Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 3 April 2017

Gani ga Wane complete

adsense here πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™† πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™† πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™† πŸ™†πŸ™†πŸ™†πŸ™† πŸ™†πŸ™†πŸ™† πŸ™†πŸ™† πŸ™† *GA NI GA WANE......* *A TRUE LIFE STORY* _BY MAMAN USSEEY😘_ 0⃣1⃣ To πŸ”š " *Bissimillahir rahamanir raheem Dasunan Allah mai rahama mai ginkai wan nan labari yafaru ne da gaske da fatar zamu kiyaye da duk abinda wan nan dan guntun labarin zai Karantar Allah yasa mudace Ameen Mai wan nan labarin ta boye sunan garinsu cox of gudun magana*" " Sunana Hafsat, amma a k'auye mu ana kira na Hafsee shekaru Na 24 Mahaifinah, headmaster k'auyen mu ne, Mahaifiyata ita kadaice matarsa , mu shidda ne a gurin Iyayenmu, maza 5 Sai kuma ni kadai mace, Tun inna ss1 abokin yayanah ya nuna, " Yana sona, a lokacin Yana ABU Zaria yana karatu, iyayena suka bashi damar magana da ni, amma Dana kai karshen ss2 sai maza suka yi ca akaina kowa na sona da aure kasan cewa ni wankan tarwadace ce , dogowa ga gashi kai wasu ma suna mini kirari da *African beauty queen* Lol😜, Amma duk wannan bai taba yaudara ta ba , tunda nayi ma *Yusufa* alkawari ban kara kula kowa ba, Ko samari sunzo gidan mu zance wuri na bana fita , har ya kai Mahaifina ya fara fita da kanshi Yana gayawa duk wanda ya zo wuri na anyi mini miji. A kwana a tashi na gama secondary lokacin *Yusufa* Yana NYSC a Kaduna, ni kuma da saka makon SSCE na ya fito na ci sosai duk da inna k'waunar *Yusufa* Ina da burin karatun aikin asibiti (ko likitanci ko nurse) domin in samu in taimaki yan uwana mata a fannin haihuwa, Amma kas......! Mahaifina ya k'i , ya ce Yana tsoron bari na zuwa garin da ba dangi karatu kada mazan zamanin nan su yaudare ni. " Haka na hakura nayi zaman jiran *Yusufa* har ya gama NYSC ya samu aiki a Secondary School a Kaduna a kayi biki muka tare Kaduna da zama. Gidan haya ya kama daki 2 da falo , cikin gidan apartment 4 ne , duk cikin matan babu wace ta wuce shakaru 25 munyi zaman ammana da hadin kai, kasance ni mace dayace a gidanmu, sai na dauke su tamkar yan uwa. A Kwana a tashi na samu ciki na haifi Faisal, Yanada wata 6 nasake samu wani Cikin....nayi kuka Sosai amma sai *Yusufa* yayi ta bani hakuri,Ya nuna mini Haihuwa ai Arzikice kuma shiyanaso yara. "Haka na hakura har cikin ya girma na fara zuwa asibiti awo. A lokacin *Yusufa* ya samu aiki da CBN, kuma muka yi sa'a aka ajeye shi a office dinsu na Kaduna bayan training da suka yi a Lagos. *Yusufa* yayi mini alkawari Idan na haifu lafiya zan rubuta JAMB don ci gaba da karatuna. Ammah kuma sai dai kash...??? " Na haifu lafiya , na kuma rubuta JAMB na ci 231 kasan cewa *Yusufa* Yana kuya mini kuma ya samu mini lesson teacher Wanda yake koyamin abubuwa da dama . _Alhamdullah nasamu admission Bsc nursing_ "Zamu fara registration Sadiq yafara rashin lafiya😭, abun yaki ci yaki cinyewa , muka je asibitin a kayi duk Wani binciken da Za'ayi daga karshe dai sai a ka gano Sadiq Yana dauke da kwayar cutar *HIV*😳 " Likitta na fidin haka na daga kai na kalli *Yusufa* nace abun da ka dauko mana a wajen training din Kenan ko....??? ka cuce ni *Yusufa* 😭😭😭Ka cutarda yaron da baisan komaiba Zuciyata ta rufe na fara gani Biyu2 Faduwa nayi Kasa sumammiyya. "Bayan wani lokaci na. Farfado sai naga Yusufa na zaune akan kujera a gefe na Yana kuka, nace munafuki kukan me zaka yi , bayan ka cuce ni , Yusufa yace wallahi sweetie na rantse miki da Allah ban kula ko wacce mace ba , ba ma a lagos ba tun ranar da son ki ya shiga raina har zuwa yau da kika kasance uwar yayana . " Na ce rufe mini baki , ka samu bindiga kawai ka zo ka karasa ni. Yusufa yayi shiru daman can ba me yawan magana bane. Bayan Kwana biyu a ka salemu daga asibiti, bana ma Yusufa magana , ranar Monday da ya tafi office na tattara Kaya na, da yara na, na tafi kauye. Iyayena suka yi mamaki gani a gida ba tare da Yusufa ba, da na huta na Mahaifiyata ta bukaci jin Abinda yakawoni dan tasan wan nan Zuwan ba Lfy ba...Ban b'oye komai ba na labarta mata tun Farkon Rashin Lafeeyar Sadeeq har yanxu xuwana gida. Bayan Mahaifina yadawo gida aka Sanar dashi Dalilin zuwana gida bai dauki Zafi ba hasalima Yasaka aka kirani Tambayar Farko daya yi mini itace Tare da *Yusufa* Akayi muku gwaji...?? nace A a Sadeeq ne kawai akayi ma Yace nakoma Zai kira *Yusufa* Taji daga gareshi. Karfe 8 na dare mahaifina ya dau waya ya kira *Yusufa* yace mishi idan ba zai damu ba gobe da shi da ni da yaran zamu je Kaduna Domin Muje asibiti ayi msna Gwaji gaba ki Dayanmu, *Yusufa* yace toh Baba, amma yanzu haka Ina hanyar zuwa domin naje gida banga ban ga Hafsa ba na San Tayi yaji ne, shi yasa na biyo ta , nan da mintuna 20 zan iso gari Babana yace Allah yakawo ka lafeya ya ce amin kamin ya ajiye wayar. Isorwar *Yusufa* keda wuya Babana ya tambayi *Yusufa* me ya faruwa tsakani na dashi *Yusufa* ya maimaita mishi labarin kamar yanda nafadawa babana, Bayan yagama ne ya shigo ya gaida ummatah!!! " Babana yace mini ki shirya gobe da safe zamu je . Kaduna asibiti da maigidan ki domin ayi muku gwaji toh na amsa Banma bi takan *Yusufa* ba. "Washe gari kuwa tunda safe natashi na shirya nida yara muka kama hanyar kaduna har Babana ma a Motar *Yusufa*Da isarmu bamu tsaya ko ina ba sai Asibiti Bayan mungana da likita aka debi jinina Dana Yara da kuma na *Yusufa* _30mns_ " Akafito da Result Sai dai abin mamaki nawa dana. Sadeeq *Positive* na *Yusufa* da Faisal kuwa *Negative* .Ina Ganin haka nace. How comes..?? Ni ban sam ban yarda ba. Sai dai In *Yusufa*ya hada baki da likitane dan ce shi bayada To amma abin mamaki harda Faisal ma bayada sai ni kawai da Sadeeq...?? Mahaifina Da likita da *Yusufa* suka yi mini duk bayani amma ban yarda ba. Daga karshe suka ce in fadi wani asibiti muje , haka muka je wanni asibiti sakamako yanuna ni da dana Sadiq muna dauke da *HIV* Yusufa da Faisal kuma Basuda Komai. Nan fa na yarda nafara kuka ina rantsuwa ba San komai akan wanna cutar ba kuma ban taba ko maganar soyyaya da wani ba da nake budurwa har zuwa aure na" " *Yusufa* yace yi hakuri Hafsa ni na cancanta in bada wanna shaidar a kanki. Ni nafi zargin asibitin da kika haifu, Yusufa ya ci gaba da ce wa tun lokacin da aka ce sadiqu na dauke da *HIV* na san akwai wani abu a boye da ba mu sani ba amma kin ki bani lokaci muyi shawara. "Yanzu lawyer zan dauka Zanyi karan asibiti da kika haifu zanyi. *Yusufa* dai yayi Karan asibitin , maganganu yafara yawa a unguwa matan da muke zaman haya suka juya mini baya basu kula ni , zaman Kaduna ya gagare ni dole na kuma k'auye da zama. 5 Month da Yusufa ya kai kara aka Kore kara sabida rashin kwakwaran shedu daga bangaren mu. Ciki matan da muke zaman haya gida daya dasu dayar ita ma ta je asibiti awo aka gano da ita da maigidanta suma suna dauke da kwayar cutar *HIV* , sauran majajen gida suka kai mata su gwaji a ka gano dayar matan na dauke da cutar *HIV* amma mijin da yaran duk babu. Abun dai ya zama abun mamaki da ban tsoro , mata Hudu a gidan haya da mazan su na dauke da *HIV* a lokaci guda , ko meye dalilin..........? cCkin mazajen wasu na zargi matansu matan ma haka , har ya kai dayan ya saki matarsa kasance war bashi da shi a lokacin gwajin. Bayan kwanaki wani likita a unguwan ya bawa mazajen mu sawara da a tara mu a bincike mu,Wata k'ila akwai wani abu da muka sani dangane da wan nan lalurar. *Yusufa*ya zo k'auye ya dauko ni, daman tun a lokacin na ki zaman Kaduna nace ya sake ni kawai tunda shi bashi da cutar amma ya ki. Da muka iso aka fara binciken mu duka mu fadi wani abu da muke saya ko sha dai2 sauransu Binciken dai yanunawa cewa duk kanmu Muna yawan, *AMFANI DA MAGANIN MATA* " Wata Hajiya Haleema da mijinta yarasu a abuja shekaru 4 da suka wuce itace me kawo mana mu saya. " Haka aka kira ta aka tambaye kotanada masaniya akan hali da muke ciki kuma ina take samun maganin da take sayar mana, sai tace a kasuwa take saya wasu kuma tana hadawa da kanta. Daga na suka ce ko zata taimaka a je asibiti da ita Domin ayi mata gwaji *HIV* Sam taki amincew ta fara ruwan Bala'in wai za'ayi mata sharri ne tace bazara ba abu karma wasa saida a ka kaita police station, yan sanda Sukasa akayi mata gwaji abin dai ba'acewa komai Har za'a turamu koto , nan fa ta fara kuka tace mijinta ya mutu da *HIV* Shine ya Laka mata Shine ta Kudiri niyar Itama saita Likawa wasu Sabida batajiba bata, ganiba aka Roro mata Bala'i . Tace: akwai ranar da ta sayi maganin matan a kasuwa na ruwa wanda ake sawa a gaban mata , sai ta bude duk kwalba 20 da ta saya ta ringa diba ruwan gaban ta tana hada wa da magani sai ta rufe kwalban, ranar ne ta zo gidan mu dama mun saba saya, tace mana ga sa maza tsalle , yafi duk Wanda muke saya kwau, #1000 each muka saya a lokacin ina dauke da ciki 7 months. Duk muka saya mukayi amfani da shi cikin daren ranar washe gari muku gayawa junan mu munji dadi magani: Fatima ce kawai tace batayi amfani da shi ba saboda Bakonta dayazo cikin dare, bayan kwana biyu mijin ta. Yana neman allura da zare zaiyi dinki ya gani , ya tambayi Fatima me zata yi da wannan sai tayi shiru ya dauka ya jefar yace daga yau idan kika sake yin amfani da wannan magunguna ba yafe ba, daga lokaci Fatima bata sake saya ba kuma bata tayi mana bayani ba sai yau Dalili da yasa Fatima ta tsira daga cutar *HIV* kenan Halima mai maganin mata ta ci gaba da cewa ba ta San yawan mata da ta sayar wa maganin ba. In takaita muku labarin rayuwata, yanzu shekaru biyu da faruwan haka, Halima ta rasu, Aisha matar da mijin ta ya sake ta ita ma ta rasu daga complications from cervical cancer, khadija kuma suna tare da mijin nata suna Shan magani. Sai dai kash..... 😰😰😰😰😰, ni mun rabu da *Yusufa* kasancewa shi bashi da cutar *HIV* bayan duk wannan shekarun . "Yanzu haka na sake rubuta JAMB na samu 267 an bani MBBS 1, *Yusufa* Bawan Allah bsi ajiyeni ba ya saya mini gida da mota da masu aiki, kuma duk wata Yana bani albashi domin kulla da yaran da ni kaina, kuma yayi mini alkawari biyan kudin makaranta da text books ko wani shekara. Faisal dai Yana makaranta amma Sadiq gashi nan dai yau lafiya gobe ba lafiya, duk da maganin da muke sha😭😭 *Maganin mata yazama silar rabuwata da mijinah Dakuma jin dadinah* _END_ *SHAWARATAH GAREKU* _Please my Dear Sisters. Dan Allah kusan Irin Maganin da Zakuyi amfani dashi Wallahi Koma ba wan nan ba Akwai Ciyoyoka dayake coursing da dama irinsu. Cancer Infection Ciyon sanyi Dadai sauran Cututtuka Da Dama , kungadai Abinda yafaru ga Malama Hafsat In kunne yaji jiki Ya Tsira kukan Kurciya Jawabi ne Mai Hankali yake Ganewa......._πŸ‘‰ *UR'S ZEENAT YUSUF MRS. LAILABA* _Dedicated to all museums ummah_πŸ‘ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *