Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, May 23, 2017

JALALUDEEN complete

adsense here

🐾Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD✍🏻* Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai. Yanda zan fara rubutun nan lafiya, ina rokon Allah dayasa in gamashi lafiya, sannan abinda ke ciki na kuskuren Allah ya yafe mana, wanda muka fad'a daidai kuma Allah ubangiji yasa masu karatu su amfana dashi(Ameen). Ina godiya ga masoyana akan kullawar da kuke nunamin. Hope zaku biyoni danjin wannan labarin............luv u all😘 Episode 1⃣ Wani irin ihu ta sake mai tsananin kara, duk mutanen dake cikin gidan sai da hankalinsu ya tashi, mazan dake zaune a dinning suna breakfast suka kalli juna sai kuma suka mik'e da gudu sukai sama, masu aikin gidan suma duk suka hau gudu sai rige rigen hawa beni akeyi, mutum d'ayace bata ko d'aga kafar taba bare insa ran zatasa gudu kamar kowa, tsaki ma naga taja ta wuce d'akinta. Sukam duk sun isa kofar d'akin da ake ihun suka shiga knocking jin kofar a kulle, babban cikinsu wanda ina tunanin ma mahaifinsune ya matso jikin kofar yace "my swthrt open the door please. " Daga cikin d'akin cikin wata murya mai sanyi akace " Dad kaga fuskata kuwa? Banasan ganin kowa." Kallan juna sukai shida mazan dake gun guda 2 sukai murmushi, wanda takira da dad d'in ya kalli wasu turawa dake sanye dakayan aiki kana ganinsu kasan masu aikine garin irin kayansu, ya musu alama da kai yace "Spare key." Cikin sauri sukace "ok Sir." Suka juya. Basu dad'e ba sai gasu sun dawo, dasauri suka mik'a makullin. D'an saurayin cikinsu ne wanda da alama shine karami ya amsa tare da bud'ewa, suka d'uru cikin d'akin dukansu, azaune suka ganta a kasa ta rufe fuskarta ta hannunta biyu. Dad yai murmushi ya karasa kusa da ita yace " My Swthrt meke ya faruwa? Bazaki bud'e ido ki kalli fuskar Dad d'in naki ba?." Cikin shagwab'a ta sauke hannun tare da bare baki tasa kuka tace " Dad kalli fuskar Princess d'inkafa?" Dariya suka kunshe dukansu, d'ayan namijin yace " Wai! Wai! Wai! Seemah kin ganki kuwa? gaskiya na tausaya miki." Yafad'a tare da kunshe dariyarsa. Seemah ta kalleshi tace " Yaya Janaid da gaske?" Takalli dad takara sa kuka tace " Dad dama na fad'a maka shi yasa banso kuka ganni ba." Dariya karamin yai yace " Ohhhh ni yazanyi? Kanwata takasa girma," ya fad'a tare ta tab'a kasan id'anta ya lakutu bakin abu, yace " wannan ba Mascara bane Seemah? " Sai alokacin ta kalleshi tace " do u think so?" Ya d'aga mata kai alamar eh,ta kalli masu aikin tare da mik'ewa taje kusa dasu, ta tsaya a kusa da d'aya tace "Anna mascarar dana sa jiyace tamin haka?" Anna tace "Sorry Madam it's my fault." Seemah takarasa jikin madubi ta kalli kanta kamar wata aljana da sauri ta rufe fuska takalli karamin saurayin tace " Ya Ammar to ya akai hakan ta faru dani? Jini fa? Zai fita ma kuwa?" Dariya sukai su dukansu, dad ya kamota ya zaunar a bakin gado, yace "Anna zo ki gyara mata fuska. " Dasauri tace "ok sir" Ammar yace "amma meyasa kika kwana da kwalliya?bana hana ba?" Ta turo baki tace "laifin Anna ne kullum in nai bacci ita take zuwa ta gogemin, amma shine jiya bata gogemin ba." Junaid yai dariya yace "da alama da asuba dakikai alwala duk ya zazzago miki, ke kuma shugabar bacci baki kulaba ki ka kwanta bacci." Tace" I think so yaya." Dariya sukai dukansu. Dad ya mik'e ya kalleta yace " Swthrt zamuyi late bari mu fita." Tai murmushi tace "nima inada lectures yanzu zan shirya." Shafa mata kai yai yace "yauwa baby na." Suna fita Anna tashigo ta goge mata fuska sannan Seemah ta shiga wanka. Su dad na sauka kasa suka taradda matar d'azu ta fito daga d'akinta, ran dad ya b'aci ya kalleta cikin b'acin rai kafin yai magana su Ammar suka ja jakarsu sukai waje gun mota, ya kalleta, itama tsoron mai zaice take. Ta d'aure tace "bakuyi breakfast d'in ba? na shiga toilet ne sai yanzu na fito." Dad ya maka mata hararra yace " Yanzu in wani abu serious ne yasamu Seemah sai ki wuce toilet?" Ta d'aure tace " it's a relief ai tunda ba serious bane." Yace " oh da kikai kamar baki sani ba? Kin kyauta." Ya fad'a tare da yin kwafa ya wuce waje. Tabishi da kallo tace yau koma me za'amin na tab'o 'yar gwal? Sun bar yarinya duk tagama sangarcewa, datayi magana sai yacemata kar ta manta aurantama dayai saboda Seemah ne, tsaki tai ta wuce kitchen. Seemah na fitowa daga wanka ta kure disco tana rawa tanasa kaya, Anna na tayata shiryawa, riga da wando tasa sanna ta zura suwaita doguwa a sama tasa karamin nayafi ta yane kanta, ta fito tare da d'aukan karamar jakarta. A hankali ta sauko kasa ta kalli dinning kamar yanda masu aiki aka umarcesu, sun jera mata nata kayan abincin, ta karasa dinning ta bubud'e kwannukan, ta kalli matar dake zaune itama tana nata breakfast d'in tace " Small Mom banajin zan iya cin abinci, in dad ya kira ya tambaya please kicemai na ci."bata jira amsar taba tai waje, tana gyad'a kai. Haushi yakamata tace "Small mom? Da haka ki kirani da sunana mana Sadiya" Seemah na fita ta taradda driver ya gama goge mota yana tsaye yana jiranta, ta kalleshi tace " da wace mota zamu? " Dasauri ya nuna mata wanda yake tsaye, tsaki tai tace "ni bana santa kujerar cikinta basu da laushi sosai, muje a waccen." Tafad'a tare da nuna wata. Da sauri yace to madam. Kallan garin tai tace " it's snowing." Takarasa ta shiga mota suka fita daga gidan. Garin England yau sun tashi ana ruwan kankara sai dai sukam mazauna garin sun saba da wannan rayuwa, hada_hadar su kawai sukeyi, nikam banda rawar sanyi ba abinda nakeyi, nace kaii! Ina zan iya rayuwa a nan? Seemah na kallah dako ajikinta, nace uhmm keda aka haifeki anan dama.......wayarta ce takatseni datai kara, da sauri Seemah tad'aga ganin sunan dake jiki Big Bros. Cikin shagwab'a tace " Yaya Habib." Yace " Princess dafatan kin tashi lafiya?" Tace "lafiya lau Bros bayan kak'i zuwa?" Ya kalli matarsa dake kusa dashi yace "Ai zuwa zai ban wahala yanzu d'an company d'in dad na bukatata sosai." Seemah Tace " dama za'a barni inzo im ganka, If you think it yaya ban tab'a zuwan garin iyayena ba, gashi kai yanzu ka koma can, sannan su Ya Junaid da Ammar suna zuwa duk bayan 5 month haka ma Dad amma ni bandani." Habib yai murmushi yace "gaskiya kam, kunyi hutun skul?" Cikin zumud'i tace "yau zamu gama exams, kasan kuma inmun gama shikenan an gama zuwa sai an dawo." Yace "Good, zan ma Dad magana yabarki kizo ko 1 month ne kimana." Dakarfi tace " *YESSSS* Kai Bros shiyasa nake sanka sosai." Nan sukai sallama akan sai ya tambayi dad. ************************* Seemah cikin farin ciki ta isa makaranta, ra k'osa taga ya Nigeria take, suna isa ta sauka daga motar tare da shiga cikin skul d'in, tana taka kafa zata ciga class d'insu taji ansa ihu ana fesa mata spray, mamaki ya kamata ta kallesu zatai magana taga abokinta Alex yazo kusa da ita yayi knell down tare da miko mata flower, yace " Seemah will you date me?" Ihu yan class d'in suka sa suna tafi suna cewa " ACCEPT IT!!!!!!" Kallan Alex tai cikin mamaki tace " Alex what's going on? " Ya kara m'iko mata flower yace " Seemah please accept my love." Kallansa ta sake yi ta d'an tab'e baki tace " Alex will you stop all this drama?" Alex ya mik'e tare da cewa " Seemah!!!" Hararsa tai sannan tace " do I look easy to u? Meyasa kowa yake neman raina min hankali? Rannan Abokin ka yazo min da zancen yana sona, yau kuma kai? Am I a toy to u? " Alex zai yi magana ta amshi flower hannunsa ta kalli wata mate d'insu datake sanshi, kowa na skul d'in ya sani har shi Alex d'in ta ajiye mata flower a gabanta sannan ta kalleshi ta wuce ta zauna, Alex ya bita da kallo, abokanansa sukace kaima kasani ai yarinyar nan datakejin kanta kamar 'yar gidan sarauniyar England itace zata so ka? Get a hold of yourself buddy!!!....... Tana zama waya ta d'aga tama Ammar text, tana ajiye wayar ya kira, yace " Princess ya akai? Ki kace wani ya miki proposing?" Tace " eh mana yaya wai kuma ka san wa? Alex fa?" Dariya yasa yace " yanzu ya akai?" Tace " ya akai kuwa? I reject him kaima kasani yaya Alex is not my type." Dariya Ammar yai tace " nifa yaya wanda zan aura dole ne sai ya cika abubuwa guda 5, na farko kyau, na biyu ya d'inga bani respect, na uku bai isa yamin abinda zai b'atamin raiba, na hud'u ya zama mai kud'i d'an ni ban taso a babu ba, na biyar in har nace kaza to lalai sai an min." Ammar yasa dariya sosai yace " anya kuwa zaki samu duka?" Tace "umm wait an see yaya I will definitely find him." Ammar yace kai amma na kosa inganshi. Dariya itama tai tace "yaya plz kasa baki a barni naje Nigeria. " Yace "ok ba matsala, ai kin kai 20yrs ya kamata dad ya barki." Tace tnx Yaya Ammar yace "ki share kiyi exams d'inki a nutse." Murmushi tai tace "ok tnx Oppa". ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Zaune yake a gaban mahaifiyarsa ga kanwarsa dake kwance bata da lafiya, tun tana 'yar shekara 10 ciwo ya kamata, take a kwance har yau Allah bai bata damar mik'ewa ba, komai yi mata ake. Goge mata bakinta yai da miyau yake zuba, ya kalli umma yace " umma ina tunanin tau zan koma." Tace " Jalal in ka tafi wannan karan ka d'inga bari sai sati bibiyu, daga Abuja zuwa binin_gwari da nisa." Murmushi yai yace" zan duba, amma Abba fa? Naga har zan tafi bai dawoba." Tace "yaje kai Zainab kauye ne gun iyayenta, ta damu tanasan zuwa," tai shiru can tace jalal nikam har yanzu baka duba maganar dana cema ba? Na auren Zainab? Kaga 'yar uwace gata ba ruwanta." Jalal ya mik'e tare da cewa " Umma bari na wuce, zan kiraki a waya." Takalleshi tare da cewa "to Allah ya kiyaye hanya." *Jalaludeen* kenan talakawa ne sosai sai dai mutum ne shi da bayasan a rainashi dan bashi da hali, kuma baya tab'a kaskantar da kanshi akan wani mai hali, baya d'aukar raini, ba kuma ya so a rainashi. ************************** Seemah na gama exams da sauri ta shige mota dan batasan su had'u da Alex tana shiga, ta kira yaya Habib, yai murmurshi yace " lalai na yadda kanwar nan tawa ta kosa tazo ta ganni" Seemah tace " yaya ya kukai da dad?" Yace "ya ce ba matsala indai zan kula dake." Ihu tasa tace" wow yaya amma nifa tunda na gama exam so nake a satin nan, in fact gobe ko jibi na k'osa inganka." Habib yace " bakomai zan duba flight na kusa nima na k'osa inga my kanwa." By[truncated by WhatsApp] 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JALALUDEEN*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No 2⃣ Seemah tana isa gida a falo ta tarad da Matar babanta tana kwance ta mik'e akan kujera, ta saka apple a gaba tana ci, haushi ya kama Seemah itakam yanda matar takeyi yana bata haushi sam bata santa, ita tanaso taga mutum ya damu da ita bakamar wannan ba. Shiga tai tare da tsaya a inda take kwance, ta kalleta tace "Small mom bakiga na dawo bane?" Tad'aure ta d'an kalleta kasa kasa tace " to in kindawo Seemah so kikeyi in mik'e in shiga tsalle? Ga 'yar shugaban kasar England ta iso?" Kallaman sun ma Seemah ciwo ta kalleta tace " a gurin iyayena na fi wata sarauniyar England matsayi, amma ina tunanin dole yau injira Dad yazo d'an ya tabbatar miki da hakan." Tana kainan ta juya tai d'aki ta fad'a gado, d'an shagwab'a irin na Seemah ta hau kuka baji ba gani, sai data daidaici lokacin dawowar dad ta sake ware murya tana kuka. Itakam mata hankalinta ya tashi, gashi batajin zata iya ba Seemah hakuri. Dad tare suka dawo su 3 kamar yanda suka fita, haka suke dawowa kullum. Dad na shiga ya kalli falon ya saba yana shigowa Seemah zata rugo da gudu ta rungumeshi, ganin ba ta nan yasa ya kalli matarshi yace " Sauda ina Seema?" Cikin rawar murya ta nuna sama, dasauri dad yai hanyar suma su junaid suka bishi. Seemah kam jin motsinsu yasa takara sa kuka da sauri suka bud'e kofar, dad ya karasa tare da cewa " Baby menene? Waya tab'amin ke?" Seemah Cikin kuka tarik'e hannun dad tace " Dad tambayar ka zanyi, tsakanin ni da sarauniyar England wayafi matsayi a gunka?" Da sauri Dad yace " wace irin tambaya ce wannan Seemah? Wake wani zancen sarauniya bayan ni kece sarauniya ta?" Ta kalli junaid tace kaifa yaya? Ya kalleta yace " Haba princess yama za'ayi ki mana wannan tambayar? Ai ko d'an sarauniyar ne ya nemi yana sanki saboda matsayinki bana jin zamu iya amincemai har sai ya yadda da dokokin mu bare kuma ace matsayi." Dariya tai tace " yaya Ammar fa?" Dariya yai ya matso tare da rik'e kunnenta kad'an yace " waye ya miki wannan banzar tambayar ke kuma har kika rik'e a ranki?" Tad'anyi kara tare da kallan Dad tace " Small mom ce." A zabure Dad ya mik'e ranshi ya gama b'aci ya juya yai waje da alama gun matar tashi zai je. Ammar ya kalleta yace "da baki fad'aba Seemah, Dad bazai mata dasauki ba dama ta b'ata mai rai da safe." Seema ta murgud'a baki tace " wayace karta d'inga kula dani? Ni fa yaya banasan mutumin da bai damu dani ba, nafisan kowa na duniyarnan ya soni kar kowa yad'inga nunamin halin ko in kula." Dariya Junaid yai yace " lalai Seema ai kuma hakan bazai yiwo ba, tunda mu muna sanki ba shikenan ba? Karki damu dan wani bai damu dake ba." Kallanshi tai tadai jishi amma bata aminta ba, itafa tafisan kowa ya sota yakawai...... Nikam nace tab da matsala........ *********************** Dad kam yana fita ya tarad da Sauda a tsaye a kasan beni, ya kalleta yace " waya baki izinin kid'inga had'amin 'yata da wasu can mutane? Harki samin ita kuka?" Tai shiru can tace" Alhaji bafa haka bane kasan me?...." Katseta yai cikin zafin rai yace " bansan komai ba, kuma banasan insan komai, abu d'aya nakeso in sani, a wani dalilin kike samin 'yata kuka? Ko d'an ke bakisan darajar d'a ba? " Cike da mamaki ta kalleshi tace "Alhaji yazaka fad'amin wannan kalmar? Abinfa bai kai nan ba." Yace " what? Bai kai nan ba? In bai kaiba meyasa 'yata na sameta tana kuka? Karki manta zan iya jure komai amma banda hawaye daga idan 'yata, banga d'an Adam d'in dazai wahalarmin da 'ya ba nikuma in kasa d'aukar mataki ba, na aurekine d'an ki kularmin da 'ya kuma akan haka kuka amince daga ke har iyayenki, kukace ku kuma so kuke in barki kiyi karatu a nan kasar na aminta, sannan ni na cika nawa kin gama masters d'inki sai nine bazaki cika min ba?" Sauda ta had'iyi wani abu, ta d'aure tace " kayi hakuri, ba da wani abun na fad'aba amma tunda abin ya kai haka amin hakuri." Dad baice komai ba ya juya ya hau sama, ta bishi da kallo ranta yakai matuka gun b'aci, tasan sarai me yake nufi da ya hau sama wato ta biyoshi ta bada hakuri. Itakam ta rasa wani irin so sukema Seemah, itakam da Seemah gwara a mata kishiyoyi guda 3 su zama su hud'u, in kishiyoyine bata tunanin zasu samu wannan damar, haka ta d'aure tahau sama. Seemah na zaune suna hira da shewa sai labarin abin dariya suke bata, itakuma tanayi, can ta d'aure tace "Dad please ka barni inje Nigeria. " Dad yace " Seemah mu jira sai wani hutun, ban shirya missing d'inki wannan hutun ba." Turo baki tai cikin shagwab'a tace " Dad please ka barni, bafa dad'ewa zanyi ba, sannan ga waya." Tafad'a tana d'aga wayarta. Ammar tad'an kalla da alama magana tamai ta ido, shima yace " eh Dad ka barta please ko d'an taje ta gaida su Inna." Dad zaiyi magana sallamar Sauda ya katseshi, suka amsa ta karaso ta tsaya a kusa da Seemah, ta saki murmushi tace " Haba Princess daga wasa ashe kinji haushi? Na d'auka tsakanin d'a da mahaifi akwai lokacin wasa?." Seemah ta kalleta zatai fitsara Ammar yai saurin toshe mata baki yace " Aunty ba komai ya wuce." Takalleshi tace " Seemah ina kike san zuwa nazo shigowa naji ana zancen." Tai maganar tana murmushi. Seemah tai shiru can tace" gun Yaya Habib nakesan zuwa amma naga Dad kamar bayaso." Yanda tai maganar ne yasa tabasu dariya, junaid yace " da alama yau zamu ganku a rana Dad." Hawayene ya zubo mata tace "dad kaji ko? Gashi ka bari su yaya Junaid zasu mana dariya." Da sauri ya jawota ya rungume yace " barshi da gulmarshi, so yake yaga munyi fad'a tunda bai tab'a gani ba, zuwa gun Habib kuwa na amince." Ihu tasa ta kara rungume dad tace " Dad shiyasa nake bala'in sanka." Dariya suka mata Dad yace " Amma in zaki inaji sai na had'aki da securities da zasu d'inga kula dake, haka kawai Habib na can gun aiki ke kuma kina guri ke kad'ai bazan bar hakan ta kasance ba." Ta kalli Ammar tad'an lagwab'ar dakai kamar zatai kuka Ammar yace " Dad amma ina ganin kabari kawai in yaso in taje can sai a sanar da Habib ya samarmata bodyguards dazasuna kula da ita. " Dad ya kalle Ammar yace "kana ganin hakan ya fi?" Dasauri Seemah tace eh mana Dad. Nace uhmm.................. **************************** Yau Seemah tun Safe akai wanka dan flight d'in sukai booking, Sauda tafi kowa murnar wannan tafiya d'an ko Seemah dazatai tafiyar ta fita murna. Seemah ta shirya cikin riga da wando d'an ita banaji akayanta akwai atamfa ko ince bata tab'a gwada sawa bama, bayan tasa riga da wandon sai kuma ta d'auko rigar sanyi tasa, d'an garin sai da rigar sanyi, ta yi kyau Anna ta kalleta tace " Madam I will miss you." Harararta Seemah tai tace " bayan yanzu kin rage damuwa dani?" Anna ta karaso ta rungumeta a hankali kwalla ya zubo mata, Seemah ta juyo tace " wasa nake Anna na sani kin damu dani sosai, tun ina karama, nima I will miss u." Tare suka fito Anna na rik'e da jakarta, a falo sukaga Sauda sai murmushi take, suna saukowa ta kalli Seemah cikin tsananin farin cikin da kana gani zaka gane tace " Seemah yanzu tafiya zakiyi? Sai kuma yaushe?" Seemah ta kalleta ta had'e rai tace " Small mom nasani kinfi kowa murnar tafiya tai, sai dai ba dad'ewa zanyi ba."tana kainan tai waje gun dasu Dad ke jiranta a mota. Kowa yana zaune a cikin motarsa da driver d'insa, ta kallesu tare da sa dariya tace " Dad ahaka za'ayi rakiyar? Kowa na motarsa? Nima in shiga tawa?" Junaid yace " to a ya za'ayi?" Ta bud'e motar junaid tace yaya fito, junaid ya fito, ta bud'e motar Ammar tace bros kaima fito, shima ya fito, sukace me za'ayi? Motar Abba ta bud'e ta gaba tace Ya junad shiga nan, ya kalleta yace tohh. Nan ya shiga ta kalli driver d'in Dad tace fito shima ya fito ta kalli Ammar tace bros jamu.........tafad'a tare da shiga kusa da Dad. Dariya sukai nan suka shiga tare da fara tafiya, Dad yace " kai Seema zamuyi missing d'inki, baki tab'ayin tafiya ba tunda aka haifeki." Tai raurau da ido tace " yauwa, dole ne kowa a rana ya kirani sau 5 in ba so yake muyi fad'a ba." Haka suka cigaba da tafiya ana raha, Dad yace" na fad'ama Habib ya kularmin dake sosai duk abinda kikeso a tabbatar an miki shi." Dariya tai tace " inada Dad irinka me zai dameni?" Sun isa takira Habib tafad'amai zasu taho. Sai da aka gama musu checking suka shiga jirgi sannan suka juya zuciyarsu duk ba dad'i. ************************** Habib na isa company d'insu ya fara shiga meeting, sun dad'e kafin su gama suka fito sukai sallar azahar, ya duba agoggo akala saura hour d'aya su seemah su iso, yana komawa yataradda wani aikin ya kara tasowa dolene su shiga wani meeting d'in gashi baisan sanda zai fito ba, Secretary d'insa ya kalla yace " Kanwata tana hanya gashi zamu shiga meeting kasa wani ya je airport nan da minti 30 ya jirata ta iso ya tahomin da ita nan, sunanta Seemah, ka tabbatar wanda ka tura mutum ne mai hankali yakuma je ya jirata yanda tana isow zai kawomin ita." Secretary d'in ya amsa da to, nan ya shiga tunanin wazai tura, abokinshi ya tuno, dasauri ya danna number, daga can aka d'aga yace " ya akai Sagir?" Sagir yace " Jalal please kataimakamin meeting zamu shiga da Chairman to kuma kafin mu fito kanwarsa ta iso shine ya keso a taimaka d'aukota, nikuma banyi tunanin kowa a company d'in nan ba sai kai." Jalal yai tsaki yace " ta hawo taxi mana? Dole sai an d'aukota? Ni ma aiki nakeyi." Sagir yai dariya yace " Taxi jalal? Kanwar Chairman d'in company d'inmu fa nace? Kuma bana tunanin ma ta tab'a zuwa kasar'" Jalal ya nisa yace" to kanwar Chairman tafi karfin taxi?" "Nidai plz kataimakamin abokina d'an Allah, sunnanta Seemah, bari na shiga meeting zan ba da makullin motar chairman d'in akawo maka, nan da 30mins zasu iso."Sagir nakainan ya kashe wayar. Tsaki Jalal yai sannan ya kalli takardun da aka bashi yai sorting, shifa baisan rainin hankali, shi driver ne? Dandai Sagir ne amma da ina.............. By *Ayusher Mohd* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JALALUDEEN*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* NO 3⃣ A hankali Jalal ya mik'e ganin minti 30 d'in tayi, tsaki ya sakeyi yace amma Sagir ya ci mutuncina. Kallan 'yan uwansa nagun aiki yai yad'an sosq k'eya yace " zan d'an fita gun wani friend d'ina." Sukace sai ya dawo, waje yai yana cewa haka kawai da mutuncina an sani karya, makulli ya amsa tare da tambayar security d'in ina motar take? Nan ya nuna mai, ya kalli motar tayi kyau sosai, bud'ewa yai ya shiga tare da jaa.... Ya isa airport sa alokacin yashiga tunanin wai ma yazaiyi yasan itace? Zuwa zaiyi yai ta tambayar mutane Seema ko me? Shiru yai can yace " Seemah? Amma sunan kamar ba na kasar nan ba, yai kama dana india, to amma Sagir yace wai kanwa" yai shiru a ranshi yace da alama Sagir d'in bai fahimta bane. Ya dad'e a zaune baiga jirgi ya sauka ba, haushi ya isheshi ya kalli agoggo kusan mintinsa 30 kenan da zauwa, haushi ya isheshi ya mik'e zaiyi hanyar waje, karar jirgin dake alamar sauka ne yasa ya koma ya zauna. Kallan mutane ya shigayi wad'anda sukazo d'aukar 'yan uwansu, to shi wai ya zaiyi ya ganeta? Ganin mutane sun fara tahowa yasa wata idea tazo mai, juyawa yai yaga wasu rik'e da manyan abu d'auke da sunayen wad'anda sukazo tarba, a ranshi yace nima bari nai haka. Jakarsa ya bud'e ya d'auko littafin rubutunsa, ya gutsuro takarda karama, tare da rubuta Seemah da biro a jiki. A zahiri in ba kazo kusa ba bazaka tab'a ganin me aka rubuta ba. Nikam dariya ne ya rufeni ganin wata 'yar takarda d'auke da sunan Seemah gashi sai kunyar rike takardar yake da kyar ya d'aure ganin zai b'atama kansa lokaci yasa ya d'an rike da hannun hagu. 'Yan jirgi sun fara fitowa, Seemah kam duk ta gaji a jirgi ta fito sanye da glass ta cire rigar sanyin datasa ta jacket ta rik'e a hannunta, ga takalmin da tasa mai masifar tsinine, rigar jikinta takai gwiwarta sai wando pencil dake jikinta, tasha jambaki pink, gaskiya tayi kyau sai dai tunda ba al'adarmu bace hakan yasa kowa take kallanta, itakam ko ajikinta. Raba ido kawai take taga an rubuta Seemah a katon symbol wanda zai d'au hankalin mutane, sai dai duk wanda ta leka sai taga ba sunanta, mamaki ya kamata nan tace ko dai yaya yana kunyar rubutawa ne? Nan ta shiga duba mutane ko zata ganshi, mamaki ne ya kamata ganin har ta iso gun da mutane ke tsaye suna jira bataga yayanta ba. Jalal kam ya baza ido sai neman ba india yakeyi, sai dai turawa kad'an da suka fito. Seemah da sauri ta kunna wayarta, sakon yaya ne ya shigo na zai shiga meeting amma ya turo a d'auketa, haushi ya kamata tace " akwai meeting d'in daya fini mahimmanci ne?...." Maganarta ce ta katse ganin wata 'yar karamar takarda wani saurayi sanye da coat yana rik'e dashi, dariya ne yazo mata tace " lalai wasu basuda mutunci, yanzu wannan 'yar iskar takardar da ita za'a tarbi mutum? Da alama dai mutumin nan ko bashi da mutunci ko kuma mammako ne ya mai yawa. Hartazo kusa dashi tana d'an duba mutane, to ta ina zata gane d'an aiken? Ga wayar yaya a kashe, idanta ne yakai kan rubutun dake jikin 'yar takardar, in batai kuskure ba *SEEMAH* taga an rubuta, wani kululun bakin cikine ya ziyarceta, badai ita Seeman ba d'an itakam tasan tafi karfin wannan takardar. Karasawa tai kusa dashi, daidai nan shikuma wani Sagir ya kirashi, Jalal ya d'aga cikin kunnar rai yace " Sagir me kad'aukeni? Tun d'azu ka aikoni d'auko wata banza itakuma tana neman b'atamin lokaci, ce maka akai banda aikin, yi ko me?" Sagir yace " Sorry Jalal yanzun ma ba gama meeting d'in mukai ba, Chairman ne ya kalleni, hakan yasa na gane so yake yaji maganar kanwarsa, dagani yanaji da ita." Cikim zafinrai Jalal yace" me yadameni da wani ji da ita dayake? In hakane ya bar meeting d'in yad'aukota mana, ni mubar wannan maganar, india ce kome? Naji kace Seemah?" Seemah dake tsaye tana jinsa bakin ciki yazo mata wuya, ita ake ciwa mutunci? Haushi ya kamata ta juya ta kara juyawa nan taga wani rike da d'an karamin cup da alama ko lemo ko ruwa ko tea yake sha, ajiye trolly d'inta tai ta karasa gun mutumin, addu'ar ta d'aya Allah yasa tea ne mai zafi. Tana isa gunsa tace sannu bawan Allah, ya kalleta ganin shigarta yasa yad'an had'iyi yawo, yace " mekikeso madan?" Murmushi tai tace " please abinda kake sha nake so, " Da sauri ya mik'a mata cup d'in ta kalli ciki, tea ne mai madara yaji milo sai dai abin haushi ba zafi sai dumi dai kawai, godiya tai ta juya tai gaba shikuma ya bita da kallo. Seemah na isa kusa da mutumin, sai ta juya kai kamar bashi take kallo ba, shi kuma ya zak'e sai fad'a yake a waya sam bai kula da itaba, Seemah na matsowa ta saita takalminta ta takamai kafa da karfi, zai juyo ta kwaramai ruwan tea a cikin kayansa wajen farin coat d'in na ciki cikin tsananin mamaki Jalal ya d'ago d'an ganin wace 'yar duniyar ce wannan? Yana d'agowa Seema ta kwad'amai jacket d'inta, da karfi ya zare jacket d'in takard'ar hannunsa ta fad'i. Cikin wani irin takaici yace " wani irin hauka ne wannan?" Kallansa tai shima ya kalleta, tab'e baki tai tace " Sorry ban kula ba." Tafad'a tare da juyawa, da karfi Jalal ya d'amko hannunta ta tsaya tare da d'an kara d'an taji zafin damkar, ta juyo tace " Malam wani irin rainin hankali ne wannan? Sakeni ko?" Jalal yai wani mugun Murmushi yace " me da me kika ce? Bakiga ke abinda kika min ba?" Ya fad'a yana kallan kayan jikinsa ga kafarsa dake zafi. Tace "sake ni ko? Kai meye dalilinka na tsaya a hanya? Ko nan gidanku ne dazaka tsaya kana gulmar mutane a waya. " Jalal yazabura yace " Gulma? Ke tsaya in ma gulmar ce meye naki a ciki? Ohh shine kikamin haka da sanin ki kenan ko me?" Seemah ta kalleshi tace sakeni ko? Jalal ya zare hannunshi tare da cewa " tambayar ki nake? Meke damunki? Kuma a wani dalilin zaki min haka? Banasan rainin hankali kuma akanki bazan jura ba, kawai kiyi godiya d'aya ke macece dabadan haka ba I don't know what will happen. " Seemah ta makamai harara tace " ka kuma d'auko jakar ka taho mu tafi." Jalal kam ranshi ya kai matuka gun b'aci yace " what?" Seema tace "kanaso in kara fad'ane? Ko ba Seemah kazo d'aukaba?" Jalal yai wani murmushi yanzu ya gane wai itace yace " ko ita nazo d'auka bata isa tasani ind'aukar mata jaka ba, d'an banaji nid'in mai aikinta ne." Yafad'a tare dayin gaba yace " kibiyoni zan jiraki a mota." Seemah ta bishi da kallo tare da d'anyin kara tace " wannan wani irin mutum ne? Wayyo bakin ciki zai kasheni." Yazatai? Haka taja jakarta, yana tsaye jikin mota takarasa fuskarnan a had'e duk da da glass a idanta. Jalal ya shiga mota, itama ta karasa ta shiga baya ta zauna, lalai ba shakka sai ta gyarama mutumin nan zama, shi harya isa? Shid'in wa? Tafiya suka fara bamaima kowa magana, shi haushinshi ma maidashi driver datai, Seemah kam waka tasa a wayarta ta kuma kuri volume, Jalal ya juyo tare da ciro earphone ya cilla mata yace " malama yi amfani da wannan banaso a cika min kunne." Cillamai a binsa tai tace " sai kuma naga kamar ba a kanka nake ba, sannan ta kalli motar ganin abin bit da ta ba yaya habib a jikin madubin gabar motar yasa tace "sai kuma naga motar yayanace bana tunanin kanada iko da ita." Jalal yai tsaki tare da juyawa, yanaji bai tab'a ganin mace 'yar rainin hankali irin wannan ba. Seemah ta kauda kai a ranta tace wannan wani irjn mutum ne? Da alama kuma ba wani kud'i gareshi ba ganin coat d'in jikinsa bamai tsada bace. Yana talaka shine zai raina mata hankali? Tafi karfin a wulakanta, ita datakesan taga kowa na mutuntata yana santa shine yau zata had'u da wannan wanda ko kwayar mutinci bataji yanada shi. By *Ayusher Mohd* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* 4⃣ Har suka isa Company d'in ba wanda yama wani magana a cikinsu, haushi duk ya cika Jalal aikuwa da yazo taka burki da karfi ya taka har sai dayasa Seema ta bugi kujarar gaba, cikin b'acin rai ta d'ago tare da dafa gun kamar tai kuka dan taji zafi. Jalal ya juyo yace " Sorry bankula bane." Ta tuna itama haka tace data mai tsiya a airport wato ramawa yai ko me? Juyawa tai ta kalli Company d'in, babban ne sosai duk an bishi da glass lekawa tai taga kamar mutane sun taro daga bakin kofar, ido ta kura nan ta hango yayanta, wani murmushin dad'i ta saki tanaso taga ana ji da ita, wannan tarbar da aka mata yasa taji zafin goshin ya tafi, kallan Jalal tai dake miko mata key, yace " gashi kyaba yayanki." Ta kalleshi tace " bud'emin kofa." Jalal ya kalleta cikin rashin fahimta yace " what did you just say? " Ta murgud'a baki tace " bakaga an taro ana jirana ba? Ko so kake ka b'atama yaya na rai?" Jalal yad'an yi wani dariya dakanaji kasan ta bakin ciki ce, yace " Servant d'inki ne ni?" Zatai magana taga an bud'e mata kofa, cikin mamaki ta kalli waje, wani saurayi ne yace " Welcome Madam" A hankali ta zuro takalminta mai mugun tsini sannan ta fito, sai dataje tsakiya yanda jalal zai jita haka kuma mutanen dake jiranta zasu jita, ta juyo cikin wani rainin hankali takalli jalal dake tsaye jikin mota, tace " Mr Pride d'an Allah jakata na manta nan kawomin." Jalal ya kalleta tare da nuna kansa da hannu yace " Me?" Ta d'aga kai tace" Sorry." Wanda ya bud'e mata kofa yace " bari na anso miki madam. Seemah tace " barshi shi nakeso ya kawomin." Tana kainan ta cigaba da tafiya. Jalal ya furzar da wata iska cikin takaici ya bud'e boot ya d'auko trolly d'in. Seemah ta karasa gunsu yaya tana tafe tana murmushi, Habib na gani ta kusa zuwa ya karasa tare da rike hannuwanta duka biyu, tab'e baki tai tace "yaya haka ake oyoyon?" Yace " Sorry Seemah ta bakiga da mutane bane? Kuma kinsan a kasa na suke kar su rainani." Tace " nagane, oh ni yaya ashe zanganka?" Dariya yai yace "mu wuce office d'ina muyi murnar ganin juna, ko?" Cikin zumud'i ta d'aga kai, nan suka fara tafiya, nan ta waiga ko zataga d'an rainin hankalin nan, sai dai ga mamakinta duk inda ta duba bayannan mamaki ya kamata, ina yaje? Jakarta ta hango a hanyar shiga, wato har ya ajiye ya tafi? Lebenta tad'an ciza tare dayin kwafa a hankali. Sun isa mutane na ta gaisheta tana amsawa, farinciki ya cikata tanasan kulawa, har suka isa office d'in kowa ya gansu sai ya gaidasu, suna isa suka rungume juna, ta rik'e hannun Habib tace " Yaya I really miss you. " Yace "nima kanwata, ni kad'ai nasan dad'in danakeji na ganinki." Dariya tai tace " yaya sai yau nazo mahaifata, bakaji dad'in da nakeji ba dan ma d'an......." sai kuma tai shiro. Habib yai dariya yace" badai daga isowar kanwata har an samu rikaken dazai b'ata mata rai ba? " Ta turo baki tace " sosai ma kuwa yaya, kuma nad'au alwashin sai ya tsugunna ya nemi yafiyar abubuwan dayamin." Dariya sosai Habib yai yace " namanta ashefa Seemah aka tab'o wacce bata hakuri in aka mata abu." Tai dariya itama tace " yaya dad'i nakeji sosai." Sun dad'e suna hira, har waya sukai dasu dad yakara tunamai ya kular masa da Seemah, suna gama waya Habib yace " kai dad ma sai a hankali, tun kafin kizo yake tunamin in kula dake." Dariya tai tace " ai nasani dad duk yafi sona akanku, bayasan abu ya tab'ani." Habib yace "muma duk muna sanki sosai, yanzu dai dolene in samarmiki wanda zai dunga kula dake a duk harkokin da zakiyi a nan kasar, amma kamar mutane nawa kikeso?" Shiru tai can wani abu ya fad'o mata wani mik'ewa tai tare dayin tsalle, tace " kaii!!!!! Amma naji dad'i." Kallanta Habib yai tare da tambayarta mene? Ta tsugunna agabanshi tace " yaya wani abu nakesan kataimakamin dashi." Yace menene wannan? Seemah ta saki murmushi tace " akwai wanda nakesan yazama driver na kuma bodyguard d'ina." Habib ya kalleta da mamaki yace " au yanzu daga shigowar ki gari har kinsan wani da kikeson ya kula dake?" Tace " sosai kuwa yaya, kuma shid'in nan nakeso yad'inga min aiki." Habib yace "ba matsala in dai har ba ma'aikaci bane." Cikin shagwab'a tace " nidai ko ma'aikacin ne shi nakeso Yaya, in yaso sai a tsayar dashi in na koma sai ya koma aikinsan tunda ba dad'ewa zanyi ba." Habib yace " dole a miki duk abinda kikeso Princess. " Wani murmushi tasaki, harta hango tana sashi aiki yana mata....hahhh lalai zataci dariya. *************************** Jalal kam yana kai jakarnan ya wuce department d'insu yanashiga, ya zauna a kujerarsa cikin b'acin rai, shugabansu nagun aiki ya shigo tare da cewa " Jalal bakai nagani yanzu ba? Rik'e da jakar kanwar Chairman? " Wani takaici ya kamashi ya kasa magana, shugaban yasake cewa " kai amma kaji dad'i gwara daka kama kafarta, d'an ancemana Chairman d'in Company d'inan nasan kanwar nan tasa, kasani ko tamaka hanya ka zama mai office d'in kanka ba irin wannan ba na kusan mutane biyar?" Jalal ya mik'e cikin tsananin bakin ciki da sauri yai waje tare da bugo kofar office d'in da karfi. kama kafa? Kamar shi? Da iliminsa da komai? Ajiyar zuciya yai tare da kiran Abbansa, bayan sun gaisa ya tambayi jikin kanwar sa, Abba yace " jiki nanan yanda yake." Sun d'anyi hira kafin suyi Sallama. By *Ayusher Mohd* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* *NO*5⃣ _*This page is dedicated to you Beely Badaru*_😍😍 Sun fito rike da hannun juna, kana ganinsu kasan suna cikin tsananin farin ciki, suna tafe ana gaidasu, sai gulma da mutane sukeyi ganin abun banbarakwai,nan suka shiga motar Habib, suna baya driver na jansu. Seemah takalleshi tace "yaya amma d'azu ba wannan bane yazo d'aukana?"taimaganar tana nuna drivern da ido, Habib ya kalli mai tukin sannan yace mata" yaje gida ne d'azu 'yarsa ce bataji dad'i ba." Ta d'aga kai tare da tuno birkin da ya ja ta k'umu, kallan Habib tai tace " amma yaya wannan waye?" Habib yace " bansani ba gaskiya."da sauri tace " yaya ban gane ba?" Habib yace " Sagir nasa ya tura wani ya d'aukoki."turo baki tai cikin shagwab'a tace " au yaya kanwar taka zata dawo bama kasan waya tafi d'aukota ba?" Ta juya kai tare da hard'e hannayenta, dariya yai yace " kanwata ayi hakuri ko sai na kira Dad ya bada hakuri a madadi na." Har suka isa gida Habib na lallab'ata suna shiga daga gate tashiga kallen gidan, gida ne karami daidai saidai tsarin gidan yayi kyau sosai, suna parking wata had'ad'iyar mace ta fito da wata kuma sa'ar Seemah, suna tsaye daga jikin kofa suna murmushi, Seemah ta kallesu ta tabbatar matar yaya Habib ce dan taganta a hotuna, sai dai wace take sa'arta ce bata san ko wace ba. A hankali suka karasa gun da sauri matar yayan ta karaso tare da rungume Seemah cikin tsananin farinciki tace " Kanwata sannu da zuwa, naji dad'in ganinki sosai." Seemah ta saki murmushin dad'in taji dad'in yanda aka nuna mata so, yaran suka taho da gudu su biyu mace da namiji, Seemah ta rungumesu tace " Ra'is da Ra'isa sai yau naganku." Sun dad'e kafin matar habib tace muje ciki kanwata. Sun shiga ciki, nan sa'ar seemah taja jakar seemah tai ciki da ita, kallan matar yayanta tai tace " Aunty Farida amma kanwarki ce ko? Naga kama." Daga mata kai tai tace " D'aukota nai d'an kiji dad'in hutun anan kinsan in akwai sa'arka kafi jin dad'i" dariya Seemah tai tace " naji dad'i Aunty amma ya sunanta?" Jisukai ance " Aisha Mohd Rabi'u" da sauri Seemah ta juya tare da dariya tace " Aisha irin wannan fad'ar suna har ka ka?" Nan sukasa dariya dukansu. Tayi sallah sannan aka jera abinci kala kala a dinning, Sun zauna Seemah tai murmushi tace " Auntyna duk wannan na welcome ne?" Habib yace " I Farida na sanki sosai seemah tanaso kizo, yanzu tunda kika samu zuwa kuwa ai ba dama........... Sun gama cin Abinci suka shiga d'aki suna hira, duk da ba sabawa sukai ba amma Aisha na kok'arin janta da hira, itadai ba wani sakewa take ko jin dad'in hirar takeyi ba, tunanin cin fuskar da aka mata yau takeyi, aiya sanin rayuwarta sai dai ita tacima mutum mutunci badai ita a mata ba, tai shiru tana hango sanda ya kumeta a kujera, wai sorry? Jitai Aisha ta tab'ata tace kinajina? Seemah tace " naga magrib ta kusa bari na shiga wanka, amma nikam garin nan sam ba sanyi." Aisha ta kalleta da mamaki tace "sanyi kuwa, ke bakyaji?" Seemah bata amsa mata ba ta shiga toilet, Aisha ta bita da kallo tace " sai a tambayi mutum kuma inya bada amsa sai ta shareshi" tsaki tai tace nifa bansan rainin hankali. Seemah na fitowa bayan tayi sallah batare datama Aisha magana ba kawai ta fita daga d'akin. Su Ra'is ta jiyo kamar suna wasa, hartaje zata shiga taji Yaya yace " kanwata?" Da sauri ta juyo tare da murmushi tace " yaya? Ashe kana nan?" Alama yamata data karaso, dasauri taje inda yake, tare da cewa" yaya nima ina san irin kayansu Aunty Farida." Cikin mamaki yace " Atamfa?" Tad'aga kai yace " ba matsala in yaso gobe sai kuje ke da ko Aisha ne." Hannunshi ta rik'e cikin shagwab'a tace " ni da kai nakeso yaya." Tafad'a tare da turo baki. Ya saki ajiyar zuciya yace " shikenan in yaso gobe ina tasowa daga gun aiki sai muje." Tace eh yayana. Sun dad'e suna hira kafin Farida ta iso itama ta shiga aka cigaba dayi da ita. Seemah ta mik'e zata tafi tace " yaya yaushe kuma zani gurun iyayen su mumy na da dad?" Habib yai shiru, can yace " zan tambayi Dad." Seemah ta kalleshi tace Ok ************************** Seemah ta kwanta da niyyar bacci sai dai ta rasa dalilin dayasa ta kasa, tai tunanin hala canjin guri ne d'an tunda aka haifeta a can take. Wayar Ammar ce ta shigo, da sauri ta d'aga yace " kin kasa bacci ko?" Tace " yaya shiyasa nake sanka dayawa, kasan ni sosai." Cikin wani yanayi na tausayi yace " to yanzu ya za'ayi?" Tace "oho kasan yanda zakai kawai inyi bacci nidai." Dariya yai sosai sannan yace bari na baki story, nan ya shiga bata labari hartai bacci jin shiru yasa ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi shima ya kwanta. ********************* Da safe Seemah sai 11 ta tashi, tana tashi tai wanka sannan tasa kaya ta sauko, su Ra'isa har sun tafi makaranta, sannan Aisha bata d'akin, a falo ta gansu suna hira, ta karasa tare da gaida Farida, cikin sakin fuska ta nuna mata dinning sannan tad'an harari Aisha, nan Aisha ta juyo tare da k'akaro murmushi tace " Seemah kin tashi? Aunty ta hanani cin abinci wai sai kin taso." Cikin ko in kula Seemah tace " Aunty da kin barta ai ni nafisan cin abinci ni kad'ai indai har bada family's d'ina bane." Ba Aisha ba har farida taji haushin wannan maganar sai dai bata nuna ba. Seemah kam ko a jikinta ta wuce dinning taci abinci,tana gamawa ta taso ta dawo falon tace " yaya na office ?" Farida tace eh, Aisha ta kalleta ta sannan tace " nima yanzu zan fita skul ina da lectures by 1 zanje da wuri d'an akwai abinda zanyin." Seemah tad'an kauda kai ko meta tuna sai kuma ta juyo tace " nikam Aisha kin iya driving? " Aisha takalli farida tace " inadai koya." Seemah tace" mu fita tare inyaso sai ki ajiyeni a office da motar sai ki hau Taxi." Aisha ranta yakara b'aci amma ganin yanda farida tai yasa ta d'aure tace " towa zai dawo dake? " inada driver acan ai abinda Seemah tace kenen, Farida tace " gun Habib zaki? Memakwan ki zauna muyi hira?" "Am sorry Aunty akwai abinda nakesan yine a can." Nan ta mik'e. Aisha ta bita da harara tace kamar in kifa mata mari nakeji wlh. Farida tace " banasan haka Aisha ki rufan asiri wannan yarinya akanta Habib zai iya sakina."tana kai nan ta mik'e tare da mik'a mata key tace kuma kuyi a hankali kinga baki da licence. ************************* Sun fito sun shiga mota,Seemah ta shiga baya, Aisha bakin ciki ya kamata sai dai ya zatai? sai da sukai d'an nisa Seemah tace " namanta phone d'ina a gida." Aisha tace mukoma ne? Seemah tad'an kauda kai tace " mutafi kawai." Sun kusa isa office zasu shiga kwana sam Aisha bata kula da wanda ke kokarin shigowa ba, da karfi ta taka burki, Seemah tad'an gwaru da kujera, cikin b'acin rai tace " Aisha meye hakan? " Cike da tsoro Aisha tace " Seema wani na kusa kad'ewa.........bata karasa maganar ba taji anyi knocking d'in glass d'in motar inda zake, cikin tsoro ta zuge, wanda aka kusa kad'ewa cikin had'e rai yace " muga licence d' inki?" Miyau ta had'iya tace " hmmm namanta da shi gida," Seemah dake jinsu sai dai tana tunanin wannan muryar, Aisha kam kallansa kawai takeyi, kwarjinshi ya hanata magana sosai, kirjinsa takalla, mai fad'in gaske da gani yana motsa jiki ganin yanda jikinsa yake da fad'i, jitai an katseta ance " in baki iya mota ba meye naki na ja? Ku mutane sai ku d'inga abu ba tunani." Da sauri Aisha tace yahakuri, cikin b'acin rai Seemah ta bud'e bayan motar tafito, idanunta in bai mata k'aryaba mutumin jiya ne, kuma ga mamakinta coat d'in nan ta jiya ce kawai dai an wanketa ne, Jalal ta kalleta sarai ya ganeta amma bai nuna mata ba ya kalli Aisha yace " you hav to be careful." Ya juya zai wuce. Da karfi Seemah cikin takaicin yanda ya shareta tace " Kai driver?" Jalal ya juyo cikin b'acin rai sannan ya karaso inda take ya junata da ' yatsa yace " kisan me zaki d'inga fad'a niba drivernki bane kuma bana tunanin zan zama d'aya." Seemah tai wani murmushi tace " ko zanyi doubling d'in albashinka?" Tafad'a cikin salon rainin hankali, Jalal haushi ya kamashi batare da ya amsa mata ba ya juya zai wuce, da sauri Seemah ta riko hannunsa tace " Who gave you permission to live? According to whom? " Jalal ya kalleta tare da zare hannunshi yace " According to me." Yana kainan ya juya, da sauri Seemah ta sha gabanshi tace " malam magana fa nake, a ka'idata in ina magana dole ne a tsaya in gama kuma dole ne a ji, d'an haka ka wuce muje ka karasa dani Company d'in yayana." Jalal zaiyi magana yaga text ya shigo mai, shiru yai idanunsa suka kad'a sukai jaa, meya sami kanwar sa? Gashi daga office yake ko kud'i bai fito da shi ba, jiyai Seemah na cewa " Driver dakai nake magana wato kaji zancen doubling d'in kud'i shine ka kasa kagana ko?" Ta kalli Aisha dake tsaye tace bani key ki wuce skul d'in. Aisha ta mik'a mata ita kuma ta mik'ama Jalal dake tsaye duk tunaninsa ya kule, kallan key d'in yai yace " meye hakan?" Tace " ka wuce muje ko?" Jalal ya kalleta da alama sai ya gyara yarinyarnan, key d'in ya amsa yace " muje ko?" Murmushi tai tace " aikin kawai a ido kamar kud'i bazai rinjayeshi ba, dama ai hakane d'an adam inyaji kud'i?" Ta saki tsaki, Jalal na jinta yai kwafa tare da shiga mota, itama ta shiga baya. Jalal ya fizge mota ya juya yai hanyar fita daga gari, Seemah ta kalleshi cikin mamaki tace " ina kuma zamu? Duk da ni ba ' yar garin bace amma nasani kwarai nisan company d'in bai kai haka ba." Jalal ko kulata baiyi ba kawai gudu yakeyi tunaninshi d'aya meyasamu kanwarsa da har zainab ta turomai sako??????? Seemah kam ganin sun bar gari kuma gudu yakeyi yasa tsoro ya fara kamata, ta fara masifa, malam meye hakan? Me kake nufi dani? Ina kake k'okarin kaine? Jalal bai kulata ba tafiyarsa kawai yake, Seemah ta shiga ihu, ta d'auka ko fyad'e zai mata ko wani abun, tunda ita batasan ana satar mutane ba, duk masifa da ihun datake Jalal bai kulata ba, gashi bata d'auko sayarta ba, a hankali ta shiga bashi hakuri ganin tsoro ya kamata da gaske Jalal yace " Sorry akwai inda zani ne,ba wani abun zan miki ba." Cikin hawaye tace ina zanyarda dakai? Bansan gari ba kazo ka fita dani kawai kana gudu dani a titi, kayi hakuri in har haushi kaji nacema driver. JALAL bai sake magana ba, itama tun tanayi har ta gaji ta takure a gefe har suka isa binin/gwari, Jalal ya karasa gidansu yai parking tare da rufeta a mota, ya wuce ciki, kuka take sosai itakam tasan yau karshen rayuwarta yazo. BY *ÀYUSHER MÒHD* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 No6⃣ Seemah duk tagama rud'ewa kafin a isa birnin/gwari har ta gaji da kuka tayi shiru, sai ajiyar zuciya take, jalal kam na isa lungun gidansu yai parking d'an mota bata shiga gun, ya juyo ya kalli Seemah kwarai tabashi tausayi, shikanshi baisan meyasa yamata haka ba, daurewa yai yace " Kid'an jirani kad'an." Kafin tai magana ya fita tare da kulle motar tsoro yakara kamata mr zai jeyi? Jijiga kofar tashiga yi sai dai yariga ya kulleta. Jalal kam da sauri ya karasa gida, Umma na zaune a barandar tayi shiru tare da zuba tagumi, Sallamar dataji ne yasa ta mik'e, Jalal ya shiga da sauru tare da rik'e hannunta yace " Umma ya jikin Zaheedan? Umma ta kalleshi tace " Jalal menene hakan? Ya akai ka tahu yay bayan kasan yau kanada aiki?wama yafad'ama bata da lafiya?" Jalal bai maganaba kawai yazare hannunsa daga gun Umma yai hanyar d'akin kanwarsa, a kwance yaganta yanda dai take, ajiyar zuciya yai sannan ya rike hannunta idansa taf kwalla, bacci takeyi hakan yasa bayan yagama mata add'ua ya fito daga d'akin, Umma ya kalla yace " meya sameta umma? " Umma ta kalleshi cike da tausayi tace " Jalal bafa wani abu bane, kawai d'azu ne ta shiga yin jijjiga, sai kuma kumfa data d'inga fitowa daga bakinta, amma ana kiran likita ya dubata, yace bakomai yana mata allura kuwa tadaina." Ajiyar zuciya yai ya kallin hanyar toilet jin motsi, Zainab ce d'aure da zane sai hijab datasa da alama daga wanka take, kallanta yai, itama da sauri ta gaidashi, ya amsa sannan ya juyo ya kalli umma yace " zan wuce inada abinyi, sannan kicema Abba zan turo kud'in." Umma ta kalleshi tace " to Jalal Allah ya tsare." Juyawa yai da sauri Zainab tace " yaya?" Juyowa yai batare da ya sake rai ba, tad'an matso, ganin haka yasa umma tai ciki. Kanta a kasa cikin nutsuwa da hankali tace " Kayi hakuri yaya laifinane." Yace namefa? Tad'ago a hankali tace " natasoka na fad'amaka Zaheeda batada lafiya." Fuska yad'an saki kad'an yace " nagode sosai kuma inaso in wani abun ya faru ki d'inga fad'amin kamar yanda kikai yau." Kai tad'aga tare da cewa " Allah ya tsare. Juyawa yai yai waje da sauri ya koma mota, ga mamakinsa mutane ya gani a gun, cikin sauri ya karasa gun tare da tambayarsu lafiya? Kallamsa sukai suka kalli maccen dake cikin mota tanata bubuga glass, hakuri ya basu yace " batada lafiya ne asibiti zan kaita. Jin haka yasa suka wuce tare da musu sallama. Jalal ya shiga mota tare da kallanta, duk ta gama rikicewa, wani tausayinta ne ya kamashi, me ya kaishi yin haka, kasa magana yai kawai ya juya mota suka fara tafiya sunyi nisa sosai kafin Seema ta d'aure tace" har yanzu bamu iso inda kake shirin lalatamin rayuwar ba?" Kallanta yai ta glass ya d'auka tagama tsorata lalai yarinyarnan wato fitsara dai bazata daina ba, bai amsa mata ba hakan yasa ta shigaba, " kada kai tunanin zan tsorata akan wani banzan sharri dakake shirin yimin, sai dai ka makaro dan ni bana shakkar komai, sqi tausayinka danake, d'an in ka bari yayana ko mahaifina ya kamaka?" Tai ajiya zuciya tace "I don't think you will go away easily. "Tafad'a tare da yin kwafa. Murmushi yai a ranshi yace " she is bold, wato ko tana tsoro bataso ta nuna?." Seemah kam zuciyart fal take da tsoro, sai dai batason raini. Sunyi nisa sosai d'an baifi saura 1hr su isa Abuja ba, mota tafara nuna musu danger, Jalal ya kalleta yarasa mai zaice ga ba kud'i a gunshi, ya d'aure yace " ba mai a motar, zaki iya ban aron kud'i?" Kallanshi tai sannan tasa wata dariya, tace " What did you just said? " ran Jalal ya b'aci yace " ban fito da kud'i ba ga magrib ta kawo kai ko so kike muyi dare a hanya?" Tsaki taja tace " wannan matsalarka ce kuma, ba dare ba mu kwana ma mana ni ina ruwana." Haushi ya kamashi, ga motar tama fara kokarin mutuwa, gashi gun daji ne, parking yai a gefe sannan ya juyo ya kalleta sannan ya nunata da yatsa yace " don't you dare do that to me again, d'an ba abinda na tsana irin a min tsaki, bare ke mace macema yarinya." Dariya tasake yi kad'an tace " in kuma na sake fa? Me zakamin?" Tafad'a tare da matse kafofinta dake d'an rawa. Ya harareta yace" ko zaki gwada?" Ta murgud'a mai baki tace " oho kuma yau ina tausaya ma dan watan barin aikinka ya kama." Jalal ya juya yana kallan titi ya zasuyi? Ganin zaman bazai mai amfani ba yasa ya fita tare da fara tsaida motocin da suke wucewa, sai dai abin haushi duk ba wanda ya tsaya kowa wucewa kawai yakeyi. Seema dake zaune a mota ta makamai harara tace" kalleshi kamar na kwarai, kirjinsa takalla, da sauri tai tsaki tace "irin wad'an nan mutanen nafi tsana a rayuwa ta masu nuna su na Allah ne bayan kuma ba haka bane a ransu." Jalal ganin abun yaki ci yaki cinyewa gashi magrib har tayi yasa ya dawo mota yai shiru, wayarsa ya d'aga wa zai kira to? Shi duk abokanansa ba wani abota bace ta kud da kud kowa in ya ganshi da yarinyarnan zarginsa zaiyi. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Habib kam da rana ya k'ira Farida d'an jin lafiyarta, itakam cike da mamaki tace " Seemah ai tun wajen 12 ta taho gunka office." cikin tsananin mamaki yace " Farida mai kike nufi da wannan zancen? Wani irin Seemah tazo? Bayan ni ban ganta ba? Kuma wama zai kawota? D'an nasan bata iya driving ba." Tsoro yakama Farida tace '"tare suka fita da Aisha bari na kirata inji." Da sauri Habib ya kashw wayar ya kara k'iran wayar Seemah datun dazu bata dauka ba. Farida tak'ira Aisha itakam nan ta sanar da duk abinda ya faru. Farida cikin tsoro ta kashe kafin takira Habib yasake k'iranta, yace " ya sukai?" Cikin tsoro ta shiga fad'amai abinda akai. Yana gama ji ya kashe wayar tare da jawo coat d'inshi take lankaye, yasa ya fita da sauri, nemanta ya shigayi sai dai abin tambayar? Wanene wanda auka tafi taren? Itadai Aisha batasani ba bare kuma su Habib. Nan aka sanar da Security's na Company d'in aka shiga nemanta, har police station aka sanar mawa, ganin abun yaki cinyewa yasa aka baza cigiya gidan radio da Tv. Hmmmmmmm ●●●●●●●○●●●●●○●●●●●○ Jalal kam kansa ya dafe, can ya juyo ya kalli Seemah dake rik'e da ciki da alama yunwa takeji, shikanshi yunwa yakeji, fita yai daga motar ya rufeta yai d'an dajin, bishiyar mango yagani rigarsa ya cire ta sama ya hau kad'owa, ba laifi ya samo guda 5 sakosu yai a rigarsa ya koma mota, yana zuwa ya mika mata, ta kalleshi tare da hararsa tace " ce maka akai yunwa nake ji?" Kalanta yai yace " im ba yunwa kikeji ba ki barsu." Yana gama fad'ar hakan ya bud'e mota ya fita, Seemah ta harareshi tare da jawo mango d'in nan ta shiga sha. Shikam wayarsa ya d'auka ya k'ira Sagir, Sagir na d'agawa yace " Mutumin ina ka shiga?" Jalal yace " ba wannan ba da matsala fa, yarinyar nan fa na tare da ni." Cikin rashin fahimta Sagir yace wacce? Jalal yace wace nad'auko jiya. Cikin tsananin mamaki Sagir yace " What? Jalal meke faruwa? Dama kaine wanda kuka fita tare? Kasan yanda ake nemanta kuwa? Jalal in akasan kaine da......." Katseshi Jalal yai yace " man mota ya kare inaso ka sanar azo a d'auketa ko kai kazo ka d'auketa, nan ya mai kwatance ya kashe wayar. Sagir yabi wayar da kallo, bai tsaya wani tunani ba ya zari key. ...... Seemah kam sai datasha guda 4 tad'aga na karshen zata sha sai kuma ta kalli Jalal dake tsaye a waje gashi da alama sanyi yakeji yanda taga yana takurewa,zuge glass d'in motar tai tace " ungo na k'oshi? " kallanta yai sannan ya juya kai gefe kamar bai jita ba, tai tsaki tace " mutum sai rainin hankali," Komawa tai ta zauna tace oho cikin wa? Can kuma tace ba dai poison yasamin ba? Da sauri ta kalleshi sai kuma tace " ah ai kayan fruit ne" can kuma tace in yai injecting d'in mango d'in fa da poison? Sai kuma tace "kaiii yaushe har ya fita dashi, Can kuma tace wayyo in kuma ya shirya fa? Da sauri ta bud'e motar taje kusa da shi ta mik'amai mango d'in, ya kalleta tare da juya kai, kallansa tai tace " wato magani kasa min na guba ko?" Kallanta yai kamar ya? Ta kara mik'amai tace " sha in gani." Kansa ya kara juyawa sannan ya mik'a mata rigar coat d'insa takalleshi tare da kallan rigar, sai dayai d'an nisa kad'an yace " nafi karfin nasama mutum guba, sannan kisa rigar d' an na tsane inga mace da irin kayan nan tana tallar kanta." Ha! ha! ha! What? Talla? Leb'enta ta tad'an ciza sannan ta kalli coat d'in. Mota suka koma ba wanda yai magana can Seemah tace " wai anan kake tunanin zan kwana?" Jalal baiyi magana ba" tace namanta da jakata ne nima ban fito da kud'i ba, bai kulata ba, ganin haka yasa ta mik'amai coat d'insa tace "nima nafi karfin sa wannan rigar." Baiyi magana ba ya fita ganin kamar mota na nufosu. By *Ayusher Mohd* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *Ayusher Mohd* No 7⃣ Seemah dake zaune a mota ta bishi da harara. Jalal kam yana ganin motar har tazo kusa dasu ta tsaya, Sagir da sauri ya bud'e motar yazo gun Jalal yace " Jalal tana ina?" Kallansa yai sannan ya kalli motar hakan ya sa Sagir yagane tana motar kenan, da sauri yakarasa motar ya bud'e baya tare da kallanta, ba tantama itace da sauri ya gaida ita, ita kanta kallansa take da mamaki ta amsa tare da tambayar " kai ma accomplice ne?" Da sauri Sagir yace " a'a Ranki ya dad'e, yanzu ya k'irani na taho, amma ya akai haka?" Kallansa tai sannan tace " kai waye da zakamin wannan tambayar?" Sagir yace " baki gane ni ba? Secretary d'in yallab'ai ne." Kallansa tai tare da kauda kai gefe tace " maidani gida." Da sauri Sagir yace " to ranki ya dad'e yanzu ma kuwa." Fitowa tai nan taga Jalal a tsaye, ta harareshi tare da kauda kai gefe, Sagir ya kalli Jalal yace mutafi. Jalal ya kalleshi yace ina? Sagir yace gida mana. Kallan Seemah yai yace " so kake laifina ya shafeka? Na tab'a 'yar gwal kana tunanin zan bari laifina ya sha feka?" Sagir yace to yaza'ayi Jalal? A ranta ta na nata sunan *JALAL* *JALAL* *JALAL* Jala yace " manka za muyi sharing a motar in yaso sai in maidata da kaina." Sagir yai shiru amma shikam yasan tabbas da matsala, in har Habib yagansu bayaji Jalal zai tsira da aikinsa. Seemah ta kalleshi tace " nidai ka barni na tafi, banasan tafiya da kai sai dai in kuma wani abun kake shirin yi min." Jala ya watsa mata wani kallo yace " ni na ba kaina makulin motarki? Ko kuwa kidnapping d'inki nai? A iya sanina ke da kanki kika shiga mota kika kuma bani makulli, so I don't think kinada hujjar da zaki yanke hukunci akan wannan maganar." Seemah wani kululun bak'inciki ya kamata ta bugamai wani kallo, wani k'arin bak'incikin kuma ko kallanta baiyi ba magana ma yake da Sagir, jitai kamar tasa ihu d'an bakin ciki. Shikam sun sa tiyo sun d'an zuk'i man motar Sagir suna gamawa Jalal ya kalli Seemah yace wuce muje ko? Takalleshi tace "in naki shiga fa?" Jalal ya kalleta yace "ko zaki gwada ne kiga abinda zai biyo baya?" Sagir ya kalli Jalal yace "Jalal ka d'inga hakuri d'an Allah." Sannan ya kalli Seemah yace " kiyi hakuri ranki ya dad'e haka yake hakuri muke dashi muma." Jalal ya kalleshi yace " Sagir banaso karkasa yarinya karama ta rainani." Yanakainan ya juya sai dayaje wajen motar yace kizo mu tafi dare na yi. Sagir ya kalleta yace " kiyi hakuri Madam haka yake, a hak bazaki gane ba amma Jalal mutum ne nagari sosai." Kallansa tai ta tab'a baki wayaga na gari, ju yawatai itama takarasa motar, ta bud'e ta shiga baya. Jalal ya tada mota ya hau kan titi, sunyi nisa sosai ba wanda yace komai, can Seemah ta d'aure tace " dama d'an kawai ka ci mutuncina ka jani a motar? Ko d'an na cemaka driver?" Jalal yai shiru can yace " tambaya kike?" Haushi ya kamata tace " ba tambaya nake ba, ina dai tausaya maka ne na shirin dakai ya ruguje." " Bana tunanin yarinya dake harkin kai matsayin dazaki rugujemin shirina." Ya fad'a yana kallan titi. Tad'an matso da kanta jikin kujera sannan tace "ina tausaya maka abin da zai faru dakai." Jalal yad' an waigo kad'an yace " bana tunanin kinkai shekaru 20 in case in ma kinkai bana tunanin kin wuce, kinga kuwa baki kai lokacin tausaya ma wani ba sai dai ke atausaya miki." Turo baki tai kamar tai kuka cikin shagwab'a tace " Wlh kacigaba da abinda kakemin, karkuma kai tunanin tsoro nake ji." Baisan sanda yad'anyi murmushi ba yace " da alama ke mammah girl ce." Tanajin haka tai shiru, idanunta suka cika da kwalla, Jalal jin shiru yasa ya cigaba da tuk'insa, anfi minti 5 da maganar jiyai tace " Banda mahaifiya ai, ban ma santa ba zance." Itakanta batasan meyasata fad'amai ba d'an a zahiri ko 'yan skul d'insu basu sani ba. Shiru yai jikinsa yai sanyi, tausayinta yakamashi da kuma maganar dayai, ya rasa mai zaici, shikanshi mamakin kanshi yai dayaji yace " Bakomai ita dama rayuwa haka take, mutum baya samin komai, Allah yajikanta." Kallansa tai idanunta taf da kwalla, sun shiga garin Abuja ya kalleta ta madubi yace " kinsan gidan?" tace " bazan gane ba gaskiya ban tab'a zuwa kasar nan ba sai jiya." Juya kai yai yace " bana tunanin na tambayeki ko kin tab'a zuwa." Tace " What? Kai wai wani irin mutum ne da ba'a iya maganar mutunci dashi?." Jalal bai amsa mata ba ya d'aga waya ya kira Sagir nan yamai kwatance, sun kusa isa gidan Jalal ya kalleta ta madubi a ranshi yace da alama bata tab'a shan wahala irin ta yau ba, dan yaga harta fuskarta ta canza. Ajiyar zuciya yai, shi kanshi yasan yayi laifi, Seemah ce ta katseshi da cewa dafatan ka fahimci kwatancen na gaji da wannan zirga_zirgan. Jalal ya kalleta yace " to ko ke zaki zo ki jamu?" Tace ni driver ce? In fact ni ko mota ban tab'a tunanin koya ba." Jalal yace " karki kuskura kisa a ranki wai d'an na ja ki a mota kina baya yana nufin nid'in driver d'inkine, sai dai hakan na nufin banasan zama guri d'aya......." Katseshi tai tare da murgud'a baki tace " whatever banasan jin komai nidai ka kaini gida." Jalal yad'anyi murmushi daga gefe sannan yai kwana, suna zuwa kofar gidan yai parking tare da juyowa ya mik'a mata key, ta amsa tare da kallan gidan, jitai yace " badai bakisan inda kika kwana ba?" Hararsa tai tare da d'an murgud'a baki kad'an tace " ce maka akai ban gane ba?" Kofa ya bud'e batare da ya amsa mata ba ya juya ya fara tafiya, da sauri ta fito tare da cewa *JAL* cike da mamaki ya juyo jal? Meke nan? Daga inda yake yace " Jal? Da wa kike?" Cikin wata murya tace " bazan iya fad'an sunan duka ba yamin yawa." Murmushi yai kad'an yace " waya fad'a miki sunana? Kuma ni sunana in baza'a fad'a duka ba banaji zan iya amsawa." Tad'an tab'e baki tace " ka ce baka da kud'i dame zaka karasa gida to?" Yace " Don't tell me u are worried about me? " Tace " wa? Ni? Allah ya sauwake." Juyawa yai yacigaba da tafiya kawai yasamu kansa da murmushi. Itama murmushin tai sannan tai knocking. ........ ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Habib kam yakasa zaune ya kasa tsaye ko ruwa ya kasa sha masifa kuwa farida harta gaji itada Aisha, kowa yai jugum banda waya ba abinda yakeyi. Mai gadi na bud'ewa cikin mamaki ya kalleta yace " kamar Hajiya ko?" Seemah tace nice, nan ya bud'e mata yana cewa ina kika shiga Hajiya sai cigiyarki ake. Bata amsa mai ba tai cikin gida, tana shiga ta murd'a kofar a hankali, tare da turawa, dukansu sun kurama kofar ido suna san suga wanene, ga mamakinsu Seemah ce ta shigo, da gudu Habib ya karasa cikin tsananin mamaki, yana zuwa ya rungumeta, ya shiga tambayarta Seemah ina kika shiga? Kinsan yanayin da kika sani? D'agowa yai ya kalleta yaganta tana lumshe ido, yace Seema are u alright? Kafin ya kara cewa wani abun yaga tayi baya luuu ta fad'i. Farida ta taho da gudu nan suka shiga jijigata, Habib yace a k'ira likita. Sun kaita d'akin sun kwantar, Aisha taji wayar Seemah na kara, karasawa tai ta d'au wayar gani tai ansa *Special Bros* d'agawa tai jitai ance "Seemah na wato kinzo gun yaya kin manta dani ko?" Aisha a hankali tace ba ita bace, Ammar da mamaki yace " waye? Ina Seeman?" Aisha tace "hmm ta shiga toilet zan fad'a mata inta fito." Yace alright yana kai nan ya kashe wayar. Aisha tabi wayar da kallo ba shakka anaji da yarinyarnan kod'an yanda taga yaya Habib yayi. By *AYUSHER MOHD* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* NO 9⃣ Waya ta d'aga ta k'ira Ammar yana d'agawa cikin shagwab'a tace "yaya!!!!" Cikin rud'ewa ya tambayeta " Seemah menene? Waya tab'amin ke?" Takara shagwab'ewa tace " yaya an wulakantani yau." " waya isa ya wulakanta min ke kanwata? Banaji an haifeshi, kinaso yayanki yazo yad'au hukunci?" Ammar yai maganar cikin b'acin rai. Seemah tasa dariya tace " Kai yaya ni kainan inajin dad'in kasancewa kanwarka, amma a yau inaji amai uzuri amma in har ya sake zan fad'ama kad'au min mataki." Shima dariyar yai yace " kin hucce?" D'aga kai tai kamar yana ganinta tace " sosai ma." Hira sukai tayi sai dayaga ta ware sosai sannan sukai sallama. Murmushi tabi wayar dashi sannan ta koma ta zauna a kan kujera. Seemah kwafa tai sannan ta leko ta k'ira Sagir, tace zo kasamin number office d'insu abokinka, ta fad'a tana nuna landline na office d'in, Sagir ya karaso ya nuna mata tace tnx, yana fita ta kira number. Manager d'insu ya d'aga tare da tambaya, Seemah tace " daga office d'in chairman ne, inaso a turomin Jalal yanzun nan." Tana kainan ta kashe. Cike da mamaki manager d'in yabi wayar da kallo, Jalal? Jalal kam ya dad'e agun kafin ya d'aure ya sauko, sai dai yana zuwa office d'insu Manager d'in yace " kaikuma ina ka shiga?" Jalal yace na d'an fita ne, "Kayi sauri ana nemanka a office d'in Chairman." Manager d'in yai maganar yana kallansa. Gaban Jalal ne ya fad'i sai dai bai bari Manager d'in ya gane ba kawai ya juya ya fita, yana zuwa ya bude kofar tare da kallan Sagir, yace " Ana k'irana ko?" Sagir yace bari in sanar sai ka shiga. Nan ya mik'e daga mazauninshi yai knocking office d'in, Seemah ta bada izini ya shiga ya sanar mata yazo, tace ya shigo, nan ya juya ya fita. Kallan Jalal yai yace " ka shiga." A hankali Jalal ya karasa yai knocking ta bashi izini ya shiga da sallama, Seemah na tsaye jikin window tana kallan waje kallanta yai da mamaki yace " ke kika kirani?" Juyowa tai tare da yin murmushi tace " ayya shikenan ma je ka." Jalal da mamaki ya kalleta bangane ba. Kallansa tai tace " nace ka tafi na fasa." Cikin b'acin rai ya fito tare da bugo kofar da karfi, ko Sagir bai kallaba ya juya ya fita, yana koma wa office d'insu ya sake had'uwa da Manager a kofar office d'in yace " Jalal kayi sauri Madam tace ka koma." Jalal ya kalleshi yace " daga gunta fa nake tace in komo." Yace " kayi hakuri ka koma tace lalai kaje yanzu." Jalal cikin mugun takaici ya koma, yana zuwa ko Sagir bai jira ya neman mai izini ba ya bud'e kofar ya shiga, tana tsaye jikin fridge d'in office d'in tana shan ruwa, ta juyo tace ka koma na fasa, Jalal ya kalleta wani takaici ya kamashi karasawa kusa da ita tare da fizge jarkar ya ajiye sannan cikin b'acin rai ya kalleta yace " am I a joke?" Kallansa tai tace " bakaga ruwa nake sha ba?" Jalal ya nunata da yatsa ya kara matsowa kusa da ita yace " bazan d'auki wannan rainin hankalin ba d'an haka don't you dare repeat that to me." Yana gamawa ya juya zai fita. Hannunshi ta kamo tace " ka manta ni kanwar mai Company d'in ce?" Yace " if u need respect then act right." Sannan ya juyo yace " Sakeni in tafi ko?" Tace " waya baka damar tafiya?" Tafad'a tana hararsa. Ya juya tare da fizge hannunsa sannan yace " ni naba kaina." Yana kainan ya fita da sauri, kallansa tai da mamaki sai ta sami kanta da sakin wani sansanyar murmushi, sai kuma can tace "Not Bad." Nikam Ayusher nace mefa? Jalal ya fito cikin takaici ya karasa office d'insu sai da abinda yakara d'aure mai kai Manager ya kara gani a tsaye a kofar, yace lafiya? Manager yace " ance in kaika da kaina, d'an haka wuce muje." Jalal ya kalleshi yace ina? Hannunsa manager d'in ya kama suka fara tafiya, Jalal ya kwace hannunsa yace itace dai? A hankali Manager ya d'aga kansa alamar eh, Jalal yace zanje da kaina, nan ya fara tafiya yagama shirya yawan rashin mutuncin dazai kwara mata. Da karfi ya bud'e kofar ko sallama baiyi ba, sai dai me? Habib ya gani zaune a kujerar sa Seemah na tsaye tana waya jikinsa ne yai sanyi a hankali yace "am sorry." Habib ya kalli Seemah dake ta shagwab'a a waya, Jalal kam takaicin yanda take shagwab'a yakeyi amma da alama ko saurayinta ne, sai dai jin tace " Dad sai anjima." Yasa ya d'ago, Dad? Maganar Habib ce ta katseshi dayace " Seemah wannan ne?" Seemah ta kalli Jalal tace eh yaya please. Habib ya kalleshi yace " d'an Allah so nake ka taimakamin, kanwata ce kesan zuwa yin shopping to nikuma inada aikin yi shine tace tanaso kad'an kaita." Jalal da mamaki ya kalli Seemah ya mata kallan jiya baki daddara ba ko? Baki ta murgud'amai tace " ni yaya dama shi ka bani a matsayin driver na." Wani kallo da Jalal ya watsa mata ba ita ba har Habib sai dayasha jinin jikinsa, ganin yanda ya kafeta da ido yasa ta had'iyi wani yawo tace" Wasa nakeyi maida wukar." Habib ya d'an kakaro dariya yace " karka damu akwaita da tsokana, she is just joking." Sai a lokacin Jalal yad'auke idanunsa, sannan yace " yau ne kad'ai zan kaita ko?" Habib ya d'aga kai yace yau ne kad'ai, in ka kaita ka karasa da ita gida, Jalal yace to sannan ya kalleta yace " muje ko Madam?" Seemah ta anshi key sannan ta fito. Sunje shiga mota Seemah harta bud'e baya Jalal ya sa hannu ya fizgota ya sata a gaba sannan ya rufe shima ya shiga, kallansa tai tace " meye hakan kuma?" Jalal yace tambaya kike? Batace komak ba kawai ta juya kanta tana kallan window, Jalal ya tada mota sun d'an fara tafiya tace " wato bazaka bani hakuri ba ko?" Jalal ya kalleta yace " laifin menai dazan baki hakuri? Bakya tunanin ke zaki bani?" Juyowa tai tace " kamanta me kamin ne?" Jalal ya saki murmushi yace " au duk wannan abun da kikemin so kike in baki hakuri?" Ta d'an turo baki tace " eh mana, kuma inaso kabani yanzu." Jalal yace " lalai kin da aiki a gabanki." Tace sai in taka burk'i yanzu, ko in bud'e kofar motar, uhmmm ko insa ihu in ma sharri. Ga mamakinta dariya taga Jalal yasa abinda bata tab'a gani ba, dariya sosai yai, sannan ya kalleta yace ko zaki gwada? Ganin yanda take kallansa yace " kallan fa?" Ta kifta ido tace " dama kana dariya?" Da sauri ya had'e rai yace " baki gani daidai bane, ba dariya nai ba." Seemah tai murmushi tace "yau naga side d'inka kala kala, d'azu ka makamin kallo kamar zaka dakeni yanzu kuma dariya?" Jalal ya had'e rai ya cigaba da tuk'insa, Seemah ma shiru tai sai dai murmushi bai bar fuskarta ba...... © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No. 1⃣2⃣ Habib kam sam jiyai gidan ya isheshi hakan yasa yace zasu wuce, sun musu sallama sannan suka fito, harsun zauna a mota yaga yanda idan Seemah ya kad'a yai jaa kawai ya bud'e motar ya koma ciki, suna zaune sunyi tagume sallamar Habib ne ya katsesu, da sauri suka mik'e suka fito. Habib yace " har na shiga mota naga kamar ya kamata inji menene dalilinku na k'in sakema Seemah?ko d'an bata tab'a zuwa ba sai yau?" Kawo yai saurin cewa shine dalili yaza'ayi ace sai yau zata tab'a zuwa gaidamu? Kallansa Habib yai bayajin zuciyarsa ta gamsu da maganar saidai tunda sunce hakan yace " ayya amma kawo kasan ba laifinta bane Dad ne yake hanata zuwa." Hajiya tace to jeka ku tafi ko ka manta kanada aiki ne? Nan Habib ya juyo ya shiga mota, dad'insa d'aya yana shiga yaganta tana waya da Ammar sai dariya take, hakan yasashi dariya, sun fara tafiya shima yanata janta da hira, bayan sun shiga Abuja ne ta kalleshi tace "yaya muje Company sai anjima sai in koma gida." Yace "shikenan dama yau driver d'inki zaizo sai yazo ya d'aukeki" Murmushi tasaki a ranta tace Jal we will meet again. Suna isa Company d'in Sagir yazo ya sanar ma habib akwai meeting dazasuyi yanzu, nan ya kalli Seemah yace kije office d'ina tace to nan ya juya a hankali tace Sagir? Juyowa yai yazo kusa da ita, tace " ina Abokink?" Cike da mamaki ya kalleta? Yace wa kenan? kallansa tai batare datace komai ba hakan yasa yace Jalal? Ta had'e rai tace " yana ina? D'an yau sai na zabgamai rashin mutunci. Kai ya jinjina yace hmm yana office a k'irashi ne?, tad'an juya kai tace inane office d'in ku ba meeting zaku shiga ba? Nuna min kawai. Yace a third floor yake kina shiga daga hagu zakiga Department d'insu, tace ok ta juya tai gaba, Sagir yace " Yau kuma wani fad'an za'ayi?" Elevator ta hau ganin ba kowa yasa tad'an fito da madubi daga jakarta tad'an duba fuskarta murmushi tai sannan tad'an sa janbaki kad'an tace " yau sai ka kasa ganeni." Tana isa tai inda akace tare da murd'a kofar tai sallama, office ne babba sai dai kowa da desk d'inshi sai gurin da aka kewaye ma manager, sunajin sallamar suka juyo gaba d'aya suka zuba mata ido, kallansu ta shiga yi sai dai bataga Jalal ba, karasawa tai ciki tace " Jalal nake nema?" Wani ya matso kusa da ita yace ga desk d'inshi nan ya fita inaji ko kasa yaje submitting d'in proposal. Desk d'in ta kalla sannan tace bari na jirashi, karasawa tai ta zauna a inda yake zama tare da bud'e takardun dake gun, kowa sai kallanta yakeyi, manager d'inne ya fito ganin Seemah yasa ya karasa da sauri yace " Ranki ya dad'e me kikeso? Ai da baki zo ba kin turo kawai." Had'e rai tai tace " inasan ganin Jalal ne d'an yau banajin zan iya kyaleshi." Yawo ya had'iya aransa yace Jalal me kayi? A fili yace " ayi hakuri Madam......." Katseshi tai tace " asa a k'irashi yanzun nan." Nan ya fita da sauri yai waje, Seemah ta kalli ragowar tace " kucigaba da aikinku." Wata mace ce tad'an matso kusa da ita tace " laifin me ya mik'i? Naji dad'i da kikace zaki hukuntashi dama haushi yake bani, farkon zuwa na ina bala'in san mutumin nan har abinci nake zama a gida in had'omai sai dai duk wannan wahalar danake bazai ci abincin ba kuma baya kulani, rannan ma ba ka ra yacemin bayasona." Seemah ta saki dariya tace " ke meya kaiki san wanda baya sanki? Ai kece mak kuskuren ba wani ba." Haushi ya kama matar ta juya ta zauna a ranta tace " Allah yasa kema kiyayyace ba so kike masa ba." ☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Jalal ne ya shigo da sauri yana neman me nansa, kallan kowa ya shiga yi yaga suna nunamai desk d'insa karasawa yai desk d'in d'an baya gano kowaye tunda ta juya kujerar baya tana game, jin sallamar Jalal yasa ta kashe game d'in tana jiran k'arasowarsa. Jala mamaki yake wani rik'eken ne wannan? yana zuwa gun yace " excuse me" Seemah ta juyo da kujerar ta cik'e da mamaki ya kalleta yace " You?" Gira yad'agamai sannan ta mik'e tare da had'e rai tace " Follow me." Tana kainan tai waje, hartaje kofa taga bashi da niyyar tahowa haushi ya kamata ta juyo tazo inda yake cikin magana mai rad'a tace " so kake in jaka da kaina?" Yace muje. Sun fito ta kalleshi tace " kar mutane suganmu ka sameni a gun jiya rooftop, tana kainan ta wuce. Iska ya furzar yace " Ahh wannan tagama rainani, me? In sameki a ina?" Sai a lokacin ma yabi bayanta da kallo, atamfa? Shi da sam bai kula bama, daga kanta yafara kallanta har kan takalmin datasa mai tsini sosai, tayi kyau sosai, wani b'angare na zuciyarsa ya fad'a da sauri ya girgiza kai sannan ya wuce shima. Ta rigashi isa hakan yasa ta karasan can bango tana kallan kasan titi yanda motoci suke wucewa, Jalal ne ya bud'e kofar tare da kallan inda take tsaye murmushi yai sannan ya karasa gun, gefenta kad'an yaje ya tsaya, batare da ta kalleshi ba tace " a haka mutum sai yaga kamar kowa na duniya yana cikin kwanciyar hankali." Kallanta yai sannan ya kalli kasa yace " a binda mutum yake gani daga nesa dama haka yake ai sai kiga kamar kowa yana walwala, amma me ya kawo ki office d'inmu?" Juyowa tai ta kalleshi sannan tace " ya kagan ni?" Kallanta yai kad'an sannan yad'auke kai yace " bangane yaran ba?" Leb'enta tad'an ciza sannan tace " kalleni da kyau ka gani baka ga komai ba?" " Banga komai ba, akwai abinda yakamata in gani ne?" Ya fad'a yana kallanta. Haushi ya kamata ta juya cikin fishi zata wuce tsinin takalminta ne ya shige d'an rami tai wala wala zata fad'i da sauri yasa hannu ya tarbota kallan juna suka fara, Seemah kam zuciyarya sai duka take, kallanta yai sannan yace " da saninki ko? So kike in tare ki." Harararshi tai tace " nina saka?" Baya yai da ita kamar zai saketa, kara tad'an saki yace " au ashe kina tsoro." Cikin shagwab'a tace " da yarda ni zakai?" Kai ya rangwab'ar yace " sai in yadda ke indai baki fad'amin me zan gani ba." Hannu tasa ta rufe idanta a hankali tace bakaga kayan danasa ba? D'agota yai ta tsaya daidai sannan ya juya ya kalli titi yace " au sai yanzu na kula ai." Haushi ya kamata tace " hakama zakace?" " a ina kika ari kaya? D'an a yadda kika nuna baki da wani kayan hausawa sannan jiya kika siyo naki nasan a k'ala baza........" Zuciya ta kawo mata wuya jakarta ta d'aga ta kwad'a mai a kafa, tace " kace ka gani ko yamin kyau shine bazaka iya ba? Gwara ka cimin mutunci?" Juyowa yai yace zan iya tafiya? Haushi yakara kamata tace kabar kasar ma, Juyowa yai zai tafi sai dayaje kusada kofar fita ya juyo yace " kayan kasarmu sunfi miki kyau." Yana kainan ya fita, kallan kofar tai sannan tai murmushi tace " kafad'i hakan tun d'azu shine bazaka iya ba?" Baki ta murgud'a sannan ta juya ta cigaba da kallan titi tana kallo tana murmushi. ..... © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* NO8⃣ Likita yazo ya dubata, wahalace kawai da yunwa suka had'un mata nan ya bata magani ya tafi, Habib ya kalli wayarsa dake ka ra yai shiru ya rasa mai zaice d'an tun rana Dad ke k'iransa akan yaji Seemah shiru, yanason lale abashi 'yarsa suyi magana. Kallanta yai sannan ya kalli wayar, jiyai ance " Dad ne ko?" Habib ya kalli Seemah yace " eh" hannu ta mik'amai ya bata wayar daga kwance ta d'aga wayar tare da cewa " Dad d'ina." Dad yace " Princess ina kika shiga? Bayan tun rama nake nemanki, sannan ya naji muryarki haka?" Da sauri tace " Dad bacci fa nakeyi yaya ya tasheni." " Ayya kiyi hak'uri ban sani ba, tunda naji muryarki yanzu mayi waya da safe." Dad ya fad'a cike da namaki ganin seemah ba baccin wuri takeyi ba. Seemah tace "to Dad nyt, love u." Tana kai nan ta kashe wayar tare da sakin ajiyar zuciya. Habib ya kalleta yace " Bari a kawo miki abinci." Kafin ya mik'e Farida ta shigo d'auke ta tire ta ajiye kusa da Seemah tace " Seemah tashi kid'an ci wani abun." Habib ya taimaka mata ta zauna, Farida ta zuba mata nan tafara ci, tad'anci dayawa kafin tace ta koshi, Farida ta zuba mata juice ta sha sannan tajingina. Habib ya kalleta yace " Seemah meta faru wai?ance da wani kuka tafi, waye shi?" Tai ajiyar zuciya tace " Yaya irin wannan tambaya?" Habib ya had'e rai sosai yace " ki fad'amin wanene in ba haka ba indai nai bincike da kaina, banajin zan barshi haka." Shiru tai can tace " nima ban sanshi ba yaya, kawai dai da Aisha takusan kad'ashi ne na fita bashi hakuri sai yake cemin kamar jiya ya ganni a Company d'in dayake aiki, nikuma ganin a Company d'inka yake aiki yasa nace ya karasa dani shine yai wani gurin dani." Habin ya mik'e cikin b'acin rai yace " ki kwanta ki huta gobe karfe 10 zansa a d'aukoki ki duba kaf ma'aikatan Company d'in ki nuna min shi." Gaban Seemah ya fad'i a hankali tace to yaya. Nan ya juya ya fita ta bishi da kallo, itakam menene nata na kare Jal? Meyasa batasan asan shine? Mik'ewa tai ta shiga toilet tai alwalata dawo ta tada Sallah, bayan ta idar ne ta mik'e ta hau gado, Aisha ce ta kalleta tace Sannu Seemah, sannan d'azu Special Bros ya k'iraki, da sauri ta d'au waya ganin missed call 40 ta duba duk yayinta 3 sun nemeta da kuma dad sai dai na yaya habib yafi yawa tunda shi kad'ai yasan meke faruwa, layin Ammar ta d'anna, ringing 2 yad'aga ta saki murmushi tare da cewa" Oppa ya? Da alama yau kayi missing d'in kanwarka dayawa." Murmushi yai yace " Seemah kinsan dai bana jure rashinki ko? Sanda na tafi South Korea wani Conference sau nawa muke waya dake?" Dariya tai tace " Kai yaya wayar fa damukeyi yawanci ni nafi nemanka." "Seemah ni dai banasan haka daga yau na k'ayade mana waya sau 8 a rana, ni zan k'ira sau biyar ke ki k'ira sau 3 duk wanda yai missing k'ira ko d'auka zai biya kud'i." Dariya sosai tayi tace " shikenan yaya deal?" Yace deal. Sun dad'e suna waya Aisha dake kwance tanata mamaki wannan dabad'an yayanta bane lalai sai ta ce su masoyane. 《《《《《《《《《《《《 Seemah ta kwanta bacci tad'ade kafin tai baccin sam ta rasa meke damunta, sai dai 1 thing is cleared sai tai ta hango Jalal sanda yana tsaye a waje ita kuma tana mota, bargo taja ta rufe kanta gaba d'aya sai dai duk da haka ta sake ganinshi yaye bargon tai sannan ta d'an sa ihu kad'an tace " Frustration! !!!!! Yau kuma meke damuna? Can tace nama gane, tsabar tsanar dana mai ne." Tadad'e bata bacci ba sai can ya sace ta. ♢♢♢♢♢♢♢♢♢ 9 ta tashi tai wanka tasa kayanta, yau doguwa ce rigar sai dai ta kanti ce mai bin jiki ta d'auko har zata fito sai kuma ta koma ta cire ta kara duba akwatinta, riga da wando ta d'auko na pakistan da yaya junaid ya siyo mata dayaje india tasa tare da yafa mayafin, tayi kyau sosai. Ta sauko kasa ta taradda Aunty Farida kad'ai nan tai breakfast ko tambayar Aisha batai ba, kafin ta gama har driver yazo, Nan sukai sallama da Farida ta fita. Suna isa company d'in ta sauko a hankali, Habib tagani a tsaye mamaki ya kamata a hankali ta karasa, sai dai abinda yabata mamaki tun daga cikin bakin kofar company d'in mutane suka jeru, ajiyar zuciya gai takarasa gun habib, yace " muje ki duba ga kananan ma'aikata anan manyan kuma na inda muke meeting." kallan yaya tai a hankali tace to. Sun fara dubawa tana tafe yana binta a baya, sai kallan mutane takeyi, kowa tagani tace bashi bane, sai da suka zo kusan karshe, idanunsu ya had'u da Jalal, kallan juna sukai ta kuramai ido mamakinta babu alamar tsoro a idanunsa, jitai Habib yace " Shine?" Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, mamakine ya kama Jalal da sagir, me take nufi? Jitai Jalal yace ki kara dubawa dai. Yawo ta had'iya sannan ta kalleshi ta wuce na gaba dashi, har taje karshe tace ba kowa, nan sukai hanyar inda manya suke, ba shakka sunji haushin wannan rainin hankalin, wai an tarasu saboda wata 'yar yarinya, Seemah ta duba nan ma tace ba kowa, Habib yai shiru can ya kalli Sagir yace kaita office ni zamuyi meeting. Suna fitowa suka had'u da Jalal, ya matso kusa dasu kad'an yace " Follow me. " Tad'an harareshi tace dalili? Yace " karki b'atan rai ki biyoni ko?" Nan ta kalli sagir tace ina zuwa. Elevator ya bud'e ya shiga itama ta shiga, sun yi shiru har suka isa last foor suna zuwa ya karasa sama itama ta bishi, saman ba komai a gun sai flowers da kujeru, suna shiga gun Jalal ya kalleta da karfi yace " What are you doing? " Seemah ta kalleshi da mamaki tace " haka zaka cemin?" Jalal ya matso daf da ita tad'anyi baya ya bita sai da sukaje jikin bango yasa hannu d'aya a jikin bangon, tsoro ya fara kamata, Jalal cikin b'acin rai yace " Do you find me pitiful? Don't tell me kinaso in miki godiya akan abinda kike tunanin kinmin." Cike da mamaki da takaici tasa hannu ta ture hannunshi zuciya tazo mata wuya, ta d'unkule hannunta ta kaima duka a kirji cikin takaici da hawaye tace " haka kake? Me yasa bazaka duba alkairin mutum ba? Sai ka d'inga kok'arin juya alkairi zuwa sharri." Ta had'iye wani abun sannan ta cigaba, "you don't want me to pity you? Ko kuwa kana tunanin kafi karfin hakan?" Tai shiru tarasa me zatace juyawa tai kawai tai ta wuce. Jalal ya bita da kallo yarasa me yasa yakejin zuciyarshi ba dad'i, zama yai a gun tare da dafe kai..... Seemah kam da gudu ta karasa elevator tana shiga ta tsugunna a ciki tasa kuka mai ban tausayi, can wata zuciyar tace me kikema kuka? Mik'ewa tai da sauri ganin har sun zo, office d'in Habib ta wuce, Sagir ganin fuskarta yasan Jalal ya b'ata mata rai. Seemah na shiga ta rufe kofar tare da jingina da kofar idanta na zubar da hawaye............ Na *Ayusher Mohd* © *NWA* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No. 1⃣0⃣ Can Jalal yace " me zaki siya wai? Dakika sani na taso?" Kallansa tai sannan tace " so nake nima na fara shiga irin ta kasata, d'an naga alama wasu kallan 'yar iska sukemin, wasu ma harda cewa......." Kallanta dayai yasa ta kasa karasa maganar, baisan sanda ya saki wani murmushi ba, jitai zuciyarta ta buga, da sauri ta d'auke kanta tace " ehem, Jal me kakema dariya?" Kallanta yakarayi da murmushi a fuskarsa yace " da alama kin k'ulaceni." Baki ta turo ta d'an harareshi tace " ina tausaya yama matarka, zatai fama." Jalal ya had'e rai yace " waya baki pass d'in hirar matata? Bayan b'an yarje miki ba?" Kallanshi tai cikin b'acin rai ta kafeshi da ido, wayarsa datake kara ya d'aga ganin ansa Zainab yasa ya d'aga da sauri. Seemah da itama taga sunan jiki yasa ta juya kai jikin window da sauri ta had'iyi wani yawu tarasa dalilin ta najin ba dadi. Jalal ya d'aga wayar tare da amsa sallamar da akamai, ya cigaba" Zainab ya akai? Jikin Zaheedan ne?" Cikin sanyin muryarta ta amsa "a'a yaya k'ira nai inji jiya ya ka isa Abuja?" Yace " Lfy lau Alhamdulila, Abba fa?" Tace " ya fita d'azu." Jalal yace " keda ba kud'i kike dashi ba me makon kimin flashing?amma bari na kashe zan turo miki kati yanzu." Godiya tai sosai nan sukai sallama. Seemah kam tanajinsu, da sauri ta juyo tace " kanada aure ne?" Jalal ya kalleta yace " meya dameki in inadashi ko bani dashi?" Itama ta had'e rai tace " me kuwa ya dameni, tausayin ta kawai nakeyi, kuma in kasan bata da kud'i a waya meyasa tun farko ka d'auka? Sai ka kashe sai ka k'irata kai kuma." Jalal ya karasa gefen titi yai parking, yace " ina zan kaiki? Kim barni sai tafiya nake, kinzo kina shiga abinda bana tunanin ya shafeki." Kallansa tai ta tab'e baki sannan tace " nasan garin ne? Ka kaini inda zan sai kayan kasar mu." Girgiza kai Jalal yai yace " to ai banaji matata ce zatai fama dani, da alama kece za'ai fama dake." Cikin shagwab'a da b'acin rai tace " *YOU?*" Jalal yace " What? " juyawa tai kamar tai kuka, kara girgiza kai yai yace tab lalai....... Wuse Zone ya wuce, ya shiga Bengari Street, a Sahad Store yai parkin, ta d'aga kai ta kalli store d'in, yace " sai kin fito, kuma karki kuskura ki shanyani a waje." Kallansa tai ciki da mamaki tace "au ni kad'ai zan shiga?" Jalal yace " da ni ne mai siyan kayan? " leb'enta ta ciza idanta ya ciko tace " wai kai wani irin mutum ne? Yama za'ayi ka cusa mace cikin shagon da bata tab'a zuwa ba kuma ita kad'ai?" Kallanta yai yace " a tunanina kawo ki kikace inyi bawai in rakaki siyayya ba?" A zuciye ta fito daga motar tare da rufo kofar da karfi, ta fara tafiya, murmushi yai sannan shima ya fito tare da rufe motar, a baya ya bita. Seemah kam ran nan nata a had'e take tafiya tana shiga taja shopping cart tafara tafiya, jitai ance bana zakiyi ba, dasauri ta juya jin muryar Jalal cikin shagwab'a tace " Jal da saninka kenan?" Bai kulataba yafa tafiya, binshi tai tana tafe tana smiling, sunje wajen atamfofi dasu shadda da lesuka nan ta fara zab'a kallan Jalal tai dake tsaye yana danna waya, karasawa tai gunsa tace " Jal tayani zab'a." kallanta yai sannan ya cigaba da kallan wayarsa yace " ina duba time ne, minti 30 na baki ki gama zab'a minti 10 ki biya kud'i minti 5 mu koma mota minti 15 ta maidamu, so nake in koma office a cikin 1hr." Kallan mamaki Seemah tamai a ranta tace harda wani lissafi? Hmm aikuwa zakaga 1hr. Juyawa tai batare da ta kara magana ba, a hankali take duba kayan ta gama da kaya sannan ta kalleshi tace " inasan turaruka da kayan makeup," Agoggon hannunsa yaduba yace " kinfa cinye time d'inki anan." Tace "to ko in k'ira yaya ya nemarmin izinin wasu lokutan?" Juyawa yai yace biyoni... Nan ta fara binshi tana murmushin mugunta, juyawa tai taga yawanci maza ne ke jan cart d'in hakan yasa kawai tad'ansa kara kad'an tare da tsugunnawa, da sauri Jalal ya juyo yace lafiya? Kallansa tai tare da kallan kafarta data rik'e, ya kalleta yace bigewa kikai? Kai tad'aga tace " eh, sam bankula ba ina kallan wani abun na bige." Jalal ya matso tare da cewa " ke da kika taso a England har akwai abinda zai sa ki kallansa har ki bige baki kula ba?" Kasa tai da idanta, yace to tashi muje kima b'ata min tym, mik'ewa tai irin da kyar d'in nan yace muje to, har ya fara tafiya tace Jal? Cikin b'acin rai ya juyo da masifa yace " sunana wai kenan?" Kallansa tai ta kalli cart d'in tace " bazan iya ja ba." Oh God!!!!! Jalal ya fad'a sannan ya karaso tare da ansa ya fara turawa, jitai dariya na neman ka mata haka ta d'aure tana d'an d'ingisa kafa, ta gama siyayyarta sai dai Jalal ya kullu sosai ganin a siyayya sai data kai 1hr, sunje gurin biyan kud'i ta mik'a Atm, Jalal kam kallan uban kayan data siya yake sai dai in ya tina yayanta waye sai yaga ba komai bane. Sun fito Jalal rik'e da ledoji sukasa a booth, Jalal ya kalleta yace shiga muje, ga mamakinsa gani yai bata d'ingishi, kallanta yai harta shige mota inda ta zauna d'azu, a ranshi yace ni kikai fooling? Kwafa yai sannan ya shiga shima. Baice mata komai ba sai dai fara tuk'i dayai, basuyi tafiya mai nisa ba yaga wani asibiti, gangarawa wa yai tare da yin parking a asibitin, Seemah da mamaki ta kalli asibitin tace" baka jin dad'i ne?" Murmushin mugunta yai yace muje, kallansa tai tace harda ni? Nifa banasan ko shiga asibiti. Jalal yace " ni ce miki akai inasan shiga store?" Jin haka yasa ta bud'e motar a hankali ta fito. Suna shiga akace sai sun sai kati, Jalal yace muna d'an sauri ne ba likita zamu gani ba allura kawai za'a mata ta tetanus, nan aka nuna masa inda nurses suke, ya kalleta tare da mata alama da hannu, suna shiga ya kalli nurses d'in yace " bata d'an ji dad'i bane, ba big'e da karfe ne shine nake tunanin ko da abinda za'a mata ko allura ne." Seemah da sauri cikin tsoro ta kalleshi, ba abinda ta tsana irin allura, cikin in ina tace " ahh ah ba big'e wa nai ba takalminane yad'en bugeni kad'an."nurse d'in tace " matso mu duba" ai tanajin haka ta fara baya baya, Idanunta suka kad'a Jalal ta kalla tace " Jal mu tafi please." Ganin yanda idanta ya kad'a yasa ya kallesu yace " kuyi hakuri inajin ni na d'aukaka abin maybe ba serious bane. Tanaganin haka Seemah tai waje da sauri, Jalal ya karaso ya bud'e mota tana shiga ta d'au waya ta k'ira Ammar, yad'aga tare da cewa " Seemah na ya kke? Yau naji dad'i ana kirana." Kallan Jalal tai sannan ta sa hannu tasa wayar a hand's free tace " Yaya Ammar saura kad'an yau a min allura." Daga can b'an garen cikin tashin hankali Ammar yace " Seemah waya isa yasa a miki allura bayan bakyaso? Me ma yasameki? Ya Habib ne?" Kallan Jalal tai tace " bashi bane wani d'an gadara ne." Ammar yace " Seemah anya ana kula dake yanda ya kamata kuwa? Anya bazanzo dakaina ba? Ko kuma ke ki dawo ba?" Jalal ta kalla da ya kafe ta da wani mugun kallomaka, ta murgud'a mai baku tacigaba" karka damu yayana I will take care of myself. " tana kai nan ta kashe ta kalli Jalal tace "what? Ka kaini asibiti a min allura? Shiyasa na nuna maka matsayina, banaji yayuna in sukaji me kamin zasu kyaleka tun balle wanda mukai waya dashi yanzu. Jalal ya kalleta yace " da alama baki daddara ba kenan, har ni zakima pretending? Kisani aiki?" Dariya ne ya kamata auuuu yanzu tasan dalili, darita tasa sosai, Jalal ya saki baki yana kallanta, tad'an tsagaita tace "ohhhh dama haka ne?" yace " Do u just laugh at me? " Dariya tasakeyi tace " au sorry, amma yazanyi dariya kake bani." Jalal ya furzar da wani iska yace " mene? Dariya nake baki? Nid'in?" Had'iye dariya tai tace " ni ai ban gane saboda haka ka kaini asibiti ba ai, amma lalai u r really funny." Jalal jiyai kamar yasa ihu, kamar shi acemai funny? Bai kulata ba da karfi ya fizgi motar suka hau titi, Seemah a ranta tace " zakasan ni ka kai asibiti, ka gano weakness d'ina d'aya nima na gano d'aya, bakasan ama dariya nikuma banasan allura." © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No. 1⃣3⃣ Jalal na fita ya saki murmushi sannan yai hanyar office d'insu, yana shiga yaga duk sun yo kansa da mamaki ya kallesu yace "Lafiya?" Sukace " me ta maka? Korarka za'ai ko suspension za'a baka?" Tsaki yai sannan yace " kubani hanya please." Nan suka matsamai ya wuce yana zama wannan macen tazo kusa dashi tace " Sanka take ko?" Cik'e da mamaki Jalal ya d'ago ya kalleta yace " Sara baki da aiki sai gulma ko? Ke yanzu a tunaninki yarinyarnan ce zata so ni? Kedai sai ki d'inga abu ba tunani." Matsowa ta kara yi tace " kudai maza wani sa'in u are too slow, ni ai daga yanda naga tanayi nasan sanka take." Jalal ya had'e rai yace " Get lost" Matsawa tai tare da tab'e baki tai tace " Zamu gani ai." Sai dai me? Kalmar ta tsayama Jalal a rai sai nanatawa yakeyi sai dai ya girgiza kai yace " No" ○●○●○●○●○●○●○●○●○●○● Seemah kam Office d'in Habib ta koma Sagir ta gani tace " har kun gama?" Ya kalleta yanaso yaji me tama Jalal amma yana tsoro, hakan yasa yace " a'a takardu nazo d'auka." Tai gyaran murya tace " Uhmm number abokinka zaka bani." Eyyye? Sagir ya fad'a cikin tsananin mamaki, juya kai tai tace " kai banasan fassara nemansa nakeyi d'an banaji zan iya kyaleshi yaci mutuncina jiya yanzu kuma naje office d'in baya nan." Sagir yace " Au hoo na zata......." Da sauri ta katseshi tace banasan wani shirme, kada ka kuskura ka kawo komai a ranka d'an nafi karfin abinda kake tunani. Da sauri Sagir ya bata number sannan ya bata hakuri ya juya. Number ta kalla tad'an rangwab'ar da kai tace "me zan sa? Jal? Mr pride? Jerk? Kind? Ahhh so frustration." Tafad'a tare da tagumi. Ta kara kurama number ido tace me kakeso insa maka Jalal? Gefe ta kalla kawai taga Jalal ya kashe mata ido yace " *SPECIAL*? Kai ta girgiza tace noo, tana juyawa taga bayanan kai ta rik'e tace meke faruwa? Jitai anzauna kusa da ita, da sauri ta d'ago jitai Jalal ta gani, ya had'e rai yace " karki kuskura kisamin sunan mutunci kisa *Bad guy* kallansa tai sai taga bayannan, ihu tasa da karfi tare da marin fuskarta tace " I think I am going crazy." Da sauri ta ajiye wayar a gefe tana girgiza kai, jitai wayarta tayi kara ido ta runtse sannan ta d'au wayar Ammar ne hakan yasa tai ajiyar zuciya ta d'aga, Ammar yace " Swthrt Dad yace strike yakeyi tunda wai ke bakya nemanshi kullum shi yake k'iranki." Shiru tai Ammar yace Seemah? Tace " yaya da alama bani da lafiya," yace meya sameki? Ajiyar zuciya tai tace " Bakomai ina Dad d'ina?" Ammar yace ya fita ki kirashi." Tanaji haka ta katse wayar tare da kallan number Jalal da sauri tasa " No name." Ta ajiye wayar tare da shigewa cikin cinyoyinta, sai dai me? Jalal ta hango sanda ta kusa fad'uwa ya tarota, bud'e idanta tai da sauri tare da d'aukan waya ta k'irashi. Jalal na zaune yaga new number, hakan yasa yad'aga tare da sallama a sanyaye, Seemah najin muryarsa ta kasa magana Jalal nata hello? Hello? Hello? Jin shiru yasa ya katse, kallam wayar tai tace lafiyata kalau fa na fito daga gida, d'an haka dolene in k'irashi inji meyamin nazama haka. Kara k'iranshi tai nan ma takasa magana ya k'ara kashewa tare da sakin tsaki yace network ne ko iskancin mutane?. Yana ajiye wayar aka sake k'ira sai data kusa katsewa ya d'aga tare da fita daga office d'in yace " wai meye hakan? In baza'ai magana ba meye dalilin k'iran?" Har zai katse yaji ance " wato kai haka Allah yayika baka da hakuri ko?" Cike da mamaki yace "Seemah?" Murmushi tai tace " Suprise!!!" Da mamaki yace a ina kika sami number ta? Tab'e baki tai tace " Agun Sagir na ansa saboda in ina nemane kaini wani gurin karnasha wahala." Cike da masifa yace " What? Inkina neman me?" Katse wayar tai sannan tace " bana cikin hankali na, me zanyi da mutum irin wannan?" Jitai ance Seemah me kike a kasa? Da sauri ta kalli Habib tace yaya ka dawo? Tafad'a tare da mik'e wa. Yace" na dawo, zaki gida ne?" Tace eh yace ok bari na k'ira driver d'in..... Jalal kam wayar yabi da kallo yace " meke nan? Wai ni meyasa yarinyar nan ta gama rainani? Shine har waccen zatace me? So? Yarinya ta gama rainan hankali lalai ina bukatar seta ta." Yama kainan ya juya ciki..... °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Sun fito itada Habib ya kalleta yace " Seemah badai abinda ya faro a Suleja bane yake damunki?" Kallansa tai tare da sakin murmushi tace " basu da laifi yaya, ace ina jikarsu amma ko sau d'aya ko a waya ban tab'a k'iransu bafa shekara 20 kenan fa." Habib yai shiru shidai har ga Allah bai yadda wai rashin zuwantane yasasu haka ba, tabbas akwai wani abu zai k'ira Dad...... Seemah ce ta katseshi da cewa "Yaya karfa kafad'ama Dad kasan yamda yake ji dani bazaiji dad'i ba." Ya kalleta yace to seemah. Ta shiga mota, suka fara tafiya wak'ar Kabhi Kushi Khabi Gam ke tashi a motar, haka kawai tasamu kanta da lumshe ido tare da jingina kanta saman kujerar motar wak'ar har cikin jikinta take jinta. Har suka isa gida bama tasan sun iso ba sai da Bala driver ya fad'a mata sun iso, sannan ta kalleshi tace cassette ne? Yace eh tace ciromin, nan ya ciro mata ta amsa tai ciki. Tana na shiga gida taleka falo taga Farida na zaune a gaban laptop da alama aiki take, Sannu da gida kawai tace mata ta wuce d'aki, Aisha batanan da alama tana skul hakan yasa Seemah ta fad'a gado tai ajiyar zuciya ........ © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No. 1⃣4⃣ Juyi ta shiga yi akan gado, hartazo bakin gado bata sani ba tana juyawa kuwa ta murgino jikake tummm, zafin fad'owar datai yasa ta saki kuka, Farida na jinta a ranta tace " wannan shagwab'a tayi yawa wlh." Aikinta ta cigaba dayi. Seemah kam kuka tai tayi ta d'ade kafin ta daina ganin ba mai lallashinta waya ta d'auka tace inkirashi? Kai rainani zaiyi, saurin kiran Junaid tayi yana d'agawa cikin shagwab'a tace " yaya fad'owa nai daga kan gado." Dariya yasa yace " tunanin me kanwara take har ta fad'o bata sani ba? Ko barci kike?" Ta turo baki tace " ni kaina bansan tunanin danakeyi ba yaya." Cikin zolaya yace " ba dai tunanin soyayya takeyi ba ko?" Da saurin tace " haba yaya ni d'in? Bafa san sa nake ba wlh." " dagaske kenan akwai wanda kike so?" Ya fad'a yana jiran amsarta. Tace " wlh yaya a'a kawau bansan meke damuna bane jiya da yau." Yace " uhmmm kanwata u look suspicious, da alama akwai wani abu a kasa." Saurin katse labarin tai da cewa yaya ina wannan budurwar ta ka? yace" Seemah kedai bari ta rainamin hankali ashe bani takeso ba kud'ina takeso, kai mata akwai matsala." Cike da mamaki Seemah tace " yanzu yaya duk yanda take nuna maka da kulawar datake baka dama ta karya ce?" Yace " u have to be carful." Dariya tai tace " ai ni yaya wanda zan aura sai ya bani jinin jikinsa saboda tsabar soyayya sannan sai ya amince akan duk abinda nakeso." " tab lalai zanso ganin wannan saurayin, da alama Ammar ne zai nemo miki saurayi mai halayyarsa d'an inba wanda yake sanki kamar shi ba banajin zaki samu abinda kikeso." Turo baki tai tace " Dama ai nasan duk cikinku Ya Ammar yafi sona gashinan ka fad'a da kanka." Dariya yasa yace " Seemah tun kina karama baki ga yanda yake ji dake ba, sanda kina yarinyafa indai kika zazzabi to shima sai yayi. " Murmushi tai tace " nima ai shiyasa duk nafi sanshi." Sun dad'e suna hira kafin suyi sallama, Seemah tabi wayar da kallo number Jalal ta bud'e tace in k'ira? Wata zuciyar tace ki k'ira kice me? Wata kuma tace ki k'ira ko muryarsa kyaji. Dialing ta d'anna har ya kusa shiga ta kashe da sauri sannan ta bud'e gub text, ta rubuta " me kake yi?" Tana gamawa ta goge ta sake rubuta " Kana office?" Nan ma ta goge ido ta rufe tace " what should I do?" Kara d'aga wayar tai tasa " kana ina?" Bata sani ba hannunta yai sending ihu tasa tara da danne kanta da pillow tace ya zanyi, me zai ce. Jalal ya fito zaije masallaci yaji text ya shigo da mamaki ya kalli number sannan ya bud'e text d'in, tambayar ta d'aure mai kai dialing d'in number yai Seemah najin ringing takalli wayar sai datai ta ajiyar zuciya tare da furzar da iska tana cewa Cool Down kafin ta d'aga wayar, Jalal da mamaki yace " Waye? Kuma bangane tambayar inda ta dosa ba." Cikin takaici Seemah ma tace " waye ban gane maganar da kake yi ba, kasan number daka k'ira dai ko." Jalal yai murmushi yace " Au kece?" Tace " nice sai me? Karkuma kai tunanin na tambayeka ne saboda wani abun ko na damu naji kana ina, na tambayeka ne d'an ina wani guri so nake ka maidani gida." Kai ya girgiza sannan yai murmushi yace " da alama dai damuwar ki kai dani, tunda a tunanina dai ban tambayeki ba." Mik'ewa tai tsaye tace " inji wa? Ni na damu dakai? Ha ha ha, ko a mafarkina." Murmushi kawai yakeyi tana gamawa wata dabara ce ta fad'omai yace " au to shikenan dama na d'auka kin damu danine yasa kika k'ira har zanyi tunanin k'iranki nima akai akai amma tunda ba haka bane shikenan." Da sauri tace " a'a ba cewa nai bandamu dakai ba gaba d'aya amma da gaske ne zaka d'inga k'irana?" " zancen k'ira kuma ai ya roshe tunda ba damuwa kikai dani ba, sai anjima." Yana kai nan ya katse layim tare da sakin wani sansanyan murmushi yace " yarinta ke d'ibanta ko gatane ya mata yawa?" Seemah kam wayar tabi da kallo tare da fad'awa gado rigim kamar wacce ta suma a hankali tace " shikenan na bada kaina, dama ya rainani gashi na kara bada wata kofar." Sai kuma tai shiru can ta mik'e zaune tare da d'aura pillow akan cinyarta tace amma shima menene namin wannan tambayar? Juyawa tai kawai taga Jalal a tsaye ya juya baya sai kuma ya juyo cikin salon soyayya yace " saboda naga kin damu dani." Kwanciya takara yi ta rufe kanta cikin bargo tana cewa No! No! No!........... Jitai an yaye bargon kad'an Aunty farida ta gani kallanta tai kamar me bacci tace " ya akai Aunty?" Farida tace " Bake bace dama? Inatajin ana kamar magana ne nama d'auka kece." Jan bargon ta sakeyi tace bani bace. Farida ta fita tana mamaki to daga inane? © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣5⃣ *_Washegari_* Habib ya nutsu a office yana aiki, wayar Dad ce ta shigo da sauri ya d'auka tare da gaidashi, Dad yace " kunje Sulejan?" Munje d'azu Habib yai maganar cikin damuwa, cikin tsananin tsoron abunda zai faru Dad yace "ba dai abinda ya faru a can d'in ko?" Habib najin haka yace " Dad ka fad'amin gaskiya kama su Hajiya laifine? Ko Seemah ce ta musu?" Jikin Dad yai sanyi abinda yake tsoro kenan shiyasa ya hanata zuwa kasar cikin sanyin murya yace " zanzo nan da 2wks amma karka fad'ama Seemah zanzo inje Sulejan sannan sai mu dawo da ita. Kafin Habib ya kara wata maganar Dad ya katse layin, da mamaki yabi wayar da kallo, meke nan? Seemah kam tun safe take a kwance akan gado ta kasa tashi, tanaji Aisha ta tafi skul, Aunty Farida ma tace zata fita daga nan zata duba ko an gama d'inkinta, itakam tana cikin bargo banda san ganin Jalal ba abinda ke damunta, ganin abin bazai cinyeba yasa ta mik'e da sauri ta fad'a toilet tai wanka, kayan Aisha ta duba ta d'auko wani had'aden material dinkin yayi kyau sosai ta saka sannan ta d'aura d'ankwali simple taduba mayafin daya shiga da kayan tasa ta fito, a waje taga Bala suna hira da nai gadi tace " Bala kaini gun Yaya." Nan suka mik'e suka fito, Suna isa ta kalli Bala tace ka hau taxi ka koma gida kabani key d'in akwai wanda zai maidani." Da mamaki ya kalleta alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa yace " Hajiya ai......" katseshi tai dacewa kuma karka fad'awa kowa inda nake zan koma gida da wuri. Ta amshi key d'in tare da mik'amai 500naira tai ciki. Inda suka had'u jiya tai tana shiga elevator ta d'aga waya tama Jalal text " Rooftop. " Jalal dake zaune suna meeting na sabon project d'in da zasuyi jin karar text yasa ya d'aga waya yana gama karantawa ya d'ago suka cigaba da meeting d'insu. Seemah kam ganin har minti 10 bai zoba yasa ta kara mai text tace "inajira fa." Jalal ya karanta text d'in suka cigaba da meeting sai dai wannan karan sam hankalinshi yarabu kashi biyu, yanzu ne yagane waye ke jiransa, manager ya kalleshi yace " Jalal kanaji kuwa naji kayi shiru bayan kaike bayani tundazo." Kallansa yai yace sry mu cigaba, nan suka cigaba sai dai yanzun ma yana yi yana kallan wayarsa, ganin hankalinsa ya ki kwanciya yasa ya kalli Manager yace " please ina zuwa." Yana fad'ar haka yai waje da sauri, ido suka bishi dashi suna mamakin yau Jalal ne ke neman excuse ana meeting? Jalal kam da sauri shima ya nemi elevator ya hau yana tsayawa ya fito da sauri tare da karasawa kusa da kofar, sai dayad'an tsaya kad'an kafin ya bud'e kofar a hankali, sai dai yaga wayam ba kowa, cike da mamakin ko harta tafi, ya shiga ciki yana fubawa, a zaune ya ganta akan d'an karamin baranda d'in da akai agun ta sa kanta a cinya, ji take kamar tasa ihu, kamar ita ace tazo neman Jalal amma ya shareta? Kallanta Jalal yai tare da jingina da bango idanunsa na kanta, Shi kansa baisan tunanin me yakeyi ba, Seemah kam ganin ba ha za yasa ta mik'e da niyyar tafiya tana d'agowa tayi arba da kafar mutum daga d'an nesa kad'an da ita kallansa tafara daga kafa ahankali takai kan fuskarsa zuciyarta nata harbawa, tana kallan kwayar idanunsa ta lumshe ido ya d'auka ko shirmen da takeyi ne na ganinsa, karkatar da kai Jalal yai tare da cewa " kin k'irani kuma bakice komai ba." Idanu ta zaro a ranta tace dama shine? Hancinta tad'an ja da hannu kamar me mura tad'an juya kai tace ka ga dama kazo? Dana d'auka bazaka zo ba ai. Kai Jalal yad'an jinjina yace " alright tinda bakiso nazo ba bari na juya." Ya fad'a tare da yin kamar zai tafi, da sauri tace " ina kuma zaka?" Juyowa yai tare da had'e rai yace " inda na baro mana." Cikin wani salo da ita kanta bata san ta iya ba tace " karka tafi plz." Kallanta yai cike da mamaki me take nufi? Karasowa yai kusa da ita sannan ya zauna kusa da ita kad'an yace " me kike nufi da kar in tafi?" Kallansa tai sannan ta juya ta kalli gabanta tace " banda abokin hira so nake muyi hira da kai." Murmushi ya saki yace " ni abokin hirar ki ne? Ko kim manta ke kikace ba'a iya hira dani?" Baki tad'an turo tace " ai dagaskene wani sa'in ko wace magana zaka fad'a sai ka fad'i wacce zata kona ran mutum. " Yace " Ahhh tunda haka ne mai kuma zai sa a nemi yin hira dani?" Ta kalleshi tace wannan kuma ai........sai kuma tai shiru, fuskarsa ya karkato inda take yace " wannan kuma me?" Da sauri tasa hannu ta rife fuskar ta tace " yaushe kake tafiya gun matarka?" Dariya yad'anyi kad'an yace " me kika gani?" Ta sauke hannunta tare da cewa " nasan dai kamar ba a nan suke ba ko? Amma ka dad'e dayin auren ne?" Ajiyar zuciya Jalal yai yace" banajin yazama dole in sanar dake sirri na." Hararsa tai cikin jin haushi tace " rike zancenka banamaso." Tafad'a tare da juya baya tacigaba" laifinane ma dana kawo kaina." Mik'ewa yai yace " bari in tafi naga kamar fad'a kike ji, bana tunanin da bakina na tab'a ce miki inada aure." Ya juya ya fara tafiya da sauri ta mik'e tasha gabansa tace " me kace? Banji da kyau ba." Jalal ya kalleta yace " amma ke yarinyace sosai ko?" Tace " me ka gani?" Yace " me kika gani kika ce inada aure? Bayan bana tunanin na tab'a fad'amiki hakan da kaina? Ta harde hannu tace hmm ni bansan ya ake gane mai aure ba sannan naga bakafi sa'an yaya Ammar ba to naji a Nigeria da wuri akema mutum aure shiyasa nai tunanin haka. Dariya yad'anyi kad'an hakwaransa suka fito yace " a da kenan ko? Mu ma yanzu ba kowa bane ke aure da wuri." Murmushi ta saki ganin ta kasa rufe baki yasa Jalal yace " menene na farin ciki d'an banida aure?" Juya mai baya tai takarayin murmushi itakanta takasa controlling d'in kanta Jalal ya dawo ta gabanta tare da matso da fuskarsa saitin idanunta ta zaro ido tare da d'anyi baya ya kara kallanta sannan ya d'aga yad'an kalli kefen fuskarta yace " Don't tell me you. ..?" Da sauri cikin rawar baki tace " tell you what?" Duk ta rikece ya kara kallanta tare da kankance ido yace " anya?" Seemah ta kara had'iyar yawo ta girgiza kai tace " anya me? Me kake sakawa a ranka wai?" Jalal ya nuna ta da yatsa sannan yace " u? Sannan ya nuna kansa yace me?" Seemah ta shiga hura iska tace " bafa haka bane kadaina wannan tunanin." " u look suspicious, badai abinda nake tunani gaskiga bane?" Saurin juyawa tai tare da tsugun nawa ta toshe kunnenta da hannuwanta biyu, Jalal yai murmushi sannan ya tsuguna kusa da ita yace " a bar maganar nima naga kamar it doesn't make sense." D'agowa tai tace " ko? Ka gani kaima ko?" Ya d'aga kai alamar eh yace " bari na koma office." Seemah ta kalleshi tace " zuwa naifa in ka gama abinda kake ka kaini inga gari." Kallan daya mata ne yasa tace " Please." Murmushi yai yace " shikenan bari inje in dawo ki jirani a nan. Itama murmushi tai tace to. Mik'ewa yai ya fito, sai dai har ya isa office murmushi bai bar fuskarsa ba. © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MOHD* No. 1⃣1⃣ Bai sake kulata ba har suka isa gida, mai gadi ya bud'e gate kallanta yai yace " a nan za'a bar motar?" Kai ta d'aga hakan yasa ya shiga da motar, yai parking, kallansa tai tace " mezance? Godiya zanyi ko me?" Jalal yad'an matso kusa da ita sosai, ya kai bakinshi kefen kunnenta a hankali yace " ki rik'e godiyar ki ko rashin ta, ki kama hanya ki kwashi kayanki d'an banaji ko tsinke zan d'aukar miki." Juyo da fuskarta tai ta kalleshi sai kuma ta saki murmushi tace " na hutasheka ko ka manta munada masu gadi da masu aiki a gidan, kai dai nake tunani ko kanada kud'in da zai maidakai." Tana kainan ta juya da niyyar bud'e kofa, hannunta Jalal ya fizgo ta koma ta zauna tare da juyowa, Jalal yace " me kika ce?" Seemah tad'anyi shiru kawai tana kallanshi, fuskarnan tasa a had'e haka kawai sai taji ba dad'i rau rau tai da ido tace " Jal jiya ka banni da yunwa da wahala yau kuma hannuna kakesan b'alawa? Da alama yau ne rana ta karshe dazan yi amfani da hannun, oh ni Allah sarki ni." Yanda tai maganar ne yasa Jalal ya saki hannunta da sauri yace "haka ake b'alla hannu a garin ku?" Hannunta ta kalla tare da langwab'ewa tace " shikenan hannuna....." da sauri Jalal yad'an tab'a hannu kara tasa kad'an tace " Jal hannuna......" rud'ewa yai sosai yace menene? Da gaske ciwo yake? Dariya sosak Seemah tasa tace " amma kanada saurin shiga." Kallanta yai shima baisan sanda yasa dariya ba, yace amma wlh yarinyar......bakinshi tai saurin toshewa da hannunta tace " basai ka karasa ba." Hannu yasa ya ture hannunta sannan yakara yin dariya tare da girgiza kai....kallansa kawai Seemah take ta karkatar dakai tana murmushi. Jalal ya kalleta sannan yace " Na tafi." Ya fad'a tare da bud'e kofa, itama da sauri ta bud'e kofar ta d'aura kanta a saman mota tace " Sai yaushe kuma?" Tsayawa yai tare da juyowa ya kalleta yace " Saurayin ki ne ni da zaki tambayeni sai yaushe?" Da sauri ta d'auke kanta sannan tai d'an juya kai tace " ce maka akai haka nake nufi?" Murmushi yai yace " bari na turo miki mai gadin dan da alama baisan kinada kaya ba." Yana kainan ya cigaba da tafiya, Seemah ta bi bayanshi da kallo har ya fita, a jiyar zuciya tai tare da cewa " not bad." Mai gadi ne ya karaso tare da kwasar kayan, Seemah tai ciki da sauri, jin gidan shiru yasa tai d'akinta. A kwance ta taradda Aisha da alama waya take kallanta tai taga yanda ta wani shige bargo tana wani kashe murya, Seemah tai tsaki sannan ta yau gado ta kwanta tare da rik'e wayata da alama game takeyi. Aisha ce ta taso tazo kusa da ita bayan ta gama wayar tad'an tab'ata, Seemah ta mik'e tare da kallanta tace "lafiya?" "Seemah d'an Allah inada tambaya, misali saurayinka kullum badai shi ya k'iraka ba sai dai kai ka k'irashi sannan wani sa'in in ka k'irashi ma sai yace yana wani aikin ne zai k'iraka, kuma fa bazai k'iraba, dan Allah me hakan yake nufi?" Seemah ta mik'e zaune ta kalleta tace " me kuwa yake nufi, banda ke kike sansa ba shi yake sanki ba? Sannan alamace ta yana buk'atar ki barshi ya huta." Ta mik'e tare da d'aukan towel sai datakai wajen toilet ta juyo ta kalli Aisha tace " narasa meyasa mata bakwa sanin 'yancin kanku, har akwai namijim daya isa ink'irashi ya dizgani haka? Ba'a haifeshi ba." Tana kainan ta bud'e kofar toilet ta shiga. Aisha ta bita da kallo idanta kamar tai kuka tace " mene? Alamace ta me...? " sai kuma tai kwafa tace " Allah ya nunamin sanda soyayya zata rufe miki ido... Seemah kam wanka take amma tana mita a ranta..... ■■■■■■■■■■■■■■■■■■■ Da daddare suna zaune dukansu a falo a na hira Seemah na kusa dasu Ra'is tana koya musu homework, Habib ya kalli Seemah yace " D'azu ba dai abinda ya faru ko?" Tace name fa? Yace" da kuka fita siyayya, naga kamar guy d'in nan basan zuwa yake ba." Murmushi ta saki tace " Auu wannan? Ya kula dani yanda ya kamata kuwa, yaya a haka ne zaka ganshi kamar mara kirki amma a zahiri he is not a bad guy." Habib da mamaki ya kalleta yace " ya akai kika sani? Bayan a tunanina yau ce had'uwar ku ta biyu?" Da sauri tai kasa da kai tace " hmm kawai nima yau d'in ne naga kamar......." Farida ce ta katseta tace " kodai kanwata ta fara san wa.......... Cikin wani irin tsawa Habib yace " banasan haka Farida, ke meyasa sai ana maganar mutunci sai ki d'inga fad'o abinda ba'a tambayeki ba?" Cikin sanyi jiki Seemah ta kalli Habib sannan ta kalli Farida, mik'ewa tai taja su Ra'isa sukabar falon.... Tana kaisu d'aki ta koma d'akinsu ta kwanta sai dai ta kasa bacci sam, fuskar Jalal take hangowa, nan yana dariya, can yana murmushi, can kuma ya had'e rai......ajiyar zuciya tai ta saki murmushi....... ♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Washe gari da safe Habib ya mata waya yace ta shirya zasuje gaida kakaninsu, murna sosai Seemah tai, Farida da kanta tazo ta duba had'ad'un kaya a cikin na Aisha ta zab'ar mata wata atamface da aka mata d'inki zamani riga da siket ne yau ce rana ta farko da ta tab'a saka kayan hausawa, sai dai kayan sun karb'eta sosai, Aisha ta zauna ta d'aura mata d'ankwalli, Seemah tayu kyau sosai ita kanta dad'i takeji inta kalli kanta, tarasa dalilin dayasa Jalal ya fad'o mata, tunaninta d'aya inya ganta mezaice? Sun fito Habib sai wasa ta yakeyi suka shiga mota, nan suka fara tafiya zuwa Suleja inda iyayen Dad ke zaune. Suna tafi suna hira har suka isa sunyi parking a daidai gate d'in wani karamin gida flat house mai kyau, Habib ya kalleta yace muje ko? Kallansa tai tace " Yaya why am I feeling so nervous? " hannunta ya rike yace " keda zakiga kakaninki mai zai saki jin haka?" Murmushi tai sannan ta saki ajiyar zuciya tare da fitowa daga motar. Habib na gaba tana binshi a baya, suna knocking akazo aka bud'e, wani almajiri ne ya gaidasu sannan Habib yatambayeshi ina hajiya? Yaron yace tana d'aki, nan sukai hanyar d'akin. Sallama yai, wata datijiwace ta fito fuska a sake tana cewa maraba da babban jika na, dariya yai yace " ya akai kika gani muryata? Kafin ki fito?" Fuskar nan cike da fara' a takalleshi tace " haba Mai gidan ya za'ai in kasa gane ka?" Idanunta ne suka kai kan Seemah kallanta takeyi taki d'auke ido, cikin rawar murya Seemah tace "ina kwana Hajiya?" Batare data amsa ba ta kalli Habib tace ku shigo ciki, amma ban gane waccen d'in ba, nan suka shiga suna zama Mai gidanta ya shigo cikin murna yana cewa yau munada baki ashe? Lale da zuwan mai sunana. Ciki ya shiga shima tare da zama kusa da Habib, Seemah kam jikinta rawa yakeyi ganin hajiya ta kafeta da ido, Habib ne ya rik'e hannunta yace " Hajiya Seemah ce, Auta sai yau Allah yai zuwanta." Ba Hajiya ba hatta Alhaji gani yai sun had'e rai sunyi dif, a hankali Seemah tace " ina kwanan ku?" Sai dai abinda ya basu mamaki ba wanda ya amsa, Habib cike da mamaki yace " Hajiya gaisheku take fa? Baku gane ta bane?" Fuskar nan ba a sake ba, kawo yace " lafiya ya kika baro yan gidan?" A hankali tace lafiya. Sunyi shiru dukansu, Habib na mamakin wannan al'amari shikam bai fahimci wannan abun ba, itakam Seemah kasa tai kawai da kanta idanta kawai ya ciciko da hawaye. © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣6⃣ Jalal na shiga office ya shiga duba takardun d'azu wayar Zainab ce ta shigo hakan yasa ya tuna kalaman Seemah na in da gaske ne yabari ta katse sai ya k'ira, yana kallan wayar harta katse sannan ya k'irata yana d'agawa tace " Yaya ya zakayi?" Cike da mamaki yace name fa? Tace " dazu su baffana sukabar gidan nan dashi da Abba wai sun yanke auran mu zasuyi." Jalal cikin b'acin rai ya mik'e yace " me?" Zainab hawaye ya zubo mata tana tsananin san Jalal hakan yasa batasan wani abinda zai b'atamai rai ciki kuwa harda auranta gani take in bayaso to fa zata iya hakura sai dai batajin zata auri wani..... Jalal ne ya katseta da cewa nagode kanwata bari na k'ira Abban, kana katsewa yak'ira Abba tare da fita daga office d'in, Bayan sun gaisa Jalal yace " Abba yanzu Zainab ta........" Cikin fishi Abba yace " kai ko kunya bakaji ba Jalal? Yarinyar nan tun tana shekara 12 mahaifinta ya baka ita sannan alokacin ta dawo gidanmu take taya mahaifiyarka kula da kanwarka da kuma aiyukan gida, har kawo iyanzu, sannan duk sanda na maka maganar auranta sai ka wayance da wani abun, gashi ta girma mahaifanta nasan suga tayi aure, shine ko kunya dan munyi zancen auranku zaka k'irani ka nemi yin korafi?" Jikin Jalal yai sanyi ya sani sarai Zainab nada hankali gashi tun tana karama take musu wahala, sai dai shifa bai tab'a jin santa ba banda na 'yan uwantaka, cikin sanyin murya yace " Abba ba haka nake nufi ba." Abba yace " karka kuskura ka b'atamin rai, kai ba wata kakeso ba yanzu shekarunka 28 to me kake jira? So kake sai ka tsufa ko me?" Jalal yai shiru dakyar yad'aure yace " Abba yahakuri." Abba yai shiru can yace " Jalal karka manta ba komai garemu ba, da abinda zamuci a rana ma wahala yake mana cikin wannan tsananin kai karatunka har ka samu aiki, kaine gatanmu damu da kanwarka banaso zuciya tad'inga saka maka abinda bazai amfane ka ba." Jalal yace " nasani Abba." Abba najin haka ya katse layin dan zuciyarsa tafara raunana, yana katsewa ya kalli Umma dake zaune idanunta taf da kwalla tace " Alhaji kad'inga mai a hankali kasan wahalhalun dayasha a da, ni nasani Jalal mai biyayya bazai bijire maka akan auren Zainab ba." Abba ya kalleta shima cikin tausayi yace "Har yau bana manta wahalar da yaron nan yasha, ga makaranta secondary ga aikin karfi dayake yi na tara kud'in makarantar dazai shiga jami'a da ita, ga rashin abinda zamuyi amfani dashi a gida, haka zai fasa asusunshi ya bani kud'in,a ciki za'ai amfani da na gida dana magani Zaheeda," ajiyar zuciya yai yace " Ni kuwa ina zan manta hajiya? Kawai ina tsoro ne, kar d'an yaje birni wata 'yar masu kud'in ta nemi jan ra'ayinsa." Umma ta share hawayen dake gudu a fuskarta tace " Ai *Jalaludeen* namijin duniya ne, tun yana karami yake kula damu hakan kuma banaji yanda yake da dakkakiyar zuciya akwai yarinyar da zata nemi juyamai tunani." Shiru sukai a hankali idan Umma yakai kan Zaheeda dake kwance idanunta a rufe suke amma hawaye da zubowa ta gefen idanunta kura mata ido tai a ranta tace Allah yabaki Lafiya....nace Amin. Jalal suna gama waya da Abba yatsaya agun yai shiru kara text ne ka tseshi daga tunanin da yake, wayar ya d'aga ya karanta sakon, " Ka gama?" Ido ya runtse sai kuma wata zuciyar tace " menene na damuwa? San Seemah kake?" Da sauri yace a'a mezanyi da wannan karamar yarinyar da shagwab'a da yarinta suka mata yawa, iska ya furzar sannan ya koma office ya d'auko takardu yai kasa, sqi daya gama sannan ya mata text akan ta sauko su tafi. Seemah kam takaice ya ishe ta kamar ita? Ace tayi hour 1 tana jiran d'a namiji ina....da sake, sai dai ya zatai tunda ta kori Bala, haka ta sauko fuska a d'aure, a kusa da motarta ta ganshi batace mai komai ba ta mik'amai key ya shiga itama ta zagaya tashiga ya ja mota suka fara tafiya, sunyi nisa ba wanda yama wani magana shi abinda ke damunshi daban itakuma takaicinta ko hakuri ma bai bata ba, cikin b'acin rai tace " Yanzu da gaske baka da niyyar bani hakuri?" Kallanra yad'anyi sannan yamaida fuskarsa kan titi yace da nai me fa? Takalleshi tace " mene? Ka barni a waje sama da hour 1 kace me? Dakai me?" Jalal ya karasa gefen titi yai parking sannan ya juyo cikin b'acin ran abinda ake shirin yimasa yace " me? Na barki na hour 1? Ko kin manta aiki nake kika sani na fito? Ido ya rufe sannan ya ware hanayyensa ya nunata dasu yace " Seemah I am not in a good mood d'an haka kibini a hankali karki b'atamin rai." Seemah yanda yake mata fad'a yasa ta tsorata tunowa tai d'azun nan fa suka gama hira da murmushi yanzu kuma menene hakan? Tad'auka zai bata hakuri komai ya wuce, cikin halin ko in kula tace " amma nikam kai wani irin mutum ne?" Jalal ya juyo ya maka mata wani mugun kallo sannan ya fizgi motar a guje, ganin yanda yake gudu ta had'iyi yawo tace " amma ko me aka maka nina maka?mutum sai kace mai aljanu?" Shidai Jalal bai kulata ba gudu kawai yake yana zuwa kofar gidansu kafin a bud'e yai kashe motar ya fito daga motar dakarfi ya rufo motar yai gaba, Seemah ta bishi da kallo baki bud'e tace " Ha ha Ha me kenan?" Cikin takaici itama ta fito daga motar a kofa tacema Bala ya shigo da motar tai ciki. Tana shiga tai d'aki ta fad'a gado batama kula Aisha na zaune ta baza tagumi ba, Aunty Farida ce ta shigo tace " Seemah kin dawo?" A hankali tace eh. Farida ta karasa gun Aisha tace " wai ke wace irin soyayya kike yi hakan? Ba tunani ba kuma tsari?" Aisha ta d'ago idanunta tace " Aunty yazanyi da san Muftahu?" Farida tace " Shiyasa yake miki abinda yaga dama tunda ya kula ke kika damu dashi, yaushe rabon ya k'iraki? Sai ke kece uwar soyayya ko? To wlh indai haka zaki cigaba gaba ko a titi yaganki d'auke kai zaiyi yai kamar be ganki ba." Seemah tayi shiru tana jinsu itama da alama ita take neman Jalal duk da ba soyayya suke ba amma ta kula shike jawo mata raini. Farida tacigaba " kinsan me akecema *Hard to Get?*" Kad'a kai tai alamar a'a Ta cigaba bani wayarki nan ta mik'a mata Farida tace yasan duka layinki biyu? Tace a'a da Mtn kawai muke waya kinsan bana waya da Airtel sosai, Farida ta bud'e wayar tare da cire sim d'in Mtn d'in tace daga yau karki kuskura ki kara kiransa, duk san ki k'irashi dazakiji kar ki nemeshi, shikuma rashin ganin kiranki da farko zaiji dad'in kin kyaleshi amma ahankali abinzai fara damunsa, wannan shi ake kira Hard to get. Seemah ma ta mik'e tana kallan Farida tace " kai Aunty kice shiyasa kika rikitamin yaya. Dariya tai tace "Allah Aishan ce haushi take bani kuma wlh ki kuskura ki kirashi inji."tanakainan tafita. Seemah ma tace nima dole inyi hakan. © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣7⃣ Farida na fita itama ta kashe wayarta ta zuge jakarta tasata tare da kara kwanciya, Ammar takesan k'ira sai dai bazata kunna wayarta ba, daga bayama mik'ewa tai ta dawo falo ta zauna gun su Ra'is, ganin ansa wani indian series *JODHA AKBAR* a tv yasa tafara kallo, sai dai abin haushi tamaji gaba d'aya yawancin maganar dazasuyi sai sunce _Jalal_ jitake kamar da da ita suke haushi ya kamata ta canza tasha, Farida da Aisha dakw zaune suna kallo sukace Seemah lafiya? Aisha tace"Dramar fa tanada kyau sosai banaso ko kad'an a wuceni." Haushi ya kama Seemah tace " meye wani Jalal in suna san abin ya birge mutane sai su nemo suna mai dad'i ba wannan ba." Cike da mamaki farida tace " meye da sunan? Nikam ina san sunan har tunani nake in na k'ara haifar namiji a samai....... Seemah ta mike tare da katseta tace " mene? Aunty badai wannan sunan ba gaskiya." tana kai nan ta juya tai ciki, Aisha ta bita da harara tace wlh Aunty wannan da kanwatace zaneta zan d'ingayi sam ta raina mutane. Farida tace ya isa haka ni kaina abinda takeyi ba dad'insa nakeji ba amma akanta zan iyacemiki Habib zai iya rabuwa dani, d'an tun kafin muyi aure yakemin zancenta sannan sanda za'a kawo kud'i harda wani cewa zai nuna mata hotona ya tabbatar tana sona." Tai ajiyar zuciya tace " Bakisan abubuwan da akamin na takaici akanta ba daga baya dana gane san da suke mata ne yai yawa yasa nima nafara cusa kaina gunta kankice me tafara sona ko kunya Habib kecemin yaji dad'i da Seemah take sona nima nake santa d'an bazai iya zama da wacce batasan kanwar sa ba." Ta kalli Aisha data saki baki tanajin zancen tab'e baki tai tace " tab lalai kice inyi a hankali mu rabu lafiya." Farida tabi inda Seemah tai da kallo tace " Gaskiya kam." Seemah kam d'aki ta shiga ta zauna a bakin gado tare da turo baki gaba masifar da Jalal yamata dazu, kwafa tai tace amma nima banza ce kuma dayamin masifar banajin nafad'amai abinda zai dameshi.... ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Dad sam yakasa tsaye bare zaune abin duniya ya dameshi, ya zaiyi ya birne kar a kara tada maganar da akasha gwagwar maya a baya d'an binne ta? Tsoronshi d'aya kar lokacin da Seemah zatazo ace za'a aurar da ita magana ta tashi, ya zaiyi shikam, bayaso sam ran Seemah ya b'aci bare har taji wannan labarin da zai ruguza farin cikin rayuwarta, iska ya furzar sannan ya zauna a gefen gado tare da rik'e kansa, ya rasa ina zai fara jawo mafita. Matarsa ce tashigo tare da zama kusa dashi hannu tasa da dafashi cikin salon jan hankali tace " Dad d'in Seemah me ke damunka ne? Wani ne ya b'ata maka rai?" Hannunta ya ture daga jikinsa yace" dan Allah fita ina inasan nakasance ni kad'ai." Kallansa tai tare da manna mai kiss na kissa a kunci, mik'ewa yai cikin b'acin rai yace in bazaki fita ba ni bari na bamiki d'akin. Yana kai nan yai waje tabishi da harara tace " wlh badan kud'inka ba banga dalilin dazai zaunar dani kanamin abinda kaga dama ba. Dad kam falo ya fito anan yaga Junaid da Ammar suna hira, zama yai tare da cewa Ammar kunyi waya da Seemah kuwa? Nak'ira wayarta d'azu a rufe, Ammar yai ajiyar zuciya yace " Dad nikaina bansan meke damun kanwata ba, a iya sanina bata tab'a kashe wayarta sai dai in ba charge sannan kullum mukai waya sai inji kamar tana cikin damuwa." Junaid yasa dariya yace " kaii Ammar gaskiya ina tausayama wanda zai auri Seemah d'an na kula dakai da Dad bazaku barsu ba, kuna jin ranta ya b'aci zaku bazama zuwa gidan." Dad ya harareshi yace " dama kai na kula baka san kanwarka sosai shiyasa baka damu da ita ba." Junaid yace " wlh Dad ina bala'in san Seemah banaji in wani abu ya sameta zan iya rayuwa, ai Dad tun tana jaririya kariga ka cusa mana santa shiyasa kowa ke kishin gata da so da muke mata." Ido Dad ya lumshe yace " yanzu misali in wani abu ya sameta na tsanani zaku gujeta?" Da sauri Ammar yace " Haba Dad ai bana tunanin akwai abinda zai sameta muna raye in kuma Allah yatsara hakan zai faru kaima kasan soyayyar da muke mata bazatasa mu gujeta ba sai dai muzame mata makafa." Junaid ma yace " Dad adaina maganar nan." Nan suka d'auko hirar abin dariyar Seemah datana yarinya..... Dad kam hankalinshi duk baya kan hirar sosai. □□□□□□□□□□□□□□□□□□□ Jalal bayan sunyi Sallar Magrib ya fito waje d'an d'akin nasu ba dadin zama su hudu ne a d'aki kwaya d'aya tun safe in ya fito basan komawa yake ba saj bacci, zama yai a wajen kantin wani abokinsa wayarsa ce a hannunsa yanata juyata, abinda yama Seemah d'azu ne ya fad'omai yace " did I go too far?" Kansa ya sosa yace nasan halinta ba wani haushi zataji ba, kafin gobe zatamin text ko bata k'irani ba. Mai shagon ne ya kalleshi yace " Jalal tunanin me kakeyi haka? Ko dai ka fad'a ne?" "Ina na fad'a kuma?" Dariya mai shagon yai yace " kai Jalal gaskiya kaima sai a slow, nifa ban tab'aji kace ga budurwarka ba, duk matan dake sanka, ka manta matar nan mai mota....." " naji ya isheni karma ka tado min da wannan bakin cikin" "Amma Jalal matar nan kamar fa zata haifeka," Kai Jalal ya girgiza yace " ni dai d'an Allah kabarni, yauwa dan Allah Nafi'u ga tambaya, nasan ka namamajo ne kai, inajin 'yan matanka sun kai 5, d'an Allah ya keke gane mace na sanka." Dariya sosai Nafi'u yai yace " lalai Jalal abin naka babba ne amma kafin ka nemi sanin ana sanka ai kanka zaka fara tambaya, kanasan wace kake so........" D'aga mai hannu yai tare da mik'ewa yace kai fa matsalata dakai kenan, ce maka nai ni nakesan ji ko me? da zaka faramin zancen banza nifa banaji akwai wani guri a zuciyata na soyayya, aiki na shine a gabana burina inga......." Sai kuma yai shiru tare da cewa na tafi, yana kainan ya wuce ya fara tafiya. Nafi'u ya bishi da kallo yace " Jalal kenan ko baka fad'aba na kula kafara fad'awa san wata, d'an tunda nake dakai yauce rana ta farko daka fara tambayata akan soyayya. Jalal yana shiga d'akinsu yaga ba kowa, tunani yai bari ya d'auko takardun dasuke aiki a kai ya duba kafin su dawo su cikashi da magana, sai dai me? Kaf ya duba inda yake ajiya ya rasa cike da mamaki yake tambayar kansa to ina nasa? Nasan dai tabbas na fito dasu daga office har nabiya gun Assistant Director na nuna mai nakuma fito dashi, to ina nakai? Kansa yad'an buga kad'an yace " motar Seemah? Oh Gosh" gashi dole gobe zasuyi amfani da takardun da sauri ya d'au waya ya k'ira ta sai dai abin haushi wai a rufe, text ya mata akan inta bud'e waya ta kirashi sai dai shima bai yi delivery ba, yama rasa ya zaiyi, lalai dole gobe kafin ya tafi gun aiki ya biya ya anso. © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣8⃣ Da safe Jalal yana tashi ya shiga k'iran wayar Seemah sai dai a kashe ba shiri yai wanka ya fita gidansu ya wuce direct duk da bayasan Habib ya ganshi, yayi sa'a yana shiga layin motar Habib na fita daga unguwa karasawa yai tare da tambayar me gadi a k'iramai Seemah, kallanshi mai gadin yai sannan yace wani abun ne? Jalal yace ka k'irata mana sai ka gani. Nan ya juya ciki, bayan ya kwankwasa Farida ta bud'e tare da tambayarshi menene? Yace wani ne ke neman Hajiya Seemah, mamaki ya kamata tace " Seemah dai?" Yace eh. "Bacci takeyi kuma ba'a tashinta in tana bacci" ta fad'a tare da juyawa ciki. Mai gadin ya karaso ya fad'ama Jalal haushi ya kamashi, bacci? Kuma ba'a tashinta? Juyawa yai ya koma Company. Yayi sa'a sai 12 zasuyi meeting d'in hakan yasa ya zauna ya cigaba da aikinsa. 《《《《《《《《《《《《 Seemah kam sai 10 ta tashi tai fad'a toilet tai wanka, Kaya ta gani a gefen gadonta guda 5 ta kalli kayan sannan ta fito daga ita sai towel tai falo, a dinning tagansu suna breakfast tace " Aunty kayan meye a side-bed d'ina?" " d'inkinkine jiya danaje nasamu ya gama wad'an nan" Tace ok nagode, ta fad'a tare da juyawa, ita meya dameta da d'inkin bayan Wanda tasai kayan dan shi ya shareta, muryar Farida ta jiyo tana cewa na manta Seemah yayanki yace inkin shirya kibishi office in ya fito sallar Azahar zai kaiki gidan Baffa(kanin dad) farin ciki ne ya bayyana a fuskarta ta juya tai ciki da sauri, ni kaina na kasa gane farin cikin me take, na zuwa gidan baffa ne, ko na zuwa company ko zataga Jalal? Atamfa tasa d'inki ya zauna mata sosai, ba wani kwalliya takema fuskarta ba tana gama da d'ankwali Aisha ta shigo tace kawo in d'aura miki, nan ta zauna Aisha ta d'aura mata ta kalli kanta a madubi tace " Aisha kin iya d'auri." Mayafi ta d'auko tasa sannan ta d'auko takalminta me bala'in tsini tasa, Aisha tace " Seemah bakya gajiya da tafiya da wannan takalmin?" " ni in bashi nasa ba ban fiya jin dad'i ba" tafad'a tare da lank'aya jakarta ta fito. Bata wani ci abincin kirki ba ta fito. Suna fita kad'an Jalal ya kara zuwa mai gadi yace yanzun nan ta fita, cikin damuwa yace ina? Mai gadin ya kalleshi yace saurayi wai kai d'in waye? Tunani yai maybe company d'in zata hakan yasa bai ba mai gad'in amsa ba ya juya yai gaba akan machine d'in daya kawoshi. Seemah motarta ta tsaya a Company d'in ta kalli Bala tace " bala d'an tsalaka can layin ka siyomin kati ta fad'a tare da mikamai 1000." Zuciya d'aya ya amsa tare da fita, ta kalleshi tace oh ko a ina nasan wani layi da ake sai da kati, u are the fool for believing me. Hoda ta d'auko ta shiga gyara fuskarta tad'auko jambaki pink zatad'an kara taji an kwankwasa mata glass daga gefen da take, a hankali ta d'ago tare da saurin maida kayan kwalliyar. Jalal ta fad'a a ranta, kallansa tafarayi shi kanshi kallanta yakeyi, can ya d'aure yace " meya sami wayarki?" Dad'ine ya ziyarci zuciyarta tad'an juya kai tace " ka k'ira ne?" "Sosaima in fact tun jiya nake k'iranki" murmushin farinciki ne ya kamata ta juyo tare da cewa " naga jiya da masifa muka rabu k'iran kuma nameye?" Cikin ba zatan kalmominshi taji yace " mantuwa nai a motarki" Kuramai ido tai cikin jin haushin kalaman tace " mantuwa?" Kai ya d'aga yace d'an mikomin takarduncan? Ya fad'a tare da nuna gefen gun da take da hannu, ita sai alokacin ma ta gansu haushi ya kamata ta janyo wani blank sheet dake kasan motar tace wannan? Jalal yace bashi ba, ta d'an juya kai alamar tana neman wani abun kwalin cassette tagani ta d'auko tareda cewa "oh wannan? Kai Jalal ya girgiza sannan ya zagaya d'ayan bangaren ya bud'e motar tare da tura kanshi itama ta turo kanta zata d'auka jisukai kansu ya gwaro kum! Kara tad'anyi tare da janye kanta ta rik'e gun shima d'an baya yai tare da kallanta, d'agowa tai zatai shagwab'a sai kuma ta kwashe da dariya ganin yanda yake kallanta, shima dariyar yasa harda zama a motar dariya sukai sosai, Sai da suka tsagaita Seemah tace " dama kana dariya haka?" D'an d'aure fuska yai yace " wato da saninki kenan kinsan takardun da nake nufi jan magana ne ko?" Murmushi ta saki tace " eh mana baka b'atamin rai da cewa wai ka k'irani bane kawai d'an takardu ba?" Kallan yanda take magana yake ta juyo tace menene? Yace Seemah nikam duk maganarki kamar shagwab'a kike kodai nikike ma haka? Harara ta makamai tace " kai kuma a me kenan?" Zuciyarsa taji ba dad'in kalmar sai dai daure wa yai ya d'au takardun yace shikenan. Da sauri tace " Deen" Juyowa yai ciki da mamaki, ya kalleta. Murmushi tai tace " naga kamar bakasan nace maka Jal sai naga ni sunan naka ne bazan iya fad'a ba to bari na d'au karshe." Kallanta yatsaya yanayi zuciyarshi na saka mai abubuwa, harya fara tafiya ya dawo ta window yace" yaushe zaki tafi?" Kallansa tai tace " wani abun ne?" Shiru yai sannan yace " kawai dai tambaya nake." Ta lumshe ido tace " bansani ba amma nasan wajen azahar zamu fita da yaya." Tafad'a tana kare ma fuskarshi kallo. Baiji dad'i ba yace ok shikenan bye. Da sauri tace in na dawo zan iya k'iranka mu had'u a wani gun? Kallanta yai sannan ya saki Murmushi yace " za'a barki?" " nifa in nace inasan abu barina ake inyi." Zaiyi magana Bala ya dawo tare da cewa malam lafiya? Jalal ya mik'e tare da nuna kata da hannu alamar ta k'irashi yai ciki. Sai daya shiga ya tsaya yace " meke damuna? Meyasa bama iya controlling kaina in ina kusa da yarinyar can? Wai yau nine ke tambayar wata......ahhh Jalal yaushe ka zama haka? Seemah kam fitowa tai tare da shiga Company d'in kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, tana shiga taga Jalal a tsaye, kallansa tai shima ya kalleta wani sansayar murmushi sukama juna ta wuce shima ya wuce. Hmmmmmmmmmm © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣9⃣ Haka ta karasa Office d'in Habib fuskarta d'auke da murmushi, da sagir suka gaisa sannan ta karasa kofar Habib tai knocking, nan ya bada izini ta shiga da Sallama, a zaune ta ganshi yana duba abu a laptop ga takardu a kusa dashi, tana shigowa ta karasa kusa dashi ta baya ta zuro kanta jikin screen d'in tace " Yaya baka ga kanwarka bane?" Juyo wa yai tare da zare medical glass d'inshi yace " Seemah kin iso?" Ta mik'e tare da hard'e hannuwanta tace " da alama bakaji dad'in ganina ba." Hannunta ya jawo sannan ya juyo yana kallanta yace " Sorry Kanwata wasu takardu ne zan tura Company d'in Dad na England." Kallansa tai ta turo baki cikin shagwab'a tace na hakura tunda dad d'ina zaka turama, yace yauwa zauna ki jirani na gama, amma fa sai munyi azahar zamu? Tace nasani yaya, ta fad'a tare da kallan agogon dake makale jikin bango, 11? Ashe zan d'ade? Mik'ewa tai tace "Yaya kai aiki a hankali ni bari inzaga inga Company d'in, yace to Seemah amma ki kula fa, tace ok. Fitowa tai direct tai hanyar gun aikin Jalal itakam bata ganin wani abun ne in taje gunsa, d'an su acan England mace d'an taje gun namiji ko ba saurayinta bane ba wani abun bane, Office d'insu ta isa ta murd'a tare da Sallama, juyowa sukai suka kalleta, karasowa tai cikin halin ko in kula tace " zaga yawa nake nazo kusa danan shine nace bari inshigo ku gaisa, kallanta sukai suka ce Shigo mana, Kallansu tai yanda taga suna za-zaune yasa ta game meeting suke, Jalal ta kalla, kallanta yake shima fuskarsa d'auke da murmushi, shigowa tai ta karasa ta zauna daga gefensu, tace " karku damu dani kucigaba da aikinku." Nan suka juya suka cigaba da meeting d'insu sai dai jefi jefi suna kallan juna a sace itada Jalal, suna cikin meeting ne wata tai knocking tare da bud'e kofar ta shigo, Seemah ta kalleta kana ganinta kasan Christian ce daga yanayin shigarta, siket ne iya gwiwa da riga coat sai da bata rufe mab'alin saman rigar ba hakan yasa inta sukunya zaka iya gano kirjinta. Cikin salo ta karaso tare da tsayawa kusa da Jalal, Seemah kam idanta na kanta, matar ta kalli Jalal tare da mik'amai takarda cikin kissa ta zubar da takardun Jalal ya sunkuya zai d'auko itama cikin salo ta sunkuya, tare da rike hannunsa tace " Barshi........." da karfi aka katseta tare da cewa " Let go of that hand." Da mamaki kowa ya juyo ya kalleta Jalal ya fizge hannunsa tare da makama matar harara yace " what are you doing?" D'agowa tai ta kalli Jalal sannan ta kalli Seemah tace " Who is She?" Karasowa Seemah tai tace " what? Baki da da'a ne? Ko dama tambada ne ya kawoki nan?" Matar ta kalleta tace " meye damuwarki a ciki?" Yanda tai maganar zakasan hausan bata gama zama mata ba. Harararta Seemah tai tace " meye nawa kuwa a ciki? Sai dai bazan bari ina kallo mace irinki ta nemi lala......" Jalal ne ya katseta yace " ya isa haka, abar maganar haka." Seemah cikin takaicin da batasan kanshi ba ta kalleshi sannan tai waje da sauri, Jalal ya bita da kallo sannan yacema matar ta fita, abokanan aikinsa suka kalleshi sukace ina taje? Ido ya runtse sannan yace ina zuwa yai waje da sauri, dubata yafarayi tundaga office d'insu sai dak bai ganta ba, tunanin gun da suke zama ne ya fad'omai dasauri ya karasa gun elevator ya tab'a sai dai abin haushi tana kasa hakan yasa kawai ya wuce beni yafara hawa da sauri, matatakalar nada yawa sosai amma sam bai kula ba yana isa yai saurin karasawa kofar ya bud'e, tare da duba inda take zama, a zaune ya ganta ta had'e kai da gwiwa tana kuka ita kanta batasan meke damunta ba sai dai abu d'aya daya bata haushi katseta da Jalal yai tana magana, Jalal ya karaso gabanta ya tsugun na, cikin sanyin murya yace " me kike anan?" D'ago jajjayen idanunta tai ta kalleshi cike da mamaki yace kuka? Meya saki kuka? Harara ta makamai sannan tasa hannu ta share hawayenta jiyai zuciyarsa ba dad'i yace " Haushi kikaji? D'an ta rik'eni?" Cikin masifa tace " Yama za'ai ka d'inga bari mata na tab'aka?" Yace " kin kula kuwa? Bafa da saninta bane." Cikin abin kuka tace " kare mata zakai? Bayan ina ganinta? Tashi ka bani guri tunda kare mata zakai, daga yanzu kuma bazan kara damuwa ba in wata ta tab'aka." Murmushi yai yace " Don't tell You are jealous? " Da sauri tace " ni? Inji wa? Akan me zanyi kishin?" Ya kara sakin murmushi sannan yace " haka ne bayan na san kin tsaneni." Nan ma da sauri ta kalleshi tace " nidin? Injiwa? Waya fad'ama na tsaneka?" Kasa yai dakai yana murmushi idanunsa ne suka kai kan kafarta da alama takalmin yajima dunduniyarta ciwo garin sauri ko gudu datai d'azu, hannu yasa ya zare mata takalmin kafarta, kallansa tai cike da mamaki tace " menene?" D'agowa yai tare da had'e rai yace " gudu kike d'azu?" Kai tad'aga tare da kallan sa, iska ya d'an furzar yace " in zaki d'inga gudu kidaina sa irin takalmin nan gashi kinjima kanki ciwo." Murmushi ta saki sannan tai kasa dakai ahankali tace "are u worried about me? " D'agowa yai ya kalleta nan suka kurama juna ido a hankali ta lumshe ido, Jalal ya kura mata ido shikam bai tab'ajin abinda yakeji a wannan lokacin yana tsirgamai ba, itama idanun data lumshe jitake kamar me, wani irin so ne ke tsirga mata. Ajiyar zuciyar da Jalal yai ne yasa ta bud'e ido ta kalleshi yace " nabar wayata a office nasan za'a nemeni bari naje mu karasa, ko zakizo mu koma?" Tace " inafa zan koma bayan na gamajin kunya." Murmushi yai sannan yace " karkisa takalminki ki bari sai na dawo zan taho da plaster." Kai ta d'agamai nan ya juya yai gaba. Kallo ta bishi da shi basai ta tambaya ba soyayya ce ke yawo da ita, yau ta tabbatar da hakan dan ita kad'ai tasan metaji da taga mace tana neman jan ra'ayin Jalal, ajiyar zuciya tai tace " My First Love?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannayenta alamar kunyar kanta take. Jalal na komawa suka shiga tsokanarsa meye tsakaninsu, had'e fuska yai yace " meye tsakaninmu kuwa? Kufa kun iya gulma bana kuma san haka, aiki mukeyi muyi mu rabu banasan a d'inga sako personal matters aciki." Jin haka yasa sukai shiru nan suka cigaba. Basu wani dade ba suka gama, da sauri Jalal yai waje.......... Da sauri ya fita yaje ya siyo plaster ya koma ciki, saidai yana zuwa cikin zumud'i ya bud'e kofar tare da shiga, sai dai abin daya bashi mamaki ba Seemah ba alamarta nan ya shiga duba gun sam batanan kansa ya shafa tare da cewa ina taje? Waya ya d'aga ya k'irata sai dai wayar a kashe take, juyawa yai ya fito. © *NWA* 🏌‍♀ © 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 1⃣9⃣ Haka ta karasa Office d'in Habib fuskarta d'auke da murmushi, da sagir suka gaisa sannan ta karasa kofar Habib tai knocking, nan ya bada izini ta shiga da Sallama, a zaune ta ganshi yana duba abu a laptop ga takardu a kusa dashi, tana shigowa ta karasa kusa dashi ta baya ta zuro kanta jikin screen d'in tace " Yaya baka ga kanwarka bane?" Juyo wa yai tare da zare medical glass d'inshi yace " Seemah kin iso?" Ta mik'e tare da hard'e hannuwanta tace " da alama bakaji dad'in ganina ba." Hannunta ya jawo sannan ya juyo yana kallanta yace " Sorry Kanwata wasu takardu ne zan tura Company d'in Dad na England." Kallansa tai ta turo baki cikin shagwab'a tace na hakura tunda dad d'ina zaka turama, yace yauwa zauna ki jirani na gama, amma fa sai munyi azahar zamu? Tace nasani yaya, ta fad'a tare da kallan agogon dake makale jikin bango, 11? Ashe zan d'ade? Mik'ewa tai tace "Yaya kai aiki a hankali ni bari inzaga inga Company d'in, yace to Seemah amma ki kula fa, tace ok. Fitowa tai direct tai hanyar gun aikin Jalal itakam bata ganin wani abun ne in taje gunsa, d'an su acan England mace d'an taje gun namiji ko ba saurayinta bane ba wani abun bane, Office d'insu ta isa ta murd'a tare da Sallama, juyowa sukai suka kalleta, karasowa tai cikin halin ko in kula tace " zaga yawa nake nazo kusa danan shine nace bari inshigo ku gaisa, kallanta sukai suka ce Shigo mana, Kallansu tai yanda taga suna za-zaune yasa ta game meeting suke, Jalal ta kalla, kallanta yake shima fuskarsa d'auke da murmushi, shigowa tai ta karasa ta zauna daga gefensu, tace " karku damu dani kucigaba da aikinku." Nan suka juya suka cigaba da meeting d'insu sai dai jefi jefi suna kallan juna a sace itada Jalal, suna cikin meeting ne wata tai knocking tare da bud'e kofar ta shigo, Seemah ta kalleta kana ganinta kasan Christian ce daga yanayin shigarta, siket ne iya gwiwa da riga coat sai da bata rufe mab'alin saman rigar ba hakan yasa inta sukunya zaka iya gano kirjinta. Cikin salo ta karaso tare da tsayawa kusa da Jalal, Seemah kam idanta na kanta, matar ta kalli Jalal tare da mik'amai takarda cikin kissa ta zubar da takardun Jalal ya sunkuya zai d'auko itama cikin salo ta sunkuya, tare da rike hannunsa tace " Barshi........." da karfi aka katseta tare da cewa " Let go of that hand." Da mamaki kowa ya juyo ya kalleta Jalal ya fizge hannunsa tare da makama matar harara yace " what are you doing?" D'agowa tai ta kalli Jalal sannan ta kalli Seemah tace " Who is She?" Karasowa Seemah tai tace " what? Baki da da'a ne? Ko dama tambada ne ya kawoki nan?" Matar ta kalleta tace " meye damuwarki a ciki?" Yanda tai maganar zakasan hausan bata gama zama mata ba. Harararta Seemah tai tace " meye nawa kuwa a ciki? Sai dai bazan bari ina kallo mace irinki ta nemi lala......" Jalal ne ya katseta yace " ya isa haka, abar maganar haka." Seemah cikin takaicin da batasan kanshi ba ta kalleshi sannan tai waje da sauri, Jalal ya bita da kallo sannan yacema matar ta fita, abokanan aikinsa suka kalleshi sukace ina taje? Ido ya runtse sannan yace ina zuwa yai waje da sauri, dubata yafarayi tundaga office d'insu sai dak bai ganta ba, tunanin gun da suke zama ne ya fad'omai dasauri ya karasa gun elevator ya tab'a sai dai abin haushi tana kasa hakan yasa kawai ya wuce beni yafara hawa da sauri, matatakalar nada yawa sosai amma sam bai kula ba yana isa yai saurin karasawa kofar ya bud'e, tare da duba inda take zama, a zaune ya ganta ta had'e kai da gwiwa tana kuka ita kanta batasan meke damunta ba sai dai abu d'aya daya bata haushi katseta da Jalal yai tana magana, Jalal ya karaso gabanta ya tsugun na, cikin sanyin murya yace " me kike anan?" D'ago jajjayen idanunta tai ta kalleshi cike da mamaki yace kuka? Meya saki kuka? Harara ta makamai sannan tasa hannu ta share hawayenta jiyai zuciyarsa ba dad'i yace " Haushi kikaji? D'an ta rik'eni?" Cikin masifa tace " Yama za'ai ka d'inga bari mata na tab'aka?" Yace " kin kula kuwa? Bafa da saninta bane." Cikin abin kuka tace " kare mata zakai? Bayan ina ganinta? Tashi ka bani guri tunda kare mata zakai, daga yanzu kuma bazan kara damuwa ba in wata ta tab'aka." Murmushi yai yace " Don't tell You are jealous? " Da sauri tace " ni? Inji wa? Akan me zanyi kishin?" Ya kara sakin murmushi sannan yace " haka ne bayan na san kin tsaneni." Nan ma da sauri ta kalleshi tace " nidin? Injiwa? Waya fad'ama na tsaneka?" Kasa yai dakai yana murmushi idanunsa ne suka kai kan kafarta da alama takalmin yajima dunduniyarta ciwo garin sauri ko gudu datai d'azu, hannu yasa ya zare mata takalmin kafarta, kallansa tai cike da mamaki tace " menene?" D'agowa yai tare da had'e rai yace " gudu kike d'azu?" Kai tad'aga tare da kallan sa, iska ya d'an furzar yace " in zaki d'inga gudu kidaina sa irin takalmin nan gashi kinjima kanki ciwo." Murmushi ta saki sannan tai kasa dakai ahankali tace "are u worried about me? " D'agowa yai ya kalleta nan suka kurama juna ido a hankali ta lumshe ido, Jalal ya kura mata ido shikam bai tab'ajin abinda yakeji a wannan lokacin yana tsirgamai ba, itama idanun data lumshe jitake kamar me, wani irin so ne ke tsirga mata. Ajiyar zuciyar da Jalal yai ne yasa ta bud'e ido ta kalleshi yace " nabar wayata a office nasan za'a nemeni bari naje mu karasa, ko zakizo mu koma?" Tace " inafa zan koma bayan na gamajin kunya." Murmushi yai sannan yace " karkisa takalminki ki bari sai na dawo zan taho da plaster." Kai ta d'agamai nan ya juya yai gaba. Kallo ta bishi da shi basai ta tambaya ba soyayya ce ke yawo da ita, yau ta tabbatar da hakan dan ita kad'ai tasan metaji da taga mace tana neman jan ra'ayin Jalal, ajiyar zuciya tai tace " My First Love?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannayenta alamar kunyar kanta take. Jalal na komawa suka shiga tsokanarsa meye tsakaninsu, had'e fuska yai yace " meye tsakaninmu kuwa? Kufa kun iya gulma bana kuma san haka, aiki mukeyi muyi mu rabu banasan a d'inga sako personal matters aciki." Jin haka yasa sukai shiru nan suka cigaba. Basu wani dade ba suka gama, da sauri Jalal yai waje.......... Da sauri ya fita yaje ya siyo plaster ya koma ciki, saidai yana zuwa cikin zumud'i ya bud'e kofar tare da shiga, sai dai abin daya bashi mamaki ba Seemah ba alamarta nan ya shiga duba gun sam batanan kansa ya shafa tare da cewa ina taje? Waya ya d'aga ya k'irata sai dai wayar a kashe take, juyawa yai ya fito. © *NWA* 🏌‍♀ © 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣0⃣ Nan ya sauko yana tafe yana nemanta, sai dai sam bai ganta ba, gangarawa yai yaje Office d'in Habib ya bude tare da kallan Sagir, Sagir na ganinshi ya mik'e tare da cewa shigo mana Jalal, nan Jalal ya karasa tare da mikamai hannu, suna gaisawa amma yana waige waige, Sagir ya kalleshi tare da zare hannunshi yace " Jalal me kake nema?" Kallansa yai yace " Na'am? Kawai nazo mu gaisa ne." Nagode kwarai, abin ya ban mamaki baka tab'a ko zuwa inda nake ba sai dai ni na nemeka amma yau da kanka? Sagir ya fad'a tare da zama, Jalal yajuya yace bari na wuce ai mun gaisa, ya fad'a yana kallan office d'in Habib. Sagir yace nagode Jalal, har yakai kofa ya juyo yace" Chairman shi kad'aine a office?" Da mamaki Sagir ya kalleshi yace shikad'aine zaka shiga ku gaisa ne? Da sauri yace no, na tambaya ne kawai. Yana gama fad'ar haka yai waje. Jalal na rufo kofar yai ajiyar zuciya yace ina taje? Nan ya cigaba da nemanta gajiya yai da yawo ya samu wata kujera ya zauna yana d'an maida numfashi, ya d'an dade kafin ya koma inda suka saba zama, yana bud'e kofar ya karasa jiki a sanyeye zuwa inda take zama, sai dai abin mamaki jiyai ance " Deen ka dawo?" Da mamaki ya kalleta idanunwansa cike da tambayoyi karasa wa yai inda take tsaye ta jingina da bango tana kallansa, kusa da ita yaje ya saki ajiyar zuciya yace " ina kika je? Kinsan neman da namiki kuwa?" Wani sansanyar murmushin kauna ta saki sannan tace " naji dad'i daka nemeni." Had'e rai yai sannan ya lankwaso babban yatsansa dana kusa dashi ya d'ana mata a goshi da sauri tasa hannu agun ta kalleshi kamar zatai kuka cikin shagwab'a tace me kuma nai? Hararar wasa ya mata sannan yace " tambaya kike? Ina kika je? Kika sani nemanki?" Gun takara sosawa sannan ta matsa daga jikin bangon tace suprise!!! Kallan gun data matsa yai kwali ne mai fad'i a jiki akwai hoton pizza sai kuma ledar da yana hango lemon kwallin dake ciki, kallanta yai yace " nameye?" Kai ta girgiza sannan ta zauna ta mai alama da hannu ya zauna nan ya zauna yana kallanta yace " menene?" Hararsa tad'anyi tace "lunch zamuyi kafin in tafi." Murmushi ya saki sannan yace " abinda kika sauka yi kenan?" Tace " eh so nake muci abinci tare." Kallanta yai sannan yace next time in zamuci abinci nizan siya banaso kid'ingayin abinda namiji ya kamata yai." Aranta tace ina gani ba hali gareka ba yaza'ai in d'inga d'aurama wahala. Sai alokacin ta tuna meya ce mata yanzu. Ido tad'an rufe sannan tace " next time in zamuci? Kana nufin ba wannan bane last kenan? " Ehem gyaran murya yai bai magana ba, Had'e rai tai tare da bud'e pizza sannan ta gutsira ta mik'amai sannan nan ya ansa suka fara ci, ta kalleshi tace Deen what are we? Kallanta yai shima jikinsa yai sanyi cikin sanyin murya yace "we? Kodayake I think munzama we?" Jiyai tace me kake cewa? Tafad'a tare da bud'e mai lemon ta mik'amai ya ansa tare da kallanta mantawa tai taci abinci da hannun kawai ta rufe idannunta, yaji ne ya shigar mata ido ta saki wani kara, tare da kokarin goge idannun da sauri Jalal ya rik'e hannun da take kokarin kaiwa sannan yai saurin kurbar ruwa ya kuskure bakinsa sannan ya matso a hankali ya fara hura mata idan da yajin ya tab'a, batasan sanda ta ware idanun ba, sam jitai yajin ya tafi kallansa take idannu a bud'e zuciyarta kuwa sai bugawa take da karfin gaske, karkatar da kai yai sannan yagyara zamansa, yace " u are soo clumsy taya zaki......." Ganin yanda take kallanshi yasa ya hura mata ido yace Kallanfa? Da sauri ta mik'e tsaye d'an jitake kamar bazata iya numfashi ba ta mik'e tana bubuga kirjinta, da sauri Jalal shima ya mik'e yaje gabanta ya kalleta tare da cewa menene kikeyi hakan? Idanunta ta zaro tana kallanshi sannan ta runtse idonta tad'anyi baya daga inda yake, da mamaki ya kalleta yace " Mekike hakan?" Juyawa tai sannan ta zauna agunta nad'azu tace " kawai nidai kad'an dingayin nesa dani." Kallanta yai da mamaki yace " Bangane ba? Bakyaso inzo kusa dake? Ko me kike nufi?" Seemah a hankali ta d'ago ta kalleshi tace " bafa haka nake nufi ba." Fuskarsa ya matso kusa da tata ya shiga jujuya kai itakam jitai numfashinta ya d'auke, idanuwansa kawai take kallo? Yad'an daga sannan yace " kince bakyason inzo kusa dake amma idanunki sun nuna kinaso me kenan?" A hankali tai ta furzar da iska tana cewa "Cool Down Seemah." Kallanta yai sannan ya d'au pizza ya kara ci, sai da ya gama ya matso kusa da ita tare da kamo kafarta ya ciro plaster d'in daya siyo ya sa mata a gun dataji ciwon nan, itakam kallanshi kawai takeyi, d'agowa yai yace ba fita zakuyi ba? Kallansa tai tace karfe nawa? Agoggon hannunsa ya duba yace 1 nima tashi zanyi inje mosque, nan ya mike tare da gutsirar katuwar pizza ya tura mata a baki yace " ba kallo ba kice abinci kije kar yayanki yai ta jiranki." Ya juya ya fara tafiya, sai dayai d'an nisa ya juyo yace kuma ki kunna wayarki. Ya juya ya fita, kallo ta bishi da shi jitai shakuwa ta zo mata, cire abinda yasa mata a baki tare da kara wata shakuwa, juice d'in ta d'auka tasha sannan ta baza tagumi tace " Seemah ya zakiyi? Haka ake soyayya ko kuma nawa ne hakan?" Sama ta kalla hasken rana yasa tai saurin yin kasa da kanta, tace dole inyi tambaya kila ko ciwon zuciya gareni ko wani abun. Tagama cin abinci sannan ta sa ragowar a leda ta mik'e. Habib bayan sunyi Sallah ya kira wayar Seemah a kashe nan ya tura Sagir yaje ya dubo office d'in ko tana can. Yana shiga ya tadda ta idar da sallah itama yace " madam ana jiranki." Nan ta mik'e tare da cewa to, nan ta fito. Sun shiga mota, Habib ya kalli Seemah yace " Kanwata me kike tunani?" Juyowa tai tace " Yaya baka tunanin wani abun zai kara faruwa ko? Ina tsoron kar abinda yafaru agidansu Hajiya ya kara faruwa. Kallanta yai jiki a sanyaye ya sa hannu akanta yace " karki damu Seemah insha Allah ba abinda zai faru." Tace ka fad'ama dad zamune? Yace a'a ai ba sai na fad'amai ba in zamu gaida 'yan uwa, tace to. © *NWA* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣1⃣ A wani katon gida suka tsaya, mai gadin da sauri ya bud'e motar tare da mika gaisuwa, sunyi parking sannan Habib ya kalli Seemah yace muje ko? Kallansa tai idanunta sunyi raurau kai ya d'aga mata alamar it's okay. A hankali ta zuro kafarta ta fito, nan suka jero tare da nufar gidan. Bayan sunyi knocking aka zo aka bud'e wata yarinya ce wanda a haife batafi Seemah ba, tana ganin Habib ta saki fara'a tace " Yaya Habib yau kaine a gida?" " Tafi shan ni ba ruwana dake ai." Ya fad'a tare da shiga, Seemah na biye dashi. Matsawa tai d'aya gefen tace " Haba yayana na kaina ai nasan bazaka iya fishi da ni ba." Kunnenta ya kama tasa kara tare da cewa yaya Habib da zafi fa? Seemah ce ta kalleshi ta saki fuska tace " kai yaya Habib daga isowa sai a fara da cin zali? Amata hakuri." Sakinta yai yace " kinci darajar kanwata mai daraja." Kallan Seemah tai tace " badai mai darajar nan wannan sakaliyar kanwar taka ba.....?" Hararar da Habib ya maka mata ne yasa tai shiru kallam Seemah yai yace " kyaleta kanwata wannan da kika ganta batajin magana." Jisukai ance lale maraba da Habibullah, juyawa sukai inda maganar ke fitowa, wata babbar macece wanda kana ganinta kasan takai misalin shekara 50, sai dai tasha kayanta ta kuma d'aura d'ankwali abinta dagwas, fara'a ce sosai a fuskarta Habib ma fuska ya saki sosai ya ja hannun Seemah suka karasa gunta, zama tai suma suka karasa suka zauna a kusa da ita a kasa, Habib ne ya gaida ita sannan Seemah, ta amsa tare da cewa " Zara na neman hanaka hutawa ko?" Kallan wacce aka kira da Zara yai yace ai Ummy wannan yarinyar tana bukatar bulala a gurina. Dariya suka saki dukansu, Ummy tace tashi ki kira Abbanku, nan ta mike tana cewa yaya habib zanzo Allah, amma sai yaya Ammar yazo kasar. Da mamaki Seemah ta kalleta Ammar? Habib ne yace " Gwara ma kizo d'an Allab ba wai saboda Ammar ba kinfi kowa sannan yace bayayi dake." Da sauri ta karasa b'angaren Abba fuska a had'e, tana dawowa, Abba na shigowa, Abba shima ya taho yana farinciki, Ummy yaji tace " Habib wannan fa? D'an ban tab'a ganinta ba?" Murmushi Habib yai yace " Kanwa tace Seemah." Ummy ta maimaita Seemah? Seemah? Abba dake tsaye idanunsa suka tashi daga farin ciki, su ka kad'a sukai jaa, sunan yake maimaitawa a ransa da kuma abinda ya faru a baya, abinda ya ruguzama kaninsa rayuwa ya kuma tada hankali duk zuri'arsu suka zama abin nuni ga duniya, yana tsaye Zara tace "Abba yaka tsaya anan?" Juyowa sukai dukansu suka kalleshi Habib ya saki Murmushi ya mik'e tare da tahowa gunsa, Ummy kam tunda taji sunan itama jikinta yai sanyi, shiru tai kawai tana kallan Seemah. Habib na zuwa kusa da Abba ya kama hannunsa tare da cewa " Abba na dade banzo gaisuwa ba ko?" Kallansa Abba yai idanunnan jawur, zaiyi magana sukaji ance " Hello My Ummy Ur Son is back." Gaba d'aya kowa ya juya ya kalli kofa, saurayine da baifi su Ammar ba sai dai yasha kayan nigogi kana ganinshi kaga saurayin dake ji da kansa, idanunsa nakaikan Habib ya karaso da sauri yace "Hello Bros long time no see" Baki Habib ya saki sannan ya kalleshi daga sama har kasa yace " Zaid kanannan a yanda kake, nikam yaushe zaka girma?" Baki yad'an karkata irin salon ' yan gayo maza d'in nan zaiyi magana idanunaa suka kai kan Seemah da sauri yakarasa kusa da ita ya matsa daf da ita yana kare mata kallo, itama kallansa tai tare da kokarin matsawa, mikewa yai yace Wow ummy she is just my type. Idanu Seemah ta zaro tare da kallansa, Zaid ya kanne mata ido d'aya dasauri tai kasa da kanta, gun Abba ya koma yace " Abba kumin aure please, nan da 1 week inasan auran yarinyarcan." Cikin tsawa Abba yace " Ashe haryanzu zaid bazakai hankali ba? Daga ganin yarinya kawai kafara min zancen banza? Kasanta ne? Ko kasan tsatson ta?" Kowa sai daya tsarata a falon. Cikin rashin fahimta da raahin jin dad'i Habib yace " Abba baka tambayeni ba ai, Kanwatace fa, Seemah." Abba ya kalleshi cikin bacin rai sai kuma ya juya ya koma ciki da sauri, Habib ya bishi da kallo, Seemah kam tumda take yauce rama ta farko da tsawa ta girgizata, jitai idanunta sun ciciko, Zara ta kalleta tace " Yaya Habib Gimbiyarku na neman yin kuka da alama bata sabajin tsawa ba." Da sauri Habib ya taho, Zaid yasa gudu ya rigashi zuwa, kusa da ita yakara zama shima kamar me shirin kuka yace " Babyna kiyi hakuri, haka sirikinki yake sai dai nima na dade banga b'acin ransa haka ba, but karki damu tunda ni inasanki zan kareki daga komai." Matsawa Seemah tai baya kad'an tana mai kallan mekakeyi hakan? Ummy ce tace " Zaid ka bari mana." Tafad'a tare da mikewa tace Habib inasan ganinka. Nan suka juya, Zara ta girgiza kai tace Seemah ina tausaya mikk kin had'u da cingam d'an manne, itama ta mik'e ta bar falon. Zaid ya kara matsowa gun Seemah yace " Babyna nasha wahala gurin nemanki,meyasa kika wahalar dani sai yau kika bayyanamin kanki?" Seemah ta kalleshi da mamaki tace " ni kuma? A ina ka tab'a ganina?" Jitai ya damko hannunta yakai saitin zuciyarsa yace " anan baby na." Da sauri ta fizge hannunta tare da nik'ewa tace " Banasan haka." Shima mikewa yai yace me kikeso to? Fad'amim in miki cikin gaggawa. Harara ta makamai tace " Zaid kake ko? To bari kaji nifa ba ka ra gareni ba, sannan ba tsoro gareni ba, wannan abin da kakemin bakomai bane illa sallon yaudara ta samari masu ji dakansu, saidai me? Am sorry d'an na riga na gano lagwanka, bakuma na tunanin hakan zaiyi tasiri a guna." Kallanta yakeyi kawai tana gama magana ya fad'i zaune rugub ya sa hannu a kirjinsa yace " wow! Kaiiii!!! I really like ur boldness, Baby na." Harararsa takara yi sannan taj hanyar waje. Habib nezaune a falon ummy, ta kalleshi tace " Habib kad'au yarinyar nan kubar gidan nan tun kafin Abbans Zara ya kara fitowa, dan banaji abin zaizo da sauki, kallanta yai yace " dab Zaid yace yanasanta ko me?" Ido ta runtse tace " kaidai kai abinda nacemaka please Habin banasan abinda aka birneshi da kyar a kara hakoshi." Kallan mamakin kalamanta yake sai dai ya daure ya mike yace shikenan bari mu wuce. Zaid bin Seemah yai a tsaye a jikin mota ya ganta, karasawa yai tareda mika mata wayarsa yace ur number is needed here! Juyawa tai tace" bazan iya bada wa ba." Zaid yace "Kefa kanwatace, d'an haka dole ne ki samin number dana bukata." Murmushin mugunta ta saki sannan ta amshi wayar tasa number tai dialing ringing 2 ta katse tace gashi nasa in naje gida zan gani dan ban fito da wayata ba." Murmushi ya saki yace " Amma Ammar yaci amana ta dabai tab'a nunan hotonki ba." Kallansa tai tace " ko kuma mutuncin dake tsakaninku bai kai ya kawoba ba, tunda dai ko abokanansa sunsan hotonane akan screen d'insa." Matsowa yai kusa da ita yace " Wow I really like ur Style dear. " Mota tai saurin bud'ewa ta shiga tare da kulle kofar, Murmushi zaid ya saki sannan ya juya. Habib ne ya fito fuskarsa d'auke da tambayoyi kala kala waya ya d'aga ya kira Dad tare da cewa " Dad munzo gidan Abba amma......" Jiyai Dad ya katseshi yace " Habib meyasa kukaje? Meyasa baka tambayeni ba? Ina Seemah ba abinda ya faru da itadai ko?" Habib da mamaki yace " Dad menene kake kokarin boyemin? Yaza'ai kace meyasa mukazo gun Abba?" Dad kam duk ya rud'e yace " Habib, Seemah fa? Is she alright? " Habib yace eh tare da kashe wayar, meke faruwa? © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* *Bang🔫* *Bang🔫* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣3⃣ Nan ya fara nuna mata yanda ake tuki, tafara ja sunayi suna kallan juna wani so ne ke kara ratsa dukansu, bayan sun gama suka fito waje, Seemah ta hau saman bayan mota Jalal ya tsaya a gabanta ta kalleshi tace " wani irin farin cike ne ke ratsani Deen." Kallanta yai cikin so sai dai kafin yai magana wayarsa tai kara yacirota, yana dubawa yaga Abbansa hakan yasa yad'an matsa kad'an da Seemah, bayan sun gaisa ne Abba yace " Zaka shigo wannan weekend d'in?" Kallan Seemah yai sannan yace " Wlh Abba bansanj ba tukun na ya jikin Zaheeda?" Abba yace " Da sauki dama zancen kai kudin ka ne, a cikin kud'in da kake turowa akwai ragowa ina ganin ya kamata mukai karshen satin nan." Jalal jiyai kamar an d'au bokitin ruwan sanyi an shekamai a jiki, dakyar ya daure yace kud'i kuma Abba? Da wuri haka? Yad'an kara matsawa hakan yasa Seemah hankalinta ya gaza kwanciya, saukowa tai tare da zuwa ta bayanshi kad'an. Abba yace " Jalal me za'a jira to? Munada d'akuna dayawa kasani Zainab ba irin yan matan zamani bace da zatace sai kaza take so,to me zamu jira?" Idan Jalal ya kad'a yace " Amma Abba ita Zainab d'in ta fad'a tana so nane? Karfa ayi abinda bazaiyi dad'i ba, d'an Allah Abba a d'an tsagaita maganar kai kud'in ka ga........" Abba ya katseshi yace "Jalal anya zaman Abujan nan bai fara lalatamaka dab'iun ka ba? Ka tab'amin musu akan al'amuran dana yanke a kanka? Yau kai ne da kanka?" Ajiyar zuciya Jalal yai zuciyarshi tai ba dadi yace " Abba ba haka bane kayi hakuri d'an Allah." Katse wayar Abba yai Jalal yanata Hello hello jin shiru yasa ya duba wayar, gaba d'aya jiyai jikinsa ba dad'i juyowa yai da niyyar ganin Seemah sai dai a bayanshi ya ganta idanunta taf da kwalla da sauri ta juya zata wuce, hannu yasa da sauri ya riko hannunta, tana tsaye batare da ta juya ba sai dai hawaye a hankali suka fara sauka daga idanunta, Jalal ne ya matso ta gabanta tare da kallan fuskarta, da sauri tai kasa da ido tana hawaye jikimshi ya karayin sanyi, dakyar ya daure tare da jan hannunta suka fara tafiya, gun zamanta ya bud'e mata ta shiga shikuma ya tsugunna daga setin kafafunta hanayensu na rik'e, yadaure yace " Meemah kinji komai?" Kallansa tai da raunanan idanunta hawaye suka zubo ta luntse ido tare da had'iyar wani abu tace " Deen aure za'a maka?" Shiru yai baice komai ba tace " dama a can England ana yawan cewa First love bai fiya kai mutum ga aure ba, Deen ban tab'a soyayya ba sai akanka, na d'ade da fara sanka amma sai yau Allah yai zamu fad'ama juna sirrin zuciyoyin mu ashe yau ne kuma rana ta karshe da......." da sauri yakai yatsarsa bakinta yace shiiiiiii Meemah don't say something like that. " Kallansa tai hawaye nakara bin kuncinta hannu yasa yana share mata yana cewa " Meemah iyayen na ke san auramin ita, kuma bansan yanda zanyi in hana ba, d'an haka na taso ban iya musu ga mahaifina ba." Hannunsa dake kan kuncinta yana goge mata hawaye ta rik'e kallanta yai da mamaki tace " Deen please don't live me." D'ayan hannunsa yasa ya kara damke hannun nasu yace " I won't live you Meemah, but ke kina tunanin za'a barki ki aureni?" Kallansa tai tace "menene da kai? Ni komai yamin naka." Dariya yai yace "ba wannan ba, kinsan dai duniyar da nake ciki da wacce kuke ciki va d'aya bace." Tace" Duk abinda nace inaso ahi akemin a gidan mu so karka damu da wannan, kai nake so ba wani abu naka ba." Murmushi ya saki sai kuma ta fizge hannunta tare da hard'e su, ya kalleta yace " lafiya?" Tace " ba dai auran waccen zakai ba sai kuma kai tunani kara aure na ba?" Kallanta kawai yake yana mamakin kalamanta tacigaba" Jal nifa a tarihin rayuwata babu raba miji." Kallanta yai ya guntse dariyar dake neman fitowa ya mik'e tsaye tare da cewa " Shikena da na d'auka ko mata uku gareni tunda muna san juna ba wani abun bane amma yanzu na gane." Yai maganar fuska a had'e. Seemah ta kalleshi tace uku? Da sauri ta fara waige waige Jalal ya kalleta da mamaki wani shago taganu daga nesa da sauri ta fara tafiya, Jalal yasha gabanta yace ina kuma zaki? Bata mai magana ba kawai nunamai shagon tai, yace me kikeso? Alama tamai da ruwa, yace koma bari in siyo, nan ya karasa yace abashi robar ruwa, nan mai shagon yace naira 100, Jalal ya zaro ido yace ya pure water naira 5 shikuma wannan har 100? Mai shagon ya kalleshi da mamaki, wallet d'insa ya d'auko 200 ne a ciki ya mika tare da ansar ruwan, ya juya yana zuwa ya mika kata, ansa tai tasha sannan ta mikamai tace kuskure bakinka, yace bangane ba? Cikin shagwab'a tace nidai ka kuskure bakinka banasan tuna kalamanka dakai na mata uku. Dariya ce ta kamashi yace " haka kike da kishi? Tace ba kishi bane ba amma ai......... Dariya yasa tare da girgiza kai, komawa yai mazaunin driver yace " Yamma ta farayi kar a nemiki a gida." Juya kai tai tana kallan window, Jalal yai murmushi ya tada mota, sun fara tafiya ya sa hannu ya anshi ruwab hannunta ya sha, kallobta bishi dashi tace "cewa fanai ka kuskure baki ba fa ka shanye maganarka ba." Kallan bakin jarkar yai saitin inda shatin jambakinta yake nan ya kara kafa rubar yasha tare da sakin wani murmushi shikanshi mamakin kansa yakeyi. Fizge robar tai tace " bazaka amsamin ba?" Kallanta yai kad'an sannan ya maida kallansa zuwa titi baice komai ba. Tafiya suka cigaba ba tare da kowa yayi magana ba haushi ya gama kama Seemah kara ta saka da sauri Jalal ya kalleta yace " Seemah menene? Da sauri ya gangara gefen titi tare da maida hankalinshi gaba d'aya kanta hannayenta ta sa ta rufe fuskarta, ciki damuwa ta sa hannu ya zare hannun data rufe fuskarta yace " Meemah menene?" Idanunta a rufe suke yace " wani gurin ne ke miki ciwo?" A hankali ta bud'e idanunta tace" banasab ina maka magana kana k'in bani amsa, it hurt me." Kallanta yai batare dayace komai ba ya gyara zamanshi tare da fara tuki, kallansa take rai a b'ace jitai yace " Wani sa'in ne bana sanin me zan ce miki, ban tab'a shiga ciki hali irin wannan ba inji wai bansan me zance ba sai a kanki." Juyowa yai yad'an kalleta sannan yacigaba " Ban tab'ajin irin haka ba a tsawon rayuwata." Kallansa takeyi jikinta yai sanyi, kalamansa sun tab'ata idanu ta lumshe tare da jingina kai tace " I will take ur word as ni ka fara so a duniya." Kallan hanya kawai yake yana murmushi itama lumshe ido tai tana murmushi, wani irin so takema Jalal da ko suna tarr jitake tana missing d'insa, zuciyarta na bugawa a duk lokacin dayake kusa da ita, kalamansa kesa zuciyarta da ganganjikinta su yi lum cikin wani shauki, ya zatai in wani abu ya bemi shiga tsakanin............wayar Ammar ce ta katseta, basai ta duba ba d'an ringing d'insa daban ne a wayarta, d'auka kawai tai tare da gyara kwanciyar kanta zuwa kallan Jalal, tace " Yayana ya? Ammar yace " Seemah yanzu Zaid ya kirani wai a lalai shi ya d'auka number kice, murmushi tai tana kallan Jalal tace " Shareshi yaya shi wai a dole sai na bashi number ta shine na bashi ta ka." Ammar yai Dariya yace " Kai Seemah, me yasa? Bai miki ba?" Tana kallan Jalal tace " inafa zaimin bayan na riga na kulle zuciyata?bana kuma tunanin wani zai samu damar shiga." Kallanta Jalal yai wani farin ciki ma ratsashi bai tab'a ganin yarinya kamar Seemah wacce bata kunyar kalamanta ba, ko d'an ba anan ta taso ba? Sam bata kunyar fad'ar abinda ke ranta. Da mamaki Ammar yace kamar ya? Tace " there is something like that. " Tana kainan tace yaya bye zan k'ira anjima. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* *FIGHTING* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣4⃣ Sun isa gidan Jalal yai parking a waje sannan ya kalleta yace " zan wuce." Kallansa tai tare da d'aga kai alamar eh, Jalal na fita itama ta fito tare da Kallansa ta baya, sannan tai ajiyar zuciya ta shiga gida, a tsatsaye taga su Farida da Aisha, suna ganinta Farida ta hau cewa Seemah ina kika shiga? Ko kallanta batai ba ta karasa gun Bala ta mik'amai key tace ka shigo min da mota, sannan ta karasa inda suke, tace " sannunku da gida yaya fa?" Wani kululun takaicine ya kamasu duka, Aisha ta zuciya tace " bakiji tambayarki ake ina kika je ba? Kinsan neman da muka miki ne?" Wani irin kallo ta watsa mata tare da cewa " ke in kin fita nemanki ake? Me kuka d'aukeni? Jaririya? Ko me? Ko kuwa ban isa in fita ba?" Tana kainan ta kallesu tai ciki, Aisha tai kwafa tace " wlh Auntu na tsani yarinyar nan." Farida ta bi Seemah da kallo tace " in muka duba kalamanta bata fad'i karya ba, in kika fita ba nemanki akeyi ba, meyasa ita bata isa ta fitaba sai muhau nemanta." Aisha tai shiru, Farida tace " Aisha na kula Seemah ba yarinyar banza bace kawai yanda zatai responding magana ne bata iya ba, ita kawai abinda ke ranta take fad'a bata damuwa ko kalaman zasu b'atawa wanda aka fad'awa rai." Aisha ta jinjina kai, nan sukai ciki gani za'a bud'e gate a shigo da mota. Seemah kam tama shiga a bakin gado ta zauna ranta a b'ace, dasauri tai dialing number Jalal yana d'agawa yai sallama, ajiyar zuciya tai jin muryarsa sai taji duk bakin cikin ya tafi murmushi tai sannan ta katse layin tare da kwanciya ta rungume pillow, wani shaukin so ne ke ratsata, Aisha ce ta shigo tare da kallanta tace "Seemah me kikeyi hakan?" Bud'e idanu tai tace " Bazaki gane ba ko na fad'a miki." Aisha kam ta sani batasan Seemah sai dai wannan hali nata ma birgeta ko anyi fad'a da ita yanzu in har ka mata magana to komai ya wuce. Zama tai a bakin gadon tace " nakula dai soyayya ke ratsaki." Seemah najin haka ta mik'e tare da cewa kun shirya da saurayin ki? Tagumi tai tace " inafa haryau bansan a ya muke ba." Seemah tai ajiyar zuciya tace a ganinki yana sanki? Aisha tace I can't tell d'an shekara 1 da suka wuce ne ya ganni a hanya yace ya sona, to ni tun daganan muka fara waya, sai dai bai tab'a zuwa inda nake ba sannan ba nemana yake ba. Seemah ta kalleta tace " Just 4get him, d'an banaji yana sanki ko kuma mayb akwai wacce ya gani yanaso daga baya." Aisha ta kalleta tace " ni kaina inasan in manta dashi sai dai na kasa, amma ke kamar naga kwanan nan kina cikin wani yanayi. Seemah tai murmushi tare da cewa " wani nake masifar so sai dai ni kaina nasan nafi sanshi." Aisha tace ya akai kika sani? Seemah ta rufe ido tace " ni bai dameni ba d'an nafi sanshi abinda na damu da sani shine shima yana sona," tai ajiyar zuciya tace "that's all I need. " Aisha ta kalleta gaskiya wannan boldness na Seemah da kuma halin ko in kula yana birgeta. Jalal kam ya kwanta bacci sai dai sam ya kasa bacci sai juyi yakeyi shi kad'ai why is he feeling uneasy? ganun abun bazai kare ba yasa ya mik'e ya d'auro alwala tare da fara salolin nafila. Da safe wajen karfe 10 Seemah dake kwance ta bud'e ido a hankali, sai dai abinda ta gani ne yasa ta kara lumshe ido, DAD ta gani ya na shafa kanta, bayan ta kara bud'e idon tau murmushi tace " Dad I miss u alot." Ita duk ta d'auka mafarki take jitai yace " kin tashi Sweetheart? " Mik'ewa tai da sauri ta zauna ta zaro ido tace Dad? Dad ya kalleta yace " dafatan Princess d'ina tana lafiya." Rungumeshi tai tare da cewa Dad yaushe kazo? Ya shafa bayanta yace " nayi missing daughter ta dayawa shiyasa nazo in ganta mukuma tafi tare." Dagowa tai cikin mamaki tace " Dad satina fa d'aya?" Dad yace tashi kiyi wanka kiyi breakfast ni zan d'an fita im ma dawo sai muje yawo, murmushi ta saki tare da dunkule hannunta ta bar babbar d'an yatsa tace " Dad u are the best." Dad ya mik'e tare da cewa sai na dawo tace " ok" shima yace ok. Farida ya tadda a kasa yace bari in wuce, tace Dad bakai breakfast ba? Yace naci abinci a jirgi zani Suleja ne. Bayan Dad ya isa Suleja ya fito ya shiga gidansu, Hajiya na zaune a tsakar gida ta baza tagumi yai sallama, tare da shiga amsawa tai tana kallan hanyar kofar. Dad ya shiga yana cewa " Hajiya meyasa ake barin kofar nan a bud'e." Kallansa tai cikin wani farincikin ganin d'anta shikanshi jira yake yaga ta mike sai dai abinda ya bashi mamaki gani yai ta koma ta had'e fuskarta, shiyasan laifin amma gani yake yanzu ai yaci ace an daina. Karasawa yai ya zauna a kusa da ita tare da gaisheta, ta amsa fuskarnan a had'e, kofar band'aki aka bud'e mahaifinsa ne ya fito Dad cikin farinciki yace kawo ka fito. Kawo ya karaso ya zauna Dad ya gaida shi, sai dai kawo bai amsa ba sai fad'a daya biyo baya, Isma'il ni zaka cima mutumci? Har kaine zaka turomin yarinyar nan gidana? Dad ya kalleshi tare da cewa " Kawo naga wai ai yanz....." Katse shi kawo yai yace " Yanzu me? Ka d'auka zamu manta? Ko kuwa d'an ka raina mu? To wlh bari kaji ko mutuwa nai bana bukatar yarinyar nan ta min zaman makoki." Dad idanunsa suka kad'a yace " Haba Kawo in muka duba abin nan yarinyar nam ba itace mai laifi ba me ta sani?" Hajiya ta katseshi" haka zaka ce? Yarinyar da dalilinta ya ruguzamana farinciki, ya sa mukai hijjira daga garin mu, kacemin me? Ba ruwanta?" Jikin Dad yai mugun sanyi yace " Dan Allah kubar maganar nan." Kawo ya mik'e cikin fad'a yace " kai wai wani irin mara zuciya ne? Ko kuwa san Fatima ne ya maka yawa? To wlh bari kaji na fad'ama, magana ma sai tazo aure, kai kana tunanin zaka iya boye maganar ne har karshen rayuwar ka?" Dad ya runtse idanu da karfi, meyasa kowa bazai fahimceshi ba? Suna tunanin abinda ya faru shi bai ji zafin abin bane ko me? Hajiya tace " sannan kayima yaranka waya su dawo Nigeria na hana zaman kasar wajen, dama d'an kar muga fuskar yarinyar yasa muka ce kabar kasar amma yanzu tunda kai dakanka ka aikota har cikin gidan mu sai ka shirya shirin dawowa, karkuma ka kuskura kamin musu akan maganar nan." Dad yace " naji zan dawo amma maganar karatun Seemah fa?" Kawo yace " kai wannan ya dama ba mu ba." Sunyi shiru kafin dad yace " Dama abinda ya kawoni shine ina tsoron kar Seemah ta iso lokacin aurene zancen da aka burne ya taso, sannan banaso yarinyar ta fuskanci wannan gaskiyar mai wahalar gaske, shiyasa nake tunanin aura mata Ammar." Hajiya ta watsa mai wani kallo tace " me? Ammar? Kanada hankali kuwa?" Dad yace " dan Allah Hajiya ku yanda da shawarar nan, in yaso sai ince Ammar ne ba d'ana ba." Kawo ya ce lalai na yadda Isma'il ka fara zarewa, tashi kabar mana gida sannan kamasu Junaid waya su tattaro su dawo, in ka kuskura ka koma kasar nan zakaga maizai biyo baya. Dad kamar wanda akama duka ya mik'e abin mamaki Hajiya ganitai hawaye yana kwaranya daga gefen idanunsa, ita kanta jikinta sai yai sanyi. Hmm Turkashi. ...... Seemah kam tana fitowa daga wanka ta k'ira wayar Jalal shima yana zaune a office, ganin kiranta yasa ya mik'e ya fita yana sallama ta lumshe ido wani sanyi na tsata itama ta amsa, Jalal ya saki wani murmushin dad'i yace " Meemah kamar na dad'e ban gankiba nakejina." Wani dad'i ne ya kamata tace " kasan me? Yace a'a tace "jinake kamar nayi shekara 1 da fara sanka, ji nake kamar bazan iya rayuwa ba in wani abun ya rabani........" Jalal ne ya katseta yace"Karki karayin wannan furucin, ba abinda zai rabamu in sha Allah, in kuma kina bukatar b'acin raina kisake fad'ar haka." Kan gado ta fad'a tare da lumshe idanunta tace " Deen ina masifar sanka, ni na sani nafi sanka akan yanda kake sona." Karfe dayake gun ya dafa yad'an kwanto yace " haka dai kike tunani amma ni anawa sanin nafi sanki, yau zamu had'u amma ko?" Tace " Dad yazo yau zamu fita dashi sai dai komin dare inajin in ban gankaba za'a iya samun matsala." A tare sukai murmushi yace bari inkoma aiko tace to Deen. Yana katse wayar ta rungume wayar a kirjin ta idanunta a lumshe hango Jalal takeyi kawai a idanun nata. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣5⃣ Dad ya fito jiki a sanyaye, mota ya shiga tare da dafa kansa da sitiyarin motar, zuciyarshi a ciki take fall da damuwa, yanzu ba wanda zaibi bayanshi a birne maganarnan da Ammar? Yasan halin yayansa sarai bazai bi bayan shawarar nan ba sai dai bashi da wani zab'in daya wuce yayan nashi. Nan ya tada mota yafara tuki, yana gaf da shiga layin Seemah ta k'irashi tace Dad yaushe zakazo kad'auken? Dad yace " Seemah ina d'an wani abin ne bansan how long abin zai kai ba , ko zamu bari sai gobe muje?" Seemah ta turo baki tace " shikenan Dad, Allah yakaimu." Yace Amin. Suna Sallama ta kalli kanta a madubi da sauri ta rufe fuskarta da hannu biyu sannan ta bud'e ta kanne ido d'aya tace "See you My Deen." Tana fad'ar haka tasa dariya tare da kara rufe fuska tana murmushi. Wayarta ce tai kara ta jawota ganin no name yasa tai sauri zata d'auka sai kuma ta ce haba Seemah d'an tsaya mana,Cool down, kinfiya azarb'abi, nan ta tsaya sai da ta kusa katsewa ta d'aga tare da cewa " ya akai?" Kallamanta sun bashi mamaki yace " ban gane ya akai ba? Bakiso na k'iraki ba ko me?" Seemah tai shiru tanajin wani sanyi a zuciyarta, Jalal yace shikenan sai anjima, zai katse tai saurin cewa Deen? Jalal ya maida wayar, Seemah tace " irin jan ajin nan na mata fa zan maka kaikuma ba hakuri." Dariya ce tazoma Jalal yace" to ni nasan ba wannan tsakanina dake, in fact ma ba haka kike ba." Cikin masifa Seemah tace " Me kake nufi da ba haka nake ba? Lalai ma Deen wato kana so kace bani da aji ko me?" Jalal yace" kema kinsan ba haka nake nufiba, nufina sanda kikemin nasan bazai barki kimin haka ba, kuma nima........" Ha what? Deen mai kake nufi? Wato harkasan sanda nake maka? Ni bansan wanda kake min ba." Jalal yace "oh my God! Seemah meke damunki yau? Ko kin tsaya kinji karshen maganata?" Dariya Seemah tasa tace" just teasing you! Kasan me? Inaso inga ima tsokanarka." Iska Jalal ya furzar sannan yace " zan rama ne." Tace guess what? Dad ya fasa zuwa muje d'an haka zamu iya had'uwa. Wani sansanyan murmushi Jalal ya saki yace inzo gidanku mu tafi? Tace a'a zan zo wajen Company d'in sai kazo mu tafi, yace alright nan sukai sallama tabi wayar da kallo tarr da manna mata kiss. Dad yana shiga yai parking har ya nufi ciki yaji ance " Mazan England ne a kasar tamu?" Juyowa yai jin muryar d'an uwa rabin jikinsa, a zaune ya ganshi daga gefen garden d'insa yana rik'e da jarida, nan dad ya juya zuwa inda yake, suna haduwa suka rungume juna Dad yace Yaya ashe kana waje? Abba ya kallesa yace baka fad'amin zakazo ba? Dad yai ajiyar zuciya tare da zama a d'aya kujerar yace " Yaya su Seemah sunzo ko?" Wani mugun kallo Abba ya sakar mai ya had'e fuska kamar zaki dama shi bashida fara'a, yace" Isma'il da hankalinka ka turo yarinyar nan kasar nan?" Dad yace " Yaya ya zanyi? Yarinyar nan takai shekara 20 'yan uwanta da ita kanta sun damu akan tazo nikuma sai naga kamar lokaci yaja yaci ace magana yanzu ta wuce." Abba yace " kai kana tunanin magana irin wannan tana wucewa ne? Ko ni dana ganta jinai komai ma neman dawomin sabo." Dad ya runtse ido yace " Yaya ka taimakeni yanda ka taimaken a baya, mu binne maganar nan da auranta da Ammar, in nace Ammar ba d'ana bane ba wani abu, nasan Ammar sarai bazai damu ba." Abba idanunsa suka kad'a yace " wai Isma'il kanada hankali kuwa? Bakasan tsatsonta ba amma me? Ka aura mata Ammar? Wai kai wani irin mutum ne da bashi da zuciya, banda bala'in da mahaifiyarta ta ja maka yanzu kuma me? Ammar?" Dad idannunsa suka ciciko yace " Yaya karka tunamin da abinda ya faru d'an Allah yaya, yanzu ni yaya matsalata d'aya banasan abinda zaisa Seemah cikin bakin ciki bare har tasan wannan mumunan al'amarin." Abba ya mik'e cikin zafin rai yace " Bazan goyi bayanka akan lalatamana zuri'a ba, sannan bazan yanda kasama Ammar bakin ciki akan wata banza da ba'a............" Da karfi Dad ya rufe ido yace " Yaya Please stop saying anything, please. " Abba ya kalleshi yana tausayin Kanin nasa sai dai bazai yadda da hukuncinsa ba, nan yace " Isma'il inka warware mayi maganar ka gama tunanin ka shigo ciki."yana kainan yai ciki, Dad ya fara saukar da numfashi sama sama, kansa na sarawa, hannu yasa ya rik'e kansa jiyai hawaye na zubomai. Seemah tana gama shiryawa ta fito a falo taga farida tace "Aunty zan danje ganin gari." Tace Seemah kinsan halin yaya...... Seemah ta katseta da cewa" ai shima bai hanani ganin gari ba." Tana kainan tai waje, sun fito ita da bala sai dai motarsu na fita Zaid ma kokarin shigowa sai dai ganinta a baya yasa ya saki murmushi tare da juya kan motar ya bita, sam ita batasan yana binta ba. Suna zuwa wajen company d'in tace Bala yai parking ta mik'amai kud'i tace ka koma gida, yace madam yau dai d'an Allah......, ta katseshi da cewa " so kake in koreka daga aikin ko me?" Da sauri ya amsa tare da bata hakuri, yana fita tama Jalal waya ta iso, jitai anbud'e d'ayan gefen datake zaune ta baya da mamaki ta kalli kofar kafin tai magana Zaid ya shigo, ta kalleshi da mamaki tace " malam ya dai?" Zaid ne ya juyo da fuskarsa tare da cewa " Wow I really miss u a lot. " Ta kalleshi tare da nunashi da yatsa tace " You?" Yatsar ya rik'e tare da ajiyar zuciya yace " yeah Baby is me, wow har naji wani sanyi." Hannunta ta fizge sannan ta kara nuna shi da yatsa tace " Ya Zaid don't you dare try to touch me again." kai ya kwantar ajikin kijera yace woooo kai baby u are killing me with your charm. Leb'e ta ciza sannan ta fito daga motar cikin takaici ta jingina da motar. Zaid ma ya fito yazo daf da ita tare da cewa ina zamu ne Baby? Harara ta nakamai tace matsa min ko bakaga a yanda kake bane? Tafad'a tana kallan yanda ya babbaketa, murmushi ya saki sannan yace " Baby I........" Naushin da aka mai a fuska ne yasa bai karasa ba, jikake tim ya fad'i a kasa, Jalal cikin hucci yake kallan shigarsa kana gani kasan ta samarin zamani ne da sukejin kansu a sama, Seemah ganin naushin nan yasa ta kalli Jalal zatai magana taga ya kara d'agoshi zai makamai wani, da sauri ta rik'e hannun Jalal tace " Deen?" Idanunsa sun kad'a sunyi jaa, ya kalli Zaid sannan ya kalleta yace waye? Zaid kam zafin dakemai zugi a baki ne yasa yakai hannu gefen bakinsa mezai gani? Jini? Wani kara ya saki yace jini? Jalal ya makamai harara yace kamin shiru kosai na karama wani? Zaid ya kalli Seemah yace " Babyna waye wannan da......." Jalal ya dunkule hannu saura kiris ya bugamai, sai kuma ya tsaya tare da kallan Seemah, sannan ya kalli Zaid yace baby? Seemah ta kalli Jalal tace " My Deen sakeshi d'an uwana ne he is just joking, baka ga yanda yake magana ba? Kana gani kasan na mayaudara ne ai." Jalal ya maimaita sunan a ansa My Deen? Tamasan ta fad'a kuwa? Kallanta yake cikin wanj shauki sannan ya tura Zaid gefe yace " Meemah me kika ce?" Ta kalleshi tace name fa? Yace " Abinda kikace yanzu da zakimin magana." Kai ta juya tana murmushi tace muje ko? Jalal ya d'an canza fuska. Zaid ya kalli Jalal yace " wai d'an tacema My Deen? Ahh amma kai gara ne, kamar bakasan mata da yaudara ba? Sai suce ma mutum My Heart sai ka duba wayarsu kaga ansa maka Jerk. Jalal ya kalleshi da mamaki sannan ya kalli Seemah tare da cewa muga wayarki? Kasa tai da ido tace " So kake kabar Ya Zaid ya had'amu dakai?" Zaid yace " Ahaf da alama ma bakada sunan mutunci a wayar." Yana kai nan yad'agama Jalal hannu yace " Boxing Man nayi nan. Jalal ya d'auke idansa daga kan Zaid ya kalli Seemah tare da cewa muga wayarki? Miyau ta had'iya ta tina No name tasa, da sauri ta zagaya ta shiga mota sannan ta danna horn, Jalal ya bud'e motar ya shiga fuska a had'e gani yake kamar jerk d'in ma aka samai. Seemah ta kalleshi ganin yanda yakejan mota da karfi, sai da sukaje can wanj guri sannan ya gangara yai parking tare da mik'a mata hannu alamar ta bashi, d'an yaga ta d'auko wayar da alama so take ta canza, ganin bata da niyya yasa ya fizge wayar tare da fitowa daga motar, wayarsa yadaga ya kirata, me zai gani No name ne ya bayyana akan wayar kurama sunan ido yai No name? Da rashin suna ai gwara jerk d'in ma, Seemah ce ta fito tazo kusa dashi jiki a sanyaye tace " My Deen amma......" wanj kallo daya buga mata yasa ta kasa karasa maganar, tafiya ya farayi itama tana binshi a baya, takalmi mai tsini ne a kafarta sam bata kula ba ashe dutse ne a gun kawai tai tuntube da takalmin Kara ta saka Jalal ya juya da sauri, sai dai ina? Har ta fad'i ta fara gangarawa dama kwari ne a gun, cikin tsananin rud'o ya lekata, ganinta a ya she a gefe yasa yai saurin d'ilikawa, yana sauka ya d'agota duk ya rikice ya shiga jijigata tare da k'iran sunanta, a hankali ta bud'e idanunta ta saukesu a kansa, kallansa takeyi shima kallanta yakeyi jiki a sanyaye yace "Seemah are u alright? " Murmushi ta saki tare da cewa a hankali" ba wai rashin me zan sa maka bane yasa na saka No name, nasane saboda a time d'in ina sanka gashi fad'a kawai ke had'amu da kai shi yasa......" Yatsa yasa a leb'anta cikin sanyin murya shima yace " Ya isa haka Meemah it doesn't matter ko me kikasa, abu d'aya na sani ina ganin sona a idanunki kamar yadda nima nake sanki." Ta lumshe ido tace " then why?" Kin manta nace miki zan rama? D'azu da mukai waya? Banyi tunanin abin zai jawo har ki fad'i haka ba." © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* *To u My Beely Badaru, Happy Birthday Sis, wish you long life and Prosperity.* ........😍😍😍😍😘 *Have fun it's ur day Beely.*🎂💃🏻💃🏻💃🏻 No. 2⃣6⃣ Mikewa Seemah tai tare da zama a kasan gun shima Jalal ya zauna kusa da ita kallan nesa da gun tai daji ne a gun, sannan tace " Deen Inama zan iya tsayar da lokaci?" Kallanta yau sannan shima ya kalli gun yace in kika tsayar da lokaci muna nan yaushe zamuyi aure kenan? Murmushi tai sannan ta juyo takurama ido tace " kana ganin za'a amince dani a gidanku?" Kai ya d'aga mata yace " karki damu da wannan ni nasan me zanyi akai." Ta d'auke idonta daga kanshi sannan tace " Ban tab'a tunanin zanji ina bukatar kasancewa da wani har inji inasan inyi aure ba." Ajiyar zuciya yai ya kura mata ido ji yake kamar ya d'auketa su gudu, Juyowa Seemah tai itama ta kalleshi idanuwansu ya had'u da juna, jitai ta kasa d'auke ido daga kanshi, wani irin kallo sukema juna mai ciki da ma'anoni daban-daban a hankali Jalal yakai hannu gefen fuskarta yace " Meemah I promise you this, I will always love you." Idanu ta lumshe sai ga hawaye sun zubo mata, Jalal ya kalleta yace menene? A hankali ta bud'e ido tace " Deen akwai time d'in da hawaye ke bani mamaki, suna zuwa a lokacin bakin ciki, sai dai akwai lokacin da in farin ciki yama yawa sai kaji hawaye." Sauke hannunsa yai daga fuskarta sannan ya mik'e yace " Okay tunda haka ne mu gudu mubar garin." Mik'e wa itama tai tana dariya tace " what? Mu gudu muje ina?" Juyowa yai ya d'ana mata hannunsa a goshi ta rik'e gun cikin shagwab'a tace ka sake ko? Yace wasa nake miki so nake insaki dariya ke kuma naga kina neman d'aukan abin serious. Juyawa tai tana kokarin haurawa sai dai ganin abin da wuya yasa ta juyo ta kalleshi tace na kasa, Murmushi yai sannan ya matso tare da mik'a mata hannu yace " kina da ni shine kike cewa kin kasa?" Hannu ta bashi nan suka fara hawa, suna isa suka shiga mota suka juya zuwa gari, sun tsaya a traffic light sai ga wani ya kawo agoggon hannu, guda 2 ne a kwallin iri d'aya sai dai d'aya na mace ne d'aya kuma na namiji komai na agoggon iri d'aya ne, Seemah ta kalli me agoggon tace bani wannan, nan ta siya yana tafiya Jalal ya kalleta yace dama kina siyan abin kan hanya? Hannunsa ta kalla dake jikim sitiyarin mota bata tankamai ba kawai ta fara sa mai agoggo, kallanta yai da mamaki yace me kikeyi hakan? Bata tankamai ba sai data gama sannan itama tasa nata ta jira hannunta kusa da nashi kallan agoggunan yai komai nasu iri d'aya murmushi yai yace anko kikeso muyi ko me? Hannu ta buga a goshinta tace "Oh God ya zanyi da Deen? Baisan komai a harkar soyayya ba." Jalal ya had'e rai yace " to in ba anko ba menene wannan?" Ta kalleshi tace " Couple watch ne baka sani ba?" Had'e rai yai ganin an basu hannu yaja motar, Seemah ta kalleshi tace kasan meye ma'anar abindq mukasa? Bai amsa mata ba ta cigaba da cewa " it will always bring us together, haka ake cewa a England magic d'in abin kenan, sannan daga yanzu karka tab'a cirewa daga hannunka in ba haka ba........" Sai kuma tai shiru kai ya girgiza yace " in ba yarinta ba mezai sa kiyi believing akan wannan shirman in na shire kuma sai me? Sai mu rabu ko........" Da sauri tace "please kai shiru, kasan me? Mu acan in tsakanin saurayi da budurwa wani ya cire nashi to yana nufin wanda ya cire d'in bayaso a cigaba da relation ship d'in." Jalal yace " inkuma ya tsage ko wani abun fa?" " worse scenario kenan, alamar akwai bad abu dazai faru tsakanin masoyan." Hararta Jalal yai yace " Kuma ke kina fad'amin kin yadda da wannan shirman?" Tace " ba hadda bane mu acan munyi believing da haka ne." Kai Jalal ya kara girgizawa yace " na manta ashe 'yar 20 yrs ce." Harara ta makamai batace komai ba ta juya kai tana kallan titi. Sunje daidai shiga kwanar gidansu motar Habib na fitowa daga layin, clashing sukai Habib yabi motar da kallo, tabbas motarsa ce, Kallan na ciki yai baidai gane ba saboda suna tafiya yadai ga namiji sannan a kwai mace a gefensa kamar Seemah. Har sun hau titi hankalinsa ya kasa kwanciya ya kalli Driver d'insa yace mu koma gida, Seemah kam Jalal na ajiyeta a waje yace bari na wuce zan d'an tsaya a company kafin na wuce, ta kalleshi tace dagaske gobe zaka Birnin gwarin? Kai ya d'aga mata yace " dole insan abinda zanyi kafin sukai kud'i." Kai ta d'aga tace " I will miss you." Shima yace mee too. Fitowa yai ya fara tafiya yana kallan motar ta wuce sai dai Habib bai ga fuskarsa ba sai bayansa daya gani, Suna zuwa kofar gida Seemah na fitowa, tana ganin motar Habib ta karasa kusa da motar, Habin ya zuge glass yace" Kanwata daga ina kike?" Ta kalleshi tace guri mai dad'i yaya. Gaban Habib ne ya fad'i guri mai dad'i? Ya fad'a yana kallanta, tace " yaya kaje ka dawo yau da daddare sai muje gun Dad inada abinda zan fad'a muku, tafad'a tana kallan agoggon hannunta. Habin ya gyad'a kai yace shikenan ba dad'ewa zanyu ba, amma wanda ya kawoki kamar ba Bala bane? Murmushi tai tace Some One Special ne yaya, ka bari zancen dazamuyi dakai kenan da daddare. "Okay bari inje, Amma Some.........." Katseshi tai tare da cewa bye yaya, tafad'a tare da shiga ciki, key kawai ta ba Bala ta shiga gidan fuskarta d'auke da tsantsar farin ciki. Dad sai jeka ka dawo yakeyi a d'aki, yarasa daga inda zai fara tufko zaren sam komai ya cud'e mai, Ammar shine kad'ai solution d'insa, waya ya d'aga ya kira Ammar, yace Ammar ka taho Nigeria gobe, inyaso kabar Junaid akan harkokin aikin shi kad'ai, wani farin ciki ne ya kama Ammar yace amma Dad step mom fa? Shi Dad sam yama manta da harkarta, yace kabarta acan ai ba wani abu bane, kuma za'abar gida ba kowa ne? Ammar yace " Dad na gode kamar kasan hankalina nakan Kanwata wlh, Dad yai murmushi yace kaje kai booking flight, nan sukai Sallama. Ammar wani sanyin farin ciki ne ya kamashi ashe zai ga kanwarsa kafin 1month? Kaiii shi harya kosa goben tayima. Hmmmm © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ . 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣7⃣ Jalal zaune yake akan kujera rik'e da takardu inka ganshi zaka zaci karantawa yake sai dai sam hankalinsa baya kan takardun, Seemarsa kawai yake gani a jikin takardar tana murmushi, ya kurawa takardar ido a hankali shima ya saki murmushi jiyai an kwankwasa masa desk, da sauri ya d'ago ganin manager d'insu ne yasa ya mik'e tare da cewa " Manager yaushe ka shigo." Kai ya girgiza yace " Jalal kwana biyu meke damunka? Sam baka maida hankali akan aikinka, gashi ka tsiri wani d'aukan excuse inka fita sai ka dad'e baka dawo ba." Kasa dakai yai baice komai ba, da fa kafad'arsa yai yace " Please Jalal ka koma yanda na sanka, yanzu ka duba maganar project d'in nan namu, sam ka kasa maida hankali akai gashi kasan kaf Team d'in nan namu da kai muka dogara." A hankali Jalal ya d'ago ido ya kalleshi jikinsa yai sanyi a hankali ya furta" I will work really hard Manager." Yace " thank you Jalal." Yana kainan ya bud'e office d'insa ya shiga, Jalal kam fita yai ya shiga toilet, ruwa ya zuba a fuskarsa sannan ya sa hannayensa biyu a kuncinsa yace " Wake Up Jalal, Get a Hold of Yourself. " yana kainan ya fito ya koma office ya fara aikinsa, sai dai jefi jefi yana kallan agoggon hannunsa. Seemah kam tagama yanke hukuncin fad'ama su Dad maganar Jalal saboda sam batasan sud'inga zuwa wanj gun in zasuyi zance, bayan tayi Sallar magrib ta fito falo, anan ta taradda Farida dasu Ra'isa, suna ganinta suka fara murna ta karaso kusa dasu ta zauna tace homework akeyi? Suka d'aga mata kai, tace to azo nizan koya muku, da gudu suka mik'e daga kusa da Farida suka dawo kusa da Seemah, dariya tai tace Aunty na mik'i kwace. Cikin sakin fuska tace " ni naji dad'in kwacen ma dan dama na gaji." Seemah ta dukufa tana koya musu homework har ya Habib ya dawo, da sauri ta mik'e taje kusa dashi tace " Yaya ka dawo? Ka fad'ama Dad?" Kanta ya dafa yace " oh ni kaina nakosa inji me Autarmu zata fad'amana haka, na fad'ama Dad yace muje gidan da yake." Da mamaki ta kalleshi tace " wani gida yake?" " ni kaina ban sani ba ashe Dad daga can yasa Abbansu Zaid ya d'inga masa gini, yana turo kud'in sai d'azu ya fad'ama." Ta jinjina kai tace " ohhhh lalai Dad da alama yayi tanadin bikina, kasan ku maza ne a gidan Abba akai taronka haka ma za'ai nasu ya junaid, duk da banzo bikinka ba amma naji a jikina bayan bikin kane Dad yafara min tanadi." Dariya sosai Habib yai yace " lalai kanwata kin girma, mene? Tanadin bikinki? Hahhhhh lalai zan sanar ma Dad 'yarsa aure takeso." Idanu ta rufe sannan tace " yaya mu tafi to ko?" Yace " haba kanwata a barni inga 'ya'yana da matata tukunna mana." Baki ta turo ta juya baya alamar fushi, Farida data dawo daga kai briefcase d'insa d'aki ta tsaya tana kallam ikon Allah, Habib yace "naji muje to tunda haka kikeso." Juyowa tai ta saki ihu tace " yauwa my bros." Da gudu ta wuce d'akinsu d'auko mayafi, tana kallan Aisha a zaune ko kulata batai ba taja mayafi tai waje, Aisha ta bita da tsaki tace " wani sa'in ta kulani, wani sa'in kuma ta nuna batamasan inagun ba." Seemah na fita, Habib ya kalli Farida yace " sai na dawo" sannan yabi goshin su Ra'is da kiss suka juya sukai waje, suna shiga mota Ammar ya k'irata, tad'aga wayar ta shiga zubamai shikuma yana biyeta,bai gayamata gobe zaizoba saboda yanasan ya bata suprise. Habib ya girgiza kai yace " Seemah in baki shawara?" Tace tame fa? Yace " karki kuskura kuyi waya da Ammar a gaban saurayinki ko wanda zaki aura, in fact karma ki bari su had'u. Da mamaki tace "meyasa? Bayan yayana yafi ji dani nima kuma haka." Habib yai murmushi yace "shine matsalar ai, yanda kukeji da juna in saurayinki ne ko budurwarsa sukaga yanda kuke zasuyi zargin wani abu." Dariya sosai tai harda tafa hannu tace " Zargin me zasuyi bayan yayana ne uwa d'aya uba d'aya?" Habib yace " wannan shikad'ai ne hujjar zai sa suyi shiru." Takarasa dariya tace " to da wannan hujjar da mezai sa suyi zargin wani abu? Kaidai kawai yaya kanaso ka cina nine." Haka yai ta tsokanarta har suka isa wani katon gida, bawai kato bane sosai sai dai yana da nasa girma d'an yayi biyun na Ya Habib, Habib ya kalli gidan yace " Lalai Dad har yai gida babban a garin nan ni babban d'ansa ban sani ba? Tace kamanta na fad'a maka? Yace auuuuuu na manta ai ashe fa na bikin Seemah me. Tai kasa dakai tana murmushi, an bud'e musu gate sun shiga, Habib ya kara kallan gidan fitilon da akai kwalliya dasu a waje sun kara fito da filin gun, Seemah tace wow yaya bazan bika ba, na dawo gidanmu kenan. Ya d'an ja kunnenta yace " ina kika isa? Ai kafata kafarki, kuma ma kinga ai ba masu girki a gidan, ko kin iya abinci ne? Ta ciji leb'enta tace " yaya fad'ar bakar magana ko? Zan baka mamaki ne." Tana kai karshen maganar ta bud'e kofar motar ta fito, ta nufi gidan, Habib ma ya fito sunyi knocking sosai har Habib yafara kokarin k'iran Dad sai kuma aka bud'e kofar, Dad ne tsaye sanye da jallabiya, yace " Sorry my Princess na barki a waje ko?" Ta had'e rai tace " da alama Dad bakai farin cikin ganina ba." Hannu yasa ya jawota ciki yace " Sorry Swthrt kema kinsan ba haka bane wani tunani nakeyi sam banjin kwankwasa kofar ba." Ta furzar da wata iska sannan tasa hannu tad'an biki goshinta tace " Oh God! Yazanyi da Dad d'ina? Dad kamanta an hanaka tunani mai zurfi? Ko kake hawanjinin ka ya tashi in shiga uku?" Shiga ciki yai yana murmushi, Habib ya matso kusa dashi ya kara kallan falon komai ansa na furniture's da kayan kallo, yace " kaiii Dad yaushe akai gidan nan da har komai an saka?" Dad ya kalleshi yace " kaidai kanada aure karma kai tunani zan baka aran d'aki a gidan nan." Ya juya zai ma Seemah magana sai dai bata gun, ya waige waige yace " Seemah!!!" Tace naam, ya juya da sauri inda maganar ke fitowa, tana kan matattakalar beni, yai murmushi wato d'akinta take nema tunda tasan Dad yasan tafisa Sama, kallanta yai yace muje in nuna miki d'akinki. Da gudu ta karasa Sama tare da bud'e d'akin datake tunanin shine, baki ta bud'e ta kasa karasawa ciki Habib ya karaso da dariya yace " hala d'akin naki ba komai sai katifa........" Shikanshi kallan d'akin yake komai na d'akin pink ne sai ratsin milk, ya juyo ya kalli Dad, da sauri Dad ya juya baya yana sosa keya, Seemah da gudu ta juya ta fad'a jikin Dad tace " Dad thank you soo much, Dad duk wani abu danakeso kafin na fad'a kake min, I love you soo much." Da sauri ta sakeshi ta koma d'akin ta shiga kallan komai, Habib ya kalli Dad yace " Dad amma yaushe ka gyara d'akin nan?" Yai murmushi baice komai ba, ji sukai Seemah tace " Dad ku shigo mana," nan suka shiga suka kalleta ta baje akan gado, suna shigowa ta mik'e ta kamo hannun Dad ta zaunar akan gadon, tace " Dad na fad'a soyayya mai karfi, yazanyi inbanyi shekara 2 a d'akin nan ba?" Tai maganar cikin shagwab'a, da mamaki Dad ya kalleta sannan ya kalli Habib yace " me kikace Seemah? " ta mik'e tace ehem, Dad kasan me? Ya girgiza kai, tace wani guy nake bala'in so, ban tab'ajin abin da nakeji ba sai a kansa. Gaban Dad ne yai wani irin mugun fad'uwa, cikin tsoro ya kalleta yace " just now what did u say?" Ba Dad kad'ai ba ko Habib yasha jinin jikinsa, shima yace " Seemah me kikace?" Tace" ahhhhh so nawa zan maimaita, yaya shine wanda ka tambayenk d'azu, ah kama sanshi ai jalal na gun aikinka." Dad ya runtse ido abinda yake tsoro shikenan yana shirin faruwa, Habib cikin b'acin rai yace " Haba Seemah wannan yaron kike so? Yaron da ko kayan jikinsa kika kalla kinsan abinda zasuci a gidansu ma da alama wahala yake basu, shi kike cemana kina so?" Dad cikin tsoro da mamaki ya kalli Habib yace " mene?" Seemah ta mik'e taye taje kusa da Habib ta rik'e hannunsa tace " Yaya nifa a hakan nace ina sansa, meyasa bazaka bani goyon baya ba? Yaya bazaka gane irin san danake mai b..........." Jitai an wanke ta da mari, cikin firgice ta kalli Dad da itadunsa suka kad'a sukai jajjawur, kamar me shirin zubar da kwalla mai zafi, Cike da mamaki Habib ma ya kalleshi, bai tab'a ganin Dad a wannan yanayi ba, cikin fad'a Dad yace kada ki kuskura ki kara min zancen yaron nan, sannan ku wuce ku koma gidan Habib dare yayi, Seemah data kasa tantance meke faruwa, mafarki take ko kuwa gaskiya ne, kamar bata motsi take kallan Dad, Dad ya kalli Habib yace " sannan kada ka kuskura ka kara barin Seemah ta fita, in fitar ta zama dole sai ka sanar dani." Yana kainan yai waje. Seemah tabi bayansa da kallo, tama kasa kuka kawai hannunta ne a gun, Habib ne ya tako a hankali yazo kusa da ita zai dafa ta, juyawa tai da gudu tana hawaye tai kasa, mota ta bud'e ta zauna ta saki wani irin kuka mai ban tausayi. Habib ya sauko tare da kallan Dad dake zaune a kan kujera idanunsa a rufe, yasan halin Dad da kuma yanda yake san Seemah, da alama ya mareta ne amma a zahirin gaskiya yafita jin zafin marin, harzai mai magana yaga kamar gwara ya kyaleshi, shima yai waje. Yana shiga mota yaji kuka da Seemah take ya b'aci cikin damuwa ya kalleta yace " Seemah is okay kema kinsan Dad bawai yaso dukanki bane, ko ya tab'a dukanki?" Ta girgiza kai cikin kuka tace " Yaya menene laifina? D'an inasan Jalal ko d'an bayaso inso talaka?" Habib yace " ya isa haka, gwara ki bar maganar wani Jalal d'an ko Dad bai hanaki ba ni zan hanaki." Takara sa kuka, meyasa kowa bai fahimceta ba? Ita tad'aurawa kanta soyayyar nan? Basa ganin inta rabu da Jalal ta rabu da farin cikin ta ne? Jalal kam jin d'akin ya isheshi ga sai hira suke da shewa yasa ya fito waje, yana tsaye a kan hanyar layin banda tunanin Seemah ba abinda yakeyi, gobe zaije gida ya sanar dasu...........wani me keke ne yayo kansa gadan gadan da sauri Jalal ya tsalle daga gun zuwa jikin bishiyar dake gun, hannunsa ne ya bugi bishiyar yai ajiyar zuciya tare da kokarin mekewa, mai keken ne ya taho da sauri ya taimaka mai yace " kaji ciwo ne? Jalal ya kalleshi yace a'a, amma wani irin tuki kake haka?" Yace " Yahkuri wlh fitilar kekence ta mutu sam ban kula ba." Jalal ya kalleshi yace to Allab ya kiyaye, mutumin ya juya, hannunsa Jalal yaje kad'ewa mezai gani? Agogonsa ne ya fashen, cikin takaici ya kalli agogon kamar yasa ihu, kalaman Seemah ne suka dawomai, na in agogon ya tsage akwai Bad abu dazai faru da su. Dariya ya saki yace " Jalal meke damunka? How can you believe that?" © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* *_This page is dedicated to you My Intimate Friend Aisha Muhd Umar, May almighty Allah grant all your good wishes_* ........ No. 2⃣9⃣ Jalal haka ya zauna yaci abincin nan bayan ya gama ne ya kalli Zainab dake gogema Zahee jiki yace " Umma fa?" Tace tana d'akina, ya mik'e tare da cewa bari in ganta tace to, har yakai bakin kofa a hankali yaji tace " Yaya?" Jalal ya tsaya ba tare da ya juyo ba, tace " nasan akan me ranka ya b'aci saboda Abba yaje aiki ne, sai dai kayi hakuri yaya amma Abba saboda harkar auranmu yake tara kud'i" da sauri Jalal ya juyo ya kalleta tai saurin yin kasa dakai tace " tun bayan ankai kud'i Abba kullum sai ya fita yin aiki, duk dabansan wasu aiyukan yakeyi ba amma naji dakansa ya fad'i dalilin aikin da Umma ta tambayeshi." Jalal jiyai kamar an kwaramai ruwan sanyi, cikin sanyin jiki ya zuge labulan ya fita, ya na fita ya tsaya a jikin bango ya zaiyi? Shidai gaskiya magana d'aya ba yazan Zainab, a matsayin kanwa ya d'auketa ba wai a soyayyar aure ba, yai shiru can ya taka zuwa d'akin Zainab, bayan yayi Sallama Umma ta amsa daga ciki ya zuge labulan d'akin a bakin kofa ya tsaya, ko ba komai yasan Zainab akwai tsafta da san gyara, kallan Umma yai cikin sanyin jiki yace " Umma inada magana." Ta d'ago ta kalleshi, sannan tace ka zauna sai muyi maganar, a kasan ledar d'akin ya zauna sannan yace " Naso sai Abba ya dawo in fad'a muku gaba d'aya amma yanzu sai nai tunanin gwara ma fara sanar dake." Ta kalleshi cikin damuwa tace " menene Jalal? Wani abun ne ya faru?" Kai ya jijiga mata yace "ko d'aya kawai dai inasan insanar daku abinda ke rainane." Umma batai maganaba amma ta tattara hankalinta gaba d'aya kansa, Jalal yai kasa dakai yace " a gaskiya Umma inada wacce nakeso, ina santa sosai kamar raina, sannan banaji zan iya auran wata ba ita ba.." Gaban Umma ne ya yanke ya fad'i cikin tsananin firgice da tsoron kalaman Jalal tace " Jalal me kake nufi da kalamanka?" D'agowa yai ya kalleta yace " Umma kinsani sosai tunda ke kika haifeni, kinfi kowa sanin Zainab a matsayin kanwa ma d'auketa kamar yanda Zahee take a guna." Umma ta mik'e taye ta matso kusa dashi ta rik'e hannayensa cikin rud'ani tace " Jalal dan Allah karkabar mahaifinka yaji wannan zancen, d'an inyaji daga ni har kai bansan abinda zai mana ba." Jalal ya runtse idanunsa yace " Umma please ku barni ko sau d'aya nai abinda nakeso, tun dana taso bam tab'a yima Abba musu ba arayuwata, hatta abinda zan karanta a jami'a shiya zab'amin da kansa ba wai san raina bane, d'an Allah Umma wannan karan ya shafi rayuwata gaba d'aya ki taimakamin......" Idanunta suka ciciko ita kad'ai tasan wahalar da d'anta ya sha, to amma ya zasuyi? Ko ita tanasan Zainab. Zatai magana aka yaye labulan da karfi akace me kace Jalal? Juyawa Umma tai da sauri ta kalli Abba da idanunsa suka kad'a sukai jaa na b'acin rai, Jalal yai kasa dakai yace " Abba ina kwana?" Ran Abba yakara b'aci yace nace me kace? Ya fad'a tare da shigowa ciki, Jalal ya d'ago a hankali yace " Abba inada wacce......." Cikin tsawa Abba yace " kada ka kuskura ka kara maimaita kalaman nan, kafi kowa sanin Zainab itace matarka ko kaki koka so." Jalal ya d'ago ido ya kalli Abba, shikansa yasan yauce rana ta farko daya tab'a musanta maganar mahaifin nasa yace " Abba dan Allah ka barni na auri wacce nake so, wlh yarinyar nan itama ba ruwanta." Abba ya fusata yace " yau ni Jalal zaka kalla ido cikin ido kacemim wai in barka ka auri wacce kake so? Anya kuwa kaine Jalal?" Kasa kawai Jalal yai da ido jiyake zuciyarsa na tafasa, Abba cikin takaici ya bar d'akin yai waje da sauri, Umma ta kalli Jalal cikin tausayi sai dai batasan me zatace ba itama ta fito, Zainab data fito daga d'akin Zahee jin hayaniya ta kalli Umma tace " Umma lafiya?" Umma takasa amsa mata kawai d'aki ta wuce. Jalal kam jin zuciyarsa na zafi kawai yai saurin kiran Seemah, tana zaune kusa da Ammar tana ganin kiransa ta kalli Ammar tace "yaya saurayina ya kirani." Da mamaki ya kalleta sai dai kafin yai magana ta gudu d'aki, tana shiga ta d'aga tare da sakin ajiyar zuciya, jin shiru yasa tace Deen? Kanaji na? Wani abu ya had'iya sannan yace " Meemah ya kika tashi?" Ta kwanta akan gado tare da jan bargo tace " na tashi lafiya sai missing d'inka dake neman yimin yawa." Bai san sanda ya saki murmushi ba yace " Na isa fa?" Da sauri ta yaye bargon tace " da wuri haka? Hmm kunyi maganar? Sun yarda? Ya kukai?" Dariya yasa sosai yace " duk ni kad'ai? Wanne akeso in amsa?" Dasauri tace" ya kukai please? Fad'amin kaji?" Murmushi yai yace bamuyi maganarba tukun yanzu na iso, tai ajiyar zuciya tace " ahhh jinai kamar zuciyata zata fito dan tsoro." Ya kara sakin murmushi yace" da ina kusa dana ba ki......" da sauri ta sa hannu a goshinta tace " wayyo zafi" tai maganar cikin shagwab'a, dariya ya saki tace " Deen me na maka ka d'ana min?" Dariya sosai ya d'ingayi yace " Ahhhh that's My Meemah you always make me laugh." Tai murmushi tace " In mukai aure sau 10 zan saka dariya a rana." Dariya ya sakeyi zai magana yaga Zainab a tsaye a bakin kofa idanunta sai zubar da hawaye sukeyi, kallanta yai sai yace ma Seemah" zan kiraki anjima." Tace okay miss u...... katse layin yai ya kalli Zainab, ya mik'e zai zo gunta da sauri ta juya da gudu tai waje , kai ya dafa yace " Ya Allah gani gareka." Seemah kam kwanciya tai ta rungume pillow a kirjinta tace I miss you Deen Muah......sai kuma tai saurin liliba da bargo wai ita a dole kunya jitake in aka rabata da Jalal to lalai karshen rayuwarta yazo. Mikewa tai ta sauka kasa ta zauna kusa da Ammar, kallanta yai yace " kingama waya da saurayin?" Ta rufe idanta da hannu biyu sannan ta bud'e ido ta kama hannunsa tace " Ya Ammar ina tsananin san Deen, jinake in aka rabani dashi kamar........" Had'a rai Ammar yai yace " bana ce karki kuskura kiyi irin wannan soyayyar ba?" Ta kalleshi tace " ni kaina Yaya bansan ya akai nazama haka ba." Ya mik'e tsaye yace da alama ma kinfi sanshi akaina, dariya ta saki tace kai yaya ka manta kai Special Oppa ne? Ya harareta baice komai ba, ta taso ta rike hannunsa tace " yaya bansan meyasa Dad bayasan Jalal ba." Da mamaki Ammar ya kalleta yace " ya ganshi ne?" Tace " a'a kawai daga fad'amai inada wanda nakeso naga ransa ya b'aci." Ammar yai murmushi yace" that means ba saurayin naki bane baiso, bayasan kiso wani ne." Tai shiru can tace kuma fa hakane to meyasa? Ya ce inazan sani? K'ila bayasan ki raba hankalinki ne, kina karatu ga soyayya. Ta jinjina kai Ooooops Nagane maganar. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 2⃣8⃣ Suna isa gida ta wuce da gudu d'akinsu tana zuwa ta fad'a gado ta cigaba da kukanta, Jalal kam sai kiranta yake a waya bata d'agaba, sam hankalinsa ya gaza kwanciya, Habib ma d'aki ya wuce ya zauna a bakin gado, ya rasa meke faruwa, da sauri ya d'au waya ya k'ira Sagir bayan sun gaisa ya tambayeshi ya labarin abokin ka kuwa? Sagir yace wa fa? " Jalal mana, ni a wani gari yake ne?" Sagir yai shiru yana mamakin tambayoyi sai can yace " a birnin gwari yake, yaron nan yallabai abin tausayi ne." Habib yace " ayya iyayensa acan suke kenan?" Sagir yace " eh nidai ban tab'a zuwa ba amma nasan talakawane sannan yana da kanwa da take kwance ba lafiya, yallabai yaron nan tare mukai makarantar jami'a ma tausaya mai kwarai, ga karatu ga sana'oi dayake saboda harkar makarantarsa dakuma iyayensa." Habib yai ajiyar zuciya lalai Seemah batada hankali, amma a fili yace " na tausaya mai, iyayensa basa wani aiki kenan." Sagir yace " gaskiya banaji, d'an inaji kamar mahaifinsa harkar ko gona yakeyi ne, bandai san takamaimai me yakeyi ba." Habib yace " okay Allah ya rufa asiri, sai da safe." Yana kainan ya katse layin tareda rik'e kai, lalai Seemah yarinta na damunta, ai ko Dad bai hanaba shi bazai bari ta aure wani Jalal ba. Seemah kam ganin kukan ya isheta yasa ta mik'e zaune tare da d'auko waya d'an ta fad'ama ya Ammar, ganin missed calls d'in Jalal ne yasa ta saki wani murmushi sannan ta mai text, tana gun ya Habib ne suna hira. Jalal na ganin text d'in yai ajiyar zuciya tare da kwanciya. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Duk yanda Dad yaso hankalimsa ya kwanta yai bacci abin ya gaggara sai juyi yakeyi, tunaninsa d'aya yazaiyi ya warware wannan al'amarin ba tare da Seemah tasha wahala ba? D'an bazai yadda da auranta da wani bare ba, kar azo maganar aure abinda yake a b'oye ya fito fili. *Washegari* Da wuri Jalal ya shirya ya nufi tasha, yai sa'a yana zuwa ya samu motar dazata birnin/gwari, nan ya shiga suka d'au hanya........ Seemah kam ta tashi da ciwon kai sakamakon kukan data sha jiya, zama tai a kan gado, tana tunanin matakin daya kamata ta d'auka, Ammar da Junaid su kad'ai suka rage mata, da gudu Ra'isa ta shigo d'akin tace mata "Aunty kizo Uncle Ammar yazo." Cikin mamaki had'i da farinciki ta kalli Ra'isa, tace " Ra'isa dagaske kike? Ya Ammar d'inna ne yazo?" Kai ta d'aga mata, sam ta manta rigar bacci ce a jikinta da gudu ta diro daga kan gado tai falo tana zuwa ta kalli Ammar dake tsaye, ai da gudu ta fad'a kansa duk yanda yaso ya d'aure amma ina sai da suka fad'i kasa, Farida ta girgiza kai, wannan dab'iar fa? Seemah kam d'agowa tai ta kalli Ammar tace " Yaya sorry na yadda kai, amma yaya ya akai haka?" Ammar yai murmushi sannan ya kalleta sai yanzu yaga kayan baccin dake jikinta, shara shara ne ana hango half-vest d'in data sa, yace " d'aga ni to, d'an naga alama neman karya wannan yayan naki kike." Tai dariya tare da d'agashi tace " yaya tsaya d'an mintsineni a fuskata kad'an, so nake inji ko mafarki nake." Dariya sosai tai sannan ya matso ya kama kumatunta da karfi sai datai kara, yace " ya? Yanzu kin gane?" Kara shigewa jikinsa tai sannan tace "yaya kamar kasan ina tsananin nemanka." Yai ajiyar zuciya tare da kallan gefe yace " yazanyi da kanwata? Ai in tana nemana dole jikina ya bani." Ta zaro ido tace " dagaske kake yaya? Saboda haka kazo?" Dariya yai har da zama akan kujera yace " lalai kanwata bata girma ba haryanzu zolayar ki nake." Turo baki tai tare da harararsa sannan tace yaya bari nai sauri nai wanka zamuyi magana. Ya d'aga kai, ta juya da sauri, Ammar ya bita da kallo fuskarsa d'auke da murmushi, wani sanyi ke ratsashi dayaga Seemah. Jalal an isa gida lafiya a waje ya tadda Zainab tana wanke-wanke, kallanta yai cike da tausayi tana ganinsa ta mik'e da sauri tare da gyara hijab d'in dake jikinta, yana mamaki shidai ko a d'akinta take tanaji da hijab take zama, bai tab'a ganinta ba hijab ba, katseshi tai cikin murna tace " yaya? Kaine? Sannu da zuwa." Murmushi yai yace " aiki kike?" Tai kasa da kai ya kalleta yace " sannu zainab, ana sanyi kina wanke-wanke a wajen nan?" Ta kasa kawai dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta, umma ce ta fito tace " kaima dai ka mata fad'a Jalal, duk yanda nai da yarinyarnan tabarni nai amma bata yarda sam hanani komai takeyi." Tausayinta ya kara kamashi, jiyai tace " Umma ina zan bari kiyi aiki? Bayan kema hutu kike bukata? Kullum kina gun Zaheeda kina kula da ita." Umma tai dariya tace Jalal kajita ko? Jalal kam kallanta yake cike da tausayi, Zainab ta d'ago ta kalleshi ganin yana kallanta yasa tai saurin yin kasa da ido, tace " yaya ka shiga ciki sanyi akeyi." Kallanta yai ko rigar sanyi babu a jikinta sai hijab amma wai shida yake sanye da jacket tama cemai ana sanyi, matsowa yai kusa da ita yazare Jacket d'in ya mik'e mata yace " kisa" ta amsa tana kallansa, Umma ta saki murmushin farin ciki ya sani ko Jalal baisan Zainab bazai wulakantata ba, Jala kam yama gani ta amsa ya matsu kusa da Umma yace Umma mushiga, nan sukai ciki. Kusa da Zaheeda ya zauna idannunsa sunyi jaa, itama idanunta na kansa, sai dai kana ganin alamun fuskarta kasan tana farincikin ganinsa, murmushi ya k'akaro tare da shafa kanta yace My Zahee kinyi missing d'ina ko? Idannu ta lumshe alamar eh, ya had'iye wani abu sannan ya juyo ya kalli Umma yace Umma ina kwana? Tace lafiya lau Jalaludeen, ya aikin? Yace Alhamdulila, Umma ya jikin Zahee? Takalli Zaheeda tace gatannan dai jiya iyau, sai dai kwanan nan jikin baya wannan tashin. Jalal ya kalle Zahee yace " Abba fa?" Tace " yafita wai akwai wani mutumi dake neman masu mai lambu, shine sukaje shida Sani, Jalal ya gyad'a kai, yace " amma Umma kema ya kamata kid'inga hanashi wannan sana'ar da ba amfani take mai ba." Umma tai shiru tace " kaima kasani bayasan zama guri d'ayan nan." Jalal ya runtse ido yace " amma Umma kima ganin yanda kafarsa d'aya take? A dalilin me zai d'inga zuwa yanama wasu aiki bayan shi kanshi yana neman hutu? Sannan inya gama kwata kwata nawa suke bashi? Ya wuce dubu 1 ko 2?" Umma tai shiru, Jalal yacigaba " Umma please ki taimaken ki hana Abba wannan yawon, in kuma lalai sai yayi sana'a ne, to ina ganin in na d'au albashi wannan watan mufara gina karamin shago a wajen gida inyaso in muka gama sai muji me yakesan ya zuba." Umma ta kalleshi tace ka manta yace " bayasan kasuwanci?" Cikin zafin rai da takaici Jalal yace " Umma wai menene dalilin dazaisa yak'i kasuwanci? Bayan muna halin rashi ne?" Umma ya share kwallar data zubo mata tace " Jalal wani babban al'amari ya faru a shagon mahaifinka ne a shekaru masu yawa da suka wuce, 'yan garin nan suka sama shagon wuta, basu san me ya faruba bakuma su duba halin da maishagon yake ciki na bakin cikin abinda ya faru a shagonsa ba." Jalal ya mik'e cikin b'acin rai yace" nasan wannan Umma, duk dabansan abinda ya faruba amma nasan wannan nasan kuma akan abunda ya farune kafarsa d'aya ta zama haka, sai dai tunda kinki sanar dani abinda ya faru bansan me zance ba" Yai ajiyar zuciya yace" amma kome ya faru bakya ganin shekaru masu yawa sun wuce da za'a ajiye wannan al'amari?" Umma ta kara share hawayenta tace " Jalal d'an Allah karkama mahaifinka zancen kasuwanci, ba'abinda ya tsana irinshi." Jalal ya kalli Zaheeda da yaga hawaye na zuba ta gefen idanunta, sama ya kalla d'an boye hawayesa, ya tsugunna kusa da ita ya saki dariya" ha ha ha Zahee karki damu hira kawai muke da Umma ba wani abu bane kinji." Umma ta kalleshi cikin tsananin tausayi, ganin yanda yake neman faranta ran kanwarsa yasa taji zaman yana neman ya gagareta, da sauri ta mik'e tai waje, Zainab da ta taho kawomai kunu da kosai, duk taji abinda sukai, ita kanta hawaye take sosai, ajiye kwanon tai ganin Umma ta fito, har zata bita taga kamar be dace ba, nata hawayen ta goge sannan ta shiga d'akin da fara'a, tace " Yaya kanaba Zahee labari ne?" Ya juyo ya kalleta yace " sannu zainab. " ta zauna a d'aya gefen Zahee itama tana bata labari. ■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■■ Seemah da sauri ta wanka ta zura kaya ta fito, akan dinning ta sami Ammar da ya Habib, taje kusa da Ammar ta zauna ta gaida Habib, Habib yace " baxan amsa ba tunda dai baki zauna kusa dani ba." Ta kalli Ammar tace " Sorry Ya Habib naga tsohuwar zuma, kasan tafi zaki." Ammar yasa dariya yace " Yaya sai dai kai hakuri kasan ni special ne." Habib ya girgiza kai yace " lalai Seemah ni zaki ma haka ko? Shikenan nima zan rama." Ta kalli Ammar tace " ya Ammar I miss you alot." Ya shafa gefen fuskarta yace " ban yarda ba, bayan banga kin rame ba sai kiba danaga kinyi?" Zaro ido tai ta kalli Habib tace " Ya Habib da gaske ban rame ba?" Habib ya harareta yace " sai kiba dakikai kamar me...." Ahhhhh ya zanyi? Ta mik'e ta shiga zirya tace ya Ammar ya zanyi? Kasan fa banasan nai k'iba? Noo bazanyi breakfast ba, ta kalli farida datai sakwalo tana kallanta, taje ta rik'e hannunta tace " Aunty azumi zan fara." Habib da Ammar kam banda dariya ba abinda sukeyi......... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣0⃣ Dad zaune kusa da Abba dayazo ganin gida, Dad ya kalli Abba yace "Yaya haryanzu banji kace komai ba?" Abba ya kalleshi fuska a had'e yace " Meyasa baka fahimta ne Isma'il? Taya zaka had'a jininka dana....." Dad ya katseshi dacewa" Haba Yaya meyasa bakwa fahimta ne, Seemah 'yatace akoda yaushe, duk da a baya nima nayi tunanin kaita gidan marayu, amma daga baya na gane haka Allah ya kaddaramin, kuma inaji a jikina Seemah Amanace Allah yabani." Abba ya kalleshi cike da tausayi yace " Nafahimci abinda kake nufi amma kai kana tunani su Hajiya zasu yadda da wannan fatawar taka?" Dad yace " nasani yaya shiyasa nake rokon ka daka taimakamin, Yaya banaso wani abu da zai d'aga ha kalin Seemah." Cikin takaicin hali irin na kaninsa Abba ya m'ike yace " Seemah Seemah Seemah!!! Haba nagaji da yanda ka damu da yarinyar, anya ma kana kaunar 'ya'yanka kamar yanda kake santa? Ko dai akwai wani abu dabaka sanar dani ba? Bana tunanin akwai mutum irinka a duniya, mahaifiyar yarinyar nan tajaza maka masifar da bazaka tab'a iya wanketa ba amma kai kamar mara tunani." Hawaye ne suka taru a idan Dad ya mik'e shima ya kalli yayan nasa yace " Yaya alokacin kunki fuskarta ne amma ni kad'ai nasan halin datake ciki." Cikin takaici Abba yace " Nikarka karamin zancen wata mata can da banasan in tunama nasan ta, sannan ni haryau ban yarda ma........" Cikin zafin Rai Dad yace " haba yaya! D'an Allah karka kara furtamin kalaman nan." Abba a zuciye ya bar gidan, Dad ya zube a kasa kawaa yasa kuka kamar karamin yaro, gyambun dake birne a zuciyar sa ya famu, kuka yake sosai bai masan sanda Habib ya shigoba, dayake Abba a bud'e yabar kofar, Habib ya tsaya a bakin kofar yana kallan mahaifinsa jiyai kawai jikinsa ya d'ebi rawa baisan sanda shima hawaye suka fara zubomai ba, kallan mahaifinsa yake cikin wani yanayi mai wahalar fahimta, meyasamu dad? Me akamai? D'an da alama kukan daga zuciya yake fitowa bawai ciwo yaji ba ko rashin lafiya bane. Habib a hankali ya karaso kusa da Dad ya rungumeshi ta baya baice komai ba sai kuka shima da yakeyi, A hankali Dad ya fara kokarin saita kansa, ya juyo da fuskarsa kan Habib, baice mai komai ba Habib ya rungumeshi yace " Dad menene yakecin zuciyarka haka? Menene ke damunka da har zakai irin wannan kukan? Dad ni babban d'ankane kuma Abokinka ko kamanta haka kake cemin in ina cikin damuwa?" Dad ya kalleshi kawai girgiza mai kai yake, Habib ya kakaro wani murmushi yace shikenan Dad na d'auka munyi shakuwar dazamu d'inga raba matsalolinmu. Mik'ewa yai ya fita Dad ya bishi da kallo cikin tausayi sai dai yana tsoron furtama Habib maganar. Jalal kam ganin zaman da yake ya isheshi yasa ya mik'e da sauri yai waje shima, ya fara neman Zainab, yana tunanin ita kad'ai ta rage masa a mafita yasani inya sanar da ita abinda ke ransa zata goyamai baya. Sai dai duk yanda yaso nemanta bai sameta ba, haka ya gaji ya koma gida, yana shiga ya ganta a tsakar gida tana shara, cike da mamaki ya karasa gunta yace " Zainab inasan magana dake." Jiyai Umma tace " bazata ba, Jalal yaushe ka zama haka? Nasani sarai abinda kake tunani." Jalal yace " haba Umma meyasa bazaki fahimceni ba?" Zainab ta d'ago fuskarta duk ta b'aci da kwalla, ta kalli Jalal shikin bakin ciki tace " Yaya yaushe ka zama haka? A da na d'auka kai mutum ne mai tsananin girmama iyayensa, menene dalilin dayasa ka canza? Nice bakasan aure? Saboda ni kake wannan abun?" Jalal ya had'e rai wani kallo ya buga mata yace "in ima magana da Umma karki kuskura ki kara katseni." ajiyar zuciya tai idanunta suka kara zubar da kwalla tace " Umma d'an Allah kubar shi ya auri wacce yakeso." Tana kainan tai d'aki da gudu ta rufo kofar, kallo Jalal ya bita dashi, Umma tace " Jalal ka bani mamaki." Itama ta juya ciki. Iska ya furzar daga bakinsa wayarsa ce tai kara ya cirota daga aljihu, ganin Sagir yasa ya d'aga wayar Sagir yace " Jalal kana ina? Kazo Habib na nemanka." Jalal yace " bangane yana nemana ba? Yau asabar ban fahimci dalilin dazaisa a nemi ni ba bayan ina hutun weekend. " Sagir yace " to d'an ka'ida amma please kazo yanasan ganinka wajen 5 yace it's urgent." Harzai musa sai kuma yai tunanin da alama maganar bata aiki bace mayb tsakaninsa ne da Seemah, da sauri yacema Sagir okay zanzo. Yana katse wayar ya shiga d'akin Umma, a zaune ya ganta ta baza tagumi, ya karasa kusa da ita ya zauna ya kalleta yace " Umma?" Juyo da fuskarta tai ta kalleshi, yacigaba" Umma ko nace dole sai na auri Seemah baza ki amince dani ba?" Tace kwarai, yai ajiyar zuciya yace " ko nace Seemah ce jigon rayuwata bazan iya rayuwa ba sai da ita bazaki amince ba?" Kallansa tai da mamaki tace " Jalal!! " Yace " ko nace in ba da itaba bana tunanin zan iya zama da wata a matsayin matata bazaki amince ba." Kallansa take cike da kulawa tace " Jalal yaushe ka fara soyayya haka? Ban tab'a tunanin zaka so mace haka ba? JALAL meya sameka? Baka tunanin sun maka asiri?" Mik'ewa yai ya juya mata baya yace " nikaina bansan ya akai na zama haka ba Umma, bansan yaushe zuciyata tai rauni akan mace haka ba, in tana dariya sai insamu kaina cikin farinciki, in tana bakin ciki sai inji nafita damuwa, in taji ciwo jinshi nake kamar a jikina, in ina tare da ita jinake kamar kar mu rabu, Umma bansan meke damuna ba." Idanun Umma ne suka cika da kwalla, ta kalleshi cikin tsananin tausayi, lalai ta fahimci halin da d'anta yake ciki amma ya zatai da Zainab? Mik'ewa tai ta dawo ta gabansa tace " nafahimceka kwarai Jalal sai dai Jalal abinda baka sani ba shine, rayuwar aure ba soyayya ake nema ba kawai. Kai ya girgiza yace " Umma ban damu da wad'an nan ba." Shiru tai jikinta duk yai sanyi, Jalal ya kalleta yace zan koma Abuja yanzu ana nemana zanzo wani satin, Umma d'an Allah kitaimaken kishawomin kan Abba. Takalleshi tace daga zuwa? Yace eh oganmu ke nemana, tace to Allah ya kiyaye. Direct tasha ya nufa ya shiga mota, tunani yakeyi ta ina zai fara shawo kan lamarin. A company d'insu ya sauka, office d'in Habib ya wuce, ba kowa saboda yau weekend, knocking d'in kofar yai daga ciki akace ya shigo, shiga yai da Sallama, Habib ya bashi izini zama, shikam yana tunanin harda maganar san Jalal da Seemah take yasa Dad cikin wannan halin dukda baisan takamaimai dalili ba sai dai shikanshi bazai yarda da wannan soyayyar ba. Zama Jalal yai sannan Habib ya mik'amai hannu, sun gaisa Jalal yace " akace kana nemana?" Habib ya kalleshi tare da ajiye takardun hannunsa, yace " kasan kanwata?" Kai Jalal ya d'aga, Habib yace " akwai wani abu a tsakaninku ne?" Cikin rashin fahimta Jalal yace " kamar me fa?" Habib yace " kamar abinda ke tsakanin mace budurwa da namiji." Jalal yai murmushi sannan yace " eh, we like each other. " Habib ya tattara hankalinsa kan Jalal sannan ya zaro envelope ya tura masa abansa, Jalal ya kalleshi da rashin fahimta yace na meye? Habib yace ka bud'e, Jalal ya zaro abinda ke ciki check ne na million 3, cikin tsananin mamaki da tambaya ya kalli Habib yace na meye? Yai maganar tare da ajiye envelope d'in. Habib yace " wannan kud'in ina tunanin ya isheka ka fara business d'an haka inaso kabar garin nan kaje wani gun ka fara kasuwancinka." Jalal ya kalleshi yace "bangane in fara kasuwanci ba? Kuma kai a matsayin me kake a guna da zaka bani kud'i ka kuma umarceni akan wasu sharad'u dabata shafi aiki ba?" Habib yaji zafin kalamansa amma ya daure yace " ina nufin ka rabu da Seemah, kai kanka kasan tafi karfinka, ko kana tunanin kanada abinda zaka kula da ita ne?" Jalal ya saki wani murmushi yace "Ahhhh dalilin kenan? Sai dai yaza'ayi yaya Habib bana tunanin zanyi accepting wannan offer taka." Yana kai nan ya mik'e cikin tsananin b'acin rai, zai iya jurar komai amma ya tsani amaidace gara wanda za'a iya siya da kud'i. Habib shima ya mik'e zaiyi magana kawai sukaga an turo kofar, Seemah ce da Ammar suna dariya, dariyar ta tatsaya ne sanda taga Jalal, da mamaki ta kalleshi tace " My Deen me kake a nan? Ba kace kana birnin gwari ba?" Idanunsa ta kalla ba shakka ransa a b'ace yake matuka, Jalal ya kalleta sannan ya kalli Ammar ya juya ya kalli Habib yace na wuce, ta kusa da su yazo ya wuce bai kula Seemah ba, Ammar ya bishi da kallo haka kawai yaji bayasan guy d'in. Seemah kam kallan Habib tai tace " yaya lafiya?" Bai amsa mata ba kawai ta juya tai waje da gudu, Ammar na k'iranta amma inaaa, da kyar ta tadda Jalal yana jiran elevator da sauri tasha gabansa tana hakki, tace " Deen menene? Yanaganka haka? Kana ganina baka min magana ba." Kallanta yai sannan yace " haka kuke dama masu kud'i? Komai bakwa iya solving d'insa sai da kud'i? What do u people think of me? Kije ki sanar dasu halaye na." Gaba d'aya Seemah takasa fahimtarsa, bai jira amsarta ba yana ganin Elevator ya tsaya ya danna ya shiga ya barta a tsaya tana maimaita kalamansa. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* _To you all my fans, wish you happy new year🍥🍥 May Almighty Allah help us Ameen_ No. 3⃣1⃣ Juyawa tai da sauri ta koma office d'in Habib. Ammar ne ya tsaya kallan Habib cike da mamaki yace " yaya waye waccan d'in?" Habib ya juya baya yace " bakaji abinda Seemah tacemai ba? Shine wanda takeso, bakuma soyayya ta wasa ba harda maganar aure take nufi." Dariya Ammar yai yace " haba yaya kamar bakasan kanwata ba? Na sani guy d'in daya fita yana da cikar zati da kirar jikin da maza ke so, amma kanwata bata damu da wannan ba, wanda takeso shine wanda zai kula da ita, wannan kuwa kana ganin yanda yaganta ya wani d'auke kai?" Habib ya matso kusa dashi ya rik'e hannayensa yace " Ammar, Dad fa nacikin tsananin damuwa bansani ba ko shine dalilin ko kuma da wani abun." Ammar yace " Dad kuma? Nifa na kasa fahimtar abinda kake nufi? Kanasan kacemin yaran nan shi Seemah keso.................." Da karfi sukaji an bud'e kofar, suka juya atare Seemah ce tsaye fuskarta a had'e, ta karaso kusa da Habib ta kalleshi ido cikin ido tace " Yaya mai kawa Deen?" Habib ya had'e rai shima yace waye wani Deen? Ta kara had'e fuska, tace " Jalal, mekamai?" Ammar da mamakin abinda yake gani yace " Seemah waye waccan d'in dahar zai sa ki zo ki tsare yayanki da kike girmamawa?" Idanta ne ya ciko da kwalla ta kalli Ammar tace " Ya Ammar na rasa dalilin dayasa akemin haka, na d'auka kowa yana da right d'in dazaiso abinda zuciyarsa take so?" Ammar kam yama kasa furta wata kalma, haka kawai yaji ransa na b'aci, me yarinyar nan take nufi? Bai ankara ba kawai yaga ta tsugunna tare da rufe kanta da hannu tana kuka, cikin kukan take cewa" Ya Habib please karku rabani da Deen, yanzu gashi ya tafi bansan ya zanyi ba." Habib haushi ya kamashi kawai yai waje da sauri duk da yanajin kukan kanwartasa har cikin ransa. Yana fita Ammar ya tsaya kawai yana kallanta, Jin idanunsa suna neman kawo ruwa saboda kukan datakeyi yasa ya matso ya zauna shima kusa da ita a hankali ya jawo kanta ya kwantar akan kafad'ar sa. Kwanciya tai lamu, ta fara share hawayenta, Ammar cikin sanyin murya yace " Seemah do u love him that much?" Kai ta d'aga sannan tace " yaya bansan ya zanyiba yayi fishi dani?" Ran Ammar yakara b'aci sai dai ya d'aure yace " Seemah kinsan me? Ta girgiza kai, yace" Falling in love is so easy but keeping that love is very difficult., bansan yaushe harkika fara soyayya haka ba, but karki bari soyayya da kikeyi tajawo fad'a tsakaninki da iyayenki da kuma 'yan uwanki." D'agowa tai ta kalleshi ta kara share kwallarta, sannan ta kalli idanunsa da kwalla ta taro murmushi ta saki, tace " yaya please please kar ka k'i abinda nakeso, in har kaima kak'i Deen it will make it difficult for me. " Murmushi ya kakaro wanda kana ganinshi kasan a iya leb'ensa suke, ta mik'e tace "yaya kataimaken please kaji?" Yace name fa? Tace ka k'ira Jalal a wayarka kacemai yai hakuri duk dabansan me ya Habib ya mai ba. Ammar ya kalleta cikin mamakin gaske yace what? Me? Kai ta d'aga cikin halin ko in kula tace " kaine best bro d'in na kaikad'ai nake tunanin zakamin abinda nake so kuma, kaji yaya please? " Kallanta yake da mamaki, sai dai haka ya sabar mata bai iya ce mata a'a ba akan duk abinda tace, wayar ya mik'amata tai tsalle tare da ansa tasa number tai dialling. Jalal kam yana fita waje yai kawai tafiya yakeyi, zuciyarsa taf take da tunani kala kala, yarasa meya kamaceshi, sai dai abinda yafi bashi takaici kud'in da Habib ya bashi, me ya d'aukeshi? Jin karar waya yasa ya zarota daga aljihu ganin number ne yasa sai data kusan katsewa ya d'aga tare da Sallama, Seemah naji sallamarsa tai saurin mekama Ammar waya, Ammar ya mik'e tare da ansa duk da ransa bayaso, ya amsa tare da cewa "Yayan Seemah ne da muka had'u a office d'in Habib yanzu." Ran Jalal ya kara b'aci yace " Wani kud'in kaima zaka kara bani akan in rabu da Seemah ko me?" Sai a lokacin Ammar ya gane abinda ya faru, amma saboda bayaso Seemah tagane yace" Hmm da Alama wannan saurayin na kanwata yanada zafin rai." Jalal ya kara had'e rai kamar Ammar na ganinshi yace " Ya akai to?" Ammar yai ajiyar zuciya tare da kallan Seemah data rik'e hannunsa tana rokonsa, ajiyar zuciya ya sakeyi yace " Kanwatace tace in k'ira in baka hakuri." Jalal yace " me kace?" Ammar ya kara kufula yace " Kanwata ce ta damu da yanda taganka shine takeso naji ko komai lafiya." Jalal yace " kana nufin saka tai ka k'irani ko me?" Ammar ya had'e rai sai dai yazaiyi? Yace " gata tana san magana dakai." Yana kainan ya mik'ama Seemah wayar yai waje da sauri. Seemah na amsa tace " My Deen ka sauko?" Jalal yace " wannan yayankine?" Tace " eh special brother na ne." Ya d'an tab'e baki kad'an yace" shine kikasa ya k'irani? Yama za'ai ya biye miki? Kuma ce miki akai in kika k'irani bazan d'auka ba?" Turo baki tai tace " menene d'an nasashi yamin abu? Ni duk abinda nace masa inaso yimin yakeyi, sannan yanda naga kayi shine yasa nai tunanin bazaka d'aga ba." Murmushi Jalal yai a ransa yace lalai an sangartata dayawa, a fili yace naji, zan k'iraki a wayarki anjima. Tace zan jiraka fa? Yace eh zan kira. Sunyi sallama ta kashe wayar tare da sakin murmushi. Jalal ma yabi wayar da kallo ya saki murmushi. Ammar kam yana fita toilet ya shiga yai ta watsama fuskarsa ruwa, kalaman Jalal ke dawomai, mirror d'in toilet d'in ya kalla sannan ya goge fuskarsa ya fito. Habib na fita daga office ya nufi gidan Abba, ba yan sun gaisa da Zahra ne ya tambayeta mahaifiyarta, tace " taje Suleja d'azu da safe." Habib yace wani abun ya faru ne? Zara ta girgiza kai tace " wlh bansani ba Yaya naga dai da safe Abba ya k'irata tana dawowa tace suleja zata." Habib ya d'aga kai sannan yace" Abba fa?" Tace yana falonsa kaje, Habib ya tura kai b'angaren Abba. Yai sallama Abba ya amsa tare da bashi izini, Habib ya shiga, a zaune yaganshi kamar yanda ya saba da jarida a hannunsa, bayan Habib ya shigo ya ninke jaridar tare da kallansa, Habib ya karasa ya zauna a kasa tare da gaidashi. Abba ya amsa yace " Habibu daga ina haka?" Habib ya d'ago yace " Abba wani abu ke damuna." Abba ya kalleshi da mamaki. Habb yace " d'azu naje gun Dad na ganshi a wani yanayin da bazan iya fad'a ba, Abba abin nan ya dameni ya hanani sukuni, da farko nai tunanin ko Saurayin da Seemah takeso ne bayaso, amma yanzu kaina ya kulle, bansan menene ba." Abba ya gyara zama yace, saurayin da Seemah takeso? Kamar ya? Akwai wanda takeso ne?" Habib ya d'aga kai yace " eh tasanar mana ni da Dad jiya." Abba yai shiru, wato wannan ne dalilin dayasa Dad yake tunanin abubuwa kala kala? Yanzu gashi ganin seemah da Hajiya tai dakuma zuwan Dad dayai yasa ta takwanta d'an ciwonta ya tashi. Habib ne ya katseshi yace " Abba ya za'ayi?" Abba yace " zamuyi magana da Isma'el d'in sai dai inaso kaima inkaje gida ka kwace wayar Seemah ka kuma hanata fita harsai mun gama yanke hukunci da Mahaifinka." Habib yace " to Abba amma Seemah zata yarda kuwa? Tanasan yaron....." Katseshi Abba yai ya mik'e yace " Seemah gwal ce? Kai meyasa kaida mahaifinka halinku yake d'aya ne? In kasan abinda mahaifiyarta taja mana bazaka tab'a bin bayanta ba." Habib ya kalleshi da mamaki yace " bangane mahaifiyarta ba? Ba Maman mu bace ta haifeta kake cewa ko me?" Sai a lokacin Abba ya tuna, Habib da Jalal da babban d'an Abba Jafar tare suka kaisu karatu tun suna yara yan 15yrs da Habib da Jafar, junaid kuma 12yrs aka kaisu England gun Kanwar mahaifiyar Jafar dake zaune acan, Abba shiya had'asu ya biya musu karatunsu, a lokacin da abin ya faru suna can, Ammar ne kawai a gaban mahaifiyarsa lokacin yana d'an shekara 5. Habib ya sake cewa" Abba bakace komai ba?" Juya baya Abba yai yace " wani abune a raina, sam hankali na yana gun, kaje ka aiwatar da abin da nasaka kawai." Yana kai nan ya juya yai d'aki, Habib ya bishi da kallon mamaki, me Abba yake nufi? Daga yanda Abba yai maganar yama za'ai ya yarda wai badashi yake ba? Shidai a iya saninsa Seemah mahaifiyarsu tana haifarta tabar duniyar, wannan shine abinda suka sani kuma dashi suka taso, to amma me Abba yake nufi da kalamansa..........? ❓❔❓❔❓❔❓❔da alamar tambaya......injini😂 © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣2⃣ Ammar ne ya fito daga toilet, a bakin kofar toilet d'in ta ganshi yana fitowa ta d'aneshi, tace "yaya godiya sosai, thanks to you munshirya da Deen." Ammar ya had'iye wani bakin cikin sai dai ya kakaro murmushi yace " are you that happy?" Kai ta d'aga sannan ta d'ago ta kalli Ammar tace " yaya inasan Deen sosai, kasan me?" Kallanta yai zuciyarshi kamae ta fashe duk yanda yaso ya b'oye bakin cikin dake ransa ya kasa, Seemah tai murmushi tace " amma kasan wani secret yaya? Na kasa tantance wayafi matsayi tsakaninka da shi a guna." Ammar ya kalleta jiyai zuciyarsa bazata juri ganin ta ba, shi zata had'a da wani bare da ko wata da had'uwa basuyi ba? Juyawa yai ya fara tafiya batare da ya tankamata ba, da sauri tasha gabansa ta rangwad'ar da kai tace " Ohhhh my bro ba dai haushi kaji ba?" Idanunsa ya runtse saboda bazai iya fad'a mata magana mara dad'i ba, gashi bai san ya mata magana, cewa yai" Seemah matsa mu wuce, Dad nake san gani." Ya matsa kad'an daga kusa da ita, hannunsa ta kamo tace " wasa nake yaya." Juyowa yai ya kalleta tai murmushi tace " yaya inasan Deen sosai amma yama za'ai in had'ashi da kai? Ko kamanta ne? In na kwanta zazzab'i saboda shakuwarmu kaima sai ka kwanta?" Tai murmushi sannan ta cigaba" tsokanarka kawai nakeyi, Deen soyayyar macen dake bala'in san saurayinta nake mai kai kuma soyayya ce ta jini yama za'ai ka had'a?" Murmushi ya saki sosai ta had'a yanayenta biyu ta tafamai tace " yauwa my dear bros yanzu kafimin kama da yayana." Ajiyar zuciya yai, yace " Seemah nima bansan meyasa naji haushin ba d'an kin had'ani da wani, na sani sarai soyayyar jini dake tsakaninmu." Ta furzo iska ta sa hannu a goshinta tace " oh God my bros sai yaushe zamu dauka ne?" Dariya yai, ta kalleshi tace " ji kafar yaya kamar wanda bata aiki?" Yace ni d'in? Gwalo tamai ta ruga da gudu, binta yai da gudu shima, suna gudu suna dariya. Jalal kam jin yanayin jikinsa ba daidai ga magrib takawo kai yasa ya wuce d'akinsu ya bud'e, abin haushi 'yan d'akin suna zaune sun kure radio, jiyai kansa na juyawa haushi yasa shi ya fita tare da zama a waje, sanyin dake ratsashi yasa ya tabbatar zazzab'i keneman rufeshi, waya ya d'aga abin haushi ya rasa wama zai k'ira? Sagir ne ya fad'omai hakan yasa yai dialing number, ringing 2 Sagir ya d'aga tare da cewa " Jalal kaga Chairman d'in?" Yace " Eh amma sagir please kana ina?" Sagir yace ina gida ya akai zaka zo ne? Jalal yai shiru, Sagir yace " please kazo tun yaushe nake rokanka? Har cewa nai ka dawo gidanmu mu d'inga zama a d'akina ka k'i bansan meyasa kake haka ba. Jalal kam sai nishi yake jiyake kansa na wani irin sarawa, ka karar disco duk ta isheshi, a hankali ya firta Sagir please kazo ka d'auken a wajen d'akinmu kaina........... Jiyai kansa yayi kinkirikim, hakan yasa ya sauke hannunsa, Sagir ya saki kiran sunanshi, jin shiru yasa ya zari makulli da sauri ya fita. Da gudu ya zuro motarsa, yana zuwa yaga Jalal a waje ya jingina da jikin bishiya, da sauri ya karasa kusa dashi, yanasa hannu ajikinsa yaji kamar wuta, da sauri ya d'auke hannunsa yace " Jalal meke damunka haka? Ya za'ai kanajin zazzabi haka bazaka gun likita ba, Jalal ya d'ago ya d'an saki murmushi yace " Sagir ka iso? Nagode fa." Sagir ya kalleshi cikin tausayi, yace Jalal tashi muje asibiti, kai ya girgiza mai yace " muje chemist kawai, ina sha magani zai tafi." Sagir ya amince da shawararsa, nan ya nemi taimaka mai Jalal yai murmushi yace " me kad'auken Sagir? Zan iya tafiya da kaina, is not a big deal." Sunje chemist nurse d'in ya kalli Jalal yace " ya kamata kaje asibiti gaskiya, jikinka na burning dayawa." Jalal yace bani magani kawai, nan ya bashi magani yana mamakin taurin kai irin na Jalal, Sagir ya kallu nurse d'in yace " haka yake indai Jalal ne." Sun fito suka shiga mota Jalal sai kallan wayarsa yakeyi, da alama k'ira yake jira ko kuma yakesan yi. Sagir ya kalleshi yace " ka tabbatar ba matsala?" Jalal ya d'aga kai, Sagir yace " amma maganar me kukai da Chairman d'an da alama ba maganar aiki bane." Jalal yai d'an karamin tsaki yace " banasan ma tunawa amma Sagir wani irin mutum ne Chairman?" Sagir yai murmushi yace " mutum ne mai mutuncin gaske sai dai yanda na ga alama yana tsananin san family d'insa, yana girmama mahaifinsa sannan yanasan kanwar nan tasa." Jalal yad'an tab'e baki, Sagir yace "amma maganar me kukai?" Jalal ya maida kanshi jikin window baice komai ba. Dad yana zaune a wajen gidansa, motar Habib ta shigo, mamaki yasa ya kalli motar har Habib ya karaso ciki, yai parking, Dad ya kalleshi kallo d'aya zakamai kasan akwai abubuwa dayawa a zuciyarsa. Yana karasowa ya gaida Dad, Dad ya amsa tare da cewa " na d'auka Ammar ne zaizo." Habib yace " anan zai kwana yace, nasan anjima zaizo suna tare da Seemah ne." Dad ya d'aga kai tare da murmushi yasani ai, da za'abar Ammar da a gidan Habib zai kwana. Habib ne ya katseshi da cewa " Dad ina da tambaya?" Kallansa yai yace tame fa? Habib yace " Ummi mahaifiyar mu, ita ta haifi Seemah?" Gaban Dad ne ya fad'i ya kalli Habib cikin tsananin mamaki, yawo ya had'iya sannan yai saurin kauda kai, yace " wani irin shirme kake fad'a? Bansha sanar daku sanda Maryam zata rasu ba tana haihuwar Seemah ta rasu? Ko so kake inyi ta tisa maganganu na?" Habib ya dawo ta gaban Dad ya kalleshi, yace " a'a Dad akwai wani abun bayan abinda muka sani, akwai abinda kake b'oyewa bayanan." Dad ya had'a rai kamar me, yace " karka kara tunanin ba mahaifiyarku d'aya da Seemah ba, inba sokake ranka ya b'aci ba." Yana kai nan yai saurin yin haryar ciki, sai dayai nisa ya juyo yace ka gaidata in ka koma, sannan kace mata nayi missing d'inta. Yana kai nan ya karasa ciki. Daga yanda Habib yake kallan Dad zakasan bai aminta da kalaman da Dad ya fad'a ba, dole dole akwai wani abun da ake b'oyewa kod'an yanda dad yake saurin katse maganar in an fara. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣3⃣ Jalal har sun d'anyi nisa sam haji hankalinsa ya kasa kwanciya juyowa yai ya kalli Sagir yace " Sagir please d'an taimaka ka ajiyeni anan, akwai inda nakesan zuwa." Sagir ya girgiza kai yace " Kai Jalal, baka da lafiya na d'aukama zaka yadda na wuce dakai gidanmu, ina kuma zaka?" Jalal yai ajiyar zuciya yace " gidan su Chairman akwai wacce nakesan gani." Mamaki yasa Sagir yai baki sannan ya juyo cikin namaki yace " ban gane ba?" Jalal ya juya kai yace " I don't know why but I feel that I must see her." Sagir ya kalli Jalal yace " jalal me kake nufi da kalamanka? Wazaka gani? Ko ince wa kakesan gani?" Jalal yai shiru, sagir yace badai Seemah ba ko? Jalal yace " Sagir bari na sauka nagode sosai." Dasauri Sagir yace " a'a bandai san meke faruwa ba amma bazan iya barin ka katafi kai kad'ai ba." Jalal ya kalleshi tare da cewa tnx alot. Sun fara tafiya kad'an Seemah tak'irashi. Murmushi ya saki tare da d'agawa, tace " My Deen!" Jalal yai ajiyar zuciya tare da cewa " kina ina?" Tace gida d'azu muka dawo da ya Ammar. Yace ganinan zuwa, yanajin karar datai tace " haba? Dagaske? Wayyo naji dad'i, ka kusa isowa?" Murmushi yai yace " nad'auka zakice mezan zo yi?" Tace "wa? Ni? Kaima kasan ko kullum zamu had'u bazan ce haka ba." Yace " tsokanarki nakeyi bari inzo shaf shaf in ganki." Sagir kam tuki yake amma gaba d'aya hankalinsa na kan Jalal meke faruwa? Soyayya suke ko me? Anma anya Seemah ce? Kodai wata ce a gidan? Suna isa suka parking a gefen gidan, Jalal na mata flashing kafin wayar ta katse yaga ta fito, kamar irin tana waje tana jiranshi d'in ne. Kodayake hakan ne d'an suna gama waya taji hankalinta ya kasa kwanciya, gyara fuskarta tai tad'an fesa turare ta sauko, a falo taga farida ta tambayeta Ammar tace ya fita yanzun nan inaji ya tafi, ta fito ta tsaya a waje. Sagir ya fita daga motar ya kurama Seemah ido itakam dayake hankalinta baya kanshi bata na kula dashi ba, kawai juyawa tai tana neman Jalal, murmushi Jalal yai sannan ya fito daga motar tare da d'aga mata hannu, murmushi ta saki sannan ta karaso inda yake, Jalal ya kalleta ya saki murmushi itama murmushin tai tace " yau meya sameka? Nemana na ba zata haka?" Ya kalleta yai ajiyar zuciya yace " meya sameni? Ahhh ni kaina ban sani ba, ko d'an d'azu bamu rabu ta dad'i bane? Kawai nakejin kamar ina tsananin san ganinki." Murmushi tai sosai tasa hannu a kirjinta tace " wow naji dad'i sosai for this honour." Tad'an rangwab'ar da kai tace " amma kamar numfashinka yana fita da sauri." Murmushi yai yace " kawai maybe ko d'an kaina na ciwo ne." Ai batasan sanda takai hannu goshinsa ba jin zaffin zazzab'i mai karfi yasa ta rik'ice, tace " My Deen ya haka? Meya sameka?." Hannunta ya zare daga goshinsa yace " Don't worry ba wani abun bane, bari mu wuce." Kallanshi tai idanunta sukai raurau kamar me shirin kuka tace " My Deen kaji jikinka kuwa? Yama za'ai kacemin karna damu?" Kai ya kwantar a jikin kujera yace " karki damu in nasha magani komai zai dawo normal." Sagir kam mutuwar tsaye yai, kawai kallansu yake, basu ankara ba kawai sukaji cikin muryar fad'a sosai ance " Seemah uban me kike anan?" Da sauri ta juyo jin muryar Ya Habib, Sagir ma ya juya da sauri, Habib ya maka mata harara cikin zafin rai yace " ba magana nake miki ba?" Jalal ya fito daga motar tare da kallan Habib yace " Chairman what do you mean by me takeyi anan?" Habib ya had'e rai sosai wanda yasa cikin Seemah ya d'uri ruwa, ta kalli Jalal sannan ta kalli Habib tace " Yaya Deen bashu da lafiya please kamai a hankali." Ran Habib ya kara tuzura yacw yace" kin wuce gida ko kuwa? Me yadaman da abinda ke damunshi?" Zatai magana Jalal yace " Sorry Yaya zata shigo amma nan da minti 5." Habib yace " what?" Jalal yai murmushi yace " ban fahimci me kake nufi da metake yi anan ba bayan kafi kowa sanin meke tsakanin mu, bana tunanin kana zargin wani abun datake anan da ya wuce ganina." Habib yace " mene?" Jalal ya matso kusa dashi yai murmushi yace " yaya ka shiga ciki, yanzu kanwarka zata shigo sallama kawai zamuyi nima sauri nakeyi." Habib sai hucci yakeyi ransa ya gama b'aci, lalai ma Jalal d'in nan, meya d'aukeshi? Jalal ya juya kusa da Seemah ya rangwab'ar dakai yace " da alama dole muyi sallama yanzu, naga kamar yayanki jiranki yake." Ta kalleshi hawaye suka zubo mata, kai ya girgiza mata yace " banasan kukan nan please. " ta kalli hannunsa tace " agoggonka?" Tai maganar cikin raunaniyar murya, da sauri yasa hannun a aljihu, idannunta suka sake zubar da kwalla, meya sami agoggon mu? Jalal ya kalleta yace " karki damu." Share hawayen tai tana kallansa, yace ki shiga gida. Habib ganin rainin hankalin yafara yawa kawai ya matso tare da fizgar hannun Seemah, tafiya suke da Habib anma kaba d'aya ta juya fuskarya kallan Jalal kawai take tana hawaye, shima shi kad'ai yasan me yakeji. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣4⃣ Ammar gidan Dad ya wuce kai tsaye, saboda ganin yanda Dad yai ta k'iransa, ya dade yana knocking kafin Dad yazo ya bud'e mai, yana ganin Dad yace " Dad saura kiris in b'ata ai gashi na iso a gajiye amma ka k'i bud'e min kofa." Dad ta d'an hararesa sannan ya kamo kunensa da karfi ya jawo shi ciki, Ammar ya saki kara tare da cewa " Dad so kake d'an saurayin d'an naka ya rasa kunne daga nan ya rasa matar dazai aura?" Dad yasa hanunnsa a hab'arsa ya d'an karkata yace " Wato tun safe daka iso sai yanzu zakazo ganin mahaifinka ko?" Ammar ya dariya tare da cewa " Dad kasani kaima inda nake ai, balle na d'ade banganta ba, kasan me?" Bai jira amsar Dad ba yacigaba" wlh yanzun ma gudowa nai ban bari munyi sallama ba ina tsoron kar inmuka kara had'uwa in kasa tahowa." Dad ya girgiza kai yana wani murmushin farin ciki yace " Alhamdulila nasani ko yanzu na mutu Ammar bazaka bari swthrt d'ina ta wulakanta ba." Dariya yai yace " yanzu dai ka huce kenan?" Kara kama kumnensa Dad yai ya jashi cikin falon, Ammar ya rik'e kunnen yana cewa Dad yanzu in na kawo matar dazan aura taga anamin haka ai rainani zatai. Dad ya sakeshi tare da cewa " ka kusa kawota ne? Na d'auka bakada wacce ta kwanta maka?" Ya d'anyi kasa dakai yace " Dad anya lafiyata kalau kuwa? Narasa meke damuna, duk macen dana gani wlh sam bata birgeni, har addu'a nake Allah yasa in samu wacce zata dinga birgeni ko kwatan yanda Seemah take birgeni ne." Dad ya kara sakin murmushi baice komai ba amma a zuciyarsa fal take da farinciki. Ammar ya kalli Dad yace "Dad nasani abu kakesan fad'amin ko?" Dad yai ajiyar zuciya yace " eh Ammar amma kuma ina tunanin, maganar nan dole sai Habib yana nam za'a yita, ka k'irashi kaji in zai saku damar zuwa to, inkuma sai gobema dai to duk d'aya ne." Ammar yace ok bari na k'irashi, waya ya d'aga ya k'ira number Habib. Habib kam bayan ya shiga da Seemah cikin gida, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsu ya saketa ta zauna a bakin gado tare da turo baki tace " Ya Habib wai meke damunka kwana biyu ne? Ko ka daina so nane?" Had'e fuska yai yace " Seemah bawai san ki bane na daina sai dai bazan yarda kiyi abinda zai ja miki dana sani ba har karshen rayuwarki." Cikin rashin fahimta ta kalleshi tace " San Jalal ne zai ja min dana sani? Ko kuwa me?" Had'e fuska ya sakeyi yace " bani wayarki?" Da sauri ta mik'e tsaye tace " ban fahimta ba?" Habib yace " ki bani wayarki nace ko?" Seemah ta mik'e tare da turo baki gaba cikin shagwab'a tace " Ya Habib kasan dai bazan iya rabuwa da wayata ba ko?" Matsoyai kusa da ita tare da fizge wayar yace " kanwata ajiye miki zanyi, sannan gobe kishirya mu fita yawo." Yana kainan yai hanyar waje, zubewa tai a kasa tafara kukan shagwab'a tana bubuga kafa, tasani indai tafara wannan kukan to kome takeso sai an mata shi koda kuwa ba'a san yi mata, sai dai mamakinta yau Habib ko juyowa baiyi ba, duk da kasan zuciyarsa kukan na tab'ashi sosai sai dai bazai bari rayuwarta ta salwanta ba saboda yarinta ba. Yana shiga d'aki ya kashe wayar ya bud'e drawer ya sata sanna ya zauna a bakin gado yana tunanin mezai wa Seemah dazai sa ta manta wani Jalal. Wayar Ammar ce ta shigo ya d'aga wayar kamar bayaso, Ammar yace " Dad ne kesan magana da kai amma yace in akwai abinda kake ka bari......." Katseshi yai da sauri da cewa ganinan zuwa yanzun nan, yana kainan ya katse wayar tare da yin waje da sauri, tunaninsa d'aya "Dad ya sauko zai sanar dashi komai." Da sauri ya fito falo yai hanyar waje, Farida data fito daga kitchen rik'e da tire ta yanka kayan marmari aciki, ganin ya fito da sauri yasa ta shiga k'iransa sai dai inaaaa hankalinsa yayi waje sam bai kula da ita ba. Ajiyar zuciya tai sannan ta koma kitchen d'in. Habib da kanshi ya shiga mota ya fara driven ya fito yabi inda da Jalal ya tsaya da wani kallo ganin basanan yasashi yin tsaki. ●●●●●●●□□□□□□□●●●●●●●●●●●□□ Jalal kam bayan Seemah ta shiga gida Sagir ya shigo motar tare da kallansa yace " Jalal sam ban fahimce meke faruwa ba, dan Allah kamin bayani." Kansa ya rik'e dayakeji yana sara mai ya juyo a hankali yace " muje Sagir zan fad'ama." Nan Sagir ya tadda mota suka d'au hanya, sunyi tafiya mai nisa kafin Jalal yace " Sagir ina san Seemah." Juyowa Sagir yai ya kalleshi sannan ya maida kansa titi yace " Jalal amma kasan........ Wani irin murmushin kafin hali Jalal yai yace " I am not worthy ko?" Sagir yace ba haka bane, ni a guna you are far much more worthy sai dai su a gunsu......... Jalal ya kwantar da kansa yace " Nasani Sagir, su sunfisan 'yarsu ta auri wanda yake the same class da su." Yai ajiyar zuciya sannan yace " Sai dai abinda ban fahimta ba shine, na d'auka in mace da namiji suna san junasu shikenan, na farko ita yarinyarnan tasan banida hali kuma a hakan ta aminta dani, na biyu yarinyar nan tana sona, so ni ina tunanin kamar abinda akeyi baya dacewa." Sagir ya d'an kalli Jalal yace " haka ne Jalal abinda kafad'a haka yake sai dai yanzu rayuwar da ake ciki kenan." Jalal ya furzar da wata iska sannan cikin kakkausar murya yace" Sagir kasan me? " sannan ya saki murmushi yace " a farko nayi tunanin kamar da wahala a barmu tare da Seemah sai dai d'azu zuciyata ta sanar dani wani abu, bazan rabu da Seemah ba duk tsanani da abinda zasu ce, sannan bazan yarda su wulakantani ba, wannan alkawari nama zuciyata." Sagir ya kalleshi yace " Jalal please nidai shawarata d'aya shine ka hakura da yarinyar nan, ni yaushe ka fara soyayya haka dakake jin zaka jure komai na abinda za'a maka? " Jalal ya maida kallansa jikin window yace " yanzu nafara shiyasa nakeji kamar nafi kowa kamuwa da soyayya." Dariya sosai Sagir yai yace lalai Jalal......... Nima nace Lalai............. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣5⃣ Habib yana isa gidan da sauri ya bud'e mota ya fita ko kofar bai rufe ba, yai cikin gidan da sauri, bayan ya shiga da Sallama suka amsa mai yasamu guri ya zauna, Ammar na kasa kusa da Dad yana daddana waya, Habib shima ya karasa bangaren dake kallan Ammar ya zauna. Ammar ya kalleshi tare da cewa "Yaya ka iso?" Habib ya d'aga nasa kai alamar eh yamaida kallansa kan Dad dayai shiru, a zuciyarsa kam addu'arsa d'aya ce Allah ya taimakeshi akan abinda yake shirinyi. Habib ganin Dad yayi shiru yasa yace " Dad kayi shiru?" Ya sauke idanunsa akan Habib sannan yamaida kallansa kan Ammar yai gyaran murya tare da cewa " inaso ku bani aran hankalinku nan." Gaba d'ayansu suka maida kallansu kanshi, Dad ya had'iyi wani abu sannan yace " abinda nake shirin sanar daku shine......." Duk sun zak'u gashi maganar Dad ta katse bai karasa ba, jin shirun dayai yasa Ammar yace " Dad yaka tsaya?" Dad yai shiru sannan ya sauko tsakiyansu ya zauna tare da dafa Ammar idanunsa taf da kwalla yace " Ammar kasani inasanka ko?" Murmushi Ammar yai yace " haba Dad harsai ka fad'i haka?" Dad ya kakaro murmushi sannan ya mik'e tare da takawa gaba dasu kad'an ya hard'e hannayensa ta baya, ya juya musu baya ya cigaba " lokaci yayi daya kamata in sanar daku wani sirri da baku tab'a sani ba, Ammar banaso ka sa wani mugun abu a ranka dalilin dayasa na yanke shawarar sanar daku shine Ammar nakeso ya auri Seemah." Ba Ammar ba hatta Habib mik'ewa yai a zabure, Dad kam idanu ya runtse, Ammar da Habib a tare suka had'a baki suka ce *What?* Ammar ya cigaba da magana " ban fahimci me kake nufi ba Dad, ni in auri kanwata? Me kakesan fad'ane Dad?" Habib ya amshe maganar da cewa " Dad me kake nufi da kalamanka? Wani irin zance kakeyi haka? Kana nufin akwai aure a tsakanin Ammar da Seemah ko me?" Dad ya d'aure tare da share hawayen da suka kwaranyo ta gefen idanunsa, ya juyo tare da cewa " haka ne Habib akwai aure a tsakaninsu domin kuwa Ammar ba d'ana bane." A tare suka kara cewa *what?* gaban Ammar ya fad'i zubewa yai kasa tare da kallan Dad cikin wani irin rud'ani, Habib ma ya kalli Ammar sannan ya kalli Dad yace " ban fahimceka ba Dad kanasan kacemin Ammar kanina ba kaine mahaifinsa ba?" Dad ya d'aga kai tare da cewa " nasanar dakune saboda inasan had'shi aure da Seemah shiyasa na aika yazo kasar nan." Girgiza kai Ammar ya shigayi da sauri ya mik'e yai waje da gudu, Dad ya runtae ido shikad'ai yasan meyakeji, Habib ya matso kusa da Dad, ga mamakin Dad gani yai Habib ya saki murmushi yace " Dad do u expect me to believe that? Mene? Ammar ba d'anka bane? Banda tsananin kama da kukeyi? Da muma mukeyi dashi? Me kakesan cewa dad?" Dad yai saurin juya baya tare da cewa " kanina da nake tsananin kama dashi shine mahaifin Ammar yana haifarsa sunyi tafiya sukai hatsari shida matarsa wannan dalilin ne yasa na anso Ammar tare da alkawarin kula dashi kamar d'ana." Habib yai shiru tare da jinjina kai yace " ayya meyasa baka tab'a fad'amin ba Dad?" Ganin Habib ya yarda da kalamansa ne yasa Dad ya juyo yace ba wannan bane da muwar da ya kamata muyi yanzu, Seemah kana tunanin zata rabu da waccen banzan yaron? Habib yai shiru sai can yace " Dad Allah ne kawai ya sani, amma yarinyar nan sai anyi da gaske wajen rabasu, har kud'i na bashi d'azu akan ya bar aikin dayake a company d'ina ya bar garin nan amma yak'i, Dad yaron nan yanada taurin kai." Dad yai tsaki tare da cewa duk taurin kansa ai baifi karfin iyayensa ba, su kuma iyayen nasa nasan basufi karfin kud'i ba,ka bincikomin garinsu zanje har gidansu in basu kud'i su sa d'ansu yabar aiki a company d'inmu. Habib ya jinjina kai yace " wannan ma is a good idea." Dad yace " naso in d'auketa mubar kasar amma kuma sai nai wani tunani, inaso kafin mu koma ai baikonsu da Ammar inyaso daga baya sai ai auren." Habib yai shiru bai amsa ba, shidai tana mamakin wannan al'amarin. Nan yai sallama akan gobe zai turo address d'in gidansu Jalal. Jalal kam da kyar ya lallab'a Jalal suka wuce gidansu, sunje shiga gate d'in gidan Yaga k'iran Abba, da sauri ya d'auka tare da saisaita murya ya gaida shi, Abba ya amsa tare da cewa " Ashe ka koma?" Jalal yace " wlh k'ira na akai na gaggawa." Abba yace " ba wani abu dama na k'iraka ne na sanar dakai na yanke hukunci ranar Juma'a rana ita jiya kenan, za'a d'aura maka aure da Zainab, ka kuma tabbatar ka iso da sassafe." Cikim razana Jalal ya bud'e murfin mota ya fita tare da cewa " Abba ban fahimci me kake nufi ba, bangane Aure ba?" Abba ya had'e rai yace " na yanke hukunci kuma baka isa ka bijirema hukuncina ba kafi kowa sanin hali na, sannan bazan yarda da wani shirmenka ba." Jalal yace " Amma Abba......." Cikin fad'a Abba ya katseshi da cewa karka kuskura Jalal kace zaka d'inga musu dani, kai ko kumya bakaji ba? Yarinyarnan tun tana karama take taimakon mahaifiyarka da kanwarka, kai kana tunanin dabadan Allah yasa tana nan ba wani abun ai mahaifiyarka bazata iya jura ba." Jalal zai kara magana Abba ya kara katseshi da cewa " ka kuma tabbatar ka zo ranar juma'a da wuri d'an intanine gobe ma za'a d'aura auran sa'a kaci mahaifiyarka ta nemi izini zuwa juma'a." ABBA nakainan ya katse layin. Bin wayar Jalal yai da kallo meke faruwa? Dasauri ya danna number Umma sai dai lokacin tana zaune kusa da Abba hakan yasa tak'i d'aukan wayar d'an umarnin Abba ne kar kowa ya d'auki k'iran Jalal. Ganin taki d'auka yasa ya k'ira Zainab tana zaune akan sallayar datai salla tana lazimi, ganin k'iran Jalal yasa tai murmushi sai dai data tuna me ya mata da kuma umarnin Abba yasa ta canza fuska ta koma kalar tausayi, sai dai inaaaaa bazata iya ganin wayar Jalal ta katse ba tana zaune, saura kiris ta katse ta d'aga tare da sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Zainab meke faruwa? Ban gane aure wani satin kai tsaye ba?" Zainab tai kasa da kai a hankali tace " Yaya bansan nima meya faruba gaskiya kawai tun sanda Abba ya fita d'in nan, inaji gidan mu yaje, d'an bai dawoba sai daf da magrib, bansan meya faruba kawai yacemin inyi hakuri lefe da wani sha'anin biki ayi daga baya in inaso amma wani satin za'a d'aura mana aure amma anan zan zana kafin ka samu gida." Jalal yaja dogon ajiyar zuciya tare da cewa " it can't happen." Yana fadar haka ya katse wayar tare da neman number Seemah, sai dai duk yanda yake k'ira layin a kashe yake matar take sanar dashi. Hannu yasa ya shafi kansa sannan ya furzar da wata isa tare da naushin jikin bango da hannunsa, yaji zafi kwarai sai dai baikai zafin da yakeji a zuciyarsa ba. Sagir ne ya matso ya dafashi, baice mai komai ba. Seemah kam taci kuka harta gaji, Aisha sai dariya takeyi, d'an karma tai lallashi yasa taki shiga d'akin, gani take gwara a saita mara kunya da sakalci. Farida kam shigarta uku tana bata hakuri amma inaaaaa seemah taki hakura sai kuka takeyi itadai a bata wayarta. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* No. 3⃣6⃣ *Washegari*.......... Seemah na kwance tana bacci Dad ya karaso gidan, bayan sun gaisa da Habib da matarsa da 'ya'yansa kasancewar yau lahadi kowa na gida, Farida ta kwashe su Ra'isa suka barmusu falon, Dad ya kalli Habib yace " yaya ka nemo gidan?" Kai Habib ya d'aga tare da cewa na nemo Dad dama na tab'a tambayar abokinsa Sagir a wani gari Jalal yake shine yacemin Birnin/gwari, to shine nasa akamin bincike a garin, ya fada tare da mik'amai takarda. Habib ya kara kallan Dad yace " Amma Dad kana ganin hakan ne ya dace?" Dad yai murmushi yace " Habib kenan, ban tab'a ganin yaran ba amma tunda kar baiji kunyar kallan Seemata ba yace yana so hakan ya nunamin he is stubborn sannan iyayensa ne kad'ai zasuma tufkar hanci." Habib ya gyad'a kai alamar gamsuwa, Dad ya amshi takardar tare da cewa yauwa Habib nagode, sannan ina so anjima ka shirya kaje Suleja ance jikin Hajiya ya tashi. Habib ya amsa ta to, tare da cigaba da cewa " Amma Dad ya maganar Ammar?" Dad yai murmushi tare da cewa "karka damu yana Nordic Villa, sai wajen 1 na dare dana dameshi da waya shine yamin text." Habib yai kasa dakai yana tausayin kanin nasa, Dad ya mik'e tare da cewa ina baby na? " Tana d'akinsu mayb bata tashi ba." Dad yai hanyar d'akin kai tsaye a raina nace lalai rayuwar turai ta zauna muku amma mu anan yaza'ai uba ya wuce cikin gidan d'ansa kai tsaye? ????? Yana isa kofar d'akin daidainan Aisha ta fito daga d'akin,, ganin Dad yasa tai saurin risinawa ta gaida shi, Dad ya amsa fuska a sake yace " Seemah fa?" Ta kalli d'akin tace " tana bacci." Bai amsa mata ba ya tura d'akin tare da sallama, a kwance take tama baccinta zama yai gefenta yana kallanta, ba shakka tana tsananin kama da mahaifiyarta, sai dai ko d'an shi kansa bai san uban bane???? Hannu yasa ya shafi gefen kanta a hankali Seemah ta bud'e ido ta saukeshi akan Dad, murmushi ta saki cikin abin bacci tace " My Dad yaushe ka iso?" Yanzun nan ya fad'a yana kallanta. Ta mik'e zaune tare da rik'e hannayensa, tace " Dad please kad'aukeni mukoma gidanmu kaji?" "Bakyasan gida Habib d'in ne ko me?" Sake hannun Dad tai ta turo baki tace " banaso Dad ni Yanzu nama daina san Ya Habib, Dad please mukoma kaji? Gani gaka ga ya Ammar hakan yafi dad'i." Dariya Dad yai yace " Seemah kinsan ba mace a gidan dazata d'inga girki da sauransu." Ajiyar zuciya tai tace " Nidai to banasan gidan nan" Dad ya mik'e tare da kallanta yace " Amma yanaga idanunki haka?" " banacr maka banasan gidan nan ba? Dad dan dai bakasan me ya Habib yamin bane, yanzu ko waya ma bandashi, narasa meyasa bayasan Deen bayan ni zan........." Wani kallo da Dad ya maka mata yasa tai shiru tare da cewa " ni duk kun daina sona ma ina Ya Ammar d'ina?" Dad ya saki fuska yace " yauwa dama abinda nazo fad'a miki kenan, Ammar bayajin dad'i shiyasa nakeso kije gunsa." Dirowa tai daga kan gado tace " me ya sameshi? Jiya fa lafiyarsa kalau." Ganin yanda ta rud'e yasa Dad yai dariya yace " Yana Nordic villa kishirya kije." Da sauri ta zari towel d'in wanka tace " Dad nayi nan." Dariyar farinciki Dad yai yanasan yanda sukesan junan. Fitowa yai sukai sallama da Habib da kuma Farida ya fad'a motarsa driver ya jashi sai binin gwari. Jalal kam sam jiya kasa barci tai saboda bayasan takurama Sagir yasa ya kwanta kamar mai bacci harsai da yaga Sagir yafara bacci sosai sannan ya mik'e ya d'auro alwala ya fara sallah a neman mafita agun Allah sai wajen karfe 3 bacci ya d'aukeshi akan sallar. Da safe bayan sunyi wanka Sagir yabashi d'aya daga cikin kayansa yasa, nan ma dakyar Jalal ya yarda, Sagir ya nunashi da yatsa yace " gaskiya Jalal bansan irinka ba? Meyasa ne sam bakasan kai amfani da abin wani?" " Sagir tun ina karami haka na taso, Hali nane, banasan amfani da abinda ba nawa ba ko neman alfarmar wani ko kuma bari kud'i su nemi cin galabata." Kai Sagir ya jinjina yace " shiyasa kowa yake respecting d'inka, wlh ko ni ina bala'in ganin girman ka." Murmushin dabai wuce iya leb'e ba Jalal yao sannan ya d'aga waya ya kara k'iran umma sai dai yanzun ma bata d'aga ba, ajiyar zuciya yai tare da kallan Sagir yace " tunanin zuwa birnin gwari nakeyi." "Yanzo? Ba jiya ka dawo ba?" Ido Jalal ya kankance ya kurawa wani gun ido baice komai ba. Sagir ya daga kafad'ar sa yace " Calm down Jalal." Kallansa Jalal yai yace " how can I? In this situation? Ga nakasa samun Seemah?" Sagir zaiyi magana yaga Jalal ya mik'e tare da cewa " Inaji gidansu Seemah zani." Zaro ido Sagir yai yace " Jalal meke damunka wai? Yaushe kazama haka wai? Taya za'ai kaje gidan da inagani a ido ba sanka ake ba in fact ni tsorona ma karka rasa aikinka." Jalal yasaki wata dariya yace " I wish zasuyi tsautsayin korata daga aiki, dana nuna musu shayi ma ruwa ne." Sagir ya kalleshi da alamar tambaya yace " kamar ya?" Jalal ya had'e hannayensa ya fara takawa yace kai kana tunanin in suka koran daga aiki ban musu laifin komai ba zan barsu haka? Takarda zan tura harsai sun sanar dani menai dana cancanci kura, in ba haka ba su amsa k'iran hukuma." Sagir yasa dariya tare da tafi yace " Jalal kenan u are really smart suma nasan bazasuyi wannan gangancin ba, amma dai duk da haka ka kula." Jalal ya juyo yace " nagode Sagir amma please in ba inda zaka aramin motarka yanzu zan dawo. Sagir ya mik'amai batare da yace komai ba, Jalal ya amsa tare da godiya ya fita. Seemah ta isa inda Ammar yake, sunje shiga daidainan wani babban mutum ko ince d'an siyasa babba, ya fito tare da mutanensa da 'yan goya kai baya, Seemah ta kalleshi baifi sa'an dad ba amma ko ba'a fad'a ba kasan d'am siyasa ne, idanta ta d'auke daga kansa sai dai maganar dataji ne yasa ta maida hankalinta da kallanta gun. D'an siyasan nan taji yana fad'a kamar zai yanka mutanen dake gun, mamaki abin ya bata ta kara dubawa dawa yake fad'an? Wani dattijo tagani a tsugunne yana rokarsa jitai mutumin yace " wai ku mutane wasu irin dakikai ne? Sau nawa ina sanar dakai za'a baka kud'in gidan ka? Nifa banasan hauka kuma wlh karka kuskura ka kara zuwa inda nake, in banda darajar kai tsoho ne da tuni nasa an d'aureka." Tsohon sai hannu yake had'awa alamar ban hakuri, sam Seemah batajin ke yake cewa da alama ma baya iya magana da karfi saboda tsufa, tsaki tai tace " na tsani mutane irin wannan dabasu san darajar tsofaffi ba aikin banza kawai...... Ta juya wasu 'yan jarida ne suka shigo cikin harabar hotel d'in securities na cemusu su tafi amma ina....sai da suka karasa gun wannan mutumin, Seemah ta juya ta kallesu, da mamaki ta kara kallan gun me zata gani? Wannan mutumin daya cima tsohon nan mutunci tagani ya kama hannun tsohon yama bashi hakuri, ga 'yan jarida nata d'auka, da mamaki ta kara kallansu, mutumin taji yace " Baba kayi hakuri munanan muna kok'arin yanda zamuyi kud'inku su fito amma ga wannan, batasan nawa ya mik'a ba amma tasan kud'ine masu kauri, mutumin taga ya kara kankame hannun babban harda kwallarsa wai Baba ka yafe mana, mukanmu mumajin tausayin halin da kuke ciki, ko bacci bana iyayi saboda tausayi. Seemah dariya tasa tace " what? Me nake gani? Wannan wani irin mutum ne? 2 face? Ahhhhh yau naga abinda ban tab'a gani ba, harara ta maka mai duk da baimasan tanayi ba ta karasa ciki, tana tafe itakad'ai tama masifa. D'akin da Ammar yake ta jarasa tare da danna kararawa, bata dad'e ba Ammar yazoya bud'e d'an ya d'auka masu aikin hotel d'in ne, ganin Seemah yasa ya tsaya kawai yana mata kallan mamaki, itama kallam mamaki take mai ta sa hannu akan fuskarsa yace "yaya menene haka? Meya sameka?" Ammar bai amsa mata ba ya koma ciki tare da komawa karshen bango ya zauna, kamar yanda yake d'azu, Seemah da sauri ta karasa kusa dashi tace " yaya menene hakan?" Bai ko kalleta ba bai kuma amsa mata ba, Seemah mamaki ya kara kamata ganin yanda duk ya canza a daren jiya yasa ta matso gabanshi tasa hannayenta akan fuskarsa idanunta suka ciciko tace " Yayana menene?" Kallanta Ammar yai sai dai duk yanda yaso ya mata magana ya kasa, hawaye ne suka sauka a idanunsa, itama hawaye suka zubo mata tace " yaya wani abun ne? Please ka fad'amin." Tafad'a tare da kallan d'akin, da alama ko kan gadon bai hau ba gashi kuma kamar abincin ma da aka kawomai d'azu ma bai ciba. Kallansa tai da mamaki, bata tab' a ganin Ammar haka ba, mutum mai barkwanci? Mik'ewa Amnar yai kawai ya shiga toilet ta bi bayansa da kallo tare da share kwalla, wayarsa tagani akan gado da sauri ta k'ira Dad sai dai bai d'auka ba, ta kira junaid yace mata zai kirata yana aiki ne, haushi ya isheta gashi ita bazata k'ira Habib ba, da sauri tasa number Jalal. Jalal kam har ya iso gidan yana shirin fita daga mota wayarsa tai kara ya d'aga jin muryar Seemah yasa ya koma ya zauna tare da cewa "Meemah ina kika shiga nakasa samun layinki? Do u know how worried am I?" Ajiyar zuciya tai sannan taxe " My deen ina nan Nordic sai dai narasa meke faruwa da Ya Ammar yak'imin magana gashi duk ya canza." Duk da Jalal baiji dad'i ba amma sai ya daure yace " ahh ina my cute Meemah ta shiga ne? Wacce kesa mutum dariya ko bai saba ba?" Murmushi tai tace " let me try." Yace " amma I want to see you ya za'ai?" Ajiyar zuciya ta kara saki ta kara rik'e wayar tace " My deen ni kaina inasan ganinka ga ba waya a hanuna, kawai nanda 20mins kazo nan sai in fito." Ya saki wani sanssanyar murmushi yace " ok see u later." Tai murmushi tare da katse layin, wani energy ne taji ya zo mata ta mik'e tsaye tare da karasawa bakin toiler d'in da Ammar yake....... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 3⃣7⃣ Seemah ta shiga knocking d'in toilet d'in Ammar na tsaye jikin kofar tunaninsa d'aya ya ya zai kalli Seemah yanzu? A matsayin me? Ganin yaki bud'ewa yasa Seemah ta zame ta tsugunna a jikin kofar tare da cewa a hankali " Yaya nice fa? Nad'auka tsakanina dakai babu 'yar haka, ko me ya faru ya kamata in sani indai har abin ya shafeka." Ammar shima ya tsugunna a jikin kofar ta ciki yana sauraranta, Seemah tai ajiyar zuciya tare da cewa " yaya please ka bud'e muyi magana? Please? " Ammar ya motsa baki har zaiyi magana kuma ya fasa, Seemah ganin yayi shiru yasa tace " yaya kasan me? Ni yanzu na daina san Yaya Habib d'an haka mu koma kawai gidan Dad ni dakai muzauna." Nan ma shiru yai sai dai yanda na kalleshi naga fuskarsa tad'an saki, Seemah tai murmushi sannan ta cigaba " yaya amma in muka koma wazai d'inga mana abinci? Kasan ban iya girki ba." A hankali murmushi ya bayyana a fuskar Ammar, Tab'e baki tai ta cigaba " yaya nasan dai kaima ba wani abinci ka iya ba, to ya zamuyi?" Murmushi sosai Ammar yai, jiyai zuciyarshi tayi haske, Seemah kam ganin yak'i kulata yasa ta mik'e tare da cewa " yaya nasan kanaji na amma tunda kak'i kulani, shikenan bari nai tafiyata." Jin alamun ta mik'e yasa Ammar ya fito daga toilet da sauri, yana zuwa ya rungumeta ta baya, a hankali tace " Yaya?" " wait for a moment please." Ya fad'a cikin wata murya dayasa Seemah tasha jinin jikinta, Ammar ya dad'e a haka kafin a hankali ya saketa, juyowa tai ta kalleshi tace " Yayana meke damunka wai?" Murmushi yai tare da cewa Seemah.......wayar sa ce ta katsesu da kara, da sauri Seemah ta d'aga wayar ganin number Jalal, cemata kawai yai yazo, tace ok, sannan ta juyo ta kalli Ammar tace " yaya my Deen yazo bari in d'an fita waje ina zuwa." Bata jira amsarsa ba tai waje da sauri, Ammar ya bita da kallo zuciyarsa ba dad'i. Seemah kam tana fitowa ta kara kallan inda taga wannan mutumin sai dai ganin ba kowa yasa tai tsaki tare da fita neman inda Jalal yake. Jalal kam daga nesa ya ganta, murmushi ne ya bayyana a fuskarsa ya bud'e motar ya fita, kansa ya samu da d'aga mata hannu, tana ganinshi itama ta saki murmushi ta karaso a hankali cikin tafiyarta, tana zuwa kusa da shi suka kalli juna suka saki murmushi a tare kana ganinsu kasan suna tsantsar farinciki na ganin juna, Seemah ta kalli Jalal tace " My Deen ya jikin naka?" Yace " Ahhh!!!! Ni sam na manta ma banda lafiya a jikina." Da mamaki tace " ban gane ba?" "Zuciyata tana rashin lafiya wazai damu da ciwon dake gangar jiki?" Dariya Seemah tasa sannan ta rik'e hab'a tace " tooh? Oh ni? Yaushe my deen yazama malamin kalamai? " Hararta yai yace " bawani malamin kalamai abinda ke damuna na fad'a" Zagayawa tai ta shiga mota, shima ya koma ya zauna tare da juyowa yace " ya Ammar d'in?" Tai ajiyar zuciya tace " I don't know, haryanzu bai cemin komai ba." Jalal ya d'an matso da fuskarsa kusa da ita yace " ko dai bayasan ya fad'a miki ne? Ko sirri ne?" Ta murgud'a mai baki tace " ba wani sirri tsakanina da yayana." Jalal yace " naji, amma meyasami wayarki?" Ta had'e rai tare da cewa " ba yaya Habib bane ya kwacemin waya." Jalal ya koma ya zauna jikin kujerar, sannan ya daure yace " because of me?" Ta kalleshi idanunta suka ciciko, tace " karkadamu Deen komai zai zo da sauki, ni takace, kaji?" Murmushi yai sannan ya matso tare da d'anjan kumatunta, kai ta karkatar tace " ya kukai a Birnin gwarin?" Jalal ya kalleta tare da neman zare hannunsa, da sauri ta rik'o hannun sa tare da kura mai ido, murmushi ya kakaro yace " karki damu kinji?" Daga yanda yai maganar tasan akwai wani abun, sakeshi tai tare da cewa " Deen ina tsoron kar a rabamu da......." Ya tsarsa yakai bakinta yace " please Meemah karki karasa, ba abinda zai fari sai alkairi." Hawayen da take boyewa ne suka zubo, yasa hannu ya share mata sannan yace " banasan ind'inga ganin idanun dana fiso a duniya suna zubda hawaye, abin takaicin kuma nine nake sasu zubar da hawayen." D'agowa tai ta kalleshi tare da girgiza kai, Jalal jiyai kamar shima hawayen zaiyi, da sauri ya bud'e motar ya fita, Seemah ta bishi da kallo, tare da kokarin fita, vibration d'in dataji wayarsa nayi yasa ta kalli wayar *ZAINAB* abinda taga ya fito a jikin wayar kenan kawai sai ta samu kanta da d'aga wayar, Zainab kam kai tsaye tace " yaya ya zakayi? Su Abba fa da gaske suke d'azu ya fita kaiwa abugo Iv na d'aurin aure, da alama next week d'in nan za'a d'aura." Jikin Seemah ne ya shiga rawa, batasan sanda ta yarda wayar ba, duk bata hankalinta, bud'e kofar tai tafito, Jalal na ganinta ya taho, sai dai ko kallansa batai ba tafiya kawai take, ganin haka yasa Jalal yasha gabanta yace Seemah menene? D'agowa tai ta kalleshi, jitai kamar tasa ihu, matsawa tai gefensa ta cigaba da tafiya, Jalal ya riko hannunta ta baya yace Seemah? Janye hannunta tai kawai tasa gudu ta koma cikin hotel d'in, binta yai da kallo sannan shima yai ciki, sai dai inaa, sam bai ganta ba, securities sukazo sukace ya fita. Dad ya isa Birnin gwari lafiya, bai sha wahala sosao ba wajen neman gidan, saboda unguwar kusan duk sunsan gidansu Jalal, tunda ya fara shiga lokon da kafa ransa yake a b'ace, mamakinsa amma lalai Jalal d'in nan yagama raina musu hankali, sai ma daya isa gidan, ba gate bane kawai koface ya d'an bubuga jiyai ance ana zuwa, ba'a dad'e ba wata yarinya budurwa sanye da hijabi tazo ta bud'e tare da mai kallan mamaki, sai kuma can tai saurin cewa " ina kwana?" Lafiya dad ya fad'a tare da cewa nan ne gidansu Jalal? Kai ta d'aga tace " nan ne amma bayanan." Dad ya kara kallan wajen gidan yace " nasani iyayensa nake nema." Zuciyar zainab ce ta buga, badai laifi yai ba ko? Ahankali tace shigo, Dad yasa kafa cikin gidan, yabi gidan da kallo, Umma ce ta fito tare da cewa sannu da zuwa, ya kalleta yace yauwa, tace shigo, wani kallo yakarama gidan sannan yace " basai na shiga ba dama zuwa nai akan ku jama d'anku kune, yasan matsayinsa, 'yata Seemah namata miji ya fita daga harkarta tun kafin rai yazo yana b'aci gwara ayi magana a mutunce." Jikin Umma yai sanyi, tace " bawan Allah kayi hakuri mu kanmu kaga wace mukeso ya aura kuma ma wani satin za'ai auran, d'an haka ka kwantar da hankalinka." Dad ya matso tare da ajiyema Umma envelope yace " nagode da fahimtarku, ga wannan kyautace ba yawa, ku bawa d'anku shawara d'an masani shine ya makallewa 'yata." " ka koma d'an kuwa kayi zuwan banza." Da sauri Dad ya juya jin furucin daga bayansa, juyawa yai ya kalleshi harzai yi magana sai kuma ya kura mata ido sosai, shi kanshi Abba kalansa yakeyi, a hankali Dad ya karaso kusa da Abba, Dad yace " malam kamar na sanka ko?" Abba shima da mamaki yace " nima kamar na sanka," Dad ya d'an juya kai yace ya sunan ka? Da mamaki yace Ahmad. Idanun Dad ne suka rik'ed'e cikin wani yanayi ya riko wuyan Abba ya jashi zuwa jikin bango, yace Amadu mai shago? Idanu Abba ya zaro, Umma da zainab mamaki ya kamasu menene hakan. Cikin tsawa da fad'a Dad yace " Amadu ne? Kai ne?" Abba ya kara zaro ido yace " Isma'il?" Matsashi sosai Dad yai har numfashin Abba ya fara rawa, da sauri Umma da zainab suka matso sunamai magana, Dad cikin masifa yace " Amadu? Kaine? Yama za'ai in mantaka? Mutumin dakajazama rayuwata, ka lalatamin rayuwata." Umma najin haka tafarayin baya baya tana jijiga kai, idanunta na zubar da ruwa, zainab kam ganin yanda Abba yakeshan wahala yasa tai saurin tsugun nawa ta rik'e kafafun Dad. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 3⃣8⃣ Dad ganin Abba na kakari yasa ya sakeshi sannan yace " me kakeyi a nan?" Kafin Abba yai magana Zainab tayi saurin zuwa kusa dashi tace " Abba sannu." Hakan yasa ya gane wato gidan sa ne, cikin tsananin mamaki da takaici Dad yace " Jalal d'anka ne?" " Eh" zainab ta fad'a sannan ta cigaba" amma malam menene hakan?" Wani kallo Dad ya mata yace " dama ina 'ya'yan Amadu zasuyi tarbiya? In ba haka ba yaza'ai yarinya dake kid'inga shiga maganar manya?" Da sauri tai kasa dakai itakanta batasan ya akai tai magana haka ba, jitai Umma tace " Zo ki wuce ciki." Simi-simi Zainab tai ciki, Abba ya d'ago yace " Isma'il!!!" Dad ya nunashi da yatsa yace " karkaga wai na maka magana ka d'auka wai na yafe maka abinda kamin ne a shekarun baya, Amadu kaine mutum na farko kuma na karshe da bazan tab'a yafema ba, alhakina dama Fatima shine yasa ka kasa ci gaba, kuma wlh kaji na gaya maka kayi gaggawar fad'a ma d'anka ya barmin 'yata tun kafin na aikashi prison. " Yana kainan Dad yai hanyar waje, Umma ce da sauri ta matso ta tsugunna a bayansa hawaye na zuba a idanunta sosai, tace " Malam d'an Allah kayi hakuri ka yafe mai, na sani......." Dad bai jira ta karasa ba yasa kai ba bar gidan, yana fita waje ya juyo ya k'ara bugawa gidan kallo, sannan yai gaba. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Jalal kam a waje ya tsaya ya rasa meya faru da Seemah ta canza lokaci guda haka, to amma yazaiyi? Sun hanashi shiga, wayar sa ya d'aga kawai ya k'ira number Ammar sai dai tanata ringing ba'a d'aga ba, cilla wayar yai gefen kujera ya shafi goshinsa tare da cewa Ya Allah! Seemah kam tana shiga d'akin ta tadda Ammar a tsaye ta jikin window da gudu ta karasa ta rungumeshi ta saki wani irin kuka mai tab'a zuciya, Ammar kamar ta sosa mai inda yake mai kaik'ayi shi kansa so yake yai kuka kamar haka, jiyai idanunsa ya shiga kawo ruwa, d'an kukan gar zuciyarsa yake tab'awa, Sam ya kasa cewa tai shiru sai ma shima kukan da yakeyi, sunfi minti 10 a haka kafin cikin kuka Seemah tace " Yaya ya zanyi?" Ta karasa maganar tare da d'agowa ta kalleshi, ganin yana kuka shima yasa ta shiga girgiza kai tana hawaye tace " yaya me yake damunka please? " hannu yasa ya goge hawayen yace " fad'a kukai da Deen d'in naki?" Baya ta juya ma Ammar tace " yaya shikenan, rayuwata tazo karshe." Da sauri Ammar yadawo tagabanta ya rike kafad'arta yace " Seemah me kike fad'a haka?" Hawayene ya zubo mata tace " yaya aure za'amai nextweek." Ta karasa maganar da fashewa da wani kuka, Ammar ya kama hannunta ya zaunar a kan gado, sannan shima ya zauna a gefenta ya juyota setinsa yace " Seemah?" Kallansa tai da mamaki jin yanda ya kararra gurin k'iran sunan, yace " Seemah!!" Tace " yaya inaji menene? Ka tsoratani." Fasa fad'ar abinda yai niyya yai ya wayance da cewa "Seemah ki rage wannan soyayyar da kikema Jalal bana tunanin yana sanki kamar yanda kike sansa." Hawaye ta share tace " kaima haka kake gani ko yaya? Na sani yaya, nasan nafi sansa akan yadda yake sona, in fad'ama gaskiya yaya ni na fara cewa ma ina sanshi." Ammar ya juyo ya kalleta, hawayenta suka cigaba da zuba, tace " amma yazanyi yaya? Ina sanshi sosai, kome nakeyi yana raina, in ban ganshi ba ji nake zuciyata kamar zata fashe, in muna tare kuma ji make kamar kar mu rabu." Tai ajiyar zuciya tace " ya Ammar banaji zan iya rayuwa ba Deen." Ammar duk da kalamanta sun mai zafi a zuciya amma bai nuna ba murmushi ya kakaro ya matso kusa da ita yace " Seemah yaushe zuciyarki ta kamo haka?" Tace " ban sani ba Ya Ammar ni kaina ban sani ba." Ta karasa tare da sa kuka, jawota yai jikinsa yana shafa bayanta alamun lallashi. Jalal ya dad'e agun ganin Seemah tak'i fitowa yasa ya juya gidansu Sagir, yai parking motar yashiga gun Sagir, d'akin a bud'e yake sai dai ba kowa a ciki, shiga yai ya hau kan gado ya kwanta tare da d'aura hannayensa akan goshinsa, tunanuka sun mai yawa a hankali hawaye suka ziraro ta gefen idanunsa, sam bai ji sallamar Sagir ba, sai da yaji an dafashi, kallan Sagir yai sannan ya mik'e zaune yace " Sagir ina kaje?" "Ummanmu ce zasu fita shine na musu sallama" Jalal yace " Amma bansan sunanan ba dana gaidasu ai." Dariya Sagir yai yace " kana cikin tension ina zan fad'ama?" Ya cigaba " amma ya? Ka ganta?" Kai Jalal ya d'aga alamar eh, Sagir yace " Amma kamar baka farin ciki, fad'a kukai?" Ajiyar zuciya Jalal yai yace " nikaina bansani ba, da alama Seemah hard to get take neman yimin, sai dai ni a wannan lokacin batasan banasan muyi fad'a ba sam d'an ni kad'ai nasan me nake ji." Sagir ya kwashe da dariya yace " Lalai Mr Romeo." ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♢♡♢♢ Habib ya isa Suleja sai dai jikin Hajiya ba dad'i sosai kusa da ita ya zauna, ya kalli Kawo yace mu wuce Abuja kawai kawo a kaita asibiti, kaga Abba da Dad duk suna can, Kawo yace haka ne wannan ma shawara ce. Hajiya ya kalla ya rik'e hannunta, jiyai itama ta kama hannunsa da karfinta tace " Isma'il bakasan mahaifin yarinyar nan ba kai kanka, taya za'ayi ka nemi had'a zuri'ata da jinin da bamu sani ba." Idanu Habib ya zare da jin kalamanta ya kalli Kawo a zabure me Hajiya take fad'a? Da sauri kawo ya d'an matsar dashi ya zauna kusa da Hajiya yace " Amina kalle ni nam ba Isma'il bani Habibu ne me kike fad'a haka?" Jikin Habib ne yafara rawa ya mik'e tsaye a rud'e yace " Kawo me take nufi da kalamanta?" Kawo ya kalleshi cikin tsoron furucin da Hajiya tai, yanzu me za'a ce? © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 3⃣9⃣ Habib ya matsa kusa da kawo ya tsugunna agabansa idanunsa sunyi jaaa yace " kawo meke faruwa wai? Nine babban d'a agun mahaifina meyasa zaku d'inga b'oyemin abu? Gaba d'aya kun birkita min lissafi ance ba mahaifiyarmu d'aya da seemah ba? Dad yazo yace wai Ammar ba d'ansa bane, yanzu kuma Hajiya tana maganar ba'asan mahaifinta ba, in maganar mace takeyi da Seemah kenan take, gaba d'aya na kasa fahimtar abinda ke faruwa." Kawo yai kasa dakai yace " Habibullah maganar da ake b'oyema........" Amman da Hajiya ta shiga kwarawa ne yasa maganar ta tsaya, gaba d'ayansu suka mik'e suka nufi gun, hajiya amai takeyi sai dai da alama ba komai a cikin ganin yanda take kak'aro aman, Habib da sauri ya d'agowa yace kawo tayani mu kaita mota, nan suka d'auketa d'an ta galabaita sukai mota da ita, kawo ya zuba musu kaya a jaka suka ja gida suka rufe suka shiga mota. A hanya ba wanda yai magana d'an Hajiya numfashi kawai take saki. Dad kuwa harya kusa fita daga birnin/gwari wata magana ta Hajiya datamai randa yaje ta fad'o mai, lokacin har yaje fita daga gidan yaji muryar ta tace " Isma'il kasan ma mahaifin yarinyar ne? Itadai bazata tab'a yarda da yarinyar da ba'asan mahaifinta ba." Tunano kalaman ne da Dad yai yasa ya kalli drivern sa yace mukoma inda muka fito nayi mantuwa. Nan driver ya juya da kan mota suka koma, Dad sai tunanin abinda yafaru a baya yakeyi, bai tab'a tunanin zai had'u da Amadu ba, abinda yafi d'aure masa kai wai Jalal d'in da Seemah takeso d'ansa ne. Ya zarfafa cikin tunani bai san ma harsun iso ba, sai da driver d'in yace " Alhaji mun iso. " lungun gidan Dad ya kalla ransa na kara tunzura d'an bakin ciki, haka ya daure ya fito daga mota ya nufi gidan. Abba kam tun bayan tafiya Dad ya zauna a waje shi da umma sai dai ba wanda ya iya yima wani magana a cikinsu, sai can Umma ta daure tace " Malam ne dana mahaifin yarinyar da Jalal keso?" Abba ya had'iyi wani abun bai iya ce mata komai ba, tacigaba " mun shiga uku malam yanzu in Jalal yasan..........wani kallo da Abba ya buga mata ne yasa tai shiru, sai dai abinda ke zuciyoyinsu na da yawa. Jin an kwankwasa kofa ne yasa Umma ta d'aure ta mik'e ta nufi kofar, ta bud'e ganin mutumin dake tsaye ne yasa ta fara ja da baya da baya, tare da cewa Malam? Abba dake zauna ya taso tare da cewa "ke kuma menene inaji da......" ganin Dad ne yasa shi yin shiru, Dad ya makamai wani mugun kallo yace " inasan ganinka." Yana fad'ar haka ya juya. Abba ya kalli Umma itama cikin tsoro tace " Malam mun shiga uku." Takalmansa ya d'auko ya fita sai dai kana ganinsa kasan ta maza kawai yakeyi anma a tsorace yake. A d'an gaba da gidansa yaga Dad ya karasa gunsa, yace " Isma'il gani." Juyowa Dad yai ya kalleshi cikin d'aure fuska yace " tambaya ta karshe nazo in maka, daga wannan in har ka sake min karya wlh kaji na rantsema wannan karan ba kamar da bane dazan kyaleka, wlh sai nasa an d'aureka." Abba ya kalleshi a tsorace, Dad yace " Wayama Fatima fyad'e?" Gaban Abba ne ya fad'i ya kalli Dad sannan ya had'iyi yawo bakinsa na rawa yace "Malam Isma'il!" Dad ya d'agamai hannu yace ba abinda nazo ji kenan ba, ka fad'amin abinda na tambayeka ko kuma wlh zakasha mamaki. Abba yace " Malam Isma'il alokacin wlh ba asan raina......" Dariya sosai Dad yai sai dai kana gani kasan ta tsabar bakin ciki ne, yace " Amadu kenan, karka sake tunanin zan yanda da kalamanka, kalma d'aya nakesan ji daga gareka, waye ya k'etama Fatima mutuncin ta?" Abba ya kalleshi idanu a zare, Dad ya karkatar da kai yace " Don't tell me kaine?" Da sauri Abba yace " Me kake fad'a? Ni kuma? Akan me? Kaima kasan ba hali na bane." Dad yai murmushi yace "a shekaru masu yawa kenan nai tunanin ba halinka bane amma daga baya na gane babu babban munafikin dana tab'a gani irinka, sannan dama na sanar dakai wannan shine tambaya dazan maka ta karshe, yanzu sai ka jira d'anka d'an inaji shi kad'aine zai iya jin amsarka." Dad nakainan ya juya ya tafi, Abba ya rikice, sai dai kafin ya dawo hayyacinsa Dad har yayi gaba. Da sauri ya koma gida ya tadda Umma a tsaye tana jeka ka dawo, tana ganinshi ta rike hannayensa tace " ya kukai?" Abba yace " ya tafi yace Jalal zai fad'ama." Zubewa Umma tai a kasa jin haka tace " Malam meke damunka? Kataba tunanin in Jalal yaji maganar nan abinda zai yi?" Ta mik'e tace "Ko dai nima kana b'oyemin wani abu ne? Indai har abinda ka fad'amin shine gaskiya meyasa bazaka fad'ama Malam Isma'il ba? Karka manta abinda ya faru da shi da iyalinsa saboda kalma d'aya daka furta." Abba ya kasa magana sai zufa kawai yakeyi, ya kalleta yace " Ban b'oye miki komai ba, kema kinsan haka." Yana kainan yai waje da Sauri.... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣0⃣ Zainab kam tunda ta shiga d'aki hankalinta ya kasa kwanciya, ba shakka wannan wulakancin da aka ma Abba ya k'ona mata rai, bata fiya fishi ba haka take sai dai in ranta ya b'aci bata ganin komai, wayarta ta d'auko ta danna number Jalal, ringing uku Jalal ya d'aga tare da sallama ta amsa sannan tace " Yaya dama akwai lokacin da zaizo har ka fifita soyayya akan iyayenka?" Cikin b'acin rai Jalal yace " ke Zainab meke damunki? Ni kike fad'ama wannan banzan zancen?" Zainab rai b'ace tace " meye ma bazan fad'ama ba yaya? Akwai abinda yafi b'acin rai irin a wulakanta iyaye? Mahaifinta Har da shake ma Abba wuya? Sannan kai kuma anjima kazo kace kana santa ko me?" Jalal ya mik'e tsaye idanunsa suka kad'a sukai jaaa, cikin fad'a yace " me kika ce?" Shiru tai bata amsa ba, tsawa ya daka mata yace "ME KIKA CE?" Nan tai ajiyar zuciya ta shiga fad'amai abinda akai a gabanta, cilli naga yayi da wayarsa kan gadon Sagir, dama Sagir baya nan, wani hucci ya shiga saki ni kaina sai dana tsorata alk'alamin dake hannuna sai daya fad'i, tun yana karami ko a wasa bayasan irin zagin nan na yarinta da ake, d'an shi ko kad'an baya san a zagi iyayensa, bari har me?? Shakemai wuya?. A zuciye naga ya fito daga d'akin ai da gudu nai gaba nikam kar a huce akaina..... Ammar kam tunda Jalal ya tafi yake faman lallab'a Seemah sai dai dakyar ya samu tai bacci, sai dai kamar wata yarinya tana bacci tana ajiyar zuciya, Ammar dake tsugunne saitin fuskarta ya saki murmushin ganin yanda take ajiyar zuciya, a hankali naga fuskarsa ta koma ta damuwa, ya matso da fuskarsa saitinta ya kwantar, ya k'ura mata ido, a hankali ya furta " Seemah wani irin so nake miki? Na jini ne? Ko kuwa na 'yan uwa ne?" Ko kuma soyayya ce ta d'a namiji?" Shiru yai kawai yana kallanta can baisan sanda zuciya ta d'aukeshi ba, a hankali yakai bakinsa kan kuncinta ya sumbata, motsin datai ne yasa ya mik'e tsaye da sauri tare da sa hannu a bakinsa, jiyai d'akin yamai zafi duk da A.C da kuma sanyin da akeyi, bakin window yaje ya tsaya yana firfita da hannunsa. ♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧ Habib kam suna isowa Abuja yai asibiti da Hajiya, suna shiga akai emergency da ita dan gaba d'aya bata hayyacinta, kawo duk ya rikice hakama Habib, dakyar Habib ya lalubo wayarsa ya k'ira Abbansu Zaid sannan ya k'ira Dad, Dad dake hanya jin mahaifiyarsa ba lafiya yasa ya rikice, ya kalli driver yace kara gudu hajiyata ba lafiya, nan ya amsa da to tare da kara gudu. Habib na kashe wa ya k'ira Ammar, Ammar yana kallan wayar sai data kusa katsewa ya d'aga ba tare dayace komai ba, Habib yace" Ammar kazo Asibiti Hajiya ba lafiya." Da karfi Ammar yace " me ya sami Hajiyar?" Seemah dake bacci ta bud'e ido, tana kallan Ammar, Habib ya cigaba " bansani ba nima Ammar gata dai a emergency tana jin jiki." Ammar yace " *Inalilahi wa ina ilaihi raji'un* bari muzu yanzu." Yana kainan ya katse. Juyowa yai ya kalli Seemah dake zaune akan gado, ta kalleshi tace "yaya me ya sami Hajiyar?" Kai ya girgiza alamar a'a yace "Seemah bansani ba ki tashi dai muje." Da sauri ta sauko ta gyara d'ankwalinta ta yafa mayafi suka fita. A asibiti kuwa Likitoci sundai yi nasu k'okarin sai dai su kansu sunsan inaaaa, ganin dai ta dawo hayyacinta yasa aka bata d'aki, kawo ya zauna kusa da ita, ya rik'e mata hannu, yace " Sannu Hajiya!! Bakiji yanda naji ba nad'auka kema mutuwa zakiyi ki barni kamar yanda sauran matan nawa sukai." Hajiya tai murmushin karfin hali tace " Isma'il fa?" Kawo yace " yana hanya." Habib ne ya shigo shi dasu Abba da mami, da sauri Abba ya karasa kusa da ita, yace " Hajiya?" Ta kakaro murmushi tai tace " D'an nan kaima tasoka akai?" Sannu hajiya abinda ya fad'a kenan, ta d'aga kai sannan ta kalli Mami dake mata sannu, tace yauwa Allah ya muku albarka, sukace Amin. Abba ta kalla zatai magana sallamar su Ammar ta katseta, suka shigo shi da Seemah, Ammar ya kalleta duk ta rame yace " matata ya banje gaidake ba sai in ganki akan gadon asibiti?" Tace " yaushe ka shigo?" Murmushi yai sannan ya gaida kawo dasu Abba, Seemah ma ahankali ta gaidasu, sai dai mami ce kawai ta amsa, Ammar ya kalli Abba da kawo yace" wooo yanzu kanwar tawa mai tsada tana gaidaku shine kukai shiru?" Kawo ya kalleshi yace " Ammar kana nan dai yanda kake." Hajiya kam tunda Seemah tai gaisuwa ta kafe ta da ido, Abba ganin haka yana tsoron kar ciwonta ya tashi yasa yace " Seemah d'an fita waje, Habib dake tsaye ya kallesu, ba shakka matsalar daga Seemah ne ba Ammar ba. Seemah ta d'ago ta kalli Abba, tsawa ya daka mata yace "bakiji me nace ba," Duk ta rikice tama rasa hanyar fita, Ammar ne ya jawota jikinsa yace " me kakeyi hakan Abba? Yaza'ai yarinya tazo gaida kakarta ka nemi korarta?" Abba yace " Ammar ina wasa dakai ne?" Ammar yai ajiyar zuciya yace " yahkuri in na b'atama rai Abba sai dai ba inda Kanwata zataje inkuma anaso ta fita to sai dai ku fita tare." Yana kainan ya jata sukai waje. Seemah duk ta rikice kawai hawaye takeyi. Jalal kam a sukwane yaje gidansu Habib sai dai mai gadi ya sanar dashi yanzun nan motar Farida ta fita suna asibiti, hakan yasa da sauri yasa mai machine d'in yabi bayan motar. Sun isa asibitin, Farida ta fito da sauri tai ciki, shima ya bita, a harabar gun ya kallo, wata kamar Seemah, hakan yasa ya tsaya yana kallanta, Seemah kam hannun Ammar ta rike kam dan jikinta duk rawa yake, ganin haka yasa Ammar ya jawota jikinta ya rungume, Jalal dake tsaye yaji ransa yayi mugun b'aci, karasa wa yai inda suke Ammar ya d'ago ganin kafar mutum ya kalleshi, da mamaki yace " Jalal? Me kake anan?" Seemah najin sunan tai saurin d'agowa ta kalleshi. Idanunsa sun kad'a sunyi jaa dama ga bakin cikin abinda aka mai ga kuma wani sabon salo, babban yaya namiji ya kama rungume kanwarsa, Seemah ta kalleshi da idanunta dake hawaye tace " My Deen?" Kallanta yai yace " Meemah me kike anan?" Ta kalli Ammar sannan ta kalli Jalal, Ammar yace " kai ya kamata kabada wannan amsar, mu tinda ka ganmu anan ai akwai dalili, Jalal yace " Dad nake nema." Ammar ya jinjina kai sannan yace " tunda Dad kake nema bayanan." sannan ya kama hannun Seemah zai koma cikin asibitin da ita, da sauri Jalak ya kamo d'ayan hannunta, ta juyo ta kalli Jalal ta lumshe idanunta, Jalal ya sakar mata murmushi sannan ya kalli Ammar yace " sry yayan Seemah inasan magana da ita." Wani kishi ne ya kama Ammar ya bugamai wani kallo, Jalal mamaki ya kamashi, ba shakka wannan kallan ba kallan yaya bayasan shi bane kallan kishi ne, amma......Ammar ne ya katseshi da cewa " ka manta me ka mata?" Jalal da sauri ya kalli Seemah, meya mata? Nan Seemah ta tuno kalaman Zainab, a hankali tai fara baya, tana kokarin zare hannunta, jisukai ance " *Me kukeyin hakan?* Da sauri suka juya dukansu, Dad ne a tsaye rai a b'ace. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣1⃣ Dad yana karasowa gun ya kalli Ammar wanda ya kauda kai, yace " me kakayi anan bayan a ciki ya kamata in ganku?" Seemah ta matso kusa da Dad tace " Dad ni na fito dashi, kayi hakuri." Ammar ya kalleta yace " Dad taya za'ayi ace Abba ya kore Seemah daga ciki? Ban fahimci me hakan yake nufi ba." Da sauri Seemah tace " Dad ba wani abun bane, Ya Ammar kaya ya d'au abin da zafi ne." Jikin Dad yai sanyi ya kalli Seemah cikin tausayinu sannan ya maida idansa kan Jalal harzai mai magana ya fasa ya juya tare da cewa Seemah muje ciki, itakam idanunta nakan Jalal shikansa kallanta yakeyi, kallan juna suke cikin wani yanayi, Ammar ya kalli yanda Seemah ke kallan Jalal jiyai ransa ya sosu, Dad ya juyo ganin Seemah batada alamar tahowa, Dad a harzuk'e yace " Seemah wuce nace ko?" Dasauri tace " to dad." Tana juyawa Jalal yace " Dad inada magana." Dad ya juyo ya bugamai wani kallo, ba shakka Jalal yananan kamar yanda yasanshi, sai dai yasan dabadan abinda ya faru ba yasan da amintarsu da Ammar bazata rabu ba. Had'e rai yace " Jalaludeen sunan ka ko?" Jalal ya d'aga kai yace " Eh, amma ban fahimci menene dalilin dayasa kaje har gidanmu kacima mahaifina mutunci ba." Dad yace " me kace?" Ammar ya matso yace " kai gyara bakinka wani shirman kake fad'a?" Seemah ta kalli Jalal sannan ta kalli Dad tace "Dad kaje gidansu ne?" Dad dake kallan Jalal yace " ka koma ka tambayi mahaifinka abinda ke faruwa bawai kazo nan kanamin shirme ba." Jalal ya kalli Dad yace " Na d'auka maganar ni da Seemah a tsakanin mu zai tsaya amma yaza'ayi kamar kai kaje har ka shake mahaifina? Me yayi?" Dad yai d'an wani murmushi a ransa yace " Jalal kenan bai mantashi ba halayensa nanan, tun yana karami baya shakkar tambaya." A fili yace " bakaji amsata bane? Nace ka koma ka tambayi mahaifinka wanda a fili za'a d'auka mutumin arzik'i ne amma a zuciya" ya jijiga kai...... Ran Jalal yakai matuka gun tunzura, Seemah ta kalli Jalal ganin yanda idanunsa sukai yasa jikinta yai sanyi, Kallansa tai idanunta sun cika da kwalla, Jalal ya kalli Dad yace " ban fahimci kalamanka ba? Kasan mahaifi nane? Ko kuwa a ganinsa dakai yau shine yasa kake fad'ar haka?" Dad ya kalleshi yace " indeed you are smart tunda har kai tunanin haka, sai ka koma ka tambayi Amadu ko ya sanni." Amadu? Jalal ya maimaita, ba shakka wanda yasan Abba ne yake fad'a masa haka, to amma ta ya? Dad ya kalli Ammar dake jin kalamansu cike da mamaki yace " Ammar muje ko? Ina bukatar ganin Hajiyata." Bai jira abinda Jalal zai fad'a ba yai gaba, Ammar ya bishi a baya, Seemah ta kalleshi tace " Deen meke faruwa?" Kallanta yai idanunsa a kad'e yace " Meemah I don't know, ni dai kawai ancemin Dad d'inki yaje gida har shakema Abbana wuya yayi, shiyasa nazo inji, to amma yanzu I am confused, ya akai Dad yasan Abba?" Seemah ta kalleshi jiki a sanyaye, tace " Deen nasan Dad d'ina kwarai, duk da nasan bayasan alakarmu hakan bazai sa ya shakema Abba wuya ba, akwai dai wani abun." Jalal ya d'ago ya kalleta jiki a sanyaye ya jinjina kai yace " karki damu kije gun mara lafiyar." Yana kai nan ya juya, har yad'anyi nisa tace " Deen?" Tsayawa yai tare da juyowa ya kalleta ta matso kusa dashi kad'an tace " Can you promise me something? " kai yad'an langwab'ar tacigaba " can you promise me you will always love me?" Wani sansanyar murmushi ya sakar mata ya lumshe ido sannan yace " u are my first love how can I stop loving you? " Itama murmushi tai tace " yazanyi ind'ingajin muryarka bani da waya?" Wayarshi ya mik'a mata tare da zare layinsa dayake amfani dashi yabar Etisalat d'in da ba wanda yasanshi dashi dama saboda browsing yake amfani dashi. Ta kalleshi sannan ta kalli wayar tace ta meye? Yace kiyi using wannan ni nasai wata. Murmushi tai harsai da fararan hak'oranta suka fito tace " karka damu nasan yanda zanyi inada idea." Yad'an harareta kad'an yace a hakan? Tace zaka gani. Tana kainan ta juya ta fara tafiya, tsayawa yai kawai yana kallanta zuciyarshi tayi wani sanyi....... Dad kam yana shiga Abba yace " Isma'il tund'azu ina ka tsaya Hajiya na nemanka?" Da sauri Dad ya matsa gunta, ya rik'e hannayenta, tana ganinshi ta rike hannunsa itama tace " Isma'il nasani ka ga rayuwa, kaga tashin hankali duk da dai muma mun gani a shekara 20 data wuce, sai dai abinda ka gani bai kai namu ba." Dad ya kalleta sam yamanta da Habib da Ammar agun d'an hankalinshi nakan mahaifiyarsa, Hajiya ta cigaba" nasani haryanzu bakamanta azal d'in daya fad'a maka ba, 'yan gari sun tsaneka saboda abinda bakai kayi ba, matarka mahaifiyar 'ya'yanka wannan abin shine ajalinta, wannan dalilin yarabaka da kasarka muma dole ne yasa mukabar garin." Tai ajiyar zuciya tare da share hawayen dake zubo mata, ba itaba hatta mamie da Dad hawaye suke, Ammar kam da Habib kallansu kawai suke mamakin kalaman nan suke. Hajiya tasa hannu ta share mai hawayensa tace " kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il ka rik'e yarinyar nan amana....." Kawo ya kalleta yace " ya isa Karki kara tada ma kanki hankali ki kuma k'ara tadama d'anki." Kallan Isma'il tai zatai magana numfashinta ya fara yankewa Dad ya rik'ece yace " a yi sauri ka k'ira Likita." Duk ya rikice Habib yai saurin fita, Yana bud'e kofa yana fita, yaga Seemah tsugunne a waje, bai kulata ba yai sauri yai gaba. Ammar kam gaba d'aya kwakwalwarsa ta rufe, meke faruwa? Me kalaman Hajiya ke nufi? Wa aka rike? A iya saninsa 'yar Dad mace d'ayace Seemah to mekenan? © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* _This page is for you my Yar uwas, my cwty my chocolates, much luv to you😍 Maijiddah_ ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣2⃣ Seemah kam gaba d'aya kanta taji yana wainawa, bata fahimci inda maganar ta dosa ba saboda ta baro gun Jalal tazo zata shiga ta tuna d'azu ance ta fita, hakan yasa ta jingina da kofar sai dai adaidai lokacin taji Hajiya tace " Kuma duk abinda ya faru dakai Isma'il kuma ka rike yarinyar nan Amana." A iya saninta mahaifinta ne Isma'il to wace yarinya ya rik'e amana? Dawowar Habib da likita ne yasa itama ta mik'e ta wuceta sukai da sauri, tabishu da kallo tare da tsayawa a bakin kofar, Duk 'yan d'akin sun rikice ganin yanda jikin Hajiya ya tashi sosai, sai dai har yanzu hannunta kankame yake dana Dad, likita na zuwa suka shiga kok'arin daidaita numfashinta, sun wahala sosai ganin jikin ba dad'e yasa sukace kowa ya fita ya barsu, nan Dad suka fito kowa jikinshi a sanyaye, idanun kowa ka kalla kasan suna cikin tsananin tashin hankali, Dad na fitowa yaga Seemah a tsaya tana hawaye ganin yanda jikin hajiya yake, hannun ta ya kama sukai waje. Nan aka rufe kofar, kowa yayi jugum yana addu'oi, sai da likitocin sukai minti 30 kafin su fito, suna share zufa, Abba da Dad da kawo suna ganinsu suka matsa kusa dasu, Abba yace " ya jikin nata?" Likitan yace " kushiga sai dai kuyi a hankali karku kuskura kuyi abinda zai tada mata hankali ko taga abinda bataso, yin hakan babbar matsala ce, sannan kar ad'inga hayaniya a kusa da ita. Suna kai nan sukai gaba, Habib ya matso kusa yace " Abba ya kamata ku koma gida, munyi yawa a asibitin gudun hayaniya ya kamata ka d'auki Mami da kawo ku koma gida, shima Ammar ya d'au Seemah su tafi inyaso ni zan zauna anan." Abba yace " haka ne amma sai dai zuciyata bazata iya kwanciya ba in na tafi." Kawo yace " nima kunsan bazan iya zuwa wani gun ba inbar matata anan ba." Sunyi shiru kafin Dad yace " mu zauna anan ai mu ba maganar da zamuyi, kai Habib ku koma gida." Habib ya kalli Dad yanasan yai musu anma yana tsoro, Dad ya kalli Kawo yace "kawo kaima kaje gidan yaya kai wanka kaci abinci inyaso da daddare sai ka dawo." Haka suka yanke shawara Dad da Abba suka shiga ciki, Habib ya kalli Ammar yace " Ammar ka d'au mami da kawo gida." Mami ta kalli Seemah itakam kasan ranta tana tausayin yarinyar tace " Mu wuce da Seemah ma kwana acan, sai ta kwana gun Zara." Seemah ta kalleta jiki a sanyayi, Mami ta d'aga mata kai tare da mata murmushi, Ammar ya kalli Seemah sannan yace "muje kawo." Sun fita Habib yabi bayansu da kallo, bayaji zai bar asibitin nan, juyawa yai ya shiga ciki, Dad da Abba na zaune jugum-jugum. Ya koma gefe ya zauna. Jalal kam yana fita daga asibitin ya shiga k'iran wayar Abba, sai dai bai d'aga ba, hankalinsa ya tashi ya rasa me ma zaiyi ga shi gobe monday yanada aiki bare ya tafi birnin/gwari yanzu, ga yamma tayi. Haka ya cigaba da gwada number Abba sai can harya cire rai sannan yaji an d'aga, da sauri yace " Abba?" Jiyai ance " waye?" Da mamaki Jalal yace " ba number Abba bane?" Mutumin yace " wlh bamusan wayar waye ba d'azu muka ganta a shagon nan k'ila wani ne ya mantata." Jalal yace " ina ne nan d'in?" Mutumin yace " gurin buga kati ne." Gaban Jalal ya fad'i wato da gaske Abba yake? Ya d'aure yace " ku ajiye wayar zan k'ira azo a amsa." Nan sukai sallama, Jalal ya k'ira number Umma, sai data kusa katsewa ta d'aga tare da Sallama, Jalal ya amsa tare da cewa " Umma d'am Allah Abba fa?" Tace " ya fita yanzun nan yamanta wayarshi a shagone shine yakesan yaje ya duba." Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Umma d'an Allah kinsan wani Alhaji Isma'il?" Yai tambayar cikin sanyin murya. Umma kam gabanta ne yashiga dukan uku-uku, tace " Jalal anya kuwa?" Yad'an jinjina kai sannan yace " maybe ke baki sanshi ba amma ba shakka Abba yasanshi, bakomai bari in kara neman Abba." Dasauri Umma tace " Jalal ba ruwanka, karka kuskura ka tambayi mahaifinka Malam Isma'il." Da mamakin kalamanta Jalal yace " Malam isma'il? Da alama kema kinsanshi kenan, d'an nidai a sanina Alhaji nace ba malam ba, kuma daga yanda kika fad'i sunan Umma ya nuna kinsanshi." Umma ta had'iyi yawo tace " Jalal ka rufamana asiri d'an Allah kabar yarinyar nan, in a da ina tunanin zai iya yiwuwa ka aureta sai dai yanzu......" Tana zuwa nan tai shiru idanunta suka zubo da kwalla, ganin tana alamar kuka yasa ta katse wayar tare da zana a gun, tace a filin Jalal yazamuyi? Ya Allah gani gareka!! Abba ne ya shigo tare da kallanta yace " menene kuma?" Umma ta taso tazo kusa dashi tace " Malam ya zamuyi? Jalal fa yasan kasa Malam Isma'il." Abba sai da jikinsa ya amsa, ya kalli Umma kawai ya shige d'akinsa, yawo ya farayi a tsakar d'akin "Yasan Halin Jalal sosai, idan yaji abinda na aikata ta dalilinsa bana tunanin zai tab'a yafe ma kansa." Idanu ya runtse ya tuno laifin daya aikata saboda tsoron kar a tab'amai d'ansa, bai taba tunanin abinda ya aikata zaizo ya damesu a wannan lokacin ba, shi daga baya ma yafara tunanin ko rashin lafiya da zaheera ke fama dashi alhakin abinda ya faru ne, yasani sosai ya aikata lefi mai karfi anma ya zaiyi? Jalal kam wayarsa yabi da kallo mamaki kalaman Umma ne suka dameshi, lalai akwai wani abun a kasa kuma dole ne yasan menene wannan abun, tunani yafara gun Dad yakamata ya koma ko gun Abba? Ajiyar zuciya yai yace " Abba zaiyi wuya ya sanar dani, zan kara komawa gun Dad inji ko shi zai fad'amin." Da wannan shawarar ya shiga cikin d'akinsu. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣3⃣ Seemah kam tunda suka shiga mota ba wanda yai magana kowa da abinda ke damunsa, har suka isa gidan itadai Seemah kanta na kasa bayan sun isa mami da kawo suka fita Seemah ta kalli Ammar tace " yaya ni kad'ai zan kwana anan?" Murmushi ya mata yace " ke kad'ai ce anan d'in? Ga Zahra ga mami nan?" Tace " kasan bamu saba ba please ka shigo kaima saika kwana gun Ya Zaid inkananan sai hankalima yafi kwanciya." Yai shiru shidai sam bayasan kwana a gun Zaid saboda Zaid hana shi bacci yakeyi ya d'inga mai surutu kenan sannan in 12 tayi kuma sai ya shiga waya da 'yan mata sam ya hanashi bacci, amma ya zaiyi? Bazai bari Seemah ta takura ba. Seemah ta kalleshi jin shirun yayi yawa tace " Yaya na!!!!" Ya kalleta yace " to kanwata muje ko?" Wani dad'i ne ya kamata sannan ta bud'e motar ta fito. Tare suka shiga Falon, Zara na tsaye a bakin window dama tunda mami tace da Ammar sukazo take lek'ensa, ganin ya fito yasa ta kara gyara fuskarta ta tsaya a bakin kofa. Suna kwankwasa wa ta bud'e tare da wayancewa tace " Seemah na d'auka sai nazo na d'aukoki da kaina." Seemah tad'anyi yake tace " Zara ya kike?" Lafiya ta fad'a sannan ta kalli Ammar tace " laaaa Ya Ammar ai ban kula da kaiba." Hararar wasa ya mata yace " anya kuwa kanwata? Bayan naga haske d'azu ta mota kamar da mutum a tsaye ta labule yana lek'e?" Idanu ta rufe tace " kai yata bansan waye yake lek'e va." Dariya Ammar yai yace gaskiya kam da alama ku 2 ne a falon. Ta turo baki tace " yaya ai ko ka sani sai ka basar haka fa akeyi." Seemah tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsunta, Ammar baiba Zahra amsa ba yace " kanwata kuje ciki kiyi sallah nima bari nai sai in dawo muyi hira ko?" Kai Seemah ta d'aga alamar eh, Ammar ya kalli Zahra yace " Zara a kuma kularmin da kanwata." Bai jira amsartaba yai waje, Zahra tabi bayanshi da kallo tana Murmushi sai daya fita sannan ta kalli Seemah tace " muje ciki." bata amsa ba kawai itama ta fara binta sun shiga d'aki Zahra ta nuna mata toilet, Seemah ta wuce ta shiga. Tsaye tai a toilet tana kallan kanta a madubi, itakad'ai tasan me takeji a zuciyarta, Deen zai yi aure? Ta maimaita kalaman Zainab data mata a waya, hawayene ya ziraro mata ga mamakinta jitai kuka ya b'arke mata sosai, tsugunnawa tai kawai tana kuka. Zahra dake d'aki ta na jiyuta matsowa tai jikin toilet d'in tace " Seemah menene?" Kuka sosai takeyi Zahra mamaki ya kamata ta dad'e tana bugawa amma bata bud'e ba, Seemah kam ta dad'e tana kuka kafin ta daina, ita dana saninta d'aya dama batazo kasar ba kwata kwata da bata had'u da Jalal ba bare har sanshi ya kamata haka. Alwala tai ta fito, Zahra ta kalleta tace "Seemah menene?" Jijiga mata kai kawai tai alamar a'a ta wuce ta d'au sallaya. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆ A asibiti kuwa Hajiya ta samu bacci mai karfi saboda allurar da aka mata, da daddare Habib da saninshi ya kwanta yai lamo kamar bai bacci, Abba ganin kamar Habib yayi bacci ya kalli Dad yace " Isma'il inada magana da kai." Dad ya kallleshi yace " inaji." Abba yaja numfashi sannan yace " Isma'il tambayar dai dana maka shekara ashirin da suka wuce ita nakesan in sake maka, Isma'il tsakaninka da Allah bakasan mahaifin Seemah ba?" Dad ya kalli Habib ganin da alama bacci yake yace " yaya wlh wlh bansan komai akai ba, sau nawa kakesan in rantsema." Ajiyar zuciya yai sannan yace "yaya kasan wa nagani yau?" Abba ya girgiza kai, Dad yace " Amadu nagani." Mik'ewa Abba yai yace " dafatan kasa an rufe mana shi?" Dad yai tsaki yace " ai ni abinda nagani yasa ma nakasa mai abinda ya kamata, kasan mahaifin waye?" Abba ya girgiza kai, Dad yace " wai mahaifin Jalal d'in da Seemah keso ne." Da mamaki Abba ya koma ya zauna yace " mene? JALAL? Taya hakan zata faru?" Dad ya runtse ido yace " kabari kawai Yaya abin ya d'auremin kai, ko ya akai Jalal har yazo company d'in mu yana aiki har suka had'u da Seemah? Har hakan ta faru?" Abba yace " Ikon Allah kenan, amma ai yanzu komai yazo gidan sauki, shi kansa Amadun ai ko kace ga Seemah ka bashi bazai aminta ba." Dad ya kalli Hajiya bai kara magana ba. Habib kam ya gama daskarewa agun da yake, meke faruwa? Ba Dad bane mahaifin Seemah kenan, sannan me? Bai masan mahaifin Seemah d'in ba? Meke faruwa kenan? Sannan mahaifin Jalal mene?" Inaaaaa ai ko mai zai faru dole ne gobe a bashi amsoshin tambayoyinsa d'an kuwa shine babban d'a kuma dolene yasan sirrin gidan su, bazai kara bari a sashi a cikin tunani haka ba. Jalal kam kwata kwata idanunsa basuga bacci ba zuciyarshi cike take da tunanuka kala kala, me ake nufi da Abba yasan Dad? Fitowa yai daga d'akinsu bai damu da daren dayai ba a waje ya zauna yai shiru yanaso zuciyarsa ta bashi amsar tambayoyinsa sai dai sam ya kasa lissafo komai abu d'aya dai daya tabbatar ma ransa shine, tabbas Dad yasan Abba kuma alak'ar dake tsakaninsu ba wai alak'ace ta mutunci ba, yazaiyi da auransa da ake shirin yi ranar asabar? B'angaren Seemeh kuwa tana zaune a falo kusa da Ammar, Zahra nata jansa da hira, itakam Seemah a zaune kawai take ba ta sa musu baki ba, can Ammar shirun Seemah yafara damunsa ya kalleta yace " Kanwata menene?" Kallansa tai batace komai ba, Zahra cikin zolaya tace " ba dai kuka zaki sake mana ba ko?" Seemah ta kalleta kawai tai kasa da kanta, Ammar jin haka yasa ya kalli Seemah yace " kanwata kuka ki kai?" Shiru tai hakan yasa Ammar yagane matsalar, Zahra ya kalla yace " Zahra d'an bamu guri muyi magana please. " Zahra ta kallesu sannan ta mik'e jiki a sanyaye ta fita, Ammar ya kara matsowa kusa da Seemah yace " Kanwata menene?" Idanunta ne sukai rau rau tace "yaya kaima kasani ai." Goshinsa ya rik'e yace "oh God Seemah akan Jalal ne?" Kallansa tai cikin kalar tausayawa tace " yaya dama banzo kasar nan ba." Murmushi yai yace " Seemah kenan." Ta kalleshi tace " Yaya inasan intambayeka wani abu, d'azu naje shiga d'aki naji ana zancen Dad duk abinda suka mai wai kuma ya rik'e yarinyar amana." Tai ajiyar zuciya tace " Yaya ban gane kalaman me suke nufi ba." Ammar yai shiru can yace " Seemah ni kaina ban fahimci inda kalaman nan suka dosa ba, a farko na d'auka da ni suke to amma daga baya na gane ba ni bane, to amma me kalaman suke nufi?" Ta jinjina kai tace " mu tambayi Dad gobe sai muji ko?" Kai ya d'aga alamar eh ... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣4⃣ A daren ranar Jalal da Habib idanunsu basuga bacci ba. Washegari ya kama litinin, Habib zaune a d'akin da Hajiya take kallan Abba da Dad kawai yake yana tsananin mamakin yanda suka iya b'oye wannan sirrin batare da sun sanar ba, bayan ya gaidasu ya koma gun Hajiya ya zauna ya kalli Dad yace " Dad bari naje gida in dawo sai kuma kuje." Abba yace to in kaje daga nan ka biya tagurin Mamie ka amso min sak'ona, Habib yace "to" sannan ya mik'e ya fita. Agoggon Hannunsa ya duba karfe 7 na safe kenan, gida ya wuce yai wanka ya sa kaya sannan ya fito, gidan su Zaid ya wuce. Bayan ya isa a bakin gate yaga Ammar, nan suka gaisa sannan Ammar ya tambayeshi jikin Hajiya, Habib yace " Da sauki, sai dai inasan magana da kai." Ammar ya kalleshi da mamaki yace " akan me fa?" Habib ya dafa kafad'ar sa yace " inaso ne kazo kuje gurin Mamie ina tunanin a wannan lokacin ita kad'ai ce zata warware mana abinda ke faruwa." Ammar ya jinjina kai yace " ni kaina ban fahimci kalaman da Dad da Hajiya sukai jiya ba kuma da alama mu 2 ne kawai bamu san me suke nufi ba a d'akin." Habib yai shiru can yace " Nagano maganar akan Seemah ne duk da bansan gaskiyar abinda ke faruwa ba." Gaban Ammar ne ya fad'i ya kalli Habib yace " amma yaya........" Habib ya katseshi yace karka damu mud'ai je ciki tukunna. Nan suka shiga cikin gida, Zahra suka gani tana goge goge tana ganin Ammar ta mik'e tare da gaidasu, Habib yace " Zahra ina Mamie?" Ta amsa da "tana d'aki." Basu kara mata magana ba sukai hanyar d'akin mamie, sun isa suka kwankwasa, daga ciki Mamie tace su shigo, nan Habib ya murd'a kofar tare dayin sallama, Mamie ta amsa tare da mik'ewa ta rufe littafin Husnul Muslim d'in dake hannunta. Ta kallesu tace " Habib kai ne?" Habib ya shiga tare da zama a kasa kusa da inda take, Ammar ma ya zauna nan suka gaidata ta amsa fuska a sake tare da tambayar jikin Hajiya. Sunyi shiru kafin can Habib yace " Mamie jiya da daddare sam idanuna sun kasa runtsawa tunani kala-kala sai daga karshe zuciyata tabani amsar tambayoyina." Yai shiru bayan yazo daidai nan a kalamansa, Mamie ta kalleshi tace " ina jinka Habibu, mecece amsar?" Habib yai ajiyar zuciya ya d'ago ya kalli Mami. Daga d'aki kuwa Seemah ce ta fito daga toilet, tai saurin sa kaya ta fito a falo taga Zahra tace" Zahra ina ya Ammar? " Zahra tace " yanzu sukai d'akin Mamie shida Ya Habib." Murmushin farin ciki tayi tai hanyar d'akin da sauri fuskarta d'auke da murmushi tazo daidai zata kwankwasa kofar taji muryar Habib yace " Mamie da farko dai na gano abubuwa guda 2, na farko Seemah ba 'yar Dad bace, sannan abu na biyu babu alak'ar jini tsakanin Mu da Seemah wannan dalilin ne yasa Dad yake san had'ata aure da Ammar." Tunda Habib yafara magana Ammar yake kallansa idanunsa cike da tsananin mamaki, kallan Habib yai yace " Ya Habib meye hakan kake fad'a? Kasan me bakinka ke furtawa kuwa?" Habib ya d'ago ya kalli Ammar sannan ya maida dubansa ga Mamie data runtse ido ta sani tun jiya a asibiti dole ne zargin kalaman da Dad da Hajiya sukai ya bayyana. Habib ya kalli Ammar yace " Mamie dan Allah ki sanar damu abinda ke faruwa, wannan ne kad'ai hanyar dazai sa mu taimaki kanwarmu sannan shirin auren da Dad yake sai munsan dalili tukunna abin zaiyiwu d'an ni tun sanda Dad yace Ammar ba d'ansa bane sam zuciyata bata aminta ba." Seemah kam ta kame a tsaye silalewa tai ta zube akasa kamar abinda ba ya motsi haka ta koma. Mamie tai ajiyar zuciya ta kalli Habib tace "Habibu?" Habib ya kalleta yace " Mamie d'an Allah karku k'ara kokarin b'oye mana wani abu, d'an gaba d'aya na kasa fahimtar inda kuka dosa." Mamie tai shiru can tace " Ni kaina banasan wannan b'oye-boyen, sai dai ina tsoron yanda zaku d'au al'amarin." Ammar kam shi kansa ya kasa magana, kawai jinsu yake, Habib yace " Mamie babu wani yanda zamu d'auki al'amarin gaskiya kawai muke san ji." Mamie ta runtse ido sannan tai gyaran murya....... ♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢♢ Jalal kam har ya isa office ya zauna sai dai sam hankalinsa ya kasa nutauwa akan aikinsa mik'ewa yai da hanzari ya fito daga office d'in, asibitin da aka kwantar da Hajiya, inda suka had'u da Ammar ya tsaya jiya nan Jalal ya tsaya yana tunanin a ina zaiga Dad, cikin ikon Allah sai ga Dad da Abba sun fito daga wani d'aki da likita a kusa da su. Da hanzari Jalal ya karasa gun, likita na tafiya Jalal yace " Dad ina kwana?" Juyowa Dad da Abba sukai suka kalli Jalal, da mamaki Dad yace " Jalal kai kuma lafiya?" Jalal ya karasa kusa dasu tare da kara gaidasu, Dad da Abba suka amsa Dad ya kara cewa " Jalal lafiya?" Jalal ya d'ago ya kalli Dad yace " Dad kayi hakuri, sai dai hankalina ya kasa kwanciya, so nake naji mai mahaifina ya maka ka shak'e mai wuya? Naso in bar abin sai dai sam hankalina ya kasa kwanciya menene dalilin da zaisa kama mahaifina haka? Saboda inasan 'yarka ne ko me?" Dad ya kalleshi da mamakin Kallamansa yace " Banace kaje ka tambayi mahaifinka ba?" Jalal yace " haka ne haka kacemin sai dai a tunanina kai da ka mai hakan kai ya kamata in tambaya d'an zai iya yiwuwa shi baisan me ya maka ba." Ran Abba ya fara b'aci yanzu ya gano wannan shine d'an gidan Amadun cikin b'acin rai yace " kai bakaji kunyar zuwa ka tsaremu ka fara mana tambayar banza ba? Ko rashin kunya ce?" Jalal ya kalli Abba yad'anyi murmushi kad'an yace " ta ya za'ayi tambaya ta zama rashin kunya? Kamar yanda Mahaifina yake a guna haka Dad yake a gun Seemah, taya zan mai tambayar banza?" Yai ajiyar zuciya sannan yace " sai dai duk inda d'a na gari yake dolene yaji haushi in har aka cima mahaifinsa mutunci ko da kuwa mahaifin nasa d'an fashi ne." Dad ya kalleshi sam baya jin tsanar yaran zaiyi magana Abba yace " ka koma gun mahaifinka ga sako zan baka, kace masa yaci darajar Isma'il ne yaje gunsa ba ni bane da nine da wlh sai ya kwana a prison, ka kuma fad'ama mahaifinka sharrin dayama Kanina in ma laifin nasa ne ya rufe ko kuma akwai wani abu daya sashi yimai sharri, ko kuma so yake yaga kanina ya tozarta, to ka koma kasanar dashi matsayin Isma'il a wannan lokacin ka kuma sanar dashi a company d'in d'ansa kake aiki." Abba na kainan ya ja hannun Dad suka shiga d'akin suka rufo sukabar Jalal a daskare a tsaye, sai da yai ta maimaita kalaman da Abba ya fad'a a ransa kafin cikin tsananin b'acin rai ya juya ya fita. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _For you Maman Shaheed, I sincerely dedicated this page to you😍thanks alot, Allah ya raya mana su Shaheed amin_ No. 4⃣5⃣ Mamie ta ja numfashi tace " Habib bazan iya baku labarin abinda ya faru ba saboda ni kaina ban san kanun labaren gaba d'aya ba sai dai zan iya sanar daku abu guda biyu zuwa uku. Da farko dai kamar yanda ka fad'a tabbas Isma'il ba shine mahaifin Seemah ba. Sannan Mahaifiyarta wato Fatima fyad'e aka mata sai dai mu kanmu bamusan waye ba sai dai bayan an mata fyad'en mai shagon da akai fyad'en yace Dad ne ya mata. Wannan kalma d'aya daya furta yasa komai ya ruguje saboda alokacin saura kwana 2 a mata aure, alokacin wanda zai aureta ya fasa, Isma'il kuma 'yan gari suka tsaneshi har wuta aka sa a gidan Hajiya da kuma shagon da akai abin." Habib yace " mene?" Ammar kam hawaye ne kawai ke zuba daga idanunsa, me yake ji haka? Mamie ta kallesu tace " abinda na sani kenan, bayan abin nan ya faru Fatima ta fiskanci wulakanci ta kowani b'angare har cikinta ya kawo haihuwa tana haihuwa tace ga garinku nan." Habib ya mik'e tare da rik'e kansa, da sauri yai hanyar kofa ya bud'e yana bud'ewa yaji mutum ya biyo kofar, da sauri ya kalli kofar Seemah ya gani ta fad'i rim, jin karar fad'uwa yasa Ammar da mamie suka juya suma. Habib da sauri ya tsugunna, Ammar ya taso da gudu yazo kusa da ita ya shiga jijigata yana k'iran sunanta sai dai inaaa Seemah kam ta suma. Ammar ya kalli Habib idanunsa na hawaye yace " yaya kodai taji komai?" Kallan kallo sukai da Mamie, Mamie ta d'aure tace " akaita d'akin su Zahra." Nan Ammar ya d'agata cak yai d'akinsu Zahra da ita, ya kwantar da ita, Ammar ya tsugunna a kusa da ita a rik'o hannunta idanunsa na zubar da kwalla, fita Habib yai daga d'akin d'an duk da yanajin tausayin Seemah a ransa amma yanajin haushin abinda akama mahaifinsa akan ta ta mahaifiyar. Seemah kam ruwa Ammar ya shafa mata a fuska, hakan yasa ta bud'e idanunta tare da jan wani dogon numfashi, Ammar ya kalleta yace " Seemah!" a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ta kurawa Ammar ido, alokacin abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata. Da sauri ta fizge hannunta tana girgiza kai cikin kuka mai ban tausayi kawai Dad take k'ira, Ammar ganin haka yasa tausayinta yak'ara kamashi ya mik'e tare da fita falo, Dad ya k'ira. Daga can b'angaren Dad ya d'aga tare da cewa " Ammar ya akai?" Ammar yace " Dad kazo da matsala fa." " Matsalar me fa?" "Dad kazo gidan Abba d'an Seemah na wani hali." Cikin rud'ewa Dad yace " meya sami Seemar? Waya b'ata mata rai?" Shiru Ammar yai kafin can yace " Dad bansan me zance ba." Jin karar alamar sa makulli yasa ya juya da sauri ya kalli d'akin, da sauri yace " Dad kazo yanzu da matsala." Yana kainan ya kashe wayar tare da saurin karasawa kofar d'akin ya shiga jijigawa, jiyai ansa sakata. Hannu bibiyu yasa ya shiga bubuga kofar yana k'iran sunan Seemah. Mamie, Zahra da Zaid da sauri suka zo jin ana bubuga kofa, nan suma suka shiga k'iranta. Ganin ba alamar bud'ewa yasa suka tsaya jugum jugum Mamie tace " gashi babu wani makullin." Ammar kam haryanzu bai gaji da bubuga kofar ba, yana k'iran sunanta cikin wani irin murya. Sun dade agun kafin Dad ya iso da sauri yana zuwa ya kallesu yace " menene?" Shiru sukai Mamie tace "nice na fad'i abinda bai kamata ba kuma ina tunanin ta ji." Gaban Dad ne ya fad'i ya sa hannu zai buga kenan yaji muryar Habib yace " Zaid d'an Allah kaida Zahra kud'an bamu guri." Zaid ya kalli Habib cikin b'acin rai gani yake kamar rainin hankali ne hakan, a zuciye yai waje. Habib ya maida dubansa kan Dad yace " Dad da alama Seemah tasan komai a kanta, menene dalilin dayasa zaku b'oye wannan babban sirri ga kowa? Sannan taya za'ayi a maka sharri saboda mahaifiyarta amma ka rik'e yarinyar da ba kaine mahaifinta ba." Dad ya kalli Habib cikin takaicin kalamansa, kafin yai magana yaji Ammar yace " lalai ya Habib, wato kai abinda ya dameka kenan? Yarinya tana cikin d'aki Allah ne kad'ai yasan meke faruwa da ita a ciki anma kai abinda kake tunani kenan?" Dad ya kalli Ammar kallon jin dad'i ga kalamansa, Dad yai baya sannan ya taho da gudu ya big'e kofar, sai dai bata bud'e ba, haka sukai tayi shida Ammar har sukai sa'a kofar ta bud'e, da sauri suka shiga ciki sai dai ba kowa a d'akin, ga mamakinsu kuma karar zubar ruwa sukeji daga b'an d'aki. Ammar ya karasa da sauri tare da bubuga kofar toilet d'in. Seemah kam tana cikin bathroom ta tsugunna a cikin ta saki shaya, ga bata cire kayan jikinta ba, ga ruwan sanyi ta sakar ma kanta, hakan yasa ruwa duk ya jikata jakaf, sai dai ko damuwa batai da jikinta ba kawai kuka takeyi, gani take wannan itace hanyar da ya dace da ita, ita kad'aice hanyar dazatasa takasa gane yawan hawayen datake zubarwa. Kuka sosai takeyi sai dai ruwan dake zuba jikinta yasa baza'a gane ba. Dad ya matsa jikin kofar ya shiga k'iran sunanta, tana jin muryarsa ta mik'e jikinta na rawar sanyi, sai dai bata bud'e ba, Dad ya shiga lalashinta, can cikin lallashi yace " fito Seemah inhar kika fito zan fad'a miki duk abinda ya faru a baya, na miki wannan alk'awarin." Jin wannan kalaman yasa ta bud'e kofar a hankali, kofar tana bud'uwa Dad da Ammar sukai saurin shiga ciki, kallanta Ammar yai hawaye na zubo mai, kanta ya kalla sannan ya kalli yanda jikinta ke d'iga da ruwa, dukansu har Habib sai da sukaji tausayinta ya kamasu sosai. A hankali sukaji tace " Dad kafad'amin abinda naji ba gaskiya bane, ka fad'amin kaine mahaifina, ka fad'amin gaskiya d'an Allah." Dad ya share hawayensa ya matso ya rungumeta yana hawaye sosai, yace " Seemah ki kwantar da hankalinki." Kai ta girgiza tace " Na fahimta dagaske ba kaine mahaifina ba kenan, mahaifiyata karuwa ce, tsintata akai?" Kallanta Habib yai cikin tausayi da alama bataji komai ba kenan, Dad ya d'ago tare da share nata hawaye yace ki canza kaya Seemah zan fad'amiki komai, amma ko kusa Fatima ba karuwa bace, ba kuma tsintarki nai ba." Kallansa tai ta kasa yin komai, sai hawaye da suke tsere a idanunta, Mamie ta kwallama Zahra ido, tana zuwa tace " taimaka mata ta canza kaya." Dad ya kalleta yace " ki shirya ki fito fallo zan sanar dake komai." © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣6⃣ Zahra ta taimaka mata tasaka kaya, hannunta ta kama suka fito falo. A falo kuwa Dad na zaune a saman kujera yayi shiru zuciyarshi na cikin damuwa, mami na zaune daga can b'angaren itama, Habib kuma da Ammar suna zaune a kasa, Zahra ce ta fito rik'e da hannun Seemah ta zaunar da ita a kasa kusa da Dad, hannu Dad yasa ya shafi kanta. Kamar ba Seemah ba sam ta canza ga lab'anta duk sun bushi gwanin tausayi, Ammar ma ya kalleta tausayinta na k'ara ratsa gab'obin jikinsa. Dad ne ya d'aure yai gyaran murya. *TUNA BAYA* Malam Isma'il wato Dad kenan, ya kasance malamin makarantar boko ne, a garin Birnin/gwari dake kaduna, yana zaune a jikin gidan mahaifinsa ne saboda rashin hali, gashi anyi sa'a dama gidan kawo gida ne babba, kawo matansa 3 ne, sai dai duk Allah bai basu haihuwa ba sai akan mahaifiyarsu Isma'il. Hajiya 'yaranta biyu wato Dad da Abba (Abubakar) anyi sa'a Abba tun yana saurayi ya samu wani babban mutum d'an kasuwa a garinsu yake d'aukansa suna yawan kasuwancinsu tare, ganin kwazo dasan aiki irin na Abba yasa ya aura masa 'yar sa wato Mamie(Bilkisu) sannan ya d'aurashi akan harkokin business d'insa dake Abuja, tun daga nan ya koma can da zama. Dad an masa auren zumunci da mahaifiyarsu Habib wato Samira, duk da baso yakeyi ba sai dai a lokacin bashida wacce yake so kuma zab'in iyayensa shine zab'insa, bayan auransu ne Kawo ya basu b'angare d'aya suka zauna a gidan. A kwana a tashi har Samira ta haifi d'anta Habib, sannan ta sake haihuwar Junaid sai dai akwai ra ta a tsakaninsu, lokacin da Samira take da cikin Ammar ne ranar Isma'il ya dawo daga makaranta yaga wata bus tayi parking a mak'otansu, yarane 'yan mata su 4 suka fito daga motar, kana kallansu kasan fulanuwa ne aka kawo su irin aikin nan na aikatau. Isma'il ya kauda kansa tare da wucewa gidansu, yaje daidai zai shiga yaji ance " Malam Isma'il?" Juyowa yai da fara'arsa saboda ya gane muryar, ya kalleshi yace " Amadu kaine yau a gidan namu?" Wanda ya k'ira da Amadun yai murmushi tare da cewa" wucewa nazo yi shine naga kamar ana sauke 'yan aiki na d'auka kaine ka d'aukarma Samira." Yai maganar cikin zolaya. Isma'il ya d'an kallesu caraf suka had'a ido da d'aya daga cikinsu, d'auke kai yai yace " lalai kai dai yakamata ka d'aukarma matarka." Sun dad'e suna hirarsu har 'yan matan suka gama shiga da kayansu suma suka shiga, Isma'il ya kalli Amadu yace " ni dama shagon ka naje na amso ma Samira kayan shayi, naga kamar wannan cikin na wahalar da ita sosai bata iya cin abinci." Amadu yace " Hmm nima haka nake fama da Hauwa'u inata so in tambayeka dama haka masu ciki suke shan wahala." Isma'il ya maida jakarsa d'aya hannun yace " A'a wlh yanayi ne dai yake zuwa kaga Samira data haifi Habibu da Junaid ai duk batasha wahalar laulayin nan ba." Amadu ya gyad'a kai yace " muje shagon in baka da har na kulli zance ganin Hauwa anma saboda kai zan koma." Suna tafe suna hirarsu har suka isa Babban Shagon Amadu ya shiga ciki ya had'omai kayan shayi, Isma'il ya bashi rabin kud'in yace sauran sai karshen wata. Haka Isma'il ya taho yan tafe ana gaidashi saboda ganin girmansa da mutane keyi, har ya isa gida. Yanzun ma yazo shiga ya k'ara ganin 'yan matan sun fito sai dai ta d'azun nan tana matsar kwalla da alama kukan rabuwa sukeyi, wucewa yai ya shiga gida. A kwance ya tadda Samira ta kasa komai, nan ya taimaka ya had'a mata shayi ta sha, da kanshi ya shiga gyara d'akin sannan ya taimaka mata ta kwanta a kan gado. Ganin lokacin shiga makarantar su Habib da Junaid yayi ga kuma babban d'an Abba yasa Mamie ta ba Abba shawara akan akaisu England gun kanwarta, Abba yayi farincikin wannan shawarar ya k'ira kaninsa ya sanar dashi. Ba Dad ba hatta matan gidan sun tayasu murna, su Habib sai murna sukeyi sukam, bayan sati biyu da maganar Dad dakanshi yakaisu Abuja suka wuce ta can. Dad ya dawo daga Abuja a gajiye ya shiga gida anan ya tadda Samira ba lafiya su Hajiya da ragowar matan kawo na kanta, ya kallesu yace "Hajiya lafiya dai ko?" Hajiya tace " fita waje nak'uda ce." Dad ya kalli Samira yaga yanda takeshan wahala yace " Kodai akaita asibiti?" Hajiya tace " bakaji me nace ba?" Jiki a sanyaye Dad ya fita ya zauna akan dakalin gidan, bai dad'e da zama ba sai gata ta dawo daga kai nik'a, a hankali cikin sanyin muryarta yaji tace " Ina wuni?" D'agowa Dad yai ya kalleta ranar daya fara ganinta kaya daban daban ne a jikinta gashi tayi zanen baki duk a fuskarta yanzu kuwa ba wannan shirman a fuskarta sannan kayanta tsaf,ba shakka tanada kyau sosai. Dad yace " ina gajiya." Yana fad'ar haka ya kauda kai, matsowa tai kusa dashi tace " Malam menene? Naga kamar kana cikin damuwa." Kalanta yai da mamaki, baisan sanda yai murmushi ba yace " Ta ya akai kika sani?" Ta saki murmushi itama tace " kullum ina ganinka ai in na fito anma ba haka nake ganinka ba." Dad yai murmushi yace "a ina kike ganina?" Tai kasa dakai batace komai ba, yace " kije kikai aikenki kar a miki fad'a." Ta d'ago ta kalleshi sannan tace to, wucewa tai ta shiga gida, ya bita da kallo haka kawai yaji damuwarsa ta ragu sosai, anma ya akai yarinya karama da bata wuce shekara 18 ba tagane yana cikin damuwa? Yarinyar tana shiga gida ta kai markad'an sannan ta kalli matar gidan tace " Hajiya in d'an fita?" Ta kalleta tace " Fatima ina zaki ke kuma? Naga yamma tayi." Tace " yanzun nan zan dawo." To sai kin dawo ta fad'a, da sauri Fatima ta juya ta fita, sai dai abin haushi tana zuwa taga ba kowa agun, waige waige ta fara yi sai dai bata ganshi ba, jitai anzo daidai kunenta ance " Fatima me kikeyi anan?" Da sauri ta juya ta kalleshi, d'an gidan da take aiki ne ko ince d'an lele, da sauri ta matsa ya kalleta sannan ya kalli abokansa jitai sun kwashe da dariya, kifkif da ido tai tace " menene?" D'an lelen wato Abdul yace " Abokaina kesan ganinki nace musu ankawo mana kyakyawar mai aiki shine nakeso su ganki ko zasu kyasa kamar yanda na kyasa." Kallansa tai da mamakin kalamansa tace " mene?" Dariya suka kara kwashe mata dashi, kana ganinsu kaga tantirai, Fatima kam ba abinda ta tsana irin Abdul ya shigo gida ya d'inga nanik'e mata kenan ita kuma batasan haka. Cikin takaicin abin yasa tai saurin shigewa gidansu Isma'il. © *THE SEEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣7⃣ Fatima na shiga gidan ta ga mutane a zazaune anata murna, idanu suka had'a da Isma'il, jitai ance " Baiwar Allah lafiya kika shigo ba sallama?" D'auke idanta tai daga kansa tai saurin cewa Salamu Alikum, dariya suka sa mata Hajiya tace " daga ina kike?" Fatima tad'an saci kalan Isma'il sannan ta nuna da d'an yatsarta tace daga nan gidan, Goggo(uwar gidan Kawu) tace shigo ki zauna nasan kukan yaro kikaji shiyasa kika shigo ko? Kallan yaran tai a hannun ta murmushi ta saki sannan ta karasa tare da gaishesu, suka amsa goggo ta mik'a mata d'an, Kuramai ido Fatima tai tana san yara itakam, a hankali ta d'ago tad'an kalli Isma'il ga mamakinta shima idanunsa na kanta da sauri tai kasa da ido tace " Allah ya raya." Sukace Amin. Goggo tace " Isma'il ko zaka dubo mai kazar ko ya fito, naga tun d'azu mahaifinka bai dawo ba, ga shi ya kamata ama mai jego farfesu." Isma'il yace " bari naje." Ji sukai Fatima tace " bari ni naje nasan gurin." Hajiya takalleta fuskarta da fara'a tace " keda kikazo barka, ya za'ai musaki aiki sannan ga magriba ta kawo kai." Isma'il ya mik'e tare da cewa bari naje. Yana fita, Fatima tace " bari naje gida zan dawo gobe." Nan suka mata sallama ta fito da sauri. Can taganshi har yayi nisa, da sauri ta shiga binsa har da had'awa da gudu, tai sa'a ta kusa isa gunsa, a hankali tace " Malam." Ga mamakinta gani tai ya juyo d'an batai tunanin zai jita ba. Tsaya tai tana hakki, Isma'il ya matso kusa da ita yace " yana ganki anan?" Cikin hakki tace " biyoka nai." Kallanta yai da mamaki yace " abu kikesan fad'amin?" Kai ta gyad'a sannan tace " Malam alfarma da taimako nakesan kamin." Isma'il ya kalleta yace " namefa?" Tai shiru tare dayin kasa dakai, ya kara kallanta yace " ke nake jira." Tana wasa da 'yan yatsun hannunta tace " Karatu nakesan ka koyamin." Dariya Isma'il yasa yace " in kinasan karatu sai kice a saki a makaranta." Tai kasa dakai tace " ni na islamiya nakeso, kullum Hajiya sai tace in tashi inyi sallah nikuma a garinmu sai mutum yayi aure yakeyin sallah to in ina kula da yanda takeyi sai inga tana motsa baki amma bansan me take cewa ba, shine nakeso ka koyamin na islamiya insan yanda ake sallah." Kallanta yai cikin tausayawa, gata dai 'yar kauye mara ilimi sai dai komai nata na birgeshi, da wani ne haka zai karashi rayuwarsa ba tare dayace a koyamai ba." Yaja dogon numfashi yace " yanzu kije gida gobe kisame ni da yamma a kofar gida, sai insan yanda zamuyi karatun." Murmushi ta saki tace " nagode Malam. " Tanakainan ta juya ta fara tafiya, kallo ya bita dashi ya shagala yana kallanta yaji an dafa kafad'arsa, ya juyo a zabure Amadu ne ya kalli inda Isma'il yake kallo yace " kasanta ne?" Isma'il yai saurin wayancewa yace " wa?" " wacce kake kallo mana." " ni kaga ina kallan wata? Kawo nake lek'awa munjishi shiru tun d'azu daya fita siyo kaza." Isma'il yai maganar yana waige-waige. Amadu yace " Niba wannan ba gurinka fa zanje yanzu." " haba? To gani Allah yasa lafiya." Amadu yasa dariya yace " Habiba ta sauka d'azu da rana na k'ira wayarka bansamu ba shiyasa na yanke hukuncin zuwa gunka." Fara'ar Isma'il ce ta k'aru yace " kai haba? Amma naji dad'i, nima yanzun nan Samira ta sauka, oh ikon Allah kaga sun haihu a rana d'aya." Amadu ma fara'ar fuskarsa ya fad'ad'a yace " ikon Allah meta samu?" "Namiji." "Nima Namiji. " A tare suka sa dariya tare da rike hannu Amadu yace " lalai wad'annan Aminai zasu zama da alama." Nan Amadu ya raka Isma'il gun mai kaza anan suka tadda kawo, sun siya suka taho tare kawo na tayasu murna yace " Lalai naji dad'i Allah ya kare mana su." Amin suka fad'a a tare. Har gida Amadu ya rakasu, nan matan kawu suma sukai ta tayashi murna, ya d'auki d'an cikin farinciki yace " Isma'il tunda mun haihu a tare sai muyi canje, ni zan rad'ama d'anka suna kaima sai ka rad'ama nawa." Duk suka kwashe da dariya kowa ya shiga cewa lalai hakan yayi. Amadu ne ya rad'ama Ammar suna na gaskiya sunan mahaifin Amadu wato Kabir sai yasamau sunan daza'adinga cemai Ammar. Shima Isma'il da kansa yaje gidan ya rad'ama yaron Jalaludeen saboda sunan dayasu rad'ama Ammar kenan. Murna agun mutane ba'a magana saboda kowa yasan amintar dake tsakanin Amadu da Isma'il. Washegari da yamma yana zaune a dakalin kofar gidan Fatima ta fito, cikin tafiyarya mai nutsuwa, tana ganinshi tai kasa dakai tana murmushi, Isma'il ya shiga kallanta harta karaso gurin, ta gaidashi a hankali, shima ya amsa tare da cewa " na d'auka kin fasa koyar karatun ganin kin dad'e baki fito ba." Yai maganar cikin zolaya, abinka da rashin wayau sai tace " bayan yanzu kazo tun d'azu nake lekowa bana ganinka." Dariya yai yace " ashe da gaske takesan koyan karatun." Kasa tai dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Isma'il yace na yanke shawara, duk ranar asabar da lahadi shine bani da makaranta da safe, wajen karfe 11 sai ki d'inga zuwa islamiya ina koya miki zuwa karfe 1, kinga karfe 2 ne ake fara karatu." Kai ta d'aga tace to "Malam na gode, amma wannan yaron d'anka ne?" Isma'il ya kalleta da mamakin tambayarta, yace " meyasa kikesan sani." D'agowa tai a hankali ta kalleshi batace komai ba ta maida kanta kasa tare da cewa " sai ranar asabar d'in." Ya amsa da "Allah ya kaimu." Ta juya tai ciki, kallanta yai tare da murmushi. Itakam tana shiga ta d'au tsintsiya ta hau shara ba gaira ba dalili bayan gun a gyare yake tas, shara take Hajiyar Abdul na zaune taji karar tsintsiya ta mik'e tare da fitowa, Fatima tagani tanata zabga shara zatai magana taji muryar Abdul yace " Faty Shara kikeyi ne?" Kallansa tai ta kaida kanra kan shara, itakam zuciyarta batasan ace d'an Isma'il ne d'an ita tanada mugun kishi shiyasa bazata iya auren mai mata ba, zuciyarta tace anya kuwa kamar malam zai rasa mata?" Jitai Abdul ya dafata yace " meke damunki haka?" Ta d'ago tace " d'an Allah ina rokonka kadaina tab'ani in zakamin magana." Ga mamakinta jitai yace " Sorry na daina." D'agowa tai tana mai kallan mamaki tace " ina abokan naka?" Yai dariya yace " suna gidansu." Tai kasa dakai tare dad'an tab'e baki a ranta tace " da walaki, d'an dama inshi kad'ai ne zakaga yanada saukin kai kuma bashi da rashin mutunci, anma da zarar sun had'u da abokansa shi kenan kuma sai rashin mutunci ta ko ina." Kallanta ya tsaya yanayi tana shara, sai murmushi yakeyi, Hajiya dake tsaye tana kallansu tai murmushi itama, da alama Fatima ce zata sa d'anta ya shiryu d'an wannan shine addu'arta yaran maraya ne bashida uba, sai dai yabiyema kawayen banza sun canza mai halaye. *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 4⃣8⃣ Anyi suna lafita kowa na murna, Abba kam shima a lokacin Mamie nada tsohon ciki hakan yasa batazo ba, sai dai tunda akai suna jikin Samira yak'i dad'i kullum cikin cuta. Fatima kam duk karshen sati suna zama da Isma'il a makaranta ya koya mata karatu, a sanu a sanu wata shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu batare da Isma'il ya farga ba, sai dai bai tab'a tunanin zai iya furta mata yana santa ba saboda sau dayawa yanaji tana zancen batasan kishiya. Rayuwa kenan yanzu an wayi gari shekararsu Jalal 5, kusan kullum Jalal na gidansu Ammar inkuwa baizo ba to zakaga Ammar a nasu gidan. Jalal ya taso yaro mai zuciya, shikuma Ammar hakuri gareshi, a duk lokacin da yara sukaso rainama Ammar hankali, Jalal ne ke zuwa ya musu shegen duka, hakan yasa suka daina tsokanar Ammar. A b'angaren Fatima kam tana shiga gidansu Isma'il sosai sai dai a randa tasan yanada aure harda 'ya'ya ranar tasha kuka harda zazzab'inta, yanzu Fatima ta kile sosai d'an inba fad'ama akai ba bazaka tab'a cewa 'yar kauye bace. Samari kuwa dake santa a k'aueyen nan yawa garesu, sai dai ita zuciyarta nakan Isma'il, ta kasa tsayawa da wani sam. Kamar yanda ta saba yau asabar ta gama duk ayukanta, tace " Hajiya zan fita." Hajiya tace " Fatima jiya da daddare sai nawa Abdul ya shigo?" Fatima ta kalli Hajiya tace " Hajiya wlh bansani ba nidai harnai bacci banji motsin bud'e kofa ba, amma ai dama yace Campain yakeyi." Hajiya tai shiru tace " wani campain me da daddaren Allah? Keda kin yarda? So yake yaja min zagi dama mutane nacemasa d'an mace tunda mahaifinsa ya rasu da daddewa." Fatima ta matso kusa da Hajiya tace " Hajiya Allah ya gani kinayin daidai kokarinki ga matsalar kafar da kike fama da ita sannan ni fa hajiya? Kinsan iyayena sun rasu tun ina karama agun kanwar mahaifina na taso." Hajiya tai murmushi tace " jeki ko ba gun karatu zaki ba?" Mik'ewa tai tana murmushi ta mata sallama ta fita, Hajiyar Abdul ta bita da kallon k'auna. Tazo fita taji an cafko hannunta, ko bata juyaba tasan waye hakan yasa ta dage ta fizge hannunta da karfi, Abdul haushi ya kamashi, yana takaicin yanda take nunamai kamar tana kyamarsa, sa hannu yau ya fizgota ya matseta jikin bango, ta d'ago tare da had'e rai, Abdul ya kalleta ya saki wani mugun murmushi yace "Fatima na yanke hukuncin muyi aure kawai." Batasan sanda ta bugamai wata harara ba, batai auni ba taji ya kifa mata mari yace " ni kike harara? Ko kin manta ni waye?" Kasa tai da kai tare da rik'e gun, ya saketa yace " ankusa nad'ani Chairman a garin nan, in har mai aikin gidanmu bata bani girma ba wa zai bani?" Ta kalleshi a ranta tace " tir da wannan mik'amin da ake shirin ba ka." Ya saketa tare da shiga ciki, cikin takaici itama ta wuce waje. Abdul na shiga ya gaida hajiya tare da cewa " Umma nikam aure nakeso." Kallansa tai cikin mamaki da kuma murna tace " wa kakeso Abdul? Naji dad'i?" Ya d'an sosa k'eya yace " ni Fatima zaki auramin." Murmushin fuskarta ne ya fad'ad'a tace " Da gaske Abdul?" Yai murmushi yace " sosai ma, amma d'an Allah Umma tunda yarinyar nan a gunki take kuma anan gidan zata zauna asa auren nan da sati 2." Dariya ta saki tace " Abdul matsuwar ta menene haka?" Yace " ni kawai so nake ayi nan kusa." Shiru tai lalai dole ta yarda ai nan kusa, d'an tasan inka ga namiji ya matsu da aure sosai to gwara amai kafin abin kunya ya ratsu ciki. Tace to naji jeka. Nan ya mik'e tare da Murmushin mugunta, d'an shikam kullum da sha'awar ta yake kwana. Fatima kam tana fitowa a waje kan dakali taga Jafar da Ammar, ta matsa tare da cewa " Me kukeyi a nan?" Jafar ya kalleta yace " a zaune kawai muke." Fatima tai murmushi tace " ku bakwa wasa irin na yara?" Jafar ya kalli Ammar yace " yaran ne 'yan rainin hankali, munfisan muyi wasanmu mu biyu." Tace " Ammar ina Babanka?" Yace ya fita, tai murmushi tad'auko naira goma a jakarta tace " ungo kusai alawa." Jafar ya kalleta yace " mun gode amma bazamu ansa ba." Ta kalleshi sannan tace "Ammar kaifa?" Kallan Jalal yai yace "a'a mun gode. " Ta d'an yi kasa dakai alamar rashin jin dad'i sukam sauka su kai suka shiga gidan da gudu. A hankali take tafiya, samarin garin kowa na sha'awar yanda take da hankali ga kyau, harta isa makaranta, ta tadda Isma'il a zaune, ta gaidashi ya kalleta cikin kulawa yace " yau kin d'an dad'e Allah yasa lafiya." Ido ta kuramai kamar batasan me yake cewa ba, ganin yanda take kallansa yasa yai murmushi yace "da alama kunyar fulani tabar jikinki." Da sauri ta d'auke ido tace " Malam duk kunyata?" "Hmm a da ba? Yanzu naga harkin fara kurama mutane ido." Ta had'e rai tace " kaine mutane?" Yai murmushi ya wayance da cewa " matso muyi sauri matata batajin dad'i." Had'e rai sosai Fatima tai dama yasani, shikuma harga zuciyarsa yasan yanasanta sosai, sai dai yasani bazata iya auransa ba, ga 'ya'yan masu kud'i na santa samari, ina zai so abinda yake neman fin karfinsa?shiyasa yakesan itama ta daina sanshi. Mik'ewa tai cikin tsananin kunar rai ba tace mai komai ba tai hanyar waje. Isma'il ya kalleta yace " nayi zuwan banza kenan?" Tsayawa tai cak batare da ta juyoba idanunta na zubar da kwalla, mai yasa zuciyarta bata iya b'oye so ba? Haka ta juya sukai karatun ba dad'i. Tana dawowa gida Hajiya tasanar da ita zancen aurensu da Abdul, cikin mamaki ta kalleta tace " ni kuka Hajiya? Mai zai yi dani 'yar kauye?" Hajiya tace " Fatima kitaimakeni bad'an shi ba d'an ni ayi auren nan,wannan shine buri na d'aya da ya rage min a duniya, d'azu na k'ra kanwar Babanki bakiga murnar datai ba." Fatima ta d'ago a ranta tace tayi murna mana tunda taji zan auri mai kudi. Murmushin yake Fatima tai mata sannan ta mik'e ta shiga d'an d'akinta, tana isa ta fad'a gado kuka sosai ta shiga yi, meyasa ba wanda zai tambayeta ko akwai wanda takeso? Tasani da mahaifanta nada rai dasai sun tambayeta ko tanaso, ta dad'e tana kuka kafin ganin ba mai lalashi ta mik'e. Isma'il kam ya dawo yana shiga d'aki, ya tadda Samira a zaune, ya shiga shima ya zauna, tamai sannu da zuwa tare da cewa" dagaske kaima kanacikin jerin masu san Fatima?" Da mamaki ya kalleta yace " me kike fad'a haka?" Ta juyarda kai tace " d'azu na fita gunsu Hajiya naji wani saurayi yazo kawo musu kara wai kana santa duk asabar da lahadi sai kun had'u a makaranta kunyi zance." Ya mik'e tsaye yace " kuma sai kika yarda da zancen nakejan yarinya zuwa makaranta inayi?" Juya kai ta sakeyi hakan yasa ya gane wato ta yardan kenan, a zuciye ya fito waje, Hajiya ya gani dasu Goggo suma suna maida zancen, kallansu yai cikin takaicin abinda kowake fad'a zaiyi magana sai ga Jafar ya shigo, ya kalli Isma'il yace " Dad wai ana magana dakai." Yace " Jafar inji wa?" Yace " Abba nane." Tare suka juya sukai waje, bayan sun gaisa da Amadu ne yace " Amadu ya akai?" Amadu yai shiru can yace " haryanzu kana koyama Fatima karatu ne?" Kai ya gyad'a alamar eh, Amadu ya dafa kafad'arsa yace "kayi hakuri ka rabu da yarinyar nan, nasan ka sosai Isma'il nasan kuma kana santa, wani karatu kake koyamata har shekara 5?" Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba " kaga d'azu a shago naji ana gulmarka, sannan naji ma yarinyar yaron gidan zata aura, Isma'il ka hakura kasan Abdul wanda za'aba Chairman ba mutunci garesu ba su da abokansa." Isma'il zuciyarshi ta tab'u dajin wai anmata miji, ya d'aure yace " nagode Amadu, insha Allah kuma mungama karatun." Tun daga wannan rana bata sake sa Isma'il a idanunta ba, zuciyarta takasa hakura da rashinshi, wani sa'in har gidan take zuwa sai dai kowa taga ya daina sakar mata fuska, ga abin takaici shirye-shiryen bikinsu kawai sukeyi ba wanda ya damu da halin da take ciki. Isma'il kam shima komai nasa ya canza bai fiya magana ma sosai ba, duk 'yan gidan hatta Samira sun fahimci yanasan Fatima sosai, sai dai yaza'ayi? Abdul kam abokansa sai dariya sukemai wai zai auri 'yar kauye, yace " nimafa bawai d'an inzauna da ita d'ind'ind'in nakesan auranta ba, d'an kawai in kauda kwad'ayi nane, dariya suka kwashe dashi sukace " in wannan ne ba kawai sai ka....." Shidai kam zuciyarshi batasan wannan kawai....d'in. Yau saura kwana 2 biki, d'anginsu Fatima sun cika gida, itakam kallan kowa take a baibai, sai dai ba yanda zatai, duk ta rame ta canza. Dad nakawo nan yai shiru tare da kallan Seemah dake zubar da kwalla kamar an bud'e famfo, Ammar ma hawaye ke zubar mai, ya kalli Habib shima haka. Yai shiru can yace " Ana saura kwana 2 auranta ne Ammar yazo ina zaune kusa da Samira da ba lafiya ya sanar dani wai matar nan ta gidan nan, tace d'an Allah tanasan ganina a shagon Abban Jafar. " Samira dake kwance ba lafiya na kalla, na share maganar tare da kallan matata, Samira ta juyamin baya tana zubar da kwalla, tausayinta dana kaina ya kamani hakan yasa na watsar da maganar Fatima nasan ganina. A b'angaren Fatima kam tun karfe 2 tazo gefen shagon take tsaye, har la'asar, Amadu tausayinta ya kamashi yace " Fatima anya zaizo kuwa?" Ga mamakinsa murmushi yaga tayi tace " zaizo." Anan shagon ta la'asar Amadu yabata biscuit da lemo, duk da yunwar datakeji taki amsa, duk k'iran da Amadu yake makama Isma'il a waya sai ace wayar a kashe, ga magrib ta duso, Jalal ne yazo gunsa, yace " yauwa Jalal zauna ka taya Aunty hira bari naje gidansu Ammar in dawo." _Dad ya kallesu tare da matse kwallar sa_ Yace " Seemah bansan meya faru ba, nidai Amadu yazo mukai sallar magrib a massallaci tare muna fitowa yasanar dani komai, da sauri muka nufi shagon ni dashi. Sai dai me? Shagon muka gani kamar ba kowa, hakan yasa na shiga ciki da sauri shi kuma ya zagaya, ina shiga na tadda Fatima tsirara ba kaya a kwance, kamar ma ta ruga ta suma, kana ganinta kasan ta karfi aka mata, na matsa da sauri na tallabota idanuna a rufe na riko zaninta na lil'iba mata, Amadu ya leko cikin tsoron abinda ya faru ya zube agun, nikam rungumeta nai na shiga wani irin kuka mai ban tausayi, ban farga ba naji mutane a waje ana hayaniya. _Dad ya share kwallarsa_ _Seemah kam kukanta ya tsananta anan_ Amadu ne ya kallan yace " yi sauri ka fito da ita samarin garin nan ne bansan wa ya k'irasu ba." Na d'agota tare da nad'a mata zani, ina fitowa aka fara jifansa da dutse, ganin zasu sameta yasa na juya sukai ta dukana, wani daga cikinsu ma bamusani ba ashe yasa kalanzir kawai sai ashana mukaga an kyasta, haka na d'aureta abayana dakyar mukasha zuwa gida. Sai dai me? Bala'in dana tarar a gida a wuce nacan, Hajiya harta suma, Samira ma ciwonta ya tashi, sai numfashi kawai takeyi, tana ganina d'aure da Fatima kawai tayi baya luuuu, abinda ya firgitani agun tace ga garinku nan. Kuka ma rahama ne, a wannan ranar hawaye ma kasa zubomin sukai, Kawo da jama'ar gurin suka had'u aka fara zancen yima Samira wanka, nan Kawu ya kalli Amadu a tsakiyar mutane yace " Amadu ka tabbatar da abinda ka fad'a cewar Isma'il shiya mata fyad'e?" Da mamaki na kallesu ni kuma? Abinda ban tab'a zataba sai jinai Amadu yace wai eh, ya ganni da idanunsa. Kuka sosai kawu yai, kowa ya shiga ala wadai dani, Abdul ya koma gida cikin taron jama'ar biki yace " bazai aure Fatima ba, d'an ankamata da wani a shago." Tsinuwa kuka nashata, wani abin takaicin Fatima data farfado, sai kuma ba baki, ta kasa magana, duk yanda taso tai magana ta kasa, anan aka fara jifana akan lalai kafi namata da alama ma abu nasa na danne bakinta, yunk'urin ihun dataitayi yasa muryarta ta tafi. Dad ya kallesu hawayensa sun tsanan ta yace ban tab'a ganin bala'i kiri kiri irinta wannan ranar ba, kowa ya gujeni, A lokacin na ba Fatima takarda akan ta rubuta min sunan wanda yamata fyad'e, tana kok'arin rubutamin, Tayi baya luuu, bakinciki harya gama cin jikinta, haka na kaita asibiti aka bata gado, sai dai kamar ba rayayyiya ba, tana kwance ne kawai sai numfashi, d'anginta suka sallamata aka watse da ala tir. Fatima na asibiti har wata 2, Kawu da Hajiya sunyi sunyi inrabu da ita sai dai gani nake in na kyaleta mutuwa zatai d'an bakin ciki, alokacin ne kuma akace tanada ciki. Ganin zaman garin na neman gagararmu yasa muka dawo Suleja, anan ne har Fatima ta kawo watan haihuwa, tana haihuwa tace ga garinku, Hajiya kam da Kawu sun ma dainamin magana sam, yaya ma duk yanda yaso da in rabu da Fatima sai dai na kasa, haka na zauna agun gawar naita kuka kafin aje amata sitira. Dad na zuwa nan yakasa magana Seemah kam jitai kanta na juyawa Ammar ya matso kusa da ita yace " Seemah, in ihu ne kiyi amma karki had'iye komai a ranki." Kallansa tai kawai tai baya luuuuuu, Habib ma kuka yake sosai, Dad ya mik'e dasauri ya d'auketa yai waje da ita. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com *_This Page is for you my dearest Friend Umma, and also my Swt kanwa Somaya😍 Miss Hot Purple luv u soo much_* No. 4⃣9⃣ Jalal kam yana tsaye a gate d'in gidan su Habib, mai gadi ya kalleshi yace " Bawan Allah d'an Allah ka tafi na fad'ama Hajiya Seemah bata nan." Jalal ya kalleshi sannan yace " naji ai baba kuma na yarda to so nake naji tana ina?" Zaiyi magana sai ga Aisha ta fito da alama asibitu zata kai abinci ganin basket d'in kuloli a hannunta, kurama Jalal ido tai kamar tasan shi, can ta matso tare da mik'ama Bala basket d'in yasa a mota. Ta kalli Jalal tace " Kamar na sanka ko?" Jalal ya kalleta yace " anya kuwa? Amma da alama daga gidan kike, Seemah fa?" Sai alokacin ta tuna shine yaja Seemah rannan da suka fita tare, ta sakarmai murmushi sannan tace " tana gidan Yayan Babanta amma yanzu ya Habib yai waya yace wai ankaita asibiti da alama batajin dad'i." Jalal yace " mene? Meya sameta? Zazzab'i take?" Dariya Aisha tai tace " wanne zan amsa daga ciki? Bayan nima bansan komai ba? Yanzu dai zanje asibitin sai ku tafi tare." Jalal ya runtse ido sam hankalinsa ya gaza kwanciya, nan Bala ya fito da mota Jalal ya shiga gaba suka wuce asibiti. Seemah kam bayan ta farfado sai ta hau rawar sanyi, nan likitan yasa mata drip sannan ya roki da abarta ita kad'ai da alama taji abinda ya firgita tane. Abba, Dad, Kawo, Ammar, Habib, da Mamie suna zaune a d'akin da aka kwantar da hajiya, itama dai jikin ba dad'i a zaune kawai suke amma kowa da abinda ke ransa. Sun isa asibiti, Aisha ta kalleshi tace " zamuje tare ne?" Jalal ya tuna kalaman Dad na d'azu hakan yasa ya kakaro murmushi yace " Jeki kawai karma asan tare muka zo." Ta kalleshi da mamaki amma bata tambaya ba ta ce to, sannan tai gaba. Jalal kam zuciyarshi ta gama dakewa abu d'aya kawai yasa a ransa awannan lokacin shine bazai tafi ba tabbas sai yaga Seemah, saboda gobe yakesa ran zuwa Birnin/gwari d'an yaji menene tsakanin Dad da Abbansa. Karasawa yai bakin d'akin da aka kwantar da Hajiya bai shiga ba kuma bai kwankwasa ba kawai a tsaye yake, sam baisan d'akin kusa da Hajiya nan aka kwantar da Seemah ba. Bayan Aisha takai Abincin ta fito ne wajen bud'e kofa yasa Habib ya hango Jalal, ransa ya k'ara tunzura a zuciye ya fito waje yazo kusa da Jalal ko kofar bai rufe ba, a lokacin ne hankalinsu yakai kansa. Habib na zuwa kusa da Jalal, kafin Jalal yai auni yaji an makamai naushi a kunci, dukan ya shigeshi d'an sai da gefen leb'ensa ya fitar da jini, Habib ya mik'e zai k'aramai wani Jalal ya rik'e hannun. Daidai nan 'yan d'akin suka fito, Kallan kallo suka fara kafin Jalal yace " Ya Habib mena maka kuma?" Fizge hannunsa yai da karfi sannan ya nunashi da 'yatsa yace " Jalal wallahi id'an har baka bar nan cikin minti 5 ba bansan me zan ma ba." Kallansa yai da alamar tambaya yace " na maka wani abin ne? A iya sanina ban ma abinda zan cancanci duka ba." Muryar Abba ce ta katsesu yace " Habib meye hakan kake?" Habib ya bugama Jalal wani kallo sannan ya wuce d'akin, kowa ya koma d'akin aka rufe kofar, Jalal yabi kofar da kallo, jiyai ansake bud'ewa Ammar ne ya fito yazo kusa dashi tare da mik'amai handkerchief, Jalal ya kalleshi da jajayen idanunsa sannan ya amsa, a hankali ya furta thanks. Ammar ya kalleshi yace " please Jalal ka tafi." Jalal idanunsa suka kara kad'awa yace " Ammar menai? ni Seemah kawai nakesan gani naji ance bata da lafiya, banaji zan iya tafiya ba tare da na ganta ba." Ammar ya runtse ido shima idanunsa suka ciciko, yace " Banaji itama Seemah zata so ganinka a wannan lokacin." "Meyasa? Taya akai kasani? Banaji itama akwai abinda zaisa takisan ganina." Ammar ya dafa kai sannan yace " ni kaina daurewa kawai nake amma basan magana dakai nakeba, ka koma ka tambayi mahaifinka waye ya rad'ama suna? Da wa aka haifeku rana d'aya? Sannan wani irin sakayya yama babban amininsa?" Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba" wad'annan amsoshin sune zasusa kagane meke faruwa." Ammar nakainan ya bud'e d'akin da Seemah take yasa kai, daidainan Jalal ya hangota kwance akan gado ana mata k'arin ruwa, daga nesa ya hango fuskarta jiyai kamar zuciyarsa zata fito, kofar ce ta rufe sakamakon turata da Ammar yai, Jalal yabi kofar da kallo idanunsa sunyi jaa ga sun ciciko, kurama kofar ido yai, ga magrib tayi. Wucewa yai yaje massalaci, suma sun firfito sallah, bayan sunyi sallah kafin su koma shi ya rigasu isa, harya sa hannunsa zai bud'e kofar, yaji bazai iya ba tabbas bazai shiga ba harsai ance ya shiga, kuma bazai tafi ba harsai ya ganta. Komawa yai ya tsaya a gunsa na d'azu, ga mamakinsu duk sun d'auka ya tafi sai dai ganinsa yasa suka d'auke kai suka shiga, Dad da Ammar sukai d'akin Seemah, suna shiga daidai nan ta bud'e idanunta a hankali, haryanzu jikinta zafi tsau kamar garwashi, ta kurawa Dad ido, ita kad'ai tasan me take tunani, kallanta yai tare da cewa " Swthrt kin tashi?" Ta k'ak'aro murmushin da kana gani kasan yak'ene ga leb'enta ya bushe, a hankali tace " Dad tambaya nakesan yi?" "Inajinki 'yar Dad." Had'iyar wani abu tai sannan tace " Jafar da aka haifa rana d'aya da Ya Ammar, wanda mahaifinsa yama sharri ya kuma cutar da mahaifiyata, shine........?" jitai ta kasa karasawa sai motsa baki take tanasan magana amma kuka ya hanata, Ammar ya share hawayensa tare da matsowa kusa da ita yace " Dad zan bata amsa jeka kawai." Dad ya mik'e jiki a sanyeye, Ammar ya matso kusa da ita ya zauna, tare da kallanta yace " Seemah sai me? Inshine Jafar d'in da kikeso? Meye zaisa ki k'ara tada hankalinki?" Kai ta shiga jijigawa tace " akwai komai kuwa yaya." Hannu tasa a saitin zuciyarta tad'an buga kad'an tace " taya za'ayi zuciyata taso wanda d'ansa ya taimaka wajen ruguza rayuwar mahaifiyata? Meyasa nakejin zuciyata tana zafi?" Kuka ne yaci karfinta hakan yasa ta kasa karasawa, Ammar ya share kwallarsa yace " Seemah please kidaina please Seemah." Kuka take sosai ta kasa tsagaitawa, dakyar ta daina sai kuma ta shiga ajiyar zuciya akai akai. Jalal kam har karfe 12 yana nan a tsaye, harsu Kawo da Abba da Habib suka koma gida sukabar Dad agun Hajiya, Ammar agun Seemah. Kowa mamakin yanda yak'i tafiya yakeyi, gashi a tsaye yake ko gajiya baiyi ba ne ko me? Dad yana tsaye ta window yana kallansa, har bacci yafara d'aukan Dad, Ammar kam gun Seemah ya koma, ya kalleta yace " Seemah, Jalal fa na waje tun kafin magrib yake a tsaye a waje." Kallansa tai cikin mamaki idanunta suka ciciko tace " Yaya?" Jinjina mata kai yai yace " ko na karshe ne ki ganshi kuyi sallama." Ta share hawayenta tare da cewa "Ya Ammar?" Mik'ewa yai ya fito tare da kallan Jalal da kana ganinsa kasan dauriya ce kawai yakeyi ta jaruman maza amma tabbas ya gaji, ya kalleshi yace ka shiga. Jalal ya d'ago ido tare da murmushi yace " tnz Ammar." Sai dai me? Sam ya kasa d'aga kafarsa jiyai kafar tamai nauyi, sai Ammar ne ya taimaka mai ya shiga d'akin, a tunanin Ammar Dad yayi bacci, sai dai Dad jin magana yasa ya lek'o ta window yana kallansu har Jalal d'in ya shiga. Kusa da Seemah ya zauna, sam ta d'auke kai daga kan Jalal, Ammar ya fita ya basu guri. Jalal ya kalleta baisan sanda hawayen da yake b'oyewa suka zubo ba, a hankali yace " Meemah ya jikin?" Jin sunan Meemah da yak'ira sai da zuciyarya ta amsa, batasan sanda ta kalleshi ba, idannunta na hawaye, yace " ya akai kika rame haka a kwana d'aya? Bakya cin abinci ko? Hala shiya haifar miki da zazzab'i." Ta had'iyi wani abu sannan ta kalleshi tace " meyasa kazo nan? Bayan banasan ganinka?" Jalal ya girgiza kai hawaye ya zubo mai yace " ta ina zakik'i san ganina bayan zuciyarmu na tare?" Ta share hawayenta tace " a da kenan." Jalal kalmar har ransa ta tab'a amma ya d'aure yace " bana tunanin a da ne, tunda haryanzu zuciyoyinmu basu rabu ba." Mik'ewa tai ta zauna fuskarsu na kallan juna ta goge hawayenta tace " Deen I can't be with you ko da kuwa sanka shine zai zama ajalina, mahaifinka ya cuceni, ya cuci mahaifiyata, ya cuci Dad d'ina bama haka ba ya cuci duk zuri'ata data Dad banajin zan iya yafe mai." Jalal ya kalleta cikin mamaki, idanunsa ya zaro yace " Meemah me kike nufi da kalamanki." Hannu tasa ta fara dukan kafad'arsa tana kuka tace " Meyasa zuciyata bazata tsaneka ba why?" Jalal ya rik'e hannunta yace " Meemah me mahaifina yai?ban gane ba?" Ganiyai jikinta ya shiga rawa, duk ya rud'e tare da K'iran sunan ta, ai ganiyai tayi luuu gab'a d'aya jikinta. Da karfi yake k'iran sunanta yana hawaye, Amnar ya shigo da sauri, ganin haka yasa ya fita k'iran likita. Abinda yaban mamaki, Jalal nagani ya tsuguna yana kuka kamar mace, a raina nace baka fara bama d'an saurayi. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣0⃣ Jalal ganin Seemah a sume ya rasa inda zaisa kansa kuka kawai yake, yarasa meke faruwa shikem, addu'a kuwa duk wacce tazo mai yi yakeyi, kallanta yakeyi zuciyarshi sai kuna takeyi, Ammar ne yashigo da likita da sauri, nan likitan ya shiga duba Seemah, ya samu ta dawo daidai ya kalli Ammar da Jalal yace " ba nace kar a tada mata hankali ba? A barta ta samu nutsuwa ba? Ina tsorace muku abinda zai faru inbaku kiyaye dokukin nan ba." Yana kai nan yai waje, Jalal ya kalli Ammar da idanunsa da suka sha zubar da kwalla, yace " Ammar am.........." Ammar ya katseshi da cewa " Jalal please get out." Jalal ya kalleshi cike da tausayi yace " amma......" Ammar ya d'aga mai hannu tare idanunsa taf da kwalla yace " Jalal kake kawai please. " A hankali Jalal ya karasa kusa da Seemah ya kalleta cikin tsananin tausayi da bege sannan ya juya harya kai kofa yaji muryar Ammar yace " idan kaje katambayi Mahaifinka waye mahaifin Seemah, shikad'ai ne abinda muke bukata yanzu daga gareka." Juyowa Jalal yai cikin tsantsar mamaki bai fahimci inda kalaman suka dosa ba, me suke ba Dad bane mahaifin Seemah ko me?" Dad ya gani a bakin kofa, wani irin kallo Dad yamai, Jalal yai kasa dakai tare da cewa " Yahkuri na sab'ama umarnink......" Hanya Dad ya nuna mai alamar yai waje, hakan yasa Jalal ya taka a hankali yai waje, yana fita yazauna akan dakalin gun, tare da rik'e kansa dake wainawa, agogon hannunsa ya kalla karfe 2 na dare ya buga, mik'ewa yai a hankali bayaji zama ya kamaceshi dole gobe da sassafe ya dira a birnin/gwari d'an jin me mahaifinsa ya sani dangane da abinda ke faruwa, kofar d'akin Seemah ya kalla tausayinta ya kara ratsashi, da alama yau tasan ba Dad bane mahaifinta sannan me ake nufi da Abbansa ya sani? Da alama Abba ne kad'ai yasan amsar tambayoyin nan. Seemah kam sai karfe hudu ta bud'e ido a hankali, Ammar ta kalla dake zaune akan kujera yana bacci, ta mik'e a hankali tare da yaye bargon da aka rufa mata, tai bakin kofa, a hankali ta bud'e kofar gudun karta tasheshi. D'akin Hajiya ta shiga, Dad na zaune shima yana bacci, ta karasa kusa da Hajiya tare da rik'e hannunta da hannuwanta biyu, Hajiya ta bud'e idanunta ta kalleta, Seemah hawaye suka zubo mata tai kasa da ido tace " Hajiya kiyi hakuri nasani dolene ki tsaneni, ko nice akama d'ana haka dolene in tsani duk masu hannu a harkar, sai dai nasani a kasan ranki baki tsaneni ba." Kallanta Hajiya tai da alamar tambaya, Seemah ta matse kwalla tare da kakaro murmushi tace " da kin tsaneni nasan da kin tilastama Dad ya rabu dani, da bazaki bari har ya rainani izuwa yanzu ba." Ta zare hannun hagunta ta share hawayen dake mata gudu tace " Nagode Hajiya da taimakonki, nagode sosai Allah ya saka da alkairi." Hawaye ke zuba a idanun Hajiya a hankali tasa d'ayan hannunta akan Seemah sai dai abinda takeji a kirjinta mai nauyi yasa ta kasa magana, Seemah ta girgiza mata kai tace " A'a hajiya basai kince komai." Tai ajiyar zuciya sannan tace " Hajiya na rok'eki ki yafema mahaifiyata da ni, d'an Allab ba dan mu ba." Seemah na kawo nan taji kuka na neman kufce mata, Seemah tasa kanta a jikin gadon ta shiga kuka mai tab'a zuciyar mai sauraro. Dad kam tunda ta shigo yanajinsu, kawai dai yayi shiru ne, Hajiya tasa hannu ta d'ago fuskar Seemah tare da share mata hawaye. Sun dad'e a haka kafin Ammar ya shigo da sauri, a firgice yake da alama yad'auka ko Seemah ta gudu me ko wani abun, ganinta kusa da hajiya yasa ya saki nannauyan ajiyar zuciya, Seemah ta kalleshi tare da mik'ewa. Bayan Sallah asuba su Dad sun tafi massalaci, suna dawowa suka ba kamar yanda suka barta ba, da sauri Dad ya karasa tare da tab'ata sai dai inaaaa.... Allah ya d'auki ran abarsa. _Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin_ Ba karamin tab'asu tai ba wannan rasuwa, abu goma da ashirin. Sun dawo dukansu gidan Abba anan aka mata wanka, Seemah ma ta matsa dole itama ta dawo gida. Jalal kam yana sallar asuba ya wuce tasha, a mota a zaune kawai yake zuciyarsa taf take da tunani kala kala. Sun isa birnin gwari ya hau mashin ya karasa gida, yana sauka ya tsaya a kofar gidan tare da kwankwasawa, ba'ai minti 2 ba akazo aka bud'e, ga mamakinsa kanwar mamansa ce, tana ganinsa ta saki guda ya shiga tare da cewa " Goggo yaushe kika zo?" Ai ba gama rufe baki ba yaga 'yan uwan Abba da Umma suna ta fitowa ya kallesu da mamaki yace " toh! Taran me ake haka?" Goggo ta harareshi tace " Lalai wannan Angon ba kunya, watoma da alama bakasan a taru ayi zumunci a bikinka." Jalal ya maimaita kalmar Ango? Umma ce ta fito fuska d'auke da fara'a tace " Jalal me kake a tsaye bazaka shigo ka kwashe gaisuwa ga 'yan uwa ba?" Ya d'anyi murmushi kad'an sannan ya shiga ya zauna sannan ya fara gaishesu, kowa sai tsokanarsa suke, ya mik'e tare da tambayar Umma ina Abba?, tace " ya fita d'azu zaije siyo kayan abinci." sai alokacin ya kuka da har fenti anyi a gida, badai da gaske suke ba? Yace "Zaheeda fa?" Tace " tana d'aki." Nan ya wuce ransa duk a dagule, kusa da Zaheeda ya zauna, ta kalleshi tare damai murmushi yace " Kanwata da alama kina cikin farinciki, ko duk ganin 'yan uwa ne?" Muryar Umma yaji tace " Dad'i takeji zaka auri 'yar uwarta Zainab." Jalal ya juyo ya kalli Umma yace " Wai Umma meyasa kuke min haka? Nifa ban d'auka abinnan da gaske kuke yi ba." Umma ta had'e rai tace " baka sani ba mai ya kawoka to? " Jalal yad'an furzar da iskar bakinsa yace " Zuwa nai muyi magana da Abba, ni banajin ma zan iya jiranshi ya dawo, Umma kawai fad'amin inda yake." Umma ta kalleshi tace " Ba dai cewa zakai ya janye auren ba?" Jalal yad'an juya kai yace " ni auran nan ba'a gabana yakeba Umma, abun da ke damuna yafi karfin wannan auran." Umma ta kalleshi da mamaki tace " Badai......" Jalal yai saurin cewa " Umma d'an Allah ina Abba?" Tace" Yana lambun Basiru." Jalal ya mik' e tare da kallan Zaheeda sannan ya juya, Umma ta matso kusa dashi tace " Jalal yanaga kamar ka fad'a? Sannan da alama akwai abinda ke damunka naga gaba d'aya fuskarka ta canza." Kallanta yai sannan ya runtse ido yace " Umma banaso 'yan uwa susan abinda ke damuna shiyasa nake kok'arin b'oyewa kibari inje gun Abba tukun." Tai ajiyar zuciya tace " to sai ka dawo." Jalal ya fito, sai tsokanarshi ake, shikam sai yake kawai yake musu, yana fita Goggo ta shigo gun Umma tace " Yaya Habiba nikam kamar Jalal baya farin ciki." Umma ta kalleta tace " meyasa kikace haka?" Goggo ta d'an rik'e hab'a tace " gaskiya bama haka Jalal yake ba sam, naga kamar ya canza, halayarsa ma kamar ta canza, Allah dai yasa ba wani abun bane." Umma ta kalleta sai dai ta kasa bata amsa, Addu'arta d'aya Allah yasa ba zancen nan Jalal zaina Abbansa ba. Jalal kam kai tsaye Lambun Basiru makocinsu ya isa, yanazuwa Basirun yace " yanzu kuwa yabar nan, ya koma gida." Jalal ya juya yai hanyar gida, wayarsa ya rik'e wazai k'ira ya tambaya jikin Seemah? Da sauri ya k'ira Sagir bayan sun gaisa yace "Sagir d'an Allah ka dubomin halinda Seemah ke ciki." Sagir yace " to, nan sukai sallama." © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣1⃣ Seemah zaune take kawai, a rakub'e a jikin gado, sai kallan y'an uwa take suna zuwa gaisuwa, sam ko magana batayi bare cin abinci, duk ta rame ta canza a kwana d'aya. Tana zaune tana jan carbi taji sallama, jin muryar yasa ta d'ago da sauri, Junaid ya kalleta tare da sakar mata murmushi, kuramai ido tai a hankali hawaye suka zubo mata ya matso kusa da ita tare da cewa " Kanwata ai saura kiris in kasa gane ki, wace irin jinya kikai haka?" Kallansa tai kawai ga mamakinsa sai yaga ta fashe da kuka, kallanta yai da namaki, sai kuma can yace " Seemah mutuwa fa ba'a san a d'inga mata irin wannan kukan, bare Hajiya da batasan kuka addu'a kawai zamu mata." Seemah ta d'ago a hankali tanasan mai magana, yace " anma wani irin cinwo kikai haka?" Zahra ce ta shigo ganin Mutum yasa tai kasa dakai tare da gaisheshi, Junaid ya d'ago ya kalleta yace" Badai badai ba?" D'agowa tai tare da nuna shi tace " yayana?" Kallanta yai yad'an kanne ido yace " badai badai ba?" Tace " badai yaya bane wannan?" Dariya yai yace " na d'auka kin manta inkiyar tamu." Tai murmushi tare da matsowa tace " yayana yaushe a gari?" Yace "d'azu na shigo ya hakurin mu?" Tace " Alhamdulila" Kallan Seemah yai yace " Kanwata mey........" Da sauri Zahra ta katseshi tace " tashi yaya muje ka gaida Mamie." Ya mik'e tare da kallan Seemah, nan sukai waje, Seemah ta share kwalla Allah sarki rayuwa, a da tad'auka 'yan uwanta ne na jini yanzu kuwa ta gane ashe bata da alaka da dukansu, itafa? Inane cibiyarta? Suwaye 'yan uwanta?. Jalal yayi sa'a a kofar gida yaga Abba, da sauri ya karasa gunsa, Abba ya kalleshi yace " Jalal kai nake jira ai, na shiga ciki aka sanar dani ka iso." Jalal ya kalli Abba tare da cewa " Ina Kwana?" Abba ya amsa tare da rik'o hannun Jalal yace " Nagode Jalal da baka bani kunya ba kazo tun kafin ranar bikin, nagode kwarai, Zainab ta koma gidansu acan zasuyi taron su." Jalal kallan Abba kawai yakeyi, can yace " Abba inada magana mai mahimmanci dakai." Kallansa Abba yai yace " Jalal wace magana ce haka da bazaka bari sai bayan biki ba?" Jalal ya girgiza kai yace " Abba banajin zan iya runtsawa sai naji abinda ke faruwa." Gaban Abba ne ya fad'i ya kalleshi cikin tsoro yace "Jalal me kakesan ji?" Jalal yai ajiyar zuciya sannan yace " Abba meye tsakaninka da Dad d'in Seemah?" Da sauri Abba ya juya baya gabansa ya cigaba da fad'uwa, Jalal ya kalleshi sannan ya matso ta gabansa, yace " Abba bai kamata ka cigaba da b'oyemin wani abu ba, me ka musu suka tsaneka haka? Meye tsakanin ka dasu dahar suke tunanin kafisu sannin abinda si basu sani ba?" Abba ya had'iyi yawu sannan cikin tsoro yace " Jalal banasan maganan nan na kuma hanek da karamin." Ga mamakin Abba kawai gani yai Jalal ya tsugunna a gabanshi, yace " Abba d'an Allah ka fad'amin bakasan yanda nakeji a zuciya ta bane a wannan lokacin." Abba yai ajiyar zuciya yace "naji zan sanar dakai abinda yafaru amma da sharad'i sai ka min alkawari." Zuciyar Jalal ta matsu taji komai yace " na ma Abba koma akan menene." Abba ya kalleshi idanunsa sunyi ja, yace " tun ranar da Isma'il yazu gidan nan nasan sirrin nan dole ne ya bud'u, in har kuma kanasan insanar dakai sai kamin alkawari tsakaninka da Allah cewar ko menene tsakanin mu bazai hanaka auren Zainab ranar Asabar ba." Jalal ya d'ago da sauri ya kalli Abba yace "Abba me kake nufi?" Abba yace" bazan sanar dakai ba har sai ranar da aka d'aura muku aure da Zainab." Jalal ya mik'e a zabure yace " Abba d'an Allah......" Abba ya katseshi da cewa " In har kanasan kaji to sai ka jira ranar auranka, alkawari na maka kaima kamin, haka ya kamata mu barshi." Abba na kainan ya wuce cikin gida, Jalal bai kula bane amma hannun Abba rawa yakeyi. Jalal ya naushi bango da hannunsa yana huci ya rasa mai zaiyi. Wayar Sagir ce ta katseshi, ya d'aga da sauri tare da cewa " Sagir ya Seeman?" Sagir yai shiru, Jalal yace Sagir ya kai shiru? Sagir yace " Jalal kakarta ta rasu." Jalal yafara " *Inna lilahi wa ina ilaihi Raji'un*" Nan ya kashe wayar tare da silalewa ya zauna a dandaryar kasa, hannu biyu yasa ya rufe fuskarsa zuciyarsa na k'una, wani hali Seemah take ciki? Ance in tambayi Abba mahaifinta shikuna yace sai na auri Zainab, idanu ya runste sai ga hawaye sun zubo, Seemah ya zanyi? Mutane sai wucewa suke suna kallansa. Ya dad'e a gun kafin ya mik'e ya fara tafiya, wayar Ammar ya d'aure ya k'ira, daga gun Ammar dake zaune gun amsar gaisuwa ganin k'iran Jalal yasa ya mik'e yai gefe tare da d'agawa, Jalal yai sallama Ammar ya amsa, Jalal yace " Ammar ya hakuri? Ya kuma jikin Seemah? Tanacin abinci kuwa?" Ammar yai shiru can yace" Jalal baka fahimci abinda muke nufi bane? Ko kuwa idanunka ne suka rufe?" Jalal yai shiru, Ammar ya cigaba " abu d'aya muke buk'ata agunka ka tambayar mana mahaifinka waye mahaifin Seemah shikad'ai mukesan ji daga gareka."yana kai nan ya katse wayar, tare da kasheta gaba d'aya. Jalal ya samu wani dakali ya zauna kamar maraya, kalaman Ammar kawai yake tunawa........ © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣2⃣ A goggon dake d'aure a hannunsa ya kalla, sannan ya jawo wayarsa dake gefensa, number Seemah ya kurama ido, ya bude gun da nufin aika mata da sako, sai dai sam ya rasa mai ma zai ce mata, a goggon wayar ya kalla karfe 1 na dare, ya runtse ido da nufin yai bacci sai dai inaa, sam ya kasa sai ma wani irin ciwo dakan ke yi masa, zama yai, yaji zaman ba dad'i ya mik'e tsaye can kuma ya kwanta, tunawa yai ashefa daren jiya baccin awa d'aya da rabi ya samu. Shawara d'aya ya yanke, a yanda yakejin San Seemah a ransa yana tunanin zai iya sadaukar da farincikinsa ita ta samu, indai har auren shi kad'ai ne mafitar da zaisa Seemah ta san mahaifinta ta kuma yi farinciki da ganinsa, to ba shakka zai iyayin abinda ya fi wannan, sannan shi yasani bai isa ya take hukuncin mahaifinsa ba, sai dai a da yaso gwadawa ya rok'eshi akan ya hakura da auran sai dai bukatar Seemah yasa bazai iya tambayar hakan ba. Ya rik'e kansa dake rad'ad'i tare da rufe ido, ya dad'e yana tunani kala kala kafin Allah ya taimakeshi bacci yai gaba dashi. Washegari......... Ranar Alhamis kenan ya kama kwana d'aya da rasuwar Hajiya sannan a d'aya b'angaren kuma yau ne ake shagalin kamun Zainab, sai dai itama Zainab ba wani farin ciki take sosai ba ga kawayenta sai tsokanarta suke, wai basuga tana waya da angon ba bare ma har yazo ganinta, murmushi kawai takeyi a ranta tace " inafa zanganshi bayan ba nice a ransa ba?" Jalal kam da bacci ya d'aukeshi sai karfe 10 ya tashi, shi kansa yayi mamakin ganin karfe 10, da sauri ya mik'e Alhamdulila yaji ciwon kan ya tafi, ya fad'a toilet yai wanka sannan ya zura kaya ya fito, yayi mamki daya shiga cikin gida ya taddasu suna ta hidimar su ta biki, wasu kuma suna shirin wai tafiya gidansu Amarya, Jalal ya had'e rai sannan karasa ya gaidasu Goggo ta kalleshi tace " Ango anya ma kuwa kaje ganin Amarya?" Ya d'ago ya kalleta yace " Goggo sai kace ban santa ba? Ganinta kuma name?" Goggo ta shiga tafa hannu tace "lalai wannan shine bagidajen, kai an fad'ama ko a kauye ana haka ne?tsaya ma anya kuna d'an tab'a wayar nan kaji matsalarta?" Jalal ya kalleta yace "Goggo kenan, wace matsala zata samu yarinyar dake gidan iyayenta?" Goggo ta shiga salati sannan tace " oh ni yau me nake ji haka? Ni ko d'akin da aka gyara muku ma banga kaje ka gani ba." Jalal ya kalleta zaiyi magana karar wayarshi ta katseshi, Manager d'insu ne hakan yasa ya mik'e tare da cema Goggo yana zuwa, yana fita ya d'aga wayar, Manager yacemai "Jakal ya? Ka tura takardar kuwa?" Jalal yace " oh God wallahi na manta amma bari na musu sending yanzu." Ran Manager ya b'aci yace " Jalal wai me ke damunka ne? Sam ka daina maida hankali akan aikin ka sannan yanzu kayi tafiya ba rubuto takarda nakasa fahimtar ka yanzu." Jalal yai kasa dakai baice komai ba, ganin haka yasa Manager ya katse wayar. Komawa yai kan dakalin kofar gidan ya zauna, Umma ta aiko yazo yaci abinci, ya kalli d'an aiken tare da cewa " banajin yunwa sai dai anjima." Daga bayama mik'ewa yai ya tafi can bayan gari ya zauna shi kad'ai. Rana bata karya, a yau ne ranar asabar uku ga mutuwar Hajiya haka kuma a wannan lokacin ne aka gama d'aurama Jalal aure a massalaci, kana ganinsa zakaga ya rame sosai, sannan sam ya canza Umma kam harta gaji da fad'an rashin cin abincinsa, ana gama d'aurin aure ya wuce gida ya shiga d'akinsa, abokai 'yan uwa da iyaye sai cigiyarsa sukeyi a d'au hoto sai dai an nemishi an rasa, shikam yana kwance cikinsa na mai wani irin ciwo, agoggonsa kawai yasa a gaba yana kallo. 'Yan d'aurin aure sun watse, Abba ya taho gida shikanshi farincikinsa ragaggene d'an yana tsoron abinda zai faru a yau tsakaninsa da Jalal. Yana isa kofar gida kuwa yaga Jalal a tsaye, kallan mamaki yamai yace " Jalal meye hakan? Kasan dole ne a nemeka amma shine kayi tahowarka gida ko?" Yai kasa da kai yace " Yahkuri Abba banajin dad'i ne." Abba yamai kallan tausayi duk ya canza, Jalal yace " Abba jiranka nakeyi, akan alk'awarin dakamin." Abba ya d'ago a tsorace yace "Jalal!!!." Jalal yace " Abba d'an Allah na rok'eka daka cika alk'awarinka na fad'amin d'in dakace zakai." Abba yai shiru sannan yace " muje d'akinka." Nan suka juya suka shiga soro inda d'akin Jalal yake. A b'angaren Seemah kuwa tunda ta tashi da asuba, taketa maimaita wannan ranar a ranta, lungun gado ta samu ta rakub'e duk yanda Zahra tai da ita inaa abin yaci tura ga maza duk suna gun karb'ar gaisuwa, agoggon hannunta ta cire tare da rungumeshi a kirjinta, idanunta sun kad'a sunyi jaa. Kalma d'aya ke yawo a ranta " *Deen an d'auramai aure da wata.*" Daga karshe Zahra da Aisha sai zuba mata ido kawai sukai. Jalal zaune a kasa, Abba nakan katifarsa dayake kwanciya, Jin kwankwasa kofar yasa Abba yace " Shigo." Jalal yabi kofar da kallo, Umma ce ta shigo rik"e da tire, da samiru d'aure a kai, ta ajiye a gaban Jalal, Abba yace " Jalal bismilla." Kallansa Jalal yai yace "Abba amma ni......" Abba ya katseshi yace " in har kanaso kaji sai kaci abinci, bansan inkaci wannan abincin kuma sanda zaka karacin wani ba." Jalal ya kalleshi da mamaki, Umma ta zauna a gefen Abba tare da bud'emai kwannon shinkafa da miyar da akai, nan Jalal ya fara cin abinci sai daya cinye tass sannan Abba yace " Habiba kema ki zauna ." Nan Umma ta zauna Abba ya kalli Jalal cikin tausayawa sannan yafara bashi labari tun daga farko........................ Har sai da yazo kan ranar da Fatima tazo shagonsa, Jalal hawaye kawai yakeyi na tausayawa Fatima. Abba yai ajiyar zuciya yace " Nafita kiran Isma'il ne a lokacin dana bar d'ana a shagona shida Fatima akan su jira ni, na fito naga maza guda 5 sun nufo shagon, karasawa nai kusa dasu tare da cewa d'an Allah ina sauri ne amma in kunje akwai d'ana a shagon sai ku bashi kud'in. Sai a lokacin na kuka da kamaf abu suke sha, jin warin abin ma yasa na gane wiwi ce, na d'an ja baya sannan nace " hmm kuyi hakuri nad'auka shagona zaku. Ogan cikinsu dana kula shi bayashan komai ya matso kusa dani yace " Amadu Tambaya, Fatima wai na shagonka?" Na kalleshi sai a lokacin na gane Chairman d'in garin mune wanda ake tunanin nad'awa a satin, kuma yaron gidan da Fatima ke aiki, kuma mijin da zata aura nan da kwana biyu. na kalleshi nace " Chairman nemanta kake?" Yace " Eh yanzu abokaina sukace tun d'azu suka ganta a shagonka." sam har kasan zuciyata na d'auka ko k'iranta ake ko kuma shi ke san ganinta ko saboda wani abu, na kalleshi nace " Chairman kayi hakuri yanzun nan zata koma gida......." Kafin na karasa maganata naji an kifamin mari, da sauri na kalli wanda ya naren d'aya daga cikin abokan Abdul d'in ne nace " Kai meye hakan kuma?" Wanda ya maren d'in yace " Wai Abdul kai wani irin mutum ne? Ya za'ai kana Matsayin Chairman ace wani banza mai shago har zai kalleka yad'inga ma tambayar banza? Banace ka barni nai handling d'in komai ba? Kobakasan ka d'ana ne?" Abdul ya kalleshi ga mamakina kamar me tsoransa naga yaja baya, daidai nan cikin rashin sa'a ashe d'ana na kallanmu d'an muna kusa da shagon, ganinsa mukai yazo tare da kallan wanda ya maren d'in yace " Malam me Babana ya maka?" Wata muguwar dariya ya saki sannan yace " Good haka nake so." Ban kawo komai a raina ba kawai sai gani nai an cafke min d'ana, an kuma samai wuka a wuya, nan fa ya shiga kuka. Na rikice sosai, kuka yakeyi sosai nima na shiga rokonsu,dariya suka samin na d'azun da ko sunanshi ban sani ba ya cilla ma wani d'an nawa tare da matsowa kusa dani yace " karkuma kai tunanin wannan ne kad'ai matarka tana hannunmu, ahh abin tausayi ko?" Sannan ya kalli Abdul d'in yace " kayi tafiyarka ko itama tafi karfin ka?" Abdul ya girgiza kai yace " ai ko d'aureta ne sai nayi, ina gani ya nufi shagona ina ihu akan karyayi....... Kallansa nai duk na gana rikicewa nace d'an Allah kuyi hakuri, karku lalata mata rayuwa. Naga tashin hankali a lokacin kuma abin da yaban mamaki ba wanda yazo wucewa, gashi kamar sun tambaya, ba wutar nefa gashi dama a lokacin ba gen ake kunnawa ba. Dariya suka samin dashi sannan aka kwad'ama d'ana k'otar wuka a goshi wani ihu yasa kawai sai ga jini kankace mai...... Kuka nake sosak, suka cemin matarka da alama bata ma da lafiya ko? Na d'ago da mamaki d'an ko ni ban sani ba, suka kwashe min da dariya sukace dataji azaba cemana tai wai muyi hakuri karmu bari abin cikinta ya zube. Nan na matso tare da rik'e kafafunsu, tashin hankali ne ya karune a sanda suka fito da bindiga, suka nunani sannan suka nuna d'ana sannan sukace " kaje ka k'ira ma Fatima wanda take jira kayi sauri kafin Abdul ya mata ila." Na d'auka tausaya mata sukai hakan yasa da sauri na wuce na tadda ana fitowa daga masallaci nan na gyara fuskata na shiga cikin masu fitowar, Isma'il na gani na d'aure na sanar dashi Fatima na nemansa na gaggawa. Mun taho gabana sai faduwa yake, muna zuwa zan shiga sai naga sun min alamar inzo, hakan yasa Isma'il ya shiga shi kad'ai ni kuma na je gunsu, sukamin tafi sukace yauwa ka kyauta. Na kallesu nace d'ana fa? Mugun ya tab'e min baki sannan ya kalli Abdul da nima sai a lokacin na kalleshi yanasa wando, zaro ido nai nace " meke faruwa?" Hoton D'ana aka nunomin an saitashi da wuka sannan matata ansaita ta da bindinga, sukace abu d'aya zakai ka cecesu. Kuka nake sosai ina rok'onsu, ban farga ba kawak naji karar mutanen gari, sukace cewa kawai zakai Abokinka Isma'il shiya mata fyad'e. Girgiza kai na shigayi ina kuka, mugun yace " to shikenan ka taimaki abokimka in yaso matarka da d'anka, da wanda ba'a haifa ba kwa had'u a lahira. Abba na zuwa nan yai share hawayensa, Umma ma haka, Jalal kam kukan ya kafe kaf kawai Abba yake kallo wani irin kallo daban fahimceshi ba ni kaina. Jinai cikin wata irin murya Jalal yace" Saboda tsoron kar ama matarka da d'anka ila yasa ka ce Amininka ne ya mata fyad'e?" Abba ya kalli Jalal sannan ya kara goge kwalla yace " Akan d'ana ba abinda bazan iyayi ba, ina ganin ansama d'ana wuka za'a yankashi mezai sa inkasa fad'ar kalma d'aya?" Jalal ya mik'e ya shiga jijiga kai sannan ya kalli Abba sai a lokacin wasu zafaffen hawaye suka fara zubo mai, Abba ya matsu tare da kokarin rik'e hannunsa Jalal yayi baya. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM.* *Gaisuwa ga duk Masoyan littafin nan ....I Luv u Ol*❤😍😍 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _*This Page is Dedicated to you 🅿herty😍 wish u ol the best in ur Exams..... Thanks once again*_ No. 5⃣3⃣ Jalal jikin bango ya jingina a sulale ya tsugunna hawaye ke malala a kuncinsa, Umma dake zaune itama tana kuka ta taso ta matso kusa dashi tace Jalal! Wani irin kara yayi da duk sai da suka tsorata kuka ya wuce da shi kamar wani karamin yaro, Umma tsoro ya fara kamata ta kalli Abba tace " Meyasa ka fad'amai? Yanzu in wani abu ya sameshi fa?" Abba ya kalleta cikin wani yanayi, yace " daga sanda Isma'il yazo gidan nan nasan ban isa in b'oye sirrin nan ba, da wani a waje ya fad'amai mahaifinsa yaci amanar Amininsa gwara ni dakaina insanar dashi. " _Nikaina Ayusher yanda naga Jalal na kuka sai da naji hawaye ya zubomin a hankali nayi waje d'an bazan iya zama ba._ A b'angaren Seemah kuwa bayan mutane sun ragune Ammar ya shigo d'akin, ya kalleta a rak'ub'e a gefen gado, tausayinta ya kara kamashi ya matso inda take tare da d'agata, kallanshi tai kamar wacce hankalinta baya jikinta tace " Ya Ammar am d'aura ko?" Kallanta yai idanunsa suka ciciko, hannu yasa a kafad'arta yashiga jijigata yana cewa " Get hold of your Self Seemah, please. " Ya d'ad'e yana jijigata kafin ta kalleshi tace " Yaya ya zanyi?" Yace " Seemah England zamu koma ranar bakwai inajin shi kad'ai ne zai sa ki manta komai." Ta d'aga kai tace " na yarda Yaya ni kaina haushin kaina nakeji." Nan ya mike yai waje, bai dad'e ba sai gashi ya dawo rik'e da plate na abinci, Zama yai kusa da ita tare da d'ebo abinci a cokali da niyyar ba ta, ta kalleshi sannan ta amshi cokalin tace " Zanci da kaina Oppa." Murmushi ya mata sannan ya mik'a mata spoon d'in, ta fara ci, yace " Matar Dad tazo ta dubaki?" Ta d'an tab'e baki har zatai maganar rashin kunya ta tuna ashefa ta fita matsayi yanzu, tai kasa dakai tare da cewa " Ta l'eko d'azu." Ammar yai d'an karamin tsaki yace " bansan ya akai Dad ya aureta ba, sam batada kara." Seemah tai shiru can tace " Ka manta Yaya? It is all my fault, bakaji Dad nacewa saboda ni ya aureta ba? Na sani saboda yanaso akula da......." Kasa karasawa tai saboda hawaye, Ammar ya kallera yai murmushi yace " Oh yazanyi da wannan kanwar tawa mai saurin kuka?" Ta kalleshi tare da share hawayenta tace " Yaya?" Yad'an rangwab'ar dakai yace " Seemah rufe idonki." Ta kalleshi tad'an turo baki kad'an, sannan ta rufe, hannu yasa a aljihunsa, sannan yace "bud'e." Da sauri ta bud'e tanasan ganin menene, kwalin waya ya mika mata, ta kalli wayar Iphone 6 ce, tace " yaya inafa da waya?" Yace " Dad ne yace kar abaki waccan." Tai murmushi sannan ta amsa tace " Thanks Bro." Yai murmushi shima yace " Ahhh naji dad'i kinyi murmushi, sannan kinci abinci." Ta kalleshi tace " saboda Deen ne ba'asan abani d'ayar wayar?" Ammar ya kalleta bai amsa ba, ta kara murmushu tace " karkadamu yaya, yama za'ai in sake ganinshi? Sannan bazan bari effort d'inka ya tafi ba yanda kasa naji zuciyata tayi sanyi ba." Ammar kallanta kawai yake, ta kara sakar mai murmushi sannan ta hure mai ido tace " Yaya kallan fa?" Mik'ewa yai da sauri tare dasa hannu a aljihu duk ya rikice yace " Ehem dama dama fita zan d'anyi, nan zafi ko bakya ji?" Batasan sanda tasa dariya ba, tace " Zafi kuma yaya? Nan d'in?" Kallanta yai yace " Seemah just now dariya kikai ko? Badai hallucination na gani bako?" Tai kasa dakai tana murmushi tace "kai yaya kai d'in ne wai zafi." Kallan yanda take murmushi yasa ya farajin zafin na karuwa, da sauri yai waje, yana fita daga d'akin ya fara furzar da wata iska yanacewa " Cool down Ammar." Can kuma yace " meke damuna?" Junaid ne ya dafashi yace " Ammar agidan gaisuwar ba kunya kake soyayya?" Kallan Junaid yai a tsorace, Junaid yai murmushi yace " Ya Habib ya fad'amin komai karka damu." Ammar yai ajiyar zuciya sannan ya kuma kalleshi da mamaki yace " ban gane soyayya ba kuma?" Junaid yace " in ba soyayya ba me kake a d'akin?" Ammar ya kalleshi da mamaki yace " What? Seemah ce fa a d'akin." Junaid ya d'an jinjina kai yace "ai sanin Seeman ce yasa na fad'a, Ammar ka nutsu ka tambayi zuciyarka, wacce irin soyayya kake mata?" Junaid na kainan ya juya yai gaba yabar Ammar da binsa da kallo. Jalal kam bayan su Abba sun fita yana nan dai a gun da yake, ya dad'e agun kafin ya daina kukan, yafara cewa " ya zanyi Seemah?" Jin ba amsa yasa yai shiru can yace " Abdul?" Cikin zafin nama ya mik'e yai waje, a waje yaga Abba, Abba na ganinsa wani dad'i ya kamashi da alama harya sauko kenan, Jalal ya kalleshi cikin d'aure fuska yace " Abdul d'in yana ina yanzu?" Abba ya girgiza kai yace " Jalal ka rufamin asiri d'an Allah wannan mutumin yafi karfin mu bani ba har Isma'il d'in dayake da kud'i." Jalal ya kalli Abba yace " Abba ina Abdul d'in yake yanzu? Dole ne ya nemi yafiya agun Seemah da iyayenta, kaima kuma Abba dani dolene mu nemi yafiya, duk da ba lalai a yafemana ba, wayasan wace irin rayuwa suka shiga akan kalaman nan guda d'aya?" Abba ya kalleshi a tsorace yace " Jalal ninaji zan bada hakuri ko mai za'amin bazan damu ba amma Jalal ba ruwanka da harkarnan, dama tun farko baka san komai ba, d'an haka yanzun ma ka nuna bakasan komai ba." Jalal idanunsa suka ciciko yace " Me kace Abba? In nuna bansan komai ba? Taya zan iya?" Hawaye suka zubo mai yacigaba " akan Mahaifiyar Seemah ne fa da kuma Wanda ya rik'eta kamar 'yarsa Amininka kuma." Yai ajiyar zuciya sannan yai d'an murmushin yake yace " Tunda naji labarinnan nasan ban cancanci auran Seemah ba, ko da kuwa iyayenta zasu amince dani, Ammar shine ya dace da ita koda har karshen rayuwata zan kasance cikin tsananin begenta bazan kuskura inkara gangancin cewa ina santa ba." Kalaman Jalal sun ratsa zuciyar Abba shima ya share kwallarsa yana kallan Jalal, cigaba da magana yai da cewa " Shiyasa nakeso ko ban aureta ba insamu in mata wani abinda zaisa ta rage tsanar datamin hakan ne zaisa ta manta dani." Ya kara share kwalla sannan ya kalli Abba yace " Abba kataimakeni inma Seemah abu guda d'aya a rayuwar duniyar nan." Abba bai san sanda ya rungume Jalal ba, yace " Jalal a koda yaushe ina alfahari dakai, kafi wannan mahaifin naka tunani mai tsawo." Jalal idanu kawai ya runtse, shikad'ai yasan rad'ad'in dayakeji a ransa. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣4⃣ Jalal ya d'ago ya kalli Abba yace " Shugaban kasa ne shi ko me?" Abba ya kalleshi yace "Jalal Sanate ne yanzu wanda kuma ake ji dashi haka kuma mutane na sanshi, ina tsorace maka abinda zai biyo baya." Wata muguwar dariya Jalal yai wacce sai da abin ya tsorata Abba, sannan ya tsagaita yace " mene? Sanate? Wasu mahaukatan ne suka zab'eshi? Kuma shi ko kunya mutumin dabai san darajar d'an Adam ba harya iya cigaba da siyasa?" Abba yai ajiyar zuciya yace " nidai yanzu kabar komai kaga gobe za'a kawo Zainab." Jalal ya kalli Abba shi harya manta da wani auren Zainab, ya juya kai batare dayace komai ba. Ganin haka yasa hankalin Abba yad'an kwanta, mutane mak'ota ne suka fara zuwa halan yasa Jalal ya koma ciki, shiru yai yana tunani can ya d'auko wayarsa yafara duba senate na kasa, kan wani yazo *ABDULLAHI UMAR* Ya kalli hoton mutumin dakyau gabansa ne ya fad'i ba shakka wannan shine mahaifin Seemah bawai kama sukai sosai ba sai dai in har ka kalleshi ka kalli Seemah zakasan akwai alak'a ta jini sannan ga tarihinsa daya karanta, ransa yakai k'oluluwar b'aci sanda yaga yanda ake ji dashi da kuma yanda mutane ke masifar sanshi wasu har so suke ya tsaya a matsayin shugaban kasa na zab'e ma gaba. Haushi ya ishi Jalal ya cilar da wayarsa kan gado sannan ya mik'e cikin zafin rai kawai wayarsa ya d'auka ya fita. Tasha ya nufa kawai ya shiga motar abuja, sam idanunsa sun rufe. Dad da Abba da kuma kawo ne zaune a d'aki, Abba ya kalli kawu yace "Wani hukunci ka yanke?" Dad yai saurin cewa " Kawu nidai dan Allah kadawo nan da zama me zakayi a suleja yanzu? Dama can ba garin mu bane." Kawu yai shiru cam yace " naji amma dai kai Isma'il kaima ina fatan kadawo nan da zama kenan?" Dad ya d'ago ya kalli Kawo sannam ya kalli Abba jikinsa yai sanyi, Abba yace " gaskiya kam ya kamata kaima ka dawo kazauna anan." Dad a hankali ya furta "karatun Seemah fa? Ina tunanin yimusu baiko itada Ammar sai in koma can inyaso in ta gama karatun sai mu dawo gaba d'aya." Abba yai shiru can kawu yace " naji bayananka sai dai nima na yanke nawa hukunci na." Ya kallesu sannan yace " In akai bakwai d'in marigayiya nakeso wahsegari ai baikon Junaid da Ammar, in yaso sai ka d'auki matarka ku koma England har zuwa sanda zata gama karatu, da zarar ta dawo za'a had'a ayi auren." Dad ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan can ya kalli Abba sannan ya kalli Kawu yace " Amma junaid yanada budurwa ne?" Nan Abba ma ya kalli kawu da mamaki, Kawu yai murmushi yace " ba wani taro za'ai ba saboda rasuwar da akai mana kawai dai za'asa rana ne a kuma bada kud'in gaisuwa." Abba ya kalli Kawu yace " amma kawu......" Kawu yai murmushi yace "Mahaifiyarku babban burinta bai wuce tayi had'in aure a tsakanin 'ya'yan ku ba, tunda shi Ammar yanada Seemah shiyasa nake tunanin had'a auren Junaid da Zahra." Kallan juna Dad da Abba sukai, Kawu yace " na amince da auran Ammar da Seemah sai dai kamar yanda mahaifiyarku tace dole ne kafin ranar auren asan mahaifinta." Dad yai murmushi tare da cewa gaskiya ne naji dad'in had'in nan, Abba ma yai murmushi. Jalal sai bayan magrib ya iso Abuja, wayar Umma ce ta shigo sai alokacin ma yai tunanin ashe bai fad'a musu ba, da sauri ya d'aga wayar yace " Umma?" Tace " Jalal kana inane? Tun d'azu ana nemanka." Jalal ya kalli cikin garin Abuja yace " Umma kiyi hakuri d'an Allah wani uzuri ne ya tasomin ina Abuja yanzu." Tace " Abuja kuma?gobe fa za'a kawo Amarya." Jalal ya runtse ido jin an anbaci Amarya yace " kiyi hakuri Umma." Tace " naji amma ka tabbatar gobe ka dawo da wuri banasan mutane su fara zargin wani abun." Yace "insha Allah." Nan suka kasje wayar. Yana sauka yai sallah sannan ya nemi d'an machine yace " kasan gidan Sanate Abdullahi?" D'an machine d'in ya kalli Jalal daga sama har kasa sannan yai dariya yace " kasan me kake cewa kuwa?" Jalal ya had'e rai yace " mahaukaci ne ni dabazan san me nake cewa ba ko me?" D'an machine yace " A'a muje inkaika." Aransa yace ko mai aiki ne a gidan? Sun isa wata had'ad'iyar unguwa manyan gidajen dake gun da kuma tsarinsu zai tabbatar maka da guri ne manyan mutane. A kofar wani had'ad'an dank'araren gida yai parking, Unguwar shiru kamar ba mutane, d'an machine ya juya yatafi bayan ya cemai nan ne gidan. Jalal yabi gidan da harara yace " Dama irinkune masu hana kasar mu cigaba, kun tara zunubai a kanku kuma kunzo d'an yaudarar mutane." Kofar Gate d'in ya karasa tare da tunanin ta inda zai fara, wani security ne ya fito tare da kallansa yace " me kake anan?" Jalal ya kalleshi yace " Gidan Sanate Abdullahi ne?" Mutumin ya kara had'e rai yace " eh amma kai waye?" Jalal ya d'an daure tare da sa hannu a aljihu yace " nemansa nakeyi." Security d'in ya jara kallansa yace "baka da hankali ne? " Jalal yace " what?" Nunashi da bindiga yai irin doguwar nan yace " waye kai?" Nan fa idanun Jalal sukai tsuru tsuru, husur security d'in ya hura nan da nan wasu securities d'in suka fito, ya kalli Jalal yace " a dubashi da kyau ban yarda da shiba." Jalal haka suka ririk'eshi suka shiga lalubamai jiki kamar yai ihu d'an bakin ciki, suna gamawa suka sakeshi tare da cewa " nothing suspicious Sir." Ya kalli Jalal yace " tashi ka kara mai karkuma insake ganinka anan." Jalal ya dake zuciyarsa yace " ganina kuwa dolene d'an bazan tafi ba harsai naga mutumin gidan nan inkuwa kuka hanani to sai dai ku fita da gawata." Mutumin ya kalli Jalal yai murmushi yace " I wish kayi karatun Soja da anyi jarumi." Jalal ya juya kai, mutumin ya cigaba sai dai inhar baka tafi ba zakuwa a fita da gawarka. Jalal ya kara dakewa tare da jingina da katangar gun, ran mutumin ya b'aci ya d'aga kasan bindiga zai bugama Jalal, sai sukaji karar horn, da sauri suka jeru aka bud'e gate, motoci uku ne suka shigo Jalal ya kalli motocin har sukai parking sannan wata yarinya ta fito daga motar sanye da riga da wando sun matseta, tana tafe tana jijiga kai alamar rawa, Jalal yaja karamin tsaki yace "Allah ya shirya." Juyowa tai d'an taji alamun kamar ana kallanta caraf suka had'a ido da sauri Jalal ya d'auke idanunsa, d'an takaici aransa yace "yanzu wannan kanwar Seemah ce fa ko?" Baisan tazo kusa dashi ba sai jiya tace " waye wannan?" Securitin ya kalli Jalal yace " Sorry madam." Yanda take magana ma ya tabbatar ma Jalal ba'a hayyacinta take ba, ta nuna Jalal tace " Kai." Jalal ya kalleta tare da girgiza kai yarinya karama dabata wuce shekara 18 ba amma....... Zata sake magana taji daga saman beni ance "Me kikeyi anan?" Da sauri Jalal ya d'aga kai, baban mutum ne da dukda baikai su Abba ba amma kasan baba ne, Jalal ya kara cusa ido ya kalleshi tabas mutumin da yake nema ne. Dabara ce ta fad'o mai, Yarinyar zatai magana Jalal da karfi yace " Sannu Dad dama cewa tai inzo gunka akan maganar soyayyarmu." Securities suka kalleshi da mamaki itama ta juyo duk da a bige take ta nuna shi sannan ta nuna kanta, murmushin rainin hankali ya mata yace " Ko Sweety?" Kai ta d'aga sannan ta kalli Mahaifinta wanda ransa yai mugun b'aci yace ku shigo ciki. Jalal yai wani murmushin rainin hankali sannam ya kalli Securities d'in yace " Sorry bansanar daku da wuri ba." Fatan Alkairi gareku " _*MUM HAMRA, MOM FARHAN, FRESH, AGRA, RAHANCY DA MOM FAROUK*_ " Hope anyi weekend lafiya.......😍😍 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com *This page is for you Ramalurv......*😍😍😍😍 No. 5⃣5⃣ _I am really sorry jiya da shekaranjiya kun jini shiru, wani uzuri ne ya hanani typing. ......luv u ol_ Jalal ya kalli yarinyar ya mata wani murmushi yace " muje ko? Ta kalleshi sai dai idanunta nuna mata wani guy datakeso yake, hakan yasa ta d'aga kai da sauri tare da natsowa tana k'okarin kamamai hannu, Jalal yad'anyi baya tare da cewa "kiyi gaba ina binki." Tad'an tab'e baki kafin tai gaba, wani tafkeken falo ta bud'emai ya shiga da sunan falon baki sai dai duk dakiya irin ta Jalal sai da jikinsa ya amsa d'an kyan falon ya wuce inda mai karatu zaiyi tsamani, ta nuna mai kujera, Jalal ya zauna tare da karabin falon da kallo, sam ya shagala baiyi tsamani ba yaji mace ta zauna kusa dashi tare da sakalo hannunta, zabura yai ya mik'e cikin mamaki yace "me kike yi hakan?" Ta tab'e fuska kamar zatai kuka, jitai ance tashi ki shiga ciki, atare suka kalli mai maganar, ta mik'e tana layi tai ciki shikuma Jalal ya sake kuramai ido. Har mutumin yazo ya zauna tare da kunna tv Jalal na tsaye sai da yace " zauna mana." Sannan Jalal ya farga tare da zama a kasa, yace "Ina wuni?" Mutumin bai amsa ba yabi Jalal da wani kalan wulakanci sannan yace "kaine kesan Huda?" Jalal a ransa yace Huda sunanta? A fili ya d'ago ya kalleshi, zaiyi magana taji yace " Naji dad'i dana ganka haka, dama nafisan talaka wanda yake nema, yanda duk abinda na gindaya mai dole ne yabi, d'an haka ka sanar da iyayenka d'an nima na gaji da wannan iskancin nata da jamin magana datakeyi, a d'aura muku aure sai in turaku Australia kuje can kuzauna har karshen rayuwarku." Jalal ya d'ago ya kalleshi da tsananin mamakin kalaman fayake furtawa a matsayinsa na mahaifinta. Daurewa yai tare da cewa " niba saurayinta bane sannan ni maganar danazo ma da ita......." Jiyai an katseshi da cewa " what? Kaikasan ko ni waye zaka rainamin hankali? Da kace gunta kazo yanzu kuma me? Ko dama ba da aure kake santa ba?" Ya mik'e yana kare ma Jalal kallo, Jalal ya dake tare da d'agowa ya kalleshi yace" akan maganar d'aya babbar 'yar taka nazo." Kallan mamaki yamai yace " Da alama bakasan ma mai kazo yi ba, bayan huda ragowar kannanta maza ne guda uku sai karama yanzu wacce ko shekara 4 bata kai ba." Cikin takaici ya fara kokarin juyawa. Jalal gani haka yasa yai saurin cewa " Ka manta Fatima ne? Ta garin birnin/gwari?" Da sauri ya juyo ya kalleshi idanunsa suka kad'a da sauri ya dawo kusa da Jalal ya d'agoshi tare da rik'emai kwalar riga cikin fad'a yace " Who are you? D'an jarida ne kai?" Har zuciya Jalal yaji tsoro sai dai da ya tuno Seemah sai ya dake yace " Ni ba d'an jarida bane, Sunana *JALAL* D'an gidan Amadu mai shago dake garin birnin/gwari." Sakeshi yai sannan yace " What?" Jalal ya gyara tsayuwarsa, yace " 'yarka tananan lafiya agun mutumin da kuka ma sharri ya rik'eta, sai dai ko bata fad'a ba nasan itama tanasan ganin mahaifinta." Wata mahaukaciyar dariya Jalal yaji an fara mai kallan Abdul yai cikin tsoro, Ya dad'e yanayi kafin ya tsagaita yace " What?'ya ta?" HA HA HA HA Ya cigaba " ko a da ba 'yata bace banga dalilin dazaisa yanzu ta zama 'yata ba." Jalal yai ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna a kasa, yace " ka manta Fatima fa wacce kuka ketama......." Tsawa ya dakamai yace " na keta mata ko Isma'il ya keta mata?" Jalal ya d'ago cikin mamaki yace " me yasa kana babba kakesan take gaskiya? Me yasa bakajin kunyar karyata abinda kasan tabbas shine gaskiya?' Ya kalli Jalal yace "in ma turo ka akai ko d'an kanka kazo sai ka kama hanya ka fita, duk duniyar nan banga wanda zaizo ya wargazamin harkar siyasa ta dana shiryata da gumi na ba, dan rainin hankali sai da nakai wani matake sosai ina shirin kara hawa sama shine zakazomin da zancen banza d'an kasamin bak'in jini gun mutane? Da can bakuzo ba sai yanzu?" Ya nuna Jalal da yatsa yace " Wallahi kaji ma fad'ama ba 'yataba? Ba kuma matata ba ko mahaifiyata bata isa ta kawomin cikas a harkar siyasa taba in kyaleta bare kai da wata yarinya daban ma santa ba, in kud'i takeso kaje kace ta fad'i ko nawa ne, Ni Abdullahi nad'au alkawarin ba ta." Jalal wani irin kallo yake binsa dashi na tsananin ban mamaki da kuma tsoron furucinsa, wani irin mutum ne wannan? Siyasa ce ta maidashi haka ko kud'i ne? Ko kuma dama can haka yake?" Kafin Jalal ya k'okarta yai magana haryakai bakin kofa, Securities ne suka shigo suka kalli Jalal sukace " fito ko mu fitar dakai." Jalal ya kalli mutumin cikin takaici ya dake ya matso kusa dashi kad'an yace " Wallahi kaji na rantse maka in dai ina raye sai ka tsuguna a gaban Seemah ka nemi yafiyarta da abinda kama mahaifiyarta, idan kafi karfi na ai bakafi karfin hukuma ba, Allah kuma na tare dani kajira ka gani." Dariya Abdul yai tare da zaro 'yan bandir d'in dubu d'aya ya mik'amai yace " Daga kai har yarinyar har hukumar bakufi karfin wannan ba." Jalal cikin takaici yake kallansa ya kakaro murmushi yai sannan yace " in kafi karfin hukuma ai baka fi ta Allah ba." Yana kainan yai waje. Ko securities d'in bai kula ba ya fita, kafa kawai yake sawa, yana tafe yana mamakin abinda idanunsa suka ganemai, kuma kunnensa suka jiyemai, a hankali wasu kwalla suka zubo mai, a fili yace " Seemah ya zamuyi?" Seemah kam tana zaune a kan gado rik'e da waya, tarasa abinda ke mata dad'i, d'azu Zaid yazo yace mata wai za'a sanya musu rana da Ammar, itakam ta rasa mema zatayi, motsin bud'e kofa ne yasa ta kalli kofar, Dad ne ya shigo tare da sallama, ta amsa tana neman kakaro murmushi, ya karaso kusa da ita ya zauna tare da kamo hannunta yace " me kikeyi anan bayan kowa na falo?" Tai kasa dakai batare da tace komai ba, yai murmushi yace " Kinji labari?" Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace " name fa Dad?" A ranta kuwa addu'a take Allah yasa ba zancen Zaid yake nufi ba. Dad ya sake murmushi tare da shafa mata kai yace " burina ya kusa cika Seemah, babban burina bai wuce inga kin auri d'aya daga cikin 'ya'yana ba, na sani kuma kowa ya sani Ammar ne yafi dacewa dake, shiyasa nakesan ki daure kicire san Jalal a ranki." Seemah jitai kafarta na rawa da sauri ta hawuda ita kan gado kar Dad ya gane, ta kakaro murmushin yake sannan tace " Dad nasani ya Ammar zai kula dani sosai. " Dad yasa dariyar farin ciki yace " ko? Ashe kema kinsani, shiyasa muka yanke za'a samuku rana sai mukoma ki karasa karatunki sai ai auren." Tai murmushi tare da cewa hakan yayi Dad, burina bai wuce inga nasanyaka farinciki ba." Takarasa maganar cikin rawar murya. Dad ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "kicire komai a ranki ki koma yanda kike da nakuma gode sosai da amincewar da kikai." Ta d'ago tare da girgiza kai tace " nice da godiya Dad koda ace zan bauta maka har karshen rayuwata banaji zan biya kwatan abinda kamana nida mahaifiyata." Dad cikin wasa yace "oh ni Seemah yaushe zaki daina maimaita abin nan?" Tai kasa da kai tana murmushi ya mike ya fita ta bi bayanshi da kallo tare da cewa "Deen yazanyi?" Jalal tsaye a kofar gidan Abba yanaso ya musu gaisuwa sai dai inaaa kunyar ma shiga yake in ya tuna abinda ya faru, gani yai an dalleshi da fitila, hannu yasa yad'an kare fuskarsa, a hankali mai fitilar yazo kusa dashi ya nuna shi da yatsa tare da kwashe wa da dariya yace " I am right kaine." Yafad'a tare da nuna kansa alamar naushi. Jalal ya kalleshi sannan yai 'yar dariya yace" ashe baka manta ba." Zaid yace " ya za'ai in manta bayan an nemi a gurd'eni?" Jalal yace " Kayi hakuri time d'in....." " baka hayyacinka ne saboda kishi ko?"Zaid ya karasa mai. Jalal yai murmushi baice komai ba, Zaid ya rik'e hannunsa yace " muje ciki kuyi sallama da Seemah an kusa sa mata rana." Bawai baiyi tsammanin ranar zatazo bane, bawai kuma tsoron hakan yake bane, bawai kuma baisan hakan a faru bane a'a shi aganinsa hakan ne daidai sai dai jin kalmar ya sa ya ja burki ya tsaya, gabansa ne yashiga fad'uwa, idanunsa suka canza kala, Jalal ya daure yace " dare yayi mubari sai gobe nazo." Zaid ya haska agoggon hannunsa yace "karfe 8 da rabi shine dare? Tab lalai inbaka gantaba yau banaji zaka kara samun wani lokacin." Jalal ya kalli Zaid sannan cikin sanyin murya yace " muje." Yana tafe yana " *_INALILAHI WA INA ILAHIHI RAJI'UN_*" har yai sa'a gaban nasa ya daina fad'uwar. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣6⃣ Jikin Jalal yai sanyi haka suka shiga gidan, Zaid yace " ka ga ka nausheni ashe kaima gaba kai za'a nausa?" Jalal yai murmushi yace " hakane dama, to amma karfa mu shiga cikin gidan ka d'inga cewa na nausheka." Dariya Zaid yai yai alamar zip a bakinsa, Jalal yai murmushi, sun shiga falon mami, mata me 'yan uwa a zaune, nan Jalal ya tsugunna kansa a kasa ya gaishesu, suka amsa suna kallansa, ya musu ya hakuri, Zaid ne ya kalli mami yace " mami kin ganeshi? Jalal d'in........" Kafarsa Jalal ya mintsina da karfi, Zaid yai 'yar kara tare da kallan Jalal, da sauri ya mik'e yace " Sai da safenku." Ya fad'a yana kallan Zaid, muryar mami suka ji tace " Ka kaishi ya gaida su Abbanka." Jalal ya kalleta jiki a sanyaye, da alama ta ganeshi tunda sun had'u a asibiti, Zaid ya kalli Jalal yace muje ko? Nan suka wuce falon Abba, a hanya Jalal ya kalli Zaid yace " d'azu mai kake san fad'a?" "AUUUU wannan? Hmm dama cewa zanyi Jalal d'in Seemah in na fad'a za'afi ganewa." Jalal ya kalleshi cike da mamaki yace " mene? Jalal d'in Seemah?" Dagewa yai ya takamai kafarsa da karfi Zaid sai da yai 'yar kara yace " Wai ni menai?" Girgiza kai Jalal yai yace " lalai Zaid mema kai kake tambaya? Da alama........." Ammar ne ya karaso gun yana cewa " Zaid meye hakan?" Ya fad'a yana kallan wanda ke tsaye, kalan kallo suka shiga yi, Jalal ya daure tare da mik'a mai hannu, Ammar ya mik'amai shima suka gaisa. Jalal ya kalli Zaid sannan ya kalli Ammar yace " Gaisuwa nazo." Gyad'a kai yai alamar gamsuwa sannan ya nuna mai kofar falon yace " muje?" Nan suka shiga su uku tare da sallama, Abba, Dad, da kawu suna zaune a falo ga Junaid a kasa da alama nasiha ko fad'a ake mai, jin sallama yasa suka amsa, Junaid ya kalli Kawu yace " Zan rik'eta amana insha Allah." Yana kainan ya maida kallansa kansu Ammar, Zaid ne ya fara shigowa, sai Ammar sai Jalal a baya, dukansu suka canza fuska shikam Junaid kallan Jalal yai nan suka karasa suka zauna a kasa. A hankali Jalal ya gaidasu, suka amsa kamar basa so, ya musu ya hukuri, nan ma suka amsa kamar d'azu, sunyi shiru a falon kafin Junaid yace " daga ina?" Jalal ya kalleshi suna kamada ya Habib hakan yasa ya gane shine d'ayan yayan Seema, mik'ewa yai a hankali ya dawo sautinsu Dad a hankali yakai gwiwowinsa kasa, kallan mamaki suka mai, idanun Jalal suka cicoko ya d'ago a hankali ya kalli Dad yace " Nasani banida bakin magana, bankuma san da wacce kalma zan fara ba, da ace abin bai faru bane shine zan sami karfin gwiwar yin magana." Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba" na sani dani da mahaifina bamu da bakin da zamu nemi yafiya daga gareku, sai dai.......sai dai....." Hawaye ne yafara zubomai hakan yasa ya kasa karasa maganar, kansa ya durkusar a kasa yana hawaye sosai, dukansu tausayinsa ya kamasu, Junaid ma ya gano shine Jalal d'in, Dad yanasan Jalal tunsanda aka haifeshi, ganinsa cikin wannan yanayi yasa shikansa yaji idanunsa sun ciciko. Ammar mik'ewa yai yaje kusa da Jalal a hankali yace " Tashi mu tafi." Jalal ya runtse ido, ba tare da ya motsa ba, Ammar ya kalleshi cikin tausayawa, Zaid ne ya mik'e shima ya kalli Jalal yace " Katashi ka tafi Jalal." Nan ma bai motsa ba, Zaid ya kalli su Dad cikin b'acin rai d'an shi baisan meya faru ba, yace " Abba shiya muku laifi? Me yai? Meyai muku da zai tsugunna yana neman yafiya amma dukanku ku shareshi? Bayan yarinyar dayakeso take sanshi kun......" Da karfi kuma cikin tsawa Jalal yace *ZAID* kowa sai da ya kalli Jalal, Zaid a zuciye yai waje, a zahiri shikam ya kasa gane menene dalilin dazai sa a hana yarinya yaron da takeso. Jalal yai ajiyar zuciya tare da kara share hawayensa ya kakaro murmushin da kana gani kasan na bakin ciki ne ya kalli Dad yace "Dad an d'auramin aure." Kallan sa sukai su dukansu, ya sake murmushi sannan ya kalli Ammar yace " Ammar ina tayaka farinciki, naji an kusa sa rana." Ya sake wanni murmushin tare da goge kwalla ya maida kallansa kansu dad yace " Dad Allah yasanya alkairi, naji dad'i." Hawaye suka kara zubomai, yace " Bakomai in har zuciyarka bazata iya yafemin ba, na sani wannan wani gyambo ne da ke zuciyarka, tunda Amininka ne ya cuce ka." Yai murmushi har hakoransa suka fito, ya share hawayensa sannan yace " Amma nikam a kasan zuciyata nayi tunanin wani abu guda d'aya, naji dad'i daya kasance kaine ka raini Seemah har kawo wannan lokacin, da Allah ne kad'ai yasan wace rayuwa zatayi a gidan wannan mutumin da zuciyarsa ba imani." Ya share kwalla sannan yace " in na duba abin ta fuskar daya kamata sai inga Allah ne ya taimaki Seemah......." Dukansu tausayin Jalal ya ratsasu sosai, dan Dad sai daya kauda kai ya share kwalla a fakaice, Junaid ma idanunsa sun ciciko, Ammar kam shima hawayen yakeyi, a hankali Abba yace " Kasan mahaifinta ne?" Jalal ya kalli Abba yana hawaye yace " nasanshi, sai dai ba amfani a sanin nashi." Dad ya mik'e yazo kusa da Jalal yace " Me kake nufi?" Jalal yai murmushin takaici yace " Dad karka damu, bazan iya fad'a muku ko waye a wannan lokacin ba, sai dai nama Ammar alkawari, kafin a d'aura masa aure da Seemah sai mutumin nan yazo da kansa yaba Seemah hakuri koda kuwa hakan shine zai zamo abu na karshe dazanyi a rayuwa ta." Dad ya kalleshi cikin tsananin tausayawa, Ammar ya share kwalla ya kalli Jalal yace " kar ka kuskura kayi abinda zai jama matsala a rayuwa da sunan alkawari." Jalal yai murmushi, ya mik'e yazo kusa da Ammar ya dafashi, baice komai ba yai hanyar kofa. Zaid kam yana fita gun Seemah yaje, tana zaune da waya tana rubuta sunan Jalal sai ta goge, ta sake ta kuma sake gogewa, tafi hour 1 tana abu d'aya, Zaid ya shigo ya kalleta yace " Seemah albishir?" Kallansa tai batace komai ba, yace " Jalal yazo yana gunsu Dad gwiwowinsa a kasa." A zabure ta mik'e ta zauna tare da cewa " Deen?" Deen? Deen d'i.....? Zaid ya d'aga mata kai, fita tai da sauri d'an ko mayafi ta manta bata d'auka ba, sai datakai kusa da falon ta tuna ashe fa sun rabu, hartayi alamar juyawa taji motsin bud'e kofar falon, tsayawa tai cak ta baya gabanta na dukan uku_uku, Jalal shima yana fitowa daga d'an nesa kad'an ya kalleta, gabansa ne ya fad'i a hankali Seemah ta juyo, cikin tsoron wanda zata gani, Jalal ma idanunsa na kanta. Tana juyowa suka kafe juna da ido, dukansu idanunsu ya ciciko da kwalla, Seemah jitake kamar taje ta rungumeshi, a hankali Jalal ya fara takowa, suna kallan juna, har yazo kusa da ita kad'an, ya fara kokarin maida kwallarsa tare da kakaro murmushi ya rasa me zaice mata, itakam kallansa kawai take. Can ya dake yace " Long time?" Ta kalleshi tare da share kwalla tace " ka rame" Yai murmushi yace " kema." Ta d'an d'auke idanunta, a hankali yace " bantab'a tunani zan ganki ba." Ta d'ago ta kalleshi tace " nima bansan ya akai nazo nan ba." Murmushi mai cike da tausayin juna sukama kansu, ya kalleta yace " an kusa ko?" Kai ta d'aga mai, yace " Congrats. " Itama tace " anyi ko?" Shima kai ya d'aga mata, ta share kwalla tace " I see." Shiru sukai suna kallan juna can Jalal yace " bakya cin abinci ko?" Ta kalleshi batace komai ba, yace " do you not resent me?" D'agowa tai ta kalleshi, ya jinjina kai yace " dole ne ko?" Kallansa kawai take batace komai ba, yace " bazan nemi yafiyarki yanzu ba, sai na cika alkawarin dana d'auka." Ta bud'e baki zatai magana, taga Ammar ya fito daga falo, cak ya tsaya daga nesa kawai yana kallansu, itama kallanshi takeyi, hakan yasa Jalal ya juya........... Ruguntsemi sai ran sallah🎧 Ruguntsemi sai mata🎹 ranar bikinmu akwai shagali Ruguntseminmu da nairori🎧😂 oh ni Ayush ina ganin haka kawai ma tuno wakar daa....... © *THE MEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣7⃣ Jalal ya kalli Ammar sannan ya juyo ya kalli Seemah jikinsa ya kara wani yin sanyi, murmushi yama Seemah sannan a hankali cikin wata murya yace " Nagode Meemah da duk abinda ya faru bai hanaki ganina ba, nagode sosai." Yana kai nan ya fara tafiya ya wuce Seemah, Ammar na tsaye ganin Jalal ya fara tafiya shima jikinsa yai sanyi, har Jalal ya d'an wuceta kad'an Seemah tace "Deen?" Tsayawa yai cak batare daya juyoba sai idanunsa da suka kara cicikowa, wato haka dama rabuwa take? Seemah ma bata juyaba tace " In ka tafi yanzu shikenan kuma ko?" Idanu Jalal ya runtse zuciyarshi ta shiga k'una, sai dai ya kasa amsa mata, kuma ya kasa wucewa, Seemah can ta kalli Ammar daya juya baya ta fara takawa ahankali har ta isa inda yake, sannan ta juyo ta kalli Jalal, daidainan shikuma yaji shirun yayi yawa ya juya d'an ya ma ta sallama, gani yai bai ganta ba nan ya shiga dubata, daga nesa ya hangota da Ammar, juyawa yai da sauri d'an zuciyarsa na wani irin zafi, a hankali ya d'inga takawa har ya fita. Seemah kam Ammar ta kalla tace " Yaya?" Juyowa yai a hankali d'an baiyi zatan zai jita a kusa ba, ta kalleshi ta mai murmushi tace " Kayi hakuri na........" Girgiza mata kai yai yace " Kar kice komai, naji dad'i ma da kika fito daga d'aki, d'an nagaji da ganinki kullum a d'akin nan." Tai kasa dakai tana neman abin cewa can tace " yaya ni ban ma san......." Hannu yasa akan leb'enta yace " karkice komai." Ta kalleshi kawai batace komai ba, a hankali tad'an juya baya ta zata yananan, gani tai ba kowa agun, ga mamakinta jitai Ammar yace " Ya tafi." Da sauri ta kalleshi jikinta yai sanyi tace " nifa ba wanda nake nema." Yai murmushi yace " nasani, kin tambayeshi mahaifinki?" Idanunta ne suka ciciko ta d'ago ta kurama Ammar ido, yace " Seemah?" Share hawayen daya zubomata tayi tace " Banasan sanin ko waye shi." Zaiyi magana sukaji ana tafi,juyawa sukai suka kalli Junaid. Ya karaso yana dariya yace " iyee? Abin ma ba kunya a kofar falon Abba? Da alama kun kosa a d'aura." Yai maganar cikin zolaya. Ammar ya kalleshi yace " Kai fa meza'ace?" Junaid yai dariya tareda karasowa yace "ne nai ni kuma?" Kallan Seemah yai yace " Kanwata kema bakya mamaki? Ace wai Junaid an had'ashi aure da Zahra amma ko meta baiyiba sai ma farin ciki dayake?" Seemah tai dariya tare da kallan Junaid tace "Gaskiya ne yaya nima ina wannan mamakin, itakanta Zahran da na d'auka kai takeso, amma da akace mata Ya Junaid za'a bata na d'auka zatai kuka sai naga kamas." Dariya sukai su dukansu, Junaid yace " Wato kukuma 'yan sa ido kenan ko?" Seemah ta kalli Ammar tao murmushi, ido ya kura mata yana mata wani irin kallo, Junaid ya rik'e hab'a zaiyi magana yaji Ammar yace " Farin cikina bai wuce in ganki kina cikin farin ciki ba." D'agowa tai ta kalleshi, batare datace komai ba ganin yanda yake mata wani kallo yasa tai saurin d'auke idanta tare da kallan Junaid ta wayance da cewa " Ya Junaid ina Ya Zaid?" Hakan yasa Ammar ya d'auke idansa, tare da kallan Junaid, tai sa'a yace " bazai wuce wajen gate ba." Ta juya da sauri ba tare da tace komai ba, kallo kawai Amnar ya bita dashi. Jalal kam har yakai waje zuciyarsa ba dad'i, yana fita gate ya samu gefen gidan ya zauna, idanunsa ne suke gano mai Ammar da Seemah, da sauri yasa hannayinsa biyu yad'an bubuga fuskarsa yana cewa " Wake up Jalal me ke damunka? Kamanta alkawarinka? Katuna abinda mahaifinka yamata ta dalilin cetanka fa?." Wata nanauyiyar ajiyar zuciya yai tare da cewa " Gaskiya ne, nasani kuma Ammar ne yafi cancanta da ita." Ya dad'e a zaune kafin ya mik'e ya tafi, sam ya mantada cikinsa wanda tun d'azu yake kara, gidan Sagir ya wuce. Bayan sun gaisa Sagir ya kalleshi yace " Mutumin yaushe a gari haka?" Yai murmushi baice mai komai ba, Sagir ya dafashi tare da cewa " duk ciwon soyayyar ne yasa ka rame haka?" Murmushi Jalal yai yace " Sagir sorry zan d'an takurama kad'an." Ya fahimci me yake nufi, ya d'an harareshi yace " Jalal me yasa kake min haka?" Hannu biyu Jalal ya had'a irin na ban hakurin nan suka shiga d'aki, gado Jalal ya fad'a Sagir ya matso kusa dashi yace "daga ina kake haka?" Jalal yai shiru, hakan yasa Sagir yace " Jalal ba dai......" Katseshi yai da cewa " yau fa aka d'auramin aure." What? Me kake nufi? Jalal ya juya baice komai ba. Sagir ya mik'e tare da sa hannunsa a kafad'ar Jalal irin na tausa ya fita. Jalal ya hard'e hannayensa tare da zarfafa cikin tunani, abinda mahaifin Seemah ya fad'a yafi komai tada mai hankali, dama akwai uban da bazai so ganin 'yarsa ba? Shi ya d'auka inyaji zancen hankalinsa ne zai tashi ya kuma nemi ganin 'yar tasa cikin gaggawa bayan laififukan daya tafka. Wata iska mai zafi ya furzar tunaninsa d'aya tayaya zai sa mutumin nan ya shiryu? Sagir ne ya shigo, ya zauna kusa da Jalal yace " tunanin me kake?" Jalal ya mike da sauri ya fuskanci Sagir yace " Sagir kasan Senate Abdullahi?" Sagir ya kalleshi da mamaki yace " kai kuma ina kasanshi?" Jalal yai shiru, Sagir yace " Amaryarsa kanwar Ummana ce." Jalal ya d'ago yace " What?" Sagir yad'an tab'e baki yace " hmmm ni sam mutumin nan ba wani burgeni yake ba ita kanta Aunty tun bayan auransu da wata 2 ta fara kawo kara." Jalal yai tsaki yace " ai da alama, amma ita mai yakaita auransa? Ba'ai bincike bane?" Kallan mamaki Sagir yama Jalal yace " lalai Jalal, mutum kamarsa wanda yakeda kud'i ga mulki shine kake tunanin za'ai wani bincike? Ita kanta Auntyn ai kud'in ne ya rufe mata ido." Jalal yai shiru, Sagir ya dafashi, yace " ka ga ka raba kanka da mutumin nan Jalal, a yanda Aunty take zancensa sam..." Kai ya girgiza kawai, Jalal yai shiru ya shiga tunani, Tayaya zaiyi yasa mutum kamar Senate yaba 'yarsa hakuri kafin auranta? Dafashi Sagir yai, Jalal ya kalleshi zai yi magana cikinsa yai wani kara, murmushi Sagir yai yace " Bari in kawo ma abinci." Ya fita yana dariya. Jalal ya dad'e yana tunanin mafita kafin bacci ya d'aukeshi. Washegari ya shirya ya koma Birnin/gwari. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 5⃣8⃣ Sagir na dawowa daga raka Jalal mai gadi ya mikamai wata takarda, kallan sa yai yace " nameye?" Mai gadin yace "d'azu da zaku fita wanda kuke tare ya bani yace in kun dawo in baka." Sagir ya amsa yana mamakin takardar miye acikin envelope? Yana shiga d'aki ya fito da farar takarda, abinda idanunsa suka fara gani nai ya kad'ashi, letter of resignation an yi rubutun da manyan harufa ankuma ja layi, wasik'ar barin aiki? Hannu yasa a aljihu ya kira Jalal, Jalal kam sun d'au hanya ya d'aga wayar, Sagir yace " Jalal me nake gani haka? Ban gane wasik'ar barin aiki ba?" Jalal yai shiru, Sagir yace " Jalal menene hakan?" Numfashi yad'an ja kad'an sannan yace " Please kamin submitting d'in takardar, bazan iya zuwa dakaina bane." Cikin rashin fahimta Sagir yace " aiki ka samu? Ko me?" " ba wani aiki akwai babban dalilin dabazai sani na cigaba da aiki a company d'in ba." Sagir ransa ya b'aci yace "saboda soyayya zaka hallaka rayuwarka ko me? Jalal wai me yasa kek neman barin soyayya ta rufema ido?" Jalal ya d'anyi murmushi inama ace soyayyarce kawai ba wannan babban al'amarin bane? Ya daure yace " Sagir kenan." Haushi ya kama Sagir ya kashe wayar tare da jefata kan gado, shikam yana mamaki ace wai mutum yabari soyayya ta nemi hargitsamai rayuwa? Zahra ce ke ta shiga d'akuna tana kaima mutane abincin safe, ta taho da flask d'in abincinsu Junaid tai d'akin, takalman dake bakim kofa ta kalla, takalmin Zaid ne kawai hakan yasa tai sallama tare da tsayawa a kofar d'akin, Junaid dake kwance ya amsa a kasalance, zuciya d'aya ta shiga tana cewa " kai dai ya Zaid kaji jiki ace kowa ya tashi amma kanannan akwance kamar ba namiji ba." Junaid jin maganarta yasa ya fara murmushi tare da kara shiga bargo, ta matso cikin tsokana tafara jan bargon daya rufu dashi, Junaid ya zaro ido tare da kallan kayan jikinsa, vest ce sai gajeran wando, da sauri shima ya ja bargon nan suka fara jaye_jaye, tana ja tana cewa " Allah yau sai ka tashi kai ko kunya bakaji Yaya?" Junaid ya kara jan bargo, hannu ta hard'e tare da sa kafarta a kan gado ta kamo bargon da karfinta, ai kam ta fizgo bargon, Kallan mamaki tama Junaid tare da bud'e baki cikin mamaki, Junaid ya fizgo bargon da karfi, itakuma gaba d'aya nauyinta nakan bargon, ai kuwa tabi bargon ta fad'a jikinsa, Ta d'ago ta kalleshi cikin mamaki murmushi ya mata na karfin hali dan shima kunya yaji, yace " Zahra kece?" Mik'ewa tai da sauri tare da juyawa tai waje da gudu, Junaid ya bita da kallo fuskarsa na wani irin murmushi, Zahra d'aki ta fad'a da gudu tare da sama d'akin makulli ta matso kusa da Seemah dake zaune rik'e da agoggon Jalal, Zahra ta fado kusa da Seemah kamar mai shirin kuka tace " Seemah an kashe ni?" Seemah ta kalleta tace " an kashe ki kamar ya?" Zahra ta mik'e ta fad'a gado tai rufda ciki tare da rufe fuska tace " Seemah naga Ya Junaid da vest." Tana fad'a tare da tura kanta jikin katifa, dariya Seemah ta kyalkyale dashi wanda rabon datai dariya haka harta manta, dariya sosai tai sai data tsagaita tace " Haba? Kuramai ido kikai?" Zahra ta bubuga kanta tace " Eh mana?"tafad'a kamar mai kuka. Seemah ta kara sa dariya tace " lalai Zahra wato ba kunya? Kika kuramai ido?" Zahra ta mik'e zaune tace " wayyo wlh ba da sanina bane nifa bansan shi bane." Seemah ta guntse dariyarta tace " kyama fad'i gaskiya da alama ma dama haka kika so, yanzu Zahra ko kunya? Hmmm" Zahra ta mik'e da sauri ta matso gun Seemah ta rik'e hannayenta tace " Seemah yazanyi? Shima zaiga kamar banda kunya ko? Nashina da wani idon zan kalleshi?" Seemah ta kara guntse dariya tace " gaskiya kam wannan kam fitsira ce." Zahra kula datai Seemah cinnata takeyi yasa ta kalli Seemah tace " tsaya! Shi yayan naki waya ce yaki fad'amin shine? Ai ni banida laifi." Seemah tai dariya tace " ahhhh gaskiya ba laifin yaya na bane a dai duba." Haka tai ta tsokanar Zahra. Jalal kam har ya isa zuciyarsa ta rasa bashi mafitar alkawarin daya d'auka, yana isa gida yaga mutane a cike, shiga yai duk da ransa ba so yake ba, nan suka shiga gaisawa da jama'a wasu 'yan uwan Zainab ne wasu nashi, yana gama gaisawa ya wuce d'akinsa ya kwanta, Abba ne ya shigo d'akin ya tsaya a bakin kofa yace " Jalal?" Jalal bai juyaba yace " Naam" Abba yai shiru cikin sanyin jiki yace " kaga Abdullahin?" Jalal yace " eh amma...." Sai kuma yai shiru, Abba ya kalleshi yace " Jalal mutumin nan ba mutunci gareshi ba ka karfi na dukiya da mulki dayake dashi bana tunanin kanada hanyar dazaka sashi abinda baiyi niyya ba." Jalal yai shiru, tabbas yasan haka abin yake, Abba ya cigaba " Kai ba Lawyer ba, ba kuma D'an jarida ba mai zaka iyayi? Bayan ko shari'a yafi karfinta?" Da sauri Jalal ya mik'e ya yace "d'an jarida? Lawyer?" Kallansa nai nima cikin mamaki mai yake nufi? *HUSSYLURV, BILLY, AENART, AMAL, HADIJA, ZEE BALA, UMMU NAFISA, RAMBI. DAFATAN KUNYI WEEKEND LAFIYA.* © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _Ina kara ba masoyan littafin nan hakuri na jina shiru da kukai kwana biyu, a min afuwa ina cikin taro ne.......Nagode kwarai da kulawarku da kuma kaunar da kukema littafin nan_ No. 5⃣9⃣ Abba ya kalleshi shi kanshi bai fahimci mai Jalal ke sakawa a ransa ba amma mamaki ne bayane a fuskarsa ganin Jalal na murmushi. Daurewa yai yace " Jalal kazo ka fita gun abokanka anjima kad'an za'a kawo amarya." Ya kalli Abba yace " yanzu Abba inza'a kawo Zainab gidan nan har sai na fita? A gidan nan take da fa, sannan ni gun wa zani kasan ba abokai garan ba." Abba yace " Al'ada ce hakan yaza'ayi akawo Amarya kuma Ango na cikin gidan? Ai sai daga baya zakuzo siyan baki da abokanka." "Siyan baki? Bakin wa kuma zan siya?" Yai maganar cikin mamaki. Abba yai murmushi yace " Jalal ya akai bakasan komai na aure ba? Ai in aka kawota sai kunzo kun ba kawayenta kud'i sannan su tafi." " Ah wannan ba siyan baki bane, neman kud'i dai kawai." Abba yace " Haka dai akeyi d'an haka kazo ka fita sannan ga wannan." Ya mik'a mai bakar leda an d'an nad'eta, Jalal ya amsa yana kallan Abba. Abba ya cigaba " 'Yan uwanka ne suka tara maka, sai ka ciri wani abun kaba 'yan siyan baki sannan a ciki ka siyo kaza da madara ko yogurt ko lemo, na fad'ama su Kafilu suzo su rakako anjima." Jalal ya irga kud'i dubu 20 ne cif, ya kalli Abba yace " Yanzu Abba meyasa akasa su tara kud'i haka?" Abba ya sake Murmushi yace " ba wanda ya sasu, dama haka akeyi, had'awa akeyi kowa ya kawo nawa yai niyyar bayarwa." Jalal yai shiru yana kallan kud'in, Abba ya juya tare da cewa, kai wanka kasa sabon kayanka kazo ka fita. Jalal yace to, sannan yace " Amma Abba baka tambayeni......." Abba ya juyo ya kalleshi yace " nasani Jalal, amma daga baya mayi maganar." Yana fad'a yai waje. Kallo yabishi dashi sannan ya zauna a bakin gado, shifa sam baiyadda wai shine akama wani aure ba, shi da yad'auka in mutum aka mai aure wani farin ciki ne ke mamayeshi, to shi ya yake jinsa ba wani farin ciki? Sai ma wani bakim ciki na mahaifin Seemah dake nukurkusar sa? Ga zafin rabuwa da abinda zuciya da gangar jiki ke bege." Ya zaiyi? Haka dai ya mik'e yai wanka ya zura shaddarsa sabowa da Umma ta d'inkamai ya fita, cikin gida ya kara shiga ya musu godiya sannan ya fita. Waya ya d'auko ya kira Sagir, shikam Sagir haushin Jalal duk ya isheshi, da kyar ya d'aga wayar, Jalal yace " Sagir d'an Allah tambaya, a tsakanin Lawyer da d'an Jarida wanne yafi d'aukan lokaci wajen gama karatunshi?" Haushi ya kara kama Sagir yace " Au bama zancen aikinka ka k'ira kamin ba?" Jalal ya saki Murmushi yace " Sagir d'an Allah kabani amsa." Sagir baice komai ba ya katse layin. Jalal ya girgiza kai fuskarsa d'auke da murmushi, jiyai am dafashi ta baya, ya juya Kafilu(d'an gidan goggo) ne da abokansa, Jalal ya kara sakin fuska yace " Kafilu?" Kafilu yasa hannu a hab'a dayake shi mutum ne mai barkwanci, yace " Haba tun dana karyo kan lungun nan nake ganin haske d'an nima hasken na d'inga bi, abin mamaki hasken ya d'ireni anan." Jalal ya kalleshi yace " Au nine nake haskem kenan?" Dariya Kafilu yasa yace "Sosai ma, abinka da sabun shiga, saurayi zaiyi sabon aure." Ya fad'a yana kallan abokansa, Dariya dukansu suka kwashe mai dashi, har Jalal d'in. Ya cigaba " ni gashi ina shirin kara ta uku amma kai sai yanzu zakai d'aya gaskiya dai anji kunya." Kallan mamaki Jalal yamai yace " Kafilu? Ka rufa mana asiri ina zaka kai mata uku?" Dariya suka sakeyi Kafilu yace " ah to kaidai ba d'an boko ba sai kayi ta zama ni ai sai na ciki hud'un nan rass." Jalal ya girgiza kai yace " Lalai abin naka babba ne, kaje kana kwance a kwarama ruwan zafi." Suka kara sa dariya, Kafilu yace " tab, ai sai dai suyi ta fad'a akaina ni kuma inzauna akan kujera ind'inga kad'a kafa." Jalal ya kalleshi cikin mamaki yace " Allah ya shirya, wato kai fad'an ma dad'i yake maka." "Sosai ma." Sun dad'e suna hira suka d'anje yawo. Seemah kam duk motsin datai sai ta tuna, Shikenan Jalal ya zama ba nata ba, yana can yau za'a kaimai matarsa, wani sabon kishi da takaici ne ke nukurkusarta, kwankwasa kofar dataji ne yasa ta mik'e tare da bud'e kofar, Ammar ne ya kalleta fuskarsa d'auke da murmushi ya bud'e mata hannayensa yace " Suprise! !!! " Ta kalleshi tare da matsamai, Ammar ya shiga yana cewa " Kodai in koma? Kamar wannan kanwar batai farin cikin ganina ba." Seemah ta shiga ciki batare data amsa ba, a kan kujera ya zauna tare da nuna mata kusa dashi, ta karaso ta zauna, ya kalleta ya d'an langwab'ar dakai yace " ko in tafi?" Kai ta girgiza mai, alamar a'a yace " in bakyasan na tafi to lalai ki saki fuskarki." Ya fad'a tareda had'e fuska, Seemah ta kalleshi cikin shagwab'a tace " Fuskata fa a sake take." Ya juyo yai murmushi sannan ya mik'e ya dawo gabanta ya tsugunna, ta kalleshi tare da yin murmushi ganin yanda yake kallanta, tace " Yaya kallan fa?" Ya kara kafeta da ido yana mata wani kallo yace " Seemah bansan ganinki cikin damuwa kema kinsan haka." Ta d'auke idanunta da sauri tare da juyar dakau tace " Yaya?" Ya mik'e tare da juyawa ya fara tafiya, jikin gado yaje ya tsaya, ba tare da ya juyo ba yace " na sani Seemah, soyayyar da kikemin ta 'yan uwantaka ce bawai ta saurayi da budurwa ba, a da na d'auka nima wannan soyayyar nake miki, amma bayan sanin ba jinin mu d'aya ba na gane cewa soyayyar danake miki kala biyu ce." Ya juyo ya kalleta idanunsa sunyi jaa, yace " in har bazaki iya aurena ba wani abu, ni zan iya hakura koda kuwa sanki zai kasheni zan jure, abinda bazan iya jurewa ba shine inganki cikin bakin ciki." Seemah hawaye suka gangaro mata, ta kalleshi cikin tausayi, sai dai ta kasa magana juyawa yai yafara takawa, da niyyar barin d'akin, mik'ewa Seemah tai da sauri ta zo ta rungumeshi ta baya (abinka da rainon da ba na kasar nan ba, bare sun taso tare basu d'auki hakan komai ba.) Cak Ammar ya tsaya, tare da had'iyar wani abu, idanunsa na neman kawo ruwa, Seemah cikin kuka tace " Ba haka bane Yaya, ba haka bane." Hannunta ya zare tare da juyowa saitinta, hannu yasa ya share mata ta tsugunna a kasanshi tasa kuka tace " Yaya ya ya zanyi? Ni kaina haushin kaina nakeji, banasan abinda nakeyi, tayama za'ayi zuciyata ta kasa tsanar wanda mahaifinsa shine sanadiyyar wulakantar mahaifiyata, kila ma shine sanadin rasa rayuwarta?" Ta kalli Ammar idanunta na zubar da kwalla abin tausayi tace " Yaya inaji bana cikin hankali na, a da nad'auka ko ganinsa bazan nemi sakeyi ba, amma da kaina na fita gunsa, kuma na kasa ko tambayarsa bare inyi masa masifa, yaya anya mahaifiyata zata yafemin?" Ammar ya share kwallarsa shima, ya tsugunna kusa da ita tare da rike hannayenta, ta cigaba da kuka sannan tace " Yaya ka taimakeni kasa na manta da Deen d'an Allah, in daina mafarkinsa da tunaninsa, banasan na........" Hannu yasa ya rufe mata baki, ta kalleshi hawaye na cigaba da zubowa, har kan hannunsa, baice mata komai ba, sun dad'e a haka, Kafin a hankali Ammar ya zare hannunsa daga kan bakinta ya kalleta yace " Ya isa kukan haka, banasan ki zubarda hawaye koda kuwa akainane bama akan wani ba, hakan nasa zuciyata shiga wani hali." Kallansa tai ta kasa magana, yace " bari naje masallaci." Ta d'aga kai a hankali, ya mik'e ya fita, ta bishi da kallo, jikinta ya kara sanyi, taya zata ki jinin Dad, a yanda takejinta koda Dad wani can talakan gaske ya d'auko yace Seemah wannam nakeso ki aura, bataji zata bijire masa bare Ya Ammar? Mutumin datasan bazai tab'a barinta ta wulakanta ba bare yasata kuka, jinin Dad, sannan a 'ya'yan Dad d'in ma wanda tafi shakuwa dashi tafi kuma sansa? To amma meyasa take neman b'ata masa rai saboda Deen? Meyasa? Wani sabon kuka ne ya kara zuwa mata........ An kai Amarya, mutane sun cika a gidan Jalal su kafilu a gaba suka sashi aka siyo kaza da lemon kwalli da hollandiya mai sanyi, Kafilu sai tsokanarsa yakeyi, sunje shiga gida Kafilu ya kalleshi yace " Jalal sai naga kamar farincikinka baikai zuciya ba." Kallansa Jalal yai baice komai ba, Kafilu yai dariya yace " ko duk ka kosa ne kayi......." Harara Jalal ya dokamai yace " kai wannan ya dama mai iyalai." Kafilu ya kalleshi yace " Kai!!!!! Ai abin ne....." Jalal ya kara makamai wata hararar yace " bamasan jin sirrinka uban 'yan surutu, Allah ya shiryeka." Nima nace Ameen, d'an kuwa fad'ar sirrin aure babbar illa ce......Allah yasa mu kiyaye Ameen. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* ⛹🏻‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _I Sincerely dedicated this page for you *ASY KHALEEL*._😍 No. 7⃣0⃣ Sun shiga cikin d'akin, nan Kafilu ya samu abinda yake so wato hira, shikam Jalal ko kallan Zainab dake lullub'e cikin mayafi baiyi ba, Sai can d'aya daga cikin abokin Kafilun ya tab'ashi yace " ya kamata mu yafi fa." Nan suka ba kawayen Amarya dubu biyar kud'in siyan baki sannan akai addu'a suka fita. Toh fa!!!! D'aki ya rage daga Zainab sai Jalal, zaman dukum sukai wato zaman kurma har na wajen minti talatin, kafin can Jalal ganin zamanshi anan bashi da amfani ya mik'e ya kalleta, yace " Zainab?" "Naam"ta fad'a cikin sanyin murya. Yace " bud'e fuskarki mana muyi magana." A hankali ta zare mayafin idanunta a kasa, tasha kwalliya d'an kuwa tayi kyau, sai dai wanda akai dominsa baimasan tayi ba, kallanta yai yace " ungo wannan." Ya fad'a tare da mika mata leda, hannu tasa ta karb'a tana kallansa. Yace " Abincine ki samu kici, inadai kinyi Sallah?" A hankali ta furta " eh, amma kai yaya kaci abincin ne?" Ya d'an juya kai yace " ni na koshi, kedai kici abinci sannan ki shiga d'aki ki kwanta d'an nasan kingaji." D'agowa tai ta kalleshi, duk da dai itama tasan ba santa yake ba amma bata tab'a tunanin abinda zai ce mata kenan ba. Kai kawai ta d'aga, yai cikin d'akinn, dama d'aki d'aya ne da toilet a cikin d'akin sai falo, toilet d'in ya shiga yai alwala yai sallah a d'akin. Itakam dakyar ta iya cin cinya guda d'aya sai yoghurt d'in data d'an kurb'a tai shiru tana tunanin wannan abu, kawayenta jiya sun bata labarin yanda maza ke kula da mace ranar da aka kaita, yau gashi ita taga wani abu. Jalal bayan yayi addu'oinsa ne ya fito falon tare da kallanta yace " kinci abincin?" Ta d'aga kai, yace " Good, kishiga ki kwanta." Ta kalleshi tare da mik'ewa tai d'aki, har takai bakin kofa tad'an juyo, ganinshi tai ya kwanta akan doguwar kujera, tace " yaya kaifa?" Ya kalleta kad'an tare da cewa ni inanan. Kallan mamaki tamai sannan tace " yaya." Jalal ya had'e rai yace " to so kike inshiga mu kwanta tare?" Shiru tai tana kallansa, yace " ki wuce kije ki kwanta karki damu dani." Shiga tai cikin d'akin ta zauna a bakin gado tai shiru, ta rasa ma me zatai, shikam Jalal waya ya d'auko yai tai binciken abinda yasa gaba wato sanin harkar karatun law dana mass com. Yana cikin binciken ne yaga wata kungiya masu bada scholarship na PTDF sun bud'e a fara siyan form. Nan fa ya sai katin yana fatan Allah yakaimu gobe ya tafi cafe yaje ya cike. Haka rayuwa ta cigaba, 'yan taron biki sun watse, sai dai tsakanin Jalal da Zainab, intai abinci ta bashi ya ci sai kuma gaisuwa, kamar yanda ta saba kullum tana cikin gida kamar da, wannan ne ya rage mata kewa da kuma sanya abin aranta. Hmm rana bata karya, yau tun safe ake ta shirye_shirye a gidan Abba kowa ya shiga hidima, kowa murna yake yi banda Seemah wacce kwai yake take yima kowa, tana tsaye a kitchen d'an Mami tasata kullum ta d'inga shiga kitchen tana ganin yanda Zahra da mai aikinsu ke girki, yau dai ita kad'ai ce a kitchen d'in tana dafama Dad indomie babban burinta Dad yaci abincin ta, Ta dage tana ta aiki sai kace mai dafa sakwara duk ta b'ata kitchen d'in, ji tai an rufe mata ido ta baya, tai murmurishi tace " Ya Ammar ka tashi?" Sakinta yai tare da juyowa saitinta yace " Seemah ya akainkiga ganeni?" Ta d'an harareshi kad'an tace " lalai ma Yaya, tambayar dazakamin kenen? Inada hanyoyin sanin kaine dayawa." Ya kalleta cikin jin d'adin kalamanta, ta kalleshi tare da cemai "yaya yau Dad nakema girki." Ammar ya hau saman kanta daga gefe ya zauna tare da cewa " lalai duk wannan d'in na dad ne kenan? Bama a tuno da ni?" Ya d'an matso ta da fuskarta kusa dashi yace " ur husband to be." Kasa tai dakai da sauri sannan ta d'ago ta d'an kankance ido tace " oh ni yaya yaushe ka zama haka wai?" Murmushi yai sannan ya nunata da hannu yace " yazanyi tunda kanwata ta maida ni haka?" Ta d'an juya kai tace " gobe dai zan tafi ai." Yad'an bata rai yace "gaskiya ji nake kamar zan biki, bansan ya zanyu ba inkika tafi MEEMAH." Da sauri ta d'ago ta kalleshi gabanta ya fad'i, idanunta yaga sun ciciko, cikin tsoro yace " SEEMAH? Menene?" Ta share hawayenta tare da saurin maida kanta kan girkinta tace " please yaya karka kara cemin Meemah." Ammar da mamaki yace " meyasa? Naga kinasan sunan?" Ta kara goge kwallar vata amsa ba kawai ta cigaba da yanka albasa, aranta tace" sunan da Deen ke kirana dashi ne, na rabu dashi ina fatan zuciyata ta manta dashi sai dai banasan wannan sunan ya fito daga bakin kowa sai shi, tunda mun rabu dashi wannan sunan inasan ya zama tarihin daya rage tsakaninmu." Ammar kallanta kawai yakeyi, har ta gama nan ya tayata gyara kitchen d'in. A ranar da yamma aka sanya ma Ammar da Sewmah sannan Junaid da Zainab ranar aurensu nan da shekara 2 daidainan Seemah ta gama karatunta a hankali ta dawo sun karasa shiri, itama Zahra ta gama nata. Washegari Seemah da Dad da matarsa suka calla England. Jalal kam yayi sa'a ya samu wannan scholarship d'in murna kamar yai me, nan ya fad'ama Abba shima ya tayashi murna duk dadai a kasan ransa yasan manufar Jalal, nan fa yafara shirin tafiya dan kasar Germany ya cike karatun d'an Jarida, d'an yaga a can shekara 2 ne an gama. Yagama komai shima sannan ya calla kasar Germany d'an yin nasa karatun. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* ⛹🏻‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣1⃣ *Bayan Shekara Biyu* Seemah nata sauri dan ganin lokacin fita makarantarta yana neman kurewa yau ne suke taron kammala karatun degree da sukai, ta fito cikin riga da wando, rigar pink ce an rubuta sunanta a baya sai wando jeans baki, shigar da kowa zaiyi kenan, mayafi ta d'auka black tai rolling d'in kanta dashi tayi kyau sosai ta zura abaya baka ta d'au jaka ta fita. A falo ta tadda Dad na karatun jarida ta gaidashi ya amsa yana cewa baby kin fito? Ta d'an turo baki tace " A'a Dad nifa nace banasan Baby nan shekarata fa 22 yanzu." Yai dariya tare da cewa kiyi sauri ki fita sai mun iso, ta juya tana mai bye bye da hannunta, motarta ta fad'a ta kunna wakar data saba ji ta Kabhi Kush nan ta fara tuki cikin kwarewa, agoggon ta data ajiye a saman kan motar ta kalla tai murmushi tace " Good morning Deen." Ta fad'a tare da murmushi, tana isa makaranta tai parking sannan ta fito, ta shiga cikin kawayenta turawa da indiawa suka hau murna dan kuwa ba karya ranar murna ce. An gama shirya komai nan mutane suka fara isowa, taro ya fara gudana, Seemah kam sai zirga zirga takeyi fuska a had'e waya ta d'aga ta kira Ammar abin haushi bai d'aga ba tai kwafa sannan ta kara kiransa, nan ma bai d'aga ba, haushi ya turnuko ta ta kira Ya Habib, ringing biyu ya d'auka ta shagwab'e murya tace " Yaya sun taho?" Habib ya kalli Ammar yace " Wayyo kanwata kiyi hakuri bazasu samu damar zuwa ba." Idanunta sukai rau rau tace " Harda Ya Ammar?" Habib ya guntse dariyarsa yace " Ahh Ai Ammar ma bayanan ya tafi meeting. " Cikin masifa tace " Meeting?" " eh akwai wani babban Project da muke san yi ne to shine......" Katse wayar tai a zuciye ta koma ciki. Zama tai tare da hard'e hannayenta lalai ma Ya Ammar d'innan, ko a mafarki bata tab'a tunanin zai fifita aikinsa a kanta ba kwalla ta zubo mata, ta share tare da d'aukan wayarta kamar yanda ta saba, numberta datai saving ta bud'e ta tura ma kanta sako kamar haka " Deen yau an b'atamin rai, Ya Ammar da Ya Junaid bazasu hallaci taron kammala karatu na ba." Tana gamawa ta turama kanta, tun bayan tahowarta duk abinda ya sameta sai ta tura ma kanta sako da zummar Jalal ta turama hakan na saukaka mata zuciyarta duk da kuwa tasan ba zai gani ba. Tana nan a zaune wata kawarta yar Korea Yoo jung ta shigo, dafata tai tace mata " Someone is looking for you." Seema ta kalleta tare da tab'e baki tace " Yoo Jung I am not in the mood to joke with you. " Tai mata murmushi tace " 3 handsome men and one young girl." Seemah ta kalleta da sauri sannan ta mik'e tsaye tace " are you sure? " Ta d'aga mata kai tana murmushi da sauri Seemah ta waje. A tsaye ta hangosu daga nesa, Ya Junaid, Ya Habib, da Ya Zaid, ta saki murmushi ganin Zahra a kusa dasu, juyawa ta d'anyi da kanta da alama wani take nema, ganin ba kowa yasa ta karaso kusa dasu, tare da kallan Ya Habib tace " Yaya shine d'azu baka fad'amin bako?" Zahra ta matso kusa da ita tace " Seemah oh ni ashe zan ganki?" Seemah ta d'an harareta tace " ni bansan wani dad'in baki yausge rabon da ki kirani?" Junaid ya d'an matso kusa da Zahra yace " yanzu kuma metayi? Daga zuwa ganinki?" Seemah ta juya kai tace " dama nasani ai yaya yanzu ka daina sona." Zaid ya matso saitin kunnenta yace " kyalesu ni kaina bana shiga harkarsu sun zama super glue. " Dariya tasa ta kalli Zaid tace " Ya Zaid at least kai nasan kana bayana." Sun je shiga kawai taji jikinta ya bata kamar ana kallanta juyawa tai a hankali, da sauri ya lab'e a jikin bango, ta d'an kurawa gun ido kad'an Zaid ya kalleta yace " muje mana." Ta d'an juya kai maybe mistake take, wanda ya lab'e ya fito tare da bin bayanta da kallo yai murmushi yace " Congratulation Meemah." Ya juya yana murmushi, direct Airport ya nufa. Seemah kam suna zazzaune a sama akan kujera ana kiransu d'aya bayan d'aya ana basu kwallin karatun diploma d'insu, kallan kofa take tayi d'an bataga Dad ba har a lokacin, kanta ta sukuyar fuskarta ba yabo ba fallasa, an kira sunanta kenan, ta mik'e a hankali tare da kara kallan kofa, wa zata gani? Ammar ta gani a tsaye ya hard'e hannayensa yana mata murmushi, itama murmushin tamai wani farin ciki ya kara kamata, a hankali ta karasa ta amsa sannan aka tafa mata ta koma ta zauna fuskarta d'auke da fara'a. A hankali Ammar ya karasa ya zauna yana kallanta, ana gamawa ta mik'e da sauri ta karasa kusa dashi, Ammar ya kalleta cikin tsananin bege yasa hannu a hab'arda yace " Ahhh anya kuwa Seemah tace? Ba sai na shiga bincike ba?" Ta ballamai harara tace " Yaya nifa nayi fishi dakai." Yad'an saukar da kai kasa yace " Shikenan tunda bakiso ganina ba bari na juya na koma." Ya fad'a tard da fara tafiya, da sauri ta karasa kusa dashi ta rike rigarsa ta baya tare da cewa " Wasa fa nakeyi yaya." Ya juyo tare da sakin sansanyan murmushi yace " nima wasa nake, ya za'ayi in tafi in bar amarya ta?" Ta d'an sadda kai kasa itakam ta kasa sabawa in yai irin wannan zancen bata iya mayar mai. Zaid ne ya karaso kusa dasu yace " hmmm yau fa ba kanta Ammar yaga Seemah." Seemah ta kalleshi tace " Yaya Zaid?" Zaid ya girgiza kai yana nuna Ammar yace " wannan mutumin? in kinsan abinda yakemin kullum da dadd......" Da sauri Ammar ya matso ya toshemai baki yace " To shigaban san magana banaji an tambayeka ko?" Seemah ta kallesu tai dariya nan su Ya Habib suka matso aka cigaba da hira. Jalal kam yana isa da kusan hour 1 sannan suka tashi zuwa kasar mu, a kasar Abuja suka sauka, ganin dare yayi yafara tunanin ko zuwa hotel. Mota yahau ya wuce hotel yana shiga d'aki ya cire coat d'in jikinsa ya fad'a toilet, bayan ya fito ne ya kunna wayarsa sannan ya kira wata number, ringing biyu aka d'aga, Jalal yai sallama, da sauri mutumin ya amsa tare da cewa " Haba Malam Jalal tun wancan satin nake jiran kiranka amma shiru banji ka kira ba." Jalal ya mik'e tare da zuge labulan window ya kalli waje tare da cewa " Director na amince da aiki a gidan tv d'inku sai dai inada sharad'i guda d'aya." Ya saki wata dariya sannan yace " nagode sosai journalists Jalal tun kana Germany yanda naga kanada kwazo da kuma kwarewa yasa nake fatan yin aiki dakai, naji dadi." Jalal ya kalli waje yace " bakaji conditions d'in nawa ba ai." Ya kara sa dariya yace " Ai duk abinda zaka fad'a nasan bazai wuce kanasan adinga biyanka dayawa ba ko kuma akwai program dakake san yi." Jalal yai wani murmusho yace " Indeed you are smart sai dai ba haka bane burina abu guda d'aya nakesan in fara gabatarwa kafin muxo kan wannan maganar." Tattara hankalinsa yai gun Jalal yace " ina jinka." Jalal yace " inaso ka gayyato mana Senate Abdullahi wanda yake kokari takarar zama shigaban kasa muyi hira dashi a program d'in dakasan yafi komai bunkasa ta tashe a gun mutane." Shiru yai yace " Menene dalili......" Jalal ya katseshi da cewa " karka damu ba abinda zai faru, kawai dai nasanshi ne ina kuma san inga na fara aiki dashi kafin in fara komai." Ya jinjina kai yace " ba damuwa zan aika da takarda gayyata, inasa ran kuma zai hallarta dan mutum me shi mai san a sanshi." Jalal ya daga gira yace " nasan da haka shiyasa banaji ta gunsa." Suna gama waya Jalal ya kurama waje ido sannan yai murmushi yace " Malam Abdul sai mun had'u." Sagir ya kira yace ya kawo masa abinda yace ta tattaromai yana hotel. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣2⃣ Yana gama waya da Zaid ya kira Abbansa, bayan sun gaisa ne yace " Abba kun isa lafiya?" Abba ya kalli Zahida dake kwance, yace " gamunan tun azahar muka iso, gaskiya asibitin nada kyau ga kulawa." Jalal yai murmushi yace " Mai suka ce gama da ciwon ta?" Abba yai shiru can yace " Sunce ba wani abu bane serious kawai dai tun tana karama ya dace mukaita asibiti sai dai barin kashinta da mukai har yai kwari haka shine zai sa a sha wahala kafin ta mik'e." Jalal ya jinjina kai sannan yace " Dad ya dawo yau." Gaban Abba ne ya fad'i yai shiru baice komai ba, Jalal ya cigaba " Bai tsaya taron kammala karatu Seemah ba naga yataho." yai ajiyar zuciya sannan yace " tunda ka duba komai na asibitin sannan Umma nacan ka dawo muje ka roki gafarar Dad hakan zaisa Allah ya dubi zuciyarmu ya ba Zaheeda lafiya." Abba ya runtse ido sannan yace " gaskiya ne Jalal na auna naga gudin nan danakeyi ya isa haka, abinda yafi dacewa dani shine in nemi gafarar Isma'il ita kad'ai ce zatasa hankalina ya kwanta." Jalal ya d'an murmusa kad'an yace " yaushe zaka taho nan d'in?" Abba yace " gobe ma, mai zan jira?" Jalal ya jinjina kai yace " inkazo gobe sai muje jibi." " Allah yakaimu, amma ka kira Zainab?" Jalal yad'an tsuke fuska kad'an yace " Zan kirata." Abba yace " Jalal ba dan ni ba saboda darajar aure agun ma'aiki zaka duba, nasani sarai Zainab bata gabanka ba kuma santa kake ba, sai dai kada ka manta d'aura muku aure akai, hakkinta dake kanka yazama dole ka saukesu in dai kana neman rahamar Allah. " Jalal yai shiru, can yace " Zan kirata Abba." Nan sukai sallama. A bakin gado ya zauna ya kurama sunan ta ido dake kan wayarsa, Zainab yasa ya dade yana kallan sunan kafin ya daure ya kira. Zainab kam ita kad'ai aka bari a gidan hakan yasa ta d'auko kanwarta, suna zaune suna 'yar hira sama sama ita wani sa'in mantawa ma take tanada wani aure, ganin kiran Jalal yasa taji gabanta ya fad'i rabonta dashi har ta manta, mik'ewa tai ta shiga d'aki da sauri, ta zauna a bakin gado sannan ta d'aga wayar. A hankali tai sallama, Jalal ya amsa tare da cewa ya gidan? Tace lafiya kalau, shiru sukai dan basusan me zasu cema juna ba, can Zainab ta daure tace " Umma tace yau zaka dawo kasar nan ko?" Jalal yace "nama dawo ina Abuja ne." Zuciyarta taji ba dad'i amma ta daure tace " Yaushe zaka dawo nan kenan?" " Ina da aiyukan yi anan zan d'au lokaci kafin in dawo." Ta jinjina kai a ranta tace " Lokaci? Shekara 2 tayi kad'an kenan?" Jalal ya katseta da cewa "ba abinda kike bukata ko?" A zuciyarta tace " me nake bukata kuwa banda inganka?" Amma a fili tace " babu." Yace " okay" batai auni ba taji ya katse wayar, tabi wayar da kallo idannunta suka ciciko da kwalla ya zatayi? Jalal kam agoggon hannunsa ya kalla wanda yakai aka canza mai glass d'in kullum yanzu shi ne a hannunsa ko da wasa bazakaga yasa wani agoggonba bayan shi, murmushi yai yace " Yau nasan kina cikin farin ciki mai yawa." Kan kujera ya zauna ya d'auko laptop d'insa ya bud'e yafara aikinsa. Jalal kenan in ka ganshi yanzu bazaka ce shi bane da, kwarewa da kwazo sun canzashi, kaifin tunaninsa ya karo sosai fiye dana da, tunda yabar kasar nan ya fara karatu ya samu wani company na gidan radio yana musu aiki, in zasu dauko rahoto ko wani bincike dashi ake zuwa, hakan yasa ya samu experience dayawa akan harkar karatunsa, haka kuma kud'in da suke biyanshi mai d'an kauri ne, ga kud'in da aka basu na scholarship. Sunso rikeshi acan amma inaaa ai ko da wasa bai tab'a sawa a ransa zai iya zama a wata kasar ba. Seemah kam sun gama taro an d'au hotuna kala kala, sun koma gida abin haushi wai Dad har ya tafi Nigeria shida matarsa, haka suka baje a falo akai ta hira, Seemah kam ganin hirar taki karewa yasa ta sulale ta gudu d'akinta, tana shiga tana kokarin Zama a bakin gado tace an murd'a kofar, ta kalli kofar da sauri, Ammar ne ya shigo da sallama ta kalleshi tad'an had'a rai kad'an tace " Yaya baka kwankwasa bafa?" Ya had'a hannunsa biyu yace " au amin afuwa." Ya fad'a tare da komawa ya rufe sannan yai knocking, tad'anyi dariya sannan tace shigo, nan ya shigo yana cewa " yanzu dai banyi laifi ba ko?" Ta d'aga kai tare da zama, ya matso ya zauna kusa da ita sannan yace " ya kamata ki kwanta da wuri d'an nasan kin gaji gashi gobe zamu tafi." Ta kalleshi sannan tace " Yaya?" Yace " Ummm" Ta girgiza kai tace " Shikenan ma." Yad'an d'aure fuska yace " So kike muyi fad'a?" Ta girgiza kai tare da cewa " ba fa wani abu important bane." Ya harareta tare da kafeta da ido, tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta tace " Yaya dama so nake ka tambayar min Dad a wani gari mahaifiyata take sunan kawai nake san ji." Ya kalleta cikin tausayawa yace " Karki damu insha Allah kafin aurenmu zan kaiki har garin." Kai ta girgiza mai tace " basan zuwa nakeyi ba nima kawai sunan nake san ji." Ya kalleta kawai baice komai ba, cam ya wayence yace "Saura wata d'aya bikin mu ba wani abu da kikeso ko kike tunanin yi?" Kallansa kawai tai sannan ta girgiza kai, alamar a'a, jikinsa yai sanyi amma ya daure ya shiga bata labari har sai da ta saki ranta, sun dad'e suna hira kafin Ammar yai shiru, kallansa tai tace " Yaya lafiya?" Ya mik' e jiki a sanyaye ya tsugunna a gaban Seemah tare da rik'o hannayenta, a hankali ta d'ago ta kalleshi ta kasa furta komai, Ammar idanunsa na kanta, ganin bazata iya jure kallan dayake mata ba yasa tai saurin yin kasa da idanta, Ammar cikin wata irin murya mai ban tausayi taji yace " Seemah wani abu na damuna." D'ago wa tai ta kalleshi idannunta sukayi raurau tace " Name fa?" Ya kalleta a hankali yace " Tunda aka fara zancen auren mu ba wanda naji ya tambayeki ko kin amince da hakan, na sani sarai haryanzu son da kike ma Jalal bai bar zuciyarki ba haka kuma bana kaunar wani abu dazai sa in zama nine sillar tauye miki rayuwar farin cikin ki, Seemah ina tsoro......." Hannu tasa ta rufe mai baki hawaye suka zubo mata a hankali ta shiga girgiza mai kai, tace " Ya Ammar na san sarai meke ranka haka kuma nice na zab'a ma kaina auranka bawai d'an ance ba, a'a sai dan nima na amince, kasani sarai bazan iya auran Deen ba bayan abinda ke tsakanin iyayenmu bazan tab'a bin san zuciyata ba akan farin cikin ka dana Dad, nasani kuma ko ince jikina ya bani da ace mahaifiyata nada rai itama wannan zab'in zata min." Ta share hawayenta sannan ta zare hannunta daga bakin Ammar tad'an yi murmushi tace " Karka damu Yaya nasani a hankali zuciyata zata manta da Deen sannan ka manta shima yayi aure? Maybe ma ya manta dani." Ammar ya goge kwallar data zubo mai yace " Seemah?" Mik'ewa tai da sauri tad'an juyamai baya tace "Yaya nafi kowa sanin babban farin cikinka a duniya bai wuce ka ganni ina cikin farin ciki ba na sani sarai da hakan sai dai nima bazan iya jurar ganinka cikin bakin ciki ba." Ammar ya matso kusa da ita baice komai ba sai dai kalamanta sun mai dad'i sosai, juyowa tai ta kalleshi sannan tamai murmushi. Kasa magana yai hakan yasa ta rangwab'ar dakai tace " Yaya baza'a barni in kwanta da wuri ba?" Da sauri yai hanyar waje yana cewa " Inafa zanso hakan." Ta kalleshi har ya fita, yana fita ta sulale ta tsugunna a katsa tare da rufe fuskarta da hannu biyu, hawaye ne suka gangaro mata ta d'aga hannu sannan tace a fili " Allah na rok'eka ka yayemin san Deen daga Zuciyata kakuma taimaken soyayyar danake ma Ammar ta 'yan uwanta ka ta juye ta koma soyayyar aure." Nan ta shafa sannan ta zauna a gun....... Washe gari da safe suka hau jirgi suka baro kasar England.... Nima nace Allah ya tsare... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣3⃣ Jalal kam da safe ya shirya ya fita, gidan Tv d'in *KARAMCI* ya nufa yana isa ya kira director Abbas, nan ya turo aka shiga dashi ciki, sai da aka gama yawo dashi ya gama kallan ko ina kafin ya karasa cikin office d'insa, yana shiga yaga mutane guda uku, nan ya mik'a musu hannu suka gaisa, bayan sun nutsune Director ya kalli Jalal sannan ya kallesu yace " Shine wanda nake baku labari, wanda da kyar ya amince da aiki damu." Suka kalli Jalal sukai dariya d'aya daga cikinsu yace " lalai munsha labarinka tunda ya dawo daga Germany bashida hira sai ta ka." Jalal ya d'an yi murmushi kad'an sannan yace " naga ko ina ba komai yayi sai dai na duba programs d'inku kamar akansu ne zamuyi gyara sannan bakwa zuwa neman rahotanni da kanku, in har munaso gidan Tv d'innan ya zama ba kamarshi to sai mun dinga yawon d'auko rahotannin dazai sa hankalin mutane ya raja'a a kanmu." Director ya kwashe da dariya yace " hakane kam, ya kuka ga Journalists d'in namu?" Nan suka shiga tafamai sukace lalai munyi dace. Jalal ya juya kai shi mamaki yake gani yai abin baikai abin dariya ba ko tafamai ba amma ya kasa gane meyasa sukeyi. Nan ya fara tambayarsa akan program d'in dayace yanaso yai, Abbas yai murmushi yace " Jalal anyi dace shi da jiya dana kirashi ma cewa yai ko yau ne ayi saboda dama zab'e ya kusa yanasan ya nunama talakawa yanda yake kaunarsu." Jalal yai wani mugun murmushi yace " gaskiya ne yanzu ka d'an kirashi muje ko gobe yanada lokaci." Ba musu Abbas ya kirashi, PA d'insa ne ya d'auka nan Abbas ya mai bayanin dalilin kiran, PA d'in yace "ok ba damuwa in ya fito daga meeting zan kiraka." Bayan sunyi sallama ya kalli Jalal tare da fad'amai abinda ya faru, Jalal yace " ba wani abu nizan koma yanda kukai naji, sai dai ina so ka fad'amai shirin da zamuyi dashi LIVE zamuyi, munayin shirin alokacin kuma mutane suna kallo ba wai sai mun gama anyi editing ba ko wani abun." Abbas ya jinjina kai yace " zam sanar mai." Jalal ya musu sallama ya fita, gun Sagir ya wuce ya tattara takardun dayasa Sagir ya had'amai sannan yace " Sagir gida nake nema ina tunanin zan fara aiki anan gwara in nemi gida." Sagir ya kalli Jalal yace " Karka damu zansa a dubama amma wani iri kake so?" Jalal yai shiru can yace " gida dai dabazai wuce daidai karfina ba, kamar falo d'aya da d'akuna uku, saboda ina tunanin in nace zan dawo nan sai an tilastani d'auko Zainab." Sagir ya girgiza kai yace " Yanzu Jalal matar taka ce sai ma an tilastaka zaka d'auko ta?" Harararsa Jalal yai yace " mubar maganar nan kar raina ma ya b'aci." Sagir ya girgiza kai yace lalai Jalal, wayarsa ya d'auko ya kira Abba, bayan sun gaisa ne Abba yace yanzu zamu taho inaji wajen magrib dai zamu iso, nan sukai sallama. Su Seemah an dawo gidan Abba, kowa murna yakeyi,nan Dad ya sanar musu cewa ya shirya 'yar karamar walima gobe na taya Seemah murnar gama karatunta. Dadaddare Abbas ya kira Jalal ya sanar dashi Abdul ya amince gobe da karfe 2 zai zo su gabatar da wannan shirin, Jalal ya saki wani murmushin farin ciki, Abba dake zaune yanacin abinci ya kalleshi yace " Jalal kai da waye naga kana farinciki haka?" Jalal ya girgiza kai yace " ba komai, gobe in Allah yakaimu sai dai kai ka fara zuwa gidan su dad d'in ni sai zuwa la'asar zan karaso." Abba ya jinjina kai yace " gwara hakan ma dama banasan muje tare insaka bada hakuri akan abinda bakama sani ba." Jalal yai shiru baice komai ba, komawa yai kan kujerar da aka ware a d'akin hotel d'in dan masu aiki ya kunna laptop d'insa ya fito da takardunsa ya shiga dudubawa, har Abba yai bacci sai wajen karfe 1 sannan shima ya kwanta a kasan carpet d'in d'akin. Jalal tun karfe bakwai da rabi ya fita sai dai ya samu wani driver da taxi ya sanar dashi karfe 1 yaxo ya d'auki Abba yakuma mai kwatancen inda za'akaishi, gidan Tvn Karamci ya wuce nan suka shiga shirye shiryen gun da zasuyi program d'in haka kuma tun jiya aka d'inga tallan shirin a gidan tv har yau da safe, komai ya shiryu yanda ya kamata. Karfe 1 Abba ya fito duk da jikinsa a sanyaye yake sai dai inya tuno Zahida sai yaji bayajin shakkar ko ma menene. Sukam gidan su Abba kowa yana cikin farin ciki, sani ne ba'ai ba amma Abba da Dad sun sa Mami da matar dad sun gama shirya komai na lefe yau ne kuma suke sa ran a nunama yaram tunda dai komai a gida ne, gida sai farin ciki akeyi, Abba ya karaso gidan ya tsaya a bakin kofa, mai gadi ya kalleshi yace " Malam gun wa kazo?" Abba jiki a sanyaye yace " Isma'il nake nema." Mai gadin yace " yana ciki zaka shiga ko a kirashi?" Abba ya d'aga mai hannu yace " bakomai bari na shiga." Nan Abba ya shiga harabar gidan ya tsaya yai shiru,; Ammar dake zaune a harabar gidan ne ya kalleshi da mamaki ya taso yazo kusa dashi, hannu ya mik'amai suka gaisa, Ammar yace " wa kake ne....." Kamar Jalal dake d'auke a fuskar Abba ne yasa Ammar kasa karasawa, A ba yai d'an murmushin yak'e yace " Isma'il nanan kuwa bawan Allah?" Ammar ya kara kallansa yace " yana ciki anma....." Abba ya katseshi da cewa " Amadu sunana mahaifin Jalal." Da sauri Ammar yai baya cikin mamaki yake kallansa, Abba yai murmushi yace " Ka ganeni kenan d'an saurayi, da gani kai sa'an Jalal ne nasan bazai wuce Ammar ba ko?" Ammar ya kalleshi idanunsa sunyu jaa, Abba yai jinjina kai cikin kalar tausayi yace " ga kamanan ai nagani." Ammar ya daure dakyar yace " muje yana ciki." Abba ya gyad'a kai sannan yabi bayanshi. Sun isa kofar falon, Ammar ya kwankwasa, Abba, kawu, Dad, da Habib suna zaune suna hirar yanda suke tunanin auren zai kasance, jin kwankwasa kofa yasa suka maida hankalinsu kan kofar. A hankali Ammar ya murd'a kofar ya shigo, kallanshi sukai sai dai gani sukai shima yana kallan kofa, hakan yasa suka maida hankalinsu kan kofar d'an da alama wanine zai shigo. Abba ne ya matso a hankali kansa a kasa, Dad ya kura masa ido, gani sukai Dad ya mik'e cikin b'acin rai ya nuna Abba yace " Amadu me kakeyi anan?" Abba ya d'ago idanunsa da suka ciciko, Abban Zaid ma ya mik'e a zuciye yace " kai ko kunya bakaji ba ka zo gidan nan?" Abba cikin wata murya yace " Ku bani izinin shigowa dan Allah." Dad zaiyi magana kawu ya katseshi da cewa "ya isa haka, bakon mu ne bako kuwa ku menene ba'a wulakantashi." Kawu ya kalli Abba yace shigo ko? Jiki a sanyaye Abba ya shiga gwiwowinsa ya sa a kasa ya sadda kansa kasa, duk yanda yaso ya b'oye hawayensa sai da suka zubo ya share tare da d'agowa ya kalli Dad yace " Isma'il na fi kowa sanin yanda ka tsaneni haka kuma nafi kowa sanin dalilin tsanar dakamin, naci amanarka na kuma yaudareka, nasakaka a kuncin rayuwar da duk farin cikin da kake ciki bazai d'aikema wancan bakin cikin ba." Ya goge hawayen dake zubo mai yacigaba " Na rok'eka ka yafemin ba wai dan ni ba sai d'an darajar ma'akinmu, Isma'il naga ishara kala kala akan cin amanar abotar danai, yarinyata tana kwance ko mek'ewa batayi haka magana tun tana karama take a kwance." Ya kara goge hawayensa yacigaba " ga yaron da nakeso Jalal san da yakema Seemah ya wuce duk yanda kuke tunani saboda ita ya canza karatunsa sannan mun mai aure amma inaa babu alamar shakuwa ko wani abun tsakaninsu, wannan abun danai yasa d'ana haka cikin yanayin daban tab'a tunani ba sam yadaina farin ciki......." Kuka ne yaci karfinsa, kowa yai shiru Ammar ya share kwallarsa, Dad kam kansa yai kasa dashi Abba ya d'ago cikin tsananin kalar tausayi yace " Isma'ila ka yafemin ni nasan abinda na gaji tun bayan faruwar abin nan muke cikin rashi mai karfi, Jalal shi yai wahalar karatunsa haka kuma ya taimakemu, sai yanzu da Allah yataimakeshi ya zama wani abun, ka yafemin ko d'ana zai fara aiki cikin sa'a sannan yarinyata ta samu lafiya." Sunyi shiru kowa ya kasa magana sai dai tausayin Abba ya ratsa kowa, agoggo Abba ya kalla, ganin karfe 2 daidai yasa ya kalli Abban Zaid yace " D'an Allah a kunna tashar Karamci Jalal yace yanada sako mai amfani dazai isar, sannan Seemah ta taimaka itama ta kalla." Kallan mamaki sukai mai, Habib ya mik'e da kanshi ya kunna sannan ya kalli Ammar yace " ka kira Seemah muga sakon." Ammar ya juya ya fita. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣4⃣ Seemah ta shigo falon itada Ammar da Zaid, kowq ya tattara hankalinsa akan Tv d'an ganin me Jalal ke kokarin isarwa. A b'angaren Jalal kuwa bayan sun gama shirya komai, Senate Abdul ya shigo cikin isa directors da producers d'in kowa ya fito yana gaidashi, Jalal kam na zaune akan kujerar da zai gabatar da shirin, bayan sun gama gaisawa ne Senate ya kallesu yace " da wa zamu gabatar da shirin ne? Ban samu na ganshi ba." Abbas ya juya yana neman Jalal can ya hangoshi gaba d'aya ma hankalinsa baya kansu, da karfi yace " Jalal?" Juyowa yai ya kalleshi, Senate ma ya kalli inda director d'in yake kallo, Jalal ya musu murmushi sannan ya d'aga musu hannu, Senate ya kara kallan Jalal yace " waye shi dabazai zo gaidani ba?" Abbas yai gyaran murya yace " hmm dashi zaku gabatar da shirin takardun da zakuyi amfani yake dubawa, ai shi haka yake bashi da magana." Abbas kam yai kokari gurin kare Jalal. Abdul yai murmushin jin dad'i a ransa yace indai bashida magana ai hakan sai yafi dad'in yin shirin. Kara kallan gun da Jalal yake yai kamar yasan fuskar amma a ina? Watsar da tunanin yai nan ya karasa ya zauna a kujerar dake kallan ta Jalal. Jalal ya sakar mai murmushi tare da gaidashi, Abdul ya aksa tare da cewa lokaci yayi mu fara? Ina d'an sauri ne. Jalal ya d'aga kai sannan ya mik'e ya duba komai, sai daya tabbatar komai yayi sannan karfe 2 dot da buga, suka fara gabatar da shirin kamar haka. Jalal ya gaida mutane sannan ya sanar musu da sabon shirin su na yau da kuma babban bakon da suka gayyata wato *Senate Abdullahi* wanda yake tunanin neman kujerar shigaban kasa. Bayan Senate ya gaishesu ne shima Jalal ya kalleshi yace " Honourable Senate kayi mukamai da dama tun daga kan Chairman har zuwa matakin da kake yanzu, shin ka tab"a fuskantar wani matsala a harkar siyasarka?" Senate yai murmushi yace " hmm gaskiya ban tab'a samun matsala ba sai ma kaunar da talakawa ke nunamin inajin dad'i kwarai da yanda suke bani had'in kai." Jalal yai murmushi yace " Gaskiya ne mutane na sanka, Allah ya kara d'aukaka." Senate ya amsa da Ameen. Jalal yace " Yanda mutane kesanka baka tunanin ka tab'a bata ma wani rai ko musgunawa talakawa da saninka ko cikin rashin sani?" Senate ya had'a hannayensa biyu tare da kara sakin fuska yace " a iya sanina ina kokari gurin kyautatawa talakawa da mutane ina kuma kaunar talakawa kamar yanda nakesan nawa 'yan uwan to menene zaisa ni na wulakantasu? Bayan sun zama jinin jikina." Jalal ya saki wani mugun murmushi ba shakka wannan mutumin ya iya siyasa Jalal ya cigaba " Gaskiya ne kam kana kokari gurin kyautatawa mutane, sai dai ina fatan Allah yasa yanda kakesan talakawa 'ya'yanka ma su so ka haka." Gaban Senate ya fad'i me mutumin nan yake nufi? Bai amsa mai ba Jalal yai saurin cewa " yanzu 'ya'yanka nawa?" Abdul ya kalleshi me ya kawo zancen 'ya'ya nan? Amma ya daure yace " 'ya'yana uku mata 2 sai namiji yanzu yake primary 6." Jalal ya jinjina kai yace " Allah sarki, Allah yaraya manasu." Abdul ya amsa da Ameen. Jalal ya kalli Camera yace " Kada ku manta kuna tare da babban d'an siyasan nan wanda talakawa ke kaunarsa wato Senate Abdul. " Nan aka sake nuno Senate yana murmushi. Jalal ya kalleshi yace " Sanda ka fara siyasa kayi aure ne?" Abdul ya girgiza kai yace " A'a lokacin dai an kusa yin auren." Jalal ya jinjina kai yace " munji labarin matar da zaka fara aura Allah baiyi auren tsakaninku da ita ba ko?" Abdul ya bugama Jalal wani kallo tunawa dayai live ake d'aukansu yasa ya saki murmushi yace " gaskiya ne, matsala aka samu aka fasa auren." Jalal ya d'an gyad'a kai alamar tausayi yace "Ayya!!! Na tabbata matsalar badaga kai bane." Abdul ya d'anyi kasa dakai kamar me shirin kuka yace " amanata taci." A ran Jalal yace " thank God." Jalal ya kalleshi da mamaki yace " Amana kamar tame fa? Na tabbata masu kallo suna san ji." Abdul ya had'iyi yawo yace " Amanata taci da wani banasan tuna asiri irin wannan a bainar jama'a." Jalal yace " gaskiya ne ai tona asiri ma bashi da dad'i sai dai muce Allah ya rufa asiri." Abdul yace " Ameen." Jalal ya kalleshi yai murmuaji yace " Yanzu amma nasan ka yafe mata ko?" Abdul ya kalli Jalal yace " na yafe mata d'an ni mutum ne mai saukin kai banasan kulatar mutum." Jalal yace " I see, amma shi wanda yaci Amanar taka fa? Kana da wani sako zuwa gareshi ne ko kuwa shima ka yafemai?" Abdul ransa ya fara b'aci ya kalli Jalal sannan ya daure yace " ba wani sako danake dashi, Amanata ya riga yaci nikuma na yafemai ." Jalal ya d'an rangwab'ar dakai sanar ya murza ido, yana bud'e idanunsa Abdul yaga idanunsa sun kad'a sunyi Jaa kana ganinsa kasan b'acin rai ne karara a bayyane a idanunsa tsoro ya fara kama Abdul. Jalal ya kalleshi da jajjayen idanunsa yace " Amma a binciken da mukai sai mukaji kamar fyad'e akama matar da zaka aura?" Ba Abdul ba hatta ragowar masu recording sai da suka kalli Jalal cikin tsananin mamaki, a falo kuwa gaba d'aya sun kame kallan tv kawai sukeyi. Abbas ya rasa yanda zaiyi yama Jalal magana tunda dai abin live ne. Abdul ya kasa magana, Jalal ya d'an murmusa ta gefe yace " Ina mamakin namijin dazai iya yafema wada yama matarsa fyad'e ana saura kwana biyu auransu." Abdul idanunsa shima suka fara canza kala, tsoro ya fara kamashi, Jalal ya kara wani murmushin yace " gaskiya na jinjina maka ba kowani namiji bane zai iya yafemasa." Abdul hannunsa ya fara rawa cikin rawar murya yace " haka ne ni amma daga baya nai tunanin rashin d'aukan abin da zafi hakan ne yasa na yafemai." Jalal ya d'aga kai tare da had'e fuska yace " amma sai naji kamar wanda akace yayi fyad'en shi kuma yace sharri aka mai" Abdul ya zazzaro idanuwa cikin tsananin tsoro yace " me kake nufi da kalamanka?" Jalal yai murmushi yace " ni d'an jarida ne ba lawyer ba bincike ba nawa bane sai dai a labarin da mukaji Kamar fyad'an ba shine yai ba sharri akamai, zai iya yiwuwa wanda ya mata sharrin ko bayasan auranka da ita yarinyar ne ko kuma santa yake, ko kuma......" Jalal yai d'an karamin hucci yace " nayi mamaii a binciken ku da bakuyi bincike ba cikin wannan al'amarin." Abdul ya mik'e a zuciye yace " me kake nufi? Wani nakusa dani ne dan bayasan na aureta ya mata fyad'e ko kuwa so kake ma kace ni na mata gaba d'aya , gayyatata kukai d'an ku wulakantani ko me? a iya sanina Fatima ta rasu, to waye zai ce nine na......." Murmushin da Jalal ya sakar masa ne yasa yai saurin rufe bakinsa sam yamanga abin live ne, Jalal ya rike baki irin abin mamakin nan yace " badai kaine ka.....ahhh nasan haka bazai faru ba da kaije da tuni ka nemi 'yarka tunda ance har haihuwa tayi sannan da ka sanar damu 'ya'yanka 4 nasan ba kaibane to amma ban fah........" Abdul ya fusata a zuciye ya d'aga hannu zai wankama Jalal mari, murmushi Jalal ya masa sannan yace " karka bari mutane su fahimci b'oyayen halinka da kake kokarin b'oyewa." Cikin tsananin takaici da bakin ciki Abdul ya fita. Jalal ya kalli Camera yace " muna sa ran kuto zatai kokari wajen gano mana gaskiyar wannan al'amarin kar muzu mu zab'i shugaban da ake kokwanto a kansa Bissalam." Abdul ya fita a zuciye sai dai me? Yana fita zai shiga mota yaga mutane dayawa da ragowar 'yan gidan wasu tv d'in da gidan radio suna juranshi. Jikinsa ne ya shiga rawa ya kasa tunanin komai... Seemah kam da gudu ta mik'e tabar falon. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣5⃣ Abdul ya kara kallan mutanen a zuciye ya koma ciki, Jalal kam yana ma mutane sallama da kuma sai sun jisu a sabon shiri na gaba kawai yaji an shakumo mai riga, kallan Abdul yai cikin mamaki sam idanun Abdul ya rufe ya manta shiri akeyi kuma live, cikin masifa da bakin ciki yace " kai waye kai? Me na maka ko ince menene tsakanina dakai da zaka aikama ragowar 'yan jaridu dasuzo? Dama can ka shirya ci min mutunci ne bawai shirin mutunci kaso yi ba ko?" Jalal ya kalleshi yace " Senate me kake yi haka bakaga shiri akeyi ba? Mutane fa suna kallanka." Cikin masifa yace " da a kalleni da kar a kalleni ai ka riga ka gama cimin mutunci ya fad'a tare da nunamai Jaridar da P.A d'insa ya kawo masa yanzu." Jalal ya kalli head line d'in inda ya bud'e " *SHIN DA GASKENE SENATE ABDULLAHI BASHI DA HANNU AKAN FYAD'EN DA AKAI?* Jalal yai murmushi tare da ba masu aikin umarnin su daina d'aukan rahotannin, bayan sun daina Jalal ya kalleshi ya sakar mai wani mugun murmushi yace " Bana tsoronka, ba kuma na tsoron abunda zakamin, ka manta kalamaina lokacin dana je gidanka?" Abdul ya kalleshi da mamaki "kai ne kaje gidana?" Jalal ya d'aga mai gira yace " Kayi tunani dakyau, sanda nazoma da zancan 'yarka wani cin mutunci kamin ko ince kama yarinyar da ba ruwanta?" Nan fa Abdul ya tuno jikinshi ne ya shiga rawa ya sake Jalal yana girgiza kai, kamar zararre. Jalal yad'an zumburo baki yace " ayya I pity you, gashi yanzu na kai kararka kuto kana zuwa gida zakaga sammaci." Kai Abdul ya cigaba da girgiza wa yace " karya kake d'an talakawa, ko Amadu bai isa yaja dani ba bare kai, inada arziki da karfin da ba wanda ya isa ya ja dani." Jalal ya jinjina kai tace " hmm gaskiya ne wannan ni kaina na shaida, sai dai wannan karan dukiyarka da matsayinka bazasuma amfani ba, d'an kuwa al'uma sunga halin da ake ciki kana tunanin wani zai taimaka maka bayan shima yana tsoron kar mutane su tsaneshi irinka?" Abdul cikin tsananin takaici ya d'aga hannu zai mari Jalal, hannu Jalal yasa ya rik'e hannunsa sannan yamai murmushin rainin hankali yace " wlh wlh kaci darajar jininka ne ke ya wo a jikin Seemah da wlh sai na maka abinda yafi wannan, sai naci ma zarafin da har karshen rayuwarka bazaka manta da abinda kama Fatima, Dad wato Malam Isma'il, Mahaifiyarsu Ammar da kuma Mahaifina Amadu ba da sai na sa ka fisu wulakanta a doron kasar nan." Abdul ya kalli idanun Jalal yanda sukai jaa, tsoron kalaman Jalal ne ya fara kamashi ya kalli Jalal a tsorace sannan ya fizge hannunsa, Jalal ya had'iye wani abu sannan yace " ka b'atama mutane dayawa rayuwarsu tayaya ma zakayi rayuwa cikin farin ciki? 'Yar ka da batama sanka ba baka tab'a tunanin nemanta ba saboda giyar mulki na d'ibanka." Harya bud'e baki zai sake magana sai kuma ya fasa ya juya ya fara tafiya, har yad'anyi nisa ya tsaya tare da cewa " sai na ganka a kuto." Jalal ya wuce su Abbas da duk sukai tsuru tsuru suna kallansu cikin tsoro. Jalal fita yai direct yahau sabuwar motar daya sa Sagir ya siyomai, kirar Mercedes benz fara tas, gidan su Abba ya wuce. Sukuwa a b'angarensu Abba jikin kowa yagama yin sanyi, Dad ya share hawayen daya rasa na dadi ne ko name, ya kalli Amadu yace " Amadu a wani dalilin zaka bar Jalal yai wannan abu mai hatsarin gaske? Me kakeyi da bazaka hanashi ba?" Amadu ya share kwallarsa yace " Isma'il wlh sam bansan me yaron nan yake shirya wa ba nidai kawai cemin yai ince a kunna tv a kuma kira Seemah." Abban Zaid ya kalli Amadu yace " Abdul bazai bar jalal haka ba, amma dama Abdul shine yama Fatima fyad'e?" Nan Amadu ya warware musu komai na abinda ya faru. Sunyi shiru kowa na tunanin mafita, samari 'yan gari kuwa sun fito da sanduna suna zanga zanga a kofar gidan Abdul akan dolene ayi bincike dan suma basu yarda ba. Jalal kam bayan ya isa gidan yai parking motarsa ya fito, a harabar gidan yaga Zahra da Zaid a tsaye, jiyai Zahra tana cewa " Yaya Zaid kazo ka duba Seemah inajinfa ba lafiya take ba wani abu takeyi kamar ba'a hayacinta take ba." JALAL ya matso da sauri yace " ina Seeman?" Zahra ta kalleshi da mamaki, Zaid yace " Jalal zo muje." Nan sukai d'akin da Seemah ta rufe kanta a ciki, Ammar suka gani a tsaye a kofar yana kwankwasawa tare da kiran sunanta. Jalal yasha jinin jikinsa, tsayawa yai cak batare da ya karasa ba. Ammar ya kara buga kofar yace " Seemah meyasa kike min haka? So kike kiga hankalina yayi matukar b'aci ko kuwa?" A hankali Seemah ta mik'e tazo ta bud'e mai kofa tana bud'ewa ta fad'a jikinsa ta rungumeshi tana wani irin kuka, Ammar ma kwalla ce ta taro mai a ido, yace " Seemah menene? Mahaifin naki ne bakyaso ko kuma nakiso akacimai mutunci ba?" Kai ta girgiza tace" ni ba mahaifina bane, Dad ne kawai mahaifina, sai dai Ya Ammar nasan mutumin nan, na tab'a ganinshi a hotel d'in daka zauna, yaya bashida mutunci na tsorata da gani mutum irin haka. " Jalal ya share hawayen daya zubo mai sannan ya kakaro murmushi tare da juyawa zai fita, Seemah zata sake magana kawai ta hango kamar Jalal, da sauri ta saki Ammar sannan cikin kakusar murya tace " *DEEN WAIT* Tsayawa Jalal yai cak ba tare daya juyo ba, Seemah ta kalli Ammar tace " Yaya in mai magana?" Gaban Jalal ne ya fad'i jin kalaman Seemah, amai magana? Au in zata mai magana sai ta nemi izini? Idanunsa ya runste. Ammar ya d'agama Seemah kai sannan ya juya ya bar falon, ba shakka yaji dad'in yanda Seemah tabashi matsayi. Zaid ma ya juya yai waje, Jalal baisan Seemah ta karaso ba jin kanshin turarenta yasa ya fahimta, a hankali ya bud'e idanunsa ya zubasu akanta. Seemah ta kuramai ido gyambon data d'auka ya warke ne ya motsa, hawaye ne ya zubo mata, shima hawayen ne ya zubo, bakinta ya fara rawa ta kasa mai magana. Jalal ya goge hawayensa sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace " how have you been?" Kallansa kawai take ta kasa magana, Jalal ya d'aga kai ya d'an ja hanci yace " I see, ya za'ai ma in tambayeki haka bayan nagani you are fine." Ya had'iye wani abu yace " kinga abinda akai?" Kai ta d'aga mai tana hawaye, Jalal ya share nashi hawayen tareda cewa " meyasa ruwan nan yaki daina zubowa daga idona, inaji wani abu ya fad'amin ne." Kallan tausayi tamai tace " Deen me ya kaika shiga harkar mutumin can? Kasanshi kuwa? Kasan wani irin mutum ne?" Jalal ya kalleta ya d'anyi dariya tare da cewa " Koma wani irin mutum ne ai baifi karfin Allah ba, sannan ni ba tsoronshi nake ba kin manta nine?" Tasa hannu ta dakeshi da karfi a kirji tace " Deen meyasa kake abu domin ni? Meyasa bazaka manta dani ba? Why? Why are you making me miserable. " Ta sa wani irin kuja tare da tsugunawa akasa. Jalal ya kalleta zaiyi magana Ammar ya karaso gun ya d'agata sannan ya kalli Jalal, Seemah ta kara sa kuka tace " Ya Ammar?" Ammar ya mata alama datai shiru yace " wuce d'aki." Ya fad'a tare da goge hawayensa. Seemah ta juya tai d'aki tana tafe tana waiwayen Jalal. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣6⃣ Ammar ya dawo da hankalinsa kan Jalal hannu ya mikamai suka gaisa, Ammar ya kalleshi yace " Jalal mutumin da kai magana dashi wannan mara mutuncin shine kakeso kacemana mahaifin Seemah ko me?" Jalal ya kalli Ammar yace " ni kaina dana fara ganinshi ban amince ma idanuna ba." Ammar yace " inaaa... da sake taya za'ayi Seemah wacce ba ruwanta me mutunci ace ta fito daga tsatson wannan mutumin? I just can't believe it." Jalal yad'an dafashi yace " Ammar kamar ka manta fyad'e yana mahaifiyarta? Duk mutumin da zai ma wacce saura kwana biyu ya aura fyad'e ai kasan sai a hankali sai dai koni banyi zatan rashin imani da mutuncin sa yakai haka ba." Ammar yai shiru, Jalal yai murmushi yacigaba da cewa " kamanta Allah ne ke fitar da rayyaye acikin mattace kuma mattace acikin rayayye? Please Ammar ka daure zuciyarka idan zuciyarka ta karaya tun yanzu ya kakeso Seemah tayi?" Ammar yad'an ture hannunsa daga kafad'ar sa ya kifta ido yace " waya fad'ama zuciyata takaraya? Sannan ce maka nai mun zama abokai da har zaka wani dafani?" Yanda yai maganar ne yasa Jalal yasa dariya yace " Ammar bansa kanada wannan cute site d'in ba, duk sanda muke had'uwa cikin d'aurewar fuska muke." Ammar ya d'an harareshi yace " yanzun ma acikin b'acin ran nake ai." Jalal ya kalleshi yace " tuba nake Ammar nasan akan me kake cikin b'acin rai sai dai nasani tuni Seemah ta cireni a ranta kaima kasani dazatamin magana fa sai data nemi izininka." Ammar yai shiru kawai yana kallan Jalal aransa yace Jalal kenan. A fili ya wayancewa da cewa " kaje falo nasan Dad nasan ganinka." Jalal ya d'aga kai alamar to sannan ya kalli kofar d'akin da Seemah take ya wuce. Ammar bayan yaga Jalal ya wucene shikuma ya wuce d'akin Seemah, knocking yai dama tana tsaye jikin kofar tanasan jin me suke cewa sai dai ta kasa jiyosu, bud'ewa tai Ammar ya shigo. Kallanta yai ta kalleshi tanasan tambayarsa meya cema Jalal sai dai inaa bazata iya ba, ta daure tace " Yaya amma ai ba mutumin nan bane mahaifina bako?" Ammar ya kalleta kai ta girgiza tace " haba dai yaya it can't be, mahaifi fa akace, da mahaifinane ina ganshi ai ina tunanin jikina zai bani munada alaka dashi amma ni farkon ganina da tsanarsa na wuce ta ya zakuzo kucemin mahaifinane?" Ammar yad'an harareta yace " na d'auka Seemah ta tace ba ruwanta koma waye mahaifinta itadai Dad ne nahaifinta." Da sauri tace " eh haka ne amma...amma...amma.." Ammar yasa dariya yace " amma me? Yau kece kike in ina?ko rasa abin cewa kikai?" Ta juya yai tare da rangwab'ar dakai, Ammar yai murmushi yace " karki damu kinji kinmanta nabarmiki Dad nina koma d'an gidan Abba?" Juyowa ai tana dariya tace " kai yaya." Yace "ahhbhh aikina ya biya tunda kinyi dariya." Kallansa kawai tai batace komai ba, ya matso kusa da ita tare da turo fuskarshi kusa da ita yace " kallam fa?" Tasa hannu tad'an ture fuskarshi kad'an sannan tace " kai Yaya." Tai maganar kamar zatai kuka, yai murmushi sannan ya fita, har yaje kusa da kofa ya tsaya, jitai yace " Jalal nagunsu Dad." Da sauri tace cema akai inasan insan inda yake?" Yanakai nan yai waje yana murmushi, Seemah kam yana fita ta furzar da wata iska tace " Deen me kakeyi acan?" Jalal kam bayan ya shiga azazzaune ya taddasu suna maganar Abdul, Dad yace " nasan Abdul fa, bansan ya akai ya canza haka ba, duk ba bayaji amma iskancinsa baikai haryai fyad'e ko shan giya ba, nadaisan yana shan taba, ina mamakin yaushe ya koma haka." Abban Jalal yace " Abokan fa? D'an alokacin bazan manta ba shima kamar bayasan shawarar fyad'en da kuma kama Jalal kawai dai sun sugashi ne sannan yana kwad'ayin hakan dama a kasan ransa." Abban Zaid ya kalli Jalal yace " matsonan Jalal." Nan Jalal yazauna kusa da Junaid tare da gaidasu, Dad yai ajiyar zuciya yace " Jalal kasan mutumin nan mai karfi ne tunda Senate ne da mutane ke sanshi meya kaika yimai haka? Sai ka sanar damu." Jalal zaiyi magana wayar Sagir ta buga Abban Zaid yace " d'aga mana." Jalal ya d'aga tare da cewa " Sagir ya akai?" Sagir cikin tashin hankali yace " Jalal duk an tsayar da saida Jaridun nan sannan duk 'yan jaridan nan sun watse daga gidansa." Jalal yace " What?" Sagir yai ajiyar zuciya yace " Jalal yazamuyi? Nasan yanzu kanka abin zai dawo." Jalal yad'an mike daga gunsu Abba zai d'an fita, Dad ne ya rikosa yace " yi wayar anan." Kallansa Jalal yai sannan ya daure yace " Sagir karka damu ai dama nasan hakan zata faru, in ba'ai hakan ba kenan ba mutum bane mai matsayi." Sagir yace " to sai kazo." Nan suka kashe wayar, Jalal ya kalli Dad yad'anyi murmushi yace " Dad is not a big deal." Junaid ha kalleshi yace taya zakace haka bayan da alama Abdul is out to get you." Jalal ya kalli Abbansa sannan ya kalli Dad yace " Dad zan koma Birnin gwari yanzu nasan nan zai nufa dan cimin zarafi." Dad kallan Jalal kawai yake, Abban Zaid ne ya daure yace " Jalal ka cire hannunka daga abun mutumin nan, mu zamu karasa abinda ka fara." Jalal ya girgiza kai yace " me kenan akai Abba? Na fara abu sannan inbarku ku karasa? Idan Abun yazo da downfall d'ina sai in jawoku mu fad'i gaba d'aya kenan?" Ammar ne ya katseshi da cewa " Ni zan rakashi muje Birnin gwarin tare, Abba dukanki please karkusa hannu a wannan harkar." Jalal ya kalli Ammar yai murmushi, Ammar yai saurin juya kai tare da cewa " malam daina min murmushi bancema munzama abokai ba tukun." Dariya dukansu sukasa a falon, Abban Jalal yace " nufinka kenan kunzama abokai, dama can abokan ne ku." Ammar yai saurin juyawa ya fita, Jalal yai kasa dakai yana murmushi, Junaid ya matso kusa dashi yace " Ammar tsoro yake karka tafi kai kad'ai wani abun ya sameka." Jalal ya jinjina kai yace " nagane nima, bayaso ya fad'i abinda ke ransa ne." Nan suka sakeyin murmushi. Ammar d'akin Seemah ya koma, a bud'e kofar take, Seemah tana zaune Zahra na tsaye tana 'yar mita yanzu shikenan baza ai partyn ba? Nafa fad'ama kawaye na, wai meke faruwa agidan ne?" Seemah ta girgiza mata kai tace " kedai fad'i gaskiya bawai partyn kikeso ba so kike kiga an kawo miki lefen ki." Zahra ta turo baki tace " eh d'in nibama lefe ba na kosa ma ai auran." Seemah tace " dama ai na sani basai kin fad'a ba da alama kekam kin gaji da gida." Zahra ta murguda mata baki tace " kefa? Baki kosa a d'aura muku aure da Ya Ammar ba?" Seemah tai shiru zatai magana Ammar yai saurin katseta da shigowa yace " Ahh Zahra na kula kina neman takurama Seemah ta." Seemah ta kalleshi, Zahra tace " haka kace yaya? Shikenan nima zan rama ai." Tana fad'a tai waje. Ammar ya kalli Seemah yace " baki mamaki ba daga fitata harna dawo?" Tai murmushi tace " nasani Yaya damuwa kai da halin da nake ciki." Yatsarsa ya nunata dashi yace "hmm wannan kanwartawa ta gama sanina." Ta juyar da kai tace " wa zai sanka bayan ni? Tare fa muka taso yaya?" Yai ajiyar zuciya yace " Haka ne kinci gari, amma naji dad'i naga kin ware." Tace " ba dole ba duk yanda kai kokari gurin sani dariya?" Ammar har kasan ransa yaji dad'in kalaman nan yace " ina neman izini." Tace " name fa?" Yai shiru can yace " Zan d'anyi tafiya ne, amma yau zan dawo." Ta kalleshi tace " Yaya inzakai tafiya sai ka nemi izini ai kawai sanar dani zakai." Yace " haka ne amma ni nafisan in nemi izinin." Tai murmushi sannan tace " an baka Allah ya kiyaye hanya." Yace Amin, sai naji kamar......." Harararsa tai tace " zaka fara ko yaya?" Ammar yace " sorry na daina, sannan ya d'aga mata hannu yai waje." Tabi bayansa da kalli tare da cewa " Deen ko ya tafi shima? Ahhh yazanyi?" Kai ta girgiza tace " me ya dameni ma da koma ina yake? Meye tsakanina dashi dazan damu?" © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _'Yan Uwa rabin jiki godiya! Jinjina! Ga 'yan uwana._ _Na sadaukar da wannan shafin ne zuwa gareku My Sweet babbar Yaya Aunty Faty, Yaya Faen and my dearest kanwa Meema ('yar fara) love you sooo much_😍😘 No. 6⃣7⃣ Ammar ya koma falon inda Jalal yake, nan suka mik'e tare da yima su Dad sallama, Zaid ne ya shigo falon ko sallama baiyi ba ya kalli Jalal sannan ya kalli Ammar yace " shine zaku zame ku barni?" Ammar ya kalleshi yace " Zaid mu zame kamar ya?" Zaid ya burtso baki yace " ko ma miye I am in, dan kuwa dani za'ayi tafiyarnan." Abbansa ya kalleshi yace " kai kuma me zakaje kayi? So kake kaje kawai ka hargitsa komai kome?" Zaid ya shagwab'e fuska yace " ni wai meyasa akemin haka ne? Ni ba namiji bane? Koma menene nidai dani za'aje." Jalal ya kalleshi yace " baka tsoro?" Hararar Jalal yai yace " tsoro? Farauta zaku ko me? " Junaid yai murmushin mugunta yace " Abba ina ganin ya kamata abar Zaid yaje, waya sani ko shima akwai tasa mahimmiyar gudun mawar dazai ba da?" Abbansa yace " waye zai bada mahimmiyar gudub mawa? Wannan?"yafad'a yana nuna zaid da hannu. Zaid cikin shagwab'a ya matsa gun Dad yace " Dad kaga Abba ko? San na kula bai yadda dani ba kallan soko kawai yake min." Dad yace " to ya isa haka, yanzu dai kaje ka shirya kai ma ka je." Zaid yace YES!!!! Sun fito su uku, Seemah na tsaye a jikin kofar falo tana d'an lekowa kad'an,, ganin Ammar, Zaid da Jalal sun nufi mota a tare yasa tai saurin bud'e kofar ta fito, kallansu tai cikin mamaki. Daurewa tai tace " Ya Ammar!" Ammar ya juyo ya kalleta, murmushi ya mata sannan ya kallesu yace ina zuwa. Zaid ya tab'e baki tare da girgiza kai yace " kuma wlh kar a shanyamu a tafi soy........"kallan Jalal dayai ne yasa ya kasa karasa abinda yake shirin fad'a. Jalal dayakejin wani abu na kishi na tasomai ya daure tare da yin yake yace " karasa Zaid karka damu dani." Yana fada ya kalli inda Seemah take, idanunta na kansa, ga Ammar na tafe kusa da ita, Jalal ya kurama Seemah ido, itama kallansa kawai takeyi har Ammar yazo kusa da ita bata kula ba. Da mamaki Ammar ya kalli inda take kallo, ganin tana kallan Jalal yai shiru batare da ya katsesu ba, sai dai kasan zuciyarsa wani irin kuna ne ke ratsashi, haka zai zauna yana kallan Seemah daga gefe tana kaunar wani ba shi ba? Jalal ne yai saurin dauke kansa daga kallan Seemah tare da saurin karasawa jikin mota ya bude ya shiga. Seemah ta bishi da kallo harya shiga mota sannan ta juyo ta kalli Ammar da mamaki tace " yaya!" Ammar ya kalleta sai dai duk yanda yakeso ya danne zuciyarsa karta gane ransa ya baci ya kasa. Kallanta yai yace " naam" Baki ta motsa dan ta fahimci ya dade agun, kasa tai da kanta da sauri tace " yaya I......." Kai ya girgiza mata yace " Zamu wuce kar dare ya mana." Ta kalleshi da mamaki tace " yaya wai da deen zaku tafi?" Yamaimaita sunan Deen? Hmm haka ne da deen zamu tafi. Ta kalleshi da mamaki yanda ya bata amsar, tace " yaya amma...." Ammar ya kalleta tare da yi mata murmushi yace " karki damu Seemah kin manta kin bani izini?" Ta d'an hade rai tace " amma ai bansan ba kai kadai bane." Ammar yace " me? Bakyasan ki ganmu tare?" Kai ta girgiza da sauri tace " a'a bafa haka nake nufi ba." Yai sake yin murmushi yace " inje? Kar suyi ta jirana." Ta daga kai tare da cewa " Amma me zakuje yi?" Ammar yai shiru kawai yana kallanta. Tai murmushi tare da cewa " shikenan Allah yakaiku lafiya." Ya amsa da Ameen sannan ya juya. Mota ya bud'e gaban mota gefen Jalal ya zaune. Zaid ne a zaune ya hakimce. Ammar a kalleshi yace " malam Zaid dan koma baya ko?" Zaid ya kalleshi yace " kamar ya?" Ammar ya furzar da wata iska yace " ahhh da ina tunanin baka number wata hadaddiyar yarinya dana gani amma da alama zan fasa." Da sauri Zaid ya kalleshi yace " da gaske?" Jalal ya guntse dariyarshi yace " gaskiya kam da alama zakai rashin yarinya. Ai kan Jalal yagama magana Zaid ya haura baya da sauri. Ammar yazauna tare da yin dariya Jalal ma dariya yasa basu san sanda suka tafa ba. Sai da suka tafa kuma kowa ya kalli window irin waskewar nan. Zaid ya matso da kansa yace " dariyar fa ta meye?" Jalal ne ya tada mota yaja batare da ya bashi amsa ba. Haka suka tafi Zaid na tasasu dariya har ya gaji yai shiru, motar tayi shiru kamar ba kowa, can cikin wata murya Jalal yace " nayi mamaki danaji zaka biyoni." Ammar ya kalli window yace " sai ka daina mamakin tinda dai gamu a hanya." Jalal ya jinjina kai baice komai ba. Muryar Ammar yaji yace " Meyasa ka zama dan jarida?" Jalal ya dan kalli Ammar kadan yace " Long wish dinane." Ammar ya kalleshi ba tare da ya gamsu ba. Jalal yai murmushi yace " why?bakai tunanin haka ba? Ko ka dauka saboda Seemah na zama?" Ammar ya kalleshi da mamaki yace " me? Ba hakan bane?" Jalal ya kalli Zaid dake bacci ta mirrow sannan yace " nidai nacema ba haka bane." Ammar ya furzar da wata iska baice komai ba. Shiru sukai har suka isa ba wanda ya sake magana. Suna isa suka fito dukansu suka nufi lungun, Zaid kam ya kasa jurewa yace " wannan lungun fa...." Ammar ne ya harareshi hakan yasa ya hadiya maganarsa. Sai dai me? Suna isa suka tada sai watsi ake musu da kaya daga ciki ake cilo kaya zuwa waje, abubuwa sai farfashewa suke. Idanun Jalal ne suka kada sukai jaaa, wani mugun bakin ciki ne da takaici suka ziyarceshi, a zuciye ya shiga cikin gidan daidai nan wanda ke watsi da kayan ya daga tabirma zai cillo. Jalal ya kalleshi, bai taba ganin shiba, ga Zainab a tsugunne a kusa dashi tana kuka tana kuma bashi hakuri, Mutumin sai ihu yake yana cewa a kira mai Jalal. A zuciye Jalal ya karasa ya rike tabirmar, mutumin ya kalleshi yace " kai kuma waye?" Jalal ya dage ya wankamai mari tare da cewa " bakama san wanda kake nema ba?"wani irin ihu mutumin yai yace " ha ha ha! Yau ni aka mara? Ni Kumurci sarkin yaki, ba wanda ya isa yaja dani wanda kuwa yai gaggawar tabani to kuwa kabarinsa ne yake bukatar ziyararsa, ihuuuu sai ni Gatari bai sare namomin daji ihu ihuhu...." Jalal ya kalli Zainab da ganinsa yasa ta mike da sauri tana hawayen tausayi, Jalal ya maida kansabkan mutumin yace " ba kumurci ba ko zaki ne kai baka isa kazo gidan iyayena ka dinga mana watsi da kaya ba." Ya matso tare da nunashi da hannu yace " tun kafin in fasa ma baki ka koma ka sanarda wanda ya turo ka, in har yana san yamin wani abu to sai dai yazo da kansa bawai ya turo wasu tsolayen mutane kamar ka ba." Yana kai nan ya fizgo hannunsa, yafara kokarin Jansa, Ammar ne ya matso ya kama dayan hannun nasa suka turashi waje suka rufe gidan. Jalal ya kalli Ammar sukama juna murmushi, Zaid kam tafi ya fara yace " wow kaii Jalal ka burgeni dayawa." Jalal ya girgiza kai sannan ya juya ya kalli Zainab, kusa dashi ta matso tace " yaya mai yasa ka fadi haka? In kuma ya turo wasu mutanen dayawa fa?" Jalal ya kalleta duk ta canza ta rame, tausayinta ya kamashi, yace " ke kadai ce a gidan?" Tace " nida kanwata ne to ta tafi islamiya ne." Jalal yai ajiyar zuciya yace " shiga ciki zan gyara gun." Kallansa tai tare da cewa " zan tayaka." Jalal ya dago ya kalleta da sauri ta juya ta shiga ciki, da mamaki Zaid ya matso ya kalli Ammar yace " wacece?" Ammar ya kalleshi yace " Zaid please keep quiet. " © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 😍😘 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 6⃣8⃣ Kallan kayan yai gaba daya ma kayan sun tsufa kamar irin kayan bulan nan, yabi kwanukan Umma da kallo idanunsa ne suka ciciko, yanaji tun kayan auranta ne a gidan, sai yan kwanukan da aka dinga siya a hankali daga baya in an dan samu wani abun, Ammar ne ya matso ya dafa kafadar sa, jiki a sanyaye Jalal ya juya ya kalleshi, Ammar yace " Jalal me kake tunani?" Jalal ya kalleshi sannan ya kalli kayan, yace " Ammar duba kagani, me nakeyi har kayan mahaifiyata suka kona haka? Kalli kwanukan da kayan sawarta?" Hawaye ne suka gangaro ta ta gefen idansa yasa hannu ya goge, Ammar ya kalli kayan shima jiki a sanyaye, sannan yace " me kakeyi kamar ya? Jalal in baka da halin canza musu satowa zakayi ko me? Kayi iya naka kokarin suma sun sani Allah ma ya shaida, kudi kake dashi a lokacin ko me?" Jalal ya runtse ido ganin kayan Abba ma duk sun kod'e yace " Amma Ammar ban nemi kudi bane a da sosai, ai da zan iya....." Ammar ya jijiga mai kai, yace " Jalal don't make ur life hard, na sani duk dabansan yakai rayuwa ba da nasan da kanada hali bazakabar iyayenka haka ba, sai dai yanzu da ka samu aikin dayafi waccan nesa ba kusa ba sai kayi kokarin cika burin dake ranka." Jalal yai shiru yana kallan Ammar, Ammar ya sakeshi tare da cewa " me kakeyi a tsaye? Munfara gyara gun ko?" Murmushi ne ya bayyana a fuskar Jalal, nan ya sukunya suka fara kwashewa, Zaid dake waje yana waya ne yashigo da sauri yace " Jalal wasu mutane ne sunzo wai hakimi ya aiko ana kiranka." Jalal yace " ni kuma? Dama akwai wani hakimi a nan garin?" Zaid yace " to nidai gasu can a waje." Ammar ya kalleshi yace " muje mu duba mana." Zainab dake tsaye ta window tana kallansu, ta sulale ta zauna a jikin bango, hawaye suka zubo mata a fili tace " Allah na rokeka Allah kasa ba wani abun Ya Jalal yai ba." Jalal na fita ya kallesu kayan fadawa ne a jikinsu, ya mika musu hannu suka gaisa, sukace " a cikin ku wanene Jalaludeen?an isar mana da sakon ya iso garin nan yanzu." Jalal ya kallesu yace " nine, menene?" Suka kalleshi dayan yace " Hakimi ne ke nemanka zakuje gurin sarkin birnin gwari tare." Jalal yace " ban gane zamuje gun sarki tare ba a wani dalilin kenan?" Suka hade rai dayan yace " kai dan gidan talakawa in an baka umarnin abinda zakace kawai shine to bawai ka dinga tambayar wanu abu daban ba." Jalal zai yi magana Ammar ya katseshi yace " bakomai muje." Jalal ya kalli Ammar fuska a hade, Ammar ya ja hannunsa gefe, bayan sun dan matsa ne ya kalli Jalal yace " Jalal calm down, muje sai muji me zasuce ai basu isadai su hukuntaka ba akan abinda bana gaskiya ba." Jalal yai tsaki yace " ni rainin hankali ne banaso, me ya damen da wani sarki dazasuzo su sani a gaba?" Yai shiru can yace " muje." Ammar ya danyi murmushi. Sunje gun hakkimi aka wuce dasu gidan sarki, Zaid ya kalli Ammar yace " amma dai ba hukuntamu za'ai bako?" Ammar ya fizge hannunsa yace " kayi wani abun hukunci ne ko kuwa?" Sunje shiga fadar hakkimi ya kalli Jalal yace " wadannan su tsaya a waje." Ammar yace " ban gane ba?" Jalal yamai murmushi yace " nima banasan mu shiga tare, at least in laifi nai I won't drag you down. " Ammar zai sake magana, Jalal ya kalli Hakimin yace " muje." Nan aka musu iso suka shiga, Sarki na zagaye da fadawa, sai dai bayan sun zauna yamusu umarni su fita,nan suka fita dukansu akabar Jalal da Sarki sai hakkimi. Sarki ya kalli Jalal yace " kaine Jalal?" "Nine Jalal." Yafada tare da kallansa. Sarkin ya dan gyara nadin rawanin daya kusa rufemai baki ya kalli Jalal yace " an turo sunan ka daga sama ance kayi babban laifi na wulakanta Senate dakai shine aka bani umarnin hukuntaka ba tare da hukuma ta sani ba." Jalal ya kalleshi yace " in kace Sama kana nufin....." Kai sarki ya daga mai, Jalal yai wata dariya yace " lalai mutanen nan basa tsoron Allah." Ya kalli Sarkin yace " I don't think kanada shirin hukuntani." Sarki ya kalleshi yace " meyasa kace haka?" Jalal yai murmushi yace " in har hukuntani kakesan yi bana tunanin zaka aiko a kirani kuma har ka sanar dani ai aiko a hukuntani." Hakimi ya kalleshi yace " kai gyara yanayin kalamanka ko ka manta a gaban Sarki kake?" Sarki ya kalli Jalal yace " indeed u are smart, ba hukuntaka zan farayiba harsai naji abinda ya faru a kasata shekara Ashirin din daka fada a jarida ko gaskiya ne." Jalal ya kalleshi cikin rashin tsoro da sadaukarwa yace " zan iya fadama amma sai in har na tabbatar zaka taimakeni gurin bada hukunci ga wanda yai lefi duk matsayinsa kuwa." Sarki yai shiru can yace " idan kuma na kasa yin hukuncin fa? Ko kuma sai ka gama sanar dani incanza shawarata?" Jalal ya kalleshi tare dayin ajiyar zuciya yace " Ka sa a kulleni kamar yanda aka fadama." Sarki ya kalli Jalal da mamaki yace " kamar ya?" Jalal yai murmushi yace " haka nake nufu kasa a kulleni sannan ka sanar da wanda ya ya bugoma wayar ina da evidence akan laifin da Senate Abdul ya aikata, sannan in har baizo gobe ba na ba Abokina zai aika kuto." Sarki ya kalli Jalal cikin tsananin mamakin kalamansa yace " Jalal ban fahimceka ba." Jalal yai murmushi yace " kai ma mutum ne mai matsayi sannan akwai mutane dayawa da suke samanka kamar Senate Abdul, bazan iya sanar dakai komai ba tukunna, in ka amince da olan dina to in kuma ba haka ba shikenan sai in tashi in tafi." Shiru sarki yai na wasu 'yan dakiku yace " Don't trust me, dan bansan me kake shirin yi ba, kar inje daga baya inga bazan iya ba inyi betraying dinka, daga baya kazo kace ban fadama ba." Jalal yai murmushi yace " I don't trust you, sai dai daga sanda kace fadawanka su fita nasan at least kai ba kamar su bane hakan na nuna bakasan aji maganar da zamuyi." Sarki ya jinjina kai yace " okay na aminta da shawarar ka sai dai baka tsoron Abdul?" Jalal yace " inada 'yan uwa a waje tare mukazo dasu ba kuma na tunanin zasu bari wani abu ya sameni." Sarki yace " shikenan zan kulleka kamar yanda ka bukata, zan kuma yi abinda kace in har baifi karfina ba sai dai inaso ka fadamin kalma daya, da gaske Abdul ne yai fyaden dayaja matsaloli da dama a shekarun baya?" Jalal ya dago yace " Zan iya rantsuwa akan shine yai wannan fyaden." Sarki yace " Na aminta dakai, ka birgeni sosai na dade banga wanda ya zauna dani yai magana kanshi tsaye ba haka kamar kai, ba ka tsoron in an gama in ma hukunci?" Jalal yai kasa dakai yace " In har na gama abinda nakeson yi ba wani abu bane in ka hukuntani." Hakimi kam ya zama kurma dan ya kasa sa baki a wannan al'amarin shikam sam bai fahimci me suke nufi ba shiyasa ma yai shiru kawai. © *THE SEEMA[truncated by WhatsApp] 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No.6⃣9⃣ Jalal ya fito daga fadar mai martaba gunsu Ammar ya nufa, Ammar na ganinsa ya taho da sauri, hannunsa ya rik'e yace " Jalal menene?" Jalal yai murmushi yace " ba wani abun, kawai dai I am gambling with my life ne, I don't trust him sannan banida solution a wannan lokacin daya wuce in yarda dashi." Ammar yace " Jalal akan Abdul ne?" Jalal ya jinjina kai sannan yace " turowa sukai amin hukuncin da bazan iya sake magana ba, sai dai bazan iya ba." Ammar yai shiru, Jalal ya dafashi yace " karka damu Ammar dolene musa mutumin nan ya biya laifin daya aikata tun a duniya, inba haka ba banaji Seemah zatayi rayuwar farinciki har abada." Ammar kallanshi kawai yake, Jalal yai murmushi kamanta alkawarin dana maka ne? Na cewar kafin bikinka sai na sa Abdul ya tsugunna agaban Seemah ya nemi yafiyar abinda yai." Ammar yace " amma Jalal......." Jalal ya katseshi da cewa " ba abinda zasu iyamin nasan bazaka bari wani abu ya sameni ba." Ammar ya makamai hararra yace " in wani abun ya sameka banaji zan iya yafema kaina." Jalal yai murmushi tare da cewa "bama abinda zai faru." Waya Jalal ya fito a ita ya kira Umma, ringing 2 ta daga cikin farinciki tace " Jalal kai nake nema ai tun dazu ai, albishirinka." Jalal yace " goro." Tace " Jalal jiya da daddare anma Zahida aiki yanzu ta fara magana a hankali." Jalal cikin tsananin farin ciki yace " Da gaske? Yanzu Zahii tana magana?" Umma tai dariya tace " dazun nan likita yasata ta fara gwadawa." Jalal ya shiga cewa " Alhamdulila." Umma tai murmushi tace " Sai dai muna bukatar abubuwa na amfani ga mahaifinka bayannan." Jalal yace " bakomai zan turo a kawo muku ." " toh Jalal Allah yamaka albarka." Yace Amin. Yana kashe wayar ya kalli Ammar cikin tsananin farinciki yace " Ammar Zahii tafara magana." Murmushi sosai Ammar yai yace " Naji dadi sosai, Allah ya kara mata lafiya." Jalal yace Ameen sannan ya furzar da wata iska yace "Yarinyar nan tun tana karama akace za'a mata aiki mai tsananin cin kudi, duk yanda Abba yaso ya tara kudin amma inaaa, ko kwatan kwata bamu isa hadawa ba, haka muna ji muna gani take a kwance ga kudi suka cigaba da karuwa." Yai ajiyar zuciya, Ammar yai murmushi yace " Allah ya riga ya kaddara sai a wannan lokacin zata samu lafiya, amma naji kana maganar sako ya za'ayi?" Jalal yace " shine ai, tana wani babban asibiti ne a kaduna na Dr Bilal to yanzu ga abinda ya faru." Ammar yace " bakomai ni sai inje da kaina." Jalal ya kalleshi yace " anya kuwa? Da so nakeyi ka nemo mana manyan 'yan jarida wadanda kasan masu amana ne ko ta hanyar su Dad ne, akwai abinda nakesan a dauka bayan Abdul yazo, sannan inasan a inda za'a kulleni a sa camera yanda zata dinga daukan komai dazai faru tsakanina dashi inyazo." Ammar ya jinjina kai yace " Amma Jalal daukan evidence ba tare da mutum ya sani ba, ba illegal bane?" Jalal yai dariya yace " a'a a law ai in har wanda ya dauki rahotan, dashi a cikin video din yazama legal, ai abinda ba'aso shine daukan shaida a boye ba tare da sun sani ba su dukansu " Ammar ya jinjina kai yace " hmmm na gane yanzu." Jalal yai murmushi yace " Zaid fa?" Ammar yai tsaki yace " ya fita daga ganin wata yarinya ta fito daga gidan ya bita." Jalal ya girgiza kai yace " Kaiii Zaid sai a hankali." Jalal yacigaba" Ammar dan Allah ka taimaka kahe gida ka fadama Zainab nace ta koma gidansu, in komai ya kammala zanzo in daukota." Ammar yace " gwara kam, zamanta ita kadai shima matsala ne bamusan me wannam mutumin zai yi ba." Nan suka zauna Jalal a dinga fadama Ammar plan din yanda abin zai kasance, Kwarai Ammar ya gamsu, fatansu dai daya kar Sarki yaci amanarsu. Nan Jalal ya koma ciki, shiru Ammar yai yana tunani baima san Zaid yazo kusa dashi ba, Zaid ya tabashi yace " Ammar me kake tunani?" Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid me kake tunani akan sadaukar da komai da Jalal yai dan ganin yaba Seemah farinciki?" Zaid yai dariya sosai yace " Tsananin san da yake mata ne." Ammar yai shiru can yace " tare muka taso da Seemah shekararmu Ashirin tare, shiyasa nake jinta a kowace gaba ta jikina amma ina mamakin ya za'ayi Jalal daya hadu da Seemah kwata kwata na wata daya yake neman sadaukar da rayuwarsa saboda ita?" Zaid ma yazauna tare da cewa " nikaina ina mamakin wannan soyayyar, sai dai ita soyayya nasan a ganin farko ma take shiga zuciya, sai dai irin wannan soyayya ce ban sani ba." Ammar yai shiru, a ransa yanata maimaita Shekara 20, da wata 1. Can ya daure yace " Zaid me kake gani a naka tunanin? Dani da Jalal waye yafisan Seemah?" Zaid ya kwashe da dariya yace " ina zan sani? Inba zuciyarku aka tsaga na duba ba?sai dai nasan dukanku kuna santa kuma dole dayane zai aureta." Yanakainan ya mike yai hanyar waje, Ammar yai shiru yana tunanin da ni kaina ban sani ba. Jalal kam agabanshi Sarki ya kira Abdul bayan sun gaisa ne yace " Senate na kama yaran kamar yanda kuka ce amma me za'amai?" Senate yace " ni kawai ayi yanda za'ayi yabar kasarnan ko a turashi niger." Sarki ya kalli Jalal wanda wayar a handsfree take kuma suna recording sarki yace " Amma yaran nada taurin kai fa, dan da alama akwai shaidu daya tara akanka ina tsoron kar ya yad'asu a kafafen yad'a labarai ba tare da mun sani ba." Gaban Abdul me ya fadi yace " Wannan wani irin jarababben yaro ne? Me yake so danine?" Sarki ya kalli Jalal sannam yace " nidai bansani ba amma yace tabbas in gobe bakazo ba yasa abokinsa ya kai shaidun kuto da kuma gidan tv." Abdul ya mike yace " what? Nashiga uku wannan wani irjn jarababe ne? Ko kudi zan bashi mai uban yawa?" Sarki yace " nidai bansani ba sakonshi dai daya ne tabbas gobe kazo ko kuma kaga takarda." Abdul yai shiru can ya kalli PA jikinsa sai rawa yake yace " naji zanzo gobe dan Allah karka barshi yai abinda bai kamata ba." Sarki yace " to shikenan." Nan sukai sallama Sarki ya kalli Jalal yace " yaro wai baka tsoro?" Jalal yai shiru can yace " ko inajin tsoro ai tunda na fara ban isa ingudu ba ballema banaji, ni yanzu taimakon da zakamin shine kataimaka kasa 'yan sanda suzo gobe dan nasan inhar ba mutum mai matsayi irinku bame bazasu zo ba." Sarki yace " insunzo kana tunanin akwai abinda zasu iya yima Senate guda?" Jalal yai murmushi yace " nima babban burina shine karsuyi komai din kamar yanda suka saba." Sarki yace " Jalal u are really smart ko ni bana fahimtar komai da kake nufi sai dai kar ka bari smartness dinka ya lalata ma rayuwa." Jalal ya kurawa wani gun ido baice komai ba. Shidai abu guda daya yasani kuma yasa a ransa, dolene Abdul yaba Seemah hakuri sannan yaba mahaifinsa da Dad hakurin abinda ya musu, sannan in anzo bikin Seemah ace mahaifinta ya hallarta, ya sani ko bata fadaba dole ne kasan zuciyarta zaiyi radadin wannan al'amarin, ko bata nuna ba zataso ko da mahaifinta mutumin banza ne ace a tarihin rayuwarta ace mahaifinta dai ya hallarci bikinta. Hawaye ne yaji yana neman zubomai, da sauri ya mike tsaye, Sarki ya bishi da kallo, ba shakka irin wadannan mutanen kasarmu take nema, sai dai a wannan lokacin bayaji akwai namijin da zai sadaukar da rayuwarsa saboda hukunta wanda yafi karfin hukuma. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 7⃣0⃣ Duk wani tsare tsare na plan din Jalal ya kammala, sai da komai yai daidai sannan Ammar ya kalleshi jiki a sanyaye yace " Zainab nakaita har tasha ta hau mota, sai dai Jalal are you sure ba abinda zai faru in mutumin nan yazo?" Jalal ya dafa Ammar yace " Ammar karka damu koda wani abun zai faru insha Allah sai alkairi." Ammar ya kalleshi sannan yace " ni ina....." Jalal ya danyi dariya yace " Ammar are you worried about me?" Da sauri Ammar ya fizge kafadarsa yasa hannu yadan bigi cikin Jalal yace " ana cikin wannan yanayin shine ko kunya kake tsokana?" Jalal ya dan hade fuska irinta tsokanar nan yace " Ahhh namanta na daina." Atare sukai dariya, Ammar ya kalli Jalal yace " magrib tayi mu bari mu nemi hotel mu kwana tinda kai yanzu ka zama prisoner. " Jalal ya dan harareshi tare da sa hannu a kuncinsa yace " ka tabbatar dai zaka iya bacci ko? Karfa ka kwanta tunanin halin danake ciki yasa ka kasa yin baccin." Ammar ya girgiza kai yace " Jalal na kula sam baka tunanin komai." Jalal yai murmushi baice komai ba. Ammar yace " nidai gobe da sassafe zanje kaduna in kaima Umma sakon sai in juyo amma me suke so?" Jalal ya kalli Ammar cikin jin dadin kalamansa yace " Ammar!" Ja baya kadan Ammar yai yace " menenen?" Jalal ya saki murmushi yace " nagode sosai." Ammar yace " nifa da a yanda na daukeka na dauka mutum ne kai mai zafi mara kuma san magana amma na kula bayan ka dawo karatun nan kamar ka canza daga yanda nake ganinka." Jalal yai murmushi yace " ni kaina ina mamakin in ina tare da kai bakina bayasan yin shiru." Murmushi sukama junansu, Jalal yace " ga Atm dina dan ba kudi a hanuna." Ammar yace " eh dole ka bani Atm dinka tunda ni banda abinda zan iya basu ai dole kace haka." Jalal zaiyi magana Zaid ya karaso da sauri yace" nikam yunwa nakeji wai meyasa ku bakwa maganar Abinci? Su haka gidan sarautar suke bazasu bamu abinci ba?" Jalal ya harareshi yace " ai a matsayin baki mukazo ba dole a bamu abinci ba." Zaid ya turo baki cikin shagwaba yace " Mami kitaimaki danki yunwa zata kasheshi." Dariya suka kwashemai dashi. Ammar yace " Bari mu siyo abinci take away sai muzo nan muci dakai." Jalal ya girgiza kai yace " a'a kamanta ni prisoner ne dolene in jure yunwa kodan Abdul inya ganni gobe ya fahimci an wahalar dani." Ammar da mamaki yace " Jalal ban gabe ba?" Da sauri Jalal ya fara turasu, yace " kuje sai da safe." Yana kaisu bakin gate ya koma ciki da sauri, Ammar yabi bayansa da kallo zuciyarshi ba dadi. Sun gama cin abinci wanda Ammar kadan ya iyaci sunyi isha'i sannan suka kwanta, Ammar yayi shiru zuciyarshi ta cika da tunani kala kala, abinda yake tambayar kansa a zuciyarsa shine, Shi yafi cancanta da Seemah ko kuwa? Wayarsa da ya kashe ya kalla so yake yaji muryar Seemah sai dai inaa bayasan ta tambayeshi me sukeyi anan bayan bazai iya mata karya ba. A wannan dare mutane 4 idanunsu baiga baccin kirki ba. Jalal wanda yake tunanin ya gobe zata kasance musu, Abdul wanda bakincikin abinda Jalal yamai yasa mutane duk sun fara juyamai baya ciki kuwa harda shugaban kasa, dan da sukai meeting duk yanda Abdul yaso yabama shugaban kasa nashi ra'ayin a lokacin suna meeting ya hanashi, inzaiyi magana sai ai saurin katseshi, shi yasa ya kosa gobe tai danya dau babban hukunci akan wannan Jalal din. Sarki wanda tunani ya hanashi barci, yana tsoron abinda zai faru gobe cigaba zai kawoma kasarshi ko kuwa matsala? Sai Ammar wanda tunanin abubuwa suka hadu sukamai yawa. Washegari da sassafe Abdul ya kamo hanya, Ammar ma ya wuce cikin garin Kaduna, baisha wahala ba wajen samun asibitin saboda kwarewa da suna da asibitin yai. Number dakin da Jalal ya turomai ya nufa, tsaye yai a waje yana kwankwasawa, wani likitane yazo wucewa ya kalli Ammar yace " ba shiga zakai ba?" Ammar yace " shiga zanyu amma naji shiru." " Ka shiga patient din maganarta bata fitowa ita kuma mahaifiyar tata tana gu likita." Ammar yamai godiya sannan ya tura kofar ya shiga. Zahida na kwance sai motsa jikinta takeyi tana kiran Umma cikin muryarta da bata fitowa sosai, da sauri Ammar ya karasa gunta ya tsaya ta baya, Zahi najin motsi tace " Umma sosa min bayana kaikayi nakeji, jinake kamar wani abun na yawo." Ammar yai tsaye yana kallan yanda takeyi rasa yanda zaiyi yai, Zahida takara cewa " Umma dan Allah ki sosamin zan mutu." Ammar yasa hannu daya ya rufe fuskarsa sannan ya sa hannu a aljihu ya dauko biro yafara sosa mata a baya fuskarsa na gefe. Zahi jin kaikayin yayi yawa ga umma ba gun take sosa mata ba tace " Umma dan Allah ki sosa min sosai ba nan bane." Idanu Ammar ya zaro tunaninsa daya ina umman take to? In taganshi yace mata shine wa? Gashi kuma bazai iya sa mata hannu a baya ya sosa mata ba, Zahida ta rasa ya zatai, zatai magana Umma ta shigo dakin, Ammar ta kalla da mamaki tace " Bawan Allah me kake a ciki?" Da sauri Zahida tace " Umma? Waye?" Umma ta matso ta gabanta tace " wani namiji ne." Idanu zahida ta zaro bakinta na rawa tace " Umma ina yake?" Ammar ne jiki a sanyaye ya dawo ta gabanta, ai tana ganin namiji ta saki ihu da karfinta na gaske, tare da runtse idanunta. Umma tai mamakin yanda muryar ta tafito, ta kalli Zahida tace " menene? Wani abin ya miki?" Ta fada tare da kallan Ammar da sauri Ammar ya girgiza kai alamar bai mata komai ba. Zahida ta bude ido a hankali tare da sa kuka cikin kuka tace " Umma hannu fa yasamin a bayana." Da sauri Umma ta kalli Ammar cikin mamaki tace " Hannu?" Ammar ya kalli Zahida yace " yaushe na sa miki hannu? Kingani ne sanda nasa hannun ko kuwa?" Zahi ha harareshi tace " to me kamin?" Umma a zuciye take kallan Ammar tace " bawan Allah kai ko kunya bakaji ba? Baiwar Allah bata da lafiya shine zakazo ka sa mata hannu a baya?" Ammar ya nuna mata biro yace" kinga abinda nasa mata nan, Umma tunda na shigo take kiranki akan ataimaka mata kaikayi ya isheta shine fa nasa biro nadan sosa mata, batasan banbancin hannu da biro bane?" Umma ta kalli Zahida datai kasa dakai, Ammar yadan harareta yace " memakon ki godemin shine zakimin ihu?" Zahida ta dago ta kalleshi, kaikayin ne ya cigaba da damunta tace " Umma bayana." Umma ta kalli Ammar tace " dan Allah kadan kira mana likita." Ammar ya fita, yana fita yai dariya a fili yace " lalai wannan kanwar Jalal din." Jalal kam an kulleshi a can bayan gidan sarki a wani dakin da ko window babu sai daga can sama akadanyi hudi kadan kadan haske yana shigowa, yunwa yakeji sosai dan tana neman galabaitashi, duk yanda sarki yai dashi akan yaci abinci jiya amma yaki yarda. Jin ana bude kwad'an dakin da aka rufeshi yasa yai saurin komawa lungu ya rakub'e, ana gama budewa Abdul ya shigo wasu maza kosassu suna biye dashi, Jalal ya kalli Camerar da suka saka yanda ba wanda zai gane, kasa yai da kansa. Abdul ya shigo cikin isa, ya kalli Jalal tare da kwashewa da wata muguwar dariya, Jalal ya dago a hankali ya kalleshi, Abdul ya kalli dakin tare da jinjina kai yace "good dama haka nakeso ni wannan ma ya maka dadi dayawa." Jalal ya kafeshi da ido, Abdul ya kalli mutanen yace ku fara. Ai kafin Jalal ya fahimci mai zasu fara yaga sun matso sun kama dukanshi, sai da sukamai duka sosai, sannan Abdul yace " ya isa haka." Sannan ya basu umarni su fita, kusa da Jalal yaje wanda duk jikinsa an jimasa ciwuka ya dago yana layi, Abdul ya sakeshi yamike tare da cewa " Jalal kai yaro ne, bakasan komai na rayuwa ba, taya zaka hada kanka dani? Nine fa Senate Abdul, akan can wata yarinya da kake kira da sunan 'yata daban santa ba har zaka nemi halakamin rayuwa? Kai din banza, me kake dashi? Me kuma zaka iya?" Jalal cikin layi yace " Anya kuwa kanada imani a rayuwarka? 'Yarka ce fa? Baka tausayin abinda kama mahaifiyarta?" Abdul ya kalleshi tare da nunashi da hannu yace " karka sake cewa 'yata wato so kake rayuwata ta hallaka ko? Meyasa tunda sanda ina karamin dan siyasa bakuzomin da zancenta ba sai yanzu da kukaga na girma ina neman wuce matsayina?" Yai ajiyar zuciya yace " Fatima ta rasu, sannan banaji kunada wata shaidar da zata tabbatar da ninai fyaden nan, in kuma kanada ita ka tabbatar ka bani tun kafin nasa a kama iyayenka." Jalal ya mike tare da yin wata dariya yace " me? Bamu kawo maka zancen ta ba tunda? Ita kanta yarinyar banaji zataso ganinka a rayuwarta, saboda tafi karfin ace mutum mai irin wannan zuciyar shine zata kira a matsayin uba, kuma tazauna dashi." Abdul ya matso tare da wankama Jalal mari yace " Nima baso nake ta kirani da hakan ba, sannan daga kai har Amadun sai na nuna muku banbancin da dakuma yanzu." Jalal yai murmushin karfin hali yace " Ko tambayar Malam Isma'il ma bakayi? Mutumin da kama sharri ka wulakantamai rayuwa." Abdul yai murmushin mugunta yace " Isma'il? Ha ha ha au hardashi kuka hadu zaku wulakantani?" Jalal yai shiru, Abdul ya matso tare da cewa " Ka koma ka sanar dasu abinda na maka sannan ka fadamusu nine na mata fyaden me zasu iya min? Yarinyace nace ta fadi kudin datake so nizan bata amma bawai a matsayin 'yata ba." Alhamdulila Jalal ya fada burinshi ya cika Abdul ya aminta da bakinsa shiya ma Fatima fyade. Wani abu ya danna, kan kace me sai ga 'yan sanda sun taho sun zagaye dakin gaba daya.... *Gaisuwa My Samra Thanks alot Sis......*❤❤❤ © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No.7⃣1⃣ Abdul jin loudspeaker yai ana kiran sunansa, jikinsa ne ya shiga rawa ya matso kusa da Jalal tare da shakemai wuya da karfinsa, Jalal ya fara kakari, ko meya tuna kuma sai yai saurin sakinsa yana yin baya baya yana cewa " nafi karfin wannan, nine Senate Abdul wanda mutane ke so." Jalal yarasa dalili kawai ganin yanda yake rawa da jikinsa yasa tausayinshi ya fara ziyartar zuciyarsa, kallansa yai idanunsa sun ciciko da kwalla matsowa yai kusa dashi ya rike hannunsa yace " wacce irin rayuwa kai? Bayan rashin adalcin dakama Fatima baka jin tausayinta da dana sanin abinda ka aikata a kasan zuciyarka?" Hawaye suka zubo ma Abdul ya kalli Jalal yace " Fatima ta rasu dolene ni danake darai inyi rayuwar danakeso." Jalal cikin wata sanyin murya ta ban tausayi yace " zaka iya rantsuwa tun bayan abinda yafaru baka taba dana sani ba? Sannan baka taba tunanin 'yar ka ba?" Bakin Abdul ya fara rawa, kai ya shiga girgizawa hawaye na zubomai, Jalal ya kara matsowa kusa dashi yace " Zaka iya rantsuwa?" Abdul ya dago jajjayen idanunsa yace " in ma nayi dana sanin ko tunaninsu menene amfaninsu yanzu? Fatima ta rasu ba tare da na nemi yafiyarta ba, sannan yarinyar data haifa ban taba ganinta ba bare inma san sunanta kana tunanin akwai amfanin da tunanin zaimin ko dana sanin?" Jalal yai ajiyar zuciya yace " You are not a cruel person, da ace kai mugune da randa nazo gidanka dazancen nan bazaka barni na fita ba sannan da bazaka ce sarki ya kamani ba sawa zakai a kasheni ba tare da kowa ya sani ba, sai dai na kasa gane kai wani irin mutum ne da kake kokarin canza abinda ke zuciyarka." Abdul ya kalli Jalal tare da share hawayensa yace " da farko I am not greedy but zama da abokai da cusa min ra'ayuyuka da kuma matsayi na power danake samu ba, hmmm bansan sanda nima na riked'e gaba daya na zama haka ba, bana tausayin kowa burina daya ne insamu abinda nakeso......" Kasa karasa maganar yai, jiki a sanyaye ya dago tare da yima Jalal murmushi yace " hmm inaji Allah ne ke nemana da rahama shiyasa ya baka damar tsayar dani daga cigaba da abubuwan danakeyi." Hanyar kofa ya nufa, da sauri Jalal ya riko hannunsa yace " 'Yar ka fa?" Abdul ya runtse ido yace " a'a karka sanarda ita komai, in har bata gan ni cikin mutuncina ba bazan bari ta ganni cikin wannan yanayin ba." Yana kainan ya bude kofar 'yan sanda suka matso tare da samai ankwai. Shiru Jalal yai zuciyarshi kuma ta shiga radad'i abinda yake fata ne ya tabbata but meyasa yakejin shi haka?. Ammar ne suka dawo shida likita, suna shiga dakin Zaid ya kirashi a waya, yace na siyo kayayyakin kana ina? Ammar ya fadamai number dakin nan Zaid ya taho, likita bayan ya duba Zahida yace bari yasa a kawo mata magunguna, yana fita Zaid ya shigo, Umma ta kallesu tace " ban gane ku bafa?" Ammar yai kasa dakai tare da gaisheta yace " Ammar ne dan gidan Malam Isma'il." Cikin tsananin mamaki Umma ta kalleshi tace " Ammar?" Zaid ya matso tare da cewa ni kuma Zaid, ta kalli Zaid da mamaki tace " tare kuke?" Ammar ya daga kai, Zaid ne ya karasa kusa da Zahida dake jingine da gado, fuskarta ya tsaya kallo, inya kalli nan sai ya juya kansa ta daya barin, Zahi ta gaji da wannan abin nasa ta kalleshi tace " malam lafiya?" Zaid yace " wow! Ahh dan sake fada kinji?" Zahi tace " me zan sake?" Zaid ya rike kirjinsa bangaren zuciyarsa yace " Ammar wannan muryar tamin dayawa." Kai Ammar ya girgiza ya kalli umma yace " karki damu Umma haka yake." Umma tai murmushi tace " da alama yanada san wasa." Zaid ya dago cikin shagwaba ya kalli Zahida yace " Yanzu bazaki sake fada ba." Zahi ta makamai harara tare da cizan leb'enta tace " Naki d'in, kuma ka matsamin daga sai tin fuska." Zaid ya sa dariya tare da toshe baki yace " in naki fa? Me zakiyi?" Ya fada tare dasa hannu a haba, Zahi ta juya kanta gefe tace " Umma kice ya matsa min." Tai maganar kamar zatai kuka, Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid ka matsa mata mana tace bataso." Zaid ya kalli Ammar yace " meya dameka? Hira muje tsakanin masoya ko patient. ...ahhh dama karatun likita na karanta." Zahi tai wani irin dariya ta kularwa tace " masoya? Ha ha lalai mutumin nan da alama kai player ne, harda wani dama karatun likita ka karanta? Ahhh Allah yasa duk da akwance nake inajin labarai, dan yayata tana karantamin har littafin hausa, nasani sarai in naga mutun na neman yaudara." Ta hade rai tare da juya kai. Zaid ya matso kusa da Umma yace " Umma kun tabbatar yarinyar nan mara lafiya ce da gaske? Bakinta abude fa yake?" Umma tai murmushi tace " to ko zata mik'e ta rakaka unguwa?" Da sauri Zaid yace " Eh Umma in....." Kafa Ammar yasa ya takamai kafa da karfi Zaid yai kara tare da cewa " me kuma nai? Ammar yace " bata fa tafiya akwance take tun tana karama, Zaid meke damunka ne?" Jikin Zaid ne yai sanyi ya kalli Zahi sannan ya kalli Umma yace " Bansani ba Umma nadaiji jiya ana cewa ta fara magana nadauka matsalar ta magana ce kawai. " Umma tai murmushi tace " ba komai zuwanku ma ya isheni farinciki tun balle ganin Ammar danai wanda ban taba zata ba." Ta fada tare da kallan Ammar. ...© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No.7⃣2⃣ Seemah na xaune a daki tana cin Abinci Dad ya shigo, kallansa tai cikin sakin fuska tace " Dad shigo mana." Dad ya karaso tare da zama kusa da ita ya anshi cokalin da take cin abincin ya deba tare da kaiwa kusa da bakinta yace Ahh.... Murmushi tai sannan ta bude bakin ya zuba mata, tanaci tana murmushi, Dad ya kalleta cikin tsananin kulawa yace " babban farinciki na bai wuce inganki kina cikin farin ciki ba." Murmushi Seemah tai tace " Dad daga yanzu ko banasan dariya inna ganka zan dinga washe baki." Dariya yasa mata yace " ni bance kuma a dingamin haka ba." Kallansa tai cikin kulawa tace " Dad su ya Ammar fa? Sam na kasa samunshi a waya." Dad yai shiru batare daya bata amsa ba cikin wata murya yace " Seemah?" Kallansa tai cikin mamaki da tattara nutsuwarta saboda yanda ya kirata. Dad ya kalleta cikin kulawa yace " Seemah bakyajin ba dadi ko bacin rai? " Cikin mamaki ta kalleshi tace " saboda me kenan Dad?" Yai murmushin karfin hali yace " Seemah nasani sarai Jalal kike so amma na hadaki aure da Ammar bakyajin haushin hakan a kasan ranki?" Iska tadan furzar sannan ta rangwabar da kanta ta kalli Dad tace " Dad a kaf duniyan nan bani da kamarka, ko dan garuwa wanda bashida kwabo ka ce in aura to tabbas shi din nan zan aura babu musu balle tambayar dalili bare Ya Ammar?." Tai ajiyar zuciya sannan tai murmushi tace " Dad bazan boyema komai ba saboda a haka muka taso banaiya boye ma komai da gaske inasan Deen sai dai duk sanda nake masa bazan iya ture Ya Ammar in zabeshi ba koda kuwa bansan abinda ya faru da ba, balle kuma yanzu na sani." Hannun Dad ta kama tace " karka damu Dad bazan bari hallacin daka mana nida mahaifiyata ba ya kare akan san zuciya ta ba." Dad idanunsa suka dan ciciko, yace " Seemah na sani naso kaina dayawa dana hada auranki da Ammar, sai dai babban burina daya ne a duniyan nan, bai wuce inga zuri'ar Fatima da tawa sunyi aure sun hayayyafa ba." Seemah tai murmushi tace " Karka damu Dad insha Allah wannan burin naka zan cikama shi, tunda na taso agunka ni nake neman abu agurinka baka taba neman wani abu aguna ba sai wannan, ka sha wahala sosai akanmu nida Mahaifiyata insha Allahu wannan burinaka nizan cikama shi." Tai magana tana kokarin boye hawayenta, Dad cikin tsananin sanda yake mata yace " Seemah inhar auren Ammar bazai......" Da sauri tasa hannu ta rufemai baki, tace " karka karasa Dad kafi kowa sanin yanda Ya Ammar ke sona, tun ina karama har kawo yanzu, hawaye wannan bayaso yaga nayi, nima kasan yanda na damu dashi, insha Allah zanyi kokarin juya soyayyar danake masa ta 'yan uwantaka ta koma ta......." Kasa tai dakai bata karasa ba, Dad ya kalleta shima baice komai ba tunani yakeyi, anya ya kyauta ma Seemah kuwa? Jalal ma a yanda ya gani yana tsananin santa. Katse mai tunani tai da cewa " karka damu Dad zanyi kokarin ganin na cire san Deen a raina sannan na maka alkawari zan kula da Ya Ammar sosai, inaji a jikina wannan shine abinda zanyi wanda zaisa dukda mahaifiyata batada rai zatai alfahari dani." Idanunsa ne yaji suna neman zubar ruwa da sauri ya mike yai waje, binsa tai da kallo tare da yin murmushi hawaye suka fara zubo mata, tafara cewa " Is Okay Seemah, cool down." Jalal kwance akan gago yayi shiru tare da kankame memory din daya cire na cikin camera din daya daukesu shida Abdul, nurse ne ya shigo ya kara dubashi tare da bashi magunguna, Jalal ya sha tare da mikewa ya zauna yace " wayata please. " Nan nurse din ya mikamai, Jalal ya amsa tare da kiran Zaid, dan yasan wayar Ammar a kashe take. Ringing uku Zaid ya daga yace " Jalal ya akai? Ina cikin shaukin kauna zaka kirani?" Jalal ya girgiza kai yace " Zaid matarka zatai fama, ni ba Ammar please. " Zaid yasa dariya tare da cewa " ai matar tawa kanwarka ce kaga sai kushirya yin faman dakyai." Jalal yace " me kake nufi?" Dariya Zaid yai tare da mikama Ammar wayar, Ammar dake tuki suna hanyar dawowa ya amsa tare da cewa " Jalal ya? Allah dai yasa ba wata matsalar bace?" Jalal yace " Ba wata matsalar Senate din sun wuce dashi police station sai dai....."sai kuma yai shiru. Ammar cikin damuwa yace " menene? " Jalal yace " tunani nakeyi anya ya kamata mu bada evidence din nan? Naga kamar zuciyarshi ta karaya shi yasa nake tunani." Ammar yai shiru nadan sakwanni sannan yace " Haka ne mu barshi kawai kodan Seemah ma ina tsoron kar tagani dan ko bata fadaba nasan abin zai zamar mata gyambo a zuciyarta." Jalal ya jinjina kai yace " kuna ina yanzu?" Ammar yace " muna hanya munkusa shigowa birnin gwarin ma, Jalal yace " nagode Ammar sosai...." Ammar ya katseshi " Zaka fara ko?" Jalal yai murmushi yace " Sorry amma me dazu Zaid yake nufi?" Ammar ya girgiza kai yace " kasanshi ai, daga gani Zahida wai ita yakeso kuma yanzu." Jalal yai dan dariya kaan yace " kaii Zaid sai a slow...." Nan sukai sallama suka kashe. Jalal na zama wani bafade yazo yace " mai martaba na nemanka." Jalal ya mike suka fita tare, zaune yake a kasa, mai martaba yace " ya jikin naka? Jalal yace " da sauki." Sarki yace " ya ya ina abinda aka dauka nima na gani?" Jalal yai shiru, Sarki yace " ya akai kuma?" Jalal ya kalleshi yace " matsala aka samu ai, ashe bamu kunna recording ba a lokacin." "OHHHH abin dai baiyi dadi ba amma ba komai naji ance ya aminta da lefin yimata fyaden a station din 'yan sandan." Jalal ya kalli shi jiki a sanyaye, yace " mun gode sosai da taimakon da ka mana, zan wuce nima yanxu 'yan uwana suna hanya." Sarki ya jinjina kai tare da cewa " Kuma Abujan zakuyi?naji shima can za'a wuce dashi " Jalal yace " eh." Nan yamai Sallama zai mike Sarki yace " Jalal?" Juyowa Jalal yai ya kalleshi, Sarki yai murmushi yace " ka birgeni sosai, I wish ina da yarinya da na hadaka da ita, sai dai inaso kaje ka duba ko wani gun aiki ne indai har ya maka kanaso to ka sanar dani ni kuma zan nemar maka aiki a ko inane a doron kasar nan." Jalal yai murmushi yace " na gode." Nan yamai sallama ya fita, Sarki yai murmushi cikin gaskiya Jalal ya kwantamai a ransa. Jalal gidansu ya koma ya dan shishigar da kaya, yana gamawa su Ammar na isowa nan suka shiga mota suka kama hanyar Abuja. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 7⃣3⃣ Sunyi nisa a hanya Zaid duk ya ishe Jalal da zancen Zahida, hakan yasa Jalal ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da rufe ido kamar mai bacci, Ammar ma yasa earphone a kunnensa tare da maida hankalinsa kan titi, shikam Zaid sai zuba yakeyi, ganin shariyar tayi yawa yasa shima haushi ya isheshi yai shiru, sunyi nisa jin Zaid yayi shiru yasa Ammar ya lekashi ta glass din mota, ganin Zaid yayi bacci yasa ya zare earphone din tare da kallan Jalal kadan yace " Bacci?" " Nope kawai idona na rufe." Ammar yai ajiyar zuciya yace " Me ka tsara yanzu zakai?" Jalal idanunsa a rufe yace " Ina tunanin neman aiki a kaduna ne so nake mu koma can gaba daya, banajin zaman Abujan nan yanzu." Shiru Ammar yai hakan yasa Jalal ma yai shiru, sunyi shiru kawai Jalal jiyai Ammar yace " Saboda Seemah?" Cikin mamaki Jalal ya bude ido ya kalli Ammar sai dai ya kasa magana, Ammar ya maida kansa titi tare dacewa " Hakane kenan?" Jalal ya mike zaune ya kalli Ammar yace " Ammar." Ammar ya dan kalleshi tare da yin murmushin karfin hali yace " Jalal menene matsayin Seemah a gunka?" Jalal ya kalli Ammar cikin tsananin mamaki yace " Ammar meyasa kake wannan maganar?" Ammar yace " Jalal tambaya kawai na maka amma in kana ganin bani amsar zatai wuya mubar maganar kawai." Komawa Jalal yai ya kwanta tare da kallan window yace " Ammar karka manta ankusa aurenku da Seemah saboda haka karka fara sa wani abu a ranka." Gefen titi Ammar ya koma da motar yai parking tare da tattara hankalinsa kan Jalal yace " Jalal bazaka gane me nakeji bane a wannan lokacin, kawai dai ina daurewa ne nai murmushi na kuma ci abinci amma kasan zuciya ta jinake kamar I am useless, na ka sa yima Seemah komai kai kuma ka sadaukar da komai naka akanta, bazaka fahimci me nakeji bane." Jalal ya kalleshi cikin wani yanayi yace " Ammar kenan, haka kake tunani a ranka? Ni a zuciyata nine nake useless mahaifina shine dalilin lalatama mahaifinka rayuwa, sai dai duk da haka baiyi tunanin komai ba ya rike Seemah kamar 'yarsa, kana tunanin wannan dan abinda nai yakai kwatan abinda mahaifinka yai?" Ammar ya juya kai yace " Jalal ka manta ne? Mahaifina fa kace bani ba, na sani Dad yayi komai domin Seemah amma ni fa?." Ya juyo ya kalli Jalal idanunsa suka kada yace " Jalal what about me?" Jalal yai wani murmushi yace " Ammar taya zaka fadi haka? Kaine kuwa ka mata komai kasan tun da muka hadu da Seemah zancenta daya Ya Ammar, na tabbata da tun farko tasan kai ba Yayanta na jini bane da ko kallona Seemah bazatai ba." Ammar kallan Jalal yake kawai, Jalal ya dafashi yace " nayi tunani mai yawa bayan naji abinda ya faru tsakanin iyayenmu, zance daya ne ya tsayamin na kuma tabbatar dashi, Ammar shine mutum na farko a duniyarnan da nakeji zai iya rike Seemah fiya dani, zai kuma bata kulawar da ya kamata, zai kuma sa ta manta abinda ya faru da mahaifiyarta." Ammar ya runtse ido tare da kallan window, a hankali yace " Jalal I I I......" Sai kuma ya kasa karasawa, Jalal ya kalleshi da mamaki yace " Ammar na san ya kakeji aranka saboda abinda naji kenan a lokacin da naji abinda mahaifina yai, sai dai abu daya na sa a raina, zanyi kokarin ganin na rage gaba da tsanar dake tsakanin mahaifanmu, inaji kamar in nai hakan ne zaisa mahaifanmu su koma kamar da." Ammar yamai murmushi tare da cewa " Jalal na gode sosai." Jalal yamai murmushi yace " Ammar ba wanda Seemah ta dace dashi kamarka, zaka kula da ita sama dani na shaida hakan." Murmushi sukama juna, Ammar ya tada motar tare da hawa kan titi yace " Jalal nagode sosai, sai dai Seemah fa? Inaji ajikina kamar...." Jalal ya katseshi da cewa " Ammar trust in ur self, Seemah yarinyace bata gama sanin menene so ba sannam karka manta macece ita, nina fadama ka sa a ranka ko shekara bazaku rufa da aure ba zakaga Seemah ta manta dani." Ammar yadan harareshi yace " ce maka akai inasan ta manta dakai?" Jalal yai dariya yace " to me kakeso?" " taya zata manta dakai bayan amintarmu nanan?" Jalal ya sakeyin dariya kadan tare da nuna Ammar cikin zolaya yace " yanzu ka aminta da amintarmu kenan?" Ammar yai murmushi tare da cewa " Jalal bansan meyasa ba abinda bazan iya fadama Junaid ko Habib ba inaji a jikina zan iya fadama, banaji zan iya boyema komai." Jalal ya dan furzar da iska yace " nima haka Ammar jinake kamar munyi shekaru dayawa tare." Dariya sukai nan suka shiga hirar rayuwa. Sun isa Abuja Jalal yace " Ammar saukeni anan." " ina zaka haka?" Jalal yace " inasan ganin Sagir ne akan gidan danace ya samomin, yanzu banajin zan zauna anan." Ammar ya mai wani kallo yace " Jalal please kazauna a inda ka samu aiki taya zakaki zama anan bayan ka riga kasamu aiki, kai zamanka kawai kenan kana so kacemin in mukai aure zumuncinmu ya tafi kenan?" Jalal yace " Ahhh to bari inji me Abba zaice tukunna, amma yanzu saukeni tukun." Nam Ammar yasamu guri yai parking Jalal ya fita tare da cewa " oh ni wannan Zaid din taya namiji zai zake yai ta bacci haka?" Jiyai Zaid yace " Idona biyu nadai barku kuyi magana ne." Da sauri Jalal ya kalli Ammar shima Ammar ya kalleshi, Jalal ya hadiye yawu yace Ammar sai munyi waya ko?" Ammar ya daga mai kai, nan Jalal yai waje, Zaid ya kwashe da dariya yace " au wai kunya kukaji?" Ammar ya tada mota ya wuce baice komai ba. Sunkusa isa gida Jalal yakirashi, nan Ammar ya daga, Jalal yace " Ammar yanzu aka kirani daga police station sun iso dashi nan Abuja, amma kana ganin ya kamata Seemah taje?" Ammar yace " mu bari tukunna ya nemeta da kanshi." Jalal ya jinjina kai nam sukai sallama. Suna isa gida Ammar ya shiga ciki da sauri, falo ya duba baiga Seemah ba Zahra ya gani ta fito daga daki yace " Zahra tana ina?" Zahra tace " tana kitchen, abinci takema." Wani sansanyar murmushi yai sannan ya wuce kitchen fin da sauri, tana tsaye tana gurza karas a greater, Ammar ya lalaba ta bayanta ya rufe mata fuska, murmushi tai tace " Ya Ammar ka iso?" Saketa yai ya dawo ta gabanta yace " ohh na dauka bazaki ganeni ba." Tai murmushi tace " Yaya na fadama taya za'ai in kasa gane ka?" Turamai kujera tai tace zauna yaya ka gani. Ammar ya kalleta yace " taya zanyi inzauna ke kuma kina aiki?" Tace " me? Zaka tayani ne?" Kai Ammar ya daga mata alamar eh, tai murmushi sannan ta dauko albasa da wuka da kwano ta mikamai tace " To gashi." Hararar wasa ya mata yace " hmmm wato wayau ko? Kin dauka bansan albasa yaji gareta ba?" Tadan hade rai kadan tace " shikenan tunda ba tayani zakai ba kawo na karasa kayana." Tafada tare da kokarin dauke kwanon. Ansar kwannan yai a sauri yace " cewa nai bazan yi ba?" Tai murmushi tare da ajiyemai, can ta daure tace " ina kuka je?" Ya kalleta yace " mun danje birnin gwari ne." Ta kalleshi kadan tace " da Deen?" Kai ya daga mata tare da kura mata ido, murmushi tai tare da saurin wayancewa tace " ahh Yaya albasar dai ba yaji ko?" Daurewa yai shima yace " akwai amma kadan." Suka kalli juna sukai murmushi. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _Ina bawa masoyana hakuri najina shiru da kukai, kuyi hakuri amma insha Allahu zanyi kokarin ganin na kammala littafinan acikin satinnan, nagode kwarai da san da kukema littafin nan....Luv U Ol ❤_ No.7⃣4⃣ Abdul zaune yana kallan uwargidansa kallan tsananin mamaki yace " Rabi kinsan me kike fada kuwa? Ban gani in sakeki ba ina cikin wannan yanayin ba?" Wata dariyar rainin hankali tamai tace " me? Kana tunanin soyayya ce tasa na aureka?" Tai wata dariyar rainin hankali tace " are you naive or fool? Kai kana tunanin duk mutanen dake kusa dakai saboda suna sanka ne ko suna san kudinka? " Abdul cikin mamaki ta kalleta yace " Rabi da kikazo na dauka abu na farko da zaki fara tambaya shine meya faru a shekara 20 din? Da gaskene? Sannan ki tambayeni halin da nake ciki a gidan yarin nan amma......" Katseshi tai cikin fada tace " so kake inzauna ka fadamin wani shirme dakai a baya? Ko ce maka akai na damu da halin da kake ciki? Takardata nake bukata dumin inasan barin kasar nan cikin gaggawa kafin laifinka ya fara kokarin shafata." Abdul ya kalleta cikin tsananin mamaki yace " me ne? 'Ya'yan mu fa? Ko kin manta da 'ya'ya a tsakanin mu?" Rabi ta saki wata dariya taban haushin mai sauraro tace " 'ya'ya? Ahh haka ne ashefa kai baka sani ba ko? Amma ina mamakin ina hankalinka yake, sai dai kayi hakuri 'ya 'ya nawa ne ba ka da hadi dasu." Abdul cikin mamaki yace " me kike nufi nufi da kalamanki? " Tai tsaki tace " malam inka ga dama ka saken in bakaga dama ba kai ta ajiye da sakinka zan koma dubai da abokinka Marfuz wato uban 'ya'yana inka ga dama ka aiko mana da takardar saki can." Tana kainan ta mike, cikin zafin rai ya riko hannunta yace " marfuz? Abokina? Me kike nufi?" Hannu tasa ta fizge hannunta da karfin gaske tace " matsalarkace, tana kaiwa nan tai waje." Kai ya shiga girgizawa ya tuna shine sanadiyar arzikin marfuz kuma shine abokinsa da ya dinga zigashi akan abubuwa marasa kyau ciki kuwa harda fyad'en dayama fatima. Ihu yasa cikin tsananin takaici ya rike zuciyarsa dake kuna tare da tsugunnawa a kasa, lalai kuka ma rahama ne, jiyai sam ya kasa kuka, sai wani irin zafi da zuciyarsa keyi. Guard din dake bakin kofa ya kalla yace " dan Allah......." Ai bai karasa ba yaji numfashinsa ya rike, nan guard din ya matso da sauri ya shiga danna mai baya, dakyar numfashinsa ya dawo. Abdul sam ya kasa cin komai, a zaune kawai yake shikadai yasan me yakeji. Jalal kam ya zama celebrity a gari ko ina ka duba kaga hutunshi a magazine ko a jarida ansa Jarumin da baya tsoron hukuma sai gaskiya, duk shirin dayace zaiyi kuwa a gidan tv to lalai zakaga mutane sun zako akan ganin me jarumi kuma matashi zak gabatar. Biki ya matso, sai dai Zahra ce kadai take shirin bikin amma sam Seemah batasa baki a harkar in Zahra tazo mata da xancen ya zasuyi kaza, kya kacinta kawai tace to, dama ba fita take ba inba gidan Ya Habib taje ba, yau saura sati daya biki, gida ya fara cika, hakan yasa yau Seemah ta tattara kayanta kamar yanda Dad yace akan ta koma gidansa saboda matarsa tazo itama, ta gana cikin gada kayantane ta ci karo da agoggon ta kurama agoggon ido tai nan fa ta fara tunano rayuwarsu ita da Jalal, kallan agoggon take ta kuma zarfafa cikin tunani, Ammar dake tsaye a jikin kofa ya taho da saurinsa zai nuna mata katin biki na dinner daya amso, ganinta a zaune tasa a goggo tana kallo yasa ya tsaya, hannu a harde tare da jingina da jikin kofar, basai Seemah ta fadamai ba yasan agoggon da take kallo me yake nufi dan kuwa agoggon dake hannun Jalal kenan kullum, ya kuma gansu iri daya sak, jiki a sanyaye ya juya harzai fita sai kuma ya fasa ya koma ya tsaya tare da cewa " Kanwata ko in juya ne?" Kallansa tai da sauri tare da juyawa ta goge hawayenta ta mike tace " yaya yaushe kazo?" Ammar yadan hade rai kadan yace " nafi awa biyu fa anan." Cikin tsananin mamaki ta kalleshi tace " da gaske? " Dariya yai yace " lalai taya za'ai ki yarda?" Harararsa tai tace " Yaya wato dai kai na kula inba tsokanata kaiba sam bakajin dadi ko? " Shiga ciki yai kusa da ita ya tsugunna kasa ya dauko agoggon data yar tana saurin mikewa, kallan agoggon yai sannan ya mike tare da mika mata, kallansa tai batare da ta amsa ba, kallanta ya sakeyi yace " amsa mana nasan abune mai mahimmanci a gunki." Kallansa tai tareda shan jinin jikinta tace " Yaya ba......" Murmushi ya mata yace " ansa mana." Hannu tasa cikin sanyin jiki ta amsa, yace " me? Kinaso ki mai sallama ne kafin biki?" Kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ta juyamai baya tace " bafa haka bane yaya, kawai ganin agoggon nai." Ya dawo gabanta tare da daga kai yace " nasani Seemah nasan komai hakan ne yasa banaso kidinga boyemin komai, nine na tambaye ki bawai ke kika tambayeni ba." Idannunta ne suka ciciko ta girgiza kai tare da cewa " how can I......?" " I am okay!" Ya fad'a yana kallanta, tai kasa dakai, yace " banaso ki dinga tunanin bakimai sallama ba..." Ganin tayi kasa dakai ya juya tare da cewa " in bakyaso shikenan." Yana fada ya juya kamar zai wuce, jiyai ta riko hannunsa ta baya, ya tsaya batare da ya juya ba, duk da kishin dake damunsa amma bayaso yaganta cikin wannan halin saboda shi. A hankali Seemah tace " Yaya zan iya?" Bai juyo ba ya daga mata kai tare da daurewa yace " banine na ce ba?" Ta goge hawayen ta da d'aya hannun tace " yaya zan mai sallama tare da ajiye duk wani ragowar abu dake zuciyata, bazan sake tunaninsa ba bare insa ka kaji ba dadi ba." Ammar ya daure ya juyo ya kalleta tare da mata Murmushi yace " karki damu Kanwata farincikina bai wuce naganki kina farinciki karki damu dani farincikina na tattare dake." Yai ajiyar zuciya tare da cewa " in har kinaso ki ganni ina farinciki to ke zan jira kiyi farinciki kafin ni." Seemah ta share kwallarta jikinta yai mugun sanyin, tausayin Ammar ya kara shigar mata zuciya, zare hannunsa yai yace " kishirya in ajiyeki, in yaso sai ya dawo dake." Yana kainan ya fita, kallon tsananin tausayi ta bishi dashi, zama tai a gun tare da runtse ido tace " Seemah meke damunki? Taya zakice zakije bayan kinsan koyace kije dolene yaji haushi?" Ta dade a zaune kafin Ammar ya kirata yace tafito yana jiranta. Jalal kam zauje yake a dan karamin gidan daya kama, saboda ya sai gida babba yanzu a kaduna inda Umma da kuma matarsa Zainab suke zaune acan, Zahida kam itama jiki ya fara sauki sosai Zaid kam kusan duk karshen sati sai yaje, tun Zaheeda na wase wa harta fara saki gashi ba laifi yanzu tana iya takawa kadan kadan inta rike sanda. Takardu ya gama dubawa sannan ya mike danjin yunwa ta fara kamashi, kallan calendar dakinsa yai ya zagaye wata number da jan biro, karasawa yai jikin calender yace " saura 7 days?" Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli wayarsa dayaji tayi kara alamar text, dagata yai yaga sako ne ga mamakinsa daga police station ne, wai Abdul na nemansa, yataimaka ya ziyarceshi." Wata iska ya furzar yace a fili " Allah yasa ya daidaita tunaninsa akan 'yarsa." Window ya zuge ya kurama titi ido, yaushe rabansa da Seemah? Kai ya girgiza tare da cewa " Ahhhh...." © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀. Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com _Ina kara godiya da jinjina gareku 'yan group d'ina na *Queen Bee* da kuma *Ayusher Fan Club* na gode kwarai da kaunar ku.......Allah yabarmu tare Ameen_ No. 7⃣5⃣ Jalal na tsaye jikin window yaji kiran Ammar daga wa yai yana tsokanarsa Ango da kanka? Ammar ya kalli Seemah dake zaune a gefensa tayi shiru yace " ka fito ina wajen gidanka." Jalal yace " ok ganinan dama ina so muce wani guri dakai." Ammar yana kashe wayar ya kalli Seemah datai shiru, yace " zaki kai minti nawa?" Kallansa tai idanunta suka dan canza kala tace " ni kati kawai zan bashi sai sallama da godiya daxan mai sannan in bashi hakur....." Ammar jiyai zuciyarshi takasa jure wa ya kalleta hakan yasa tadan juya fuska tace " kajirani anan yana fitowa zan fita minti 10 ma ya isa." Ammar baice komai ba ya juya ya kalli hanyar kofar da Jalal zai b'ulo, itama shiru tai tana tunanin anya ta kyautama Ya Ammar? Kallan inda Ammar yake kallo tai daga nesa ta hango Jalal ya fito, Jallabiya ce a jikinsa fara sai dai tamai kyau, ido ta kuramai gani tai kamar yanzu yafi da kyau jitai zuciyarta ta shiga bugawa ta kasa dauke idonta daga kanshi, Ammar daya juyo dan yi mata magana yaga yanda take kallan jalal jiyai wani kishi ya taso mai, haushin kanshi ya fara ji menene dalilinsa na barinta taga Jalal? Anya yasan me yakeyi kuwa? Har Jalal ya kusa isowa motar, Ammar ya kalleta tare da daurewa yace " Ki sauka kije kinga cema Dad nai xamu anso dinkinki, kallan Ammar tayi tace " yaya mu tafi kawai." Da mamaki ya kalleta yace " kin fasa sallamar daban hakurin?" Kallansa tai idanunta sun ciciko tace " Yaya banaji zan iya......" Ammar zai yi magana kawai Jalal shikuma zuciya daya ya bud'e kofar inda Seemah take da tunanin zama a gun dan suje inda yace, glass d'in motar irin wace na ciki yana ganin na waje ne amma na waje baya ganin na ciki, ga mamakinsa Seemah ya gani zaune da sauri ya maida kofar ya rufe jikinshi a sanyaye, zuciyarshi ce ta fara bugawa da sauri. Juyawa yai kawai maimakon ya koma gida kawai ya kama tafiya, Ammar ne yabishi da kallon tausayi sannan yace " Seemah bazakije ba?" Jiki a sanyaye ta bud'e kofar, dan tunda suka hada ido da Jalal taji gaba daya jikinsa ya kama rawa ta fita tare da kallan Jalal daya tsallaka titi kamar ta kula kawai tafiya yake hakan yasa ko Ammar bata sakema magana ba balle ta rufe kofar tai gunsa da sauri. Sam hankalinta nakan Jalal, So take ta tsayar dashi gashi batasan ya zatai ba, Ammar na jingine a mota yana kallanta, tazo tsallaka titi wani mai babur ya taho a guje, karar da Ammar yai na kiran sunanta yasa Jalal juyowa, da gudu ya taho gunta, itakam sam hankalinta nakan Jalal ganin ya nufota da gudu yasa ta tsaya cak, ta manta sam a titi take. Saura kiris mai babur yai gaba da ita Jalal ya fuzgota, yai baka tim, Tsoro ne ya kamata, ta dago cikin firgice, tare da fara jijiga Jalal, hawaye sai malala suke tana kuja tana kiran Deen! Deen. Ammar ma daya taho da gudu yai turus ganin Jalal a kasa, ganin yanda Seemah take kuka yasa hankalinsa ya dawo, matsowa yai tare da cewa " Jalal!" Ido Jalal ya bud'e tare da kallan Ammar yace " Ammar dan taimaka ka tayani na mik'e." Seemah ce ta kalleshi cikin mamaki au dama yana jinta? Mik'ewa tai tare da fara goge hawayenta, tace " Ya Ammar kacemai mu tafi asibiti a dubashi." Mamaki ne ya kama Jalal, bai kalleta ba shima ya kalli Ammar daya mikamai hannu ya kama sannan yace " Ammar kacema matarka basai naje asibiti ba." Ammar ya karasa dagashi tare da kallan Seema sannan ya kalli jalal yace " ni ba sakon wanda zan isar, Amma Jalal ka tabbata zaka iya tafiya?" Jalal ya dan cizi leb'ensa kadan yace " karka damu z......" Seemah ce ta katseshi da kallan Ammar tace " Yaya a'a mu kaishi asibiti please kaga saboda nine." Jalal bai kalleta ba yace " nace bazani ba, gida zan koma." Seemah kam daurewa tai ta matso daf da Jalal sun kusa isa mota, tace "kalleni." Jalal yaki kallanta, ta kalli Ammar sannan ta kara cema Jalal " Deen please. ..." Jin yanda tai maganar yasa Jalal ya kalleta a sanyaye tace " Deen muje asibiti please. " Ammar kam da tundaga faduwar Jalal yasa duk jikinsa yai sanyi, ya kalli Jalal yace " Jalal muje asibiti a dubaka inba sokake hankalinmu yaki kwanciya ba." Jalal bai magana ba har suka karasa motar, Seemah da sauri ta bud'emai gaba, ya kalli Ammar yace " A baya zan zauna." Jiki a sanyaye Seemah ta maida kofar ta rufe tare da bud'ema Jalal baya, Ammar ne yataimaka mai ya shiga, gyambon dayake fatan ya warke shine ya mik'e shikadai yasan meyakeji ganin Seemah a kusa dashi kuma wai ankusa bikinta, jiyai kamar ya dauketa su gudu, hakan yasa bayasan kallanta bare yimata magana saboda shikadai yasan meke ranshi. Sun fara tafiya Seemah dai a zaune kawaj take sai dai akai akai tana goge hawayenta, Ammar yai shiru a mota kawai tuki yake, sai taimakon Seemah da Jalal yai shi kuma ya buge, ga Seemah tun dataga Jalal ya buge take kukan nan , wani irin so Jalal kema Seemah? Tambayar dayake nanatawa a zuciyar sa kenan har suka isa asibitin, bayan yaga likita nan akasa a mai X ray. Seemah tai shiru a wajen dakin daya shiga tana tuno yanda Jalal ya buge, Ammar kam yana gurin likita, Jalal na fitowa ya dan tsaya a jikin kofa yana kallan Seemah batare data sani ba, jin kamar ana kallanta yasa ta juya, da sauri Jalal ya dauke idansa tare da cewa " Ammar fa?" Seemah ta mik'e tsaye tace " ba dai wani abun ko? Ba dai wani abun ko?" Kallanta Jalal yai zuciyarshi ta kara karyewa, a hankali yace " kar ki damu ba wani abun." Ta matso kusa dashi tace " Deen meyasa d'azu zaka taimakamin? Kana tunanin zanfi farin ciki ne in ni banji ciwo ba kaikuma ka ji?" Kallanta Jalal kawai yake cikin wani yanayi, ta share hawayenta tace " me yasa baka barni ba? Kasan yanda nakeji kuwa ganinka cikin wannan yanayi a maimakona?" Jalal ya d'auke idansa tare da daurewa yace " ko waye ma naganshi cikin wannan yanayi zan taimaka mai, ya wuceta zai wuce, sai dai tsayawa yai cak ganin Ammar ya juya baya, da alama ya gansu tarene yasa ya juya baya, Jalal na kallansa ya gangara yai wata hanyar. Tausayin kansu ne ya kamashi, me yasa zuciyarsu zataso mutum daya? Why? Muryar Seemah yaji kamar tasan me yake cewa tace " Deen ka taba tunanin ya nakeji a cikin raina? How can u walk away from me bayan kana ganin waye ya kawoni dan inma sallama? Meyasa zuciyarka bata tunanin halin danake ciki?" A hankali Jalal ya juyo idanunsa sunyi jaa sosai kamar masu shirin kawo ruwa cikin raunanniyar murya yace " Meemah I am okay! Kije gun Ammar I think shine yake bukatarki." Kallansa tai jiki a sanyaye tace " bam gane ba." Ya kalleta da raunannan idanunsa yace " ta ya ma zakisa Ammar ya kawoki nan? Me yasa bakya duba halin dazai shiga? " Jiki a sanyaye ta kalleshi, Jalal ya juya kamar zai tafi da sauri tace " I am Scared." Cak ya tsaya batare da ya juyaba, ta cigaba " zuciyata na tsoron kar inyi aure ba tare da na ganka ba." Jalal ya juyo ya kasa kuma danne abinda ke ransa, cikin wata irin murya yace " what about me?" Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, yace " kinsan halin da nake ciki me zai sa kizo gurina ki nemi tada min hankali dayawa? Meemah kin dauka ni basan ganinki nake ba?" Yai ajiyar zuciya tare da girgiza kai yace " noo." Kawai banaso ran mutane dayawa ya b'acine ta sana diyyar mu." Ya danyi hucci kadan sannan ya juya ya fara tafiya, kuka Seenah ta cigaba dayi, tun tana kallansa har ya bace mata. Jalal kam gate kawai ya wuce ya tari babur yahau. Sai text yama Ammar akan yaje ya dauki Seemah shi ya wuce gida, karya damu buguwar batai karfi ba. Ammar na ganin sakon ya taho gun da sauri, a tsugunne yaga Seemah tana kuka wiwi, tsayawa yai daga nesa kawai yana kallanta zuciyarsa sai kuna take, ba abinda ya tsana irin hawayen Seemah. Sai data gama sannan yaje ya mikar da ita suka wuce gida. Jalal kam da yamma yaje gun Abdul, rokansa Abdul yai akan yana san ganin Seemah. Jalal ya fadamai zai sa Ammar ya kawota duk da yasan ba lalai tazo ba. Jalal duk ya canza da ya dade bai ga Seemah ba amma yanzu tunda ya ganta yaji hankalinsa yaki kwanciya jiyake kamar yafi santa yanzu ma. Haka Seemah tun bayan sun rabu da Jalal ta zama maman shiru, tsakaninta da kowa a gidan bai wuce gaisuwa sai eh da a'a. Ammar kam shima ya shiga wani yanayi balle tunda yaga Seemah ta canza gaba daya, Jalal ya sanar dashi Abdul na nemanta amma daya sanar da Dad yace " ya bari sai andaura aure sai suje tare." Duk abinda akasama rana tofa lalai zaizo da sauri, yau gashi ta kama ranar alhamis ranar kamu kenan, hidima kam sai yinta akeyi, kowa ka kalla yana cikin farin ciki yake. Jalal kam yau da zazzabi ma yatashi a jikinsa, a kwance yake tun dare gashi ba kowa a gidan shikuma baisan kiran ko Sagir ne, Seemah ma kawai yake takeyi dan batasan Dad da Ammar su gane. Sai dai Ammar tun da suka bargun Jalal yasan halin datake ciki. Anyi kamu na gani na fada a gidan Abba, Amarya Zahra da Seemah ansha kyau, haka aka gama taru lafiya sai kuma washe gari daurin aure. Ammar na kwance a d'aki yana kallan number Jalal ya dade kafin ya daure da kirashi, sai dai duk yanda ya kira Jalal bai daga ba ya kalli agoggon bango na dakin karfe takwas na dare, yasan tabbas baiyi bacci yanzu ba. Ya dade yana kiran Jalal sai dai duk da haka bai daga ba, kallan Zaid yai dake faman waya da Zaheeda yai dan bugemai kafada yace " tashi muje gun Jalal." Zaid ya cema Zahi yana zuwa sannan ya kalli Ammar yace " ban gane ba." Ammar yace Jalal yaki daukan waya inaji ba lafiya ba. Nan yai waje tare da cewa " Zaid ka biyoni muje." Sunje gida sukaita kwankwasawa, Jalal dakyar ya mik'e dan tun dafe ba abinda yaci ga zazzabi mai zafi dake damunsa...... Yana bude kofar ya fadi kasa....... © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🏌‍♀ 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com No. 7⃣6⃣ Ammar na tura kofar yaga Jalal a kwance a kasa cikin kid'ima shida Zaid sukai mota dashi, asibiti suka wuce dashi hankalin Ammar yayi dubu gun tashi gani yake kamar shine sanadiyar wannan ciwon, suna zuwa asibiti akai emergency dashi, Ammar ya tsaya a wajen dakin jiyake kamar yai ihu, Zaid ya kalleshi yace " kazo likita nasan ganinka." Ammar jiki a sanyaye ya karasa ciki, likitan yace " kaine Guardian dinsa?" " eh, wani abun ne?" Likitan yace " me kukeyi har jikinsa yakai haka? Ga bigewar dayai abayansa baizo anyi treating dinsa ba sannan ga rashin cin abinci dan da alama rabonsa da abinci tun jiya da rana, ga damuwa mai karfi dake ransa, so kuke ku kasheshi ko me?." Yai ajiyar zuciya sannan ya kalli Ammar wanda gaba daya abinduniya ya dameshi likitan ya daure ya dafashi, yace " ba komai zamu dubashi dakyai." Ammar ya kurama Jalal ido, nan likitan yasa akaja gadon Jalal akai wani dakin dashi, Ammar ya kalli Zaid yace " ka fito da wayarka?" Mikamai Ammar yai yana cewa ya kamata asanar da su Zahee ko? Ammar bai amsa mai ba ya danna number Dad. " Ammar kana ina ne kawu na nemanka?" Ammar cikin sanyin murya yace " Dad ina asibiti." A zabure Dad ya mike yace " kana asibiti kamar ya? Me a sameka? Ciwo kaji?" Ammar ya girgiza kai kamar yana ganinshi yace " Dad kazo please, Jalal na kwace ba lafiya sosai." Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Dad yace " inalilihi wa ina ilaihi raji'un, Ammar meya sami Jalal din?" Ammar dake kallan Jalal yace " Dad nidai kazo please. " Dad yai ajiyar zuciya yace bari na zo. Jiyai Ammar yace " kazo kai kadai please Dad." Dad ya amsa tare da fitowa. Sunyi shiru, a inda Jalal ke kwance, Dad ya kalli Zaid yace " tsaya anan Ammar ina da magana dakai." Sun fita waje can gun da ba mutane sosai, Dad ya kalli Ammar yace " meya sameshi haka? Duk ya canza?" Hawaye ne suka dan gangaroma Ammar yasa hannu ya cire yace " Dad ya zanyi? It's all my fault. " Dad yai shiru yace " Ammar!" " Dad." Yai maganar cikin wata murya, Dad yasan halin Ammar da tausayi dafashi kawai yai yace " kaje gida nizan tsaya anan." Kai Ammar ya girgiza yace " bazan iya tafiya ba Dad sai naga Jalal ya ware." Kai Dad ya jinjina yace " to Ammar amma kaga dare yayi ga gobe karfe 10 za'a daura auren nan baka tunanin ya kamata kaje gida?" Ammar yai shiru, can yqce " Dad in Seemah tasan Jalal bashi da lafiya ya zatai? Balle intasan ciwon a dalilinta ne?" Dad ya kalleshi batare da yace komai ba, Ammar ya cigaba " Dad ya zatai?" Kai dad ya juya yace " Ai ba fada mata za'ai ba." Ammar ya runtse ido sannan ya bud'esu idanunsa sun cika taf yace " Dad baka gani muna shiga hakkin ta?" Da mamaki Dad yace " Ammar me kake nufi haka?" Ammar ya had'iyi wannan abun yace " Dad babban bakin cikina aduniyar nan bai wuce inga Seemah cikin damuwar da harzai kaita gayin kuka, amma Dad kasan kukan da nasa Seemah ta dalilin yaron nan? Sau nawa ina ganinta tana kuka akan abinda baifi karfina ba ko ince akan abinda nine xan iya daidaitashi, amma haka nake ganinta tana kukanta bana iya tab'uka komai saboda wani buri na zuciyata." Hawaye ne suka gangaro kumatunsa, ya kalli Dad yace " Dad nan!!!!" Dukan inda zuciyarsa yake yai, da karfi yace " nan gun Dad ni kadai nasan ya nakeji inaga Seemah na hawaye, sannan ina tuna Sadaukar da rayuwarsa da Jalal yai saboda Seemah, kanwarsa batada lafiya amma baije gunta ba......" Dad ya dafashi yace " Amma ai ita Seemah itama ta zab'eka." Ammar ya girgiza kai yace " tadai zabi farin cikin ka ne Dad, yarinyar nan bataso ko kadan taji tama abinda bazai faranta maka rai ba ciki kuwa harda sadaukarwa da farincikin rayuwarta, na sani zan kula da ita, ina santa kamar raina sai dai nasan inda zuciyarta take , Seemah na bala'in sona amma son 'yan uwantaka takemin." Dad yai shiru sai dai jikinsa yayi mugun sanyi yakasa furta komai. Ammar yacigaba tare da share hawayensa yace " Dad duk farincikin da Seemah takeso nima inasan shi sai dai ina bakin cikin zuciyata tana neman canza min tunani na." Dad ya kalleshi, Ammar ya tsaida hawayensa yace " Dad na tsaida solution gobe auren nan da Jalal za'a daura bazan iya ganin abokina da kanwata danafiso a duniya cikin damuwa ba nikuma ina farin ciki ba." Kallan tsananin mamaki dad yamai yace " Ammar kasan me kake fada kuwa?" Murmushi Ammar yai wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne yace " Dad ka taimaketa ne saboda son da kake ma mahaifiyarta da kaunar da kake ma yarinyar ko?" Dad ya daga kai tare da cewa " hakane amma...." Ammar yace " ka taimakesu ne saboda Allah na sani Dad." Dad yai shiru, Ammar ya cigaba " in har munaso ladanmu ya karfafa agun Allah mu bawa Jalal Seemah sai kaga Allah yakara daukaka mu ya kuma biya mana da mafificin gidan Aljanna." Dad ya kalli Ammar cikin tsananin kulawa yace " Ammar kaifa? Ni gani nake kamar sai kafi Jalal shiga wani hali in aka rabaku da Seemah." Kai ua girgiza yace " a'a dacan a matsayin kanwata take yanzu ma a haka zata zauna, na sani sanda nake mata ya wuce duk yanda kowa ke tunani amma tunda ni kadai nake santa haka banaji wani abun zai sameni." Dad kam kalaman Ammar sun ratsa jinin jikinsa, yace " shikenan Ammar." Murmushi Ammar yai yace " Dad dan Allah karmu fadawa kowa sai Abba kowa yaji a gidan bayan an daura in ba haka ba wani sai ya nemi canzama ra'ayinka." Dad ya dafa Ammar yace " Ammar ka tabbata ba komai?" Kai Ammar yadaga yace " marainiyar Allah itace first ni daga baya, sannan sai kamin addu'a Allah yabani wata." Rungumeshi Dad yai yace " Ina Alfahari dakai d'ana ka fahimtar dani abinda ban yi tunani ba, Jalal yaron kirki ne tun yana karami, naji dadi sosai da kaunar da kukema juna kuna yara ta dawo muku yanzu." Sun dade agun suna hira kafin su koma ciki, dad da Zaid suka koma gida. Washegari kowa ya tashi anata hidima, Seemah ta rasa dalilin dayasa gabanta keta faduwa, Ammar ta kira sai dai taji Junaid ya d'aga, tace " yaya Ammar fa?". Junaid ya kalli Zaid wanda yace Ammar yace kar afad'a mata inda yake, yace " yad'an fitane." Ta kashe wayar tare da d'an had'e rai. Zaune suke a massallaci an fara add'uoi za'a daura aure. Abba zaune yayi shiru yana tunanin kalaman Dad, na jiya daddare, ajiyar zuciya yai alokacin da akace waliyin Jalal yaji dad yace " ganinan." Dad ya riga ya sanarda mahaifin Jalal wato Amadu nan yai farin cikin da hakan har kuka sai dayai. An dauren auren Junaid da Zahra, Jalal da Seemah akan sadaki dubu d'ari wanda da kudin da za'a bada na Ammar ne. Mamakine ya kama 'yan uwan mahaifin Dad dana mahaifiyarsa, Habib ya kalli Dad cikin mamaki sai dai aikin gama ya gama. Zaid ne ya kira Ammar dake asibiti gun Jalal yace " Ammar an d'aura." Runtse idanunsa yai jiyake kamar yasa ihu, dakyar ya daure yace " ka fad'awa Seemah mijinta na asibiti ba lafiya." Zaid yace " Ammar inzo in daukeka?" Ammar ya d'aga kai, Zaid ya daga kai tare da cewa " Jalal din ya farka?" Ammar ya girgiza kai yace " a'a ko ido ya bud'e sai dai inga ya maidasu, sai dai likita yace abarshi ya huta stress sunmai yawa ga damuwa." Zaid ya d'aga kai. © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM* 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com *Luv u oll my fans.......* No.7⃣7⃣ Seemah na zaune tayi wanka tana jira agama ma Zahra kwalliya sannan a mata, rigace doguwa ta atamfa a jikinta aiki ne a jikin rigar har wajen ciki d'inkin yayi masifar kyau, a zaune kawai take amma gaba daya batajin jikinta daidai, jitai an fara kud'a hakan yasa gabanta ya sake fad'uwa, suka shigo d'akin sukace an d'aura, Seemah kasa tai da kanta ganin wayarta tai kara yasa ta daga, Zaid ne da sauri tace " Ya Zaid ina ya Ammar? Jinake kamar wani abu ya sameshi." Zaid yace " Seemah ki fito ina waje mijinki ba lafiya." " Naam? Me kake nufi?" Kashe wayar yai dan jiyai baisan me zai ce mata ba, A zabure Seemah ta mik'e ko hijab bata dauka ba d'ankwalin data yafa akanta kawai ta sura tai waje ko takalmi batasaba. A waje taga mutane sun taro anacewa " waye kuma Jalal?" Tsayawa tai turus, can kuma sai tai tunanin ko ba Jalal d'in ta suke nufi ba, waje tai da sauri ta fada mota Zaid ya kalleta sannan ya ja motar, duk ta rikice tace " Ya Ammar meya samu Ya Ammar d'in?" Kallanta yai jiki a sanyaye yace " Kunyi magana da dad?" Ta girgiza kai tace " a'a yadai kirani da safe yacemin, ko mai na rayuwa mukaddarine, haka kawai yacemin." Suna isa asibitin suka fito, duk Seemah ta rikice, harsunje shiga d'akin wayar Zaid tai kara, ya kalleta yace " nan ne ki shiga." Ko kula shi batai ba ta fada dakin, daga nesa tafara ganin kamar ba Ammar ba, jiki a sanyaye ta karasa kusa da gadon, turus tai ganin Jalal a kwance duk ya rame sai bacci kawai yake. Hawayene suka fara zubo mata a hankali takai hannu gefen fuskarsa hawayenta ne suka shiga d'iga kan kuncinsa, sai zubowa sukeyi ta kasa magana sai hawaye kawai take. A hankali Jalal yad'an bud'e ido jin ruwa na d'igarmai, kallan Seemah yadauka mafarkine yasa ya kara lumshe ido, hawaye kawai takeyi, can ya sake bud'e ido daidainan ta kalleshi, idanu suka had'a yad'an motsa bakinshi kad'an yace " Meemah?" Hawayene ya cigaba da zubo mata tace " Deen? Me ya sameka haka?" Sai a lokacin ya tabbatar ba mafarki yake ba kallanta yai tare da cewa " me kike anan?" " Naam?" Tafad'a tare da kallan d'akin sai a lokacin ta tuna kamarfa Ammar ne yakamata ta gani ba shi ba, ta d'an juya tace " Ni cemin akai inzo in duba mijina na d'auka ya Ammar ne bashida lafiya." Jalal ya d'an juya ido yace " meya sami Ammar d'in?" Ta d'aga wayarta ta kira Zaid ga mamakinta Ammar ne ya d'aga. Cikin tsanin damuwa tace " Ya Ammar kana ina?" Yace " Seemah?" Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi ta kasa amsawa. Cikin wata murya yace " ki kula da mijinki, ke yake bukata a wannan lokacin." Da mamaki tace " ban gane ba? Kana ina?" Yai shiru can ya daure yace " An daura muku aure da Jalal karki damu dani ko kiyi tunanin wani abun, kawai ki kulada lafiyar mijinki." Jitai kalaman sun shigar mata kunne banbarakwai sai dai kafin ta sake magana Ammar ya kashe wayar. Kallan Jalal tai sai dai ganin yanasan tashi ya kasa saboda cikin dake bayansa, yasa ta daure matsowa tai zata taimaka mai, kallanta Jalal yai yace " bashi kawai, ki nemomin likita." Bata kulashi ba kawai ta shiga taimaka mai, tana gamawa ta duba ga kayan shayinan da abinci hakan yasa ta hadamai shayi ta mikamai tace " ina zuwa." Kallanta yai yace " kina zuwa ina? Me zaki dawo yi anan? So kike ran Ammar ya sake b'aci?" Kallan yanda ya rame tai ta kauda kai tare da cewa ni kaina ban fahimci abinda ya Ammar d'in yake nufu da an d'aura mana aure dakai bane shiyasa nakesan ganinsa. Bata jira mai zaice ba tai waje, Jalal ya kara maimaita kalamanta. Seemah na fita taga Dad yana tahowa shida Abba, da sauri takarasa gunsa yace " Seemah muje ciki." Kallan mamaki tamai sai dai ba zata iya musu ba. D'akin Jalal suka koma bayan sun zauna shiru, nan Dad ya warware musu duk abinda ya faru jiya zuwa yau. Seemah kuka take sosai, yana gama maganar yace " dan haka ki zauna anan ki kula da mijinki ki bar sha'anin biki su Zahra sayi." Ta kasa magana haka ma Jalal wanda yakejin maganar kamar ta tsuniya, ganin halin da suka shiga yasa Dad ya mik'e shida Abba sukai waje. Seemah ganin sun fita yasa ta mike da gudu ta bi bayan Dad ta baya ta rungumeshi tana wani irin kuka, Dad ya daure ya juyo da ita setinsa yace " Seemah?" Cikin tsananin kuka tace " Dad meyasa ka bar Ya Ammar yai haka? Kamanta nace na hakura? Sannan babban burinka ne fa?" Dad yad'an shafa kanta sannan ya kalli kafarta da ko takalmi babu yace " a haka kika fito ba ko takalmi?" Hawayenta ne ya karo tace " Dad ina Ya Ammar d'in? I have to meet him. " Dad yai murmushi yace " karki damu yayanki yace ki kulada Jalal." Yad'an zareta daga jikinsa yace " karkiyi tunanin komai sai mijinki." Yana kainan ya juya ya fara tafiya. Tsugunnawa tai a gun ta shiga kuka, ta dade agun sosai mutane sai wucewa suke suna kallanta dakyar ta daure ta mike tai cikin d'akin ga mamakinta Jalal ta gani ya mik'e yana sa rigarsa, da sauri ta karasa inda yake? Idanunta duk sun canza tace " Ina kuma zaka?" Kallanta yai yace " me Ammar yake tunani? Ni zanje in mai magana." Cikin kuka tace " ni ina zansan me yake tunani, amma kaidai bazan barka ka fitaba bayan ba lafiya gareka ba." Kallanta yai cikin wani yanayi yace " Meemah tunanin halin da Ammar yake ciki nake." Ta goge hawayenta tace " naji wannan amma ka koma ka kwanta sai inkira Ya Ammar d'in." Jiki a sanyaye Jalal ya zauna, ta mikamaj wayarta tareda dialling d'in number Zaid. Ammar ya d'auka, Jalal yace " Ammar meke faruwa?" Ammar yad'anyi murmushi kad'an yace " meke faruwa dame? D'an na bar maka Seemah ko dan kana tare da ita?" A zuciye Jalal yace " Ammar meke damunka ne? How can u joke now." Ammar yai ajiyar zuciya yace " kai dai dakake lovesick yanzu sai ka ware." Jalal yace " Ammar ban aminta da...." Katseshi yai da cewa " ka saketa to." Yanakai nan ya kashe wayar, shiru Jalal yai yana maimaita kalmar saki. Seemah ta zauna kusa dashi kadan tace " me Ya Ammar d'in yace? Wasa yake ko?" Jalal ya kalleta cikin mamaki yace " da alama dagaske yake tunda haryake cemin wai in sakeki ." Ta kalleshi da mamaki, mik'ewa tai da sauri tace " Me Ya Ammar yake tunani?" Tafad'a tare da hura iska. Jalal ya daure yace " taimaka min in kwanta please. " Harararsa tad'anyi tace " akan me?" Kallanta yai sannan ya daure yace " hmm kiramin ko nurse ne." Ta d'an tab'e baki tace " nurse d'in ai kala biyu ne, maza da mata wacce kakeso a kira ma?" Jalal ya kalleta tunowa yai da masifarta ta da yace " auu kiramin koma waye ai ni patient ne." Ta makamai harara tare da turashi gado da d'an karfi, zafi yasa sai daya saki kara yace " me kuma nai kinsan dai ba lafiya ce dani ba, irin wannan tureni?" Ta harareshi tare da komawa gefe ta zauna, Jalal ya juya kai kamar mai bacci dan jin abin yake banbarakwai. Text tama Ammar kamar haka. _Ya Ammar na sani sarai kayi haka ne dan farin ciki na sai dai Ya Ammar aikin gama ya gama bani da abincewa a wannan lokacin, kalma daya zan iya fadama shine Allah ya sakama da mafificin gidan aljanna ya kuma baka matar data fini._ Tana turawa ta 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 🐾 *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*🐾 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Na *AYUSHER MUHD* ayushermohd.blogspot.com *LAST PAGE* No. 7⃣8⃣ Can gida kuwa wasu abin nan ya basu haushin gani suke Dad bai kyauta ba, wasu kuwa harda habaici na dama yarinyar da batada mahaifi me zaisa ya had'ata da d'ansa?" Zahra kam taji ba dadi dasu Junaid sai dai ya za'ai tunda dai an riga da angama, Ammar ko gidan baije ba, sun riga sun shirya yin dinner sai dai Zahra ce da Junaid kawai zasu. Jalal kam suna kwance, sai can Seemah ta farka, tana ganin Jalal idanunsa biyu da sauri ta mik'e tsaye tare da wayancewa da hmm ina toilet din ne? Tafad'a tana dubawa da gudu tai nufi kofa ta bud'e ta shige. Jalal ya bita da dariya ganin yanda ta rikice. Tunanin wayarsa ce tazomai yasa ya jawo wayar Seemah ya kira Abbansa. Abba ya daga, Jalal ya gaidashi. Cikin zumud'i Abba yace " Jalal kaji abin alheri ko? Bansan mezancema Ammar da Isma'il ba." Jalal yadanyi murmushi yace " Zainab fa?" Abba yai shiru, Jalal ya danyi murmushi kad'an nasan bazatai farinciki ba. Abba yace " Jalal kayi tunanin inda Seemah zata zauna?" " hmm ina tunanin tambayarta ko nan kaduna ko kuma nan, ni abin ne banbarakwai nake jinsa." Abba yai dariya yace " ba wani banbarakwai Allah ya riga ya tsara Seemah matarka ce." Jalal ya kalli kofa inda yaji motsin Seemah, yace " Abba sai anjima wayar Seemah ce." Nan sukai sallama tare da kashewa, Seemah ta harareshi kad'an tare da cewa " wa yace a d'aumin waya?" Jalal ya dan yi murmushi yace " yayarki na kira." A zabure ta karaso kusa dashi tace " wacce yayata?" Kallanta yai yace " haka ake jinyar baza'a bani abinci ba? Yunwa nakeji." Ranta a b'ace ta bud'e kular da ta gani a d'akin fatan dankali ne yaji kifi sosai, ta zubamai a plate sannan ta mikamai, tace " wacce yayata?" Jalal yadan rik'e ciki kadan yace " haka ake kula da miji ko abincin baza'abarshi yaci ba?" Juya kai tai aranta tace " su miji manya." Yana gama ci ta kalleshi tace " wacce yayata? " Hannu yasa ya riko ta tare da zaunar da ita kusa dashi yace " Meemah bamuyi tunanin inda zaki zauna ba?" Ta turo baki tace " inafa zan zauna?" Ya kalleta yace " inda zamu zauna nida ke a kaduna ko anan." Ta mik'e tare da cewa " ni yazanyi iyi sallah ko mayafi ban fito dashi ba, kallanta yai yace " ai kuwa sai dai kiyi waya a kawo miki dan bazaki fita a haka ba......" Kusa dashi ta matso tace" to ya kakeso inyi?" Yace " bana fadamiki ki sa a kawo miki ba nidai matata bazata fita a haka ba mutane su kalleta." Ta sa dariya sai data tsagaita ta kalleshi tace " lalai mai mata." Lumshe ido yai yace " sosai ma, Ammar ne ya bani matar da nakeso wacce ji nake duk numfashina tana tattare dani." Dariya ta sakeyi tace " Kai Deen yaushe ka zama haka?" Jawota yai jikinsa yace " ke kika maidani haka, mu zauna a abuja ko? Kinga kusa da Dad d'inki." Ta turo baki tace " bayan bani kad'ai bace matar ka?" Yai ajiyar zuciya yace " Meemah amma kinsan ai...." Saurin cusa kanta tai a kirjinsa alamar kunya tace " na sani amma a da dan rannan tafiya kai ka barni." Ajiyar zuciya yai yace " Meemah banasan zama a asibitin nan mu roke likitan ya sallamemu please kinji?" Tace " naki wayan baka warke ba ta ina zamu tafi? Kuma ni banshirya tarewa yanzu ba." Hararta yai yace " a ina? Ai kafata kafar matata Amnar yamin abinda ban taba zatoba ta ina nikuwa zan barki kije wani gida? Mu tafi gidana inyaso sai insa a nemarmana gida." Baki ta turo tace " an fa kai min kayana can gidan Ya Ammar kuma kwasowa za'ai ko me?" Jalal ya rungumeta yace " bakomai sai musai wani." Ta mik'e tace naki wayan. Washe gari kuwa sai da Jalal ya matsa aka sallameshi duk lokacin abinci ana aikowa daga gidan su Dad. Ammar kam hotel ya koma kawai ya tare, su Dad basu sani ba ashe yayi booking d'in jirgi, washe gari da safe yazo ya sanar da Dad zai koma England amma ba dadewa zaiyi ba, ba musu Dad ya amince saboda yasan halin da Ammar din ke ciki. Bayan Jalal ya warke da kanshi ya kaita gun Abdul, nan ya nemi yafiyarta tare da alkawarin canza halayensa, sunyi ziyara har garin iyayenta nan sukaje taga 'yan uwanta. Jalal ya kama gida a Abuja inda suka zauna shida Seemah, kulawa kaunar dake tsakaninsu ta wuce duk yanda zan kwatanta muku, Yau yakama wata tara kenan da auren su, duk karshen mako yake tafiya kaduna Seemah ita ta tsara mai hakan saboda tana ganin yanda yake rashin damuwa da Zainab hakan bazai mata dadi ba, shikanshi yanzu yana daidai kokarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sam Zainab bata jin haushin Seemah ita gani take ma auren da Jalal d'in yai shine sanadiyyar kulata da Jalal yake, Seema na d'auke da tsohon ciki, itakuma Zainab laulayi takeyi. Jalal ya shigo gidan ganin yanata sallama ba'a amsa ba, a rude ya shigo gidan ya fara neman inda Seemah take, har daki ya shiga batanan, d'akinshi ya nufa, yana budewa yaga ta fesheshi da wani farin abu, baya yai yana mamaki, nan ta matsamai ya kalli d'akin, candle ne kanana an jera shi a kasa anyi kwalliyar I♡U dashi kwaliyar tayi kyau, ya kalleta cikin mamaki, kayan bacci ne a jikinta shara shara ya sakar mata wani sansanyar murmushi tareda karasowa ya rungumeta, murmushi itama tai tace " My Deen kardai a manta da babynmu." Sassauta rikon yai sannan ya d'ago a hankali ya kai bakinshi cikin nata, wani irin salon kauna sukema junansu, jitai kafarta naneman kasa d'aukanta, Jalal ya riko kugunta nan suka cigaba da aikama juna sakwanni, a hankali Jalal ya jata kan gado sannan ya tare neck tie d'insa ya cigaba da sumbatarta, cikin salo a kuma hankali ya bakinshi na nata ya zare mata 'yar rigar dake jikinta, itama mab'allin rigarsa ta dinga cirewa har ta cire su duka, sumbatar kirjinsa ta fara nan fa suka shiga cikin wani yanayi wanda su kadai sukasan halin da suka shiga. Sai da suka gama sannan ta kwanta akan kirjinsa, shikuma yana shafa kanta, yace " Meemah wannan gyaran fa? Decoration d'in yayi kyau, kara kwanciya tai a kirjinsa tace " a internet na dubo yanda akeyi." Yai ajiyar zuciya yace " Meemah in miki wani alkawari?" Ta d'aga kai, tare da juya fuskarta saitinshi, yace " indai mace kika haifa sunan Mahaifiyarki zamusa mata Fatima, in kuma namiji ne to sunan Ammar ko Dad sai kizab'a a ciki." Murmushi tai tace" nagode sosai Deen, amma ya maganar Ya Ammar?" Yace " yace next week zai dawo." Tai ajiyar zuciya tace " kaii nayi missing d'in yaya." Mikewa yai ya sunkuceta sukai toilet, kafin suyi wanka sai daya wanke mata kai da kanshi, dan tace bata iya sunkuyawa, nan sukai wanka suka fito a tare, shi ya shafa mata mai sannan itama ta shafa mai tana shafamai tana tambayar yasu Ya Zainab?" Yace suna lafiya....... Ammar ya zaune a cikin jirgi yana karanta jarida watace a zaune a kusa dashi ta zake sai bacci take, haushi ya kama Ammar ya juya kansa jikin window, tana gama baccin ta mik'e tare da yin mika, ta kalli Ammar tace " dan Allah awa nawa mukai?" Kallanta yai yace " ke agoggonki tsayawa yai?" Agoggon hannunta ta kalla ashe da agoggo a hannunta da sauri ta juya fuskarta, yai murmushi sannan ya juya, mai service ce ta karaso ta kallesu tace " mai kukeso a kawo muku? Tea ko coffee? " A tare sukace " Coffee." Kallan juna sukai sai sukai dariya, matar tai dariya itama tace " da alama ku couples ne kunyi matching sosai." A tare suka kara cewa " a'a." Tai sake dariya sannan ta tafi, tana tafiya Ammar ya kalleta kadan kyakyawa ce sosai, juyawa yai jiyai tace " A Abuja kake?" Yace " eh kefa?" Tace nima........... Murmushi sukama juna a tare. Zahra ma ankusa haihuwa, Dad da Abban Jalal aminta ta dawo sosai, yanzu Abban Jalal yananan yana kasuwancinsa a babban shagon da Jalal ya bud'e mai. Zaid ma saura wata d'aya ya auri Zaheeda wacce ta warke sumul, har malami Jalal ya d'aukar mata yana koya mata karatu. Abdul kuma an sakeshi yana zaune a dan karamin gidansa shida matar sa 'yar uwar Sagir, Ya canza kamar bashi ba. Jalal da Seemah masha Allah kauna kam suna san junansu sosai........nace To Allah yasauketa lafiya Nima nace mu had'u a wani littafin nawa in Allah ya yarda....... *GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU* *Yan Group d'ina* *THE QUEEN BEE* *AYUSHER FAN CLUB* Sannan ina godiya gareku 'yan *NAGARTA* BEELY BADARU GROUP 'YAN SAUYI NA KCK EXCELLENT HAUSA WRITERS MU SAN JUNA TALENTED HAUSA WRITERS MARYAM MAI DALA HAUSA NOVEL MY BLOG FANS HAUSA NOVELLA BE A LADY WITH FASHION Da kuma ragowar group d'in da duk nake ciki ina godiya gareku. Ina alfahari daku *MY BEELY BADARU* *SIS PHARTY* ASY KHALEEL MAMAN SHAHEEDA MUNAY SADNAS AUNTY KYADY FATTY Ahh gaisuwa gareki babbar Aminiya *AISHA M.UMAR....* *NI AYUSHER MUHD ke muku fatan alkairi*😘😘😘😘 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *