adsense here
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
17/8/2016 8:30am
Written by Aysha M. Gana
***********************
1-5
'Kinsan allah xainab banson tafiyar nan, yaya samir ne ya takura min in ba haka ba ba abunda xai kaini abj... Zainab tace aimana kenan nasan abinda yasa baki son zuwa saboda mutuminki, kinsan Allah aimana da abbanku zai burgeni ya hadaku aure keda hakeem naga yanda xakuyi in ganku gida daya"
Nai mata wani irin mugun kallo nace"lallai ma zainab ban taba tsammanin xaki min irin wannan mugun baki ba sai yau, ashe baki sona ki rasa wanda zaki min fatan na aura sai wanda idonsa ya bude da yawon dunia ya saba rayuwa da gogaggun yanmata ya saba holewa dasu, me xanyi dashi allah ya sauwake min, ni ummu aimana bana fata shida daya ganni gwanda yaga muturwa da xata daukeshi ina xaman xamana ki rika yimun mugun baki bana so gaskia'.... Zainab tayi daria tace aimana kenan kinsan kowa da irin nasa salon soyayyar, haka taku salon soyayyar ku take, Allah yasa mu dace kawai" nace aii ke dama zainab bakya sona don duk maison aimana ba xai mata fatan auren abdulhakim ba " zainab tace to miye matsalar sa dan kawai kuna takun saka na dan wani lokaci xaku bari, baki ji ance wani son idan yai yawa ya kan zama kiyayyya ba, wani kin ya kana xama so mai karfi har xuwa karshen rayuwa.kinsan allah duk abinda yake miki da an hadaku gda daya xai daina, baki ji ance *Biri a hannun malamai yake karya ba inko yaje gdan arna yasan kwanan sa ya kare. Ai wlh aimana yadda kuke haka din nan lokaci kadan zaki juyar masa da kwakwalwa,kina da kyau,kina da diri, duk inda mace takai kin kai, ai banga namijin da xai daga miki hankalinki ba sai dai ke ki daga masa hankali, Aimana allah ya baki baiwar kyaun da duk namijin daya kalleki sai yayi sha'awan mallakanki a matsayin matarsa ta aure.... Nace, 'to malama xainab bama hada mun xa'ayi ba balle ki rika mun kakalan tsiyarki. Zainab tace, 'aimana allah ya bamu rai da lafia musha kallo' nace, 'xainab dan allah ki fito fili ki fada wlh in kina sonsa ne, allah ko ba matsala kinga saimu sha biki xako kiji dadi cikin family dinmu' zainab tace, 'Allah baki hkr aimana abinma bai kai haka ba"....... Haka muka karaci hirarmu har lokacin tashi yayi malam musa yaxo ya daukeni, direban gdanmu kenan shi yake kaimu duk inda xamu kuma ya koma ya dauko mu aikinsa kenan a cikin gdanmu,abbanmu duk wata yake biyansa'...
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
******************5-10
ASALINSU
Sunana Ummu Aimana, mahaifina Alhaji mansur su biyu iyayensu suka haifa shida yayanshi Alhaji kabir wanda ake ce mishi 'alhaji babba....yana da mata 1 da yaya uku babbansu shine Abdulhakim sai yasira wacce take sa'a na sai kuma autarsu hanifa....mu kuma mu biyu iyayena suka haifa yaya sameer shine babba saini ummu aimana.. Mun taso cikin shakuwa da kaunar juna tsakanin nida yasira da hanifa amma babu wanda na tsani na gani irin ya hakim bama shiri ko kadan... Gashi kuma ayau ne xamu je abj gdansu nida yaya sameer....
CIGABAN LABARIN
Da sallam na shiga gda umma ta amsa, ita kadai ce kawai a cikin falon. Umma tace, "har kin dawo aimana" nace, ' eh umma mun dawo kinsan yau juma'aa kurarren lokacine saboda xuwa masallaci sallah " umma tace, "hakane fa, to saikiyi maxa ki fara shiri kafin yayanki ya dawo yace kifito,nasan ki da nawan tsiya,in dai akan kwalliya ne kin rinka bata lokaci kenan, shiasa ma na hada miki kayanki saiki duba idan akwai abunda xaki kara saiki qara da sauri" nace, "yawwa umma kin hada mun har da kayan da na karba wurin ja'afar tela?umma tace ban saka ba bansan inda kika ajiyesu ba" "Na manta ashe suna cikin wordrobe dinki. Umma tace, "meya kai kayanki cikin wordrobe dina? Bana hanaki ba allah baki sa'a na kuma gani sai daii ki dawo ki samesu a waje na watso miki. " nace ''allah baki hkr umma baxan kuma sawa ba''.
Harna kammala shirina ya samir bai dawo ba naita jin dadi saboda na gama shirina a tsanake dan shi ma wani lokacin akwai shi da fada kaman ya hakim, amma shi yafi ya hakim saukin kai yaya hakim kam! Sai fadin ran tsiya, sai yaita ma wanda ya damu dashi, ni kam ko a jikina bai ma isheni kallo ba balle har abinda yake yi ya dameni.
Muna xaune ya samir yai sallama muka amsa yace, '' ina fatan kin shirya ko? " nai dariya nace, '' ai yaya kai kawai nake jira sai yace, '' umma kinga har xamu tafi abba bai dawo ba balle muyi sallama. '' umma tace, '' kawai ku yi tafiarku indai abbanku ne ba ynxu xai shigo ba. '' ......muka dau kaya muka saka a cikin booth din motar sai ya sameer yace, '' to mudai umma sai allah yai mana dawowa. '' umma tace to allah kaiku lafia banda dai gudun tsiya ku tafi a hankali sannu-sannu bata hana isa saidai a dade ba'a je ba. '' muka amsa da to umma''
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
10-15
**************
Mun dau hanyar birnin tarayya muna isa ana kiran sallar magariba, nan danan ya samir yai ma masu gadin gidan horn, sai da suka fito suna ganin ya samir sai suka bude da saurin su.
''Oga barka da xuwa. '' cikin farin ciki da murna ya samir ya amsa musu mukai cikin gdan, daidai lokacin hanifa ta fito tana ganin mu sai tai cikin gda da gudu saiko ga yasira da saurinta tana xuwa ta rungumeni.
Tace, ''oyoyo yar uwata, oyoyo aimana mafarki nake kodai haka idona yake gani? '' sai nai murmushi nace, ''nice yasira kina mamaki ne? " tace, "kwarai ma kuwa yaushe rabonki da garin nan sai nace to yau Allah ya kawoni shikenan ko. " taja hanuna muka shiga ciki, lokacin mami tana sallah, muma sallah muka wuce yi.
Bayan mun idar da sallah sai yasira tace " To aimana sai muje ku gaida mami dama kullum tana maganar ki waii ta dade bata ganki na. "
Muna shiga falon mami da murnarta ta tareni tace, '' Oyoyo yar mami har maminki tayi fushi dake tunda ko dan hutu baki xuwa yi mana, ko dai hajia hadixa ke hanaki xuwa yi mana hutu? Dama ina da niyar xuwa in taho dake sai gashi allah ya kawoki. "
Nidai tunda take maganar ba abinda nake sai murmushi nace, ''mami dama ina da niyar xuwar sai kuma ga yaya sameer shine muka taho tare. '' mami tace,''Oh! Ni bilki girman ya mace ba wuya kalli yadda yar tawa ta xama babbar mace sai aure ko aimana? "
Bance komai ba sai yasira ce take dariya, mami tace" ki gama darian ki tare xa'a hadaku a aurar. '' yasira tace "mami ni ba ynxu ba sai nan da shekara uku"
mami tai mata wani irin kallo tace ''ko goma ba, kinaso ki tsufa mun a gida kenan to ku fara shirin yin aure a yan shekarun nan. " yasira tace''mami akwai ta da iya tsokanar mutum'' mami tace ''oh! Tsokanarki ma nakeyi ko to naji aje a ina tsokanarki shikenan allah kaimu. Saita juya kaina tace, "amman dai aimana kin dawo nan kenan ko?
Nace, '' aa mami kwana biyu kawai xamu yi saboda makaranta. '' mami tace," to sai ku tashi kuyi sallahn isha'i lokaci na neman kurewa, sai kuci abinci. Muka ce, ' to mami''
15-20
Muna idar da sallah kande mai aiki ta dire mana abincinmu tuwon shinkafa ne miyar ganye, sai da mukaci mukayi kat! Mukai hamdala sannan muka mike.
Nace,"to nifa yasira kwanciya xanyi don a gajiye nake so nake nadan huta'" yasira tace " da kyau yar hutu".
Shiko yaya sameer yana can shida mutuminsa basu shigo ba sai wurin karfe tara na dare lokacin ba kowa a falo daga abba sai mami suna kallon NTA news. Ya samir ya durkusa yana gaida su mami.
mami tace" na xata wurin hakim din kaxo shiyasa baka xo mun gaisa ba. " ya sameer yace, " Allah sarki mami mun tsaya yin sallah ne shiasa'" Mami tace, " ni dama ga yar gdana nan ina tare da ita kuma sai kuje ku karata kaida hakim din" ya hakim yace, '' mami muba yan gdan naki bane? " tace, ''ehh" ya samir yace, '' to mami ai mana afuwa abba kasa baki, '' Abab yace '' ba wani bakin da xansa a cikin maganar, ai gaskia mamin taku ta fada'' hakim yace '' to munji munyi laifi ayi hakuri, mami an kai mana abincin ne? " eh, kande ta kai muku bangaren ka." sai suka tashi sukayi wa su mami saida safe. Abba yace da mami''hajia bilki ina yar tawa ne banganta ba? Mami tace " aiko tai bacci kasan yar taka yar hutu ne" abba yace to allah kaimu gobe na ganta da kyau".
20-25
Washe gari da safe yaya samir suka je gaida abba, Abba yace "samir inace dai kuna xuwa ga sauran yan uwa ko? "abba muna xuwa'' to Alhamdulillah haka muke so ku rika karfafa xumunci a tsakaninku ko bayan ranmu bance ku yadda zumunci ba kuso junan ku,ku xama tsintsiya madaurinku daya"suka ce ''abba insha allah xamubi abunda kakeso" Abba yace '' Allah ya muku Albarka ''Ameen''.
Muna zaune nida yasira muna hira sai tace ''aimana tashi muje mu gaida su yaya, don ka'idar gidannane a kullum sai munje mun gaida shi inko ba haka ba muka yarda ya shigo sai munci duka. " Nace''saiki tashi kije aii keda kika saba xuwa gaishehi ni ba inda xanje tunda ba shiri muke dashi ba''daria yasira tayi sannan tace ''kinsan allah daria kke bani in kika ce bakwa shiri har ynxu, kawai ki shareshi kixo muje mu dawo, naga dai baku da yadda xaku yi kufa yan uwan junane, amma kun dau gaba kunsa wa ranku ta bnxa.'' nace '' kema kinsan halinshi akwai fadin rai''yasira tace kekuma" girman kai" nace '' sai kowa ya xauna a maxauninsa bai xama dole na gaida shi ba tunda ba wurinshi naxo ba" yasira tai daria '' ni dama abba ya hadaku aure naga yanda xakuyi da juna kuna gda daya" Nai mata wani kallon up and down nace '' Allah ya sauwak dana aureshi gwanda na xauna banyi aure ba" yasira tace " Aimana kenan allah ya baki hke kinga tafiyata''
Tana shiga ta gaidasu yaya samir yace ina aimana take? ''tace tana daki yace''ita ba xata xo ta gaida mutane bane ta xauna aciki yasira tace nace taxo tace aa ya samir yace to ai shknn ita ta sani.
Haka na yini a daki saboda kwata-kwata banaso mu hadu da yaya hakim wanda tunda naje banyi ido biyu dashi na, yasira ko ba xama biki suke na wata kawarta makociyarsu ce shiasa muke dan jin hayaniyar mutane. Ina xaune naji karar fita da mota sai na leka ta window naga ashe ma motar shice, a xuciata nace _Alhmdllh ynxu na dan sarara tunda baya nan na samu na fito, haka kurum yaita ma mutane kallon banxa da wannan idon nashi kamar na maye. Saina bude wordrobe na fito da wani pencil jeans pink sai nasa blue din riga ban saka dankwali ba sainayi parking din gashina dana kalla kaina a mirror ni kaina nasan nayi kyau... Fitowa nayi naga wani guri kaman garden nan na samu guri na xauna ashe bayan windown ya hakim ne sai ji nayi an daka mun tsawa "ke! Da sauri najuya mukayi ido 2 dashi na murguda masa baki ''miye na mun tsawa saikace ka samu yarka... Ke mani kike gayawa magana '' eh din an fada din nan ya fara kokarin cire belt dinshi ina ganin haka da gudu na shiga gda mami tana falo na buya a bayanta saiga shi ya shigo sai huci yake kaman wani zaki''mami tace meyake faruwa nan na kwashe lbr na fada mata '' kefa aimana baki da kunya sa'anki ne shi da xaki murguda mishi baki? To karna sake ganin kin mishi rashin kunya ta juya gun hakim ta bashi hkr a sannan ne ransa ya sanyaya ya wuce cikin gda kome xai dauko oho mishi, nikuma nayi kwanciyata akan kujera ya gama abunda xaiyi ya fito ina ganin shi na kwashe da wani daria ashe darian danayi ya kona mishi rai banyi aune ba naji saukan mari bansan lokacinda na tsala ihu ba saiga mami ta fito da sauri...
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha M. Gana
*******************
25-----30
Mami tace meya sameki? Saboda xafin marin ban iya magana ba sai daii nuna shi nayi da hanu......mami ta kalle shi a fusace tace, '' ynxu kai daii hakim ban ida dakai ba ko shiasa kaqi wucewa sashinka ka shiga ciki ashe da abunda ka kudurta a ranka, a gabana nasa ta baka hkr ashe baka hkr ba ko, to nagode ka kyauta bari alhaji ya dawo shine zaiyi maganin abun tunda ni ka raina ni......
Sallamar wata aminiyar mami ce ta katse fadan da mami take ma ya hakim''inata sallama kinta fada keda yayan naki. " mami tace kedai bari kawai hajia binta yaron nan ne nake fama dashi sai kace karamin yaro, fada suke shifa yar uwar tasa ina bada baya ya mareta. " hajia binta tace, " kaii haba abdul baka kyauta ba ina kai ina fada da mace macen ma kanwarka, karka bani kunya mana yadda nake yabon hankalinka ka dinga hakuri kaji hakeem. " mami tace, '' da kin barshi kawai hajia binta karma yayi hakuri tunda abin nashi ma iskanci ne to aimana ta dawo gdan nan da xama kenan kinga saiya hada kayanshi ya bar gdan tunda baxai iya xama da ita ba'' ina ganin fadan mami ya tsananta sai na mike na bar wurin, tunda mami take fadan baice komai ba amma ransa a bace yake.
Mami tace, '' fita ka bani wuri''
Yana fita hajia binta tace, '' kaddai ince itace wanda kike fada mun xaku hadasu aure?
Mami tace,'' ita dince.'' hajia binta tace '' ikon allah to ku kuna ganin za'ai abun arziki a nan? " mami tace '' rabu dashi kinsan bason hadin yake yi ba so yake ace an fasa shiasa yake haka kuma bai isaba so yake yaita yawo haka ko yaje ya kwaso mana mai xaginmu" hajia binta tace''allah dai ya shirya mana yaranmu''mami tace '' ameen.
Washe gari muna xaune da yasira tace" aimana ki shirya muje wurin lunching din ni'ima" na kalleta nace '' kema dai kinsan bana xuwa gayyar sodi an gayyaceni ma banje ba balle kuma ba'a gayyaceni ni ba salon a rinka nuna ni ana mun kallon bnxa kinsan ba kyalewa zanyi ba gwanda kar naje wurin" sai tace '' kai aimana don allah waxai miki kallon bnxa, ke bakisan yanda ni'ima take sonki bane" nace ''a ina ta sanni balle ta soni? Tace''aii na bata lbrnki tun lokacin take son ku hadu, ko jiya ma ta shigo ku gaisa kina bacci tace in gaidaki in kin tashi wani abokin ya hakim ma xata aura imran,allah ki shirya muje kinji''nace kaii yasira kin fiye naci,xanje to shknn tace ywwa tawan haka nake sonji daga gareki....
Karfe hudu na shiga toilet na tsalo wanka sannan na gabatar da sallahn la'asar sannan na tsaya gaban mirror inda na dau lokaci wajen kwalliya, ni kaina saida na tabbatar da kwalliyan dana yi yayi saboda yanda nayi kyau sosai kamar nice amaryan,sannan na fito falo.....
Mami ta kalleni tace '' kai amman yan matan nan tawa ta iya kwalliya kamar xaki xaben fidda sarauniyan kyau aiko amaryar baxa ta kaiki yin kyauba" wani swiss less ne a jikina red mai touches din green na yafa gyale grewn takalmi da jaka ma duka green sai sarka da dankunne red kasancewa na fara kayan yayi matukar amsata... Mami tace wannan kwalliyan saina bada tukuicinta" lokacin yasira ta fito ita ma tayi kyau sosai, mami tace ''yasira dauko mun jakata''bayan ta dauko jakan mami ta bani dubu goma tace nai ma amarya liki sannan ta bawa yasira ita ma dubu goma mukai mata sallama muka fito,bayan mun fito ne yasira tace ''ywwa aimana karki ga an kira sunanki kiyi xaton bake bace xaki hau mana high table '' nace ni asuwa na hau high table sai kace wata kawata''yasira tayi ta rokona tukun nace xanhau...
Muna iska naga wuri yayi wuri ya cika makil da yayan manya, in kaga yanda akayi arranging din gurin saiya baka sha'awa sautin kida kawai yake tashi a wurin, ba'a bata lokaci ba aka fara kiran sunayen masu hawa high table, sunan yaya hakeem aka fara kira da yake shine babban abokin ango. Banyi aune ba naji an kira sunana nanfa kowa ya xura ido yaga waye ummu aimana, shi kanshi yaya hakiim inda yasan tare xamu hau mu xauna baxai taba bari ba ko yasira shiya hanata hawa a matsayin babban kawar amarya, wai indai xata hau baxa hau ba ya xa'ayi a hada shi da kanwarsa salon ta raina shi, sai gashi an hadamu kuma yasan aikin yasira ne xasu gamu xata sani.
Daga ido yayi ya kallan daga lokacin bai kuma kallo naba illa hada rai da yayi kamar an aiko mishi da saqon mutuwa, amma dukda haka bai hanashi yin kyau ba saboda gaskia ya hakim akwai kyau. Ganin yanda yayi yasa nima na hada raina masu hoto ko duk inda muka juya sai dai kaga haske yana tashi.
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha M.Gana
35-----------------40
***********************
Tsawa ya hakim ya daka ma yasira yace, '' ke me kukeyi anan har ynxu baku tafi ba? Ta rasa irin amsar da xata bashi, sai ya koma kaina yace, '' ke bar nan wurin, '' nai kaman banji shi ba, wata muguwar tsawa daya daka mun bansan lokacin da nabar wurin ba, sai ya koma kan jamil yace, '' kai baka ji abunda na fada maka ba ko? To baka ba ita inba haka ba xaka raina kanka a garin nan, '' saiya juya yai tafiyarsa...... Muna barin wurin mota muka hau raina yai mugun baci nace, '' ynxu dan allah yasira abunda ya hakim yai mana ya kyauta kenan a gaban saurayina ya cimun mutunci, '' yasira tace kema dai aimana saida na fada miki yana xuwa ya samemu fada xaiyi amma baki ji ba, '' nace akan me xai takura min Allah ya kaimu gobe tafia gda xanyi basai ya kuma ganina na sannan yai mun wulakanci, " yasira tace yanxu ke saboda shi saiki tafi sai kace wurinsa kika xo'' nace '' nasan ba wurinsa naxo ba amma ya takuramin da yawa sai kace ni kadai ce a gdan, kuma muna komawa saina hadashi da mami'. Tace '' ke dadi na dake akwai baya wucewa a gurinki, '' nace saboda bake yai mawa ba shiyasa kika fada haka,'' yasira tace nima nawa yana jirana Allah yasa ma karya bugeni, dama dama xan dinga yi saboda nasan halinsa da saurin hanu kamar mai tabin hankali".
Bayan mun dawo gda mami ta kallen tace''yar mami ya naga fuskan ki ya canja ne ba kamar yadda kuka fita ba, '' yasira tai sauri tace mami fada sukayi ita da ya hakim a wurin lunching, ' tana shirin fadar abunda ya hadamu, karaf! Sai muka ji sallaman shi da gudu yasira tai bayan mami. Yace, '' ke ni idan kika ce xaki rainani wlh xan balla ki wawiya kawai, '' ya kama hanya xai wuce sai mami tace, '' kaii xonan wai kai wani irin mutumne ka cika xafin xucia, kullum cikin fada kake da kannen ka kamar sa'annin ka to bari kaji raina ka xasuyi tsoron da suke maka ma su daina, ku kuma ku tashi ku bani wuri..... Muka tashi sum-sum muka wuce, mami tace, '' mai kuma ya hada ka da aimana? Yace, '' mami yarinyan nan ta raina ni'' nan ya kwashe yanda a kai ya fada mata ya kuma cewa, " mami kuma kuna cewa xaku hadamu haka xamu xauna ban isa na fada mata tayi ba, gaskia mami da sake a sako shawara''mami tace''da kyau ubanmu ai dole mubi yadda kke so saboda kada ka tsine mana mubi dunia" yace '' mami wlh ba laifina bane kunce ga yadda kuke so kuma na amince sai kuma ta riqa rainani gaskia baxan yarda ba'" nandai mami ta riqa baiwa ya hakim hkr harya hakura ya fita.
Bayan mun cika kwana biyun mu washe gari da safe na tashi na fara hada kaya yasira tace" kar dai ince har hada kayan tafia? Nace''ina ruwanki da hada kaya na ko laifi ne dan na hada? Tace''aa allah baki hkr. Da sallamata na shiga falon abba yana nan kasan cewar yau weekend ne, daga shi sai mami ne a falon ya kalleni yace, ummu aimana ya akai ne? Nace dama abba naxo nai maka sallama ne ya samir yace da wuri xamu tafi''yace, da wuri haka aimana na xata xaki mana kaman wata guda''sai nai dan murmushi nace, abba ai akwai makaranta shiasa '' yace hajia bilki kinaji yar taki wai tafia xatai ta barmu''mami tace alhaji dama ina so nai maka wata magana yace ta mefa mami tace '' mai xai hana aimana ta dawo nan da xama inyaso saita karasa karatun ta dama ina da burin rikonta tun tana karama allah ne bai yiba,kaga saisu kara shakuwa da yan uwanta'abba yace kwarai kuwa bilki kin kawo shawara haka ko xa'ayi '' ni kuwa wata irin faduwan gaba ne ya sameni nan ko gumi ya rinka ketomin saika ce wadda aka kama xa'a kai gdan yari innalillahi wa inna ilaihi raji'un kalman danake ta nanatawa kenan a xuciata, na shiga uku ni aimana da rayuwata ta yaya xamu xauna gda daya da ya hakim alhalin bama jituwa dashi? Sai da nace ma ya samir baxan xoba ya takura mun irin abunda nake gudu kenan... Mami ta lura dani yadda na canxa tace '' yar mami ya naga kinyi shiru kodai baki son xaman ne? Nace aa mami ba komai Abba yace '' bari na kira mansur dinma nan take abba ya kira numbern abbana bugu daya xuwa uku ya dauka cikin ladabi yake amsa wayar '' yaya ina kwana''yace kalau muke abbana yace ''yasu hajiar da yara '' duk suna lafia'' Abba yace '' dama ina son sanar dakai cewan karkaga samir ya dawo shikadai to na kwace yata ta dawo wurina da xama abbana yace''haba dai yaya har saika fadamun ai duk yanda kayi daidai ne kagaida mun hajia da yaran '' abba yace '' insha allahu xasuji '' haka sukai sallama.... Mami tace ' to yar mami kin xama yar abuja ki saki jikinki komai kike bukata ki sanar mana karki cuci kanki nan ma gda kika xo.....
To fa Ku biyoni don jin yaya xaman Aimana da Abdulhakim Xai kasance.
Luv u oll😘
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCi🐾🐾
Written by Aysha M. Gana
*****************
30------------35
Can sai ga wani daga cikin abokan ango ya zagayo kusa da yaya hakeem yace, '' ya kai abdul wannan babe din fa? Sai ya kallan ta gefen idonsha yace, '' kanwata ne kuma tana da miji ba ruwanka da ita kai abinda ya kawo ka. " mutumin yace,'' shknn abokina tunda kaimin bakin cikin samun xukekiyar budurwa ko ince mata amma ba komai in rabo nane xan samu'' ya hakim ko bai kuma asa magana ba, nan aka kira abokin ango dan bada tarihin ango, ita kuma yasira ta bada tarihin amarya, bayan sun gama aka bukaci ango da amarya domin su fito suma su chashe a fili, nanfa DJ ya saki sauti da wakar da akai ma amarya da ango kudi ko like su ake kamar ba gobe.
Banda wulakanci irin na yasira anama amarya da ango liki amman ita nida ya hakim take mawa sai daukan mu hoto akeyi, da naga haka saina zame zan fito daga fili sai ta riko mun gyalen dana yafa.
Tace, '' haba dan allah ina xakije? "
Nace, '' nidai ki barni kawai nagaji ne gda ma xani. ''
Tace, '' saboda me ba'a gama ba xaki tafi '' nace saboda sa'idawa sunyi yawa duk inda mutum ya gilma ido na kansa shiasa xan bar wurin''tace, '' yi hkr dan allah mana a tashi ai an kusa tashi ba wani dadewa xa'a kuma yi ba" Haka na koma har aka tashi, muna fitowa mukaci karo da mai hoto har yaje ya wanko hotunan, yasira ta karba ta bashi kudin. Nace, '' mu gani'' tace, '' baxan bada ba salon ki yaga''nace, '' oh ashe ke kika sashi ya rika mana hoto, '' tace '' eh mana kuma mami xan kai mawa ta gani''nan da nan na marairaice mata nace, '' dan allah karki kai mata ki yagasu''tace''lallai ma haka kurum na yaga kudina''nace to ga wani kudin sai na baki a yagasu don allah hkr''ta kallan tayi daria tace, '' kanki ake ji wai mahaukaci ya fada rijiya yace ni ku kyale ni wanka na nake yi. ''nace ynxu haka xamuyi dake yasira? Tace to waii miye abun damuwa kawai don ka dau hoto da dan uwanka naga aiba komai bane karin *HADIN ZUMUNCI*ne''nace a wurinki ba don kinyi hakane dan ki kulla mun sharri a wajen su mami, to yadda kika kulla haka xaki kwance muguwa kawai''sai tai tamin daria.
"Assalamu alaikum"
Sai muka juya domin muga mai sallama,wa xan gani inba mutumin daya xo wurin ya hakim lokacin muna cikin *hall*,muka amsa sallamar sa kaman yanda ya mana.
Yace dan allah malama aimana idan baxa ki damu ba ina son magana dake''sai muka juya muka kalli juna nida aimana sai naga kaman ranta baiso ba.
Nace, '' ya naga kaman ranki bai soba? Tace, '' ni wlh bana son naga kina kula samari''nace''kamar yaya aure gareni ko rana aka samun? Tace lallai aimana wuyarki ta isa yanka, nidai kiyi sauri kiji abunda xaice kar ya hakim ya fito nace nima ba dadewa xanyi ba sannan na karasa gunshi nace''malam ya akayi kasan sunana? Yace''kinsan in mutum yana son abu dole ne kabi diddigi har ka gano wani abu daga gareshi, cikin lokaci kankani sonki da kaunarki sun mamaye xucia ta ina fatan xan samu karbuwa.. Nace, " allah sarki ngde da irin kaunar da kke mun allah xaba mana abunda yafi alheri''yace a wani gari kke? Nace''a kaduna nake '' yace ni anan iyayena suke da xama amma ni costume ne ina aiki a lagos bikin nanne ya kawoni sunana Jameel alkaseem muna xaune a maitama''ni kuma naxo hutun gdan yayan babana alhaji kabir '' yace oh minister? Nace eh yace kice ke yar manya ce,nidai murmushi nayi saiya miko mun rafar kudi har naira dubu goma yace''gashi kwa sha ruwa''nace''gaskia nidai baxan karba ba" yace haba aimana baki san ba'a maida hanun kyauta baya ba, maida hanun kyauta baya sai shaidan nace"hakane yace to tunda kinsan da haka saiki karba indai ba kin raina ba.
Na saka hanu xan karba kenan sai ga ya hakim nan ya fito,wani mugun kallo da yai min saida hanjin cikina ya motsa yasira ma nan da nan jikinta ya fara rawa...
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾07017251433
Written by Aysha M.Gana
40-----------45
*********************
Haka rayuwata ta kasance a garin abuja maganar jituwa kuwa bbu ita tsakanina da ya hakim kullum muke nan fada kaman kaji, mami taita fada har abun ma ya isheta tasa mana ido, shiko abba abunma daria yake bashi idan yaga muna fada. Har mami ta gaji ta same abba a daki tace'' ynxu alhaji haka xa aita xuba ma yaran nan idanu suna tashin hankali? Abba yace''kedai kawai ki rabu dasu kuruciya ce ke damunsu wata rana xasu daina so nake ma naje kaduna danmu tattauna maganar aurensu shida aimana daga xaran ta gama makaranta sai a fara shirin biki''mami tace''ywwa hakan ma yafi in sukayi auren idan suka ga suna gda daya aii dole su hkr, amma alhaji yaushe xaka je? Abba yace''ranan asabar insha allah mami tace to allah kaimu abba yace '' amiin''.
Ranar asabar abba ya tafi kaduna naso na bishi amma mami tace aa, muna xaune a falo saiga mami tace''ku shirya yayanku xai kaiku kasuwa ku xabi abunda kuke so'' yasira da murnarta tace''to mami ynxu ko xamu shirya kar ya dawo yaga bamu shirya ba yace ya fasa'' niko raina ya baci dan kawai kar mami tayi fada ne da wlh ba inda xani da wannan mugun mutumin ko hanya bana so mu hada balle tafia mai tsawo.
*** KADUNA***
Abba yana isa kaduna kai tsaye gdanmu ya wuce bayan yaje ne suka gaisa da umma da abbana sannan abba yace''mansur dama naxo ne akan maganan aimana da hakim ya kamata mu tsayar da lokaci da xaran ta gama makaranta sai a fara shirin biki '' abbana yace to yaya''duk yanda kace haka xa aii allah ya tabbatar mana da alheri '' amiin''sannan ya mike yace shi xai koma saboda ba kwana xaiyi ba nandai abbana da umma na suka rako shi ya shiga motan shi saii abj.
****ABUJA****
Ya hakim bai dawo gdan ba sai wurin karfe uku na rana yana shigowa mami ta kirashi tace''ka shirya xaka raka su yasira kasuwa aimana xata kara kaya naga kaman kayanta suna so suyi mata kadan a karo mata sababbi'' yace '' mami baxan samu xuwa ba akwai inda xani''wani mugun kallo mami tamai saida ya dukar da kansa tace '' da kyau har uxurinka yafi nawa kodan kaji ance aimana xaka raka shine kke so ka xamar da tafiyar to wlh saika je,ni dama nasan ka raina maganata amma idan alhaji ya dawo saina sanar dashi a daura muku aure akai maka ita in yaso sai muje mu dauko gawarta anan ne xamu gane kiyayyar da kke mata.... Nan dai mami taci gaba da xuna mishi masifa nan da nan ya durkusa har kasa yace, kiyi hkr mami allah ya huci xuciar ki, su shirya na kaisu idan na dawo saina wuce inda xani '' mami tace ywwa allah maka albarka yace '' amiin.
Muka shirya muka fito sanye nake da wata atamfa riga da skirt, na dauko gyalr na yafa kalar atamfar yasira ta kallen tace, '' allah yasa kar ya hakim ya yaga miki wannan gyalen da kika yafa, amma koda yake bakwa shiri baxai ce miki komai ba. Muna fitowa shima yana fitowa daga bangaren shi cikin shigar kananan kaya sun masa kyau muna hada ido dashi sai ya hada rai yace''ke baki da kunya ko yasira bata fada miki basa yawo da gyale ba'" nima na hada rai nace''bata fada mun ba sai daii in kai ynxu xaka fada mun''tsawa ya daka mun yace ba rashin kunya nace kimin ba tambayarki nake, duk wata muguwar dabi'an ki sai kin barta indai muna gda daya dake kuma ki koma ki cireshi na fada miki''na yamutsa fuska nace '' ni bani dashi haka kurum sai aita takura ma mutum kuma idan yai magana ace bashida kunya kamar shiya kawo rashin kunya dunia'' yace ' oh! Baki dashi ko to xakiyi shi da kudina xan sai miki allah yasa karki saka kiga yadda xamu kwashi yan kallo nida ke''yadai yita fadanshi ban kulashi ba ya gaji ya hkr.
Wuse market mukaje a bakin wata plaza mukai parking muka fito muka shiga wani babban shago ya hadu sosai, kayan da nake xaba daban kayan da yake xabar mun daban sai kace shi xai saka. Ya juyo ya kallan yace''wannan kayan da kike xaba kina da kudin da xaki biya ne? Nace''kai xaka bada kudin" yace" to ba suyi mun ba don ba irinsu xa'a sai miki ba''nace wai kai meyasa kke mun irin haka ne bafa kai xaka saimun ba amma kace sai wanda ya maka xan saka''saiya juyo ya kallan tare da hade rai''yace karna kuma jin kinyi magana".
Saiga wani saurayi ,dama tunda muka shigo yake kallonmu ya karaso inda muke yace, nawa ne kudin kayan data xaba saina biya'' ya hakim najin haka saiya hada rai yace, kai malam bamuyi kama da irin wanda xaka biya ma kudi ba, ko ance maka bamu da kudin biya ne'' sai mutumin yace ba haka bane nayi niyya ne kawai badan komai ba sai dan na yaba da hankalinta ne'' ya hakim yace''mungode jeka da niyyar ka bama so" mutumin yace haba abokina ya ina son nai abun alkhairi kana so ka hana, ko baka so ka bani kanwarka ne? Ya hakim ranshi ya baci yadaka mun tsawa" wuce muje" jiki na rawa muka bar wurin don a lokacin yadda na ganshi yana iya kaimin duka idan na tsaya taurin kai, ni abunma har mamaki yake bani ba dama ace ana sona a gabanshi sai yaji haushi, ko ina ruwanshi oho! Wannan shine karfin hali barawo da sallama kaki sona kuma ka hana a soni, raina a bace muka tafi har wurin da muka kai dinki shagon mus'ab tailor , shine tailor din mami ya hakim ne ya xabi dinkin da xa'ai mun ina kallon sa bance komai ba, don ko nace maganata baxa tai amfani ba yasira kuwa muguwa sai faman daria take yi har muka dawo gda. Da abin ya isheni nace''wai ke dawa kike darian nan? Tace" allah baki hkr bani na kar zomo ba rataya aka bani shi xaki yiwa bani ba.... Wai hayaniyar me nake ji ne an tafi lafia an dawo da hayaniya " mami take tambayarmu yasira ta kwashe yadda akai ta fada wa mami, sai mami tace xonan yata kyalesu shima xai xo nan ga sameni, ke kuma kar ki sake mata daria na fada miki".
Am srry rashin typing da wuri bani da charge ne ga wannan kuyi manage kafin nayi charge.
Aisha💞
[6:16PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
45----------50
*******************
Haka muka cigaba da xuwa makaranta tare dasu yasira kuma abba ya daukar mana lesson teacher yana mana kuma muna ganewa cikin ikon allah. Shima mai takuramin baya kasar abba ya turashi spain ya duba kamfanonin sa da suke can, bamma san lokacin da xai dawo ba shiasa nake cin karena ba babbaka.
Mun kammala karatunmu cikin nasara kuma da sakamako mai kyau jira kawai muke a fara bada admission mu fara xuwa jami'a har wannan lokacin ya hakim bai dawo ba mun daiji mami tana cewa yai waya cikin satin nan xai dawo amma bai fadi rana ba.
Ranar juma'aa muka shirya sai maitama gdan su wata frnd dinmu da mukai sch tare ranar acan muka wuni sai wurin magriba muka dawo mami ta dinga fada wai munje mun jima muka ce mami mun dade bamu hadu bafa shiasa tace "to naji in kunyi sallah sai kuje kuyi ma yayanku sannu da dawowa yasira tace" mami ashe yaya ya dawo " eh ya dawo bai jima ba yasira tace" aimana tashi muje muyi wa yaya barka nace" ba xani ba haka yasira ta kama hanya ta tafi nace allah raka taki gona. Bayan kwana biyu abba ya kirani falon sa yace ya kamata kije kaduna ki gaida iyayen ki tunda baku fara xuwa sch ba sauran kuma in kikaje kiqi dawowa muyi fada dake daria nayi nace" abba ai kuma na riga da na saba daman ko naje xan dawo gurin mami na abba yace da kyau yar mami ai daman mamin tana shagwaba ki daria kawia nayi sannan na tashi na koma daki.
Bayan munyi sallar magariba mami ta kwalla mun qira naje da sauri tace in dauki abinci ya hakim na kai mishi daki saida gabana ya fadi saboda tunda ya dawo banje na mishi sannu ba haushina yake ji kaman ya kasheni.
Haka badan ina so ba na dauka na wuce da sallamata na tsaya a bakin kofa yasan nice amma yake tambayar wanene dana ga xai raina mun hankali kawai saina kutsa kqina cikin dakin zaune yake kan doguwar kujera riga ce armless a jikinsa sai 3 quarter, wuce shi nayi naje kan table xan aje kenan yace kawo min nan da kamar baxan juya ba sai kawai na durkusa na ajiye a gabansa xan tashi kenan ya riqe mun hanu da karfi saida nayi kara yace waya ce ki shigo mun daki da yake baki da mutunci na dawo kowa yaxo yamin sannu da dawowa amma ke baki xo ba saboda ban isa da ke bako xaki bani hakuri ko kuma, nai shiru '' magana nake miki fa " naqi magana saiko ya take mun dayan hanun dana yi dafe dashi bansan lokacin dana ce kayi hkr yaya sannan ya sakeni, ina xuwa bakin kofa nace anki xuwa gaida kai din nina aikeka da xaka dameni wlh sa'a ma kaci dana xo wannan kuturun dakain naka, yace''to sarauniyan marasa kunya yi waje kuma kinsan allah xan kamaki saikin yi fitsari xan kyaleki nace " a hayye ashe aimana tana da matsayi tunda har an nada ni sarauniyan marasa kunya kasan allah tunda kaqi kama girmanka raini ynxu na fara maka shi da idonka kaman na mujiya aiko da gudu ya tashi xai biyoni aikuwa da gudu na ari na kare ina xuwa mami tace kinkai masa nace eh...
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
50------------55
********************
Muna cikin tafia gdan wata kawar hajia mariam mami nida yasira tace" niko bana son xuwa gdannan haidar da jabir sun cika sa ido shiasa bana son xuwa nace" kema dai yasira ina ruwanki dasu wurinsu kika xo da xaki dami kanki akan me, sallama mukayi falon tana xaune muka gaidata tace hajia bilki ce ta aiko ku ko? Mukace eh tace gashi kuma ba'a kawo sakon ba amma kuce mata tayi hkr ana kawowa da kaina xan kawo mata muka ce to. Muna fitowa muka hadu da jabir din mukai kamar bamu ganshi ba, shine yace ko gaisuwa bbu? Muka ce kayi hkr ina wuni yace saida na roka yasira tace ba haka bane kasan ance hankali ke gani ba ido ba, sai ya kallen yace ke kuma madam ya sunanki? Murmushi nayi nace ummu aimana yace" kai sunan ya dace dake mukace bari muje kada dare yai mana yace " to saina xo" saida muka wuce yasira tace ke aimana kinyi kasuwa fa , nace " wani irin kasuwa me ya dameni dashi ya dade bai xoba shiya sani yasira tace " kedai kibi a hankali ku rabu lafia muna dawowa mukaci karo da ya hakim ko kallonshi banyi ba muka wuce gda....
A gurguje plss....
Typing akwai wahala😢
55-------60
Soyayya ce me karfi ta shiga tsakanina da jabir ranan muna xaune nida shi sai hira muke yi cikin nishadi munyi sallama xai tafi ya miko mun wata leda saida ya matsamin sannan na karba na kaiwa mami nace" mami ga abunda jabir ya bani yadda na lura da mami sai naga kaman ranta baiso ba, amma bata nuna mun ba tasa hanu ta karba bata sake cemi komai ba nima haka... Mami ce ta tashi kai tsaye falon abba ta nufa abba yace" ya a kayi ne mami tace alhaji maganan yaran nan ne kaga fa har samary sun fara xuwa suna son aimana ni abinda na gani tun kafin soyayyar wani ta shiga xucian ta ya kamata ai wa tufkar hanci abba yace hakane in kin fita ki turo mun ita mami tace to, tana fita kai tsaye dakinmu ta shigo tace aimana kije abbanku yana kira nace to mami da sallamata na shiga na durkusa nace gani abba yave" dama inaso na miki magana tun baya sai naga karatu kike, ina so ki sallami duk wani mai xuwa gunki saboda na miki miji ba kowa bane face dan uwanki abdulhakim innalillahi wa'inna ilaihi raji'un nan da nan naji wani gumi yana keto mun ba komai nake tunani ba illa na hangi tsanar dake tsakaninmu da ya hakim wai ace shine mijin aurena lallai akwai rikici nan gaba sai dai ba yadda xanyi na bar wa Allah xabinsa kawai , abba yace ya naga kinyi shiru nace ba komai abba allah sa haka shine yafi alheri abba yace '' amin yata nan na mike na fita......
To fa! Ana wata ga wata
SHIN YAYA JABIR ZAIYI?
ANYA KUWA ANA YIN AUREN NAN?
YAYA ZAMAN MA'AURATAN ZAI KASANCE?
Ku biyoni domin jin amsoshin tambayar nan.....
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
60---------------65
*********************
Cikin wannan satin abba ya kira family meeting anan yake sanar musu da abunda ya Yanke, nan fa kowa ya fara fadin albarkacin bakin sa nan dai abba yace yau muna daya ga wata to ansa auren xuwa karshen watan nan. Farin ciki bai misaltuwa a cikin wannan family illa mu kadai tundu mu ba son auren muke ba.
Bayan sati daya da saka mun rana ina xaune a waje sai ganin mutum nayi a kaina kaida ganin sa kasan ba cikin kwanciyar hankali yake ba ya samu waje ya xauna yace aimana na dago kai na kalle shi sai naji tausayin sa ya kamanj yace''dama kina da wanda xaki aura shine baki fada mun ba saida sonki ya kamani nayi xurfi cikin sonki shine naji wai xaki auri wani lallai baki mun adalci ba nace " don allah kayi hkr jabir wlh bani da niyyar yaudarar ka nima bani da masaniya hakan kuma bani da yadda zanyi duk da na gari yana son yayi wa iyayensa biyayya kai hkr ina maka fatan alheri allah ya baka wacce ta fini. Yace" shikenan aimana xan mika kuka na xuwa ga allah nace" kayi hkr nima ba haka naso ba. Kira naji ana kwala mun muryan yaya ne yace me kike anan maxa kibar gurin kafin ranki ya baci sannan ya wuce ciki sallama mukai da jabir ya kawo wata leda ya bani na karba nayi godia ....naxo shiga gda ban sani ba ashe ya hakim yana nan saiji nayi an janyo hijabi na har saida naxo dab dashi, muna jin numfashin juna yasa daya hannun ya kwace ledar hanuna yace dama abinda kike so kenan kiyi ta amsar kayan mutane kina ci ke gaki mayya ko ya nunani da yatsa yace" waike ga yanmata ko kinsan allah randa kika shiga hanuna xaki sani nace" naji nan gani nan bari dumamen mayya kuma miye na rike min hijab kasan allah in baka sakeni ba xan maka ihu, yai wata irin daria yace kiyi mana kina kara magana saina darje bakin ki na rashin kunya nace" nidai ka ban ledata na tafi bai bani ba saida ya gama ganin abunda yake ledar sannan yace amshi tsiyar ki nace" aa kadai tafi dashi naga kamar ranka naso yace " allah kiyaye idan naci wannan ai sai nayi amai saike ai tsamiya asaka a kunu nayi daria nace" kaine kunun danko kai kayi kama da kalar kunun tsamiya kauce ni kabani guri banda lokacin ka yace" dama waya ke da lokacin ki kalleta kawai, damma kin samu xan rufa miki asiri na aureki kallon raini na mishi nace kaima kasan na wuce a kallen ace xa'a rufa mun asiri sai dai kaii na taimaka mawa na aureka amma bani ba rasa bakin magana yayi tsayawa kawai yayi yana kallona na tofar da yawu nai gaba abuna.
Hakeem ne xaune a daki sai xancen xuci yake yi a gaskia shi ba son aimana yake ba dan akwai wata yarinya da suke soyayya da ita sosai zinat amma ba damuwa ko bayan auren mu da wancan maras kunyan ne xai san yadda xa'ai ya aure zinat.
Cikin satin nan abba ya shirya mana tafia kaduna kwana uku kawai xamuyi saboda shirye shiryen biki. Washe gari da wuri muka shirya na saka kayanmu a booth cikin motar yaya xamuyi tafiar kwalliya mukayi sosai munyi kyau muna fitowa muka ga ya hakim nan muka dau hanyar kaduna muna ta hira harda shewa nida yasira yace " kai miye haka sai kace kuna gdan biki yana yin shiru nace" yasira ban fada miki ba tace" miye? Nace" sabon saurayi nayi guy din ya hadu iya haduwa ba irin su wa'eh ba tace" ban lben nasha nace" ke dai ki bari saimun sauka xan fada miki kar asa mana ido kinsan ni sarkin laifine ynxu sai ace nayi wani mugun kallo yai mana nan yasira ta shiga taitayin ta bata kuma magana na, ni dama nayi ne don yaji haushi kuma yaji. Har muka isa kaduna umma da murnarta ta tare mu nan dai aka xauna aka ci abinci sannan aka shiga hirar dunia nan dai umma tayi tamun nasiha haka muka karashi kwanakin da xamuyi muka dawo abj.
Hakim ne tare da abokinsa abbakar a dakinsa cikin hirar sune abbakar yace ' wai kai baxa kayi inviting din kowa bane" yace" ka barni kawai abokina ba wanda xan gayyata gacan I. V din tunda abba ya bani ban ba wa kowa ba... Abbakar yace" yawwa baka nuna mun matar naka ba balle mu gaisa, hakima yace" in kana so ka ganta saika aiska a kira maka ita abbakar yace" kai mata waya mana"...muna xaune naji ya kira yasira yace" kice aimana ta fito ana son ganinta" tace to yaya tana xuwa tace" nida yayane wai kije ana son ganin ki kuma wlh in bakije ba xan fadawa mami " nace" gaskia yasira kina shiga rayuwata nan dai na tashi na nufi dakin shi sallama nayi abokin nasa ne kawai ya amsa mun na samu waje na jingina da kujerar bakon yace" amaryan mu harkin iso na danyi yake" nace ina wuni " lafi lau ya shirye shirye? Nace" yana wurinku yace" yana dai wurinki keda angon ki shiru na mishi yace" ywwa dama ina so na tambaye ki wani irin event kika shirya mana kinga saiki hadamu da frnds dinki saimu tattauna ko nace" ni babu abunda na shirya wanda kukayi ya wadatar Abbakar yace" kinko san irin tanadin da mukai wa bikin nan kuwa don muna so mu bar tarihi a garin abuja ko ba haka ba abokina ya juya ya kalli ya hakim yace" kai idan xakuyi maganan ku kudaina saka ni a ciki nace" dama waya kasa dakai balle ka kwasa" nai tsaki yace" ya isa haka barmin dakina tun kafin ki xageni Abbakar yace" kada ku bani kunya mana banda abinku yaushe amarya da ango suke fada? Nace" bari in wuce ni ina da abunyi" yace " bamu gama tattaunawa ba kuma xaki tafi nace" kuyi abunda kuka ga danni ba ruwa na da harkan biki kuma ba inda xani" ya hakim yace" ke din bnxa sai dai in ba'a ga damana saki kiyi ba na kalle shi sama da kasa nace" dama kana son naje shine kke borin kunya dama ance tabarmar kunya da hauka ake nadeta yace" wa xanma borin kunya allah ya sauwake, fitar mun a daki nace" ko baka fada ba xan fitar ma a cikin kuturun dakin ka.......
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
65------------------70
**********************
A yau ne aka fara biki misalin karfe hudu da rabi aka gama shiryawa xuwa wurin lunching kowa yasha ankonsa milk and peach .wani rantsattsiyan less na saka maroon sai aka daura mun head milk yaimun kyau sosai mami tana shigowa ta feshe mun jikina da turare mai kamshi sannan ta bani takalmi milk da jaka milk.... Muna xuwa wurin muka ga a cike yake makil da jama'a kowa ya dau wanka na kece raini ni kaina me kawo muku rahoto nasha adona can na daga idona na hango sis dayyiba da hafsat matori sun sha ado sai xuba kamshi suke yi, ina cikin kallon su ne naga su fatyma lame, mssblue, roukayya, karima suna ta deban drinks suna sakawa a cikin jaka😂 saiga hafsat bawa da amira na hango sai yagan nama suke yi suna ci suna sawa a cikin jaka 😂😂.
Nandai aka fara gudanar da biki karfe 7 aka tashi inda kowa ya watse nima mai rubutu ina ta faman jan su karima akan suxo mu tafi amma ina wai sai sun gama kwashe nama ai kuwa naga amarya xata shiga mota da guduna na fito na biyota a baya domin daukan rohoto...... A yaune juma'aa da misalin karfe hudu na yamma bayan sallan la'asar aka daura auren ABDULHAKIM KABIR da UMMU AIMANA akan sadaki dubu 50 daurin auren daya samu halartar dumbin mutane daga kasashe daban daban.... Da daddare aka kaini gdan ya hakim inda nasha kukana nida yasira haka kowa ya watse aka barni ni kadai nan naji tsayuwar motoci tabbasa su ya hakim ne ina jinsa ya shigo da sallamar shi ko motsi banyi ba balle na amsa yace" aimana ki fito ku gaisa da abokaina suna falo nace''wai kai malam meye haka xaka takura mun saiga ya hakim yana marairacewa kamar bashiba saiya bani tausayi nace" kaje xanxo ko saika tasani a gabane kamar nai maka sata saiya wuce sumi-sumi kamar mara gaskia a xuciyan shi kuwa cewa yake "habawa yarinya lallabaki nake yi kawai kafin na sallami bakina daga nan xaki gano waye abdulhakim " wai wata irin darian mugunta. Yana fita na mike na tsaya gaban mirror na gyara fuskata nai waje suna xaune suna hira, nai sallama sannan na gaishe su suka amsa mun cikin mutunci na samu gu na xauna ban kuma magana ba sukai ta mana nasiha mai ratsa jiki sannan sukai sallama suka tafi bayan sun ajiyemin kayan siyan baki ina ganin sun fita na tashi na wuce dakina tare da sawa kofata key. Shikuwa ya hakim yana dawowa sai yaga na wuce saiya kwashe kayan ya kaisu kitchen ya ajiye su sannan ya wuce dakin shi.
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
75--------------80
*******************
Kallo ya bini dashi harna wuce daki sannan ya kunna tv yana kallo kiran waya ya shigo masa yana dubawa yaga zinat baby da sauri ya daga " hello babyna tace" hey durln ya kke? "" lafia lau babyna sai tace" baka kwanta bane na xata ma kana tare da amarya, yace" wata amarya kuma wacce tun daxun tayi kwanciyarta sai tayi darian farin ciki tace" maimakon kaje ka tayata kwanciyar shine kabarta ita kadai ta rungume pillow alhalin gaka sai yace" kema kinsan ba inda ya kamata na kwanta bane da ynxu ina can ina shan gara ko ba haka ba? Cikin kishin maganar daya yi tace" lallaima abdul wuyarka ta isa yanka shine kke fadamin haka sai yace oh! Srry babyna ashe fa kina kishina sai tace lallaima hakim haka ma xaka cemin ko nagode kaima kasan in akwai mai kishinka to nice baka san har ynxu ina nan ina kishin auren da kayi ba ka kyaleni.
Sai yace" haba babyna me yasa kike fadan haka kiyarda dani mana nine fa abdulhakim dinki ki saki ranki aure kamar munyi mun gama sai tace" to shikenan durln sai kaje ka kwanta kaida amaryan ka yace" kema kinsan ba inda xani dama kaman kece da ba saikin fada ba tace" hakane fa nima nasan babu wata mace da xata xo tace xata ture gwamnati na a cikin xuciar ka yace " hakane zinat dina shi yasa nake bala'in sonki tace''haba nawan dan allah kai wani abu akai nifa na kosa naxo gdanka muyi rayuwar aure mai kyau dan gaskia na gaji da rayuwar da muke ba aure a tsakaninmu yace " shknn babyna amma nafi son mu samu kaman 5months saina samu alhajina da maganan tace " to shknn saida safe.
Yaune na cika sati biyu da auren kaddaran da akai mun da ya hakim kasancewar yau asabar ce xaune yake yana karatun jarida naxo na tsaya nace" malam kana sane da cewa monday xan fara xuwa sch ko daga kai yayi ya kalleni sama da kasa yaci gaba da karatun sa nace malam magana fa nake maka kai banxa dani saiya dago kai a fusace yace" ke karki dameni bakin fadi maganarki ba kije sai nayi shawara akai nace" har saika yi wata shawara ko, kinga wuce ki bani wuri banson surutu kin wani tsayamin akai sai kace wani sa'an wasanki nace" oho nidai na fada maka xuwa ba fashi na juya ina rangajin masifa shi kanshi saida abun ya bashi daria amma haka ya gimtse ya cigaba da karatun shi.
Yau kasancewar monday ne da wuri na kammala aikina na shirya nai shigar wani material pink colour doguwar riga rigar mai A shape yai matukar amsata na yafa gyale akaina na fito falo na xauna nagansa yana brkfast daga idonsa yayi ya kallen yace ke kuma sai ina? Tambayar taxo mun wata iri na juya na kalle shi nace" ka manta inda xani yau sai yace ban sani ba amma ina so ki sanar dani a xuciata nace" lallai ma wannan mutumin akwai shida rainin wayo danma ya samu ana sanar dashi shine yake so yayi ma mutum iyayinsa daya saba" shirun da yaji nayi yace" tunda baki da niyyar amsawa saiki koma ciki abinki bakin ciki duk yabi ya dameni gashi nama rasa bakin magana nakai kusan 10 minute a tsaye lokacim shima ya kammala brkfast yasa kai xai fita nai karfin hali nace" ya hakim juyowa yayi yana mun kallon rainin daya saba yace" kingama tsayuwar na xata xaki samu kamar awa daya kina tsaye ya kuma cewa" yace baki shirya tafia ba tunda kikai irin wannan shigan kina ganin xan barki ki rika fita da shigar da kika ga dama ne sam baxa ki jamin zagi a gari ba da kuma wurin su mami saboda haka idan kina son karatu ki sake shawara karki ga ina miki haka ki xata kishin ki nakeyi a'a xanyi hakane danna kare mutuncina tunda mutane da dama sun san akwai aure tsakaninmu, daga yau na miki iyaka da irin wannan shigan kuma ki fita matukar kina cikin gdan nan a matsayin matata ke koma inane na fada miki xabi ya rage naki tunda yake maganar kallon sa kawai nake yi a xuciata nace" lallaima ya hakim yadda naci burin karatun nan yace sai dai na barshi ba xai yiwu ba " haka na koma na saka hijab nasan dama saboda shi yake magana mutum kenan sai allah, kana so naka ya shiryu amma kai kana lalata na wasu allah kyauta. Harna bude sabuwar mota na wanda abba ya bani xan shiga yace" daga nan bance ki wuce ko ina ba inba hala ba ranki xai baci ko kallonsa banyi ba balle ya samu amsar tambayan sa.
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
70------------------75
***********************
Washe gari tunda nai sallan asuba ban farka ba sai karfe 9 na shiga wanka nayi tare dayin brush na tsala kwalliya cikin wata red super wax dinkin yamin kyau sosai kitchen na nufa nomin samarwa kaina abun da xanci. A falo ma sameshi shingide jikin kujera three seater yana kallon tv ko kallonsa banyi ba balle ya samu arxikin gaisuwa kallo ya bini dashi yadda yaga ina rafia kaman baxan iya taka kasa ba. Kitchen din ya hadu sosai babu abinda babu a kayan abinci, ba wani abu mai wahala na dafa ba illa chips na soya da kwai na gasa bread na hada da ruwan lipton ina gama wa na diba na xuba a plate na wuce falona ina cikin yin brkfast dina har na kusa gamawa sai kawai ganin mutum nayi ya tsaya min akai kamar wani soja yace" ke baki da kunya ko, baki iya gaisuwa ba nai banxa dashi yace " dake fa nake magana kinyi bnxa dani nace" au ashe dani kake aiban sani ba.... Ke! Ya dakamin tsawa ba rashin kunya na tambayeki ba na kalleshi sama da kasa nace kaso rashin kunyar tunda kaxo inda nakr, sai yace" ina brkfast dina? Ni mai aikinka ce daxan dafa maka na kawo maka tabdi ba dai aimana ba idan ka matsu sai dai kaje ka diba da kanka ni ba abinda ya dameni yace" amma xan iya kawowa kici ko? Nace kwarai kuwa tunda aka ajeni cikin kadararren gdan nan dole a nemo a bani saiko yace, dama irin wannan gdan bai dace da irin kuba sai yai ficewar shi yana ta surutu, kitchen din ya nufa dole tunda ba yanda ya iya.
Tunda yake a rayuwarshi bai taba shiga kitchen ko saboda daukar cokali ba amma sai gashi wai shine ya shiga dauko abinci lallai dole ya dauki mataki. Yana gama abinda yake ya shirya sai dai jin tashin mota naji ina fitowa naje na tsabtace inda na taba a kitchen na dawo falo nai kwanciyata akan kujera ina karanta littafin " ko wani tsuntsu" na ummu nass nayi nisa cikin karatun sai naji bugun kofa da sauri naje na bude saiga yasira da wata kawarmu na makaranta faty nace" na xata baxa kuxo bane ai faty tace" kinsan ba'a xuwa gdan amare da wuri saboda kar a katsemusu hanxari nace" wani irin hanxari kefa yar iska ce nan dai muka yi ta hira har girkin rana suka mun favorite food din ya hakim suka yi sai wajen yamma suka mun sallama nan na cika su da kayan kwalliya bayan tafin sune na dawo nayi kunun aya yaji madara na ajiye a falo na shiga dan nayi sallah aiko ya hakim yana shigowa da yunwar shi ya nufi kitchen ai kuwa yaga abunda yafi so nan ya xubo a plate ya fito falo nan idonshi ya sauka akan kunun aya na ai kuwa ya dauka ya kafa bakin shi ya hau sha harda lumshe ido kamar ance na fito aiko na hangoshi ina karasawa na wafce a hanun shi nace" sannu mai bakin sha maiyasa inda kaje baka sa an maka ba tunfa safe kuke tare saini baiwa ko to baka isa ba dariyar mugunta yayi yace" kinsan ita din yar hutuce kuma nasan ina da mai aiki a gda shiasa ban damu ba haushi ya kamani nace an daiyi asara ba abinda aka iya sai dai bin matan bnxa ya isa haka karki kara furta mummumam kalma akan matar aurena na fada miki nace" oho dai inka isa gbe a daura muku aure yace karki damu indai zinat ne kamar na aureta ta shigo gdan nan nace" tobta shigo mana ai ba'a kaina xata xauna ba kasan sai kana son abu kke kishin sa niko ko a jikina ina ruwan kallo da gajia kama daukota ku riqa kwana tare karshen soyayya kenan nayi tsaki na wuce dakina.
Aisha 💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
80-----------------85
*********************
Ban dawo gdan ba sai karfe uku, falo na yada xango nai kwanciyata saboda ban jin yunwa nan barci yai awon gaba dani kiran sallahr la'asar ne ya farkar dani na mike nai hamdala ga ubangiji toilet na shiga na watsa ruwa hadi da dauro alwala na gabatar da sallah. In banda dole ba yanda xa'ai na shiga kitchen yadda na gajin nan amma sarkin masifan nan yana shigowa yaga table empty sai a sauko mun gonar masifa kwando kwando, aini aimana haka allah ya jarabeni da wannan rayuwar *HADIN ZUMUNCI*ko bata xumunci kana xaman xamanka a hadaka da alakakai kai magana ace kacika rashin kunya sai kace kaika kawo rashin kunya dunia ni wlh auran nan ba Karamin takura ni yayi ba kullum kana xaune a gda a jabe kaman kayan wanki in dana godema allah ma karatun dana ke xai rika ragemin bakim cikin danake ciki, ga dai gda har gda amma maigida babu halin kirki allah ya sauwake.
Tare suka shigo shida abbakar da wani abokin sa lawan ina xaune ina naxarin wani littafi sai jin sallamar shi nayi da kyar na amsa ya shaka soaai yace " sallamar ma saikin ga daman amsawa sai kace ba musulma ba ko kallan shi banyi ba hakanne ya kara sashi jin haushi, dama shi ya tsani yai magana a share shi muguwar tsawa ya daka mun saida hanjim cikina ya motsa nan hankalina ya dawo jikina ban nuna masa naji tsoro ba cikin gadara yake magana " ina abincin da kika dafa nayi baki ki xubo ki kawo musu raina ya kara baci nace" kaje mana ka dauka ko nan nake ajewa salon neman magana baka san inda kke xuwa ka dauka bane ko me yace" ke nake so ki kawo nace" nifa baxan fito ba saboda nima kuku bace sa'annan ba mai aiki aka kawo maka ba balle kace saina maka abinda ranka yake so, dan ma ka samu ina dafa maka shine kake wani daka mun tsawa sai kace wata yar cikinka cikin sauri yace " insha allah yar cikina bada tamun haka ba nace" oho dai kaika sani a tafi abani wuri kar a samun ciwon kai gda shiru daka dawo shikenan sai fada yace " to ki koreni mana ko kuma daga yau ki hanani shigowa cikin gdan idan naki ne, nace" oho yarage naka kuma.......... Haka ya hakura ya dauko musu da kanshi sai ganinsa suka yi niki-niki da tray abbakar yace "a'ah abokina ina madam din take na ganka haka ya hakim yace" ai ta riga tai bacci kasan taje sch ta gaji sannan ga aikin gda yayi haka ne dan kar lawan ya gane lawan yace" kasan mata akwai su da saurin bacci balle idan sukayi aiki sun gaji, kai allah yai ma mata albarka abbakar yace" amiin shiko ya hakim a xuciarsa yace wasu matan ba ,banda irinsu aimana wanda basu san darajan aure ba.
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
85----------------90
*********************
Yau kusan watana biyu kenan da aure amma babu abinda ya taba shiga tsakaninmu na dangantakar data shafi aure, sai dai kawai yai harkar gabansa nayi nawa.
Yau lahadi ce zaune nake shawar taxo mun ya kamata naje gdan mami tunda shi baida tunanin da zaice naje, gashi har mami tayi fushi dani ta hana kowa xuwa inda nake gashi ba halin kiran waya ya dauko min waya ya canxamin sabuwa da sabon layi haka nake xaune kaman kifin rijiya ban kira ba'a kirana.
Zaune yake a falo ya daura kafa daya akan daya waya ma yake amsawa yana hangoni ya hada rai karasowa nayi, yakai minti goma yana waya naga dai baida niyyar saurarata saina samu kujera na xauna naga ikon allah kana ganinsa kasan cikin nishadi yake kuma da mace yake wayar saboda gabadaya ya mayar da hankalinsa kan wayar, amma dan rashin mutunci irin nashi yana kallona harda kara kashe murya yana jefa mata kalaman soyayya masu xafi, xuciyata ko taxo mun iya wuya gashi dukda ba sonshi nake na amma na tsinci kaina da jin xafin abinda yaimin ni gashi ban isa nai haka ba.
Na gaji nace''ya hakim wannan wane irin wulakanci ne tun tuni naxo ina son nai maka magana kai bnxa dani saboda kana waya da wannan bnxan yarinyan nan kasan allah taraka kawai nakeyi duk abinda kakemin akan wannan karuwar ko....... Tsawa ya daka min yace" daga yau idan ina amsa waya karki kuma xuwa inda nake karuwar da kike magana akanta tafi mun ke tsaki yaja ya wuce.
Nan take kukan bakin ciki ya subuce min wannan wace irin rayuwace wai mijin auranka shine yake amsa wayan yan mata a gabanka kai wannan rayuwa da nake ciki ni aimana allah ne kadai xai fidda ni dakina na shiga kai tsaye toilet na wuce nayi wanka kwalliya nayi cikin less baqi mai ratsin golden kudi na dauka sannan na fito na shiga motata na fita kai tsaye wani super market na tsaya nayi wasu mami tsaraba ina shiga gdan da sallamata yasira na gani tace" aimana kece a gdannan nace" ke wlh bnxa ne idan bani bane to waye nan dai ta rakani na gaida su mami sannan muka wuce daki yasira tace "kin ganki kuwa ko dai mun samu baby ne nace " zaki fara iskancinki ko tace" gaskia yaya ya iya kiwo kiga yanda kikayi fresh gaskia cikin nan ya miki kyau nace" da kyau likita harkin gano ciki ne dani ni aimana allah sauwake nandai yasira tai ta tsokanata ta nace kedai kika sani karfe biyar nayi mami tace inxo na tafi haka suka rakoni wajen motata na shiga.
Aisha💞
[6:17PM, 21/12/2016] +234 701 725 1433: 🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
90---------------95
*********************
Ina isa cikin falon na fara jin shewa abunda yafi tayarmin da hankali shine muryan mace dana jiyo innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kalman dana keta fada kenan har na samu nutsuwa lallai ya hakim abun nashi ya kai ya kawo har cikin gda ni aimana naga ta kaina da lamarin ya hakim muna hada ido da ita saida jikinta yai sanyi shima ya lura da haka sai yace ki saki jikinki babyna meta isa ta miki cikin jin tsoro tace nidai gaskia dear mu tafi tunda ta dawo sao yai murmushi yace muje ko tunda kinji tsoronta niko bakin ciki ne ya hanani magana lallai ma ya hakim ni xai dauko ma karuwa ya kawo cikin gda lallai ya hakim ya cuceni ya gama xubar mun da mutunci a idon mutane amma ba komai wlh ni aimana saina koya wa ya hakim yanda xai soni nai wata daria na wuce dakina.
Washe gari da safe bani da lecture dana tashi na shiga kitchen na hada ma ya hakim brkfast sannan na koma daki nayi wanka na saka wani riga mai hanu daya da wani pencil jeans nayi parking gashina sannan na fesa turare mai suna "passport for luv" sannan na fito kai tsaye dakin ya hakim na wuce cikin tsoro ina turo kofan na ganshi yana kokarin saka neck tie da sauri naje nace" ya hakim ina kwana mamaki ne karara a fuskan shi ya bini da kallo tun daga sama har kasa gabadaya ya kasa dauke idonshi a kaina saida yaga ina kallon shi sannan ya hade rai yace" lafia kika shigo mun daki? Nan na karasa na karbi neck tie din hanun shi na fara daura mishi saiya samu kanshi da qin hanata nace" laifine danna shigo dakin mijina? Tsayawa kawai yayi yana kallona baice komai ba ya dauki briefcase dinshi ya fita raina ya matukar baci amma ban nuna ba nace " saika dawo allah kiyaye hanya bai kulani ba ya fice, nan na tsaya ina tunanin yanda xanyi na jawo hankalin ya hakim kaina yanda xai manta da zinat dana ga tunani baxai mun ba kawai saina hau gyara wa ya hakim daki na wanke mishi toilet sannan na fito na dau wayata na fara game.
Misalin karfe 1:30 bayan na idar da sallah na tashi na shiga kitchen na dafa shinkafa da miya bayan na gama na hada hadadden zobo na na saka a cikin jug sannan nasa a fridge kana na dauki abincin na jera a dining sannan na koma daki na yi wanka bayan na fito na tsala kwalliya ta cikin wata doguwar riga wanda tunda ga kasa tsagu ne har xuwa cinya sannan na gyara gashina banyi parking ba saina barshi a haka ya xubo a kafada na falo na koma na duba agogo saura minti goma ya hakim ya dawo tv na kunna ban jima da fara kallo ba naji tsayuwar motar shi ko minti uku baiyi ba naji ya bude kofar falon da sauri na tashi na karbi briefcase dinshi tare da bashi peack a kumatu tsayawa kawai yayi yana kallon ikon allah danaga kallon yayi yawa saina hure mishi ido nace" ya dai honey na banyi xaton xai mun magana ba kawai saiji nayi yace" ba komai kinyi kyau fari da ido nayi nace" tnxx swt luv kana nace ka xo muje kayi wanka sannan kaci abinci kama hanun ya hakim nayi xuwa daki shikuwa sai bina yake kaman wani akuya😂 har kofan toilet na raka shi bayan ya shiga toilet ne na nufi wordrobe dinshi na fito mishi da fari sol din jallabiya na feshe shi da turare kana na fito na koma falo sh kuwa ya hakim yana fitowa daga wanka yaga na ajiye mishi kaya murmushi kawai yayi a ranshi yace" aimana kenan ina xaune a falo ya fito kai tsaye dining ya nufa ina ganin haka nayi sauri na tashi na fara serving dinshi sannan na koma na xauna gara cin abincin yayi dadi ne yaji ya ratsa har cikin kunnen shi ina lura dashi a haka yaci abincin nan sosai sannan yace" aimana nace" na'am ya hakim yace" wai ko kina da aljanu ne nace" aljanu kuma yaya yace" to naga yau tunda safe u have been acting so strange i thought ko aljanune suka shafe ki daria nayi nace" ko kadan yaya dama so nake na rokeka yafiya akan duk irin abunda nake maka dan allah kayi hkr ka yafe mun ynxu ya kamata ace mun yada duka makaman mu mun rungumi kaddara ya kamata mu xauna lafia ko dan su mami suyi alfahari damu tunda na fara magana ido kawai ya hakim ya xuba mun....
To fa masu karatu kuna ganin Hakim zai yarda da shawaran Aimana? Duka amsoshin ku yana cikin page na gaba kuma na karshe ku biyoni dan jin amsoshin tambayar.
Aisha💞
🐾🐾HADIN ZUMUNCI🐾🐾
Written by Aysha Gana
95-----------------100
***********************
Nace " ya hakim baka ce komai ba numfashi ya hakim yaja sannan yace" aimana kenan asali ni dama ban tsaneki ba halinki ne na rashin kunya da tsiwa bana so shiasa kika ga ina miki haka amma tunda keda kanki kika nema mu shirya shknn allah ya qara hada kanmu nace" amin ya hakim nandai hira ya barke a tsakaninmu wanda mu kanmu abun mamaki yake bamu sai kace ba aimana da hakim ba wanda kullum cikin fada muke kaman kajii amma wai sai gamu a karkashin inuwa daya muna zaune harda tadi lallai kam sai ynxu muka ga wautan mu na rashin bin umarnin iyayen mu wanda suka ce mu xauna lafia amma mu kenan kullum cikin tashin hankali sai kace a filin yaqi lol......
Da daddare bayan na idar da sallahn isha'i na shiga kitchen na dafa mana indomie wanda yaji ingredients sannan na hada mana kunun aya na saka a fridge kana na koma daki na tsalo wanka na shafa mai me shegen kamshi sannan na ciro wata nyt gown red mai shegen kyau na saka na feshe jikina da turare har lokacin ya hakiim bai shigo ba falo na fito na xauna ko minti biyar banyi da xama ba sai gashi ya shigo da sallamar shi tsayawa yayi yana kallona tashi nayi na isa gabanshi na tsaya har ynxu ni yake kallo hure mishi ido nayi nace " ya hakim irin wannan kallo haka yace" gani nayi kin chanja mun aii kinyi kyau murmushi nayi nace " kaxo muje kayi wanka ga abinci yana jiranka daki ya shiga ni kuma na koma falo na xauna can sai gashi ya fito sai bula kamshi yake yi nan dai muka zauna nayi serving dinshi cin abincin yake yi amma gaba daya idonshi yana kaina wani irin kallo yake mun a haka muka kammala cin abincin yaya yace" aimana yau kam aii xaki tayani kwana ko? Sunkuyar da kaina kasa nayi nace"duk yanda kace tashi yayi ya kamo hanuna kai tsaya hanyar dakin shi ya nufa ni kuwa mai kawo muku rahoto na tsaya ina sude sauran indomie din da suka ci sai gani nayi sun nufi hanyar daki da gudu na tattaro littafina da biro na dan binsu dakin amma ko kafin na isa har sun rufe kofar su, asuba ta gari hakim and aimana.
Cikin satin nan wata irin shaquwa ce me karfi ta shiga tsakaninmu wani tattali yake nuna mun kullum inya dawo daga aiki muna tare komai tare muke yi rayuwa muke cikin farin ciki wanda muke fatan ya dore har karshen rayunmu.
*YA LABARIN ZINAT*?
Kullum cikin kiran hakim take yi a waya wataran ya dauka wataran yaqi dauka duk hankalin ta ya tashi ta rasa gane kan hakim a cikin yan kwanakin nan ranan kamma da ta qira shi ta gwammace dama bata kirashi ba domin kuwa aimana ce ta dauka lokacin ya shiga wanka xinat tace" hello aimanaa tace " ke karaman yar bariki karki kuskura ki qara kiran mijina domin kuwa yafi karfin ki ke bakya ma jin kunya ace ke kike bibiyar namiji bashi ba ya kamata ki shiga makarantar ta nutsu kije ki nemi miji kiyi aure domin kuwa hakim mijin mace daya ne idan kuma kika kuskura kika yi gigin shigowa gdana to wlh gdana kaman wuta yake bnxa kawai shashasha sannan ta kashe wayar zinar kuwa ranan yini tayi tana kuka.
Mu kuwa Soyayya muke sha nida ya hakim kullum muna tare munje gdan mami taji dadin ganinmu a haka ta qara mana nasiha anan ma take fada mana an saka auren yasira da ya samir nayi murna sosai...... Shirye shiryen bikin yasira muke yi wanda a satin ne kuma na tashi da wani irin xaxxabi ga yawan barci nan dai ya hakim ya daukeni sai asibiti gwajin farko likita yace ina da ciki murna a gun ya hakim ba'a cewa komai nan da nan ya yada a cikin dangi kowa sai murna yake yi.
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah a ynxu haka cikina ya shiga wata tara ranan muna xaume da ya hakim tsifa yake mun nan naji ciwo ya hakim yana lura dani nan dai ya kwashe ni sai asibiti nan aka karbeni aka yi dakin haihuwa dani ya hakim sai sintiri yake ya kasa xaume ya kasa tsaye su mami ya qira a waya basu jima ba suka iso nan dai suka tsaya likita ne ya fito fuskar shi dauke da fara'a yace "alhmdllh ta sauka lafia an samu twina mace dana miji alhmdllh shine abunda su mami suke fada nan dai aka tarkata mi sai gdan mami, ranan suna yara suka ci suna Musharraf da musharrifa, zaune nake ina bawa musha nono ya hakim ya shigo yace" maman twins murguda mishi baki nayi yace to " sarauniyan marasa kunya" nace " Allah na gode ma ashe aimana tana da matsayi tunda har an nada ni sarauniyan marasa kunya" daria duka mukayi saboda mun tuna baya nan dai yaya ya karbi musharrifa yace " aimana my Heart luvs u like a candle. It burns and beat only to shower luv for you, just like a candle sacrifices itself to give light in darkness the only difference is that my heart will always luv u till eternity" nace" ya hakim u are my best frnd when i need one, my man when i'm in your arms, my guide when i need help . I feel very lucky to have you as my life partner i luv u. Haka dai sukayi ta exchanging luv words masu dadi har saida suka ji yaran sun fara kuka tukun na.......Anan nima na tattara komatsai na Allah ya kara dankon soyayya Aimana da Hakim.
Anan na kawo karshen littafin *HADIN ZUMUNCI*kuskuren dana yi Allah ya yafe min saimun hadu a sabon littafina mai suna *HAKKIN UWA*....
Aisha💞
07017251433
Luv u oll😍😘
adsense 2 here