adsense here
[10/28, 1:22 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 1-5🍒
Tana bacci taji saukar ruwa saman kan ta, take ta zabura tana rabon ido.
Shegiya sai asamu damar tashi, waye bawan ki, koni Zan fita rafi d'ebo miki ruwanne?
Nan ta tashi ta nufi buta da niyyar alwala, take ta Kai Mata duka, tana cewa wallahi ba zaki tab'a ruwannan ba har sai kinje rafi kin d'ebo, kuma in kika bari na taradda ke can na lahira zai fiki jin dad'i, shegiya Mai Kama da aljanu.
Bahijja ta tashi tana kame-kame ta d'auki tulu ta fito daga gidan, koda ta fito wani gurin ko sallah ba atada ba, ga kuma yanayin gari da sanyi.
Koda ta fito yana rakub'e k'ofar gidan, nan ya mik'o Mata hannu ya karb'i tulu yace muje.
Tace Murtala da ka basshi, kaga kullum in ka rakani d'ebo ruwa baka samun sallar subahin, kuma kaga tana da muhimmanci da kuma d'inbin lada.
Nan yayi murmushi yace ba komai Bahijja, wataran in mun dawo ina samun masallacin malam Atiku, kuma kinga ke Mace ce bai dace Ana barin ki fito wa da subahin ba.
Nan take idon ta suka kawo ruwa tasa gyalen ta ta goge hawayen, tace na rasa me na tare ma Gwaggo lami, kullum da kalar azabar da nake fuskan ta.
Murtala yace kiyi hak'uri komi yayi farko zaiyi k'arshe, watarana sai labari.
Yace muje kar ki dad'e ki dawo ta hauki da duka.
Nan suka Kama hanya sai rafi, ya mik'a Mata ledar hannun shi yace tayi sauri tayi sallah zai cika Mata tulun.
Tayi alwala ta zazzage kayan Ashe hijab ne da dadduma, nan ta shimfid'a tayi sallah a gurguje ta gama, ta ninke kayan ta saka a Leda.
Nan ya d'auko Mata tulun suka nufo hanyar gida, tace Murtala ka kawo tulun in d'auka kayi sauri kaje ka samu jam'i, sai in k'arasa gida.
Yace to kije da kayan gida mana.
Nan ta gwalo manyan idon ta tace wallahi Gwaggo zata iya yan kani akansu, kaje dasu kawai nagode.
Yace Mata Ina ganin Maigari zai tura ni sokoto ne sayen wasu kaya kuma k'ila zanyi kwana biyu can.
Kinga ba kida abin sallah in kin fito, kuma babbar damuwa ta ba Wanda zai raka ki rafi.
Nan tashin hankali ya bayyana ga Bahijja jin kalaman shi, sai ga hawaye shar sun wanke fuskar ta.
Nan dai ya samu ya rarrashe ta kan cewa kamin ya wuce zai San abinda zaiyi akai.
Jin tada sallah masallacin Mal Atiku yasa yayi saurin wuce wa saboda ya samu jam'i, ita kuma ta wuce gida.
® *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:22 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 5-10🍒
Shigar ta gidan keda wuya Gwaggo lami ta sauke tulun daga saman kanta kamar abin arzik'i, sai ta hau ta da jibga tana fad'in shegiya kullum na aike ki rafi sai kin yi tsaye-tsayen ki saman hanya.
Kuma kinsan Zan d'ora ruwan kunu, kina yimin bak'in cikin abinda Zan samu.
Jin turo k'ofar gidan ne had'e da sallamar Mal salisu yasa ta rik'o hannun ta tana fad'in sannu Bahijja, Ina fatar bakiji ciwo ba, tashi in gani.
In har da sabo Bahijja ta saba da wannan makircin na gwaggo duk azabar da take ga namata in har Baban ta na gida to zata yita tarairayar ta tamkar k'wai.
Nan malam ya k'araso da saurin sa ya tada Bahijja yana Mai duba jikin ta, yace me ya sameki?
Nan Gwaggo ta karb'e tana Mai cewa "kasan halin ta da son aiki, tana sauri ne zata d'auki tulu zuwa rafi taci Karo da ice shine ta fad'i.
Mal yace Bahijja ki dinga yin abubuwa a hankali duk da nasan ki da natsuwa.
Tace to Baba, tana Mai kakkab'e jikin ta.
Yace tashi kiyi wanka kamin Gwaggon taki ta gama kunu.
Ta ebi ruwa duk da taga mugun kallon da Gwaggo ke binta dashi, ta wuce toilet saboda in har zata tuna yau kwanan ta hud'u rabon ta da wanka.
Dama in har ta samu wanka gidan to Baban ta ke gidan.
Hakan ta fad'a ta darji jikin ta da ita kanta kejin tsamin shi.
Koda ta fito Gwaggo ta dama kunun, agurguje ta d'auko wasu kod'add'in kaya Nata Zane daban Riga daban ta saka.
Shigowar Gwaggo taji, nan take ta zabura.
Nan ta Kai Mata rank'washi ga Kai, tace wallahi dakin dawo sai kin ebo ruwan da kika d'iba, wato gaki y'ar gata Mai uba ko.
To wallahi bud'e kunnen ki da kyau kiji abinda Zan gaya maki, duk kika kuskura yau kika dawo min da ragowar kunun wallahi na lahira sai ya fiki jin dad'i, shegiya Mai Kama da mujiya.
Nan Bahijja ta fito daga d'akin jikin ta na rawa, ta d'auki bokitin kunu ta fita zuwa in da take Kai kunun.
Cikin ikon Allah kamar ita ake jira mutane Nata zuwa saye, saboda Bahijja akwai farin jini ga Sana'a.
Hakan ta had'a kan kud'in ta tayo hanyar gida, nan ta had'u da Murtala suka gaisa.
Yace yau baki ajiyemin kunun ba?
Tace na jika shiru ne, na zata ka wuce sokoto d'in.
Yace wallahi tafiyar ce bata yuyu ba inaga sai wani sati, don haka gobe Zan zo muje rafi tare, nan tayi murmushi tace baka gajiya Murtala, nagode sosai da kulawa.
Nan ya rako ta har suka kawo k'ofar gida sannan ya wuce.
Tana shiga gida ta damk'a ma Gwaggo kud'in, sannan ta durk'usa ta gaida Baban ta, har ta tashi zata wuce akurkin d'akin da take zama.
Yace zo kisha kunu y'ar Baba, hadda k'osai na fita na siyo muna.
Nan ta zauna suka karya tare da Baban ta, nan yace to zai fita kasuwa sai ya dawo.
Tana shiga akurkin ta ta zauna kenan, sai ga Gwaggo ta fad'o tamkar wadda aka jefo.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:23 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA*10-15🍒
Gwaggo na shigowa d'akin ta hau ta da jibga, wato ke gaki y'ar gata, har da mik'e k'afa kisha koko da k'osai tare da uban ki, ni sai dai bani kad'an ga hannu.
Wayyo Gwaggo kiyi hak'uri bazan k'ara zama da Baba in karya ba.
Rufemin bakin ki shegiya Mai Kama da aljanu, tashi maza kije rafi ki d'ebo min ruwa na da uban ki yasa kika iba kika yi wanka, ke ga Mai tsafta ko, ta koma kaima rank'washi ga Kai.
Nan ta zabura jiki na rawa ta fito ta d'auki tulu.
Gwaggo tace zo nan, nan ta Fara yarfe hannu tana dire k'afa k'asa tamkar Mai jin fitsari.
Tsawar da ta daka Mata ne sai gata gaban ta durk'ushe bata shirya ba.
Nan ta Kama Mata kunne ta murd'e sai da ta sako fitsari kad'an, tace wallahi muddin kika fita kika dad'e sai na kusa yanka ki a gidannan.
Kinga ga tukunyar wake can saman wuta tana jiran ki zaki fita talla.
Nan ta tashi tana rawar jiki tana kuka, sai murza kunnen ta take yi Wanda take ji tamkar zai cire daga mazaunin shi.
Tana fitowa taga k'awar ta lantana waje tana jiran ta suje rafi.
Lantana ta tarbo ta ta karb'i tulun daga hannun ta, tace har Zan shiga gidan Ku naji waccan masifaffiyar matar na maki kashe di, shiyasa na dawo daga waje na tsaya.
Kinsan ni bama shiri da ita, don Ina Mai tabbatar miki in Ina shiga gidan ku watarana sai an karb'e ta hannu.
Nan Bahijja tayi murmushin dole, tace ni abinda ma keban mamaki da ita, wallahi gaban Baba sai ta dinga tarairaya ta tamkar ta had'i yeni.
Lantana tace gaskiya inni ce sai na gayama Baban abinda take yimin.
Bahijja tace da wataran sai ta yanka ni, kesan bata da imani Ko kad'an.
Haka suka yita tad'i har suka je rafi suka dawo.
Lantana tace kiyi sauri ki d'auko wake da shinkafar ni ko Zan d'auko alale sai muje tallar.
Tace to Allah yasa kar in taradda wani aiki, da saurin ta ta fad'a gidan.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:23 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 15-20🍒
Sun fito suna tafiya suna tad'in matsalar Gwaggo lami, kowa da abin Sana'ar shi saman Kai.
Dai-dai zasu karyo kwanar inda suke ajiye abinci saiga mota ta karyo aguje, nan ta kwashe Bahijja ita ko lantana ta samu ta kauce.
Ai ko Mai motar ya fito da sauri ya nufosu, daka kalli Bahijja kasan tana cikin tashin hankali.
Gashi duk man waken ya b'ata Mata jiki, kuma ta d'an goge a gwuywar hannun ta da kuma yatsan ta dake fitar da jini.
Mutane sun taru saman kanta ana duba jikin nata, amma ita cewa take yi ta shiga uku yau sai Gwaggo ta yanka ta, nan lantana ta k'araso kusa Gare ta tana fad'in ya jikin naki?
Tace ki taimaka min lantana yau zata kashe ni, ta d'ora hannu a ka tana na shiga uku.
Nan Shureim ya bita da kallon mamaki, yace baiwar Allah ki bari agani in baki ji ciwo ba.
Ta bishi da kallo tana cewa zata kashe ni wallahi.
Lantana ta Kama ta ta mik'e amma daka ganta kaga zararra, nan ta ja ta suka yi gefe, shima Shureim ya bisu.
Nan yake basu hak'uri kan kuskuren da aka samu, ya d'ora da cewa wallahi akasi aka samu Ina sauri ne.
Lantana tace ba komai bawan Allah sai dai gaskiya akwai Matsala babba, nan ta kwashe komai ta gaya Mai.
Yace ba matsala, Ina ne chemist d'in garinnan sai muje ayi Mata dressing d'in raunin da taji.
Lantana ta bashi amsa da cewa yana kan hanyar da ya biyo, can baya kad'an.
Yace to Ku shiga mota muje a duba ta.
Nan lantana ta zaro ido tace kaje mu zamu biyo bayan ka, amma ya zamu yi da wa'annan kayan?
Yace kinga waken ya zube duka ba abinda zai amfanu daga ciki kawai Ku had"a kayan Ku, nan ya Kira yara yace lantana ta raba masu alalen.
Bayan sun je an Mata dressing d'in ciwukan ya basu kud'in da shi kanshi bai San adadin su.
Nan suka had'a kayan su suka yi mar godiya suka nufi hanyar gida, shi ko yana k'ara basu hak'uri.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:23 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 20-25🍒
Gidan su lantana suka zarce, suna shiga Inna Habiba ta buga taslima tace me ya faru Bahijja kika yi wujiga-wujiga haka?
Lantana tace wallahi Inna wata k'addara ce muka gamu da ita, nan ta kwashe komi ta gayama Inna.
Inna tace ai anyi arzik'i, tunda abin ya tsaya iya nan, injin jikin naki da sauk'i?
Bahijja tace eh Inna sai dai yatsana dake min zogi.
Tace to Allah ya sauk'ak'a, ta d'ora da cewa gaskiya kun samu mutumen arzik'i, saboda y'an birnin nan ance wulak'anci ne dasu.
Lantana tace gaskiya Inna wannan yanada mutunci, kinga ma kud'in da ya bamu ina ga har sunfi k'arfin kayan mu.
Nan Inna ta karb'i kud'in ta Saki baki bayan ta irga, tace yo ni duka alalen d'ari uku da hamsin na d'ora maki, kefa Bahijja?
Tace duka cemin tayi Inna kawo k'asa da d'ari takwas sai ta b'allani.
Inna tace to kinga shi dubu biyar ya Baku, nan suka zaro ido suna kallon Inna.
Tace yi sauri Bahijja kisa kayan ki ruwa ki wanke in suka bushe kisa ki wuce gida.
Tace Inna banni a hakan in naje gida na wanke.
Inna tace ga kud'in na cire nawa na alale wa'annan sai ki kaima Gwaggon ki.
Tace a ah Inna ki ajiye muna gurin ki nida lantana, ni Zan wuce gida.
Nan ta d'auki kayan ta ta nufi hanyar gida, jikin ta sai b'ari yake yi, tana shiga ta hango Gwaggo zaune gaban murhu tana hura wuta.
Taje gurin ta tace Gwaggo barka da gida, bata ko ansata ba saita mik'o hannu alamar ta bata cinikin, nan ta damk'a Mata, ai ko sai ga haurun Gwaggo waje sai dariya take yi.
Tace hala wani dan arzik'i kika had'u dashi ya yi maki juye?
Nan ta bata labarin abinda ya faru, har tana nuna Mata ciwukan da taji had'e da maganin da Shureim ya bata.
Take ta warce maganin har tana had'awa da yatsan ta da akayi mata dress d'inshi.
Nan ta Saki wata k'ara takai zaune dab'ass.
Gwaggo tace da kisha wannan maganin k'ara in saka shi wuta, shegiya Mai shegiyar fuska, aini naso ace da motar ta d'auke ki kar ta dire ki sai lahira in huta da jaraba.
Bahijja na nan zaune tana kuka jikin ta duk ya fara tsami saboda ciwon da gab'ob'in ta keyi, ga kuma yatsan ta da takeji tamkar zai gundule.
Gwaggo tace tashi maza ki b'ace min da gani, kin tsare ni da idon ki masu Kama dana mage.
Tana d'aga hannun ta zata kai Mata duka, sai ta tsin kayo sallamar Malam.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:24 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 25-30🍒
Hannun ta sauke ta ringa goge Mata jikin ta, tace Bahijja ki dinga kula da hanya kina tafiya a hankali.
Nan Malam ya k'araso yana fad'in meke faruwa?
Gwaggo tace wallahi wani Mai mota ne ya kad'e ta, duk tayi b'arin kayan kaga jikin ta duk Mai ne.
Tace sannu kin ji tashi ki cire kayan in wanke maki.
Tace basshi kawai Gwaggo Zan wanke.
Malam yace y'ar Baba garin yaya hakan ta faru?
Nan ta kwashe komi ta gaya Mai, Gwaggo ta d'ora da cewa ai mutumen yana da mutunci don ya biya kud'in har chemist ya Kai ta.
Nan Malam yace ni dai wannan tallar na soke ta, banga abinda na rage ku da shi ba a gidannan, y'ar Baba na neman halaka garin yawon talla.
Ko yanzu da Allah bai tak'aita ba da sai dai mu rasa ta.
Nan Gwaggo ta d'ora hannu saman Kai ta fasa kuka, oh ni lami! Naga ta kaina.
Babu komi dama nasan duk dad'ewa sai an goran tamin rashin haihuwa.
Yarinyar nan tun tana k'arama nake wahala da ita, sai yanzu da zanci moriyar ta za a nuna min bani na haife taba.
Kuma duk Sana'ar nan da nake yi ita nake ajiye ma kayan d'aki koda auren ta ya tashi.
Ita dai Bahijja ta bita da kallon mamaki, in har da sabo ta saba da wa'annan abubuwan.
Ganin take yi duk duniya babu makirar macce sama da lami.
Malam yace kiyi hak'uri lami, Bahijja dama y'ar kice halak malak, kuma ban rai nama kulawar da kike bata ba.
Allah ya saka maki da mafificin alkhairin sa, kiyi hak'uri kin ji lami.
Nan ya Kama hannun Bahijja ya Kai ta d'akin shi, yace bara in Kai maki ruwa kiyi wanka zaki d'an ji damar jikin ki.
Ya cika roba da ruwa ya Kai Mata toilet, tana shiga ya d'auko kayan da ta cire yasa ruwa.
Gwaggo ta taso tace kawo Malam in wanke.
Yace jeki huta Zan wanke, gashi na b'ata maki rai.
Nan tayi murmushin mugun ta, tace ai ba komai Malam ya wuce.
Bakasan ya nake jin Bahijja a raina bane shiyasa, haka nake jin ta tamkar ni nayi nak'udar ta.
Nan dai suka yita hira har ya wanke kayan ya shanya.
Bahijja na fitowa Gwaggo ta bita da kallon zamu had'u ne.
Nan ta fad'a d'aki jiki sai rawa yake Mata, ga zazzab'i ga tsoron gamon ta da Gwaggo.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:24 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 30-35🍒
Shureim na shigowa gidan Dad d'in shi na saukowa daga stairs, yace Dad na Kai mashi kuma jikin nashi da sauk'i sosai.
Dama na gaya ma wannan tsohon ba wani ciwo ke damun shi ba face kwad'ayi.
Dad yace son ubanka ne Mai kwad'ayi ba mahaifina ba, nan Shureim yayi dariya sosai.
Mum tace Kai dai kayi rok'on Allah mahaifan ka su kai tsufan shi da nagartar shi, suna tare da Kai.
Shureim yayi murmushi, yace Mum yau naga ikon Allah.
Wallahi yarinya na kad'e da mota kowa ya taru ana jimamin abinda ya faru, amma yarinyar nan kukan waken da ya zube take yi.
Mum tayi murmushi tace kai mutumen k'auye sai a barshi, baiwar Allah yana yuyuwa shine hanyar cin abincin su.
Yace Ina tunanin wadda ta d'ora Mata tallar kamar kakar ta ce ko kuma kishiyar mamar ta.
Mum tace wasu mutanen basu da imani, duk yada aka basu amana sai sun yi zalinci, Allah dai ya shige muna gaba.
Ya amsa da Ameen, har ya tashi zai shige Mum tace Lateefa tazo muna Hutu d'azu, tana ta Neman ka.
Nan ya had'e fuska yace yayi kyau, kawai ya wuce d'akin shi.
Koda ya watsa ruwa ya fito daga toilet ya taradda ita zaune saman gado.
Tace S.S kimba kwana dayawa, in har bani nazo ba Kai ka Saki zumuncin.
Sai da ya k'ara had'e fuska sosai, sannan ya cemata get out of My room.
Jin maganar da yayi cikin tsawa ya bata tabbacin bada wasa yayi maganar ba.
Nan take ta fito falo taga Mum zaune na kallo ta fad'a saman jikin ta tana kukan sangarta.
Mum tace waya tab'a min ke Latee?
Shureim yace Mum har yaushe Zan gaya ma yarinyar nan ta daina shigomin d'aki ba excuse, na gaya Mata duk abinda take so ta Bari sai na fito falo muyi maganar.
Lateefa tace gaskiya ni nagaji da wulak'an cin Kimba, yau Zan tattara kaya na in koma gidan mu inda Nafi gata da tarairaya.
Bayan ta wuce fuuu d'aki, Mum tace haka kakeso ko son?
Yace wallahi Mum don kun sangar ta tane, kamar wannan k'atuwar zata rik'a yiwa mutane Abu tamkar y'ar sha biyu.
Mum ta karb'e da cewa sai ka bita d'akin ka rarraso ta ko zata sauko.
Yace Mum ni rashin tarbiyar Latee ne bata yimin ba, haba dube ta ta saka wasu kaya tamkar gidan inyamurai.
To ka rik'a yi Mata a hankali zata gane, cewar Mum.
Nan ya haura sama ya tunkari d'akin da take sauka in tazo gidan, yana tura d'akin zai shiga da k'arfi ya janyo k'ofa yana maida numfashi.
Sai da ya k'wank'wasa k'ofa ta bashi iznin shigowa sannan ya koma.
Koda ya shiga ta saka kayan ta, dama abinda ya fitar da shi Karon farko, koda ya shiga ya taradda ita daga ita sai bra da mini siket.
Ya samu wuri ya zauna yace "Latee kiyi hak'uri, ba wai bana son kusanci na dake bane, shigar da kike yi ce bana so.
Kinga bai dace ace duk yanda kika so hakan kike zama ba, dubi ko yanzu shigar da kika yi.
Ya nuna ta da yatsa yace dube ki wai wannan Riga ce kika saka, cibiyar ki sake gaban ki ma hakan, siket ke kan ki baki samun tafiyar walwala, haba Latee ya Kama ta ki gyra d'abi'un ki.
Nan ta bishi da kallo cikin muryar ta ta sangar ta tace nifa Kimba kasan bana iya d'aura Zane takuramin yake yi.
Yace to ki rik'a saka dogayen riguna mana ko kuma irin Pakistan haka, tunda sune Riga da wando.
Yace kishirya mu fita in siya miki, amma fa ba zaki Bini hakan ba ace an ganni da Wata k'abila, yana maganar had'e da murmushi a fuskar shi.
Tace yanzu Kimba nice k'abilar? Ta had'e fuska tana buga k'afa sai wani turo baki takeyi.
Yace yi hak'uri k'anwa ta tashi muje, nan ya nufi trolley d'in ta ya duba kayan ba wasu kayan arzik'i a ciki.
Da k'yar ya samu wani dogon wando ciki, ya koma d'akin shi ya d'auko wata suit d'in shi ya bata yace ta saka.
Yana falo zaune ta shirya ta fito da dama ba laifi, ta d'ora wata hula saman kan ta.
Nan Mum ta bita da kallo tace sai Ina Latee?
Ba Kimba ne ya yita yimin fad'a ba, har da cemin ina Kama da k'abila.
Nan Mum tayi murmushi tace k'yale shi Latee ai kinfi shi kyau shiyasa yake k'yashin hakan.
Tace Mum za muje shago ne wai zai yimin sayayyar kaya ne, kinsan saura k'iris ya zama ustaz, duk yada ka saka kaya bakayi dai-dai ba.
Nan ya bita da harara yace komai zaki ce kice, amma ba ke ba saka k'ananan kaya a gidannan.
Nan dai suka fito Mum tace sai kun dawo amma fa kar Ku fita ka yita takura ta.
(Masu kiran ojoro wannan ya isa ko ak'ara? _lolx_😜)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 35-40🍒
Gwaggo na shigo d'akin ta hango Bahijja lullub'e cikin Zane jikin ta sai kyarmar sanyi yake yi.
Duk da hakan saida ta Kai Mata rank'washi ga Kai, tace zaki tashi ne kuma zamu gamu dake, Mai Kama da bebin roba.
Mal ya shigo yace ya jikin nata?
Gwaggo tace da sauk'i sai dai akwai zazzab'i, sannu kinji y'ar Baba.
Yace bara inje chemist d'in hamisu in Kira shi yazo ya bata magani, in ya dace ayi allura duk ya had'ama ta da ita.
Yana fita Gwaggo tace tashi zaune, hakan tayi k'arfin hali ta tashi sai addu'a take jerawa a zuciyar ta na neman kariya da muguntar Gwaggo.
Kamar addu'ar ta Kama ta sai kuma tace koma ki kwanta zamu had'u ne in kika samu sauk'i, sai ta juya ta fita daga d'akin, Saida Bahijja ta Saki ajiyar zuciyar da ni kaina sai da na jiyo ta.
Jin sallamar malam shida hamisu ne ya sa Gwaggo tayi saurin dawowa d'akin, saboda tana tsoron kar asirin ta ya tonu cewa an bada magani ta karb'e ta k'one.
Bayan sun shigo ne ya duba ta sai yakai duban shi ga malam yace ai d'azu Wanda ya kad'e ta da mota yaje da ita guri na har magani an bata, naso in had'a Mata da allura tace bata so.
Nan Bahijja ta Kai duban ta zuwa ga Gwaggo, suna had'a ido da ita ta watsa Mata mugun kallo cikin sauri ta kauce fuskar ta.
Nan ta Kama in-ina tana fad'in immm ina.. Nidai, Baban ya bita da kallo yace ki natsu y'ar Baba ki gayamin ina maganin.
Cikin muryar ta tsoro da kuma zafin ciwon da ke damun ta, tace Ina ga Mai motar ya manta ne ya wuce da maganin don bai bani ba.
Hamisu yace lantana fa ta karb'a da kanta.
Cikin ran Gwaggo tace wannan shegen Mai bin k'wakk'wafi tamkar d'an jarida yana so ya tona min asiri.
Tsinkayo muryar Bahijja tayi tana cewa ai bayan mun fito ne ya karb'a yace zai duba in maganin bai lalace ba, daga hakan inaga mantawa yayi bai bamu ba, nima mantawa nayi.
Nan Gwaggo tayi wata b'oyayyar ajiyar zuciya, hamisu yace to yanzu bara ayi Mata allura sai abata wani maganin.
Nan idon ta ya kawo ruwa tace "Baba bana son allurar abani magani Zan sha.
Yace kiyi hak'uri y'ar Baba ayi allurar bana son zazzab'in nan ne, kuma kinsan yada zazzab'i ke wahalda ke.
Nan ma Gwaggo tasa baki tana cewa ki Bari ayi maki zazzab'in zai sauka.
Ganin Gwaggo ta taso tace bara a rik'a ta yasa ta zabura da k'arfi, don tasan muguntar da zata yi Mata sai tafi allurar zafi.
In har bata manta ba akwai lokacin da tayi wani zazzab'i akazo za ayima ta allura Gwaggo tazo rik'e ta, amma tana ta mintsi ninta da wani Abu tamkar allura, Wanda ita kanta bata gane miye ba.
Ganin ta mik'e ne tace azo amata yasa Gwaggo ta bita da murmushin mugunta.
Nan hamisu ya yimata allurar ya bada magani, bayan ya gama ne Malam yace ta ara mashi kud'i zai sallami hamisu in ya fita kasuwa ya dawo zai bata.
Ba kudin ne bata son ba dawa ba saidai ganin su sababbi dal take dubin yada zata rabuwa dasu, don a tunanin ta in har zata yi wani waken zata je gidan mero Mai adashe ne tabata rancen kud'i in tayi an saida ta bata kud'in, (_lolx_ Gwaggo anga sababbin kud'i.)
Nan dai ta fitar bada son ranta ba taba Malam suka fita.
Bayan ya sallami Hamisu ya dawo ya ebi ruwa ya shiga d'akin yace y'ar Baba tashi kisha magani.
Nan Gwaggo ta karb'i magani tana b'allawa tana ba Malam shiko yaba Bahijja, da hakan har Tasha maganin.
Malam yace in akwai ragowar waken ki sakama y'ar Baba ko zata ci, kamar zata ce babu bansan me ta tuna dashi ba zumbur ta mik'e ta ebo Mata ta kawo.
Nan Malam ya matsa Bahijja sannan ta ci waken duk da tana jin yunwa sosai, saidai tsoron Gwaggo ya hana taci sosai.
Ai wallahi don ina tsoron in hana ta waken nan ne malam ya karb'e ragowar kud'in yace zai je ya siyo Mata abinci, shiyasa na saka Mata waken, zancen da Gwaggo keyi a zuciyar ta kenan.
Tace amma ba komai shegiyar zata tashi ne wallahi duk Zan fanshe kayana ajikin ta, zatayi bayani ne.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA*40-45🍒
Yau kwana biyu ne kenan Murtala bai sa Bahijja a idon shi ba, sai mamaki yake yi me ya hana mata fitowa.
Yau dai ya yanke shawarar cewa zai je k'ofar gidan su yaduba meke faruwa.
Yana isowa k'ofar gidan su lantana zata shiga gidan.
Nan ya tsaya suka gaisa, yace Ina mutuniyar kwana biyu ban ganta ba?
Nan ta gayamai meke faruwa, ta d'ora da cewa zazzab'i ne ke damun ta shiyasa, amma raunin da sauk'i.
Yace in tana iya fitowa kiyi min magana da ita Zan duba ta.
Suna maganar ne saiga Malam ya fito daga gidan, nan Murtala ya durk'usa har k'asa ya gaida shi, itama lantana ta gaida shi.
Lantana tace Baba yazo duba jikin Bahijja ne.
Malam yace to Ku shiga daga ciki mana, Kai da gidan ku Murtala, Ina maigari da jiki? kwana biyu ban samu lek'awa ba sanadiyyar ciwon y'ar Baba.
Yace yaji sauk'i sosai har ma yana fitowa yanzu.
Malam yace to kushiga daga ciki ni Zan d'an fita ne, in ka koma Ina gaida maigari, inshaAlla Zan lek'o zuwa gobe.
Lantana tayi mashi jagora suka shiga gidan, nan Gwaggo ta tsare su da masifar me suka zo yi gidan ta?
Inda sabo lantana ta saba da masifar Gwaggo don da wuya ta shigo gidan basu saida hali ba.
Lantana tace munzo duba jikin Bahijja ne, tace to taji sauk'i sai asamu damar juyawa gayyar tsiya wai arna a idi.
Lantana ta doshi hanyar d'akin Bahijja, tayi banza da Gwaggo nan ta taradda ita dunk'ule amma jikin da sauk'i tace kid'an taso Murtala ne yazo duba jikin ki.
Hakan ta tashi jiki ba k'wari ta fito, nan suka gaisa da Murtala yana tausaya Mata, har cikin ranshi yake jin bak'in cikin halin da Bahijja take ciki.
Hakan ya fita ya bar gidan Gwaggo na binshi da muguwar harara, lantana ta zauna suka yi hira da Bahijja Gwaggo na binsu da zagi da muguwar harara.
Tana shakkar dukan Bahijja gaban lantana saboda akwai ranar da ta dake ta lantana tace sai ta gayama Malam, dak'yar Bahijja ta shawo kanta ta bar maganar.
Saboda tasan cewa in har lantana ta gayama Baba zata sauke haushin saman kanta tunda dama bata dukan ta gaban shi.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Bayan sun je ya yimata sayayya ne suna kan hanyar dawowa tace "tace Kimba yaushe za ayi maganar auren mu?
Yace Latee ban manta da maganar muba, amma fa Ina da sharad'i guda in har kin kiyaye to Ina Mai tabbatar miki auren mu ba zai wuce wata d'aya ba.
Nan ta bishi da kallon murna had'e da tambayar miye sharad'in?
Ya bata amsa da cewa matsala ta d'aya ce dake, saka matsattsin kaya a gaban kowa kuma ki fita dasu ba tare da kin damu ba.
Wannan ba tarbiya bace kuma ba wayewa bace, in har kika gyra Ina Mai tabbatar miki auren mu na kusa.
Tace in dan wannan ne kar ka damu, kasan cewa Ina yima son da duk abinda kace in daina Zan daina.
Amma fa nima inada nawa sharad'in.
Nan ya bita da kallo had'e da murmushi a fuskar shi, yace Lateefa rigima, Ina sauraren naki sharad'in.
Tace Kimba bani ba kishiya a gidan ka, saboda wallahi nak'i jinin kishiya a rayuwata, bazan iya shearing d'in ka da wata ba, ranar da duk ka yimin kishiya Zan iya kashe Kai na.
Nan ya bita da kallon mamaki, "yace nima a matsayi na na doctor bani da tsarin yin Mata sama da d'aya, sai dai wani iko na ubangiji, saidai in kanada niyya ta bashi amsa.
Hakan suka doshi hanyar gida kowa da abinda yake tunani a zuciyar shi.
Suna shiga Mum ta tari Latee tace kun dawo?
Ta bata amsa da eh, Mum tace ta shiga ciki ta gwada kayan.
Hakan tayi ta gwada kayan tana fitowa Mum na yaba kayan, tace kinga kayan duka sun maki kyau tamkar don ki akayi su.
Shureim ya karb'e da cewa sai ta fitar da wa'ancan ayi sadaka, nan ta bishi da harar wasa ta shige d'akin.
Shureim duk jikin sa yayi sanyi da maganganun Lateefa, dama haka kishi yake ga Mata, gaskiya abin yayi yawa.
Maganar Mum ta dawo dashi hayyacin shi, tace zaka samu zuwa kaiwa Maigari sak'o ko in aiki direba?
Yace Zan duba in inada time, nan shima ya wuce part d'in shi.
(Dank'ari mak'ari, Lateefa muje zuwa, _lolx_🙊)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 45-50🍒
Bayan ya shigo garin ne direct yaje shagon Hamisu suka gaisa, nan yake tambayar shi gidan su yarinyar da ya kad'e da mota.
Hamisu yace oh Bahijja, jiya ma sai da naje aka yi Mata allura.
Shureim yace inaso ne ka gayamin gidansu zanje in duba jikin Nata.
Nan hamisu ya yimai misali har ya gane, saboda dama garin ba bak'on shi bane.
Ya kawo gidan kenan malam zai shiga, nan ya durk'usa har k'asa ya gaida shi, yace dama Baba nazo ganin Bahijja ne saboda ni ne tsautsayi ya fad'a na kad'e ta da mota.
Malam yace Allah sarki, sannu yaro zo mu shiga daga ciki.
Suna shiga Gwaggo anga bak'o daga birni jiki ya Fara rawa, nan aka d'auko shimfid'a sabuwa aka shimfid'a.
Sannu da zuwa malam, ina muka had'u da bak'in birni,? sai washe baki take yi.
Yace shine Wanda ya kad'e y'ar Baba yazo duba jikin ta ne, take annurin fuskar ta ya kau.
Ko me ta tuna sai kuma ta Saki fara'a tace bara akira ta.
Nan ta shiga d'aki ta sassauta murya tace yanzu don kina makirar yarinya saida kika gayama Wanda ya kad'e ki gidan Ku, saboda azo aduba ki abaki sababbin kud'i, shegiya Mai mugun hali.
In ma an rasa mashinshi ni ne za a lab'a ga wannan kinsan dai ba abinda d'an birni zaiyi da kucaka irin ki.
Jin malam yace ko bacci take yi ne yasa tace tashi muje kin sako min ido haka tamkar shege a rabon gado.
Har k'asa ta durk'usa ta gaida d'an birni, ya amsa had'e da tambayar ya jikin nata?
Tace taji sauk'i sosai.
Ya cewa malam zai k'arasa cikin gari dama yazo gidan maigari ne.
Malam yace ko Kaine d'an gidan sulemanu na birni?
Yace eh nine Baba, yace Allah sarki ya Baban naka kwana da yawa bamu had'u ba?
Ya bashi amsa da yana nan k'alau zai ma shigo gobe inshaAllah.
Malam yace to madallah, in ka koma kagaya Mai malam salisu na gaida shi.
Yace Zan gayamai, nan ya fitar da kud'i ya aje gaban malam ya tashi.
Malam yace Kai ko yaro har da wata wahala, nan ma Gwaggo ta saka baki tana cewa an gode yaro Allah yayi albrka, Allah ya maida ka gida lafiya.
Malam ya raka shi har waje yana k'ara godiya.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Sun had'u shi da Murtala sai Sheri suke wa maigari.
Murtala yace ka ganshi nan yak'i tafiya yabamu wuri haka nan.
Shureim ya karb'e da cewa k'ila ya zata kujerar maigari muke so ya bar muna gado, ni ko ban komai da ita kujera ta ta doctor ta ishe ni, sai in Kai zai bama.
Murtala ya karb'e da cewa ni ma ban komi da ita.
To ja'irai babu Mai gadon kujerar daga cikin Ku, kun zo kun saka shi gaba da jarabar surutun ku, cewar Baban Murtala.
Nan suka gaida Baban suna dariya.
Yace yaushe Baban naka zai shigo?
Shureim yace gobe zai zo, nima Mum ta matsamin sai nazo na kawo ma maigari dambun nama tare da ferfesu.
Baban yace ai gaskiya hajiya safiya akwai k'ok'ari, Allah dai ya saka mata da alkhairi ya nuna Mata naku matan sun yi Mata.
Nan suka amsa da Ameen.
Shureim yaja Murtala suka fita waje, nan yake bashi labarin yarinyar da ya kad'e.
Murtala yace ayyah Bahijja kenan marainiyar Allah.
Yace yanzu haka inaso in kaima Baba maganar ta saboda ita nake so in Aura.
Nan take gaban Shureim ya fad'i, sai kuma yace ni da nake da Lateefa Me zanyi da wannan y'ar k'auyen, amma nasan tana bani tausayi sosai.
Maganar Murtala ta dawo dashi daga tunanin, yace inaga in baka tashi ba sai na Riga ka aure, da Dad yazo gobe zanyi maganar.
Shureim yace in baka rigani ba Zan rigaka, don nima magana ta da Lateefa na nan inshaAllah.
Yace to Allah ya taimaka kuma ya nuna muna lokacin.
Shureim yace sai yaushe zaka b'ullo?
Yace kasan rigimammen tsofon nan ne ya tsaida ni in ya samu sauk'i Zan shigo.
Nan suka rabu Shureim ya Kama hanyar garin su.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:26 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 50-55🍒
Baban Shureim yazo duba jikin maigari Wanda ciwon nashi ya had'a da tsufa, nan Murtala ya tunkari Dad da maganar yana so aje nema mashi auren Bahijja.
Hakan suka kwashi jiki sai gidan Malam salisu, nan akayi gaisuwar yaushe rabo kuma suka tattauna kan maganar nema ma Murtala auren Bahijja.
Malam yace ba komai Alhj Kai kanka Mai bada auren Bahijja ne, amma duk da hakan na bawa Murtala ita halak malak.
Amma Ina neman alfarmar a d'an d'agamin k'afa in har na shirya maganar auren Zan tunkari Alhj saminu inshaAllah.
Alhj yace in har maganar da ka fad'i cewa d'iya tawa ce to Zan so kabar komai a Hannuna, ni Zan d'auki nauyin komai na Amarya da ango.
Kuma inaso a d'aura aure yanzu, saboda gobe Zan wuce England wurin wasu harakoki nawa.
A hakan aka d'unguma sai babban masalacin garin aka d'aura auren ```Murtala``````Saminu```
Da
*Bahijja* *Salisu*
A kan sadaki Mai sauk'i.
Ansamu halartar mutane da dama saboda lokacin sallar azahar ne, kuma in har Alhj ya shigo garin to mutane zasu k'ara taruwa, saboda shi mutum ne Mai yawan kyauta da taimakon mutane.
Hakan suka rabu kowane b'angare suna murnar had'a auren yaran su.
Sai dai sun ajiye maganar kan sai wani sati Mai zuwa za ayi sauran al'adun aure sannan Amarya ta tare gidan ta.
Hakan Malam ya doshi gida cikin murna da farin ciki, saboda ganin yau Allah ya cika Mai burin shi na ganin ya aurar da y'ar Baba.
Yana shigowa Gwaggo ta tarbeshi, tace malam yau na ganka cikin farin ciki meke faruwa?
Nan ya kwashe komai ya gaya Mata, Gwaggo tayi wata irin zabura tace ban gane ba malam, wane irin aure d'iya tamkar d'iya roba za ayi neman aure da d'aurin aure lokaci guda.
Kawai malam kace ka saida y'ar ka saboda kaga kud'i, aini yau an nunamin iya kata kuma an nunamin ban Haifa ba.
Nan taja wani irin kuka had'e da sharce majina tace yau da ace uwar yarinyar nan na raye na tabbata ba za ayi Mata hakan ba.
Haka taci kukan ta da gunzar ta tamkar wadda aka yiwa mutuwa.
Malam yace kiyi hak'uri lami nima ban san da zuwan maganar ba, kuma kinsan Alhj yafi k'arfin komai a guri na.
Mun taso tare tun muna yara, kuma duk sana'ar da nakeyi kinsan da bazar shi nake rawa, kinga ko in har na hana yaron shi y'ata banyi halacci ba.
Da k'yar malam ya shawo kan lami ta sassauto, nan tace to yanzu yaushe ne tarewa?
Yace sai nan da sati, don ina so gobe inje aljannare in gayama dangin mahaifiyar ta saboda a fita hakk'in su.
Lami tace ko baka jeba babu komi, nima na isar musu, malam yace aah kam lami gara agaya masu.
Zanso ma inje musu da ita koda wuni ne ta yi masu.
Hakan Gwaggo ta tashi tamkar zata had'iyi zuciya ta mutu kan tsabar bak'in ciki da hassada.
Bahijja na d'aki tana sauraren maganar Gwaggo da Baban ta, sai murna take yi cikin ran ta jin cewa an d'aura Mata aure, duk da cewa bata San miye auren ba.
Amma tasan ana canja ma mutum gida daga gidan su zuwa wani gidan.
Ita kam in hakane zata yi murna da cewa zata bar gaban Gwaggo ta koma gidan su Murtala da zama, amma fa tasan zata yi kewar Baban ta.
*************
Koma war Dad gida yake gayama Mum an d'aura auren Murtala yau.
Mum tace yaushe Murtala ya nemi Mata har magana tayi tsayi haka?
Dad yace zuwa na ne yake gayamin cewa yana tausayin yarinyar kuma tana shan uk'uba ga matar Baban ta.
Asali ma yace bai ta6a furtama yarinyar yana son ta ba, suna dai mutunci sosai da ita, kuma yarinyar bata ma isa aure ba nan garemu saidai can d'in, y'ar wajen abokina ce Malam salisu.
Mum tace ayyaah, yanzu to ina zasu zauna?
Dad yace shine nake tunanin inda za agyra Mai kamin nan da sati d'aya.
Mum tace me zai hana cikin gidannan abasu part guda, kaga gidan yana da girma kuma akwai part kusan biyar da ba kowa a ciki.
Dad yace kin kawo shawara, nan ya Kira wayar Shureim yace Son kazo falo Ina Neman ka.
Yana zuwa Dad ya gaya Mai maganar auren Murtala, ya d'ora da cewa inaso ka duba part d'aya cikin gidannan duk abin da ake buk'ata asaka nan zuwa sati d'aya.
Shureim yace lallai Murtala ya yimin wayo, Allah ya sanya alkhairi.
Dad ya kar6a da Ameen, yace saura Kai, kuma ka bincika Jega international furnitures show room, ka za6a ma yarinyar kayan d'aki, komai ka tabbatar ansa saboda ni gobe Zan wuce England.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:26 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 60-65🍒
Yau ne Bahijja ta cika sati biyu da aure, ta murje tayi jikin ta dai-dai gwargwado.
Duk wata iya kwalliya ko dressing tana koyo wurin Lateefa.
Lateefa ta Mai data tamkar k'anwar ta, duk in da ka gansu gidan suna tare.
Mum tasa an saka Bahijja makarantar islamiya kuma an samo wani malami dake yi Mata lesson gida, gwargwado tana fahimta ba laifi, saboda akwai ta da saurin d'aukar Abu cikin kanta.
Tana zaune part d'in Mum ta fito daga kicin kenan taji sallamar Shureim.
Nan ta kar6a ta durk'usa har k'asa tace yaya Shureim sannu da dawowa.
Yace yauwa Bahijja, Ina Mum halan?
Tace yanzu ta shiga wanka.
Yace latee fa?
Ita ma ta kar6a mashi da cewa tana d'aki bacci take yi.
Nan ya girgiza kanshi ya wuce d'akin shi, ita ko ta gama jera kaya a dinning ta yi part d'inta domin tayi wanka.
Saboda wannan na daga cikin al'adar da Lateefa ta koya Mata cewa duk ta shiga kicin ta k'are girki to tayi wanka.
Hakan ta shiga tayi wanka ta fito, ta yi kwalliyar ta dai-dai gwargwado duk da bata iya sosai ba.
Shureim na falo zaune yana kallo sai ga Mum ta fito, bayan ya gaida ta yace Mum wai me yasa kullum Zan shigo Zan taradda Bahijja na taya ki aikin gida, amma Latee na d'aki tana bacci ko charting?
Mum tayi murmushi ta bashi amsa da cewa nima matsalata guda da ita bata k'aunar shiga kicin ko kad'an, inaga ko ruwan coffee bata San ya ake dafa suba.
Shureim yace Mum ki rik'a saka ta girki mana.
Tace son kasan halin Lateefa zata iya aikin komai amma bada girki ba kam, sai dai ayi ta hak'uri zuwa gaba in kun yi aure nasan tunda tana son ka zata yima.
Tace kaga yanzu haka Bahijja in dai tana part d'innan bai ta6a yuyuwa in shiga kicin ba tare da ita ba koda kuwa zance tayi zaman ta, yanzu haka ta fara gano kan wasu girke-girke.
Nan ya ta6e baki yace Allah ya kyauta, ya tashi ya yi nashi d'akin.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*WA CECE* *LATEEFA*?
Lateefa d'iya ce gun Alhj Isma'il Mai dala da Hjy Saratu.
Alhj Isma'il fitaccen Mai kud'i ne kuma sananne a garin Jega, yana da yaran shi Mata guda hud'u, Wanda Allah bai bashi d'a namiji ba.
Ta farko itace Nafeesa wadda tana sokoto tana aure da yaran ta uku, sai kuma Bilkisu dake aure a Birnin kebbi da yaron ta guda.
Sannan Lateefa, Shema'u itace Autar su, Lateefa ta taso cikin jin dad'i da sangar ta Wanda duk abinda tayi ga mahaifan ta bata laifi, musamman gun Abban ta, don ma Hjy Saratu na k'ok'arin kwa6ar ta in tana wasu abubuwan.
Da Hjy Saratu da Hjy Safiya mahaifan su guda su kad'ai iyayen su suka haifa.
Tun tasowar Lateefa Allah ya had'a jinin ta da son zama gidan su Shureim, Wanda yanzu hakan ake gab da auren su.
*******************
A yau ne iyalan gidan maigari Alhj Abubakar suka tashi da bak'in cikin rasa maigari, Wanda ciwon shi ya tashi jiya akayi dai-dai da ajali.
Dama ya d'an jima baida lafiya Wanda an yita yawo dashi asibitoci da dama har Egypt Alhj Suleiman ya fita dashi, sai dai ciwon ya had'e da tsufa.
Hakan su Hjy Safiya suka Kama hanyar Kimba domin zuwa zaman makoki, Wanda har da Bahijja aka zo.
Gidan su na garin suka sauka, dama suna da gida a garin wanda in Abu ya samu nan suke sauka.
Haka su kayi koke-koken su suka hak'ura, saboda sun yi rashin dattijo Mai nagarta da kamala.
Nan aka yi mashi sutura sai gidan shi na gaskiya.
Bayan sadakar uku ne Mum tace Bahijja ki shirya muje gidan Ku ki gaida mutanen gida.
Nan take gaban Bahijja ya rik'a bugawa, saboda har ga Allah tama manta da wata halitta Gwaggo, tun auren ta da sati d'aya da Gwaggo taje ranar ma taci masifa har da rank'washi aka Kai Mata.
Hakan dai ta wuni gidan ta hana Bahijja sakewa, data tashi tafiya Hjy Safiya ta had'a Mata sha tara na arzik'i, amma duk da hakan Saida ta kwashi sabulayyen wanka dana wanki, ta ebi mayukkan Shafa duk da wasu bata Masan ya ake amfani da suba.
Maganar Hjy ta dawo da ita daga tunanin da ta Lula, tace ki tashi muje kinsan gobe zamu wuce.
Hakan ta tashi jiki babu k'wari suka nufi gidan su Bahijja d'in.
Sun shiga gidan Gwaggo ganin Hjy aka tashi jiki na rawa aka shimfida tabarma hakan suka zauna aka kawo ruwa da fura taji nono, nan suka sha aka gaisa, sai ga malam ya shigo suka gaisa ya yima Mum gaisuwa.
Ya Kai duban shi ga y'ar Baba yace haka kika koma, kin k'ara girma kinyi 6ul-6ul.
Tayi murmushi ta ce Baba kaga Mum ta sakani islamiya kuma yanzu na iya karatun boko.
Nan yayi murmushi ya yima Hjy godiya sosai.
Gwaggo sai binta take yi da harara tamkar ta shak'e ta take ji.
Hakan Hjy ta basu kud'i suka fito, nan Bahijja tace Mum Ina so in lek'a lantana ga gidan su nan mak'waf tan mu.
Nan suka shiga gidan lantana na ganin ta ta shek'o suka rungume juna, saiga Inna Habiba ta fito nan suka gaisa da Mum.
Hakan mak'wab ta ke lek'o wa ana kallon Bahijja sai mamaki ake yi yadda ta koma.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:27 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* 65-70🍒
*BAYAN* *SATI* *UKU*
Yau ne dubban mutane suka shaida d'urin auren
*SHUREIM* *SULEIMAN*
*DA*
*LATEEFA* *ISMAIL*
Bayan d'aurin aure da shagul gulan biki Amarya ta tare a gidan angon ta.
Shureim yaso ya zauna part guda daga cikin gidan su, saidai Lateefa ta nuna cewa gaskiya bata iya zama gida guda da Mum, dole suka tare tasu anguwa daban.
Bayan masu kawo Amarya sun watse abokanen ango suka rako shi, bayan y'ar nasiha da tsokanar juna da suka yi nan Muftah ya rufe taro da addu'a.
Nan Shureim ya raka su suka wuce ya dawo ya rufe gidan.
Ya umurce ta data tashi ta d'auro alwala domin gabatar da nafila, bayan sun idar ya yima ta tambayoyi gwargwado ta kar6a wa'anda ta sani.
Nan ya fitar da kazar amarci suka ci saida sukayi k'attt (ina gefe ko taya ni basu yiba sai had'iyar yawu nake yi).
Da suka k'are ne suka yi wanka, su Lateefa Amarya sai tashin k'amshi ake yi, hakan suka zo suka kwanta saman gado Mai alfarma Shureim ya ja masu bargo.
(Koda na fito daga nawa wankan Shureim ya rufe k'ofa Ina waje, ```lolx```😜)
********************
*WAYE* *SHUREIM*?
Shureim d'a ne gun Alhj Suleiman da hajiya Safiya, Wanda shi kad'ai ne Allah ya k'addare su da haihuwa.
Ya taso cikin gata b'angaren iyayen shi duka, hakan bai hana mashi samun tarbiyya yadda ya Kama ta ba.
Yayi karatun shi na boko da Arabic duk a garin Jega, daga baya ne ya fita India ya had'a masters d'in shi b'angaren likita akan matsalolin Mata.
Yawancin abokanen shi sunfi kiran shi da S.S Kimba, wato Shureim Suleiman Kimba.
Kimba ta samo asali ne sanadiyyar k'auyen mahaifin shi, saboda Can ne tushen shi.
Alhj Suleiman da Alhj saminu sai Gwaggo Fati sune y'ay'an maigari, Wanda tun tashin Alhj Suleiman yake da sha'awar shiga jega ya siyo kaya yazo Kimba ya sayar.
Cikin hakanne Allah ya had'ashi da mahaifin Safiya wato Alhj Ilyasu, Wanda rik'on amanar shi yasa ya jashi jikin shi har ya zama tamkar d'an gida.
Daga hakan ne Allah ya had'a jinin shi da Safiya, saboda Mace ce Mai hankali da sanin ya Kama ta, kud'in Baban ta basu sa ta wulak'an ta mutum.
Hakan akayi auren su har zaman shi ya koma can Jega duka.
*****************
```Murtala``` kuma yaro ne gun Alhj saminu k'anen Alhj Suleiman, tun tashin shi yake d'an zama wurin Alhj Suleiman d'in.
Har ya fara Sana'a can sanadiyyar shagon sayar da yadukka daya bud'e Mai, sai dai yaje Kimba yayi kwana uku hud'u ya koma.
Baiyi karatun boko Mai zurfi ba, iya kacin shi primary da secondary.
*WASHE* *GARI*
Bayan tashin su daga bacci, Lateefa an yi wanka an fito tsab sabuwar Amarya. Mum ta aiko direban ta ya kawo musu breakfast.
Nan suka karya, sai bak'i ke zuwa masu ciki kuwa har da k'anwar ta Shema'u da kuma k'awar ta Shafa'atu.
Nan suka shige d'aki sai shewar su kake jiyowa.
*BAYAN* *SATI* *DAYA*
Suna zaune suna hira Shureim yace inaga yau ya kamata ki fara girki saboda Mum ta huta da kawo muna abinci hakanan, ko ya kika ce?
Tace ai inaga kabar shi kawai Mum ta rik'a aiko muna.
Nan ya bita da kallon mamaki yace ban fahimce kiba.
Tace ni gaskiya kasan ban iya shiga kicin girki saboda ban saba yi ba.
Shureim yace kenan Mum ce zata rik'a ciyar damu mu ko muna zaune gamu masu Uwa.
Da taga ya takura ta da magana, tace shikenan zata yi girki da dare d'in.
Hakan yasa yaji dad'i ya janyo ta saman jikin shi ya Kai Mata kiss.
Yau yana gidan Mum sai da akayi kiran magriba ya tashi yayi salla nan masallacin gidan shida Dad da Murtala, basu shigo gidan ba sai da akayi isha'i.
Nan Mum tace ko azuba abinci yaje masu dashi?
Yace basshi Mum nasan koda Zan koma Latee ta gama girki yanzu.
Nan Murtala ya shiga tsokanar shi kan cewa za aci abincin uwargida babu ko gayyata.
Yayi murmushi yace zaku ci saidai ba yau ba kam.
Hakan ya fita gidan ya biya ya siya musu kayan buk'ata, yana shiga gidan Lateefa ta tarboshi ta kaimai kiss, tace dear kafa dad'e a waje.
Ya bata amsa da cewa wurin Mum yaje shiyasa.
Nan suka shiga d'aki ta rage Mai kayan jikin shi ta had'a Mai ruwan wanka, koda ya fito ta fitar Mai da jallabiya Fara k'al ta feshe ta da turare, nan ya shirya suka fito falo sai danning.
Suna zama ta bud'e cooler ta zuba abinci ga filet, shiko yana waya da Muftah.
Yana k'are waya ta turo Mai filet tana murmushi, yana jawowa zai Fara ci, me zai gani.
(Fan's Ku taya ni addu'ar saduwa da rahmar ubangiji zuwa ga margyayi Babba *HASSAN*)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:30 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *75*- *80*🍒
Shureim nakai duban shi zuwa ga abinci yaga indomie, nan ya maida duban shi zuwa ga Lateefa ita ko sai murmushi take yi.
Yace yanzu don Allah Lateefa indomie ce abincin dare?
Tace haba Kimba ai ko indomie ce abinci saboda ni ita nake ci da daddare in kwanta.
Yace amma ni dai kina zama gurin Mum kinsan favorite food d'ina.
Tace haba Kai ko Kimba ya Kama ta yada rayuwa ta canja abinci ma ya canja, kuma fa kasan ban girki ko a gida, yanzu ka takurani na yima duk da hakan banyi gwanin taba.
Ganin cewa ta 6ata fuskar ta yasa ya hak'uri ya janyo filet d'in, yana Kai lomar farko take ya zabura ya Fara lezaya amai tamkar zai amayar da hanjin shi.
Ita ko ta bishi da kallon takaici, to miye illar wannan abincin, gashi nima naci tawa har na k'oshi, don ma in k'ara gyra mashi ita har da k'wai na saka aciki, zancen da take yi azuciyar ta kenan.
A fili kuma ta taso tana yi Mai sannu had'e da tambayar miye?
Nan yakai duban shi gare ta yace yanzu fisabilillah Lateefa haka ake dafa indomie, kin tashi kin zabgama Abu tarugu haka, ga k'arnin k'wai na tashi, sannan kin cika gishiri.
Tace duk Kai ka jiyo wa'annan abubuwan ni dai naci abata lafiya lau.
Hakan yaja jiki ya shiga kicin ya had'a tea yasha, sannan yayi wanka yayi kwanciyar shi.
Jin shiru yasa Lateefa ta biyo bayan shi koda tazo har ya kwanta.
Hakan tazo kusa dashi ta kwanta sai k'amshi take zabgawa, tace Kimba kayi hak'uri kar ka fara kawo muna matsala a rayuwar auren mu.
Yace Lateefa matsala ta d'aya dake rashin kulawa ta 6angaren girki, ko so kike yi afara tsegumin cewa mijin ki na yawon restaurant?
Tace to kabari muyi ma Mum magana ta samo muna y'ar aiki.
Yace au bama ki koyi aikin ba sai dai anemo Mai aiki.
Tace gaskiya sai dai kayi hak'uri ni ban iya zaman shiga kicin girki.
Hakan suka yi ta rigima tsakanin su saida Shureim yace shikenan za asamo y'ar aiki d'in, nan suka shirya sai gashi anfara shan soyayya, nan na fito na janyo k'ofa har Ina cin Karo da k'ofa ```lolx```
******************
*WACE* *CE* *BAHIJJA*?
Bahijja d'iya ce gun malam salisu da Inna uwani.
Gwaggo lami itace Mace ta farko a wurin malam salisu, auren zumunci ne akayi dashi da ita.
Sun kusa shekara takwas da aure Gwaggo lami ko 6atan wata bata ta6a yi ba.
Daga baya ne Allah ya had'a malam da uwani wurin yawon saye da sayarwar shi ya had'u da ita can k'auyen raha.
Lokacin da yazo da maganar Gwaggo lami hauka ce kawai bata yi ba, duk iya abinda zata yi tayi amma kash Allah ya k'addari sai uwani ta shigo gidan.
Bayan anyi aure ne uwani ta tare, ta Fara cin karo da uk'uba hd'e da masifa gurin Gwaggo lami.
Amma fa duk abinda take yi bata yi gaban malam akan tsananin makircin ta.
Cikin hakan Allah yaba uwani ciki Wanda Gwaggo na hango hakan ta k'ara tsanan ta k'iyayyar ta had'e da takurawa zuwa ga uwani.
Ta yita samo abubuwa masu zubar da ciki tana bata har tayi nasarar zubar da ciki uku.
Akan Bahijja ne Allah yayi ikon shi da iyawar shi har aka haife ta.
Zun azab tu kuma sunga takura a hannun Gwaggo, har uwani ta had'u da ciwon hawan jini Wanda yayi ajalin ta.
Koda ta rasu Bahijja nada shekara uku da haihuwa, y'an uwan uwani sun so su kar6e ta malam ya basu hak'uri ya rik'e abar shi.
Tun tana da shekara biyar ita ke ebo ruwa rafi ta cika duka kayan gidan.
Lokacin har islamiya malam ya saka ta cikin makircinta ta janye Bahijja daga zuwa makarantar saboda yawon talla.
Ta boko ma malam yaso ya saka ta Gwaggo tace makarantar y'an iska ce.
Hakan ya hak'ura ba don baya so ba sai don baya da yadda zai yi ne.
Akwai lokacin da yayan uwani yazo duba Bahijja ya d'an yi Mata siyayya, nan Gwaggo ta kar6e kayan ta k'ona su, kuma ya nemi alfarmar zuwa da Bahijja ta yi masu kwana biyu Gwaggo ta hana saboda lokacin malam bai gari.
Hakan Bahijja taga renon azaba hannun Gwaggo har zuwa yanzu da aka yi Mata aure tana da shekara goma sha hud'u.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:33 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *80*- *85*🍒
Kwanaki sun shud'e, watanni ma haka har gashi shekaru sun shud'e.
A cikin hakanne Bahijja take batun zana jarabawar junior living.
An samu fahimtar juna sosai tsakanin ta da Murtala.
Ta waye sosai ta 6angaren girki da kuma kwalliya, hakan ma tana tarairayar mijin ta dai-dai yada ta iya.
Cikin hakanne arzik'in Murtala ya bunk'asa kasuwan cin shi sai ci gaba suke yi.
****************
Lateefa ta kowane 6angare tana bama Shureim kulawa, sai dai matsala guda har yanzu tak'i mayar da hankali 6angaren girki.
Lokacin da abin yayi yawa har Mum yaje ma da maganar, kuma ta yi iya yin ta Abu ya gagara, dole haka ta hak'ura ta basu Bizzy ta rik'a taya su aiki.
Sai dai koda tazo itama girkin sai a slow saboda gurin Mum ba girki ta keyi ba goge-goge da shafe-shafe ne aikin ta sai kuma shara.
Koda tazo tayi girki ranar farko ta dafa farar shinkafa da miyar tumatur, hakan Shureim ya daure yaci ba wai don abincin ya yima shi ba.
Shiyasa Mum ke bashi shawa ko ruwan tea bata bari y'ar aiki ta dafa Mata.
Yanzu da ace Ina da mata biyu ko Lateefa bata iya girki ba ai d'ayar ba zata rasa iyawa ba.
Tuno da furucin ta akan kishiya yasa gaban shi ya fad'i dammm.
Koda ta shigo d'akin yana shiri gaggauce zai je asibiti, hakan ta yi sauri ta kawo Mai ruwan tea ta had'a Mai.
Nan dai ya jure yasha ba wai don ya yi mashi dai-dai ba.
Tare suka fito ta shiga gidan mak'wab ciyar ta Mmn zahra, saboda Allah ya had'a jinin su.
Tana shiga suka gaisa nan suka shiga hirar duniya, har suka fad'o kan wata mak'waf ciyar su da za ayima abokiyar zama cikin satinnan.
Mmn Zahra tace kinji ranar assabar za akawo ma Mum Zee abokiyar zama ko?
Take ta zabura ta gwalo ido waje tace yaushe Abban Zee ya dai na son ta?
Mmn Zahra tayi dariya sosai tace ke ko Lateefa waya ce maki in an daina son Kane ake yima kishiya, ai shi aure nufin Allah ne kuma matar mutum k'abarin sa.
Kuma kin ga ita Mum Zee wallahi tamkar bata damu ba, saboda matar akwai ta da tawakkali.
Lateefa tace bata dai son mijin ta, in har tana son shi dole zata yi kishin sa.
Eh to shi kishi wani Abu ne da Allah ke dasawa k'ark'ashin zuciyar Mace, kuma ko wace Mace Nada kishi duniya amma na wata yafi na wata.
Saboda akwai masu kishin hauka, kuma akwai Mai na tsabta.
Lateefa tace ke nifa in zaki sauke min littafin kishiya ban ta6a gane wannan bitar, maybe ma koda aka haifeni 6angaren d'aukar wannan bitar ya shafe duka.
Mmn Zahra tayi dariya sosai tace to Allah ya kyauta.
Ta amsa da Amin tace kin dai ji magana.
Tace ya Kama ta ranar auren mu daure mu lek'a Mata.
Lateefa tace ke ni fa ko gidan da keda Mata biyu bana shiga.
Mmn Zahra tayi murmushi tayi tace ki daure muje kinsan Mum zee akwai k'ok'arin sada zumunci.
Tace ya yi Zan duba in har Zan iya zuwa to Zan Kira ki.
*********************
Yau ne Bahijja ke ta shirye-shirye zata je suna k'auyen su, sanadiyyar lantana k'awar ta data haihu.
Murtala ya yi Mata siyayyar kayan jarirai da sabulai yace takai ma lantana, ya had'a Mata da kayan da zata kaima iyayen ta ciki kuwa har da kayan abinci, hakan ma ya had'a na iyayen shi.
Amma dai ba can zaki kwana ba ko?
Tace naso kabar ni in kwana d'aya, amma tunda kace ba sokoto zaka kwana ba nima Zan dawo yau.
Yace to shikenan in kin shirya direba zai kaiki don munyi magana da Mum tun jiya.
Tace nima mun yi magana har ta bada sak'on da za aje dashi.
Hakan ya gaggauta shirin shi har ya fita kuma ya dawo ya gaya Mata magana cikin kunne, tayi murmushi ta soke Kai, ya sumbaci goshin ta ya wuce, har ya tada mota tana tsaye tana yi Mai bye-bye.
Ta juya ta shiga part d'in Mum bayan ta gaida ta take gaya Mata ta shirya, nan tayi ma direba magana ya fitar da mota yasa kayan ta suka d'auki hanya sai Kimba.
Gidan su Murtala ta fara sauka nan aka yita tarairayar ta, k'annen Murtala duk sun cika d'aki ana murnar Bahijja tazo.
Bayan ta sallame su ne tace zata lek'a sunan lantana daga nan ta shiga gidan su, haka yaran gidan suka cika mota sai k'ofar gidan su.
Gidan su lantana ta Fara shiga nan suka rungume juna suna murna, ta kar6i jaririya ta ganta.
Inna habiba sai murna ake yi Bahijja tazo, sai ga yara sun cika gida Ana lek'en ta ana cewa eh wallahi y'ar Baba ce.
Hakan ta cika su da goma ta arzik'i sannan ta shiga gidan su.
Baban ta ta fara cin Karo dashi ta durk'usa ta gaida shi, ya rik'o ta yace mashaAllah y'ar Baba, kina jin dad'in ki.
Tayi murmushi, ta juya ta gaida Gwaggo.
Ta amsa ba yabo ba fallasa, sai harara take binta da ita, nan dai suka ta6a hira ta fitar musu da nasu kayan.
Baba nata godiya yana saka Mata albarka, Gwaggo ko cewa take yi an gode.
Hakan tayi sallama da kowa ta Kama hanyar Jega saboda tana so ta yima Murtala abinci kamin ya dawo.
Tana shigowa part d'in Mum ta Fara shiga bayan sun gaisa ta tashi tace Mum Zan shiga in dafama Murtala abinci, munyi waya yace ya kusa k'arasowa.
Mum tace ai na ajiye maku abinci in kika tashi ki shiga maku dashi, keda kika dawo yanzu ko hutawa baki yi ba.
Tace Mum an gode sosai, nan ta zauna suka rik'a hirar k'auyen su Bahijja.
Can taji wayar ta na ruri cikin jaka, koda ta d'auko taga Murtala ne takai duban ta ga Mum tayi murmushi tace inaga ya iso.
Tana d'aga wayar take gaban ta ya fad'i jin muryar wani daban.
Tace eh nan ne, kawai Mum taji ta furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, take ta fad'i k'asa sumammiya.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:34 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *85*- *90*🍒
Mum ta yi saurin tasowa ta gir gizata sai dai bata numfashi, nan Mum ta jawo wayar Bahijja ta duba no taga Murtala ne ya Kira, nan ta Kira taji ko lafiya can taji wani ya d'aga nan ya yimata bayanin Allah ya yiwa Mai wayar rasuwa yanzu haka suna asbitin Aleru.
Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, hakan Dad yaji Mum na furtawa da k'arfi.
Koda ya sauko yaga Bahijja zube k'asa bata ko numfashi ga Mum tsaye kanta duk ta rud'e.
Nan yake tambayar meke faruwa haka?
Mum ta gaya Mai saiga Dad zube saman kujera cikin tashin hankali da rud'u.
Mum ta yi sauri ta d'auko ruwa fridge ta zuba ma Bahijja nan take taja wani dogon numfashi, Mum ta rik'a ta ta tashi sai ido take bin ta dashi.
Dad ya Kira Shureim ya gaya Mai meke faruwa, yace yaje asibitin Aleru yazo da gawar Murtala.
Kamin kace kwabo duk inda y'an Uwa suke labari ya Kai musu.
Mutanen Kimba sun zo cikin tashin hankali, in da akazo da gawar shi aka yimai sutura sai gidan shi na gaskiya.
Ashe lokacin da zai dawo daga sokoto har ya kawo Aleru sai wani sa ya gitta Mai wurin ya kauce Ashe akwai tilera bayan shi, hakan direban yayi k'ok'arin kauce mar amma abin ya faskara saida yabi ta kan shi shida wasu mutum biyu saman mashin inda su duka uku basuyi rai ba.
Bayan an Kai shi gidan shi na gaskiya ne aka zo zaman makoki.
Duk Wanda ya kalli Bahijja sai ta bashi tausayi komi rashin imanin shi, dai-dai da Gwaggo yau an d'an tausaya ma Bahijja.
Saboda da ita da mutum mutumi basu da maraba, bata yiwa kowa magana sai dai tabi mutum da ido.
Yau kwanan Murtala biyu da rasuwa Bahijja duk ta fita hayyacin ta, tun jiya babu mahaluk'in da ta yiwa magana har yau, sai dai ko gaisuwa ake yi Mata ta bi mutum da ido kawai.
Abin har ya Fara bawa mutane tsoro, har yau Dad ya shigo da Baban ta har d'akin da take ciki.
Baban ta na kallon ta shima ya rik'a Shafar hawaye, yace y'ar Baba haka kika koma, kiyi hakuri ki barwa Allah, Wanda ya bamu Murtala yafi mu son shi ya kar6i abinshi.
Kiyi tawakkali kinji Bahijja, Kai kawai ta d'aga Mai sai hawaye dake zubowa duk sun wanke Mata fuska.
Lateefa na gefen ta tana sa tissue tana goge Mata fuska ita ma tana hawaye.
Babu abin da ke damun ta sai rashin maganar Bahijja, abinci ma ta kasa ci sai da k'yar Lateefa ke samu tasha fresh milk.
Baban ta yace in akwai zam-zam kusa abashi.
Nan Mum ta tashi ta d'auko ta bashi ya yi addu'a yaje da kanshi kusa ga Bahijja ya bata yace tasha, nan ta kauda kanta.
Ya k'ara bata, ta kalleshi taga ya had'e ran shi, nan Lateefa ta kar6a ta bata tasha kad'an.
Ko ruwa ta sha ji take yi tamkar zuciyar ta zata k'one.
Duk Wanda yazo gaisuwa yaga Bahijja sai ya tausaya Mata yanayin da take ciki.
Lokacin sallar la'asar tayi zata tashi tayi sallah kawai akaga ta zube, nan kuka ya koma sabo.
Nan Mum ta Kira wayar Shureim daga waje tace tayi sauri ya shigo.
Hakan aka Kama Bahijja aka shiga d'akin Mum da ita.
Shureim na shigowa kallo d'aya ya yi Mata ya kauda fuskar shi saboda duk ta zabge tamkar wadda tayi sati kwance.
Nan ya fita ya siyo allura da ruwa aka yi Mata k'arin ruwa.
Lateefa ta kasa d'agawa daga wurin ta, ko sallah da k'yar aka rarrashe ta sannan ta je tayi.
Tana k'are addu'a tazo gurin ta ta zauna, malam ma yana gefen ta yana tofa Mata addu'a.
Sai bayan isha'i sannan ta farka, tabi d'akin da kallo, koda ta Kai duban ta gefen ta Lateefa ta gani zaune idon ta sunyi jazir, sai Mum dake saman dadduma tana lazimi, malam ma na gefen ta.
Tamkar a T.V komi ya dawo Mata take ta tuna meke faruwa, nan ta fashe da kuka tana cewa Murtala haka zaka yimin, ka tafi baka cika burin ka akaina ba.
Nan Mum ta taso tana rarrashin ta, malam yace a k'yale ta tayi kukan shima rahama ne gare ta.
Sai da taci kuka ya ishe ta sannan tayi shiru, nan ta tashi tayi sallolin ta ta fara lazimi duk da hakan sai dai tabi mutane da ido.
Dangin mahaifiyar ta suma sunzo gaisuwa daga raha Mata uku maza biyu.
Dangin malam ma gwaggon shi kawai ta rage Mai da yaran ta biyu suma duk sun zo gaisuwa.
Yau ne kwana uku da rasuwar Murtala kuma yau ne za ayi addu'a kowa ya watse.
Da k'arfe biyar aka yi addu'a, nan mutuwar ta koma ma dangin shi sabuwa su da Bahijja.
Kowa ya Kama gaban shi sai dangi na kusa, irin su Hindatu k'anwar margyayi da Lateefa, sai kuma Gwaggo da tace zata zauna sai an kwana biyu, Gwaggo Allah yasa zaman arzik'i ne zaki yi.
( اللهم اغْفر لحيّنا وميّتِنَا ولجميع الْمسلمين والمسْلِمَات)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:35 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *90*- *95*🍒
Yau ne Bahijja ta gama takaba.
Duk Mai imani ya gan ta zai San cewa mutuwa ta ta6a ta, duk ta kod'e ta fita hayyacin ta.
Bayan sati d'aya da gama takaba d'in ta an raba abinda yake hakk'in ta an bata.
Malam yazo saboda zuwa da Bahijja gida, Dad na wurin da Baban margyayi da Mum.
Nan Mum tace malam salisu ina neman alfarma da Ku bar min Bahijja har zuwa lokacin da Zan cika burina akan ta.
Kaga yanzu ta gama makarantar gaba da primary har anfara ciku-cikun shigar ta health sai ga wannan rasuwar Allah ya kawo.
Nan malam yayi shiru ya kasa magana.
Sai da Mum ta sake magana sannan ya Kai duban shi zuwa gare ta.
Yace yanzu abinda nake dubi kinga can k'auye za a yita maida magana cewa mijin ta ya rasu amma nabar ta wurin Ku zaman kwad'ayi.
Sai yanzu Baban Murtala yasa baki yace malam salisu yanzu ba abiyar ta mutane, kuma shi d'a na kowa ne, kaga ko bada auren margya yiba in har zaka duba zaman takewa to zaka iya bama Alhj Suleiman Bahijja.
Kuma in har Kai ga taka zuciya zaka iya bashi ita har ta gama karatun ta to kar kabi ta surutun mutane.
Malam yace to shikenan, Allah ya saka maku da alkhairi kuma yabar k'auna.
Mum ta amsa da ameen, ta d'ora da cewa inshaAllah duk juma'a zata sa direba yakai Bahijja can gida Kimba ta zaga y'an Uwa in yaso lahadi ya koma ya d'auko ta.
Da hakan suka tashi ya samu ke6ancewa da Bahijja ya k'ara yi Mata nasiha da kuma hak'uri da k'addarar da ta samu bawa.
Tace ba komai Baba, amma ina jin kewar ka har cikin raina.
Yace to kiyi hak'uri kinga hajiya Safiya tace duk sati zata sa akai ki kiyi muna kwana biyu, ke dai ki kula da karatun ki kuma ki tsare mutuncin ki.
Tace tau Baba Allah ya Kai Ku gida lafiya, ka gaida min su Gwaggo.
Bayan angama ciku-cikun shiga makaran tar Bahijja, ta Fara karatun ta ba laifi tana maida hankali, kuma bata cika shiga sabgar mutane ba dama tun farko bata da tarkacen k'awaye lantana ce kawai k'awar ta.
Yanzu ma ta had'u da k'awa guda wadda tasu tazo d'aya wato Aisha Yagani.
Babu ruwan su da shiga sabgar mutane karatun su kawai suka sakama gaba.
****** *********
Can kuma 6angaren Shureim yana fama da matsalar Lateefa, tana bashi kulawa ko ina musamman wurin kwanciya, amma fa har yanzu bata shiga kicin da sunan girki.
Tun Bizzy na Jagal-gala musu abinci har ta fara iyawa ba laifi, Mum da Mamar Lateefa sun yita fad'a har sun gaji sun saka Mata ido.
Wani lokaci haka k'anwar ta Shema'u zata zo gidan ta yi Mata girki Mai rai da lafiya, saboda ba kalar girkin da Shema'u bata iya ba, don ma'abuciyar son girki ce tun tana k'arama.
Tana zaune falo tana waya da Bahijja tana complain kan cewa bata son tahowa gidan su.
Tace kiyi Anty Lateefa Zan zo satinnan amma fa sai na fasa zuwa Kimba kenan.
Lateefa ta ce gaskiya kam abamu wannan satin.
Jin sallamar Mmn zahra yasa ta tsinke wayar.
Nan ta zauna suka gaisa ta kar6i zahra tana Mata wasa.
Maman zahra tace ki tashi mu shiga gidan Mum zee muyi Mata Allah sanya alkhairi tunda bamu samu zuwa auren ba sanadiyyar rasuwar da aka yi maku.
Har zata Fara complain kuma tayi shiru ta figi gyalen ta suka wuce.
Suna shiga gidan sukayi part d'in Mum zee bayan sun gaisa sun Mata Allah sanya alkhairi, sai suka shiga hirar duniya duk yawancin hirar tasu akan kishiya ne.
Sun tashi zasu wuce ta raka su part d'in Amarya, nan ta tarbesu hannu biyu suka gaisa mutunce suka tashi.
Lateefa ta kalli Mum zee tace yanzu wannan kishiya ce kenan, kun raba miji kenan.
Tayi murmushi tace ba laifi muna zaman fahimta tsakanin mu, don tana bani girma na.
Hakan suka fito ta dubi Mmn zahra tace in banda jarabar namiji me wannan amaryar zata nuna ma Mum zee.
Nan Mmn zahra tayi murmushi tace baki ganewa ne.
Tace banko ta6a gane wa in dai akan kishiya ne.
Hakan suka rabu kowa ya shige gidan shi.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:37 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *95*- *100*🍒
Lateefa ta shirya ta dawo falo tana jiran shi, yana fitowa suka wuce, saboda zai sauke ta gidan su Muftah shiko zai wuce wurin d'aurin aure.
An d'aura auren *MUFTAH* da matar shi *BILKISU* *BILYAMIN* sai dai fatar zaman lafiya tsakanin su.
Sai zuwa dare da aka Kai Amarya Shureim ya rako ango sannan ya wuce da Lateefa.
Nan yake yiwa Muftah sharri kan cewa sai sun zo barka nan da wata tara, saboda naga zumud'in naka yayi yawa.
******** *********
Yau tun safe Lateefa ke Kai kawo a gidan, tana ba Bizzy umurnin abinda zata dafa.
Can ta shiga d'akin Shureim yace wai yau me ya hana ki zama haka?
Tace ka manta na gaya ma Sis zata zo muna yini yau.
Yace OK shine kike ta rawar Kai haka, ni na zata daga wata k'asa za kiyi bak'i, saboda naga wataran baki tashi daga bacci sai k'arfe goma, amma yau kece da tashi tun takwas.
Tayi murmushi tace Kimba wallahi Ina ji da Sis Bahijja ne tamkar k'anwata Shema'u, naga Kai ko tausaya Mata baka yi.
Nan yayi murmushi yace asha aiki lafiya, koda bak'uwar taki ma sai dai taci girkin y'ar aiki ya bita da gwalo.
Gane cewa tsokana yake ji yasa ta k'yale shi ta shiga wanka.
Koda ta fito ta shirya sai ta dawo falo ta zauna, bata fi minti goma da zama ba sai ga Bahijja ta iso ita da k'awar ta Yagani.
Hakan ta shek'o ta rungume Bahijja sai murna take yi, tace ma Yagani bismillah zauna mana.
Hakan suka zauna tasa Bizzy ta cika masu wuri da kayan tand'e-tand'e da lashe-lashe.
Suna zaune suna hira ne sai ga Shureim ya fito cikin shiga ta alfarma, ya saka k'ananan kaya ga sajen shi ya kwanta luf, ya had'u iya had'uwa ga kwarjini da ya cika fuskar shi.
Nan Bahijja ta durk'usa har k'asa tace yaya ina wuni.
Ya amsa da k'alau ya d'ora da cewa ya karatun, ya kuka baro Mum?
Tace k'alau Alhmdulillah.
Nan ma Yagani ta gaida shi, ya amsa yace to akula da karatun.
Nan yakai duban shi ga Lateefa yace to ni zan fita, nan ta rakashi sai da ya tada mota sannan ta dawo.
Bayan su Bahijja sun ci iya abin da zasu ci, nan ta jasu har bedroom d'in ta suna ta hira, Lateefa tace yaushe zaku gama karatun?
Tace nan da shekara guda.
Jin kiran azzahar ne yasa suka tashi domin sauke farali.
Bayan sun gama sallah ne Bahijja ta shiga kicin ita da Yagani ta had'a masu abincin dare, sannan suka kimtsa zuwa tafiya gida.
Lateefa tace kiyi hak'uri Kimba ya dawo sai ya sauke Ku nima inaso in bishi in gaida Mum.
Da k'yar ta samu suka zauna, sai da Shureim ya dawo yaci abinci yayi wanka ya canza kaya yayi shigar manyan kaya.
Nan ya kwashe su suka wuce, Yagani ya fara saukewa Lateefa ta bata ledar kayan Shafa tayi godiya sannan suka wuce gida.
Nan suka zauna gurin Mum suna ta hira sai daga baya suka wuce.
********** **********
```BAYAN``` ```SHEKARA``` ```D'AYA```
Yau ne Bahijja suka gama exam d'in su ta k'are health, daka dube su zaka San cewa suna cikin farin ciki.
Bayan fitowar su da kar6ar address d'in juna kowa ya Kama gaban shi.
Hakan kowa yaje gida cikin farin ciki da murna.
_BAYAN_ _KWANA_ _UKU_
Kamar yadda suka yi alk'awari da Mum kan cewa in ta gama karatu yazo ya wuce da ita.
Hakan yasa yau malam ya zo domin zuwa da Bahijja gida, koda yazo ya taradda Baban margyayi ma yazo hakan suka zauna aka tattauna rayuwar yau da kullum.
Cikin hakan ne Dad yace malam salisu Zan k'ara Neman wata alfarma Karo na biyu zuwa gare ka.
Malam yace haba Alhj wace irin alfarma ce wannan, na gaya ma babu shamaki tsakanin mu.
Ya yi murmushi yace d'an ka Shureim zaka bawa Bahijja aure.
Baban margyayi yace Alhj ya akayi kasan abinda ke cikin zuciya ta, dama wannan maganar ce ta kawo ni.
Nan dai suka yi maganar aka aje d'aurin aure sati guda masu zuwa.
Malam yace to zai je da Bahijja gida sai ranar alhamis zata dawo.
Hakan suka d'ungu ma sai Kimba, saida suka sauka malam yake gayama Bahijja meke faruwa.
Tace Baba don Allah ka taimakeni Ku janye wannan maganar, bazan iya auren Yya Shureim ba, innayi hakan na yaudari Anty Lateefa.
Yace kiyi hak'uri y'ar Baba ba yin kaina bane, kuma kinsan mutanen nan sunfi k'arfin komai a wurin mu.
Gwaggo tace kiyi hak'uri shi aure nufi ne na ubangiji, nan suka rarrashe ta sannan ta tashi ta koma d'aki.
Tana shiga d'aki ta fasa kuka maicin rai, tace mutuwa Mai yankan k'auna, yanzu da wane ido Zan kalli Anty Lateefa naje Mata matsayin kishiya.
Tana cikin tunanin ne taji Gwaggo saman kan ta, tace shegiya mayya kin lashe musu yaro ya mutu yanzu kin koma ga d'an cikin su.
To wallahi Bari in gaya maki ko Zan tafi tsira ra ba zaki aure shi ba, makwad'aiciya Mai idon cin nera ta Kai Mata rank'washi sannan ta fita.
Bayan taje ziyara dangin innar ta, kuma taje gidan su margyari har gidan lantana sai da taje.
Yau Mum ta turo direba ya koma da Bahijja, sannan tasa aka d'auko Mata Lateefa.
Nan ta had'a su tana yi masu nasiha sannan ta furta ma Lateefa abinda ke faruwa.
Dama an gaya ma Shureim ya amsa ba yabo ba fallasa sai dai fargabar had'uwar shi da Lateefa.
Lateefa ta bi Mum da ido tace bangane ba.
Mum tace saura kwana biyu auren Shureim da Bahijja.
Idon sun k'ank'ance ta bud'a baki zata yi magana kome ta tuna, sai ta zabura ta nufi hanya tamkar zararra.
Mum na kiran ta ko waiwayo ta bata yiba da saurin ta tafita daga gidan.
Bahijja ta rik'a kuka maicin rai tace Mum kiyi hak'uri ki janye maganar nan, kin ga Lateefa ba zata ji dad'i ba.
Mum tace mu mukasan dalilin wannan had'in, in kema zaki bijiremin ne kamar yada Lateefa ta yimin to bisimillah, ta tashi ta wuce d'akin ta tabar Bahijja nan.
Yau ne mutane suka shaida auren
_SHUREIM_ _SULEIMAN_
*DA*
_BAHIJJA_ _SALISU_
A garin Kimba, Allah ya basu zaman lafiya.
(Masoyan Bahijja Ku fito Ku taya ta zaman kishi da Lateefa, _lolx_)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 1:38 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *100*- *105*🍒
Duk mutanen k'auyen Kimba sun shirya an yi mota uku har da dangin innar Bahijja sun nufi jega gurin auren Bahijja.
Amma koda aka yima Gwaggo magana kan a shirya sai tace su tafi zata zo daga baya sai ta kar6oma d'iyar ta wasu abubuwa.
Bayan sun wuce Gwaggo tayi gurin bokan ta, tace boka d'an dugaji na rasa ya Zan yi da wannan shegiyar yarinya nidai yanzu na yarda akashe ta ko a 6atar da ita.
Hhhhhhhh dama tun farko nace ki bari ayi hakan kika k'i, amma yanzu tunda kin amince Zan baki wasu ruwa ki k'ok'ar ta kamin a fita da ita zuwa gidan mijin ki saka Mata su cikin ruwan wanka, hakan zai yi sanadiyyar 6acewar ta har abada.
Da sauri ta tari mota tayi sa'a da saura mutum guda ta fad'a suka kama hanya.
Har sun kusa isowa jega wata babbar mota tabi ta kan motar su, nan aka kwashe su sai asibiti wasu sun rasu, wasu kuma sun ji rauni.
********* ***********
Lateefa na shiga gida ta fad'a saman jikin mamar ta sai kuka take yi.
Umma tace lafiyar ki kuwa, wa ya rasu?
Da k'yar tayi shiru ta gaya ma Umma meke faruwa.
Nan Umma taja dogon tsaki tace in zai yi aure shine me, dama cewa aka yi dake kad'ai zai zauna sha-sha-shar banza da wofi.
Kuma ni hakan yayi min dai-dai sai shegen kishi amma bakisan ya zaki gyra tumbin mijin ki ba, dama nasan hakan zai faru komi dad'ewa.
Tana cikin yi Mata fad'an ne sai ga Abban ta ya sauko nan yake tambayar meke faruwa.
Umma ta yi Mai bayani nan ya Fara fad'a yace Lateefa ta tashi ta shiga dakin ta, ya d'ora da cewa ba inda zata je yaje ya zauna da amaryar shi.
Umma ta Kai duban ta zuwa gare shi tace ina fatar ba kashe ma y'ar ka aure zaka yi ba, gaskiya kana nuna ma yarinyar nan gatan da bai dace ba.
Yace ko ke da kika haife ta nace Zan yima kishiya sai anga tashin hankali ballan tana ita, ai kishi a jinin Ku yake.
Nan ya sa Kai ya fice yana ta faman fad'a.
********** ***********
Can gidan su Shureim kuwa an ji Gwaggo shiru kuma ba waya take da ita ba har k'arfe goma bata zoba sai kawai aka yanke hukuncin aje akai amarya d'akin ta k'ila gwagg ta fasa tahowa.
Hakan aka d'unguma Kai amarya, ciki kuwa har da Blkisu matar Muftah su lantana da Hindatu k'anwar margyayi.
Nan dai aka yi Mata hud'uba kowa ya wuce sai Blkisu da Aisha Yagani.
Sai k'arfe goma sha d'aya ango ya shigo shi da Muftah nan ya had'asu ya k'ara yi masu nasiha kan hakk'in miji akan matar shi da kuma hakk'in Mata akan mijin ta.
Bayan yayi addu'ar zaman lafiya ya sa matar shi gaba, Shureim yace su sauke Yagani gida, bayan sun wuce ya rufe gida ya dawo ya taradda Bahijja ta wuce d'aki.
Part d'in shi ya wuce ya watsa ruwa yasa kaya marar nauyi sannan ya fito ya d'auki kayan da ya shigo dasu ya shiga d'akin Bahijja.
Koda ya shiga tayi wanka ta saka kayan bacci, nan ya aji ye kayan yaje kicin ya d'auko plate da cups ya dawo d'akin, ya zuba komai yace ta sauko suci.
Cikin sanyin muryar ta tace yaya na k'oshi.
Yace ki sauko kici ko kad'an ne, ganin cewa bata iya yimai gardama yasa ta sauko, kuma tun fil azal nauyin shi take ji sosai.
Hakan suka ci suka k'oshi, sannan ya umurce ta da ta tashi tayi alwala suyi nafila.
Nan ta rik'a soke Kai ta kasa magana, jin ya maimaita maganar ne yasa ta furta period take.
Hakan yaji ba dad'i duk da bai k'udurta ma ranshi wata doguwar mu'amala tsakanin su.
Hakan suka kwanta saman shimfid'a guda ya janyo ta ya manna saman k'irjin shi.
********* ************
Lateefa kuwa tana gidan su sai juyi take yi saman gado zuciyar ta tamkar zata k'one saboda suya.
Anyi-anyi ta koma d'akin ta tace Sam ita ta gama da Kimba don bazata iya had'a shimfid'a da shiba yaje ya had'a da wata ba.
Ko su Anty Nafeesa sun zo auren Shureim duk yada ake bada baki sun bata kan ta koma d'akin ta amma Abu ya faskara.
Daga baya ma munafukai ta rik'a ce musu tana cewa har da kwaso jiki suzo aure don za ayi Mata kishiya, kuma kishiyar ma data rik'a tamkar k'anwar ta shema.
Anty Nafeesa tayi murmushi tace koda auren ki ko babu dole muje ma Mum auren Shureim.
Duk yada ake bada baki Shureim ya yi amma tak'i sauraren shi, ko ya Kira waya bata d'auka, yayi text message har ya gaji ba reply.
Kuma ko yazo gidan su data jishi take rufe k'ofar ta.
Shi kuma Abban ta yace ba zai takura taba abar ta sai ranar da ta sauko da kan ta.
Yau da safe aka yi bincike Gwaggo bata Kimba bata Jega nan hankalin mutane ya tashi kan rashin takamemen ina take.
Shureim na breakfast shi da Bahijja yana tsokanar ta sama-sama kan cewa abinci ne bata ci sosai shiyasa tak'i yin k'iba.
Ita ko sai murmushi take yi tana soke Kai, cikin hakan ne wayar Shureim ta hau ruri koda ya duba Dad ne ya Kira shi.
Bayan ya d'auka suka gaisa yake ce Mai yayi sauri yazo yana Neman shi sai ya kashe wayar.
Gaggauce ya gama breakfast ya d'auki key d'in mota har ya Kai k'ofar fita daga falon ya waiwayo idon su suka had'e sai ta soke Kai tana murmushi.
Yace Mata dubo kigani, tana tayar da kan ta ya yima hannun shi kiss ya hura Mata iska ya wuce.
Cikin ran ta tace Ashe haka yaya yake da dad'in zama.
Yana shiga ya gaida iyayen shi, nan aka Kora Mai abinda ke faruwa take ya Kira Muftah yace ya bincika Mai asibiti koda akwai masu hatsari, hakan ya Kira sauran doctors na asibitoci da dama yana basu cigiya.
Ba afi minti goma ba sai ga kiran Muftah yace Mai akwai su nan asibitin su kuma ance akwai y'an Kimba ciki.
Nan suka d'unguma shi da Mum da Dad sai asibitin, cikin bincike ne aka gano cewa tana cikin masu rai sai dai k'afar ta d'aya ta karye d'ayar kuma k'ashin k'wauron ta duk ya tartse fuskar ta duk taji rauni.
Nan Dad ya Kira direba yace yaje Kimba yazo da Baban Bahijja, shiko Shureim ya Kira wani friend d'in shi asibitin F.M.C Birnin kebbi kan cewa yanzu zai turo gwaggon shi aduba ta.
(Fan's na gode sosai da kulawar ku, wasu sun Kira sun yimin ta'aziya, wasu sun yimin ta p/chart, wasu ta groups na gode sosai Allah ya bada lada.)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 2:08 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *110*- *115*🍒
Tana d'akin ta Shema'u k'anwar ta ta shigo tace Anty kin yi bak'i.
Tace daga Ina, nifa banson takura wallahi.
Ta ce Mata inaga kamar wannan mak'ociyar ki.
Tace to ki shigo dasu, nan ta fita ta shigo dasu.
Suna shigowa taga cewa maman Zahra ce da Mum zee, nan ta tashi ta taryo su cikin murnar ta da sakin fuskar ta.
Nan Shema'u ta kawo musu kayan motsa baki da abinci.
Bayan sun gaisa Mmn Zahra tace shikenan kin gujemu ko waiwaye babu.
Tayi murmushi tace ba gamu tare ba yanzu, kuma muna waya.
Mum zee tace wallahi baki kyauta ba wa yace maki ana tashi gidan miji saboda kishiya, shifa lamarin duniya sauk'i Gare shi sai Wanda ya wahalda kanshi.
Kuma kishiya abokiyar zama ce don wani lokaci zaka ci amfanin ta itama zata ci naki.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa har fa kullum kina yabon halayen Bahijja kuma kin fad'a da kan ki cewa kullum kina yi Mata addu'a Allah ya bata miji nagari.
In kin manta in tuna maki har cewa kika yi da kina da d'an Uwa namiji da kinsa ya aure ta.
Me yasa ba zaki yarda cewa mijin ki shine mafi alkhairi a gareta ba.
Yanzu mum zee ba zata zama ishara gareki kisan cewa ba duka aka taru aka zamo d'aya ba, gasunan suna zaman su lafiya tamkar ya da k'anwa.
Nan Lateefa ta saukar da wata nauyayyar ajiyar zuciya, tace nifa kar kuga abinda ke tayar min da hankali tamkar Amarya ta shigo cikin gida ta nemi fitar da uwargida.
Wata ma in kina da yara zata nemi hanyar da zata bi ta wulak'antar da su ga ubansu.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa yarda kika San amare da tasu matsalar to ko uwayen gida suna da tasu matsalar, saboda wata uwargida ba zata fitar da Amarya ba amma wallahi zata yi silar wulak'anta ta yarda ko y'ar aiki zata fita daraja, ke dai kawai muyi fatar Allah yadatar damu da kiyoshi na gari masu zuciyar imani.
Mum zee ta kar6a da ameen tana Mai cewa kuma gaskiya kinga wani lokaci uwayen gida Nada tasu matsala.
Abu na farko zaki ga wata da zarar ance za ayi Mata kishiya to zaki ga ta Fara hauka tana sakin maganganu da zasu fita har sukai ga kunnen amarya kinga girma ya fad'i.
Abu na biyu azo ayi aure uwargida ta k'i kama girman ta, shima hakan na kawo raini tsakanin zama saboda kin sake taga makwancin ki.
Amma gaskiya muddin kika rik'e girman ki koda Amarya ta shigo bazata raina kiba kuma in kin dace da tsayayyen miji saboda ko su da tasu matsala.
Mmn Zahra tace yanzu miye ribar ki kinfita kinbar gida, kuma hakan bai hana auren ba don yanzu haka suna Dubai shida Amarya, kinga kuwa kin d'aga musu k'afa susha amarcin su hankali kwance.
Nan tashin hankalin Lateefa ya k'aru saboda batasan sunyi tafiyar ba, Umma ta hana agaya Mata saboda ko y'an gidan ta rage mu'amala dasu ko yaushe tana d'aki.
Nan take ta mik'e ta lalabo layin ta data d'ebe ta saka shi a waya saiga text message d'in shi na shigowa na ban hak'uri, sai ga wasu zafafan hawaye na sauko wa daga idon ta na tausayin kan ta.
Nan dai suka rarrashe ta har ta sauko kuma tayi masu alk'awari zata ba Kimba mamaki don zai dawo ya taradda ita d'akin ta.
*******************
A can Dubai kuma su Shureim sun shirya sai asibiti domin su duba jikin Gwaggo.
Suna shiga Bahijja ta had'a Mata tea Mai kauri tasha sannan ta jik'a towel ta shafe Mata jikin ta.
Nan Gwaggo ta rik'a kuka tana cewa y'ar Baba ki yafemin na cuce ki na zalunce ki yanzu gashi dake da mijin ki ke wahala dani.
Malam yace ki daina wannan kukan bayada fa'ida.
Tace malam dole in yi kuka nan ta rik'a zayyano irin cutar da ta rik'a yima Bahijja har zuwa yanzu data so 6atar da ita Allah ya nuna Mata abinta.
Ta d'ora da cewa ko mahaifiyar ta nice nayi silar zuwan ta barzahu, saboda ciwon ta na tashi malam ya fita kasuwa ni na saka filo na danne ta saida ta daina numfashi.
Nan Bahijja ta fad'i sume, malam ko yayi mutuwar tsaye inda Shureim ya bita da kallon tsana ji yake yi tamkar ya k'arasa gundule k'afar ta d'aya.
Sannan ya durk'usa yana jijjiga Bahijja da k'arfi yace _Heeja_.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 2:12 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *105*- *110*🍒
Koda aka je da ita asibiti duk bata San in da take ba, nan suka yi aune-aunen su Dr Musa yace gaskiya sai an fita da ita Dubai.
Nan take Dad yasa aka yi biza uku ta tafiya, da malam salisu ya Gan ta sai da yayi kuka sosai, yace lallai tabbas rayuwar duniya ba bakin komai bace.
KO kamin su wuce Dubai sai da yaje gidan su Lateefa tak'i Bari ya Gan ta ta shige d'aki ta rufe, abin har ya Fara bama Umma haushi tace ma Shureim ya je kawai ya k'yale ta.
Hakan suka d'unguma da Gwaggo sai Dubai, har suka shigo k'asar Bahijja kuka take yi saboda tausayin halin da Gwaggo take ciki, nan Shureim ya Kama musu d'aki biyu su d'aya Baban Bahijja d'aya.
Bayan ya ajiye su masauki ne aka wuce da Gwaggo asibiti, bayan gwaje-gwajen su suka ce dole d'ayar k'afar wadda k'wauron ta ya tartse sai an yanke ta, d'ayar kuma za ayi Mata d'orin kariya na asibiti, hakan Shureim ya yi duk abinda ya Kama ta sannan ya koma masauki saboda baije da Bahijja ba akan kukan da take yi.
********** ********
Yau kwanan su Bahijja uku da tafiya Mum ta shirya taje gidan su Lateefa.
Tana shiga suka gaisa da Umma tace gani nazo bikon y'ata.
Umma tayi murmushi tace ke kike wahalda kan ki akan wannan sha-sha-shar kawai Ku saka Mata ido har ranar da duniya ta yimata fad'a.
Mum tace ai ba ayi haka ba, suna maganar ne Shema'u ta kawo ma Mum kayan motsa baki, bayan ta ajiye ta durk'usa ta gaida ta.
Mum ta amsa tace shiga ciki ki Kira min Lateefa.
Suna cikin hira ne sai ga Lateefa ta iso nan ta gaida Mum ba yabo ba fallasa.
Mum tayi murmushin su na manya tace Lateefa har yanzu ba agama fushi Dani ba?
Nan ta had'e rai tayi shiru bata ce komai ba.
Mum tace Lateefa kiyi hak'uri shi aure nufi ne na Allah, kuma wannan matar kinsan ba Shureim ya furta cewa zai aure ta ba Dad d'in Ku ne ya yi wannan had'in, kiyi hak'uri ki bar ma Allah kuma kinsan waye Bahijja bata da matsalar zama kiyi hak'uri kinji y'ata.
Tace to shikenan Mum sai na shirya Zan koma.
**** **** **** ****
A can Dubai kuma an yi aiki cikin nasara saura jiran shan magani da sauran warkewar Gwaggo.
Kullum da safe zasu je su duba jikin Gwaggo sai marece su koma masaukin su.
Kullum Bahijja kesa towel ruwa ta shafe ma Gwaggo jikin ta, sannan ta zauna ta rik'a ba ta abinci.
Koda Shureim ya dawo daga masallaci ya taradda Bahijja na sallah, bayan ta idar ne suka zauna suka ci abinci suna k'arasawa yakai duban shi zuwa Gare ta yace Sister shine ba ko sanarwa.
Fahimtar inda ya dosa yasa ta soke kan ta.
Yace na kusa fitar da wannan kunya taki saboda tana takura min.
Nan tayi murmushi tace yaya ka Kira Anty Lateefa?
Yace Antyn ki bata sauko ba har yanzu tana fushi kin k'wace Mata sankacecen saurayi.
Nan take ta zare ido dai-dai ya tada kan shi sai suka had'a ido ita ko ta sunne kan ta tana murmushi.
Hakan ya taso ya rik'a hannun ta ya mik'ar da ita ya yi mata rad'a cikin kunne, da sauri ta fizge hannun ta tayi cikin d'aki.
Yana shiga yace taje tayi alwala zasu yi sallah, hakan tayo alwala sai gaban ta ke dukan uku-uku.
Bayan sun gama ya yi Mata tambayoyin da suka shafi addini kuma tana da ilmin ta gwargwado.
Hakan taje tayi wanka ta feshe jikin ta da turare, shima hakan.
Suna kwanta wa ya Jan yota saman k'irgin shi ya yi Mata kyakkyawar runguma ya ja masu bargo.
(Nidai Jegal nace Allah ya bada d'an Dubai, *LOLX*)
~~~~~~~~~~
~~~~~~~~~~
*WASHE* *GARI*
Yana tashi daga bacci yaje yayi wanka sai da yayi sallah sannan ya had'a ruwa masu d'imi yazo ya yaye bargon da ta rufa dashi ya sunkuce ta sai toilet.
Shi ya yi Mata wanka ya gasa ta, tana cewa nidai yaya banaso tana soke Kai.
Sai da ya gama sannan ya d'auko ta ya nad'e cikin towel ya ajiye ta ya d'an fita.
Ko kamin ya dawo ta lalla6a tayi sallah har ta shirya.
Ashe gurin Baban ta ya shiga suka d'an ta6a hira saboda k'a idar asibitin da aka Kai Gwaggo Mai jinya bai kwana can.
Yana shigowa ya iso ya zauna gefen gado yakai dubanshi zuwa Gare ta sai kuma ya Jan yota ya Kai Mata kiss ita ko duk kunya ta ishe ta.
Yace Heeja Ina son in yi maki wata tambaya d'aya.
Tace Ina jin ka yaya, tana Mai Kai duban ta zuwa gare shi.
Yace ya akayi na same ki budurwa bayan kuma kin yi aure sama da shekara biyu sannan Allah ya kar6i ran margyayi?
Nan idon ta suka yi rau-rau tamkar ta yi kuka.
Ya k'ara Jan yota saman jikin shi yana bubbuga bayan ta cikin rarrashi yace kar kiyi kuka.
Tace ka bari in mun yi breakfast mun je dubo jikin Gwaggo mun dawo Zan gayama.
Ba hakan yaso ba saboda ya matsu yaji ya akayi hakan ta kasance, sai dai baison takura ta.
(Nima dai na matsu in ji yadda hakan ta kasance👂🏻)
© *SDY* *JEGAL*
🍒 *BAHIJJA* *110*- *115*🍒
Tana d'akin ta Shema'u k'anwar ta ta shigo tace Anty kin yi bak'i.
Tace daga Ina, nifa banson takura wallahi.
Ta ce Mata inaga kamar wannan mak'ociyar ki.
Tace to ki shigo dasu, nan ta fita ta shigo dasu.
Suna shigowa taga cewa maman Zahra ce da Mum zee, nan ta tashi ta taryo su cikin murnar ta da sakin fuskar ta.
Nan Shema'u ta kawo musu kayan motsa baki da abinci.
Bayan sun gaisa Mmn Zahra tace shikenan kin gujemu ko waiwaye babu.
Tayi murmushi tace ba gamu tare ba yanzu, kuma muna waya.
Mum zee tace wallahi baki kyauta ba wa yace maki ana tashi gidan miji saboda kishiya, shifa lamarin duniya sauk'i Gare shi sai Wanda ya wahalda kanshi.
Kuma kishiya abokiyar zama ce don wani lokaci zaka ci amfanin ta itama zata ci naki.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa har fa kullum kina yabon halayen Bahijja kuma kin fad'a da kan ki cewa kullum kina yi Mata addu'a Allah ya bata miji nagari.
In kin manta in tuna maki har cewa kika yi da kina da d'an Uwa namiji da kinsa ya aure ta.
Me yasa ba zaki yarda cewa mijin ki shine mafi alkhairi a gareta ba.
Yanzu mum zee ba zata zama ishara gareki kisan cewa ba duka aka taru aka zamo d'aya ba, gasunan suna zaman su lafiya tamkar ya da k'anwa.
Nan Lateefa ta saukar da wata nauyayyar ajiyar zuciya, tace nifa kar kuga abinda ke tayar min da hankali tamkar Amarya ta shigo cikin gida ta nemi fitar da uwargida.
Wata ma in kina da yara zata nemi hanyar da zata bi ta wulak'antar da su ga ubansu.
Mmn Zahra ta kar6e tana Mai cewa yarda kika San amare da tasu matsalar to ko uwayen gida suna da tasu matsalar, saboda wata uwargida ba zata fitar da Amarya ba amma wallahi zata yi silar wulak'anta ta yarda ko y'ar aiki zata fita daraja, ke dai kawai muyi fatar Allah yadatar damu da kiyoshi na gari masu zuciyar imani.
Mum zee ta kar6a da ameen tana Mai cewa kuma gaskiya kinga wani lokaci uwayen gida Nada tasu matsala.
Abu na farko zaki ga wata da zarar ance za ayi Mata kishiya to zaki ga ta Fara hauka tana sakin maganganu da zasu fita har sukai ga kunnen amarya kinga girma ya fad'i.
Abu na biyu azo ayi aure uwargida ta k'i kama girman ta, shima hakan na kawo raini tsakanin zama saboda kin sake taga makwancin ki.
Amma gaskiya muddin kika rik'e girman ki koda Amarya ta shigo bazata raina kiba kuma in kin dace da tsayayyen miji saboda ko su da tasu matsala.
Mmn Zahra tace yanzu miye ribar ki kinfita kinbar gida, kuma hakan bai hana auren ba don yanzu haka suna Dubai shida Amarya, kinga kuwa kin d'aga musu k'afa susha amarcin su hankali kwance.
Nan tashin hankalin Lateefa ya k'aru saboda batasan sunyi tafiyar ba, Umma ta hana agaya Mata saboda ko y'an gidan ta rage mu'amala dasu ko yaushe tana d'aki.
Nan take ta mik'e ta lalabo layin ta data d'ebe ta saka shi a waya saiga text message d'in shi na shigowa na ban hak'uri, sai ga wasu zafafan hawaye na sauko wa daga idon ta na tausayin kan ta.
Nan dai suka rarrashe ta har ta sauko kuma tayi masu alk'awari zata ba Kimba mamaki don zai dawo ya taradda ita d'akin ta.
*******************
A can Dubai kuma su Shureim sun shirya sai asibiti domin su duba jikin Gwaggo.
Suna shiga Bahijja ta had'a Mata tea Mai kauri tasha sannan ta jik'a towel ta shafe Mata jikin ta.
Nan Gwaggo ta rik'a kuka tana cewa y'ar Baba ki yafemin na cuce ki na zalunce ki yanzu gashi dake da mijin ki ke wahala dani.
Malam yace ki daina wannan kukan bayada fa'ida.
Tace malam dole in yi kuka nan ta rik'a zayyano irin cutar da ta rik'a yima Bahijja har zuwa yanzu data so 6atar da ita Allah ya nuna Mata abinta.
Ta d'ora da cewa ko mahaifiyar ta nice nayi silar zuwan ta barzahu, saboda ciwon ta na tashi malam ya fita kasuwa ni na saka filo na danne ta saida ta daina numfashi.
Nan Bahijja ta fad'i sume, malam ko yayi mutuwar tsaye inda Shureim ya bita da kallon tsana ji yake yi tamkar ya k'arasa gundule k'afar ta d'aya.
Sannan ya durk'usa yana jijjiga Bahijja da k'arfi yace _Heeja_.
© *SDY* *JEGAL*
🍒 *BAHIJJA* *115*- *120*🍒
Da sauri Baban ta shima yayo kan ta.
Nan Shureim yayi sauri ya Kira Dr yana shigowa ya bada umurnin a shigar da Bahijja wani d'aki na kusa da Gwaggo har zuwa lokacin bata numfashi.
Dak'yar likita ya samu ta farfad'o sai numfashi take Mai dawa sama-sama.
Dr ya dubi Shureim yace a daina tayar Mata da hankali don ta razana sosai.
Shureim yace za a kiyaye inshaAllah.
Baban ta na ganin ta farfad'o yayi hamdala, yace ma Shureim su tashi su koma masauki.
Shureim yace Baba lokacin komawar mu bai yiba fa.
Yace to ni kasa akaini Ku Ku zauna, hakan Shureim ya rik'o hannun Bahijja suka samu taxi sai masaukin su.
Har suka je idon Bahijja basu daina zubar da hawaye ba.
Shureim yakai duban shi gare ta yace Heeja ki daina kukan hakan nan ya isa, ko hakan Gwaggo ta rayu taga k'ask'anci.
Lallai duniya abin tsoro ce yanzu akan kishi mutum zai iya kashe d'an uwan sa.
Bahijja ta nisa tace banzaci k'iyayyar da Gwaggo ke yimin har takai hakan ba, na zata abin nice bata k'auna Ashe ko mahaifiya ta tasha wahala Gare ta.
Yace *Heeja* kiyi hak'uri wannan tsakanin ta da ubangiji ne ko zata mutu ta taradda abinda ta shuka, ranar da na kad'e ki da mota na hango tsananin tashin hankali cikin k'wayar idon ki Wanda har Mum sai da nagaya ma.
Nan dai ya yita rarrashin ta tare da nuna Mata salon tashi k'auna zuwa gareta.
Yace *Heeja* ki d'an bani tak'aitaccen tarihin zaman ki da margyayi.
Nan ta nisa tace zaman mu da margyayi zama ne na tausayawa da kuma k'auna irin wadda ke tsakanina dashi, don tun muna k'auye yake tausaya min sosai akan ganin uk'ubar da nake ciki.
Silar kuma samu na da kayi cikakkiyar budurwa wannan ya faru ne sanadiyyar alk'awarin da ya d'auka kan cewa ba zai sadu daniba har sai na mallaki hankalin kaina nasan miye aure.
Saboda ga wannan lokacin kawai na zata Mace ta yiwa mijin ta girki yaci shine aure.
In har ban manta ba akwai lokacin da muna kallon wani film na Hausa naga wata Mata nata kwarara amai har na tambaye shi mike damun ta.
Yaba ni amsa da cewa ciki ne da ita, sai na cemai to naga mijin baima bata abinci ya aka yi har cikin ta yayi k'ato.
Nan yayi murmushi yace lallai Bahijja kina da saura ko yanzu.
Ana saura kwana biyu ya rasu yaso ya cika burin shi akai na to ganin cewa na tsora ta sosai yasa ya k'yale ni.
Wannan shine babban tashin hankali na da aka ce ya rasu sai Ina ganin tamkar ban kyauta mashi ba, nan wani kuka yazo Mata.
Har cikin ran shi yaji zafin kukan nata sai yake ganin cewa tamkar tafi son margyayi akan shi.
Wata zuciyar tace Mai to dama cewa ta yi tana son ka, in har baka manta ba ai Dad ne ya had'a Ku aure.
D'ayar zuciyar tace to ai tun ranar da ka Fara d'ora idon ka akan ta ka Fara jin tausayin ta, kuma lokacin da margyayi ya gaya ma ita zai aure ka tuna da damuwar da ka shiga.
Ganin cewa ta yima nisa ne yasa ka ya kice ta daga zuciyar ka.
Amma hak'ik'anin gaskiya yadda yake jin *Heeja* har cikin ran shi baya jin son Lateefa hakanan, saboda Lateefa ita ta nuna soyayyar ta zuwa gare shi har ya amince Mata suka Kai ga aure.
Jin kukan ta ya tsanan tane yasa ya dawo hayyacin shi, hakan ya kori shaid'an daga zuciyar shi dake ingiza shi kishi da matacce.
Ya Jan yota jikin shi yana rarrashi daga hakan suka Lula duniyar ma'aurata.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
Yau ne Lateefa ta koma gidan Shureim domin ta bi shawarwarin k'awayen ta data Kira aminnan k'warai.
Da taimakon Mum Zee da Mmn Zahra ta jajirce gurin koyon girke-girke, sun saka ta group na koyon girki ta whatsap, kuma sun had'a Mata da littafai su ma na girki domin su k'ara taimakon ta.
Amma fa can k'asan zuciyar ta ta d'aukar ma kanta wani k'udiri Wanda ita kad'ai tasan dashi.
Yau kawai taji tana son zuwa gidan Mum, bayan ta shirya ta cema Bizzy ta shirya suje tare.
Suna shiga Mum ta tarbe ta tace Lateefa kin gama fushi da Mum d'in ki?
Tayi murmushi ta soke Kai nan ta zauna suka yita hira da Mum har ta taya ta aikin dare tace Mum don Allah kar ki gayama Kimba cewa na dawo inaso inyi surprise d'in shi ne.
Mum tace ja'ira kawai kina zaman ki lafiya da mijin ki kishiya zata fitar da ke saboda shegen kishin ki na tsiya.
Cikin ran ta tace Mum dake San k'udiri na da baki yi murnar ganin na sauko ba.
Da hakan tayi sallama da Mum suka wuce ita da Bizzy.
(Anya kuwa wahalar Bahijja ta k'are ko kuma zata fad'a ta kishiya ne🙆🏼)
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 2:17 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *120*- *125*🍒
Yau ne su Bahijja suka cika sati biyar a Dubai, kuma ba laifi Gwaggo tana taka k'afar ta d'aya, d'ayar kuma sai da sanda take tafiya.
Har yanzu malam fushi yake yi da Gwaggo saboda ko a mafalki baiyi tunanin zata iya kashe koda kiyashi ba barranta na mutum.
Tabbas yana jin mutane da dama na cewa Gwaggo na wahalar da Bahijja, amma ko kad'an tunanin shi bai bashi abin gaskiya bane saboda yana ganin yarda take tarairaya da ita, ya zata kawai ana son had'asu ne.
Haka suka tar kato kayan su sai gida Nigeria, koda suka sauko daga jirgi direba yazo d'aukar su daga gidan su Shureim.
Gidan su Shureim suka Fara sauka sai da Mum ta cika musu cikin su da abinci, sannan aka k'ara ja jantama Gwaggo da jiki, ita ko sai kuka take yi tana k'ara yi masu godiya.
Bayan sun huta ne malam ya k'ara yima Alhj Suleiman godiya kan d'awai niyarda ya d'auka ta lalurar Gwaggo.
Alhj yace haba malam salisu ai an zama d'aya kuma yanzu tsohuwar abota ta motsa tunda d'iya sun k'ara had'a mu, nan suka tafa suna dariya had'e da d'auko hirar zaman k'urciyar su.
Zuwa k'arfe biyar Alhj yasa direba ya kaisu Kimba, nan suka rabu da Bahijja har da guntun hawayen ta na rabuwa da Baban ta.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
Suna isa garin su suka ga gidan su ya canza, malam na fito wa yayi tsaye yana waige-waige.
Nan direba ya fitar da key d'in gidan yaba malam, ya d'ora da cewa tun tafiyar ku Alhj yasa aka rushe gidan Ku aka maida shi haka, kuma duk wani abin amfani ya zuba maku aciki.
Nan malam yayi mutuwar tsaye har da guntun hawayen shi na murna.
Bai k'ara sarewa da lamarin Alhj ba sai da ya shiga gidan, babban Falo ne da d'akuna uku cikin shi, ko wane d'aki ciki da falo ne da toilet ko wane da gado da wardrobe acikin shi, sai kuma falo da aka zuba saitin kujeru.
Sai kuma filin gida da aka yi dogon d'aki na saukar bak'i da toilet aciki.
Nan Gwaggo ta zube sai kuka take yi tana Mai k'ara nadamar abinda ta aika ta.
Kota kanta malam bai koma ba ya shige d'ai daga cikin d'akunan sannan ya fita ya sallami direba yana k'ara yimai godiya tamkar shi ya bashi kyautar gidan.
Yace ka yimin godiya ga Alhj kamin inzo, ya amsa da to sannan ya tada mota ya hau hanya sai gidan margyayi maigari saboda sauke kayan abinci da Alhj yace ya kawo masu.
Kamin kace kwabo y'an ganin gida da y'an Allah sanya alkhairi da y'an gulmar ganin yada Gwaggo ta koma suka cika gida.
Can na jiyo hirar wasu mata su uku bayan fitowar su daga gidan.
D'ayar tace jummai kinga yada Allah ya mayar da lami ko, nan da can bata iya d'agawa saida sanda.
Wadda aka Kira da jummai tace ke dai bari ladiyo don ma ance surikin Bahijja ne ya taimaka ya kaita k'asashen waje aka yi Mata aiki aida yanzu wallahi ta ru6e sai tsutsa.
Can Hasana ta kar6e tace lallai lami taga jarabawa don azabar da ta gana ma y'ar Baba ba k'ara maba ce don ma Allah ya tak'aita Mata abin ya tsaya a haka.
Ladiyo tace nidai jin nayi ance wai malam salisu sayar da Bahijja yayi ga wani Mai kud'i shiyasa ya gyra Mai gidan shi haka.
Jummai tace wallahi ba haka bane d'an gidan margyayi Mai gari ne, baki ganin duk karkarar nan babu gidan da yakai gidan su kyawo, kuma mutum ne Mai son taimaka ma talakawa.
Kina ganin ko garin nan ya shigo yadda yake rabon kud'i ga mutane, an ce ma can birni rijiyar kud'i ne dashi.
Nifa duk Ina jin wannan labari ne daga kaka ta, saboda kishiyar tace k'awar Mai aiki gidan margyayi Mai gari.
Nan suka kar6e su biyun suna cewa ahhh lallai dole kisan labarin gidan.
Jin gyran murya bayan sune yasa suka waiga Ashe malam ne zai fito daga gidan su ko sun tare hanya.
Nan ko wacen su taja raggan k'afafun ta tayi gaba sum-sum, shiko yayi murmushi ya girgiza Kai alamar yaji maganar su, _lolx_.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 2:21 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *125*- *130*🍒
Bayan sun huta ne Bahijja tace yaje kawai ita gurin Mum zata kwana saboda tayi kewar Mum.
Shi ko Shureim yace sai dai su kwana gidan gaba d'aya kuma a part d'in shi.
Jin hakan yasa Mum tace su kwashi kayan su wuce gidan su.
Bahijja na kumbure-kumbure ta shirya suka wuce, suna cikin mota sai tsokanar ta yake yi yana cewa haka kawai ki k'yale bawan Allah shi kad'ai ki je ki mak'ale gurin Mum.
Tana murmushi tana binshi da harar wasa, da hakan har suka Kai gidan.
Lokaci guda zuciyoyin su suka rik'a bugawa da k'arfi saboda abinda suka ci Karo dashi cikin falo, wato Lateefa zaune tana kallo.
Da murnar ta tazo ta rungumeshi ta Kai Mai wani irin kiss Mai nuna alamar tayi kewar shi.
Hakan ya tarye ta cikin murnar shi ta nuna shima yayi missing d'inta.
Maganar Bahijja ta dawo dasu daga duniyar da suka Lula, cewar da tayi Anty Ina wuni, da fatar mun same Ku lafiya, cikin muryar ta Mai fargabar wace irin tarba zata yi Mata matsayin ta na kishiyar ta yanzu.
Muguwar hara rar da ta bita da ita ne yasa dole ta soke kan ta.
Tace da ban wuni ba zaki ganni?
Tunda kin za6i zaman kishi dani sai kizo mu gwabza, banza kawai y'ar talakawa y'ar masu neman maula.
Nan take idon ta suka kawo ruwa cikin k'unar rai ta wuce ta nufi d'akin ta.
Shureim ya Kai duban shi ga Lateefa yace wannan kuma shine miye?
Ina hankali da nutsuwa had'e da taimakon marasa shi da kike da?
Yau har kece zaki kalli wani ki Kira shi da Kalmar matsiya ci.
Gaskiya kin ban mamaki, duk ina so kulawa had'e da tarairaya da kike nuna ma Bahijja, yau koni bazan gaya maki halayyar Bahijja ba saboda kin fini sanin waye ita.
Kin sha muna hira kina bani labarin ta da kuma yabon halayen ta na Kirki da girmamawa.
Nan ta nisa tace nidai muje kayi wanka kazo kaci abinci saika huta.
Jin wucewar su d'akin shi yasa damuwar ta ta tsananta, lallai tsakanin Mata da miji sai Allah, kuma dole ta sakama zuciyar ta hak'uri da dangana akan duk abinda yazo Mata, Wanda ya zauna da Gwaggo wace irin hantara ce bazai iya d'auka ba.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
```BAYAN``` ```SATI``` ```DAYA```
Zaman su na nan ba yabo ba fallasa gwargwado Bahijja na bawa Lateefa girman ta yadda ta saba fiye da wancan lokaci.
Yau ma a daddafe ta gama abincin rana saboda tun safe take jin alamar zazza6i ga kuma tashin zuciya.
Tana kammalawa ta jera a dinning table taje tayi wanka.
Saboda duk da masifar Lateefa tare suke cin abinci har Shureim don ya tsayu da gidan sa yana d'ora doka kuma dole abita.
Hakan suka zauna cin abinci har suka k'are ba magana saboda da Shureim ya Fara hira zata ce ya karkata hankalin shi ga Bahijja.
Suna k'are cin abinci ta shiga d'akin ta ta fad'a toilet sai amai, jin k'arar aman ne yasa Shureim ya bita d'aki ya shiga toilet ya tallafota yana fad'in Heeja mike damun ki? Abincin ne ba kyaso?
Bayan ta gama ne ya d'auko ta ya dawo d'aki da ita yana rungume da ita.
Kawai jin amai yayi saman jikin shi, kuma so take ta k'wace jikin ta daga nashi.
Nan ya ajiye ta saman gado ya gyra Mata jikin ta ya cire kayan jikin shi ya saka a Wash machine.
Cikin k'ank'anin lokaci Bahijja ta fita hayyacin ta duk rashin imanin ka zaka tausaya Mata in ka ganta.
Cikin kwana biyar ta koma wata iri ba ci ba sha kullum amai ga k'arin ruwa da Shureim ke yimata kusan kullum, Mum taso ta dawo gurin ta Shureim ya hana yace zai kula da ita duk da yanayin aikin shi sai dai ya sakar ma Muftah ayukkan office.
Blkisu ma tazo ganin ta Karo biyu duk anan take wuni sai Muftah ya taso daga aiki ya biyo ya wuce da ita.
Yau ma Shema'u ta zo ma Lateefa wuni ganin shige da ficen da ake yi d'akin Bahijja yasa tace Anty hala meke faruwa?
Ta ta6e baki tace wai bata da lafiya ne, nifa rabon in saka ta a ido na tun ranar da tafara ciwon ta na k'arya.
Shema'u ta mik'e ta nufi hanyar d'akin Bahijja.
Lateefa tace Ina zaki je?
Tace Zan shiga in duba jikin ta ne, sanin cewa Shema'u akwai kafiya yasa ta k'yale ta.
Tana shiga d'akin ta Han gota kwance an sa kamata drip ga Aisha Yagani kusa gareta.
Nan ta gaishe ta da jiki abin gwanin tausayi ko magana bata yi duk ta jeme.
Tana fita ta taradda Lateefa ta koma d'aki, nan ta bita tace Anty yaushe tausayin ki da imanin ki suka ragu?
Don Allah ki taso muje kiga Bahijja wallahi abin gwanin tausayi.
Da k'yar ta shawo kanta sannan suka tashi sai d'akin Bahijja.
Tana shiga d'akin ta dask'are inda take, har ga Allah bata zaci ciwon nata yakai haka ba, kuma ta tausaya Mata over.
Da saurin ta takai gurin da take ta tallafota saboda drip d'in sun k'are an cire, tace Sister haka kika koma?
Me kike so Wanda Zan dafa maki kici ya tsaya maki?
Zaki ci d'an wake? Duk tana tambayar ne tana hawaye saboda Lateefa akwai rauni gare ta.
Ta Kai duban ta ga Shureim tace yanzu Kimba haka Sister ta koma ba a kaita asibiti ba?
Yayi murmushi yace kin manta nine asibiti gaba d'aya, dama ciki ne da ita yake wahalar da ita.
Nan ta Kai duban ta ga Bahijja da murmushi a fuskar ta, har ga Allah tana jin tausayin ta yadda ta koma, dama shaid'an ke k'ara ingiza ta abubuwan da take yi Mata.
"Da saurin ta taje kicin ta d'ora ruwa ta Kira Shema'u ta taya ta don tana da garin wake da Mmn Zahra ta bata kwanakin baya.
Cikin minti ashirin Lateefa ta had'a ta Kai mata, kuma cikin ikon Allah taci kad'an ya tsaya Mata taji dad'i har cikin ranta.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
Yau Baban Bahijja ya shirya zuwa godiya ya gayyaci abokin shi malam Ado suka je tare.
Bayan sun iso ne Mum ta shirya musu abinci suna ci suna hira.
Malam salisu ya yi mashi godiya har da guntun hawayen shi.
Alhj yace haba salisu miye haka, har yaushe Zan gaya ma cewa an zama d'aya.
Ya d'ora da cewa ni garin nan ma naso in baka d'aya daga cikin gidaje na, sanin hali yasa na gyrama naka.
Nan suka yi dariya malam salisu yace lallai kam banga abinda zai rabani da k'auyen mu.
Alhj ya yi murmushi yace sai ka biya kaga d'iya ta tana jin jiki, saboda na kusa Kai ga jika.
Malam yayi murmushi yace ko dai na kusa Kai da jika ba, don 6angaren namiji sunfi k'arfi, nan suka yi dariya su duka.
Kai tsaye suka biya suka ga Bahijja, lallai tana jin jiki gaskiya, nan ya yi Mata addu'a suka wuce har k'asan zuciyar shi yake tausayin yadda laulayi ya maida ita.
Nan suka Kama hanya sai garin su Kimba.
© *SDY* *JEGAL*
[10/28, 2:25 PM] +234 803 325 6478: 🍒 *BAHIJJA* *130*- *135*🍒
*BAYAN* *SHEKARA* *HUDU*
Shureim ne zaune matan shi sun saka shi a tsakiya sai hira suke yi cikin walwala da sakin fuska.
Nan yakai duban shi ga Lateefa yace ki shirya hajjin bana dake a ciki.
Tace nafa gaya ma sai dai ka biya muna muje nida sister Kai kuma kayi zaman ka.
Nan ya yi dariya sosai yace Lateefa rigima, ai kwa duk kin 6ata little Latee da irin rigimar ki.
Ya maida duban shi ga Bahijja yace to ke sai ki shirya muje tunda ita bata zuwa.
Nan tayi murmushi tace kaje Kai kad'ai in yaso daga baya mu maje.
Yace tabbb ina ga baku da rabon jifar shaid'an bai rama ba, wato Ku had'in Kai ni kun maida ni saniyar ware.
Nan suka yi murmushi Lateefa tace Kaine baka bada had'in Kai da sai mu d'an jona ka mu zama y'an uku.
Nan yayi murmushi yace to shikenan Ku shirya zamu je mu duka daga nan zamu wuce Egypt muyi sati d'aya.
Nan suka rik'a murna had'e da godiya.
Shigowar yara biyu ne da gudun su yasa suka mai da hankali garesu.
Alamein ya fad'a kan Bahijja yace Ammi kinga little zata kar6e min sweet, kuma yanzu Mum Blkisu ta bani.
Bahijja ta Kai duban ta ga little tace Ina taki sweet d'in?
Tayi narai-narai da ido tace ya shanye tashi shine ya kar6e min tawa don yaji nace sai na kaiwa Abba da Umma ta sun sha.
Nan Lateefa ta Jan yota tana rarrashi tace k'yale shi kin ji little kwad'ayi ya Mai yawa, jeka d'aki ki d'auko sweet d'in ki da Mum Shema'u ta kawo maki, kuma kakki sammai kin ji.
Nan ta yimai gwalo ta wuce shi ko ya rik'a kukan shagwa6a.
Suna hakan ne sai ga Muftah da Blkisu sun kawo masu ziyara.
Nan Bahijja ta kar6i y'rta Teema tana yi Mata wasa, nan suka zube falo su duka suna hira.
Muftah yace aboki nayi ma murna sosai da samun k'arin matsayi, yanzu yaushe zaku wuce abuja d'in?
Yace sai mun dawo daga saudiya sannan mu wuce.
Yace Allah sanya alkhairi yasamu a danshen Ku.
Nan suka kar6a da Ameen suka cigaba da hira.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
Yau dai sun shirya kan zasu je suyi bankwana don saura kwana hud'u su wuce saudiya.
Gidan Mum suka Fara zuwa, daka kalli Mum zaka San cewa tana cikin farin ciki saboda ganin matan Shureim sun had'a kan su komai tare suke yi.
Tace Lateefa Ina zaku barin ya ran Ku tun da kun had'e ma son Kai dole sai yaje daku.
Nan little tayi tsagal tace ni gidan su Umma ta Zan zauna.
Shiko Alamein cikin gwaran cin maganar shi yace wurin Mum zai zauna.
Lateefa tayi murmushi tace shikenan Mum an raba.
Da azzahar suka wuce gidan su Lateefa, sai murna little ke yi an zo gidan su Hajiyar ta, nan ma sai la'asar suka fita.
Kai tsaye suka biya gidan Aisha Yagani saboda yanzu auren ta wata uku kenan.
Daga nan suka shiga mak'otan su wurin Mum Zee da Mmn Zahra.
Gab da magrib suka koma gida tare suka fad'a kicin suka yi aiki suka gama, sannan ko wanen su ya shiga wanka domin haramar sallar magrib.
*BAYAN* *KWANA* *BIYU*
Yau kam shirin tafiyar su Kimba zasu je, tun safe suke shirye-shirye zuwa goma sun gama suka hau hanya.
Ko da suka isa duk wani shirin tarbon bak'i malam yasa Inna habiba ta yi Mai matar abokin shi malam Ado kuma iyayen lantana.
Haka aka tarbe su ba laifi, su Gwaggo ana nan zaune d'aki in ba jurewa mutum yayi ba bai iya shiga d'akin da take, saboda d'akin duk wani k'azni yake yi dalilin wasu k'uraje da suka fito Mata anyi magani har an gaji sun k'i warke wa.
Nan suka gaida ta, ta amsa tana kuka tana k'ara rok'on gafarar Bahijja.
Bayan sun fito ne suka je gidan su margyayi Murtala, nan ma su little sun ga tarairaya, har gidan lantana taje kuma ta Kai Mata sutura ita da yaran ta uku ta had'a Mata da kud'i tace ta samu Sana'ar da zata Fara, har kukan murna tayi tana ta godiya.
Sai azzahar suka je raha garin innar ta, su ma ta yi masu goma ta arzik'i saboda kakar ta wadda ta haifi innar ta da sauran k'annen innar ta duk suna nan.
Nan suka kama hanya da tsara bar su ta nono da manshanu.
© *SDY* *JEGAL*
🍒 *BAHIJJA* *135*- *140*🍒
*BAYAN* *SHEKARA* *BIYU*
Abubuwa da dama sun faru a ciki kuwa har da mutuwar Gwaggo wadda taga k'ask'anci saboda ko masu yi Mata sallah dak'yar aka same su cikin garin basu wuce mutum biyar ba.
(Allah yasa muyi kyakkyawan k'arshe)
"Bahijja ta biyawa Baban ta makka cikin gadon ta na margyayi Murtala shima yaje ya sauke farali ya dawo.
Anan cikin garin su yasamu wata dattijuwa Baraka ya aure ta, gata da mutunci in ka gan ta tsakanin ta da Bahijja zaka rantse ita ta haifeta.
Yaran sune ke wasa a cikin gardener, su ko iyayen suna gefe sun yi shimfid'a suna shan kayan fruits suna hira.
Shureim yace yaushe ya kamata mu je ganin gida?
Lateefa tace mu Bari zuwa sallah babba sai muje, don gaskiya sallah babba garin nan ba dad'i.
Shureim yace shikenan mu basshi a hakan in munje sai muyi sati biyu mu dawo, yayi ko?
Bahijja tace eh ba laifi zamu yi maneji.
Suna maganar ne tari ya sark'e Shureim kowaccen su ta tashi daga ginciren da take.
Lateefa ta rik'a bubbuga bayan shi tana yi Mai sannu, ita ko Bahijja ta d'auko ruwa ta bashi sannu kawai take jero Mai.
Bayan abin ya lafa ne ya kallesu yace gaskiya kuna ji da tsohon nan naku.
Nan suka yi murmushi, Bahijja tace ai mu gurin mu yaro kake rass, baka ganka ba in kayi zanzaro zaka je office tamkar d'an 25.
Lateefa tace wama zai gan ka yace kana da yara hud'u.
Nan yayi murmushi yace tunda ban tsufa ba ya Kama ta in samu sankaceciyar budurwa cikin Abuja d'innan in auro, sai Ku samu k'anwa.
Tare suka rik'a yin dariya Lateefa tace Allah ya kawo ta lafiya, amma fa sunan ta sorry.
Shureim yace dama an ce in Mata biyu gare ka to ta uku ba zata ga nema komai ba, ni ko hakan kun isheni har agidan aljannah.
Nan suka yi murmushi suka ce Allah ya had'a mu aljanna d'in.
Yace Ameen Ameen, ya d'ora da cewa Ina ga fa gobe kayan Ku zasu iso daga Dubai.
Lateefa tace tun jiya Shema'u ta Kira ni cewa in kayan sun iso a tura Mata lace goma materials goma.
Bahijja tace saura a tura ma Anty Maijidda nasan zata saye ta bamu kud'in mu.
Lateefa tace haka ne gaskiya tun da kinga zamu wuce Jega sallah.
Shureim ya bisu da murmushi yace wai Ku y'an business, ya d'ora da cewa ya kama ta Ku fitar da kud'in mota guda cikin account d'in Ku sai in cika maku Ku siyi motoci.
Nan suka hau murna da godiya had'e da addu'ar Allah ya k'ara bud'i.
🌸🌸🌸 🌸🌸🌸
Yau kwana uku da dawowar su daga Abuja, Lateefa ta wayi gari da nak'uda saboda dama tana da tsohon ciki.
Nan gida Shureim ya kar6i haihuwar ta ta samu yaron ta namiji.
Murna gurin little tamkar ta had'iye yaron sai cewa su Alamein take yi ita ma yanzu ta samu k'ane su daina yi Mata kuri su uku suke d'akin su.
Ranar suna gida ya cika mak'il da jamaa 6angaren Bahijja sun zo suna ciki kuwa har da Blkisu da yaran ta biyu, Yagani da yaron ta d'aya, Shema'u da yaran ta biyu.
Su Mum zee da Mmn Zahra sune masu sallamar bak'i.
Mmn Zahra tace kinga yadda zaman su yayi dad'i ko, abin gwanin sha'awa.
Mum zee tace inda ma suka fi burge ni kamar had'in kan yaran su, ba zaka ta6a cewa Bahijja ce ta haifi little Lateefa ba, sannan ba zaka ce Lateefa ta haifi Safiya (Ilham) ba.
Nan nima mamaki yayi min yawa nidai naga yara amma ban tantance ga na wannan da wannan ba.
Little Lateefa da Alamein da sudais sune yaran Bahijja.
Ita kuma Lateefa ita keda Safiya (Ilham) da wannan jaririn da yaci sunan Shureim (Khaleefa)
Hakan taro ya watse Ana yabon wannan families.
Washe gari bayan kowa ya kimtsa ne Shureim yasa matan shi tsakiya da yaran shi suka yi selfie don tarihi.
Ni ma Jegal sun burge ni, Allah ya had'a muna kan zuri'ar mu, Ameen.
Tammat bi hamdillah, anan nakawo k'arshen wannan novel nawa Mai suna Bahijja, kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min.
Matsayi na na jinjira acikin writers Ina fatar zaku yi hak'uri da yadda littafaina biyu suka zo maku wato.
Fateema & Bahijja.
Nayi wannan buk ne da sunan ki Bahijja (Bebeelo) kuma na sadaukar da shi zuwa gare ki sanadiyyar k'aunar da ke tsakanin mu.
Gaisuwa zuwa ga
Musha karatu group
Taskira group
Zarah B~B fan's
Mumbarin novels
Greatest women
Matan so group
Zumunci group
Kuna cikin raina har kullum
Mmn Shakur
Zarah B~B
Princess Meenat
Blkisu Blymnu
Aunties d'ina
Anty Innah
Anty fateema
Anty Jidda Musa
Anty Ybk
Kin fi kowa son wannan buk
Yaha Saddik (Yaha na)
Taku gaisuwar ta daban ce
Umma ta Lubiee Mai tafseer
Safiya Ummu Abdul
Hindatu shehu
Fati Salihu
Mrs Atiku
Princess Jamila
Jamila Muhd Ali
Zainab M. Bawa
Hafsat Mai sharifai
Mmn haneef
Kuna raina
Zainab Musa (Mmn miemi)
Lawiza Musa
Yara manyan gobe
Halima
Maryam
Khadeeja
Abduljalal
Allah ya rayamin Ku akan sunnah
Fata na gari zuwa ga k'anne na
Assy Jegal
Sumee Jegal
Hauwa Jegal
Allah ya Baku mazaje nagari
Two Star
Asmee Jegal Mrs Ibrahim Mai dabo (Mmn Ammar)
Blkisu Jegal Mrs Imran
Three Star
Sis Hindu
Sis Nafee
Sis Ayshat
Abokanen karatu na
Amnya Hjy shafa'atu zakariyya
Shema'u Bello Bari
Saratu Abubakar
Yazzali
Yar gidan Ango
Ban manta da kuba
Murja Madelty
Hajiya babbah
Mum Zee
Mmn Zahra
Aisha Bizzy
Aisha Yagani
Maryama (Mmn Mu'allim)
Ummu Marwah
Mmn zeenert
Shatoo
Mrs zannah
Anty Ummy
Nafi Jaudat
Masoyana
Innah Habiba
Salmatun Innah
Husnah
Hassy
Pharty JJ
Mrs Alamein
Jiddah Mx
Maryam sani
Habiba yayaji
Khadija Abdul S
Maryama
Muneeebah
Yagana Habib💄
Ummin Alamein
Maryam (Mmn Mamee)
Matar Mu'az
Mmn Hanan
Mmn amatullah
Fatimatuz-zahra
Zaarah gwandu
Murjanatu yar baba
Halimatussadiya
Miss softie
~@Ag
Sophy md
Faeeza
Teemseey uthman
Laurat (Mrs zubair)
Aisha misilli
Leemcy
Mmn walida
© *SDY* *JEGAL*
adsense 2 here