Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 3 April 2017

DR HANEEFA

adsense here [11/28, 2:54 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ1 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Bismillahir-rahmanir-rahim Darasi ake musu amma hankalinta baya kan abinda ake koyarwa musu, zubawa malamin idanu tayi kamar mai fahimtar abinda ake. Qararrawa aka kada domin canza malami fitarsa ke da wuya itama ta tashi domin bin bayansa nan take hadiza da ta lura da yanayin da tashiga tabita a baya. Nesa da ajinnasu tayi sannan ta samu wani lungu ta tsaya, hawayene kebin kuncinta sai taji an dafata kafadarta. Ganin hadiza yasa ta fashe da kuka sosai tare da sulalewa ta zauna kan wani dutse, kuka take sosai hadiza bata ce da ita komai ba, ganin ta saida kuka da kanta hadiza tace haba haneefah duk abinda ya faru hakuri zakiyi tare da cigaba da addu'a yariga ya wuce kuka da damuwa bazai zamto solution ba, murmushin takaici haneefah tayi taga aminiyar tata tace hadiza ba lamarin nazir ke damuna ba nasan ina sonshi ya yaudareni yayi aure lamarin abbanane har yanzu bansan me zan mishi na birgeshi ba, sun hadani da abbana kullum cikin ganin laifina yake bansan mezanyi in wanke kaina ba, cike da tausayi hadiza tace kada ki damu Allah na tare take duk daren dadewa gaskiya zata bayyana, abinda nake so dake ki kwantar da hankalinki, ki dage da karatu insha Allah wata tana sai labari da irin wannan kalamai hadiza ta rika kwantar mata da hankali suka koma aji. Alhaji hamisu shine mahaifin haneefah sannan umma salamatu itace mahaifiyar haneefah. Haifaffun garin kano ne,Yana da mata biyu hajiya hafsa(inna) da salamatu (umma). Inna yaranta takwas biyar mata uku maza salim shine danta na farko, bilkisu, zainab, jibril, zuwaira, Ibrahim, shukra da sadiya sannan yaran umma Nana khadija itace babbar yarta sai ahmad, haneefah da kannenta biyu amal da bintu. Alhaji hamisu adaline tsakanin matansa da yaransa yanada rufin asiri daidai gwargodo domin ma'aikacin gwamnatine, bayi da buri kamar yaga yayanshi sunyi karatu badon su zama wani abuba, domin duniyar yanzu karatu nada muhimmanci arayuwar dan adam. Inna ta daurewa yaranta gindi wajen yin abinda suka ga dama shiyasa sam basu aje hankalinsu wajen yin karatu ba kullum cikin bin yan mata suke matan ko dakyar suka qarasa karatunsu na sakandari aka aurar dasu sai kannensu qanana shukra da sadiya haka yan maxan karatu yaga garesu suka nuna aure suke so aka aurar dasu banda ibrahim. Akullum alhaji hamisu yana takaicin halin yaransa domin shi mutum ne mai son karatu domin yasan muhimmancin sa amma babu yadda zayyi tunda haka suka ga yafi musu. Itako umma ma'aikaciyace, macen kirki marason magana sannan takasance ta tashi tsaye kan tarbiyyar yaranta da ilminsu hakan yasa take gaban goshi wajen maigidanta, hakan yasa inna kishiyarta ta dauki alwashin sai ta tarwasa su, Allah cikin ikonsa lokacin Alhaji yayi retired, rayuwa yayi halinsa, yau akwai gobe babu hakan yasa yacanza makarantun yayanshi izuwa na gomnati. Umma su biyune gun mahaifan su, yayarta hajiya lubna. Tun suna qanana Allah yayiwa haifinsu rasuwa mahaifiyarsu ta dauki dawainiyar karatunsu har lubna ta kammala ta samu miji tayi aure, yanema mata aiki a ma'aikatar ilmi hakan yasa ta samu kwarin gwiwar dauko kanwarta taci gaba da karatu ta kammala har tasamu miji tayi aure. Lubna yaranta bakwai hudu maza auwal, sadiq, musa, khalifa uku mata muhibbat, humaira da amina. Auwal, muhibbat da humaira suna da aure da yaransu. Duk dukiyar da Allah ya azurtasu hakan baisa sun sangarceba, duk sun kasance yara masu tarbiyya. Sannan burin umma da mama suga kan zuri'arsu a hade. Cikin ikon Allah sun girma suna kaunar junansu. Haneefah yar shekaru 17 aduniya yarinyace mai biyayya da hankali, sannan takasance yarinya mai barkwanci, bata son raini sannan bata kaunar ta rainamutane, saurin fushi gareta ga saurin hucewa sannan yarinyace mai tsananin bincike kan abinda tasa gaba, ga ilmi. Yarince mai son kwalliya tare da yin duk wani gyara na diya mace, tana matukar son abubuwa daya shafi mata, sannan ita ba kyakykyawa bace ba mummuna bace JININ KYAU GARETA domin ta iya kwalliya. Haneefah itace yar gaban goshi gun mahaifiyarta da yan uwanta suna matukar ji da ita, hakan yasa bata da tamkarsu kullum burinta son faranta musu da wuya kaga sun samu sabani tsakaninta da su domin burinta kullum su hade kai. Yarinyace mai saurin shiga rai duk inda ta zauna tana dibar jama'a saboda yawan fara'arta, hakan da inna ta fahimta shine ta dada karkatar da hankalinta ga haneefah domin lalata mata rayuwa. Kishi sosai inna da yaranta suke nunawa umma, duk da haka umma bata bi takanta ba saida taga sun fara shiga rayuwar yaranta ta soma taka musu birki, duk da haka saida tayi nasarar bata sunan haneefah gun abbanta. Haneefah komai tayi baya birge abbanta hakan yana damunta ga yan uba sai wahalar da ita suke, duk da wani lokaci ba raga musu take ba shakkanta suke. A haka ta soma soyayya da wani matashin yaro mai suna nazir, tana sonshi sosai domin ya hadu iya haduwa. Tana matukar sonshi domin irin mutananne da basu iya so ba, akarshe ya auri wata duk da abin nadamunta kawai ta watsar dashi tare alkawarin bazata qara yarda da wani namijin ba... Amma burinta gyara tsakaninta da abbanta [11/28, 2:55 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ2 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Gidane babba amma an rabawa kowa mashiganshi tun daga bakin gate. An taso daga makaranata ta hade kan kannenta suna tahowa tare dashike tsakaninsu da makaranta babu nisa, dai dai sunzo shiga gida taga yaya jabir da abokinsa suna tsaye idanu sunyi jajaye, daganinsu kwayoyi suke sha ta girgiza kai cikin takaici tare da cewa Allah shiryeku tayi nasu gidan su shukra ma suka shige. Bayan shiganta sahabi yadubi abokinsa jabir yace aboki ya maganar haneefah saifa shareni kake da zarar na kawo maganarta cike da maye jabir yace ai dama so nake ta kammala makarantarta tunda yanzu tana ss3 amma tunda ka matsa ku daidaita tsakaninku inyaso agudanar da biki inta kammala cike da zumudi sahabi yace to shikenan nagode. Zai juya ya tafi jabir yace anjima ka dawo daga zarar an idar da sallan magriba, yace zan dawo daukeda murmushin mugunta jabir ya shige nasu gidan. Agajiye tashigo gida bayan sun taso daga islamiyya ta tarar da yayarta a kitchen tana girki tace sannu Dr da aiki yau baki dawo gida da wuri ba, tace bari kawai yau muka fara fita asibiti shine kumayi yamma inaga kullum haka zan kasance, haneefah tace tab yanzu a asibitin zaki iya wuni wlh nikam bazan iyaba, cike da zolaya tace toh accounter haneefah, ta hada girar sama da kasa tace bayan kunce sai dai na zamo Dr, to wai dukka zamu hadu a fanni daya ayyakamata mu karanta abu daban-daban cike da murmushi nana tace zamu karanta health line amma fannin kowa daban kinga..... Tun kafin ta karasa takatseta tace nidai bazanyi ba yadda nake burin accounter zanyi ko banyi ba.... ta gyada kai tashige ciki nana namata dariya. Bayan ta idar da sallah tana lazimi amal tashigo tace ana sallama dake a wace, tayi mata nuni data tsaya ta kusa kammalawa, bayan minti biyu tayi fatiya cike da tsoro tace waye? Abokin yaya jabir cike da mamaki. Sallama tayi ya amsa cike da murna yace nasan zakiyi mamakin ganina amma ba abin mamaki bane, inasonki kuma da niyyar aure nazo bude baki zatayi magana taji an bude gate, kallon da taga abbanta nayi mata ne yasa hankalinta ya dada tashi bai ce da ita komai ba yayi wucewarsa cike da bakin ciki tace wlh kaci sa'a, ko kunya bakaji ba wai kana sona? Toh wlh nakuma ganin kafarka cikin gidannan ta kyada kai ta wuce. Zama tayi bakin gado ta rasa mezatayi, tunani kala-kala yanzu kuma wani hukunci za'a yanke mata? Cikin wannan hali nana tazo ta tarar da ita tace haneefah yau meya faru? Me kika gani? Yanzu nakaiwa abba abinci yake surutu yaushe zaki gyaru, imma auren kikeso kituro amma shiya fita hakkin ki wajen ganar dake, har dan shaye shaye kika kawo masa gida ransa ya baci sosai, nasan bazaki aikata haka ba sai dai turosa akai, nan take haneefah ta dago kai idanunta cike da hawaye, murmushi tayi tace ba komai Allah na tare dani, cike da tausayi yar'uwar tata tace kada ki damu zaizo yagane gaskiya cike da bacin rai haneefah tace yaushe? Tun na taso yataba saurarona? Komi aka fada mishi daukawa yake, yazama dole in masa biyayya da zan entar da kaina damuwar da nake ciki. Tunda ta fara magana ta kafa mata idanu, tabbas tananuwa haneefah so amma tana tare da kyakykyawar tarbiyya data bata bazata iya aikata irin wadannan abubuwan ba. Taqaraso ciki ta zauna kusa da haneefah tace in fada miki mafita? Tace eh umma zanyi, umma tace toh yazamto mai biyayya gareshi tare da kusanto farin cikin shi ko da ke zai baqanta miki rai, kinsan farin cikin sa yaga kuna karatu sosai, inaso ki kwantar da hankalinki kiyi karatu sosai domin fita da saka mako maikyau sannan ki hada kanki da yan uwanki duk da su ba hakan take agun suba, sannan ki dage da addu'a sosai kan Allah yaraba ki dashi lfy last one shine ki daina damun kanki, ki kawar da kanki kinji? Ta rungume ummanta insha Allah zanyi ta shafa kanta that's my haneefah. Tun daga wannan rana haneefah ta kudurci aniyar yin karatu, ta tattare hankalinta gurin kararu tare da dagewa da addu'a. Ta fita harkansu inna duk da dama ita ba shiga tsabgarsu take ba. *** *** *** *** Kwanci tashi ba wuya cikin nasara haneefah ta zana jarabawarta na SSCE kuma ta fito da saka mako mai kyau cike da farin ciki ta nunawa mahaifinta shima ya yaba mata sannan ta ce tana da ra'ayin tafiya nursing ganin yadda ta dage yasa shi farin ciki tare da yi mata alkawarin zai nema mata. Ranar haneefah tayi farin ciki ganin mahaifinta na farin ciki haka yan uwanta suma sun taya ta. Alhamdulillah ta fara ganin sassauci gun mahaifinta kuma cikin ikon Allah ta samu admission a nursing, tare da kawarta hadiza. Farin ciki ba'a magana gun haneefah, kowa ja mata kunne yake akan tayi karatu cike dajin dadi tace da yan uwanta duk abinda kukeso ina so bazan baku kunya ba. Hakan ko akayi, hadiza da haneefah an dage basu dauki sabbin kawaye ba domin sun aminta da juna sosai dukkaninsu ma'abota son karatune duk da anason kawance dasu amma basu bawa kowa dama ba. Sun tashi daga aminai sun zama yan uwa. Hadiza kyakykyawace sosai domin tafi haneefah da kyau tun suna ss1 hadiza ta aminta da haneefah dakyar ta shawo kanta suka zama aminai, domin haneefah ita kowa natane. Cikin nasara suka cinye shekara daya da rabi saura daya da rabi sannan a asibiti zasu karasa. Babu matsalar da haneefah ke fuskanta kamar rashin iya turanci sosai, ta iya amma bazata dade tabayin shiba wato kadan-kadan takeji, tana iya karatu sannan ta fahimta amma mayarwane bata iyawa, wannan matsalar na damunta. [11/28, 2:56 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH*πŸ‘©πŸΌ 3 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Zaune take tana nazarin wasu littattaifa nana tashigo tace sannu da kokari tace yauwa atakaice tace me kike dubawa ne? Tadanja tsaki tace gobe zamu fita asibiti kuma inaga ranar ante-natal (awon cikine) kinsanni da surutu Amma kada abani topic da ban kware akaiba, nana tace inaga za'a baku kuyi takaitaccen jawabi kan awon cikine, mata diyewa in sun fara zuwa awon ciki kalilanne suke kammalawa harsu haihu, hakan ko bashi da kyau sannan da dama basa son shan magani kamar yadda aka kayyade musu hakan na kawo matsala musamman in mace tazo taihuwa, kamata yayi in mace ta lura tana da juna biyu ta rinka ziyarar asibiti ba fashi harta sauka lfy, in munajin kanmu babu matsala bamusan yaushe matsalan zata auku ba bari in takaita miki yadda zaki jawabi Bayan kinyi sallama tare da tambayarsu kowa lfy saiki soma bayani kamar haka; Zamuyi bayanine akan awon ciki ga wadda bata taba haihuwa ba kuma tana jinta kalau, ya dace tayi gwaje-gwajen da akeyi a awon ciki sannan sume akeyi a awon ciki? Yana da kyau sosai ko da kalau kike jinki ki je a gwada lafiyarki yayin da kike da juna biyu, musamman ma idan na fari ne. Wannan shi ake kira awo. Bari a yi miki bayani mai dan gamsarwa game da awon. Awo wata hanya ce ta amfani da gwaje-gwaje, domin tabbatar da lafiyar uwa da jaririnta da kuma gano matsaloli da ke tattare da yanayin juna biyun, don magance su da wuri tun kafin su zama alakakai. Wato dai hanya ce ta kariya daga galabaita a yayinda ciki ke girma ba kuma lallai bane a auna kowanne a ziyararki ta farko, a’a yau a duba wannan, wani zuwan a duba wancan. A wasu matan da aka ga juna biyunsu ba shi da hadari sosai, ba lallai ne a auna komai ba. Ga abubuwan da aka fi aunawa a zayyane: Na farko ana auna tsayin mai ciki domin duk matar da tsayinta ya gaza mita 1.5 tana cikin hadarin yin doguwar nakuda. Don haka sai a sa alama a katinta cewa wannan matar idan ta zo haihuwa a shirya sosai, ko da doguwar nakuda za ta kamata. Sai kuma nauyi, wanda idan ya wuce misali shi ma ana kyautata zaton ko dai mai juna biyu ta iya samun hawan jinni, ko ciwon suga a wannan lokaci na ciki. Domin wasu matan a lokacin ciki suka fi samun wadannan ciwuka ko da ba su gada ba, kuma yawan nauyin mace kan sa a fara tunanin hakan. Kamata ya yi mace mai ciki ta rika kara rabin kilo na nauyi a mako guda da zarar ciki ya fara tsufa. Amma idan aka samu nauyin da ya wuce wannan, an san akwai matsala. Sai kuma awon cikin shi kansa. Duk sati ciki ya kamata a ce yana kara kwatankwacin santimita guda, don haka ana aunawa ne a gani ko jariri na girma yadda ya kamata ko kuma a’a. Idan awon ciki bai kai daidai watannin cikin ba, to yaro ba ya girma sosai, kuma akan dauki mataki, idan kuma awon ya wuce yadda ake so to shi ma yana nuna wani abu daban, wato ko dai cikin tagwaye ne, ko jariri na girma fiye da yadda ake so (kamar yaran mata masu ciwon suga), wanda hakan kan jawo doguwar nakuda. Za ta iya kasancewa kuma ruwan da yaron ke ciki ya yi yawa sosai, wanda shi ma alama ce ta illa a jariri. A wannan lokaci akan hada da hoton scanning da zai nuna halin da jariri da mahaifa suke ciki. Na hudu sai a auna bugun jini don a tabbatar ba hawan jini a tare da mai ciki. Idan akwai a ba da magani da sauran shawarwari. Sai kuma a tura mace auna yawan jini. Saboda bukatar da jariri ke da ita na wani kaso na jini, kowace mai ciki sai an duba yawan jininta a gani ko isasshe ne. Akan ba da magungunan karin jinni, ko ma shi kansa jinin daidai da bukatar matar. Akan ba su shawara su rika yawan cin nama da koren ganye, saboda suna daga cikin abinci masu kara jini sosai (suna dauke da sinadarin iron). Sai kuma a auna yawan suga. Shi ma don a tabbatar matar ba ta da ciwon suga, idan kuma akwai a fara ba da magunguna. A lura cewa da hawan jinin da ciwon sugan da aka samu a lokacin ciki za su iya warkewa bayan an haife cikin, ko kuma su ki warkewa. Sai kuma a ce mai juna biyu ta ce ta yi fitsari a kwalba, don a gwada sinadaran da ke cikin fitsari. To a nan ma ana iya gano ko akwai matsalar ciwon jijjiga ko na suga a jikin matar. Wadannan su ne muhimman abubuwan da ake aunawa. Ban da tsayi, kusan duk abubuwan da aka zayyana a sama ba sau kadai ake aunawa ba, wato kusan duk zuwa sai an sake aunawa saboda lokacin da ciki ke kara tsufa, lokacin hadarinsa ke kara yawa. Allah baku ikon zuwa ya saukeku lfy [11/28, 2:56 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH*πŸ‘©πŸΌ 4 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Saiki shirya da amsar tambayoyi domin baza'a rasaba, haneefah dake kallon nana tace yanzu haka mutum zai tayi? Wlh ni bazan iya cigaba da health ba ,innayi gaba canza abuna zanyi. Nana tace kici gaba yar uwa, al'umma na bukatar irinku, ke yarince mai tausayi sannan zaki aje uzurinki domin wasu na tabbata zakiyi taimako, haneefah tace wannan shine dalilin naki? Ayyuka da dama al'umma na bukatar taimaka amma ai lfy yafi koma cewar nana. Haneefah tace yauwa sis yaushe zamusha bikine Allah duk na kagu kinga kin gama makaranta. Nana tace da saura, abba so yake muyi karatu sosai haneefah tace haba nana ai karatun da kikai is ok, aiki yarage miki fa! Haneefah ina matukar so naga nacikawa mishi buri, in kikai la'akari da yanayin gidannan cikin yaran inna babu wadda karatunsu yayi zurfi, duk da yakasance bayida arziki irin na baya amma yana mana kokari sosai, inason nayi aure kuma umma tanaso amma zan bari ba yanzu ba sai nayi MBBS zaro ido haneefah tayi tace kina da kokari, shine ko kula samari bakyayi? Eh bazan kula kowa ba sai naga komai ya dai-daita. Ajiyar zuciya haneefah tayi tace haba nana, kin dan samu karatu ai saiki godewa Allah, bakyaga irin yadda kasarmu take ciki? Wace yar talaka kikaji tana MBBS duk yayan masu kudine sannan aure ai baya hana karatu, ina mamkin wasu iyaye da suke dagewa yaransu akan sai sunyi karatu koda sun nuna aure suke so, dayawa yara suke shan wahala wajen danne kudurinsu su faranta ran iyayensu, wai shin karatun boko meyake so ya zamane? Yadda mutane suka dauka muhimmanci suka bashi, zakiga yaron da ya iya turanci yana kokari anfi tarairayarsa amma ba'a kula da na addini ba, yaro daya dace ya taso addininsa yasani amma yafi sanin kan boko, zakiga wasu yara masu shekara 7 basusan banbancin tsakanin wuta da aljannah ba amma an hada suda tv babu abinda basu sani ba. Muyiwa kanmu fada kamata yayi yara su taso da Qur'an a bakinsu ba sanin story books ba Allah sa mugane ameen, nana tace kina da gaskiya na dogara ga Allah kuma insha Allah inna samu admission ko apart 1 me zanyi aure haneefah tace karma kiyi mana. Suna taba karatu ahmad ya leko yace kuzo umma nakiranku. Zaune suka taddata haneefah tace sannu da hutawa ta amsa mata tace yauwa, ta kalli haneefah cike da murmushi tace dama lokaci yayi dama batun zaki bude account ne, lokaci yayi da kema zaki fara adani kamar yan uwanki nana da ahmad, ajiyannan da zakiyi zai amfanar dake damu watarana, dubu goma ne a ko wacce wata, nasan yanzu ba wani sutura kika damu dashi ba tunda kullum cikin uniform kike, gabama in zaki saya kisiya daidai karfin ki sannan ki rage tambayar abbanki kudin makaranta sai wadda ya dace ki tambaya ina fata kuna jina? A sanyaye tace eh sannan ko lokacin auran ku yazo bazamu sha wahala sosai ba ammafa sai kuna tattali, Allah ya muku albarka tashi ku tafi. Haneefah tana matukar son mahaifiyarsu, duk kudin da take samuwa akansu yake karewa tasan tanayin hakanne domin su kauda idanunsu akan abin hannun jama'a, duk da basu da kodayi amma ummansu tana wadatar dasu da komai. Gaskiya iyaye abin tausayawa ne musamman uwa, zata salwantar da dukkanin farin cikin ta domin ta faranta ran yaranta, babu abinda ya'ya yadace suyiwa iyayensu kamar su faranta musu sannan su bisu da addu'a. Washe gari ta tashi da tsananin tsinkar zuciya, ta idarda sallah tayi dukkanin abinda ya dace kuma ta saba na ibada amma stil zuciyar bata daina ba. Kokarin shirin fita take amma takasa shiryawa cike da mamaki tace yau kuma mezai faru. Dauko Qur'ani tayi ta zauna karatu, a hankali taji zuciyar ta lafa, ta dauko carbi ta soma addu'a. Takai kimanin minti ishirin sai ta tashi ta shirya taje yiwa umma sallama, umma ta bata kudin da zata bude account tayi musu sallama ta fita. Zaune take a ward (pediatric) dinsu amma takasa tabuka komai sai addu'a take a zuciyarta, zaman ya gagareta ta tashi ta nufi gun aminiyarta dake labour ward. Kasa shiga tayi domin jirine ke daukanta intaga jini. Tana cikin tsaye sai ga hadiza ta fito tace ah yar'uwa kece kika tsaya anan, haneefah tace so kike abani gado kenan domin nikam fadiwa zanyi, dariya hadiza ta soma yi domin sarai zata iya tace meya fito dake lokacin lunch bayyi ba? Haneefah tace wlh yau nakasa gane kaina tun dazu wani iri nakeji. Hadiza cike da damuwa tace kodai wani abu yafaru ne? Aa babu komai tace kiranka anbato _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musi bati wakhlifni khairan minna_, haneefah tace inshaa Allah zanyi nagode, zan tafi bank yanzu innatashi zan wuce gida tace toh Allah kiyaye hanya ki gaida gida. Saukowa tayi cikin adaidaita sahun da ya kawota ta sallameshi ta shiga bank zuciyarta na dada tsananta wajen bugu. Zaune take tana jiran a sallami wadda suke gabanta tana karewa cikin kallo tana kara sha'awar zama accounter. Daidai wani bakin ko fa da yayi lungu ta tsugunna take cika forms da aka bata, zata mike takai takardun tana kara dubawa batare da ganin gaban taba. Gaisawa yayi da abokinsa zai wuce office din manager hanakalinsa nakan abokin nasa, tafiya yake baya duba gabansa ya juya yana yiwa abokin sallama cikin sauri. Dab zai karyo kwanan yaji yayi karo da wani abu, tarwatsewar takardune ya tabbata mishi mutum ne. Cike da tsiwa ta dago zata fara magana hada idanun da sukai me yasa fasa abinda take shirinyi. [11/28, 2:57 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ5 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Kallo cikin ido suke, a take taji wani irin nishadi ya lullubi zuciyarta, kimanin dakika goma suka dauka, tayi saurin kawar da kanta ta sunkuya ta fara daukan form da suka tarwatse. Baice da ita komai ba saida ta kammala ta dago yace am sorry, najuya ina maganane batare da kula da abinda yake gama naba. jin muryar tasa take tamkar kada ya daina magana tsaban dadi, bata tabajin murya irin tashi ba. Batare cewa komai ba zata wuce yace kinji? Ta daga ido cikin wani salo da itama batasan tayi ba ta murmusa tayi gaba abinta batare da tace dashi komai ba. Ta kammala komai ta nufi gida. Misalin karfe goma da rabi ta kammala shirin baccinta ta kwanta, idanunta a lumshe ta soma karanto suratul mulk (yana tsare dan adam da azabar kabari) sannan ta soma neman gafarar mahaliccinta tana ambaton _ASTAGFIRULLAH WA'ATUBU ILAIK_(yana dakyau mu koyawa kanmu wannan dabi'ar, yin istigfari har bacci ya daukemu. Allah sa mudace) bayan ta kammala tanemi bacci ta rasa, kalaman wannan mutumin suke mata yawo a kunne, ta tsinci kanta da son sake jin maganarsa koda sau dayane.... tunani takeyi sosai taga ba mafita bane ta dauro alwala ta fara jera nafiloli saida bacci ya dameta sosai ta kwanta kan sallayar bacci ya dauketa. *** **** **** **** Dr Hassan ke zageye da daliban da suke zangon karshe, duk cikin su an angagara wadda zai dauki jinin yaro, duk yabi ya tada musu hankali shi baza'a dauki jininsa ba, mum kice su tafi allura a hannunsu kuka yake yana maganar..... tazo wucewa Dr Hassan ya daka mata tsawa tare da kiranta, cikin hade rai yace inason ki debamin jinin yaronnan cikin harshen turanci, zuciyarta ke bugu domin tsoron kada ya dameta da yaren da bazata iya tsawaita magana ba. Ta dauki allura ta nufi gefen gadon ganin yana kuka yasa ta ajiye alluran, bayan sun gaisa da mamar tasa da dubi yaron tace sannu ya amsa da yauwa. Tashiga share mishi hawaye tace ya sunanka? Habib masha Allah suna mai dadi saitaga yayi murmushi, tace ina fata jiki da sauki yace eh, tace kana son zaman asibitinne? Yace aa inason tafiya gida. Dr dake tseye yana kallonta yace shine aikin da nasaki? Bata kulasaba taci gaba da cewa habib in kanaso ka tafi gida toh ya zamto..... tsawan da aka daka matane yasata mikewa cikin bacin rai, tafara magana cikin harshen hausa kai ka sani amma ai ina kanyi ne ko haka zanzo gun yaro in riko hannun shi yana fizgewa allaura ta karye ace ban iya aiki ba? In bazaka zubamin ido ba ga alluran wadda kasasu agaba su dauka. Ta mika masa allura, cikin fusata zayyi magana Dr Mubarak dake bayanshi yariko shi ya kalli haneefah yace kici gaba. Ta juyo kan habib tace tunda kanason komawa gida in anzo yi maka allura kada kayi kuka, kuma nasan kana da dauri ko ? Yace eh I'm strong like ninja, tace yauwa kuma zan sayo maka choculate muddin kamin alkawarin bazaka sake kuka ba cike da jin dadi yace toh, tace ka rufe idonka saika mikomin hannun ka bazaka ji zafi ba... haka ko yayi ta rinka lallashinsa baisan sanda aka dauka jinin ba, ji yayi tace bude idonka, yana budewa yace aunty babu zafi gobe kizo ki kara daukawa. Tayi masa murmushi tace toh. Dukkansu suka zuba mata ido, ta mikawa Dr ta juya gun mum din habib ta mika mata dari biyar tace kisiya masa choculate. Zata wuce Dr Hassan yace kina wani level? 200 cike da mamaki ke kallon sauran daliban nan ya soma surutu kan su aje hankali suyi karatu. Dr Mubarak yace kisame ni a office tace toh. Tun wuce warta ya zuba mata ido tabbas itace wacce jiya suka hadu a bank, yadda tashawa kan yaron cikin kankanin lokaci yafi birgeshi atake zuciyarsa ke raya masa wani abu da bazai iya fassarawa ba. Haka kawai yaji yana son yi mata magana. Sallama yayi gun mara lfiyr da yazo dubawa amma kash ya dubata ko ina bai ganta ba gashi gobe yake son komawa gurin aikinsa. Zaune kan kujerar shi ta same shi, ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a tare da bata izinin zama. Yafara magana cike da damuwa zakiyi mamakin kirana sbd nasan baki taba ganina ba tace hakane, yace taimako zakimin a sannan ta dago ido tana kallonshi Allah sa zan iya ta amsa mishi, wato inada mata da yara biyu mace da namiji, ina matukar son matata domin auren soyayya mukai. Ina matukar son yara dayawa amma ta kafe biyu sun ishemu nayi nayi amma taki karshe tace cire mahaifa zatayi, inaso in rufa mana asirine bana son maganan yaje kunnen manya domin za'a iyace in qara aure ni kuma bana tsammanin zanso wata daban kamar yadda nakesonta yakarashe maganar kamar zayyi kuka. Cike da tausayi haneefah ke kallonsa, tace yanzu me kake so ayi? Gobe misalin karfe 9:30 kizo da ciwon ciki zamu karasa sauran insha Allah. [11/28, 2:57 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH*πŸ‘©πŸΌ 6 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Tare suke shigowa asibiti da hadiza daga restaurant karaf idanunta suka sauka kanshi, jingine yake jikin wata CRV 2015. Yayi bala'in kyau cikin manyan kaya, sannan ta kare mishi kallo, fari ne amma ba sosai ba, shiba dogo ba, ba gajere ba ba amma yadan fita tsayo. Idanunta suka dada hango kwantacciyar gashin kanshi kamar balarabe sannan sajenshi da ya matukar karbeshi. Kallo daya zaka mishi ka fahimci nutsuwa da kamala tattare dashi. Kallo shi take sai dai ta fahimci kamar wani yake nema domin idanun sa nakan mai fita da shigowa. Karaf suka hada ido ya sakar mata murmushi daya kara mishi kyau, gani tayi ya nufo inda suke ta kawar da idanunta akanshi. Sallama ya musu suka amsa, ya gaishe su hadiza kadai ta amsa. Kallonsa ya koma gun haneefah dake kallon wani guri daban yace sister nazo na dada baki hakuri domin naga baki amsa min ba. A hankali ta juyo suka hada ido tace ba komai, taja hannun hadiza suka soma tafiya yace in bazaki damu ba inason magana dake! Budar bakinta tace matar aure ce. Hadiza cike da mamaki ke kallonta harsuka wuce ward dinsu. Binsu yayi da kallo tare da tsananin mamaki. Ba matar aure bace take yabawa kansa amsa, amma me dalilinta nasarar dani? Bincike ya soma tunanin farawa sai dai jirgin yamma zai yau ya wuce gurin aikin sa. Murmushi yayi daya tuno inda zai samu information akanta, ya juya ya nufi motarsa. Dakatar da tafiyan hadiza tayi tare da jan hannunta suka koma kan wani benci suka zauna. Haneefah mesa kikace kina da aure? Banason dogon surutune yasa na katse zancen, aina kuka san juna? Nan ta labatar mata da abinda ya faru. Hadiza tayi murmushi tace in yazo da batun so fa? Haneefah cike da mamaki tace har tunanin haka kika? Hadiza tace babu yadda Allah baya hada bayinsa, mesa zai tako yazo domin amsa hakurinsa? Haneefah tayi murmushi tace da aminiyarta haba yar uwa, kallo daya zaki masa kinsan dan masu kudine, sannan yafini kyau nesa ba kusa ba kuma tabbas mazan yanzu sai wadda tafisu kyau taya tayaya kike tsammanin zai soni? Cike da mamaki hadiza tace ban taba tunanin kemai irin wannan tunanin bace, kinsan so saboda Allah baya duban ilmin mutum ko kudi ko kyawu? Abinda yake bukata shine kikasance mai gaskiya da rikon amana babu cuta babu cutarwa! Haneefah tace tabbas ina sane da hakan amma cike da murmushi, amma ina jiyewa kaina randa za, fada tarkon so sbd ban iya shiba. Hadiza tace in tambayeki mana? Ina mai sauraronki, shin wani irin miji kike burin aura? Lumshe idanunta tayi tare da soma magana ina son namiji wadda yasan darajar dan adam, wadda ya wadatu da ilmin addini wato mai tsananin tsoron Allah, wadda duniya bata gabansa wadda zai soni tsakani da Allah ya nunamin tsantsar kauna da kulawa, wadda annabinmu Muhammad (S.A.W) ya kwadaitar damu mu aura, wadda..... hadiza tayi saurin dakatar da ita tace ai kin gama komai insha Allah kin samu, kijira lokaci amma kada ki manta duk mabukaci baya bacci ki dage da tsayuwar dare, ta murmusa tace insha Allah. **** **** **** **** Washe gari misalin karfe 9:30 yasameta a kofar Dr Mubarak, idonta cike da hawaye ta turo kofar yashiga. Zaune suke suna fuskantar juna, hade rai yayi ya dago fuska yace waya baki izinin shiga? A sannan haneefah ta fashe da kuka tana cewa cikina cikin tsawa yace fita? A hankali kyakykyawar matarshi wadda fuskarta alamar tausayi tace haba Dr, ka dubata mana shine zata shigo babu excuse? Ganin bata ce komai ba kuma kar planning nasu ya rushe yace ga guri zauna, wani irin ciwon ciki? Tace nidai tun da dare nake fama amma yanzu ya tsananta, yace in period naki zaizo wani irin alama kike? Yana ciwo amma ba ko wanni lokaci ba, ok. Yace yaushe ne next zuwan shi? Ina kanyi... a matsayinki na student of health bazaki iya banbanta menstrual pain ba? Haneefah ta sunkuyar da kai, ki tashi kibani wuri. Ta dago tace, Dr ina banbantawa, babban burina shine inyi aure in hayayyafa, shine nake tsoron duk wata ciwon ciki domin kada ya tabamin mahaifa. Cike da mamaki matar Dr ke kallon haneefah, Dr yace shekarunki nawa? 19 tabashi amsa ya juya gun matarsa yace kindai ji abinda take cewa, yarinya karama tun kafin tayi aure take tunanin future ta, amma ke kokarin cire mahaifa kike. Zuro ido tayi ta fuskanci inda take kallo tare da cewa aunt gun Dr kika zo domin a cire miki? Mesa? Tana so tayi magana haneefah ta katseta ta hanyar cewa baki da wata hujja nayin hakan. Ko kinsan cewa babu wadda ya isa yayiwa wani kyautar da ko ya inba mahaliccin muba? Kina da tabbacin za'a maida miki mahaifane? Duk yawan yaranki kinsan zasu dauwama tare dakene? Yau Allah ya baki daman da mutane da dama suka rasa amma zaki nemi rasashi da sanin ki da wayonki? Akwai mata da dama da suke tunanin yawan haihuwa na tsufar da mutum da wuri, abin ba haka bane. Kiyiwa mijinki kwalliya in yaran kikarasa su kiyi meh? Kina takamar mijinki na sonki? Hmm kallesu da ido kawai, yaranki sune rayuwarki, Kisani cewa duk sonda mijinki ke miki muddin kika rasa yara zai iya rage sonki ya auro wadda zata hayayyafa mishi kuma ta mamaye masa zuciya a barki da kunar zuciya, sannan yan uwanshi su gujeki. Wasuma tsabar rashin tausayi jarirai suke hadawa da fida saboda basaso nonuwansu su zube, namijin banza, kinsan sinadarai da suke dauke da nono kuwa? Abincin yaro kuma lafiyar yaro. Nidai shawarata kada ki soma domin dana sani na gab da zuwa miki, mahaifarki itace abin alfaharinki a gidan miji, kada kibiyewa kawaye domin wasun tsantsar muguntane a zukatansu. Ki zauna da mijinki lfy kada aji kanku inma bai sani ba kada ki fada mishi, in kika fita bakisan gidan wa zakiba, kimin afuwa in maganganuna sun bata miki rai. Dago kanta tayi hawaye na tsiyaya a kuncinta tace, ya sunanki, haneefah. Ta kama hannunta gam ta rike tace hakika nayi nakusa fadawa rami mai zurfi wadda babu wadda ya isa fiddoni, sai gaki bansanki ako inaba kinzo kin haskamin gabana nagane ramine. Dayawa muna cutar da kanmu, yarana biyu, na manta akwai rashi. Sai yanzu kika tunomin, bansan da wani irin baki zan gode miki ba. Murmushi haneefah tayi tace ba komai Allah shige mana gaba a al'amuranmu. Dr Mubarak bai tabajin cewa akwai yara masu baiwa masu ilmin addini da kaifin hankali irin haneefah ba. Ya kalli matarsa yace kin janye? Tace eh najanye sannan ina neman afuwanka, kai hakuri ka yafemin. Haneefah tace zan wuce a sanyaye. Matar Dr tace pls inaso in kulla zumunci dake, murmushi haneefah tayi tace toh. Matar tace sunana Barrister Ramlat ga lambata. Haneefah ta karba ta fice ta barsu. [11/28, 2:57 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH*πŸ‘©πŸΌ 7 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Ward nasu ta wuce ta duba abinda zata duba ta wuce ward dinsu hadiza. Agajiye ta shigo gida domin tasha aiki a labour ward, ta tarar da nana a sakar gida zata shiga falon abbansu. Nana ta nufota tace wadda suka taba aiki da abba yakawo ziyara kije ki canza kayanki ku gaisa. Cikin ladabi suka gaidashi ya amsa yace masha Allah ya karatu? Haneefah tace Alhamdulillah nana tagama nice da saura haryanzu. Cike da murmushi abokin abban nasu yace toh Allah bada sa'a, tare suka ce amin gaba da mikewa suka shiga ciki. Alhaji mudassir ya dubi abokinsa Alhaji hamisu bayan fitarsu yace masha Allah, nana tagama makaranta aiki take ko takusa aure? Abba yace babu ko daya jiran admission take amma har yanzu shiru. Cike da mamaki Alhaji mudassir ya dube shi yace irin matsayina a garinnan amma yaranka su nema admission har so biyu? Abba yace ai komai da lokacinsa, bazayyu in rika daurawa wasu nawi ba. Wannan shine zumunci? Nasan abinda kake gudu amma kasani bana daya daga cikin mutanennan. Metake so ta karanta? MBBS. In bazaka damuba ka kawo requirment dinta saura dalibai biyar yarage na wannan fannin wadda zasu kasan Egypt (scholarship)sai insa hannu su tafi. Abba yace har Egypt? Abokin nasa yace tunda tayi niyya kada kahanata tunda ta samu wannan damar, sannan binta zakai da kyakykyawar addu'a. Abba ya numfasa yace to shikenan, nayarda da tarbiyyarta ,nagode kwarai da gaske. Magana yaje kunnen su haneefah sai murna ake. Umma ko ranta bai so ba, tafison yaran suyi aure amma dai batai shishshigi lamarin ubangiji ba, addu'a tayi maata na samun nasara. **** **** **** **** Zaune yake ya kurawa files din gabanshi ido, ya kasa aiwata komai sai tunanin wannan yarinyar yake. Runtsa idanunsa yayi a hankali ya bude. Kwanan sa biyar kenan yana abu daya wadda ya kasa tantance meye. A hankali ya dauko wayarsa da ke kan table dinsa ya fara dialing no. accounter, ajiyar zuciya yayi jin layin a kunne ana dagawa yace haba accountr tun yaushe nake kiran layinka? Daga daya bangaren aka amsa, am sorry, wlh wayanne ya fadi naje nayo welcome back, toh bai fara aiki ba sai yau kuma ban gane mai magana na. yace ba komai, engineer yusuf ne. Allah sarki ina fata kana lfy? Alhamdulillah amma wata alfarma nake so kamin, accountr yace ina jinka. Kwanaki nazo bank naku, sai na hadu da wata yarinya taje bude account domin naga form a hannunta, abinda nake so shine informations nake so akanta like her phone number & address. Accounter yayi dariya yace toh yanzu inba kaiba, ai customominmu suna dayawa, yusuf yace abinda nake nufi shine zaka turomin hotunan duka customomin ta WhatsApp saina zani wadda nake neman pls yanzu aboki, yace badamuwa ya bukaci date, sallama kan zai masa text. Cikin qanqanin lokaci yaga sako dauke da abinda ya bukata. A hankali har idanunsa suka sauka a kanta. Babu bata lokaci ya qara turawa accountr wadda yake nema. Take ya kuma aiko mishi da abinda yake bukata. Da daddare misalin karfe 9 suna zaune da nana ana hiran yadda tafiyan zai kasance taji wayanta na qara. Ganin babu suna ta katse ya kuma kira ta dauka tare da yin shiru jin mai maganan. Amincin Allah ya tabbata gareki taji ance, cike da mamaki ta amsa wadda ke magana amma bata nuna ba, yace kin gane wadda ke magana? Aa tabashi amsa. Yace wadda kika hadu dashi a bank last wk, tace ok lfy? Kuma aina ka samo lambata? Murmushi yayi kamar tana gabansa yace hakuri zan dada baki da....... tun kafin ya qarasa ta katseshi tace nagode. Kiransane ya qara shigowa tadaga yace pls kada ki katse aiko yana fada ta qara kasewa. Dafe kansa yayi, ya zanyi? Kodai matar aure ce da gaske? Aa yabawa kansa amsa. Jawo wayarsa yayi ya shiga WhatsApp. Farin ciki yayi ganin tanayi, bai dauki lokaci ba yayi mata sallama tare da rokanta kada tayi blocking nashi. Kamar jira take sai gata online taga sako. Murmushi tayi tace bazanyi ba, amma narokeka karabu dani. Yace ba cutar dake zanyi ba, Allah nasane. Toh me kake so aguna? Nace na hakura! Yace in bazaki damu ba inaso muzama frnds. Tace duk abokanen ka maza basu ishekaba saika hada dani? Kuma ai babu tsari yaza'ai ina matsayin mace zakai abota dani? In matarka ta sanifa, nidai baruwana bazanyi abinda nima banaso amin ba. Banida aure kuma yabata amsa, Allah kawo tagari da zuri'a nagari cike da jin dadin addu'a yace ameen. Nan takashe wayan gaba daya don ji take wani irin abu daban tada kasa fassarashi tunda suka soma magana. Washe gari ko kunna wayan batayi ba haka ta fita zuwa asibiti. Ward dinsu aminiyarta ta nufa ta jawota gefe hadiza tace yau kuma wani lbr muka samu mai dadi. Nan haneefah ta labartar mata da komai. Hadiza tace nina sanki nasan halinki tunda muka taso bamu taba abota ko da class mate ba, abinda nake so ki fahimta shine bakisan Allah ya turoshi ya zamto silar wani abu bane. Ki karbeshi da zuciya daya, kada kiyi tunanin mugun nufi sannan ki tuna hadisi na ashirin da takwas An ruwaito daga Abdullahi bn Umar -Allah ya kara yarda a gare su- ya ce: Manzon Allah -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: *Muminin da ke shiga cikin mutane, ya ke kuma hakuri kan cutarwarsu ya fi girman lada akan muminin da baya hulda da mutane, kuma baya hakuri da cutarwarsu*. [11/28, 2:58 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ8 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Haneefah ta numfasa tace maganarki hakane, amma inya wuce gona da iri wlh zanyi maganin shi. Murmushi hadiza tayi tace ji nake ajikina alkhairi ne agareki, ta qara da cewa nextwk usman manyansa zasu zo asa ranar aure. Haneefah dake kokarin kunnan wayarta ta daka tsalle ta rungumeta tare da tsananin farin ciki tace nayata ki murna Allah sanya alkhairi yasa gidan kine har abada tace ameen kema Allah kawo nan bada jimawa ba kafin ta bata amsa wayanta ya soma ringing Ganin lambar jiya yasa ta dauka tare da sallama amsawa yayi ya gaisheta. Murmushi tayi tace ai kaine babba nice da gaisuwa, farin cikine ya lullubeshi jin yasamu karbuwa. Bayan sun gaisa take tambayarsa yadda yasamu lambarta, bai boye mata komai ba ya sanar da ita. Ita kanta tayi tunanin haka. Tace tana asibiti sukai sallama Bayan ta koma gida da dare sukai waya tare da sanin junan su atakaice. Ba laifi ta sake jiki dashi domin ta dauki shawarar kawar tata. Cikin sati biyu suka gama fahimtar junansu baki daya, domin ya tashi daga aboki zuwa yayanta. Sannu a hankali shakuwa ke dada shiga tsakaninsu. Shidai yusuf ya tabbatar son haneefah yake domin irin matar da yake so ne. Yasha alwashin saiya koyawa haneefah soyayyar shi. A sannan haneefah ta gane wanene yusuf, mutum ne mai hankali wadda yasan darajar dan adam, wadda yake da ilmin addini sosai sannan mai aiki dashi. Zuciyartane ya fara saka mata abubuwa da dama kanshi amma tafi fassarashi da shakuwace. ***** ***** ***** ****** Gab suke da zana jarabawar tsallakewa shekarar gamawa. Ansa ranar bikin hadiza wata biyu masu zuwa. Tun a sannan haneefah ta fara shiri domin tana matukar ji da kawar tata. Shirye shiryen tafiya haneefah take yiwa yayar tata. Sunje dangi da abokan arziki sunyi musu sallama, kowa na yiwa nana fatan alkhairi domin yarince mai nutsuwa kowa na alfahari da umma da yaranta, domin kyakykyawar zuciyarta da hakurinta. Zauna suke su biyar ranar alhamis daidai yake da washe garin juma'ar zasu wuce abuja domin can jirginsu nana zai tashi sannan haneefah kadai zata rakata. Nana ta kalli kannenta sosai tace nidai zan tafi kamar yadda na sanku ku dada hada kanku, kunga yadda su inna sukai baqin cikin tafiyana amma Allah ya kaddara saina tafi harda ta kaiga suna yadawa a anguwa abba yaki aurar damu sai boko. Abinda nake so da ku shine ku toshe kunnuwanku akan dukkanin abinda zaije ya dawo. Nasanke haneefah kina da karancin hakuri, kidaina biye musu wata rana sai lbr. Sannan ku maida hankalinku sosai gun karatu domin cimma burin mahaifan mu. Ahmad ka kara hakuri insha Allah zaka samu admission duk da abba yana da hanyar samuwa mutanen duniyar nan sai a hankali, domin shi yana da gaskiya Idan kana so gaskiya ta yi saukin fadi a harshenka, kuma mutane su kiyaye ka, to ka nisanci kwadayi kuma kar ka ji tsoron kowa sai Allah, in lokaci yayi zaka samu. Sannan ke haneefah kema ki dage da karatu kinyi nisa a health babu zancen accounting sannan ki dada hakuri akan hadaki da abba da suke a hankali zai gama sanin komai kudai ku zuba musu ido, babu maida martani. Nasiha sosai yayarsu ta musu sannan ta bukaci shiga suyiwa su inna sallama. Abban su dake bakin koma yazo shiga yayi saurin barin gurin. Bangarenshi ya nufa yayi alwala tare da godewa Allah daya bashi zuri'a masu albarka. Suna shiga suka tarar da zuwaira bakin kofar suka gaisheta suka wuce. Gaida inna sukai sannan suka samu guri suka zauna. Nana ce ta fara magana tace dama nazo in muku sallama ne. Inna ta dubesu a wulakance tace naji gobe zaki tafi, Allah kiyaye hanye, haneefah gudun kada wani magana ta taso taja hannun nana zasu fice taji ance sai kiyi abinda ya kaiki domin kada a zo mana da jikan da zamu nema uba mu rasa cewar zuwaira, inna ta karba tace gaskiya kam sbd muna furci suka mallake shi suka kwashe kudin zasu qasan waje su cinye. Jabir da ya salim daya shigo yace munafukai wlh sai Allah ya saka mana ku da matsiyaciyar uwarku. Saukan mari yaji ras a fuskar sa, cike da mamaki ya bude baki yake kallon ta, suma duk suka taso cike da mamaki ganin wadda yayi mari [11/28, 2:59 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ9 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Haneefah idonta dake cike da hawayen bacin rai ta nuna shi da dan yatsa tace duk zagin da zaka mana zan lamunta amma kada ka kuskura ka sa mahaifiyata ciki, kai har kana da bakin da zaka ce da munata TSIYA? Gaku matsiyata, duk girman da muka baku bakwa gani? Meza mu muku mu burgeku? Muda kake gani ka cire idanu a kanmu domin Allah na tare damu. Gwamma ka fuskanci rayuwa na kwarai kaji dadin duniya da lahira, Idan kana so ka zauna lafiya: Ka bar kallon rayuwar wasu, ka kalli taka kawai ka bar duba mai wane yake da shi, ka kalli abun da kai kake da shi ka wadata da shi, ka bar kokarin sai ka zama abun da wane ya zama, in ba ka tsaya a in da Allah ya ajiye ka ba to ka hadu da wahala ta har mutuwa sannan duk abun da kake nema, ka nema a wajen Allah, ka bar tunanin Mutum zai maka, ko da a ce ya shigo rayuwarka a matsayin sila, wata rana zai iya goranta maka. Kai namijine ka tsaya ka nemawa yaranka ilmi sannan ka datar da rayuwarka da tsoron Allah. Tana kaiwa nan zata juya ta fita ya fizgota zai wanka mata mari yaji an sake marin nasa. Abba suka gani tsaye cikin bacin rai, ya kalli inna da yaranta yace nagode miki ya juya yafice tare da su haneefah. Zaune take zuciyarta na mata kuna, jawo wayanta tayi ta kira yusuf. Sallama yayi ta amsa suka gaisa suka somo hira ko zata dan mance bacin rai, yace meke damunki cike da mamaki tace me kagani? Ji nayi a muryarki. Murmushi tayi tace babu komai. Yace bazan matsa miki ki fada min ba amma ki sani in kakasance cikin bacin rai ko farin ciki dole akwai wadda zaka ware ka fada mishi duniyarnan, nayi zaton tuni na tashi matsayin aboki na koma yayanki, amma bansan ko kina shakkata bane. Haneefah tace ko daya kawai dai banajin dadine, zazzabi ke damunki? Aa yace toh tashi masha ki dauro alwala ki fara karatun Qur'ani har bacci ya daukeki. Cike da murmushi ta amsa ta katse wayan. Yusuf na matukar birgeta musamman in suna hira sayya sako mata batun addini, tana matukar jin dadin hakan. Washe gari misalin karfe goma suka dau hanya kan zasu sauka gidan auwal (yaron mama) domin ya koma can da zama. Nana na ta kuka har suka iso birnin tarayya. Sun sami kyakykyawan tarba. Da misalin karfe 5 na yamma haneefah tace da matar auwal tana son sudan fito su zaga anguwa. Sanye take da dogiwar riga abaya, tadan shafe bakinta da jan baki, sannan tayi rolling dankwalin abaya da dan takamin ta mai tudu. Tayi matukar kyau sosai. Tafe suke suna hiran manyan gidajen abuja kamar ba Nigeria ba. Cike da mamaki yake kallonta har suka zo suka wuce. Suko basu lurama da ana kallonsu ba. Tafiya suke sai matar auwal taga kanin kawarta yayi parking ya fito suna gaisawa. Ya dubi haneefah dake kallon wani gida yace kannen kine? Tace aa cousins nashi ne. Yace Allah sarki aunty banyi hanzari ba zaki aramin wannan minti biyu ya nuna haneefah tayi dariya tace bismillah. Suka danyi nesa dasu. Kafin ya soma magana tace haba mallam ya zaka ce abaka aroma sai kace kaya tana magana tana hade girar sama da kasa. Dariya sosai ta basa yana dariya. Yusuf dake cikin mota yaji wani irin abu ya tokare masa wuya. Me tace dashi har yake mata irin wannan dariya? Cike da bacin rai ya bude motan ya fito ya nufufi gunsu. [11/28, 3:01 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH*πŸ‘©πŸΌ10 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Kawar da kanda zatayi tagan shi ya nufosu. Yayi matukar kyau cikin kananan kaya. Kallon shi take harya iso cike da murmushi zatayi magana yace waye wannan? Kanin auntynane. Shine kika tsaya akan layi da mutum. Shigo ganin anzo an tsare ta da tambaya yace mallam lafiya? Yusuf ya juyo cike da bacin rai yace kada ka sake furta mata wata kalma, ya juyo kanta biyoni. Itako cike da mamakin abinda yayi take bin bayansa har suka iso inda motarsa take. Yadan jingine tare da dubata yace yaushe kika shigo shine ko waya bazaki mun ba? Dariya tayi tace yau nazo kuma gobe zan koma, na rako nana ne zata fita karatu, shine bazaki fadamin ba sai dai inji kinzo kin tafi. Tadanyi murmushi ta juya zata koma gun yan uwanta taga suna nufota. Duk da ya girmesu yadan risina ya gaishesu suka amsa. Yace in bazaku damu ba zan kaiku inda kuke muradi? Aunty tace aa gida zamu koma babu nisa. Duk da haka saida yace zai kaisu. Yayi parking suka sauka yace aunty anjima zan iya zuwa. Tace Allah kaimu. Haneefah zata fita yace minti daya, ta juyo suka hada ido taji wani irin shock take ta sunkuyar da kanta. Yace na katse miki hira da saurayinki shine kike fishi? Allah baki hakuri. Ta juyo tace ba komai ta fice ta barshi. Karfe takwas ya same shi a gidan yayi sallama ya shiga. Zaune ya tadda auwal a parlour, suka gaisa. Ya mishi bayanin gurin haneefah yazo. Ya shiga yakirata. Sanye take da himar har kasa ta zauna mesa dashi ta gaishe shi kanta a sunkuye domin tsoron hada ido take dashi yadda nan take takejin wani iri. Nazarinta yayi sosai sannan yace haneefah in tambayeki? Ina mai sauraronka. Shin kin yadda dani? Kai tsaye tace eh. Mesa ya qara jefo mata tambaya? Sbd ka kasance mutum nagari. Shiru yayi yakasa ce komai. Inaso in sanar dake ko ni wanene. Tace ina sauraron ka; Kamar yadda na sanar dake sunana yusuf. Haifaffen garin kano ne ni, anan nayi dukkanin karatuna nakaranta computer engineering. Bayan na kammala nayi masters dina sannan nasamu aiki a garin kano. Daga baya ne akamin transfer zuwa nan. Mahaifina Alhaji ismail da da mahaifiyata Hajiya hauwa wadda muke kira momy. Mahaifina dan kasuwa ne babban sannan mahaifiyata lecturer ce a university. Hausa fulani ni ne, mahaifina mutumin kano, mahaifiyata daga adamawa suke. Nine first born gidanmu, sai kanne na salma, aisha da autanmu alkali. Salma tana da aure da yaronta daya sannan ma'aikaciyace a PHC agency dake kano. Ita ko aisha na university 200lvl autanmu kuma yana jss3. Cike muke da kaunar junanmu, iyayenmu sun wadatamu da kyakykyawar tarbiyya. Amma nafison aisha cikinsu. Ya mika mishi wayarsa dauke da family picture. Haneefah takurawa hoton ido, suna da matukar kyau. Dukkaninsu fararene sannan kyakykawan jikansu na kwance jikin kakanshi. Idonta ya fada kan aisha taji tana sonta. Batasan sanda ta soma addu'an Allah ya bata ikon shiga cikin suba. Tace masha Allah, Allah dada kawunanku, ya albarkaci zuri'arku. Cike dajin dadi yace ameen. Ya saci kallonta yace sannan abu daya. Mahaifiyata naji da kanwarta umma nusaiba. Ita umma nusaiba yarta daya ne. Wadda mahaifiyata ke shirin hadani da ita aure. A sannan haneefah ta dago ido suka hada ido, taji wani irin faduwar gaba da bazata iya fassarashi da menene ba. Ganin yana kallonta ta sakar mishi murmushi ta hadiye hawayen da ke shirin zubomata tace Allah sanya alkhairi yaba ku zaman lfy. A sanyaye yace ameen. Amma haneefah bana son aure, kusan shekara biyar amma sai dauko min da maganar ake. Cike da mamaki take kallon sa tare da cewa zabin mahaifiyar taka? Nayi nayi in saba da sonta amma nakasa, nayi musu bayani amma sun kasa ganeni aisha ce kadai ke tausayamin, amma tace dani zan auri zabina amma itama in auri zabinta. Kabsha!!! Da yana ganin zuciyar haneefah ko zancen bai dauko mata ba. Hamman karya ta kirkiro tare da mitstsike ido alamar bacci. Tace in zaka dauki shawarata ka aureta saboda babu wadda takai mahaifiya. Ce mata zayyi ina sonki amma ya gagareshi. Sallama sukai akan gobe zaizo su koma kano tare. Tadai amince amma tayi hakanne domin ya tafi. Ban daki ta wuce ta ta zauna bakin bafon wanka, hawaye taji yana tsiyaya a kumatun ta. Ji take kamar ta kurma ihu. Toshe bakinta tayi ta soma kuka mai tsuma zuciya. Shin kishi take? Hakan na nufin tanason yusuf? Innalillahi tashiga furtawa a zuciyrta. Abinda nake gudu kenan yanzu ya zanyi? Addu'a ta bawa kanta amsa. Take ta dauro alwala ta fito domin kai kukanta ga mahaliccinta tun kafin abin yayi tsanani. Bayan ta idar da raka'o inta ta zauna yin addu'a. Bayan ya koma gida ya kasa zaune ya kasa tsaye. Meyasa baya iya furta mata yana son ta? Yanzu in wani ya rigaka fa? Iya saninta da yayi basu tana hiran wani ba. Dauko wayansa yayi yashiga kiranta. Zaune take tana addu'a taji kiran wayarsa busy ta danna masa. A naga bangaren kuma kodai tana wani abinne? Jiran kiranta yake amma ya ji shiru. Itako ta kasa rintsawa sai faman tunani take tare tsare kanta da tambayoyi yaushe ta fara sonsa?? Mesa take bata lokacinta? Kusan idanunsu biyu. Ta gama yanke shawarar rabuwa dashi tunda ba sonta yake ba. Shima ya dauki alkawarin zuwa gobe zai sanar da ita zabinsa. [11/28, 2:59 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ11 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Washe gari misalin karfe takwas da rabi yasamesu a airport sbd karfe tara dai dai zirginsu nana zai tashi. Nana kuka take na barin gida, ita ko haneefah kukan rabuwa da yar uwarta take da soyayyar da yayi mata ba zata. Sanda akai kiransu kamar sun rabu kenan take kuka. Suna ji suna gani suka rabu. Tunda tazo gida takasacin komai inbanda shayi. Auwal yayi fadan harya gaji. Zaune take duk tabi ta dami kanta tsakanin jiya da yau. Ta kammala shirinta ta tuno da maganar yusuf inda yake cewa; Duk lokacin da kake so ka zama cikin mutanen da suka rabauta, to ka kiyaye abubuwa kamar haka: *_Kar ka takurawa kanka akan wani abu da bai iso gare ka ba_* *_Kar ka damu da me zai faru gobe?, domin idan ka inganta yau dinka, to gobenka ma za ta yi kyau_* *_Ka tsarkake zuciyarka daga hassada, mugunta da kyeta_*. Goge kwallar da suka zubo mata tayi. Mesa zan dami kaina? Nan take ta fara addu'a Allah bata ikon fin karfin zuciyarta. Tagama shirinta tsaf ta fito. Ta ganshi zaune a parlour shida auwal. Bude baki zatayi magana auwal yace gata ta fito, yanzu nake shirin shiga in kiraki, kin gama zaku wuce ko? Rasa abin fada tayi. Shiko ganin idonta a kumbure alamun tayi kuka sosai sai hankalinsa yadan tashi. Cikin sauri ya tashi ya mikawa auwal hannu yace kada mu makara zamu wuce. Sukai sallama. Tuki yake amma hankalinsa baki daya na kanta. Ita ko tunda ta shiga ko kallon inda yake batayi ba. Ina kwana yace da ita tace lfy atakaice. Tabbas akwai wani abu domin tunda yake da ita bata taba amsar gaisuwan shiba sai dai ta kara gaishe shi. A sanyaye yace jiya nakira amma baki samu daga waba. Tace eh wani abin nake. Tambayanki nakeson yi. Kina da ra'ayin auren mai mata? Lumshe ido tayi sannan tadan kishin gidu tace meye aibunsa in har yana tattare da abubuwan da annabi ya kwadaitar mu auren irinsu? Wasu matan suna wahalar da kawunansu wajen zaban miji, suna ganin aure shine jin dadin rayuwa. Duk macen da fassara aure haka ko shakka babu cikin wahala zata kasance... mika al'amura ga Allah yafi komai. Murmushin jin dadi yayi yace zaki aure ni? Dariya tambayar ta bata tace auren irinku sai mata masu ilmi da class kyawawa irinku ta karashe maganan da zolaya. Yace bakisan irinku kunfi tsada ba? Ga namiji wadda yasan me yakeyi baya bukatar komai gun mace sai kyawun tarbiyyarta. Murmushi tayi ta rufe idanunta sannan tace aikai ka samu. Mu kabari a baya. Dadin hira take ji dashi, haka shima. Cikin yar tafiyannan sun dada fahimtar juna, kusan ra'ayinsu daya. Sun shigo garin kano tace ya sauketa ta karasa gida yace kiyi hkr in kaiki. Ba yadda ta iya haka ta hakura tafada mishi anguwan nasu. Dab zasu shigo layinsu tace saukeni anan. Ya dubeta inane gidan? Tace nidai bazan qarasa dakai kofar gida ba. Parking ya gyara sannan ya dubeta yace haneefah kalleni. Dagowanta suka hada ido yace ina sonki haneefah, so na hakika. Batace komai ba sai hawayen da ta soma zubarta. Motan ta bude ta fito ta dauki kayanta sannan tayi wucewarta. Kwala mata kira yayi amma kamar bada ita yake ba. Jan motarsa yayi yadau hanyar gidansu. [11/28, 3:00 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ12 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– A hankali ya bude motar ya fito. Ganin motar abban nasa yasa ya nufi bangaren shi. Zaune suke suna tattaunawa ganin dansu yasa suka dakata tare dayin murmushi. Sallama yayi suka amsa. Cike da nutsuwa yake gaida iyayen nasa. Abban nasa yace ko sanarwa babu. Murmushi yayi ya sunkuyiyar da kansa sbd. Momy tace tashi kaje ka huta zansa aisha ta kawo maka abinci, yace toh ya mike ya fice. Sallama tayi ta tura kofar, kwance ta taddashi sanye da jallabiya. A hankali ya bude idanunsa yace sannu aisha. A ajiye tiren hannun nata ta fara zuba masa abinci ta soma gaidashi, cike da kulawa yake amsawa. Ta mika masa ya fara ci suna hira irinta wa da qanwa. Bayan ya kammala ta kalleshi sosai ta fara magana, yaya yanzu bazakai wani abu game da auren ka da Rahma ba? Wlh bata dace da kaiba. Yarinya an sangartata bata da nutsuwa ba tarbiyyar kirki ba? Murmushin takaici yayi yana kallon kanwarsa dake matukar tausaya masa yaace toh ya zanyi? Babban sirrin zaman rayuwa da jin dadin gobe kiyama ya tabbata ga mutumin da shine wadda yake yiwa mahaifiyarsa biyayya, nabi ko wace irin hanya domin in kawar da zancen auren amma maganar har yanzu tananan. Allah na mikawa lamurana ya dubamin yabani ikon rabuwa da ita lfy. Na danne zuciyata zan auri zabinta tunda itama zata barni in auri zabina. Cike da tausayawa aisha tace Allah tabbatar da abinda yafi alkhairi agaremu yace ameen. Bayan fitar ta ya kawo waya domin kiran haneefah domin muryarta kadai yake sonji amma yaji wayar a kashe take. Tafe take tana sharar hawaye. A hanya suka hadu da ahmad tayi saurin goge hawaye yace kukanne har yanzu baki daina ba? Girma yazo miki gomma kin hakura. Murmushi tayi domin ita kadai tasan abinda ke damunta. Tarar da umma da kannenta tayi suna kallo, suka mata sannu da zuwa. Tadan taba hira sannan ta wuce dakinsu. Kwance take tana tunanin kalmar yusuf. Ya cancanci a soshi amma yaushe ne auren sa da zabin mahaifiyarsa? Mafita dayane matakin da na dauka yayi. Hira suke amma hankalinta nakan yusuf. Shi take gani tunaninsa ya hanata sakat. Mikewa tayi ta musu saida safe ta nufi dakinsu. Tagama shirinta tsaf ta hau kan gado a sannan taji kewar yayarta sosai tace Allah sarki nana da kinanan hiran kafin mu kwantama daban. A hankali ta bude wayarta. Babu wani tunani takirashi. A hankali yake magana cike da ladabi momy baqin maganarki nake ba. Kimin uzuri ayyukane suka shigemin gaba. Tace yusuf hakurin mu yakare shekaru biyar ba wasa bane, yarinya kowa ya fito tace kai take jira to wannan karan ya zamo maka dole ka aureta ko in hanaka auren zabin taka tunda yan matanne ke naka wasa da hankali. Cikin sauri ya dago kai yace aa momy baza ai haka ba, na miki alkawari zuwana nagaba sai afara shirin bikin. Badan taso ba tace Allah kaimu. Yana shiga dakinsa yaji wayansa na ringing, daga wanda zayyi yaga sunanta cikin sauri ya daga tare da yin sallama. Amsa sallamar tayi daganan bata karace komai ba, katse wayar yayi ya sake kiranta. Tace ya gajiya, Alhamdulillah ya amsa. Shiru kamar dakiku biyar tafara magana yusuf nagode da kasancewar cikin rayuwata sannan nagode kwarai da gudunmawarka kan cigaban addinina amma kasani bazan iyaci gaba da zama dakai ba... shakuwar inta yawaita zan kasance cikin tsananin damuwa, kai kuma aure zakayi kaga ko gonda na hakura kaje ka auri zabin mahaifiyarka. Ajiyar ziciya yayi yace haneefah pls kece zabina, kada kisa wannan ya zamo hujjar rabuwarmu, ina sonki so na hakika, ina kwadaitar wa zuri'ata samunki a matsayin uwa, sannan suruka wajen iyayena. Nasanki na yarda da tarbiyyarki. Jin yayi shiru tace hakane amma ina gudun bacin raine, iyayena da yan uwana suna sona nima ina sonsu, bakin cikinsu nawane musamman mahaifiyata, ina tsoron kada wani abu yaje ya dawo. Murmushi yayi yace haba haneefah? Duk wanda ya ji tsoro zai samu damuwa a zuciyarsa, amma ban da wanda ya ji tsoron Allah. Shi kam wanda ya ji tsoron Allah zai samu aminci da kwanciyar hankali a zuciyarsa... addu'a makamin mumini ce ... Don haka muyi riqo da addu'a kuma mu dogara da Allah ko yaushe komai zaizo mana da sauki, nidai pls amincewar ki nake bukata. Gaba ki daya ya gama daureta. Itadai tana son shi amma kamar tana hango akwai matsala.... sannan yayi gaskiya duk zuciyar da tayi riko da Allah to tabbas babu wani sauran damuwa da zai dameshi. Jin tayi shiru yace momy ta bani daman auran wadda nake so, ko bakya tunanin zanyi adalci tsakanin? Murmushi tayi tace kai mutum ne da zaka zaunar da wasu ka musu nasiha kan suyi adalci tsakaninsu, ina da tabbacin kai adaline. Murmushin jin dadi yayi yace godiya nake. Taci gaba da cewa zan kasance tare dakai, sannan na baka amanar rayuwata baki daya, yadda ka tarbiyyantar da ni matsayin masoyiyarka haka zan kasance. Cike dajin dadi yace kin amince kina so na kuma zaki aure ni?? Tace eh na amince Allah tabbatar mana abinda yafi alkhairi kuma in hakan ta faru pls I banason zama gida daya tare da ita in zayyu. Cike dajin dadi yace ameen, nayi alkawarin rikeki amana sannan zanyi haka da yardan Allah. Nan suka soma hira tamkar sun jima suna tare. ***** ****** ****** ****** Cike da takaici tayi wulli da wayar dai-dai inda mum tata tashigo. Cike da damuwa ta qaraso ganin yartata kamar wani abu na damunta. Baby rahma waya tabamin ki cikin kuka tace mum tun dazu nake nemanshi amma number busy ko da wa yake waya, wlh mum kiyi wani abu hakurina ya kare kibarni kawai in auri wani. Haba rahma saida aski yazo gaban goshi? Mum baya so na, masu kudi da dama sun nuna suna so na do ki bari ince wani ya fito ni wlh nadai na sonshi, cikin cigar lallashi tacewa yar tata aurenma ai kowanne ba iri daya bane, dan uwan naki na da kudi kuma harkanshi bunqasa yake.. zaki fi jin dadi zamanki acan, in kukai aure kika haifo na miji saiki fito ki auri wadda kike so in kinyi hakan kin gama min komai. Cike da kauna ta riko hannun mahaifiyar tata tace mum na miki alkawari aikata abinda zai saki farin ciki, amma ki gaggauta aikata hakan. Mum tace to shikenan in watannan ya kare da kaina zanje kano sai ansa ranar aurenku zan dawo. [11/28, 3:00 PM] ‪+234 806 778 9477‬: *Dr HANEEFAH* πŸ‘©πŸΌ13 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)πŸ’– Zaune suke ita da hadiza cikin makaranta kasancewar zasu fara zana zarabawar sati mai zuwa, sunzo duba time table. Hadiza tayi murna jin maganar kawartata sosai tayi mata fatan alkhairi. Suna cikin magana taji wayarta na ringing, cike da murmushi ta daga tare da yin sallama, shima murmushi ya saki suka gaisa yace ina cikin asibiti. Haneefah tace mun koma makaranta yace ok ina zuwa. Kawarsu suka hango ta inda suke zaune mai suna sadiya. Tayi sallama ta zauna ta ciro powder ta fara. Haneefah data kasa hakuri tace sadiya ina zaki haka da safe kina kwalliya? Wlh wani saurayinane zaizo shine nake dan shafe shafe domin nayi haske a idonsa, kinsan mazan yanzu in baka kwalliya ko na soyayya bazaka samu ba bale na aure. Sama har kasa haneefah ta ke kallonta hadiza dake mintsininta alamar tayi shiru haneefah tace wlh saina fada, sadiya mesa matan yanzu kuke wahalar da kanku? Dubeki kina da kyau kina da haske amma saida kika kara da bleaching, kinsan hakan zai taba lafiyarki ko? Wato baza'ai so Dan dan Allah ba. Na kasa gane meke yawo a kawunan mu, kowa ya damu daya kasance yana da saurayi ko aure wannan abinfa nufi ne na Allah, misali matan yanzu sun damu da sai sunyi aure dan sunga kawayensu duk sunyi, sun manta cewa kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwar, tun kafin muzo duniya Allah yarubuta mana duk abinda zamuyi kuma da lokacinsa. Muyi la'akari da auran yanzu kowa zaman hakuri yake, babu wadda yake zaman kwanciyar hankali 100% sai kinyi shi domin Allah zakiji dadin hakan.... lokaci bai kure mana ba mu dage da addu'a Allah kawosu lokaci mafi alkhairi kuma wadda zamu kasance domin Allah. Hadiza ta nunfasa tace tabbas maganarki gaskiyane, gaggawa aikin shaidan musamman a lamari irinta aure. Matan yanzu sun fison a musu karya, wani namijin dan yana sonki zakiga ya fada wannan harka. Abin takaici akwai matanda basa biye kodayinsu, wani namijin zaita kashe miki kudi da zarar ya aureki shikenan, wani bazai kashe ba sai kinshi go gidanshi, shiyasa ake cewa mu dage da addu'a sannan mubarwa Allah sabinmu. Allah bamu mazaje nagari dukkaninsu suka amsa da ameen. A sanyaye sadiya ta tashi tabar gurin, suka ci gaba da tattaunawa kan matsaloli irin ta rayuwa. Suna zaune taji wayarta na ringing tana dagawa ta masa kwatancen inda zai sameta. Sanye yake da fararen kaya fari tas, komansa fari da glass da ya matukar karbeshi. Sai daya kusa hadiza ta lura da irin kallon da haneefah take mishi hadiza tace malama aja aji irin wannan kallon, harara ta daka mata. Ya karaso tare da sallama suka amsa, hadiza ta basa guri ya zauna tace Alhamdulillah kawata ta sanar min komai, naji dadi kwarai, sannan ina tayaka farin cikin samun haneefah, badan ita kawata ba, haneefah ta kasance diya tagari wadda kowani irin namiji zayyi alfahari kasancewa da ita matsayin mata. Allah ya tabbatar mana abinda yafi alkhairi. Dukkansu suka amsa da ameen banda haneefah data amsa azuciya domin tun isowarshi kanta sunkuye, kunyarshi sosai takeji. Hadiza ta musu sallama ta tafi. Kallon ta yake yanajin wani irin jin dadin. Yafara magana a hankali bazaki dago ki kalleni ba? Shiru tayi. Murmushi yayi yace nagode wa Allah daya nunamin wannan rana gani gake a matsayin masoya. Allah bamu ikon cimma burin mu. A hankali tace ameen. Yace yaushe zaki gama makaranta? Shekara mai zuwa insha Allah warhaka mun gama, yace Allah nuna mana ameen ta amsa. Ya qara jefo mata tambaya kina da ra'ayin muyi aurene ko sai kin kammala? Bani da raayi nafiso inna kammala sai ayi bikin amma anan zamu zauna ko? Yace aikin nawa fa cike da zolaya tace saika ajeni anan, inda nake aiki zamu zauna nima zanso ki kammala amma kafin inaso inje gida su abba susan da ni. Tace ba komai yaushe zaka je? Ko yanzuma a shirye nake domin nayi sallama da mutanen gida inna tashi zan wuce. Tace yanzu dai babu kowa gida sai dai in kazo wani lokacin. Toh shikenan duk yadda kikace. Suka dan taba hira sannan ta damesa da ya tashi ya tafi kada ya makara. Taku suke a tare har suka iso inda yayi parking. Tace next month insha Allah auren hadiza zaka zo? Yace mezai hana in aka gayyo to ni, Allah kaimu. Yace inga wayar da kike amfani ta nuna masa gionie p4 yace shikenan. Allah baku sa'a a exams naku, nasan kina maida hankali sosai a karatu, ni mutum ne mai son karatu sosai dan haka ki dage kinji ? Ta amsa tare da murmushi. Sallama sukai kamar kada ya rabu da ita. Nana takirata take sanar da ita sun iso lfy har sun gaisa da umma da abba. Cike da farin ciki haneefah ta sanar da ita batun yusuf, fatan alkhairi tayi mata sukai sallama. Bayan sun kammala abinda zasuyi haneefah ta wuce gidan auntin ta muhibbat. Taci sa'ar samun humaira, anan take sanar dasu batun yusuf sannan take sonjin ra'ayinsu game da lamarin. Humaira tace yanzu wazai fara aura? Ke ko ita? Kuma har kinsawa ranki zama da kishiya, dukkanin mu bamu da kishiyoyi haka muke fatan kuma ku soma shiga as first wife, sbd ko yaushe mune kan gaba, don me kike gaggawa? Haneefah tayi murmushi tace tabbas naji mata da dama suna fadin haka, amma nawa ganin ba dukkanin mata suke rike matsayin first wife, sbd duk sanin da kikai masa danya qaro aure in kika daina, wadda yazo tazo ta fiki kwazo ta karbeshi kenan. Mata mudaina gadara da hakan... lokacine da zamu ninka kyautatawarmu ga mazajenmu. Kinga wlh banajin tsoron tazo ta sameni ko in sameta abin bukata shine ki tsaftace zuciyarki sannan ki dage da dukkan abinda zai dauke masa hankali.... muhibbat ta buge kafadunta tace shisa muke ji dake haneefah, Allah tabbatar muku da alkhari dukka suka amsa da ameen. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *