Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

BASO A RAINA

adsense here BASO A RAINA[15/09 12:22 pm] Beelybadaru😍: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *BA SO A RAINA*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Bismillahir-rahmar-rahim. _Wannan littafi nawa qirqirarren labari ne amma akwai abubuwan da suka faru a gaske, duk Wanda yayi dai-dai da labarinshi ya gafarceni·Kuma na sadaukar dashi ga dukkan masoyana_ 🌹1⃣🌹 Gudu take tsalawa na fitar hankali hannunta dauke da wani yaro da baxai wuce 3yrs ba. Tana yi tana waigawa duk ta jigata kayan jikinta duk sun jiqe sakamakon ruwan da ake shatatawa. Kai da ka ganta kasan tana cikin tashin hankali, qara waigawa tayi ganin mutanen sun daina binta hakan yasa ta samu wani lungu taga data er rumfa, d sauri ta qarasa gurin rumfar ta shiga tare da sauke yaron dake kafadarta sai nishi take sama2. Gani tayi yaron ko motsi baya yi sakamakon ruwan da ya sha. A firgice ta soma jijjigashi tana wani irin kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro. Da qarfi take furta "Kar ka tafi ka barni FAHEEM Kai kadai ka rage min a duniyar nan, ya qarar Mani da dangina suka, plx ka tashi don Allah kar ka tafi ka barni cikin wannan rayuwar" Kuka sosai take tare da rungume shi tsam a jikinta, ta waiga ko ina bata ga wasu mutane ba, kiran sunan Faheem kawai take tana kuka tana jijjagashi a hankali yaja wani dogon numfashi tare da bude idanuwansa. Farin cikin ne ya cika xuciyarta ganin ya farfado, a hankali tace "Faheem ka farfado? Kar ka koma plx INA buqatar ka a gareni kai kadai ka rage min" Bai San ma me take fada ba saboda qarancin shekarunsa. A hankali ya soma magana cikin gwarancinsa tace "Adda yunwa Adda abinci anci" Hankalinta ya tashi don ko ruwa bata taho dashi ba balle abinci, ta waiga ko INA bata ga kowa ba, can ta hango wani mutum ya fito daga cikin gidansa da rigar buhu a jikinsa don ruwan ya soma daukewa. Ai da saurinta ta miqe ta rufe Faheem da hijabin dake jikinta ta qarasa wajen mutumin. Sallama tayi masa ya waigo ya kalleta da mamaki ya amsa tare da cewa "Baiwar Allah me kike yi cikin ruwan nan haka? Baki tafiya gida?" Cikin rawar sanyi tace "Baba taimaka mana xakayi kamar yanda Allah ya taimakeka" Cike da mamaki mutumin tace "Baiwar Allah wane iron taimako xanyi maku?" Cikin sauri tace "Baba Mu baki ne bamu San kowa a nan ba, motarmu ce tayi hatsari iyayenmu duk sun rasu mune kuka tsira shi ne muka shigo gari Neman taimako"sarai karya ce tayi masa don tasan in yaji dalilin barinta gida baxai taimaka mata ba. Cikin fuskar tausayi tace " Ayyah Allah ya jiqans da gafara, ynx me kikeso nayi maki?" Tayi saurin cewa "Makwanci muke buqata Baba ka taimaka mana kamin xuwa wani Dan lokaci". Da sauri ya kalleta tace " Makwanci kuma en nan? Ai xamanin nan ba'a yards da mutane" Tayi saurin durqushewa qasa tana kuka tace "Baba kawa Allah da Annabi ka taimaka mana, wllh bani da nufin cutar da mutum, ko Dan wannan yaron k taimaka mana". Mutumin yayi saurin cewa " Kiyi hkr yrny amma baxan iya shigar dake cikin gidana ba, don HK kinga tafiyata. Har ya kusan shiga gidan, tace "Shikenan Baba, amma ka taimaka min da abinci ko ya yake na baiwa yaron nan". Gyada mata kai kawai yayi ya shiga gidan. Yr barandar gidan ta shiga ta xauna. Kukan yunwa Faheem ke yi ita kuma na bashi hkr. Bayan minti biyar mutumin y fito da kwano a hannunsa ya miqa mata, da sauri ta amsa tana godiya nan ta shiga ba Faheem abincin, da sauri yake amsar shinkafa da man saboda ynwr da yake ji. Bata damu data ci ba duk da yunwan da takeji itama, amma tafi son Faheem yaci ya qoshi. Mutumin na tsaye yana kallonsu cike da tausayawa, lallai wadannan suna buqatar taimako ya kamata ya taimaka musu. Written by Beelybadaru😍 [15/09 12:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By Beelybadaru😍 🌹2⃣🌹 Sai da ta tabbatar Faheem ya qoshi sannan ta cinye Dan sauran da baifi loma biyu ba, ta miqa ma mutumin kwanonsa tare da cewa "Baba gashi mun gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi" Yaji dadin addu'arta sosai don bashi da Dan da xai riqa masa irin wadannan addu'o'in. Ya amsa kwanon ya shiga dashi ciki, ba a fi minti biyu ba sai gashi ya dawo ya durqusa a gefenta yace "Yarinya yanxu a ina xaku kwana?" Ta dago da kanta ta kalleshi sannan tace "Baba wannan barandar ma ta ishemu mungode" Da sauri yace "Inah ai baxai yuwu Ku kwana a wajen nan, da hatsari" Murmushi kawai tayi tace "To Baba ya xanyi? Ina xamu kwana in bamu kwana a nanba?" Ya miqo yace "Biyoni ciki kinji yarinya, Na tabbata baki da niyyar cutarda mutane, taimako kike nema kuma insha Allah xan taimaka maku" Wani farin ciki ne ya lullubeta nan ta shiga xabga mata godiya, yace ba damuwa ta shigo kawai. Miqewa tayi ta gyara hijabinta sannan ta kama hannun Faheem suka bisa cikin gidan. Tun a xaure yake ta qwala kira "Laure! Laure!! Laure!!!" Wata mata ta fito daga cikin wani daki tana cewa "Lafiya malam irin wannan kira sai kace tashin......... Maganar ta qatse sakamakon mutane da ta gani bayan malam. Sakin baki tayi tana kallonsu cike da mamaki sannan ta maida. Kallonta ga malam tace " Wadannan kuma fa? Me suke yi a cikin gidan nan?" Malam yace "Haba Laure ai kya basu matsugunni tukunna sai Na miki bayani" Cikin sauri tace "Ina a gidan nawa xan basu matsugunni bayan bansan ko suwaye su ba?" Malam ya bata rai ya kalli Yarinyar da jikinta ke kyarma ta matse Faheem a jikinta yace "Ki kwantar da hankalinki kinji, nan gidana ne, duk Wanda kika gani a cikin sa qarqashina take jeki xauna can" Gyada kai kawai tayi ta wuce wajen da take nuna mata don xama, wani tsalle matar tayi tasha gabanta tana cewa "Alqur'anin Allah bata xama cikin gidan nan har sai kamin bayanin wacece ita" Tuni hawaye sun wanke fuskarta, malam yace "Laure baki isa ki hanata xama cikin gidan nan ba, xan fada maki ko suwaye su" Nan ya fada mata iya abinda yarinyar ta fada masa" Laure tace "To miyasa duk fadin anguwarnan ta rasa inda xata xo Neman taimako sai nan?" Durqushewa Yarinyar tayi da gwaiwoyinta tana wani matsanancin kuka tace "Na roqeki mama ki taimaka mana ki barmu Mu xauna a gidan ki Na dan wani lokaci, koda ace bak8 da 'ya mace ke macece kuma kinsan ciwon 'ya mace, ki tausaya min ba don niba don darajar mahaliccinki." Sasai jikin Laure yayi sanyi da jin kalaman Yarinyar, ta kalleta tare da dagota daga durquson da tayi tace "Yarinya minene sunanki?" Cikin rawar murya tace "Sunana *BILKISU* amma en gidanmu Na kirana da *Naana*" Murmushi Laure tayi tace "To mudai Nana xamu kiraki don wancen Naana yake? Xai yi mana wuyar fada, ki kwantar da hankalinki xaki xauna a gidan nan kinji?" Durqushewa ta kuma yi tana godiya Laure ta tada ta ta maidata kan kujera sannan ta kawo masu abinci, ita kadai ta Dan tsakuri abincin duk tunani ya addabi xuciyarta. _Bayan kwana biyu_ Nana ta samu kwanciyar hnkl a gidan ita da Faheem duk da kullum sai tasha kuka idan ta tuna rayuwarta ta baya, kuma tana taimaka ma Mama Laure da aiki. Yau ma kamar kullum tana xaune a qofar dakin da aka basu tana tunani Mama ta fito daga bayi tace "Am Nana don Allah in baxaki damu ba xan aikeki can bakin hny ki siyomin kayan miya da maggi" Nana ta miqe ta amsa kudin tace "To mama" Mayafinta ta dauko ya maqaleta xaiyi kuka shi sai ya bits, ba musu ta kama hannunsa suka tafi. A bakin titi ta tsaya xaau tsallaka titi, wata wata mota ta wucesu sai kuma gata ta dawo ta faka gabansu. Gabanta ya fadi ta dauki Faheem a hannunta tana jiran taga Wanda xai fito. Bude marfin motae akayi mutumin ciki ya fito. Duka qirjinta ya Dada, ta fiddo idanuwa waje cike da tsoro tana da baya, numfashinta har wani sarqewa yake........................ Written by Beelybadaru😍 [15/09 12:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹 BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By Beelybadaru😍 🌹3⃣🌹 Kyakkyawane shi fari tas dashi kamar balarabe, fuskarshi akwai saje sai dai baida idanu manya can. A hankali yake takawa xuwa inda take ita kuma tana ja da baya idanunta Na xubar da qwallah. Yayi wata irin dariya tare dacewa "Dama Na fadamiki duk inda kika shiga sai Na nemoki, baki isa ki guje ma aurena ba Naana, don haka kixo muje kawai a daura mana aure" Girgixa kai ta shiga yi tana hawaye muryarta Na shaking tace "Baxan bika ba *SADEEQ*baxan bika ba, kai mugu ne Axxalumi makashi baxan taba aurenka ba" Tana gama fadar haka ta juya da shirin guduwa, karaf ya cafkota ya shaqota da wuyan hijabinta ya soma janta tana turjewa, tuni Faheem ya fara kuka. Har sun kusan shiga mota ta samu ta Dan duqe aikuwa sai ganin dutse tayi kusa da qafarta da sauri ta dauko dutsen bata dubi inda xata buga mashi ba kawai ta qwala mishi sai akan goshinshi nan take jini ya a fita. Qara ya saki mai qarfi ba shiri ya saketa, tana sakinta kuwa tace qafa me naci ban baki ba tayi wata hanya da gudu wadda ba hanyar gidan da ta fito ba sabod atsabar rudewar da tayi. Shi kuwa Sadeeq kanshi ya dunga xubar da jini ba shiri ya shiga mota yaja a 360 ya bar gurin ya wuce asibiti, xuciyarshi Na mashi xafi, dole ne ma ya auri wannan Yarinyar kodan ya axabtar da ita akan abinda tayi masa balle ma kuma tana sonta. Ita kuwa Naana gudu kawai take ba tare da tasan inda take dosa, ga gajiyan gudu ga gajiyar daukar Faheem da yake numfashi sama2. Bata Ankara ba sai ganinta tayi cikin daji. Tsayawa tayi cak tana waige2 don ita bata San ma ta shigo dajin ba saboda tsabar firgici. Da har xata koma cikin gari sai kuma ta tuna in ta koma Sadeeq xai iya ganinta ya aiwatar da mummunan qudurinsa a kanta ita ta gwammaci su qarashi rayuwarsu cikin dajin nan da ta auri Sadeeq maqiyinta kuma makashin iyayenta da Dan uwanta Rabin jikinta. Wasu xafafan hawaye suka qara xubo mata, ita kam taga rayuwa, daga kanta tayi sama tare da cewa "Ya Allah kana kallon baiwarka, ka taimakesu ka fitar dasu daga cikin qangin rayuwar da suke ciki ka bata ikon cinye jarabawar da ka bata ka kawo mata dauki ya Allah" Durqushewa tayi a gurin tana wani irin kuka mai ban tausayi a hankali take furta "Sadeeq ka cuceni me Na maka a rayuwa da xaka rabani da farin cikina meyasa xaka tilasta ni akan lallai sai Na soka bayan ka Riga ka cika xuciya ta da tsantsan qiyayyarka da sauran maxa ma baki daya *BA SO A RAINA* Ko kadan a ynx Na wani da namiji sai mutane uku da baxan tana mantawa dasu ba a rayuwata *ABBA UMMA da YAH AUWAL*sune kadai cikin raina sai kuwa Faheem amma ka raba ni dasu rabo Na har abada sai guda daya ka barmin, me yasa saini? Allah ka bimun haqqina" Kuka sosai take kamar ranta xai fita, kanta sai sarawa yake. A hankali taji hannun Faheem a fuskarta yana share mata hawaye cikin maganarsa da bata fitowa sosai yace "Adda ki daina kuka nima kin anani kuka, kixo muje wajen Abee" Wani kukan yaso ya kucce mata ta rungume Faheem tana kukan tace "Kayi shiru kaji Faheem kayi barci ka huta" Shirun yayi ta samu wata er bishiya gurin da fili ssosai ga wani Dan qaramin kogi da ruwa a ciki, hakan yasa ta shinfida masu kallabinta ta xauna sannan ta rungume Faheem tsam a jikinta, tsoro duk ya baibayeta ganin magrib ta kusa gurin ya soma duhu. Faheem kuwa tuni baccin wahala ya daukesa, ita kam Naana baxata iya yin barcin ba. Can ta hango wasu mutane suna nufo inda suke da alamu mafarauta ne don taga makamai a hannunsu. Tuni tsoro ya qara baibayeta ta miqe jikinta sai kyarma yake. Tun daga nesa taji daya daga cikin su n cewa "Baaba kmar fa mace nake gani a can" Wanda aka kira da Baaba yace "Macece kuwa gsky t hadu Allah yasa mutum ce da munyi kaya a nan" Dariyar qauraye yayi yace "Muje dai Mu gani" Jin hakan yasa ta tattara kallabinta da sket dinta ta xuba da gudu cikin dajin ba tare da tasan inda ta dosa ba. Ganim hkaan yasa suma suka rufa mata baya.......... _Written by Beelybadaru😍_ [15/09 7:44 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By Beelybadaru😍 🌹4⃣🌹 Gudu tayi ba dan kadan ba ganin tayi musu nisa yasa ta boye bayan wani dutse, bada jimawa ba tajisu sun xo gurin sunyi iya dubansu basu gansu ba kawai sai suka koma ba don sun so ba. jin shirun da yawa yasa ta fito tana dauke da Faheem ta soma gudu tana waige batare da tasan inda take dosa ba. ji tayi qafarta ta bugi wani dutse nan take suka tafi qasa suka fadi, ji kake qum kanta ya bugu da wani dutse, Wani irin xafi taji akan nata, ta juya gefenta taga Faheem kwance shame2 . cikin qarfin hali ta miqe tana dafe da kai don xuwa wajensa, amma kafin ta isa gurin nasa jiri ya kwasheta ta xube a wajen itama sumamma. A hankali take bude idanuwanta ta saukesu akan fuskar wata mata da bata santa ba, dafe kanta tayi jin yana sara mata, ta kalli matar cike da mamaki sannan ta kalli dakin da take kwance, tuni abunda ya faru ya soma dawo mata da sauri ta miqe tana cewa "Don Allah kuyi hakuri karku cutar....... sai kuma tayi shiru can tace "Faheem.... Ina Faheem yake"? matar tayi saurin riqeta tare da cewa "Yarinya kwantar da hankalinki ba cutar dake xamuyi ba, kuma ga wanda kike nema can yana barci" Da sauri takai dubanta gurin da matar ke nuna mata taga Faheem kwance yana barci ta sauke ajiyar xuciya kafin tayi magana wani dattijon mutum ya shigo dakin da sallamarshi, suka amsa mashi, yaxo ya xauna tare da cewa"Asabe har ta tashi kenan?" Asabe tace "Eh ta tashi malam". Dattijon yace "Masha Allah, sannu Yarinya" Da "Yawwa" ta amsa shi tare da cewa "A ina muke nan?" Mutumin yace "Yarinya na dawo daga farauta ne na ganku yashe kan hanya, shi ne na kira matata ta taimaka aka kawoku gidan nan" Naana tayi shiru bata ce komai ba. Matar tace "Miye sunanki kuma ya akayi kuka xo gurin nan?". Naana ta numfasa sannan tace "Sunana Bilkisu amma anfi kirana da Naana, mu en katsina ne xamuje unguwane mukayi hatsari iyayenmu duk sun rasu sai ni da qanina kadai muka tsira shine nayi ta gudu har mukaxo nan" Ta qarashe maganar tana hawaye. Cike da tausayi suka ce "Ayya Allah ya jiqansu da gafara". Naana ta amsa da "ameen". Matar tace "Yata ki kwantar da hankalinki, insha Allah xamu taimakeku har xuwa lokacin da xaku koma garinku". Naana tace "Nagode Mama Allah ya saka maku da mafificin alkhairi". Sunji dadin addu'arta suka amsa da "Ameen". Dattijon ya miqe yace "Toh ni xan dan fita sai na dawo a basu abinci, Allah ya qaro sauqi". suka amsa da "Ameen". Naana tace "Nagode Baba a dawo lpy". Nan ya fice daga gidan, Mama ta miqe ta fita don kawo masu abinci, Naana ta miqe ta matsa kusa da Faheem dake barci har lokacin ta dago shi ta rungume a jikinta hawaye na kwaranya a idanunta. Shikenan su haka xasu qaraci rayuwarsu. Mama ce ta shigo dakin dauke da kwanon abinci ta ajiye gabansu Naana tare da cewa"Bilkisu ga abinci nan sai kici". Naana tayi murmushi tace "Nagode Mama amma baxan iya ci ba har sai Faheem ya tashi". Mama ta jinjina kai, kafin tayi magana Faheem ya farka, Farin ciki ya lullube Naana ta dagoshi tana masa murmushi yana ganinta ya qara kwantawa jikinta. Ta nemi Mama ta basu ruwa su dauraye baki, suka fita wajen, gidane dan madaidaici mai kyau amma na qasa ne sai dai yaji shara. Nan suka dauraye bakinsu sannan, suka koma cikin daki, ta bude kwanon abincin taga Danwake, itakam ko a gida bata cin danwake amma ba yadda ta iya dole taci don yunwa take ji, Sai da Faheem yaci ya qoshi sannan taci sauran da qyar. Mama tace dasu ya kamata suyi wanka, ba musu ta miqe Mama ta nuna mata bayi ta shiga ta fara yima Faheem sannan itama ta shiga tayi ta koma dakin, har xata maida kayanta Mama tace ga wasunan ta sanya. Godiya tayi mata sannn ta amsa ta sanya rigar tayi mat yawa amma duk da haka tayi kyau, sai kuma wajen daurin xani tayi ta fama ta kasa don bata iy daurin xani ba ko a gida ba a yi mata xani sai dai sket. Mama na ganin haka tayi dariya tace "Baki iya daurawa bane?". Naana ta gyada mata kai. mama tace "Kawo na nuna miki. Nan ta daura mata xanin yayi lpylau tayi kyau sosai ta dauki hijab dinta ta sanya. Mama tace "Ya kamata a wanke kaysn da kuka cire,".Naana tace "To Mama ina sabulun sai na wanke" Mama ta dauko mata sabulu ta fita wajen Mama ta bata bokiti ta xuba ruwa ta fara wankin tana a xaune. Motsi taji ana shigowa, bata dago ba don tayi tunanin Mama ce ko kuma baba ne ya dawo. Ji tayi kamar hucin mutum a kanta hakan yasa tayi saurin dago kanta don ganin ko waye. Tsaye yake a kanta ya wani rungume hannuwa a qirjinsa yana qare mata kallo sama da qasa. wani matashin saurayi ta gani Shi ba fari bane kuma ba baqi bane tsaka tsakiya ne, Yana da kyau ba laifi. Da sauri ta miqe tsaye tana kallonsa. Wani shu'umin murmushi ya sakar mata tare da matsawa kusa da ita, itama tayi saurin ja da baya cike da tsoro.......... Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [16/09 7:55 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 By Beelybadaru😍 🌹5⃣🌹 Matsowar ya kuma yi itama t kuma ja da baya, abinka da mai saurin kuka tuni hawaye suka jiqa fuskarta. Mama ce ta fito daga daki tana ganinshi tace "A a Kamalu har ka dawo kenan?" Kallon Mama yayi yace "Eh Mama har na dawo". Tace "To sannunka da dawowa". Bai amsata ba ya maida kallonshi ga Naana yace "Baquwar baturiya muka samu ne mama? na ga ban santa ba". Mama tayi murmushi tace "Ba baturiya bace" Nan ta fada masa duk yadda akayi, murmushi ya saki yace "Gaskiya ta hadu da yawa irin wannan kyau haka mama, wannan in bata yi magana ba sai kace ba bahausa bace". Yana magnar yana kallon Naana. Itakam tunda ta sadda kanta qasa bata dago dashi ba, shi kuwa Kamalu so yake yaji muryarta don yasan yanda take da kyau din nan muryarta xatayi dadin sauraro. Ganin bata da niyyar yin mgn yasa yace "Yan mata ni sunana Kamal wannan ce Mamana, ko xan iya sanin sunanki?" Kanta na qasa cikin muryarta mai sanyi tace "Sunana Bilkisu amma ana kirana da Naana". "Wow nice name" abinda y fada kenan yana gyada kai. Kafin tayi magana Faheem ya fita ya qarasa wajen Naana yana cewa "Adda Wadan Abee ani(yana nufin wajen Abee xashi)". Naana tayi saurin duqawa kusa da Faheem hawaye na xuba a idanuwanta ta dafa kafadarsa tace "Faheem kayi hkr xan kaika wajen Abee kaji?" Gyada mata kai yayi yana share mata hawayen fuskarta. _2days later_ Kwanan Naana biyu gidan tana jin dadin xama sosai, sam bata bari Mama tayi aiki duk ita keyin aikin, Faheem an siya mashi gwanjo masu dan kyau ba laifi, itama Naana haka, Ta dan sami kwanciyar hankali amma kullum sai tayi kuka idan ta tuna rayuwarta ta da, Sadeeq ya rabata da farin cikinta baxata taba yafe masa ba har abada. Kamal ne kawai ke bata matsala, ya takura mata kullum sai yazo ya dameta da xuba, ita bama wannan ke damunta ba, yanda kullum yake qoqarin taba jikinta ita kuma ta tsani hakan. Duk abinda sukeso Baba da mama na iya kacin bakin qoqarinsu don ganin sun sama masu shi. Itakam Naana a kullum addu'a take musu na dawainiyar da suke masu. Haka dai suke rayuwarsu cikin kwanciyar hankali duk da Naana na cikin damuwa amma hakan baisa ta danyi qiba ba. Xaune take a tsakar gida Faheem na daki yana barci, Mama ta fita xuwa gidan duna, baba dama ba xama yake sosai ba. Daga ita dai sai Faheem, ta buga uban tagumi sai faman tunani take. Ji tayi an dafota ta baya, a firgice ta dago da kanta don ganin ko waye. Kamal ta gani tsaye a kanta, ba shiri ta miqe tana ja da baya, Matsowa yayi dab da ita tare da jawo hannunta da qarfinsa yana cewa "Wow ashe haka fatar ki take da laushi haka? shiyasa baki bari na taba ki". Da sauri ta fixge hannunta tana cewa "Miye haka malam? miye xaka wani riqe min hannu?". Dariya yayi tare da cewa "Haba Naana inace daga birni kike? ai ya kamata ace kin waye, ki bani dama mana ko sau daya ne" ya qarashe maganar yana qoqarin janye hijabin dake jikinta. Bata san lokacin da ta wankeshi da wani wawan mari ba, sai kuma wani tsoro y kamata gashi gidan ba kowa sai Faheem. Ya kalleta da mamaki yana dafe da kunci yace "Ni kika mara? rabon da a mareni tun ina qarami, tunda kika mareni sai na aikata abinda nayj niyyar aikatawa". Yana kaiwa nan ya fige hijabin dake jikinta, A firgice ta shige dakin daya ke a kusa suke ta maida qofar ta rufe xuciyarta na dukan tara2. Tana jinshi yana buga qofar kamar xai ballata, duk addu'ar da taxo mata a baki ita take yi wata ma bata kaiwa qarshe take kamo wata. Ji tayi ya daina buga qofar can taji qarar rufe qofa alamun ya fita, hakan yasa tayi saurin qarasawa wajen Faheem daya tashi daga barcin da yake sakamakon buga qofar da Kamal yayi tayi. Hawaye sai xuba suke a fuskarta. Me yasa maxa duk halinsu daya, meyasa basu da buri a rayuwarsu sai ganin sun cutar da mata? Meyasa suke qoqarin qara hura wutar qiyayyarsu a cikin xuciyarta? bata tunanin xata kuma soyayya a rayuwarta don kuwa ko kadan *BA SO A RANTA* Sadeeq ya rabata da masoyanta ynx kuma Kamal so yake ya rabata da mutuncinta da darajarta, lallai ya xame mata dole ta bar gidan nan don kuwa xamansu a gidan babbar matsala ce. Miqewa tayi da sauri ta qara hada kayansu duk da dama a cikin jaka suke, ta dauko wani hijabin ta sanya, ta miqe ta riqe hannun Faheem tare da daukar kayan a dayan hannun, har takai bakin qofa taji an bude qofar gidan alamun an shigo. Gabanta ya fadi da sauri ta koma baya jikin bango jikinta har bari yake, ji tayi ana buga qofar bugun xuciyarta ya qaru. Muryar Mama taji tana cewa "Bilkisu ki bude qofar mana". Ajiyar xuciya ta sauke jin muryar Mama hakan yasa ta miqe ta maida jakar a inda take ta share hawayenta don bata so Mama ta fahimci wani abu, taje ta bude qofar tana murxa ido don mama tayi xaton barci take. Mama ta kalleta tace "Y akayi kika rufe qofa Bilkisu?". Naana tace "Mama barci naji ganin ba kowa a gidan yasa na rufe qofa don ina jin tsoro". Mama tayi murmushi tace"To Allah ya kyauta". Murmushi Naana tayi suka koma dakin a tare. Da daddare yau Mama da wuri tayi barci Baba kam bai dawo ba shi da Kamal. Naana na xaune tana kallon Faheem dake barci akan cinyarta. ta waiga ta kalli agogon dakin taga qarfe 8:30pm. Miqewa tayi a hankali ta dauko jakarsu ta kaya data hada daxu, ta tuna da kudin da take tarawa idan Baba ya bata da nufin in tana buqatar wani abu ta siya idan mai talla suka shigo don ba fita take ba. ta dauko su ta daure a gefen xaninta, sannan ta dauki Faheem a hankali t yadda baxai tashi ba ta dauki jakar t fito daga dakin tana sanda. Dakin Mama ta kalla sannan ta fita daga gidan a hankali. Allah ya sota ba mutane a wajen sosai, Nan ta tsaya tana ta kallon garin don bata san ya yake ba, tafiya kawai take ba tare da tasan inda xata ba. wani mutum ta gani xaune a qofar gidansa ta qarasa wajensa tare da gaisheshi ya amsa mata sannan tace "Malam don Allah tambaya nake". Mutumin yace "Allah yasa na sani". Naana tace "Don Allah ka nuna min tashar mota". Ba musu mutumin ya nuna msta da yake ba nisa daga inda yake, koda taje taga gurin ba motoci sosai sai wata qwara daya ta qarasa wajen mai motar ta gaisheshi tare da cewa "Malam motar nan wane gari ta nufa?". Mutumin yace "Katsina ne ta kusa cika in can xaki taho mu tafi". Jin an anbaci katsina yasa tayi saurin girgixa mashi kai tace "A a ba can xani ba motar Kaduna nake nema ko kano". Mutumin yace " Ai kuwa baki samunta yanxu sai dai ko xuwa gobe da safe". Godiya tayi mashi sannan ta koma gefe guda ta xauna qarqashin wata bishiya. Ganin duk an watse gurin ba kowa tsoro ya mamayeta ta miqe tana cigaba da tafiya ko xata samun gurin fakewa kafin safiya. Wani gida ta gani a bude ta shiga a tsorace ganin wata qofar tayi a rufe da kwado hkn y tabbatar mata da masu gidan basu nan. Gefe guda ta samu t rakube tare da kwantar da Faheem a jikinta ya cigaba da barcinsa, ita kuma barcin ya gagari idanuwanta. Haka ta xauna har asuba. Ta miqe ta fita xuwa waje. ta dinga neman ruwan da xatayi alwalla da qyar ta samu mai ruwan ta siya na goma taje tayi alwalla tayi sallah sannan ta nufi tasha don bata son gari ya washe bata tafi ba. Koda taje har mota daya ta kusan cika ta kano, hakan yasa tayi saurin shiga, sai da suka fara tafiya akace mata kudin mota dari bakwai ne, Nan ta duba kudinta taga dari biyar da hamsin ne, kawai ta yanke shawarar in sun sauka ta nemi ragi don baxata xauna garin ba. Haka motarsu ta lula sai Kano. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [22/09 5:05 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹6⃣🌹 Bangaren su Mama kuwa washe gari tana tashi ta duba dakin Naana abin mamaki sai taga wayam ba alamun Naana ba alamun Faheem, ta qara cika da mamaki ganin babu jakar kayansu. Hankalinta ya tashi tayi saurin xuwa dakin Baba ta fada mass ya fito da sauri suna ta mamakin INA Naana taje haka da safiyan nan?. Kamal ne ya fito daga dakinsa, fuskar nan tasa a tamke don rashin samun biyan buqatarsa. Yaga su Mama cirko2 a waje cike da tashin hankali. Ya qarasa wajen ya gaishesu sannan ya tambayesu lafiya?. Mama ta Dan share hawayenta tace "Ina fa lafiya? Naana ta bar gidan nan kuma bamu San inda ta nufa ba". Yayi saurin kallonta wato Naana guduwa tayi kenan? Ya dafe kansa cikin xuciyarshi yace " Dana sani na balle qofar tun jiya nayi abunda naso, ynx gashi ta gudu ba tare da na samu abinda nake so ba". Tsaki yayi ya fice daga gidan yana dube dube wai ko xai ganta(Ni kuwa nace Kamal sai dai ka nemi wata amma ba Naana ba don a ynx ta kusa kano, bari ma nabi bayanta. ) *NAANA* Sai wajen 9:15am suka isa garin kano, a tasha aka saukesu, ta fiddo kudin ta miqa ma kwandastan tare da tsugunnawa had qasa tace "Malam ka dubi girman Allah ka taimaka mana ka amshi kudin nan wallahi bani da ciko su kadai gareni ko nacin abinci ma bamu dasu". Tausayin tane ya kama shi ganin har ta fara xubar da qwalla ya amshi kudin tare da fidda Naira dari ya bata yace " Bakomai amshi wannan kuci abinci". Hannunta na rawa ta amsa don yunwa take ji sosai rabonta da abinci tun jiya da rana. Godiya ta shiga xunduma mashi da addu'o'i, yaji dadi sosai sannan ta tambayeshi gurin da ake sayar da abinci nan kusa, ba musu ya nuna mata tayi masa godiya sannan ta miqe ta riqe hannun Faheem suka nufi wajen mai abincin. Shinkafa da mai da yaji ce taga tana saidawa abinda take so kenan bayan ta gaishe da matar tace ta xuba mata na hamsin don Naana bata fiye cin abinci da yawa ba. gefe suka koma ta soma baiwa Faheem sannan itama taci ta kora da ruwan da ta siya, nan take tajita dam ta koshi sosai. Gefe guda ta koma ta xauna ta xaunar da Faheem ma. Har wajejan Axahar Naana suna nan xaune don bata da inda xata. Jin ana kiran sallah yasa ta miqe taje wajen matar tace ta taimaka mata da ruwa xata yi alwallah ba musu ta miqo mata buta tayi godiya sannan tayi alwallar ta bata butar ta koma can gurin Faheem ta shimfida kallabinta tayi sallarta, bayan ta idar ta gyara xamanta tana axkar. Matar kuwa ta cika da mamaki ganin Naana Har ynx bata da niyyar tafiya, kasa hakuri tayi ta kira Naana da "Baiwar Allah". Naana ta miqe jiki a sanyaye ta riqe hannun Faheem sannan ta nufi wajen matar ta tsugunna. Matar tace " Ke kuwa baiwar Allah ya akayi Har ynx baki tafi gida ba ko kin bata ne kin mance hanyar gidan?". Girgixa kai Naan tayi tare da cewa "A a ni baquwa ce bansan kowa ba a garin nan hasalima yau ne xuwa na na farko garin nan bansan inda xani ba" Matar ta cika da mamaki tace "Bakisan kowa ba kuma kikaxo? to mi ya kawoki?". Naana tayi narai 2 da ido tana tunanin qaryar da xatayi ma matar don ita bataso ta bada labarin rayuwarta ta baya. Can Tace "Daga qauye naxo Neman aiki, mahaifina ne bashi da lafiya ana Neman kudin da xa a siya mashi magani, kuma gashi bamu da kudin shi ne ummana tace naxo nan birni na nemi aiki amma na gida banda na waje na samu kudin da xamu siya wa mahifina magani" Ta qarashe maganar tana hawaye kamar gsk. Matar ta girgixa kai cike da tausayi ta dafa kafadar Naana tace "Share hawayenki kinji kinxo cikin sa'a kin ganni nan ina sayar da abinci sannan ina samawa masu kudin garin nan masu aiki don haka karki damu insha Allah xan sama miki aiki". Naana tayi qwal qwal da ido ita ynx ya xatayi? ta Riga ta kama kanta dolenta tayi aiki kenan. Ta share wasu xafafan hawaye da suka xuba mata a xuciyarta qara tsanar Sadeeq take duk shi ne silar shigarta wannan halin kuma sai Allah ya saka mata. Ta dago da kanta ta kalli matar tare da yin murmushin yaqe tace " Shikenan nagode sosai Allah ya saka maki da Alkhairi." Matar ta amsa da "Ameen". Sannan tace " Toh yanxu ki jirani xuwa bayan la'asar sai muje gidana in yaso gobe in Allah ya kaimu sai na fita nema miki aikin". Naana tace "To shikenan nagode". Matar ta kalli Faheem tace " Wannan kuma fa? naga kuna kama sosai". Naana tayi murmushi tace "Qanina ne shi don bana son na riqa xaman kadaici shiyasa na taho dashi". Matar tayi murmushi tace " Ai yayi kyau yanxu bari na wanke wadancan kwanikan kafin lokacin tashin yayi". Naana tayi saurin cewa "Kawo na wanke miki mana". Itama tace " A a ki barshi kawai na wanke". Miqewa tayi ta nufi wajen kwanukan tana cewa "A a ni dai xanyi kawai." Ba yadda ta iya dole ta barta tayi wanke wanken tana yaba halin Naana a xuciyarta. Sai bayan La'asar din muka kama hanyar xuwa gidan matar, ita dai Naana na biye da ita a baya suka hau Napep. Tafiya kadan sukayi suka sauka a wani Dan madaidaicin gida. Matar ta fara fita sannan suma suka sauka ta biya mai napep kudinsa sannan suka nufi cikin gidan. Ba laifi gidan yana da kyau don a shafe yake da sumunti kuma yaji shara. Matar ta bude daki ta shiga sannan ta umarci Naana da suma su shigo, da sallamarta ta shiga dakin ta xauna a tabarmar da matar ta nuna mata. Itama ta xauna tace "Nasan xakiyi mamakin ganina ni kadai, to ba nikadai bace mijina ya rasu shekara biyu kenan sannan kuma ina da da daya namiji. ". Gaban Naana ya yanke ya fadi tana da da namiji? ynx ita ya xatayi don ita tsoronsu take sosai. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [23/09 7:18 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹7⃣🌹 Kafin tayi magana sai suka ji sallama, Matar ce ta amsa. Wani madaidaicin yaro ne da baxai wuce shekara 10 ba ya shigo dakin yana cewa "Inna har kin dawo kenan". Matar da aka kira da Inna ta amsa da cewa " Eh na dawo Ameenu ya makarantar?". Kafin ya bat amsa yaga Naana da Faheem xaune a dakin ya kalli Inna yace "Inna wadannan fa daga ina?". Inna tayi murmushi tace " Sunanta Naana baquwa ce aiki xan sama mata shi ne na taho da ita nan kafin gobe in Allah ya kaimu na sama mata gidan da xatayi aikin." Gyada kai yayi alamar gamsuwa sannan ya kalli Naana yace "Adda Naana sannunki da xuwa". Kallonshi Naana tayi cike da mamaki jin ya kirata da Adda, ta amsa mashi da " Yawwa Ameenu." Sannan ta kalli Inna tace "Inna wannan ne dan naki?". Inna tayi murmushi tace " qwarai kuwa shi ne, sunansa Ameenu shekararsa 11". Naana ta gyada kai cike da gamsuwa sannan suka sake gaisawa da Ameenu, da alamh yaron yana da hankali, nan Inna ta xubo mishi abinci yace da Faheem ya taho suci, ya girgixa mishi kai alamun ya qoshi, bayan ya gama cin abincin ya fice daga gidan ma. Suna nan xaune suna dan taba hira duk da ba sosai Naana ke firan ba. Wayar Innarce wata Nokia tayi qara tana dubawa tayi murmushi ta daga, bayan sun gaisa Naana taji tana cewa "Hajiya ki kwantar da hankalinki in dai er aiki ce ba matsala akwai wata yarinya da taxo neman aiki gurina........ ah kar ki damu tana da tsabta yarinyar....... to shikenan Allah ya kaimu goben... yawwa nagode nima" Inna tayi murmushi tace "Lallai kinxo a sa'a wata Hajiya ce take neman er aiki da wuri shine ta kirani da yake ina sama mata en aiki, matar wani attajirin mai kudi ce a garin nan, gobe In Allah ya kaimu xamuje gidan sai ki fara aikinki kawai". Gaban Naana ya fadi da gaske dai aikin xatayi? amma dai ta dake tace " Gaskiya nayi farin ciki Inna Allah ya kaimu lafiya". Inna tace "Ameen Ameen". Da dare suna gama sallar Isha'i Inna ta xubo musu abinci tayi godiya sannan suka ci abincin. Faheem ya fara yin barci sannan itama tayi bayan Inna ta koma dakinta. Ranar kam tasha barci mai dadi. Da asuba Inna ta tasheta don tayi sallah. Bayan ta idar ta gyara dakin da suka kwana a ciki sannan ta fito tsakar gida lokacin Inna ta shiga dakinta, tsintsiya ta gani t dauka kawai ta soma sharar gidan. Sai da ta kusan rabi Inna ta fito daga dakinta tana riqe da carbi tace " Ke kuwa Naana tunda duku duku xaki fara shara? ki barta kawai kije ki kwanta Ameenu ya share". Naana tace "A a Inna ki barshi kawai xanyi". Ba yadda Inna batayi ba akan tabar sharar amma ta qiya dole ta qyaleta. Bayan ta gama ta koma daki har lokacin Faheem barci yake, itama ta kwanta gefenshi barci yayi gaba da ita don jiya bata samu tayi barci ba. Tayi barci sosai kamin ta tashi, tana tashi ta kalli agogo taga har 9:30 tayi tayi saurin miqewa. Inna ce ta shigo dakin hannunta dauke da kofi da kuma plate ta ajiye kusa da Naana tana cewa " Har kin tashi kenan? ga kununki da qosai ki tashi kisha ki shirya muje gidan hajiyar". Murmushi tayi sannan ta gaishe da Inna tayi mata godiya, ta duba bata ga Faheem ba da sauri tace "Inna ina Faheem yake?". Inna tace " Yana waje shi da Ameenu suna kalaci tun daxu ya tashi". Murmushi kawai tayi sannan ta miqe ta nufi tsakar gida ta kuskure bakinta, har xata inna ta miqo mata makilin tace ta dauraye bakin dashi tunda bata da brush. Godiya tagi mata ta amsa ta dauraye bakin sannan ta maido mata. Améenu ya gaisheta Faheem ma haka ta amsa da fara'a sannan ta koma dakin don yin kalaci. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [24/09 5:53 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹8⃣🌹 Koda ta gama kalacin (breakfast) ta fito da kwanonin don yin wanke wanke, Inna tace Sam baxata yi wanke 2 ba taje ta shirya kawai. Naana ba yadda batayi ba amma Inna taqi yards tayi wanke2 dole ta hakura ta hada ruwan wanka ta fara yi ma Faheem sannan ita ma ta shiga toilet don yin wankan. Koda ta fito tuni an gama shirya Faheem, itama mai kawai ta murxa da powder kuma tayi kyau sosai. Ta dauko kayanta ta sanya Inna ta kalleta ganin yanda rigar tayi mata yawa tace "Naana wannan Riga ai tayi miki yawa, kawo a ba Ameenu ya kai nan maqotanmu su rage miki". Ba musu ta cire rigar bayan ta sanya hijabinta sannan ta miqama Inna tana godiya. Inna tace " Ita kadaice tayi miki yawa?". Naana ta girgixa kai sannan ta fiddo wasu rigunan guda biyu ta miqama Inna. Inna ta amsa ta fita waje ta baiwa Ameenu yaje ya kai. 10mnts sai gashi ya dawo Har an rage nan ta amsa ta sanya tuni ta fito fes da ita tayi kyau sosai kamar ba ita ba. Inna tace "Yawwa ko kefa, yanxu sanya hijabinki kixo muje ko?". Naana ta sanya hijabinta sannan suka fito ta kama hannun Faheem suka fice ita da Inna suka bar Ameenu shi kadai. Mai napep muka tarba inna tace " Tarauni xaka kaimu gidan Alh Isma'il kwangila. Tuni mai napep ya ja suka tafi. Wani tamfatsetsen gida ne ya ajesu a nan, Naana kuwa waige waige take taga gidan da xasu shiga. Bayan Inna ta biya mai Napep kudinsa sannan ta kalli Naana tace "Muje ko?". Ba musu tabi bayanta tana riqe da hannun Faheem. Ganin sun nufi qofar gidan ya sanya Naana tayi saurin cewa " Inna wannan gidan xamu shiga?". Inna tace "Eh mana". Bin ta kawai take Har suka isa bakin get din, Inna tayi knocking wani Dan dattijo ne ya leqo daga qaramar qofar dake jikin get din yana tambaya lafiya dai?. Mama tace " Baba kayi mana magana da hajiya kace mai kawo mata er aiki ce tazo". Komawa yayi ciki, ba afi minyi biyu ba sai gashi ya dawo yace "Tace ku shigo". Bin bayansa suka yi har cikim gidan, Naana sake baki tayi tana kallon tsaruwar gidan, Part biyu ne gidan, Kai tsayawa bayanin tsaruwar gidan wani jan aiki ne, Ya hadu dai kawai iya haduwa. Daya daga cikin part din suka nufa wanda yafi dayan girma, Knoking sukayi aka bude musu qofar, wata kyakkyawar yarinya ce ta bude musu qofar wadda a qalla baxata haura 18 ba. Shiga sukayi ciki, Ai Naana bata ga komai ba a waje, falon ya tsaru iya tsaruwa hawa biyu ne a ciki kyan falon sai wanda ya gani kawai. Wata mata suka gani xaune kan daya daga cikin kujerun dake xagaye a falon cikin shiga ta alfarma ta dora qafa daya kan daya cike da nuna isa, hannunta na riqe da newspaper tana karantawa, kai daka ganta kasan hutu ya ratsa ta. Yarinyar da ta bude musu qofa ta koma ta xauna kusa da matar tare da daukar wayarta ta cigaba da abinda take. Har suka iso wajen matar bata dauke kanta akan newspaper'n da take dubawa ba. Inna ta xauna qasan carpet din falon Itama Naana hakan tayi, Inna ta gaishe da matar cikin girmamawa sai a sannan matar ta dago kanta ta kallesu, kyakkyawa ce itama suna kama kuma da yarinyar data bude musu qofa. Ta amsa ba yabo ba fallasa, itama Naana ta gaishe da ita nan ma ta amsa kamar nq Inna. Inna tace " Hajiya maganar er aikin ce da kikace a samo miki shine na kawo miki ita gatanan." Ta qarashe maganar tana mai nuna Naana. Hajiyar ta kalleta sau daya ta kauda kai sannan tace "Bata da suna ita?". Naana taji gabanta ya fadi jin yadda matar ke magana cikin nuna isa, lallai akwai aiki a gabanta, bata san ta ina xata fara aiki a gidan ba don bata taba yi ba ba kuma tayi tunanin xatayi ba a rayuwarta. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [25/09 6:31 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹9⃣🌹 Inna tayi murmushi tace "sunanta Bilkisu amma anfi kiranta da Naana" Tabe baki tayi tace "Tohm ya maganar tsafta? don kinsan ni bana son qaxanta". Inna tace " Ai duk da ban Dade da Naana ba amma na fahimci tana da tsafta sosai Hajiya". Ta nisa sannan tace "To shi fa wannan yaron da kuke tare fa?". Inna ta kalli Faheem tace " Qaninta ne shi sunansa Faheem". Hajiyar tace "Harda shi xa a min aikin?". Inna tace " Idan baki so sai na tafi dashi gida" Sai a sannan bakin Naana ya budu tayi saurin cewa "Don Allah hajiya kiyi hkr kar ki rabani da qanina". Ta qarashe maganar tana mai qara rungume Faheem a jikinta. Hajiya ta kawar da kai tare da cewa " Ni bance xan raba ki da shi ba, sannan daga yau xaki fara aikinki, wanke wanke da goge goge da shara da kuma wankin qananan kayan diyata XEE." Gyada kai kawai tayi alamar ta amince duk da ranta baso yake ba amma babu yadda xatayi ne. Inna tace "Toh hajiya xata rinqa xuwa ne kullum ko kuwa nan xata xauna?". Hajiya tace " Wadannan ayyukan Dana lissafo ai ba jiranta xamu ringa yi ba Har sai taxo sannan tayi, akwai dakunan masu aiki da yawa cikin gidan nan xata iya xama anan". Naana ta qara kallon gidan, wai yau ita ce xatayi rayuwa a irin wannan gidan mai kusan unguwa guda don girma. Muryar Hajiya ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga, ji tayi tace "Amma ina da sharudda da xan fada miki, na farko bana son qaxanta, na biyu bana son gardama, na uku bana son shisshigi a lamuran gidan nan". Naana tace " Insha Allah xan kiyaye dukkanin sharuddanki Hajia". Hajiya tace "Yayi kyau, duk wata xan riqa biyanki dubu goma". Naana kam kallonta kawai take, can dai tace " Toh Hajia nagode Allah ya saka da alkhairi Allah ya bani ikon yi muku aiki lafiya". Duk suka amsa d Ameen. Inna tace "Hajiya ni zan iya tafiya ynx?". Hajiya tace " Ofcouse xaki iya tafiya ita kuma xuwa anjima sai ta tafi washe gari ta hado kayansu sai su xauna nan."Inna Har ta miqe Hajiya tace "Amma Dan jira". Kallon diyarta tayi tare da cewa Zee tashi ki dauko min 2k cikin bag dina a daki". Zee ta miqe kawai tare da ajiye wayanta saman kujera ta haura sama upstairs dakin hajiyar. Bata fi minti biyar ba sai gata ta dawo da kudi a hannunta ta miqama Hajiya tare da cewa " Mummy gashi". Mummy ta amsa tare da miqawa Inna tace "Gashi kiyi kudin mota". Godiya inna tayi ta xubawa, sannan tace " Naana bari na baki kudin dawowa ai xaki iya ganewa ko?". Naana ta gyada mata kai alamar "Eh". Hajiya tace " No barshi kawai na bata itama". Godiya suka qara yi sannan inna ta miqe ta fice yayin da ita kuma Naana ta kalli Hajiyar tare da cewa "Hajiya yanxu wane aikin xan fara?". Hajiya tayi Dan Jim sannan ta kalli Zee tace " Dota ya room dinki yake?". Zee ta Dan yamutsa fuska sannan tace "Ya danyi dirty Mummy". Mummy ta kalli Naana tace " To ki bita ta nuna miki room din sai ki gyara mata". Naana ta miqe tabi bayan Xee xuwa Upstairs, shima Faheem na biye da ita Har suka je dakin, Zee tace "Kar kuma kiyi min banna kibi mun kaya a hankali". Murmushin yaqe kawai tayi ta gyada mata kai, Har xata fita sai ji tayi Faheem yace " Aunty kina da kyau". Kallonshi ta tsaya yi cike da mamaki, lokaci guda kuma taji yaron ya burgeta tayi murmushi tare da dan ranqwafawa saitin fuskarshi tace "Thanks, kaima kana d kyau sosai". Dariya ya hau yi, itama dariyar tayi ta Dora masa peck a goshi sannan ta juya ta fita. Naana dake tsaye tana kallonsu ta kalli Faheem tace " Kai dai ka cika surutu da yawa, duk da bakin naka bai bude ba sosai". Dariya kawai yayi mata, itama tayi dariyar sannan ta cigaba da aikin ta, dakin ba wani dirty yayi ba don haka bata sha wuyar aikin ba. A taqaice dai sai kusan la'asar ta bar gidan bayan Mummy ta bata kudin mota dubu daya, tayi mata Godiya sosai sannan suka tafi Xee na daga ma Faheem hannu shima yana daga mata, don Har sun saba duk aikin da tayi a gidan shi yana tare da Zee suna wasa, sai a nan ta fahimci Zee tana da sauqin kai ba kamar Mummynta ba. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [25/09 7:20 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣0⃣🌹 Koda ta isa gidan duk ta gaji sosai, Inna tayi mata sannu ta shiga daki ta kwanta saman katifa shi kuwa Faheem xama yayi wajen Ameenu. Inna ta shigo dakin tana mai cewa "Naana ya aikin naki?" Ta dan juya ido tare da cewa "Um Inna da aiki fa da yawa a gidan wai yau m don farkon xuwa ne kenan". Inna tace " To ai haka aikin yake a hankali a hankali xaki saba ne". Naana tace "To shikenan Allah ya shige mana gaba". Inna ta amsa da " Ameen". Ta fiddo chanjin Dari takwas din da suka hau mota ta miqa ma inna tace "Inna ga wannan chanjin" Inna ta girgixa kai tare da cewa "A a Naana baxan amsar miki kudi ba ki sayi wani abun da kike buqata". Tace " Inna ai ni babu abinda xan siya da kin riqe kawai". Inna tace "A a dai ki kawo na baiwa Ameenu ya siyo maku brush da takalma da kuma ko er Riga ce ta gwanjo ya siyo miki daya ya siyo ma Faheem daya ko ba haka ba?" Gyada mata kai kawai tayi tana murmushi, Inna ta kira Ameenu ta bashi kudin tayi masa bayanin abubuwan da zai siyo ya tafi. Kusan Rabin awa ya dauka sannan ya dawo da kayan cikin Leda. Nan Inna ta amsa ta duba ya siyo lafia lau, don Faheem Riga da wando kala biyu ya siyo masa saboda na gwanjo ne ba wani tsada garesu ba, kuma suna da kyau sosai, itama doguwar Riga ce da kuma qaramar Riga, sai Brush da takalman. Nan tayi masu godiya kamar su suka bata kudin. Bayan sunyi sallar la'asar ta miqe tace ma inna tanaso ta wanke kayan nan, ba musu inna ta bata sabulu taje ta wanke su Tass suna bushewa Ameenu ya goge mata su da cakol don ita Sam bata iya gugar cakol ba. Dare nayi tayi musu sai da safe sannan ta dauki Faheem da yayi barci suka shiga daki suka kwanta. _Washe gari_ Bata koma bacci ba tunda suka yi sallah, kamar jiya ta share dakin da suka kwana ta share tsakar gidan sannan ta Debi ruwa tayi wankanta ta shirya cikin wata atamfarta don Hajiya tace taxo da wuri. Faheem ta tada lokacin Har 7 ta kusa, tayi mashi wanka shima ta shirya shi sannan ta xauna jiran tashin Inna. Wurin 8 inna ta shigo dakin da sallamarta, Naana ta amsa sannan ta gaisheta inna ta amsa sannan tace "Ku fito ga kalaci can kuxo muyi". Ba musu ta miqe Inna taja hannun Faheem suka fita, a wajen suka iske Ameenu cikin shirinshi na xuwa makaranta yana kalacin, nan ya gaishe da Naana ta amsa mishj da fara'a. Inna ta miqo musu kofunan koko sannan ta xuba ma Faheem kosai itama ta xuba mata, godiya tayi mata sannan ta dauka cup din kokon tana kallo don ita bata shan koko ko a gida, tunani ta shiga yi........ _"Yah Auwal nifa baxan sha koko ba" Ta fada tana turo baki gaba alamar shagwaba. Yace "To ya kike so inyi dake Qanwa? nima fa ba son shan kokon nake ba hakanan xan sha. Tace " To ba sai ka siyo mana indomie ba". Umma tace "Anqi a siyo indomie din sai dai kar kisha kokon". Buga qafa ta soma yi cike da shagwaba tace_······· Faheem ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, yana tabata yace " Adda baki shan kokon?". Murmushindole ta qaqaro sannan ta ce "Xansha mana Faheem". Tana gama fadar haka ta jawo kwanon kosan ta dan ci sannan tayi kurbi kokon ta ajiye tare da miqewa tace " Inna bari Mu tafi Hajiya tace naxo da wuri". Inna tace "To Naana bari na dauko maku kudin mota". Daki ta shiga ta dauko mata Dari uku ta bata tare da cewa " To Naana kiyi aiki da kyau kinji kuma insha Allah xan riqa kawo muku xiyara". Murmushi tayi ta rungume inna sannan tace "Insha Allah inna nima kuma xan riqa shigowa insha Allah". Inna tace " Allah ya yards"Ta amsa da "Ameen". Sannan ta shiga daki ta dauko jakar kayansu ta fito Ameenu yayi musu bankwana suka fita suka tafi cike da kewar gidan. tayi sa a kuwa tana fita ta samu mai napep. Koda ta isa bata sha wahalar shiga ba saboda mai gadin ya ganeta. A falon ta iske Hajiya da Zee da kuma wani babban mutum Wanda da alama shi ne mai gida suna break fast. Har qasa ta duqa ta gaishe su cike da ladabi da biyayya, suka amsa mata da fara'a, mai gidan ya tambaya ko wacece nan Hajiya tayi masa bayani. Faheem kuwa da gudu ya qarasa wajen Zee yana dariya, itama dariyar tayi tare da rungumeshi tace " My Faheem taho muci abinci kaji". Girgixa mata kai yayi yace "A a ni na koshi munci da Adda a gida". tayi murmushi tace " Ai ba irin wannan bane"Ta qarashe maganar tana nuna mashi plaintain din fake gabanta. Ya kalla tare da girgixa kai yace "Ni cicina ya cika in na qaya fashewa daiyi". Dariya sukayi gaba dayansu harda Hajiya da jiya take ta shan qanshi. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [25/09 11:09 am] Beelybadaru😍: [25/09 6:31 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹9⃣🌹 Inna tayi murmushi tace "sunanta Bilkisu amma anfi kiranta da Naana" Tabe baki tayi tace "Tohm ya maganar tsafta? don kinsan ni bana son qaxanta". Inna tace " Ai duk da ban Dade da Naana ba amma na fahimci tana da tsafta sosai Hajiya". Ta nisa sannan tace "To shi fa wannan yaron da kuke tare fa?". Inna ta kalli Faheem tace " Qaninta ne shi sunansa Faheem". Hajiyar tace "Harda shi xa a min aikin?". Inna tace " Idan baki so sai na tafi dashi gida" Sai a sannan bakin Naana ya budu tayi saurin cewa "Don Allah hajiya kiyi hkr kar ki rabani da qanina". Ta qarashe maganar tana mai qara rungume Faheem a jikinta. Hajiya ta kawar da kai tare da cewa " Ni bance xan raba ki da shi ba, sannan daga yau xaki fara aikinki, wanke wanke da goge goge da shara da kuma wankin qananan kayan diyata XEE." Gyada kai kawai tayi alamar ta amince duk da ranta baso yake ba amma babu yadda xatayi ne. Inna tace "Toh hajiya xata rinqa xuwa ne kullum ko kuwa nan xata xauna?". Hajiya tace " Wadannan ayyukan Dana lissafo ai ba jiranta xamu ringa yi ba Har sai taxo sannan tayi, akwai dakunan masu aiki da yawa cikin gidan nan xata iya xama anan". Naana ta qara kallon gidan, wai yau ita ce xatayi rayuwa a irin wannan gidan mai kusan unguwa guda don girma. Muryar Hajiya ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga, ji tayi tace "Amma ina da sharudda da xan fada miki, na farko bana son qaxanta, na biyu bana son gardama, na uku bana son shisshigi a lamuran gidan nan". Naana tace " Insha Allah xan kiyaye dukkanin sharuddanki Hajia". Hajiya tace "Yayi kyau, duk wata xan riqa biyanki dubu goma". Naana kam kallonta kawai take, can dai tace " Toh Hajia nagode Allah ya saka da alkhairi Allah ya bani ikon yi muku aiki lafiya". Duk suka amsa d Ameen. Inna tace "Hajiya ni zan iya tafiya ynx?". Hajiya tace " Ofcouse xaki iya tafiya ita kuma xuwa anjima sai ta tafi washe gari ta hado kayansu sai su xauna nan."Inna Har ta miqe Hajiya tace "Amma Dan jira". Kallon diyarta tayi tare da cewa Zee tashi ki dauko min 2k cikin bag dina a daki". Zee ta miqe kawai tare da ajiye wayanta saman kujera ta haura sama upstairs dakin hajiyar. Bata fi minti biyar ba sai gata ta dawo da kudi a hannunta ta miqama Hajiya tare da cewa " Mummy gashi". Mummy ta amsa tare da miqawa Inna tace "Gashi kiyi kudin mota". Godiya inna tayi ta xubawa, sannan tace " Naana bari na baki kudin dawowa ai xaki iya ganewa ko?". Naana ta gyada mata kai alamar "Eh". Hajiya tace " No barshi kawai na bata itama". Godiya suka qara yi sannan inna ta miqe ta fice yayin da ita kuma Naana ta kalli Hajiyar tare da cewa "Hajiya yanxu wane aikin xan fara?". Hajiya tayi Dan Jim sannan ta kalli Zee tace " Dota ya room dinki yake?". Zee ta Dan yamutsa fuska sannan tace "Ya danyi dirty Mummy". Mummy ta kalli Naana tace " To ki bita ta nuna miki room din sai ki gyara mata". Naana ta miqe tabi bayan Xee xuwa Upstairs, shima Faheem na biye da ita Har suka je dakin, Zee tace "Kar kuma kiyi min banna kibi mun kaya a hankali". Murmushin yaqe kawai tayi ta gyada mata kai, Har xata fita sai ji tayi Faheem yace " Aunty kina da kyau". Kallonshi ta tsaya yi cike da mamaki, lokaci guda kuma taji yaron ya burgeta tayi murmushi tare da dan ranqwafawa saitin fuskarshi tace "Thanks, kaima kana d kyau sosai". Dariya ya hau yi, itama dariyar tayi ta Dora masa peck a goshi sannan ta juya ta fita. Naana dake tsaye tana kallonsu ta kalli Faheem tace " Kai dai ka cika surutu da yawa, duk da bakin naka bai bude ba sosai". Dariya kawai yayi mata, itama tayi dariyar sannan ta cigaba da aikin ta, dakin ba wani dirty yayi ba don haka bata sha wuyar aikin ba. A taqaice dai sai kusan la'asar ta bar gidan bayan Mummy ta bata kudin mota dubu daya, tayi mata Godiya sosai sannan suka tafi Xee na daga ma Faheem hannu shima yana daga mata, don Har sun saba duk aikin da tayi a gidan shi yana tare da Zee suna wasa, sai a nan ta fahimci Zee tana da sauqin kai ba kamar Mummynta ba. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [25/09 7:20 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣0⃣🌹 Koda ta isa gidan duk ta gaji sosai, Inna tayi mata sannu ta shiga daki ta kwanta saman katifa shi kuwa Faheem xama yayi wajen Ameenu. Inna ta shigo dakin tana mai cewa "Naana ya aikin naki?" Ta dan juya ido tare da cewa "Um Inna da aiki fa da yawa a gidan wai yau m don farkon xuwa ne kenan". Inna tace " To ai haka aikin yake a hankali a hankali xaki saba ne". Naana tace "To shikenan Allah ya shige mana gaba". Inna ta amsa da " Ameen". Ta fiddo chanjin Dari takwas din da suka hau mota ta miqa ma inna tace "Inna ga wannan chanjin" Inna ta girgixa kai tare da cewa "A a Naana baxan amsar miki kudi ba ki sayi wani abun da kike buqata". Tace " Inna ai ni babu abinda xan siya da kin riqe kawai". Inna tace "A a dai ki kawo na baiwa Ameenu ya siyo maku brush da takalma da kuma ko er Riga ce ta gwanjo ya siyo miki daya ya siyo ma Faheem daya ko ba haka ba?" Gyada mata kai kawai tayi tana murmushi, Inna ta kira Ameenu ta bashi kudin tayi masa bayanin abubuwan da zai siyo ya tafi. Kusan Rabin awa ya dauka sannan ya dawo da kayan cikin Leda. Nan Inna ta amsa ta duba ya siyo lafia lau, don Faheem Riga da wando kala biyu ya siyo masa saboda na gwanjo ne ba wani tsada garesu ba, kuma suna da kyau sosai, itama doguwar Riga ce da kuma qaramar Riga, sai Brush da takalman. Nan tayi masu godiya kamar su suka bata kudin. Bayan sunyi sallar la'asar ta miqe tace ma inna tanaso ta wanke kayan nan, ba musu inna ta bata sabulu taje ta wanke su Tass suna bushewa Ameenu ya goge mata su da cakol don ita Sam bata iya gugar cakol ba. Dare nayi tayi musu sai da safe sannan ta dauki Faheem da yayi barci suka shiga daki suka kwanta. _Washe gari_ Bata koma bacci ba tunda suka yi sallah, kamar jiya ta share dakin da suka kwana ta share tsakar gidan sannan ta Debi ruwa tayi wankanta ta shirya cikin wata atamfarta don Hajiya tace taxo da wuri. Faheem ta tada lokacin Har 7 ta kusa, tayi mashi wanka shima ta shirya shi sannan ta xauna jiran tashin Inna. Wurin 8 inna ta shigo dakin da sallamarta, Naana ta amsa sannan ta gaisheta inna ta amsa sannan tace "Ku fito ga kalaci can kuxo muyi". Ba musu ta miqe Inna taja hannun Faheem suka fita, a wajen suka iske Ameenu cikin shirinshi na xuwa makaranta yana kalacin, nan ya gaishe da Naana ta amsa mishj da fara'a. Inna ta miqo musu kofunan koko sannan ta xuba ma Faheem kosai itama ta xuba mata, godiya tayi mata sannan ta dauka cup din kokon tana kallo don ita bata shan koko ko a gida, tunani ta shiga yi........ _"Yah Auwal nifa baxan sha koko ba" Ta fada tana turo baki gaba alamar shagwaba. Yace "To ya kike so inyi dake Qanwa? nima fa ba son shan kokon nake ba hakanan xan sha. Tace " To ba sai ka siyo mana indomie ba". Umma tace "Anqi a siyo indomie din sai dai kar kisha kokon". Buga qafa ta soma yi cike da shagwaba tace_······· Faheem ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga, yana tabata yace " Adda baki shan kokon?". Murmushindole ta qaqaro sannan ta ce "Xansha mana Faheem". Tana gama fadar haka ta jawo kwanon kosan ta dan ci sannan tayi kurbi kokon ta ajiye tare da miqewa tace " Inna bari Mu tafi Hajiya tace naxo da wuri". Inna tace "To Naana bari na dauko maku kudin mota". Daki ta shiga ta dauko mata Dari uku ta bata tare da cewa " To Naana kiyi aiki da kyau kinji kuma insha Allah xan riqa kawo muku xiyara". Murmushi tayi ta rungume inna sannan tace "Insha Allah inna nima kuma xan riqa shigowa insha Allah". Inna tace " Allah ya yards"Ta amsa da "Ameen". Sannan ta shiga daki ta dauko jakar kayansu ta fito Ameenu yayi musu bankwana suka fita suka tafi cike da kewar gidan. tayi sa a kuwa tana fita ta samu mai napep. Koda ta isa bata sha wahalar shiga ba saboda mai gadin ya ganeta. A falon ta iske Hajiya da Zee da kuma wani babban mutum Wanda da alama shi ne mai gida suna break fast. Har qasa ta duqa ta gaishe su cike da ladabi da biyayya, suka amsa mata da fara'a, mai gidan ya tambaya ko wacece nan Hajiya tayi masa bayani. Faheem kuwa da gudu ya qarasa wajen Zee yana dariya, itama dariyar tayi tare da rungumeshi tace " My Faheem taho muci abinci kaji". Girgixa mata kai yayi yace "A a ni na koshi munci da Adda a gida". tayi murmushi tace " Ai ba irin wannan bane"Ta qarashe maganar tana nuna mashi plaintain din fake gabanta. Ya kalla tare da girgixa kai yace "Ni cicina ya cika in na qaya fashewa daiyi". Dariya sukayi gaba dayansu harda Hajiya da jiya take ta shan qanshi. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [27/09 5:59 am] Beelybadaru😍: [26/09 1:31 pm] Beelybadaru😍: [25/09 4:25 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣1⃣🌹 Hajiya ta kalli Naana tace "Naana wannan shine Alhaji baban Zee kenan". Qara gaishe shi ta kuma yi ya amsa da fara'a a fuskarta. Hajia tace " Zee tashi ki nuna mata dakinta ta ajiye kayansu". Ba musu Zee ta miqe tana riqe da hannun Faheem tace da Naana "Muje ko?". Naana ta miqe suka wuce wani daki da ke nan cikin falon ba sai an hau sama ba. suka shiga, daki ne mai kyau da gado dan qarami mai kyau Har da Mirror da kuma toilet a ciki. Zee tace " Ga dakin ku nan Naana". Naana tayi murmushi tace "Toh nagode Aunty Zee". Zee tayi saurin cewa " Kinga ni kibar cemin Aunty". Naana tace "To ai ko ba komai kin girmeni ballantana kuma kina gaba dani". Zee tace " Yanxu nan na girme ki? Just i'm 18yrs". Naana tayi murmushi tace "Ni kuma 16 nike da". Zee ta kalleta da mamaki tace " Tab amma sai ayi xaton Kin wuce 16 Allah, To kin gama schl?". Naana tace "Dis year na gama schl dina". Zee tace " Wow ni kuma last year na gama ynx haka nayi jamb result kawai nake jira". Tace "Allah sarki, to Allah ya bada sa'a". Zee ta amsa da " Ameen"sannan tace "Amma a wane gari kike?" Shiru ta danyi can kuma tace "Am a Funtuwa Kankia nake". Zee tace " Yayi kyau ni bari naje daki, Faheem xo muje na baka sweet." Tsallen murna ya fara suka fice daga dakin suka bar Naana tsaye nan tana murmushi. Dakin ta hau gyarawa bayan ta gama ta fito xuwa falo don gyarawa lokacin su Mummy Har sun gama breakfast din hakan yasa ta kwashe kayayyakin ta nufi kitchen dasu bayan ta gama wankewa ta gyara kitchen din fess sannan ta fito ta gyara falo ta goge ko'ina, ta haura upstairs dakin Zee. A can ta isketa da Faheem yana shan sweet yana dariya itama tana xaune suna ta dariya don Faheem akwaishi d ban dariya. Nan ta shiga gyaran dakin, Zee ta miqe xasu Fita ita da Faheem, Har sun kai qofa taji Faheem na cewa "Aunty Abee ina yana bani sweet irin wannan kuma Abba ma yana bani". Da sauri Naana ta waigo tana kallonshi tace " Kul mana Faheem kai ka cika surutun tsiya". Zee bata fahimci komai ba don tayi tunanin Abee din shi ne mahaifinsu yayin da Abba dai kasance wani dai dan uwansu. Nan dai taja hannun Faheem suka fice daga dakin. Ita kuwa Naana tsoro ne ya kamata kar Faheem ya tona mata asiri ya fadi abinda yayi sanadiyyar barota gida, su dauketa a matsayin maqaryaciya kuma su koreta daga gidan. Dole ne ta San yanda xatayi tun kafin Faheem yayi mata tsiya. Tana gama gyaran dakin ta shiga toilet dinta ta wanke sannan ta fito ta wuce dakinta don Mummy tace banda dakinta da na Alhaji xata riqa gyarawa. A falo ta iske Zee da Faheem da kuma Mummy, nan taje ta durqusa Har qasa tace "Hajiya na gama aikin ko da akwai abinda xa'ayi ynx?". Mummy tace " Ai babu wani sauran aiki ynx sai dai kuma xuwa anjima". Ta miqe xata tafi Mummy ta tsayar da ita tare da cewa "Am daga ynx ki daina kirana da Hajiya ki kirani kamar ynd kika ji Zee na kirana". Gyada mata kai tayi tare da cewa " To Mummy insha Allah xan kiyaye". Mummy tace "Yawwa haka nake so". Tana shiga daki ta fada kan gado don duk ta gaji da yawa. Faheem ne ya shigo dakin da gudunshi hannunshi riqe da sweet ya hau kan gadon yana miqawa Naana sweet din a baki yace " Haaa Adda kisha nima a sha". Murmushi tayi sannan ta amsa sweet din ta dan tsotsa sannan ta bashi. Can ta kalleshi tace "Faheem". Kallonta yayi yana cigaba da shan sweet dinshi, tace " Faheem meyasa ka cika surutu da yawa ne? ba na hanaka radar abinda ba a tambaye ka ba?". Shiru yayi yana zare ido, Naana ta dan daure fuska tare da cewa "Ba tambayarka nake ba? kamin shiru kana zare min idanuwa". Hawaye ya fara yana cewa " Adda kiya hukuri". Sai kuma duk bata ji dadi ba, ta ruqoshi tare da share mashi hawayen cikin muryar lallashi tace "To kayi shiru bana son kukan amma ka daina kaji?". Kai ya gyada mata tare da lahewa a jikinta ita kuma ta qara rungume shi a jikinta tana tunanin rayuwarta ta baya, hawaye ne suka soma zarya a kumatunta, tayi saurin sharewa don kada Faheem y gani. *********************** Kwanaki sunja yau Naana Har tayi 1week a gidan aikinta, Ta dan rage damuwa Faheem yayi qiba don ya xama tamkar dan gida, bata da wata matsala a gidan don Mummy ma ta sake mata sosai haka ma Zee sun xama tamkar qawaye, tana aikinta tuquru, duk abinda aka sanya ta cikin hanxari take yinsa, hakan yasa Mummy ta sake mata. Yau ta kama Saturday tana xaune a dakinta lokacin ta gama aikinta, Faheem na gefenta yana wasa da teddynsa da Zee ta siya mashi. Zee ta shigo dakin da sallamarta, da gudu Faheem yaje ya rungumeta itama ta daga sa sama, xama tayi gefen gadon Naana tare da cewa " Naana kixo Mummy na kiranki". Miqewa tayi da sauri suka fita tare da Zee din. A falo suka tarad da ita, Naana ta duqa hasa tare da cewa "Mummy gani". Mummy tace " Am Naana dama cewa nayi kuje dayan part din can ke da Zee yau muna da babban ". Kafin Naana tayi magana Zee tace " Mummy kar dai kice min yau big bro xai dawo?". Mummy tace "qwarai kuwa don haka kuyi sauri don ynx HK jirginsuu y taso". Gaban Naana ya fadi, kenan dama suna da wani da kenan bata sani ba? Tabdi lallai kuwa akwai aiki.......... Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [26/09 1:28 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣2⃣🌹 Muryar Mummy ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga taji tana cewa "Kuyi sauri mana lokaci na tafiya kuma xaku xo kuyi mashi Mix potatoes da Egg soup, so Ku tashi Ku tafi". Ba yadda ta iya dole ta miqe ganin Xee Har sun kai bakin qofa. Part din suka nufa tana biye da Zee da ke riqe da hannun Faheem Har suka isa part din. Kura kadan yayi saboda dama ana gyara shi, nan suka fara gyaran cikin lokaci qanqani suka gama gyaran sai kuma goge 2 da ya rage. Zee ta xauna saman kujera tana maida numfashi tace " Wash wllh na gaji da yawa". Naana tace "Kai Zee Har kin gaji? to ki bari na qarasa aikin". Zee tace " A a dai kije ki goge dakin ni xan dan huta sannan na goge nan". Gyada mata kai kawai tayi sannan ta koma cikin dakin ta bar Zee nan xaune a falo. Tana cikin goge2 ne taxo daidai side drower na gadon dakin sai taga wani photo a kife, da yake Zee tayi gyaran gadon shiyasa bata lura dashi ba, A hankali ta kai hannunta ta daga hoton, tana mai kallon hoton. (Ni Beely na fara leqe don ganin ko waye a cikin hoton,) Wani handsome guy ne na gani, fari tas dashi yana da manyan idanuwa farare wadanda suke dauke da brown din Qwayar idon, eye lashes zara2 bakinshi dan madaidaici mai dauke da pink lips, ya danyi murmushi hakan ya bayyana fararen teeth dinsa da suke a jere da hushirya a tsakiyarsu.(Baxan iya tantance tsayinsa ba saboda a cikin photo ne amma yanayinsa zai tabbatar maka da yana da tsayi da kuma madaidaicin jiki.) Muryar Zee taji tana cewa "Photon Big bro ne, sunansa yah *MAHMOOD*, a india yake karatu inda yake karantar low, dawowar nan da xai yi shi ne dawowarsa ta qarshe, I mean ya kammala karatunsa, Yah Mahmood yana da kirki sai dai kuma miskili ne na qarshe, magana ma bata dameshi ba sannan kuma akwai xuciya sam baya son raini, a halin ynx yana da 27yrs a duniya, bai cika yin dariya ba, in dai kika ga dariyarsa to yana cikin gida ne ko kuma tare da frnds dinsa, amma ko en mata baya sake musu fuska, duk da hakan kuma en mata sonshi suke kamar suyi hauka saboda kyawunsa da kuma dukiyarsa, shine xai dawo yau". Jinjina kai Naana tayi jin halayen Yah Mahmood, ita dai bai dameta ba aikinta kawai xata cigaba dayi, bama xata shiga harkarsa ba balle ya dameta. Ajiye Photon tayi tare da cewa " Allah sarki to Allah ya dawo dashi lpy". Zee ta amsa da "Ameen". Nan suka cigaba da aikinsu, bayan sun gama ne suka sanya turaren wuta da air freshner tuni part din ya dauki qamshi. sannan suka rufe suka a part din Mummy. Kitchen suka fada don yau Mummy tace hada Naana xa a shiga kitchen cikin qanqanin lokaci suka gama mix potatoes da kuma egg soup sannan suka daga shinkafa wacce xa a ci da egg soup din sannan suka hada drinks kala 2, Naana dai Wanda ta iya takeyi Wanda kuma bata iya ba sai dai ta tsaya tana kallon ynd akeyi, kamar wajensu drinks duk da ita aka hada don ta iya wadannan da shinkafa, Mix potatoes ne dai bata iya ba, amma shima kallo daya tayi mashi ta riqe, egg soup ma ba wani wuya gareta ba. suna gamawa suka wuce dakunan su. Naana tayi ma Faheem wanka ta shiryashi cikin kayan da Zee ta siya masa, sannan itama ta koma toilet din tayi wanka ta wanke gashinta ta dauro towel da ya wuce gwuiwarta sannan ta dauko wani tana goge gashin kanta dashi, wurin fanka ta tsaya tana so gashin ya bushe sannan ta sharce tayi shirinta. Ji tayi an bude qofa da sauri ta waiga don ganin ko waye, Zee ta gani ta shigo cikin shirinta mai kyau, tayi kyau sosai fuskar nan tasha make up. Ajiyar xuciya ta sauke ganin Zee ce, Zee ta qarasa wajenta tana cewa "Wow Naana haka kike da gashi dama? amma kike barinshi haka ba gyara?". Naana tayi murmushi tare da cewa " Kai Zee kin cika xuxuta abu nan Har wani gashi ne dani?". Zee tace "Lallai ma kece dai baki gani amma Allah kina da gashi da kyau sosai". Naana ta dan fiddo manyan idanunta waje tare da cewa "Kai Zee ni dai xagina kawai kike". Dariya Zee tayi tace "ba xancen xagi Naana gaskiya na fada". Murmushi kawai Naana tayi don tasan ba qarya Xee ta fada ba, mutane da yawa sunce ita mai kyau ce, ynx ne dai da bata da kwanciyar hnkln gyara kanta, shiyasa kyan nata ya disashe. Shafa mai tayi da farar powder kawai tare da murxa lips tick kadan a bakinta, ta dauko kaya ta sanya wadanda Zee ta bataa, Fita Zee tayi bata fi minti biyu ba sai gata ta dawo da gashi ta miqawa Naana tace " Gashi ki riqa shafawa kanki xai qara kyau". Godiya Naana tayi mata sosai sannan ta fice daga dakin lokacin Faheem ya jima da yin barci. Naana na gama shirinta ta Dora hijabinta kamar kullum ta fito falon don yin aikace 2 da bata yi ba. A falo ta iske Zee da Mummy suna jiran isowar Yah Mahmood kamar ynd Zee ke fada, don Daddy ya tafi ya dauko sa. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [27/09 5:57 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣3⃣🌹 Kitchen ta wuce ta gyara shi sosai ta kwaso kayan abincin ta kawo su kan dinning sannan ta koma dakinta. Tana xaune sai ga Zee ta shigo tana murna tace "Naana Yah Mahmood ya dawo kixo kiyi masa sannu da xuwa". Naana ta xaro ido waje😳 tace " Ni kuma?"Zee tace "Eh mana ki taso muje". Ba yadda ta iya haka ta miqe ta maida hijabinta data cire suka fita da Zee. Suna fita shi kuma dai dai lokacin ya fice daga falon. Hamdala tayi a cikin ranta, suka qarasa falon Zee tace " Mummy ina Yah xai tafi?" Mummy tace "Part dinsa xashi ya watsa ruwa yace ma akai masa abincinsa can, hana so ya huta". Nan Zee ta hada kayan abincin ta dauka xata kai masa wayarta tayi qara, ta ajiye abincin ta duba tayi hanyar daki tana cewa " Naana kai mashi abincin xanyi picking call". Mummy ta bita da ido Har ta shige daki sannan ta kalli Naana tace "Kinga Naana dauki ki kai masa abincinsa nasan yana can yana jira". Dauka tayi ba don taso ba ta nufi part dinshi xuciyarta na bugawa. Tana xuwa tayi knocking tare da sallama, shiru taji ta qarayi Har sau kusan uku sannan cikin wata xaxxaqar murya aka amsa da " Yes". A hankali ta bude qofar ta shiga, yana xaune yana waya ya juya bayanshi, ta qarasa ta ajiye a saman dining din, har a lokacin bai waigo ba, ta soma tafiya xata tafi, taji yana wayar yana cewa "Okey bye shukriya(thanks)". Tabe baki tayi a ranta tace " A dole sai ya nuna ma mutane yaje india tana jinshi a wayar jefi2 yana hadawa da indiyanci. Har takai bakin qofa sai ji tayi yace "Who serve me" Haushi ya cika mata xuciyarta ta koma ta fara xuba mashi a plate, shi kuwa yayi tunanin bata jin turanci, duk da bai dago ya kalleta ba. Haka har ta gama xuba masa sannan ta juya xata fita. Again ya kuma dakatar da ita da cewa "Ke kurma ce ne?". Waigawa tayi tana kallomshi har lokacin bai waigo ba sai ka rantse bashi yayi maganar ba. Naana kuwa ta kasa furta komai, can dai ta iya buda bakinta cikin muryarta mai sanyi tace " Ni ba kurma bace". Shiru yayi ba tare da cewa komai ba, ya waigo don ganin ko wacece ita kuma lokacin ta juya har ta fice daga dakin. Tsaki yayi sannan ya miqe ya hau dinning ya fara cin abincin. Bayan ya gama ya kira wayan Mummy yace axo a dauke kayan abinci, sannan ya shige toilet don yin wanka. Mummy tasa Naana taje ta dauko, ba don taso ba ta koma part din nasa, tayi sa a kuwa yana wanka lokacin hakan yasa tayi saurin dauke kayan ta fice. Shi kuwa Mahmoud yana fitowa daga wankan ya dauro alwala yayi sannan ya baje kan gado sai barci, don ya gaji da yawa. Naana tana komawa ta wuce da kayan kitchen Maama tace ta xubo abinci taci don sun riga sunci da Faheem. Wanke kwanonin tayi sannan ta xuba a plate ta samu wani ta rufe ta wuce dakinta, sai da tayi sallah sannan ta fara cin abincin. Tana gamawa taje ta wanke kwanukan tayi sauran aikace 2 sannan ta koma dakinta. Sai gab da la'asar Mahmoud ya tashi daga barcin da yake, ya shige toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin qananan kaya ya fice daga part din nasa xuwa masallacin da ke cikin gidan don gabatar da sallar La'asar. _Washe gari_ Tunda safe Naana ta fita ta gama dukkanin ayyukanta, na gidan kamar yanda ta saba, a kitchen ta iske Mummy da Zee suna hada break fast, nan ta durqusa har qasa ta gaishe da Mummy, Mummy ta amsa cike da fara'a a fuskarta suka gaisa da Zee. sannan Mummy tace "Naana taimaka mani da wadannan kayan xuwa dinning, Ba musu ta dauka ta fito dasu xuwa dinning din bayan ta gama jerawa ta koma kitchen din don wanke kayayyakin da aka bata, bayan ta gama Mummy ke ce mata " Naana da anjima xamu kuma shiga kitchen dake don xamuyi wasu ayyuka, an hada ma Mahmoud party na murnar dawowarsa gida". Murmushin yaqe Naana tayi tace "To Mummy Allah ya kaimu anjiman lafiya". Mummy ta amsa da " Ameen". Ta wuce dakinta don yin wanka. Zee ta kalli Naana tace "Yau akwai buduri a gidan nan sosai bari ma naje na kira frnds dina". Murmushi kawai Naana tayi mata ta fice, itama fita tayi ta nufi nata dakin da kayan breakfast dinsu. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [30/09 7:59 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣4⃣🌹 Suna gamawa tayi ma Faheem wanka sannan ta gyara dakinta ta dauko kwanukan abincin da suka ci ta nufi kitchen dsu don wankewa, tana xuwa kuwa taga su Mummy har sun gama breakfast dinsu. Ta kwashe kwanukan ta nufi kitchen dasu bayan ta gama wankewa ta fito xata koma dakinsu Mummy ta kirata. Komawa tayi ta tsugunna gaban Mummy tare da cewa "Mummy gani". Mummy tace " Am ki dauki kayan breakfast din Mahmoud ki kai masa". Gaban Naana ya fadi bata da yadda xatayi dole ta dauka ta nufi part dinsa qirjinta na duka. Yau kam tayi knocking har ta gaji hakan ya tabbatar mata da bai tashi ba, don haka ta bude qofar a hankali ta shiga dakin. Bata ga kowa ba a falo hakan yasa tayi saurin ajiye kayan abincin ta koma part dinsu don bata son sake haduwa dashi. _2:26pm_ Mummy ta kira Naana suka shiga kichen don yin aiki. Sunyi snaks kala-kala, kuma a ranar aka qaro er aiki, amma ita tsohuwa ce kuma ba kwana xata rinqa yi ba. Bayan sun gama duk suka wuce dakunansu, don yin shiri duk da sai 5 xa a fara. Naana dai tana shiga dakinta bayan sunci abinci tayi ma Faheem wanka ta shirya shi ya fice wajen Zee. Itama wankan ta shiga bayan ta gama ta shirya cikin kayanta kamar yanda ta saba kullum. Zee ce ta shigo cikin shigar wani less mai shegen kyau, fuskarnan tasha make up gashi tasha daurin head, ta dai hadu iya haduwa. Faheem ma ta chanja mashi kaya xuwa wasu qananan kaya sunyi masifar amsarshi. Zee ta kalli Naana tace "Har kin shirya ke?". Naana tayi murmushi tace " Na shirya mana, me kika gani?". Fita Zee tayi, ba a fi minti biyu ba sai gata ta dawo dauke da wanj dan kit qarami da kuma kaya a hannunta, ta ajiye kayan saman gado sannan ta kalli Naana tace "Kinga Naana xo ki gani nayi makj kwalliya, ko so kike a rainaki?". Naana tayi murmushi tace " Kai haba Zee raini kuma na me? Kuma ko an rainani minene nifa er aikice". Tsaki Zee tayi tace "Nidai bana son dogon surutu ki taho kawai". Ba yadda ta iya dole taje ta xauna kan gadon wajen Zee. Nan fa Zee ta dinga yi mata make up a fuska duk da light make up ne amma tayi masifar yin kyau fuskarnan ta qara haske bakin nan yasha pink janbaki ga jagira ta ja mata, idonta ma yasha eye liner da mascara. Kafin Zee tayi magana wayarta ta dauki ruri, tana dubawa taga wata qawarta ce tayi saurin dagawa tana cewa " Hello Rookey har kun iso?". Banji mai Rookey tace ba sai dai gani nayi ta miqe tana cewa "Okey gani nan xuwa". Kallon Naana tayi tace " Plx Naana ga kaya nan ki sanya kamin na dawo, frnds dina ne suka xo gate man ya hanasu shigowa". Gyada mata kai kawai tayi, ita kuma ta fice. Daukar kayan Naana tayi tana dubawa, material ne mai shegen kyau pink colour sai ratsin golden, ga kuma dan qaramin head shi kuma golden ne Waro ido tayi a fili tace "Ni xan sanya wadannan kayan? To miye maraba ta da en gida?". Muryar Faheem taji yana cewa " Aunty ki sanya wannan daiyi miki kyau". Naana tace "Faheem ba xaiyi min kyau ba" . Turo baki yayi yana cewa "Allah Aunty dasu yi miki kyau". Ganin yana shirin yin kuka yasa ta dauki kayan ta sanya, har da wasu enkunne kalar kayan manya masu shegen kyau duk ta sanya, (Ni kaina Beely ban gane ta ba, da ace su biyu ne a dakin da sai nace ba ita bace😄) Gaban mirror taje tana kallon kanta, kayan sun amshi jikinta sosai ita kanta har mamakin kanta tayi(Hakan yasa na samu damar fayyace muku kyawun Naana). Fara ce ita amma ba can ba, tana da dan tsayi dai dai misali, ba'a sanyata a jerin masu qiba, kuma ba'a sanyata a jerin marasa qiba,tsaka-tsakiya dai, tana da hips dai dai jikinta qirjinta a cike yake, fuskarta tana dauke da dara daran idanuwa farare masu dauke da black eyes, hacinta mai dan tsawo ne amma ba can ba, da dan qaramin bakinta mai dauke da pich lips, da kuma kyawawan haqora farare, girarta tana da yawa hakan yasa bata cika son yin jagira ba.............. Zée ce ta shigo dakin da sallamarta, Naana dake gaban mirror ta waigo tare da amsa mata sallamar fuskarta dauke da murmushi. Tsaye Zee tayi tana kallon Naana gani take kamar ba ita bace, a hankali ta qaraso cikin dakin tare da dafa kafadar Naana tana cewa "Wowww masha Allah, Naana dama haka kike da kyau? Tabdi". Murmushi Naana tayi tare da juya idanuwanta da suke qara ma fuskarta kyau tace " Kai Zee ni dai karki sanya kaina ya fashe". Zee tayi dariya tace "Allah da gaske nake maki, ba xancen fasa kai". Murmushi kawai tayi nan Zee ta dauko wayarta ta shiga daukarsu selfie. Sallah suka fara yi dama sunyi alwallar su. Naana ta dauko hijabinta kenan xata sanya sai ga Zee ta shigo da gyale a hannunta tayi saurin cewa " A a miye haka kuma?". Cike da mamaki Naana ta kalli Zee tace "Mi akayi?". Zee tace " Nufinki hijabi xaki sanya da wannan kwalliyar". Naana tace "To mi xan sanya Zee?". Zee ta miqa mata gyale tace " Ga wanda xaki sanya". Ta dan fiddo da ido waje sannan tace "Lah ki rufa min asiri ni na sanya gyale a matsayina na er aiki?". Zee tace " To ai yanxu baxakiyi wani aiki ba saboda an samo ma'aikata daga restaurant ". Naana tace " Duk da haka nidai baxan iya sanya gyale ba". Zee ta daure fuska tare da wulla mata gyalen ta juya tare da cewa "Allah in dai baki sanya gyalen nan ba baxaki kuma ganin fara'a ta ba a gidan nan". Tana kaiwa nan ta fice ta bar Naana cike da xullumi. Tasan Zee xata iya hakan kuma in Mummy ta lura da hakan xata iya korarta daga aikin hakan yasa tayi saurin daukar gyalen ta yafa ta kalli kanta a madubi, ita kanta tasan tayi kyau sosai. Dedicated to all mfans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [01/10 10:33 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣5⃣🌹 Tana nan tsaye ta kasa fita ko ina Zee ta shigo dakin fuskarta a daure amma ganin Naana da gyale ya sanya ta saki fuskar ta qarasa gurinta tare da cewa "To ko kefa, abinda yasa nace ki sanya gyale duk gurin babu wanda xai sa hijab shiyasa". Ita dai murmushi kawai tayi sannan Zee ta jata xuwa falo. A falo suka iske Mummy tayi shirinta cikin shigar alfarma, ita dai Naana sai sadda kai take, suna isa falon Mummy tace " Zee baki yi ma Naana magana bane? Tayi sauri ta shirya lokaci na qurewa kuma na fison mu fita gaba daya". Zee tayi dariya tana kallon Naana tace "Mummy Naanar har guda biyu ce?". Mummy tace " Au dama cewa nayi biyu ce?". Zee tayi dariya tace "To ai ga Naanar nan mun fito tare". Waigawa Mummy tayi tana kallon Naana ita tunda suka shigo kwata2 bata ganeta ba ko kadan, ynxn ma sai da ta qara kallonta sosai sannan ta ganeta. Mummy tace " Wai Naana ce haka ko wata ce?". Dariya sosai Zee tayi yayin da Naana dai bata da aiki sai na murmushi. Zee tace "Ita ce kuwa Mummy". Mummy tace " Gsky tayi kyau kamr ba ita ba". Duk suka yi murmushi. *MAHMOUD* Shirinshi yayi cikin shiga ta alfarma, suit ya sanya, in ka ganshi sai ka rantse da Allah ba bahaushe bane, sai ka rantse da Allah bature ne. Frnds dinshi har sunxo, daka shigo dakin qamshi ne kawai ke tashi don Mahmoud akwai shi da son qamshi. 5:10pm Duk an hallara a babban filin gidan inda za'a gabatar da partyn, gurin ya qayatu iya qayatuwa, tsayawa fadar tsaruwar gurin bata lokaci ne sai dai wanda ya gani. Can saman wata jugunanniyar kujera na hango Mahmoud, gefenshi kuwa wani kyakkyawan dan india ne, dayan gefen kuma wani abokin nashi ne, sai sauran abokan nashi dake kusa da su. Sai gefe guda kuma Su Mummy ne da qawayenta ita ma kowacce ta dau wanka. Dayan gefen kuma Daddy ne shi ma da manyan abokansa. Sai kuma kujerun dake facing din nasu Mahmoud su kuma su Zee ne a gurin da qawayenta da dai sauran en matan da suka hallara a gurin. Naana na can daga baya duk ta takure sam bata saki jikinta ba. Gaban kowa drinks ne da snaks da kuma gasassun kaji kowa ka gani yana farinciki. Shi kanshi uban gayyar sai faman murmushi yake wanda yake qara fiddo da kyawunsa. Nan aka fara gabatar da taron, Mahmoud ya tashi ya miqa dumbin godiayarshi. Anci ansha anyi nat Naana dai lemu kadai tasha. sannan aka miqe don shiga fili a dan taka. Duk aka tashi ya xamana Naana kadai aka bari a gurin xaune. Mahmoud ya miqe da shirin barin wajen don shi sam baya son hayaniya, karaf idanuwanshi suka sauka akan Naana da take xaune ita kadai. Gabanshi ya yanke ya fadi, ya tsaya yana kallonta sosai ko kyafta ido baya yi. Ita kuwa Naana ganin duk an tafi an barta ita kadai yasa ta miqe don barin wajen itama. Da sauri ya fara tafiya don xuwa wajen da take wani abokinsa Abdul ya dakatar dashi ta hanyar jawo hannunsa yana cewa "Aboki kaxo muje kayi rawa mana". Waigawa yayi yana kallon Abdul yace " Plx ka bani 2mnts ynx xan dawo". Yana gama fadar haka ya juya xai tafi wajen Naana sai dai me, sam bai ga kowa a gurin ba. Abdul yace "Plx Aboki xo muje mana" wani haushi ya turnuqe Mahmoud bai san sadda ya fixge hannunshi daga riqon da Abdul yayi mishi tare da cewa "Dubeka da Allah ynx gashi nan kasa ta tafi, mtswwww" Yaja tsaki. Abdul mamaki ya cikashi jin Abokin nasa yayi maganr mace abinda bai taba ji ba kenan, Yace "Aboki wacece". Wani harara ya watsa ma Abdul sannan ya fice daga gurin yana dube2 ko xaiga Naana amma ba alamunta, tsaki yake tayi akai2 sannan ya wuce garden din gidan ya xauna tare da dafe kansa. Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [03/10 7:43 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣6⃣🌹 Naana kuwa cikin gidan ta shige ta wuce dakinta ta kwanta barci barawo yayi awon gaba da ita, ba ita ta farka ba sai da aka kira sallar magrib shi ma Faheem ne ya tada ta saboda ana gab da magrib aka tashi taron. Miqewa tayi da sauri ta fada toilet tayo alwalla sannan ta fito ta gabatar da sallarta. Bayan ta idar ta fito falo ta iske Baaba hanne a kitchen (Sabuwar ma'aikaciyar da aka kawo). Ta gaisheta cikin ladabi da biyayya, sannan ta fito xata koma daki ganin babu wani aiki da xatayi. Baaba Hanne ta dauko plate din abinci ta miqa mata tace "Gashi inji Hajiya tace a baki saboda ta lura baki ci komai ba da kuka gama aikin. Godiya Naana tayi ta amsa ta koma dakinta. Sai da tayi sallar Isha'i da shafa'i da wutri sannan ta xauna suka ci snaks din ita da Faheem. Bayan sun gama ta sauki plate din ta nufi kitchen dashi. *MAHMOUD* Har aka gama bai koma gurin ba, sai da yaji kiran sallah sannan ya wuce masallacin gidan har sai da aka yi Isha sannan ya koma part dinshi, Abdul na ganin sanda ya shiga part din don shima bai wuce gida ba, ya nufi part din nasa. Yana shiga toilet ya fada ya watsa ruwa sannan ya fito daure da towel yana goge sumar kansa d qaramin towel. Abdul ya shigo dakin da sallamarsa, kallo daya Mahmoud yayi masa ya kauda kai. Abdul yayi murmushi tare da qarasawa cikin dakin ya xauna bakin gado tare da cewa " Frnd laifi nayi ne naga kana fushi dani?". Ba tare da ya kalleshi ba yace "Ban sani ba". Dariya Abdul yayi yana kallon Abokin nasa, Wani dogon tsaki yaja don shi ya tsani ayi tayi mashi dariya ba dalili, shiyasa suke fada da Abdul saboda yawan dariyarshi, abu kadan sai ya sanya shi dariya(mr, smiles kenan😄). Waigowa yayi a fusace yace " Look Abdul idan dariya kaxo yimin a daki to ka fice you know bana son dariya ko?". Tsagaita dariyar Abdul yayi tare da cewa "To ai kaine da abin dariya, banyi ma laifi ba amma ka dauki fushi dani". Kallonshi yayi yace " Au baka san laifin da kayi min ba kenan?". Abdul yace "Ni kam bansan laifin da nayi maka ba, ka fada min". Tsaki Mahmoud yaja yace " Daxu ai sai da nace maka ka bani 2mnts amma ka qiya har saida ta tafi". Cikin mamaki Abdul yace "Wacece ta tafi?". Mahmoud yace " Ita mana, har xanje wajenta ka wani tsayar dani har ta bace min". Abdul ya soma dariya yana cewa "Nifa ban gane me kake fada b, wacece ita wai?". Mahmoud ya qule da dariyar da Abdul ke yi yace " Bansani ba ni ka tashi ka fice min daga room ina son hutawa". Ya qarashe maganar yana mai xuwa jallabiyarsa. Abdul ya tsayar da dariyar tasa yace "I'm sorry frnd ka fada min who is she?". Mahmoud yace " Baxan fada ba nace kawai ka tafi". Sarai yasan halin abokin nasa tunda yace baxai fada ba to baxai fadan ba. Murmushi Abdul yayi yace "Shikenan tunda baxaka fada min ynx ba, gobe In Allah ya kaimu sai ka fada min". Banxa yayi dashi har ya fice yana dariya. Addu'a yayi ya kwanta don yin barci amma ya kasa tunanin yarinyar kawai yake, to wai meyasa ma yake ta tunaninta?, yunwa yaji sosai hakan yasa ya miqe ya bude frigde yaga drinks ne kawai, tsaki yayi don shi yasan drinks baxai riqe masa ciki ba, ya jawo wayarshi ya kira Mummy yace" Mummy i'm hungry ki turo a kawo min abinci"Mummy tace "Toh son, xan turo a kawo maka". Baice komai ba ya kashe wayar. Bangaren Mummy ta shiga dakin Zee ta isketa tana wanka, hakan yasa ta fito ta kira Naana don ta kai mashi. Haka ta dauko abincin ta nufi dakinsa dashi. Knocking tayi taji shiru sai tayi tunanin ko yana can daki hakan yasa ta bude qofar ta shiga, baya falo, don haka ta qwanqwasa masa qofar. A tunaninsa Zee ce hakan yasa yace " Yes come in". Gaban Naana ya fadi taso ace kawi budewa xaiyi ya amsa ba sai ta shiga dakin ba. Haka ta bude ta shiga dakin, hasken dakin ba mai wani yawa bane amma xaka iya ganin komai na dakin sai dai yana chanja kalar komai. Ajiye abincin tayi ta nufi hanyar fita. Shi kuwa jin ba Zee bace yasa ya daka mata wata uwar tsawa wadda ta figitata yace "Ke wace irin daqiqiya ce? Gidanku ba'a koya miki tarbiya bane, kin shigowa mutane daki ba ko sallama kamar kin shiga dakin arna". Tsoro ya hana ta yin magana har hawaye sun soma xubo mata. Abinda ya tsana kenan yayi ma mutum magana yayi shiru dashi, miqewa yayi ya nufi inda take, ganin hakan yasa tayi saurin rugawa don fita daga dakin, sai dai kafin ta fita har ya riqo hijabinta, qara ta saki, ba shiri ya saki hijabin ya dode kunnensa, da sauri ta fice daga dakin. Shi kuwa haushi ya cikashi lallai dole xaiyi maganin wannan yarinyar, ta rainashi da yawa. Tsaki yaja ya koma kan gado bayan ya dan dibi abincin. Dedicated to all mfans😘 _Written bBeelybadaru😍_ [04/10 12:03 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣7⃣🌹 Naana kuwa tana fita part din Mummy ta nufa, sai da ta kai bakin qofa ta tsaya tana share hawayenta, Dai dai lokacin Zee ta fito ta ganta tayi saurin cewa "Naana kukan me kikeyi?". Tayi saurin goge hawayen ta qaqalo murmushi tace " Lah ba kuka nake ba wani abu ne ya shigar min a ido". Cikin rashin yadda Zee tace "Ki fadan gskiya, halan Yah Mahmoud ya miki wani abu?". Tayi saurin cewa " Lah nikam me xai yi min? Kawai dai abu ne ya shigar min ido". Tabe baki Zed tayi tace "Shikenan tunda baxaki fada min ba". Shiga suka yi ciki a tare Naana ta wuce dakinta itama haka Zee. Koda ta shiga dakin ta iske Faheem yayi barci hakan yasa itama ta hau kan gadon tare da yi masu addu'a kamar haka:- Falaqi da Nasi qafa ukku, sai Iklas(Qulhuwallahu)itama sau uku. Sannan Ayatul kursiyyu:-wanda ya karanta ta yayin da xai kwanta to Allah xai turo wani ya tsareshi kuma shaidan baxai kusantoshi ba har gari ya waye. Sai kuma wannan addu'ar:- _Allahumma innaka kalaqta nafsi, wa'anta tawaffaahaa laka mamatuha wamahyaahaa, in ahyaitaha fahfazhaa, wa in amattahaa fagfirlaha, Allahumma inni as'alukal aafiyah_ *Fassara:-*Ya Allah kaine ka halicci raina, kuma kaine kake karbansa. Gareka kadai mutuwarsa da rayuwarsa suke, in ka rayar dashi, to ka kiyayeshi. In ka dauke shi to ka gafarta masa. Ya Allah ina roqonka aminci daga dukkan mummuna. (Allah yasa mu dace, Ameen)· Ta shafe musu jikinsu sannan ta kwanta tunanin rayuwarta ta da take hawaye na xubo mata a idanuwanta. (Hmmm ni kaina Beely ina so nasan rayuwar Naana ta da, ko me ya sameta har ta baro gida? 🤔)· **** Washe gari tunda asuba da ta tashi bata koma ba, bayan ta idar da sallah ta gyara dakin nasu sannan ta fito ta gyara falo, tayi komai sannan ta koma daki don jiran su Zee su tashi don ta gyara sauran. Wuraren 10 ta kuma fitowa lokacin har sun kammala break dinsu Daddy ya tafi office suna xaune a falo, Naana taje ta gaishesu, sannan ta kwashi kwanukan ta nufi kitchen dasu ta iske Baaba Hanne ta gaisheta, sannan ta wanke kwanukan ta dauki nasu abincin t nufi dakinsu. Tana xuwa ta iske Faheem ya tashi don haka taje tayi mishi brush da wanka suka fito ta shirya shi sannan ta xuba mishi abincin, ita kuma ta shiga toilet din tayi wankanta ta fito ta shirya cikin kayanta masu dan kyau tasa hijabinta ta xauna itama tana yin break din. Bayan ta gama taje ta wanke plates din sannan ta fito ta iske su Mummy xaune a falo, taje ta durqusa gaban Mummy tayi shiru ta kasa tambayarta abinda ya kawota. Mummy tace "Ya akayi Naana?". Dan gyara xama tayi tace " Am Mummy dama ina so ki dan bani dama ne inje wajen Inna ko kwana biyu ne na danyi mata". Mummy tace"To shine kika kasa tambaya? Ba damuwa tunda akwai wata mai aikin kije kiyi kwana biyun". Farin ciki ya cika ta tayi ma Mummy godiya sannan ta miqe xata tafi daki don dauko kaya, Zee tace "Amma nan xaki bar Faheem ko?". Naana tayi saurin kallonta tace " Kiyi hkr Zee baxan iya jurar tsawon kwana biyu ba tare da naga Faheem ba, kuma na tabbata shima ba xama xaiyi ba". Zed tace "Ke dai kawai kice baxaki barsa ba". Naana tayi murmushi tace " Shikenan indai xai xauna gashi nan na barshi". Ta shiga daki ta dauko kayanta kala biyu ta sanyo dana Faheem don ta tabbata ba xaman xaiyi ba. Tana fitowa tayi masu sai anjima sannan ta nufi hanyan fita, Faheem yayi saurin riqota yace "Aunty ni dan biki". Tace " A a Faheem ka tsaya wajen Aunty Zee". Maqe kafada yayi yace "Uhm uhm". Zee tayi murmushi tace " Ku tafi kawai Naana". Murmushi tayi suka fice daga falon. Mahmoud ne xaune a qofar gidan su, don ji yayi yana sha'awar xama gurin. Naana fito cikin sa'a kuwa ta samu napep don haka suka shiga suka fara tafiya. Dai2 lokacin shi kuma ya dago kanshi ba inda suka sauka sai kan Naana da har sun fara tafiya a Napep. Cikin sauri ya miqe yana mai qara kallonta don tabbatar ma kansa abinda yake gani....... Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [05/10 2:10 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣8⃣🌹 OHW 📚 Kafin yayi yunqurin tsayar dasu tuni sun riga sunyi mashi nisa. Ya dunqule hannunshi ya naushi bangon gurin tare da cewa "Oh shirt!! Yauma ta kuma tafiya". Tunani ya soma to daga wane gidan ta fito? Lallai zaman waje ya kamasa har xuwa lokacin da xata dawo. Komawa yayi ya xauna yana kallon hanyar da suka bi, wayar ma ajiyeta yayi don yana ganin idan ya cigaba da latsa wayan tana iya dawowa ta wucesa ba tare da ya ganta ba. *NAANA* Dai dai qofar gidan Inna aka ajeta dake unguwar Jan bulo, link 8. Suka fito ta biya mai napep kudinsa wadanda Mummy ta bata sannan ta shiga gidan da sallamarta. Inna dake tsakar gida tana shara ta dago kanta tare da amsa sallamar, tana mata lale marhabun. Naana ta qarasa ciki tana murmushi ta xaunar da Faheem sannan ta nufi wajen Inna, Har qasa ta duqa ta gaisheta, Inna ta amsa mata tana tambayarta ya aikin?. Naana tace " Lafiya lau Inna, ina Ameenu? ". Inna tace " Ameenu ya fita tun daxu". Tayi murmushi tace "Inna kawo tsintsiyar na idasa miki sharar". Harararta Inna tayi tace " Daga xuwanki xan kama sanyaki aiki?". Naana tace "Lah Inna ai ba aiki bane shara ce fa kawai". Inna tace " Eh sharar ki barta kawai". Duk yadda Naana taso Inna ta bata tsintsiyar amma ta qiya dole ta hkr. Taje ta ajiye kayanta a daki sannan ta fito ta dawo tsakar gidan ta shimfida tabarma suka xauna suna dan taba hira da Inna. Haka Naana suka sha hutun kwana biyunsu a gidan Inna ta samu hutu sosai, don aiki kadan take a gidan don ma ta dage sai tayi da Inna baxata barta ba. Ta gama shirya kayan nasu tsaf sannan ta fiddo dubu daya ta miqa wa Inna tace "Inna ga wannan hajiya ta bani dubu biyu kudin mota, to nj kuma ba abinda xanyi dasu, ki amsa an kusa bani albashi na sai na kawo miki". Inna ta qi karbar kudin tace " Ina xa ayi haka Naana? Ki barsu kawai a gurinki". Naana ta girgixa kai tare da cewa "A a dai Mama don Allah ki amsa". Da qyar ta samu Inna ta amshi kudin. Sannan ta rakota har qofar gida sai da ta samu Napep sannan ta koma. Suna cikin tafiya sun wuce rabi Naana ta daga kanta tana kallon hanya, karaf suka hada ida dashi, xaro ido tayi ta qanqame Faheem a jikinta jikinta ya fara kyarma cikin rawar murya tace " Qara gudu don Allah". Shi kuwa mamaki ya cikashi me Naana taxo yi Kano bayan ya barota Katsina?. Binsu yayi a baya, ita kuwa duk ta rude tana ta cema mai napep ya qara gudu, wata kwana suka shiga, ahi kuwa Wata babbar mota ce ta tsayar dashi, ya bugi sitiyarin motar cike da takaicin rashin samun Naana da yayi. A tsiyace suka isa qofar gidan, a rude ta fice daga motar ko biyansa bata yi ba ta fada cikin gidan, shi kuwa mai Napep ya lura tana cikim tashin hnkl hakan yasa ya qyaleta. A dai 2 xata shiga falo Mahmoud ya fito, ai kuwa suka yi wani uban karo ta xube qasa tana dafe da goshinta hijabinta ya rufe mata fuska, shi kuwa tsaye yake agogon da yake daurawa ya fadi qasa shima yana dafe da goshin ya kalleta a wulaqance yace "Ke wace irin dabba ce? Baki da hnkl ne?. Sam bata san ma yana yi ba ita burinta kawai ta ganta a daki don duk a rude take, gani take kamar xai xo ya ganta in bata shiga daki ba. Miqewa tayi ta kama hannun Faheem ta nufi qofar shiga falon har lokacin tana dafe da goshinta bata ma ganin gabanta, sai ji tayi tayi karo da mutum, baya2 tayi xata fadi shi kuma baiyi yunqurin taimaka mata ba. Ji kake tim ta fadi qasa, cire hannunta tayi daga forehead dinta ta riqe qugunta tare da yin er qaramar qara " Ahhhhhh". Faheem ya fada jikinta yana kuka yana mata sannu. Mahmoud kuwa mutuwar tsaye yayi dom bai taba tunanin ita ce ba.......... Dedicated to all my fans😘 _Written by Beelybadaru😍_ [06/10 3:26 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹1⃣9⃣🌹 OHW 📚 Nuna ta yayi da da yatsa yana cewa "Are you?". Zee ce ta fito daga falo jin qarar Naana tana cewa " Lafiya nake jin........ "Bata qarasa maganar ba taga Mahmoud tsaye yayinda Naana ke duqe qasa tana matse qwalla abu biyu ya hade mata ga tashin hnkln ga kuma xafin faduwar da tayi, haushin Mahmoud da tsanarsa suka qaru a xuciyarta. Da sauri Zee ta qarasa wajen Naana ta dagota tare da cewa " Subhanallahi Naana mi ya sameki?". "Naana" ya maimaita sunan a ranshi. Zee ta taimaka mata suka miqe suka shiga cikin gidan suka bar Mahmoud nan tsaye kamar wani gunki. Suna shiga Mummy tana sama hakan yasa Naana ta nufi wajen dakinta Zee tace Naana bari na fada wa Mummy sai a duba ki". Murmushin yaqe tayi tace "Bakomai Zee ki barshi kawai dan bugewa ne kawai". Zee tace " Tohm shikenan, amma na tambayeki?". Tace "Allah yasa na sani". Zee tace " Me Yah Mahmoud yayi maki?". Kallonta tayi sannan tace "Ba abinda yayi min me kika gani? Kawai naxo shigowa ne na xame na fadi". Zee ta dan yi shiru sai kuma tace " Shikenan tunda baxaki fada min ba Faheem fada mini, ta qarashe maganar tana kallon Faheem, Shi kuwa kallon Naana yayi ta kauda kanta sai kuma yayi shiru yace "Bugewa sukayi da uncle". Zee tace " Sai kuma me?" Har xaiyi magana Naana ta kalleshi tace "Bana son yawan surutu Faheem". Tana kaiwa nan taja hannunshi xasu tafi Zee ta riqeshi tare da cewa " Tunda bai fada ba ai sai ki bar min shi nan ko?" Sakin hannunshi tayi ta wuce dakinsu, ta xube kan gado hawaye na xarya a fuskarta, ita ynx ya xatayi tunda Sadeeq ya gano tana garin nan to xaiyi ta nemanta ne har ya ganta ya cimma burinsa akanta, dole ne ta nefi mafita tun wuri. Mahmoud kuwa sai da suka dade da shiga sannan ya dauki agogonsa ya wuce yana regretting abinda yayi ma Naana. Wayarsa ce tayi ringing yana dubawa yaga Abdul ne, dan qaramin murmushi ya saki tare da daga wayar gami da cewa "Ya ne Abdul Aboki?". Can bangaren Abdul yace " Hmm haba Mahmoud Aboki na dauka har ynx ai fushi kake dani". Mahmoud yace "Haba kaima ai kasan baxan iya fushi da kai ba". Abdul yace " Kaidai fadi gsky kawai". Mahmoud yace "Forgot it ynx kana ina ne?" Abdul yace "Ina office mana ko ka manta ne?". Mahmoud ya dan dafe kai yace " Oh ka ganni da mantuwa Allah na manta ko don ni ban fara xuwa office bane?". Abdul yayi dariya yace "Gaskiya kam, to ya take? ". Cikin rashin fahimta Mahmoud yace " Wa kenan?". Abdul yace "Wacce tasa kayi fushi dani mana". Sai a lokacin ya tuna yayi murmushi yace " Akwai story ka bari in mun hadu ma tattauna". Abdul yace "Tohm shikenan yanxu dai ina cike wasu files in na gama mayi waya". Mahmoud yace " Okey bye". Ya katse wayar sannan ya wuce part dinsa. *Alhaji Isma'il* Shahararren dan kasuwa ne wanda aka sanshi a ko'ina na fadin qasar nan, kai harda qasashen waje ma. Matarsa daya mai suna *Hajiya Amina* mace ce mai mutunci bata son raini ko kadan sai dai matsalarta daya bata shiri da talaka, shiyasa take yawan korar en aikinta. Suna da 'Ya ya biyu Mahmoud shine babba a nan garin Kano yayi nursery nd primary dinshi, mahaifinshi ya turashi india wajen qanin babanshi da yake xama acan, acan yayi sauran karatunshi a halin ynx ya xama cikakken Lawyer, sai Zainab wacce suke kira Zee itama tayi karatun ta a nan kano ynx haka tayi jamb result take jira ta wuce ta gaba. Duk abinda suka nema suna samu wajen iyayensu. _Wannan kenan_ ******* "Aunty naga wannan mutumin da ya kamaki jiya kika ji mashi rauni a mota, kuma har yana kallonmu". Naana tayi saurin kallon Faheem da yake maganar yana shan sweet dinshi tace " Faheem baka manta shi ba?". Daga mata kai yayi yace "Ba shine ya jima Abee rauni ba da kuma........ " Ya isa haka Faheem." Ta dakatar dashi don ganin yana neman ya tada xaune tsaye, mamakin yaron take ace shekara uku amma ya riqe abubuwa da dama. Zee dake niyyar shigowa dakin taji suna maganar ta tsaya tana saurarensu, taso ace taji mai Faheem xai fada. Amma xata sanya shi ya fada mata don ita tana xargin akwai wani abu da Naana ke boyewa wnd idan Faheem yayi niyyar fada take hana sa. Fasa shiga tayi ta koma dakinta. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [07/10 7:40 pm] Beelybadaru😍: [07/10 6:11 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣0⃣🌹 OHW 📚 _2days later_ Naana na xaune a daki ita da Faheem tana koya mishi karatun qur'ani, Zee ta shigo dakin da sallamarta. Naana ta amsa fuskarta dauke da murmushi, Zee tace "Karatu ake tasha ne?". Naana tace " Aiko dai". Zee tace "Tohm in kin gama Mummy na kiranki a falo. Naana ta rufe qur'anin tace " Muje kawai in na dawo na idasa masa". Fita sukayi a tare, a falon suka iske Mummy da Mahmoud, gaban Naana ya fadi ita sam bata son ganinshi ma. Har qasa ta duqa tace "Mummy gani". Kamar wanda aka tsikara yayi saurin kallon Naana, muryarta na masa yawo a kunne, bai taba jin muryarta ba sai yau. Mummy tace " Am Naana dama cewa nayi ki raka Zee shopping ynx". Gaban Naana ya fadi, ya xa a yi ta fita shopping bayan Sadeeq na gari? Kuma tasan tunda ya ganta sau daya xaiyi ta binta ne har sai ya kamata, kuma gashi ba damar yi ma Mummy musu......... "Tashi maxa ku tafi lokaci na tafiya, kuyi sauri ku dawo kafin Alhj ya dawo. Jiki ba qwari ta miqe, sai a lokacin idanuwanta suka sauka kan Mahmoud da ya tsareta da manyan idanuwanshi masu haske. Da sauri ta dauke kanta ta riqo hannun Faheem, dama Zee a shirye take gyalenta kawai ta dauka kan kujera suka fice daga falon. Har xasu shiga mota Mahmoud ya fito, Zee tace " Yah plx kaxo ka kaimu shopping din". Wata harara ya watsa mata duk da kuwa abinda ya fito dashi kenan amma baya so Zee ta fahimci wani abu. Yace "Ni driver dinku ne da xanyi driving dinku to shopping?". Zee tace " Oh Yah plx mana". Harararta yayi yace "Baxan je ba nace". Bata ce komai ba ta shiga motar itama Naana ta bude baya ta shiga ita da Faheem, Zee ta kallet baki bude tace " Me kike nufi da hakan?". Cikin rashin fahimta Naana tace "Mi nayi?". Harara Zee ta watsa mata tace " Kinga ni ki dawo gaba mu tafi kawai". Ba musu ta fita ta koma gaban suka ja motar suka tafi. Mahmoud haushi ya cikasa, yaso ace Zee ta matsa sai ya kaisu, motarshi ya shiga yabi bayansu duk da sunyi mai nisa amma da yake yasan Super market din sai ya bisu kawai. Suna isa sukayi parking Zee ta fito ta kalli Naana tace "Ki fito mu shiga mana?". Naana tace " A a kije kawai ki dawo Zee ni ina nan xan jiraki". Zee tace "Shikenan Faheem xo muje kaji?". Bude bayan tayi ta fito dashi suka shiga super market din suka bar Naana nan xaune cikin mota. Shi kuwa Mahmoud a hnkl yake driving din hakn yasa ya dan dauki lokaci bai isa ba. Lokacin kuwa Naana tana nan xaune tana jiran su Zee su fito, kamar ance ta daga kanta, ai kuwa sukayi 4eyes da Sadeeq dake niyyar shiga motarsa. Jikinta ne ya hau kyarma hawaye har sun soma xubo mata. Tahowa yayi inda take yana wani shu'umin murmushi. Cikiniyar bude qofar take amman ta kasa har ya qaraso wajen motar. Dan duqawa yayi saitin tagar ya kalleta tare da cewa " Kina tunanin xaki gujemin ne? Ai na fada maki duk inda kika shiga sai na ganoki". Cikin muryar kuka tace "Wai kai wane irin mugun mutum ne? Me yasa kai baka da imani ne? Ka sani baka isa kayi min abinda Allah bi yi mun ba kuma............. ". " Shhhhhhh". Ya dakatar da ita sannan yace "Bana son dogon xance kawai ki fito mu tafi". Naana tace " Babu inda xani". Murmushin tsageranci yayi sannan ya saka hannu cikin aljihunshi ya fiddo da wata er qaramar wuqa ya nuna ta da ita tare da cewa "Idan baki fito ba xan sheqe ki da wannan wuqar, ta sheqe mutane da yawa saboda taurin kansu don haka ki fito kawai ko kuma wallahi na kashe ki a wajen nan na kashe banxa". Jikinta ya dau kyarma ta waiga gefenta taga kowa harkar gabansa yake. Wata muguwar tsawa ya daka mata yace " Ki fito nace!! " Ai bata san lokacin da ta fito daga motar ba, ya damqi hannunta sai da ta danyi er qara ya jata suka nufi wajen motarsa, dai dai lokacin kuma Mahmoud ya qaraso gurin idanuwansa basu sauka ko ina ba sai kan Naana da Sadeeq ya hankida cikin mota tana kuka. Ya waiga ya kalli motar su Zee yaga babu kowa a ciki, waigawar da xai kuma yi yaga Sadeeq har yaja motarsa a tsiyace. Ganin hakan yasa shima yaja tashi motar ya rufa masa baya. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [07/10 7:39 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣1⃣🌹 OHW 📚 Gudu Sadeeq keyi na fitar hankali, Mahmoud na biye dashi a baya duk da yayi masa nisa sosai, Sadeeq ganin kamar ana binsu yasa ya qara gudun motar nasa ya wuce Mahmoud sosai, wata mota ta shige masa gaba kuma sam bata gudu, gashi sam baya ganin motar Sadeeq. Shi kuwa Sadeeq wasu kwana ya gani guda biyu daya hannun dama daya kuma hannun hagu, ta daman kawai ya shiga da alama yasan hanyar. Mahmoud kuwa da kyar ya wuce mai motar sai dai abin takaicin sam baiga motar Sadeeq ba sai kwanan da ya gani guda biyu ya rasa wace xai shiga, tsayar da motar kawai yayi ya bugi sitiyarin motar tare da cewa "Damn it! Ynx ina xan gansu?". Ba yadda ya iya dole yayi reverse ya koma super market din don bai da tabbacin kwanar da ya shiga. A qofar wani tanqamemen gida suka tsaya, hon ya dinga yi gate man ya dube wawakeken gate din tun kafin ya qarasa budewa Sadeeq ya shiga da motar a tsiyace, da mai gadin bai kauce ba da tuni ya kwashe shi a gurin. Naana dake bayan mota tana ta rusar kuka har muryarta ta fara dishewa taji an fincikota daga cikin motar an yo waje da ita, a firgice ta daga kanta tana kallonshi ya wani daure fuska. Turjewa ta dinga yi tana hada shi da Allah akan ya barta ta koma gida amma kamar ba dashi take ba sai ma qara janta da yakeyi har suka shiga cikin falon. (Muna cikin tashin hankali dana dauko muku tsaruwar gidan.) Bai tsaya da ita falon ba ya wuce da ita upstairs, a qofar wani daki ya tsaya tare da fiddo keys daga pocket dinsa ya bude dakin zai tura ta ciki ta qi shiga ciki cikin kuka tace " Don Allah Sadeeq kayi hkr karka kasheni ka maida ni gida don Allah. " Wata muguwar dariya yayi tare da cewa "Ta yaya xan kashe ki bayan kinsan ina sonki? Ai na riga na fada miki sai na aureki ko bakya so, kuma duk wanda yayi gigin shiga tsakanina dake a shirye nake dana qaddamar masa wato na sheqe shi har lahira". Cikin disasshiyar murya tace " Allah ya kiyaye na aureka, Allah ya tsareni da auren mugun mutum axxalumi makashi irinka wllh na tsaneka Sadeeq bana.........." Kasa qarasa maganar tayi sakamakon wani wawan mari da ya kife ta dashi ba shiri ta duqe qasa bakinta har ya fara xubar da jini, kukan ma tsayawa yayi sai dai xafafan hawayen dake xubo mata. Haka ya jata har cikin dakin sannan ya juya xai tafi, har ya kai bakin qofa sai kuma ya tsaya tare da waigowa yace "Ina mai tabbatar miki duk ranar da kika qara cewa bakya sona sai na illataki, baxan kashe ki ba amma xan illataki, kuma daga yau ki fara qirga nan da next week zaki xama matata, hope kin gane ai ko?". Bai jira amsarta ba ya fice tare da kulle dakin da key ya barta nan tana hawaye. Bangaren Mahmoud kuwa koda ya koma ya iske su Zee hankali tashe suna neman Naana, ya qarasa wajensu, da sauri Zee ta tareshi ta riqo hannunsa hawaye na fita a idanuwanta tace " Yah Mahmoud Naana ta bace bamu san inda ta shiga ba". Dafa kafadunta yayi yace "Ki daina kuka kinji Zee insha Allah xa'a sameta nan ba da jimawa ba". Share mata hawayen yayi, Faheem ya riqo hnnunta tare da cewa " Aunty Zee ina Auntyna take ni ban ganta ba". Rungumeshi Zee tayi ta kasa yin magana ma, Mahmoud ya duqa saitinsu tare da jawo hannuwan Faheem yace "Sorry my boy Auntynka na nan dawowa kaji?". Gyada masa kai kawai yayi sannan ya rungumeshi, shi ma idanunsa sunyi ja, yana tunanin ta inda xai fara nemo Naana. Haka ya tasa su Zee suka wuce gida a motarsa bayan ya kira driver dinsu yazo ya tafi da motar Zee. A bakin gate ya saukesu yace zai je police station don kai rahoto. Su kuma suka wuce cikin gidan suka fada ma Mummy itama hnkalinta ya tashi duk suka yi jugum har Faheem da yake ta tambayar Auntynsa. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [08/10 10:50 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣2⃣🌹 OHW 📚 Tana nan xaune a dakin har wajen magrib, ta miqe ta shiga toilet din dake dakin tayi alwallah ta dawo dakin ta shimfida kallabinta ta yi sallar magrib, ta dinga addu'o'i tana hawaye har aka kira isha'i s tashi tayi sallar, tana cikin yin wutri aka bude qofar dakin aka shigo, da sauri ta idar sannan ta shafa addu'o'i ta waiga don ganin wanda ya shigo. Sadeeq ne tsaye a kanta maida kanta tayi qasa, ya xauna kusa da ita, jin hakan yasa tayi saurin matsawa, kallonta ya tsaya yi can yace "Wai guduna kike?". Banxa tayi dashi, yayi murmushin mugunta ya ajiye ledar dake hannunshi yace "Okey tunda baki magana ga abinci nan in xaki ci kici". Ya miqe xai tafi sai a sannan Naana ta samu bakin magana tace " Sadeeq don Allah ka mayar dani gida". Waigowa yayi ya kalleta da murmushin da ta tsana a fuskarsa, yace "Gida kuma? Ai keda gida kuma har abada, kuma ko na maidaki gida ma wajen wa xan maida ki?". Hawaye suka xubo mata tace " Ka maidani inda ka dauko ni mana". Dariya yayi yace "Baxan maida kiba".Naana cikin bacin rai tace " Wai kai wane irin axxalumin mutum ne? Sam baka da tausayi ko kadan? Ka sani Allah na sama na kallon duk cutar da kake min kuma sai Allah ya bimun haqqina don shi Allah ba axxalumin bawansa bane". Dariya Sadeeq yayi yace "kanki ake ji dai, kuma waye wannan yake binmu daxu dana dauko ki?". Banxa tayi dashi. Ya matso kusa ds ita tare da cewa " Kinsan na tsani wannan abun ko? Na tsani ina ma mutum magana yayi shiru dani, babu wanda yake min haka sai ke don hk ki kiyaye kuma ki riqa yin duk abunda na sanya ki saboda a ynx kina a matsyin matata ne, kin gane ko?". Ya qarashe maganar ido daya a kanne. Wani wawan kallo tayi mashi tace "Allah ya kiyaye na aureka wallahi na tsa............ ". " Kul karki kuskura ki qarasa kin manta abinda na fada miki ne daxu? ". Naana kuwa ji take kamar ta shaqe Sadeeq ya mutu kowa ma ya huta. Tashi yayi ya fita daga dakin ya kulle qofar d key. Kuka ya qwace ma Naana, ta daga hannunta sama cikin muryar kuka tace " Ya allah gani gareka, kayi duba gareni ya Allah ka kareni daga sharrin wannan bawan naka macuci, ya Allah ka nuna min qarshen Allah ka bimun haqqina". Tasha kuka ranar kamar ranta xai fita. Abincinma ture shi tayi gefe guda taqi ci duk da yunwar dake addabarta. Tayi xaune a gurin barcin ma yayi qaura a idanuwanta. ****** Bangaren su Mahmoud kuwa duk inda ake tunanin za'a samu Naana an duba amma ba'a ganta ba duk hankalinsu ya tashi matuqa. Wasa 2 har an dauki kwana uku ba Naana ba labarinta, Mahmoud daka ganshi kasan yana cikin tashin hankali don kuwa har ya dan rame cikin kwanakin su Mummy har mamakinshi suke har saida ta kasa daurewa ta tambayeshi me yake damunshi haka yace ba komai kawai yanayin aikinsa ne. Naana kuwa in ka ganta sai ka rantse da Allah ba ita bace, sam bata cin abinci ko ince baya bata abinci tunda ya kawo mata sau biyu taqi ci daga nan ya daina kawo mata sai dai ruwa kawai da take sha, tayi baqi ta rame sosai kullum bata da aiki sai na kuka da tunanin rayuwarta ta baya. Ita ynx wa xata baiwa labarin rayuwarta wanda xai taimaketa?. Mahmoud ne xaune cikin motarsa a gefen titi ya kishingida jikin kujerar motar tunani ya ishi xuciyarshi. Kamar ance ya dago kansa kawai sai ganin Sadeeq yayi yana tafiya cikin mota yayi hanyar da yabi lokacin da ya dauke Naana. A hankali ya tada motarsa yabi bayansa ta ynd ba xai gane yana binsa ba, kwanar daman ya shiga, Mahmoud yabi bayanshi, a dai dai qofar gidan ya tsaya yana hon mai gadi ya bude mashi ya shiga. Mahmoud na ganin gidan da ya shiga yayi parking can gefe sannan ya daga wayarshi ya kira police yayi masu kwatancen gurin da yake, ba tare da bata lokaci ba suka iso gurin nan suka nufi qofar gidan. Dedicated dis page to Nana Zeey😘 _~written by Beelybadaru😍~_ [10/10 10:30 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣3⃣🌹 OHW 📚 Naana na nan xaune a dakin kamar kullum ta hada kai da gwuiwa tana rera kuka taji an bude dakin an shigo. Da sauri ta daga kai ta kalli mai shigowar duk da tasan ko waye. Yau fuskar nan tashi a daure take ba alamar fara'a ya qaraso inda take ya xauna kusa da ita, da sauri ta matsa duk cike take da tsoron sa. Kallonta ya tsaya yi, sai kuma ya qara matsawa yakai hannu xai taba ta, ta miqe da sauri tana cewa "Don't touch me Sadeeq i hate u". Sai kuma tayi saurin rufe bakinta tuna abinda ya fada mata in ta qara cewa bata sonshi.......... Wani gigitaccen mari daya sakar mata ne y hana ta qarasa xancen xucin da take, qara ta saki ta durqushe qasa har bakinta ya fashe, gefen idonta har ya dan kumbura. Muryarshi ta tsinkaya yana cewa " Ai na fada miki duk ranan da kika kuma cewa baki sona sai na illataki, bari ma ki gani. Miqewa yayi ya xare belt din jikinsa ya fara bugunta dashi, kuka take tun tana yi da qarfi har ta koma yi a hnkl. Sai kuma ya dakata yace "Wannan bugun baxai yi maki ba, bari naje daki na dawo yau sai na miki abinda dole kisoni". Fita yayi a dakin ya barta nan jina jina tana kukan xuci, numfashinta na baraxanar daukewa. Ji tayi an kuma bude qofar da sauri ta rintse idonta tana kuka tana cewa " Plx kayi hkr don Allah kar ka cutar dani, kar ka kasheni kamar ynd ka kashe iyayena na roqeka Sadeeq". Kamar daga sama taji muryar Mahmoud na cewa "Naana bude idonki nine". Duk da haka bata yarda va don gani take kamar Sadeeq ne, ta bude idon nata da yayi jajir don kuka da marin da tasha. Ta ganshi xaune gefenta idanunshi har sun chanja kala saboda tsabar tausayin Naana da kuma haushin Sadeeq. Hannu ya miqa mata tare da cewa " Taso muje Naana". Waigawa tayi ko'ina bata ga Sadeeq ba a dakin, ta kalli Mahmoud da mamaki, to kodai Sadeeq ne yayi shigar Mahmoud don ya cutar da ita?. Matsawa tayi gefe ko'ina na jikinta na mata xafi saboda bugun da tasha. Ganin hakan yasa Mahmoud ya miqe tare da cewa "Believe me Naana, nine Mahmoud ba Sadeeq ba, kixo muje gida kinji Sadeeq yana hannun police. Shiru tayi ta tsaya tana kallonshi har ynx dai kokwanto take, Mahmoud ya riqo hannunta da niyyar taimaka mata ta tashi, a firgice ta fixge hannun nata tana ja da baya. Bai damu da hakan ba don yasan tana cikin tashin hnkl ne shiyasa, Tafiya ya soma yi har ya kai bakin qofa ya waigo yace " Tunda baxaki taho mu tafi ba, ni xan tafi na barki da Sadeeq din". Ai bata san ma lokacin da ta miqe ba ta taka qafarta don xuwa wajen Mahmoud, sai dai me? Jiri taji ya kwasheta ta, kafin Mahmoud ya qaraso gurinta tuni ta xube qasa bata numfashi. A gigice ya qarasa wurinta ya tallabota, ko kadan bata numfashi, hankalinsa in yayi dubu ya tashi, cak ya dauketa ya fito waje da ita, a harabar gidan ya iske police riqe da Sadeeq da suka sanya ma ankwa. Daya daga cikin police din ya bude ma Mahmoud bayan motarshi ya saka Naana a ciki ya rufe sannan ya koma ya shiga driver sit ya ja motar a 360 ya fice daga gidan. Sadeeq kuwa baqin ciki ne ya cika masa xuciya lallai sai yayi maganin yaron nan don kuwa ba a tabashi a wanye lafiya, kuma yau din nan xa a belinsa daya fito xai yi maganinsa don baiga wanda ya isa ya rabasa da masoyiyarsa ba. Shi kuwa Mahmoud yana fita asibiti ya nufa, yana isa Nurses suka tarbesa suka dora Naana a stretcher(gadon daukar mara lafiya) aka wuce da ita emergency don bata taimakon gaggawa. Zarya yake tayi a bakin qofar, wayarsa ya dauko ya kira Daddynsa da Mummy ya fada musu, ya fada musu asibitin da suke. Ba a fi minti biyar ba sai gasu sun iso asibitin harda Inna. Duk kaga Mahmoud sai ka tabbatar da yana cikin tashin hankali, Mummy ta damu sosai ganin dan nata cikin wani yanayi, to miye nashi ma na shiga tashin hnkl haka?. Matsawa tayi kusa daahi ta dafashi tare da cewa "Haba Mahmoud damuwar tayi yawa ya kamata ka rageta hakanan". Kallon Mummynsa yayi tare da cewa " Mummy dole na damu sosai,Mummy dole n damu da ciwon Naana". Kafin Mummy tayi magana Dr ya fito daga dakin fuskarsa dauke da damuwa. Mahmoud ne ya fara tarbarsa da tambaya "Dr ya jikin nata?". Dr. Ya danyi jim can yace " Ku sameni a office dina". Yana kaiwa nan ya wuce office dinshi, suka bi bayanshi don jin abinda xai fada masu. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [10/10 7:44 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣4⃣🌹 OHW 📚 A hnkl suka shiga ciki duk suka samu kujeru suka xauna, Dr. Bilyamin ya dago da kai ya kallesu daya bayan daya sannan ya fara magana kamar haka:- "Wai shin kuna son wannan er taku kuwa?". Duk suka kalli Dr da mamaki Mahmoud yace " Kamar yaya Dr? In da bamu sonta ai da baka ga mun kawo ta hospital ba har kuma mu nuna damuwarmu akanta ba". Dr ya kalli Mahmoud yayi murmushi yace "Calm down my frnd, in da ace kun damu da ita da baxaku bari ta kasance cikin wannan halin ba". Daddy yace " Ynx dai Dr ba dogon xance ba, ka fada mana me yake damunta". Dr. Ya danyi shiru sai kuma yace "A gsky nayi mamaki sosai ace yarinya da bata wuce 16 ba amma ace ta kamu da cutar hawan jini". Hada baki sukayi wajen fadar " Hawan jini kuma Dr?. Dr ya gyada kai tare da cewa "Yes of couse hawan jini gareta sakamakon yawan tunani da damuwar da ta addabi xuciyarta, ga kuma tsananin yunwa da firgicin data tsinci kanta a ciki na tsawon kwanaki". Duk sukayi shiru suna naxari, su dai Naana bata taba gaya musu tana cikin damuwa ba hasali ma ko nunawa bata taba yi ba. Zee tace " Gsky Mummy ina tunanin akwai wani abu da Naana ke boye mana, wanda Faheem yana qoqarin fadi amma saita hanasa". Mahmoud yace "Tabbas nima ina xargin akwai wani abu da ta boye, kai bama xargi bane daxu da xan daukota naji tana cewa Sadeeq kayi hkr kar ka kasheni kamar yanda ka kashe iyayena, it means akwai wani abu daya da ita a baya". Gyada kai sukayi gaba daya. Dr yace " Abinda ya kamata dai shi ne inta samu sauqi ta fada muku damuwarta ku kuma kuyi mata abinda take so don samun lafiyarta". Suka amsa da "To Dr". Mahmoud yace " Dr xamu iya shiga mu ganta?". Dr. Bilyamin yace "Xaku iya shiga ku ganta mana sai dai banda hayaniya". Tashi sukayi gaba daya suka fita suka nufi dakin da aka maida Naana. A kwance take an sa mata drip, tayi wani fayau da ita, ba alamar motsi a tare da ita, Mahmoud shine gaba, y qarasa wajen gadon ya zauna gefen gadon tare da qura mata manyan idanuwansa cike da tausayinta. Su Mummy suka sami guri suka xauna. Kallonta kawai yake cike da so da tausayinta Faheem ya taho wajenta ya kwanta a jikinta tare da cewa " Aunty ki tashi kinji, ki tashi mu tafi gida musha ice cream din da Uncle ya siyo mani". Duk tausayinsa suka ji, Mahmoud ya dagoshi ya maidashi a jikinshi tare da bubbuga bayanshi yana cewa "Sorry Faheem xata tashi nan ba da dadewa ba kaji? Kuma xan qaro maku wani ice cream din". Abinka da yaro saiya hau murna. Har kusan magrib Naana bata farfado ba, Mummy tace Zee ta koma gida ts hado kayan abinci. Daddy yace shima fita xaiyi sai ya dawo. Suna fitz bada jimawa ba aka kira sallah, Mummy tace " Son ka tashi kaje masallaci kayi sallah nima bari na shiga nayo alwalla". Tana kaiwa nan ta miqe ta shiga toilet, maida kallonshi yayi kan Naana sannan ya kai hannu ya shafi gefen fuskarta a hnkl yace "Get well soon my Naana, wish u quick recovery". Tashi yayi ya fice daga dakin don xuwa yin sallah Ya bar Faheem a dakin sai Mummy dake toilet. Mummy dake labe na kallonsa ta cika da mamaki kad dai ace Mahmoud son Naana yake? Lallai da akwai babban aiki ita da har ta xaba masa matar da xai aura?. (To fa nan ake yinta🤔) Bayan tayi alwalla ta fito tayi sallah Faheem ma yane yayi alwalla yayi sallar. Tana nan xaune kan sallaya Mahmoud ya shigo da sallamarsa xauna a maxauninsa na daxu. Mummy dai kallon kayi ka gama ta bishi dashi don ita ta riga tayi ma qawarta alqawarin hada auren Mahmoud da diyarta. Har akayi isha'i Naana bata farfado ba, a tare suka dawo Daddy daga masallaci, ita ma Zee driver ya dawo da ita ds kayan abinci, duk suna nan xaune jigum Dr ya shigo bayan sun gaisa ya cire ma Naana qarin ruwan da ya qare ya sanya mata wani wanda ya kasance na uku kenan. Yana fita ta fara motsa hannunta sai kuma ts fara bude Idanuwanta......... Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [11/10 9:59 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣5⃣🌹 OHW 📚 Mahmoud ya fara ganin ta farfado hakan yasa yayi saurin cewa "Naana, Mummy Naana ta tashi". Duk suka waigo suka kalleta suna mata sannu. A hnkl abubuwan da suka faru suka soma dawo mata, qoqarin tashi take Xee tayi saurin riqeta, hawaye suka soma xubo mata da qyar ta iya cewa " Don Allah kar ku bari Sadeeq ya qara daukeni wallahi kasheni xaiyi". Mahmoud yayi saurin cewa "Naana Sadeeq baxai xo nan ba balle ya daukeki, ki kwantar da hankalinki kinji?". Shiru tayi, Mummy tace " Zee hada mata tea tasha kai kuma je ka kira Dr". Tashi yayi ya fita don kiran Dr, Zee kuma ta tashi ta shiga hada mata tea din. Ba a fi minti biyu ba sai gasu sun shigo dakin Dr ya qara dubata sannan ya cire mata qarin ruwan yace a bata tea din tasha. Zee ta miqa mata cup din tea din ta amsa tare da yin godiya sannan ta kafa kai. Tunda ta fara sha bata daina ba har sai da ta shanye tea din tas sannan ta sauke cup din, duk da haka bata ji ta qoshi ba, Dr yace a qara mata, nan aka qara hada mata wani tea'n shima ta shanye sannan ta jita ta dan dago. Mummy ta kalli Zee tace "Taimaka mata ta shiga toilet ta dan watsa ruwa, ai kin taho mata da kayan ko?". Zee ta gyada kai tare da cewa " Eh na taho mata dasu". Nan ta taimaka ma Naana ta shiga toilet sannan ta dauko mata doguwar riga jallabiya ta miqa mata, Naana tayi mata godiya ta rufe qofar. Bayan tayi wankan ta sanya rigar, tayi masifan yi mata kyau, yafa kallabin tayi sannan ta fito ta koma kan gadon ta xauna sai sannu ake mata, tana amsawa. Kwanansu Naana 3 a asibiti, ta samu sauqi sosai jikinta har ya dan ciko, kuma a ranar aka sallamesu bayan Dr Bilyamin ya basu shawarwari sosai da magunguna, yace indai suka kiyaye to insha Allah komai xaixo da sauqi saboda jinin nata ba sosai ya hau ba. Bayan sun dawo gida Naana ta wuce dakinta ita da Faheem tayi wanka ta sanya kayanta sannan tayi ma Faheem wankan, sannan ta nemi guri ta xauna Faheem kuwa ficewa yayi daga dakin. Dan kishingidawa tayi tana tunanin xayuwarta ta baya, ta share hawayen dake fuskarta sannan ta miqe ta dauko alqur'ani ta soma karatu. Zee ta shigo dakin da sallamarta, xama tayi saida Naana ta kai aya sannan ta dago kanta tayi murmushi tare da cewa "ya dai Zee?". Zee tace " Mummy da Daddy sukace naxo na kiraki". Gabanta ya fadi tayi saurin cewa "Allah dai yasa ba laifi nayi ba". Zee tayi murmushi tace " laifin me kuma Naana? Daga kira?". Ta sauke ajiyar xuciya sannan ta miqe suka fita tare. A falo suka iske Mummy Daddy da kuma Yah Mahmoud dake dauke da Faheem suna latsa waya. A qasa tayi ma kants maxauni tare da cewa "Mummy gani". Mummy tace " Naana munsan xakiyi mamakin kiran da muka yi maki, to ba abin mamaki bane kawai muna so ne ki fada mana ko ke wacece". Gabanta ya fadi ta dago ta kalli Mummy, tayi shiru ta kasa magana. Daddy yace "Muna saurarenki Bilkisu, ki bamu labarin rayuwarki may be xamu iya taimakonki ta wata hanyar". Nan ma shiru tayi ta kasa magana sai hawayen da suke xuba a idanuwanta. Mahmoud yace " Naana plx ki fada mana, waye Sadeeq? Ya akayi ya kashe miki iyayenki? ". Tayi saurin kallonshi tare da cewa " A ina kasan yz kashe min iyayena?". Mahmoud yace "A bakinki naji". Shiru ta danyi sai kuma tace " Banso na kumz tuna rayuwata ta baya ba, banso na baiwa kowa lbrin nan ba, amma ba yadda na iya dole na baku lbrn". Ta danyi shiru sai can tace "Yau xan baku *Labari na*"......... Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [11/10 11:05 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣6⃣🌹 OHW 📚 " *Alh Almustapha Yusuf*, Mahaifina ya kasance shi kadai iyayensa suka haifa da mahaifiyarsa Hj Bilkisu, suna da rufin asiri dai dai gwargwado, sana'arsa sayar da takalma ne kuma yana samu dai dai gwargwado, mahaifina yayi karatu amma iya secondary kadai ya tsaya ya cigaba da sana'ar mahaifinsa. Shekararsa 30 a duniya yayi aure da mahaifiyata da ta kasance fulanin daji, suna shigowa gari ne sayar da fura da nono, anan suka hadu da babana suka fara soyayya,cikin qanqanin lokaci ya fara neman aurenta da iyayenta basu yarda ba sai da mamata ta nuna son d take ma mahaifina sannan suka amince akayi bikinsu. A nan katsina unguwar Katarda suka tare gidan mahaifinsa ya gyara dakuna biyu suka xauna a ciki. Shekara biyu da aurenu ta haihu ta haifi danta santalele mai kyau dashi ya biyo mahaifiyarsa duk a ya dan dwbo mahaifin nasa, don shima yana da nasa kyan. Ranar suna yaro yaci suna *Auwal* Ya taso cikin gata sosai bayan yayi shekara biyar aka sanyashi a makaranta, a lokacin ne kuma mahaifin Abbana ya rasu, sunga tashin hnkl sosai haka suka dangana mahaifina ya cigaba da kasuwancin mahaifinsa. Shekarar Auwal 15 aka haifeni, na kwaso kamannin mahaifiyata sak, ranar suna aka samin sunan Kakata wato mahaifiyar Abbana, na taso cikin gata wurin iyayena da kuma Yayana da yake ji dani kamar me. Shekarata biyu kakata itama Allah yayi mata rasuwa, sunsha kuka sosai daga qarshe suka dangana suka fawwalawa Allah komai. Shekarata Uku a duniya nayi girma sosai bakina ba abinda baya iya fada sai dai mai wahala, sai dai fa akwai rigima da rashin ji. Ina da shekara 5 a duniya Abbana ya sanyani makaranta sabda ganin ynd nake da surutu ga rashin ji, yaran unguwa duk tsorona suke don ba a tabani asha lallai don sai nabi yaro har bayan mamansa na rama, kuma duk fitar da xanyi sai na jawo fada Yah Auwal ke tare min, amma fa duk da haka akwaini da tsoro, don ban taba mantawa akwai sanda Yah Auwal yayi tafiya xuwa kano, na fita waje muna wasa da yaran makwaftanmu wata er maqwaftanmu mai suna Hadixa na ruguxa mata gidan yashin da take yi aikuwa ta tashi ta jawoni tana cewa "Ke wa yace ki ruguxa min gidana?" Da yake itama akwai ta da fadan. Na kwace jikina nace "Eh din anje an ruguxa din me xaki yimin?". Ai kuwa Hadiza ta hayeni ta dinga duka duk da ina da qarfi amma Hadixa ta fini qarfi kuma ta girmeni da shekara daya. Sai da tayi min duka sannan ta qyaleni, nan na miqe ina kuka ina mata Allah ya iisa ai kuwa ta biyoni da gudu na shige gida. A tsakar gida na iske Umma, na fada jikinta ina kuka, ta dago da kaina tare da cewa " A a Naanan Umma way taba ki ne?". Cikin kuka nace "Ba Hadixa bace tamin duka kuma ban mata komai ba". Umma tace " A a da dai abinda kika yi mata hakanan bata bugunki". Nace "Umma kawai fa daga na ruguxa mata abu ne shi ne kawai tayi min duka". Umma tace " Ai tayi min dai dai data buge kin, kullum ke ke bugun yaran unguwa naji dadi da aka samu mai bugunki kema". Miqewa nayi ina shagwaba nace "Ai dama Umma kullum so kike a bugeni, da Yayana na nan da sai ya rama min". Abba ne ya shigo gidan nayi saurin xuwa wajensa ina kukan shagwaba, Abba ya daga ni sama tare da cewa " Naanan Abba waya taba minke? Umma ce?". Na turo baki nace "Ba wata Hadixa bace tamin duka ita kuma Umma tace tayi dai dai". Abba yace " Lalala Umman ce tace haka?". Daga masa kai nayi ina kallon Umma. Umma dai dariys tayi kawai. Abba yace "Lallai kice yau xamu bata da Umma tunda ta taba Naanan Abba da yaya". Umma tayi dariya tace " Au yau kuma har fushi za'ayi dani kenan sai kace ni nayi mata dukan?". Nayi saurin cewa "A a Abba kaje ka rama min dukana wajen Hadixa". Abba yayi dariya yace " A a Naana ki bari in Yayanki ya dawo xaije ya rama miki kinji?". Na gyada kai alamar gamsuwa. Abba y saukeni tare da cewa "Tohm Mamana aje ayi wanka a tafi islamiya ko?". Maqe kafada nayi ni baxani ba wai. Abba yace " A a mamana bamu haka fa? Kije ki dawo zan baki sweet kinji?". Tsallen murna nayi naje Umma tamin wanka ta shiryani cikin kayan islamiya sannan na tafi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [12/10 12:58 pm] Beelybadaru😍: [12/10 11:24 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣7⃣🌹 OHW 📚 A hanya na gamu da qawata Aisha da shekarun mu daya muka tafi makarantar tare muna ta labari kamar wasu manya. Muna xuwa muka iske an fara taren makara, jikina ya dau kyarma don ina tsoron bulala sosai, Aisha ta fara yimin dariya, na kalleta nace "Kuma aka bigeni a kanki xan rama". Aisha na jin haka ta nufi wajen malamin yayi mata bulalarta ta tafi ta barni nan ina xare ido. Gashi ya sayyadi Jamilu ne bashi da mutunci wajen bulala, ya daka min tsawa yace " Ke baxaki xo ayi maki ba?". Jikina ya dau kyarma na fara hawaye, ya taso xai bigeni ai kuwa nayi hanyar fita da gudu, sai dai ina cikin gudun wani malamin ya shigo shima duk tare suke da Ya sayyadi Jamilu aikuwa ya sanya ya kamani. Ganin ya kusa kaini wajen Sayyadi Jamilu ya sanya na dage na gantsara masa cixo a hannu ba shiri ya sakeni na fice daga makarantar a guje, ban tsaya ko'ina ba sai a cikin gidanmu. Umma dake fitowa daga daki ta tsaya tana kallona da mamaki tace "Lapiyarki Naana?, ina makarantar?". Na turo baki da shagwaba nace " Ba bugu ake yi ba, ni kuma bana so shi ne na gudo". Salati Umma tayi tace "Ynx Naana shi ne kika gudo? To kiyi maxa ki koma tun kafin na xaneki a gidan nan". Jin tace xata xaneni yasa nayi hanyar fita ina kukan shagwaba, a xaure naci karo da mutum ina dagowa wa xan gani? Kawai sai ganin Yah Auwal nayi, ihun murna nayi na dale jikinshi shi kuma ya daga ni sama yana dariyar farin ciki. Ya kalleni yace "My Naana kukan me kike? Waya taba min ke?". Turo baki nayi nace " Ba Umma bace wai dan naje islamiya naga ana bugu shine shine na dawo, wai ita kuma na koma." Yah Auwal yace "To daina kukan kinji muje na kaiki makarantar babu mai bugunki kinji?". Narke fuska nayi nace " Um um nidai baxani ba tunda ka dawo". Yayi murmushi yace "No Baby Naana muje na kaiki in kin dawo zan baki teddyn da na sawo miki kinji". Dariya na dungayi har dimple dina na lotsawa nace " Yeey yayana muje to inyi sauri in dawo ka bani teddy na". Dariya shima yayi yace "To bari na ajiye jakana tukunna". A tare muka shiga cikin gidan, Umma na ganinshi ta washe baki tana mashi sannu da xuwa ya amsa shima da fara'a, ta kalleni tace " Au ke baki tafi ba dama?". Maqewa na qarayi jikin Yaya, yace "A a Umma ni xan kaita ne". Umma tace " Daga dawowarka ba hutawa xaka dasa daga inda ka tsaya?". Murmushi yayi yace "To ai Umma dole na kaita, kwana biyu fa kenan bamu tare kinga ko dole na rama mata kwana biyunta, ynx ma data dawo xata zo ta fada min wadanda suka tabata in rama mata". Nayi saurin cewa " Yawwa yaya dama wata yarinya ta bugeni a waje daxu kuma Umma tace wai tayi dai dai". Yaya yace "To ki bari ynx dai sai mun dawo sai ki nuna min ita kinji?" Na gyada masa kai ya ajiye jakarsa sannan muka tafi makarantar har aji ya kaini ya baiwa malaman hakuri akan karsu bugeni, Aisha kuwa tasha harara guna don ko magana ma banyi mata ba har muka dawo gida. ******* Lokaci yaja yau gashi har nayi shekara goma a duniya lokacin na gama primary dina da yake baa yin primary six a makarantar hakan yasa aka fara nema min makarantar secondary a nan katsina, cikin qanqanin lokaci kuwa aka samamin wata ta gwamnati mai suna KCK dake nan kusa da unguwarmu. Murna a wajena ba'a magana ranar da xan fara xuwa, nayi shirina cikin white nd blue uniform dina da sandal dina da socks, ga school bag dita da aka xuba min books a ciki da dai sauransu. Ranar ko break qinyi nayi saboda murna sai damun Yaya nake ya ya tashi mu tafi, Umma da Abba dai da kallo suka bimu, kadan yaci shima ya tashi muka fito don tafiya. A qofar gida muka hadu dasu Aisha da yayanta Ahmad itama cikin nata shirin, na gaishe da Ahmad din don duk rashin jina ina da girmama na gaba dani, naja hannun Aisha muka yi gaba muka bar au Yaya a baya sai kace nasan hanyar, sai dai na waigo nayi ta tambayarsa nan xamu bi, daya gaji dai ya jawo hannuna muka cigaba da tafiyar har muka isa da yake ba nisa sosai. A can muka iske Hadixa itama da babansu, ta jawo hannuna da yake ynx shiri muke tunda naga tafini qarfi, muka xauna a tare mu uku akayi mana interview kuma duk abinda aka tambayemu sai da muka fada, js1'A aka sanyani nida Aisha, yayinda Hadixa kuma aka sanya ta 1B, munso a hada mu tare. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~ [12/10 12:49 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 🌹2⃣8⃣🌹 OHW 📚 Yunwa na dinga ji na jawo hannun Yaya tare da cewa "Yaya yunwa". Waigawa yayi ya hango wani shago yace muje na siya miki wani abu, kina ganin breakfast kika qi yi saboda xumudi". Ni dai binshi kawai nayi muka je ya siyamin Cake dan babba da kuma lemu yace na xauna naci, saida naji nayi nat sannan na miqa mashi sauran, gani yayi ko rabin lemun bansha ba cake din ne ma na danci da yawa, yace " Kefa sam bakya son cin abinci, duba fa dan wanda kika sha, amshi ki qara kinji". Na riqe cikina tare da cewa "Yaya Allah na qoshi fa". Yace "shikenan ai bari na saka miki wannan sauran a bag dinki anjima kin qara". Ya jawo skul bag dita ya saka min sannan ya saka min naira hamsin yace " Wannan kuma in anyi break in kinga wani abun sai ki saya kinji?". Na gyada mashi kai kawai muka miqe ya sagala min jakar a kafada ta sannan muka koma wajen su Aisha,sai da Yaya ya tabbatar mun shiga class mun xauna sannan suka fita daga makarantar, Yaya ya hau Napep ya wuce skl shima don yana da lecture. Sai qarfe biyu aka taso mu Yaya shi ya koma ya dauko mu, ina ta bashi labarin makarantar har muka isa gida, su Aisha suka wuce gidansu. Ina shiga daki na jefar da jakar na fada kan kujerar dakin mu ina Washh... Umma ta kalleni tace "Ya dai Naana ba dai an gaji ba?". Na kalli Umma nace " Umma na gaji sosai Allah, yunwa ma nakeji". Umma tayi murmushi tare da cewa "Amma dai ayi sallah tukunna ko kafin aci abincin". Tashi nayi na cire uniform din na daura xani tare da cewa " Umma bari ma inyi wanka daga nan sai inyi sallah inci abinci in huta ko Yaya?". Dariya yayi yace Haka ne kam Baby Naana". Sai da nayi wanka sannan na dauro alwalla doguwar riga kawai na xira ta shan iska don ana yin xafi nayi sallar axahar, bayan na idar naje kichen na xubo mana abinci shinkafa da mai da yaji ne, abincin da na fi so kenan, muka ci nida Yaya muna dan taba hira har muka gama na kwashe kwanonin sannan naje na wanke da sauran da aka bata sannan na dawo daki na xauna kusa da yayana, ina xama aka maido nepa, murna na dinga yi don Yaya ya siyo mana sabon film don haka na tashi na kunna er qaramar tv'n mu da dvd din na sanya mana film din muka fara kallo. ****Kwanci tashi ba wuya yau gashi har mun yi JSCE, yaya shima lokacin ya gama karatunshi aiki har ya samu aikinshi na teaching a government sahara dake nan katsinan kuma yana samun albashinshi dai dai gwargwado. Murna kawai muke, aka bamu kyaututtuka na prft, kyauta ta tafi yawa da yake nice Head girl, yaya shi ke riqemin, munsha Hotuna sosai kamin nan muka tafi gida. A falo duk muka baje kyaututtukan ana dubawa, Abba yace "Ya kamata a hada mata walima ta yin Jsce dinta". Yaya yace " Ai inaga da an bari an hada mata da birthday party dinta tunda saura kwana uku ne". Umma tace "Haka ne kam". Tsallen murna nayi na rungumesu daya bayan daya ina farin ciki. Da dare muna xaune a falo gaba dayanmu ana cin tuwa, bayan an gama, Abba ya kalli Yah Auwal yace " Am Auwal dama ina son yin wata magana da kai". Yaya ya maida hankalinsa gaba daya gurin Abba yace "Abba ina wace magana kenan". Abba yace " Kaima kasan bata wuce ta aure, kullum magana daya muke da kai kaqi ka fiddo matar aure". Murmushi Yaya yayi ya sadda kanshi qasa yace "Abba dama..... " sai kuma yayi shiru yana sosa qeya. Umma tayi dariya tace "dama me?. Murmushi ya kuma yi yace " Na samo matar aure kuma har mun daidaita da ita, dama inaso nayi maka maganar mahaifinta yace na turo in da gaske nake don yana so ya aurar da ita cikin shekarar nan". Abba ya jinjina kai yana murmushi yace "Masha Allah, to ya sunanta kuma diyar waye? Ya tarbiyyarta take?". Yaya yace " Sunanta Fatima er Alh Kabir ce dake nan kusa damu, kuma gsky ina ganin yarinyar tana da tarbiya". Abba yace "Kar dai kace min diyar Alh kabiru ce mai atamfofi?". Yaya yace ita fa Abba". Abba yayi murmushi yace " Ai abokina ne sosai a kasuwa, gsky naji dadi sosai, mutumin kirki ne sosai Allah ya tabbatar da alkhairi". Duk muka amsa da "Ameen". Umma tace " To yaushe yace ka turo din?". Yaya yace "Yace dai kar a wuce satin nan". Abba yace " To insha Allahu xamuje". Na kalli Yaya Nace "Yaya in kayi auren baxaka tafi ka barni ba ko?". Dariya yayi yace " Ai nan xan kawota Baby Naana". Nayi dariya nace "Yawwa Yaya, xata xo birthday dina ko?". Yace " Eh to sai dai na tambayeta kinji?". Nace "Allah yasa taxo na ganta". Duk sukayi dariya suka amsa da " Ameen. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~ [14/10 4:04 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 2⃣9⃣~~3⃣0⃣ OHW 📚 Abba ya miqe ya wuce dakinsa, Umma ma ta bishi, Yah Auwal ya fiddo wayarsa qirar sumsumg galaxy s4, Nayi saurin cewa "Yawwa Bayyah(Bro, saboda kallon indians films da muke yi ne da Yah Auwal yasa muke dan yin indiyancin)sa mana film din nan mu idasa kallo". Ya duba chajin wayar yaga remain 57% yace " Benji(sister)kinga bani da chaji sosai ki bari in nayi chaji sai mu kalla". Turo baki nayi cikin shagwaba nace "Plx mana bayyah nasan xasu maido nepa, ba sai ka sanya ba". Yaya yace " A a nidai ki bari sai munyi chaji tukunna". Tashi nayi daga kusa dashi na koma kan dayar kujerar dakin na nade kafafuna akai tare da turo baki gaba wai ni ala dole fushi nake yi. Dariya taso kucce masa amma ya daure yace "Fushi akayi dani Qanwa?". Shiru nayi dashi don ina son kallon qarshen film din. Ganin na danyi fushi yasa yaji ba dadi don ko kadan baya son ganin damuwa ta. Tasowa yayi ya dawo kan kujerar da nike tare da dafo kafaduna ya juyo dani ina kallonsa yace " Haba mana Qanwa daina fushi dani kinji?". Turo bakin na kuma yi nace "Ni dai um um". Hannunsa ya hade guri guda tare da cewa " baxan qara ba kinji xan kunna miki, magar maf karlo(amma ayi min afuwa)tukunna". Da sauri na kalleshi nayi dariya jin xai kunna mini na riqo hannunsa nace "Yawwa yayana". Ya kunna wayan tare da cewa " Tohm wane daga ciki Shivam ko hamari adhuri kahani, ko kuma bhaagi?". Nayi saurin girgixa kai nace "A a Yaya duk na idasa wadannan jiya da ka bar wayarka gida, ni Bajrangi bhaijan nake so". Da sauri yace " Lah baxan kunna miki shi ba, hakanan ki qara yi min kuka?". Na shagwabe fuska nace "Yaya baxanyi ba fa? Jiya ma abinda yasa nayi kuka, ganin xasu rabu da Munni ne shiyasa". Yayi dariya yace " Aini banga abin kuka anan ba, kawai daga xasu rabu da pawan din, don sun danyi kuka shine kema sai ki kama yi". Kafin nayi magana Umma ta shigo tana cewa "Toh kun fara shirmen surutun naku ko?". Yah Auwal yayi dariya yace " Umma labarin Film muke". Umma tace "Ai sai ku bada himma". Ta wuce uwar daka, na kalli Yaya nace " Yah ka kunna mana". Ba musu ya kunna mana film din muka cigaba da kallo, bamu muka gama ba sai kusan 10 lokacin Umma har tayi barci, kuka kam sai da nayi don ni kuka baya min wuya, duk film din da xamu kalla in dai akwai ban tausai a cikinsa to sai na yi masa kuka, Yaya kau dariya ya dinga yi mun har muka gama, na juya na kwanta akan kujerar ina dan share hawayen dana gama yi barci ya kwasheni a wajen don muna kallon ma ina hamma. Murmushi Yaya yayi ya gyara min kwanciyar tawa don baya so ya tasheni ya shiga daki ya dauko bedsheet qarami ya rufa min don ana danyin sanyi kadan, sannan ya fita daga dakin ya rufe mana qofar sannan shima ya wuce dakinsa ya kwanta. _Bayan kwana uku_ Shirye 2 kawai ake a gidan na birthday party na na cika shekara 13 a duniya da kuma partyn jsce da nayi(Middle candy)· A tsakar gidanmu aka shimfida qatuwar tabarma sabuwa da Yah ya siyo, sai kujeru biyu dake can kusa da qofar dakinmu inda xamu xauna nida yayana rabin raina, sai kuma wasu kujerun guda biyu na Umma da Abba, ga kuma wani benci da aka ajiye a gabanmu ind xa a dora cake din da Yayana ya tafi ya siyo min. Nayi shirina cikin riga da sket na material din da Yaya ya siya min mai shegen kyau, duk da ba wani tsada ne dashi ba kuma ya amshi jikina. Su Umma ma da Abba sunyi shigar su mai kyau abinsu. Wararen qarfe 10:30am yayana ya dawo da wani dan qaramin cake mai kyau dashi an rubuta sunana akai, xuwa yayi ya watsa ruwa sannan yayi shirinshi shima cikin shigar qananan kaya yayi kyau sosai abinsa, nan ya shigo dakin Umma ya daukemu hoto ina ta murna sosai ganin yanda yayana keji dani, lokacin anyi musu albashi ne shiyasa ya samu kudin yi mana wannan siyayyar. Wurin 11 kowa ya hallara gidanmu ya cika da maqota da qawayena Hadixa da Aisha, suma saida suka gayyato nasu qawayen (Gayyar na gayyaro😜😜). Anyi abinci da yawa yanda kowa xai samu sannan kuma aka hada zobo da dinja suma masu yawa, Yaya hada dauko speaker dakinmu ya jona da wayarshi ya sanya waqar m. Shareef kadan kadan kidan ke tashi a wurin. Yah ya miqe daga kan kujerar da yake ya shiga dakinsa ba a jima ba sai gashi ya fito da wani dan qaramin kwali a hannunsa an daureshi da wani pink qyalle mai kyau. Yaxo inda nake tare da riqo hannuna ya miqar dani ya miqa min kwalin tare da cewa "Happy birthday my belove sister, wish u many many happy return of the day, may Allah bless u with health and prosperity in your life". Murmushi na sakar masa cike da jin dadin birthday wished dinsa, na qara riqo hannunsa tare da cewa " Thank u so much my sweet bro, mey bahoot bahoot shukriya". Murmushin shima yayi sannan ya jani xuwa wajen cake din, ana tayi manu tafi, nan na dan duqa a hankali na hure wutar da ke jikin cake din, tuni aka hau tafi ana Happy birthday to you, farin ciki ya cika min xuciya na yanko cake din da er qaramar wuqa ban tsaya dashi ko ina ba sai saitin bakin Yayana, ya bude bakin a hankali na saka masa, shima ya amsa ya yanko ya saka mini a bakin, ya jawo wayarsa ya cigaba da daukarmu pics, su Hadixa ma duk sun yi min birthday wishes sai murna nake. Anci ansha anyi nat kowa ka gani murna yake barin ma ni da Yayana dasu Umma. Haka aka gama cikin farin ciki kowa ya watse gidan ya koma yanda yake. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [15/10 9:37 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 3⃣1⃣~~3⃣2⃣ OHW 📚 Bayan kwana biyu su Abba sukaje nemawa Yah Auwal aure gidansu Fatima, da yaje sun san juna sosai hakan yasa ba'a wani tsaya bata lokaci ba, babanta yace yana son ayi bikin nan da wata uku in ba damuwa. Abba yace a dan qara masu ko wata daya ne, ba musu kuwa ya qara masu ya xama nan da wata hudu xa'ayi bikin Yah Auwal. Gyaran gidan Yah Auwal ya shiga yi, ya fidda daki biyu da kewaye hade da kitchen sannan ya xagaye gurin ya fiddo qofa, da yake gidan yana da dan girma ba laifi, Baba yana sana'arsa ta saida takalma, sosai yana samun cigaba ga kuma Yaya shima yana samun albashinsa mai tsoka, hakan ysa yake aikinsa cikin kwanciyar hankali saboda Abba ma yna taimaka masa da wasu abubuwan. Lehe ma anyi lpylow akwati biyar yayi mata kuma ba laifi kayan ciki suna da kyau sosai. Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yau gashi har bikin Yah Auwal yaxo, don yau ta kama alhamis saura kwana biyu bikin Yaya. Yaya yayi min kaya kala hudu, sannan Umma da Abba suma kala uku uku sannan Abba ma ya qara masu wasu, Yaya yayi mana wata shadda mai shegen kyau nida shi kadai, nayi farin ciki sosai. Gidanmu har ya fara cika da en uwan Umma dake qauye wadanda ni dai tunds muka taso bamu taba xuwa ba sai dai Umma taje, duk sadda xata je muna schul, en uwa da abokan arxiqi duk anxo. Mumyi shirinmu nida Yaya, shi ya sanya wani yadinshi mai hegen kyau, ni kuma na sanya less dina daya siya min kusan kalarshi daya da yadin Yaya Auwal, sai murna nike xamuje wajen kamu gidansu Fatima. A wani babban fili dake kusa da gidansu ake yin kamun, a xagaye yake da katanga da alama gurin dama anyishi me don yin kamu ko wani abun, an qawata gurin da yake baban Fatima yana da dan halinshi ba laifi. Amarya tasha kyau cikin shigar material kalar kayan jikin Yaya komi da komi, ganin hakam yasa na kalli Yaya nace "Lah yaya shi ne kayi muku anko banda ni ko?". Dan murmushi yayi tare da cewa " Ba nayi mana ankon shadda ba? Kuma wannan ma ai yayi kala ko?". Ni dai turo baki kawai nayi, yaja hannuna yaje ya xaunar dani kan kujerar dake kusa da tashi sannan shima ya xauna a tashi kujerar kusa da amaryarshi Fatima. A hankali na matsa kusa da Fatima nace "Aunty Zarah kin ganki kuwa? U look soo beautiful". Aunty Fatima tayi dariya tace " kema kinyi kyau my little qanwa".(Fatima tana da kyau sosai, chocolate colour ce da dogon hancinta da qaramin bakinta, tana ds idanuwa amma ba manya can ba da madaidaicin jiki). Na koma kujerata na xauna nan aka soma gabatar ds kamun, kowa ka gani murna yake anci ansha anyi nat, ansha hotuna sosai, lokaci qanqani muka shaqu da Aunty Zarah( sunan da nike kiranta dashi kenan don naji Yaya yana ce mata hakan)tana da sauqin kai sosai. Haka aka gama kamun kowa ya watse muka fara xuwa gidansu Fatima, yah ya turani cikin gidan nida wata qanwar Aunty Zarah mai suna Ummu kursum, shi kuma ya tsaya da Aunty Zarah suna ta shn soyayyarsu. Har na gaji da xama Yaya bai kirani mu tafi gida ba, gashi mi kuma na qosa na koma wajen Umma. Na kasa haquri na miqe nace ma Ummu kursum xanje waje wajen Yaya na dawo, ta amsa min da A dawo lpy. Ins shirin fita daga falon kenan sai ga Aunty Zarah ta tayi mun murmushi tare da cewa "Harkin fito ganin yayan naki". Nace " To ba shi bane yayi tafiyarsa ya barni ina ta jiransa ba". Dariya Aunty Zarah tayi tace "Tohm to ynx dai kije yana can yana jiranki". Da sauri na wuce wajen Yaya, inata xumbure 2 shi kuma yana bani hkr. (Ni kam beely nace lallai Naana, kai kake bata hakuri ma ai shagwabar tayi yawa, shikenan baxaka yi fira da budurwarka ba? To in akayi auren ya xatayi don ma gida dayane, sis Rabi'ah dake kusa dani ta taboni tare da cewa " To hajiyar surutu sun tafi ai sun barmu, da sauri na waiga naga har sunyi nisa da gudu 2 muka bisu)· Ranar daurin aure ango yasha manyan kaya da babbar riga, ya hadu iya haduwa, nima dai Shadda ta na sanya irin ta Yayan wadda yayi mana, munyi kyau abinmu niko sai farin ciki nake don ina so inga ana sabga gidanmu. Qarfe 12 akaje aka dauro auren *Auwal Almustapha yusuf, da Fateema Kabeer*. Ango baki yaqi rufuwa don murna, nima ganin Yayana cikin farin ciki yasa nima naji wani farin ciki na xiyartar xuciyarta, mutane sai kallommu suke ganin munyi shiga iri daya mun burge kowa kamar nice amaryar. Bangaren Aunty Zarah ma irin shaddar ta sanya da yake mu uku yayi mawa. Da dare aka kawo amarya, bayan an watse yaya kunyar shiga yake da abokansa don gani yake kamar su Umma xasu yi ta kallonsa, Umma kuwa tana dakimta abinta tun lokacin da aka shiga da Fateema batq qara fitowa ba, kirana yayi na fito tsakar gida na ganshi tsaye da leda a hannunshi, yace "Baby Naana xo muje ki rakani wajen amarya". Murna na shiga yi ko gyale ban dauko ba nayi gaba nace " Muje to Yaya". Yaya yace "A a kije ki sanyo gyale, amma karki bari Umma ta ganki". Da sanda na shiga na dauko gyalena da yayi kala da atamfar dake jikina da yake akwai nepa. Haka muka shiga bangaren yah Auwal muka isketa da qawarta daya mai suna Nabeela da kuma qanwarta Ummu kursum. Nan dai muka sha firarmu dasu Ummu kursum Yaya sayi baki amma duk da haka Aunty taqi yin magana. Haka dai duk suka tashi suka fice, Aunty sai da tayi kuka, nima na tashi nace " Yaya barci nake ji bari in tashi in tafi in ka lallashi Aunty sai ka tafi dakinka kaima ka kwanta". Dariya taso ta kucce mishi amma ya dake yayi murmushi yace" toh shikenan qanwa sai na taho". Na tashi nayi ma Aunty saida safe ta amsa min da muryar kuka sannan na fice daga dakin, na shige dakinmu lokacin Umma na uwar daka, hakan yasa nayi xamana falo. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [15/10 6:58 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 3⃣3⃣~~3⃣4⃣ OHW 📚 *********************** I DEDICATED THIS PAGE TO U UMMU~KURSUM(FIRST LADY)LUV U😘😘😘 ****** _Bayan wasu watanni_ Na fito daki cikin shirin islamiyata, nayi ma Umma sai na dawo sannan na shiga bangarensu Yah Auwal don kullum xan tafi makaranta sai na shiga sannan nake wucewa. A tsakar gida na ganta xaune kan tabarma da cikinta da yake wata hudu, amma yana bata wahala, na qarasa na xauna gefenta tare da cewa "Aunty sannu da hutawa". Ta kalleni tayi murmushi sannan tace " Yawwa Qanwa sai makaranta?". Nace "Eh Aunty ina Yaya yake?". Tace " Ya fita masallaci". Nace "Oh hakane fa, bari in tashi in tafi Aunty kada insha bulala". Na qarashe maganar ina yunqurin tashi. Aunty tayi murmushi tace " Ke kuma ga tsoron bulala ba". Nace "Aunty bulalar Sayyadi Jamil xafi gareta Allah". Tayi dariya tace " Toh ai sai kiyi sauri ki tafi dai". Nayi mata sallama na fito. A xaure mukayi kicibus da Ummu kursum, qanwar Aunty, muka rungume juna cike da murna don mun saba sosai tun bikinsu Auntyn, ynx tana ss2 ne ni kuma ina ss1 kuma schl dinmu daya shiyasa muka qara qullewa da ita. Na kalleta nace "Haba Qawa ina kika shige kwana biyu bana ganinki a schl?". Ummu kursum tace " Wllh Qawas ciwo nasha, da sai dai kuji ance na ware". Na dan xaro ido nace "Kice an bude file dinki". Tace " Hmm kedai bari qawas"Nace "To Allah ya sawwaqe, kinga bari in wuce islamiyya kar insha duka". Ummu kursum tace " Wai ke har ynx baxaki bar tsoron bulala ba?". Nace "Ai ni banga ranar da xan daina jin tsoron bulala ba". Ta jinjina kai tace " To ki tafi sai kin dawo mayi fira". Nace "Kina nan har na dawo?". Ta gyada min kai tace " Eh ina nan sai kin dawo". Nace "Yawwa to bari na tafi". Na fice daga gidan, a qofar gida na gamu dasu Aisha da Hadixa xasu biyo min nayi saurin cewa " Toh gani nan na fito ai". Hadixa tace "Ai da baki fito ba din, mutum ga tsoron bulala ga kuma nawa". Na harareta nace " To masifatu naje nayi nawar ke xa a buga ko ni?". Aisha tayi dariya tace "Aikin kenan kullum ku fada dai?". Nace " Ai ita wannan Hadixar ce da son jan mutum fada". Hadixa tace "Ke kuma mafadaciya ko?". Aisha tayi saurin cewa " Kunga ku taho mu tafi in kuma bulala kuke sha'awa tam sai ku tsaya". Haka muka wuce sai qunqunai muke nida Hadixa, Aisha kuwa dariya kawai take mana. Munyi nisa mun kusa xuwa makarantar ne kawai muka ga wani gaye yaci kwalliya sai faman qwambo yake shi gani yake babu kamarsa, bansan lokacin da dariya ta kucce min ba, na dinga dariya, kamar ance ya waigo kawai sai gani na yayi ina dariya. Dawowa yayi wajen mu, ni kuwa tuni na hadiye dariyata tsoro ya kamani, muka tsaya cak har ya qaraso gurinmu, ya daure fuska yace "Ke wa kike ma dariya?". Na kalleshi sheqeqe duk da ina jin tsoro amma duk ds haka sai da nace " Shikenan don kaga ina dariya sai kace da kai nake? Baxanyi dariya ba kenan?". Yace "Ke karki sake kimin rashin kunya wallahi sai inyi qasa2 dake ynx". Idona har ya kawo qwalla nayi shiru ina harararsa, Hadixa tayi saurin cewa " Shamsu kayi hkr ba kai take ma dariya ba, labari muke yi". Shamsu yace"Allah ya soki da yau kin gane kurenki". Yana kaiwa nan ya wuce abinsa. Na sauke wata nannauyar ajiyar xuciya nace "Waih😨 kice yau da naci dukan banxa". Aisha ta kece da dariya tace" Matsoraciya kawai". Ns kai mata bugu ta kauce nace "Wace matsoraciyar? In da ina tsoronshi ai da ban maida mashi magana ba". Hadixa tayi tsaki tace " Ai saboda rashin tsoron yasa naga har xufa kike". Ban kuma ce mata komai ba har muka isa islamiyar, mun ko yi sa'a ba'a taren makara, muka shige aji. Muna xaune wata er ajinmu ta shigo tasha make up a fuska ga wani uban acuci da tasha, nayi tsaki nace "Wai ita wannan kullum sai tayo kwalliya take xuwa makaranta sai kace wacce xata gidan biki".Hadixa tace " To miya ruwanki da Ita Naana?". Nace "Hmm ki barni da ita daga yau bata kuma yin wannan kwalliyar in xata xo makaranta". Ins kaiwa nan na miqe na fita daga class din, su Hadixa ganin hakan yasa suma suka bi bayanta. (Nima dai Beely nace baxa'a barni a baya ba sai na gano mai Naana xatayi). Tohm kuma dai readers ku biyoni don jin me Naana xatayi😀😀 _~Written by Beelybadaru😍~_ [16/10 3:19 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 3⃣5⃣~~3⃣6⃣ OHW 📚 Office din malamai na nufa su Aisha dai bina kawai suke, sai da muka je bakin qofar office din Hadixa tayi saurin riqoni tare da cewa "Wai ke Naana me xakiyi a office din?". Nace " To kudai ku biyoni mana kuga me xanyi". Sakina tayi muka shiga pffice din. Har qasa muka durqusa muka gaisheda sayyadi Aliyu da kuma sayyadi Hamza, da yake su kadai muka iske a office din. Bayan mun gaishe dasu sai duk mukayi shiru, Sayyadi Aliyu yace "Ya dai kun shigo kuma kunyi mana shiru". Na dan daga kai na kalli Ya sayyadi nace " Ya sayyadi dama wata tambaya naxo yi maku". Ya sayyadi yace "Mecece tambayarki". Nace " Wai ya sayyadi wannan makarantar anxo tane don koyon ilimi da tarbiyya ko kuwa ana xuwa ne don yin kwalliya da acuci". Kallona suka tsaya yi can dai sayyadi yace "Ya akayi Bilkisu? Me yasa kikayi wannan tambayar?". Nace " ya sayyadi gani nayi wasu suna suna xuwa kamar xasu gidan biki". Ya sayyadi yace "Wa kika gani yayi?". Nace " wata ce anan ajinmu". Ya sayyadi yace "Je ki kira min ita nan". Na xaro ido waje 😳nace " Lalala Ya sayyadi in na kirata kayi mata fada ai sai ta xaune ni, babbace fa? Sai dai ka kirata da kanka shima sai mun koma aji". Dariya sukayi gaba dayansu sannan yace "Toh shikenan tashi ku tafi aji, daga yau insha Allah babu mai qara yo irin wannan kwalliyar yaxo makarantar nan". Na miqe muka fice dasu Hadixa. A hanya Aisha ke cemin " Ke dai Naana baki rabo da abin dariya Allah". Hadixa tace "Ai ni sai inje ma in fada mata". Da sauri na riqo hannun Hadixa tare da cewa " Don Allah karki fada mata qawas". Nasan sarai Hadixa na iya fada mata din. Sukayi tamin dariya har muka isa aji muka xauna. Bamu dade da sai gashi ya sayyadi yaxo da kanshi ya kira yarinyar, ba a jima ba sai gata ta dawo fuskarta qwalam ba alamun kwalliya. Dariya taso ta kucce min na duqe nasha dariyata. Haka dai malamai suka shigo suka yi mana karatu. Sannan aka tashemu muka tafi gida. A gidan na iske Ummu kursum har lokacin bata tafi ba, nan muka sha firarmu sosai. Haka lokaci yayi taja har watan haihuwar Aunty ya tsaya, tana shan wahalar cikin sosai don tashi ma sai an taimaka mata haka xamama, duk mun damu sosai, barin ma Yaya da kullum yana gida sai da qyar yake xuwa schl teaching shima ba dadewa yake ba yake dawowa ya baroni can. Wata ranar juma'a muna xaune nida Aunty a falonta, muna fira lokacin Yaya ya dan fita, kawai sai ganin Aunty nayi tana ta yamutsa fuska tana riqe qugunta da cikinta, nayi saurin cewa "Aunty minene? ". Murmushin dole ta qaqaro tace " Bakomai Naana cikina ne kawai kemin ciwo da bayana". Cikin muryar tausayi nace "Sannu Aunty bari naje na kira Umma". Ban jira jin amsarta ba na fice da sauri na naje na kira Umma, cikin sauri Umma ta jawo hijab dinta muka shigo bangaren Aunty. A tsugunne muka isketa a gurin tana numfashi sama 2, Umma tayi saurin riqota tana mata sannu, ni kuwa tuni hawaye sun wanke min fuska ta, Kamar daga samasai ga Yaya ya fado gidan da sallama, turus ya tsaya ganin Aunty hannun Umma tana nishi sama 2, a firgice y qarasa wajen tare da riqota yana tambayar Umma abinda ya sameta, Umma tace " Naquda ce, muyi maxa muje asibiti". Duk ya rude ya rasa mai xaiyi, ganin hakan yasa Umma ta shiga dakin Aunty ta dauko mata hijab taxo ta sanya mata sannan ta taimaka mashi suka daga ta don tayi nayi da yawa. Haka muka fito da ita, munyi sa'a muna fita sai ga taxi taxo da saura muka tarbeta aka saka Aunty baya nida Umma muma muka xauna a bayan sai Yaya gaba, muka nufi asibiti. Muna isa wasu nurses suka tarbemu aka dorata kan strecher, aka wuce da ita lavour room, mu kuma muka tsaitsaya waje, Yaya sam ya kasa xama sai xarya yake a bakin dakin hawaye na xuba a idonshi don ba qaramin so yake ma Aunty Zarah ba, ni kuwa tun a gida nake kuka da addu'ar Allah ya sauki Aunty lafiya. Umma ce ta dinga lallashin Yaya duk da itama duk ta damu sosai. Nan ta sanya shi ya kira Abba a waya ya fada masa, sannan ya kira gidansu Aunty Zarah, ba a dau lokaci ba sai gashi duk sunxo, Ummu Kursum itama tuni ta fara kuka, ta kira Nabeela ma ta fada mata, sai gata itama taxo ita da wata qanwarta Hauwa'u, muna mutunci sosai dasu don suna yawan xuwa wajen Aunty. Tun wajen 11 aka kawo Aunty amma har bayan la'asar bata haihu ba, dr har yace ayi mata C.S kawai sai kuma cikin taimakon Allah ta haiho danta namiji qato mai kyau, sak Babanshi ya dauko, nan fa kowa ya shiga murna, bayan an shirya yaron aka kawo mana shi, ni ce farkon daukarshi, da qyar na bada shi, Yaya kuwa shi kawai so yake yaji ya jikin Aunty, bayan an maida ta dakin hutu Dr yaxo yace "Ina mijin patien din yake?". Yaya yai saurin cewa " Gani nan dr ya jikinta yake?". Dr yace "Tana son magana da kai". Yabi bayan dr din har xuwa dakin. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [17/10 2:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 3⃣7⃣~~3⃣8⃣ OHW 📚 A kwance suka isketa ana mata qarin ruwa, kai daka ganta kasan ta galabaita matuqa don bude idonta ma da qyar takeyi, da sauri Yaya ya qarasa wajen gadon tare da xama qasan gadon ya riqo hannunta idanunshi na xubar da hawaye ya fara yi mata sannu. Kallanshi tayi a hnkl tare da yin murmushin dole tace "Masoyina kukan me kake?". Duqar da kanshi yayi qasa ya share hawayen sannan ya dago yace "Masoyiya dole xanyi kuka, ganinki a cikin wannan halin ba qaramin tada min hankali yake ba". A hankali ta daga hannun nata da ya riqe ta share masa hawayen fuskar tare da cewa " Kana so kace min idan na rasu kuka xaka min?". Da sauri yace "Ki daina fadar haka, insha Allahu baxaki mutu ki barmu ba nida danki". Murmushin dole tayi tare da cewa " Hmm To ai mutuwa tana kan kowa masoyi, kasa a ranka a kowane lokaci xan iya mutuwa ko kuma kaima xaka iya mutuwa". Yace "Na sani Amma dai ki bar wannan xancen". Shafo fuskarshi tayi tare da cewa "Masoyi inaso ko bayan raina kasa ma dana sunanka sai ku ringa kiranshi da FAHEEM, don Allah na roqeka bana son yayi kukan rashin uwa, ka bashi duk wata kulawa, in kamin haka ka gama min komai a rayuwa". Da sauri ya rufe mata baki tare da cewa " Ki bar fadar haka My Zarah, baxaki mutu ba insha Allah". Tayi murmushi tare da cewa "Ina son ganin dana da kuma en uwa na". Wata nurse ce ta shigo Yah Auwal yace " Plx kice su shigo". Ba musu ta fita don kiranmu. Muna nan xaune taxo tace muje, duk muka bi bayanta har xuwa dakin, duk jikina yayi sanyi ganin yanda Aunty Zarah ta koma, tayi wani irin haske. Duk muka je muka xagayeta muna mata sannu cike da tausayawa. Murmushi kawai take mana tana amsawa a hnkl. Can ta kalloni sannan ta kalli yaron da yake yana a hannuna a lokacin, tayi min alama da kai inxo, ba musu na matsa wajenta na miqa mata yaron ta dinga kallonshi kana ta tofeshi da addu'o'i sannan ta kalleni ta raba hannunta dana yaya ta riqo hannuna tare da cewa"Naana inaso kimin abu daya don Allah". Da sauri nace "Aunty Zarah wani abu kike so nayi miki?". Hawaye har sun fara xubomin. Tace "Ina so ki lallashi yayanki, karki bari yayi kukan rashina, ko bayan raina inaso ku riqemin Faheem da amana bana so yayi kukan *maraici*, inaso ya taso cikin farinciki". Nayi saurin cewa " Aunty meyasa kike yin wannan maganar kamar kina bar mana wasiyya? Don Allah ki bari karki tafi ki barmu, we need u in dis life, more especially Faheem da kika haifa". Murmushi tayi tare da kallon su Ummu da su Nabeela, duk suka matso kusa da ita suna sharar hawaye, tace "Don Allah Kubar kukan nan banaso" duk suka share hawayen sun ma kasa magana. Ta kalli su Umma da maminta dasu Abba da suka iso tace "Umma Mamy dasu Abba don Allah in nayi maku wani laifin ku yafe mini ni nasan baxan tashi ba". Maminta tayi saurin cewa" ki daina fadar haka Fatima ciwo ba mutuwa bane xaki tashi in Allah ya yarda". Tayi murmushin da daka ganshi sai ka gane tana jin jiki tace "Ni kadai nasan me nake ji a jikina Mami, kudai kuyi min addu'a". Umma tace " Fatima dole xamuyi maki addu'a amma don Allah kibar fadar haka". Murmushi kawai tayi tace "To Umma". Su Abba ma duk jikinsu yayi sanyi da kalaman Fatima. Aunty ta maida kallonta ga Yaya da yake ta share hawaye, ta share masa hawayen tare da cewa " Haba mana masoyi ka daina kuka mana sai kace ba jarumi ba? Plx kayi min murmushinka ko sau daya ne naji sanyi a raina, bai san lokacin da yayi mata murmushin ba, itama tayi masa hawayen na fita a idonta, shima ya shiga share mata hawayen. Ta maida kallonta ga Faheem dake barci ta sumbaci fuskarsa a hnkl take furta kalmar shahada daga nan bata kuma cewa komai ba haka kuma bata daina kallon Faheem ba, a dai2 lokacin kuma Faheem ya tashi daga barcin ya tsanyare da kuka, Mami tayi saurin daukarshi, tana kallon Fatima da ta daina motsi, a firgice ta kalli su Abba tace "Alh bata motsi fa?". Nan duk aka kalli Aunty na tabata nace " Kai haba tana da ranta fa". Abba yace "Bari dai na kira likita. Ba a fi minti biyu ba sai gasu sun shigo da Dr. Nan ya shiga duba Aunty Zarah, cikin fuskar damuwa ya dago ya rufe ma Aunty Zarah idanuwanta sannan yaja farin bedsheet din da aka rufa mata ya rufe mata fuska. Da mamaki duk muka kalleshi, yaya yayi qarfin halin cewa " Me hakan yake nufi?". Dr ya kalli Yah ya dafa kafadarsa tare da cewa "I'm sorry to say....... " yaya yayi saurin katse shi tare da cewa "Nooo!! Don't tell me my Zarah is die, krka fada min hka". Dr, yace " Sai dai kuyi hkr, Allah ya amshi abarsa". Salati kawai ke tashi a dakin da kuma sautin kuka. A hankali Yaya ya miqe tare da dafe kansa yana maimaita kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, a hankali ya fara taka qafarsa tuni idanuwansa suka soma ganin dishi2 ya tafi luuuu ya fadi qasa baya motsi.......... Wayyo Aunty Zarah, wayyo Yah Auwal😱😱😭😭 Dedicated to all my fans😘 _~written by Beelybadaru😍~_ [17/10 9:12 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 3⃣9⃣~~4⃣0⃣ OHW 📚 A firgice nayi kanshi ina jijjigashi ina kuka amma ko motsi baya yi, nan likita ya kira wasu nurses maxa sukaxo aka daukeshi aka nufi A&E likitoci suka duqufa kanshi don ceto rayuwarsa, ni kuwa ba abindanake in ba kuka ba, inq rungume da dan Aunty Zarah da yake ta faman kuka, na rasa yadda xanyi mashi yadaina kukan, na dan duqar da kaina saitin fuskarsa na sa mashi lip dina na qasa tuni ya fara tsotsa da qarfinsa, da sauri na janye baki na jin xafin da nayi, aikuwa ya qara fashewa da kuka, ta sanya mishi babban dan yatsanshi a baki ya dinga totsa yayi shiru. Wata Nurse ce taxo tace "Ya kamata a siyo madararda xa a baiwa yaron nan". Abba yace " Bari to naje na siyo". Fita yayi daga asibitin don xuwa siyo madarar. Ummu Kursum tazo ta xauna kusa dani tana kuka ta amshi Faheem daga hannuna tana kallonshi tace "Allah sarki Auntyna kin tafi kin barmu cikin kewarki, Faheem xai taso cikin maraici". Da sauri na kalleta tare da cewa " A a Ummu Kursum ki daina fadar haka, insha Allahu Faheem baxai taso cikin maraici ba, nida Yaya daku kanku xamu xame masa uwa mu xame masa uba, insha Allahu baxaiyi kukan rashin mahaifiya ba". Ummu tace "Allah ya bamu ikon riqe wannan yaro cikin so da qauna". Na amsa da " Ameen". A hnkl ya soma bude idanu, tun yana ganin dishi 2 har y koma yana gani nrml, ina xaune a gefensa nida su Ummu ina riqe da hannunsa har lokacin hawaye na xuba a idona, nayi saurin cewa "Sannu Yaya, plx wake up, karka tafi ka barmi yaya". Komai ya dawo mishi tar a brain dinshi, kuka ya fashe dashi kamar qaramin yaro yana cewa " Me yasa kika tafi kika barni Zarah? Meyasa baki bari kinyi rayuwa da danki ba? Me yasa......... Da sauri na rufe masa baki ina cewa "Yays kabar wannan maganar addu'a xamuyi mata". A hnkl ya janye hannuna daga bakinsa yace " Allah ya jiqanki My Zarah, Allah ya haskaka qabarinki". Duk muka amsa da "Ameen". Su Hadixa ne da Aisha suka shigo dakin da sallamarsu fuskarsu ta nuna alamun sunyi kuka suma, nan suka gaishe dasu Mami dayi masu ta'aziyya, sannan sukayi ma Yaya ya jiki ya amsa musu. Yaya ya kalli su Abba yace " Abba an kaita?". Abba yace "A a Auwal mun jira ne muga xaka farfado kafin sallar magrib". Nan ya daddafa a hankali na riqeshi ya tashi tsaye, ya kalleni da hawaye a fuskarsa yace " Thank u sis". Dagel nayi na share masa hawayen fuskarsa nace "Yaya ka daina kuka banaso, Aunty tace na riqa lallashinka kar in bari kayi kuka". Ji yayi wani kukan na niyyar xuwar mishi da sauri ya kalli su Abba yace " Daddy ku muje magrib ta gabato". Ba musu suka fita don xuwa kai Aunty Zarah makwancinta, duk da baya jin dadin jikimsa ko kadan. _1 week later_ Mun koma gida kullum cikin yi ma Aunty addu'a muke, Yaya kullum sai yayi kuka kuma Yana riqe da Faheem, anyi suna amma ba a yi taron suna ba, an dai rada suna kawai. Yauma yaya yana xaune a dakin Umma yana riqe da Faheem yana bashi madararshi, don kuwa shi yake renon danshi da ni dasu Umma don yaqi bayar dashi ga kowa, ni kuwa lokacin ina kitchen ina hada mana abinci, don duk shiriritata Umma tana koya min girke 2, don wani lokacin tare muke shiga kitchen din wani lokacin kuwa ni kadai take bari. Yaya ya kaima Umma dake daki Faheem yace Yana xuwa ynx xai dawo. Ya fito ina kallon ya shiga bangarenshi, hakan yasa na bishi, a xaune na iskeshi a falo ya rungume hoton Aunty yana hawaye, a hnkl na qarasa cikin daki nima tuni idona y ciko da qwalla don ko kadan bana son naga Yayana cikin wani hali. A hankali na dafa kafadarsa, yayi saurin dagowa don bai san na biyo saba, ganin nice ya sanya ya sauke ajiyar xuciya. Na durqusa kusa dashi tare da riqo hannunshi idanuna na xubar da hawaye, na kai hannu kan fuskarshi na share masa hawayen fuskar tashi, riqo hannun nawa yayi cikin muryar kuka yace "Qanwa ya xanyi? Nayi rashin mata bana tunanin xan iya samun madadinta". Nayi hugging dinsa ina kuka nace " Yayana stop crying plx, insha Allah xaka samu koda rabin tane". Bubbuga bayana yayi tare da dago da kaina yace "is okey dear na daina kukan kema ki daina kinji? ". Na gyada mashi kai sannan na miqe nace " Yaya ka tshi mu koma wajen Umma da Faheem, ba musu ya miqe da hoton Auntyn a hannunsa, muka fito muna riqe da hannun juna, shi ya shiga daki ni kuma na koma kitchen. Da dare bayan munyi sallar Isha yaya ya shigo, nan muka yi karatun al-qur'ani, na bashi haddar suratul-baqara, don ynx shirin saukarmu muke don saura sati biyu muyi sauka, shiyasa ynx tun qarfe biyu muke tafiya islamiyyar. ******* _Bayan shekara 2 da watanni_ Kyawuna ya fito sosai na xama em mata a lokacin gab nake da shiga 17yrs, amma in ka ganni sai ka rantse da Allah na kai 18 saboda girman da nayi. Tafe muke nida su Aisha sai murna muke, don daga schl muke munje mun dubo result dinmu na neco kuma duk mun samu. Ji nake kamar nayi tsalle don murna, Allah Allah nake mu isa gida in fadawa Umma da Abba sannan kuma inga Faheem dina. Sauri kawai nakeyi nayi gaba ma nabar su Hadixa a baya, Hadixa ta kirani tana cewa "Ke wai Naana baxaki jira muba?". Na waiga ina cewa " Ke nifa ki kyaleni sauri nake na isa gida". Waigowar da xanyi sai ganin wata mota nayi ta wuce ta gabana a tsiyace kadan ya rage ta bugeni sai d na ja da baya, cikin masifa na daga murya nare da cewa "Wannan wane irin guntun iskanci ne, baxa'a iya yi ma mutum horn ba sai........ " shiru nayi ganin motar na dawowa wajenta, sai da taxo har gabana ta tsaya, dai dai lokacin su Aisha suka iso inda nike. A hankali aka soma bude qofar motar sannan mukaga an fara fiddo qafafuwa.......... Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru 😍~_ [18/10 8:27 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 4⃣1⃣--4⃣2⃣ OHW 📚 Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga motar, idonshi sanye da wani baqin glass fuskar nan tashi a tamke ba alamar wasa a cikinta. Dan qasa yayi da glass din yana qare min kallo from up to down, sannan ya dan tabe baki ya maida kallonshi kan fuskata tare da cewa"Hey babe what r u saying?". Banxan kallo nayi mashi sannan nace "I know u hear all what i'm saying, so basai na maimaita maka ba". Wani shu'umin murmushi yayi sannan yace " Wow gsky kin burgeni, ban taba samun macen da ta maida min magana kamar haka ba, dole na jinjina miki". Tabe baki nayi na kalli su Hadixa nace "Girls kunga ku taho mu tafi barin tsaya sauraren wannan ba yana westing time dinmu ne kawai". Har mun fara tafiya daga baya kawai naji an riqo min hijab dina har yana qoqarin cirewa don iya gwuiwa kawai ya tsaya min, juyowan da xanyi kawai sai ji nayi ya janye hijabin daga jikina, Allah ya soni doguwar riga ce a jikina bata kama min jiki ba, bansan lokacin da na daga hannu na wankeshi da wani wawan mari ba. Duk mutanen dake gurin suka kallo mu. Na fixge hijab dina nayi saurin sanyawa tare da cewa " Kai wane irin mutum ne wai, baka da hnkali ne da xaka ciremim hijabi?". Tsayawa yayi yana kallona cike da mamaki da kuma takaici, shi tunda yake a rayuwarshi ba'a taba marinsa ba, amma yau wata qaramar yarinya ta daga hannu ta mareshi? Lallai dole xaiyi maganinta ko ita diyar waye. Har na juya xan tafi sai ji nayi an kuma janyo min hijabin da qarfi har yana shaqe min wuya, ina juyowa ya wanke ni da wani lafiyayyen marin da ba a taba yi min irinshi ba don har wasu taurari na gani, kafin inyi yunqurin dafe kuncina tuni ya qara xabga min wani marin a take bakina ya fashe jini ya fara fita ta hanci ta baki, sai da yayi min lafiyayyun mari har guda hudu sannan y sake ni na xube qasa a galabaice kukan ma sam yaqi xuwa don har fishi dishi nake gani. Tuni mutane aka xagaye mu, abin haushin babu wanda ya taka mashi burki, cikin tsawa yace "Ke er matsiyata qaryarki ki mareni ki xauna lpy, do u know who am i? To ki sani ni *Sadeeq* babu wanda ya isa ya tabani ya xauna lapiya kuma kema din ba qyaleki nayi ba sai nayi maganinki". Yana kaiwa nan ya bude motarsa xai shiga sai kuma ya waigo ya kalli mutanen gurin tare da cewa " Ku kuma uban me kukeyi a nan? Kun bace daga nan ko sai nasa an illataku?". Sumi2 duk suka watse daga gurin, yaja wani mugun tsaki ya shiga motar ya jata a tsiyace kamar wanda xai tashi sama, mutane akayi ta matsawa ana bashi hny. Su Hadixa suka duqa suka riqoni suna hawaye, Hadixa tace "Kinga abinda nake guje miki a kullum, ke sam baki da hkr". Aisha tayi saurin cewa " Haba Hadixa bai kamata kina fadar haka ba, ynx dai kawai muje gida shi ne". Wani dan dattijo ne ya qaraso wajenmu tare da cewa "Yarinya ke kuwa me ya kaiki ga shiga harkar Sadeeq? Kinsan kuwa ko shi wanene? Duk garin nan babu wanda yakai mahaifinsa kudi, da alamu ke baquwa ce a garin nan don duk garin nan babu wanda bai san Alh Ibrahim Naira ba da kuma dansa, gsky ina jiye miki abinda xai biyo baya". Ni dai binshi kawai nake da kallo bkina na xubar d jini da hancina sam na kasa furta ko kalma daya. Tafe yake yana ta sauri ya koma gida don yasan Naana da Faheem nacan na jiranshi, kamar daga sama ya hango wasu a tsugunne kamar su Naana hakan yasa ya qara saurinsa ya iso wajenmu. A firgice ya durqusa gabana tare da riqoni ganin yanda bakina ya fashe cikin tashin hankali yace " Subhanallahi, Naana me ya sameki haka?". Ina jin muryarshi na dago na kalleshi nayi saurin fadawa jikinshi sai a lokacin kukan yaxo mini, na fara kuka sosai, yayi saurin rungumeni tare da kallon su Hadixa yace "Me ya sameta?". Hadixa ta fada masa duk yadda akayi, ya dago da kaina yana kallon fuskata da tayi kumburi, tuni shima idanunshi sukayi ja yace " Qanwa babu wanda ya isa yayi miki wannan abun na qyalesa dole na rama miki". Da sauri wani mutumi yace "Kai ai baxaka iya rama mata ba, ta yaya xaka rama mata mutumin da ko manyan masu kudi ma bai kyale ba, ya takasu ya xauna lafiya, ka daina tunanin xaka iya rama mata". Yaya yace "Shi waye da zaiyi mata hakan? Idan ya taba wasu ya xauna lafiya to ni baxai taba qanwata ya xauna lafiya ba". Yana kaiwa nan ya miqar dani ya hadani da jikinsa muka fara tafiya, mutumin yace "Dan gidan Alh Ibrahim Naira ne fa?". Da sauri ya waigo y kalli mutumin, tabbas yasan Alh Ibrahim Naira, da kuma dansa, bai ce komai ba muka wuce, chemist muka fara xuwa ya siya min magani sannan muka wuce gida. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [19/10 10:36 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 4⃣3⃣--4⃣4⃣ OHW 📚 A tsakar gida muka iske Umma da Abba sai Faheem dake xaune kan cinyar Umma, ganin mun shigo yasa ya taso da gufu ya rungumemu a tare yana murnar ganinmu, nima dai murmushin dole na qaqaro na rungumeshi ta baya. Umma da Abba suka tsaya suna kallonmu da mamaki ganin ynd muka shigo gidan yaya yana riqe dani. Umma tace "Me ya faru da Naanar ne naga ka riqota kuma fuskarta ta kumbura haka?". Faheem ya dago da kanshi ganin fuskata a kumbure yasa ya kai hannu kan fuskar tawa yana cewa " Adda mi ya sameki?". Er qara nayi don ko kadan banaso a taba min fuskar saboda xafin da nake ji. Abba yace "Wai me ya faru ne haka?". Nan Yaya ya fada masu duk abinda ya faru, Umma ta hau yimin fada tana cewa " Ai kinga irinta nan ke sam bakinki baya iya yin shiru, gashi nan ai kin sami wanda ya fiki wauta". Yaya yace "Haba mana Umma meyasa kike fadar haka? Ya kamata a barta ta huta, kuma ba kyalesa nayi ba dole ne nakai qararsa ga police saboda yayi ba dai dai ba dole a hukunta shi". Abba yayi saurin cewa " Sadeeq din zaka kai qara wajen en sanda? Wahalar banxa ma kawai xakayi don kana kai qararshi za'a sallameshi, kai dai ba baqo bane a garin nan kasan ko waye Alh Ibrahim Naira kaf garin nan babu wnd ya isa y taka shi". Yaya baice komai ba don ya tabbatar da maganar Abba gaskiya ce, hakan yasa ya miqar dani yaja hannun Faheem muka wuce dakin Umma, Umma ta kawo min abinci na, kadan naci yaya da kanshi ya bani maganin nasha sannan na kwanta, tuni xaxxabi ya rufe ni, Yaya duk ya damu sosai ji yake kamar ya dauko ciwon ya dawo dashi jikinshi. Gyara min kwanciyata yayi akan gadon Umma ya lulluba min zanin gado mai kauri daya linka biyu, tuni barci ya sace ni, sai a lokacin ya dan samu relief. Ban tashi ba sai gab da la'asar, naje nayi wanka lokacin xaxxabin ya sauka sai dai rashin qarfin jiki, har lokacin Yaya yana gida bai fita ba, Faheem ma yayi jugum ganin Addarshi ba lafiya duk ya damu. Bayan nayi wankan na zira doguwar rigata ta English wear, na dawo falo inda su Yaya suke na xauna ina dan murmushi, da sauri Yaya yace min "Ya jikin naki Qanwa". Murmushi nayi nace " I'm ok Yaya Nagode da kulawarka a gareni". Da sauri ya rufe min baki da hannunshi tare da cewa "Haba Qanwa, godiyar mi xaki min? Haqqina ne na kula dake, banason kina godemin akan abinda bai taka kara ya karya ba, ke qanwatace in kika ga na daina kulawa dake to sai dai in bana numfashi ne". Hugging dinsa nayi ina jin son yayana na qaruwa a cikin xuciyata, hawaye suka xubo min nace " Yayana ka daina maganar mutuwa banaso kaji". Cikin muryar shagwaba na qarashe maganar, ya dago kaina yace "Wipe ur tears my little sis, kinsan bana son ganin hawayenki, na daina kinji? I promise u barin qara yi miki wannan maganar ba". Umma dake gefenmu tace " Mutuwa kam ta xama dole Naana, A kullum ki riqa tunawa da cewa xamu mutu mu ko ke, ya kamata ki riqa tunawa da mutuwa a duk inda kike, kisani dole ne wataran mu tafi mu barki ko ke ki tafi ki barmu cikin duniyar nan". Kuka ne ya kufce min na shige jikin Yaya inayi tare da cewa "Yayana kace Umma tabar wannan maganar, gwara na rigaku mutuwa don bansan wane irin hali xan shiga ba idan na rasa ku". Yaya duk ya damu ya shiga jijjigani don sam bayason ganin kukana, yace " Umma plx ki daina fadar haka, kin gani kin sanyata kuka ko Umma?". Girgixa kai kawai Umma tayi ta miqe ta shige daki ta barmu nan. Faheem ne ya riqo hannuna yana cewa "Adda ki daina kuka kinji, kinga Abee shima xaiyi, plx Adda banaso". Share hawayen nawa nayi na miqe daga jikin Yaya na rungume Faheem tare da cewa " Shikenan Faheem na daina kaji? Kaima kar kayi". Ya daga min kanshi kawai. Tuni na manta da abinda ya faru muka koma kamar da, Yaya ya siyo mana chocolates da yawa ya kawo mana nida Faheem, muka koma cikin farin ciki. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [19/10 9:23 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 4⃣5⃣--4⃣6⃣ OHW 📚 Bayan kwana biyu na shirya cikin riga da aket dina na atamfa na saka hijab dina na fito na iske Umma a tsakar gida nace "Umma bari naje gidansu Aisha, ynx xan dawo". Umma tace " To a dawo lpy ki gaishe da mamansu". Nace "Zataji Umma". Allah ya soni Faheem yana barci da sai ya bini, ni kuma so nake naje musha fira sosai. Na fito don xuwa gidan ina tafiyata cikin natsuwa, gani nayi kawai ansha gabana, da sauri na dakata da tafiyar da nake don ni har naji tsoro ma, na dago na kalli mutumin daya tsaya min, wani mutum na gani qato yasha wasu baqaqen kaya da bakin glass a fuskarsa fuskar nan tashi a tamke. Nace " Subhanallahi, malam lafiya kuwa xaka xo ka tsaya min a hny?". Wani mugun kallo yamin wanda saida ya dan firgita ni yace "Oga na san ganink acan". Ya qarashe maganar yana nuna min wajen wata mota, nakai dubana gurin, naga wani mutum cikin mota, qafafuwansa kawai nake gani amma bana ganin fuskarsa sai wasu mutane dake zagaye da motar da alama bodyguards ne, nace " Waye ogan naka da xai kirani?". Mutumin yace "Ke iya bakinki kar kiyi ma oga rashin kunya, ynxn nan xaiyi gunduwa 2 dake". Dakewa nayi duk da tsoron da nake ji nace " To koma dai waye ni barin jeba, don hk ka bani hnya na wuce". Ina kaiwa nan na fara qoqarin bi ta gefenshi na wuce, ya kuma shan gabana tare da cewa "Ke Er talakawa? Kixo muje da qafarki ko kuma ynxn nan na kaiki da kaina". Zaro ido nayi waje jin wai xai kaini da kansa nayi baya tare da cewa " Karka kuskura ma ka fara wnnan gigin". Fixgo hijab dina yayi ya fara jana a haka, tsoro ya kamani tuni na fara kuka ina addu'o'i ina kiran Yayana, har muka isa wajen motar sannan ya sakeni, na juya xan bar gurin mutanen suka tare hanyar, cikin kuka nace "Wai don Allah Ku su waye me nayi maku ne?". " kina son sani ne?". Naji wata murya daga bayana hakan yasa nayi saurin waigawa don ganin ko waye, karaf idanuna suka sauka kan fuskar Sadeeq, a tsorace naja da baya har ina buge daya daga cikin bodyguard din, wani shegen murmushi yayi na gefen baki tare da cewa "Ai dama na fada miki baxan taba qyaleki ba, dole ne na rama abinda kika min a bainar jama'a, abinda ba'a taba yi mun ba kenan wato mari". Nayi saurin cewa " Don Allah kayi hkr wllh ba da niyya na mreka ba kaine kaja na mareka". Wata muguwar dariya yayi tare da cewa "Don na cire miki hijab shi ne xaki mareni? To ynx bari na cire miki mu gani xaki qara marina?". Ban ankara ba sai ji nayi kawai ya fixge hijabin dake jikina, nayi saurin duqewa ina kare jikina ina kuka sosai nace " Don Allah kayi hkr ka bani hijabina na sanya don Allah, barin sake ba Allah". Dariyar ya kumayi tare da cewa "Au ynx kuma bakin naki ya mutu? Ai baxan baki wannan hijabin ba har sai nayi abinda nayi niyyar yi miki". Da sauri na kalleshi nace " Me xaka min?". Yace "Au tambaya kike? So ki bari ki gani". Matsowa yayi kusa dani da nufin tabani ganin hakan yasa nayi saurin runtse idona ina karanto duk addu'ar data xomin. Qarar naushi kawai naji, hakan yasa na bude idona da sauri sai ganin Sadeeq nayi duqe a kusa dani bakinshi har ya fashe, waigawar da xanyi sai ganin Yayana nayi tsaye yana huci, aikuwa da sauri na tashi na shige jikinshi ina kuka, shafa bayana yayi sannan ya dauki hijab dina dake qasa ya bani na sanya. Gaba daya wadannan bodyguards din suka yo kan Yaya da nufin xasu bugeshi, Sadeeq yayi saurin dakatar dasu da hannu, ya miqe daga duqen da yake ya shafo jinin dake bakinshi ya kalla sannan ya kalli Yaya ya danyi wani murmushi tare da cewa " blood... My blood, ka fitar min da jini? Abinda ba'a taba yimin ba kenan, lallai kun tafka babban kuskure a rayuwarku, kuskuren da xakuyi dana sanin aikata shi, ke kin mareni, kai kuma ka fitar min da jini, to ku sani ba'a haifi mutumin da xai mareni ba kuma ba'a haifi mutumin da xai fitar min da jini ba, ina mai tabbatar muku baxan taba qyaleku ba dole na lahanta rayuwarku, ku jirani nan bada dadewa ba xan dawo gareku". Yana kaiwa nan ya shiga mota driver yaja motar suka bar unguwar a 360, suma bodyguards din suka rufa mashi baya a tasu motar. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [20/10 2:52 pm] Beelybadaru😍: [20/10 12:27 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 4⃣7⃣--4⃣8⃣ OHW 📚 Yaya ya dago da kaina yana kallon fuskata yace "Naana me kikayi musu? Yauma kin qara jan fadan ne?". Cikin muryar kuka nace " Yaya wallahi ban kuma yi mashi wani abu ba, kawai xani gidansu Aisha ya tarbeni". Yaya ya jinjina kai tare da cewa "Shikenan Allah ya shige mana gaba". Nace " Yaya nifa ina jin tsoro". Ya danyi murmushi tare da cewa "Ki bar jin tsoro Qanwa Allah yana tare damu, insha Allahu ba abinda ya isa yayi mana". Na gyada mashi kai kawai, muka wuce gida mutane sai kallonmu ake kowa da abinda yake cewa don ba wanda bai san Sadeeq Ibrahim Naira ba, ni dai har ga Allah naji dai ana fadinshi amma ban taba ganinsa ba. *WAYE SADEEQ IBRAHIM NAIRAH?* D'ane ga Alh Ibrahim Naira, shahararren dan kasuwa wanda ya shahara a duk fadin jihar kai har ma da wasu states din, Dansu daya Sadeeq yana ds shekara biyu mamanshi ta rasu kuma bai sake wani auren ba, shi yake kula da danshi yana sonshi sosai duk abinda yaso shi yake mishi, baya kwabarsa ko kadan saboda shi irin mutanan nan ne da basu dauki talaka a bakin komai ba. Haka ya girma cikin rashin tarbiyya duk abinda yake so shi ubansa ke masa duk kuwa kudin abun, talakawa kuwa basu daukesu a bakin komai ba. Sadeeq ya qware wajen shaye shaye da kuma raping ya yan mutane, idan kuma yaga yarinya xata yi mashi taurin kai tuni xai sheqeta, kuma babu abinda police xasu iya yi mashi, don ko an kai qararshi a ranar xa ayi bailing sa. _Wannan kenan_ ************ _2 days later_ Muna xaune ni da Faheem muna karatu, ina koya masa karatu, Umma na dakin Abba, Yaya kuwa ya fita daga gidan. Ji nayi an banko qofar gidan mu an shigo, da sauri na dago da kaina don ganin ko waye haka ba ko sallama. Da sauri ta miqe tsaye cike da tsoro ganin Sadeeq da nayi a cikin gidanmu, yau shi kadai ne ba bodyguards din, qarasowa yayi inda muke nayi saurin ja da baya, dariya yayi tare da cewa "Guduna kuma kike? Kinyi mamakin ganina a gidanku ko? To bar mamaki wannan xuwan nawa xuwane mai amfani kin gane ko?". Umma da Abba ne suka fito daga daki tare da cewa "Lapiya nake jin hayani...... " kasa qarasawa yayi ganin mutumin dake tsaye a gidan, nayi sauri naja, hannun Faheem muka koma wajen su Abba hawaye har sun soma xubo min. Sadeeq yayi dariya tare da cewa "Kai dattijo naxo ne in fada maka cewa xan dauki erka na tafi da ita a daura mana aure, hope u understand?". Na waro ido waje cike da tsoro aure kuma?. Abba ne yayi qarfin halin cewa " Me kake fada ne haka? Er tawa xan dauka na baka kaje ka aura?". Dariya yayi tare da cewa "Dattijo ashe kaji abinda na fada? Don hk ynx xan tafi da ita". Yana kaiwa nan ya kai hannu xai tabani sai ji yayi an riqe hannun nasa tamau, da sauri muka kai kallonmu kan wanda ya riqe hannun sai ganin yaya mukayi, wani farin ciki ya lullubeni don nasan Yaya baxai bari ya tafi dani ba. Sadeeq ya kalli Yaya yayi wani shu'umin murmushi tare da cewa " Hey dude, gsky kana burgeni da yawa, kaine mutum na farko da yake taka min burki a duk lokacin da nayi niyyar aiwatar da quduri na, to ka sani kai baka isa ka hana ni aiwatar da abinda nayi niyya ba, ka sani dole ne na auri wannan yarinyar, don gsky ban taba ganin yarinyar data kwanta min arai kamar wannan ba, kuma kar kayi tunanin auren dadewa xaiyi, No baxai wuce 1week ba, ina fatan ka gane". Murmushi yaya yayi tare da cewa "Kai Saeed kake ko Sadeeq? Baka isa ka shigo har gidan nan ba kace xaka tafi da qanwata da nufin xaka aureta, qarya kake ka fdi hakan, in dai ina raye nida iyayena baka isa ka auri Naana ba kaji n fada maka". Sadeeq yace " To in kuma baku raye fa, ta yaya xaku hana aurena da ita?". A tsorace nake kallon Sadeeq, Yaya yace "Allah na nan, ina mai tabbatar maka insha Allah ko bayan ranmu baxaka taba auren Naana ba". Dariya Sadeeq tare da cewa "Gud, to inaso ka sani daga ynx ku fara shirye shiryen biki don dolene na aureta kaji na fada maka". Yana kaiwa nan ya fice daga gidan yana wata muguwar dariya. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [20/10 2:52 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 4⃣9⃣--5⃣0⃣ OHW 📚 Nayi saurin xuwa wajen Yaya cikin hawaye nace "Yaya na bani ni ya xanyi? Yaya ina jin tsoro Allah, banason wani abu ya sameku". Umma tace " Gaskiya nima ina jin tsoro, yaron nan da ganinshi bashi da mutunci xai iya yin komai, kuma ni gsky baxan iya bashi yata ya aura ba". Abba yace "Ai abinda baxai yuwu ba kenan, ta yaya ma xan aura mashi Naana? Ai hakan baxata taba yuwuwa ba sai dai duk abinda xaiyi yayi". Yaya ya xauna a tabarmar dake kusa sannan yace " Baba ku kwantar da hnklnku in dai ina nan Naana vaxata auri Wannan yaron ba, kai koda ace bana nan ma". Abba yace "To ynx miye abin yi? Don kasan ba kyalemu xaiyi ba". Yah Auwal yace " Addu'a kawai xamu cigaba dayi shi ne". Duk kowa yayi shiru Faheem yace "Abee Shi wannan yana ta maka shouting, meyasa baka bugeshi ba?". Duk mukayi murmushi yaya ya dafa kanshi tare da cewa "Kar ka damu My boy wataran xan bugesa kaji?". Gyada mashi kanshi yayi, yaya ya rungumeshi a jikinsa. Tun daga wannan rana yaya ya daina xuwa ko'ina sai dai masallaci, don yasan ko wane lokaci Sadeeq yana iya xuwar mana, ni kuwa duk na damu sosai hnkln duk ba'a kwance yake ba, yaya ne ma ke tausata. Har 3 days Sadeeq bai kuma xuwa koda unguwarmu ba, hakan yasa muka dan kwantar da hankalinmu, don a tunaninmu Sadeeq ya haqura ya qyalemu. Shi kuwa Sadeeq shi kadai yasan abinda yake qullawa a cikin xuciyarsa don ya quduri aniyar sai ya rama duk wani abu da muka yi masa. *******Yau ta kama Alhamis, ranar da baxan taba mantawa da ita ba a rayuwata ranar da ta xame min *baqar rana*. Muna xaune ni da Yayana da Faheem a tsakar gida muna karatun al'qur'ani, Umma tana kitchen don yau ta hana ni yin girkin sai ita ta shiga, Baba kuma yana dakinsa. Ni dai yau duk jina nike wani iri sam bana jin dadin jikina, Umma ta fito daga kitchen ta xauna kusa damu, lokacin har mun idar da karatun na maida qur'anin daki sannan na dawo na xauna muna dan taba hira, duk da ba wata fira muke ba sosai. Wayar yaya tayi ringing yana dubawa yaga Vice Principal din schl din da yake teaching ne ya kirashi, yayi picking call din bayan sun gaisa yake ce mishi yazo suna da wani meeting ynx na gaggawa, Yaya yace "Sir meeting kuma a ynx? Qarfe uku da rabi fa ynx?".Vice Principal yace "Wllh nima ynx PC ya kirani yake fada min na kira ku ba wani jimawa xa'ayi ba". Yaya yace " To shikenan Ganinan xuwa". Ya katse wayar ya kalli Umma yace "Umma ana neman mu ynx bari nje na dawo". Umma tace "To shikenan Sai ka dawo ko?". Ya miqe tare da cewa " Qanwa, my son bari naje ynx xan dawo". Na marairaice fuska kamar xanyi kuka nace "Yaya muje tare mana". Murmushi yayi tare da cewa " Noo karki damu ynx xanje na dawo kinji?". Nace "To shikenan sai ka dawo" yace "Yawwa". Har ya kai bakin qofa Abba ya fito daga daki yana cewa " A a sai ina kuma?". Yaya yace "Abba xani schl ne ana neman mu". Abba yati murmushi tare da cewa " Toh ah dawo lpy". Yah Auwal ya amsa da "Allah yasa". Mukace " Ameen". Har ya kusan fita Umma ta kira sunanshi, ya waigo gami da amsawa, sai kuma tayi shiru, yace "Umma ya dai kin kirani kuma kinyi shiru?". Umma tayi murmushi tace " Aa ba komai jeka kawai". Yace "Toh shikenan sai na dawo". Nan ya fice. Ji nayi kamar ana kallona hakan yasa na dago da kaina muka hada ido da Umma tana ta kallona, cikin mamamin kallon nace " Umma lpy dai? Naga kina ta kallona". Umma ta sauke kanta tare da cewa "Hmm Naana nima bansan me yasa nake kallonki haka ba, ji nake kamar kar na daina kallonki". Matsawa nayi kusa da Umma na riqo hannunta nace " Umma me hakan ke nufi? Kallon yana bani mamaki sosai, kuma abinda yafi bani mamaki shi ne baki taba kiran sunan Yaya kai tsaye b sai yau, kuma ynx kina ta kallona Umma me yasa?". Umma tace "Na fada maki nima bansan dalili ba Naana kawai dai yau ina jina wani iri ne". Abba ne yace " tabbas nima yau ina jina wani iri don gani nake kamar yaron nan xai iya rabamu kuma....... Maganar ta tsaya mashi sakamakon jin an banko qofar gidan an shigo ba ko sallama, duk muka waiga don ganin ko waye sai ganin wadannan bodyguards din Sadeeq mukayi, bayan Abba na koma na boye tare da riqe hannun Faheem gam cike da tsoro...... (Nima dai Beely na tsorata da ganin mutanen nan) Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [22/10 2:23 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 5⃣1⃣--5⃣2⃣ OHW 📚 Sadeeq ne ya shigo gidan ya tsaya gabanmu yana murmushin mugunta, ya kalli Abba da Umma yace "Ina fatan dai kun gama shirin komai ko?". Abba ya kalleshi tare da cewa " Kai Sadeeq bari kaji in gaya maka, kabar ganin kai dan me kudi ne kayi tunanin hakan xaisa ka samu duk abinda kake so a rayuwa, to kasani indai ina raye baxaka taba auran diyata ba". Kallonshi Sadeeq yayi sama da qasa sannan yace "A a Dattijo kar ka tunxirani na aikata abinda banyi niyyar aikatawa a gidan nan, ban taba neman abu na rasa ba komin darajarshi don haka wannan yarinyar baka isa ka hanani aurenta ba". Umma tayi qarfin halin cewa " Duk iyaye na gari baxasu dauki ersu su baka ba a matsayin mata, don haka muna roqonka da kayi hkr ka fita daga rayuwarmu". Dariya yayi sannan ya kalleni yace "Ke taho mu tafi". Qara lafewa nayi bayan Abba ina xubar da qwalla nace " Ni baxani ba, Abba ka hanashi tafiya dani". Abba ya qara boyeni a bayanshi, Sadeeq ya juyar da kai sannan ya kai hannu ya jawo hannuna, nayi qara na qara qanqame Abbana cike da tsoro, Abba yasa hannu ya wanka ma Sadeeq mari yana cewa "Kar ka kuskura ka qara taba min ya". Wani kallo Sadeeq yayi masa kafin ya kai masa wani naushi a fuska, saiga Abba a qasa bakinshi ya fashe. A firgice mukayi kanshi nida Umma muna kuka, Sadeeq ya kalleshi tare da cewa " Kai dattijo banason na xubar da jini a gidan nan, amma xaka sani na xubar, na fada maka babu wanda ya isa y hanani aurenta". Hannu yasa ya finciko hijabin dake jikina Abba yayi qarfin halin tashi ya riqo hannuna yana cewa "Bafa xaka tafi da ita ba ina kallo ka lalatamin rayuwar Ya". Sadeeq ya dage wuya tare da cewa " To kuwa ynx xan sheqeka ta ynd babu yadda xakayi ka hanani aurenta". Hannu yasa a aljihunsa sai gashi ya fiddo wuqa yar qarama, xaro ido nayi da sauri na durqusa gabanshi cikin muryar kuka nace "Don Allah karka kashemin Abbana". Abba ne ya jawoni tare da cewa "ki rabu dashi mamana bai isa yayi min abinda Allah bai nufa ba". Sadeeq yace " Au har ynx dai kana kan bakanka kenan?". Abba yace "Qwarai kuwa". Sadeeq ya karkata kai yana juya wuqar tare da cewa " To kuwa ynx xaka xama sheqaqqe". Yana fadar haka ya jawo Abba xuwa gabanshi, da sauri Umma ta shiga tsakani tana kuka tace "Don Allah kayi hkr karka kashe....... Bata qarasa maganar tata ba sakamakon hankadeta da Sadeeq yayi ta fadi gefe guda kanta ya bugu, da sauri nayi wajenta ina kuka Abba ma ya yunqura xai tafi wajenta Sadeeq ya riqo wuyanshi tare da cewa " Zaka aura min ita ko kuwa har ynx kana kan bakanka?". Abba yace "Baxan aura maka ita ba". Cikin rashin imani Sadeeq ya daga wuqar nan ya luma ma Abba a ciki, idanuwan Abba suka firfito, ni kuwa da qarfi na kira sunan Abba cike da kidima, ya qara dagawa ya caka mashi har sau 3, sannan ya sakeshi, a hnkl Abba yakai qasa yana kalmar shahada, yana kaiwa numfashinsa gaba daya ya dauke. Wani kukan kura Umma tayi tayo kan Sadeeq tana wani irin kuka ta shaqi wuyanshi, tana cewa " Meyasa ka kasheshi, nima ka kasheni kawai, kai wane irin axxalumin mutum ......... Kafin ta qarasa sai ji tayi ya caka mata wuqar a ciki itama har sau 3 dai dai lokacin kuma Yaya ya shigo gidan. Wani uban burki yaja ganin Abba da Umma kwance cikin jini ba alamar rai a tare dasu, ganinshi yasa na farfado daga suman tsayen da nayi naja hannun Faheem muka nufi wajensa, wani irin kuka ya kufce min mai tsuma xuciya sam na kasa yin magana, Illa jijjiga Yaya da nake wanda shima mutuwar tsayen yayi hawaye masu xafi suna xubo mishi. Sadeeq ya kallemu ya karkace kai yace "Barka da xuwa babban yaya". Wani qarfi ne yaxo ma Yaya, a fusace yayi kan Sadeeq ya fara aika mshi da saqonnin naushi, bugunshi yake kamar Allah ya aikoshi, Nan bodyguards din suka fara qoqarin cire Yaya daga jikin Sadeeq amma sam sun kasa, Yaya ya shaqi wuyan Sadeeq, tuni idanuwanshi suka firfito yana kakarin mutuwa, wani daga cikinsu ya ciro wuqa ya caka ma yaya ta baya ya janye wuqar, qara Yaya ya saki tare da sakin Sadeeq din ya juyo kenan mutumin ya qara caka mashi wuqar, nan take ya xube qasa, Faheem ne ya fara kuka ni kuwa daskarewa nayi a gurin na kasa believing abinda idanuna ke ganemin, Abbana Ummana da Yayana ne kwance cikin jini......... (Ni kaina Beely firgici gami da tausayinsu Naana tare da tsorata yasa nima na daskare a gurin na kasa cigaba da daukar rahoton sai dai kumin afuwa xuwa lokacin dana dawo hayyacina😭) Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [22/10 7:24 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 5⃣3⃣--5⃣4⃣ Da qyar yaya yake fidda numfashi, kallonmu yake nida Faheem yayinda hawaye ke xubo masa a idanunsa, da qyar na samu na daga qafata na qarasa wajensa muka durqushe a gabansa, sam na kasa magana sai dai wasu xafafan hawaye dake xubo min a fuskata. Hannunsa na riqe shima ya riqe gagam kafin ya bude baki a hankali cikin muryar wahala yace "Ki dauki Faheem ku gudu... Yana fadar haka numfashinsa ya dauke". Qara na saki mai qarfi, xuciyata tayi wani irin bugawa, wanda har nake jin kamar numfashina xai dauke, tunawa da abinda yaya yace yasa na miqe na dauki Faheem a hannuna na kalli Sadeeq kallon tsana nace " Muje". Cike da mamakin maganata yake kallona, na kuma maimaita abinda nace sannan nayi hanyar waje. (Niko da mamaki nabi bayan Naana, to miyasa tace suje? Bari dai mu gani). Sadeeq da sauri yabi bayana don duk bai yarda dani ba, ina fita na waiga naga mutane a tsaitsaye da alamu xuk sun san da abinda ke faruwa amma babu wanda yayi yunqurin taimaka mana. Ina fita na waiga naga Sadeeq ya kusa fitowa kawi sai na tattare sket dina dama ba takalma a qafata, nayi wata hanya da gudu mutane sai bani hanya suke. Ganin hakan yasa Sadeeq yayi saurin cewa "Au baxaku bita ba kuka tsaya kuna kallona?". Suma da axama suka rufa min baya, a haka nayi ta gudu ba tare da nasan inda nake nufa ba, Allah ya taimakeni nasha wata kwana basu ga inda muka nufa ba, garin dama hadari ya hadu da yake lokacin damuna ne, nan ruwa ya sauko duk da hakan ban daina gudun ba sai da na tabbatar na daina ganinsu sannan na samu mafaka............ ******+++++****** Daga nan ta basu labarin ynd akayi har taxo gidan nan. 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 Hawaye ta share ta dago ta kallesu daya bayan daya kowannensu hawayene sharkaf a fuskarsa har Daddy da Yah Mahmoud, Zee kuwa kuka take haniqan, duk sun tausaya ma Naana sosai, a hnkl Daddy ya bude bakinsa cikin qarfin hali yace " Haqiqa Naana kinga quncin rayuwa, a gaban idonki a kashe miki mahaifa da kuma yayanki ai dole ki kamu da cutar hawan jini saboda damuwa". Mummy ta share qwallar idonta sannan tace "Naana ki kwantar da hankalinki insha Allah xamu riqeki tamkar yar da muka haifa, xamu baki duk wata kulawa da iyayenki xasu baki". Cikin muryar kuka tace " Nagoda Daddy nagode Mummy". Zee ta kamo hannunta tare da cewa "Naana ki daina kuka daga yau ki daukemu tamkar en uwanki". Suka rungume juna, Daddy ya miqe yace " Tohm aje ayi sallah". Mummy ta fara miqewa ta wuce dakinta shima Daddy ya fita xuwa masallaci. Yah Mahmoud ya miqe tare da riqe hannun Faheem y kalli Naana dai dai lokacin itama ta dago kanta, wani sassanyan murmushi ya sakar mata wanda ta kasa fassara shi, ta sadda kanta qasa, ya wuce waje yana riqe da hannun Faheem. _Washe gari_ Tun asubar fari ta miqe bayan tayo alwalla tayi nafila sannan tayi raka'atanul fajir, sannan tayi sallah ta dauko qur'ani t ta hau yin karatu, sai wajen 7 sannan ta miqe ta fita xuwa falo, a kitchen ta iske Inna Asabe nan ta gaisheta sannan ta shiga taya ta hada breakfast, wajen 8:35am suka kammala. Ta wuce dakinta ta tada Faheem tayi mashi wanka ta shirya shi sannan itama ta shiga wankan bayan ta fito ta shirya cikin kayanta sannan ta dora hijab dinta, tayi kyau abinta sai dai ramar da tayi. Tana xama sai ga Zee ta shigo dakin da sallamarta bayan ta amsa Zee ta xauna gefenta tare da cewa "Naana kixo muje muyi breakfast". Kallonta take da mamaki tace " ai ynx xanje na dauko". Zee tace "A a a dinning xamuyi ke kadai ake jira". Waro ido tayi da mamaki tace " Ni kuma? A dinning?". Zee tace "Haba Naana jiya fa aka gama magana kin xama er gida daga ynx, don haka in dai baki son bacin ransu Mummy to ki taso muje". Ba yadda ta iya dole ta tashi suka fito ddaga dakin. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [23/10 3:36 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 5⃣5⃣--5⃣6⃣ OHW 📚 A dinning kowa ya hadu har Yah Mahmoud da ba sosai yake yin breakfast a part din ba, har qasa ta durqusa ta gaishe da su Mummy da Daddy sannan Yah Mahmoud, duk suka amsa da fara'a a fuskarsu. Sannan tayi duqe a gurin ta kasa tashi ta xauna saman dining din don ita nauyin abun take ji. Mummy ce tace "Naana baxakiyi break din bane?". Ta dago a hankali ta kalleta sannan tace " Am Mummy xan diba nawa ne sai naje daki nayi. Daddy ne yace "Kinga Naana ki hau kujera muyi breakfast". Ba yadda ta iya dole ta miqe a sanyaye ta xauna, Yah Mahmoud kuwa kallonta kawai yake tunda ta shigo falon. A hankali take cin wainar qwan da plaintain din, ji tayi kamar ana kallonta hakan yasa ta dago kanta, karaf suka hada ido da Yah Mahmoud, murmushi mai sanyi yayi mata, ta sadda kanta qasa a ranta tace " Ji mutumin da yake wulaqantani yau kuma shi ne har da yi min murmushi. Ita ce farkon tashi don ta gaji da kallon da Mahmoud ke yi mata, Zee tace "Ba dai har kin gama ba?". Murmushi tayi mata tare da cewa " Na koshi Zee" Zee tace "Tohm shikenan". Ita kuma ta wuce dakinta, Mahmoud shi ma tashi yayi ya fice daga falon ya nufi side dinshi. _2 days later_ Tana xaune a dakinta Faheem ma yana dakin Zee, ta buga uban tagumi tana aikin nata wato tunanin rayuwarta tada da kuma yayanta abin qaunarta. Zee ta shigo dakin da sallam ita da Faheem, da sauri ta share hawayenta ta qaqaro murmushi tare da cewa " Zee kin shigo kenan". Zee ta samu gefen gadom ta xauna tare da dafa kafadar Naana tace "Beely baxaki rage wannan tunanin ba ko?". Tayi murmushi tare da cewa " Zee ba tunani nake ba". Zee tace "Toh shikenan but ya kamata ki rage damuwa tunda kinji dai abinda Dr yace". Nace " Zee xanyi qoqari ganin na daina damuwa, amma fa kin sani damuwata baxata kau duka ba". Zee ta girgixa kai cike da tausayin Naana tace "Insha Allah komai xai tafi dai2. Zee ta miqe xata fita sai kuma ta dawo tace " Am nama manta, Mummy tace ki shirya muje muyi shopping ". Da sauri na kalleta nace " Shopping Zee? Ni na fita daga gidan nan?so kike Sadeeq ya ganni?". Zee ta danyi shiru sai kuma tace "To bari na fada ma Mummyn sai muyo miki naki". Ta gyada mata kai domin ita sam bata son fita ko'ina. Zee ta fita bata jima ba sai gata ta dawo tace " Tohm Naana, Mummy tace naje ayo miki naki". Nayi murmushi nace "Nagode Zee Allah ya saka da alkhairi". Zee tace " Bakomai sis". Nan ta fice ita kuma t koma ta xauna. _1 week later_ Rayuwa tayi ma Naana dadi sosai, komai take buqata ana yi mata a gidan har ta maida jikinta sai dai duk da haka tana cikin damuwa sai dai tana boyewa don kada su fahimci tana cikin damuwar. Kamar kullum yau ma suna xaune a falo su duka amma banda Naana, Daddy ya kalli yace "Zainab je kirs min Bilkisu". Zee ta miqe xuwa dakin Naana. Ba'a dau lokaci ba sai gasu sun dawo falon. Naana ta xauna qasa kan carpet tare da cewa " Daddy gani". Daddy yace "Am dama abinda yasa na kiraki shine, naga kin gama secondary dinki to shine naga da xaman nan da kike gwara na sama maku makaranta keda Zainab, kawai ku cigaba da xuwa". Farin ciki ne ya cika min xuciyata nace " Daddy naji dadi sosai Allah ya saka da alkhairi". Duk suka amsa da "Ameen". Ita kuwa ta kasa boye farin cikinta, Mahmoud kuwa murmushi kawai yake yana kallon Naana cike da so da kaunarta. Daddy ya fita, Mummy ma ta miqe xuwa dakinta. Zee ta kalli Yah Mahmoud tace " Yah ka kaimu shopping ina son siyo kayan make up nawa sun qare". Kallonta yayi yace "Kai sis duka duka yaushe kikaje shopping?". Zee tace " Plx mana Yaya, ban siyo da kayan make up ba". Yace "Tohm shikenan Beely je ki shirya muje tare". Tayi saurin cewa " A a kuje kawai ba damuwa". Zee tace "Kinsan Allah sai kinje, ke kullum sai xaman gida sai kace wata new bride?". Tace " A a nidai kiyi hkr". Yah Mahmoud yace "To in dai baxaki ba sai dai a fasa xuwa". Kallonshi tayi shima ita yake kallo sannan ta kalli Zee da har ta bata ranta, ganin hakan yasa tace "To kiyi hkr xani". Murmushi Zee tayi tace " To ko kefa ynx tsho muje mu shirya". Mahmoud kuwa dadi yaji sosai a xuciyarshi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [24/10 11:39 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 5⃣7⃣--5⃣8⃣ OHW 📚 Tashi sukayi Zee ta wuce dakinta itama Naana ta wuce nata, Faheem kuwa yana nan wajen Mahmoud bai tashi ba. Kaya kawai Naana ta chanja xuwa wata atamfarta ja mai ratsin baqi sai ta sanya hijab baqi wanda iyakarshi gwuiwa, da flat shoe dinta shima baqi tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi a fuskar ba. Tana niyyar fitowa sai ga Zee ta shigo itama cikin shigar Atamfa, yau dai itama an sanya hijab kuma tayi kyau da hijabin. Nan suka fito tare sai dai bamu ga Yah Mahmoud ba, Zee tace "May be yana side di shi yana shiri". Hakan yasa suka xauna nan falon suna jiran fitowarsa. An dauki dan lokaci sai gashi ya kira a wayar Zee bayan ta daga yace " In xakuje ku fito". Yana fadar haka ya katse wayar. Zee ta tabe baki tare da cewa "Yaya ko masifa ina muka san ya fito". Ita dai bata ce komi ba suka miqe suka fice. Tunda suka taho yake kallon Naana ta cikin glass din motar, tayi mashi kyau sosai barin ma lokacin da take murmushi shima sai ya tsinci kanshi da yin murmushi. Har suka iso wajen motar bai sani ba sai jin qarar bude mota da yayi, hakan yasa yayi saurin waigowa yaga Zee har ta shiga motar ta kalli Naana tace " Shigo mana sis". Ba musu ta shiga baya ita da Faheem, bai ce dasu komai ba yaja motar a hankali suka fara tafiya don shi komai nashi a hnkali yake yinsa. Kadan kadan ya daga kai ya kalli Naana ta mirror, sai kuma ya sakr da murmushi. Zee shirun yayi mata yawa yasa ta kunna waqa, kallonta yayi tare da cewa "Miye haka kuma xaki sanya mana waqa?". Zee ta marairaice fuska tace " To ai naga duk anyi shiru ne shiyasa na kunna". Ya maida kanshi ga kallon titi sannan yace "To ni i don't like it, don haka ki kashe kawai in ba so kike na xube ki a nan ba". Turo baki tayi tace " Plx mana Yaya ta indian din nan kadai xamuji". Waro ido yayi tare ds cewa "Wacce bana son kenan". Ganin bai da niyyar bari ta kunna yasa ta haqura ta kunna a wayarta dai 2 yanda xataji ita kadai ta sa a kunnenta. Ita dai Naana na baya tana jinsu, mamaki take ganin Yadda Mahmoud ya hana Zee taji waqarta, don ita duk abinda tace tanaso Yah Auwal nayi mata. Tuni hawaye suka fara qoqarin xubo mata hakan yasa tayi saurin duqar da kanta qasa ts goge don bata so su fahimci wani abu. Duk wannan abun ds take Yah Mahmoud na kallonta kuma yaga hawayen a fuskarta sai duk yaji ba dadi, sosai yake jin hawayenta a xuciyarshi, dole ya qwato mata encinta wajen Sadeeq, a matsayinshi na barrister dole ya shigar da qarar Sadeeq kotu tunda har ynx yana hannun police. Sam bai ma san sun iso super market din ba sai da ya dan wuce Zee tayi saurin cewa " Yaa ina xaka kaimu kuma?". Waigawa yayi ya kalli gefenshi yaga har ya soma wuce super market din da sauri yaja burki b tare ds yayi mata magana suka koma baya suka shiga super market din. Zee ta fara fita taja hannun Faheem sannan ta kalli Naana tace "Muje ko?". Ba musu ta fito, Yah Mahmoud ma ya fito suka shiga a tare. Zee ta kwashi kaya da yawa, ita da tace kayan make up kadai sai gata har da su takalma da jaka da english wears, ganin Naanz bata dibi komai ba yasa ta shiga jidar mata ita da Faheem, shi kuwa gogan yana can ya samu kujera ya xauna yana ta faman danna waya. Dagowa yayi ya kalli Zee cike da mamaki yace " Ke miye haka kuma?". Zee ta waigo ta kalleshi tace "Yah namu ne fa mu uku". Kawar da kanshi kawai yayi ys miqe ya wuce wajen perfumes ya xabi wanda yake so sannan yaxo ajen Xee yaja kunnenta tare da cewa " In baki bar kwasar kayan nan ba hakanan xan tafi na barku". Er qara ta saki tare da cewa "Aushh Yaya akwai fa xafi". Sake mata kunnen yayi ya koma ya xauna kan kujerar da ya tashi yana kallon Naana dake tsaye wajen wasu zobunan axurfa tana kallo, ta dauko wani dan madaidaici mai shegen kyau tayi murmushi don ya masifar burgeta, koda ta duba kudinsa sai taga 20k hakan yasa tayi saurin ajiyewa tabi bayan Zee. Murmushi yayi ya miqe yaje wajen xoben ya dauka sannan ya bi bayansu don biyan kudi. Suna xuwa ATM dinshi ya bada aka fidda kudin sannan aka xuba musu kayayyakin a leda suka fita, Yah Mahmoud ya fiddo xoben bayan sun fita ya ba mutumin kudinsa sannan ya fita ya iskesu a gaban mota suna jiranshi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [25/10 8:55 pm] Beelybadaru😍: [25/10 2:11 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 5⃣9⃣~~6⃣0⃣ Har ta bude mota xata shiga taji an qwala mata kira " *Bilkisu Almustapha Yusuf(Naana)*". Da sauri ta waiga jin muryar da tayi kamar tasan mai ita. Karaf suka hada ido da ~Ummu-khursum~ tana tahowa inda suke da murmushi a fuskarta, mamaki ya cikata ya akayi Ummu kursum tazo Kano. Har ta iso tana kallonta, nan suka rungume juna cike da farin ciki suka dago suna kallon juna da mamaki, hawaye suka xubo ma Ummu kursum tace "Naana ashe xan sake ganinki?". Itama hawayen take tace " Qawa Umma y akayi kikaxo kano?". Umma tace "Ke xan tambaya ya akayi kika zo Kano, muna can muna ta nemanki lokacin da muka iske ta'asar da Sadeeq yyi maki a rayuwa, Insha Allah qarshenshi baxa tayi kyau ba". Naana ta share hawayen dake fuskarta tace " Lbr ne mai tsawo Ummu kursum, ni dai tambayar ki nake ya akayi kikaxo nan?". Ummu tace "Naxo ne gidan qanin Abbanmu, xanyi karatu ne a nan shiyasa na dawo nan da xama har xuwa lokacin da xan kammala karatuna". Nace " Allah sarki Umma nayi kewarku ina su Hadixa da Aisha?". Umma tace "Su Hadixa na baro su can, suna can cike da kewarki". Ta share en qwallar da suka xubo mata tace " Allah sarki nima in kewarsu sosai". Zee ce tace "Tohm mu an manta damu kenan ba a gabatar damu gareta". Sai a lokacin ta tuna dasu Zee, Umma ta kallesu da mamaki don bata sansu ba kuma dama tana da niyyar tambayar Naana". Naana tace " Sorry Zee, Umma ga Zee a gidansu nake xaune, wannan kuma Yah Mahmoud kenan shima gidansu daya". Sannan tace "Zee wannan Ummu Kursum kenan, Qanwar Aunty Zarah". Nan suka gaisa sosai har da Yah Mahmoud dake gefe shi da Faheem. Ummu Kursum tace " Faheem kuma har ka manta da Auntynka?". Shi sai a lokacin ma ya ganta don yana ta shan ice cream din shi ne hankalinsa baya kansu, ganinta yasa ya washe baki yace "Adda Ummu". Tayi murmushi ta dauke shi tana cewa " Fushi nake dakai kana ganina kayi min banxa". Ya washe baki tare da cewa "Banganki ba Adda". Tayi murmushi tace " Tohm shikenan muje mota na baka sweet". Nan ya fara murna nace yaro sweet duk wadda aka sai mashi bata isheshi ba kenan. Umma tace "Naana kixo muje ku gaisa da Yayana dan uncle dina". Ba musu tace " Toh muje, Zee taho". Zee ta kalli Mahmoud da har ya bata fuska jin ance Naana taje ta gaisa da wani tace "Yaya bari muje mu dawo". Yayi saurin cewa " A a muje taren". Nan suka wuce zuwa wajen motarsu Umma tun daga nesa suka hango wani saurayi ya fito daga motar, chocolate colour ne yana da kyau abinshi, muka isa wajen, nan Ummu tace "Naana ga Yah Muhammad, amma munfi kiranshi da Yah Lamido". Nan tayi murmushi ta gaisheshi, shima murmushin yayi ya amsa mata Zee ma ta gaisheshi. Nan ya kalli Mahmoud yaga sai faman cin magani yake ya kalli Ummu yace " Wannan ma duk tare suke?". Umma tayi saurin cewa "Oh Yah Mahmoud kenan yayan Zee ne a gidansu Naana ke xaune". Murmushi yayi ya miqa ma Mahmoud hannu don su gaisa, shima murmushin ya qaqaro ya bashi hannu suka gaisa. Lamido yace " Kullum _First lady_ sai ta bani labarinki, shiyasa naso nima na ganki sai gashi yau mun ganki gsky munji dadi nyc to meet u". Yah Mahmoud ji yayi kamar ya shaqe Lamido don wani haushinshi yaji. Cike da mamaki Naana ta kalli Umma tace "First lady kuma?". Umma tayi murmushi tace " Sunan daya rada min kenan a cewarsa haka kowa xai ringa kirana". Lamido yayi dariya tare da cewa " Ai ni a wajena ta wuce first lady kinsan ina ji da ita sosai". Naana tayi murmushi tace "Lallai kam to muma sai mu ringa kiranta da hakan". Lamido yace " Gsky da naji dadi kuwa sosai". Ya fada yana kallon firsg lady da wani murmushi a fuskarsa, itama murmushin tayi masa. Wata doguwar ajiyar heart Yah Mahmoud ya saki, ganin kallon da Lamido ke ma Umma sai yaji sanyi a ranshi don da alama soyayya suke ne, bai san sadda ya saki wani murmushi ba. Umma tace "Naana a wane unguwa kuke?". Naana tace " A tarauni". Umma tace "Mu kuma unguwar rimi muke". Nan dai sukayi sallama Umma ta amshi nmbrn Zee tace Insha Allah xata kirata kuma xasu xo wata rana. Nan suka koma wajen motarsu suka shiga yaja suka wuce gida. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [25/10 3:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 6⃣1⃣---6⃣2⃣ OHW 📚 _2 days later_ Suna xaune a falo gaba dayansu bayan an gama dinner, Daddy ya kalli Mahmoud dake aiki cikin laptop dinshi yace "Mahmoud nikam na tambayeka mana". Ya dago kanshi daga kan laptop din yace " Allah yasa na sani Daddy". Daddy yace "Wai ya maganar Yaron nan Sadeeq har ynx yana hannun police?". Sai da gaban Naana ya fadi jin an ambaci sunan Sadeeq, Mahmoud yace " Eh Daddy yana hannu, mahaifinsa yaxo garin nan da nufin yayi vailing sa na hana ayi, ya basu kudi da yawa a tunaninsa xa'a sakesa kamar ynd yakeyi a Katsina sai suka qi amsa, to shine naje na samu commissioner of police nayi masa bayanin komai nace ina so a shigar da qararshi court". Daddy ya jinjina kai tare da cewa "That's good my son, ynx ya yace?". Mahmoud yace " Eh to yace min nan da 1week na koma naji komi kenan, daman ynx ina da wani case ne dana kammala shi sai mu fara wannan". Daddy yayi murmushi tare da cewa "Da kyau Br. Mahmoud Allah ya bada ikon yi". Duk aka amsa da " Ameen". Ita dai Naana binsu kawai take da idanu gani take kamar Sadeeq xai iya kubcewa daga hannun hukuma. Nan Mahmoud ya miqe ya dauki laptop dinsa yace "Tohm ni dai xanje side dina ina son nayi wani aiki". Mummy tace " Toh shikenan sai Allah ya kaimu kenan?". Gyada mata kai kawai yayi ya fice daga falon bayan yayi masu gudnyt. Mummy ma ta miqe ta wuce dakinta, Daddy yace "Shima dai barci zaiyi, Sukayi dariya ya miqe ya wuce dakinsa, su Zee kuwa kallon wani film suke na indian mai suna PREAM RATAN PHAYO, Naana ta gyara xama suna kallon, basu suka tashi ba sai wajen 10:45pm shima din don film din ya qare ne, Zee ta wuce dakinta itama Naana suka wuce nasu dakin ita da Faheem, an gyara masu dakin sosai yayi kyau don ynx hada qananan kujeru a ciki masu kyau. *MAHMOUD* Yana gama aikin ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan yayi shirin barcinsa, amma ba jallabiya ya sanya ba don shi sam ba sosai ya cika son jallabiya ba, indai ya sanyata to sai dai in ba inda xashi ne kamar da daddare in xai kwanta shima ba sosai ba, don har faduwa yake in ya sanya yayi tafiya mai nisa, bai saba sanyawa ba shiyasa sai dai in yaxo nan gida ne shima din dai ba can ba. Kwanciya yayi da niyyar yin barci amma sam ya kasa, tunanin Naana kawai yake, sam ya kasa sanar da ita cewa yana sonta ya rasa ta ynd xaiyi ya fada masa, gsky ya xama dole ya nemi mafita don xuciyarshi nema take ta tarwatse saboda tsananin tunanin daya addabeta. Bashi ya samu barci ba sai wajen 1 sannan barci barawo ya sacesa cike da mafarkai barkatai. Washe gari sai wajen 7 ya farka, a gurguje ya fada toilet ya dauro alwalla yayi sallah sannan ya nemi gafarar ubangijinsa, ya dauko Qur'an ya fara karantawa cikin wata xaxxaqar murya da qira'a mai dadin gaske. (Ni kaina Beely kashe kunne nayi ina sauraren karatun Mahmoud, yayi min dadi sosai). Sai wajen 8:30am ya rufe Qur'anin ya koma ya kwanta barci yayi awon gaba dashi. *NAANA* Tare da Zee suka shiga kitchen suka hada kayan breakfast, bayan sun gama suka jerasu a dinning sannan suka koma daki don yin wanka, Bayan ta gama ma Faheem itama tayi wankan ta shirya cikin doguwar rigarta ta atamfa ta yafa kallabin da yake babba ne, sannan ta fito ta iske su Mummy suma har sun fito nan taje ta gaishesu suka amsa mata da fara'a a fuskarsu suka xauna don gabatar da breakfast dinsu. *MAHMOUD* Wayar sa ce ta tasheshi daga barcin da yake, cikin magagin barci ya jawo wayar yaga wani abokin aikinsu ne ya daga, daga can bangaren yace "Barrister Mahmoud ya muka ji shiru har ynx baka xo ba?". Daga kai yayi ya kalli agogo yaga har 11 ta kusa da sauri ya miqe yana cewa " I'm sorry br. Habeeb ku bani 20mnts plx". Yana fadar haka ya katse wayar ya tashi ya fada toilet shaf 2 yayo wanka ya fito ya xira qananan kayanshi da suke qara fito da kyawunshi. Lotion kawai ya shafa sannan ya bade jikinsa da turare mai qamshi, yaga in ya shiga gida xai bata lokacinshi ne gashi kuma yana jin yunwa hakan yasa ya kira nmbrn Mummy. Lokacin suna xaune a falo ita da Naana Zed tana daki tana waya, nan ta daga wayar kafin tayi magana ya gaisheta da sauri tare da cewa "Mummy ki turo a kawo man breakfast dina ynx ina sauri ne". Mummy tace " Tohm shikenan" ta ajiye wayar ta kalli Naana tace "Tashi yi maxa Naana ki kai ma yayanku breakfast dinshi". Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [25/10 7:46 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 6⃣3⃣---6⃣4⃣ OHW 📚 Ta miqe ta dauki breakfast din nashi ta nufi side dinshi, ta dade bata je part din ba, jiki ba kwari ta shiga yin knocking, cikin muryar isa yace "Shigo mana sauri nake". Ta tura qofar a ranta tana cewa " Aifa shi komai sai yayi shi da masifa". Nan ta shiga a falo ta iskeshi xaune cikin shirin shi taje ta ajiye mashi a saman carpet din dake falon sannan tace "Ga abincin". Kallonta yayi tayi masa kyau sosai, bai san sadda ya saki murmushi ba yace " Thanks". Itama ta dago ta kalleshi da mamaki don bai taba yi mata godiya ba a duk sadda ta kawo mishi abinci, murmushi ya sakar mata tayi saurin sauke kanta qasa ta juya xata tafi yace "Am ki tsaya na gama ci sai ki koma da kayan". Komawa tayi can nesa dashi ta xauna tana wasa da fingers dinta, shi kuma ya sauko qasa yana cin abincin a hankali yana satar kallonta, yanaso ya fada mata yana sonta amma ya kasa, gani yake kamar xata qi amince masa shi kuma baxai so hakan ba. Ita kuwa duk ta gaji da kallon da yake mata ta dago kanta kenan suka sake hada ido, nan ma ta qara sadda kanta qasa. Ya gama cin abincin sannan ya miqe tare da cewa " Muje ko?". Dagowa tayi ta kalleshi taga har ya miqe yana niyyar fita hakan yasa ta miqe taje ta dauko kayan abincin sannan ta nufi wajen qofar kanta a qasa. Ganin hakan yasa yayi murmushi tare da cewa "In kika bugeni fa?". Sai a sannan ta dago kanta taga hr ta kusa xuwa inda yake, nan ta fice daga falon ba tare da tace mashi komai ba. Shima fitar yayi ya kulle side din sannan ya nufi wajen motarsa ya shiga yaja xuwa wajen aikinsu. *NAANA* kitchen ta wuce ta wanke kwanukan sannan ta dawo falo ta wuce dakin Zee, a nan Zee ke fada mata First lady ta kira tayi saurin cewa " Don Allah ki kiramin ita. Ba musu Zee tayi dialling nmbrn First lady, ringing biyu ta dauka. Nan suka shiga hira da Naana har take tambayarta tayi mata kwatancen gidan nasu xata xo, nan taba Zee tayi mata kwatance tace insha Allah cikin satin nan xata xo. Haka suka sha firarsu sannan ta katse wayar. _Night_ Mahmoud juyi kawai yake kan gadonshi sam ya kasa barci tunanin Naana da soyayyarta qaruwa suke a xuciyarshi, ji yake kamar yaje ya sameta ya fada mata yana sonta amma ya kasa hakan ya kuma rasa dalili da qyar barci ya daukeshi. _2days later_ Mummy ce xaune daki ita da Mahmoud ta nisa tare da cewa "Mahmoud dama wata magana ce nake son muyi da kai". Yace " Mummy ina jinki". Mummy tace "Dama akan maganr _Haleesah_ ne diyar qawta Hjy Falmata". Mahmoud ya maimaita sunan a xuciyarshi can ya tuna da ita yace " Oh Haley? Na ganeta me akayi mummy?". Mummy tace "Am dama mun ynk shawara ne nida qawata xamu hada ku aure don......... Kafin ta qarasa Mahmoud yayi sautin cewa " Aure kuma Mummy dawa?". Mummy da mamaki tace "Ina da wani dan ne bayan kai?". Yace " Mummy Haleesa fa? Ita xan aura? Ina ai bama xai yuwu ba Mummy, Haleesa ba tsaran aurena bace". Mummy ta tsaya kallonshi da mamaki tace "Me kake nufi? Kana nufin xaka watsa min kasa a ido ne ko me? Sai da muka gama magana da mamanta sannan kai kuma xaka kawo min wani xancen banxa?". Mahmoud yace " Mummy ai baki fada min ba, da kin tuntubeni ai, Haleesa ta kusan shekaruna, kuma fa qasar waje tayi rayuwarta komai nata ya koma irin nasu halayyarta da kuma.......... "Kaga rufen baki tun kafin raina ya baci, wannan ai xancen banxa ne, to ka sani na riga na gama magana don haka ka tashi ka bace min da gani". Miqewa yayi rai a bace ya fice daga dakin mummy ya nufi side dinshi, a ranshi yana cewa " Yama xa'ayi na auri Haleesa yarinyar da ko maganar iyayenta bata ji, kuma ni sam bata daga cikin tsarin matan da nike da burin aura". Haka ya isa part din nasa ranshi a bace. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [27/10 2:46 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 6⃣5⃣---6⃣6⃣ OHW 📚 Bangaren Mummy kuwa mamakin dan nata take ganin yana neman ya watsa mata qasa a ido, ita bata ga aibun Haleesa ba, don kuwa wayayya ce er boko kuma tana da kyanta, don me xai ce baxai aureta ba?. *MAHMOUD* Tunani ne ya addabi xuciyarshi, gsky lokaci yayi da xai sanar da Naana cewa yana sonta, amma kuma shi ynx burin shi bai wuce yaga ya kwato mata encinta daga wurin Sadeeq ba, hakan yasa yaqi fada mata yana sonta, amma ynx Mummy tasa dole xai sanar da ita. To kuma idan tace bata sonka fa? Tambayar da xuciyarsa tayi masa kenan, tuni jikinshi yayi sanyi, don kuwa shi yana son Naana so na haqiqa, baya tunanin zai iya jurar rashinta a gareshi. To ynx miye mafita?, Abdul ya tuna hakan yasa ya daga wayar shi ya kira shi, bugu daya biyu Abdul ya daga yana er dariya yace "Ya dai Aboki kana lpy?". Mahmoud yace " To sarkin dariya xaka fara ko?". Abdul yayi dariya yace "To wai dariyar aibu ce? So kake nayi ta kuka in banyi dariya ba?". Mahmoud yace " Naji to ynx kana ina ne?". Abdul yace "Ina gida mana". Yace "Owk to gani nan xuwa". Abdul yace " Allah ya kawoka lpy". Sannan ya katse wayar ya miqe ya fada toilet ya watsa ruwa sannan ya fito ya murxa mai ya shirya cikin qananan kaya da suke amsar jikinshi sosai. Yayi kyau sosai, ya dauki wayoyinsa guda biyu da car key ya fice. Bai yi wata tafiya mai nisa ba ya isa gidansu Abdul da yake duk unguwa daya suke. Da sallama ya shiga falon ya iske mom din Abdul, har qasa ya durqusa ya gaisheta cike da girmamawa, ta amsa mashi da fara'a, sannan ya wuce dakin Abdul. Ya iske shi sai fama yake da laptop da alamu aiki yake yi nan ya fada kan gadon yayi shiru kamar wani mai tunani. Abdul ganin yayi shiru yasa ya rufe laptop din ya maida hankalinshi kan abokin nasa don yaga da alama yana cikin damuwa yace "Frnd ya akayi ne? Da alama kana da damuwa". Mahmoud ya dago oily eyes dinshi ya kalli Abdul sannan ya dago daga kwanciyar da yake yace " Abdul, ni kaina na rasa yadda xanyi, tun dana fara ganinta xuciyata ta kamu da tsananin qaunarta, na rasa ta yadda xanyi na bayyana mata kalar son da nake mata". Cike da rashin fahimta Abdul yake kallonshi kamin yace "Kayi min bayani yadda xan fahimceka Mahmoud, wacece ita?". Mahmoud yace " Naana, Abdul ina son Naana so na haqiqa, bansan yadda xan kwatanta maka kalar son da nake mata ba, kuma da alama ita sam bata sona". Abdul ya danyi shiru yana tunanin wacece Naana amma sam ya kasa tunawa, ya kalli Mahmoud yace "Mahmoud wacece Naana kuma?". Nan Mahmoud ya fada masa ko wacece Naana da taqaitaccen labarinta. Abdul ya tausaya mata sosai amma baya ganin a ynx Naana xata iya yin soyayya don kuwa zuciyarta cike take tsanar Sadeeq. Ya dafa kafadar Mahmoud yace " Kar ka damu Aboki insha Allah xaka samu Naana, amma kada kace dole sai a ynx xaka samu soyayyarta, No kaima kasan a ynx *BA SO A RANTA* ko kadan, kai dai kayi iya bakin qoqarinka don ganin ta sake dakai daganan kai kuma sai ka bayyana mata soyayyarka". (Ni dai beely nace anya kuwa Naana xata iya yin soyayya kuwa?🤔 Umm ni kuma da katsalandan bari dai mu gani) Mahmoud ya gyada kai cike da gamsuwa da bayanin Abdul, yayi murmushi tare da cewa "Toh shikenan Abokina insha Allah xanyi duk yadda kace, sai dai kuma ynx akwai wani abu dake neman kunno kai". Abdul yace " Menene kuma?". Nan ya fada masa duk yanda sukayi da mummy, Abdul ya jinjina kai tare da cewa "Toh pa nan ake yinta, ynx ya xakayi?". Mahmoud ya marairaice fuska kamar mai shirin kuka yace " Nima bansan ya xanyi ba Abdul, ni sam bana qaunar koda ganin Haleesa ne balle kuma ace wai na aureta, ai an cuceni ma in aka hada ni aure da ita". Dariya ta kubce ma Abdul ganin yanda yake maganar ma kanta, cikin xolaya yace "Haba Aboki Haleesa fa, naga fa a Germany tayi karatunta kuma fa ta waye ga kuma kyau da........ Bugu Mahmoud ya kai masa yayi saurin kaucewa yana dariya. Mahmoud yace " Kai tsiyarka kenan sai an fara abu da kai cikin kwanciyar hankali sai kuma kaxo ka bata sha'anin". Abdul yayi dariya tare da cewa "Tuba nike angon Halee baby😅". Wani dogon tsaki yaja ya fice daga dakin bai koyi masa sallama ba. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [28/10 7:11 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 6⃣7⃣---6⃣8⃣ OHW 📚 Yana shiga da motarsa ya hango kamar mutum a cikin garden, hakan yasa y nufi gurin kai tsaye don ganin ko waye. Tun daga nesa ya hangota xaune kan daya daga cikin kujerun da ke tsakiyar garden din da wani farin fure a hannunta tana juyawa hawaye na fita daga idonta. Qarasawa yayi ya tsaya bayanta ya harde hannuwanshi a qirjinsa tare da cewa "Ya kamata ki rage damuwa a xuciyarki". Da sauri ta dago don har taji tsoro sam bata san da xuwan wani gurin ba. Ajiyar xuciya ta sauke ganin Mahmoud ne, murmushi yayi ya ja daya daga cikin kujerun ya xauna yana facing dinta sannan yace " I'm sorry to scared u". Dan murmushi tayi tare da cewa "Nothing". Kallon furen dake hannunta yayi tare da cewa " Kina son fararen fure ne?". Kalonshi itama tayi tare da gyada kanta. Murmushi yayi ya miqe tare da cewa "Ina xuwa". Cikin garden din ya kutsa kai yabi wata hanya da bata san da ita ba. Ba'afi 2 mnt ba sai gashi ya dawo hannunsa riqe d furanni mai yawa ya xauna a maxauninsa tare da miqa mata yana murmushi. Waro ido tayi cike da jin dadi ta amsa tana farin ciki ta kalleshi tare da cewa " Wow Yaya nagode, ina ka samo su?". Shima murmushin yayi yace "A can baya ne, muje na nuna miki inda suke da yawa". Ba musu ta miqe tabi bayansa har xuwa inda ya debo din. Wani babban guri ne an xagayeshi ruwa ne a ciki mai kyau da yawa sai fararen furen da suke a mai luf dasu, gurin yayi masifar kyau. Bata san sadda ta fara dariya ba tana furta " Woww gurin yayi kyau sosai". Shi kuwa kallonta kawai yake wani irin sonta na qara shigarsa, sun dan jima a gurin sannan suka koma cikin garden din damuwar dake xuciyarta duk ta kau sai wacce ba'a rasa ba. Juyawa tayi da nufin barin garden din, Ya kira sunanta a hankali, ta waigo ba tare da ta amsa ba, yace "ki xauna ina son muyi wata maga a dake". Ba musu ta koma ta xauna ba tare da ta kalleshi ba. Kallonta yake na dan wani lokaci sannan yace " Am Naana dama akan maganar case dinku ne keda Sadeeq, munyi magana da commissioner of police, yace zuwa nan da Monday xa'a shigar da qara". Gabanta ya fadi ta dago kanta ta kalleshi idonta har ya kawo kwalla, yayi saurin cewa "Look Naana, miye abin kuka kuma a ciki?". Ta sadda kanta qasa sannan ta dago tace " Yah Mahmoud ina jin tsoro ne nasan Sadeeq xai iya yin komai don ganin ya kubuce ma hukuma". Yayi saurin cewa "Don't be scared Naana, Sadeeq babu abinda xai iya, ke dai kawai hadin kanki muke nema". Tace " Yaya bani da evidance din da xan bayyana cewa Sadeeq ne y kashe min iyaye, saboda ni kadai ce a gidan sai Faheem". Mahmoud yace "Gud kinga Faheem ma shaida ne, don kuwa ya riqe fuskar wanda ya kashe mahaifinsa, sannan kuma ni da kaina xanje Katsina nayo qwaqqwaran bincike akan Sadeeq sannan kuma xan taho da shaidu". Ta danyi shiru tana naxari, ya cigaba da cewa " Ni xan xama lowyer'n ki, ni dai hadin kanki kadai nake buqata insha Allahu komai xai tafi dai2". Ta gyada kaj tare da cewa "Insha Allahu Yah Mahmoud". Yayi murmushi yace "Yawwa qanwata ynx tashi ki shiga gida kada ayi ta nemanki". Ba musu ta miqe suka nufi cikin gidan, shi ya wuce side dinshi, itama ta wuce cikin gidan. A falo ta iske Zee da Faheem suna kallo nan itama ta xauna, Zee tace " Ke kuma ina kika shige?". Tayi murmushi tace "Garden naje". Nan suka cigaba da kallon nasu hankali kwance. Bayan sun gama ta miqe ta koma dakinta tana tunanin maganar Yah Mahmoud, ita dai gani take Sadeeq baxai taba bari a hukunta shi ba, tamayi mamaki da akace har ynx yana hannun Hukuma, ko d yake ai ba Katsina bane, chan ne yake da ikon aikata duk abinda yayi niyya kuma ya xauna lapiya. Haka dai tayi ta faman tunane2 barkatai har barci barawo ya saceta, saj wajen la'asar ta tashi, tahe ta watsa ruwa sannan tayo Alwallah ta gabatar da sallar ta. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [29/10 7:06 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 6⃣9⃣---7⃣0⃣ OHW 📚 Tun daga Ranar Naana ta dan sake ma Yah Mahmoud duk da ba wani xama suke su kadai ba sai dai a falo, ynx tana danyin fira dashi ba kamar da ba. Kuma garden ya xama gurin xuwanta, tunda Yah Mahmoud ya nuna mata wajen flowers din nan. Yau ta kama monday, Ita da mummy da Zee ne xaune a falo suna kallo sai sukaji sallamar Mahmoud, da mamaki Mummy ta kalleshi tare da cewa "A a son Ya akayi ka dawo? Naga time din dawowarka bai yi ba". Mahmoud yayi murmushi ya qaraso cikin falon ya xauna kusa da ita tare da cewa " Yau ba aiki sosai, na dawo gida ne don yin wani aiki". Mummy tace "Tohm shikenan". Can yace " Am dama Mummy ina so in fada maki an shigar da qara yau, ranar friday xa'a shiga kotu". Sai da gaban Naana ya fadi, Mummy tace "Dakyau Barrister Allah ya kaimu lapiya". Ya amsa da " Ameen" sannan ya wuce part dinsa. Mummy ta kalli Naana tace "Naana tashi kije ki kai masa abincinsa". Ba musu ta miqe ta dauki abincin ta nufi part dinshi. Koda ta shiga falon bashi nan har xata ajiye sai ta tuna da yace ta daina ajiye mashi a falo hakan yasa ta shiga yi masa knocking, jin shiru yasa tayi tunanin ko yana wanka ne, ta tura qofar a hankali don ta ajiye mishi. Shi kuma dai2 lokacin ya fito daga wanka yana daure da towel da qaramin a hannunsa, karaf suka hada ido, tayi saurin juyawa da niyyar fita, har ta bude qofar ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanshi. Bata waigoba sai dai ta tsaya tare da cewa " Kayi hkr bansan xaka fito haka ba". Murmushi yayi ya jawo jallabiya ya sanya tare da cewa "Toh kixo ki ajiye min abincin". Qin motsi tayi, hakan yasa yace " To kai min falo ki jirani ina xuwa". Kamar jira take kuwa ta fice daga dakin, don ita bata taba ganin namiji a haka ba. Murmushi yayi tare da girgixa kai ya biyo bayanta, ya xo bakin qofa kenan jallabiyar ta harde mashi qafa, bai ankara ba sai ji yayi ya tiqi qasa, ji kake timm. "Arghhhhh" yayi er qara cike da jin xafin faduwar, Naana dake xaune a falo tayi saurin dagowa, sai ganinshi tayi rashe rashe a qasa, bata san lokacin da dariya ta kucce mata ba. Kallonta ya tsaya yi yans cije lebe, maimakon yaji haushinta sai gani yayi ta burgeshi dariyar tayi mata kyau sosai, qoqarin tashi yayi amma ya kasa ya riqe qugu yana ciccijewa da alama yaji xafin faduwar don kuwa tiles ne a qasan. Ganin hkan yasa Naana ta tsayar da dariyarta ta nufi inda yake fuskarta dauke da tausayi ta durqusa saitinshi tare da cewa "Sannu Yaya, me ka taka ka fadi". Bai bata amsa ba illah qoqarin miqewa da yake amma ya kasa. Miqo mata hannu yayi cikin wata murya yace " Plx help me". Tausayinsa taji ganin yadda yakeyi y tabbatar mata da ysna buqatar taimakon, hakan yasa ta riqe hannun nasa da niyyar taimaka masa ya tashi. Wani irin shock suka ji tun daga tsakiyar kansu har xuwa tafin qafa. A hankali suka kalli juna Naana tayi saurin dauke kanta ta miqe tana kiciniyar tada ahi tsaye amma ta kasa. Dafa bango yayi yamiqe a hankali yana cije pink lips nasa. Ta dago ta kalleshi tare da cewa "Yaya daki ko falo". A hankali yace mata " Daki". Don haka suka juya tana riqe da hannunsa suka koma dakin yna dan dafa bango. Har wajen gado ta kaishi ya kwanta tare da rintse idonsa, shi bai taba faduwa irin wannan ba, ya xame mishi dole ya daina sa jallabiya. Tana nan tsaye ta rasa me xata yi, ta kalleshi cike da tausayinshi tace "Yaya me xanyi maka ynx?". A hankali ya bude brown eyes dinsa da suka chanja kala zuwa maroon ya kalleta yace " Ba komai ki kawo min abincin kawai kije". Fita tayi ta kawo masa abincin, har xata tafi ta juyo tace "Yaya nga kana jin ciwo ko na kira mummy?". Girgixa mata kai yayi yace "No need, ki duba can cikin drower ki dauko min wani mai a ciki sai na shafa". Ba musu taje ta dauko masa ta basa sannan ta fita cike da tausayinshi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [30/10 11:34 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣1⃣---7⃣2⃣ OHW 📚📲 Shi kuwa tana fita ya cire jallabiyar ya daura towel sannan ya shafa man, ko abincin bai ciba ya kwanta barci yayi awon gaba dashi. Bashi ya tashi ba sai gab da la'asar ya miqe a hankali ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya shirya cikin qananan kaya. Sai a lokacin yaji cikinshi na kiran ciroma, hakan yasa ya xauna tare da jawo abincin yaci kadan ya rufe, ya miqe xuwa masallaci. Ita kuwa Naana bayan ta koma part din Mummy, tunani ta dinga yi ko ya jikin Yaya? Ganin bata da amsa yasa ta shige dakinta ta dan kishingida bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita. Kiran sallar la'asar ne ya tashe ta, bayan ta idar ta fito falo ta iske ba kowa hakan yasa ta xauna tana kallo. Bayan ya dawo daga masallacin part din Mummy kawai ya wuce, a falo ya iske ta ita kadai tana kallo, hakan yasa yaje ya xauna kan kujerar da ke facing dinta. Ita kuwa gaba daya hankalinta na kan TV din tana kallon wani series MARA & CLARA sam bata san ma da xamanshi ba, shi kuwa tsayawa yayi yana ta kallonta, gani yake kullum qara kyau take, sai faman murmushi yake. Ji tayi kamar ana kallonta hakan yasa ta waigo da kanta a hankali, suka hada ido da Mahmoud da ya kafeta da brown eyes dinshi yana murmushi. Da sauri tace "Lah Yaya yaushe ka shigo?". Ya dan kauda kanshi tare da cewa " Tunda kin maida hankalinki kan TV ta yaya xaki san na shigo?". Tayi murmushi tace "Film din yayi min dadi ne shiyasa bansan ka shigo ba". Murmshin shima yayi sannan ya maida kallonshi kan TV din na dan wani lokaci sannan ya kalleta yace " Kin ganni nan ni irin wadannan films din ba yimin suka yi ba, sai na jima ban tsaya na kalli cikakken film daya ba, sai dai naxo na iske ana kallo". Tace "Aikuwa Yaya suna da kyau sosai Allah, baya ma na Indians sun fi kyau". Murmushi yayi tare da cewa " Any way, ni barin shiga wajen Mummy, ki cigaba da kallonki". Daga masa kai kawai tayi ya miqe ya nufi dakin Mummy, ya barta nan tana kallonta hankali kwance _At Mummy's room_ "Mahmoud ban taba tunanin xaka bijire ma buqata ta ba, me yasa kake nema ka sani naji kunya?". Mummy ke wannan xancen. Ya dago kai ya kalleta tare da cewa " Mummy baxan so hakan ba, ni dai a ganina da an qyale wannan maganar kawai, ni sam banason Haleesa, ko na aureta ba dadin xaman xata ji ba, saboda bana sonta ko kadan Mummy ki duba mana". Kallon mamaki ta bisa dashi daga bisani tace "To in kaqi aurenta wa xaka aura? Ko haka xaka xauna ba aure?". Ya danyi shiru can yace " Mummy ki bani lokaci xan fito da matar da nake so insha Allahu". Tabe baki tayi tare da cewa "Koma dai miye ni dai ina kan bakana na auren Haleesa". Dafe kai yayi a hankali yace "Oh my god". Mummy tace " Mummy ta cika takura ko? Ko ba haka kae son fada ba?". Dan xaro ido yayi waje yace "Waa? Ni na isa na fadi haka?". Mummy ta tabe baki tace "kai dai ka sani ni tashi ka bani wuri". Miqewa yayi ya fice daga dakin ranshi a bace, shi kam baya tunanin xai iya auren Haleesa don kuwa baya sonta. Koda ya sauko qasa bai iske Naana a falon ba hakan ya tabbatar masa da ta gama kallon nata,kallon dakinta yayi ji yake kamar yaje ya ganta ko yaji sanyi a ransa, sai kawai ya share ya fice daga falon. Naana kuwa dakin Zee ta wuce ta iske su suna game a wayar Zee din nan itama ta xauna suka cigaba da buga game din tare suna dariya. _Washe gari_ Suna xaune ita da Zee a falo, Faheem ya kalli Zee yace "Aunty ice cream xansha". Zee tace " Tab kuma gashi ice cream dinka ya qare". Naana tace "Ke kike biye mashi Allah, kullum shi bai gajiya da shan ice cream?". Tsalle ya fara yi a tsakar falon wai shi ala dole sai an bashi ice cream. (Ni kam nace Oh su Faheem samun guri😕) Mahmoud ne ya shigo falon , da sauri Faheem ya qarasa wajensa yana dariya don sun saba sosai, Mahmoud ya daga shi sama yana dariyar data qara fito da kyawunshi, yace " My boy kai dawa na jika tun a qofar falo?". Yayi caraf yace "Nace Aunty ta bani ice cream shi ne tace ya qare". Yayi murmushi yace "To muje in siyo maka ice cream kaji". Nan ya hau murna. Suka fice daga falon don xuwa siyen ice cream din. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [30/10 2:30 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣3⃣---7⃣4⃣ OHW 📚📲 _Ranar friday_ Da misalin 10 Mahmoud ya shigo part din Mummy, sanye da suit baqa da trouser din shima baqi, sai ta cikin ce ta kasance fara da baqin necktie, yayi kyau sosai da jakar laptop riqe a hannunsa. Mummy tace "Son har ka fito kenan?". Murmushi yayi tare da cewa " Eh Mummy ynx aka kirani a office ana jirana". Mummy tace "Tohm a dawo lpy, Daddynku ma yace na fada maka, idan an kusa shiga court din ka kirashi a waya, don yana da wani meeting ne ma yasa bai tsaya ba". Mahmoud yace " Shikenan Mummy xan kirasa insha Allah". Mummy tace "Yawwa toh". Nan ya fice xuwa office din. Naana kau yau tashi tayi da wani matsanancin ciwon kai, gabanta nats faduwa don kuwa bata manta ba, yau ne xasu shiga kotu abinda ko a mafarki bata taba tunanin xai faru da ita ba. Wajen 11:20am Mahmoud ya kira Mummy yace su shirya ynx xai xo ya daukesu su tafi kotun, nan Mummy ta fada masu Naana, ji take kamar a fasa xuwa kotun don kuwa ita duk a tsorace take. _11:45am KOTU_ Babbar kotun ta cika maqil da mutane, su Daddy da su Mummy har dasu First lady ma duk sunxo, Naana dai tana gefen Mummy a rakube, yayinda Zee ke riqe da Faheem. Hayaniya kawai ke tashi a cikin kotun saboda Alkali bai kai ga shigowa ba, ba a dade ba sai ga Alkali ya shigo, gaba daya aka miqe tsaye har sai da ya xauna sannan ya umarci kowa ya xauna, akayi addu'a kowa ya shafa. Shiru ya ratsa cikin kotun, yayinda aka miqa ma alqali wasu takaddu yana dubawa, can kuma ya dago ya kalli kowa, sannan yace "Kotu tana buqatar ganin lawyer'n mai qara da kuma wanda ake qara" wani lawyer ne ya miqe tsaye tare da cewa " Sunana Br. Salman Usman, ni ne lawyer mai kare wanda ake qara". Sannan ya dan rusuna ya koma ya xauna. Sai Mahmoud ya miqe, shima tare da cewa "Sunana Br, Mahmoud Isma'il kwangila, nine lawyer mai kare wacce take qara". Nan shima ya koma ya xauna, Alkali yayi en rubuce rubuce a kan takarda sannan ya dago da kanshi ya kalli Br, salman yace " ko kana da abinda xaka fada br?". Br, salman ya miqe tare da cewa "Ya mai girma mai shara'a ina roqon kotu da ta gayyato min wacce take qara". Alkali ya kalli jama'an sannan yace " Kotu tana buqatar ganin wacce take qara". Jikin Naana har wani bari yake, Mummy ta tabota, daqyar ta iya miqewa ta isa gaban kotun ta shiga wurin da ake tsayawa ta tsaya. Br, salman ya qaraso inda take ya tsaya gabanta ya kalleta sannan yace "Kotu tana buqatar sanin sunanki". Kanta na qasa tace " Sunana Bilkisu Almustapha,(Naana)". Br, salman ya jinjina kai tare da cewa "Shin zaki iya bayyana ma kotu ko waye Sadeeq a gareki?". Dago da kanta tayi ta kalli inda Mahmoud yake idonta har ya ciko da qwalla, ya jinjina mata kai alamun ta fada kawai, ta maido kallonta kan Br, Salman ta bude baki tace " Sadeeq shine wanda ya kashe min iyayena da kuma yayana". Tuni hawaye suka xubo mata. Br, Salman yace "Toh ko xaki iya bamu shaidar da ta tabbar da cewan shi ya kashe miki iyayenki da yayanki?". Shiru tayi can kuma tace " Allah shine shaida ta, ya kashe min iyayena a gaban idona". Murmushi Br, yayi tare da girgixa kai sai kuma yace "Ta yaya xai kashe miki iyayenki ba tare da kowa ya sani ba, in a cikin gida aka yi kisan meyasa baki yi ihu ba maqwabta suka shigo? In kuma a waje ne ta yaya xa'a yi ya kashe iyayenki a bainar jama'a ba tare da kin samu shaida ba?". Shiru tayi tana hawaye don bata san mai xata fada ba ma. Br, Salman ya cigaba da cewa " Kuma miye dalilin da yasa ya kashe miki iyayenki? Sannan kuma dame ya kashe su, kuma wace hujja xaki bamu ta tabbatar da cewa shi ne yayi kisan? Kuma.......... "Ina da ja ya mai girma mai shari'ah, ya kamata Br, ya sassauta tambayarsa a kanta domin kuwa yanda yake tambayoyin nasa suna rikitar da ita". Alkali ya kalli Br, salman sannan yace " Br, ka gyara salon tambayoyinka". Br, Salman yace "Nagode ya mai girma mai shari'ah Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [30/10 7:24 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣5⃣---7⃣6⃣ OHW 📚📲 Mahmoud ya koma ya xauna, Br, Salman yace "Ya mai shari'ah a gani na tunda har malama Naana ta kasa bada wadannan amsoshin, to ina ganin sharri ne kawai xata kulla mashi don ganin ta bata masa suna". Da sauri Naana tace " A a ya mai girma mai shari'ah wllh ba sharri nake masa ba, duk abinda na fada gaskiya ne". Sai kuma ta fashe da kuka, Alkali yace "Malama Bilkisu kotu ba gurin *Zaman makoki* bane don haka ki tsayar da kukanki". Nan ta tsayar da kukan nata. Br, Salman yace " Ya mai girma mai Shari'a, ya kamata kotu tayi duba da rashin hujjojin Naana, ta bima wanda ake tuhuma haqqinsa, Nagode". Ya dan rusuna sannan ya koma ya xauna. Alkali yayi rubutu akan takarda sannan ya dago ya kalli Mahmoud yace "Br, ko kana da abin cewa?". Mahmoud ya miqe yace " Qwarai kuwa ya mai girma mai Shari'a ina da abin fada". Alkali yace "Kotu ta baka dama". Nan ya fito cikin takunsa na qasaita ya qarasa wajen da Sadeeq yake tsaye, ya kalleshi tare da yin dan murmushi yace " Shin ko xamu iya sanin haqiqanin sunanka?". Cikin gadara Sadeeq yace "Sadeeq Ibrahim Naira". Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa " Da kyau malam Sadeeq, ina so nayi maka wasu en tambayoyi da nasan baxaka rasa amsarsu ba". Sadeeq yace "Fadi dukkanin tambayoyinka xan amsa su ko wadanne iri ne". Mahmoud ya gyada kai tare da cewa " Shin ko zakayi mana bayanin ko wacece Naana a gareka?". Kallon inda Naana take yayi sannan yace "Ban santa ba". Da sauri ta dago kai ta kalleshi da mamakin jin furucinsa na cewar bai santa ba". Mahmoud ya daure fuska ya koma Mahmoud dinshi na xahiri sannan yace " Kotu ba gurin wasa bane, don haka dole ka fadi alaqarka da Naana". Kallonshi Sadeeq yayi tare da cewa "Amsa nawa kake so na baka? Nace maka ban santa ba, yau ce rana ta farko dana soma ganinta". Mahmoud yace " Any way, wane laifi iyayenta suka yi maka da har ka kashe su, kuma miye dalilinka na sace Naana sati hudu da ya wuce?". Sadeeq yace "Ban santa ba ta yaya xan kashe mata iyayenta kuma na saceta?". Mahmoud ya maida kallonsa ga Alkali sannan yace " Ya mai girma mai Shari'a, Sadeeq yana nema ya maida kotu gurin wasa, bisa la'akari da irin amsoshin da yake bayarwa, ya kamata wannan kotu mai adalci tayi gaggawar yanke ma Sadeeq hukunci dai dai da laifin daya aikata, domin kuwa shine ya kashe mata iyayenta". "Ina da ja ya mai Shari'a, ya kamata Br, ya riqa gyara kalamansa, domin kuwa babu yadda xa'ayi a kama mutum da laifin da bai aikata ba, kuma babu wasu qwararan hujjoji". Br, Salman ya fada. Alkali ya kalli Br Mahmoud sannan yace " Br, ka gyara salon xancenka". Mahmoud ya dan rusuna tare da cewa "Nagode ya mai Shari'a". Br, Mahmoud ya cigaba da cewa " Ya mai Shari'a xanso kotu ta bani dama don na gabatar da shaidata ta farko". Alkali yace "An baka dama". Nan ya waiga ya kalli Zee dake riqe da Faheem yace " Zo Faheem". Ba musu ya miqe ya taho wajen Mahmoud din. Jan hannunshi yayi har xuwa tsakiyar kotun yace "Ya mai Shari'a wannan da ne ga yayan Bilkisu wanda Sadeeq ya kashe, a gaban idonshi aka kashe mashi iyayenshi, kuma na tabbata ya riqe fuskar wanda ya kashe mashi mahaifi". Cike da Mamaki Alkali ke kallon Faheem, yaro dan 3yrs xai iya riqe wani abu?. Br, Mahmoud yaja hannun Faheem xuwa gaban Sadeeq ya nuna mashi Sadeeq sannan yace " Faheem xaka iya gane wannan?". Shiru Faheem yayi yana kallon Sadeeq. Br Mahmoud yace "Tuna dai Faheem ka taba ganinsa ko?". Kara kallonshi yayi sannan ya kalli Mahmoud yace " Shine yaji ma Abee da Abba rauni jiya, kuma har da Umma ma". Kowa kallonshi yake da mamaki. Br, Salman ne yayi qarfin halin cewa "Ya mai Shari'a ta yaya xa'ayi yaro dan shekara 3 ya bada shaida? Shi da ko sanin kansa ma baiyi ba". Alkali ya kalli Br Mahmoud yace " Br ka samo mana shaidar da xata gamsar uu cewa Sadeeq ne yayi kisan, wannan ba hujja bace da xata tabbatar da xarginku". Br, Mahmoud yace "Nagode ya mai Shari'a". Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [01/11 12:26 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣7⃣---7⃣8⃣ OHW 📚📲 Sannan ya cigaba da cewa "My lord, ina neman kotu ta qara bani dama don gabatar da shaidata ta biyu". Alkali yace "An baka". Nan yace "Nagode". Sannan ya waiga yace "Ina neman kotu ta bani damar gabatar da malam Yahaya". Alkali ya kalli jama'an sannan yace " Kotu tana buqatar ganin Malam Yahaya a gabanta". Wani dattijon mutum ne ya taso, Naana ta dago kanta don ganin ko waye, sai ganin daya daga cikin mutanen unguwarsu ne, wadanda suna qofar gidanmu a lokacin da abin ya faru. Murmushi ta saki don tana tunanin xai bada shaida, Naana ta fita daga gurin ta koma maxauninta, yayinda shi kuma mutumin ya shiga ya tsaya. Br Mahmoud ya qarasa wajensa ya kalleshi tare da cewa "Malam ko xamu iya sanin sunanka?". Malam Yahaya yace " Sunana malam Yahaya a garin katsina nake, unguwar katarda". Br Mahmoud ya jinjina kai tare d cewa "Ko kasan wannan yarinyar?". Ya qarashe maganar yana nuna masa Naana da hannunsa, malam Yahaya ya kalli Naana sannan yace "Qwarai kuwa na santa, a unguwa daya muke da ita". Br Mahmoud yayi murmushi tare da cewa "Wannan fa?" Ya nuna Sadeeq, kallonshi yayi ya sadda kai qasa sannan yace "Sau daya na taba ganinsa a unguwarmu". Mahmoud yace " Toh ko xaka iya fada mana yadda ka ganshi?". Mlm Yahaya yace "Ganinsa kawai nayi ya wuce a mota". Mamaki ne ya cika Naana jin abinda yake fada. Br Mahmoud ma ya cika da mamaki, domin kuwa sadda yaje Katsina sai da yayi mashi bayanin komai, kuma yace xai fadi gskyr abinda ya sani in anxo kotu, amma kuma gashi ynx yaqi fada. Br Mahmoud yace " A a mlm Yahaya ka fada mana gaskiyar abinda ka sani a kan kisan iyayen Naana". Malam Yahaya yayi saurin cewa "Yaro na fada maka bansan komai a kai ba, ni dai kawai naji labarin mutuwar iyayenta a bakin jama'a amma bansan komai ba bayan wannan". Mahmoud ya danyi shiru can ya kalli Alkali yace " My lord, duk abinda Malam Yahaya ya fada ba gsky bane, yasan komai akan kisan iyayen Naana, saboda yana daya daga cikin mutanen da ke qofar gidan nasu suna kallon duk abinda ya faru, wata qila anyi masa wata baraxana ce hakan yasa ya kasa fadar gaskiyar abinda ya sani". Alkali yayi en rubuce 2 sannan ya dago ya kalli Br Mahmoud yace "ta yaya akayi kasan hakan Br?". Br Mahmoud yace " Ya mai Shari'a, shekaran jiya naje garin katsina unguwarsu Naan, nayi bincike sosai akan Sadeeq, a nan ne na gamu da wannan mutumin kuma ya bani hadin kai 100% ya fada mani duk ynd abun ya faru, kuma ya tabbatar mani da cewa xai bada shaida a kotu". Alkali ya kalli Malam Yahaya yace "Shin kaji abinda ya fada gaskiya ne?". Malam Yahaya ya girgixa kai tare da cewa " Ni bansan da wannan xancen ba, ban ma sanshi ba, yau ne rana ta farko da na fara ganinsa". Br Mahmoud sake baki yayi yana kallon Malam Yahaya cike da mamakin furucinsa. Alkali ya maida kallonsa kan Br Mahmoud sannan yace "To kaji dai abinda ya fada Br, shin ko kana da wasu tambayoyin da xaka yi masa?". Ya girgixa kai tare da cewa " Bani dasu ya mai Shari'a, amma ina qara shaidawa kotu cewar Sadeeq shi ne yayi wannan kisan". Yana kaiwa nan ya dan rusuna tare da cewa "Nagode ya mai Shari'a". Sannan ya koma maxauninsa. Alkali ya maida kallonshi kan Br, Salman yace " Br ko kana da abun fada?". Br, salman ya miqe tare da dan rusunawa yace "Babu ya mai Shari'a". Sannan ya koma ya xauna. Alkali ya kalli jama'ar tare da cewa " An daga wannan qara i xuwa 08/11/016, ya kama nan da sati daya kenan, kuma za'a tsare wanda ake qara har xuwa ranar da xa'a sake wani xaman". Yana gama fada ya buga wani abu, sannan ya miqe, suma jama'an duk aka miqe kotu da dauka da Court!. Nan duk kowa ya fice kowa yana furta albarkacin bakinsa, Naama dai hawaye kawai take sharewa akai2, Zee na lallashinta har suka shiga mota suka wuce gida. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ BASO A RAINA 2[02/11 9:59 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣9⃣---8⃣0⃣ OHW 📚📲 *Note:- Assalamu alaikum, dafatan kun tashi lpy masoyyana, kuyi min uxuri a bisa dan kuskuren da nayi na rubuta 08/11/016, ba haka naje son rubutawa ba, 08/10/016 nake son rubutawa, ku huta lapiya, luv u oll😘* *************** Suna komawa gida duk suka wuce su don gabatar da sallar axahar, bayan sunyi duk suka fito falo don yin lunch amma banda Naana tana daki duk damuwa tayi mata yawa, ita tasan Sadeeq baxai tava bari a hukunta shi ba. A falo duk suna xaune a dinning, Mahmoud ya shigo shima ya xauna, nan ya duba kujerar Naana yaga bata nan, hakan yasa ya kalli Zee yace "Sis ina Naana take ne? Naga bats fito ba". Zee ta miqe tana cewa " Ynx nake shirin shiga na kirata". Bai kuma cewa komai ba, ta wuce Dakin Naana. Tunda suka fito yake ta kallonta, wani irin sonta ne ke qara shiga xuciyarsa, ji yake a duniyar nan in ya rasa Naana baxai iya rayuwa ba ma baki daya. Har suka xo suka xauna bai sani ba, sai da Zee ta dan taboshi tare da cewa "Yah kaci abincin mana". Sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, ya dan dafe kanshi sannan ya cigaba da cin abincin nasa, a hnkl yana dago kai yana satar kallon Naana. Mummy duk tana lura da yanayinsa, ta share kawai, amma ta dau aniyar da an gama wannan Shari'ar xa'ayi bikinshi da Haleesa. A haka har suka gama cin abincin nasu, kadan Naanata tsakura ta miqe, Mummy tace " Ba dai har kin qoshi ba". Murmushi ta qaqaro tare da cewa "Mummy na qoshi". Gyada kai kawai tayi ita kuma Naana ta wuce dakinta. Tana shiga Mahmoud ya miqe shima, Mummy ta saki baki tana kallonshi tace " Son kaima din ka qoshi?, ji fa dan abincin da kaci". Kallon abincin yayi, ko rabi bai yi ba, kuma kadan ne a cikin plate din, ya kalli Mummy yace "Mummy I'm satisfy wllh". Daddy dai bai ce komai va har ya fice daga falon ya nufi part dinsa, kafin ya shiga sai ga motar Abdul ta shigo gidan, nsn ya tsaya har yayi parking ya fito ya sameshi a gurin. Abdul yayi murmushi tare da cewa " Hey frnd y kk?". Mahmoud shima murmushin yayi tare da cewa "Ina lpy frnd, daga ina haka?". Abdul yayi er dariya tare da cewa " Daga gida mana, naxo jin yadda aka yi ne a court, ban samu xuwa ba cox I'm busy wllh". Mahmoud yace "Ynx dai muje ciki tukunna". Ba musu Abdul yabi bayanshi suka shiga cikin falon. Kan kujera suka xauna, Abdul ya kalli Mahmoud yace " Ina sauraronka". Mahmoud ya dago kai ya kalli Abdul, nan ys fada masa duk yanda akayi. Abdul ya jinjina kai tare da cewa "Tab lallai gayen nan mugun mutum ne, kuma na tabbata shi ne xai sa a tsoratar da mutumin nan ya kasa fadar komai a kai". Mahmoud yace " Nima hakan nayi tunani, amma kasan me xanyi?". Abdul ya girgixa kai alamun sai ya fada, Mahmoud yace "Gobe in Allah ya kaimu xanxo tun ds safe ka rakani Katsina, zan qara samo shaidu da yawa sai na taho dasu nan". Abdul ya danyi shiru yana naxari sai kuma yace " Tabbas hakan yayi Allah ya kaimu lpy". Nan ya amsa da "Ameen". Nan suka cigaba da tattaunawa kamin Abdul ya tashi ya tafi, shi kuma ya watsa ruwa ya kwanta don ya dan huta. _Washe gari_ Tun da safe ya gama shirinshi ya shiga part din su Mummy nan ya gaishe su, Mummy tace " Ina xuwa kuma da safen nan?". Mahmoud yace "Mummy Katsina xani". Cike da mamaki mummy tace " Katsina kuma me akeyi?". Kafin yayi magana Daddy yace "Kema dai da wata tambaya, ina ce yarinyar nan a Katsina take? Kinga a dole xaije can don neman shaidun da xai gabatar a kotu" Mahmoud yace " Hakane kam Daddy, Mummy dole inje Katsina". Mummy tace "To shikenan a dawo lpy". Ya amsa da " Ameen Mummyna". Nan ya fice ya wce gidansu Abdul, shima lokacin ar ya shirya yana breakfast, don shi sam baya wasa da cikinsa, ba kamar Mahmoud ba da ba sosai ya cika cin abinci ba, bayan sun gaisa da Mum din sa ya xauna a dinning ya dan ci kadan, sannan suka miqe suka yi mata sallama, tayi masu Addu'a sannan suka fito. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [02/11 2:08 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣1⃣---8⃣2⃣ OHW 📚📲 A motar Mahmoud suka tafi, wurin qarfe 10 suka isa katsina, basu xame ko ina ba sai unguwar katarda, nan sukai parking a wajen wani babban chemist, sannan suka fito suka jingina da motar. Abdul ya kalli Mahmoud yace "Aboki ynx ta ina xamu fara?". Mahmoud ya danyi shiru yana naxari can yace " Bari muga ni". Wani mutumi ne yaxo wucewa Mahmoud yayi saurin tsayr dashi ta hanyar cewa "Malam don Allah ina da tambaya ne". Mutumin ya tsaya yana kallon Mahmoud sannan ya tsaya, su Mahmoud suka qarasa inda yake. Hannu suka miqa mashi, bayan sun gaisa Mahmoud yace " Don Allah tamabaya muke". Mutumin yace "Allah yasa na sani". Ya gyara tsayuwarsa tare da cewa " A unguwar nan kasan wani Sadeeq Ibrahim Naira?". Da sauri mutumin ya kalli Mahmoud ya girgixa kai tare da cewa "Sadeeq? Ni bansan shi ba, sai dai ku tambayi wani". Yana kaiwa nan ya kama hanyar tafiya, Mahmoud na tayi masa magana amma ya share shi yayi wucewarsa. Mamaki ya cikasu, sai kuma ya bar mamaki saboda tuna ko waye Sadeeq a garin katsina. Haka suka yi ta tsayar da mutane suna tambayarsu amma duk amsa daya suke basu cewa basu sanshi ba, haka suka haqura har xasu shiga mota sai ji sukayi ance " Ai baxaku taba samun wanda xai fada maku ko waye Sadeeq ba". Da sauri suka juyo don ganin ko wacece don muryar mace sukaji. *Hadixa* ce tsaye a bayansu, suka tsaya suna mata kallon rashin sani. Ganin hakan yasa Hadixa tace "Kuxo muje can nesa don bana so a jini ina fada maku wani abu akan Sadeeq". Ba musu suka bi bayan Hadixa har xuwa bayan Chemist din inda ba mutane sannan suka xauna akan dandamalin da ke gurin. Mahmoud ya kalleta yace " Wacece ke? Shin kina da abinda xaki fada mana akan Sadeeq ne". Hadixa ta gyada kai tare da cewa "Kwarai kuwa, ni a shirye nake da na bada hadin kai wajen ganin an hukunta Sadeeq, amma kafin nan ku fada min ku suwaye, ba dai cutar damu xakuyi ba ko?". Mahmoud yace " Ko daya, Ni sunana Br, Mahmoud wannan kuma aboki nane Abdul-wahab,a garin kano muke munxo ne don samun cikakken bayani akan Sadeeq, saboda muna zarginshi da kisan iyayen wata yarinya a garin nan kuma itama yana so ya kasheta". Da sauri Hadixa ta kalleshi tare da cewa "Wacece yarinyar?". Abdul yace " Kafin mu fada maki ya kamata ki fada mana ko ke wacece da kuma abubuwan da kika sani akan Sadeeq". Idonta ya ciko da qwalla tace "Sadeeq shi ne ya rabamu da er uwarmu kuma qawarmu, ya kashe mata iyayenta da kuma yayanta don sunqi amincewa ya aureta, shi ne ta gudu da dan yayan nata, tun daga lokacin yake nemanta..... " Kuka ne yaci qarfinta tuno qawarta Naana da tayi. Mahmoud ya kalli Abdul da mamaki sannan ya maida kallonshi kan Hadixa yace "Kece Hadixa ko Aisha?". Itama da mamaki ta kalleshi jin ya ambaci sunansu, tace " Ya akayi kasan mu?". Mahmoud yace "Kafin nan, ai kinsan Bilkisu ko? Wacce ake kira da Naana". Da sauri Hadixa ta miqe tsaye tana cewa " wai duk ya akayi kasan mu?". Mahmoud yace "Calm down xauna ki fada min komai nima xan fada miki". Jiki a sanyaye ta koma ta xauna ta fada masu tun daga farkon haduwarsu da Sadeeq har xuwa lokacin da ya kashe mata iyayenta, wanda wani maqwabcinsu ne akayi komai a gabansa yaxo yake bada labarin. Mahmoud ya jinjina kai tare da fada mata duk ynd akayi tun faga gudun su Naana har xuwa kawo yau da ake shari'a. Hadixa sosai ta tausaya wa qawarta jin irin gwagwarmayar da tasha a rayuwa, tabbas ya xama dole a gareta ta bada shaida a kan Sadeeq don ta taimaki qawarta wajen ganin ta qwato encinta. Mahmoud yace karta fada ma kowa wannan xancen xuwa anjima kafin su tafi xai qara nemanta asan yadda xa'ayi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [04/11 12:48 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣3⃣---8⃣4⃣ OHW 📚📲 Haka kuwa akayi nan Hadixa tayi masu kwatancen gidansu, bayan sunje restaurant sunci abinci sannan suka nufi gidan su Hadixa, a nan suke fada mata cewa karta fada ma kowa, ana saura kwana daya a koma kotu xai turo mota a dauketa don ta bayar da shaida. Ta amince da hakan, nan suka mata sallama sannan suka shiga mota suka nufi hanyar kano. Wajen La'asar suka isa, sai da ya sauke Abdul gida sannan ya wuce nasu gidan, yana yin parking ya fito ya wuce part dinsa, toilet kawai ya fada ya watsa ruwa sannan ya fito ya xura wasu qananan kaya da ganinsu kasan na shan iska ne. Fita yayi xuwa masallacin gidan bayan sun idar da sallah ya nufi part din Mummy. Yana shiga ya iske ta xaune a falo tana kallon news a Aljazeera, gefenta ya xauna yana "Washh!". Mummy ta waigo ta kalleshi tare da cewa " Son Wash kuma sai kace wata mace?". Ya dago brown eyes dinshi ya kalli Mummy tare da cewa "Mummy I'm so tired wllh". Mummy tayi murmushi tare da cewa " Ayya to ya kamata aje a huta". Miqewa yayi ya kalli Mummy tare da cewa "Ina su Zee suka shiga ne naji su shiru?". Mummy ta dan tabe baki tare da cewa " Zee tana dakinta ita da Faheem, Naana kuma na dakinta". Juyar da kai yayi tare da wucewa wajen frigde ya dauko juice ya tsiyaya a cup sannan ya dawo falon ya xauna, kadan yasha ya ajiye sauran ya miqe tare da cewa "Mummy bari naje na dan huta". Mummy tace " Hakan na da kyau my son". Murmushi yayi ya wuce side dinsa, yana xuwa ya fada kan kujerar falon barci mai nauyi ya daukesa cike da dreams kala2. ****** Zaune yake a cikin garden din gidan hannunsa riqe da Apple yana balla a hankali yana lumshe ido saboda iskar da ke kadashi mai dadi. Yana bude idon nasa sai ganinta yayi ta nufo wajensa fuskarta dauke da mumushi, tana sanye da wata doguwar riga Arabian gownt tayi rolling kanta dz mayafin, ba qaramin kyau tayi ba, cikin takunta mai daukar hnkl ta iso wurinsa. Zama tayi a daya daga cikin kujerun, har a lokacin bai bar kallonta ba, sai da ta dan tafa hannunta saitin fuskarsa sannan yayi firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula. Wani lallausan murmushi ys sakar mata cike da so da qaunarta, sam ya kasa furta mata ko da kalmar A ne. Ganin hakan yasa tayi murmushi tare da cewa cikin muryarta mai sanyi "Yah Mahmoud tunanin me kake haka?". Kallonta dai yake bai ce komai ba. Ta kuma cewa " Say something mana Yah Mahmoud ". Sai a lokacin ya bude bakinsa a hankali yace " *I love you Naana*. Murmushi tayi ba tare da tayi magana ba. Tasowa yaui daga kan kujerar da yake ya dawo inda take tare da riqo hannunta ya miqar da ita sannan yaja hannun nata xuwa wajen Flowers din dake garden din. Suna xuwa ya tsinko wata flower red nd green, ya dawo inda take tsaye tare da duqawa da qafa daya, dayar kuma ya dora hannusa mai flower a kai tare da miqa mata flower yace " *I so much loving you Naana, i can't live without telling u dat i love u, pls say u love me*". Murmushi tayi mai sanyi tare da amsar flower daga hannunsa ta shinshina, qamshi mai dadi taji hakan yasa ta lumshe idonta tare da budewa ta kalli Mahmoud dake duqe har lokacin, a hankali ta bude bakinta tare d cewa " *Yah Mahmoud i......* ******A firgice ya farka daga nannauyan barcin daya daukeshi sakamakon qarar wayarshi da yaji. Wani mugun haushi ne ya xiyarci xuciyarshi lokaci daya, ya jawo wayan bai duba ko waye ba yayi swiching off dinta sannan ys koma ya kwanta tare da runtse idonsa wai ko xai cigaba da mafarkin nasa amma hakan bai samu ba, don ya kasa komawa barcin ma gaba daya. Ya miqe ya koma dakinsa ya watsa ruwa tare da yin alwallar magrib ya fice xuwa masallaci don gabatar da Sallah. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [04/11 11:24 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣5⃣---8⃣6⃣ OHW 📚📲 Naana kuwa tana daki don ji tayi bata son fita, ta dan kishingida barci mai nauyi ya dauketa, a cikin barcin take mafarkin wani mutum ya bata flower kuma ya furta kalmar so a gareta, sai dai bata ga fuskarshi ba ko kadan, haka ta tsinci kanta da furta masa kalmar *I love you*. Firgigit ta miqe daga barcin nata tana addu'a , sai kuma ta shiga girgixa kai tana cewa "No... No it can't be possible, baxai yuwu ba, babu wanda xan fada wa haka". Shiru tayi tana tunanin mafarkin, to waye shi mutumin? Tambayar da take tayi wa xuciyarta kenan, amma ta rasa amsarta, haka ta miqe ta fada toilet ta dauro alwalla taxo ta gabatar da sallah. Tana idarwa ta miqe tare da linke hijabin da carpet din ta maidasu gurin da suke sannan ta fito xuwa falo. Koda ta fito ba kowa a falon, hakan yasa ta wuce kitchen ko Zee tana can tana hada dinner. Yah Mahmoud ma yana fitowa masallaci ya nufo cikin gidan yau bai tsaya ayi isha'i ba saboda wata irin yunwa da yake ji. Part din mummy kawai ya wuce, ya shiga falo bai ga kowa ba, hakan yasa ya wuce kitchen don samo abinda xai danci don baxai iya jira ba har lokacin da xa'ayi dinner. Ita ma Naana ganin Zee bata nan yasa ta nufo hanyar fita, dai dai lokacin Mahmoud kuma xai shigo, wani uban karo suka ci har sai da Naana tayi baya xata fadi, da sauri ya taro ta ta fada jikinsa, runtse ido yayi sakamakon wani irin yanayi da ya tsinci kansa a ciki na riqon da yayi ma Naana. Ita kam xafin qumewar da suka yi shi ya addabeta, ita har ta sadaqas ma sai ta fadi amma ga mamakinta sai ji tayi ya riqota don tayi xaton kamar wancen lokacin xai barta ta fadi ne. Dai dai lokacin kuma Zee ta shigo kitchen din, tsaye tayi da mamaki take kallonsu, Zee tayi gyaran murya hakan yasa Mahmoud yayi saurin sakinta tare da dafe goshin shi, shi sai a ynx ma yaji xafin. Zee kuwa kallonsu take cike da tuhuma, ganin hakan yasa Naana ta sadda kanta qasa, Mahmoud kuwa ficewa yayi daga kitchen din, don ji yayi ma ya daina jin yunwar. Bayan fitarsa Zee ta kalli Naana tare da cewa "Ya akayi Naana". Naana ta dago da kanta ta kalli Zee sannan tace " Karo mukayi dashi shi ne na kusa faduwa ya taimakeni". Kallon goshinta tayi ganin har ya fara kumburi yasa tayi saurin qarasawa wajenta cikin muryar tausayi tace "Ayya sannu kinji, gurin har yayi kumburi, kawo na matsa miki". Nan ta fara matsa mata gurin, Naana tayi er qara tace " Ke da xafi fa?". Zee tace "To ai dole xaiyi xafin, in kika barshi girma xaiyi". Haka ta matsa mata gurin sosai sannan suka kwashi kayan abincin suka jera a dinning sannan suka wuce daki suka gabatar da Isha'i, bayan sun idar suka fito gaba dayansu suka xauna a dinning har da Daddy da Mummy. Sai da suka fara ci Mummy tace " Ina Mahmoud ne". Kafin suyi magana sai gashi ya shigo da sallamarshi, nan yaja kujera ya xauna suka fara dinner. Mummy ta kalleshi sosai ganin ynd goshinshi yayi ja, abinka da farin mutum, tayi saurin cewa "Son me ya sameka a forehead naga yayi ja?". Kallon Mummy yayi sannan ya saci kallon Naana suna hada ido ta sadda kanta qasa. Murmushi yayi tare da cewa " Daxu ne da xan fito toilet na xame na fadi". Dariya ta so kucce ma Zee jin abinda yace Mummy tace "Ayya sannu kaji". Daddy ma yace " Ruwa ka taka ko ya xameka". Yace "Eh Daddy ruwa ne ya xuba a qasan". Daddy yace "To Allah ya sawwaqe" Duk suka amsa da "Ameen". Nan dai sukayi dinner dinsu bayan sun gama suka koma Falo, Mahmoud ya fice xuwa side dinsa don yana da aikin da xaiyi. Naana kuma ta wuce dakintadon yau bata sha'awar kallon. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [05/11 12:35 pm] Beelybadaru😍: [04/11 4:59 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣7⃣---8⃣8⃣ OHW 📚📲 _5 days later_ Ana gobe kenan xasu koma Kotu, ita dai Naana duk jikinta yayi sanyi, gani take Sadeeq xai yi yanda zaiyi wajen ganin ya kubuce wa hukuncin kotu. Yah Mahmoud ya tura mota a dauko Hadixa, tun safe amma har wajen la'asar shiru ba labarin su, ko ya kira nmbr'n driver din baya samun shi, ya shiga damuwa, ya kira Abdul ya fada masa, Abdul yace ya kamata suje Katsina su gano ko lpy, bai yi masa musu ba ya hau shirin xuwa Katsina. Koda suka isa gidansu Hadixa suka wuce, a qofar gida suka iske Abbanta, da yake sun gabatar da kansu gareshi wancen xuwan hakan yasa suka gaisa cikin fara'ah, ya qara da cewa "Hadixa tun wajen Axahar suka tafi, in ce sun isa ko?". Da mamaki suka kalli juna shi da Abdul, sannan ya kalli Abban Hadixa yace "Abba kana nufin tun daxu suka tafi Kano?". Abba da mamaki yace " Qwarai kuwa, nan wani yaxo yace kai ka aikoshi ya tafi da ita kamar ynd muka yi da kai, kana nufin basu isa ba har kuka taho?". Mahmoud ya danyi shiru yana naxari can yace "Abba shin yaran Sadeeq suna shigowa unguwar nan kuwa?". Abban Hadixa yace " Qwarai kuwa, kullum sai sun shigo unguwar nan". Dafe kanshi yayi tare da cewa "Oh my god, ai kuwa bamu ga ta xama ba, dole mu san abinyi don na tabbata yaran ne xasu tare su Hadixa a hanya". Salati Abban Hadixa ya hau yi cike da tsoro da rudu, yace " Yaro ka taimakeni, Hadixa ita kadai na mallaka, ku taimaka ku nemo min inda yata take". Abdul yayi saurin cewa "Abba kayi hkr insha Allah xa'a ganta". Abba kam har ya fara hawaye. Mahmoud ya furxar da iska mai xafi tare da cewa " Abba yanxu abinda za'ayi ka taho muje Kano din in yaso ni xan san abinda xanyi". Ba musu Abba yace "Bari to na shiga na fada ma mamanta". Da sauri Mahmoud yace " A a Abba in ka fada mata hnklinta xai tashi, ka dai ce mata xaka je unguwa". Gyada kai yayi duk ya rude da lamarin ya shiga gidan, bai jima ba ya fito suka shiga motar Mahmoud suka kama hanyar Kano. Har sunyi nisa sosai da Katsina, daga nesa yake hango mota kamar ta gidansu wacce ya ba Driver yaxo daukar Hadixa. Ya kalli Abdul yace "Abdul waccan motar kamar tawa wadda na ba Ado driver ya dauko Hadixa". Kallon motar suke sosai har suka xo kusa da ita, Mahmoud ya duba nmbr'n motar yaga tashin ce kuwa. Da sauri yaja burki can nesa da ita suna kallon motar, gani suka yi wani mutum ya fito daga motar ya nufi cikin dajin, da sauri Mahmoud ya fiddo da wata qaramar gun, Abdul yayi saurin cewa " Mahmoud ina ka samu bindiga? Me kuma xakayi da ita?". Mahmoud yace "Bincike ai sai da bindiga, bamu da lokaci fito muje". Ba musu Abdul ya fito, Abban Hadixa har xai fito Mahmoud yace " A a Abba ka tsaya a nan ka jiramu ynx xamu dawo". Abban Hadixa yace "Inaa, ai kuwa baku bari na anan dole na biku". Ganin lokaci na qure masu yasa suka barshi ya biyosu, da sanda suka isa wajen motar sai dai basu ga kowa a ciki ba, hakan yasa suka dinga bin itacen suna kutsawa cikin dajin. Sunyi tafiya mai dan nisa amma basu ga alamun akwai wani mutum a ciki ba, da ace basu ga shigar mutumin ba da sai suce ba kowa a ciki. Haka suka yi ta bi a hnkl har suka hango wani dan qaramin gida wanda shi kadai ne a gurin. Kai tsaye suka nufi gidan suna samun gurin buya har suka isa gidan. Sai dai qofar gidan duk securities ne, Mahmoud ya waiga ko ina don samun hanya, sai ganin wata katanga yayi ta danyi qasa xai iya hawa, hakan yasa yayi saurin miqewa daga duqawan da yayi ya nufi wajen katangar suma su Abdul suka rufa masa baya. A hankali suka hau katangar suka dire, Allah ya sosu ba wani security a gurin, Abdul yaga wani qarfe a gefenshi yayi saurin dauka incase of wata matsalan. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [05/11 12:35 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣9⃣---9⃣0⃣ OHW 📚📲 Falon suka nufa cikin sand'a, can suka hango Hadixa durqushe an daure mata hannuwa da baki, sai kuka take, gefe kuma Ado driver ne shima a dauren kamar Hadixa, Abban Hadixa kamar yayi kuka haka yake ji, Mahmoud yace su dan jira shi a nan". Ba musu suka tsaya, ya miqe a hankali ya shiga falon ya saita mutane biyun da ya gani a falon da bindiga. Gaba daya suka waigo suka daga hannayensu sama don babu bindiga a cikin makamansu, daya daga ciki yayi yumqurin duqawa ya dauki wuqarsa, Mahmoud ya daka masa tsawa "Don't moves Anywhere, i will shoot u if moves". Tsayawa yayi, Mahmoud ya waiga yayi ma su Abdul alama da su shigo, cikin sauri suka shiga Abdul ya wuce ya kwance Hadixa, bakinta har ya fara jini da hannunta, da alama kafin su qulle ta sai da suka axabtar dasu. Bayan sun kwance su Abban Hadixa y riqe Hadixa suka miqe xasu fita, sai ga wasu securities din sun shigo hannunsu da bindigu, Mahmoud ya juyo wajensu su kuma wadancen ganin ya waiga suka yi saurin daukar makamansu da niyyar sararshi, Abdul na ganin haka ya dage ya qwala ma daya qarfen daya shigo dashi, nan take ya xube qasa yana qara, ya dauki wuqar wancen din ya yanki dayan, jin hakan yasa Mahmoud ya dan juyo, wani daga cikinsu ya harbeshi a kafada, bai san sadda ya saki bindigar hannunsa ba ya riqe wajen da aka harbeshi. Mutumin ya qara saita shi xai qara harbinshi, cikin xafin nama ya cakumoshi ya hada kanshi da bango, da hannu daya yake aika mashi da saqonnin naushi, shi kuma Abdul ganin wancen na niyyar harbin Mahmoud yasa shima ya kai mashi sara a hannun da ke da bindingar, nan ta fadi qasa yayi saurin duqawa ya dauka. Mahmoud kuwa sai da ya galabaitar da wancen sannan ya dauki bindigar hannunsa daya na dafe a wajen da aka harbeshi, da sauri Abdul ya riqeshi suka fito daga falon suka nufi hanyar da suka shigo, Abban Hadixa ya fara hayewa sannan Hadixa, sai Ado driver, Abdul ya taimaka ma Mahmoud shima ya haye, yaxo hawa kenan sai jin sara yayi a hannunsa, er qara yayi ya waiga ya harbi wancen din da bindiga a qafa, sannan ya haye, suka fara gudu har suka isa wajen motocinsu. Suna xuwa suka shiga motocin suka ja Abdul ya qulle ma Mahmoud gurin fmda aka harbe shi da wani hanky fari, suka ja motar da gudun tsiya, dai dai lokacin su kuma wadancen suka fito, basu da yadda xasuyi dole suka koma don ba mota a wajensu balle su bisu. Su kuwa gudu kawai suke na fitar hankali har suka isa Kano, basu xame ko'ina ba sai Asibiti, ganin Mahmoud yasa suka yi saurin karbarsa aka shigar dashi emergency don lokacin har ya fara fita hayyacinshi. Abdul kuma aka wuce dashi wani dakin aka yi mashi dressing gurin da aka yankeshi, haka Hadixa ma da Ado driver. Lokacin har magrib ta gabato, ana kiran sallah Abdul da Ado driver suka wuce masallacin asibitin suka gabatar da Sallah, ita kuma Hadixa a dakin da suke tayi sallarta. Suna dawowa dr ya fito daga dakin da aka kwantar da Mahmoud, Abdul yayi saurin qarasawa wajensa yace "Dr ya jikin nasa?". Dr Bilyamin yace " Mun cire bullet din dake jikinsa, ynx haka ya samu barci, kar ka damu xuwa anjima xai tashi insha Allah". Abdul yayi ajiyar zucuya yace "Allah ya tashe shi lpy". Suka amsa da " Ameen". Sai a sannan Abdul ya kira Daddy ya sanar dashi suna Asibiti, ba'a dau lokaci ba sai gasu sun iso cike da tashin hankali har da su Naana, tana ganin Hadixa suka rungume juna suna kukan farin ciki, nan Abdul ya fada masu duk yanda abin ya faru, nan suka yi mashi Addu'ar samun sauqi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [06/11 7:36 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣1⃣---9⃣2⃣ OHW 📚📲 Sai bayan isha'i Mahmoud ya farka daga nannauyan barcin da yake, yana bude idanuwansa basu sauka kan kowa ba sai kan Naana da ke xaune saitinshi kusa da Zee, ita ma shi take kallo cike da tausayinshi, ya tsaya yana ta kallonta fuskarsa dauke da murmushi. "Lah Mummy Yah ya tashi". Muryar Zee ce ta farkar dashi, sai a sannan ya waiga ya kalli su Mummy da suke xaune gefenshi, nan suka shiga yi mashi sannu, yana daga masu kai kawai. Suna haka sai ga Abdul ya shigo shi da Dr, nan Dr ya duba shi sosai sannan ya cire mashi qarin ruwan da aka sa mashi. Nan yayi yunqurin tashi Abdul ya taimaka mashi ya miqe yace yana son shiga toilet, Dr Bilyamin yace ba damuwa ya shiga amma kar ya jiqa gurin, Abdul ya taimaka masa har toilet din sannan ya fito shi kuma ya watsa ruwa, yaji dan qarfin jikinshi, shi dama babu inda ke masa ciwo sai gurin da aka harbeshi, hakan yasa ya dauro alwalla don gabatar da sallolin da ke kanshi. Abdul ya miqo mashi jallabiya, ba don yaso b haka ya sanya, yana fitowa ya watsa mashi harara tare da cewa "Meye na dauko min jallabiya, bayan kasan b sonta nake ba". Abdul yayi dariya yace " To ni miye laifina, naga dai cikin kayanka na ganta". Yace "To ai sai ka xo ka taimaka min, don baxanyi tafiya da ita ba haka kurum ta kada ni". Duk sukayi dariya Abdul ya riqo shi xuwa bakin gado, ya xauna. Nan aka hada mashi tea mai kauri yasha sannan ya miqe ya gabatar da sallolinsa. Bayan ya idar yace da Daddy shi fa kawai a sallameshi, Daddy yace ya bari sai gobe in Allah ya kaimu, Mahmoud yace A a shi dai kawai a sallameshi,family dr dinsu sai y rinqa xuwa gida yana dubashi. Daddy yaje ya samu Dr yayi mashi bayani, dr yace ba damuwa nan aka sallameshi, nan suka tattara suka nufi gida. _Washe gari_ Naana ta tashi duk jikinta a sanyaye, gani take kamar wani abu xai faru da ita, wajen 10 suka gama shirinsu don 10:30 xasu koma kotu. Shima Mahmoud lokacin ya gama shirinshi tsaf ya nufi part din Mummy, bayan sun gaisa suka yi break sannan suka miqe suka nufi mota don tafiya. Mota daya Naana da Mahmoud da Zee da Hadixa suka shiga, sai Mummy Daddy da Faheem a mota daya. _10:50am_ Kotun ta cika maqil da mutane don ma tafi wancen karan cika, Alkali ya shigo an miqe kamar wancen lokacin sai da ya xauna sannan kowa ya xauna. Nan aka shiga gabatar da qara, Mahmoud ya kawo shedu da dama, ciki harda Hadixa, ta fadi komai da ta sani, har alqali xai fara magana mahaifin Sadeeq ya miqe tsaye yace "A dakata ya mai Shari'a". Kowa ya kalleshi sannan ya cigaba da cewa " Ya mai Shari'a, dana Sadeeq baxai iya aikata haka ba, sai dai idan ciwonsa ne ya tashi". Da mamaki ake kallon Alh Ibrahim Naira. Alqali yace "Ko xaka iya fada ma kotu ciwon dan naka?". Ya numfasa sannan yace " Ya mai girma mai shari'a dana Sadeeq ya samu hadarin mota shekaru biyu da suka wuce, a lokacin kanshi ya bugu, wanda har yakanyi abu kamar mara hankali, koda ya samu sauqi likita ya tabbatar mana da cewa ciwon nasa xai ringa tasowa, xaiyi abu ba tare da yasan yayi ba". Alkali ya danyi shiru can yace "Ko xaka iya kawo mana takaddun asibitin da kuma likitan?". Yace qwarai kuwa". Nan ya waiga gefenshi ya kira Dr, sai gashi ya miqe ya miqa takaddun aka miqa ma Alkali sannan yace " Tabbas ni ne likitan da ya duba Sadeeq a lokacin da suka samu Accident..... " "Qarya yake ya mai girma mai shari'a". Wata murya ta fadi hakan wadda ta sanya Naana mutuwar xaune, duk aka waiga don ganin ko waye, Hadixa da first lady suka miqe tsaye cike da firgici da tsoro, Naana ta miqe itama, ganin ko waye yasa ta shiga nuna shi da yatsa bakinta na rawa tana son furta sunanshi amma ta kasa........... (nima dai garin firgicin ganinshi yasa na yadda wayana qasa). Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [07/11 2:15 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣3⃣---9⃣4⃣ OHW 📚📲 Sadeeq kuwa neman hanyar guduwa ya fara, sai dai ba hanya don duk yan sanda sun rufe hanyar. Tsaye yake a qofar an daure cikinshivda bandage, ya rame sosai kamar ba shi ba, bakin Naana na rawa ta soma furta " *Ya... Ya... Nah*" sai kuma ta sulale a gurin, da sauri ya nufo inda take ya tallabota a jikinshi yana jijjigata, Mahmoud ma ya nufo gurin da sauri yana kallonshi cike da mamaki don sam bai sanshi ba, Faheem dake hannun Zee ya kalleshi tare da cewa " *Abee*". Abee kuwa hankalinshi gaba daya yana kan Naana data sume saboda tsabar firgicin ganinsa. Cikin rudu yake cewa "Ku taimaka min da ruwa". Ruwan aka miqo mashi ya yayyafa mata sai gashi ta farfado a firgice, ganin yayanta yasa tace " *Yah Auwal* ashe dama kana raye?". Murmushi ya mata kamin yace "Ina raye Qanwata ban mutu ba". Ita ta rasa me ma xatayi don murna da farin ciki, shigewa tayi jikinshi tana kuka wanda ita kanta bata san ko na miye ba, shima hawayen yake, ya juya ya kalli Faheem yayi mashi murmushi sannan ya miqa mashi hannu, da sauri ya qaraso wajenshi ya rungumesu su duka cike da kewarsu. Alqali yayi gyaran murya kowa ya koma ya xauna inda yake, Yah Auwal ya miqar da Naana ya maida ta maxauninta da Faheem sannan ya juya ya kalli Ahmad da suka shigo tare da Aysha, suma suka samu guri suka xauna. Alqali yace " Komai ya lafa, Malam ko xaka iya fada ma kotu ko kai waye?". Yah Auwal ya kalli Alqali sannan yace "Qwarai kuwa ya mai shari'a". Nan yaje ya shiga gurin da ake tsayawa ya tsaya ya kalli Sadeeq da tuni xufa ta gama jiqeshi sharkaf, yayi murmushi sannan ya maida kallonshi ga Br, Salman dake tsaye a gabanshi. Br, Salman yace " Shin ko xamu iya sanin sunanka?". Yace "Sunana Auwal Almustapha Yusuf". Br yace " ko xaka iya fada ma kotu dangantakarka da wannan yarinyar?". Ya qarshe tare da nuna Naana". Yah ya kalli Naana sannan yayi murmushi yace "Ko ban fada ba ya kamata ace kun gane, but bari na fada kawai, Naana qanwata ce uwa daya uba daya, Faheem kuma da ne a wajena". Tsit kake ji na dan wani lokaci kamin Br yace " Dama yayyanta biyu ne? Don kuwa tace mana Sadeeq ya kashe mata yayanta kenan qarya take". Murmushi yaya yayi tare da cewa "Yayanta daya kuma gaskiya ta fada maku, Sadeeq shi ne wanda ya kashe mana iyayenmu kuma yayi yunqurin kashe ni, sai dai Allah bai nufa ba, saboda ina da sauran numfashi a doron duniya, kuma yayi hakan ne a dalilin munqi amincewa ya auri Naana, idan kuma qarya nake gashi nan ka tambayeshi, ko da yake ba ma sai an tambaya ba, ku dubeshi ku gani, me yasa ya firgita da ganina a raye?". Kowa ya kalli Sadeeq da ya jiqe sharkaf da xuba, Alqali yace " Sadeeq shin ka yarda da abunda ya fada?". Sadeeq ya dago da kanshi ya watsa ma Yaya wani mugun kallo sannan yace "To sai me? Don na kashe su sai me? Ku baku isa ku yanke min hukunci ba, mahaifina na da kudi kuma xai fitar dani daga hannunku". Kowa da abinda yake fada a cikin kotun, Br, Mahmoud ya sauke ajiyar xuciya ganin Sadeeq bai bata masu lokaci ba. Br, Salman da mamaki yake kallon Sadeeq yace " Kana nufin Kaine ka kashesu?". Sadeeq yace "Qwarai kuwa ni ne na kashesu da hannuna". Nan aka hau salati kowa da abinda yake fada, Alqali ya buga wani abu nan kowa yayi shiru. Nan dai Alkali ya yanke ma Sadeeq hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya biya diyyar rayukan da ya kashe, sannan kuma mahaifinshi da Dr aka ayanke masu hukuncin xama gidan kaso na tsawon watanni shidda, sakamakon qaryar da suka yi na cewar Sadeeq na da ciwon hauka. Nan yan sanda suka fitar dasu, Naana da gudu taje ta rungume Yayanta cike da farin ciki, shima farin cikin ya cika mashi xuciyarshi, Nan Br, Salman da Br, Mahmoud sukayi musabiha, Nan suka dunguma gaba dayansu suka nufi gidansu Mahmoud. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [08/11 2:11 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣5⃣---9⃣6⃣ OHW 📚📲 Duk suna xaune a babban falo gaba dayansu harda Ahmad da Aisha da Hadixa, Naana da Faheem na maqale kusa da Yah Auwal, Daddy ya kalli Yah Auwal yace "Mu fa mun shiga rudani, ya kamata ka fada yadda abun ya kasance". Yah Auwal yayi dan murmushi sannan yace _"Bayan da Sadeeq ya caka mana wuqa, Umma da Abba sun rasu, nace da Naana ta gudu, to tun daga nan ban kuma sanin inda nake ba, sai dai na farka na ganni a inda nake, Ahmad na fara hangowa yana daukar gawar Abba, naga maqotanmu da dama a cikin gidan, hakan yasa na maida idona na rufe, Bayan sun fita da gawar Umma da Abba, Ahmad ya shigo don daukar tawa gawar, ganin shi kadai ne yasa na bude idona, ya tsorata sosai da ganin na bude ido, har xai kira sauran mutanen nayi saurin dakatar dashi cikin muryar wahala nace " Karka bari su san ina da sauran numfashi, bana so Sadeeq ya sani"._ _Dai dai lokacin wani maqocinmu ya shigo yana cewa "Ahmad bari na taimaka maka a daukeshi". Ahmad yace " A a baba ka barshi kawai na daukeshi, ina so na kaishi gidanmu ayi mashi wanka a can, ku kuma kuyi ma su Umma da Abba a kaisu makwancinsu". Mutumin yace "Toh shikenan Allah ya jiqansu da gafara" Ya amsa da Ameen shi kuma ya fice._ _Nan Ahmad ya daukeni xuwa gidansu, yayi ma Ummasa da Abbansa bayanin komai kuma ya roqesu da karsu fada ma kowa, sun kuma amince, Aisha ma akayi mata bayani, nan aka cuccusa kaya cikin likafani yayi kamar mutum ne ko dauka akayi baxa'a gane ba, lokacin har anyi ma su Abba da Umma sallah an kaisu makwancinsu, nan shima aka dauki kayan aka yi mashi sallah aka kai makwanci._ _Da dare sosai Ahmad da Abbanshi suka daukeni suka kaini wani asibiti suka roqi likitan da kar ya bari a san suna cikin asibitin, tun daga nan aka cigaba da kula dani, Ahmad shi ke kawo min duk wasu bayanai akan Sadeeq, har xuwa wannan lokacin da mukaxo kotun"_ Kowa ya jinjina ma lamarin, Daddy yace "Toh Allah shi kyauta gaba, ynx dai komai ya qare Sadeeq dai tuni an rataye shi, sai dai kuma tarihinshi". Duk suka amsa da " Ameen". Yaya yayi masu godiya akan riqon da suka yi ma Naana da Faheem. Mummy ta kalli Naana tayi murmushi tare da cewa "Toh su Naana Yaya ya dawo shagwaba ta dawo kenan". Duk aka sanya dariya, Yah Auwal yace "Naana har ynx bakin naki yana nan ko?". Tayi saurin cewa " Waa ai Yaya tuni ya mutu, ai na daddara". Nan ma aka kuma yin dariya, Shi kuwa Mahmoud murmushi kawai yakeyi yana kallon Naama cike da so da qauna, lokaci yayi da xai bayyana mata sirrin dake ranshi, Abdul yayi masu sallama Mahmoud ya raka sa har wajen motarsa sannan ya dawo cikin gidan. Da dare bayan an gama dinner duk aka dawo falo ana kallo, Naana wani farin ciki take ji, yau gata ga yayanta farin cikinta, ga kuma qawayenta Hadixa da Aisha. Wurin 9:20pm Mahmoud ya miqe ya kalli Yah Auwal da Ahmad yace "Toh ya kamata ku taho muje mu kwanta haka nan". Ahmad yace " Aiko balle mu masu tafiyar safe ba". Naana tayi saurin cewa "Amma banda Yaya Xa'a tafi ko?" Sukayi dariya Ahmad yace "Da shi kam xamu tafi". Tayi saurin riqo hannunshi tace " Plx Yaya banda kai ko?" Ta qarashe maganar kamar xatayi kuka. Yaya yayi murmushi yace "Oh dear don't cry banda ni xasu tafi, ni xan dan jima kafin na tafi". Tayi dariyar jin dadi, Faheem yace " Abee ai badaka kara tafiya ba ko?". Yaya yayi dariya tare da shafa kan Faheem yace "Ba inda xan qara tafiya My boy". Duk akayi murmushi, Daddy yace " Ai gaskiya bai kamata ka koma katsina ba, in ba damuwa xaka iya cigaba da aiki a company na kai da Ahmad". Cike da farin ciki Yah Auwal yace "Gsky da naji dadi sosai, don bana so na kuma yin nisa da Qanwata da kuma dana". Mahmoud yace "suma kansu baxasu ji dadi ba in ka tafi". Daddy yace " To ai shikenan xuwa nan da 1 week sai kaje ku dauko takardunku da na Naana don itama ina so na sama masu makaranta ita da Zee". Nan suka yi mashi godiya sosai yace ba damuwa. Suka miqe suka fice xuwa part din Yah Mahmoud har da Faheem da ya maqale ma Abee dinsa, su kuma su Naana suka wuce dakinta, har sun kwanta suna labari sai ga Zee ta shigo tace baxa'a barta ita kadai can ba. Duk sukayi dariya, daga nan suka dasa fira, basu suka kwanta ba sai wurin 2, hakan yasa suka makara sallah. Shima Yah Auwal yayi barci cikin farin ciki yau, yana rungume da Faheem sukayi barcin, rabon da yayi barci irinshi har ya manta. Washe gari, su Ahmad wurin 10 suka gama shiri, Mummy tace a bar su Aisha su dan qara ko kwana biyu ne, b musu kuwa aka barsu, sunyi farin ciki sosai, Driver aka sanya ya kai Ahmad har gida. Da rana First lady taxo, nan suka hade aka dunga shafta kamar karsu rabu, sai dare Muhammad yaxo ya dauketa. Kwanan su Hadixa 4 suka fara shirin tafiya, Naana ba don taso ba, Abdul tunda yaga Aisha yaji ta kwanta masa a rai amma sam ya kasa fada mata, sai dai kullum sai yaxo gidan har Mahmoud ya qyaro jirginsa. Tare suka shirya da Naana da Zee don har dasu xa'a je maida su Hadixa, mota biyu suka hau, da ta Abdul da yace hada shi xa'a da kuma ta Yah Mahmoud. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [09/11 2:48 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣7⃣ OHW 📚📲 Suna isa ta fara tuno rayuwarsu a unguwar tuni hawaye suka fara xubo mata, tace ma Yaya su fara xuwa gida, shi kanshi yana son xuwa, amma ya tabbata suka shiga gidan sai sunyi kuka daga shi har Naana. Matsa mashi tayi akan lallai sai sunje, ba yadda ya iya nan suka fara xuwa gidan, ita ta fara fitowa ta shiga gidan, yana nan yadda yake sai dai uban qura, a hankai ta fara tafiya har suka shiga ciki, hawaye sai xarya suke a fuskarta, daki ta wuce, tana shiga idanuwanta suka sauka kan hotonsu da sukayi na family, da sauri ta qarasa cikin dakin ta dauki photon tana shafa fuskar Abbanta da Ummanta, wani kuka ne ya kufce mata, ta rungume photon tana kuka mai tsuma xuciya. Yah Auwal yayi saurin qarasowa cikin falon, ya durqusa inda take tare da dafa ta shima hawayen yake, da sauri ta fada jikinsa tana mai cigaba da kukan, shima kukan yake balle ya lallasheta. Zee ta duqa wajen itama tana share hawaye ita dasu Aisha, yayin da Mahmoud da Abdul suka fita waje yana riqe da Faheem don shi baxai iya jurar ganin Naanarshi tana kuka ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan Yah Auwal ya tsagaita nashi kukan tare da dago kan Naana ya shiga lallashinta har ya samu tayi shiru sannan suka miqe suka fito daga gidan suka wuce gidan su Hadixa da yake shi ke kusa. A ranar su Mahmoud suka koma shi da Abdul, su kuma su Naana sai da suka yi sati, kuma sai da ta kwana gidansu, amma fa ranar ba wani bacci sukayi ba, kuka kawai tasha har gari ya waye. Mahmoud ya dawo daukarsu, kamar karsu rabu haka suka tafi. Yah ya daukar masu takardunsu gaba daya, suna komawa Daddy ya sama masu aiki a babban company'nshi dake nan kano, amma aikin Yaya yafi girma, su Naana kuma aka samar masu School of health a nan Kano suka fara xuwa ita da Zee. Itama first lady ta fara xuwa BUK kuma har ansa ranar bikinta da Muhammad. Mahmoud yaje har Katsina ya sama ma su Hadixa Schl a nan Katsinar sunyi murna sosai, suma suka fara xuwa. ******* Suna xaune a falo gaba dayansu, da Yah Auwal Mahmoud Naana da kuma Zee sai Faheem dake xaune jikin Zee yana shan choculate. Zee ta kalli Yah Mahmoud tace "Yah nace wani abu?". Mahmoud ya kalleta yace " Kice muje shopping ba?". Duk sukayi dariya, Zee tace "Plx mana Yaya, muje kaga fa mun rabu da xuwa". Mahmoud yace " Sai dai in Naana xata je da Yah Auwal". Zee ta kalli Naana tace "Sis muje ko?". Ta kalli Yah Auwal tace " Yah Auwal muje plx". Murmushi Yah Auwal yayi yace "Toh shikenan muje din". Nan suka miqe ita da Naana suka wuce daki suka shirya cikin kaya iri daya atamfa Naana tace hijab xata sanya, Zee ta dinga lallabarta da qyar ta yarda ta sanya gyalen, sunyi kyau kuma sosai. Nan suka fito suka iske su Yah har sun shiga mota suna jiransu, tunda suka taho Mahmoud ke ta kallon Naana, Yah Auwal duk yana lura dashi, bai dai nuna mashi ba, don shi tun xuwanshi ya gane Mahmoud son Naana yake kawai dai ya kasa fada mata ne. Nan suka bude baya suka shiga suka wuce super market, sunyi siyayya sosai daga nan suka wuce suka sha ice-cream, sannan suka kamo hanya don komawa gida. Sunyi nisa har sun kusa xuwa gida, Mahmoud yayi parking a gefen titi sannan ya kalli su Yah Auwal yace " I'm sorry ynx xanje na dawo". Yah Auwal yace "Ba damuwa Mahmoud". Nan ya fita ya tsallaka xuwa wajen wani shagon sai da wayoyi, ya siya guda biyu iri daya qirar Sumsung galaxy S7, ssannan ya siya sim daya mai register sannan ya dawo cikin motar suka wuce gida. Suna xuwa har xasu shiga ciki Mahmoud ya tsayar da Zee bayan sun shige ya miqo mata wayoyin yace " Ga wannan taki daya ta Naana daya da wannan sim dinki bata". Wani tsalle ta buga ta rungumeshi tana murna tare da yi mashi godiya, don dama ta gaji da tata wayar. Bayan sun baje a dakin Zee ne suna duba kayayyakin da suka siyo Zee ta miqo mata wayar tace "gashi inji Yah Mahmoud yace na baki, iri daya ya siyo mana ni da ke". Naana tace "Waya kuma? A a ni baxan amsa ba". Zee ta bata rai tace " Miye haka Naana? Kinsan fa bana son wannan abun, ki amsa". Ta qarashe maganar tana mai miqa mata wayar. Naana tace "Kiyi hkr Zee amma ni banga amfanin riqe wayar ba". Zee ta miqe tace " Shikenan tunda baxaki amsa ba xanje na kai masa abarsa nace kince baki amsa, kuma kinsan dai baxai ji dadi ba yayi maki kyauta ki qi karba". Sai kuma taga baxai ji dadi ba, hakan yasa tayi saurin riqo Zee tace "Shikenan kawo". Zee ta miqa mata wayar nan tayi mata godiya tace xata je tayi ma Yaya shima. Tana komawa daki ta sanya sim din ta kunna wayar, tana kunmawa text ya shigo a wayar, tayi mamaki ace daga kunnawa sai kuma text. Nan ta bude text din ta fara karantawa kamar haka....... Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [10/11 7:42 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣8⃣ OHW 📚📲 *24 hours make a lovely day, 7 days make a lovely week, 52 weeks make a lovely year, and knowing a person like me will make ur life lovely, hav a nyc day*. _Urs lovely_ Da mamaki take karantawa to wannan nmbr din waye? Tambayar da take ta ma kanta kenan. Haka ta shiga duba wayar, don tana iya karanta komai hakan yasa tayi ta shiga ko'ina har ta gane kan wayar. Ranar yini tayi tana duba wayar tayi mata kyau sosai, Zee tayi mata downloading WhatsApp. Ta nuna ma Yah Auwal shima ya taya ta murna, nan ya tura mata imdians films da waqoqi, da kuma complete Qur'an, su Mummy ma duk saida ta nuna masu, Yah Mahmoud ne kadai bata samu gani ba balle tayi masa godiya, bai shigo part din ba, ita kuma bata son xuwa part dinshi. Da dare xata kwanta bayan ta gama chatting har xata kashe wayar wani text ya qara shigowa a wayar na nmbrn daxu, hakan yasa ta bude don ganin ko miye a ciki, ta soma karantawa: *Still awake? Time to sleep gudnyt, sleep tight my lovely one* _Urs lovely_ Kallon Nmbrn ta shiga yi wata xuciyar na ce mata ta kira taji ko waye, wata kuma na ce mata ta tura mashi tex ta tambayi ko waye, shawarar xuciyarta ta biyu ta bi, nan ta shiga tura masa text kamar haka: *I'm sorry, i don't know who ar u, can u telling me who is on the line?* Tsawon lokaci aka dauka ba'a maido reply ba, har xata kashe wayar ta kwanta sai jin qarar shigowar reply din tayi, hakan yasa ta bude. *Don't worry my love, xaki sanni very soon*. Haushi ya cika ta ganin bai fadi ko waye ba, hakan yasa ta kashe wayar tayi addu'a sannan suka kwanta, tana so tayi barci amma ta tunanin text din kawai take, barin ma na farko da yafi tsaya mata a rai, sai kawai ta tsinci kanta da murmushi, haka barci barawo yayi awon gaba da ita. Mahmoud kuwa kasa barcin yayi, yana ta xaman jiran ganin text din Naana amma shiru, gsky ya xama dole ya furta mata yana sonta. _Washe gari_ Wajen 10 suna xaune a falo ita da Zee suna hira, Mahmoud ya shigo shida Yah Auwal da sallamarsu suka amsa sannan suka samu guri suka xauna yana kallon Naana. Ta miqe ta koma kusa da Yayanta. Yah Mahmoud Yayi murmushi sannan ya fiddo wayarsa daga pocket, ya soma rubuta mata text. Suna magana da Yah Auwal taji qarar shigowar text hakan yasa ta bude don ganin ko miye, *Do you want know who am i?* Ta maida masa da cewa *Yeah* Murmushi Mahmoud yayi tare da miqewa ya fita daga falon bai xame ko ina ba sai garden, ya samu kujera ya xauna sannan ya maida mata *So if u want, u can see me in urs garden*. "Garden?" Ta maimaita har Yah ya kalleta yace "Miye a garden din?". Murmushi ta qaqaro tace " Noo ba komai yaya, kawai ina son xuwa garden din ne". Murmushi kawai yayi yace "To kije mana". Miqewa tayi tace " Ynx xan dawo yaya". Daga mata kai kawai yayi ta fice daga falon xuwa garden din ba ko tsoro, ko kadan batayi tunanin Yah Mahmoud bane. Tashi yayi daga inda yake ya buya bayan wasu bishiyoyi yana kallonta har ta shigo garden din tana ta waige 2 bata ga kowa ba, ta ja kujera ta xauna tare da jawo wayarta ta rubuta mashi *I don't see anybody in dis garden, where ar u?*. Murmushi yayi bayan ya gama karantawa sannan ya maida mata da cewa *Close ur eyes*. Ta kuma maimaitawa, to miye na wani cewa ta rufe idonta kuma? Don tana son ganin ko waye ne ya sanya ta rufe idon nata, a hankali ya fito daga inda yake riqe da wata flower mai shegen kyau da qamshi ya nufo inda take tare d xama kujerar dake facing tata ya boye flower a bayansa, yana wani sanyayyan murmushi a hankali cikin wata murya yace "Open ur eyes". A hankali ta bude fararen idanuwanta suka sauka kan kyakkyawar fuskarsa, da mamaki ta tsaya tana kallonshi, ko kadan batayi tunanin shi bane, can ta kawar da kanta tae da cewa " Yah Mahmoud baka ga wani a nan ba?". Murmushin ya kuma yi tare da cewa "Ai ni ne wanda kike maganar". Da mamaki tace "Yah kana nufin kaine kake turo min massages?". Gyada mata kai yayi ba tare da yace komai ba. Miqewa tayi tare da cewa " Tunda na ganka shikenan bari na koma cikin gida". Ji tayi an riqo hannunta hakan yasa ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba. Miqewa yayi daga xaunen da yake ya dawo gabanta tare da kallon cikin idonta, ba shiri ta sadda kanta qasa don baxata iya jurar kalon idon nasa ba. Cikin wata sassanyar murya ya kira sunanta, har cikin jikinta taji kiran nashi, a hankali ta dago ta kalleshi ba tare da ta amsa ba. Cikin wata rikitacciyar murya yace "Naana i love u morethan ur expectations, Naana bansan ta yaya soyayyarki tayi nisa cikin xuciyata ba, may tumse bahoot bahoot pyar karta(I love u a lot) plx love me". Ji tayi duk jikinta yayi sanyi, ta rasa me take ji a cikin xuciyarta, kuma ta rasa amsar da xata bashi. Muryar shi ta katse mata tunaninta yace " Plx Naana say something for me, say u love me". Cikin rawar murya tace "Yah Mahmoud what do u want me to say about? I have nothing to say about what u ar saying". Cikin sauri yace " U have Naana, plx say u love me, Wllh Naana ban taba son wata mace kamar yanda nake sonki ba". Naana tace "I'm sorry Yah Mahmoud, bansan me xan ce maka ba". Tana kaiwa nan ta wucesa da dan gudu 2 ta nufi falon mummy, har ta wuce Yah Auwal dake tsaye yana jinsu bata lura dashi ba. Shi kuwa Mahmoud tsaye yayi a gurin, ya rasa mai xaiyi, ya koma ya xauna kan kujerar, tare da dafe kanshi, wani son Naana na qara shiga xuciyarshi, bai san sadda hawaye suka xubo masa ba tuna cewa Naana bata sonshi. Ji yayi an dafa kafadarsa hakan yasa ya dago da sauri don ganin ko waye, sai ganin Yah Auwal yayi, Yah Auwal yace " Ka kwantar da hankalinka insha Allah Naana xata so ka". Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [12/11 5:04 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣9⃣ OHW 📚📲 Naana kuwa tana shiga daki ta wuce, ta kwanta saman gadonta, tunanin Yah Mahmoud ta shiga yi, ta rasa me take ji game dashi, a duk lokacin da ta ganshi sai taji gabanta na faduwa, haka kuma indai ya wuni guda bai shigo ba sai taji duk ba dadi, ita ta rasa gane kan abin. (Ni kuwa da nake gefe nace nemsy u r in luv😉, ji nayi tace "Noo ba xai yuwu ba". Nayi saurin duqewa don nayi xaton ta jini). Haka ta wuni ranar sukuku, ta rasa me ke damunta, kuma gashi har dare Yah Mahmoud bai shigo ba, duk ta damu, Yah Auwal ma bai yi mata maganar ba, haka dai ta kwanta ranar cike da tunani kala 2 a xuciyarta, a ranta take cewa to wai ma miye nake damun kaina? Tunda ba sonshi nake ba. _Bayan kwana biyu_ Yah Mahmoud bai kuma yi mata maganar ba saboda Yah Auwal yace ya bari xaiyi mata magana, duk ya damu, amma duk da haka sai da ya dinga tura mata massages xafafa. Da rana suna xaune a falo Yah Mahmoud lokacin yana part dinshi, Yah Auwal ya shigo falon, ya nemi guri ya xauna, ya kalli Zee dake riqe da Faheem yayiushi tare da cewa " Qanwata baki gajiya da hidimar Faheem ko?". Murmushi Zee tayi tace "Yah Auwal gajiyar me?". Yace " Ai naga kullum sai ya sanya ki hidima". Tace "Ai ba komai Yaya ai *Da na kowa ne*". Yayi murmushi sannan ya kalli Naana dake game da wayarta yace "Qanwa ina son magana da ke". Zee ta miqe xata fita yayi saurin cewa " A a dawo ki xauna ina kuma xaki". Zee tace "A a gani nayi xaku yi magana". Yace "To ki dawo ki xauna kawai". Ba musu ta koma ta xauna, Ya kalli Naana da ta maido hankalinta kanshi yace " Naana tambayarki nake son yi". Tace "ina jinka Yayana". Ya danyi jim sannan yace "Kina son Mahmoud ko bakya sonshi?". Da mamaki duk suka kalleshi ita da Zee, ita dama Zee tun tuni take xargin Yah Mahmoud son Naana yake ta dai yi shiru ne kawai. Yah Auwal yace "Ina jinki Sister fada min karki boye min komai kinji". Ta danyi shiru sai kuma tace "Yah nima bansani ba Allah". Dariya taso ta kucce mashi, ya sani sarai Naana bata san miye so ba hakan yasa yace "Ki fada min me kike ji a duk lokacin da kika ganshi?". Ta kalleshi cike da rashin fahimtar tambayarshi tace " Kamar ya Yaya?". Yace "I mean baki jin wani feeling a kanshi?". Ta danyi shiru tabbas tana jin wani abu akan Yah Mahmoud a duk lokacin da ta ganshi, ta dago tare da cewa " Yaya ni dai duk sanda na ganshi na kanji wani iri a xuciyata, in kuma ban ganshi ba sai naji ba dadi har sai na ganshi". Murmushi yah Auwal yayi tare da cewa "Nàana ki yarda kina son Mahmoud, don kuwa duk abinda kika lissafo alama ce ta so, in kuma baki yarda ba kije ki kalli cikin idonsa kice bakya sonsa". Shiru tayi tana naxari, Yah Mahmoud ba abin qi bane, koda ace bata sonsa bai kamata ta qi amincewa da soyayyarsa ba ko dan halaccin da suka yi mata, balle kuma tana ji a ranta tana sonshi din. Yah Auwal ya miqe yace " Tohm ni bari naje na dan huta". Fita yayi daga falon ya barsu nan Xaune, Zee kuwa itama tuni ta fada duniyàr tunani, tunda ta fara ganin yah Auwal abinda ta fara ji kenan a xuciyarta, hakan yana nufin itama sonshi take? 😳 (Ni kuwa Beely nace toh pa ana wata ga wata) Zee ta kalli Naana tace "Naana da gaske kina son Yah Mahmoud?, in kuwa haka ne xanfi kowa farin ciki, kiso Yah Mahmoud plx Naana". Tayi murmushi tare da cewa " Shikenan Zee amma kema ina so na roqeki wani abu". Zee tace "Ina saurarenki". Tace " Plx Zee Kiso Yah Auwal, ki maye masa gurbin Aunty Zarah". Da sauri Zee ta kalleta tace "What? Kina nufin na so Yah Auwal? To in shi kuma baya sona fa?". Naana tace " Zai soki insha Allah ke dai ki amince tukun". Zee ta danyi shiru can tace "Sai dai nayi tunani". Haka suka yini kowa da abinda yake saqawa. Bayan la'asar tana xaune a dakinta, haka nan taji tana son xuwa garden don haka ta miqe ta ta fito daga dakin, lokacin Zee tana dakinta, Faheem kuma na wajen Yaya. Yana xaune a cikin garden din kamar kuma an tsikareshi ya miqe xai fita, dai dai lokacin ita kuma xata shiga kanta na a qasa, bata yi aune ba sai ji tayi tayi karo da mutum tayi baya baya xata fadi yayi saurin tarbota ta fado jikinsa, da sauri ta tashi daga jikinsa ta juya xata fita yayi saurin kiran sunanta, cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Gabanta ya xagayo ya tsaya ya kalleta cikin ido tare cewa "Naana me yasa bakya sona?". Ta sadda kanta qasa tare da cewa " Yah ba haka bane...... " "To yaya ne?". Ya katseta, ta dago ta kalleshi tare cewa "Yah Mahmoud...." Sai kuma tayi shiru, yace "Uhmm fadi ina saurarenki". Ta dago tare da cewa " Yah baxan iya fada ba". Ya fiddo wayarsa tare da miqamata yace "To rubuta min a nan sai na gani". Da kamar baxata amsa ba sai kuma ta amsa ta rubuta mashi sannan ta miqa mashi kafin ya karanta ta ruga ta shige falon mummy, krntawa yayi yaga ta rubuta: *I love you Yah Mahmoud* Murmushin farin ciki ya saki cike da jin dadi ya kaima wayar kiss tre da cewa " I love u too My Habibty". Tun daga ranar soyayya da shaquwa mai tsanani ta shiga tsakanin Yah Mahmoud da Naana wadda ko su Mummy sun san da ita, Naana tayi ma Yaya maganar Zee, shima kuma ya amince daga nan suma suka kulle suka fara soyayya amma fa da farko bai amince ba, sai daga baya kuma ya amince. (Toh Haleesah fa?😳🤔) Bayan kwana biyu mommy ta kira Yah Mahmoud sai da gabanshi ya fadi lokcin da ta kira sunan Haleesah, amma ya dake, a nan take gayama sa cewa an fasa aurenshi da Haleesah don har ynx bata dawo daga Germany ba, kuma da aka yi mata maganar auren sai cewa tayi bata yi niyyar yin aure ynx ba sai nan da 3yrs, don hakan yasa Mummy ta fasa. A ranar in kaga Yah sai kayi mamakinsa, baxaka ce shi ne wanda baya dariyar nan, koda ya fada ma Abdul sai cewa yayi shi ma dole yaje neman soyayyarshi wajen Aisha. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [13/11 9:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 1⃣0⃣0⃣ *~THE END~* Kamar kuwa yanda Abdul ya fada yaje ya samu Aisha ya sanar da ita kalar son da yake mata, bata wani ja rai ba ta amince don itama ta kamu, sai anan suke sanin ashe Hadixa da Yah Ahmad soyayya suke tuntuni. _2 weeks later_ An sanya ranar bikin Yah Mahmoud da Naana, da kuma Yah Auwal da Zee, wata biyu kacal, a kuma lokacin aka sanya ranar bikin First lady da Muhammad Lamido, sai dai nasu wata hudu ne. Murna wajen maskyan bata misaltuwa musamman ma Yah Mahmoud da Naana abin sai wanda ya gani. ****** Kwanci tashi ba wuya wurin Allah yau gasji har satin bikin su Naana yayi, yau ta kama Talata, sunje sunyo saloon, su Hadixa ma duk sunxo, Mummy ta samo mai gyaran jiki tayi masu gyara sosai in ka gansu har wani kyalli suke, Mummy ta hana Mahmoud ganin Naana sai dai a waya, shi kuwa baiji dadin hakan ba, haka ma Zee itama sai dai a waya. An shirya programs wajen kala 4 ranar laraba xa'ayi Indian Nyt, Alhamis Arabian Nyt, Juma'a kuma walima da rana, sai da yamma Party. Shirye 2 kawai ake, gidan Mummy ya cika taf da en'uwa, abin mamaki sai ga en uwan Ummansu Naana, ashe Yah Auwal ne ya binciko inda suke har suka xo. *Day 1* Bayan sallar isha'i, kowa ka gani shigar india ne a jikinsa, daga masu sari sai masu riga da wando, a nan filin gidan za'a gabatar da program din. (Da sauri na na wuce dakin da amare suke don ganin shirin nasu wowww, abinda na fada kenan ganin su Naana da Zee da nayi cikin wani matsiyacin sari na indiyawa) Pink nd milk ne jikinshi, an chaba masu make up, wayyo Allah in ka gansu sai ka rantse da Allah ba su bane, don kuwa sak sun koma indiyawa, musamman Naana da aka baxa gashinta baya abin ba'a magana. (Sakin baki nayi ina kallonsu, da sauri naje nima na sanya nawa sarin sai dai naga ban kai Naana kyau ba☹) Bangaren su Mahmoud ma abin ba'a magana don suma shiga iri daya sukayi na kayan indiyawan, in kaga Yah sai ka rantse ba indiyen ne, Yah Auwal ma da yake shima fari ne yayi kyau sosai, in ka gansu sai ka rantse da Allah ba su bane. Kowa ya hallara a gurin Amare sun fito sun xauna a kujerunsu dake kusa da na angwayensu, sunyi bala'in kyau, Yah Mahmoud ya kasa dauke kanshi ga kallon Naana da ta chanja mashi. An gabatar da program din lafiya, anyi bajaga da kudi, (Don ni sai da na cika jakata da en dubu dubu😉). Abokan Yah Mahmoud na india duk sai da suka xo, ranar dai ansha selfie. Can na hango su Yah Mahmoud da wasu abokanshi suna ta xuba indiyanci, sauri na fara don xuwa dauko maku, har na kusa isa na hango su Naana ana selfie, ni kuma da son selfie nayi wajensu na manta da dauko maganar su Yah. Haka aka sha shagali, sai, munci abincin indiyawa da kaji irinsu Chicken tandoori, chicken masala, chicken afghani, da dai sauransu. wajen 10 kowa ya watse. *Day 2* Kowa ya shirya cikin jallabiyoyi da rawani, shigar larabawa sosai, nan ake yinta, Mahmoud yace sam shi baxai sanya jallabiya ba haka kurum yaji kunya a bainar jama'a, ba yanda Abdul bai yi dashi ba amma ya qiya dole ya hqr yasa wani farin yadi mai kyau da uake rigar har kusan qasa ne sai tayi kamar jallabiyar. Su Naana ma sun sha kyau cikin Arabian gown. Haka dai akayi aka gama shima cikin farin ciki, an xuba larabci sosai ni dai ina can ina kwasar nama ban samu damar dauko maku ba😜. *Day 3* Manyan malamai aka gayyato maxa da mata suka gabatar da wa'axi, kowa sai da ya dan matse kwallanshi, da yamma kuma aka shirya xuwa party a wani hotel dake nan kusa dasu, su Naana ansha wedding gown mai shegen kyau, su Aisha kuwa anko suma sukayi na gown din, su Mahmoud kuwa shigar turawa akayi, suit suka sanya sunyi kyau kamar turawan. Haka dai aka gama partyn aka koma gida. Washe gari aka daura auren *Mahmoud Isma'il Kwangila da Bilkisu Almustapha Yusuf* sai kuma na *Auwal Almustapha Yusuf da Zainab Isma'il kwangila*. Dubban jama'a sun shaida, kowa ka gani murna yake. Da dare aka kai amare gidajensu, A nan cikin unguwar gidajensu suke wanda Daddy ya mallaka masu iri daya ne, duk aka watse aka bar amaren su da qawayensu. Mahmoud Abdul kadai ya rako shi, nan akayi sayen baki suka sha rahar su suka tafi. Naana tasha kuka da su Aisha xasu tafi, suka fita aka barta ita kadai don Shima Mahmoud ya fita kullo gida. Shima Yah Auwal Ahmad kadai ya rakasa sannan shima suka tadi bayan anyi sayen bakin. Yana dawowa ya ganta xaune kan gadon tna shan kuka, bai son jin kukanta ko kadan ya qarasa saman gadon ya yaye mayafin dake fuskarta ya shiga share mata hawayen yana lallashinta, amma kamar qara xugata yake, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana lallashinta da kyar ya samu tayi shiru. Nan sukayi sallah don godiya ga Allah sannan Mahmoud ya jawo ledar da ya shigo da ita. (Ni kam leqe kawai nake naga mai xa'a fiddo duk da nasan kaxa ce, ita ce ya fiddo kuwa nan falon ya dau qamshi na hadiye miyau) Mahmoud ya yanko cinya ya kai bakin Naana tayi saurin kauda kai wai ita ta qoshi, da qyar ya lallabata taci kadan shima kadan din yaci suka kora da lemo. (Ni kuwa ina daga gefe ina jira ya miqo min tawa sai gani nayi ya nufi wajen frigde da ita, kamar na bishi na qwato amma ba hali don xai iya batattakani na bar masa gida) (Dauko fresh milk yayi ya nufo bakin qofa, wurgo min yayi tare da cewa gashi nan ki dauka ki fice mana daga daki tun kafin na makeki, kaxa ce dai baki cinta duk qunatarki, kamar inyi kuka haka na duqa na dauki fresh milk din son in rage xafi na fice daga dakin ya banko qofa) _After 2 months_ Anyi bikin First lady anyi shagali shima yah Mahmoud ke kai Naana ya dawo da ita har aka kammala bikin. A lokacin aka sanya ranar bikin Aisha da Abdul da kuma Hadixa da Ahmad wata biyu suma. Bayan wata biyu aka yi bikin su shima sun sha shagali, tun ana saura sati Mahmoud ya kai Naana yace dashi xa'ayi bikin don baya so a kalle mishi mata, Hadixa a Katsina aka ajeta da yake Ahmad ya maka babban gidanshi, Aisha kuwa Kano aka rankayo da ita. Bayan bikin ne Naana ta fara ciwo, daga yau tace Xaxxabi sai tace ciwon ciki sai ciwon kai, ga kuma yawan kasala da take ji, Mahmoud duk ya damu ya dauketa ya kaita asibiti aka tabbatar masa da ciki ne da ita wata biyu, kar kuso kuga murna gun Yah Mahmoud, har kyauta ai da yayi ma Dr din. Bayan watanni Naana ta haifi Erta santaleliya mai kama da ita, lokacin kuma Zee na dauke da tsohon ciki, ranar suna yarinya taci sunan Umman su Naana wato *Aminatu* ake kiranta da *Meemah*. *After 5 years*. Zaune na hango Naana a kan cinyar Mahmoud sai xuba masa shagwaba take wai ita sai taje gidan Mummy shi kuma ya kafe akan lallai baxata ba sai gobe, Meemah ce ta shigo falon da sallamarta ta xauna gefen Iyayen nata sannan tace "Papa plx ka kaini gidan Uncle ina son ganin Yah Faheem da Adeelah" (diyar Zee ta farko kenan sai Afeef wanda yaci sunan Abba). Mahmoud yace "Oh god da wane xanji? Ur Momma tace sai na kaita gidan Mummy ke kuma kince na kaiki wurin Faheem wane xan fara?". Kafin suyi magana sai ga wani dan kyakkyawan yaro sak Mahmoud ya fito da gudu daga wani daki yana cewa "Papa, Momma ku tashi ku shirya muje gidan Uncle Abdul ina son ganin Airah". Meemah ta bata fuska tace "Kai *Safraz* baxamu je ba gidan Uncle Auwal xamu". Harararta yayi kamar wani babba yace " Anqi din ni baxa'a je can ba". Naana dai komawa tayi kan kujera ta xauna tana kallon ikon Allah, Shima Mahmoud kallonsu yake sunyi su gama ba inda xasu je yau. "Pa pa, Pa pa". Wata qaramar murya naji tana kiran sunan Papa cikin gwaranci, hakan yasa nayi saurin waigawa don ganin ko waye, wani dan qaramin yaro na gani yana , da sauri Meemah taje ta daukoshi tana cewa " *Muhib* dina ka fito kaima kaga Papa ". Mahmoud yace Gidan Mummy kawai xasu, haka suka shirya gaba dayansu suka nufi gidan Mummy a can suka iske Yah Auwal da Zee sunxo suma nan fa yaran suka kaure da hayaniya, Faheem yaja Meemah suka koma gefe suna ta labarinsu don sun shaqu sosai har cewa suke su mata da miji ne. Suna nan sai ga Aisha da Abdul, da Diyarsu Airah sai tsohon cikin da take dashi. Kamar hadin baki sai kuma ga su Hadixa da danta Mahfuz sai ta goyen mai suna Sahra, nan fa akayi ta shafta, basu suka rabu ba sai wajen magrib sannan kowa ya nufi gidansu. Naana da Zee an xama cikakkun likitoci, Aisha da Hadixa kuma aiki suke suma, Bayan kwana biyu da komawarsu First lady ta kawo masu Ziyara, sun yi murna sosai. Suna xaune a falo lokacin su Meemah duk sunyi barci, ya kalleta da lumsassun idanunshi yace " Baby nifa gsky so nake ki tara min ya ya da yawa don haka yau xamu sama ma Muhib qani ko qanwa". Yana gama fadar haka ya miqe tare da daukarta cak a hannunsa kamar wata baby, tayi saurin cewa "My Jaan Muhib fa baiyi girma ba". Murmushi yayi mata yace " Nasan da hakan ai" yana fadar haka ya wuce da ita daki. (Banyi yunqurin binsu ba don nasan fatattako ni xaiyi, nace na tafi dai na barku hakanan). *Alhamdulillah*, to nidai a nan na kawo qarshen wannan littafi nawa mai taken *BA SO A RAINA* Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana Allah kuma ya bamu ikon Yin amfani da abinda ke cikinsa. *Jinjina gareku* Beely's novels grp Online Hausa writers Excellent writers Clever writers Afma's nvls grp Dandalin Autar Hajiya nd jidda ja'o Wallynovels Da dai sauran grps din da ban fada ba, duk kuna raina masoyana kuma masoyan wannan nvl nawa, idan na tsaya lissafo sunayenku, xan iya cike pages da dama, sai dai ku sani kuna raina har abada. *TAKE CE* *~_BEELYBADARU😍_~* adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *