Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 2 March 2017

ALJANA CE KO MUTUM COMPLETE

adsense here [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *ko* πŸ’ 🎭 *MUTUM* 🎭 πŸ’ *BY* *Nusnim* πŸ’ *Assalamu* *Alaikum* *ya ayyuhal* *Muslim in*, *ina* *mika* *sakon* *gaisuwata* *ga* *dukkan* *yan* *uwana* *musulmai*, *dafatan* *zaku* *kasance* *dani* *acikin* *sabon* *novel* *dina* *mai* *suna* *ALJANA* *KO* *MUTUM*, *Wanda* *nida* *kaina* *nakin* *kira* *labarin* _Allah_ _yabani_ _ikon_ _Isar_ _da_ _sakon_ _dake_ _ciki_. 1⃣ &5⃣ kwance yake saman makeken katifarsa dataji lallausar zanin gado' sai juyi yake ya kasa bacci, tunani yake ina zai sake ganinta? ina zai sake tozali da wannan kyakkyawar fuskar dake hana zuciyarsa sukuni dare da rana? wani irin haske yaziyarci idanuwansa, wanda yayi sanadiyyar saurin runtse idanun don hasken yayi yawa, jiyayi ance bude idanunka mosoyina, gani nazo gareka don insanyaya maka zuciya tareda sanyata nishadi" saurin bude idanunsa yayi sukayi ido hudu da kyakkyawar fuskarta, yayi saurin tashi zaune cikeda jindad'in ganinta' don Allah kada kisake tafiya kibarni, ina matukar sonki, inason kasancewa tare dake' inason mukasance a inuwa guda (aure) tace" kayi hakuri mosoyina inasonka, amman banajin zamu iyayin aure yanxu kusa' saboda wasu dalilai' na farko baka sanni ba' baka san koni wacece ba, akwai babban hatsarin dake tattare da arayuwata' banason wani mummunar abu yafaru da rayuwarka' hawaye yaji ya siraro a idanunsa, ya dafe saitin zuciyarsa dake baraxanar faso kirjinsa sbd tsabar sonta dayakeji' wani irin had'arine? wani irin had'arine arayuwarki dazai hana mana mana kasancewa da juna? jiyayi ance cikin tsawa ina ruwanka da rayuwarta, inaso kafita hanyar wannan yarinya' inba haka ba rayuwarka zata salwanta, ke kuma yau saikin d'and'ani azaban da baki taba sha ba arayuwarki, ba an hanaki zuwa wajan wannan mutumin ba? afusace matar ta fizgo hannunta 6at suka 6ace' wani irin zazzafan hawaye ya gangaro a kuncinsa" meyasa zuciyata zatamin haka? meyasa zata fad'a soyayya da wacce ba jinsinmu guda ba? meyasa zataso wacce ba mutum ba, ohh Allah" hannunsa ya d'aga sama yana cewa ya Allah ka kawo min agaji arayuwata' kacire min son abunda bazai ta6a yiwwa ba. tashi yayi yaje ya dauro alwala don gabatar da sallan raka'atanin fijir, kasan cewar ansoma kiraye2n sallah farko. bayan ya dawo daga masallaci ya dauko book da kanwarsa ta kawo masa jiya daddare don yayi mata assignment, yana gamawa ya kwanta bacci har 9am na safe *NAWWAR* bai tashiba. mami hafsat ce zaune a parlo tana breakfast, yar autar tace tashigo me suna *mimi* zama tayi kusada maminta tareda gaisheta" mami hafsa tace autana har kin tashi baccin? eh mami nah natashi, gashi duk jikina ciwo yake min wlhy, ayya sannu ga abincinki can keda yayanki idan kikaci sai kisha magani" yau naga shima bai fito da wuri ba, ko lafiya?jeki ki duboshi, to mami, ta tashi ta nufi hanyar dakin shi, abakin kofa sukaci karo. TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *nusnim*πŸ’ *phyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA*🎭 πŸ’ *CE* *ko*πŸ’ 🎭 *MUTUM*🎭 πŸ’ *BY* *Nusnim*πŸ’ 5⃣&1⃣0⃣ Abakin kofa suka ci karo shima yafito cikin shiri, yace a'a autar mami ya akayi? lafiya lau hamma nah, mami ce tace inxo in dubaka, yau baka tashi da wuri ba? eh wallahi assingment din kine ya hanamin bacci da wuri, saboda wannan *nahawun* yad'an bani wahala, kai hamma" kai da ka haddace nahawul wadi shine zai baka wahala? nikam ban yarda ba? dariya yayi yace autar mu baki da dama. suka karasa wajen *mami hafsah* duk suka zauna kusa da ita, *Nawwar* yagaisar da maminsa cikin girmamawa, ta amsa tare da cewa nawwar yau lafiya baka tashi da wuri ba? ko bakajin dadin jikin ne? a'a mami lafiyata kalau. kawai assignment din wannan autar naki ce ya hanani bacci da wuri, mami tace dafatan dai kagama mata? eh nagama, cikin murna mimi tace yauwa hamma nah nagode sosai, kace yau ni zanyi ta d'aya a ajinmu, murmushi yayi yace aah nibance ba" kika sani ma koban rbt dai2 ba? fuska ta yamutsa cikin shagwa6a tace mami kina jinsa koh? wlhy kabari aka sakamin ziro saina gayama abba, dan nasan ka iya nahawu sosai' idan naci xiro nasan kana sane kamin' kuma mami kicema hamma yadaina min fatar cin zero' ta karashe mgnr tana turo baki" dariya sukayi gaba d'aya mami tace rabudashi autana jeki kawo muku breakfast kuyi kuci kutafi lkc na wucewa, to" mami ta gyara zamanta da kyau ta kalli Nawwar tace kaima yakamata ace zuwa yanxu kafitar da matar aure, tun kafin baban ku yaza6o maka matar da bakaso, tunda ya dade yana baka lkc. wani irin faduwa gabanshi yayi, sai gumi yasoma hadawa a goshinsa' yayin da zuciyarshi ke har bawa, saboda tuno abar sonshi, shiru yayi"mami sai magana take amma kamar hankalinshi bai jikin shi, data gama maganar ne tayi shiru ta zuba masa ido, shi bai ma san tayi shirun ba. hankalin shi gaba daya ya tafiga tuno masoyiyarsa' kafad'arsa mami hafsa ta dafa , yayi saurin sauke ajiyar zuciya, ya dago kai ya kalleta, idanunshi har sun kada sunyi launin "JA" , mami hafsa duk ta tsorata da ganin yadda yanayinshi ya sauya cikin dan lkc, cikin damuwa tace lafiya *nawwar*? daga maganar aure har yanayinka yacanza, shin bakada lafiya ne ko aurenne baka so? ajiyar zuciya ya sauke tare da karnto addu'ar nutsuwa, a hankali ya riko hannun mami dake kan kafad'arsa' yace wlhy mami nikam tsinci kaina a cikin tashin hankali da damuwa aduk lokacin da akamin maganar aure, sai inji zuciyata tana suya, cikin raunanniyar murya yace mami nah please kitayani da addu'a babu wacce tafi cancanta na fadama damuwata sama dake, akwai wacce nake matukar so tana yawan zuwa min a mafarki da zahiri sai dai kuma ba mutum bace, mami tazaro ido waje, yace wallahi mami ina tsananin sonta jinake bazan iya rayuwa babu ita ba. dayar hannunsa yasa ya goge hawayen daya gangaro a idanunshi, sosai mami ta tausaya ma danta, itama tuni hawaye yaciko a idanunta' tace wannan wace irin masiface? ina nata6ajin anyi syy tsakanin *aljana* da *mutum* ta jinjina kanta tace Allah mai iko. *nawwar* kaci gaba da addu'a insha Allahu nima zantayaka dayin addu'an Allah ubangiji yacire maka son abunda bazaiyu arayuwarka ba, amma gaskiya naji tsoro, ba jinsin mu daya ba, meyasa zasu Shiga rayuwar d'ana? meyasa ita wannan aljanar tazabi tayi soyayya da kai alhalin tasan kai ba jinsin su bane? gsky bata kyauta mana ba, insha Allahu addu'ah itace magani, kaima nasan kayi sakaci da addu'ar ne shiyasa' mimi da ta dade da kawo musu breakfast tazauna tanajin abinda mami da hammanta suke tattaunawa,itama ta tausaya masa kuma taji mamakin al'amarin, tace *hamma* nah kamar yadda mami tace maka addu'a itace magani, toh ita zaka dingayi nima zantayaka kaji hamma nawwar, murmushi yayi yace nagode autar mami. yaji dadin yadda mahaifiyarsa da kanwarsa suka fahimceshi tareda kwantar masa da hankali, da kuma nuna masa muhimmancin addu'a" nan sukayi breakfast dinsu, bayan sun gama mimi tayi saurin saka kayan islamiyarta don nawwar ya sauketa a makarantarsu, tare suka fito farfajiyar gdan mami hafsa tarako su tana daga masu hannu har suka fita gidan. TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *nusnim*πŸ’ *phyar*πŸ’‹ πŸ’ *EID* *KUM* *MUBARAK*πŸ’ *TAQABBALALLAHU MINNA WAMINKUM* [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ 🎭 *MUTUM* 🎭 πŸ’ *BY* *Nusnim*πŸ’ 1⃣0⃣&1⃣5⃣ nawwar ya ijye Mimi a islamiya" shi kuma Yakama hanyar zuwa hospital dinshi, yana tafe yana tunanin maganar da sukayi da Mami, yana cikin tunani wani abu ya diro mishi kan motar shi, yayi saurin J'an burki" tare da kifa kanshi kan sitiyarin motan yana maida numfashi, dago kan dazaiyi " yayi ido hudu da wannan matar da dauke mashi abar sonshi lokacin data zo mai, yayi saurin zabura tare da karanto *innalillahi* *wa'inna* *ilaihiraji'un*, da sauri ya rufe glass din motarsa" gani yake kamar zata shigo. itako tana tsaye tana kallon abunda yake yi, tasaki wani irin gitattaccen dariya, tare da nunasa da dan yasa" cikin babban murya, tace *Nawwar* nazo maka gargadi ne kafita Daga rayuwar *sameeratun* *nawwara* idan kuma ba haka ba , kai da'ita zaku fuskanci" mummunan tashin hankali arayuwar Ku, don baza mu kyale kowani bil adama ba yashiga cikin rayuwar mu. yanxu haka *sameeratun* *nawwara* tana can tana fuskantar mummunar hukunci, saboda tasaba mawa dokar mu, *nawwar* yayi saurin cewa don Allah Ku kyaleta karku" mata komai, ta daka mashi tsawa tare da cewa, kai har ka isa kafada mana abunda zamuyi, ina kara gargadin ka" akaro na biyu, Daga fita Daga cikin rayuwar da bata shafe ka ba, Idan kunne yaji Gangar jiki yatsira. zai yi magana kenan wuf ta bace mai, ya sauke ajiyar zuciya tare da hawaye mai radadi dake gangaro mai, zuciyarshi sai har bawa take kamar zata fito, sboda tsananin zafin dayake mai. jikinshi duk ya mutum kamar Wanda akamai duka, dakyar ya iya Jan mortar sa zuwa hospital" lokacin dayayi parking din mortar sa alokacin abokinsa shima yayi parking din nasa" nawwar ya bude mortar zai fito yakasa ganin halin dayake ne yasa abokinshi me suna awwal" ya karaso wajan da Sauri cikin kidimewa, yana fadin nawwara lafiya naganka haka? meke damunka? cikin karfin hali nawwar ke nuna mawa awwal zuciyar alamun ita ke mai zafi, amma yakasa magana" awwal ne ya taimaka mashi suka karasa cikin hospital din. dayake shi doctor be a fannin zuciya, ya kwantar dashi kan gadon sake office dinsa ya dubasa da kyau, tare dayi mashi allura da bashi magani" har bacci yayi awon gaba dashi" awwal ya zauna shiru yana tunanin wani irin damuwa ne abokinshi yake ciki" da har ciwon zuciya takamashi, Allah sarki nawwar, Allah ya yaye maka koma menene. *************** tun lokacin da sameeratun nawwara tabar gun nawwara ake gallaza mata azaba aduniyar su ta aljanu" don ta taka dokan da aka mata, daure take jikin wani bishiya ta tsafi duk kaca ne jikinta, yayin da wasu irin halittu ke jibgarta da bulalan wuta, tana ihu saboda tsananin azaban zafi. gefe daya kuma wani mutum ne azaune cikin kayataccen kijera ta alfarma irinta sarauta da alamu shine shugaba" sai dariyan keta yakeyi, irinta ta mugaye. yana kallon yadda ake wahalar da sameeratun nawwara, saida da ya bari tasha wahala sosai har bata motsi sannan yace adakata" ya karaso wajanta dai dai fuskarta yasa hannunshi yadago fuskarta, yace haryanxu, kina cikin bakanki na kin" aure na, tayi karfin hali tace eh, bazan aureka ba, ba zan aureka ba, koda zan rasa raina ne , kamar yadda " kuka rabani da farin cikin to kuma har abada bazaku taba samun naku farin cikin ba, don nawwar shine mijina, na har abada, *Ambar* yayi saurin ja da baya yana cewa, cewa karyanki ne kija dani sameeratun nawwara, sai kinzama tawa, banga wani bil adaman daya isa yashiga gonata ba , mahaifinki shi yaja miki sameeratun nawwara" ni nan *ambar* sai na mallake ki, duk cikin tsawa yake maganar nan, kuma sai naga bayan wannan nawwar din, tanaji ya ambato nawwar dinta , itama cikin Daga murya tace karya kake ambar , indai INA da sauran numfashi baka Isa ka halaka nawwar ba, don yafi karfinka" ji tayi an wurgo mata wani katon dutse dai dai saitin bakinta" har Saida hakorarta yafadi, ta dafe gun tare da juyowa" taga wanene , ido hudu sukayi da kanwar ambar, me suna *kiyara* tana dariyar mugunta. cikin tsawa tace baki da hankali kike fada mawa shugaban mu magana " saina koya miki darasi, cikin iska tazo da gudu zata shake" wuyan sameratun nawwara, sai taji ansha ke nata wuyan, bataganin Wanda, yashake ta" saboda wani irin guguwar iska ce" ke tashi, *kiyar* da *ambar* sunshiga rudu saka makon ganin wannan halittar, cikin yaransu wannan halittar take cewa " duk da na mutu baza kubarni na huta ba, sai kun binci koni. TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *nusnim*πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA*🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ πŸ™πŸ» *MUTUM*πŸ™πŸ» 1⃣5⃣&2⃣0⃣ duk dana mutu ma bazaKu barni na huta ba? sai kun bincikoni kun hanamin kwanciya cikin natsuwa?, bakin kiyara yafara rawa, cikin rawar murya tace kiyi hakuri sameeratun nawwara bamu san kina tare da itaba, ambar shima yashiga bata hakuri, cikin daga murya tace" ya isheku haka, meyasa zaku takura ma rayuwar ta? kun manta abunda nace kafin na mutu" kenan baku rike amanar dana barmuku ba? ambar yace a'a ba haka bane, toh inba haka ba meyasa zaku takura rayuwarta? kiyara tace Allah yaja zamanin gimbiya sameearatu, ta taka dokan da aka kafa mata ne shiyasa, soyayya taje tanayi da jinsin bil adama, wanda hakan kinsan yasabawa dokan da aka gindaya mata" gimbiya sameeratu tayi saurin zabura cikin kakkauran murya tace soyayya da bil adama, me kukeyi har tafara soyayya da bil adama? tuntuni kuka kasa daukar wani mataki da wuri sai yanxu?, duk cikin fushi da d'aga murya take maganar, nan take ran gimbiya sameeratu ya kara mugun baci, babu abinda ta tsana arayuwarta irin bil adama, saboda su sukayi ajalinta tabar duniyar su. *sai agaba zamuji wacece gimbiya sameeratu, kuma menene alakarta da sameeratul nawwara* ambar ne yayi saurin cewa kiyara janyo wancan kahon ki busa ma gimbiya sameeratu" da saurinta ta aikata abunda yace mata, tana busa kahon nan take gimbiya sameeratu tasaki wani irin hargitsatstsan kara mai karfi tare da zuwan guguwa mai karfi, har sai da su ambar suka rike bishiyar dake kusa dasu sbd karfin guguwar zata iya tafiya dasu, zuwa can wajan yayi tsit kamar ba abunda yafaru, ambar ne ya taimakama kiyara data fad'i kasa ta mike. dube duben sameeratun nawwara suka somayi, can suka ganota kwance gindin bishiya, suka karasa wajan, kiyara tayi tsafin su suka bace daga wajan. haka sameeratun nawwara taci gaba da rayuwar kunci da wahala akan nawwar dinta, duk sanda ta zauna babu abinda take sai tunanin rayuwarta tada mai dadi cikin kwanciyar hankali da y'an uwanta, hawayen fuskarta take gogewa tace kai kajamin wannan rayuwar bakin ciki da tashin hankali ayanzu babana" kaine silar komai ga rayuwata" gashi duk cikin yan uwanta aljanu ita kadai ce musulma, amma sam bata iya ibadan taba, gashi tanason bautama ubangijinta, sai dai bata san yadda zatayi ba, dalilinda yasa take matukar son hamma nawwar kenan. *mafarin haduwar tada hamma nawwar shine*, tashigo duniyar bil adama zagayawa, yakasance ranar sallar su ta EDI can ta hango wani kyakkyawar matashin saurayi yana sallah acikin natsuwa da kwanciyar hankali, bayan ya idar da sallah, taga ya daga hannayenshi sama yana kwararo kirari ga ubangijinsa" sannan yasoma rokan Allah bukatocinsa na alkhairi, ya kuma kareshi daga mugun abu. duk tana tsaye tana kallonshi yana addu'oi, ya matukar bata sha'awa' tafara tunanin kamar itama ada ta taba irin wannan addu'an, amma kuma meyasa yanxu bata iya ba" wani bangare na zuciyarta yace wani boyayyan sirri ne tattare da rayuwarki, wanda amayar da wannan sirrin bakaramin haddasa bala'i zaiyiba tsakanin bil adama da jinsin aljanu, birne wannan sirrin acikin kokonta zaifi zaman lafiya ga mutane dubu" taja wani dogon numfashi tare da karkata hankalinta gun nawwar daya gama addu'oin shi yakama hanyar gida. haka tayi ta bibiyar rayuwar nawwar da yadda yake tafiyar da ibadunshi, anan take son nawwar yasoma mamaye duka sassan jikinta, taji bazata iya rayuwa batare dashi ba" tun daga lokacin zuwa duniyar bil adama yazame ma sameeratun nawwara wajan zuwa,,tun tana zuwa ma nawwar amafarki, har takai da zuwa mai azahiri, anan ne shima yasoma kamuwa da son sameeratun nawwara, yakasa tantan cewan *Aljana ce ko mutum?* kuma taki bashi dama yamata tambayoyin dazasu gamsar dashi, taki gaya masa wacece ita, yana cikin tsaka mai wuya. *wannan shine mafarin kulluwar soyayyar su* *******************bayan nawwar yatashi daga bacci awwal yasa aka kawo mishi abinci yaci" sannan yabashi magani yasha, Dr awwal ya gyara zama da kyau ya kalli nawwar, wanda haryanxu tun tashinsa baiyi magana ba. Dr awwal yace nawwar meke damunka halan? jin yayi shuru bai amsa masa ba, yakuma cewa wani irin damuwa kasama ranka haka? wanda ke barazana da lfyr ka, duk irin amintar dake tsakaninmu ka kasa fada min matsalarka?, kana wasa da lafiyarka nawwar, gashi ciwon zuciya na kokarin kama ka, what" sai a sannan yayi mgn, ciwon zuciya fa kace doctor, kai ya d'aga masa alamar tabbatarwa, mekasa aranka haka? me kanema karasa, me kakeso wanda baka samu ba? kana so ka kashe kanka ne, kar ka manta kaifa likita ne, mai kare lafiyar al'umma, to meyasa kai kake wasa da taka lafiyar? hawayenda awwal yagani a idanun nawwar shiyasa shi saurarawa ga tambayoyinda yake jero masa, jikinsa yayi sanyi, duk yabi ya rude, yasan ba karamin abu zaiza jarumin abokinsa kuka ba" haba nawwar meye damuwarka? kafada min ko zan iya taimaka maka," nawwar ya kalli auwal, yace duk akan *SO* ne awwaal,,Allah ya jarrabi zuciyata dason *AlJANA* bama *MUTUM* ba, a tsorace Dr awwal ya mike tsaye da sauri, yana yima nawwar kallon wanda yayi gamo, yace anya nawwar kana cikin hankalin ka kuwa, kataba ganin Inda akayi soyayya tsakanin aljana da mutum , wlh nawwar kayi gamo, kana bukatar rukiyyar gaggawa, idan ma mafarki kakeyi,kara ka farka, wannan abu ne da bazai taba yuwa ba" kafin nawwar yabashi amsa sai ji sukayi ance , karya kakeyi awwal sai na auri nawwar koda zan rasa raina ne wlhy saina aureshi, ae tuni awwal ya kwasa a guje sai bayan kofa yana salati jikinsa na karkarwa" *EDITED* *BY* *UMMEE* *ADNAN* _TAKU UMMU RUMAN_ πŸ’ *nusnim*πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ πŸ™πŸ» *MUTUM* πŸ™πŸ» 2⃣0⃣&2⃣5⃣ taci gaba da cewa awwal karka shiga hurumin da ba naka ba, kar kasa nawwar ya gujeni, zuciyata bazata iya jurar rashin saba" awwal ina matukar son nawwar" idan ban sameshi ba banajin zan cigaba da numfashi a duniya!! shi dai nawwar yananan akan kujera ya zuba maa sameeratun nawwara ido, cikin wani irin matsanancin sonta" dakuma jindad'in ganinta aransa' tabbacin yanxu andaina azabtar da ita kenan, kamar yadda matar nan tafad'a masa" awwal da har yanxu yananan a bayan kofa' ji yake kamar kasa ya bude yanitse aciki, saboda tsabagen tsoro' tuni ya rufe idanunshi, cikin dauriya yake cewa baiwar Allah kiyi hakuri baso nake nashiga rayuwarki ba, ina so ne inceto amini na daga hadarin daya shiga" sbd zuciyar shi tana dab da bugawa" wanda hakan zai iya rasa ranshi ako wani lokaci ta dalilin sonki" nawwar ya runtse idanunshi, ya juya da kallonshi wajan awwal, yace aboki na taho ka zauna baza ta maka komai ba!!! saneeratun nawwara tayi dan murmushi, tace awwal kenan, ni ba muguwa bace kuma banida niyyar cutar da mutane, kasaki jiki dani, kutaimaka ma rayuwata kai da nawwar. sai alokacin nawwar yafara magana yace baiwar Allah me na mikine kike wahalar da rayuwata? kin hana min sukuni"" sonki yana azalzalan zuciyata, ban taba zama nayi second guda ba tare da tunaninki ba, sannan kuma ban san ke wacece ba? ban san ke wace jinsi bace? shin ke ALJANA ce ko MUTUM? meyasa kuma kika zabe ni amatsayin nazama abokin rayuwanki? dan Allah don son annabi ki amsa min tambayoyi na, shima awwal dake mak'e haryanxu a bayan kofa yace kitaimaki abokina please. Ta numfasa tace duk naji bayaninku, tabbas baku san koni wacece ba' hakazalika nima bansan nid'in wacece ba" illa abunda nasani shine!!! sunana sameeratun nawwara, nakasan ce aduniyar aljanu' nataso naganni a fadar sarki *GULMIYANU* tare da ya'yan shi biyu mace da na miji *Ambar* da *kiyara* ambar ne yake son aure na, ni kuma bani sonshi adalilin hakan ne nake fuskantar mummunar azaba" ban san su waye iyayena ba, kawai nata so naganni awajan kanwar sarki" *gulmiyanu* wato me suna *gimbiya *sameeratu* duk fadin duniyar aljanu ana jin maganar *gimbiya samiratu* sbd ita take mulki alokacin, amma yanxu ta mutu kuma bil adama su sukayi ajalinta, wanda ban san dalili ba" nayi nayi binciki afada min ni wacece amma haryanxu ban samu amsata ba"haka rayuwata taci gaba da gudana. Akwai watarana da bazan taba mantawa ba ina zaune bakin ruwa ina wasa da tsuntsaye domin suke debe min damuwar dake zuciyata!! sai naji abayana ana min magana juyawan dazanyi, naga wata kyakkyawar matashiya kuma bafulatana" dauke da kwaryan nono tana min murmushi, tace nawwara ko zan iya zama kusa dake? na daga mata kaina tare dayin murmushi, kafin tazauna sai naji tace *bismillahi*sannan tazauna na kara kallonta, itama ta kalle ni, sai naji ta ambato sunana, tace nawwara, nasan baki sanni ba kuma baki taba ganina ba" amma ni nasanki, nasan asalinki, nasan labarinki me dauke da tausayi. kullum in zan wuce ta bakin ruwannan ina ganinki kina cikin damuwa, abun na damuna" shiyasa nace bari yau nazo nafada miki asalin wacece ke, kuma suwaye iyayenki, kuma infada miki" awani jinsi kika fito , *jinsin aljan* ko *mutum* dannasan shine abinda kikafi damuwa akai" cikin murnata na rungumeta ina cewa nagode yar uwata, tace bakomai, yar fulani taci gaba da cewa amma inaso kimin alkwarin bazaki fada ma kowa idan nafada miki asalinki ba" sbd idan akaji sai ankasheni. kuma addinina dana su ba daya bane, ni musulma ce sunana *Ameena Bintu saifullah* , taci gaba da cewa nawwara ke diya ce ga abdullahi da asma'u, kin kasan ce ajinsin _____ sameeratun nawara tayi ajiyar zuciya, awwal yace kinyi shiru baki karasa ba,ta dago idonta wanda yayi jajir ta kallesu, nawwar ya rikice yace lafiya nawwara" cikin murya mai rauni tace Aminatu bintu saifullah bata karasa fada min ba, naji tasaki wani uban ihu tafadi kasa, juya wan dazanyi naga *kiyara* ce da wasu kartan maza, su suka aikata ma ameena haka, ashe sunji abunda ameena zata fadamin shiyasa suka mata haka" nashiga rokon kiyara dasu bar azabtar da ameena amma ina, tun ameena tana cewa nawwara ki taimakeni nawwara kitaimake ni, nayi nayi iya kokarina" intaimaki ameena amma ina sun bace da ita!!! nawwar da awwal wanda hawaye yagama wanke musu fuska nawwar yace yanxu ina suka kai ameena bintu saifullah? tana raye ko bata raye? tace tana raye amma tana cikin wani ma ajiyan mu da ake kulle me lefi, tana shan azaba kala kala, banta6a mantawa lokacin dana yima ambar wayau ta sigar soyayya daya kaini wajan ameena dana ganta, da kyar ya amince" da mukaje naga duk ta canxa kamanni sbd azaba, kalmar data fadamin shine, tace nawwara kibazama duniyar bil adama kine mi addinin musulunci domin shi zai iya taimaka miki wajan gano asalin jinsin da kike. *EDITED* BY *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *nusnim*πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ πŸ™πŸ» *MUTUM* πŸ™πŸ» 2⃣5⃣&3⃣0⃣ Tun daga lokacin da ameenatu bintu saifullah tace nabazama duniyar bil adama don neman addinin islama"daga ranar na dau niyyar shiga duniyar bil adama, da haka rayuwata taci gaba da tafiya, ba abunda nasa agabana sai neman addinin musulunci, nayi yawo dayawa acikin duniyar bil adama, narasa wazan tunkara da wannan batu nawa" ana haka ne ranar sallar ku ta edi na hadu da kai, alokacin da kake k'ask'an da kanka wurin ubangijinka' kana addu'a, kana niman taimakon Allah. tun a lokacin naji ka burgeni' zuciyata ta aminta dakai, naji bawanda yadace na tunkara sai kai, daga ranar nafara bibiyarka, atunani na kaine zaka taima kamin gurin gano wacece ni, kuma ka koyar dani addinin islama""nawwar kataimaki rayuwata ina cikin tsaka mai wuya, ka taimakeni ka tsamoni daga duhun jahilci" ta karashe mgnr muryarta na rawa" Nawwar ya numfasa yace sameeratun nawwara naji bayaninki, amma wannan batu da kika zo dashi daidai yake darasa rayuwar mutum, ayanayin labarin da kika bada na fahimci duk wanda yayi yunkurin taimaka miki gurin gano asalinki, to shima dai dai yake da rasa tashi rayuwar gun wad'ancan azzaluman!!" amma addu'a itace takubin mumini, *innallaha laa' yamli lizholimin.* _lallai Allah baya kyale azzalumai_ da sannu zai nuna musu isar sa.... zan taimaka miki don Allah da kuma son dana ke miki, sannan da yar dan mahaifiyata" idan ta amince shikenan sai mu tsananta addu'a Allah ya mana jagora. Tace nagode nagode sosai kuma insha Allahu wani abu bazai taba samunka ba, namaka alkawarin haka" kuma mami hafsat baza ta hanaka taimako ba da yardar Allah"" dr awwal ne yayi gyaran murya yace wani hanxari ba gudu ba, kun manta abu guda daya, kar ku manta sai da taimakon ameenatu bintu saifullahi zaku samu cikan burinku, saboda ita ta turo nawwara duniyar bil adama don tasamu mutumin daya rike addu'a don suje su taimaketa tafito daga hannun su ambar, ta bakin ameena ce za agano wacece nawwara!!! yanzu dai abunda zakuyi shine kutaima keta tafito, ko ba hakaba" sameeratun nawwara tace tabbas gskyan kane awwal dole sai yar fulani tafito, amma gurin da take akwai hatsari, nawwar yace karki damu da taimakon Allah zata fito. toh yanxu dayaushe ne zaka fara koya min addininna ku?, inshaAllah nan da sati daya ok nagode, bayan sunyi sallama sai ta bace. nawwar da awwal sunshirya yadda zasuyi su samu mami hafsat da wannan zance, labari har yakai kunnan mami hafsat, sai da ta girkiza dajin labrin" amma dayake da awwal ne kuma shi yake mata bayani sai ta amince musu tare dayi musu addu'an samun nasara,nawwar yaji dadi sosai da maminsa ta amince daman mace ce mai hakuri da tawakkali!!! *wanene nawwar* da'ne ga alhaji isma'il da hafsat, alhaji isma'il haifaffan garin yola ne iyayenshi duk acan suke gaba da baya shi ba fulatani ne, yayi makarantansa tun daga primary zuwa universty abti yola, yayin daya gama ne, aminin mahaifinshi wato alhaji kasim shiyasa ma mishi aiki a jahar kaduna" isma'il tun yana karami alhaji kasim ke sonshi" anan gdan alhaji kasim na kaduna isma'l ya zauna, yana da yaya mata uku, maza biyu babban dan alhaji kasim namiji ne me suna abdalla, sai ibrahim, sai hafsat da mariya sai khadija autar su kenan, mahaifin isma'il takanas yazo kaduna wajan amininshi alhaji kasim, don ne mama dansa auren hafsat, , kasan cewar dan nasa yaje masa da batun son auren hafsat , alhaji kasim yaji dadi sosai" kuma antambayi hafsat din itama ta amince, mafarin auren iyayen nawwar kenan!!" bayan auren su da shekara biyu Allah ya albarkace su da d'a namiji wato nawwar sai kuma sulaiman, daga sulaiman sai autar mami wato, maryam wace ake ma lakani da mimi, macen ta daya tal maza biyu,, mami hafsat ta bama ya'yanta tarbiya dai dai gwargwado, ga kuma addini daya ratsa jikin su, dukkansu suna da haddan alqur'ani mai girma, don shi sulaiman ma baban malamine a islamiya, yayin da nawwar shi kuma doctor ne, sai autar su mimi itama karatun take afannin boko tana ss 1, afannin islamiya kuma tana *sanawiyya* . wannan shine lbrin su nawwar. ***************** *dunyar aljanu* sarki gulmiyanu ya tara dukkan aljanu yana shaida masu" nan da wata daya za ayi gaga rumin bikin dansa *ambar* da *sameeratun nawwara*, nan take taji gabanta yafadi, shi ko ambar da kiyara me zasuyi inba murna ba har gaban mahaifin nashi yazo yana godiya" ambar ya dago ido yana sakar ma nawwara murmushin samun nasara, sarki gulmiyanu yaci gaba da cewa' nan da sati biyu ina son akashe ameenatu bintu saifullah' cikin tashin hankali samiratu taje gaban sarki ta tsugunna tana rokonshi da abar yar fulani da ranta!!" amma ina sarki yaki amince wa, ganin sarki yaki sauraronta" tuni ta garzaya duniyar bil adama wajan nawwar don neman mafita, tafada mashi abunda ke faruwa shima hankalinshi atashe yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un , la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin"" ai bashiri nawwar yashiga koyar da sameeratun nawwara addinin islama, addu'oi iri2 yasoma koya mata' kan kace kabo sameeratu tayi zurfi sosai, idan yana koya mata wani abun ma sai ta dinga tunanin kamar ta tabayin abun ada:!!. akwana atashi ba wuya a wajan Allah, a yaune su awwal da nawwar da sameeratun nawwara, suka shirya hanyar da za adauko *ameenatu bintu saifullah* _sai ku biyoni agaba don jin shin zasu samu nasarar ku6utar da ameenatu bin saifullah ????._ *EDITED* by *UMMEE ADNANπŸ’—πŸ’•* ~TAKU A KULLUM UMMU RUMAN~ πŸ’ *nusnim*πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA*🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ πŸ™πŸ» *MUTUM* πŸ™πŸ» 3⃣0⃣&3⃣5⃣ sameeratun nawwara ta kammala shirinta tsaf tare da daukan makaman ta, saboda tsaro , bayan tagama ne ta garzayo duniyar su nawwar , ayayin da ta iskesu suna zaman jiranta shida awwal' nawwar ke kara karfafama awwal gwiwa akan wannan tafiya daza suyi.ganin yadda duk yake a tsorace, yace haba abokina" kada kabada maza mana' kadafa kamanta *Allah yace yana nan aduk inda bayawansa yake tsammaninsa'* kasa aranka Allah yana taredamu kumashi zai taimakemu" inafatan dai kayi azkar d'in safiya, da addu'ar dana baaka jiya? murmushi awwal yayi cikeda kwarin gwiwa yace nayi Allah ya taimakemu' Ameen... Sallamar sameeratu ne ya katsesu da karatun suratul yaseen dasuke bayan sungama karanta wasu ayoyi acikin suratul baqara" takaraso ciki, dukansu suka amsa mata sallamarta,fuskarta dauke da murmushi yayin da take kallon nawwar, shima ya mai da mata martani, tace masu *masa'un khair* suka ce mata *masa'u *noor*. auwal ne yace ai nayi zaton baza kixo ba, tace tab mai zai hanani zuwa, yanxun ma duk nakosa muje, nawwar yace ' ki kwantar da hankalinki insha Allahu zamu samu nasaran zuwa wajan ameenatu bin saifullah, tace toh Allah yasa nagode sosai" awwal yace ya naganki da makamai, tace ai saboda tsaro na dauko, yayi dariya, yace haba ai ayar Allah kadai ta ishemu makami' sbd haka karki samu damuwa, to awwal, yanxu sai kutashi muje don lokaci na kurewa. nawwar yace to amma bari mugabatar da addu'a kafin mutafi, suka ce to, nan suka karanta *suratul iklas* *falaq* da *nas* sai *ayatul kursiyu* sannan suka shafa, sameeratu tace kurufe ida nuwanku, yadda ta umur ce su haka sukayi. *duniyar aljanu* awani kurmin k'ogo suka sauka' tace subude idanunsu" nawwar ne yafara budewa tare dayin addu'ar neman tsari, shiko awwal yakasa bude idonshi saboda tsoro, don bai San me zai fara gani ba idan yabude idon. nawwar da nawwara suka dubi awwal cikin mamaki, nawwar yace awwal lafiya bude idanunka mana mun isofa, cikin rawar murya awwal ya soma magana , yace nawwar wallahi tsoron budewa nakeyi" sameeratu tace kar ka damu ba abunda zaifaru da kai kabude , nawwar yace haba doctor be a man mana, Kasa aranka kana tareda sojojin kariya daga Allah , ahankali awwal ya bude ido shima tare dayin addu'a. haka sukabi wajan da kallo cikin kurmin dajine , sameeratu tace nayi mana Rabin zuwa, sauran tafiya kuma da kanmu zamu karasa, saboda bani da karfin da zanjamu a iska mukarasa wajan, suka ce to " nan da nan suka doshi hanya tafiya suke sosai kowannan su da abunda yake tunani azuciyar shi, tafiya suke babu kakkautawa, har suka gaji suna samu gefe don su zauna suhuta. Duk abunda ke faruwa su sariki *gulmiyanu* ba su sani ba' sbd kafin sameertu sutafi sai da taje ta to she madubin da suke ganin hangar da zai sadasu da ameenatu bin saifullah , cikin ikon Allah kuma dukkansu babu wanda ya hankalta da hakan, itako ameenatu tananan cikin dakin azaban da aka ijyeta, tanaji ajikinta sameeratun nawwara natunkaro wajanta don taimako. awwal yace sameeratu wai bamu iso bane! wlh nagaji nikam, sameeratu tace yi hakuri saura kadan mukarasa, Allah dai ya kaimu lafiya amin. *Ambar* ne zaune da kiyara suna hira sai sukasa ajuyo musu madubin dazai sada su da ameenatu bin saifulllah , aiko anajiyo dashi sukaga abu bakin kirin, Akbar yayi saurin mikewa, yana cewa garin yaya wannan abun yafaru?tayaya ba aganin hoto? kiyara tace lallai akwai wani bakon al'amari ayi sauri aje abin cika, sannan kuma akira sameeratun nawwara , labari yaje kunnan sarki shima hankali tashe don ba'a taba mishi irin wannan abun ba. kiyara ta dawo cikin sauri tace babu sameeratu , nan take aka bude madubin da kyar , kafin subude su nawwar sun Isa ga ameenatu , duk sun kashe masu tsaronta da ayar Allah, sameeratu ta rungume ameenatu bin sai fullah, daidai lokaci sarki dasu ambar, suka hango abunda ke faruwa, ambar yasaki wani irin gigitaccen kara nabakin ciki, saida su sameeratu sukaji , ameenatu tayi saurin cewa maza maza kuzo mu wuce dan sun ganomu, su nawwar gabansu sai faduwa yake, yana ta karanto addu'a" haka awwal ma. sarki yace garin yaya haka tafaru bil adama har suka samu damar daza su shigo mana duniyar mu, cikin huci kiyara tace wannan duk aikin sameeratun nawwara ce, ambar yace mufar musu baza abar su da rai ba. nawwar suna ganin bak'in abu natasowa da sauri duk suka tsorata , sameeratu tace ameenatu kiyi sauri kifitar da mu gasu nan zuwa, tace to ni yanxu ina zamuje, nawwar yayi saurin cewa musauka aduniyar mu kawai, aiko dafda wani guguwar iske ya kusa dasu suka mace bat, cikin nasara, sai gasu aduniyar bil adama, cikin office din doctor awwal , suka zube akasa awwal da nawwar kamar wasu matattu, can suka farfado bakinsu d'auke da addu'a' nawwar yace anya baza su iya biyo mu nan ba? aminatu tace a'a, nayi wani abun da baza su iya gano inda muke ba, nawwar yace akwai wani gdna dake kusa da asibitin nan, yakamata muje can. suka ce to kowannan su zaune awwal dai shiru yayi don sai yanxu yakejin gajiya, bayan kwana daya da dawowan su duk kan su zaune afalo, idan kuka ga sameeratu da ameena bin saifullah sai ka rantse da Allah mutanene, sbd idan zasu hadu da bil Adam sukan fito asuffan mutane , yauma hakan takasance . nawwar yace naje nasamu malamina nayi mishi bayanin komai, kuma ya amince dashima yataimaka mana , gashinan zuwa nan da yan mintuna, don agabanshi za awarware wannan kullalliyar al'amarin, amenat tace tabbas kayi tunani nawwar , hakan nada kwau ,bata gama rufe baki ba mallam yayi sallama , suka amsa nawwar yanuna mai waje ya zauna" duk suka gaisar da malamin. saida mallamin yayi doguwar addu'a sosai sannan ya bukaci ameenatu bin saifullah data bayyana wacece sameeratun nawwara" kowa ido yazuba mata donson jin abun da zata fada, tace Allah y gafarta mallam sameeratun nawwara takasan ce ajinsin_____? *kubiyoni agaba* don jin me zai faru. *EDITED by UMMEE* *ADNAN* TAKU A KULLUM UMMU RUMAN *KUYI HAKURI DAJINA SHURUN KWANA 2 HAKAN YA FARUNE ASANADIYYAN LALACEWAN WAYAR TAWA AMMAN YANXU ALHMDLLH KOMAI YA DAI²TA* πŸ’ *nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:32 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 *CE*πŸ’ πŸ’ *KO* πŸ™πŸ» *MUTUM*πŸ™πŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 3⃣6⃣➡4⃣0⃣ A hankali *Ameenatu bintu saifullah* tace Allah ya gafarta mallam hakika sameeratun nawwara ta kasance acikin jinsin bil adama gaba da baya, awwal ya zaro ido, yayi saurin cewa kina nufin asalinta mutum ce ba aljana ba? tace tabbas mutum ce ba aljana ba, nawwar da nawwara sai kallon aminat suke cikin mamaki da d'aurewar kai. Nawwar yace ameenatu munaso kifad'a mana tayaya sameeratu tazama aljana" alhalin kuma kince asalinta mutum ce, daman mutum na rikid'ewa ya koma aljan? ta dago ido ta kalli mallam da baice dasu komai ba sai kallonta yake hana nazarin wasu abubuwan" ta juya takalli su nawwar da suka zuba mata ido suna jiran amsarta, sannan ta maida kallon ga sameeratu data matsu taji ko ita wacece' dafata tayi ,tace karki damu yau zakiji asalinki" kuma zakiji ko suwaye iyayenki. πŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”ΉπŸ”Ή *shekaru bakwai* *da suka wuce* πŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”ΈπŸ”Έ Akwai wani bawan Allah me suna Alhaji idrisa da matarsa hajiya maimuna, dukkan su haifaffun garin kano ne, Alhaji idrisa dan kasuwa ne kuma Allah ya hore mashi arziki, babban danshi na mijine me suna muktar, sai nabiyu mai suna isma'il sannan na uku macece mai suna sauda sai abba, sameeratun nawwara sannan zainab, yayanshi biyar kenan ukun sunyi aure , sai yarage daga sameeratun nawwara sai zainab. sameeratun nawwara yarinya ce me hazaka sannan tana da kyanta daidai gwargwado, tsakaninta da kanwarta zainab babu wani jaa, don ba ayaye sameeratu ba aka samu cikin zainab. gidan Alhaji idrisa babba gida ne, daya gada ga iyayensa" gidan hade yake d gdan gona, ko ta ina acikin gdan akwai bishiyoyi, kama daga bishiyar mangwaro, kashu, Tsamiya, dalbejiya, zogale, kukan Fulani, da dai sauran su"" lokacinda sameeratu na karama mamanta kan shimfida taburma da yamma sai ta ijye nawwara akai ita kuma tana aiki ga kuma tsohon ciki datake fama dashi, da haka sameeratu take gangarawa cikin wayannan bishiyoyin tayita wasa da y'ay'an aljanu, duk mahaifiyarta bata sani ba, dan duk sanda ta gama aiki tazo d'aukarta, zata isketa a inda ta barta" da haka yarinyar tasaba dasu, yakasance duk lokacin dabata je wajanba ta dinga kuka kenan, tun mahaifiyarta na hanata har ta kyaleta. akwai wani rana da ake meeting na aljanu, wacce shugaban aljanu itace *gimbiya sameeratu* ta garde akan kujeranta na sarauta kowa na girmamata, ga kayan marmari anjere mata agabanta, alokacin ne hajiya maimuna ta ijye nawwara agefenta don tayi sallar magriba afalo, tafara sallah bada dadewa ba nawwara ta rarrafa tafito waje har ta Isa wajan da aljanun suke taro ba su lura da itaba, sai dataje daidai kusa da gimbiya sameeratu, sukayi ido hudu, abunka da yaro sai nawwara tasakar ma gimbiya sameeratu dariya, itama ta maida mata tare da daukan nawwara tabata kayan marmarin dake gefenta, tundaga lokacin gimbiya sameeratu taji tana son nawwara, alakacin ne ambar yaji shi bawadda yake so aduniya irin nawwara. dahaka dai nawwara tashiga ran aljanu, amma tana karamanta ne take ganin su, data fara girma sai sukayi kamar sunbarta , alhalin basu barta ba, Alhaji idrisa yasa ansare duka bishiyoyin gdansa inda yatada Gini aciki, sare bishiyoyin nan bakaramin tashin hankali ya afku a duniyar aljanu ba" don alokacin daza asare bishiyoyin gimbiya samiratu tana kwance tana hutawa, abun ya afka da ita daidai tsakiyar cikinta aka sare, sai yatsar ta mai duke da wani shegen zobe mai kyau yafado kasa, daidai saitin dakin nawwara" . anan rai yayi halinsa, duniyar aljanu sungirgixa da mutuwan gimbiya sameeratu, sarki gulmiyanu yayi takaicin rasa yar'uwar shi da sauran aljanun su," mutumin dayasare bishiyar ba ayi kwana biyu ba yarasu , mutane suka fara jita jita akan cewa ai bishiyan daya sarene agdan Alhaji idrisa na aljanune, kuma ba shakka su suka kashe shi, kuma daman sai da akace ma alhjy karyasa asare don dadewar bishiyoyin , yace shi sam bai san da wasu haittu aljanu ba, kuma koda akwaisu badai a gidansa ba" bayan mutuwan gimbiya sameeratu da sati daya, nawwara ta tsinta wannan zoben gimbiya akofar dakinta, taji yabata sha'awa tasaka a hannunta, ya mata kyau sosai. suko can duniyar aljanu sun kudirta aniyan raba alhaji idrisa da farin cikin shi kasan cewa Allah ya daura mai son nawwara, gashi yarinyar akwaita da haddan alqur'ani akanta,tana zuwa islamiya sosai. tun lokacin data sa zoben nan taji kamar bata da lafiya, kuma tayi rauni akaratunta, tun mahaifiyarta namata fada har tagaji takyaleta, ikon Allah kuma babu wanda ya ta6a lura da zoben hannun ta. akwai wata rana taje islamiya taji sam takasa zaman ajin duk ranta abace yake kuma tarasa dalili' tashi tayi tafita waje tasamu wuri ta zauna' me zai faru kawai sai jitayi ance sameeratun nawwara kitaho gareni zan yaye maki damuwarki' zan baki duk wata kulawa data dace ke tamuce har abada, a tsorace take waige² bataga kowa ba" mikewar dazatayi saiga___? *EDIDTED by UMMEE ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *nusnim*πŸ’ *pyar* [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 *CE*πŸ’ πŸ’ *KO* πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 4⃣1⃣➡4⃣5⃣ Mikewar dazatayi saiga maciji yayi saurin bi ta kafafunta, tasaki wani uban ihu tare da sumewa kasa , nan take yan makaranta suka rufa mata, aka kira mallamin su, yasa yan ajin sanawiya su dauke ta sukaita aji. yasa aka kawo mai ruwa a kofi yayi addu'oi aciki ya watsa mata fuska, a firgice ta farka tana cewa gasunan suna kirana, wayyo Allah zasu..... mallam yayi saurin cewa suwaye ke kiranki nawwara? kasa magana tayi ta tafi suuu zata fadi aka tare ta, shugaban makarantar ne yazo, yace yana ganin alamar jinnu ne ajikin yarinyar nan" ayimata ruqiya agani idan aljanun ne za'a gane" mallamin su yace hakane don nima nayi tunanin haka. nan aka shiga yiwa sameeratun nawwara ruqiya , nanda nan aljanun suka bayyana ajikinta, alokacin ambar ne ajikinta, abisa umurnin mahaifinsa dayace yasoma bayyana gareta " don ya isar musu sakon dasuke dashi. mallam yace kai waye' kuma me kuke nema awajen wannan baiwar Allah'n, me tamuku kukeson cutar da ita? shuru ambar yayi' mlm yace zakuyi mgn kosai na kona ku da ayar Allah, cikin wani irin murya da babu dad'inji ambar yafara magana "" yace mallam kar ka kona mu zamu fita dama sakone muke son isarwa ga mahaifinta" kiransa zakayi mufad'a masa ko kai zamu barwa sakon ka isar gareshi!" mallam yaga idan yace akira mahaifin nawwara ana iya d'aukar lokaci, ga yarinyar nabuk'atar taimakon gaggawa" tunda sunce zasu iya bada sakon aba mahaifinta ai shikenan' yace wace irin sako ne! kafad'a zamu isar zuwa gareshi" ambar yayi wata irin dariya tukum sannan yace ciki tsawa mallam muna so afadama mahaifita zamu dauke sameeratun nawwara zuwa duniyarmu...... mallam yace wa'iyazu billah meyasa zaku aikata wannan mummunan abun, ambar yace sbd mahaifinta yaraba mu da farin cikinmu, saboda haka muma zamu rabashi da farin cikinsa ta hanyar d'auke y'ar wacce yafi so aduniya" daman kuma tamuce. mallam yace menene wannan abun daya rabaku dashi!, ambar yace yasa ansare bishiyoyin dake gdansa batare daya sanar mana ba, balle mu kwashi muhimman ajiyarmu' kuma alokacin gimbiyarmu me suna sameeratu, tana kwance akan gadon hutawarta abun ya afka da ita' da sauran yan uwan mu, saboda haka baza mu yarda ba, muna so a Isar masa da wannan sakon" mun sassauta hukuncinmu akansa ne sbd sonda muke ma nawwara" badan hakaba damun dad'e da d'aukar mummunar fansa akansa" kafin mallam yace wani abu har yafita daga jikinta , ita kuma sai tari take aka bata ruwan addu'a tasha sai bacci ya dauketa. Bayan kwana daya da faruwan haka shugaban makarantansu da mallamin ajin na su suka je gdan Alhaji idrisa , bayan sun gaisa ne suke bayyana mishi abunda ke faruwa, yace sam shi bayyarda da wasu aljanu ba, yar shi kuma bazai wuce maleria bane ke damunta, ai wannan ma tatsuniya ce, aljanun banxa aljanun hufi, duk wannan ta tsuniyace, da karyan yara, mallam yace a'a Alhaji, kar kamanta fa Allah da kansa yana fad'a acinkin alqur'ani cewa ( *wama khalakatul jinna wal insa illa liya'a budun* _bamu halicci mutane da aljanu ba face dan su bauta mani_ ) Ashe kuwa kaga aljanu gskya ne, su suna ganin mu amman mu bama ganin su, kuma maganan gsky sare bishiyan nan da kayi batare da kasan matakan daya dace kayiba kafin hakan akwai matsala, sannan kasan bishiyoyinnan sunyi sama da shekara talatin da y'an doriya ba asare su ba sai yanxu? kaima kasan dole asamu matsala, zaman lafiyarka da iyalinka shine kabasu hakuri, inba haka ba, watarana zakayi kuka da idanun ka, don bakasan kaidin aljanu bane shiyasa, muna kara baka shawara da kabasu hakuri kawai" dan tsira da iyalanka" , Alhaji idrisa mutum ne mai taurin kai da kafiya akan ra'ayinsa, da kuma karyata aljanu, ya tashi cikin fushi yace mallam dan Allah kutashi kutafi sun dad'e basu dauke ta dinba makaryata kawai, cikin fushi suma suka bar gdan. aljanun sunji duk abunda Alhaji idrisa yace, kuma sun dau alwashin sai sun dauke sameeratun nawwara, duk ranar da taje islamiya sai suntashi mata kuma sai sunkara fada zasu sace ta. Ranar jumma'a sameeratun nawwara taci kwalliya zataje gdan yayar babanta ta gaidata daganan ta wuce shagon dinkin su"" dayake tana koyan dinki, bayan taje gdan goggon nata ta wuce shagon su, kawar tace khadija tace kin makara nawwara yau nariga ki zuwa , nawwara tayi murmushi" tace wlh nabiya gdan goggona ne, Ayya ke kadai ce ashagon ina aunty marry, khadija tace taje kasuwa ,ok, nan sukaci gaba da hirar su har la' asar tayi, nawwara tace Khadija bara nashiga gdansu baba rabi nayi sallah tunda ke kina fashin sallah, tace to fad'awa duniya bana sallah yau takarashe fad'a tana dariya, nawwara tayi dariya. ta kama hanyar zuwa gdan kenan sai ga wani guguwar iska yataso ya dumfaro nawwara, kiyara ce tazo ta dauke ta, tun daga lokacin nawwara bata sake sanin ita wacece ba, kawai ta ganta ne aduniyar aljanu , duk sun tsafeta da abubuwan su tazama irinsu, amma kuma kana ganin nawwara sai kace ruwa biyu ce, wato aljana da mutum, haka takoma"" wannan zoben dake hannunta shi yakara bata duk wani karfin tsafi, shiyasa tazama kamar aljana, amma kuma akwai wajajen dabaza ta iya zuwa ba aduniyar aljanu, kasan cewarta ita ba asalin aljanar bace. in baku manta ba ko wajan da aka daure ni bata karasa daku ba sai da kafa fuwanku kuka karasa, sbd batada karfin isacan, da sunyi niyyan kasheta ne sai ambar yace yana sonta , acan kuma duniyar bil adama, khadija tajiki shiru baki dawo ba. nan aka bazama neman nawwara lbrin batanta yazagaye ko ina, har makarantar islamiyar su, mallaman su sunyi takaicin haka' shiko mahaifinta kamar zaiyi hauka, yana cewa karya kuke kud'auke min yarinya ta, yayi ta sambatu yana tsine musu, abu wasa² har anfidda tsammanin ganinki, kowa ya dangana anmik'ama Allah lamuransa" sai bayan batanki ne mahaifinki yafara daya sani sai alokacin mahaifinki yayarda da akwai aljanu, shi sam daya karyata aljanu, yana ganin duk karya ne, damuwa tamasa yawa' wanda hakan ya kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu sannan y warke duk yan uwanki sun dangana. ke kuma kina can kina rayuwa da aljanu, sun gusar miki da kwakwalwa, wannan shine abunda ya faru deke nawwara, awwal saida ya zubda hawaye , nawwar yace wai meyasa mutane ke son karyata aljanu, bayan kuma Allah yafada, da akwai, acikin aljanun ma akwai masu bauta mai, kamar yadda akwai amutane akwai musulmai a kwai kafurai, sameeratu dake zaune tazuba musu ido tarasa meke mata yawo a kwakwal warta. nawwar yace to meza ayi mata ta dawo yadda take cikakkiyar mutum,ameenatu bin saifullah tace kunga wannan zoben dake hannunta za'ayi kokarin cireshi, sannan kuma sauran aikin malllam ne yasan yadda za'ayi. mallam ne yayi magana yace nawwara ba ita kadai bace akwai gimbiya sameeratu ajikinta kuma karya wayannan asiren dake jikinta bakaramin aiki bane, zamuje da ita Maiduguri, don nikadai bazan iyaba , bai gama rufe bakinshi ba sukaji gdan y girgiza yayin da nawwara ta xube kasa wani bakin abu nafita Daga bakinta,duk kan su suka nufo kanta cikin tsoro wutan dakin ya dauke ko ina bakin kirin. *EDIDTED* BY *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 *CE* πŸ’ πŸ’ *KO* πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 4⃣6⃣➡5⃣0⃣ wutan dakin ya dauke ko ina bak'ik'irin baka iya ganin komai" ameenatu bin saifullah tace mallam ya kamata kayi wani abu don suna dab da isowa inda muke, kuma ga nawwara cikin wani yanayi, wannan bakin abun dake fitowa daga bakinta alamun suna son fitowa ta jikinta ne, wanda hakan daidai yake data rasa rayuwarta, nawwar yana jin haka yace mallam kataimaka dan Allah. bani son in rasa nawwara arayuwata" shikansa mallm al'amarin yasoma firgitashi' bayyi tsammanin abin yakai hakaba' karatu yasomayi cikin gaggawa, suma su nawwar suna karanto duk ayar datazo abakinsu"saida sukayi kusan minti 30, sannan hasken dakin yasoma dawowa , gdan kuma yadaina girgiza, nawwara ta bud'e ido, sai dai takasa magana, sai binsu take da kallo kamar wata tab'abb'iya. *DUNIYAR ALJANU* lokacin da su ambar suka karaso basuga su ameenat bin saifullah ba' don sunriga sun bace musu, sunyi sunyi su bisu amma ina sun kasa" sarki yayi takaicin haka sosai, suna tunanin ta ina zasubi suje duniyar bil adama, saboda wani katanga dake tsakanin su, sunyi tsafin su amma ina sunkasa rusawa, shine suka yenke shawaran fitowa ta jikin nawwara, amma ina basu sami hanyar fitowa ba, saboda karfin addu'ar da mallam keyi don saida ta kona wayansu, dole suka koma ta katangan suka fara aikin rushewa. *MAIDUGURI* Tunda suka kama hanyar zuwa mai duguri, mallam yafad'ama babban mallaminsa gasunan tafe, sun isa lfy an tarbesu cikin karamci, inda akayi musu masauki da kayan abinci' mallam ne zaune da babban mallaminsa isma'il maiduguri"" yana fayyace mishi matsalan dake tafe dasu akan nawwara"" sai daya numfasa sannan yace lallai rayuwar yarinyar nan yana cikin had'ari. amma insha Allahu komai zai daidaita zata dawo yadda take da izinin Allah, nan mallam yasa aka kawo mishi nawwara sam takasa hada ido dashi""yayi mata magana bata amsa shiba" d'aya daga cikin almajiransa yakira yace yad'au kasko yasamo garwushin wuta acikin gida" garin hantiti yad'ibo yazuba acikin kaskon, yamik'ama nawwar man jeedah y'ar saudiyya' yace yashafa mata a fuska" dakyar nawwar yasamu yashafa mata" da taimakon awwal dayarik'e mata hannaye" mallam isma'il yasa aka kira mai sauran malaman dasuke karatun dasu". yatashi yahada magani misk habbatus sauda da zaitun sai man ta farnuwa, da kuma gayen magarya duk yahada waje daya, sannan ya karanto addu'oi ya tofa aciki, ya umurci wasu malaman dasu sake riketa dakyau, ya matso yashafa mata a fuska da kafafuwanta" wani irin uban k'ara sake tana fizge fizge, tace mallam kusakeni kada ku kasheni, ni ban zamto daga cikin jinsin bil adama ba, niba jin___bata karasa ba sai ta fadi sumammiya, zoben dake hannunta yana fitar da hayaki, nan take yakoma launin ja, sai alokacin ne mallam ya hango zoben, yasa hannunta acikin wani kokon magani don cire zoben" da kyar zoben yafita. amma kuma me zai faru ana cire zoben sai sukaji kara acikin zoben kamar ana cewa kar Ku karasani tuni mallam yasaka shi cikin wani kwalbar magani ya narke , juyowar dazasuyi gareta kuma sai sukaga halittan nawwara yacanxa, bakaman da datake ruwa biyu ba, yanxu ta dawo asalin nawwararta. awwal yace mallam yanxu duk asirikan dake jikinta sun karye kenan, yace a'ah da sauran kadan dama babban matsalan itace wannan zoben, shine karfin asirin , yanxun kuma mun cire shi alhamdulillah, jira muke ta farfado sai ad'ora da ruqiya"" ameenatu Bini saifulla dake gefe, tace lallai babu abun bautawa da gsky sai ubangijin mu Allah, yanxu da ayoyin Allah akacire wannan zoben mai karfin tsafin, kuma anriga da angama halaka wannan zoben da me zoben wato gimbiya sameeratu. yanxu saura sarki gulmiyanu da mukarrabansa' dan bazai ta6a yafewa ba" gwara ma a halakasu duka, don muma musamu yancin kanmu da yadda zamu bautama ubangijinmu Allah , _Allahu sami'ul Aleem_. duniyar aljanu kuwa afadan sarki gulmiyanu' masarautar su tana girgixa yayin da wayanxu suka fadi suka mutu, saboda wannan zoben da aka kona , gininsu sai zubewa kasa sukeyi yayin da ruwa yacimma masarautan, suna neman ceto, sarki da kiyara da ambar suntsira da kyar, sarki yace ankona zoben nan shiyasa wannan abun ke faruwa, cikin huci ambar yace baza su yarda ba sai sun d'au fansa" kiyara tace mu koma jikin nawwara mudagargaza naman jikinta,munakasa ta tareda duk wanda keson ganin bayan mu, sarki yace haka za ayi.ta kalli ambar cikin 6acin rai" tace ai duk laifin kane' badan ka nuna kana sontaba aida tuni mun dad'e da mance shafinta" can kuma kowa ya bude alqur'ani donyin karatu sai sukaji ihun nawwara tana cewa wayyo zasu kasheni, ameenatu tace mallam kuyi kutaimaketa zasu kasheta wlhy,tunda hartayi silar tarwatsewar komai nasu bazasu barta da rai ba" nandanan suka fara karatu sosai, su sarki dasukaga za a kona su, sai suka fara cewa zamufita karku kona mu, itako ameenat cewa take mallam kuci gaba kada kubarsu azzalumai ne basa yafiya' zasu iyayin abinda yafi wannan idan aka barsu" duk yadda su sarki da ambar sukaso fita sun kasa' sbd yadda d'akin gaba daya yake warin magunguna ga kuma ayoyin Allah dake fita abakin manyan malaman cikin sauti" karatu suke har sai da suka tabbatar dasun konasu kurmus, sannan suka daina. ita kuma ta fadi kasa kamar matatta ,mallam yace alhamdulillah komai ya daidai ta ankona su, yanxu kawai mujira muga yanayin tashinta, ameenatu, tace mallam mun gode sosai yanxu ni zanyi tafiyata duniyar mu, tunda komai y daidai ta, idan nawwara ta farka agaisar min da ita, ta juya ta kalli nawwar da awwal tayi musu murmushi tace musu saduwar alkhairi, nawwar kari ke nawwara da amana, duk da dai nasan ayanxu idan ta farfado baza tasan waye kai ba, bazata tuna komai akan soyayyar da kukayi ba, amman nasan kai d'in jurumine, adalilin sonda kake mata ka tsamota daga aljanu zuwa asalinta (mutum) ka saida rayuwarka donka ceto abar sonka "" jarumtarka ta burgeni, sai dai kash ina mai tausaya maka saboda yanxu zaka sake shiga cikin wata jarabawar so' dan asalin nawwara bata soyayya' hasalima duk wanda yace yana sonta to daga ranar yazama makiyinta' don acewarta haryanxu bata had'u da namijinda yayi dai² da ra'ayinta ba" koda ta farfad'o yanxu batasan da soyayyar kaba, ba lalle bane ta amince maka, sai dai nasan kaid'in mijine wanda za'a kira dasunan namiji acikin jaruman maza" kayi hakuri da duk abinda zai biyo baya' inshaAllah komai zai dai²ta take anan nawwar yaji gabansa ya fadi' idanu yazaro cikin wani sabon tashin hankali" gumi tako ina ajikinsa........ _kutara agaba donjin anya nawwar yana daga cikin tsarin mazan da nawwara take so kuwa._ *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 *CE* πŸ’ πŸ’ *KO* πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» 5⃣1⃣➡5⃣5⃣ gumi yake tako ina ajikinsa' innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a zuciyarsa, ameenatu tace nabarku lafiya cikin amincin ubangiji, cikeda kewar nawwara da tausayin nawwar ta tafi, ganin yadda duk ya d'aga hankalinsa akan abunda tafad'a masa" nawwar dake zaune cikin matsanancin damuwa kasa amsawa ameenatu sallamar data keyi musu yayi' sai tunanin zuccin dayake" anya zai iya jure rashin nawwara a kusa dashi kuwa? dan ba karamin illa soyayyarta yayi masa a zuciya ba; awwal ne ya dafa shi, yace kar kadamu abokina, insha Allahu kana cikin tsarin irin mazajen da nawwara zataso, kuma da yardar ubangiji sai kasamu soyayyar ta. uhummmm to Allah yasa' amman awwal na tabbatar da kaddara ce tafado min, kowani dan adam da kalar tasa kaddarar, fatana ubangiji ya kawomin agaji acikin al'amarina, awwal yace hakane doctor Allah ya shige mana gaba Ameen. nawwara dake kwance tasoma motsi alamun tashi kenan, awwal ne ya lura da hakan , da sauri ya ta6a nawwar yace kalla kaga tana motsi' barin kira mallam, su duka biyun suka shigo , mallam yace karku damu zata tashi da kanta, yana gama rufe baki, nawwara tayi mika tare dayin salati, bud'e idon dazatayi sai taga bak'in fuskoki akanta tsaye' tayi saurin waro idanu, tace nashiga uku lafiya naganku adakina, nan tafara laluben Neman hijabinta don ta kulle jikinta. karaf sukayi ido hudu da nawwar wanda yaji gabanshi yafadi, ita kuma tace mallam lafiya katsura min ido sai kace kaga sabuwar halitta? cikin tsiwa take maganar, cikinsa ne ya murna alamun kamar zaiyi zawo, nan kuma ta saki kuka tana kiran hajiya hajiya nashiga uku wasu mutane adakina' dan Allah kuyi hakuri kufitar min a d'aki" mallam yayi murmushi yace alhmdllh lallai kam sauki yasamu, sai ta juya ta kalli mallam da alamun tambaya abakinta, sannan kuma takara duban dakin data ke"" taga ashe ba gidan su bane, sai ta fashe da kuka, tana cewa ina ne nan kuka kawoni, mallam yace yi hakuri sameeratu baki da lafiya ne shiyasa, yanzu dai kitashi kiyi wanka ki canza kaya sai in miki bayani," batare data musa ba tace to, mallam yace dasu nawwar da su fito subata waje. mallam yakira yar uwarsa da ta taimaka mawa sameeratu tayi wanka, tace to mallam, tashiga tasamu nawwara ta tashi amma jikinta yana mata kamar ciwo ciwo, da taimakon matar nan tayi wanka da ruwan magani sai taji jikin nata ya mata dadi, ta fito wanka matar ta kawo mata kaya tare da abinci, bayan tagama ne , mallam yace tafito tasamesu a falo, bayan ta zauna suka kara hada ido da nawwar taga ita yake kallo sai taji ta tsane wannan nawwar din don tak'in jinin kallo , shiko zuciyarshi sai har bawa takeyi, kamar zata fashe, don ya hango tsagwaron kiyayyar sa a idanun nawwara, mallam yayi gyaran murya yace sameeratu, nasan baki San Ina ne nan ba , kuma baki san suwaye muba, wato kin dade baki da lfyane tsawon shekaru bakwai dasu ka wuce, tayi saurin zabura tace shekaru bakwai fa kace ? wannan wani irin ciwo ne dake damuna har natsawon shekara bakwai ban sani ba? mallam yace kar ki damu a sannu zaki san komai. yaci gaba da cewa zaki iya tuna yaushe rabonki da gida? tayi shiru tare dayin tunani, sai tatuna abunda yafaru lokacin daza taje sallah gdan baba rabi sai ga wani guguwar isaka yatasu, tayi saurin cewa wallahi jiya ne danabar shagon dinkin mu zanje gdan baba rabi sallah sai ga wani guguwan iska yataso. abunda kawai zan iya tunawa kenan, mallam yace yauwa, toh ba jiyabane yanxu kusan shekaru bakwai kenan da faruwan wannan al'amarin, ta dafe kirjinta tace nashiga uku mallam, toh yanxu ina iyayena? badai tsawon shekaru bakwai bana tare dasu ba! , wayyo Allah abbana, wai meya sameni hakane? Kai malam ya d'aga mata alamar bata tareda iyayenta" toh yanxu nan wani gari ne! yace maiduguri, idanu tazaro, sai kuma tasaki kuka, to waye yakawoni maiduguri! mallam yace labarine mai tsawo kuma cike da al'ajabi da tausayi: yanxu dai kibari idan kin huta zakiji komai in Allah ya yarda" kuka kawai take tana cewa dan Allah sukaita wajan iyayenta taga awani hali suke" mallam yace ya isa haka nawwara kiyi hakuri insha Allah zamu sada ki da iyayenki, tace to ngd' nawwar da awwal tabasu tausayi sosai," mallam yace tashi kije ki kwanta abunki kar kisaka damuwa aranki kinji, kai tad'aga masa tana sharar kwalla. bayan tashiga ciki mallam isma'il ya kalli mallam da su nawwar yace yakamata mukai yarinyar nan wajan iyayenta, awwal yace haka ne kam sai muje gobe ko? tunda kano ne wajan bazai yi mana wuyan ganewa ba, hakane Allah ya kai mana rai. yaune ranar dasu mallam isma'il da su awwal zasu kano da nawwara, tafiya suke cikin mota kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa har suka isa kano. *KANO* Alhaji idrisa ne kwance Afalonsa yana tunanin rayuwa" hajiya maimuna takawo masa ruwan sha da abinci, zama tayi kusadashi, tace mallam haryanxu bazaka daina yawan tunanin nan ba! yace haba maimuna' ai tunani ya zamemin dole yau ace shekara bakwai babu nawwara babu alamar ta" yau koda gawarta nagani daya fiyemin kwanciyar hankali , bamu san awani hali take ciki ba , hakane Alhaji, haka Allah y kaddaro mana muciga ba dayin addu'a, insha allahu zamu sami mafita , suna cikin magana ne wani yaro yazo yace ana sallama da Alhaji wai baki Daga maiduguri, yace to kace su shigo. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ kuyi hakuri da wannan banajin DADI ne [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 5⃣6⃣➡6⃣0⃣ yace to kace su shigo, dan Aiken ya koma yace wasu mallam isma'il ance su shiga, nawwara tana cikin mota zaune da badan su mallam sun dakatar da itaba da tuni ta falla da gudu ta shige gdan, sai tsaki take ta ja, shiko nawwar kallon ta kawai yakeyi, yadda ta hade giran sama data kasa" azuciyarsa yace wannan yarinya za ayi daru da ita. muryan mallam ne ta katse masa tunanin sa, mllam yace sameeratu fito kimana jagora cikin gdannaku, kamar ko jira take amata magana, cikin murna ta fito waje tana washe hakora" tace to mallam, yace to bismilla mujenku, itace agaba tana tafiya cikin nutsuwa. suna karasowa tsakar gdan sukaci karo da zainab tana wanke wanke, karaf sukayi ido hudu da sameeratu, zainab ta saki kwanon hannun ta, ta arce cikin gidan da gudu tana ummu ummu ummu, gatanan gatanan, yayin data fada jikin Hjy maimuna, tace ke lafiyarki kuwa, alhajine yace zainab wakika gani kike gudu haka"" sai haki kike. ji yayi ance abba nice kunnuwan shi ce ta jiyo mishi muryar da bazai taba mantawa dashi ba, muryarda a kullum yake mafarki da tunanin Allah yasake had'a fuskokinsu kafin mutuwarsa" atare suka d'ago idanu cikin sauri shida hjy maimuna, suka zubasu ga kofa, nawwara ce tsaye tana hawayen farin ciki. Alhaji idrisa da hjy maimuna sukayi zumbur suka mike tsaye, kowanne bakinsa na rawa sun kasa furta kalma d'aya" dakyar kamar had'in baki sukace sameeratu kece kuwa, karasowa tayi falon da gudu ta rungume iyayen nata , tana kukan murna, abba umma nice nawwaran Ku, ban mutu ba inanan. su nawwar dake gefe sun basu tausayi, har sai da kwalla ya fito musu, nawwara tace zainab nice fa sis dinki wacce kuke kwana daki daya, da gudu zainab ta rungume nawwara, sister nah ina kika je nayi kukan rashinki na tsawon shekaru, amma kin dawo kenan baza ki koma ba ko?, nawwara ta share mata hawaye. tace karki damu sister zee na dawo kenan insha Allahu bazan sake tafiya na barki ba, Allah sarki dama yan magana sun ce sabo turkin wawa,sai alokacin Alhaji idrisa ya kalli bakin kofa inda su mallam isma'il ke tsaye cikin tausayi. ya karasa wajan su tareda mik'a musu hannu sukayi musabaha, sannan ya nuna musu waje suka zauna, aka gaggaisa, mallam isma'il ne yafara magana, yace Alhaji mu baki ne daga maiduguri, munxo ne don mu sadaka da yarka sameeratun nawwara, sannan kuma mufayyace maka abubuwan da muka sani, Alhaji yace ikon Allah ashe duk shekarunnan da suka shude sameeratu tana maiduguri bamu sani ba. mallam yace a'a bata maiduguri tana duniyar aljanu har natsahon shekara bakwai nawwara tazaro ido waje tareda dafe kirji tace duniyar aljanu kuma? mallam yace eh, Alhaji ya jinjina kai, yace lallai kam nayarda, sbd na tafka babban kuskurenda ko makiyina bazan masa fatar shiga halin dana shiga ba, nan dai mallam ya kwashe labarin bacewar nawwara har izuwa lokacin da aka ganta, babu abinda Hjy maimuna alhaji idrisa da ita kanta nawwaran keyi sai kuka, nawwara tana cewa yanxu nice nayi tarayya da aljanu, abbanta yace nawwara kiyafe min, duk ni naja miki na rashin d'aukar shawara da maganar malaman islamiyyarku. a'a abba ni baka min komai ba kaddara ce kawai tafado mana, Allah ya yafemu baki d'aya" ta d'aga ido tayiwa su mallam godiya, mallam yace ba sai kin mana godiya ba, kiyawa Allah godiya sannan kuma ki gode masu awwal abisa sadaukar da ransu da sukayi sbd ceto taki rayuwar, sannan kuma ameenatu bin saifulla duk da wannan tariga ta koma duniyar su. nawwara takalli su nawwar tace yaya awwal yaya nawwar , ina matukar godiya akan tsamoni da kukayi daga aljana zuwa mutum, Allah ubangiji yasaka muku da mafificin alkhari, yabaku abokanan rayuwa na har abada, yasa aljanna fiddausi ce makomar ku" kowa yace amin su nawwar sunji dadin addu'ar ta," mallam yakara yiwa Alhaji idrisa nasiha akan shiga hurumin aljanu, da yawaita addu'oin kariya,, nan dai mallam yayi tanuna musu abubuwa masu muhimmanci dakuma hanyoyinda za'abi dan gujema shed'anun aljanu, Daga bisani aka kaisu dakin bak'i tare da abinci da abunsha, ankarramasu sosai. nawwara da kanwar ta suka fad'a daki ana hiran yaushe rabo, Alhaji idrisa ya hana afadama kowa dawowan nawwara, yace sai tayi kwana biyu lokacin ta huta,, kwanan su mallam biyu suka tafi' kowa ya kama hanyar garinsa tareda abun arziki,dakyar suka amsa, nawwar ya tafi cike da begen abar sonshi. kwanan nawwara biyu a gida cikeda jindadin ganin y'an uwa da abokan arxiki anzo tayasu murnan dawowarta" harda mallaman islamiyarsu da aminiyarta khadija, wanda sai da sukayi kukan farin cikin sake ganin juna' sauda kuwa wato yayar nawwara,harda dan kwarya²n walima ta shirya ma nawwara , mami hafsa da autar ta mimi" sunyi murnan dawowan su nawwar, mimi tashirya ma yayan nata abinci kalala, bayan yayi wanka yaxo yaci abinci, sannan yabasu mami lbarin abunda ya faru"" mimi tace lallai hamma kai jarumine, da kowace mace zataso samunka amatsayin namijita, gasky aunty nah nawwara, tayi dacen gwarzon namiji dan kwalisan matasa, hamma zan so inga wannan auntyn nawa, harara yatsa mata' yace kajimin yarinya da iyayi' ke harkinsan wani jarumi! murmushi tayi tarufe idanunta tace laaa hamma aida gske nake koh mami!' mami tace gsky nima zanso inga wannan nawwaran data kad'a kwakwalwar hamman nawa. suka sa dariya, mami tace dafatan dai bakayi kauron baki wajan furta abunda ke xuciyarka ba, nawwar yace mami cikin raunanniyar murya,da wuya sameeratu ta soni, don yadda ameenatu tace mana kwata²ita bata da lokacin wani d'a namiji, sannan kuma da alamun ta tsaneni, mami tace meyasa kace haka, nan yabata labarin sbunda aminatu bin saifullah tafada masa daza ta tafi, da yadda kuma nawwaran ta nuna masa a maiduguri. mami ta tausayama d'anta, lallai jarabawa ce ke binka nawwar" abunda zan ce maka kadage da addu'a insha Allah idan nawwara alkhairi ce agareka babu makawa saika aureta, murmushin jindad'i yayi yace nagode mami nah, Allah ya barmin ke kiga jikokin ki. bayan kwana biyu da dawowansa yana kwance akan gado yana tunani nawwara, da yadda zai tunkareta maganar soyayyarsu" ya tuna yadda yaga farin cikinta a lokacin da sukaje gidansu taga iyayenta, yayi murmushi, tare da lumshe idanun shi, yace ana hubbiq tartin ya samra, ,hubbee ilaiki abadan ya samra,yakara sakin murmushi, jiyayi antab'ashi. *EDIDTED by UMMEE ADNAN* _TAKU UMMU RUMAN_ πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» 6⃣1⃣➡6⃣5⃣ ji yayi anta6a shi' yayi saurin bude idanunsa yana cewa nawwara kece kikazo, sai kuma yaga ashe kanwarsa ce mimi, yace au sorry, auta ya akayi ne, mimi ta karasa zama wajenda yake, tare da cewa hamma nah lallai kayi zurfi sosai acikin son aunty sameera. yayi murmushi, hamma pls karage wannan son da kake mata" don karya maka illa, don so bala'i ne idan yayi yawa , cikin mamaki yake kallon auta mimi, yace auta badai harkin fara soyayya ba? me kagani hamma , yace to inba hakaba' tayaya kikasan so yanada illa idan yayi yawa? dariya tayi tace kai hamman aiba abin mamaki bane don nasan kalmar so' da illar zurfafawa acikinsa" idan kayi la'akari da yanayin zamaninnan namu" damu yara muke tashi da kallace² ko karance²n littafan soyayya' yace a lallai mimi naga alama kin isa aure.to ke a ina kk san ma'anar so? kai hamman ni bance aure nakeso ba, kawai dai nasan kalman sonne abakin kawayena dayake duk suna da samarai, nice dai bana kula samari ,kuma suna bani labarin samaransu da irin sonda sukema juna, baki ta turo tace sannan kuma ma ai na isa auren tunda shekarata 17 yanxu, tana fadin haka tabar dakin da gudu don kunyar yadda taga yayannata ya kafeta da ido" saida takai kofa tace Dr awwal ne ke nemanka, OK, cemasa yashigo. awwal yashigo dakin da sallama nawwar ya amsa mai, bayan ya zauna suka gaisa , awwal yace wato kananan kana wannan banzan tunanin naka ko, hmmmm ajiyar zuciya nawwar ya sauke, yace awwal ya kamata muje Kaduna plx, don zuciyata bazata iya hakura da sameera ba" ina so in fada mata abunda ke raina koda bazata amince min ba, zandai fad'a mata ne ko zuciyata ta daina zuginda take" awwal yace hakan ma yayi inshaAllahu nasan zata amince maka. kai dai kacigaba da addu'a,. yau jumma'a sameeratu zaune adaki suna hira da zainab kanwarta da umman su, khadija tayi sallama tashigo, tare da gaida umma, zainab ta gaisheta, umma ta basu waje, zainab kuma ta tashi don shirin zuwa islamiya, khadija tace sameera result dina ya fito fa, na jamp kuma nasamu, nawwara tace natayaki murna sosai, nima abbana yace yaba da kudi azana min lokacin da su zainab zasuyi, khadija tace uhumm kedai nawwara babana yace na fitar da mijin aure inyaso daga baya naci gaba da karatun adakin mijina. sameera tace haba dai' kice zamusha biki sosai, to waye gwanin naki! dry khadijat tayi" tace kema ai kinsan idan ba mallam abdullahi na islamiyar muba sai rijiya mai kwalabe, dan ustaz dina, lallaima khadija, wato auren ma yakusa, shine sai yanxu kk gayamin" tayi murmushi, kedai bari kawai zamusha bikin ustazai". Kema nawwara yakamata ace kin fidda mijin kafin abbanku ya miki maganar aure, kinsan halin tsofaffinnan namu" sameera tace kayya keleni nikam, ni haryanxu banga wanda nake soba, kai sameera baza ki daina ruwan ido ba ko,kina son zainab ta rigaki aure ne, to inta rigani sai me dubu nawa suke aure subar yayyen su, uhmm to mudai bamu fatan hakan ta kasance, sameera tace kinganni nan wlh ni soyayya ma tsoro take bani, ki kallafa kawar mu murja yadda nasan suke zabga soyayya da nasir dinta amma farad daya ya juya mata baya, ya nuna bai santa ba, sbd ya had'u da wacce tafita, duk gashi tazamo abar tausayi, kai al'amarin maza yana bani tsoro wlh" Allah dai ya zab'a mana mafi alkhairi, ya bamu mazaje nakwarai, wayanda zasu rikemu da Amana amin. sameera tace nikam ki dan rakani gdan yaya sauda mana , ina son kai mata kayan dinkinta ne wanda na karbo mata, khadija tace OK ba matsala sai muje, bayan tasanar da umma tace Allah ya kiyaye hanya , adai dinga addu'ah duk inda za aje, to umma in Allah ya yarda. suna cikin tafiya sai sukaji wani sassanyar murya mai dad'in sauraro abayan su, ana cewa Assalamu alaikum, gaba ki dayan su suka amsa tareda juyowa, zaune yake akan mashin dinsa (wanda ake ce ma wayyo kudina) sanye yake da shadda pink clr wandansa dai² idon sahu , fuskarsa dauke da saje wanda ya kwanta luff² gwanin sha'awa, idonsa sanye da tabarau' kallonsu yake cikeda annuri a fuskarsa" atakaice dai ustaz ne kyakkyawa ajin farko. ya karaso wajan su nawwara, yace inbazaku damu ba kudan bani minti biyu don Allah' nawwara tayi saurin cewa bakomai muna jinka, Khadija ta kalli nawwara da kyau cikin mamaki, abunda bata tab'a ganin nawwara tayiba kenan, yace da farko nidai sunana Yusuf mahammad ni dalibi ne a makarantar state universty (kasu)ina karantar islamic studies Kuma ni mazaunin kinkinau ne, ina yawan zuwa nan layin wajen aboki na, Allah ne ya hadani daku kuma take naji ina sonki kuma da aure nake sonki shiyasa bantsaya maki kwana2 ba' sonake kizamto uwar y'ay'ana, khadija ta katseshi da cewa wacce daga cikinmu? yace wannan kawar taki yanuna nawwara, itako nawwara tunda yafara zance shitake kallo muryarsa mai dadi take sauraro' yadda yake fitar da lafuzan cikin kwanciyar hankali, murmushi tayi, shima ya maida mata da martani, ya kuma cewa ko zan iya sanin gdan Ku do nakawo miki ziyara, naga kamar tsaida Ku danayi anan bai dace ba , nawwara tace ba matsala, nan tayi mishi kwatancen gdan nasu, tare da fada mashi sunanta, sukayi sallama suka wuce. sameeratu ta kalli khadija wacce ke binta da kallon, tace dijana yau naga irin mijin danake burin aure arayuwa ta, yusuf yamin sosai khadija, khadija tace ikon Allah , kice faraddaya har kin kamu, amma gsky zaku dace, course din dakike son karanta gashi shima shiya keyi, amma nataya ki murna Kawata, nima naji ya kwanta min arai, suka tafa nawwara kamar an sata a aljannah"" Allah sarki nawwara ko ya zaiyi. awwal ne da nawwar agaban mahaifin sameera sun zayyana mishi abunda ke tafe dasu, kuma yaji dadi sosai, dan yasan nawwar me kaunar yarsa ce, ko bayan ranshi baza tayi kuka da idanunta ba, yace musu shibashi da matsala, ya amince masa ya nimeta, idan sun sasanta kansu shikenan, sunji dadin maganar abban, Alhaji idrisa yasanar da hjy maimuna itama ta nuna murnan ta, nawwara taji lbarin zuwan su nawwar, inda ummanta tace taje su gaisa,, don ba wanda ya fada mata abunda ke faruwa, su awwal na zaune a falo , sameera ta shigo cikin sallama. ta gaishesu cikin faran faran, har suna zolayar juna, awwal yayi gyaran murya, sannan yafara jawabi game da abunda ke tafe dasu, ji yayi tace SO kuma da karfi. *EDIDTED* by *UMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim*πŸ’ *Pyar*πŸ’‹ kuyi hakuri sungullo line suka sha gabana [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA*🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 6⃣6⃣➡7⃣0⃣ so kuma, gaskiya ina jin kunyar ku, abar maganan nan dan Allah, awwal ya miki don basu waje" bayan fitarshi nawwar yace sameera Allah ne ya jarabce da sonki, bani na Dora mawa kaina ba, sannan kuma ke kika shigo rayuwata. nawwara bazan takura ki soni ba, amma kuma rasaki arayuwata akwai Matsala, sameera munyi soyayya dake alokacin daki ke aljanna sosai amma yanxu wannan soyayyar ta rushe, Allah sarki dama da zata dawo, sameera ki zauna kiyi tunani sameera, idan nawwar ya dace da rayuwarki ki sanar dani idan kuma bai dace ba kisanar dani ga katin number nah, cikin raunanniyar murya yace nawwara karki manta ina sonki ina kaunar, koda baki aureni ba bazan taba mantawa dake ba. yana gama fadin haka ya fita yana share kwalla, awwal yace kayi hakuri Dr komai mukaddari ne Daga Allah, idan Allah yasa nawwara matar kace to tabbas ba makawa sai ka aure ta, idan kuma ba matar ka bace to sai ka fawwala ma allah lamarinka. jikin nawara yayi sanyi da jin kala man nawwar don ya bata tausayi, amma kuma ita zuciyar ta Yusuf yake so, baza ta iya rabuwa da Yusuf ba. bayan kwana biyu, sai ga Yusuf ya zo gdan su sameera , lokacin kuma Alhaji idrisa zai shiga GDA suka hadu Yusuf ya mai sallama, tare da durkusawa kasa yana gaishar da alhajin, Alhaji yace bawaye kaba dan samari, Yusuf yace dama nazo wajen Kane abba. to bismillah mushiga har falo suka shiga yusuf ya zauna akasa,Alhaji yace me ke tafe dakai ne dan samari, nan Yusuf yafada mawa Alhaji komai game dashi, da kuma abunda yazo nema. Alhaji ya gamsu da maganan Yusuf , kuma ya yaba da halinshi, yace yusuf inta wajenane babu matsala, sai Kane mi ita sameeran in kun daidai ta shikenan, Allah ya muku albarka, amin abba, nagode sosai. bayan shigan abba cikin gda yace zainab tafada mawa nawwara tana da bako afalo Yusuf, nawwara naji taji dadi yarufeta sosai tasha kwalliya tafeshe jikinta da turare, tashigo cikin falon cikin sallama, ya amsa mata"" yana murmushi, itama ta maida mai da martani. a'a gimbiyata kin karaso tayi murmushi barka da zuwa habibina dafatan kana lfy, lfy lau , gsky naji dadin ganinki sameera, Allah ko, eh mana malamina kenan, cikin zolaya yace taya ya nazama malaminki. ta kanne ido daya cikin shagwaba tace SBD zaka dinga koya min kalaman soyayya , kasan ance ustazai sun iya soyayya, ko ba haka ba aris dina, yayi dariya, baki da dama gimbiyata. soyyay tayi karfi tsakanin nawwara da Yusuf, har ta kai da ta manta maganan da sukayi da nawwar, abvanta yasa aka kirata, yace mamana nikam wa aka tsayar ne amatsayin mijin? tarufe fuska alamun jin kunya, abba ni Yusuf nake so , kintabbata mamana, eh abba, , Alhaji yace kije kiyi tumani dai mamans, ki nutsu, kiga waya fi dacewa da rayuwar ki, to abba, tafita dakin tana tunanin maganan abba. nawwar ne akwance cikin matsinacin wani hali yau kwana biyu bashi da lfy amma yaki yabari asani, turo kofan akayi, yana kwance cikin bargo sai rawan sanyi yakeyi, Mami hafsat ne ta karaso cikin Saudi tana nawwar lafiya naganka a kudundu ne. zaiyi magana ne sai tari ya sarke shi, jinine ya dinga fita Daga bakin sa Mami ta rude, tana hamma meke damunka, ka boye bamu sani ba, tana ganin kamar numfashin shi yana sama, tasaka kara, Allah yaso sulaiman bai fita ba, duk suka shigo harda Mimi, mami tace sulaima kusa shi amota mukaishi asibiti, , Mimi sai kuka takeyi ,nawwar yayi ma Mami alamu da hannu tazo daidai saitin bakinshi, yana cewa Mami kiyafe min, kwanana ya kare , dib sai taji shiru, Mami tasaka wani uban ihu, tuni ta sumu. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kulli nafsin za ikatul maut. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim*πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO*πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» 7⃣1⃣➡7⃣5⃣ An wuce da nawwar asibiti da gaggawa, sulaiman ya kira awwal yasanar dashi, sun amshe shi don ceto rayuwar sa, Mami kuma Mimi ce tayayya fa mata ruwa, ta tashi tana kuka, , tace Mimi nawwar ya rasu ko? Mimi tace suna asibiti da yaya sulaiman, Mami tace maza tashi muje, a'a Mami ki kwanta ki huta ni zanje, insha Allah hamnan zai tashi da izinin ubangiji"" kai Mimi bazan iya zama agida ba ban San awani hali nawwar yake ba. To Mami tashi muje, lokacin dasu Mami suka karasa asibitin suka CI karo da sulaiman , yana safa da marwa acikin asibitin"" , yana jirin fitowan likita, Mami tace sulaiman ya ake ciki ne, hamman ya rasu ko, yayi saurin cewa a'a Mami yananan da ransa addu'a yake bukata. suna cikin magana ne Dr awwal yafito duk suka dumfaro shi Mami tace Dr lfy. yace karku damu mun samu kanshi yanxu hakama yasamu bacci insha Allah , zai dawo yadda yake karku damu. Mami ta sauke ajiyar numfashi tace mun gode , dukkan su suka shiga dakin dayake yana kwance, Mimi ta karasa wajan gadonshi tarike hannun shi, tana Allah sarki hamman na, adalilin son nawwara ka kamu da wannan cuta, hamman na isha allahu nawwara matar kace INA ji ajikina. sameeratu zaune adakinta ita da khadija, tana bata labarin abunda abbanta yace mata, khadija tace sameera me kika gano cikin maganar abba, na lura abba yana son na mijin dazai rike mishi ke sosai kuma ya kauna ce ki, shiyasa yace kije kiyi tunani. hakane Indai wannan AI nasamu, tunda ga Yusuf yana matukar sona hakane, yauwa nawwara nikam ya zancen maganar nawwar ne, nawwara tace ni Sam na manta da wani nawwar ma. khadija ta kalleta da kyau tace sameera inda zakiji ta tawa ni aganina, duk duniyar nan babu mai sonki kamar nawwar, shi yafi dacewa da yazamo mijinki, ki kalla fa irin kasadan da yayi adalilin sonki, ya kamata kixau na ki duba zancena. sameera tayi shiru kamar mai tunani, sai alokacin ta tuna da katin numbern wayan daya bata, ta sauke ajiyar zuciyarta, Allah dai yashige mana gaba amin, cikin mafarki sameeratu taji kamar ana ce mata. sameeratun nawwara karki yada soyayyar da nawwar ya miki kimishi halarci, shine masoyinki na asali, mai kaunar ki, mai tausayinki, kuma shine mijin da iyayenki suke son ki aura ki daure ki amshi soyayyar sa, don yanxu haka yana cikin wani hali kitaimaki nawwar dan Allah. tayi saurin bude ido tana dube dube cikin tsoro ta kudundune tana addu'a. nawwar zaune a asibiti ya samu sauki Mimi na bashi abinci abaki tana mai hira yana dariya, Mimi tace hamma dan Allah ka daina dumawa in Allah y yarda sai ka auri aunty sameera, yayi murmushi, yace Allah ya yarda yar kanwata. ansaka ranar auren nawwara da Yusuf sai shirye shiryen biki akeyi, abun mamaki kuma Sam nawwara bata zumudin yin auren Yusuf din , hankalinta na kan nawwara. tana son sake ganinshi don tasan halin dayake ciki, SBD tana tayawan mafarkai mafar kai, duk ta sukurku ce. biki sai matsowa yakeyi nawwar kuma ya warke amma har yanxu yana tunanin nawwara, kuma gabanshi na yawan faduwa, addu'oi kawai yasa gaba. yau jumma'a ya kama ranar auren sameeratun nawwara da Yusuf, wajen daurin aure ya Tara mutane da dama ga ustazai ango Yusuf sai washe baki yake. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *PYAR*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» 7⃣6⃣➡8⃣0⃣ Ango Yusuf sai washe baki yakeyi, yayin da abangaren amarya ji take kamar tayi hauka saboda bakin ciki, jitayi bata son auren"" hankalinta y karkata kan nawwar. tana son ta kuma sashi a ido kafin akaita dakin aurenta, khadija ne ta dafata tace lfy nawwara kike irin wannan tunanin? tun da'zu nake miki magana amma hankalinki ya tafi wani wajen, gashi baki shirya ba kuma kin San ana sauko Daga daurin auren abokanan ango wajenki za su zo. sameeratu ta sauke ajiyar zuciya tace khadija kin San Allah Sam bani son auren nan da da yadda zanyi Dana warware auren, vaki galala khadija ta bita dashi cikin mamaki. tace nawwara kinsan me kike fada kuwa anya kina cikin hankalin ki kuwa?bafa auren dole ake miki ba, ke kika zaba mijin da kanki, ko kin manta ne, nawwara tayi murmushin da bai kai ciki ba, tace tabbas ni nazabi Yusuf daya zama mijina amma kuma yanxu Sam bani sonshi , hankalina y karkata kan nawwar, ina son Insan halin dayake ciki khadija. sai ga hawaye yana gangaro a idanunta, ni ban San meke damuna ba, da nayi tunanin Yusuf shi yadace da rayuwata, sai Daga baya nagane, nawwar shine mijin dayafi dacewa dani, shine mutumin daya kaunace ni tun fil azal, har gida ya biyu ni, yana rokon barar soyayyata, ayayin da idonshi cike da hawaye, muryar shi adaushashe. kalma na karshe daya furta min yace nawwara koda baki aureni ba, bazan taba daina sonki ba har abada, taci gaba da kuka , tace khadij sai yanxu nasan ina son nawwar fiye da yadda kike zato, amma ina lokaci yakure, nayi Dana sanin da banta bayi arayuwata ba khadija. takara fashewa da kuka, khadija na lallashinta da ban hakuri, dakyar tasamu kanta har tashirya, alokacin kuma abokanan ango da shi angon sun isu har an daura aure. Abangaren nawwar kuma tunda aka daura auren nawwara gabanshi ke fadi sai addu'oi yakeyi, duk kan su suna zaune afalo suna hira Mami da nawwar da sulaiman da Mimi, duk sunsha ado, Mimi tace hamman na yace na'am autar Mami, yau zan maka wani kyauta Dana Dade ina son in maka, yace Allah ko,. eh mana ko bakaso ne, me zai hanani son kyautar da autar mu zata min sai suka saka dariya, yauwa hamman nah, shiyasa nake sonka, amma menene goron albishir dina, yace duk abunda kike so zan baki. tace ko menene natambaya zaka bani , sosai ma, to shikenan Allah y kaimu anjima, Mami yaya sulaiman duk kuna shaida ko, suka ce muna sheda Mami tace Mimi yau yaushe zaki fitar mana da mijinki mugani , cikin shagwaba Mimi tace kai Mami dudu du nawa nake, amma koda yake nayi sabon saurayi very soon zaku Ganshi, sulaiman yace Allah yashirye ki Mimi Sam baki da kunya, agaban mu kike wannan zancen. cikin shagwaba mimi tace hamman kana jin yaya sulaiman ko, yi hakuri rabu da sulaiman yana kishi ne din jiya budurwar shi tace bazata auri mai gemu ba sai ya aske, duk kan su suka kwashe da dariya. karfe biyar na rana inda za awuce da amarya gdan angonta dake kaduna , bayan iyayenta sun mata nasiha sosai tayi kuka rabuwa da iyayenta jitakeyi kamar ta gudu, da zainab kanwarta akatahu da khadija sai aunty sauda da kanwar baban su. sun iso Kaduna lfy Inda aka wuce da amarya gdanta dake malali halliru dan turo, gdan da aka kai amarya ya basu mamaki, gdane tsararre komai nashi dadai, amma kuma basuyi zaton yasuf yana da kudi hakaba, SBD dan makaranta ne shi. baki an vasu dakin daza su kwana ita kuma amarya tana dakinta tsakiyar gado sai sheshshekar kuka takeyi, tana bakin cikin kasan cewarta haka amatsayin matar Yusuf. Mimi ce tace hamman kai fa muke jira sulaiman ma yashirya Mami tace nikam wai ina zaku hakane, wlh Mami wani waje zamuje, sai ga hamman ya fito cikin tsadacciyar shadda Wanda Mimi ta dinka mishi sai kamshi yakeyi, yafito a fillon shi saf, duk kansu sunyaba da kwalliyarshi, don yayi kyau, kamar wanda baida damuwa. hon din mota sukaji awaje awwal ne shima yazo dashi za atafi, dukkan su suka fito haraban gdan , suka shiga muta suka wuce, hon sukayi mai gadi ya bude musu suka shiga cikin gdan, nawwar mamaki ne yacika shi, inane nan kuma, Yusuf ne da abokinshi suka karaso cikin murna suka tarye su, yayin da aka masu ISO cikin gda. mimine tace hamman dina kaga wancen dakin to kashi ga kyatar Dana maka yana ciki , dan Allah ka isa ga kyautar nan hamma n kuma kamin alkwarin zaka karba kyautar nan. yayi murmushi me hade d mamaki yace ya amince, yakarasa wajen daki gabanshi sai faduwa yakeyi, yabude dakin tare da sallama, nawwara dake kan gado taji gabanta ya fadi don bazata iya manta muryannan ba, icon nawwar ya sauka akan abunda ya hango kan gado yana mamaki yakarasa wajen batare da ta dago ba, kirjinshi na har bawa itama haka , cikin tsoro yasaka hannu ya Daga gyalen dake rufe afuskar nawwara dago kai tayi, suka hada ido da nawwar kowannan su ya zaro ido waje cikin tsoro. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TKU UMMU RUMAN πŸ’ *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 8⃣1⃣➡8⃣5⃣ suka hada ido da nawwar kowannan su ya zaro ido waje, yayi saurin sake gyalen tare da mike wa tsaye, yana ja da bays, itama saurin tashi tayi tana murxa idanuwanta shin mafarki takeyi ko da gaske ne . har sai da ya Isa bakin kofa zai fita yaja burki ya tsaya, yayin da zuciyar shi ke harbawa, ya juyo don kara gasgata abunda ya gani, still dai nawwaran ce ba wata ba. yashiga tunani me kanwarsa take nufi ne, tana nufin sameeratu ce kyautar data mashi? sameera data zuba mawa nawwar ido takasa magana itama azuciyarta, tunanini take, anata zaton nawwar abokin mijinta ne Yusuf. cikin murya sassanya sameeratu tace yaya nawwar, ya juyo da dubanshi gareta, tare da kara so wa wajenta, hawaye na zuba a idanunshi, yana mata wani irin shu'umin kallo na soyayya, yayin da itama haka. takara cewa yaya nawwar kaya fe min nayi kuskuren daya zame min Dana sani, nakin amsar soyayyarka, alokacin son Yusuf ya rufe min idona, bana ganin kowa sai shi, sai da akasa mana ranar aure, sannan hankalina ya dawo gareka, gashi yau Yusuf shine matsayin mijin Dana aura takara fashewa da kuka. nawwar najin haka yaji jiri na son dibanshi zai fadi kenan, ta taho da sauri cikin kidima ta tareshi ya zauna bakin gado ya dafa kanshi da hannayen shi, yana salati" yace sameeratu lokaci ya kuri narasaki har abada, tace kayi hakuri nawwar nice da wannan kaicon don xuciyata tana tare da kai, baxan taba manta ka ba Nima sai ta fashe da kuka. ya matse wani hawaye mai radadi tare da cewa narasaki har abada nawwara, ji sukayi ance hamman dina Baka rasata ba hasalima kun kasance a inuwa daya wato mata da miji. gaba ki dayan su suka tashi don kallon mai magana, Mimi ce ke karasowa cikin dakin, yayin da Yusuf da awwal da khadija da zainab suka shigo" cikin murmushi, Yusuf yace kaji masoyan asali Mimi tace aikuwa. nawwar yace Mimi mekike nufi, tace hamman nah ina nufin aunty sameera matar kace itace kyautar Dana maka, nawwara ta kalli Yusuf don Neman Karin bayani. tace Yusuf kafahimtar dani abunda naji, yace nawwar abunda kikaji gsky ce da nawwar aka daura miki aure, ta kara kallon khadija da zainab suma suka Daga mata kai alamun haka ne. nawwar da nawwara kamar sun hada baki sukace atare, tayaya hakan ta faru, awwal yace yanxu Mimi zata fada muku. Mimi ta soma magana tace, hamman in baka manta va lokacin da aka kwantar da kai a asibiti na maka alkwarin insha allahu sai ka auri nawwara, to tunda ga lokacin nadauki aniyar nemo nawwara, SBD bana son in rasaka, da haka naje nasamu Dr awwal nafada mishi kudirina , shima ya aminta. takanas mukaje kano dashi, alokacin ma ana shirye shiryen bikin nawwara da Yusuf, lokacin ZANU shiga gdan sai muka ga zainab da khadija, muka gabatar musu da kanmu da abunda ke tafe damu, sun nuna farin cikin su sosai. kuma sun Samar mana nawwara bata son auren da Yusuf, muka rasa ya zamuyi mutunkari Yusuf da maganar, ashe Yusuf dan makarantar su yaya sulaiman ne kuma abokinshi ne, to shine nasanar masa, shikuma yafada mawa Yusuf cikin sauki Yusuf ya amince, SBD amintar dake tsakanin su da yaya sulaiman, daganan kuma muka dunguma wajan abbban nawwara muka sanar mishi. shima yayi murna dajin wannan labarin , Yusuf yace kar asanar ma nawwwara sai dai kawai taganta da nawwar, Nima haka nace kar asanar mawa nawwar, sai Mami kadai da Abban mu, to kunji yadda akayi. nawwar ya rungume yar autar su yana thank you my sister, Ashe haka kike sona daya, lallai na jinjina miki Allah ubangiji y baki miji mafi alkhairi, kowa yace amin. itako tace Allah ya bani Yusuf hamman nah, nawwar yace mene cikin dariya sulaiman yace AI Yusuf ke sonta. itako nawwara tana jikin khadija tana kukan murna da Allah ya nuna mata wannan rana, gaba ki dayansu suka fito falo don su Mimi zasu koma GDA, nawwara da nawwara sai Satan kallon juna suke. khadija taci Mimi AI nikam binku zanyi don idan na kwana gdannan zan kwashi kayan haushi SBD nasan za agurji soyayya gara nayi can, bakiga ma yadda nawwara ke harara ta va, alamun bata son inkwana don karna takura su, sameeratu takai ma khadija duka. Yusuf ya ijye musu gazan amare da su drinks yace amarya da ango mun barku lafiya, so Ku nuna mawa duniya kunfi *king* *laisu* da *rumana* na takaddan *kutausaya* *min* iya soyayya dukkan su suka kwashe da dariya. bayan tafiyan su nawwar ya janyo nawwara cikin jikinshi ya rungumeta yana ma Allah godiya daganin wannan ranar, bayan sunci sunsha sun gabatar da sallan da akeyi, tare da addu'oi, daganan kuma sai zance ya canxa salo, inda suka Lula duniyar ma'aurata, ina ganin haka nayi waje abini don kunya, amma nabar hjya seeema, zasu gano muku. kubiyoni agaba donjin wani soyayya zata kasance agdan ma'auratan nan. *EDIDTED* by *UMMEE* *ADNAN* TAKU UMMU RUMAN πŸ’. *Nusnim* πŸ’ *pyar*πŸ’‹ [12/25, 8:33 AM] Nusnim: 🎭 *ALJANA* 🎭 πŸ’ *CE* *KO* πŸ’ πŸ™ŽπŸ» *MUTUM* πŸ™ŽπŸ» πŸ’ *By* *Nusnim*πŸ’ 8⃣6⃣➡9⃣0⃣ su Mimi sun Isa gda tare da ba mawa Mami labarin yadda suka baro su hamman din, Mami taji dadi sosai kuma tayi musu addu'an fatan zaman lafiya da dorewa. Mimi tace Mami ina aunty sauda, Mami tace AI tun lokacin da aka kawota, ta kwanta SBD gajiyan biki, hakane kam gashi sunsha hanya. ASUBA TA GARI. nawwar ne yatashi Daga bacci don yin alwala SBD zuwa masallaci, ya tsura mawa nawwara ido"" yana kallonta, yayi murmushi tare da shafo gefen fuskarta. bayan tafiyar shine itama ta tashi donyin wanka sannan tazo tayi sallah, bayan ta idar tafara karatun alqur'ani, lokacin kuma nawwar ya dawo masallaci. ya yaba da hazakarta, don da ka take karantawa, bayan ta gamane ta juyo sukayi ido hudu dashi ta sunkuyar da kanta kasa tana gaisheshi, ya amsa mata cikin murmushi, tare dace wa y gajiyan biki da sabon wuri kuma, tace gajiya kam tabi gado. yace masha Allah haka akeso, yace nawwara ki saki jikin ki dani ni mijinki ne mai kaunar ki, in Allah y yarda bazan taba barin wani abu y same kiba , nan suka fayya ce mawa junan su irintarin son da sukeyi wa juna, daganan kuma suka koma bacci" sai wajajen karfe Tara suka tashi, ya wuce bangaran sa don ya shirya. itama tashiga wanka bayan ta fito ta tsara adonta mai kyau cikin atamfa , tana cikin shirya wane taji hayaniya a falo, su khadija ne suke hamman tsiya Mimi tace ango kasha kamshi, irin wannan kwalliya haka, sai kace za aje gasar kyau,, lallai aunty mu ta iya shirya ka"" suka kwashe da dariya" dai dai lokacin nawwara tafito. duk suka zuba mata idanuwa Mimi ce takara sa ta rungumeta tare da cewa barka da safiya auntyn mu, yauwa Mimi iyayen surutu, tundaga daki nakejin muryanki kina ma angona tsiya. khadija tace a lallai nawwara har kin samu bakin magana, zainab tace aunty khady ba dole ba, zama da masoyi dadine dashi fa,, Mimi tace hakane kam, suka bushe da dariya. Mimi tace ga breakfast dinku nan Mami tace mukawo muku, nawwar yace AI yanxu nake son dama muje wajan mamin don taga amaryata"" ya janyota jikinci tare dacewa muje muyi breakfast, suko su khady zuba musu ido sukayi cikin sha'awa. bayan sun gama suka dunguma can gdan Mami tayi murnan ganin nawwara kuma rayaba da ita'. tayi musu nasihohi masu ratsa jiki, aunty saudama tayi musu. bayan wata uku dayin bikin sameeratu akayi na khadija, alokacin ne nawwara taje ganin GDA , SBD tund tayi aure bataje ba sai da bikin khadija ya tashi, tare da sulaiman da Mimi sukaje, shi sulaiman zuwanshi da biyu yayi SBD zainab kanwar nawwara. lokacin nawwara da cikin wata biyu ajikinta, iyayenta sunyi murnan ganinta, don takara kyau alamun hankalinta akwance,, SBD nawwar na tattalinta suna gurje soyayya, daidai da girkima shi yake mata, ga Mimi kuma nataya ta wasu ayyukan SBD gata da akanuna mata. bayan wasu yan watanni nawwara ta haifo santalelen danta mai kama da babanshi, kar kuso kuga murna wajen Mami kamar zata cinye yaron, anti suna Inda yaro yaci suna Ahmad ana kiranshi da (usaimin). suna samun kula, bayan sunyi arba'in ne akayi bikin Mimi da dan ustaz Yusuf da anso a hada dana sulaiman waje daya, ska fasa SBD hidiman zayyi yawa. nawwara ta sake yin JAM na state uni dake Kaduna wato Kasu inda zata karanta Islamic studies, cikin sauki tasamu masugunni a Kasu, tafara karatun ta cikin sa'a, arzikin mijinta bunkasa take. usaimin awajen Mami yake zama SBD makarantar nawwara, anxo anyi bikin zainab da sulaiman , abun gwanin ban sha'awa . akwana atashi bawuya wajan Allah shekaran auren su nawwar 6, yau weekend duk suna gd babu aiki tare da yaran su guda biyu Ahmad (usaimin) sai maimuntu (mubina) , duk suna zaune afalo ana hira, nawwara ta kwanta acinyar nawwar, yayin da shi kuma yana mata susa akai, mubina tace, daddyna kana cirewa mummy kwarkwata ne dukkan su suka kwashe da dariya, nawwara tace, mubina a ina kika San kwarkwata? tace mummy awajen Hjy kaka wai nace ma Hjy kaka tabani dan kwalinta na daura sai tace min baza ta bani ba wai ina da kwarkwata a gashine, ta karashe maganan cikin shagwaban kuka. usaimin ya kwashe da dariya, yace hakane mana kina dashi, nan da nan tafara ihun kuka tana daddy kaga yaya usaimin ko, ya turekan nawwara y janyo mubina jikin shi yana lallashinta, bawwara tace lallai kam SBD wannan sha gwababbiyar zaka tureni bara ka gani, aiko tadare jikinshi, shima usaimin ya taho duk suka zauna jikin nawwara suka rungumeshi suna dariya yace I love you all. TAMMAT ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN ALJANA CE KO MUTUM, BADON NASO TSAYAWA ANAN BA, SBD SUNGULLO LINE SUKA SHIGE MIN GABA. *sannan* *INA* *baran* *Addu'an* *Ku* *Banda* *lafiya*. *godiya* *ga** *dukkan* *masoyana* *na* *nesa* da *kusa* *Allah* *yabar* *zumunci*. bazan manta da kuba GRP na nawa,don kunfi kowa son novel dina *ALL* *DOSTIS* *of* *NUSFULLHAYAT* da sauran grps din. *ban* *manta* *daku* *ba* *masoyana* Ummee adnan Hansai zozo hafsat rano al'eeman ummu yahaya nafee anker fati azland m jabo qurratul ayni ummu abrar jamila muhm Ali ayusha ilyasu Sheedat autar hjya *Ashnurpyar* da dukkan writers. ban mance dake ba *Ummee* *adnan* adalilinki wannan novel ya karbo, *jinjina* ta *bangirma* *Allah* ya *baki* *lafiya* *ya* *raya* su *dnan* sai kinyi ko ba poster *Ummee* *dnan*. wannan novel nawa ke na mallaka mawa *my* *shona* *shahrazad* *Allah* ya *barmin* *ke* my *shazee* soyayya cikin kwando *shahrazad*, *pyar* *hogaya* *dil* *se* *muhabbat* *se* *ana* *ashiq* *bijunun* *shahrazad* *ana* *hubbiq* ya *habibti* *lahazatil* *kalbi* *minal* *hubb* *shahrazad*. LITTATTAFEN NUSNIM *adalilin* *Sonya* *hanta* da *jini* *Kuncin* *rayuwa* *labarin* *ni'imah* *kutausaya* *min* *Aljana* *ce* *ko* *mutum*. sai kuma mai zuwa *SON* *MA* *SON* *WANI* TAKU A KULLUM UMMU RUMAN NUSNIM *BISSALAM*πŸ’ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *