Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 23 May 2017

DANGIN MAHAIFINA

adsense here

[11/12, 2:30 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧 Na ZEE YABOUR Page 1-5 Ta bude idonta na ta ganta kwance cikin kurmumin daji,ta duba gabas da yamma banga kowa ba face iskan itatuwa dake kadawa Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ta fara fada,ta karanto kullakuzai sai a lokacin ta fara tuno abubuwan da suka faru ta da ita.Ta tashi jikinta duk ya mutu tana tafiya har ta kawo bakin titi,daga gani titi ne da matafiya ke wucewa.A bakin titi ta zauna ta dukar da kant kasa tana zubar da hawayen bakin ciki.Bayn mintuna kadan wata mota jeep prado tayi parking dai-dai saitinta.karar motar ce ta sata dagowa wata mata ta bude kofar ta fito cikin kasaita daga gani naira ta zauna mata.Ta karaso inda take ta dafata tace baiwar Allah me kike yi anan? Cikin kuka tace dama kin tafi kin barni na cigaba da zama anan har ranar da Allah zai dau raina na mutu na huta da wannan rayuwar dan banga amfanin zamana a duniyar nan ba.Haba baiwar Allh bai kamata kina fadar irin magangunun ba,ki tashi ki biyo ni muje gidana In shaa Allahu zan miki magani duk wata damuwarki da matsalarki indai bata fi qarfina ba.Murmushin takaici tayi tace baki da wata hanya da xaki bi ki magance mun matsalata da kawai kin tafiyarki.Ni kuwa bazan tafi na barki a wannan halina ba kina matsayin mace a gaskiya kina buqatar taimako dan haka kawai ki amince da buqata ta,cike da mamaki take kallonta tace ke yanzu a wannan zamani da ba'a yarda da mutane xaki ganni a titi ki dauke ni kice zaki kai gidan bakya tsoron wani abu ya biyo baya.Bana tsoron komai,Allah yaga xuciyata da nufin alkhairi xan taimaka miki kuma banaa fatan komai ya biyo baya sai alkhairi,a koda yaushe ana son mutum ya kyautata zato.Nan ta fara mata godiya.A'ahh ni ki daina gode mun Allh zaki yiwa godiya shi da ya hadu mu dan haka taso mu tafi kin ga akan titi muke.Suna ta shan disco a motar,da ya'yanta biyu mace da namiji.Ba mai cewa kowa komai har suka isa wani katafaren gida,maigadi ya bude get.Masu aiki suka fito suka fara kwasar kaya.suna shiga falo wani sanyin Ac ya daketa wanda rabon da taji irinshi har ta manta,matar ta umurci daya daga cikin masu aikin da takai baquwar guest room tayi wanka taci abinchi ta huta. Tafi 30minutes a toilet kafin ta fara wanka saboda tsabar bakin cikin da ke damunta.Ta da fito wanka ta tarar an ajiye mata sababbin kaya ta dauka tasa,ga abinci nan an ajiye mata kala kala da kayan tea,a ranta tana mamakin kirki irin na matar nan da daukota,ba abunda taji tana buqatar ci dan haka sallah ta kabbara,tana cikin sallah taji sallamar matar gidan,wuri ta samu ta zauna tana jiranta ta iddar da sallah.Bayan ta iddar tace ina wuni? Lfy lau,ya naga baki ci komai ba,wlh ji nake bazan iya cin komai ba,A'ahh ba zamy yi haka dake ba ko tea ne kisha Dan Allah zaki dan jin karfin jikinki,bata son yin jayayya da matar dan haka ta hada tea kakkaura ta sha.Yawwa ko kefa matar ta fada tare da yin murmushi. Toh ni dai sunana khadija abubakar,yar'gombe ce kauyen ashaka,ina zaune tare da mijina Adnan Buba anan kaduna,amma ya dan yi tafiya ne,shi ne muka je ganin gida a hanyarmu ta dawowa ne kika gan mu,Muna da ya'ya biyu Ashraf 6yrx sai Afra 4yrx,muna matuqar son juna ni da mijina kuma muna zaune lafiya.Toh!kinji takaitaccen tarihina ko zanyi jin naki.Wasu zazzafan hawayen suka dinga kwaranya daga idanunta tace labarina mai cike da tausayi ne,ban mamaki da al'alaji.khadija ta sauko daga kan gado ta zauna kusa da ita.Tace ina jinki......................... [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 6-10 Sunana Aysha wacce aka fi kira da basma.Alhaji Yusuf Mubi shine mahaifina asalinsa dan garin Adamawa ne kauyen mubi.Su biyar ne gidansu shine dan'auta,yayyensa basa son sa ko kadan sun dau tsanar duniya sun daura mai tun suna yara.Hamshakin mai kudi ne yana da gidajen mai,hotels,kamfanoni,gidaje da dai sauransu.Yana son yan'uwansa kuma yana taimaka musu duk lalurar su shi ke yi.Su hudu ne gidansu,Adda hajarah ce babba anan abuja take aure,sai hamma Ahijo shima nan yake zama anan daddyna ya samar mai aiki,Adda bongel itama anan abuja take aure,sai mahaifina shine na qarshe.iyayensu sun rasu.Mahaifiyata Awathif Sudais yar'asalin lebanon ce balarabiya ce gaba da baya,mahaifinta shi ne sarkin Yemen danginsu nada arziki sosai,Mahaifina yaje aiki can yemen aka sauke shi agidan sarkin yemen a can suka hadu,bai sha wata wahala ba wajen samun soyayyarta ba bata lokaci aka yi aurensu ya taho da matarsa nigeria.Lokacin da ya zo da ita nigeria sai da abun ya zama tsegumi tsakanin yan'uwansa amma duk ya toshe kunnensa.Suna matukar son junansu shi da mahaifiyata.Mu biyu kadai suka haifa Ya safwan 25yrx yana baze university Abj final year sai ni ss3 a el-amin international school.17yrx.Iyayenmu na matuqar son mu duk abunda muke so,shi ake mana tun bani ba.Rayuwar gidanmu an gina tane a bisa soyayya,kaunar juna da tausayawa juna tsanta.Na dawo daga scul,na tarar da momyna zaune a falo na fada cinyarta ina cewa momyna oyoyo.oyoyo babyna ya scul din,lfy lau momyna ina dadyna da Ya safwan,Daddynki bai dawo ba but i knw ynz zaki ganshi ya dawo cin lunch,shima safwan nasan duk inda yake ynx yayo hanyar gida.ohh!ya safwan sarkun yawo ba'a iya zama in banda abunki kin taba ganin inda namiji ya zauna gida.shi dai na ya safwan yayi yawa,bari inje in cire uniform.Kowanne abinchi tare muke ci mu duka akan dining table duk inda mutum yake idan lokacin cin abinchi yayi toh dole mutum ya dawo gida,ko daddy duk aikin da yake dashi da lkcin cin abinchi yayi sai ya bar aikin ya dawo gida.Bayan na watsa ruwa wadrobe dita na bude ina tunanin kayan da zan sa doguwar riga na jawo dinkin dubai nasa.na fesa turare dama akwai ni da son turare da kwalliya na sauka kasa.ina saukowa naji ana knocking a kofa nasan daddyna ne da gudu naje na bude kofar daddyna sannu da xuwa,yawwa babyna ya scul? Lfy lau daddy.ya riqo hannuna muka karasa parlour.Au ya safwan dama ka dawo.Au baki ma lura dani ba sanda kika sauko daga kasa.Allah banga ka ba.momyna tace ina fa zata ganka hankalinta na can wajen daddy.Ai nayi fushi,na langabe kaina nayi fuskar tausayi haba!my one en only bro Am sorry.Mmmm....su lil-sys an iya fuskar tausayi idan anyi laifi toh na haqura ba don halinki ba.Yawwa cwt bros.Muka yi dariya,muka nufi dining table.Ni nayi serving kowa dama kullum nike serving,mukayi addu'a bayan mun gama ma mukayi addu'a.Da daddy zai koma office har mota muka raka shi,muna dagawa juna hannu haka muke yi kullum.......... [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👧 NA ZEE YABOUR PAGE 7-8 A parlour kwance kan cinyar momyna,nace momyna tace na'am babyna,wallahi ni kam ina mamakin masu kai ya'yansu boarding kamar basa son su,ba rashin so bane babyna boarding na gyara yaro tana koya mai zama da mutane daban daban da rayuwa ai kema university hostel zamu kaiki,na tabe baki alamun kuka tabb!! Wlh ba zan yarda ba.Momyna ta kyalkyace da dariya tace wa isa ya rabani da babyna ma mai raba ni dake nima wasa nake miki ai ko kwana daya bazan iya yi ba ba tare da na ganki kusa dani ba.Nayi dariya nace nima haka momyna.Daddy ne da Ya safwan suka shigo tare.Daddy yace me ake tattaunawa ne bamu?? Daddynq wai momy ke cewa zan koma hostel idan na shiga uni.Inaaaaa!!!wannan zancen banza ne itama ta fada ne kawai taji dadin bakinta.Ya safwan yace tab! ai na tabbata da ranar ba mai ya barci a gidan nn,tunda muke fa ba wanda ya taba tafiya ko na kwana daya ba tare da saura ba,Mummy tace Allah dai ya barmu tare Mu duka muka ce Ameen.Ni,mummyna da Ya safwan muna zaune a falo muna kallon wani indian series "Silver lining"Muka ji an bankadu kofar falo ko sallama babu har munji tsoro ashe Adda hajarah ya'yar daddyna.Ina wuni?muka gaisheta,da ban wuni ba da zaku ganni Ina yusuf din yake,nace yana office,ke me shegen bakin ke na tambaya da uwarki nake ko bata da baki ne.momyna tace yana office kamar jira take tayi magana ta hau masifa sai yanxu kika ga damar bani amsa,dama baki da aiki kullum yana office ko yana barci,kin hana kowa ya rabe shi daga ke sai ya'yanki zaki gane kurenki idan taqamarki asiri,Ta wuce fuuu kicin ta bude fridge tana kwasar kaji,ta dau katon din drinks uku dama haka suke yi duk suka zo gidanmu,momyna bata ce mata komai ba har ta gama ta bar gidan,duk abunda zasu yi ma momyna bata taba bude baki ta rama tana girmamasu sosai,momyna na da haquri sosaii.Tana fita ni da Ya safwan muka fara ba momyna haquri,ba komai kar ku damu nima abun bai dameni ba inda sabo ai ya kamata mu saba da halinsu dan haka bana so abun nan ya taba damunku,kuma ku cigaba da girmamasu a matsayinsu na yayyen mahaifinku watarana sai labari Addu'a shine naku.Ni kalmar munafukar da suke ce miki momy ita take bata mun rai.momyna tayi murmushi tace Zagi na fitowa a jikin mutum ne,na girgiza kaina alamar A'ahh toh dan haka kada wannan ya taba damunki nace toh momyna.Kuma ina so kada ku gayawa daddynku abunda ya faru kunga in yaji ba zai ji dadi ba.Muka ce toh momy In shaa Allah.Yawwa Allah yayi muku Albarka,Ameen. Irin shawarwarin da momyna ke bamu shi ke sa in kara sonta. Haka muka cigaba da rayuwarmu cikin jin dadi,so,kauna da kwanciyar hankali,makota da duk wandanda suka san mu sha'awar rayuwarmu suke,suna cewa kafin a samu haka da wuya.Akwai ranar da na dawo school lokacin muna mock bana samun isasshen barci kullum karatu,kaina na masifar ciwo,na leka dakin momyna tana sallah sama na nufa dakina uniform kadai na cire,nabi lafiyara gado barcin kasa yin shi nayi saboda kaina dake masifar ciwo.Shiru-shiru momyna bata jini ba ita a tunaninta ina school.Ya safwan ya shigo yana tambayar wai ina lil-sys ko bata dawo daga school bane,wlh nima shiru nake jinta amma bari na tambayi masu aikin nan Larai!! Na'amm hajiya,basma bata dawi daga school bane ta dawo tun daxu,bari in duba dakinta ko lafiya ya safwan ya biyo bayanta,da sauri ta qaraso inda nake ganin na qudundune cikin bargo,ta yaye bargon lafiya babyna,ta taba kaina zafi rau idona sunyi jawur,me ke damunki babyna kaina ke ciwo,shine baki sanar dani ba babyna tashi mu tafi asibiti,ita da ya safwan suka kamani.Muna xuwa,muka samu ganin likita,bayan ya mun wasu tambayoyi ya rubuta mun drugs,sannan ya buqaci muyi exchanging contacts wai ko da wata matsala ta taso sai in kira shi ba musu na bashi numbernta,ya bani card dinshi yace akwai numbers dinshi a jiki.Muka koma gida a hanya aka tsaya aka siyanmu drugs da chocolates coz dama ni mayyar chocolates ce. Dr.Muhammad Bashir wanda ake kira da Dr moha shine likitan da ya duba ni,likitan da ya amsa sunansa likita.Mahaifinsa Bashir mai taya dan asalin garin kano ne kauyen shanono,shine minister of agriculture,mahaifiyarsa Binta yar'adamawa ce,Su uku iyayensu suka haifa shine babba sai kannensa mata Nabila 15yrx da nusaiba 7yrx.Kyakkyawa ne fari,dogo,ga hanci,saje da dan qaramin bakinsa infact kawai ya hadu yana cikin jerin maza ajin farko boko da arabiyya ba inda aka barshi a baya,Yammata na daye masa.Dan kimanin shekara ashirin da bakwai da haihuwa.Yayi karatunsa a Egypt.Bayan ya dawo ya fara aiki a wata private hostipal anan abuja,bai cika zama asibitin ba kuma asibitotoci da yawa na daukarsa aiki su biya shi kasancewarsa kwararren likita ne kuma yasan kan aikinsa amma yafi ba da muhimmanci kan harkar business,Yau ma suka hadu da basma yaje asibitin kenan sun kira shi zai duba wani mara lafiya,sai ya hango basma kuma yaga alamar bata da lafiya shine yace musu yau shi zai duba duka patients din da aka kawo yace haka dan kar yace zai duba basma ita kadai suyi suspecting wani wani abu ba,ba qarami mamaki suka yi ba da yace haka Dr moha da a rana idan ya duba mutane da yawa to biyar ne amma yau shine mai cewa zai duba duka patients yayi hakane don kawai ya samu damar kebewa da basma.ko da muka koma gida har daddyna ya dawo ba qarami tashi hanklinshi yayi ba jin cewa bani da lafiya ya rungumeni yana cewa babyna ya jikin naki? Da sauqi daddyna.Su dukansu suka rakani dakina momyna ta lullubeni da bargo suka mun sai da safe.Ranar basu ci abinchi dare ba saboda bani da lafiya.Daddyna yace ina tausayawa basma,Ya safwan yace ji nake kamar na mayar da ciwon a kaina,momyna tace wlh ko qoda bana son inga ya taba mun basmata.Daddy yace Allah dai ya bata lfy.Suka hada baki Ameen..................... [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👪👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAFINA👨‍👨‍👦👨‍👨‍👧. PAGE 13-14 Har karfe 12 na kai ina barci nayi wanka na sauka kasa.Ranar weekend ne daddyna yana gida a parlor na same su su duka,suka hada baki ya jikin ki? Naji sauqi Tun dazu ke muke jira muyi breakfast na zaro ido baku yi breakfast ba,daddy yace banda abunki ya za'ayi muyi breakfast bakya nan nayi murmushi ba tare da nace komai ba.Bayan mun gama breakfast na zauna tsakiyar momyna da daddyna na daura kaina a kafadar daddyna muna hira,momyna tace uhmmm babyna sarkin son jiki,kyaleta inbata hau jikina ba jikin wa zata hau mukayi dariya.Daddyna yace yawwa babyna yaushe xaku yi hutu,next week Dama ina so muyi tafiya ne wacce kasa kuke so? Ya safwan yayi saurin cewa London na tabe baki nace wanne irin London kuma ko wancan hutun fa can muka je muje turkey mana tunda bamu taba xuwa ba,Yawwa can zamu babyna Ya safwan yace uhmm lil-sys burinta ya cika ni bana gajiya da xuwa London,kasar kawai tamun dan kawai bazan iya rabuwa daku bane da can zanyi karatuna,daddyna yace ai kuma kana so bazan kai kaba kana nan tare damu ba mai raba mu sai mutuwa,mutuwar kanta da ina da hali da sai ince ta daukemu lokaci daya,momyna tace Allah yasa mu cika da imani muka amsa Ameen.Jikina yayi sanyi ina tunanin ranar da zamu wayi gari ba daya daga cikinmu bansan irin halin da zamu shiga ba ,a raina ina roqon Allah yasa na riga su mutuwa.kirar sallar da muka ji yasa kowa ya tashi ya nufi sallah. Wayata kirar IPhone 6+ tayi ringing new number ce nayi receiving Assalamu Alaikum wa'alaikissalam ina wuni?lfy lau ya jikin naki? Lfy,Alhamdulillah sai dai ban gane mai maganar ba,ohh kinji sauqi shiyasa ba zaki damu kisa numberta a phone dinki ba toh!Dr.Moha ne,ohh! Allah sarki wlh ba haka bane Ya aiki? Ba wani aiki pha sai aikin tunaninki,Tunanina kuma? Yeah of course kinsan mu Doctors bamu da wani tunani da ya wuce na patients dinmu,Allah sarki ai kuna qoqari Allah kadai ne zai biya ku,Ehh hakane sai da safe dama na kira ne naji lafiyarki duk sanda kika ji wani pain u can call me ba sai kinje asibiti ba in ta kama har gida sai inzo feel free wif me am ur bro ohkay! Olryt!tnx alots,no need byee.Na ajiye wayar ina tunanin kirki irin na Dr moha ni dai yana burgeni tun jiya da muka hadu ban ankara ba naji na fara tunaninshi naja tsaki a raina nace why zan dinga tunaninshi na bude fridge din dakina na dauko drink na jawo system dita ina operating but jefi-jefi Dr.moha na fado mun a rai. Da daddare har nayi shirin barci naga kiran Dr.Moha shi kuma lafiya yake kirana by diz time.hello! Ya kike? Lfy lau ,Yanzu dai kin gane mai magana koh,ba Dr moha bane,au kina ma doubting kenan,no ai nayi saving number kuma ko banyi ba zan gane ta voice dinka ohh!really Yeah,but naji dadi sosai,na kira ne dama naji lafiyarki da muryarki,muryata kuma Dr,Eh mana baki san duk wanda yaji voice dinki sau daya ba zai so ya kara ji a karo na biyu,hmm Dr kenan ,Eh mana,ni dai sai da safe har nayi shirin barci,kin gaji da jin cracking voice dina ko gashi ni kuma ban gaji da jin sweet voice dinki ba but sai da safe kar na takura miki no ba haka bane am sleepy,ba wani nan gudnyt tek kia, bye tanx.Na kashe wayar tare da jin kalaman moha na mun wayo a kunnena haka nai barci da tunanin Dr a raina.kullum sai munyi waya da Dr moha kusan sau 5 a rana,kalaman da yake gaya mun suke qara sa naji ina son shi a raina duk da cewa bai furta mun yana sona ba but alamunsa son nuna har su momy sun san Dr.moha bani da labari sai nashi. Mun gama mock an bamu hutun 3weeks kafin mu fara waec,Daddyna yana ta muna shirye-shiryen tafiyarmu turkey,Dr Moha yace yana so yazo gidanmu akwai wata magana da zamu yi,Ranar farin ciki ba'a magana wajena,da kaina na shiga kitchen na hada mai abinchi kala-kala da pineapple en coconut drink,mango juice da snacks.Bayan la'asar mukayi dashi zai xo ina iddar da sallar la'asar na shiga toilet nayi wanka na saka riga da skirt atamafa(super) dinkin charas dai dai ni na zauna kan dressing mirror ina tsala dama gani gwanar kwalliya,ranar ni kaina nasan nayi kyau, Ah!Ah! Wannan kwalliya haka babyna ko dai dashi za'ayi ne inji daddyna kunya ta kamani na fada jikin momyna ina rufe fuskata ni dagani mara kunya Ya safwan yace umm...lil-sys an kai ga miji,Gafara can ai gwara ita da kai,gaka nan har yanxu ka qi samun mata,no daddy ina so ne sai na gama service In shaa Allah,hmm! Allah ya nuna mana Ameen daddy Falon baqi na sauke Dr.moha tunda na shiga yake kallona kunya ta kamani na samu wuri na zauna masu aiki suka shiga kawo mai abubuwan motsa baki.Yace basma kinga kyan da kika yi kuwa? Ina fatan dai wannan kwalliyar ni aka yiwa na gyada kai alamar ehh!,Ya wani lumshe ido yace kai amma naji dadi kuma nagode sosai sai ki gyara in miki pic ko,kunya ta kamani na dukar da kaina kasa Yayi murmushi yace yau ni ake jin kunya kuma duk surutun da nake sha a waya,murmushi nayi nai qarfin halin cewa ga abinchi nan dan naga bashi da niyyar ci kuma har ga Allah idan bai ci ba baxan ji dadi ba saboda yadda na dage na girka shi.Yayi murmushin dake qara mai kyau yace wa ya dafa? Nace ni ce yace are yhu sure? Yeah To zuba mun inci inji ko kin iya girki yadda ake cin abincin kanshi ba qaramin burgeni yayi ba a natse,kaii!! Infact ni dai komai nashi burgeni yake.Ya ajiye plate din yace uhmmm...gaskiya kin iya girki delicious!! Har cikin raina naji dadin yaba girkina da Dr yayi.Basma ya kira sunana cikin sanyin murya sai naji dadin kiran a kunnena,Na'am na amsa cikin lallausar muryata.Ya lumshe ido wanda hakan ke qara burgeni game dashi Basma tunda na ganki a asibiti naji zuciyata ta kamu da sonki ina so in kasance tare dake har qarshen rayuwata kece wacce nake burin aure,basma ina sonki ina son komai naki kyanki,maganarki,natsuwarki,surarki infact everything ki taimaka ki amince dani i promise to be the best husband ever,i 'll always be with u,i'll never ever betray you i promise.Wani farin ciki naji ya lullubeni kamar nayi ihu dan dadi Yau Dr.Moha ya furta yana sona abunda na dade ina jira ina addu'a kullum,Amsarki nake jira kusan 15min ba wanda yace komai,Ya miqe tsaye to ni zan wuce na lura kunya kike ji,plz ina jiran amsarki ko ta txt mssg ne but plzzz a taimaka a mun adalchi Ya fito da wata yar'qaramar leda daga aljihunshi ya ajiye a kujera ga wannan.Yana fita na hau tsalle ina murna na bude ledar perfurm ne a ciki designer irin na 30k da zobe cikin case dinshi yana shining.da sauri sauri gudu gudu na shiga babban falo momy momy Dr.Moha yace yana sona zai aureni kinga abunda ya kawo mun,Momyna mamaki da tsoron Allah ya kamata wannan irin murna da nake haka tunda take dani bata taba ganin ina murna irin haka,to ke wacce amsa kika bashi,cikin shagwaba nace kunya nake ji bance masa komai ba momyna ta kyalkyace da dariya tace su babyna ansan kunya Allah ya kawo mu zamani,Daddyna ya fito daga dakinshi yana tambayar me ya faru? Momyna ta sanar dashi komai,Yayi dariya yace in har da gaske yake ai sai ya turo iyayensa,Haba!daddyn basma kamar dai mun gaji da ita A'ahh ba ina nufin aure zan mata yanxu,bana so ya'ta na tsayawa da samari ne kinsan yadda zamanin nan,idan har zan bar ya'ta tayi soyayya toh da wanda zata aure ne manya suka sa baki bana son shashancin soyayyar nan da bata dorewa wacce ke karewa akan titi,Eh da gaskiyarka dan zamanin nan namu sai shiriyar Allah ba yan'matan ba ba samarin ba sai wanda Allah ya shirya. Dakina na koma ina ta murna sai ga kiran Moha yake cemun ya kira ne yace mun ya isa gida lafiya kuma yana jiran amsar sa.Soyayya mai qarfi qullu tsakanani da Dr.Moha kullum sai yazo gidanmu kuma ko da yaushe muna cikin waya,Ya barshi sai mun dawo daga turkey zai turo iyayenshi............ [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 15-16 Ana gobe zamu tafi,Daddyna yace mu shirya muje muyi wa su Hamma Ahijo sallama.Gabana ba qaramin faduwa yayi ba dan nasan lokacin da zamu tarar ni nama fi jin momyna dan bana son bacin ranta ko kadan. Muka shirya,Ya safwan ke driving daddyna a gefenshi,ni da momy a baya.Gidan Hamma Ahijo muka fara xuwa kananan yaranshi muka tarar a falo suna kallo,daddy yace su kira babansu,matarshi ta fara fitowa da far'arta Ah! Su Alhj Yusuf ne a gidan namu muka gaisa da ita ta kawo mana ruwa da lemo,Hamma Ahijo ya fito fuskar nan tasa a murtuke da na ganshi sai da gabana ya fadi, Ina wuni? Muka gaishe shi da ban wuni ba da zaku ganni,Daddyna cikin ladabi yace dama mun xo yi muku sallama ne zamu yi wata yar'tafiya Ina zaku hala? Turkey,Aikin kenan yau ba ku wannan kasa gobe baku wancan kasa mu kuwa daga saudia sai saudia kanka kadai ka sani sai iyalanka Allah wadai da hali irin naka,Da daddyna yaga fadan ba mai qarewa bane ya zaro dubu dari ya bashi ya qarba ba kunya ba tsoron Allah daddy yace kayan abinchi na nan xuwa gobe,ba godi balle nagode sai wani huci yake kamar ya ba daddy ajiya,Matarshi kadai ta rakomu tana godiya.Gidan Adda hajarah da Adda bongel suma haka suka zabga mana nasu wulaqancin,kowaccensu sai da daddy ya bata 50k,ba wacce tayi godiya cikinsu,nuna sukayi ma kamar sun raina. Haka muka dawo gida ina mamakin hali irin na DANGIN MAHAIFINA wacce irin tsana ce haka uwa daya uba daya na dau alkawarin idan muka dawo zan tambayi daddy dalilin wannan kiyayyar ina cikin wannan tunani moha ya kirana muka sha waya muna bayyanawa juna irin kaunar da muke wa juna. Hadda shi aka rakamu airport da qannenshi naby da nusy kamar zamu yi kuka da zamu rabu dan kowannenmu sai da yayi kwalla.Mun sha hutu a turkey munje wurare daban daban hadda wajejen tarihi [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👧 NA ZEE YABOUR PAGE 17-18 Daga turkey muka wuce Yemen sun tarbemu hannu bibbiyu suna ta murna da xuwanmu,Yan'uwa kowa sai xuwa yake yana gaishemu a raina ina cewa ina ma ace haka DANGIN MAHAIFINA suke da bani da wata matsala a rayuwa.Kwanan mu biyu Yemen muka dawo 9ja.Moha har airport yazo tarbonmu motar shi na shiga xuwa gida,basmata nayi missin dinki sosai,ba kai kadai ba har kagawa nayi na dawo 9ja saboda kai,hmm! Baki kaini ba ba kiga har ramewa nayi ba kullum tunaninki ba ni da wani aiki.Toh Yanzu dai gani na dawo,Jiya banyi barci ba ina ta Alla-alla gari ya waye Basma i really luv yhu,i luv you too my moha haka muka cigaba da hira har muka isa gida.Akwati guda nayi wa moha tsaraba,akwati guda ta systers dinshi da yazo the next day na bashi shi kuma yazo kawo mun kayan success zamu fara Waec ranar monday,Gidanmu kowa ya bani abun success.Daddyna yayi promisin dina idan results dina yayi kyau zai mun babbar kyauta,Nace daddyna mai zaka bani,A'ahh babyna sai results din ya fito.Yawwa daddyna dama ina so in tambayeka,ina jinki babyna,Wai me yasa su hamma Ahijo suka tsane ka haka.Daddyna yayi murmushin takaici yace baby kenan,ba wani abu bane illa son da fifiku da iyayenmu suka nuna a kaina fiye dasu,lokacin iyayenmu na da rai sun fifita ni saman yan'uwana komai ni kasancewar nafi so ladabi,biyayya da qoqari,kowa sona yake duk inda na shiga shine abun ke baqanta musu rai wasa-wasa abun har ya zama tsana ko wasa basu yi dani balle suci abinchi dani sai dai inci abinchina ni kadai,mahaifinmu na tsawata musu a gaban idonshi sai su nuna suna sona bayan idonshi su dinga gallaza mun har Allah ya dau ranshi abun sai yayi gaba dan dama basa jin maganarta,tayi tayi ta shirya mun amma abun ya faskara har ta rasu.Tun ina primary nake karbar scholarship har na gama university da first class,na samu aiki a wani company a matsayin accountant ina nan har Allah ya mun arziki na gina nawa na kaina haka arzikina ya dinga habbaka.Ganin haka yasa suka qara tsanata,hassada ta cika musu zuciyoyinsu,amma ni ko a lokacin ina qoqarin kyautata musu har ila yau kuna gani ya qarasa maganar da kwalla a idonsa,Dukkanmu sai da kuwa yayi kwalla saboda tausayin daddyna ace yan'uwanka uwa daya uba daya sun tsaneka mai ya kai wannan baqin ciki.Daddyna yace bana son haka bana gaya muku bane dan ku tada hankalinku a'ahh sai dai ku sani kada rai yayi halinsa in barku cikin duhu kuna neman mai gaya muku,dan nasan baza su taba gaya muku gaskiya ba,idan kuna tunanin bani da kowa bagaku ba wlh kun ishe ni zaman rayuwar duniya kuma ina da abokan arziki abunda nake so shine ku riqe zumuncinku dasu kada ko bayan raina kada ku taba yanke zumunutar ku dasu saboda duk wanda ya yanke zumunta Allah zai yanke sa daga rahamarsa.In shaa Allahu daddy muka amsa gaba daya Yawwa ku tashi ma mu tafi park yayi hakane dan ya kawar mana da tunani. Mun fara examz bani da lokacin kowa,moha ma bai fi muyi waya dashi sau 1 a rana ba,duk ya kosa in gama examz haka yan gidanmu dan yaxo wani zama cikinsu yanxu. A Kwana a tashi ba wuya a wajen Allah yau na kammala jarabawata,ranar farin ciki wurin a,yan gidanmu da moha ba'a magana dan dama bazan yi NECO ba.Ranar da daddare Dr.Moha yazo.Nayi wanka na tsala kwalliyata.Shigar da yayi yau jikin jeans da wata polo shirt ga ganshi kanshi da ya kwanta lub-lub sai walkiya yake yayi masifar kyau,kamshin turarenshi duk ya game falon.My luv i really miss you diz dayz da kina examz bana jin muryarki sosai ballatana infa kyakkyawar fuskar nan taki,i miss yhou too ha coz kullum kana raina dake nake kwana nake tashi,Wlh nima haka my luv har sai da Ammi(mahaifiyarsa) tace ko dai mutuwa basma tayi ai iyakar shiga damuwar kenan gida da anga na dan yi shiru za'a ce basmar ce koh,Allah sarki Ammi ya kamata na kira na gaisheta kwana biyu ban kirata ba but nusaiba da nabila kullum sai sun kirani mun gaisa.Ai ni nace musu duk ranar da basu kira ki sai na zane su infact ma dai gidanmu kuwa na sonki nasan ko bance su kiraki basu kira nayi dariya nace haka kaima kowa gidan nan ke sonka.Allah ya tabbatar da alkhairi my luv Ameen dear,Anyway jibi su Abba zasu zo.Allah ya kawo su lafiya Ameen,Ni zan tafi dare yayi,na kalleshi cikin sigar so nayi fuskar tausayi ko bakya so in tafi ne,na daga kaina alamar ehh!! Sorry my luv dare yayi 11:40 fa,toh! Gudnytt ina gaida systerx dina zasu ji.Har motarshi na raka shi na dawo cikin gida momyna na shirin shigewa daki,Uhmm...babyna sarkin soyayya hala ya tafi ne,na rufe fuskata na haye nayi shirin barci na jawo pillow na rungume ina tunanin moha son shi na ratsa dukkan sassan jikina.Na sanar dasu daddyna xuwansu Abban moha.An tarbesu hannu bibbiyu cikin qaramci da mutuntawa,abinchi iri-iri,su pepper chicken duk aka musu,Iyayen sun amince da zance aurena ni da moha an barshi nan da shekara daya.Miliyan daya suka bayar da goro,sweets,chingum,drinks da atamfofi wai duk kayan an gani ina so.Sunji dadin karramawar da akai musu moha har kirana yayi yana mun godiya nace ai nice da godiya.Su momyna sunji dadin kayan da iyayen moha suka kawo an kaiwa su adda bongel hadda kudi kowannensu dubu dari sunyi baqin ciki sosai dan ga ya'yansu nan duk sun girmeni ba wacce aka taba xuwa neman aurenta suka dinga tsegumi wai kudi muka gani,duk da cewa ba abunda su moha zasu nuna mana.Soyayyar mu da Dr.moha kullum qaruwa take har nusaiba da nabila ke xuwa gidanmu su wuni in yazo da daddare ta tafi dasu.Ranar wata laraba bazan taba mantawa ba daddyna ya taramu Yace ina so ku natsu,ku fahimceni kuma kuyi haquri nima ba'a son raina haka ta faru ba,A tsorace nace me ya faru daddy? Kuyi hqr wata tafiya ta kamani unexpected xuwa india,Ya safwan yace why baza ka damu ba daddy kasan baka saba tfya kai kadai ba muma bamu saba zamq ba tare da kai ba,Nasan da haka safwan tare da wasu manyan mutane zamu yi tafiyar,wlh nima bazan ya tafiyar nan zata kasance mun ba dan wani iri nake ji game da tafiyarnan gashi ta zaman mu dole,kwalla naji sun cika mun ido nace Allah yasa haka yafi zama alkhairi Ameen.Ranar gidanmu ba mai walwala wannan ita ce rana ta farko da na fara ganin haka, The next day muka raka daddyna airport muna ta hira kafin su tashi Yace babyna me kike so in siyo miki ,Chocolates Yanxu ke babbyna ki rasa abunda xaki ce sai chocolates,Ai duk nafi son shi,suka kyalkyale da dariya ina ganin daddyna ya tashi zasu wuce na fara kuka ya rungumeni yana lallashina kiyi shiru babyna ba dadewa xnyi ba ina so ki kasance yarinya mai haquri da juriya,ki daina kuka idan bakya so in tafi da bacin rai,nai saurin goge hawayena,momyna ma sai da tayi kwalla Ya safwan ta maza kawai yayi amma shima kamar zai yi kuka muna ta dagawa juna hannu har ya shige cikin jirgi.Haka muka koma gida kowa rai baci,wurin kwanciya kowa ya nufa.Ina tashi da aafe na fara tambyar momyna daddy bai kira ba tace bai kira ba ina ga aiki ne ya mai yawa,Wlh momy am eager naji muryar daddyna,nasan zai kira da ya samu sukuni,Ya safwan ji nake kamr yayi sati da tafiya nace kai dai bari kawai Ya safwan,muna ta hirar missin daddy da muka yi just for a day phone din momy tayi ringing toh ga daddynku dinku nan,na daka tsalle nace ni zaki fara ba momy.Ta dauka hello!dear Please am i speaking to the family of Alhj Yusuf mubi,Yes,Sorry to say he had an accident after he have arrived yesterday on dia way to mumbai so he is death.Daddy ya rasu kalmar da naji momyna ta fada kenan ta fadi sumammiya,kamar tsawar aradu haka naji kalmae a kunnuwana nima sai na bita.KULLU NAFSEEN ZA'IKATUL MAUT😭😭😭😭😭😭,INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN Dadyn basma ya rigamu gidan gaskiya.Toh! Masu karatu sai ku biyoni dan jin ya. rayuwar iyalan Alhj Yusuf mubi zata kasance tun ba yar'lelensa basma......A gaskiya na tausaya musu......... [3:42pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 19-20 Kuka ne yaci qarfinta ta kasa cigaba da labarin,Khadeeja itama kukan take,Suka tashi suka yi sallah dan a lokacin magrib tayi sannan suka dawo suka zauna dan cigaba da labarin.Khadeeja tace ina jinki basma ya rayuwarku ta kasance daga wannan lokaci,Basma ta goge hawayen dake zuba a fuskarta ta cigaba:Kan gadon asibiti na tsinci kaina Nace ashe ma mafarki nake daddyna bai rasu ba amma me ya kawo ni asibiti? Ba mafarki kike ba Allah ya yiwa Yusuf rasuwa inji Adda bongel nan na fara kuka ina ihu wallahi bn yarda ba,daddyna bai rasu ba Daddy! Daddyna dan Allah kazo in ganka Plzzzzz daddyna kar ka tafi ka barni.Adda bongel ce ta daka mun tsawa Dallah ki ma mutane shiru duk kin cika asibiti da ihu,kanki aka fara rasa uba ,ya riga ya tafi baxai taba dawowa ba Har abada HAR ABADAAA HAR ABADAAAAA naji ya mun yawo a qwaqwalwata wani ihun na saki mai qara ita kanta Adda bongel din sai da ya gigita ta,Da gudu Dr.Moha ya shigo dakin a rude a rungumeni jikinsa kyam kamar wata matarsa,Yar'sa ko qanwarsa shima qwalla yake Yace kiyi haquri basma Allahn da ya qarbeshi yafi mu son shi,Moha da gaske daddyna ya rasu haquri zaki yi basma Wani ihu na qara saki Wayyo Allah! Na shiga uku shikenan na rasa gatana me yasa daddyna ka tafi ka barni bazan iya rayuwa ba mutuwa zanyi Daddynaaa........Numfashina ya dauke na sume.Hankalin Dr.Moha ya qara tashi duk ya rude yama rasa ta ina zai fara kuka kawai yake kamar wani qaramin yaro tausayina duk ya kamashi,wasu doctors ya kira suka yo kaina dan ceto rayuwata,bayan na farfado aka mum allurar barci.Daga momyna har Ya safwan duk an kwantar dasu anan asibitin,momyna bata aiki sai sumbatu da koke koke,gwara Ya safwan shi ya dan yi qarfin hali.Na dau awanni ina barci kafin in farfado,Ina tashi na tuna daddyna wani sabon kukan na dasa ni kadai a dakin ina ta magana ni kadai shikenan daddyna ya tafi ya barni bazan sake ganinshi ba in hau jikinsa in mai shagwaba in gaya mai damuwata,Wayyo ni Allah na rasa gatana ashe rabuwar qarshe muka yi dake daddy Allah ya jiknka yai maka rahama ina ta kuka kamar raina zai fita Dr.Moha ya shigo idonshi jajir daga gani yasha kuka,ya zauna kusa dani yana share mun hawaye da handkercheif kiyi haquri basma INNALLAHA MA'AS SABIRIN ki daina kuka Addu'a yafi cancanta ki masa ba kuka ba,nasan mutuwar uba na da daci sosai ballatana ke yadda kika shaqu da naki amma haqurin nan shi zaki yi da juriya.Ina momyna da ya safwan? Duka sun nan asibitin Ina son ganinsu ki bari anjima zanzo muje tare.Adda bongel tunda na ganta sau daya ban qara ganinta ba ko wani DANGIN MAHAIFINA.Shiru shiru banga Dr.Moha yaxo ba har na fara jin barci a raina ina cewa Allah yasa ba wani abu ya samesu yake boye mun ba a hka nayi barci wata nurse ta tayani kwana.Can cikin dare na tashi nayi sallah ina roqawa Daddyna rahamar ubangiji na kuma roqi Allah ya bamu ikon dauriya da jure rashin Daddy da muka yi nan na zaune ina karanta surorin da na haddace har safiya,naji sanyi a zuciyata radadin da nake ji ya rage sosai.Gari na wayewa sai ga Dr.moha ko kallon inda yake banyi ba,ya duqa gabana yace nasan nayi laifi kiyi mun afuwa,bana so na kai ki ne a yadda kike jiya kuka ga juna hankalinku a qara shine na yanke shawarar na bari sai kin samu natsuwa.Alhamdulillah! Naji dadin ganinki a haka,jiya at all banyi barci ba infact a asibiti nan na kwana ban shigo wurinki ba dan kar kice dole sai na kai ki wajensu,Toh! Ni dai yanzu tashi muje.A dakin da momyna take na tarar da Ya Safwan duk ya rame ya fita hayyacinsa,Jikin momyna na fada ina kuka Dr.moha kasa tsaywa yayi ya fice,itama kukan take yi shiru basma ba kuka ne namu ba,addu'a tafi dacewa mu riqa yi mai.Ya safwan yace munyi dai babban rashi yanzu bansan wa zai jagoranci al'amuranmu dangin daddy basa sonmu sau daya suka zo asibitin nan.Momyna tace Allah dashi muka dogara yana sane damu.Ya safwan ta miqe zan tafi nasan an kusa isowa da gawar daddy don jiya da daddare suka ce an sako ta jirgi toh!safwan a dawo lfy.Ni kam kuka kawai nake,Basma kukan naki yana qona mun rai bana son kukan ki,Dan Allah kiyi shiru,Mu rungumi qaddara,hakanan na gimtse kukan da nake zuciyata na mun zafi.Da Ya safwan ya dawo yake sanar damu daddy ya samu mutane sosai kuma duk wanda ya bude baki alkhairi yake fada akan daddy,Allah sarki daddyna ya riga mu gidan gaskiya.......Ranar tare da momyna muka kwana nayi shimfida a kasa babu yadda Dr.Moha bai yi ba na koma dakin da aka bani kar na kwanta a qasa naqi,abun mamaki shine momy ko tashi bata iya yi daga kwanciya sai kwanciya.Dr.Moha yace gobe za'a mata x-ray dan gane me ye matsalarta.Washegari na zaunar da momyna ina bata abinchi a baki,Ya safwan na zaune gefena kan kujera,Dr.Moha ya shigo bayan ya miqa wa Ya safwan wata takarda bai ko jira ya safwan ya tmbayeshi ta me cece ba yasa kai ya fita,yana budewa ya karanta naga ya dafe qirshin shi yana fitar da qwalla ya miqo min takardae ina karantawa naga momyna ta samu paralyzed rabin jikinta ya daina sakamakon faduwar da tayi INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN NA RIQA MAIMAITAWA hawaye na zuba daga eyes dina kamar zasu tsiyaye,Lafiya kuke ta kuka? Muga takardar nayi qarfin halin miqa mata,ALLAHUMMA AJIRNI MUSABATI........Ta fada tana karanta takardar,ku daina kuka haka Allah ya qaddara babu wanda ya isa ya wuce qaddararsa Wanna jarabawa ce daga Allah Ina rokon Allah ya bamu ikon cinyeta Ameen,ina so ku cigaba da Addu'a itace makamin mumini,ta cigaba da yi mana nasiha har sai da naji dangana ta sauko mun. A ranar aka sallame mu duk wasu magunguna da ake buqata Dr.Moha ya siya ya kaimu har gida da motarshi.Gidan ya cika da mutane DANGIN MAHAIFINA suma suna nan sai harkokinsu suke kamar ba mutuwa aka yi ba,Yan'uwan momyna suzo mamanta(Ummi) da kannenta (Jawhara,Nahar,Abdul-rahman da Shureim)sai qanin mahaifinta Mahad.DANGIN MAHAIFINA basu da aiki sai da suci su sha suyi ta labarai suna kyakyatawa kamar ba dan'uwansu ya rasu ba idan an musu magana suce so kuke mu zauna muyi ta kuka kamar marasa aikin yi ko kukan mu zai dawo dashi,halin nan da suke na masifar qona mun rai.Kwana uku muna zaman makoki tare da iyayen moha.Kowa ya Watse Yan'uwan momyna ma sun tafi,sun so tafiya da ita tace a'ahh bata so ta rabu damu.Duniya kenan rayuwata ta chanza mana lokaci daya yanzu gidanmu so bored ba wani mai walwala,duk na rame na zama ga dai ni nan,kullum sai moha yazo ya duba lafiyar momyna munyi hira dashi ba abunda ya chanza game da soyayyata dashi,DANGIN MAHAIFINA ko sau daya basu taba zuwa duba momyna............... [11/12, 2:30 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [3:43pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👧 NA ZEE YABOUR PAGE 21-22 Bayan rasuwar Daddy da sati biyu ranar juma'ahh wannan ranar na daya daga cikin ranakun da bazan taba mantawa dasu a tarihin rayuwata ba.Momyna ta tashi da matsanancin ciwo ga kafarta na ciwo ga kuma zazzabi sosai jikinta yayi zafi rau,na kira Dr.Moha ina kuka cikin mintuna kadan sai gashi ya dan duddubata yace zai je ya siyo mata wasu drugs ya dawo kuma sai an mata allura zai je ya dauko hadda allurar har ya sai kai zai fita,momyna ta kira shi ya dawo gabanta ya tsuguna tace Moha ka yafe mun,Momy ni baki mun laifin komai ba,Ga basma nan Amana in Allah yayi aurenku Dan Allah ka riqeta Amana nasan mutuwa zanyi,momyn ki daina fadar haka,Hmm!basma kenan ni ina ji a jikina bazan tashi dga nan ba,Dr.Moha yace In shaa Allah momy ki na da sauran kwanaki bari inyi sauri inje in dawo,ya fice.Safwan ka basma nan bata da kowa sai kai ka kula da ita idan bikinta ya tashi,kayi qoqari kayi mata duk wani da kasan uba na ma yar'sa yanzu kai ne uwarta,kai ne ubanta ko ina da rai ko bani da rai,don ko ina da rai ba wani abu da zan iya yi ..Allah ya yi muku Albarka...Ameen,Ya safwan ya tashi ya nufi masallaci ni kuma na shiga toilet yin alwala,da na fito daga toilet momyna naga kamar barci take har momy ta isa yin barci daga shiga inyi alwala,na kira sunanta momy shiru,na jijjigata shiru,na dinga jijjigata ina cewa Momyna ki tashi Dan Allah kada ki tafi ki barni kamar yadda Daddyna ya tafi,Momyna !momyna!!! In wasa kike plzzzzz ki daina,Nan take numfashina ya dauke....A ranar Dangin momyna suka zo suna ta kuka,an mata sutura an kai ta makwancinta ta samu mutane dai dai gwargwado,rayuwa ta qara jagule mun na fahimci cewa duniyar nan na komai bace kuma komai yayi farko sai yayi qarshe.Satinsu daya suka shirya komawa suka ce suna son tafiya dani,in koma can da zama shi Ya safwan ya zauna nan tunda namiji,DANGIN MAHAIFINA suka ce sam sam basu yarda,suka cima dangin momyna mutunchi daga abun arziki hadda cewa suna kwadayin daddy dan sunga yar'su ta rasu bata da gado yanzu shine zasu tsiri cewa zasu riqe dan su samu wani kaso sunyi hakane saboda wata manufa daban but sun san dangin momyna sunfi qarfin dukiyar mahaifina gaba dayanta ballantana kason da za'a bani.Ransu yayi matuqar baci,basu biye musu aka yi ta hayaniya ba don su ba tashin hankaline ya kawo su ba kuma basu saba da rigima ba,ba shiri suka nufi hanyar airport dan sunce su ba abun wulqantawa bane ko talaka a wurinsu ba abun wulaqantawa bane balle su da mulkinsu da kudinsu,sun dau alqawarin cewa basu qara xuwa 9ja ba sai dai mu muje.Ban so akayi rabuwar tsiya tsakaninsu da DANGIN MAHAIFINA ba.Daga ni sai Ya safwan muka cigaba da rayuwarmu sai fa yan'aiki,DANGIN MAHAIFINA ba ruwansu damu but muna zuwa gaishe su duk bayan kwana biyu duk da bama samun tarbon arziki sai an biyo mu da baqaqen maganganu bamu fasa zuwa ba saboda nasihar da daddy ya mana.Baby abunda muka nema muka rasa naci,sutura da duk wani abun lalura ko ba'a raba gado ba muna da isassu kudi a account dinmu don kowanne month daddy sai ya sama 100k ni da Ya safwan kuma bama amfani dasu kawai dai yana sa mana ne in case,sannan Ya safwan shine tun daddy na da rai ya bashi kyautar company daga cikin kamfanonin shi so ana samu sosai. Ya safwan da Dr.Moha na kula dani sosai,yana yawan kawo mun su naby su debe mun kewa.Results dina ya fito,na fito da excellent performance ranar nasha kuka dana tuna daddyna da yace idan result dina yayi kyau zai bani babbar kyauta,Ina ma yana da rai ta gani.Aunty basma kinyi baqo inji larai mai'aiki,kice masa ina xuwa nasan ba kowa bane illa Dr.moha.Na wanke fuskata,na saka hijabi.Falo na tarar dashi zaune Haba!basma yaushe zaki daina kukan nan,duk kin rame kin fita hayyacinki,kukan nan pha ba zai magance miki komai ba sai dai ya sa miki matsala.Nayi murmushin karfin hali bazaka gane bane moha......Ya katseni Ni dai duk ba wannan ba,Congratulations! Here is your gift ya miko mun anyi rapping,ya sake miqo mun wani wannan kuma inji nabila da nusaiba,Thanks ots i reallt appreciate ,No basma you deserve more than this,Wai ni yaushe zaki shirya aurenmu? Ni kam a shirye nake sai dai kai,da gaske kike,Yeah! To me zan zauna yi moha,karatu ne zan iya yinshi a gidanka ko da can saboda su momyne bana sa rabuwa dasu nake ja baya toh ya zu mai rabawa ta raba ni dasu.Ihu ne kawai Moha bai yi ba tsabar murna amma naji dadi sosai dana koma gida zan sanar dasu Abba don su ko gobe aka ce a daura a shirye suke shima safwan zan same shi muyi magana.Da Ya safwan ya aikawa DANGIN MAHAIFINA kan maganar aurens cewa sukayi ina ruwansu da can da farko dasu aka fara qullawa ba sai dai aka kawo musu kayan an gani ana so ba dan haka yanxu ma ba hannunsu a ciki,Dama basan zai yi wuya su shiga lalurar aurena.Ya safwan ya samo Hamma Ahijo yace yana so a raba gado tunda ga lalurar bikina ta taso,Yace wai har yanzu ba'a gama tantance iya abunda daddy ya bari ba,Ya safwan yace haba! Hamma wata nawa ana abu daya,Kasan mahaifinku ya bar dukiya mai yawa gidaje da sauransu to shine muke qoqarin ganin an tattara komai an san iya adadin abunda ya bari,Allah ya sawwaqa kawai ya safwan yace ya tafi.Tun kafin su momyna su rasu sun siyan mu komai na kayan daki tun daga kan gadaje har xuwa kayan kitchen.Yan'uwan momyna sun aiko da 5million gudunmuwarsu sunce ba zasu samu xuwa ba,Daga ni sai Ya safwan sai qawayena da muka yi sec scul muke shirye -shirye bikin sai pha dangin moha .Ya safwan da kudinshi da kudin da yan'uwa momyna suka aiko yake amfani yana shirye shiryen bikin,kullum muna cikin zirga-zirga ni da frndx dina................ [3:44pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 23-24 Da kaina na gayyato wata yar'sudan tazo ta mun gyaran jiki,fatata tayi laushi,tayi kyau,qawayena suka raka ni saloon aka gyara mun gashi yayi santsi yayi laushi.Yar'sudan ta bani turaruka masu qamshi dasu tsimi,wata qawata Hanan ita tayi aure yanzu 3months da aurenta itama ta bani wasu haden haden. ___Anyi biki sosai sai dai kash! Babu dangin amarya abun nan ya mun ciwo sosai but Dr.moha ya nuna mun ba komai. →→→ Ranar da za'a kaini Yar'sudan ta qara gyareni ga turaruka duk inda na wuce har in bar gurin yana kamshi kai ka rantse wankan turare aka mun.'''' ' Da daddare bayan isha'i aka kaini gidan moha, Gidan ya keru matukar keruwa,tsayawa bayyana muku irin haduwar gidan kauyanci ne. _____Ina zaune kan tsaddaden gadona Dr.moha ya shigo,yasha shaddarshi blue tayi mai masifar kyau,shima yasha qamshi.''''Ya zauna gab da dani yace Alhamdulillah!Allah ya cika mun burina ,gaki a gabana a matsayin matata bazan iya bayyana miki farin ciki da nake ciki ba yau,babu watarana da tafi wannan muhimmanci a rayuwata ranar da na mallaki abun sona,Allah ya barmu tare har abada nace Ameen.'''''Shiru nayi zuciyata fal da farin ciki a raina ina cewa ni kam nayi sa'ar miji.Ya janye mayafin da na lullube fuskata dashi yace bismillah ga abun motsa baki koh,nasan baki ci komai ba,Da kanshi ya riqa bani a baki ni kuwa duk kunya ta kamani har sai da nace na qoshi sannan ya dauko lemo shima a baki ya bani nasha kadan nace ya isa.Yayi murmushi yanzu sai ki tashi muyi nafila mu godewa Allah koh."""""Da muka iddar da sallah naji duk na gaji barci nake son yi,gashi ina so in watsa ruwa amma kunyar Dr nake ji.Sai naji yace zanje in watsa ruwa kema sai ki tashi ki watsa,naji dadin jin haka ,na fada toilet nayi wanka da sabulu mai kamshi wanda yar'sudan ta bani,na fito wanka na shafa mai,na dauko rigar bacci na iya gwiwa amma shara-shara ce ana ganin cikinka.Da har nayi kamar ba xan sa rigar ba dan gani nake kamar moha zai daukeni yar'iska na manta cewa yanzu ni matarshi ce,mallakinshi,na feshi jikina da turare nai saurin hawaye kan gado na lullube da bargo dan kar moha yazo ya ganni a haka.''''Daga shi sai singlet da boxes ya shigo dakin,ya hau gado ,naji ya daga bargon ya shigo,sai da gabana yace daradamm🙄🙄🙄.Ya rungumoni yana shinshinar jikina na tabbata turaren jikina yake shaqa,nan naji ya kama lips dina ya fara kissing,Tun ina qoqarin kwace kaina har na sallama mai,Ranar na sha sumbatu 🙈🙈Allah ya jikan iyayenki,Wayyo Allahna😂😂😂,Allah ya miki Albarka Ina sonki,wlh ina sonki sosai,i will never leave you,i promise to be wif u forever.~~~A raina nace ashe dai sumbatu da ake cewa maza nayi gaskiya ne.___Nayi wanka nai sallar asuba na koma barci dan shima ya tafi masallaci bayan ya dawo,naji ya hau gado ya rungumoni na fara ina kuka ina cewa plzzzzz moha don't,Ya qyalqyace da dariya Yace Dallah matsoraciya ba abunda zan miki kawai ina son in jinki kusa dani ne but you're sooooo sweet💋💋pha i never thought hka kike dga yau kin koma swty yayi kissing dina a goshi,ya sake matseni a jikinshi bacci ya daukemu.Ina bude idona na kalli agogo qarfe tara saura 5min,na zare jikina daga jikin moha,na shiga toilet nai brush nayi wanka.""""Lace na saka dinkin riga da skirt dinkin ya mun kyau,ya fito da sharp dina sosai,na feshi jikina da turare,na nufin kicin na hada breakfast chips,plantain da miyar qoda kicin duk ya bade da kanshi,na jera da kayan tea akan dining table ina jiran moha muyi breakfast tare.Wayata tayi ringing Ya safwan ke kirana Hello one and only bro;Amarsu ta ango kin tafi kin barni da kewarki;nima ina ta missing dinka;ba wani missing dina kina tare da mijinki;kaima ya safwan kayi aure ka huta da kadaici;Don't worry very soon ,ina so na gama da settling zancen gadonmu dan naga hamma Ahijo so yake ya danne dukiyar;Aikuwa bai isa ba dan nima naga taken takenshi but plz do sumtin about it Ya safwan;kar ki damu lil sys i will try my best ki gaishe da moha,Bye;Bye kamshin turaren moha ya sani juyowa Yace morning swty ,hada idon da muka yi dashi ya sani saurin sunkuyar da kaina kasa coz kunyarshi🙈🙈nake ji saboda abunda ya faru daren jiya nace ina kwana? Lfy lau swty.kwalliyar nan taki tayi kyau,thanks,But ke baki yaba tawa ba kuma ke nayiwa(shiga yayi cikin english wears jeans en t-shirt yayi kyau sosai) kayi kunya,Zama kizo ki daina jin kunyata ne dan ko yau ba qyaleki xanyi ba,yanzu ma tausaya miki ne ganin jiya na wahalar dake but kwalliyar nan taki........🙊🙊🙊.Lallai maza basu da kunya wallahi.A plate daya muka yi breakfast,yana bani a baki Yace mmm....u're gud@bed,dressing,cooking infact everything,I luv yhu soooo much♥♥♥ gaskiya na dace mata. ______Ta gefen su Adda bongel an kai musu kayan biki hadda soverniers sun sha mamaki ganin irin uban soverniers din da aka yi.Fadeela(first born din Adda bongel)ta kalli calendar tace mijin kyakkyawa daga ganinshi naira ta zauna mai,Adda bongel tace dan minister pha ,Fadila ta zaro ido minister lallai basma ta more miji,Allah ya bamu danshinta,Adda bongel tace ya mata muje gidanta ganin kwam nasan dukiya na can an baza,Aikuwa mama.Muna ta shan soyayyarmu da Dr.Moha baya xuwa ko'ina yace sati daya,yanar kwasa amarci kullum muna manne da juna._____Ranar nayi shiri riga da wando na dame abuna,nayi packing gashina kaina ba dan'kwali na dai yi fresh da ka ganni kasan ina cikin kwanciyar hankali ina kwance kan cinyar moha,yana shafa mun kaina yana yaba kyan da yayi.knocking muka ji Dr.moha ya tashi yana cewa su waye zasu katse mana jin dadi,ya leqa yace su Adda bongel ne sannan ya wuce daki,Nayi mamakin ganinsu don ko a mafarki ban taba tunanin zo gidana ba,ita da ya'yanta biyu(fadila da farida)suka zo.Na gaisheta ta amsa da far'arta sai kalle-kalle suke,na kawo musu drinks,soyayyen kaza,snacks da abinchi,suka saki ciki suka dinga kwasar abinchi basu rage komai ba,sauran snacks da kajin suka juye a leda suka sa a jaka,mamaki duk ya kamani sai kace wasu da suka zo daga qauye.Suka ce zaku tafi har zaku tafi,erh ,bari na kira Dr ku gaisa,ina kallon fadila ta saki baki tana kallonshi har suka gama gaisawa ya nufi hanyar daki ta bishi da kallo sai da farida ta tabo ta.Daga daki ya qwalla mun kira swty naji kunya nace ko ya manta akwai baqi ne ya kirana da wannan suna.suka kalli juna swty suka maimaita suka tabe baki,na musu rakiya har mota ina musu godiya,na dawo cikin gida muka dasa love dinmu."""A mota fadila ke cewa basma na cikin daula,ji gidan da take ciki ga wani kyau da ta qara yi,ga mijinta ya hadu.Adda bongel tace hmm! Ta girgiza kai."""Da suka koma gida fareeda tace wai Ya fadeela lfy kika dinga kallon mijin basma? Hmm!farida kinsan ke qanwata ce bani da abokiyar shawara sai ke bama boyewa juna sirrinmu wallahi son shi nake tun ranar da na fara ganinshi a calender naji duk duniya babu wanda nake so sai sai shi komai nashi ya mun,ga kudi kuma kinsan ni a rayuwata ina son miji mai kudi kyakyawa,Babbar magana da kawai kin haqura dashi ,Na haqura dashi pha kikace yanxu ma na fara son shi kuma wlh ko da zanyi yawo tsirara sai na auri Dr.Moha ,bazan iya haqura dashi ba ke har na hango ni gidan Dr.moha ,ita pha basma ya zakiyi da ita gashi na sanki da masifar kishi,Tayi wata dariya mugunta waje xanyi da ita kafin in shiga,shegiya sys da kuwa mun wataya kika shiga gidan daular nan,suka tabe suka yi shewa ,fadila tace bari ma kiga inje in sanar da mama nasan zata bani goyon baya,Ta fice ta nufi dakin Adda bongel............ [3:44pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: . 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧 NA ZEE YABOUR PAGE 25-26 ````Mama!na'am fadeela ya akayi mmmmm....dama dama,dama me fadi mana ina ji,Dr moha ne tun ranar da na fara ganinshi a calender bikinsu naji duniya babu wanda nake so sai shi mama wlh son shi idan ban aure shi zan iya rasa raina ta fashe da kuka,Toh me ye na kuka ki kwantar da hankalinki kin manta nice mahaifiyarki kamar kin auri Dr.moha kin gama ko da baki son shi ina da niyyar lalata aurensu don bana son ganin iyalan Yusuf cikin daula da kwanciyar hnkli(kuji wannan tsana kamar ba dan'uwanta ba uwa daya uba daya)don haka kisa ranki a ruwan sanyi."""""Dr Moha ya shirya tsaf zai fita na rako shi duk nayi fuskar tausayi da zai shiga mota yace ki saki ranki mana swty ba fa dade zanyi ba anan gida zanyi lunch,na turo baki to ai kafin ka dawo ni kadai zan ta zama,ohkay toh zan sa a kawo miki nusaiba ta tayaki zama kafin ki dawo,nayi murmishi but deep inside my hrt nasan ko an kawo mun nusaiba bazan fasa kewarsa ba,Allah ya kaika lfy Ya bada sa'a Ameen swty.'''Na koma cikin gida naji duk gidan ya mun fadi so kawai nake naji moha kusa dani na kunna kallo amma naji kwata kwata bana son kallo nace ni admission dina ma yayi ya fito in fara xuwa makaranta in huta da kadaici."""Da gudu nusaiba ta shigo ta rungumeni oyoyo my nusin wa ya kawo ki ,Driver ,Ina nabila Tana gidan Aunty bebi(qanwar Ammi)Aunty basma nayi missing dinki sosai,nima haka my nusin,Ammi na gaisheki tace tayi fushi tunda kin manta da ita ko ki kawo mata ziyara,Allah sarki Ammi In shaa Allahu zanje in gaisheta amma dai zaki mun kwana biyu koh?Ehh but banzo da kayana ba,Okay bari idan moha ya dawo sai yasa a kawo miki.~~~~~Nusaiba ta kama mun na hada lunch,Rice en stew sai fried plantain da mango juice."""Na sake wanka na tsantsara kwalliya cikin riga da skirt English wears sun mun kyau sosai,ina bakin dressing mirror naji an rufe mun ido,Mmmm.....My dearest moha sannu da zuwa,Ya bude mun ido yace yawwa swty Wlh na gaji sosai ,ka shiga toilet ka watsa ruwa sai kazo muje muyi lunch.~~~~~Yana cin abinchi yana zuba santi ni da nusaiba sai dariya muke masa,Da muka gama cin abinchi yace zai dan kwanta ya huta yaji bazai iya komawa asibitin ba coz ya gaji sosai Yace sai na raka shi,ina kaishi daki nace toh!ni zan koma falo na bar nusaiba ita kadai,Dawo ba inda zaki tare zamu yi barcin,No moha nusaiban fa she will feel lonely,Okay toh bari na kira azo a dauketa,A'aah,Toh zo mu kwanta,ba musu na hau kan gadon a raina ina tunanin nusaiba,Ya rungumoni jikinsa yana kissing,ban ankara ba naji yana qoqarin samun hannu cikin roga na riqe hannun nace No!moha plzzz basma kar ki mun haka,Diz iz not d right time ,moha why not ka bari sai anjima,Plzzz swty ynx nake so,Toh! Idan ka matsa mun zan tafiyata,Am sorry na daina haka ya haqura ya rungumeni har barci ya daukesa,da naga barcinshi yayi nisa na zare jikina daga jikinsa na fita dakin.""""A falo na tarar da nusayba tana kallo abunta,Aunty basma ina kika tsaya ina ta jiranki,Na tsaya gyara wadrobe dina shine baki kirani na taya ki ba,No bana so ki wahala da yawa ai tare dake mukayi abinchi,Still dai Aunty,okay nxt tym."""Da ya tashi daga barci yace mun shine kika gudu kika barni ko?To ai ni bana jin barci,Shikenan nima zan rama Yawwa ki shirya muje mu gaida su Ammi daga nan mu mayar da nusaiba,Ai nusaiba tana nan kayanta dai zata dauko,waaa ba'a nan gidan ba,Haba my dear why? Ba zata zo ta hana mana jin dadi ba yau ma saboda ita kika so kiqi kwanciya tare dani,Zaman nusaiba ba abunda zai chanza game da soyayyarmu just few days din da zata yi ba fa anan zata tabbata ba,Ni dai nace No! Na bata raina ya janyoni jikinsa haba my swty kiyi tunani mana Am sorry if i hurts yhu,bana son ganin bacin ranki smile plzzz,Hakanan dai nayi murmushi but banji dadin rashin barin nusaiba ta zauna ba.~~~~Ammi tayi murnar ganinmu mun taba hira da ita sannan muka tafi tana ta sa mana Albarka.Gidanmu muka biya wajen Ya safwan.A parlor muka same shi yana kallon ball,yayi farin ciki ganinmu bayan mun gaisa yace dama ina son ziwa gidanku muyi magana dake basma kan zance gadonmu Jiya hamma Ahijo ya kira ni yake sanar dani wai ana bin daddy bashin 2billion dan haka zai biya bashin kuma zai qara yin bincike idan ba'a bin daddy bashi sannan a raba gado kuma nasan ba'a bin daddy wani bashi wata makarkashiyar dai suka hada but zanyi maganinshi don na yanke shawarar shigar da qara kotu me kika gani? Hakan shi ne dai dai na goyi bayanka,Moha yace ohh mutane basa tsoron Allah qanin mahaifinka,Ya safwan Yace yanzu duniyarce kowa kansa ya sani ba amana Allah yasa mu dace kawai Ameen.Tashi mu tafi basma dare nayi,Ya safwan ya mana rakiya."""Zuwan gidanmu da mukayi shi ya tuna mun da rayuwar da mukayi dasu momyna tun a mota nake kuka har muka isa gida moha nata lallashina yana mun nasiha har shima ya fara kukan,Kukan da naga ya fara shi ya sani yin shiru sannan muka yi shirin bar i,Mukayi barcinmu cikin soyayya da kauna❣❣."""""""Ya safwan har ya shigar da qara kotu an aikawa Hamma Ahijo da sammaci ganin takardar da hamma ahijo yayi ya ciji dan'yatsa yace Ni yaron nan zai kai qotu bai san halina bai san abunda zan iya aikatawa ba akan kudi zanyi maganinshi kafin ranar zuwan mu kotu,Yayi dariyar mugunta............ [3:44pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: . 👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 27-28 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Na samu admission Baze university Abuja Medicine nayi farin ciki sosai coz babban burina shine in zama Medical Doctor.""""Bayan Moha ya dawo,na tarbe shi ina cewa muje ya watsa ruwa,Yace before dat muje waje i have a suprise for you,Sabuwar mota dal VIBE Ya nuna mun,ya miko mun key yace it yours ban san sanda na daka tsalle na rungume moha nai kissing dinshi nace thanks my luv ,yasa yatsanshi a lips dina shhhh bana so kina mun godiya na siya miki saboda xuwa ckul bana so kisha wahale transportation tunda nima ina zuwa aiki balle ince zan riqa kaiki.Nayi farin ciki sosai kuma nagodewa Allah da ya bani miji mai sona.````````Ta bangaren su Adda bonel suna sun suna kulle kullen yadda zasu rabani da Moha,Fadila ta aureshi,sun yanke shawarar su fara korata a gidan sannan su hada fadeela da moha. Na fara xuwa makaranta dama na iya driving tun su momyna na da rai Ya safwan ya koya mun idan mun fita daahi yake koya mun har na iya,Naji dadin lectures din kuma na fahimci abunda akayi.Na fito daga leture hall ina qoqarin shiga motata naji an mun sallama na juyo naga wani saurayi kyakkyawa zai yi sa'sn moha ko kuma moha ya girmeshi da kadan,Na amsa sallamar Dan Allah ko zaki iya bani 2min ,See dakata malam ni matar aure ce Yayi murmushi ko kadan baki yi kama da matar aure ba dama haka kuke yan'matan nan idan baku son kula saurayi sai kuce kuna da aure,Toh! bana daga cikinsu ni matar aure ce akwai memon bikinmu a hannuna dashi nayi jotting abunda aka mana yau na mika masa kalli ka gani,Ya qarba ya gani ya girgiza kai alamar gamsuwa na yarda ke matar aure ce amma ba wanda zai ganki yace kin......ban jira ya qarasa maganarsa ba naja motata sai gida.""""""""""Moha shima bai dawo gida ba,hijab kawai na cire na fada kicin hada dinner don lecture 4-6 nayi ,sai around 8:00 na gama hada komai,na sake wanka nai kwalliya na zauna parlor na kunna kallo ina jiran Dr.Moha."""""Around 9 ya dawo sannu da xuwa my luv,Yawwa swty Ya lectures din ?lfy lau hope dai ba wata matsala? Yeah babu.Toh Allah ya taimaka Ameen,Safwan yace mun yana ta kiran wayarki switch off,eh hkn da zan shiga lectures na kashe wayar da na dawo gida na manta ban kunna ba dama akan maganar gadonku ne yace Gobe za'a shiga kotu but call him for more details,ok tashi muci abinchi,OMG yanxu sai da kika dafa abinchi,Me ya faru? kinje le tures kin gaji u suppose to rest har na ba Rabi'u ya siyo mana take away,Take away fa kace to ba'a gidan nan ba dama ka kirashi kace ya barshi,dole moha ya kira Rabi'u yace kar ya siyo,Allah ya miki Albarka my swty,Ameen my luv......Da muka gama cin abinchi na kwashe kwanukan na wanke sannan na kunna wayata na kira Ya safwan""Hello sys Ya safwan ya kake?lfya lau ina ta kiranki wayarki switch off ina scul ne,Anyway ki shirya gobe around 10 zan zo in dauke mu tafi court,bye ina kan hanyar zuwansu mukhtar ,ohkay bye miss you,miss you more lil-sys.""""Tunda da sassafe moha ya fita yace yana da appointment da wasu but yace in ya samu tym zai zo.Har azahar shiru banga Ya safwan ba na dauko wayata na kirashi duka wayoyinshi switch off Ah! Ah! Me ya faru naji duka wayoyin Ya safwan kashe shi da baya kashe wayarshi ko da phone dinshi daya a kasheta take to sauran a kunne suke bai taba kashe wayoyinshi duka ba.Hijab na dauko na saka na dau mukullin mota na nufi gidanmu Masu gadi na fara tambaya ina ya safwan?suka ce rabonsu dashi tun jiya da daddare,Dama ya taba kwana ba'a gida,A'ahh bai taba ba wannan ce rana ta farko.Ikon Allah toh ina ya safwan yaje ne tuna gidan frnd dinshi mukhtar nai da yace mun zashi na tuna mun taba xuwa dashi ya barni a mota ya shiga ya qarbu saqo,mota na fisga sai gidan a harabar gidansu na tarar dashi zaune yana shan iska Basma lfy na ganki haka? Dan Allah ya safwan baya gidan nan,Jiya dai yazo nan har dare muna tare dashi around 9 yace zai koma gida wani abu ya fari dashi nan nake sanar dashi ,Yace subhanallah duk wasu frndz dinsu sai da mukhtar ya kira but duk suka ce baizo wurinsu,Hankalina duk ya gama tashi,na kira moha na sanar dashi meke faruwa,Yace in mai kwatancen gidansu mukhtar gashi nan zuwa.In few minutes sai ga Moha yace muje police station mukai report.Muka dawo gida hankalina a tashe duk na kasa natsuwa ina addu'ar Allah yasa ba wani abu ya faru da Ya safwan dina ba shi kadai ya rage mun,Daga ni har moha ba wanda ya runtsa kwana mukayi sallah muna roqon Allah.""""Da sassafe Yan'sanda suka zo gidanmu A rude nace musu Ina Ya safwan ku ganshi? Daya daga cikinsu Yace kuyi haquri bamu ganshi ba munyi iya bincike amma ba ko alamunshi duk da haka ba zamu yi qasa a gwiwa ba zamu cigaba da bincike har Allah ya bayyana shi.Zuuuuu naji jiri na dibata ina qoqarin faduwa Dr.moha ya riqe ni ya jani cikin gida.Yana mun nasiha kiyi tawakkali da Allah,komai da kika gani muqaddari ne daga Allah,duk wadannan abubuwan da kike gani suna faruwa dake jarabawa ce daga Allah ,Allah jarabtar bawansa dan yaga qarfin imaninsa.An jarabci Annabawa da mutanen kirki kuma ba don Allah baya son su ba,A'ahh sai dan yaga qarfin imaninsa kema sai ki dage kici wannan jarabawr karshe sai kika riba,Dukkan tsanani yana tare da sauqi,ki dage da addu'a itace kawai mafita.""""Hakanan na haqura na dangana na fawwalawa Allah komai,Ina roqon Allah.""""Bayan kwana biyu sai ga Fadeela tazo,moha baya nan,nusaiba da nabila sunzo.Ah!fadila sannu da zuwa,Ya kike? Lfy lau Yasu Adda bongel lfy lau suke,Nabila kawo mata lemo,Dama nazo ne in miki jaje ne abunda ya faru da Ya safwan,Allah sarki nagode sosai kuma naji dadi Allah ya bar zumunci,Ameen wlh tun ba yau ba bana jin dadin yadda kuke dasu mama abun na mun ciwo yanzu ma ce mata nayi zani gidan qawata shine nazo nan,Allah sarki wlh kin kyauta,Ta miqe ni zan tafi kar taga na dade,Bari ina zuwa na dauko atamfa da turare na saka a leda Gashi fadeela nagode,Nima nagode.Bayan ta tafi nake cewa su naby ita kam fadeela ba ruwanta bata biyo halin mamanta ba Allah yasa suma su chnza su naby suka ce Ameen. """""""""""""""Adda bongel,Fadila da farida suna zaune tsakar gida fadila ke cewa shegiyar ta zata da gaske nake har da bani wata atamfa da turare,Adda bongel tace Yawwa kinga haka zaki dinga shige mata kina nuna mata ke mai qaunarta ce har mu cimma burinmu.Suna ta tattaunawa yadda zasu cimma burinsu.................~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ GAISUWA MAI YAWA GAREKU MASOYANA KUMA FRNDZ DINA INA JIN DADIN YADDA KUKE NUNA SOYAYYARKU GA NOVEL DIN NAN NAWA 💖Zakiya musa bala💖 💖Asma'u skebbi Yabour💖 💖Amyna m lawal💖 💖Yhasmeen Buba💖 💖Hauwa M Bello💖 💖Khadeeja Manu💖~~~~~~♡♥♥ LOTS OF LUV XEE YABOUR♡♥♥ [3:44pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 29-30 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ A scul ina xaune a lecture hall kafin lecturer ya shigo mutumin ranar naji ya mun sallama Mallam lfya? Haba baiwar Allah ya kamata ki mun uzuri kiji me ke tafe dani,Na gaya maka ina da aure ,Nasan kina da aure sunana Usman Sadeeq ,Course mate dinki ne buh 400level nake,Toh!yanxu me ye amfanin duk wadannan bayanan da kake na tambayeka,Sorry!nasan baki tambayeni ba but ke new student zaki iya neman taimako ko kuma buqatar wani da zai riqa koya abunda baki fahimta ba Am ready to help plzz kar kice a'ahh nasan ke matar aure ce so zan kiyaye our relationship ba zai wuce karatu ba i promise,Naji,Plzzz ko zaki iya bani numbernki,ba tare da nayi wani tunani na qarbi phone dinshi nasa numberta,dan na kagawa ya tashi a kaina."""""""""Around 12 na koma gida naji wata irin kasala nake ji nan naji wani zazzabi ya rufe ni ina ta amai,Moha ya tarar dani a wannan hali ya daukeni sai asibiti yace ba zai iya dubani da kanshi ba.Bayan yan wasu gwaje gwaje da aka yi Dr.Ameenu Yace Congrats Mr&Mrs Moha,Dr.Moha Your wife is 2 months pregnant,Alhamdulillqh ya furta,Sai ka riqa kula da ita sosai kasan she is young lokacin shekarata 19.""""Farin ciki waje moha ba'a magana,ranar har goyani yayi da na dan yi motsi kadan zai zabura lafiya wani wuri ke miki ciwo,ni kuma inyi murmushi ince A'ahh?Nima nayi farin ciki sosai da samun cikin. ""Moha ya samo mun mai'aiki dake xuwa ta tayani aiki amma bana take kwana ba saboda cikin na bani wahala ga kuma xuwa makaranta.Tun bana kula Usman har na dawo ina kula shi don yawan laulayin da nake,Shi ya taimaka mun nayi sauran registration dina shi ke taikamun da assignment and duk abunda ban iya ba shi ke koya mun.Ban sanar da moha komai game da Usman ba bai ma san ina tare dashi a scul ba ina tosron gaya masa kar yace in rabu da Usman dan nasan shi da zafin kishi ni kuma har ga Allah a lokacin ina buqatar taimako dom cikin na wahalar dani abunka da sabon shiga idan ba usman ba banga wanda zai iya mun wahalar nan ba. Muna tare da Usman yana koya mun karatu,Usman nagode sosai da irin hidimar da kake mun Allah ya saka ma da Alkhairi,Ameen basma but Plzz ki daina mun godiya kina buqatar taimako a matsayinki na mace,Hakane amma ba zan fasa yima godiya ba,Yayi murmushi ya cigabq da mun bayani.""""Mun saba sosai da Usman yana respecting dina a matsayina na matar aure ba wata alaqa tsakana ni dashi in bata karatu ba,ban taba bari wani zance ya hada mu ba."""Moha yana asibiti,Yana zaune ofis dan yanxu yana zama asibiti sosai kasancewar sun roqe shi dan Allah ya riqa zama yana taya su da duba marasa lafiya don sun yaba da aikinshi.Text message ya shigo wayarshi Yace yanzu haka yan'Mtn ne subi duk su ishe mutane Ya bude ya karanta "KA BINCIKI MATARKA KARATU TAKE ZUWA YI MAKARANTA KO SOYAYYA" Ya sake karanta text din ,Ya kira numbern,Yaja tsaki it can't be Basma ba xata yi haka ba,dey must be mistaken bani za'a turowa msg din nan ba ynxu haka mistake suka yi wajen rubuta number to me ye na kashe waya anyway ina ma ruwana ol i knw basmata will not do is.Ya cigaba da aikinshi ya basar da maganar.Sai la'asar moha ya bar asibiti ya taho gida. Ina kwance daki dan bana jin dadin jikina,naki moha ya rungumoni ta baya,my baby me ke damunki? Bana jin dadin jikina Allah sarki swtyna Cikin nan na wahalar dake yasa kanshi kan cikina yace babynmu Dan Allah ka daina wahalar mun da swty idan ba haka ba idan kaxo duniya zanyi punshing dinka,Nayi dariya nace ohh moha kenan,Yai kissing dina Allah dai ya sauke ki lfya,Ameen my luv."""Fadeela na zuwa gidana akai-akai ,muyi hira da ita sosai,tana nuna mun bakin cikinta akan alaqarmu dasu Adda bongel har cikin raina naji ina qaunarta dama ko da rana daya ban taba ji na tsani DANGIN MAHAIFINA ba illa halinsu kadai na kyamata.Ta kan taimaka mun da wasu ayyukan dan mai'aikin aure zatayi ta daina xuwa,na so in samu wata,fadeela tace a'ah ba sai na samo ba zata zo ta riqa tayani da wasu ayyukan.Nace mata bata tsoron Adda bongel ta gano tana zuwa gidana,kar ki damu nasan yadda zanyi ba zata gane ba,Shikenan Fadeela nagode Allah ya bar zumunci,Ameen Basma.......................... [11/12, 2:30 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👧 NA ZEE YABOUR PAGE 31-32 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Muna tare da Moha,fadeela na kitchen tana wanke wanke,ta dauko wayarta ta kira Hello!Suna tare ka kirata Yanzu,Ya amsa toh! Ranki ya dade, kar fa ka tsaya bata lokaci ka kira yanzu nan,An gama ranki ya dade.Ta dawo bakin kofa tana sauraron me zai faru?"""Phone dita tayi ringing na duba naga Usman ne kawai na basar naki dauka,Moha yace baki ji ana kiranki,No Yan Etisalat ne,haka suke suyi ta damun mutum da kira nima haka suke mun,Nai ajiyar zuciya a raina nace wai!! Da moha ya gano namiji ke kirana da na shiga uku yau zuciyata nace mun ki gaya mai ki huta tunda ba wani abu ke tsakaninku dashi ba sai harkar karatu,Kaii!!inaaa nasan hali moha cewa zai yi in rabu dashi ko zan gaya mai sai naga Allah ya sauke ni lfy lokacin da zan iya yin komai da kaina bana buqatar taimakon kowa ina cikin wannan tunanin sai ga wani kiran usman ya qara shigowa nai saurin danne wayar kafin ta fara ringing kawai nama kashe wayar gaba daya,Ya kira Fadeela yake ce mata ta kashe phone din gaba daya Naji kawai tace mai ta kashe wayar ta koma cikin kitchen tana cizon yatsa plan dinta bai yi ba."""A school nake cewa Usman Me yasa zaka kirani ina gida kuma na gaya maka halin mijina yana da kishi,Dan Allah kiyi haquri na kira ne in tambayeki assignment din nan typing za'ayi ko hakanan za'a miki submitting,Typing ne but na gaya maka ai,Wlh na manta,Ohkay Dan Allah Usman a kiyaye,In shaa Allah bazan qara ba Am sorry.""Fadeela ke cewa mama ni gani nake anya text din da muka turawa Dr.Moha ya gani kuwa dan naga ba abunda ya chanza game da soyayyarsu ,Adda bongel tayi dariya me kike ci na baka na zuba ai yanzu ne farko,ba yana gani zai dau mataki ba a hankali dai muje xuwa,Yanzu sai mu shirya next plan dinmu,Mama ni dai ayi a raba su,na matso ta bar gidan nan in shiga duk sanda na gansi tare ji nake kamar an soke ni da kibiya,Ni fiki matsowa fadeela amma sai munbi abun a hankali.""""Yau 5th March na cika 20yrx ,Birthday cake uku moha yasa aka mun,ya bani tsadaddun laces guda biyu da super daya,holland daya.Fadeela itama ta bani turaruka biyu da birthday card.""Moha ya tafi dauko su naby coz xamu yi dan qaramin celebration yan gida kawai.Mai gadi yayi sallama riqe da leda a hannumshi Yace gashi ,Wa ya aiko ka na tambayeshi,Wani mutumi ne bai fadi sunanshi ba yace in kawo miki.To Waye Wannan mutumin ,Takalmi da jaka ne sai birthday cards guda biyu cikin ledar naga dan qaramin written note USMAN NE ,USMAN How comes yasan birthday na,yasan gidana i know ban taba gaya mai,I hv to ask him diz questions buh sai mun hadu a scul infact i have to warn him yanzu da sun hadu da Moha pha a bakin gate what is he expecting me to tell moha,Sallamarsu Naby ce ta katse mun tunanin da nake nai saurin boye takardar cikin rigata,HAPPY BIRTHDAY AUNTY suka hada baki suka miqo mun nasu gifts,Moha yace Wannan gifts din pha wa ya kawo miki ya nuna kayan da usman ya bani,Mmmm.....qawata ce ta bani,Yai murmushi yace Nice ta kyauta,Bari inje in shirya nai saurin cewa dan bana so mu cigaba da maganar."""Munyi rawa,Munyi pics,an daukemu picz da yawa ni da Moha,diff style mukai tayi ana daukarmu wani ya dauke ni,wani yayi kissing dina a chicks,wani muna feeding juna cake haka dai muka yi tayi,Fadeela kamar zata suqe dan haushi. """"USman Why on earth zaka kawo mun gifts har gida kuma da kanka na gayawa ma bana son relationship dinmu da kai ya wuce a school a scul din ma karatu buh why are you doing all this,Ta ya aka yi ma kasan Date of birth dina kasan gidana????? Am Sorry Basma i dnt mean to hurt you,A matsayin zaman tare yasa na baki but idan na bata miki rai Plzzzzz kiyi haquri ,Date of birth dinki da address a credentials dinki na gani.WHY Usman Whyy zaka riqe Date of birth dina da address,me kake tunanin kana yi kana son mum creating problem ne a aurena,No! Basma ko kadan bana fatan hakan ,Am sorry ba zan sake ba,LOOK! Usman idan har zaka cigaba da haka zamu raba hanya dakai,bana son duk wani abu da zai taba aurena da moha,Plzzz basma Am sorry one last chance,Ka kiyaye,In shaa Allah. """"" Yau ma an sake turo ma Moha txt message but da different number《MATARKA BATAA GAYA MA GASKIYAR WANDA YA BATA GIFTS BA,KA SAKE BINCIKARTA KUMA KA BINCIKI MAI GADINKA》.AH! AH! Wannan na nuna cewa text din ranar nan ma ni aka turowa ba mistake bane,Toh waye ke turo mun txt msgs din nan gashi numbers din are different,Ya kira numbern switch off Why suke kashe number in son turo text,ko dai wani ke hada wata makarkashiyar,i have to go home now,Moha nata sake-sake har ya isa gida,Maigadi ya fara tambaya Ranat birthday din Basma wata taxo nan gidan banda fadeela??A'ah ba wacce tazo amma wani saurayi yaxo nan ya bani saqo yace in ba hajiya. """A fusace moha ya shigo gida,Basma! Basma! Naji yana qwala mun kira,A tsorace na fito moha me ya faru? Basma me yasa zaki mun qarya? Karya kuma? Ya daka mun tsawa Eh karya wa ya baki gifts din da kikace qawarki? Muryata na rawa nace kawata ce school dinmu daya,Basma bana son karya ki gaya mun gaskiya,Allah gaskiya nake gaya ma,Idan qawarki ce ta baki waye yazo nan ya kawo saqon,Gabana ya bada DARADAM wa ya gaya ma moha na tambayi kaina,Ya sake daka mun wata tsawar tambayarki nake kinyi shiru,Naji idea ta fado mun nace brothernta ne,kin tabbata? Beleive me Moha,Yayi ajiyar zuciya ya wuce daki,Nabi bayanshi na duqa gabanshi Am sorry Moha,Ya jawoni ya rungume basma ni ya kamata in baki haquri Am sooo sorry basma,baka mun komai ba Moha so stop apologizing,No!basma na miki ihu na miki tsawa na miki fada na mik.......shhh nasa hannuna kan lips dinshi Ya isa haka but plzz ka rage kishi,Dole inyi kishi akanki baki san yadda nake sonki ba I Luv You Basma❤,I Luv You Too Moha❤.Ina ji kamar in gayawa Moha gaskiya am nt suppose to continue hidng the truth from him,naji duk nayi hating kaina Moha yayi trusting dina sosai wata zuciyar tace No basma ki fada mai No!nasan ko na fada ba zai fahimceni ba zai ce na mai qarya,Me yasa at first ban gayawa moha ba na biyewa son zuciya ,Nasan duk ranar da moha ya gano ina tare da usman na shiga uku kila sai na bar makaranta Ya kamata in sanar da Moha as soon as possible but Ta ya zan fara mai bayani in fahimtar dashi.........Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah ka kawo mun mafita..... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 33-34 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ A Kullum bani da tunani da ya wuce yaya zanyi in tunkari Moha da Zancen Usman,na fara shiga damuwa,Fadeela ke tambyata Basma me ke damunki? Kwana biyu naga duk kin chanza ko wani abu mohan ya miki? Ba komai fadeela Cikin nan ne kawai,Idan akwai wani abu ki gaya mun kar ki manta ni yar'uwarki,Inda akwai wata matsala zan gaya miki ai,Shikenan basma Allah ya sauke ki lfya,Ameen """""Yau da murna fadeela ta koma gida a tunaninta moha da basma fada suke samun matsala,plan dinsu ya fara aiki.''''Mama in gaya miki basma na cikin damuwa nasan ta babe musu,Alhamdulillah haka nake son ji,Mama ni cikin da take dauke dashi ya kamata musan yadda zamu yi dashi dan bana so ta haihu da moha,Abunda za'ayi ki shirya muje gidan Mallam na kan tudu aikinshi kamar yankam wuqa cikin nan ba dai ta haifeshi ba. """""Da sassafe suka shirya suka tafi gidan Mallam,Bayan sun gama gaya mai buqatarsu,Ya dauko wani magani a yar'qaramar kwalba ya basu yace su yayyafa a bakin qofa data tsallaka cikin zai bace aljanu zasu dauke,Suka dawo gida suna murna.Na fito falo zan shiga kicin,Moha na zaune falo,fadeela na kicin.Ina sa qafata daya kitchen naji jiriii kan kace haka na fadi kasa,a guje moha ya shigo kici jin qarar faduwa ta,Bai tsaya wata wata ba ya daukeni sai asibiti fadeela ta bishi."""Muna isa asibiti Doctors suka yo kaina kaina aka shiga dani emergency.Dr.Ameenu da ya fito Moha yayi kanshi yana cewa Ya basma,Basma x fine but tana buqatar rest so yanzu mun mata allurar bacci in two hours tym she will ohkay,Abunda ke cikinta fa,Watan cikin Basma nawa,5,Sai dai kayi haquri Moha but ba cikin basma,kamar ya ba cikin basma,Eh toh gaskiya ba wata alama da ta nuna misscarriage tayi kuma faduwar nan da tayi bata da alaqa da fitar cikin,kawai mun duba munga babu komai a cikinta abu kamar dai aljanu,Anya matarka bata da aljanu,No basma bata da aljanu,But gaskiya abun da mamaki.Moha kuka ya riqa yi kamar wani qaramin yaro yaji ciwon rasa cikin nan yadda ya qwallafa ransa wai ma garin yaya basma ta fadi ya tambayi fadeela dake gefe tana kukan munafunci,Nima haka kawai naga ta fadi anya maganar da Doctor ya fada ba gaskiya bace basma nada aljanu dan nima ina yawan ganin tana abubuwa kamar mai aljanu,A fusace moha yace kar ki qara cewa matata nada aljanu Qaddara ce kawai daga Allah but bansan ya basma zata ji idan taji ba cikinta bayan wahalar da ya riqa bata,Fadeela tana wani shessheqar kuka wlh nima abunda nake tunani kenan.""""""Da aka sanar dani cikina ya zube nayi kuka kamar raina zai fita,Moha nata lallashina yana qoqarin kwantar mun hankali. """"""Na cigaba da harkokina,Na kanyi tunanin me ya jawo cikina ya zube gashi likita yace ba wata alama da ta nuna zubewar cikina Allah kadai yasan Gaibu shi yasan dalili,na ma daina damuwa. """""""""Moha babu yadda bai yi dani ba in huta kwana biyu in bar makaranta Naqi bana son missing lectures da attendance."""""Gobe muna da test,Munyi da Usman zamu hadu Yau after lectures zai koya mun."""Moha ranar yana gida bai fita ba,Kamar yadda aka saba Yau ma text aka turo mai ,da yaga sabuwar number sai da gabanshi ya fadi hannunshi na rawa ya bude message din《DA FARKO NA GAYA MAKA MATARKA NA TARE DA WANI ,KA WATSAR DA ZANCEN ,KAJE MAKARANTARSU YANZU BAYAN LIBRARY DAN GANEWA KANKA》.""""Waye wannan ke nema tarwatsa mana farin cikinmu Yake son lalata mana aurenmu da basma,in har naje gana ba haka ba ,The person sending ol diz text messages must pay for it. """"""Duk sanda Zamu yi karatu da Usman wurin da ba mutane,ba hayaniya muke samu mu zauna.""Cikin mintuna kadan Moha ya iso makarantarmu Direct bayan library inda muke karatu.Usman ya miqo mun lemo Nace no usman Thank you,Ashe ya hango moha sai yayi kamar zai bani a baki ,Moha na ganin haka ya fisgi mota sai gida yana ta huci yana jiran in dawo."'Usman me kake qoqarin yi Are you out of your sense,lemo fa kake qoqarin bani a baki,Am soo.......,Dakata ba wani haquri da zaka bani,daga yau bani ba kai ko a hanya kar ka qara nuna ka sanni,na lura baka da mutunchi,Na kwashe littafaina da jakata na shiga motata ,Basma basma plzzz ki tsaya,na figi motata nayi hanyar gida. """"""Usman ya kira fadeela ya fada mata duk yadda aka yi,Don't worry usman ko ta yanke alaqarta da kai,ka gama aikinka yanxu sauran namu ne,Toh ranki ya dade.Ta kashe wayar tana murna ta gayawa Adda bongel duk yadda aka yi,Adda bongel tace sai ki sauri ki shirya kije kiga yadda zasu kwashe. ""Moha sai zirga zirga yake a falo,yana cewa wato duk text din da ake turo mun gaskiya ne.......Nai sallama,na shiga falo,Saukar marai naji a fuskata sai da na kusa faduwa kafin in dago ya qara kai mun wani marin.""Da waye na ganinki yau a makaranta yana qoqarin baki lemo a baki? Take yan'hanjina suka bada qololu jikina ya hau rawa,Zaki bani amsa ko sai na tattaka ki,Nama rasa mai zancewa moha,Dama dama........Dakata Ashe duk abunda ake gaya mun a kanki gaskiyane Basma kin ci amanata kin yaudareni,kinsan bakya sona tsakani da Allah me yasa kika aureni,Moha stop saying dat ka tsaya ka saurareni ,Ba abunda zan saurara daga gareki kin zama maqarciya basma naga komai da idona,Kanki ki yiwa,Ya wuce daki nabi bayanshi ya rufe da key,Moha Dan Allah ka bude kaji me zan gaya maka abunda kake tunani ba haka ba,Nayi ta buga kofar yayi banza dani Shima kukan yake."""Na tashi na koma dakina na fada kan gado ina kuka ,Ni na jawowa kaina,I hate you Usman,Allah ya isa tsakanina da kai,kai ka haddasa rikici tsakanina da mohana,Da na fadawa moha tun farko da duk haka bata faru ba,Wayyo Allahna😭😭😭 kuka nake ba kakkautawa,Fadeela tazo tana lallashi a gabanta akayi komai,kiyi haquri komai yayi zafi maganinshi Allah,Zafin kishina yasa ya miki haka zuwa anjima zai huce,idan ya huce ki same shi kiyi mai bayanin komai amma basma kinyi ganganci ba'a boyewa mini irin wannan ,Fadeela banyi tunanin haka abun zai zama ba kuma har ga Allah ina da intention din sanar dashi na rasa ta yadda zan fara mai maganar sai gashi haka ta faru,Wannan muqaddari ne daga Allah sai ki kiyaye gaba ni xan tafi kar mam taga na dade............... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👧 NA ZEE YABOUR❤ PAGE 35-36 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ ======Yau ce rana ta farko dana kwana ni kadai ba tare da moha ba tun aurenmu kasa barci nayi ga rashin moha kusa dani gashi moha na fushi dani,Tashi nayi ina ta sallah ina gayawa Allah matsalata. =====Moha shima ya kasa barcin yana tunanin basma ko wane hali take ,can kuma ya tuna ganinta da yayi dazu tare da wani wani haushi da kishi yaji sun dirar mai a lokaci daya,Tashi yayi yayo alwala ya fara sallah. """"""Da safe na hada breakfast na jera akan D.Table kamar kullum, ina jiran fitowar Dr.Moha,Zuciyata nata dukan Uku-Uku ko a wane hali fito Yana fushi ko ya huce haka na dinga wasi-wasi,Qamshin turarenshi da naji ya sani juyowa,Fuskarsa murtuke ,Muryata a sanyaye nace Ina kwana? Ko kallo ban ishe shi ba naga yayi hanyar fita,Ga fa breakfast dinka,Banza yayi dani ya fita ya buga kofar."""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Na shiga uku,Ya zanyi da raina Moha na fushi dani,Nan na zube qasa ina ta kuka.Fadeela ta sameni a haka,Subhallahi Ba dai qara dukanki yayi ba,Na girgiza kaina alamar A'aah,To me ya faru sakin ki yayi,Na dago da sauri na kalleta Saki fa kika ce kar Allah ya nuna mun wannan ranar ,Ameen nima bana fatan haka,Ki gaya mun me ya faru?Fadeela moha fushi yake dani ko breakfast din da nayi mai bai ci ba ya fita abunshi Ya Zanyi da raina,Yi shiru basma In shaa Allah Komai zai yi dai dai kamar ba'ayi ba.Fadeela nata bani haquri ni kuma sai kuka nake,Wayarta ta fiddo tana recording kukana. ======Data koma gida ta kunna musu《Recording din kukana》 Suna ta kyalkyata dariya suna murna.Fadeela Tace Amma har yanzu ya kasa daukar mataki a kanta,Ni shegiyar da naga tana kuka na dauka ma bankarta yayi,Adda bongel tace ke dai muje zuwa nan gaba zaki ga mai zai yi,gajiya zai yi da ita.Suka sake kwashewa da dariya. =========Gadonmu an bar maganarshi wai sai an gano Ya safwan Yana raye ko a mace. """"""Yau kwana biyu Moha baya kulani baya cin abinchina,ko gidan bai cika zama sai ya fita tun safe sai dare zai dawo. Duk na rame bana iya cin abinchi,bani da aiki sai kuka,bani da wanda zan gayawa matsalata Ya share mun dama momyna,Daddyna ko Ya safwan na nan da sai in sanar dasu suyi mai bayani to duk babu su,Ya Allah bani da kowa sai kai,kai mun jagora. Nusaiba da Nabeela suka zo ranar,Nusayba ke cewa me ya sameki Aunty basma idonki yayi ja kin rame baki da lafiya ne? Nayi murmushin qarfin hali Nace Eh!Nusaiba ,Naby tace Ina Ya moha? Yana dakinshi sama,ohkay Aunty plz kira mana shi,A'ah kuje da kanku. ======Moha na daki,Ya zauna jigum yana fitar da qwalla ,Yana magana shi kadai:Ina son basma,Ina qaunarta,duk abubuwan da nake mata danne zuciyata kawai nake but deep inside my heart Ina son kasancewa tare da ita ko kadan bana son inyi nisa da ita bazan iya rabuwa da ita ba amma dole in nuna mata fushina in horata kaii inta kama barin makarantar zata yi gaba daya,Abun da na kasa ganewa shine Basma na sona ko kuwa tsabar Yaudara ne. """""""Yana jin shigowarsu Naby yayi saurin goge hawayenshi,Suka qarasa gababshi Suna cewa Yaya me ya sameka kake kuka? Aunty Basma itama munga idonta yayi ja daga gani kuka amma tace mana bata da lafiya,Nima bani da lafiya ne,Are you sure? Yes ya daga kai alamar Ehhh,Allah ya baku lafiya Ameen.Naby tace to kazo muje kasa,A'aah ku barni anan bacci nake ji,Tohm sleep well,Suka dawo falo."""""""Sun debe mun kewa sosai sai dare suka tafi a daki suka sami moha suka ce mai sun wuce.Suna isa gida Nabila tace Ammi Ya moha da Aunty basma basu da lafiya da mukaje suna ta kuka,Subhaballahi Kuka?? Ehh Ammi,Amma Muhammad bai gaya mun basu da lafiya ba kuma wannan wane irin ciwo ne zai zasu kuka dole inje gidan gobe,Nusayba tace momy duk sun rame,Ah! Ah! To me ke faruwa dasu???? """""""Tun da sassafe Moha ya fita,Ammi tazo gidanmu a falo ta sameni ,Nayi nisa a tunani ban ma san tazo ba sai ji nayi ta tabani Nayi firgigit Nace Ammi Ina kwana ? Lafiya lau lafiyarki kuwa,Lafiyata lau Ammi,Ta zauna bayan na kawo mata abun motsa baki da lemo Tace basma naga fuk kin rame idonki sun kankance ,Na qaqalo murmushi nace kawai dai bana jin dadin jikina ne,Bana son karya basma,kada ki boye mun komai ni mahaifiyarki ce ko dan cikin ki ne da ya zube?? A'ah Ammi,Toh ki gaya mun me ke damunki? Nay shiru in gaya mata ko inyi shiru kai wannan wata hanya ce da zata magance mun matsala,Mahaifiyarshi ce ita tasan yadda zata lurar dashi,kinyi shiru basma,Na gaya mata komai tun daga farkon haduwarmu da usman ba abunda na boye mata,Garin yaya har ta kai ku ga haka,basma baki kyauta ba da baki sanar dani ba ai na dauka kin daukeni matsayin uwa,Kunyi ganganci ku dukanku ai ba'a boyewa miji irin wannan shi kuma kamata yayi yai kwararren bincike kafin ya dau hukunci,Ina Muhammad din ?? Ya fita. Shikenan yau din nan zan kirashi in lurar dashi,A kiyaye gaba kuma kuyi ta addu'a ni zan koma gida,Nagode Ammi na mata rakiya.na dawo a raina ina cewa Allah yasa karshen fadan mu da Moha Yazo. ========Ammi ta kira Moha,Ta mai bayanin komai ta mai fada sosai akan ya lura kuma ya riqeni Amana kar ya manta ni marainiyace bani da kowa sai su tunda DANGIN MAHAIFINA dasu da babu duk daya. =========Ina dakina na idar da Sallar isha'i Ina karanta Al'Qura'an,Mutum naji tsaye a kaina kaina na daga sama dan ganin waye ido hudu mukayi da moha ya sakar mun murmushi,Wani sanyi naji ya ratsa zuciyata kamar an zuba mun qanqara ,Kneeling yayi Am sooo sorry basma,i have cause you alots if pain ba da laifinki ba plzzzz forgive me,Na tashi tsaye na riqe hannu nace tashi my luv,Nice nama laifi i lied to you,Yana miqewa ni kuma nayi kneeling Am really soo shhh ji nayi ya daga ni sama ya daukeni ,Ya jefa ni kan gado,Ya rungumeni tsam,plzzz basma kar ki qara boye mun wani abu game dake kin zama ni na zama ke,En plzzz ki yanke duk wata alaqarki da usman,In shaa Allah haka ba zata qara faruwa ba,Yawwa my swty ,I really miss you ,Ba wani missing dina da kayi tunda har a kyaleni,Daina ma fadar haka ,Na turo baki Ehh mana,bakin kawai naji ya kama ya fara kissinf sai da muka yi kusan 5min muns kissing juna,I really miss kissing diz ur swt lips,Plzz moha kar ka sake punishing dina da rashinka kusa daniU know I really luv you i can'i live without you,Don't worry my swty,i also can't live without you,u're my life my everything.""'Tashi ki sa kayan bacci,zanje dakina Am waiting for you kinsan yau kin zama sabuwar amarya,Nayi dariya zuciyata fal da farin ciki,Na shiga toilet nayi wanka nasa rigar baccina iya gwiwa na feshe jikina da turaruka masu kamshi."""" Mun bayyanawa juna so ❤❤da qauna 💘💘a daren.Bamu tashi ba sai 8am ko sallar asuba banyi ba. """"""""""Mukayi sallah ,Na tafi dakina nai wanka na shirya,Mukayi breakfast ,Bayan mun gama breakfast na daura kaina akan kafadar moha,muna ta soyayyarmu💞💞.A haka fadeeka ta same mu,A ranta tace Sun shirya kenan,Lallai son da moha kema basma bana wasa bane sai mun dage sosai zamu iya raba su.Tai saurin kawar da tunanin tana far'a tace uhmm...Masoyan Asali kenan basma maimaikon ki kirani ki mun albishir kun shirya da habibinki,A'ah na bari ne kizo ki gani da kanki kinsan ance gani ya kori ji ,Toh!Allah ya bada zaman lafiya,Ameen,Nan ta zauna falo muna hira. ======Da kuka fadeela ta koma gida .Lafiya Ya akayi Adda bongel duk ta rude tana tambayarta,Mama basma da moha sun shirya,Ta dafe qirji da gaske kike? Ehh!mama kinga son da suke nunawa juna tun ba moha ba kamar zai hadiyeta,Wannan ya nuna duk makircin mu baxai sa ya rabu da ita ba tunda yana sonta sosai dan haka sai mun hada da Mallam na kan tudu,Masoyan juna ko nayi alqawarin sai na rabasu ko zan tsiyace ki rubuta ki ajiye kafin rana ita yau basma ta bar gida moha............................ [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👦‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 37-38 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Adda bongel da Fadeela suna zaune gaban mallam,Adda bongel ta gaya mai matsalar da ta kawo su Tace Muna so ka sa mai tsanarta a zuciyarshi Yaji baya sonta baya sonta kusa dashi komai nata baya burgeshi.Mallam yayi dariyar mugunta Wannan ai mai sauqi ne Gobe kuzo ku karbi hadin da zan baku a abinchi zaku sa mai da yaci hhhh ya sake dariyar mugunta sai kunzo yi mun godiya nima nan zanyi wasu yan tsibbace tsibbace. ★★★★Wata sabuwar soyayya mai qarfi ta kullu tsakanani da moha,Kullum addu'ata Allah ka barni da Moha har karshen rayuwata. ★★★★★ Na yiwa Moha rakiya bakin mota,Har ya shiga mota yace Yau ina marmarin dan'wake,Nayi dariya nace dan'wake kuma,Erh shi nake son ci,Toh shikenan,Mai zan taho miki dashi,ba komai ,Kin tabbata,Ehh! .""Ina ta tunanin ina zan samu garin dan wake bana son yin na fulawa nafi son asalin garin,Fadeela ta fado mun a rai,na dauki waya na kirata bayan mun gaisa take cewa kinji ni shiru koh,No ma ba haka ba Dan Allah Garin dan'wake nake so,Yau kuma dan'wake kike marmarin ci ko dai kin samo wani cikin ne,Ke dai fadeela bakya rabuwa da tsokana Ni bana ma cin dan'wake Moha ke so,Muna ma dashi a gida sai in debo miki,Yawwa nagode,Haba! Ba komai ai Yanxu nan zanxo in kawo miki.Adda bongel ta yatsina fuska tace Hala shegiyar can ce ta kira? Erh iita ce wai garin dan'wake take so,kinga mama yazo a sauqi sai in zuba maganin a ciki,Kin kawo shawara mai kyau toh yi maza ki diba ki zuba ki kai maya kada ta ji ki shiru.Fadeela ta zuba maganin a cikin garin dan'waken ta chacchakuda ba zaka taba gane an zuba wani abu a ciki ba. ★★★★★★★Allah yasa ban bata miki lokaci ba go slow ne ya riqe ni a hanya,Nai murmushi Ai ba sauri nake ba Mohan ma ba yana nan sai da yamma zai dawo,Ai na dauka yanxu yake son ci har ina ta sauri,A'aah pha sannu da qoqari Nagode,Ki daina mun godiya ai yiwa kaine kuma zanso ki yiwa Moha abunda zai faranta mai rai,Nayi dariya ina godewa Allah da ya hada ni da fadeela mai kaunata kuma ba komai a cikin DANGIN MAHAIFINA akwai mai qaunata.Fadeela ta kama mun nayi dan'wake,Na yanka tumatir da Albasa qanana da dafaffan kwai na jera a dining table da wani yaji mai dan karan dadi😋😋 ★★★★★Moha na shigowa falo yace Uhmm......Duk kamshin dan'waken ne haka shi zan fara ci kafin na watsa ruwa.Dining table ya nufa,Nayi serving dinshi kasancewar bana cin dan'wake ni kadai na riqa bashi a baki sai da yace mun ya koshi,Yayi Hamdala. Na hada mai ruwan wanka,ya watsa ruwa da ya fito toilet ya riqe kanshi yace Waaash,Lafiya Moha?? Kaina naji yana sarawa,Eyyah! Barci ne da gajiya sannu Yace Yawwa,Ka kwanta ka huta na kama shi ya kwanta Na rufe shi da blanket. Fadeela ke tambayata ina mutumin naki kika fito kika barshi ? Ya dan kwanta ne kanshi ke ciwo,Allah sarki nasan gajiya ce,Ehh gajiya ce da rashin isasshen barci.A ranta tace GREAT JOB! Basma kin bar gidan nan kin gama ke mai miji koh,Very soon zaki zama bazawara ★★★★Moha ya dade yana barci har magrib nace bari in tada shi sallah,Na janyen bargon jikinshi a hankali dama haka duk zan tashe shi,Wani tsaki yayi yaja bargon ya sake lullube kanshi,Lafiya Moha ke tsaki ina ga ma bai san yayi ba Nayi dariya ganin yadda ya sake qudundunewa cikin bargo,Na sake janyewa a hankali,Tsawa naji ya daka mun Dalla Mallama ki kyaleni me zan miki,Tuni jikina ya hau rawa Mamaki da tsoron Allah sun cikani Yau moha ne ke mun tsawa daga na tashe shi daga barci,Bakina na rawa nace Gani nayi lokacin Sallah yayi shine nazo tada kai,Naji toh,Tsayawa nayi cak me yasa moha yake mun haka Anya Aljanu basu shafe shi ba,Ni malama tashin mun kai kin wani zo kin tsaya mun a kai kamar soja,Wani jiri naji yana dibata da kyar na iya kai daki wai yau Moha ne ke hantara ta shi da a kullum burinshi in kasance kusa dashi,Kukan zuci na riqa yi hawayen sun ma qi fitowa tsabar qunar da zuciyata keyi,Da sake naga ba wani laifi dana mishi ko dai an sake gaya mai wani abu a kaina ne i have to ask him.""Dakin na koma na sameshi ya idar da Sallah kenan.Na durkusa gabanshi ""Dan Allah Dan Annabi idan laifi na maka ka gaya mun in baka haquri kuma in daina" Ba komai kawai dai ina son samun hutu ne bana son kowa kusa dani,Har ni Moha,Har ke ko baki ji me nace bane KOWA,Ban sake cewa komai ba na fita ina mamakin Moha. ★★★ Moha a zuciyarshi wata irin tsanar basma yake ji da bai san inda ta samu asali ba ,Yaso ya karyata zuciyarshi cewa bai tsani basma ba amma ina shi akan me ma zai tsaneta,Ji yake baya son ganinta kusa dashi. ★★ ★Kullum abun sai gaba yake tun ina zuwa kusa dashi yana hantara ta har daina xuwa na fawwalawa Allah komai.................................... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👦 NA ZEE YABOUR PAGE 39-40 ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ ★★★Moha na zaune a office dinshi abun duniya duk ya ishe shi He can't believe wai shine Yau ya tsani basma Yake jin baya son ganinta He prefer to look @ a dog than her,Haka yake ganinta kamar mujiya,Bude kofar office din aka yi hade da yin sallama,Ya kalli kofar y amsa sallamar wata nurse ce ta shigo ta miqa masa wani Envelope gashi aka ce in baka,From Who? No bai fadi sunanshi,its ohkay Thanks Ya ajiyae akan table din dake gabanshi""Yanzu haka Yan neman alfarma ne inje asibitinsu ko wasu family suna so in duba wani member nasu ,ba su san halin da mutum ke ciki ba,Yaja tsaki ya dauki envelope din ,Papers ne guda biyu a ciki duk a nannade(Folding) babba da qarama,Ya fara bude paper da tafi girma 《ASLM YA MALLAM MOHA MAI MATA,WACCE KAKE SO KAYI TRUSTING DUK KARYAR(LIES) DA ZATA GAYA MA ZAKA YARDA BA TARE DA KAYI WANI BINCIKE AKAI BA.ANYWAY MATARKA TA BOYE MA GASKIYAR TSAKANINITA DA USMAN,IDAN HAR BA SOYAYYA SUKE BA ME YASA ZATA BOYE MA ALAQARSU AT THE VERY FIRST BEGINNING KANA MATSAYIN MIJINTA AND INA KA TABA GANIN BA SOYAYYA JUST MUTUNCI NAMIJI ZAI DAUKI ABU YABA MACE A BAKI KNOWING THAT SHE IS A MARRIED WOMAN BUT DUK SO YA RUFE MA IDO KA KASA GANE WANNAN DAMA HAUSAWA SUNCE SO HANA GANIN LAIFI(LOVE IS BLIND) KA SAKE TUNANI. ABU NA KARSHE DA ZAN GAYA MA IDAN KA GA DAMA KADA KAYI BINCIKE AKAI SHIMA KA BARI SO YA RUFE MA IDO BUT NI DAI NA GAYA MA::CIKIN MATARKA DA YA ZUBE BA ZUBEWA I GUESS DR AMINU YA GAYAMA BA WATA ALAMA DATA NUNA MISSCARRIAGE TAYI,LET ME MAKE IT CLEAR TO YOU ZUWA TAYI AKA CIRE MATA CIKIN TWO DAYS BEFORE TA FADI A KITCHEN ITA DA MASOYINTA USMAN WANDA TACE MA HE IS JUST HELPING HER AT SCHOOL D REASON IS DAT BA CIKINKA BANE NA SHI NE ,ASIBITIN DR.YAKUBU ASIBITIN DA BA KOWA YASAN DASHI BA ,KAJE ASIBITIN KA BINCIKI DR.SALIS SHI YAYI AIKIN LASTLY GA WATA SHAIDAR NAN KAFIN KAJE ASIBITIN ,DAYAR TAKARDAR YA BUDE YAGA SA HANNUN MUTUM BIYU DAYA SA HANNUN EXACTLY NA BASMA,DAYA NA WANI WANDA HAKAN KE NUFIN NA USMAN NE CEWA SUN AMINCE A ZUBAR DA CIKIN》Moha yace but who is diz dat know so much about me and my wife,I have to find who the person is but i have to find the truth about what diz letter is saying first before knowing who the person could be???? """Double ya rika gani, at the same time yaji tsanar basma ta karu a zuciyarsa,Mukullin motarshi ya dauka Sai Asibitin Dr Yakubu wani local hospital ne da ba kowa ya san dashi ba,Yana zuwa yace yana son ganin Dr.Salis nan take a kaishi office din Dr.Salis. " A gurguje suka gaisa ya fiddo takardar sa hannun Yace Plzz kasan wani abu related to diz ya mika masa paper,Dr.Salis ya karbi paper ya duba Ya girgiza kai ofcourse Yes! nima nayi aikin ko ba wata Yarinya Basma ba da mijinta Usman,Yeah su ,Nan suka zo suka ce suna so in cire cikin basma,Na tambayesu don me suke so a ciren cikin bayan dan'sunnah ne ba ta hanyar banza aka same mishi ba Suka ce Cikn na bata wahala ,She is too young and tana zuwa school abun zai mata yawa.Moha ya daki table din dake gabanshi da Dr.salis da karfi ya dafe kanshi dan wani irin sarawa yake mai,Dr.Salis Yace Lafiya ?Akwai wata matsala ne?? Moha yayi karfin halin cewa No babu,Zuciyarshi nata tafarfasa ji yake kamar zara fashe,Yana ta gudu da Mota so kawai yake ya ganshi a gida,Basma u betrayed me,Kin cuceni I will never ever forgive u,u have to pay for this i promise " Dr Moha na fita office din Dr.Salis ya dauki ya kira Adda bongel Yace Hajiya Yanzu nan ya fita office dina Anyi duk yadda kikace,Toh madalla Sai kaji alert na sauran kudinka《ALLAH KA RABA MU DA MAKIRAI WAI YAN'UWAN MAHAIFINKA SUNE KE SON GANIN BAYANKA,DAMA ANCE MAKASHINKA NA NAN TARE DA KAI YADDA BASMA TA DAUKI FADEELA DA ZUCIYA DAY BUT ITA GA ABUNDA TAKE SAKA MATA DASHI》 ★★ Da Karfi yake buga kofar kamar zata balle,A tsorace na bude kofar ,Saukar maruka naji a fuskat dan ni kaina bansan iya adadin su ba Charger ya dauko yana ta dukana ko ta ina""Macuciya,Mayaudariya Azzaluma Allah ya isa tsakani na dake Ashe ba cikina bane na dan'iskan saurayinki ne shiyasa kika je aka cire shi Basmata kinci amanata,Kwakwalta naji tana juyawa Nace innalillahi wa'inna ilaihir raji'un A ina kaji Wannan Zance Wallahi Sharri ake mun,Dalla rufe ma mutane baki Munafukar banza da wofi Na rufa miki asiri baki da kowa Na rike ki Amana amma sakayyar da zaki mun kenan Allah ya isa tsakanani dake Basma Mazinaciya Fasiqa"""Kamar an watsa mun tafasassun ruwan zafi haka naji kalmar Mazinaciya fasiqa,Nace Moha ni ba mazinaciya bace ko da ina budurwata na tsani zina ban taba aikatawa ballatana yanzu haba moha think.""Ba tsayawa zanyi sauraren dadin bakinki ba,Basama bana sonki bana qaunarki bana sonki kusa dani bazan cigaba da zama da mazinacoya ba zan iya jure duk wani halinki but banda zina dan haka kije NA SAKE KI SAKI UKU """"""Wayyo Allahna Na shiga Uku Na qanqameshi Ina cewa Dan Allah kar ka mun haka Moha Wallahi baxan iya rayuwa babu kai ba,bani da kowa sai kai idan ka rabu dani ina zanje dan Allah ka rufa mun asiri,""Kije dan'iskan da ya miki ciki ya aureki ,Wallahi Moha sharri ake mun babu wanda ya taba sanina a matsayin Ya'mace sai kai,""'Shut up! Mayaudariya Ya fincikeni daga jikinshi ya tunkude Bani bake har abada,I hate You,Na riko rigarshi plzz Moha kaji qaina kada ka rabu dani idan ka rabu dani mutuwa zanyi,Ya buge hannuna ya sake tureni So What ki mutu mana Ina ruwana Ina so kafin naje na dawo ki tattara kayanki babba da qarami ki bar mun gidana ko kuma ki fuskanci wulakancin da baki taba gani ba a rayuwarki Ya fice fuuu. "" Nan na duqe ina ya kuka kamar raina zai fita,Ban yarda ba moha bai sakeni ba Mafarki nake na mari kaina ko na farka Ya Ilahi yaushe zan farka daga mafarkin nan,Shikenan mutuwa ta tazo Moha shi kadai ya rage mun bani da kowa sai shi gashi yau ya sakeni yace in bar mishi gida Da iyayena nada rai ko ya safwan moha bai isa ya wulkantani ba,Ya Allah kai mun sakayya akan duk wanda ya mun sharrin nan Ya Allah ka yaye mun Wannan masifar da nake ji.Wayata naji tana ringing kamar bazan dauka ba,na dai dauka Fadeela ce,Nace hello cikin shessheqar kuka, Subhanallahi ya naji kamr kina kuka,Moha Ya sakeni,Ya sake ki,Innalillahi........Gashi bana gari ina zaria kira ma nayi ince miki na tafi zaria kar ki jini shiru kwana biyu but bari in kamo hanya gani nan xuwa yanxu nan. "" Wani tsalle fadeela ta daka ta rungume Adda bongel Ya saketa ,Alhamdulillah!! Fareeda tace Ya fadeela dole yau muyi party,Dole yar'wanwata bari inyi sauri in kira mutanen can,Ta danna kira Hello!ku tsaya wajen area da ta fito ko dauketa kar ku barta da rai ku tabbatar kun kasheta but kisan da baza'a tsargi kowa ba,An gama ranki ya dade. """ Kamar daga sama naji muryar moha Au baki tafi ba Uban me kike jira ,Moha plzz,Dakata! Zamana dake ya qare ko baki ji me nace bane dazu in sake maimaita miki Na sake ki saki uku,Moha ka tausaya mun dan Allah,""Maigadi da kai da Rabi'u kuzo ku fitar mun da ita."""Tsaya sukayi suna shakkar tabani Ya daka musu tsawa nace ku fita da ita, A fusace nace ENOUGH! Moha dan cin mutunci Maigadi da mai sharar tsakar gida ne zasu fitar,Moha ka sani nafi karfin ka wulakantani ka bar ganin ina roqonka zan bar maka gidanka ko da kaine autan maza yau sai na rabu dakai,In dai ni yar'halak ce sai kayi nadamar wulaqantar da kayi ,Nadamar rabuwa da mazinaciya never,Nagode naji ni mazinaciya ko ba dade ko ba jima gaskiya zata tayi halinta Nagode nayi hanyar fita,Ina zaki baki kwashe kayanki ba ,Bana buqatarsu na fice. ""Nabi titi ina tafiya zuciya na daci da kunar bakin ciki bansan ina zani ba,ba zanje wajen DANGIN MAHAIFINA BA nasan can wata wahalar zan tarar gwara inbi hanya in mutu duk in huta tunda na rasa masoyana,Ina tafiya ina roqon Allah ya dau raina Naji an rufe mun baki an jefa ni cikin mota Daganan ban qara sanin inda kaina yake ba sai da na bude na ganni a dajin da kika Ganni................. ★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★★ TAMMAT BI HAMDILLAHI ANAN NA KAWO KARSHEN PART DAYA SAI MU HADU A KASHI NA BIYU............. ZEE YABOUR❤❤❤ [11/12, 2:38 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~~~PART II~~~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE ^^^1~~~2^^^ *********************************************************************************** . Basma kuka take ba kakkautawa,khadeeja itama kukan take tace A gaskiya Basma kinga rayuwa labarinki kamar a film,Moha ya zalunceki kuma jarabawace daga Allah bai kamata kina wa kanki fatan mutuwa ba,Allah na son masu haquri ki miqa dukkan al'amuranki zuwa ga Allah shi zai miki sauyi da mafi alkhairi,Ina so ki daukeni a matsayin yar'uwarki wacce kuka fito ciki daya ,ki dauka nan tamkar gidanki ne,Basma tayi murmushi tace nagode sosai,Allah ya saka miki da Alkhairi.Ameen taso muje falo. . Afra da Ashraf na zaune parlor suna kallon cartoon,Khadeeja tace Afra,Ashraf na'am mummy,kunga wannan Aunt dinku ce ta nuna basna sunanta Aunty Basma,Afra tace but mummy i have never seen her befote Aunty su'ad dasu Aunty jidda kadai na sani,Ashraf yace nima haka,Khadeeja tayi murmushi ehh bata 9ja ne buh now she x going to be staying here with us,Yeyyy Afra tayi tsalle na samu Aunty dama kullum ina cewa Aunty su'ad ta dawo nan gidan sai tace zata dawo but sai taqi xuwa in tazo zan mata gwalo ince mata na samu wata Aunt din,Afra kin cika surutu,Ashraf yace Mum she x talkative ,Afra ta tabe baki mummy kin ganshi ko,Ashraf ka daina.Basma taji yaran sun burgeta har tana murmushi. . Afra tazo kusa da ita ta zauna tace sunana Afra,basma tayi mumrmushi tace Nice name,Ashraf yazo ni kuma Ashraf Uhmm...nice name too,Afra tace to ba dai Aunt dinka bace tawa ce ni kadai. Yaran kyawawa farare sol duk da cewa khadeeja baqa ce,Ashraf yafi kama da ita dan dai shi fari ne,Afra ko kadan bata kama da ita,basma take cewa maybe Dad dinsu suka biyo wajen fari,Afra nata ma basma surutu,Khadeeja tace Oya! Ku tashi kuje ku kwanta gobe school,Okay mummy kowannensu yazo yayi dinta suka ce gudnytt mummy en Aunty basma,Sweet drmx my kids,Night kadai basma tace musu. . Basma tayi zurfi ciki tunani Allah mai iko Yau ita ce a gidan wasu da bata hada zumuntar komai dasu ba,Rayuwa kenan kana naka Allah na nashi ko a mafarki bata taba tunanin zama da wasu da ba familynta ba buh destiny. . Khadeeja hankalinta na can kan wani indian series "king of hearts" but akai-akai tana juyawa ta kalli basma wacce ta kafawa Tv'n ido kamar mai kallo but a zahiri hankalinta baya kan kallon tayi nisa cikin tunani, Khadeeja tace ko kina jin barci ne naga kamar kina lumshe ido? Basma ta gyada kanta sama,Banda abunki kina jin barci ai sai kije ki kwanta,ki saki jikinki basma nan gida ne ki daina damuwa,Tace Toh . Kwance take a kan gado ta rufe idonta tana tuna wulaqancin da moha ya mata,Ni moha zai wulaqanta ya kore ni daga gidanshi ya mun saki uku Allah kai mun sakayya,Gashi ina son Moha bansan ya zanyu da son shi a zuciyata ba,Allah ka cire mun son Moha a zuciyata ka mu sanya mun da mafi alkhairi,Allah ka jikan iyayena ka bayyana mun Ya safwan a raye ba'a mace ba ko na rage wani zafi . Kwana tayi sallar dare tana rokon Allah ya chanza mata rayuwarta da mafi alkhairi Yasa Zamanta a gidan nan Alkhairi ne . An kawo mata breakfast daki kayan tea da Yam balls with sauce,Tea kadai ta sha sai Yam ball taci kwara biyu shima dan kar khadeeha tace bata ci komai ba,Khadeeja ta sami basma daki,Ina kwana basma ta gaisheta,lfy lau kin dai yi breakfast ba ko,Eh nayi,Ta bude foodflask ai baki ci komai ba ki qara mana,No wlh na qoshi,ohkay tohm kiyi wanka ki shirya zamu fita tare,Toh . Tayi wanka ta saka sababbin kayan da ta tarar akan gado da hijabi kalar kaya . Khadeeja ke driving motar tana jan basma da hira.Wani haddaden Boutique suka je ta kasowa basma english wears da dogayen riguna masu bala'in kyau,sannan suka je shoppinf Mall ta siyo mata atamfofi,laces,materials da kayan kwalliya(cosmetics) da perfumes(turaruka),Basma dai taga khadeeja nata kwasar kaya a tunaninta kanta taje daukar ma,khadeeja tace Basma ki zabi abunda kike so,bana son komai,kinga basma kar muyi haka dake dan Allah ki dauki kuma me ye,Body spray ta dauka khadeeja ba yadda bata yi da ita ta qara wani abu ,taqi. . Suka dawo gida itama tayo siyayyar gida,Ta cire kayan basma gefe tace wannan naki ne basma,anjima zan kira Tailor yaxo ya gwada ki,Basma mamakin kirki da mutuncin irin na khadeeja take a ranta tana jin kaunar a zuciyarta. . Aunty kayan nan sun mun yawa dan Allah ki rage,Basma bana jin dadin irin haka da kike sai inga kamar baki daukeni a matsayin yar'uwarki ba,A'ahh Aunty ba haka bane,toh idan har ba haka bane ki daina mun irin haka ,Toh Aunty nagode sosai Allah ya biyaki ,Ameen tayi murmushi. Basma ta saki jikinta ta cire duk wata damuwa a ranta ,Ta fara sabuwar rayuwa ,khadeeja na nuna mata so sosai ita da ya'yanta.Sun saba sosai da khadeeja suna zama suyi hira sosai,labarin khadeeja a kullum na mijinta ne da irin yadda take son shi,Basma ita dai tsoronta Allah yasa mijin khadeeja ya amince da zamanta gidan ,but khadeeja nace mata mujinta nada kirki sosai ,son mutane da taimako ta kance Allah yasa da gaske take. Khadeeja Banker ce a UBA bank nan kaduna.Ta shirya tsaf zata tafi office ta leqa dakin basma,Na wuce office,ohkay aunty deeja sai kin dawo,Plzz a kula da gidan ,In shaa Allah Aunty. . Ta cigaba da kwalliyarta dama kwalliya take,Basma tayi fresh abunta,ta qara kyau.Basma kyakkyawa ce sosai,ga sexy eyes,dan qaramin pink lips dinta ,ga uwa uba hips ,gashi bata da qiba ,Da ka ganta kaga balarabiya sak,ba zaka taba cewa kayi aure kamar ba yar 20-12yrx kai kace she is 17-18yrx .Tana jin dadin zamanta bata da wata matsala fargabarta daya ko ADNAN BUBA zai amince da zamanta gidan ko zai koreta ne OHO! [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~~~~PART II~~~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE ^^^3~~~4^^^ ********************************************************************************************************* ^ Masu aikin gidan sun saba da ita sosai kuma suna sonta,Tana shiga kitchen ta taya su aiki,khadeeja tayi-tayi ta hanata tace ma khadeeja bata son ta zauna hakanan bata aikin komai ta riga ta saba a gidan moha. . Tana kitchen tana taya masu aikin hada abinchi da gudu Ashraf da Afra suka zo suka rungumeta Aunty basma Oyoyo! Oyoyo my lil-kids ta shafa kansu muje a cire uniform koh,ta cire musu uniform tasa musu wasu kayan"""Bayan sun huta sunci abinchi ta shirya su suka tafi islamiyya kafin xuwan basma wata nanny ce ke kula dasu tun haihuwar Ashraf aka samo ta kasancewar Khadeeja x always busy(office),shi kanshi Adnan ba ko da yaushe take da time dinshi dan dai shima ba mazauni bane sau da yawa masu aiki ke sawa suyi mai wani abu duk da masifar son shi da take,ba yadda bai yi da ita ba kan ta ajiye aikin ta zauna gida ta kula da yaranta dashi buh taqi a cewarta Aikin nata zai taimaka musu ko xuwa nan gaba idan Allah ya dauki ranshi pha wa zai kula da ita da yaranta,Yace mata ta bar aikin for now ta bari in ya mutun sai ta nemi aiki wai a'ah bata da tabbas zata samu aikin da albashinta yakai wannan haka ya haqura ya kyaleta ba don ranshi ya so ba,Sun shaqu da basma sosai har assignment dinsu ita ke koya musu,Sunfi sabawa da ita akan mamansu,da daddare sai weekends kadai ne take da time dinsu . Khadeeha nata faman gyare-gyaren gida ,tasa masu aiki nata share-share da goge-goge ita da basma suka shiga kitchen suna hada abinchi iri-iri dan Yau Adnan zai dawo khadeeja nata murna tana cewa Basma Yau dai babansu Afra zai dawo Wlh i can't wait to see him nayi missing dinshi sosai,Basma tayi dariya tace Allah ya kawo shi lfya ""Ameen Basma but basma naga kamar bakya tayani murnar dawowarshi, A'ah Aunty deejah ina tsoron kar ya dawo ne yace bai yarda da zamana gidan nan ba,khadeeja tayi smiling ta dafa kafadar basma tace kar ki damu Basma,Adnan na da sauqi kai yana da kirki da tausayi Am sure ba zai qi ki ba kuma Abunda nake so shi Adnan ke so bayan son ganib bacin raina akwai kyakktawar fahimta tsakaninmu,So Relax! Basma tayi murmushi a ranta tana cewa Namiji ba dan goyo bane ji yadda Aunty deeja ke rawar kafa akan Adnan bazai hana in ya tashi ya rufe ido yaci mutuncinta ba kamar bai taba ganinta ba kamar yadda Moha ya mata anyway mazan ma suna suka tara but ni kam daga kan Moha bazan sake yarda da wani namiji kaii ni da aure ma har Abadaa(Anya kuwa haka basma zata yi ta zama🤔)ba wanda zan taba so kamar Moha,Moha ka zalunceni Allah ya saka mun,taji hawaye na qoqarin gangaro mata tayi saurin gogewa,Khadeeja ta taba basma ,Whats Wrong? Tai saurin cewa nothing,Basma ki kwantar da hankalinki Adnan ba zai qi ki ba."""Abinci kala-kala suka yima Adnan dan khadeeja tace Adnan Values food alots,Ya tsani yaga mace bata yi girki ba. . Bayan sun gama khadeeja ta sake wanka ,ta chaba ado Riga da skirt atamfa sunyi mata kyau but basu yi fitting dinta ba kasancewar bata da hips da boobs sosai haka take a shafe Lol😉,Yar'gayu ce sosai,Kyakkyawa black beauty . Basma itama wankan ta sake dan duk tayi qaurin abinchi,Doguwar riga tasa na wani material rigar tayi fitting dinta sosai charas charas tunda ita akwai su ba kamar su khadeeja ba da ake a shafe lol😉,Simple make-up tayi dama ita bata heavy make-up ta daura dan'kwalunta gashinta duk ya kwanta a gaban goshinta Tayi kyau sosai so Take away👌🏻 . Aunty basma!Aunty basma Afra ta shigo dakin,Woow Aunty basma stunning,Thanks myvl little(sunan da basma ke kiranta kenan),Kitso zaki mun Aunty basma bana so daddy ya dawo yaga banyi kitso ba fada zai mun,Oya! dauko comb,hair liner da hair cream da gudu taje ta dauko ta dawo ,""Afra nada gashi sosai yana da santsi da laushi,Basma na mata kalaba tace my little gashin wa kika biyo NeNe,Wacece Nene,Mummyn Daddy,Uhmm...gashinki mai kyau,Thnkx my aunt,Basma da ta gama mata kalaba ta sa mata beads,ta mata wanka ta dai gyare Afra tass. ""Iyeee Babyna wa ya gyra ki haka inji khadeeha,Aunty basma ce,iyee yar'gidan Aunty basma . Basma a ranar wani irin bacci take ji sosai dakinta ta koma ta kwanta. . Around 7pm Adnan ya iso gida da gudu Ashraf da Afra suka tarbo shi,Ya dauki Afra wow my Afra kinyi kyau wa ya miki kitso ,Aunty basma (thinking wata mai kitso ce) basma khadeeja ta rungumeshi welcome my dear,Yayi murmushi yayi kissing dinta a goshi . Khadeeja bata ga basma ta fito ba,Tace oh!basma ta kasa jikinta,Adnan is a very simple and understanding person,khadeeja tace my dear taso muje kaci abinchi,Yace no bari in fara yin sallah,olryt xan jiraka nan . Dakin hutawarshi ya nufa,Mutum ya gani kwance kan gado ,Ya qarasa bakin gadon dan ganin mutum ne a kwance kan gadon ko idon shi ne,Basma na kwance nata sharar bsrcinta with her smiley face ko tana barci smiling take tsayawa yayi ya zubawa halittar Allah ido shi tunda yake bai taba gani kyakkyawa kamar basma ba,A ranshi yace yau yayi gamo da aljana tsayawa yayi yana qare mata kallo ita kuma ta bude idontq kenan suka yi four eyes👀 INNAHU MIN SULAIMAN WA'INNAHU BISSMILLAHIR RAHMANEER RAHEEM Ta fada ranta Yau nayi gamo da aljani dan a cikin mutane ba handsome kamar wannan Zuba ido suka yi suna kallon juna duk da a zuciyoyinsu suna tsoron juna(a tunanin kowannensu aljani/aljana ya gani) . Adnan fari sol dashi,ga hanci da dan qaramin bakinshi,gashin kanshi ya kwanta lub-lub yana sheqi kamar ya shafa mai,Adnan mutum ne mai son tsafta da gayu ya haduwa iya haduwa irin su Adnan in suna wuri wane su Moha . Basma tai saurin kawar da kanta gefe Yana ganin haka yai sauri ya fita yana tsoron kar ta juya ta cutar dashi,Ta juyo taga wayam bata ji alamun fitar mutum ba lallai tabbas Yau nayi gamo but ko waye a cikin aljanun sai an tona za'a samu handsome kamar shi Ni to me ya hada ni da aljani da zai xo mun har cikin daki mtchwww Ta Allah ba tashi ba,ta tashi tayo alwala ta kabbara sallah . Adnan dakinshi ya tafi yana cewa daga dawowa 9ja sai in fara gamo da aljana Yaushe gidan nan aka fara ganin aljanu but gaskiya Aljanar nan is soooo beautiful Nurul Aini ko cikin aljanu samu irinta sai an tona...................... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~~~ PART II~~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^5~~~6^^^ *********************************************************************************** . Alwala yayi yai sallah ,ya sauka kasa.Basma data idar ta sallah take cewa ko babansu Afra ya dawo ko in leka kasa in gani kai ba zani ba ,Nan ta zauna daki ta dauki Al'qur'an tana karantawa. . Adnan sosai yaci abinchi da suka girka mai,kwata-kwata bai ma khadeeja maganar gamon da yayi ba(a tunaninshi) Su Afra nata damunshi da surutu duk da gashi da son yara but bai cika son yawan surutu ba dan haka yace suje su kwanta,Afra dakin Basma ta nufa dan dama ita ke taya ta kwana ,Aunty basma kina nan daki daddy ya dawo pha? Ohh Allah ai ban sani ba,Ya dawo tun dazu,ohkay tohm bari in gama surar nan sai inje in gaishe shi,Afra tace toh ta haye gado ta kwanta . Khadeeja nata zuba ido taga saukowar basma shiru,Tayi niyyar kiranta sai kuma tace bari ta bari sai tama Adnan bayanin komai tukuna.Basma ko abinchin dare bata sauko ci ba (tana tsoron haduwarsu da Adnan) .Khadeeja ta zuba ma basma abinchi a plate ta kai mata daki . Basma nasan kina nan kina fargaba shiyasa baki sauko ba,kar ki damu ba wata matsala ina so ya qara hutawa ne sai in mai bayanin komai,ga abinchi na ki tabbatar kinci kafin ki kwanta,Toh Aunty nagode,olryt basma sai da safe,Allah ya tashe mu lfya,Ameen . Khadeeja da Adnan na kwance daki kan gado ,Tace My dear ina son sanar da kai wani abu buh am sorry tun farko ban nemi shawararka sanda zanyi abun tausayi ne ya cika mun zuciya,What it is?? Ta gaya mai komai daga kan inda ta tsinci basma har labarinta,Har da qwallarshi dan dama akwai shi da tausayi,A gaskiya she suffered alots tana buqatar taimako,na tausaya mata kin kyauta sosai da kika taimaketa baki barta a dajin nan ba Allah kadai yasan abunda zai sameta da kin barta acan,Allah ya biya ki,Ameen my dear.Toh ko itace yarinya da na gani a dakin hutawa na kaii it can't ba ,wannan ba za'a samu mai kyanta cikin mutane ba but lemmi ask basma ,Wane daki kika bata? Khadeeja tace Guest room(cause shima guest room ne buh ya maida shi dakin hutawarshi) Ohkay kawai yace a takaice,Ba ita bace din ba,No way ma ace ita ce,Khadeeja tace tana ta tsoron kar ka dawo ka koreta,Haba! How will i do such a thing ai duk wanda yaji labarinta dole ne ya tausaya mata,So gobe zan kirata ka fada mata da bakinka ba zaka koreta ba ko zata samu peace of mind,Allah ya kaimu,Ameen. . Basma tunda tayi sallar Asuba bata koma ba,ta hada breakfast na gidan,ta shirya su Ashraf suka tafi school haka take kullum sannan ta koma ta kwanta . Data gama ta koma barci,ba ita ta tashi ba sai 12pm ,Khadeeja tayi ta lekowa dakin taga in basma ta tashi ta hada ta da Adnan kafin ya fita har ya fice,Da sauri tashi ya fada toilet tayi brush tayi wanka,Riga da skirt ta sa na Swice lace(Red and black) yayi mata bala'in kyau ,ya haskata kunsan yadda Red kema farin mutum kyau,Simple make-up tayi ta yafa dankwalinta a kanta . Aunty deeja ina kwana? Lafiya lau Basma Yau kinsha barci ina ta jiranki ki tashi ku gaisa da Adnan har ya fita,Basma tace Allah sarki,Sai dai in ya dawo,Toh!Allah ya dawo dashi lfy,Ameen Basma . Khadeeja yau bata je office ta basu excuse,A cewara zata zauna ne yau throughout da Adnan su sha soyayya tunda sun kwana biyu basa tare sai gashi an kira shi ana nemanshi wajen aikinsu(MINISTRY OF FOREIGN AFFAIRS) Shine Ambassador Of America representing Nigeria but yaqi komawa permanently saboda baya son nisa da gida sai dai yana yawan xuwa baya 1month a 9ja . Adnan Buba dan'asalin garin Zaria ne,Iyayenshi fulani ne yan'zaria but suna zaune a kaduna Malali ,Mahaifinshi Alhaji Muhammad Buba yana da arziki sosai yana cikin masu fada aji a garin kaduna,Fatima ita kadai ce matar Muhammad Buba ,Adnan ne dansu na farko 31yrx buh idan ka ganshi zaka dauka bazai wuce 25yrx ba,Sajeeda 25yrx tana aure a kano da ya'yanta biyu,Fahad 22yrx yana India karatu sai yar'autarsu Su'ad 20yrx tana KASU level 2. . Basma anan falo ta bingire tana barci,Khadeeja bata lura basma barci take yi ba dana tana ta up and down wajen ganin ta hadawa Adnan abinchin da zai burgeshi. . Adnan na shigowa falon idonshi suka kai kan basma;Aljannar jiya ce wlh dan dai tafi jiya kyau to me yasa take bina ,kasa motsawa yayi ko'ina ya tsaya yana kallonta Wannan wacce Aljannace mai kyau haka take bibiyata,Kamar an taba basma ta tashi tana bude idonta suka sauka kan Adnan da ya tsura mata ido,Ihu ta saki tare da cewa Auzubillahi minash shaidanir rajeem.....Aunty deeja!Aunty deeja kizo ki ceceni,Adnan duk ya kidime ya zama confused mai wannan aljannaar ke nufi(dan har yanxu ya kasa beleiving cewa mutum ce), A guje khadeeja tazo lafiya Basma ta riketa ,jikinta sai rawa yake tana nuna Adnan Ya akayi ne? Shi....shi...shi..ne,Shine wa?? Aljanin da yazo dakina jiya yau ma gashi ya sake biyoni ya sake biyoni nan ,khadeeja ta tuntsire da dariya amma basma da shirme kike Adnan ne fa kilan dai mafarki kikayi ,Wata kunya ta kama basma ta sunkunyar da kanta a kasa a ranta tana cewa Ashe Adnan ne a gaskiya ya hadu dole Aunty deeja ta dinga rawar kafa a kanshi,Adnan tsaye yake mamaki duk ya cika shi Ashe mutum ce shima haka take tunanin aljani ne What a coincidence but gaskiya she x sooo beautiful . Khadeeja tace wannan ita ce basmar da nake gaya ma,Yace Basma sannun ko,Muryata a sanyaye tace Ina wuni? Ji take kamar ta nutse a kasa ta matso ta bar falon,Ya amsa lfya lau ,yana cewa a heart dinshi ba kyau kadai ne da ita ba har muryata ma dadi.Sumi-sumi ta tashi ta haye sama. . Ta fada kan gado tana cizon yatsa tana cewa a gaskiya nayi sakarci ko da yake ba laifi na bane kyaunshi ne duk wanda ya ganshi zai zata aljani na coz he is soo handsome dole aunty deeja ta so shi Allah yasa dai yana da halin kirki ba kyan bane kawai. . Adnan wuri ya samu ya zauna yana tunanin basma da jin muryata mai dadi a kunnuwanshi tana cewa Ina wuni? Ya tsinci kanshi da jin nishadi yana wa Allah godiya da yasa mutum ce,(Wannan shi ake kira love at first sight).................... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: . 👨‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👧 ~~~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE 7-8 ***************************************** I DEDICATED THIS PAGE TO ZAKIYA MUSA BALA❤❤ (THANKS FOR ALWAYS SHOWING YOUR LOVE TO THIS NOVEL) *************************************************************** . Da qyar ta iya saukowa kasa dan yin abinchin dare.A kitchen ta sami khadeeja na hada miya,Tace Aunty miyar me kike hadawa ne? Tayi murmushi tace Egusi soap,Da gajin kamshin zata yi dadi kuwa,Ta bude tukunyar da aka daura tuwo taga shinkafar ta nuna ta dauki muciya tana tuqawa . Uhmm.....kamshi duk ya cika gidan nan me ake dafa ma ne Aunty deeja,khadeeja tace Su'ad yaushe kika zo?? Shigowata kenan Aunty naji kamshi duk ya bade gidan me kike dafawa haka Aunty? Miyar egusi ce,Woow! My favourite kice yau naxo gidan a sa'a,Ai fushi nake dake dan haka baxaki ci miyar nan ba,Kaiii! Aunty deeja me kuma nayi? Yaushe rabonki da gidan nan ko da na dawo tafiya baki xo kin mun sannu da xuwa ba buh yanxu kinxo yiwa ya'yanki ko,Wlh exams muke sai jiya muka gama yanxu ma xuwa nayi in muku kwana biyu,Eyyah Ya examz din?? Alhamdulillah Ina su Afra?? Suna falon sama suna kallo,ohkay bari inje wurinsu i miss them alots,khadeeja tace baki ga bakuwa bane su'ad,sai a lokacin ta lura da basma dake ta famar tuqa tuwo,ohhh!sorry ban lura da ita ba,sannunko tacewa basma,Yawwa sannu basma ta bata amsa,Wacece Aunty deeja? Qanwata ce buh ban santa ba na dai san jidda,Erh! Ba anan take bane,Allah sarki gaskiya duk ta fi ku kyau ya sunanta Basma,nice name,Aunty bari inje wurinsu Afra ta fice . Khadeeja tace Su'ad ce sistern Adnan,Ohh!Allah sarki,Kinga kin samu friend ko ince sister xaki ji dadin zama da Su'ad,She is nice and friendly,Murmushi basma tayi a ranta tana jin dadi dan tun shigowar su'ad taji ta kwanta mata a rai . Duk suna zaune a falo,Har da Adnan,Basma ta takure waje daya duk kunyar Adnan take ji,Afra ta haye kan cinyarta tana koya mata assignment,Su'ad tace Yau Afra ni kikewa Butulci wato kin samu New Aunt kin shareni ko,Afra tace bake bace kullum in nace ki dawo nan gidan sai ki qi to yanzu na samu wata Aunt din da ke kwana anan tana mun komai,Suka kyalkyale da dariya gaba dayansu.Khadeeja na manne da Adnan tana ta mai shagwaba kamar wata qaramar yarinya ko kunyarsu Basma bata ji shikuwa hankalinshi na kan Basma yana ta satar kallonta dan ji yake tana burgeshi(duk wani motsi nata burgeshi yake).Tana gama koya ma Afra assignment ta tashi zata hau sama,Khadeeja tace Ina kuma zaki basma ana zaune ana hira,Zanje inyi sallah ne banyi isha'i ba,Ya akayi baki yi sallah da wuri ba ke da bakya wasa da sallah,Na shafa'a ne,Ohkay tohm ji kiyi sallah ki dawo,Toh ta amsa . Kallo ta kunna dama tayi sallah ta cewa Aunty deeja hakane kawai dan ta bar falon saboda Adnan dan wata kunyarshi da nauyinshi take ji more especially idan ta tuno wawanci da tayi na cewa shi Aljani ne . Adnan nata raba ido yaga saukowar basma,dan tashin da tayi duk sai yaji falon so boring shiru-shiru bata sauko ba shima tashi yayi ya bar falon(dan bai ga amfanin cigaba da zaman falon ba da shi ba zaman falon yake ba ganin basma ma ne yasa shi zama falon dan ya riqa kallonta yana jin muryata mai dadi duk da bata wata magana sai can ba a rasa ba)Tsakanin jiya da Yau duk ya birkice akan tunanin basma da ya zauna ita yake tunani har mamakin kanshi yake yadda farat daya ya kamo da son basma buh taya ma zai fara son basma bayan ga khadeeja kuma yasan ko da sama da kasa zata hade khadeeja ba zata taba bari ya auri basma ba dan tasha gaya mai ko da qanwarta uwa daya uba daya ya auro mata a matsayin kishiya sai ta kasheta,Ta ya zai furta yana son basma??? He have to change his mind dole ne ya cire son basma kafin yayi nisa . Su'ad tai sallam ta shigo dakin basma,Basma ta amsata dauke da murmushi a fuskarta,Nan kika dawo abunki kina kallo,Ehh ina kallon wani indian series ne bana so nayi missing naga ku kuma BBC kuke kallo,Ohh Eyyah,Nan ta zauna suna ta hira da basma har take tambayarta Me yasa baki taba kaduna ba Aunty deeja ko bikinta ban ganki ba,Basma tayi murmushin takaici hawaye taji na gangaro mata,Lafiya basma tambayar da nai miki ita ta saki kuka? Su'ad Aunty deeja ta miki hiding identity dina,But ni ba qanwar aunty deeja bace tsintu ni tayi a hanyarta ta dawowa kd,Su'ad ta zaro ido waje As in how? Ban gane ba,Nan basma ta bata labarinta,Su'ad har da kukanta Allah sarki Basma na tausaya miki at your young age kinyi facing challenges da yawa na rayuwa,But plxx ki manta past dinki and face the future kada ki bari past dinki na damunki although nasan abu ne me wuya ki iya manta past dinki buh try ur best,ki far sabuwar rayuwa yanzu,In shaa Allah Allah zai mu sanya miki da mafi alkhairi,plzz ina so ki daukeni as your sister i promise to be always there for you,Basma ta riqo hannun Su'ad tace You re already my sister Su'ad,Toh Allah barmu tare Su'ad ta fada,Ameen.Sun dade suna hira kafin suyi barci . Washegari basma tare da su'ad suka hada breakfast suka jera kan dining table,Basma tace Su'ad muyi breakfast dinmu yanxu,Mu jira su Aunty deeja su tashi sai muyi all together tunda yau weekend,Su'ad da dai munyi yanxu,Basma You are part of our family now so we are going to have our breakfast all together,Basma tace ok ba dan ranta ya so ba dan bata so yin Breakfast tare da Adnan) . Sama suka koma,Suka yi wanka Basma ta saka ABAYA ta mata kyau sosai kuma ta mata charas-charas kamar dan ita aka yo Abayar ta yafa mayafin abayar ,Su'ad ta kalleta tace sai kika fito a balarabiyarki ,Basma tay dariya,Allah basma ina son larabawa sai naji dama ace ni balarabiyace ko na hada jini dasu,Basma tace ai ko yanxu kuna kama da larabawa kin ma fi wasu larabawan kyau,Kaiii! Basma,Allah am serious Su'ad.Zo muje kasa nasan Su Ya adnan sun tashi,Kiran sunanshi da Su'ad tayi sai da gaban basma ya fadi (ta rasa dalili duk sanda aka kira sunan Adnan sai gabanta ya fadi) .. Yammatan nan kunyi kyau,Mun gode Aunty deeja suka hada baki,Sai naga kuna kama,Su'ad tace An ma kin cuci Basma da kika hada ta dani,Khadeeja ta fashe da dariya tace kin jiki su'ad wani na ya ganku zai dauka gidanku daya,Ai gidanmu daya but basma ta fini kyau,Dariya sukayi(Basma da Aunty deeja) . Mummy! Aunty basma! Aunty Su'ad Ina kwana Ashraf da Afra suka fada a tare,Lafiya lau suma suka amsa su a tare, mummy ina daddy? Ashraf ya tambaya,Daddy na zuwa yanxu nan,Duk sun zauna akan dining table suna jiran Adnan . Kamshin turaren Adnan ne ya gane falon,Basma taji wani qamshi mai dadi ya daki hancinta wanda hakan ya sata waigowa dan ganin waye wannan qamshin turaren mai dadi(kwata-kwata bata kawo Adnan bane) Four eyes suka ti ya sakar mata murmushi wanda shi kanshi bai san sanad yai mata shi ba,Kanta tai saurin dukarwa kasa a zuciyarta tana cewa gaskiya Aunty deeja ta more miji wannan kyawo da Allah ya bashi gashi dan'gayu ban taba ganin wanda yafi Moha kyau ba sai Adnan,Allah yasa Adnan Ya riqe Aunty deeja Amana kada yayi betraying dinta kamar yadda Moha ya mata,Su'ad ta taba ta tunanin me kike?? Tai murmushi tace ba komai,A plate daya su'ad ta zuba musu ita da Basma.A hankali A hankali a natse basma ke ci kafin takai spoon daya a bakinta sai ta dauki kusan 2min,Idon Adnan na kanta yadda take cin abinchin duk ya tafi da imaninsa bata lura da kallonta da yake ba haka ba wanda ya lura har suka gama......................... [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~~~PART II~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^9~~~10^^^ ************************************************************************************ . Parlor suka baje su dukansu ana ta hira ana cracking jokes Basma ta dan saki jiki ana hirar da ita buh ba sosai take sa baki ba coz taga there is no point ta cigaba da jin kunyar Adnan akan abunda ya faru buh duk da haka tana dan jin kunyarshi,Shikuwa Adnan duk wani motsi nata akan idonshi👀 but wisely yake kallonta yadda ba wanda zai gane yana kallonta.A Zuciyarshi yana jin sonta na shigarshi,yana son ya daina kallonta dan sonta ya rage shigarshi dan duk kallon da ya mata sai yaji sonta ya kara shigarshi ko da kuwa kallon 100 ya mata to sonta sau dari nan zai karu ya zuciyarshi har mamakin kanshi yake wannan wane irin SO ne(TIRKASHI) . Haka Basma ta cigaba da rayuwarta a gidan cikin jin dadi,Sun saba sosai ita da Su'ad a yan'kwanakin.Su kan fita yawo tare da yake Su'ad nada mota an siyan mata saboda xuwa school,Yau ma sun fita Kasuwa suka je,Su'ad ta siyo musu atamfofi iri daya suka biya suka kai dinki,dinkin iri daya suka ce ai musu,Sun biya Super market suka siyo abubuwan kwalama tun ba basma ba sarkin son zaki sannan suka dawo gida. . Suna shiga falo da gudu Ashraf da Afra suka rungume basma,Suna cewa Ina tsabarmu,Su'ad tace ni baza ku mun oyoyo ba sannan suka je wurinta,No nayi fushi bana son oyoyon,ko ajikinsu suka koma wajen basma suna ina tsabarsu,Kowannensu ta bashi leda daya suka fara tsalle suna murna suka yi garden a guje(inda suke wasan su),Adnan na zaune falon yana kallonsu,Basma bata ma lura dashi ba tayi wajen fridge dan ajiye ice-cream da chocolates din da ta siyo,Su'ad ta qarasa falon tana cewa Yaya kaga butulcin da Su Afra ke mun,Yayi murmushi(dimples dinsa suka lotsa) yace Ai basma ta fiki kirki shiyasa,Auu Yay haka ma zaka ce,Yace Yess!!,Shikenan ba komai,Muryarshi da basma taji tasan yana falo ta haka ta juya dan ta gaisheshi,Tace ina wuni(da muryarta da Adnan ke jinta Soo sweet kamar Zuma dan dadi😉) Lfya lau Basma ya amsata ,Ta juya zata hau sama,Adnan yace ki dawo mana muyi hira(dan ji yayi ita kawai yake so yai ta kallo) Ta dawo ta samu wuri ta zauna ta wani rakube,Ya kira sunanta Basma(yadda ya kira sunan nata ba karamin dadi ya mata ba sai taji kamar duk duniya ba wanda ya iya kiran sunan nata kamar shi) Muryata a sanyaye tace Na'am,Ya dago kai yana kallonta ita kuma kanta a sunkuye kasa Yace ki saki jikinki plzz Am just like your elder brother yadda Su'ad take sisterna haka kema kike sisterna but i don't why kike dari-dari dani ya qarasa maganar da alamar damuwa(Abun na damunshi Yana son basma ta riqa feeling free with him atleast suna dan hira zai samu some releive) Shiru basma tayi ta kasa cewa komai ,Su'ad tace nima ina mamakin idan ta ganka sai ta kasa sakewa Yaya ina ganin fa tsoronka take ta qarasa maganar tana dariya,Ya dan zaro ido kadan waje" Tsorona ,Tsorona kike ji basma? Basma ita abun ma dariya ya bata fashe da dariya ,Na baki dariya koh? Ta gyada kanta sama,Now tell me tsorona kike ji ina miki kama da mugu ne,A'ahh ta bashi sama ,ko kuwa har yanzu kin dauka ni aljani ne? Wata dariyar ta sake fashewa da,Ita sai yanzu ma abun ke bata dariya(ta tuna yadda ta riqa ihu ita a dole taga aljani😂),Murya a marairaice kamar wani mai lallashin qaramin yaro Yace Toh! Idan har ba tsoro kike ji ba,Please ki daina dari -dari dani Feel free with me Am your bro bana jin dadin yadda kike behaving in kin ganni . Su'ad tace Basma ki daina jin tsoron Ya Adnan he is not a monster buh a simple and nice guy(Adnan yaji dadin yadda Su'ad ta yabe shi gaban basma)"Basma for the first time ta saki jiki da Adnan suna ta hira . A ranar kwana tayi tunanin Adnan da kyakkyawa fuskarshi yadda yake mumrmushi ta rasa dalilin da zai sa ta zauna tana tunanin Adnan har mafarkinshi tayi,Ta farka tayi nafila Ta roqi Allah ya cire mata tunanin Adnan a ranta dan tun ranar da ta gano ba aljani bane ta tsinci kanta da yawan tunaninshi da kuma son ganin shi(Duk da tana jin kunyarshi inta ganshin buh anytime she sees him sai taji wani sanyi da dadi a zuciyarta) Ta rasa dalili ta dai san ba son shi take ba don ba wanda zata so kamar MOHA (hhhh A tunaninta kenan buh already ta riga ta fada tarkon son Adnan itama dai love at first sight ) . Khadeeja ta yiwa Adnan magana kan cewa a nemarwa Basma school ta cigaba da karatunta akan zaman banzan da take a gida sosai yaji dadin zancen khadeeja shima yana da niyyar yiwa khadeeja maganar,Yace ta kira Basma dan suji ta bakinta............. [11/12, 2:38 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [10:21pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👩‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^11~~~12 ************************************************************************************** DEDICATED THIS PAGE TO ALL 《A GOOD AND PIOUS MUSLIMAH GROUP(MEMBERS》 KULLUM KUNA RAINA❤❤❤,INA KAUNARKU WALLAHI😘😘😘😘😘 ************************************************************************************* . Basma na zaune ita da Su'ad tana tayata shirin kayanta dan yau zata tafi,Sanye take da riga da skirt English wears sun mata kyau sosai sun fiddo mata coca-cola shape dinta LOl😉,ta daura dan'kwali akanta gashinta ya kwanta a gaban goshinta lub-lub, . Afra tace Aunty basma mummy na kira, Tace ohkay ta riqe hannun Afra suka fita tare ba tare da ta saka hijabi ko wani mayafi ba dan a tunaninta Adnan baya nan . Adnan na zaune kan daya daga cikin Sofa chairs dake falon ya daura kafa daya akan daya, Data ga Adnan a falon sai da gabanta ya fadi taji wata irin kunya ta kamata,taji kamar ta koma ta dauko hijabi kanta a sunkuye tace Aunty deeja gani,Yawwa Adnan ne ke son magana dake(Rasss gabanta ya fadi jin an ambaci sunan Adnan) . Yana kallonta gabanshi ya fadi yaji wani irin Yarrr yai saurin kawar da kanshi gefe(maganar zuci:lallai Anyi halitta anan dama shi yana son mace mai hips😉 gashi khadeeja bata da shi ina ma ace in auri basma da sai a lokacin zan san nayi aure) . Yace Basma maganar school ce kina so ki cigiba? Kai ta daga sama,Toh shikenan In shaa Allahu zanyi qoqari a samar miki admission coz in your case sai da hanya anyway wane course kike so ko kina so ki cigaba da Medicibe din ne,Ta bashi amsa Ehh!,Kice nan gaba muna da Doctor mun huta zuwa hospital suka yi dariya ita da khadeeja . Daki ta koma tana ta tsalle da murna,Su'ad ta tayata murna,Su'ad tace Ummm....Bari in tashi in tafi,Basma ta marairaice tace kaii!! Su'ad tun yanzu,Wallahi NENE ke ta mun waya inyi sauri in nasan gobe school kiji pha kamar wata yar'secondary school ko primary,Ai kece Auta shiyasa take ganin ki kamar yar'karamar yarinya ni kam zanso inga Nene yadda nake jin labarin nan nata a wurinki,Su'ad tai murmushi:Da ace Aunry deeja zata bari da sai muje ki gaisheta sai ki dawo ko zaki tambayeta,Basma tace a'ah next time ma je tare ko in Aunty deeja zata zo sai in biyo ta,Su'ad ta bude baki Wa! Lallai in dai Aunty deeja zaki jira har ta tashi xuwa kina da aiki bakya ganin ko su Ashraf ba'a kaisu,Basma tace to me yasa? Su'ad tace Aunty cewa take she is always busy su Ashraf kuma na zuwa school bata so suyi missing school idan sunyi hutu kuma mostly suna America ko wani country din ko ta kwashe su su tafi Gombe,Basma tace lallai au zumunci yafi gaban komai kuma kakarsu ce pha suna gari daya,Ummm....bake kadai kika fadi haka ba Nene tayi fada har ta gaji shi kuma Ya Adnan ba zai iya magana ba duk abunda Aunty deeja tace tana so shi ake yi gashi nan kamar "Mijin Hajiya" Basma Tayi dariya tace Su'ad da wani zance kike baki san in so yai so ba yana sa mutum ya riqa tattalin da bin matarshi sau da qafa har wasu su riqa tunanin asiri tai mishi,Su'ad tace hakane kuma dan Ya Adnan na masifar son Aunty deeja,Wani daci basma taji a zuciyarta Ta cewa kanta me ke shirin faruwa dake basma Dan me zaki ji haushi dan Ance Adnan na son Aunty deeja ba matarshi bace??? Allah ka kare ne daga wannan baqon al'amari dake shirin faruwa a kaina.Tunanin me kike basma? Ba dai tunanin dan'iskan mohan can kike ba,Basma ta fashe da dariya tace ai ni tuni nayi deleting dinshi a rayuwata(Fada kawai take but tasan abu mai wuya ne ta cire moha a zuciyarta) Yawwa ko ke fa dan wallahi nayi hating dinshi saboda abunda yai miki Cause jinki nake tamkar jinina basma,Nima haka nake jinki su'ad.kiran nene ya shigo wayar su'ad tace umm na tafi kinga nene na sake kirana xan cewa nene ta kira Aunty deeja tace a kawo mata su Afra sai kuzo tare,Da kuwa kin kyauta,tai mata rakiya har bakin motar ta,kamar zata yi kuka dan sun riga sun saba da Su'ad . Da safe Aunty deeja ta tafi office ko da ta tafi Adnan na barci shi sai 10 zashi office.Around 9:30 basma na zaune kan dining table tana breakfast,Adnan ya fitk sanye yake da Shadda blue ya kashe hular tsakiyar kai yayi masifar kyau ga kamshin turarenshi ya game falon,Basma ji tayi kawai tana son sa shi a ido duk yadda taso dakewa kar ta kalleshi ta kasa,Tana daga kai suka yi ido hudu👀 cikinsu ba wanda ya iya kawar da idonshi dan duk sun yiwa juna masifar kyau sunyi like 3min suna kallon juna sannan basma tayi saurin cewa ina kwana? Lafiya lau ya amsa plxx kawo mun breakfast(Dama most of the time masu aiki ke kawo mai breakfast coz khadeeja na rigashi tafiya office) . Basma tana magana a zuciyarta yanxu Aunty deeja bata bashi breakfast ta fita ba lallai Aunty deeja ta dauki aikinta da muhimmanci fiye da aurenta(kuskuren da matan yanxu keyi yanxu kenan shiyasa suke ja ana musu kishiya dan shi namiji kamar kwai ne dole sai mace na tattalinshi) . Already an hada breakfast din daukowa kawai tayi ta ajiye a gabanshi yace ta zuba mai,Ta zuba tana maganar a zuci:Abunda ya kamata matarka ta maka but saboda aiki ta tafi tabar wata nama,Yace thanks,Ta tashi zata tafi,Yace dawo ki zauna,ta dawo ta zauna tana cewa me yake nufi da haka,Yana ci yana satar kallonta ji yake kamar ace matarshi ce mallakinshi da ya more😉 ita kuwa hankalinta ya tafi kan kallo . Ya gama ci ya tashi zai tafi yace mata na wuce office tai kamar bata ji shi ba dan tama rasa mai zata ce masa,Ya sake maimaitawa na wuce office(hakanan yaji yana son sanar da ita kamar wata matarshi) Toh! Kawai ta iya cewa da kyar,bai ji dadin amsar da ta bashi ba . Tunaninshi ta shiga yi ,kallon da suka yiwa juna na mata yawo cikin kwakwalwa tana jin nishadi,Why tun farkon haduwarmu da Adnan bani da wani tunani da ya wuce nashi na kan so na riqa ganinshi ko ina jin muryarshi gashi komai nashi burgeni yake ba dai hakan na nufin son shi nake ba duk wadannan abubuwa dana lissafo alamomi ne na ka kamo da son mutum saboda haka na riqa ji akan Moha sai dai kuma yadda nake ji akan Adnan har yafi yadda na riqa ji akan Moha,idan kuwa na kamo da son Adnan to na shiga Uku,Ya ma za'ayi in fara son shi IMPOSSIBLE! YA ALLAH! Kar ka daura mun son abunda nasan bazan samu ba,Ko gama warke halib da moha ya sani ciki ban gama ba sai kuma in fara son wani(wanda nasan bazan taba samunshi ba ) Taya ma zan fara son mijin wata ,Watar ma Ainty deeja,Allah ka cire mun son Adnan a zuciyata kafin yai nisa................... [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR❤ PAGE^^^13~~~14^^^ ********************************************************************************************************* . Yau ta kama saturday Aunty deeja tace su shirya zasu je wajen su nene(Saboda Nene ta kirata tace tana so akai mats su Ashraf),Murna wajen Basma ba'a magana zasu hadu da Su'ad kuma zata ga Nene.Taci kwalliyarta cikin atamfarta tayi kyau sosai,Ashraf da Afra ma ta shiryasu tsaf,Khadeeja ta tuka su zuwan gidan:Mansion house ne gidansu Adnan,Ya hadu iya haduwa but duk haduwarshi bai kai gidan Adnan ba dan kab unguwarsu(unguwar kaji) ba gidan da yakai na Adnan kyau da keruwa. . Nene na kishingide a falo ga kayan marmari(Fruits) a gabanta tana sha,Ashraf da Afra suka ruga suka dane cinyarta,Basma na ganin Nene gabanta ya fadi saboda masifar kama da ta mata da momynta,kan ace haka ta fara hawaye,Nene da Aunty deeja suka hada suka ce Lafiya? Me ya faru daga shigowarki sai kuka,Basma cikin kuka tace Nene ce naga tana kama da momyna,Nene tace Allah sarki ta rungumo basma a jikinta kiyi shiru,ki daina kuka,daga yau na zama momynki,ki daukeni tamkar wacce ta haifeki kinji,Basma ta gyada kanta sama(Nene taji tana son basma kuma tana tausaya mata dan taji labarinta wajen Su'ad),Itama basma taji tana son nene saboda kama da take da momynta sai dai nene tafi momynta fadin fuska,momy kuma ta fita fari . Ina su'ad ?Basma ta tambaya ,Tana dakint Afra kai ta dakin su'ad inji nene.Suka rungume Juna ,suna murna kamar wadnda suka yi shekaru ba suga juna ba bayan kullum cikin waya suke,Ya naga kamar kinyi kuka,Wallahi nene ce naga tana kama da momyna,Ohh!Allah sarki dama hakane sai kaga mutane biyu basu taba sanin juna ba amma suna kama shikenan sai tayi replacing momyn taki,Basma tai murmushi tace har cikin raina naji ina son nene kamar wacce ta haifeni dama Aunty deeja zata bari na dawo nan,Su'ad tace waii aikuwa Aunty deeja ba zata bari ba,yadda Aunty deeja ke masifar sonki kullum cikin yabonki take gasu Afra sun saba dake sosai,Nima bana son nisa dasu but gani nene yasa naji zan iya rabuwa dasu dan in zauna da ita,su'ad tace lallai son nan na gaskiya ne,Suka yi dariya.Sai dare driver ya maida su gida dan khadeeja suna gama gaisawa ta koma gida. . A parlor suka sami khadeeja da Adnan,khadeeja kwance kan cinyar Adnan yana mata tsifa,Basma wani abu taji yazo ya tokare ta a maqoshi(kishi) tana kallonsu sau daya bata sake kallonsu ba ko gaishe su bata yi ta haye sama da sauri tare da jin wasu zazzafan hawaye,khaddeja tace Basma da kunya take, ganinmu haka yasa ta kasa tsayawa falon nan,Adnan murmushi kawai yayi yana ji ina ma ace basma ce kwance kan cinyarshi . Kan gado ta fada ta cigaba da kuka sai da tayi mai isarta sannan ta dawo hankalinta take cewa kanta: wai me ke damunku Basma?? Me kike yi haka? Ta ya zaki fara son mutumin da bai san kina yi ba har kike kishin shi ko yasan kina yi ba zai aureki ba yana da matarshi wacce yake so yake kauna kaii ko da ma ace yana sona bazan aureshi ba dan bazan iya cin amanar Aunty deeja ba . Adnan ta hanya ya samu ma basma Admission a KASU 200 Level suka bata,Medicine.Basma tayi farin ciki sosai dan burinta na son zama Medical Doctor na nan,Level dinsu daya da su'ad but su'ad Edu.biology take karanta(Studying).Basma ta fara zuwa school driver ke kaita yana daukota. . Duk bayan kwana biyu tana xuwa wajen Nene kuma tana kiranta ta gaisheta,Nene na sonta sosai duk taje sai ta bata kyautar wani abu. . Ashraf da Afra suna ta fada a falon sama ta akan remote Ashraf na cewa "Henry Danger" zai kalla a Nickelodeon,Afra na cewa"Sophia da first" zata kalla a Disney junior,basma ta jiyo su tazo tana raba su,Adnan shi kuma ya hawo sama kenan yaji hayaniyarsu yaje falon dan rabasu sai yaga basma na raba su ya tsaya kawai yana kallonta,Basma ta karbi remote din hannunsu tace kunsan me zai faru ,Suka ce a'ahh ,Tace ina addu'ar dana koya muku jiya suka ce ehh,To duk wanda ya karanta ta dai-dai shi zai kalli channel din da yake so,Ashraf ya fara karantawa ya karanta dai dai,Afra itama ta karanta daia dai ,Basma tace Mashaa Allahu Barakallahu(Adnan yaji ta burgeshi lallai wannan ita ce kalar matar da mutum ya kamata ya aura ga addini ,kyau ,natsuwa kai komai ma ta hada,Ya Allah! idan basma rabona ce Allah ka bani ita).Afra tace Aunty Basma to kuwa ya karanta dai-dai yanzu wa zai kalla,waye ba zai kalla ba,ta dan buga kanta kadan kamar tana tuno wani abu sannan tace Yawwa kunsan me zai faru next tunda kuwa ya iya zan rufe idona zaku gudu buh a cikin falon nan duk wanda na kama yayi loosing dole ya haqura ya bar ma daya ya kalla,Ta cire dan'kwalin da ke kan Afra ta daure idonta,tana binsu suna gudu sai taxo kamo su su ruga,tana ta lalibensu da hannunta kawai taji tana tattaba abu kamar mutum, mutumin ma babba tai saurin kwance dan'kwalin dan taji tsoro,suka hada👀 da Adnan tai saurin juyawa ta bashi baya kamar ta nutse a kasa dan kunya,Yai ta maza yace Kunan nan kuna wasa abunku,bata bashi amsa ba sai su Afra ne Sukace ehh! Daddy,Da yaga ta kasa motsawa daag inda take hakan ya tabbatar masa da kunya taji ya fice dan baya son takura mata buh inta shine ya fi so ya tsaya yai ta kallonta,Tana jin fitar ta turo kofar falin ta rufe su Afra na cewa Aunty basma mu cigaba da wasar,Ta sake rufe idonta suka cigaba(A ranta tana cewa Innalillahi yau na taba Adnan Me zai daukeni ko da da yake ai yasan idona a rufe da a bude ne bazan taba shi ba,me ya kawo shi falon nan ko ihun su afra yaji coz suna ta dariya suna ihu da tana binsu zata kama su(dan a tunaninta bai dade da shigowa falon ba) .......................... #⃣NOTE:PLEASE TO YOU READERS;;DUK WANDA YACI KARO DA WANI ABU A NOVEL DIN NAN NAWA DA YAYI KAMA DA WANI NOVEL DA KIKA KARANTA PLEASE KI DAUKESHI A MATSAYIN "COINCIDENCE" SABODA WANNAN LABARI IDEA TA CE KAGAGGEN NE,NI NA ZAUNA NAYI TUNANI SOSAI HADE DA YIN NAZARI NA RUBUTASHI BAN DAUKI IDEA KOWA NA HADA DA TAWA BA,DAN ALLAH A FAHIMTA.NAGODE🙏🏻🙏🏻🙏🏻 ❤❤ZEE YABOUR❤❤ [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👩‍👩‍👦‍👦 ~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR❤ PAGE^^^15~~~16^^^ ********************************************************************************************************* . Basma kullum addu'a take Allah ya cire mata son Adnan amma kamar roqo take Allah ya qara mata son shi dan son shi dake karuwa a zuciyarta,Duk ranar da bata sa shi a ido ba ranar da dan qaramin zazzabi take kwana,Haka shima Adnan saboda ita ne har yanxu ya kasawa komawa America ana ta kiranshi but sai excuses yake basu . Dukkansu sun rasa yadda zasu yi da son juna ,Basma tana ganin tana son maso wani (mutumin da bai san tana yi ba kuma ko ya sani ba wata mafita),Adnan shima haka yake gani yana son maso wani(wacce bata ma san yanayi ba) ko ta sani zai yi wuya ta amince dashi dan shi yanzu burinshi daya ta ya zai furta mata tasan yana masifar sonta❤ . Basma taci kwalliyarta,ta yafa gyalenta(wanda ya shiga da kayanta) ta sakala jakaeta,Ta sami khadeeja a falo tace Aunty deeja na wuce school,Tohh! Allah ya bada sa'a ,Ameen,Amma wannan kwalliya haka ko dai an saman mu suriki ne a makarantar ,Suriki Aunty deeja,khadeeja tace basma wai ke da an miki maganar aure sai ki nuna baki so,Basma tayi murmushi tace wallahi bana tunanin zan sake yin aure har in mutu ni yanzu babu wani namijin da zan sake yarda dashi,Haba! Basma ki daina fadar haka ai ba duka aka taro aka zama daya ba,Hmm! Aunty ni dai na tafi,a dawo lafiya . Adnan dake zaune kan dining table yana cin abinchin rana yana jin su(basma bata ma lura dashi har ta fita),Hankalinshi ya tashi jin kalaman Basma,lallai akwai aiki babba wannan na nuna cewa ko ya fada mata yana sonta baxata saurare shi kila ma ta dauke shi mayaudariya,Khadeeja ce ta katse mai tunani tace Basma na bani mamaki daga mutum daya ya yaudareka sai kace ba zaka sake aure ba,Adnan hmm!! Kawai yace,Abincin ma yaji ya fita ranshi,ya tashi zai tafi daki,Khadeeja tace ina zaka baka cinye abinchin ba,Na koshi dakin zanje in kwanta barci nake ji,muje muyi barcin tare ta taso ta riqe hannunshi shima ya kama nata . Kwance yake kan gado,khadeeja ta daura kanta kan qirjinshi tana ta mai wasu salailayi shikuwa abun duniya duk ya ishe shi Basma tace Ba zata sake aure ba shi ya zaiyi da rayuwarshi ga Azababban sonta da yake ,Son da yake ji zai iya sadaukar da ransa a kanta . Basma ta fara shiga damuwa akan Adnan gashi ba wanda zata iya tunkari da zancen tana son Adnan ballantana ya bata shawara . Basma bayan ta dawo daga school,khadeeja na office,Ashraf da Afra yau ba islamiyya suna garden suna wasan ruwa da tiyo suna jiqa juna,Taji zaman cikin gidan ya isheta,ta tafi garden dan ta sha iska ,Tana xuwa Su Afra suka fara jiqata suna cewa Aunty basma zo muyi wasan ,Nan ta shiga cikinsu suna ta wasan ruwa,wannan ya karbi tiyo ya jika wannan,wani shima ya karba haka suke tayi . Turn din basma ne ta qarbi tiyon tana ta jiqasu ta rufe idonta ,Adnan yazo garden kenan dan shima ya dan sha iska, Basma ta hau jikashi da ruwa ya wani lumshe ido yana jin saukar ruwan a jikinshi,Can taji shiru ta daina jin ihun su Ashraf(Wanda tuni Afra tabi Ashraf da gudu ya kwace mata chocolate ta bishi tana ya bata abunta) . Ta bude idonta Adnan ta gani tsaye a gabanta duk ya jike da ruwa ya rufe ido daga ganin yana cikin nishadi,Ganin idonshi a rufe ta yadda tiyon ta ruga da gudu cikin gida(Me yasa abubuwa ke faruwa haka tsakanina da Adnan).Jin daina zubawar ruwa a jikinsa da yayi ya sa shi bude ido ,Yaga Wayam ba basma hakan ya tabbatar masa da ganinshi tayi shiyasa ta tafi,Yace Basma kenan baki san yadda nake kaunarki ba shiyasa,Nan ya zauna garden yana hutawa . Khadeeja da Adnan na zaune na kallon wani hausa film "kishiya da kishiya",khadeeja tace wallahi bana son kishiya na tsaneta ko kasheta zan iya yi,Sai da gaban Adnan ya fadi yace Haba! My dear ki sassauta kishin nan naki,Lallai baka san yadda na tsani kiahiya bane ,ai wallahi gwara mutuwata da kishiya ina fatan dai ba zaka mun kishiya ba,kanshi kawau ya daga sama,Yawwa dan kai nawa ne ni kadai . Adnan na maganaar zuci:OMG! Ya zanyi nasan duk ranar da na furta ina son basma ,khadeeja zata iya illata ta ko tace zata koreta ,in ta koreta ina zata gwara in haqura da fadar cewa ina son basma akan ta illata mun ita ko ta koreta,Ni nasan SON Basma shi ne Ajali na dan idan ban sameta ba mutuwa zanyi................................. [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👩‍👩‍👧👩‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR❤ PAGE^^^17~~~18^^^ ****************************************************************************************************************************** . BASMA fitar da take zuwa makaranta samari har da manyan mutane nata kai kawo a kanta amma duk tayi biris dasu dan ba aure zata yi ba ga son Adnan da ya addabi zuciyarta. . Adnan duk ya sukurkurce akan son Basma gashi nan dai ,da ka ganshi kasan akwai matsalar dake damunshi,Khadeeja tayi ta tambayarshi me ke damunshi? Sai dai yace mata ba komai,Hakanan ta kyaleshi ba dan ta yarda ba.Ya yanke shawarar dole ya sanar da BAPPA(Mahaifinshi)halin da yake ciki coz duk duniya bashi da abokin shawara kamar mahaifinshi duk wata matsalar shi shi yake gaya ma baya boye mai komai haka suke kamar Abokai amma duk da haka yana matuqar girmama mahaifin nashi bayan haka akwai wani dalili da yasa zai sanar da mahaifinshi nashi(KO ME YE DALILIN NASHI🤔🤔) . Basma ta fito wanka kenan taji wayarta na ringing kafin ta dauka kiran ya tsinke Su'ad ce ke kiranta,Tayi dialing Numbern Su'ad din Hello Su'ad Basma Ya kike? Lafiya lau Yasu Nene? Ga Nene nan bata jin dadi Me ke damunta? Mura ce Gani nan zuwa in dubata Mura ce fa kawai basma da kinyi zamanki Allah in ban zo na dubata ba hankalina ba zai kwanta ba Shikenan sai kinzo . Ta kashe wayar,Su'ad nata mamakin wannan so da basma kewa Nene,Basma ta gama shirya tsaf,Ta sami khadeeja Tace mata tana so taje ta gaida Nene,Khadeeja tace ki jira Ku tafi tare da Adnan dan naji yace gidan zashi yana so yaga Bappa,Basma tace toh,Ranta bai so ba ji tayi kamar ta fasa. . Adnan ya shirya cikin Manyan kaya yayi kyau sosai da ka ganshi gaka hadadden Guy mai ji da naira buh idan ka kalleshi sosai zaka gane yana cikin damuwa(kai ka rantse bashi da aure ),khadeeja ta gaya mai tare da Basma zasu tana so taje ta gaida nene( haka ya mai dadi) . Da tazo shiga mota kamar ta shiga baya sai kuma ta ga kar yace ta raina mai wayo,Ta bude gaban mota ta shiga Gabanta nata dukan UKU-UKU,Motar tsaf tsaf sai kamshi take ,Yaja motar Suna tafiya ba mai cewa komai sai wakar hausa da ya kunna wacce ake cewa"NI NAGA YARINYA NA SATA A ZUCIYA ,YA ZANYI NE INJE GARETA NA FURTA".Intentionally ya kunna wakar saboda Basma a tunaninshi idan taji wakar zata dan gano wani abu game da son da yake mata,Basma bata kawo komai a ranta ba sai cewa ma da tayi wannan wakar na magana ne kawai akan the feelings i have for Adnan . A tare suka shiga cikin gidan,Sun wani jera kamar mata da miji,Fahad dake zaune a falo(Jiya ya dawo)Yace Wow! Kun hadu fa,Perfect match Yaya yaushe kayi amarya baka sanar dani ba,Basma da Adnan a tare suka kalli juna suka kawar da kai,Adnan yace No! Sistern khadeeja ce,Fahad Yace Ohh!!ai na dauka sabuwar Amarya kayi amma gaskiya kun dace da juna👌🏻,Su'ad dake zaune kusa dashi tace Baru Aunty deeja taji ka kayi mata bayani(but itama a ranta sun mata sai taji dama ace mata da miji ne ,wai!! Da anyi Best Couple ever) . Nene bata falon tana daki ,Basma ta sameta a daki.Nene ya jiki? ,Nene tace da sauqi Basma mura ce kuma na sha magani,Allah ya kara sauqi,Ameen Basma,ki daina shan ruwan sanyi sosai nene,Ai basma Zafin nan sai da ruwan sanyi,hakane amma ki daure ki daina kinga saboda lafiyarki,Toh Basma zan rage In shaa Allahu(Tana kaunar basma taso ace ta hada jini da basma ko kuma ace basma yar'ta ce,Da Fahad bai mata yaro ba ai da ta hada su aure da basma,Shi kuma Adnan tasan yadda yake son khadeeja ba zai auri basma ma ba . A Daki ya samu mahaifin nashi bayan sun gaisa,Bappa yace me ke damunka Adnan naga duk ka rame??? Adnan yai murmushi yace Bappa wata magana nake so na sanar da kai wacce nasan ba wanda zai bani shawarar da ta dace kamar ka,Bappa yace akan me ye Adnan? Adnan ya fada mai komai game da Basma tun farkon haduwarsu da kuma tsoron da yake ji na sanar da ita saboda khadeeja da abunda Basmar tace Na ba zata sake aure ba har abada.Bappa ya gyara murya Yace Toh!Adnan tunda har kai ka furta cewa kana son Basma, nasan lallai son nata kake da gaske dan tunda nake da kai ban taba ji ka bude baki kace kana son wata ba sai kan basma ,kuma ni na taba maka alkawarin cewa duk ranar da ka kawo mun matar da kake so zan aura ma ita,dan haka ina goyon bayanka dari bisa dari,Game da cewa da tayi ba zata sake aure ba Ta fada ne saboda har yanxu tana jin zafin abunda tsohon mijinta ya mata but da ta samu wanda take so zata janye wannan kudirin dan haka kaje ka nemi soyayyarta,Ita kuma khadeeja barazana ce take maka dan kar ka mata kishiya kuma banyi zaton haka daga gare ta ba dan tasan yadda aka yi aurenta da kai ,Dan haka kaje ka nemi soyayyar Basma idan ta amince da kai,Banga abunda ya isa ya hana Aurenku ba sai Allah,Sannan ina so ka zama Namiji Be a Man kada ka riqa jin tsoron kalaman khadeeja haka mata suke da wannan barazanar dan su tsoratar da mazansu kar suyi musu kishiya,So kar ka taba bari kalaman khadeeja su tada ma hankali ita bata isa ta hana abunda Allah ya halatta ba,kai dai yanzu kaje ka nemi soyayyar Basma,Adnan yace Toh!Bappa nagode zan koma gida,Toh a sauka lafiya(A ranshi yana godewa Allah da ya bashi mahaifi kamar Bappa mai hangen nesa,tabbas ne abunda babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba) .Haka ya fita Sashen Bappa cike da farin ciki tare da jin karfin gwiwa, Yanxu bai ga abunda zai hana shi furtawa Basma cewa yana sonta,Kaii! A Yau din nan ma za furta mata cewa yana sonta, He can't waitt any longer ba tare da fada mata The kind feelings he have for her.................... [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧👪 ~~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE ^^^19~~~20^^^ ********************************************************************************************************* . Basma ta dawo falo suna ta hira ita Su'ad da Fahad har sun saba da Fahad(yaji yana son basma),Haka basma ke jinsu kamar family dinta anyway They are her new family now . Adnan ya shigo falon yana far'a,ba kamar sanda yazo ba,Fahad yace Ya Adnan Albishirin me Bappa yai maka kake murna haka,Adnan yace ba ruwanka tsakaninmu ne,Fahad ya tabe baki yace Uhmm....... . Adnan yace Basma tashi mu tafi ko,Su'ad tace kaii!! Ya Adnan tun yanzu,Yess!! Ina so in kuma gida ne in shirya ina da appointment da wasu mutane by 4:00 and its already 3:30,Toh ka barta sai driver ya kawota anjima,No! Ai ba driver ya kawota ba ni na kawota dan haka ni zan mayar da ita,Su'ad tace Plzz Ya....Ya katseta da daka mata tsawa wai yaushe na fara wasa dake,Taja bakinta tayi shiru tana mamakin me zai sa ya riqa insisting sai Basma tabi shi sun koma gida tare . Basma ta tashi ta nufi dakin Nene dan yi mata sallama Su'ad tabi bayanta,Su'ad tace Nene please ki yiwa Ya Adnan magana ya bar Basma anjima sai driver ya kaita ko Ya Fahad,Nene tace Basma kina son komawa gida yanxu,A'ahh Nene,Muje in ma Adnan din magana,Da kanta ta same shi falo tace Adnan ka bar basma anan anjima Fahad zai kawota,Toh Nene idan khadeeja na Needing dinta a gida fa kuma bata ce mata zata kai dare ba,Nene tace toh ni nace Ta zauna,Adnan yace shikenan ni zan wuce,Allah ya kai lafiya,Ameen . Ranshi ya masifar baci sun bata mai plan,he was having the intention tun a mota ya fada mata yana sonta kafin suje gida dan da sunje gida khadeeja na nan da kyar ya samu chance din kebewa daga shi sai Basma,But ko yanzu ba zai yi given-up ba,A Yau sai ya gaya mata yana sonta bari ta dawo . Yana isa gida khadeeja ta fara tambayarshi ina basma? Tana can sai dare Fahad zai kawota ya bata amsa a takaice,Ya naga kamar ranka a bace my dear,Wani dan'mashi ne ya bata mun rai kinsan su da rough driving (Yai karya),Khadeeja tace Calm down my dear muje in baka ruwan sanyu kasha zaka huce,Ta tsiyaya ruwa a kofi ta bashi a baki ya sha ko kadan Zuciyatshi bata rage qunar da take ba na bai sanar da Basma yana sonta ba . Gab da Magrib hadari ya game gari,kan kace haka Ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya,Ruwa ake sosai da qarfi hade da iska mai karfi irin iskan da zai iya dauke mutum,Ba yadda za'a yi mutum ya iya driving cikin ruwan nan,Nene tace Basma ta bari ruwan ya tsageta sai akai ta gida . Adnan hankalinshi duk ya tashi ganin Basma shiru bata dawo ba sai addu'a yake Allah yasa Ruwan nan ya tsaya dan yasan ruwan ya hana Basma dawowa.Ruwan sai karuwa yake da karfi har 10 na dare bai tsaya ba,Nene tace Basma ta kwana gobe sai ta tafi gida tunda dare yayi kuma har yanxu ruwan bai tsaya ba,Sosai taji dadin hakan . Zaune Adnan yake a falo ya kasa motsawa ko'ina har 10pm tayi Basma bata dawo ba,ba dai can zata kwana ba ,No its can't be bari in gani zuwa 11,Ya Allah🙏🏻kasa kar Basma ta kwana,A Yau nake son fada mata ina sonta Bana so yau ta wuce ba tare da na fada mata ba, haka nake gani kamar idan ban fada mata Yau ba it will take me longer kafin na fasa mata OH! GOD HELP ME THROUGH🙏🏻 . Khadeeja tace wai!my dear ba zaka zo muje mu kwanta ba,No je ki gani nan zuwa,Ta zauna kusa dashi tace my dear na kasa gane kanka all this days kana acting strange as i can see akwai abunda ke damunka but you are hiding it from me,I told you earlier ba wani abu if to say akwai wata matsala zan sanar dake kawai yanayi ne na rayuwa,Are you sure? Believe me my deeja ya shafi fuskarta da hannunshi,Shikenan,Ohhh! No har yanxu Basna bata dawo ba maybe ruwan nan ne ya tsayar da ita,Ohh! Bata dawo ba ya tambayi khadeeja irin he don't know din nan,Khadeeja tace bata dawo ba buh lemmi call her Hello Basma Aunty deeja yanxu nake so in kiraki ince miki Nene tace na bari sai gobe dare yayi kuma har yanxu ruwan bai tsaya ba,Shikenan Basma Allah ya kaimu,Ameen Aunty.She hang-up the phone . Jin khadeeja tace Allah ya kaimu he can't even wait ta mai explaining ya fara tambaya Me tace?,Khadeeja tace wai Nene tace ta bari sai gobe(ta fada with irin i don't care din nan). OH SHIT! Ya fada da qarfi tare da buga kafarshi a kasa bai ma san sanda yayi haka ba,Khadeeja tace ya dai anything wrong? Sai a lokacin ya tuna abunda yayi ,Yai saurin wayance yace Furan nan ce da Nene ta saba yi mun tace Zata bayar a kawo mun idan basma zata dawo gashi ina son shan ta yau shiyasa kika ga ban ci abinchi ba sosai co nasan za'a kawo mun fura(dan kwata kwata ma ya kasa cin abinchi spoon uku yayi ya ajiye,Khadeeja Eyyah! Kayi haquri gobe sai ka sha(Ta yarda da abunda yace saboda ta san yana son Fura sosai),Amma gaskiya na so shan furan nan ,Sorry kaji my dear Muje akwai youghurt a fridge sai ka sha,No bazan sha ba fura nayi niyyarshi tunda ban samu ba sai in haqura . Da qyar ya iya yin barci,Ba haka yaso ba,Yaso ace Yau ya fadawa Basma yana sonta but gobe In shaa Allahu zai sanar da ita . Su basma raba dare sukayi suna hira ita su'ad da Adnan sai around 2 suka kwanta . Tun da asuba 5:00am aka yiwa Adnan waya ana nemanshi wajen aikinsu"America" Its Urgent dole ya bar duk wani abu da yake yazo a yau,Ya so ya basu excuse suka ce ba wani excuse din shi da zasu saurara dole yaje a yau din nan.Yana hanging-up Call din ya dafe kanshi kamar zai kwalla,Khadeeja tace Me ya faru? Wai dole in tafi America Yau ,Tayi dariya to me ye abun tada hankali my dear Yau aka saba kiranka ace ka tafi America a ranar ,Ba zaki gane bane my deeja,Toh me ye my dear? Kawai bana son tafiya yau,Hakanan zaka yi haquru ka tafi tunda sun ce dole ka tafi Yau,YA ILAHI Ya fada.Khadeeja ta hau shirya mai kaya . Hankalinshi ya riga ya gama tashi,Me yasa basu tashi cewa ya tafi America ba sai yanxu da yake shirin fadawa Basma abunda ke ranshi game da ita,Sai yanxu da ko 2hours yayi bai ganta ba yake shiga wani hali,Yanzu ya zaiyi ya fadawa Basma yana sonta kafin ya bar 9ja(NIGERIA)................. [11/12, 2:38 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👦‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧👪 ~~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^21~~~22^^^ ***************************************************************************************************************************** AM SORRY DEAR READERS OR LEMMI SAY MY FANS I KNOW KUNA TA JIRAN POST DINA KWANA BIYU SHIRU,WHATSAPP DINA YA SAMU MATSALA NE TWO DAYX *********************************************************************************************************** . Around 6:00am Yana zaune kan dining table,khadeeja ta hada mai breakfast tana bashi a baki tusawa kawai yake but ba don yana son ci ba.Wadanda zasu tafi tare dasu (Yan wajen aikinsu) nata mai waya yayi sauri jirginsu ya kusa tashi,Khadeeja tai mai rakiya har bakin mota Driver yaja suka tafi,Su Afra nata barci basu ma san Daddynsu ya tafi ba.Yaso ya biya ta gidansu Yace yazo yai musu sallama dan ya samu yayi magana da Basma but idan tace yaje zai yi missing flight dinshi,He was just thinking what to do, Suddenly idea ta fado mai bari ya kira Su'ad yace ta bashi Basma(dan bashi da numbern Basma) . Cikin barci Su'ad taji wayarta na ringing kamar ba zata dauka ba can kuma ta duba taga Adnan ke kira,Tayi Receiving Hello Su'ad Basma na kusa dake Eh! Me ya faru Ya Adnan Bata wayar Barci take ki tasheta . Basma! Basma! Ki tashi ko motsi batayi ba kasancewar barcin da basu yi da wuri ba wani irin nauyeyyen barci Basma ke yi.Su'ad ta cigaba da tashinta Umm...Umm kawai take cewa Su'ad amma taqi bude idonta . Adnan dake ji cikin waya Yana cewa OH GOD! Please wake-up Basma Don't let me go without telling you I LOVE YOU.Bargon da Basma ta lullube dashi Su'ad ta janye tace Basma tashi, cikin barci Basma tace Wai me ye,Ki tashi Ya Adnan ke son magana daje,Umm...kawai tace taja bargo ta sake qudundunewa ta cigaba da barcinta.Yaya Wallahi taqi tace,OMG!! Ya fada,Wani abu ne Yaya ka bari in ta tashi zan kira ka sai kuyi magana,Su'ad yanxu haka kan hanya xuwa airport zan tafi "America" idan banyi magana da Basma ba yanxu sai kuma idan na dawo,Toh Yaya me ye zaka gaya mata ka fada mun idan ta tashi daga barci sai in gaya mata,No Su'ad barshi kawai《Yafi so ya fada mata da kanshi baki da baki (kunsan ance waka a bakin mai shi tafi dadi)》.Bai jira ta sake magana ba yayi hanging -up.Su'ad tace To me Ya Adnan ke son fadawa Basma da ba zai iya gaya mun ba and he seems worried Allah yasa dai lafiya,Ta ajiye wayar kan side drawer(dake gefen gado) Ta cigaba da barcinta . Haka ya tafi cikin kunci da bacin rai kadan ya rage yayi kuka . Da suka tashi daga barci Su'ad ke cewa Basma Ya Adnan ya kira dazu kina barci yace yana son magana dake nayi ta tashinki kika qi tashi,Magana dani kuma?ta fada unbelievable,Yes! Daga ji maganar da yake son yi dake is very important and he seems worried ,Basma taji ta damu jin cewa Adnan na cikin damuwa to me yake son gaya mata?? Tace Su'ad please call him inji me yake so gaya mun,Su'ad tace ai aikin gama ya riga ya gama yanxu haka Ya Adnan na cikin jirgi zai tafi "America". . Basma gabanta taji ya fadi Adnan ya tafi America ta tambayi Su'ad,Yes! Wani abu ne naga hankalinki ya tashi,Ta hadiye miyu tace ba komai,Su'ad tace wai me ke faruwa ne bake ba ,ba Ya Adnan din ba . Basma ta kirkiro dariyar karfin hali tace Ba komai pha kawai Aunty deeja nake tunani yadda zata yi kewarshi dan kullum tana ce mun bata so a nemi Ya Adnan "America"bata so yayi nisa da ita ko kadan ,Su'ad tace to ya zata yi tunda Allah ya hada ta da miji da ba nan yake aiki ba dole tayi hakuri naga this time ba ya dade bai tafi ba Ai Allah ya qara ma da ya tafi ita da take tafiya office tun safe sai dare take barin shi a gida fa Ta san tana son shi bata son yayi nisa da ita take tafiya ta barshi a gida,Basma tace kai!! Su'ad baki da dama,Allah kuwa basma the thing is annoying ace kana da miji amma ka fita ka barshi tun safe sai dare Ya Adnan din shi yaji zai iya,Basma dariyar karfin hali kawai tayi but tafiyar Adnan duk ta dameta Kwana nawa zata yi bata kalli Kyakkyawar Fuskarshi ba bata ji sweet voice dinshi ba ba zata iy jure rashin ganinshi ba Tana son ganinshi all the time(but tasan ba zata aure shi ba )Wai shin me yake so ya gaya mata ??? Ta so ace ya gaya mata kafin ya tafi ,Sai Yaushe zai dawo ya gaya mata abunda yake so ya gaya mata? Tambayoyin da ta riqa jerowa kanta kenan wanda bata da bai bata amsarsu . Ana yi sallar Azahar driver ya maida ta gida,Ba kowa a gidan sai yan'aiki Khadeeja na office ,Su afra na school,Dakinta ta nufa ta dauki Al'Qur'ani tana karantawa (tana cike da damuwa) . Kwana biyu da tafiyar Adnan Basma duk ta gama shiga damuwa ,Abinchi bata iya ci sosai,barci da kyar,School ma bata concentrating bata da aiki sai tunanin Adnan tayi missing dinshi sosaii Wannan wane irin si nake wa Adnan tambayar da take wa kanta kenan kullum addu'a nake Allah ya cire mun son shi but kullum son shi karuwa yake,Khadeeja a tunaninta ko Basma ta tuna iyayenta ne datz why ta shiga damuwa (not knowing she is in love with her one and only ADNAN BUBA),Tana ta mata nasiha da kokarin ganin ta kwantar mata da Hankali . Adnan yama fi Basma shiga damuwa dan shi at all ma baya iya cin abinchi sai dai ya sha ruwa ko lemo duk ya rame,Friends dinshi na can sunyi tambaya har sun gaji sai dai yace musu ba komai,Yau kwananshi uku Yaso a ce ya dawo a ranar coz yayi missing Basma like hell but wani aiki ya taso sai ya bari sai the next day . Kannen khadeeja(Jidda da Zahra) sun zo daga Gombe bikin wata Friend dinsu.Basma bayan ta dawo daga school ta masifar gaji gashi wani jiri take ji bata jin dadin jikinta sosai.Bata ga Aunty deeja a parlor da kitchen ba dan haka ta nufi dakin Aunty deeja,Khadeeja suna ta hira da su Jidda.Basma tace Aunty Ina wuni? Lafiya lau Basma Ya School din? School lafiya,But naga kamar kin gaji sosai kije ki kwanta ki huta,Suka gaisa dasu Jidda(ta gane su dan taba ganin Pics dinsu a phone din Aunty deeja),Suma sun ganenta ta sunanta da khadeeja ta fada but basu taba ganinta ba.Jidda tace Ya deeja wannan ita ce Basmar,Basma har ta rufo daki jin an ambaci Basma ya sata tsayawa bakin kofar,Khadeeja tace Eh! Itace ya akayi ,Jidda tace Tab! Lallai Aunty deeja taya zaki ajiye santaleliyar budurwa kyakkyawa kamarta a gidanki bakya tsoron ya kwace miki miji,Zahra tace nima shi nagani,Khadeeja ta fashe da dariya tace wallahi da ban dariya kuke ku kanku kunsan bazan ajiye budurwa wacce bata ma kai Basma a gidana ba ballatana kamar Basma ba tare da na TAKI wani abu ba kar ku manta Adnan a tafin hannuna yake sai yadda nayi dashi Adnan ba zai taba ganin wata yarinya ta burgeshi ba ko kin manta abuda Bokan nan yace ba tare dake muka je ba wancan zuwan,Jidda tace hakane na manta tsoro naji dan kyaunta yayi yawa,Khadeeja tace Adnan ba zai so ta ba(Ni Zee nace So kuma sai dai kar a kuma😀)Ni kadaice a cikin Zuciyarshi Adnan nawa ne ni kadai,Basma dake bakin kofa tana jin su kasa yarda tayi da abunda take ji Wai Aunty deeja ke bin Bokaye Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Allah yasa mafarki nake Zuciyarta taji tana mata zafi kanta nata jujjuyawa nan ta fadi kasa Sumammiya................................... [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👦‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^23~~~24^^^ ********************************************************************************************************* . Bayan mintuna kadan,Su Ashraf sun dawo school suna ta kiran mummy! Aunty Basma Suka ji shiru ,dakin Khadeeja suka nufa . A bakin kofa suka ga basma sumammiya,Ihu suka tsala Ashraf yace mummy!mummy! Zo ki ga Aunty basma ,a guhe khadeeja,Jidda ,Zahra suka fito Suka ci karo da Basma a bakin kofa,Dukkansu suka zaro ido waje khadeeja tace subhanallahu jikinta sai rawa yake tace Afra dauko mun phone dita a daki,Family Doctor su ta kira,Sannan suka ciccibi Basma suka kaita daki suka kwantar da ita kan gado . In few minutes tine sai ga Doctor yazo,Bayan wasu yan-gwaje gwaje da yayi mata Ya cewa khadeeja Basma tasa damuwa ne sosai a ranta wanda hakan ke son taba lafiyarta dan haka tana bukatar kula sosai kuma ayi kokari a riqa mata duk abunda zai faranta mata rai,Khadeeja tace In shaa Allahu mun gode Doctor,Yace A'ahh ba komai zuwa anjima kadan zata farka,Yai sallama da khadeeja ya tafi . ***ONE HOUR LATER*** . Basma ta farfado tana bude idonta suka sauka kan khadeeja tai saurin runtse su ba tare da khadeeja ta lura ba,Maganganun khadeeja taji sun dawo mata jikin kunnuwanta Sai hawaye😭,She can't believe Aunty deeja na aikata wannan mummunan Sabon Shirka fa kenan take yi Allah ya shiryeta . Ganin hawaye a fuskar basma khadeeja ta tabata tace Basma! Da qyar Basma ta iya cewa Na'am tana jin wani zafi a zuciyarta,Sannu basma ki daina kuka tana share mata hawaye bari in hado miki Tea,Ta tashi ta tafi hadowa a Basma Tea(shayi) . Basma tace Aunty deeja ga ki da kirki,mutunci da tausayi amma sai dai kash! Kin bata imaninki idab miji kike son mallaka ai akwai hanyoyi da yawa da zaki bi ki mallakeshi ba boko /mallam but matanmu naYanzu fail to understand that Allah ya shirya,Adnan ya fado mata a rai tace Ya Adnan baka yi sa'ar mata ba na tausaya maka amma Ina rokon Allah ya shiryata . Ta hado ma Basma k Tea yaji madara sosai da milo da Toast-Bread,Ta zaunar da ita tana bata a baki,Basma na maganar zuci:Ina ma ina da hanyar da zan bi inyi wa Aunty deeja naseeha ta bar abunda take dan ni dai ina sonta bana so ta cigaba da fadawa halaka . Su Afra sunyi shiru sun daina kuka ,Tana falon kasa tana game da phone din khadeeja,Call din Adnan ya shigo,Ganin hoton Adnan akan screen din yasa Afra tasan daddy dinta ne ta dauka Hello! Daddy Afra my dear Ya kike lafiya lau Daddy shine ka tafi baka gaya mana ba ohhh sorry my baby nina ban san da tafiyar ba Ina mummynki? Tana wajen Aunty Basma bata da lafiya Bata da lafiya Afra? Yes Daddy she even fainted Me ya sameta? I don't know Daddy Ohkay! Ohkay! Ya kashe wayar. . Duk ya rude hearing (jin) Basma bata da lafiya,Dole in koma 9ja yau inje inga halin da Basmata ke ciki bazan iya kara kwana daya a garin nan ba,kayanshi ya hau shiryawa sai Airport dama su ta private jet suke tafiya . Su jidda sun tafi dama ba'a nan zasu sauka ba gidan da friends din Amarya zasu sauka can zasu.Khadeeja nata tarairayar basma,Ta zauna gefen gado suna dan taba hira khadeeja nata ba Basma labaran da tasan zasu sata nishadi da farin ciki . Basma tasan babbar matsalarta bata wuce Adnan ba da zata ganshi da ta rage radadin da take ji a zuciyarta . Kamar daga sama suka ga Adnan a dakin,Basma ta ma dauka Gizo yake mata ba shi din ne da gaske ba (dan ta saba duk kwanakin nan sai tai ta ganin kamar shi sai ta murza idonta sosai ta kara bude su sanna taga bashi bashi,Yanxu ma idonta ta murza ta qara fiddo su waje Still Shi ta gani a tsaye ,sai da taji Khadeeja tace Are you the one??(sannan tace ashe shi dinne da gaske taji wani dadi da sanyi sun ziyarci zuciyarta a lokaci daya) Ta nuna Adnan da dan'yatsa(finger)Suprisedly,Yayi murmushi yace Yes!! ,But ya akayi ka dawo ba notice nothing nothing,So nake na baku suprise,Khadeeja tace Uhmm.......But am sooo happy to see you ta taso ta rungumeshi tai kissing dinshi shima ya mayar mata.Basma taji wani haushi😡 da kishi . Adnan ya kai kallonsa kan Basma wacce tuni ta Suqe da kishi(Ni kuwa Zee nace lallai Basma kina da aiki mutum da matarsa dole sai kina kawar da ido) Yace Basma ba lafiya ne? Ta gyada kanta Sama ,Ya juyo ga khadeeja yace meke damunta,khadeeja ta fada mai duk yadda Doctor ya fada mata.Adnan na magana shi kadai:Ba wanda ya dace da Basma sai ni, ba wanda zai bata farin cikin da zan bata, Ina tausayin Basma ina so na chanza mata rayuwarta zuwa rayuwar jin dadi,farin ciki da kwanciyar hankali Allah yasa Basma ta amince dani . Yace Basma me ke damunki? Tai shiru a ranta tace kai ke damuna Adnan kai ne silar halin nan da nake ciki,Basma kinyi shiru ko kina tuna parents dinki da Moha ne? Ta gyada kanta sama,Addu'a ya kamata ki riqa musu kuma kiyi tawakkali da Allah,Allahn da ya karbesu ya fiki sonsu shi kuma Moha kiyi deleting dinshi from your life ki manta dashi kamar ba'a taba yinshi a duniya ba,Ta daga kanta sama,khadeeja tace nasan Basma zai yi wuya ki iya cire Moha ranki amma.......kafin ta karasa maganar a fusace Adnan yace ya zama dole ta manta dashi a duk sanda aka ambaci sunan Moha wani kishi yake ji ya turnikeshi,dole ce kawai ta sa shi ambatar sunan Moha dazu don yana so yaji ko har yanxu Basma na son shi (Ni Zee nace ikon Allah Mutumin da kasan ba aure tsakaninsu yanxu(since saki uku ya mata) kake kishi a kansa,da kasan irin son da Basma kema da baka bata time dinka kana kishi akan Moha ba(Ko me kuka ce Readers) . Khadeeja da Basma suka tsaya kallonshi suna mamakin Reaction dinshi,Ya wani maze yace Yes! Coz in bata manta dashi ba zata cigaba da shiga damuwa wanda hakan zai shafi lafiyarta(Adnan sarkin Shan kwana😀,Akwai wayo,He get brain fa🤔).Khadeeja tace hakane So please Basma ki cire Moha a zuciyarki,Basna tace In shaa Allahu Aunty.Khadeeja ta riqo hannun Adnan muje ka huta koh,Yace toh ba don yaso ba,Yaso ace ya cigaba da kallon beautiful face din Basma...................................... [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~PART II~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^25~~~26^^^ ****************************************************************** THIS PAGE IS FOR YOU MEMUH DANDUTSE💞❤❤ ************************************************************************************* . Yau Basma ta samu tayi barci dan taga farin cikin rayuwarta unlike before da sai tayi da gaske take iya barci . Adnan kuwa juye-juye kawai yake kan gado yana tunanin ko wani hali Basma ke ciki ko ta iya yin barci Wata Zuciyar na cewa kaje ka dubata ka gani can wata zuciyar tace No idan bata yi barci ba fa kace me ya kawo ka dakinta da tsakar daren nan,Haka ya danne zuciyarshi tare da bata haquri(Zuciyar😂) Can barci barawo ya sace shi . Basma jiki yayi sauki dama hadda rashin ganin Adnan ne to gashi ya dawo,Ta tashi tayi wanka taci kwalliyarta cikin riga da skirt (Atamfa Purple)Tayi kyau sosai but daka kalleta zaka ga ta dan rame,Da ta gamawa shiryawa taji Adnan kawai take son gani . Adnan sanye yake da jeans en Polo shirt sun mai kyau,gashin kanshi nata walkiya ya gama feshe jikinshi da turaruka masu bala'in kamshi da tsada(Duk macen da ta ganshi zata so ace mijinta ne coz ADNAN BUBA karshe ne) Yaje gaban madubi ya tsaya Ya kalli kanshi yana magana shi kadai:Basma Am coming to you ,to express my feelings, to tell you the kind of love i have for you,Ya bude Trolley dinshi da ya dawo da ita from America ya fiddo wani Zobe(Ring) sai walkiya yake is made with diamond a saman zoben anyi designing dinshi da wata yar'karamar heart♡ a cikin♡ din an rubuta A&A (Meaning Adnan and Aysha in baku manta ba real name dinta kenan Aysher) a America yasa a ka maishi,Yayi kissing Zoben yasa a pocket dinshi(aljihu) . Phone dinshi ya dauko yayi texting Basma (Jiya khadeeja na barci ya dauki Number Basma a wayarta) NAMIJI🤔🤔 . Kiiiiiii Basma taji wayarta tayi kara alamar shigowar txt message"MEET ME AT THE GARDEN ,I NEED TO TELL YOU SOMETHING" * ADNAN* . Wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta ,Adnan zai gaya mun abunda yake so ya gaya mun ranar da zai tafi America,To me ye zai gaya mun Allah yasa Alkhairi ne,She was so excited.Ta dauki hijabinta tsaya ta kalli kanta a madubi ta dan kara gyarawa ta nufi garden sai da tazo shiga garden din sannan kirjinta ya fara duka Uku-uku(Nasan Su ilham za'a ce toh ina khadeeja kar ku manta khadeeja na zuwa office) . A zaune ta same shi kan daya daga cikin fancy chairs dake garden,Muryata a sanyaye tace Ina kwana? Lafiya lau basma yai mata nuni da kujerar kusa dashi ta zauna,Ya dan yi Shiru gabanshi na faduwa yana jin tsoron ya fada mata tayi rejecting coz idan tayi rejecting dinshi Allah kadai yasan halin da zai shiga,Zuciyarshi nace mau Be strong ,Common! Haba kamar ba namiji ba ka fada mata kada kayi loosing opportunity dinka"OPPORTUNITY COMES BUT ONCE" . Muryarshi kasa kasa ya kira sunanta Basma,Na'am ta amsa da lallausar muryarta,I know Su'ad ta gaya miki na kira ranar da zan tafi America ina son magana dake,Tace Ehh . Ya sake kasa da murya ,muryarshi ta koma kamar mai shirin yin kuka:Basma I want to tell you this But i never get chance to ,Since the first time i set my eyes on you Basma I fall for you Nayi kokarin cire sonki a zuciyata buh na kasa kullum sonki karuwa yake a zuciyata Basma,I Love you Aysha Basma I want to marry you pleaseeeee Don't let me down . Basma kanta taji yana juyawa mafarki take ko da gaske ne Adnan ke furta mata wadannan kalaman . Adnan yazo gabanta ya durkusa ya fiddo Zoben daga aljihunshi ya kamo hannunta zai sa mata ta fisge hannunta Tace da karfi NOOO! YA ADNAN tana girgiza kanta tana fitar da kwalla takaici(Yau wanda take so tafi kauna a duniya ya furta cewa yana sonta but she can't accept him,She can't marry him) . Adnan bakinshi na rawa he can't believe Basma na kokarin rejecting dinshu Yace Ba..bas..ma.. Whaaaa What dooo yo..you meannn,Ta rufe idonta tana kuka tace I Can't Love You Back Ya Adnan ba zanci Amanar Aunty khadeeja ba,Adnan ya sake riko hannun Basma Yace Basma I Love You I can't live without You Please Basma save my life,Girgiza kanta kawai take tana kuka,Ta fisge hannunta No! Ya Adnan ba zanci Amanar Aunty khadeeja ,Ta ruga da gudu cikin gida,Adnan kuka yake yan kiran Bas.....maaa Bas..maaa Please don't do this to me I can't live without you,Yanxu ya zai yi who can help me out ya shawo mai kan basma yayi convincing dinta,SU'AD YES SU'AD Ya fada phone dinshi ya zaro daga aljihu yayi dialing number su'ad,Hello Yaya,Su'ad Please ki taimakeni,Lafiya yaya(hankalinta duk ya tashi jin yana kuka abunda bata taba gani ba ko ji),Please kiyi convincing Basma ta soni wallahi ina son ta zan iya rasa raina a kanta please please Su'ad help me ,Ohkay Yaya Don't worry i will try my best,Record everything she says,ok Yaya.Ya kasa hakura kafin Su'ad tai mata magana shima yayi texting dinta . Basma kuka kawai take Tana son Adnan Tana kaunarshi tana son kasancewa tare dashi but she can't marry him,she can't betray aunty khadeeja and still tana tsoron maza akan abunda Moha ya mata,Karar text taji ya shigo wayarta Ranta ya bata Adnan ne Ta bude text message din"BASMA PLEASE SAVE MY LIFE I TRULY LOVE YOU MORE THAN YOU COULD EVER IMAGINE DON'T BE AFRAID TO LOVE ME BACK,KHADEEJA IS A SIMPLE AND UNDERSTANDING PERSON SHE WILL UNDERSTAND MY SITUATION" . Tana gama karanta txt din ta sake rushewa da kuka,Ya Adnan you trust Aunty deeja soo much you don't know what she is capable of doing i know who she is,Ko ma ba haka ba i just can't cheat Aunty deeja And da kake cewa Am afraid to say I Love you,I have to pretend in nunawa Ya Adnan bana son shi ya daina tunanin ina son shi saboda Aunty deeja ne naki admitting ,I know I love you Adnan more than anything more than my own life sef buh i won't admit it to anyone zan cigaba da barin shi wa kaina har in mutu . Su'ad ke cewa kanta Tunda naji Ya Adnan a wannan halin to ya fada tarkon son Basma da gaske kuma zai iya fadawa wani hali idan ya rasa ta,I have to help out ,Veil(gyale)ta phone dinta da keyn mota ta dauka sai gidansu Adnan.............. [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👨‍👦‍👦 ~~~~~PART II~~~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^27~~~28^^^ *********************************************************************************** ******************** . A daki ta sami Basma sai kuka take,Su'ad ta dago ta ,Basma na ganin Su'ad ta rungumeta tana kuka mai tsuma rai,Su'ad nata lallashinta tana cewa kiyi shiru Basma Ya Adnan ya gaya mun komai,Basma Me ya sa kika yi rejecting Ya Adnan??? Tana kuka tace bazan iya auren shi ba ba zan ci Amanar Aunty khadeeja,Su'ad tace ki gane Basma wannan ai ba cin amana bane,Ta girgiza kanta tace NOO Su'ad bazan iya ba,Basma Ya Adnan na sonki zai iiya shiga wani hali inda bai sameki ba ko da ya kira ni yana kuka Me yasa ba zaki tausaya masa ba,Su'ad idan na tausaya mishi Aunty khadeeja ita wani halin kike tunanin zata shiga idan taji Adnan na sona kuma na amince dashi kuma ko ba haka ba zan iya sake sauraren namiji ba ballatana ince zanyi soyayya dashi,Su'ad tace kar kice haka Basma,Su'ad soyayya guba ce na taunata ta kusa illata ni bana bukatar ta sabuwarta ko tsohuwa(Lol at SAIWATARANA) bana son sake fadawa halin da na shiga a sanadiyyar Moha shiyasa kika ga bana kula samari aure ne bazan sake ba har abada,kar ki manta ba duka aka taro aka zama daya ba,ba dan Ya Adnan na yayana ba amma nasan ba zai miki kwatankwacin abunda Moha ya miki ba Ya Adnan na sonki Basma,Basma tace Ni kuma Bana son shi Su'ad Bana son shi(har ranta sai da taji zafin kalmar da ta fada na bata son shi dan tasan tana son shi) Ba zan taba aurenshi ba Kiyi haquri Su'ad,Su'ad har ta fara kwalla dan ta tausaya ma Yayan nata halin da zai shiga,Su'ad tace bakya son shi Basma,Ehh!! Bana sai kuma ta kasa karasawa Su'ad tace Nasan kina son Shi Basma kawai kina boyewa ne saboda reasons dinki amma ina son ki san wani abu Basma,Ya Adnan bai taba cewa yana son wata mace ba sai ke kuma ban taba ganin yana kuka ba sai yau a dalilinki Basma ta kalli Su'ad da alamar tambaya a fuskarta akan abunda Su'ad tace bai taba son wata mace ba Aunty khadeeja fa Su'ad ta katse mata tunani Nasan zaki yi mamakin abunda na fada but Yau zan gaya miki wani abu baki sani ba: Alhaji Abubakar Ashaka shi ne mahaifin Aunty deeja,Abokai ne sosai da Bappa(Best of friends) ,Ya Adnan bayan ya gama karatu ya samu aiki ga business da yake,Bappa yace ma ya fito da mata yai aure,Ya Adnan yace shi ko girlfriend bashi da shi bai ma taba soyayya da wata ba(Dan Ya Adnan baya kula mata duk kowa dimbin matan dake kawo kansu gareshi su Shoter ma anyi nacin har an gaji Adnan yaqi kulata Lol😜),Bappa yace mai to daga ranar ya fara neman mata aure zasu mishi ga agemates dinshi nan duk sunyi aure wasu hadda Ya'ya.Ya Adnan ya shiga damuwa sosai dan shi bai ga matar da mai ba.Da Bappa yaga Ya Adnan bashi da niyyar fidda mata Ya yanke shawarar hada su da Aunty deeja,Ya Adnan yasha bakin ciki amma hakanan ba musu ya amince dan baya so ya sabawa umarnin Bappa ,Jin dadin biyayyar da Ya Adnan ya mishi yasa Bappa yace mai alkawarin duk ranar da ya kawo mai wacce yake so zai aura mai kuma zai gayawa iyayen khadeeja su gaya mata zai iya yi mata kishiya dan haka nan gaba idan yace zai yi aure kar tasa rigima(a baya in baku manta ba shiyasa Adnan ya gayawa mahaifinshi yana son basma kuma mahaifinshi yace yayi mamakin khadeeja) Ko da rana daya bai taba wulakanta Aunty deeja ba yana zaune da ita amma bai damu da ita ba ganin haka yasa ta fara bin malamai tare da yin amfana da kisisina da salailayi iri-iri har Ya Adnan ya dawo yana kulata yana bata duk wani hakkinta na aure ,Suna zamansu lafiya har kika zo kika same su amma ni nasan Ya Adnan baya son Aunty deeja kawai malaman da take hadawa da sune da kuma kissarta.Basma ki tausayawa Ya Adnan bayan shekaru masu yawa bai samu wacce yake so ba sai ke Basma kukanta ya tsananta ta tausayawa Adnan amma Inaaaa ! Duk da hali irin na Aunty deeja tafi tausaya mata akan Adnan tasan Aunty deeja na bala'in son Adnan saboda son shi ne take bin bokaye idan taji yana sona halin da zata shiga sai yafi halin da Adnan zai shiga kuma zata ga naci Amanarta,Tace Su'ad Am sorryy bazan iya ba Su'ad tace shikenan Basma amma ki sake tunani ni zanje wajen Ya Adnan,Ta latsa wayarta ta kashe Recording din da ta kunna dan tun shigowarta ta kunna,duk maganarsu wayar tayi recording Adnan na zaune na kallon sararin samaniya hawaye na gangarowa ta gefen idanunshi yana rokon Allah yasa Basma ta amince dashi Yana ganin Su'ad yayo kanta yana cewa What did she say?? Did she accept me??? Wasu hawaye Su'ad taji tausayin Adnan ya sake kamata ,Recording din kawai ta kunna ta mika mishi wayar Yana gama saurare Yayi wata kara NOOO! Ya jefar da wayar idanunshi sun kada sunyi red sosai haka face dinshi abun ka da farin mutum Yana magana kamar wani tababbe Basma don't do this to me i can't live without you Zuciyarshi yaji tana wani zafi kamar an hura mai wuta 🔥cikinta ya rike kirjinshi kanshi nata juyawa yana ganin jiri kan ace haka Ya fadi ya sandare idonshi duk sun kakkafe baya motsi,Su'ad tayi kanshi da gudu tana jijjiga shi Please Yaya ka tashi Kar ka tafi ka barmu Basma loves you she will marry you....Tana ta kuka😭😭😭😭😭............................... [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧‍👧👩‍👩‍👧DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👨‍👦‍👦 ~~~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^29~~~30^^^ ************************************************************************************ Su'ad ta dauko wayarta wacce har screen protector'n ya tsage,Jikinta na rawa ta kira Fahad ta sanar dashi Mintuna kadan Fahad ya iso gida suka dauki shi sai a asibiti suna isa Likitoci suka yi kanshi aka shiga dashi emergency,Sannan suka kira Bappa da Khadeeja suka sanar dasu Dukkansu sun hallara a asibiti(Bappa,Nene,khadeeja,Su'ad da Fahad) Hankalinsu duk a tashe sai addu'a suke Allah ya bashi lafiya.Basma na gida bata san abunda ke faruwa ba da taji Su'ad shiru ta dauka gida ta koma. Doctor na fitowa daga Ward din da aka shiga da Adnan su dukkansu suka yi kanshi suna tambayar ya jikin nashi?"Doctor yace kar ku damu nan da wasu yan'hours zai tashi,Bappa yace to amma Doctor me ya same shi ne? Doctor Yace Am sorry to say Adnan ya kamu da hawan jini saboda yawan damuwa da tunani da yake but jinin nashi bai hau sosai ba(140) so please ayi kokari wajen ganin an hana shi yawan tunani da damuwa. Sautin kuka da innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai kake ji,Nene tace Hawan jini Me ke damun Adnan da har ya kamu da hawan jini,khadeeja mutuwar tsaye tayi sai da Su'ad ta kamata ta zaunar da ita.Ba wanda yasan me ke damun Adnan daga Bappa sai Su'ad. Afra da Ashraf sun dawo school suka sami Basma a daki Ta idar da Sallah kenan suka rungumeta,Wellcome my kids Ya school? Lafiya lau Aunty,Afra tace eyes dinki red Aunty basma,Barci nayi,Ina Daddy? Ashraf ya tambaya,Kun duba dakinshi? Yes mun duba ko'ina baya nan,Basma tace maybe ya fita,Afra tace Car dinshi na nan,to ko ya fita da wata motar,Ashraf yace duka 8 cars din na nan,Basma tace to ina yaje maybe dai yana cikin gidan nan basu duba sosai bane Ta katse tunanin tace Oya! Muje kuci abinchi lokacin islamiyya ya kusa Ta shirya su suka tafi islamiyya ,Ta zauna ta cigaba da kuka(Me yasa na fara son Adnan gashi son shi na neman illata ni) Sun shiga dakin da Adnan yake har yanxu bai farfado ba.Nene ke tambayar khadeeja wai me ke damun Adnan ne ?? Khadeeja tace wallahi nima ban sani ba nayi ta tambayarshi sai dai yace mun ba komai,Nene tace to me ye ke damunshi??? Allah ya baka lafiya Adnan Khadeeja ta kira Basma Hello!Aunty ta fada a sanyaye Na'am Basma Aunty me ya sameki naji muryarki kamar kina kuka Basma gamu nan asibiti Adnan bashi da lafiya yanxu haka he is unconcious *Daradammm gaban Basma ya fadi jikinta ya hau rawa ta kasa cewa komai* Please ka hado kayan tea ki same mu a hospital Muryarta na rawa tace To.... Aunty deeja na kashe waya,Wayar ta sulale ta fadi daga hannun Basma *Na shiga uku! Wayyo Allahna! Ya zanyi da Raina Adnan na asibiti bashi da lafiya saboda ni Ina da hanyar taimakonshi amma ba zan iya taimakonsh ba* Kuka take sosai tana buga kanta a bango ,Daya daga cikin masu Aikin (Saratu) ta hawo sama kenan taji kara Dum dum daga dakin Basma ta leka dakin taga lafiya Basma ta gani nata famar buga kanta a bango da sauri ta karasa wajen basma ta rikota lafiya Basma?? Basma goshinta har ya fashe yana jini amma kwata kwata bata jin zafin ciwon illa radadin halin da Adnan ke ciki Kan gado ta fada ta cigaba da kukan bakin ciki.Da gudu Saratu taje ta dauko First Aid box ta zaunar da basma tana mata dressing wurin da taji ciwon ko da aka shafa mata Spirit sam bata ji zafinsa ba(Adnan ne kawai a zuciyar) ta gama ta sa mata plaster a wurin Nagode Saratu,Ba komai Basma amma me ya same ki ?(Saratu nada hankali kuma suna shiri da basma duk da ta girmi Basma) Basma tai mumrshin karfin hali tace manta kawai yanxu dai Dan Allah a hada kayan Tea kuma a yanka fruits(tasan zasu mai amfani) akai mota ace ma Driver gani nan Zuwa,Tace Toh ta fice Basma ta dan gyara kanta but still she is looking pale,ga kuma plaster'n dake goshinta Da sallamarta ta shiga dakin kanta a sunkuye,Suka amsa mata sallamar Driver ya biyo bayanta ya aje kayan ya fita.Idonsu duk a kanta ganin ta fita hayyacinta ,Nene tace Me ya same ki basma ? Ba komai Ya zaki ce ba komai bayan ga ciwo nan a goshinki,Bigewa nayi da Bango ,Allah sarki sannu amma daga gani kinji jiki ,Suna ta mata sannu, Idonta ya kai Kan Adnan dake kwance kan gado,idan ka kalleshi dole ya baka tausayi duk ya fita hayyacinsa.Duk yadda Basma taso ta gimtse kukan da yazo mata ta kasa gaba daya tausayinshi ya kamata ta tashi tai saurin shiga toilet din dake dakin Su'ad ta bita da kallo tana girgiza kai ta gane kuka take kuma tasan Basma na son Adnan kawai ba zata ita fada bane Ta rufe kanta a toilet tana ta kuka sai da tayi mai isarta sannan ta wanke fuskarta,Ta fito kenan shi kuma Adnan yana farfadowa ya fara cewa Basma! Basma Dan Allah ki amince dani Basma ina sonki ina kaunarki Basma bazan iya rayuwa babu ke,Tana jin haka ta koma toilet da sauri ta jingina da kofa tana kuka Nene mamaki ne ya cika ta(khadeeja bata nan ta sun fita ita da Su'ad siyo drugs din da Doctor ya rubuta ,Ni Zee nace wai🙄🙄🙄 da jinya ta koma kan khadeeja LOL) Adnan kenan Basma yake so in hakane kuwa Alhamdulillah naji dadi sannan tayi kan Adnan wanda tuni Bappa da Fahsd sunyi kanshi sun rirrikeshi dan sai fisge fisge yake kamar wani tattabe,Nene tace ka kwantar da hankalinka Adnan Basma taka ce Nene dan Allah kuce basma ta soni ta aure ni Wallahi ina sonta,Shikenan Adnan Basma zata aureka ,Nagode Nene ya rungumeta,Ita kam Nene murna duk ta cika ta Adnan na son Basma shikenan burinta ya cika Basma na toilet na jin su tace Bazan aure shi ba Nene,ba zan auri Adnan ba.Yanzu wacce hanya zan bi in nisanta kaina Adnan ya daina ganina nima na daina ganinshi ta haka zamu cire son juna mu manta da juna,Hanya daya ce Shi ne in bar Gidan inyi nisa da familynsu Adnan To na bar gidan ina zani,Yemen wajen dangin momy ya fado mata a rai ,wannan ne lokacin da yafi dacewa na koma wajen dangin momyna Nayi nisa da Adnan amma wa zai biya mun kudin jirgi Nene ita zan roka nasan zata ji tausayina......................................... [11/12, 2:38 PM] ‪+234 813 461 8338‬: [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^31~~~~32^^^ ************************************************************************************************************** Su khadeeja sun dawo sun tarar da Adnan zaune Nene na bashi fruits a baki,Khadeeja tace Alhamdulillah! Ya jiki,Kanshi kawai ya daga sama (alamar da sauqi) Jim kadan khadeeja tace ina basma? Nene tace Tana toilet tun dazu ko me take? Khadeeja tayi knocking Basma,Na'am Aunty gani nan.Tai saurin goge hawayenta ta dan gyara fuskarta sannan ta fito,Adnan na ganinta ya saki murmushi ,Kanta a kasa tace Ya jiki? Alhamdulillah Basma ya amsata(Tun dazu bai yi magana ba in kai mai magana sai dai ya daga kai )Waje ta samu ta zauna Sai dare Aka sallamesu suka dawo gida,Khadeeja nata tarairayarshi,Ta bashu drugs dinshi yasha yana sha sai barci dan akwai mai sa barci aciki Basma ranar bata yi barci ba ,Tunanin barin gidan kawai take ta tashi tayi sallar dare tana rokon Allah yasa barin gidan nan da zata yi shine mafi Alkhairi a gareta Su'ad ta gayawa Nene komai tsakanin Basma da Adnan bata boye mata komai ba,Washegari da Safe Nene ta kira Basma tace tazo gida tana son magana da ita,Tasan maganar Adnan ce zata mata dan haka tayi Nafila Raka'a biyu tana rokon Allah ya daurata kan Nene ta amince da kudurinta Basma naji duk abunda ya faru tsakaninki da Adnan amma ina so ki sani Basma khadeeja bata isa ta haramta abunda Allah ya halatta ba kuma ni da kaina zan kirata in lurar da ita ta yadda baza tace kinci amanarta ,Zancen cin amanar da Moha ya miki ki ajiyeta gefe ba'a daukar halin wani a daura ma wani Kowa da halinsa,kinsan muhimmancin aure ,Aure raya sunnar Manzo(SAW) sannan kice baza kiyi ba Basma ki chanza tunani ki amince da Adnan nasan waye Adnan zai kula dake zai baki duk wani farin ciki na rayuwa.Hawaye ne ya cika idon Basma Tace nasan da haka Nene but Aunty deeja itace wacce ta taimakeni a lokacin da bani da kowa Ta tsince ni akan titi ta ba tare da jin tsoro ko kyama ba kawoni gidanta Da ta kawoni gidan nata bata maidani yar'aiki ba ta daukeni tamkar kanwarta wacce suka fito ciki daya Aunty deeja ta mun halacci ta kula dani ko Ya'yata uwa daya uba daya abunda zata mun kenan sannan ace na rasa da me zan saka mata sai auren mijinta idan na mata haka ban mata adalchi ba kuma duk wanda yaji halaccin da Aunty deeja tamun amma na dawo na auri mijinta sai yayi Allah wadai dani kuma hakan zai sa mata su rika tsoron taimakawa wasu matan ko su hana mazan su taimaka musu Nene tace kinyi gaskiya Basma but abunda zaki duba shine ke Adnan yake so ba wacce ya taba cewa yana so sai ke,Me yasa ba zaki tausaya mai ba a halin yanxu Adnan ya kamo da hawan jini Basma a tsorace tace Hawan jini? Eh Hawan jini Dan Allah Basma ki tausaya masa ki amince ki aure shi kar ya fada wani hali Basma tace hanya daya ce zata kawo mafitar wannan abu? Wacce hanya ce Basma, Basma tace Inyi nisa da Adnan idan nayi nisa dashi a hankali zao cire sona har ya manta dani Nene tace A'ahh Basma ba zai yiyu ba Basma ta durkusa ta rike kafafun Nene tana kuka mai tsuma rai Dan Allah Nene ki barni na tafi Yemen ki tausaya mun ki duba maraicen da nake ciki wannan lokacin ne yafi dacewa na koma wajen Dangin momyna Please Please Nene kar kice a'ahh Tausayin Basma ya kamata ta riko Basma tace Tashi tashi ya isa haka daina kuka Basma , ba zanyi son kai ba saboda da'na in tauye miki hakkinki na amince da tafiyar ki ,Ta rungume Nene tana cewa Nagode Nagode Nene,Nene tace Amma kinsan khadeeja da Adnan ba zasu amince da tafiyarki ba,Tace ba sai sun san da tafiyata ba mu barshi daga ni sai ke Nene tace bai kamata a barki ki tafi ki kadai ba dama zanje medical check-up Dubai nan da 1 week sai ince zaki rakani daga can sai in kai ki Yemen idan na dawo nasan abunda zance musi Nagode nagode Nene ,Ba komai Basma ai ke ya'ta ce ba abunda bazan iya miki ba for your happiness Da farin ciki Basma ta koma gida Yanxu zata yi nisa da Adnan ta manta dashi shima ya manta da ita Adnan ke tambayar Nene wai tama basma magana? Nene tace Ehh! Na mata kuma ga dukkan alamu zata amince da kai tace a bata sati daya zata yi tunani,Har sati daya Nene ,kamar yau ne ai yanda kwanaki nan ke gudu kuma ina so kar ka sake yi mata wata magana har sai sati daya idan ba haka ba she can easily change her mind,Toh! In Shaa Allahu zan kiyaye ni zan koma gida ,A gaida gida Adnan ya bata tausayi wannan ne karo na farko data fara mai karya but Basma tafi bukatar taimako ita da take marainiya ya kamata ta hadata da danginta Nene tasa anyi ma Basma passport da Visa ana sauran 3days su tafi ta kira Adnan ta sanar dashi ba damar ya mata musu dan shi baya iya yiwa Iyayensa musu ko kadan bai ji dadi ba kuma a ranar ne basma zata bashi amsarsa yana da niyyar idan ta amince dashi ya hada mata wani suprise buh nene ta kwafsa tace da ita zata tafi *3 days later* Basma ta shirya kayanta tsaf amma ba duka kayanta ba Adnan ya sami nene yace mata Kince yau Basma zata fadi decision din da ta yanke gashi har zaku tafi bata fada ba,ka kwantar da hankalinka zata fada ne,Yace Allah yasa to,Nene tace Ameen. Daga gidansu Nene zasu wuce airport duk sun hadu nan . Nene sai da ta faki idon kowa sannan ta dauki phone din Basma tayi texting Adnan Phone dinshi na hannunshi yaji karar text message ranshi ya bashi Basma ce numbernta kuwa ya gani *I LOVE YOU ADNAN,I WILL MARRY YOU* Wani tsalle ya daka yai kissing wayar ya daga hannu yana godewa Allah,Yayi Replying back *THANK YOU SOOOO MUCH MY BASMA,I CAN'T EXPRESS HOW HAPPY I AM TODAY, I WILL ALWAYS LOVE YOU* Phone din na hannun nene ta karanta tayi deleting dama tayi deleting wanda tayi sending .Tace Adnan sai dai kayi haquri amma Basma ba rabonka bace zata maka nisa Sun raka su Airport su Afra har da kuka basu sun rabuwa da Basma,itama sai da tayi kwallan(a ranta tana cewa Shikenan na tafi na barku my kids I will really miss you banso rabuwa daku ba amma ta kama dole ne) khadeeja ,Su'ad,Fahad da Adnan nata daga musu hannu har suka shige Adnan murna kawai uake finally Basma tayi accepting dinshi idan ta dawo zai nuna mata so da kaunar da duk duniya babu wanda ya taba mata irinshi(Allah sarki Adnan bai san Basma is leaving him forever ) *SOME HOURS LATER* Sun isa Dubai,A Buruj khalifa hotel suka sauka.Duk sun gaji Abinchi kawaii suka ci suka yi sallah sai barci Kwanansu Biyar dubai suka wuce Yemen,Suka ce ma Dan Taxi din da ya dauke su gidan sarkin Yemen zai kaisu Securities dake bakin gate sun gane Basma so basu hana su shiga ba Direct Sashen Ummi(kakar Basma) Suka nufa Nahar(kanwar momyn Basma) ce kwance a kan doguwar kujerar dake falon tana kallo,Tana ganin Basma duk ta rude don murna suka rungume juna ,Nahar tace Ummi ummi zo kiga Basma(tana maganar da larabci) Ummi ce ta fito tana( dangasa kafa alamun tsufa Basma ta rungume Ummi daga ita hara Ummin sai hawayen farin ciki,Ummi tace Basma ashe zaki zo gare mu Ina safwan Ina mijinki naki Wasu zazzafan hawaye taji tace ga Nene ku gaisa tukun tare da ita Muka zo Ummi na kai idonta kan Nene gabanta ya fadi,Tayi wajen Nene ta jawo right-hand din nene ,(Su Basma Bin ta suka yi da kallo sun zama confused) Tana kallon hannun tace ita ce wallahi Afaf ce tasa hannunta tana shafar fuskar nene tace Ashe zan sake ganinki Afaf dama kina raye da har mun cire rai da ke......... Ita dai Nene kallon Ummi kawai take ta kasa gane inda Ummi ta dosa................ [10:22pm, 30/10/2016] Memuh S: 👩‍👩‍👧‍👦👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👦‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^33~~~34^^^ ********************************************************************************************************* Ummi ta juya kansu Basma tace Afaf ce ,Nahar tace kina nufin Ya Afaf ce da kike bamu labarin ta bace tun kafin a haifeni ,kafin tabs Nahar amsa itama Basma ta jefo tata tambayar kina nufin twin sis din momy,Ehh! Ita ce,Nene tace kun sani a duhu please ku fahimtar dani Ummi ta zauna tana share hawaye tace *Bayan aure na da Abi Da shekara daya na haifi mata yan'biyu(Awathif da Afaf) kyawawa dasu,Haka suka taso gwanin sha'awa kowa yana son su bayan na haifesu da shekara Uku na haifi Jawhara.Afaf ta kasance tana son wasa da ruwa sau da yawa idan ta faki idon mutane sai ta shiga toilet ta kunna ruwa sai ya taro a bucket sannan tayi ta wasa dashi.Ranar by mistake ta kunna famfon ruwan zafi maimakon na sanyi sai da ya cika sannan tasa hannunta(Right-hand) tana sawa ta kone kunji dalilin da yasa na gane ita ce saboda wannan tabon konar da ke hannunta* Nene tace Ina ga dai munyi kama da wancan Afaf din ne kuma duk mun kone a right-hand dinmu amma ba ita bace Ni sunana Fatima kuma Inna ta gaya mun ina yarinya na kone da Ruwan zafi na flask Ummi tayi murmushin takaici tace kin taba ganin inda uwa ta manta danta,Afaf naji a jikina kece Afaf dita kamaninki na nan basu bace mun ba sai dai tsufa da kika yi shima tsufan ba'a gani dan daga gani kina cikin hutu,Kuma tabon konar da kika yi shine dai a hannunki exactly inda nasan anan kika kone Nene tace kai ina ga dai coincidence ne but Ita Afaf din ya akayi ta bace??? Ummi tace *Shekaru 45 da suka wuce a lokacin kuna shekara biyar Munje London hutu tare daku Ranar da zamu dawo mota daya muka shiga ni da Abi xuwa airport ke Awathif Jawhara da Nanny dinku mota daya Mun biyata ta wani supermarket anan kika bace amma ba wanda yasan ba dake muka tafi airport ba Su Awathif sun dauka ko in dawo motarmu ne dan dama kina ta damunsu wajen Ummi kike so Awathif ma nata rigima sai ta bi ki Mu kuma a tunanin duk kuna tare tunda dama a dayar motar kike Sai da muka isa airport sannan aka ga baki Nanny ke cewa sun dauka tana motarmu Nan take muka koma Supermarket da muka tambayesu suka ce basu ganki ba hankalinmu ya tashi muka shiga nemanki fasa tafiyar mukayi Babu inda bamu yi cigiyarki ba babu ke Nasha kuka kamar raina zai fita haka Awathif tai ta kuka tana tambaya ina Afaf dinta Shekaru nata wucewa Shiru ba labarinki har muka hakura muka fidda rai* Nene tace Amma kina da wata shaida da zata tabbatar ni ce ba mistaken kike ba,Ummi tace Ehh ina da ita Ta shiga daki ta dauko wasu Pictures dinsu ita da Awathif(momyn Basma) da suna yara,da wanda take ita kadai hadda hoton konar da tayi Nene ta karba tana dubawa tace Tabbas nice wannan da ina yarinya dan naga hotona na wajen Inna kuma na yadda kece mahaifiyata dan nima na jiki a jinin jikina kuma haka naji Basma lokacin da na fara ganinta,bayan na bata kenan su Inna suka tsince ni dole in kirasu dan jin wannan al'amarin Ummi tace ki kirasu nasan zasu fadi yadda aka yi kika je hannunsu Anan take Nene ta kira Bappa bayan sun gaisa tace Dan Allah ka shirya kuzo Yemen dasu inna(yasan da xuwansu Yemen dan haka bai yi mamaki ba da tace Yemen) Yace Yemen kuma me ya faru?? Idan kunzo zaku ji kuma me ye,Shikenan zuwa jibi In shaa Allahu zamu zo,Please kar ka sanar dasu Adnan zance zuwanku,To shikenan ya ajiye wayar Basma ta rungume Nene tace Ashe kece Twin sis din momyna shiyasa naji ina kaunarki,Nene tace nima naji ina kaunarki Basma tun ranar da na fara ganinki ashe ya'ta ce Basma ta basu labarin tun bayan rasuwar momynta har yadda akayi tazo gidansu Adnan da dalilinta na dawowa Yemen Ummi tace Allah mai iko haka Allah ke al'amuranshi Everythig happens for a reason,Wani lokacin wani abu zai sameka da kai baka so amma shine mafi alkhairi a gareta kinga da baki bar gidan Moha ba, ba zaki taba haduwa da Yan'uwanki ba ke kuma Afaf baki yi son zuciya ba kin taimaki Basma gashi sanadiyyar taimakonta kin gane Iyayenki da yan'uwanki na ainihi,Hakane suka hada baki(Basma,Nene da Nahar) Ummi ta daga hannu sama tace Alhamdulillah! Allah nagode ma da na sake sa ya'ta a ido kafin na mutu ita kuma Awathif Allah ya jikanta ya gafarta mata An sanar da Abi da sauran Yan'uwa an gane Afaf,Murna sosai suka yi kuma sunyi mamakin bayan shekaru masu yawa an ganeta. Nene taga kannenta(Jawhara,Abdul-Rahman,Shureim,Abdul-azeez da Nahar)da bata sani ba.Duk suna ta murna A daki daya Ummi da Nene suka kwana Basma kuma da Nahar(ita kadai ce bata yi aure ba) *2 DAYS LATER* Bappa,Inna da Baba(iyayen Afaf) Sun zo ,an karbesu hannu bibbiyu cikin karamci Bayan sun huta,Dukkansu suka hallara a falo har da Abi Ummi ta sanar dasu dalilin da yasa aka ce suzo Baba yace Allah mai iko babu yadda Allah baya al'amuranshi Tabbas Fatima bamu muka haifeta ba Shekarun baya da suka wuce,Munje London Asibiti ni da Inna kan matsalar rashin haihuwa A ranar da kuka ce ta bata muma a ranar muka je Supermarket dan a ranar zamu dawo nigeria Mun isa airport sai muka ga yarinya a can seat din baya da yake motar prado ce (ni da Inna muna zaune tsakiya bamu san tana can baya ba) Tana ta barci har munji tsoro nai karfin halin tashinta tana bude ido tace why did you wake me up?? Na tambayeta ya akayi ta shiga motar nan,Tace su ummi na shopping naji barci nake ji shine na dawo mota na kwanta ku su waye ina ummina (hakan da muka ji tace ya tabbatar mana daga supermarket ta biyo mu ta dauka motarsu ce ta shigo tamu) Mun koma supermarket muka tambayesu suka ce ba wanda yazo cigiyarta maybe kafin ku koma mu muka je,Daga nan muka yanke shawarar mu dauketa kila Allah yaga rokonmu ne shiyasa ya bamu ita Muka tafi da ita Nigeria,Tayi mana kuka da kyar muka lallasheta,Tace mana sunanta Afaf amma muka maida ta Fatima don sunan da muke ta so mu sama yar'mu kenan A hankali ta saba damu ta manta da iyayenta ta dauka mune iyayenta,Ganin mun samu Fatima yasa muka daina damuwa da rashin haihuwa,Mun nuna mata so da gata sosaii da ba wanda zai dauka bamu muka haifeta ba har muka aurar da ita Kowa nata mamakin wannan al'amari hade da murna gano yar'uwarsu,Ummi da Abi nata musu godiyar kula da Afaf da suka yi Baba yace ba komai,Yar'mu ce ai Fatima ko Afaf,Abi yace Fatima dai ai ynxu yar'ku ce,Suka yi dariya gaba daya............. [4:27pm, 31/10/2016] XEE YABOUR😘: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👨‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👦 ~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^35~~~36^^^ ********************************************************************************************************** Kwanansu biyu a Yemen suka ce zasu koma. Nene ta kira Basma suka kebe su biyu.Nene tace yanxu tunda Adnan dan'uwanki ne na jini ,me zai hana ki amince da aurensa Basma tayi murmushi tace Duk da na gano Adnan jini na ne bazan iya aurensa ba in kalli Aunty deeja da wani ido sai ince mata dan yana dan'uwana na aureshi idan nai mata haka bn mata adalchi ba Nene tace shikenan Basma Allah ya zaba mafi Alkhairi,Ameen Yanxu yaushe zaki zo mana hutu, In shaa Allahu Zan zo kuma dan Allah kar ku gayawa Su Adnan cewa baki muka hada dake kika kawoni Yemen kice musu a can Dubai muka hadu da Ummi itama taje asibiti ,Nene tace Shikenan Basma Sunyi bankwana da Yan'uwa an raka su Airport Basma tana ta kewar Nene ,Duk yadda taso ta manta Adnan ta kasa son shi bai fasa karuwa a zuciyarta ba tayi missing dinshi sosai tana son ganin kyakkyawar fuskarshi tana son jin muryarshi but ta riga ta daukarwa kanta alkawarin ko da son Adnan zai kashe ta baza ta koma kaduna ba sai ya cire ta a ranshi ya hakura da ita Adnan nata murna Yau Basmar shi zata dawo Bappa bai gaya musu exact time din da zasu yi landing ba kar suje daukosu da wuri suga su Inna coz basu san shima Bappa yemen yaje ba ce musu Dubai zashi wajen Nene Suna isa Driver'n su Inna ya dauki su ya wuce dasu zaria,Su Bappa suka tsaya jiran su Adnan *30 Minutes Later* Adnan dasu Afra Ya zo daukarsu Yana ta waige-waige ko sai hango Basma bai ganta ba,Zai tambaya kenan ina take? Su Afra suka riga shi,Bappa ina Basma Afra ta tambaya,Bappa yace Basma na nan zuwa,Adnan yace Yanxu tana ina?? Bappa ya dafa kafadarshi yace Muje gida tukun. Har ya fara rudewa yace Bappa dan Allah kar kuce min Basma ta tafi ta barni,Bappa yace ka kwantar da hankalinka Bata tafi ta bar ka ba muje gida Hankalinshi ya kasa kwanciya Addu'a yake Allah ba wani abu ne ya sami Basma ba,ko ta tafiyarta ne daga can Dubai din idan kuwa daya daga ciki ya faru to shima zasu rasa shi Su Su'ad suka tarbesu suna murna suna tambaya Ina Basma? Nene tace Basma na nan,Fahad yace Ina?? Ku kwantar da hankalinku zaku ji kuma ina ne.Sajeeda tazo daga kano da ya'yent(Shuraih da Aseef) Bappa yace Adnan ya kira Khadeeja tazo Mintuna kadan sai gata tazo tana zuwa ta fara tambaya Ina Basma Bappa ya fada musu komai (sai dai ya chnza yadda aka yi suka je Yemen kamar yadda Basma ta bukata ayi) Ya kuma ce musu Basma tace zata zaune can amma zata rika zuwa hutu nan Sunyi mamakin faruwar wannan al'amari at the same time sunyi murna sosai Adnan yafi kowa murna he can't believe Basma Yar'uwarshi ce jininshi but Me yasa bata dawo muyi aure ba,Dole in bita Yemen Aunty deeja tace umm su Basma butula an tafi an barmu Su'ad tace ko waya,Suka yi dariya .Fahad yace Yaushe zamu je ne muga Yan'uwanmu na can da Granny ashe Inna ba ita ce Granny'nmu ba Nene tace itama Granny'nku ce ,Ku bari Su'ad tayi hutu sai ku tafi ba saura 2weeks ba,Su'ad tace Eh Adnan Yace Ni bazan jira su ba Gobe zan tafi kar lokacin da zasu tafi ina da aiki is better naje yanxu(Ni dai Zee nasan ba wannan dalilin ne ya sashi cewa zashi gobe ba....Basma ce😀) Bappa yace Allah ya kaimu Yace Ameen Adnan ranar bai runtsa ba khadeeja kuwa Sharbar barcinta kawai take bata ma san idonshi biyu ba dama da fushin shi ta kwana dan taso ayi.........Shi kuma yaqi coz ba macen da yake son kasancewa tare da ita sai Basma Ta bangaren Basma itama Tunanin Adnan kawai take sai da tasha maganin mura mai sa barci sannan ta iya yin barci Tunda safe Basma ta tashi ta tsala kwalliyarta ta tafi gidan Jawhara (Sistern Momy) Hakanan kuma taji gabanta nata faduwa ta rasa dalili *8:00am* Adnan na cikin jirgi,Yayi jigum ya lumshe ido yana tunanin Basma:Ranar haduwarsu ta farko da ta biyu da ta rika ihu Aljani :Lokacin da suke wasa da su Afra ta taba shi bata sani ba:da lokacin da ta rika jika shi da ruwa haka ya rinka tuno abubuwan da suka faru tsakaninshi da Basma yana jin nishadi............... KUYI HAKURI YAU BAN MUKU TYPING DA YAWA BA AND PLEASE IN KUNGA ANY MISTAKE JUST IGNORE IT BAN SAMU NAYI EDITING BANE YAU ZEE YABOUR❤❤ [11/12, 2:38 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^37~~~38^^^ *************************************************************** _*DEDICATED THIS PAGE TO ALL MEMBERS OF ZEE & HUSSY NOVELS GROUP*_ ****************************************** Suna isa Driver'n da aka aiko ya daukeshi dan sun san da Zuwanshi Ummi nata murna taga jikinta Nan aka dabaibayeshi da kayan ciye ciye ,Raba ido kawai yake ko Basma xata fito,Shiru bai ji ta ba ya kasa daurewa Yace Ummi ina Basma ne?? Ummi tace tana gidan Jawhara ya kamata ma kaje gidan iyayen naka. Abunda yake so kenan yace Gaskiya kam Bai wani ci abinchin sosai ba hankalinshi na can so kawai yake yaga Basma Aka kaishi part din Abi yayi murnar ganin Adnan yana tambayarshi ina yan'uwanshi ? Yace suna Nigeria suma zasu xo,Abi yace Allah ya kawo su lfy,Adnan yace Ameen Driver ya kaishi gidan Jawhara,Basma da ya'yen Jawhara nata hira a falo Kamshin turaren Adnan taji ya daki hancinta Aranta tace wannan kamshin turaren Adnan ne ba dai yazo Yemen ba,Kaii!! It can't be Kamar ance daga kanki sama suka yi four eyes da Adnan,Tace wato biyoni yayi at the same time Wani sanyi da dadi taji zuciyarta gashi ya sakar mata murmushin dake kashe mata jiki 30 seconds Suna kallon juna Basma tayi saurin kawar da idonta Adnan ya gaisa da ya'yen jawhara yace ma karamar cikinsu ta kira mamansu(da turanci ya gaisa da so dan basu jin hausa daga Larabci sai turanci) Basma ji tayi ta kasa barin falon tana so ta riqa jin kamshin turaren tana satar kallonshi Adnan ma ita yake kallo amma bai san tana kallonshi coz ta dukar da kanta kasa buh ita tana ganin yana kallonta Da ya gaisa da Jawhara Yace Basma ki same ni waje,Tace Toh ta dauki gyalenta ta yafa tabi bayanshi A tsaye ta same shi ya jingina da Mota Ta tsaya nesa dashi kadan,Yace matso mana Basma,Ta kara matsowa kadan gabanta na duka uku-uku Ya wani yi fuskar tausayi yace me yasa kika zabi zama nan ba zaki koma Nigeria muyi aure ba?? Tace Ya Adnan ai na riga na riga na gaya ma bazan aure ka ba Yaushe koma kika chanza decision Dama ai tun farko wannan shine decision dina Ranar da zaku tafi Dubai kin turo mun text message cewa zaki aurena Basma ta dan zaro ido waje tace Ni,Gaskiya bani bace Numbernki ce karba ki gani ,Ta karba tace Eh Numberta ce amma bani na turo txt message din nan ba sai dai wani yayi amfani da phone dita ya tura ma Ya danyi shiru yana tunani zuciyarshi ta bashi Nene Yace Naji whatever it is yanzu ni dai ki amince mu koma Nigeria ai mana aure in ma nan kike son zama sai in samar miki gida anan ni na rika zuwa Basma tace Ya Adnan hakurin nan dai shi zaka yi Ta juya zata shige gida ya riko hannunta ta baya ta juyo suka hada ido Son shi na ratsa dukkan sassan jikinta, Please kar ki mun haka Basma I truly Love You baxan iya rayuwa babu ke ba Ta fisge hannunta tace kayi hakuri ta shige ciki tana kuka Nan ya duke yana kuka yana maganganu kamar mahaukaci har ya daina numfashi Jawhara tace Ya akayi ne Basma? Ina Adnan din?? Cikin shesshekar kuka tace yana waje Jawhara tace to lafiyarki kike kuka? Taso ta tsayar da kukan ta kasa Jawhara tace bari na sami Adnan din inji me ke faruwa( Duk da turanci take magana dan itama ba hausar ta iya ba) Salati ta rafsa hade da yin ihu ganin Adnan kwance baya numfashi da gudu Su Basma da ma'aikatan gidan suka fito Basma a gigice tayi kanshi tana girgiza shi tana cewa _Dan Allah Ya Adnan ka tashi kar ka mutu Ina so....._ Sai kuma ta kasa karasawa _I never mean to hurt you_ Tana ta jijjagashi tana kuka hawayenta sauka kan fuskarshi,A hankali ya fara motsi ya bude idonshi ya sauke su kan fuskar Basma da har ta fara ja saboda kuka Yana daga kwance ya rungumota ta fada jikinshi ya matseta kan kirjinshi yana shafa bayanta Sorry my dear ki daina kuka,ba abunda ya sameni Basma a wani irin yanayi ta ji ta sai taji kamar suyi ya zama haka ita da Adnan ammw ina ba zai yiyu ba Tayi kokarin raba kanta da jikinshi amma ya sake matse ta Tace Please let go of me,Su Aunty Jawhara na kallonmu fa Sai a lokacin ya tuna dasu yai saurin Sakinta Daga Basmar har Adnan duk suka ji wata kunya ta lullubesu ganin idonsu Jawhara a kansu Jawhara murmushi kawai tayi ba tace komai ba Adnan da yazo tashi yaji ya kasa jikinshi yayi weak Ya'yan Jawhara maza biyu suka kama shi ya mike Jiri ya fara ji yana ganin dishi-dishi Ya tafi Zuuu zai fadi duk basu lura ba sai Basma da gudu ta rike ya fada jikinta Yana wani irin nishi da ya jawo hankalinsu gare shi Suka kama akasa shi mota sai asibiti Suna zuwa aka basu gado Doctor yace hawan jinin shine Doctor na fadar haka Shaa sai ga hawaye sun wanke fuskar Basma Tasan itace Silar halin da yake ciki,Oh!Allah kai mani maganin wannan al'amari Jawhara ke cewa Gaskiya Adnan na bukatar kula sosai hawan jini ba karamin abu bane,ya kamata ya daina yawan damuwa da tunani .Tausayinshi ya sake kama Basma Inteesar yar'jawhara tace Garin yaya ya suma? Basma tace Ni dai lafiya lau muka rabu dashi Ummi,Abi da sauran Yan'uwa duk sunzo asibitin Sun tausayawa Adnan suka yi ta mamaki me ya jawo mai hawan jini da gatanshi da komai Ummi ta fita daga daki ta kira Nene ta tambayeta me ya sawa Adnan hawan jinin??? Nene ta fadawa Ummi komai Ummi tace ai ba za'a biyewa ra'ayin Basma Nene tace naga marainiyace kar a shiga hakkinta Ummi tace au ba cutar da ita za'ayi ba Adnan dan'uwanta ne jininta ne b yadda za'ayi tace bata son shi ko yaya ne tana son shi idan ma bata son shi bayan aurensu a hankali zata fara son shi Matarshi bata isa ta hana auren nan ba,ba za'a bar Yaro yana wahala ba,Allah ya halatta abu sai ace a haramta saboda da wata,Auren Adnan da Basma kamar anyi an gama ki bar komai a hannuna Nene tace Toh Ummi tace Yawwa ki gaida yara ta kashe wayar Ita dai Nene bata so a tursasa Basma dole sai ta auri Adnan haka kuma tana so Adnan ya auri Basma tana tausayin danta gata nan dai a tsakiya Duk Yan'uwa sun cika a dakin hadda Basma Adnan na kwance amna idonshi biyu Ummi ta shigo ta kalli Adnan ta kira sunanshi Adnan, Yace Na'am Ummi Yau zan kawo maka karshen matsalarka muna da damar da zamu ceto rayuwarka ba zamu bar ka ka rasa ranka ba dan haka *AURENKA DA BASMA NAN DA WATA DAYA KUJE KU FARA SHIRI* Ihu ne kawai Adnan bai yi ba dan murna godiya kawai yake ta ma Ummi Kowa wurin yaji dadin wannan zancen ban da Basma Kuka ta fara tace Dan Allah Ummi kar ku hada ni Aure da Ya Adnan Ummi tace Bana son jin komai na riga na gama magana ta fice......................................................................... PLEASE IN KUNGA ANY MISTAKE JUST IGNORE IT BAN SAMU NAYI EDITING BA [11/12, 2:39 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~~PART II~~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE ^^^39~~~40^^^^ ************************************************************** _*DEDICATED THIS PAGE TO MY DURLINGS ILHAM MAIWADA,KHADY MASKA EN AYSHER ALQERLY*_ *************************************************************** Basma nan ta fadi kasa tana kuka kamar ranta zai fita tace Dan Allah ku roke ta kar ta hada aurena da Ya Adnan Nahar tazo ta rike ta tace wacce irin magana ce kike haka? Ni dai Dan Allah kar a mun aure wallahi bana son aure na tsani aure kuma a rasa wanda za'a hada ni dashi sai Ya Adnan Adnan zuciyarshi yaji tana tafasa yazo gaban Basma ya rike hannayenta ya matse su suna facing juna yace Basma me nai miki wai bakya sona bakya tausayina Kanta ta girgiza tace ba haka bane Ya Adnan ni dai kar ka bari ayi auren nan Basma in dai akan Khadeeja ne she will understand everything Ya Adnan aure ne na tsana tun kan Moha Yace Basma trust me ba halinmu daya da Moha ba _I love you with all my heart_ Har ta motsa bakinta zata ce _I love you too_ sai kuma tayi shiru Ki fadi abunda kike son fada Please ka hana auren nan A fusace ya saki hannunta ya mike tsaye Yace Bazan hana ba idan kinga an fasa auren nan to sai dai in mutuwa nayi Su Jawhara na kallonsu sun basu tausayi su dukkansu Basma kuka take ba kakkautawa Su Nahar nata lallashinta Adnan fita yayi dakin dan ba zai iya jure jin kukanta ba,Wata kujera ya samu ya zauna a corridor'n Ward din Kuka yake ya kasa gane Basma sai kace kanta aka fara *Saki* Tana kiran cin Amana to me ye cin Amana dan ta aureni _*Ni dai nace banga laifin Basma ba Ta rike amana tasan me ye halacci Saboda Khadeeja ta hana zuciyarta abunda take so duk da ta gano Adnan dan'uwanta ne sabanin wasu matan da tun kafin su gano dan'uwansu ne zasu amince su manta da alkhairin da khadeeja ta musu amma Basma bata yi haka ba bata yi son kai ba*_ Ta tuna hadisin" *MANZO SAW DA YAKE CEWA IMANIN DAYANKU BA ZAI CIKA HAR SAI YASO MA DAN'UWANSA ABUNDA YAKE SO MA KANSA* Basma tasan idan ita akayi wa haka ba zata ci dadi ba shiyasa bata son rushewa wani farin ciki saboda nata farin cikin *1 DAY AFTER* Aka sallami Adnan daga Asibiti Duk yadda Adnan yaso ya hadu da Basma taqi yarda ta rufe kanta a daki anyi ta knocking taki budewa suka kyaleta dan a tunaninsu barci take Adnan na zaune falon Ummi yayi jigum yana jiran fitowar Basma suyi sallama dan yau zai koma Ummi ta shigo falon ta same shi jigum tace Ba zama zaka yi kana jiran fitowar ta ba idan ka biye ta tata ba za'a ayi auren nan ba dan haka ka tashi ka tafi kuje ku fara shirye shirye muma nan zamu yi namu shirye shiryen kafin mu same ku can ayi biki Adnan yace Ummi kin gama mun komai bansan da wane baki zan miki godiya ba Ba komai Adnan yanxu ka tashi ka tafi Ya mike yace to na wuce Allah ya tsare ya kai lfya Ameen A gaida su Afaf Zasu ji Yayi sallama da Yan'uwa aka kaishi airport,Murna Fal a cikinshi damuwarshi daya bai ga Basma ba Wata zuciyar tace mai me ye na damuwa bayan ta kusa zama mallakinka Sai kuma yaji dadi Khadeeja da ta gama shiryawa Adnan abinchi Ta zauna falo tana chanza channel ta kawo kan Sunna Tv Tace Yau dai bari na kalli Sunna Tv naga Gombe ne dama ban taba jin wa'azinshi ba Sheikh Kabiru Haruna Gombe ne ke ta sharara😂 wa'azi akan mata masu zuwa wajen Bokaye/Malaman tsibbu Yana fadar hukuncin masu xuwa wajen boka Jikin khadeeja yayi sanyi hankalinta ya tashi sai kuka Tayi regretting(nadamar/dana sanin) fadawa wannan mummunar hanya amma ba wanda ya jefa ta sai Mamanta(Wa iyazubillah Wasu iyayen suke halaka Ya'yansu) Ya Allah ka yafe mun a bisa rashin sani na aikata haka bansan haka hukuncin masu xuwa wajen Boka yake ba(Khadeeja dama bata da ilimin addini gidansu basu damu da ilimin addini boko kawai suka sa a gaba yan'gidansu basu zuwa islamiyya ,To kunga ga abunda rashin ilimin addini ya jawo mata but da yawa yanxu munfi ba ilimin boko muhimmanci akan na addini dafatan iyaye zamu gyara Allah yasa mu dace Ameen) Mama itama ya kamata na mata wa'azi ta tuba ta daina tun kafin mutuwarta a waya ba zai yi ba sai dai naje Gombe bari Adnan ya dawo Allah nagode da na gane gaskiya kafin mutuwata Ta tashi tayi alwala ta fara nafilfili tana rokon gafarar ubangiji *YEMEN* BACK Basma na daki na jin maganarsu(Ummi da Adnan) Tana jin fitarshi ta fito Fuskarta da idonta sun kumbura sunyi ja da ka kalleta dole ta baka tausayi Ta durkusa gaban Ummi tace Ummi ina rokonki Dan Allah ki janye zance aure na da Ya Adnan Ummi tace ba zan janye ba Basma aurenki da Adnan kamar anyi an gama Ummi Dan Allah pleasee pleaseee Basma ki daina rokona dan ba saurarenki zanyi ba ,ba zan bar Adnan ya rasa ranshi ba ina tausayinshi idan ke bakya tausayinshi Basma tana kuka tace Shi kina tausayinshi ummi amma ni bakya tausayina bakya tunanin nima zan iya rasa ran nawa shi a taimaki rayuwarshi ni kuma a ruguza tawa shi da yake namiji kuma yana da iyaye ni fa macece nasan da su momyna nada rai ba zasu mun auren dole ba Ummi ta riko Basma tace ba haka bane Am doing this for both of you Basma naga Adnan dan'uwanki ne zai kula dake yana sonki yana tausayinki shiyasa naso hada ku aure ba wai bana sonki bane duk cikin jikoki ba wanda nake so kamar ki son naki ne yasa na hada ki da Adnan dan ba wanda yafi dacewa da ke sai shi amma tunda bakya so shikenan Ba zan so kiga na takura miki ba na danne miki hakkinki saboda iyayenki basa raye Basma ta rungume ummi tace nasan kina so kuma ba zaki zabar mun abunda zai cutar dani ba ni dai aure ne bana so Ai shikenan ya wuce ba za'a miki ba ki daina kuka tana ta lallashin Basma................................................................................ *_ZEE YABOUR_* [11/12, 2:39 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👦‍👦 ~~~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^41~~~42^^^ *************************************************************************************** Khadeeja da kanta taje dauko Adnan airport Suka rungume juna Yace Yau da kanki kika zo daukata ba ko driver Yes ta daga kai Nayi missing dinka sosai Yace Just 1day fa Ko 1hour ne am always missing you in dai baka kusa dani I Miss you too my deeja(Hakanan yaji ta bashi tausayi yanzu fa kishiya zai mata bai ma san ta ina zai fara gaya mata ba) Ina su Afra Suna islamiyya Ya riko hannunta to muje gida Suna isa gida ta ja shi toilet ta hada mai ruwan wanka yai wanka ta taya shi shiryawa Sannan suka dawo falo ta kawo mai abinci iri-iri ta rika bashi a baki Haka ta ringa tarairayarshi ,tarairaiyar da tunda suka yi aure bata mai irinta ba duk da tana kula dashi amma ta yau ta daban ce Shi mamaki ne ma ya cika shi a ranshi yace kamar tasan zan mata kishiya Yace My deeja yau naga kamar kina cikin farin ciki Tayi murmushi tace ba wani farin cikin da nake ciki jin jikina ma nake ba dadi sai ina ji kamar zamu rabu da juna Tausayinta ya kama shi bai san lokacin da ya rungumata ba Yace ba abunda zai raba mu my deeja muna tare har abada Ta fashe da kuka yana lallashinta,Ya dauketa ya kai ta daki ya kwantar da ita kan gado. Nan ya fara romancing dinta itama ta fara mayar masa da martani har dai suka zarce....🙈 dama abunda take so kenan shiyasa ya mata haka dan ya faranta mata rai Washegari da safe ta cewa Adnan tana so ta tafi Gombe Mama bata da lafiya ,Ya amince tare da mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya Su Ashraf nata kuka sai sun bita da kyar ta lallashe su suka hakura *YEMEN* Basma nata jin dadi an fasa aurenta da Adnan but still she loves him,harkokinta kawai take har an fara neman mata admission ,ta cigaba da School Ummi ta gayawa yan'uwa ta janye zancen auren Basma da Adnan duk basu ji dadi ba,Adnan ne har yanzu ta kasa gaya mai bata san wane hali xai kara shiga ba idan yaji *NIGERIA* Khadeeja ta isa Gombe lafiya ta sami kowa lafiya Ta ma mamanta wa'azi sosai kuma ya shige ta tayi nadama,Tace khadeeja ta yafe mata ,Khadeeja tace a'ah mama baki mun komai ba ai a bisa rashin sani ne,Tana ta sama khadeeja Albarka *2 DAYS LATER* Ummi ta yanke shawarar sanar da Adnan kar sai lokaci yayi sannan yaji an fasa gwara ya sani tun yanxu Ta kira shi but Number busy Adnan ne ke waya an kira shi : _Su khadeeja sunyi accident a mararrabar jos yanxu haka tana asibitin Giwa(Kaduna) dan shi Driver'n anan take ya rasu Adnan Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai yake maimaitawa ,A 360 yake driving kamar zai tasha sama, A guje ya shiga dakin mutuwar tsaye yayi ganin injuries din dake jikin Khadeeja har ta chanza kama ,Da kyar ya karasa inda take ya rike hannunta yana kuka Yace khadeeja haka kika koma da na sani ban barki kin tafi ba Tana kuka tace Haka Allah ya kaddara Adnan ni dai ina rokonka ka yafe mun nasan mutuwata tazo My deeja baki mun laifin komai ba in ma kin mun na yafe miki da wanda na sani da wanda ban sani ba amma ki daina cewa mutuwa zaki yi Hmm Adnan ina ji a jikina bazan kara awa daya a duniya ba No! My deeja zaki warke zamu cigaba da rayuwarmu tare Adnan kenan alfarma daya nake nema a wajenka Ina ji my deeja Dan Allah bayan raina kar ka auri kowa sai Basma ba, ita kadai ce zata iya kula dasu Ashraf kamar yadda zan kula dasu Adnan shiru yayi yana kuka Khadeeja tace kayi shiru Adnan Yace shikenan my deeja Ka mun Alkawari Na miki alkawari amma Basma ba zata amince da aure na ba Tace dauko wayarka Ya fiddo wayarshi daga aljihu Tace kunna voice recorder Ya kunna Tace: _My Basma bamu hadu dake ba gashi ajali na yazo nasan bazan tashi daga gurin nan ba naso ace mun sake haduwa dake my basma amma haka Allah ya tsara Ina neman wata alfarma daya a wajenki please bayan raina ki auri Adnan nasan ke mutuniyar kirki ce zai samu kwanciyar hankali kuma ba zai ji rashina sosai ba Su Afra zasu samu uwa nasan zaki kula dasu ba zasuyi maraici ba please basma fulfill this my wish Ki yafe mun kuma ina neman addu'arku a ko da yaushe ki sa Su Afra su rika mun addu'a I love you all Allah ya hada mu a aljanna_ Kuka Adnan yake sosai ya kasa cewa komai khadeeja ta bashi tausayi sosai sai yau yasan son khadija Kalmar shahadar da khadeeja tayi yasa shi dagowa ya kalleta yaga idonta sun kafe bata numfashi Ya fasa ihu da karfi yace khadeeja ya fada kanta yana kuka yana jijjigata Please my deeja ki tashi kar ki tafi ki barni ni dasu Afra muna sonki please kar ki mutu khadeeja Yana ta kuka kamar ranshi zai fita *KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT* Khadeeja ta riga mu gidan gaskiya _*Wayyo Aunty deeja*_ 😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 [11/12, 2:39 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^43~~~44^^^ ****************************************** *************************************************************** Da kyar nurses suka daga Adnan kan khadeeja Kamar tababbe haka ya rika yi a asibitin Daga nan akw dauki gawar khadeeja sai gida Ashraf da Afra na jin hon din mota suka fito da gudu suna cewa Mummy oyoyo Adnan ya fito daga motar yana kuka ya rungumesu Sukace Daddy me yasa kake kuka? Ina mummy Yace ba komai kaina ne ke ciwo muje cikin gida Ina mummy?? Mummy suna kan hanya Afra tace Allah yasa mummy ta siyo mun chocolate din da tayi promising dina,Ashraf yace See you instead of kiyi mata addu'a Allah ya dawo da ita lafiya buh ta chocolate kike To wa ya gaya ma ban mata addu'a Tausayinsu ya kama Adnan ya jasu cikin gida Ya barsu a falo ya shiga daki yana kuka Su Nene hankalinsu ya tashi sosai Da kuka suka zo gidan Nene ta sami Adnan a daki tana mai nasiha tana bashi hakuri Su'ad ta kira Ummi ta sanar da ita Ummi taji mutuwar khadeeja duk da bata taba ganinta ba Tace wa Basma ta shirya gobe zasu 9ja Basma tace ni dai gaskiya ba zani ba Ya zama dole kije Saboda me ummi Idan munje zaki gani Ta dai Basma tunani take me zai sa ummi tace zasu 9ja Allah yasa lfya Yan'uwa khadeeja sunzo suna ta kuka A ranar aka kaita(Makwancinta wato kabari inda kowa zai yaje Allah ya haskaka mana kabarinmu Ameen) _Dukkan mai rai mamaci ne yanxu ga karshen Aunty deeja nan kamar bata yi rayuwa a duniya ba, Ya kamata Yan'uwa mu hankalta mu sani mutuwa zata iya riskar mu a ko da yaushe Allah yasa mu cika da imani_ Ashraf da Afra sun ga mutane sun taro a gidansu ana ta koke-koke basu san me ke faruwa ba Sai da dan'yayar khadeeja he is 10yearx Yace musu Mamanku ta rasu amma baku yin kuka wasa ma kuke Afra tace mummy bata rasu ba tana gombe Wa ya gaya miki mommynku accident tayi ta rasu kuma baki ga Su maman gombe sunzo nan suna kuka ba Afra da Ashraf a guje suka nufi dakin Adnan tunda aka dawo kai khadeeja ya koma daki Suka ce Daddy wai mommy ta rasu,A firgice yace wa ya gaya muku Sameer ne Ya rungumesu yace ku rika mata addu'a kunji she need your prayers Ashraf da Afra sai kuka Ashraf na cewa Mummy why did you leave us Adnan ya rufe mai baki Yace Don't say that just pray for her *12:00pm* Su Basma na garin kaduna Gabanta nata faduwa suna shan kwanar gidan bugun kirjinta ya karu da sauri fat fat fat Motoci ta gani birjik da mutane Gabanta yayi wani mummunar faduwa ranta ya bata kawai Adnan ne ya rasu Ihu kawai ta fasa a motar tace Wayyo Allahna! Nayi sanadiyyar mutuwar Ya Adnan sai kuma numfashinta ya dauke Akan gado ta ganta Su'ad na mata fifita Tace Su'ad Ina Ya Adnan Yana daki Alhamdulillah Allah nagode ma ashe bai mutu ba me ya faru naga motoci da mutane bakin gidan nan Su'ad tayi shiru tana tunanin ta ya zata gayawa mata Basma tace kinyi shiru kar dai kice mun daurin aure na da Adnan ne ake Ba daurin aurenku bane Aunty deeja ce ta ra...ra...su(ta karasa da😭😭😭) Basma kankame su'ad tayi tana kuka tace Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Allah ya jikan ki Allah ya gafarta miki Aunty deeja ashe rabuwar karshe muka yi dake Ashraf da Afra ne suka shigo dakin da gudu suka rungume Basma suna kuka suna cewa Aunty Basma mummy ta rasu ,Basma tama kasa lallashinsu ta yasu kukan kawai tayi Kwana uku ana zaman makoki ,Kowa ya watse Afra da Ashraf suna manne da Basma duk inda zata suna biye da ita Mutuwar Khadeeja ba karamin girgiza Basma tayi ma duk da cewa wannan ba shinw karo na farko ba da somebody close to her ya rasu *2 weeks later* Basma da Adnan kwata kwata basu hadu ba coz gidansu Nene take kwana ita dasu Ashraf ko yazo bata bari su hadu Su ummi sun koma tunda akayi sadakar uku taso tayi zancen auren Adnan da Basma sai kuma taga kar ace daga rasuwa sai fara maganar aure,Basma tace zata zauna saboda su Ashraf har su saba Adnan kullum sai yazo gidan yau ma yazo Duk yazo sai ya aika a kira Basma sai taki fitowa Yau ya aiki Afra ta kira ta Aunty Basma Daddy na kira,Tace toh Yau tace bari dai taje taji kiran me yake mata kuma dama tayi missing dinshi like hell tana son ganinshi Jiki a sanyaye ta dauki hijab ta saka A falo ta same shi zaune Ya rame abun tausayi Murya a sanyaye tace in wuni? Yace ai ni fushi nake kinsan halin da kika sani kuwa Tace a gafarce ni Ya Adnan Yace amma dai kin wahalar da zuciyata da son ganinki Tace Ya hakurinmu ta kawar da zancen dan bata so Angode Allah Allah ya jikanta Ameen kafin in ce komai karba ki saurara Ya kunna mata maganar Aunty deeja tana ji sai sana'ar wato kuka😭😭😭 ta mika mashi wayar ta tashi zata bar falon Yasha gabanta suna fuskantar juna ido cikin ido (Eyes din da ba komai ciki sai kaunar junansu tsantsa)kowannesu shi kadai yasan yadda yake ji a jikinshi game da daya A hankali yasa hannu yana share mata hawaye Yace stop crying Addu'a zaki mata ba kuka ba tayi shiru ya riko kumatunta yace Now tell me can you marry me for the sake of khadeeja Tayi shiru, Yace nasan bakya sona amma saboda khadeeja A ranta tace Bana sonka da kasan irin son da nake ma da kayi mamaki son da ke ratsa jinin jikina Ya sake cewa kinyi shiru Ta saukar da kanta kasa tace Na amince zan aureka Ya Adnan Da gaske Basma Ta daga kanta sama Ya dunkule hannunshi ya daga shi sama yayi kasa dashi yace Yes! Alhamdulillah anan yayi sujjada yana godewa Allah Yace 1 minute ina zuwa Basma itama farin ciki take Motarshi yaje ya dauko Zoben nan (da lokacin da ya fara mata proposing yayi niyyar sa mata)da kuma wani bracelet a jikin bracelet din akwai heart idan ka bude heart din hoton Adnan ne a half hrt din,half hrt Basma Bracelet din ya hadu 👌🏻made with diamond Kneeling yayi gabanta ya kama hannunta ya sa mata Zoben da bracelet Yace _I really love you my basma I love you with all my heart body and soul You re my life once you are taken away am death so please stay with me forever.My love for you is deeper than the deepest ocean taller than the tallest mountain hotter than the hottest desert and denser than the densest of forest Basma_ Basma ta ma zama speechless jin kalaman Adnan Yace Basma i know you don't lo...... Tai saurin ce mai shhhh ta runtse ido tace _I love you too Ya Adnan Your love conquers my heart My love for you is Endless_ Wani irin murna da farin ciki ya kama shi da bazan iya misalta muku ba kowacce kawai tayi imaginating irin murnar da yayi 😉 Dariya ya fara yace ha....ha...ha..ya ma kasa magana sai can yace mafarki nake ko da gaske Basma please repeat what you just said Tace _I love you Ya Adnan Your love conquers my heart My love for you is Endless_ Ya rungumeta yace ohh no i can't believe wat em hearing yau kince kina sona yau dole nayi sadakar 1million nagode wa Allah kina sona Ta dago ta kalleshi da mamaki tace 1million fa kace Ya daga mata gira yes my sunshine bazan iya bayyana miki farin cikin da nake ciki ba yau let me tell you ranar da aka daura aurena dake sadakar 10million zanyi nagodewa Allah da ya bani Beautiful Angel like you Mamaki ne ya cika Basma kawai ta bishi da ido Yace kina mamaki ne ki ma daina mamaki kadan daga cikin abunda zanyi kenan idan Allah ya bani ke,So tell me yaushe kike so asa bikinmu Haba Ya Adnan daga rasuwar Aunty deeja sai maganar aure ni dai ka bari sai anyi kwana arba'in sai a fara maganar biki What wallahi ba zan iya jurewa ba wato ma sai after 40days za'a sa rana kinsan kuwa yadda na matso ki zama matata baki san yadda nake ji bane duk sanda na ganki Rufe fuskarta tayi ta bar falon da gudu Adnan ne ya gyara kwanciya akan gado kawai ya farka daga barcin da yake Yace Ohh Gosh! Yanxu ashe mafarki nake ya dafe kai yace Subhanallah *Hhhhhh Dudes ashe Adnan mafarki yake nasan har kun fara murna finally Basma tayi accepting proposal din Adnan Ooo No Sorry for you😂😂😂* *_Em just kidding na reality Basma accepts Adnan no be dream inaso ne kawai na tsokane ko 😂😂😂😆😆_* ZEE YABOUR❤ [11/12, 2:40 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~~PART II~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE ^^^45~~~~46^^^ *************************************************************** DEDICATED THIS PAGE TO AUTAR HAJIYA❤ ************************************************************************************ Basma ta fada kan gado Ta kalli zobe da bracelet din hannunta taga yadda aka yi designing zoben Tai kissing zoben sannan ta bude heart din jikin bracelet taga pic dinsu ita da Adnan bata san lokacin da tace wow its really beautiful but ina Adnan ya samu pic dina only God Knows tai kissing bracelet ta daura hannun kan kirjinta tana tuna kalamanshi son shi na ratsa dukkan sassan jikinta Su'ad ta shigo dakin tace Lafiyarki kina ta wani rungume hannu a kirji Basma ta tashi zaune ta mika mata hannunta tace Take a look Su'ad tace Woww kice kinyi accepting Ya Adnan Basma tace Yes,Su'ad ta daka tsalle tace i will be the first to break this news to our family tayi hanyar fita,Basma tace ke fa haka kike bakya jin abu kiyi shiru Su'ad ta fice Babban falon gidan ta sami Bappa,Nene,Sajeeda da Fahad zaune Tace na kawo muku albishir Muna jinki Bazan fada ba sai kowa ya bani goron Albishir,Sajeeda tace ai ke matsalarki kenan,To nama fasa fada,Fahad yace sorry kar ki biyewa Ya sajeeda fada mana Su'ad tace Basma tayi accepting proposal din Ya Adnan Fahad Yace Amma naji dadi Kowa baki yaqi rufowa murna kawai suke,Su'ad na barin falon waya ta dauka ta kira Ummi ta gaya mata tayi farin ciki sosai Around 10:00pm Basma har ta fara barci Taji phone dinta na ringing taja tsaki wa ke kirana da daddaren nan Tayi receiving Hello My sunshine(taji muryar Adnan har tsakiyar kwakwalwarta taji dadin sunan😜) Ya kake? Umm gani nan dai ne kawai Waz wrong?? Em just missing you ina son jinki kusa dani please ki tausaya mun ayi auren nan da wuri Ya Adnan kayi hakuri kamar yau ne No my sunshine i can't wait for more than 40days Ok zance ma na fasa(tana maganar da shagwaba) No! No! Kar kisa yau na kwana hospital Ta kyalkyace da dariya Au dariya ma na baki ko shikenan gudnyt nayi fushi Em sorry bana so ka kwanta da fushina a ranka Really Yeah I love youu my sunshine I love you too Bari na barki ki kwanta but ba dan na gaji da jin sweet voice dinki ba banqi mu kwana muna waya ba Don't worry you soon will get enough of my voice I will never ever ko zaki yi shekara kina magana ba tare da kin tsaya ba bazan taba gajiya da jin muryarki ba Gudnyt Cwt drmx muahhh Tai saurin kashe wayar dan taji kunyar kiss din da ya mata blowing Ta rungume pillow tana murmushi son Adnan na kara shigarta har tayi barci,Shima Adnan haka kwana da tunanin Basma tunanin Basma sonta na kara shigarshi *_A gurguje_* *40 DAYS LATER* Soyayyar Adnan da Basma kullum gaba take sai wanda ya gani Yan'uwa an hadu ansa biki nan da 2weeks Shirye-shirye kawai yan'uwa ke yi kai kace bikin saurayin da budurwa ne za'ayi ko wasu saurayi da budurwan ba za'ayi irin wannan shirye shiryen ba Adnan ya hada ma Basma lefen da sai da ya girgiza kowa Akwati dozin uku(datz 38) Kaya tsadaddu duk ba wanda ya siya a Nigeria Komai designers kuma guda dari(100) Hatta inners(Pant,Bra ,underskirt en Vest) duk designers ne daga na Victoria secret sai mac's and spencers Turaruka suma designers (Channel,Caroline herara da sauransu) Takalmi da jaka suma daga na(Nine west,calvin klein,Ducci &Garbana ) masu arha a ciki sune Vine Atamfofi daga super sai holland,Laces ba na kasa da 100k,Da akwati guda na gold en diamond Kai Adnan dai ya zuba ma Basma kaya bana wasa ba kayan da irinsu sai gidan governors da ministers Basma tayi matukar mamakin irin kayan da Adnan ya zuba mata Ta kira shi ta mai godiya Yana dauka yace Hello my sunshine Na'am ya kake Ke ya kike Ni ina lafiya To nima ina lafiya kinsan lafiyarki ita ce tawa Dama na kira ne nayi maka..... Wait ya katseta in godiya xaki mun kar ki fara you deserve more than that,gani nan ma kan hanya zanxo na dauke ki i have a suprise for you Suprise Yes suprise sai nazo Ya aje wayar Basma dariya tayi tace I love you my babylove Mintuna kadan ya iso,ya kirata yace ta fito ba sai ya shigo ba Hijabinta tasa kalar kayan ta fita Yana ganinta yai saurin fitowa daga mota yazo ya bude mata Yace Bismillah Get in Tsayawa tayi tana kallonshi Ya daga mata gira yace ya dai Nothing Ok then get in Ta shiga ta zauna ya rufe mata sannan ya koma Driver's seat yaja motar Hirarsu ta masoya suke a natse ita dai bata san ina zasu ba tunda suka shiga Governor road ta fara hango wani hadadden mansion house Gidan anyi shi da Glass da marble A ranta tace gaskiya gidan nan ya hadu daga gani naira tayi kuka wajen gina shi Adnan yace ina so ki rufe idonki kar ki bude har sai nace ki bude,Tace ok your wish is my command Ta rufe idonta Mansion house🏤🏚 da Basma ta hango anan naga Adnan yayi hon Yan'sanda sunfi biyar ke gadin gidan daya ya bude musu gate suna ta gaida Adnan Yayi parking mota ya bude ma Basma ya rike mata hannu suka shiga ciki idonta a rufe Lungu lungu naga yana bi da Basma har ya kawo wani daki ya kunna wutar dakin yace open your eyes Basma ware ido tayi tana kallon dakin Bangon dakin wallpaper ne an raba shi gida uku, Side daya anyi decorating in pink & purple An rubuta a jiki: _I love you Basma_ _You are my life_ _Ever since the day i set my eyes on you my heart stopped beating for me its beats for you saying i love with every beat_ Words din soyayya ne iri-iri a rubuce Dayan side din hotonanta ne kala-kala a jiki wasu ma bata san lokacin da aka yi snapping dinta ba Dayan side din kuma katowar heart ce a jiki a cikin heart din an rubuta _Adnan for Basma_ _Basma for Adnan_ *_MANAN_* Ma for Basma and Nan for Adnan Sai Balloons masu shape din heart♥ duk an hurasu a dakin da manya manyan Love cards Basma mamaki ne ya cika ta baki a bude Yace how does it look Tace ha..ha..ha. Extraordinary beau...beau..ti...ful Ta rungume Adnan tace I love you my babylove ban taba tunanin son da kake mun ya kai haka ba _My sunshine i love you beyond your imagination i promise to love you en always keep you happy for the rest of your life i will always be by your side Promise me you will stay with me forever_ I promise Ya Adnan Ya zagaya da ita gidan ya nuna mata ko'ina har sai da kafafunta suka yi ciwo saboda girman gidan idan nace na tsaya gaya muku irin kyan da gidan yayi sai in dau 3 hours ban gama ba.Kowacce kawai tayi imaginating haduwar gidan.Sai da suka fito taga ashe mansion din da ta hango ne.Tace babylove yaushe ka gina gidan,Yace tun lokacin da na fara sonki na fara gina gidan nan kullum mafarki na muyi rayuwa dani dake a ciki Tace Wow gaskiya ya hadu Sai da ya biya da ita ya siyo mata ice-cream different flavors,chocolates iri-iri da dai sauran kayan kwalama sannan ya kaita gida Basma har an fara mata gyaran jiki wata mata aka dauko tun daga Sudan tun ana saura sati daya take fara ma amarya gyaran jiki Duk wani maganin mata da aka san yana gyara mace ya maida ta kamar budurwa an ba Basma tasa wani tasha Gyara dai tana ta shan shi ko fita an hana ta wai kar rana ta taba ta Adnan kullum sai yazo duk yazo sai yaga Basma ta qara kyau, a wani irin yanayi yake komawa gida ya kusa ayi bikinsu ji yake kamar ya jawo kwanakin..... ZEE YABOUR❤ [11/12, 2:40 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^47~~~48^^^ ************************************************************************************* Basma ta cewa Adnan bata so ayi wani biki a daura aure kawai ayi walima Yace Shi sai anyi hadadden bikin da zai zama talk of the town coz wannan shine auren shi na farko dan wancan ba'a son ranshi aka yi ba wannan kuma He is marrying the love of his Life kuma dama shi yana son harkar big time Invitation Card din kanshi abun kallo ne a cikin wata yar'box yake Gold plated wasu har decoration suka rika yi dashi😂,Adnan ya gayyaci Abokansa da mutanen arziki na kusa da na nesa Basma itama ta gayyaci friendz dinta na school Su'ad an shige gaba ana ta shirye-shirye itace matsayin best friend din Amarya Duk wanda yaga invitation card sai yaji yana son zuwa bikin dan yaga haduwar da zai yi, tun kan invitation card abun kallo ne to ina ga Events din A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah yau ranar laraba aka fara bikin Adnan da Basma(Manan) Mutanen Yemen da Zaria duk sunzo An fara da kamu a Murtala Square kaduna aka yi Kamun ya hadu sosai an gayyato (Yan sebom-bom,Buzun kaduna ,Adam A Zango ) Anci ansha an koshi Basma da ta dawo gida ta gaji sosai ta watsa ruwa ta kwanta Adnan ya kira ta suka sha wayarsu❤ Anyi sauran events irin su Bridal shower, Barbecue,Fulani day,Arabian night Saura Walima da dinner Yau ranar asabar Aka daura auren Adnan da Basma(Manan) Maroka da mawaka sun taro a kofar gidansu Adnan yana ta zuba musu kudi sai washe 32 teeths dinshi yake😂😂 Ranar za'ayi Dinner a Hotel Seventeen, Dinner da Adnan ya dade yana tsara ta ya gayyato manyan mutane da Friends dinshi masu ji da naira *8:00pm* Ana ta shirye-shiryen tafiya Dinner Amarya Basma an shiryata tayi masifar kyau kamar ka saceta Ango Adnan shima ansha kyau Hall din an kayatashi Yayi bala'in kyau Amarya da Ango na dosu kai cikin hall din kallo ya koma kansu Sun masifar yin kyau Suna kama kuma sun dace da juna perfect match,Kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake wasu suce Amarya tafi ango kyau wasu suce Ango yafi amarya kyau Amarya da Ango sun zauna a inda aka tanadar musu An gayyato mawaka daban daban irinsu olamide,Korede Bello,Umar.M.shareef da Nura m inuwa An sha rawa omo zo kuga ruwan kudi dollars kawai kake gani Abinci sai wanda ka zaba Can na hango Shoter,Faty Ali,Mami,mariya,Zakiya duk akan table daya suna saka loma😂 Mallama Amal ana ta yagar cinyar kaza lol😂 Wajen yanka Cake Adnan ya fara cutting ya sama Basma a baki sauran da bai shige bakinta ba yasa bakinshi ya gutsura Wuri aka hau ihu da tafi(Ni kaina abun ya burgeni) Amarya da Ango aka ce su fito suyi rawa tare da olamide(Fav musician din Adnan) Suna cikin taka rawa Kafar Basma ta murde (Coz high hill ne a kafarta kuma bata saba sawa ba) Ta tafi zuu zata fadi Adnan yai saurin riketa ta fada jikinshi daukarta yayi kamar Baby Kowa sai ihu da tafi wasu na cewa Wow amazing,Basma kunya ta kamata Adnan ko a jikinshi kawai ya maze,Ya kaita ya zaunar da ita Abun ya burge kowa Dinner tayi kyau an raba soverniers na gani na fada,Kowa ya watse Basma yau duk tafi gajiya akan sauran ranakun sai da ta gasa jikinta da ruwan zafi sai barci Washegari tunda safe aka sake gyara mata jiki tasha turaruka ,Fatar ta tayi kyau laushi da santsi sai sheki take Ga gashinta da yasha gyara shima yana ta kyalli A gidan Amarya za'a yi walima idan an kai ta Basma tayi kyau sosai sosai ba kadan ba,Sanye take da atamfa (Holland)sai alkyabba aka daura mata akai An kayata filin gidan ,Kowa nata maganar haduwar gidan wasu na cewa Basma ta more Sheikh Kabiru Gombe aka gayyata yayi wa'azi sosai akan aure mai ratsa jiki Gab da magrib aka watse walima aka kai amarya dakinta tana ta kuka Nene da Ummi sun mata nasiha sosai mai shiga jiki Bayan sallar isha'i suka tafi aka bar Basma ita kadai Gabanta nata faduwa tana tunanin yadda first night dinsu zai kasance ita da Adnan saukinta ma ita ba virgin bace balle taji zafi Tana zaune kan tsadadden gadonta tana hawayen farin ciki ta auri abun kaunarta Adnan ya shigo dakin tare da yin sallama,Ta amsa sallamar murya a sanyaye Yazo gabanta ya tsuguna ya daga alkyabban ya dago kanta suna kallon juna Murya can kasa yace kuka kike my sunshine bakya farin cikin aurenmu ne Tace farin cikin ne ya sani kuka Its ok ki daina kuka tashi muyi alwala muyi sallah Ya jasu jam'in ya rike goshinta yayi addu'ar da ma'aurata ke yi idan sunyi aure Ya bude ledar da ya shigo da ita dakwala dakwalan kaji ne guda biyu sai lemon kwali guda uku Yana gutsura yana bata a baki har tace ta koshi,ya tsiyaye lemo ya bata tasha Yace yanxu ki tashi ki watsa ruwa ki rage kayan jikinki Tace to Ko na kama miki ne Tai saurin cewa A'ah Ohkay ni zanje dayan dakin na shirya Basma tayi wanka da sabulu mai kamshi Ta shafa mai (mai santsi da kamshi) Ta saka rigar barci iya gwiwa da ita da babu duk daya dan ana ganin cikin ka(a cikin kayan barcin ita ce mai dama dama) Ta feshe jikinta da turaruka masu masifar kamshi Tana kokarin packing gashinta Adnan ya shigo bata ji shigowarshi ba Kamshin turarenta ne ya daki hancin shi yana ganinta tuni ya rude Ji tayi an daga ta samaa an kaita kan gado tana kokarin magana,Yasa yatsanshi kan lips dinta yace shhhh,Ya kashe wuta dakin Kissing dinta ya fara yi yana shisshinarta kamar tsohon maye😂 Nan suka fara romancing juna Tasha sumbatu wajen Adnan har ya mafi moha Basma kam tasha kuka tana rokon Adnan amma ko kadan bai tausaya mata ba Da safe da tazo tashi kasawa tayi,Adnan ne ya dauketa ya kaita toilet yai mata wanka(duk yadda taso ta hana shi kar ya mata sai da ya mata) Da ya gama mata wanka ya dauko ta ya zaunar da ita kan dressing mirror,Yana kokarin shafa mata mai Tace no thanks i will do it myself ta fisge man a hannunshi Yazo saitin kunnenta ya rada mata You are soo sweet my sunshine Wallahi kinfi wata virgin din Thank youu soo much Allah ya miki Albarka ya barmu tare yana kokarin kissing dinta tasa hannu ta ture shi tace ni mun bata tunda baka da tausayi Yayi kneeling yace Am sorry my sunshine bazan iya jure fushinki ba Tace da shagwaba promise me baza ka sake mun irin na jiya ba I promise zan rika sassauta miki kece you are soo sweet Tace to tashi na hakura Thank you Ya fice Basma ta zauna ta tsantsara kwalliya ta saka dankareren lace cikin na lefenta dinkin ya mata kyau sosai charas-charas Kitchen ta sauka ta hada musu breakfast Stuffed french toast,plantain balls da Rice pudding Da ya gama shiryawa shima ya sauka kasa a plate daya ta zuba musu tana bashi a baki shima yana bata Da suka gama ci Yace dauko hijabinki zamu je wani guri Ta dan zaro ido waje tace ina zamu Yace ke dai kizo muje ba dadewa zamu yi ba Tace to ta dauka hijabinta tasa tana tunanin to ina za su kwana daya da aurensu Wani hadadden gida taga sun tsaya Adnan ya sauka ya bude gate suka shiga ciki A harabar gidan motoci ne guda biyu(kirar Benz da Ford) sababbi dal a leda Gani tayi yasa hannu a aljihu ya fiddo keys Ya mika mata yace My sunshine wa 'innan cars din naki ne da gidan nan tukwicin jiya da daddaren Mamaki ne da murna suka cika Basma ta rungume Adnan tace nagode babylove bansan da wane baki zan ma godiya ba Yace shhh nine da godiya my sunshine ko da zan mallaka miki duka dukiyata bazan biya ki abunda kika mun daren jiya ba Tasa hannu ta rufe fuskarta A ranta tana godewa Allah da ya bata miji kamar Adnan Buba ya bata wanda yafi Dr.Moha komai Ya jasu suka koma gida.............................................. *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~PART II~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^49~~~50^^^ ************************************************************************************ Sun dawo gida Basma na cike da farin ciki Anan falo suka zauna Basma na kwance kan cinyar Adnan suna hira Tace Babylove wai yaushe za'a dauko su Afra ne? Yace ba yanxu ba To sai yaushe,Sai mun gama shan amarcinmu Ta fara shagwaba tace ni dai gaskiya Babylove a kawo su can fa su kadai ne nasan suna missing dinmu,Kina so suzo su hana mu shan amarci ne No babylove ba zasu hana mu,Ok to naji zansa a kawo su Tace Yes my babylove tai kai mai peck a kumatu Shima ya mayar mata tare da cewa I love you my sunshine Wayarshi ta fara ringing Yayi receiving Hello Nene ina wuni Lfy lau Ango ina Amarya Gata nan lafiya lau Toh madallah dama Afra ce ke ta kuka ita a kawo ta wajen Basma Ok a hada musu kayansu asa driver ya kawosu Toh!shikenan a gaida Basma Zata ji Yayi hanging-up call din Tace Babylove ya akayi ne? Yace wai Afra ce ke kuka tana son zuwa wajenki Allah sarki my little Basma na kitchen na hada lunch,Adnan na zaune gefe kan kujera yana taya ta hira ba yadda bata yi dashi ba ya fita kitchen din yaqi wai yafi so yai ta kallonta ba zai iya zama falo ko daki shi kadai ba Da gudu Afra da Ashraf suka shigo kitchen din suka rungume Basma Munyi missing dinki Aunty Basma Ta kama kumatun su tace nayi missing dinku nima my kids Sannan suka juya wajen Adnan suna cewa we miss you Daddy,Yace I miss you too my kids kunsan me Sukace A'ah,Yace daga yanxu no more Aunty Basma Mummy zaku rika ce mata she is now your momma Suka ce ok Daddy Yanxu kin zama mummynku ko suka fada suna kallon basma,Ta daga kai sama tace Yes my kids,Yeeeey suka yi tsalle,Ta rike hannunsu tace muje in nuna muku rooms dinku Ashraf da dakinshi,haka Afra suna ta tsalle da murna ganin yadda dakunansu ya hadu *1 WEEK LATER* Basma da Adnan nata shan amarcinsu kullum suna manne da juna ,tunda suka yi aure ko bakin gate bai fita ba Yau ya shirya tsaf,ya duka Basma ta sa mai hula ta dauko turare ta fesa mai,Tace kayi kyau my babylove,Yace thank you my sunshine ai ke kika shiryani dole nayi kyau Tayi murmushi tace Allah yasa kar wata ta kwace mun kai Yace daina ma zancen nan kece kwallin kwal a zuciyata duk namijin da ya aureki ba zai iya hada ki da wata ba,Tace ni dai ka daina zugani Yace Am telling the real fact shiyasa nake kara ma Allah godiya da ya bani ke Nima ina godewa Allah da ya bani kai masoyina na gaskiya Tai mishi rakiya har mota ta bude mai ya shiga Ta rufe ya tada mota tana waving dinshi har ya fita gate.Ta dawo cikin gida Ji tayi gaba daya bata jin dadin jikinta saboda ta saba duk kwana nan suna manne da juna ita da Adnan Wani irin masifaffan son take wa Adnan sai a yanxu take ganin soyayyar da suka yi da Moha shirme ce kuma yaci amanarta yaci amanar soyayya da bai yi trusting dinta ba aka gaya mai abu ba tare da yayi bincike ba ya yanke danyen hukunci a kanta saki uku a lokaci daya Tabbas baya sona tsakani da Allah da sona yake tsakani da Allah duk abunda za'a gaya mai a kaina ba zai yanke wannan danye hukuncin ba Allah ya saka mun Afra da Ashraf nata mata surutu, su suka debe mata kewar Adnan Da azahar ya dawo ta kama mai ya watsa ruwa ya sa kayan shan iska Yace Rufe idonki i have a suprise for you Tace kai dai baka gajiya da suprising dina Yace ke dai rufe idonki ki miko hannunki tayi yadda yace ya daura mata abu a hannu sannan yace bude idonki Ta bude idonunta ta sauke su kan hannunta Yace ticket dinmu ne for our honeymoon to Paris Basma tace Wow I soo much love you Babylove You are the best You are also the best my sunshine love you more Tace su Afra fa ina zamu barsu Yace wajen su Nene,Kasan ba zasu zauna ba why not mu tafi tare dasu See honeymoon zamu fa so ba inda zamu dasu ki fara shiri gobe ne tafiyar Ta zaro ido waje tace Gobe yace Yes morning flight so anjima za muje wajensu nene daga nan mukai su Afra ,Tace ok Da daddare suka shirya suka tafi gidan Nene bayan sun gaisa dasu nene Su'ad da Basma suka shige dakin Su'ad nata ma Basma tsiya tana cewa umm ji be ta kamar ba ita bace ake cewa bazan aure shi ba bana son shi amma gashi yanxu honeymoon za'a Basma tace Wallahi ba abunda kika aje sai tsokana kuma har yanzu kinqi fito da miji musha biki Um wallahi Basma mazan ne basu da tabbas har yanzu ban samu wanda ya mun ba kuma kinsan shi aure lokaci ne,Basma tace hakane Allah ya zaba mafi alkhairi Su'ad tace Ameen ,Suna ta hira Adnan ya kirata a waya yace ta fito su tafi Da lallashi da wayo su Afra suka yarda suka zauna Jirgin safe suka bi Sun isa garin paris lafiya A wani hadadden hotel suka sauka na masu hannu da shuni Bayan sunci abinchi sun huta sun rama sallolin da ake binsu ,Suka watsa ruwa suka kwanta Duk da gajiyar da suka yi hakan bai sa Adnan ya saurara ma Basma ba Basma taga soyayya wajen Adnan wadda irinta sai dai ta gani a film ko novels ko koda(fly) baya so ya taba ta haka yake tarairayarta kamar kwai Sunje wurare daban-daban na shakatawa da more rayuwa Satinsu Biyu suka dawo gida Nigeria Su Ashraf nata murna Sun dawo da sati daya Aka kira Adnan ana nemanshi America Basma hankalinta ya tashi sosai ba zata iya jure rashin shi kusa da ita ba ko na kwana daya ko fita yayi ya take ji ballantana ace yayi tafiya Yana ta lallashinta Kiyi hakuri my sunshine ba dadewa zanyi ba just 1week zanyi na dawo,Tana hawaye tace Ni gaskiya ba zan iya jure har 1week ba shikenan sai ka tafi ka barni ni kadai Kiyi hakuri my sunshine kinji, Gangar jikina ce kawai bata tare dake amma ruhina na tare dake Da kyar ya lallasheta ta hakura .Nan suka fara wasannin su na ma'aurata suna dariya da nishadi Basma duk ta shiga damuwa kwana biyu tana tunanin tafiyar Adnan Ana saura kwana biyu ya tafi Suna zaune ita shi dasu Afra ,Yace mata yana zuwa Sama ya hau, 2minutes ya dawo Wani Envelope mai dan girma haka ya mika mata yace bude ki gani Tana budewa passport dinsu ta gani nata da nashi da na su Ashraf Ta bude wata paper da ta gani a ciki Admission ta gani da sunanta Na *Harvard University of Boston, America( Best medical university in the world)* Wani tsalle ta daka ta rungume Adnan Tace babylove ka gama mun komai a duniya nagode nagode Yace shhh bana son kina mun godiya duk abunda kika ga ina miki kinyi deserving ne saboda kema kina mun duk abunda zai faranta mun rai.Tace dama suprising dina kake son yi, Yace Yap a tunaninki zan iya tafiya ne ba tare dake ba dama na dade ina mana shirye shirye komawa can da kuma neman admission dinki ina so kiyi karatunki na Medicine a best medical university in the world ki zama professional medical Doctor Tace Wow kullum kai dai kana cikin suprising dina da abubuwa masu faranta mun rai nima In shaa Allah watarana sai nayi suprising dinka biggest suprise Afra ta katse su tace mummy murnar me kike? Tace my little zamu koma America da zama a tare Ashraf da Afra suka daka tsalle suka ce Yeeee💃🏻💃🏻💃🏻 Suka rungume Adnan sukace Thank you daddy Yace You are wellcome my kids Basma nata shirye musu kayansu Adnan yace kar ta debi kaya masu yawa idan sunje can sa siya Sunyi Bankwana da Yan'uwa su Nene sunji ba dadi za suyi kewar su tun ba Su'ad ba zata yi kewar Basma Sun isa America garin Boston Anan Adnan ya samar musu gida Gidan ba wani babba bane sosai amma ya hadu 3 bedrooms 2 parlor sai kitchen da tsakar gida da dan karamin garden Ba abunda babu a ciki na amfani da more rayuwa Basma,Adnan dasu Afra zasu fara sabuwar rayuwa a America............................ *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~PART II~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^53~~~54^^^ ************************************************************************************* Adnan ya kira yan'uwa da abokan arziki ya sanar dasu wasu ta text message Ummi tayi murna sosai An sallami Basma daga asibiti daga ita har twins suna cikin koshin lafiya Ashraf da Afra na ganin twins sai murna sun samu kanne Ana ta zuwa barka kowa yazo sai yace twins din na da kyau Mashaa Allahu Akwatuna dozi daya(guda 12)Adnan yama Basma na fitar suna kaya tsaddadu Yan'uwa duk sunzo hadda yan Zee&hussy novels grp da fans din dangin mahaifina Anyi gagarumin bikin suna Twins sunci Suna Awathif da Afaf(Mommy da Nene) amma za'a rika kiransu Seema da Seemna Anyi soverniers sosai da hoton Babies a jiki Basma nata wankan jego Adnan ya matso tayi arba'in kullum tana makale da waya suna shan waya Dan ko yazo sai dai akai mai twins Nene ta hanata ta rika zuwa wajen shi A kwana a tashi ba wuya wajen Allah ,Basma tayi arba'in anyi abubuwan sadaka irinsu Waina,Sinasir,Alkubus da sauransu an rarraba Suna ta shirin komawa America An hada Basma da wata tsohuwa wacce zata taya ta da Raino saboda rainon twins is not easy Basma ta kara kyau tayi fresh Fatar ta sai sheki take kamar ba mai jego ba ,Adnan ya matso su isa America can inda ba mai takura musu shan soyayyarsu Ranar da suka koma Adnan da Basma(Manan) Sun sha soyayya kamar zasu hadiye junansu coz sunyi missing kasancewa tare da juna sosai Basma ta cigaba da zuwa school amma ba tare da twins ba a gida take barinsu wajen Inna(tsohuwa) *AFTER 4 YEARS* Bikin graduation dinsu Basma ake ,Basma ta karbi gifts da yawa ta fito da First Class infact itace overall best ,Ta Zama Cikakkiyar Likita Dr.Aysher Basma Farin ciki wajen Adnan da Basma ba'a magana Yan'uwa ana ta kiranta ana congratulating dinta Yara na hango Su hudu Sun nufo wajensu Basma Sanye cikin English wears Sunyi kyau kamar ya'yen turawa Babban Ashraf (12yrs),Afra(9yrs) sai twins Seema da Seemna yan shekara hudu(4yrx) Kowannensu rike da gifts a hannu One by one suka rika mika ma Basma suna cewa Congrats Mummy,Tana karba tana cewa Thank You Yanzu sai komawa Nigeria dama shekara daya kenan da lokacin komawarshi yayi Basma ya tsaya jira ta gama Sun so ta tsaya nan tayi aiki tace A'ah zata koma tayi ma kasarta aiki Sun dawo gida Nigeria Seema da Seemna tun suna jarirai rabonsu da Nigeria Su Nene nata mamakin girman twins Yaran kyawawa dasu gwanin sha'awa ,Ga gashi yala yala har gadon baya(kamansu daya da Basma ba inda suka barta) kamar ka sace su ba sai jin hausa sai turanci Adnan ya gina ma Basma tantsamemen Hospital,Asibitin ya ginu ya hadu ba karya.Ya tambayi Basma wane suna za'a sa ma asibitin Tace *Manan Specialist Hospital* Yaji dadin sunan da tace An zuba kwararrun likitotoci yawancin su ba Nigerians bane Kafin a ce haka asibiti ta game garin kaduna ba kamarta kab garin Kowa asibitin Dr.Aysher Basma duk wani mai ji da naira asibitin yake zuwa Basma ta kware kan aikinta tana da tausayi wasu ma idan sunzo basu da kudi haka ake treating dinsu kyauta Asibitin Basma yanxu tayi suna ba kaduna kadai ba ta game duka Nigeria,Mutane daga garuruwa suke zuwa Asibitin Adnan is soo proud of his duk inda ya shiga nuna shi ake ana cewa ga Mijin Dr.Aysher Basma Ga Basma Yar'gayu,Twins ma na shan gayu, Gasu very intelligent sune best a class dinsu Kowa sun so yake Wani lokacin Weekends Basma na zuwa dasu Asibiti,Doctors nurses hadda patients masu zuwa suyi ta daukarsu suna sha'awarsu Ashraf ya kai js1 an kaishi boarding Great British Abuja(Basma taso ta hana Adnan kar ya kaishi Yace sai ya kaishi) Dr.Aysher Basma na zaune hadadden office dinta Tana duba wasu files,Phone dinta yayi ringing Hello mummy Na'am Seema ce ko seemna (dan ita kanta bata gane muryarsu) Seema ce Ok Seema my dear ya akayi ne Mummy kin manta kinyi promising zaki kaimu shopping yau Ohhh! Sorry my dear na manta gani nan zuwa yanzun nan ku shirya kafin nazo Ok mummy love you Love you too my dear Ta harhada files din ,ta fito tana ta sauri kawai tayi kacibus da nurses na tura wani sai aman jini yake yana cikin critical condition bai ma san inda kanshi yake ba Tana kai idonta wa zata gani.............. Readers kuyi guessing *MOHA* Gabanta ya bada daradam tace yanzu moha ne a wannan halin kawai ta tuno korar karen da ya mata hadda cewa mai gadi da mai sharar tsakar gida ya fita da ita Taji wani kololun bakin ciki yaxo ya tsaya mata Da karfi tace musu Waitt suka ja suka tsaya Tace ina wa'inda suka kawo shi? Daya daga ciki tace Wanda ya kawo shi ya tafi ciro kudin treatment dinshi a ATM Tace ina so ku gaggauta fita dashi daga asibitin nan Dukkansu sunyi mamakin jin furucinta sun santa da tausayi Daya daga ciki zatai magana Basma tace Don't say a word just do as i say Kuma ko gayawa Doctors duk wanda ya kuskura yayi treating dinshi a bakin aikinshi ta wuce fuuu Mamakin ne ya cika su basu taba ganin Basma tayi reacting this way ba ,bata fada kullum cikin far'a take idan ranta ya baci to taga basu yi treating patient da wuri ba amma yau itace ke cewa a fita da wani daga asibitinta lallai akwai wani abu a kasa Ta figi motarta sai gida da tunani kala-kala a ranta Me ya samu Moha yake aman jini Anyway datz not my business Alhakina ne ya kama shi bana son sake sa shi a idona Duk da furucin nan da take taji tausayin Moha kawai tana jin zafin wulakancin da ya mata ne Tana parking mota da gudu Seema da Seemna suka fito suka rungumeta Ta daga seema sama tai mata peck a goshi sannan ta daga Seemna ita ma ta mata peck a goshi Afra an girma tace Sannu da zuwa mummy,Basma tace See you come and a give me a hug you are still my baby ki bar ganin kin girma,Afra na dariya tazo ta rungumeta Suka shiga cikin gida Basma ta watsa ruwa ta chanxa kaya Suka fita Wanda ya kawo Moha da ya dawo Yace Lafiya baku yi treating dinshi ba Wata nurse tace mai Doctor Aysher ta hana tace duk wanda yayi treating dinshi a bakin aikinshi Yace ko me ye dalili Tace nima ban sani ba ta juyo ta tafi, ta barshi nan tsaye yana mamakin me zai sa tace kar ayi treating dinshi yasan ance mai asibitin nan nada tausayi dole nayi finding out dalilinta... Ya kama moha ya sa shi mota Basma duk yadda taso ta manta halin da taga Moha ta kasa duk ta damu Har Adnan ya lura Tana kwance kan kirjinshi Yace my sunshine me ke damunki ? Tace wata patient ce aka kawo asibiti yau tana cikin critical condition ta bani tausayi sosai Allah sarki ai in kana asibiti zakai ta ganin abubuwa daban Tace hakane,Yace Allah ya bata lafiya Ta amsa da Ameen......... *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~PART II~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^51~~~52^^^ ********************************************************************************************************** An nemar ma su Ashraf school sun fara zuwa Basma itama ta fara zuwa tana maida hankali sosai bata wasa dan ta riga ta daukarwa kanta burin zama Medical Doctor Lecturers sun yaba da kwazonta tana cikin best student duk da cewa university ta hada mutane daban daban from different part of the world(Countries) Yau weekend dukkansu suna gida Adnan yace ya kamata mu fita yawo Basma tace haka ya kamata Yace to ku tashi mu tafi Sunje wurare shakatawa daban daban Suna ta kashe selfie kai ka rantse da Allah ba daga 9ja suke ba Wasu turawan nata cewa Adnan da Basma(Manan) sun burgesu Adnan ya dawo daga office Basma ta tarbeshi ta karbi briefcase dinshi, Yace Am so tired kafafuna duk sunyi ciwo Tace Zauna in maka tausa Yace no bazan saki wahala ba kema kin dawo school kin gaji ni ya kamata na miki,Ba wani wahala ni dai kawai ka zauna in maka Toh naji zan yarda but on one condition idan kika mun nima zan miki Tace na yarda ya zauna tana ta mai tausa(massaging) ,in ya motsa ya kai mata peck itama ta mayar masa haka suka yi tayi Yace its ok is my turn Basma ta mike kafafu ya fara mata tausa Haka rayuwa ta cigaba musu cikin jin dadi da kwanciyar hankali *AFTER 5 MONTHS* Basma ta shirya su Afra sun tafi school ,Adnan ya tafi office ita kadai ce a gida yau bata da lectures Taji bata jin dadin jikinta kan ace haka zazzabi ya rufe ta,Ta qudundune cikin bargo a daki Adnan da ya shigo gida yaga Basma bata zo ta tarbeshi ba kamar yadda ta saba Yace Lafiya kuwa kuma banji motsinta a kitchen ba,Daki ya nufa Ya yadda briefcase din hannunshi yayi wajenta,Ya yaye bargon Yace my sunshine me ya sameki? Ya taba jikinta zafi rau Yace tashi mu tafi asibiti Tana yunkorin tashi sai amai ta kwaro mai a jiki bai motsa ba ta cigaba da kwaro mai aman a jiki har sai da ta gama sannan ya tashi(Wow soyayya dadi waye zai yadda a rika sheka mai amai a jiki Tab) Ya wanke jikinshi ya chanza kaya itama ya chanza mata ya gyara wajen da aman ya taba Ya dauketa kamar Baby yasa mota sai asibiti Bayan Dr yayi yan aune aune shi Yayi Congratulating dinsu cewa Basma nada ciki wata hudu Murna wajen Manan (datz Adnan en Basma) ba'a magana kai kace Adnan bai taba haihuwa ba saboda murnar da yake Har tukwicin kudi yaba Doctor'n Duk wani aiki mai wahala Adnan ya hana Basma yi har girki yaso hanata taqi yarda,Gyaran gida ya samu mai'aiki tana zuwa tayi ta tafi Basma da tace Wasshhh zai zabura Yace Lafiya Bata fasa zuwa school ba zuwa school din ma Adnan yaso ya hanata wai stress yayi yawa ta bari sai ta haihu ta cigaba, da kyar ta shawo kanshi ya yarda Ta cewa Adnan a nigeria take son haihuwa yace ta bari sai cikin ya shiga wata takwas sai su tafi 9ja Kullum cikin siyan kayan Baby suke unisex(wanda maxa zasuyi iya sawa mata ma zasu iya sawa) Coz Basma taqi bari ai mata scanning tace bata yarda ace ga abunda zaka haifa ba Allah kadai yasan gaibu sau da yawa za'a ce ga abunda zaka haifa kuma azo bashi ka haifa ba,Ita duk abunda ta haifa mace ko namiji Alhamdulillah! Zata godewa Allah Cikin Basma ya shiga wata na takwas ana sauran kwana hudu suzo Nigeria Suna kwance ita da Adnan da daddare Ta tashi tana Wayyo cikina zan mutu A firgice Adnan ya tashi yana lafiya Me ya sameki bari in dauki mukullin mota mu tafi asibiti Yana kunna fitilar dakin Basma ta kyalkyace da dariya tace April fool ka manta Yau first April.Tsaki yaja yace kin ganki ko wallahi kin tsoratani da yawa amma zan rama Basma nata kyalkyata dariya har da rike ciki (katon cikinta da yayi tsini)tana imitating(kwaikwayon) yadda yayi,Shi kuwa kallonta kawai yake dariyar na burgeshi har ta gaji da dariyar ta daina Suka cigaba da barci(dama Alarm tasa dan kawai ta tashi tai mai April fool) Washegari Adnan ya dawo office Basma ta tarbeshi fuskar nan tashi ba annuri,Hankalinta ya tashi bata saba ganinshi a irin yanayin nan ba Tace Babylove me ya faru ne? Ba lafiya ba my sunshine yanxu kan hanyata ta dawowa gida na bige wani yaro yanxu haka yaron yana asibiti unconcious bani da tabbas ko zai rayu ko ba zai rayu ba Basma daga tsaye bata san lokaci da takai zaune ba tace Allahumma ajirni fi musabati wa aklifli khairan minha.......sai hawaye Adnan ya fashe da dariya yayi pointing dinta da finger yace April fool nima na rama shikenan anyi trade by barter Pillows din kujerun falon ta dauka tana jefarshi dasu ,Shikuma yana sa hannu yana tarewa yana dariya Bayan kwana hudu Sun iso Nigeria Su'ad da Fahad suka zo daukarsu airport ,Su'ad nata tsokanar Basma Tace Su Basma an tsofa wannan katon ciki haka daga gani yaron xai yi girma kila ba mai iya daukarshi ,Basma tace Allah ya kaimu ranar da zan ganki da ciki kin bani dani Suka yi dariya Nene murna sosai take ganin Basma da ciki zata samu jika daga Basma Anan gidan tace Basma zata zauna har sai ta haihu,Adnan bai so haka ba sai yaji dama basu dawo daga America ba,Nene nata kula da Basma Adnan kullum na gidan Cikin Basma ya shiga wata tara,Kowa jiran haihuwarta kawai yake Ranar jumu'a da la'asar Nakuda ta kama Basma mai tsanani aka dauketa sai asibiti Adnan hankalinshi duk ya tashi Addu'a yake tayi Allah ya sawwake ta lafiya Nurse ta fito wacce ta karbi haihuwar Basma(dan Adnan yace ba zai bari wani katon banza ya kallan mai mata ba) Dukkansu suka yi kanta suna tambaya ta sauka? Tace Eh ta sauka lafiya ta samu twins(yan biyu) mata Adnan ya daga hannu sama yana cewa Alhamdulillah Nurse tace amma tana bukatar jini dan tayi wasting jini da yawa Adnan da sauri yace muje a debi nawa,blood group dinku daya Erhh,Ok muje yabi bayanta An qarawa Basma jinin Adnan _Jininshi na yawo cikin jinin jikinta Soyayya ta karu kenan dama kuma jininshi ce Yar'uwarshi ce_ Adnan ne rungume da twins(farare sol dasu kyawawa) yana musu huduba da ya gama nene ta karbesu.Ya rike hannu basma yace _My sunshine Allah ya miki Albarka kin gama mu komai da kika haifa mun kyawawan twins Nagode_ Tace Allah zaka godewa shi ya baka Yace nagodewa Allah kuma nagode miki Allah ya miki Albarka Ya barmu tare Tace Ameen,Yace shikenan kin haifi momy da nene ,Basma tayi murmushi tace aikuwa dan dasu ma suke kama Ki daina hada twins dina da tsofaffi sun fisu kyau Nene tace ka ji shi mara kunya ko kaqi ko kaso damu suke kama Aka yi dariya......... *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~~PART II~~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^55~~~56^^^ ************************************************************************************ Washegari Basma tayi shirinta tsaf zata asibiti idan ka kalleta dole ta burgeka daga yanayin shigarta,tafiyarta infact everything da ka ganta kaga yar boko gogaggiya mai ji da naira Tunda bakin gate take amsa gaisuwa har ta kawo office dinta Wuri ta samu ta zauna ta kasa yin komai tunanin halin da taga moha jiya kawai Wata nurse ta shigo tace Madam kinyi bako yana son ganinki,Kice masa ya shigo Sallamar da aka yi ya sata dagowa Readers ku sake guessing wa zata gani....................... *YA SAFWAN* Baki a bude tace Ya safwan Yace Lil-sys dama kece mai asibitin nan Allah mai iko Sai kukan farin ciki Tace Ya safwan ina ka shiga duk shekarun nan Yace hmm..lil-sys itx a long story zauna tukun Ta zauna shima ya zauna Ya fara: _Bayan na bar gidan Abokina Mukhtar a daren nan Na hadu da wasu miyagun mutane wa'inda nasan Hamma Ahijo ya turo su suka tare ni,Suka kama ni suka daddaure suka maida ni bayan mota Dayan yaja motar Muna ta tafiya a wani daji naga sun yadda ni daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba ashe haukacewa nayi na zama mahaukaci ina bi bola bola a wani kauye a zaria Anan nai ta rayuwa watarans tsautsayi na fito bakin titi inda matafiya ke wucewa ina ta hauka Mota ta kadeni ashe mai motar Moha ne nan ya daukeni ya kaini asibiti bayan na farfado ya gane na haukace Ya kaini wajen wani malami malamin yace asiri aka mun sati biyu ana mun addu'a da magani na warke Nake tambayar Moha ina kike Yake gaya mun duk abunda ya faru yace kuma a ranar da kuka rabu ya bar nigeria shekararshi biyu can sannan ya dawo nan nayi bakin ciki sosai nasha kuka ba dan taimakon da ya mun da hukuma zata rabani dashi a lokacin Ya daukeni muka koma Abuja Ya sani harkar business muna zaune gida daya kullum cikin cigiyarki da neman miki muke Moha na nadamar abunda ya miki ga sonki da ya addabi zuciyarshi har ta kai ya kamu da ciwon zuciya shine akace mu kawo asibitin nan da na dawo naga ba'ayi treating dinshi ba nake tambaya aka ce kince kar ayi shine nazo naji dalili Ashe lil-sys dita ce Dr.Aysher burinki ya cika kin zama medical Doctor_ Tayi Murmushi tace Alhamdulillah an godewa Allah Safwan yace hakane Ta bashi labarin bayan barinta gidan moha Safwan Yace Ikon Allah yanzu ashe gidan yan'uwanmu kika je ba tare da kin sani ba *Wani al'amari*(Sabon Littafina mai zuwa nan gaba) sai Allah i can't wait to see my twins Tace tashi muje gida Suna isa gida kamar kullum su Seema suka fito tarbon mum dinsu Safwan yaji yaran sun shiga ranshi Sun burgeshi Basma tai musu nuni da Safwan tace Uncle dinku ne Suka dan duqa suka ce Uncle ina wuni? Yace lafiya lau Ya daukesu Suka shiga cikin gida Adnan na zaune a falo Yar'kallo kallo suka tsaya yi shi da Safwan,Safwan yaga mai kama dashi haka shima Adnan yaga mai kama dashi Basma ta katsesu tace Ya Safwan ne Yace Really ,Ya bashi hannu suka gaisa Basma ta gaya ma Adnan duk yadda aka yi suka hadu da Safwan Bayan sunci abinchi sun huta suka shirya gaba daya suka tafi gidan Nene,Yana ganin Nene yaga sak mummynsu Yana ganin Su'ad kuma gabanshi ya fadi itama gabanta ya fadi(Ni Zee nace Tooo🙄 kuma love @first sight din ne) Nene ke tambayarshi Ina Mohan? Yace yana asibitin Giwa with his familt dazu suka zo daga Abuja,Nene tace aje a dauko shi a maida shi asibitin Basma Basma tace Ni gaskiya ba za'a kaishi asibitina ba Nene tace Haba Basma ki duba taimakon da yayi ma Safwan ki taimaka mishi Tace toh yaci albarkacin taimakon da Yama Ya safwan Safwan da Adnan suka ce zasu je su maida shi *Manan* Basma tace please kuzo mun da Nabila da Nusaiba,Safwan yace anqi Tace ka fara tsokanar taka ko,Suka yi dariya Safwan ya gaya musu komai,Su nusaiba were so excited suna cewa akaisu wajen Basma,Moha na kwance na fadin ina Basma? Please ku kirata ,Adnan wani kishi ya turnike shi bai san lokacin da yace tazo tai maka me??? Yace ina son ganinta,Adnan ficewa yayi daga dakin dan idan ya cigaba da tsayuwa yana jin kalaman moha zai iya sharukeshi duk da kuwa ciwon da yake fama dashi An maida shi asibitin Basma,Adnan da Safwan da zasu koma gida nusaiba da nabila suka bisu sun girma an zama yan'mata Sunyi farin cikin ganin juna Suna ta yaba kyan Twins Safwan ya ma Basma maganar ta yafewa Moha Tace yafe mai saboda taimakon da yama safwan Yace taje asibiti ta ganshi,Tace ba zata ba sai da izinin Adnan.Safwan ya roki Adnan ya bar Basma taje,Adnan ya amince ba don ran shi yaso ba(kishi) Moha na ganin Basma Ya fara cewa ki yafe mun Basma na yanke danye hukunci akan ki ba tare da nayi bincike ba,Basma tace ba komai na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya Yace Please Basma ki dawo gareni mu cigaba da soyayyarmu kamar da, Tayi murmushin takaicin tace lallai Moha a tunaninka zan bar Adnan na dawo gare ka never ever ,Basma ki tuna soyayyar da kike mun Basma tace _Ada kenan na so ka Moha son da ban taba tunanin zan ma wani da namiji shi ba but not anymore Tuni na dade da mantawa da kai a rayuwata me zaka yi da mazinaciya ,fasikai dan haka zai fi kyau idan kowa ya tsaya a matsayinshi_ Ta fice Kuka yake yana kiran Basma kar ki tafi ki barni Ya fisge drip din da ake mai karin ruwa ya bita a guje, ko da ya isa har ta ba motarta wuta. Ammi da Babanshi suka daga shi suka mayar dashi daki,Yana ta kuka yana kiran Basma ina sonki please ki dawo gareni, Ammi tace ka hakura da Basma ka fidda ta a ranka matar wani ce ,Kuka kawai yake kamar ranshi zai fita Basma ta koma gida ta cigaba da harkokinta da murnar gano Ya safwan Moha yaga ba sarki sai Allah ya hakura da Basma ta mai fintinkau yana ta dana sanin abunda ya aikata,Yanzu Basma tai mai nisa tama taka sahun dashi bai taka ba sannan mijinta Adnan Buba yasha gabanshi a komai da yaga Twins a ranshi yace da yanzu ni zata haifawa kyawawan twins din nan Sun koma Abuja,Safwan yayi promising Moha zai rika kawo mai ziyara Adnan yasa Safwan harkar business din da yake na siyar da mototoci Ya bashi gida ,Safwan yayi murna sosai zai yi godiya Adnan ya hana shi yace you are my brother ai Safwan tunda yaga Su'ad yaji yana sonta ba bata lokaci ya gaya mata ta amince dan itama tana son shi Tasha tsokana wajen Basma Manya sun sa baki ansa bikinsu nan da wata uku Basma da Adnan na zaune da twins suna ta wasa Adnan yace my sunshine ya kamata ace Su Seemna na da kani,Tace to laifin wa? Yace laifinki Laifinka dai Au haka kika ce,Basma harda cewa Eh Ji tayi kawai ya dagata sama tana ta wuntsila kafa ya ajiye ta yaqi Yace bakin ce laifina bane yanzu zaki ga aiki da cikawa Tace Wallahu na tuba bance ba, tasan halin Adnan ko lafiya lau ma ba tausaya mata yake ba ballatana yanzu da ita ta tsokano shi,Duk birgimar da wuntsile wuntsilen da take bai sa ya kyaleta ba haka ta hakura ta sallama masa Adnan ya fito haka yaga Basma har yanzu kwance Yace ki tashi kiyi wanka my sunshine Basma ta turo da wasu yan matan hawayenta da suka makale a cikinta idonta tace ni ka kyaleni kar ka sake yi mun magana Yazo ya riko hannunta yace haba!my sunshine taso muje nai miki wankan,Ta fisge hannunta tace ni ka kyaleni ta tabar dakin Ya girgiza kai yace my sunshine huka sai da lallashi Ya shirya cikin kayan shan iska ya same ta dayan dakin ta fito wanka kenan ,Ya jawota ya hada jikinshi da nata har suna hada numfashi Ya kalli cikin kwayar idonta (dan yasan data kalli cikin idonshi duk wani fushi da take dashi zai gushe) Tana kallon cikin idonshi kawai ta tsinci kanta da mishi murmushi ya kama lips dinta suna kissing juna sun kai 1min suna yi Shi ya shafa mata mai yasa mata kaya Nan suka zauna daki suna shan love ❤dinsu............... *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~~~PART II~~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^57~~~58^^^ SECOND TO THE LAST PAGE ********************************************************************************************************** Anyi Bikin Safwan da Su'ad a lokacin Basma nata laulayin ciki An kai Amarya Su'ad gidan mijinta Safwan Asibitin Basma kara habbaka kawai yake itama sunanta ya kai ko'ina *Dr.Aysher Basma* Tana zaune office dinta Wani doctor ya shigo rike da newspaper a hannu yana murna yace Doctor duba ki gani,Tace menene lafiya kake ta murna? Yace karbi dai ki gani Tans dubawa *READERS GUESS WHAT* Hotonta da Sunanta ta gani an bata *Minister of Health* saboda yabawa da kokarinta,kwazonta da jajircewa wajen ganin samun lafiyar al'umma(Minister da kanshi yayi resigning Yace a ba Basma tafi cancanta) She can't believe it Hannu ta daga sama tana ma Allah godiyar daukakar da ta samu a lokaci daya ko a mafarki bata taba tunanin zama commissioner ba ballanta Minister Kan ace haka office dinta ya cika da Doctors,Nurses,Cleaners da dai sauran ma'aikata suna ta congratulating dinta Tayi sallama dasu ta koma gida Nene,Bappa,Safwan,Su'ad,Fahad da Adnan duk suna gidan Tana isa suka fara congratulating dinta ,Suna jubilating Ranar Basma tasha kira da messages daga mutane daban daban suna mata fatan alkhairi Yan'asibiti sun hada mata Party na taya ta Murna,Anci an sha an koshi Su Basma sunyi packing an koma Abuja Gidansu hadadden a maitama wanda yaci uban na kaduna Basma anyi kudi,Shima Adnan ba daga baya ba ta ko'ina kudi shigo mai suke a rana sai yaji alert din miliyan hamsin Duniya tasu Suna cin duniyarsu da tsinke Basma ta gina wani asibitin a Abuja Kullum tana zirga-zirga but duk da haka tana ba mijinta da ya'yenta cikakkiyar kulawa ga kuma cikinta ya tsufa Basma tayi popular sosai a fadin Nigeria ba dama ta fita sai an samu wa'inda zasu tare ta suna son Numbernta An bata police wa'inda zasu rika take bata baya tace bata so ,Tafi son simple life dinta,ko driving da kanta take yi bata bari driver yaja ta Tana cikin motarta ita kadai zata koma gida,An tsayae dasu kafin a basu hannu taji ana buga mata glass ana bara,Tana waigowa idonta suka sauka kan Adda bongel rike da kwanon bara a hannunta, Tai saurin saukar da glass tace Adda bongel,Adda bongel tace Basma kece Basma tace shigo mota Adda an kusa bamu hannu Adda bongel ta bude bayan mota ta shiga Adda bongel garin yaya haka ta faru? Basma ke tambayarta Adda ta fashe da kuka tace mun ci amanarki Basma mun zalunceki ga sakayya nan muna gani a gaskiya cin hakkin maraya na karamin abu bane Basma tace yanzu dai duk ba wannan ba garin yaya haka ta faru Adda bongel tana sharar kwalla tace Duk matsalar da ta rika faruwa tsakaninki da Moha mune sila nan ta kwashe komai ta gayawa Basma Bayan barinki gidan moha muka ji labarin Moha ya bar kasar gaba daya munyi bakin ciki ba kadan ba haka muka cigaba da rayuwa ,Fadeela na fama da ciwon son Moha kullum bata da aiki sai kuka,Wani Alhaji ya fito yana sonta tace bata son shi ita sai Moha da kyar na shawo kanta ta amince da aurenshi saboda naga yana da kudi.Bayan aurensu muka shiga bin bokaye da malamai dan ganin ta mallake mijin dan yana da mata,Haka muka dinga cimma burinmu kwatsam ranar Allah ya tona asirinmu Alhaji yama Fadeela saki uku anan take taci kuka tana cewa duk ni naja mata da babansu yaji abunda muka aikata nima kuwa ya mun saki daya ya koreni gidanshi ba irin rokon da ban mai ba yaki jin tausayina(Kama tudini tudan duk abunda kai ma wani sai an maka) Ba inda zani Hamma Ahijo ya haukace yanxu haka yana gidan mahaukata(Reshe ya juye da mujiya asirin da yama Adnan) Adda hajarah itama yanzu ba jin dadin gidan mijinta take ba tana zaman hakuri ne kawai sai a lokacin na tuna da Yusuf(daddyn basma) nayi takaicin da dana sanin irin yadda muka rikamusguna mai har Allah ya dau ranshi da yana raye da gidanshi zanje,A wani kongo(Uncompleted building) nake kwana tare da wasu baroroji da safe in fita bara dan abunda na sami dashi nake ciyar da kaina Basma ki yafe mun ko in na mutu zan samu rahamar ubangiji Na yafe miki Adda bongel Allah ya yafe mana baki daya Ameen Yanzu In shaa Allahu komai yazo karshe zamu je gidana dake,Kin sake wani auren ne? Nan ta bata labarin bayan barinta gidan Moha abunda ya faru,Adda bongel tace Ikon Allah duk yadda muka so muga bayanki Allah bai nufa na gashi Allah ya daukaka,mu kuma masu son ganin bayanki mun wulakanta kai hassada,bakin ciki da zalunci ba abu masu kyau bane muna DANGIN MAHAIFINKI maimakon mu tausaya miki muji kanki a lokacin da kika rasa iyayenki amma sai muka musguna miki Basma tace ki daina maganganun nan Adda komai ya riga ya wuce................................. *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👦👨‍👩‍👧‍👧 ~~~~~PART II~~~~~~ NA ZEE YABOUR PAGE^^^59~~~60^^^ **************************************** *DEDICATED THIS PAGE TO MY YASMEEN MUSTAPHA BUBA(MUCH LOVE💕)* **************************************** *THE END* *FINAL* Adda bongel baki ta saki tana kallon haduwar gidan Basma Basma tayi introducing dinta ga Adnan Ina safwan take tambayar Basma,Bari idan kin huta kinci abinci kin huta sai muje gidanshi Shima ya dawo Abuja da zama dan shima yanzu ya Zama DON(Hamshakin mai kudi) Sunje gidan Safwan dake Gwarinpa Adda bongel ta roke shi gafara ya yafe mata. Basma tace ya kamata suje su ga su Fadila Basma,Adnan,Su'ad,Safwan da Adda bongel suka hadu suka je Fadeela tayi farin ciki ganin Basma dan ta samu ta roki gafararta,An kira Adda hajara taxo anyi sulhu an yafi juna.Su Basma sun roki Babansu Fadeela ya maida Adda bongel ,Ya hakura yace ya maidata Nan suka barta suka koma Basma ta aika musu da kayan abinchi da yawa da kudi,Suna ta godiya tare da na sanin abunda suka mata ita da iyayenta gashi tana saka musu da alkhairi Fadeela har yanzu tana son Moha wani irin masifaffan son take mai Ta roki Basma Dan Allah tasa Moha ya aure ta,Basma tace shikenan zata mai magana Ta samu Moha akan maganar Fadila Moha nazo neman wata alfarma a wajenka Allah yasa zan samu,Moha yace ba abunda zaki roka a wajena naqi yi miki shi Basma sai dai in yafi karfina dan haka fadi ina jinki Tace Dan Allah idan har kana sona tsakani da Allah to please ka auri Fadeela ,Ya mike tsaye whatt bazan iya ba ke kadai nake so babu wacce zata iya maye gurbinki a zuciyata ,Tace Moha kar kace haka you have open your eyes and face the reality na riga nayi wani auren yanxu ka cireni a rayuwarka ka fara sabuwar rayuwa Fadeela na sonka ta canza halinta ka amince da aurenta please do this for my sake Yace naji Basma zan aureta ba abunda bazan iya miki ba Nagode Moha Allah ya baku zaman lafiya Ameen Ba bata lokaci aka sa bikin Fadeela da Moha Adnan ya dawo daga office Ya watsa ruwa,Yaga sababbin kaya dal (Suit)masu bala'in tsada agogo sabo dal(Rolex) wa'inda yasan bashi ya siya ba a kan gado Yace my sunshine wa'innan kayan fa Tace Su nake so kasa,Ba musu yace to,Ta kama mishi ya shirya Itama ta sake wata shigar cikin wani dankareren lace tayi kyau sosai,Sannan tace mai fita zasu yi,Yace ina zamu tace ina so mu kaiwa su Ya safwan ziyara ne ,Yace amma shine zaki sa nasa kayan nan kema kisa na jikinki Yes hakanan ra'ayi Yace ok noo pee Ita tace zata ja motar,Tace ya rufe idonshi kar ya bude har sai tace ya bude,Yace ban gane ba ke da kika ce zamu gidansu Safwan to me ye na rufe Ohh no babylove me yasa kake hakane ni dai kawai ka rufe eyes dinka Ok my sunshine ya rufe idonshi A Sheraton hotel tayi parking,Tana rike da hannun Adnan har suka shiga cikin sannan tace ya bude Hall ne an kyatashi ya tsaru,Ga mutane nan zazzaune hadda friends dinshi Birthday party ta hada mishi Grand one He was sooo suprised,Tace dama nace ma watarana sai nayi suprising dinka nima with the biggest suprise to gashi nayi Basma tayi long speech akan Adnan irin son da take mishi kuma ta yabe shi sosai Kowa a gurin was impress by her speech Adnan speechless ya zama,Anci an koshi Adnan yayi receiving gifts (expensive abubuwa)daga mutane daban daban kowa ya watse Adnan yaji ya kara son Basma sonta ya ninka nada sau biyu a zuciyarshi Basma ta haifi santalelen Yaro(Bouncing Baby boy)mai kama da Adnan Buba sak kamar yayi kakinshi Zo kuga murna wajen Adnan baki yaqi rufowa Anyi suna wanda ya tattaka nasu seema kunsan yanzu Basma minister ce,Ansa ma Yaro suna Yusuf(Daddyn Basma) za'a rika kiranshi da Aseem Anyi bikin Moha da Fadeela Yanzu dukkansu kansu a hade *Sun zama One Big family* *TAMMAT BI HAMDULLAHI ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN NAWA DANGIN MAHAIFINA* *GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA YA BANI IKON KAMMALA SHI LAFIYA ALLAH YASA ABUNDA NA RUBUTA YA AMFANEMU GABA DAYA AMEEN* SAI KUN JINI A LITTAFINA NA GABA .... *ASALINA* Dafatan zaku biyoni dan jin me ye Asalin nata Gaisuwa mai taren yawa gareku *Excellent Writers* *Online Hausa writers* *Clever's writers* *Best Writers Group* *Zee &hussy nvls grp* *Good en muslimah grp* Dama duk sauran grps din da ba ambata ba Jinjina gareku Online writers Mss Zuhra Aunty Jamila Muhd Leemcy Autar hajiya Humairah B Melody Zarah Bukar Ilham Muhd Husna (Hussy) En oll online writers Allah ya bar kauna ya kara hada kanmu online writers Makiyanmu da Mahassada kuma Allah ya kare mu dasu *Kawayena kuma masoyan wannan littafin nawa ina mika gaisuwa kuma ba abunda zance muku sai nagode Allah ya bar kauna* _Zakiya Musa Bala(Kinfi kowa son novel din nan nawa wlh naji dadi sosai sosai yadda kika nuna kaunarki ga littafin nan Allah ya bar kauna😘_ Mami Memuh Dandutse Shoter Amina m lawal(Besty) Khady maska Amal Ilham maiwada Naeema I bala Aysher Alkali Hafsat Salisu Asmy sa'ad Mariya yahya Yasmeen Buba Aysher Madaki Husayna M Faty Ali Meenerh Magaji Dama sauran da ambata ba duka kuna raina *_LOVE ALL MY FANS_* 08134618338 *ZEE YABOUR*❤ [11/17, 2:42 PM] ‪+234 813 461 8338‬: ✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔✔ *LESSONS OF THE NOVEL* *DARUSSAN LITTAFIN* ✅✅✅✅✅✅✅✅✅ 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧‍👦DANGIN MAHAIFINA👨‍👩‍👧‍👧👨‍👩‍👧‍👦 1⃣*_Basma na zaune da iyayenta cikin jin dadi,So ,Kula da kauna bata taba tunanin zata rasa su ba dan haka mu sani cewa ba lallai ne mu rayu da iyayenmu ba, kuma ba lallai mu dawwama a cikin rayuwar da muke ba ta dadi ce ko ta wahala Mu kyautawa iyayenmu dan zamu iya rasa su a kowane lokaci_ 2⃣ _Bai kamata matan aure muna hulda da mazan da ba muharramanmu ba ko zamu yi hulda dasu to da izinin mijinmu, boyewa miji wani abu da ya shafeki da kinsan hakkinshi ne ya sani babban kuskure ne dan zai iya jawo miki matsala a aurenki duk ranar da ya gane ,kamar yadda Basma tayi ta boyewa Moha tsakaninta da Usman wanda hakan ya zame mata babbar matsalar a aurenta da Moha_ 3⃣ _Idan mun ji abu kafin mu yanke hukunci mu fara yin bincike if not you will end-up regretting(yin dana sani) haka ya faru Moha da yayi bincike kafin ya yanke danyen hukunci akan Basma gashinan yanzu yana dana sani(Duk da cewa an hada da asiri )but investigation is good_ 4⃣ _Komai da muka gani ya same mu a rayuwa na sharri kada mu taba jin haushi or feel frustrated wani lokaci shine mafi alkhairi a gare mu faruwar wani abun qin wani lokacin sai ya zama sillar farin cikinmu, kamar yadda Basma sanadiyyar barinta gidan Moha ta hadu da yan'uwanta da bata taba sanin su ba, wanda da ace tana gidan Moha ba zata haduwa dasu ba ko ta hadu dasu ba zata san yan'uwanta bane_ 5⃣ _Mu sani Boka/Malaman Tsibbu makaryata ne suna kawai batar da mune kuma zuwa wajen wanin Allah neman taimako babban zunubi ne kuma mutum yayi shirka wanda yaje bai gaskatata abunda yace ba ba za'a karbi sallarsa ta kwana arba'in to ina ga wanda ya gaskatata mu sani Wallahi boka/malamin tsibbu makaryatan banza ne zasu yi taci miki kudi ne a banza ,kamar yadda Khadeeja ta yarda da zancen Boka cewa Adnan ba zai taba kallon wata ya mace ta burgeshi ba ko ya sota,sai gashi a haduwar farko ya kamo da son Basma_ 6⃣ _Rikon Amana da sanin halaccin da mutum yai maka abu ne mai kyau da matukar muhimmanci da ganin cigaban rayuwa, Basma ta rike amanar khadeeja tasan halaccin da khadeeja ta mata shiyasa a lokacin da Adnan yace Yana sonta taki amincewa dashi duk da kuwa irin son da take mishi ta danne zuciyarta sai gashi Allah ya bata shi cikin sauqi_ 7⃣ _Kada mu rika son kai(selfishness) mu tauyewa wani hakkinshi saboda namu farin cikin Ga Nene bata yi son kai ba ta taimaki Basma gashi sakamakon taimakonta da tayi ta gane Asalinta wanda da ta biyewa son zuciyarta taki taimakon Basma ba zata gane iyayenta da yan'uwants ba_ 8⃣ _Mugunta fitsarin fako Ance in zaka gina ramin mugunta gina shi dan karami *Dangin mahaifin Basma* Sun fara ganin sakamonsu tun nan duniya Hamma Ahijo ya haukace(Reshe ya juye da mujiya) kamar yadda yayi sanadiyyar haukacewar Safwan shima gashinan ,Adda bongel da Fadeela duk an sake su kamar yadda suka sa aka saki Basma duk abunda kama wani sai an maka_ Zumunci babban abu ne kuma umurni ne na Allah dan haka wajibi ne a tsaida shi ko kuma ince a sadar dashi Allah yace duk wanda ya yanke zumunci to shima zai yanke sa daga rahamarsa Cin amanar maraya da cin dukiyarshi tare da musguna mishi babban zunubi ne kana cima kanka wuta Allah ya bamu ikon sadar da zumunci da kula da hakkin maraya Akwai wasu darussan da dama a cikin littafi nasan idan kun karanta zaku gansu,kuskuren da nayi a ciki kuyi min afuwa duk dan'adam ajizi ne Allah ya yafe mana baki daya *Ameen* *ALLAH YASA WANNAN LITTAFIN YA AMFANEMU GABA DAYA YA KUMA ZAMA FADAKARWA GA YAN'UWA MUSULMI* AMEEN adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *