laifuka ko bakiyi karatun addini bane,
Kina diya mace zina lalata miki tarihin rayuwarki zatayi,
Zinat abuna farko da zina zata jawo miki shine kin warware mubaya'arki da Annabin Allah(s.a.w)
Sannan zina ga ya'mace tamkar jefa rayuwarta da zuri'arta ne cikin masifa,
Abdullahi Ibn Mas'ud yace:
Idan mace tasan zina,in an bata duniya da abinda ke cikinta ta aikata,wlh bazata karba ba,haba zinat
Ibnu Qayyum yace:
Idan da guba zaa danne mace abata,dayafi mata alkhairi akan wannan maniyin xina da aka xuba mata a mahaifa,domin zaiyi tasiri cikin xuciyarta da ruhinta yadda guba kebin jikin dan Adam,
Yake yar'uwa wannan maniyi masifa aka zuba miki,domin xai lalata miki mahaifa ne,kisani cewa duk dan daya kwanta cikin mahaifar da aka zuba maniyin xina,yana zuwa duniya daban ne,
Domin yana rasa tausayin zumunci,ma'ana bazaiji tausayin uwarsa ba,kannensa,yayyansa da sauran yan'uwansa,
Hadin kai yakanyi karanci ga yayan dasuka kwanta a mahaifar da aka zuba maniyin xina,,,
Shin yar'uwa wannan ba masifa bace,ko xaki iya gyara wannan da kudin da aka baki yayinda kikayi xina,Kaico😞
Kinsan cewa babu wanda ya raina Allah irin mazinata,
Bakuso iyayenku su ganku
Bakuso yan'uwanku su ganku,
Bakuso jama'a su ganku
Amma kun manta yayinda kuka kebe kuka kulle ko ina kofar Allah bata kulluwa,shin kunyarsa da girmansa bazaisa ku fasa ba😞
Zinat ki nutsu ki sauya rayuwarki ki hangi illar zina matsayinki na diya mace,kada ki sakawa iyayenki da haka,bayaga haka kin xubda cikin,shin kinsan cewa kisan kaine???
Domin ranar kiyama cikinnan da kika xubar yaron xaixo ya tuhumeki laifin me yayi miki kika kashe shi Shin kin tanadi amsar
Bashi?xaki cemai sbd kunyan duniya,ina kunya ga wanda baijin kunyan Allah kaico kaico zinat
Saidai inaso kisani har yanxu kinada sauran dama,Allahu gafurur rahim,Allah mai yafewa bayinsa ne don haka ki nutsu kifara sabuwar rayuwa,ki tuba ki nemi gafarar Allah
"Innal laha yubibbut tauwabinaa"
Lallai Allah yanason masu tuba,amma fa kisani....cikin sharudan tuba baa komawa aikata wannan sabon da akayi alkawarin barinsa har Abada.
Rayuwarma nawa take,yau kaine gobe babu kai,mutuwa bata knocking sannan bata barin wani don wani,Ina fata zinat xakiyi amfani dawannan tunin dana miki,Dukkanninmu muna sabon Allah saidai na wani yafi nawani,the best thing kawai muyi kokarin gyara rayuwarmu mu koma ga Allah don samun kyakkyawan karshe da dacewa a lahira,
Zan cigaba da tayaki da addua,Allah ya shiryemu baki daya yasa mugama da duniya da iyayenmu lafiya.
(ni hauwa da jikina yayi sanyi jin maganganun nasrin nace AMIN YA ALLAH)
Zinat wacce tun fara maganar nasrin taketa faman kuka domin maganganun nasrin sun ratsata,kuma tasan ba karya ciki,ta dago idonta wanda tsabar kuka suka kankance suka koma ja tace
Nasrin bansan iyakar godiyar dazan miki ba u really put sense in me,wlh NAYI NADAMA,gaskiya kincika🌹AMINIYAR KWARAI🌹ga duk wadda tasameki matsayin aminiya,wlh nasrin am deeply feeling guilty,Nasan baya nayi asararriyar rayuwa,Amma Insha Allah daga yau xan sauya rayuwata inkoma mace tagari,duk dadai gyara baikaiwa kashi,😭kaico,wannan to KADDARA KO TSAUTSAYI ne,kai bako daya nice najawa kaina😭 Ya Allah na tuba nakomo gareka ka karbi tubani da tsarkakakken xuciya da niya xanyi😭😭😭
Nasrin nagode nagode nagode,nasrin wacce zinat tasoma bata tausayi tamatsa kusa da ita tafara rarrashinta,haba zeenat its ok,Insha Allah all will be well again,godiyan nan is enough,what are friends for,muma bawai Allah yafison mu bane yayimu haka,Allah ya cigaba da shiryar damu bisa tafarkin tsira.
Nasrin ta taimaka mata ta tashi tahau gado,yayinda itama tayi shafa'i da wutiri ta haye gado cikeda tunanin halinda Abbansu haydar ke ciki,gashi a kwanakinnan wani sabin son NY ke shigarta wadda ta kirashi da jarrabawa tana kuma fatan cinyewa👏🏼
Asuba tagari NASZEE🌙
Taku a koyaushe,Jikar NAYAYA,Mrs Abdul..
Ummu Arif💞
📚✏Excellent Writers📚✏
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [11:04am],[26/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
7⃣1⃣to7⃣5⃣
Kiran na gab da tsinkewa tayi picking "Salamu alaikum,NY ka mantani koh haka aminta take? nagode"
Abinda ta furta kenan,
Murmushi NY yayi yace "Wa'alaikissalam nassy baby haba-haba na isa na manta ki kina raina wallahi, Abubuwa ne suka yimin yawa kuma bana so na dameki da kira nafiso ki nutsu kiyi karatu, Dafatan kina lafiya"
Murmushi itama tayi sannan tace mishi "lafiya ta kalau dafatan kaima haka yasu Hajiya?".
Yace "bana kaduna amma jibi zan dawo Abbana baiji dad'i ba"
"Ayya Allah yabashi lafiya yasa kaffara ne,Nagode da gaisuwa" cewar nasrin, shima yace "Amin amin nasrin Nagode sosai, Idan na dawo zan zo in ganki, mukwana lafiya"
Tace "Ok,Allah dawo dakai lafiya Asuba ta gari,".
Wayar ta k'urawa ido kamar me son ganin fuskanshi ta ciki "Allah kasa na cinye wannan jarrabawa ta son Ny" ta k'areshi maganar tana goge hawayen dake k'ok'arin zubo mata. Duk sai taji karatun ma ya gundureta, tashi tayi ta kwanta abinta.
***********
Yamma lilis tadawo daga makaranta,Tana shigowa band'aaki ta nufa tayi wanka da alwala ta fito, ta shafa mai ta zira abaya tayi sallah.
Bayan ta idar ne taji shashek'ar kuka, wazata gani.... Zinat ce akan gadonta ta had'a kai da gwiwa sai kuka take, Nasrin tayi mamaki meya sata kuka to?
Tashi tayi taje ta zauna gab da ita sannan ta fara magana "Zinat na fuskanci a cikin kwanakin nan kina cikin damuwa yau abun har ya kai ga kuka, idan bazaki damu ba zan so ki fad'amin koda taimakon da zan miki"
Zinat ta d'ago kai ta dubi nasrin da jajayen idanunta da suka sha kuka cikin shashek'ar kuka tace "Nasrin wallahi bakomai ke damuna ba illa nadama, Na rasa budurcina, na zubar da mutunci na da kimata na di'ya mace, Ta yaya zanyi in maido su, kaico dana bi rud'in duniya, tabbas dana sani k'eya ce, Kinji abinda ke damuna Don Allah ki bani shawara"
kukan ta ya tsananta, nasrin ta rungumo ta tana bata baki, sai da zinat ta nutsu tukun nasrin ta kalleta tace ''Zinat idan na fahimce ki so kike ki dawo da budurcinki, kimarki da mutuncin ki koh?"
Zinat ta gyad'a kai alamar eh, Nasrin ta Cigaba "Zinat budurci dai ya tafi ba dawowa har abada, mutunci da kima kuwa zaki iya dawo dasu. Kinyi kuskure k'warai wajen sayar dasu sai dai ina godiya ga Allah da yasa baki yi nisa ba kika gane kuskuren ki, kike son shimfid'a sabuwar rayuwa,Wannan ma Rahama ne".
Ta Cigaba
"Zinat matsayina na 'yar uwarki Musulma wacce ta 'danyi karatun addini kuma nake sa ran zama cikakkiyar likitan mata nan gaba Insha Allah.
Dukkan wata di'ya mace da kike gani da budurcinta ake haifanta, budurcin nan in miki a taqaice wata fata ce dake gaban kowacce d'iya mace wacce bata da wuyan fashewa domin kuwa bata da 'kwari.
Takan fashe ne ta hanyoyi da dama, Amma mutane da yawa sun 'dauka cewa hanyar fashewan ta 'daya ne. Saidai Alhamdulillah Malamai suna ta wayar da kan mutane wajen fad'akarwa cewa ita wannan fatar akwai hanyoyi dabam-dabam na fashewan ta, Amma ke tabbas kinsan meya fasa naki Allah shi kiyaye gaba".
Zinat tace "Amin" a sanyaye.
Nasrin ta Cigaba "Zinat akwai gyara da zakiyi wanda ke kanki zakiji canji duk da dai ance wai 'Gyara baya kaiwa kashi' Amma it would help your situation alot(Zai taimakawa halin da kike ciki sosai) Idan kikayi, la'alla in kinyi aure mijnki ya fahimci baki da budurci, la'alla ya kasa fahimta Sanin gaibu sai Allah".
Cike da zumud'i zinat tace "Nasrin meye kenan zanyi? ko nawa zan kashe zanyi wallahi"
Murmushi nasrin tayi tace
"Zinat kenan,ba wani kud'i zaki kashe ba kawai ki saurare ni,
Zinat inda hali ki daina tsarki da ruwan sanyi kwata-kwata sai na d'umi, Ki yawaita amfani da ganyen magarya, bagaruwa, tafarnuwa, Ma'ana kina tsarki dasu.
Ki yawaita yin lalle idan so samu ne, Sannan kina sirace dashi.
Ki yawaita shan ruwa, rake, cin fruits (ya'yan ita'tuwa) da Vegetables (ya'yan ganye)
Ki dinga shan kunun Aya, na Alkama, Shan nonon raku'mi dana shanu, insha Allah Zakiji canji sosai sannan basuda illa ga lafiyar ki Allah yasa a dace."
Nasrin ta tashi taje kitchen tasha ruwa sannan ta dawo ta zauna ta d'aura daga inda ta tsaya
"Zinat ina mai jan kunnen ki da shaye-shayen magungunan zamanin nan, Abun ya zama kamar hauka ban gajiya da mamakinsa. Wallahi in kinji wani abun kyace wacce tayi amfani dashi jaka ce, because of illiteracy a woman inserting animal dung into her vagina(saboba jahilci mace tana cusa kashin dabbobi a gabanta), Zinat a musulunce ma yin magani da najasa haramun ne amma abin takaici yanxu kar kiga yadda kasuwar Magungunan hausa take ci. Ace mace cusa wannan, yi matsi da wancan yi hayak'i da wancan ta maida gabanta kamar wata bola, wallahi akwai had'ari sosai wurin amfani da magungunan nan mara asali".
Nasrin ta dubi agogo tukun taci gaba "Zinat bana cire tsammanin kina da k'awayen zamani wa'yanda zasu ce dake Ay akwai maganin da zaki sha ki dawo budurwa da dai sauransu, to wallahi yaudaranki zasuyi, tunda kika k'udirta sauya hali da rayuwa, Ya kamata ki rabu dasu, Akarshe ina miki fatan alkhairi, Allah yakarb'i tuban ki ya dad'a shiryamu abisa tafarkin gaskiya yasa mugama da duniya da iyayen mu lafiya".
(Nima ummu arif a sanyaye na amsa da Amin, domin maganganun Nasrin gaskiya ne gashi sun shigeni)
Zinat ma Amin di'n tace sannan ta fara jerowa Nasrin godiya, Nasrin tace "Zinat please Godiyan ya isa haka meye amfanin zaman tare kedai Allah mana jagora".
Daga haka suka tashi suka gabatar da sallar isha'i, Nasrin gado tahau tafara wayar ta na fama da 'yangidansu yayin da zinat ta kwanta da tunanin maganganun da nasrin tayi mata, Ta k'udirta amfani dashi da sauya rayuwa domin dacewa da rahamar ubangiji.
Can Jos kuwa, shirye-shirye aka fara na bikin yaya naufal wanda ya rage saura wata uku.
Zai auri yar' wani lecturer a Jami'ar Jos, Nawwara Abdallah Abbas. Nawas ko cewa yayi baiga matar aure ba har yanxu, Abba da yaji haushi cewa yayi "nawas ka mutu ba aure in kaga dama"
Nasrin ko murna take za'ayi biki a gidansu domin ba'a tab'a ba.
Tana ta Allah-Allah jarabawa yazo suyi su gama ta koma Jos kar ayi biki ba ita.
Wannan kenan.
Da shike yau ta kama Sunday(lahadi) nasrin na kwance sai goma ta tashi tayi wanka da breakfast (karin kumallo)
Tana kunna wayarta saqon NY yashigo "On my way to Kaduna" ta duba taga tun bakwai ya turo tace k'ila ma yanxu yana gida. Tayi mishi reply kamar haka "Sannu da hanya fatan ka iso lafiya? Agaida su Hajiya da Abba da jiki"
Tana tura mishi ta tashi ta zura hijabi ta fita zataje tayi printing wani assignment (aikin gida)
NY tara da rabi ya iso Kaduna, Yana shiga gida goma dai-dai. Gidan shiru da yake lahadi ne sunata aikin barci. Falon Abba ya nufa ya sameshi a zaune yana lazimi, yaje ya rungumesa yayinda ya fara tambayarsa jikinsa yana duddubawa, Murmushi Abba yayi yace "Nasiru kenan d'an albarka kwantar da hankalinka na warke sosai, ita dai wannan yarinya Allah yayi mata Albarka".
NY ya amsa da Amin, tukun yace "Abba kasan Abubuwa sunyi yawa ban samu na kirata ba amma yanxu bani lambar agabanka na kirata nayi mata godiya"
Abba ya dau'ki wayarsa dake gefensa ya jero mishi lambar Nasrin Yayinda NY ya rubuta ya danna domin ya kira Amma me zai gani..... Sunan Nasrin ne ya bayyana a fuskan wayarshi, Yace Abba dai-dai kaban lambar kuwa?
Abba ya kuma karanto mishi yayinda ya sanya ya kuma k'ira yaga dai sunan Nasrin ne dai ya dad'a bayyana kan fuskar wayarshi. Abba ne ya kallesa yace "Nasiru lafiya........."
Taku Akoda yaushe
Ummu Arif💞
® Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [3:06pm],[25/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
6⃣6⃣to7⃣0⃣
Washegari Nasrin da wuri ta tashi,ta gyara musu daki ta wanke toilet tahada breakfast sannan tasawa zinat ruwa me xafi ta tasheta taje tayi wanka bayan ita tayi nata wankan.
Zinat na fitowa tashafa mai tasa kaya,nasrin ita harta gama shirinta suka zauna sukayi breakfast,bayan sun gama nasrin takwashe plates din tadawo tabawa zinat wasu tablet tasha sannan ta roketa da kada taje ko ina tayi mata sallama ta nufi cikin school domin tanada lectures.
Tare suka iso bakin lecture hall itada lecturer din,ta risina tagaishe shi ya amsa fuska ba yabo ba fallasa yayinda yabata hanya tawuce ciki.
Sai 11 suka fito daga lectures,fitowarta keda wuya taji wayanta na ringing ta duba taga sabuwar number,kamar bazata daga ba saikuma ta daga,Taji anyimata sallama,ta amsa cikeda girmamawa,Nasrin baki gane mai magana ba koh,Nasrin tace eh,Hajyan su haydar ce,Nasrin tace laaa barka da safiya hjya,ya kwanan Abba?hajiya tace lafiya lau,Nasrin tace gani nan xuwa yanxu nafito lectures,hajiya tace to yar'albarka saikin iso,cikeda jin dadi nasrin ta kashe wayan ta karasa bakin titi ta tare keke napep tahau bayan ta fadamishi inda zai kaita.
Koda ta isa asibitin saida ta tsaya ta siya fruits sannan tashiga ciki,kafin taqarasa ciki tahadu da haydar ya rako abokansa,yana ganinta murmushinsa ya fadada suka gaisa yayinda shida friends dinsa suka dada mata godiya tace musu bakomai tayi ciki abinta.Tana xuwa taga kofar a bude domin akwai mutane,tayi sallama tashiga ciki,da gudu kannen hydar sukazo suka rungumeta sannu da zuwa nasrin,murmushin nasrin ya fadada sannunku da safiya,dafatan kun tashi lfy,lfy lau suka amsa dukkansu,taje tagaida hjya cikeda girmamawa itama hajiyan godiya tadada yimata,sannan tagaida kowa na dakin ta nufi gadon Abba.
Abba ina kwana,katashi lfy,ya jiki kuma??Abba wanda tun shigowar nasrin dakin yake binta da kallo saboda ta matuqar burgeshi,Murmushi yayi mata yayinda ya bude hannunsa nasrin ta kwanta jikinsa,har cikin ranta tana jinsa kamar Abbanta,Muryarshi tajiyo yana cewa nasrin bansan iyakar godiyar dazan miki ba domin kinmin abinda ko jinina iyaka,yanxu hakama jinin kine mai amfani a jikina,Wato na jinjinawa iyayenki,Nagode sosai nasrin,Allah yabani damar taimakonki kamar yadda kika taimaken,Allah yayi miki albarka yasa kigama da duniya da iyayenki lafiya.
Nasrin wacce taji dadin maganganun Abba tace mishi Abba nidai godiyan ta isa haka,jiyafa dakina cika yayi da godiya da kyar nasamu wurin kwanciya😀😀😀duk yan dakin kowa saida ya dara,yace nasrin kenan kamar Nasiru kike wajen raha,😊murmushi tayi tace waye shi,Abba yace babban wan su haydar yana abuja amma next week xai dawo,Nasrin tace Allah dawo dashi lfy.
Nandai sukaita hira cikin wasa da dariya inka ga nasrin cikinsu zaka rantse dama can yan'uwa ne.Saida tayi sallar Azahar tukun tayi musu sallama bayan ta tabbatar musu cewa gobe xata zo.
Haka nasrin tayita kula da zinat da zaryan zuwa asibiti,zinat tadawo kamar wata mai jego,har farfesun hanta da ogun leaf nasrin tayi mata sannan ga soyayyan kaza,kullum cikin godewa nasrin take.
Satin Abba daya a asibiti aka sallamesa,harda nasrin suka tafi taga gidansu taji dadi matuqa yadda suke sonta,Abba ya isar da saqon dansa Nasir na godiya ga nasrin,ya dada da cewa nabashi numbernki xai kiraki,😊murmushi nasrin tayi wadda ke kara fiddo da kyaunta,tace Abba wai duk godiyan bai isa haka,daya barshi wlh,aa yata ina,yace inya dawo takanas xaixo har skul dinku ya miki godiya,Ta kuma murmushi bakomai yasata hakan ba sai tuno NY dinta tanason me suna Nasir,duk sai taji ta kosa taga Nasir din Abba don tanada yaqinin yanada irin halayyarsu,Haydar akasa yakaita har skul.
Sati biyu Nasrin tayi tana jinyar zinat,zinat har wani kyau tayi da yar'kiba😜tayiwa nasrin godiya sosai da jinjina da fatan samun irin halayyarta,Murmushi nasrin tayi tace ay kinci baya in kika samu irin halayyata Allah yasa kifini shine cigaba zinat tashi tayi ta rungumeta tana mata godiya harda kwallah.
Zinat ta dauki nasihar nasrin domin rayuwarta ta sauya matuqa,abun yabawa kowa mamaki amma dasukayi la'akari da room mate dinta sai suka jinjinawa nasrin.
Zaune take kan sallaya bayan ta idar da sallar isha'i tanata duba handout dinta domin gobe akwai wani presentation da zatayi na meye yake causing yoyon fitsari.Ringing din wayanta ne ya katse mata karatun,😳😳 wazata gani NY,ashe be manta taba.....😞
Ummu Arif💞
®Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [8:51am],[28/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
7⃣6⃣to8⃣0⃣
Abba ne ya kallesa yace"Nasiru lafiya kuwa,kodai ya'ki shiga ne?"
NY wanda ya cika da mamaki yace"Eh Abba,ko zaka kira da taka wayar?"
Ba musu Abba ya danna lambar nasrin ringing daya-biyu ta dau'ka dawowan ta kenan daga shagon printing.Cike da Zumi'di ta da'ga"Salamu alaikum,Abba Barka da safiya."
"Barka kadai ya'ta Kin tashi lafiya,Ya karatu?".Cewar Abba,Nasrin tace"Lafiya lau Abba,ya jiki-jiki,ina fatan ka samu lafiya"
Murmushi yayi cikin jinda'di yace"Nasamu sau'ki sosai ya'ta,Nagode da kulawa,ga yayanki Nasiru dana ce miki yayi tafiya ku gaisa".
Abba ya mi'ka ma NY wayar,Yana amsa ya karata a kunnensa"Salamu alaiki"Abinda ya furta kenan,Nasrin tace"Wa'alaikassam Yaya Nasir,fatan ka dawo lafiya ya me jiki kuma?"
Murmushi yayi jin muryar nassy baby wanda baya tunanin zai iya manta ta sannan yace"Lafiya lau Yan'mata,Mai jiki yaji sau'ki,Mungode sosai-sosai Allah saka da alkhairi"
Nasrin ta'dan yi shiru kamar me tunanin wani abu tukun tace"Haba yaya nasir,godiyar is enough(ya isa haka) ay yiwa wani yiwa kai ne,fatana Allah ka'ra mishi lafiya"
Cike da jinda'din maganganun ta NY yace,Amin amin,Nabarki lafiya"
Ya mi'ka ma Abba wayar suka yi sallama.
NY yace "Abba kace me sunanta ma?" Abba yace"Nasrin"
NY yayi murmushi yace "Wallahi ta burge ni Abba ga sanin ya kamata,Allah dai ya biya ta".
Abba ya kalli NY yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace"Amin,ka shiga ciki kayi breakfast(karin kumallo)koh".
Ya amsa da"to"yayinda ya tashi ya nufi gefen su hajiya.
Nasrin ko bayan sun gama waya da su Abba,Tunani take tayi ina tasan muryar wannan yaya nasir di'n,Ba makawa muryar NY din'ta ne.
Kenan Abba mahaifinsa ne,Anya kuwa,ki'la dai wani nasir din'ne me irin muryar NY din'ta,Koma dai meya Muryar NY taji.Haka dai tayita surutai ita ka'dai a da'ki domin zinat taje gida kasancewar weekend(karshen mako)ne,Amma zuwa yamma zata dawo.
Ina Nazira??????
Nazira tun bayan gama school di'nsu bata kuma sa nasrin a ido ba,Ta rasa wata hanya ne zata bi domin samo lambar NY ta wargaza duk wani aminci dake tsakanin Nasrin da NY.
Ta janye ku'dirinta ne na shiga tsakanin su yayinda wata ranar lahadi tana fallonsu tana zaune sai taji ana Wa'azi a WISAL HAUSA T.V me taken🌹Aminta a Musulunci🌹,haka kawai sai taji tana son saurara.Ta nutsu kuwa ta saurara kusan awa da'ya tana zaune har malamin ya dakata badon ya gama ba,sai don lokaci.
Jiki a sanyaye ta tashi tayi da'kinta,ta zauna tana ta tunanin yadda malamin nan ya siffanta🌹Aminin kwa'rai🌹cikin wa'azin sa,lallai bata cika aminiyar kwa'rai ba,Tabbas wannan sai Nasrin,"Gaskiya nayi rashin aminiya Amma insha Allahu zan neme ta in nemi gafarar ta. Mu koma yadda muke a da,Allah ya cika mata mafarkinta ya bata NY matsayin mijin Aurenta"cewar nazira wacce nadama ta baibaye ta.
Aisha kuwa NTA College ta shiga abinta,jifa-jifa suna waya da nasrin,nan ne ma take sanar da nasrin an kawo sadakin aurenta.Gaskiya Nasrin ta tayata murna,tayi mata fatan alkhairi.
***************
Zinat rayuwa ta sauya,duk shigar banzar nan ta daina,zuwa su chasu duk ta watsar tasa karatunta a gaba da zumar gina rayuwa sabuwa mai tsafta.
Mutane da dama sunyi mamakin canjin ta yayinda wasu ko basu yi ba domin sunada ya'kinin da taimakon Allah da taimakon abokiyar zamanta(Nasrin) ta nutsu.
Nasrin ce zaune a da'ki tana karatu bayan sun gama shan hira a waya ita da nawas.Dayake sun kusa fara jarrabawa,so bata da wani lokaci saina karatu.
Wayar ta taji tana ringing(kara) ta duba taga NY ne,murmushi tayi ta da'ga wayar"Aminin kwa'rai ina gaisuwa"cewar nasrin,Murmushi yayi yace"Aminiyar kwa'rai nima ina gaisuwa,gani a waje ki shirya ki fito mu'dan zaga Kaduna",sai da ta dan'yi jim tukun tace"to ina zuwa"
Tashi tayi tasa doguwar riga jaa ta na'da bakin gyale a kanta,tayi light make-up(kwalliya yar' sarau-sarau)tasa takalmi ba'ki da jaka ta'dau wayarta ta kulle da'kin ta fita daya ke zinat bata nan.
Tun kan ta isa ya keta mata murmushi itama murmushin take yi masa harta ka'rasa inda yake.Bai ce da ita ka'la ba,bu'de mata mota kawai yayi yayinda ya keta yi mata murmushinsa mai burgeta,ba musu ta shiga,ya shiga shima ya tada mota sai..........
Taku a koda yaushe Mrs Abdul.
Ummu Arif💞
® Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [12:05am],[2/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
9⃣6⃣to1⃣0⃣0⃣
Nasrin.......yau dai kizo kiga mummy na tunda Allah bai nufa kinje ba,cewar Zinat wacce taketa kwalawa Nasrin kira tun kan ta iso cikin d'akin, Nasrin kan har bacci ya fara kwasheta.Domin so take ta'danyi baccin saita tashi tayi karatu.Zinat na shigowa ta ganta a kwance tace"iyye jinda'di,Mummy shigo mana"
Mummyn Zinat ta shigo ta zauna tana k'arewa Nasrin kallo wacce take barcinta cikin kwanciyar hankali,murmushi tayi domin ji kawai tayi yarinyar ta burgeta, ta cewa Zinat karta tasheta ta bari ta tashi da kanta sai su gaisa.Zinat tace to tashiga kitchen ta kawowa mum d'inta d'an abin motsa baki sannan ta shiga toilet don ta watsa ruwa.
Nasrin ko barci yayi da'di harda mafarkin NY,Allah sarki gaskiya kinsha DAKON SO,Allah yasa ya zame miki alkhairi.
Zaune take a wani fili wanda ya yawalta da fure kala-kala masu matu'kar d'aukar hankali,tunani take yau saura kwana uku d'aurin aurenta amma batasan waye mijin ba.
Ji kawai tayi an rufe mata ido,duk da ba'ayi magana ba tasan NY ne domin hancinta bai ta'ba mance qamshin sa ba,A hankali tace"NY ne gara ma ka zagayo"murmushi yayi ya cire hannunsa a idonta ya zagayo yace"Nasrin da me kika gane ni ne, ka'da kai tayi tace "wollah da abubuwa da dama"
Murmushi yayi yace "kamar me da me ba"
Tace"Kaidai bari,abun sirri ne"
Murmushi yayi,,,ta kuma cewa "NY please ka fa'damin waye ango na"
Kwashewa yayi da dariya,tukun yace"lallai yau ni naga amarya mara wayo,shawarar dazan baki kada kibari wani ya sani baki san waye angon ki ba,domin zakiji kunya"
Ya kareshe maganar cike da zolaya,Ita ko binsa tayi da ido tukun tace"to d'an fada'min"
Murmushi yayi ya tashi ya bar wurin sai da yayi nesa da ita tukun yace"Nasrin angonki na tare dake ko yaushe"bataji abinda yace ba ta bude baki tace"Ny please tsaya ka"
Firgit ta mik'e ta fara salati,tsaki tayi data tuna cewa mafarki tayi.
Juyuwan da zatayi taga Zinat tare da wata mata duk murmushi suka bita dashi, itama murmushin tayi musu sannan taji Zinat tace Nasrin ga mama na. tashi tayi tsam taje gabanta ta rusuna ta gaisheta yayinda mum din Zinat ta amsa fuska a sake,sannan tace"Mummy kiyi ha'kuri ban samu damar zuwa ba wallahi abubuwa ne suka yimin yawa"
Mummy tace"Bakomai Nasrin,ay nasan yanayin karatun naku,Allah dai ya taimaka,yasa agama lafiya"
Cike da jin da'din addu'ar mummy Nasrin ta amsa da"Amin",,,, Nan suka yi ta hira da mum daga bisani suka rakata mota ta tafi.
NY na komawa gida a gajiye yake lis don haka gefensa ya nufa ya watsa ruwa ya'dan mi'ke.
Bai tashi ba sai bayan maghriba a gurguje yayi toilet ya d'auro alwala ya gabatar da sallar maghriba,ranshi duk a dagule sanadiyar rasa jam'i da yayi,a haka yatashi ya nufi b'angaren hajiya.
Yana shiga ya tarar da ita akan salla ya,ya gaisheta ta amsa fuska a sake sannan tace"Nasiru lafiya na ganka haka"murmushi yayi yace"hajiya wollah nayi rashin jam'i ne", tace "ayya, ay bawai ka rasa da gangan bane,bare ma ay jami'i baya wuceka Nasiru yauma dai akasi aka samu,don haka ka kwantar da hankalinka kaji d'an albarkah"
Cike da jin da'din maganganunta yace"Nagode hajiya,barin shiga masallaci naji ana shirin kiran isha'i"
Tace"to, inka dawo akwai maganar da muke son muyi dakai nida Alhaji ka same mu a sama"
Yace"to hajiya,Allah kaimu"
Yana tashi ya nufi masallaci.
Bayan an idar yayi addu'a ya tashi nufi gida.
Direct falon Abba ya nufa,yana shiga kuwa ya taddasu suna cin abinci, nan ya zuba shima ya fara ci.Suna cin abincin gwanin sha'awa.sai da suka kammala tukun Abba yayi gyaran murya yafara magana kamar haka"Nasiru dama ba komai yasa nace hajiya ta kirawomin kai illa wani alkhairi dana hangan mana gaba d'ayan mu, Nasiru matsayina na mahaifinka mai k'aunar ka kasan bazan ta'ba yin wani abu wanda zai zame maka damuwa ba, tun kana k'aramin ka kake yimin biyayya,yanxu ma so nake kayi min duk da inada ya'kinin zaka yimin domin baka ta'ba sa'ba umarni na ba".
Abba ya'dan dakata yayinda Nasir ya 'kagu Abba ya Cigaba domin jin me yakeso yayi mishi ya'ki fa'da mishi direct bayan yasan zai yi mishi,
Abba ya Cigaba"Nasiru so nake kaje kasamu Nasrin ku fahimci juna, bi ma'ana so nake na ha'da ka aure da ita"
NY da sauri ya d'ago kanshi ya kalli Abba a zuciyarsa kuwa nanata sunan Nasrin yaketa yi.
Abba ya Cigaba"Nasiru ko kai kanka kasan yarinyar ta fito ne daga gidan dattako bare ni, domin ka rigani saninta a d'an 'karamin lokacin nan dana santa na fuskanci halayyarta, Insha Allah zata zame ma mata tagari,baza muyi dana sani ba da'na tashi kaje, Allah yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya, Hajiya me zaki ce?"
Murmushi tayi tace "Alhaji ay ka fa'di komai saidai kawai ince Allah yi musu Albarka ya sanya Alkhairi"
NY yaji da'din addu'ar mahaifansa garesa yace"Amin amin,Nagode sosai,Insha Allah zan zama me muku biyayya, Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Sunji da'di sosai da furucinsa suka kuma sanya masa albarka.
Abba yace mishi na sanar da Nasrin sai dai bata san waye ba cikin ku don haka ta bangarenta inaga bawani matsala, Tashi kaje Allah ma Albarka.
Bayan fitar NY ne Alhaji yake sanar da hajiya yadda yake jin Nasiiru a ransa,Murmushi kawai tayi ta kalleshi,A zuciyarta kuwa cewa take Duk son da kake mishi Alhaji bai kai kwatan-kwacin wanda nike mishi ba.
NY ne kwance a gadon sa yanata juyi yana kuma ta nanata sunan Nasrin,a iya sanin shi da Nasrin bata da makusa na kyan jiki kona hali, kyakyawa ce ajin farko,sai dai akwaita da tsokana sannan ko ka'dan baiji k'inta a ransa ba,domin tun ba yau ba ya fuskanci akwai wani b'oyayyen al'amari game dashi da yake gani a idon Nasrin.
"Ko ba komai ta cancanci in so ta domin tamin halacci"
A daren dai NY ya k'udirta a ransa zai so Nasrin ko don ya farantawa mahaifansa...Ya d'aga waya xai kirata sai kuma ya fasa,ya tura text kamar Haka"Slm Nass baby hope kin yini lafiya,Ya exams kuma?Allah yasa ku gama a sa'a ku fito da kyakkyawan sakamako,ki kwana lafiya". da haka yayi addu'a ya kwanta.
Nasrin na zaune tana ta karatu Zinat ma karatun take,sai taji text ya shigo wayar ta, tsaki tayi tace hala MTN ne sai ta samu kanta dason duba text d'in tana kallah ta ga NY cikin hanzari ta bu'de ta karanta fuskarta d'auke da murmushi, tana gama karantawa tayi mishi reply kamar haka"Na yini Lafiya🌹Aminin k'warai🌹 fatan kaima haka, nagode da addu'a Fatan alkhairi gareka ko yaushe, Asuba ta gari"
Tana tura mishi ta Cigaba da karatunta, kasancewar tanajin barci yasa sha'daya saura ta ajiye littafai gefe tayi addu'a ta haye gado.
********
Nasrin tarasa meyasa kwana kin nan NY yake yawan kiranta,duk da dai rabin hirar tasu tsokana ne amma abun na bata mamaki.
Sai ta danganta hakan da jin da'din taimakon mahaifinsa data yi.
Ta gama exams d'inta lafiya.Harta fara shirin komawa jos don tayi missing familyn ta sosai tana matu'kar so ta gansu, Zinat tayi-tayi ta 'kara kwanaki Biyar Nasrin tace taji tagani bazata 'kara ba dole Zinat ta ha'kura ta 'kyalle ta.Tabar tafiyan sai ranar Jumma'a.
Don haka da wuri ta shirya ranar alhamis don taje tayiwa gidansu NY sallama sannan taje kasuwa tayiwa 'kannenta tsaraba.
Tana sauka a keke napep idonta akan NY suka fara sauka, take taji wani sanyi ya ratsata shima nashi b'angaren hakan take.
Wani murmushi ma tsuma zuciya ya sakar mata yayinda itama ta sakar masa,sun shagala da kallon juna sai ji kawai sukayi ance.........
Ummu Arif💞
OHW
®Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [7:56am],[30/1/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWA'RAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
8⃣1⃣to8⃣5⃣
Tu'ki yake hankalinsa kwance yayinda kowannen su yayi shiru kamar ba sarakan magana ba.NY ne da yaji shirun yayi yawa yace"Nasrin hala yau dai azumin magana kike koh?"Murmushi tayi tace"Wollah abinda nake shirin tambayar ka kenan"
Dukkan su kwashewa suka yi da dariya yayin da sabuwar hira ta bar'ke tsakaninsu.
Suna ta hirar su gwanin sha'awa(ummu arif tace"wollah kamar sabbin aure")
Nasrin dai taga NY baida alamar shiga da ita cikinb gari kamar yadda yace domin taga sunyi yo unguwar su Abban hydar.
Ahankali tace"NY ina zaka kaini?"
Murnushi yayi yace"sayar dake zanyi"
Itama murmushi tayi tace"wollah ko mafarkin haka nayi zanyi tir da mafarkin bare a zahiri"
Yace"Nasrin gidanmu zan kaiki,kiga iyayena da yan'uwa na.ko bazaki bane"
Tace"Haba-haba ay da saina zama butulu,kazo gidanmu na'ki zuwa naku, Allah kaimu lafiya, Amma zaka rakani gidansu Abban hydar in gaishesu domin naga unguwar kamar kusan da'yane"
NY yace "waye kuma Abban hydar?"
Murmushi tayi tace"Wani Abbana ne,kai dai kawai ka amsa zaka raka ni"
Yace"naji zan raka ki"
Tace"yawwa ko kaifa"
Haka suka Cigaba da tafiya suna hiransu.Amma me...........
Nasrin ce taga NY ya tsaya dai-dai gidansu Abban hydar yayi horn, maigadi yazo ya bude mishi ya kutsa kan mota yayi ciki.Nasrin tace"NY dama...."
"Shhhhhh"abinda yace mata kenan, tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
Yayi parking tun kan su fito k'annensa suka fito a guje Nasrin, Nasrin,Abinda suke fa'da kenan yayinda fuskokin su ke d'auke da farin cikin ganinta.
Ta fito jiki a sanyaye taje ta rungume su,mamakinta ya da'du ne yayinda taji sun ce"Yaya Nasir hala Abba ne yace ka kawota koh"murmushi NY yayi yace "ku shiga da ita ciki,zanje na d'an watsa ruwa na mi'ke".
Kallon mamaki da tuhuma nasrin ta bishi dashi,ya'ki yace da ita uffan illah murmushi kawai da yake ta mata har ya wuce gefensa.
Ta bi k'annensa ciki,tana shiga ta tarar da hajiya a zaune ta rusuna ta gaishe ta,hajiya ta amsa cike da jin da'din ganin Nasrin tace"Amal kaita sama gun Abban ku koh"
Nasrin ta tashi tabita suna shiga murmushin fuskar Abba ya fa'da'da murmushin sa, yace a'a ya'ta saukar yaushe,tayi murmushi tace"Abba tare da yaya nasir muke", Abba yace"lallai Nasiru ya cika alkawari"
Nan Nasrin ta zauna suka dinga hira da Abba har NY ya gama baccinsa ya hauro saman ya taddasu tare suna ta hira,yace"Abba an samu Nasrin an mantani"
Dariya suka sa dukkan su,Nasrin ta mi'ke tace"barin koma makaranta don Abba ya tuna ka"
Murmushi shima yayi yace"wasa nake Nasrin d'in Abba,zauna abinki"
Tace wollah ni zan wuce yanzu domin zanje nayi karatu" Tace yawwa Abba asani a addu'a satin sama zan fara jarrabawa"
Abba yace,"Masha Allah,Allah ya taimaka yasa a fara a sa'a, a gama a sa'a"Nasrin da NY tare suka ce"Amin"
Nan dai Abba yayi mata alkhairi sosai hajiya ma ba'a barta baya ba,yace NY ya kaita har makaranta yayinda K'annensa suka rako ta har bakin mota bayan sun d'auka hotuna.
A cikin mota Nasrin sai satar kallon NY take,kallo ne mai cike da mamaki da tuhuma,amma don tsabar iya tsokana da gwalewa NY ko kallon inda Nasrin take baiyi ba.Saida suka d'an yi nisa tukun ya juyo ya kalleta fuskan nan rmtashi cike da murmushi yace"Nasrin yau dai kinga family na koh,sai dai su hydar basu nan baki gansu ba,Nagode sosai da taimakon Abbana da kikayi Allah ya saka miki da mafificin alkhairi,sai dai inaso in tambaye ki,wai me kika yiwa Abba ne kika sace xuciyar shi?"Ya kareshi maganar cikin zolaya.
Murmushi Nasrin tayi tace"Wallahi tun ranar da Abba yabani waya muka gaisa na cewa kaina da NY nayi waya,domin nidai na tabbata muryanka naji sai dai banyi tunanin ko kana da wani ala'ka da Abba ba,kawai dai nayi tunanin ko wani ne mai irin muryarka dud da dai na k'osa naga Nasirun Abba,uhhhmm ashe kaine,gaskiya ka shamma'cen".
Murmushi yayi"yace nidai muna da'da godiya kin'ki fa'damin me kika yi kika sace zuciyar abba?"
Dariya tayi tace"Abinda kayi ka sace tashi, shi nayi na sace ta"
Yace hhhhhhh Allah kuwa Abba na sonki gashi naga kema kina son Abbana, nima ina sonki Nasrin,Allah bar zumunci"A hankali tace "amin"
Tun daga haka kowa yayi shiru cikinsu,sun kawo dai-dai wurin wani shopping mall,NY ya samu wuri yayi parking yace da nasrin ta jira shi yana zuwa pls,tace inka da'de zaka nemi ni ka rasa"murmushi kawai yayi mata yasa kai ya shiga.Tana nan cikin motan a hankali abubuwa suka ringa dawo mata.
Lallai ba k'aramin so take yiwa NY ba,ashe sonshi ne ya shafi mahaifansa da yan'uwa,shi yasa ganin su na fari taji tana sonsu,Allah sarki duniya,ji take kamar in NY ya shigo ta fa'da mishi abinda ke ranta amma ina..........ko zata mutu da sonshi ba zata iya ba, Da'dinta daya yanxu ta d'an samu kusanci dashi dalilin taimakon mahaifinsa da tayi, Murmushi tayi yayinda ta share kwallar dake zubo mata tace"Ya Allah bana cire rai da rahamarka ya Allah ka mallakamin NY matsayin mijin aure na, na har abada".
(Ummu arif tace"Amin ya mujibur-rahman)
Tana nan zaune tana ta tunane-tunane har ya shigo bata sani ba saida ya danna horn tukun ta dawo daga duniyar tunanin data ke yi.Suna tafiya suna hirarsu da suka saba mai k'unshe da tsokana har suka iso school din su Nasrin.
Ta fito yayinda shim yafito,siyayyar da yayi mata har kofar da'ki ya rakata dashi,tayi ta yi mishi godiya,yayi murmushi yace ta cancanci fiye da haka,yayi mata sallama ya tafi abinsa.
Nasrin data koma da'aki gado tau ta nata tunanin yadda abubuwa suke faruwa kamar a mafarki,lallai Allah alhakim ne.
A haka har bacci ya kwasheta.ji kawai tayi cikin baccinta ana tashin ta,bude idon da zata yi wa zata gani.....
Ummu Arif💞
OHW
[11:07pm],[30/1/2016]Hauwa Hassan Nayaya:
8⃣6⃣to9⃣0⃣
Nawas tagani a kanta,ta dai rufe idonta ta bude ta ga ko mafarki ne amma ina zahiri ne ay kuwa ba shiri ta tashi taje ta rungumeshi tana kukan da'di,yace"lil sis wannan kuwa fa,pls kiyi shiru koh"tace"yaya nawas kukan da'di ne,wallahi baka ji yadda nakeji ba ganinka da nayi"
Murmushi ya sakar mata,itama ta mayar mishi,ta tashi xata kitchen kenan ya ri'ko ta yace"ina zuwa kuma?"tace zanje in kawo ma abinsha in d'aura ma girki"
Yace"haba-haba,ba girkin da zakiyi wallahi,tashi ki shirya mu zaga Kaduna daga nan mu samu wani eatery mu d'ame ciki sai in dawo dake in wuce masauki na"
Ba musu nasrin ta kwashi kayanta ta shiga toilet ta canja,ta fito tayi kyau abinta tace"bro muje koh"
Ba musu ya tashi ta bishi a baya ta sanya key a kofarsu,suka nufa inda ya ajiye mota suka shiga ya tayar sai cikin gari.
Yawo dai sun sha ba laifi,sunci sun koshi abinsu.
Sun saya ice cream kenan sun fito zasu shiga mota sai suka ji ance"Nasrin,you by this time of night(ke acikin wannan daren)"
Ba tantama muryar NY d'inta ne,juyowan da za tayi kuwa sai taga shine amma fuskan nan tashi kamar bai ta'ba dariya ba ya kuma cewa"Nasrin meye kike yi a waje a daren nan, na tambayeki kin'ki bani amsa"
Tace d'azu bayan ka dawo dani skul yayana daga jos yazo dubani, shine muka fito cin abinci domin yace kar nayi girki,Yaya nawas dana ke fa'dama"
girgiza kai yayi alamar eh ya tuna,tukun yace "where is he?(ina yake)"
Zaga yawa tayi taje ta kira nawas daya nutsu a cikin mota yana sauransu,yana isowa kuwa NY cikin zuciyarsa yace"eh lallai ba tantama wannan yayan nasrin ne domin kamarsu ta 'baci"
Hannu nawas ya mi'ka mishi sukayi sallama yayinda Nasrin tace"NY ga yayana, bro ga NY da nake fa'dama,lokacin daya zo kana turai so inaga wannan ne haduwar ku ta farko"
Dukkansu murmushi suka sanya,suka kuma gaisawa tukun nawas yace su zasu wuce dare nayi zai maidata school,NY yace yakama kam.
Yace"Nassy baby wollah da dawani naganki cikin wanga dare da kinga yadda ake zane yarinya"
Tayi dariya tace"kaima kasan wuce nan"
daga haka ta shige cikin mota tana mai d'aga mishi hannu yayinda nawas yaja suka nufi skul d'in su Nasrin.
A hanya ne nawas ke tambayarta meye ala'karta da NY,da yake bata boye mishi komai,nan ta zayyano mishi komai dake faruwa,Ta gama tana mai sharar hawayen data kasa tsaida shi,Nawas ya tausaya mata matu'ka a cewarsa DAKON SO da SON MASO WANI ba
k'aramin wahala da ciwo bane.
Yace"lil sis yanxu ba wani way out(mafita)
Tace"mafita d'aya,addua bro", yace hakane sis,Allah yasa ki cinye wannan jarabawar,tace,"Amin"
Da haka ya sauya hiran da jokes duk don ya sata raha har suka iso makarantar,ya raka ta har bakin hostel yayi mata sallama bayan ya mata alkawarin gobe zaizo kafin ya wuce.
Nasrin bayan ta shiga d'aki sallah tayi,tayi wanka,domin ta tarar zinat har tayi bacci.Ta zauna a bakin gado tana tunanin abinda ya faru d'azu a gun shan ice cream,domin taga kishi k'arara a fuskan nasir,shin yana sonta ko me?
Wata zuciyar tace mata a'a Nasrin kawai dai yana kishin ki ne matsayinki na k'anwar sa kuma aminiyar sa.
Murmushi tayi tace"Allah ka kawo kaddarar da zata sa NY ya zama mallakina"
Da haka ta d'auko littafanta ta fara dubawa domin exams ya matso,sai wajan sha biyu tayi bacci.
Washe gari karfe goma dai-dai Nawas yazo suka d'an taba hira da Nasrin bayan ya da'da kwantar mata da hankali tukun yayi mata sallama ya tafi bayan ta tabbatar mishi cewa tana gama jarrabawa zata taho.
*************
A yaune Nasrin ta fara zana jarabawarta,wanda tazo mata da sau'ki domin tayi karatu ba na wasa ba.
Ta dawo gida a gajiya ta tarar da zinat tayi mata abinci,domin zinat cewa tayi ta maida hankalinta ga jarabawar ta zata dinga yi musu girki da share-sharen d'aki,da dai sauran ayyuka.Nasrin taji d'adi matu'ka tayi ma zinat godiya sosai.
Wanka tayi ta sanya kaya tayi sallah,sannan ta zauna tana cin abinci tanata santi yayinda zinat take ta mata dariya.
Suna ta hirarsu gwanin sha'awa yayinda wayar Nasrin ta fara ringing,ta duba taga sabuwar lamba tayi tsaki ta'ki d'agawa.Kiran na tsinkewa aka k'ara kira ta kuma tsaki ta d'auka tace"Hello,wai waye ne?", can d'aya b'angaren ji tayi ance Nazira ce.Cike da mamaki Nasrin tace"Nazira dama kina nan,lallai,sannunki,kwana dayawa?"
Nazira tace"Wallahi ina nan Nasrin,fatan kina lafiya,don Allah abunda na miki ki yafemin mu Cigaba da 'kawancen mu", murmushi Nasrin tayi tace"Nazira kenan ay ni tuni komai ya wuce,Allah yafe mana baki d'aya,Ya bayan saduwa yasu hajiya?"
Cike da jin d'adi tace"Lafiya lau,gidanku naje na anso lambarki,mum tace kina karatu a Kaduna koh,Allah ya taimaka"
Nasrin ta amsa da"Amin,Nagode"
Sannan Nazira ta kuma cewa
"Nasrin don Allah so nake na tambaye ki,Wani nagani gidanku waishi Nasim,ya nuna yana sona,so har yanxu ban bashi amsa ba inason sanin halayyar sa"
Nasrin ta ta'be baki tace mata"Yaya Nasim ne,yaron abokin Abba ne,yana da kirki da mutunci iya sanina dashi,Allah ya tabbatar da Alkhairi k'awata."
Can k'asan zuciyarta kuwa cewa take kayi hakuri yaya Nasim,bawai bana sonka bane,son wani ya riga naka shiga zuciyata,ba yina bane muk'addari ne(ni ummu arif nace yoo yana gabanki ne kike ta zuba)
Nazira ko taji da'din shaidar da Nasrin tayiwa Nasim,domin acewarta gayen ya hadu,ta mata godiya suka yi sallama.
Zinat ce tace"Nasrin don Allah inkin gama exams ina so muje ki gaishe da hajiya ta"
Murmushi Nasrin tayi tace"Allah ya kaimu"
Ta fara karatu kenan sai ga kiran Nawas,nan ta d'auka suka sha hira bayan sun gaisa da mum, Yaya Naufal,Nabil da Najwa,gaskiya tana kewarsu,har tsaida ta'dan tsokana yaya naufal tace"Angon kasha k'amshi"nan dai suka gama hirasu suka yi sallama cike da kewar juna.Ta Cigaba da karatun ta, saida taga sha biyu saura tukun ta tashi tayi addu'a ta kwanta.
Washe gari bata tashi da wuri ba kasancewar sai sha biyu take da paper,sai goma saura zinat ta tasheta.A gurguje tayi wanka taci abinci sannan ta nufi skul don tayi bita kafin su shiga.
Tana nan zaune a bakin hall tana duddubawa kafin su shiga saiga wata course mate d'inta me suna zulaihat wanda ta da'de tana son 'kulla 'kawance da Nasrin amma taga ba fuska dole ta ha'kura.
Ta samu gefenta ta zauna suka gaisa,suka fara karatun tare, har lokaci yayi suka shiga hall.
Sai Biyu ta fito,direct hostel ta wuce tunkan ta 'karasa ta hangi mutum yana ta mata murmushi,sai da taje gab dashi tukun taga ashe Abban su NY ne,murmushinta ya fa'da'da tare da mamakin me Abba yazo yi mata.
Tana isa ta rusuna tafara gaishe shi yayinda shima murmushinsa ya fa'da'da,yace
"Nasrin........."
Masoyana pls kuyi hakuri ban typing sosai this days na koma skul ne,Nagode muku sosai,luv u all.
Ummu Arif💞
OHW
®Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [8:13pm],[1/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
9⃣1⃣to9⃣5⃣
Abba yace"Nasrin kina lafiya,ya exams kuma?"
Cike da jin kunya tace"Abba lafiya lau"
Yace "zuwa nayi in duba ki", Sai taji kunyar ta k'aru mata tace"Abba maimakon ka kirani sai inje in ganka mu gaisa harda wahalar da kanka"
Murmushi yayi yace"Nasrin shin laifi ne uba ya ziiyarci yar'sa a makaranta?"
Tace"A'a Abba"
Yace"to kar in kuma ji"
Fuskar ta d'auke da murmushi ta ri'ke kunnenta tace"Am sorry"Abba yace"its ok"
Sannan yayi gyaran murya yace"Nasrin inaso ki nutsu ki saurare ni,sannan inaso duk abun dana tambayeki,ki fa'damin gaskiya"tace"to Abba insha Allah"
Yace,"Nasrin Abbanki ya bada ke ga wani ne,ma'ana yayiwa wani al'kawarin aurenki ne?"
Cike da mamakin maganar Abba da kuma kunyar sa ahankali tace"A'a Abba"
Yace"Masha Allah"
Sannan ya kuma cewa"Shin kina da wanda kuka yi alk'awarin aure dashi ne?ma'ana kuna soyayya da kuke sa ran zata kai ga Aure?"
Ta kuma cewa"A'a"
Abba ya kuma cewa"Masha Allah"
Sannan yayi gyaran murya ya fara mata magana kamar haka"Nasrin naji da'di k'warai matu'ka da jin amsoshin da kika bani domin kinyi alka'warin fa'damin gaskiya,Nasrin nazo neman alfarma ne a wajenki,sannan bawai umarni zan baki ba,kawai dai alfarma nake so kiyimin inda halin yin hakan. Nasrin Inaso ne cikin ya'yanmu in ha'daki aure da d'aya domin zumuncin mu ya d'aure,wallahi Nasrin jinki nake tamkar yadda nake jin Nasiru a raina,na matu'kar yaba kyawawan halayen ki,Shiyasa na yiwa d'aya daga cikin ya'yanmu kwa'dayin aurenki,baya ga haka banso kiyi nesa dani Nasrin,kin min halacci a rayuwa,"
Ya numfasa tukun ya Cigaba"Bana so ganin girma na yasa ki tauyewa zuciyarki hakkinta ki fa'damin sa'banin abinda zuciyarki take so,Inaso ki fa'damin gaskiya Nasrin,domin bana son in miki dole,don Allah kibani amsa ta gaskiya kinji ya'ta",. Ya kareshi maganar fuskar nan tashi d'auke da murmushi,Nasrin ko wacce tunda Abba ya fara magana kanta ke k'asa tana sauraron sa ba tare da wani tunani ba tace"Abba Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Murmushinsa ya fa'da'da,ya amsa da Amin yayinda ya fara jero mata godiya,Albarka da Addu'a kam tasha shi wurin Abba.
Ita ko Allah-Allah take ya tafi domin wani irin kunya da nauyinsa take ji ba ka'dan ba,Da haka ya mata sallama yaja motar shi ya tafi.
Ta da'de a tsaye a wurin tukun jiki a sanyaye ta nufi d'aki.
Tana shiga sallah tayi,taci abinci ta'dan mi'ke.
Tana kwance ne ta fara tunano abinda suka faru d'azu,firgit ta tashi ta fara magana ita ka'dai"Nasrin me kikayi kenan,tunani me kyau?anya bakiyi kuskure ba kuwa?ya salaam me nayi???"
Ta Cigaba"Uhmmmmm it's like i've made the right decision,Indeed its rightly says you don't always get wat u want,but at least you can get close to it(ga dukkan alamu na yanke shawara me kyau,lallai da akace ba ko yaushe ne kake samun abunda kake so ba amma zaka d'an samu kusanci dashi)"
Tayi murmushin ya'ke tukun ta Cigaba"Banyi dana sanin amsawa abba ba,domin duk da dai ban san wani d'a abba yake shirin bani ba cikin ya'yansu inada ya''kinin cewa ba NY bane,sai dai Alhamdulillah na samu babban kusanci da NY,Sannan na d'au aniya duk wanda Abban su haydar ya za'ba min cikin ya'yansu zan amshe shi da hannu bibbiyu,zan so shi matsayinsa na mijina,sai dai duk iya son da zan mishi bana tunanin zan so shi kwatan-kwacin yadda nake son NY,sai dai zanyi iya ko'ka'rina,
Ko ba komai NY zai zama ka'ni ko wan mijina". Ta ka'reshe maganar cike da jin da'di duk da dai tunda tafara maganar hawaye ya'ki daina zuba daga idanunta.jin kiran sallar la'asar ne yasa ta mi'ke ta shiga toilet ta watsa ruwa tayi alwala ta fito,tayi sallah yayinda ta da'de tana kai kukanta ga Allah.yinin ranar kwallah bai daina bin k'uncinta ba, ta inda ma ta gode Allah Zinat ta yini gida.
Abban su haydar kuwa murna ya dinga yi Nasrin zata zama surukarsa in Allah ya yarda,lallai yarinyar nan tasha tarbiya,wallahi ta da'da samun matsayi a zuciyarsa,Allah yayi mata Albarka.
Yana isa gida sama ya nufa,,hajiya ya kira a waya yace mata tazo ta same shi.
Bada jimawa ba saiga hajiya ta iso d'auke da tire kayan itatuwa ne daban-daban akai an yankasu ka'nana gwanin sha'awa ta dire shi agaban Abba yayinda ta fara jero mishi sannu da zuwa.
Ya amsa fuskan nan kamar gonar audugu(lol),hajiya tace "Alhaji ni kam meya faru ne kamar wanda aka yiwa albishir da gidan Al-jannah?",Dariya Abba yayi yace"kedai bari"Nan ya labarta mata ko meye ya faru tsakaninsa da Nasrin,ita kanta taji da'din abun ta kuma sanyawa Nasrin albarka.
Sannan tace anma Alhaji niko ga shawara,"me zai hana a ha'data da Nasiru,domin sun sha'ku sosai"
Cike da mamaki Abba yace"Hajiya ban gane ba,sun san juna kenan tun daa can?"
Itama murmushin tayi tace"K'warai da gaske,Nasiru aminin Nasrin ne tun da da'dewa,har gidansu yaje sanda tayi candy d'inta,sun ha'dune suka 'kulla abota sanda ka aikesa gun Alh yusuf na jos",
Jinda'di iya jinda'di Abba yaji sa,domin tabbas ya tuna sanda ya aike sa gun Alh Yusuf,"Allah sarki"Abinda Abba ya furta kenan,Allah ya tabbatar mana da alkhairi hajiya,dukkansu suka amsa da "Amin"
Ya tabbatarwa da hajiya cewa nasiru na shigowa su hauro gunsa tare,hajiya ta amsa da to yayinda ta tashi ta nufi k'asa don taga wata wainar yara ke tauyawa....
Nasrin yau dai kizo ga......
Ummu Arif💞
OHW
®Online Hausa Writers®
?
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [4:48pm,][3/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
1⃣0⃣1⃣to1⃣0⃣5⃣
Ji kawai suka yi ance "A'a Nasrin yaushe kika zo", Firgit! dukkan su suka juyo suka kalli mai maganar.Abba ne
Sai duk kunya ta rufesu musamman ma Nasrin.Abba ya katse shirun yace"Nasiru ku shiga ciki mana,barin sallami ba'kinnan nazo mu gaisa ko ya'ta".
Murmushi tayi NY yayi ciki ta bishi a baya.
Suna shiga fallon hajiya k'annensa suka taho da gudu suka rungumeta yayinda murmushinta ya fa'da'da.Suka gaisa sannan suka kawo mata abin motsa baki, Tana zaune saiga hajiya ta shigo ta rusuna ta gaisheta, saita tsinci kanta dajin kunyar hajiya sosai.
Bayan sun gaisa ne Hajiya ta fuskanci wani mayataccen kallo da NY ke bin Nasrin dashi,murmushi tayi ta tashi tabar musu fallon.
NY ne ya matso kusa da Nasrin yace"Wollah ko kici ko in miki d'ure"itama murmushin ta sanya tace"Wuce nan"
Yace"Allah yarinya ta cika baki ta gani"
Tace"hhhhhh,so nawa ana fa'din haka"
Nan dai sukayi ta hiran su cikin wasa da dariya shidai yanata jin wani abu game da ita amma ya rasa menene.
A nata b'angaren kuwa wani da'di take ji wai yau gata ga NY cikin gidansu suna hira"Ina ma ace mu masoya ne", cikin ranta take fa'din haka sai dai kash bakin al'kalami ya riga ya bushe Abba ya bada ta ga waninsa.
Sallamar Abba ne ya katse musu hirarsu da zancen zuci da suke ta sa'kawa.Ya zauna yayinda Nasrin ta sauka k'asa domin gaidashi, Nan take sanar mishi cewa gobe zata tafi jos.
Yace mata za'a zo d'aukanta ne?
Tace mishi A'a,ita dakanta zata tafi domin Abbanta da Naufal sunje Sokoto,Nawas kuma baida lafiya.
Abba yace Allah dawo dasu lafiya,Shikuma Nawas Allah bashi lafiya.....
Yayi gyaran murya yace"Nasiru gobe In Allah ya kaimu saika kaita koh,sai dai kuyi sammako don kar yamma tayi muku a hanya".NY yace"Abba
duk yadda kace haka za'ayi"
Murmushi jin da'di Abba yayi, Nasrin kuwa godiya tafara yi mishi duk da dai wata irin kunyarsa takeji.
Hajiya tazo da sauran k'annensa da Abba sukayi sallama da Nasrin cike da kewarta.
Har bakin mota dukkansu suka rakata domin Abba yace NY ya maidata makaranta bayan ya jaddada mata ta shirya da wuri domin so yake zuwa takwas na safe su wuce.
A cikin motar ma kowannen su shiru yayi da Abun da yake tsa'kawa a ransa.Nasrin ce tace"Driver na pls zan tsaya a kasuwa in d'an yi siyayya" ta k'areshi maganar cike da zolaya, juyowa yayi yace"Lallai, Abba ne yasa kika raina ni,amna yarinya zan kamaki saina matse bakin nan me cemin driver"
Dariya tasa tace"Da'dina dakai ragonci tun yaushe kake zaka kamani,yanzu ay gani gaka koh"
Murmushi yayi yace"Nassy baby baza ki gane ba,zan dai kamaki a ruwan sanyi"
Tace"Na saba jin wannan"
Haka suka dinga hira tana ta tsokanar shi,ya'ki ya biye mata.har suka kawo dai-dai wani mall ya fita yace ta jira shi yaje yayi mata tsaraba ya fito yaja mota sai KASU.
Suna isa ya taimaka mata suka shiga da kayan, Tukun yayi mata sallama ya tafi bayan ya jaddada mata cewa gobe takwas zaizo su wuce.
Nasrin tana shiga wanka tayi, tayi sallar la'asar tukun ta'dan mi'ke.Sai biyar da rabi ta tashi ta shirya kayanta ta aje su wuri d'aya, sannan taje tayi sallama da course mates d'inta wa'yanda suke mutunci tana dawowa ta tadda zinat a d'aki murmushi ta sakar mata tace"kin kyauta biki da'di koh sai maghrib kike dawowa", Zinat wacce tayi kalar tausayi da fuskarta cewa Nasrin tayi"Wallah wurin ne daga nan da nisa shi yasa kika ga na da'de".
Nasrin tace"Ok,Allah sanya allhairi ya fidda mu 'yan baya"
Dariya Zinat tayi tukun tace"Amin, saidai mu mu ro'ka ku kam sai godiya ga Allah" Nasrin tace"Zinat ban gane ba"
Zinat ta'dan matso daf da ita tukun tace"Nasrin kenan,kina tunanin bansan soyayyar ki da Amininki bane, Gaskiya kinyi dacen miji Allah ya tabbatar da Alkhairi"
Nasrin wanda hawaye ya cika idonta 'ka'kalo murmushin dole tayi tace"Amin"
Tana fa'din haka tayi ban'daki taje taci kuka tukun tayi alwala ta fito.
Ko abinci ta kasa ci sai uban zumu'di, tea kawai tasha suka sha hira da Nawas tukun sukai sallama.
Tana kwance tana tunanin NY sai kuwa ga kiransa ya shigo wayarta cike da farin ciki ta d'auka ji tayi yace cikin dakakkiyar murya"Me kike yi har yanzu bakiyi barci ba"
Cikin muryan ta me da'din sauraro ta langwa'be tace"Yaya Nasir nayi waya ne da yaya nawas dasu mum,na kwanta barci ya'ki zuwa inata tunanin...."
Sai kuma ta fasa kareshe maganar tayi shiru.B'angaransa kuwa bai so ta daina magana ba domin ratsa jikinshi muryanta yake,Shi kanshi yana mamaki a cikin kwanakin nan komai na Nasrin canja mishi yake,shin ta canja ne?
Tambayar da babu mai amsa ma sai zuciyar ka, Nidai ummu arif nace bata canja ba kaine dai kake jin wani sabon abu game da ita.
Murmushi yayi yace"Tunani na kike koh?
Tace"Tab tunaninka hhhh, Nahi NY"
Murmushi yayi yace kedai fa'di gaskiya zan baki lollipop"
Tace"Promise"
(alkawari), Yace"Yeah i promise"(eh nayi alkawari)
Tace"Tunaninka na keyi kawai sai ga call d'inka"
Yace "me yasa kike tunanina??"
Murmushi tayi tace"Ba tun yau nake tunanin ka ba, Duk sanda nake cikin yanayin na raha da nisha'di saina tuna abokin tsokana ta🌹Aminina na Kwarai🌹,me sani dariya,mai kawar da ba'kin cikina, mai bani shawarori, uhmmmm abubuwa dai da dama ke sani tuna ka"
Murmushi yayi mai burge Nasrin,sai yaji yarinyar ta 'kara burgesa wato duk dakon son shi da ta da'de tana yi bazata iya furta mishi ba, lallai ya jinjina karfin zuciyarta.Sannan yace"Nasrin indai hakane ya zama kenan ko yaushe ina ranki, domin nasanki da son raha", Tayi caraf tace"eh hakane kuma amma kai kana tunani kuwa?" Ta kareshe maganar cikin shagwaba.
Ay kuwa maganar ba k'aramin ratsa shi tayi ba duk sai yaji kasala, a hankali yace"Nasrin ko yaushe kina raina,wollah wannan murya taki kasala take samin, kinga ki kwanta gobe zamuyi sammako kin tuna, so gudnyt swt dreams koh"
Murmushi tayi tace"Same to u bye"
Da haka ta kashe wayan tayi addu'ar bacci cike da nisha'di jin NY yace ko yaushe tana ransa.
B'angaren NY kuwa bacci ya gagara duk juyinshi jin muryar Nasrin yake sanda tace"Amma kai kana tunani na kuwa?"
Addu'a yayi abinshi,ya Cigaba da tuno Nasrin bai san sanda barci ya sace shi ba,
Nima ummu arif ji kawai nayi ana sallama a masallaci an idar da sallar asuba, Ay ba shiri na mi'ke nayi toilet a guje don inyi sallah in shirya, Yasin dani su NY zasu jos......
Ummu Arif💞
[2:23pm][5/2/2016]:Hauwa Hassan Nayaya
1⃣0⃣6⃣to1⃣1⃣0⃣
Washe gari tun shida Nasrin ta tashi tayi wanka tayi breakfast ta shirya tana jiran NY, Zinat sai taji wani irin Nasrin tana tsaye daga bakin cikin sai k'arewa d'akin kallo take yi.
Zinat ce tace"Nasrin lafiya kuwa?"
Murmushi Nasrin tayi tace"Wallahi Zinat ji nake kamar bazan kuma dawowa d'akinnan da zama ba"
"Uhmmmmmm Nasrin kenan wato zaki tafi ki barni Allah yasa rashin dawowanki alkhairi ne"cewar Zinat
A sanyaye Nasrin tace"Amin Zinat nagode sosai"
Tana gama fa'din haka kuwa taji karar text ya shigo wayarta, tana dubawa taga NY ne"Baby ki fito ina waje"
Murmushi tayi tace"NY da sabon salon tsokana wai nice baby"
Tace "Zinat tayani fidda kaya NY yazo?
Zinat tare da wasu course mates d'inta su suka kai mata kaf kayanta NY ya bu'de boot yasa yashiga ya zauna yana jiranta.
Saida ta da'da yin sallama da mates d'inta tukun tafito Zinat har bakin mota ta rakota"Nasrin tace pls Zinat ki kula da kanki ki ri'ke min al'kawari kada a koma gidan jiya, Allah sada mu da Alkhairi"
Hawaye ne ki bin 'kuncin Zinat cikin Zuciyarta wani sabon son Nasrin ne ke wanzuwa, A sanyace tace"Amin,Insha Allah Nasrin ba abun da zai kuma faruwa, Nagode Allah ya kiyaye hanya agaida su mum"
Tana fa'din haka ta juya ta bar wurin domin kuka yaci k'arfinta
Nasrin ma saida tayi k'wallah tace"Zasuji insha Allah, nagode"
Ta bu'de mota ta shiga yayinda ta fara gaishe da NY,kallonta kawai yake yi domin wani kyau yaga tayi mishi,sai da ta natso daf dashi ta hura mishi iska a ido tukun ya daidaita nutsuwarsa sannan tace"hey me kake kallo ko ka hango wata ce in fita inyi mata magana?"
Murmushi yayi a zuciyar shi kuwa cewa yayi ke nake kallo, a fili kuwa cewa yayi"Uhnmn nassy bby wallahi wani tunani nake dabam, kin kwana lafiya"
Tace"lafiya lau, kaifa?"
Yace"same"
Murmushi yayi sukayi addu'a tukun yayi bismillah ya kunna mota sai jos.
Suna tafe kowa da abinda da yake sa'kawa a ransa, NY ko satar kallonta yake jifa-jifa shi kanshi tambayar kanshi yake me yake damunsa sai dai amsa d'aya zuciyarsa take bashi sonta kake, murmushi yayi yace"Am in love"
Baisan maganar zuci ta fito fili ba sai ji kawai yayi Nasrin tace" with who??"cikin tashin hankali wanda ya bayyana k'arara a fuskar ta.
Juyowa yayi ya kalleta yaga yanayinta ya sauya sai duk ta bashi tausayi sai yacr"Am in love with my phone,haba ay inda da wata kece zaki fara sani"
Ya'ke tayi wanda yafi kuka ciwo tace"Uhmmm Allah yasa"
Yace"yawwa Nasrin yaushe ne aurenki ni kuwa?
"Uhmmmmm ka tambayi Abba" ta bashi amsa a ta'akaice
Yace"To yanzu ya za kiji in akace amininki ya zama angonki?"
Dariya tayi mai isar ta sannan tace"Tab'di angona mai sa oversize shoe ga rigunansa maji gaba, lallai banni yarda"
Dariya suka yi dukkansu tukun NY yace"Wollah karya kike yarinya,lokacin da nazo walimarki nasan bakiso na tafi ba kinga gaye d'an k'wallisa"
Tabe baki tayi tace "Sannu magori"
Yace"Eh anji d'in"
Haka dai suka dinga tsokanar juna,can dai NY yace "wai da gaske in tambayi Abba maganar aurenki?"
A hankali tace "Allah kuwa"
Yace"Uhmmm,ai ni nasan angon,sai dai baison hira sosai saikin koya mishi bayan aure kanari, Don haka dani za kina hiran yana gefe yana jinmu"
Tace"kut, wai da gaske kake?"
Yace" sosaima"
Ta ta'be baki tace"Shikenan"
Tun daga tayi shiru tanata tunani, yanzu shikenan mafarkinta na son mallakar NY ya ruguje, Allah yasa hakanne mafi alkhairi.
Ta d'auko sandwich d'in da tayi musu ta'dan ci ka'dan tukun tace NY ya tsaya ta koma baya tayi barci kanta na ciwo.
Ba musu yayi parking ta fita ta koma baya ya ja suka Cigaba da tafiya.
Ita ko data kwanta tunani ne ya addabi zuciyarta ta ro'ki Allah yasa barci ya d'auketa nan bada jimawa ba, cikin ikon Allah ko barci mai nauyi ya d'auke ta.
NY ko ya lura da yanayin data shiga tunda yace mata yasan angonta, sai duk yaji ba da'di amma hasashen da yake yi kanta gaskiya ne ma'ana tana da matu'kar sonsa.
Murmushi yayi yace "Nasrin Insha Allah zan ninka miki son da kika yimin duk da dai bansan iya lokacin da kika d'auka kina DAKON SO na ba Allah sarki nassy baby Ina mai matu'kar jinjina miki saboda DAKON SO masifa ne, nagani kan wani abokina.
Bi'iznillah Nasrin naki yazo karshe"
Shi ka'dai yake tu'ki yake magana abinsa, Abin kawai daya ke tunani shine lallai so halitta ne.
Yana ta tu'ki abinsa gashi mai taya shi hira nata barci abinta kuma bayyi tunanin tashinta ba.
Sha biyu saura dai-dai yayi horn a 'kofar gidansu Nasrin, Maigadi ya taso da gudunsa ya bu'de mishi gate ya shiga ya parking.
Nabil ya fara fitowa ya nufo motar yana ganin NY mamaki ya baibaye fuskar sa yace"Yaya Nasir barka da zuwa,gashi adda Nasrin bata nan"
Murmushi NY yayi yace tana baya bu'de ka tasheta, yana le'kawa kuwa ya ganta ay cikin hanzari ya bu'de ya fara Adda Nasrin!Adda Nasrin!! Ta bude ido a hankali taga Nabil ta kulle ta kuma bu'dewa hakan ya tabbatar mata da cewan ba mafarki bane ay kuwa tashi tayi ta rungumesa tana murna, NY bin ta kawai yayi da ido komai nata yanxu burgesa yake.
Ya fito su Nabil da Najwa suka shigar da kaya tukun suka jera shi da ita har cikin fallon su, Ai kuwa da gudu ta fa'da jikin mum tanata farincikin ganinsu.
NY ne ya fara gaisheta tukun ta saki Nasrin ta amsa fuska fal fara'a.
Hayaniyar suce ya tada Nawas ala dole ya nufo fallon yaga me ke faruwa, Ai yana ganin lil sis rai yaga rai da gudunsa ya taho itama haka ta taho suka rungume juna.
Hakan yayi dai-dai da tasowar wani kishi a zuciyar NY(mr kishi bro dinta ne inji jidda) ko zaka bugesa ne???
Masu karatu ayi hakuri dani na rashin typing wlh skul ne,Mrs Abdul
Ummu Arif💞
⭐OHW⭐
® Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [8:00pm][20/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
136 to140
Princess ta gani cikin shiga ta alfarma, murmushi ta sakar ma ta yayinda itama princess ta mayar ma ta zuwa tayi ta rungume ta sannan ta ja ta suka zauna tace"Princess sannu da zuwa,yasu Abba da hajiya ke dawa kuka zo?"
Murmushi princess tayi tace"lafiya lau amaryar mu, kowa na gaishe ki, tare da ango muke ga kayan fitar biki nan" ta nuna ma ta wasu manyan akwati guda biyu, murmushi Nasrin tayi tace nagode sosai.
Nan suka haye sama suka je suka dinga hira ango kuma yana tare da Naufal kasancewar Nawas baya nan.
Sai biyu dai-dai NY ya kira princess a waya yace tazo zasu wuce,suka gangaro da Nasrin har k'ofar parlour amma Nasrin ta'ki fita princess tayi-tayi taje su gaisa da angonta amma k'ememe Nasrin ta'ki zuwa tace ma ta kunyarsa take ji kuma in banda abinsa ai an kusa kaita garesa koh,da dai princess taga ba ta da niyyar zuwa sai ta k'yale ta suka yi sallama tayi musu fatan isa gida lafiya.
Shi ko NY yana mota yana hangen duk abun da suke yi, da yaga princess ta taho ita ka'dai sai tausayin Nasrin ya kamashi yasan ba don komai ta'ki zuwa ba sai ganin wanda zata aura zai da'da ma ta tashin hankali, a hankali yace"nassy baby kin kusa dawwama cikin farin ciki hak'uri da addu'a zai miki rana"
Yana gama fa'din haka princess ta iso ta bu'de mota ta shiga ta zauna ya maido da kallonsa gareta yace"ta'ki zuwa koh?"
Princess tace"eh kunyar ka take ji amma tace in gaisheka Allah kiyaye hanya"
Murmushi yayi yace"Amin, nagode"
Yasan ta Fa'di hakanne kawai bawai tana nufinsa ba, sukai sallama da Naufal yaja mota sai Kaduna.
Nasrin ko da ta koma d'akinta ta nufa yayinda yan'uwansu suka bu'de akwatu nan kowa na tofa albarkacin bakin ta.
Key tasa ta kulle ta fa'da gado sai taji wayarta na ringing ganin NY ne me kiran yasa ta goge hawayenta ta picking tayi sallama, can b'angaren taji NY yace"ai munyi fa'da tunda kika'ki zuwa gaishe da ango"
Murnushi tayi tace"kunyar sa nake ji shiyasa, kace yayi ha'kuri"
Yace"bakomai da dai kinje kin ganshi da kinji da'di" tace"uhmmmmm kwana nawa ne zamu kasance tare"
Yace"hakane barin concentrate ina driving we talk ltr koh"
Tace"ok safe journey bye"
Da haka ta katse wayar ta ajiyeta gefe ta fara aikin kuka.
NY yana tu'ki yana ta tunanin Nasrin domin yaji damuwa tsantsa cikin muryarta ji yake kamar ya sanar da ita shine wanda zata aura ko ta samu sukuni, amma ina yayi al'kawari sai an kai ta gidansa zata ga shine mijinta amma zuciyarsa ta fara rauni baya tunanin zai iya cigaba ganinta cikin damuwa.
Koda mum ta tambayi Nasrin ko tana son yin wani program ne a bikin? ce ma ta tayi kawai ayi saukar Al'quran ayi addu'a a ci a sha kowa ya watse, mum tayi matu'kar jin da'din mganar nan ta sanya mata albarka ta fita ta barta sai dai ta fuskanci Nasrin d'in kamar tana cikin damuwa ga rama da ta yi, sai tayi tunanin ko barin gida da zata yi ne ya sanya haka.
Ana gobe sa lalle Zinat ta diro jos bayan an gama sauka anyi addu'a sosai kowa yaci yasha aka rarraba jakan kuna masu d'auke da sunan ango da amarya, amma da yake ance hankali shine mai gani ba ido ba Nasrin bata kai idonta ga duban abubuwan da aka raba ba, asalima tashi tayi tashiga ciki abinta.
Ganin zinat kuwa ba k'aramin sanya Nasrin jinda'di yayi ba ta kuma samun y'an hira dama tun ranar laraba cousins d'inta suka zo tare da k'awarta Aisha da Nazira a cewar su har Kaduna zasu raka amarya.Ko da zuwan su ma ita bawani saka baki a hirarsu takeyi ba banda waya da NY domin a wannan lokaci shine ka'dai ke kwantar ma ta da hankali duk da dai ba ta fa'damishi tana cikin damuwa ba shine ya fuskanci hakan amma yasan komai yazo k'arshe da yardar Allah.
Ranar sa lalle ranar ne gidan matar naufal za suyi kamu a permanent side saboda haka yan'uwan maman Nasrin da na Abba suka shirya domin zuwa wurin kamun Nawwarah.
Sauran yan'uwa kuma suka d'auki hanyar zuwa kaduna don yiwa amarya Nasrin jere.
B'angaren gidansu NY kuwa ba masaka tsinke gida ya cika ma'kil domin Abba zaiyi bikin d'ansa na fari, Abba mutum ne mai kirki wa danginsa masu shi da marasa shi da abokan arziki, hajiya ma ba'a barta baya ba domin mace ce me mutunci da ganin girman manya, uban biki kuwa Nasir halinshi kaf unguwa da dangi ro'kon Allah suke ya baiwa ya'yansu irin halayyar sa shiyasa dangi uwa da uba suka zo bikin NY.
Ango kuwa baki har kunne zaiyi auren biyayya da kuma so da k'auna domin shi mutum ne mai son mace me sonsa tsakani da Allah sai gashi Allah ya bashi Nasrin baiwar Allah me kwana da tashi da sonsa shiyasa ya d'au al'kawarin faranta mata har iya tsawon rayuwarsu.
Masu zuwa jere kuwa sai biyu da rabi suka isa Kaduna, a gidansu NY suka ya da zango suka yi sallah suka ci abinci tukun aka yi musu jagora zuwa gidan amarya dake unguwar malali inda suka jere ma ta kayanta, gaskiya iyayen Nasrin sun zuba ma ta dukiya koni ummu arif da na ga d'akuna nan musamman ma kitchen wollah na zaci a turai nake abin dai sai sam barka ko su yan'uwan NY sun jinjinawa iyayen Nasrin domin sun b'ar da naira.
Can jos kuwa anata bidiri wurin kamu amaryar Naufal Nawwarah tasha kyau har ta gaji tayi ado cikin wani tsaddadan net ba'ki mai adon golden ta sa gwaggwaro da jaka, sar'ka da d'ankunne gold, tayi kyau sosai.
Sai da aka kusa kammmalawa ango Naufal yazo da Abokansa inda yayi shigarsa ta alfarma cikin farar shadda gezna da agogon rolex ga takalmi na gucci da hula ba'ka mai suna minister yayi kyau sosai shima, ya d'an taka rawa da amaryar sa inda yan'uwa da abokan arziki suka yi ta musu li'ki tukun shida abokansa su ma suka yi b'arin naira suka k'ara gaba.
An gama kamu kowa ya koma gida yana sanya alkhairi, yan'uwan Naufal suna ta murna domin anyi musu kar'ban mutunci a wurin ka mun iyayen nawwarah sunyi bajinta sosai.
Masu zuwa sa lalle daga Kaduna zuwa jos sai k'arfe bakwai suka iso, su kuwa wa'yanda suka je jere sunce sai an kawo amarya tukun zasu koma nan aka basu masauki.Amarya tasha k'unshi da kitso tayi kyau sosai kawaye ma ba'a barsu baya ba su zinat k'irjin biki ansha kyau, Nasrin dai in tana tare da su tana k'ok'rin danne damuwarta sosai don kada su fahimta.
Nasrin ce kwance a d'aki taji anata ranga'da guda an dawo daga sawa matar yaya Naufal lalle tasan tabbas saura ita ji tayi wasu zazzafan hawaye na gangaro ma ta k'arar wayar ta ne ya katse ma ta tunanin da take yi ta kai hannu ta d'auka don gannin me kiran ta, murmushi tayi domin......
Kunjini shiru 2days wollah banjin da'di ne,Mrs Abdul luv u all.
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writer's Association.
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [10:04pm],[15/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
120 to 130
Murmushi NY yayi ma ta tukun yace"Nasrin an bada sadakin ki, zuwan da muka yi dama akan maganar auren ne cikin saa kuwa ashe Abban Nasim yasan Abbana shine abu yazo da sau'ki ba bu'katar dogon bincike kawai yayan Abbana ya mi'ka sadaki an sanya bikin wata d'aya da kwana Ashirin daga yanxu wato dai-dai da na Naufal kenan, Nasrin ina miki fatan alkhairi Allah ya kai ran mu.
Nasrin nasan akwai wanda zuciyarki ta da'de tana so amma kiyi ha'kuri ki amshi duk wanda kika gani matsayin mijin ki, ki sani cewa wani hanin ga Allah baiwa ne san nan sanin kanki ne Abba bazai za'ba miki wanda bai da tarbiya ba don haka nake ba ki ha'kuri Allah ya bar zumunci mungode".
Nasrin tunda NY ya fara magana jikinta yayi sanyi hawaye ya yi ta zuba a idonta ka sa cewa komai tayi NY ne ya ciro handkerchief da ga aljihunsa ya matso gab da ita ya cire hannayen ta da ga fuskarta ya fara goge ma ta hawayen. Dukkansu sai da suka ji wani yarr a jikin su domin in ba yau ba ko mayafin ta NY bai ta'ba ri'kewa ba, ahankali ta kar'bi handkerchief d'in da ga hannunsa ta ci ga ba da goge fus'karta bayan tace mishi ta gode a ta'kaice.
Mamaki ne ya yi ma ta yawa shin da ma NY yasan akwai wanda take so?, ko dai ma yasan shi take so?
Ji take kamar ta tambaye shi da ma yasan tana dakon son wani ne? sai wata zuciyar tace ma ta kada ki soma kawai ki'dau shawarar da ya ba ki tunda haka rayuwa ta zo miki sai ki kar'beta ki gode Allah, tayi zurfi cikin tunani da zancen zuci hura ma ta iska da aka yi ne a fuska ya maido dubanta ga NY.
Murmushi ta yi mishi tukun tace"Nagode sosai Nasir Allah ya k'ara zumunci ya saka muku da mafificin alkhairi" ta k'areshe maganar tana zubda hawaye NY sai duk yaji ba da'di kamar yace ma ta shine angon sai kuma ya fa sa ya sauya hirar tasu ta koma tsokana har sai da ya ga Nasrin ta ware tana ta dariya tukun yaji da'di cikin ransa.
Da haka suka tashi suka nufi fallon da su Abba su ke, sukai sallama yayin da su Abba sukai ta yiwa iyayen Nasrin godiya.Har bakin mota su ka rako su suka yi musu fatan isa lafiya, NY ya ja mota suka d'au hanyar Kaduna bayan ya tabbatarwa da Nasrin su na isa zai kira ta.
Tana shiga ciki d'akinta ta nufa ta kulle 'kofa ta hau gado tasha kuka daga baya barci yayi gaba da ita.
Sai bayan la'asar ta tashi kasancewar mum da nawas sun san halin da ta ke ciki shiyasa ba wanda ya tashe ta, sallah tayi tukun ta sauko k'asa ta samu su mum suna hira sannu kawai ta musu ta nufi kitchen ta zubo abinci taje kan dining tana cin abinta tana sauraron wa'azin shiek muhammad kabir gombe a wayarta.
Nawas ne da yaji shirun na ta yayi yawa yace"lil sis yau y'ar hiran ma babu ne?"
D'ago kai ta yi ta kalleshi tayi murmushi tace"bro nemana kake da magana, dana sauko bance sannunku ba"
Yace" ai sannunku ba magana bane, kawai kizo nan muyi hira amaryar kwanan nan"
Ya k'areshe maganar da zolaya, tasowa tayi takai plate d'in kitchen tazo ta zauna tace ma nawas"to gani koh"
Murmushi Nawas yayi mata wanda ke k'ara fiddo mishi da kyawunsa yace"ai labari zaki bamu me da'di" mum da ke gefe ta fuskanci akwai abin dake damun Nasrin amma tasan koma meye yana da nasaba da kawo sadakin ta, murmushi tayi tace "Nasrin lafiya na ganki haka?" Itama Nasrin murmushin tayi tace "lafiya lau mum"
Duk da dai mum bata yarda da amsar da ta ba ta ba tashi tayi ta nufi d'aki tace Allah ya sawaqe.
Nawas ne ya matso kusa da Nasrin yace "yawwa lil sis ban wayarki inga al'kawarina"
Murmushi tayi ta mi'ka mishi da ma al'kawari tayi mishi zata nuna mishi k'annen NY da room mate d'inta Zinat.
Yana kar'ba kuwa ya shiga gallery ya fara kallon pics d'in ba tantama k'annensa ne domin kama da suke sai dai akwai wata cikinsu wacce taja hankalin Nawas.
Shi tunda yake bai ta'ba yiwa mace kallo sama da biyu ba amma sai gashi sai kallon wannan y'ar budurwa yake yayinda yake ta murmushi, nasrin ta fuskanci kamar akwai abinda ya d'auke hankalinsa cikin wayarta ta zaga bayan sa a hankali ta ga ya k'urawa hoton Anisa ido.
K'anwar NY ce wacce ba ta wuce shekara sha takwas ba yarinyar akwaita da kyau na d'aukar hankali duk da dai ba fara ba ce ga ta ba ta da surutu sosai she's very calm kusan duk gidan ta fisu kyau shi yasa suke ce mata PRINCESS.
Nasrin kuwa yau abun tsokana ya samu tayi caraf tace"wai-wai-wai rana bata k'arya,kai yau wacce rana yaya nawas na yiwa wata d'iya mace kallon k'urilla gaskiya princess ta d'aga tuta, murmushi yayi yace"Nasrin lower your voice please zagayo muyi magana"
Sai dai tayi dariya sosai tukun ta zagayo.
Nawas yace lil sis wallahi inajin wani abu game da yarinyar nan duk da ban sani ba so ne idan kika yi la'akari da kallonta dana dinga wanda a tahirin rayuwata ban ta'ba ba, murmushi Nasrin tayi tace"wannan shine love at first sight"
Yace"kedai bari, yanzu meye abinyi?
Nasrin tace "bro kabar komai a hannuna zan yiwa NY magana anjima sannan daga baya sai inyi mata"
Cike da zumu'di yace"pls do that for me sis, nagode"
Nan dai suka Cigaba da hirar su Nasrin nata mamakin Nawas lallai so halitta ne.
Sai bayan sallar isha'i NY ya kira Nasrin yace mata sun isa tuntuni kasancewar bata son d'anuwansa shine kota kira su koh,yayi dai ta k'orafi,ita dai hakuri take ta bashi domin tayi ta kira ya'ki shiga amma ya tsaya ya saurare uzurinta sam ya'ki k'arshe ma katse wayar tayi.
Nasrin bin wayar tayi da ido kasancewar hakan bai ta'ba faruwa tsakaninta dashi ba ai kuwa sai kuka kamar wacce aka buga, tayi ta kiranshi amma ya'ki picking daga k'arshe ta yanke shawarar kiran...
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writer's Association.
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [8:21am],[10/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
111 to 115
Nasrin Murna Nawas Murna.Sakinta yayi yayinda ya fuskanci wani kallo da ba'kon Nasrin yake yi mishi.Nasrin ce fuskar nan kamar gonar auduga tace"My Nawas meet NY, NY meet My Nawas"
Cike da mamaki Nawas yake kallon NY domin lokacin daya rungumi Nasrin yaga kishi tsantsa a idon NY amma sai ya basar yaje gareshi ya mi'ka masa hannu sukayi musabaha nan fa suka fara gaishe-gaishe.
Nawas ne yace"Nasir muje ciki ka watsa ruwa koh kayi sallah sai akawo ma abinci, ba musu NY yabi Nawas ciki.
Bayan yayi wanka yayi sallah Nawas ya gabatar mishi da Abinci.Yana ci suna hira nan NY ya bashi labarin yadda Nasrin ta taimaki mahaifinsa cikin rashin sanin waye shi har jininta aka k'ara mishi, nawas baiyi mamakin taimakon data yiwa Abban NY ba domin yasan sis d'inshi zata yi fiye da haka, mamakin da yayi kawai shine yadda bata gane shiba.
Suka Cigaba da hira yayinda Nawas yakejin da'din abinda sis d'insa tayi cikin ransa.
NY ya Cigaba da labarta mishi yadda suka yi da Abban sa na son ya aure Nasrin kuma shima ya amsawa mahaifinsa.
Sai dai b'angaren Nasrin bata san wanda Abba na ya bata ba domin ce mata yayi cikin ya'yansa zai ha'data aure da wani.
NY ya tashi ya d'an matsa kusa da Nawas ya numfasa tukun yace"Nawas Nasrin ta amsawa Abba ne badon taso ba sai don tana ganin girmansa,kuma tanajin wani b'oyayyen al'amari game dashi sannan kuma tana sonsa bisa ga son daya nuna mata lokaci guda, wato Allah Al-hakim ne son da Nasrin take yimin shine ya shafi mahaifana da yan'uwa, tunda takai Abbana asibiti har aka sallame shi kullum sai taje duba shi, kwa'dayin halayenta ne Abba yayi sha'awar ha'data aure dani domin baida masaniya cewa nasan Nasrin da da'dewa, in ta'kaice maka zance dai Insha Allah nine ANGON NASRIN sai dai ina so kar tasan nine wanda abba ya za'ba mata, gaskiya halayyar Nasrin sunyi".
Nawas wanda tunda NY ya fara magana k'wallah ke bin k'uncinsa murmushi yayi na jin da'di bayan ya yiwa Allah godiya yace
"Nasir wato na yarda Maha'kurci Mawadaci lallai Allah maji ro'kon bawa ne, nasir baku da'de da fara k'awance da Nasrin ba kyawawan halayyarka suka dasa mata sonka a zuciyarta.Allah sarki sis tasha dokon sonka na lokaci mai tsayi domin har yanxu tana kai, Saboda sonka ta kasa barci,ta yini d'aki ta kwana kuka, ta kori ko wanne saurayi daya zo mata, addu'arta kullum Allah ya mallaka mata NY matsayin Abokin rayuwar ta, duk 'yan gidan nan kowa yasan halin data ke ciki na sonka.Amma yau kaine a gabana kake sanarmin cewa burin lil sis ya kusa cika Alhamdulillah".
Matsawa yayi ya rungumi NY cikin jinda'di yayinda yake tayi masa godiya, murmushi NY yayi yaji duk tausayin Nasrin ya kamasa lallai haka abin yake, yace"Nawas nine da godiya bisa ga taimakon da Nasrin ta yiwa Abbana Allah tabbatar mana da Alkhairi, zan kwana anan gobe saina wuce pls kabari saina tafi ka sanar da mum kada na fara jin kunyarta".
Nawas kwashewa yayi da dariya yace"Ai yanxu kuwa zan sanar mata"
Dariya suka yi duka suka Cigaba da hirarsu cikin jinda'di da nisha'di.
***********
Nasrin ko ana can anyi d'ai-d'ai a gado wai ita nan ta gaji.
Sai hu'du saura ta tashi don kanta domin mum cewa tayi kada a tasheta.
Da sauri ta nufi toilet tayi wanka ta d'aura alwala ta fito tayi sallah tukun ta shafa cream ta zira doguwan riga ta sauko k'asa.
Parlour shiru ba kowa, kitchen ta nufa domin ta jiyo hayaniya amma me zata gani........Nawas ne da NY sanye da apron suna ta faman girki mum na zauna tana basu order Nasrin tsabar dariya saida takai k'asa lokaci d'aya suka juyo suna kallonta cike da mamaki ko meye ya sata dariya oho.
Sai da tayi dariya ma'ishiya tukun tace"Yau zamuci kwa'do yanzu mum don Allah sune suke girki, don Allah dubesu kowannen su ya gwafe sai aiki yake kamar da gaske harda sanya apron"
k'ara kwashewa da dariya tayi, mum ta kalleta tace"In anyi kar kici uwar tsokana"
Nawas kuwa wanda ya fara k'ula cewa yayi
"lil sis dama muna hakane, kece sabon ganina ina girki tambaye su nabil su baki labari sanda bakinan wake girki"
"Uhmmmmm"abinda tace kenan, sannan tace"Ba girin-girin ba"
NY kuwa tun shigowar Nasrin kitchen d'in yake jin wani sanyi na ratsashi koda ta fara magana baiso ta daina ba, murmushi yayi yace"kardai mugama yarinya tazo k'ari ehe"
Itama murmushin tayi tace na gaida"Chef NY da Nawas"
Daga haka tabar kitchen d'in ta nufi d'akin nabil.
Ta taddasu yana koyawa Najwa Assignment nan ta zauna tace itama ayi da ita.
Chef NY da Nawas sun kammala girkinsu sun jereshi a dining table, jollof macaroni ne sai farfesun kayan ciki sai lemun Tufa da Abarba da suka yi Abincin yayi kyau a ido Allah sa dai a baki ma hakan take.
Suka nufi D'akin Nawas don yin wanka da gabatar sa sallah.
Nasrin na mamakin NY sam bashi da ba'kunta,murmushi tayi tace"Nima fa haka nake cikin yan'uwansa.
Sai bayan sallar isha'i kowa ya hallara dining, bayan su Nasrin sunyi waya da Abba da yaya Naufal, abba ya tabbatar musu cewa Insha Allah suna nan tafe ranar litinin.
Nawas ne yace kowa ya serving kansa haka kuwa akayi saidai NY ne ya serving mum taji da'di matu'ka. Nasrin tace"Nasir bari na serving d'inka"
Murmushi yayi yace "Nagode"
Ta serving d'inshi ta serving kanta Sukai Bismillah gaba d'ayan su, suka fara bawa ciki hakkinsa.
Kasan cewar Al'adarsu in suna cin abinci basu magana hakan yasa Nasrin yi musu alamu da hannu irin abincin yayi da'di fa, murmushi dukkan su suka yi mata suka maida hankali ga cin abincinsu.
Bayan angama cin abinci ne Nasrin da Najwa suka gyara dining d'in.
Dawowar su keda wuya hira ta b'arke yayinda Nasrin ta jinjina musu wajen iya girki, tayi mamaki sosai ya akayi suka iya girki haka wannan abincin ko ita tayi iyaka kenan.Mum dai da taga hirarsu bata da k'arshe jan Najwa tayi suka yi d'aki bayan su Nasrin sun mata sai da safe.
NY ne ya kira Abba suka gaisa ya bawa Nasrin ma suka gaisa yayi mata ban gajiya harda Nawas ma sun gaisa tukun daga bisani sukayi sallama.
Nabil ne ya tashi yace"Brothers, adda Nasrin mukwana lahiya"ya nufi d'akinsa parlour ya rage saura Nawas, NY da Nasrin.
Suka Cigaba da hirar su cikin jin'dadi musamman ma Nasrin wacce bata gajiya da kallo da jin muryar NY, b'angarensa ma hakan take.
Nawas ne cikin zuciyarsa yace ya kamata fa...............
Ummu Arif💞
[7:39pm],[11/2/2016]Hauwa Hassan Nayaya
116 to 120
Nawas ne cikin zuciyarsa yace"ya kamata fa in d'an basu wuri su d'an zanta domin gobe Nasir zai wuce"
A fili kuwa cewa yayi"Guys barin shiga in fito koh"suka amsa da"ok"ya tashi ya shiga ciki.
Shigar sa keda wuya Nasir ya k'urawa Nasrin ido, ita dai murmushi kawai take mishi abinma harya soma bata mamaki.Can dai da taga bai da niyyar daina kallon sai tace cikin sanyin murya"NY wannan irin kallo haka, ko zaka rasu ne ko kuma ni?"
Murmushi yayi yace"Matsoraciya babu ko d'aya, kawai dai kinga gobe zan tafi so ina kallonki ne don in fa'dawa bro d'ina yadda na baro ki beside nima zan missing d'inki"
Murmushi tayi wanda ya narka zuciyar NY tace"Am gonna miss u more, ni ko bro d'inka na sona kuwa?"
Yace"uhmmmm me yasa kika fa'di haka"
Tace"Najishi shiru ba call ba text ba komai, but I trust Abba ba zai za'bamin mara sona ba" ta kareshe maganar tana murmushi, shima murmushin yayi yace"Ai bro d'ina sai ha'kuri yace ina mishi hiran so karki damu anytime you're welcome sannan zanna yawan kiranki inji mishi lafiyarki, yana sonki he is just busy ne kinji nassy baby"
Tace"uhmmmmm shikenan Allah sa hakanne mafi alkhairi"
Yace"Amin"
Tace"gaskiya kaje ka kwanta domin dare nayi kuma gobe zaka yi tafiya fa"
Yace"To madam yadda kikace haka za'ayi"
Murmushi tayi shima ya mayar mata, Daga haka suka yi sallama ta rakashi har d'aki tukun ta dawo itama tayi nata d'akin.
Koda ya shiga d'aki tarar da Nawas yayi yana chatting, murmushi Nawas ya sakar masa sai NY yaga kamar Nasrin domin suna matu'kar kama da Nasrin yace"Har hiran ya isheku haka?"
NY yace"Wato ma da biyu ka tashi koh, ai hiran mu ba zata k'are ba kawai tace inje in kwanta saboda gobe zanyi tafiya"
Nawas yace"Kaji masoya"cike da zolaya.
NY yace Nawas"Wallahi na hangi tsantsar so na cikin idon Nasrin, na maka Al'kawari zan so ta fiye da yadda take sona, zan zamto mata abin alfahari zan bata dukkan gata, kulawa, so da tattali, zan zame mata miji nagari, nawas trust me insha Allah Nasrin ba zata ta'ba dana sanin aure na ba, kaidai Allah tabbatar mana da Alkhairi".
Cike da jin da'din kalaman NY, nawas yace"Amin ya rab" bayan ya jero mishi godiya da haka kowannensu yayi addu'a ya Kwanta.
Nasrin kuwa data kwanta tunani take tayi na wannan aure nata.Aure ba wata soyayya gashi ba hira a waya bare mu d'an saba, koda shike ni macece in munyi auren zan saito sa beside zanna hira da NY duk sanda naso Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi.
Washe gari Nasrin sai bakwai ta tashi kasancewar lahadi ne dama basu tashi da wuri.
Ta shiga kitchen ta ha'da breakfast ta shirya a dining taje tayi wanka ta komo k'asa.
Tana zaune tana kallon tashar manara sai goma saura saiga kowa na fitowa kamar wa'yanda suka ha'da baki.
Gaba d'ayansu gaishe da mum suka yi tukun su ma kowa ya gaida kowa sannan suka nufi dining.Bayan sun gama karyawa ne NY yake sanar da mum zaiyi wanka ya wuce, Ta mishi godiyan ziyara sannan tayi mai fatan isa gida lafiya da cewar ya mi'ka gaisuwarta ga mahaifansa sukayi sallama ta tafi makaranta.
NY ya tashi ya shiga ciki domin ya shirya Nasrin kuma ta tashi ta gyara parlon taje ta gyara kitchen ma. Najwa na d'akin Nabil suna karatu.
Tana zaune a parlour k'amshin turaren NY ya bugi hancinta murmushi tayi domin tasan shine ya fito Ai kuwa sai jin muryar shi tayi yace"Nassy baby ba'ko zaiyi halinsa".
Ji tayi kamar ta bisa su tafi tare amma ba dama murmushi tayi tace"Ba'ko ya kuma kwana biyu"
Yace"Tab kisa Abba yamin duka"
Kwashewa da dariya tayi tace"Waya ga ana dukan ka"
Shima dariyar yayi yace"Allah ma ya kyauta"
Tace"Amin"
Saida suka d'anyi hira tukun Nawas ya shigo
Su Najwa sukai mishi sallama yayinda Nasrin da Nawas suka yimishi rakiya har bakin mota.
Suka yi sallama yaja motar sa ya tafi bayan ya mata al'kawari zai dawo sannan yana isa Kaduna zai kirata.ya tafi zuciyoyi biyu na kewar juna.
Nasrin lokaci-lokaci takan kirasa taji ya hanya, sai shida da kwata ya shiga Kaduna.
Mum koh bayan ta dawo ne Nawas ya risketa a d'aki ya fa'da mata komai da suka tattauna da NY, mum taji da'di k'warai har salla tayi raka'a biyu ta yiwa Allah godiya k'arshen wahalar zuciyan Nasrin yazo saidai itama ba zata fa'da mata ba kamar yadda NY ya bu'kata.
A fallon Abba ya sauka, sunji da'din ganinsa matu'ka.Nan yake sanar dasu irin kar'bar da akayi masa a gidansu Nasrin har yace"Abba kasan me? Jiya fa mune mukayi girkin dare nida yayan Nasrin me suna Nawas gaskiya suna da kirki"
Murmushi Abba yayi yace "wato ko kunyar suruka bakaji ba ka zage kayita sha'kiyanci"
NY yace "Abba ba haka bane kasan banda ba'kunta"
Karan wayarshi ne ya sa bai kareshe maganar ba yana dubawa kuwa yaga Nasrin ce murmushi yayi ya d'aga tare da yin sallama.
Suka gaisa yace mata gashi parlourn Abba, tayi mishi ban gajiya yayinda Abba ya bu'kaci a bashi wayar domin su gaisa shima d'in gaisawar suka yi yayi mata godiya, suka gaisa da hajiya ma tukun suka yi sallama.
Abba ne yace "Nasiru inaga sati me zuwa insha Allah za muje Jos wurin Abban Nasrin don haka ka shaida mata" Nasir yace"Angama Abba, ni barin shiga ciki
Hajiya ki bada abinci na a kawo min bazan kuma shigowa ba"
Tace"To Nasir Ahuta gajiya" Da haka ya tashi ya nufi gefen sa..
Da shigarsa Nawas ya kirashi sai Da suka d'an zanta tukun sukai sallama ya tashi ya shiga toilet don yin wanka da alwala.
***************
A ranar da Abba ya dawo Nawas uban Zumu'di ya sanar mishi da komai daga Abba har Naufal sunyi matu'kar jinda'din maganar suka ce Allah Tabbatar da Alkhairi.
Washe gari Nasrin wani uban ado taci cikin wata jar super tayi mata kyau sosai tace da Mum ta tafi ziyara.
D'akin Naufal ta shiga ta gaishe shi kasancewar sun dawo daga tafiya yace bazai je wurin aiki ba sai ya huta.Ta langwa'bar da kai"tace pls yaya Naufal mota zaka bani zan fita ziyara"
Yace"Ga key can kan dressing mirror ga dubu uku kisa mai sai ki kiyaye ki lura Adawo lafiya" Zuwa tayi ta rungumesa ta sumbace sa a kumatu tace"Nagode yayana na kaina Allah barmin kai"Daga haka ta zari key d'in tayi waje, murmushi yayi yace"Amin Nasrin uwar da'din baki"
Nawas ne ya fito ya goge mata motan, sukayi sallama bayan ya garga'deta da ta kula sannan yayi mata fatan dawowa lafiya.
Tana fita Total ta nufa tasha mai tukun ta nufi cikin gari.
Tana traffic hold up dai-dai Zololo juyawa gefe da tayi suwa zata gani.......
Masoyana ku Cigaba da bina da kuma Ha'kuri dani na delay d'in typing, mrs Abdul luv u all.
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [4:13pm],[12/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
121 to 125
Nasim da Nazira ta ga ni a cikin mota su ma hold up ya tsayar da su, suna ta hira abinsu gwanin sha'awa murmushi tayi ta kau da kanta tace"Allah k'ara don'kon so".
Ita ko Nazira kamar ance juya kawai idonta ya sauka kan Nasrin wacce ta mayar da duk hankalinta ga titi.
Gani tayi ta da'da wani kyau sai dai ta d'anyi rama, ga kayan da ta sa sunyi ma ta kyau sosai.Wayar ta ta d'aga ta dialing numbern Nasrin ringing biyu ta picking kasancewar tana hold up ne amma sam in tana tu'ki bata ansa kira."Hello Nasrin"cewar Nazira, nasrin tace"Yes Nazira kina lafiya" Nazira tace"lafiya lau, pls inkin crossing ki'dan parking mu gaisa mu ma muna hold up ne"
Tace"to" ta ending call d'in.
Tana wuce wa kuwa ta samu wuri ta parker.
Ji tayi ana knocking glass d'inta wa zata gani.......Nasim ne, murmushi tayi ta sauke glass d'in suka gaisa bayan ya mata wani kallo mai fassara da da ma, Nazira ma ta zo suka gaisa yaushe gamo k'awa ta ga k'awa su ka d'an zanta tukun tayi musu sallama a cewar ta batason yin dare zata wurare da dama.
Gidajen yan'uwa ta fara bi tana yi musu gaisuwa, duk inda ta shiga bata fin minti goma ta fito da haka ta je gidaje da da ma ta sada zumunci a k'arshe ta je gidansu Aisha inda suka sha hira tukun tayi ma ta sallama ta nufo gida.
Ta shigo gida biyar saura a gajiye sannu kawai ta yi wa su mum ta haye sama kasancewar tana hutun sallah ruwa kawai ta watsa ta fito ta haye gado towel ne kawai a jikinta ko mai ba ta sha fa ba bare tasa kaya.
Ringing d'in wayar ta ne ya tashe ta, duba wa ta yi ta ga takwas saura lallai tasha barci a hasale ta d'aga wayan"Hlo" d'ayan b'angaren taji an ce"Nass baby lafiyar ki kuwa?" Jin muryar NY abin k'aunar ta yasa ta wartsake, Cewa tayi"NY kana lafiya"
Yace"Amaryar mu ina lafiya, u sound somehow is everything ok", murmushi tayi tace"Lafiya lau na d'an je ziyara ne na dawo a gajiye so shine na kwanta kaine ma ka tashe ni" yace"Ayya sannu ko kiyi ha'kuri na tada ki so nake inji lafiyar ki" tace"Nagode, lafiya ta lau hope kaima haka yasu Abba?"
Haka dai hirar ta su ta Cigaba su ka d'au kusan awa ita dai Nasrin tana mamakin yadda NY yake furta mata kalaman soyayya in tayi magana sai ya ce bro d'inshi ne yasa shi yana gefe amsarta ka'dai kesashi jin da'di,ai kuwa ta za ge tayi ta bada amsa ita dole tana hira da saurayi(wauta)
*************
Haka dai lokuta suka dinga wuce wa NY kullum sai ya kira Nasrin a waya tun bata biye mishi harta fara domin inta yi mishi maganar ina bro d'inshi sai ya kira hydar ya bashi wayar su gaisa yace mata ai yana kusa yana jin su gaskiya ta iya hira in sun yi aure zata koya mishi.Hakan yasa Nasrin amince wa da gaske bro d'in na gefensa shi yasa ta saki jiki su sha hira abinsu.
NY ya sanar ma da Nawas cewan suna nan tafe shida su Abban sa ranar asabar.Nawas ya sanarwa da Abba, abba ya kira Abban su Nasim ya sanar mishi cewa ranar asabar za suyi ba'ki masu neman auren Nasrin don haka ya zo da wuri.
Naufal biki ya matso ba zama sai tsayu wa yana ta shirye-shirye.
Duk wannan abun da ake yi Nasrin bata sani ba domin NY cewa yayi ba zai fa'da mata ba zai mata zuwan bazata yan'gidansu ma kowa ya'ki sanar da ita har mum.
Ranar Asabar da wuri mum ta tashi Nasrin su ka shiga kitchen su ka soma girki-girke ko da Nasrin ta tambayi mum, ce mata tayi Abba ne zai yi ba'ki daga haka ba ta kuma ce ma ta komai ba.
Sai wuraren goma suka gama aiki tukun su ka nufi d'akunansu don kintsawa.
Sha'daya dai-dai Suka iso jos direct gidansu Nasrin suka nufa.Sun samu kar'ba me kyau gaskiy, nan suka zauna suka gaggaisa ashe Abban hydar da Abban Nasim abokai ne abin yayi musu da'di sai sam barka.
Abba ya yaba da hankalin NY matu'ka daya ke abu ne na ansan juna take yayan Abban hydar ya ciro sadaki ya mi'ka bayan sun gama tattaunawa Abban Nasim ne ya kar'bi sadaki yayinda Abban ya bada shawara akan a ha'da auren dana Naufal kawai, nan ta ke kowa yayi na'am da shawarar aka sanya auren dai-dai dana naufal kowa ya sanya albarka, daga haka aka gabatar musu da abinci.
Nasrin ko tana d'aki bata san ma ba'kin sun iso ba, NY ne ya kira ta a waya yace ta fito, cike da mamaki tace"In fito" yace"yes" daga haka kashe wayar yayi.
Ta d'au mayafin doguwar rigarta ta yafa ta sauko k'asa ta nufi hanyar fita abin mamaki tana fita wa za ta gani.......NY ne tare da Nawas a tsaye su na magana tsananin mamaki ka sa magana ta yi sai ido da ta bi su dashi domin yayi ma ta ba zata sosai.Nawas ne ya katse ma ta mamakin da cewa"Nasrin ki je ki serving Nasir koh, sannan ki shiga ki gaida su Abba
"To" kawai tace mishi ta yi ciki NY ya bi bayan ta.Direct NY dining ya nufa yaje ya zauna, Nasrin ta shiga kitchen ta ha'do mishi abinci ta kawo mishi ita ma ta samu kujera kusa da tashi ta zauna.
NY ne ya d'ago idanunsa ya k'ura mata ido sai duk taji jikinta ya mutu tace"Nasir barin gaisa da Abba in zo" bata jira amsar shi ba ta tashi ta nufi hanyar fallon ba'ki, da sallamar ta ta shiga Abba ne ya amsa yayinda murmushin sa ya fa'da'da bu'de hannayensa yayi yana"oyoyo yar'albarka" cike da kunya ta k'arasa jikinshi, yace "Ya'ta kina lafiya" tace"Lafiya lau" ta gaida sauran yan' fallon ta tashi ta fita.
Komawa tayi ta tarar da NY na ta cin abincin sa ta zauna ta sakar mishi wani murmushi shi ma murmushin ya mayar mata tukun yace"Nasrin Albishirinki" tace"Goro" yace kuma cewa"fari ko ja"
Tace"uhmmmm fari abani nasha"
Yace"well ban san ya zaki d'auki me zan fa'da miki ba, hala kiji da'di hala akasin haka.Wato Nasrin an.......
Taku a koda yaushe Mrs Abdul
Ummu Arif💞
⭐OHW⭐
® Online Hausa Writers®
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [12:06],[16/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
131 to 135
Abba ta kira, bugu d'aya biyu ya d'auka suka gaisa tayi mishi sannu da hanya jin tayi shiru yace Nasrin lafiya kuwa? ahankali tace mishi da ma na kira yaya nasir ne inyi mishi sannu da hanya bai dauka ba.
Murmushi yayi irin na su na manya har cikin ransa yaji da'di sosai domin hakan ya tabbatar mishi da cewa Nasrin tayi na'am da za'binsa, cewa yayi bari a kirashi sai in kira in bashi koh"to" tace a ta'kaice sannan ta kashe wayar.
Sai kuma ta fara tunani anya ba tayi rashin kunya ba kuwa sai kuma tace yooo ai ba wanda zan aura na tambaya ba, ba ta gama zancen zuci ba wayarta ta so ma ringing tana dubawa ta ga Abba ne sai tayi picking tayi sallama muryar NY taji yace "nassy baby k'ara ta kika kai koh" murmushi tayi tace"nifa ba k'arar ka na kai ba kawai naga ba ka picking call d'in bane shi yasa"
Yace "to ya akayi ne amaryar mu bayan yau kin manta ni"
Murmushi tayi tace"to ba na kiraka ka'ki picking bane"
Ta k'areshe maganar cikin shagwa'ba baiso ta daina ba.
Yace"to kiyi ha'kuri our bride mun isa lafiya fatan kema kina lafiya"
Cike da shagwa'ba tace" lafiya lau"
A haka dai suka sha hirar su da ga k'arshe suka yi sallama ba don zuciyoyi sun so ba.
Nawas yaji shiru-shiru Nasrin ba ta kuma yi mishi maganar princess ba gashi son ta kullum da'duwa yake a zuciyarsa dole zuciya ta tirsasa shi ya kira NY.
Bayan sun gaisa ne Nawas ba kunya ya sanar da NY abinda ke ransa game da yar' k'anwarsa har cikin ran NY yaji da'di yayi fatan alkhairi bayan ya tabbatar wa da Nawas cewa zai ma ta magana insha Allahu bazai gagara ba Nawas yaji da'di matu'ka yayi ta yiwa NY godiya daga bisani suka yi sallama kowannensu najin da'di cikin ransa.
Soyayya me k'arfi ce ta k'ullu tsakani Nawas da princess, shi kanshi mamaki yake domin bai ta'ba tunanin zai tsaya yana fa'din magana ga wata mace ba sai gashi har rarrashin princess da kukan k'arya yake mata banda kalaman so da yake fa'da mata domin princess kamar ni Ummu Arif take tana so a sota,a shagwa'bata sannan yawaita fa'damata kalaman so wanda suke tafe daga zuciya ba na k'arya ba, ai ko Nawas aiki ya gan ka.
Biki nata k'aratowa yayinda Nasrin ta koma gidan auntyn ta domin an kawo wata mata daga Niger me gyaran amare don ta gyara Nasrin.Ai kuwa amarya tasha gyara da ma gata fara kyakkyawa sai ta da'da kyau jikinta kamar a ta'ba jini ya fiti ita kanta tasan ta gyaru ga wani k'amshi ko zama tayi a wuri sai k'amshin ya kama wurin amarya dai sai sam barka.
Ita ko komai yinshi a dole domin tasan auren biyayya zata yi ba auren soyayya ba shiyasa bata wani damu d auren ba don ma tana k'ok'arin danne damuwarta.
Waya da NY kuwa abin sai da'duwa yayi ita data keso ta yi nesa dashi domin bai san yadda take ji bane amma kullum da'da kusantar ta yake acewarsa shine kan biki komai take bu'kata ta sanar mishi.
Ko wajen fidda anko ma wasu cousins d'inta ne suka fitar ita ko a jikinta suka kaiwa Aisha da Nazira da ma ita ba wasu tarkacen k'awaye gareta ba, ta d'au pic din ankon a waya ta turawa zeenat ai kuwa taji da'di tayi mata al'kawari zata zo insha Allah.
Wajen kai d'inki ne kawai tace a ba ta kayanta zata kai, haka kuwa akayi kayan fitar biki kala goma a kayi mata duk ciki bana k'asa da dubu goma ta kaiwa tailor d'inta ta za'bi ha'da'dun d'inkuna domin Nasrin akwai son gaye ta biyashi kud'inshi yayi mata al'kawari bayan kwana bakwai zai kawo mata.
Biki saura sati biyu aka kai lefen Naufal,akwati set biyu amarya Nawwara tasha kaya ba laifi iyayenta ma sun nuna murnarsu domin sun ba da tukwici ba ka'dan ba.
Ita ko uwar biki Nasrin wacce ji take kamar ana gab da sata cikin prison ne akwatin ta goma sha biyar set uku,zinare biyu ga gold dasu azurfa tasha kaya gaskiya, wajen bada tukwici ba'a bar iyayenta baya ba sunyi bajinta sosai abin dai sai ni UMMU ARIF dana gani.
Ranar ko Nasrin kwana tayi kuka shikenan zata rabu da NY, me yasa ya kasa gane son da ta da'de tana mishi,tashi tayi ta fara nafila har aka kira sallar asuba tukun ta d'aura sallar nan barci yayi gaba da ita kan sallayar.
Tailor ya kawo mata kayan ta d'inkunan sunyi kyau matu'ka yayinda ta d'aga su tana kallo saida tayi kwallah inama da NY za'a d'aura ma ta aure da anga bidiri, haka ta tattara kayan ta chusa cikin wardrobe ta shiga toilet ta soma aikinta na kuka.
Washe gari ne Nasrin tana kwance misalin sha biyun rana aka ce mata ta fito tayi ba'ki daga kaduna, fitowan da za tayi wa ta gani....
Masu karatu pls kuyi ha'kuri na jina shiru kwana biyu wayana ta samu matsala ne, Mrs Abdul luv u all.
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writer's Association.
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [8:45am][22/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
141 to 145
Murmushi tayi domin ganin sunan NY daya bayyana a screen d'in wayar, sai ta fara jin wani sanyi da farin ciki ita kanta tana mamaki in dai tana hira da NY manta damuwar ta take.
A hankali ta d'aga tace"Yayanmu barka da dare" wani da'di yaji yace"Amaryarmu barka kadai, ansa lalle ne in gu'da" murmushi tayi tace"yanzu dai za'a sa ko zaka zo ka samin ne?" yace"rufamin asiri kar ace banda kunya, yanzu dai barin barki in ansa lallen nasan za kiyi ta musu shagwa'ba zan kiraki in sanya yar' farar fuskar nan murmushi"
Jin ana knocking yasa tayi saurin cewa"to nagode" a ta'kaice ta kashe wayar badon taso ba.
Hijabinta ta sanya ta nufi k'ofar ta bu'de a hankali ai kuwa bu'dewar ta keda wuya aka fara shigowa d'akin su Nazira ne farkon shigowa suka jata sai kan gado sai yan'uwan su NY da suka zo daga Kaduna da yan'uwan mum da Abba da abokan arziki d'aki ya cika ma'kil aka sakawa amarya lalle yayinda take jin zafi a zuciyarta idaniya kuwa sun'ki su daina zub da hawaye.
Ko da NY ma ya kirata picking kawai tayi amma sai kukanta take yi ji yayi inama yana kusa ya rarrashi abinshi amma da yake ya karanci halayyarta tsaf a hankali yayi ta kwantar ma ta da hankali sai gata tana ta dariya kamar ba ita, su kansu su Aisha sunyi mamaki sannan sun jinjinawa NY gaskiya wannan soyayyar tasu ta daban ce kusan awa suna rarrashinta amma cikin mintuna ya sanya ta dariya.
Sun da'de suna hira kamar baza su daina ba domin Nasrin ce mishi tayi"yanzu shikenan daga gobe mun daina waya" murmushi yayi yace"ai kuwa daga gobe ne muka fara waya", "uhmmmm bansan da'din baki kaje ka kwanta nasan gobe zaku taho jos da wuri saboda d'aurin yaya Naufal sha 'daya ne" cewar nasrin, yace"naki kuma d'aya da rabi koh"
Ya'ke tayi tace"eh,NY ka kwanta sai da safe Allah sada mu da Alkhairi" ta k'areshe maganar cikin muryar kuka, sam yaji ba da'di kamar ya sanar da ita gaskiya amma ya fasa duk da dai kukanta shine abinda yafi tsana.
Cewa yayi"Nasrin kuka kike yi" tace "a'a nidai ka kwanta sai da safe" bata tsaya jin me zaice ba ta kashe wayar duka yayinda k'walla ke bin kuncinta tayi addu'a ta kwanta.
Su ko k'awaye Nana,Aisha,Zinat,Nazira,Fahima lokacin suka soma hira daman sun san ba sauraron su zata yi ba, haka NY ya kwana da tausayinta.
Washe gari ya kama Saturday, ranar da za'a d'aura auren Naufal da Nawwarah a k'ofar gidan babanta dake dilimi misalin sha da'ya na rana sai kuma na Nasrin da Nasir a masallacin Al-bayan dake gaba da gidansu mi
salin d'aya da rabi na rana.
Shiyasa Abban su NY suka shirya tafiyar su k'arfe takwas domin suna so su samu d'aurin auren Naufal sannan a d'aura na Nasir.
Takwas dai-dai kuwa na ranar asabar layin su NY ma'kil da motoci masu tahowa jos d'aurin aure ango yasha ado cikin shaddar sa gezna light Brown da takalmansa da agogo duk na Gucci d'inki babbar riga yayi, ya h'adu sosai fa, sauran abokansa da yan'uwa suma yawanci anko suka yi sai da aka d'an d'auki hotuna tukun akayi addu'a kowa ya shiga mota sai jos, nidai ummu arif motoci arba'in na k'irga banda wa'yan da akace zasu biyo baya Allah kai su ango jos lafiya.
Can jos kuwa gidansu Nasrin ba masaka tsinke saboda jama'a don ma ba'ayi girki ba order akayi daga hotel daga na yan'uwa harna su angwaye.
Amarya tasha kyau cikin wani tsaddaden lace da aka kawo ma ta da ga gidansu NY tayi kyau sosai, k'annenta ma ba'a barsu baya ba su najwa ma ansha kyau Nabil ko da Nawas anko suka yi da ango Naufal abin dai sai ni ummu arif dana gani.
Nan akayi ta d'aukan hotuna yayinda k'awayenta ma ko wacce ta b'ar da kama dama dukkansu gwanaye ado da iya kwalliya ne musamman uwar biki Nasrin, mum kuwa tsabar kyau da ta yi wollah da k'yar na gane ta.
Dalilin nasihar da Nawas yayiwa Nasrin dole ta danne damuwarta ta dinga fara'a dama gata gwanar kyau.
K'ofar gidansu Nasrin ma'kil da mutane y'an zuwa d'aurin aure,na Abba ne, Nawas d'in ne da kuma jama'ar ango ga yan'uwa da abokan arziki.
Abba ma yasha kyau wollah anko suka yi shi da Abban Nawas, nawas ko sai da na hange sa ne naga ashe anko suka yi da Nazira wai su masoya, soyayyar su NY tafi burgeni wollah lol.
Can gidansu Nawwarah kuwa itama tasha kyau ba laifi suna ta shirye-shirye domin in an gama d'aura aure za suyi mother's day kafin da yamma a d'au amarya ayi gidan Naufal da ita.
Ita ko Nasrin Allah-Allah take a d'aura taji waye angonta domin yau taji ta tana cikin farinciki duk da dai akwai sauran damuwa cunkushe a k'asan zuciyarta.
K'arfe goma da minti arba'in convoy d'in mutan Kaduna suka iso k'ofar gidansu Nasrin da ma dai su ake jira ba'a tsaya wani dogon gaisuwa ba saboda yanayin lokaci direct gidansu Nawwarah tawogar NY da na Nasrin suka nufa domin d'aurin Auren Naufal da Nawwarah.
Masha Allah taro yayi jama'a inda Alhaji Bashir K'anin baban Nasrin ya wakilci Naufal aka d'aura aure kan sadaki naira dubu d'ari.
Nan fa aka fara gaishe-gaishe da d'aukan hotuna, NY yana cikin mota abinsa kasancewar baya son rana yana ta tunanin yar'amaryar sa Nasrin bazai jure rashin jin muryarta ala dole yayi dialing number d'inta sai dai har ya gama ringing bata picking ba, haka ya sake dialing nan ma ta'ki picking k'urawa wayar ido yayi kamar meson sanin wani abu game da wayar.
Nasrin ko tana wurin k'awayen mum suna ma ta nasiha taji wayarta na ringing amma ta'ki d'agawa domin bata duba taga me kiran nata ba, sai da suka gama ta shiga toilet d'in mum don ganin waye me kiranta ai kuwa tana dubawa mamaki ya bayyana matu'ka a fuskarta, ita ka'dai ta fara magana "Allah sarki Nasir ban tsammanin kiran ka ba, kodai......
Ku Cigaba da bin jikar Nayaya,luv u all.
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writer's Association.
27/02/2016, 11:26 AM - Ummu Arif💞: [2:53pm][23/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
146 to 150
"Allah sarki Nasir ban tsammanin kiran ka ba, kodai kana jin me nake ji ne uhmmm koma dai menene aikin gama ya gama".
Numbern shi ta dialing bayan ta gama magana ita ka'dai shi ko yana kishingi'de cikin mota ya k'urawa hoton ta ido wanda ta d'auka da su princess ya cire rai da zata kirashi kawai sai ganin sunanta yayi ya bayyana a fuskar wayarsa cike da zumu'di ya picking"Hello Nasrin ina kika shiga ne ango naso yayi magana dake?
Cikin murya sassanya tace"ina tare da k'awayen mum ne, hope kun iso lafiya"
Sai yaji wani da'di cikin ranshi tabbas Nasrin na son s.Murmushi yayi yace"lafiya lau muna wurin d'aurin auren Naufal harma an d'aura anjima kuma sai na....." sai kuma yayi shiru, jin yayi shiru ta goge hawayen fuskarta tace"Allah ya sanya alkhair mungode, ana kirana we talk later koh" bata jira amsar sa ba ta katse wayar domin gani take kamar rainin wayo ne yasa yake kiranta bai san me kiran yake k'ara mata ba, sai da tayi kukanta ma'ishi tukun tafito ta koma cikin friends d'inta.
Koda aka kammala d'aurin aure da d'aukan hotuna gidansu Nasrin aka dawo aka baje aka ci abinshi, abin dai sai ni ummu arif dana gani wani nau'in abincin ma sai a bikin Nasrin nagani gaskiya kam anci da'di anyi brush da kaji da d'awisu ga drinks kala-kala biki dai yayi sosai.
Su Abban Nasir ma sunji da'di yadda aka kar'besu aka karrama su.
Bayan sun gama ne suka yi sallar Azahar tukun aka d'unguma sai masallacin Al-bayan don gabatar da d'aurin auren Nasrin da Nasir, Abban Nawwarah ma da jama'arsa ba'a barsu baya ba.
D'aya da rabi dai-dai aka fara gabatar da d'aurin auren mutane kuwa tun daga junction d'in elden har masallaci niko ina ma'ke a boot d'in motar Abba tun ina k'irga mutane da motoci har na ka sa saboda yawa, Abban Nasim shine waliyin NY Abban NY kuwa shine waliyin Nasrin abin dai ya burge sosai ina daga cikin boot naji a microphone ana cewa An d'aura Auren
NASIR YAHAYA da NASRIN NAZIR kan sadaki Naira dubu d'ari ga key d'in mota na amarya da kujeran makkah kyauta daga Mahaifin ango.
Su Nawas da su Naufal sunji da'di matu'ka suna ta godiya murmushi Nasir yayi yace"Nawas kaima kasan yadda muke jin Nasrin a ran mu we can sacrifice even our happiness for hers, so ka daina gode mana ta yiwa Abba biyayya ka ga kome yayi ma ta bai fa'di ba" murmushin jinda'di Nawas yayi murmushi yace" mungode sosai ina da ya'kinin my sister will happy with you thanks again "
Murmushi dukkansu suka yi suka rungume juna NY wani da'di yake ji wai yau shine ya aure Nasrin abin kamar a mafarki.Abba Nasrin ma ba'a barshi baya wajen yiwa Abban NY godiya sauran yan'uwansa sai da suka yiwa su Abban Nasir godiya domin sunji da'di sosai.
Abba ko yayi hakanne domin son Nasrin da yake ba ya ga haka tayi mishi biyayya da halacci yana jinta har cikin ranshi sannan zai zame ma ta kowanne gata.
Inka hangi fuskar NY zaka tabbatar yana cikin farinciki har hawayen da'di yayi sanda za'ayi musu hoto da Abban Nasrin, Nan aka bubbu'de boot d'in mota aka dinga rabawa jama'a dardumai, jakankuna,Qur'anai,C.D na wa'azin mallaman sunnah, memo, jallabiya da dai sauransu kowa sai sanya Albarkacin bakinsa ya ke domin taro yayi albarka.
Can gida Nasrin nata neman Nabil don ya fa'damata sunan Ango amma ta nemeshi ta rasa daga k'arshe ta shiga toilet ta goge hawayenta ta sanyawa zuciya sukuni da rarrashi ta k'udirta duk wanda ta gani matsayin mijinta zata yiwa Allah godiya domin za'binshi shine za'bi da haka ta sauya kaya ta gyara make-up ta fito sai wani haske da k'yalli take kamar zara ta gefen wata, ga murmushi dake d'auke kan fuskarta kowa yayi mamakin Nasrin nan fa aka fara sabon d'aukan hotuna.
Ana cikin d'auke-d'auken hoton ne k'anwar mum me suna hajja zulai ta zo ta yiwa Nasrin ra'da a kunne sai naga Nasrin ta bi ta, ni kaina ummu da nake gefe banji me tace ma ta amma ga dukkan alamu fa'da za'a ma ta.
Kasancewar gidan ya cika ma'kil da mutane yasa hajja zulai ta wuce direct bedroom d'in mum da Nasrin.
Shigarta keda wuya ta samu wuri ta zauna jin kiran sunanta da mum tayi ne yasata da'gowa nan taga sisters d'in mum da yawa da kuma na dad, mum ce ta fara mata nasiha mai ratsa jiki yayinda sauran kowa ta d'aura nata akai.Nasrin na zauna hawaye kuwa kamar an kunna famfo idon nan farare sun rine zuwa jaa mum ma shiga toilet tayi taci kukanta tukun ta gyara ta fito kasancewar bata son ta karyawa Nasrin gwiwa yasa ta'ki yin kukan gabanta.
Koda y'an d'aurin aure suka fara dawowa nan labari ya bazu irin kyautar da baban ango ya yiwa amarya, mum taji da'di sosai ta sanya alkhairi sauran mutane kowa na tofa albarkacin bakinsa da masu farin ciki da masi ba'kin ciki.
Nasrin ko da taji cewa tabbas angama d'aura aure tasan tafiya da ita yazo kenan nan fa tafara wani sabon kuka me bawa duk me sauraro tausayi.
Anyi anyi tayi shiru amma ina kamar tunzurata ake wata k'anwar mum ce tazo tana rarrashinta da encouraging words tukun ta'dan ta'kaita kukan.
Can wurin d'aurin aure kuwa Abba sunyi godiya sosai ga Abban Nasir sannan suka yi musu fatan komawa gida lafiya kamar yadda suka zo lafiya.
Su Abban Nasir suka ha'da kan jama'arsu bayan sun bar motoci goma da y'an sauran jama'a wanda zasu d'auko amarya ciki koh harda ango domin k'in bin su Abba yayi.
Bayan Su Abba sun gama sallamar jama'arsu ne suka dawo gida kowa zuciyarsa fal farin ciki,dawowar su kuwa kamar k'ara birkita Nasrin yayi domin tasan tabbas tafiyarta yazo.
Tana kwance cinyar aunty ne hajja zulai tazo tace mata ta tashi ta nuna ma ta sauran kayanta ta harha'da, jiki ba k'wari ta tashi ta nuna ma ta aka zube su a akwati aka fita dashi tofa sabon tashin hankalin Nasrin.
Wa'yanda suka sa lalle dama sune zasu tafi da amarya, zinat suka kira suka tambayeta ina Nasrin? ce musu tayi tana ciki daga haka ta bar wajen.
D'aya daga cikinsu ce taje ta samu hajja zulai tace musu su fa sun gama amarya kawai suke jira, ha'kuri hajja zulai ta basu tace don Allah su bari ta gana da mahaifinta tukun ba musu sukace bakomai.
Dai-dai lokacinda hajja zulai taje ta samu mum don sanar da ita sa'kon dangin NY, dai-dai lokacin Nabil yazo yace" Mum, Abba yace a kawo Adda Nasrin suna fallon sama" ya kareshe maganar yana goge k'wallah tukun ya kuma cewa"Mum........"
Taku ako yaushe
Ummu Arif💞
®NWA®
29/02/2016, 11:08 AM - Ummu Arif💞: [9:55am][28/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
151 to 155
"Mum yanzu shikenan adda Nasrin zata tafi ta barmu nima zan rakata pls mum"
Murmushi mum tayi ta goge hawayen fuskarta tukun tace"Nabil ai aure ba rabuwa bane kowa ma haka yake barin gida badon ya so ba sai don ya zama dole garemu, kayi ha'kuri duk sanda kuka so ganinta ai zaku ganta, je kace musu gata nan zuwa"
Jiki a sanyaye Nabil yabar wurin yaje yace musu tana zuwa tukun yayi waje gun Nawas.
Hajja zulai ce ta shiga ta tayar da Nasrin ta sauya shigarta tukun ta ri'ko hannunta sai falon da su Abba suke.
Suna shiga Abban Nasim ya taso ya ri'ko Nasrin hajja zulai kuwa tayi waje abinta.
Zuwa yayi ya zaunar da ita tukun yace"Nasrin kinci abinci"
Kai ta d'aga alamar a'a tukun ta goge hawayen fuskarta,
murmushi ya janyo flask gefensa ya zuba jallof macaroni da pepper chicken tukun ya tsiyayo chi exotic a kofi ya dawo gabanta yace to Nasrin bismillah sannan bana son kuka.
Ai kuwa tayi tsit ya dinga ba ta abincin nan tana ci su Abba dai suka zama y'an kallo.
Saida Nasrin taci abincin nan Abba ya tabbatar ta k'oshi tukun ya kawar da plates d'in sannan yace ma Abba da yay'yansa to bismillah.
Nan fa su Abba suka fara yiwa Nasrin nasiha mai ratsa jiki, tun tana dauriya harta kasa ta b'arke da kuka amma basu daina ba sai da suka kammala.
Abba yayi sallama da Nasrin shima duk jikinshi yayi sanyi ganinta da yayi tana kuka sai da yayi kwallah yabar D'akin bayan ya da'da yi mata fatan zaman lafiya da Alkhairi.
Ganin Abbanta ya fita shikenan ba zata kuma ganinsa ba sai bayan wani lokaci ai kuwa nan kukanta ya tsananta, Abban Nasim ne ya le'ka ya kira wata cikin mutan bikin yace ta kira hajja zulai, ba a jima ba sai kuwa gata nan yace ma ta ga Nasrin su dai sun gama nasu Allah bada zaman lafiya shima yasa kai ya fita.
Hajja zulai ta gangaro da Nasrin zuwa fallon mum inda sauran ba'ki suke zaune,nan kowa ya yiwa Nasrin irin tashi nasihar ita dai ido ba daina yoyo ba.
Can waje kowa ya shiga mota har wasu sun fara gaba domin su zinat da najwa sunyi gaba, Ango dai cewa yayi shi zai tu'ka Nasrin har kaduna.
Yan'uwansa wa'yanda suka zo sa lalle suka fito da kaya niki niki a kasa a boot,mamakine ya kama NY domin yasan sune ya kamata su fito da amarya amma baice komai ba tukun yana dai tsaye tare da Nawas yana jira yaga ikon Allah.
Ai kuwa sai ga Nabil ya nu fo su NY da gudu "Nawas wai kazo Adda Nasrin ta'ki fitowa"
Ai kafin nabil ya k'arasa magana shi da NY sun nufi cikin gida.
Suna shiga suka tarad da Nasrin kamar wata k'aramar yarinya kuka take ba ji ba gani kowa cikin yan'uwansu daya ri'kota zata fizge kamar me iska, ashe yan'uwan ango sunyi sun gaji ne shine suka fito,ita dai taji ta gani bazata bar gida ba.
Nawas wanda duk tausayinta ya kamasa ta maza yayi ya d'auki Nasrin kamar baby NY sai da yaji wani kishi, tana fizgewa ina amma k'arfinta ba d'aya da nasa ba sai surutai take kamar ta'ba'biya da dai taga baida niyyar sauke ta gashi har sun iso gate kawai sai luuu ta suma.
A haka aka sata a mota da manya biyu sai direba NY da Nawas aka yi Kaduna da Nasrin.
Ko da ake tafiya ma da ta farka kukan tacigaba dayi daga bisani sai bacci.
**************
K'arfe bakwai da kwata suka isa kaduna a gidansu NY suka sauka domin nan za su kwana harda amarya sai washegari a kaita gidanta a dawo da y'an rakiya jos.
Kasancewar su Najwa sun rigasu yasa sukan har sunyi sallah sun ci abinci suna hutawa.
Su ko su NY da isarsu baya yayi da motar ya parking daidai fallon dad na k'asa domin yasan bakowa ciki.
Suka fito ya kira princess yace tazo baya, ba'a jima ba sai gata yace ta tafi da sauran matan nan sannan ta kawo musu abinci shida Nawas, matan suka ce amaryar fa" yayi murmushi yace"karku damu zan kula da ita in case an tambayeku kuce tana barci" suka ce "to" su kayi gaba.
Nawas na tsaye yana kallon ikon Allah cancak NY ya d'au Nasrin bai dire ta ko'ina ba sai a d'aya daga cikin kujerun da suke fallon Nawas yabi bayan sa.
Suka shiga suka watsa ruwa tukun suka fito sukai sallah suna idarwa princess na shigowa da abinci Nawas anga sweet heart sai wani fi'ili yake ita ko princess badai kunya ba da gudunta tabar d'akin.
Suna cikin cin abincin ne Nasrin tayi motsi da gudu NY ya nufi inda take, a hankali take bu'de idonta domin hasken kwai NY shita fara gani a gabanta ta rufe ta bu'de still dai shi'dinne tukun tace"NY kaine ko mafarki nake" ganinshi kawai ya sanyata mance damuwarta(lol lover girl) mnurmushi yayi yace"yes nine Nasrin ga Nawas can"ya matsa taga Nawas nan fa komai ya fara dawo mata.
Ri'ke kanta tayi ashhhh, NY wanda yake ru'de cewa yayi "baby lafiya" , "kaina ke ciwo" haka kawai tace, sai ra kuna cewa "NY ina nake?
Yace"kina gidanmu gidan surukanki a Kaduna fallon Abba na k'asa"
Take kwallah ya fara bin kuncinta, ha'kuri ya shiga ba ta da sata dariya harta d'an ware suka je taci abinci sosai amma Nawas ne ya ba ta NY kishi fal zuci.
Hajiya ta kirashi cewan yana ina?
Nan ya sanar da ita inda yake, baa jima ba sai ga ta lokacin Nasrin ta koma kan kujera NY da Nawas suna d'an tattaunawa, direct wurin Nasrin ta nufa ganin jikinta na rawa nan fa hankalin NY ya tashi hajiya tace Nawas ya lalla'basa ta rungumo Nasrin har shashin da jama'a suke.
Nan dai tayi k'arfin halin yin magana ta yiwa su nabila da sauran friends d'inta da yan'uwanta ya hanya sannan su kayi ciki da hajiya.
Kasancewar hajiya taji jikinta ba zafi bedroom d'inta taja Nasrin ta shiga toilet da kanta ta ha'da mata ruwan ne zafi tace taje tayi wanka.
Tana fitowa taga sleeping dress akan gado ta d'auka tasa abinta taje mirror ta shafa mai ka'dan da turare ta dawo ta haye gadon ta kwanta, d'akin tas-tas sai k'amshi yake kamar ba'a gidan biki ba.
Tana kwance sai ga hajiya ta shigo d'auke da ruwa da tablets a hannunta ta bawa Nasrin tasha sannan tace kona ki kwanta ki daina kuka Nasrin nan ma gida kike, Allsh sawa'ke ki kwana lafiya daga haka tasa kai ta fita, Nasrin taji da'di yadda hajiya tayi mata murmushi tayi sannan tace ta gode.
Bacci mai nauyi ne yayi awon gaba da ita har batasan sanda hajiya da junior suka zo suka kwanta ba.
Su Najwa ma da sauran ba'ki an basu d'akuna masu kyau duk sun kwanta sunyi barci abinsu.
B'angaren oga NY saida hajiya ta tabbatar mishi Nasrin taji da'di har tayi bacci tukun shima ya runtsa domin k'in fita ma yayi su haydar ne suka ji da sauran ba'ki.
Washe gari.........
Mrs Abdul luv u all.
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writers Association.
29/02/2016, 6:14 PM - Ummu Arif💞: [11:10am][29/2/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
156 to 160
Washe gari Nasrin tunda tayi sallan Asuba ta koma bacci ba ita ta tashi ba sai goma na safe.
Cikin gida kuwa kowa ya tashi tun takwas sunyi wanka sun ci breakfast anata girke girke, su Najwa ansha ado kamar itane amaryan.
Nawas ko da ya tashi yayi wanka yaci ado kiran princess yayi a waya ko wanka bata yi ba ta zira hijabi ta nufi garden ta sameshi tare su kayi breakfast kasancewar yau zai wuce jos shiyasa ya keso su'dan samu time shida princess d'inshi su'dan zanta.
Nasrin koda ta tashi toilet ta shiga tayi wanka ta fito ta shafa mai ta 'dan zauna bakin gadon bataso ta fito domin taji kamar akwai mutane a fallon shiyasa tayi zamanta.
Tana nan zaune sai ga hajiya ta shigo ganin Nasrin yasa taje kusa da ita ta zauna tukun tace"Nasrin kin tashi lafiya? kan ya daina ciwo koh bari akawo miki breakfast da kayanki, ki saki jikinki nan gidanku ne kinji"
Cike da jin kunyar hajiya Nasrin tace"Na tashi lafiya mum, fatan kema haka nagode sosai"
Murmushi mum tayi tukun tabar d'akin.
Bata jima da fita ba sai ga Najwa tana shigowa taje ta rungume Nasrin tace"Amarya bakya laifi shine jiya ansamu hajiya aka manta mu"
Murmushi tayi tace"najwa zancen kikeso"
"Ga kayanki nan kisa kiyi breakfast ki fito kowa ke yake jira jiya ba'a ganki ba"
Tace"Najwa yaushe kika iya magana ne?"
Dariya Najwa tayi tace"Adda Nasrin kenan barin barki ki shirya" bata gama rufe baki ba saiga wata ta shigowa Nasrin da breakfast ta gaisheta tukun tayi waje Najwa ma ta tashi ta fita.
Ango daya tashi hajiya ya fara kira yaji ya jikin Nasrin sai da ta tabbatar mishi taji sau'ki tukun ya tashi yayi wanka yayi breakfast sannan yayi ado cikin wata shadda ubansu ruwan toka d'inki babbar riga akayi mishi yayi kyau matu'ka, kunsan me?
Wollah anko suka yi da haydar komai nasu iri d'aya inka hangi bayansu bazaka gane waye angon ba inko baka san waye angon ba zaka d'auka dukkansu angwaye ne,
nan fa suka jero tare har waje kowa ya yaba da kyan da suka yi aka dinga gaisawa ana watsa pics.
Can jos kuwa bayan an tafi da Nasrin da y'an awanni aka je aka d'auko amaryar Naufal inda aka kaita gidanta wanda bai da nisa da na su Naufal d'in.
Bayan isha'i kuwa aka rako ango domin ba wani yini da za'ayi angama biki a ranar, aka siya bakin amarya aka sallami k'awaye ango yaje yayi rakiyan abokansa ya dawo gun amaryarsa Nawwarah, nidai tunda ya shigo na fita naja musu k'ofa domin ba kyau gani ko sanin sirrin mata da miji nai musu fatan alkhairi nayi gaba abuna.
Mum kuwa ji tayi gidan yayi mata wani iri musamman da ta haura sama ta ga d'akin Nasrin wai don ma akwai ba'ki, Abba ma sai da yaji wani iri babu Nasrin mai yimai hidima fatan su Allah basu zaman lafiya da farin ciki dawwamamme.
Washe gari bayan sallan azahar ne wasu ba'kin suka fara tafiya wasu kuwa sun ce sai talata zasu tsaya su taya mum gyara gida.
Can Kaduna kuwa Nasrin bayan ta gama breakfast taci uban ado cikin wata atamfa Holland yellow mai adon ja ajiki ta d'auko lifaya ja auntyn NY ta Na'da mata ta sanya sar'ka,d'ankunne, awarwaro da takalmi ja, tayi kyau sosai ta fito tare da Yayar mum d'in NY tuni kowa yazo yana rungumeta kowa na tofa albarkar bakinsa gaskiya Nasir ya iya za'bar mata masha Allah da dai sauran surutai.
Nan kuma aka fara watsa pics ita da sauran yan'uwa su NY.
Can sai ga angwaye sun taho NY da haydar ne a gaba kowa nata ihu ango kasha k'amshi Nasrin da ta gansu sai da gabanta ya fa'di domin ta tabbatar haydar ne angonta domin tana ji in akace ango inda yake wani fa'di da jin kai dama kuma NY tuni sun shirya hakan tun a d'aki wato in a gaban Nasrin ne haydar ya amsa sunan ango burinsu dai bai wuce kar matan nan su b'ata musu shirinsu ba.
Suka iso Nasrin nata murmushi gashi tayi kyau haka aka dinga yi musu hotuna da camera, waya ne da dai sauransu ga video da akeyi domin NY zuwa yayi ya tsaya kusa da Nasrin yayinda haydar yaje d'aya gefen Nasrin ce ta juyo ta d'an matso kusa da NY a hankali tayi mishi ra'da tace"Nasir wallahi kayi kyau" murmushi yayi yace"har na kaiki kyau saidai bana son kallo"
Murmushin itama ta kuma yi bata kuma cewa komai ba.
Haydar ne ya'dan matso kusa dasu yace Yaya Nasir nayi ba'ki pls ka kulamin da amarya ina zuwa, hakan duk cikin shirinsu ne domin anaso a d'auki ango da amarya hoto, haka kuwa akayi sunsha pics.
Bayan angama pics d'in ne aka d'ebo souvenirs aka fara rabawa jama'a lokacin Nasrin an kaita gun Abba domin yayi mata nasiha kafin a mi'kata gidan mijinta.
Abba yaji da'din yadda yaga Nasrin tare da hajiya da sauran y'anuwansa suka yi ma ta Nasiha tukun aka fito da ita sauya kaya don zuwa gida mijinta.
Nawas ko sai lokaci suka baro garden ansha soyayya, a gurgurje princess tayi wanka ta dressing cikin ankonsu tayi kyau sosai abinta.
Shiko Nawas da ya shiga gun su NY kunya ce ta kamashi murmushi kawai NY yayi mishi domin yasan daga inda yake.
An fito da Amarya Nazira da Aisha da sauran yan'uwa da dangin su NY za'a kai amarya gidanta, kuka take ba k'ak'k'autawa domin tasan su Najwa suna kaita su ma zasu d'auki hanyar jos.
Haka dai kowa ya shiga mota aka raka amarya gidanta ciki harda Nawas.
Mintuna ka'dan sai gasu a malali dai-dai k'ofar gidan amarya kowa ya fito ya shiga don ganin gida Nasrin da k'yar ta shiga domin saida Nawas yace zai d'aga ta cak tukun ta shiga tana wani kuka mai tsuma rai.
Direct bedroom d'inta Nawas ya nufa da ita ya kaita har kan gadonta yayi ma ta nasiha mai ratsa jiki tukun yayi ma ta sallama bayan ya ma ta al'kawari zaizo dubata bayan sati biyu.
Nan fa Nasrin tace bata san zancen ba domin k'an'kameshi tayi tanata kuka har saida tasashi k'wallah da k'yar ya kwace ya fita aka kulleta a d'akin, su Najwa sai kuka su keyi su ma duk sai ta window suka yi mata sallama aka jasu aka sa su a mota suka d'auki hanya sai jos zinat kuma tayi gida abinta.
Nasrin kuwa tana nan tanata kuka kamar ranta zai fita da k'yar princess da wasu cousins d'inta su biyu suka shawo kanta tayi shiru taje tayi wanka taci dinner tukun ta canca'da kwalliya bayan tayi sallan isha'i tasha kyau abinta ta zauna a tsakiyar gado su princess suka rufe ta da wani d'an ubansu lifaya wanda yake ta kyalli.
Jin shigowar angwaye yasa su princess suka fito fallo, gaishesu kawai suka yi domin duk yay'ye ne tukun suka yiwa Nasrin sallama suka je suka mota suna jiran su haydar.
Angwayen ma daga fallo suka yiwa amarya Allah sanya alkhairi ango ya raka su kowa yayi gida abinsa.
Y'an jos kuwa sai takwas suka isa ganin dare yayi mum tace Aisha da Nazira su kwana gobe sai Nawas ya kai su gida, haka ko akayi suka baje a gadon Nasrin cike da kewarta.
A hankali ya bu'de kofar yayi sallama ta amsa ciki-ciki yazo kan gado gaf da ita ya zauna, jin an zauna kusa da ita ne kuma anyi shiru yasa ta d'aga mayafinta don ganin waye amma to her greatest suprise NY ta gani fuskarsa d'auke da murmushi ita ko mamaki ne fal fuskarta a hankali tace mishi"yaya nasir yanzu ango zai dawo yaje rakiyan abokansa ne fa ka tashi ka tafi nasan tsokanata kazo yi"
Ya'ki cewa komai illah k'ura ma ta ido da yayi domin tayi mishi wani kyau ne sosai, da taga bai da niyyar daina kallonta kuma kamar tunani ma ya keyi matsawa tayi kusa dashi ta hura mishi iska a fuska firgit yayi yadawo daga duniyar tunanin da yake ya ma ta murmushi ya fita.
Mamaki ne sosai ya kama Nasrin tana nan zaune taji ango shiru bai dawo, ji tayi an da'da bu'de kofa again NY ta gani d'auke da fresh milk da smoke chicken zuwa kawai yayi ya ajiye ma ta fuskan nan tashi d'auke da murmushi yana ajiyewa ya yi hanyar fita caraf Nasrin tace"Nasir.......
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writer's Association.
07/03/2016, 9:48 PM - Ummu Arif💞: [9:58am][1/3/2016]
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMININ KWARAI
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
Na,
Hauwa Hassan Nayaya
161 to 170
"Nasir ko dai wanda Abba ya aura min baya so na ne, daga rakiyan abokai har yanzu bai dawo ba Abinda ya kamata shi zayyi kaine kake yi Pls Nasir....."
Kuka yaci k'arfinta ba ta iya kareshe maganar ba.
Shi ko yana nan tsaye bai ce komai ba amma fa kukan nan kamar hura masa wuta ake a zuciya domin jin kukan Nasrin na d'aya daga cikin abin da ya tsana, baiyi niyyar sanar da ita wannan daren cewa shine mijinta ba amma yasan hakanne kawai zaisa ta daina kuka sannan ta daina tunanin Abba ya aura ma ta mara sonta.
A hankali ya taka zuwa gefen gadon, kanta na k'asa tana kuka mai tsuma zuciya ba ta ma san yazo wurin ba. Gadon ya hau ya matsa daf da ita zuciya da gangar jiki sun kasa daurewa, ji kawai tayi NY ya rungumota jikinsa ya matse ta tsam ba damar k'watar kanta.
Ai kuwa take jikinta ya fara rawa taji sabon yanayi da kuma mamaki ga tambayoyi fal bakinta garesa ta d'ago kai zata yi masa tsantsar masifa domin fararen idanun nan sun koma jaa kuma ya matseta ba daman k'watar kanta bu'de bakinta kenan ko furta abinda zata ce ba tayi ba kawai taji bakin NY cikin nata, Nasrin suman xaune tayi wollah duk k'ok'arinta na son k'wacewa ta gagara abisa dole ta dangana ta fara addu'a a zuciya domin tana ga NY wani abun ya sameshi ne amma sam ba haka yake ba.
Sai da yaga ta nutsu tukun jikin ta yayi sanyi sannan ya kyaleta dama nutsuwarta yake nema,
Juyowa yayi suna kallon juna ido cikin ido tukun yace"Nasrin ina so ki saurareni da kunnen basira kinji" a hankali ta girgiza kanta alamar eh, yayi murmushi ya shafi gefen kumatun ta tukun ya fara magana.
"Nasrin kar kiyi mamaki idan nace miki nine mijin da aka d'aura miki aure dashi jiya"
Bu'de idanunta tayi alamar tsantsar mamaki hawaye ne ya fara bin k'uncinta ga murmushi mai nuna tsantsar farin ciki da ya bayyana a fuskarta,
shima murmushin yayi tukun ya cigaba"Nasrin kar kiyi mamaki idan nace miki nasan kin da'de kina DAKON SO na, sai dai abinda ya burgeni nake k'ara ganin kimarki baki ta'ba bu'de baki kin fa'dama min ba that really earn you a great respect from me, kowa na gidanku yasan ni zaki aura sai dai sun min al'kawari baza su fa'da miki ba domin muyi miki suprise Nasrin kinga haka Allah yake abinsa,ha'kuri,biyayya da taimako ga samako nan da abun da kike matu'kar so Nasrin bazan miki k'arya ba wallahi ina matu'kar sonki sannan na yiwa iyayenki da yan'uwanki al'kawari zan baki dukkanin farin ciki, Allah nagode maka daka bani Nasrin matsayin matata ya Allah ka bamu zaman lafiya da zuri'a dayyiba
dukkansu suka amsa da Amin.
Bu'de hannunsa yayi cike da kunya Nasrin ta shiga jikinsa sun d'an jima a haka tukun suka tashi suka nufi toilet su ka d'auro alwala su ka gabatar da nafila raka'a biyu tukun NY ya bawa Nasrin fresh milk da kaza ka'dan taci kasancewar taci abinci shima yaci ya k'oshi yadda take kallonshi kamar wani ba'ko shima kallon ta yake domin ya ga gaba d'aya ta canza mishi duk sanda d'ayansu ya kama wani na satar kallon wani murmushi suke sakarwa junan su mai ma'anoni daban-daban.
Yana kammalawa ya kwashe plates d'in yakai kitchen yace ma ta ta tashi tayi shirin kwanciya daga haka yayi d'akinsa.
Yana shiga yayi bathroom ya watsa ruwa ya fito ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyin k'amshi ya sanya jallabiya fara sol ya nufi d'akin amarya Nasrin.
B'angaren Nasrin ma NY na fita ta shiga ban'daki ta watsa ruwa ta fito ta shafe jikinta da kulacca sannan ta feshe shi da turaruka masu sanyi k'amshi ta d'auki wata fitinanniyar night gown tasa tukun ta kashe wuta ta haye gado abinta cike da tsantsar farinciki, Niko ina ganin NY ya bu'de k'ofar d'akin Nasrin nima nayi hanyar waje abuna bayan nace mishi a sha amarci lafiya lol.
Washe gari ma ban koma gidan amare ba domin ba kyau jin sirriin ma'aurata.
Gidan su NY na le'ka naga ana ta share-share wasu ba'kin kuwa sai himman tafiya suke, can gidansu Nasrin ma hakan take.
************
Ban koma gidan Nasrin ba sai bayan sati guda ga dukkan alamu ango NY ko fita baya yi domin ko rabo na dashi tun ran da aka raka ango.
Ai kuwa ni naga soyayya, ina shiga na hangi Nasrin kwance a cinyar NY sai zuba shagwa'ba take shiko ango NY sai biye ma ta yake yi domin yana son shagwa'ba wollah sun bani sha'awa.
Nasrin ce ta d'ago tace "Aminina next week zamu koma school" shiru yayi kamar baiji me tace ba ya Cigaba da wasa da yatsunta tasan yaji ta sarai murmushi tayi tukun ta sauya salo da murya ta shafi gefen kumatun sa tukun tace"Aminin Nasrin baka ji ba ina magana"
Yace"Yes aminiyata fa'di damuwarki in baki magani" murmushi tayi tace"Next week zamu koma school"
Yace"ok love Allah ya kaimu" cike da farin ciki ta bashi hot kiss sannan tace"amin, nagode"
Murmushi yayi yace"muje ciki mu shirya zamu gaida su hajiya, ai Nasrin najin haka ta mi'ke cike da zumu'di tayi bedroom NY yace"ba jira koh"
Ta juyo ta masa gwalo tace"eh d'in" ai kuwa a guje ya bita tayi ciki.
Sun fito sun jero abinsu sunyi kyau barin ma Nasrin NY ne ya bu'de ma ta mota ta shiga tukun shima ya shiga saleh maigadi ya bu'de musu gate bayan ya musu fatan dawowa lafiya.
Suna tafe suna hirarsu abin sha'awa, mintuna ka'dan ya kaisu gidansu NY , suna shiga fallon hajiya kuwa sisters d'in NY suka yo kan su, sunji da'din ganinsu sosai musamman hajiya da Abba suka sha hira abinsu.
Hajiya da Abba suka kuma yi musu nasiha da fatan alkhairi tukun suka musu sallama suka yiwo gida, kasancewar sun yi sallan isha'i kuma sun ci abinci suna shigowa hira suka d'an ta'ba tukun suka watsa ruwa suka bi lafiyar gado.
Can jos ma Naufal da Nawwarah ba k'aramin soyayya suke zubawa ba, inda Nawas da princess ma ake ta raya flower haka ma Nasim da Nazira.
Ansa bikin Nawas da Nasim wata uku masu zuwa hakan yasa NY yayiwa Nasrin al'kawarin zuwa jos ganin familinta.
Ko da aka koma skul ma NY ne me kai Nasrin ya dawo da ita wani lokacin kuma ta tu'ka motar ta ta tafi abinta ta dawo abinta. k'awance ne mai k'arfi ya k'ullu tsakanin ta da Zinat a makaranta kullum suna tare nan zinat take sanar da ita ta samu mijin aure sai dai yana da mata da ya'ya biyu, Nasrin ta taya zinat murna sosai tayi ma ta fatan alkhairi.
**********
Biki ya matso Nasrin ba zama sai tsayuwa sintiri take tsakanin garuruwa biyu, a haka dai aka yi biki lafiya aka watse inda aka kai Nazira gyaran quarters Princess kuwa aka kawo ta jos cikin gidan su Nasrin aka ware ma ta flat d'inta mai d'an karan kyau.
Aisha ma bayan bikin su Nawas da sati biyu aka d'aura nata auren Nasrin ba ta samu zuwa ba saboda skul amma tayi ma ta alkhairi..
Bayan bikin Aisha da wata d'aya Nasrin da Abba da haydar da NY suka k'etare hazo zuwa k'asa mai tsarki inda suka gabatar da ibadar su tsafta-tacciya suka yi Addu'oi ga duk masoyansu da Al'umar musulmai da Nigeria baki d'aya. Daga bisani suka dawo k'asarsu ta gado wato Nigeria inda yan'uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa musu barka da dawowa,kowa ko ya samu tasa tsarabar, Musamman mum d'inta da hajiyar NY da Abbanta.
Bayan an shiga sabuwar shekara ne Nasrin taje jos ita da hajiyan NY domin ance Princess tayi b'ari kwana biyu kawai suka yi suka dawo abinsu domin mum na matu'kar kula da princess saboda y'ar ta shiga ranta, bayan hakama ai dole taso ta domin yadda iyayen princess suke jin Nasrin a ransu ko su suka haifeta iyakaci.
A haka dai rayuwa ta Cigaba NY da Nasrin suna zaman su lafiya sannan suna k'ok'arin farantawa juna rai.
Zuwan su Najwa biyu Nawas ne yake kawosu tare da princess.
Wata ranar friday NY ya sauke Nasrin a makaranta ta fita kenan tayi mishi fatan alkhairi yace"Aminiyata zo nan" ba musu tazo, tukun ya kuma cewa"love kinsan kwana biyu nan naga sai wani kyau da fresh kike yi meye sirrinne?"
Murmushi tayi cike da jin kunya tace"kafini sanin sirrin" daga haka tayi cikin makaranta, shima murmushin yayi yace"zamu ha'du a gida yarinya zakiyi bayani" tukun yaja mota ya tafi a ziciyarsa yana addu'ar Allah yasa tunaninsa ya zama gaskiya.
Alhamdulillah tunanin NY ya zama gaskiya Nasrin na d'auke da ciki harna tsawon wata biyu murna wurin family biyun nan ba'a cewa komai, Nasrin ko ta zama cikakkiyar y'ar gata wurin NY ne, hajiya da Abba ne ga sisters d'in NY ya zamana ma ba ta aikin komai sai karatun makaranta domin likita yace ta daina aiyukan da zasu stressing d'inta.
Bayan wata bakwai...
Nasrin na hango zaune cikin jeren wa'yanda suka yi induction yau a KASU tayi kyau cikin graduation gown duk da dai ciki ya fara tsufa amma kyan nan yana nan, duk sanda suka ha'da ido da NY sai ya blowing ma ta kiss murmushi kawai ta keyi domin tanason yadda yake kula da ita da baby. Angama taro lafiya yayinda Nasrin ta zama cikakkiyar likitar mata suka koma gida cike da farin ciki.
Kwance suke akan gado NY yana mata massage yace"My love inaso in fa'da miki wata magana amma ki fahimceni kinji" murmushi tayi tace"Am all ears love"
Good yace tukun ya fara"My love after all this years da kikayi kina karatu I know is not easy Allah ya sanya albarka, amma ina mai baki ha'kuri Aminiyata bana so kiyi aiki nafison in rin'ka ganinki kullum a gida sannan komai kike bu'kata insha Allah in dai baifi k'arfina ba zan miki kinji my love"
Sai da tayi dariya ishashiya tukun tace"dama kan wannan ne harda wani ragemin murya kana bani ha'kuri its ok duk yadda kace haka za'ayi" , zagayowa yayi ya bata peck a kumatu tukun yace"thanks my love I love you so much" tace "I love you much more".
Bayan sati biyu da induction d'insu ne Nasrin ta haifi y'arta fara kyakkyawa family biyu sunyi farin ciki sosai ga kuma oga NY baki baya rufuwa don murya.
Ranar suna baby taci sunan ummu arif Hauwa'u Kululuwa Maijidda, taro yayi sosai domin yayi albarkar jama'a, Baby Hauwa wadda ake kiranta da husna ta samu kaya da kyautuka sosai hakama Nasrin taro ya watse cikin farin ciki.
Nasrin da NY suka cigaba da rainon d'iyarsu husna tare da taimakon wata y'ar dattijuwa da hajiya ta kawo mata.
Bayan shekara biyu...
Wata mota nagani ha'da'diya mai tinted glass ta shiga gidan Abban NY, guess what Nasir nagani da Nasrin sun fito tare da d'iyarsu me kama da Nasrin wollah sun tafi dani domin sunyi kyau ba ka'dan ba suka shiga fallon hajiya. Shigarsu keda wuya najiyo wani irin ihun da'di ashe princess tazo tayi kyau abinta da y'ar d'iyarta khairi, khairi ta d'anyi kama da Nasrin kasancewar kamannin babanta Nawas ta d'auko.
Nasrin ta shiga bedroom d'in hajiya tayi waya da su mum harda Abban ta domin tace musu tana nan zuwa nan bada da'dewa ba fitowarta fallo kawai taga zinat ai da gudu suka rungumi juna, Nasrin tace "zinat wayace miki ina nan?" Zinat tace "wallahi ba kowa, naje gidanki naga a kulle sai maigadi shine na taho nan ko zan sameki"
Nasrin tace"gaskiya naji da'di na gode zinat, naga jiki yayi nauyi"
murmushi zinat tayi tace"kedai bari Allah ya raba mu lafiya" princess data shigo daga waje ta amsa da"Amin"
Nan suka yiniwa hajiya har dare amma zinat bayan la'asar ta tafi su Nasrin kuwa saida Abba ya dawo suka gaisa tukun suka wuce Abba ba k'aramin jin da'din ganinsu yayi ba, kasancewar husna ta samu abokiyar wasa khairat yasa ta'ki bin iyayenta gida su Abba ko sun ji da'din barinta da akayi domin yarinyar ta shiga ransu gata da masifar wayau.
Nasrin sunyi sallama dasu princess sun fito zasu shigo mota kenan sa'kon Nazira ya shigo wayarta ta haifi d'anta Namiji safiyar yau, take ta kirata tayi ma ta murna tace ma ta in princess zata dawo tare zasu taho tazo taga small Nasim.
Bayan sun koma gida wanka kawai suka yi suka bi gado abinsu.
Suna kwance ne NY yace"Ummu husna yaushe za'ayiwa husna k'ani ne?"
Murmushi tayi tace"Abban husna da neman zance kake to sai husna tagama jami'a "
Cikin watsa ya'dan matse mata baki yace "wollah baki isa ba, wai ma wurin wa kika koyo iya magana da zolaya ne" dariya tayi sosai tukun tace "Duk cikin koyarwan🌹Aminin kwarai🌹 ne"
dariya suka sa gaba d'ayansu tukun suka Cigaba da hirar su irinta masoya har barci yayi gaba da su. Murmushi nima ummu arif nayi tukun na janyo musu k'ofa bayan nayi musu fatan Allah dawwamar dasu cikin farinciki da so da k'aunar juna, asuba ta gari iyayen Husna, aminan kwarai, masoyan juna, Nasrin Nasir.
Alhamdulillah a nan na kawo muku k'arshen AMININ KWARAI.
Godiya ta tabbata ga Allah ma'daukakin sarki mai kowa mai komai daya bani Ikon fara littafin nan lafiya da gamashi lafiya, Alhamdulillah.
Ako yaushe kana raina masoyin k'warai AAM,fatan alkhairi gareka always.
Sadaukarwan wannan littafi naka ne yayana aminina NY(Abu farhan) duk inda kake ina maka fatan alkhairi.
Kunfi kowa son littafina
Ameela(daughter)
Sahiba(Aisha Ishaq)
Sadiya S Nayaya(ummu fadila)
Sadiya M Nayaya
Amina Shehu
Amina Jajere
Fatima Engerwar
Amina B Moh'd(babas)
Saudat
Sis Maryam
Nanatu, da sauran masoya littafina luv u all.
Marubuta Masu yayi Na gaishe ku
My Khairi
Amarya Azland
Ummu samha
Kausaralle
K'awalli ummu aisha,lol
Kdeey Mrs trouble,lol
My lubiee
Reporter, da sauran marubuta Allah k'ara ilimi da basira.
Ban manta ku ba
Hajara gamji
Mrs Ibrahim
Jinjina ga Wa'yan nan groups d'in
Nagarta Writers Association(NWA)
Tauraruwar Mace
Excellent writers
Duniyar Makaranta
Khairi Hausa Novel
Babbar Mace
Gorgeous Ladies
Dandalin Hausa Novels
Dama sauran groups duk ina jinjina gareku.
SHARHI
Labari Aminin kwarai d'an ta'kaitaccen labari ne da yake nuni ga amfanin hakuri, biyayya da kuma taimako.
Da fari Nasrin taso NY kamar ranta amma taga kamar bazai zama nata ba ta ha'kura ta mi'kawa Allah komai, sannan tazo ta taimaki mahaifinsa ta kuma yi mishi biyayya duk cikin rashin sani.Sai kuma daga k'arshe ha'kurin nan da tayi, taimako,biyayya ya zame mata alkhairi.
Baya ga haka mutane da suke tunanin mace me abota da maza y'ar iska ce ko kuma mazan y'an iska ne ya kamata ku dinga tsamewa duk da dai ansa akwai b'ata gari saidai karku manta mutanen k'warai basa k'arewa, sai dai mu kasance masu yawan Addu'ar neman tsarri ga sharrin zuciya da kuma bin zamani.
Sannan B'angaren zinat lokacin da ta cire rai da kuma zama mutuniyar arziki ba da taimakon Allah da kuma Nasrin rayuwarta ta sauya completely.
Ina kira ga sisters d'ina mata out there who enjoy giving their body in exchange for money ko kuma tsantsar so, thinking that you can't start a new life it is wrong, though Zina yana d'aya daga cikin manyan laifi a addininmu but remember ba shirka bane you can be forgiving idan kin tuba da niyya mai kyau sannan baza ki k'ara komawa ga laifin ba, Allah is Ar-rahim(The all merciful) Al-gaffar(the forgiving)
Please repent and give yourself a second chance remember death knocks no one door.
Ku kasance tare dani cikin sabon littafina mai suna WATA RANA SAI LABARI🌹SOYAYYATA DA AISHA 🌹 wanda zai fito nan bada jimawa ba.
Taku ako yaushe jikar NAYAYA
Ummu Arif💞
⭐NWA⭐
®Nagarta Writers Association.
adsense 2 here