Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 3 May 2017

Mijin marainiya complete-1

adsense here

[4:21PM, 11/19/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ story & Written Fadeela Lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ Bismillahir rahmanir rahim 1-3 Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta faman share hawaye wata dattijuwan mata ce ta fito daga daki tana fadin , kin fara ko, dama ke idan tsohon munafunci ki ya tashi ba mutunci gareki ba, wlh uwarki ta bar miki mugun gado, ki zauna kiyi ta kuka salon iya ta ce ana miki wani abu, matsuwa tayi ta rike mata kunne tace ai baki ga komai ba safna sai rada na koreki gidan nan , zakiyi kuka, yadda uwar ki tasani kuka ta tura min bakin ciki kema sai na tura miki bakin cikin da zai kashe ki . Safna taji zafin wannan ruko, fitsari ne yake bin kafafun ta, tace goggo dan allah kiyi hakuri , indai kuka ne na daina. Kar ma ki daina dan jakar ubanki, tashi maza ki wanke kafafunki ki dauki rake , kuma karki dawo gidan nan sai ya kare. Jiki na rawa safna ta mike ta dauki bukiti taja ruwa a rijiya ta shiga bayi, cikin sauri safna ke wanka dan gudun fadan goggo. goggo na tsaye safna ta fito da bukitin wanka a hannun ta goggo ta bita da harara , da sauri tashiga dakin ma haifiyar ta, wanda a yanzun ita kadai take kwana acikin sa, cikin sauri ta jawo ledan kayan ta, ta fara cirowa tana dubawa duk tsun mukara ne , masu dan kyan goggo ta kwashe tayi kyauta dasu, haka dai ta dauki daya daga ciki ta saka, tadauki raken goggo ta kama hanya. tafe take tana hada hanya domi ita bata iya tallah ba sai dai idan mutun ne yakira ta ,haka tai ta tafiya ko nera ba tayi ba, ta gaji ta koma gida. goggo na zaune a tabarma ita da yaran ta guda biyu iro da salma, safna ta shigo , goggo ta mike yanzun nan dawo min da raken nan kikayi , iro tashi kaba yarinyar nan kashi rashin duka ke damun ta. Kamar jira yake yamike da sauri ya fara kai mata duka daga kar she ma dukkan su suka taron mata wannan na duka wannan nayi , sai da suka ga bata iya motsi suka bar ta WAIWAYE malam musa mutumin kirki ne matan sa biyu goggo itace uwar gida, sai mahaifiyar safna wanda suke kira Inna, tunda malam musa ya auri goggo ta haifi iro bata kara haihuwa ba dan haka iya mahaifiyar malam musa ta matsamai ya kara aure, duk inda malam musa yaje neman aure ba a bashi saboda masifar matar shi, wata rana malam musa na cikin tafiya akan tsuhuwar mashin dinsa yaci karo da wata bafulatana batafi shekara sha biyar ba tana tafiya tana kuka, tsayawa yayi ya tam baye ta lfy take kuka, sai da ta share hawaye sannan tace wata yaya tace tayi aure a binni tunda mijin ya tafi da ita har yau bamu sake ganin ta ba, shine muka fito neman ta su baffah suka ce na jira su karkashin wata bishiya tunjiya har yanzun basu dawo ba, malam yace ina ne garinku , kame kame takama malam dai yagane bata san sunan garin su ba, goya ta yayi abayan mashin din sa dan su kara duba wajan ko iyayan ta sun dawo, suna zuwa suka duba babu kowa awajan , dan haka malam musa yace ma wani abukin sa dake zaune a waja bayanin cewa ko da iyayan ta sun dawo ya kawo su gidan shi. malam musa gidan iya ya wuce da yar fillo saudatu dan yasan halin matar sa, iya ta kar beta hannu biyu tare da mamakin wauta irin na filani, sai da saudatu tayi shekara biyu awajan iya ba labarin iyayan ta ,dan haka iya ta matsawa malam musa ya auri saudatu, malam musa yabi umarnin ma haifiyar shi dan shima yafara tunanin haka. bayan an daura musu aure da wata uku goggo ta sake haihuwan salma itako amarya saudatu sai da ta shekara biyu sannan ta haifi safna , saudatu tasha wahala a gun goggo dan ma tana samun kariya agun malam safna nada shekara sha hudu tafiya ta kama malam zuwa kauyen su iya dan kai masu ziyara, iya tace atafi da saudatu tunda bata taba zuwa ba. lokacin safna nazuwa makarantar primary tana aji shidda dan haka suka barta gun goggo, bayan wani dan lokaci da tafiyan su labari ya same su, motar da suka shiga ta kone kurmus babu wanda yayi rai, haka su kai ta kuka a yanzun haka shekaran su daya da rasuwa inda goggo tahana safna makaranta sai tallan rake. Abduljalal wani matshin yaro ne me ji da kanshi daka ganshi kaga dan gata bazai wuce shekara ashirin da bakwai ba, dogo ne sosai yanayin tsawan shi sai ka zaci ya wuce shekarun shi haka fari ne tas, bashi da yawan fara,a. Idan kaga jalal na dariya to da ummin sa ne , ko kuma cikin abokan sa, zuwa yayi ya samu ummin sa zaune a falo, yaje ya fada jikin ta yana fadin ummi yinwa nake ji. ummi tace jalal karfa ka karya ni, wai kai baka san ka girma bane. haba ummi wanni girma nayi ne, kodan kinga kin samu wata. tace ba haka bane jalal ya kamata ka fahimci cewa ka girma yanxun fan ba da bane, ga abinci nan kaci , karani gida hajiya sahura. cokali daya ya kai bakin sa yace ummi na gaji zo ki bani abaki. gargiza kai ummi tayi ta matso ta fara bashi abaki sai da ya koshi yace ummi bar shi haka na koshi. sai da ummi ta shiga ta gama gyara wa sannan ta fito, ta samu jalal na zaune a falo kanan kaya ne a jikin shi yayi kyau sosai, idan kaga jalal da ummin sa sai ka rantse yayar sa ce, jalal ne ke jan motan ba, suna tafiya suna hira . sunyi nisa sosai sun shiga unguwan su hajiya saratu abduljalal ya hango wata yarinya tana tafe tana kuka ga kuma rake akan ta, yace ummi ji wata yarinya yar karama an daura mata talla, yanzu dan Allah ummi wa zai sha wannan raken kofa kan kare shi ba,ayi ba. ummi tace kai kake ganin haka jalal kazamai yan uwan ta zasu sha. jalal na kawowa kusa da yarinyar ya tsaya ya kira ta da gudu ta karaso, yace me yasa meki kike kuka? tace idan na koma gida raken nan be kare ba duka, duka za,ayi min, jalal ya tausaya mata ya kalli jikin ta yaga shedan bulala, yace ummi zan saya raken nan. da sauri ummi tace amman dai ba a mota ta zaka zuba wannan kazamin raken ba. yace sai ta bawa almajirai , ya sunan ki ya tam baye tace safna sai da ya maimaita sunan sannan yace raken na nawa ne? tace nera dari, dari biyu ya ciro ya mika mata, tamiko hannu zata karba , ummi ta daka mata tsawa taja baya da sauri, jalal yace ummi me tayi ? yaro ban yadda ku hada hannun da yarinyar nan ba ka aje mata akasa sai ta dauka [1:22PM, 11/23/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ story & written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 4-6 Jalal yace haba ummi ai ba taba ta zanyi ba, bata kawai zan yi. ummi tace ashe tsaftar ka ta banza ce , idai ka bawa yarinyar nan da hannun ka kuwa. juyawa yayi ya ajewa safna kudin akasa, da saurin ta ta tsuguna ta dauka tana ma jalal godiya, ummi ko hararar ta kawai take. bayan sun dawo gida ummi ta lura jalal fushi yake da ita, dan haka ta bishj har dakin sa, tace jalal me ya same ka, kake ta fushi? abduljalal be iya boye wa ummi komai dan haka yace ummi yarinyar nan ce take bani tausayi, ummi da,a kwai yadda zanyi dana tai make ta. ummi hada rai tayi tace yaro halin ka yana bani mamaki in banda abinka ina ruwan ka da yayan talakawa da har zaka damu kan ka, akan wata banza yarinya kazama, da kikiya. ummi bazaki gane ba nasan da dady ne zai fahimce ni, ummi raken nera dari ne fa akanta, ummi kuma gashi yarinyar kyakyawa da ita. zoro ido ummi tayi tace yaro kai ne kuwa, kaga yarinya mumuna kace kyakyawa ko dai gamu kayi ne, to naji kyakyawa ce me kake nufi yan zon. ummi ni ba abinda nake nufi kawai dai inason ki tai maka mata ne. kaga jalal karna kuma jin manar yarinyar nan abakin ka, ta mike da sauri tabar wajan. itako safna zuwa tayi gurin wasu almajirai tana raba musu, iya na daga gefe tana kallon safna, saida ta gama ta juya zata tafi iya ta kwala mata kira , ai tana ganin iya ta roga da gudu ta kamkame ta, cikin rudu iya ta daga kan safna tace a ina kika samu rake kike rabawa Jama,a? Safna ta kwashe labari kaf ta fadawa iya, salati iya ta shiga yi, tana fadin ina can zaune za,a lalata min jika, wanne dan iskan ne, yabaki kudi? iya nima ban san shi ba kawai gannin su nayi amota. be miki komai ba dai ko? ba abinda yayi min, iya tasa keyar safna tayi tace muje na samu goggon taki, in kaskiya ne ta daurawa salma mana. suna shiga iya ta fara fada taita fada tundaga ranar rokon safna yadawo hannun iya, safna dadi takeji sosai agurin iya babu ta kura, iya duk ta. hada dan kudin da take da shi ta mai da safna makaran ta, haka iya tai ta wahala da safna ana haka safna ta gama primary schools, gashi iya nason safna ta ci gaba da karatu kuma bata da kudi Dan haka ta fara toya kosai a kofar gida, iya bata barin safna tazo gurin tuyan kosan ta sai dai aikace aikacen cikin gida duk da cewa iya ba wani karfi gareta ba, amman safna ta murje tayi kyau kamar ba ita ba. a yanzun safna tana J S2 dan haka iya ta fara tunanin aurar da safna dan duk da cewa safna bata wuce sha bakwai ba, itako safna babban burin ta shine ta tayi karatu me zurfi. ana cikin haka rashin lafyya ya kama iya dan kosan da take yi ya gagara, safna ta rasa ya zatayi , tana kuka ta nufi gidan goggo, ta gaya mata iya babu lafiya. fada ta fara tana fadin aiga irin ta nan, kina nan muna neman kudi tazo ta dau ke ki, sai yanzun da ciwo yakama zaki taho to bamu da kudi, wacce ki bani waje karna kara ganin ki gidan nan, haka safna ta juya tana tafe tana kuka. haka safna ta dawo ta samu iya kwance cikin amai, ta shiga gyara wajan bayan ta gama ta fara tunani yadda zata samo ma iya abincin da zata ci, tashi tayi ta fita ta gama bulayin ta bata somo komai ba ba yadda zatayi dole ta koma wurin goggo sai da ta gama zagin ta sannan ta bata ragowar tuwan jiya da sauri ta nufi gida tana ta sauri , tun kafin ta isa kofar gidan ta hango muta ne tana shiga gidan kara kamkame tuwan ta tayi ta sheka da gudu tana shiga taga an lulube ta da zani, safna fadawa tayi jikin ta tana kuka. Wata makociyar su iya ta taho ta dafa safna tace kiyi hakuri safna ki daina mata kuka Allah ya karbi abinsa kuma ya fimu santa dan haka sai muraka ta da.ardu,a haka safana taita kuka har aka kai iya makwanci ta safna bata bar kuka ba. bayan anyi bakwai da yamma goggo ta hada kayan ta ko salama batawa safna ba ta wuce gida, gidan iya kuwa safna ce ka dai aciki sai ta tsince kanta cikin matsanan cin tashin hankali, haka safna ta kwana ita kadai acikin gidan, safna na tashi hankalin ta kara tashi yayi musamman da ta leka dakin iya taga wayam dan haka ta tsoguna abakin kofar iya ta saki Kara. makociyar iya baba dije taji kukan safna aguje ta zagawo tace Ina goggonki . safna tace ta tafi tunjiya au yanzu nan nufinta baza ta rike kiba, lalai abin nata babba ne, tashi ki hada kayanki na rakaki . cikin tashin hankali safna ke hada kayan ta tana ganin ita meye amfanin ta tuda ba iyayen ta iyar ma da take takama da ita ta tafi ta bar ta itama da mutuwar kawai tayi. suna shiga gidan goggo suka same ta tana tankadan garin tuwo, tana ganin safna ta hada rai, bayan sun gaisa tace yazaki tafi kibar yarinya ita daya acin gida. cin sauri goggo ta fara rantse rantsan ita sam bazata rike safna, baba dije ta fahimci da gaske ta keyi tace to naji to me zai hana ki kaita gun dangin iya. cinkin sauri goggo tace ina naga kudin motan da zan kai ta. kwance haban zanin ta tayi takwaso gudin wajan duk ta mikawa goggo ta sannu ta karba harda fadin yauyau zan kai ta. goggo bata tashi kai safna ba sai gaf da mangariba tace dauko kayanki mutafi , safna ta dauki kullin kayanta suka kama hanya, motar cikin gari suka hau , safna tace azuciyar ta dama motar garin su iya acikin gari ake hawa ,take farin ciki ya rufeta ko banza yau zataga gidaje masu dan banan kyau . suna isa aka sauke su garin kamar rana saboda fitilun da suke haka ko,ina gidaje kuwa fadan kyansu bata lokaci. suna ta tafiya taki karewa ita dai safna bin goggo kawai take suna zuwa gurin wata katuwar bishiya, goggo tace safna zoki zauna anan naje na dawo , haka banzayen kakannin ki sukama uwarki har ta mutu bata kara saka su a idon taba. [2:05PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed 7-9 Itako safna bata fahimci me goggo ke nufe ba dan bata da wannan labarin , haka tai ta zaman jiran goggo har ta gaji tun tana ganin wucewan mutane daidai har ta daina gani dan haka tsoro ya shige ta, mikiwa tayi tabi hanyar da goggo tabi , tana tafiya tana dubawa ko Allah zai sa su hadu da goggo. wata mota ce ta shigo layin tun daga nesa motar ke hasko ta, dan haka ta tsora ta , motar na zuwa kusa da ita ta tsaya, wani dake cikin motar yace yace ke ina zaki da daddaren nan, kisan ko karfe nawa kuwa? cikin kuka me ban tau sayi ta girgiza kai wanda ke mazauni direba yace kabir ina ruwan ka da ita ne kasani ko aljana ce yanzun 12:15 pm fah ,yace yarinyar ar zikice za aganta a waje awannan lokaci, kabir yace kuma fah haka ne aboki na, motar su kaja suka mike layin. Safna ko babu abin da take ban da kuka, gaba tayi kadan ta samu wani dan dutse ta zauna sautin kukan ta kawai kake ji awajan wasu samari ne suka zo wucewa su uku irin yan shaye shayen nanne sun sha sun bugu daya daga cikin su yace kai kunga wata baby danya, da sauri suka isa wajen ta suka fara ja mata dan karamin hijjabin dake jikin ta safna ko kuka take tana kokarin guduwa amman Ina sun riga sun rike ta dukkan su ukun har sun yaga mata riga dama bawani kwari ke gare suba suna kokawan kwance mata zani . wan,nan motar ta dazun ce ta sake dawo ,mutun daya ne acikin ta sabani dazun da suke su biyu jin uhun yariyar yasa shi tsayawa ya haska su da fitalan motar yaga abinda ke faruwa da sauri ya fito yafara takawa zuwa wajen yana musu tsawa cikin fada ya daga murya sosai . daya daga cikin su yace kai kuzo mu gudu yaya abduljalal ne da gudu suka kwasa abduljalal ya matso kusa da ita ya tsoguna ya dauko hajjabin ta ya mika mata ta karba ta saka kuka kawai take abduljalal yace yanzun ina zaki? tace goggo nace tabar agun wata bishiya tace na jirata kuma naga ta dade bata dawo ba, sheni na biyo hanya ko zan ganta. cikin mama jalal yace kina nufin mahaifiyar ki kece abarki a titi. a,a kishiyar mama tace. yace to ke ina mamar ki? cikin kuka tace suyi hatsari har baba na sun rasu. Jalal ya tausaya mata sai dai har yanzun be gama yar da, da yarinyar ba yana ganin kamar dai ta fito yawo ne, ya juya yace Ina yan uwan ku suke, tace nibasan kowa daga cikin dangin muba kakata kawai na sani itama ta rasu jiya akayi bakwai, shine akace ma goggona takaini gun dangin kakata, shine ta barni tace najira ta tadawo. hankalin jalal ya tashi ya rasa yan zun ya zai yi da yariyar nan gashi dare na dadayi , zuwa yayi yabude motar sa ya shiga da gudu safna ta biyo shi tana fadin dan Allah karkabar ni anan. ai bazan barki a nan ba ya bude dayan gefen yace shiga mutafi , bayan tashiga ta zauna jalal yace ya sunan ki? tace sunana safna. Jalal ya sake maimaita sunan safna da sauri yafara neman fitilan motar haske ya baiyana yace safna bake bace shekarun baya na saya rake wajen ki, dama ke ma rainiyace. cikin kuka tace eh. Yace to kibar kuka safna insha Allahu zakiji dadin rayuwan ki , jan mutan yayi ya fara tafiya yana tunani yadda zasu kwashe da ummin sa. lokacin da ya isa gida me gadi yabude mai ya shiga yarasa yadda zaiyi da safna dan yasan yanzun ummi batayi bacci ba saitaga dawowan shi , kilama yanzun tana kallon shi, dan haka dibara tafado mai yace safna inazuwa bari naje nadawo. cikin sauri safna ta rokoshi tace dan Allah karka gudu ka barni kaima. cikin kwatar da murya yace bazan guduba safna yanzun zan dawo ai nan gidan mune da guduwa zanyi ai bazan shigo dake cikin gidan muba, ban so ne ummi na ta ganki daddaren nan saboda kartayi wani tunani daban kuma nasan tananan tana jiran shigowa ta, sabo da haka kijirani yanzun nan zan dawo. Gyada mishi kai kawai tayi amman bata son ya bar ta anan. yana shiga ya samu ummi sai zagaye falon take da sauri shi yaje ya rungume ta, hannu ta tasa ta tukude shi. abinda kuma zaka fara kenan yawon dare Ina ka tsaya har 1:30 shiyasa babanka yake cewa ninake sangarta ka. tsugunawa yayi ya kama kafar ta yace immi kiyi hakuri kabir ne be fito da motar saba sai da nakaishi gida kuma ummi kisan gidan su da nisa amman ummi dan Allah kiyi hakuri bazan kara ba. hannun ta tasa ta dago shi ta rungume tace jalal dole hankali na ya tashi kaikadai nake kallo naji farin ciki ya lulubeni nazaci kai kadai ne kwaina a duniya sai daga baya Allah ya kawo mana Kairat alokacin dana cire tsanmani kuma har yanzun baji sonka ya ragu azuciya taba, jalal nakosa naga matarka zataga gatan da babu wacce ta taba samu a gurin sirikar ta, balle kuma naga yaran ka. dukar dakai yayi yana murmushi , ummi tasake cewa jalal baka fara tunanin aure bane har yanzun. da da durkusar dakanshi kasa yayi yana sosa keya. ummi tace yau kuma kunya ta kakeji , hmmm jalal mayan kasan, abin da nake so dakai in katashi nemu mata kasamo mana yar manyan mutane kar ka sake kawo mana yar matsiya ta. 07014197556 [9:30PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed 10-12 jalal ya dago ya kalli ummi yace ba komai ummi karki damu, ummi bari naje na kwanta tace to ba damuwa Allah ya tashi mu lfy,mikewa yayi yanufi hanyar dakin shi ummi ta bishi da kallo tana murmushi har ya Kule. shiko jalal ko dakin shi be shiga ba yabi ta kofar baya ya fita, ya bude murfin mutan yaga safna tayi zuru zuru roko mata hannu yayi suka shiga ciki ya bude dakin shi suka shi , yace kinaji yunwa ne? tace a,a . to ga bayi nan kishiga kiyi wanka inki fito kisaka wannan rigar yanuna mata wata karamar rigar shi. in kin gama ki hau gado ki kwanta da safe zan shigo karki sake ki fito. futowa yayi falo ya kwanta washe gari jalal najin kiran sallah subahi ya mike ya shiga dakin ya tashi safna dake bacci akan makeken gadon shi, sannan ya wuce masallaci. bayan safna ta idar da sallah tana zaune kan darduma, taji anturo kofar da karfi , wata yar yarinya ta gani ba zata wuce shekara biyar ba , tana fadi yaya jalal jiya inata jiranka har nayi bacci baka dawo ba ,waige waige ta fara da safna su kai ido hudu dan haka ta saka kuka ta juya aguje tafita adakin, tana fita sukaci Karo da jalal , yarike ta yana fadin me ya sa meki ? dakin ka naji neman ka ban gan kaba sai wata aljana nagani . Jalal dariya yayi sosai sannan yace ba aljana bace anty ki ce na kawo miki amman karki gayawa ummi. da sauri tace sabo da me baka son ummi ta sani. saboda bana son ummi ta koreta koke kina son ta kore ta. a,a to yaya matar kace. a,a kairat itama kanwa tace kamar yadda kike kanwata , janta yayi suka shiga cikin dakin. lokacin safna na zaune abakin gado tayi tagumi. ya dade tsaye akanta bata masan ya shigo ba. sai da safna ta kwana uku ummi bata san da zuwan ta ba. ummi ko na lura da jalal baya kwana dakin shi kuma yanzu baya cin abinci sai dai yakai dakin shi , sabanin da yana ci yana sha gwaba, dan haka tace azuciyar ta koma me yake baye mata yau zata gain. yauma kamar kullum jalal ya dauke abincin shi ya nufi dakin sa ummi na kallon shi, tana nan zaune har ya fito, binshi da kallo kawai take, ya dade zaune ya mike yace ummi sai da safe, to kawai tace dashi. Yashiga kenan ya zauna yaji anturo kofar , razana yayi ya mike yana fadi ummi lafiya, ummi bata bi ta kansa ba zuwa tayi ta dago safna dake kwance akan gadon jalal tayi wurgi da ita. jalal ya mike da sauri ya daga ta yasa ta ajikin shi yana rarashin ta dan har ta fita hai yacin ta. ummi ce ta kara matsowa cike da mamaki tace yaro Ina kasamo yarinya har ka ajeta adakin ka ban sani ba. kallon shi tayi taga yasa ta a kirjin sa , sai faman rarrashin ta yake, cikin daga murya tace jalal kaine ka kawo min karuwa har cikin gida kasata a kirjin ka agabana dan ka nunamin kai tantirin dan iska ne ko? cikin sauri ya sake safna yace ba haka bane ummi wlh ummi ban taba zinaba kuma wlh safna ba karuwa bace marainiya ce bata da uwa bata da uba kuma abin da yasa na kasa gayamiki nasan bazaki fahimce ni ba ne. ummi tace shi yasa ka muna fun ce ni , to maza maza ka tarkata ta ka fitar min da ita agidan nan, dan kaga na kwalfa rai akanka shine zaka neme ka watsa min kasa a ido , kasani sarai bana hada guri da talaka. abduljalal yace to naji zata fita ummi amman nima bazan xauna ba zan je na nemar mata gurin da zata zauna tunda mu arzikin mu talaka bazai amfana da shiba. cikin taga murya tace ni kake mayarwa da magana akan wata banzan yarinya, to katafi din in baka tafi ba karai na Allah kuka tasa harda kururuwa yau ga dan ta na cikin ta yana mayar mata da magana, tace indai ko kabi yarinyar nan Allah ya isa nono na ?da kasha. Jalal ya zaro ido yace ummi abin har yakai haka, to shi kenan ummi na hakura ke safna tashi ki tafi , safna tana kuka ta mike ta fita daga dakin. Jalal ma tsugunawa yayi ya soma kuka yana fadin ummi,ba ta san kowa ba fa , kuma bata da inda zata ummi marainiya ce fa , ummi ko gezau bayi ba. suna cikin haka suka ga alhaji mustafa rike ta safna ya shigo har dakin abduljalal, ummi da sauri tace alhaji shine bayi waya kana hanya yau ba sai dai kawai muganka. jalal mikewa yayi yakoma jikin dady ya kwanta alhaji yace wanan wacece na ganta Waje tana kuka . cikin sauri ummi tace bamu santa ba. alhaji yace karya kike yi zaliha duk naji abin da ya faru wai kece kike kin talaka dau la yasa kin manta asalin ki, to tun da kin manta bari na tuna miki [9:07PM, 11/25/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn yazeed 13-15 ummi kuka ta fara ta fita adakin da sauri ta shige nata dakin. alhj ya kalli abduljalal yace akan wannan har kake zubar da hawayan ka, meyasa tunda kaji kana son ka tai maketa baka kirani awaya ka gaya min ba, kar ka kara zubar da hawayen ka, bama wannan yariyar ba duk wanda kake son ka tai maka ma kamin magana kabar biyewa ummin ka kaje ko. jalal kwanciya ya da da yi ajikin daddy yana murmushi. alhj ya sake cewa jalal zamu zauna tare da yarinyar nan zan sata makaranta zan riketa kamar yarda na hai fa idai har zakai farin ciki da hakan, amma da sharadi guda daya, sai nayi binkece na tabbatar maganar da yarinyar nan ta fada gaskiya ne. Jalal tsuguna wa yayi yana ma alhj godiya tare da amicewa da maganar alhj. har alhj ya fita ya dawo ,yace jalal raka yarinyar nan dakin kairat, kar na sake ganinta a barayin ka. cikin sauri jalal ya amsa , haka yakai safna har dakin kairat ,kairat batayi bacci ba dan haka taji dadin ganin anty safna a dakinta. bayan alhj ya shiga dakin ummi ya same ta tana zaune bakin gado tana share hawaye, kusa da ita yaje ya zauna ya dafata yace zaliha meye kuma abin kuka. dole nayi kuka alhj naga kana neman ka tona min asiri agaban dana har da wata bare, wadda bamusan asalinta ba, kuma ni din da kake neman wulakantani ai a gaban iyaye na gaje ka aure ni, kuma duk gorin da zaka min nasan be wuce kace ka ganni ne lokacin da nake kora shanon mahaifina ruga ba har kaji kana sona , ai baza a hada da wannan banzan yarinyar ba, kuma ni abinda yafi damu na kar fa jalal yace son yarinyar nan yake dan nikam ko zanyi yawo tsirara bazan bari yaro ya aure taba. alhj ya gama sauraran ummi cike da mamaki yace zaliha kina bani mamaki to meye a ciki dan yace yana son ta, ni dai na dauki alkawarin zan riketa kamar sauran yarana, kuma kema inason kireta kamar yar da kika haifa. ummi tace naji zan riketa amman sai dai in jalal yayi min alkawarin ba aure tsakanin shi da ita. Hmmm zaliha kinan dai akan bakan ki kenan yanzun kuma amiki magana kice ammiki gori, to shi jalal din da kikace sai yayi miki alkawari bazai ce zai aure ta ba, yasan gaibu ne, be saurari me zata sake cewa ba ya fita adakin afusace. ummi kasa bacci tayi dan haka washe gari da safe ta nufi dakin jalal ta same shi kwance akan gado ya najin shigowan ta ya miki, kusa dashi taje ta zauna yace ummi dama yanzun nake shirin nazo na ganki nasan kina fushi dani ummi safna abin tausayi ne , tausayin ta ya kamani. cikin dibara ummi tace na fahimceka jalal komai ya wuce safna zata zauna tare damu amman da sharadin nan gaba baza kace zaka aure taba dariya sosai jalal keyi cikin dariyar yake fadin haba ummi dama akan haka kike tada hakalin ki , idai wannan ne ki kwantar da hakalin ki , ummi me zanyi da safna ga haddadu babys a gari haba ummi ni wlh ummi kin ma bani mamaki yama za ai haka ta faru. ummi ji tayi zuciyar ta fes tundaga ranar ta fara jan safna ajikin ta, hakalin safna ya kwan ta ta koma makaranta ita da Kairat suke ta fiya . akwana atashi gashi yau safna kusan shekaran ta daya da wani abu agidan jikin ta yayi kyau ya murje tayi fes in kasan safna ada kagan ta yanzun zaiyi wuya ka iya shai da ta, fari tayi sosai har nema take ta wuce ummi a fari ga gashin har gadon baya ga cikar halitta ummi ayanzun inta kalli safna har mamaki abin yake bata saika rantse yar wani hamshakin mai kudi ce. shiko jalal rabon shi da ganin safna yama manta dan tunda ya lura ummi bata son ya rabeta ya rege shiga barayin su gaba daya saidai jefi jefi yakan shiga amman allah besa sunci karo da safna ba, sai dai yana samun sakon gai suwata agun kairat dan kulum sai taje dakin sa kuma tana shiga zata ce yaya anty safna na gai da kai hakan na mishi dadi. itako ummi tunda ta lura safna kyakyawa ce murna ta kamata lallai ta samu jari dan haka tafara hada ta har ka da yayan manyan mutane dan acewan ummi safna matar manya ce. yaran masu kudi ne ke zuwa gun safna duk da cewa SS 2 safna take ayanzun amma ita ummi barin ta kudi. yauma kamar kulum safna na zaune ita dawani saurayin ta a harabar gidan ,halal ya faka motar sa bayan yafito yakalli gurin da su safna ke zaune, sultan ya gani zaune agefe sai dai yarinyar be gane ko wacece ba amma fah Allah yayi halitta agurin nan, azuciyar shi yake tunani me ya kawo sultan da budurwar sa tadi gidan su, inda wani shashi na zuciyar shi kecewa Ina ma ace ya mallake yarinyar nan, dawan nan tunani ya shiga gida, yana shiga ya samu ummi zaune a falo , zuwa yayi ya kwanta ajikin ta. ummi tace yaya dai yaro, lfy naga jikin ka a sanyaye? ummi wata yarinya nagani ita da sultan awaje. murmushi ummi tayi tace jalal safna ce baka gane ba. jalal tashi yayi ya zauna yace ummi kina nufin safna ce ke tadi da sultan? ita ce mana ai safnar tamu ta waye sultan ya rikice akanta, ummi bata gama fadan maganar bakin taba taga jalal ya mike cikin fusatan da bata taba ganin shi cikin saba, itama mikewa tayi tana fadin me ya tada maka hankali ne jalal. waje yayi da sauri ummi bayan sa tabi tana kiran jalal jalal. amman ina besan ma tayi ba sai da ya isa gurin ya kare mata kallo riga da wando ne jikinta sun kamata sosai tabas kamanin ta basu bace masa ba, cikin fada yace da sultan malam tashi ka fita agidan nan. sultan cike da mamaki yace ban gane na fitaba ai ba gurinka nazo ba. eh koma gurin wa kazo karna kara ganin ka gidan nan, cikin tsawa yace ke tashi kishiga gida. cikin sauri tamike zata bar wajen, sultan ya tashi ya rike safna yana fadin babu inda zata sai mungama maganar da muke. duk abinda suke ummi na daga kofa tana kallon su, jalal ji yayi ya kara kulewa waton sultan ya saba rike safna kenan, jalal jiki na rawa ya fara kaiwa sultan naushi [7:41PM, 11/26/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn yazeed 16-18 ummi karasowa tayi da gudu ta rike jalal tana fadin jalal baka da han kaline ,me yayi maka, da ker ummi ta janye jalal daga jikin sultan, hancin sa har ya fara fitar da jini. ummi matsawa tayi kusa da sultan tace sultan jeka gida zan zo na same mamar ka, yace ummi amman dai kin ga abinda yayi min ko? na gani kuma zanyi maganin sa, ka kwantar da hankalin ka. sultan girgiza kai kawai yayi, ya shiga motar sa yabar wajen. Jalal na tsaye sai huce yake yi , safna kuwa dama tun da taga fada ya kaure ta ruga da gudu ta shiga gida ummi ce ta juyo ta kalli jalal dake tsaye ban da huce babu abin da yake yi, tace muje ciki, gaba ya shi ga ummi nabin sa a baya. suna shiga ummi tace me kake nufi da kake koran ma safna saurayi. sai da ya dukar dakai sannan yace ba abin da nake nufi ummi kawai tarbiyan da akama safna ne ban ji dadin ganin ta ahaka ba, kuma ummi be kamata abarta tana kula samari ba, ummi sultan fah ba mutumin kirki bane lalata yaran muta ne kawai yake yi. sai da ummi ta karewa jalal kallo san nan tace, jalal ni fah na haifeka kar ka manta kamin alkawarin babu aure tsakanin ka da yarinyar nan , to meye naka na tada hankalin ka dan ka ganta da wani, to bari kaji na fada maka daga yau babu ruwan ka da safna sultan auren ta zai yi kar na kara ganin kaje kusa da su , inhar kana son azauna lafiya. amman dai ummi ai be kamata ace za,a mata aure yanzun ba. babu ruwanka ba abinda ya shafe ka, suna cikin haka suji sallaman hajiya baturiya mahaifiyar sultan tana rike da hannun sultan, jalal be sauri me zasu ce ba, ya nufi dakin kairat ya samu safna kwance sai kuka take, ya dade tsaye akanta bata ma san ya shigo ba, sai da ya kare mata kallo sannan yace safna, da sauri ta dago ta kalleshi. Ya sake cewa safna kina kuka na korar miki saurayi. gargiza kai tayi tace ba haka bane yaya ni fada ne bana son naga anayi. Jalal murna ta kama shi ashe dai tana da hankali. yace safna daga yau karki kara zuwa gurin sultan , ba auren ki zaiyi ba kamar yadda ummi take fada, in na kara ganinki da sultan ranki zai baci, ya sake kwantar da murya yace ko kina son sultan din ne? Shiru tayi, tayi kasa da kai dan jalal ya mata kwar jini da yawa, dan gani tayi ya kara mata kyau duk wanda tayi dace ta samu jalal a matsayin miji ta more. Jalal sake maimaita tambayan sa yayi safna nace ko kina son sultan din ne. kanta akasa tace ni dama ummi ce take tura ni. dadi yaji sosai ban da shi akwai wasu da ke zuwa gurinki ne? eh tace dashi. to daga yau koma wanene yazo karki Kara fita, kuma safna me yasa kike fita waje a haka, har ki zauna kina hira da wani dubi jikin ki fah duk awaje yake, kanki ko dan kwali babu, haba safna sai kace ba yar musulmai ba, baki da hijjab ne ko gyale. safna ta kalli jikinta gaskiya jalal ya fada kwata kwata be tace ba, tace ina dashi yaya amman ummi tace na dai na sanya hijjab idan zan fita. Jalal shiru yayi nadan wani lokaci san nan yace karki kara saka irin wadan nan kayan, mijin kine kawai ya kamata ya ganki da su, kuma inzaki fita ki sanya hijjab ko gyale , kinji ko? juyawa yayi zai fita safna ta bishi da kallo har ya kule. lokacin da jalal ya fito ummi kadai ya samu a falon dan haka besan me suka shirya ba, zuwa yayi ya wuce ummi da sauri ya shiga dakin sa, ummi binshi tayi da kallo ta mike ta shiga dakin safna, wani mugun kallo ta mata sannan tace jalal nan ya shigo? eh. me yace miki? cikin in ina tace ba komi. saukan mari taji a fuskar ta ke dan ubanki ni zaki ma karya zaki gayamin ko sai na miki illa. safna tana kuka tace cewa yayi karna kara fita gurin wani. Lallai kuwa ashe ba zaman lafiya kinzo har gida zaki rabani da dana, to baki isa ba Bayan kwana uku da yin haka jalal yasa ma safna ido sosai dan yanzun yana zama agida sosai . yau ko ya kula ummi shirye shiryen fita takeyi, ya name guri ya zauna afalo duk da cewa ummi fushi take dashi, ba kamar da ba. kalon shi tayi taga bashi da niyar tashi tace yau bazaka fita bane? zan fita amman sai an jima. tabe baki tayi ta kira safna tamika mata wata leda tace kaya ne aciki maza ki sa kizo mutafi, ta karba ta juya. jalal ko jira yake yoga wani irin kaya ne. ummi ta gaji da jira, ta sake daga murya tace wai me kikeyi har yanzun. cikin sauri tace ummi ganinan zuwa ta kara kasa da murya ummi yaya jalal fah yace na daina yawo a haka. ummi tsaki tayi, ki fito kina bata min lokaci, ta mike ta fita, jalal na zaune saiga safna ta fito ta matse riga da wando ne jikin ta sai wani dan kamin gyale, a tsorace ta wuce shi ya bita da kallo, har ta fita yaga bazai iya jurewa ba ya mike yabi bayan su Lokacin tuni ummi ta shiga cikin mota,itako safna kokarin shiga take, jalal yace safna karki sake ki shiga cikin motar nan. cikin fada ummi tace wai kai jalal Ina wasa dakai ne ko ni abokiyar wasan ka ce, ummi wlh safna bazata fita tsirara ba [8:04PM, 11/27/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 19-21 Bude murfin motar tayi ta fito, ta zagayo ta rike safna tana tura ta cikin motar, jalal ma riketa yayi yace ummi ki dai na irin wannan babu kyau fah, cikin tamke fuska tace sake ta jalal idai ba kana son ranka ya baci bane. ummi dan Allah kibari ,ta canxa kaya sai ku tafi. zuwa tayi gaban shi tace wlh wlh in baka sake yarinyar nan ba ranka zaiyi mummunan baci, kasake ta kawai. dukar dakai yayi ya kara rike gefen rigar safna ciki tashin hankali ya dago ya kalli ummi ya sake dukar da kai. Safna na tsaye tsakiyar su tayi tsuro tsuro, ummi ta sake cewa ba dakai nake magana ba, gani tayi ko motsi ba yayi dan haka ta taho gadan gadan ta kwashe shi da mari. da sauri jalal ya saki safna ya dafe wajen dan shi atunani shi babu wanda ya taba dukan shi. jalal kallon ummi yayi cike da mamaki, yace ummi nine fah, jalal dinki ne fah. ummi bata saurari me jalal yake fada ba ta tura safna mota suka bar wajen. binsu yayi da kallo yana bakin cikin wai mahaifiyar shice take wannan dabi,a wai yaushe ummi ta canza , shi dai yasan ummi na son farin cikin shi. Yana nan tsaye drive ya dawo da kairat daga makaranta, tana fitowa ta hango jalal da gudu ta karaso ta rikeshi, gani hawaye tayi yana bin kuncin sa tace yaya waye ya dake ka. Jalal da besan hawaye na fita ba yasa hanu ya shafa idon sa yace idona ne yake ciwo, riko hannuta yayi suka shiga gida, kairat taso ta bishi dakinsa yace mata bacci yake ji. tunda jalal ya shiga daki yasa key, yau dau ki waya ya kira mahaifin sa har ta katse be dauka ba, ya ajiye wayar ya kwanta ,da matsa nan cin bacin rai yau da ummi ba mahaifiyar shi bace da sai ya dauki mumunan mataki akanta, shi bema san me yake damun saba illa dai kawai yasan yana matukar kishin safna wanda ko mace yar uwanta baya son yaga ta cika kallon ta da yawa, bare kuma na miji. su ummi basu dawo ba sai wajan 9:00 shiko jalal tun yamma zazzabi ya rufe shi dan ko sallah ma a daki yayi ta. ummi na shigowa hara bar gidan taga motar alhj tace wai nikam me yasa alhj yake min haka, inzai dawo bazai sanar dani ba saidai na ganshi kwatsam. da sauri ta fito safna ma ta fito ummi tace ke dakata duba cikin ledan cen ki dau hijjab ki sanya, safna ta juya ta dauko wani zumbulelen hijjab har kasa ta sanya. suna shiga alhj na zaune afalo ya rufeta da fada, kwantar da kai tayi tai ta bashi hakuri, safna kuwa sumi sumi ta shige daki. sai da yagama zazzaga bata sannan yace ina abduljalal tare kuka fita? a,a mun barshi gida. toh ina yaje kuma sunce kwata kwata yau beje office ba wai me yasa yaron nan yanzun duk yabi ya rikice ne, shifa ya matsa sai na bude mai kamfani kuma dan me yanzun zai sanya wasa, dazun nakira shi wayar shi kashe take, wai me yaron nan yake nufi ne. ummi tace haba alhaji sai faman fada kakeyi kayi hakuri duk ma inda yake nasan hankalin sa na gida. ********* barin zancen sukayi suka kama wata hirar, kairat ce ta fito tana dari daddy daman kadawo shine baka kirani ba. cikin murmushi ya rike ta yace kairat na rude ne har yanzun abduljalal be tadawo gida gashi wayar shi kashe take. cikin sauri tace daddy dazunfa an daki yaya jalal a office din su yana ta kuku, amman sai yayi min wayau yace wai idon shi ke ciwo kuma yaki bari na bishi daki wai shi barci yake ji, cikin shagwaba ta karasa zance ta. ummi kuwa Cikin ta kara ya fara dan bata zaci zai dau abin da zafi haka ba. alhj ko kallon ummi beyi ba yatashi ya nufi dakin jalal ya tura kofar yajita kulle , juyowa yayi ya kira ummi yaron nanfah bashi gidan nan, cikin rudewa tazo ta wuce alhj ta isa kofar ta fara Kira yaro yaro shiru, jalal jalal nanma shiru kuka ta saka tana fadin nashiga uku, alhj ya daga murya yace abduljalal, da sauri ya amsa na am daddy. yace zoka bade min kofa. yana rawan sanyi yazo ya bude kofar rige rige suka fara kowa na kokarin kai hannun shi jikin jalal komawa gado yayi ya kwanta . alhj ya dafa jalal yace me ya same ka, waye ya tabaka dan waye agarin nan, ka gaya min waye uban sa. ummi ce ta kawo hannu zata tabashi, yace daddy kace mata karta tabani daddy kace ta fitan min adaki. alhj yace jalal ummin kace fah wai baka cikin hankalin kane. ina sane daddy cikin hakali na nake kawai bana son ganin ta ne. tsawa alhaji yayi wa jalal mahaifiyar ta ka kake cewa baka son gani kar na kara jin wannan kalman abakin ka. shuru jalal yayi yana kuka kasa kasa ummi na makure jikin bango , alhj ya dago yace to ya isa dai na kuka sai kace ba namiji ba lallai ummin ka tayi laifi, abduljalal gayamin me ummin ka tamaka da zafi haka har kake zubar da hawaye. Jalal juyar da kansa gefe yayi sannan yace daddy ummi nasa safna nayin shigan banza tana fita waje, kuma nayi magana ummi ta mareni. mari ? zaliha ke kika mari jalal akan me, alhj mikewa yayi ya daki kirjin shi yace dana kika Mara 07014197556✍ [7:59PM, 11/28/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido MmnYazeed๐Ÿ“ *Gaisuwa zuwa gare ki Faty afreen marubuciyar* ๐ŸŽพNIDA SOJANA๐ŸŽพ *bansan taya zan mika godiyata a gareki ba saidai nace Allah yasa kifi haka๐Ÿ‘๐Ÿป* *Jinjina agareki* *Ummi Ridwan* *da duk daukacin* *members na* _Precious writer's porum_ *kuna burgeni๐Ÿ˜˜* 22-24 Akan wani dalili kika mare shi ? ciki sanyi murya ummi tace alhj mun shirya zamu fita da safna har nashiga mota amman jalal yasa hannun shi yarike safna wai bazata shiga ba dan ya raina ni. Jalal ya bude baki yace ai shigar da tayi ne be kamata ta fita dashi ba. Cikin fada ummi tace kasan shigan da tayi be dace bane kai kasa hannun ka ka taba ta, ko muharramar kace ita. shiru yayi ya juyar da kansa gefe alhj yace to ya isa ke zaliha daga yau karki kara dukan jalal, inbanda ma abinki ya za,ai ki mareshi gaban safna, kanwar sace fah. haushi ya bani alhj. to shikenan kisan yanzun me zai faru, daga yau kar safna ta kara fita gidan nan inhar ba makaranta zata ba, ya juya yace jalal magana ta kare ko ? shiru jalal yayi alhj ya sake cewa ko akwai saura ne halal eh daddy, da sauri ummi ta harareshi dan haka yayi shiru. sai da alhj yasake cewa ina jinka abduljalal meye kuma? daddy kuma fa har samari zuwa gurin safna suke kuma ai karatu take. alhaji dariya yayi yace abduljalal kai duk matsalan ka agurin safna take, toh jalal kodai son safna kake ne? sai da ya kalli ummi san nan yace a,a. itama ummi kallon sa take. alhj yace ya hausan a,a jalal karfa kai kwauron baki wani yama kafa ya sake yin dariya, san nan yace ke zaliha kina fah shige mana hanci, kuma daga yau kar safna ta kara fita wajen wani. haba alhj wai me yasa kakeyin haka jalal ne zai rinka juyamu agidan nan duk abinda ya fada kawai sai ka yan ke hukunci. murmushi yayi yace naga kamar yana son ya fiki hankali ne, be jira me ummi zata ceba ya fita adakin itama bayansa tabi. ************ suna fita yaji zuciyar sa tamai fes tare da mamakin ya akai daddy ya dago shi ai lokaci beyi ba, ba yan zun ya kamata su sani ba sai ya samu soyayar safna neman zazzabin yayi ya rasa. washe gari ana kiran sallan subahi ummi ta nufi dakin jalal yana kwance yana bacci ummi ta fara tashin shi yaro tashi kayi sallah, tashi yayi ya zauna, ummi tace yajiki ko asibiti zamu, da saurin sa yace naji sauki ummi nama warke. bayan ya dawo daga masallaci be koma barci ba kamar yadda yake yi ada sai ya fara shirye shiyen fita kananan kaya ya saka yayi kyau matuka ya fito falo ya zauna babu kowa afalon ya nan zaune safna ta fito da gudu bata san cewa da mutun afalon ba taci karo da kafar jalal har ta fadin kasa kara ta sake dan taji zafi sosai. da sauri jalal yamike yazo gaban ta ya tsuguna yace sorry safna kawo na duba miki. cikin kuka tace bana so bakai bane kasamin kafa, badu baki yayi cikin mamki yace yazanyi nasa miki kafa bake kika fito da gudu ba, be jira me zata ceba ya kama kafar ya matsa, fashewa tayi da kuka sai da su ummi da alhj suka fito suna fadin lfy. ganin jalal sukayi rike da kafar safna itoko kuka take cikin daga murya ummi tace me ya faru? Jalal yace faduwa tayi ina tunani kamar buguwa tayi . ummi tace alhj wai wannan ne kake cewa yana da hankali ji inda ya ke taba ta . mikewa yayi yana fadin ummi wani irin magana kikeyi, safna tashi muje asibiti ummi bata so jalal yakai safna asibiti ba, domin bata son sultan yagan su tare dan suyi da hajiya baturiya yau zasu turo mata makudan kudi, tayiwa safna sayayya duk da cewa hajiya baturiya tasan halin danta ba aure ne agaban saba, amman duk yarinyar da ya nuna yana so sai taita kashe kudi dan ta faran ta mai rai. Jalal kuwa tundaga ranar ya kasa ya tsare safna bata fita ko ina dan ummi na tsoron mijinta kwarai. jalal ko jan safna yake ajiki sosai harta fara sakin jiki dashi kullum daddare zai aika kairat takira safna suyi ta hira suna dariya. ummi na kwance adakin ta taji sai dariyar jalal da safna take ji ta daga kai ta kalli agogo 11:38 gaban ta ya fadi karfa ace jallal soyayya yake da yarinyar nan wani bangare na zuciyar ta nacewa ai kwanakin baya baban sa ya tambaye shi yace a,a to amma kuma wannan wani irin sabon salon ne, koma dai menene bazata taba bari jalal ya aure safna ba, yarinyar da sultan yayi soyayya da ita kilama yanzun tana dauke da cuta da wannan tunani ta zabura, tana fadi baza ta sabu ba cikin sauri ta fito jalal naganin ta yace ummi bakiyi bacci ba. eh banyi ba, tashi ka wuce daki tun daga ranar ummi ta hana safna fitowa hira jalal na zuwa falo saidai yaga ummi har tsawo sati daya besa safna a idon saba hankalin jalal ya tashi, itama safna kewan jalal take sosai. washe gari da safe jalal ya fito cikin shirin shi na tafiya office bayan ya gaida ummi yamike ya nufe dakin safna, ummi ta kirashi ya dawo ina kuma zaka, inace office zaka tafi? eh fita zanyi amman ina son naga safna kafin na fita. Me zaka mata? ummi na dade bansa ta a idona na ba fah ,ganinta kawai zanyi na wuce wai yaro ni zaka munafunta karka mance kamin alkawarin bazaka aure safna ba inma ka fara tunanin aure ne sai kaje gida yayata ka auri yarta aliya dan tun tana karamar ta take sonka. toh ummi naji munyi waya da daddy yace yau zai dawo inya dawo sai muyi maganar adawo lfy, jalal yasake cewa ummi naje naganta kona minti biyu ne? Kiri kiri ummi ta hana haka ya tafi jiki babu kwari yamma likis jalal ya nufu gida yana shiga falon yaje jikin alhaji ya kwanta ummi bata gurin sai safna da kairat dan alhaji fira yake sosai da su safna ta juya takalli jalal taga yayi dare dare jikin daddy ta kwashe da dariya tace daddy kace ya daina hawa maka jiki karya karya ka. daddy ma dariya yayi yace safna ai ke bakiga komi ba sai in beda lafiya zakiga har kuka yakeyi. Kairat da safna sukara saka dariya. jalal yatashi ya zauna yakali safna yaga sai dariya take yace ke ya isheki, daddy kaga zakasa suraina ni. suna cikin haka ummi ta fito tana fadin ai jalal ya girma ne besan ya girma ba dazun nace mai yaje gurin aliya su daidai ta. alhj yace wacce aliya yar wajan Rabi? eh ita kuwa ashe baka manta suba. au yanzun kuma kintuna dasu, inace zuwan su gidan nan nawa kina musu korar kare, to waima bari na tambaye ki, kisan inda su baffa suke yanzun, ummi mikewa tayi zata bar wajan, alhaji yace dan dakata zaliha na samar wa jalal yarinyar da zai aura safna ma na mata miji. Jalal zabura yayi yamike ya rike kafan daddy yace daddy karka min haka dan Allah ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ [9:11PM, 11/29/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 25-27 Alhaji ya kalli jalal yace jalal ko kana da wacce kake so ne? jalal ya bude baki zai yi magana ummi tace babu wata wace yake so alhaji haka yayi daidai. safna mike wa tayi tana kuka ta shige dakin su, alhj yabi ta da kallo, ya juyo ya kalli jalal dake tsugune agaban sa, yace jalal in kana da magana kayi mana. amman jalal da zaran ya daga kai zai yi magana sai ya kalli ummi ya dukar da Kai. alhaji ya lura da haka yace jalal tashi ka zauna an jima kasame ni dakina sai muyi magana. Jiki babu kwari jalal ya mike be zauna afalon ba dakin shi ya shiga. ummi ko abin nema ya samu dawowa tayi ta zauna alhaji a ina kasamo wa jalal yarinya? Yar wani amini na ce yarinyar akwai hankali idai mukai sa,a jalal na santa toh gaskiya munyi dacen sirika. ai alhaji ba biye musu zakayi ba daga shi har safna. a,a zaliha ai ko zamanin mu ba,amana auren dole ba bare yanxun, kina ganin jalal aka hadashi da yarinyar da baya so akwai zaman lfy ne, ai gara ma safna ina ganin ko bata so zata zauna dan naga yarinyar akwai hankali, amman jalal ai rikitatce ne. amman alhaji gaski indai zaka dauki shawara ta karka saurari kowa acikin su. alhji saida ya kaikaice yace zaliha ban hankalinki, ina son kicire hannuki cikin wannan maganar, ni akwai abinda na shirya kibarni dasu in nagama magana dasu zan gaya miki. amman dai alhaji bakayi min adalci ba, in ba azayi shawara daniba akan auran safna ai kayi dani akan na jalal, saboda ina da hakki akansa kuma nina san zafin sa. cikin fada da hargagi alhaji yace nikuma bansan zafinsa ba saboda roroshi nayi ko? a,a nidai ban ce ba gadai rorarriyar ce wacce ba,asan asalinta ba, wlh alhaji idai kana son naci gaba da zama gidan nan sai safna ta bar gidan nan, yau din nan. toh dama dai akwai wani abu azuciyar ki akan safna meta miki, me yakawo maganar safna toh safna bazata bar gidan nan ba in kinga zaki tafi kitafi inzaki zauna ki zauna wannan ruwan ki, baki isa ki juya ni agidan nan ba, dan kinga inasonki yasa kikemin abinda kikaga dama, gashi ina ji ina gani yan uwana basa zuwa gidana saboda sungaji da bakin halin ki. ******* ummi cikin zafin zuciya ta mike to alhaji nagode tunda idon ka ya rufe akan tsintaciyar mage zakamin rashin mutunci alhaji ma zafi ya dauka yana magana da karfi ai bakiga rashin mutunci ba sai kinci gaba da mayar min magana zaki gane koni Waye. Suna cikin haka jalal ya shigo yana share hawaye yace daddy dan Allah kuyi hakuri ku bari. alhaji kunyace ta kamashi ya manta yaran suna cikin gidan, yace bakomai jalal jeka abin ka, kasa tafiya yayi ya nemi guri ya zauna dan haka alhaji ya shige dakinsa, ummi ma tashi tayi ta shige nata dakin. tun daga ranar gidan ya rikice kowa zuciya babu dadi ana cikin haka alhaji ya gama kwanakin sa ya koma, safna ko duk abinda yafaru ta sani har azuciyar ta take tunanin itako me tama ummi ta tsane ta, jalal kuwa jira yake yaga daddyn sa sun shirya da ummi ya gaya masa shifa safna yake so. wata rana ummi na zaune afalo saiga wata kawarta tazo ummi ta mike suka rungumi juna janta tayi suka zauna ummi tace madina kinga yadda kika koma kowa. dafa ummi tayi tace ke kowa ina gidan mijina hankalina kwance bani da matsalan komi, ummi tariya tayi tace hmm madina kenan, madina kar kacewa tayi tace akwai matsala ne zaliha? ummi bata boyewa madina komi ba, har rikicin su da alhaji. madina fada ta farawa ummi ke ko sai kace wata karamar yarinya meye naki na fada da miji, baki iya kissa bane har zaki zauna kina bata ran ki, shima jalal ai be kamata ki nuna mai baki son yariyar ba tunda kinyi sake ya fara sonta, yanzun kina nuna baki sonta sai ya juya miki baya , madina ta ciza yatsa Allah baya ba me wuka nama da nice da tuni na wargaza su, haka madina taita ma ummi fanfu da shawar wari iri iri , madina batabar gidan ba saida tasa ummi ta kira alhaji tabashi hakuri. alhaji yaji dadi sosai dan bashi da roko kuma yana son matar sa, bayan kwana uku alhaji ya dawo, tabbas yaga canji agurin ummi iri iri , da daddare ummi takaiwa alhaji abincin sa har dakinsa suna cikin cin abinci jalal ya buga kofar alhaji yayi mai umarni ya shigo ganin ummi a dakin abin yabashi mama yanai mi guri daga gefe ya zauna, alhaji ya kalleshi yayi murmushi yace zaliha sai naga kamar jalal ya rame, ummi kallon jalal kawai tayi yake dan tasan kome ke damun sa. Jalal yace daddy nazone muyi magana ba kwanaki kace zamuyi magana ba? eh hakane jalal maganar auren ku ko? jalal bece komi ba ya kalli ummi yace daddy ko mubari sai gobe ne? a,a ke zaliha bamu guri zamuyi magana. dariya tayi tace haba jalal yanzun nice bazaka iya magana gaba na ba, kuyi maganarku babu ruwana nina kosa ma naji wacece sirikar tawa. alhaji yaji dadin maganar ummi dan haka yace jalal wacce yariyar kake so? jalal ya dokar dakai yace safna. alhaji daure fuska yayi yace jalal lokaci ya kure nariga na bada safna , saida na tambaye ka da farko kace basanta kake ba. [7:29PM, 11/30/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 28-34 Dagowa yayi da sauri ya kalli daddy yaga daddy ko ajikin shi, abincin shi ma yaci gaba daci, ya mayar da kanshi kasa, cikin murna ummi tace jalal kayi kuskure da kasani ka fada da wuri gashi yan zun kama kan ka. ummi lokaci fa be kure ba sai dai in kun zabi wani akaina, ya miki zai fita alhaji yace kashirya anjima kaje kaga yarinyar, bece komi ba ya fata adakin. yana fita alhaji yayi dariya yace zaliha kifara tanadi dan baza,a sa da yawa ba, cikin murna zaliha tace ai alhaji shiri zanyi sosai yara biyu fah, jalal yana barin dakin daddyn sa, dakin safna ya shiga ya same ta zaune tayi kuka idonta duk sun kunbura, tana ganin shi ta durkusar dakai, jalal yaje daf da ita ya zauna safna kuka kikayi har idon ki suka kunbura haka , me yake damunki ko kema baki son auren ne? shiru tayi ta kasa magana bazata iya gayawa jalal cewa shitake soba itama kanta tana ganin lefin zuciyar ta datake son wadda yafi karfinta, jalal ne ya katseta safna nifah bazan bari amin auren dole ba, safana zan tambaye ki amman ina son kimin alkawarin zaki gaya min gaskiya tsakanin ki da Allah . me zai hana yaya jalal indai na sani zan fadama ka. safna tsakani da Allah babu wani da kika taba jin kina son ki aura. hawaye ne suka gangaro mata dan bata zaci wannan tambayar ba ,tace akwai. jalal yace waye wannan safna? yaya jalal mubar wannan maganar ai kai ma baka fadamin yarinyar da kake so ba. Safna ni bani da budurwa saidai ko zakimin hanyar kawar ki sai na aura. tace to aigashin nan daddy yasamar maka. shi ko jalal so yake yayiwa safna wayau yaji ra,ayinta kuma ya rasa tayaya zai fara kuma yana tsuron karya fada tace bata sonshi, dago kan shi yayi ya kalli safna yace, ni bana so ta gurin daddy ta gurinki nake so. wai kai yaya dan Allah da gaske babu wacce kake so? jalal yace gaskiya akwai safna amman tsoron gayamata nakeji kartace bata sona. safna mantawa tayi dawa take magana tace , kai๐Ÿ‘‰๐Ÿป yaya jalal wacece zata kalleka tace bata so. cikin dauki yace da gaske safna,saboda me kikace haka. yaya wlh babu wacce zata ce bata soka komai kyanta komai kudin gidan su sai dai kawai inbata samu ba, kai baka san ka hadu ba ne, wlh yaya kai kyakyawa ne kana da kyau sosai. dadi sosai jalal yaji ya kashe murya yace toh safna ko zaki taimaka ne ki aure ni. Sai alokacin safna tatuna tayi subutar baki ciki tashin hankali ta mike zata fita tana fadin mezaka ci dani? da sauri jalal yamike ya rike safna yace karki kara cewa haka safna, na dade Ina sonki Ina tunani karkice baki so nane shiyasa ban gaya miki ba, fashewa tayi da kuka tace me zakayi Dani rorarriya mara dangi bani da kowa fah jalal , kaikuwa dan gata ne ummi da daddy suna matukar sonka. tausayin safna yakama jalal besan lokacin da yasata akirjishi ba itama lafewa tayi kamar karama yarinya yace safna kema suna sonki, nima kuma Ina matukar sonki dan haka karki kara cewa baki da kowa, mune dangin ki. a,a yaya ummi bazata bari ka aure ni ba. a hankali yace safna karki kara kiran sunan ummi akan wannan maganar ba runwan ki ,nidai kawai abinda nake so dake , idan daddy ya tambaye ki kice ni kike so , kinji? suna cikin haka sukaji anturo kofar miryar ummi sukaji tace jalal. zabura sukayi da sauri yasake ta. ummi tace zoka wuce daddyn ka nakira, jalal wucewa yayi yana sosa kai yabar ummi adakin. *********** safna bakin gadon tabi ta zauna, ummi ta harare ta, tace yar iska kawai zata koyawa yaro iskanci, in Allah ya yarda saikin bar gidan nan, baza kizo ki lalata mana yaro ba. bayan kwana biyu hakalin jalal ya kara tashi dan yaga sai shirye shirye ake agidan ya sake koma wa wajan alhaji ya kara gayamai shifa babu wacce yake so sai safna alhaji yace wai dama da gaske kake ne, aina dauka wasa kakeyi, to kabari zanyi shawara. ran jalal beso haka ba amman yasan abinda zaiyi yace daddy yau gidan hajiya zani. alhji yace ya kamata jalal inkaje ka gaida ta, yace tare da safna zantafi, kafin alhj yace wani abu ummi ta shigo Ina zaka da safnan kuma? gidan hajiya zamu. alhaji karma barshi ya tafi da ita ban yadda da jalal ba ,ya canza hali. alhj yace wani irin magana ne wan kuma. wlh alhaji rannan ganin jalal nayi rungume da safna kaga kuma be kamata suna fita waje tare ba. alhaji ya kalli jalal, yace abduljalal haka ne? shiro yayi ya dukar da Kai, alhji yace tashi ka bani waje. jalal yaso ya leka gurin su safna amman ya fasa ya wuce gidan hajiya. hajiya mahaifiyar alhaji ce kakar jalal tana matukar son jalal dan duk cikin jikokinta shi kadai ne namiji sauran duk matane kuma kanana ne yayanta guda uku ne mahaifin abdul jalal shine babba sai kaninsa wadan yanzun ne ya samu haihuwa yarssa mace kusan garman su daya da kairat sai kanwar su mace anty nusaiba bata dade dayin aure ba tun lokacin da alhaji ya kawo zaliha amatsayin wacce zai aura, hajiya ta nuna batayi na am ba, amman daga baya taga ya matsa ta hakura akayi. bayan ummi ta haifi jalal suka gane bata son mutane duk wanda yaje gidaรฑ saita mai wula kanci, dan haka suka hakura da zuwa gidan. jalal ya shiga gidan hajiya tun abakin falo yake fadin matassss. ah,ah dan duniya saiyau ka tuna damu daidai lokacin jalal ya shiga falo yaje kusa da ita ya zauna, yace wlh hajiya kina raina abubuwa ne suka min yawa, shiyasa baki ganni ba. kai dai kace mahaifiyar ka ta hanaka zuwa koda yake harda laifin baban ka aishi kullum yana zuwa ai sai ya tasoka gaba, amman ku kuka sani, nidai kujera ce. jalal yace hajiya kiyi hakuri ni bawan da ya hanani zuwa, ni yanzun ma akwai abinda ya kawoni. toh ina jinka me ya kawo ka. ya kwashe duk abinda yake faruwa ya gayawa hajiya. dariya tayi tace jalal ai ina da lbrn komi baban ka yagaya min komai tsokanan ka yake amman har an tsai da ranar biki sati uku masu zuwa , karka kara tada hankalin ka , me yasa baka taho da safna ba, ko baka son naga kishiya ta. hajiya wai dan Allah da gaske kike yi? jalal na taba irin wannan wasan ne dakai? hajiya bari naje gobe zan dawo yana shiga gida yasamu alhaji afalo alhji yayi dariya yace jalal kadawo daga kai karar tawa ne? jalal ya sosa kai yace ba haka bane daddy ni gai sheta naje . jalal kana nufin ban san halin da kake ciki bane, nagane kana son safna tun ranar da naga kishinta karara a idon ka, amman sai kamin karya kace basan ta kake ba, kuma nama haka ne dan kar ka ga kasa meta asauki nan gaba kace zaka wulanta ta jalal safna itama mutun ce kamar kowa duk son da nake maka inhar ka wulakanta ta , zamu raba hanya dakai kuma daga yau na haramta ma shiga dakin safna, inzaku yi hira kuyi afalo , suna cikin haka ummi ta fito , alhaji yace kafin kizauna kiramin safna. ummi ta shiga ta kama kunnen safna ta rike sannan tace idan alhj ya tambaye ki kina son jalal kice a,a, idon safna cike da kwalla tace toh ummi. suna zuwa safna ta zauna akasa, ummi ko tunkan ta fito tawashe fuska, alhj ya kalli safna yayi murmushi yace yace safna ki fara shiri bikin ku nan da sati uku masu zuwa na zaba miki yayan ki jalal. zufane ya fara karyo ma ummi tace alhj ita baka tambaye ta ko tana sonshi ba. a,a basai na tambaye taba nasan ma tana sonshi ai dama tare muka gansu. Jalal ya kalli safna yayi murmushi, itako safna kanta na kasa banda far gaba ba abin da yake damun ta. alhj yace jalal naga kamar bakinka akwai magana? daddy ranar ne naga kamar yayi yawa ko za ,a dan rage ne ummi mikewa tayi ta buga tsaki tashige daki, tashiga tunani gakiya nayi kuskure dahar na bari wata alaka tashiga tsakin sultan da safna gashi aure yana neman shiga tsakanin ta da dana kuma zaiyi wuya ace sultan bashi da H.I .V [7:02PM, 12/1/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 35- 40 Ummi kwana tayi kuka ta shiga damuwa mutuka atake tunanin iyayan ta ya fado mata haka iyaye sukeji idan suga dan su zai shiga cikin wani hali, to yanzun wani hali iyayan ta suke ciki na rashin ta da sukayi, yau she rabon ta da ganin su, tun kusan shekara goma shatara da suka wuce lokacin jalal yana karami, bazata manta ba tun lokacin da sukazo kawayen ta na gidan tace musu suyi sauri su koma gida kar kawayan ta sugan su tanan zuwa, suka tafi cikin bacin rai, suna fadin tunda baki son agan mu a matsayin iyayenki karki kara zuwa inda muke, taso washe gari tabisu tabasu hakuri amman tana cikin shirin tafiya saiga yayarta rabi tazo cikin kuka tana gaya mata cewa jiya dasu baffa suka zo gurinki sun taho da saudatu ba aganta ba taba ce, sanadi haka baffa yana cen ba lfy mama ma ba lfy ta cika ba, yan zon nazone kizo muje nemanta ko Allah zai sa adace, ummi kin binta tayi ta dauko kudi ta mika mata tace kije ki duba ta nima ba lfyr gareni ba, in nashiga rana ciwona zai iya tashi kije duk halin da ake ciki kizo kisanar dani. yaya rabi batayi musu ba ta wuce , haka yaya rabi tayi ta zaga gari har tsawon kwana uku tasake dawowa gurin ummi akarshe dai ummi koran kare ta mata tun daga ranar babu wanda ya sake zuwa gidan ayanzun haka ummi bata saniba ko anga saudatu ko ba,agan ta ba, amman ita tana ganin angan ta, haka ummi taita tunanin baya, tare da ganin wautan ta da ta bari har haka ya faru, yanzun ya zatayi ta shawo kan iyayen ta kilama alhakin iyayen tane gashi yanzun har ansa ranar auren jalal dan cikinta amman ba,ayi shawara da itaba, dan ba,a dauketa abakin komai ba alhj yanuna mata iyayen sa suna da mahim manci yaje yayi shawara dasu hakadai ummi taita tunani kafin gari ya waye idon ta yayi ja sunkun bura. koda alhaji ya shiga dakin ummi da safe yasame ta cikin wannan hali yayi tunanin kin auren ne ya dame ta, bece komi akaiba yayi mata sallama ya fito. alhj da jalal ne tafe amota alhji yace jalal kasan ina zamu ,jalal yace a,a zan kaikane kaga wani abokin ka, tafiya sikayi sosai sannan suka isa wani gida dan madai daici mai kyau, suka shiga da sallama, wata tsohowa ya gani tana shara tana ganin alhaji ta sake tsin tsiyar cikin Fara,a , ta dauko tabarma ta fara kokarin shinfidawa sannu da zuwa alhaji bari na fadawa baban Ku, bayan wasu yan mituna baffa ya fito yana fadin sanu da zuwa kai dawa kake tafe yau kuma, yace baffa jalal ne. cikin bacin rai baffa yace ba munyi dakai daga mahaifiyar shi har shi bazaka nuna wa kowa nan ba. alhaji yace baffa kayi hakuri ganinayi bayi da lefi kuma be dace muyi ta tafiya ahaka ba, yanzun gashi jalal har zaiyi aure, haka alhaji yayi ta jan hankalin baffa sannan ya kalli jalal yakama hannun shi yace kodan maihaifin ka ,bana kika ba, abduljalal maifinka yamin abinda 'yata da haifa ta kasa yi min, mahaifiyar ka kunya ma takeji ace mune muka haifeta saboda tayi kudi baffa kasa magana yayi ya fashe da kuka mama ma tana daga gefe tana share hawaye. jalal da be gane suba dan rabon shi dasu tun yana karami sai a magan ganun sune ya fahimci kakannin shine iyayan ummi, tausayin su ya kama shi daman ba wuyar kuka gareshi ba, tuni hawaye suka fara ambaliya afuskar shi ya kama hannun tsohon ya shiga bashi hakuri sai da yaga hankalin su ya kwanta sannan yace yauwa baffa ina anty saudatu yanzu? nan danan suka kara barkewa da sabon kuka suna bawa jalal lbrn batan saudatu haka sukai ta kuka har jalal , jalal ji yayi ya tsani ummin sa kwata kwata ya dade yana tambayan ta su sai tace yabar maganar bata so. haka sukawa su baffa wuni sai yamma suka taho bayan sun cika su da tsara ba, saidai sunce su ba wanda zaizo biki daga barayin su, saidai wata rana yakawo musu amarya su gani jalal yanata basu hakuri, amman suka ki. ****** shirye sheryen biki nata tafiya gidan hajiya kamar cenne gidan bikin acan ake shirya komai . ummi bata kara tada zancen auren ba illah hankalinta ba akwance yake ba, kulum cikin kuka take, tarasa yaya zatayi ta dakatar da wannan auran. Jalal kuwa ayanzun gani yake mahaifin shi beyi dacen mata ba yakamata daddy ya kara aure dan koshi da ana cenza uwa da ya cenza ummi dan ko ganinta bayasan yi. ana jibi daurin aure kanwar alhaji anty nusaiba da matar kanin alhaji hajiya fatima da wasu mata su hudu yan uwan hajiya, suka faka faka jibge giyar motan su a haraban gidan alhaji, rabon su da zuwa gidan sun dade, wata motar na biye da nasu, direban motocin suka fara fito da akwatuna masu kyau daga cikin motar sukuwa matan tuni suka shiga gidan. sunata sallama a falon har suka gaji ba,a amsa musuba suka nemi guri suka zauna , bayan anshigo da akwatunan ne , aka fara shigo da kayan abinci, anty nusaiba ce take nuna inda za,a ajiye komai, ummi dake kwance tana kuka taji mutsi yayi yawa ta share hawayen ta tafito, mutane ta gani cike da falon, nusaiba kawai ta shaida. nusaiba ta fara mata bayani anty munshigo munata sallama gidan shiru. eh wlh kaina ke cewo nadan kwanta. nusaiba tace gakayan safna nan mun kawo ki duba ki gani. ummi ta zauna suka fara budewa lallai alhaji ya kashe kudi wannan uban kayan duk na safna ne , aikowa safna bazata sasu ita daya ba, bayan sun maida akwatin sun rufe, anty nusaiba tace mufa munzo kenan sai bayan baki. ummi tayi yake tace ai yakamata tunda kune kirjin biki. hajiya fatima tace ina amaryar tamu ko taje kunshi ne? sai alokacin ummi ta tuna da wata safna, tace anya kuwa inajin tana daki. anty nusaiba tamike tashiga dakin ta hango safna makure agado ta xata bacci take sai da ta taba ta taga ashe kuka takeyi. itako safna ta zata ummi ce dan haka ta mike afirgece, da sauri anty nusaiba ta riketa suka kalli juna, nusaiba tace safna me yasame ki kike kuka, ko baki son auren ne? girgiza kai tayi. to me yake damunki? koda safna bata san anty nusaiba saita tsinci kanta da cewa tunanin iyayena nakeyi da kakata, nusaiba ta tausaya mata tace safna ardua zakiyi musu ba kuka ba, tana buye hawayen ta sake cewa me yasa bakiyi kunshi ba, zo naga kan ki, ta bude kan taga tsohon kitsone, ta kwatar da safna akan cinyar ta tafara warware mata kitson , haye na zuba afuskar ta ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ 07014197556✍ [8:34PM, 12/2/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed 41-45 Anty nusaiba na tsefe wa safna kai tana tunanin ga yarinya me kyau amma gwanin ban tau sayi, bayan ta gama tsefe mata kai taji muryar jalal suna gaisawa da mutane afalo dan haka ta kwala mai kira, ya amsa ya mike ya nufi dakin safna ummi ce ta dakatar dashi yadawo tace ba alhaji ya hanaka shiga dakin safna ba? eh amman yanzun bakiji anty na kira na bane. rasa abin cewa tayi dan haka jalal ya juya ya shiga dakin lokacin da jalal ya shigo dakin safna tana bayi tana wanka. Jalal yace dama ke kadai ce adakin? anty tace nida safna ne yanzun ta shiga wanka, kai kuma haka ake yi baza ka ba amarya kudin lalleba ko haka kake son akai maka ita. toh ni anty babu wadda yace na bada kudin lalle agidan nan nifah da daddy kawai muke shirye shiyen mu agidan nan kinga mu bamu san yadda akeyi ba, anty kinsa ma wani abu kuwa rabon da naga safna na man ta in na,aika kairat ta kirata sai tace ta cemin tayi bacci, ko kiranta nayi awaya bata dauka, ni ina tunanin ma babu wanda ta gaiyata katin ma dana aiki kairat takai mata dawo min dashi tayi wai bata da wanda zata bawa, dan haka na barta . anty nusaiba ta nisa tace ai irin wannan da sai ka gayawa ummin ka ta mata fada. wace ummi, ai ummi bason auren nan take ba, ni ina tunanin kamar ma itace take firgita, ta haka sukai ta tattanawa tsakani su, anty nusaiba tace wai safna har yanzun baki gama wanka bane? safna dake tsaye abayi duk firan da suke tana jinsu tace nagama anty, namanta ne ban shigo da hajjab ba. anty tace au haka ne cikin dariya tace jalal tashi ka fita inta gama shirya wa sai kadawo. jalal yace a,a anty ta fito kawai ni babu ruwana da ita ba kallonta zanyi ba. anty tayi tayi jalal ya fita yaki fita, tashi da kanta ta dauko hijjab kato ta mikawa safna, tasa sannan ta fito kanta akasa dan yanzun wani irin kunyar jalal takeji, tashige cen longu ta zauna ta fara shafa mai, acikin hijjab take shafawa jalal Nata kallon ta, cen yace bazaki gaishe ni bane, kafin ya rufe baki tace ina wuni, shiru yayi sai cen yace bazan amsa ba, saida naroka, safna tace ina fa shirin gaisheka kayi magana. toh nidai bazan amsa gaisuwa daga nesa ba, saikin matso kusa dani. safna tana kokarin ajiye man shafawa tace inazuwa bari nasa kaya. a,a kizo ahaka. anty tana gefe ta jin su tace ke dauki kayanki kishiga bayi ki saka, wai dama jalal ashe baka da kunya haka, agaba na . jalal yace to menayi kuma daga nace ta matso kusa dani. safna bata saurari me suke cewaba tashiga bayi tasaka kaya dogowar riga tasaka na atamfa tayi kyau duk da bawani kwalliya tayi sosai ba, ta dora karami hijjab akai sannan ta fito, gurin jalal ta nufa tace ina wuni, mamayan ta yayi ya rike hunnuwan ta, yace tsorona kikeji kuma. tsugunawa tayi tana boye fuskar ta cikin cinyoyinta shiko jalal yana rike da hannuwan ta yana kokarin daka kanta, ciki ciki suke sosai safna da jalal waishi dole sai yaga fuskarta itakuma taki bari , safna taga jalal yafi karfinta dan haka ta fara kiran anty kin ganshi ko? anty dake gefe tana kallon ikon Allah tace wlh jalal zan bata maka rai, ko kunyata bakaji nazama babba banza kenan . dasauri ya sake ta yana fadin na bari Anty na mance ne, ya mike yace bari naje anty , yaza ayi maganar kunshin ? karka damu yanzun zankai ta amman inaga acen zan barta ta kwana dan naga bawani gyara da aka mata. jalal yaja ya tsaya anty kuma harda kwana toh abar kunshin mana ai badole bane kallon jalal tayi tace ai yan zon baka da ikon hanata fita saika bari sai an daura auran. ********** haka anty nusaiba tadauki safna ta kaita gidan kawar ta hajiya asata me ygara amare, hajiya asata tana ta yiwa anty ko rafin me yasa ba,akawo ta da wuriba sai ana jibi biki. bayan anty ta dawo gida tasamu alhaji awaje ranshi abace saboda ummi ta kitsa mashi magan ganu iri iri. tun daga nesa alhaji ya farawa anty nusaiba fada, nusaiba ina kukaje har dare yayi haka? wlh yaya nakai safna kunshi ne. shine kuka kai dare haka, to yanzun ina safna. yaya tana cen sai gobe zan koma nadauko ta. alhaji ya fara fada ta inda yake shiga battanan yake fita ba. lokacin da nusaiba ta shiga ciki ta samo ummi da kawayen ta sai shewa suke suna ganin nusaiba suka fara yadda habaici. Madina ta kalli dayar dake kusa da ita to amara kirjin biki komai shishige wanki dai, dan nan namu ne, kuma duk inda akaje dole adawo [8:23PM, 12/3/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmnyazeed๐Ÿฝ๑‡Š 46-50 Nusaiba bata ci gaba da sauraren suba ta wuce dakin safna, anan ta samu su hajiya fatima, tace ya naga kun dawo nan kuma. hajiya fatima tace to me gidan tace mushiga daga ciki zatayi baki, shiyasa muka yo nan. anty nusaiba nisawa tayi tace anya kuwa zamu zauna agidan nan har agama biki, kodai zamu koma gidan hajiya ne muyi namu acen, dan nifa gaskiya bazan dauki wula kanciba . Hajiya fatima tace nima nayi tunanin haka amman saina tuna hajiya fah da zamu taho tana ta gargadin kar muce zamuyi fushi muyi hakuri da duk abin da muka tarar dan haka gara mu hakura mu zauna ko dan kan ran hajiya ya baci. nusaiba tace bari na kira hajiya muyi shawara, ta daga waya ta kira hajiya ta gaya mata halin da ake ciki har fadan da alhaji yayi mata, ran hajiya ya baci tace kark taho ku zauna nima gobe zan taho da Jama,a ta, washe gari kuwa saiga hajiya ta dira agidan dan nata, da misalin 10:12 am rabonta da gidan tunda tazo barkan abduljalal. jalal na zaune shida wasu abokan sa, ya hango hajiya na fitowa daga muta da sauri ya karaso yana cewa hajiya lfy kuwa? hajiya na murmushi tace nazo bikin mijina ne. Jalal yace hajiya kodan kishin nan bakiyi ne kama hannuta yayi, ya waiga gurin da abokan sa suke yace faisal kuzo ga amaryar ta iso, dariya sukayi suka matsu suka gaida hajiya sannan sufara diban kayan da sukazo dasu suna shiga dashi cikin gida. ummi na zaune ta fara ganin ana shigo da wasu kaya tace wannan kayan fa daga ina? daidai lokacin jalal yashigo yana rike da hannun Hajiya, ummi ta mike tana fadin sannu da zuwa, hajiya ta amsa Mata ba yabo ba fallasa, sannan tace ina su nusaiba ban gansu afalon ba, ko basukai su zauna anan bane. ummi tace a,a ba haka bane naga dai sun fita tun safe, ina sukaje? basu gayamin inda za suje ba. hajiya ta sake cewa me gidan fa baya nanne, ummi tace yana ciki bari na kira shi da saurin shi ya fito yana fadin hajiya da kanki, Allah yasa dai lfy, lfy nazo ne ayi komai akan idona dan ni bana son tashin hankali, nidai na gargadi iya laina kaima inason ka gargadi matar ka bama son tashin hakali. alhaji yace hajiya ki kwantar da hankalin ki babu wani abunda zai baru. tace toh nima ai nafi son haka. wayar alhaji ce tayi kara ya dauka bayan ya sauke wayar yace ina nusaiba cikin sauri ummi tace bata nan ta fita. alhji yace kash gashi kuma kamafani da zasu kawa kayan safna sun isa gidan. Hajiya tace ka Kira ta awaya mana. kafin hajiya ta rufe baki, ummi tace alhji key na wajan tane. a,a gashi agurina nusaiba tace ya kamata mace ta tsaya agurin. ummi tace hakane alhji toni ai da nasan gidan da naje, alhji dadi yaji sosai yace ai jalal nannan awaje sai ya kaiki. hajiya taso ta hana sai kuma taga karta cika takura masu dan haka tayi shiru. itako ummi dadi taji dan dama jira take afadi gidan da jalal zaizauna su cika kudurin su ita da kawar ta madina. bayan sun dauki hanya dukkan su gaba suka zauna ummi ta daga waya zuwa cen tace dona madina tama bayani ko ? , jalal beji amsan me aka bataba, ta kashe wayar tana murmushi Kara kiran wayar tayi tace madina har yanzun baku zoba, nagaji da jira gani ma zantafi gidan danki za a zuba kaya agidan , bayan ummi ta gama waya jalal yace ummi naga kina shashshare bikin nan ne. tace ba haka bane jalal aini babu wadda yakaini farin ciki ayanzun na fahimci kana son safna da yawa dan haka nima na fara jin Ina sonta , saidai abu daya yake damu na , ban so ka aure yariyar da sultan yayi soyayya da ita ba, saboda sultan fa dan duniya ne. Jalal be gane inda ummi ta dosaba yace ummi ki daina tuna wannan yariga ya wuce kuma sultan ai babu abinda ya isa yayi min, nidai burina kawai adaura auren. ummi ma ta gane jalal be fahimce taba, da wannan tunani suka isa gidan, kan kace meye har angama gyara gidan, ummi tsayawa tayi tana kallon dukiyar da aka zuba agidan, alhaji ya kashe kudi saikace kairat zai aurar, badan madina tace tabi komai ahankali ba toh da yau saisun kwashi rigima da alhaji, haka suka kamo hanya ita da jalal amota jalal sai santin gidan yake. gani inda yake ta murna ummi tace gaskiya jalal guri yayi kyau. cikin murmushi ya waigo yace ummi ai bakiga kyauba sai safna ta shiga gidan, zakiga yadda zai kara haske. kulewa tayi sosai amman bata bari ya gane ba tayi mai murmushi kawai. Jalal kuwa dadi yaji ummi ta fara son safna tuni ya nemi haushin ta da yakeji da ya rasa, dan haka yashiga zuba mata shagwaba, ummi kinsan menene? tace a,a yaro sai ka fada. yace safna fah sai kin dan mata fada bata sakin jikinta dani, kamar ma tsorona takeji kuma dacen ba haka take minba, cikin shagwaba ya fadi maganar. ummi daurewa tayi tayi murmushi tace jalal manya, kabari mana adaura aure duk zata Bari da haka suka isa gida lakacin yamma tayi sosai, tana shiga falon sukayi ido hudu da safna tana kusa da hajiya a zaune ganin tayi ta kara kyau da sheki gawani zanen filawa wadan tunda take zuwa bikin yaran kawayen ta bata taba ganin wada yakwai haduwar wannan ba, sai satar kallota take , tare da kara jin haushin anty nusaiba tasan tayi ne dan jalal ya rikice, bayan ta gaida hajiya ta shige dakin ta. hajiya ta kalli safna tace me yasa baki gaishe da ummin ku ba, maza ki bita daki ki gaida ta. safna tashi ga da sallama ummi ta dago ta kalle ta, tace yaushe kuka dowa? tace bamu dade da shigowa ba. tasake cewa jalal yasan kundawo? nima basan ko yasani ba, tabe baki tayi tace fita kibani waje. da daddare gidan ya kaceme gidan biki sosai sai haya niya ake aharabar gidan kuwa su jalal ne da abokan sa sai hayaniya sukeyi. zuwa cen kawayen ummi suka fara shigowa wannan karon basu tsaya a falo ba barayin ummi suka shiga, zuwa cen suka saki sauti. bayan ansaka safna alalle tana ta kuka yau itace za,ama aure ba dangin ta ko guda daya ita da zata samo ko goggo ce tagani agurin bikin nan da zatayi farin ciki da haka da ace babu kowa nata kasa bacci tayi sai juye take babu wadda tafi fado mata arai kamar iya taso Allah ya bar mata iya, haka taita share hawaye dan bata son anty nusaiba ta juwota, daga cen ta fara jiyo muryar alhji yana fadin innalillahi wa,ina ilaihir raju,un sai maimaitawa yakeyi mikewa tayi ta zauna ,tana kallon su hajiya suka fita akabarta ita kaidai adakin, dan haka tabiyo bayan su, gani tayi duk sun tsaya sunyi cirko cirko, alhaji ko sai share zuba ya keyi jalal na gefe daga shi sai gajeren wando, ummi kuwa sai rusa kuka take, cikin rudu safna tace me yafaru? anty nusaiba tace karku gaya mata saida safe. ummi tace ai gara agaya mata tunda kowa yasani, safna gidan da zaku zauna ya kone babu abinda aka dauka acikin sa. safna neman kujera tayi ta zauna ta rufe ido bata sam ma me zata ceba. jalal kuwa kansa akasa yake, yaki dagowa. alhji yace bakomai kowa ya koma ya kwata saida safe Allah yasa haka shine mafi alheri. ummi tace ai alhji bamuga ta barciba munfah gaiyata muta ne gashi gobe ne daurin aure, yaka mata asan abinyi, ni ina ganin kawai adaga bikin kawai hankali kwance. bata gama rufe baki ba jalal yace ni gaskiya ban yaddaba ummi, ni dai kawai ayi. cikin fada alhaji yace kai jalal baka da kunya ko ya manya suna magana zaka saka baki, ai biki yazama dole adaga shi, wuce kaba mutane waje. da sauri yabar wajen ya shige dakin shi ya bogo kofar. hajiya tace toh yanzun kayanke hukunci ne kabamu umarni mu watse koko shawara kake nema. sai lokacin ya tuna mahaifiyar shifa tana wajen dan haka yace hajiya kiyi hakuri nayi kuskure, shawara nake nema yanzun yaya kamata ayi. hajiya tace toh nidai ban yadda adaga ba kowa yaci gaba da abinda yake biki nanan babu fashi 07014197556.....✍ [8:48PM, 12/4/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 51-53 Alhaji yace shikenan hajiya duk inda kikace haka za,ayi,haka kowa ya koma ya kwanta kowa zuciya babu dadi, jalal kuwa bayan ya koma daki kuka ya saka gidan da aka dade ana ginawa saida aka gama kashe kudi, zargi kala kala ya ziyarci zuciyar shi gaskiya yana zargi sultan da mahaifiyar shi ,kafin safe idon jalal yayi jazur sun dan tasa . karfe bakwai jalal ya fito sanye da jallabiya fara sol , da bakin glass a idon sa, saboda baya son afahimci halin da yake ciki , saida ya fara gaida su hajiya sannan ya wace dakin alhaji, yana shiga yacire glass din ya rike ahannun shi, alhaji ya kalli jalal yace wai kai ba kasan kaddara bane ji inda fuskar ka ta koma saikace ba musulmi ba. Jalal yace daddy ba haka bane abin da yake bata min rai nasan gidan nan kona shi akayi kuma wlh nasan bazai wuce sultan bane dan nasan shi kadai ne zai min haka. dakatar dashi alhaji yayi cikin fada karna kara jin kafadi wannan maganar mubarwa Allah kawai shiyafi, kuma daurin aure nanan insha Allah ajima za,a daura . dadi sosai jalal yaji yace daddy nagode yana fitowa dakin ummi ya shiga suna saune ita da wata kawar ta data kwana agida. ummi tace kardai kacemin kuka ka kwana kanayi jalal kana sone kayi kanka illa akan yariyar da badamuwa tayi dakai ba. dokar dakai yayi yace ummi me yasa kikace haka, ni nasan safna nasona kawai domuwa ne ya mata yawa shiyasa ma nafi son adaura auran ko hakalin ta zai kwanta, nima kaina hakali na ba,a kwance yake ba bare kuma safna. hajiya adama kawar ummi dake zaune agefe tace rabo da ita jalal kaji , ance maganar bikin nanan ko? eh yana nan in Allah ya yarda hajiya adama tasa ke cewa toh yanzun a ina zaka zauna kenan? yace nima ban sani ba. jalal ya gaji da tambayoyin su dan haka yace ummi bari naje bayan ya fito yayi tunani yaje yaga halin da safna take ciki dan haka ya doshi daki, dakin cike yake da mutane, su anty nusaiba ne sauran dai duk besan suba, bayan yagaida su, ya hango safna daga cen bayan anty nusaiba, yace anty dan turomin yariyar cen, yajuya zaita fi anty ta tsaida shi tace zoka zauna kuyi maganar adaki dan abin ya fara bani tsoro, mikewa sukayi suka fita jalal yashigo cikin dakin ya zauna abakin gado yace safna tashi mana, ke wacce irin amarya ce har yanzun kina kwance. mikewa tayi ta gaida shi, jalal yace safna kinji abinda ya same mu ko, dan Allah karki ce zakisa wannan abun a zuciyar ki ya dame ki, tace bakomai yaya Allah yasa haka shi yafi alheri ameen safna . ta sake cewa yaya me yasame ka a ido naga yayi ja? jalal yayi mamakin ya akayi ta gani bayan ba kallon shi take ba kanta akasa, dariya yayi yace ta yaya akayi kikaga idona bayan ba kallona kikeba? juyar da kai tayi tace nifa gani nayi kamar yayi ja Eh ai naji shine nake tambaya ko kina da ido ne atakiyar kai dan ni kanki kawai nake gani. safna bata ce komai ba tayi shiro tana wasa da yatsun hannun ta. daidai lokacin aka kirashi awaya yadauka yana fadin amir kun iso ne, ok to ganinan zuwa. juyawa yayi yakalli safna yace, yarinya zama ki bari ne, dan yau a gado daya zamu kwana. dasauri ta kalli jalal ta sake yin kasa dakai. jalal yace a,a ki kalleni da kyau. karfe 2:30 Jama,a da dama suka shaida daurin auren abduljalal da safna acikin wa,inda suka shaida daurin auran harda baffa wanda alhaji yaje ya taho dashi yaso yaki zuwa amman alhaji yace yayi danshi, dan haka ana daura auran alhaji yaba da mota aka mai dashi gida, jalal kuwa da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki. acikin gida kuwa safna ce da wasu kawayen ta su biyu bata san waya gaya musuba sai dai kawai ganin su tayi,tana ganin su kuwa suka shiga fira tuni ta manta da bacin ran dake damunta anty tashigo ta ajewa safna wasu kaya tace maza kisaka kije waje jalal na kiranki zaku gaisa da abokan sa. tun safe safna bata fitoba sai yanzun tana fito falo su hajiya ne da mutanen ta cike afalo suka saka guda, safna kuka tasaka musu yau gata atsakiyan dagin miji bata da kowa, dagin miji sune gatan ta wannan abu kawai in tatuna yana sata cikin baccin rai sai a yanzun wani kalma na goggo yake fado mata ki zauna anan bari naje na dawo haka banzayen kakan ninki suka ma uwarki har ta mutu bata kara sakasu a ido ba, goggo tana nufen mahaifiyar tama haka abarta, ko shiyasa bata taba gani wani dan uwan mahaifyar taba kara rushiwa tayi da kuka hajiya tace fatima kawo ta nan, hajiya fatima ta kawota har gaban hajiya kwatar da ita tayi ajikinta taita mata nasiha. bayan ta dan natsu hajiya tace tashi kije ki gaida ummin ko, sai ki wuce gurin su jalal din. sun shiga ita da kawayenta ta gaida su suka amsa ba yabo ba fallasa. sun doshi gurin rinsu jalal, jalal ya hango su tun daga nesa da sauri ya daga waya yace anty dan Allah ki leko ki mayar da safna gida tasaka hijjabi. dariya tayi tace haba jalal kabarta mana yau daya dai kafin yakara wani magana sun iso wajen dan haka ya daure fuska suka gaida su cikin sakin fuska suka amsa dayan daga cikin abokan ne wadda suke kira amir ya farawa safna tsiya amaryar mu kirike shi da kyau duk abinda yake so abashi dan kinsan shagwabebbe ne ko cokali be iya rikewa ba. jalal yace toh malam ya isheka haka kuma. amir yace be isaba safna kinajina nina san halin jalal tare mukayi karatu jalal bashi da matsala amman yanada fushi idan antaba shi, ya kalli jalal yayi murmushi sannan yace safna abu nagaba jalal nada tsananin kishi . da sauri jalal ya kalli amir yace wai amir lfyr ka kalau kuwa, ke ku wuce gida. amir yace yazaka koresu ka barsu mana ai ban gama ba, hirace ta barke takanin safyya kawar safna da amir amir , jalal zuwa yayi yakama hannu safna yashiga da ita har cikin gida. da daddare mutane suka fara watsewa bakin hajiya kowa duk sun wuce gidan ta ,sai hajiya da anty nusaiba kawai suka rage barayin ummi kuwa daga ita sai kawarta madina safna kuwa na dakin su da ita sai kairat, kairat tace anty safna kikace da bikin ki zamuyi shagali amman yanzun sai naga ba,ayi komai ba, natabayi yaya yace wai kece baki so ayi. Safna tace haka yace miki wayau yayi miki shine baya so,kairat tace ai dama yaya yacika wayau haka ma da yace in kukayi aure zai tafi dani yanzun kuma yace wai wasa yake min, kuma wlh bazan yarda ba saina biku yaya zaku tafi kubar ni ni kadai agida safna tace ai bama inda zamu bakiga gidan ya kone bane. suna cikin haka jalal yashigo dakin yace safna kizo hajiya nakiran ki tamike suka fito tare ahanyar su ne jalal ya ce safna koda an tambaye ki Ina kike son zama kafin musami wani gidan kice abarki adakina. dauri safna ta fara kuka wlh yaya bazan iyaba . yace daurewa zakiyi safna ,ko kin fi son hajiya ta wuce dake, ni indai hajiya ta wuce dake bazan iya barciba wlh me zanyi agidan nan, to sai dai nima na biko. gani tayi kamar ba,a cikin hakalin shi yake ba, matsowa yayi yariketa safna ki taimakeni karki bari atafi dake. safna ko azuciyar ta tafi son tabi hajiya dan gidan nan kwata kwata baya yi mata dadi jita take kamar a kaya take. Suna shiga falan alhaji ,suka ga kowa kowa ya hallara har ummi da kanin alhaji bayan sun zauna aka fara yi musu nasiha kanin alhaji baba salisu yace to jalal hajiya nason ta tafi da safna gidanta kafin agama gyara ma gidan ka dan haka nace bari muje ta bakinka tukuna dan yanzun kai kake da iko da ita, meye ra,ayin ka? shiru yayi kansa kasa. Safna ko tunani take azuciyar ta wato jalal shi yakasa magana ita kuma zai sata tayi rashin kunya. Jalal beyi magana ba saida baba salisu yakara maimaita tambayan shi. sai da jalal ya juya gurin hajiya sannan yace toh hajiya harda ni zaki tafi ko? duk falon dariya suka saka banda safna da ummi dan ummi kara tamke fuska tayi. baba salisu yace ja,iri ai dani zakayi magana bada hajiya ba. Jalal bece komai ba sai faman sosa kai yakai yake. baba salisu yace indai na kula da kyau, jalal be yadda atafi mai da mata ba. anty nusaiba tace toh hajiya kibar mai matarsa kawai tunda baso yake ba, da sauri ummi tace nima dai abinda nagani kenan. hajiya tace a,a nima ba matsawa nayiba kusha zaman Ku, in ma dakinka zaka kaita bisimillah. hajiya ta sosa mai inda yake mai kaikayi dan haka ya farawa anty nusaiba alama da ido , banza tayi dashi kamar bata gani ba. baba salisu ya kula dan haka yace jalal kamar kwai magana abakin ka, nusauba me jalal yake gaya miki. dariya tayi tace yaya nima ban fahimce shiba. yace toh kuje waje kuyi magana duk abinda yake so ya fada kar yaji kunya ai matar sa ce. anty tace jalal kayi hakuri mana kasan fa mamar ka bazata yarda dahaka ba. anty nidai kawai ku kaita dakina ina da dalilina inhar kuka tafi baku kaita dakina ba nasan ganin safna ma sai ya gagareni ummi zata iya hanani shiga dakin su safna. suna komawa anty tace yaya shifa wai so yake ta koma dakinsa. baba salisu da alhaji suka hada baki to dan wannan shine ka kasa fada kai da matar ka, nusaiba kai mishi matar sa daki kizo mutafi. ummi mikewa ta tasaka kuka agidan nan, za,yi wannan kwama calar wlh wlh bata isa ta hada gado da jalal ba [7:43PM, 12/5/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 54-57 Han kalin kowa koma wa yayi gurin ummi safna kuwa hawaye ne ke zuba a idanun ta kamar an bude faffu hajiya tace me kike nufi da wannan kalmar taki? hajiya nidai gaskiya ban yadda da wan shawarar ba kawai ya bari sai sun samo gida amman wannan ai bai dace ba. hajiya tace to muna sauraran ki sai ki gaya mana yadda ya dace tun da kin fimu hankali. bude baki tayi zata yi magana alhaji ya dakatar da ita yanzu nan dan baki da kunya magana zakiyi , mikiwa tayi tabar wajen . hajiya ta juya tace ke nusaiba rakata dakin jalal daga dakin alhaji aka wuce da ita dakin jalal ban da kuka babu abin da safna take, abakin gado ta zaunar da ita, rabon da ta shiga dakin jalal tun farkon zuwan ta gidan . anty nusaiba juyawa tayi tace safna sai da safe Zan kiraki awaya kema idan kina son wani abu ki kirani kigaya min. kasa amsawa tayi sai kuka take dan gaskiya dan zaman nan da sukayi da anty suyi matukar shakuwa da juna tanan zaune tafara tunanin wannan wani irin aure ne dan dai bani da gatane da inada gata baza akawo ni dakin jalal ba, da sai dai nazauna agidan iyaye na ,tana cikin tunani taji an turo kofar ta zata jalal ne sai taga anty tana shigo da akwatuna harta gama shigo dasu gaba daya sannan takuma yi mata sallama ta fita. zuwa cen taji tashin motar su takara saka kuka. shiko jalal bayan sun tafi yayi masu alhaji sai da safe ummi shiru tayi bata amsa ba. bayan jalal ya wuce ummi ma ta wuce dakin ta ,alhaji ya bita da kallo ji yayi babu dadi suda suka aurar da dan su kamata yayi suyi farin ciki , dan haka yabi bayan ta yana shiga ya fara rarrashin ta sannan ya tambaye ta me yasa bata son auran safna da jalal. ummi tace au sai yanzo ne zaka tambaye ni ,ai aikin gama yariga ya gama kuma, ba, anyi ba ,har kunsa masa ita adaki , to meye Kuma zaka zo kana tambaya ta. alhaji dai da yaga ummi baza ta gane ba ya tashi yabar mata dakin. alhaji na fita takira madina ta gaya mata halin da ake ciki. madina tace gaskiya zaliha ke kike jawa kan ki nace miki kwatar da kai zakiyi karki bari kowa yagane baki son auran , irin wannan ai sai ki tona kin ki. ummi tace yaushe kuma aisun riga ma sun gane, ni ba wannna bama, madina bakiga inda jalal ke rawar jiki ba, a yadda naga take taken sa ,yau bazai iya hakuri ba sai ya kusan ce ta, ni kuma abin da natsana kenan . madina tace ni wlh mamaki kike bani ke baki san yadda zakiyi ki hana yarinyar kwana adakin ba cikin kissa da dubara, kuma karki kara nuna baki son yarinya shi kuma jalal kija shi ajiki kamar da, indai kikai haka sai kiga kafin su tare auran ya kare. bayan sun gama waya da madina ummi ta fito ta nufi dakin jalal jalal kuwa yana manne jikin safna sai rarrashin ta yake, bayan tayi shiru yace to ki saki jikin ki mana keda dakin ki, cire gyalen kisha iska, kara rike gyalan tayi , jalal yayi dariya yace kicire gyalan mana ki kwanta ni ba abin da zan miki. safna shiru tayi kamar bada ita yake magana ba, dan haka jalal ya rike gyalan yana kokarin cire mata, suna cikin haka sukaji. anturo kofar jalal ya sake gyalen ya juwo da sauri sai da gaban shi ya fadi ganin ummi adakin safna kowa mikewa tayi afirgice. jalal yaje ya rike safna ajikin sa , sannan yace ummi lafiya kuwa? jalal lfy lau, safna ni kika gani kika firgita haka sai kace kinga dodo, daga na fada gaskiya, lallai dama jalal yace kina son sa sai yanzun na tabbatar da haka. zuwa tayi har jikin jalal ta jawo safna jikin ta, tace ki kwatar da hankalin ki kinji yata, niba kin ki nake ba, duk abinda jalal ke so dole nasoshi jalal dadi yaji har ran sa ,sai murmushi yake. ummi jan safna tayi zuwa kojerar dake gefe suka zauna ta kwatar da ita ajikin ta tana shafa kanta, tace safna kinyi kyau sosai, sai dai nasan ba ,dan gyara kiba, da jalal zai yadda yadan kara mana kwanaki da an gyara ki. jalal ya kalli ummi yace wani irin gyara ne wannan? tace gyaran jiki mana irin namu na mata, kai nasan bazaka fahimta ba kabani ita kwai koma meye zaka gani. au ummi gyaran ma har sai tabar dakin nan, to abar gyaran mana ko yanzu ma ai a gyare take. ummi dariya tayi tace jalal ko sati biyu ne kabani na dan gyara ma ita, kai dan baka da kunya ma ina ma magana kana mayar min, ke safna rabu dashi tashi muje. jalal bin bayan su yayi yana fadin ummi ni dai gaskiya bana son wani gyara. tsayawa tayi tace au biyomu kayi, jawo safna tayi tace jeka da ita, ai bansan tsumuwar taka takai nan ba. kunyar ummi ce ta kama jalal yace kai ummi me yayi zafi kuma toh shi kenan kuje, kafen ya gama magana ummi tayi gaba, dan haka jalal ya rike mata hannu yakai ta har dakin ummi yace ummi gata nan. ya juya ya fita ummi ta juyowa tayi ta kalli safna tana murmushi tace jeki dakin ku, ki kwanta kinji 'yata. cikin dare jalal kasa bacci yayi sai juyi yake agado yaso ya kasan ce da matar sa tunani kala kala ne azuciyar shi yana mamakin ummi, wani irin abu ne wannan da fah ta nuna bata son akawo safna dakin sa, har tana ikirarin safna bata isa ta hada gado dashi ba, lallai akwai wata akasa mikiwa yayi ya fara zagaye dakin to ummi me take nufe akwai abinda take shir yawa so take taraba ni da safna, lallai kwai rigima sai dai ummi tace bani da kunya amman dau ko matata zan yi. fitowa yayi ya wuce dakin ummi ya nufi dakin su safna ya tura kofar ya jita kulle ya fara bugawa ahankali muryar safna yaji tace waye, haka ya tabbatar mai ba bacci take ba, dan buga kofar da yayi be isa ya tada me bacci ba, yace nine bude min kofa. bayan ta bude kofar ya kama hannun ta yace zo muje. cijewa ta fara yaya ummi fa zata yi fada. tsawa ya daka mata babu ruwan ki kizo muje kawai. kin zuwa tayi yaya kairat fa, ita kadai zan bari. eh barta zo muje , haka jalal ya wuce da safna dakin shi. ya daura ta agadon shi komawa yayi ya sawa kofar key [11:33AM, 12/6/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ 58-60 Jalal dawowa yayi gurin safna ya zauna daga gefe ya kalli agogo karfe 01:11 yace safna ina cikin wani haly , yanzun yaya zamuyi? safna shiru tayi dan bata fahinci me yake nufe ba. safna yaya ina magana kin yi min shiru. yaya toh me zan ce maka nifa tsoro nake ji kar ummi ta ganni anan dan Allah ka barni na koma . safna bana son irin wannan maganar ki bari babu inda zaki , tashi kije kiyi alwala. kallon jalal tayi taga ya daure fuska dan haka ta mike jiki babu kwari ta shiga toilet lokacin da ta fito hawaye ne afuskar ta tafara boyewa dan kar jalal ya gani, shi ma tashi yayi ya shiga toilet be jima ba ya fito bayan sun ida sallah jalal ya bude daya daga cikin akwa tunan ta ya dauko wata rigar bacci me kyau ya mika mata kin karba tayi yace bada ke nake magana bane safna me yasa kike min haka, kinga fa dare kara yi yake. kalon rigar tayi ta ganta yar karama ko hannu bata dashi kuma bazata wuce cinyar taba dan haka tace nifah sanyi nakeji. murmushi yayi yace sanyin sosai kikeji ko kadan? da saurin ta tace sosai. jalal yace yauwa kin gama daidai kenan karba kisaka ni dama zafi nakeji kinga kenan zamuyi daidai. mika hannu tayi ta karba ta tsaya tarasa yaya zatayi tacire kaya gaban jalal. jalal ya fahince ta yace safna kona rufe ido nane? eh tace dashi ahan kali, jalal ya juya baya yarufe ido. tana cikin saka rigar jalal yace na bude kin gama ? a,a ban gama ba. mikewa yayi yafara taho wa yana fadin toh ni gaskiya na gaji kina so ido na yayi ciwo ne? dasauri ta dauki zanin da ta cire tana kokarin daurawa akan rigar. jalal ya kama zanin ya aje shi gefe toh tun daga nan fah labarin ya cen za daga karshe ma daukan ta yayi ya sata agado , safna kuwa tun tana daurewa taga abu nason yafi karfin ta tafar yan koke koke. Jalal yace safna kina son ummi ta jimu ne? dasauri tasa hannu ta rufe bakin ta, jalal kuwa cigaba yayi da abinda yake. ni dai da naga abin yafi karfi na saka hannuwa na nayi narufe ido๐Ÿ™ˆ zuwa cen naji safna sai kuka take tana fadin jalal kashe ni zakayi, dan Allah kayi hakuri kabar ni wlh nagaji , waida ma haka kake baka da imani ne, zucen naji ta fara Allah ya isa. jalal be bar safna ba sai waje karfe 2:56 tana kwance agefe dan ki tayi jalal yata tabata daya kawo hannu zata bige hannun, zuwa cen ta fara kokarin tashi. jalal yace ina zaki? tafiya zanyi dakin mu. ai ba inda zaki anan zaki zauna, rokon shi tafara akan yabar ta tafi ita tsoron ummi takeji. jalal yace to naji tashi muje kiyi wanka sai na raka ki, daukan ta yayi yakaita bayi da kan shi ya gasa ta. bayan sun fito ta maida kayanta na jiya. saida jalal yaje bakin kofar ummi ya kasa kunne ko zaiji mutsin ta, sannan ya juya ya dauko safna ya kaita har kan gadon su, kairat kuwa na gefe tana ta sharar baccin ta jalal yace kinga lokacin sallah ya kusa kina yin sallah saiki kwanta. shikuwa jalal yana koma wa dakin cire zanin gadon yayi ya hada da rigar safna ya wanke sannan yayi wanka ya wuce masallaci ******* washe gari da safe ummi ta fito lukacin karfe 7:00 wai ita gani take tayi sammako, ta doshi dakin safna ta ganta kwance ita da kairat sai barci suke , ta jawo musu kofar ta fito jalal ko da ya fito be tam bayi safna ba, saida ya fita ya dawo . yana shigowa dakin su safna ya dosa yasa meta ita da kairat. safna tana tsaye taga jalal ya shigo, wurgar da wayan dake hannun ta tayi ta shiga bayi da gudu, jalal ya tsuguna ya dauka, ya matsa kusa da kofar yayi ta bugawa yaji shiro haka yagaji ya tafi. da daddare jalal kasa bacci yayi kamar jiya banda tunanin safna babu abin da yake dan haka yafara tunanin yaje ya dauko ta, daga kai yayi ya kalli agogo 12:37 ya miki ya fita , yana zuwa bakin kofan ya fara bugawa ahankali har ya gaji ya koma daki. washe gari jalal beyi bacci ba haka ya fito idon shi duk sun kankan ce, dakin daddy ya shiga anan ya sami ummi, jinkin daddy sa yaje ya kwanta. alhaji yace lfy kuwa, angon safna me ya faro ne? daddy kai na ne yake min ciwo, kuma daddy safna na fushi dani bata min magana saboda na mata lefi kuma taki bari na bata hakuri. alhaji dariya yayi sosai yace wai kai jalal wanni iri ne kai, kana yin abu kamar ba namiji ba, ji inda duk ka fita hai yacin ka. yi yayi kamar zaiyi kuka yace nidai daddy ka kirata kawai ka bata hakuri. ummi ko azuciyar ta cewa take na shiga uku jalal zai haukace akan safna anya kuwa ba asiri tamai ba, afili kuwa cewa tayi jalal na safna. 07014197556 [6:47PM, 12/6/2016] ‪+234 814 451 1180‬: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & writte by Fadeela Lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ 61-63 alhaji ya kalli jalal yace duba nan jalal tashi ka zauna , kasan yazun yaya za,a ,tashi zakayi kaje ka lallashi matar ka, koma me ka mata kaje ka bata hakuri zata saurare ka. shiru yayi ya ya mutsa fuska ni dai daddy ka tai makeni ka bata hakuri. alhaji juyawa yayi ya kalli ummi gace zaliha ke kika lalata garon nan shagwaba tama sa yawa kuma yanzun ke kin zame kinbar ni dashi. dariya tayi wani irin na zame nima fah yana min. alhaji ya juya ya kalli jalal ya kwashi da dariya yace zaliha maza Kira min safna naga abin babba ne . ummi waya ta daga ta kira safna daure wa kawai take tana yashe baki dan bin shawarar kawar ta madina. safna tashigo tare da sallah ma dasauri ummi tace zonan 'yata safna ta karasa kusa da ummi, ummi tasa hannuta ta jawota ta daurata akan cinyar ta , tace safna me jalal yayi miki da zafi haka ne ? ummi ni baiyin min komai ba. jalal yace a,a safna namiki laifi kedai kawai bazaki fada bane. alhaji yace zonan safna ,sauka tayi ta koma gaban alhaji kusa da jalal ta zauna. yace koma me jalal yayi miki kiyi hakuri ki yafe mishi kinji yasan cewa yayi laifi kiji ko? daga kai tayi ,alhaji yace yauwa safna haka akeso jalal kuwa bin safna kawai yake da kallo alhaji yace to jalal tashi ka dauki matar ku kutafi shi besan cewa ummi ta raba musu daki ba. bayan sun fita ummi nata sauri tabi bayan su alhaji ya dakatar da ita. zaliha ina da magana dake , ta koma ta zauna . yace kina zuwa gurin su baffa kuwa? a,a kwana ki naje akace sun tashi alhaji wani abune ya faru? a,a ba abinda ya faru, amman me yasa baki neme inda suke ba . mike wa tayi zata bar wajan. alhaji yace saboda basu da kudi ko. komawa tayi ta zauna tace aini dama tunda naga yan uwan ka sunzu bikin nan nasan sai su kulla min wani sharrin. alhaji yace basu suka fada ba baffa da kanshi ya fada haka. mikewa tayi alhaji aina kaga baffa? aini tunni nasan inda suke tun bayan koran ron su da kikayi kokaci bananan baya sati biyu na dawo tun kafin nashigo gida jalal ya gaya min baffa yazo kin kore su, abin ya bani mamaki amman bayi miki magana ba na nufi gidan nasa me su cikin ma wuyacin hali bafffa ba lfy mama haka , sai yaya rabi ce akan su itama kuka take.anan take gaya min saudatu ta bata wanda har yau ba,a ganta ba. bayan nakai su asibiti kwan su uku aka sallame su. tunda ranar nakai su wani gida na dana saya baffa kin shiga gidan yayi, wai bai son abinda zai sake hadaki dashi da ke๐Ÿ‘‰๐Ÿป dan haka namai alkawarin bazan gaya miki inda suke ba, san nan ya yarda. duk wata nake zuwa ina kai musu kayan abin ci, in takaice miki har daurin auran jalal baffa yazo, inata jira inga ranar da hakalin ki zai karka gare su amman sai naji shiru kamar an shuka dusa dan haka naga innabar ki ahaka banyi miki adalci ba, amfanin zaman tare kenan in kaga wanda yake kusa dakai zai bata kasa shi ahanya dan haka idai bakibi iyayen ki ba toh matakin da zan dauka bazai yi miki dadi ba. ******** kafin ya gama magana hawaye ya wanke wa ummi fusku yanzun dama tuntuni ba,aga saudatu ba, amman basu nemi ni ba lalai su bafffa suyi matukar fushi dani. tsuguna wa tayi ta fara wa alhaji magiyar ya rakata ta nemi gafarar su. alhaji yace indai nine bazan taba kaiki ba kije ki nema da kan ki. shiko jalal bayan sun fita dakin sa ya nufa da safna ya kara kwasan gara bayan tayi wanka jalal ya shiga , kamar jira take tana ganin ya shiga wanka tamike ta leko bataga kowa ba ahanyar ta fito saf saf ta shige dakin su. jalal ya fito bega safna ba dan haka yana saka kaya ya fito, daidai lokacin ummi ta leka dakin dakin safna tagani ko jalal ya wuce da da ita dakin sa. tana ganin safna hankalin ta ya kwanta juyawa tayi dai lokacin suka ci karo da ummi. ganin ummi yayi abirkice yace ummi lfy kuwa? wucewa tayi zuwa dakin ta ta fada gado tasaki kuka, jalal ya shigo dakin yace ummi me ya faru ne. mikiwa tayi cikin kuka ta kwashe duk abinda yake faruwa ta gaya mishi. dadi ya kama jalal Allah ya karbi Andu,ar shi ummi ta fara tunanin iyayen ta. yace ummi ki kwatar da hankalin ki ,ni nasan gidan zan rakaki. ummi cikin sauri ta dauki gyale tace muje jalal. jalal yace ummi ki bari sai gobe mana. eh ai kana tare da uwarka da ubanka dole kace na bari sai gobe. Jalal yace Allah ya baki hakuri ummi muje, sun fito kenan saiga safna da kairat zasu fita jalal yace ina zaku ? kairat tace waje zamu muga gari safna ko shiru tayi jalal yace koma gida. kairat kuka ta fara toh ni ummi zanbi. ummi tace zo muje yar auta ta. safna na kallo suka shiga mota sai daga musu hannu take. bayan sun isa jalal ne ya fara shiga gidan sunata murna baffa har yana tam bayan jalal ya baka taho da amaryar ba, ko kana tsoron karta ganin tace ni take so. jalal dariya yayi yace baffa ni da baki ne fah, nabar su a mota. a,a banda abinka ya zaka baro so akofar gida jekace su shugo. waya ya dauka yace shi go. shigowa tayi da sallama rike da hannun kairat idon ta hawaye ne kawai ke zuba. baffa ya mike ya nuna ummi yace zaliha mama dake tsugune tana zubawa jalal abinci ta sake kwanan ta dau ko itacen dake cikin murhun ta fito tana fadin ina zalihar take. baffa ya nuna zaliha yace kinzo ki koremu ne daga gidan da mijinki ya bamu? tsugu nawa tayi ta fashe da kuka tana fadin baffa nazo neman gafarar kune dan Allah ku yafe min. bata rufe baki ba ta fara jin saukan itace ajikin ta. jalal saifaman ba baffa hakuri ya keyi, yaju ya yaga anata jabgar ummi mikewa yayi yazo ya karbi icen yana bawa mama hakuyi. baffa yace ta fita karta kara nufo inda muke, shi ya dade da cireta acikin 'ya'yan shi. wani makocin baffa ne yaji hayaniya tayi yawa ya zagayo. me yake faruwa ne? baffa ne ya fara gayawa makocin shi, malam buba yace kinyi kuskure yarinya, nan ya shiga bawa baffa hakuri amman baffa ya kekashe kasa yaki hakura ummi sai man share hawaye take, ahankali mutane sai taruwa suke anyi anyi su hakura suki. jalal ya tsuguna ya rike kafar bafffa yana rokon shi. baffa yace mike abduljalal idan ina kallon ka gani nake kamar mahaifin ka ne zan yafewa mahaifiyar ka amman da sharadi. sharadin kuwa shine karta kara zuwa inda nake har sai ta nemo min 'yata saudatu. ummi saka hannu tayi aka, yanzun a ina zata nemo wadda tayi wajen shekara 20 da bata๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป๐Ÿ™†๐Ÿป [7:35PM, 12/7/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written. by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 64-66 bayan sun dawo gida ummi da gudu ta shige dakin ta ban da kuka ba abinda take. jalal ma dakin shi ya shiga ya fara zubar da hawayen bakin ciki, amman koma meye ummi ita tajawa kanta. haka ya kwanta yayi ta kuka. kairat ma duk da yake tana da karancin shekaru sai da tashiga da muwan ganin abin da akawa ummin ta. da daddare safna ta fito falo ta zauna yau abin mamaki jalal ko awaya be ne meta ba , taita zama ita kadai har ta gaji ta wuce dakin su. kasa barci tayi bata san tana matukar son jalal ba sai yau, sai juyi take agado gaskiya tana son ganin mijin ta, daukan waya tayi ta kira jalal har sau 4 be dauka ba, gani tayi bazata jura ba, ta mike. zuwa tayi ta taba kairat dake kwance akan gado , dasauri ta zabura. safna tace dama bakiyi bacci ba, wai yau me ya same ki tunda kuka dawo sai faman fashi kike. duk da karancin shekarun kairat sai taji bata son ta fadawa safna abin da ya faru dan haka tashiga tunanin me zata fadawa safna, cen tuna yaya jalal idan bai son ya fadi gaskiya sai yace kansa ke ciwo, dan haka da sauri ta ce anty kaina ne yake min ciwo, amman yamin sauki. safna tace sannu da kuwa aiken ki zanyi gashi kince kanki na ciwo. ai yayi sauki, tashi tayi tace ina zaki aikeni gun yaya jalal? eh kije dakin sa ki gani lfyr sa kalau san nan kuma kice mai nace ina gaida shi. da gudu ta nufi dakin jalal . ummi na kawance tana ta faman aikin kuka taji takun tafiya tace azuciyar ta wannan ba yafiyar jalal bane da sauri ta mike ta fito . hango kairat tayi ta taba kofar jalal tace ke kuma ina zuwa? ummi anty safna ce ta aike ni gun yaya. toh naji jeki karki dade, tura kofar tayi tashiga ta same shi yana zaune ya hada kai da gwaiwa. zuwa tayi daf dashi ta zauna ta kira sunan shi yaya baka da lfy ne ? dagowa yayi cikin fada yace ke fita ki bani guri. kairat tace yaya fah anty ce ta aiko ni. me tace? tace wai tana gaishe ka. dadi yaji har ransa wannan ne karo na farko da safna ta nuna ta damu dashi amman saidai yau baya cikin farin ciki. yace kairat kice mata ina amsawa . juyawa tayi da gudu , jalal yasake tsayar da ita yace kice mata nace tabar wayar ta a kun ne zan kira ta. ummi na zaune afalo kairat ta fito ta wuce ta tashiga nasu dakin. da sauri safna tace me yace mike kairat ta gaya mata abin da yace. tunani ta shiga yi gaskiya akwai abin da yake damun jalal, haka taita jiran jalal yakira ta taji shiru har gari ya waye. 8:30 ummi ta shiga dakin jalal tasa meshi yagama shiryawa tace yauwa jalal dama so nake ka rakani gidan yaya rabi. ummi da yau ina son na koma office ne kinga tun biki ban koma ba kar daddy yayi fada. jalal ina cikin wannan halin har kake maganar office har ina tunanin kana tausaya min. jalal yace ummi bawai bana tausa sayin ki bane dama tsoro nake ji kar ran daddy ya baci, amm ba komai zo muje. suna fitowa falo yace ummi bari naje na danga safna. daurewa tayi tace to karka dade *********** yana shiga yace kairat jeki falo da gudu ta fita, shi kuwa jalal zuwa yayi ya hau kan gadon ya daga safna dake kwance ta rufa da bargo, fuskar ta duk hawaye, yace safna me ya faru? da sauri tace bakai bane kaki daukan waya na kuma kace zaka kirani amman kaki Kira. daukan ta yayi ya daura ta ajikin sa kiyi hakuri safna bansa kinkira niba kuma jiya bana jin dadi ne shi yasa baki ganin ba, safna dama zaki shiga da muwa idan baki ganni ba? tura kanta tayi cikin kirjin shi tana dariya. Shima kara matseta yayi yana dariya suna cikin haka saiga kairat ta shigo. da sauri jalal ya ajiye safna yace ke bacewa nayi kije gurin ummi ba. a tsora ce tace ummi ce tace na dawo na zauna. sai alokacin jalal ya tuna ummi na jiran shi, sau kowa yayi yaje kunne safna ya rada mata wasu magana ya fita yana dariya ita kuma tasa hannu ta rufe ido. yana fitowa yace ummi muje kallon jalal tayi ta daure fuska ahaka zaka tafi kayan ka a yamutse. [7:56PM, 12/8/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written by Fadeela lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ 67-69 Sai alukacin jalal ya kalli kayan sa sun yamutse amman saiya dake ya kalli jikin shi yace muje kawai ummi. Wlh bazaka fita a haka ba ,kai kadai ne me mata, ko akan ka aka fara, haka kaga sauran maza suna fita? shiru yayi mata bece komai ba. suna cikin haka alhaji ya fito yace me yayi ne naji kamar kina mai fada? cinki daure fuska tace jifah kayan shi wai haka zai fita. alhaji yace me kayan nasa sukayi? jifa inda kayan shi suka ya mutse sai kace akan shi aka fara aure. alhaji hada rai yayi yace jalal jaka abin ka. da sauri jalal ya juya ya shiga dakin sa. alhaji ya kalli ummin yace wai zaliha ko hauka za kiyi ne, ina ruwan ki da kayan sa, irin wannan ai sai ya raina ki, yaya mutun da matar sa zaki saka masa ido. alhaji bazance sa ido bane maganar gaskiya ne, ai wannan rashin kunya ce. toh shikenan nasan maganin abin ai in da suna gidan sune baza ki saka musu ido ba, haba na menene zakibi kita kurawa yara wucewa yayi ya fita ya ta fada. bayan jalal ya canza kaya ya fito suka dau hanya ahanya ne ummi ta kalli jalal taga fuskar shi murtuk tace jalal fushi ka keyi dan na gaya maka gaskiya . a,a ummi ni ba fushi nake ba. ta sake cewa jalal ni bawai ina kinka da safna bane, abinda yake damuna shine sultan ya taba neman safna kuma kasan sultan ba irin yan iskan da be nema ba, ina jin tsora kar ace ya shafa mata ciwon zamani shiya sa nake tsoron karka kusan ce ta, ta shafa maka. jalal yace ummi dan Allah karki kara irin wannan maganar ba komai atsakanin su kuma lfyr ta kalau. kar kace zaka shede ta dan ni na taba ganin su da ido na . jalal yace dan Allah ummi kibar maganan nan ni bana so. ai ina gaya maka ne dan ka kiyaye. toh zan kiyaye eh ummi naji zan kiyaye. ganin da tayi kamar ya shiga damuwa yasa ta murna tafara nasara. shikuwa jalal yasan cewa shi ya fara bude matar sa a leda, amman zuciyar shi ta fara raya mishi anya kuwa sultan be lalube safna ba kuwa , dan haka ya kosa ya koma gida ya tuhu meta. da haka suka isa kofar gidan yaya rabi , ummi ce kadai ta shiga, jalal ya tsaya a mota. ummi ta shiga tare da sallama yaya rabi ta fito daga cikin dakin ta sukayi ido biyu da ummi. ta fara fadin zaliha kodai gizo idona kemin. ummi tace ba gizo bane yaya rabi nice. aguje yaya rabi ta fada jikin ummi tana kuka, ummi ma kuka ta saka , haka sukai tayi babu mai lallashin su . bayan sun natsu suka shiga tattauna wa akan halin da suke ciki, ummi ta kwashi duk yadda sukayi da baffa ta gayawa yaya rabi. yaya rabi tace banga lefin baffa ba zaliha . ummi tace nima banga lefin saba amman matakin da ya dauka yayi tsauri yanzun a ina zan nemo saudatu, kawai ina ganin bazai yafe min bane shiyasa yace saina nemo ta. toh nidai abinda nake gani zaliha ki jaraba ki gani ko Allah zaisa adace. toh ni yanzun ta ina zan fara, alhaji yace min wai agidin wata bishiya aka bar ta ko? dan Allah ina son ki tambaye min su baffa wacce bishiya ce kuma awace unguwa ne. murmushin takaici tayi sannan tace zaliha kenan ko kisan saida nayi shekara biyar ina zuwa gidin bishiyar ina zama ko Allah zai sa na ganta amman ko me kama da ita ban gani ba. ummi nisawa tayi sannan tace kuma kin tamya agurin? tambaya kuma ai sai da na zama kamar mahaukaciya duk wanda nagani saina tambaya. ummi shiru tayi sannan tace yaya rabi banida saura wata dama ila kawai ki gayamin gurin inje in jaraba ingani yaya rabi tace kusa da unguwar ku ana cewa unguwar 'yan mangorori, akwai wata katuwar bishiya agurin ada amman ayanzun babu bishiyar amman akwai wata tsohowa tana kasa kayan miya. tuni ummi ta gane kwatance domin tasan unguwar sosai sai dai unguwar talakawa ne. jalal ne ya fara kiran ummi awaya tace au na manta nabar jalal awaje yaya rabi tace shine ya tsaya awaje sai kace bako. mikiwa sukayi suka fito tare, jalal na zaune idon nan jawar ya kosa ya koma gida ya tambaye safna ko sultan ya taba taba mata jiki. bayan sun gaisa da jalal suka dau hanya jalal yaso su wuce gida amman ummi tace sai sun biya yan mangorori. suna isa ummi ta sauka ta isa gurin tsohuwa me kayan miya bayan ta gaida ta , tace dan Allah mama tambaya nake? yar tsoha cikin murna tace Allah yasa na sani hajiya. dan Allah mama shekaran ki nawa agarin nan? ai ni hajiya agarin nan aka haife ni ban taba zuwa ko ina ba. nan ummi tashiga karanto mata tambayar ta. tsohuwa tsayawa tayi tayi shiru zuwa cen tace, nidai kamar nasan lbrn nan amman na manta tasake yin shiru ummi kuka tashiga yi tana fadi mama ki nutsu ki tuna ahankali, ko kudi kike so zan biya ko nawa ne kowa. tsohowa tace yarinya ki kwatar da hankalin ki insha allahu zan bincika miki kinga yanzun zan tattara kaya na gobe ki dawa kin ga gidana cen koda baki ganni anan ba sai ki shiga ciki. haka ummi ta aje ma tsohuwa kudi masu yawa ta wuce. Suna komawa gida jalal ya fita amotar da sauri yariga ummi shiga gida , ummi binshi tayi da kallo tazata maganar da tagaya mishi ne yake damun shi , shikuwa jalal cewan da tayi ta taba ganni su da idon ta shine abinda yake tayar mai da hankali. yana shiga falo yaga safna kwance tana bacci besan lokacin da ya finciko taba yafara janta yana kokarin shiga dakisa da ita. safna cikin firgita ta fara ihu dai dai lokacin ummi ta shigo , hango jalal tayi yana jan safna idon shi arufe. ummi tarogo da gudo tana fadin jalal metayi maka. ai jalal babu magana jan safna kawai ya keyi [4:35PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written Fadeela Lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ 70-72 Daker ummi ta kwaci safna ahannun jalal ta kaita dakin su . da sauri ta juya ta nufi dakin jalal dan tana tsoron kar yagayawa alhaji dan idan yaji maganar nan kashinta ya bushi. tana shiga ta same shi sai faman share zufa yake tace jalal kardai maganar da mukayi dazun ce tasa ka shiga cikin wannan halin ? jalal yace ummi kefa kikace kin taba ganin su da idon ki a,a jalal bahaka na ke nufi ba, karufa min asiri kar alhaji yaji wannan maganar, nidai nace kayi hakuri kabari ayi mata test , kuma ko safnan ban ce kagayawa waba bare baban ka. toh ummi ai bai kamata ayi shiro ba ya kamata kowa yasani. nidai nace karka gayawa kowa, kai wlh duk kabi karice akan safna. jalal kallon ummi yayi cike da ta kaici wato haryan zun tana nan akan bakan ta saita raba mu , wai ita ummi bazata gyara halin taba ne, tana cikin wannan halin baza ji da abin da yake damun taba. yace shike nan ya wuce, ummi mikewa tayi ta fita, dasauri jalal ya dauki wayar shi yakira safna bata dauka ba saida yakira sau biyar yaji shiru ya tabbatar safna fushi tayi mikewa yayi yaje kofar dakin su yaji ta kulle, yasan ko ya buga ba budewa zata yi ba haka ya koma dakin sa. washegari 8:00 jalal ya fito cikin shiri shi na tafiya office bayan yayi wa ummi sallama ya leka dakin safna har yan zun kofar akule take, ya juya ya fita. ummi ma guri 12:00 ta bar gida ta nufi yan mangorori, sai safna kawai ta rage agidan, dan kairat ma tana makaranta. safna na zaune ita daya agidan dan me aikin gidan ma tayi tafiya ga yunwa ta dame ta rabonta da abinci tun jiya da rana gashi kuma yau hakanan ta tashi da son cin zogale . mikewa tayi ta shiga kitchen ta duba bataga wani abu da ya bata Sha,aw ba bude wata roba tayi nan taci karo da garin daddawa murna ce ta kamata tun daga nan tafara lasa tana lumshe ido, da sauri ta daura miyar daddawa tana gamawa tayi tuwo ta dai dai cikin ta tafito falo ta fara ci ,saiga kairat ta dawo makaranta, zuwa tayi ta zauna zata saka hannu dan sun saba cin abinci tare. kairat tace anty wannan miyar meye na ganshi baki. safna tace kedai in zakici kici miyar daddawa ce. da sauri tajanye hannun ta tana toshe hanci anty dama anayi miyar daddawa ne. safna tace ke nidai kawai yunwa nakeji ,bayan ta gama cin towan ta dauki miyar ta fara sha kenan saiga jalal ya shigo. safna naganin jalal ta mike da miyarta ahannun ta zata bar wajen. da sauri jalal yasha gaban ta ya tsareta da ido sai kallonta yake, itako kasa tayi da kai. jalal yace miye wannan kike sha? banza tayi dashi tana kokarin aje miyar dan ta samo daman guduwa tana aje miyar kuwa ta mamaye shi ta sheka aguje ta shige daki. jalal binta yayi da kallo yasan safna nashiga rufewa zatayi dan haka bebi taba. tsugunawa yayi ya dauki miyar ya koma ya zauna yalli kairat dake kwance akujera yace kairat faten meye wannan? kairata ta kwashe da dariya tace yaya ba fate bane , miyar daddawa ce. miyar daddawa kuma a ina ta samo shi? ita tayi da kan ta tace yinwa takeji yunwa babu kayan abinci ne a kitchen din sai daddawa, mikewa yayi yace kairat tashi kije ki zubar da shi. ummi bata dawo ba sai yamma jalal na zaune aharabar gidan yana shan iska , ummi ta nufoshi tun daga nesa jalal ya fahin ci babu nasara. bayan ta zauna jalal yace ummi akwai nasara kuwa? ummi tace ba wata nasara jalal , yau nasha bakar wahala jalal , rabon da na wahala haka na manta, munyi yawo nida tsohowar nan har mun gaji amman bamu dace ba, duk gidan wani tsoho da yake garin muje amman babu lbrn ta, ummi ta fara share hawaye jalal ina cikin wani hali banda me tausaya min duk duniyar nan sai kai, sai kuma yaya rabi dubi duk abin da na mata bata juya min baya ba, amman dubi alhaji yana shirin ya juya min baya, babu ruwan shi da damuwa ta kamar ma dadi yakeji. ummi ki daina fadin haka kuma ki kwatar da hankalin ki insha allahu indai tana raye za,aganta ummi fashewa tayi da kuka to yanzo jalal inta mutu ne yaya zanyi kenan su baffa bazasu yafe min ba. jalal yace ummi insha allahu zasu yafe mike amman ummi kunje har gidan me unguwa? ummi tace a,a Jalal yace ummi ni gobe zanje na bin cika. washe gari da wuri jalal ya fito yasamu ummi afalo kamar jira take ya fito , mikewa tayi tace jalal mutafi. jalal yace a,a ummi ki zauna agida ki huta. ummi tace nidai kawai mutafi haka suka tafi badan ran jalal yaso. suna zuwa gidan me unguwa suka tambaya aka nuna musu bayan sun isa sun tarar da wajen cike da mutane dukkan su suka sakko suka isa gurin tare da sallama, ummi ce tayi bayanin abin dake tafe da su. me unguwa ya nisa yace da kamar wuya ku me yasa tuntuni baku nemeta ba sai yanzun, aiko tana raye kila bata garin nan, har sun mike zasu tafi me unguwa yace amman bari akai ku gurin babana kuyi mishi bayani ko zakuci sa,a ya fahimci me kuke fada, dan ya dade kwance babu lfy. bayan an kaisu gurin shi tsoho ne sosai ummi ta mai baya ni. tsoho yayi shiru zuwa cen ya kira dan sa me unguwa yana magana ahankali me unguwa yasa kunne me kake cewa baba. baba tsoho yace karaka su gidan iya me kosai. me unguwa yace baba ai iya ta dade da rasuwa. sai gani hawaye sukayi yana bin kuncen baba tsoho ya sake cewa kukai su gurin danta malam musa. Me unguwa ya sake cewa baba malam musa yariga iya rasuwa sai dai matar sa [9:31PM, 12/9/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written Fadeela Lamido Mmn yazeed๐Ÿ“ 73-75 Da sauri ummi tace toh ku tai maka ku kaini gurin matar tasa. suna fitowa ummi ta nufi mota mutumin da me unguwa ya hada su dashi yace hajiya ai mota bata shiga unguwar. nan suka bar motar suka yanka a kafa tafiya suke tafiya taki karewa ummi ta gaji jalal yace ummi ko zaki zauna ki huta ne? a,a jalal mu tafi kawai kafin su isa ummi taci bakar wuya takalmin ta har ya bare zufa ke yanko mata ta ko ina kafar nan futo futo kamar ba itaba, suna zuwa ya nuna musu gidan. ummi ce ta shiga jalal yana waje sallama tayi acikin gidan ,goggo ta taho da sauri tana fadin hajiya batan kai kikayi ne ummi tace a,a baki ne mu , munzo gurin mijinki sai muka same lbrn rasuwar sa. goggo tace ayya malam ai ya dade da rasuwa, shigo ki zauna dauko tabarma tayi ta shin fida. ummi ta zauna tana fadi ba zama ma zamuyi ba muna sauri ne. goggo tace ai ban shai da kiba hajiya kin dai yimin kama da wata wadda na sani. cikin murna ummi ta gayawa goggo abinda yake tafe da ita. goggo tace ikon Allah ni ko na san saudatu kishiya ta ce tunda malam ya tsunto ta shekarar ta uku babu wanda yazo neman ta dan haka malam ya aure ta amman Allah yayi mata rasuwa tare da malam sukayi hatsarin mota su rasu. da karfi ummi tasa ka kuka , jalal dake waje yaji kukan ummi ya shigo aguje. yana shigowa ummi ta fara cewa abduljalal saudatu ta rasu. jalal yayi tabawa ummi hakuyi, yace tashi mutafi sun mike zasu tafi goggo tabi ummi da kallo matar nan ta bata tausayi tana son ta kaya mata saudatu tana da yarinya amman tanajin tsoro dan bata san inda safna take ba. sun mata sallama zasu fita kenan sai ga wata kawar goggo ta shigo gidan. tace baki kikayi ne? goggo tace wlh yayar saudatu ce sai yanzun Allah ya bai yana yan uwanta matar tace Allah sarki Allah ya kara muku hakuri saukin ta ma tanada yarinya. dasauri ummi ta sake hannun jalal tace dama saudatu tabar yarinya shine baki fada mana ba. tuni goggo ta fara rawar baki em dama mantawa nayi dayake yarinyar ba a gurin na take ba tana cen gurin dangin kakar su shi yasa bari ma kika hotunan saudatu shiga daki tayi da fito da hoton saudatu da malam da yar karamar yarinyar su dayan kuwa saudatu ce kadai ummi ta dauki wadda suke harda yarinyar ta kurawa yarinyar ido gani tayi kamar ta taba ganin yarinyar tuni tafara share hawaye tana fadin jalal yariyar nan kyakyawa ce tafi saudatu kyau tace jalal yarinya nan saina nemota saina mantar da ita rashin mahaifiyar ta da tayi. jalal yayi murmushi yace ummi nima naji ina matsanan cin son yariyar. bayan goggo ta musu kwatan cen garin su iya a zaria jalal yace yasan unguwar suna zuwa da alhaji. haka suka ma goggo sallama bayan sun bata gudi masu yawa suka baro ta. jalal ya cire takalman kafar sa ya mikawa ummi taki karba , dan haka ya tanbaya a ina ake saida ta kalmi aka nuna masa yaje ya sayo ma ummi silifas ne yama mata yawa ta karba tasa. bayan sun isa gurin me unguwa sukayi godiya sannan abduljalal ya dauki kudi masu yawa yace akai baba asibiti. haka suka isa gida ga farin ciki ga bakin ciki. suna fitowa a mota suka hango safna da kairat suna zaune agurin da jalal yake zama , kairat ce ta fara mikewa ta nufu gurin su ummi, dan haka safna babu damar guduwa itama gurin su ta nufu da miyar daddawan ta ahannu tana sha da cukali. kairat tana hango ummi ta fara sheka dariya tace yaya kalli takalmin ummi daga kan ta tayi takalli jalal taga fararan kayan shi sunyi jawur idon nan zuro zuro takara fashewa da dariya tana cewa anty safna kalle su. safna dariya ke neman kwace mata Amman tsoran ummi ya hanata yi. ummi tariko kairat tana fadi almura dan bamuje dake bane dasai kin fimu datti, ummi ta juya zata shiga gida jalal ya ruko safna kairat dake rike ahannun ummi tace anty safna wlh ki gudu zai shafa mike datti. ummi ta yaigo tace jalal meye haka. sakin safna yayi ya fara tam bayanta meye wannan kike sha, ko faten daddawan ne? banza tayi dashi yace wai har yanzun baki huce bane? nan ma babu amsa da haka suka isa falon, lokacin da suka shiga sun samu ummi tana nunawa kairat hoton saudatu da yar ta . kairat ta nuna karamar tace wannan wacece? ummi tace antyn ki ce kinga mamarta kanwata ce kairat tace ummi yaya sunan ta? ummi tace๐Ÿ˜ฌ na manta ban tamyi sunta ba, dai dai nan jalal ya shigo shi da safna. ummi tace jalal yama sunan yariyar nan. jalal yace au ummi baki tambayi sun ta bane? ummi kasa magana tayi ta dafa kai. Jalal yace ba komai ummi karki damu suna ba matsala bane kwanan zamu gano ta. nisawa tayi tace Allah yasa haka jalal, Allah yayi maka albarka. jalal yaji dadi sosai yace ameen ummi , juyawa yayi ya kalli safna sai fama shan abu take yace ummi kalli abinda yariyar nan take sha. ummi tace menene shi? jalal yace wani abune baki wai faten daddawa? ummi tace faten daddawa ko dai miyar daddawa, safna kawo nagani. safna ta mike ta nufi gurin ummi ummi ta kalla tace miyar daddawa ce bar ta taita sha kila ta saba sha akauyen su. Safna takalli ummi ta sunkuyar da kai tunda take da ummi bata taba mata rai kamar na yau ba, ta karbi miyar ta juya zata tafi jalal ya mike ya karbi miyar yana fadin bazaki sha ba. safna tace kabani miyata ina ruwan ka. jalal yace akwai ruwana wlh bazaki shaba. safna na ja jalal naja safna ta juya taga ummi tana kallon su da sauri ta sakar mishi ta wuce daki tana kuka. jalal zuwa yayi zubar da miyar yabi bayan safna yana shiga yasa meta ta fito bayi, yace wlh karna kuma ganin kinsha wanna abin kinji ko, inkuma kinki zan gayawa daddy, barima nagayawa anty nusaiba, dauko waya yayi aljihun sa yana dannawa. safna ta mike da gudu saboda wani amai da taji yana taso Mata . jalal na kokarin neman anty nusaiba yafara jiyo kakarin aman safna . [8:27PM, 12/10/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & written by Fadila Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ DEDICATE dis page to *Husaina Faji* _( Faji Rilwan)_​ *Gaisuwa agare ku* *zulehat mohd njidda* *hjy wasila dan sanwai, deeje oga* *fatima bello ahmad* *rashida ummar* _da duk sauran da ban fada ba, ina gaisuwa agare ku_ 76-78 Da sauri jalal yabi bayan safna ya kamata haka taita amai jalal na mata sannu, bayan ta gama da kansa ya wanke mata ya kamo ta suna kokarin fita kairat ta shigo tace yaya ummi na kiran ka . to yace da ita ya wuce da safna kan gado ya kwatar da ita , sannan yace toh yanzun me zakici nasan kina jin yinwa. da saurinta tace miyata zaka bani. au bazaki bar zancen miyar bako baya gashinan ya lalata miki ciki, amma bazaki bar shan taba. wlh ni ita kawai nake son sha dan Allah ka dauko min. jalal yace ai nagaya miki baza ki sha shiba ni nama zubar da shi. safna najin ya zubar mata da miya ta fara kuka. jalal mikewa yayi yana fadi abin naki babba ne , yasa kai ya fita. yana zuwa falo ya samu ummi har tayi wanka ta fito tace jalal memakon kaje kayi wanka ka hota . ummi safna ce wannan abun da take sha ya lalata mata ciki sai faman amai take. wuce kaje kayi wanka karabu da ita ita tasa ni. cikin mamaki jalal ya wuce dakin sa yana mamakin wanne irin tsana ummi tayiwa safna yana cikin wanka ya jiyo kairat tana yiwa daddy oyoyo sauri ya kara dan dama ya kosa dady ya dawo . yana gamawa kuwa yafito kananan kaya ne ajikin sa, kayan sun amshe shi yayi kyau matuka. yana shiga ya nufi daddy, tun daga nesa daddy yace jalal karka karaso nan dan bazaka haumin jiki ba mutun sai girma yake amman shi be saniba jalal be tsaya ba dariya ya fara yana fadin daddy nafa dade ban ganka ba, yana isa ya zauna daf da daddy ya daura kashi akafadar daddy yace ina wuni daddy. lfy lau jalal, ya safna? ai daddy mun kusa batawa da safna, bata jin magana ta. meya faro kuma kaida safnar taka? daddy wai daddawa take dafawa tana ci, nayi nayi ta bari taki bari. murmushi daddy yayi sannan yace jalal karka kara hanata ka bar ta taci, wata kila Sha,awa take. daddy yau fa ya lalata mata ciki amai tai tayi fah dazun, yanzun ma tana cen kwance, bayan sun fito safna har lokacin bacci take, gidan hajiya suka wuce suna isa alhaji ya shiga yana fadi , jalal tashi yariyar nan ta kwanta sosai. jalal na taba safna ta mike ta fito amman jiri sai dibanta yake, jalal ya riketa, ahaka suka shiga ciki, wannan shine zuwan humaira na farko gidan hajiya, saidai kuma jikinta babu kwari. folo suka same su har anty nusaiba suna shiga hajiya tace kawo ta nan kusa dani ta kwanta, anti nusaiba ce ta dafa safna tace safna meya sameki, duk kinbi kin lalace sai kace ba amarya ba. sai alokaci safna ta sake kuka, anty ni yunwa nakeji , kuma nasha wahala nayi miyata yaya ya zubar min wai bazan shaba. da sauri anty ta juya barayi jalal tace me yasa ka zubar mata, kana hauka ne? jalal yace anty kisan abinda ta mayar abincin ta, daddawa fa take tafawa taita faman sha , kamar wata mahaukaciya. daddy na daga gefe yana jinsu. hajiya tace wata kila kaine mahaukacin banda abinka jalal dacen tana ci ne, tunda kaga tana ci ai saika tuhume ta, amman ba laifin ka bane, zaliha ce babban me lefi. jalal har yanzun bai gane me suke nufiba. hajiya ta sake cewa safna sai ki fada wani abun da kike so adafa miki . safna kasa tayi da murya tace ni irin miyata nake so. da sauri anty tashi ta shiga kitchen. jalal matsawa yayi kusa da safna yace wai ke lafiyar ki kuwa. be gama rufe bakiba yaji ta kwaro mai amai ajiki, jalal be damu da aman dake jikin shi ba yaje ya rike safna. hajiya ta mike tarike safna tace jalal jeka ka gyara jikinka, jalal fita yayi arude alhaji ya bishi da kallo. jalal na fita aman ya tsaya toilet ta wuce da ita tahada mata ruwan wanka, fitowa tayi ta wanke kayan safna ta shanya, safna nafitowa anty nusaiba tayi daki da ita, zanin hajiya ta bata ta daura ta hada mata da karamar riga, tace to muje ga miyar cen na gama. suna fitowa suka samu hajiya suna ta fira da alhaji, jalal kuwa ya kwanta akan kujera, babu riga ajikin sa sai faman danna waya yake. safna ko tana shigowa ta toshe hancinta. anty nusaiba ta kalli safna tace meye kuma? daurewa kawai tayi tace babu komai anty ni daki zan zauna. anty tace a,a ki zauna cikin mutane zakifi jin dadin jikin ki. haka safna ta zauna badan ranta ya soba dan ita kusa da jalal ne bata son zama saboda wani irin wari yake mata. karban miyar tayi ta fara sha, dadi sosai ya mata domin anty har hanta ta zuba aciki, daddy kuwa kalon safna kawai yake yana murmushi, shikuwa jalal gani yake be kamata su biye mata taita shaba. zuwa cen safna tace anty kicewa yaya jalal yaje waje. anty tace akan me zai fita? Jalal ma tashi yayi ya zauna yana jira yaji me zata ce. safna tace anty wlh wani irin wari yake min, zai sani amai. da sauri jalal ya nufo safna Ina wasa dake ne , dan kin rainani zakice ina wari. 07014197556 [9:34PM, 12/11/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 79-81 Alhaji ne ya da katar da jalal kar ka taba yariyar nan kabar ta taji da abin da yake damun ta. daddy bakajin abin da take cewa ne wai nine nake wari. eh naji zo muje gida gobe kazo ka duba ta. daddy to safna fa anan zamu bar ta? alhaji yace eh, ke nusaiba gobe ki tam yi mijinki in yabar ki kizo ki kaita asibiti, nusaiba ta amsa, alhaji ya juya yana fadin jalal zomu tafi. jalal kuwa ya kulu iya kuluwa yana gani daddy ya fita yace wlh zaki sani bakin ga suna goyan bayanki ba har kike cewa ina wari ko, yana gama fadan haka ya fita da sauri. ahan yar su ta zuwa gida ne alhaji yace meye naka na damuwa dan ance kana wari, kasani ko ciki gareta. jalal yayi shiro cen yace daddy cikin haihuwa? eh mana ko baka sone? sai alokacin kunya ta kama jalal ya dukar da kai. alhaji yasa ke cewa dakai fa nake magana. jalal yayi kasa da murya yace ina so. kana so amman kake ta mata fada? jalal ya sake cewa daddy ai ni ban kawo tuna nin haka ba, nadauka kawai kwadayi ne. alhaji yayi dariya yace wa yaga jalal da d'a jalal ma dariya yayi, ya shiga tunanin yanzo in ummi ta sani yaya zata yi, gaskiya be so ciki yanzon ba yaso sai sun tare agidan su. sun kusa gida gaban jalal sai faduwa yake kar fa daddy ya fadawa ummi dan yaga daddy marna yake sosai bakin shi yaki rufowa. jalal ya fara sosa kai, alhaji yace jalal akwai magana kenan, gaya min me yake damun ka. daddy dama zan ce ne karka gayawa ummi. tuni murmushin dake kan fuskar sa ya gushe yace saboda me? rasa abun da zaice yayi sai cen yace ina ganin kamar bazata so bane. fada alhaji ya fara kada Allah yasa taso, abon kunya kayi, ko cikin shege ne? da sauri jalal yace a,a bayan sun shiga gida ummi ta tare su da murna jalal ya wuce dakin sa. bayan wucewan jalal ummi duk ta kwashe yadda akayi zuwan su gidan goggota gaya mai, alhaji nisawa yayi sannan yace ya kamata agayawa baffa domin su tabbatar ta mutu hankalin su ya kwanta kuma suyi mata ardu,a. ummi tace alhaji bazan iya tunkaran su da wannan maganar ba, da dai ace na samo yariyar ne sai naje. alhaji yace kibani hotan na tafi dashi sai nayi musu bayani. bayan subar wannan zancen alhaji yace zaliha wai yaya kike ganin yaran nan jalal da matar sa suna dai zaune lafiya ko? ummi ta tabe baki tace nidai alhaji a inda nake ganin su kamar basa zaune lfy, shima da yake rawar kai naga ba kamar da ba. alhaji yace nikuma sai naga kamar yarinyar ciki ne da ita. haba dai alhaji wani irin ciki kuma. alhaji yace ban gane haba dai ba, sai kace wadda bata da miji. da sauri ummi tasha kwana a,a alhaji ai dama ba cewa nayi bata da miji ba, nidai banga alamun ciki bane, atare da ita. ai dama bazaki gani ba saboda ba kula kike da itaba, da jalal ne bayi da lfy har yake amai bazaki ce baki sani ba. eh alhaji jalal ya gayamin safna tana amai amman alhaji ai ba lallai sai ciki ba ne ake amai. alhaji yace toh yariya dai tana ce babu lfy. mikewa tayi bari na gan ta. alhaji yace ai gidan hajiya muka baro ta, ummi ji tayi babu dadi. washe gari jalal ya fito da safe zai tafi gidan hajiya. ummi tana ganin shi tace ina zakaje da sasafen nan bayan yau babu aiki. ummi zanje gidan hajiya ne, in duba safna. zonan ka zauna babu inda zakaje. ummi bata fah da lafiya ne. eh naji zoka zauna bayan jalal ya sauna ummi tace wai me yake damun safna? jalal yace nima ban sani ba. ummi ta sake cewa toh waye yace wa alhaji safna tana da ciki? gaban jalal ya fadi da saurin sa yace ummi ban sani ba. ummi ta sake cewa jalal ina fatan dai babu abinda ya shiga tsakanin ka da safna? shiro yayi kan shi akasa, gaban shi kuwa sai faman faduwa yake dan gaskiya yana matukar jin kunyar ummi sa, kartaga yaki jin magarta. cikin fada ummi tace dan ubanka bada kai nake magana ba. sai alokacin jalal yace ummi babu komai kasa ka rasawa yayi dai dai lokacin alhaji ya fito. alhaji yana fitowa yace jalal kana nufin cikin da safna take dauke dashi ba na ka bane?? jalal mikewa yayi yace nawa ne daddy. mikewa ummi tayi tace wlh alhaji karya yake zai dai rufa mata asiri ne , amman bata taba kwana dakin sa ba. alhaji ya juya yace haka ne jalal, ka fada min gaskiya? jalal ji yayi kamar ya tsaga kasa ya shige ayau zai kar yata mahaifiyar shi kuma in yayi shiru beyiwa safna adalci ba. alhaji ya sake cewa jalal dakai nake magana, dama baka taba kwana daki daya da safna ba?? dukar da kai yayi hawaye na zuba afuskar shi yace mun taba daddy sau biyu [8:40PM, 12/13/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 82-85 Ummi kalon jalal tayi cike da mamaki batace komai ba illa dafe kanta da tayi ta koma ta zauna jabar. alhaji kuwa ajiyan zuciya yayi tare dayin hamdala azuciyar shi, kallon jalal yayi yaga duk yabi ya rikice sai kace mara gaskiya alhaji yace ni abinda nake son na sani shine yaya akayi safna tabar dakinka bayan tun randa aka daura aure aka kaita dakin ka? jalal ya bude baki zaiyi magana ummi tai sauri tace alhaji yariyar ce, alhaji be bari ummi ta karashe maganar taba yace ba dake nake ba ki rufemin baki, jalal ina sauraran ka? cikin en ina jalal yace ai tun ranar tabar dakin. alhaji yace saboda me? jalal juyawa yayi ya kalli ummi yasa ke dukar dakai. alhaji ma kallon ummi yayi yace toh toh na fahimta jeka abinka. da sauri jalal ya shige dakin sa dan dama ya kosa ya bar wajen. yana shiga daki alhaji ya farawa ummi fada zaliha al,amarin ki ya fara bani tsoro dama nalura da take taken ki baki son auren jalal da safna, yanzun saboda Allah zaliha abinda kikayi kin kwauta kenan, akaiwa yaro amarya kije ki raboshi da ita dan dai ki lalata masu farin cikin su, toh gashinan Allah yanuna miki iya karki dan yanzun nusaiba takira ni take gayamin safna ciki gare ta, ni abinda yake daure min kai wai me yariyar ta mike da har kike neman ki raba su? shiru ummi tayi tana dafe dakai idon ta a rufe. alhaji yace toh bari kiji karki kara gigen raba musu aure dan idan har auren su ya mutu kema naki zai mutu, mahaukaciyar banza mahaukaciyar hofi. da sauri ummi ta bude idon ta da sukayi ja takalli alhaji tunda take alhaji betaba fada mata bakar magana kamar nayau ba. shi kuwa yana gama maganar sa yayi waje, ko sallama be mata ba. ummi tana son ta zubar da hawaye amman ta kasa ashe kuka ma rahama ne, jitayi duniyar na juya mata tun daga nan bata kara sani me ya faruba. jalal ne ya fito ya same ummi cikin ma woyacin hali kinkiman ta yayi ya nufi motar sa da it a. bayan sun isa asibiti aka mata yan gwaje gwaje suka tabbatar wa jalal jininta ne ya hau sosai sun so sukwatar da ita amman taki yadda, dan haka suka bata magun guna suka koma gida. jalal dakan sa ya bata magani tasha sai da yaga tayi barci ya koma dakin sa. ya koma daki da tunani kala kala azuciyar shi yana son yaje ya duba jikin safna kuma baya son yabar ummi. har dare jalal be fita ba sai zarya yake dakin ummi, zuwa cen yaji da wowan alhaji dan haka ya shirya ya fito da nufin tafiya gidan hajiya. dakin ummi ya fara shiga ya same ta zaune ta fito wanka neman guri yayi ya zauna yace sannu ummi ya jiki? Waigo wa ummi tayi tace tashi ka fita kabani guri dan iska kawai, na barwa safna tunda ka zabeta akai na ,kai dadi mata har ace ina cikin gidan nan kuka maidani baho. tsugunawa yayi ummi dan Allah karkiyi min haka kiyi hakuri ummi gani nayi mata tace. au zakaci gaba damin rashin kunyar ne, ai gara kanuna min ka girma, saida nagama cin kashin ka da fitarin ka, ni bazan ma baki ba amman karka kara zawa inda nake niko ganin ka bana sonyi. da sauri jalal ya mike yace ni ummi baki son ganina, me nayi miki da zafi haka, kuka ne ya kwace masa, amma duk da haka be bar maganar ba, sake cewa yayi ummi anya kuwa ke kika haifeni? ummi tace au mamaki kake yi ai dan ma bagida na bane da koran ka zanyi. jalal ya fara share hawaye yace toh ummi nagode da saurin sa yabar dakin. dakin sa ya koma dan bazai iya fitaba yana shiga ya sake kuka kamar karamin yaro. safna kuwa tun bata damu da rashin zuwan jalal ba, har ta fara tunanin meye ya hana shi zuwa.gani tayi har dare yayi ta zauna tayi tagumi, gurin karfe 8:30 mijin anty nusaiba yazo daukan ta. safna tace anty tafiya zakiyi? anty tace au da kin dauka kwana zanyi toh ko na kwana ne? cikin shirin kuka tace a,a ba haka nake nufi ba, yaya ne yaki zuwa har yanzun. murmushi anty tayi tace safna ai na dauka baki son jalal yazo kusa dake ne, tun da kina son ganin shi bari na kira shi, anty takira wayar jalal tajita kashe dan haka ta musu sallama ta wuce. safna mikewa tayi ta shige dakin Hajiya kuka ta fara ta dauki wayar ta tagwada kiran jalal har yanzun wayar shi kashe take, kukanta karuwa yayi ita fa gaskiya in bataji muryar sa ba zata iya barci ba hajiya ce ta shigo ta samu safna sai faman kuka take tace ke lfyr ki kuwa? mikewa tayi ta nufi gadon hajiya tana fadin ba yaya bane yaki zuwa. hajiya tace ikon Allah yaran zamani babu kunya, yanzo nan duk kukan jalal din ne. kwanciya tayi ta juya baya tayi shiru. hajiya ta dauka bacci tayi dan haka itama ta kwanta, gurin 10:45 hajiya ta farka ta fara juwo kukan safna kasa kasa, daukan wayar ta tayi ta kira alhaji, alhaji yana dauka yace lfy kuwa hajiya hajiya tace lfy lau ina abduljalal ne yau bamu ganshi ba, nusaiba takira shi wayar shi kashi. toh inaga yayi barci ne gobe zai zo da safe. ai ni safna ta hanani barci sai faman kuka take bataga mijin taba. alhaji dariya yayi yace bari na tado shi tunda ta hana ki bacci gara kowa ya tashi [7:59PM, 12/14/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Writeen Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ _*DEDICATE*_ *_dis page to_* _Faty afreen_ *Gaisuwa agareki* *๐Ÿ’‹Big girl๐Ÿ’„* *marubuciyar NUFIN ALLAH* *KUNA RAINA* *Sa,adatu lamido* *Anty rabi lamido* *Sa,adatu abdullahi* _(ummita)_ *Rukayya sani gini* ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜ 86-88 Sauko wa yayi ya nufi dakin jalal ya tura kofa yajita kulle dan haka ya shiga bugawa. jalal dake kwance sai faman juyi yake agado ya bude baki a hankali yace waye? muryar daddy yaji yana fadi nine, sakowa yayi cikin sauri ya bude kofar alhaji ya shigo ya kalli fuskar jalal yace me ya same ka? shiru yayi yasa kan sa akasa. girgiza kai alhaji yayi sannan yace kai da mamar ka ne ko? jalal be amsa ba kuma be daga kai ba. alhaji ya sake cewa me tace maka? ba komai daddy kwai dai nasan tana fushi dani ne. toh dan wannan kake tada hankalin ka, kabar ta zata sako , kaji ko, me ya hana ka zuwa ka duba jikin safna? daddy naga ummi bata da lafiya ne, kar na fita kuma jikin ta ya tashi. kai ka dai na biyewa ummin nan taka wanne irin ciwo take lafiyar ta kalau dama abin da take so kenan. jalal yace wlh daddy bata da lfy jininta ya hau sai da nakai ta asibiti dazun. shiru alhaji yayi zuwa cen alhaji ya matsa bakin gadon jalal ya zauna yace matar ka keson magana dakai, warshi ya danna ya mikawa jalal sannan yace inka gama ka kawo min daki , dakin ummi ya nufa, yagan ta kwance tana bacci dan haka ya wuce dakin sa. shikuwa jalal bayan yasa wayar akunne sa murya hajiya yaji tana fadin an tado shiko? jalal yace hajjaju ya gari, har yanzu bakiyi bacci ba, yanzun fah 11:14. ina ni ina barci safna tasani gaba sai kuka take. kuka kuma, me aka mata? hajiya tace wai dan rashin kunya tun dazun take kuka wai baka zoba. duk da halin da yake ciki sai da yayi dariya, sannan yace Ina take? hajiya na mikawa safna wayar ta tashi ta fita. safna na karbar wayar ta saka mishi kukan sha gwaba, jalal ya rasa yaya zaiyi mata inama suna kusa da juna. a halin yace safna ya isa haka, kiyi shiru, kara sautin kukan ta tayi . jalal ji yayi yana yin jikin shi ya fara cen zawa babu abin da yake so ayanzu ila ya ganshi kusa da safna. daker ya bude baki cikin kashe murya yace safna kina tayar min da hankali fah, dan Allah kiyi shiro gobe zan zo. cikin kuka tace ni yan zon nake so. jalal yace safna bakiga dare bane yanzun, kibari gobe da wuri zan fito. toh naji karfe nawa za kazo, jalal yayi murmushi yace ke zaki fada tace karka wuce 9:00 am. toh ba damuwa insha Allahu zan zo haka din, yaya jikin ki? wlh yaya ni babu wani saukin da naji karuwa ma yake yi, yanzun ma fah ko ruwa bana son gani miyar nan ma dana ke sha yanzon bana son ta, kasan me nake son ci yanzun? jalal yace sai kin fada. zugale nake so da mangoro gobe inzaka zo kataho min da shi. jalal yace a,a safna ban miki alkawari ba ni bansan inda ake sai dawa ba , ki gayawa hajiya ne. toh mangoro fah? Jalal yace ai yanzun ba lokacin ta bane, jalal gani yayi zata sake rikice mashi, yace toh ya isa zan duba kwanta kiyi bacci, da haka sukayi sallama kallon agogo yayi yaga har 12:03 yasan yan zon daddy yayi bacci ajiye wayar yayi ya kwanta ya rungumi filo tunani ya shiga yi wato safna cikin nan bayan kwadayi har da surutu yasa ta jalal be samu bacci ba sai da yayi sallah asuba ya kwan ta dan haka be tashi da wuri ba, koda ya tashi ya duba agogo sha daya saura da sauri ya tashi yashir ya ya fito sai da ya duba dakin ummi bata ciki dan haka ya wuce dakin daddy acen ya sami ummi bayan ya gai da alhaji yace ummi ina kwana, kin amsawa tayi alhaji yayi kamar besan me suke ba jalal yasa ke cewa ina kwana ummi, wayar ta tasa akune tafara magana, alhaji ya kalleta yace jalal tashi mu tafi, mikewa yayi suna cikin tafiya alhaji yace jalal nagama gyarama gidan da zaka zauna sai dai karami ne, ban sani ba ko zaka so hakan. da saurin sa yace ina so daddy . alhaji yace yauwa jalal shiyasa nake son ka kwata kwata baka dauki duniya da zafi ba, mamar ka ko ban san ina ta samu wannan karyar ba, kaga wancen gidan ma daya kone sai da tayi korafin yayi maka kadan, toh yan zon yaushe zaku tare dan anriga anzuba komai agidan. daddy ni duk ranar da kace. murmushi alhaji yayi yace nifa so nake ku tare ayau dan bana son kowa ya sani hanta mahaifiyar ka kuwa. kwana alhaji yayi yakai jalal gidan ya gani gidane karami mai kyan gaske me dauke da dakuna biyu kowan ne da bayi aciki sai falo da kitchen jalal ya yaba tsarowan gidan sai yaga kamar ma yafi wancen kyau girma kawai wancen zai nuna ma wannan, gadiya ya shiga yiwa daddy. lokacin da suka nufi gidan hajiya daya saura dan haka ya samu safna ta cika tayi taf, alhaji kawai ta gaida ta juya ta shige daki, alhaji ya kalli jalal yace duk wayar da kuka kwana kunayi baku shirya ba. jalal yana dariya yace daddy time ta bani nikuma bacci ya kwasheni ban tashi da wuri ba yana fadan haka yamike yabi bayan ta , hajiya na fadin kardai ka zama mijin tace yana shiga ta mike ta zata fita falo jalal ya tare ta nan da nan ta saki kara sakinta yayi da sauri yana fadin baki da hankali ne bakiga daddy na falo ba, safna bata tsaya sauraran jalal ba ta nufi falo kujerar dake kusa da ta alhaji taji ta zauna akasa, tana zama jalal ya fito yasan ta zauna agurin ne dan kar yaje kusa da ita dan haka kujerar bayan ta yaje ya zauna. yana zama yasa kafarsa abayan ta yana dan zungurin ta, dakewa tayi kamar bata jishi ba zuwa cen ya fara mata waiwayi ta fara gan tsarewa tunda daddy yaga safna tana zabure zabure yasan jalal ne amma sai ya dauke idon shi daga waje. shikowa jalal so yake ya dame ta har ta gaji ta koma daki, zuwa cen yasa kafar sa ya daga rigarta ta baya ya fara mata cekulkuli, zabura tayi tare da sakin kara ta matsa cen tana soshe soshe. daddy ya waigo yace safna lfy.? daddy wani abu ya saka min ariga. alhaji yace kaga jalal karka firgeta yariyar nan tashi daga gurin nan kadawo nan. jalal mikewa yayi yakoma cen gefe kusa da hajiya. alhaji yace safna ki shirya anjima nusaiba zata rakaki gidan ki. dasauri tace daddy abari ba yanzun ba 07014197556✍ [6:11AM, 12/16/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 89-91 Alhaji ne ya kalli safna yace sabo da me zakice bayan zon ba? daddy abari sai naji sauki bani da lfy fah daddy d'aga hannun shi yayi ya mata dakuwa kinci gidan ku, yau din nan zaki wuce dakin ki kin fi son ki zauna anan kina hana hajiya bacci ko? daddy nifa bance kada tayi bacci ba ita da kanta tashi ta zauna, dariya hajiya tayi tace toh safna ba dole na tashi ba ni ina bacci nafara jin gunjin kukan ki. to aini kaina ne yake min ciwo lokacin. alhaji yace ai ko bakin kine yake ciwo yau zaku tafi, nima hankali na ya kwanta tunda aka daura auran nan hakali na ba,a kwan ce yake ba, buri na kulum be wuce nagan ku acikin gidan Ku ba. Safna shiru tayi ita gaskiya fushi take da jalal, muryar daddy taji yana cewa safna kuyi hakuri da junan ku ban da fada , kai jalal kaine babba banda saurin fushi , babba da hakuri aka sanshi, ke kuma safna ki sani jalal mijin ki ne dan haka kimai biyya, tuni safna ta fara kuka ji tayi auren ya dawo mata sabo. alhaji juyawa yayi gurin jalal yace jalal ya maganar karatun safna, ina fatan dai kana da burin taci gaba karatu? eh daddy insha Allah . alhaji yace to yayi kyau Allah yayi muku albarka ya baku 'ya'ya masu albarka. gaba dayan su kasa amsawa sukayi sai hajiya ce ta amsa. safna kuwa ta kifa kai sai faman kuka take. alhaji yace jalal zan tafi ko anan zan barka? a,a daddy tare zamu tafi ai ban fito da mota ba sun mike zasu tafi safna ta dago jajayan idonta ta harari jalal, yace Allah ya huci zuciyar ki. daddare kamar yadda alhaji ya tsara nusaiba tazo ita da matar baba salisu suka raka safna gidan ta, har bakin gado suka zaunar da ita sai faman kuka take. wurin takwas suka ceto mufa zamu wuce dare nayi. safna tace anty dan Allah karku tafi tsoro nakeji. nusaiba tace wani irin tsoro to bari na kira jalal. shikowa jalal lokacin da anty nusaiba ta kira shi yana kokari zuba akwatunan su amota ta kofar dake baya yake fitar da akwatin daddy na sakawa amotar har suka gama, jalal yaso yayiwa ummin shi sallam ko bazata amsa ba amman daddy yace ya rabu da ita, dakan shi ya raka jalal har cikin falon su , su anty nusaiba kuwa suna jin zuwan su suka tafi bayan daddy yasa musu albarka ya wuce gida , da niyar shima da safe zai wuce gurin aikin sa alhaji na fita jalal ya mike ya leka dakin safna daga bankin kofar ya tsaya ya kalli fuskar ta da sauri ta dukar da kai kasa, murmushi yayi yace ina zuwa, waje ya fita yafara ciro akwatunan su daga cikin mota, saida ya fara shigar mada safna nata sannan yashiga da nashi daki, yana ajewa ya shiga wanka bayan ya fito yasa ka kaya marasu dauyi ya nufi dakin safna. yana shiga ya same ta daidai ta fito wanka tana goge jikin ta tana ganin shi ta jawo hijjabi ta dake gefen gado tana kokarin sakawa. dariya taba jalal sosai ya matso kusa da ita ya zauna, yace to meye kuma na saka hajjabi me zaki boye min. gani yayi ta kara rudewa dan haka ya matsa ya riketa yace safna meya sameki? cikin muryar kuka tace bacci nakeji. murmushi kawai jalal yayi dan yasa ba gaskiya ta fada ba. yace to waye ya hanaki bacci. shiro tayi. Matsawa jalal yayi yace zoki kwan ta. zuwa tayi ta kwata ta kudun dune cikin hijjabin ta jalal ya fahimci safna bata sone ya nemi wani abu awajen ta, kollon ta yayi ko mai bata shafa ba, yace safna. amsawa tayi batare da ta waigo ba, yace haka zaki kwanta baki shafa mai ba bare kuma turare. yaya ai ni yanzun bana shafa mai. saboda me? tace wari yake min jalal yace wari man nakine yake wari, kitashi kawai ki shafa ke da kin ga baki son abo saikice yana wari, haka ranan kikace ina wari. Wlh yaya ban son warin man ne , sabolon ce ma na bayi na kasa wanka dashi ahaka niyi babu sabulu. jalal yace kina nufin ba sabulu kikayi wanka, kice ba wanka kikayi ba kin jiko datti, ai irin wanna saiki fada irin wadda kike so asiyo miki. batace komai ba ta juya tayi shiru ganin ta kwanta shima ya hau gadon ya kwanta zuwa cen ya fara kai hannun shi jikin safna , yi tayi kamar tayi bacci ahankali tafara jin hannun shi acikin hijjabin ta har zuwa marrar ta taso ta rike hannun amman sai tai tunanin in yaga tayi barci zai barta dan haka tayi kamar tana bacci saiji kawai tayi yana kwance towel din da yake daure jikin ta dasauri ta rike hannun shi, tace yaya jikina fa akwai datti , bakace na tayar da datti ba. cikin rauna nan niyir murya jalal yace ni banji wani datti ba yace gaba da abinda yake tun safna na ture jalal har sakon ya fara kaiwa gare ta, ta fara mayar mai da martani, nidai daga sun rikece, nayi waje aguje๐Ÿƒ๐Ÿผ๐Ÿƒ๐Ÿผ๐Ÿƒ๐Ÿผna jawo musu kofar. washe gari da safe 9:10 akafara buga kofar falon su da karfi, safna dake kwance jikin jalal ta zabura shima mikewa yayi da sauri ya saka jallabiya ya fita har yanzun buga kofar ake [7:25PM, 12/16/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 92-95 Abduljalal a tsora ce ya isa kofar dan gani yake kamar ummi ce , yasa hannu ya bude kofar yariyar dake aiki gidan anty nusaiba yagani tsaye da kayan abinci a hannun ta wani haushi ya turnekeshi besan sanda ya daga hannun shiba ya wanke ta da mari. a tsora ce yariyar ta dafa kuncin ta, ta ajiye abin cin ta arta aguje, abduljalal ya tsuguna ya dauki basket din yakoma afalo ya jiye yakoma dakin safna ya same ta sai faman raba ido take, yace ki kwatar da hankalin ki wannan yariyar ta gidan anty nusaiba ce, mikewa tayi cikin sauri tace bari naje nasan anty ce ta aiko ta kama hannuta yayi yace ai ta tafi abinci ne ta kawo, koma wa tayi ta zauna tayi shiru tafara tunani, lallai ummi bata son auren nan gashi yanzun tun daga gidan anty nusaiba aka kawo mana abinci kuma ai munfi kusa da ummi. muryar abduljalal taji yana fadi safna tunanin me kike? yaya tunanin kairat nakeyi mun barta ita kadai. yace karki damu idan muka gama cin amarcin mu zan dauko ta tadawo nan da zama gaba daya. safna tace yaya ummi ko zata bari? da sauri yace safna bar wannan maganar kisan tunanin me nakeyi . gargiza kai tayi yasake cewa ina tunanin gashi kin haifi yaro me kama dani. Safna tace nidai yariya nakeso. nima inaso safna amman nafiso ki fara da namiji dan nasa mishi sunan daddy. safna tace toh yaya in mace ce wani suna za,a sama ta. bude baki yayi ahankali yace na baki zafi. safna ta sake cewa baza,a samata sunan ummi ba? mikewa yayi yace taso muje muci abinci. safna ta lura yaya ko sunan ummi beson yaji ta Kira suna cikin cin abin cin ne wayar abduljalal tayi kara ya dauka yasa akunne sa, yana fadin ina kwana anty. anty bata amsa gai suwan shiba ta shiga yimai fada jalal me bilkusu tayi maka ka mareta har fuskarta ta kunbura haka? anty zuwa tayi muna barci taita buga kofar, safna duk tabi ta firge da sauri anty tace lallai jalal safnar yariyar goye ce da zakace wani an firgita ta, har yanzun dai kanan da bakar zuciyar ka , ita kuma safna tana kallo kamari yariyar muta ne ko, toh shike nan idan ka kuma ganin bilkisu agidan ka kasa bulala ka zaneta ba mari ba yana kukarin yin magana ta kashe wayar. ture abincin yayi gefe ya sake kiran ta bata dauka ba mikewa yayi ya shige dakin sa. safna binshi tayi da kallo domin bata fahimci abin da suke fada ba, ta fara kwashe kayan da suka bata takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito har lokacin jalal be fito ba, wuce wa tayi dakin ta tayi wanka kwalliya ta tsaya tayi sosai sannan ta nufi dakin jalal tana tura kofar tajita bude sallama tayi . jalal dake ciki ya amsa , tana saka kai ta ganshi tsaye ga dukkan alamu wanka yayi dan daga shi sai gajeran wando ga dogon wando a hannun sa yan kokarin sakawa. safna naganin haka ta juya baya , murmushi jalal yayi ya aje wandon hannun shi ya iso gare ta jin shi kawai tayi ya rogumeta, ta baya yana kaimata kiss ta ko ina kamar zai hadiye ta, zuwa cen yadan dakata ya leko da kansa zuwa daidai fuskar ta dan jalal dogo ne sosai, yace har kinyi wanka, Allah yasa dai yauma ba haka kikayi wankan ba sabulu ba. safna na rugume jikin jalal tace ai na samu wani sabulu acikin akwati na bashi da wari sosai. jalal yace jinan safna in kinji abu namiki wari ki daina cewa yana wari cewa zakiyi bana son kamshin shi, dan kinsan Allah idan kika kara cewa ina wari saina fasa miki baki. kallon shi tayi da mamaki tace yaya yanzo nan kai sai ka dake ni. me zai hana na dake ki ,kiyi abin dokan kigani. haba nina san bazaka dakeni ba in kuma zaka iya bismillah. jalal yace ai baki min komai ba yanzun. dan tureshi tayi kadan ta rike hancin ta tace yaya jalal wari yake. murmushi kawai yayi yace Ina binki bashin duka idan kika haihu zan miki. a,a ni ban yadda ba yanzun nake so. matso wa yayi ya riketa yace daidai ina zan daka. safna cikin ta, tanuna tace ka daki nan dariya jalal yayi yace lallai safna ke muguwa ce ,toh naki. haka zaman su yaci gaba da kasan cewa cikin farin ciki da kwanciyar hankali jalal yana nuna mata so daidai gwargwado har wani cika su kayi suka kara haske sukan leka gidan hajiya da daddare gidan ummi kuwa tunda suka tare ko jalal be leka ba bare safna, amman bata san cewa jalal baya zuwa ba gashi har sun kwashe sati uku da tarewa alhaji kuwa tun washe garin ranar da ya raka jalal gidanshi yabar garin ko sallama bema ummi ba. itako ummi ranar ta wayi gari daga ita sai kairat acikin gidan tayi tunanin wato jalal fushi yake da ita ko ganin shi baya bari tayi, alhaji kowa abakin kairat taji lbrin ta fiyar sa. tun tana ganin abi kamar wasa ne har ta fara tsora ta. kiran alhaji tayi har ta gaji be dauka ba, ta fara tunanin kiran jalal, amman kuma da kunya takira shi bayan tace mai bata son ganin shi, fadi tayi a fili me yake shirin faruwa dani ne, iyayena sunki karbata saboda halina dagin mijina basa sona saboda halina mijina dake takama dashi ya juyamin baya saboda yana kuka da halina, dana dake matukar so shima ya hakura ni ,afili take fadi kamar mahaukaciya zuwacen ta sake kuka haka taita yi babu me rarrashin ta yau ummi ta tashi da matukar so taga jalal tuni ta lura jalal kwata kwata baya shigowa gidan a lissafin ta sati hudu kena da barin su gida wata zuciya tace kodai tare sukayi tafiyar da alhaji be. mikewa tayi ta nufi dakin jalal tana tura kofar taji ta bude shiga ciki tayi me zata gani duk wani abu na amfanin jalal babu shi adakin, juyawa tayi gurin da aka aje a kwatunan safna nanma wayam babu komai. rawar jiki ta fara tana haki take fadin na shiga uku, dakin ta tafada ta dauki gyale drive takira tace zoka kai ni gidan hajiya, rabota da gidan hajiya ta dade. hajiya na zaune taga ummi tashigo kamar ankwato ta daga bakin kura 07014197556✍ [6:31PM, 12/17/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 96-99 Hajiya tsoro ne ya kama ta cikin kidima tace zaliha daga ina haka? cikin kuka take fadi hajiya nazo neman gafararki dan Allah kiyafemin a yanzun nagane kure na , kuka take sosai. hajiya tace alhamdulillahi dama haka ake so naji dadi da kika fahimce haka ni daman ban kullace kiba tunda ismail yakawo ki amatsayin matar sa dole nasoki balle kuma ga yara har biyu atsakani. ummi tace nagode hajiya tana share hawaye. hajiya tace amman zaliha bayan wannan akwai wani abun da yake damunki ko? hajiya aini duniyar gaba daya ta cakude min iyayena suki karbata amatsayi yar su saboda lefin da na aikata , nan ta shiga bawa hajiya lbr hajiya tace ikon Allah abin mamaki baya karewa , toh zaliha banda abinki ina kika taba jin mutun yaki iyayen sa, toh ai dole kirasa kwanciyar hankali kadan ma kika gani, ai iyaye ba abin wasa bane, karki kara ai kata nakaman cin wannan, kinji ko? In Allah ya yarda bazan kara ba nagode hajiya. hajiya tace tashi kije kitchen ki debi abinci. hajiya bana jin yinwa naci abinci agida. shiru sukayi nadan wani lokaci sannan hajiya ta kalli zaliha tace megidan fa yaushe zai dawo? tofah hajiya ta sosa ma ummi inda yake mata kaikayi wani sabon hawaye ne yake fita a idonta tace hajiya aini rabon da naga alhaji sati hudu kenan sanda zaitafi ma ko sallama bemin ba kuma ko kiransa nayi baya dauka jalal ma basan inda yake ba, hawaye take sosai. hajiya ta tausaya mata tace ya isa haka share hawayen ki, kikace rabon ki dashi sati hudu? eh hajiya tace toh ai yadawo yayi kwana biyu ya koma, yau kwana biyar da tafiyar sa, kina nufin ba,a gida ya kwana ba kenan,toh ko kin masa wani abune? shiro tayi tana ta share hawaye. hajiya tace toh kidaina kuka ai tunda kukayi aure shekara kusan talatin ban taba jin kan kuba, mijiki nasonki yayi hakuri da ke duk da cewa yasan baki son yan uwan sa, ina ganin dai akwai abinda kika masa. hajiya wayar ta dauka ta shiga daki number alhaji takira bayan ya dauka tace me matar ka ta maka katafi kabar ta babu ko sallama? alhaji yace lallai zaliha bata da kunya gidan ki tazo shakaran ta nawa batazo gidan ki ba. hajiya tace nidai ba wannan na tambaye kaba babu ruwanka , koma me tayi maka kayi hakuri bakaga inda ta fita haiyacin taba ta rame tayi baki kai ko kunya bakaji abokan ka su ganta ahaka, ai sai ace wahala take Sha. hajaya kirabu da zaliha makirar mata ce, inda kisan halin ta bazaki yarda da tubanta ba, kice mata kawai ta wuce gida saina dawo. nidai nace ka kira ta, ka kwatar mata da hankali abin ya mata yawa jalal ma kai ka hana shi zuwa gidan kenan, toh yanzun yaya kake son tayi. alhaji yace shike nan hajiya zankirata. ummi bata tafi gida ba har dare gashi kuma har yanzun alhaji be Kira taba sai gurin 7:30 taga kiran shi jiki na rawa ta dauka tafara gaida shi be amsa ba yace kina ina ? cikin sauri tace ina gidan hajiya. yace toh maza kitattra kayan ki kije gidan iyayen ki sai Nazo, kin shirya wani munafuncin ne dan kirabani da mahaifiya ta, toh baki isa ba, kinyi kadan,maza ki bar gidanan . hajiya nadaga daki tajiwo ummi tasaka kuka me ban tausayi, fitowa tayi tace zaliha yaya akayi? ummi ta gayawa hajiya abinda ya faru, ran hajiya ya baci afili tace Ismail kuma abida beyi da kuruciyar shi bane yanzon zaiyi, toh shikenan, ke kuma wannan ya isheki ishara dan yasan baki da gurin zuwa ne shiyasa yace kitafi . ummi kuka take sosai tace yanzun hajiya yaya zanyi baffa yace idan nakara nufu gidan shi batare da nacika sharadin da yabani ba Allah ya isa. hajiya nisawa tayi tace kizauna anan kafin yadawo muji abinda yake nufi kuma ko yakiraki awaya karki dauka, ke kima kashe wayar baki daya, dan naga alamar ran shii a bace yake dake kar yazo ya aikata abin da yafi haka . godiya tayima hajiya sosai suna zaune sunyi jugun jigun saiga kairat ta shigo tana kuka ummi shine kika tafi kika barni, kwantar da ita tayi akan ciyarta tana rarrashin ta. ranar da ummi ta wayi gari agidan ummi, jalal kuma agidan sa ya tashi da matsanan cin mura da zazzabi tun yana daurewa har ya gaji yace safna zoki rufeni, zuwa tayi ta taba jikin shi taji zafi rau tace yaya katashine muje asibiti . cikin rawar murya yace safna bazan iya tuki ba, bari sai anjima, rufeshi tayi ta fita zuwa kitchen domin karasa girkin da ta daura. bayan ta gama takoma dakin tasame shi ya ture bargon sai faman kira sunan ummi yakeyi, ta dauka wasa yake saida ta karasa kusa dashi ta gane da gaske yake yi, dariya ta fara tace meye haka yaya saika ce kairat. ai ko sauraran ta beyiba kiran ummi kawai yake yi zuwa cen ya jawo safna zama tayi agefen gadon ya dago kanshi ya daura aciyar ta sai faman sanbatu yake tun abin nabata dariya har yasoma bata tsoro zuwa cen taga ya fara kuka hawaye shabe shabe, da sauri ta sauke kan jalal daga jikinta karamin hajjab tasa tayi waje. tana fitowa gate din gidan su gidan dake jikin nasu ta nufa dan taga me gidan suna yawan gaisawa da jalal, gate din gidan ta fara bugawa me gadi yazo ya bode yace lfy ? safna ta rasa me zatace dan ko sunan mutumin bata sani ba, hango shi tayi rike da hannun matar sa zasu shiga mota hango safna da me gadin su ya hana su shiga karasowa gurin sukayi safna ta gaida mutumin tace ni makociyar kuce anan gidan nake ta nuna gidan su da ahannu ,miji nane bashi da lfy dan Allah ku taimaka min ku kaimu asibiti. mutumin yace kece matar abduljalal dakai ta amsa, yace toh babu damuwa muje na dubashi, duk suka rankayo har matar sa, suna shiga falon suka tsaya, safna tace muje yana ciki, mijin yace a,a je kigaya mai idan zai iya fitowa yafito inkuma bazai iyaba saina shiga. safna tana shiga tasame shi yadda tabar shi be daina surutun ba,tasan jalal batashi zaiyi ba tace yaya dan Allah kadaina magana kayi shiru gayinan za,aduba ka, bece komai ba sai kokari riketa yake taje tace wa mutumin yace kashiga. safna bata koma ba zama tayi kusada matar, ta kalleta tace ki kwatar da hankalin ki in Allah ya yarda zai samu sauki , tasake cewa gashi muna kusa amman bamu sanjuna ba, ya sunanki? waigowa tayi gefen ta tace sunana safna kefa? tace nikuma khadija, suna cikin haka mutumin ya fito yana murmushi yace madam karki damu murace tamai mugun kamu amman dazaran yasha magani zai samu sauki, yajuya barayi matar sa yace khadija zomuje nabaki magani ki kawo mata. bayan kadija takawo magani tare da yi mata bayani ruwa ta dauka ta nufi dakin ta same shi kwance yadai rage surutun da yakeyi tace sannu yaya tashi kasha magani. jalal ya bude baki cikin murya kalan na me sambatu yace aini bana shan magani safna ki tambayi ummi kiji. kalon shi tayi da mamaki tace toh ai ko saika sha yama za,ayi kace wani baka shan magani saikace wani karami yaro. nidai gaskiya katashi kawai kasha. jalal ya sake cewa safna ki aje maganin nan ko ganin shi bana son yi. kuka ta saka da karfi, tana fadi toh ni ya kake son nayi gashi bacci nakeji kaikuma sai faman sambatu kakeyi. jalal yana kokari jan bargo ya rufe jikin shi saka makon zazzabin da ya dawo mishi yace zoki kwanta na bari. ni sai kasha maganin zan kwata yace toh naji kawo nasha. mika mishi tayi ya karba yasa abaki ya karbi kofin ruwa yakai bakin sa, kasa hadiyewa yayi ya fara sheka amai. safna na rike dashi har ya gama hawaye nata zubo mata gashi itama ba kwari gareta ba haka ta kamashi takai shi bayi ta wanke mai jiki, dakinta ta wuce dashi sannan ta dawo ta gyara wajen tanayi ne tana kuka bayan takoma gurin jalal ta dauki wayar jalal takira alhaji. yana dauka yace jalal, safna tasaka kuka tace daddy yaya bayi da lfy kuma yaki shan magani, saikiran sunan ummi yakeyi. alhaji yace toh fah, tashin hankali, ciwon jalal wuya gare shi, to ya isa ki daina kukan, share hawayen ki, bari nusaiba zata zo yanzun [8:23PM, 12/18/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 100-102 Bayan ta aje wayar ta zauna ta zuba tagumi zuwa cen taga bacci ya dauki jalal itama kwanciya tayi nan da nan bacci ya dauke ta lokacin da anty tazo gidan shiru ,tai ta sallama babu amsa zama tayi afalo ta shiga kiran wayar safna, aza bure ta tashi ta nufi wayar tasa akunnen ta, anty tace safna gani afalo, wani sanyi taji azuciyar ta ta nufi falo da sauri bayan sun gaisa anty tace yaya yace jalal babu lfy ko, yana Ina safna tace yana kwance ya samu bacci. jeki tasoshi yasha magani anty ai baya iya tashi bakiga inda ya ragwar gwabe ba. anty tace muje nagani Suna shiga anty ta fara tashin jalal yabude ido yafara fadin ummi kaina zai fashi cikin fada anty tace ya fashe din dan baka da lfy kuma duk sai kabi ka damu mutane da surutu saikace karamin yaro. jalal yasake cewa safna kira min ummi. safna hannu tasa ta dauki wayar jalal anty nusaiba tace safna ajiye wayar nan baza akirata ba idan kamatsu katashi katafi da kan ka katon banza kawai, haka zaka haifi yara suga ubansu yana wannan tabaran jalal yace toh naji tashi ki tafi gida. tace babu inda zani tashi zakayi kasha magani dan me shagwaba kan bata nan. kalon safna yayi yamaida idon shi ya rufe daker anty ta shawo kan jalal yasha magani saida ta dama mai acukali. bayan yasha be jima ba bacci ya kwasheshi . washe gari jalal yatashi jikin shi yayi sauki sosai ya shiga bayi yayi al,wala yafito ya fara tashin safna tashi kiyi sallah. mamaki ne ya kamata ta kasa daurewa tace yaya kaji sauki ne? daure fuska yayi yace eh. safna kwashewa tayi da dariya tana fadin Allah yakara sauki. kara tamke fuska yayi yace to meye abun dariya kuma, juyawa yayi yana tafiya yana fadin bari nadawo zaki sani. 12:42 alhaji ya faka motar sa ahabar gidan jalal awaya yakira shi yace yajiki jalal yace yayi sauki daddy yaushe zaka dawo? alhaji yace nadawo gani ma akofar gidan ka mikewa yayi cikin sauri ya bude kofar ya fita , yana isa ya rugume daddy. har cikin falon alhaji ya shigo ya zauna jalal yace daddy bari nakira safna. cikin murna tafito tana yashe hakora bayan ta gaida alhaji bata zauna ba kitchen ta nufa ta fito da abinci. daddy ya kalli safna yace wanna fah nida nazo duba mara lfy kuma sai na bige da cinye muku abin ci safna ta bata rai tace dan Allah daddy kaci ai shi yaji sauki dama fa mura ce kawai amman duk yabi ya langwabe harda su kuka. dariya alhaji yayi safna ma dariya take yi daddy yace jalal wai haka ne kayi kuka? jalal yace karya take daddy ,ya juya yana hararan safna. alhaji kalon jalal yayi yace nasan kayi ne jalal idan bakayi ba bazata fadaba, kaga irin abinda nake fada maka ko? jalal yayi murmushi yace daddy dandai ba ita bace shi yasa take fadan haka bata San abinda nakeji bane, kuma kukan ma ai itama tayi. safna kasa tayi da murya tace amman aini ban ta kiran sunan ummi ba , duk da tayi kasa da murya be hana daddy jin abinda tace ba. jalal kuwa filon dake hannun sa ya wurgawa safna, tare da fadin ina wasa dake ne. daddy dariya yayi sosai sannan yace wlh jalal ka canza halinka kai ga son girma kuma ga.... jalal ne yayi wa daddy alama da hannu karya fada, dan haka daddy yabar maganar, bayan alhaji yaci abinci yayi musu sallama ya tafi, tare da dubin farin cikin yadda ya samesu gwanin ban Sha,awa. ************* gidan hajiya ya nufa yana shiga yaga ta daure fuska bakamar daba. bayan ya gaisheta yaji bata kara cewa komi ba dan haka shima yayi shiru, zuwace yaga ummi tayi sallama ta shigo ya daga kai ya kalleta , batace mishi komai ba ta shige dakin hajiya. alhaji yace hajiya zaliha kuma me takeyi agidan nan? cikin fada tace inaruwan ka da ita dama jiranka nakeyi kadawo kagayamin abinda kake nufi, tunda ninayi magana baka dauki maganata abakin komai ba. alhaji yace hajiya kiyi hakuri bawai nakijin magarnar ki bane, Ina sone ta gane wani abu wanda shekara da shekaru ta kasa fahimta. aikoma Meye tunda nasa baki sai ka bari yanzun bakajin kunyar jalal yaji ka korar mai mahaifiya. alhaji yace hajiya ai jalal yasan halin ta, shima ba magana take masa ba , dan ko gaisheta yayi bata amsawa . hajiya tace me yayi mata shi kuma? duk akan auran nan ne bansan abin da yasa ba zaliha kwata kwata bata kaunan yariyar nan. Hajiya ta daga murya takira zaliha bayan tazo ta zauna alhaji azuciyar shi yake fadin jita kamar mutuniyar kirki. hajiya tace zaliha zokibawa mijinki hakuri kuma duk abinda kike kinsani ki gyara halinki. tun anan ta fara bawa alhaji hakuri , baza yayi da ita bece mata komai ba. hajiya tace bakaji tana magana ne ko maganar bata wuce bane, da girman ka inda kuma jalal yayi kace masa me? alhaji yace to shikena hajiya ya wuce, ki shirya anjima zamu tafi gida. ummi dadi taji sosai, ta farawa hajiya godiya. Firace ta barke tsakanin hajiya da alhaji ahirar ta sune ummi ta fahimci jalal yatare agidan sa, dan taji yana bawa hajiya lbrin ciwon jalal. basu tashi tafiya gida ba sai yamma, alhaji yace ni nafita kisame ni a mota . ummi gyalan ta ta dauka tana cikin yiwa hajiya sallama saiga alhaji da wata mata yar kwaye yana rike da kullin kayan ta, suna shiga falon matar ta zauna akasa, hajiya binta tayi ido dan bata gane taba, alhaji ya lura da haka yace hajiya baki gane ta bane, matar marigayi yaya musa ce. hajiya tace Allah sarki kiyi hakuri bangane ki bane, yaya yaran. tace suna lfy yanzun ma bikin salame ne ya tashi nace bari nazo na fada muku. ummi ji tayi kamar tasan muryan dan haka tazo har gaban matar, take gabanta ya fadi tace kamar goggo kishiyar saudatu 07014197556✍ [7:01PM, 12/20/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 103-105 *❤❤❤ godiya agare ku makaranta wannan novel gaskiya naji dadi sosai ganin jiya kadai banyi typing ba na samu kiran muta ne da dama, suna tambayar lfy ta nagode sosai ina muku fatan alheri๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•๐Ÿ’•* Itama matar dago kanta tayi takali ummi gaban ta yake ya fadi cikin da burcewa take fadi a,a bani bace, ina ganin dai kama ce. ajiyan zuciya ummi tayi sannan tace amma ko kamar tayi yawa bayan sun gaisa da matar ummi ta karayi wa hajiya sallama ta fita tana waiwayen matar. itama hajiya kara gaisawa sukayi da goggo sanna ta farawa hajiya bayanin bikin salame ne ya taso nace bari naxo na sanar lokaci sai kara tahowa yakeyi amman bani da komai da zan kai mata. hajiya ta nisa tadayi murmushi sannan tace hanne kenan sai yanzon kika tuna da mune dangin ubanta, aida cen kin manta damu dan kinga babu idon iya sai yanzon da matsala ta kawoki? goggo tace hajiya wlh ina son zuwa kudin mota ma gagara na yake, yanzon ma mokota nashiga na ranto. toh aishi kenan yanzon wacce ce zatayi aure , yar wajen kice ko yar wajen amaryar ki? tace ta wajena ce ai waccen tana gurin dagin mahaifiyar ta. hajiya tace Allah sarki ai lokacin rasuwan iya tana karama yanzon nasan itama ta isa aure, me yasa baki turo mana su , zumun ci fah ba abin wasa bane, irin wannan saika hadu da naka baka san shiba, niyanzon ba kamar da bane girma ya kamani . toh hajiya in Allah yarda zanturo su, shiru sukayi na dan wani lokaci zuwa cen goggo ta kalli Hajiya tace hajiya wannan matar da suka fita da alhaji wacece ? hajiya tace matar sace. goggo ta sake cewa ya kara aure ne? a,a itace dai matar sa maman abduljalal , suma basan zumun cin suke ba, ai inaga ko iya ma bata santa ba bare ke. haka suka ci gaba da tattaunawa goggo ta tsorata sosai da taji ummi surukar hajiya ce dan tasan indai asirin ta ya tonu ta shiga uku, dan haka washe gari goggo na tashi tashirya tayiwa haji sallama bayan ta hada mata sha tara ta ar ziki. itako ummi bayan sun koma gida hakalin ta kara tashi yayi so kawai take taga ta daidaita da iyayen ta dan haka ta farawa alhaji kuka ya taima keta ya daidaita da iyayen ta hakuri ya shiga bata ki kwatar da hankalin ki baffa yayi rantsuwa babushi babu ke tunda kikai silar rabowan shi da 'yar shi har ta mutu basu ganta ba, zaliha nazaci idan baffa yasan cewa saudatu ta rasu hankalin shi zai kwanta amman sai naga hankalin shi ya kara tashi, zaliha abinda na lura dashi babu abinda baffa yake so ayanxon illa yaga yariyar da saudatu ta haifa. kukanta karuwa yayi tace nima haka alhaji ina matukar son naga yariyar nasan yanzon ta girma , kuma alhaji idan nakalli huto yariyar sai naga kamar na taba ganin hoton. alhajj yace kin taba gani mana tunda yariyar da saudatu take kama. haka sukaci gaba da ta tattaunawa akan yariyar saudatu , zuwa cen ummi ta sako maganar jalal alhaji ashe jalal ya tare shine ko kugaya min atakai ce yace eh ya tare. ta sake cewa Amman alhaji ya kamata ace yana zuwa gida ana gaisawa. toh ganinayi gurin wa zaizo ni bana gari ke kuma ba amsa masa gaisuwa kike ba, toh me zaizo yayi. toh alhaji komai ya wuce kabashi hakuri dan Allah yazo gida. washegari da safe daddy yayiwa jalal waya ya tambaye shi jiki yace yayi sauki, dan haka alhaji yace idan zaka iya fitowa kazo gida ummin ka nason ganin ka . toh kawai jalal yace, ya juya yace safna shirya muje gida cikin sauri suka shirya suka kama hanya. Suna shiga jalal ya nufi dakin daddy safna kuwa falo ta zauna tana raba ido. lokacin da jalal ya shiga dakin ya samu ummi sunata hira da alhaji dan haka murmushin dake fuskar shi ta ragu, daddy ko murmushi ya saki yana fadin jalal ka iso. kusa da alhaji yaje ya zauna bayan ya gaida alhaji ya juya barayin ummi yace ummi ina kwana. cikin sakin fuska ta amsa tare da tambayan shi jikin shi, bayan ya amsa ta sake cewa ya safna? dadi sosai jalal yaji yace lafiyar ta lau tare muke tana falo. alhaji fada ya farawa jalal yazaka bar ta afalo saikace wata bakuwa jeka shigo da ita. jalal zuwa yayi ya riko hannun safna suka shiga falon alhaji bayan ta gaida alhaji ta juya ta gaida ummi ta amsa ba yabo ba fallasa. ummi kara kallon safna tayi sosai gani tayi takara cika tayi kyau sosai cikinta harya fara fitowa, juyawa tayi gurin jalal ta fara janshi da hira harya fara sakin jikin shi. sai yamma su safna suka bar gidan su ummi jalal sai washe hakora yake . kwanci tashi ba wuya gashi har cikin safna ya isa haihuwa suna jiran haihuwa ko yau ko gobe , komai sun tanada anty nusaiba na kula da safna sosai dan akai akai take zuwa dubata da tace ina son kaza anty nusaiba saita nemo itako ummi ta rage nuna tsanar safna afili jalal kuwa jitake kamar ta hadiye shi, babu abinda yake damun ummi ayanzo ila rashin samun yar da saudatu ta bari . safna ce ta fito daga daki tana fiya daker, har ta isa gurin jalal tana zama ta kalli jalal dake kwance ya rufe ido, taba shi tayi tace yaya ka tashi nasan idonka biyu. tashi yayi ya zauna yace safna nasan maganar muguwar matar nan zakiyi min, ni kuma bana sojin ko sunanta. [7:06PM, 12/20/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 106-108 safna kasa tayi da murya tace yaya dan Allah kayi hakuri ka kaini inason naga nima ina da 'y an uwa kamar kowa kaga ko badan goggo ba kodan yaya iro da salame ai naji . kara daure fuska yayi yace yan zon kina nufin harkin manta da wula kancin da mahaifiyar su tamiki toh bazaki ba indai nine mijinki bazaki wajen wannan muguwar matar ba idan ma kina tunanin ni zan kaiki toh kima cazan tunani dan wlh bazan jeba, waima me kike nema awajen su, me kika nema kika rasa da zaki nace sai kinje wajen su? kuka safna ta fara tace yaya yan uwa nane fa, bani da kowa fa sai su kara kulewa jalal yayi ya fara magana cikin fada baki da kowa saisu ko, haka kice ko, ni ma ba komai bane awajen ki ko, duk abin da ake miki baki gani, kin raina ko? a,a yaya ba haka nake nufi ba nidai kawai inason naje naga yan uwa na dan Allah kayi hakuri ka barni naje. Jalal kara daukan zafi yayi yace wlh safna idan kika kara cemin 'yan,uwan ki saina mareki susan tarajar kine suka wurgar dake a titi. safna ta kara fashewa da kuka tace yaya gori kuma kake min? eh ammiki gorin kiyi abinda zakiyi wawiya kawai mara wayau. safna daki ta nufa cikin matsanan cin bacin rai taita kuka. shikuwa jalal bayan ya gama fadan gidan ya bari sai dare ya dawo, ya samu dakin safna rufe dakinshi ya wuce dan yasan fushi take. Washe gari bayan ya gama shir yawa ya fito yaga falon na nan yadda yake yagane safna fata fitoba ji yayi babu dadi a zuciyar shi ya isa bakin kofar yayi ta bugawa taki budewa hankalin shi ya kara tashi waryar shi ya ciro ya dannan number daddy yana dauka ya fara fada mai safna ta rufe daki tun jiya taki budewa. alhaji yace wani abu ya farune ko kunyi fada ne? shiro jalal yayi bece komai ba dan ya tuna kargadin daddy akan safna. Alhaji yace jalal baka da gaskiya kenan, bari nakira safna. safna dake zaune adaki taci kuka ido duk sun kunbura taji ankira wayar ta tana dubawa taga daddy ne tasa wayar akunnen ta tana kuka ahankali alhaji yace safna me ya faro ne, jalal ne ko, gayamin me yayi miki? kasa magana tayi ta kara fashewa da kuka. alhji yasake ciwa jinan safna daina kuka bakisan wannan kukan zai iya miki ila ba, tashi maza ki shirya ya kawaki koma me yayi miki zanyi maganin sa, kinji ko. jalal na zaune amota safna ta fito ya kalli fuskarta yaga tayi jawur saboda kuka dogowar rigace jikinta da hajjab madaidaici . suna isa ta bude motar ta fita , ta samu alhaji shida ummi afalon ummi ta mata wani irin kallo, zamatayi akasa ta gaida su, suna cikin amsawa jalal ya shigo alhaji yace kai jalal baka da hankali ko, waya gaya maka ana tayar ma me ciki da hankali? shiro yayi yanemi guri ya zauna. Alhaji ya kara cewa ina murna zan samu takwara ko mata zaka mana sa... be karasa maganar saba ummi tace Allah ya kiyaye karku sake kusa sunana dan ni ba sa,ar wasan ku bace asa mata sunan uwar ta amman bani ba. safna ta daga jajayan idanun ta, ta kalli ummi ta fashe da kuka, tare dajin matsanan ciyar tsanan ummi azuciyar ta . alhaji yace zaliha tashi ki bamu guri tunda ke ba,a magar hakali dake. tana tashi alhaji yace safna gayamin me jalal yayi miki? Cikin dashashiyar murya ta gawa alhaji abinda ya faru. alhaji yace ah ah jalal yayi laifi sosai toh kai jalal banda abinka haka akeyi ba yafiya, tunda tace tanason ganin su aisai kayi hakuri ko baka so kabarta taje, itama ta hakura ta yafe bare kai. sai alokacin jalal yayi magana daddy ai itama dan bata da hankali ne shiyasa ta yafe. murmushi alhaji yayi yace jalal ai wannan abinda tayi shine hankalin abun da kawai ban yadda tashi ba tafiya da ciki dole kiyi hakuri har ki haihu nida kaina zan sa akai ki, kai kuma ka kiyaye bakin ka inrai ya baci hankali baya gushewa, haka alhaji yayi ta musu nasiha sannan yace kutashi kuje gida. tana mikewa jalal yace zomuje muyiwa ummi sallama haka safna tabi bayan shi badan ranta yaso ba. sun sami ummi zaune abakin gado tayi ta gumi jalal yace ummi zamu tafi tace ku gaida gida safna ta juya zata fita ta daga kai taci karo da tangamemen hotun iyayen ta tana rike ahannu su, daga hannun ta tayi sama tana nunawa jalal , yaya kallah bata karasa ba jalal yaga tana kokarin faduwa [6:51PM, 12/21/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ ​ *dedicate*​ ​​dis page to hajiya amina lamido Kilishin yamma๐Ÿ‘๐Ÿป *gaisuwa agereki* *Aysha mazoji* *marubuciyar* *Zaheedah* *Jaleelah* _The boss wife_ ​ 109-1012 Da sauri jalal ya tare safna ta fada jikin shi, ganin inda safna keta nuna hoton yasa ummi ta zaro ido ta mike tazo kan safan tana fadin kar dai ace safna yar saudatu ce, jalal be saurari me ummi take fada ba kiran sunan safna kawai yake amman shiru babu amsa ummi ce ta lura jini na zuba ta kasan safna da gudo ta fita tana fadi alhaji dauko mota safna babu lfy . da ummi da jalal ne suka kinkimi safna suka sakata amota, jalal ya fita haiyacin shi ummi ko kamar mahaukaciya sai fifita takewa safna da gyalen ta, bayan sun isa asibitin aka shiga da safna ciki jalal yaso ya shiga suka dakatar dashi. Komawa gefe yayi amman ya kasa tsayuwa guri daya sai naushin hannun shi na hagu yake da hannun shi na dama. ummi kuwa tunani ne ya dame ta dan haka ta matsa kusa da alhaji tana share zufa tace alhaji kasan abin da safna ta gani ta shiga wannan halin, hoton saudatu ta gani. da sauri alhaji ya mike ya cire hular sa ya fara fifita da ita ya na zaware kamar yadda jalal keyi, ummi ta mike tabi bayan shi tana kokarin magana alhaji ya dakatar da ita karki ce komai kibari muga lfyr yarinya tukuna. komawa tayi ta zauna zuwa cen ta sake mikewa. daga cen su kaga an turo kofar Dr sulaiman ne ya fito dasauri alhaji yabi bayan shi, jalal ma mikewa yayi amman alhaji ya waigo yace koma jalal. bayan ya shiga Dr sulaiman yace alhaji haihuwa ce sai dai muna tunanin yariyar bazata iya haihuwa dakan ta ba sakamakon jinin ta ya hau sosai saida kuyi ta mata andu,a . haka alhaji ya fito jiki babu kwari jalal ya mike yace daddy mutuwa tayi. a,a jalal tana nan daran ta haihuwa ce amman jalal kayi ta mata andu,a Allah ya rabasu lfy . jalal be yadda da abinda daddy ya fada ba dan haka ya fara share hawaye. alhaji yakira anty nusaiba yagaya mata halin ta suke ciki nan da nan saiga su ita da matar baba salisu suna rike da kayan baby ganin ummi agurin abin ya basu mamaki. 2:46pm sukaji safna tayi kara mikewa jalal yayi zai shiga anty ta rike shi ta bude baki zatayi magana suka sake jin wani ihun, wannan karon sai da alhaji yasa hannu suka iya tare shi, yana fadi daddy kuka fah takeyi haka sukai ta bashi baki juyawa yayi ya fita yasamu wani dan dutse ya zauna yata share hawaye. yana zaune agurin anty ta fito da gudu tana dariya jalal albishirin ka. mikewa yayi yana kokarin share hawayen shi yace anty ta haihu ne? Jalal mu godewa Allah safna ta sauka lfy mun samu yan biyu. jalal ya zaro ido yace anty da gaske cikin sauri ya nufi ciki ya same su alhaji sai dariya suke alhaji ya dafa jalal yace jalal kuka ya kare ko? kunya ce ta kama jalal yayi kasa dakai yana murmushi yace daddy wai da gaske yan biyu ne? alhaji yace 'yan buyu ne jalal mace da namiji kana mamaki ko, ikon Allah kenan. bayan angama gyara jarirai aka basu damar shiga ummi ce kan gaba tana shiga ta sauke idanun ta akan safna da sauri ta rintse ido gurin ta ta nufa takira sunan ta taji shiru, alhaji yace zaliha kirabu da ita kila bacci takeyi daidai lokacin nusaiba ta dauki macen takalle ta sannan tamikawa alhaji tace yaya ga matar ka ta juya zata dauki dayan ta ganshi hannun matar baba salisu haka suka taro suna kallon yaran gwanin ban Sha,awa. Shiko jalal gurin gurin matar sa yake son zuwa amman ummi tana jikin gadon dan haka ya kasa zuwa wajen. alhaji ne yace jalal yanaga ka koma gefe kazo kaga yaran mana. sosa kai yayi ya kalli safna yace daddy ina zuwa. alhaji ya fahimce shi yace kazo ka gansu mana safna ai bacci take. da saurin sa yace daddy ba bacci take ba idon ta biyu. sai da alhaji ya kalli safna sannan yace zaliha fito daga nan gurin. cikin sauri ummi ta fito daga gurin duk arude take so take kawai safna ta tashi . Jalal yana isa gurin ya duka yanawa safna magana cikin kunne zuwa can ta fara magana ahankali cikin kuka, jin safna na kuka yasa duk suka maida hakali gurin su, amman basajin me suke fadi, jalal ya dago hankalin shi atashe ya kalli ummi ya hada rai. ummi ta tsargu tace jalal me safna tace maka. yi yayi kamar beji ba ya mikawa alhaji hannu ya bashi yaran ya kure su da ido. lokacin da aka sallame su ,alhaji yace awuce da ita gidan hajiya motan jalal ta shiga su anty nusai ba ma haka. hajiya ta tare su da murna nusaiba ta mika mata yaran ta kalle su tace ikon Allah ga jalal ga safna , hajiya fatima ta shigo rike da safna ta zaunar da ita akan kujera jalal ma ya shigo dauke da kaya ya ajiye agefe hajiya ta kalli jalal tace yaya haka kuma jalal menene haka kaida ka samu karuwa kuma menene naka na hada rai, ta kalli safna tace au kema kuka kikeyi toh abin naku bana lfy bane anty tace jalal nima nakula akwai abun da yake faru har anty zaliha ma akwai abun da yake damun ta ko kallon yaran batayi ba hajiya tace tunda sunki mgn ku kiramin alhajin har zalihar ,wannan ai iskanci ne Allah yayi muku kyauta kuzo kuna tur bune mana fuska. suna cikin haka alhaji ya shigo ummi na bishi abaya hannu ta rike da wanan huton. bayan sun zauna hajiya tace nifa kun sani aduhu wai me yake faruwa ne? alhaji yace hajiya wani babban al,mari ne yake shirin faruwa ya karbi huton ahannu zaliha ya mikawa hajiya yace wannan haton safna ta gani kawai sai gani sukayi ta fadi shine muke tunanin ko ta sansu ne . hajiya kallon huton tayi tace wannan ai musa ne. alhaji yace hajiya wani musa kuma ? tace musan iya mana ko kana nufin baka gane shi bane. alhaji kallon huton yayi sosai yace innalillahi wa,inna ilaihir raju,un Safna na daga gefe kuka kawai take murya hajiya taji tana fadin safna kinsan musa ne? cikin dashewar murya tace babana ne. hajiya ta zaro ido a,a safna ko dai kama suka miki wannan fa dan yayata ce uwar mu daya uban mu daya, yanzun nan kina nufin ke jikar iya ce. cin kuka tace eh. kowa afalon gumi ne yake karyo mishi itako ummi hankalin ta yafi na barawo tashi. hajiya ta share zufan da ya karyo mata tace ke zaliha Ina kika samu wannan huton ? jalal najin anyi ma ummi wannan tambayan ya fita afalon dan yanajin kunyar abin da ummi tayi. cikin kuka tace hajiya wannan matar itace kanwa ta da nake baki labari, zaro ido safna tayi ta mike tace ummi kina nufin kece yar mahaifiyata, ina wlh wlh bazai wuyo ba gara naga mutuwa ta da naga wannan ranar๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ [8:57PM, 12/22/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 1013-1016 Anty nusaiba ta kama safna ta zaunar da ita tana fadin safna ki natsu mana baki san jikin ki babu kwari ba ne. safna tace anty ni ki sakeni tafiya zanyi wlh bazan zauna ba. kowa afalon share hawaye yake sautin kukan ummi kawai kake ji. alhaji yayi gyaran murya yace safna zo ki zauna, batayi musu ba kusa da hajiya ta zauna , hajiya ta kalli safna tace tabbas biri yayi kama da mutun lokacin da hanne tazo gidan nan zaliha ta tambeye ta amman sai tace ba, ita ba ce, kuma nima na tambaye ta ina yar da kishiyar ta tabari sai tace min tana gurin dangin mamar ta , hajiya ta nisa takara cewa toh me hanne take nufi da haka. alhaji ne ya dago yace hajiya ga dalilin ta nan bata san inda yarinyar take ba kame kame take tunda su tace musu tana gun dangin baban ta ke kuma ga abinda tace miki. hawaye ne yake zuba afuskar hajiya tace amma ko indai haka ne ni kaina naci amana, dan tun lokaci da aka ma iya aure da baban musa dangin mu duk suka guje ta saboda mijin da ta aura bame karfi bane babu me zuwa inda take sai ni dama mu biyu ne mata sai yayyen mu maza guda uku haka in naje iya zatai ta min korafin ita ba me zuwa gurin ta, nice me lallashin ta har sai naga hankalin ta ya kwanta, ana cikin haka nima aka aurer dani, tun daga lokacin ban sake zuwa garin ba sai da iya ta haifi musa mijinta dakan shi yazo ya fada balefi dagi sunje tun daga sunan musa ban sake zuwa ba sai dai ita tana zuwa gida na akai akai dan haka ban cika damuwa ba ,dan bata rufe wata bata zoba haka muka ci gaba da tafiya sai dai rashin lafiya ko wani babban abu muke zuwa gurin ta duk da cewa ita ko da yaushe tafe take, kuma duk wani Sha,ani sai dai in bataji ba, ko koma bata da lfy bana mantawa zuwan ta na karshe gidan nan nasiha tai tamin akan zumunci ko sati daya ba,ayi ba mukaji lbrn rasuwan ta kuka ne yaci karfin hajiya ta jawo safna tana fadin naci amanar iya. safna lafewa tayi jikin hajiya tana kuka hajiya ta dafa kan safna hawayen ta na diga jikin safna tace safna ki yafe min nina saka ki a halin da kike ciki da ace sanda nazo gaisuwar iya na dauke ki da haka be faru ba, ninayi tunanin hanne zata hada da nata tarike, sai nake ga kamar idan idan aka dauke ki zata ce annuna mata banban ci , bansan cewa bakin hali gareta ba. safna kara rugume hajiya tayi dan ita duk wani abu da yashafi iya gir mamashi take kuma ai tun haduwan ta da hajiya na farko bata nuna mata tsana ba, kuma bata taba nuna mata babbaci tsakanin ta da jalal da yake jikan ta ba, dan haka hajiya da 'ya'yata sun gama mata komai tun da sun sota alokacin da basu san waye ita ba, dan haka ta dago ta fara sharewa hajiya hawaye da hijjabin ta. ummi ko tana cen gefe uwa kazar da aka tsamo ta daga cikin ruwa. anty nusaiba ce ta katse musu shirun ni dama tunda naga safna sai da naji ta a raina, take naji son ta ya kamani ashema 'yata ce. alhaji yace ai irin abin da nake gayawa zaliha kenan yazun gashi inda abu ya koma, yanzon me zakice wa yarki safna. Ummi kuka kawai take ta kasa cewa komai, ana haka jarirain suka soma kuka anty nusaiba tace safna tashi muje kiyi wanka kiba yaran nan nono, kamar jira take ta mike ta shige dakin hajiya. bayan anty ta gama gasa mata jiki suka fito ta sanya kaya ta haye gadon hajiya ta kwata anty tace safna ba kwanciya zakiyi ba kibari yaran sudan ji dumin jikin ki mana. anty nifa nagaji bacci nakeji. ban ga ne kin gaji ba me kike nufi ko kallon yaran nan bakiyi ba fah . anty ni bana so akai ma ummi ta rike ai su bazata ce basu da dangi ba. anty kallon safna tayi tace karki haka safna yaran nan basu suka miki laifi ba, zadai kidau hakkin sune kawai, ai irin haka jalal bazaiji dadi ba. ai ni dama banson yaji dadi duk wani abu da ya shafe ummi ban son shi me sonshi ma bana son gani wani sabon kuka ta saka tace anty dan Allah ku sa shi ya sakeni wlh bana son shi ko ganin shi bana sonyi. anty tace inalillahi wa,inna ilaihir raju,un kar ya kike safna kina son jalal, kar ki yadda laifin ummin sa ya shafe shi dan baya goyan bayan ta suna cikin haka hajiya fatima tashigo da yaran ta daura macen jikin safna tace bata nono tasha sai kuka takeyi. safna kallon yariyar tayi take taji son ta ya kama ta amman tana bakin cikin kallon wani abu da shafi ummi dan haka ta fara kuka, hjy fatima tace safna bata mana. sukuyar dakai tayi ta rufe ido, anty tace ai tace bazata basu nonon taba. hajiya fatima ta bude baki zatayi magana su kaga jalal ya shigo bece komai ba illa mika hannu da yayi hjy fatima ta saka mai na mijin ya sake cewa bani dayar batayi musu ba ta daukota ajikin safna tamika mai juyawa yayi ya fita. yana fitowa ya samu ummi makure taci kuka har ta gaji ya tsuguna ya mikawa ummi yaran yace ummi gasu safna tace bazata basu nonon taba. cikin tashin hankali ummi ta mike, dakin ta nufa ta samu safna ta kifa kai tana kuka ajeye yaran tayi abayan safna ta tsuguna tarike kafar safna tace safna dan girman Allah kiyi hakuyi kiyafe min, nasan na tafka babban kuskure nayi nadaman abin da na ai kata safna ina cikin wani hali, dan Allah ki tausa yama yaran nan, haka ummi taita magana safna batace ta komai ba ga yaran sai faman kuka suke, gani tayi safna bazatayi magana ba ta mike ta fita zuwacen sai gasu da alhaji . alhaji na shigowa ya zauna akan wata kujera dake gefe yace safna wannan hukuncin da kika dauka yayi tsauri da yawa ni bance karki nuna fushin ki ba, amman inason fushin ya tsaya akan zaliha ka dai, ya sake cewa safna indai kin daukeni uba agare ki toh na umarceki da ki dauki yaran nan kibasu nono. cikin sauri tasa hannu ta dauke mace dan ita ke kuka na miji har yagaji yayi bacci, daddy na kallon safna sai ciki cikin rike yarinyar take, yajuya yace zaliha tashi mutafi gida. suna fita falon alhaji yace nusaiba je ki nuna mata yadda zatayi, alhaji sallama yayi wa hajiya suna fita suka samu jalal awaje ya hada kai da gwuiwa [9:03PM, 12/23/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 1017-1019 Alhaji yace jalal tashi muje gida, jalal beyi musuba ya tashi ya shiga mota ko acikin mota babu me ma wani magana har suka isa gida, ummi taso suyi magana da alhaji amman yace ta bari sai gobe, haka ta shiga daki badan ran ta yaso ba. alhaji ko rike hannun jalal yayi suka shiga daki bayan sun zauna alhaji yace jalal ka kwatar da hankalin ka insha Allahu komai zai wuce. cikin sauri yace daddy naji fah abin da safna take fada wai bata sona har tana cewa wai ace min na sake ta. alhaji yace ya isa jalal kayi hakuri bacin rai ne ya sata fadan haka, kama ta uzuri yariyar tana da hankali,lallashin ta zakayi zata sakko. washe gari jalal yana shir yawa ya nufi gidan hajiya yana zuwa ya samu hajiya da anty nusaiba suna hira bayan ya gaida su hajiya tace dama yanzon muka gama mgn akan sunan da za,a sama yaran nace sai asa sunan iyayen ka. jalal yace a,a hajiya abarsu da sunan su ummi ma bata so asa sunan ta. hajiya tace ai jiya muyi mgn da ita tace asa ma macen saudatu. hajiya dan allah ki dai na biyewa ummi kuma ni nafison abar su da sunan su, be sake cewa komai ba ya shige dakin ya sami safna zaune tana cin tuwo hada fuska tayi nema guri yayi ya zauna kusa da ita. shiru tayi bata ce komai ba, jalal yace safna ba gai suwa. gani yayi bata da niyar magana yace toh ni bari na gaida ki inakwana ? ban za tayi dashi ya sake cewa safna fushi kike dani to me na miki? daga kan ta tayi tace kawai ganin ka ne banaso, sabo da tun da na samu lbrn mahaifiya ta naji na tsani dangin ta, mahaifiya ta tayi rayuwar bakin ciki na rashin iyayen ta har ta koma ga Allah bata gansu ba wannan ya nuna min basa kaunar ta da suna kaunar ta basu manta da ita atiti ba dan haka bana son wani abu ya hadani da dangin ta bana sonsu bana kaunar su. shiru jalal yayi ya dukar da kai zuwa cen yace safna kinga duk cikin wannan abun ummi ce me laifi tunda ita ce ta bata musu rai har suka manta sun taho da ita. ciki kuka safna tace bawani bacin rai da zaisa ka mance da danka yan zon Kai zaka dauki dan ka ka,ajeshi atiti kace mai bari kaje kadawo, su mahaukata ne? jalal yace naga alaman baki da hankali mikewa yayi zaifita safna ta bude baki tace kaine dai baka da hankali. juyo wa yayi ya dawo yace abin har yakai haka? eh yama wuce haka tun da kafito ta tsotson ummi. jalal ji yayi kamar ta caka mishi allura azuciyar shi , yace safna kar ki manta fa ummi mahaifiya tace. safna bude baki tayi tace jalal ai uwa batafi uwa ba. tun da suke da safna bata taba kiran shi da sunan shi ba sai yau, kara kule wa yayi yace toh nagane abin naki rashin mutunci ne toh kisan magar da zata rika fitowa daga bakin ki dan bazan dauki wula kancin ki ba inkuma kina ganin wasa ne kikara fadan wata magana kiga ni wlh mugun duka zan miki. daidai lokacin su hajiya dake falo suka soma jin hayaniyar su aguje suka shigo daidai lokacin da safna take cewa sai dai mudake juna, jalal kuwa yayi kanta gadan gadan anty ce ta riko shi iya karfin ta amma sai kwacewa yakeyi hajiya ce ta shiga tsakiyan su ta girgiza jalal tana fadin abduljalal dubeni nan me yayi zafi hake, kai da nake yabon ka. yace hajiya wannan yar karamar yariyar zata duga fadamin mgnr da taga dama ni sa,anta ne? hajiya tace a,a kayi hakuri fita muje, juyawa yayi ya fita yana huci anty tabi bayan shi. Hajiya ta kamo hannu safna data manne da bango ta zaunar da ita bakin gado tace safna kintaba jin laifin wani ya shafi wani, shi meye nashi, me lefi daban wanda ake hukun tawa daban, karki kara safna dan Allah kisawa zuciyar ki salama. safna kuka take sosai tace hajiya toh kice mishi ya sake ni. cikin fada hajiya tace yazon dai kina nufin babu wanda zaigaya miki mgn kiji ko ? girgiza kai tayi bahaka bane Hajiya ni cewa nayi ya dai na min magana. haba safna ban da abinki ta yaya zakice ya daina miki mgn mijin kine fa dan Allah karna kuma jin wannan mgnr abakin ki kuma kije ki bashi hakuri, safna ki daina gayawa jalal munanan mgn akan ummin sa uwa uwa ce safna kuma hannun ka baya rubewa ka yanke kayar , safna yanzon zaliha ta gane kuran ta ya kamata ki yafe mata, tana cikin wani hali ki taimaka mata ta samu ta daidaita da iyayan ta, saboda ayanzon ke da baki da iyayen kin fita kwanciyar hankali dan kin rabo dasu lfy , itako ga iyayen tana kallon su amman ba dama taje gurin su, sabo da suna fushi da ita, toh dan Allah kiyi hakuri ki yafe mata, yanzon anriga an zama daya, ban da matsayin ta na yar mahaifiyar ki, kuma ga jikokin ta nan agaban ki, dan Allah mu yafi juna kwata kwata duniyar ma guda nawa take. jikin safna yayi sanyi tace shikenan hajiya amma ni abin da yake bani haushi yaya za,ayi mutun ya manta da dan sa. hajiya tace bar wannan maganan safna kandara ce haka Allah ya so. tace dama hakane sai mutun yayi abu da gangan yace wai kaddara ce. hajiya tace safna bar wannan maganan tashi kije kibawa jalal hakuri dan naga yayi fushi sosai . suna fitowa suka samu anty nusaiba tana rarrashin jalal yana zaune idon shi ja wur kallon safna yayi ya girgiza kai itama kallon shi tayi ta neme guri ta zauna tayi shiru. anty nusaiba ciki ta shiga hajiya ma barin gurin tayi aka barsu su biyu, cikin sauri jalal ya mike zai fita safna ta tashi ta riko rigar sa, kallonta yayi yaga tayi kasa dakai bece mata komai ba, ahaka suka tsaya safna na rike da rigar jalal har tsayon minti 15 ba wanda yace wa kowa komai 07014197556 [6:58AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 120-122 Gani yayi bata da niyar magana dan haka ya zame rigar shi yayi gaba. safna naganin ya wuce ta fara kuka, sai da ta gaji da tsayowa ta wuce daki, ta shiga ta samu jarirain sai kuka suke, cikin tausayawa ta dauke su ta sasu acinyar ta. tana cikin haka taji muryan alhaji da ummi suna gaida hajiya, bayan yaran sun sha nono ta kwantar dasu tamike dan gai da daddy sai da ta saka hajjabi sannan ta fito. alhaji naganin ta ya washe baki , gwaiwan ta tasa akasa ta gaida shi ya amsa, ta juya barayin ummi kanta akasa ta gaida ta, amsawa tayi cikin farin cikin . safna mikewa tayi zata bar wajan alhaji ya dakatar da ita. ahaji yace wata magana nake son muyi me mahimmanci hajiya kisa mana baki dan naga safna har yanzon bata huce ba, hajiya gyara zama tayi. alhaji yace yazon daga gidan baffa muke nashiga ni kadai na mai bayani abin da ke faruwa amman kwata kwata yaki saurara ta wai mun shirya karya ne nida zaliha daga karshe cewa yayi indai da gaske ne , toh nakawo mai yarinyar. alhaji na kaiwa nan yayi shiru hajiya tace toh amman da naso abari ayi suna tukun, shiru suka yi na dan wani lokaci zawacen hajiya tace, safna tashi ki shirya. mikewa tayi cikin daure fuska ta shiga daki ,bata jimaba ta fito ,ummi ce tabita da kallo taga bata fito da yaran ba, bata ce komai ba ta mike ta shiga ta kwaso yaran ta fito ganin inda safna ta daure fuska yasa hajiya ta mike tana fadin bari na dauko gyale na, naraka ku. bayan sun shiga mota hajiya tace ina jalal ya kamata ace tafiyar nan dashi akayi ta. alhaji yace kwarai kuwa bari na kira shi, daga wayar shi yayi ya kira jalal, yana dauka alhaji yace jalal kayi maza ka same mu gidan baffa gamu ahanya harda safna. jalal najin an abaci safna yaji ranshi ya baci dan haka yace daddy bani da lafiya ne kaina namin ciwo. alhaji yace ka daure dai kazo ina jiran ka, bayan ya kashe wayan yace safna halan kunyi rigima da jalal ko? shiru tayi bata ce ko maiba, sai hajiya dake zaune kusa da safna tace ai kowa dai yau anyi tsiya sosai dan naga jalal ya tun zura alhaji yace yauwa dan indai kaji jalal na fadin kansa na ciwo toh akwai bayani. nan dai alhaji ya farawa safna nasiha har suka isa gidan. bayan sun fito daga motar dukkan su suka shiga cikin gidan safna tun akofar gidan ta fara kuka. sun shiga da sallama wata dattijiyar mata ta fito daga daki cikin sauri safna tabi da kallo ,cikin sauri ta karaso ta rike safna ta kalli fuskar ta sosai ta juyar da idonta kafar safna cikin kuka ta fara kiran baffa tana mai magana cikin fillanci. fitowa yayi arude ya nufi safna kafar ta ya kallah shima kuka ya fara yana fadin Allah da girma yake tabas yar saudatu ce kafar su iri daya cikin sauri yace rahane sa mana tabarma. bayan ta shinfida tabarma kowa ya zauna ummi ko sai rabe rabe takeyi. Itako safna tunda baffa ya rike hannun ta be sake ba tana zaune kusa dashi, abayan sun gaisa alhaji ya gabatar da mahaifiyar shi agurin baffa da matar sa rahane, baffa dadi yaji sosai sannan ya shiga yi mata godiya akan abinda alhaji yake mai yabon alhaji yayi sosai daga bisani ya shiga saka mishi albarka. hajiya ma dadi taji sosai ganin inda baffa kesawa danta albarka dan haka tace toh baffan yaudai gaka ga yar saudatu dan haka yanzon sai mu yafi juna dan Allah abar tuna baya dan zaman duniya dan hakuri ne, kuma in mune yau ba mune gobe ba dan Allah ka yafewa zaliha . sai alokacin baffa ya kula da ummi data makure agefe yace hajiya ina jin bakin ciki idan na tuna rashin mutuncin da yar isakar yariyar cen tamin tasani atashin hankali da bakin ciki badan ina da tsawon kwana ba toh da bakin cikin yariyar nan ya kasheni tun lokacin da aka daura mata aure da alhaji babu wanda yasan gidan sai yayar ta rabi, dan haka da muka ta dade bata zoba na yanke shawaran nadauki mahaifiyar ta da kanwarta muje mugano ta ita da danta har gidan yayarta naje tamin kwatan cen gidan . bayan mun sauka amota sai muka fara tafiya da kafa dan iya kudin mu kenan kona komawa gida bamu dashi tafiya taki karewa har saudatu ta fara gaji danaga ta gaji sosai gata ba karama ba bare adauke ta , sai muka zauna gindin wata bishiya saudatu na zama ta fara gengyadi ganin yama na karatowa mamarta ta tashe ta amman sai tace bata huta ba dan haka muka barta wajan mukace bari muje mudawo, cikin ikon Allah muka isa gidan tunda me gadin ya fada mata ga baki sai gata rike da hannun jalal yana karami cikin bacin rai tace wai lfy kuwa. har yau na kasa mance wannan kalmar haka na daure nace naga kusan wata shida baki zo bane nace bari muduba ko fly, cikin sauri tace lfy ta kalau kuje gida inanan zuwa, mahaifiyar ta na kokarin magana tace a,a mama dan Allah kuyi sauri kar kawaye na su fito su ganku zasumin dariya har tana kiran me gadin wai ya bude mana kofa. haka muka baro gidan cikin bacin mahaifiyar ta ttun anan ta soma kuka haka muka zauna mukayi ta kuka sai yamma likis muka tuna da saudatu saida mukayi tafiya me tsayi muka isa wajen, wayam muka samu gurin babu kowa duk muka duba unguwar bata ba lbrin ta gashi dare yayi ganin haka muka nufi gida akafa ko Allah zaisa gida ta nufa, sai tsakar dare muka isa gida tunda lokacin ban sake samun lfy ba har yau sai dai sauki kowa agurin kuka yakeyi daidai lokacin jalal ya shigo ya same su cikin wannan hali. ummi mikewa tayi taje gaban baffa ta tsuguna tana neman gafarar shi. bece mata komaiba yana rike da hannun safna, dan haka hajiya taje har gabasa itama tsunawa tayi tace baffa kaduba girman Allah yafewa yarinyar nan, ganin hajiya da yayi akasa cikin sauri yace Allah ya yafe mana baki daya. [7:32AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 123-125 Godiya tayiwa baffa sosai sannan tasa hannu ta daga ummi ta kaita gaban mahaifiyar ta. mama rahane kin amsawa tayi ta juyar da kanta gefe sai da hajiya tasa baki. baffa yana rike da safna mama rahane tazo tarike safna tana fadi ya sunanki ne? safna shiro tayi tana zunbura baki, hajiya tayi murmushi tace sunan ta safna ai fushi take daku tace dama cen baku son saudatu tunda har kuka manta da ita. baffa yace ayya yarinya barashin so bane akwai yanayi na rashin wayewa ada bakamar yanzon ba, amman munji mun dauka kiyafe mana kaddara ce . kowa agurin murmushi yayi banda jalal dake tsaye, alhaji yace kai kuma yaya zaka zo katsaya mana akai. yace daddy inason naje gida ne , bana jin dadi. alhaji yace ka bari muma yanzon zamu tafi, baffa yace alhaji kafin kutafi bari akira mamar ta rabi ta ganta, ya fara kira rahane dauko mayafi kije gidan rabi ki gayo mata, cikin sauri ummi ta mike tace bari naje, kiran jalal tayi suka fita tare. bayan sun dau hanya ummi tace jalal me ya hadaka da safna? mamaki ne ya kama jalal dan haka yace ummi wani ne yace miki munyi fada. hararar shi ummi tayi tace ina tambayar ka kana tambaya na, dan baka da kunya. bahaka bane ummi ai naga baki cikin gidan ne lokacin. toh ina sauraron ka me ya hadaka. ummi rashin kunya take min kwata kwata ta raina ni. dakatar dashi ummi tayi jalal inason kayi hakuri da duk wani abu da safna zata maka bana son in sake jin ance kunyi rigima kajiko, kuma yan zon kaje ka bata hakuri. da sauri jalal ya kalli ummi yace inbata hakuri fa kika ce ai ita ce tamin laifi ita ya kamata tabani hakuri. eh na sani ka dai bata hakuri bana son ganin yariyar cikin bacin rai. ummi ni gaskiya bazan bata hakuri ba, kin ga inda take gaya min magana ne. ummi shiru tayi bata sake cewa jalal komai ba har suka isa gidan, yana tsayawa ta bude ta fita bata jima ba sai gata sun fito da yaya rabi har da yarta aliya sai murna suke. baya suka shiga ummu na gaba suka kama hanya ahanya ne jalal ya kalli aliya yace ummi na dade banga aliya ba tun tana karama , sai kuma naga kamar tana kama da safna. ummi banza tayi dashi sai yaya rabi ce tace ikon Allah itama zaliha haka tace, nina zaku ma naganta wlh. jalal ya juya gurin ummi yace ummi lfy kuwa? banza ta sakeyi dashi, yaya rabi tace zaliha abduljalal na magana kinyi banza dashi. rabu dashi yaya, jalal bashi da kunya ninace mai yayi abu yacemin shi gaskiya bazaiyi ba, kiri kiri. nan da nan yaya rabi tashiga yiwa jalal fada , har suka isa gidan fada takemai. suna shiga ta gane safna ta juya barayin ummi tace amman zaliha kin ban mamaki da har kikai zama mai tsayi da safna baki gane taba, hannu tasa ta daga safna, safna ma gani tayi kamar mamarta sunyi kama da mamarta sosai dan haka ta rungume ta tana kuka take taji son yaya rabi ya kama ta jinta take kamar mahaifiyar ta, duk da cewa da kaga yaya rabi kasan tana cikin yanayi na talauci. aliya tazo ta baya ta tsaya tace anty safna. Cikin sauri ta waigo sukayi arba da juna safna sakin yaya rabi tayi ta rike aliya haka sukaita murnan ganin juna sai gurin la,asar suka fito, safna na rike da aliya wai ita adole sai dai sutafi da ita. mama rabi tace safna kibari ran suna in munzo sai tazauna tamiki kwana biyu kinga yazon kayan ta duk suyi dauda. safna tace mama toh basai ta saka nawa ba. ummi tace yaya ai hakuri zakiyi kawai mutafi da ita. mama rabi tace toh Allah ya tsare sai munzo suna. bayan sun dauki hanya hajiya tace toh kodai zamuyi gaba daya ne daga nan mu wuce gidan goggo safna cikin murna tace eh Hajiya. alhaji ne yace toh bari akira jalal agaya mishi dan motar sa daban kar ya wuce gida. bayan alhaji yagama waya da jalal yace yaran dai zamani basu da kunya kunga wai jalal tunanin yaran shi yake wai cewa yayi za,a kwasar musu iskar mota, dariya sukayi ummi ta kara rufe jariran ta rungume su ajikin ta, suna isa gidan malam musa alhaji da hajiya ne kadai suka sauka amotar suka shiga gidan da sallama, goggo ta fitoh daga daki tana fadin wai wai hajiya kece da kanki sannun ku da zuwa tabarma ta shin fida bayan sun gaisa goggo tace bari naje na sowo muku shinkafa da wake. hajiya tace a,a ni ba zama nazoba nazone naga jikokina. cikin fadowan gaba tace aiko basa nan iro yana gun yansan da an kamashi itako salame yanzon ta dauki tallan gyada. cikin mamaki hajiya tace a,a batayi aure ba? hawaye ta fara sharewa tace ai ya fasa tunda yagano ciki gare ta. hajiya ta girgiza kai tace toh kizo ki raka mu gidan da dayar yariyar take naganta. goggo tace ayya ai sun bar garin nan kwata kwata yanzon bansan inda suke ba. alhaji yace tohfah mukuma gashi ganinta mukazo ya sunan tane ? baki na rawa tace safna , suna cikin haka saiga ummi sun shigo da jalal goggo ta zabura tamike tami tana fadin yau na shiga uku karya ta takare dan Allah ku rufamin asiri wlh bansan inda safna take ba, nan da nan tashiga basu lbr tana kuka . bayan ta gama ne hajiya tace to yanzon meye ribarki? babu wlh kawai bakin kishi ne ya debeni har na aikata haka gashinan alhakin ta na bibiya ta yara na duk babu nagari kuka goggo taci sosai babu me lallashin ta hajiya fadi take kigama kukan kije ki ne momin jikata dan ba yadda zanyi ba. Idon goggo duk sun fito waje kuka harda majina. alhajine yama jalal umarnin ya shigo da matar shi, dan haka ya juya ya shigo da safna safna na shigowa goggo ta kara tsorata , tace dama kunsan safna ne, a Ina kuka same ta, zuwa tayi ta fara duba jikin safna tace ikon Allah safna ce haka kamar yar wani hamshaki , ni inan cikin bakin ciki da tashin hankali muta ne na nunani wasu suce min uwar karuwa wasu sucemin uwar barawo, cikin kuka take maganar ki yafemin safna na tuba bazan kara ba. hajiya tace kima Kara mana, ina zaki ganta bare ki kara ita da take dakin mijin ta cikin fada tace ku kuma kutashi mutafi, duk mikewa sukayi suka fita safna ko tsayawa tayi tana kokarin daga goggo hajiya tazo ta jata [10:21AM, 12/28/2016] Fadeela lamido: ๐Ÿ’˜๐Ÿ’๐Ÿ’MIJIN MARAINIYA๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’˜ Story & Written by Fadeela Lamido Mmn Yazeed๐Ÿ“ 126-130 Lokacin da suka koma gidan hajiya mangariba tayi dan haka alhaji yana sauke su hajiya da su safna suka wuce gida harda jalal, jalal dai fushi yake da safna sosai dan har suka rabo basuyi magana ba. suma suna sauke ummi masallaci suka wuce saida sukayi sallar ishsha suka dawo gida. bayan sunja girki ne jalal ya mike yace daddy bari naje gida. alhaji yace me zaka je kayi agida bayan matarka batanan kayi zamanka mana anan, koba haka ba zaliha? ummi tabe baki tayi tace alhaji ni yanzo jalal yafi karfi na. Alhaji yace me kuma ya faru kai jalal dawo nan ka zauna, jalal na zama alhaji yace me yake faruwa, me ka mata? sunkuyar dakai yayi yace daddy akan maganar safna ne, yanzun kwata kwata ta rainani rashin kunya take min, kuma wai ummi tace wai dole ni zan bata hakuri, daddy ai ni ya kamata taba hakuri, amman yaya za,ayi kuma ace ni zan bata hakuri ai sai taji dadi nan gaba ta kara yimin. alhaji yace zaliha yaya haka, haka ake hukunci? alhaji nifa bana son ganin safna cikin bacin rai, dan haka ni dai kawai kaje ya bata hakuri, shi wanene da bazata mai rashin kunya ba, ai nima gashi nan kanamin rashin kunyar, wlh inhar bakaje ka rarrashi yariyar nanba zakaga abin da zan maka. kallon ummi yayi yace toh shike nan ummi naji, a han zar ce ya bar wajen dakin sa ya nufa. alhaji yabi jalal da kallo yace zaliha bafa haka akeyi ba kina nufin yanzon kinfi son ganin nashi bacin ran akan na safna? Alhaji aishi babba ne kuma cewa nayi yayi hakuri yabata hakuri.. Katseta alhaji yayi yace aiko indai haka zaki ringayi bakice su zauna lafiya ba dan zaki samai tsanar ta, ai shi amatsayin shi na namiji baxai so matar sa ta raina shiba, kuma nina tabbata ta bata mai rai ne shiya sa yayi fushi da ita amman yana son matar sa bakuma wai dan jalal yana dana bane na yabe shi, dukkan su yaya nane kuma daidai gwargwado nasan halin su. haka alhaji yayita ma ummi nasiha me ratsa jiki. zuwa cen ummi ta fara kuka bakin ta yana rawa tace alhaji akwai abin da yake damuna ina tunanin idan kaji mgnr zaka tsora ta dani amman yazama dole na fada dan innemi gafarar ka amman dan Allah ina neman wani alfarma karka gayawa kowa wannan maganar dan idan maganar nan ta fito toh lallai naji kunya kukanta karuwa yayi saida ta waiga ko akwai wani dake tahowa sannan tace alhaji gidan jalal daya kone... Alhaji be Bari ummi ta karashi maganar taba yace nasan komai xaliha bake da madina kuka shirya komai ba ai tuni nasa aka kama madina da kanin ta duna sai da madina ta kwashe sati buyu gurin yan sanda, shiko duna har yanzun yana hannu . kuka ummi take sosai tana rokon alhaji gafara tana fadin sharrin zuciya ne. alhaji ya fara share mata hawaye yace bar kuka zaliha ni tuni na yafe miki komai yawuce sai dai muce Allah ya kiyaye gaba. nagode alhaji har ina tunanin inkaji wannan maganar zaka sakeni ashe kai kallona kawai kake. alhaji yake yayi yace aitun lokacin tarewar jalal nasan komai dan lokacin na tsane ki shi yasama dazan tafi ban miki sallama ba dan gani nake zaki iya kisa. washe gari karfe 7:30 jalal ya fito cikin shirin shi na zuwa office sallama yayi ma ummi ta amsa bakamar yadda jalal ya zata ba, sannan ya mike yace nafi. waigowa tayi tace zaka biya gurin yan biyu ne sannan ka wuce ko? Jalal yace a,a saina tashi office saina tsaya acen. a,a jalal be kamata ba kadai biya ko atsaye ne ka gansu sai ka tafi, ga kairat cen katafi da ita daman ta dame ni wai bataga yan buyu ba. suna isa gidan kairat ta fita aguje ta shi gidan lokacin da jalal ya shiga ya same tana rike da yaran sai faman jagwalgwala su take wai ita tana musu wasa . saida ya gaida hajiya ya tabaye ta anty nusaiba bataxo ba, hajiya tace na nan tafe. safna nazaune kusa da hajiya tace ina kwana. kasa kasa ya amsa yamike yaje gaban kairat ya tsuguna ya sunbaci yan biyu ya mike yace hajiya na tafi. safna ta mike tabi bayan shi, yana fita daga falon ta rike shi, juyowa yayi yace safna sakeni karki ya mutsamin kaya anjima zan dawo . kara shagwar gwabewa tayi tana buga kafa kamar yanda kananan yara keyi tare da kuka ahankali . murmushi jalal yayi yasa hannu ya riko safna yace toh ya isa haka safna, me kike so. cikin kuka tace bakai bane kaketa fushi ko kallona baka yi. Jalal yace safna kenan bake kikace na daina miki magana ba, har kina min rashin kunya. toh kayi hakuri banzan kara ba. dadi jalal yaji yace shikenan safna ya wuce shiga ciki idan na dawo zan zo . haka safna tacigaba da zama gidan Hajiya cinkin kwanciyar hakali kowa kokari yake ya faranta mata rai Ana gobe suna su yaya rabi suka iso gidan hajiya ita da mama rahane washe gari akayi suna nagani na fada alhaji da ummi sun kashe kudi sosai, jalal kuwa ya tara abokan shi sosai itako safna dama bawasu kawaye gare taba dan haka bawasu mutane ta tara ba daga safiya sai halima su kadai ne adakin sai kuma kanwar ta aliya haka taro ya tashi lfy yaran sukaci sunan ummi da daddy wato yusuf da zaliha. Washe gari suna saiga goggo da salame sunayin sallama hajiya tace su fita mata daga gida kuka goggo ta saka tana fadin hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari na neme gafarar safna. safna tana daki ita aliya suka fara jiwo kukan goggo fitowa tayi da sauri , goggo nagani safna tace safna naxo neman gafarar ki ne karna mutu da wannan nauyin dan Allah ki yafemin itama safna share hawaye tayi sannan tace goggo kitashi ni dama na yafe miki komai ya wuce, kallon salame tayi taga cikin ta har ya fara fitowa sai yama suka tafi safna ta roko su har bakin gate ta basu kudi masu yawa tare dace ma goggo idan suna bukatar wani abu su mata magana. bayan shekara uku jalal da safna ne tafe a mota daddy da ummi suna baya sai faman surutu suke , safna tace yaya wai ina zamu ne? yace yau gidan ummi zamu tun da ke baki cewa zaki, ke sai dai gidan mama rabi ko kunyar ummi bakiji sai dai ita idan taji ganin ku tazo. kunya ce ta kama safna tace ba haka bane yaya abin da yasa nafison gidan mama rabi muna hira da aliya. hararan ta jalal yayi bawani ai ummi ma tana jinki da hira saiki ta wani zilzillewa. daddy ne ya leko da kanshi saitin jalal yace abba ni gidan baffa nake so bana son gidan ummi. tsawa jalal yayi mishi tare da fadi daddy In na sake jin kace baka son gidan ummi saina zane ka. cikin murna ummi tace yauwa abba kamai balala ni ban da ni inason gidan ummi. Jalal yace yauwa ummina ashe dai kin gane. Jalal ya juya barayin safna yace kinga kin koya ma daddy kin gidan ummi ko. safna shiru tamai domin miyau ne ciki da bakin ta daha suka isa gidan Kairat ta fito da gudu ta rike hannun ummi da daddy suka shiga ciki, sun same ummi da alhaji afalo gudu ummi karama tasake hannun kairat ta fada jikin ummi daddy ma da gudun shi ya nufi alhaji cikin dariya alhaji yace au wato kun raba kenan safna ce ta shigo jalal nabinta abaya sai fada yakeyi. alhaji yace na kula jalal so yake yazama mafadaci daga shigowa sai fada. daddy wai yariyar nan idan bata son tamin magana sai ta tara miyau abikin ta. ummi tace a,a jalal bada gangan take ba saidai idan ciki gare ta. cikin sauri jalal yace ummi ai idan tana da ciki bahaka take yi ba daddawa take ci dariya sukayi gaba dayan su sannan ummi tace jalal ai ko wani ciki da kalar sa. *ALHAMDULILLAH* _anan na kawo karshen wannan lbrn_ Fadeela Lamido Mmn yazeed 07014197556 *Ni makauniya ce ido na baya ganin comment din kowa saina masoya na๐Ÿ˜œ* adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *