Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 12 April 2017

UWA KOH YA complete

adsense here

Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 *💟💟UWA KO 'YA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU💚* *Edited by:ANEELURV😍* ```Dedicated to my lovely MOM😍``` *Page 1▶2* "Feenerh come on kitashi ko zakiyi late", "Ohhh mommy ki dan barni mana iyi barci koda na minti daya ne", "Feenerh rana fa ya fito,kuma kinsan halin daddyki", "Mom ,the sun is out and I know that but am not a plant you know,I don't need to photosynthesise kuma kibar dad kinsan shima baya son Ina wahalat din kaina", "Whatever feenerh , nidai kitashi", "Okay mom,natashi". Feenerh da mamanta kenan , kullum ana jayayya da safe. Feenerh dai asalin sunnanta safiya zubair ne. Ita kadai ce a wurin Mr and Mrs zubair ,babanta attajiri ne kuma hamshakin business man kuma baya wasa da aikinsa. Mamanta kuma is soft hearted . kuma tanada kirki sosai and she loves her daughter very much. Feenerh dai is a very beautiful girl,ebony in complexion kuma tanada ilimi sosai saboda iyayenta basa wasa da karatunta. Ta kammala karatunta na primary dana secondary a lafia. Anan suke zama DA iyayenta a G.R.A. Sannan she came out with an excellent results, presently tana federal university Wanda ke lafia in her first year. ~back to reality~ "Feenerh nace ki tashi". Feenerh ta tashi da kyar ta shiga bathroom, tayi brush sannan tayi wanka tafara shirin zuwa skul while mommynta ta wuce tana cewa"haka za'ayi skul din feenerh ,da wannan sleeping sickness din naki". Bayan feenerh tagama shirin sai tafito yin breakfast, dama already maid dinsu ta soya mata omelette da toasted bread,sannan ta hada mata tea. Bayan tagama breakfast, tafito direbar ta ya kaita skul,tana shiga Auditorium friend dinta Kadija taxo ta hugging dinta tana cewa"my dear friend, kamar kullum kin yi late", "Khadija kibari kawai ,yawan baccina na soratar dani", "Anyway ,yanzu mth111 zai shigo sai musamu waje mu zauna", "Ohhhh my God ,khadija kinsan yanda na hating mth", "Nasani ,amma kinsan baki dawani zabi,zakiyi shi na two semester", "Toh, Allah ya bamu sa'a", "Ameen". "Yauwa khadija, after this lecture kizo muje ki rakani gurin technologist Musa", "Hmmmm, feenerh kenan kedai da wannan Musa nan naki", "Yes,kinsan ina sonsa sosai,amma na tabbata shi baya sona", "Toh in banda ke feenerh , waze iya resisting epitome of beauty kamar ki", "Musa", Khadija tamata dariya sannan tace "toh feenerh ki fita harkarsa mama, tunda he is not interested in you", " kema kinsan bazan iya ba,because he is the first man that ever catches my heart,bazan iya barinsa ba". Suna kan maganan ne,lecturer dinsu yashigo sannan suka closing chapter din. *Tnx for reading....* *FAREEDAH😘* *💟💟UWA KO 'YA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU* *Edited by:ANEELURV😍* Dedicated to my lovely mom😍 *Pg 3 ▶ 4* Bayan lecture,feenerh da khadija suka wuce zuwa physics lab wajen Musa. Sun isa kofar office ďinsa khadija tace, "gaskiya feenerh an an zan tsaya saboda kinsan banason in shiga private conversation ďinku", "Kai khadija ,meye kuma so private akan abinda zan faďa masa bayan wanda kika sani", "Nidai baran shiga ba", "Toh ,shikenan". Feenerh ta shiga da sallama, "Assalamu alaikum" "Wa alaikum sallam", Musa ya amsa. "Good morning sir", "Morning feenerh,yakike", "Am fine sir". "Okay, meya kawoki", "Bakomai ,dama nace barin shigo ne mugaisa", "Nagode kwarai feenerh,gaskiya kina 'ko'karin zuwa gaisuwa", "Bakomai sir". "Yawwa feenerh inada magana da'ke, I hope dai baki da lectures yanzu", "A'a babu sai 'karfe biyu (2pm)", "Okay toh ki zauna". Feenerh ta zauna,zuciyar ta na bugu saboda tana ganin kamar daga 'karshe yafara gano cewa tana sonsa. "Feenerh , nasan 'kila bazaki yarda da abinda zan faďi maki ba", "Ba damuwa sir ,kafaďi inaji" ******************************** Musa yayi murmushi , sai ya kara fito da dimples dinsa. Atakaice dai Musa kyakyawa ne,fari kuma yanada tsawo. Yatashi a gida ne mai yawa,yanada kanne maza da Mata kuma babansa yana 'ko'korin yaga sunyi karatu. Musa ya kammala karatunsa na primary a lafia sai ya tafi Keffi yayi secondary sannan ya karanta physics a state university dake Keffi, yanzu kuma yana aiki a laboratory a federal university dake lafia. Amma tunda ya hadu da feenerh shine gaba daya hankalinsa ya karkato ya koma kanta, duk lokacin da tayi murmushi sai ta tuno mashi da wata special girl data ta'ba kasancewa a rayuwarshi,Kumar tana burgeshi sosai shiyasa ya deciding yau zai faďa Mata abinda ke ranshi,gaskiya yanason ya faďa mata komai. "Feenerh ,tunda na hadu dake my mind have not been at rest,saboda duk lokacin da kikazo gaidani inason in fada maki amma Ina tunanin bazaki amince dani ba kuma inason mu kulla kyakyawan zumunci a tsakanin mu". **************************** Feenerh bata yarda da abinda Musa ke faďi , yanxu dama Musa na sharing thesame feelings da it's,lallai dama tasani da ta faďi masa gaskiya tuntuni,da bata wahalar da kanta ba. Wow ,yau kam tana cikin farin cikin da baya misaltuwa. "Sir yanzu dagaske ,Kai kake faďin duka wannan", "Eh nine feenerh ,kuma ki daina kirana sir,sunana Musa", "Toh sir,A'a Musa". Musa yayi murmushi sannan yace,"feenerh kenan, yanzu kiban numbanki saboda mu dinga communicating", "Badamuwa ,zanbaka number na ,da Facebook username dina,da kuma handle dina a Instagram", "Duka ni kaďai feenerh". Tayi murmushi sannan tace"eh ,murna nake sosai saboda mafarkina yafara zamanto gaskiya". *tnx for reading* *FAREEDAH😍* *💟💟UWA KO 'YA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom* Pg 5▶6 "Mafarki kuma feenerh , wani mafarki", "Hmmmm,it's a long story amma gaskiya itace na daďe ina sonka amma bansan taya zan bullo maka ba ,saboda gani nake kamar abin kunya ne ace nina fara cema Ina sonka". "A'a feenerh ba abun kunya bane in namace tace ma namiji tanason shi,kuma ba abun kaskantawa bane", "Toh nagode Musa ,naji daďin waýenan kalmomin da ka faďi min" Musa yayi murmushi sannan yace "bakomai you deserve everything", "Toh ni zan koma saboda kawata na jira na awaje ,ga wannan paper na rubuta information din aciki", Feenerh ta sallame shi sannan tafito tana mai murmushi sosai. "I hope dai komai yatafi daidai feenerh ,wannan irin murmushi fa" kawarta khadija tace, "Kibari kawai khadija,Ina cikin wani farin ciki ne yanzu", "Ko zan iya sanin dalilin", "Musa yace yanasona,yace yanasona"! Tafaďi tana Salle. "Dagaske feenerh", "Wallahi dagaske nake khadija ,dana shiga ne ya ambato min wannan maganan", "Lallai kinci sa'a feenerh ,yanzu dai burinkin ya cika ,Musa yazama naki", "Hakane kawata ,ki tayani murna", "Toh amma khadija ,bakya ganin Musa yamiki babba ,kefa you are just 18(shekara goma sha takwas)", "Babba fa kika ce khadija, nawa ne shekarun Musa ,shekarunsa fa 34 kuma ni haka nagani in a so", "Toh ai da yayi auren wuri daya haifi irinki", "Kinga bansan wannan wasan khadija,toh sai me in har ya isa ya haifeni ,nidai haka nakeson sa". "Toh kiyi hakuri kawata, kuma gaskiya Musa baiyi fuskar shekarunsa ba", "Yawwa haka nakeson ji kawata ,ki dinga supporting dina", "Ako wani lokaci kawata" khadija ta amsata. Sun koma Auditorium domin lectures ďin CHM111 , feenerh na bala'in son wannan course ďin kuma tana bashi dukkan hankalinta domin sauraron lectures ďin da kyau. Karfe uku suka kare lectures na yay,feenerh da khadija suka wuce masallaci don yin sallar azahar ,bayan sun idar feenerh ta kira direbar ta ya zo ya ďauketa. Suna jiran zuwan direbar sai ga Kira a wayan feenerh ,ta duba sai taga new number, "Hello", "Assalamu alaikum", "Wa alaikum salam,dawa nake magana" "Baki gane muryar ba", Feenerh ta ďanyi tunani sannan tace " Musa ?", Yace,"eh nine", "OK,bangane muryar da sauri ba,kayi hakuri", "Ba damuwa feenerh ,dama nace ne barin in Kira saboda ki saving numban a waýanki". "Toh shikenan ,nagode sosai", "A'a nine da godiya saboda kin aminta dani batare da wani damuwa ba", "Hakan tafaru ne saboda yadda kakeji nima haka nakeji a zuciyata", "Ban taba zaton zaki amshi soyayyata ba feenerh ,nagode sosai", "Ba damuwa", "Toh shikenan ,sai anjima zan kira in kin koma gida", "Toh bye". Feenerh ta kashe wayar,khadija dake gefenta tace, "Hmmm,feenerh kenan soyayya daďi". *Tnx for reading* *FAREEDAH😍* Follow for more of my writeup...www.f-novels.blogspot.co.ke *💟💟UWA KO 'YA💟💟* *written by:* *FAREEDAH* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *page 7▶8* Soyayyar Musa da feenerh yayi nisa saboda yanzu students ďaďďaya ne basu san dasu ba . Suna chatting ta WhatsApp sannan kuma suna magana ta waya sosai, yau ma feenerh ba lectures saboda haka ta tafi office ďin Musa Don suyi hira. "Feenerh ,ya karatu I hope dai komai na tafiya daidai"Musa ya tambayeta, "Eh ,everything is fine (wato komai lafiya) kawai na missing ďinka ne nace bari inzo in ganka", "Hmmm feenerh nima na missing ďinki , aiki ne yamana yawa kinsan kun kusa fara jarabawa", "Wallahi fa, har ka tunomin da exams dinmu", "Amma fa ki tabbata kina karatu sosai saboda ki passing exams ďinki , kinga tukkuna kike first year dinki kuma yakamata ace result ďin first year yayi kyau sosai", "Eh Ina karatu sosai, sometimes nida khadija muna zuwa library karatu inbamu da lectures", "Toh ki kokarta ,saboda niman ilmi nada kyau mussaman na ýa mace", Musa ya faďi a raunane. Feenerh ta noticing kamar ya tuno wani abune saboda taga fuskarsa ya canza, "Wani abu ne yafaru?", "A'a bakomai , kidai kula da karatunki Sosa", "Toh nagode da nasihar da kamin", Feenerh suka cigaba da hirar su har lokacin next lectures ďinsu yayi sai ta sallameshi ta wuce class. Tana shiga lecture room ,ta hadu da khadija a zaune tana karate. "Kai kawata,karatun test ďin kenan ba wasa", "Lallai feenerh ,wato kin mayar da test ďin wasa KO, kinsan yanzu zamu rubuta koh", feenerh tayi murmushi ,tasani amma dayake chm111 me, ba damuwa saboda best course ďinta ne kuma ta riga da tayi karatu a gida. "Ba damuwa kawata ,zamu kokarta Allah kuma yaba mu Sa'a", "Ameen kawata"khadija ta amsata. Sun rubuta test ďin cikin kwanciyar hankali kuma test ďin yamusu simple sosai don haka suka gama da wuri suka fita don zuwa ýin sallah. Kamar kullum , feenerh ta Kira direbar ta yazo ya ďaukesu ,daganan ta sauke khadija a gidansu sannan ta karaso gida. "Mommy na dawo" feenerh ta tashiga gida tana kirarin mamanta , "Naam dear, sannu da dawowa ya makarantar", "Lafiya kalau mommy", "Yawwa feenerh inada magana dake ,so in kinci abinci , kin watsa ruwa ki sameni a da'kina", "Toh shikenan mommy". Feenerh ta tafi ta ajiye jaka sannan tafito zuwa dinning table Don taci abinci sannan ta watsa ruwa a jiki tayi sallar la'asar sai ta nufi dakin mamanta. "Assalamu alaikum ", "Wa alaikum salam" mamanta ta ansa, "Mommy sannu da hutawa". "Yawwa ýata ", "Mommy wani magana zakimin ďazun DA kikace inzo dakinki", Mommy tayi shiru sannan tace "ýata tunda kikasamu wannan admission ďin bamu zauna munyi magana ba, I have some words dana keso in miki so listen carefully", "Ina jinki mommy", " feenerh kinga ni dai ban kammala karatuna ba akamin aure , I was just 15 (wato shekara goma sha biyar) babana ya hadani da babanki Wanda shi yaron amininsa ne,alokacin gani suke kamar in har mace tayi karatu toh raini ne ga mijinta ko Kuma bai kamata ba,bansan daďin karatu ba,kuma bansan yanda university life take ba ,koda mukayi aure da babanki bai bari na kammala karatuna ba cewa yayi its too late amma still hakan baisa naji haushinsa ba saima Kara respecting ďinsa da nayi", Feenerh tayi ajiyar numfashi sannan tace "mommy ,duk Wanda ya ganki in besani ba bezai taba cewa baki kammala karatu ba, saboda you are more educated than other educated women", "Hakane feenerh, shiyasa nakeson mu tattauna dake akan wannan al'amari mai muhimmaci, jiya nida daddynki munyi magana akan makarantarki kuma we have reach a conclusion, muna sonki fito da miji nan da shekara daya!!!!". *tnx for reading....* *FAREEDAH©* *💟💟UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 9▶10* *(bayan sati daya)* Feenerh na zaune a mosque gefe daya hankalinta gaba daya baya jikinta. Khadija tashigo tayi sallama amma feenerh bataji ba,ta ta'bata amma still bataji ba saida ta ta'bata da karfi sannan tace "keh!!!”. Feenerh a razane ta juyo tana waige waige saitaga khadija a gefen ta sannan ta saukar da numfashinta , "Haba khadija ,ji yanda kika soratar dani", "Lallai feenerh hankalinki ya dauku, irin wannan sai a sace ki ma bara ki sani ba", "Haba dai ,sata kuma" feenerh tace, "Wai shin meke damunki kwana biyu ne feenerh , ko a lectures room dazun ina miki magana amma duk hankalinki baya wurin,kodai akwai wata matsala ne kawata", "A'a babu" feenerh ta faďi da sauri. Koda khadija ta ďago cewa feenerh karya take faďi mata sai tace"yanzu feenerh har kawancen namu ya kai haka, ban ta'ba zaton akwai wani abu da zaki iya boyemin ba ,lallai so feenerh yanzu na zama stranger ko, thanks nina wuce", khadija tayi yunkurin tashi sai feenerh ta kamo hannunta, "kiyi hakuri kawata,wallahi banyi niyar bata miki rai ba am just confused shiyasa", "I know feenerh ,shiyasa nace ki faďa min ,kinsan cewa a problem shared is a problem solved", "Hakane khadija ,zauna kusa dani zan faďa miki komai", "Toh ina sauraronki" khadija tace. "Wato khadija ,wani magana ne mukayi da mommy last week shi yake dauke min hankali", "Wani magana?,i hope dai bata gano kina soyayya da musa bane", "A'a khadija ba wannan ba", "Toh menene kawata", "Khadija , mommy da daddy sun yanke hukuncin min aure nan da shekara biyu kuma sunce in fito da miji nan da shekara daya", Khadija tayi salati sannan tace , "What feenerh ,this early", "Wallahi fa khadija koni kaina am surprised ,kuma ni gaskiya i dont know what to do saboda banason ganin bacin ran iyayena", "Hmmmm lallai feenerh wannan babban magana ne,toh yanzu ya batun makarantarki, bara su bari ki karasa ba", "That's the aim dayasa sukace nan da shekara biyu ,saboda alokacin ina 400lv zanyi auren,kinga aina kammala ,sauran kuma a gidan mijina", "Tohhhh, yanzu ya za'ayi", "Shine nima bansani ba ,khadija am so confused", "Kinsan me kawata , ki kwantar da hankalinki basunce nan da shekara daya ba", "Eh" feenerh tace, "Toh kinga ai nan da shekara daya soyayyarku da musa tayi nisa kuma zaki iya kai shi gida a matsayin mijin dazaki aura", Feenerh tayi shiru na ďan wani lokaci sannan tace , "Kuma hakane fa kawata ,what you said is true , hakan za'ayi nagode sosai khadija", "Bakomai feenerh, what are friends for", "Hakane , a friend in need is a friend indeed". Suna kan maganar ne ,course mate dinsu ruqayya tashigo mosque tayi masu sallama ,bayan sun amsata sai tace,"dama kuna nan nake ta nemanku", "Meya faru" feenerh ta tambayeta, "First semester results ne yafito sannan kuma an kori wasu malamai saboda wani laifi da sukayi , an placing information ďin a notice board dake lab", Nan da nan zuciyar feenerh ya tashi ,ita bama ta results take ba malamai da akace an kora daga aiki ne yake damunta. "Khadija tashi muje mu duba", "Amma feenerh da wuri haka ,kodai kina doubting result dinki ne", "A'a so nake inga wasu malamai aka kora", Khadija tayi dariya sannan tace ,"lallai feenerh soyayya daďi", Feenerh tayi murmushi sannan ta tashi tafito tasa takalmin tana jiran khadija tafito. Suna zuwa notice board ďin ,bata ko duba result ba,idon ta na kan sunnayen lecturers ďin,"inna lillahi wa ina ilaihi raji'un"!!! ta faďi hawaye nafitowa a idanunta. *Tnx for reading* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH* *Edited by :ANEELURV😍* *dedicated to my lovely mom😍* *pg 11▶12* "Meya faru feenerh , an koreshi ne", Feenerh ta kasa magana sai hawaye, "Ki ansani mana feenerh" khadija tace, "A'a khadija, ankara masa matsayi ne", "Toh meyasa kike kuka", "Bakya gani ne khadija , anbashi scholarship zuwa New York ya karasa karatunsa na masters acan", Khadija tasaki numfashi sannan tace "Lallai feenerh , wallahi har kin tsoratani , sawa nayi ko an koreshi ,toh mena kuka ai wannan abin murna ce", "A'a khadija ,musa zai tafi ya barni har na tsawon shekara ďaya , wallahi bazan iya rayuwa bashi kusa ba", "Hmmm feenerh har soyayyar taku tayi karfi haka ,toh kisani dole zakiyi hakuri saboda yaje ya kare karatunsa kema kiyi naki karatun", "Anya khadija zan iya kuwa", "Ya zamanto miki dole , nidai bari in duba result ďina in kin gama kukan kya duba naki". Feenerh ta rasa ya zatayi ,musa zai tafi ya barta yanzu ma kenan zuciyarta na mata zugi toh ya in ya tafi yaza tayi, ya Allah kasamin sanyi a zuciyata. Khadija ce ta katse mata tunaninta, "Keh munyi passing duka wallahi", Feenerh tayi shiru tana kallonta sannan tace mata,"toh ai dama nasani", "Taya kika sani", "Saboda nina rubuta exams ďin", "It's not funny feenerh", "Toh naji ,yanzu muje kirakani office din musa", "Dama nasani ai ,abinda ke zuciyarki kenan". Sun kai office ďin sai khadija ta tsaya a waje as usual, feenerh naso ta bude kofar kenan sai taji a kulle yake, ta juyo tace ma khadija a kulle yake, "Maybe ya fita ne, ki kirashi a waya mana", "Yeah hakane, bari in trying numbanshi" . Feenerh takira numban yayi ringing ba amsaba ,tasake kira har 5 missed call ba amsa ba , "Khadija ,no answer", "Ki bar damuwa feenerh ,everything will be alright kinji", "Toh muje". Sun koma mosque suka zauna amma sam hankalin feenerh ba a kwance yake ba ,har lokacin sallah yayi. Bayan sun idar da sallah kenan sai wayarta yafara ringing ,tana dubawa sai taga musa da sauri ta dauka, "Hello dear", "Hello *D* (wato darling) yakike", "Lafiya kalau ,nakira numbanka amma baka picking ba", "Eh wallahi *D* muna meeting ne shiyasa nasa shi a silent", "Okay ina son muyi magana ne", "Toh ki sameni a office, yanzu na dawo". Ta kashe wayar sannan ta sanarwa khadija cewa zata tafi office ďin musa. "Okay toh ina jiran ki a mosque". Feenerh ta shiga office ďin ta same shi zaune tace ,"assalamu alaikum", "Wa alaiki salam *D*" ya amsa muryarsa a sanyaye, "Dear ya aiki", "Lafiya, ya karatu", "Kalau", "Naji ance results ďinku yafito " "Eh yafito", "Toh i hope dai komai yayi kyau *D*", "Eh", "Tohhh *D* konayi laifi ne, naga harma 5 missed call", "Eh, babban laifi ma", "Hmmmm *D* kenan, toh menayi", Feenerh ta ďanyi kitsitsina sannan tace ,"haba dear ,ya za'ayi ina jin irin wannan news ďin a notice board", "Wani news kuma *D*", "Kafini sani ai", "A'a sai kin faďa", "Maganar zuwanka states don karasa karatunka na masters acan", "Ohhhh *D* wannan , am truly sorry, actually am on my knees, naso in faďi maki but i wanted to surprise you, bansan zasu manna a board ba ,am really sorry *D*". *tnx for reading....* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU💚* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 13▶14* Akwana a tashi ,su feenerh sun fara jarabawa sannan kuma musa na shirye shiryen zuwa turai amma feenerh bataji ďadin abin ba ,gani take kamar in yatafi can mantawa zaiyi da ita sannan yasamu wata sabuwar budurwa. *lectures hall* Feenerh ke zaune a kujera bayan sun gama zana jarabawar yau wanda kuma itace ta karshe. "Feenerh?" Kiran sunnan da khadija tayi ne ya fitar da ita daga tunaninta. "Ohhh khadija har kin shigo", "Eh na shigo amma ga dukkan alamu kin fara waýenan tunani tunaninki ko", "Toh ya za'ayi kawata ,masoyina zai tafi ya barni kina ganin inada wani kwanciyar hankali ne", "Tabbas feenerh in bakiyi a hankali ba ,tafiyar musa zai sa kiyi ciwo", "Kawata ciwo ma bazata iya kwatanta abinda nakeji a raina ba, haba khadija taya zanyi long distance relationship kinsan wahalarsa kuwa", "Aini ko nasan wahalarsa , ko kin manta ja'afar na uganda ,banafa ganinsa sai sau daya a shekara", "Am sorry kawata wallahi na manta ne ,gaba daya wannan maganar ya dauke hankalina", "Bakomai ,i understand". "Toh yanzu ya za'ayi", "Yanzu muje kisami musa ki masa maganar da kukayi da mommynki saboda ku sami mafita", "Kuma fa gaskiyarki kawata ,kinga yanzu inya tafi bazai dawo ba sai nan da shekara ďaya", "Hakane so lets go", Suka kama hanya zuwa office ďin musa ,feenerh ta kwankwasa sannan tashiga. "Assalamu alaikum", "Wa alaiki salam *D*, "Dear yakake, ya aiki", "Toh aiki alhamdulillah *D*, yanzu ma nake tunanin kiranki a waya", Feenerh tasamu wuri ta zauna. "Toh gani nan, koda wani sa'ko ne", "No kawai missing ďinki nayi", "Koh", "Eh *D* bansan ya zan iya shekara ďaya batare da ganinki ba,i feel like marrying you right now", Gaban feenerh ya buga, kamar yasan zancen da tazo mashi dashi kenan. "Dear inada wata magana dakai", "Toh bismillah *D* inaji", Feenerh ta zayyana masa yadda sukayi da nahaifiyyarta sannan ta faďa masa dokokin da suka bata. "Lallai *D* iyayenki sunyi gaskiya , bakowwani namiji zai yadda ya auri wanda ta experiencing university life ba , nima saboda *muna tare da juna ne* shiyasa", "Amma dear don't you think it's too early, nifa yanzu kwatakwata shekaruna nawa?", "It's doesn't matter *D*,wasu na aure tun basu kai shekarunki ba", "Toh yanzu dear mekake ganin zamuyi yanzu", "Toh atakaice dai *D* biyyaya zamu musu ,tunda yanxu *mun aminta da juna* mezai hana infito gun iyayenki da neman auranki", "Dagaske dear", "Eh *D* dagaske nake ,amma kinsan bezai yiwu intafi yanzu ba,kibari inna dawo daga karatuna alokacin komai yayi daidai sai in turo magabata na zuwa ga iyayenki", "Dear har kabani kunya", ta faďi kanta a kasa, "Kunyar mekuma", "Yadda kake wannan maganar a gabana", "Ba abin kunya bane ,abin farin ciki ne because i can't wait inga kin zama matata", "Nima haka dear", Ahaka suka cigaba da hirar soyyayarsu har lokacin sallah yayi ,ta tashi ta wuce massallaci. *Bayan sati ďaya* A yau jirgin su musa zai tashi zuwa New York, feenerh koh sarkin kuka tayi har ta gaji .Ta rakoshi har zuwa airport saboda ta mashi sallama irin ta masoya". *tnx for reading...* *©Fareedah*. *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU💚* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 15▶16* Kira ya tayar da feenerh da daddare ,tamanta batasa wayar a silent ba. "Hello", ta faďi muryarta a ciki, "Hello *D*", Nan da nan idon feenerh ya kwashe, "Dear", "Naam *D*, yakike*", "Lafiya kalau , dear kun kai lafiya", "Kalau *D*, kwana biyu ban kira ba saboda ban siya sabon sim bane, abubuwa sun min yawa", "Bakomai dear, nayi missing ďinka sosai", "Nima haka *D*, shiyasa nafara launching sim ďina da numban ki", "Owww thanks dear", "Toh *D* nasan bacci kikeyi ,gobe zan kira ki saboda muyi hira sosai", "Toh shikenan dear, gud night i love you ,sweet dreams", Feenerh ta kashe wayar tana murnushi ,atlast musa ya kirata yanzu zata samu kwanciyar hankali, she can't wait gobe yayi saboda su kara yin magana. Anan tayi bacci da wayar a manne da kirjinta . "Feenerh!!!" Feenerh ta bude ido da kyar sai taga mamanta a tsaye , "Oh mommy gud morning", "Kema haka, wato daga sallar asuba sai kika koma bacci koh, saboda yanzu ba makaranta", "Wallahi mommy bahaka bane, nagaji ne sosai shiyasa", "Wani aiki kika yi har kika gaji", Feenerh tayi shiru ,batason mommy tasan jiya tayi night call da musa", "Mommy nayi karatu ne jiya shiyasa kinsan mun kusa dawowa school", "Lallai toh kitashi saboda yau daddynki yace yana son magana dake kafin ya tafi wurin aiki", "Allah mommy, toh gani nan zuwa yan zunan". Feenerh ta sami daddynta a zaune a falo ya gama shirin zuwa gurin aiki , "Daddy ina kwana", "Lafiya kalau safiya, antashi lafiya", "Lafiya kalau daddy", "Toh safiya, abinda yasa na aika mamanki ta kira shine akan maganan da kukayi da ita ,kin tuna", "Eh na tuna daddy", "Toh yawwa ,wani decision kika dauka akai", "Daddy naji abinda kuka ce kuma na gamsu da dakkan kalamominku ,nan da shekara daya in sha allah zan fito da miji kamar yadda kuka kayyatamun", "Yawwa safiya,ýar albarka kinga inkika yi hakan shi zai fiye miki saboda kowace mace gidan mijinta shine aljannarta", "Toh daddy", "Shikenan zaki iya tafiya yanzu", "Toh daddy nagode". Feenerh ta koma dakinta ,ta zauna shiru yanzu dai iyayenta da gaske suke son auran da ita ,kodai sun gaji da ita ne amma ai ita kaďai suke da ,baya yadda za'ace sun gaji da ita. Toh maybe shiya fiye mata alkhairi tunda ance abinda babba ya hango ,yaro koya hau saman tsauni baxai gani ba. Kirar wayarta ne ya katse mata tunaninta tana dubawa sai taga kawarta ne khadija , "Hello khadija", "Naam feenerh yakike", "Kalau kalau babe ,ya hutu", "Lallai muna nan muna shan hutu , ni duk na kosa ma mu koma", "Nima haka kawata", "Toh yanzu dai kina gida ne ", "Eh ina nan", "Toh gani nan zuwa ,i hope dai kin ajemana gist", "Akwai gist kam sosai kawata", "Toh gani nan zuwa", "Sai kin shigo". *tnx for reading....* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH GURKU💚* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 19▶20* Feenerh na zaune a falo tana kallo bayan wucewar khadija ,tasa AIT a dstv daidai ana jenifa's diary(best comedy ďinta) tana kallo tana dariyar yanda turancin jenifa yake ,wayar ta na ringing amma bataji ba saboda karar tv sai da aka kira na uku tukkuna taji vibration kusa da ita sannan tasan ana kiranta ta duba sai taga masoyinta ne wato musa. "Hello dear", "Hello *D*", "How is you", "Tohhh *D* wannan turancin kuma fa", Feenerh tayi dariya, "Turancin jenifa namaka", "Ohhh wannan comedy ďin", "Eh ,wallahi inason wannan comedy ďin", "Lallai kam toh *D* ya dai", "Kalau kalau dear", " ina missing ďinki sosai *D*", "Nima haka dear, kamar inyi tsunsu inzo wajenka", "Allah sarki *D*", "Tun dazu naketa jiran kiranka amma shiru", "Eh kinsan lokacin mu ba daya bane,ina bacci ne shiyasa", "Okay toh good morning", Musa ya ďanyi dariya sannan yace, "Morning *D*", "Dazun khadija ta bar nan ,tacemin ja'afar zai dawo next week", "Ohh har ya kammal kenan", "Eh", "Bawuya abun", "Eh wallahi", "Toh kinga nima nan bada jimawa ba zakiji nagama har ina hanyar dawowa", "Dear ko kwana ďaya ka tafi yi zan missing ďinka balle har shekara ďaya", "Toh *D* ai wahalarsa shine farawa amma in har anfara ba wuya ake kammalawa", "Hakane", "Toh yasu mama da baba", "Lafiyarsu kalau", "I hope dai kina kula dasu sosai", "Eh sosai ma", "Kamar da gaske ,ni nasan bakya aikin komai a gida", "Lahhh dear waya faďa maka", "Kawai haka nake gani,amma inna aure ki kullum sai kin tuka tuwo", "Haba dai dear, tuwo kuma kullum, gaskiya bazan iyaba", "Toh ai sai ki koya donni na fi son tuwo fiye da komai", "Ai sai in dauko house help", "House help? A gidana , ena *D*,keza kina min abinci kowani lokaci", "Haba dear ,baza dinga hutawa ba", "A'a ba hutu", "Toh in muka samu babyn mu fa ,wa zaina kula da dashi", "Zan dauko masa nanny amma baxan dauko househelp ba", "Lallai dear kenan,very principled", "Eh na yarda ,nifison cin abincin matata", "Yes sir", Musa yayi dariya ,wai yau shine sir, "Ni kike kira sir", "Eh mana,aika cancani sunan", "*D* kenan", "Feenerh!!!",mommy ta kirata "Dear mommy nakirana ,zuwa anjima zamu karasa maganar", "Toh shikenan *D* bye". Ta kashe wayar sannan ta nufa dakin mommynta, "Naam mommy", "Feenerh ,babanki yayi azumi yau kuma yace yana bukatar fruits salad,akwai fruits ďin a fridge sai kije ki hada masa saboda laraba bata iya hadawa ba", "Toh shikenan mommy", Feenerh ta tashi ta nufi ta fridge ta dauko fruits ďin sannan ta dawo falo tana kallo kuma tana yanka fruits ďin. "Assalamu alaikum", muryar daddy ne yasa ta juyo sai taga har ya iso inda take, "Sannu da zuwa daddy", "Yawwa safiya ,yau ke zaki hada min kayan iftar ďin", "Eh daddy", "Toh allah yamiki albarka ,ina mommynki", "Tana ďaki", "Okay toh", Feenerh ta juyo tachigaba da aikinta. *tnx for reading...* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by :* *FAREEDAH GURKU💚* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 23▶24* "*Meke faruwa*", "Name fa dad", "Tunda kika shigo falon nan ďazun nagane akwai abinda ke damunki,sannan ďazun a dinning naga yadda fuskarki ta canza amma kika yi saurin kauda da kanki saboda kar in gane", Toh atlast ja'afar the CID yafara aikinsa ,dama saida khadija tayi warning ďinta yanzu ita mai zata ce ma dad ďinta. "Ina jinki feenerh ,ki faďi min abin da ke damunki", "Dad it's a long story", "Cut it short", Anan feenerh ta bashi labarin yadda suka hadu da musa ,da yadda relationship ďinsu yafara sannan ta sanardashi yadda sukayi da mommy dakuma daddy. "Yanzu abinda yake saki wannan tunanin kenan", "Eh dad", "Toh ai wannan ba abin dazai saki dami kanki da tunani bane,i understand your feeling amma Adu'a zaki mishi saboda yasamu ya kammala karatunsa lafiya,kinji ko?" "Toh dad", "Sannan maganarsu umma kuma ki barshi ba yanzu ba tunda sai nan da shekara ďaya aikinga kina da sauran lokaci so ki daina tayar da hankalinki ,kinga har kin fara ramewa", "Thanks alot dad,shiyasa nake sonka wajen bada advice,i really missed you", "Nima na missing rigimarki sosai", "Wani rigima kuma dad", "Rigima kamar wannan yanzu badun na gano da wuri ba haka zaki boyemin ko", "A'a ,i planned to tell you one day", "Lallai wato planning rannan dazaki fadamin kikayi", "Am sorry dad", "Bakomai, yanzu ki kwantar da hankalinki ,kibar komai ga Allah sannan ki kara da adu'a", "Nagode sosai dad", "Kibani numban musa ďin saboda mu gaisa sannan in san wa zai auran min dota na", "Toh bakomai zan sending maka", "Yawwa,toh ni dota zan wuce gida saboda inje in huta gajiyar hanya", "So soon", "Karfe tara fa yayi, kuma inaso in ďan duba khadija kafin in koma gida", "Lallai yau wannan outing namu ne", Ja'afar yayi dariya yace,"eh wannan nakune", Bayan sunyi sallama da su daddy sai ya wuce. Fitar ja'afar bada ďa ďewa ba musa ya kirata a waya, "Hello dear", "Naam *D*,yakike ,ya kowa da kowa a gida", "Duka suna nan lafiya", "*D* yau muke lectures ďinmu", "Toh Allah yasa albarka aciki", "Ameen, *D*", "Yau ja'afar ya dawo daga makaranta", "Okkk,toh ya dawo lafiya", "Lafiya kalau", "Toh madallah", "Yace in bashi numbanka ,yana so ku gaisa", "Okay toh,i will be expecting his call", "An mafa kayi a hankali, he is a little protective", "Tohhhh", "Eh kasan shine school dad ďina a boarding", "Toh shikenan ,kinsan duk wanda ya kula min *D* ďina nima zan kula dashi sosai ,so no problem", "That's why i love you", "Love you too *D*", "I hope dai ba wata baturiyar da ke son kwace min kai", Musa yayi dariya sosai, "Haba *D* har akwai wanda zai iya kwace post ďinki", "Kasan baturan nan sun iya kitsitsina ,kuma akwai su da son blackmen", "Toh ko suna so ma ,this one is taken", "Yawwa dear", "*D* kenan ,toh bazan barki kiyi bacci saboda nasan dare yayi acan", "Eh dear kamar kasan bacci ma nakeji", "Toh shikenan *D* good night and sweet dreams", "Bye dear". *tnx for reading....* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 25 ▶26* Yanzu hankalin feenerh ya kwanta tun lokacin da ja'afar ya advcing ďinta ,tana kuma adu'a akan karatun musa yazame masu alkhairi. Ayau feenerh ta deciding zata fita outing saboda ta ďa ďe bata fita ba. Ta sanar da iyayenta cewa tanason tafita yawo ita da kawarta khadija, daddy yasa direbar su yayi full tank sannan ya gargadi feenerh akan karta kai dare a waje daga karshe yabata wasu kudi saboda ta ďanyi shopping sannan ta ziyarci wasu places ďin. Bayan tagama shiri ,tafito tasamu direbarsu david yana wanke motar kirar toyota (hilux) ,ta ďan jira shi kaďan ya kammala sannan suka kama hanya zuwa gidansu khadija. Ahanya takira khadija ta sanarda da ita tayi shiri gatanan zuwa zasu fita outing. As usual saida khadija tamata sharri akan cewa yau wani rana har ta deciding tafita daga cave ďinta. Sun isa gidan su khadija sai feenerh tashiga gidan ďon ta kirawo kawarta. "Assalamu alaikum", "Wa alaikum salam ",kanwar khadija ,fati ta amsa wanda ke zaune a falon, "Yaya feenerh sannu da zuwa", "Yawwa fati, yakike", "Lafiya kalau", "Ya makaranta", "Toh alhamdulillah", "Yaushe zaku koma ", "Sai September 11", "Ohh ai an kusa ma, tunda yau muke September 1", "Eh", "Toh allah bada sa'a kanwata", "Thank you yaya feenerh", "Khadija na daki ko", "Eh tana ciki", Feenerh ta karasa ďakin khadija ta sameta a gaban mirror tana kwalliya. "Lallai uwar makeup", Khadija ta juyo taga feenerh a tsaye a bayanta,saita ta juya tachigaba da kwalliyarta, "Toh in banyi kwalliyar ba taya zan fita outing ďin", "Toh nifa ,kinga nayi wani heavy makeup ne", "Ai baza kiyi ba saboda kinsan oga baya gari", "Ohhh khadija, yanzu dama saboda dad ya dawo ne kike wannan heavy makeup ďin", "Eh mana ,ko kina so amin kwace ne", "Toh ai naga batare dashi zamu tafi outing ďinba", "Nasani, amma ai zamuyi selfie saboda in tura masa ta whatsapp zuwa anjima", "Hmmm dagaske kikeyin abinki kawata", "Eh mana". Feenerh tasamu wuri ta zauna akan gado saboda tana ganin kamar wannan kwalliyar zai bata lokaci kuma ta gaji da tsayuwa, "Umma na gida", "A'a sun fita dazun, sun shiga kasuwa da mairo (house help ďinsu)" "Okk", "Yawwa feenerh ,ya kukayi da ja'afar rannan", "Meya faru ,ya faďa miki wani abune", "A'a cewa yayi kawai wai ni ban kula mashi da dota ďinshi ba gashi har ramewa kikayi", Feenerh tayi dariya, dad kenan akwai shi da bincike, "Kaman ba kinsan yadda dad ďina yake ba, saboda CID character ďinshi sai da ya gano cewa something is going wrong", "Ya akayi ya gano", "Cewa yayi wai tunda yazo ya gane akwai abinda ke damuna kuma yaga kamar na rame", "Ai dama na warning ďinki akan wannan tunanin naki", Feenerh ta turning eyes ďinta ,kamar tasan sai khadija ya smashing mata wannan maganar a face ďinta. "Toh naji, kin warning ďina but khadija bansan ya zan hiding feelings ďina ba especially when dad yana tunomin da musa", "Ok toh naji kawata ,amma i hope dai ja'afar baiyi anything stupid ba kinsan he is a little protective", "Bansani ba ,amma dai na bashi numban musa ,yace min wai yanason su gaisa ne", "Shikenan kawata,lets hope for the best" "Hmmm hakane babe", Feenerh ta jira khadija ta karasa makeup ďinta sannan suka kama hanyar zuwa outing ďinsu. *tnx for reading...* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 27▶28* "Feenerh ina zamuje yanzu", Khadija ta tambayeta, "Akwai wani boutique da aka bude around the corner, nan zamu je saboda ance suna da kaya masu kyau", "Meza kisaya kuma", "Ina son in saya jallabiya ne kamar three pairs haka dakuma jaka one pair ,kinsan zamu shiga winter ne so inason insamu kayan da ya dace da wannan season ďin ", "Ok toh". Sun isa boutique sai feenerh da khadija suka shiga ,gaskiya boutique ďin ya hadu sosai sanna sunada kaya designers masu kyau abinda yakama da ,diors,gucci,jimmy choo and the rest. Feenerh ta zabi jallabiya masu kyau sannan tasamu jaka product of jimmy choo multi colors mai kyau ,itama khadija ta siya takakama guda biyu. "Khadija inaga muje loremm hotel,saboda suna serving Wonderful foods a resturant ďinsu", "Ok no problem ,muje", Bayan sun kai loremm hotel,sai david ya packing motar sannan ya biyo bayansu saboda sometimes yakan acting kamar security personnel ďinta. Sun ordering fried rice and chicken shikuma david ya ordering jollof rice and beef. Sun idar da cin abincin sai zagaya hotel ďin har izuwa swimming pool ,bayan wasu lokuta sai suka fita suka kama hanya zuwa next location ďinsu. Ranar kam feenerh taci yawo har ta gaji atlast suka branching lavista(eatery) suka siya shawarma da ice cream saboda suyi saraba gida. "Feenerh ,barin kira ja'afar yaxo ya daukeni anan ya kaini gida", "Kedai kinaso ki wahalar da dad ďina ne", "A'a bahaka bane ,kinga yamma yafara yi banaso ki koma gida late ne", "Ok toh kirashi", 5 minutes later ja'afar ya iso wajen su, dama wai yana neighborhood ďin ne so bai wani bata lokaci ba. "Hello Ladies", "Hello dad",feenerh ta amsa , "Su dad manya" khadija ta fa ďi tana dariya, "A'a kinga karki mana sharri nida dota ďina ,bamai shiga tsakaninmu", "Eh hakane ",feenerh ta goyi bayan dad ďinta, "Ohh so kuke ku min taron dangi,ai nima inada masoyana",khadija tace madu. Sun zauna sun ďanyi hira sannan kowa ya kama hanyarsa,ja'afar shi ya dauki khadija ya kaita gida while feenerh tashiga hilux ďinsu david ya kaita gida. Tashiga gida da sallama, "To mutanin gidan nan na dawo,tashiga ta kitchen ta sami mamanta da laraba, "Mommy na dawo", "Ohh har kin dawo daga yawwon kenan", "Eh", "Toh sannu da dawowa", Mommy kubar yin girkin nan,na kawo shawarma da ice cream", "Toh in muka bari,daddynki fa kinsan baya iya kwana in baici tuwon nan ba", Feenerh tayi murmushi har ya tuno mata da musa(wai yau dad ďinta nema ya tuno mata da musa..lolx). "Ok toh laraba jeki ki huta yau ni zan ma daddy miyan", "Toh lallai feenerh in the kitchen" mommy ta fa ďi tana murmushi. Ahaka sukayi girkin suna hira har suka kammala sannan laraba ta jera flasks ďin a dinning table. Feenerh ta retiring back to her room tayi sallah sannan ta dauko wayarta ta kunna data. Messages kala kala suke shigowa na groups daban daban,groups kamar su *Aneelurv novels*,da *faxy novels* ,da *mata adon gari*, dama sauran su. Gaskiya tana bala'in son groups ďin saboda suna tura novels kala kala sannan writers ďin suna trying best ďinsu saboda suga sun faranta ma readers ďinsu,gaskiya jinjina ga writers,readers dama ýen groups gaba ki daya especially to her best writer *ANEELURV*. *tnx for reading...* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by:ANEELURV😍* ```I wish my mentor(ANEELURV) quick n speedy recovery ameeen``` *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 29▶30* *Around 6:00 am* Wayar feenerh yayi ringing but as usual ba bacci takeyi ba because tariga da ta saba awannan lokacin musa ke kiranta. "Hello dear", "Hello sleepy head,har kin tashi", "Eh ,but actually ba bacci nakeyi ba", "Ok *D*,hope dai banine reason ba saboda banaso kina hana kanki bacci because of me", "A'a bakai bane ,morning azhkar nakeyi",feenerh tayi karya. "Ok Hakan yayi kyau", "Yawwa ",ta fa ďi yayin da takeson boye dariyar da takeyi, "So nake dama in zama na farko da zai wishing ďinki happy independence", "Ohh dearest ,har na manta", "Kin manta? ,you are not a good citizen, yau kasar mu na celebrating birthday ďinta kuma kice kin manta", "Toh nida nake gida ,taya zan kula ma da date, kasan tunda yanzu ba school nake ba bana cika damuwa da date", "Ok to,happy independence", "Thanks dear", "*D* i have decided inna dawowa bazan wasting time ba zan turo neman aurank", "Toh ,soyayya ne ya moso yau da safen nan dear", "Ai kullum soyayyar mosowa yakeyi ,am just missing you like crazy", "Miss you more dear", "*D* kenan,kamar da gaske nasan har yanzu su tanko da abu suna kan zuwa", Feenerh ta kyalkyale mashi da dariya, "Su waye kuma abu da tanko,kafara zolayarka ko", "Ai ke kin fini sanin su,amma kice musu ga sako *nobody is taking you away from me ,only death", "Yes sir", "I like it when you call me sir", "Toh daga yau dashi zanna kiranka", "No, nafison dear", "Allah ko", "Eh saboda in kasance kullum ina zuciyarki", "Ai kullum kana zuciyata dear, sometimes inna tuno baza kadawo ba sai nan da shekara ďaya kwalla nakeyi", "Kidaina min kuka *D* ,adu'a zaki min saboda in samu nasara a abinda nake nima", Feenerh da musa kenan,soyayyar su abin sha'awa , in wasa yazo suna ýinsa sosai,in seriousness ne toh zasu dauke shi da mahimmaci sosai gashi suna kaunar juna kamar zasu cinye junar su , "Toh shikenan dear, allah yaba da sa'a ,yasa abinda ake nima asamu", "Ameen *D*", "Yawwa", "Toh *D* inada afternoon classes yanzu ,zan kira zuwa anjima inna fito", "Ok dear, love you", "Love you too ,bye". Feenerh tafito daga ďakinta zuwa ďakin iyayenta don ta gaishe su ,tayi musu sallama sanna tashiga, "Ina kwana mommy", "Lafiya kalau", "Ina kwana daddy", "Lafiya safiya", "Kun tashi lafiya", "Lafiya kalau",suka amsa gaba ďaya, "Yawwa safiya,inada magana dake", Zuciyar feenerh ya buga ,kar dai daddy ya changing mind ďinshi akan maganar auranta ne,kodai ya maso dashi kusa ne,toh in yayi hakan yazatayi tunda yanzu musa na america. "Safiya ,yaushe zaku dawo makaranta", Nan da nan da saukar da numfashi, "Nan da two weeks daddy", "Ok toh nawa ne school fees ďin", "#45,000 ne", "Toh zan baki jibi ki biya saboda kinga yau da gobe public holiday ne", "Ok toh daddy", "Toh shikenan zaki iya tafiya", "Nagode,yawwa daddy happy independence sannan kuma happy anniversary for nasarawa at 20", "Same to you dear", Feenerh tafita tana murmushi. *tnx for reading....* *©Fareedah*. *💟💟 UWA KO ÝA 💟💟* *Written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 31▶35* Akwana atashi ba wuya,su feenerh na shirye shiryen komawa skul. Feenerh zata shiga skul yau saboda zasu fara registration kuma tayi magana da khadija ta sanar da ita cewa ta sameta a skul. *bayan awa biyu* "Gaskiya khadija na gaji ,ga kuma rana", "Toh ai feenerh waje ďaya ya rage amana signing ,kinga ai mun gama", "Toh shikenan ,amma inaga muna gamawa mu wuce canteen kawai ,saboda yunwa nakeji", "Okay". Bayan sun gama sai suka wuce skul canteen , "Wat will u lyk to order", Waiter ta tambeyesu. "What is special today",feenerh ta faďi "Local rice and stew", "Okay ,two plates please", "Okay ,ma'am wat would you lyk in your stew,beef or chicken", "Chicken rather", "Okay ma'am,coming ryt up", Feenerh suka samu wajen zama ,an kawo abinci ,sukaci in silent bayan sun gama ,suka tashi don suje su biya bills ďin. "How much ",feenerh ta tambayesu, "That will be 1200", "Okay",tasa hannu a jaka zata cire sai taji ance , "No problem,it's on us", Tana juyowa saita ga samari ne guda biyu kuma da ganinsu students ne. "Sannu ku fa ladies", "Yawwa sannu", "Don allah in baxaku damu ba,muna son magana daku", "Badamuwa", "Ko zaku iya fa ďa mana sunanku", "Meyasa,saboda ni bantaba saninku ba ,so meyasa zan baku sunana", "A'a ,kawai so muke mu zama friends ďinku", "Ohh sorry ,amma mu matan aure ne kuma mazajenmu sun hana mu magana da samari", "Haba,ya kike irin wannan maganar nafa saba ganinku a campus kuma nayi tambaya nasan baku da aure", "Toh meyasa baka tamabayi messenger ďinka sunanmu ba", "Saboda nafi son inji daga bakinku,kinsan ance *waka a bakin maishi ya fi da ďi*", "Toh gaskiya kam,maishi bai da niyyar rerawa yanzu,kinga kawata mu wuce gida", "Haba ýan mata ,lefin me mukayi ,suna fa kawai muka tambaya", "Wai ku bakwaji ne ,tace maku aure ne damu ,why not ku facing studies ďinku ku daina neman matan aure",khadija tasa baki acikin zancen. Samarin biyu suka basu hakuri sannan suka wuce, "Ohni khadija mun gode ba'a waje suka taremu ba ,kinga yanzu da dad ya gansu", "Eh fa don yacemin yana jiran mu a waje,unserious types waýenan yaran harda rannar registration", "Eh mana,kinsan rannar ne aka fi taruwa sannan ranar ne kawai zasu iya magana da mata saboda bayan wannan ranar bara ma su gansu ba", "Lallai fa kowa na lectures". Suka fita waje ,suka sami ja'afar acikin mota ya ďan kwantar da sit ďin yana hutawa, "Assalamu alaikum dad"feenerh tace yayin da ta bude kofar baya ta zauna, "Wa alaikum salam dota,har kun gama kenan", "Eh fa ,munyi sauri ko", "Lallai kam", Khadija ta zagaya ta bude kofar gaba ta shiga ta zauna, "Keh hajiya ba gaisuwa ne", "Ohh dad aina aza baka ma ganni ba", "Shine da sharri haka", "A'a nina isa", "Kin ma fi haka,toh yakike", "Lafiya kalau", "I hope dai rana bai dameminki sosai ba dear", Feenerh ta kallesu nan da nan kwalla ya taru mata a ido,saboda sun tuno mata da musa. Ja'afar ya sauketa a gida sannan ya kai khadija daga nan suka wuce da hirarsu. Feenerh ta shiga ,tafara jin hayaniyar mutane ,toh koh dai wani abune yafaru agidan ,bata ankara ba taji an rungumota ta baya ana cewa, "Aunty feenerh kin dawo", Ta juyo taga ashe ma cousin ďinta ne zuwaira, "A'a zuwaira kune a garin yau", "Eh aunty", "Shiyasa naga anyi rana sosai yau", "Haba dai aunty ,har da zolaya kuma", "Tohh,yakike zuwee", "Lafiya kalau", "Tare da mamanki kukazo", "Eh da aunty fati,da aunty ramat da sauran kannena", "Wai lallai yau munada babban baki a gidanmu", Feenerh ta karasa ta ďakin mamanta taga dukkan waýen da aka lissafo mata a zaune a ďakin,ta durkusa ta gaishesu, "Feenerh har kun dawo" aunty larai ta tambayeta, "Eh aunty", "Toh ya makaranya ýan boko",aunty ramat tace, "Lafiya kalau aunty ramu",feenerh ta kirata da lakabinta, "Toh sannu ki da zuwa ,amaryan gobe",aunty fati tace, "Bana son sharri aunty fatee",ta karasa ta zauna suka cigaba da hira suna dariya. Ashe bikin yarinyar yayan mamanta suka zo yi wato hadiza. "Toh amma aunty larai ai bikin saura kwana goma sha hudu,yanaga kunzo da wuri", "Mun zo da wuri ne saboda mutaya kanwar mu shirye shiryen bikinki", "Kai aunty ,bikina kuma", "Eh mana kobaki isa bane", Feenerh tayi dariya, "Aunty kenan to ai in kunji daidai ,bikina sai nan da shekara biyu", "Eh mana ,mun sani mun zo mu fara tattaunawa ne kafin lokacin ,kinsan in muntafi bazamu dawo ba sai in bikinki yaxo". *tnx for reading...* *©Fareedah*. *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by :ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 36▶40* Angama biki lafiya,kowa ya koma gida amma feenerh bata ma tambayi mamanta ya sukayi da aunty larai ba saboda bata ma kaunar jin maganar aurenta yanzu. ************************************ Karatu yaci gaba,anshiga tsakiyar semester so karatu sukeyi sosai saboda jarabawa ya kusan gabatowa. Ja'afar kuma yasamu zuwa NYSC ďinsa a first batch sannan kuma an tura shi gari mai nisa har zuwa lagos. Ranar da zai tafi kamar khadija zatayi kuka ranar,amma yabata hakuri sannan yace mata da yardar allah yana dawowa za'afara maganar aurensu. Musa da feenerh kuwa soyayyar su tayi gaba domin yanzu kam suna video chatting ta skype so shiyasa kewarsa da takeyi yanzu ya ragu. Yau weekend ,feenerh na gida tana hutawa a falo , "Feenerh?", Mommy ta kirata. "Na'am mommy",mommy ta karaso falon ta zauna, "Feenerh inada magana dake", "Toh amma mommy i hope ba abinda kuka tattauna da aunty larai bane" "A'a", "Okay inaji mommy", "Magana ne akan auranki", "Aurena kuma mommy ,amma kince min ba maganar da kukayi da aunty larai bane", "Eh bashi bane,amma wannan ďinma is about you", "Toh mommy", "Feenerh,ni mamanki ne yakamata ace kina consulting ďina akan wasu abubuwa ,ana cewa a mom is her dota's best friend", "Hakane mom, amma ai mommy duk abinda zanyi sai da saninki kuma bantaba boye miki wani abu ba", "Feenerh ai bance kin boyemin wani abu ba,amma baki nimi advice ďina akan wasu abubuwa ba", "Mommy wasu abubuwa kuma", "Kamar yanda kika sanar da ni da daddynki cewa nan da shekara daya zaki fito da mijin aure amma gashi har rabin shekara shiru", "Mommy ai lokacin baiyi ba", "Nasani amma kamar ni mommynki baki fa ďamin sunanshi ba,ko daga ina yake kuma baki fa ďamin halayarsa ba,kobaki son insani ne ko kuma advice ďina ne bakya so", "Allah sarki mommy ,wallahi ba haka bane", "Toh yanene", Feenerh tayi shiru, "Gashi ko sunanshi ma bansani ba", Mommy tachigaba da magana, "Mommy sunanshi musa", "Musa?", "Eh mommy", "Me sunan iyayenshi", "Sunan babanshi abdullahi ,sunan mamanshi kuma fatima", "Musa abdullahi", "Eh". Mommy tayi shiru tana nazari,anya shine kuwa amma toh za'a iya samun matsalar suna maybe bashi bane, "Mommy wani abu ne yafaru", "A'a bakomai ,toh wani aiki yakeyi ko ďan makarantane", "Lab technician ne a makarantar mu", "Toh meyasa har yanzu baixo yayi gaisuwa ba", "Mommy baya gari ,yasamu scholarship yanzu haka yana New York don karasa masters ďinshi", "Masters kuma feenerh", "Eh mommy", "Kice ya ďan manyanta kenan", "Eh", "Toh alhamdulillah ba waýenan kananan samarin kikasamu masu rashin kunya ba" "Waýensu irin samari kuma mommy", "Irin waýenda suke gaisuwa a tsaye sannan suke magana kamar masu sarki a aljihu", Feenerh tayi dariya sannan yace,"mommy kenan", "Toh feenerh shi musa yaushe zai dawo,i hope dai kin fa ďa mishi abinda daddy yace", "Eh mommy na fa ďa mishi kuma yace ya yarda", "Toh ya batun dawowarsa", "Zai dawo nan bada da ďewa ba saboda yanzu dai kam watanni bakwai ya rage mai ya gama course ďinsa", "Alhamdulillah ,nai masa murna allah kuma ya bashi sa'a " , "Ameen mommy", Sukaci gaba da hirar su irin na *uwa da ýa*. Bayan sallar isha,feenerh ta kira musa ta video chat na skype,yana ansawa fuskarsa ta fito a screen ďin, "Hello *D*", "Dear yakake", "Lafiya", "Ya karatun yau", "Kalau kalau *D*", "Koda naga fuskarka sai naji sanyi a zuciyata", "Nima haka *D*,tun dazu nake tason inkira ki amma kin rigani", "Toh kaima kasan in bankiraka ba bazan iya bacci ba", "Same here *D*", "Yau mukayi zancen ka da mommy", "Tohhh ,i hope dai ba laifi nayi ba", "A'a ,kawai hira mukayi kuma ta bukaci in bata labarinka shi kenan", "Okay allah sarki,nima ai nayi laifi yakamata ace naje na gaishesu kafin na tafi", "Bakomai dear,ai itama batace komai kawai cewa tayi allah sa albarka a karatunka", "Ameen", "Meye labari dear", "Wallahi *D* munkusa zana jarabawar karshe,kinga ina gama zan dawo saboda a daura aurenmu", "Allah ko dear", "Da gaske kinga inata siyeyen kayan aure a nan", "Da wuri haka dear", "Wuri kuma *D* ,ai gara ayi komai da wuri banson in bata lokaci da yawa", "Dear kenan,yawwa dama mommy tace tanason gaisawa da kai ,ko inje in kirata", "Eh badamuwa", Feenerh ta tafi ďakin mommy takirata ,suna shigowa taga blank screen,ashe ta manta batasa shi a charge ba har ya mutu. "Tohhh mommy ,ya mutu", "Badamuwa,sai wata rana". *tnx for reading....* *©Fareedah*. *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by:ANEELURV😍* *Dedicated to my lovely mom😍* *pg 41▶45* Musa sun gama zana jarabawar su da yardar allah amma ance su jira nan da wata biyu saboda result ďinsu yafita kafin su koma gida.so zai jira saboda yanzu in yakoma gida bazai dawo ba sai in har sunyi aure da feenerh. A 'bangaren feenerh kuma suna kan rubuta final paper ďinsu na aji biyu. Sun gama lafiya kalau kawai jiran dawowar musa takeyi koda dai ya fa ďa mata sai nan da wata biyu ,bataji da ďi ba amma ba yanda ta iya tunda ta iya jira har na shekara ďaya,na wata biyu ne bazata iya ba. Sai dai tayi tamai adu'a allah sa result yafito kuma yayi kyau. Bayan sun gama jarabawar zasu fita su wuce gida sai khadija tace mata ta rakata kasuwa tanason ta duba wani abu. "Wani abu kuma zaki siya khadija" feenerh ta tambayeta, "Kawata dama wani zani ne na gani kuma yamin kyau shine nace ki rakani saboda ki gani ko zaiyi kyau da anko", "Anko?,anko fa kikace khadija", "Eh mana feenerh, kinsan ja'afar ya dawo daga bautar kasa kuma yace gobe zai aiko gidanmu gaisuwa", "Kice allah kawata", "Dagaske nake feenerh", "Yanzu shikenan khadija zaki aure", "Eh kawata", "I hope dai inkinyi aure baza ki dinga mana rawwar ganinki ba", "Wannan kuma sai ki tambayi daddynki saboda nikam bazan zama matar kule ba", "Lallai amaryan zamani", "Toh yaya son ranki". Sun isa kasuwa ,suka wuce wajen zanuwa ,feenerh taga zani kuma yayi kyau sosai dan haka suka tambayi mutumin kozai iya kawowa in bulk saboda anko zasuyi dashi, ya ce masu badamuwa. Feenerh takoma gida tasami mommynta ta zayyana mata yadda sukayi da khadija akan maganar aurenta. "Toh bagashi ba ,kawarki ma zatayi aure", "Mommy don kawata zatayi aure shikenan nima sai inyi yanzu", "Toh in bakiyi ba dawa zakina yawa a makaranta kinsan dai in khadija tayi aure mijinta bazai yadda kuna yawo kamar da ba sannan kuma iya sanina dake ita kadai ce close friend ďinki", "Hakane mommy,amma kinsan ba laifina bane saboda yanzu yana wuya a samu miji kamar daddy shiyasa nakeson insamu na kaina kafin inyi aure", "Gaskiya ne feenerh,amma yadda kike magana akan musa koda bansanshi ba yanada kirki kuma zai kula da ke sosai", "Eh mommy,musa nada kirki sosai kuma zai kula dani sosai amma shi da kansa ma yace inyi karatu sosai saboda yanada muhimmanci", "Lallai yamiki shawara mai kyau ,kullum zancen da kike akanshi kara yarda dashi nake akan yana sonki sosai", "Mommy musa na sona sosai kuma na tabbata bazai muzguna min a rayuwa ba", "Haka mukeson namiji yazama,kuma haka mukeson mijin *ýar* mu yazama", Feenerh ta ďan sukuyar da kanta kasa wai ita kunya. "Toh feenerh tashi muje kicin ,kinsan daddynki na gari kuma yace tuwon acha yakeso", "Toh mommy muje", Sun shige kicin don girkin abincin daddynta bayan sun gama sai feenerh ta dafa indomie da kwai don ita bata jin cin tuwon acha yau. *Bayan wata biyu (2)* Feenerh na zaune a ďaki tana karanta novel ďin *jini ďaya* na *aneesa .a. rimi (aneelurv)* sai kiran musa yashigo, "Hello", "*D* nagama ,nagama", "Masha allah dear ,congratulations ", "Thanks *D*", "Am so happy for you dear ,allah ya sanya alkhairi aciki", "Ameen *D*", "Toh yaushe zaka dawo ", "Gobe", "Banda zolaya fa dear", "Da gaske nake *D*,gobe zan dawo na riga da na booking flight ďin gobe", "Dagaske dear,yanzu gobe zaka dawo", "Eh *D*,am coming home", "Ashe yau bazan iya bacci ba", "Meyasa ", "Saboda kar bacci ya daukeni in kasa tashi gobe da wuri saboda inason inzama first person da zai ganka gobe", "Badamuwa *D*, zaki iya bacci saboda flight ďin sai karfe hudu zai isa", "Still dai ,murna bazai bari inyi bacci ba", "Am happy too *D* saboda nayi missing ďinki sosai", "I miss you more", "A'a ban yarda ba ,i miss you more", "Toh shikenan in ka dawo za'a tambayi khadija zata mana shaida", "Toh har ankai maganar Court ", "Eh!", "Toh amin afuwa na yarda you miss me more but i miss you much", Feenerh tayi dariya, "Dear kenan ,kanada different ways ďin sa mutum dariya", "Dole ai ,in bansaki ba wazai saki", "Dear inaso in canza maka suna", "Tohhh dawani suna za'ana kirana", "Zauji (wato miji na da larabci)", "Har na kai wannan matsayin ,thanks alot *D*", "You are welcome, i can't wait for tomorrow". Ahaka feenerh tayi bacci da waya a manne a kunninta har safe yayi. *tnx for reading...* *©Fareedah*. Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:* *FAREEDAH💚* *Edited by:ANEELURV😍* *in dedication to my lovely mom😍* *pg 51▶55* Ayau anata shugulgula don kar'ban bako wato musa ,a gidan su feenerh anyi abinci kalakala sannan an gyara gidan ko'ina yana walkiya. Su musa sun isa gidan su feenerh sai sukayi sallam a kofar waje,laraba ce ta ansa sannan tashigo dasu falo suka zauna. Laraba takoma ciki ta sanar da dasu cewa ba'kinsu sun iso. Daddy da mommy suka fito dan gaisawa dasu amma da isarsu falo sai mommy ta tsaya chak tana kallon musa. Anya kuwa shine kodai kammani ne ,kila mafarki takeyi,musa abdullahi ne saurayin ýarta kuma shine ýarta zata aura,nan da nan ta juya ta koma ciki batareda sunyi gaisuwa da mutanin ba. Daddy natajin mamakin ,yaba mutanin hakuri sannan yakoma don kirawo mommy. A bangaren musa,shi baima ga fuskar mommyn feenerh ba har ta koma ciki ,ya dai ji labarin cewa she is not that old kuma ance she married young. "Lafiya kuwa aisha", Daddy yashigo ďaki ya same ta a zaune akan gado tana nazari , "Lafiya kalau daddyn feenerh", "Toh meyasa kika baro falo", "Nayi mantuwa ne shiyasa", "Toh ai da kin sanar kafin ki fita haka ai,kinsan baki mukayi kuma zasu zaci ko jan aji mukeyi", "Kayi hakuri daddyn feenerh", "Bakomai ,yanzu tashi mutafi", "Toh", Mommy ta tashi suka koma falo tana biye da daddy. Musa na ganin mommy nan da nan shima fuskarsa ya canza ,anya aisha ce kuwa kodai mafarki yakeyi ko kuma mai kama da ita ne. "Sannuku da zuwa", Daddy yace, "Yawwa sunnu mu fa",kawon musa ,mallam labaran ya amsa. "Kuyi hakuri ,dazun matata ce tayi mantuwa shiyasa ta koma ciki", "Bakomai", "Yawwa", "Ni sunana malam labaran kanin mahaifin musa ,ataikace dai musa ya samemu a gida kuma ya sanardamu cewa akwai wanda yakeso kuma ita yakeson aura,koda muka tambayeshi ko ýar waye sai ya ambato sunanka kuma gaskiya a garin nan mutani kalilan ne basu sanka ba kuma a gaskiya mun yaba shiyasa muka ce toh bari mu tataka har zuwa nan saboda mu nema ma yaronmu auran ýarka", "Toh alhamdulillah ,naji ďadin zancenka kuma gaskiya abin alfahari ne aga wani naka ace ana so, ýaýa na kowa ne kuma tunda yace yana sonta kuma itama ta amince ai shikenan ,allah ya tabatar mana da alkhairi", "Ameen", Malam labaran yacigaba dacewa,"ga kayan gaisuwa mun kawo kuma da kudin gaisuwa " ya mika ma daddy a hannusa. "Toh mungode", "Kuma munaso asa mana sadaki saboda mu koma asamana ranar aure", "Duk abinda zaku kawo alhamdulillah ,ko kuma shi musa ya tambayi safiya metake bukata a matsayin sadaki saboda ita keda hakkin wannan", "Agaskiya mun gode ma tarban da kuka mana ,muna matukar godiya", "Bakomai allah yabamu ikon ganin ranar", "Ameen", "Toh aisha sai ki tafi ki kawo masu abinci ko", "Toh ". Koda musa yaji an anbaci sunan aisha sai jikinsa ya girgiza ,yanzu dama abinda yake kokwanto yazama gaskiya. Nan take ya dauki izinin fita waje sannan yaje motar sa ya zauna shiru yana tunani ,mai yafaru bayan rabuwa,yanzu dama itace maman feenerh ,a gaskiya tun ranar farko daya hadu da feenerh yaga kammani a fuskarta, lallai jini jini ne musamman *jini daya*, yanzu ya zaiyi. A bangaren mommy kuwa takoma kicin taba laraba umurnin kaima baki abinci ita kuma takoma ďaki ta zauna shiru tarasa mezatayi,sallamar da akayi ne ya dawo da ita, "Mommy har sun wuce", "Ohhh feenerh kece,harkin tsoratani", "Meya faru mommy ,duk hankalinki ya tashi", "Bakomai ýata", "Yaza kice bakomai mommy,duk fa zufa kikeyi kowani abune yafaru ne", "A'a bakomai", "Nidai ban yarda ba", "Feenerh...... " bata karasa ba taji kiran daddyn feenerh ,ta tashi da sauri ta fita. "Toh bakinmu zasu wuce ,kuma suna son ganin feenerh saboda su gaisa", "Shikenan,bara a kirawota", Feenerh!!!, "Naam mommy", "Kitaso ki saki abaya saboda baki nason ku gaisa", "Anya zan iya kuwa ,inajin soro", "Soron me", "Gani nake kamar bazasu soni ba", "Wayacemiki haka,ofcurse zasu soki", "Allah yasa mommy", Sun shigo falo,feenerh tayi gaisuwa dasu gaba daya sannan suka bata tukuicin gaisuwa kuma sun yaba da ita sosai. Toh daga karshe dai baki sunyi sallama da kowa sannan suka tafi. Mommy har yanzu hankalinta baya a kwance kuma feenerh tarasa gano meke damunta ,saboda haka tace yau zata gano komai, "Mommy sannu da hutawa", "Yawwa ýata", "Mommy inada tambaya" "Kekika haifeni", "Wani irin tambaya ne wannan ", "Saboda in kekika haifeni bazaki boyemin abinda ke damunki ba,mommy banason ganin bacin ranki kuma mommy kinki fa ďa min komai" ta fa ďi tana kuka. *tnx for reading....* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:FAREEDAH💚* *edited by:ANEELURV😍* *dedicated to my luvly mom😍* *pg 56▶60* "Feenerh", "Na'am mommy", "Bazaki gane abinda ke damuna ba kuma ko na fa ďamiki baza kiji ďa ďinsa ba", "Koma meye ne mommy ki fa ďa min,ke *UWA* tace kuma zan iya barin komai saboda ke", "Hmmmm ýata kenan" mommy tachi gaba da cewa "a very long time ago" *February 1997* *FGC KEFFI* "Aisha ki fito mana", "Haba faty bakya ganin ban gama kwaliyya ba", "Wani irin kwaliya kuma aisha,ko kin manta lokaci ya kure zamuyi late for assembly", "Toh gani nan", Aisha da kawarta faty suka fita a guje izuwa assembly ground. Sun samu yanzu aka fara yin assembly "I want the students to always be early and neat for assembly ,understand", principal ďinsu kuma labor master ďinsu mr ojukwu yace. Bayan sun gama assembly ,aisha ta hango musa yana xuwa. "Faty gashi nan fa", "Uhm kedai da wannan musan ,wai shin aisha baxa ki rabu dashi ba ko ko kinmanta kin kusa komawa gida ne", "Ba sai kin tunatar dani ba faty nasani", "Toh in kinsani mekike yi dashi har yanzu, wannan sai dai ya auri ýarki", "Haba dai faty,wani irin magana ne wannan", "Eh mana gaskiya nafada,har yaushe zai gama makaranta ballatana yafara maganar niman aiki har yaxo ya aureki ko kinmanta iyayenmu baxasu yarda da hakan ba", "Nasani mana faty ,amma ya zanyi ina sonsa", "Yakamata ki ajiye wannan son gefe guda wallahi", "Gaskiya baki fito halin yayana ba dukda sunanku daya", "Oho nidai na fa ďamiki gaskiya" , "Toh naji kawata". Musa ya iso wajensu sannan ya musu sallama, "Sannuku fa", "Yawwa musa", faty tace "Dan allah inason magana da aisha ne", "Ni?", "Eh", "Toh muje", Sun kebe gefe guda sai yace "kwana biyu", "Lafiya kalau, "Ya karatu", "Toh gashi nan munayi", "Wallahi fa ,mun dai kare junior waec lafiya", "Eh wallahi", "Ok dama kwana biyu bamuyi magana ba shiyasa nace barin inzo mu ďanyi hira", "Allah ko", "Eh", Toh, Sun ďanyi hira na wasu lokaci kafin lokacin komawa aji yayi. *march 1997* "Faty",aisha ta shigo hostel da kuka ta zauna a bonk "Ya akayi aisha", "Daga office ďin principal nake", "Meya faru", "An aiko da sako ne shine ya kirani inxo in karba", "Me akace a sakon", "Nan da sati za'azo a daukeni" ta kare maganar da kuka, "Yanzu aisha bazasu bari ki karasa ba", "A'a ,abbanmu yace ya isa haka", "Dakace abba bashi da kudi ne dana ce talauci ne yasa yayi wannan maganar amma bakomai kiyi shiru ya isa haka", "Yanzu ya zanyi ,cewa yayi wai zai auran dani ma yaron amninsa", "Yaron amininsa?", "Eh", faty ta danyi shiru sannan tace, "Kin wayeshi ne", "A'a", "Hmmm aisha tabbas sai kinayi kina adu'a kinji kawata komai zai zama daidai", "Nagode faty,yanzu me zance ma musa", "Kar ki damu zance mai baki da lafiya kin koma gida", "Nagode sosai faty", "Bakomai kawata". *ranar asabar misalin karfe sha daya na safe* "Allah ya kiyaye hanya aisha", "Ameen faty ,sai mun kara haduwa", "Da yardar allah kawata" , Aisha ta wuce gida saboda afara shugulgulan biki. Bayan sun iso gida ,kowa ya fito don suyi gaisuwa sannan ta koma ďaki ta kwanta a saman gado sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, "Aisha ashe baxaki bar wannan kukan ba",yayarta larai tace, "Ya zanyi yaya ,kuma yanzu haka aka maku", "Eh mana kanwata,kisa hakuri a zuciyarki komai zai zamanto lafiya". Anyi biki lafiya kuma ankai amarya dakin mijinta kyakyawa dashi dukda dai yabata shekaru masu yawa. An mata nasiha sosai sannan akace tabi tsawon mijinta saboda sune aljannarta. "Assalamu alaikum" ango yashigo da sallama, "Wa alaikum salam", "Yakike amarya", "Lafiya kalau", "Yawwa ,inada magana dake", "Inaji", "Nasan ba auren soyayya mukayi ba kuma nasan akwai wanda kike so amma ina rokanki dan allah karkiyi wani abu da zamuyi dana sani nan gaba,mu zauna lafiya koda ba dan iyayenmu ba ,dan allah ,ina fatan zakimin biyayya kuma nima bazan tsaba maki ba", Magaganunshi ya kwantar mata da hankali sannan ta aminta dashi. Anan ne soyayyarta da musa ya kare kuma anan ne ta bude wani sabon shafin soyyaya da angonta. *back to 2016* Koda feenerh tagama jin labarin sai ta fa ďi ta tsume,nan take mommy tayi ihun sunan daddy ,da wuri aka kai feenerh asibiti. *tnx for reading...* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:FAREEDAH💚* *edited by :ANEELURV😍* *dedicated to my luvly mom😍* *pg 61▶65* Feenerh ta farka a gadon asibiti taga mommy da daddy a gefen ta a take ta fashe da kuka. "Feenerh ya isa haka ", Mommy tace, "Mommy yanzu ya zanyi", "Feenerh kidaina kuka", "Safiya duk abinda yafaru da dalili",daddy yace. Feenerh ta juyo ta dubeshi ,"daddy ,yanzu kaima kasan ni kenan", "Eh nasani safiya,lokacin da na auri mamanki tasanar dani komai amma aganinta yaranta ne alokacin saboda kwatakwata basu gama secondary school ba", "Amma daddy taya kasani", "Alokacin da kika fa ďa ma mamanki cewa saurayiki musa abdullahi tazo ta sanardani sannan nasa akamin bincike akanshi kuma mun tabbatar eh shine amma bamu ga fuskarsa ba tun daga lokacin nace ma mamanki ta shirya fa ďamaki", Feenerh ta fashe da kuka,iyayenta baza su gane yadda takeji ba ,taya zata yi aure da wanda yayi soyayya da mommynta ta tabbata tunda musa yaga mamanta son daya kemata zai gushe saboda tasan yafison mommynta,yanzu zai zaba tsakanin *uwa da ýa*,lallai wannan baiyi tsari ba yanzu yaya zatayi. "Mommy ,daddy?", "Naam",suka ansa gaba daya , "Na fasa auren musa", "Meyasa feenerh",mommy ta tambayeta. "Saboda na tabbata musa baya sona kuma", "Feenerh,musa na sonki sosai", "Mommy amma nasan har yanzu bai manta dake ba ,ya taba cewa ina mai kama da wata kuma na tabbata ke yake nufi mommy", "Inkince musa bai manta dani ba zan yadda,amma inkince yana sona bxan yanda ba", "Meyasa mommy", "Saboda alokacin da muke bincike akanshi,mun gano cewa a rayuwarshi ba wanda yafi so kamar ki ,ko a gida in anaso yayi wani abu in har an ambato sunanki toh shikenan zai aikata ,waýenan dalilin kuma yasa daddy ya yarda ya aureki kuma kisani abinda yafaru tsakanina da musa bakomai bane illa yaranta ,duk mun girma kuma mun sami masu sonmu,yanzu haka daddynki shi kadai nakeso kuma na tabbata shima musa ke kadai yakeso,yanzu na yarda da batun faty na cewa *sai dai musa ya auri ýata*,lallai tafimu gaskiya datanan data gani ma idonta", "Ina ta tafi mommy", "Mun rabu tun a makaranta ,sun kona garinsu da zama kuma alokacin ba waya sosai saboda haka bamu samu numban juna ba", "Yanzu mommy kina ganin musa zai yadda ya aureni" "Ki tambayeshi da kanki,yana waje yana jiran in mun fita zai shigo", "Yana waje?", "Eh feenerh ,kisani nida daddynki muna sonki sosai kuma musa ma yana sonki sosai saboda haka dont make the wrong choice", mommy ta sumbace goshinta sannan suka fita. Tana daga ido taga musa ya shigo, "*D*", ya fa ďi a tsanyaye duk idonshi yayi ja alamun kuka yayi "Naam zauji", yayi murmushi, "Kin tabbata har yanzu naci wannan sunan", Ta girgiza kai alamun eh, "*D* wallahi na tsorata koda akacemin kina asibiti abinda nafara yi shine kuka saboda nasan duk *sanadina ne*, "Ba laifinka ba ne zauji", "Laifinane *D* ,banso insa kwokwanto a zuciyarki ba saboda ina bala'in sonki kuma batun ko in zaba tsakanin *uwa ko ýa* bai tasaso va saboda bazan iya rayuwa bake ba *D* wallahi ke nakeso kuma bazan iya manta ki ba *D* ki yafemin *D* dan allah ki yafemin", Feenerh ta fashe da kuka ,gaba dayansu kuka sukeyi daga karshe feenerh tace, "Nima bazan iya rayuwa batare dakai ba zauji,na yafemaka kuma nima ka yafemin saboda nasa ka zaba tsakanin *uwa ko ýa*", "Bakomai *D* evrytin is okay in love". Anan iyayensu suka shiga sannan akayi sulhu akacigaba da hira da wasa kamar kullum. *bayan wata ďaya* Ansa ranar auren su khadija da ja'afar ,da zarar sun gama exams ďin first semester 300lv za ayi kenan nan da wata uku. Rayuwar musa da feenerh tacigaba kamar da sannan yanzu soyyayar su yafi karfi saboda sun gano cewa dayansu bazai iya rayuwa batare da ďaya ba. Mommy da daddy sun tafi vacation a canada dan haka feenerh takoma gidansu khadija don tayata shirye shiryen biki tunda yanxo bikin ya gabato. *ranar auren khadija da ja'afar* Gaskiya wajen auren ya kayatu sosai kamar ba kasarnan ba komai white ne ,ango da amarya kuma suka sa white and red,gaskiya aure dadi saboda irin farin cikin da ja'afar yakeji ayanzu khadija tazama matarshi. "Dad i hope dai bazata kwace min kaiba", Khadija tayi dariya sannan tace, "Wai shi feenerh ,are you my friend or his's ", Feenerh tayi dariya sannan ta barsu taje cigiyar angonta. "*D*", Ta juyo ta ganshi abayanta , "Zauji kai nake nema", "Toh gani", "Kawai ina son in ganka ne", "Hmmm *D* watarana fa aurenmu haka za'a zo", Feenerh tayi murmushi. *tnx for reading....* *©Fareedah* *💟💟 UWA KO ÝA💟💟* *written by:Fareedah💚* *edited by :Aneelurv😍* *dedicated to my lovly mom😍* *pg 66▶70* *THE END* *AUREN MUSA DA FEENERH* Ranar taxo ,ranar da feenerh ke candy kuma ranar auranta ,lallai gaskiya ne da akace ranar aure ranar farin ciki ne. Ayau zata auri mosoyinta ,angonta wanda bazata iya rayuwa bashi ba Duk abinda yafaru a baya sun gushe,yanzu sabon rayuwa zasu bude na farin ciki da annashuwa. Mutane da yawa sun hallarci bikin ,su khadija,aunty ramat,aunty larai,aunty fati,*aneelurv* (best writer ďinta)duk sun zo wannan babbar bikin. Agaskiya ya hadu,talk of the town kuma har jaridu a buga. Anyi biki lafiya ,acikin koshin lafiya,duk waýenda suka halara sun koma gida lafiya. Ankai amarya dakinta hadadde wanda ke GRA,gaskiya su feenerh ansha kyau,anan na barsu susha amarci lafiya. *💟💟💟💟💟FEENERH LOVES MUSA💟💟💟💟💟💟💟💟💟* *ALHAMDULILLAH* _Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) dayabani ikon kammala wannan littafi lafiya._ *itx is a fiction novel,if your name is mention den please dont be offense* *JIN-JINA A GAREKI MY MENTOR:* *ANEESA ABUBAKAR RIMI(Aneelurv😍)* bisa namij k'ok'arinki don ganin wannan littafi yatsaru batareda kura-kurai ba,nagode Allah yasaka maki da alkhairi yaraya mana *Ayman* ameen. *GAISUWA TA MUSAMMAN GAREKU:-* *aneelurv novels* *mata adon gari* *galz are amazing* Da sauran duk wanda ban anbataba. *SADAUKARWA* _Wannan littafi sadaukarwa ce agareki mahaifiyata uwa tagari abun alfaharina maisharan kukana,ubangiji Allah yak'ara nisan kwana *My lovely Mom*_ *fadakarwa🎆👑* Littafin uwa ko ýa na magana akan relationship between ýa da uwa kuma yanda kawaye ke playing important role a rayuwar mutum,sannan so na asali. *ilimantarwa📑🎓* Wannan littafin ya taba kowani bangare na rayuwar makaranta da yadda take sannan ya nuna yadda ilimi keda mahimmaci a rayuwar dan adam. *Tnz alot for reading en we will meet again in my new book ..till den.* *Special greeting goes to u all ONLINE HAUSA WRITERS👍🏻* F-novels.blogspot.co.ke follow up for more write-ups. *©Fareedah* Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *