adsense here
HADUWANA DA FARIDA
Karar shigowan sakon Whatsapp a wayata ne ya
farkar dani daga baccin da ya fara daukata a kan
keken dinkina. Kamar ba zan duba wayar ba,
saboda idan da sabo na saba. kulli yaumin
sakunan WhatsApp din basa rabo da zarya a
wayata na mutane dabam- dabam a sassan
kasar nan masu bibiyar labaraina a facebook......
Idan na ce biye musu zanyi, ba barina zasu yi
neman abin sawa a bakina ba, shi yasa a duk
lokacin da nake a shagon dinkin bana kula
sakunan. Amma ga mamakina yau sai naji ina
bukatar duba wayar in ga sakon waye ya shigo.
Kamar kullum yau ma bakuwar lamba naci karo
da ita da gajeren sakonta na sallama. Kamar ba
zan amsa ba sai dai na daure na mayar da
martanin sallamar. Wanda wanna shine farkon
sanadin jefa kaina cikin wani mummunar hadari
mtws dana sani keyace... Sakon lambar ya ci
gaba da shigowa Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ko?
Eh! Da wa nake magana? Na bada amsa tare da
yin tawa tambayar. Farida, daya daga cikin fans
dinka a Dandalin facebook, aka bani amsa, naga
wani post da kayi kwanakin baya, naji dadin post
din shi yasa nace bari nayi adding dinka nan in
nuna maka jin dadina. Allah Sarki! Wane post
kenan? Na sake tambayarta. Post din Hasashe
game da matsalolin maza, gaskiya naji dadin post
din sosai, ta bani amsa. Na gode, kuma da yardar
Allah zan ci gaba da yin wasu post din wadanda
suka fi wannan dadi. Allah ko? Gaskia ko yusuf
idan ka ci gaba da nishandantar dani zan ji dadi
sosai, saboda zaka sa in manta da bakin cikin da
ke damuwata. Ke kuwa wane bakin ciki ne
wannan? Na jefa mata tambaya cikin zakuwa da
son jin damuwarta. Murmushi tayi gami da cewa
kar ka damu idan lokaci yayi zaka sani. Ba zan
iya tantance dogon lokacin da na dauka ina hira
da baiwar Allar nan ba, abinda kawai na sani a
ranar bata barni nayi dinki ba har lokacin barina
shagon yayi. Tunda daga wannan lokacin
shakuwa mai karfi ta kullu tsakaninmu da farida,
duk yanda zanyi in samo labarin da zan tura
mata wanda zai sakata nishadi sai nayi. Wani
lokacin idan labaran suka kakare min sai naji
kamar na koyi halin hankakar da wasu ke yi a
duniyar fesbuk akan labaran mutane, sai kuma in
tuna da yanda zuciyata ke tafasa a duk lokacin da
naga wani ya satar min labari ya mayar da shi na
sa, dole sai in fasa. Ranar da duk kuwa ban yi
postin labari ba ko na tura mata a WhatsApp ba
ranar zan sha kiran wayarta, a duk lokacin da ta
kirani na kan samu karyar da nayi mata. A irin
haka ne wata rana labaran suka kakare min, duk
wata kafa da nake tunanin samun labari ta toshe
na samu kusan kwana uku ba wani labari, sai ga
kiran mutuniyar, bayan mun gaisa, ta fara aikinta
wato tambayata a kan na daina nishadantar da
ita, rasa karyar da zan yi mata nayi saboda ban
son fada mata cewa labaran ne babu, karya nayi
mata cewa bani da data ne a wayata Suscribtion
dina ya kare. Har ga Allah na yi mata wannan
karyar ne saboda bana tunani mace zata iya tura
wa namiji kati babu wata alaka ta jini a
tsakaninsu, amma ga mamakina bayan mun
gama waya da ita kawai sai ga sakonta na tes ya
shigo, ina dubawa lambobin kati na gani kasansu
kuma tayi rubutu kamar haka:- yusuf ga kati nan
kayi maleji dashi 1500 ne ba yawa. Ina gama
karantawa kiranta nayi, tana dagawa nace Haba!
Farida ya zaki min haka? Gaskiyi ki bar katinki
bana so, ina da kudi zan saya da kaina. Nayi
juyin duniyar nan akan ta barshi ta kiya, da taga
na matsa sai cemin tayi sai dai idan ban so kar
in loda in bai wa wani don ita ta riga ta bani
kuma na raina kyautarta ne shi yasa na ce ba na
so, kuma ta gode. Da naga ta hasala dole na
dawo bata hakuri, da kyar ta sauko, sannan nayi
mata godiya na kashe wayata. Ai kuwa tun daga
ranar kati ya daina katsewa a wayata. Idan har
bani da kudi a wayar a kalla ka sameni da naira
dubu ciki, ba kuma ni nake saya da kaina ba ita
ce da take turomin. DANA SANI KEYACE. Wannan
dalilin jefa kaina cikin wahala na yanka kazan
wahala ma kaina kumana fige naci karoda wani
babban dutsen daya fasan zuciya asanadin
farida.... Wannan fa..?ADUWANA DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 2
HADUWANA DA FARIDA part 2
Yau ma kamar kullum bayan mun gama gaisawa
da farida a WhatsApp sai take cewa dani. In
tambayeka mana. Ina jinki. kana da aure?. Na
shafe kusan minti uku ina nazarin tambayar tata,
ko zan gano dalilinta nayi min wannan tambayar
amma ban gano ba, daga karshe dai na bata
amsa tare da jefa mata tawa tambayar No i'm
single, but why asking? ( A'a bani da aure, amma
kuma me yasa kika tambayeni?) shiru ne ya ratsa
tambayar tawa, har na tsawon minti goma, da
dai naga shirun yayi yawa sai na sake tura mata
wani sakon Hello! Farida kina kusa kuwa? Eh! Ta
amsa min, Na rasa yanda zan baka amsar
tambayarka ne. Saboda me? Na sake tambayarta
Ina jin nauyin fitar maganar ne daga bakina,
saboda ban san yanda zaka dauketa ba Tace
dani. Feel free farida Just express your mind (kar
ki ji komai kawai ki fadi abinda ke ranki). Ba zan
boye maka komai ba... wutar soyayyarka ta dade
tana ruruwa a zuciyata, har ta kai ga yi wa
zuciyata mummunar illah, irin illar da in har baka
bani daukin gaggawa ba, ko shakka babu
tarwatsewa zata yi. Jin maganar tata nayi a wani
bambarakwai, na jini duk wani wani iri, saboda
wannan shi ne karo na farko a rayuwata da wata
'ya mace ta taba furta min kalmar SO, hasalima
ni ko soyayya bana yi. Bakina da 'yan mata
gaisawar mutumci. Shiru taga yayi yawa, ta
kauda shirun da Hello! Ko maganata ta bata
maka rai ne? In na bata maka rai kayi hakuri,
nayi ta kokarin danne damuwata a zuciyata, na
kasa ne shi yasa na fito fili na fada maka...... Ko
daya farida baki batamin rai ba, hasalima
farantamin rai kika yi, ai ko da wasa mutum yace
yana sonka ya gama maka komai, ballanta
kyakkyawa kamarki, kuma Babbar yarinya. In
takaice muku zance. A ranar muka kulla
yarjejeniyar Soyayya, muka aminta da zukatan
Juna. ***** Tun daga ranar da muka kulla
soyayya da farida, abin ya sauya salo, saboda a
koda yaushe muna makale da juna, idan bama
Chatting to waya muke. RASHIN SANI YAFI DARE
DUHU... WATA SAFIYA..... Kamar kullum yau ma
Chatting muke da Masoyiyar tawa sai musayar
kalaman soyayya muke a tsakaninmu ta
WhatsApp, sai nake cewa da ita. My dear kin san
wani abu kuwa? No! my one sai ka fada.
Idanuwa na sun kagauta suyi tozali da
kyakkyawar surar nan taki, kunnuwana cike suke
da daukin jin sautin muryarki kai tsaye ba wani
shamaki a tsakaninmu, hancina ya kagauta da ya
shanshani kamshim turaren jikin abar kaunata,
yaushe ne mafarkin nan nawa zai zama gaskiya?
Ka yi hakuri my one!, idan baka manta ba a ranar
da muka fara haduwa na fada maka ina da wata
damuwa har ka bukaci in fada maka damuwar
nace ka bari in lokaci yayi zaka sani, yanzu
lokacin da ya kamata in sanar da kai wannan
damuwar. Hakika iyayena sun zabamin miji
wanda ni kuma ba abinda na tsana a duniya
kamarsa, shi yasa a duk lokacin da na tunashi
sai inji gaba daya duniyar tayimin kunci, ba mai
yayemin wannan kunci sai kai da labaranka,
fahimtar da suka cewa na tsaneshi shi yasa suka
sakamin tsatstsauran mataki na hani hulda da
kowane irin namiji, ka kuwa ga yanzu haduwarmu
da kai akwai matsala, amma na fara shawo kan
iyayen nawa sun fara gano illar da ke tattare da
auren dolen da suke so su yimin, sun fara yin
sanyi, saboda haka ka kara hakuri da na ida
shawo kansu, suka janye waccan maganar, to a
lokacin sai ka gaji da ganina. My dear kenan,
dama masoyi yana gajiya da ganin masoyiyarsa
ne? Ina rokon Allah Ya nuna mana lokacin da
matsalarmu zata yaye. Ameen cewarta. Na gama
sakankancewa a zuciyata cewa nayi gamo da
katar, kuma hakana yana gab da cimma ruwa,
wai ashe da sauran rina a kaba. Kwana biyu da
yin wannan maganar, ina shago bisa kekena ina
dinki, wayata ta fara kururuwar neman agajina,
ina dauko wayar kiran wata bakuwar lamba na
gani. Nayi dana sanin daga kiran nan, Wallahi da
na san za'a yimin wannan kiran da banyi fatan
mallakar waya a rayuwata ba. WANNAN SHI NE
BABBAN KUSKUREN DA NA TABA TAFKAWA A
RAYUWATA. KU DAKACENI IN GAMA ZUBAR DA
HAWAYEN NADAMA.A DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 3
HADUWANA DA FARIDA part 3
Posted by Bashir Sani Fesan on 20 Jan 2017 - 22:57
Daga wayar nayi tare da yin sallama, aka amsa
daga daya bangaren. Samari kai ne saurayin
farida ko? Aka tambayeni. Kafin amsa maka
tambayarka, zan so sanin matsayinka ga faridar.
Mahaifinta ne ni. Aka bani amsa sai bayan ya
bani amsa, nayi nadamar yi masa tambayar, kayi
Hakuri Abba ban san kai ne ba shi yasa, Ni ne
masoyinta na bashi hakuri tare da amsa masa
tambayarsa. Munyi magana da ita akan ta fitar
da wanda zata aura tace kai ne zabinta shine na
karbi lambarka a wajenta. Haka ne, na amsa
masa ina so ne in ganka muyi magana saboda
haka ka sameni gida gobe da sassafe. To! Abba
sai dai ban san gidan ba. Ok bari zan turoma da
adireshin gidan yanzu. Cike da farin ciki muka yi
sallama da shi. Na dade ina jinjina al'amarin a
cikin raina bayan na gama karanta adireshin
gidan, wai dama ashe da diyar kwamandan soja
nake soyayya ban sani ba. An ya ban kira ruwa
ba kuwa? Na dade ina shawara da zuciyata, daya
sashen zuciyata na cewa kar ka je Saif daya
kuma na cewa kaje me zai faru idan kaje, don
mahaifinta na soja ai ba zai dakeka baka yi masa
laifin komai ba, daga karshe dai na yanke
shawarar zanje komai ta fanjama fanjam. Wannan
shi ne ganganci mafi girma da na taba aikatawa
a rayuwata. Uhm waiyo rashin sani** Tun a
lokacin nayi ta kokarin kiran layin farida amma
yaki shiga, ina son fada mata wannan albishir ne
duk da na san ta rigani sani, a WhatsApp ma
sako uku ina tura mata ba reply. Daga karshe dai
nace a raina wata kila caji ne babu a wayarta.
WASHE GARI DA SAFE Gabana na faduwa na
cusa kan babur dina cikin Barikin soja wannan
shine karo na farko da na taba shiga barikin
Sojoji na jaji dake KADUNA dukda yana garinmu
ne. bayan tulin tambayoyin da na sha daga sojoji
barkatai, aka sadani da gidan Kwamandan. Bayan
na samawar wa babur dina matsugunni a kofar
gidan, sai naje ga kofar na kwankwansa, wani
mataccen Soja ya leko, ke ce bakon oga? Ya
tambayeni da gurbatattar Hausarsa. Eh ni ne, na
bashi amsa. Kai tsaye ya budemin kofa na shigo
ya nunamin wata kujerar roba ya ce in zauna,
zamana ke da wuya sai ga wasu samudawan
sojoji guda biyu wadanda tunda nake a duniya
ban taba gani sojoji kakkarfa kamar su ba, sai ji
nayi sun rufeni da duka da wasu kulake, suka yi
ta dukana har sai da suka sumar dani. Sanyin
ruwan da aka zubamin shine yayi sanadiyar
farfadowata daga suman da nayi wanda ba zan
iya tantance iya adadin lokacin da na dauka a
some ba, har yanzu dai Samudawan nan ne tsaye
bisa kaina. Shegiya kwarton oga yau zaki ci
ubanki, tashi kiyi sallen kwado suka umarceni da
gurbatattar Hausarsu. Naga ta kaina ba irin
nau'in azabar da basu ganamin ba a ranar, har
sai da nayi dana sanin zuwana duniya, basu
kyaleni ba sai da suka tabbatar bani da sauran
mamora a tare dani sannan suka kwasheni kamar
kayan wanki suka zube a wani matsakaicin daki
wanda nake zaton na maigadi ne. Sai a lokacin
nadama ta fara zomin, na tuna yanda mukayi da
abokina AYS, ba yanda bai yi dani akan in kyale
yarinyar nan ba, amma naki daga karshe ma da
naga ya takuramin sai cewa nayi dashi yana
bakin ciki ne dani don yaga na tsinci dami a kala.
ko jiya sai da muka sha fama dashi yana kokarin
hanani zuwa ni kuma nace sai na je sai yanzu na
gano illar rashin bin shawara a lokacin fa ruwa ya
kare wa dan kada bai gama wanka ba. Ina cikin
wannan sake-saken najk an bude gambun dakin,
kallo daya nayi masa na fahimci ko shi waye
dogo ne mai faffadan kirji yana sanye da suit
baka akwai sanko a kansa yana da tsawon fuska,
shekarunsa zasu doshi sittin Kwamanda ne. Kayi
kuskure dan samari neman matar soja, kuma a
sojojin ma matar kwamanda. Duk da yanayin da
nake ciki na azaba hakan bai hanani dago fuska
na kalleshi cikin kaduwa ba ina mai jaddada
girman maganar da ya fada a raina. WATA
SABUWA... WAI DA MATAR AURE NAKE SOYAYYA
ASHE. DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 4
HADUWANA DA FARIDA part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 20 Jan 2017 - 22:59
Kai tsaye kwamanda ya nemi kujera yazauna. ci
gaba da maganarsa, ban yi tunanin zaka shigo
hannuna da wuri haka ba, koda yake kuma ba
abin mamaki ba ne domin kuwa Hausawa sun ce
kuda wurin kwadayi ake mutuwa, to kai a kudan
ma ka zarta kowa a kwadayi. Na rasa gano me
ke damunku 'ya'yan talakawan nan ba zaku iya
tsayawa a matsayinku ba ku nemi 'ya'yan
talakawa tsaranku, sai kullum ku ne like da
kyawawan mata, matan da aka yi don masu
hannu da shuni in ban da wauta irin taku
talakawae zai kai ku wurin. Ba sai na tambayeka
ba dan samari ga mamaki nan karara a fuskarka,
na san kana mamaki ne jin na ce maka farida
matata ce, a farko kuma na ce maka 'yata ce ban
maka karya ba dan samari a tarin shekaru na
haifi farida, sai dai a zamantakewa ta aure
matata ce, na san ba yanda za'a yi ta sanar da
kai tana da aure ahi yasa nima na ce da kai ni ne
mahaifinta saboda na san zaka fi saurin shigowa
hannu, yanayin wahalar da nake ciki bai hanani
gano dogon mutumin dake tsaye gabana mai
wakiltar sunan kwamanda,,,, Allah yayi masa
baiwar tarin surutu kamar waziri Aku ba. Ba tare
da la'akari da me zan ce ba ya sake dorawa,
babu abinda nake so a duniyar nan kamar matata
farida, idan kuma akwai abinda na tsana a
duniyar nan to abinda zai rabani da ita ne. gashi
kai kana kokarin ka kwaceta daga gareni. Don
girman Allah kayi hakuri, Wallahi ban san matarka
ba ce, hasalima ban san tana da aure ba Wallahi
da ko kusa ba zan nemeta ba. Na tari
numfashinsa ina masa magiya. Murmushi
Mugunta yayi min, sannan ya sake ci gaba da
maganarsa kwantar da hankalinka ai na san baka
san matata ba ce da ba zaka yi gangancin zuwa
gidan nan ba domin rijiya ba wurin wasar makaho
ba ne. Sai dai rashin sa'a daya kayi, ba na iya
yafewa duk wanda ya rabi farida da sunan so, to
kai gashi har soyayyar kuke yi. Lokaci daya kuma
sai ya turbune fuska kamar wanda aka aikowa da
sakon mutuwar faridar, sannan ya kira
Samudawan nan da suka jibgeni dazu. Ku
mikaminshi wurin M.P (Military Police) a yi masa
horo mai tsanani har sai na waiwayeshi.
Hankalina in yayi dubu a lokacin sai da ya tashi
jin Kwamanda ya bada umarnin a kai ni wurin
masu ladaftar da sojoji idan suka yi laifi wato
Military Police, ihu na shiga yi ina masa magiya a
kan yayi hakuri amma kamar baya jina. Wasa
farin girki dukan da na sha a baya ba ko duka ba
ne yanzu zan fara shan azaba Cakumata suka yi
kamar tsumma suka yi waje, muna tafe ina sake-
sake a raina ko shakka babu da za'a yi nadin
sarkin wawaye to babu wanda ya dace a nada sai
ni. Yaya daga haduwa da yarinya WhatsApp
muna soyayya ban taba ganinta a zahiri ba haka
ita ma bata taba ganina a zahiri ba sai dai a
hoto, kawai wani ya kirani a waya wai mahaifinta
ne yana son ganina sai kawai in tashi in tafi, in
ma har da gaske ne ai ita ya kamata ta sanar
dani sakon na mahaifinta ba wai shi ya kirani ba,
a gefe daya kuma ina tunanin irin azabar da zan
sha a hannun M.P. maganar wani abokina da ya
taba zuwa tirenin din soja ta fadomin wai ko soja
yayi laifi yana tsoron M.P su kamashi soboda
azabar da zai sha a hannunsu. soja kenan, to ina
ga ni farar hula, a farar hular ma zan fi dacewa
da a kirani da mace mai tsohon ciki wata tara, a
kan a kirani namiji saboda ragwancina. Da
wadannan sake-saken muka isa suka hannuntani
a hannunsu suka kama gabansu. Tashin hankali
ba'a sa maka rana kwanana biyu cur a hannun
M.P suna ganamim azaba har sai da na rika
tunanin anya ba mutuwa ne nayi ba, a lahira ne
nake shan wannan azabar, saboda kwata- kwata
azabar bata yi kama da ta matambayan duniya
ba. A washe garin kwana na uku kwamanda ya
bada umarni a sakeni bayan ya gargadeni a kan
ko mai sunan farida na kara kulawa na san
sauran.. Satina uku cur a gida ina jinyar raunukan
da M.P suka yimin ko kofar gida bana iya fita.
ina kwance ina jinya na toshe duk wata kafa da
nake ganin zan iya tuna farida nayi blocking dinta
a facebook da WhatsApp, na goge lambobin
wayarta da duk wasu hotuna da ta turomin nata.
ina ganin mun yi bankwana kenan har abada,
ashe wai da sauran rina a kaba . Bayan kamar
wata daya da gama jinyata, ina zaune shago bisa
keken dinkina na dukufa sai dinki nake wata
madaidaiciyar mota launin ruwan siminti ta yada
zango bakin kofar shagon dinkin, wani abokina ya
taba fadamin sunan motar wai ko Continue
Discussion ne sunanta. Irinta ne mijin kanwana
hauwa.u jidda yake shiga Gabana ba karamar
faduwa yayi ba lokacin da naga wata matashiyar
budurwa ta fito daga motar kai tsaye ta kunno
kai cikin shagon doguwa ce sai dai ba sosai ba
tana da matsakaiciyar fuska mai dan tsawo
dauke da dara-daran idanu da matsakaicin baki
tana da saje a fuskarta launin fatarta kuwa
wankan tarwada ce, shekarunta zasu iya kaiwa
ashirin da uku zuwa da biyar, kallo daya nayi
mata na shaidata kasancewar na saba ganin
hotunanta. Farida ce. me kuma ta zo yi a
shagona? tambayar da nayi wa kaina
kenan...xakasanine..? Inka qara komawa chan..!♥
Home / HADUWANA DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 5
HADUWANA DA FARIDA part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 20 Jan 2017 - 23:01
Kamshin turaren da ya gauraye madaidacin
shagon shi ya kara tabbatarmin da shigowarta
ciki, gabana sai tsananta bugawa yake kara yi,
tunanin masifar da zan sake shiga ya sani
tsurewa. Sallamar da tayi min ce ta sa ba shiri
na daidaita kaina nayi kokarin boye fargabar da
ke kokarin bayyana a fuskata. Sannunka Tela,
tace dani. Yauwa sannunki, na amsa mata. Dinki
nake so kayimin, ta gabatarmin da bukatarta Ga
shi kuwa kin zo a makare. Na fada cikin gatse.
Murmushi tayi sannan tace wane irin makare sai
kace wacce ta kawo dinki daren Sallah kuma tace
yanzu take son a dinke mata. Ba wannan
makarar kika yi ba Hajiya, ina nufin kin zo a
lokacin da na daina yi wa mata dinki, na fadi
haka ne saboda tsayuwarta cikin shagon ta fara
gundirata kuma a koda yaushe gani nake
Kwamanda zai iya fadowa cikin shagon. Maganar
da na fada maimakon tayi sanadiyar barinta
shagon, ga mamakina sai gani nayi ta nemi
kujera ta zauna. Dan rainin hankali shi ne ka
wani shareni kamar baka ganeni ba, to wurinka
na zo magana nake so muyi, ta fada tana kokarin
kakaro murmushi. A ina kuma kika san wannan
sunan nawa? Na tambayeta Wane suna kake
magana? Ta tambayeni ita ma. Dan rainin hankali
mana. Na fada mata Dariya tayi har sai da
kyawawan hakoranta suka bayyana. Au! Dama
sunanka ne kenan? Kai dai ko yaushe baka rabo
da abin dariya. Na gode amma zai fi kyau kiyimin
bayanin ko ke wace ce? Na fada ina kokarin rufe
babin wasar da take kokarin budewa. Na san ka
san ko ni wace ce, amma tunda ka nuna baka
sani ba zan kara sanar da kai, farida ce. Kona ce
faridarka ce Ta sanar dani. Wace farida kenan?
Na sake tambayarta. Haba my one kar ka mun
haka please, yanzu ashe duk soyayyar da kake
nunamin a waya yaudara ce ba sona kake yi ba?
Ta fada cikin murya mai rauni. Look! Farida ba fa
zan yarda ki sake jefani a wani bala'i ba, ba ni
kadai ne saurayi a garin nan ba, zai fi kyau ki je
ki nemi wani ki kara yaudararsa ni wacce kika
yimin ta isa haka. Ka tsaya ka fahimceni yusuf ba
wata yaudara tsakaninmu. Ta fada tana kokarin
tabbatarmin da abinda ta fada har cikin zuciyarta
ne. Dago fuskata nayi na kalli fuskarta ga
mamakina hawaye na gani suna sartu a kan
kyawawan kumatunta. Hawayen sun karayar dani
amma sai na dake. Farida kenan, abinda baki
fahimta ba shine an dade ana ruwa kasa na
shanyewa. Kalamanki na yaudara ba zasu kara
tasiri a gareni ba. Yanzu ke ko kunya ba zaki ji
ba da aure a kanki ki rika bibiyar samari kina
jaza musu fitina? Ka daure ka saurareni yusuf
Wallahi gaskiya zan fada maka. Tace dani Ina
jinki. Tasowa tayi daga inda take zaune tazo dab
da telata, kusancin dake tsakaninmu har sai da
na rika jin bugun numfashinta. Ka kalli kwayar
idona ka fadamin idan ka ga yaudara a ciki. Ta
bukaceni. Idan kin manta akwai bukatar na
tunatar dake cewa ke matar aure ce fa, saboda
haka kawai ki fadamin abinda kike son fadamin
ina saurarenki. Kayi hakuri da masifar da na
jefaka, da kuma boye makan da nayi cewa ni
matar aure ce, ban yi haka don in cutar da kai ba,
nayi ne saboda na san idan har na sanar da kai
ni matar aure ce ba zaka kulani ba. Kuma ban
san mijina ya dakeka ba sai daga baya, da ba
yanda za'a yi na bari hakan ta faru, na san babu
yanda za'a ka yarda da zancena idan har ban
sanar da kai ko ni wace ce ba. Ina jinki.... Nace
da ita saboda kalaman nata na yaudara sun fara
isata. Kwamanda bai maka karya ba ni matarsa
ce, amma ba na sonsa ba kuma da son raina na
aureshi ba, iyayena ne suka auramin shi saboda
la'akari da mukaminsa da kuma dukiyar da yake
da ita, basu yi la'akari da cewar bana sonsa ba,
kuma me zai je ya dawo bayan auren. Me yasa
bakya sonsa? Na katseta da tambayata. Baka
bukatar dogon bayani yusuf, ba sai na fada ba kai
kanka kasan kyakkyawa kamata bata dace da
tsoho mai tarin shekaru irin na Kwamanda ba. Na
tsinci kaina a cikin kunci bayan tarewata a gidan
Kwamanda, ba wai ya gaza wajen bani jin dadin
duniya ba ne, ko daya, kawai dai na tsaneshi ne,
wannan ne yasa ni fadawa a social network ko
zan hadu da kawaye masu debemin kewa.
Lokacin da na fara facebook shafukan bayar da
dariya da saka nishadi nayi ta nema ina shigarsu,
a garin lalubena ne na ci karo da kai wata kawa
nane taban labarin indai labari nakeso na nemi
Magana Jari nasha labari, Kuncin da nake fama
da shi ya ragu, saboda labaran da nake
karantawa a wadannan shafukan, sai dai duk
cikin shafukan ba kamar naka domin kai gwanine.
Kai DAN'ZAKI NE wane yaro Lokacin da na fara
cin karo da lambarka ta WhatsApp ba karamin
farin ciki nayi ba saboda naga hanya mafi sauki
da zan rika samun labaranka. Yawan karanta
labaranka da nake yi, sai naji ka fara birgeni,
sannu a hankali sai naji na kamu da sonka. Ba
karamar barazana na fuskanta ba Sabod a na san
ba abu ne mai yiwuwa ba nayi soyayya da kai
alhalin da aure a kaina,UWANA DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 6
HADUWANA DA FARIDA part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 20 Jan 2017 - 23:03
Farida taci gabada cewa, Ba karamar barazana
na fuskanta ba Saboda na san ba abu ne mai
yiwuwa ba nayi soyayya da kai alhalin da aure a
kaina, Wannan ya sa na shiga tunanin mafita,
daga baya na yanke shawarar na boye maka ina
da aure. Idan har ba yaudarata kike yi ba
maganar da kika fada gaskiya ne ya akayi
Kwamanda ya san muna tare? Akasi aka samu
nayi rashin lafiya ne mai tsanani wacce ta kaini
ga kwanciya asibiti, bana raba daya biyu
WhatsApp dina ya shiga yai min bincike anan
yaga Chat dina da kai, kuma har kaje gidan ka
dawo ban san an yi ba ina Asibiti. To ya aka yi
kika sani? Bayan kin ce ba ki gidan. Shi ne ya
sanar dani bayan naji sauki. To wane mataki ya
dauka a kanki? Hmm! Yusuf kenan, idan akwai
abinda Kwamanda ya tsana a rayuwarsa to bacin
raina ne, shi yasa duk abinda nayi bayamin fada
bare har ya dau wani mataki a kaina. To yanzu
me kika zo yi wurina? Kuma me kike so in yi
maki? Hakuri na zo baka, a kan abinda yai maka,
sannan kuma naga kayi blocking dina a facebook
da WhatsApp shi ne na so jin dalilin hakan?
Zancen Hakuri nayi, zancen Blocking kuma
saboda ba zai yiwu in ci gaba da soyyaya da
matar aure ba, a matan auren ma kuma matar
soja. Sojan ma kwamanda Ba soyayya zamu ci
gaba da yi ba yusuf, kawai gaisawa zamu rika yi
kuma ka ci gaba da turomin Labarai. Ta fada
tana yi min wani kallo, wanda ni a ganina na
yaudara ne. Ba zai yiwu ba farida, zai fi kyau ki
kama gabanki kar ki sake jefani a wata musibar.
Ka gasgatani yusuf nayi maka Alkawarin babu
abinda zai sameka wancan karon ma akasi aka
samu. Tace dani Na fada maki fa ba zai yiwu ba,
ki sani ko wannan hirar da muke yanzu zunubi ne
muke kwasa saboda haka kawai ki kyaleni kar ki
sani fadawa cikin fushin ubangiji. Ba irin magiyar
da bata yi ba, amma naki amincewa, dole ta
hakura. Da zata tafi kudi ta dauko daga jakarta
wadanda ba xan iya cewa ga adadinsu ba, amma
a kiyasin da nayi kudade ne masu tarin yawa ta
ajiye a kan telata, Na meye? Na tambayeta. Baka
nayi, na san ba zaka rasa 'yan hidindimu a
gabanka ba. Tace dani tana kokarin fita. Kuma
sai na ce dake bani da kudin da zan yi hidindimun
nawa ko? Kar ki mayar dani wata haja mana,
wacce zaki rika saye da kudi a duk lokacin da
kika ga dama. Na fada a fusace. Kayi hakuri ba
nufi na ba kenan, gani nayi ba komai ba ne don
na baka kyauta, amma tunda kayi min wata
fassara, shi kenan ba zan kara ba. Zai fi kyau
hakan, nace da ita ina kokarin mika mata kudin.
Na dauka ta hakura kamar yanda ta nuna ashe
tana kasa tana dabo, gwara ma a ce na amince
da bukatarta a kan abinda ya biyo baya HAKAN
SHINE BABBAN KUSKURENA DAYAFI NABAYA..
Hankalina ba karamar kwanciya yayi ba ganin
cewa na yadda kwallon manguro zan huta da
kuda. Bayan kamar kwana biyar da zuwan farida
shagon da nake dinki. Da sassafe ina kwance
dakina dake kofar gidanmu na ji kanina Hafizu
yana kwankwasamin kofa, koda na bude yake
shaidamin wai nayi bakuwa tana nan kofar gida
tana jira. Kaina ba karamar daurewa yayi ba jin
cewa wata ta zo nemana har gida domin kuwa
wannan shi ne karo na farko da mace ta taba
zuwa nemana a gida. Duk matan da nake yi wa
dinki sai dai su zo nemana a shago kuma ko
basu sameni ba Aminu wanda muke dinki tare zai
kirani a waya in zo. Cike da mamaki na fito daga
dakin na nufi kofar gidanmu, tun daga nesa na
hango mota tsugunne a kofar gidan, bana raba
daya biyu motar farida'ce gabana ya bada rass!
Kamar in juya sai dai na daure na isa. Ta bude
kofar sashen mai tuki ta zuro kafafunta waje
sanye cikin jan material rike da waya kirar Sony
Ericson Xperia tana chating. Farida ce. Murmushi
ta jefeni da shi yayin da ni kuma na daure fuska
tare da jeho mata tambaya. Me kika zo yi a
gidanmu? Wurinka na zo yusuf ta fada tana
kokarin mikewa tsaye. Haba! Farida yanzu kina
ganin ya dace a matsayinki na matar aure ki rika
zuwa wajena, kuma baki tunanin zuwanki
gidanmu zai iya haifarmin da matsala wajen
iyayena? kuma kin san mijinki yai min tsakani da
ke. Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda
gaba daya na gama tsinkewa da al'amarinta.ADUWANA DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 7
HADUWANA DA FARIDA part 7
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Jan 2017 - 17:18
Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda gaba
daya na gama tsinkewa da al'amarinta. Laifinka
ne Darling saboda na fada maka ba zan iya
rayuwa ba kai ba, na bukaci ka bari mu ci gaba
da waya kuma mu dinga communicating a social
network kamar da amma ka ki, na yi iya kokarina
in ga cewar na fitar da kai cikin raina abu ya
faskara. Ta fada tana yi min fari da idanunta.
Amma kuma ai ya kamata ki san cewa cikin
fushin ubangiji ne kike son jefani, ta yaya zan
amince da wannan bukatar taki, kuma idan ma
ban ji tsoron Allah ba ai ko don gudun azabar
mijinki dole in kaurace maki. Na ce da ita Calm
down mana yusuf in dai matsalar mijina ce nayi
maka alkawarin ba zai koma tabamin kai ba. Tayi
saurin katseni.... Wasa-wasa farida ta maida
unguwarmu kamar gidansu kusan kullum sai ta
zo wajena in bata zo gidanmu ba to zata sameni
shago kuma kullum ta zo zancen daya ne, ba irin
magiyar da ban yi mata ba akan ta daina zuwa
wajena, sai cewa tayi idan ina so ta daina zuwa
inda nake to in bari mu ci gaba da hulda a social
network kamar yanda muke a da, tun abin baya
damuna har ya fara damuna ga mutanen
unguwarmu sun fara tsegumina,gidanmu kuwa
mahaifiyata kullum sai tayi min fada akan yawan
zuwan da farida ke yi nemana tun inai mata
karyar dinki ne ke kawota har ta daina yarda da
karyar. Da na fahimci ba zata daina zuwa ba tilas
na amince da bukatar.... BABBAN GANGANCINA
KENAN DANAYI ARAYUWA. Amincewar da nayi
wa farida muka ci gaba da hulda a social network
da kuma ta waya kamar da, ya sa ta daina zuwa
unguwarmu. Ko da yaushe sai dai mu rika
haduwa a facebook, ko WhatsApp, ko kuma ta
kirani a waya. Haka Al'amarin ya ci gaba da
kasancewa har zuwa wasu 'yan kwanaki... Yau
ma kamar kullum zaune nake a kan keken dinkina,
ina dinki. Kamar daga sama nagansu, sun fado
cikin shagon, basu tsaya cewa dani komai ba
cakumoni kawai suka yi suka yi waje dani suka yi
jifa dani cikin motarsu kirar Hilux, kamar fitar
kibiya daga kwari, haka suka figi motar suka yi
gaba dani. Yaran Kwamanda ne (Sojoji) Tun cikin
motar suka fara nukurkusata, koda muka isa
barikin tuni na fice daga hayyacina. Koda
hankalina ya dawo jikina, na ganni ne a wani daki
da zan iya kira da kurkuku mafi kunci a duniya.
Ba sai na tsaya wani bincike ba na san
Kwamanda ne ya sa aka kamoni saboda kunnen
uwar shegu da nayi da gargadinsa. Nadama ce ta
zomin irin wacce ban taba yinta a rayuwata ba
tunanin wahalar da na sha kwanakin baya a
hannunsa ta ya zomin, lokaci daya kuma tsanar
farida ta shigeni lokacin da na tuna da alkawarin
da ta yi min a farkon zuwanta shagon dinkina.
Tabbas farida annoba ce a rayuwata... Karar bude
dakin ce ta katseni daga tunanin da nake yi lokaci
daya tsoro ya dabaibayeni na tsura wa kofar
idanu, don ganin wa zai shigo. Kwamanda ne ya
shigo. Sanye yake cikin kaki (Uniform) ba kamar
wancan karon ba, kallo daya nayi wa fuskarsa na
fahimci ransa yayi mutukar baci. Kunnen kashi ne
da kai ko yaro? Ya jefamin tambaya. Bai bani
damar amsa masa tambayarsa ba kai tsaye ya ci
gaba da magana. Ko da yake laifina ne da na
baka damar da zaka bijirewa umarnina, da na
batar da kai tun a wancan lokacin da tuni nayi
maganin taurin kan nan naka. Amma ko yanzu
ban makara ba, ina da damar yin hakan. Ban
ankara ba sai ganinsa nayi rike da bindiga yana
kokarin saita kokon kaina. Saboda firgici ban san
lokacin da fitsari ya kubucemin a wando ba,..nan
danan nahau addu'an daduk tafadomin
abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji
saukan bindigar akaina amma shiruUWANA DA FARIDA novels / HADUWANA DA FARIDA part 8 the end
HADUWANA DA FARIDA part 8 the end
Posted by Bashir Sani Fesan on 21 Jan 2017 - 17:21
nan danan nahau addu'an daduk tafadomin
abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji
saukan bindigar akaina amma shiru karshen
labarin na rufe idanuna ina jiran saukar harsashe
a kokonkaina. Na share akalla mintina uku ina
jiran saukar harsashi a kokon kaina. Shirun da na
ji ce ta sani bude idanuna. Ganinsa nayi ya ajiye
bindigar ya samu wuri ya zauna sai faman huci
yake kamar wata kasa. Ko me ya hanashi harbe
kokon kan nawa? Kamar yanda yayi ikirari.
Kamar ya san amsar da nake bukata, sai kawai
ya fara amsamin. Kaci sa'a, ko kuma in ce Allah
Ya yi lokacin mutuwar bai yi ba, shi yasa naji
tausayinka. Wannan shi ne karo na farko da na
saita bindigata akan wani mutun, da nufin
harbinsa, kuma ban harbeshi ba. Saboda haka
yanzu zan maka Adalci daya. Wancan karon na yi
maka hukunci da laifin GANGANCI, alhalin baka yi
GANGANCIN ba. TSAUTSAYI ne yasa ka yin laifin,
yanzu kuma kayi min GANGANCI, hukuncin
ganganci ne ya kamata in zartar a kanka, amma
ba zan yi hakan ba, zan yi maka rangwame, in
yima hukunci da wancan laifinka na TSAUTSAYI.
Zan karya hannuwan nan naka biyu, wadanda
kake amfani da su kana chatin da matan mutane.
Sojoji biyu ya kira daga waje ya basu umurnin
karya hannuwa duka biyun sannan ya ficewarsa.
Ina ji, ina gani suka rika kokowa da hunnuwana
kamar masu kokowa da icce har sai da suka
kakkaryani, saboda zafin ciwo ban san lokacin da
na some ba. Lokacin da na farka, cikin shagon
dinkina na ganni mutane sun kewayeni, bayan sun
tambayeni inda ke min ciwo nayi musu bayani
wuraren da na karye. Suka kwasheni sai wurin
mai dori aka doramin hannuwan nawa sannan
suka dawo dani gida domin jinya.. yadda kuka
Nayi zaton tunda kwamanda yasa anmun hukunci
na karshe shikenan na huta. Ashe akwai abunda
yafi hukuncin kwamanda zafi. Kaikanka me karatu
dakasha mamakin abunda nagani. Zuciyana ta
kone hanjin cikina yakada domin abunda kunnuwa
suke jiyemun nayi kukan nadama awannar ranar.
Nakwana da mamakin halin mata. Ashe dama
haka mace take da sharri? Nida abokaina
'yan,uwana munsha mamakin abunda muka gani.
Barida nabaku labarin kawai GAYADDA ABUN
YAKASANCE Washe gari ina kwance cikin
gidanmu, abokina waziri aku ya zo dubina, muna
hira. Gefena kuma 'yar autar dakinmu ne.
Hauwa'u jidda. Tayimun kirki sosai na kayan
cikin saniya. Zaune take tana zubar da hawaye
domin tausayin datake gwadawa akaina
kasancewar itane kaf dakinmu allah ya hada
jinana danata. Samada sauran 'yan.uwana sai ga
sakon farida ya shigo wayata na ce da waziri aku
ya karantamin sakon kasancewar bani da
hannuwan rike wayar bare ina karantashi da
kaina. Ga sakon kamar haka.. "Gareki Wawiyar
zuciya mai cike da kwadayi, ka bani mamaki
Hussaini domin kuwa ban zaci zan yi nasara a
wannan wasan da sauki haka ba. Na zaci wasan
zai yimin wahala ganin cewar da gwani ne zan yi
wasar, sai gashi na sami akasin hakan, ashe
hangen kitse ne nake yi wa rogo, a yanda nake
ganin rubuce-rubucenka na dauka kai gwani ne a
wannan wasan ashe wai baka ma san yanda a ke
buga wasan ba. Na san zaka bukaci sanin dalilin
buga wasan, to zahirin gaskia lokacin da na fara
karo da labaranka, haka kawai na ji na tsaneka,
na dade ina nazarin dalilin da yasa na tsaneka,
sai daga baya na fahimci ba komai ne ya sa ni
tsanarka ba sai ganin cewa kai ba wani marubuci
ba, amma ka dage, wai kai sai kayi rubutu kuma
wani abin karin haushi duk rubuce-rubucenka su
kan kare ne a wance ta yaudareka, wance ta ci
amanarka, wance kuma tayi maka wulakanci,
zancen duk daya ne. Shi yasa na ga ya kamata
idan duk wadancan da kake fada sharri ne kake
musu, to ni bari in yi maka na gaskiya sai kayi
mai dalili Da nayi niyyar kyaleka a dukan farko da
mijina yai maka sai kuma naga ai baka doku ba
tunda gashi baka daina abinda kake yi a da ba,
don haka sai na ga wancan wasan first half ne
muka buga ya kamata a ce mun buga second
half. Yanzu kam wasa ya kare tunda nayi nasara.
Kar ka manta da ni domin kuwa nima ba zan
manta da kai ba. Hawayene ke zuba idon domin
jin wannan mummunar sakon na farida nasha
mamaki nayi zaton sone na gaskiya ashe cutane
dama Tabbas wannan mata ta kai Azzaluma nq
fada a raina Bata yi kuskure ba da ta kira
zuciyata da wawiyar zuciya kuma mai kwadayi,
domin kuwa su ne suka bata damar yin nasara a
wannan basajar da tayi min wacce ta kira da
wasa, sai dai tayi kuskure da ta ce ban san
yanda a ke buga wasan ba, domin kuwa ni
malamin wannan wasar ne kawai dai idanuna sun
rufe saboda kwadayi da kuma wauta, shi yasa na
kasa gano bakin zareb wasar, ga shi garin
kwadayin nawa na rasa hannuwan da nake
rubutun da su, kuma nake dinki ina neman abin
sakawa a bakin salati. Karyata ta kare.... Shi
yasa da na samu sauki naga ya kamata in zo wa
duniyar facebook da wannan labari ko 'yan uwana
samari zasu tsira daga tarkon Basajar matan
social network. . KARSHE WANNAN SHINE
KARSHEN LABARIN
adsense 2 here
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more
Mutane uku ne a duniya
1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}