Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

Bazawara

adsense here [4:40pm, 3/21/2016] Sajna: ■■■ BAZAWARA(THE WIDOW)■■■ ©MISS HAFCY ®NWA ■ TAK'AITACEN LABARI■ `1` Yau ta kasance Laraba ta bawa rannar samu, gashi kuwa gari yayi kyau sosaii sakamakon ruwan sama da'aka idar a yammacin yaran, gari yayi sharrr gwanin sha'awa, a cikin wani madaidacin gida, wata matashiyar mace tana zaune a wani d'an madaidaicin d'aki, gefenta kuwa yaro ne dabe wuce shekara shekara d'aya ba, yana kwance akan katifa yana bacci ita kuwa tayi tagumi ta fad'a duniyar tunani. Wata dattijuwar mata ta shigo d'akin fuskarta sam ba alamar fara'a, ta kalle ta tace " ke BAZAWARA in kinga dama ga abincinku can a d'akin girkin kije ki d'auka ki ci,kuma ko da wasa kar kizo kina neman k'ari domin umarni ne daga babanki abincin da'ake baki da a dinga raba shi a biyu, ana baki kaso d'aya, kina dai jina ko BAZAWARA?" wadda aka kira da Bazawarar ta sunkuyar da kai sannan tace " Iya dan Allah dan annabi idan bazaki kirani da sunana ba, to gwanda kice min "KE" amma dan Allah ina rok'onki da ki dena cemin BAZAWARA" Iya ta juyo da mamaki " iyeh lallai yarinyar nan wuyanki ya isa yanka ni kike fad'awa wannan maganar?" Cikin sanyayar murya tace " Iya kinsan a iya zamana dake ina miki biyayya, daidai da ranna d'aya ban tab'a sab'a miki ba, wannan ma dan naga abin yayi yawa ne kuma bana san suna ko kad'an shiyasa na miki magana amma ki yafe ni" ganin an bud'e kofa an shigo Iya ta fashe da kuka " yanzu yarinyar nan duk irin abinda nake miki sakayar da zakimin kenan? Ni zaki kalla ki zaga? Na shiga uku yau ni Indo" Mutumin daya shigo ya k'araso da sauri " lafiya Indo kike kuka meya faru?" Iya ta k'ara fashewa da kuka " yanzu Mal duk irin k'ok'arin dana ke akan yarinyar nan ni zata kala ta zaga?" Malam yace " zagi?!" Ta share hawayenta "kwarai kuwa" Malam yace " lalllai lokaci yayi da zan fara dukanki a gidanan(ya kalli Iya) samo min bulala, Iya da sauri ta shiga ta d'auko ta mik'a masa ita kuwa BAZAWARA ba abinda take sai kuka,ya shigo d'akin ya shiga lafta mata bulalar tana kuka, tana bashi hak'uri amma sam be kulata ba, ihuntane yasa yaron ya farka, ya tashi shima ya k'ank'ameta yana kuka, a zatona Mallam ze dena dukanta amma da mamaki sai naga ya cigaba da lafta musu bulallar ita da yaron sai kuka suke suna ihu, sai daya musu akala guda goma sannan ya fito daga d'akin yana huci " 'mutuniyar banza kawai, kina zaton da kin kashe aurenki kin fito hakan zesa na saurara miki, to duk sanda makamancin haka ya sake faruwa ko ma wanda be kaishi ba saina miki yafi haka, mutuniyar banza kawai, ya fita ya fara lallashin Iya. Ita kuwa tana kuka tana rarashinta yaronta ta duba hannuwansa duk sunyi shatin bulala ta sake fashewa da kuka shima kuwa kukan yake abun tausayi, tashi tayi ta goya shi tana jijiga shi ko zeyi shiru amma sam yak'i ta bankad'a akwatinta tana duba wani abu kona wasa ne da zesa yayi shiru, can ta hango alawa lolipop da murnanta ta sako shi ta bashi aikuwa abinka da yaro sai yayi tsit ya cigaba da shan alawarsa hakan ya bata damar sake maida shi baya be dad'e ba kuwa yayi bacci ya barta nan tana ta sharbar kukanta, bayanta duk yayi rud'u-rud'u yayi ja abinka da farin mutum, ga zafin bulala da ya isheta, ganin yaron yayi nisa a bacci ta sauko shi ta rungume shi tana hawaye "ina sonka d'ana, kai kad'ai ne me share min kukana, nasan kai kad'ai ne bazaka guje ni ba, Allah ya raya min kai MUHSIN, ta kwantar da shi ta share hawayenta sannan ta tashi ta nufi kitchen domin ta kauda yunwar data addabeta, futowar ta keda wuya sukayi karo wata budurwa, ai kuwa budurwar ta juyo cike da fushi ta wanka mata mari, " ke har kin isa ki bangajeni na kyaleki dan kina tak'ama kin girme ni, to wallahi kika kuma bangaje ni sai na miki fiye da haka, banza BAZAWARA kawai, taje ta kaso aurenta zata zo ta dami mutane mtsw" Bazawara ta juyo cike da fushi ta.......... DEDICATED TO ALL MUSLIMS WIDOW'S http://hafcy.mywapblog.com [4:40pm, 3/21/2016] Sajna: ■■ BAZAWARA■■ ©MISS HAFCY ®NWA ■ TAK'AITACEN LABARI■ `2` Ta wanka mata mari ji kake tas! " hak'urina ya kai mak'ura na gaji, BILKI kar ki manta fa ke k'anwata ce na girmeki , amma zaki d'auki hannu ki mare ni? To ki sani shiru-shiru ba wasa bane gudun magana ne , dan haka ki kiyaye," tana gama fad'an haka ta wuce kitchen ta d'auko abincinta sannan ta koma d'akinta, tabar Bilki tsaye tana mamaki dan bata tab'a zaton zata tanka mata ba, balle har ta rama. Tayi kwafa sannan tace " Allah ya taimakeki Iya bata nan da sai kin gane kuranki, woooo BAZAWARA kawai " ta shige d'aki tana zage-zage. ■ASALIN LABARI■ Malam Ahmad Muneer,shine sunan mahaifin NUSAIBA BAZAWARA, d'an kasuwa ne wanda yake saida atamfofi a kasuwar kwari dake kano, yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado, Asalin iyayensu fulanin adamawa ne amma shi a kano aka haife shi a nan ya tashi. Matarsa ta farko itace BINTA, sunyi auren soyayya na saurayi da budurwa, sun zauna tsahon shekara biyar ba haihuwa ,sannan Binta ta haifa masa d'a namiji lafiyaye aka sam mai suna MUNEER, bayan shekara biyar(5) ta sake haifa masa yarinya kyakyawa aka samata NUSAIBA, daganan kuma sai haihuwar ta tsaya, suna zaune cikin rufin asiri kwatsam Malam Ahmad ya k'ara aure ,ya auro wata hatsabibiyar mace mai suna INDO, cikin shekara uku(3) ta haifa masa "yaya mata guda biyu babbar me suna FALMATA,wadda a yanzu haka tana can Jigawa tana aure, sai kuma auta BILKI wadda ita budurwa ce ko auren fari bata yi ba. Tun bayan haihuwar 'yayan Indo sai ta shiga kula mak'ircin yadda zata raba Malam da Binta saboda taga Malam yafi san Binta kuma d'ad'in d'ad'awa gata itace mahaifiyar tilon d'ansa namiji wanda yake ji dashi, dan haka ta shiga wajen bokaye da malamai dan su raba auren, watarana kuwa kwatsam sai Mal ya saki Binta, ya kuma ce karta sake ko da wasa ta tafan mai da 'yayansa, haka tana kuka suna kuka, ta rabu da su ta koma gidansu, cikin ikon Allah tana gama iddar ta, ta sami wani Alhaji dake aiki a Lagos ya aure ta , yanzu haka tana Lagos da zama hadda yaranta suna zaune cikin kwanciyar hankali. Gida ya rage sai Indo kawai ,sai abinda tace za'ayi Malam kuwa ko kara ta saka tace kar ya tsalake to ko kusa da karan baze zo ba , balle har ya tsalaka shi, Muneer da Nusaiba kuwa sun zamo kamar wasu bayinta, sune yi mata wanki ita da 'yarta Bilki, sune shara, wanke- wanke, aike, kai da komai ma na gidan, girki ne kawai bata barinsu suyi. Malam kuwa ko k'ala baya iya cewa don dama ta riga tasa boka ya rufe masa baki. Muneer ya kamala karatun sakandire a dadafe, cikin ikon Allah ya samu gurbun karatu a ABU ZARIA inda ze karanci Medicine, murna a wajensa ba'a magana,amma in ya tuna ze tafi ya bar k'anwarsa cikin wani hali duk sai yaji ba d'adi, cikin ikon Allah kuwa Malam ya biya komai da komai, Muneer ya tafi makaranta, ba'a san ransa ba, dan yana hangen irin wahalar da k'anwarsa zata sha bayan baya nan, domin wani lokacin in yaga aiki ya mata yawa shine ke tayata suyi su gama, Nusaiba ma tasha kuka da kyar ya lallasheta tare da yimata nasihar ta dinga addu'a sannan tasa hak'uri a zuciyarta domin wataran sai labari kuma mahakurci mawadacu ne, bayan tafiyarsa Nusaiba a gida kullum cikin wahala take aiki kuwa haka take yinsa kamar jaka bata hutawa sam, sai lokacin kwanciya, wani sa'in abincima gagarata yake ta zamo abin tausayi ga uwar rama datake yi. Sannu bata hana zuwa har Muneer ya kamala karatunsa na Medicine ya fito da sakamako me kyau, ita kuma Nusaiba tana aji na hud'u a makarantar sakandire (Ss1) kuma tana da shekara goma sha biyar(15) duk da karatun a dadafe ta keyinsa kullum cikin makara da fashi dan ma tana da k'ok'ari. Muneer kuwa nan da nan ya sami aiki ya fara samun kud'i, indai kuwa ya sami kud'i ko nawa ne a gida hud'u yake rabi shi, kaso d'aya ya kaiwa mahaifiyarsa( duk da tana auren mai halin amma hakan be hanasa bata duk abinda ya samu ba) kaso na biyu kuma ya bawa Malam domin yayi cefene da saurarn abubuwa, kaso na uku kuma ya siya k'anwarsa Nusaiba kayyayki dama duk wani abu datake buk'ata, sauran kuma ya rik'e, haka yake a kodayaushe, hakan ba k'aramin k'onawa Iya rai yake ba, hakan yasa ta shiga kula tugun makirci ta yadda zata dawo da Muneer tafin hannunta ya zamo ita ke juya shi sai abinda tace, hakan kuwa akayi ta kashe kud'i masu yawa kan asirin nan yayi don har gonarta ta gado ta siyar takaiwa boko kud'in domin yayi aiki, cikin k'ank'anin lokaci Muneer ya dawo ba shida wadda yake girmamwa yake bin umarninta kamar Iya, Nusaiba kuwa duka da tsangwama ta hantara shine ke had'a su, ya zamanto ko biyar bata shiga tsakaninsu yana ganin Iya zata dinga dukanta tana zaginta tana azabtar da ita amma bashida ikon cewa komai sai dai ma ya taya Iya fad'an, ko kuma ya tayata dukan ta, kud'i kuwa duk albashinsa akan Iya da 'yayanta Bilki da Falmata yake k'arewa, Nusaiba kuwa kullum haka take cikin kunci babu mai taimaka mata abincin ma wani sa'in gagarata yake sauk'inta d'aya in taje makaranta k'awayenta dayake sunsan halin datake ciki suna taimaka mata, kuma suna d'ebe mata kewa, Muneer kuwa ya zama d'an Iya na k'arfi da yaji mahaifiyarsa ma ya manta da ita, Iya kuwa dama tuni ta raba Binta da Nusaiba. A da Binta takan aikowa da Nusaiba kaya, kayan kawalliya da d'an kud'i amma dagabaya sai ta dena kwata-kwata, Nusaiba kuwa tun tana damuwa har ta dena. `3` Nusaiba ta taso yarinya kyakyawa kuma ga farin jinin samari amma duk da haka bata kula kowa duk wanda yazo mata da zancen soyayya ce masa take yayi hak'uri karatu zatayi aure ba yanzu ba, sab'anin Bilki duk da k'aracin shekarunta gata yarinya ce bata isa budurwa ba a lokacin, hakan be hanta kula ko wani kolon saurayi ba, ko yace yana santa ko bayaso, yara wani sa'in har ihu suke mata suna mata wak'a " ta maza, ta maza, mai wasa da maza karya" amma tak'i denawa. Nusaiba fara ce mai madaidaicin tsahon tana da manya idanuwana, sai bakinta d'an madaidaici, bata da hanci sosaii amma hancinta mai kyau ne, tana da gashinta dai-dai misali,kyakyawa ce dai Masha Allah. Nusaiba bata da wani buri a rayuwarta daya wuce ta zama Lawyer hakan yasa take k'ok'ari a makaranta bata wuce ta d'aya a position, ta maida hankalinta zuwa karatunta, duk wannan halin data shiga amma sam baya hanata karatunta ba. Watarana Kausar k'awar Nusaiba ta kawo mata ziyara suna d'aki suna hira, sai suka fara hirar wata k'awarsu da'aka cire aka mata aure, Nusaiba tace " ai ni insha Allahu sai na shiga jami'a na fara karantar Law na tabbatar da cewa zan yi kuma mijina ze barni na cigaba sannan zanyi aure, domin ni yanzu banida wani buri daya wuce naga na zama Lawyer kuma kullum cikin addu'a nake akan Allah ya cika min burina, Amin" Kausar tace " Allah ya cika miki burin ki k'awata ni kam kinga banda matsala nasan duk tsiya sai na kamala sakandire, in ma za'a min aure, kuma wanda za'a aura min insha Allahu ze barni nayi karatu, dan nima kinsan burina be wuce na zama ma'aikaciyar Lab ba", Nusaiba tace " to Allah ya cika mana burukanmu" Kausar tace " Amin" Duk wannan hirar da suke a kunne Iya tana kofa ta kasa kunne tana sauraronsu,suka cigaba da hirarsu ta makaranta, kana Kausar ta mata salama ta tafi. Iya ta koma d'akinta tayi kwafa sannan a zuciyarta tace " dama abinda nake san ji kenan, da yardar Allah yarinyar nan na kusa aurar dake kuma jahili zan aura miki in yaso naga ta yadda za'ayi ki cika burin naki, ja'irara yarinya tanaso ta b'ata min pilas(plan)" ta d'an yi jim tana tunani sannan tace " yarinyar nan ta Sa'idu mai walda ta dace! Http://hafcy.mywapblog.com adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *