adsense here

BAKIN LISSAFI COMPLETE
Awani gari, awata makaranta, awani dare,
akasamu gungun wasu matasa sukayi kukan kura
suka kutsa kai dakunan kwanan dalibai mata, da
misalin karfe 2:30 na dare, dauke da muggan
makamai, sukabisu daki daki, suna tattara
dukkan abinda yammatan suka mallaka, nadaga
kudade, sarkokin gwal, dan kunne da zobban
zinare, suka arce dasu a cikin daren, Wan nan
salon sata da fashi a makami, ya dade yana ba
mutane mamaki acikin makarantar, musamman
da safe da aka wayi gari da labarin ta'asar inda
aka iske masu gadin hostel din sunsha dauri
kamar, huhun goro ashagamu, amma saidai anyi
sa'a sosai saboda barayin basu doki daliba ko
dayaba, ko yunkurin fyade ga yammatan kudi da
sarkoki kawai suka amsa kamar yanda daliban
suka bada labari. . Amma anji kishin kishin din
cewa wata daliba mai suna, Kubrah ta gane
mutum daya daga cikin barayin na daren jiya,
wani dan ajinsu ne mai suna Mubarak, wanda ta
tabbatar da cewa ta ganeshi, saboda kayan dake
jikinsa da su ta ganshi dazu da safe sanda zasu
dauki lakcar darasin lissafi, Daidai lokacin da
kubra ke labartama wasu kawayenta biyu, cewa
ta gane mubarak dan ajinsu acikin barayin jiya,
alokacinne wada daliba mai suna jummai, ta zo
musu da wani karin labarin kan cewa, ai yanzu
kawarta fiddausi take tabbatar mata da cewa
itama ta gane mutum daya daga cikin barayin
jiyan, yusah'u ne direban gidansu, wanda wata
daya baya ya kawota makaranta amotar gidansu,
bayan sun dawo hutun karshe zangon karatu na
biyu ya sauketa yaja motar ya koma can garinsu.
Bayan yammatan sun gama tu'ajjabin wan nan
al'amari sai suka rankaya gaba daya suka nufi
kofar fita daga rukunin dakunan kwanan daliban
mata, inda suka iske wani gungu da yammata
suka taru, anan suka iske wat matashiyar
budurwace kirista mai suna Ester, an kewayeta
tana bada labarin itama fa ta gane mutum daya
acikin barayin jiya, mr. Markus ne sabon malamin
lissafinsu. Bayan dan gajeren lokaci da yammatan
suka dauka suna tu'ajjabin wan nan samame da
barayi suka kawo masu adaren jiya. . Tsam wata
budurwa matashiya mai suna TANTO, yar asalin
kabilar igbo wanda agabanta, aketa nuna alhinin
satar da akayi masu ajiya, san nan taji duka
lokacin da sauran yammatan suke fadin sunayen
wadanda suka gane aciki barayin, ta tsame jikinta
daga cikinsu ta sulale ta nufi can cikin
makarantar, da niyyar zuwa kai tsaye ga ofishin
babban baturen tsaron makarantar wato (chief
security) don tsegunta mai sunayen wadanda ake
zargi wanda budurwar ta ji sauran yammatan sun
ambata. TANTO wata budurwace mai yawan bare
bare, da son tsegumi, da son bada labari kamin
arigata, don haka cikin sauri take tafiyar, kar wani
ya rigata kaima sikuriti labarin, budurwar ta ratse
daga kan titin da take tafiya akansa, tabi ta wani
rukunin bishiyoyi da sukayi ma wani guri duhu, ta
kan wata yar siririyar hanya, wadda daliban suka
samar da ita don ragema kansu tsawon tafiya
don isa ga dakunan daukar karatu, bayan sun fito
daga hostel, wato (short cut) tana tafiya
zuciyarta cike da zumudin isa ga inda ta nufa. Ta
gitta wata katuwar bishiyar bedi ke nan, wadda
tayima wajen kawanyya, sai taji kamar an kira
sunanta ta baya, cikin sauri ta juyo, don ganin
wake kiranta, don tunda ta shigo dan dajin bata
ga kowa ba awajen, musamman da sanyin safiya
irin wan nan bakasafai dalibai kan zauna awajen
ba, sai can rana ta take tukunna, atsaye taganshi
ya jin gina da daya daga cikin bishiyoyin, yana
mata murmushi, tabbas indai ba gizo idonta yake
ba, malam Marcus ta gani, malaminsu na lissafi,
wanda taji kawarta Ester tace ta gane shi acikin
barayin daren jiya. Nan take taji gaban ta ya fadi,
ya kariko har inda take tsaye, yana kallonta yana
murmushi, yace cikin dariya, '' TANTO ina kike
nufin zuwa ne haka da sanyin safiya,?'' . cikin
alamun tsoro budurwar ta gaza hada ido dashi
tace ''zanje lakca ne,'' mr marcus yayi dariya har
sauti ya fita, yace bayan ya hade rai, '' a a
yammata, zaki je dai ofishin chief sikuiriti, kai
rahoton wadanda suka shiga dakin kwananku jiya
da daddare suka amshi kudade da gwalgwalai,
domin yau asabar nasan ba lakca'' Cikin
matsanan cin razani, budurwar Tanto, ta dago kai
ba shiri suka hada ido da malamin lissafin nasu,
yanzu tabbas fuskarsa adaure take, don haka
tasan ba wasa, dama can tasan sa, shi shiri duk
in ba na lissafa kudi bane baya a ganin fara'arsa,
don yasha nuna masu haka in yana koya masu
lissafi a aji, idan yazo wajen lissafa jimillar wasu
kudi yaji yawansu har yayi yawa, sai aga kawai
yana dariya, yana cewa inama ina tafiya in tsinci
wwadan nan kudi. Amma abinda yafi daure ma
budurwar kai shine, babu wanda yasan lokacin da
ta silalo acikin kawayenta, daga hostel din mata,
kuma bata gayama kowa cewa zataje, kai rahoto
ofishin security ba, amma taya malam marcus ya
samu wan nan labari? Waya gayamai inda zata
je? Cikin razani budurwar tanto taja baya, tana
dafe da kirjinta, tace tana rawar murya, ''malam
way...ya....gaya ma inda zani''? Mr marcus, ya
sake daure fuska, yace ''Bansani ba,'' san nan ya
sake matsowa inda take, sai ayanzu, Tanto ta
lura da kyau , hannunsa na hagu yana rike da
wata karamar bindiga ne kirar pistone, ya danyi
kasa da muryarsa san nan yace, . ''Bake kadai ba,
ina sane da cewa Kubra ta gane mubarak dan
ajinsu adaren jiya, san nan fiddausi, ta gane
yusha'u diren gidansu, ni kuma ester ce tayi sa'ar
ganeni, don haka afarke muke shirin mu,'' adaidai
lokacin ne, ya daga hannunsa mai rike da binga,
ya saita daidai ruwan cikin budurwar, yar
inyamurar ta sake rikicewa, dama gata gwanar
tsoro, tace tana kokarin fara kuka, '' don Allah
malam karka kasheni, wallahi tallahi, na rantse da
kwaran kwatsa bazan gayama kowa ba,'' da
alama yar budurwar ta gama rikicewa, mr marcus
ya zazzaro mata idanu, yace cikin murya mai dan
karamin sauti, '' maza ki gayamin mutum nawa
suka san wan nan labarin banda kubrah, da
fiddausi, da Ester dake?'' Cikin rawar murya,
Tanto tace, '' wallahi bamu da yawa bamu wuce
mu goma sha uku ba,'' amma na baro suna ci
gaba da gayama wasu'' mr marcus ya gyara
tsayuwar bindigarsa, adaidai cikin matsoraciyar
inyamurar, yace ''maza, da sauri ki koma ki
kiramin yammatan uku, ki samesu daya bayan
daya, kar wata tasan da wan nan gayyatar wanda
ba suba, in bahaka ba kuwa, kinga wan nan
bindigar,'' ya dannata acikinta, saida kan bindigar
ya taba ruwan cikinta, san nan yaci gaba da
cewa, sai ta fasa tumbinki ta ragargara kashin
bayanki, in kika kuskure baki dawo tare da su ba,
zan biyoki har hostel din, adaren yau na kasheki''
Tanto ta sake tsurewa, tace ''To malam'' cikin
rawar jiki, ta bi siririyar hanyar data shigo da ita
rukunin itatuwan ta koma inda ta fito, bindigar mr
marcus na mata rakiya daga nesa. Tunda
matsoraciyar budurwar nan Tanto, ta juya ta nufi
can rukunin dakunan kwanansu, don cika
ummarnin malaminsu na lissafi mr Marcus, ta
kira sauran yammatan da suka fara fallasa asirin
wadanda suka afka dakunan kwanan su acikin
daren jiya suka tattara komai nasu suka arce
dashi. Da sauri matsoraciyar inyamurar take
tafiya, bata iya waigawa saboda tasan saitin
bakin bindigar da mr marcus ya saitata tashi
shike mata rakiya har yanzu, . kuma aranta tana
gargadar kanta da cewa tabbas mr marcus zai
iya aikata danyen aikin daya ambata akanta,
muddun ta gaza kiran yammatan zai biyota har
dakin kwananta ya karya mata kashin baya da
harsashin bindigarsa, don kallo daya zakaimai ka
tabbatar da fuskarsa ta dade tana lissafa kudi
atakarda, wanda zuciyarsa ayanzu take ta
fafutikar son taga ta mallaki kudin da yaya
kwashe shekaru masu yawa, yana lissafasu
afararen takardu, don haka komai yana iya yi
akansu. Tun daga nesa Tanto ta hangi kawarta
Ester tana tsaye da wasu yammata biyu abakin
babbar kofar shiga gine ginen dakunan kwanan
yammatan, da'alama labarin take gayamusu, da
sauri ta isa gareta, ta jata gefe guda tana rawar
baki tace, ''ke ester asiri ya tonu, malam Marcus
nacan (forest garden) yace na kiraki, kuma
wallahi naganshi da idona bindigace ahannunsa,
yayi barazanar kashemu gabaki dayanmu,
muddun muka kara yayata wan nan maganar,
yace muyi sauri yana jiranmu,'' Budurwar yan
asalin kabilar yaroba, ester ta zazzaro ido tana
sauraron kawarta tanto, dama tafi tanto tsoro,
domin ita duk wani abu da ka iya sawa ayi
labarin mutuwa, ester bata kaunarsa ko kadan,
ance gidansu idan akayi mutuwa takanyi wata
daya cur bata gidan ko leko kofar gidanba tayi,
don haka wan nan mummunan labari da tanto ta
kawo mata, yasa nan take taji cikinta ya duri
ruwa, domin kuwa ta san akalla ta labartama
mutum sama da shida wan nan zance, tace cikin
firgici, ''yanzu to ya zamuyi'' Tanto tadan gyara
tsayuwarta, fuskarta cike da zufa, dukda iskar
safiyar da take kadawa, tace tana kallon estar ''Ai
yace harda su Kubra da fiddausi na kira su, kuma
nasan su zai wahala suje, in sukaji shi ke kira,
domin dama basu cika shiri dashi ba, musamman
fiddausi, don haka zamuce malam Kabir ke kira,
ya samu labarin abinda ya faru'' Atare yammatan
su hudu suka rankaya suka nufi cikin makarantar
don amsa kiran malam marcus, kamar yanda
yammata biyu suka san shike kiransu, sauran
yammatan kuma kubra da fiddausi, . zasu wajen
malam kabir ne, (Dean students Affairs) don kara
jaddadamai abinda ya faru dasu adakin kwanasu
adaren jiya, cikin sauri yammatan hudu suka
ratsa ta (short cut) dinsu, yar siririyar hanyar da
zata sadasu ta can cikin gine ginen makarantar
daga dakunan kwanansu, sun isa tsakiyar rukunin
itatuwar da sukayima hanyar duhuwa ne, daidai
(Forest garden) sai sukaji kamar daga sama ance
'' Barkanku da zuwa yammata,'' cikin firgici da
rashin tsammani yammata uku suka waigo inda
sukejin muryar, amma tanto wadda tasan da
zaman mai muryar awajen wan nan baisa ta
razana ba. Mr marcus ne, ya silalo ta bayan wata
bishiya, ya nufo yammatan fuskarsa adaure,
saida yazo gab da su san nan suma suka lura
hannunsa na hagu, yana rike da karamar bindiga,
nan take gabaki dayansu suka tsure, yadan yi
masu murmushin yake, san nan yace yana
dubansu daya bayan daya, ''sannuku yammata
gwanayen kamu,'' nan take kubrah da fiddausi
suka fahimci inda lissafin malamin lissafin ya
nufa, yaci gaba da magana yana kallonsu, ''Tanto
kin gama naki aikin da kika tattaromin masu idon
gane bakinsu na jiya'' mr marcus ya hada
hannuwansu biyu yayi tafi da karfi, lokaci daya
kamar daga sama, sai ga mubarak dan ajinsu,
Kubra ya fito shima daga bayan wata bishiyar
tunfafiya dake awajen yana ma yammatan
murmushi, yusha'u direban gidasu fiddausi, shima
ya biyu bayansa, yana sanye da wasu kanan
kayan daya shiga dakin kwanna yammatan dasu,
daga bayansu karin wata tawagar samarin ne
matasa wadanda dasu aka afka dakin kwanan
yammatan ajiya. bayan sunyima yammatan kuri,
sun kewayesu, sai mr marcus ya kallesu alokaci
daya, ya daure fuska, ya daka musu tsawa, yace
cikin kakkausar murya, bandaku dawa dawa kuma
suka san wan nan labarin matsa ku gayamin insa
akawomin su nan, don na yanke maku hukunci
tare'' 5 minutes ago · Sent from
free.facebook.com Ismail Sani
............................... Yammatan suka kalli
malamin lissafin nasu, mr marcus alokaci daya,
suna zare idanu, cikin alamun tsoro da firgici, da
fadawa wan nan tarkon mamuguncin malamin.
Dama tuni sunsan malamin azzalumine, bashi da
tausayi kokadan, don yasha kada dalibai ba gaira
ba dalili, a darasin lissafin daya ke koya musu,
san nan aduk lokacin daya koya masu wata
fomula ta lissafi yaga sun gaza ganeta, sai yayi
ta musu dariyar mugunta, yana fadin, (its my
time) wan nan yasa dayawa daliban makarantar
suka tsani malamin, musamman ma fiddausi, da
kawarta kubrah. Tonto da Ester sune sukafi
sauran yammatan tsorata, da irin barazanar da
marcu yake musu, don dama kabilu ance sunfi
hausawa tsoro, tun bayan yakin basasa da akayi
anigeria, akayi musu kaca-kaca, suka fada razani
da tsoro matuka, yar budurwa Ester da take gaf
da fara gudawa atsaye ta kalli mr marcus da ya
saitata da bakin bindigarsa, idonta cike da
hawaye tace '' wallahi malam wadanda na gaya
mawa bazasufi mutum tara ba, ciki harda baba
na dake can garinmu da... . '' Ester ta tsuke
bakinta ta gaza cigaba da bada bayanin ganin
idon marcus na sauyawa daga ja zuwa wani kore
kore, ranshi abace, ya sake matso kusa da ita,
yace cikin siririyar murya mai alamun zafi, ''banda
babanki wa kuma kika gayamawa agidanku?
Kuma saikin gayamin abinda kika gayamusu,
kona tarwatsa katon kan nan naki,'' ya dora
karamar bindigar adaidai goshin matsoraciyar
budurwar. Ester ta saki fitsari atsaye, cikin rawar
murya, tace ''wallahi bangaya musu komai ba,
cewa kawai nayi kaine kayi mana sata adaren
jiya, yace zaizo makarantar don adauki mataki,
bandashi ban gayama kowaba,'' mr marcus ya
dan saki fuska, don yasan barazanarsa ta yi tasiri
akan budurwar, ya juya da sauri akan sauran
yammatan, kubra dake gefensa na dama yafara
tuhuma, ke kumafa dawa dawa kika shelantama
wan nan labarin,? Kubrah tadan ja baya atsorace
ganin mamuguncin malamin yana matsota, dauke
da bindigarsa ahannu, tace nata lura da motsin
hannunsa mai bindigar ''mutum uku kawai
nagayamawa,'' ''banda sufa'' marcus ya tambaya
yana kallonta da jajayen idanunsa, ''wa kika
gayamawa agida, don in nagano kema kingayama
wani agidanku, baki fadamin ba yanzu, saina
harbi wan nan dogon hancin naki, harsashina ya
ketashi hudu, ya fada cikin kanki yayi raga- raga
dashi,, . ''wallahi bangayama kowa ba bandasu''
Mr marcus ya kalli Fiddausi wadda suka dade
suna tsama da ita, dama ya dade yana fatan
budurwar ta fado komarsa, don ya taba nemanta,
da lalata tayimai mummunan wulakanci san nan
takai kararsa ga hukumar makarantar, aka
dakatar dashi na wani lokaci, tundaga wan nan
lokacin ya samata maki, don haka yayi mata dan
murmushin dake alamta muguntarsa afili, yace
bayan yadan daure, ''ke kumafa yamamta, maza
ki gayamin wanda kika gayamawa, yau baramar
wasa bane, zan iya karya wan nan siririn wuyan
naki, duk kyawun nan naki bandamu ba, indai
akan kudine, dawa dawa kifa kwarzantamawa
wan nan labarin, maza sauri muke muje bincike
karo na gaba'' Fiddausi ta dafe kirjinta, ganin
lallai mr marcus da gaske yake wan nan furucin
nashi tace tana rawar murya ''mutum uku nima
nagayamawa, sukenan, wallahi, bangayama
kowaba baya gasu,'' Marcus ya gyada kai alamar
gamsuwa, yace ''dakyau, da kukayi dubara kuka
takaita labarin, yanzu kuyi maza ku tahomin nan
tare da sauran yammatan, da duk suka san wan
nan labarin zan hadaku da yarana mutum uku,
wadanda baku iya ganesu ba, zasu biku
amatsayin security, don fara binciken badakalar,
don haka sai ku fada musu, su basu hadinkan
tahowa dasu nan yanzu, in bahaka ba, abinda zai
biyo baya yafi wan nan muni'' yadan sarara yana
duban yammatan da tuni sun gama tsorata, san
nan ya dubi budurwa Ester wadda tuni ta gama
jike dan gajeren siket dinta, yace kece kikayi
gaggawar shaidama babanki wan nan labarinko,
yanzu kinjamai, shigowa tarkona, yanzu zanje na
taho dashi nan, shima don amsar irin
hukuncina'' . Yammatan hudu suka juya atsorace,
wasu matasa guda uku, . daga cikin tawagar Mr
marcus, suka rufa masu, baya, suna sanye da
kananan kaya, ko wannensu ya toke sun sanya
biruka agaban aljihun rigunansu, biyu sanye da
fafaren tabarau na fuska, suna tafe suna dan taba
hira da yammatan, kai kace wasu jami'an leken
asirine daga hukumar yansandan ciki, nan ko
sune barayim da sukayi kitse acikin dakin
yammatan adaren jiya suka tattare komai nasu
suka arce dashi. Mr marcus da sauran yaransa,
suka boye acikin duhuwar itatuwan dake kewaye
da (forest garden) suna jiran dawowar yaransa da
tawagar yan matan, san nan yayi maza ya sauya
musu guri don samun damar gudanar da
bincikensa akansu mai tsafta, da niyyar shima zai
bazama garinsu, matashoyar budurwa yar kabilar
yaroba Easter don gayyato babanta wanda yanzu
haka yasan da labarin su marcus ne suka shiga
dakin kwanan yammatan. . Tattaro yammatan
baiba yaran mr marcus wahalaba sosai, saboda
suna isa rukunin dakunan kwanan yammatan,
suka isa harabar gine ginen, nan da nan yamatan
suka shiga daya bayan daya suka kira yammatan,
sai dai anyi rashin sa'a wata budurwa mai suna
SUWAIBA, dake kauyen Kaimon kaura, wadda
kubra taba labarin al'amarin ta buga sammako
tun bayan fitar su kubran zuwa amsa kiran mr
marcus, ta nufi gida can kauyensu. Cikin sauri
kubra tabi bayanta har bakin karamin get din fita
makarantar, amma saidai kash tun kamin ta
karika bakin get din ta hangi motar bus ta tashi
daga bakin get din kuma tabbas matashiyar
budurwar suwaiba ta dauka, da alamama ta dade
bata samu mota ba kenan. Kubra ta dawo jiki ba
karfi, don tasan muguntar mr marcus, zai iya
dora mata laifin, amma saidai yaran marcus da
suke tare da ita sun shaida tafiyar budurwar, suka
tattaro sauran yammatan suka nufi inda mr
marcus yake tare da sauran yaransa. Mr marcus
dake makale abayan wata bishiya, ya dan dago
agogon dake hannunsa inda idonsa suka ci karo
da karfe 10 daidai na safe, nan take yayi saurin
kewayowa inda sauran yaransa suke yace cikin
daga murya, dole muyi sauri mu bar wajen nan,
don nasan lokaci ya fara ja, mutane zasu fara
yawa acikin makarantar nan domma yau week
end, Yusha'u maza ka kawo mana mota mubar
wajen nan. . Lokacin da tawagar yammatan suka
kariko gurin wata doguwar mota suka iske mai
kirar motar safa, sauran samarin na ciki, batare
da bata lokaciba, yaran mr ,marcus dake tare da
tawagar suka basu ummarnin kutsakai cikin
motar, yammatan suka shiga batare da
gaddamaba, saboda abinda idanunsu ke kallo rike
ahannun sauran matasan dake cikin motar.
Marcus dake gaba yayi murmushin mugunta, san
nan yace ''yusha'u ja mota muje,'' daya daga
cikin yaran marcus da sukaje tahowa da
yammata, yace yana kallon marcus, oga akwai
wata yarinya daya da bamu samu ba, tayi
sammakon tafiya gida, kuma kubra ta gayamata
komai game da aikin. Marcus ya juyo fuskarsa
adaure, yace ''wacce yarinyace kuma inane
kauyensu, ? Dole ayi sauri adawo da ita kamin
takai gida don kar wani yaji labarin nan daga
gareta.'Tunda Yusha'u direban gidan su Fiddausi, ya
sharari motar asukwane, atsiyace ya fita
makarantar don gudun cin karo da wani daga
cikin jami'an makarantar yaganasu. Saida suka
hau kan babban tintin dayabi ta gaban
makarantar san nan yusha'u ya dubi mr Marcus
dake zaune daga gefensa, yace ''oga ina muka
nufa daga nan?'' Mr marcus cikin mazurai ya kalli
direban dake ta caccakama motar wuta, yace
''tsohon gidan gonar Alhaji Manga zaka kaimu,
inada masaukin da aan ajiye dukkan yammatan
nan acan, san nan mu fita farautar saura. Dukkan
yamatan hankulansu atashe suke, tabbas sun san
yau sun fado tarkon azzalumin malamin
lissafinsu, mr Marcus, kowacce zuciyarta cike da
damuwa da sake saken halin da zasu iya shiga
muddun mamuguncin mutumin yakaisu inda yake
nufi, bama kamar yammatan kabilun nan Easter
da Tanto, wadanda sunfi tsurewa musamman
ganin yanda yaran marcus suka tasasu da bakin
bindiga, kusan sau bakwai kenan Ester nacewa
atsaya zatayi fitsari acikin minti ashirin, saboda
tsabar firgita. Bayan tafiyar minti talatin tawagar
mr Marcus ta sulala,cikin mataccen gidan gonan
wanda ya dade da mutuwa saboda yanda aka
kyaleshi ba'a anfani acikinsa dakomai ahalin
yanzu, yazama mafakar yan ta adda irinsu
marcus, sukayi fakin adaidai kofar shiga wani
tsohon gini, wanda da'alama rufinsa duk yafara
zazzarewa saboda dadewa da'akayi ba'a shigeshi
ba. Mr Marcus ya fara fitowa daga cikin motar,
ya nufi kofar shiga ginin gidan gonar, san nan
yasa wani karamin mabudi ya bude kofofin san
nan yayi ummarni da ashigo da dukkan
yammatan, bayan shigar yammatan dakin sunyi
mamakin yanda sukaga dakin atsaftace, an
shinfida kafet tare da jerin wasu kujerun alfarma,
kai kace gidan wani attajiri ne, yammatan sun
shiga cikin kokonton cewa lallai marcus ya
shiryama kawo nan gidan dama can tuni,
daganan suka fara fargabar Allah yasa kada suyi
yunkurin lalata masu rayuwa. . Cikin sauri mr
marcus batare daya waiwayi inda yammatan suke
ba, yacema yaransa, '' Mutum uku zasu tsaya
nan suyi gadin yammatan nan, mubarak dakai
yusha'u zakuyi maza yanzu kubi sawun Suwaiba
kamin takai kauyensu ku tabbata kun dawo da ita
nan, zaku iya tafiya da wan nan motar, ni kuma
zan tafi garinsu Easter zan taho da tsohonta, nan
da karfe 2:00 daidai na rana mu hadu anan tare
da bakin nanmu, ku kuma ku kula da yammatan
nan duk wanda nakama da yunkurin fyade ga
wata acikinsu, sai na halakashi, mu kudi muke so
da rufin asiri.'' Alokaci daya dukkanssu suka fice
daga dakin atare, marcus ya nufi garin su Ester ,
mubarak kuma da Abokinsa Yusha'u suka nufi
kauyen KAIMON KAURA don dawo da suwai ba
kamin ta gana da iyayenta. Tunda Suwaiba ta
shiga tsohuwar motar kirar Bus, daga bakin kofar
makarantarsu, zuciyarta cike da zullumin halin da
masoyinta zai kasance tun adaren jiya, shiyasa
adaidai wan nan lokaci dukda gudun damai
tsohuwar motar yake shekawa, akan kwaltar,
suwaiba ji take kamar turasu akeyi da hannu,
cikin kagara tadan gyara zaman ta san nan tace
cikin daga murya, ''direba don Allah sauri nake
kadan kara daga kafa'' Cikin fushi matashin
direban yajuyo yana kallonta, wanda yasan ya
gama kure malejin gudun tsohuwar bus din,
amma sai gashi wata tana raina gudun motar,
wanda shi yafi kowa zalamar son gudun, saboda
tunjiya aka gayamai yayo sammako TASHAR
TABARE, wani karamin kauye daka wuce hanyar
shiga KAIMON KAURA, inda zai yi lodin wasu
kwandunan tumatiri, dukda haka direban ya
hadiye fushinsa, yakara caccakar motar kukan ta
ya sauya, yaci gaba da dibar hanya. Suwaiba tayi
shuru, kaikace an aiko mata da labarin mutuwa
ne agida ake nemanta da gaggawa, acan cikin
zuciyarta ba abinda take tunani yake kaikomo
kamar tunanin saurayinta, SAMANJA, Wanda take
mutuwar sonsa, shima yake mutuwar sonta,
adaidai wan nan lokaci tasan shima hankalinsa
na kanta, domin adaren jiya tun misalin karfe
shabiyu da rabi nadare, suke free call dashi, suna
dandasa labarin soyayya, kwatsam mazajen dare
suka fado dakin, tana kokarin gayama samanja
wata kalmar soyayya da yake bala'in jin dadinta,
wuf cikin barayin wani ya fige wayar ya dadata
da kasa, nan take ta tarwatse. . Don haka
suwaiba tasan tabbas in samanja yayi wunin yau
ban sameta awayaba, babu abinda zai hanashi
niko gari ya biyota makaranta, zuwansa
makaranta kuwa zai iya zama mata hadari,
saboda muddum yaji labarin abinda ya faru, babu
abinda zai hanashi daukar mata fansa, acikin
mummunan mataki, domin sarai suwaiba tasan
halin saurayin nata, Firgigit Suwaiba ta dawo
daga duniyar dogon tunaninta, alokacinda taji
tsohuwar motar bus din takusa hantsalawa dasu,
tana kujerar baya saura kadan kanta ya bugu da
kujerar dake gabanta, ashe tsabar take burkine,
da direban yayi adaidai hanyar shiga wani kauye,
inda ya hangi wani fasinja na jiran mota, dakyar
direban ya take burkin saboda gudun dayake
shekawa yayi yawa, dukkusan fasinjojin motar
babu wanda baiyi ma matashin direban korafi ba,
ganin akan fasinjan naira ashirin zai halaka su,
don dakyar yasha kan motar tana wani irin kara,
suwaiba dai batace komai ba, [8:59PM,
8/22/2016] Usman Auwalu Zango: BAKIN LISSAFI
7 .´ Don ta lura akokarin cika burinta na sauri
direban yayi masu ganganci da rayuwa. Bayan
yadauki fasinjan ahankali yacigaba da
canccakama motar giyoyi, ta sake lulawa akan
titin, amma anja kunnansa akan lallai ya rage
gudu da motar saboda hanyar bata dakyau sosai,
san nan inyazo tsaayawa karya kassarasu abanza
Ya rinka sassauta gudu tun daga nesa. Bayan
tafiya ta kara lulawa, nan danan Suwaiba ta sake
gayyato daddadan tunanin da yake yanke mata
bakin cikinta, wato tunanin saurayinta samanja,
dukda awan nan karon tunanin yafado mata ne
arai daidai inda bai cika mata dadi sosai ba, wato
duk sanda suwaiba zata rinka tuna irin halayen
saurayin nata SAMANJA, takan dan shiga
damuwa,amma saboda irin son da take masa
yakansa ta ga halayensa kamar basu da aibu
sosai, amma amaganar gaskiya, SAMANJA,
rikakken dan dabane, wanda ya dade da samun
tikitin shiga duniyar rigima da data zaune tsaye
atsawon lokaci, gashi baida hakuri, tun yana
matashinsa shida wasu bata garin abokansa,
suka addabi kauyen kaimon kaura da sace sace,
tun a wata shekara da aka taba kamasu sunje
rigar wasu fulani suka sace masu wasu manyan
bajiman shanu, tundaga nan akakai su gidan
maza shekaru biyar, ana zaton da Samanja ya
dao zai natsu ya zama mutumin kirki, amma ina
sai akaga akasin haka, ashe acan samanja ya
hadu da manyan yan fashi da makami, ya shiga
kungiyarsu, shekarunsa uku a legas suna gudanar
da sana'ar fashi da makami, tundaga san nan aka
sallama ma, samanja. . Amma babban abinda yafi
ba mutane mamaki da babban dan ta addan
shine, duk inda yaje tabargazarsa, sai ya dawo
gida yaga sahibansa Suwaiba, an dade ana shan
mamakin irin wan nan matsanancin soyayya da
samanja kema Suwaiba, asanadiyyarta nema
ayanzu yadan rage fita yaje ya dade, saboda baya
son nisa da ita, Ayanzu abinda yafi yawo azuciyar
suwaiba game da tunanin hatsabibin saurayin
nata, shine awasu shekaru baya ya taba sare
hannun wani saurayi don kawai yace yana sonta,
san nan ya sari wani akai da adda, yayi mai
mummunan rauni, shima don kawai yace yana
son suwaiba, wan nan yasa dayawan samarin
karkarar suka kiyayi kusantar budurwar don
tabbas samanja yasha alwashin, kisa akan duk
wanda hukuncinsa ya hau na sabama dokarsa na
nesantar masoyiyar tasa. Wani kwazazzabo da
motar da tsohuwar motar tafada ita ta sake dawo
da kowa cikin hannayacinsa, da wasu mata biyu
dake kusa da suwaiba wadanda suke sharar
bacci suka farka firgigi, wan nan yasa suwaiba ta
hango babban sambol din dake nuna hanyar
shiga kauyen su na Kaimon kaura, tun kamin ta
kainga sauka, ta hangi masoyinta Samanja,
abakin titin, da'alama mota yake jira, kusa da
wata rumfar yayi da wasu masa sukayi suna
sana'ar bunburutu. Suwaiba tacema direbanA
inkaje kaimon kaura akwai mai sauka, direban ya
girgiza kai alamar yaji, daganan ya fara kokarin
take burkin motar wadda take ta sheka gudu,
dakyar yasamu ya faka bayan yayi ma hanyar
shiga kauyen nisa, wan nan yasa saida suwaiba
ta dako akasa ta dawo daidai kwanar shiga
kauyen nasu, san nan ta karika ga sahibin nata,
wanda shima tun daga nesa ya hangota ya
runtumo asukwane, tun kamin sukaiga haduwa,
sukaji karar taka burki adaidai gabansu, wata
doguwar mota fara kirar ta yan makaranta, ta sha
gabansu, cikin sauri kofofin motar ta bude wasu
samari biyu suka fito MUBARAK ne da YUSHA'U,
yaran malam Marcus.
Da fitowar samarin biyu daga motar, mubarak da
abokin ta'addancinsa Yusha'u direban gidan su
fiddausi, kai tsaye wajen yar budurwar suka nufa
Suwaibam wadda ke kokarin karikawa ga
Sahibinta Samanja dan daba, dake daga bayansu.
Sam samarin biyu, basu lura da matashin dake
daga bayansu ba, kai tasaye yar budurwar suka
nufa suna murmushi, alokaci daya Suwaiba taja
ta tsaya ganin matasan na nufota, saida suka
kara matsowa san nan tayi sa'ar gane mubarak
tabbas itama ajinsu daya dashi, shine wanda
Kubra ta basu labari yana cikin barayin jiya da
daddare, nan take Suwaiba taji gabanta ya fadi.
SAMANJA dake daga can baya yana kallon
samarin biyu sun shiga tsakaninsa da budurwar
tasa, cikin sauri ya jefar da wata tsohuwar jakar
dake hannunsa, wadda ya dade yana zuwa yawon
farauta da ita, amma duk da haka idan wata
mahimmiyar tafiya ta kamashi da ita yake tafiye
tafiyensa, ya taho da gudu, musamman yanda
yaga daya daga cikin matasan ya cakumi hannun
sahibar tasa Suwaiba suna kokarin jefata a mota.
Mubarak ya zaje kofar motar da sauri ya jefa
matashiyar budurwar aciki, san nan ya fada ciki
shima tunu yusha'u ya tada motar yana kokarin
komawa kan kwalta, adaidai lokacin Samanja ya
kariko jikin motar yanajin sautin muryar
Sahibarsa Suwaiba tana kwalla ihu da kiran
sunansa. Amma ina tuni motar ta sheka da gudu
akan titin, tare da fizgar hannun Samanja da ya
rike jikin hannun murfin kofar ta waje, nan ya fadi
agefen kwaltar saboda karfin fizgar da direban
yayi ma motar, da sauri wasu samari dake can
cikin wata runfar yayi suna sayarda man fetur na
bunburutu, dake gefen titin suka yo kan samanja
dake kokarin tashi, suna tambayarsa abinda ke
faruwa. Dakyar samanja ke nuna masu motar,
saboda zuciya da takaicin anzo har gida ancishi
da yaki, abinda ba'ataba yimaiba kenan arayuwa,
lallai dole sai yabi sahun mutanen nan ya dawo
da sahibarsa, koda dukkan garin zasu kare kuwa,
ace budurwar dayafi kauna aduniya, anzo
agabansa an saceta, lallai ba'a nemi zaman lafiya
ba, nan danan samanja ya tarbi wata mota dake
kokarin wucewa ta kan titin, ya fada ciki batare
da fadin ina ya dosa ba, yace ma direban cikin
damuwa, . don Allah malam waccan motar
nakeson kabi, wallahi sahibata aka sace yanzun
nan agabana, barayin mutanene, dayawa
fasinjojin motar sun dauka Samanja wasa yake,
don wasu ma dariya suke, saboda kallon mashayi
da suke yi masa, da siffar yan daba marasa
imani. Amma daga karshe sun fahimci da gaske
yake, saboda yanda yake karajin damuwa, ta
nuna bayan motar, wan nan yasa direban kara
sakin motar akan titin ko sa samu su isa ga
doguwar motar dake can gabansu, dukda suma
wadancan motar masifar gudu suke, motar gudu
take shakawa kamar zasu lahira, don su samu su
taddo da farar doguwar motar da suke hange can
agabansu wadda alokuta bayan lokuta takan
bace musu, saboda hawa ko kwana da gangara,
sai sun fita san nan suke iya kara hangenta.
Suna cikin masifar gudun ne an kusa shiga gari
sai suka hangi motar ta dauke kwanar shiga wani
kauye ta cikin wata hanyar burji, nan danan
Samanja yace dakaje can ka sauke ni, tunkamin
sukai samanj ya ciro kudin motar mutumin ya
bashi yana godiya, daya taimakamai ya biyo
motar da gudu. Daga bakin hanyar zuwa gidan
gonar da Mr marcus ya boye yammatan bai fi
kilomita daya ba, acikin wani daji ne, inda wasu
tsaunuka suka kewaye wajen, don haka da gudu
mubarak da abokinsa Yusha'u shuka fada gidan
gonar suka nufi dakin da yammatan suke, tare da
budurwa Suwaiba ta Samanja, suka iske Mr
Marcus da sauran yaransa, suna tsaye suna jiran
dawowarsu. Mr Marcus ya tarbesu cikin farinciki
ganin sun dawo tare da suwaiba tana ta faman
rusa kuka, saida marcus yayi barazanar tarwatsa
kanta da harsashi san nan ya samu tayi shuru,
ya kalli su mubarak dake tsaye daga baya, yace
dakyau aikinku yayi kyau, don haka tare daku
zamuje yanzu mu taho tare da Mahaifin Ester, .
da nayi niyyar tafiya nikadaine amma sai bayan
kun tafi nayanke shawarar na jira ku dawo mu
tafi tare saboda irin wadan nan kabilun namu
nasansu, suna ajiye bindiga don bacin rana, kada
ya mamayeni, amma yanzu inada yakinin tafiya
dashi acikin ruwan sanyi. Marcus yasan sarara
yana kallon yammatan yaci gaba da cewa ''
amma kamin mu tafi yanada kyau muyima
yammatan nan karin haske, don nasan har yanzu
wasu acikinsu musamman fiddausi suna mamakin
taya Yusha'u dayake direban gidansu yazo nan
makaranta, alhali shi badalibi bane, san nan taya
muka hadu dukkansu dashi, har muka yanke
shawarar afkawa dakinsu don farautar su adaren
jiya'' Marcus yadanyi murmushi san nan yace,
''yammata ku kwantar da hankalinku, asannu
zaku san nan wan nan dalilin, Yusha'u shine
wanda ya fara zuwa da wan nan labarin nan
makarantar, saboda yana aikin tuko agidansu
fiddausi tsawon shekaru yana luda da irin yanda
iyayenta ke siya mata sarkoki da kayan alatu na
mata masu tarin yawa, ni kuma nasan yusha'u
tsawon shekaru lokacin da ina sana'ar tukin mota
daga gari zuwa gari [7:48PM, 8/25/2016] Usman
Auwalu Zango: BAKIN LISSAFI 9 . yataba riyin
yaron mota, don awajena ya kiyi tuki, daga baya
muka rabu dashi, bayan na koma makaranta, shi
kuma ya sami tuki agidansu fiddausi, babanta
babban hamshakin attajirine,'' Marcus ya sake
murmushi yace na yammacin shekaranjiya
yusha'u yazomin da labarin cewa ya dawo
dafiddausi makaranta bayan hutun daka kwashe,
tabbas ta dawo da kayan gwala gwwalai masu
tsadar gaske, wanda shikadai ya isa babban jari,
wan nan yasa na gayyato yarana mubarak da
wadan nan, wadanda dama su mun dade muna
sana'ar boye dasu, fiddausi kadai muka sa
atsarin wadda zamu lalube, amma ganin
munshugo gine ginen dakunanku sai muka sauya
shawarar, samun ribar kafa, muka biku daya
bayan daya, sai gashi kuwa mun samu ribar fita
mai yawa'' Mr Marcus na zuwa nan azancensa,
ya juya yace '' wan nan kenan, don haka zamuje
mudawo duk wadda tay yunkurin guduwa ga yara
nan uku, biyu awaje daya zai tsaya nan tare daku,
zasuharbe duk mai karar kwana, na taraku ne don
bana son barain ya fita, zan tattara duk wanda
yasan labarin san nan na hukuntaku agare nan
da zuwa la'asar kowa yasan makomarsa acikin
aikina, karku damu,'' marcus yaci gaba da dariya
yana tafiya. Mubarak da Yusha'u suka take mai
baya, suka dauki motar suka fice da gudu daga
gidan gonar suka nufi garinsu Easter don taho da
mahaifinta. Samanja dake rakube abayan wata
bishiyar dorawa ya hangi fitowar motar daga
gidan gonan, kuma tabbas ya shida matasan da
suka sato sahibarsa ne aciki.. . Bayan bacewar
doguwar motar safar, wadda mr marcus da
yaransa biyu Mubarak da Yusha'u ke ciki, da
sauri SAMANJA dake boye abayan wata katuwa
bishiyar dorawa, ya fito fili daga kefen wat
siririyar hanya wadda zata sadaka da gidan
gonan da suka fito. Bayan Samanja ya hangi
motar tasha kwana alokacin da ta hau kan
kwaltar ta sheka asukwane, nan danan ya gyara
takalmin dake kafarsa, wani tsohuwar kwabane
sawu ciki wanda ya ciwoshi awajen caca a wasu
shekaru can da suka wuce, yawanci da takal,in
s,anja kanci bagu in ana wani biki akauyen ko
zashi wata mahimmiyar unguwa. Cikin hanzari ya
nufi gidan gonar, yana tafiya yana nazartar yanda
wajen yake, tabbas samanja yasan babban aikine
agabansa, na kokarin kubutar da sahibarsa daga
hannun wadan nan miyagun kamar yanda yake
fada aransa, don abinda zuciyarsa take
shaidamai game da mutanen shine tabbas yan
yankar kaine, don haka yanada yakinin saida su
mutu tare da Gimbiyarsa Suwaiba, amma bazai
iya tafiya ya barta ba, don haka asannu ahankali
zuciyarsa tafara yimain doguwar tariya, wani
zamani can baya, sanda ya taba satar toron
agwagwar wani makocinsu Malam Audu
badaskare, yatafi kasuwar gangaren masaka, zai
saida sukayi kicibis da malam Audu shima yaje
cin kasuwa, lokaci daya malam Audu ya ya gane
toron agwagwarsa, yayima Samanja ihu atare tare
acikin kasuwa, dakyar samanja yasha, bayan
yasha duka da itatuwa, tunda ga wan nan lokaci
samanja bai ko koma kauyensu Kaimon Kauraba
ya je tasha ya lalubi motar legas ya nufi gudu.
Babu abinda ya sauya bayan isar Samanja legas,
acan ya hadu da kungiyar wasu barayi yan fashi
da makami, wadanda daga karshe suka tashi
daga legas suka koma jahar Anambara, acan ne
suka dinga cin karensu ba babbaka. Ayanzu haka
da Samanja ke tunkarar gidan gonar da yake
tunanin yan yankar kaine suka sacemai
Habibinsa, ba abinda yake tuwana sai wata rana
da suka taba shiga gidan wani Inyamuri a jahar
Anambara da niyyar yimai fashi da makami, sun
isa gidan kusan karfe 3 nadare, tare da manyan
makami, ashe mutumin shine babban jagora
awata kungiyar asiri ta matsafa dake wani kauye
na OTELLUA dake jahar ta anambara, su shida
suka sami nasarar shiga gidan ogan, amma
Samanja kadai ya tsira da rayuwarsa, sauran
duka wani tsafi da iyamurin yayi ya cinyesu nan
take suka mutu, shima SAMANJA ya samu
kariyar wata layar zanane da asirin shashatau, da
wani abokinsa dan Fulani ya taba bashi, da kyar
ya gano hanyar kauyensu daga can Anambaran. .
Don haka ayanzu da zuciyar samanja take masa
tariyar wan nan rijiya dabaya dayata tsallakewa,
zuciyarsa ta dan karaya kadan don tabbas suma
wadan nan dayake tunkara baisan irin
hatsabibancinsuba, gashi kuma ya baro layar
zanarsa gida baizo da komai ba, amma dukda
haka yakan samu karfin gwiwa da zarar yatuna
Gimbiyarsa fa wadda yafi so da kauna tana cikin
gidan nan, don haka sai ya san halin da take ciki
koma ya tafi da ita, wan nan yasa ya samu
cikakken karfin gwiwa nan take ya kutsa kansa
cikin dan karamin gidan gonan, cikin taka
tsantsan da lura da motsin dake atashi aciki,
Samanja ya taka sannu ahankali cikin sanda tare
da boyewa abayan kananan bishiyoyin dake cikin
gidan gonar, bayan ya wuce wasu kanan rukunin
bishiyoyi can daga nesa ya hangesu wasu matasa
ne guda biyu kowannensu rike da bindiga ahannu
sunata sintiri agaban kofar shiga wani daki, can
kasa kasa Samanja yaji kamar tashin muryar
Sahibarsa Suwaiba tana cewa ''Wayyo Allah
sahibina Samanja maza kazo ka ceceni, don zasu
kasheni alhali banyi masu komai ba. Samanja ya dago kansa sannu ahankali, bayan
sun hada ido da matashin katon dake tsaye
abayansa yana rike da wata madaidaiciyar
bindiga, tabbas samanja yasan sharrin bindiga,
domin aduk yawon duniyarsa sunsha arangama
da jami'an tsaro, yasha gani yanda ake harbe
abokan sana'arsa suna mutuwa har lahira da
harsashi kwaya daya tal, don haka yasan sharrin
bindiga zuwa daya take ma mutum, wan nan
yasa juyowa ahankali tare da mika wuya cikin
biyayya ga matashin dake rike da bindigar.
Samanja ya tuna a sanda yana tashen kauranci,
yataba shan maganin bindiga, saidai yasan
maganin tuni ya karye, domin acikin sharadain
karyewar maganin ance mai kar ya sake yayi
soyayya da kowacce budurwa, don haka tuni yayi
fatali da wan nan sharadi ya tsunduma soyayya
da Shaibarsa Suwaiba. Gabjejen matashin ya tasa
keyar Samanja suka nufi dakin da yammatan da
aka kamo suke ciki, sai alokacinne Samanja ya
lura dakyau, she daya daya cikin masu gadin
kofarne ya shammaceshi suka hangoshi rabe
abayan itatuwa, ya kewaye ta baya ya rutsashi,
tabbas sai yanzu Samanja ya tuna da dadan
kalaman budurwar tasa Suwaiba dayaji suna
tashi acikin kwakwalwarsa, alokacin daya hangi
dakin da suke ciki, babu shakka wan nan
kururuwar zancen zucin kalaman soyayyar su
suka mantar dashi a inda yake har wadan nan
matasan suka sami nasarar hangoshi abayan
itatuwa yana rabe. , Bayan sun isa kofar dakin,
daya matashin dake tsaye bakin kofar shima rike
da tasa bindigar ya taso da sauri ya tarbi gaban
inda Samanja yake tsaye, cikin fushi da zafin rai
ya gabzama samanja kan bindigar dake hannunsa
afuska, nan take samanja ya kwalla ihu, lokacin
da kan katakon bindigar ya hadu da hakoransa,
jini yayi tsartuwa daga bakinsa, matashin farko
wanda ya taso keyar Samanja, ya sake saita kan
bindigar adaidai wuyan sa, yace cikin wata
kakkausar murya, '' Daga ina kake kuma me
yakawoka nan, ? Dan sandane kai ko soja, ko
wanne irin jami'in tsarone, kuma ku nawane ina
sauran?'' Samanja da radadin dukan bindiga ke
ratsa tsakanin hakoransa, jini na zuba, ya amsa
dakyar alokacin da ya lura daya azzalumin na
shirin kara bugamai kan bindigar aka, yace cikin
raunin murya ''Ni kadaine, nazo wajen sahibata
ne Suwaiba wadda kuka kamo dazu daga kauyen
kaimon kaura,'' Samarin biyu sukayi murmushi,
alokaci daya suka sake daure fuska, sukace atare
'' waya gayama tana nan da har zaka biyo
bayanta?'' . Samanja yayi nishi sama sama, san
nan yace ''Ni dakaina na ganku, adaidai kwanar
shiga kauyen mu lokacin na biyo bayan zani gari
nemanta, sai gata ta sauka amota, kamin mu
hadu wasu mutum biyu suka shiga tsakinmu da
mota suka daukota suka kawota nan, ina biye
dasu'' Oh daya katon ya fada yana murmushin
mugunta, yace ''dakyau masoyi, ka biyo
masoyiyarka kenan, yayi kyau, yanzu bara ka isa
gareta sai ka jira sakamakonku tare, kamin
megida ya dawo,'' Katon ya sake takarkarewa iya
karfinsa ya wanke fuskar Samanja da wani
mahaukacin duka da hannu, nan take samanja ya
fadi kasa sumamme, daga nan suka bude dakin
suka jefashi, ya fada tsakar dakin ko motsawa
baya iyayi, suka shaidama daya matashin dake
ciki yana gadin yammatan, ''wan nan bakonkane,
ka kula dashi dakyau Saurayin Suwaibane
yarinyar da Su mubarak suka kamo dazu, inya
farfado sai ka tsaya daga gefe kasha kallon
soyayya'' Suka tintsire da dariya alokaci daya
cikin isgilanci, ya ja kofar dakin suka kulle, suna
dariya da mamakin yanda samanja ke tabbatar
musu da wajen budurwarsa yazo ko tsoro babu
amuryarsa, ''lallai wan nan masoyine'' suka fada
atare suka cigaba da gadin da lura da matsin
dake kadawa awajen. Bayan shudewar wadasu
yan awanni, can Samanja yadan motsa dakyar
fuskarsa cike da radadin dukan da gabjejen katon
nan na bakin kofa yayi mashi dazu, ya juya yana
kallo dakin dayake ciki dishi dishi yake lura da
mutanen da ke cikin dakin, sai alokacin ya fara
tuna halinda ya shiga kamin zuwansa gidan da
abinda ya faru dashi bayan wani matsayin kato
ya tasoshi da bindiga. Bayan dogon motsin
dayayine, ya lura da wani kafcecen kato dake
tsaye kansa rike da bindiga, yana kallonsa yana
gyara rikon bindigarsa, dakyau Samanja ya mike
zaune, san nan ne ya fara ganin duk abinda ke
cikin dakin, wasu yammata ya gani zazzaune
wasu atsaye sun cika dakin wasu suna tagumi
wasu na kuka, adaidai lokacin ne, suka hada ido
da masoyiyarsa Suwaiba dake makure can ajikin
bango. Suwaiba ta runtumo aguje ta nufo kan
Masoyinta Samanja tana kuka, Samanja ya kalli
faskeken katon dake gadinsu, zuciyarsa cike da
sake saken yanda zai iya mai kisan mummuke,
sai da ya da sahibarsa na tunkaroshi san nan yaji
wani karfi na shigarsa duk kuzarin sa ya dawo
jikinsa, aransa ya fada ''dole sai yayi wani
babban motsi don kubutar da kansa da
masoyiyarsa daga yan yankan kan nan, kamar
yanda yake zargi. Suwaiba ta fada jikin Samanja
tana kuka, Samanja ya kalleta idonsa yayi jawur.
. *Usman Auwalu zango* . MUHADU A WANI
PART DIN NAGABA Tahanyar yin comments din
ku zangane kuna taredani don kawo maku labarin
cikin gaggawa . 07066055575 [10:57AM,
1/26/2017] Usman Auwalu Zango: BAKIN LISSAFI
11 - 12 . Ransa cike da damuwar ganin halin da
rabin ransa take ciki, sai alokacin Samanja ya
sake lura da katon matashin dake gadinsu, ya
saita kan bindigarsa adaidai goshin Samanja yana
jiran wani motsi ya sakar masa harsashin dake
makare da bindigar. Samanja ya sa habar rigarsa
yana Sharema Suwaiba hawayen dake zuba daga
idanunta, san nan ya dubi sauran yammatan dake
dakin kusan dukkansu yaran matane matasa
kamar Suwaibarsa, can acikin ransa sai yaji
tausayinsu ya kamashi, duk da rashin imanin da
ya dade yana nunawa arayuwa, amma da zarar
ya ga matashiyar budurwa yakan sassauta mata,
saboda yana tuna tasa budurwar Suwaiba. .
Yammatan duk sun zuba musu ido, suna kallon
soyayyar masoya, adaidai lokacinne Samanja ya
shammaci Faskeken katon nan dake rike da
bindiga akansu, yasa gwiwar hannunsa ya
gabzamai duka iya karfinsa adaidai kan gwiwar
kafarsa ta dama, nan take katon ya kwallara ihu,
cikin wata disasshiyar murya, ya zube da
gwiwarsa yana duba inda samanja ya dokai da
gudumar karfe kamar yanda yake tsammani, cikin
zafin nama Samanja ya sake kaftamai duka
adaidai dokin wuyansa, na nake ya sankare ya
fadi ta baya bindigar dake hannunsa ta
subucemai, suka kai wawa atare da samanja
amma ba wanda yakai gareta, saboda yunkurin
da faskeken katon yayi ya saka ya doki daidai
kwugun Samanja, Samanja yayi baya taga taga,
san nan lokaci daya dukansu suka zabura suka
mike kowa na kallon juna suna huci. Faskeken
katon ya zaburo a fusace, yayo kan samanja da
niyyar yayimai shiga daya, ya kawoma samanja
duka Samanja ya kauce dukan yabi iska, ganin
haka katon ya runbabeshi ya daga samanja
sama, zai buga da kasa, Allah yaba samanja sa'a
ya riko wani karfe mai raga raga dake daga baya
ta jikin windon dakin taga, katon yaja yaja
samanja yaki sakin karfen, can katon ya fusata
ya figa iya karfinsa adaidai lokacinne karfen
windon ya finciko da karfin tsiya ya biyo hannun
Samanja, Tundaga saman kafadar katon inda
Samanja ke cin kasuwar Sama, Samanja ya
yunkura iya karfinsa ya Bugama katon karfen
dake hannunsa na windon dakin, nan take karfen
ya lume akan mutumin, katon yayi wata kuwwa,
Samanja yayi sauri ya toshe bakin matshin katon
da tafin hannunsa, don ragema ihun karfin sauti.
Lokaci daya katon yayi baya taga taga ya hade
da jikin bangon dakin ya zube kasa yana nishi
sama sama, jini ya fara cikin kasuwa afuskarsa,
Samanja ya matsa kusa dashi yana bude ido
dakyar yana kallon samanja dishi dishi, Samanja
ya sake yunkurawa da duk iya karfinsa ya
saukemai wani mahaukacin duka adaidai kan
fuskarsa nn take katon ya fadi kasa asume baiko
kara motsawa ba, samanya yayi murmushin
mugunta can acikin ransa yace ko banza na rama
irin dukan da yan uwanka sukayi min, Anyi babbar
sa'a OGA mr marcus da yaransa da suka fita tun
misalin karfe 2:30, don gayyato gyatumin
matsoraciyar budurwa Ester, basu sha wata
wahalaba wajen gane unguwar da mutumin yake
Mr Oladinco, saidai sunyi rashin sa'a baya gida
yaje kasuwa, inda katon shagonsa yake yana
sana'ar sayar da safaya part na motoci. . Kai
tsaye marcus da yaransa suka wuce can bakin
tsohuwar kasuwa, inda mr Ola ke gudanar da
sa'arsa, mr Oladinco tsohon bayarabene wanda
ya dade da shigowa kasar hausa neman kudi, tun
awasu shekaru can masu nisa, don haka ya samu
karbuwa acikin kasuwancinsa yanada mutane
sosai wadan da yake mu'amala dasu, date da
yaran shago dayawa, da wadanda yaye ya
kakkafasu awasu shaunan nasu nakansu, An
tabbatar Mr Ola bashida ganin kyashi ko hassada
akan kasuwancinsa wan nan yasa yama mai
farinji, musamman ma awajen hausawanmu da
suke rabawa yana basu bashi ko rancen kudi,
wasu su dawomai dasu wasu kuma sai akiyama.
Bayan marcus da tawagarsa sun gama nazartar
katon bayaraben dake zaune daga kan wata
kujera abakin shagonsa, sai marcus yacema
yaransa ''ku jirani ina zuwa bara naje nasameshi
dakaina,'' marcus ya fita daga motar ya nufi
tulelen bayaraben yana washemai baki, bayan sun
gaisa, marcus ya gabataimai da kansa, cewa shi
malamine daga makarantar su Ester yarinyarsa,
yazo don ya tafi dashine don ana menan iyayesu
amakaranta saboda satar da akayi musu jiya, mr
Oladinco ya nuna rashin amincewa yabi marcus
saboda harkokin kasuwancinsu, amma yace zai
tura yaronsa yayan ester kenan, wan nan yasa
marcus tababa da maganar tsohon bayaraben,
bayan marcus ya matsa don ganin lallai sai sun
tafi tare da mr Oladinco, sai mr Ola ya fara
kokonton wan nan tafiya wan nan yasa fara
tseguntama abokan kasuwancinsa cewa shifa
baima yarda da mutanen ba, wan nan yasa lokaci
daya akayima su marcus ca da tambayoyi, inda
aka dinga samun karon zantuka, Dakyar marcus
da yaransa suka samu damar arcewa da motarsu
bisa ganin mutane na yunkurin fada musu don
nuna rashin yarda dasu.
Anyi babbar sa'a OGA mr marcus da yaransa da
suka fita tun misalin karfe 2:30, don gayyato
gyatumin matsoraciyar budurwa Ester, basu sha
wata wahalaba wajen gane unguwar da mutumin
yake Mr Oladinco, saidai sunyi rashin sa'a baya
gida yaje kasuwa, inda katon shagonsa yake yana
sana'ar sayar da safaya part na motoci. . Kai
tsaye marcus da yaransa suka wuce can bakin
tsohuwar kasuwa, inda mr Ola ke gudanar da
sa'arsa, mr Oladinco tsohon bayarabene wanda
ya dade da shigowa kasar hausa neman kudi, tun
awasu shekaru can masu nisa, don haka ya samu
karbuwa acikin kasuwancinsa yanada mutane
sosai wadan da yake mu'amala dasu, date da
yaran shago dayawa, da wadanda yaye ya
kakkafasu awasu shaunan nasu nakansu, An
tabbatar Mr Ola bashida ganin kyashi ko hassada
akan kasuwancinsa wan nan yasa yama mai
farinji, musamman ma awajen hausawanmu da
suke rabawa yana basu bashi ko rancen kudi,
wasu su dawomai dasu wasu kuma sai akiyama.
Bayan marcus da tawagarsa sun gama nazartar
katon bayaraben dake zaune daga kan wata
kujera abakin shagonsa, sai marcus yacema
yaransa ''ku jirani ina zuwa bara naje nasameshi
dakaina,'' marcus ya fita daga motar ya nufi
tulelen bayaraben yana washemai baki, bayan sun
gaisa, marcus ya gabataimai da kansa, cewa shi
malamine daga makarantar su Ester yarinyarsa,
yazo don ya tafi dashine don ana menan iyayesu
amakaranta saboda satar da akayi musu jiya, mr
Oladinco ya nuna rashin amincewa yabi marcus
saboda harkokin kasuwancinsu, amma yace zai
tura yaronsa yayan ester kenan, wan nan yasa
marcus tababa da maganar tsohon bayaraben,
bayan marcus ya matsa don ganin lallai sai sun
tafi tare da mr Oladinco, sai mr Ola ya fara
kokonton wan nan tafiya wan nan yasa fara
tseguntama abokan kasuwancinsa cewa shifa
baima yarda da mutanen ba, wan nan yasa lokaci
daya akayima su marcus ca da tambayoyi, inda
aka dinga samun karon zantuka, Dakyar marcus
da yaransa suka samu damar arcewa da motarsu
bisa ganin mutane na yunkurin fada musu don
nuna rashin yarda dasu. . Tunda suka fito garin
basu zame ko onaba sai gidan gonar da suka
boye yammatan nan, cikin damuwar aikinsu
nason baci akaron farko, Da sauri marcus ya nufi
dakin da suka tara yamatan don fara tunanin
mataki na gaba, amma abinda suka riska adakin
yafi bashi tsoro akan abinda suka baro agari,
dakin ba kowa sai yammata biyu, Suka rage Ester
da kawarta sai katon dake kwance kasa asume,
cikin kunar rai marcus ya tambayi yammatan
wayayi wan nan aikin, ? Cikin rawar murya
sukace '' samanjane'' marcus ya tambaya waye
kuma samanja? Alokaci daya atare sukacemai
saurayin Suwaiba ne, sun tafi kaimon kaura tare.
Bayan samanja ya ga faskeken katon nan ya fadi
kasa asume, bayan sun raba hammata da gwada
karfin kwanji, cikin sauri ya juyo ga tawagar
yammatan dake dakin suna kallon gumurzun daya
faru atsakaninsu, yadan saurara kadan kozaiji
wani motsi amma shuru sai karar dukan
zuciyarsa data sauran yammatan, wan nan ya
tabbatar mai da sauran masu gadin dakin dake
waje suna nesa da kofar kenan shiyasa basu iya
jiwo fadan faman da sukayi da maigadin dakin
aciki ba. Da sauri samanja ya karika jikin windon
dakin wanda tuni kofar sa abude take wayam,
saboda babbake katon karfen rodin dake jikin
windon da sukayi alokacin da suna gumurzun,
bayan ya dan leka kansa daga waje yayi nazarin
bayan dakunan wanda dajine sai gonaki dake can
sun tafi fululu. . Samanja ya juyo dakin da sauri
ya kira Suwaiba dake tsaye daga bayansa, yace
to lokacin gudu yayi, maza ki haura nan mu kama
hanyar gida, cikin azama samanja ya kama indon
ya dira daga waje, ya juyo da sauri ya tallafe
masoyiyarsa Suwaiba ya direta san nan ya kama
hannunta har sun fara gudu, sai Suwaiba kalleshi
tace cikin kasa kasa da murya, ''habibi sauran fa
suma yakamata ataimaka musu,'' samanja ya
kalleta yana kokarin share zufara dake
tsatstsafowa daga goshinsa, yace '' haba habibi
muyi ta kammu kawai, suma kowa tasa ta
fissheshi'' Suwaiba tace '' a a habibi kawayenane
fa ataimaka musu'' Cikin zafin nama samanja ya
dawo bakin tagar da gudu, yace cikin karamar
murya, ''duk wadda ke da shirin tafiya tayi maza
mu runtuama kamin azzaluman nan su dawo''
Nan danan yammatan suka fara rububin bin
bayansu, duka suka fito sai wasu yamma biyu ne
basu bi bayansu ba, ester ce matsoraciya da
kawarta, nan take samanja da yammatan suka
runtuma cikin daji asukwane zukatansu cike da
zullumin haduwa da wasu daga cikin muggan yan
ta addar. Bayan doguwar tafiya ta ratse, da bin
kwazazzaban dazuka can sukabulla wani kauye
dake bakin hanya, mai suna Kwanar gurjiya, daga
nan samanja ya ja yammatan suka boye abayan
wani ginin tsohon masallaci daya fara rushewa,
san nan ya fito bakin hanya yana tarbar musu
motar zuwa Kaimon kaura. PART 14 kuriqayin
comments don insan kuna tare dani [11:35AM,
8/27/2016] WHATSAPP N0 07066055575: BAKIN
LISSAFI 14 . Ko minti biyu bai hadaba abakin titin
ya hango wata tsohuwar motar akori kura,
tundaga nesa ya ganeta motar Alhaji Madu ne
sarkin fawan kaimon kaura da kewaye, yadawo
cin kasuwa, samanja yayi sauri ya dagamai
hannu, tundaga nesa shima yafara kokarin lalubar
birkin motar don samun damar tsayawa adaidai
inda ake tsaidashi, domin azatonsa, wani
bafullatanine yake son sayar masa da maraka don
ya hangi wata sanuwa dake kiwo daga cikin wata
gona adaidai bayan samanja . Bayan tsohuwar
motar ta tsaya dakyar, samanja ya runtuma
asukwana ya shaidama Sarin fawa halin da suke
ciki, daga nan yayi maza ya kira yammatan suka
cika bodin motar daganan Alhaji madu sarkin
fawa yaci gaba da caccakama motar giya suka
nufi kauyesu kaimon kaura tare da tawagar
yammatan. . Tunda yammatan nan biyu Ester da
kawarta, suka labarta ma mr marcus guduwar
samanja ya yammatan nan, hankalinsa ya
dugunzuma ya tashi, domin yana da tabbacin
aikinsa ya koma baya kuma da'alama yanason
baci, cikin kunar rai yayo waje daga dakin ya nufi
inda kattin nan biyu suke tsaye nesa da kofar
dakin suna gadi, cikin zafin nama ya wanke
fuskokinsu da wani zazzafan mari san nan cikin
fada yake tuhumarsu da sakacin barin yammatan
nan su gudu. Dakyar mr marcus ya iya
fahimtarsu kan cewa wani saurayin wata
budurwane aciki yazo tafiya da ita shine suka
kamashi suka hada dashi adakin, suna nan waje
suna gadi basu da labarin abinda ya faru acikin
daki. Marcus ya juya cikin fushi ya nufi motarsu
batare da yacema kowa kalaba, aransa yana
fadin koda bala'i sai yaje wan nan kauye ya dawo
da yammatan nan dama duk wanda tsautsayi
yasa yaji labarin satar dakai adaren jiyaa
amakarantar yammatan. Ganin ya wuce baicema
kowa kalaba, ya saya yaran nasa bin sawunsa,
da sauri suma suka fada motar, wan nan karon
mr marcus da kansa ya figi motar afusace ya
cilla da gudun bala'i kamar an harba kibiya suka
nufi kauyen kaimon kaura da niyyar saidai ayita
ta kare. . *** *** *** *** . Bayan Alhaji Madu
sarkin fawa ya isa kauyen kaimon kaura, tun
akan hanya kamin su karika Samanja ya sanar
dashi cewa in ya isa ya wuce kai tsaye zuwa
gidan me unguwa Malam tajo, don mika sauran
yammatan gareshi san nan anemi garuruwansu
amaidasu ga iyayensu, Ai kuwa haka akayi bayan
shigar tsohuwar motar akori kurar kauyen da
misalin wajen karfe hudu saura na yamma, sarkin
fawa bai faka ako inaba sai daidai bakin kofar
gidan me unguwa malam Tajo, saidai anyi rashin
sa'a me unguwa baya gida yaje kewaya wata
fadamarsa dake can dausayi, inda yayi rake
awakai na yawan zuwa yimai barna, amma dai
babban dan mai unguwa na nan wani
sangwamemen kato girman kauye mai suna
Sammani, wanda suka iske zaune akan wani
gungumen icce yana hutawa yau baije yammaci
gonaba duka mayen gonane. Sammani babban
dan sarkin noma shi ya shigar da yammatan
gidansu, tare da Samanja da suwaiba, akayi musu
shimfida atsakar gidan suka zazzauna, daganan
sarkin fawa ya wuce gida samanja da sahibarsa
suwaiba ma duk suka nufi gida da niyyar sai me
unguwa Tajo ya dawo gona zuwa magariba sai
suzo amaida yanda akai. Sammani dan me
unguwa bai cika wayau sosai ba, giman jikin ne
kawai saida masifar karfi kamar shara'a, amma
dai dolo dolo ne, nan da nan ya fita cikin kauyen
wata majalisa da wasu matasa zauna gari banza
abokansa suke yawan haduwa wadanda basason
zuwa gona yammaci, sai zaman kashe wando
gardamar kwallo da wasan karta da da kafsa ta
kaddama akan Ali nuhu da Adam Zango wayafi
wani tashe da iya fim, da kuma wasu daidaiku
acikinsu da sukaje birni suka waye har suka fara
dan daba shan taba, ya shaida musu cewa
gidansu anyi bakin yammata, daga birni yanzu
yanzun nan suna nan sun cika gidan. Cikin azama
tawagar samarin zauna gari banza suka runtuma
suka nufi gidan me unguwa don kowa ya zabi
wadda yake so, Sammani dai shi har ya kama
wadda yake so wata siririyar budurwa doguwa
fara yake so daya dafa cikin tawagar yammatan
sunan ta IHSAN. . Tunda Sammani yajawo
tawagar abokansa, suka nufo gidansu don kowa
ya duba budurwar da yakeso, sammani yana
gaba saura na biye dashi abaya, da alama
kowannensu zuciyarsa na cike da iya shege da
shakiyyanci irin na matasan kauye. Yan mintina
kadan yakaisu gidan mai unguwa tajo dake can
kusa da tsohuwar primary dake kusa da bayan
gari, inda kaitsaye batare da bata lokaci ba
Sammani yashiga gaba suka bishi cikin gidan,
azaune suka tadda yammatan suna hutawa cikin
al'ajabin halin da suke ciki, sammani ne yafara
nuna wata sambaleliyar budurwa yace yana
washe baki ''Ni ga tawa nan, kaima Dogara ka
zabi taka'' ya tabo wani gajeren kato baki mai
siffar yan dambe dake kusa dashi. . Wanda
Sammani ya kira dogara ya washe baki yana
kallon kyawawan yammatan, yace ''waccan
nakeso'' shima ya nuna wata farar budurwa
siririya dake daga tsakiyar yammatan azaune,
daga nan kowa ya nuna wadda yakeso, cikin
ranshin wayau da dolonci na bakauyen da ya
dade bai shiga gari ba. . Like Social media Hausa
Novels [11:36AM, 8/27/2016] WHATSAPP N0
07066055575: BAKIN LISSAFI 15 . Hankalin
yammatan yafara tashi ganin samarin kamar suna
shirin fada musu, sun kewayesu sunata musu
wawanci, zukatan yammatan ya cika da zullumin
Allah sa ba gudun gara sukayiba suka fada gidan
zago. Ganin matasan da gaske suke shakiyancin
nasu, yasa mahaifiyar sammani wata dattijuwa
mai suna Mero ta fito dakin girki da gudu rike da
mucciyar tuka tuwo ahannu, ta nufo samarin tana
surfa musu zagi, akan me zasuzo su takurama
bakin yammata. Tun kamin matar ta kariko wajen
matasan suka runtuma sukayi waje da gudu,
adaidai soron gidanne sukaci karo da mai unguwa
ya dawo gona yana tafe yana gungura wata
tsohuwar akwalar kekensa yayo ciyawar dabbobi,
wani matashi mai suna Ya'ulle shine ya banke
keken mai unguwa garin gudu ya shalllake shi
suka fada wata gonar dawa dake daga bayan
gidan mai unguwa suna dariya. Bayan me
unguwa ya kariko cikin gidan shima tundaga
bakin kofa yayi tozali da yammatan dake zaune
abakin turakarsa an baza musu wani tsohon
tamfal dinsa na fyadin shinkafa suna zaune,
bayan me unguwa ya jingine akwalar kekensa
akusa da rumfar awakinsu, sai yayo tsakar gidan
yana kwalama mero kira uwar gidansa, ''Mero
baki mukayine'', yana magana yana kallon
yammatan, uwargidan mai unguwa ta fito daga
dakin girkin idonta yayi jawur da alama wuta take
hurawa hayaki ya cika mata ido, ta fyace majina
da gefeb zaninta san nan ta kalli me unguwa
dake tsaye tsakar gidan tace '' bakine daga birni
dazu Samanja yazo dasu nan gidan yace bayan
sallar magariba zaizo kuyi magana, shida Sarkin
fawa suka zo gidan nan dazu kana gona'' Me
unguwa ya dubi yammatan alokaci daya yace
yana washe musu baki, ''Sannunku da zuwa fa
dafatan anzo lafiya ya birni?'' yammatan suka
amsa atare ''lafiya kalau'' daga nan ya shige
dakinsa, yayi alwalar sallar magariba ganin lokaci
ya kawi jiki , san nan ya fice daga gidan ya nufi
masallaci dake can tsakiyar kauyen wajen babban
dandali. . *** *** *** Tunda Marcus ya kamo
hanyar kaimon kaura bai saurara ma motar nan
ko sau dayaba, caccaka mata wuta kawai yake
yana sheka gudu kamar zasu tashi sama, cikin
kankanin lokaci suka shigo kaimon kaura, saidai
lokacin duhu ya fara domin anata kiran sallar
magariba, amasallatan dake kauyen, acan bayan
gari suka ajiye motarsu daga gefen wata gonar
masara wadda take gab dafara fiddakai, san nan
ya ummarci sauran yaransa da su jirashi abakin
mota zai shiga binciken Samanja, alokuta da
dama Marcus yafison yin irin wan nan aikin
shikadai domin yafi yarda dakansa akan kowa,
don haka cikin yakini ya kutsakai cikin garin yana
tafiya yana lura da mutanen dake wucewa kusa
dashi, can ya hangi wata yarinya tana ta sauri ta
dauko nika awani inji, tan saurin takai gida don
kada suyi daren tuwo har magariba tayi, da sauri
Marcus yasha gabanta yana mata murmushi yace
''kanwata kina sauri ko ni Abokin Samanjane
daga hayican nake, ko kinsan gidansu'' ?
Yarinyar tadanja kadan ta tsaya san nan ta kalli
Marcus dake gabanta atsaye, tace ''Aiduk kauyen
nan ba wanda baisan Samanja me dawa ba, kaga
gidacan mara kofa'' yarinyar ta nuna wani gida
dake can nesa dasu, samanja ya hangi inda
yarinyar ke nunawa yace ''kwarai na hangi gidan
gida mai jar kasa ko?'' ya tambayi yarinyar tace
''yawwa nan to nan ne gidansu Samanja dazun
nan ma naganshi ya wuce tare da mutumiyar
tasa'' samanja yayi sauri ya tarbi nunfashin
yarinyar alokacin da take kokarin wucewa, yace
''Suwaiba ko''? Yarinyar tace tabbas ai baida
wadda tafita, don yana iya komai akanta. . Mr
marcus ya juya ya nufi gidan da yarinyar ta
nunamai, zuciyarsa cike da tabbacin ya gane
Gidansu Samanja, tun kamin ya karika kofar
gidan ya rakube ajikin wata kwana, yana jiran
yaga wazai fito daga gidan, bayan wasu yan
mintina kadan baiga kowa ya fito daga gidanba,
sai ya samu wani almajiri dake yawon bara da
maraicen, yazo zai wuce ta inda yake rabe,
Marcus yace da yaron almajirin ''kasan can
gidan?'' ya nuna gidansu Samanja Al'majirin yace
''nasani gidan su Iroro ne'' waye kuma iroro''
marcus ya tambayeshi, ''kanin Samanja nem
shine abokina'' ''dakyau Marcus yace yana kallon
yaron '' yanzu maza kaje ka kiramin yaron kaga
naira Hamsin nan zan baka, marcus yazo
sabuwar naira hamsi ya mika ma Al'majirin
ahannu. Nan da nan saiga Al'amjiri ya fito tare
da wani yaro sa'ansa, yacema marcus dake
rakube abayan wani gini, ga iroron'' Marcus yayi
murmushi yace yawwa ''dan malam na gode zaka
iya tafiyarka'' Marcus ya kalli yaron da ake kira
iroro yace yana murmushi haryanzu a fuskarsa,
''ina yayanka Samanja'' Yaro yace ''ai yafita tun
dazu yana gidansu Suwaiba,'' marcus yace
dakyau, ai abokinane, wasu bakin yammata
dayazo dasu dazu suna ciki ko?'' yaron yace '' a
a ai banan yazo dasu ba suna gidan mai unguwa,
can yabarsu tunzu, sai mai unguwa ya dawo
gona, wadanda yazo dasu daga birni ko''? Yaron
ya tambaya, Marcus ya girgiza kai yace ''ok
inane gidan mai unguwan,'' Yaron yace ai
yanacan kusa da fita gari ta nan hanyar, ya nuna
inda marcus ya fito.
Mr marcus yace na gane, amma muje karakani
gidan zan baka naira hamsin kasha dan
tamatsitsi, yaro ya washe baki jin zan samu kudi,
yace muje in rakaka. mr marcus da yaron sun isa
kofar gidan adaidai lokacin da ake tayar da sallar
magaruba abban masallacin kauyen dake can
dandali, suna jiwo karar lasafikar masallacin wani
ladani mai zakin murya sai rangada kabbara yake,
wan nan ya tabbatarma da Mr marcus duk
manyan gidan basa nan don haka nan danan
yacema yaron nan ''maza ka shiga kace ance wai
yammatan nan da sukazo suzo ana kira inji mai
unguwa za aje dasu hayin Babba da jaka, gidan
hakimi'' yaron yace to ya fada gidan, da sauri,
ganin yaron ya fada gidan yasa marcus sauri ya
fada daga cikin zaure ya rabe abakin kofa ya zaro
wata karamar bindiga. Mintina kadan sai ga
yaron tare da tawagar yammatan sun fito lokaci
daya, nan danan marcus ya rutsasu da bindigarsa
yana tsare musu ido, yace cikin kakkausar murya,
duk wadda tayi babban matsi saina harbeta nan
kusa da bayan garine bawanda zaiji kumuje waje,
marcus ya tasa yammatan nan agaba, cikin
matsanancin tsoro da fargaba, yammatan suke
bin ummarninsa, marcus ya tasasu har bakin inda
suka aje motarsu, san nan sauran yaransa suka
fito da sauri suka tarbi oga tare da yammatan,
san nan suka tasa keyarsu zuwa cikin motar. mr
marcus yayi murmushin mugunta, bayan yaga
yammatan sun gama shiga motar san nan shima
ya shiga mazaunin direba yaransa suka fada
motar yajata asukwane yayi gaba yana dariya. .
Bayan Mr Marcus ya zafgama doguwar motar
giya, ya fita asukwane ya keta da gudu ta cikin
wata gonar waken suya da tayi yabanya laho-
laho, yafada wani kwarin kunya da ruwa ya taru,
ya taka motar ruwa da tabo ya fallatse ajikin
gayyen waken suyan dake gonar, gurin yayi kaca-
kaca, ya samu yakoma kan kwazazzabon hanyar
dakyar, san nan ya sake taka motar da gudu.
yammatan daya sake sacewa cike da motar
kowacce ciki ya duri ruwa, sai faman zare ido
suke zuciya cike fal da fargaba, yaransa na rike
da bindigogi suna gadin yammatan tare da lura
da motsin kowacce yarinya, cikin shirin kota
kwana ga duk yarinyar da tayi wautar kwarma ihu
ko kokarin dira ta windo, da sauri harsasai zasu
ratattaka kanta ko daidai zuciyarta. Bayan
marcun yaci gaba da tsulama motar wuta tare da
jefa mata giyoyi barkatai, don sauri tare da
kokarin barin yankin karkarar ta Kaimon kaura,
kamin a ankara da barnar da sukayo, can bayan
ya wuce wasu gonakin shinkafa guda biyu dake
makotaka da juna, alokacin duhun dare yafara
bisa rashin zato sai yaran marcus sukaga yaci
wani mahaukacin burki, dakyar motar ta tsaya,
saida ta hankada kamar zasu fadi, san nan cikin
zafin nama ya dauke kan motar tafada wata
gonar makani, yayi rubus yasake dannawa aguje
yakoma ta hanyar da suka fito ya nufi kaimon
kaura gadan gadan. Yaran marcus da yammatan
nan cikin matsanancin mamaki suka dubi marcus
dake ta kokarin karama motar giya, dakyar
mubarak ya hadiye mamakinsa ya tambayi
marcus, ''Oga ina kake da nufin zamu koma, ? Ko
ka bace hanyane,'' batare da marcus ya kalli inda
suke ba, yace yana kokarin ketare wari rafi da
ruwa ya taru akan hanya, ''Munyi tuya mun
manta da albasa, SUWAIBA da saurayinta
SAMANJA Tabbas izuwa yanzu Samanja ya gama
sanin inda kan zancen ya nufa, kunga kenan
shima yana cikin komar binciken mu'' Dayawa
cikin yaran nasa sunyi kokarin ankarar da marcus
kan cewa yayi hakuri su tafi da wadanda suka
kama, amma ya nuna musu ya fisu sanin aikin
don haka dole suka hakura, suka rabu dashi don
ganin rai zai baci. Wan nan shine babban
kuskuren marcus, dayasan abinda zai faru dashi
in yakoma kaimon kaura da niyyar taso keyar
Suwaiba da Samanja da sam bai yunkurin aikata
hakan ba, dazaifimai sauki ya sauke yammatan
ya tafi ofishin yansanda ya mika kansa
amatsayin barawon kayan mata, ahukuntasa
daidai da satar dayayi, akan abinda ke jiransa
akaimon kaura. . *** *** *** Bayan an sallame
sallar magaruba, amasallacin tsakiyar kauyen
Kaimon Kaura, da sauri mai unguwa Tajo ya
shafa addu'a batare da ya jira an yi addu'a atare
ba kamar yanda aka saba, ya fito kofar
masallacin ya kira ladanin masallacin Malam
rabu'u, ya dan labartamai halin da ake ciki da
yammatan da suka bakunci gidansa ayau, yace in
an yi addu'a ya shaidama liman abinda ke faruwa
su sameshi agida yayi gaba. Tunkamin mai
unguwa ya karika bakin kofar gidansa ya hangi
Tasi'u gardi tsaye akofar gidan, daya daga cikin
dogaran mai girma Hakimin gundumarsu ne,
Alhaji Baballe dake can kauyen TANDU, wani
bakin katone kakkarfa, yana tsaye yana jiran
zuwan Mai unguwa, me unguwa ya tambayi
kansa, wa kuma ya je har TANDU da wan nan
yammaci ya labartama hakimi zuwan yammatan
nan, har ya taso dan aike. Bayan me unguwa ya
karika kofar gidan suka gaisa da Tasi'u Gardi,
tasi'u ya sanarmai da cewa mai girma Hakimi yaji
labarin anyi wasu bakin yammata daga birni
ayammacin yau, shine ya turoni danazo na tafi
dasu can don bin ba'asi yace ka shirya mutafi
tare can TANDU yanzu yanzu. . Like Social media
Hausa Novels [11:13AM, 8/28/2016] Usman
Auwalu: BAKIN LISSAFI 17 . Me unguwa bayanda
ya iya da umarnin Hakiminsa Alhaji Baballe, dole
ya fada gida da sauri don tattaro tawagar
yammatan su nufi kauyen Tandu don cika
umarnin hakimi, bayan yan mintina kadan da
shigar Me unguwa gida da niyyar tattaro
yammata suzo su kama hanyar Zuwa kauyen
TanDu,inda matsugunin Hakimi yake, saigashi
kuma ya fito da sauri jikinsa ba kwarai adaidai
lokacinne malam Rabi'u Ladanin kaimon Kaura da
Malam Dan Haru limamin Kauyen suka iso kofar
gidan me unguwa, kowan nensu sanye da wasu
zunbula zumbulan manyan giguna malum malum,
sunata buya buya, su ga manyan gari anzo jin
yanda al'amarin yammata yakasance. . Me
unguwa tajo yayi turus agaban Tasi'u gardi
jikinsa na tsuma, ya labarta musu lallai wani
yazo ya tafi da yammatan nan amma baisan ko
waye ba, ancemaidai wani yaro aka turo kanin
Samanja mai dawa, don haka bamuga ta zama
ba' suka juya su duka suka runtuma suka nufi
gidan su Samanja. Tunda mr marcus ya juyo kan
motar nan asukwane ta nufo kauyen kaimon
kaura, da tunanin tattara SAMANJA da sahibarsa
SUWAIBA ya sake arcewa dasu, ashe bai sani ba
wan nan shine kuskure na farko daya fara
aikatawa aduk cikin aikinsa daya kwashe tsawon
wunin yau yana aikatawa. Saida ya kusa shigowa
kauyen san nan ya rage gudun motar ya sulala
ahankali ya nufi gefen hanya daidai wata gonar
Masara ya faka motar san nan ya kashe duka
fitulunta, ya fito da sauri yasa yaransa suyi gadin
yammatan san nan ya juya da sauri ya nufi cikin
kauyen shikadai gidansu Samanja ya nufa gadan
gadan, da tunanin inbaisamesu agidanba ya wuce
gidansu Suwaiba kaitsaye, yana soke da karamar
bindigarsa acikin wando, zuciyarsa cike da
yakinin itakadai zata iya tattarai mutanen kauyen
nan kaf yatafi dasu duk inda yakeso. *** *** ***
** Kofar gidansu Samanja me unguwa tajo ne
tare da Tasi'u gardi dogarin hakimin Kauyen
Tandu Alhaji Baballe, sai babban limamin kaimom
kaura, tare da malam Rabi'u ladanin kauyen, sun
tura yaro gidansu Samanja kenan don akirashi,
sai ga tawagar matasan kauyen nan sun iso kofar
gidan, Sammanine tare da abokansa, wadanda
suke son yammatan nan, sun koma gidan su
Sammani akace musu an tafi da yammatan sune
suma suka biyo bayan yammatansu, don wani
kaura acikin su mai suna Darda'u dayace yana
son wata kakkaurar budurwa acikin yammatan
yace shi ba ruwansa zai iya kashe mutum akan
matashiyar budurwar. Cikin rudani Samanja ya
fito daga cikin gidansu, jin kiran me unguwa
agidansu da wan nan lokaci, yasan wata kila
maganar yammatan nan nan ne, amma ai me
unguwa aikowa ya kamata yayi akirashi ba'ace
gashi nan yazo da kansa ba, bayan Samanja ya
fito me unguwa ya fara tarbarsa da zance ko
yammatan nan suna gidansu shi ya tura kaninsa
iroro ya kirasu, samanja yayi turus agaban Me
unguwa hankalinsa atashe yace ina ai bai kara
komawa ta kansu ba, shi yana gidansu Suwaiba
suna tare, nan danan aka kira Iroro kanin
Samanja aka tambayeshi yaushe Samanja ya
turaka ka kira bakin yammatan nan? . Iroro yayi
narainarai da idanu yana kallon mutane, suka
hada ido da jajayen idaun Tasi'u Gardi Dogarin
mai girma hakimin Tandu, nan da nan yaji
gabansa ya fadi, yace ''wani bakone yazo
yacemin abokinka ne,'' iroro ya nuna Samanja,
''shine yace nakaisa gidan me unguwa don ya ga
yammatan bayan na gayamai suna can shine
mukaje nakirasu nadaiga yayi bayan gari dasu
wajen gonar Dan Ali mai shago'' Nan take
mutanen dake wajen suka fahinci lallai wani yazo
ya sace yammatan, batare da bata lokaciba guri
ya cika da mutanen gari ana labarin barayin
yammata sun shugo gari sun sace wata tawagar
yammata sukun da guda. Wani dattijo mai suna
Dallami ya fadi cewa shi yaga wata bakuwar
motar gefen magaruba ya dawo gona, adaidai
nan bayan gari, kuma babu shakka ya hangi kan
wata budurwa aciki saidai bai sani ba sunada
yawa shidai mace daya yasamu nasarar
hangowa, nan take Me unguwa ya kira hakimi ya
shaidamai halin da ake ciki san nan ya nemi
taimakon yandoka acikin aikin atarba kauyukan
dake yankin, batare da bata lokaciba hakimi ya
sanar da D P On yansanda dake yankin aka taso
motar yansanda uku suka nufo Kauyen kaimon
kaura. . Like my new page Social Fresh Hausa
Novels [9:11PM, 8/29/2016] Usman Auwalu:
BAKIN LISSAFI 18 ****** KARSHE ****** . Batare
da bata lokaciba matasa suka zabura asukwane
tare da su me unguwa akayi hanyan bayan gari
inda akace an ga bakuwar mota dazu, aka
barbazu, ana neman yammatan da barayinsu,
wani matashi mai suna Jallo yazo wucewa ta
kofar wani gida kenan yanadauke da wani katon
icce sukaci karo da wata tsohuwa tacemai ''acan
kwanar naga wani mutum da alama bakone, yana
ta rabe rabe ku bincikashi don ni ina zarginsa''
Jallo yasha kwanar cikin sanda ya hangi dishi
dishin kayan marcus arabe jikin wata katuwar
bishiyar kuka ya sadada ahankali, yabi ta
bayansa saidayaje dab dashi san nan ya damki
wuyan rigarsa, marcus ya juyo da sauri suka
hada ido, tabbas bakone jallo ya fada yana cije
baki kamin mr marcus ya ankara saidai yaji
saukar wani abu akasan hancinsa jini yayi
tsartuwa hakoransa biyar suka tashi sama cikin
iska, san nan wani radadi ya gauraye ilahirin
bakinsa zuwa kai, jjini yafara sartu agaban
rigarsa. Ko dakika biyar ba'ayiba, Marcus na
shirin yunkurin guduwa yaji wani abu mai kaifi ya
dube asaman kafadarsa, sai da wani zafi ya biyo
baya san nan ya ankara ashe wuka Katon dake
kansa ya lumamai akafada, yafadi kasa nan take
yana kwarma ihu, daga nan katon mai suna Jallo
ya saba marcus awuya ya nufi bayan gari dashi
inda yake jiwo hayaniyar mutane, Can abayan
gari ba'asha wuyaba wajen gano wata doguwar
mota fara, an boyeta wakusa da wata gonar
masara, . kuma tabbas yammata ne aciki, amma
an kasa kusantar motar saboda karar harbin
bindiga da akeji yana tasowa daga motar, barayin
har bindiga garesu inji wani matashi, andan dade
ana cirko cirko abayan garin kamin daga baya
akasamu wasu matasa mutum Uku sukayi kukan
kura suka afkama barayin, ana tsammanin
samarin sunada maganin bindiga, sai bayan sun
rufar ma barayin ne, san nan sauran tawagar
matasan dake wajen suka mara musu baya, nan
take sukayima barayin kofar rago, aka ratattake
su da dukan itace, ana tsammanin wasu daga
cikima sun sheka bar zahu. Can bayan wani dan
lokaci ana tunanin abinyi, sai aka hango wani
Sangwamemen kato mai suna Jallo ya dauko
wani mutum akafada ya nufo inda mutanen suke,
saida ya kariko wajen san nan ya shaida musu
cewa acan bayan gidan Tanko mai gatari ya ga
matashin rabe jikin wata kuka yana lambo, shine
ya samu nasarar tarwatse shi da duka, ya jefar
da marcus akasa ya fada jikin sauran
yan'uwansa. An samu an firfito da yammatan
daga cikin motar ana cikin juyayi da tuajjabin
abinda ya faru, sai ga motocin yansa guda uku
daga hayin Tandu sun iso wajen da abin ke
faruwa, nan take matasan da sukayi aika aikar,
suka sulale suka bar wajen don tunanin kada
yansandar su zafga kame akan mai uwa da wabi,
daga nan suka kwashe marcus da sauran
yaransa suka nufi asibiti dasu dake can birni,
bayan tafiyar yan sandan ne, me unguwa tajo da
sauran dattijan kauyen suka tattara yammatan
nan kaf suka nufi Tandu fadar mai girma hakimi
Alhaji Baballe, don bin ba'asi da yunkurin maida
yammatan ga iyayensu.
adsense 2 here