Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

ASHE HAKASO YAKE complt

adsense here ASHE HAKA SO YAKE . [7:54pm, 08/12/2016] 馃懜 Meemiluv: 馃槶 ASHE HAKA SO YAKE 馃槶 (BASE ON TRUE LIFE STORY) 馃挃 馃挃 馃挃 馃挃 馃挃 馃挃 馃挃 SHORT STORY 馃挃 WRITTEN BY QUEEN MEEMI 漏NWA EPISODE 1 Tsaye nake a d鈥檃ki ina gyarawa mama kayan ta daya ke Allah yayi ta da tsafta duk wata nake Mata kwalemar d鈥檃kin da na ware kayan da za a bayar, sai goge Mata nake ,sallama naji daga can tsakar gida, kafin na fita mama dake tsakar gidan ta amsa ,鈥漟iddausi ce? sannu da zuwa鈥�? . 鈥淵awwa mama Meemi na nan鈥�?. tace tana d鈥檃ki. Falo na fito ganin fiddausi ce da gudu na rungumeta 鈥渨ata Sabon gani, dama kina nan鈥�? nan ta kalle 鈥渘i ke ba zama na zo yi ba gidan su maryam zaki rakani鈥� . Na kalle ta 鈥渟auri fa nake ina da lecture 12 to 5 fa ,sai ki jira nai wanka sai nazo mutafi鈥� Juice na kawo Mata da meatpie . 11 dai dai na gama Shiri na abaya me adon purple nasa na yane kaina da purple en k鈥檃ramin gyale na d鈥檃u black bag d鈥檌na inda handout d鈥檌na ke Ciki ,kallon Fiddy nayi 鈥渘ace tashi mu tafi鈥�. Sallama mukai wa mama muka fita motar Fiddy muka Shiga ta jamu mintuna 30 ya kaimu unguwar gyad鈥檌 -gyad鈥檌. Fiddy dake driving 鈥渢ace meemi ina ne gidan鈥�?. nuna Mata nayi dai-dai get d鈥檌n gidan muka tsaya muka Shiga maryam na zaune tana karanta novel ganina yasa ta daka tsalle kallon mamaki ta tsaya ta naiwa Fiddy tace 鈥渇iddausi Amma baki da kirki sai yau zaki zo gidan mu鈥� hira ce ta kaure maryam ta juyo ta kalleni 鈥渕eemi ya rubutu鈥� nace 鈥渕una nan muna yi鈥� tace 鈥渁i naga kina typin wani ZEENATU gaskiya book d鈥檌n yana kawo light鈥� murmushi nayi nace Mata thnk. 鈥淵awwa meemi Kinga dama Akwai wata mak鈥檕ciyar mu ran nan muna hira take cemun data iya novel data rubuta labarin ta ,to yanzu tunda gaki kizo kawai mu Garzaya鈥� . Kallonta nai 鈥渟ai kuma aka ce miki Banda abinyi to school zani鈥� Fiddy tai dariya tace ke鈥� kam meemi Kije mana鈥�. Jan hannuna tai naja fiddy muka fita, gidan dake kusa dasu muka Shiga tsaf -tsaf da tsari gidan gwanin sha awa,sallama maryam ta k鈥檞ad鈥檃 Antykhady fito nan ta fito yar bafula tana murmushi tace 鈥渕aryam karad鈥檌.duk kin cika min kunne鈥� 鈥淎lbishirnki Anty鈥� tace goro yau Ga dai Queen meemi.writer d鈥檌n online 鈥�. Washe baki matar tayi 鈥渨ow Amma naji dad鈥檌n ganin ta saboda ina son littafanta 鈥�. 鈥淕askiy marubutan online na kok鈥檃ri kuma muna k鈥檃ruwa Allah ya K鈥檃ra hazak鈥檃 meemi鈥� Gaisawa mukai maryam tace 鈥淎nty ki bata labarin naki ta watsawa makaranta Kinga duk Wanda ya karanta zai tayaki da addua ko ,duk da baki fa d鈥檃n labarin ba, Amma idan meemi tafara typin dinsa sai na karanta.鈥�. Anty tai tai dariya gaskiya naji Dad鈥檌 Tashi tai tace tana zuwa Ruwa ta kawo. waya tace tai K鈥檃ra dauka nai naga sunan ruky ina d鈥檃 gawa tace 鈥渕eemi an fasa lecture cuz malaman basa da time ,malama Amina ta tafi course Egypt yau Amma malam shettima ya bada handout saboda bashida lfy na bada ayi mana photocopy ni dake Dad鈥檌 ne ya kashe ni mukai sallama. Na kalli maryam 鈥測anzu free nake ba lecturer d鈥檌n yanzu Anty sai ki fara bani short labarin naki tunda naji kince ba shida yawa鈥� . Murmushi tayi nan ta taso kusa dani ta zauna. Pencil da paper na zaro na kalle ta ina murmushi magana ta fara Kamar haka鈥︹€︹€︹€�. Ku biyo Queen meemi don jin ya labarin yake karku manta labarin da zan bada gaskiya ne . Written By Queen meemi. [7:54pm, 08/12/2016] 馃懜 Meemiluv: 馃槶 ASHE HAKA SO YAKE 馃槶 (BASE ON TRUE LIFE STORY) 馃挃 馃挃 馃挃 馃挃 WRITTEN BY QUEEN MEEMI 漏NWA EPISODE 2 ta fara bani labarin ta kamar haka tace : . 鈥淎shekarin baya da suka wuce na samu kaina cikin matsanan cin ciwo azuciya ta duk akan soyayya da farko dai ni Suna na khadija ni haifaffiyar garin kano ce a k鈥檃ramar hukumar tarauni shekaru na 27 ,na taso cikin tarbiya saboda gidan mu gida ne na tarbiyya, 鈥榶a鈥檡an gidan mu, mu 13 ne saboda Mata biyu ne agidan mu mahaifyar mu da abokiyar zaman ta,nayi karatun boko har kuwa matakin secondry school karatun islamiyya kuwa na bashi muhimmanci matuk鈥檃 haka ma sauran yaran gidan mu duk da bokon ma ba a bar mu a baya ba鈥� nan ta tsaya ta kalleni na kalle ta nace 鈥淢asha Allah Anty khadija Ina jinki cigaba鈥� zama ta gyara San nan ta cigaba 鈥淣a ta shi da biyayyar iyaye ,kuma mahaifin mu yana sona matuk鈥檃 fiye da sauran yan uwa na,saboda biyayya ta ta bam- bamta da ta sauran ga hak鈥檜ri da juriya gashi bani da yawon magana meemi ba yawon kai bane kawai don Ina son bada labarin dai-dai n鈥� Dariya nayi nace 鈥淎nty khadija kenan aini dama nafiso ki fad鈥檌 komi ,don makaranta suji鈥� nan ta cigaba 鈥渟ai dai shi mahaifiya bashi da da burin 鈥榶a鈥檡an shi mata suyi karatun gaba da secondary a gida sai dai idan yayi ma aure idan mijinka ya yarda sai kayi鈥�. 鈥渢un tasowa ta ban tab鈥檃 soyayya da wani saurayi ba saboda harkar karatuna ne agabana domin Allah yayi.ni Ina mutuwar son karatu. karatuna na islamiyya kuwa duk malamai na na ji dani saboda k鈥檞azona da dagewa duk wata musabak鈥檃 da za ai sai anje dani kuma cikin ikon Allah nake ciyowa ,ba wan nan kad鈥檃i ma har sauran wasu gasa haka nake ciwo su ,mahaifina yasha Karb鈥檃r kyaututtuka a islamiyyar mu saboda jajircewar sa, duk wani taro da za ai sayya je yana alfahari dani saboda duk Wanda ya bud鈥檈 baki a unguwar mu da schools sayyace inada kamun kai saboda haka akwai masu sona da yawa Amma kwarjini nake musu jarrabar sa Allah ya d鈥檕ra min kuwa shine鈥�: 鈥淎 islamiyyar mu akwai wani malami sunan sa malam Abdullah Ina mutuwar son shi bansan sanda na fara sonsa ba kawai jina nayi luntsum cikin tafkin soyayyar sa,don in yana biya mana Karatu sai dai naita jin muryarsa har cikin kai na Jikina yayi lub鈥檜s ,wataran sai dai na sunkuya kasan bench nai ta murmushi Ina danna kirjina don ji nake kamar zai fad鈥檕 don wani irin soyayyar sa da nake ji Bazan iya kwatan tawa ba,ban ban tab鈥檃 ganin mutum mai tsaftar sa ba, kullum cikin k鈥檃mshi yake , har so nake yana biya mana karatu don ranar da duk da bai zoba, to aranar kamar Mara lafiya nake komawa karatun ma ba gane Shi zan ba a ranar hmm鈥� kallona tayi tace 鈥渕eemi kin San me kuwa鈥� nace Aa sai kin fad鈥檃 Anty khadija鈥� nan tace 鈥渨allahi duk wan. nan abun bai san Ina yi ba ,Amma muna mutunci da Shi da kuma fahimtar juna a tsakanin mu, kasancewar ni d鈥檃liba ce mai hazak鈥檃 don haka ana ji dani,Shi isa nake d鈥檃n samin saida ta wan nan b鈥檃ngaren鈥�. na kalle ta nace 鈥淎ntykhadija so kenan inya kama ka sai da addua鈥� nace Mata cigaba. kiran sallah ne ya karad鈥檈 ,nan tace meemi bari miyi sallah sai na cigaba miki. nan nace Mata to Anty khadija to makaranta ku biyo meemi donjin cigaban *WRITTEN BY QUEEN MEEM shared by maman ihsanASHE HAKA SO YAKE . [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: . ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 3 *Queenmeemi.WordPress.com* Mamana taga na canja kwana biyu Sam bani da kazar-kazar ga yawan tunani ko sunan sa naji an ambata sai gabana ya fad’i in kwa mai irin sunan akai wa b’atanci nakanji tamkar Shi a akaiwa so nake kawai na samu na fad’a wani Amma na bar son abdul a cikin zuciya ta saboda Ina jin kunyar agane Ina sonsa in agida ne musaman inni kad’ai ce ad’aki haka zan d’akko papers nai ta rubuta Ina sonka Abdul sai na Tara da yawa sai na yayyaga su da abin ya kai ya kawo abinci ma sai na rageci,duk a ganina ko zan Sami saida wataran har jin haushi nake Aganina Abdul ya San Ina cinkin matsalar Amma bai Kula ba,akwai wata rana da muka had’u da k’anwar sa agidan biki, sai nan nan nake da ita abubuwa na siyo na dunga bata ,gani nake kamar Abdul nakewa, muna hira sai tace na rik’e Mata warlet d’in ta wani k’araimin pic ne ya fad’o passport hoton Abdul ne kawai na k’urawa pic d’in Ido Ina murmushi ,ajaka ta na saka Shi,tunda na samu pic din nan sayya Ke d’e bemini kewa haka zan manna pic d’in a k’irjina Ina murmushi koda bacci zanyi domin suk lokacin da zansa hak’ar-k’arina na kwanta nan soyayyar sa zata bijiro min nakasa tsugun samin pic din sai ya saman sa Ida awahale nake bacci tun sanda na fara son Abdul. “Naga abin yayi yawa har kuka nake domin kullum k’irjina kamar an sa wani Abu an tokare,muryar Abdul ita k’adai Ke sa naji dai-dai to bana samun jin muryar sa sai da yamma a islamiyya. wani malamin mu na samu nace yaban adduar da zanyi wadda idan Ina son Abu a wajen wani haka ya bani tunda ya bani kullm na tashi senayi haka da yamma da dare duk inayi ne don Abdul yace yana sona ,wallahi wataran meemi Ina adduar Ina kuka domin kamar wata jarraba mamana tana Kula dani Amma kawai ta k’yaleni gashi Banda aiki kullum sai karatun alqurani da sauran adduoi wallahi duk Dan ya furtan yana sona ,har sauka nayi Amma shiru ,duk na rame na fita hayyacina Ina mamakin irin wan nan soyayya tawa. wata zuciyar tawa tana ban shawara na fad’a mai amma ina jin kunyar sa, sai Naga kamar zubda k’ima tane na ‘ya mace ,ko kwalliya dai nayi nayi domin ni kadai nasan yanda nakeji, wata rana mamana ta sameni ad’aki take tambaya ta meya sameni kwana 2 Mena sa araina ? Sai dai kawai nace ba komi,tayi- tayi na fad’a Amma na dage ba komai Dariyar takaici tayi ,tace khadija duk Randa na kuma ganin ki haka wallahi ko me nene sai kin gayan ,nan na d’aga kai nace na yarda mama”…… Ku biyoni son cin yanda zata kaya *QUEEN MEEMI* . [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 4 ina cikin wannan halin ne kwatsam mahaifina ya kira ni yake sanar min hukuncin da ya yanke a kaina zai aurar dani ga d’an yayan shi na shiga tashin hankali saboda bani da zab’i alokacin da yake gaya mini daina gani nayi ga jiri daya Ke neman kwasa ta Kaina ak’asa ban d’ago ba saida babana yace na tashi na tafi ,San nan na mik’e direct d’aki na Shiga na kulle k’ofa na hau kuka wata sabuwa kenan Bazan iya cewa mahaifina bana son zab’in sa ba ,Bayan na gama kukan na tashi Ina kai kawo tunani nake kawai Abdul baice yana sona baa. har zuwa lokacin ni kuma shi zuciya ta take mutuwar so. tunda banana yayi maganar nan bai sake kumayi ba don nasan baya magana biyu al adar gidan mu duk dare za a zo azauna Ana hira Amma Banda ni Ina d’aki na kunshe, ko ina karatu ko Ina kuka ,inkwa safiya tayi inna fito haka zakaga ‘yan gidan mu na kallo na saboda yanda duk rame ,ga ‘yan gidan mu kullm maganar bikina idan senayi sena ji kamar suna watsan barkono ne sai dai na bar gun. gashi lokacin naci burin Shiga nursing school don karatun aikin jinya ,sanin ba dama shiisa na kauda abun,haka dai nake zaune cikin kunci inde na samu sa’ida to yamma ce tayi anje islamiyya shima innaje ba fahimtar karatun nake ba ,sai bin malam Abdul da kallo da nake time to time,inkwa ya tashe ni na biya karatu bana iya wa,duk ‘yan class namu na mamakin irin canjawar danai ,shima malam Abdul din ya tab’a tambaya na meke damuna nace bakmi ,a lokacin dayake magana sunkwi dakai nayi ganin alamar hawaye zai zubo min Ina takaici nikadai Ke wahalar sonsa Shi bai son inayi ba,ganin ya matsa yasa nace Ina yawan ciwo kai ne ,addu’oi ya bani.awan nan ranar naji sanyi araina Wanda ban tab’a Samu ba tun fara sonsa ,ganin yau yanda ya nuna kulawar sa a gareni. Bayan sati 2 Naga Ana ta shigo da kaya irin su tv cooker gas da dai sauran abubuwa da ake kai mace in za a Mata aure ganin hakan yasa na tabbatar aure ba fashi,gashi mijin ma bamu Saba ba,wan nan yasa na dada k’warzabar kaina. A bisa aladar makarantar mu duk yarinyar da za a aurar akan had’a d’an taro a yi mata nasihohi da suka shafi zaman aure kuma malam abdul shine yake jagorancin irin taron ,duk dai,makarantar ba Wanda ya sani tunda bana cikin nutsuwata bikina sai gaba towa yake kuma sai a wannan tsakanin wanda za ‘a aura min ya fara zuwa wurina saboda shi yana bauchi ne mukhtar baya da makusa amma saboda bashi zuciya ta ke so ba sam na kasa fahimtar hakan,sai dai ni dashi mi shiru Shi Amma Shi yana sona tunda ya nuna sai dai yayi ta maganar sa ,nikam alokacin zuciya ta na can tunanin Abdul. *QUEEN MEEMI* shared to u by Maman ihsaaaaan sakeenatASHE HAKA SO YAKE . [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE . . (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 5. . *Queenmeemi.WordPress.com* . k’anina yazo ya samen kan maganar makaranta na taron sallamata da za ai yace Naga har yanzu basu sani ba, fuskata a had’e nace karka gaya musu kabar abin kawai ni ba sai ammun ba ,mamana dake shigowa d’akin tace “ya haka sai kace wani abun ni narasa gane kanki khadija duk kin birkice ,nan ta kalli k’anina tace yaje makarantar ya fad’a musu. haka K’anina yaje ya samu malam abdul ya sanar mishi maganar auren na, a lokacin ne wai abdul ya shiga tashin hankali wai ashe shima ya dad’e a cikin yanayin da nake ciki. haka da daddare yazo gidan mu ,wai yana sallama dani wani sanyin dad’i naji Aganina duk matsalata tazo karshe ,fita ta shine yake sanar dani irin k’aunar daya Dad’e yana min Shi ya bari ne a dad’a lokaci hawaye ne kawai suka zubo mai nima haka da k’yar ya tafi da sassafe sai gashi ya dawo gidan mu gun babanmu,nan yake sanar ma banana yana son abashi izinin zuwa guna baba yace ai aure za ai min sai dai yayi hak’uri ya riga ya bada ni kamar k’aramun yaro Abdul haka ya tsaya yana kuka agaban banana ya Dad’e yana yi banana yayi mai nasiha ya tashi ya tafi, shigowar banana cikin gida yasa akai kira na ransa ahad’e yace “yanzu wani malaminku yazo min da maganar yana son zuwa gunki nace na badake kin sanshi ne”? nace “Aa” Masha Allah yace San nan yace na tashi na tafi. lokacin da aka sa na sallamata ya taso haka malam abdul Ya k’i tsayawa wajen taron sallamata kamar yanda aka saba Bayan kwana 2 a tsakani malam abdul ya kwanta ciwo, Wanda har sai da aka dangana Shi da asibiti,tunda naji labari ta hanyar k’anina yasa na dada tashin hankali na hanya kawai nake nema naje na gano Shi ,Amma ba dama domin ba kasa fai ake barin mu fita ba ,balle ni da bikina ya matso ,ak’allah sai da Abdul yayi sati 2 a kwance San nan ya samu Sauk’i sai alokacin na samu sa Ida ,ta bangaren gidan mu kuwa ba abinda ya shalle su shiri suke sosai na bikina. Ku biyo meemi don jin cigaba *QUEEN MEEMI* [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 6 *Queenmeemi.WordPress.com* . wata rana Ina zaune sai wata k’awata tazo gidan mu tana zancen bikina sai nake tambayr ta malam abdul sai tace ai jikin nasa ya kuma tashi ,”Ke wai ashe malam abdul ke yake so” yanzu duk makaranta kowa ya sani ,kuma duk saboda Ke yake ciwo ,nan na kalleta har na bud’e baki sai kuma nayi shiru ganin mama ta shigo d’akin Bayan tafiyar ta naci alwashin duk inda gidan su Abdul yake sai na nemo ranar Friday na shirya na nemi gidan nasu kuma na samu. da sallama na Shiga gidan muka gaisa da umman Abdul,a bazata naji tace “khadija yau kece a gidan namu mamaki ne ya isheni murmushi tayi “Kina mamaki ko jin na ambaci sunanki kai tsaye ko ,to na Dad’e da jin labarin ki agun Abdul bacin haka ma duk hotunan ki akwai su d’akin Abdul,na jin- jina soyayyar Abdul agareki tun baki kai haka ba yake k’aunarki” shiru tayi San nan tace “khadija nayi jimamin auren da za’ aimiki domin ga Shi nan Abdul kullum bashida lafiya yasa abin a ransa duk dashi yayi k’auren baki bai nuna da wuri ba Amma hakan bazai sa mu kasa yarda da k’addara ba” . kallon umman Abdul nayi nace “tun rashin lafiyar sa na farko nake son zuwa sai ban samu dama ba”, ai bakomi khadija bari na dubo d’akin sa ,tana Tafiya na share k’walla saboda yanda naji soyayyar matar ya ratsan zuciya duk adaliln son D’an ta,zuwa tayi tace “kije ku gaisa” haka na tashi jiki a salub’e yana zaune jingine da filo na rakub’e a bakin k’ofa na tsugunna ta nan nabi d’akin da kallo ko Ina hoto nane an manna a bangon wani awajen musabak’a wani wajen wata gasar ,sunkai wajen hamsin hawaye na share na k’ura mai Ido shima haka hira muke kad’an -kad’an nan Abdul ya zauna duk wani dad’ed-d’en siririn zuciyar sa sai daya bud’e min ya gaya min haka nima ban k’asa agwiwa ba na warware mai irin halin Dana shiga. kuka na hauyi sosai kamar me jikina duk ya d’au zafi jinai yana khadija “kiyi wani Abu mana Kice ni kike so agida watak’il abba ya karb’I choice d’inki ko ma samu sa ida” shima kukan yake. Tashi yayi ya bud’e wani guru littafi ya d’akko ya mik’o mini na bud’e wak’ok’i ne yayi mun na larabci da turanci da Hausa ko Ina khadija khadija ,rufewa nayi na mik’e Ina kuka na fita gun maman sa, rungumeni Tayi tana min nasiha ….kuka nake sosai saboda nasan bani da mafita saboda saura sati biyu 2 weeks bikina …..haka na koma gida cike da rudani.. khadija ta kalleni tace “gaskiya Meemi so bala’i ne” Ku biyo meemi don jin cigabanASHE HAKA SO YAKE . [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 7 *Queenmee.wordpress.com* Tunda na koma gida na k’i cin abinci sai kuka da Naga wani zai shigo d’akin nawa saina rufe Ido alamar Ina bacci haka na kwana banci komi ba sai kuka,da k’yar nasha tea ,duk fa wan nan abin da nake bana bari ‘yan gidan mu su gane ,sede ramar da nai ce zai nuna maka Ina da damuwa Amma in akai duba ga duk wace zatai aure sai tayi rama shiisa ba adamu ba. da safe kuwa da k’yar na shiga kitchen don samun abinda zan sa acikina ,jinai bana buk’atar komai ,sai kawai na fara kuka jin Tafiya alamar za ‘a shigo yasa na Shiga cikin store na shige canciki Ina kuka don na rasa meke mini dad’i domin jinai wani Abu ya tokaren zuciya ta kuka nake da k’arfi Amma baya sautin baya fita,Shigar mama store d’in yasa ta gano ni kamo ni tayi na fad’a jikin ta ,wuyana ta tab’a taji zafi rau ,kafin muje d’aki nayi warwar a k’asa ko motsi banayi k’anwata dake bakin famfo ta k’wala ihu nan ‘yan gidan mu suka fito, gida ya kaure khadija ta mutu,sai koke- koke suke haka aka kaini asibiti nan aka wuce dani emergency ‘yan gidan mu kowa ka gani Ido luhu-luhu sunci kuka doctor ya fad’i abinda Ke damuna,yace damuwa tayi mun yawa ,ga rashin cin abinci,saura kad’an jinina yahau,Amma Allah ya kare aka shawo kan matsalar kowa bud’ar baki sayyace ai alhinin rabuwa da gida ne nan aka bani gado kullum Sai ank’aran ruwa saboda jikina ba k’wari,kallon mutane kawai nake Amma ni nasan me zuciya ta Ke ciki ,ganin hakan yasa aka d’aga bikin aka k’ara sati 2 haka naita jinya sati d’aya aka sallamomu na warware sarai,kwana biyu a tsakani mama ta sameni a d’aki kan sai na gaya Mata meke damuna kuka na hauyi domin dama so nake na samu Wanda zan shedawa,haka na zayyanewa mama komi nan tahau salati tare da tafa hannu ,yanzu khadija akan soyayya kike neman kashe kanki,me yayi zafi tunda bakya son sa ai sai naje na gayawa babanku ,abaki Wanda kikeso. kasa na sakko Ina rok’on mama kar tayiwa baba magana nan nace “mama zan miku biyayya har iya inda k’arfina ya k’are ayanzu in kika fad’a baba zai yi fushi dani San nan gashi angama komi badon ma rashin lafiya ta ba da tuni anyi, bana son fushin Allah ya sauka akaina zan cire shi araina ,nan mama ta rungumeni tana me jimamin halin da nake ciki domin nasan so ba wasa ba,nan tace zan taya ki da addua khadija Allah ya sanyaya zuciyar ki,haka ta tashi ta fita da yar k’walla a idon ta na tausayina..nan na Lula tunani tabbas nasan koma na sha giyar wake ba zan iya cewa baba na bana son zab’in sa ba. . *QUEEN MEEMI* [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: . , ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) ©NWA WRITTEN BY QUEEN MEEMI EPISODE-8 bayan kwana 2 na D’an samu sa ida da rad’ad’in dake raina, mamana Nacewa ina son zuwa gidan k’anwar ta duk da shrin bikina na ake hakan bai hana mama tace naje ba har sakon kudi ta ban na kai, bayan na shirya na tafi Ahankali nake takawa har naje bakin titi na hau adaidaita sahu zuuu ya tafi dani dai -dai a wani layi babur ya lalace haka na zauna yana gyara nikam na lula tunani ga jakata a gefe ban aune ba naji an wafce jakar afusace na fita daga adaidaita sahun wani gardi naga ya arta da gudu hannu na d’ora aka mai adaidaita sahu yace “hajiya ki hak’uri b’ata gari ne” kuka na saka sabida yawan kud’in da ke ciki ,tsugunnawa nayi kawai karaf idona yakai kan Abdul dake fitowa daga get din wani gida shima ni ya hango da D’an gudun sa ya tawo kaina na sunkuyar k’irjina yana wani lugude ji nake kamar ana kwaranyo mini da ruwan sanyi a zuci. magana yake sai kawai na mik’e muka k’urawa juna Ido baki na na furta nace Abdul a hankali gani nai ya rame mai adaidaita ya tsaya galala yana kallon mu gyaran murya yayi muka dawo hayyacin mu,”yace kin manta da jakar taki ne” Abdul ya juyo ya kalleni “mayya faru ne”? nan mai adaidaita yayi mai bayani banyi aune ba naga Abdul yayi Baya da gudu muna nan tsaye sai gashi da jakata cike da haushi yace sai jaka Nagani ya yar duk ba komi a jakar take ya saka hannun sa a aljihu ,ya d’ebo duka kudin da ke ajikinsa ya saka mini a jakar ya mik’on ban karb’a ba ,sai da ya dad’a mik’on San nan na karb’a haka na shiga adaidaita sahun ya fige Ni shima Abdul ya biyomu a babur din sa jinchen, bayan naje gidan na dad’e na fito don ta fiya Naga har lokacin Abdul na nan, zuwa yayi ya tsaya yace “khadija ina sonki so mai tsanani bazan yi kasa agwiwa ba domin inaji ajikina ke tawa ce hawaye na share don nasan da kamar wuya nace “Abdul kayi hak’uri saura sati d’aya fa” idon sa yayi jajawur ya dafe kai “wallahi meemi take ya fita daga kamanin sa” zama yayi ya dafe kirjii Nima na dafe nawa yanda yake bugawa haka muka zauna kowa yayu shiru wani fefen CD Abdul ya d’auko ya mik’o banyi magana ba sai hannuna dake rawa nasa gefen hijab Dina na share hawaye *YA KHADIJATU SONKI NAKE* shine sunan da nayi arba dashi a kwailen CD d’in kallona yayi khadija “wallahi zuciya ta ta makance akanki nayi k’wauron baki wajen furtawa Nikam kasa magana nayi sai hawaye kawai ke zuba haka ya k’arfafan gwiwa yace tabbas gobe zai zo da dangin sa ko za adace haka mukaita hira da k’arfafawa juna gwiwa. cike da k’arfin gwiwa na koma gida ranar kowa yaga Canji a awajena aranar zagewa nayi na Lodi abinci har kwalliya nayi d’akin yayana naje na kulle ta ci ki saboda Baya nan na saka CD d’in nan na wakar suna na naji na tashi wak’ar sosai ake rairo mini kalaman da suka sanyayan jiki da tsana nin son Abdul naji ya karu a raina ga wani irin zuzutani da ake kuka ne ya kubceni na d’auko hoton Abdul na tsaya jikin k’ofa na k’ura mai Ido ina kuka ganin ba sarki sai Allah yasa na kashe. hirar da mukai ita ta dawomin wani murmushi na saki saboda aganina matsalata tazo kar she. *QUEEN MEEMI* shared by MAMAN IHSANASHE HAKA SO YAKE . [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: . ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 9 *Queenmeemi.WordPress.com* Washegari haka na tashi cike da d’oki sai,dakon k’ofa nake can kamar 12am sai ga k’anin baban Abdul da wan sa da shikan sa Abdul d’in, har baba ya fita aka kirawo Shi haka suka zauna suna gaisawa nan k’anin baban Abdul yace sunzo neman izini kan neman auren khadija ne, baba ya d’aga kai ya kallin Abdul murmushi yayi “kai ba kai kazo ran nan ba, nace an bada ita, kasan dai ba kyau nema cikin nema ko ? tsugunnawa Abdul yayi kasamakon jin jiri da ya faraji ,kanin baban sa yace “kai Abdul da ilminka kake son nema cikin nema kana malami” siraran hawaye ne suka zubowa abdul yace “Ayi hkr baba nashiga rud’ani ne” ,haba jiya yaje gida ya same mu duk ya fita hayya cin sa domin kwanaki ance yayi ma rashin lafiya haka kawai ka d’ora kanka jarabar soyayya ” cike da tausayi babana yace “badon anrugaa anyi komai da wani ba, da babu makawa Shi ne mijin khadija ,domin soyayya Gaskiya ce Allah ke d’orawa bawan sa ita, sai dai ita maganin ta hakuri, ina bada hakuri kuma ina godia ga nuna kauna ga jinina ,khadija nada k’anne sai ka zabu d’aya aciki ,Abdul yace baba ba nak’i tayin ka ba ,Ayi hak’uri nan cike da jimami sukayi godia suka tafi tunda Abdul ya koma gida zazzabi ya rufe Shi. . Nikam ina zaune a d’akina na ji baba na gayawa mama na yanda akayi,na d’auka mama zata sanar da Shi cewar Nima Shi nakeso Amma naji bata fad’a ba,na k’uduri niya inde baba yace Shi nake so tabbas bazan cuci kaina ba fad’a zan Amma sai dai shuri kikeji bai tambayen ba nan ta kuma shiga rud’ani damuwata ta dad’a yawaita Nima hakan na fara zazzabi a tsaitsaye ,washe gari tun safe ban sa komai acikina ba,na rasa mai ke mini Dadi,ina d’aki akwance da hoton Abdul mama ta shigo d’akina ta dad’e tsaye akaina ban sani ba jinayi tace “wan nan Wace iriyar soyayya ce khadija kikeyi ne?,kuka na sa na tashi na rungume mama nace “mama ki tayani da addua k’irjina ya rik’e ji nake in banyi ihu ba bana jin Dad’i ita kanta mama na bata tausayi nan tayi mun nasiha kan yarda da k’addara tace “khadija duk soyayyar ki da Abdul in bashine mijinki ba sai dai ki hak’ura ta dole ,haka in mijinki ne dole dashi za ai nasihar datai mun yasa na samu sa ida har nasa tea acikina ,bayan fitar ta na d’au sabuwar wayata na danna Layin Abdul ya d’auka jin muryar sa sai da tsikar jikina ya tashi ,kwantar mun da hankali yayi mun dad’e muna waya shima yace mun Baya jin Dad’i nan na tabbatar soyayya Gaskiya ce saboda D’an hirar da mukai naji duk zazzabin ya gushe sai da kud’in wayar ya k’are muka hak’ura. . Yau saura kwana hud’u d’aurin aurena duk na kuma fita hayyacina komai kanne na keyi Amma Nikam nace ba abinda zanyi,ko bi ta kaina basi ba sai aiwatarwa suke Nikam ina d’aki akunshe muna waya da Abdul don ko abincin kirki bana ci domin wani irin Dad’i nakeji sosai araina,da yamma wajen k’arfe 5:30 na fita D’an bayan layin mu da yake ba mutane D’an tafiya nake ahankali iska na kad’a ni sai naji wani sanyi araina na dad’e a tsaye zuciyata tai fes ina D’an kalle -kalle wani ne ya tawo kawai sai nake ganin sa kamar abdul nawa murmurshi nayi na lumshe ido yazo dai-dai dani nace “Abdul”! mutumin kawai kallona yayi ya wuce sai kuma lokacin na gazgata bashi bane murmushi nayi nace wato Abdul gizo yayi min wajen 6 na bar gun ina tafe ina waya da Abdul na ,ina shiga gidan Naga k’annen na zab’ar furniture D’ina nan na had’e rai idona ya kawo ruwa k’irjina na fat-fat mik’o mun akai nazauna hannuna naji na rawa da k’yar na zab’a na shige d’aki na rusa kuka aranar ma da k’yar nayi sleep da taimakon jin Abdul da voice din sa,haka dai naita rayuwa da soyayyr Abdul duk wanda yaganni sayya tanka saboda ramewar danayi da sai masoyan idanuwa kawai na rage ,Sam bana fitowa ko waje kullum a d’aki ,mamace tace tabbas sai na dinga walwal saboda mutane . *QUEEN MEEMI* [7:54pm, 08/12/2016] Meemiluv: . . . ASHE HAKA SO YAKE! (BASE ON TRUE LIFE STORY). WRITTEN BY QUEEN MEEMI ©NWA EPISODE 10 *Queenmeemi.WordPress.com* haka na sake nake fitowa cikin gida Ana walwala dani Amma kasan zuciya yana manne da Abdul domin walwalar ma ta samo asaline kan mafarkin da nai an daita Aurena da Abdul a ranar har D’an kunnen gwal d’ina na bawa k’anwata, na Kula idan Ina walwala mama har jin dad’i take,haka nake daurewa ,kewar Abdul da sonjin k’ira’ar sa ya dameni, haka da yamma naje gidan su k’awata na karb’o wani karatun sa da yayi akai record saboda Allah yayi Shi da zak’in murya tunda na samo nake ji duk dare inna kwanta ,wataran kuma haka zan d’au pencil da paper nai ta rubuta sunan sa ajiki ,idan Ina rubutawa wani dad’i nakeji. sometimes zuciyata na yaudara ta tabbas Abdul ne mijina domin Nasha mafarkin ranar d’aurin aurena da muktar an fasa anyi da Abdul wannn shiya K’ara samun shakku na dad’a shiga damuwa ,saura kwana uku d’aurin aure na domin har yan uwa sun fara zuwa ,nan na kuma birkicewa kullum kuka duk jikina asanyaye na rasa wane so nakewa Abdul na gwada yakice Shi ,Amma soyayyar na manne da ruhina tamkar mayen k’arfe sai na D’an samu rlip sai ta dawo sabo fill, zan iya cewa soyayyar Abdul ta zame mun kamar cuta duk da na gwada cirewa Amma na kasa ,walimar da aka shirya agidan mu da k’yar na jeta duk kyan danayi amma na bata da kwalliya domin kowa cewa yake ,ke tun yanzu ,kin fara kukan barin gidan ,kawai kallon su nake domin kwakwalwata ta tushe, domin a gurin ma inayi Ina share hawaye wallahi Bud’a idanuwa nai tayi ko zan ga Abdul yazo ada abokan sa a matsayin shine angona Amma shiru. Washegari da sassafe na fita, gidan su Abdul naje ban Shiga ciki ba Ina tsaye k’anin sa ya fito nake tambayar sa malam abdul sai yace ai tun shekaranjiya da aka kawo katin d’aurin auren ki makaranta tunda ya dawo gida ya had’a kayansa Washegari yayi sallama da umma yace bazai iya zama wani ya aureki ba Gaskiya kinyi rashin masoyi,yanzu yabar garin nan”,ban tsaya jin mai zai ce ba kawai na koma da Baya haka nake Tafiya salo salo iska sai neman kad’ani take saboda ramar da nayi ,kamar wata zautacciya na Shiga gida ina kuka ,wayata naci Kari da msg din sa yanamin bankwana da nasiha kan nayiwa mijina biyayya, aranar haka nai ta kuka,jinai zuciyata na zafi ban iya fad’a ba amma sanin washe gari za a d’auran aure yasa naita fad’a maganar arzik’i sena hau balai mama tana lura dani sai da ta jawo ni d’aki tai min fad’a da nasiha da k’yar na nutsu har na samu bacci ya kwashe ni. washe gari da k’waarin gwiwa na tashi don nayi mafarki da abdul aka d’aura, haka na shirya Ina sonjin ace anfasa d’aura aure wajen 11 naji marok’a na an d’aura auren Khadija da muktar ,Allah yaso ban fita waje ba Ina surk’uk’in d’akin mama kawai na zube,ban sani ba ko suma nayi ko ba sumaba nide na ganni na farka sai had’a gumi nake, gud’a na jiyo daga waje Ana ga angwaye nan, da sauri na shige toilet ina ta gurshek’en kuka. Shiru Anty khadija tayi ta kalle ni, ganin idon ta ya kawo ruwa yasa naji tausayin ta ya lullub’eni nan nace “lalle Anty khadija Kinsha wahalar so” Anty khadi tace “meemi Ke nan ada na d’auka zan iya cire son Abdul Amma na kasa…sai ma jinai Tana ta k’aruwa kiran sallar la’a sar akayi da sauri na tashi naje nai alwala ,nazo na tada sallah Bayan na idar na kalli Antykhadija nace “bari na tafi gida insha Allahu tomorrow morning zanzo ki bani cigaban saboda Naga yamma tayi ,haka mukai sallam na tafi. to makaranta kubiyo meemi don jin cigaban *QUEEN MEEMI*ASHE HAKA SO YAKE . . 😭ASHE HAKA SO YAKE!😭 💔💔💔💔💔 (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BU QUEEM MEEMI ®NWA PAGE 11 *Queenmeemi.WordPress.com* Haka dai nayi ta gurshek’en kuka ba abinda na lasa a baki na ,sai da mama ta kawo mini tea mai kauri na sha San nan ta bani magani nasha zazzabi ne ya rufeni har wajen 4 kamar daga sama naji ana cewa azo akaini dayake ba a bauchin zai zauna ba Aiki ya maido dashi kano,saboda yawan kukan danai idona yayi ja sosai ana fito dani na fara amai bayan an d’aurayen jikina aka sanjan kaya wajen biyar dai-dai aka mika Ni gidana wanda na mai she Shi taskar ajalina ‘yan kai amarya suka kawo Ni suka watse, sai Ni kad’ai kamar mayya ji nake kamar na shigo wata duniyar duk da dakiyar da aka zuban Amma ko kad’an abin bai burgeni ba saboda nasan bada burina zan zauna ba,kulle d’akin nayi yakai na koma kam gado ina kuka. Bayan kamar Rabin awa sai ga muktar da abokan sa,baiyi gigin cewa angwaye a gaida Ni ba don yanda nakeji zuciya ta kamar ta fashe ,Washegari na tashi na fita muktar ya shigo d’akin ya zauna magana yayi min ko kallo bai ishen ba sai ma kuka da nasa ,ina wayyo ma shiga uku Abdul afusace muktar ya jiyo “ke waye Abdul”? nace “Nima ban sani ba”, bai K’ara magana ba ya fita ya ajen leda,kwata -kwata muktar bai burgeni asalima wani haushin sa nakeji,ganin kukan bazai kai min ba yasa na fita ina zaga gidan duk inda na kallah sai naji dama da Abdul ne, flowers nai ta tsinkewa ina kuka ina Yaushe dream d’ina zai zama true,saida duk na b’ata gun San nan na koma nai wanka ko Kwalliya banyi ba don aganina ba amfani, da rana muktar ya dawo duk ya kaasa gane kaina don dayai mini magana saina nahau kuka. Ni meemi na kalli antykhadija nace “tabdi Lalle wan nan soyayya Gaskiya love ko wahala”Anty khadija tace “ke dai bari wata soyayyar kawai jarrabawa ce daga Allah ” nace “to Allah ya sawwake cigaba” Yau satina biyu wanda ya tafi da abubuwa da dama acikin lamura na ciki kwa harda zuciyana data kasaa mantawa da burinta, hakan ya kasancen tamakar jaraba,wanda ya kasance kullum cikin kuka Yau Dana tashi ina karanta Alqur’ani naji wasai azuciyana shine ya bani damar shiga kitchen har na fara girki kawai na k’yale na dawo na zauna ina had’e rai wayata na d’auka na latso wak’ar da Abdul yayimun ina bi hawaye na zuba ,ganin hakan muktar dayake weekend be baije Aiki ba, ya tashi yazo ya d’aga Ni yace “k’anwata wai meya faru dake”?, sunkwi dakai nayi na cigaba da bin wak’ar,wayar ya karb’a ya latsa inda nake dannawa,nan ya d’ago yace “waye Abdul?” bance mai komai ba ,”msg zaki tura mai?” nan kishi ya murtuke Shi ya dau number d’in yasa awayar sa ,ya shige d’aki, ina zaune tamkar mutum mutumi naji muktar na d’aga murya, jinai yana fad’a da turanci ,tashi nayi na shiga dakin cak ma tsaya , jin yana ambatar sunan Abdul ,dai-dai lokacin ya aje wayar idanuwan sa sunyi jawur gaba nane ya fad’i na suri wayar sa dai -dai lokacin msg ya shigo a wayar na duba naga no din Abdul nai mamamkin yanda akai har ya bugawa Abdul waya ,msg d’in na karanta naga dik na bacin rai ne ,na duba na muktar daya tura mai naga har dasu maganar kai K’ara kotu muktar yace zai kai abdul,kan Abdul ya siye zuciyar matarsa. shima Abdul din bai kasa a gwiwa ba ya fada mai zafa-fa,yana mai cewa tunda aka daura aure bai sake naimana ba ,saboda yasan kimar aure San nan naga yasa har abada bazai manta dani ba kuma,kuka ne na fasa da k’arfi nace “me Abdul yayimah Zakai mai irin wan nan cin zarafi? Amma ka cucen muktar” kan gadon na fad’a ina kuka wiwi da k’arfi naji ya d’ago Ni “meye tsakanin ki dashi ya jijjigani cikin kuka nace “yanzu ya dace ka gayawa wanda nake ganin mutuncin sa irin haka ,wallahi tamakar Ni kayiwa” ya kalleni yace “ki sani da da yanzu ba d’aya bane yanzu kina k’ark’ashina wallahi ki daina domin d’aukan alhaki wallah Idan ba haka ba ,Yau d’in nan zan gayawa baba” zubewa nayi ina bashi hk’r karya fad’a k’arshen gado na zauna naci gaba da kuka ,muktar yace “inbanda D’an iska tantiri,ace kanaiwa matar aure text” Ni kam nazo iya wuya jinake kamar yana cakan k’aya araina nace “Abdul malami ne bazai haka ba karka manta nice nan nayi mai msg kuma baiyi min reply ba,Nima she’d’an ne ya tunzura Ni da so ,amma kayi hakuri,amma asalima kai ka tsokano shi, Kaine ka bugamai waya kaci mai mutunci ,wallahi akan sa zan baka mamaki” sakatoto ya tsaya yana kallona da alama bana cikin hayyacina ,yace “khadija Anya lafiyar ki Lau? yanzu kika ban hak’uri Amma kuma yanzu kinkuma ce zaki ban mamaki, nifa mijinki ne Amma kike fifita wani akaina ,murmushi nayi nace Abdul shine mijina bakai ba saukar Mari naji a kuncina take na sulale kasa asume. shared by MAMAN IHSAN SAKEENATAshe haka so yake . . ASHE HAKA SO YAKE! (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITEEN BY QUEEN MEEMI ®NWA page 12 *Queenmeemi.WordPress.com* Ashid’e na tashi sabili da ruwan da ya zuban na farfad’o kasa tashi nayi shima muktar sunkuyawa yayi ya d’ago Ni ya rungume yana ban hak’uri kuka nacigaba da rairawa sai Dana tsagaita San nan muktar ya tayardani ya zaunar dani a tsakiyar k’afafuwan sa ,yace “k’anwata ki ganamin mai nene yake faruwa “? nan nace mai “ya muktar bakasan waye Abdul ba ,kayi hak’r da irin maganar da zan fad’a wanda direct daga zuciyana suke fitowa wallahi ina son Abdul so mai tsanani wanda bansan irin son Dana ke mai ba wallahi komi yanda muke da mutum ya zagi Abdul agabana sai na tanka ,Abdul yayi rawargani arayuwata dan wallahi shine nakeso kayi “hak’uri nan na zayyano mai duk farkon soyayyarmu da Abdul” ina dasa aya na fashe da kuka,nace muktar dannamun k’irjina haka yayita dannawa bacci ne ya d’auke Ni ,kamar awa biyu na tashi naga muktar sai Aiki yake haka yazo yace ga abinci na dafa miki naci ba sosai ba. bayan na gama “yace khadija zangaya miki daga Yau banso ki K’ara ambatar Abdul agidan nan naji mafarin soyayyar ku kuma na tausaya miki sai dai yanzu kin zama tawa babu dalilin da zai sa kina maganar wani,domin ina so na tsare k’imar aure na Niba lusarin namiji bane ,kuma kema ki hankalta domin kina d’aukarwa kanki zunubi,babu ruwan Allah da son da kikema wani kamaki zai da lefi, ah to Idan kunne yaji jiki ya tsira”. Tashi nayi kawai na je d’akina na kwanta ,gabana na fad’uwa domin nasan duk abinda ya fad’a Gaskiya ne ,take na sa kuka ina istigfari, D’an jim nayi kawai kamar me na fara tunanin abdul ,Dana rife Ido sai naga murmushin Abdul kawai jinake Allah ya kawo abin da zai sa auren nan ya rabu, tashi nayi nayi tagumi nan na shiga jerro hailala,ina adduar Allah ya kawon d’auki, bacci ne ya kwasheni akaro na 2 kiran sallar la asar ne ya tada ni,da murmushi akan fuskana na tashi sakamakon wani mafarki danai da Abdul. bayan kwana 2 haka dai nayi ta fama muktar ya d’au zafi dani ko magana baya yi mini Nikam ko ajikina har kar gabana kawai nake ,ko girki mai Dad’i banayi domin Dana fara sai naga ma b’ata lokaci ne ,saboda aganina gwanda na tanadawa Abdul haka muke zaune ba yabo ba fallasa ,wani wa azi na saurara aradio kan matar datakewa mijinta rashin biyayya irin azabar da ake musu ,nan jikina yayi sanyi nasa kuka lokacin na tashi na d’ora girki bayan dawowar muktar yayi mamaki k’warai kuma yaji Dad’i nan ,haka na Dirk’usa na naimi gafarar sa ya yafen, ganin hakan yasa yaita rawar jiki sai kawai naji zuciyata na kuna da jin haushin sa, sai shigemin yake Ni kuma ina botsarewa don tukuk’in zuciyata ne ya kuma karuwa sai hararar sa nake kamar ba yanzu na bashi hakuri ba Ni kaina ina mamaki tamkar mai aljanu. kwana biyu ganin na fara sakkowa muna ‘yar mutunci dashi ammamfa zuciyata kullum Tana ga Abdul gashi sai muna bacci naita juyi ina kiran sunan abdul,abin na b’atawa muktar rai ,inaa cikin bacci naji ya d’akan duka nan na tashi na ganshi sai huci yake ,yace “akanme agidana zakina kiran wani”? ko kallo bai isheni ba na koma na kwanta fizgoni yayi na tashi na saka kuka nan jikinsa yayi sanyi ya kamoni yanasan yimin kiss nan na koma da baya Nama fice daga d’akin biyoni yayi yace “haba khadija ya zaki hanani kanki ,bayan kinsan inada hak’k’i akanki ajiyar Yau wata daya Amma kink’i amince min”! kuka nasa natashi na kuma fita zuciya ta na tuk’uk’i gani nake imde na bashi kaina kamar na rasa wani shashi nane nace Abdul “kai na tanadawa kaina ,Kaine uban ‘ya’yana jikina na bani zan zamo taka”,nan na d’aga hannu sama ina addua Allah ya kawo abinda zai raba auren mu da muktar duk hanyar Dana duba babu dama,b’angaren muktar kuwa duk ya damu ya rame domin ya rasa yanda zai dani ga kishin Abdul na nuk’urk’usar sa domin kullum bakina cikin furta sunan Abdul yake ko kallo muke sai nace ji wani mai kama da Abdul ,sai dai ya kalleni idon sa yayi jajawur. akwai ranar da muktar yasa mana kallon American film Nikam dama ba ma’abociyar kalla bace ranar ne na zauna inayi, kawai aka hasko wasu nawa junan su kiss nan na runtse Ido ina gano kaina da Abdul lumshe Ido nayi ina murmushi ,haka na kwanta na dafe k’irji donji nayi ko ina na jikina yad’au zuuum muktar na kallona ya kashe tv ya daki tebur ya shige d’aki ya fito ya ficewar sa ,nikam bansan me yake bama, dakyar na mike na fita taskar gida ina kallon tauraro da yake lokacin 8:00 kawai jinai kamar k’aran son Abdul ake ga iska na kad’ani zama nayi na hau kuka domin ji nayi duk na sare, saida nayi mai isata na koma gida haka dai mukai ta rayuwa Yau ta kasance wata 2 ina kwance muktar yace zai mini ta dole nan na hau kuka ina karka cucueni haka ya hak’ura,Ni kaina ina mamakin kaina inda ilimina ya tafi sai wataran nayi Abu kuma zan koma nayi ta kuka ina istigfari. *QUEEN MEEMi shared by maman ihssan sakeeenat ASHE haka so yake . [4:19pm, 11/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITEEN BY QUEEN MEEMI ®NWA PAGE 13 *Queenmeemi.WordPress.com* “Akwai wata mak’ociyata Tana da yaro guda d’aya sun Saba da muktar saboda akwaishi da son yara sunan sa arif,Yau mamansa ta shigo muka gaisa tace ay mai gidan na yawan bashi alawa tazo godia,muna ta hira da ita sai nake ce Mata yaya sunan sa na Gaskiya sai tace abdul ra’uf sunan su sak da nawa Abdul d’in, nan naji ina k’aunar yaron haka nai ta tulo alawowi, tundaga lokacin yake zuwa duk yamma wataran in weekend ne yana shugowa akwai ranar da ya shigo Ina cewa my Abdullah Welcm na ringumeshi nan muktar ya kalleni ,too anya k’anwata abin naki bai zautaki ba arif ne fa,na kalle Shi nace eh,na sani ai sunan sa d’aya da nawa abdul d’in na gaske Shiisa nake sonsa ,Allah sarki Abdullah na take hawaye ya b’alle sai kuka ,nace ya muktar wallahi ko kare ne,ya nuna k’aunar sa ga abdul zan kaunace Shi ko abinci na dunga bashi ,nan muktar ya yi sakatoto yana girmama soyayyar da nakewa Abdul ,nan yayi dogon naziri ya tashi ya d’au Abdul don mik’ashi gidan su. kwana 2 a tsakani muktar ya shirgo uban kaya na k’walama sai washe baki yake ,Nikam ina zaune na rafka tagumi kamar an aiko mini da sakon mutuwa kawai wani tunani na Lula ina tuna wai gai Ni da Abdul muna rayuwa gu d’aya wani murmushi nayi ganin dream d’in nawa yatafi dai-dai,tsaye muktar yayi akaina yana k’aremin kallo tabbas nason yana sona Amma som maso wani yake domin ko ina cike yake taf da dalmar k’aunar Abdul domin ta ruga ta daskare babu wani gu da wani d’a namiji zai samu,wallahi meemi wataran har zama nake taita tunani wai gashi mun rabu da muktar har tununi nayi muktar yayi hatsari ya mutu nayi aure da Abdul ,meemi dakai kalleni a wancen lokacin da sai kin mamakin ramewar danayi Gaskiya so masifa ne. Nan muktar ya tab’ani na d’ago Ido muka had’a Ido nan idona ya kawo ruwa zama yayi ya kamo Ni ya rungume yanabuga bayana, nan na b’arke da kuka ina ya muktar ya zanyi da son Abdul ina tsoron Allah bana son d’aukan zunubi nason inada aure don Allah ka yafen zuciya ta na rasa yanda zanyi nan muktar ya juyoni da salon sa wanda da alama Yau ya samo Shi nan yace sorry wife Nima yanzu na gano yanda kikeji kiyi hak’r Allah shiya tsaramiki hakan bawai don baya sonki ba yak’i baki Abdul ba, Aa sai don nuna ikonsa akanki kuma kinsan matar mutum kabarin sa ,nan ya d’akko min wata leda wan nan sak’o ne inji Abdul yace na kawo miki damm!!kirjina ya bada kida zumbur na mik’e na karb’a na Bud’a alawoyi ne da hisrul Muslim da littafin adduoi ,alawowin n Bud’a na sha nan naji sanyi araina hawaye naji ya kamani har tsikar jikina dake tashi bayan nasha na jiyo na kallo muktar nace “ya ina kasamo”? nan yace “kede anjima zan baki labarin yanda akai,aini yanzu Abdul ya zama abokina Gaskiya yana da kirki” Dad’i ne ya cikan zuciya nan na tashi na tafi kitchen jikina sai rawa yake nan na dawo nace Abdul ,au ya muktar ina dariya nace mai zan dafa ma nan yace Aa nayo take away nan na zauna inaji sai bawa muktar labarin lov nawa da Abdul nake ,idanuwan muktar kam sunyi jawur Amma ya dake don so yake ya sani farin ciki,tare da cimma burin sa. shared by MAMAN IHSANMeemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ®NWA PAGE 14 *Queenmeemi.WordPress.com* muna zauna muna hira don yanzu na D’an sake ,shima muktar bashi da aIki sai bani hirar Abdul ta hakan yake samun kaina ,muna zauna sai yake ce dani kin San wanda akai kuwa har Abdul ya bani sako na baki? Nan nace Aa sai ya gyara zama yace “ai ganin yanda duk ki figice komai Abdul sai kace wanda yayi miki asiri da yanda kika d’imauce akansa, harara na kaiwa muktar yayi dariya ya cigaba,nan yasa kishi ke nuk’urk’usa ta har inajin zan iya komai akanki, nan na da nan na shiga binciken sa har Allah yasa na gano she abokin hudu ne abokina shiya gayan ai ya dawo kano d’in ,nan yayi mini kwatancen nida Abdul ke bussness haka na je afusace domin naje ne komai ta fanjama -sanjan,nan Bayan min gaisa naja Shi gefe mukai magana jin nine mijinki kuma duk akanki ne yasa ya bada himma jikinsa har rawa yake yana tambayar yaya kike har da wai Allah yasa ina Kula dake ,zuciya tazo mun wuya naci kwalar sa nan ya ban hkr yasan shine baiyi daidai ba ,zama nai ina Gaya mai ya rabu dake nan ya kalleni yace “ai tunda kukai aure bai sake ganinki ba ,kawai gangar jikin ku ne ba atare ba Amma ruhin ku na tare yayinda yazo nan Azancen sa ,kawai sai na kaimai naushi har yayi hab’o har mutane sun fara taruwa na tarwatsa su ,sai Nazo ina bashi hak’uri,nan dai mukai maslaha har addua yayi mana wallahi khadija yanayi yana hawaye . kallon sa nayi nace sai hakr yakaMata kanemi wata nan abdul ya hararen yace barni kawai yayinda kai min farauta banganin kowce mace da gashi ,kasani aurenku da khadija yasa kaima naji ina k’aunarka saboda ita don girman Allah ka rike ta amana ina rok’anka ka yafe Mata wajen irin yanayin zamantakewar ku,don nasan tunda kazo ka sameni kan maganar nasan da walakin tabbas babu kyau Amma soyayya halittace domin true luv never end,jikinane yayi sanyi nace na d’auki maganar ka Ngd ,Abdul ya fito da leda ahannu yace ka bani izini zanyi kyauta ga matarka, Jim nayi domin daurewa kawai nakeyi saboda kishi ,nan nace ba damuwa haka ya bani yace na kawo miki wallahi khadija har bakin titi ya rakoni man mota na ya k’are haka yaje nan kusa dasu ya sayo bansani ba ya ban na dura ,tabbas Allah shike had’a soyayya na yarda da soyayyrki da Shi Amma ina mai baki hakr ki jure jarabawar da Allah yayi miki har ki fita lafiya ,domin da wuya wallahi k’anwata da wani namijin ne kike mai hakan kina begen wani wallahi da tuni ya miki kaca-kaca wani ma ya sallameki,Amma Ni babu rabuwa a atsakanin mu arazane na dago kai sai na basar ina kukan zuci,azuciyana ina cewa Dama Ni sallamata kayi d’in Dana more,nan naji kaina yayi dim soyayyr Abdul ta ninku araina ga wani tukuki da alhini da nake ji,duhu na gani kawai . sai bud’e Ido nayi na ganni kan ciyar muktar yana min firfita idonsa da alamar hawaye ,yace khadija wallahi ina matukar k’aunarki ,kiyi hkr k’addarar ki ce haka kuka na cigaba da yi yana rungume dani nan na Lula tunanin maganar da ya gayan akan Abdul ,da sauri na d’ago nace muktar yanzu kuna abokantaka dashi? murmushi yayi ya shafa gefen fuskana ,munayi mana ,ai mun zama abokai nan nace naji Dad’i wallahi sosai na dad’a baka girma haka dai rayuwar take tafiya tiryan-tiryan har na cika wata hud’u agidan aurena wanda har alokacin muktar ban bashi hak’k’in sa ba, wanda yake ta farautaa kullu yaumin,wata k’awatace tazo muna hira sai take kallona khadija naga kin K’ara haske Amma kinrame ko dai mun samu ne ,harara na kaimata nace Allah ya sawwke ai Ni.. sai kuma nai shiru ganin zanyi b’aranb’aramar zance, take na Lula tunanin gashi munyi aure da Abdul har min samu babies sai doka murmushi nake,jinai an d’akan duka firgigit na dawo hayyacina karima tace yada tunani haka nan na wayence,da daddare bayan muktar ya dawo ya kawon wasik’a na bud’e tabbas hand writing d’in Abdul ne nan na hau karantawa nasiha ce fall aciki ko ina sayya sa aya da Hadith ya fassara duk akan bin miji nayi biyayya,ahargitse na d’ago na kalli muktar ,nace ya mai kaje kacewa Abdul? nan yace wallahi “bance komai ba asalima munyi wajen 2 weeks bamuyi waya ba,kawai dai ya bada abaki ne yace shine asalin kaunar da zaina cigaba da nuna miki amatsayinki na matar aure ahanzu ,domin yasan za adinga samun matsala to baisan Allah yayi fushi dake shiisa yana nan daram akan malaminki,wani tsagwaron son sa ne ya kuma taso mini take duk na d’auke nasihun Abdul taf akaina kuma nadau damarar Aiki dasu,domin tsoron Allah ya shigeni sosai. SHARED BY MAMAN IHSAN SAKEENAT❤❤❤ASHE HAKA SO YAKE . [3:14pm, 14/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ®NWA PAGE 15 *LUV U LODI LODI MUTAN NAGARTA* Hakana dage na shiga yiwa muktar biyayya Amma kamar adole nake nasihar Abdul ta shigeni ga kuma adduoin daya rubutomin ,Kullm su nakeyi cikin kwana 2 na samu sa ida zugin ya ragu da radadin,karatu Alkur’ani shine ya Zame min abokin hira ,nan damuwana kashi saba’in ya ragu, Amma natacciyar zuciyata Tana mak’ale da Abdul wallahi meemi scan d’aya bana daina tunanin Abdul,da k’yar da sidin goshi muktar ya Maida Ni cikakkiyar mace aranar nayi kuka na zubda hawaye tabbas Allah shine malikul mulki,lamarin Allah ya wuce musali meemi nayi kokawa da k’addara gashi sai wahala nakesha abanza nan na canja akalar zama na da muktar inamai abinda yakeso Dan tsira rana gobe k’iyama Shi kuma haka yake kyautata mini ,gashi ta gefe suna mutunci da Abdul,kullum nayi sallah sai nayi wa Abdul addua a dukan lamuran sa ,ran nan muna zaune da muktar muna hira sai yake cemuni mai zai sa bazan bawa Abdul k’anwata ko k’awata ba ,damm! naji gabana ya fadi nan kishi wanda bansan ta inda ya fito ba na ji ya shigo ,kuka ne ya fito ,nan nayi sauri na Maida ina istigfari hirar daba a k’arasa ba kenan domin jinai inajin haushin duk yarinyar da Abdul zai aura naji na tsane ta haka na kullo d’aki nayi ta kuka,sai da Abdul yazo ya tambayeni meye nace kaina ke ciwo ban Nuna mai akan maganar da yayi mini ne ba ,sabida nasan baya so,haka ya lallasheni na hak’ura ,haka dai muke zaune cike da kulawa ta bangaren muktar inda yamai dani yar lele Sam baya San b’acin raina ,kome nakeso Shi yake mini,amma azuciyana sai aslow zance domin nikaina nasan bazan daina son Abdul ba gashi kullum sai nayi mafarkin sa. ina cikin wata na takwas da aure kwatsam Allah ya bani ciki aranar k’aramin suma nayi, kawai gani nake naci amanar Abdul domin nida k’anwar sa muna waya tunda dama k’awata ce haka nai sakin baki na Gaya Mata ina da ciki ,Ni nama manta munyi maganar sai gashi sati d’aya tayi min waya Tana cewa ai kinga Dana Sanar wa da ya Abdul cikin ki dirircewa yayi ya kasa magana wallahi sis hawaye na gani a idon sa nan yace min Allah ya saukeki lfiy ,zai tayaki da addua. ,kunya ce naji ta lullube Ni, na fara hawaye nace “Amma kin cucueni mai sa zaki fad’a bayan kawai ke na gayawa yanzu ya kike so Abdul ya d’aukeni na shiga uku ,nan tasa dariya to meye ai sunna ne kuma Abdul me ilmi ne kinsan ba wanda zai ganki ya kyale to Shi meye nasa aciki ,aranar a suk’uk’u na yini ina ganin kamar naci amanar Abdul ,dariya Anty khadija tayi tace meemi Idan ina Waini abin kamar wadda Banda tunani in Banda abina meye na cin amana ,nan nayi dariya nace “so kenan,Anty khdija cigaba da bani muyi mu gama saboda naga mama nayi min flash” ,dariya Anty khadija tayi tace Okey ruwa ta kurb’a San nan ta ciga haka nai ta rai nan cikin nan muktar duk Shi ke aikin gidan nan, komai ga amai da nakeyi kullum har cikin dare haka muktar zai tashi ya gyara gurun ya gyarani,komai dai shike mini gashi duk abinda nakeso Shi ke mini kyautatawa dai ta gidan duniya na shata agun muktar karkiso kiga yanda nayi kyau baba da mama sai son barka suke, hankalina ya kwanta Amma duk wan.nan bidirin wallahi Abdul na manne araina. *QUEEN MEEMI* shared by maman ihsan[3:36pm, 14/12/2016] Meemiluv: ASHE HAKA SO YAKE (BASE IN TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ®NWA PAGE 16 *GODIA AGAREKU MASOYA WAN NAN LITTAFI QUEEN NA SONKU * Mama har cemin take ja ira da kika ce ba kyasso Amma ko jibar ki ina Wani rashin so a gareki,?nan nayi murmushi mama ai farin cikinku shine nawa haka tayi ta Shi mini albarka inajin dad’in albarkar da iyayena ke sakamin innaje shike K’ara samun na zauna da muktar ,Amma himm soyayya tana ga Abdul ana cikin hakan watanni suka ja na sauka lafiya na samu baby boy nasha kuka ,meemi saboda tabbas haihuwar ta sanyayamini gwiwa wallahi k’addara ta Riga fata ranar suna muktar yasawa yaron Abdullah ,naji Dad’i sosai nan naji muktar na K’ara girmamashi,Amma fa duk da hakan gani nake wataran zan koma ga Abdul ,sati biyu Abdul yazo ganin takwaransa yana zaune a sitting room ya k’urawa boy Ido yana zuba mai addua kana ganin idanuwan sa kasan daurewa yake kaya ne jibge ya kawo Nikam ina d’aki ina matsar hawaye ,kamar Mara hankali nafara magana yanzu shikenan na rasa Abdul tunda na haihu da muktar haka muktar yazo ya samen, Allah yaso tsohuwar dake Kula dani bata d’akin kuka nasaka sosai ,chaii naji muktar na bani haushi ,magana yake mini nace wallahi ka cucueni Ni ka rabu dani bacci nakeji, jiki a sanyayae ya fita na kullo d’akin ina kuka aranar sai da aka danganani da asibiti saboda zazzabi da damuwa likita yace na rage damuwa yayi min fad’a ,haka muka dawo ina ta kuka ko yaron ban d’auka ba sai da Washegari muktar yace zai gayawa mama, San nan na hak’ura haka dai rayuwa taci gaba da tafiya har nayi arbaa’ina alokacin k’anwar Abdul tazo take gayan ai umman su ta takura sai abdul yayi aure jin hakan yasa naji gabana ya fad’i damm! na nafara in ina idona yayi ja to wace zai aura? nan k’anwar sa tace tab! ai ya Abdul taurin kai gareshi wallahi yace baya son kowa ,ke haka yace bazai aure bama tunda ya rasaki,kuka ne naji ya kubcen nace yanzu maryam mu haka Tamu salon soyayyr yazo zuciyoyin mu ahad’e Amma gangar jiki a ware” ,harara maryam ta bani tace badai kyau takamata yanzu dake dashi kuyi tawakkali saboda dama Allahu bai haliitta zaman ku tare ba ,kuka sosai nayi tayi har kaina ya fara ciwo maryam ma lallashina na hak’ura. Akawai wata rana nida muktar munje hospital kai Abdul asibiti yana mura,lokacin Abdul yakai umma shima nan muka had’u wallahi gabana fad’uwa yayi tun bayan aurena se yau na kuma ganin Abdul nan da nan na rasa nutsuwa ta haka shima ya fice da sauri kamar zai fad’i Nikam dak’yar nakai kaina kan kujera muna gaisawa da umma,nan umma tayi min nasiha tace. “Rabon wan nan yaron ne ,shiisa kukai ta wahala kai Allah shine sarki sanin gaibu sai Allah ,tabbas Allah shine mai saka so ,na d’auki darasi a rayuwarku keda Abdul domin bawanda bai tsammanin auren ku ba, ubangiji ya Baku zama lafiya da mijinki,aranar ma agida haka na yini asalub’e muktr har ya Saba da yanayina na rashin magana Dana koya.domin tun bayan haihuwata na dad’a yarda na rasa Abdul shine yasa na koyi shiru,soyayyr D’ana kuwa sosai nake mai gashi yaci suna me dadi,haka dai rayuwa tayi ta tafiya Dad’i ba Dadi haka naita fama da so wanda na kirashi cuta asaka har nayi shekara uku da aure wanda acikin hakan na kuma haihuwar baby gal siyama, San nan ga ciwon damuwa danake fama dashi wanda duk dalilin so d’inne. shekara uku da aurena ummun Abdul ta nuna fushin ta akan Abdul bashiri ta samo mai matar aure Sam baya son matar Amma ba yanda zaiyi haka akai auren shekarar matar daya ta haifi baby gal,take ya saka Mata sunana khadija naji Dad’i sosai alokacin Nima na kuma haihuwa ta uku na samu boy,da kyar da sid’un goshi nake Kula matar Abdul don haushin ta nake ji ,bayanda na iya muke mutunci da ita kuma ganin yanda take Kula da Abdul yasa na sake da ita,Amma meemi kin San wani Abu kuwa wallahi bazan k’arya ba duk kwanan duniya dad’a San Abdul nake kawai na bar abin araina ne, ban san abinda Allah ya b’oye ba ,nan taja numfashi ta tsaya Tare da d’agowa ta kalleni ,tace bari na barki haka meemi ,nan nayi murmushi nace tabbas antykhady kinga soyayya tabbas kyace ASHE HAKA SO YAKE! ,yama fi ga haka sai dai maganinsa hak’uri Gaskiya Anty khadi nayi jimamin labarin ki soyayya ta Gaskiya wadda ba algus tabbas Allah shine sarki mai kashewa da rayawa mai sa so ga wanda yaso alokacin da yaso,tabbas wan nan jarabawace Daga Allah ya jarrabeku yaga imaninku ,Kunyi soyayya Amma duk agareku ba alheri ne ga junan ku ba ke muktar shine alheri gareki ,haka Abdul matar sa itace alheri agareshi domin Allah shine masanin dai-dai,sai dai Allah ya Baku fad’an soyayyr Gaskiya da kukai wa junanku,domin ba zata tafi abanza ba ta Gaskiyace . shared by Maman IHSANN ASHE HAKA SO YAKE . ASHE HAKA SO YAKE (BASE ON TRUE LIFE STORY) WRITTEN BY QUEEN MEEMI ®NWA PAGE 17 *END* Anty khadija tayi murmushi tace tabbas meemi kinyi magana mai ratsa jiki naji dadin kasancewa dake,inaso meemi kiban shawara nan na gyara zama nace Anty khadi babu wata soyayya yanzu daya kamata kiyi irin soyayyar Allah da manzon sa ,wan nna soyayya da kika gursa keda Abdul to ki Maida ta ga annabi ,yazamo shi kikewa irin wan nan soyayyr ,to wallahi kin gama dacewa domin son manzon Allah shine soyayya Mara yankewa zaki samu shiga gun Allah da manzon sa duniya da lahira,yanzu duk fadin duniya nan babu wanda zaki mai irin soyayyr nan sai manzon Allah S.W.A a domin shiya cancanta,kuma ba a had’a soyayyr sa da wani, salati agareshi da bin abinda yayi hani da wanda ya umarta shine,kanki fita hayyacin ki aka soyayya face soyayya Allah da manzon sa. Anty khadi da hawaye ya kwaranyo mata tace tabbas maganar ki itace dai-dai Allah yayi mana mai kyau nace Amin.nan Anty khadi ta kuma kallona tace meemi San nan kinsan me wallahi jiya sai da nayi mafarki gani nida Abdul muna zaune muna hira awani guri munata dariya tunda na tashi nakejin sabuwar soyayyar sa ,inaa so ki fad’awa makaranta su tayani da addua domin shine mak’sudin ma dayasa na bada labarina saboda nasamu wasu su tayani da addua domin kullum abin sabo fill yake dawo min nasan zasu ce son zuciya yasa Aa kullum cikin adduar Allah ya ciremin nake yasamun soyayyr mijina, wallah nikaina narasa yanda nazan nan ta sunkuya tana kuka ,tashi nayi na dafa ta nace Anty kiyi hkr komai Daga Allahne tayiwu wan nan itace jarrabawar da Allah ya saka miki ,kiyi k’ok’ari ki cinyeta, kiyi amfani da shawarar da na baki,ki yawaita salati da istigfari da karatun Alkur ani duk da nasan kinayi,Amma ki dage da kinji abin ya bijiro miki ki hau tasbihi insha Allahu komai zai zama tarihi, rungume Ni Anty khadi tayi tana min gidiya tace meemi nagode da kika bani lokacinki tabbas marubuta muna godia nagode nan nayi murmushi nace bakomi Allah Nima nagode haka na tashi nayi sallar azahar ina idarwa Kiran mama na kuma shigowa nan na mik’e nayiwa Anty khadi sallama ta rikeni ta mik’on leda, nace tabdi wallahi bazan karb’a ba dariya tasa tace kin ma isa ,Ni fa yanzu kina matsayin k’anwata, Amma na baki Abu kice bazaki karb’a ba ,fita nayi ya biyoni tace inma baki karb’a ba zan bayar a kawo miki nace Nikam banaso Dan kawai na rubuta labarinki sai kin ban wani abun ,Nikam nayi don Allah da annabi ne ,fita nayi muka d’agowa Juna hannu *tammat bihamdillah*makaranta anan na kawo wan nan tak’aitaccen labarin wanda ya kasance Gaskiya ne ya kuma kunshi darussa da dama da fatan darussan dake cike kun d’auke Shi San nan Antykadija na barar adduar ku Nima meemi nace ku tayata da addua fans D’ina basai na kumai muku sharhi akan wan nan book ba domin ku da kanki nasan kun fahimci abinda sak’on ya aika.Amadadin Ni *QUEEN MEEMI* Dana kawo muku wan nan labarin nakecewa sai kun sake jina Idan maikowa mai komai ya kaimu *NEW YEAR*INSHALLAHU zakuyi tozali da new one mai suna…..sai de kunjini luv u ol *QUEEN MEEMI* shared by maman ihsan🙌 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *