adsense here
Marwa da Marwan 1to7
Leave a reply
[10/6, 2:58 PM] Hawwadamary : *MARWA
DA MARWAN*.
1
*~By Hauwadamary*
(NWA)
*BISMILLAHIRRAHMANURRAHEEEEM..*
Dedicate to *Memxiey_fulla *
Zaune nake a bisa d’an dakalin dake
qofar gidanmu ina shan iska kasancewar
munyi hutun makaranta,hakan ne yasa ban
cika zaman cikin gida ba da yamma duk sai
inji na takura matuqa,wannan ne yasa tunda
makayi hutun makaranta da zarar yamma
tayi sai na fito na zauna ina kallon jama’ar
dake shige da fice a cikin unguwar tamu
mai qarancin mutane.
Hakanan naji yau ina sha’awar d’ora ma
masoyana masu qaunar littattafaina sabon
littafi a yanar gizo,don a gaskiya na d’an
kwana biyu ban d’ora ba,hakanne yasa koda
yaushe cikin samun saqon ma’abota
karatun littafi na nake wanda mafi yawanci
qorafinsu a kan rashin d’orawar tawa
ne,nakan basu haquri da karatu ne yayi man
yawa kuma ga shirye-shiryen zana jarabawa
da mukeyi,tou yau dai na yanke shawarar na
fara rubutawa yanda kafin na koma
makaranta na samu na qarashe shi tunda
hutun namu a yanzu saura sati ukku ya
qare.
Sai dai kash! tunda na zauna nake faman
tunani ko zan samu labarin da zan rubuta
wanda ba zai d’auki lokaci mai tsawo
ba,wata zuciyar ta bani shawarar kawai na
qarashe MUTUM MUGUN ICCHE mana,naga
gaskiya idan nace zan qarashe ba qaramin
aiki zanyi ba saboda yana matuqar buqatar
natsuwa sosai don labari ne mai hargitsi da
badaqala duk a tare,moreover ba zan iya
qarashe shi ba a cikin sati ukkun da suka
rage mana,tou yau dai haka na qaraci
zamana ina tunanin mafita amma shiru kake
ji wai anyi wa mai dami d’aya sata.
Wasa-wasa yau gashi na shafe kwana
hud’u ina tunanin labarin da zan rubuta mai
sauqi amma ban samu ba,kullum idan zan
fita nakan fita ne da littafina da biro haka
kuma idan zan koma gida nake komawa da
su ba tare da na rubuta komai ba.
A zaman da nake a waje na lura da wata
mata wacce da zarar an kusa magrib take
zuwa ta wuce da mota sai chen naga ta
dawo d’auke da yara biyu a cikin motar
namiji d’aya mace d’aya da kayan
makaranta,wannan ne yasa kai tsaye na
yanke hukuncin daga makaranta take d’akko
su,ina ankare da yanda matarnan ke faman
bina da ido duk idan tazo wucewa har tasa
na soma tsarguwa.
Yau kimanin kwanana bakwai ina zaman
tunanin labari kuma har yanzu dai ban
samu ba,kawo yanzu harna haqura da
rubutawa saboda hutunmu yazo qarshe,na
gama yanke hukuncin idan mun sake wani
hutun sai na qarashe MUTUM MUGUN
ICCHE.
“Assalamu Alaiki” nayi anyi man sallama
da wata iriyar murya mai taushi da sanyi,
Na amsa gami da d’agowa don gane ma
idona mamallakiyar wannan murya,ga
mamakina wannan matar ce mai wucewa
d’auko yara daga makaranta, sai na fara
tunanin to me ya fiddota alhalin lokacin
fitartata baiyi ba a yanda nake gani tana fita
koda yaushe,Anya ko matarnan ba irin masu
satar mutane bace,koma dai da mai tazo
nafi qarfinta saboda in Allah nasa a raina,
na qara kallonta a sace,matar ba wata
babba bace don duka ba zata fi shekaru
ishirin da shidda zuwa da bakwai ba kuma
kallo d’aya zakay mata kasan naira ta
zauna..
Muryar matar ce ta katse man tunanina
da fad’in”ko dai baki maraba da zuwa na
ne,naga ko tayin gurin zama baki man
ba”ta qarashe tana kallona d’auke da
murmushi a fuskarta.
Nima murmshin nayi kana nace”haba
dai,waye yaqi baqo,ki zauna ga wuri”na
soma goge mata kusa da ni da handky d’in
hannu na.
Ta zauna gami da bismillah,daga nan gurin
ya d’auki shiru na wani d’an lokaci kafin ta
nisa tace”nikam baiwar Allah ba don kada
kice nayi maki shishshigi ba da na
tambayeki dalilinki na zama nan kullum riqe
da littafi da biro kina tunani,shin baki tsoron
wata lalurar ta same ki
*Hawwa Damary*
[10/6, 3:05 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN*.
2
*~Hauwadamary*
(NWA)
dedicated to *Memxiey_fulla *
A raina nace”ay kin riga da kin gama
shishshigin”sai dai kuma a 6angare guda
tabbas matar nan tana da gaskiya don
gaskiya yanda nake cika ma qwaqwalwata
tunani ba abunda zai hana wata lalurar ta
same ni,na qara kallonta cikin ido kana na
sakar mata murmishi a karo na biyu tun
zuwanta gurin sannan nace”haka ne,nima
wallahi ina so naga na rage tunanin amma
bai yuwuwa”
“Bai yuwuwa?” Ta buqaci qarin bayani
kana kallo na,
“Kai matar nan akwai zaqewa” nace cikin
raina,nayi kamar bazan fad’a mata ba,sai
wata zuciyar tace na fad’a mata kawai
maybe ta taimakeni,hakan kau nayi sai na
samu kaina da zayyane mata kaf matsalata
ta dalilin zamana da littafi da biro,
Ga mamakina sai naga ta kwashe da
dariya harda qyaqyatawa,hakan ba qaramin
qular da ni yayi ba naji dama ban fad’a
mata ba yanzu gashi nan ta maishe ni
mahaukaciya,eh tou mahaukaciya
mana,tunda irin wannan dariya sai kaga
abun dariya zaka yi ta ko kuma idan kaga
mahaukaci.
Saida ta kusa minti d’aya tana dariyarta
sannan ta natsu tace”in don wannan ne
kada ki samu damuwa,gobe gurin qarfe sha
biyu na rana kizo gidana da littafi da bironki
ni kuma nayi maki alqawari zan baki
labarin da zaki rubuta ma masoya
littattafanki wanda zai fad’akar dasu ya
tunasantar da su abunda mafi yawanci
mutane suka shagala suka manta sannan a
6angare d’aya ya nishad’antar da su,labarin
da zan baki labari ne da ya faru a kan
qawata ko ince maki aminiya ta,labari ne
dake cike da abun al-ajabi,tashin hankali da
kuma tsantsar damuwa ga wad’anda abun
ya shafa” sai kuma naji tayi shiru, na d’ago
don ganin dalilinta nayin shiru sai naga
hawaye na zuba daga idanunta, nay saurin
cewa”subhanallah! mai yayi zafi haka
y’aruwa,idan har labarin da zaki bani ne
sanadiyyar zubar hawayenki tou na
haqura,wallahi ki bars…tay saurin tsayar da
ni ta hanyar d’aga man hannu tace”ni nayi
niyyar baki labarin nan don haka kada ki
damu,ina jiranki idan Allah ya kaimu goben,
ba don kada kice na cika tambaya ba da na
tambayeki sunanki”
Nayi murmushi nace”ba wani abu
ae,sunana Hauwa’u amma anfi kirana da
Hauwa Damari”
Tace”tou Hauwa Damari sai kinzo”
Har ta juya nay saurin cewa”sai dai gashi
bansan gidannaki ba”
“Ops kinga nima na sha’afa ban maki
kwatance ba,kinganshi chen” ta nuna man
wani had’ad’d’en gida dake qarshen wanda
ba’a dad’e da gama gininshi ba don a
tunani na ma ba’a kaiga tarewa ba,
Nace”tou sai kin ganni goben”
Tay murmushi sannan tace”ki rinqa
had’awa da in Allah ya kaimu saboda bamu
keda goben ba,kai kana taka ne shima mai
goben yana tasa”
Nace”hakane,tou ubangiji Allah ya kaimu
goben”
Tace”Ameen”sannan ta nufi motarta wacce
sai a lokacin na lura da ita,nima juyawa
nayi na shige gida don ji nayi yau zaman
wajenma bazan iya ba,
Washegari tunda nayi sallar asuba ban
koma gado ba,hakanan kawai naji ina cikin
farinciki nasan hakan bai rasa nasaba da
labarin da za’a bani,a gurguje na gama taya
ummana aiki sannan na wuce nayi
wanka,d’akin su qannena na leqa na kira
momi da Hafsat nace suy maza suje shagon
Abu tela su amso man d’inkina, aiko ba sufi
minti biyar da fita ba sai gashi sun dawo
man da d’inkin na amsa na wuce na sanya
sannan na d’akko gyalen da na tanadar ma
atamfar na rataya na fice,dai-dai zan fita
parlour naji motsin umma a kitchen nayi
sauri na sali6e takalmana na riqe a hannu
don kada taji qara ta hanani fita,ina fita na
saka na doshi gidan da matar jiya tayi man
kwatance.
Tafiyar minti hud’u kachal ta sada ni da
gidan matar,tsayawa nayi gaban tafkeken
gate d’in gidan na qare masa kallo sannan
na qwanqwasa,wani figigin buzun mai gadi
ne ya leqo yana tambayar wanene, nace
masa gurin matar gidan nazo,ko tana ciki?
Yace”eh wa za’a she mashi”
“Oh ni y’asu,qarfi da yaji ya maida mace
namiji” nace masa yace Hauwa Damari,
*hawwa damary*
[10/6, 3:08 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN.*
3
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
Bayan kamar minti biyu da tafiyarsa sai
gashi ya dawo yace”yashe ka higa”
Nace”tou” na fiddo naira d’ari biyu daga
cikin jakkata na miqa masa,yay ta faman
zuba godiya,kai gaskiya bacin naga alamar
buzu ne da wallahi ba abunda zai hana
nace bakano ne.
Gaskiya gidan ya matuqar burgeni sai
faman kalle-kalle nake kamar wata
bakanuwa a birnin zazzau, ban ga abun
kallo ba saida na shiga daga cikin parlour
da sallamata,
Da fara’arta ta taso ta tarbe ni,yauma taci
ado kamar kullum saidai na yau har yaso ya
zartar da sauran lokutan da nake ganinta,
Hannuna ta riqe tana fad’in ae na d’auka
ma kin fasa zuwa” nace “ae ba yanda za’ae
naqi zuwa tunda har kau ni na furta hakan”
na qarashe maganar a dai-dai lokacin da
muka zauna saman kujera,ta shiga qwala
wa mai aikinta kira,kan kace me an cika
gabana da kayan tarbar baqo,
Ta kalleni da murmushi a fuskarta da
alama taji dad’in zuwannawa sannan
tace”tou Hauwa Damari bismillah”
Cikin d’an jin nauyi nace”wallahi
Alhmdullah saida na cika cikina na fito
gida”na qarashe da fara’a
Kafin ta kuma magana wayarta dake bisa
center table ta soma ruri,ta kai hannu ta
d’auka ta soma magana tana kashe murya
gami da wani langa6ewa sai ka rantse
wanda take wayar dashi yana ganinta ne,
hakan da na gani ne yasa na fahimci da
mijinta take don haka nima sai na d’auki
wayata na soma diba saqonnin mutane ta
cikin WhatsApp.
Bayan ta gama wayar kuma ta shiga
lalubar wata number,bayan an d’auka naji
tace”kuluwa don Allah idan kinje d’aukar su
miemiey ki had’a dasu daddy da daddare
zanzo gidanki na d’aukesu”
Banji me aka ce ba naji tayi dariya tace”ke
dai baki da dama wallahi,yanzu banda
lokacinki ina da abunyi”ta katse wayar, mai
aikinta ta kuma kira ta zayyana mata irin
abincin da take buqatar ayi,bayan ta gama
magana da ita ta juyo gareni tace”kiyi
haquri don Allah inata 6ata maki lokaci”
Nayi d’an murmushi nace”laaa!wallahi ba
komai”
Tace”tou bari na soma baki labarin”
Nace”don Allah d’an tsaya na shirya”
Tace”tou”
Na bud’e jakkata na fiddo littafina da biro
sannan nace”na shirya”
Tayi dariya sannan ta fara kamar haka…..
***********
Tsadadden agogon dake d’aure a
tsintsiyar hannunsa ya diba,qarfe 7 da rabi
na dara harma ta gota da minti d’aya,tsaki
yayi tare da maida dibansa ga abokannasa
yace”dallah malamai idan zaku tashi Muje
ku tashi lokaci na wucewa,idan kuma ba
zaku tashi ba ni zan wuce wallahi,dad’in
abunma nasan hanya”
Umar dake chen gefe guda yana danna
waya yay saurin cewa”kunji d’an iskan
ba,tou ka tashi ka tafi mana,ay mu ka hutar
da mu ma,ko ya kace aboki” ya kalli salim.
Dariya salim yayi sannan yace”wallahi kau
gaskiyark..”bai qarashe maganar dake
bakinsa ba wayarsa da ke gaban aljihun
rigarsa ta soma ruri,yace”yawwa ga salman
d’in nan yana kira nasan ya qaraso”bai jira
cewarsu ba ya kara a kunne,
Ta6e baki Marwan yayi ya juya masu baya
cike da jin haushinsu don shi da son ransa
ne baiqi a ce yanzu yana gaban
masoyiyarsa ba,marwansa mai kyau da iya
ado,ga tsafta gata da iya tattausan lafazi ba
don kada ace ya cika ta ba da sai yace duk
fad’in duniyar nan ba macen da ta kai
marwansa,haka zai iya bugun qirji a gaban
ko waye yace duk mazajen duniya ba Wanda
ya kaishi sa’ar mace kamila,mai addi’i na
boko da islama,ga girmama na
gaba,murmshi yayi gami da lumshe
idonsa,yana ji salim nayi wa salman tsiyar
ya dad’e yay banza da su..
*********
A 6angaren su Amarya tunda aka watse ya
rage daga ita sai qawayenta memxy
kuluwa,su suka Kama Mata suka gyara
babban gidan nata,sannan suka sake shiri
suka zauna zaman jiran angwaye, memzy
fad’i take”Allah kuluwa sakin baki zaki mu
wanke su don kinga Amaryar tamu ba
gajarabul bace”
Kuluwa tace”Ashe d’aya muke nima wallhi
tun d’azu nake wannan tunanin”
“Yawwa shiyasa nake sonki qawas” cewar
memxy,suka saka shewa tare da tafawa.
Marwa ta hararo su tace”kunsan Allah,duk
wacce ta wankan man ango sai na 6alla ta”
Suka kalli juna suka kuma kwashewa da
dariya kafin kuluwa tace”su ango anji
jiki,dad’in abunma muma mun kusa yin
auren,sai dai kiyi ma su o’e”ta qarashe tana
kallon memxy da gefen ido d’aya.
Memxy tayi tsaki tace”jaka kyadai ji dashi”
“Kanbu!aiko saikin fad’i man uban da
kikace ma jaka” ta qarashe tana qoqarin
qarasawa inda memxy take.
Cikin sauri memxy ke fad’in”haba Aunty
kuluwa,kema dai kinsan bazance maki jaka
ba,ni d’in banza”nan fa ake ga tsoro ga jan
fad’a.
Marwa tay saurin cewa”wallahi ku sauka
qasa kuyi wasanku kada ku 6alla man
kujera a banza,ku da har yanzu baku girma
ba,da kun had’u sai kun saida hali”
Memxy ta bud’e baki da niyyar maida
mata sukaji qarar shigowar motoci
*Hawwa damary*
[10/6, 3:10 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN.*
4
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
Da hanzarinsu suka tashi suka kuma y’an
gyare-gyaren jikinsu,suka feshe gurin da air
freshener ya had’e da sanyin AC dandanan
parlourn ya bada wani sanyayyen qamshi,
Salim ne ya soma kunno kai da sallama
sai uban gayyar ne ke biye da shi,salman
da umar ne a baya.
A ciki-ciki suka amsa sallamar tasu ba
tare da sun dibesu ba, salim da bai gani ya
qyale ya qare masu kallo sannan yace”yoo
ina y’anmatan amaryar ne,ko kuna nufin
kuce ku biyu ne kachal?”
Memxy ta d’ago ta zabga masa harara
dama chen ta lura shi d’an rainin wayau
ne,shiko kallonta yay yayi dariya dama
abunda yake so yaga tayi kenan,don
yarinyar ba qaramin burgeshi take ba,kuma
ya lura y’ar bala’i ce ga tsiwa..
Umar dai tunda ya qyalo masoyiyarsa
kuluwa ya koma kusa da ita ya zauna,dama
shine gwanin nata don yanzu ma baifi sati
ukku ya rage suma ayi bikinsu ba,su salman
ma zazzaunawa sukay daganan aka shiga
hira cike da barkwanci,salman da yafi
sauran malumta shine yayi ma ango da
amarya y’ar nasiha irin ta abokai daganan
ya rufe da addu’a lokacin qarfe tara saura,
Marwan da yaga basu da niyyar tafiya
yace”malamai yafa kamata ku tafi gida
hakanan,kunsan bai dace ace gwauron
mutum yana dad’ewa a waje ba”
“Allahu Akhbar! Asheikh marwan” cewar
salim” sai yanzu kenan kasan da hakan,da
kai da kake….” Yayi qwafa”bari dai abar
kaza cikin gashinta”
Umar yace”ae gara a figeta kowa yaji”
“Bar d’an iskan ma kada ya fige ae yasan
ba abun figewar ne”inji marwan
Salim yace” au haka kace ko?”
“Eh,haka nace”
Salman dai na daga gefe yana masu dariya
don shi dama chen ba ma’aboci son
magana bane don ma dai Allah ya had’a shi
da irinsu salim.
Marwa a ranta tace”oh!Ashe haka yaya
marwan yake barkwanci a cikin abokansa,ji
yanda yake ta faman annashuwa kamar
bashi bane dariya keyi ma wuya,koda yake
ai abokai daban haka y’an uwa daban,ko ni
idan cikin mutane ne ban fiye ganin
fara’arsa ba sai dai idan mun ke6e,amma
tunda har na gane haka na d’au alwashin
saka sa annashuwa a koda yaushe” kamar
daga sama ta tsinkayi muryar abokan nasa
suna fad’in zasu tafi sai sun dawo rad’in
suna,salim yay saurin cewa”sai dai kin rinqa
haquri da wannan mutumin a gurin ci,ba
qaramin rumbu bane a sati sai ya gama da
buhun shinkafa”ya qarashe maganar yana
d’an bubbuga kafad’ar marwan,duka y’an
gurin suka sa dariya,marwa ta d’ago suka
had’a ido da marwan sa faman mazurai
yake shi ala dole ga babba kada taga yana
dariya ta d’auka ko da gaske cinne da shi,
Ta sadda kanta qasa tana murmushi,ya
matso dab da ita ya riqe hannunta ya murza
da d’an qarfi yace”wa kike wa dariya?”
Ta d’an 6ata fuska kamar zatay kuka
tace”kai yaya da zafi fa”
Gira ya d’aga tare da kashe ido d’aya
yace”I know”
Umar yace”kai malam muje ka raka mu
sannan ka dawo”
Yace”tou kuyi gaba ba sai kun tasa ni ba
kamar wani yaronku”
Sukay dariya sannan suka miqa ma y’an
matan amarya 50k kud’insu na sayen
Baki,dama salim yace sai za’a tafi zai basu.
*Hawwa Damary*
[10/6, 3:14 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN.*
5
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
Suna fita umar ya d’auki kuluwansa
suka qara gaba,salman ma ya wuce don
shima nan cikin barhim d’inne gidan
iyayensa yake.
Nan memxy ta soma tsurewa ga dare yayi
sosai ga unguwar so silent baka jin komai
sai kukan karnuka,gashi ko kafin ta kai titi
na samu napep aiki ne ba d’an qarami ba,ga
tanata kiran number yayanta baya
picking,abu ne ya had’e mata goma da
ishirin,
“Ke shigo muje” a firgice ta juyo dafe da
qirji don ba qaramar razana tayi ba,ba kowa
bane sai salim”tou shi kuma yaushe yazo,ko
dai tunanin da take ne ya hana ta jin qarar
motarsa?ba shakka haka d’inne”
“Ke ki shigo mu tafi dare nayi” ya qara
mata magana,”lallaima mutuminnan wai ke
aiko ke saita shiga” duk maganar nan tana
yin su ne cikin ranta,ta d’ago ta kallesa cike
da tsiwa,taga yay murmushi ta gefe d’aya
sai yay mata kama da jaruminnan d’an
qasar Philippine(Enrique gil),
Fasa yin abunta tayi niyya tayi,tayi d’an
siririn tsaki sannan ta juyar da fuskarta,
“Lallaima yarinyarnan,” yace gami da
figar motarsa ya wuce,
Wani qululun baqinciki ne yazo ya tokare
Mata a qirji,sai ta soma datasanin qin binsa
da tayi,
Bayan kamar minti biyar da tafiyarsa a
lokacin tsoro ya qara lullu6eta,wata mota ce
ta dalle mata ido da fitilar mota,kafin mai
motar ya qaraso ta ranta ya qara 6aci da
mai motar sai da ya qaraso taga ba wani
bane fache salim, dama tasan tatsuniyar
gizo bata wuce ta qoqi,tunda taga irin
dallare idon,
Yana qarasowa yace”ke shigo muje kada ki
tsaya girman kai wani yazo ya kashe ki
cikin duhunnan”
Bata ce komai ba ta shiga qoqarin bud’e
baya ta shiga don itama a yanzu bata iya
bari ya kuma wucewa,
“Heeey!” Yay mata nuni da gaba da
bakinsa”i’m not ur driver”
Nan ma bata ce komai ba ta rufe bayan
ta bud’e gaba ta shiga,
Sunyi tafiya mai nisa ya rage sautin
kid’an dake tashi yace”ke ina mukayi?”
Tayi kamar bata ji shi ba saboda ta tsani
ke d’in da yake kiranta da shi,
A d’an hasale yace”da ke fa nake kika
qyale ni”
Itama a qule tace”malam ni fa ba sunana
ke ba,idan baka cewa maymuna sai ka bari”
Shima yace”nima ba sunana malam ba
idan baki cewa salim sai ki bari,ay ba’a dole
ko?” Ya qarashe yana kallonta don
jin,juyawa tayi ta kalli window,yay dariya
sannan yace”toh maymuna inane
unguwarku?”
Tace”g.r.a ring road near little angels
school”
Yace”Ashe ma duk kusa muke,mu muna a
kangiwa road ta bayan little angels,kullum
idan na fito strolling ta gaban gidanku ma
nake bi kenan,ina da aboki ta gurin wani
abbaty sambo”
“Tou fa!dama wannan yaron yasan yaya
abbaty” ta fad’a a ranta,haka yayta janta da
hira har suka iso, ta nuna masa gidan,yay
dariya yace”Ashe ke sister abbaty ce,no
wonder kike da tsiwa”
Tay murmushi tace”thanks” ta juya ta nufi
gida shima murmushin yayi daga bisani ya
tada motarsa ya nufi gida….
*********
ASALIN
MARWA DA MARWAN
Mahaifin Marwan Alhj Mansur Umar
Sambo da mahaifiyar Marwa Hjy Mariya
Umar Sambo, babansu d’aya haka ma
mamansu d’aya su kad’ai iyayensu suka
haifa,asalinsi y’an jahar katsina ne cikin
6atagarawa,
Sun taso cikin had’in kai da qaunar
junansu duk da kau shi mansur ya girmi
Mariya da shakaru bakwai,yanda yake sakar
mata fuska baisa ta rainashi ba sai ma
wata shaquwa ta y’an uwantaka da ta shiga
tsakanimsu..
*hawwa damary*
[10/6, 3:16 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN.*
6
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
Bayan an aurar da Mariya shima ya had’a
kayansa ya nufi America qaro karatu a
cewarsa gidan tunda ba Mariya ba zai dad’i
ba,kafin dawowarsa ne Allah yay ma
iyayensu rasuwa a hanyarsu zuwa Cairo
ganin likita kamar yanda suka saba duk
bayan wata shidda sukanje medical
checkup.
Wani babban d’an kasuwa Hjy Mariya ta
aura duk garin ba Wanda bai sanshi ba da
zarar kace Alhj Salmabu mai daloli ba,wasu
sukan kirasa da mai daloli kawai,saida suka
shafe shekara sha d’aya Allah bai basu
haihuwa ba,duk asibitin da suka je sai ace
matsalar daga mai daloli take,wannan yasa
yaba hjy Mariya shawarar taje ta auri wani
kada ya d’auki alhakinta tace ita zama
dashi daram mutu ka raba, a cikin lokacin
har mansur ya qare karatunsa na shekara
hud’u ya dawo gida ya samu mata nan
maqobtansu mai suna Asma’u ya aura,da
shekara ta zagayo ta haifo d’anta namiji
mai kama da babansa sai dai duhun
mamansa ya biyo,da ran suna ta zagayo
aka saka masa MARWAN.
Marwan nada shekara tara a duniya Allah
Ya ba Hjy Mariya ciki anyi murna
sosae,shekara na zagayowa ta haifi d’iyarta
mai kama da ita komai da komai,tunda ta
isa duniya Marwan yake zuwa
d’aukarta,kullum sai dare drivrnsa ke d’auko
sa wani lokacinma a chen yake kwana,ana
gobe suna ya dami ummansa(Hjy Mariya)da
yake sunan da yake kiranta dashi kenan,shi
lallai sai dai a sanya ma baby MARWA,
umman tasa da yake y’ar taya 6era 6ari
ce,Mai daloli na shigowa tace ga sunan da
take so,yace,shikau yay mata Alqawarin
sunan zai sanya mata.
Washegari suna kau yarinya taci suna
MARWA, anyi shagulgula iri-iri sai ka rantse
bikin wata y’ar gwamnan akeyi sai an fad’a
maka suna ne zaka cika da mamaki,
Kullum da zarar an d’auko su Marwan
daga schl zaice ma sani driver ya fara ajje
shi gurin ummansa sai ya wuce dasu firdau
gida,(mai karatu fitdausi wacce ake kira
firdau qanwa ce ga marwan ya girmeta da
shekara ukku sai ita kuma ta girmi y’an
tagwayen Hajiyarsu da shekaru
biyu,hassana da usaina)
Lokacin da Marwa ta shiga shekara ta
shidda a duniya shi kuma Marwan ya
kammala karatunsa na secondary yana da
shekara sha bakwai,Alhjinsa ya nema masa
gurbin karatu a America,ranar da zai tafi shi
kuka Marwa kuka duk da qarancin
shekarunta a lokacin,
Shekaru sukayta tafiya,sai da Marwan ya
shafe shekaru goma sha biyu bai dawo gida
ba,don harya fara aiki a chen,sai dai kullum
suna waya da kowa kuma yana jin duk halin
da suke ciki,Marwansa kau musamman ya
aika mata da waya don su rinqa
gaisawa,aiko tun daga sannan ko abinci
zata ci sai ta kira shi shima haka, wasa-
wasa suka saba da juna,akai-akai sukan yi
family picture’s su tura masa shima
haka,shi da Marwa ko kullum cikin tura pics
suke duk inda yaje zai yi ya tura mata itama
haka,sai shaquwa ya juye ya koma soyayya
tsantsa,duk wani dake tare dasu ya san sun
shaqu sosae,daga 6angaren Aminansa na
America har 6angaren qawayenta itama.
A cikin shekara ta sha biyunne Alhjnsa ya
matsa sai ya dawo gida,ba yanda ya iya
dole ya fara shirin komawa nan da sati ukku
dama abokanansa tuni sun koma,sai dai
yaci alwashin da zaran ya koma zai sanar
da Alhjnsa komai na game da tsakaninsa da
Marwa don har kawo yanzu iyayensu basu
sani ba,
Tunda Marwa taji yayannata zai dawo ta
soma murna,kusan ma tafi kowa farin ciki,
cardboard paper ta siyo tayi calendar ta liqa
saman gadonta da ta tashi daga bacci sai
tayi cancelling a haka har ya rage sati
d’aya,oasis bakery taje tace ayi mata cake
babba a rubuta welcome back bro ko nawa
ne zata biya,taje heart to heart ta sayi
had’add’un cards masu kyau da tsada sai
ta sayi wrapping paper’s da qatuwar gift
bag, bayan ta bar nan kai tsaye jifatu ta
nufa,jallabiyoyi ta dingi jida dama ita sune
kayan sawarta kasancewarta d’aliba a Al-
qalam University Katsina tana karantar
English Language,
Bayan ta gama sayayyar ne taci karo da
firdau ta kawo Hassana da Usaina suma
sunzo shopping,suna ganinta Hassana
tace”tou shanshani sarkin yawo,mun biya
maki umma tace kina nan,dama Alhj ne ya
bada kud’i yace kowa ya sayi abunda yake
so da kuma abunda zai ba yaya Marwan
gift”
Tay murmushi kawai ta bisu tana so tace
masu ta saya kuma tana tsoron suyo mata
chaa da zolaya kasancewarsu abokan
wasanta da yake y’an mace da y’an namiji
suke,basu suka gama sayayyar ba sai
yamma..
*hawwa damari*
[10/6, 3:19 PM] Memxyy: *MARWA DA
MARWAN.*
7
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicate to *Memxiey_fulla *
A 6angaren Marwan ma hakance ta
faru,tunda ya sami visa yaga ya rage saura
sati biyu ya tafi ya soma shirye-shirye da
saye-sayen kayan tsaraba,komai ya gani
idan har ya burgeshi sai ya d’aukar ma
qannensa su hud’u,Firdau,Hassana,Usaina
sai Marwansa.
Ranar daya rage saura kwana biyu ya
koma tunda ya tafi office yay sallama da
kowa,turawan kowa jikinsa yay sanyi sunyi
matuqar sabawa dashi,dukansu har y’ar
dinna sukay Alqawarin had’a masa a gidan
ogansu da daddare ana gobe zai tafi,yay
murna sosae don karamcin da suka nuna
masa,
Bayan ya bar office shopping ya tafi,bai
dawo ba sai yamma,
Washegari ya gama shirinsa ya had’a
komai da komai nasa don tunda asuba zai
tafi,gurin maqobtansa ya rinqa shiga yana
yi masu sallama,kowa jikinsa yay
sanyi,lokacin da ya dawo yamma tayi kai
tsaye wanka ya fad’a,bayan ya fito ya
gabatar da sallar magrib yayta azkhar har
aka lokacin lisha yayi ya gabatar da ita ma
sannan ya soma shirin zuwa dinner da
ogansu ya shirya masa,
Tun daga bakin qofar gidan yaga an
rubuta”we wl surely gonna mss u
blacky”(sunan da suke kiransa) yay
murmushi sannan ya shiga,yayi mamakin
ganin duka coworkers d’insa duk sun iso,yay
murna sosae ya biyu d’aya bayan d’aya yay
hugging d’insu,yazo kan ogansu wasu
zafafan qawalla suka zubo masa,ogannasu
ya dafa kafad’arsa yace”c’mon don’t cry,be
a man okay? ”
Ya gyad’a masa kai sannan yace”thanks
alot”
“For what?”
“For everything u have done to me,i’m
really grateful”ya qarashe maganar yana
qaqalo murmushin yaqe
Wani Johnny Wanda suka fi shiri dashi shi
yazo ya riqe masa hannu ya zaunar bisa
table daga nan suka soma cin abinda ke
gurin,anayi ana raha kowa na fad’in farkon
had’uwarsa da blacky, haka suka watse cike
da kewarsa.
Qarfe sha d’aya da rabi agogon Nigeria
ya buga kuma a dai-dai lokacin jirginsu
Marwan yay dirar mikiya a filin jirgin Malam
Aminu Kano dake cikin jahar kano,
A hankali mutanen dake ciki suka soma
sakkowa kowanne d’auke da annuri a
fuskarsa,Marwan shine na biyar d’in
sakkowa yana gama sakkowa ya hango
Alhjinsa da Abbansa Mai daloli sunata
faman d’aga masa hannu don ya gansu,da
hanzarinsa ya qarasa inda suke ya
rungumesu d’aya bayan d’aya,ba qaramin
dad’i Alhj Mansur yaji ba ganin d’iyan nasa
cikin qoshin lafiya,ya qara zama babban
mutum yayi kyau duk da kasamcewarsa
baqar fata amma irin baqinsa mai kyau
ne,ga y’ar qibar daya yi sai tayi masa kyau
sosae,sanye yake da qananun kaya
kasancewar inda ya fito ba manyan kaya ne
dasu ba,
Bayan sun gama gaisawa da kwashe
kayansa kai tsaye restaurant d’in cikin
airport d’in suka nufa suka cika cikinsu
sannan suka gabatar da sallar azahar sai
suka doshi hanyar jahar Katsina, a mota sai
faman qorafin ba’a zo masa da Ummansa
da Hajiyansa ba, Mai daloli yay dariya
yace”tou kai in banda abunka ae gurinsu
zamu je”
Yace”eh nidai Abba duk da haka da anzo
man dasu na gansu”
Alhj yace”kai dai kana ji da iyayennan
naka,ae da mun sani ma su muka bari suka
zo d’aukar taka,ko ba haka ba Mai daloli”
Abba yay dariya yace”haka ne kam” haka
suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha’awa.
A gida Marwa tun safe ta kira
qawayenta tace suzo su taya ta yi ma yaya
Marwan abincin tarba,
[8/30, 9:13 PM] damary9001: Ba’a d’au
lokaci ba Suka iso, Maimuna wacce
yawancin mutane ke kira Memxy d’iyar
Aminin Mai daloli ce kusan a tare aka
haifesu da Marwa,kuma unguwarsu d’aya
haka tare sukayi karatu tun daga yarintarsu
har kawo yanzu,yayanta d’aya Abbaty
Sambo sai Hauwa Muhammad Rimi wacce
ake kira Kuluwa itama d’iyar aminin Mai
daloli ce itama tsarar su Marwa ce kuma
itama tare sukay karatu sai dai ita gidansu
suna da yawa, su ukkun duk tare suke
sunsan sirrin junansu kaf,don da suna Ulul-
Albab yawancin mutane sun d’auka y’an
uwa ne saboda ko visiting za’a zo masu a
tare ake zuwa masu.
Tun kafin kace me gida ya d’auki
qamshi,abinci suka had’a kala-kala da zarar
Umma ta shigo zasu ce su dai ta barsu su
kad’ai zasu yi,ko su riqo hannunta su kaita
parlour su zaunar su kunna mata kallo,ita
ko sai faman binsu da murmushi take,a
ranta Addu’a take Allah Yasa ma MARWA
DA MARWAN son junansu har su kaiga aure
don a iya tunaninta ba wanda Marwa zata
aura ya riqe ta da Amana kamar Marwan
haka shima ba wacce take ganin zai aura
tayi tattalinsa kamar Marwa,haka tayi ta
tunaninta ita kad’ai daga qarshe da taga
zaman kad’aicin ya isheta ta kira mijinnata
tace tana so taje gidan yayan nata don a
tarbi d’an nata da ita, yay dariya sannan
yace”wannan d’a dai ana ji dashi,kije ba
damuwa ae muma mun kusa charanchi”
Tace”tou nagode nawan Allah yabarmu
tare”
Yace”Amin gimbiyata”
Bayan sun gama ta shirya ta leqa gurin
yaran tace idan sun gama komai sun shirya
su kwaso komai suzo suzo gidan Alhj, suka
ce”tou”
A chen ma gidan Hajiyan tana zuwa ta
tadda Hajiyan zaune parlour ita kad’ai tana
kallo,tace”ah!Ina yaran suka tafi ne?”
Tace”inafa,suna kitchen suna shirya ma
yayan nasu Abinci sunce kada naje su
kad’ai zasuy”
Umma tay dariya tace”munyi Anko kenan
toh ae sai mu tsaya nan muy kallo mu jira
isowar d’annamu”
Daganan suka cigaba da kallonsu sunayi
suna hira jefi-jefi..
Marwa da Marwan 8to11
Leave a reply
[10/11, 4:19 PM] Hawwadamary :
*MARWA DA MARWAN.*
8
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicate to *Memxiey_fulla *
Sosae yayi mamakin ganin yanda aka
gyara gidan nasu kamar gidan wani
gwamna,ga wasu fulawowi masu kyau
wad’anda Suka qara qawata harabar gidan.
Tunda motar tasu ta tsaya yaran suka
firfito da gudu suna masa oyoyo,binsu kawai
yake da murmushi don ba qaramin girma
yaga sun qarayi masa ba,duk da daman a
hoto yake yawan ganinsu,oh yanzu ko ya
Marwansa ta koma?
Bayan an shiga parlour an zazzaune suka
gaggaisa sai suka shiga hirar yaushe
gamo,shiko uban gayyar sai zuba ido yake
yaga ta inda Marwa zata fito Amma shiru
kake ji ba amo ba labari.
Umman tasa ce ta lura da yanayin nasa
ta d’auki waya ta kira Marwa tace me take
yi ne har yanzu bata qaraso ba,tace tana
hanya yanzu zata iso bada dad’ewa ba,
Marwan najin haka ya miqe yace zai d’an
watsa ruwa,Hajiya tace”au,ni inace sai ka
fara cin Abinci sannan”
Yace”no Hajiya zanfi jin dad’i idan na fara
watsa ruwan,kuma na kira su salim sunce
gasu nan qarasowa,nasan idan suka qaraso
zaiyi man wuya nayi wankan”
Tace”tou ay shikenan”.
Kai tsaye d’akinsa ya shiga duk an chanza
komai kamar ba d’akin nasa ba, akwati ya
bud’e ya d’auki towel ya d’aura sannan ya
nufi toilet domin yin wanka,
Bayan ya fito ne yaga an ajje masa
manyan kaya a bisa gado yay murmushi
yasan ba aikin kowa bane sai Alhjinsa
saboda shi bai cika son ganin babban
mutum ya saka qananan kaya ba,a cewarsa
basu masa kyau,jikin nasa ya fara feshewa
da body spray sannan ya murza mai ya
d’auki shaddar dake visa gadon ya sanya
ya ya fesa turare sannan ya d’auki wayarsa
ya fita.
Ba qaramin mamaki yayi ba ganin Aminan
nasa har sun iso duk sun zauna bisa table
tare da iyayen nasa,shi kad’ai ne ake
jira,yana qarasawa ya miqa masu hannu
suka gaggaisa tare da murnar sake ganin
juna cikin qoshin lafiya.
Salim,Salman da Umar Abokanansa ne
tun suna karatu a America sai dai su tunda
suka qare karatun suka dawo gida
sakamakon shi da saida ya fara aiki a
Asibitin chen qasar.
Salman d’and’an babban malamin garinne
tunda suka dawo yaqi aikin gwamnati ya
kama kasuwancin saida kayan mota,komai
kake so da ya danganci mota idan har kaje
kamfaninsa ka samu ka gama,har fenti suna
yi ma mota,kuma suna sayen tsohuwa,
Salim mahaifinsa babban d’an kasuwa ne
dake kasuwancinsa tsakanin qasashen
duniya,ya jima da rasuwa a hanyarsa ta
dawowa gida daga Morocco sukay had’arin
jirgi,salim shi kad’ai ne d’ansa a duniya sai
ko mahaifiyar salim d’in, sai ya kasance
tunda mahaifinnasa ya rasu yawancin
dukiyarsa ta dawo hannunsa daganan ya
yanke shawarar bud’e super market’s kuma
yakan d’an ta6a aikin asibiti,
Sai Umar wanda shi mahaifinsa d’an
siyasa ne har gwamnan garin nasu
yayi,tunda ya dawo gida ya soma aiki a
Federal Medical Center dake cikin jahar tasu
ta Katsina,don shi dama burin nasa bai
wuce yayi Aikin gwamnati ba,
Dukansu su hud’un Kansu a had’e yake
tunda suka isa qasar ta America, a gidan
mahaifin Marwan suke zaune har Allah Yasa
suka qare karatun suka yo gida suka bar
Marwan d’in a chen..
*Hawwa Damary*
[10/11, 4:19 PM] Hawwadamary :
*MARWA DA MARWAN.*
9
*~By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicate to *Memxiey_fulla *
Shima zaunawa yay kusa da su suka
shiga hirar yaushe gamo,Marwa wacce
tunda ya shigo take satar kallonsa Amma
shi hankalinsa baya gurin da alama ma bai
lura da ita ba,gani tay idan ba tayi magana
ba hankalin nasa baxai yo kanta ba yanda
suke ta zuba hira da abokansa, daurewa
tayi ta gaishe shi,ya juyo ya Amsa mata da
fara’a a ransa ko mamakin kyaun da ta
qara yake sai yaga a hoto ma baiga komai
ba,murmushi ya qara yace”gaskiya yarannan
kun girma sosae,yanzu Marwa ce ta zama
haka? Kamar ba ita bace lokacin da na tafi
ko rarrafe bata yi ba”
Firdau tace”haba yaya wane irin bata
rarrafe,lokacin daka tafi fa tayi wayau har ta
fara zuwa school”
Yace”oh,kinga na manta ni,tou gaskiya na
manta” ya kai dibansa ga Hassana da
Usaina wad’anna keta faman cin Abinci ba
ruwansu, yace”Gaskiya Hjy y’an biyun nan
naki sun fiye cin tsiya,shiyasa gasu nan
tubarkallah,idan ba Wanda ya sani ba sai
yace sun girmi firdau”
Hajiya tace”ba abunda ya shafeka ae
saida lafiya ake ci,saboda haka a daina sa
ma y’an biyu na ido”
Duka gurin suka sa dariya harda su Alhj,
haka suka cigaba da cin Abincin cikin
raha,bayan an qare ne kowa ya shiga miqa
masa gift d’insa,Alhjinsa,Mai daloli,Umma
da Hajiya ginin gida suke yi masa,sai salim
daya bashi mota Mercedes Benz,shi kuma
salman ya d’akko masa Akwati cike da
Manyan kaya masu tsad”a ya miqa masa
yace a kwashe na turawa a kyautar,umar
kuma dangin su hula,agogo da takalma ya
bashi masu uban yawa,sai qannen nasa
kowa da tashi, saboda farin ciki kasa
magana yayi sai hawaye, sai magrib kowa
ya tafi gida,Mai daloli ma da iyalansa suka
tafi, koda ya koma d’aki gift d’in da Marwa
ta bashi ya d’auko ya shiga bubbud’ewa a
ransa yana jin qara qaunarta,
Bayan dawowarsa da sati biyu ne
Alhjinsa ya kirasa yake tambayarsa batun
Aiki, yace,shi gaskiyar magana baya
sha’awar yin Aiki a Nigeria,da shi shawarar
da yake zai bud’e kamfanin saida motoci ya
rinqa shigowa dasu daga America,
Alhjin nasa yace”banqi ta taka ba,Amma
inaso ka sani sana’ar saida motoci yana
buqatar kud’i sosae”
Yace”Alhj ay wannan ba matsala bace
inada 3billion da y’an kai a account d’ina ko
dasu ne sai na siyo y’an madaidaita kafin
Allah Ya bud’a”
“Tou shikenan,sai ka d’auki 1billion a
Account d’ina ka qara idan naga ina da
wadatattun kud’i zan sayi fili nasa a soma
ginin kamfanin”
Yace”Nagode Allah Ya qara girma da
d’aukaka”
Yace”Ameen don rabbil izzati,sai kaje ka
samu Mahaifiyar taka ka shaida mata yanda
mukayi kasan sha’ani na mata tana iya
cewa ba’a sanar da ita ba”
Yay dariya yace”zanje insha Allah,yau ma
tace ni zanje d’auko ta gurin Aiki”
“Tou Madallah,ae saika hanzarta naga
qarfe shiddan ta kusa yi”
“Tou Alhaji” ya fad’a cikin ladabi sannan
ya fita.
Abunka da masu abun,ba’ayi wata da
maganar ba aka gama ginin kamfanin,komai
yayi tsari kamar a qasar waje,cikin sa’a ya
shigo da motoci masu masifar kyau,y’an
ubansu wad’anda sai wane da wane zasu
iya hawa,
An saka ranar asabar da lahadi za’ayi
saukar qur’ani a gurin Wanda harda Marwan
da Abokansa za’ae,sai kuma ranar litinin ayi
taron bud’e kamfanin mai suna MARWAN
MOTORS COMPANY NIG L.T.
Ranar da suka gama sauka ta qarshe da
daddare ya shirya domin ya kai ma
Ummansa ziyara don tunda aka soma
hidimar gini bai samu ya leqa ba sai dai
sukanyi waya akai-akai.
Shirinsa ya gama cikin wani yadi brown
mai tsada duk cikin kayan Salman ne ya
d’auko hula wacce tayi shige da yadin nasa
ya sanya sai ya d’aura agogo ya qara fesa
turare sannan ya d’auki key d’in motar da
Salim ya basa, ba qaramin so yake yi ma
motar ba dama duk kayan da aka basa.
Horn d’aya yayi Iro mai gadi ya
leqo,ganin ko waye yasa yay hanzarin
fitowa ya bud’e masa yana fad’in”barka da
zuwa ‘yalla6ai”
A taqaice ya qamsa gami da zaro dubu
biyu ya miqa masa,yayta zuba godiya.
*Hawwa Damary*
[10/11, 4:19 PM] Hawwadamary :
*MARWA DA MARWAN.*
10
~*By Hauwadamary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
A harabar gidan yaci karo da Mai daloli
yana qoqarin shiga mota,cikin Azama ya
qarasa inda yake ya duqa har qasa ya
gaishe shi, ya Amsa gami da tambayarsa
y’an gidan,yace”suna nan lafiya sunce a
gaishe ku”
Yace “tou Madallah,ae chen gidan na nufa
yanzu shi Alhajin yayo man waya yace yana
son ganina nasan bai wuce maganar
kamfaninka,gobe ne za’ayi taron bud’ewar
ko?”
Yace”eh,da qarfe goma na safe Insha
Allah”
“Allah ya nuna mana”
Yace”Ameen”daganan ya qarasa
ciki,Marwa ce kad’ai a parlour kwance tana
kallo a system d’inta,jin sallamarsa yasa
tayi saurin tashi tsaye tace”laaa yaya dama
kana tafe shine baka fad’a man ba”
Yace “dama so nake nayi maki zuwan
bazata,kuma da alama kin razana”
Tay dariya tace “sosae ma” daganan ta
gaishe shi,yace”naqi na Amsa tunda baki
murna da ganina ba”
“Wallahi yaya nayi murna da ganinka
sosae ma”
Yad’an duqo ya d’aga mata gira yace”da
gaske?”
Tayi murmushi tace”da gaske mana”
“Tou na yarda,ina Ummana take?” Ya
tambayeta yana d’an waige-waige,
Tace”yamzu ba dad’ewa ta hau sama
tace kanta ke ciwo zata d’an kwanta Amma
bari na tado ta”
Yay saurin cewa”a’a,ba sai kin tado ta
ba,zan jirata har ta tashi, ita kuma y’ar
umman ta taya ni hira ko?” Ya qarashe
maganarsa yana kallonta, bata ce komai ba
ta sadda kai qasa tana murmushi,
Yace”yawwa bani labarin qawayennan
naki figaggunnan wad’anda na ganku
rannan a gida”
Tace”memxy da kuluwa?”
Yace”ni ya za’ay na San sunansu,
wad’annan dai masu shegen surutun,har
gara ma mai y’ar qibar naga ita tana da
d’an hankali”
“Kuluwa kenan,Amma yaya ai itama
memxyn tana da hankalin”
Yay dariya yace”dama haka zaki ce,wai
me kukayi ne a gidan ni yunwa nake ji,gashi
ko ruwa ma baki kawo man ba”
Tace”ayi man haquri bari naje na kawo
sai na zubo maka abincin daga nan”ta miqe
Har tayi nisa ya kirata,ta juyo yace”menene
kuka dafa?”
Tace”jallof cous-cous ne sai pepper
chicken”
“No,bani son cous-cous dora man
spaghetti sai ki had’o man da pepper
chicken d’in”
Tace”tou”daganan ta miqe ta nufi kitchen
shi kuma ya kwanta bisa 3seater ya d’auki
system d’in tata ya cigaba da kallon,
Baifi minti goma ba yana kallon,memxy
da kuluwa suka shigo da hayaniya suna
qwala ma Marwa kira tazo ta raba masu
wata gaddama wai da Enrique Gil da yaron
da yay The promise (pangako sa’yo) wa
yafi kyau,ita memxy tace Enrique yafi kyau
ita kuma kuluwa tace Angelo yafi,shine suka
nufo gurin Marwa ta raba gaddama,
‘Dakin Marwan suka nufa ba tare da sun
lura da wata halitta dake zaune a gurin ba
*Hawwa Damary*
[10/11, 4:19 PM] Hawwadamary :
*MARWA DA MARWA*.
11
*~By Hauwa Damari*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla *
Sun Shiga d’akin nata basu iske ta a
ciki ba don haka suka qara kwaso
gaddamarsu suka nufo parlour, dukkansu
turus sukayi lokacin da sukay ido hud’u da
Marwan ya had’e girar sama da ta
qasa,kuluwa ce ta fara yin hankalin gaishe
shi sai memxyn ya Amsa fuskarsa ba yabo
ba fallasa a dai-dai lokacin umma ta sakko
tana fad’in”hayaniyar me nake ji ne tun
d’azu haka?”
Memxy tay karaf tace”Umma kuluwa ce
wllhy”
Kuluwa ta zabga mata harara tace”eh
lallai ma,ni da ke waye ya fara gaddamar”
“Tab,aje a tambayi mami(maman
kuluwa) ae a gabanta aka fara” memxy ta
fad’a tana hararar kuluwan itama da gefen
ido
Umma tace”duk wannan bata taso
ba,yanzu dai ku wuce gurin y’ar uwar taku
ta gaddama sai kuy tayi,daganan Ku turo
man ita”
Sukace sun diba basu ganta ba,tace su diba
kitchen,suka d’ugunzuma sukayi kitchen
d’in.
Girgiza kai kawae umma tayi kafin ta
fuskanci Marwan tace”tun dazu ka shigo
ne?”
Ya d’an sosa kai yace”eh to,ban wani
dad’e sosae ba,Marwa tace man kin d’an
kwanta ne baki jin dad’i”
Ta d’anyi tsaki tana shirin zama
tace”wallahi wani matsanancin ciwon Kaine
nake fama da shi nafi 2yrs,idan na fara
kaina kamar zai tsage”
“Innalillahi,gaskia ciwon kai baya da dad’i
ko kad’an,tou akwai maganin da kike sha
ne?
Tace”i toh da dai panadol extra nake
sha…” Ya katseta”haba umma kawai baki je
asibiti sun diba ki ba sai ki rinqa shan
qwaya,qila ma wannan baiyi dai-dai da
ciwon kan da ke damunki ba,zan turo maki
Dr Umar ya diba ki idan Allah ya kaimu gobe
da safe,amma don Allah umma ku daina
shan wannan maganin”
Tay murmushi”to insha Allah” daganan
Marwan ya gaisheta ta amsa tare da
tambayarsa y’an gida,suna cikin haka
Marwa ta shigo hannunta d’auke da tray ta
zo ta dire a gabansa ta juyo gurin
qawayenta,Sam ba haka Marwan yaso
ba,shi idan da ason samunsa ne ta zauna
yana ci suna hira,Amma ba yanda ya iya
dole ya haqura.
Sai gab da magrib prayer ya baro
gidan,kai tsaye gidansu ya nufa,tun data
harabar gidan ya soma karo da motar Mai
daloli,saboda haka sai kawai ya nufi
parloun,bayan ya zauna ya qara gaishe
su,Alhajinsa yace”dama yanzu maganar ka
muke sai kuma gaka ka iso” ya gyara zama
sannan ya cigaba”dama ba wani Abu bane
ni da Mai daloli munyi magana ne akan
tarewarka sabon gidanka munga gaskia ya
dace ace tare da abokiyar zama ya kamata
ka tare,don yanda tarbiya tayi qaranci a
zamanin nan,saboda haka idan kana da
wacce tayi maka yanzu sai ka Sanar da mu
a san abunyi”
Yay qasa da kai yana d’an murmushi cike
da jin kunya, shi yanzu ta yaya zai iya
Sanar da su marwa ce za6in ransa,kai
gaskia abun da kamar wuya,dama Alhajinsa
ne kad’ai da da sauqi…
Shirun da yayi ne yasa Mai daloli fad’in”kai
fa muke saurare”
“Um…dam..a um Marwa c…”
Tun kafin ya qarasa yaji Alhajinsa ya sama
fad’in”Alhamdullh,kaga abunda nake fad’a
maka ko”ya kalli mai daloli yana dariya irin
tasu ta manya,shima Mai dalolin dariyar
yake, A nan take suka shirya komai aka
tsayar da rana sati ukku masu zuwa,Alhajin
Marwan yace sai anji ta bakin ita yarinyar
kada ayi mata dole,Mai daloli yace,ay aure
kamar anyi an gama ne,ba wata maganar
tambayarta, tou da haka suka tashi a ranar
kowa da farin ciki,musamman ma Marwan
da yake ji kamar anyi masa kyautar rai.
Ko da sauran Y’an uwa suka ji ba qaramin
farin ciki sukayi ba kar ma dai umma taji,kai
tsaye shirye-shirye suka fara ba kama
hannun yaro kasancewar an saka qurarren
lokaci.
An sake gyara gidan da Amarya zata
zauna anyi jere na ubansun kaya daga sama
har qasa kasancewar mai bene,
Ana saura sati d’aya biki aka kawo lefe na
gani na fad’a ga mota irin wacce y’ay’an
masu hannu da shuni ke yayi a wannan
zamanin..
*Hawwa Damary*e a reply
[10/6, 12:39 PM] Hawwadamary : MARWA
DA MARWAN.
12
~By Hawwa Damary
(NWA)
A wannan hidimar shirye-shiryen ta biki ce
Allah ya had’a jinin Dr Umar da kuluwa,cikin
qaramin lokaci magana tayi qarfi da yake
Umar d’in yace ba da wasa yazo ba,an
sanya bikin su wata biyu bayan na su
Marwan.
Memxy baki har kunne qawayenta zasuy
aure ta samu gurin zuwa,har lissafi take yau
idan taje gidan Marwa gobe sai taje gidan
Kuluwa,ko kuma idan ta shafe sati tana
zuwa gidan wannan d’ayar ma haka,su duka
sukanyi dariya suce,ke kuma da yake
zamanki kenan ba zaki aure ba.
Musamman Umma ta aika nijar aka
d’auko mata Hafsat mai Amare domin
gyaran amarya,tun ranar da ta zo ta shiga
gyaran amarya aka kulle ta a d’aki ko parlor
ba’a barinta fita sai dai a shigo
gurinta,shima d’in daga qawayenta sai
Umma da ita Hafsat d’in,ko da wani Abu
take so sai dai tayi waya a kawo mata,
wannan abu ba qaramin takura ma Marwan
yayi ba,don shi baiqi ace kullum yana
manne da Amaryarsa ba.
Biki ya rage saura kwana biyu a d’aura
aure,tun daren jiya Marwan ya kasa sukuni
burinsa kawae yaga yayi tozali da abar
qaunarsa don haka tunda ya dawo masallaci
sallar Asuba bai koma ba yay shirinsa ya
bar gidan,kai tsaye gidan su Marwa ya
nufa,mai gadi na ganinsa ya bud’e masa
gate yana gaishe shi,hannu kawae ya d’aga
masa don gani yayi idan ya tsaya yi masa
magana mutanan gidan na iya jiyo sa,
Da sand’o ya nufi d’akin Marwa a lokacin
tana zaune bakin gado idar da sallarta
kenan ta d’auko waya da niyyar kiransa sai
ganin mutum tayi ya turo qofa,ba qaramin
razana tayi ba sauqin ta ma Hafsat ta shiga
toilet amma duk da haka sai da ta kai
dibanta hanyar qofar toilet d’in.
Sororo yayi yana kallonta ta chanza
masa kamanni gabaki d’aya kamar ba ita ba
har wani yellow yellow take yi ga sheqi tana
yi tayi bul-bul kamar ka ta6a jini ya
fito,gaskia ba don a d’akinta ya ganta ba da
bazai iya ganeta ba don gabaki d’aya
kamanninta ya chnaza.
Ganin baya da niyyar magana kuma ta
tabbata Hafsat gab take da fitowa yasa tay
saurin gaishe da shi,
Ya had’e fuska yace”naqi na Amsa,haka
ake gaisar da miji a garinku”ya qarashe
maganarsa yana qoqarin zama a bakin
gado,ta zaro ido tace”yaya don Allah ka rufa
man asiri ka tashi kada azo a ganmu”
“Laifi nayi don nazo ganin matata,nifa na
gaji da 6oyonki da akeyi don wallahi ba
qaramar wahala nake sha ba,saboda haka
zo nan ki zauna kallonki nazo yi” ya nuna
mata kusa da shi.
Murmushi tayi ta zo ta zauna,ya tsura
mata ido kamar zai lashe ta,wata
matsananciyar kunya taji ta kamata,sunfi
qarfin minti biyu a haka,sauri tayi ta miqe
don tunowa da tayi da Hafsa, ta marairaice
fuska kamar zatay kuka tace “pls mana
yaya kar a ganmu,kaje zamuyi waya”
Yace”tou shikenan my princess zan dai
tafi ba don na gaji da ganinki ba my
beautiful durling, I love u” ya sakar mata
sumba a goshi.
Tay murmushi kawai cike da jin kunya. Ya
dafe kai yace”gaskia dole ne nayi maganin
wannan kunyar don da alama ni zata cuta”
Ta qara yin murmushi,har bakin qofa ta
raka shi ta dawo,tana zama hafsat ta fito ta
sauke ajiyar zuciya,
Hafsat tace”naji kamar kina magana ko
Hajiya ce ta shigo?”
Tace”a’a Abba ne ya zai fita shine ya biyo
ya bani saqo”hakanan ta samu kanta da
shafto qarya,
“Nifa ince sai naji kamar muryar namiji”
“Un” kawai ta iya ce mata saboda ta lura
idan ta cigaba da biye ma Hafsat to lallai
sai ta karto ta.
Washegari y’anmatan Amarya sukay
kamu a nan harabar gida su Memzy,kamun
da ya Tara y’ay’an manyan Attajiran
katsina da kewayenta,wad’anda duk
yawanci tare sukay makaranta a Ulul-Albab.
Ranar Asabar da misalin qarfe biyu na
rana aka d’aura auren MARWAN MANSUR
SAMBO da amaryarsa MARWA SALMANU
MAI DALOLI akan sadaki dubu hamsin
lakadan ba ajalan ba,mutane fiye da dubu
ne suka shaida haka,
A dai-dai lokacin Marwa ta kulle kanta a
d’aki tayi nafila raka’a biyu ta shiga zuba
addu’o’i da fatan Allah ya basu zaman lpia
da zuri’a d’ayyiba, tana cikin haka ne taji
gud’a ta karad’e ko ina a gidan sai kawai ta
fashe da kuka shikenan ita yanzu ta zama
qarqashin inuwar wani ba iyayenta ba,
Nan abokanan wasa da y’an uwa suka
rufeta da tsokana.
Ranar tasha nasiha sosae gurin
iyaye,wannan yayi,wannan yayi har ta soma
gajiya,
Anayin sallar la’asar Abbanta yace a fito
da ita a kaita d’akin mijinta,aifa nan sabon
kuka ya tashi ta qanqame Umma tana ta
faman yi kamar ranta zai fita, da qyar aka
samu aka raba su,
Barhim estate a nan gidan nata yake sai
ddai ya banbanta da irin tsarin gidajen,hawa
biyu ne gidan,fentin brown sai aka ratsa
milk,tun daga waje zaka fara karo da
fulawowi masu kyau da qamshi.
Ana yin sallar magrib sauran y’an kawo
Amarya suka watse ya rage daga Amarya
sai Aminanta kuluwa da memxy……..
[10/7, 10:09 PM] Hawwadamary : [10/7,
9:48 PM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*
13
~Hawwa Damary
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla*
*CIGABAN LABARI*
Bayan ya dawo rakiya Abokannasa kai
tsaye inda ya barta ya nufa lokacin qarfe
tara harda minti sha biyar na dare.
Zaune take a bisa gado ta yi tagumi,har ta
qarasa ya zauna bata San ya shigo ba yasa
hannu ya zame tagumin da tayi ya had’e
fuska yace”tunanin me kike yi haka har na
shigo baki sani ba,sai kinja wata lalurar ta
sameki ko saboda kinga ba ke keda asara
ba”
Tay murmushi tace”wallahi yaya ba haka
bane,kawae dai ina tunanin su umma ne”
Cikin dariya yace”tou ko in tashi in kaiki
ne?”
Itama dariyar tayi tace”ni dai bance ba
yaya,kawai dai bazaka gane bane”
“Zan gane mana,bari dai na gama cika
cikina sannan” ya d’an shafa cikinsa”kinsan
rabona da cin abinci tun breakfast, tashi kije
freezer dake kitchen akwai wata leda zaki
ga kaza ce ciki ki d’auka kiyi mana warming
d’inta,oh sorry Ashe Amarya ce ke ko,na
manta Amarya bata aiki,tashi muje tare sai
ki taya ni hira ni inyi aikin”
Tay dariya tana qoqarin miqewa,tace”kai
dai kawae zauna ka huta waye ya ce maka
amarya bata aiki? Ai ko bata yi ni dai zanyi
ma yayana”
Har cikin ransa yaji dad’i kuma ya
tabbatar marwansa na qaunarsa kamar
yanda yake qaunarta,shima tashi yayi ya
rufa mata baya, lokacin da ya isa har ta
juye a plate ta saka a cikin warmer,bayan
sun gama suka zauna a dinning table suka
ci tare da korawa da sanyayyar
youghurt,lokacin qarfe goma saura minti
shidda.
Bayan sun kammala suka nufi parlour suka
kunna kallo suna yi,amma gabaki d’aya ba
fahimta take ba saboda ita ba ma’abociyar
son qwallo bace,duk ta gaji burinta kawae
ta ganta a bisa gado tana bacci.
Lura yayi da yanayin da take ciki ya tashi
ya kashe komai da kallo sannan ya zo ya
d’auketa chak bai dire ta a ko ina ba sai
bedroom d’inta bisa kujera,ya ajjeta yana
qoqarin su had’a ido,amma taqi,cikin muryar
mai taushi yace”my prncss ki tashi muyi
sallah muyi ma Allah subhanahu wa ta’ala
da ya kawo mu wannan lokacin da muke
zaune a qarqashin inuwa d’aya”
“Tou yaya,ka tafi to sai na tashi” cewar
Marwa
Dariya yayi ba tare daya ce komai ba ya
fita tare da ja mata qofa,
Sanyayyar ajiyar zuciya tayi tare da
miqewa ta nufi toilet ta watsa ruwa tare
da d’auro alwallah, a tsanake ta gama
shirinta sai qamshi take zubawa,
Har ta d’an zauna bakin gado sai gashi ya
shigo sanye da jallabiya fara shima dai
qamshin yake zubawa,
Da murmushi d’auke a fuskarsa ya qaraso
inda take,dama already ta sanya hijab sai ta
miqe kawae,shima ba tare da 6ata lokaci
ma ya tada masu,
Sun dad’e suna addu’o’i na neman
zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba,bayan sun
gama wannan ya dafe kanta ya shiga
karanto addu’a kafin daga bisani ya yi mata
y’an tambayoyi da suka shafi addinin
musulunci,kamar su wankan tsarki da dai
sauransu,tiryan tiryan ta Shiga zayyana
masa ba tare da wata gargada ba duk da
wani nauyinsa da take ji.
Ta matuqar burgeshi kuma har ga Allah ya
ji dad’i ko ba komai ya za6a ma y’ay’ansa
uwar da ta chanchanta, agogo ya kalla
qarfe sha biyu da minti biyu don haka suka
soma haramar bacci.
Wannan dare a garesu dare ne mai
d’umbin tarihi wanda ke cike da faranta ran
juna sai dai ga y’an uwansu da abokan
arziqi wannan dare shine yafi ko wane dare
muni a cikin rayuwarsu, ta d’an tsagaita
tare da goge hawayen da ya soma taruwa a
idonta,
Duk da nima jikina ya soma yin sanyi
hakan bai sa na lallasheta ba don bansan
me ke sanya ta wannan zubar
hawayenba,sai dai ba qaramin zaquwa nayi
ba da son jin abunda ya faru a Daren.
Maimakon naji ta cigaba da bani labari sai
naga ta miqe ta nufi hanyar kitchen, jim
kad’an sai gata ta fito hannunta d’auke da
tray cike da drinks bayanta kuma Lantana
mai aikinta ce itama d’auke da qaton tray
na manyan warmers,duk kusan a tare suka
ajje kafin Lantana ta juya ta fita,ita da
kanta matar tayi serving d’inmu.
“Ikon Allah” na fad’a a raina saboda ganin
wasu irin abubuwa da aka had’a a abincin
wad’and’a tunda nake a rayuwata ban ta6a
ganinsu ba,aifa ban tsaya nuna baqunta ba
na saki ciki na nad’i abincinnan saboda idan
na bar gidan bansan lokacin da zan qara
gani ba balle har na ci,”kai gaskia yau idan
na koma gida sai y’an gidanmu sun gaji da
labari,wallahi harda qarya zan had’a masu
duk don labarin ya qara dad’i” nay ta
wannan saqe-saqen cikin raina.
Bamu cigaba da labari ba saida muka
gabatar da sallar azahar sannan muka
zauna ta kalleni da murmushi tace”tou
Hajiya Hauwa Damari a ina muka tsaya?”
Nayi saurin cewa”a lokacin da suka kwanta
donyi bacci”
Tayi dariya sosae tace”Ashe dai baki da
mantuwa”
Nima dariyar nayi nace”ay wannan qaton
kan nawa ba banza yake ba”
Dariya ta qara yi tace”ay naga Alama,Bari
dai na cigaba maki kafin yara su dawo”
Nace”ay lallai kam
Tayi murmushi sannan ta cigaba kamar
haka……….
*Hauwa Damary*
[10/9, 11:04 AM] Hawwadamary : [10/9,
10:02 AM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*.
14
~*Hawwa Damary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulla*
Basu suka sami natsuwa ba sai qarfe
ukku da rabi da minti biyu na dare,
rungumeta yayi a jikinsa zuciyarsa cike da
farin cikin da bai ta6a yi ba tunda ya zo
duniya,kai gaskia Allah na sonsa da ya
shigo da Marwa a rayuwarsa har ta zama
matarsa,ya lalubi dai-dai saitin kunnenta
yace”I love u my prncss,I love u with all my
heart nd I promise to be with u forever and
forever moree”
Tayi murmshi tare da qara shigar da
kanta cikin qirjinsa don tsananin kunyar da
ya bata”wai shi yaya baisan kunyarsa nake
ji ba”ta fad’a cikin ranta, fiye da minti goma
suka d’auka suna jin d’umin juna kafin daga
bisani ya miqe ya nufi toilet,jim kad’an sai
gashi ya fito yana tsane jiki da towel da
alama wanka yayi,ya kai dibansa a gurin da
take tana kwance yanda ya barta ta
qudundune da bargo duk sai yaji tausayinta
ya mamaye sa,a hankali ya soma kiran
sunanta,tace”na’am” yace”ki tashi kizo muyi
sallar nafila kafin a kira sallar asuba”
Ta marairaice fuska kamar zatayi kuka
tace”yaya bana iya tashi”
Yayi murmushi tare da matsawa inda
take,baiyi wata-wata ba ya sunkuceta sai
toilet,zuwan zafi ya had’a mata a cikin
kwamin wankan sannan ya d’iga dettol a
ciki ya sanyata ciki,ya tsaya daga gefe yana
jiran ta gama,tace ita dai ya fita, yay
murmushi kawae ya juya ya fita,zanin
gadon dake bisa gadon ya cire duk da bai
6aci da jini ba,cikin washing machine yaje
ya saka tare da kunnawa ya juya,yaso ya
chanza wani sai dai yaga lokaci yana ta
harararsa don haka sai ya barshi idan ya
idar da sallar nafilar sai ya chanza kafin a
kira sallar asuba.
Wani irin matsanancin ciwon kai yaji ya
sara masa a gefen kansa na dama,yay
saurin dake kan yana karanta addu’a,sai
kuma yaji ya lafa masa don haka ya tada
sallarsa,ya duqa da niyyar yin sujjada kenan
ciwonkai ya dawo sabo na yanzu ma yafi na
d’azu don duka kanne ya d’auki zugi.
Sai da ta gama komai tsaf ta d’auro
alwallah sannan ta fito,ganin sa a sujjada
yasa ta soma sauri don kar yay ta
kiranta,doguwar riga kawai ta zura sannan
ta d’auko dogon hijab d’in da ta d’inka
musamman don yin sallah ta sanya,har
lokacin bai d’ago daga sujjadar da yayi
ba,hakan yasa ta nemi guri ta zauna a bakin
gado tana jira ya idar su yi nafilar da ya
ambata,ta diba agogo lokacin qarfe hud’u
saura minti biyu.
Sai dai abunda ya bata mamaki bai wuce
ganin har yanzu bai d’ago ba kawo yanzu
ta fara tsorata da wannan sujjadar tasa,a
hankali ta soma kiransa sai dai shiru.
Gabanta na fad’i ta qarasa gurinsa tasa
hannu ta d’an ta6a sa sai yay luuuuu ya
fad’i,a rud’e ta d’auki Hannun sa ta d’auka
ta saki sai ya fad’i yarab ga jikinnasa yayi
sanyi qalau,a gigice take fad’in”innalillahi
wa inna ilaihirraju’un”ta soma jijjiga shi
tana kira”yaya don Allah ka tashi bana son
wannan game d’in,please yaya ka tashi”tana
yi tana kuka kamar ranta zai fita”yaya ka
manta Al-qawarin da ka yi man na zaka
zauna da ni har abada,please yaya ka tashi
mu cigaba da zama har abada”amma yaya
ina, rai yayi halinsa,Allahn da ya yi sa ya
amshi kayansa,rayuwa kenan,yanzu-yanzu
kake da mutum yanzu-yanzu ace maka
bashi,duk wani mai rai sai ya d’and’ani
mutuwa,walau ta hanyar hatsari ko rashin
lafiya ko farat d’aya dole ne a mutu,yanzu
ga Marwan bai ta6a kawo ma ransa a cikin
darennan zai rasu ba sai gashi lokacin sa
na cika ko second d’aya bai qara ba,kullu
nafsin za’ikatul maut,haqiqa duk wani mai
rai mamaci ne,sai dai muyi fatan mu cika da
kyau da imani.
Iya rud’ewa to Marwa ta rud’e fiye da
zaton mai karatu,iya gigicewa ta
gigice,wayarta ta shiga laluba don ta kira
umma ta sanar da ita halin da ake ciki sai
dai kash ta manta a parlourn qasa ta manta
wayar ta shiga laluben tasa sai dai harta
karad’e ko’ina bata ganta ba,duk ta bi ta
rikice lokaci kad’an ta chanza kamar ba ita
ba,gudu-gudu sauri-sauri ta dinga had’awa
harta sauka qasa,tayi sa’a wayar tata na
bisa kujera don haka batay wata-wata ba ta
soma kiran number Umma saidai har ta
qaraci ringing d’inta ba’a d’auka ba,ta kuma
kira shima ba’a d’auka ba,a taqaice saida ta
kira yafi sau goma ba’a d’aga ba dole ta
haqura ta shiga neman number y’an gidansu
Marwan sai dai duk wanda ta kira number a
kashe,ita sam ta manta saran y’an gidansu
na da zarar goma tayi suke kashe waya,ta
d’ora hannu a kai abun duniya duk ya taru
yay mata yawa, memxy ce ta fad’o mata a
rai aiko batay wata-wata ba ta danna mata
kira,lokacin memxy na tsakiya da bacci mai
cike da mafarkin Salim,cikin bacci taji
wayarta na ringing tay banza da ita,aka
kuma kira a karo na biyu tayi tsaki gami da
janyowa,my lady ta gani a screen d’in tay
saurin d’auka cikin gigin bacci tace”shegiya
me zaki man ne kika wani daman bari sai
anjima na kiraki”qit ta kashe wayarta ta tare
da ta saurari abunda zata fad’a mata ba,
“Na shiga ukku” ta fad’a tare da qora
hannu saman kai,ta nufi kanyar komawa
sama,step biyu ya rage mata ta tuna da
baba mai gadi,juyowar da zatay keda uwa
ta take dogon hijabinta ta baya,nan ta fad’i
ta cigaba da gungure har ta isa qasa,take ta
suma jini ya soma zuba ta kai,hanci da
baki.
Baba maigadi ya fito zai kama ruwa a
bayinsa da ke wajen d’akinsa yaji kamar
qarar fad’uwar wani abu,sai bai kawo ma
ransa komai ba,da yake yayi dai-dai da
soma kiran sallah a masallacin dake wajen
gidan,sai kawae ya d’auka irin qarar nan ce
ta kunna loud speaker,don haka sai yay
sauri ya kama ruwa yay alwallah sannan ya
nufi masallaci..
[10/11, 9:12 AM] Hawwadamary : [10/11,
7:56 AM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*
15
~*By Hawwa Damary*
Dedicated to *Memxiey_fulla*
Marwa ce kwance cikin jini tana miqo
mata hannu Ta taimake ta gefe guda kuma
Marwan ne tsaye yana hawaye yana kallon
gefen da Marwan take kamar yana son
sanar da ita wani abu sai dai ya kasa, kafin
ta kaiga qarasawa gurin Marwan tuni ta
fad’i sumamma,6at Marwan ya 6ace daga
gurin da yake tsaye, firgigit ta farka tana
fad’in”innalillahi wa inna ilaihirraju’un”tare
da dafe qirji,gaskia ba qaramin kad’uwa
tayi ba da wannan mafarkinnata,hakanan
sai taji hankalinta bai kwanta ba,haka
burinta bai wuce ta san halinda y’ay’annata
suke ciki ba,ta kalli agogo qarfe biyar saura
kwata,kuma a dai-dai lokacinne aka soma
kiran sallah a masallacin unguwarsu.
Tashi tayi ta shiga toilet ta d’auro
Alwallah ta gabatar da sallar Asuba gabanta
na fad’i akai-akai. Bayan ta idar ta d’auko
wayarta don ta kira mijinta taji yanda ya
kwana kasancewar tunda aka fara hidimar
biki bata samun zuwa d’akinsa ta kwana,
11 missed calls ta gani daga Marwa,nan
take ta danna kira amma har ta qaraci
ringing ba’a d’aga ba ta,sai da ta kira sau
hud’u ba’a daga ba,abunka ga mai saurin
shiga rud’u duk sai tabi ta rud’e ta figi hijab
tayi hanyar d’akin mijinnata,taje a sa’a don
a dai-dai lokacin ya dawo masallaci,yana
ganinta face”lafiya?”
Tace”inafa lafiya”nan ta zayyana masa
mafarkin da tayi ta cigaba da fad’in”ni
wallahi hankalina ba zai kwanta ba sai na
dibo halinda suke ciki”
Yay dariya yace”matsalata da ke kenan
akwai rud’ewa,tou ki bari gari ya gama
wayewa mana”
“Gaskia ba zan iya bari har gari ya waye
ba,don baka ji yanda nake ji ba,banqi ace
yanzu na bud’e ido na ganni gidan ba”ta
qarashe maganarta cikin zaquwa, yace”tou
shikenan,sai ki tada audu driver ya kaiki don
ban yarda kiyi driving a halin yanzu ba,kome
kenan kiyo man waya,no barshi ma zan biyo
bayanki nan da 15mnts idan na shirya”
Tace”tou shikenan darling sai ka iso,Allah
ya qara girma da d’aukaka”
Ya wani lumshe ido kafin yace”Ameen
matas” har cikin ransa yana jin dad’in
rayuwa da ita,kullum cikin tattalinsa take
shiyasa gashi nan kullum qara yarinta
yake,yay murmshi a ransa yace”Allah ya
barmu tare”
Qarfe biyar da minti arba’in na safiyar
alhamis a qofar gidan Marwan tayi ma
Umma,driver nayin horn mai gadi yazo ya
bud’e masa da sauri,risinawa yay ya
gaisheta,ta amsa a gaggauce,
Qofar da zata sada ka da parlourn gidan
ta nufa,a rufe take don haka sai ta fara
knocking amma shiru kake ji wai anyi wa
mai dami d’aya sata.
Hankalinta ya qara tashi ta kira maigadi
ta tambayesa ko masu gidan basa nan ne?
Yace, suna ciki tun jiya basu kuma fita
ba,tsayi d’an tsaki tare da cigaba da
qwanqwasawa amma har yanzu ba wani
motsi,Marwan ta kira a waya gashi tana
ringing amma ba’a d’aga ba,ta kalli mai
gadin tace masa ya d’an samo mata
abunda za’a iya 6allewa,yace”to ranki ya
dad’e” ya juya ya tafi, bayan tafiyarsa ta
qannan number Hajiyar Marwan,tayi sa’a
ringing d’aya ta d’auka tana fad’in”kin taki
sa’a don yanzu-yanzu na kunna wayar,ya
gajiyar biki? Da naga kiranki baki ji yanda
gabana ya fad’i ba dama yau na tashi jikina
duk yay sanyi ince ko lafiya?”
“Ina fatan haka d’in Hajiya,gani dai a qofar
gidan y’ay’anki” ta zayyana mata mafarkin
da tayi da kuma tsayuwar da take a gurin,
Hajiya tace”ki kwanta da hankalinki in
Allah ya yarda ma ba komai sai
alkhairi,nima bari na zo gidan yanzu,Amma
fa kada mu zama sirikan banza”ta qarashe
maganartata da zolaya,
Murmushin yaqe umma tayi tace”amma
kuma a wani 6angaren ae mu iyayene,kinga
haqqinmu ne mu zo muga lafiyarsu”
Tace”eh tabbas! Da haka,tou sai na
qaraso”
Umma tace”uhmm”
Ajje wayartata yay dai-dai da dawowar
maigadi d’auke da gatari a hannunsa,bugu
biyu zuwa ukku qofar ta 6alle,Umma ce ta
soma shiga sauran suka rufa mata
baya,turus tayi ta tsaya sakamakon abunda
ta gani,
Marwa ce kwance cikin jini face-face ba’a
cikin hayyacinta ba,bata san lokacin da ta
saki wayarta ba ta qarasa gurin cikin
kid’ima ta rungumeta tana jijjigata,ruwa ta
umarci Audu da ya miqo mata cikin fridge,
yana kawo mata ta shafa ma Marwan,wata
ajiyar zuciya ta saki tare da bud’e idonta da
yay jawur don tsabar kwanciyar jini,bakinta
ta soma bud’ewa alamar tana sonyin
magana Amma ta kasa,da qyar kake
gane”ma…ma…ma..” Sai kuma tayi shiru
Allah kad’ai yasan azabar da take sha a
lokacin,ba umma kad’ai ba harta su mai
gadi saida suka zubar da hawaye,
Umma tayi qarfin halin cewa”ina Marwan
d’inne ya barta cikin wannan halin”ta kalli
mai gadi.
Yace”wallahi Hajiya bansan inda yake
ba,ni dai rabon da naga wani ya fita
gidannan tun jiya da daddare”
Ta qaure fuska tamau tace”kana nufin
Marwan d’in na ciki wannan Abu ya samu
Marwa? Zancen banza zancen wofi,” ta kai
dibanta ga Audu tace”kama man ita mu
kaita asibiti”
Sai dai ita Marwa har yanzu qoqarinta na
tayi mgn ne Amma ta kasa,da qyar ta
samu ta iya d’aga hannunta ta nuna masu
hanyar upstairs, sai kuma ta qara yin luuuu
jikin Umma ta qara Sumewa,
Tsawa umma ta daka ma audu tace”ka
kama man ita nace”
Jiki na rawa yace”tou Hajiya”
Maigadi yace”naga tana nuna hanyar
saman bene ko wani abunne take son
sanarw….”rufeman baki”umma ta katse shi
ta hanyar daka masa tsawa,tace”shashasha
Wanda baisan aikinsa ba,kana aikin meye
haka ta faru da y’ata, tou ka sani baka ci
bulus ba,zaka yi bayani gaban hukuma,kai
kuma kamata muje”….
*Hawwa Damary*
[10/11, 12:53 PM] Hawwadamary : [10/11,
9:46 AM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*
16
~*By Hauwa Damary*
Dedicated to *Memxiey_fulla*
*k*ama ta yayi suka nufi mota da
ita,suka sanya ta a baya umma ta zauna ta
d’ora kanta bisa cinyarta sannan ta
rufe,yana qoqari tada mota suka ji horn a
bakin gate,mai gadi yaje ya bud’e,Mai daloli
ne ya qaraso,ganinsu a nan yasa yay
tunanin ko ba komai,qarasowa yay inda
suke,da Marwa ya fara tozali cikin jini,
yace”subnahallah me ya faru haka?”
Nan umma ta labarta masa halinda suka
zo suka iske Marwa a ciki,
“Assha! Tou ina Marwan d’in ya shiga ya
barta a haka”
Cike da qosawa umma tace”ba wanda ya
san inda ya nufa,yanxu dai mu fara ta
lafiyar wannan d’in,sannan sai a neme sa
d’azu ma na kira wayarsa baiyi picking ba”
Abba ya kalli mai gadi da yayi tsuru-tsuru
yace”yaushe ya fita?”
Mai gadi ya shiga rantsuwa shi duk yau bai
ga Marwan ba harda hawayensa,
Yace”ni ba nace wani Abu bane,yanzu dai
biyo ni muje ciki,Ku kuma sai Ku wuce
asibitin” ya d’ebo kud’i daga aljihunsa ba
tare da ya San adadinsu ba ya miqa masu
ko za’a buqaci wani Abu a asibitin,
Ko wane d’aki da ke a qasa saida suka
diba ba Marwan,maigadi yace”yalla6ai dazu
kafin hjy ta qara suma naga tana nuna
sama da alama akwai abunda take son
sanarwa”
Mai daloli yayi d’an Jim kafin yace,su je.
Gawar Marwan na nan a yanda Marwa ta
barsa har ya soma sandarewa,suna shiga
sukayi arba da gawar,”Innalillahi wa inna
ilaihirraju’un”suka fad’a a tare,gami da
qarasawa gurinnansa ba abunda suke sai
sallallami,Abban ya kira alhjn Marwan d’in
yace yaxo ya samesa a gidan marwan
d’in,lokacin yana tare da hajiya tazo
tambayar sa,ya hanata yace ba da shi ba
za’ayi wannan abun kunyan, aiko tana jin
wayar da aka masa tace qafarsa
qafarta,yace”ay sai ki shiryo muje” tace “a
shirye nake” tare suka fita lokacin qarfe
bakwai da minti ishirin da hud’u.
Tun daga hanya suka fara karo da jini, tun
daganan suka fara shan jinin jikinsu.
Mai karatu iya tashin hankali kaf dangi da
y’an uwa sunga tashin hankali wanda basu
ta6a gani ba,gidan biki ya koma gidan
zaman makoki,ba’ay ma Marwan sutura ba
sai da y’an sanda suka zo sukayi bincike
tare da lokitoci suka gano ba abunda ya ci
ko ya same shi kawai dai ikon Allah ne
wanda baya wuce ranarsa.
Qarfe hud’u aka yi jana’izarsa aka kaisa
gidansa na gaskia,gidanda duk wani mai rai
dole ne ya je shi,
Kawo yanzu kuka yaci qarfinta,bama ita
kad’ai ba har ni da nake zaune tana bani
labari,ba mai lallashin wani idan ka ganmu
a lokacin sai ka rantse da qur’ani a yanzu
ne akayi mutuwar.
Ta cigaba cikin kuka”wallahi Hauwa’u
tashin hankali an shigeshi fiye da yanda kike
tunani, duk wani wanda yasan Marwa da
Marwan ya tsorata da wannan al-amarin
karma abokan Marwan suji,
Nay saurin kallonta nace”ita Marwan fa?”
Ta goge hawayen idanunta tace”Marwa na
nan da ranta sai dai da halin da take ciki
har gara wanda ya rasu, don zaune take
bata ji bata magana,qwaqwalwarta ta had’u
da jini,sai abun ya zamar mata kamar ta6in
hankali,anyi maganin anyi maganin Amma
ba wani sauqi sai gurin Allah,duk qasar da
akaji labarin idan anje za’a dace tou anje
amma har yanzu” “innalillahi,ya Allah
ubangiji kaba ma baiwar nan taka
lafiya,yawwa ina qawayenta memxy da
kuluwa?”
Sai naga tayi murmishi sannan tace”nice
memxy,asalin sunana Maimuna ne,ae duk
na fad’a maki a cikin labari sai kuluwa
wannan kowa yasan duk Hauwa’u kuluwa
ce,kuluwa ta auri Dr umar yanzu haka suna
da y’ay’ansu ukku sai ni kuma na Auri salim
abokin Marwan ko ince abokin fad’ana”sai
dukanmu mukayi dariya,sannan ta
cigaba”y’ay’anmu biyu gasu nan mace da
namiji”
Wai! Tabd’i jam,yanzu nan dama itace
memxy,wallahi ko kad’an ban kawo ma
raina ba,harma da y’ay’a,nace”Allah ya raya
su”
Tace”Ameen kulun majadan”
Nayi dariya kafin nace”nikam cikin
qasashen da aka kai Marwa anje saudiyya?”
Ta d’anyi shiru alamar tunani sannan
tace”gaskia ba’a je ba”
Lallai gaskia mutanan mu suna tafka
babban kuskure,sai lalura ta samu ayita
kashe uba-uban kud’i ana zuwa qasashen
arna,amma a kasa zuwa qasar
saudiyya,tab! Wannan zancen duk a zuci na
yi shi,a fili kuma cewa nayi”tou gaskia ku
d’an gwada kaita,bari na baki misali da
wani uncle d’ina,suna cikin mota zasu kano
sukayi accident shima qwaqwalwarsa ta
samu Matsala sosae, don a yanda kika fad’a
man na Marwa sauqi ne akan nasa don
abun sai ya zame masa kamar ma
hauka,amma cikin ikon Allah ana kaishi
saudiyya ko wata biyu basuy ba sai gashi
garas,Allah Ku gwada kaita akwai nasara
sosae”na qarashe ina qoqarin tashi,
Tace”insha Allah zamu gwada zanyi ma
umma magana,sai ki bani numbr ki
nextweek idan zanje gurinta sai mu je tare”
Nace”aiko nagode sosae”na Shiva karanto
mata number”08067729322″ tace”tou
nagode,d’an jirani na fito”ta shiga d’aki,jim
kad’an ta fito riqe da babbar Leda a
hannu,tace”ga cosmetics y’anmata aje ayita
yi ma samari gayu”
Nayi dariya nace”wane samari ga karatu,ai
mu da samari sai mun fara aiki”na amsa”na
gode sosae”
*Hawwa Damary*
[10/11, 2:44 PM] Hawwadamary : [10/11,
2:19 PM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*
17
~*By Hauwa Damary*
Dedicated to *Memxiey_fulla*
Har bakin qofa ta rako ni tana d’aga man
hannu,duk sai naji ba dad’a don maganar
gaskia matarnan ta shiga raina sosae kuma
nasan hakan bai rasa nasaba da labarin da
ta bani mai ban tausayi.
Gab da zan fita gate wata mota ta danno
kai,wata mata ce ke ja,sai yara ciki guda
biyar, biyu dai na gane y’ay’an hajiya
Maimuna ne, ukkun ne dai ban sansu ba,ko
da yake na manta qila matar itace kuluwa
da y’ay’anta,bari in cire kalmar qila,tabbas
kuluwa ce,ina lura da ita har na bar gate
bata bar kallona ba.
Kai gaskiya ranar y’an gidanmu sunsha
labari,kayan da ta bani na zube ina nuna
masu ina shafto qarya,har ce masu nayi
gidan harda ginin qarqashin qasa,nace harda
qofa mai magana,aiko suka rud’e idan, zan
koma zasu Bini,nace”wallahi ba wacce zata
Bini tayi man 6aqin cikin cin kayan dad’i”na
kwashe kayana na wuce d’aki.
Kamar yanda mukayi sati na cika tayo
man waya tace na shirya da yamma zamu
je gidansu Marwa,nayi farin ciki sosae har
na kasa 6oye murna ta.
Da yamma ko na shirya cikin ash colour
d’in doguwar riga na d’auki jakkata na fice,
a bakin gate nayi kichi6us da
ita,tace”yawwa kinma hutar da ni da shiga
zanyi na kiraki”
Nayi dariya kawae,a mota take sanar dani
gobe za’a fidda Marwa saudiyya,
Nace”Amma gaskia naji dad’i Allah ya
bata lafiya da zaran anje”
Tayi dariyar jin dad’i tace”Ameen y’ar
qanwata”
Nayi mamakin ganin gidan su Marwa cike
da mutane kuma duk saboda mutum d’aya
suka taru,dama Ashe haka suke duk asabar
da lahadi suke zuwa diba jikinta,qwansu da
qwarqwatarsu, gaskia sun nuna man
karamci sosae,dama ance shimfid’ar fuska
tafi ta tabarma,saima da hjy Maimuna ta
shaida masu nice na bada shawarar fita da
Marwa saudiyya nan sukayi ta zuba man
godiya harda umma harda qwalla duk sai
naji kunya ta kamani, Hjy Maymuna ta jani
ta kaini d’akin da Marwa take,gaskia Marwa
ta had’u ba qarya,ganinta yafi labarinta
kamar y’an India,tou ko ya kamannin
mariganyi Marwan yake?,kamar Hjy
Maimuna tasan abunda ke raina kenan ta
tashi ta dakko man album d’in hotunan
sa,wani shi da Marwa,wani cikin
family,wasu na ranar biki,ga hoton
kamfaninsa na motoci,a raina nace”Allah
sarki Marwan,Allah ya kai haske cikin
kabarinka.Ameen
Sai yamma lis muka dawo gida,nan
gidanmu hjy maimuna ta zauna da
y’ay’anta har akayi isha’i suka ci abinci
sannan suka tafi,
Washegari litinin na koma
makaranta,abun ban haushi a Daren da na
koma aka sace wayata,raina yay matuqar
6achi saboda rasa number hjy maimuna da
nayi,gashi ni ba gwanar welcome back ba
Koda muka dawo Hutu naje gidan mai
gadin yace man ay sun fi wata ukku
rabonsu da gidan,gwuiwa a sa6ule na koma
gida tare tsinema d’an iskan daya sace man
waya.
*********
Bayan shekara biyu na kammala Karatuna
har an sanya ranar bikina wata biyu masu
zuwa,
Ranar wata litinin da yamma naji ina son
zuwa shopping,Umar stores na nufa
kasancewar nan na saba zuwa y’ar sayayya
ta,6angaren mutanen nawa na nufa wato
dogayen riguna ina d’add’aga wa,d’agowar
da zanyi nayi four eyes da wata mata
kamanninsu d’aya da Marwa,duk cewar sau
d’aya na ta6a ganinta kuma cikin halin
lalura,da yake a lokacin na tafi da tunaninta
shiyasa wannan kallo d’aya nayi mata naga
kamannin na Marwa,sai dai wannan na fita
jiki, ina cikin tunaninnan ne har ta zo ta
gabana ta wuce ban sani ba,hakanan naji
ina mai son binta naga Wanda ya kawo
ta,wani abun mamaki ina 6ulla kwana na
ganta tsaye ita da maymuna a gurin da ake
biyan kud’i..
*Hawwa Damary*
[10/11, 3:26 PM] Hawwadamary : [10/11,
3:20 PM] Hawwadamary : *MARWA DA
MARWAN*
18
~*By Hauwa Damary*
(NWA)
Dedicated to *Memxiey_fulls*
Banyi qasa a gwuiwa ba na qarasa ina
murmushi,tana hango ni ta gane ni itama da
murmushi a fuskarta ta qaraso ta
rungumeni zuciyarta cike da murnar
ganina,fad’i take”sister Ashe rai kanga rai”
Nayi dariya nace”wallahi kam kedai
bari,har gidanki naje aka ce baki nan”
Tace”eh hakane,ai kinsan an je kai Marwa
saudiyya ko?”
Nace”eh” tace”yawwa bayan sun tafi da
sati d’aya muma muka bi bayansu,cikin sa’a
ko shekara ba muyi ba ta fara samun sauqi
sakamakon kulawar da take samu daga
gurin manyan likitocinsu,ga shi kuma kullum
sai an gungurata anyi d’awafi da ita a shafa
mata ruwan zam-zam,lokacin da muka cike
shekara gaskia ta samu sauqi sai dai
abunda ba’a rasa ba, a shekararmu ta biyu
ne ta warke sarai kamar ba ita
ba,yanzunma da kika ganmu last week
muka damo shine tace na rako ta
shopping”ta kalli Marwa da ke tsaye ta
tsura mana ido tace”Marwa wannan itace
Hauwa Damary wacce nake baki labarin
itace ta bada shawarar a kawo ki saudiyya”
Tun kafin maimuna ta gama tuni hawaye
ya wanke mata fuska ta qaraso inda nake
ta rungumeni tana fad’in”thank u,thank u
sister,thank u,word can’t express my
gratitude ,i really appreciat ur contribution, I
luv u so much” na d’agota ina goge mata
hawaye nace”don’t mention sister, I’m also
glad dat u are fine now”
Ta riqe hannuna muka koma ciki mukayi
sayayya mai rai da lafiya,bayan mun gama
kai tsaye gidansu muka wuce,
Yawancinsu sun gane ni kamar zasu lasheni
fadi suke dama bari mukayi mu gama
hutawa sannan muje har gida muyi ma ki
godiya,nace”ay ba komai”
Banbar gidanba saida nasha
kyaututtuka,Marwa ta badi mota mai
shegen kyau irin ta yayi,mai daloli ya bani
kyautar kujerar makka,hajiyansu Marwan da
Alhajinsu suka bani 3million,
Wohoho wa yaga Hauwa a makka,ga mota
sannan ga kud’i naira na gugar naira har
million ukku,ae rasa bakin godiya nayi sai
kawae hawaye……..
ALHAMDULILLAH…
HAKIKA MUTUWA GASKIYACE! Kuma
rayuwa bayan mutuwa dole ne, kamar yanda
kake rayuwa aduniya burinka kamore da
mace, ka haihu, ga gidaje, motoci,
kamfanoni/ kasuwanci ko aikin gwamnati.
Amma fa bazaka wuce shekara 150 ba, zaka
mutu. Shin? Ka tanadi abubuwan da zakayi
rayuwa mai dadi bayan mutuwarka?
Kokuma kana tunanin cewa babu rayuwa
mai dadi ko ta kunchi bayan mutuwa? Ka
tuna cewa kayi rayuwa acinkin mahaifa,
zaka iya bada labari ? To haka ma rayuwa
bayan mutuwa babu mai Baka labari sai
Allah da manzonsa. Morewa shine ka mutu
babu hakkin kowa akanka, kuma ka kasance
mai bin dokar Allah. Kada ka bari
idanuwanka,harshenka, kunnuwanka su jaza
maka wahala bayan mutuwa. Ko zaka
kiyayesu kasami rabauta? Hanyar tana cikin
alqurani da hadisai,Allah yasa mu
dace”Ameen summa Ameen.
Anan na kawo maku wannan labari mai
suna *MARWA DA MARWAN*
adsense 2 here