Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, April 3, 2017

GUGUWAR SO complete

adsense here [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣➡5⃣ By Harphsart Rano✍ Tafiya take cikin matsanancin tashin hankali wanda sam bae sa ta lura da inda take sa kafarta ba.. Tafiya kawae take hawaye ya wanke mata fuska.. Tana dana sanin kasance warta cikin wannan duniya.. Why? Why?? Shine abunda take ta nanatawa a zuciarta.. Wani matsanancin gudu yake a dalilin kiran gaggawar da akae masa cewa jikin mominsa ya rikice.. Bai lura da ita ba sam.. Sae dayazo daf da ita.. Wani wawan birki ya taka hade da danna horn iya karfinsa.. duk yanda yaso ya kauce mata be samu nasara ba sae daya bangaje ta tae wata razananniyar kara.. hakan ya jawo hankalin mutane da suke wucewa jefi jefi suka yo kanta dan kawo agaji.. Fitowa yae daga motar a rude "ohh shit damn it. Ya karasa wurin tare da nan russunawa a gabanta tana sheshekar kuka.. ta dan kurje kadan amma bata samu wani mummunan rauni ba.. mutane nata mata sannu suna Allah ya kiyaye gaba.. Ta mike jiki ba kwari ta kama hanya tana dan dingisa kafa, hakan yasa yae saurin shan gabanta tare da cewa pls kiyi hakuri dukda kece me laifi kina tafiya wt out checkin d road.. Bata tanka masa ba illa cigaba da tafia da tayi.. yace baiwar Allah ina sauri ne amma ga wannn ki saya magani.. A hankali ta furta ka barshi na gode.. Ta cigaba da tafianta tana dingisa kafa.. Noke kafada yayi alamun i dnt care ya fada motarsa ya bata wuta.. Allah Allah yake ya gansa gaban mominsa. Karfe shida da yan mintuna ya matsa horn a kofar wani hadadden get.. Me gadi ne ya leko ta wata yar kofa ganin me horn din ya sashi bude get din cikin ajama.. kafin ya gama budewa tuni ya shgo tare ta ftowa cikin sauri wanda har yaso ya mnta da rufe motar.. Ya juyo da sauri ya danna securityn motar ya haura balcony.. Momynah! momynah! Shine abunda ya shgo yana fada.. Yae saurin haurwa sama ganin ba kowa falon. Momy ya hango kwance kan sofa gefenta daddy ne,, sae twins en momy islam da iman.. Sae auta khalil wanda suke kira da little khaly , .. Saurin karasawa yayi ya rike hannun momy tare da cewa momyna ya jikin.. Shafa kansa tayi tare da murmushi tace my boy har ka iso.. Jiki alhmdlh.. Ya juya zua ga dady ya gaisheshi.. Ya amsa masa da kulawa.. tare da tambayarsa hanya .. su iman ma suka gaisheshi.. Bayan sunyi sallah sun dawo duk suna zaune a falo daddy yae gyaran murya yace dama inason na ftrda momynku india akan matsalar nan tata shine nake ganin mene shawarka?? Ya jinjina kai yace daddy shine tunanin da nake nima.. Daddy yace ina da bussnss da zae kaini india kuma atleast zanyi wajen 1month.. kaga sae mu tafi tarr.. Anan suka yanke shwaran ftar da momy india nxt week .. A hankali take tafia hadda karaso kofar wani kurkutacchen gida wanda duk unguwa babu gida mafi muni irinsa.. Tura kyauren gidan tayi hade da sallama.. Umma ta mike da sauri ta riko hannunta gami da cewa "Me faru dake nurr?? Me ya tsayar dake haka kuma naga kin shgo hankalinki a tashe ko wani abun kawun yayi miki?? Bata samu damar amsa mata ba saboda zafin da kafar ta ke mata ga wani zugi da dan yatsanta ke mata.. Umma ta cigaba shisa nace karkije karkije kika nunan ba abunda zae faru gashi nan abunda ya faru ta fada tana share kwalla da gefen zaninta.. Nurr ta fashe da kuka hade da cewa umma kafata zafi hannu na😭.. Mota ce ta bige ni umma.. Umma ta rafka salati mota nurr garin yaya?? Ta wawuro hijabinta tace wuce muje wurin habu me chemist ya dubaki.. Nurr ta riko hannun umma hade da cewa umma ina muke da kudin zua chemist.. Sai a lokacin umma ta tuno basu da ko naira biyar.. Ta rausayar da kanta gefe tace tou ya za miyi muje ko bashi ya bamu inasa ran hajia zata biyani kudina. Tace umma ba komi akwai ragowar rop bari na shafa ta wuce ciki tana dan dingisa kafa amma bata bari umma ta fahimta ba saboda taga yanda umma duk ta rikice ita kuma bata son damuar ummanta.. Cikin sauri ya shgo rike da wata bakar leda yana shgowa ya tarar da ummansa da nurr a zaune a tskar gida nurr ta bawa umma labarin yanda sukae da kawunsu dazu.. Da sassarfa ya karaso ya jawo kujera yar tsuguno yace umma sannu da gida, ta amsa da abbana sannu da kokari Allah yai maka albarka.. Amin Yace umma wlh yau aikin ne baya tafiya sosae shisa kukaga nayi yamma. Amma ga abunda na samo gami da mika ma umma ledar. Nurr ta mike ta dauki leda ta shga wata yar rumfa ta dauko wani kwano ta juye Zogale ne da kuli kuli.. Ta zo gaban umma ta ajiye hade da komawa ta debo ruwa a kwano tazo ta ajiye ta koma gefe ta zauna.. kabir ne ya lura da dingishin da kanwarsa take ya juyo cikin kulawa yace kanwata me sameki a kafa?? Umma tace wlh mota ce dazu ta bige ta tana dawowa daga gidan kawunku. Subhanallah mota umma garin yya?? Nan umma ta labarta masa yanda nurr da shaida mata. Yace ai ya kamata aje a duba ko tayi targade ne.. Amma kuci abncin sae na rakata gidan talatu ta duba ko targaden ne.. Umma ta jawo kwanon suka fara cin abinci a hankali shikuma kabir ya kwantar da kansa jikin bangon hade da lumshe idonsa yana tunanin rayuwarsu... [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 5⃣➡1⃣0⃣ By Harphsart Rano✍ Yau ta kama monday, an gama wa momy shirye shiryen komai, wednesday jirginsu zae daga zua india.. Malam Idi me gadi ne yayi sallama ya durkusa ya gaida momy ta amsa cikin sakin fuska kasancewarta mace me karamci.. Hajiya wata mata ce a waje take son ganinki.. Tace tau ace ta shigo mana malm idi Ya mike yace an gama hajiya ya fice.. Ya koma inda ya bar matar ya sanar mata hajia tace ta shga.. Ya juya bakin aikinsa. Sallama tayi Momy ta kalleta cikin murmushi ita kuma tai saurin dukawa tace sannu hajiya ina wuni?? Lafiya lau jummai ina ta zuba ido ashw zakixo. Tace wlh hajia yarinya ta ce ta haihu dole sae dana fara biyawa na duba ta.. ayya me aka samu cewa momy, Allah ya raya. Bayan sun dan taba hira hajiya ta muskuta tace jummai kinsan laraba zan tafi india akan wannan matsalar tawa jiki yaki dadi yau cio gobe lafiya, shine nakeso ki samo min me aiki dattijuwa wadda zata kular min dasu khalil.. Kanwar Alhaji ce da zatazo kuma aka samu yar matsala. Jummai tace ayya hajiya in sha Allahu zan samo miki zuwa gobe tunda jibi ne tafiyar taku. Momy tayi godiya. Salamu alaikum, salamu alaikum.. Umma ta fito daga daki tana gyara dankwali wa alaikumussalam jummai ce a gidan namu? sannu da zuwa. Bayan gaishe gaishensu jummai ta kalli umma tace dije alheri ne ta kawo ni fa, umma ta muskuta tana murmushi tace Allah jummai?? Tayi shewa tace wlh dije wata hajiya ce take niman wadda zata kular mata da yaranta guda uku zata fita india neman lafiya. Umma tae daria tace kai haba jummai, jummai tace shine naga ba wadda ta chanchanta sae ke. Amma ya kika gani?? Umma tace wlh jummai nakuwa gode me zae hana nayi dama zaman nan ya ishen ga yarinyar nan an korota a makaranta bamu da kudi. Kinga in na fara aikin zan dan ragewa kabiru wasu wahalhalun.. jummai tace tou sae ki shirya gobe da safe sae muje kiga gidan.. Umma ta rako jummai bakin zaure tana kara mata godiya da alkawarin in sha Allah zata shirya da wurwuri.. Da daddare suna zaune akan tabarma ita da umma wanda ta lura umman na cikin farin ciki, ta numfasa, umma wai me faru ne na ganki cikin farin ciki yau.. kafin umma ta bata amsa kabir ya turo kyauren ya shgo.. A ah umma da autarta ya fada yana murmushi. Nurr ta turo baki umma kinga yaya ko? umma tae daria tace kadowa abbana.. ya sami gurin ya zauna gami da cewa wash umma wlh na gaji.. Tace ai dole sannu allah maka albarka.. Nurr ta mike ta debo ruwa ta dan russuna tace yaya ga ruwa. yayi mrmushi yace nagode kanwata.. Umma me ake tattaunawa ne na shgo na ganku cikin annashuwa.. Umma tayi murmushi tace albishirinku? Na sami aikatau gidan wani alhaji dazu jummai tazo take gayan yanzu gobe zanje naga gidan.. kabir yae saurin ajiye kwanon ruan hannunsa yace umma aikatau kuma?? Me zakiye da aikatau umma?? Kin manta wulakancin da matar nan tae miki umma.. ? Gaskia sam ban amince ba umma, zanyi iya kokarina naga na kyautata rayuwarku umma.. In sha allahu koame ya kusa zua karshe.. Umma ta murmusa tace abbana bawae na raena kokarinka akanmu bane.. Amma aikin nan zae taimaka mana ko da kudin jarrabawar kanwarka , sannan kuma nasan zamu dinga samun abinci kaga an samu sauki.. Yayi yake yace umma bawai naki ta taki bane amma umma wulakanci nake gudar miki. Umma tace kayi hakuri in sha Allah hakan bazata faru ba kuma watarana sae labari.. Yae shiru na dan lokacin hakan ya bawa umma damar maida kallonta ga nurr wadda tunda aka fara magana bata samusu baki ba.. Wannan na daya daga cikin dabi un nurr bata taba magana inde ummanta da yayanta na magana. Umma tace yadae auta baki ce komai ba, tayi murmushi tace umma duk yanda kuka yanke yayi.. Kabir ya ce umma ba komi Allah zaba abu mafi alkhairi ya mike game da cewa bari na samo mana ko breadi ne ya fice.. Umma ta bisa da kallo tasan har ga Allah bae so aikinta ba amma ya za tayi zaman ya ishe ta haka.. Tunda nurr tayi sallar asubah bata koma barci ba ta tashi ta fara kichiniyar shirya gdan saboda tanaso tabi umma gidan da zata in taga zaa wulakanta ummanta dole ta hakura ita taji zatae aikin umma kuma ta dawo gida.. Umma ta fito ta tarar da ita tana shara bayan ta hada itace ta dora musu ruwa kasancewar ana dan sanyi garin.. Sannu yar albarka taji ance tae saurin juyowa da murmushi ummana har kin fto.. Ina kwana?? Umma tayi daria na fito auta sannu kinji. Ta ajiye tsintsiyar ta zari bokita ta zuba ma umma ruwa ta kai mata bandaki ta dawo tace umma ga ruan chan na kai.. Nagode miki Allah miki albarka Bakwai daidai sun gama shiryawa suna jiran jummai.. Kabir ya fto yace umma har kun shirya kenan. Tace Mun shirya abba jummai muke jira, ga kokonka chan cikin kwano.. sallama suka ji wanda yake nuna isowae jummai.. bayan gaishe gaishe suka dau hanya sae gidan Alhaji naseer.. [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣0⃣➡1⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Sun isa gidan misalin 8:30 dalilin dan tarazar dake tsakanin unguwowin biyu.. Jummai ta jagorancesu zuwa falon inda suna saka kafa Nurr taji wani ni imantaccen sanyi ya buge ta.. ta lumsje idon ta tana ayyanawa aranta lalle masu kudi sun hutu abunsu.. Wuri suka samu suka zauna suna jiran fitowar matr gidan. Nurr ta rakube a gefe tana tunanin koya zaa karbe su a wannan gidan me kama da aljannar duniya.. Allah sa kar a wulakanta su.. Suna nan zaune suka ji karar saukowa daga sama.. Zuru sukae gaba daya suna jiran suka me saukowa.. Da fara'ar ta ta karaso a ah jummai ashe kun karaso.. gaba daya muka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska.. Duba daya nurr tai mata ta fuskanci mace ce mai kirki.. Nan ta ji hankali ta ya kwanta.. Hajiya wannan itace dije wannan kuma diyarta ce Allah yasa tayi miki ta fada tana washe baki.. Hajia tai murmushi tana kallona nida ummata tace ba komai jummai tayi nagode kwarai.. Ina fata kin sanar mata kamar yadda mukae kuma Allah sa zata iya.. Sae a lokacin Ummata tae magana in sha Allah hajiya zanyi iya kokarina.. Hajiya ta jinjina kanta tace ba komae dije.. In sha Allah gobe aikin zae fara sae maganar kudin aikinki.. zamuyi wata akalla zan biyaki dubu goma yayi miki.. Umma ta zaro ido dubu goma hajiya kai amma nagode.. Wani murmushi na saki A zuciata nace Alhamdulillah.. *Next day* Kina ina ? Ko kinaso mu makara ne?? Ganinan umma ta fto rike da hijab dinta a hannu ta. Tayi wa umma murmushi tace muje umma.. Suka fito suna tafe suna dan taba hira har suka samu abun hawa kasancewar hajia ta basu kudi jiya dashi suka samu suka hau keke napep. Nassarawa Gra suka ce masa yace bismillah.. Suna zaune a falo gaba dayansu, momy, daddy,, khalil da twins mutum daya ne babu.. khalil sae zuba ma momy shagwaba yake " ni gaskia momy na sae na biki ni bazan zauna ba.. Iman ta kallesa c dis boy tau skul dinfa zakace sae ka bisu.. Islam ta karbe kyalesa sis kinsan dama shi karatun be dameshi ba.. yana jin haka ya kua kara turo baki kinji su ko momy?? Momy tayi daria tace rabu dasu little ina zua zan turo jet ya dauko min kai.. ya saki ihun murna are u crioux mom??( khalil yana son jet a rayuwarsa inde kace zaka sashi a jet zae daena abunda yke) Tace ofcourx kaide make sure u r obedient to ur sis sannan kuma banda rashin ji kaji my son. Yae nodin kansa .. A hankali suka tura gate en gidan malam idi na zaune ya gane su jia hakan yasa be dakatar dasu ba suka gaisa a mutunce Karasawa sukai cikin falon gami da yin sallama dukkansu suka juyo suna kallonsu.. momy tace a ah dije kun karaso yanzu nake tunaninku a raina.. ku karaso mana.. Muka karasa muka zube muka fara gaishe su daya bayan daya.. Momy ta kalla daddy tace Daddy wannan itace dije ita na dauko nakeso ta kula dasu little.. Daddy yae murmushi yace ba komi duk yadda kikae yayi.. Har ga Allah sae yaji matar ta kwanta masa.. Momy ta kalli su twins tace dis is ur new nanny.. Suka ce owk mom. Khalil ya mike ya karasa gurinsu umma ya tsaya yana kallon nurr.. Ya juya yace momy dis luks like barbie ta cikin cartoon din disney.. gaba dayansu suka sa dariya.. Momy tace amma fa dije na mnta ban sanar miki ba ko zaki bar nurr ta dunga kwana dasu iman kinga in kika zo kika wuni ita kuma sae ta kwana.. Sae ya zama albashinta daban Dije ta jinjina kai tace hajiya matsalar shine Nurr tae sauri cewa ba komi hajiya zan kwana dasu.. Momy tae murmushi tace na gode nurr.. Dama naga alamun ma tasu zatazo daya da little kinga ya samu abokiyar hira.. Umma ba yadda ta iya dole taja bakinta tai shiru amma zuciarta bata so wannan hukuncin da nurr ta yanke va.. Nurr din da bata fi a kula da ita ba ita zata kula da wasu.. Amma kuma ya zatai tunda ta amsa zatayi ai shikenan.. Tasan dae dole kabir yaji haushi. Umma ta dukufa aiki nurr na tayata kafin kace wannan sun kyara ko ina.. Momy ta kwala wa umma kira tace nurr taje ta shirya little cox 12 flight dinsu zae daga.. Duk sun fito suna tsaye a falo daddy yace wai ina *safwan* ne.. kinsan shifa da nauyi iman je kira bro enku tym yana wucewa.. Am so sorry dad gani na fto suka ji daga bayansu.. Saukowa yake yana daura agogo a hannunsa.. Momy ta kira umma tace ga dije nan zata zauna dasu little har mu dawo.. Batare da ya tsaya ba suka gaisa ya fice yana we are about to b late.. *12:30* jirginsu momy ya daga.. su iman suka juyo gida bayan sunga tashin su.. [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣5⃣➡2⃣0⃣ By Harphsart Rano✍ Parking yayi a daedae kofar gidansu ya juyo ya kalli khalil yace oya ku shiga gida i am goin sumwhre.. Owk bro suka amsa gami da bude motan suka fita suna waving nasa, sae daya ga shigarsu sannan ya wuce.. Zaman su da umma ba karamin dadi yake musu ba saboda Allah yayi umma mace mai kirki ga fara a da sakin fuska.. Khalil kua bashi da abokiyar hira sae nurr kullum suna tare. Umma nazuwa kullum da safe ta tafi da laasar,, Shiko dama safwan bae cika zama da rana ba sae dare yake shigowa. Yau saturday ta kama ba aiki wanda yae daedae da kwanan nurr 3 a gidan amma basu taba haduwa da safwan ba wanda taji khalil na cewa big B. Islam da iman zaune suna breakfast ya fito sanye da jallabiyya fara yaja kujera ya zauna kusa da islam.. har rige rigen gaisheshi suke.. Morning bro suka fada suna murmushi yace morning an mata momy.. Ina little?? Iman tae charap tace yana gurin anty nurr shi wai da ita zaeci.. Nurr yaeta maimaita sunan a zuciyarshi.. Owk wace nurr ya tambaya?? Islam tace laa bro baka san anty nurr ba?? Ita cefa take zama damu tunda su momy suka tafi. Owk gud ya furta ba tare da ya fuskanci wace nurr ba.. Ya jawo plate ya zuba chips ya hada tea.. Yana zaune a garden yana duba wani aiki a system dinsa ya jiyo hayaniya.. Ya tsaya da abinda yake ya kura wa hanya ido don ganin meke faruwa.. Gudu yake tana biye dashi yana ihu wooo bata kamani na.. saura kadan ta bige safwan wanda sam bata lura dashi ba.. Wata razananniyar tsawa ya daka mata wanda yasa su saurin dakatawa suka juyo duka a firgice.. " Who d hell d u think u r da zaki shgo kina ma mutane ihu da hauka?? Tae saurin durkusawa ta kama hannunta alamun tana bashi hakuri ,ta runtse idonta.. Siririn hawaye ya gangaro daga idonta.. Ya dan dube ta kadan, ina nasan wannan fuskar?? Ya shiga ayyanawa a zuciyar sa? Ganin bashi da amsa yasa ya tabe baki ya kara dubanta galala.. Get out frm here.. Ta tashi da gudu tae cikin gida tana toshe bakinta don kar kukan da yaci karfinta ya fito Ya juya ya nuna khalil come here ban hanaka ihu ba?? U kno banason hayaniya shine kake mana ihu ko?? Yai narai narai da ido m sorry bro it was a mistake.. Tsaki yae yace oya shige gida b4 i change ma mind.. Ya wuce da sauri har yana bigewa.. Ta gudu ta fada kan gado ta saki kuka.. me tayi masa zai mata wannan tsawar? Da tana tunanin batada matsala da gidan nan ashe babbar matsala na gaba, dole tae ta katsantsan don ta gane wannan shine big B da khalil kullum yake mata zancen sa.. Khalil ya shigo ya zauna kusa da ita ya kwabe fuska kamr zaeyi kuka.. m sorry anty nurr it was ma fault.. Wannan big B en ya fiya fada ki rabu dashi kinji?? Ta dago tana share hawaye yae maza yasa hannu yana tayata gogewa. Wani abu ya rada mata a kunne Sukae dariya alokaci daya suka mike rike da hannun juna.. Yau ta kama sati biyu da tafiar su momy, Suna zamansu lfy gwanin bn shaaawa, in ka gansu sai ka dauka sun dade da sanin juna, bangare safwan kuwa tun ranar da abun ya faru bata sake sashi a ido ba, wani lokacin Tana jin hirarsu da kannensa wanda yake hanata fitowa har sae sun gama taji alamun ya bar wurin.. Suna zaune a falo around 9 suna kallon cartoon a mbc2 , Nurr ta lura da khalil yana jin barci amma don kar su iman su chanja channel yaki yarda ya kwanta,, Kam kam ya rike remote en ysa tv a gaba kamar me daukar karatu.. Little naga kaman barci kake ji zo muje ka kwanta.. Ya noke kafadansa Noo ni bazan je ya amsa mata.. Chan ta lura da yanda yake rufe idonsa alamun barci yaci karfinsa.. Ta taso tazo gaban sa ta riko hannunsa zata dga shi yai saurin bude ido, tace oya muje a kwanta.. Ya kwace hannunsa , ni bazanje ba sai dae in a dakinki... Tace olryt Ta daga wa su iman hannun alamun tana zuwa. Ta zare jikinta a hankali ta mike zata fice taji an riko hannunta, ni bazan kwanta ni kadai ba ba yace.. "Ohh shit" khalil problm ta furta a hankali ta dawo ta kwanta gefensa Ka idar sa ne duk dare sae yaje ya dubasu yake kwanta wa.. yauma hakan ta kasance ya fto daga shi sae boxer sae singlt fara.. Yana saukowa yaji alamun tv a falo, Tunani ya fara kardai yaran nan basuyi barci ba?? Ya karasa shigowa falon, iman ya gani kan carpet da remote tana ta sharar barci sae islam akan kujera.. Tuni yaji tausayin kannensa ya kamasa Mesa baya zama dasu since vasu momy.. Ya shiga tunani, u r always busy en more ever baka son hayaniya wani part en zucianshi ya bashi amsa.. Daukarsu yayi daya bayan daya yakaisu daki.. ya lullubesu ya jawo kofa.. Har ya juya zae tafi ya tuno be duba little ba, Ina ya shiga? Ya juya da sauri ya koma falo, baya nan, ya hau bude bude dakunan duk ba khalil.. Dafe kansa yayi alamun damuwa a fuskarsa.. Nan take ya tuno bae duba dakin kasa ba, ya sauko da ssuri ya bude kofar Suna kwance cikin kwanciyar hankali, little ya dora kafarsa akan cikin nurr ita kuma ta rungumosa zuwa jikinta.. Karasawa yae bakin gadon ya tsaya yana kallonsu.. Ya durkusa daidai fuskarta yana kare mata kallo,. Wow shes cute zuciyarsa ta gaya masa.. buh shes young ya bawa zuciyarsa amsa.. yayi wani murmushi da baisa na mene ba, sannan ya mika hannunsa ya gyara mata gashinta da ya rufe mata fuska.. Motsawa yaga tayi yae sauri mikewa.. Ya jawo blanket ya rufesu ya juyo a fice.. [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar 🎀 2⃣1⃣➡2⃣5⃣ By Harphsart Rano✍ Bayan ya fito ya tsaya jikin kofa yana tunani.. Dama a talakawa akwai masu kyau (kaji safwan😅).. Amma kuma tayi karama ,shikuma a tsarin sa ya fison matured mace irin yar jami ah.. (lalle ma safwan dinna)..lol Ya koma daki ya kwanta ya rufe ido amma kwata kwata barci ya kaurace wa idonsa. wai meke damuna ne? Ya ayyana a ransa, mesa zan tsaya wannan yar karamar yarinyar.. Mtsw yaja tsaki gami da mikewa, yajawo system dinsa ya cigaba da aiki, duk dan ya mantar da zuciarsa.. Bayan ya shirya cikin bakar suit, ya dauko brief case dinsa ya fito yana duba tym.. 7:05am agogon ya nuna.. Zaune ya samesu sun shirya cikin uniform, suka gaisheshi cikin girmamawa.. Wayarsa ce tai kara, Ganin me kiran yasa shi saurin dagawa hade da yin sallam Lafiya kalou daddy ya ambata, hakan ya nuna da wanda suke waya. Jin haka yasa khalil matsowa da sauri kusa dashi Bayan sun gama magana da daddy, ya mika musu wayar daya bayan daya sukai magana da iyayen nasu.. Ganin khalil zae bata musu lokaci yana tai wa momy shagwaba, yasa shi saurin karbe wayar yace momy zusuyi late a skul.. Sukai sallama ya kashe. Yace me kuke jirane?? Iman tace malam habu muke jira bae zo ba har yanzu,.. lalubo number malam habu yayi yai dialin, ayya Allah ya bata lafiya ya fada yana sauke wayar.. Sae ku tashi mu wuce na sauke ko.. Malam habu bazae samu zuwa ba.. Islam tace tau in munje wazai dawo damu?? Ya shiru yana tunani, gashi yana da important abunda zaeyi yau dinnan.. Chan idea ta fado masa, yace jeka kira mun wannan dinnan, Wae anty nurr? Khalil ya tambayasa.. Umm ita, ya amsa ya fice su islam suka bi bayansa.. Yana ganin fitowarsu ya kauda kai, dauko hijab dinki ya fada ba tare da ya kalleta ba.. Ta juya da sauri duk a tsorace take dashi tun tsawar nan da yayi mata.. Daedae bakin gate din makarantar suka tsaya, su iman suka fita daga motar suna dagawa yayan nasu hannu.. Ganin bae ce mata komai ba yasa itama ta kama kofar zata bude.. Ina zaki kuma ya fada cikin husky voice dinsa, jikinta ya dau rawa.. ya dan kalleta ta mirror ya tabe baki, Inaso anjima by 12 kixo nan skul din ki dauki su khalil.. Hope zaki gane hanyar ya fada yana dubanta.. Ta dago da idonta karap idonsu ya hadu, wani shock yaji tun daga kansa har kafarsa.. Ya dan kura mata ido kadan sae kuma ya basar.. Ita dinma kasa magana tayi don ganin yanayinsa, tunani take zae kara mata wata tsawar.. Bata gama tunani ba taji yace dake nake magana, cikin inda inda tace eh zan gane.. Sae ki dawo nan mu wuce inada abinyi. Ta fto jiki na rawa ta koma gaba.. Daidai bakin gate ya tsaya ya zaro dubu daya ya mika mata.. Ga kudin napep Hannu biyu tasa ta Karba ta wuce, sae bayan ta shige ya wuce yana tunanin abunda yake damunsa kwana biyun nan.. Mesa yake jin wani irin abu akan wannan yarinyar.. Kuma shi yana ganin kamar ma ya santa.. Ya taba ganin face dinta amma kuma ya manta aina ba... Tana shiga falon ta tarar da umma tazo har ta fara aiki.. Ta ajiye hijab dinta agefe ta karba moper hannun umma ta cigaba da aikin.. Nan take bawa umma labarin abunda ya faru tsakaninta da safwan.. ita fa tana tsoron wannan yayan nasu Umma tace karta damu kanta yanayinsa ne haka... Kwanci tashi ba wuya, yau saura kwanan su uku su momy su dawo.. Bayan umma ta dawo daga gidansu safwan.. shigowarta kenan, ta dauki buta don ta kama ruwa, taji an banko kofar gidan da karfi.. A tsorace ta juyo ganin kawu tsaye yana huci yasa tai saurin ajiye butar, baki na rawa tace kawun yara kaine a gidan sannu da zuwa.. Daga mata hannu yayi sannan yace cikin zafin rai, wlh dije kinyi asara, ban kara sanin bakida tunani ba sae yau.. Ace kidau yar ki kikai ta chan wani gida karuwanci.. Umma ta dago da sauri tana kallon kawu, ya dora" emana karuwanci don ban yarda da wani aiki da akace tanayi ba, Gidan aikin da masu gidan basa nan sae yayansu.. wanne irin aiki ne wannan dan an raina mun hankali an nuna mun bani na haifeta ba.. Tau wallahi ina baki shawara kiyi gaggawar zuwa ki dawo da ita kafin kiga hukuncin dazan dauka akanki.. Ya juya fuuu ya banko kofa saura kadan ya balla kyauren.. Umma ta tsugunna a gurin kirjinta na zafe.. Wai sae yaushe ne zata fita daga wannan matsalar ne.. Innalillahi kawae take maimaitawa..... Ko wacce irin matsala umma take ciki?? Menene asalin su Umma? Ina mahaifinsu nurr?? Ku biyoni.. 🤓 Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 2⃣6⃣➡3⃣0⃣ By Harphsart Rano✍ Dafe kirjinta tayi wanda ta kejin yana mata wani zafi... Tananan a tsugunne kabir ya turo kofa ya shigo, ganin halin da umma take ciki ya sashi saurin karasowa Lafiya umma?? Meke faruwa? Kasa amsa masa tayi illa girgiza kanta da takeyi,.. Kamata yayi a hankali ya kaita daki, Ruwa ta furta a hankali wanda yasa yae saurin juyawa ya kawo mata.. Bayan tasha ruwan ta lumshe idonta. Kasancewar umma na fama da hawan jini yasa yaranta suke kokari wajen faranta mata rai. Zuciyar kabir ta shiga tunanin me ya sami umma haka?? Yasan dai lalle koma mene ya matukar bata mata rai.. Nan take ya tuno ai yaga fitar wata mota kamar ta kawunsa lokacin da yake shigowa layin.. Jinjina kansa ya shga yi, yana ayyanawa a ransa; inde kuwa kawu ne wlh sae yaje har gida ya masa rashin mutunci.. Sae yaushe ne zae kyalesu su huta, wannan karon bazata sabuba... Ya gaji da cin kashin da ake musu, dole ya dau mataki... Bayan ya idar da sallah isha, ya tarar da umma kwance alamun tana jin jiki.. Sannu Umma ya fada yana dubanta da tausayawa.. Murmushii tayi masa wanda daga gani kasan karfin hali ne.. tace yawwa abbana.. Yace Umma ya kamata gobe da safe muje asibiti a dubaki, a awna bp dinki, dazu Alhaji ya bamu kudin aikinmu(kabir yana zaman shago ne a kasuwar kwari) Umma tace a ah abba na kudin zae mana wani amfanin.. Samomin paracetamol gurin habu me chemist, Ina sha shikenan, dama cion kaine ke damuna kawai.. Cikin dare umma jiki yayi zafi, sosae take jin jiki, kabir duk ya damu yana ta mata firfita.. Allah Allah yake gari ya waye ya kaita asibiti.. Gari na wayewa ya samo adaidaita sahu ya dora ta suka wuce asbiti.. Shiru shiru nurr tana sa ran ganin umma, hankalinta ya tashi tasan dole ba karamin abu ne zae hana umma zuwa ba.. Tana nan a zaune bayan tafiyar su iman skul, ta kasa tabuka komai, safwan ya sauko, kamshin turarensa ya sata juyo wa, kafe ta yae da ido yana dan nazarinta.. Basar wa yayi ya wuce zuwa dining area, Ina kwana tace, ba tare da ya kalleta ya amsa da lafiya.. Mikewa tayi a hankali tazo ta wuce shi ta shige kitchen.. To ita kuma wannan me yake damunta? Ya ayyana aransa.. da ganin yanda take bata cikin nutsuwarta.. Har zae fice, sae kuma yaji bazai iya tafiya ba tare da ya tambayeta meke damunta saurin juyawa yayi, tsaye ya ganta a kitchen tana goge cooker gas.. Alamu taji ana kallonta yasa ta juyo tae saurin tambayar sa ko wani abin yakeso.. Murmushi ya sakar mata wanda shi kansa bai san ya iya shi ba.. Mamaki ne ya kamata wanda yasa ta tsayawa galala tana kallonsa.. Ikon Allah, ashe yasan yanda yake bala'en kyau idan yayi murmushi shi yasa bayayi.. Bata san sanda ya zo kusa da ita ba, sae ji tayi yace meke damunki?? Baki da lafiya ne?? Kasa bashi amsa tayi, mamaki ne ya kamashi, wai ko dai kurma ce,? kai ba kurma bace ai ya tuno lokacin da ta bashi hakuri.. Sake maimaitawa yayi a karo na biyu, a hankali ta furta, um um lafiya ta kalou.. Kusan mutuwar zaune yayi, dama haka ta iya magana.. Ko shisa bata son yi.. Murmushi ya kara sakar mata yace tou mesa na ganki kamar kina cikin damuwa.. Umma ta ta bashi amsa a takaice.. me sameta ya kara tambaya.. Nan take fada masa taji shiru har yanzu bata zo ba.. Shiru yayi na dan lokaci, sae kuma ya sauke ajiyar zuciya,. Ba komai karki damu.. Ba abunda ya faru da ita, kila wani abun ya tsaida ta.. dauko hijab dinki muje mu gani kinji ko, ya samu kansa da furta mata.. Daga masa kai kawai tayi ta wuce shi da sauri ta tafi dauko hijab.. Yana nan tsaye yana tunani meke shirin faruwa dashi ne? Mesa baya iya controllin kansa indai yaganta.. Ta fito da sauri.. Ya wuce gaba tana binsa a baya.. Bayan sun shiga mota yake tambayer ta unguwarsu tace masa hotoro.. Harphsart khabeer✍ [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 3⃣1⃣➡3⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Daidai kofar gidansu yayi parking, ta fita da sauri, ta tura kyauren.. Ta shiga tana kwala wa umma kira, turus tayi ganin dakin nasu an jawo shi Alamun babu kowa ya ciki, juyowa tayi da sauri tarar dashi a zaune cikin mota.. Ganin yanayin fuskar ta ya sashi saurin fitowa yana tambayar ta lfy? Tuni hawaye ya wanke mata fuska.. Banga umma ba, ba kowa a gidan.. Wani makocinsu Malam idris ne yaxo wucewa,. Tae saurin karasawa gurinshi, malam ina kwana?? Ta ambata.. Lafiya kalou yan nan.. Ya kuma me jiki?? Dazu na fto ina saurin zan tafi kasuwa, naga yayan naki sun fto da ita dijen zasu tafi asibiti da alamun bata jin dadi.. Allah yasa kaffara ne ya wuce bai jira amsarta ba alamun dai yana da wani uzurin.. Juyowa tayi tana kallonsa hankali tashe.. Wanne asibiti kike tunanin zasuje ya jefa mata tambayar.. Nima ban sani ba ta fada tana share hawaye.. Ta rasa mema zatayi?? Me sami ummanta?? Innalillahi. Kinga ba kuka zaki tsaya yi ba, In sha Allah umma zata sami sauki. Da kina da number yayan naki ne ma sae mu kirasa muji,.. Ni kuma kinga zanje aiki though ma dae na makara ya fada yana duba agogo.. Yanzu ki hau adaidaita sahu ki koma gida, anjima sae mu sake dawowa mugaa in sun dawo.. Ji tayi bazata iya masa musu ba, amma harga Allah bataso komawa ba.. Taso ta jira taga dawowarsu, amma ba yanda ta iya.. Ya juya ya shiga mota, daidai bakin titi ya tsaya, ta bude motar ta fito, ya zaro 5k ya mika mata.. Zaro ido tayi ta kasa karba, murmushin nan nasa ya sake sakar mata.. Karbi in wuce ina sauri ya ambata.. Tasa hannu ta karba, kafin tayi magana ya figi motar sa.. Adaidaita sahu ta samo ta shiga sae nassarawa GRA. Shiko safwan yana tuki yana murmushi, shi kansa yana mamakin yanda yake jin farin ciki, Mesa yake jin wani abu game da ita? Kodai sonta nake ne, Ya fada a zuciyarsa, a ah wannan ba so bane, ina tausayinta ne kawae.. ya bawa zuciyarsa amsa.. yarinyar tana da innocent face.. Haka dai yaeta tunane tunane har ya karaso Kofar AKTH..(Aminu kano teaching hospital) Masu gadin ne suka shga daga masa hannu alamun sun saba dashi.. Yayi saurin sauke glass yana dariya, Sannu da zuwa Dr, fari me farar aniya.. suka shiga yi masa kirari.. Ya saki murmushi ya wuce parkin space.. Fitowa yayi yana tafiya cikin takunsa, direct office ya wuce saboda yasan patient suna nan suna jiransa.. Sae daya zauna ya fara Duba files din mutane.. Daya bayan daya suka dinga shigowa yana dubasu Khadija kabir aka kira, yai saurin riko umma saboda jirin da take fama dashi, suka shga dakin likita.. Cikin fara'a ya kalli umma, ya ganeta suna gaisawa sumtyms.. Yae saurin mikewa.. Ya bawa kabir hannu, sannan ya kalli umma ya gaishe ta.. Ta ganeshi itama Bayan ya dubata, yaga ya dace a dan sa mata drip.. ya kalli kabeer yace zamu dan kwantar da ita saboda jikinta yayi weak.. Kabeer ya dan zaro ido, wannan kudin ma dayaya aka sameshi balle kuma ace zaa kwantar da ita.. Safwan ya danyi nazarinsa, yace baka ce komi ba.. Dr wlh ba kudi yanzu a hannuna amma zanje na nemo in sha Allah.. Sae daya ga an bawa umma daki an jona mata drp sannan ya shaida mata zaeje ya samo kudi.. Safwan kua Bai samu ya gama ba sae wajen 5.. Nurr kuwa kwata kwata hankalinta baa jikinta yake Su iman har sun dawo daga skul sun tafi islamiyya.. Tana zaune taji karar motar sa, da sauri ta fito har tana tuntube, sae de tana zuwa tsakiyar falo ta tsaya chak,.. Tunani take in taje me zata ce masa, kuma ma don ya taimaketa dazu bashi ne yake nufin ya chanja daka miskilin nan data sanshi ba Kar taje ma ya wulakanta ta, tana tsaye tana tunani ya turo kofa ya shigo, Dama yayi tunanin zae ganta tana jiransa, kuma da alamun ma shi taji ta fito.. Kallonta yayi kadan sae kuma ya basar ya haura sama.. Wani kululun bakin ciki taji, jiki ya sabule taja kafarta ta koma daki ta rafka tagumi.. Tuni taji wani zazzafan hawaye ya gangaro a fuskarta.. Lalle talauci baeyi ba, yanzu badan ita tana matsayin yar aiki ba, ai da ba abunda zae zaunar da ita.. Sae taje taji halin da ummanta take ciki.. Sae daya watsa ruwa ya dauro alwala sannan ya sauko..Lokacin an fara kiraye kirayen sallah, Direct masallaci ya wuce.. Sae daya idar da sallah yayi yan adduo insa sannan ya shigo.. Su islam ya samu suna zaune duk kansu ba walwala.. Yane twins en momy na ganku haka.. Khalil nae yae saurin zuwa gareshi yae huggin dinsa.. Big bro ga anty nurr chan tana ta kuka bamu san me akai mata ba.. Kazo muje kaji me yasa ta kuka kaji.. ya shiga jan hannunsa.. Binsa kawae ya shiga yi don ya riga yasan dalilin kukanta.. Sallama yayi ya tsaya a kofar dakin yana kare mata kallo.. Ta dago tana dubansa, sannan ta maida kanta tsakanin cinyoyinta ra cigaba da kuka.. Ki shirya yanzu muje muga umma ya ambata sannan ya juya ya fice.. Tae saurin mikewa har taso ta manta da daukar hijab dinta.. Suka fito gaba dayansu bayn sunyi ma mai gadi sallama Iman, islam da ita suna baya.. khalil kuma nagaba. Mamaki ne ya kamata ganin an dauke hanya ba hanyar unguwarsu ba.. Bata kara shiga mamaki ba sae da taga anzo kofar AKTH.. Bayan yayi pakin suka fto ya wuce gaba suka bishi a baya, kasancewarsa likiti baesa sun samu matsala da shga ba duk da ba lokacin ziyara bane.. Suka hau kan barender wanda zae sada ka da aminity.. A hankali ya bude kofar room 3 gami da sallama.. Umma ce kwance hannunta daure da drip, sae ya kabeer a gefenta.. A guje da karasa gaban gadon, saura kadan ta bangaje safwan.. Fashewa tayi da kuka ta riko hannun umma.. Sannu ta shiga yi mata ba kakkautawa.. Yaran suka gaishe da umma da ya kabeer sannan shima safwan ya gaisheta yana kara mata ya jiki. Sannu dan nan mun gode fa wannan hidimar da kayi damu Allah ya saka da alkhairi umma ta fada taba dubanshi.. Murmushi kawae yayi yaja hannun kabeer suka fita.. Sae bayan sun fta ne take tambayr umma abinda yayi take masa wannan godiyar.. Nan take sanar mata, shine ya biya kudin komae har kudin daki.. kuma shine likitan daya dubata.. Baki bude take kallonsu iman.. Dama big B likita ne?? Wlh ni banma sani ba umma.. Nan itama take bata labarin zuwan da sukae gida nemanta.. Sae 10 suka fto daga asibitin wanda da kyar nurr ta yarda zata bisu don ma umma ta nuna mata rashin kyautwa da zatae idan taki binsu.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 3⃣6⃣➡4⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Lokacin da suka zo gida already dare yayi.. Duk yaran sunyi barci.. Zagayo wa yayi ya dauki khaleel ya wuce ciki, Iman , islam ta shiga kiran sunansu.. Amma ina basu san tana yi ba saboda nauyin barci. Tana tsaye tana kokarin ganin ta tashe su don bazata iya daukar su ba.. Ya dawo bayan ya kai khaleel ya dauki islam.. Yace kije ciki zan daukosu.. Ta shiga daki ta ajiye hijab dinta ta shiga toilet dan watsa ruwa.. Bayan a fito ta saka doguwar riga me kauri dalilin ana dan sanyi a garin.. Ta saka hijab dinta ta tada sallah.. Tana sallah taji an murdo kofa an shigo.. Wuri ya samu ya zauna yana karewa dakin kallo.. Daki ne da ake ajiye masu aiki a gidan amma ta gyara shi fes fes sae kamshin turarenta mai araha da yake tashi.. Sae data yi shafa'i da wutri sannan tae sallama.. Ta juyo a nutse tana kallonsa, shi dinma ita yake kallo.. Wani abun kake bukata ta tambaya.. Eh ena bukatar ruwan lipton. Ki hada mun ki kawo mun falo amma karki sa sugar.. Tace masa to sannan ya mike ya fice.. Bayan ta hado masa ne ta sameshi a falo zaune yana duba wasu takardu.. Ya rage hasken falon sae hasken system dinsa daya haske msa fuska. Ashe shisa kullum yake busy ashe likita ne, for d first time taji ya burgeta.. Yana sanyi da doguwar riga ash, fuskarsa zagaye take da shaje me kyau wanda ya kara fito da zahirin kyawunshi.. Ga wani medicated glass da yasa wanda ya kara fito dashi.. Sallama tayi masa gami da ajiye cup din akan center table.. Ya ajiye takardun ya maida hankalinsa kanta.. Ta juya zata wuce taji yace dawo ki zauna.. inaso muyi magana.. Komawa tayi ta zauna ta takure gefe daya.. Sae daya gama abinda yake sannan ya dauki cup din ya kai bakinsa.. Kadan kadan yake sippin, ya kalleta duk ta wani takure.. Nurr ya kirata sunanta cikin wani salo, sae da taji wani irii wanda yasa ta kasa amsawa illa dagowa da tayi tana dubansa.. Ba wani abu yasa na kiraki ba illa inason sanin wani abu game da rayuwarki.. Nasan yanzu lokaci yaja dare yayi bazae yiwu ki fadan komae ba, amma inason na dan miki wasu tamboyoyi.. Ina fata zaki amsa mun tambayoyi na yanda ya kamata.. Daga mishi kai kawai tayi alamun tana jinsa.. Ko zaki iya gaya min dalilin da yasa kike aiki a nan gidan wanda a tunani na ya kmata ace kina makaranta.. Ta dan kallesa kadan sannan ta ce, ina zuwa makaranta har ma naje aji shida, dalilin daena zuwana makaranta kuwa shine rashi, iyaye na basu da karfin biya min kudin jarabawa.. Duba da yanda abinci ma wataran nema yake ya gagare mu.. Ganin zaman da nake haka ba shida wani amfani shisa nake aiki saboda na samu kudi na biya jarabwata.. Ta danyi shiru sannan ta cigaba A rayuwata inason karatu.. Ina son nayi karatu mai zurfi ko dan na taimaki ummata.. Wannan shine dalilina.. Da fatan ka gamsu da bayani na.. Naji duk abinda kikace kuma na gamsu, amma tambaya ta anan shine ko ina mahaifinku?? . Jin ya ambaci mahaifinta yasa wata kwalla ta gangaro daga idonta.. Ya rasu ta fada murya na rawa.. Ya fama mata inda yake mata cio, duk wannan rayuwar da suka shiga ta faru ne sakamakon rasuwar mahaifinsu.. Abinda yafi tayar musu da hankali shine rashin ganin gawarsa da basuyi ba.. An dae ce musu kawae sunyi accident ya mutu amma an binne shi a chan.. Kuka ta shiga rerawa mara sauti, matuka ya tausaya mata.. Haka nan kuma yaji kukan da take yana taba masa zuciya.. Mikewa yayi yazo daf da ita ya tsugunna.. Ya zaro wani farin handkerchif me kyau ya mika mata. kin karba tayi, ta cigaba da kukanta.. Sae kawae taji mutum yasa hannu yana share mata hawaye.. Kallonsa tayi ya shiga girgiza mata kai alamun ya isa haka.. A hanakali ya furta, kiyi hakuri banyi nufin bata miki rai ba.. Zuciyarta ta shiga bugawa da karfi da karfi sakamakon kafe ta da yayi da sexy eyes dinsa.. Shidin ma wani feelin yaji yana shigarsa.. Ji yayi yana neman losin control.. Kokari yayi ya tattaro nutsuwarsa ya mike ya koma kan kujera yace kije ki kwanta, zamuje asibiti da safe.. Sannan kuma kinsan jibi su momy zasu dawo so akwae shirye shiryen da zaai musu.. Ta daga masa kai ta mike ta wuce tana tafiya a hankali.. Binta yayi da kallo har ta shige sannan shima ya kwashe ta kardunsa ya kashe wuta ya haura sama. Harphsart khabeer✍ [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 4⃣1⃣➡4⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Raba dare yayi yana tunanin nurr.. Haka nan yaji yarinya tana burgeshi.. Yaji lalle yana so ya taimaka ta.. A haka har barci ya daukeshi.. Bangaren nurr kuwa tunda ta koma daki tunanin rayuwarsu ta shiga yi.. Yanda rayuwa ta juya musu.. Daki daki take tuno komae wanda take iya tunawa.. Alhaji Abubakar sumaila shine asalin sunan mahaifinmu.. Yan asalin karamar hukumar sumaila ne dake cikin jihar kano. Kakanmu malam hamza sumaila yana da mata biyu.. Inna gaje ita ce uwar gida tana da yaya biyar.. Jaafaru shine babba, sae sulaimanu, tukur, lami sai autansu kamalu.. sae baba halima amarya wadda take da da daya Habu.. Baba gaje mace ce sam wacce bata san mutunci ba.. Kwarai ta tsani kishiyarta da tilon danta.. Ba irin makarkashiyar da batai ba don ganin bayansu amma Allah bai bata saa ba.. Su kansu yayanta ta koya musu wannan mummunan akidar.. Sam basa son habu da mahaifiyar sa.. Sam zaman gidan baya wa baba halima dadi da ita da habu.. tsana da kyara suke sha.. Shi kanshi malam hamza baya iyawa da masifar inna gaje.. Haka dae ake rayuwar da dadi ba dadi.. Kasancewar habu shine karaminsu don sa'an kamalu ne.. Sai suka maidashi wani bawa.. Duk wani aikin wahala shi yake musu shi.. Ana haka su jaafaru sukai aure suka tare a cikin gidan kasancewar shi babban gida.. Ba abunda ya chanza na daga tsangwamar da ake musu.. Har matan su jaafaru basa ganin girman baba halima saboda tsoron inna gaje.. Watarana malam hamza kwanta cio me tsanani.. Ya sa aka kira masa gaba daya yayansa da matan.. yae musu nasiha akan zumunci sannan ya rokesu da su kula da baba halima ko bayan ransa.. Suka amsa kamar gaske.. bayan kwana uku da faruwar haka malam hamza yace ga garinku nan.. Mutanen garin sunji mutuwar malam hamza kasancewar shi me son jamaa.. Bayan sati biyu da rasuwar malam inna gaje da yayanta suka fara fito da salo salon wulakanta baba halima.. Kwarai take shan wuya don abinci ma wataran sae an ga dama ake basu.. Ranan dae ta dubi jaafaru yana zaune kan dakalin kofar dakin baba gaje tace "Ya kamata jaafaru a saukewa malam hakki.. Nan danan ya hayayyako mata yana gaya mata bakakin maganganu Dama ita bata damu da mutuwarsa maalam bq, dan abinda ya bari shi ta sawa ido.. Tou bari kiji in fada miki ba abinda zaa raba a baki nine nan zan cigaba da kula da kadarorin malam.. Baba halima tayi dana sanin dauko wannan maganar wanda akarshe sae data zubar da hawaye.. Cikin dare tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwa.. Habu yae sallama ya shigo.. guri ya samu yana kallonta yace, baba kiyi hakuri kome ake miki watarana sae labari.. Shikenan Ba komae Allah yayi mana jagora tace Nan suka shiga hira Inda yake sanar mata Dazu yaji mai gari yasa a sanar ,wasu baki sunzo daga gwamnatin jiha suna bukatar yara za asasu a makarantae boko... Ta jinjina kai tana tunani.. Da sanyin safiya jaafaru yazo yana bubbuga wa baba halima daki.. Ta bude da azama a tunaninta ma wani ne ba lafiya.. Ganin jaafaru tsaye fuskar nan ba walwala yasa tasha jinin jikinta. Ina habu yake ne tun dazo nazo ban sameshi a dakinsu ba.. Ki fito dashi dan yau zasu tafi birni na bada sunanshi.. Kuma ko kiinaso ko bakyaso dole yaje don na gama maganata.. Bae jira amsa ba ya juya fuuu ya wuce.. Kuka ba irin wanda baba halima batae ba ranar da aka tafi da habu... habaici kuwa ta shashi a tsakar gida har sae data gwammace bata auri malam ba.. A kwana a tashi ba wuya Assalamu alaikum, ina mutanen gidan ne?? Baba gaje ce ta fito tana gyara dan kwali.. Wanna dan iskanne ke ta mana sallama haka ne.. Turus ta tsaya ganin habu cikin kyakkawar shiga, janye yake da troly yar madaidaiciya.. Baki bude ta ke kallonsa mamaki karara a furkarta.. Shi kuwa murmushi yayi ya tsuguna har kasa yace baba ina wuni, mun sameku lfy.. Ganin bata da niyyar amsawa yasa shi mikewa yaja jakar shi ya wuce dakin babarsa.. Akan dadduma ya tarar da ita tana lazimi.. Tana ganinsa ta mike da sauri tana kallonsa.. Ta rasa wanne irin farin ciki zatae duk da tana samun labarinsa a gurin mai gari.. Ya samu wuri ya zauna yana murmushi, itama din murmushin take.. Bayan sun gaisa ne ta mike don ta kawo masa ruwa.. Baba gaje ta tarar tana zarya hankali tashe.. Baba halima ta kalleta ta watsar sannan ta wuce ciki.. Bayan ya huta ya fito don gaisawa da mutanen gida..kallonsa suke da abun mamaki.. Ganin sauyawar dayayi wanda duk su atunanin su ma yanzu ko bashi da rai.. Da laasar mazan gidan suka dawo daga gona.. Turus sukae suma ganin wanda basu taba tunanin gani ba.. Ya tashi da sauri ya karbi kayan hannu yaya jaafaru.. Baki galala duk suke binsa wanda ya lura da hakan.. Nan suka shiga kuskus tsakaninsu.. Da daddare suka hadu duka suka sa aka kira musu habu.. Ya fto a nutse kana ganinsa kaga dan boko ga kamshin turarensa sae tashe yake.. Wani zazzafan yawu baba jaafaru ya hadiya sannan ya kai dubansa ga yan uwansa.. Habu muna so kai mana bayanin yanda ka sauya gaba daya kuma ka dau wannan lokacin mai tsawo baka zo ka ganmu ba.. Nan yake labarta musu ai daya tafi kano aka kaishe makarantar kwana dake dawakin tofa, nan yayi karatunsa daga karshe gwamnati ta kara daukar nauyinsu zuwa kasar cyprust inda ya karanci bussiness and finance.. Yanzu haka yana aiki da FIRS dake abuja.. Kuma duk abinda yake faruwa ana sanar wa mai gari.. Yanzu haka ma yazo musu da maganr aurensa ne.. Sanna zae tafi da baba halima.. Zo kaga tashin hankali wajen su kuma duk yana lura dasu sarai.. Ganin basu da alamun magana yasa ya zaro kudi yan dari biyar biyar na 20k a jiye musu yace gashi nan yaya ba yawa... Ba irin haukan da baba gaje batayi musu ba, hr Allah ya isa sae data yi musu wai sun cuceta da kamalu suka kai ai ba haka ba.. Sae bayan ta nutse ne suke sanar mata da shawarar da suka yanke.. Murna ta shiga yi tana samusu albarka.. ( kome suka shirya ??)) Matuka habu yaga chanji a tattare da yanuwansa.. sae wani nan nan suke dashi.. Murna kuwa a gurinsa baa magana Allah ya shiryi yan uwansa sun gane gaskia Haka dae akae shagalin bikin habu da budurwarsa dije(umma) wadda suka hadu a gombe yaje wani seminar.. Kasancewar itama iyayenta sun mutu sae ita da yayarta suka rage.. Bayan shekara daya da auren Cikin ikon Allah umma ta haifi yaya kabiru wanda yaci sunan babanta.. Tsakaninmu da yaya kabiru kuwa shekara goma ne cip cip.. Nan aka samini suna *MARYAM*, sunan da abba na yake so.. Amma ana kirana da nurr.. iyakar jin dadi da gata muna samu wajen mahaifinmu kasancewar ya zama hamshakin mai kudi... Ya samu a makaranta mai kyau inda yaya kabiru yake jss 1 ni kuma ena primary 2.. Kwatsam muka sami sauyin rayuwa, wani babban alamari ya faru wanda shine sanadiyyar duk wani hali da muke ciki yanzu.. Jin da tayi kamar ana kiraye kirayen sallah asubah yasata mikewa da sauri.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 4⃣6⃣➡5⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Alwala ta dauro tazo ta tada sallah.. Ta dade tana addua asujadda Allah ya bawa ummanta lfy.. Sauri sauri take ta kammala komae kafin ya fto don tana son zuwa asibity.. Hatta kayanta ta gama hadawa don tana sa ran su momy na dawowa zata koma gida Bayan ta gama shirya khaleel su kuwa su iman dama sun iya shirya kansu... Sukae breakfast sannan suka fice zuwa skul.. Wanka ta fada bayan ta fto ta dan shafa mai ta kawo wata jar atamfar ta ta saka, duk da atamfar ta dan kode amma bae hana yi mata kyau ba.. Hijab ta zura ta fto zuwa falo don taga fitowarsa.. Tasan sarai zae iya tafiya batare da ta sani ba.. Turarensa ne ya fara yi mata maraba.. Kanta na kasa tana wasa da hannunta yazo ya wuce ta gaban ta.. Sae daya gama yangarsa yana lura da ita duk ta matsu ya gama.. Ya mike ganin bata da niyyar masa magana, ko gaishe shi ba tae ba.. Ya fice abunsa bai ce mata kala ba.. da sauri tabi bayansa.. Tsaye ta ganshi jikin mota yana magana da mai gadi.. Ganin ya zuya zae shiga ne yasa tae saurin karasawa.. Jifan ta yayi ta wani kallo, sannan yace lafiya?? Cikin inda inda tace dama asibiti nakeson zuwa.. Ohh sae yanzu kika ganni kenan, ko gaishe ni kin gagara yi kina kallo na fto.. Kinga malama ba inda zanje dake ya fada yana sake shiga mota.. Rau rau tayi da ido ganin da gaske tafiya zaeyi ya barya.. Da azama ta zagaya bangarensa ta tsuguna har kasa sannan tace "Ya safwan dan Allah kayi hakuri wlh bansan ban gaishe ka ba.. inason zuwa naga umma dan allah ka taimaka min. Kiris ya rage daria ta kufce masa, ganin yadda ta hade hannu ta wani runtse ido.. Hakan ya bashi damar kare mata kallo.. Zara zarar gashin idonta wanda suka kwanta kan kyakkyawar doguwar fuskar ta.. Ya kai dubansa kan kancinta wanda ya karawa fuskar tata kyau.. Dan bakinta ya kalla wanda in ka gani zakae tunanin tsokali bazae iya shiga ciki ba.. saboda kankanta.. Lumshi ido yayi ya bude yasake dora su akan face enta.. Lalle Allah yayi halitta.. Jin shirun yayi yawa yasata bude idonta.. Yanda ya kafe ta da ido ya sata jin kunya.. Tae maza ta rufe fuskarta ta tafin hannunta.. Mikewa tayi da sauri zata shige gida, yai saurin riko hannunta.. Wani irin shock sukaji dukkansu.. Tae saurin zame hannunta tana dubansa.. Ina zaki kuma?? Ban gama kallon kyakkyawar fuskarki ba.. Mamaki ne ya kamata, anya kuwa safwan ne yayi wannan furucin?.. Dariya yayi yace na baki mamaki ko?? Hmm ya gyara tsayuwa sannan ya dora.. Nurr an taba gaya miki ke kyakkyawa ce.. Kina da wani kyau me daukar hankali.. Lalle Allah yayi miki baiwa wanda ya dace ki gode masa.. Tsananin mamaki yasa ta kasa magana.. Kallonsa ma ta kasa yi amma tana tsaye kamar wadda aka dasa.. Ganin bata da niyyar tanka masa yasa shi kyara tsaiwar shi sannan yace in dae baki kalle ni ba ba inda zakije.. Shiru ya kara biyo baya.. Ganin haka yasa shi fadawa mota yace shikenan ni na wuce.. Da azama tae saurin kallonsa.. Murmushi yayi ya bude mata kofa dayan site en ta shiga suka kama hanyar AKTH... Kawu tsaye yana Jijjiga kofa, Kamar wani mahaukaci haka yake bubbuga wa yana kwala wa dije kira.. Kwafa yayi sannan ya juya yana bambamin masifa.. Dawowarsa uku yana dubawa ko sun dawo amma shiru.. Nurr kuwa bayan taje ta duba umma ta koma don kar yaran su dawo bata nan.. Gashi kuma tanason ta kara gyara gidan don dawowarsu momi. Tun safe aka sallami umma amma safwan ya hanasu tafiya.. Sai bayan ya gama ganin patient sannan suka tafi yaje ya ajiyesu sannan ya wuce jifatu store don yin shopping.. Wata doguwar riga ya gani pink colour mai masifar kyau.. Hakanan ya shiga hango nurr acikin rigar.. Da sauri yakae hannu daedae lokacin wani guy dake dayan side en shima yakae hannu.. A tare suka dago suna duban juna.. Murmushi sukayi wa juna sannan kowa ya cire hannunsa alamun ya barwa san uwansa.. Dayan guy en ne ya zagayo ya mika ma safwan hannu sannan yace ni sunana *barrister Sadeeq auwal kibiya*.. Safwan yayi murmushi ya mika masa hannu sannan yace *Dr safwan naseer mai sana'a*.. A take suka kulla abota sukae exchangin complementry cards en juna.. Gurin biyan kudi ne kowa ya dage shi zae biya wa daya.. A karshe barr.sadeeq shi ya biya saboda yafi safwan baki.. Wata leda sadeeq ya wullu masa yana kokarin tada motarsa.. Seda ya hau titi sosae sannan ya mika hannu ya jawo leda.. Wannan rigar ya gani.. Lalle wannan da gaske so yake muyi abota ya fada yana jinjina kai.. Seda yayi sallar magariba sannan ya shiga ciki.. Dukkansu ya samesu a falo, ganinsa ya sasu tasowa da sauri sukae huggin nasa. Khaleel ne yace big B wae gobe su momy zasu dawo inji anty nurr.. Daga masa kai yayi alamun Eh haka ne, yaron ya shiga tsalle yana murna.. Sai data bari sun gama masa sannu da zuwa zae wuce sannan tace masa ina wuni.. Lafiya klou ya amsa sannan ya wuce sama.. Tara daidai ya sauko ya iske su suna kallon wani indian film a zee world.. Guri ya samu ya zauna.. sae a sannan ya tuno da kayan da ya siyo.. Mikewa yayi yace musu kuzo muje mota ku tayani debo kaya.. Bayan sun gama shigowa da kayan ita kuma tana zaune tana kallo da alama film din ya tafi hankalinta.. Ki tashi ki dauki kayan nan asasu inda ya dace.. Ta mike a hankali tana waywayen tv.. Sae data gama kintsa komi sannan da dauko ledar rigar nan ta fito da ita.. Zuwa tayi gabansa ta mika masa.. Wannan fa ya ambata.. Tace bansan inda zansa wannan ba shisa na kawo ma.. Kin karba yayi ya dan dubi bangaren su iman.. kallonsu suke hankali kwance basu masa meke faruwa ba.. Ki dauka naki ne yace da ita batare da ya dube ta ba.. Nawa? ta tambaya yae mata banza kamr bae jiba.. Ganin zata sake masa tambaya yasa shi cewa oya kowa ya tashi aje a kwanta.. Kar wani ya makara na tafi airport na barsa.. Yaran najin haka yasa su mikewa da sauri suka nufi daki don basaso ya tafi ya barsu.. Juyawa tayi zata bisu batare da ta dauki ledar ba... yae saurin katseta ta hanyar cewa kawo min ruwan zafi.. Bayan ta kawo ya hana ta tafiya sae daya gama yangarsa yana sha yana satar kallonta.. Ganin shirun yayi yawa yasata cewa, um dama dama inason nai maka godiya kan kokarin da kayi da umma Allah ya saka da alkhairi.. Nan ma shiru taji yayi batare da ya bata amsa ba.. Duk ya wani tsare ta da idonunsa masu bata tsoro.. (Wannan ya fiya shegen kallo ta fada a ranta.. lol) Kada kai yayi bayan ya sauke cup en daga bakinsa sannan yace ba komai fatanmu Allah ya kara mta lafiya.. Amin ta ambata sannan tace, zan iya zuwa na kwanta ina jin barci.. Lumshe idonsa yayi sannan ya bude, yana jin dadin maganarta shiyasa inta fara baya so ta tsaya.. Ban sallameki ba tukunna ya fada sannan ya maida kallonsa ga tv.. Tun tana duba lokaci tana satar kallonsa har ta fara hamma.. Yana lura da ita amma ya share.. chan ya juyo da niyya mata magana taje ta kwanta.. Mamaki ne ya kamashi ganin har tayi barci.. Tsakaninta da Allah take barcinta ba tare da wata matsala ba.. Hannunta daya ta dafe fuskarta dashi.. Saukowa yayi yazo daedar inda take ya zauna.. Ya jawo hannunta ya damke cikin nasa.. "U av change me alaot nurr, in ina tare dake sae na kasa controllin kaina, I jst lurv everytin about u.. Ur eyes, urs smile, ur innocent face en above all ur charmin voice.. Promise u Zan taimaka miki, zan kawo sauyi a rayuwarki.. Haka yayi ta sumbatu shi kadae kamar tana jinsa.. ( woo su likita bokan turai an fada tarko). Gyara mata kwanciya yayi sannan ya lulluba mata bargo ya koma kan kujera yana jiran farkawarta.. (niko nace wayaga sabun shiga.. Barci barawo ne yayi awon gaba dashi anan wurin batare da ya shirya ba.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 5⃣1⃣➡5⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Mika yayi da niyyar juyi, ganin haske kamar na rana ya sashi bude ido da sauri.. Innalillah ya ambata yana jawo wayarsa. Karfe shida hadda minti goba.. Zumbur ya mike ya maida kallonsa inda ya bar nurr.. Wayam ba kowa.. Yai saurin fadawa toilet ya dauro alwala.. Bayan ya idar da sallah yana zaune islam ta shigo.. anty nurr ce tace nazo na tambaye ka wai da karfe nawa su daddy zasu sauka.. 12 noon jirginsu zae sauka ya fada yana ninke dadduma. Make sure kun shirya b4 d tym if nt zan tafi na barku.. Tom yaya ta fada sannan ta fice.. Duk wani shirye shirye sun gma shi by 10 duk sun matsu a tafi.. kwata kwata sun kasa breakfst saboda murna. Fitowa yayi sanye da shadda blue colour tasha aiki.. Hular daya sa da dace da yanayi aikin shaddar.. kamshin nan nasa mai dadi shine yake fara yin sallama.. Ya dan zauna kadan a falon, jin motsin ta a kitchen ya sashi mika musu key din motar. Kuje mota ku jirani yanzu zan fto.. Dama chan sun matso shisa yana fada suka mike da sauri suka fice. Foldin hannunsa yayi yana kallonta, ita kuma duk sae taji da kasa nutsuwa.. Wuka ce a hannunta tana yanka nama amma hannun sae rawa yake.. Ji take kaman ta tsaga kasa ta shige.. Wata muguwar kunyarsa takeji musamman da ta farka ta gansu a parlour suna brci.. Shigowa yayi kitchen din ya mika hannu ya rike wukar, kallonsa tayi ya kashe mata ido.. Nan ta tuno maganar gaisuwa, ina kwana ta furta a hankali.. Bazan amsa ba, kinyi min laifi, shine kina gani na na makara maimakon ki tashe ni ko.. Kayi hakuri ta fada.. Umm ni bazan hakura bafa.. Akwae ma maganr da nakeso muyi amma sae da yamma.. Ai yau zan koma gida ta bashi amsa. Nan danan yaji hankalinsa ya tashi har ya kasa boyewa.. Gida kuma ya tambaya?? Daga mishi kai tayi.. Shikenan tam, amma ki jirani ni zan mayar dake. Inason naje na kara duba umma.. Nan ma sake daga masa kai tayi.. Sae mun dawo ya fada sannan ya fice.. jin bude gate yasa ta saurin lekawa, motoci ne guda biyu suka shigo sannan suka nemi wuri sukai parkin.. Safwan shi kadae ya dawo a motarsa saboda yaran duk motar su daday suka shiga.. Momy ta fara hangowa tayi fari, alamun hutu da jin dadi ya bayyana a tare da ita.. Hannunta rike da khaleel.. Tana jin shigowarsu falo ta fto da sauri.. Har kasa ta tsugunna tana gaishe su.. Sun ji dadin ganin yaransu cikin koshin lfy.. Sun kuma jinjina wa yarinyar.. Bayan sun natsa suka hau cin abinci, farar shinkafa ce da miyar koda, sae coslow.. Kunun gyada ta dama musu yayi fari kal dashi.. ga zobo me sonyi.. Suka dinga sha suna karawa, kwarai zobon yayi wa daddy dadi.. Bayan sun huta ne tazo ta iske momy a falo, nurr naji ance yau zaki koma ko?? Bazaki zauna ki cigaba da aiki damu ba?? Kinga yanda little ya shaku dake.. Kasa tayi da kanta don har ga Allah tfi son tafiya.. Amma tana jin nauyin hajiya.. Kinga bakomae bazan takura miki ba, in kin gama shiryawa kizo in sallameki.. Shiru shiru safwan tunda ya fta ba alamunsa.. Gashi ta matsu ta tafi.. Ganin yamma zatae mata yasa ta fto kawae.. Bayan sunyi sallama da momy ta hada mata sha tara na arziki.. Sai kuma ta kasa tafiya.. Duk yaran sun rike ta musamman mutuminta.. Kuka yake sosae yana cewa karta tafi.. Da kyar aka lallashe shi bayan an masa wayon zata dawo anjima.. Haka ta fito bakin titi tana share kwalla.. Sabo turken wawa.. Umma tana kwance a tsakar gida tana shan iska, Ta sami sauki sae rashin karfin jiki.. Kabeer ya fita tun sassafe.. Alhajin da yake aiki karkashinsa ne ya kirashi yana nemansa.. Kawu tukur ne ya banko kofa ya shigo, wannan karon bashi kadae bane.. tare suke da baba ja'afaru.. Fuskokinsu a murtuke babu alamun dariya.. Umma na ganinsu sai da gabanta ya fadi.. Jiki na rawa ta mike, dan tasan zuwansu ba alkhairi bane, musamman data ga har da baba jaafaru da kansa.. Girma ya riga ya kamashi shi yasa ba kasafai ya fiya fita ba. Lalle zuwan nasu ba alkhairi bane.. Sannunku da zuwa ta fada.. Ba wanda ya tanka mata, sae da suka gama kalle kallensu sannan kawu tukur ya kalleta shakeke.. Keee Ina yaran nan suke?? Kafin ya rufe baki kabeer ya shigo hankali tashe... Yasan sunxo yiwa umma diban albarka ne, Gashi bata gama warwarewa ba. Suka juyo gaba daya suna kallonsa, ko arzikin gaisuwa basu samu daga wurinsa ba.. Ya shige ya ajiye kayan hannunsa sannan ya kalle su.. Me ya kawo ku gidan mu?? Ya fada yana zare ido.. Duban juna sukae sannan suka hada baki suka ce *kabiru* mu kake gayawa haka?? Umma ce ta daga masa hannu tace banason rashin kunya abba, ba sa anninka bane.. Kwafa kawu yayi sannan ya kalli umma, dama ba wani abune ya kawo mu ba illa ina son sanar dake zamu dauke maryama zata koma gurinmu da zama.. Bazamu zuba miki ido ki bata maata rayuwa ba.. Kuma nan da dan lokaci kadan zamuyi mata aure.. Zanxo gobe na dauke ta kuma Allah sa na tarae bata nan.. Kaikuma mara kunya ka kiyaye ranar haduwarmu don bazatae ma kyau ba. Suka juya fuuu kamar kububuwa suka fice... Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 5⃣6⃣➡6⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Adaidaita sahu ta samu ta hau sae unguwarsu.. Daidai kofar gida ya ajiyeta, ta ciro kudinsa ta bashi, ta wuce ciki.. Da murnar ta ta shiga gidan, Cak ta tsaya ganin umma da ya kabeer cikin wani yanayi.. Karasawa tayi ta zauna tana duban umma.. Umma lafiya na ganku haka?? Ko dai jikin ne?? Girgiza mata kai umma tayi sannan ta shafo kanta, kin dawo?? Sannu da dawowa.. Bayan sun gaisa, tana lura dukkansu akwae damuwa tattare dasu.. Amma basu san su nuna mata.. ganin haka yasa ta share ta shga yin abubuwan da zasu faranta ran umma.. Da daddare suna zaune, Suna tattauna batun zuwan su kawu, amma basu bari tasan gudurinsu a kanta ba.. Kabeer ne yace umma nazo miki da albishir amma ganin mutanen nan yasa duk naso na manta.. Albishir din me kuma abba?? Kodai aikin ya samu ne?? Eh tou kusan hakan ne sae de wannan ya dan banbanta.. Wato kiran da alhaji yayi mun dazu ba komae bane illa ya sanar dani na zama cikin shiri rana ita yau zanje interview abuja.. Gwamnati tayi niyyar tura dalibai kasar waje.. Shine ya bada suna na wajen abokinsa kwamishi nan ilima.. Yanzu haka har na cike form din, sae dae addu'ar Allah ya bada sa'a. Wani wawan ihu nurr ta saki ta dane shi kamar zata yarda shi.. Umma kuwa, bakinta yaki rufawa sae faman hamdala take wa Allah.. Tana fatan Allah ya bashi saa.. Dariya yake yana kallonsu, wannan farin ciki haka kamar ance yaci interview din.. Yayanah Allah ubangiji ya baka sa'a ta fada tana dan tsallen murna.. Amin kanwata Abdoul yaron makocinsu ne yayi sallama, ya gaida umma sannan yace wai ana sallama da kabeeru a waje.. Wane ne ya tambaya?? Wani ne a cikin mota nima dae bansan shi ba yaron ya fada sannan ya juya.. Tashi yayi ya fita don ganin waye ke nemansa.. Safwan ne tsaye ya harde hannunsa jikin mota, da sauri kabeer ya karasa ya mika masa hannu.. Bayan sun gaisa ne yake sanar masa yazo ya sake duba jikin umma.. Ai dama baka aika an kirawo ni ba, ai yanzu an zama daya da shigowa kawae kayi ya fada sannan ya juya yace bismillah. Ta dora kanta akan cinyar umma tana ta dariya, murna take kamar me.. Kabeer ne ya shigo, sannan ya biyo bayansa.. Umma tare fa muke da Dr ya fada yana jawo tabarma.. Sannu da zuwa likita kaine a gidan namu, ya gaishe ta nan take tambayarsa yasu hajiya suka dawo.. Sun dan taba hira a karshe ya mike zae tafi, dama tun shigowarsa nurr ta shige daki bayan ta gaisheshi.. Kabeer ne ya sake shigowa bayan ya raka shi yana kwala mata kira.. Kije dr yana san ganinki ya fada sannan ya wuce dakinsa. A jikin mota ta tarar dashi ya kurawa hanya ido.. Karasowa tayi ta dan duka kadan ta gaishe shi.. Tsare ta yayi da manyan idanunsa.. Umm kinsan kinyi mun laifi ai shisa kikai saurin gaishe ni.. Laa laifin me nayi ma?? Ta fada tana turo baki. Kinfi kowa sani ai.. Amma yanzu ba wannan ba.. Na same ki lafiya?? Lafiya klou ta amsa Ya dan mata tambayoyi tana bashi amsa.. Sannan yace Ya maganar danace zamuyi?? Umm zamu iya yinta yanzu ai ko?? Ta tambaya.. Ya dan kalli agogon hannunsa sannan yace. Owk lemme make it fast.. So nake naji Yaushe kike son komawa makaranta? Wat i mean shine kinason komawa skul dinku ne kiyi examz en achan. Ko kinfi son wata skul din kije as external student?. Kinga nan da two weeks zaa fara registration.. Nafiso nayi a skul dinmu, Kasan da tsada in dae wata skul dince.. Wannan ma da yaya zamu biya balle wata skul din.. Amma kinsan baa fiya cin examz a public skuls ba?? Eh na sani tou amma yaya zanyi,, banida zabi tunda ita ma public skul din sae mutum ya biya inde beci qualifyn ba.. Kuma kudin bae kai rabin na privt skul din ba.. Tom shikenan zan dawo in na samu lokaci.. Zanzo naga umma.. Akwae maganar da zamuyi da ita.. Duk maganar da suke kanta na kasa, bata san mesa ba batason hada ido dashi.. Kiran sunan ta yayi chan cikin makoshi, ta dan kalle shi kadan.. Mesa kike jin kunyata?? Ko har yanzu tsawar dana taba miki ce kika kasa amsawa?? Ni ba komae, kawae dae ina jin nauyinka ne.. Toh dago ki kalle ni.. Da dago da kanta a slow kamar wadda zata kalli dodo.. Da sauri ta sauke, dariya ma abun ya bashi.. Sae ji tayi mutum ya riko mata hannu, tayi kokarin ta kwace ya kuwa rike kam kam.. Zan tafi *nurr* ki shiga gida.. Toh ka sake ni, ta fada.. Kwaikwayon muryarta yayi yace um um ni bazan sake ki ba sae kin kalle ni.. Ganin bata da niyya yasa shi sakin hannunta aikuwa ta ruga da gudu ta shige gida.. Bubbuga kansa yayi yana murmushi..Sannan ya shiga mota yaja.. Ita kuwa tana shiga ta tarar da umma da ya kabeer a zaune.. Ka tsaye daki ta wuce suka bita da kallo kowa yana raya wani abu a ransa.. Cikin dare duk kansu sun kasa barci, juyi kawae suke kowa yana tuna dan uwansa.. Dukkansu ba wanda yasan soyayya cox basu taba.. Lalle koma mene wannan nakeji game da yarinyar nan me girma me safwan ya raya a zuciyarsa.(Ka fada lurv Malam jst admit it)lol.. Haka umma ma ta kwana da tunanin zuwansu kawu.. Tana jin tausayin yarta ta.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 6⃣1⃣➡6⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Da safe ta tashi cikin farin ciki.. Ita kanta bata san me yasa ta wannan farin cikin ba.. Bayan tayi share share ta samu wuri ta zauna tana jin shirin rai dangin goro.. Tana son taji ya zata kasance tsakanin masoyan cikin littifi.. Kwarai suna burgeta yanda suke tafiyar da soyayyarsu.. Ya kabeer ne ya fto da alamun aiki zae fta, gaishe shi tayi sannan ta cigaba da jin radion ta.... Dakin umma ya leka yayi mata sallama sannan ya fice.. Har yamma umma nata zuba idon ganin su kawu amma shiru.. Addu'a take tayi Allah yasa bazasu zo ba.. Sallama yayi a daedae kofar gidan, umma ce tace taje ta gano waye ke sallama.. Tana fita taci karo dashi har ya shigo zauren, sanye yake ta riga da wando jeans.. Gashin kansa ya kwanta luff alamun yasha gyara.. Murmushi ya sakar mata me kayatarwa.. Itama din dae murmushin tayi masa sannan ta juya don sanar da umma. Tare suka shigo tana gaba yana bayanta.. Duka wa yayi yace umma ina wuni?? Lafiya lou sannu da zuwa ta fada.. Ya manyan naka?? Lafiya kalou umma.. Ya kuma karfin jiki,,? Da sauki ta amsa.. Ruwa tazo ta ajiye mishi sannan ta samu gefe ta zauna.. Shiru ya dan biyo baya, chan kuma yace" umma dama nazo ne akan maganar nurr, munyi magana da ita akan karatun ta.. Ya dan numfasa, sannan ya cigaba.. Shine nakeso naji raayinki don inason nayi mata register a makarantar su khaleel.. Jin ya ambaci zae biya mata taje tayi examz yasa ta dagowa da sauri tana kallonsa.. Kashe mata ido daya yayi.. Muryar umma ce ta dawo dashi, Dr baka gajiya, an ta dawainiya damu a asibity ga kuma wannan.. Allah ya saka maka da alkhairi mungode mungode.. Ba komai umma ai duk daya na daukesu dasu iman.. Sun ce ma na gaisheku da zasu biyoni naki.. Muna amsawa.. Zanje nima in sha Allah nayi wa hajiya barka da dawowa.. So nake na dan kara samun sauki.. Allah ya kaimu ya fada.. Ita kuwa nurr murna ce ta hana ta sakat; Hangowa take kamar burinsu ya gama cika ita da yayanta.. Kallonsa ta dunga yi suna mgana da umma.. matukar burgeta yake.. Karaf ya dago suka hada ido, da sauri ta sauke idonta shi kuma yayi murmushi.. Ya mike zae tafi, bayan sunyi sallama da umma.. Ba rakiya kanwata ya fada yana kallonta.. Kefa sokuwa ce Jeki rakashi mana cewar umma.. A zauren gidan yaja ya tsaya.. ita dinta sae ta tsaya, Sunkuyar da kai tayi tana wasa da hannunta.. Nan ya samu abunda yake so, ya kura mata kallo.. Lalle ya fada tarkon so.. Ada ba abunda ya tsana irin maganar soyayya musammam ma in yaga abokansa na kula yan kananan yara.. Shi a tunaninsa raini zae jawo.. Shi kuma mutum ne mai son girma. Amma sae gashi tun baa je ko ina ba ya kamu da son yar karamar yarinya.. Ya rasa yanda zaeyi ya sanar mata.. Lalle in abokansa suka ji zasuyi masa dariya.. Amma ya zaeyi Haka Allah yake al' amarinsa.. (Dama hausawa sunce dan hakin daka raina shike tsone maka ido) Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar daya lula.. Zan shiga ciki tace.. Ya hakuri wlh wani tunani ne ya dauke kaina.. Ba komae tace.. Kinyi kyau ya furta yana mata kallon kasa kasa.. Kasa magana tayi.. Dama yasan bazatai magana ba.. Ji tayi ya ruko hannunta, ya tsuguna akan guiwowinsa.. yace _Nurr_ *kina sona*?? *Zaki aure ni??* *Bae jira tayi magana ba ya cigaba* *Allah ya dora min tsananin sonki* *tun ranar dana dora ido na akanki na kasa samun nutsuwa* *Tun daga ranar na zama wani iri, Tun ina karyata zuciya ta akan cewa ina sonki, har nazo na fara gaskata hakan* *Kece farin cikin rayuwata, I lurv u so much, i lurv u beyond imagination.. Dan Allah ki taimaki rayuwata* Kafin ya kara magana suka ji an banko kofa da karfiii, gaba dayansu suka juyo a da saurin ganin waye haka...... Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 6⃣6⃣➡7⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Tsaya wa tayi sororo tana dubansu.. Sake sake ta shiga yi a zuciar ta.. Wannan ai kamar dan gidan hajiya.. Gefen su ta bi da wuce tana kwala wa umma kira.. Dukkansu ba wanda ya tanka mata.. Mikewa yayi yana kallonta.. Baki bani amsa taba.. Ummm.. Ahhmm, duk ta duburburce. Jikinta sae rawa yake. Mtsw ya dan ja tsaki a hankali.. Wannan ta fiya kunya ya fada a ransa.. Juyawa tayi zata shige ciki, aikuwa ya tsare hanya.. Ya kafe ta da ido, ta dan kalle shi kadan, ya wani langabar da kai kamar karamin yaro.. Duk sae taji ma ya bata dariya.. Aikuwa ta shiga yi ba tsayawa.. Bai taba ganinta tana dariya irin haka ba.. Duk sae yaji ta burgesa.. Bayan ta dan tsaya da dariyar ne tace, ni ka matsa na shiga gida.. Aikuwa baki isa ba, sai dai mu kwana anan in dai baki amsa ni ba.. Wayar sa ce ta shiga kara, ya matso da bakinsa daedae kunnenta, daddy yana kirana, ki jira ni zan dawo anjima. And make sure kin tanadar min amsa na. Ni kuwa dije in tambayeki mana, yaron nan dana tarar a zaure sae naga kamar dan gidan hajiya.. Eh shine a cewar umma, yaron yana da kirki sosae.. Emmm gaskiya jummai ta fada.. Toh ko akwae wata alaka tsakaninsu da yarinyar nan ne?? Gaskiya banajin akwai wata alaka, kawae mutunci.. Amma mesa kika ce haka??.. Hmmm, Ina tunanin yaran nan soyayya suke, dalili shine.. Lokacin da nazo kofar gidan nan, na dan buga kyauren naji shi kamar a rufe.. Tunani na ma ba kowa.. Har na juya sae naji magana sama sama, wannan dalilin yasa na bugo kofar da karfi.. Aikuwa naga yaron tsugunne gaban yarinyar wajenki kamar me neman gafara.. Umma ta danyi jummm sannan tace nidai jummai bana ce komai ba tunda bansan dalilin yin hakan ba.. Amma zan tuntube ta naji.. Ita kuwa nurr yana tafiya sae ta kasa shiga gidan.. Ta dade a tsaye, ganin tsaiwar vazatai mata ba, yasa taja wani dan dutse a kusa da ita ta zauna akai. Tunani ta shiga yi, tana tuno yanda safwan ya tsaya yana fallasa mata asirin zuciyarshi.. Wani irin feeling taji yana shigarta.. hade da wata zazzafar soyayyarshi.. Ta lumshe ido ta bude, a hankali ta furta.. Ina sonka nima. Umma ta fto raka jummai kawae taga nurr a zaune, Me kike yi anan kuma?? Umm ba komai. Ta tashi ta wuce ciki. Umma tana lura da ita, duk ta zama wata silent.. Wai meke damunki ne?? Ehh?? Ba komai umma. Tai ta zuba ido taga dawowar safwan amma har suka kwanta bashi ba alamar sa.. Umma kuwa murna take da su kawo basu dawo ba gashi har dare yayi... Shi kanshi ba asan ranshi yaki dawowa ba.. Bayan yaga daddy kuma sae aka kirashi a asibity.. Ba yanda ya iya dole ya bar zuwan sae kuma gobe.. Bayan ya dawo daga aiki ne, ya shirya. Allah Allah yake yaje ya ganta.. Tsaye ya tarar da daddy a compound din gidan yana amsa call.. Jiransa yayi har ya gama.. Ya juyo da kallonsa, muje ka rakani wata unguwa.. Innalillahi ya furta, shikenan daddy ya kashe masa ranar sa.. Haka suka fita, suje nan suje chan basu suka dawo ba sae wajen tara na dare.. Aikuwa washe gari daga wurin aiki ya wuce.. Zaune take tana wanke wanke, suna hira da umma jefi jefi.. Kinga bari na shiga gidan malam bala nayi musu barkan nan.. Tom sae kin dawo.. Bayan fitar umma ya iso kofar gidan.. Kai tsaye yayi sallama, gabanta ne ya fadi.. Da gudu ta mike tayi daki, hijab ta saka sannan ta fto.. tsaye ta tarar dashi a zauren gidan.. Kwana biyun nan da bai ganta ba duk sae yaga ta kara kyau.. Bayan ta gaisheshi taja bakinta tayi shiru.. Nan ya shiga zayyano mata dalilin da ya hanashi dawowa.. Ba komai ta furta.. Ina muka kwana a zancen mu?? Kin samo min amsa ta kuwa?? Daga masa kai tayi.. Ok ina jinki.. Jin tayi shiru yasa gabanshi ya fadi.. Karfa tace bata sonshi.. In kuwa tace bata sonshi, bai san ya zaeyi da ransa ba. Muryarta ya tsinkaya tana cewa _Na amince_.. Alhamdulillahi ya furta, farin ciki fal zuciyarsa.. Sae kuma ya dan hada rai, da son ya kureta.. kin amince kamar ya?? Ban fuskance ki ba.. Kina nufin kice kina sona?? Daga mishi kai tayi.. Amsa nakeso da bakinki.. Eh inasonka ta fada, ta gudo ta shige gida.. Dariya yayi sannan ya girgiza kai.. Anyi mai wuyar, saura wannan kunyar kuma. Yasan bazata sake fitowa ba, shisa ma bai takura mata ba ya wuce.. Ana i sauran kwana daya tafiyar ya kabir abuja, suna zaune suna tattauna wa akan jarabawar.. Ita kuwa nurr duk hankalinta baya kansu, tunanin safwan dinta take, a kwana biyun nan ya koya mata wata zazzafar soyayyar shi.. Umma ce ta dan zungureta, ta juyo da sauri.. Tunanin me kike ne?? Ba komai umma. Da sassafe ya kabir ya shirya..Bayan sunyi sallama da umna, nurr Har bakin titi ta raka shi sannan ta juyo gida.. Da azahar umma na zaune tana saka, Nurr kuwa ta aike ta makota.. ba zato ba tsammani, sae ganin su kawu tayi sun shigo.. Hantar cikin umma ce ta kada, fuskar nan tasu a murtuke.. Kaĺlon kallon suka shiga yiwa juna da umma.. Tashin hankali ya hana umma ta gaishesu.. Wato dije kin rika ko?? Kina ganinmu amma baza ki gaishe mu ba ko?? Lalle wuyanki ya isa yanka.. cewar baba ja'afaru Rabu da ita yaya.. Ba wannan ne ya kawo mu ba.. Ina maryama?? Kar kiyi tunanin rashin dawowar mu akan lokaci ko mun fasa kudirinmu. Ko daya, kawai tafiyar gwaggawa ce ta same mu zuwa kauye.. Dan haka tana ina?? Ta fito mu wuce.. Sai a sannan tayi magana.. Na aika ta nan makwafta bari na kira muku ita.. Da sauri ta fice.. Sai gasu sun shigo tare.. ganin su kawu tsaye yasa tasha jinin jikinta.. Gaishe su tayi suka amsa a dakile.. Ke ba bata mana lokaci zakiyi ba, ki dauko kayanki kizo ki wuce mu tafi.. Cikin rashin fahimta tace mu tafi ena umma?? Hawaye ta gani a fuskar umma, kafin tayi magana kawu takur ya fisgota ya hankada ta waje.. Tana ihu tana turjewa haka ya turata mota suka jaaa.. Durkushewa umma tayi a wurin tana hawaye.. Ba abinda take tunawa sae halin da nurr zata shiga a wurinsu kawu.. Da kyar ta mike jiri na daukarta ta shige daki.. Haka ta wuni. Ya dade yana sallama kafin nan umma ta fito, shimfida mishi tabarma tayi sannan taja kujera ta zauna.. Bayan sun gaisa yake tambayar umma kabir fa?? Na kwana biyu ban ganshi ba.. Kabir baya nan yaje abuja interview.. Har ya gama zamansa bai ga fitowarta ba.. Umma ni kuwa ina nurr banji duriyarta ba.. Nan umma ta shiga matsar kwalla, nan yaji hankalin sa ya tashi, kar dae wani abun ne ya sameta.. Umma me ya faru?? Wani abun ne ya sameta?? Yan uwan mahaifinta sunxo sun tafi da ita.. Sun tafi min da ita bansan inda zasu kai min ita.. Ina tsoron kar su cutar da ita don nasan basu da imani. Nan kuka yaci karfinta.. Kansa ne ya kulle. Kwata kwata ya rasa inda zancen umma ya dosa.. Sai daya tattaro nutsuwarsa sannan ya shiga baawa umma baki.. Ba abunda zasuyi mata umma.. Ba yan uwan mahaifinta bane.. Ai inaga kamar bazasu cutar da ita bako?? Bakasan su waye yan uwan mahaifinsu bane shisa.. Mutanen nan sunyi nisa a zalunci.. Ni nasan halinsu.. Nan umma ta shiga bashi labarin rayuwarsu. Tun daga sumaila har zuwa lokacin da suka yi aure da babansu nurr, zaman su a abuja.. Nan ta dan numfasa sannan tace.. Ranar da bazan taba mantawa da ita ba, ina zaune a falo muna waya da alhaji,(Babansu nurr kenan).. Nan yake sanar dani ya samu kwangilar nan fa yanzu haka ma gobe zai wuce lagos.. Murna na shiga yi saboda nasan indai akai kwangilar nan mun gama warkewa.. Sallama naji, na katse wayar sannan na amsa sallamar.. Su uku suka shigo, jaafaru ne a gaba, sae tukur da sulaimanu suna bayansa.. Da sauri na mike ina gaishesu.. Ba wanda ya amsa mini sae sulaimanu.. Sae ma wani banzan kallo da suka bini dashi.. Na riga nasan halin yan uwan mijina, sam basa son shi amma basu taba nuna wa a agaban sa. Shi kuwa da zuciya daya yake zaune dasu. Ina wannan sakaran mijin naki? Yaje aiki na basu amsa, na wuce kitchen don kawo musu ruwa.. Bayan na ajiye ruwan na juya na wuce daki.. Suna zaune naji shigowar Alhaji.. Aikuwa yana ganinsu ya shiga washe baki, nan danan ya hau dawainiya dasu.. Da daddare ina jinsu suna hira, nan yake shaida musu ai gobe ma zaeje lagos akan wata kwangila.. Sunka shiga washe baki, amma a mota zakaje ko?? Tukur ya tambaya.. A ah a jirgi nakeson zuwa, suka dan dubi juna, Kai amma munso a mota zaka ai da mun bika... Don wallahi ina matukar son zuwa lagos a cewar ja'afaru.. Jim ya danyi sannan yace va komai sai muje a motar.. Yawwa kaga sai mu tafi muna hirar mu har muje.. Ranar saboda murna tare suka kwana.. Raba dare sukau suna hira.. Ni kuwa duk sai naji hankali na bai kwanta ba. Da asubah bayan ya shigo daga masallaci.. Na kira sunansa, umm ni kuwa abban yara bana son tafiyar nan taka a mota.. Hankali na sam bai kwanta ba.. Karki damu, ba abunda zai faru. Kinga sun nuna min zasuje bai kamata na watsa musu kasa a ido ba... Ba yanda na iya dole naja bakina nai shiru.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 7⃣1⃣➡7⃣5⃣ By harphsart Rano✍ Ta dan numfasa sannan ta cigaba.. Haka suka shirya ina jinsu suka fito, a falo na shirya musu a bin kari.. Sai da sukaci sukayi katt.. Shikuwa alhaji ko abincin ya kasa zama yaci.. Sun fito zasu tafi ne sulaimanu yace ai shi bazai bisu ba.. Galla masa harara ja'afaru yayi sannan yace kadda Allah yasa kaje. Na lura dakai kwata kwata bakason zumunci wlh.. Shidai shiru yayi yana sauraronsa.. Bayan da Alhaji bai yi dashi akan ya bisu ba amma sam yaki.. Haka suka ja suka tafi ko driver basu bari yaa bisu ba.. Haka kawai naji zuciyata ta cinke, kwata kwata hankali na bai kwanta ba.. Na dawo daki na zuba tagumi, chan naji dawowar yara daga makaranta.. Dole na mike na fita kafin su shigo su tarar dani a haka.. Kasancewar su yara masu wayo.. Chan dare sai ga kiran Alhaji, jikina na rawa na daga.. Jin muryarsa yasa nayi ajiyar zuciya.. Nan yake sanar dani sun isa lafiya sai gajiya.. Haka mukayi hirarmu sannan ya nema na bashi yaransa yaji muryoyinsu.. Sun dade suna zuba masa surutu daga karshe yayi mana sallama.. Tou kwanansu biyu a lagos, abinda yaje nema anyi nasaraa.. Da haka ya kirana yana sanar dani, Murna yake sosae nima na shiga tayashi.. Washegari suka shirya don juyowa... Ina zaune a parlour, Ina jiran isowarsu. A lissafin da nayi dga fitowarsu nasan suna gab da shigowa.. Tun Ina zuba ido ina duba lokaci har tara na dare babu su ba alamarsu.. Waya kuwa na kira sau ba adadi, amsar dae daya ce akashe take.. Nan fa hankali na ya tashi.. Ganin zaman bazae mun ba yasa na dauro alwala.. Ina nan akan sallaya naji shigowar mota, zumbur na mike nayi waje.. Sororo na tsaya ina kallonsu. Dukkaninsu sun sunkuyar dakai kasa.. Wani bakin mutum na gani gefensu yasha riga da wando. Babu alamun fara'a a fuskarsa.. Gabana ne ya yanke ya fadi, Muryata na rawa na shiga tambayarsu, Lafiya yaya na ganku haka?? Ina mijina?? Me ya faru ku sanar dani?? Ba wanda ya tanka min.. Na shiga rusa kuka, ganin zan tara musu jama'a yasa tukur daka min tsawa. Mijinki Allah yayi masa rasuwa.. Kuma maganar gawarsa mun riga mun binne ta achan saboda mun isa Jiri naji yana dibana bansan sanda na yanke jiki na fadi ba.. Toh bayan sati daya da mutuwar alhaji, sun tsaya sosae wajen karbar gaisuwa... Ina zaune a daki, tukur ya shigo min ko sallama babu.. Gobe ki shirya zamu je wani guri.. acewar tukur, Kuma tare da yaran, sannan bana bukatar ki dau wani abu.. Da sanyin safiya muka kama hanya.. Muna ta tafiya, sai gamu a kano.. Wannan gidan da muke ciki shi ya kawo mu ya dire, wannan shine abunda kula mallaka keda yayanki na daga dukiyar dan uwanmu.. Kuma anan nakeso ku cigaba da zama dan nima kwanannan zan dawo garin Karki tunanin guduwa da yayan dan'uwanmu, duk wani motsinki ido na na kai, yana kaiwa nan yajuya ya tafi.. Safwan ya zaro handkerchp ya goge kwallar data zubo masa.. Lallai umma kunga rayuwa, In sha Allah nayi miki alkawarin sai na kwato muku yancinku.. A ah Dr karka sa kanka cikin hatsari.. Mutanen nan basu da imani.. Ba komai umma, Allah yana tare da mai gaskiya.. Yanzu ki bani adress din shi wanda ya tfi da nurr.. Iya zamana ban taba zuwa gidansa ba amma nasan a unguwar dorayi yake.. Toh shikenan umma ni zan koma amma kiyi hakuri.. Zan shigo da safe kafin na tafi aiki.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Bangaren nurr kuwa, tunda suka tafi hanya take kuka.. Ba wanda ya tanka mata a cikinsu.. Suna isa gidan duk suka fito daga motar, ganin bata da niyyar fitowa yasa kawu zuro hannusa ya rankwasheta sannan yace toh fito ja'ira mai halin uwarta.. Zabin rankwashin taji har kwakwalwarta.. Ba shiri ta fito.. Gida ne mai kyau, Suna shiga gidan ashariya ce ta fara yi musu maraba.. Suwaiba ce matar kawu tukur take ruwan balaee.. Toh jahila dabba, kefa kwta kwata kwakwalwar kifi gareki.. Sai ihu kike kamar wata jaka.. A cewar kawu.. Aikuwa ba shiru ta juyo kansa ta fara surfa masa ruwan masifa.. Kada kansa yayi ya shige ciki baba ja'afaru ya mara masa baya.. Sai a sannan suwaiba ta lura da nurr... Sarai tasan tare suke da mijinta don tasan komai.. Amma kuma sai ta nuna kamar bata masan wace ba.. Kallonta tayi a wulakance sannan tace ke kuma fa?? Kin wani tsare ni da ido kamar mayya. Dallah zo ki wuce kafin raina ya baci.. (Har na hango idon maryama, dama ga shegen tsoro kamar farar kura🙊) Sim sim sim nurr ta wuce ta dau hanyar dakin data ga su kawo sun shiga.. Ai kuwa sae ji tayi an fisgota, na yarda baki da hankali, ina kuma zaki.. Ga inda nake nuna miki chan.. Kallon hannun ta tayi taga inda take nuna matan, wani dan kurkutacchen daki ne irin na karkashin bene.. Da sauri ta mayarda kallonta zuwa ga suwaiba, Auw wai kin zata zan kaiki daki na ne?? Lalle yarinya wuyanki ya isa yanka.. Dallah janye tsumman kafafuwanki daga nan..(wayyo Allah nurr dita😭😭) Kuka ta shiga yi ta nufi dan kurkutacchen dakin.. Suwaiba ce ta shiga tafa hannu tana salati, kuka kike yi yarinya?? Lalle kuwa hawayenki zasu kare.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Bayan ya isa gida kai tsaye daki ya wuce, khaleel na ya shigo yace yazo mummy tana kiransa.. A falo ya tarar dasu dukka, gefen islam ya samu ya zauna.. Muje dakina inason mafana dakai.. Mikewa yayi yabi bayan mommy.. A gefen gado ya zauna ya tallafo fuskarsa yana kallon mommy.. Kasan dalilin dayasa na kiraka?? A ah mommy. Toh ba wani abu bane illa jiya munyi magana da daddyn ku yace na fada maka, lallai lallai ka fada masa yarinyar da kake so, don ya lura kwana biyu kana yawan fita, kuma ana gaya masa ana yawan ganinka a hanyar hotoro. Toh yasan duk yanda akai budurwa ka samu a unguwa.. Kasan daddyn ku baya son ai prolongin abu shi yasa yace ka sanar dani sai suje su tambayar maka aurenta.. Dankari ya fada cikin zuciyarsa.. Ana wata ga wata.. Shidai yasan yana son nurr amma a halin da ake ciki bazai iya kai daddy gurin yan uwan babanta ba saboda yasan halin daddynsa.. Baya son mutane irinsu kawu.. kuma madai ya fiso ta gama karatunta Yadai? Naji kayi shiru.. Ummm dama mommy akwai yarinyar danake so amma kuma yarinya ce karama, She's jst 16 What?? 16?? Kaina kake son Yar 16yra?? I dont believ it, Anya ba raenan wayo zakai ba kuwa safwan?? Nasha jin hirarka dasu *jabeer* akan irin matar da kakeso.. Wallahi mommy da gaske nake miki yarinya ce karama.. Jinjina kanta tayi tana kallonsa.. Shikenan zan fada wa daddyn naku haka.. Tashi kaje. Sai daya bude fridge ya dau fresh milk mai sanyi sannan ya wuce.. ♡♡Thanks all for ur well wishes, Am getting much better Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 7⃣6⃣➡7⃣8⃣ By Harphsart Rano✍ ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Yana komawa daki ya fada kan gado, Dafe kansa yayi.. Tunani ya shiga yi.. Labarin da umma ta bashi ya tsaya masa rae.. And gaskiya yana suspecting wani abu.. Allah sarki Nurr dinshi ko wanne hali take ciki?? Ba shida amsar tambayar nan.. Ji yayi yana bala'een son ganinta, Amma yasan ba hali.. Zuciyarsa tae masa nauyi.. Wayarsa ce ta shiga kara, dubawa yayi yaga bakuwar number.. Bin wayar yayi da kallo harta katse, after sum minutes sae ga kiran ya kara shigowa. Tsaki yaja sannan ya daga wayar ya kara a kunnensa.. Daga dayan bangaren yaji ance haba Aboki ina ta kirankw tun last week amma baka piking.. Dan Allah kayi hakuri kila bangani bane ya bashi amsa.. Ba komai ya gida ya aiki, cire wayar yayi a kunne ya dan kalli numbar sannan ya mayar.. Sun dan gaisa sama sama, alamun da sadeeq yaji ya gane sam safwan bai gane waye ba.. Na lura sam baka ma gane waye bako?? Kafin yace komae ya cigaba,, Abokinka ne da kuka hadu a mall.. Lalalala kace naso nayi laifi, dan Allah kayi hakuri amma.. Noo ba komi i understand, nan aka sake sabon gaisuwa.. Kafin su gama wayar sae da sukae exchangin address din juna.. Cikin dare haka yayi ta juyi sam babu alamun barci a tare dashi.. Bayason sama kansa yawan tunani kasancewarsa likita.. Amma bazae iya resisting ba.. Abun da ya sami nurr kamar ya sameshi ne.. Yana sonta sosae and kuma yana jin zae iya komai akanta (Toh fa).. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Nurr kuwa Allah sarki, Ni kaina sae dana tausaya mata, kafin dare tasha masifar suwaiba harta godewa Allah.. Kuka kuwa tayishi kamar ba gobe.. Fuskar nan tayi jaaa.. Dadinta daya, kawu ya lallabi suwaiba bayan ya bata kudi akanta barta ta dunga kwana A falo. Cikin dare tana kwance a kasan carpet wanda in banda doyi ba abinda yake.. Zurr taji wani abu ya bi mata kafa.. Ta dan saurara taji ko zaa kara yi. Aikuwa taji kamar ala lasar mata kafa.. Innalillahi, wani narkeken bera ne kamar girman skul bag din ayadh🙊.. Ihu ta saki ta mike tana zazzare ido, a tunaninta suwaiba zata fito.. Ina ita bata san ma wainar da ake toyawa ba.. Tana chan ta hangame baki😧 Komawa tayi kan kujera ta dukunkune, suwaiba ta mata warning karta kuskura ta hau mata kujera amma ya ta iya,.. Kasa barcin tayi tana ta tunanin ummanta. sae chan wajen asubah barci mai nauyi ya dauketa.. Wani wawan duka suwaiba ta sakar mata a kafarta.. zambur ta mike tana raba idanu😳.. Uban waya baki izinin hawar min kujera iyeee??? Yau sae kin gane kurenki.. Hakuri ta shiga bata amma kamar kara ingizata take, sae data gaji don kanta sannan tayi shiru.. Mikewa tayi tayo alwala, tana idar da sallah taga suwaiba a tsaye akanta.. Bata jira ma tayi addu' a ba ta fara zayyana mata irin aikin da zatayi mata.. Aikuwa tunda ta fara aikin nan sae data wuni tana yi.. tana gama wannan zata jido mata wannan... Sae gap da magriba ta samu ta kyaleta.. Wanka kuwa dama baa maganarsa... ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Bayan ya shirya, ya fito.. Kai tsaye dankoli store ya wuce, Kayan abinci ya jidarwa umma da duk wani abu dayasan zata bukata.. A tsakar gida ya tarar da ita tana kokarin shimfida tabarma.. Basuyi wata doguwar magana ba ya mike saboda yana da patients da yawa.. Yara ya samu suka shigo masa da kayan.. Umma kawae gani tayi ana shigo da kaya.. Mamaki ne ya kamata, lallai yaron nan da kokari yake.. Bata kara shiga mamaki ba sae data ga dubu goma a cikin kayan.. Sae data zubar da kwallah.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Bangaren kabeer kuwa anyi interview sae jiran sakamako.. Ganin yamma tayi yasa alhaji yace ya kara kwana sae ya taho da safe.. haka kuwa akayi.. Safiya nayi ya kamo hanya sae *kano*.. Da farin cikinsa ya shigo, Umma na ganinshi ta shiga murna, Lale da mutan abuja, sannu da dawowa.. Shiru baiji mutuniyar tashi ta fito ba, umma kanwata fa?? Naji ta shiru ko kin aiketa ne??.. Nan umma ta shiga bashi labarin abunda ya faru.. mikewa yayi ya shiga balaee.. Sae daya gama dan kansa sannan umma ta zaunar dashi.. Ta dan lallabasa sannan ya hakura.. Amma ya kudurce a ransa sae yaje har gida ya dauko kanwarsa.. Gidan baba ja'afaru kawae ya sani shine da suke da zuwa in wani abu ya taso shima tunda nurr taje akae mata wannan wulakncin basu sake komawa ba.. Amma dukda haka sae ya nemo gidan.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Yau satin nurr biyu gidan kawu..har ta fara sabawa da wahala.. Ba laifi kawu yana dan raga mata.. Amma suwaiba kuwa inaa.. Suwaiba ce ta kwalo mata kira, zokije nan gidan da yake kallon layin nan ki kaimin markaden nna. Kuma saura ki tsaya wasa wlh sae na lahira ya fiki jin dadi.. Fitowa tayi tana tafiya a hankali, kwata kwata ta zama wata lazy.. Mika markadan tayi ta tsaya daka zauren gidan.. Parking yayi daidai kofar gidan, wani matashine hadadde ya fito, kana ganinsa kaga bafulatani..dogo ne sosae.. Kallon unguwar yayi sannan ya shiga danna wayarsa.. Ji nayi yace nafa karaso ina kofar gida.. Owk pls kayi sauri.. Ya katse wayar.. Yananan tsaye yana karewa unguwar kallo, gaskiya unguwar taci sunanta china😂 saboda yawan mutanen unguwar.. Fitowa tayi dauke da markaden a hannunta, hasbunallahu ya furta, Binta yayi da kallo har tazo ta wuce ta gabansa.. Ganin zatayi masa nisa yasa shi saurin binta yana yanmata yanmata.. Kamar daga sama taji ana mata magana.. Karasowa yayi suka jera, baby sannu ko.. Bata tanka masa ba.. Dan Allah ki tsaya ki saurareni.. Kinga bai ma kamata na tsaida ki a hanya ba.. Ni sunana barrister sadeeq kibiya.. Ko zaki fadi min sunanki?? Ganin bazae kyaleta ba gashi tazo kofar gida yasa tace mishi sunanta maryam sannan ta shige gida.. Dariya yayi ya daki kansa.. Komawa yayi ya tarar abokin nasa har ya fto.. A ah kai kuma dga ina?? Hmm mutumina wlh yau zuwana unguwarku na kama babban kifi.. Naga wata beautiful baby.. I jst fall for her.. Wlh lurv at first sight .. ♡♡Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 7⃣9⃣➡8⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Dafa shi kamal yayi yace haba abokina calm down.. Kasan yadda ka hadunnan ba yarinyar da zaka nema bata soka ba.. Ka fada min inane gidansu nikuma nayi ma alkawarin sae tasoka.. Hannu yasa ya nuna masa gidan da ta shiga, a rasane kamal ya maida dubansa gareshi.. Ganin sadeeq yana masa kallon tuhuma yasa ya dan wayance.. Lalle mutumina, toh karka damu zan bincika naji ko wacece duk da dae nasan yaran gidan yara ne.. Manyan duk an aurar dasu. Kila bakuwa ce tazo amma kabar komi hannuna.. Haka sukae sallama ya kama hanya yanata tunanin maryama😘. Har ya dau hanyar gida sae kuma ya fasa, waya ya ciro ya shiga kiran safwan.. Shi dae haka nan yaji safwan yayi masa kuma. Yana son suyi abota.. Jin an daga wayar yasa ya katse tunanin.. Likita bokan turai, ya gida ya aiki.. Daga dayan bangaren safwan yayi dariya yace babban barister ka fiya tsokana wlh gida lfy wlh.. Sun dan taba hira sannan yace masa ya jira sa a gida yau zae shigo bayan magriba.. Haka kuwa akayi bayan sallar magriba sadeeq ya shirya sae nassarawa g.r.a A daedae gate en gidan ya tsaya ya kirawo safwan.. Nan ya shaida masa ya karaso.. Fitowa yayi, yae masa iso zuwa falon baki.. Nan suka shiga hira kamar sun dade da sanin hira.. Tun safwan na baya baya har shima ya ware.. Yau fa nayi babban kamu aboki.. Dan Allah?? Wallahi kuwa. Nn ya bashi labari. Tafawa sukayi safwan yace gaskiya ne yallabai.. Ba sanya wato har binta kayi.. Ai abokina wanann harkar ba'a sanya.. Gobe goben nan zan koma. Babe din ta hadu over. Nurr ce ta fadowa safwan.. Allah sarki ko tana wanne hali.. Ganin yayi shiru yasa sadeeq kiran sunan sa.. Yadai aboki?? Ko dae ka tuno babe dinka ne😂.. Dariya yayi sannan ya dan harare sa.. Sae kace wani kai.. Suka tafa. Sadeeq bai bar gidan nan ba sae wajen tara na dare, sae daya shiga ya gaida mommy. Ai tuni su khaleel suka manne masa.. Ya dinga jansu da magana suna dane masa jiki.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Kabeer ne ya kalli umma, sannan yace Umma gobe zanje gidan baba ja'afaru. Inaso naji wani abu game da kanwata.. Dole su bani ita na taho da ita don wlh hakuri na ya kare.. Jin umma tayi shiru yasa yace umma baki ce komai ba. Me zance abba? Ni abun nan ya ishe ni.. Kaje kaji yanda ake ciki.. Yawwa umma dama amincewarki nake nema.. Washegari ya shirya sae gidan baba ja'afaru .. A kofar gida ya tarar da hamza dan gidan baba ja'afaru.. Suka gaisa sannan ya shiga ciki.. Baba ja'afaru na ganinsa ya damke fuska.. Mara kunya me ya kawo ka gidana?? Ko yau ma kazo kamin rashin kunya ne?? Har zae tanka sae ya tuno umma tace karya kuskura ya tanka masa. Batason rashin kunya. Dukar da kansa yayi ya shiga gaisheshi.. A dakile ya amsa sannan ya dora.. Kayi gaggawar sanar dani abunda ya kawo ka. Dama zuwa nayi naga nurr.. Ka bani ajiyarta?? Toh bansan inda take ba. Tashi ka bani wuri.. Haka ya dawo gida batare da wani kwakkwaran bayani ba ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Nurr durkuce tana wanke wanke, suwaiba kuwa tana zaune a kofar falo tana yan wake wakenta.. Duniya tayi mata dadi.. Ita fa yanzu bata wani aiki tun zuwan nurr.. Yaranta ne suka jeho mata ball daedae goshinta.. Kyalkyalewa sukayi da dariya, ganin ta taso zata kamasu yasa suka fice da gudu suna mata ihu.. Yana tsaye kofar gidan yaga yara sun fito, daya daga ciki ya kira yace ya shiga ya kira masa maryam..Kasancewar kawu tukur maryam yake cewa nurr yasa yaron ya gane wayake nufi.. makale kafada yayi yace masa bazan kirata ba sae ka bani kudi.. dariya yayi ya zaro sabuwar dari biyu ya mika masa. Aikuwa da gudu ya shiga gida yana kwala mata kira.. Suwaiba ce ta ganshi ya shigo rike da kudi yana kiran nurr.. Tasowa tayi da sauri ta rike shi, kallon kudin hannunsa take tana masa dariya.. Yawwa yaron kirki aina ka samo wannan kudin haka?? Wani ne a waje yace na kiramai maryam shine ya bani.. Washe baki suwaiba tayi.. Maza maza wanke hannunki kizo kije ana kiranki a waje, ta juyo ta sauri tana mamaki. Wani lafiyayyem murmushi ta kara sakar mata.. Taso mana karya gaji da jira kinji yar nan.. Zuwa tayi ta dauko hijab dinta, sae data zo zata fita sannan suwaiba tace karki yarda ki dawo min cikin gidan nan bako kwandala kingane ai.. Yake tayi ta wuce tana mamakin irin halin suwaiba.. Tana ftowa taga wannan na jiyan daya biyota.. gefe ta samu ta tsaya.. bae jira komae ba ya shiga zuba mata surutu.. Tambayoyi kuwa ta shasu.. Tana amsa masa wasu wasu kuma tayi masa banza.. Amma ba laifi yana da abun dariya ga saurin sabo.. yanda ya sake da ita.. Sati guda kabeer yana zaryar gidan baba ja'afaru amma babu wani chanji.. 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 7⃣9⃣➡8⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Dafa shi kamal yayi yace haba abokina calm down.. Kasan yadda ka hadunnan ba yarinyar da zaka nema bata soka ba.. Ka fada min inane gidansu nikuma nayi ma alkawarin sae tasoka.. Hannu yasa ya nuna masa gidan da ta shiga, a rasane kamal ya maida dubansa gareshi.. Ganin sadeeq yana masa kallon tuhuma yasa ya dan wayance.. Lalle mutumina, toh karka damu zan bincika naji ko wacece duk da dae nasan yaran gidan yara ne.. Manyan duk an aurar dasu. Kila bakuwa ce tazo amma kabar komi hannuna.. Haka sukae sallama ya kama hanya yanata tunanin maryama😘. Har ya dau hanyar gida sae kuma ya fasa, waya ya ciro ya shiga kiran safwan.. Shi dae haka nan yaji safwan yayi masa kuma. Yana son suyi abota.. Jin an daga wayar yasa ya katse tunanin.. Likita bokan turai, ya gida ya aiki.. Daga dayan bangaren safwan yayi dariya yace babban barister ka fiya tsokana wlh gida lfy wlh.. Sun dan taba hira sannan yace masa ya jira sa a gida yau zae shigo bayan magriba.. Haka kuwa akayi bayan sallar magriba sadeeq ya shirya sae nassarawa g.r.a A daedae gate en gidan ya tsaya ya kirawo safwan.. Nan ya shaida masa ya karaso.. Fitowa yayi, yae masa iso zuwa falon baki.. Nan suka shiga hira kamar sun dade da sanin hira.. Tun safwan na baya baya har shima ya ware.. Yau fa nayi babban kamu aboki.. Dan Allah?? Wallahi kuwa. Nn ya bashi labari. Tafawa sukayi safwan yace gaskiya ne yallabai.. Ba sanya wato har binta kayi.. Ai abokina wanann harkar ba'a sanya.. Gobe goben nan zan koma. Babe din ta hadu over. Nurr ce ta fadowa safwan.. Allah sarki ko tana wanne hali.. Ganin yayi shiru yasa sadeeq kiran sunan sa.. Yadai aboki?? Ko dae ka tuno babe dinka ne😂.. Dariya yayi sannan ya dan harare sa.. Sae kace wani kai.. Suka tafa. Sadeeq bai bar gidan nan ba sae wajen tara na dare, sae daya shiga ya gaida mommy. Ai tuni su khaleel suka manne masa.. Ya dinga jansu da magana suna dane masa jiki.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Kabeer ne ya kalli umma, sannan yace Umma gobe zanje gidan baba ja'afaru. Inaso naji wani abu game da kanwata.. Dole su bani ita na taho da ita don wlh hakuri na ya kare.. Jin umma tayi shiru yasa yace umma baki ce komai ba. Me zance abba? Ni abun nan ya ishe ni.. Kaje kaji yanda ake ciki.. Yawwa umma dama amincewarki nake nema.. Washegari ya shirya sae gidan baba ja'afaru .. A kofar gida ya tarar da hamza dan gidan baba ja'afaru.. Suka gaisa sannan ya shiga ciki.. Baba ja'afaru na ganinsa ya damke fuska.. Mara kunya me ya kawo ka gidana?? Ko yau ma kazo kamin rashin kunya ne?? Har zae tanka sae ya tuno umma tace karya kuskura ya tanka masa. Batason rashin kunya. Dukar da kansa yayi ya shiga gaisheshi.. A dakile ya amsa sannan ya dora.. Kayi gaggawar sanar dani abunda ya kawo ka. Dama zuwa nayi naga nurr.. Ka bani ajiyarta?? Toh bansan inda take ba. Tashi ka bani wuri.. Haka ya dawo gida batare da wani kwakkwaran bayani ba ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Nurr durkuce tana wanke wanke, suwaiba kuwa tana zaune a kofar falo tana yan wake wakenta.. Duniya tayi mata dadi.. Ita fa yanzu bata wani aiki tun zuwan nurr.. Yaranta ne suka jeho mata ball daedae goshinta.. Kyalkyalewa sukayi da dariya, ganin ta taso zata kamasu yasa suka fice da gudu suna mata ihu.. Yana tsaye kofar gidan yaga yara sun fito, daya daga ciki ya kira yace ya shiga ya kira masa maryam..Kasancewar kawu tukur maryam yake cewa nurr yasa yaron ya gane wayake nufi.. makale kafada yayi yace masa bazan kirata ba sae ka bani kudi.. dariya yayi ya zaro sabuwar dari biyu ya mika masa. Aikuwa da gudu ya shiga gida yana kwala mata kira.. Suwaiba ce ta ganshi ya shigo rike da kudi yana kiran nurr.. Tasowa tayi da sauri ta rike shi, kallon kudin hannunsa take tana masa dariya.. Yawwa yaron kirki aina ka samo wannan kudin haka?? Wani ne a waje yace na kiramai maryam shine ya bani.. Washe baki suwaiba tayi.. Maza maza wanke hannunki kizo kije ana kiranki a waje, ta juyo ta sauri tana mamaki. Wani lafiyayyen murmushi ta kara sakar mata.. Taso mana karya gaji da jira kinji yar nan.. Zuwa tayi ta dauko hijab dinta, sae data zo zata fita sannan suwaiba tace karki yarda ki dawo min cikin gidan nan bako kwandala kingane ai.. Yake tayi ta wuce tana mamakin irin halin suwaiba.. Tana ftowa taga wannan na jiyan daya biyota.. gefe ta samu ta tsaya.. bae jira komae ba ya shiga zuba mata surutu.. Tambayoyi kuwa ta shasu.. Tana amsa masa wasu wasu kuma tayi masa banza.. Amma ba laifi yana da abun dariya ga saurin sabo.. yanda ya sake da ita.. Kwata kwta bai mata maganar soyayya ba.. Dazae tafi ya ciro kudi ya mika mata.. kin karba tayi ta shige.. Yaro ya kira ya bawa yace yaje ya kaimata. sannan ya tafi.. Aikuwa suwaiba bakinta kamar gonar auduga.. Nan nan ta shiga yi da ita ranar bata sake yin wani aiki ba.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Satin kabeer daya yana sunturin gidan baba ja'afaru amma ba wani sauyi.. Fitowa yayi zuciyarsa na tafasa, karo yaci da hamza.. Washe masa hakora yayi sannan yace nasan inda take fa.. Da sauri ya rike shi yana murmushi.. Allah hamza?? Wallahi nasani, tana gidan wanchan tsohon banzan. Toh ai ni bansan gidan nasa ba hamza ko zaka raka ni?? Eh to zan iya raka ka amma kaima kasan eh yane yane ka gane dae.. Hamza irin yan shaye shayen nan ne.. Tuni kabeer ya fuskanci inda maganar tasa ta dosa.. Hannu yasa a aljihu ya fito da naira hamsin ya mika masa.. Dariya ya saki yace yauwa mutumina ashe dae kaima A ne.. gobe da azahar mu hadu bakin titin gidan nan sae mu wuce kawae.. Bai jira amsa ba ya shige gida.. Yana komawa gida ya sanar da umma. Murna ta shiga yi.. Da daddare safwan yazo suka dade suna tattaunawa da umma.. So yake yaga yanda zasu bullowa al'amarin su kawu.. Nan take brr.sadeeq ya fado masa.. Dole zae nemishi suyi magana.. Lalle yasan zae taimaka masa kwarai. ☆☆☆Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 8⃣1⃣➡8⃣3⃣ By harphsart Rano✍ Washe gari kabeer ya shirya, a daedae kan layin ya tsaya yana jiran hamza.. Sha da daya sukae zasu hadu amma shiru ba hamza ba dalilinsa.. Ganin tsaiwar bazatae masa ba yasa ya yanke shawarar karasa wa gidan.. A daedae kofar gida ya tsaya yana tunanin shiga. Baya so ya shiga neman hamza baba ja'afaru ya ramfo su. Tun yana sa rai har ya fara fitar da rae.. Haka kawae yaji ransa ya baci.. Juyawa yayi ya bar unguwar.. Nurr zaune ita da sadeeq suna hira.. A yan kwanakin nan sunyi bala'een shakuwa. Kwata kwata bae taba mata zancen soyayya ba. Ganinsa take kamar yaya kabeer, yana debe mata kewar zaman gidan kawu.. Wayarsa ya jawo da take ringing. Dr. safwan naga an rubuta akan screen din wayar.. Dagawa yayi. Hello safwan ya ambata. Da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunan safwan. Safwan dinta ne ya fado mata. Yana chan Allah sarki. Wani hawaye taji ya zubo mata. A wayence ta goge Kullum ta zauna ita kadae bata da aiki sae tunanin safwan da ummanta. Ba abinda tafi bakin ciki irin burin da safwan yaci akan makarantar ta.. Gashi yanzu har an fara waec dinma.. Bata ji mae yace ba sae kawae taji yana sallama alamun ya gama wayar. Kallonta yayi yace yadae kanwata?? Naga mood dinki gaba daya ya sauya?? Wani abun ya faru.. yake tayi da yunkurin boye damuwarta.. Ba komae. Bae yarda da ita ba amma sae kawae ya share ganin bata son sanar masa. Mikewa yayi sannan yace mata zae wuce saboda akwae wata yar unguwa da zashi. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ A shab'an restaurant su kayi zasu hadu.. Wajen lokaci daya suka karaso. Bayan sun zauna ya musu orderin drinks. Basu wata duguwar magana ba safwan ya shiga masa bayanin abunda ya kawo su. Tsaf ya kwashe duk labarin da umma ta bashi ya sanar ma sadeeq. Sadeeq yau shiru yana tunani.. Lallai wannan aikin zae danyi wuya. Amma kuma kasancewarsa kwararre akan aikinsa yasa ya tabbbatrwa safwan in sha Allah zae yi bakin kokarinsa. Zae fara aiki daga gobe in sha Allah. Amma dole umma sae ta basu hadin kai. Zan shigo gobe sae muje ka kaini naga umman.. Godiya safwan ya shiga yi masa sannan suka fito kowa ya shiga motar sa.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Umma zaune ta zabga tagumi, tunanin nurr take. Lalle tasan zata sha wahala a gidan kawu. Kabeer ne a gefenta yana kallon yadda ta damu.. dazu ya sake komawa ko Allah zae sa ya hadu da hamza, wani dan unguwar ya gani ya tambaya sa ko ya ga hamza.. Nan yake sanar masa ai hamza yana gida ba lafiya.. Zawo yake fama dashi wajen kwana uku da ya wuce..😜 Dole yanzu sae ya jira ya sami sauki. Da yamma yayi wanka ya shirya sae gidan alhaji. Dama ya kirashi tun rana yazo gida yana son ganinsa.. Yana zuwa ya miko masa doguwar envelope.. Alhaji wannan fa ya tambaya.. Mika masa hannu yayi yace masa congratulation kaci interview da akae harma an tura ka *cyprust* Inda zakayi karatun _civil engineering_.. Ya salam, zo kaga murna wajen kabeee. Rasa inda zae sa kansa yayi.. durkusawa yayi har kasa yana ma alhaji godiya.. Dago shi yayi yana murmushi.. karka damu kabeer ni a matsayin da na dauke ka.. Kayi mun abunda bazan manta ba. Ka rike mun dukiyaa da amana. Wannan shine sakamakon hali na gari.. A sukwane ya shigo gidan, umma sae data dan tsorota. Daga ta sama yayi yana zagaywa da ita.. Kaji mun ja'irin yaro. Maza sauke ni ta shiga fada.. Sauketa yayi yana kyalkyala dariya. Tsananin farin ciki yake ciki. Nan ya bayyaa nawa umma abunda ya sashi farin ciki.. Aikuwa umma sae data dan taka💃🏻.. Lol Bayan sun natsa sae kuma nurr ta fado musu, da tuni da ita zaai wannan farin ciki. Amma ba komae dole kafin ya tafi dole yaje ya dawoo da ita.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Sallama akae wanda yasa kabeer fita don ganin me sallama. Safwan ya gani tare da wani a tsaye. A ah dr dama kaina bari toh na sanar da umma. Bayan ya sanar da umma ya dawo yae musu jagora zuwa ciki.. Zama sukayi suka gaida umma. Nan safwan ya gabatar da sadeeq a wurin umma. Sannu dan nan kaji, mun gode kwarai. Ba komai umma. Sadeeq ne ya numfasa sannan ya kalli umma, haka nan yaga umma tayi masa kama da wadda ya sani. Amma kuma sae ya kasa tuno ko wace. Share wa yayi ya shiga aikin daya kawo shi. Ya samu gamsassun bayanai agun umma. Nan take yae figuring yanda zae bullowa su kawu.. Shikenan umma na gode. In sha Allah in wani abu ya taso zan sake dawowa. Sallama sukayi wa umma sannan suka wuce. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Kabeer ya shiga busy kwata kwata baya ko samun zuwa wajen nurr. Duk wasu information ya gama hadawa. Aiki kawae zae fara aiwatarwa. Da daddare yadan samu yayi squeezn tym dinsa ya nufi wurin nurr. Taayi murna sosae ganinsa. Koba komae tayi missin dinsa kwana biyu.. Kuma har suwaiba ta fara takura mata kwana biyo taji shiru harka bata shigowa😂.. Duk abin nan da ake kawu sam bae sani ba. Allah bae taba sawa sun hadu ba. Aikuwa ranar suna zaune saega kawu faram faram da malun malun🙄.. Yana zuwa ya dalle su da torch light.. Kai kai kai kai wa nake gani kamar maryama. Lalle yau zakici kwal ubaki. Ai tuni cikinta ya duri ruwa, shikuwa sadeeq ba shiri ya mike. Ganin ya nufosu yasa ta arcewa tayi gida. Matsowa yayi gaban sadeeq yana kallonsa. Sae kuma yaji yaron yayi masa kwarjini. Masifar da yayi niyyar yi dole ya fasa. Gaisheshi yayi sannan ya gabatar da kansa a matsayin yaga maryam ne yana sonta.. Kafin kawu yayi magana ya zaro kudi ya mika masa yana murmushi.. Ai tuni kawu ya rikice, hannu na rawa ya warche kudin daga hannun sadeeq. Saura kadan dariya ta kwache masa.. Toh toh toh yaro, kayi kyan kai daka zo kana sonta.. Lalle ka cancanci na baka aurenta.. Maryama yarinyar kani nace amma kuma Allah yayi masa rasuwa. Kaga nike da alhakin aurar da ita.. Toh karka ji komae inda wadannan suna magana ya nuna kudin hannunsa.. Toh baka da matsala. Bari na shiga ciki na turo maka ita. Ya juya yana yan wake wakensa... Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 8⃣4⃣➡8⃣6⃣ By harphsart Rano✍ Tana tsaye tana jiran shigowar kawu.. Tabbas tasan zae iya bugunta. Addu'a duk wadda tazo bakinta fada take. Jin yana kwala mata kira yasa hantar cikinta ta kada.. Rarrabewa ta fara yi a bango, hasko torchlight din da yayi ne yasa ya ganta.. A ah kaga maryama yan mata, yarinyar arziki.. Wannan yarinya Allah dae ya zunduma ki a aljanna.. Maza koma wurin saurayin nake yar albarka.. (Kuji tsohon banza) Mamaki ne ya kamaata amma tunowar da tayi cewa babu abinda zae kawo chanjin kawu ta farat daya haka sae kudi.. Lalle kudi sadeeq ya bashi.. Rabewa tayi ta wuce dan har lokacin a tsorace take. Yana tsaye ta fito.. Dariya taso ta bashi yanda take sanda kamar barauniya. Ajiyar zuciya yayi sannan ya kalle ta.. Shine baki taba fada min a gidan kawunki kike da zama ba ko maryam?? Lalle dia is alaot da ban sani ba akanki. Bae jira amsarta ba ya cigaba.. Tun Farkon haduwata dake Allah ya saka min sonki a raina.. Naso na bayyana miki tun a lokacin amma sae nayi wani tunani. Gwanda na fara shiga jikinki mu saba. Daga baya sae na gabatar da kaina. Banso na fara sanar wa da kawu ba, amma kuma dukda haka nasan bazaki kini ba. Tunda ya fara magana take kallonsa da mamaki.. Ta san zaa rina. Alamunsa duk sun nuna mata sonta yake yi. Amma ya zatayi da safwan.. Sonsa mai girma ne a ranta. Shine mutum na farko daya fara haskaka musu rayuwarsu. Lalle idan ta manta da alkhairinsa garesu ta zama butulu. Toh amma shima sadeeq ya zama wani bangare na rayuwarta.. Ya taimaka mata alokacin da take neman taimako. Kuka ta shiga, ganin tana kuka yasashi rudewa, me ya same ki?? Kardae kice mun maganar da nayi miki ce ta bata miki rai.. Kiyi hakuri, banyi dan na bata miki ba. Girgiza kanta ta shiga yi tana jaa da baya. Tana zuwa karshe kawae ta shige gida. Tana ji yana kwala mata kira amma ina bazata iya zuyowa ba. Bazata iya hada ido dashi tace masa bata sonsa ba. Kai inma tace bata sonsa tayi karya. Amma hakan ba yana nufin tafi sonshi a akn safwan ba. Dafe kansa yayi yana karanto innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Me maryam take nufi da haka?? Kardae ace bata sonsa, ya salam ya furta. Toh kenan akwae wanda zuciyarta yake so. Ganin tunanin bazae masa ba yasa ya shiga motarsa ya bata wuta. Allah Allah yake ya gansa a gida. Kasancewar iyayensa duk suna kibiya yasa shi kadae yake zaune anan. Yana shiga gida ya fada kan kujera. Bae taba tunanin zae sami matsala da maryam ba.. A yanda ya fuskanta akwae wani al'amari me girma game da yarinyar. Akwae abunda bae sani ba akanta. Zae yi bincike amma.. Jawo waya yayi ya kira safwan. Nan yake shaida masa yanda sukayi da maryam.. Kokari yayi ya kwantar masa da hankali. Ya muna masa lalle ya bata lokaci.. Shikenan aboki zanyi yanda kace. Gobe in Allah ya yarda zanje gidan baba ja'afaru. Dga nan nakeson fara aiki na.. Fatan nasara sukayi wa juna daga nan suka ajiye wayar. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ A gurguje ya shirya, tea kawae yasa a cikinsa ya fice. Sae daya biya ya dauki *Detective salim* sannan suka wuce.. Daga gefen gidan ya samu wuri yayi parking motarshi. Sun jima suna karewa gidan kallo.. suna nan zaune cikin mota sae ga baba ja'afaru ya fito Da sauri salim ya fito ya gyara zaman hularsa. Tsaf ya fto a babban mutum. Kana kallonsa zakayi masa kallon kudi. Sae ka zata irin hamshakan alhazawan nan ne kasancewarsa me jiki. Sallama yayi wa baba ja'afaru.. Mika masa hannu yayi sannan yace ni sunana alhaji wada, in bazaka damu ba inaso mu danyi magana.. Fara'a fal fuskar baba ja'afaru yace sannu da zuwa alhaji. Muje daga ciki sae muyi maganar ko.. Ba damuwa suka juya suka shige gidan. Kwata kwata baba ja'afaru ya kasa zama., sae daya tabbatar ya cika masa gabansa da ruwa da juices sannan ya samu guri ya zauna. Gaisawa suka kara yi sannan salim ya dora. Dama naji labarinku ne kai da dan uwanka, ance kunayi aikin kwangila, kuma a gaskiya yanda aka bani labari naji kamar zamu daedae ta. Wata Kwangila ta taso, zamu sa miliyan biyu biyu, kuma indae anyi gwangilar nan a kalla dukkanmu zamu sumu ribar miliyan daya daya.. Wata iri zabura da baba ja'afaru yayi sae ta ya bawa salim tsoro.. Me me me kace?? Miliyan daya?? Baba ja'afaru basa wani aikin kwangila amma dan karya bari damar ta wuce su yasa ya amsa da zasuyi.. Zan kira tukur yau yau din nan muuyi magana.. Ai wannan damar bazata wuce muma alhaji.. Murmushi salim yayi ganin ya fara samo kan baba ja'afaru. Shikenan alhaji ni zan koma, ga number wayata. Zan dawo dadaddare sae mu hadu da kanin naka gaba daya muyi magana.. Yana shiga mota ya shiga kyalkyala dariya, sadeeq ne ya tsaya yana kallonsa. Sae bayan ya gama dariyar ya jawo yar recorder sa ya kunna.. Aikuwa sadeeq ya shiga dariyar shima saura kadan ya saki sitiyarin motar.. Salim ne yace lalle mutanen nan sunyi nisa wajen son kudi.. Kaga kenan bazamu sha wata wahala dasu ba, a cewar Sadeeq Sae daya kaishi har gida sannan ya wuce asibiti wurin safwan. Nan ya kwashe labarin abunda ya faru kaf ya fada masa. Shima dariya ya shiiga yi. Suka dan kara tattuna wa akan batun sannan suka gangaro kan maganar nurr. Safwan ne ya kalli sadeeq sannan yace, abokina akwae abunda ban fada maka ba.. Nan ya shiga bashi labarin soyayyarsu da nurr har zuwa koma warta gidan kawunta.. Shisa nakeso ayi gaggawar gurfanar dasu kawu a gaban koto don nurr dita ta dawo.. Inason ta koma makaranta, inason tayi zurfi a karatunta. Dafa shi sadeeq yayi sannan ya kalle shi. Karka damu abokina. Nayi ma alkawarin sai na dawo ma da nurr dinka.. Zaka aure ta, ni sadeeq nama wannan alkawarin. Nima ka taya ni da addu'a kar maryam taki ni.. Dan Wallahi zan iya shiga mummunan halin akanta.. Sonta ya riga yayi mun mugun kamu... Nan shima safwan ya shiga bashi baki. Basu rabu ba sae da sukayi convincin junansu.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Dare nayi suka kara shiryawa sae gidan baba ja'afaru.. A mota ya kara zama yana jiranshi. Kasancewar motar tinted glass ne yasa ba wanda zae san da mutum a ciki. Yana karasawa kofar gidan ya gansu a tsaye alamun shi kawae suke jira.. Bayan dogon sharhi da tsare tsare, sun gama amincewa zasuyi harkar. Salim ne ya rage murya ya kalli baba ja'afaru. Nifa da kuka ganni nan ko ya nuna kansa. Zan iya yin komai akan kudi.. Na wuce duk tunanin mutum, in takae ce muku bayani ni din nan da kuka ganni, yayana na kashe na kuma kwace dukiyarsa. Yaransa kuwa tuni na kada su suka bi duniya, bani da wata matsala daga ni sae yayana da matata. A lokaci daya suka kalli juna, yana lura dasu, aikuwa ya cigaba da karanto musu abunuwanda zae iya yi akan kudi.. Kawu ne ya katse shi yace, ashe alhaji tamu tazo daya, mu din nan daka ganmu muma kaninmu muka batar, muka kuma ce ya mutu. A karshe muka gaji dukiyarsa. Shine dalilin da kaganmu mun kawo wannan matsayin ko yaya ya fada yana kallon baba ja'afaru. Kwarai kuwa anyi haka, sae dae mu matsalar mu daya yaran nasa, naga alamun zasu iya kawo mana matsala musamman babban. Salim ya bata fuska. Kai amma alhaji kun bani mamaki, me kuka tsaya yi baku kawar dasu ba??.. Lallai kunyi sake, amma yanzu ma tunda har mun riga mun zama daya, zan muku taimako akae. Godiya suka shiga yi masa sannan sukayi alkawarin gobe gobe zasu bada kudinsu.. Ran kowa fari kal suka watse. Yana zuwa ya rungume sadeeq.. We did it bro.. Saura shigar dasu kotu. A kotu zasuyi mana bayanin yanda suka hallaka mahaifin yaran. Sosae sadeeq yaji dadi, ganin zae cika wa abokinsa burinsa. Yana zuwa gida ya kwashe komai ya fada wa safwan.. Shima murnar ya shiga yi yana hango nurr dinsa ta kusa dawowa. Kuma farin cikin umma ya kusa dawowa. Shiko sadeeq hankalinsa duk yana wurin maryam, kwana biyu ya bata lokaci bai sake komawa ba. Amma yau kam hakurinsa ya kare. Dole yaje ta sanar dashi abunda yake ranta. Shikuwa safwan suna rabuwa ya shirya sae gidan umma.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 8⃣7⃣➡9⃣0⃣ By harphsart Rano✍ Shirya wa yayi tsaf sannan ya fto, bayan ya kukkule ko ina ya fto zuwa mota. Wani mutum ya gani a tsaye alamun yana jiransa.. Mika masa hannu yayi suka gaisa. Gabatar masa da kansa yayi. Sannan suka koma cikin falo. Sun dade suna hira kafin su fito su shiga motar sadeeq Direct police station suka wuce bayan ya dauko detective salim. Nan sadeeq ya shigar da report inda wannan mutumin ya sake maimaita abunda ya fada wa sadeeq a gida.. Godiya yayi masa sannan yace ya zama cikin shiri ko wanne lokaci zasu iya nemansa. Dalilin zuwan wannan mutumin yasa dole ya hakura da zuwa wurin nurr.. bayan ya sauke mutumin suka wuce kai tsaye gidan detective salim Sun kara tattaunawa akan yanda abubuwan zasu kasance.. Ya kira safwan ya kara sanar dashi abunda ya faru. Mamaki ya shiga yi ya gode ma sadeeq. Kasancewar yana gidan umma yasa ya kwashe komae ya sanar da umma. Tayi farin ciki sannan ta kara yi musu fatan alkhairi.. Wai umma ya maganar nurr kuwa?? Har yanzu ya kabeer din bae samu zuwa ba?? Wallahi Dr. Amma yau ya tafi ganin ko yaron da zae rakashi ya samu sauki.. Muna dae zuba ido naga shiru bae dawo ba.. Shikenan umma ni zan wuce Allah yasa muji alkhairi.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Lokacin da khabeer ya karasa gidan baba ja'afaru, hamza da abokansa na zaune a kofar gida.. Hamza na ganinsa ya taso, tafawa sukayi sannan yayi masa ya jiki.. Basu bata lokaci ba suka kama hanya sae dorayi.. Akan layin kabeer ya tsaya , shiko hamza sae ya wuce bayan sunyi plannin yanda komae zae kasance. Shiga yayi cikin gidan kai tsaye ko sallama babu.. Suwaiba bata nan, tana makofta inda suke dasa dandalin gulmarsu. Kowa a unguwar ya riga yasan halinsu. A kofar kitchen ya tararda ita tana tsintar shinkafa. Kwana biyu da sadeeq bae zo ba ta shiga takura a wajen suwaiba. Shi kanshi kawun sae daya chanza mata. Ita kanta ta damu da rashin zuwansa, ba don wani abu ba sae don ta saba dashi.. Kuma dae bata ji dadin yanda suka rabu ba ranar ko ba komae sadeeq mutum ne.. Kallonsa tayi taga ya jawo kujera ya zauna, yan mata ya fda ya dan kashe mata ido irin na yan duniya. Kawar da kanta tayi dalilin tasan halin hamza sarai lokacin da take sunturin zuwa gidan baba ja'afaru. Ganin bata da niyyar kulashi yasa ya dan rage murya.. Ke kinga fa ba jan aji zaki tsaya yimin ba.. Tare muke da kabeeru yana kan layi yana jirana.. In zaki dauko hijab dinki mu wuce in kuma ba zaki dauko ba nayi tafiyata.. Bata san sanda ta saki farantin shinkafar ba, aikuwa ta tarwatse a tsakar gidan. Bata bi ta kai ba ta jawo hijab dinta akan igiya ta zura.. Shi kam dariya ma ta bashi.. Tsayawa tayi a gabansa ganin bashida niyyar tafiya yasa ta kafe shi da ido.. Karki cinyeni wuce muje. Yana gaba tana binsa a baya. Tsoronta daya kar suwaiba ta fito daga makota.. Har suka kusa barin layin jikinta bari yake.. Suna zuwa kaarshen layi ta hango yayanta ya tsaye alamun jiransu yake. Da gudu ta karasa ta rungumeshi ta saki kuka. Ganin mutane sun fara kallonsu yasa shi janyeta.. Ki nutsu mu wuce gida kinga mutane na kallonmu.. Kamal na kofar gidansu yana kallonsu.. Wannan ai ita ce yarinyar da sadeeq ke so. Toh me ya samesu haka?? Oho ya bawa kansa amsa. Suna tafe cikin adaidaita sahu ta makale yaya kabeer kamar wani zae raba su. Hamza kuwa sae kallonsu yake, sun dan bashi tausayi. Shi kansan ya tsani kawu tukur kasancewar ya taba jin wata hirarsu da baba ja'afaru. Ba shida kirki ko kadan kuma duk wani abu shi yake sa baba ja'afaru yinsa. Sunxo inda zasu sauke hamza, kabeer ya zaro dari biyu ya mika masa. Kallonsa yayi sannan yace ba komae dan uwa ka barshi kawae Ya juya ya tafi. Baki bude kabeer ya bishi da kallo. Hamza ne yaki karbar kudi?? Lalle tou ko rashin lafiyar da yayi ne ya sashi haka. Bata jira adaidaita sahun ta tsaya ba ta fito tana kwala ma umma kira. Kamar daga sama umma taji muryar nurr.. A firgice ta fto suka ci karo a tsakar gida.. Rungume umma tayi ta saki wani kuka me cio. Umman ma kukantake.. Shikuwa kabeer harde hannunsa yayi yana kallonsu gwanin tausayi. (Ni kaina bansan sanda na saki kuka ba😭) Da kyar suka samu sukayi shiru. Kin barin jikin umma tayi, a haka suka zauna suna manne da juna. Umma sae shafa mata kai take. Hira suka fara ta yaushe gamo. Kabeer ne yayi gyaran murya yace shikenan umma an manta dani nurr ta dawo ko?? Dariya umma tayi tace ba haka bane abbana kaima kasan kaine na karfen. Duka suka kyalkyale da dariya. Nan yake sanar da umma visar sa ta fito in two weeks zasu tashi. Kusan hantsulowa nurr tayi, kallon su umma ta shiga yi alamun tana neman karin bayani.. Dariya umma tayi tace bakyanan yayanki ya samu tafiyar nan zuwa kasar waje. An gama komae ma yanzu kinji ma nan da sati biyu zasu tashi.. Tsalle ta shiga yi tana ihu. Dama sun san zaa rina.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Suwaiba kuwa bayan ta gama zaman gulmar tata ta nufo gida don ganin ko nurr ta gama girki.. Tun daga waje ta fara kwala mata kira. Tattabaru ta gani sun cika tsakar gidan, shinkafar data zube duk sun kara barbazata. Kashi kuwa ko ina sunyi shi kacha kacha. Wata uwar ashariya ta saki ta shiga kiran nurr kamar zata fasa gidan.. Shiru ba alamun akwae mutum a gidan, dama yaran gidan basa zama a gida kullum suna unguwa suna daukar magana. Kan balaee ta furta, lallai yau yarinyar nan sae ta gane kuranta. Ko gidan ubanwa ta tafi. Tana tsaye tana jarabar data saba kawu ya shigo. Ganin ta tsaye ga shinkafa baja baja yasa shi kundumo ashar🙊 Shinkafar tashi ce haka a zube, lalle ma an raina masa hankali.. A wulakance ta kalle shi sannan tace, da zakazo kana wannan sababin nima haka nazo na tarar. Nabar yarinyar nan a gidan, kafin na dawo nazo na tarar da wannan aika aikar. Kuma abin haushin ma bata gidan kwata kwata. Sae kuma ya rude, ina ta shiga? Dama tana fita ne?? Kardae ace yarinyar nan ta gudu. Aikuwa yanzu zan bita in gani, bata isa ta ja dani ba wallahi. Gashi na karbi kudin alhaji mudi akan zan bashi aurenta. Kudin kuwa ma na riga na bawa Alhaji wada akan kwangilar da zamuyi.. Duk ya zauce ya rasa inda zaeyi.. buguzun buguzun ya juya, kicibis sukayi da yan sanda har guda biyar.. Ja da baya ya shiga yi, ganin zae juya yasa wani dan sanda ya damko shi. Ihu ya shiga yi wanda yasa suwaiba fitowa ba shiri. Turus tayi ganin kawu a hannun yan sanda. Kuka ta shiga yi tana hauka. Ita a lallai sae an saki mijinta. Angiza keyarsa sukayi sae police station.. Suna isa suka ga baba ja'afaru. An riga an kamo shi tuni.. Kallon kallon suka shiga yi. Bayan an kwace komae na jikinsu aga tisa keyarsu zuwa cell.. Hamza ne tsaye cikin station din sae kai kawo yake.. Wani dan sanda ne ya dube shi sannan yace ba wani abu zaai musu ba yan tambayoyi zasu amsa indae kuwa sun amsa daidai zaa sakesu. Haka ya juya jiki a sanyaye.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Mommy zaune da yaranta safwan ya fito fuskar nan fal farin ciki. Guri ya samu ya zauna yana kallon mommynsa. Mommy anjima idan na dawo zamuyi wata magana.. Yanzu zanje wata yar unguwa. Tom shikenan ka gaishe min da ita in kaje. Dariya ya saki ganin mommy ta ganosa. Har ya kae kofar fta khalil ya taso da gudu.. Big bro kafa ce min zaka dawo mna da anty nurr amma har yanzu. Kallon mommy yayi sannan ya jawo khalil. Karka damu little kwanan nan zanje har gidansu nace ta dawo. Dnt worry owk?? Daga kai yayi ya koma shi kuma ya fice.. Tunda ya dauki hanya yake ganin kamar baya sauri. Allah Allah yake ya ganshi a hotoro. Kabeer ne ya kirashi ya sanar dashi dawowar nurr. Umma ce ta sata a gaba tayi wanka. Doguwar rigar da ya bata ta dauko mata. Light make up tayi.. bayan tasa rigar ta rollin kanta da gyale pink. Tsaf rigar ta fto mata da figure 8 enta.. Kallon kanta tayi, ita kanta tasan tana da kyau.. Tsaya wa yiwa mai karatu bayanin yanda nurr tayi kyau kamar ma bata lokaci ne. Kasancewar umma irin fulanin gomben nan ne, kuma duk yaran nata ita suka yo... Tana tsaye tana karewa kanta kallo ta jiyo sallamar shi. Gabanta ne ya fadi. Sama sama take jiyo hirarsu da umma har ta daena ji. Hakan ke nuna mata ya fta kenan. Umma ce ta shiga kwala mata kira. A kasalance ta fto. Maza kije yana waje yana jiranki. A hankali take tafiya gabanta na tsananta faduwa. Tayi tsammanin zata ganshi a zauren gidan. Ganin baya xauren yasata karasawa waje.. Tunda ta fito ya kafe ta da ido.. Bae taba ganin ta cikin irin wannan shigar ba. Ganin tana dan dube dube yasa shi sauke glass din motar. Karaso yan mata ya fada fuskar nan tasa dauke da murmushi. A hankali ta taka har wajen motar. Bude mata yayi ta shiga ta zauna. Wani sanyi taji yana bin ilahirin jikinta. Shima hakan ce ta kasance dashi. Sunkuyar da kanta tayi ganin kallon da yake mata tana wasa da zoben hannunta.. Kinyi kyau taji ya ambata, yana kallonta. Kasa dagowa tayi sae kawae tace masa nagode. Matsowa yayi daf da kunnenta sannan ya furta. Anya nurr kinyi missin dina kuwa?? Dagowa tayi suka hada ido, murmushi ta sakar masa sannan tace Nayi missin dinka sosae ma. Gaskiya ni banga alama ba, ko kallona fa kin kasa yi balle kiga yanda na rame saboda rashinki. Ke kuwa ma kibar ki kikayi abinki alamun bakiyi missin nawa ba.. Zaro ido tayi ta kama baki, ina kiba anan? Ni dana rame ma. Ka ganka kuwa yanda ka kara kyau.. Dariya yayi sannan suka cigaba da hirarsu cikin so da kauna. Sae da yaga kiran sadeeq sannan ya tuna fa sunyi zasu hadu. Kwata kwata ganin nurr ya mantar dashi komae. Dan dole ba dan yaso ba sukayi sallama ya nufi wurin sadeeq. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Police station suka nufa, a hanya safwan yake bawa sadeeq labarin dawowar nurr dinsa. Nan yake gaya masa yanzu haka ma daga chan yake. Allah aboki?? Gaskiya nayi maka murna sosae. Shisa naga bakin yaki rufuwa ya fada a wasance.. Dakar kafadarsa safwan yayi yana dariya. Ina sonta ne sadeeq, komai nata is unique. Duk wannan abunda nake akanta nakeyi. Kaga kuwa nayi ma alkawari in mukayi aure, duk sanda nurr ta haifi namiji sadeeq zan sa masa saboda kokarin ka akanmu. Dadi ne ya rufe sadeeq, aboki ka gama min komae wlh. Nan shima safwan yake tambayarsa yanda sukayi da maryam. Aboki bari kawae ban samu naje ba har yanzu. Wannan case dinne ya ke delyin dina. Aikuwa babu wani police station da zamu je yanzu sae mun fara zuwa na shirya ku. Da kyar sadeeq ya yarda suka juya akalar motar zuwa dorayi.. Sun dade a kofar gida kafin su sami dan aike. Yaron ne ya dawo yace musu wai ance batanan taje kauye. Sam basu ji dadi ba amma ba yanda suka iya dole suka ja motarsu suka wuce p.station. Lokacin da suka karasa an tsare su kawo da tambayoyi, basu nemi ganinsu ba, direct wurin D.P.O suka wuce.. Nan yake shaida musu kwata kwata sunki yarda su fadi gaskiya akan tuhumar da ake musu akan dukiyar marayun. Daya daga ciki yana da taurin kai, amma ba komae zuwa gobe in basu fadi komae ba sae mu aika su zuwa kotu. Shikenan D.P.O, Sae naji daga gareka. Har sadeeq zae shiga inda su kawu suke sae kuma ya fasa. Baya jin dadin jikinsa, so yake yaje gida ya huta.. Gidan sadeeq din suka zarce kasncewar motar safwan din tana chan.. Sae daya san jima a gidan sannan ya wuce gida.. Wanka yayi sannan ya nufi dakin mommy. Jin motsin ruwa a toilet yasa shi komawa, kitchn ya shiga ya hado coffee sannan ya dawo falo ya zauna yana kallon t.v Fitowar mommy tayi daidai da gama shan coffee dinsa. Kitchen ya mayarda mug din sannan ya dawo ya zauna. sae daya fuskanci mommy sannan ya fara bata labari.. Tun zaman nurr a gidan da irin abubuwan da suka faru har zuwu yanzu da kamen su kawu da akayi. Kallonsa ta shiga yi da mamaki, ashe safwan zae iya duk wadannan abubuwan ba tare da ya sanar da ita ba. Mommy kiyi hakuri nasan banyi daedae ba, ya kamata na nemi shawararki kafin na aiwatr da komae. Mommy mace ce mai fahimta, nan take ta nuna masa ba komae ita bata ji haushi ba.. Kuma tana farin ciki da kasancewar nurr a matsayin wadda yake so. Fatan alkhairi tayi masa sannan ta mike ta shige daki. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Nurr da umma zaune suna hira, nan take bawa umma labarin sadeeq.. Da irin rabuwar da sukayi. Tana so ta sake ganinsa, tana jinsa har cikin ranta. Fara'arsa , barkwancinsa duk take tunawa. Allah sarki, gaskiya ya taimaka miki. A dalilinsa kin samu rangwamen zama a gidan kawu cewar umma. Amma ba komai wataran zaku hadu. Sae kiyi masa godiya. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 9⃣1⃣➡9⃣5⃣ By harphsart Rano✍ ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ A nutse yake tuki, kana kallonsa zakasan ba shida walwala.. Asibiti ya fara biyawa don su wuce da safwan, ganin aiki yasha kansa yasa shi tafiya shi kadae. Station ya nufa don jin inda zance ya kwana.. Bayan sun gama magana da dpo ya tabbatar masa da an riga an tura karar kotu. Saura kowa ya dauki lawyer.. Shikenan dpo ko zan iya zuwa nagansu?? Eh zaka iya zuwa ya fada gami da kwala wa sargent kira. Har ciki ya jagorance shi.. Gabansa ne ya fadi ganin kawu maryam, me hakan ke nufi?? Kardai ace... No bama haka bane, maryam da nurr ai its a differnt name. Lalle kenan dey are related.. Kwata kwata idonsa ya rufe, yama manta a labarin da safwan ya bashi.. Bae karasa inda suke ba sae kawae ya juya.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Yau kwana uku ya rage a shiga kotu, kabeer kuma tafiyarsa saura 5days.. Nurr da safwan kullum suna jone.. Sunje ta gaida mommy, khaleel kamar zae yi hauka don murna. Sae dare suka dawo.. Chan bangaren su kawu kuwa suma sun dauki lawyer... Ana ta shirye shiryen shiga kotu, duk bangaren biyu sun gama shiryawa. Kowa yana ganin shi zaeyi nasara.. Umma kuwa kwata kwata bata ciki hayyacinta, tana jin tsoro. Tasan indae su kawu sukayi nasara toh kashinsu ya bushe. Kullum cikin addu'a take, kabeer da safwan ke kwantar mata da hankali.. Karta ji tsoron komae.. Ranar da yamma sadeeq yazo, ranar kuwa nurr bata nan. Tun Dawowarta daga gidan kawu, safwan ya maida ta islamiyya. Har suka gama zamansu bata dawo ba.. Sae da suka fto safwan yace masa gashi har zamu tafi ba ku gaisa da ma wife ba.. Noo ba komae ai ana tare, nxt tym xamu hadu ai.. Sadeeq kamar ya tambaye safwan akan kawu, sae kuma ya fasa. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Yau ta kama zaa shiga kotu, da sassafe safwan ya shirya. Dakin mommy ya nufa don sanar da ita. Addu'a tayi masa sosae da fatan nasara. Sae daya fto ya kira sadeeq donjin yanda tafiar zata kasance.. Kazo gida mu karasa shirye shiryen kafin tym en a cewar sadeeq, Shikenan to ganinan.. A gidan sadeeq suka hadu duka harda salim.. Duk wani information da suke son hadawa sun gama hadawa.. Sae dae matsalar daya akwae babban hujjar da zata warware wannan shari'ar.. Rashin zuwan wannan hujjar zae iya jan shari'ar.. sadeeq ya damu kwarai amma bae sanar da safwan komae ba. Ganin lokacin shiga kotun ya kusa yasa safwan tafiya don dauko su umma.. Yana zuwa ya tarar duk sun shirya amma kaf basa cikin walwala. Fargaba ce fall cikin zuciyarsu. Kowa da irin nasa tunanin.. Suna tsoron sharrin su kawu.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Lokacin da suka zo harabar kotun makil take da mutane. Daga gani kasan akwai babbar shari'ar da zaa gudanar.. Bayan an gama sauraron shari'ar mutanen nan alkali ya bukaci jin shari'a ta gaba.. Nan aka gabatar da shari'ar su kawu.. Shari'a ce tsakanin wasu marayu da suke tuhumar yan uwan mahaifinsu akan danne musu dukiyar da suka gada wajen mahaifinsu. Sunana Barrister *zubair malunfashi* nine lawyen da ke kare wa anda ake tuhuma. Ni kuma sunana barrister *Sadeeq Kibiya* lawyen dake kare masu kara. Bayan yan tambayoyin da barister sadeeq yayi wa su kawu.. Sun bashi amsa daedae gwargwado.. Barrister zubair ne ya bukaci ganin umma, bayan ta tsaya ya shiga jero mata tambayoyi. Bayan ta gama basu labarin abubuwan da suka faru har zuwa mutuwar mijinta. Barister zubair ya kalle ta sannan yace, a baya kin nuna wa kotu mijinki sun sami matsala da yan uwansa a baya chan.. Amma daga baya kuma sunxo sun shirya. Sannan kin nuna ma kotu irin kaunar dake tsakanin mijinki da yanuwansa ko?? Haka ne ta bashi amsa. Murmushi yayi sannan ya cigaba, ya mai girma mai shari'a ni a ganina mutanen da suke son danuwansu sosae ba zasu iya cutar dashi ba Bayan haka ya mai girma mai shari'a, wa dannan sune takardun kadarorin marigayi, ina so kotu da duba da kyau, ga sa hannun marigayin nan wanda yake nuna ya mallakawa yan uwansa duk wani kadarorinsa,.. Umma ya nuna wa takardun don ta tabbatr da sa hannun mijinta. Bayan mai girma mai shari'a ya duba ya kalli umma sannan yace Kin yarda wannan rubutun mijinki ne ko kina da ja?? Bani da jaa ya mai girma mai shari' a.. Barrister Zubair ne yayi murmushi ganin akwae alamun nasara sannan ya dora. Ko hajiya zata iya gaya mana dalilin da yasa batayi aure ba har wannan lokacin?? Objection ya mai girma mai shari'a a cewar sadeeq.. Bai kamata bartister zubair ya dinga neman shiga personal affairs ba.. korafi ya karbu barister a kiyaye.. cewar alkali.. Murmushi ya kara yi sannan ya umarci umma data koma ta zauna.. Mamaki sadeeq yake ganin shari'ar na neman juya musu.. Barrister zubair ne ya cigaba: ya mai girma mai shari'ai ina son ka duba wannan shari'a, bata da wani sarkakiya. Alkali ya kallk sadeeq yace ko barrister sadeeq yana da abun cewa??.. Eh inada shi ya mai girma mai shari'a.. Ina bukatar ganin tukur da ja'afaru domin su sake amsa min wasu yan tambayoyi.. Bayan sun fto, kawu sae kallon sadeeq yake yana mamaki, lalle dama ashe zuwan da yake wurin maryam don ya samu wasu informations ne. Jin muryar sadeeq yayi yana tambayarsu ko zasu iya yiwa kotu bayanin kwangilar da za suyi da alhaji wada?? Da sauri zubair ya mike, ya mai grm mai shari'a barrister sadeeq bae kamata shima ya shiga personal affairs ba.. Barrister sadeeq a kiyaye cewar alkali.. Kada kai yayi sannan ya cigaba, inason kotu ta gayyato detective salim.. Ina detective salim kotu nasan ganinka. Tsaf ya fito a alhaji wadan sa, shigowa yayi cikin kotu, baki galala su kawu suka bishi da kallo.. Bayan ya tsaya barrister sadeeq ya bukaci ya bawa kotu labarin abunda ya hada su da su kawu.. Nan ya kwashe komae ya sanar da kotu, karya kake inji baba ja'afaru. Mu zaka ci amana? Daka masa tsawa alkali yayi sanna yayi shiru.. Sadeeq ne yayi wani mugun smillin sanna yace ko detectv salim zae iya bamu shaida akan abunda ya fada?? Ba tare da bata lokaci ba ya jawo recordersa ya mikawa sadeeq.. Nan shikuma ya mikata zuwa ga alkali. Aka jona gaba daya muryarsu kawu ya karade kotu.. Kusan zawo su kawu suka kusa yi a wando😂😂.. Barrister sadeeq ya kalli su bayan an gama ji yace ko zaku iya cewa wannan ba muryarku bace??. Objection my lord, bae kamata barrister ya dunga neman dole sae sun amsa laifinsu ba. In akae la'akari da zamanin da muke ciki yanzu, komae zaa iya yi da computer don a samu cinma wani burin.. Jin muryarsu bashi zae nuna sune sukae maganar ba.. Koarafi bai karbu ba, barrister sadeeq go ahead, nagode ya mai grma ma shari'a.. Bayan yan tambayoyi da yayi wa su kawu barrister zubair ya nemi kotu ta daga shari'ar zuwa wani lokacin.. Kwarai sadeeq yaji dadin wannan maganar. Nan take alkali ya amince aka daga shari'ar zuwa mako mae zuwa.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Bayan sati daya, kabeer ya daga zuwa kasar cyprust✈, kuka ne sun shashi, kamar bazasu rabu ba. Bakin cikinsa daya baya nan zaa gama shari'ar amma ba komae duk yanda ake ciki yasan safwan zae tsaya musu.. Toh kasancewar mutane suna so suga yanda shari'ar zata kasance yasa kotun cika makil.. Bayan alkali ya zauna ya nemi fara shari'ar.. Shari'ar ta dau zafi duk wani hujja da sadeeq ya kawo sae zubair ya warwareta.. Kwata kwta sadeeq jikinsa yayi sanyi ganin kamar baza suyi nasara ba.. Bayan yan rubuce rubucen alkali, zare glass din sa yayi sannan ya numfasa. A bisa rashi wasu gamsassun hujjoji daga bangarorin biyu, kotu ta.... A dakata dakata wani dan sanda ya shigo yana fada. Gaba daya hankalin kowa ya koma kansa.. Wani bakin mutum ne ke biye dashi,.. Kallon kallon suka shiga yi dasu kawu.. Bayan ya sami guri ya tsaya, sadeeq ya shiga watso masa tambayoyi, labari ya shiga bawa kotu tun tafiyar su kawu lagos har zuwa neman da sukayi masa, Sun shirya akan ya tare su akan hanyarsu ta dawowa kamar yan fashi.. Suna so ya halaka musu dan uwa amma kafin nan sae dan uwan nasu yayi signin a duk wani kadarorinsa.. Haka kuwa akayi, bayan mun tare su nida yara na.. muka bukaci kudi masu yawa.. Ganin bae fito da kudi ba yasa muka yi masa barazanar halaka yan uwansa... Nan take ya rikice, ya shiga bamu hakuri, dariya nayi sannan na kalle shi.. lalle kana son yan uwan nan naka da yawa while su kuma masu sonka.. Nan suka fada masa komae da irin tsanar da sukayi masa, a take suka umarce shi daya mallaka musu komae nasa ko kuma suzo su halaka iyalinsa. Bae wani yi jayayye ba ya mallaka musu komae nasa.. haka tukur ya dauki wani katon dutse agefe ya kwala masa akae. Wata gigitacciyar kara ya saki, bae hakura ba sae daya kara kwala masa dutsen nan a cinyarsa Ni kaina sae dana tausaya masa, take ya fadi kasa ba numfashi.. Haka muka shigo motar su muka taho gida.. Kasa nutsuwa nayi bayan abun ya faru, da safe na kama hanya na koma wajen, ina zuwa na tarar da bawan Allah nan ya kwance,.. Wani farin abu na fta daga bakinsa.. A nan zan tsaya ya mai shari'a amma inaso na gabatar wa kotu da wanda zae cigaba da yiwa kotu daga inda na tsaya.. Wani mutum naga an gurguro akan wheel chair, Aikuwa kawu bae san lokacin daya sulale ya saki fitsari ba🙊🙊 waye wannan ya shigo?? Mene alakarsu da kawu?? Ku biyoni don jin yadda zata kaya. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 9⃣6⃣➡9⃣8⃣ By harphsart Rano✍ ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Wata irin zabura umma tayi, bakinta kwata kwata ya kasa furta komae, sae mika hannu da take tana kokarin yin magana.. Kirjinta ne ya buga da karfi, Tasa hannu ta dafe wajen. *ALHAJi* ta furta da karfin gaske wanda ya kara jawo hankulan mutane. kuka ta saki mai ban tausayi ta karaso wajen kujerar ta tsuguna tana kallonsa tana kuka..😭😭 Shi kansa kuka yake yi, da yana da yanda zaeyi daya mike.. Sadeeq na hango yana ta murmushi, da alama yasan wani abu.. Shiko safwan kallonsa ya shiga yi alamar yana neman karin bayani. Kotun gaba daya ta hargitse kowa na tofa albarkacin bakinsa.., Alkali ne ya bugu table sannan akayi shiru.. Da kyar umma ta mike ta koma gun zamanta aka tura alhaji zuwa gaban alkali.. Gaba daya jikin barrister zubair ya gama sanyi.. Gefe ya samu ya zauna yana kallon yadda wannan shari'a zata kaya.. Alkali da kansa ya kalli alhaji yace bawan Allah ko zaka iya yiwa kotu bayanin kai waye?? Mene alakar ka da wannan mutumin da yake tsaye ya nuna audu lauje, da kuma wadannan mutanen ya nuna su kawu.. Sae a sannan na hango kawu yayi zaman dirshan, zufa duk ta wanke masa jiki😂.. Shiko baba ja'afaru bakinsa sae zikiri yake.. Kallonsu yayi a nutse sannan ya maida kallonsa zuwa ga alkali.. Murya chan kasa kasa ya fara magana. Ya mai girma mai shari'a wa dannan bayin Allah yan uwana ne. Ubanmu daya dasu. Dukkan abunda bawan Allah nan ya fada gaskiya ne. Don kuwa bayan sun jima da tafiya sae na farfado.. Kasancewar dukan da yaya yayi mun aka yasa naji komae na manta dashi.. Bude ido nayi da kyar ina kallon wajen da nake, kwata kwata na kasa tunowa da abunda ya faru.. Haka na karasa kwana a gurin kasancewar dare ne.. Gashi ina jin wani zugi a kafata.. Inanan ina tunanin kaina, na kasa tuna komae na rayuwata.. Ji nayi kamar tafia, bana iya bude ido na sam.. bayan sun karadi naji daya yace taimaka ka kama min shi.. daga ni naji anyi an dora ni akan wani abu kamar jaki, sae da mukayi tafiya mae nisa sannan muka isa wani kauye. Sati na daya a kauyen nan na far warwarewa sae dae bana tuna komae, gashi kafata ta sami matsala bana iya tafiya.. Kullum na tambayi mutanen nan waye ni sae suce suma basu sanni ba.. Wani mutum ne ya roke su dasu dinga kula dani shi kuma zae dunga zuwa yana dubani yana biyansu. Sosae mutanen nan suka nuna min karamci tsawon shekarun nan.. Shi ko wannan bawan Allah yana zuwa lokaci zuwa lokaci ya duba ni.. Shi nake gani a matsayin dan uwana. Katsam ranar nan sae gashi yazo, bayan mun dan taba hira yawanci hirar akan abubuwan da zaesa in tuno da kaina yake mun amma kwata kwata na kasa dawowa. Sunan su yaya ya shiga fada min da karfin gaske, nan take naji kaina yana juyawa.. Ban sake sanin inda kaina yake ba sae dana farfado,.. Bin dakin nayi da kallo ina mamakin abinda ya kawo ni.. Wannan bawan Allah shi idona ya fara sauka akansa. Zabura nayi saboda bazan taba mantawa da wannnan fuskar ba.. Umartar su yayi da su bamu wuri.. Daki daki ya shiga bani labarin abinda ya faru.. Nayi kuka sosae ganin cewa duk wannan tsawon lokacin bana tare da iyalina.. Daga karshe ya nemi tafiya dani, sosae mutanen nan suka ji ba dadi.. An riga an saba kwarai, Sati na daya a gidan wannn bawan Allahn.. Sae daya tabbaatar na dawo hankali na fully sannan muka taho nan. Kuka yaci karfin sa, gaba daya kotun ba wanda bae zubar da hawaye ba..😭😭 Shi kansan alkali ina kallonsa yasa hanky ya goge kwallar data zubo masa.. Nurr kuwa kuka take kamar ranta zae fita wanda bata dade da zuwa wajen ba.. Shima ganin dole ya kamata tazo, alhaji na fara labarinsa safwan ya fita yaje ya daukota.. Alkali ne ya tattaro nutsuwarsa sannan yace.. Ko wa'anda ake kara suna da ja akan abinda wadannan bayin Allahn suka gabatar wa kotu?? Ba wanda ya iya daga kansa balle ya amsa.. (Ni ina ganin kawu saboda tsabar rikicewa sumansa goma😂😂) Toh abisa wadannan kwarararn hujjojin da mukaji, Kotu ta yankewa tukur hamza zaman gidan yari na Wata biyar, tare da tarar naira dubu dari biyar.. Inda ta yankewa ja'afaru zaman gidan yari na wata biyu.. Tare da tarar naira dubu dari biyu.. Bayan haka kotu na umartar su dasu damkawa alhaji abubakar da iyalinsa duk kadarorinsu.. Bugu table yayi sannan ya mike.. Aka tusa keyar su kawu.. Da gudu umma da nurr suka karaso wajen abba.. Kuka suke gwanin ban tausayi safwan yana tsaye yana kallonsu.. Sadeeq ne ya taho da fara'arsa, kafin ya karaso yaga wata kamar maryam dinsa.. Kara sauri yayi, yana zuwa dae dae kusa dasu yaji abban nurr yana shafa kanta.. Ya isa nurr dita kukan ya isa, ki bar kuka haka kinji maryama ta.. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...Jiri jiri ya faara ji yana daukarsa... maryam dinsa ita ce nurr din safwan... Ko gabansa baya gani, haka ya fito yana daddafa bango har ya ta fto wajen motarsa. Sae daya shiga ya zauna kawae yaji bazae iya tuka motar ba.. Yafi minti talatin ya kifa kansa akan sitiyarin motarsa. Wani kurtu ne ya lura da halin da yake ciki. Da sauri ya karaso ya shiga kwankwasa masa glass.. Da kyar ya dago kansa idonsa yayi jaa, Kallon kurtun ya shiga yi.. Sae kuma ya sauke glass din yana kallonsa. Yallabai naga ka dade anan shine nazo naga ko lafiya??.. Daga masa hannu yayi alamun ba komi sannan yaja motar.. Da kyar ya isa gida.. Fadawa yayi kan sofa, ya saki ajiyar zuciya, tunani ya shiga yi. Wani irin son nurr ke dawainiya dashi. Ya riga ya kamu da sonta dumu dumu,.. Ashe budurwar abokinsa yake so.. Bai ankara ba yaji wani zazzafan hawaye. Hannu yasa ya share.. A rayuwarsa mutum ne shi mai barkwanci. Bae fiya daukar abu serious ba at all. Komi nasa a wasa yake yinsa. Ya taba soyayya da wata yarinya a kibiya, Sosae ya shaku da ita, amma bae taba furta mata so ba. Kwatsam yaji an sa mata rana.. Tun daga ranar bae sake soyayya da wata ba sae maryam... shikenan kuma shi bashi da sa'a.. Safwan ne ya fto yana duba sadeeq, mamaki ya kamasa ganin ba motar sadeeq.. Sae da su umma suka shiga motar da su abba sukazo sannan shima ya shiga tasa.. Ya lula duniyar tunani bae san ana ta buga masa kofa ba.. Firgigit ya dawo yaji alamun buga kofa.. Da kyar ya iya tashi ya bude kofar. Safwan ya gani tsaye Kallon tuhuma ya shiga aika masa.. Malam ya na ganka haka kamar wani mara lafiya ya fada yana shiga ciki.. Mene ne ma dalilinka da zaka taho baka fada min ba.. Yake sadeeq yayi sannan ya amsa masa. Kaina kedan cio. Lalle ma barrister ban taba sanin irin zaman da muke kenan ba.. Ai ni a tunani na yanzu mun zama daya.. Banga alamun ciwon kai atare da kai ba.. Naga alamun kunchi da tashin hankali a idonunka.. Ka taimaka ka fada min dan allah.. Zuciyarsa yaji ta tsinke ganin yanda safwan ya damu.. Take yace masa kaga safwan kirana akae hajiyata bata da lafia amma dae ance da sauki shisa ka ganni haka.. Da sauri safwan ya mike, a ah zama bae same mu ba tashi tashi mu tafi.. Calm down aboki nayi waya dasu ma.. Da sauki. Tom shikenan Allah ya kara mata lafiya.. Yanzu tashi zakayi mu tafi gidansu nurr don Alhajinsu yana son ganinka.. Nasan ma yanzu sun karasa mu kawae suke jira.. Allah sarki sadeeq😭😭 Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿 📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 9⃣9⃣ By harphsart Rano✍ Baya so safwan ya zargi wani abu, dole ya mike ya fada toilet. Sae daya sauya kaya sannan suka fito. A hanya suna tafiya suna hira wanda duk safwan ke kawo hirar.. Yawanci hirar akan yanda shari'ar ta kasance.. Anan sadeeq yayi masa bayanin yadda suka hadu da audu lauje. Shine wannan da yazo Gida ya sameshi.. Yaji labarin shiga kotun. Nan yake shaida masa ai alhajin ma yana hannunsa. Nan muka yanke zae zo dashi ranar da zaa shiga kotu.. Kasancewar baeyi recoverin memory nasa a farkon zama ba, shisa basu zo ba sae yau. Suna cikin hirar har suka karaso kofar gidan.. Kirjin sadeeq sae dukan uku uku yake.. Baya so ya shiga nurr ta nuna wani expression da zae making safwan suspicious.. Sae da safwan yadan taba shi sannan ya fto daga motar jiki a sanyaye.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Lokacin dasu nurr suka karasa gida sae da abba ya zubar da hawaye ganin irin gidan da iyalinda suke ciki.. Nan umma ta vashi labarin komae har zuwa tafiyar kabeer karatu.. Yayi farin ciki kwarai da tafiyar tasa.. Nurr kuwa tana daki, farin ciki take mara misaltuwa, sae kuma sadeeq ya fado mata.. Ras ras taji gabanta ya fadi, sadeeq shine lawyern daya tsaya musu.. Shine ya dawo musu da farin cikinsu wanda suka dade da rasawa.. Lalle ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsu.. Ita kuwa dame zata saka masa?? Tana son safwan sosae amma kuma wani bangaren zuciyar ta na son sadeeq. Tana jinsu sosae a rayuwarta.. Bata ankara ba taji hawaye.. Sallamar su ce ta dawo da ita daga kogin tunanin da ta fada.. Bayan umma sun gaisa da safwan ,Muryar sadeeq taji ta doki kunnenta.. Bazata taba mantawa da muryarsa ba.. Da sauri ta fito don gasgata abinda taji, turus ta tsaya tana kallonsu.. Suma din ita suke kallo.. Kowa da irin kallon da yake mata.. Shi sadeeq ma baesan ya kafe ta da ido ba... Tsawon lokacin daya dauka be sata a idonsa ba, duk sae yaji ta kara sauya masa.. Tayi fresh da ita amma kuma ta dan rame.. Shiko safwan kallonta yake da son gano damuwar da take a kwance a fuskarta.. Bae kamata yaganta haka va ganin cewa yau ranar farin cikinta ne.. Sadeeq ne ya fara dauke idonsa a wayance yace a ah kanwarmu.. Karaso mana kika tsaya daga nan.. Ko bakiyi murna da ganinmu ba?? Ya fada cikin dakewar murya.. A hankali ta jawo kafarta zuwa kusa da su ta zauna Da kyar ta iya bude baki ta gaishesu.. Tambayoyi ne fall cikin zuciyarta. Mene ne alakar safwan da sadeeq??.. Bata da amsar tambayrta, mutum daya ne zae amsa mata tambayarta.. Sadeeq shine amma kuma ganin alamar daya nuna kamar ma yau ya fara ganinta.. Tsokanar ta sadeeq yake tayi wae amaryarsu.. Shi kuma safwan sae dariya yake. Gaba daya kanta ya kulle, kasa zama tayi a wajen bayan umma ta tafi wurin abba.. Umma ce tayi musu iso xuwa wajen abba.. Yana zaune akan wheel chair dinsa. Godiya ya shiga yi musu mara iyaka,.. Akan irin taimakon da sukayi masa shida iyalansa.. Ba shida abunda zae saka musu amma yana rokon Allah ya saka musu da gidan Aljanna.. Sun dade a gidan suna hira da abba, Anan safwan ya kira kabeer ya bashi labarin duk abunda ya faru.. Murna ya shiga yi, bashi abba suka yi yana jin muryar abba ya fashe da kuka. Daya kafe shi dawowa zaeyi ya fasa karatun.. Dak kyar abban ya lallashe shi sannan ya hakura.. Lokacin da zasu tafi nurr tayi wuff ta bi bayansu.. So take tayi magana da sadeeq.. Shiko Yana ganinta ta fto yayi saurin fadawa mota ya barta da safwan.. Safwan ne ya kalle ta ya rausayar dakai gefe kamar karamin yaro.. Me ya sami sarauniyar matan duniya?? Naga damuwa fal a kan fuskarta... Rau rau tayi da ido, common karki mun asarar hawayen ki.. Lallashinta ya shiga yi, Waya ya zaro a aljihunsa yace ki rike wannan zan kiraki.. Kinga yanzu sadeeq na jirana ko??.. Daga masa kai tayi, yauwa cutie yimun murmushi tom.. Sae daya tabbatr tayi daria sannan ya juya ya shiga mota.. Zuciyar sadeeq kamar zata tsaga girjinsa ta fto.. Bakin glass ya jawo ya saka don baya son safwan ya fuskanci komae.. Duk kokarin sa na ganin safwan bae dago komae ba sae daya gane yana cikin damuwa.. Sae daya kaishi gida sannan shi kuma ya wuce yana mamakin sudden change din daya gani wajen sadeeq.. Lalle ba karamin abu ne zae chanzawa sadeeq mood ta farat daya haka ba.. Dole zae bincika yaji koma menene.. Sadeeq abokine na gari.. Yana shiga falo ya tarar da mommy, gefenta ya samu ya zauna.. Kallonsa take tana mamaki a ranta.. Nurr ta chanza mata yaronta.. Abinda take ganin bazae iya ba dah yanzu in ance yayi ba zatayii musu ba.. Ganin mommy ta tafi tunani yasa yayi gyaran murya.. Duka ta kai masa a wasance, daria ya kyalkyale ya dukar da kansa kasa.. Sorry mommyn khaleel da twins.. Ohh kai ka zama ba nawa ba ko?? Nurr ta kwachen kai kenan tun yanzu. Anya kuwa zan yarda da zuwan nurr din nan kuwa ta fada bayan ta gimtse fuska.. Tuni ya rikece ya soma bata hakuri, wlh mommy ba haka bane pls karki rabani da nurr🙏🏿 Daria ce ta kwache mata, lalle yarona ya kamu da son nurr, kunya ce kuma ta rufesa.. Tashi ka bani wuri ni, in daddyn ku ya dawo yau zan sanar masa da komae.. Yawwa mommy tah ya fada sae kuma yaji kunya.. Da sauri ya bar falon.. Yana shiga daki ya fada kan gado.. komae da komae ya shiga tunowa daki~daki.. Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa.. Ba abinda yake tunowa irin zaman da tayi tare dasu.. Kunyarta, tsoronta shi yafi komae burgeshi da ita... He lurvs everytin about her Samun kansa yayi cikin farin ciki mara misaltuwa.. Sadeeq na ya fado masa, yayi masa taimako mara iyaka. Bae san da wanni abu zae saka masa ba.. Alamun da ya nuna kamar akwae damuwa atare dashi.. Dole nae finding out koma mene yake damun abokinah.. In ma akan maganar yarinyar da yake so ne, Zanje ko ina take na nemo masa ita.. Haka yayita ayyanawa a ransa har akae kiran sallar magriba.. Bayan yayi sallah ya dawo falo suka dasa hira da yan kannesa.. Haka daddy ya shigo ya tarar dasu.. Zama yayi shima aka cigaba da hirar dashi.. Mommy ce ta sauko ta tarar da familynta suna hirarsu gwanin sha'awa.. Gefen daddy ta samu da zauna sannan tae masa sannu da zuwa.. Hirar aka dora inda daka karshe yaran sukayi barci.. Kwalawa talatu kira tayi sabuwar yar aikin mommy tazo ta gyara musu makwancinsu.. A nutse mommy ta shiga karantowa daddy maganar nurr.. Safwan najin sun fara maganar ya mike yayi daki.. Har yakae bakin kofa daddy ya kira sunansa.. Dawo ka zauna.. Tambayoyi ya shiga yi masa yana bashi amsa.. Kwarai daddy ya gamsu da amsoshin daya bashi. Shikenan zaka iya tafia.. Duk yanda ake ciki zan neme ka.. Da farin ciki ya shiga daki. Waya ya jawo ya kira nurr.. Lokacin ya tabbatar duk wata hira da zasuyi da abbanta sun gama ta.. Ita ko dama tana kwance a daki ta kurawa wayar daya bata ido.. Hotonta ne akan screen din wanda bata san ya dauketa ba sam... Kira taga ya shigo, my number taga anyi saving din number.. Da kyar ta iya daga wa ta kara a kunneta.. Muryarsa chan ciki taji ya ambaci sunanta.. Kasa amsawa tayi, Sae daya kara kiranta akaro na biyu.. Naam ta furta. A hankali ya shga tambayarta mutanen gida tana bashi amsa.. Sun dade suna hirar, maganarsa bata wuce irin son da yake mta.. Kamar tayi masa magana akan sadeeq sae kuma ta kasa.. Tana son jin wani abu akansa.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Sadeeq kwance zuciyarsa na masa radadi, bae kara tabbatar da irin son dayake ma maryam ba sae yau daya gansu tare da abokinsa.. Kishi fal zuciyarsa, bazae iya cigaba da ganinsu tare ba.. Gobe gobe zae tafi kibiya.. Haka yayi ta juyi, sallah ce kawae take tashinsa. Abinci kuwa baa maganar sa.. Ranar kwata kwata bae runtsa ba har aka kira sallar asubah.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Ban garen abba kuwa da sassafe audu yazo, sunyi magana akan gida. Yana son ya nema musu gida mai kyau ya siya.. Haka kuwa akayi da yamma audu ya dawo, an sami gida mai kyau na miliyan arba'en. Baa dade da gama gininsa ba.. Kawae furnitures zaa zuba.. A take abba ya rubuta masa check, maganar furnitures kuwa umma ya bawa kudin... Afnan furnitures suka je ita da nurr, komae da suke bukata sun same shi.. Biyan kudin sukayi sannan suka juyo gida.. (Allah sarki rayuwa). Kwanan safwan uku rabonsa da gidan amma kullum suna makale a waya.. Yaje gidan sadeeq yafi sau hudu amma kwata kwata baya samunsa. Wayarsa ma akashe take. Damuwa sosae ya shiga da tunanin lalle laifin da yayi wa sadeeq mai grma ne.. Haka ya hakura yaga iya gudun ruwansa.. Sati daya da siyan gidan suka koma, gida ne dankarere na gani na fada.. An kashe kudi sosae wajen ginin gidan.. Kayan da aka zuba a gidan kadae abun kallo ne..Kasancewar afnan furnitures ba baya ba wajen sayar da hadaddun kaya... Bayan sun koma gidan da kwana uku suka shirya tafiya sumaila.. Haka suka kama hanya a sabuwar motar abba wacca ya saya bata fi kwana biyu ba.. Driver audu ya samo masa, tafiya ce sukayi ta cike da farin ciki.. Sun isa garin sumaila da azahar, kowa sae dayayi farin cikin ganinsu. Baba sulaimanu yafi kowa farin cikin ganinsu. Dama shi chan yasan sharrin da yan uwansa suka shirya.. Kuka yake wiwi yana bawa abba hakuri.. Shi dama chan bae kullaci yan uwansa ba.. Sae daya tabbatar ya basu makudan kudi, na gyaran family house dinsu.. Basu kwana ba a ranar suka juyo... ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Su daddy sun gama shirye shiryen zuwa gidansu nurr, safwan ne yayi musu jagora,.. A mutunce abba ya karbe su shida baba sulaimanu sae audu wanda ya zama baban na hannun daman abba.. Sun amince dukka bangarem inda suka kawo kudin aure dubu 100 suka bayar.. Haka aka tashi cikin farin ciki.. Ina sadeeq kuwa?? Ku biyoni a last episode din... M sorry for d late post.. Was kind of busy ne wlh.. Ina fara typing sae barci ya dauke ni.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣0⃣0⃣ ➡ 1⃣0⃣5⃣ By _Harphsart Rano_ Tun daka dawo kake kwance a daki, haba abubakar sadeeq ya kamata ka sanar dani damuwarka.. Gyara kwancia yayi sannan ya kalli tsohuwa, hawaye ta gani a gefen idonsa.. Salati ta shiga rafkawa kamar anyi mutuwa.. Me zan gani?? Kuka abubakar?? Lalle koma mene wannan abu ne me girma. Ganin tsohuwa zata tara masa jama'a yasa shi mikewa da kyar.. Riko hannunta yayi suka zauna gefen katifa, cikin dauriya ya shiga yi mata bayani.. Dalla dalla ya warware mata komae, cike da tausayawa take kallonsa.. Ta sani sarai soyayya ba abune mae sauki ba, musamman idan mutum yana *son maso wani*.. Lallashinsa ta shiga yi tana bashi baki, daga mata kai kawae yake amma harga Allah ba sauraranta yake ba.. Bayan ta gama zuba waazinta ta tashi ta fta, maimakon ya mike kamar yadda ta umarce shi sae ya kara kwancia.. Shigowa ta sake yi rike da kwano a hannunta.. Sae jug din ruwa.. Tashi maza kaci abinci, kaga ko iyayen naka baka je ka gaishesu ba.. Dan dole ya ci abincin nan amma na dadinsa yake ji ba.. Wanka yayi ya fto ya shrya, so empty yake jinsa.. Wayoyinsa ya jawo wanda rabonsa da kunnasu har ya manta.. Yana kunnawa messeges suka fara rige rigen shigowa, wasu na abokan aikinsa ne, detective salim, Sae na kamfanin airtel.. Dayan wayar ya kunna wadda mtn dinsa ke kai, ai kuwa messeges din safwan suka dunga shigowa a jere.. Sae daya bari suka gama shigowa sannan ya fara dubawa daya bayan daya.. Duk yawanci akan dalilin kashe wayar sa ne kuma yaje gida bae sameshi ba.. Na karshen ne ya dan bashi daria wanda ya turo shi dazu dazun nan.. Malam in ka kunna wayar sae ka dawo ga maryaman ka nan na samo maka ita.. Zancen da nake ma yanzu haka ma ta amince ta soyayyarka.. Allah sarki safwan, nagode da kulawarka gareni, amma dole nayi nisa dakae.. Na riga na sani nurr itace farin cikinka... Dukda nima itace farin ciki na amma tafi dacewa dakae.. Hakika kai masoyinta ne na gaskiya.. Shi kadae yake maganganunsa cikin kunar rae.. Kaka na gefe tana matsar hawaye.. Nima kaina sadeeq ya bani tausayi.. (Karka damu sadeeq zan baka yata *hanan*😜).. Sake kashe wayoyin yayi sannan ya fice daga gidan, a tsakar gida ya taarar da hajiyansa tana alwala.. Maraba da abubukar sadeeq, yanzu kake tafe?? Yake yayi sannan ya gaida ta.. Daki ya wuce ya samu kan kujera ya kwanta.. a zaune ya tarar da sumayya tana danne dannen waya.. Tun shigowarsa hajia ta fuskanci yana tare da damuwa.. Sae data idar da sallah sannan kalle shi.. Abubakar me yake damunka?? Kana tare da damuwa, kar kayi kokarin boye min.. Ni mahaifiyarka ce.. Mikewa sumayya tayi ta shiga daki don basu guri.. Baeyi yinkurin boye mata ba, a nutse ya warware mata komae kamar yanda ya sanar da tsohuwa.. Sallama aka shiga yi, wani saurayin yaro ne ya shigo, hajiya ina wuni? Dama wasu ne suka ce nayi musu sallama da sadeeq.. Mamaki ne ya cika sa, shiko waxae yi sallama dashi.. Mikewa yayi yabi bayan saurayin don ganin me sallama.. Kunya ce ta rufeshi ganin safwan tare da detective salim.. Safwan ya harde hannu kawae yana masa kallon tuhuma.. Komawa ciki yayi ya sanar da hajiya sannan ya shigo dasu.. Sun gaisa da hajiya cikin mutunci, ruwa tasa sumayya kanwar sadeeq ta kawo musu.. Detective salim sae kallonta yake, sae da sadeeq ya kai masa duka sannan ya wayence.. Dakinsa ya kaisu, bayan sun zauna safwan ya hayyayako wa sadeeq.. Shiru bae tanka masa ba sae daya gama balbalin sa.. Hakuri ya shiga bashi.. Dalilin tahowarka ba sanar wa sannan kuma ka kashe dukka wayoyinka nake son sani inji safwan.. Dadina dakae rigima cewar sadeeq, nifa ba don wani abu na taho ba.. Kiran gaggawa ne ya sameni.. Kafin nazo kuma chargy ne ya kare.. Tun da nazo ina gidan tsohuwa, ban samu nayi chargy ba kuma.. Haka yaeta kare kansa har ya tabbatar da safwan ya gamsu.. Hira suka shiga yi ta yaushe gamo.. A cikin hirar ne safwan yake shaidawa sadeeq ai an riga an kai kudin aure gidansu nurr.. Ras ras kirjinsa ya buga, hannu yasa ya danne wajen.. jiri jiri yaji ya fara daukarsa.. Idonsa sam ya rufe baya ganin gabansa.. kansa suka yo gaba dya suna tambayarsa.. Bashida bakin amsa musu, cigaba da ganin baki yayi daka karshe ya sulale kasa ya fadi.. Da gudu salim ya fita yana kwalawa hajiya kira.. A hanzarce ta fito tana tambayar ki lafia.. Dakin sadeeq din suka shiga lokacin safwan ya dukufa ganin ya bashi first aid.. Kuka hajiya take wiwi sumayya na taya ta... Sumayya ce ta ruga sae gidan tsohuwa.. Tare suka juyo da tsohuwar tana tafe tana sumbatu.. Tana zuwa ta fada dakin, lokacin sadeeq ya farfado amma har yanzu bugun zuciyarsa bae tsaya ba... Rike masa hannu tayi tana kuka, yanzu dan nan so kake ka kashe kanka?? Akan yarinyar dabatasan kanayi ba ehee.. Ganin kaka zata tona masa asiri ya sashi saurin rufe mata baki yana girgiza mata kai.. Safwan ne ya kalli hajiya sannan yace, hajiya inaganin dole zamu tafi sa shi asibiti dan aduba lafiarsa sosae.. Ban taho da kayan aiki na ba, kuma akwae abunda nke son na tabbatar game da rashin lafiyar tasa.. Haka suka fto gaba daya, nan tsohuwa tace ai sam bata san zance ba da ita zaa.. dole hajiya ta hakura.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Nurr kwance sae faman kuka take tun da aka ce an karbi kudin aurenta ta ke jin wani yanayi.. Ba wanda take son gani sae sadeeq, mesa zae mata haka?? Tana son tayi magana dashi.. Umma kwata kwata ta kasa gane kanta.. Tun tana lallashinta har ta hakura da zuba mata ido.. Abba ne ma mae kokarin lallashin nata.. Tambayar duniya yayi mata akan in safwan din ne bata so ta sanar masa, shiko zae mayar msu da kudinsu ya basu hakuri.. In tace bata son safwan tayi karya, kawae dae ita ta tasa dalilin da yasa take jin sadeeq sosae a cikin zuciyarta.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Lokacin da suka isa asibiti safwan yayi makinv duk wani arrangement, gado aka bawa sadeeq bayan gano yanda jininsa yayi mugun hawa.. Yana kwance an jona masa drip sumayya da tsohuwa na gefensa.. Safwan ne a shigo,ganin har barci ya daukeshi yasa yayi musu sallama akan zae je ya dawo.. Godiya kaka ta shiga yi masa sannan ya wuce gida.. Sannin cewa mommy tasan dalilin tafiyarsa kibiya yasa da taji batun rashin lafiar yasa ta tausayawa sadeeq.. Kitchen suka shiga tare da mai aiki don hada abincin da zaa kai asibitin.. Bayan yayi wanka ya shirya, abincin ya dauka ya fice, yana hanya ya kira nurr kasancewar yau tru out bae ji taba.. A sanyaye ta amsa, shi ya rasa abunda yake damun yarinyar nan.. Yayi yayi ta sanar masa da damuwarta taki.. Gaisawa kawae sukae ganin taki sakin jikinta yasa yae mata sallama.. Lokacin daya isa asibitin sadeeq bae farka ba, Allurar da yayi masa mae karfi ce.. yana bukatar hutu.. Da sallama ya shiga dakin, bayan sun gaisa da tsohuwa ya ajiye musu basket din abincin.. Matsawa gefen gadon yayi yana kallon abokinsa cike da tausaya wa.. Dole na nemo maka farin cikinka kamar yanda nima kayi kokari wajen dawowa abar sona da nata farin ckin.. A zuciyarsa yake maganar, a fili kuma ya furta, ga abinci nan inji mommy sanann in anjima zan kaiku gida wajenta ni zan kwana da sadeeq.. Mun gode sosae yaron kirki Allah saka maka da alkhairi.. ba komae tsohuwa.. Lokacin da suka zo tafiya already sadeeq ya farka... Bayan kaka ta sashi a gaba ya dan sha tea sannan suka wuce.. Sae daya kaisu wajen mommy sannan ya dauki abunda zae bukata ya koma asibiti.. A kishingide ya tarar da sadeeq, idonsa ya lumshe daga gani ba barci yake ba.. Dafa shi yayi, da sauri ya bude idonsa wanda suka yi jaa.. Pls barrister ka rage wannan tunanin, yanzu a stage din da kake u need to zero ur mind from duk wani tunani.. Pls abokina kayi mun wanan taimakon.. Murya chan kasa ya amsa yana murmushi.. Shikenan aboki na daena.. Sae daya gama duba patients dinsa sannan ya dawo dakin.. Dama yasan bazae sami sadeeq ido biyu ba.. Computer ya zawo ya shiga dube dube, Shi dama ba mae yawan barci bane.. Nan yake ganin zaai private waec nxt month.. Har ma an fara registration.. Kwata kwata bae samu wani barcin kirki ba,.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Bayan yayi sallah ya tashi sadeeq yayi sallah shima.. Sabuwar jallabiya fara ya bashi yasa bayan ya watsa ruwa.. Duk magungunan da ya kamata yasha yasha sannan safwan ya fice zuwa office.. Wajen 12 su mommy suka iso asibitin tare da tsohuwa, sumayya, iman, islam da khaleel. Direct dakin suka wuce, bayan sun masa ya jiki, an dan taba hira wanda duk hirar da ake sadeeq jinsu yake.. Safwan zaune cikin office, tunanin kiran nurr ya zo masa.. Wayar sa ya jawo ya kirata.. Tana zaune a dakinta tana faman tunani, tana jin ringing din wayar, sae data kusa tsinkewa sannan ta daga.. Bata hakuri ya shiga yi karta ga ya share ta sadeeq ne bashi da lafia.. Wata irin zabura tayi da karfi ta furta me sameshi, mamaki ne ya kama safwan ganin yadda hankalinta ya tashi.. Ji yayi kamar tana kuka?? Lafiya nurr?? Daga cewa sadeeq ba lafia duk kin rikice.. Tunowar da tayi safwan bae san alakarta da sadeeq ba yasa tae maza ta ta hadiye kukanta.. Umm ba komae zan fada wa umma anjima zamuxo mu dubashi... Alright tom Allah ya kawo ku ya fada sannan yayi mata sallama ya kashe wayar.. Mesa nurr ta chanja masa haka?? Akwae abunda take boye masa.. Koma dae mene zae bincika.. A falo ta tarar da umma da abba suna maganar fta da abba waje akan kafarsa.. Gefe ta samu ta zauna, Umma dama safwan ne ya kirani wae an kwantar da sadeeq a asibiti.. Ya salam.. Allah ya bashi lafia, cewar abba da umma.. Anjima ki shirya sae kije ki duba shi nima zanje daga baya saboda bakin sumaila da zasu inji umma. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Bayan ta shirya ta fito, kudin keke nepep umma ta bata sannan ta wuce.. Tana zuwa harabar asibitin ta kira safwan, kasancewar zae shga tiyata a time din yasa ya bata room number din.. Lokacin data karasa kofar room din sae ta sami kanta da kasa shiga.. Tana tsaye bata da niyyar shiga wata nurse tazo wucewa ta ganta a tsaye.. Malama yana ganki a tsaye ko kin bata room din ne?? A ah nan ne dakin ta fada tae saurin murda handle din kofar, chan ciki tayi sallama.. Idonsa a lumshe kasancewar su tsohuwa sun koma gida.. Sam baeji karar bude kofar ba saboda Hankali ta murde.. ji yayi ajikinsa kamar ana kallonsa, bude idonsa yayi a nutse.. Nurr ya gani a tsaye tana zubar da hawaye.. Hannu yasa alamun tazo, kallonsa take bata da alamun motsawa.. Tashi yayi da kyar ya jingina da pillow, a hankali ya furta sunanta.. Bata amsa ba sae dae ta tsaya da kukan da take, Takowa tayi zuwa gaban gadon, durkusawa tayi kamar me kneel down. Mesa zaka kaurace min?? Mesa ka gujeni a lokacin dana fi bukatarka? Mesa sae daka bari na shaku dakae sannan zaka barni?? Mene alakarku da safwan?? Ina son ka amsa min dukka tambayoyin nan.. Haba maryam, duk wannan tambayoyin ni kadae?? Ko tambayar ya jiki na baki ba?? Kunya ta rufe ta, ganin wautar da tayi.. Ya jiki ta furta, jiki da sauki nagode.. Daki daki ya shiga amsa mata tambayoyinta, kafin ya gama ta tsananta kukanta.. Kiyi hakuri maryam, safwan ya fini dacewa dake, nasan kuma kinfi sonsa akaena.. Dan Allah karki yarda ya fuskanci wata alaka a tsakaninmu kinji kanwata?? Kiyi min wannan alkawarin.. Bazata iya jure kalamansa ba, da gudu ta fice daga dakin tana jin yana kwala mata kiran. Safwan ya fto daga theatre room yaga nurr tana kokarin fta daga asibitin... M sorry fanz, naso na gama book en nan a page 100 buh due to sum risinx bazae yiwu ba.. I hope zaku yi mun hakuri for late post.. Banjin dadin jikina sosae.. Harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣0⃣6⃣➡1⃣1⃣0⃣ By _Harphsart Rano_ Mamaki safwan ya shiga yi?? Mesa nurr zataxo kuma ta tafi ba tare da ta jira sa ba, Gashi kuma da dukkan alamu ba a hankalinta take ba.. Parking space ya karasa, ya dau motarsa ya bi bayanta.. Lokacin daya karasa har ta tsaida keke napep zata shiga.. Bude mata gaban mota yayi ta zauna.. Kifa kanta tayi a kan kafarta ta cigaba da kuka kasa kasa.. Buga steering motar yayi da karfi, tsaida kukan tayi ta dago jajayen idonta tana binsa da kallo.. Shima din ita yake kallo duk yayi wani iri, juyowa tayi sosae tana fuskantarsa.. Murmushi tayi masa, sannan ta shiga goge hawayen da bayan hannunta.. Shidae kawae kallonta ya keyi.. Cikin asibitin ya koma ya samu waje yae parking.. Office dinsa suka wuce kai tsaye, gaba daya nurses din wajen sae kallonsu suke.. Key ya sa sannan ya nuna mata kujera.. Fridge ya bude ya ciro maltina mai sanyi ya ajiye mata da glass cup.. Zauna ina zuwa ya fada ya juya ya shiga toilet din cikin office .. Mikewa tayi taje gaban table dinsa ta tsaya, hotonta ta gani a ajiye akan table din.. Tausayinsa ya kamata hade da sonsa mai karfi a zuciyarta.. Tasani sarai safwan shine zabin zuciyarta.. Amma dayar zuciyarta ta tana jin tausayin sadeeq sosae... Jin alamun zae fito yasa tae saurin komawa ta zauna.. Fitowa yayi bayan ya sauya kaya daga kayan operation din sannan yazo gabanta ya zauna a kasa ya Tankwashe kafarsa.. Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da gefen mayafinta.. Kinga yanda idonki ya kumbura nurr?? Mene ne wannan abun da yake damunki?? Duk ya hana ki sukuni.. Fada min dan Allah, wallahi hankalina bazae taba kwanciya ba in baki fadan ba kinji?? Kinsan yanayin aiki na, ina bukatar nutsuwa, bazan iya cigaba da walwala ba in har kina cikin damuwa.. Please ki fada min koma mene nayi miki alkawari zan yi miki shi.. Shiru tayi bata ce komae ba, please Ki fada min ya marairaice murya.. Nifa ba komae kawae barrister ne ya bani tausayi.. Shine kike kuka?? Naji wannan tom.. Amma kwana biyu baki da walwala.. Shi kuma mene ya sa?? Ba kaine ba baka zuwa wajena sosae yanzu, sae ka dinga shareni ta fada tana turo baki.. Kuma ni yanxu baka cewa kana sona.. Kyau tayi masa sosae, murmushi yayi sannan yace am sorry my heart kinsan yanayi aikinmu ko?? Amma ba share ki nake ba, kina nan a raina. So nake kawae kiyi waec dinki da jamb, na sama maki addmission sae muyi aurenmu ko?? Ko baki so kiyi karatu?? Inaso sosae ma.. Amma Toh mesa yanzu baka cewa kana sona??.. Ina sonki sosae nurr, Son da nake miki bazan iya expressing nasa ba.. No words to express ma lurv for U.. I Jst lurv U alot.. Kunya ce ta kamata, tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta.. Ni baki ce min kina sona ba, daria tayi sannan ta sunne kanta kasa.. Yasan baxata iya fada masa ba.. Ta fiya kunya da yawa, anyway yasan dole zae koya mata yanda zata sake dashi.. Girgiza kansa yayi yana dariya, Shikenan yanzu mun shirya ko?? No more fushi ryt?,. Daga masa kai tayi alamun Eh.. Tashi muje na duba sadeeq sae nae droppin dinki a gida ko?? Um um ni ka barni anan kaje ka dawo.. Toh shikenan ina zuwa ya juya ya fice... ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Lokacin da nurr ta fita, zuciar sadeeq tayi zafi, ya zama dole na bar kasar nan gaba daya.. I cant bear it, kuka ya shiga yi kamar karamin yazo, sae da yayi mae isarsa sannan ya lallaba ya fada toilet ya dauro sannan ya dawo dakin... Sallaya ya shimfida ya shiga gaya wa Allah.. Allah ya cire masa son nurr ya zaba masa mafi alkhairi.. Ya dade yana rokon Allah sannan ya dawo ya kwanta.. Alhamdulillah sam sae ya nemi kunshin da yake fama dashi ya rasa.. Lalle ba abunda yafi karfin addu'a.. Jin an murdo kofar yasa sadeeq saurin rufe idonsa ya juya bayansa a tunaninsa safwan ne.. Shi kuma baya son ya sameshi da tambayoyi akan zuwan nurr.. Wata kyayyawar yarinya ce ta budo kofar, da sauri ta karaso bakin gadon, brooo m here wake up plsssss.. Juyo wa yayi don ganin wace wannan? Shidae yaji ba muryar sumy bace.. Yana juyowa ta ja da baya da sauri, m so sorry wlh i tot dakin da bro na ke ciki ne.. M sorry na tashe ka abarci hope u r feeling much better ta fada, bata jira amsar sa ba ta juya da sauri zata bar dakin.. Hey you! Ya fada.. Chak ta tsaya amma bata juyo ba.. U r so naughty i guess, da sauri ta juyo tana zare ido.. Yess of course U r.. Kin shigo min daki wit out sallama en zaki fita witout ma permission??.. C dis gentleman ta fada a zuciyarta.. Murguda masa baki tayi sannan ta juya tae ficewarta.. Dariya ta bashi, lalle wannan yarinyar yar rigima ce.. Amma kuma kamar zatayi dadin hira.. Allah yasa ta sake shigowa na kuma tsokanota.. Haka kawae yaji gaba daya yarintarta ta burge shi.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Safwan ne ya shigo yana am so sorry barrister, na barka kai daya, amin afwa kar naji sammaci daka koto.. Dariya sukayi gaba dayansu.. Ya jikin naka?? Akwae wani abu da yake damunka?? No babu abunda yake damuna, ni nafiso ma ai discharging dina.. Owk ba komae sae na sallame ka gobe da safe in sha Allah.. Allah ya kara lafia.. Bari naje nae dropping nurr a gida nasan kila by then tsohuwa sun dawo.. If U need anything ka kira dae number dana baka.. Tom shikenan sae ka dawo.. Bayan fitar safwan ya dan mike ya fito wajen asibitin, yau yana kin karfin jikinsa.. Tafiya yake a hankali yana dan kallon mutane.. Hango ta yayi ta dauko wani katoton yaro kamar zata fadi.. Jikin wani karfe yaja ya tsaya yana dubansu.. Tiki tiki tazo wucewa ta kusa dashi, sam bata lura da shi ba, sae masifa take ma yaron wanda bae masan tanayi ba.. Tana zuwa gefensa zata wuce yace *Naughty gal* da sauri ta waigo, aikuwa tana ganinsa ta karaso da sauri.. Yawwa my friend dan taimaka min da wannan big boy din kaji.. harda wani daga masa gira.. Shi dariya ma abun ya bashi, pls mana help me.. Ta fada hadda bubbuga kafa.. Ikon Allah, wannan wacce irin yarinya ce??. Mika hannu yayi ya dauki yaron, _lazy gal_ ya furta a hankali.. Ta jishi sarai amma sae ta share don kar yaki daukar Boy.. Next room dake kusa da nasa shine room din da aka kwantar da bro din nata.. Maimakon ta tsaya ta karbi yaron kawae sae tayi shige warta.. Ba yanda ya iya dole shima yabi bayanta.. Wata mata fara sanye da medicated glasses,Akalla zatayi 55year... gefenta wata matashiya ce bazata wuce 30years ba daga gani itace maman boy.. Sae kuma wani a kwance akan gadon marasa lafia.. Gaishesu yayi sannan ya mika musu yaron.. Babbar matar ce tace hala ganinka tayi ta baka boy ko?? Dariya yayi... Ganinta nayi zata yar da yaron a kasa shisa nayi saurin karbarsa.. ohh ni bansan yaushe *Farha* zaki bar shiririta ba.. pls kayi hakuri fa.. Laaa ba komae ya fada sannan kalli farha.. Harararsa ma take ta turo bakin nan gaba.. Ba shiri ya juya ya fice yana dariya kasa kasa... Yana dawowa daki ya tarar da su tsohuwa, harda hajiyansa.. Dadi ne ya kamasa ganin hajiyarsa.. Lalle abubakar sadeeq jiki yayi sauki harda fita yawo?? Dariya yayi ya samu waje ya zauna.. Hira suka shiga yi.. Jinsa yake cikin farin ciki sosae.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Washe gari aka sallami sadeeq, wanda a daren ranar sae da ya tabbatar sunyi exchanging number da *lazy farha* sunan daya sa mata kenan.. direct kibiya suka wuce bayan sunyi sallama da mommy.. Da alkawarin in sha Allah zumuncin su ya kullu kenan.. Nurr zaune tana yiwa umma tsifa, Nasiha umma take mata sosae tana nuna mata irin hallacin da safwan yayi musu.. Toh umma sadeeq dinfa?? Karki manta sadeeq ya taimaka mana ne ba don ke ba.. Safwan shi ya samo sadeeq ya kawo shi don ya taimaka mana.. Haka dae umma tayi ta fahimtar da ita.. sabuwar mai aikin umma ce tazo ta ajiye musu drinks akan center table.. (Lalle kawata nurr duniya sabuwa harda su mai aiki..Lol) Umma amma zaa tafi dani egypt din ko?? Sae dae kiyi wa abbanki magana ni ba ruana.. Aikuwa tana tambayar abba yace ai dole ma aje dake.. Da daddare safwan yazo ta fada masa, murna sosae ya taya ta.. Kinga kina dawowa sae ki fara examz.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Sadeeq ya warware sosae har ya dawo kano ma.. kullum suna wya da farha tana zuba masa shiririta.. Bata kasar ma Ranar da suka hadu da safwan yake masa zancen ta.. Bro kace ni taimakon ka nayi ma ashe dana kwantar dakae, gashi har new catch kayi.. Mu muna chan muna damuwa our honarable barrister ba lafia ashe kai nan wani lurv garden ka maida hospital din.. Duka sadeeq ya kai masa yana dariya.. Look bro bawae fa soyayya muke ba.. We are jst friends, by d way ma yarinya ce karama.. Look dude, wallahi sonta kake, i c it in ur eyes.. Suka kyalkale da dariya.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Toh watan su umma uku a egypyt anyi ma abba aiki har ya fara takawa.. Ganin an kusa fara examz yasa dole nurr ta dawo bayan ta biya ta cyprust wajen yaya kabeer.. Zaune take a cikin jirgi tana jiran tashin su.. Hi sis, am ur seat mate ta fada tana yarfa hannunta.. Sunana farha en U?? Murmushi nurr tayi mata, Nurr sunana..Nice name Bayan ta zauna ta fara zuba wa nurr surutu.. Tana zaune cyprust ne wajen sis dinta ta take aure a chan.. Sae da suka zo sauka sannan sukayi exchanging contacts.. Safwan ne yazo pikin dinta shida khaleel, sae da yaje suka gaida mommy sannan ya kaita gida.. Bayan fara exams din su nurr da sati daya su su umma suka dawo bayan sun biya ta cyprust.. Sosae abba ya samu sauki yana taka kafarsa ko ina sae dan dingishi kadan.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ In sha Allah zanxo muka da final episode din guguwar so gobe in sha Allah... Urs: harphsart khabeer [18/12 9:10 pm] 🌸Ummu Rabia🌸: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿 🎀Guguwar So🎀 1⃣1⃣1⃣➡1⃣1⃣5⃣ By Harphsart Rano ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Gidan mommy fall da yan uwa anata kallon kaya... Masha Allah kaya sunyi masifar kyau.. Set din akwatuna ne guda biyu.. Set daya pink colour set daya kuma maroon colour.. Kowa ya kalli kayan nan sae ya yaba.. An narka dukiya sosae.. Mommy ce tayi masa set daya set daya kuma daddy yayi masa.. So suke yamma tayi a tafi kai kayan.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Nurr na hango sanye cikin black abaya tayi rolling kanta da peach veil hannunta dauke da handout.. Tafiya take a nutse, duk inda ta wuce sae an kalleta. Wajen wata mota naga ta nufa, kafin ta karasa taji an kira sunanta.. Farha ce itama dauke da nata bunch of handout en ta nufo nurr tana daria.. Lalle ma sis wato tafiya zakiyi ki barni kenan ko?? Allah ya kamaki.. Dariya nurr tayi sannan tace ni na isa na tafi na bar besty?? Kawae na zata baki fito daga lectures bane kuma *Mon amour* yana jirana dts y.. Hmmm lurv birds kullum kuna jone... Kwana nawa ne ya rge?? Sukayi daria gaba daya suka karasa wajen motar.. Safwan wanda tun sanda suka tsaya suna hira yana kallonsu.. Sadeeq dake zaune mazauni driver yace aboki kaga yanmatan chan ko?? Ba abunda ya damesu sae hirarsu suke sun manta damu.. Dariya safwan yayi yace rabu dasu sun kusa shigowa hannu.. Kasancewar motar tinted ce yasa sam basa ganin na ciki.. Suna karasawa nurr ta zagaya ta bude gaba ita kuma farha ta bude baya.. Sadeeq ne a gaba shi kuma safwan yana baya.. Sam farha bata san da sadeeq ba haka itama nurr.. Dole sukae exchangin waje farha ta koma gaba.. Tunda suka fara tafiya safwan ke kallon nurr, ganin kallon yayi yawa yasa ta hure masa ido.. Ya akae ne _mon amour_?? Wannan kallo haka Kashe mata ido yayi sannan yace, bana gajiya da kallonki *Nurul kalb* kin sani kece hasken zuciyata.. Komi naki burgeni yake.. Ina matukar farin ciki da samun ki.. Cikin jin dadi take kallonsa... A haka sukae ta hirarsu har suka iso gidan su farha.. Shima sadeeq da farha hirar su suke cikin so da kauna... Kasancewarsu duk masu surutu yasa sukae mugun sabawa da juna.. Fadan nan nasu yana nan.. Lokacin da suka karaso kofar gidansu farha, sam sadeeq yaki sauke lock din motar.. Hira aka dasa sabuwa, inda sadeeq ke ta tsokanar nurr da cewa tayi wa umma gudun hijira don zaa kawo lefenta yau.. Kuma in nazo gidan yarinya aka kawon abinci mara dadi sae mun karo aure.. Aikuwa farha kamar jira take ta shiga tarewa kawarta.. Hadda cewa ai daga su ba kari.. Shi dae safwan sae aikin dariya yake yana kallon nurr wacce ta turo baki kamar zatayi kuka.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Chan gidansu nurr kuwa yan sumaila sun cika fall suna jiran masu kawo kaya.. An gma shirya komae da komae.. Wajen 4 kuwa sae gasu a motoci takwas.. abinda zae kara burge ka duk motacin nan mata ne suka jawo su. Wato dae babu namiji ko daya.. Hadda hajiyan sadeeq da tsohuwa.. Cikin mutunci aka karbesu.. Bayan sun gabatar da kayan aka basu tukuicin 100thounsand.. Haka suka juya suna jin dadin yanda aka tarbesu a gidan su nurr.. Kowa sae san barka yake... Two month kachal aka saka wanda yayi daedae da kammala level two dinta.. Two weeks da kae kayan safwan aka kae na sadeeq gidansu farha.. Lokaci daya sadeeq ya nema asa masa dana safwan. Ba musu suka amince.. Amaren biyu sae shirye shirye suke gwanin shawa'a.. In ka gansu zaka zata irin childhood friends din nan ne yanda suka shaku da juna.. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Wani handsum guy nagani yana saukowa daga cikin jirgy.. Sae da yazo final step ya ware hannunsa.. A hankali ya furta Welcom back home *Engineer khabeer Abbakar Sumaila*.. Murmushi yayi sannan ya shiga wara ido yana neman ta ina zae hango su Nurr ya fara hangowa sae baza idonu take alamun shi take neme, gefenta abba da umma fuskokin nan nasu dauke da farin ciki.. Cikin sassafar ya karaso, aikuwa nurr tayi tsalle ta dane shi.. Da kyar ta sake shi yaje ya rungume umma sannan abba.. Kwata kwata bakinsa yaki rufawa.. Kama hannun nurr yayi wacce take ta faman zuba mashi surutu suka wuce zuwa inda sukae parking.. Umma da abba na baya wanda dama nurr ce ke driving a sabuwar motar umma..(Duniya sabuwa) Ganin zumudin nurr yayi yawa yasa sadeeq ya kalle ta yace my little kanwa ashe mun kusa shan biki?? Ai kuwa shikenan ya kashe bakinta bata kara magana ba.. Suna zuwa gida already an shirya komae. Wanka yayi sannan ya dawo falo aka dora hirar yaushe gamo.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Saura two weeks biki, umma ta daga zuwa dubai inda zatayi siyayyar komae da komae.. Tare suka tafi da kabeer wanda nurr taso zuwa sae dae dole ta hakura don suna examz lokacin Satin su daya suka dawo inda aka fara biki.. Familyn hudu duk inda ka nufa biki ake shirya wa na kece raini.. Wasan buya buya aka shiga yi tsakani amaren biyu da angwayen.. Safwan ne suna tafiya ya kalli sadeeq yace ya aboki wen last kuwa kuka hadu da farha?? Kasan ni tunda week din nan ya kama banga nurul khalby naba.. Hmm ka rabu dasu kawae nasan hada baki sukae.. Kwana nawa ne?? Duk sae sun amsa query.. Ranar wednesday aka fara biki inda akayi kunshi ranar.. Ranar thursday akayi dinner, sunyi masifar kyau.. Gaba daya couples en sun burge kowa.. Chan na hango engineer zaune da wata course mate dinsu nurr me sunan _Nazifa_ yayi mata introducing kansa, bae wani sha wahala ba tayi accepting nasa cox taga handsome guy😜.. (Ummu sadeeq na hango dauke da sadeeq ta karasa kan stage, mika ma nurr hannu tayi sannan ta kalli safwan tace.. Ango ga little sadeeq nayi ma abokinka takwara.. Karbar sa yyi yana masa wasa gwanin shawa'a.. ohh su ummu sadeeq😜 ) Chan kuma na hango *ayadh, latifa, nazima, meelat, shamsiyya, fuzaima, halimatu, bombour, zaynab uba, dieja maleysia, sumy khabeer, ummu siyama, teemah nama'u, teema gabas* sun nufi kan stage zasu dau picx da amaren.. Su *dieja ran* sae rawar kafa ake zaai selfie da amaren Safwan ne ya matsa kusa da nurr ya rada mata, amaryata kinga yanda *ayadh* kuwa take kallona, anya bata faller ba kuwa.. Ba shiri nurr ta kwabe fuska tace ai kuwa wlh na kara kamata tana kallonka sae na kwakule mata ido😜.. Haka akayi dinner aka watse kowa yana farin ciki.. Ranar friday akayi kamu tare da walima inda aka gayyato malama *Fateema khabeer* tazo tayi lecture akan zaman aure.. Saturday aka daura auren *Barrister Sadeeq Auwal Kibiya* da amaryarsa *Farha Ismaeel* da karfe 11 dae dae, inda aka dunguma zuwa gidan su nurr inda aka daura auren *Dr.Safwan Naseer Mai jama'a* da amaryarsa *Maryam Abbakar Sumaila* Wajen karfe 8 na dare yan daukan amarya suka shiga layi a kofar gidajen biyu.. Kuka nurr take kamar ranta zae fita.. Bata taba tunanin haka rabuwa da gida yake ba sae yau.. Wata gwaggon tace ta kamata ta kaita har falon abba sannan ta juyo.. Nasiha sosae abba yayi mata.. Albarka ya dunga samata daga karshe gwaggo ta sake dawowa ta dauke ta.. An fito zaa tafi da ita ta rike umma kakam tana kuka kamar zata hadiye zuciya. Da kyar aka banbareta daga jikin umma aka sata a mota.. Bangaren amarya farha ma hakan ce ta faru.. Ita ma sae da akayi da gaske sannan aka sata amota.. Unguwa daya sukayi gidajensu.. Gidan safwan na facing gidan sadeeq.. Tsarin ginin gidan ma komae iri daya ne.. An kai amaren biyu wajen 11 kowa ya watse sae su kadae kwallin kwal.. Nurr zaune bakin gado taji an murdo kofar dakin, ya dade a tsaye yana kallon yanda ta wani dunkule fuska.. Takowa yayi ya sa hannu ya dago ta, amarya ba kya laifi tashi muje sadeeq na falo na jiranmu.. Hannunta cikin nashi suka fto falon.. Sadeeq ne ya shiga yi musu nasiha akan zaman tare.. Daga karshe yayi musu fatan alkhairi inda suka fice tare da safwan.. Gidan sadeeq din suka shiga nan ma safwan yayi musu tasa nasihar daedae gwargwado. Bakin gate sadeeq ya rakoshi sannan ya rufe gidan shima ya shige nasa.. Inda ya barta nan ya tarar da ita, umartar ta yayi da ta tashi ta yi alwala suyi sallah don nuna godiyarsu ga Allah.. Ba musu ta tashi ta aikata abinda yace.. Bayan sun idar yayi mata tambayoyi game da addini, daedae gwargwado ta amsa mashi.. Bayan sunyi yan ciye ciyensu sannan suka kwanta.. *Asubah ta gari.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ _7years later_ Nurr tsaye a kitchen tana gasa kaza a oven safwan ya shigo sadaf sadaf yayi huggin dinta ta baya.. Nurul khalb sannu da aiki, yauwa mon amour ashe ka dawo.. Shigowa na kenan naji motsin ki a kitchen.. Ko akwae abunda zan taya ki dashi?? Ehhh tou sae dae ka hada coconut juice remember yanda na koya maka last?? Ofcox na rike bari ki gani, apron ya jawo ya daura kamar yanda tayi ya shiga aikin hada coconut juice.. Ihun yaran da suka ji shi yake nuna musu sun karaso.. *Hanan* ce ta fara shigowa tana ihu Mami, mami we are back, da sauri ta fto daga kitchen din safwan ya biyo bayanta.. Rungume ta tayi tace welcome my baby Sadeeq ne ya shigo farha na biye dashi, *little safwan* da *little sadeeq* na baya, *little safwan* ya rike hannun *Afnan da afaf* (Little sadeeq da twins *afnan da afaf* sune yayan nurr da safwan, while *hanan da little safwan* yayan sadeeq da farha) Dawowarsu kenan daga kibiya satin su daya achan.. Farha wacce ciikinta yayi girma ta samu waje ta zauna.. Nurr ta karaso wajen ta tana mata sannu da dawowa.. Shiko sadeeq da safwan dayan falon suka wuce yaran kuwa suka bisu duka.. Horn mai karfi suka ji ai kuwa yaran suka fto da gudu sanin cewa *uncle khaleel* ne ya karaso cox horn din dayake musu kenan don susan ya karaso.. Tare suke da *anty iman da anty islam* wanda suka dawo daga rabon invitation card din bikinsu.. Ko zama basuyi ba *Engineer da nazifa* suka shigo tare da babynsu wace taci sunan umma suna ce mata *amrah*.. Aikuwa gida ya rike ce, dole suka tura yaran garden sannan suka samu damar tattaunawa.. Sae dare kowa ya watse aka bar safwan da nurr coz yaran ma basa yarda su zauna gunsu suna gidan sadeeq duka.. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Nurr ce ta kalli safwan tace mon amour gaskiya ya kamata mu gayyato Marubuciyar nan *harphsart rano* mu bata labarin rayuwarmu ta rubuta don inaso masu irin halin su kawu suji. Duk yanda kikace haka za ayi my wife.. A take nurr ta jawo waya ta kirani niko jiki na rawa na dauki hanya sae gidan Dr. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Alhamdulillah, Alhamdulillah.. Ina matukar nuna godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafin,.. Wannan littafin labari ne wanda na kirkireshi, banyi ne don cin mutuncin wani ko wata ba.. Kuma in an samu labarin yayi shige dana wata marubuciyar tayi hakuri kuskurene. Godiya ta musamman ga yayata *Fateema khabeer* wadda itace tayi motivating dina na rubuta littafin nan.. Nagode kwarai Allah yabar zumunci.. Ban manta dake ba *big admin Ummee Adnan* na gode kwarai da kulawarki Allah ya raya adnan.. Groups dinmu na *Hikimar mace* *Hausa novels* *Meelat kitchen* *Matan aure novels* *Khaleesat hydar novels* *Feenat ja'afar novels* *Novel chambers* *Nafee &Amrah novels* *Novel readers only* E.T.C Duk ina godiya *Abdulwasil humble* ban manta dakae ba, na gode kwarai da kokarinka na posting novel dinnan a groups da dama.. Nagode Allah ya bar zumunci.. Ina kara mika sakon gaisuwa taga group dinmu na *hausa novels* kunfi kowa son novel dinnan. Ina kaunar ku gaba daya masoyana na kusa dana nesa, wadanda na iya lissafo sunansu da wayanda fade su ba, kuma kuna raina.. Nayi dedicating littafin nan zuwa ga kawata aminiyata *maryam abbakar*.. Na baki shi halak malak Ga duk me son karanta littafin guguwar so daga farko, an bude group, duk maiso sae yayi magana ta number nan sae ayi adding nasa.. _08030811300_ Taku Harphsart Khabeer Umar a.k.a Harphsart rano adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *