adsense here
SADIQ novels / DR SADIQ part 1
DR SADIQ part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:15
Tin daga nesa Khairat take jiyo sautin waka daga
babban hotel din da ake hada Dinner. Ganin gari
yayi tsit ko ina babu motsi, babu motoci ko daya
haka yasa ta tako motar tata yadda taga dama.
Jan motar take ranta sai faman tafasa take, bakin
ciki kamar zai kasheta, zuciyarta sai faman saka
mata abubuwa daban daban takeyi. Tana isa
bakin gate din Hotel din ta saki wata uwar horn
dake nuna alamar a matse take taganta a ciki.
Cikin sauri mai gadin ya nufo bakin gate din cikin
fada yake cewa. " Dan Allah maintain mana tashi
zakayi?? Bata sauraresa ba ta sake danna masa
wani Horn din, dan bata jin me yake fada,
kasancewar glass dinta duk a rufe yake. Cikin
sauri ya bude mata yana ta famar fadansa amma
bata san yana yi ba. Gyefe daya tayi parking din
motar, cikin sauri ta fito sanye da riga da wando
duk ya matseta, kanta babu dan kwali ta kama
gashinta da ribom. Kai tsaye ta nufa shiga cikin
hall din. Tana kokarin shiga nan security ya
tsayar da ita. " Sannu da zuwa. Gate pass naki
fa??? Ta kallesa sama da kasa dan bai isheta
kallo ba, taja wata tsuka bata ce masa komai ba
ta cusa kai tana kokarin shiga. " Madam ji mana.
Ya zaki shiga hall baki da gate pass, kuma shigar
ki batayi kama da wacca zata shiga nan ba. Ya
fada yayin da yasha gabanta. Cikin tsawa tace
masa. " Amma tabbas na fuskaceka baka da
muruwa. Kai har ka isa kana security dan wahala
ka tare ni kace bazan shiga hall din nan ba.
Tabdijam! Yace: " A'ah Madam ba haka bane,
gani nayi sai da gate pass ake shiga, ance wanda
bashi dashi karna barsa ya shiga ko waye, kuma
sojojine suka ce na tsaya dan sune ke gadin
wurin, yanzu suka je cin abinci. " Lallai yau naga
ta kaina. Wai ace Dinner na DR SADIQ mutumin
dana gama bada kaina akansa a hanani shiga. To
wallahi duk hananin shiga da akayi bashi zaisa na
fasa rashin mutuncin da zan masa ba daga shi
har wacca zai aura din. Ta fada a zuciyarta. "
Okay naji zan koma, dan bani dashi. Tayi tsuka ta
hararesa tare ta juyawa ta koma bakin motarta.
Wayarta dake cikin mota ta bude ta ciro ta fara
danna lambar Dr din. Yana zaune kan High table
daga shi sai matarsa, babu abinda kake ji a hall
din sai sautin kida. Gaba daya jama'ar dake
wurin kowa ya shagala yana cin abinci kafin aci
gaba da sauran sha'ani. Wurin ya tsaru iya
tsaruwa, ko wani table mutane biyu ne mace da
namiji. Ba abinda kake gani a hall din sai hasken
flash light na camera da wayoyi masu tsari ana
daukan Amarya da Ango dan tsabar haduwar da
sukayi. Kamar daga sama Dr sadiq yaji wayarsa
na ringing. Cikin sauri ya zura hannu cikin rigarsa
ya zaro wayar, cikin mamakinsa yaga DEAREST.
Cikin sauri ya rufe da hannunsa dan kar Nana ta
gani, ita ko tini ta gane yana rufe wani abune dan
haka tace: " Ko baka da gaskiya?? Yayi
murmushin dole. " No. Karki damu. Me kika
gani?? " Ai ka boye dan kar na gani. " Okay.. Ba
kowa bane, wani ne da ban fada masa bikina ba
shine zai min korafi akai. Ya fada cikin alama na
maras gaskiya. Tayi murmushi. " To ka dauka
man. " . Ai ya katse sai ya sake kira. Ya fada
tara da mayar da wayar cikin aljihunsa. Baiko cire
hannunsa ba nan yaji sake shigowar kiran akaro
ta biyu, cikin sauri ya mike daga inda yake. " Two
minute, zan dawo. Ya fada yayin da yake kokarin
barin wurin. Ta kofar baya ya fita inda babu
hayaniya sannan ya amsa wayar. " Honey ya
akayi?? " Ban sani ba. Mayaudarin banza
mayaudarin hofi. Cikin sauri yaji gaban sa ya
fadi. " Me nayi dearest?? Cikin tsawa tace: " Kafi
kowa sanin me kayi munafukin banza kawai, ka
cuce rayuwarka ba tawa ba, kuma wallahi bazan
barka ba, saina hana auran nan, kamar yadda na
hana na farko. Wata fadiwar gaba yaji sannan
yayi saurin cewa. " waya fada miki zanyi aure
Khairat?? " Kar ka yaudari kanka mana, yanzu
haka ina cikin hotel din da kuke dinner a ciki, dan
bani da gate pass ne da wallahi saina shiga na
wulakanta maka mata. Cikin rudewa da tsoro
yace: " okay... yanzu ki fadamin kina ina zanzo
na ganki. " Kazo daki mai lamba 406, ka same ni
yanzu, idan kuma kaki wallahi saina kashe wacca,
zaka aura. Ta fada tara da kashe wayar.vels / DR SADIQ part 2
DR SADIQ part 2
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:17
Cikin sauri Dr ya mayar da wayarsa cikin aljihu
kai tsaye ya nufa Reception Room. Anan aka
masa kwatancan dakin ya nufa cikin sauri dan
yasan halin abarsa. Yana isa layin ya dinga bin
lambar dakunan daya bayan daya har ya isa
dakin mai 406. Cikin sauri yasa hannu ya
kwankwasa, daga ciki ya jiyo muryarta. " Ka
shigo. Lokaci daya yasa hannu ya murda kofar ta
bude, tara da mika mata sallama. " Wa'alaikas
salaam Angon gobe. Ta fada cikin keta. Ya kalleta
inda take zaune a bakin gado, cikin sauri ya
karasa ya zauna kusa da ita. " My. Waya fada
miki zanyi aure?? Hararan data watso masa yasa
ya shiga taitayinsa. " Karya za'a maka ba auran
zakayi ba makaryacin banza. Ko kana tunanin
zaka iya tafiya kabarni, bayan na gama
sacrificing kaina akan ka??? Ya saukar da wata
ajiyar zuciya tara da kara matsawa kusa da ita. "
Honey u need 2 came down. Auran nan bawai
zanyi bane na tafi na barki, kema kinsan ina sonki
bazan taba son wata mace ba bayanki, tinda
akan ki na fara soyayya kuma akanki na fara
sanin mace. Pls karki min abinda kika min akan
fatima, a auran da kika ruguza shi na farko. Ta
kallesa magana yake cikin lallashi da kamamman
fuska. " Lokacin da muka hadu bamuyi alkawarin
zamu aura juna ba, sannan bamuyi alkawarin
daya zai bar daya ba, ko da sunan aure.
Duniyarmu muke ci iya iyawarmu. Sai yanzu kace
zakayi aure mu zama mu biyu, daya na gidanka
ni kuma ina yawo a titi. To wallahi baka isa ba
sai dai ka aureni ko kuma a fasa auran. Wata
fadiwar gaba yaji, cikin sauri yace: " Haba Honey
kema kin san bazai yiwu ba. Iyayena su suka
zabamin Nana, kema kinsan da wiya auran nan
ya fasu dan duk abin da zaki shirya sai sun daura
min ita. " Ok.. mu zuba ni da iyayan naka, idan
basu fasa aura maka Nana ba, nima bazan fasa
kudirina ba akanta. Dan wallahi! Wallahi!!
Wallahi!!! Sai na kasheta. Sai dai daga baya nima
kasa a kasheni. Ta mike cikin sauri zata fita daga
dakin. Cikin sauri Dr ya mike yasha gabanta. "
Khairat nasan halinki zaki iya, amma me yasa
bazaki rage kishinki akaina ba, wallahi kina cutar
dani da yawa, me yarinyar nan ta miki 4
goodness sake.?? Tayi dariyar mugunta. " Idan
baka son ta mutu sai ka fadawa iyayanka su
fasa, idan kuwa suka ki ji, can ta matse maka.
Gaba daya hankalin Dr ya tashe, ya rasa me zaiyi
dan ya shawo kan mutuniyar tasa. Rage tsayinsa
yayi gwiwarsa suka sauka kasa. " Khairat
actually I really luv u kin sani, but pls why do u
plan 2 hurt me??? " Ko kadan kada kayi tunanin
haka, kawai tsabar kishinka ne da nake ji. Tasa
hannu ta jawo masa babbar rigar dake jikinsa
takai hancinta dan shakar kamshin turaran dake
tasowa. " Harda canza turare dan zaka zama
ango, ni kuma za'a yadani a kwandon shara ko.
Uhmm. Duniya kenan. " Ki taimaki rayuwata ki
bari nayi auran nan, idan ma kina so na daina
kulata zan daina, wallahi zan iya ma sakinta
saboda ke. Bana sone iyayena suji kunya bayan
jama'a sun taru kowa yazo biki. Dan Allah ki
rufamin asiri. Ya fada har yanzu yana duke a
gabanta. Ta hararesa. " Wallahi bazan hakura ba,
a fasa na Nana kamar yadda aka fasa na fatima.
Idan kuwa kaki to wallahi ita Nana kasheta zanyi,
dan ba'a haifi macen da zata so abin da nake so
ba. Cikin sauri ta juya ta fita daga dakin, shiko
nan ta barsa tsugunne idanuwan sa duk sun kada
kamar zaiyi kuka. Sai daya dauki mintina a zaune,
sannan yaji wayarsa ta fara ringing. Cikin sauri
ya ciro daga aljihunsa. Hassan ne babban
abokinsa. " Wai kana ina ne ka fita kabar
Amaryarka gata nan hankalinta ya tashi, an neme
ka ba'a ganka ba. Hassan ya fada bayan ya
dauka wayar. " Sorry gani nan zuwa yanzu. Ya
mike cikin sauri ya mayar da wayar aljihu ya fito.
Yana shiga hall din ya samu kowa yayi tsuru-
tsuru alamun hankali ya tashi. Cikin sauri ya
amsa microphone ya bawa jama'a hakuri, sannan
ya koma wurin Amaryarsa ya zauna, aka ci gaba
da sha'ani. " Ina kaje ne haka, duk kasa na fara
shiga damuwa?? Ta fada cikin shagwaba. Yayi
wata 'yar murmushi sannan yace: " Kiyi hakuri,
nadan zaga ne, cikina ne naji kamar zai baci.
Dariya ta sakar masa, dan maganar da yayi.
Shiko ya bita da kallo yana tunanin sharrin
khairat. " Nana bazan iya jure rashin ki ba, bazan
iya rabuwa dake ba saboda kece irin macen da na
dade ina nema a rayuwana, samunki yafimin
komai, rashin ki babban asara ne a rayuwana.
Dan me zance na fasa auranki, gaskiya bazan iya
ba. Cikin zuciyarsa yake magana. Karar wayarsa
da yaji yasa gabansa fadiwa. A hankali ya lumsa
idanunsa, dan ya san ba kowa bace illah khairat.
" Bari na amsa waya 4 d last time. Ya fada. Nana
ta hada rai sannan tace: " Why not ka amsa anan
din, nifa bana so naga kana yin nisa dani. "
Hayaniya yayi yawa ne Dear. Ya fada yana shirin
fita daga hall din. Yana fita ya amsa. " Ya akayi
kuma??? " Kazo ina bakin mota yanzun nan,
karka batamin lokaci. Ta fada tare da kashe
wayar. " Ya salam! Wai me yasa yarinyarnan take
min haka ne? Ya fada yayin da yake karasawa
wurin parking spaces. Tin daga nesa ya hangi
motar tata, ya karasa inda take sai gani yayi ta
bude masa kofar gaba. Bai mata musu ba ya
zagaya ya shiga. " khairat ki dan bani break
mana, kar wasu su gane abin dake faruwa fa. Ta
taba baki. " Humm.. ai sa'arka daya dan kayi
dabarar amfani da gate pass, da yau ka gane
baka da wayo. Yace: " To ki barni na koma, ki
tafi gida zanzo na sameki idan muka tashi. " Ban
yarda ba. Kana tunanin zan tafi na barka kana
sha'aninka da wata mace bani ba, ashe bani da
kishi kenan. Yanda zan fita daga Hotel din nan
yanzu kaima haka zaka biyo ni. Tayi saurin kulla
kofofin daga ban garanta.SADIQ novels / DR SADIQ part 3
DR SADIQ part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:18
Tana kokarin kunna motar Dr yayi sauri ya fisge
mukullin motar daga hannunta. " Me kike shirin
aikatawa ne wai khairat??? Ta zare masa ido. "
Ka bani mukullin motata kafin na maka rashin
mutunci. Idan kuma kasan ka cika namiji ka fita
daga motarnan ka gani. Cikin sanyin murya Dr
yace: " Honey wani irin so kike min ne da bazaki
barni na saka ba na wala. Wallahi fa ina da zafi
amma ina raga miki badan komai ba dan son da
nake miki. " Idan kana sona da gaske ka aure ni
mana, sai a fasa na Nana. Khairat ta fada. Ya
kalleta sama da kasa. " No. Ni gaskiya ban shirya
auran ki ba, ba yanzu ba, sai na fara auran wata
tukunnan. Wata fadiwar gaba taji. " Kut!!! Lallai
namiji dodone, niko idan anyi duniya dan manzon
Allah S.A.W naga uban macen da zaka aura. Mun
saka kafar wando daya dani dakai. Cikin sauri ta
fisge mukullin motar ta kunna, yana kallonta
amma ya kasa mata komai har taja motar yana
ta faman babatunsa amma bata kulasa ba. Cikin
wata babbar gidan ta dake boye a wata 'yar
unguwa nan ta shiga dasu, tayi parking gyefe
daya harda securities a gidan, sannan ta juyo ta
kallesa. " Kaga wannan katafaran gidan, da
kudinka na gina ta, dan mu biyu nayi badan kowa
ba, ba wanda ya isa ya shigo idan bani dakai ba
saboda soyayyar da nake maka. Securities ma
dana saka dan ya zama dola ne, amma da baza
kagansu ba. Dan haka ina sonka Dr sadiq dan
bazan daina sonka ba har mutuwata. Ta bude
kofa ta fita daga motar cikin sauri. Shima bai
tsaya ba ya fito ya bita a baya. A falo yaga taja
ta tsaya dan haka shima ya tsaya. " Khairat ina
ganin mamakin kaina da kike min duk abinda kika
ga dama. Wallahi babu wata mace da take takani
tamin abun da take so sai ke. Idan ba ke ba
wacece zata dauko ni a mota ta kawoni nan
wurin ina kallonta kamar solobiyon namiji.
Magana yake cikin bacin rai. Nan ta kwashe da
dariya, sannan tace: " Idan ba solobiyon ba waye.
Naga ma gangancin sojojin da suka yarda ka
zama likitan su dan bakayi deserving ba. Duk
wani bacin rai da zakayi dola kamin biyayya dan
nasan kana sona, babu macen data isa ta kamo
kafata ko wacece ita. Wata kallo ya mata mai
tarun kunci. " Sanin kanki ne ina son zabin da
iyayena sukamin, saboda suna sona sosai, kuma
nima ina sonsu. Nana ce macan da zanso anan
duniyar fiya da kowa amma bake ba, kuma insha
Allahu saita zama matata. Cikin sauri khairat ta
dauke sa da mari, lokaci daya ya firgita shima ya
daga hannu zai rama amma ya dake. " Daka
mara ai. Nonsense. Ta juya cikin sauri ta fita
tsakar gidan. Securities dinta ta kira taja masu
kunne akan kada subarsa ya fita daga cikin
gidan, sannan ta dawo ciki. + Shiru-shiru Dr
Sadiq zai dawo amma babu alamar ganin
shigowarsa. Nana ce ta dauki wayarta ta kira
amma yana ta ringing bai dauka ba, haka yasa
hankalinta ya kara tashi a karo na biyu. Lokaci
daya ta mike ta karasa inda abokanan nasa suke
ta samu Hassan. " Hassan Dr fa ya kara fita bai
dawo ba tin dazu, ya kusa 1 awa da fitarsa. Ta
fada kamar zatayi kuka. " Subhanallah. Ya sake
fita kenan. Ya fada tara da daukan wayarsa ya
kira lambar tasa, amma sai yajita a kashe. Ya
sake kiran lambar a karo ta biyo, amma ya sake
jinta a kashe take. " Ya kashe wayar fa, amma
ina ganin kaman ba lafiya ba. Nan da nan Hall ya
kara rikicewa Ango ya bata, ba neman duniyar da
ba'a masa ba amma ina shiru babu shi babu
dalilinsa, ba inda basu shiga ba a Hotel dinnan
amma Dr baya nan, sai dai motarsa kawai aka
gani. Hankalin Nana yayi matukar tashi, kuka
take yi sosai dan a ganinta an sace sa ne. Sojoji
nan da nan suka bazu tako ina cikin daran nan,
babu abinda kake ji illah saukar bindigogi iri iri,
kota ina shiga sukeyi suna searching amma shiru
babu Dr. An sanarwa iyayensa ta waya abinda ke
faruwa, suma hankalinsu ya tashi sosai. Abinda
Allah kenan ya mallaka musu a duniyar nan,
wanda suke ji dashi har yakai ga suka
shagwabasa dola sukaji tamkar cewa akayi ya
mutu. Nana kam numfashinta ma har dauke wa
yake yi saboda kuka, haka yasa duk wanda ya
ganta cikin wannan yanayin saiya tausaya mata.
Tayi kuka kamar ranta zai fita har ya kaiga ta
fara suma tana farfadowa, cikin gaggawa suka
kaita asibiti.IQ novels / DR SADIQ part 4
DR SADIQ part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:21
Yana kwance akan gado yayi ruf da ciki inda ya
kwantar da kirjinsa kan filo. Shiru yayi yana
tunani dan yasan tabbas iyayansa suna cikin
damuwa. Shigowar khairat dakin ne yasa ya daga
ido ya kalleta, suka yi ido hudu da ita yayin da
take rike da wata leda a hannunta, ta karaso inda
yake kwance ta zauna akan gadon. " Sai ka tashi
kayi wanka idan kaga dama, kaya ne na siyo
maka. Ta fada tara da fito masa da kayayyakin
dan ya gani. Ko daga kai baiyi ya kalla inda take
ba, sai gyera kwanciyarsa da yayi, ya shareta
baice mata komai ba. Ta sake magana. " Magana
nake maka kana gyera kwanciya. " To me zance
miki khairat, nagode kike so na fada??? Magana
yake ba tara da ya juyo ya kalleta ba. Tace: "
Bana bukatar godiyan ka, nayi ne dan neman
suna a wurinka, amma badan hali ba. " Har wani
hali ne dani. Na tabbata duk bad attitude nawa
nasan ban kaiki ba, dan haka kisan abin da zaki
dinga fadamin . Wata uwar tsuka taja masa. " Ko
a jikina. Nidai burina dama ka kasance kusa dani
ako da yaushe, kuma gaka nan ina ganinka ina
jindadi. Cikin sauri ya mike ya zauna tara da
juyowa yana fuskantarta da kyau. " Wai me kike
nufi ne khairat, kina nufin zan dawo na zauna
dake kenan har abada? To wasa kike yi, kima
canza tunani. Just kawai ina binki ne dan saboda
son da nake miki, tsakanin jiya da yanzu tunanin
da nake kenan ta yaya zan cire sonki cikin
zuciyata amma na rasa mafiya. But don't worry,
lokaci zaizo. Ta fasa shi da wata bakar dariya,
sannan tace: " Dr na riga na zama wani oart
daga jikin ka, wanda idan bana nan bazaka iya
functioning ba. Na tabbata soyayyar da kake min
ita ta bani kwarin gwiwar taka ka yadda nake so,
dan tin farko kai ka shagwabani da ita. Kaga
kuwa baza ka iya auran ko wace mace ba bayan
Khairat. Khairat taka ce, daga kai bata kula kowa,
kaima haka baka isa ka kula wata ba bayan ita.
Kaga true love kenan. Kureta da ido yayi ya kasa
magana, illah tunanin zucin da yake yi. " Nasan
ina son yarinyar nan matukar so, amma tana min
abinda bana so, nasan Nana bata kama kafarta
ba dan ta fita kyau da komai. To dan me zata
dinga min haka bayan ni ba auranta zanyi ba,
anya kuwa wannan so ce ko kuma hauka??? A
hankali ya saukar da wata ajiyar zuciya, sannan
ya lallabo ya matso kusa da ita ya zauna. "
Honey, kimin rai ki daina treating dina harshly.
Kinsan ina sonki kuma ina son iyaye na, dan me
yasa baza ki barni ba na tafi idan aka daura
auran sai na sake ta, na miki alkawarin ko
hannunta bazan taba ba, amma yanzu kinsa
iyayena cikin damuwa, na tabbata yanzu haka
Area din mu ba lafiya, duk a dalilin ki. Dan Allah
ki barni na tafi. " Idan kaga na barka ka fita daga
cikin gidan nan sai nan da kwanaki biyar, burina
dama a fasa auran ka da Nana, kaga nan da
wannan kwanakin an manta sai na sake ka ka
tafi. Na tabbata zumudi kake dan zaka zama
angon Nana, to nima Amarya ce sai ka sake min
soyayyar anan, amma bada wata ba. Nan da nan
ya kara hada fuska dan dama can mai saurin
fushi ne, amma baya tasiri akan khairat din sa,
dan ko hannu bai taba gwadawa a jikinta ba da
sunan duka. " Me yasa kike nema ki dinga wasa
da intelligent dina ne, dan me zaki dinga min
wasa da tunanina??? Ya fada cikin fushi. Ta
kallesa idonta a cikin nasa. " Tafiya ne nace baza
kayi ba malam. Duk wurin wadanda zaka je na
tabbata baza su kareka da komai ba kamar yadda
zaka zauna anan kusa dani. Dan me zaka batani
bayan kasan zaka butulce min, ko kana so ka
nuna min halinku na maza da ake cewa ba 'yan
goyo da zani bane. To wallahi bazan yafe maka
ba. Ta fara kukan shagwaba. Cikin sauri ya riko
mata hannu dan ya rarrasheta, amma tayi sauri
ta fisge. Cikin kuka ta sake magana. " Me
zakamin bayan ka nunamin baka kaunata a fili,
ka riga ka gama da rayuwata zaka wulakanta ni.
Amma ba komai duniya ce. Ta watsar da kayan
kasa, ta mike cikin sauri tabar dakin. Yana ta
faman kiranta amma bata dawo ba. + A dai-dai
bakin wata kogo mai dan girma khairat tayi
parking din motarta. Jakar dake kusa da ita a
dayan seat din ta rataye shi ta dauko tara da
budewa ta zaro wata 'yar karamar mayafi ta
daura kanta dashi, kasancewa cikin daji zata
shiga. Yau kam wata 'yar 3 quarter ce a jikinta
data matse ta sosai, sai 'yar top data saka shima
dake nuna ilahirin jikinta a waje. A hankali ta
bude motar ta fito tara da daukan jakar hannunta
kawai tabar ta ratayen a ciki, ta rufe motar ta
nufa cikin dajin. Wata 'yar tazara ce kadan inda
bokan nata yake dan babu nisa sosai daga bakin
motarta. Kai tsaye ta shiga cikin bukkansa da
yake ciki, yana ganinta yayi murmushi yayin da ta
samu wuri ta zauna. " Khairat 'yar baba, ba'a
miki a kwana lafiya. Bokan yayi magana. Ta taba
baki. " Hum.. baba kasan meke faruwa kuwa??. "
Sai dai ki kara bayanin ki, amma nasan komai. Ta
girgiza kai alamar taji dadi. " Baba aure suke so
su masa iyayensa, kuma kasan ba wani 'da
namijin da nake so anan duniyar fashe Dr Sadiq.
Baba idan suka masa auran nan bansan wace irin
mace zai auro ba, mayb tana da lakanin karya
asiri zata iya rabani dashi, kuma wallahi zan
shiga wani hali. Bokan ya tintsire da dariya sosai,
sannan ya fuske ya fara magana. " Yanzu me kike
so a masa??. " Baba so nake a cusa masa tsanar
yarinyar da zai aura, ya koma wurin iyayensa
yace baya sonta ya fasa. Sannan ina son a kara
dauremin shi da sarka bakwai ya zama sha hudu,
na dinga taka sa yadda nake so, duk abinda nace
yayi ya daina musayar yawu dani, yaji magana ta
fiye da iyayansa. Infact ma, ya zamo tamkar
bawa na karshe a wurina. Bokan ya kalleta yayi
murmushi. " Zan baki laya guda biyu, daya ki
saka masa a karkashin gadonsa, daya kuma ki
saka masa a kasan kwanon da zaici abinci kafin
yaje gidansu kan maganar auran. Layan da zaki
saka masa a kasan gadonsa ki tabbata cewa
awannan gadon ya kusanceki ba wani wuri ba,
sannan zaki iya amfani da duk abinda ya fito
daga jikinsa a wannan lokacin ki masa girki yaci
dashi. Kin gane ko??? " Eh na gane baba. Ta fada
yayin da take zaro bandir din kudi daga cikin
jakar hannun da take rike dashi. A kusa dashi ta
ajiye, yayin da shima ya mika mata layar guda
biyu babba da karami, tasa hannu ta amsa. "
Babban ita zaki saka masa a karkashin gadonsa,
karamar kuma a kasan kwanon abincin. Bokan ya
fada. Tana amsa ta buda jakarta ta saka a ciki
tara da mikewa ta fita ba tara data masa godiya
ko sallama ba. Dama ita tasan rules na bokan
ba'a masa sallama idan za'a shiga ko za'a tafi,
haka ba'a masa godiya tafiya kawai ake.ovels / DR SADIQ part 5
DR SADIQ part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:23
Yana fitowa daga wanka bai samu khairat ba a
dakin dan haka ya bude wardrobe ya dauki towel
ya fara goge jikinsa dashi. Yanzu kam yaji
hankalinsa ya fara kwantawa, ya dawo yana
jindadin abin da khairat din ta masa. Shigowar
khairat ne yasa yayi sauri juyawa ya kalleta tara
da sakar mata murmushi. Itama kallansa take yi
dan tabbas tasan bokan yayi aiki. " Murmushin
nan na lafiya ce kuwa??? Ta fada cikin kissa. "
Zo ki zauna kiji wani abu. Dr ya fada tara da
nuna mata inda zata zauna kusa dashi. Cikin
sanyin jiki da jan aji ta karasa ta zauna kusa
dashi tara da daura kanta akan kafadarsa. "A duk
lokacin dana jiki kusa dashi, ko na samu
farantarwa daga gare ki, actually, ina matukar
rena kaina. A gaskiya honey kin cika mace dan
kinfi min mata da dama, anan duniyar. Magana
yake cikin kwanciyar hankali. Khairat ta dago ta
kallesa tara da dafa, hannunta daya akan
kuncinsa. " Na dade ina jin irin wadannan
dadaddun kalaman daga bakin ka dear. Nasan ka
daina sona yanzu, nice dai dana kamu da maitar
sonka wacca take nema ta illatani akanka, dan
baka son ina yi ba. Kace ka yarda da zabin da
iyayanka suka maka akan wata bani ba, ni basa
sona dan sunce bana impressing dinsu. Kaga
kuwa iskace kawai take wahalar da mai kayan
kara. Dr yayi saurin cewa: " Ba haka bane
khairat. Idan su basa sonki ni kuma u really
means alot 2 me. Wallahi son da nake miki yanzu
zan iya converting nasa dana iyayena. Dan yanzu
haka yadda nake ji, Nana ta fara fita min daga
raina, dama can bana sonta anyi forcing dina ne
akanta, amma yanzu a shirye nake da nace na
fasa komai. Wata irin murmushin jindadi khairat
ta sakar, har sai da shatin fararan hakoranta
suka bayyana fili. " Allah yasa da gaske haka
maganar taka take. Yanzu ka fara bani tsoro ne
Dr, ban sani ba ko wasu ne suke son su shiga
tsakani na da kai, dan suna rivalry akan mu. "
Duk abin da zasuyi baza suci galaba akan mu ba.
Dan haka I really luv u, kuma I totally mean it. Ya
fada yana fara'a idonsa akan nata. Tace: " Okay
sai kasa kaya ka fito muci abinci ko. " Why not,
mu shirya mu fita Oasis muci, dan kinsan bana
son kina wahala akaina. " Ai dole, idan banyi ba
wa zanyi wa. Don't bother na riga na gama ma,
yana kan dinning. Murmushi kawai yayi, sannan
ya mike ya fara saka kayan nasa. + Tin da suka
shiga cikin gari da mai taxi ya fara ganin poster
din hotunan sa ta ko ina, duk akan cigiyarsa. Mai
taxi shima tin daya dauko sa ya gane sa, dan
Allah Allah yake yayi branching dashi police
station dan Samun kyautarsa da akayi wa duk
wanda ya gansa alkawari. Suna isa dai-dai traffic
yaga driver din ya tsaya, da alama yana shirin ya
shiga hannun da aka nuna musu alamar su tsaya
daya hannun kuma da aka basu hannu itace
hanyar inda zai kaisa amma bai bi taba. " Malam
ina zaka kaini ne??? Dr ya tambayesa. Driver din
bai juyo ya kallesa ba yace: " Station zan biya
dakai kafin na kaika gida, dan yau kwana biyar
kenan ana neman ka, dalilin batanka yaso ya
jawo rikici tsakanin sojoji da jama'ar cikin gari,
dan har an fara rasa rayuka da dama. Sai da
General na sojojin ruwa, wanda yace shine
mahaifinka yayi magana, sannan komaiya lafa.
Cikin fushi Dr yayi sauri yace: " Look malam, gida
nace ka kaini ba station ba, koma me ya faru ni
baidame ni ba. Cikin mamaki driver din ya juyo
zaiyi magana, nan yaga an basu hannu akan su
tafi. Cikin sauri ya taka motar yayi hanyar station
din. Dr cikin tsawa ya sake cewa. " How dear u,
kanka daya kuwa, nace ka kaini gida ko. " Ka
kwantar da hankalin ka, bazan iya komawa ta one
way ba. Suma police's din ba komai zasu maka
ba, iyayanka zasu kira su dauke ka. Ya fada
yayin da yake ta taka motarsa da sauri. " Ni fa
ba karamin yaro bane, zan iya taka birkin motar
nan unexpected ni da kai mu mutu, dan haka ka
sauke ni na fita, ko kuma na maka duka wallahi
tallahi. Cikin fushi yake magana. Ganin da gaske
yake yasa driver din yayi saurin parking a bakin
gate din station. Cikin sauri Dr ya bude kofar ya
fito yana fada. " Sai naga uban dazai biya ka
stupid imbecile kawai. Cikin sauri police's din
dake wurin suka karaso dan ganinsa. " Wannan
bashi ake nema ba, Dr sadiq yaron General???
Cikin mintina kadan magana ya bazu ko ina, nan
da nan aka cika a station din, 'yan jarida da
sauran ma'aikatan gidan redio da T.V sun hadu
sai faman tambayoyi ake masa amma yaki
magana, dan yaki nuna musu fuska. Nan da nan
jiniyar motocin mahaifinsa suka karaso wurin,
ba'a dauki lokaci ba suka daukesa a mota suka
nufi gida. Suna zaune a babban katafaran falon
gidansu na baki, da iyayansa da sauran dangi da
basu tafi ba, inda suke ta faman masa
tambayoyi. " Ka bude baki kayiwa mutane
magana, ko wani abune yake damun ka??? Hajiya
ta fada. Ya kalleta sannan ya sun kuyar da kansa
kasa. " Mum ni na gudu da kaina dan bana son
ku auramin Nana. Lokaci daya jama'ar dake
wurin sukayi salati, cikin mamaki kanin
mahaifinsa yace: " Kana cikin hankalinka kuwa
Dr, abin dakayi akan fatima zaka sake yi akan
Nana??? " Uncle hankalina daya wallahi, sonta ne
kawai bana yi, nace su auramin wacca nake so
amma sunki, dan me zan yarda amin auran dole
ina namji ba mace ba. Magana yake cikin daga
murya. Yace: " Amma me yasa earlier ka amince
da kaji ka gani, ko kana so kamayar damu
kananan yara ne??? " Shine kuwa karamin yaro,
dan ya girma ba hankali. Kodai wata ce take hure
masa kunne??? Wata 'yar uwansu ta fada. Hajiya
tace: " Ba ko wace 'yar iska bace na sani face
khairat, 'yar gidan General, yarinyar da ko a
mafarki bazan so na hada zuri'a da ita ba. Cikin
sauri Dr yace: " Mum kibar bata mata suna a
gaban jama'a mana. Dan me zaku tsana abinda
nake so, kuma wai da sunan nima kuna sona.
Lokaci daya General ya mike duk ya fusata da
maganganun Dr ya daukesa da mari lafiyayyu
hannu bibbiyu sau uku. Wannan shine karo na
farko da ya taba lafiyar 'dansa. " Idan
kwakwalwarka ta mutu zan gyera maka ita. Aure
ni nayi niyya, kumat baza a fasa ba, dan haka ka
shirya gobe dole ka zama Ango. Dola nasa a
daure 'yar iskan yarinyar nan, dan bazata
batamin zuri'a ba. Idan kai ta gagare ka, mu bata
fi karfin mu ba. Ya juya ya nufa cikin dakinsa. Dr
ya jigata sosai, hannunsa biyu a fuskarsa yana
rarraba idanu,y dan bai san yana zubar da
hawaye ba.els / DR SADIQ part 6
DR SADIQ part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:25
A daki ya samu Hajiya tana zaune tana waya da
kawarta kan maganar daurin auran nasa na gobe.
Ganinsa ya shigo yasa sukayi sallama ta kashe
wayar, ta mayar da hankalinta kansa. A bakin
gado ya zauna kusa da ita, kallo daya zaka
masa, kasan ya shiga cikin damuwa. "Mum
yanzu da gaske kuke wai gobannan zaku auramin
Nana, ko ina sonta ko bana sonta??? Hajiya ta
tsare sa da ido. " Sanin kanka ne mu ba kananun
tmutane bane, sannan mu ba mayaudara bane da
zaka dinga yawo mana da hankali. Zabin da kake
so mu baka zuri'armu tafi karfinta, batayi kama
da macen da zamu baka ita ba, dan ba 'yar
mutunci bace. " But Mum gani nayi fa kunsan
iyayen yarinyar nan, kuma mahaifinta itama
babban mutum ne a kasan nan kamar mahaifina,
dan me zakuyi tunanin nafi karfinta, bata fi Nana
ba sau dubu. Dr ya fada. Hajiya ta girgiza kai. "
Nana ta fita komai, dan kuwa mutunci shine 'ya
mace, wacca kuma bata rike mutuncinta ba bata
cika 'ya mace ba. Kasancewar ta 'yar babban
mutum baza ta kasance babbar yarinya ba a
idanuwan mu. Dan yarinyar daka kawota cikin
gidannan tsirara, baza ta zama sirikata ba. Akan
yarinyar nan mutuncin gidan nan bazai zube ba a
idon jama'a. Nan da nan ya kara hada rai. " Mum
to ni gaskiya ko kun auramiin Nana bazan zauna
da ita ba, kuma ni zan koma inda na fito ne. " Ka
dade baka tafi ba idan bariki ne, kuma ka dade
baka zauna ba idan aka aura maka ita. Idan kuwa
kace zaka fiffita mace daya akan sauran, na
tabbata zaka wahala a rayuwa, ykuma zaka jefa
kanka cikin halaka. Dan haka tin farko kasan abin
da kake yi, Nana jinin kace ba bare bace, kuma
na tabbata baza mu zaba maka mace da bata
dace dakai ba. Magana take masa cikin natsuwa.
Dr dai ya fuskanci lallai maganan da Mum dinsa
take masa ba wasa take ba, haka yasa yaji kansa
duk ya daburce ya rasa meke masa dadi. Shi dai
yasan tabbas yanzu baya son Nana ko kadan,
idan suka aura masa ita bata da wani amfani a
gurinsa, dan haka dole yayi da gaske dan ganin
an fasa auran nan. " Mum kamar bakya sona,
kamar bani kuka nuna wa so ba tin ina karami
har girmana. To dan me zaku nema ku sauya min
zabina akan naku??? Magana yake kaman zaiyi
kuka. Hajiya tace: " Tin farko kai kayi na'am da
maganar, da baka yarda ba baza mu tilassa maka
ba. Dan haka mun riga munsa rana, har lokaci
yazo baza kayi betraying din mu ba. Lokaci daya
ya mike, cikin daga murya ya fara magana. "
Mum bazan zauna ba, zan koma daga inda na
fito, idan har dola sai kun min aure, to wallahi
zan bar gidan nan. Ya juya cikin sauri yayi
hanyar fita daga dakin. Hajiya tana ta ihun
kiransa amma bai juyo ya dubeta ba. Ganin haka
yasa hankalinta ya tashi, cikin sauri ta biyo
bayansa amma bata gansa ba har ya shiga ban
garan sa. Da sauri da sauri ta nufa bangaran
General, kai tsaye ta nufa cikin falon sa nan kuwa
ta samesa zaune shi kadai. " Alhaji kasan a tare
ko wace kofa ta fita daga gidan nan, Sadiq ya
rantse zai koma daga inda ya fito fa. Magana
take cikin rudiya. Cikin sauri General yace: "
Yanzu yana ina?? " Ya nufa dakinsa, kasan
halinsa idan ya zuciya komai ma yana yi. Inji
Hajiya. Yace: " Ok... zoki zauna bari nayi waya.
Cikin sauri ya dauki daya daga wayansa, ya
danna number tara dakai kunnan sa. " Duk wata
kofa daka sani ta fita da shiga cikin gidannan ku
rufe ta, sannan ina so a rufemin kofar falon dake
bangaran Dr, bana son yayi step out din kafar sa,
koda nan da tsakar gidan nan. " Alright sir.
Mutumin ya fada. Daga nan ya kashe wayar, ya
juyo ya kalli Hajiya wacca hankalin ta ya tashi
sosai. " Ki kwantar da hankalin ki, daga yau nasa
masa tarko kenan, bazai iya tsallakawa ba. Zai
gane bashi da wayo. General ya fada. Tace: "
Yawwa hakan ma da kayi yayi dai-dai. Dr yana
shiga daki mukullin motarsa kawai ya dauka ya
juyo ya fita daga dakin. Yana kai hannunsa dan
bude kofar falon, sai ji yayi ana rufewa daga
waje. Cikin fushi ya buga kofar, da hannunsa. "
Waye wannan??? Amma yaji shiru ba'a yi magana
ba. Nan ya shiga kwalla wa sojan dake gadin
bangaransa kira,amma yaji yayi shiru bai amsa
ba. Wata takaici yaji ta kamasa dan yasan bashi
da mukulli ko daya a wurinsa, bai ma san kalar
mukullin kofar ba. Cikin sauri yayi tunanin fita ta
ban garan Mum dinsa, ya juya ya nufa wurin da
sauri dan ya fita. Bai kai ga fitaba nan yaga
Hajiya sun shigo ta wurin, yana ganinsu yaja ya
tsaya. " Dad ya zasu rufemin kofa 9:30, bayan
lokacin kwanciyata bata yiba?? Dr ya fada. " Of
course ni nasa a rufe dan kana niyyar fita daga
gidan. Daga yau ka daina fita kai kadai sai da
masu tsaro, ka dai jan mota ko wata irice sai dai
a jaka. Bani duka mukullayen motocin ka. Ya
fada tara da mika masa hannu dan ya basa. Cikin
sanyin jiki ya mika masa, dan yasan baya
musayar yawu dashi. Ya sake cewa: " Ina sauran
suke?? " Suna cikin bedroom dina. Ya fada kamar
bashi da baki. Yace: " Jeka ka kwaso ka kawosu
yanzun yanzu. Cikin sanyin jiki Dr ya juya ya
shiga dakin ya dibo mukullayen guda uku ya mika
masa. Daga nan basu kara ce masa komai ba
suka juya suka fita daga dakin, tara dasa mukulli
ta dayan kofar suka rufe. Wata ihu ya saka na
takaici da bakin cikin ya fada kan kujera yana
kuka kamar karamin yaro. + Khairat tana zaune
akan gadonta ta matsu taga shigowar mutumin
dan jin good result amma shiru. Ganin ta matsu
sosai kuma dare ya fara nisa yasa ta kira
wayarsa. Bai dade da fara ringing ba taji ya daga.
" Dear kana ina ne??? " Honey ina gida ba hanyar
fita, dad yasa an rufe min bangarena ba inda zan
iya fitowa. " Kamar yaya ba inda zaka fita, kana
nufin maganar auran yana nan har yanzu ne????
Ta fada cikin matsuwa. Yace: " Dearest nayi iya
bakin kokari amma komai yaki fasuwa, wallahi ina
cikin...... " Keep quiet! Ta daka masa tsawa. "
Fine.. dama dalilin kenan daya sa ka hanani
binka dan ka munafurce ni. Dama na fada baka
sona,ka batamin rayuwa ce kawai dan ka biya
bukatar rayuwarka. Amma Allah ya isa Dr.
Magana take cikin fushi. " Wallahi ba haka bane
Honey, bana son Nana ke nake so, bazan yaudare
ki ba dan kin wuce tunanin da nake ciki yanzu.
Pls karki fada haka. " Dola zan fada haka, dan
baka da imani mutumin nan. Iyayanka sunfi nine,
ko sunfi karfin ka ne. But ba damuwa, its not ur
fault. Iyayanka su aura maka Nana, ka dafa ta ka
cinyeta saboda tsananin son da kake mata. Ta
kashe wayar. Wata bakin cikine taji ta toshe mata
zuciya. Cikin sauri tayi wulli da wayar gyefe daya
ta kwanta kan gadon tana kuka mai sauti. " Lallai
kuwa yau za'a san an taboni. Lallai kuwa za'a
san an kwace min farin cikina. Lallai Nana zata
gane shayi ruwa ne. Basu san sharri na ba, suna
wasa dani. Zatayi nadamar auran abin da yafi
karfinta. novels / DR SADIQ part 8 - 9 - to 10
DR SADIQ part 8 - 9 - to 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:32
Cikin sauri ta taka motar tara da budewa ta fito
da sauri ta karasa inda yake kwance. Ganin
yadda jini ke fita daga jikinsa yasa tsigar jikinta
tashi, bata san lokacin data kwalla wata uwar
kara ba. Babu mutum ko daya da suka zo wurin,
kasancewar haka hanyar take ba mutane da yawa
sai daidaiku ke wuce wa. Cikin hanzari ta dago
sa daga suman da yake, amma taji ya mata nauyi
baza ta iya daukan sa ta saka sa cikin motar ba.
Ta juya ta kalli gabas da yamma kudu da arewa
amma babu alamar mota ko walkiyar mutum. "
Na shiga uku, na kashe abuna da hannuna. Cikin
kuka da karadi take magana. Cikin dabara ta
mike ta dinga jansa jini sai fita yake a wurin da
yaji rauni, da kyar ta samu ta saka sa cikin gidan
baya ta rufe, sannan ta zagaya ta shiga taja
motar. A hanyarta ta kaisa yasibiti taji
wayayoyinsa dake aljihun wandonsa sai faman
ringing suke amma bata kula suba, dan hankalin
ta duk ya tafi akan ta kashe sa. Suna isa asibitin
aka daukesa aka shigar dashi emergency ward.
Ganin yayi rauni da yawa yasa likitocida dama
suka cika kansa suka shiga treatment dinsa.
Tana tsaye ta kasa natsuwa wuri daya sai
zagaye takeyi dan hankalinta yayi matukar tashi
ta fara nadamar abinda ta aikata. Kiran daya
sake shigowa wayar tasa ce tasa takai duba ga
wayar dake hannunta taga sunan MUMCY. Haka
yasa tayi tunanin mahaifiyarsa ce, ta amsa
wayar. " Assalamu alaikum. Cikin karamar murya
ta alamar mai kuka. " wacece haka?? Ta fada
dan jin muryar mace. Khairat tace: " Mum khairat
ce, Dr ne ya samu hatsari wata mota ta bigesa
kuma ta gudu, yanzu haka muna Turkish
Hospital, dan Allah kuzo yanzu. Cikin sauri Hajiya
tace: " Innalillahi wa'innailaihi raji'un... Tara da
kashe wayar. Cikin mintina talatin suka iso
Hospital din, bayan likitocin sun gama treatment
nasa amma sun hana kowa ya shiga wurinsa.
Suna shiga suka tarar da khairat zaune, da
ganinta tayi kuka kamar ba gobe amma duk da
haka hankalinsu baya kanta burinsu suji wani hali
'dansu yake. " Ina yake, a wani ward suka
ajiyesa??? Hajiya ta tambaya cikin matsuwa. "
yana Emergency ward, amma sun hana shiga.
Basu saurareta ba suka yunkura gaba daya suka
nufa ward din da yake. Ganin ta tare da SSS yasa
likitocin suka barsa ta shiga dan sun tabbata
matar babban mutum ce. A kwance suka samesa
hannunsa daya dauke da jini, gashi an nada masa
fararan bandages da yawa a jiki. Haka yasa
hankalin Hajiya ya tashi dan ganin yayi rauni da
yawa sai data zubar masa da hawaye. Basu jima
a dakin ba nan su General suma suka shigo tara
da khairat biye dasu a bayansu. " Ya salam.
Yaushe wannan yaron ya fito daga gida har
wannan incident din ya faru a kansa, me yasa
yaron nan yake da kunnan kashine 4 God sake!
Cikin fushi da daga murya yake magana. Umar
yace: " Wallahi bamu san fitarsa ba Alhaji, muma
nemansa muka yi muka rasa. Hajiya tace: "
Watakil tambadaddiyar can ce ta kirasa. Ta fada
tara da nuna khairat inda take tsaye. Cikin sauri
kowa ya juya yana kallonta, dan wasu ma sai a
wannan lokacin suka santa amma suna jin
labarinta. General cikin sauri yace: " Ku kama min
ita, sai nayi detention nata na wasu lokuta kafin
zata barmin 'dana ya sake. " Me na masa bayan
taimakon dana masa na kawosa nan, ni me zanyi
da 'dan ku fashe shi da yake takura kansa
akaina. Kun masa aure kuna tunanin zanci gaba
da zama dashi ne, bayan bakwa sona. Ba wanda
ya isa ya daure ni tinda nima da gata ta kamar
yadda 'dan ku yake da gata a gurinku. Just kawai
iyayena basa kasar ne da wallahi wani abun ma
baza ayimin ba. Magana take cikin kuka. Uncle
dinsa yace: " Kar ki nema kiyi wa mutane rashin
kunya anan, dan naga alamunki baku da manya a
gidanku. " Rabu da ita. Yanzu zan kira mahaifin
nata daga England din da yake, zan sanar dashi.
Inji General. Cikin sauri ya kira lambar mahaifin
nata, tana tsaye tana jin maganganun da sukayi.
Bayan sun gama gaisawa yace: " General 'yar ka
khairat tana hannuna zanyi detention nata na
wasu lokuta, kasancewar 'dana. Yayi aure amma
tana distracting dinsa dan suna soyayya a baya.
Dan haka tana zaune a gidana ba duka ba zagi,
har sai 'dana ya karkatar da hankalinsa kan
matar dana aura masa zan sakota. " No. Karka
mata haka, kawai ka koromin ita ta dawo gida,
dama ina son ganinta taki dawowa ne. " Don't
bother. Zata dawo bayan na gama solving cases
na gidana. Sun dauka lokaci suna waya,sannan
daga baya sukayi sallama ya kashe wayar.
General yace: " Ku kaita gida a bata part daya
daga baya, babu fita babu shiga komai ta dinga
yi a ciki, duk abin data bukata a bata, ko kadan
karku tsawatar mata. I think haka ya isheta. Cikin
sauri sojoji uku suka tasata a gaba, tin tana
musu gardama har ta bisu suka shiga mota, suka
jata suka tafi. Sai misalin bayan mangariba
sannan Dr ya fara motsa jikinsa. A wannan
lokacin ya farfado, abin mamaki sunan khairat ce
ta fito daga bakinsa haka yasa Hajiya kanta ya
daure sosai ta fara tunanin wani irin so wannan
yaron yake ma yarinyar nan haka. " Mum ina
khairat, ta gudu ko, tace na cuce ta kuma Mum is
not my fault. Ya fada cikin karamar murya. Hajiya
ta kallesa cikin tausayawa. " Dr karka damu
kanka akan wannan yarinyar, yanzu aure ne da
kai, ya kamata ka tsayar da hankalinka kan
matarka ba akan wata ba. Yace: " Mum ni khairat
nake so, ita kadai na sani ba Nana ba, bana
sonta me kuke so nayi da rayuwata. " Yanzu da
jikinka zaka ji ko da wani zance daban, me yasa
baza ka kalla incident din daya faru dakai ba. Sai
a wannan lokacin ya duba abubiwan dake jikinsa.
" Meya faru dani, waya kawoni nan??? Hajiya
tace: " Wasu ne suka nema su kashe ka, khairat
ta kawoka. " Ina take Mum ki kirata na bata
hakuri pls Mum. Ya fada cikin nuna damuwa. "
Ba inda ta tafi tana nan, amma baza mu fada
maka inda take ba har sai ka tsayar da
hankalinka akan matarka. MU HADU A PART 9 M
gwamba 08168898969 DR SADIQ PART 9
Bangaran da aka kaita babban wuri ne wanda
babu abinda baza ta rasa ba a ciki, sai dai na
wani daban data bukata. Abin daya kara ci mata
tuwo a kwarya shine, wayoyinta da guardians din
suka kwace suka barta haka shi ya kara tabbatar
mata da cewa lallai mutanan nan sunyi daukan
serious akan ta. Yanzu kam ma idan tayi kuka
duk a banza dan tasan ita da ta kara ganin Dr
Sadiq sai wani ikon Allah. Dan mayb ma zasu
mayar dashi inda bata sani ba. A ganinta zai iya
yuwa shima mahaifinsa ya kwace wayarsa ya
canza masa sim, dan idan ba haka ba tasan
komai daran dadewa zata ga abinta, dan tasan
inda tushen son nata ya dosa. Bakin ciki ya cika
ta kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. " Wai yau nice
aka tsare kamar wacca take cikin prison, ba dan
komai ba duk akan namiji dana daura wa kaina
sonsa kamar shine autan maza. To waima wani
tsautsayine ya hadani da wannan mutumin har
na kashe kaina da soyayyarsa. Anya ina da
hankali kuwa. Ko dai haka so take, ko kuwa tawa
ce ta fita daban. Kodai shima Dr asiri yamin dan
na mutu akan soyayyarsa. Oh my God! Nidai naga
ta kaina da wahalar duniyar, sai dai bazan daina
sonka ba Dr koda kashe ni za'ayi. Maganganun
data dinga yi kenan a zuciyarta, amma ko kadan
ta kasa zaba wa kanta mafita cikin al'amarin,
dan tabbas tasan tana cikin daka mai wiya. + Ba
yanda Dr baiyi ba dan ya samu Khairat a waya
amma ko kadan layin nata baya tafiya. Haushi da
kuncin rai kamar ya kashe sa, dan kuwa gani
yake idan babu khairat bazai iya jindadin zama da
kowa ba, saboda rayuwarsa gani yake kamar
tafiyar su daya. Yanzu kam ya canza ma koma
baya sake masu, dan ko magana aka masa bai
cika kula jama'a ba duk da cewa shi mai mutane
ne, amma saboda fadin rai daya dauka na rashin
sahibar tasa yasa ya daina ganin kowa da ido a
fuska. Kwanakin Dr biyar, a asibiti aka sallamesu
suka dawo gida, dan ganin jikin nasa yayi sauki
sosai, amma shi kam bai damu da wannan ba
dan abin daya saka a ransa tafi karfin wannan a
ganinsa. Washe garin ranar abokansa suka
rakasa dakin Amaryarsa, bayan sun masa nasiha
sosai suka barosa suka dawo gida. Sai yau Nana
tasa idonta akan mijin nata tin ranar daya dawo
gida, dan asibitin ma bata samu taje ba
kasancewar hana ta zuwa da akayi. Dr baice
mata ba itama bata ce masa ba, ganin tasan hali
yana da bakar zuciya kamar jaraba yasa ta
kaskantar da kanta ta daga kai ta kallesa inda
yake zaune bakin gadon ya juya mata baya. " Na
tabbata duk wasu masoya babu ranar da yafi
farin ciki a garesa face wannan daran dazasu
kasance a inuwa daya, amma kai sai naga taka
fuskar tasha banban data kowa. Bai san tana
yiba dan kuwa ko motsi baiba balle tasan yaji
abin data fada. Ganin dai yayi shiru bai amsa
mata ba yasa ta sake cewa: " Dr kodai na maka
lefine ka fadamin na nema gafararka, dan bana
son na ganka cikin wannan halin. Pls kayi hakuri.
" Banyi mamakin dan kin samu damar ki
tunkareni da irin wannan maganar ba.
Unfortunately ada naso ki amma yanzu bana
tunanin hakan, dan kuwa an raba ni da abinda
nake so kuma duk akan ki. Bana tunanin zan
tausaya miki akan zaman da zamuyi da ke, dan
kema sai kinji radadin da nake ji akan rabani da
abin alfahari na. Cikin mamaki ta tsaresa da ido.
" Nima nasan da hakan zaiyi wiya naji dadin
zama dakai, dan tin da naga ka canza kafin auran
nan. Nima naso a fasa kowa ya hakura amma
Dad ne yaki, dan nasan nice zan wahala bakai ba.
Ta fara kuka. Sai a wannan lokacin ya juyo ya
kalleta. " Bakiyi komai ba tukunnan dai. Ba auran
zumunci kike so ba kinyi ai sai ki jure abinda zaki
tarar a cikinta. Cikin saukin kai yake mata
magana. Kuka take yi na gaske. " Dan Allah Dr
kayi hakuri, Wallahi ba lefina bane, iyayan mu ne
suka hada abin nan bani da wata masaniyya a
ciki. " Kar kiyi deceiving kanki mana, da baki ce
kina sona ba zasu tilassa miki dole sai kin aure
nine. Ni ban taba ganin mayyar mace mai nace
wa maza bama irinki. Wata fadiwar gaba taji. " Ni
ban nace maka ba, illah biyayyar da nayiwa
mahaifana dan naga na faranta musu. Dr duk
dabi'un ka ba wanda ban sani ba kan courtship
dinka da Khairat, amma na danne zuciya dan
kana 'dan uwana na aureka, amma abin da zaka
zo kana fada kenan ka daura blame din a kaina.
Cikin kuka take magana. Yace: " Kwarai kuwa
dola zan fada dan kuma lefinki zan gani, tinda
kece zaki zauna dani basu ba. Bazan miki kallon
matar da nake aure ba, kuma bazan sake ki ba.
Dama ni dan hutu ne dan haka dola ki fuskanci
bauta da wulaknci da rashin mutunci da
tozartawa daga gare ni, dan such an atom na
sonki bana ji a cikin zuciya ta. Da sunan kinyi
aure ne, amma ba aure kikayi ba slavery aka
kawo ki. Dan haka u need 2 pity ur self tin yanzu.
Ya mike ya fita daga cikin dakin. Tabbas jikin
Nana yayi sanyi sosai, dan kuka takeyi kamar ba
ita ba. Bata taba jin bakar magana ba irin
wannan tinda take, amma gashi yau aure ya jawo
mata. Lallai kam tasan ta dibo ruwan dafa kanta,
dan tsautsayine tasan ya jawota gidan Dr ba
komai ba. Tayi kukanta ta gaji dan taga bamai
karewa bane, haka yasa ta mike ta shiga toilet ta
dauro alwala ta fara nafilolin data saba. Ta dade
tana addu'o'i dan samun mafita daga halin da
zata shiga, dan tasan Dr ko kadan yadda take
jinsa bashi da kamshin tausayi ko sassauci. Har
kusan karfe daya da wasu mintina tana abu daya
gashi har yanzu bata ga shigowarsa ba, dan haka
yasa tayi tunanin watakil ma ya kwanta a dayan
dakin bazai kwana a nata ba. Dan haka tana
gama abubuwan da zatayi ta mike ta rufo kofarta
ta nema wuri ta kwanta zuciyarta cike da tunani.
Da sassafe tana cikin bacci bayan tayi sallar
asuba, kamar a cikin mafarki taji an janye mata
filon da take kwance akai. Cikin firgita ta mike
nan ta gansa tsaye a kanta sanye da doguwar
jallabiya. " Nan ba gidanku bane da zaki dinga
farkawa bacci tara ko goma, kina da aiki a
gabanki ki fito ki biyoni. Bata masa musu ba ta
mike ta bisa a baya ganin yayi gaba. Suna fita
daga dakin taga yayi hanyar fita daga falon suka
nufa tsakar gida. Bai tsaya ako ina ba sai bakin
motocin dake ajiye gyefe daya. " Kinga motocin
nan su nake so ki wanke min su gaba daya kuma
su fita sosai dan sababbine, dan kuwa zan fara
fita da daya yau. Cikin mamaki ta juya ta kalli
inda motocin suke a ajiye har guda uku. " But
kasan nifa macece, gashi ban taba wanke abu
kamar haka ba, dan bani da straight da zan iya
wannan aikin sai maza. Why not kasa securities
din gidan su wanke maka??? " U r not serious.
Na sallamesu saboda na samu baiwa daga sama,
dan haka ko kin iya ko baki iya ba practice make
perfect. Ki wanke su. Cikin nuna isa yake
magana. " Na shiga uku! Dan Allah Dr ka tausaya
min, nifa macece bana irin wannan aiki, infact ka
dubama fa ka gani yadda sukayi kura, it wil take
me alot of time akan mota daya. Dan Allah have
mercy on me, bazan iya ba. Ta tsugunna masa ta
fara kuka. Ko kadan baiji tausayinta ta kamasa
ba, sai haushinta da yake kara shigansa. " Idan
kina son kanki da arziki kiwanke, idan kuma kina
son kiyi argument da nine go ahead. Ki duba
toilet dina akwai freshener ki dauko. Ya juya ya
fita daga cikin gidan. MU HADU A PART 10 Zanyi
amfani da wanan daman in mika dinbin
gaisuwana zuwa ga 'yan uwa da abokan arziki da
sunansu bazasu kirguba ma'abota bibiyan wanan
shafin namu mai farin jini da fatan Allah ya karbi
ibadunmu. Ameen ((((G. M. B))))) 08168898969
DR SADIQ PART 10 Haka ta kuge ta daure ta fara
wanke su duk da cewa bata san yadda ake ba,
kafin ta kaiga wanke na farko duk ta gaji gashi
bata sa komai a cikin nata ba tin jiya. Takaici da
bakin ciki taji su tamkar ta hadi zuciya, dan ko
kadan bata sako irin wannan bautar a harkokin
rayuwarta ba, yau gashi 'dan uwanta ne ya saka
ta. Gajiyan da tayi ne yasa taji jikinta duk ya
mutu dan haka bazata iya shiga kicin ba, tana ji
tana gani haka ta hada tea da ruwan sanyi ta
zauna tana sha a dinning. Sai a wannan lokacin
ya dawo cikin gidan ya sameta anan falon.
Ganinsa yasa taji gabanta ya fadi, shiko ya hada
rai tamkar yaga makiyarsa. " Amma da kinyi
denying akan cewa baki iya ba, yanzu wa ya
wanke miki, ko uncle kika kira ya wanke??? Ya
tambayeta ta fuskar rainin wayo. Zafin maganar
daya mata yasa tace: " Haba Dr mai kuma ya
kawo maganan mahaifina a cikin wannan
maganar, koda baza kayi respecting nasa ba
kasan ya kusa haifanka fa. Cikin tsawa ya duka
dinning table dake gabanta sai data tsorata. "
Excuse me! Har kin samu damar da zaki fara
conversation dani, kodan kinga kin fara kwana a
daki next to mine?? Dat should be d first nd last
da zanyi magana ki amsa min. Koda mahaifin
naki na zaga aure ne ya jawo miki ba komai ba.
Shiru tayi kanta na kasa bata ce komai ba, dan
tasan tana kara tofa abu sai dan buzunta. " Kayi
hakuri bazan sake ba. Ta fada cikin sanyin
murya. Ya mata kallo cike da kaskanci sannan
yayi tsuka ya shiga cikin dakinsa. + A bakin wata
babbar Shopping store yayi parking din motar
tasa, yana daga ciki ya dauki wayarsa ya kira
wata number. " Hello Fauzy ina waje. " Okay ka
shigo kawai. Ta fada tara da kashe wayar. Cikin
sauri ya kashe wayar tara da bude motar ya fito
ya shiga ciki. Gyefe daya inda waiters ke zama
suka samu wuri suka zauna, kasan cewar ba ita
kadai bace shop keeper a wurin su biyu ne. "
Fauzy wurinki nazo ina so muyi wata 'yar
magana ce dake. Dr ya fada. Tace: " Toh fa. Ina
jinka Dr. " Dan Allah tsakanin ki da Allah ki
fadamin inda khairat take. Ya fada tara da tsareta
da ido. Cikin mamaki tace: " Ban gane ba. Antin
bata tayi ko kuma yaya??? Yace: " No ba bata
tayi ba, na nemeta ne ban ganka ba, idan kinsan
inda take pls karki boyemin komai, kinsan yadda
take a wurina, she's my passion. " A gaskiya
rabona da ganin Anty tin next week data saka
akayi supplying na kaya tazo muka fitar da prices
nasu ban sake jinta ba koda a waya ne, jiya ma
ina ta trying number nata baya shiga dan na fada
mata shagon na bukatar sababbin kaya, amma
wayar switch off. " Ya salam! Ban san yadda
zanyi ba fauzy ina missing khairat sosai, dama
kece kadai nake tunanin zakisan inda take dan
kece yarinyar shagonta. Actually nayi betrayed din
kaina da kaina. Magana yake cikin rashin jin dadi.
Fauzy ta kurasa da ido cikin rashin fahimta. " Dr
kodai wani abune ya faru da Anty??? Yace: "
Fauzy iyayena ne sukamin aure suka rabani da
khairat, a gaskiya na cutu not even a little bit. "
Allah sarki. To me yasa baka ce ita kake so ba??
Fauzy ta fada. " Ba yanda na iya ne. But kina
ganin ba wurin iyayenta taje ba a England??? Ya
tambayeta. Tace: " Ba mamaki Dr dan kayi
hurting dinta da yawa, dan Allah kaje kaga halin
da take ciki. Cikin sauri ya kada mata kai. " Insha
Allah, I will. Daga nan sukayi sallama ya fito yaja
motarsa ya tafi. + Misalin karfe tara da rabi na
dare Dr yana airport, dama yana da personal visa
nasa da yake zuwa England din. Karfe goma dai-
dai suka dauki flight bayan kowa ya hadu. Nana
kam bata ma sani ba ko gogan nata yana nan ko
baya nan, dan tasan ba dakin nata yake kwana
ba, ita kuma bata isa taje ta dubasa ba dan
tasan hali. Washe gari da safe har ta gama hada
breakfast amma bata ga fitowarsa ba, haka yasa
ta zauna taci nata sannan ta mike ta koma daki
ta kwanta. Sai kusan misali goma da rabi ta sake
fitowa dan wanke plates din abinci, amma cikin
mamakinta babu alamar anzo wurin dinning. Ta
taba baki. " Dama nasan baci zaiyi ba. Ta karasa
ta tattara kayan abinci ta shiga kicin. Har bakin
gate din gidan Drop ya ajiye sa tara da biyansa
ya fito. Yana zuwa bakin gate daya daga cikin
securities din ya taresa, nan ya nuna masa
identity card nasa sannan ya bude nasa kofa ya
shiga. A guests room aka ajiyesa sai faman
rarraba idanu yake yi ko zaiga shigowar khairat
dinsa, dan yasan dola zasu san shigowarsa gidan
kasancewar haka tsarin gidan yake kuma shi
sananne ne. Unexpected yaga General
(Mahaifinta) ya shigo cikin falon. " Ya akayi na
ganka kai kadai, ina daughter din tawa??? Ya
tambayesa cikin matsuwa. Cikin mamaki Dr yace:
" Dad ita na biyo fa, bata zo bane??? " 4 wat
excess zata zo bayan tana nan tsare a gidanku.
Ya fada cikin damuwa. Dr ya tsurasa da ido. "
Gidan mu kuma Dad? No khairat bata nan fa, da
tana nan of course, zan sani. " Mahaifinka shi ya
kirani ya fadamin zaiyi detention nata, na basa
hakuri yaki dan yace yayi maka aure amma kaki
zama saboda ita. I was amused dana ganka.
Jikin Dr yayi sanyi. " But Dad a cikin gidan mu ya
ajiyeta, family house namu??? Yace: " Don't
actually know. Kaga kenan da ina son fitina
yadda ka kawo kanka nan, nina sai nasa a
kamamin kai, but kai nawa ne ko baka auri 'yata
ba I don't bother. " Pls Dad kayi hakuri, ban san
maganan nan ba sai yanzu, nima ita nazo nema.
Amma I promise u duk inda take zan fito da ita,
zan kawo ta gida. Magana yake cikin fahimta.
Yace: " Ina son Khairat ta dawo gida, dan I
wonder how I can see my daughter physically. "
Karka damu Dad, zan kawo ta. Dr ya fada. Dr bai
kwana a kasar ba dan yanzu hankalin sa ya dawo
Nigeria inda mutuniyar tasa take. Bayan dan
wasu bata lokaci da yayi dan gana da iyayan
khairat din daga nan ya bar gidan ya shigo jirgi
ya dawo. Cikin dare ya iso bai tsaya ko ina ba
sai a Rock View Hotel, anan ya kama daki ya
huta gajiya a ciki. Washe gari misalin goma na
safe ya fito ya dauki taxi har family house nasu
ya ajiye sa. Bai shiga ciki ba ya tsaya a bakin
gate ya kira daya daga cikin securities na gidan
ya jasa gyefe daya. " Na tabbata duk abin dake
faruwa a cikin gidan nan dola kusani idan ta
fannin tsaro ne. Ka fadamin akwai wata bakuwar
da Dad yasa a tsareta??? Cikin sauri security din
ya amsa masa. " No sir, babu kowa. Ya hararesa.
" Kar kamin karya dan ba wasa nake ba, speak
out d truth. Tana nan ko bata nan??? Shiru yayi
baice masa komai ba dan an riga an masu
warning akan karsu sake su fada masa komai kan
yarinyar. " Gaskiya babu kowa, ban ma sani ba
sir. Magana yake kamar mara gaskiya. Haka yasa
Dr ya gano maganar nasa ba haka yake ba, cikin
sauri ya shakosa cikin uniform din da yake. "
Zaka fadamin gaskiya ko sai ka dauka vacation
na tsawan lokaci. Kasan dai ina da iko daku a
cikin gidan nan. Ya fada cikin buda idanu. Yace: "
Okay sir. Tana nan ciki. " A wani bangare take???
Ya fada yayin daya sakar masa rigar. " Tana last
building, ita daya ba kowa. Dr yaji dadi sosai
amma bai nuna a fuskarsa ba. Ya dafa sojan a
kafadarsa da hannu daya cikin nuna afuwa yace:
" Sorry 4 my tracing, kar kayi fushi, sannan karka
fadawa kowa maganar da mukayi. Ya mika masa
canjin dubu goman dake aljihunsa ya amsa yana
godiya, shiko ya juya ya wuce.ls / DR SADIQ part 11
DR SADIQ part 11
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:35
Inda yayi parking din motar tasa da 'yar tazara
tsakaninsa da gate din gidan nasu. A hankali ya
bude motar ya fito tara da duba agogon wayar
tasa karfe biyu saura na dare, yanzu kam ya
tabbata gaba daya securities din gidan sunyi
bacci. Cikin sauri ya mayar da wayar cikin motar
sannan ya tako dan karasowa bakin gate din
gidan. Yana isowa cikin dabara yaja wata fito da
bakinsa, nan daya daga cikin security din daya
siya ya toru kofar gate din Dr ya shiga. " Sir kayi
a hankali fa, dan an saki karnuka tin karfe daya.
Security din ya fada. Dr yace: " No karka damu
nasan inda zan shiga. Cikin hanzari ya cire
takalman dake kafarsa ya mikawa security din
sannan ya mike dan zuwa karshan building da
mutuniyar tasa take. Yana isa second gate nan
ya samu a bude take kasancewar sunyi alkawari
da security din kadda ya rufe gate ko daya har
sai sun fito. Cikin dabara da,sando ya shiga ciki
dan yasan nan wurin anfi saka masa tsaro sosai,
dan anan building din iyayensa suke. Nan kuwa
ya hangi karnukan gidan gaba daya a sake suke
sai faman zirga- zirgan su suke a wurin, nan
tsoro ya kamasa dan kuwa yasan karnuka ba
saninsa sukayi ba illah masu tsaransu. Dake
zuciyarsa yayi ya labe sai daya fuskanci sun
dauki hankalinsu wani gefan, yayi sauri ya shiga
cikin yana rabe-rabe da sando dan kar ajiyo
tafiyarsa. Haushin karnukan da yaji sun fara
masa yasa ya karasa last building din da gudu,
ya bude gate ya shiga. Cikin sa'arsa babu kowa
a wurin sai dai security light na bangaran a kashe
yake. Yana karasawa bakin falon yasa hannu ya
murda kofar amma ya jita a rufe. Yana laliba
hannunsa ya tabo mukulli a jikin kofar, nan yayi
sauri ya bude ta ya shiga. Kamar ya sani ya
karasa dakin farko dake wuri tara da tura kofar a
hankali ya shiga. Dakin duhu yake dan haka ya
laluba hannunsa ya kunna wutar dakin, nan ya
ganta kwance ta lullube da bargo. Wani dadi yaji
tara da tausayinta daya kamasa. Bai tsaya bata
lokaci ba ya karasa bakin gadon ya zauna kusa
da ita tara da janye bargon a hankali. Baccinta
take yi tukuru dan batasan da wani a kusa da ita
ba. Cikin shauki ya shafa gashin kanta, zuciyarsa
cike da farin cikin yau gashi ga khairat dinsa.
Wata sabuwar sako yaji zuciyarsa ta fara karanto
masa, har da yayi shirin biye mata, sai yayi
tunanin tabbas a cikin hatsari yake dan haka cikin
sauri ya dagota daga baccin. " Dearest tashi, Dr
dinki ne. Ya fada yayin daya dagata. Lokaci daya
ta farka dama ita bamai nauyin bacci bace. Cikin
mamaki ta kallesa inda yake zaune kusa da
ita,tara da murza idanuwanta da hannu biyu. "
Mafarki nake yi??? Ta tambayesa. Yace: " Ba
mafarki bane ki tashi mu tafi, kafin wani ya shigo.
" Ina zamuje, me kazoyi a wurina??? Khairat ta
fada. " khairat bamu da lokacin wannan maganar
yanzu, bari muyi escaping tukunnan, dan we r on
a danger. Ya fada tara da mikewa ya dagota.
Bata masa musu ba ta bisa yana rike da
hannunta cikin hanzari sukafita daga falon. " Dr
kar a kamamu fa, kasan ina cikin fitina, karka
kara sakani cikin wata. Ta fada yayin da yake
kokarin fitar dasu daga gate din wurin. Bai kulata
ba sai kara janta da yake yi kamar zasu zura da
gudu. Haushin karnukan da suka biyosu yasa
khairat ta sake rikicewa, tsoro ya cika ta, dan
haka ta dinga kokarin taga ta janye hannunta
daga rikon daya mata ta zura a guje amma ta
kasa taji ya rike ta gam. Har karnukan suka
rakosu bakin gate suka fita amma babu wani
sojan daya leko wajan. Suna isa gate din karshe
ya amsa takalminsa ya masa godiya suka fito.
Suna isa bakin motarsa Khairat ta fisge
hannunta. " Duk gwanintar da zakamin Dr bazaka
taba birgeni ba a rayuwa, yanzu nikam na tsane
ka, bazan taba kara sonka ba, ka koma wurin
matarka nima Allah zai bani nawa mijin daya fika.
Fuskar Dr cike da mamaki yace: " ina me neman
tuba gareki akan abin daya faru, wlh na sake fada
miki bana sonta ke nake so, ki yarda dani dan
girman Allah. " Ai yarda tsakanina dakai yanzu ta
kare, sai dai tsana ta bude shafinta. Wlh Dr kai
mayaudari ne na fitar hankali kuma abinda kamin
kaima sai anyi maka, idan bai faru dakai ba kuwa
zai faru da 'ya'yanka. Ta wuce ta barsa anan
wurin tsaye. Maganar data fada masa ita ta
tsaya masa a rai, yayi shiru ya kasa motsawa
balle ya mata magana. Jikinsa yayi sanyi
matuka. " Me yesa khairat ta fadamin wannan
maganar. Na tabbata an hadani da ita ne ko
kuma dai da gasken ne ta daina sona???? Cikin
zuciyarsa yake magana. Ganin tayi nisa sosai
kuma gashi cikin dare ne, haka yasa yayi sauri ya
buda motarsa yaja dan ya shawo kanta. Cikin
sauri ya tare ta da motar tara da budewa ya fito.
" Haba Honey me yayi zafi haka?? " Listen
Malam, na riga na gama maganar da zanyi dakai,
dan haka ka kama hanyarka na kama tawa.
Khairat ta fada. " Bazan iya barinki ba khairat
dan na tabbata u r my life. Koda zaki dauki wuka
ki sokeni da ita bazan barki ba. Ki taho muje
gidana ki kwana da sassafe mubar kasar nan.
Cikin tsawa tace: " Ba inda zaje Dr! Ko kai maye
ne yanda na maka wulakancin nan zakayi zuciya
ka barni, amma da yake kayar kare ya dauka. Ta
juya zata kara barin wurin. Cikin sauri Dr ya riko
hannunta ya jata zai sakata a ciki, tayi kokarin
fisgewa amma taga yafi karfinta. Nan takai
bakinta tara da gantsa masa cizo da karfi.
Radadin da yaji yasa yayi saurin sakar hannun
nata, amma ya kara dakewa ya ciccibeta sama
ya jefata a gidan gaba tara da rufe kofar. Cikin
sauri ya zaga ya bude ya shiga sannan ya kara
rufewa. Hannu bibbiyu ta shiga dukansa tana
kuka amma shiko a jikinsa ya taka motar suka
bar wurin. Ita da kanta ta gaji ta kyalesa har
suka isa gidan tana kuka. Yana parker motar bai
mata magana ba ya bude ya fita, itama ta bude
tabi bayansa. " karka kuskara tsautsayi tajaka
kakaini inda zanga matarka, dan wallahi zan
mata abin da bakayi tunani ba. Ta fada yayin da
suke kokarin shiga cikin falon. Bai kulata ba ya
shiga falon taga yana kokarin shiga daki, cikin
sauri ta jawo masa rigarsa ta baya. " Magana
nake kana kokarin shiga daki, kar kamayar dani
mahaukaciya mana. " Honey me kike so nace
miki, kin cije ni, kin rufeni da duka, kin fadamin
bakaken maganganu me kike so kuma dani.
Abinda zan iya ce miki shine, do as u wished.
Cikin sauri ta dauke sa da mari. " Macucin banza
kawai mugun namiji. Allah sai ya sakamin. Ta
fashe da kuka. Ya shafe inda ta maresa, sannan
ya matsa dabda ita tara da rungumota jikinsa
dan ya rarrasheta. A dai-dai lokacin Nana ta fito
daga dakinta dan hayaniyar da taji. " Honey ko
kadan bana son ganinki cikin damuwa dan Allah
ki yafemin har kwanan gobe ina sonki. Ita ko tayi
kwanciyarta kan kirjinsa sai faman kukanta take
yana rarrashinta. Ganin haka yasa Nana taji wata
bakar kishi ta rikota, ganin basu san ta fito ba
yasa ta juya da sauri ta koma dakinta tana
neman makamin da zata dauka. Cikin sauri ta
wawuro kwalban turaran daki daga cikin show
glass dinta, ta fito a guje ta nufo falon. Ina mai
bada hakuri akan jinkirin da muke samu kwanan
hakan ya farune sanadiyyan watan da muke ciki
me alfarma na ibada, kuma muna sanardaku
daga ranan farko na goman karshe zamu dakatar
da wanan labarin namu sakamakon zabarinda
zamu shiga akan dare mai alfarma. Mungode.SADIQ novels / DR SADIQ part 12
DR SADIQ part 12
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:36
Cikin sauri ya zaga ya bude ya shiga sannan ya
kara rufewa. Hannu bibbiyu ta shiga dukansa
tana kuka amma shiko a jikinsa ya taka motar
suka bar wurin. Ita da kanta ta gaji ta kyalesa
har suka isa gidan tana kuka. Yana parker motar
bai mata magana ba ya bude ya fita, itama ta
bude tabi bayansa. " karka kuskara tsautsayi
tajaka kakaini inda zanga matarka, dan wallahi
zan mata abin da bakayi tunani ba. Ta fada yayin
da suke kokarin shiga cikin falon. Bai kulata ba
ya shiga falon taga yana kokarin shiga daki, cikin
sauri ta jawo masa rigarsa ta baya. " Magana
nake kana kokarin shiga daki, kar kamayar dani
mahaukaciya mana. " Honey me kike so nace
miki, kin cije ni, kin rufeni da duka, kin fadamin
bakaken maganganu me kike so kuma dani.
Abinda zan iya ce miki shine, do as u wished.
Cikin sauri ta dauke sa da mari. " Macucin banza
kawai mugun namiji. Allah sai ya sakamin. Ta
fashe da kuka. Ya shafe inda ta maresa, sannan
ya matsa dabda ita tara da rungumota jikinsa
dan ya rarrasheta. A dai-dai lokacin Nana ta fito
daga dakinta dan hayaniyar da taji. " Honey ko
kadan bana son ganinki cikin damuwa dan Allah
ki yafemin har kwanan gobe ina sonki. Ita ko tayi
kwanciyarta kan kirjinsa sai faman kukanta take
yana rarrashinta. Ganin haka yasa Nana taji wata
bakar kishi ta rikota, ganin basu san ta fito ba
yasa ta juya da sauri ta koma dakinta tana
neman makamin da zata dauka. Cikin sauri ta
wawuro kwalban turaran daki daga cikin show
glass dinta, ta fito a guje ta nufo falon khairat na
ganinta aiko tace da wa anka hadani inba dakeba
yauwa daman nayi alkawarin sai na hallakaki
kucakar banza ki rasa Wanda zaki aura sai
mijinda zan aura, yau sai kin yabama aya zakinta
don yau sainaga Wanda zai rabamu a gidanan Dr,
na kokarin riketa haba Honey! mene haka? Ba
nace ki daina kulataba ai wanan bama sa'arki
bace. Kaga nidai Ka kyaleni in dauka ma kaina
'yanci tunda Ka kasa rabuwa da ita, ta fada
yayinda take kokarin nufo Nana. Rufema mutane
baki ke har wani 'yanci ne gareki da har kikebin
mazan mutane? Nana ce ta fada tareda zaro
kwalban da ta boye a bayanta, Dr, na ganin haka
yayi wuf ya tare gabanta dominkuwa yasan Nana
zata iya aikatawa don tun sanda yake da ita
baitaba ganin tayi sa'insa da wani ba. Aiko ji
kake taass! Sai a kan Dr, ya fadi kasa some jini
ya malale ko'ina kai zakace wani katon sa aka
yanka. khairat na ganin hakan ta sake yin kukan
kura tayi cikin Nana wallahi sai na hallakaki
kaman yadda kika hallakashi ta fada yayinda ta
danne Nana a kan kushin ji kake chass! Ta
cakawa Nana fasashen kwalban da ke hanun
Nana. Nana ta fadi kasa tareda shure-shure tana
kakarin fitan rai tareda kalman shahada khairat
na ganin hakan ta kwatsa ihu tareda aza hannu
bisa kai wallahi bani na kashetaba ta sheka da
gudu tayi waje sanan ta dawo ta zauna sai faman
numfashi takeyi sama-sama. karar kiran wayan
Dr, da tajine yasa tayi firgit ta tashi tana zarar
idanu kai zakace patience Jonathan ce rananrda
akayi sanarwan sun fadi zabe, lolx domin Kuwa
tasan ba kowa ke kiran Dr, ba illa mahaifinshi
waton general, tayi kaman ta daga wayar kuma
tayi tunanin tabbas idan general ya sake kamata
wanan karon tau sai buzunta, wata zuciya tace ki
gudu kawai. Har ta fita kuma ta dawo ta dauki
makullin motan Dr, kamin kace kobo har tabar
gidan kai da ganin yadda take gudu da mota kai
zakace zata tashi samane. SADIQ novels / DR SADIQ part 13
DR SADIQ part 13
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:39
Yanzun kam hankalin khairat yayi matukan tashi
domin ko Sai faman tuki takeyi tana sake-sake
cikin zuciyanta Gashi tun da ta fito kowa bata
gamu dashiba, ga titi falau! ba kowa kai zakace
kufaine gabanta sai 'dar'dar kawai yakeyi ta rasa
inda zata nufa. Chan sai wata zuciya tace ki
gudu Kawai ki bar kasanan tau amman ina zaki
samu visa a cikin darenan? Ji kake kiii! Tayi wani
dogon chin burki sai makyarkyata kawwai takeyi
yau kam asirina ya tonu. Ita duk a tunaninta yan
sanda ne, amman saidai kash! Domin Kuwa
abinda ta gani ya Kara sa saida hantan cikinta ya
kada. Wasu kartine masu jajayen idanu kai
zakace garwashin wutane. Suka daka mata tsawa
oya! Oya! Come out and lying down on d ground,
suka kwace Jakar da ke hanunta sanan suka
kwantarda ita a kasa, idan kika sake yin ihu zamu
kasheki, bindigarda ta gani hanunsu ya
tabbatarmata cewa wayanan kasurguman yan
fashine komai zasu iya aikatawa a kanta idan
bata basu hadin kai Ba. bamu makullin motarki,
hanunta na karkarwa ta mikamusu. babba daga
cikinsu ya fizge sanan ya shureta karuwar banza
ina kika fito cikin darenan? Khairat dai batace
komaiba don tasan shiru yafimata abinda zata
furta. da ya kwasheta mari saida taga wutan
lahira ta fadi kasa war-was, Sukayi ihu sai kai
Oga. khairat na ganin sun fice ta runtuma aguje
sai faman gudu takeyi batamasan inda ta dosa
ba har takai kusa da wata korama ta fadi. Har
kusan karfe 8:OO na safe khairat batamasan inda
takeba, surutun da taji anayine kaman a mafarki
yasa ta Dan bude idanunta, ita duk a tunaninta
kwance take akan gadonta duk abinda ya faru jiya
mafarkine. Ta murza idanunta amman taga lallai
ba mafarkibane domin ko ba abinda take gani
zagaye da ita sai ciyayi, tayi firgit ta tashi, ta
rasa inda take ta kara bude idonta amman ta
hango yan matanan su biyu dauke da tulu zasuje
debo Ruwa. ta matsa inda suke domin koda zata
Dan samu abinda zata sakama cikinta. suna
ganinta har sunyi batun runtumawa aguje amman
ina har tasha gabansu, haba bayin Allah nifa yar
adamce kamarku meyasa kuke guduna? Suna
diban kafanta sukaga (cover shoes) aiko suka
yada tulunansu sukace kafa me naci ban bakiba?
Khairat na ganin haka itama ta dafamusu
tunaninta mutanenanne na jiya suka sake biyota.
Aiko suna shigowa gari duk Wanda ya ganeso
kamin kace kobo shima ya shige yar bukkansa ya
rufe garidai duk ya kicime khairat ko hankalinta
sai Kara tashi yakeyi ganin yadda duk mutanen
garinan sun tsorota da ita. Hakan yasa ta samu
wata yar bishiya tayi zamanta ga yinwa na
damunta gaya kuma batada komai, jakarta ma
barayi sun kwace. Uwa uba kuma batama san
inda takeba balle tayi tunanin komawa gida
domin Kuwa yanzun ita duk burinta da fatan da
takeyi shine ta koma gida koda kuwa za a
yankemata hukuncin laifinda ta aikatane ta dauka
domin Kuwa tasan mahaifinta zai iya tsayamata.
Tana cikin wanan tunanin ji kawai tayi anyi
sallama bayanta tayi wuf! ta tashi, Don ALLAH
kuyi hakuri duk abinda ke hanuna na baku wallahi
ba komai sai wanan danyen mangoron, tana
juyawa don ta nunamusu sai taga wani Dan
saurayi kyakyawa son kowa kin Wanda ya rasa
sanye da farar jallabiya kai da ka ganshi zakace
balaraben zariyane lolx. Haba malama me kikeyi a
wanan gindin bishiyar tun da safe haka?
Dukdadai daga ganinki alamomi sun nuna ke
bakuwace, amman khairat bata cemishi uppan ba.
Idan ba zaki damuba ki biyoni muje gidanmu
domin Kuwa mutanen garinan zasu iya illataki,
khairat tayi wuf! Ta sake mikewa illatani kuma
Amman don me? Ki biyoni kawai wannan ba
lokacin tambayoyi bane. A gefe daya kuma tun
lokacinda general yaji Dr sadiq bai daga
wayarsaba ya kira Ummi itama haka yasan lallai
wani abu ya faru. Hajiya na ganishi sanye da kaki
rai bace, gasun baki a murtuke tasan ba Lafiya.
Guards dinshi na ganin ya fito duk suka 'kame
''morning sir'' ko karba musu baiyiba yace where
is sajent Jona? Yace I am here sir, ka tabbatarda
yarinyarnan bataje ko'inaba. I hope u are getting
me. Ya dan donarda kai, I am sorry sir,
yarinyanan fa ta gudu. What!!!! ta me? What!!! Ya
sake fada a karo na biyu, She escape and u are
here telling me rubbish? I gave 24 hours to make
sure she is in ur custody idan kuma tayi tirjiya ku
harbeta. make sure u brought her died or alive, is
an order. Magana yakeyi cikin bacin rai. Oya
kukuma ku biyoni haka suka kama hanya hankali
tashe kai zakace dajin sanbisa zasuDR SADIQ novels / DR SADIQ part 14
DR SADIQ part 14
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:41
Hakika Halinda suka tsinci Dr da kuma Nana yayi
matukar tadamusu hankali, domin Kuwa duk a
tunaninsa duk sun mutu. motsawar yan yatsun da
Nana tayi shi yaja hankalin kowa daga cikinsu.
hakan yasa aka daukesu zuwa asibiti. Yanzun
kam duk inda zuciyar general take tayi matukan
baci don ji yake da ya gamu da khairat sai
buzunta. Fitowan Dr Aishat yasa kowa yayi chaa!
Akanta kaman za a hadiyeta, amman saidai
yanayinda suka ganta yasa jikin kowa yayi sanyi.
Gaskiya patient dinku na cikin mawuyacin hali
domin Kuwa kwakwalwarsa ta samu tabuwa
hakan zaisa ya kasance a cikin wanan halin har
na Dan wani lokaci. Amma gaskiya ita dayan ta
samu sauki sosai saidai tana Dan bukatan hutu
Nan da zuwa awa hudu zaku iya shiga ku ganta.
Mungode sosai DR Aishat, hajiya ta fada yayinda
take kokarin binta a baya. Haba bakomai
fatanmudai Allah ya basu lafiya. A gefe daya
kuma khairat hankalinta ya fara kwantawa da
usamat domin Kuwa ganinsa takeyi kaman Dr
dinta. saidai kash! Kaddara ta riga fata,
Dominkuwa iyayensa sun dade da nema masa
matarda Zai aura wadda diyar kanin baffansane.
Nan da sati biyu za'a sha biki. Dukda dai ba
sonta yakeyiba ganin cewa shi Dan bokone a birni
ya tashi yaya zaiyi ya auri yar kauye wadda
komai bata saniba a bangaren rayuwar zamani.
Kasancewar usama yarone mai ladabi yasa dole
ya hakura da zabin iyayensa Amman badon
yanasoba. Zaune ta cimmasa yana karatun
Qur'ani bayan ta samu wuri ta zauna, ta kuresa
da kallo kai zakace bakanone ya shigo birnin
zazzau. Lolx. bata cemai ko uffan ba. Bayan ya
gama ta daga hannu sukayi Adu'a sanan ya dago
kai ya'ce kaunana kenan Yau kuma ko sallama
babu. Tayi murmushi mhhm! Sanan tace yayana
kenan ai nayi sallama bakadaijibane. Dukda
yasan batayiba Amman ya kyaleta a hakan.
Yayana wai niko in tambayeka? Hmmm! 'yan
birni kenan niko wace irin tambayace wanan?
Usama ya fada yayinda yake kokarin tsureta da
idanu. Ta Dan donarda kai sanan ta, ce wai Niko
yaya yaushe zakayi aurene naga duk yawancin
sa'aninka a garinan sunyi aure banda kai? Wanan
ita kadaice tambayarki? Tau kada ki damu kina
garinan zanyi aure domin Kuwa bazai wuce nan
da sati biyu ba, kinga zakiga yadda muke bikin
aure ba irin taku ta yan birni ba. Ya fada yayinda
yake kokarin tashi tsaye. Ina zaka kuma yaya ai
tambayar tawa bata kareba ko Ka gaji Dani ne.
Haba! Ai bako rahamane ta yaya zan gaji da
bakona? Yaya injindai ba yar kauyenan zaka
auraba? Ta fada yayinda take sake tsuresa da ido
karo na biyu. Hmmm! Khairat kenan yanzun idan
na cemiki 'yar birni zan aura zaki yarda Dani?
Haba mezai hana Dan saurayi kyakyawa irinka.
Hahaha! Yayi wata 'yar bazawaran dariya 'yan
birni akwaiku da zolayan 'yan kauye nidai bara
naje ance ummah' na nemana idan na dawo ma
Ida maganan. Wanan shine karo na farko da
khairat ta fitarda maitanta a fili kan usama.
Kwanan khairat hudu a kauyen tugga Amman
shakuwan da usamat da khairat sukayi tamkar
sun shekara goma tare. Hakan yasa iyayen
usamat suka fara tunanin rabasu don kada
wankin hula ya kaisu dare ganin auren usamat ya
gabato. Ba yadda basuyi juyin duniyaba Amman
khairat ta dage akan batasan komai akan
iyayentaba ganin za a iya rabata da usamat.
Kabir abokin usamat ne tun suna yara Amman
kasancewar iyayensa a birni suke aiki yasa a can
ya tashi. Saidai sukanzo duk sallah. wanan
karonma auren usamat ya kawoshi domin Kuwa
sune manyan abokan ango. Ganinda kabir ya
yima khairat a gidan su usamat yayi matukar
bashi mamaki kasancewar ya Santa, dominkuwa
makwabcin su DR sadiq ne amman saidai ita
bata sanshiba hakan yasa ko a jikinta. Bayan sun
bar gidan ne kabir ke cemasa Amman gaskiya
Yau naga wani ikon Allah a gidanku. Usamat yayi
dariya yace nasan ana haka abokina ai daga
ganin yadda Ka tashi fadawa cikin randa akan
kallon khairat nasan Ka kamu. Wai Na kamu
rufamin asiri indai wanan yarinyan sunanta
khairat tau gaskiya kun tabka babban kuskure
domin Kuwa itace tayi yinkuri kashe saurayinta da
matarsa yanzun haka suna asibiti. Usamat na
zaune baisan lokacinda yayi buzut! Ya mike
tsayeba. Kai! Abokina kodai mai kama da itace?
Tabbas itace idan kuma kayi gardama mu koma
Ka tambayeta ko tasan DR sadiq. Hakika wanan
labarin ya katsema usamat farin cikin da yake ciki
domin Kuwa kamin duk ya tabbatarda khairat ce
ta aikata wancan aika- aikan duk yaji ya tsaneta./ DR SADIQ novels / DR SADIQ part 15
DR SADIQ part 15
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Dec 2016 - 21:42
Haka usamat ya wuni sakaka tamkar wanda
bayada lakka a jikinsa tun iyayensa basu gane
halinda yake cikiba har yakaiga mahaifiyarsa ta
fahimci halinda yake ciki, saidai ba yadda batayi
juyin duniyaba Amman yaki ya fada sai karyar
bayada lafiya yakeyi. Yadda yaga dare haka yaga
rana domin Kuwa kwana yayi yana tambayar
Kansa waima idan khairat ce ta aikata wancan
danyen aiki menene tasa a ciki? Tau Amman idan
Ka koreta yaya zakayi da shakuwar da ke
tsakaninku? Gaya kuma tace batasan kowaba
anya wanan maganar nata gaskiyace? Itafa ba
karamar yarinyabace, Duk wayanan tambayoyin
usamat ne ke yiwa zuciyarsa, amman ya kasa
samun amsoshinsu. hakan yasa kawai ya yanke
shawaran gobe da safe kawai ya tunkareta da
wanan maganan. Washegari usamat ya tashi
bayan yaje masallaci yayi sallah kaman yadda ya
saba ya dawo ya shiga dakin mahaifansa domin
ya gaidasu kaman yadda ya saba. Bayan ya
samu wuri ya zauna ya Dan donarda Kansa kasa
cikin sanyayyar murya ya, ce amincin Allah ya
tabbata a gareku ya mahaifana. Da fatan kun
tashi lafiya? Suka amsa masa, har yana batun
tashi Amman mahaifinsa yace yauwa mai sunan
baba daman ko ina nemanka domin ko baka zoba
zan aika a nemoka. Usamat na jin haka saida yaji
gabansa yayi dakan uku-uku. Waa! ni abba?
Halan bayan kai akwai wanda yake cema mai
sunan baba gdanan? Mahaifiyarsa ce ta fada.
Usamat ya Dan shafa Kansa sanan ya koma ya
zauna yayi shiru. wai yaushe wanan yarinyar zata
bar gidanan? Usamat ya dan donar da Kansa
kasa sanan ya,ce cewa tayi tanaso taga yadda
ake bikin aure a garinan inaga bayan aurena zata
tafi. Sallamar da kabir yayi shi ya katse maganar
da usamat keyi don yasan kabir akwai surutu
kaman Suda Zai iya shiga maganar har karshe ya
bijiro da maganar jiya. Bayan ya gaida mahaifan
usamat sanan ya samu wuri ya zauna sanan yace
usamat wai Ka fadama su dad batun maganarnan
ta jiya? Wacce magana kenan? Usamat yace a'a
bakomai Abba. Kai na tambaya? Kabir fadamin
meke faruwane? Usamat nata kokarin kyallamar
ido kar ya fada Amma ina zanzari kawai yakeyi.
Abba yarinyarnan da na gani gidanan gaskiya
indai itace khairat tau lallai itace tayi yinkuri
kashe saurayinta da matarsa yanzun haka suna
kwance a asibiti. Karar faduwar akushinda ke
hanun khairat yasa kowa saida ya waiga. Khairat
ce tsaye kwalla na fita daga idanunta, ta gurfana
gaban su. Don Allah ku gafarceni tabbas duk
abinda wanan bawan Allah ya fada gaskiyane. Ba
a son raina na boyemuku halinda yasa na gujema
kaddarar da take bibiyataba sai don ba yadda
zanyi in iya kubutarda kaina akan wanan laifinda
ake zargina. Hakika ni na aikata Amman wallahi
ba a son rainabane. Ta yaya zan kashe abinda
rayuwata ta ginu a Kansa? Abba ku yarda Dani
wallahi kaddarace da rudin shaidan Amman
wallahi yanzun na yarda, dan Adam baya iya
kubucema duk wani layin kaddara da
mahaliccinsa ya shatamai. Usamat Ka gafarceni.
Ka yarda Dani amman ban zamo yadda kake
tunaninaba ina mai rokonka gafara Ka yafeni.
Mahaifiyar usamat ce ta kama hanun khaira tana
lallashinta kada ki damu duk dan Adam ajizini
mudai mun yafeki, saidai yafiyarmu ba zata taba
yimiki amfaniba har sai kin roki wayanda kika jefa
cikin halin 'ka'ka nikayi. Wanan tabbas haka yake
Allah ya yafemu ga baki daya. Mahaifin usamat
ne ya fada. Abba nima ina rokonku da ku yafemin
son zuciyane yasa naso inki bin umurnin da kuka
bani, tabbas Yau na yarda da Karin maganan da
hausawa suke cewa (abinda babba ya hango
Yaro ko ya hau jirgin Samane bazai hangoshiba)
Kasancewar kabir shi yasan asibitin da aka
kwantarda su Dr sadiq da matarsa ummi yasa shi
ya yima khairat, usamat da kuma mahaifinsa
jagora. Isarsu asibitin keda wuya inda suka
cimma jami'an tsaro da kuma 'yan jarida sunyi
dandazo kasancewar labarin yaja hankalin
mutane da dama harma wajen kasanan.
Sakamakon an baza hotunan khairat a ko'ina
yasa 'yan jarida na ganinta sukayi chaa! A kanta.
Amman tuni su sajent jonah sukayi dirar mikiya
akanta. Su usamat da babansa suna magana
Amman ina don ko 'kala basu ce musuba dole
suka hakura suka ja baya domin sunsan wurin
bindiga wane 'kyastu. Da wani kurtu ya yimata
wani mazga sai gata a kasa some, general na
ganinsu ya,ce well done. Idan ta farka ku kaimin
ita gida ku tsare min ta don jiya munyi waya da
mahaifinta gobe Zai zo ya wuce da ita turai kowa
ya huta. Haka suka kwarara mata ruwan sanyi a
jiki tana bude ido Dr sadiq ta fara arba dashi.
Amman saidai kash!! Domin ko baya iya gane
kowa sanadiyyan matsalar kwakwalwar da ya
samu, tasa hatta mahaifansa sai da baya ya dan
fara ganesu. Itama ummi ta fara jin sauqi domin
Kuwa da ita ake faman jinyan Dr. Yanzun kam ba
wadda Dr sadiq ya shaku da ita bayan ummi.
Bayan sati biyu aka sallamo su ummi da Dr,
dinta, iyayensu murna har kunne domin Kuwa
sunji dadin halinda Dr, ya shiga don Kuwa hakan
shi ya ceto rayuwan shi daga halin 'ka'ka nikayi
da khairat ta jefashi. Basufi shekaraba ummi ta
haifamasa diya tagwaye, kai da Ka gansu ba sai
an fadamakaba kasan tabbas diyan Dr sadiq
domin shi suka biyo.
adsense 2 here