Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 9 May 2017

WANI HASKE

adsense here

[10/28, 9:25 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/18, 10:41 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _*1-7*_ *JAN KUNNE*- Ban yarda wani ko wata su juya min wannan labarin ba, duk wanda ya sauya labarin ko ya cire sunan marubuciyar yasa nasa,ko kuma ya kwafi wani abu daga cikin labarin Allah ya isa ban yafeba. ~~~Cikin nutsuwa matashiyar budurwar wadda bata wuce shekaru 23 a duniya ba take harhada takardun ta wanda ke baje a saman teburin da take zaune, tako ina hayaniya ce take tashi ga kida ya cika ko wanne lungu da sakon dake cikin makekiyar babbar chochin _*(church)*_ wadda kallo daya zaka yi mata ka gane cewar masu halatarta da yawa, ciki harda wannan budurwa mai suna *GOODNESS*. Tattara takardunta taci gaba dayi har ta kammala zuba su cikin wata madaidaiciyar jaka baka ta dauki jakar ta rataya ta nufi hanyar kofa domin fita daga cikin church din, tana sanye cikin bakar body hug matsatsiya wadda ta kamata sosai, da wando jeans kanta daure da gashin kanti wanda aka yiwa kananan kitso fiyeda kimanin dari biyu, hannunta da kafarta kuwa sunsha blue farce akan zako zako din faratanta, lokacin da take fitowa tayi kicibus da saurayinta promise yana kokarin shigowa, Hannunta ya kama suka koma waje ya dan dubeta yana murmushi "dear ba dai har kin tashi ba?" Kai ta daga masa kafin ta iya bude bakinta "eh nagaji ne ina son zanje gida amma nasan ma bazata tafi yanzu ba sai anjima saboda yau da akwai night service" Kamar zai yi kuka yace"pls dear ki dan jira zuwa anjima sai mu tafi tare, kinga akwai inda nake son ki rakani" Kanta ta girgiza "am sorry promise, yanzu inada aiki agida, baba yana azumi yau, kasan yau Thursday so ina son naje na shirya masa kayan shan ruwa tunda ma bata nan" ta kare maganar tana duba agogon hannunta. Sakin hannunta promise yayi yace "babu damuwa agaida baba pls,sai mun dawo" "Ok bye bye" tafada tareda juyawa tafara tafiya da sauri domin tana son ta isa gida da wuri ta shiryawa mahaifinta kayan shan ruwa. Misalin karfe _5:30_ ta isa gidansu dake unguwar state low cost, gidan babu kowa lokacin data shiga, tana ajiye jakarta ta fito tareda shiga kitchen bayan ta kunna wakar _there is no one like you_ a wayar selularta,doya ta dauko tafara ferewa tanayi tana bin wakar. Kamar daga sama taji sallamar nura makocinsu, _"yes come in"_ tafada tana dariya domin tayi murna da ganinshi, ciki ya shigo ya janyo wata farar kujerar roba ya zauna yana cewa, "Ina ma take?" "Ma bata dawo daga church ba, nima dan baba yana azumine da bazan dawo yanzu ba wlhi" Tunda tafara maganar nura yake kallonta acikin ranshi yana mai jinjina kokarin mahaifinta wurin rikon addini ga taqwa da iya zama da mutane da yake shi Allah ya soshi da rahama sai ya bashi *WANI HASKE* acikin rayuwarsa su kuma iyalin nasa aka barsu haka, Dan murmushi yayi sannan yace "to albishirinki, yau nazo miki da babban labari yar gidana" "Hmm nura you done start ba? Ehem kazo yau ma zaka fara tsokanata ko?" Murmushi ya saki yace "yau babu maganar tsokana tsakaninmu, yau nazo ne na karbi credentials dinki zan kaiwa wani babban mutum wanda yake neman mai irin qualification dinki zai daukeshi aiki a office dinsa" _wooh, thank you God, am very grateful with this suitable job, eheeee"_ tafada tareda daka wani uban tsalle tayi watsi da doyar da take yankawa ta nufi cikin daki. Duk sai da ta hargitse dakin kafin ta iya tattaro takardun nata gaba daya ta kawowa nura tana fadin _make I go and photocopy this"_ Karba nura yayi yace bari yaje yayi mata photocopy din ita taci gaba da aikin da take, duk ta diririce haka taci gaba da aikin tana yi tana rawa tana waka har nura ya dawo ya isketa ahaka,ya bata original din takardun nata yayi mata sallama ya tafi da zummar zai kirata a waya ya sanar da ita duk halin da ake ciki. "Idan nasamu aikin nan zan tara kudi na kai baba can mecca yaje yayi aikin hajji, zan kai ma Jerusalem taje itama tayi aikin hajji, nima zanje Jerusalem, zan kai anty Bilkisu mecca" tafada tana fara'a, sai murna take alla alla take ma ta dawo ko babanta ta basu labarin abinda ya faru. Tana cikin yin aikin mahaifinta ya dawo lokacin ta kammala harhada masa abincinsa kunune kawai ya rage bata dama ba, "Sannu da zuwa baba" tafada tana fara'a, masu karatu nidai _*ummi A'isha*_ sai da na cika da mamaki ganin irin kamalar baban goodness domin mutum ne mai tsananin riko da addininsa yana rike da casbaha goshinsa manne da *wani haske* wato tambarin salla. "Yau dai da alama kina cikin farin ciki, kodai wani abun ya farune bayan fita ta?" Mahaifin nata ya fada shima fuskarsa dauke da fara'a "Baba nakusa fara aiki, dazu nura yazo ya karbi credentials dina" tafada cikeda murna, "Ato Alhamdulillah,Allah ya bada sa'a, ina maman naku?" "Baba, ma bata dawo daga church ba, yau akwai night service, may be ma su kwana acan" ta bashi amsa, "To shikenan" yafada tareda shigewa cikin dan madaidaicin falon da yake gidan, bai jima da zama ba aka kira sallar magrib yafito yayi alwala ya tafi masallaci kafin ya dawo goodness ta jere masa kayan shan ruwansa ta kule acikin daki tana sauraron irin wakokinsu wanda suka saba yi a church gefe kuma wani jibgegen Bible dinta ne take karantawa. * * * * * * * * * Washe gari tun gari bai gama budewa ba goodness ta tashi tayi wanka ta dauki Bible dinta ta nufi church, can ta tarar da mamanta,church din cikeda Jama,a masu tarin yawan gaske nanfa aka shiga bauta cikin kida da raye raye, mata da maza, manya da yara kowa ya dage sai tikar rawa yake, rawar ta dauke su fiyeda awa uku kafin aka dakata pastor ya fito yayi addu,o'i aka rufe, Saurayinta promise yana rikeda ita suka fito ma tana binsu a baya, agaban church din suka ja suka tsaya tafara bawa promise labarin ta kusa fara aiki, "Wow ashe mun kusa yin aure, tunda gashi zaki fara aiki" "By the grace of God hakane dear dan ina fara aikin nan babu kuma abinda zamu jira" "Gaskiya am very happy dear, babu damuwa Zan zo gidanku letter,ga ma can naga tana jiranki" "Thank you dear" tafada tareda juyawa ta nufi inda ma ke jiranta, "Ma nura yazo jiya fa ya amshi credentials dina" tafada lokacin da suka fara tafiya, Bata rai ma tayi ta tamke fuska tace, "Goodness bakya jin magana ko? Nace kidaina kula musulmi, babu ruwanki da muaulmi saboda addininku ba daya ba amma bakya ji" "Sorry ma,wallahi ba nice na kulashi ba shine yazo har gida yace akwai wani vacancy awani company ana neman wanda yayi irin karatuna" "Ehem, yayi kyau to amma ko kin samu aikin nan indai wurin musulmi ne ba zakiyi ba, nafi son kiyi aiki awurin Christian inda zaki kara samun training akan addininmu domin my ambition is u to become a pastor" Wata dariya goodness ta saki tace "that's my sweet ma, nima mama burina shine nazama hakan sannan ina son idan nafara aikin nan natara kudi na kaiki Jerusalem" Sai a lokacin maman tayi murmushi tace "yawwa my daughter haka nake sonki" Suna hira suna shirya yanda abubuwansu zasu kasance har suka karasa gida, goodness ce rikeda manya manyan Bible guda biyu daya nata daya na ma, lokacin da suka shiga baban goodness yana kitchen yana dafa ruwan wanka, cikin kitchen din ma tabishi ita kuma goodness ta nufi cikin daki. Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu, ranar Sunday da safe nura yazo gidan amma bai samu goodness ba saboda ta tafi church da yamma ya sake dawowa, a kofar gida suka yi clashes ita da ma suna dawowa daga church sunsha kwalliya sosai tamkar masu shirin zuwa gidan biki, ma wani dandakeken leshi tasa golden colour, tasha gwaggoro shima golden sai takalmi da jaka, Ita kuma goodness tana sanye cikin english wears masu kyau riga da skirt dukkaninsu black colour skirt din iya gwiwarta, "Welcome ma" nura ya fada yana rissinawa mama, Fuskarta babu fara'a tace "yawwa thank you" ta wuce cikin gida, Kallonsa goodness tayi duk sai taji babu dadi tarasa dalilin da yasa ma bata son mu'amula da musulmai alhalin kuma ita bata ga illar hakan ba saboda tasha zama da musulmai kuma dukkaninsu masu hali na kwarai ne, babu mugunta, babu cutarwa babu cin amana,kai to ita taya ma zata ki musulmi alhalin mahaifinta shima musulmin ne? "Nura kayi hakuri dan Allah, ma yau ranta a bace yake" Girgiza kai nura yayi yana murmushi yace "karki damu babu komai, dama zuwa nayi nasanar dake ranar monday ki shirya kije ABU AL'AMIN Company ltd,zaki karbi upper dinki sannan zaki fara aiki" Wani uban tsalle ta daka ta kaiwa nura runguma ya goce yana dariya "Nagode nura, nagode, kayi min komai, amma ranar tare dakai zamuje, kaine zaka rakani" "Kin san nima ina zuwa office fa, amma dai zan duba idan da hali zan rakaki" "Thank you nura, God bless" Cikin ihu ta shige gida tana cewa "thank you God, thank you, thank you" Kan cinyar mama taje ta fada tana murna, babanta yana zaune kan kujerar dake fuskantarsu yana sauraren su, "Ma i am a worker now, i done get a job in one comp called abu... Abu something, i have forget the remaining name but i get it, nura said i should go and collect my upper of appointment, mama pls join me to celebrate this wonderful issue" Shafa kumatunta ma tayi tana dan murmushi "my daughter i don't want to make u upset, but for frank speaking am not happy with this job" Cikin kidimewa goodness ta kalli ma tace "ma why, why" "My daughter u are the only one i have, kinga sister dinki musulma ce, and your dad is muslim, ke kadai ce kike tare dani shiyasa sometimes am fell so afraid about your relationship with Muslim, kar kema su rinjayeki kibi addininsu, if this occur i will not happy goodness" Hannunta goodness ta kama tana murmushi "ma indai akan wannan ne karki damu, bazan musulunta ba, i promised you this, kuma ai ma ko a secondary sch da musulmai na zauna harna gama sch nawa, amma babu ruwana da addininsu suma babu ruwansu da nawa, akoda yaushe suna fada min cewa addininsu ya basu dama suyi mu'amala da Christian babu haramci aciki, and when i was in the polytechnic duk course mate nawa Muslim ne suma basu da problem, kuma ma ga baba shima musulmi ne" Tsaki ma ta danyi tace "am not asking u about this rubbish, kawai ina fada miki ban yarda kiyi tarayya ko wani mu'amula da musulmi ba, sannan kiyi min alqawari cewar ba zaki musulunta ba, duk lokacin da kika zama musulma to bani ba ke, kuma sai na yanka ki, you heard?" "Am agreed ma,and i promised you i will not become a muslim, i wish my self to die under this religion (Christianity)" Shafa kanta mom tayi tace "thank you my daughter, am very proud of u" sannan ta juya ga mahaifin goodness wanda ke zaune yana sauraronsu bai ce komai ba tace, "Papa goodness kaji your daughter done get a job, so ka saka mata albarka, pls bless your daughter" "Allah sanya alkairi kinji goodness, Allah yasa wannan aikin ya zamo _*WANI HASKE*_ acikin rayuwarki, Allah ya baki nasara...." Da sauri ma ta katseshi "ah papa goodness i don't like this thing fa, nace kasawa yarinya albarka an you have started your muslim prayer, ah" "Ah ma leave him to finish pls" goodness ta fada fuskarta cikeda damuwa Tashi ma tayi ta dauki Bible dinta ta wuce dakinta ta kyalesu a falon. *Ummi A'isha*πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:25 PM] ‪+234 810 100 9022‬: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _*8-10*_ ~~~Juyowa goodness tayi ta kalli mahaifinta wanda fuskarsa ke dauke da alamun damuwa a tattare da ita, _"am sorry baba"_ tafada idonta taf da kwalla, "Kar kiyi kuka babu komai, abinda nake so dake shine kiyi hakuri da rayuwa aduk yanayin da tazo miki, duk da cewa nasan yanzu banida kalmar da zan iya fada miki tayi tasiri acikin zuciyarki saboda mahaifiyarki tasa kin taso da tsanar addinin musulunci acikin zuciyarki alhalin kuma musuluncin shine addini na gaskiya, ina yi miki addu,a kamar yadda Yar uwarki ta gane kema Allah yasa ki gane gaskiyar, Allah ya hadaki da *wani haske* acikin rayuwarki" Yana kaiwa nan ya tashi ya fita daga cikin falon yabarta zaune, Sam maganar da mahaifinta yayi bata wani tsaya mata arai ba saboda bata fahimci maganganun nasa ba kwata kwata, Channel ta canza ta kamo wata channel inda ake nuna wani Nigerian film mai suna _bad romance_ ,film din taci gaba da kallo har ma tafito ta sameta tace ta shiga kitchen tayi girki ita zata koma church yanzu, Tashi tayi tashiga kitchen din ta dora tuwon amala da miyar ogu tana yi tana yan wake wakenta _"there is no one like you, ehhh there is no one like you, ohhh there is no one like you"_ Muryar promise saurayinta ta jiyo atsakar gidan yana kwalla mata kira domin shi bashida katanga da gidan duk lokacin da ya ga dama zuwa yake, Lekowa tayi ta hango shi wuyansa dauke da wani siririyar chain mai tambarin cross ajiki, ga suma da ya tara tuli guda, faratan sa kuwa tamkar na mage saboda tsayinsu, "Welcome dear, ka shiga ciki ina zuwa" ta fada tareda sake komawa cikin kitchen din, amalar da miya ta zubo masa tazo ta sameshi a falo yana kallon film din da ta tashi tabari, Abincin ta ajiye masa ta zauna kusa dashi, "dear ranar monday zanje na karbo upper dina" Kamo hannunta promise yayi fuskarsa dauke da fara,a "congratulations my dear, nayi murna saboda nasan bikinmu ya kusa" Kafadarsa ta dan kaiwa duka "see you, kaci tuwo gashi" Hannun yasa yafara cin amalar yana dariya "dama nadade da yin mafarkin wannan lokaci, nayi mafarki zaki samu wani abu ashe wannan aikin zaki samu" "Nima fa sai da nayi mafarkin dear, kabari kawai ma taci burin wannan auren namu tayi shiri sosai don tunkararsa" "Yes oh,i like this" yafada yana kai loma, dariya goodness tayi takai masa kiss a kumatu. * Ranar monday kamar yadda nura yace haka goodness ta tashi cikeda murna,doki, da kuma farin ciki ta shirya cikin riga da wando na jeans da t shirt tasamo hill shoe mai mutukar tsini tasa tayiwa ma da babanta sallama nufi Abu Al'amin company ltd, lokacin karfe _8:30_ na safe. Lokacin da taje company din bata wani sha wahala ba aka nuna mata office din da zataje ta karbi offer dinta bayan anyi mata verification, zama tayi tana jiran mutumin da zai bata offer din domin har lokacin bai zo ba. Tana nan zaune tana ta kallon ma'aikatan kamfanin yanda kowa yake zuwa yake bude office dinsa ya shiga gashi company din kato ne yanada tsananin girma, gefe ga kuma wani dan madaidaicin masallaci, bin offices din da ido tayi ta yi tana jinjina tsaruwarsu,hawa hawa kowanne department da side dinsu, tana ta wadannan kalle kalle har wanda take yazo, ya bude kofar office dinsa ya shiga, mikewa tsaye tayi tana cewa "welcome Sir" gamida binsa cikin office din, "Are you goodness jacob?" Mutumin ya tambayeta, "Yes sir, nice" tafada tana dan rissinawa, wurin zama ya bata sannan ya karbi original din credentials dinta ya dudduba, bayan yagama gani ya dauko wata zungureriyar wasika ya bata, a lokacin ta rubuta acceptance letter ta bashi ta tafi bayan ya sanar da ita cewar next week zata fara halartar office, cikeda farin ciki ta koma gida tana zuwa ta rungume ma wadda take cikin kitchen tana harhadawa papa goodness kayan shan ruwa, nan ma ta shiga yi mata hudubar babu ita babu musulmi, kar ta yarda tayi wata mu'amula ta arziki dasu. Cikin wadannan kwanakin goodness duk tayi sune kan shirye shiryen yadda zata fara zuwa office, tayi wanki ta goge kayanta kaf, ko ranar lahadi da taje church cikeda murna take, suna tashi daga church tabi promise ta rakashi wani club inda ake wani party, sai wurin _9_ ta dawo gida ta bar promise acan yana cashewa yana kora giya. Washe gari ranar monday _9_ dai dai a office tayi mata nan aka nuna mata office dinta ta shiga a matsayinta na secretary din Genera manager wanda za arinka bata albashi akan naira _25,000_ banda wasu allowances da zata rinka samu, office din GM din ya hadu iya haduwa sanyin AC sai tashi yake tako ina, a falo office din nata yake wanda aka zuba mata kujeru da tebur ga kuma drawers na ajiye files,shi kuma ogan office dinshi na ciki. Wani dan ihu ta saka "yeeehhh" lokacin da ta zauna akan luntsumemiyar kujerarta ta aiki amma da alamar yau GM din bai zo ba saboda taji office din nashi arufe, wayarta ta zaro daga jaka tafara kiran promise, yana dauka ta sanar dashi yau gata a office kuma ga yanayin office din, kashe wayar tayi tana kallon wasu baki wanda suka shigo da alama wurin ogan suka zo nan tayi musu bayanin ance baya nan yayi tafiya zuwa abuja amma acikin satin nan zai dawo. Kwana uku da fara zuwanta office din har ta dan fara sabawa da mutanen wurin, ranar Thursday lokacin da taje Massinger yake sanar da ita oga yazo, ahankali ta bude kofar office din ogan ta shiga tana sanye da skirt baka na jeans da t shirt light blue tasa takalmi cover shoe baki, kanta daure da bakin dan kwali, "Excuse me sir" tafada lokacin ta takai tsakiyar office din, "Yes" yafada ba tareda ya dago kanshi daga file din da yake dubawa ba, hakan ya bata damar kare masa kallo, black beauty ne sosai dogo marar jiki mai dogon hanci, akwai saje agefen fuskarsa ga dan karamin gemu da ya tara, bakinshi kamar na mace domin wani dan tsut ne sai dai lips dinsa jajaye ne jur, yana sanye cikin milk colour din shadda da hula kalar kayan amma duk da yasa hular hakan bai hanata ganin tabon sallar dake manne agaban goshinsa ba saboda ya dan tura hular tasa zuwa keya, ayanda ta kwatanta shekarunsa ba zasu wuce _35_ ba a duniya, gaba daya office din ya cika da kamshin turarensa na _explorer_. Tsayawa tayi kyam agaban teburinsa tana kallonsa ko kiftawa ba tayi,shi kuwa bai dago ya kalleta ba har sai da ya kammala abinda yake yi, ahankali ya dago manyan fararen idanuwansa ya zubasu akanta, _"good morning sir"_ tafada cikin rawar murya saboda ganin baiwar surar da Allah ya hore masa, _"morning"_ yafada atakaice cikin sanyayyiyar muryarsa, juyawa tayi zata tafi har taje bakin kofa taji yace, "Aturo min director admin and finance" cikin maganarsa d'ai d'ai, domin kalma kalma yake maganar ahankali, gashi muryar sa ta cika sanyi sai kace cool water. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:25 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/20, 9:27 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _11-15_ ~~~ "Ok sir" tafada cikin in ina tareda bude kofar office din tafita tanata ayyana maganar wannan bawan Allah acikin ranta gashi wani dan gayu dashi, massinger ta aika ya kirawo masa daf din kamar yadda yace. Tana nan zaune akan kujerarta tana yan dube duben files din da aka fito dasu daga office dinshi, Karshen wata wasika ta duba wadda ya rubuta hatta wasikar kamshin turarensa take yi, sai alokacin idonta yakai kan sunansa JABIR.M. AHMAD, jabir ta maimaita sunan tana mai shafa sunan nasa da hannunta, director ne yafito yace da ita ki shiga GM yana kiranki, Tsam ta mike ta shiga office din yanzu kuma jarida yake dubawa ta daily trust ya dorata akan table din gabansa, duk da yaji maganarta amma bai dago ba har sai da yakai aya lokacin tafi minti 2 a tsaye, Dagowa yayi ya kalleta ahankali ya fara magana, "staff officer ya sanar dake dukkan ayyukanki?" Tabbas staff officer ya sanar da ita amma saboda tana bukatar taci gaba da sauraron maganarsa wacce yake yi dalla dalla yasa tace, "No sir" Dan lasar lebensa nakasa yayi ya mayar da idanuwansa kan jaridar da yake karantawa, "Ok, to aikinki ne kula da duk wani shige da fice na files din da akayi amfani dashi anan office din, sannan zaki rinka rubuta duk wata wasika wadda zata fita daga nan office din" Tunda ya fara bayanin take binsa da kallo musammam ma dan karamin bakinsa mai dauke da jajayen lips, "Kin gane" yafada a hankali, "Yes sir" "Kina iya tafiya" "Ok sir" tafada tareda juyawa tafita daga cikin office din. Kujerarta ta koma ta zauna tana jinjina isa da takama irin na wannan mutumin kodai dan yaga yana da kudine, ko dan yana da kyau? Tana nan zaune yafito daga office dinshi yana gyaggyara hannuwan rigarshi da alama alwala yayi zai tafi salla, "Adawo lafiya sir" tafada bayan ta mike tsaye "Yawwa" yafada a takaice, yafice,komawa tayi ta zauna jagwaf tana cewa "ohh wannan mutum da rashin kulawa da mutane yake". Mintuna kadan wadanda ba zasu wuce 20 ba ya dawo ya wuce cikin office din shi. Kallo ta bishi dashi har ya shige office din shi ta jiyo tana jijjiga kai. Lokacin tashi yana yi ta tattara kayanta ta nufi gida lokacin karfe _5:00_ dai dai, tana zuwa ta tarar da ma bata nan har ta tafi church sai iya babanta ne agidan, wanka kawai tayi taci teba miyar kuka wadda ta tarar an dafa agidan ta dauki Bible dinta ta nufi church. Washe gari ya kama friday kamar yadda ta saba haka ta shirya ta tafi office, lokacin da taje GM din bai zo ba dan haka ta zauna tafara karanta jaridar sa da aka kawo masa, tana cikin karantawar ne ta jiyo kamshin turare mai mutukar dadi hakan ya sata tsaida idanuwanta akan hanyar shigowa, minti kadan ya bullo yana sanye da farar shadda sai kyalli take dinkin tazarce, kansa dauke da hula ja yana amsa call, cikin sauri ta mike tsaye tana yi masa sannu da zuwa, hannu kawai ya daga mata ya wuce cikin office dinsa. Mintuna biyu da shigarsa ta dauki jaridunsa guda biyu ta shiga office din, Good morning sir" "Morning" yafada ba tare da ya dago ya kalleta ba, jaridun ta ajiye ta juya ta fita, zama tayi tana tunanin to shi wannan wanne irin mutum ne ? Sai dai kuma fa yanayinsa da wannan dabi'un nasa sun burgeta saboda ita mutum marar hayaniya yana mutukar burgeta maganar Massinger ne ya katseta, "Oga yana kiranki" Cikin sauri ta mike ta shiga ciki, ta tsaya "gani sir" Rubutun da yake yi yaci gaba dayi, "yau ba aturo min wani mail daga office din governor ba?" "Eh ba aturo ba sir" "To zasu turo,idan an kawo ko bana nan ki turawa director personnel, meeting za muyi da governor zasu bayar da kwangilar gina gidajen ma'aikata guda dari biyar" Idonta kyam akan bakinsa yanda yake mul mul da baki yana yi mata bayani ita dai wannan bakin nasa yana burgeta, jin shiru bata amsa ba yasa shi dagowa ya kalleta kur yaga ta kura masa idanuwa ko kiftawa ba tayi, "Kina jina?", yafada tareda dan buga teburin gabansa, firgigit tayi ta fara yan kame kame, "Yes sir, zasu kawo, eh zan kawo maka" Girgiza kai yayi yace "you can go" acikin ransa kuma yana cewa "anya kuwa wannan yarinyar kanta daya? Sai ayita yimata magana amma ba zata amsaba sai dai ta zubawa mutum ido" Tana fita taga wasu baki sunzo su biyu mata nan tafara binsu da kallo daya bayan daya, "Ya akayi?" Tafada lokacin da take zama akan kujerarta, "Sannu sakatariya munzo ganin malam jabir ne" daya daga cikin bakin tafada, "Yasan da zuwanku? Shi ya baku appointment?" Tafada tana yatsina fuska "Eh shine yace muzo office mu sameshi" "To yanzu dai bazai samu damar ganinku ba saboda aiki yake yi" tafada tana janyo drawer zata dauko wani file, "Haba ranki ya dade ki shiga ki sanar masa mana idan yaga zai ganmu sai mu shiga idan kuma bazai ganmu ba ahikenan" "Bazai ganku ba" Mikewa sukayi suka fita zukatansu babu dadi, kallo ta bisu dashi "an fada muku ina haukane da zan barku ku shiga wurin wannan zankadeden? Ai wannan nawane" tafada tana murmushi. Tun daga wannan rana goodness ta bullo da sabon salo domin duk bakuwar da tazo ganin GM bata barinta ta shiga mazan ma sai tayi niyya, yauma tana zaune akan kujerar ta ta hada tea saboda lokacin da ta fito daga gida bata yi breakfast ba, wata mata ta shigo yar madaidaiciya da ita tasha les mai tsada tana ta kamshi tace tazo ganin GM nan goodness tace baya nan, matar tace "munyi waya fa dashi shine yace nazo yau" Karkacewa goodness tayi tace "to sai ki kirashi ki fada masa ai" Juyawa matar tayi tafita tana zaro wayarta daga cikin jakarta, ko minti biyar ba ayiba sai gashi ya fito da kansa, kanshi ko hula babu hakan ya kara masa kyau, "Meyasa idan nayi baki bakya zuwa ki fada min sai dai kice musu bana nan? Wannan aikin nasaki? "Sorry sir" tafada tana kallon fuskarsa, "Yanzu kinga meeting zamu yi da S. A ta commerce and industry amma tazo kince mata bana nan alhalin kuma abinda zamu tattauna da ita abune mai muhimmanci" "Sorry Sir" tafada tana zare ido, "Bani mail din da aka kawo min daga code of conduct bureau" Hannu ta mika ta zaro takakardar cikin rashin sa'a kofin shayin data hada ya tuntsire akan takardar tare da sauran files din dake kan tebur din. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:26 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/21, 2:52 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _16-20_ ~~~Kallonta yayi da manyan dara daran fararen idanuwansa ya juya ya koma office ba tare da yace da ita komai ba, hakan ya sake rudata, _"ohh God help me pls, pls God"_ tafada arude lokacin da tafara diri diri acikin office din, "Allah yasa kar oga ya bani query yau" Hankalinta atashe ta dauki mail din ta bashi cikin office dinshi, lokacin da ta shiga baya kan kujerarsa, yana can kan wata doguwar kujera ta zaman baki, ya dora kafafuwansa akan dan glass table din dake gaban kujerar, yana kallon wata tasha a satellite wacce aka saka karatun alwur'ani mai girma, indai bata manta ba tun lokacin data fara shigowa office dinshi wannan channel din taga yana kunnuwa koda yaushe, "Am sorry sir" tafada tana rikeda takardar, "Je ki dorata akan table dina" yafada ba tare da ya kalleta ba domin idonshi yana kan TV, "Thank you sir" tafada tareda juyawa ta nufi kan table dinshi ta dora mail din ta juya ta fita daga cikin office din zuciyarta cikeda murna. Karfe biyar ta tashi ta tafi gida tana zuwa ta tarar da sister dinta tazo anty bilkisu sai dai ita musulma ce, suna zaune itada mahaifinsu suna hira goodness ta shiga kunnenta sakale da earphone tana sauraren d banj cikin wakarsa ta _a new day has come_ tana bin wakar ta shiga falon, ganin anty bilkisu yasata dariya, "hey when did you come?" "Tun safe nazo ashe kin fara zuwa office?" "Inata so ai nazo gidanki na fada miki ban samu time ba" "Ayya babu komai Allah ya sanya alkairi" yayar tata tafada tana kare mata kallo yadda ta dame cikin wasu riga da wando, "Amin, ma taje church ko?" "Tun dazu ta tafi" inji mahaifinta, "Oh make i quick because we have weekly prayer today" tana gama fadin haka tayi wurgi da jakarta ta shige daki ta dauko bible dinta ta ajiye akan kujera, ta shiga kitchen ta zubo abinci, sakwara miyar agushi, kusa da anty bilki tazo ta zauna tafara cin abincinta tana cewa "anty ya mijinki? Ranan mun dawo daga church nida promise da ma mun ganshi amma shi bai ganmu ba" Murmushi anty bilki tayi "ya fada min shima ya ganku" amma acan kasan ranta wani bacin rai takeji marar kwatantuwa, ace mahaifiyarta da yar uwarta basu bawa annabi Muhammad (S.A.W) gaskiya ba, Mintuna kadan ta cinye abincin ta dauki Bible dinta tafita tana cewa "anty idan nadawo na sameki to, idan kuma kin tafi kigaida mijinki" Tana fita anty bilki ta dubi mahaifinsu, "yanzu baba haka zamu ci gaba da ganin mama da goodness suna zuwa church? Addininsu daban namu daban yanzu hakan yayi daidai?" Girgiza kai yayi "Bilkisu halin mahaifiyarku sai ita, da ace tanada rabon musulunta da tuni ta musulunta to bata da rabo, tun kuna yara kanana ni na musulunta amma ita taki saboda macece mai taurin kai da kafiya, ke kuwa lokacin da ta fahimci kina sha'awar musulunci tun daga nan ta tsaneki tamkar ba itace ta haifeki ba, da salla babu abinda take miki haka zata barki kaca kaca dake amma idan Christmas tazo kar kiso kiga irin kwalliyar da take yiwa goodness, nidai ina nan ina yi musu addu'a akan Allah ya shiryar dasu, kema kici gaba da addu'a kinji?" Kwallar idonta ta share saboda tabbas tasan tasha wahala a hannun mama dalilin bin mahaifinta da tayi ta taso a musulma dama yar gata sai goodness itace shalele saboda halinsu daya da mama wurin kyamar addinin musulunci, su a kafiran ma yan akida ne, "Babu komai baba, zanje nakoma" tashi tayi tareda ajiye masa wasu yan kudi wanda ba zasu haura dariya shida ba domin yanzu baya aiki ya jima da yin retire. Lokacin da goodness ta taso daga church tare suka taho da saurayinta promise, wata yar karamar robar giya ya dauko daga cikin aljihunsa ya fara kurba, Bata rai tayi ta dauke kanta, "promise am tired with your habit, baka da aiki sai shan giya? Gaskiya yana da kyau ka daina shan giya, kazama dan gayu kadaina wadannan halayen" Kallonta promise yayi da kyau "goodness har lokaci yayi da zaki fara cewa kin gaji halayena? Goodness kece kuwa, nine fa promise dinki masoyinki, ko har kin fara mantawa dani ne?" "Ni ba wannan maganar nake maka ba kawai dai ina son kadaina wannan shan giyar ne" Jijjiga kai yayi yace "good kije gida zanzo nasameki agida" Batare da tace masa komai ba ta wuce tabarshi awurin tana tunanin ita yanzu koda zata auri promise to sai ya koma irin oganta na office wato GM, kai bama ta tunanin zata iya auran promise din. Lokacin data koma gida kwanciyarta tayi ta kunna irin wake wakensu tana saurara domin akwaita da son kida kullum bata da wani aiki sai sauraren wakoki kusan duk sabuwar wakar data fito tana da ita, shigowar ma da promise ne ya katseta ta tashi zaune, ma tazo kusa da ita ta zauna tana cewa, "Wake up, meya hadaki da promise?" Kallonsa tayi sannan ta kalli ma "ma cewa nayi ya daina shan giya" Wata tsawa ma ta daka mata "shut up, naughty girl,idan baisha giya ba me kike so yasha? Baki san nida har burkutu nake dafawa nake sayarwa ba? Babanki ne da ya musulunta yazama musulmi ya hanani sayar da burkutu, kuma bari kiji tunda yanzu kin samu aiki to bikinku keda promise ya kusa,kin jini?" Daga kai tayi, tashi ma tayi ta wuce daki, tana ganin haka itama tawuce dakinta ba tareda ta kalli promise ba, tun daga lokacin taji ta tsani promise ta tsani halinsa ko church taje bata kulashi church dinma abinda yasa take zuwa saboda ma na daya daga cikin manya manyan church dinne da daina zuwa zatayi takoma wata. Yau tunda tazo office take baza idanun ganin GM amma shiru yau bai zo ba, wani file director planning yaturo ta bayar kuma file din yana office din GM shine last wanda tayima sending din file din dan haka ta tashi ta shiga office dinshi, Office din sai kamshin turarensa na explorer yake yi tamkar yana ciki, kan table dinsa taje ta fara duddubawa amma yawancin abubuwan dake kan table din littattafai ne da suka shafi addini, drawer tafara jawowa tana dubawa nan dinma duk littattafan sane na addini, jijjiga kai tayi ganin yanda har a office ma koman shi na addini ne, dakyar ta iya gano file din karkashin wata drawer dauka tayi ta fita. Yinin ranar tayi shine cikin rashin jin dadi wanda ita kanta ta kasa gane dalili amma tafi alakanta hakan da rashin ganin GM, nan kuma zuciyarta ta shiga gargadinta gamida tunasar da ita, "Ke goodness karfa ki jawowa kanki abinda zai dameki saboda mutumin nan tsarinsa da naki ba daya bane, addininsa da naki ba daya bane, al'adarshi da taki akwai banbanci kuma koda ace yana sonki to ba lallaine ma ta yarda kuyi aure ba saboda ita tafi sonki da promise bata son ki auri bahaushe" zuciyarta ta lissafo mata wadannan bayanai alokaci guda, Tabbas hakane to amma ai shi so babu ruwansa da addini ko al'ada farat daya yake shiga koda ba a shirya masa ba, kasa hakuri tayi ta koma cikin office dinshi anan ta samu visitors cards dinshi birjik, guda daya ta dauka ta koma falo ta kwafi phone number dinshi ajiki tafara kiranshi ba tareda tasan abinda zata fada masa ba gashi gabanta sai faman faduwa yake dum dum, Kamar baza adauka ba sai kuma taji ya dauka cikin sanyayyiyar muryarsa mai haifar da kasala yace "Assalamu Alaikum warahmatullah,wabrakatuhu" "Hello sir" tafada a diririce, "Yes" yafada ahankali, "Ina yini sir? Yau baka shigo office ba gashi kanata samun visitors sir" ta shararo karya saboda bata da abunda zata fada masa, "Lfy, ki basu hakuri su dawo next time, nayi tafiyane amma yau zan dawo, gobe zan shigo office" "Ok sir adawo lafiya" bai bata amsa ba ya yanke kiran, duk da haka taji dadin jin muryarsa sosai, murmushi ta dan saki sai kuma ta bata rai saboda tuno promise da tayi, ita yanzu a duniya babbar matsalarta bata wuce promise ba, bayan shi bata da wata damuwa domin tasan auren Malam jabir kamar tayi ta gama ne. Washe gari da safe 8:30 ta shiga office lokacin duk sauran ma'aikatan basu zazzo ba hatta shi kanshi ogan bai iso ba hakan yasata shiga office dinshi ta dane kujerarshi tana juyi tana cewa "lallai oga yana shan laushi, ashe ni akan kashi nake zama ga inda laushi yake" Juyin da zatayi taga ya bude kofa ya shigo, zumbur ta mike jikinta yana rawa, "Welcome Sir, sorry sir" tafada atare, Kujerar baki ya nufa yaje ya zauna ita kuma tamkar wata munafuka ta fara takowa tana kallon kasa, daidai lokacin driver dinshi ya turo kofa ya shigo hannunsa rikeda wani kyakkyawan yaro wanda da gani babu tambaya tasan dan oga ne, jarida driver ya ajiye agabanshi ya juya ya fita, kusa dashi yaron yaje yazauna tareda kwanciya ajikinshi, "Good morning sir? Dama ina duba letter headed ne zan tura mail shine kazo ka sameni" tafada idonta akasa, "Kin ganta?" Ya tambayeta yana kallon jaridar da yake dubawa, "No sir ban gani ba" Tashi yayi hannunsa rike dana yaronshi ya nufi kan kujerarshi, "Abbu kekena ya karye" yaron ya fada tareda dalewa jikin kujerar dake gaban teburin baban nashi, "Kabari kar kaji ciwo" yafada ahankali, "Abbu cikina yana fashewa kaji" "Menene fashewa" yafada yana jawo drawer din table dinshi, "Abbu abinci da yawa ne yasa cikina yake fashewa" Dan murmushi goodness tayi ta karbi letter headed din ta juya zata fita, "Abu zanje gurin baba idi driver" bai jira amsar uban ba ya ruga da gudu har yana bige goodness, tana fitowa ta ganshi a kasa yana kuka, "Sorry big boy stop crying" tafada tareda dagashi, daukarshi tayi taje ta zauna akan kujerar ta, "Kadaina kuka kaji" Kai ya daga mata yace "dama bana yin kuka, abbu yace ni namijine na rinka abu irin na maza, kuka ba na maza bane na matane", Fashewa da dariya tayi ta shafa kansa, "ya sunanka?" "Al'amin jabir m Ahmad" yafada yana goge idonsa da bayan hannunshi, "Muje na siyo maka chocolate ko?" Girgiza mata kai yayi, "No thank you, abbu yana siyo min da yawa" "To muje ka rakani ni in siyo nawa" Kudi ta Zara a jakarta ta kama hannunshi suka fita aikin da zatayi ma bata bi ta kanshi ba haka ta tafi ta barshi, can bakin titi sukaje ta siyo chocolate packets biyu ta siyo biscuits manya manya guda biyu,acan kuwa sai nemansu ake yi basa nan gashi GM yana son tafiya dama ba zama yazo yi ba unguwa zaije shiyasa ya taho da al'amin din, lokacin da su goodness suka zo yana cikin mota yana jiran al'amin da ma'aikata suka bazu nemanshi office office, sai zubawa goodness labari yake kamar dama can ya santa, Kayan ta danka masa a hannunsa "ungo kayanka kaji idan kaje gida kasha kai kadai kar kabawa brother dinka" "Banida brother ni kadai ne" yafada yana dariya irinta ta yara,tareda shigewa cikin mota yana tsalle ajikin abbunshi, "Abbu kaga chocolate dina" GM baice komai ba sai kallonshi da yayi yakuma maida kallonshi jikin window nan ya hango goodness tana dagawa al'amin hannu. Tun daga wannan rana bai dawo office ba saima tafiya da yayi zuwa jihar katsina nan goodness ta shiga cikin damuwa amma kullum cikin yi masa waya take tana fadar karya da gaskiya dan kawai taji muryarsa shi kuwa baima san tana yi ba, ganin irin mutanen da suke zuwa wurinshi yasata tambayar massinger dinshi kodai GM yanada traditional tittle ne? Murmushi yayi yace da ita kawai dai malamin addini ne shiyasa mutane suke zuwa sosai hakan ba karamin dadi yayi mata kuma dama taga alamun hakan sai dai ita ahalin yanzu tana cikin matsala domin ma tafara tasowa da maganar bikinsu da promise wanda ita kuma yanzu bashi take so ba. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [8/22, 9:02 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _21-25_ ~~~Bayan ta tashi daga aiki tana komawa gida ta samu ma zaune tsakar gida tana tace gasarar koko yau da alama ba taje church ba ko kuma taje da wuri ta dawo, Agajiye ta zauna tana kallon ma "ma sannu da aiki" "Yawwa my daughter, daga gani kin gaji" "Ma nagaji sosai wlhi, ina baba?" "Bai jima da fita ba, sannan gobe ne birthday din promise dan haka gobe ba zakije office ba church za muje, gobe zaki sawa promise zoben alqawari (promise ring) shima zai sa miki, daga nan kuma sai maganar biki" Wata uwar faduwar gaba goodness taji saboda jin maganar da ma tafada nan ta bata rai ta kalli ma, "Ma nifa yanzu bana son promise, akwai wanda nake so, shi promise kwata kwata bai dace dani ba ni bana son mai shan giya" Ido cikin ido ma take kallonta "waye wanda kike so?" Cikin faduwar gaba tace "ma oganmu ne a office" "Musulmi ko? Bahaushe? Kina so ya aureki ya sakeki ko? Hausawa saki suke yi gashi suna yin kishiya saboda su basa yin auren zobe" Daga kai tayi "ma nayarda indai zai aureni" Matacin gasarar ma ta saki yafadi a kasa tana tafa hannu "oh chineke, goodness you want to marry hausa man? You want to marry a person that your religion and his religion are not the same, the man that your tribe and his tribe are not the same even your culture are not the same with his own culture, hmmm any where, tunda haka kin zaba, Allah yabaki sa'a amma idan kika auri hausa man duk abinda yayi miki babu ruwana, kar ki zo wurina and lastly koda kin auri hausa ba zakibi addininsu ba, idan kikace zaki bi addininsu sai na kasheki goodness" Ajiyar zuciya goodness ta saki "ma kin san dai nima ina son wannan addinin namu bazan iya rabuwa dashi ba dan haka ki daina doubting akaina" "Goodness in kin bar addininmu kin karbi nasu sai na tsine miki albarka, sai nasa Allahnmu yayi fushi dake" "Ma bazan karbi addininsu ba kidaina fadin haka" Tashi ma tayi ta kinkimu bokitin gasarar ta tayi kitchen dashi tabar goodness da tagumi tana tunanin yanzu ta ina ya dace tafara tunkarar auren GM? Tambayar da tayita nanatawa zuciyarta kenan. Daren ranar ba tayi bacci ba, asussubar fari ta dauki bible ta tafi church lokacin ma ta dade acan tana zuwa ta shiga sahun masu bauta ta zuba gwiwoyinta a kasa ta rufe ido ta fara addu'ar samun nasara awurin Malam jabir, sai da rana ta fito sannan ta dauko jakarta ta dawo gida tana kiran _"fire, fire"_ domin su a church dinsu wuta suke bautawa (Allah yayi mana tsari da ita) Tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin riga da wando matsattsu ko tea bata sha ba ta nufi office, karfe _9:00_ ta isa lokacin har GM ya dade a office dan haka jakarta kawai ta ajiye ta nufi cikin office dinshi domin ta kagu taga kyakkyawar fuskarshi gashi zuciyarta sai harbawa take yi fat fat, Kwankwasawa ta danyi kafin ta bude kofar ta shiga, can ta hangoshi zaune kan kujerarsa hannunsa rikeda wani littafi wanda ba zata iya tantancewa ba yana dubawa sannan ya kunna karatun alqur'ani kasa kasa yana saurare, yana sanye cikin farar shadda mai kyau sai kyalli take, kusan duk kayansa farare ne a yanda ta fuskanta domin bata taba ganinshi da wasu kalar ba daga fari sai milk colour, "Good morning sir" tafada tare da dan durkusawa, "Morning" yafada a hankali, sanin bazai kara magana ba ya sata juyawa zata fita, "Am kinga" yafada ahankali, hakan yasa ta dawo tace "na'am sir" "Kidaina irin wannan shigar idan zaki fito office, ki rinka sako normal kaya saboda nan kinga cikin mazane kuma mu a addininmu hakan bai dace ba, kamar yadda kuma a addininku hakan laifi ne, dan Allah akiyaye" Kur tayiwa dan karamin bakinsa da idonta lokacin da yake mata magana, dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi ta kurawa ido, "Kinji abinda na fada" Sai alokacin ta dawo hayyacinta "yes sir, nagode sir" "Ok kina iya tafiya" yafada tareda mayar da idonsa kan littafin da yake karantawa, Office dinta ta koma ta zauna tana murmushi amma kuma zuciyarta har yanzu bata daina bugawa ba, tunani tafara yi itafa duk kayanta totally babu atamfa domin bata dinkasu kuma ko ta dinka ba dinkine na cin mutunci domin sai anyiwa atamfar kaca kaca kafin a dinkata, sai anyi mata gutsi gutsi, dan haka kayanta daga riga da skirt sai riga da wando amma duk da haka zata daure ta zabo masu dan dama dan ganin tabi maganar da ya fada mata kuma hakan da yayi ba karamin sake burgeta yayi ba. Da yamma ta tashi daga aiki ta koma gida, a kofar gida ta hadu da nura cikin murna ta jashi cikin gidan domin dama tana son ganinshi, "Yanzu kin zama worker kinyi wuyar gani ko?" Nura ya fada ya dariya, "Sorry nura dama inata son nayi maka waya, nura dan Allah ka taimakeni ka sanar dani wani abu dangane da GM dinmu domin zuciyata ta kasa kyaleni in huta" Kallonta nura yayi "ban fahimceki ba, wai malam jabir kike nufi? Me ya faru?" "Nura nothing, i beg ka fada min pls nura, am in bad condition, ina bukatar jin wani abu game dashi domin ina son na aure shi" Zaro ido nura yayi "aure? Aure fa kikace goodness, taya kike tunanin wannan auren naku zai yiyu kina Christian kina ikirararin Allah ukune, kina mai yarda da cewa Annabi Isah Allah ne, kina cewa Maryam Allah ce, kina cewa Isah dan Allah ne, shikuma mal jabir yaki yake da wannan kalmar, kiran mutane yake akan su daina furta wadannan kalmomin, kira yake abi Allah shi kadai,tayaya wannan hadin naku zai yiyu? Da ace shi ba malami bane mai wa'azi tabbas may be zai iya aurenki, to amma shi mai wa'azi ne malamine wanda yayi suna ba a iya kasar nan ba har da sauran wasu kasashe na musulmai ai kinga abun kunyane agareshi aji yana auren wacce ba musulma ba" Ajiyar zuciya goodness ta sauke mai nauyi "gaskiya ka fada nura amma kuma ni rashin aurenshi agareni wlhi tamkar rasa rayuwata ne dan Allah nura ka taimakeni" ta fadi hakan lokacin da kwalla tafara bin kumatunta, "Shikenan goodness babu komai zan taimaka miki domin nasan haduwarki da malam jabir _*Wani Haske*_ ne acikin rayuwarki, zan taimaka miki har kikai ga samun wannan hasken, yanzu kin san ya za ayi? Zanje gidansa anjima da daddare zan halarci majalissinsa inda yake karantarwa bayan sallar magrib anan zan nemi fatawa cewar wata wacce ba musulma ba ta ganni tana sona shin zan iya aurenta? Kinga anan zan gane ko zai yarda ya aureki ba tare da kin musulunta ba" "Good nura nagode sosai, ina jiranka idan ka dawo" Tashi nura yayi ya fita a lokacin ma ta shigo tana rikeda bible dinta "hey goodness, meya hanaki zuwa church? Am asking you meyasa ba kije church ba? Kin fara wasa da addinmu ko goodness? Idan kinci gaba da haka pastor will punishe you nikuma ba ruwana ehem" "Sorry ma dawowana kenan daga office, gashi nagaji shine nabari sai da daddare zanje church din night service" Fara,a ma tayi cikeda murna tace "i like you my daughter, God bless you, ina babanki fa?" "Ma babu kowa agidan lokacin da na dawo ina jin ya fita" Kada kai ma tayi ta wuce cikin daki tabar goodness zaune anan zuciyarta tanata harbawa domin rashin sanin abinda nura zaizo mata dashi. Kamar yadda nura yace haka yayi bayan an tashi daga karatu ya dubi malam jabir yace "malam ina da tambaya, wata yarinya ce ta yaba da nagarta ta kuma ta yaba da rikon addinina da halayyata tace tana son na aureta to amma fa ita ba musulma bace, mahaifiyarta ma ba musulma bace mahaifinta kuma musulmi ne, to malam ya halarta na aure ta?" Kallonsa malam jabir yayi yana murmushi "ya halarta ka aureta,addini ya baka dama amma sai ta kasance wacce ba mazinaciya ba, sai ta kasance ya ba baiwa ba wannan shine sharadin, addinin Allah mai saukine, babu haramci a auren ma'abota littafi kwata kwata sai dai idan mutum bashida ra'ayi ne domin ba kowanne mutum ne zai auri wacce ba musulma ba, kaga kamar ni idan ka bani wacce ba musulma ba bazan aureta ba saboda wasu dalilai amma nasan aurenta ba haram bane". Daga kai nura yayi dama tun farko abinda ya zarga kenan, "to malam amma misali idan kaga yarinyar zata fada cikin wani hali marar kyau ai zaka aureta ko?" Murmushi malam yayi har sai da hakoransa suka fito "kune yara ku ya kamata kuyi irin wadannan taimakon" Yana kaiwa nan ya tashi ya shiga gida, tahowa nura yayi jikinsa a sanyaye, a farkon layinsu ya hango goodness tsaye tana jiran dawowarshi. Tana hangoshi zuciyarta taci gaba da dukan uku uku har ya karaso suka samu wuri suka zauna, "Goodness gandoki kin kasa zama agida kin biyoni nan" Murmushin karfin hali tayi "ya akayi" "Komai mai yiyuwane da yardar Allah amma shi dai a ra'ayinshi bashida sha'awar auren wacce ba musulma ba sai dai wannan ba shine yake nuna cewar bazai aureki ba, kinga na farko shi mutumne wanda ya karanci addini tsantsa saboda asalima baifi shekara 5 da dawowa _Nigeria_ ba daga _madina_ acan yayi karatunsa na addini wanda ya shafe fiyeda shekaru _20_ acan, bayan dawowarshi ne yayi aure yanzu yana da yaro guda daya, amma goodness mezai hana ki yarda ki karbi musulunci idan kikayi sa'a ta sanadiyyar karbar musuluncin ya aureki" Da sauri ta girgiza kanta hawaye na bin kumatunta "no, nura ba zan iya musulunta ba nidai ya aureni a haka nayi addini na yayi nashi, idan nace zan musulunta ma bazata yarda ba" "To shikenan yanzu kin san ya za ayi? Mahaifinsa za muje mu samu kiyi masa bayani, shi mal jabir mutum ne mai tsananin biyayya wa mahaifinsa, baya ketare umarninsa, nasan indai mahaifinsa ya yarda shima zai yarda" Dan murmushi tayi "Allah yasa ya yarda, nura nagode, yaushe zamuje?" "Gobe za muje da safe sai ayi masa bayani" Cikeda murna sukayi sallama ta tafi church, acan ta kwana sai da asuba ta dawo, yanzu promise ya gama gane cewar ta daina sonshi dan haka shima ya fita a harkarta. Karfe 10 nasafe suka hadu da nura suka tafi unguwar masanawa inda acan mahaifin mal jabir yake, gidane babba kato da masallaci a kofar gidan, acikin masallacin suka sameshi yana lazimi, tsoho ne dan kimanin shekaru 70 aduniya fuskarshi duk farin gashi amma jikinsa ras yake, Ita goodness bata shiga ciki ba awaje ta tsaya tasa doguwar riga yar kanti ta daura bakin dan kwali, nurane ya shiga ciki suka gaisa da tsohon yayi masa bayanin komai wanda yasani babu abinda ya boye tun daga farko har karshe sannan ya kara da cewa "mahaifinta da mahaifiyarta dukkaninsu yan okene ne amma suna zaune anan jalingo, sannan mahaifinta ya dade da musulunta tun shekaru masu yawa da suka wuce ta sanadiyyar wani makocinsa da suka zauna tare agarin jos, amma ita mahaifiyar har yanzu tana nan akan addinin yahudu da nasara" Dan murmushi tsohon yayi yace "yaro wannan mutumin da kace ya musulunta nine nabashi kalmar musulunci lokacin ina zaune agarin jos ina koyarwa a jami'ar addinin musulunci dake garin, shekarune masu yawa bana mantawa aka kawo min shi akace zai musulunta, nine nan nabashi kalmar shahada, babu komai insha Allahu jabir zai aureta kamar yadda take son ya auretan, amma ka sanar da ita idan tasan zata aureshi ne da niyyar ta cutar dashi to gara ta fasa idan kuma tsakani da Allah take sonsa to falillahil hamdu insha Allahu sai jabir ya zama _*WANI HASKE*_ acikin rayuwarta" "Mun gode malam, Allah ya kara girma da nisan kwana" nura ya fada tareda tashi ya fito inda goodness ke tsaye tana sauraronsu, duk wadannan maganganun da akayi acikin kunnenta akayi su shiyasa farin ciki ya mamaye zuciyarta marar misaltuwa, machine din nura suka hau suka bar wurin ya tafi kaita office duk da cewa yau tasan ta makara sosai amma haka zata daure taje dan ta ganshi, Murna fal acikin zuciyarta nura yana ta kara yi mata karin bayani har suka je office din ta sauka tana yiwa nura godiya ta shiga ciki, Massinger dinsu ta samu zaune shi kadai ganinta ya fara yi mata sannu da zuwa, anan yake sanar da ita oga yana conference room yana meeting da directors dinshi, wannan rana ta yau goodness na cikeda farin ciki. Sai da lokacin salla yayi sannan masu meeting din suka firfito domin zuwa salla, office dinsa ya nufa domin yin alwala, yana shigowa sukayi ido hudu da goodness, dauke idonsa daga kanta yayi yashiga office dinsa bayan massinger ya bude masa kofa, binsa ciki tayi lokacin ya cire hular kansa yana saka silifas zai shiga toilet, "Sannu sir" tafada cikin farin ciki "Yawwa" yafada yana balle clips din hannun rigarshi, "Sir yau naje unguwane shiyasa ban zo da wuri ba" "Babu damuwa amma ki kiyaye next time" "Yes sir" bai sake magana ba ya nufi toilet. *** Bayan ya tashi daga office around _5_ ya nufi gidan mahaifinshi, a babban falon shi ya tarar dashi zaune ya bude katon alqur'aninshi yana karantawa, jin sallamar malam jabir yasashi rufe alqur'anin ya juyo ya dubeshi da fara'a a fuskarshi, Zama yayi kusa dashi ya russuna ya gaisheshi,bayan ya amsa ne yace "Jabir dalilin kiran da nayi maka ayau shine kaga dai nafarko kana daya daga cikin mutanen da ake girmama su acikin garin nan ake koyi dasu, kuma kallum aikin samun lada kake yi, wannan dalilin ne yasa yau na sake kawo maka kokon barar wani aikin samun ladan, nasan Allah ya hore maka arziki, da kuma zuciyar da zaka iya rike mata biyu, wannan dalilin ne yasa na umarceka da kayi hakuri ka daure ka auri wata yarinya ma'abociyar littafi wanda nake kyautata zaton cewa idan Allah ya yarda _*wani haske*_ ce agareka kamar yadda kaima zaka kasance _*wani haske*_ agareta, ba musulma bace amma ta kamu da tsananin sonka saboda nagartarka da kyawawan dabi'unka gamida kyawawan halayenka da ta duba,ni kuma nasha mata alwashin insha Allahu zaka aure ta zaka zame mata _*wani haske*_acikin rayuwarta" Tun farko tun asali ko acikin mafarki bai taba tsammanin zai iya aurar wacce ba musulma ba saboda basa burgeshi amma yanzu bazai iya yiwa mahaifinshi gardama ko musu ba dan haka ya aminta "shikenan malam insha Allahu zan aureta kuma zan zauna da ita" "Allah yayi maka albarka jabir, amma kayi min alqawari zaka riketa bisa amana" "Malam insha Allahu zaka sameni mai rikon amana akanta tareda yin adalci" Albarka mahaifin nasa ya shiga saka masa tareda yi masa fatan alkairi acikin rayuwarsa, sallama yayi masa ya tashi ya tafi yana jimamin wannan al'amari acikin ranshi, wai a matsayinsa na mai wa'azi shine zai auri wacce ba musulma ba. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:26 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/23, 10:08 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _26-30_ ~~~Tun yana hanya ya fara laluben number uwar gidansa wato ummu al'amin kamar yadda yake kiranta, ringing biyu ta daga cikin sallama, "Abu al'amin yau baka dawo da wuri ba, duk aikin office dinne ya rike ka haka?" "Gani nan nataho yanzu, na dan biya ta gidane naga malam" "To Allah ya kawoka lafiya, ga al'amin" Karbar wayar al'amin yayi cikin murna yace "hello abbu na kaga ummu ta dakeni" "Ohhhhh al'amin rikici, laifi kayi mata ko?" "Abbu ni banyi mata laifi ba" "Haka kawai ta doke ka? To idan na dawo zan rama maka" "Yawwa abbuna sakallahu kairan wa ilal liqa" Kashe wayar yayi yana murmushi a rayuwarshi yana son yaron nan nashi shiyasa yake son yaga ya tsaya tsayin daka don ganin rayuwarshi ta inganta to amma yanzu gashi wani al'amari mai girma ya na kokarin kunno kai cikin rayuwarshi data iyalinshi, sam bashida ra'ayin auren ma'abota littafi wato (ahlul kitab) to amma yanzu hakan ya zame masa tilas ko dan samun ladan yin jahadi amma yana jinjina ta yanda zai iya rayuwa da macen da bata tsarki. Lokaci kankani suka isa gidansa dake unguwar farin gidaje, gidane na alfarma tamkar gidan wani sarkin nidai ummi A'isha nace ashe malamai suma yan jin dadine, farfajiyar gidan driver yaje yayi packing yafito ya budewa GM kofa shima ya fito ya nufi cikin gidan, part ukune part din farko shine na ummu al'amin, nakusa da nata nashi na karshen kuma empty yake babu kowa aciki, yana shiga falonta ya jiyo surutun al'amin wanda yaketa wasansa yana kallon tashar spaceton Arabiya, da sallama ya shiga, da gudu al'amin ya taso ya rungumeshi, hannunshi ya rike yabi ta kofar falon yafita wani dan korido ya shiga sashensa yana shiga daki al'amin yafito ya tafi falo yana kokarin kunna tv, wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya cikin jallabiya fara da yar hularta itama fara ya fito falonshi nan ya tarar da al'amin yana kallon tv, zama yayi kusa dashi daidai lokacin wata kyakkyawar mace yar madaidaiciya ta shigo tana sanye da doguwar riga da dan karamin hijabi shekatunta ba zasu fi 28 ba fara doguwa, Hannunta dauke da food flasks guda biyu, "barka da isowa Malam" tafada tana dan murmushi, "Yawwa yagida" yafada yana duban al'amin wanda yaketa faman dariya saboda cartoon din da yake kallo na larabci, "Tashi kaje kayi alwala mu tafi salla ko walad" "Abbu ni yanzu ba walad bane na girma" "Yaushe ka girman?" "Abbu nagirma nazama rajulin" yana gama fadin haka ya tashi da gudu ya fita, Murmushi ya rakashi dashi yayinda ita kuma matar ta matso kusa dashi "yau baka dawo da wuri ba ashe wurin malam kaje" Kai ya daga mata "malam ne ya kirani sai nadawo zanyi miki bayanin abunda muka tattauna dashi" "To adawo lafiya abu al'amin" Tare suka fito ya shiga falonta yana kiran al'amin domin yazo su tafi masallaci. Bayan idar da salla zama yayi yafara dorawa mutane karatu kan littafin da suke karantawa ako wacce rana mai suna adabul mufrad, har lokacin sallar isha yayi bayan sun idar da salla ne ya dauko al'amin a kafadar shi ya shiga cikin gida mai gadi ya mayar da kofa ya rufe. Dakin ummu ya nufa acan ya sameta zaune kan abin salla tana karatun alqur'ani mai girma, gefen gadonta yaje ya kwantar da al'amin ya juya ya fita ya shiga sashensa, abincin ya zauna ya fara ci har ummu ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta sanya hijabi babba mai hannu, "Yau baka samu kaci abinci da wuri ba" tafada tana murmushi, "Eh wlh dan ban dawo da wuri bane" ya fada cikin muryarshi mai dankaren sanyi, "Naji kace zaka yi min bayani Allah dai yasa lafiya" Abincin gabanshi ya ture ya juya ya fuskanceta, "Lafiya lau, maganar aure ne wanda zanyi" Kallonsa tayi da sauri amma tasan tunda ya fada dagaske yake saboda baya yi mata irin wannan maganar, "Aure Abu al'amin? Yaushe? Meya faru?" Girgiza mata kai yayi 'ban san dai nan da yaushe bane sai abinda malam yace" Wani bacin rai taji ya fara mamayar zuciyarta, take fuskarta ta sauya ranta ya baci ta mike tsaye, "Asshhha! Da ace mutane sun san halayenka to da basu zauna sun bata lokacinsu sun saurari wa'azinka ba, kullum kana yiwa mutane wa'azi amma kai kuma Baka yiwa kanka, me nayi maka da kake son sai kayi min kishiya?" Tsaye shima ya mike "haba Salma akan kawai nace miki zanyi aure shine zaki jefeni da wadannan kalmomin, ubangiji ne fa ya bani damar auren mace fiyeda guda daya acikin suratul nisa'i aya ta uku, yace mun halarta muku ku auri abinda yayi muku dadi daga mataye.......!" Katseshi tayi da sauri, "ya isa, sarkin wa'azi ni ba aya nace ka jawo min ba, Allah yabaka ikon yin adalci kawai" Tana kaiwa nan ta juya ta fita tanufi dakinta tana sharar kwalla,shi kam tatafi ta barshi da mamaki karara akan fuskarshi lallai mata akan kishiya basu da dama, ko sun san abu sai su take yanzu duk ilimi irin na Salma akan kishiya tana neman birkicewa. *** A bangaren goodness kuwa tun ranar da sukaje wurin mahaifin GM ita da nura bata sake komawa office ba saboda yanzu bata son taje ko GM yasan itace itace wacce take son ya aureta, Dawowarsu kenan daga church itada ma ta tarar da labari mai dadi cewar GM sun zo shida mahaifinsa wurin babanta zuruf ma ta mike "Papa goodness ban gane abinda kakeso kayi ba, kana son goodness ta auri musulmi hausa man saboda addininku daya?" "Ma ba laifin baba bane, nice nake sonshi wlh ma yanada kirki" "Shut up, poor girl, idan ya sakeki ko yayi miki kishiya kar ki kuskura kizo min nan gidan" ma tafada tana zazzaro ido, Shidai mahaifinta bai ce komai ba domin yana cikeda tsantsar farin ciki domin yasan insha Allahu goodness ta kusa samun rahamar ubangiji, "Ko kin auri hausa man to ba zaki yi addininsu ba,and papa goodness kasan dai wannan bikin a church za muyishi ko?" Ba goodness ba hatta mahaifinta sai da maganar ta girgizashi. Cikin kidima goodness take kallon mamanta kafin mahaifinta ya bada amsa "kiyi bikinki a church nikuma nayi nawa a nan shikenan?" "Yawwa haka yayi dai dai saboda zan kaita church pastor yayi mata addu'a" tana dasa aya ta tashi ta karasa dakinta, nan baban goodness ya shiga yi mata nasiha da yanda zata zauna da mijinta lafiya sannan ya gargadeta da kiyaye daukar hudubar mamanta domin bikinta nan da sati shida za ayi tunda GM babban mutum ne ba shirme za a tsaya yi ba, wani sanyi ne ya mamaye ruhinta amma bata nuna ba a lokacin har sai da ta tashi ta shiga dakinta ta fada kan katifarta tana murna ta kira nura tana fada masa anan yake sanar da ita ai shine ya jagoranci su GM din har zuwa gidansu kuma yanzu GM yasan itace wacce zai aura saboda har yayi masa maganar cewa ya sake nemo masa wanda zai ci gaba da aikinta a office, tashi zaune tayi tace "Heyyy nura don't bring female i beg you, ka samo masa namiji" Dariya nura yayi tareda kashe wayar, wani irin son GM taji yana azazzalarta tana son taji sanyayyiyar muryar nan tashi nan ta tuna da cewar tana da tsohon layi a ajiye na zain, da sauri ta bincikoshi tasa a wayarta ta fara kiran layinshi, sai daf da zata tsinke sannan ya dauka yayi sallama, shiru tayi tana sauraren muryarsa, wata sallamar ya sake yi nanma tayi shiru har sai da yayi sallama sau uku babu amsa hakan yasashi katse wayar, wata ajiyar zuciya ta saki tana mai muradin ganin ranar aurenta da GM. Acan gidan GM kuwa Ummu al'amin ta dan sauko kadan amma fa ba hakura tayi ba zuciyarta ce kawai ta bata shawarar ta nunawa abu al'amin cewar ta hakura ta yarda yayi aurenshi amma kuma zata rinka yi musu zagon kasa shida amaryar, hakan yasata yin dariyar mugunta ta tashi ta nufi sashensa wanda yake kusa da nata, acan cikin dakinsa ta sameshi yana duba wani littafi na tafsirin suratul hud, da sallama ta shiga ta zauna kusa dashi gamida riko hannunsa, littafin ya rufe ya jiyo yana kallonta "ummu ya akayi" "Abu al'amin kayi hakuri da abinda nayi maka akan maganar aurenka hakika nasan kai adali ne kawai sharrin shaidan ne yasa na fada maka wannan maganar amma kayi hakuri, Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu" Hancinta yaja yace "ya wuce ummu kidaina bani hakuri, nasan kishiya tana da zafi awurinku mata amma haka zaku daure ku rinka karbarta aduk yanayin da tazo muku" Jikinshi ta shiga tana murmushin kissa. *** Tunda biki ya rage saura sati uku mahaifin goodness ya kirawo yayarta anty bilkisu tazo yaje ya ciro yan kudadensa da ya jima yana tarawa saboda auren goodness ya basu yace suje kasuwa su iyo mata siyayyar kayan kitchen domin GM yace kayan daki da sauran tarkace ba sai an kawo mata ba zai zuba komai murna wurin anty bilki harda kuka saboda jin wanda yar uwarta zata aura,tabbas tasan goodness tana daf da samun *WANI HASKE* acikin rayuwarta wadda zai yi sanadiyyar haska danginsu baki daya, nan aka shiga gudanar da shirye shiryen biki mama ta shirya ta tafi okene domin yin tsubbuce tsubbucenta tareda tahowa da dangi, amma har yanzu goodness da GM basu haduba sai lokaci zuwa lokaci goodness tana kiransa da layin zain dinsa tayi shiru tana sauraren muryarsa, Kudi kimanin naira dubu dari uku GM ya aiko dashi akan ayi komai da komai domin shidai ba bidi'a zaiyi ba wannan kudin da zai aiko dashi za ayi mata duk wata hidima data kamata, tsalle da murna wurin goodness ba a iya musaltawa, anty bilki kuwa sai gyara yar kanwarta take saboda shirin kota kwana sannan sun shiga kasuwa sun jido kaya hadaddu sabbi english wears akwati biyu dogayen riguna ne yan kanti sai riguna da wanduna da skirts da sleeping dress da inner wears domin goodness bata iya saka atamfa ko leshi ba, ma sai da biki ya rage saura sati daya ta dawo ita da mutanensu daga okene tana dawowa gida ya kancame da danginsu ko ina agidan ka juya wani yare suke yi wanda nidai ummi A'isha bana fahimtar sa. Tunda ma tadawo kullum sai sunje church anyiwa goodness addu'a da haka har ranar bikin tazo ranar a church suka kwana anata addu'o'i, washe gari ranar friday aka daura auren goodness da GM bayan an idar da sallar juma'a a masallacin mahaifin GM, ana gama daura auren ya koma gida yana sanye da farin yadi mai laushi da kyau, da gudu al'amin yazo yana bashi labari "Abbu wancan gidan wasu sunzo sunje sunata shara aciki abbu, abbu makotan munne?" Hannunsa ya kama yana murmushi "al'amin surutu, eh makotanmu ne" "To abbu wasu fa basuda hijabi irin na ummu na" Ras gabanshi ya fadi shi sai yanzu ma ya tuna da cewar fa ashe ba musulma ya aura ba, "al'amin ya isa haka kayi shiru babu kyau yawan magana" Yafada tareda jan hannunshi zuwa sashensa. Biki yayi biki domin ma ta cashe iya cashewa a church yayinda goodness kuma taci ado cikin wedding gown fara gashi anyi mata gyaran gashi tasha attach mai kyau, kafarta da hannayenta duk an gyara mata, musamman ma ta kaita aka yi mata gyaran fuska, su gyaran gira ne duk sai da aka yi mata fuskarta tasha make up tayi kyau har ta gaji, kasancewar a church zasu gudanar da bikin yasa anty bilki ta bisu a dole amma indai bata manta ba rabonta da church tun tana yar mitsitsiya lokacin da ma take zuwa da ita. Church din an kawatashi da decoration yasha balam balam balloons manya manya kala kala, goodness tana tsugunne gaban pastor ta rufe idonta sauran jama'ar kuma suna zazzaune suna sauraren pastor ciki harda promise tsohon saurayin goodness wanda yaketa dariyar mugunta ganin mijin goodness bai zo church ba,zobuna guda biyu aka mikowa pastor (wedding ring) ya karba,zubunan masu kyau daya na gold daya na silver, na gold din goodness ta saka a dan yatsanta na tsakiya wato marriage, dayan zoben kuma akace na mijinta ne lallai lallai ta bashi yasa, tafi aka hau yi da ihu shikenan aure ya kullu nan aka shiga ihu aka saki kida ma tafito tana rawa kamar zata karye, sai around 3 suka baro church suka dawo gida, nan baban goodness ya kirata dakinsa yayi mata fada akan kar tace zata rinka biyewa ma bayan aurenta domin tana iya kashe mata aure, sannan su shirya anjima da daddare za akaita gidan mijinta, dai dai nan ma tashigo cikin dakin, "Ah papa goodness whats are you talking about? Akai goodness yau without pastor visit her house and pray? Za akaita gidanta batare da pastor yaje yayi mata addu'a ba?" Cikin fushi Baban goodness ya mike "ke chioma nafara gajiya da wannan rashin mutuncin naki, akanme pastor zaije gidanta? Ko kin san waye mijinta kuwa? Kina so ya saketa ne tun kafin akaita gidan? Kince wannan na yarda kince wannan nayarda to yanzu kam i won't accept this nonsense, i can't tolerate your nonsense, tun yaushe kuke addu'ar? Duk wacce kukayi bata isheku ba sai kun je gidanta kun kashe mata aure? It can't, impossible" yafada yana huci,wani ihu mama ta kurma ta dora hannu aka tana kuka, "Oh chineke,papa goodness what do yo mean? You mean you can't allow pastor to visit goodness house to pray? Oh people, people pls come and aid me, oh God, chineke" tashi goodness tayi ta rike ma tana bata hakuri "oh ma, pls stop saying this, am sorry ma, kinji maganar da papa yafada idan kunje zai sakeni, kiyi hakuri ma, pls and pls" Shiru ma tayi tareda share hawayen fuskarta "that's the reason why i have neva like your marriage with hausa man, i know there is too much crises around it, tun kina yar karama naso ki auri Christian wanda zakiyi rayuwar jin dadi amma see my dream didn't come true,my ambition for you to became a pastor's wife will neva Eva been....!" Tasake rushewa da kuka, nan anty Bilkisu ta shigo tana tambayar meya faru, haduwa sukayi suka cigaba da bawa ma hakuri amma dakyar ta hakura sannan aranta ta dauki aniyar ko bayan bikinne sai sunje da pastor gidan yayi addu'a. Bayan magrib aka fara shirye shiryen kai amarya GM ya turo musu motoci guda hudu amma ma karfi da yaji ta hana goodness shiga daya daga cikin motocin sai wacce pastor ya kawo wacce tasha decoration tasha balloons ita ma ta saka goodness aciki itama ta shiga suka tafi, tunda akaje gidan kowa yake santi domin gidan ya tsaru yayi kyau sosai kai in banda rabo ma to da goodness ko a mafarki ba zata samu wannan mijin da wannan gidan ba to bahaushe yace rabo sai mai shi, kowa ya yaba wannan gidan, sashenta daban kuma shine na karshe, kayan funitures din da ya zuba mata ba na wasa bane kayane masu shegen kyau da tsada, babban falo guda daya da bedrooms guda biyu, sai kitchen da dining area, abin dai gwanin sha'awa komai green, nan ma ta shiga rawa harda guda, sun dade agidan suna ganin tsarin gidan sannan suka tafi suka bar goodness wanda take kuka biyu, na dadi da farin ciki. Ko wanne irin zama za ayi tsakanin goodness da Abu al'amin? Mu saurari shafi na gaba. _*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:27 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/24, 10:31 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _31-32_ ~~~ Bayan kowa ya tafi an bar iya goodness acikin dakinne ta mike gamida tattare doguwar gown din dake jikinta wacce ta kasance light blue da adon _flowers_ pink colour ajiki, tashi tayi ta fara zagaya dakunan da suka kasance mallakinta, Kamar a mafarki take ganin abubuwan da suke faruwa, wai yau itace ta zama matar GM mutumin da yafi karfin ajinta, falo ta fita wanda girmansa kadai abin kallone yasha kayan alatun more rayuwa an zuba komai green, dayan dakin ta shiga shima ciki yana dauke da dan madaidaicin gado shima komai naciki kalarshi green, fitowa tayi ta shiga kitchen, kitchen din ya tsaru kamar a kasar turai ga kayan amfani nan birjik masu amfani da wutar lantarki, "Thank you God" ta fada tareda runtse idanuwanta nan take hawayen farin ciki suka fara sauka akan kumatunta, wani sanyi taji yana ratsa babban dan yatsan kafarta yana haurawa cikin kwakwalwarta, Cikin dakinta ta koma ta zauna akan gadonta tana tunanin yadda zata iya hada idanuwa da GM a matsayin mijin aurenta,tana nan zaune har taji bacci ya fara barazanar dauketa domin agajiye take lis gashi kwana biyun nan kullum a church suke kwana dan haka basa samun damar yin bacci, ko gown din jikinta bata cire ba haka ta matsa can tsakiyar gadonta taja pillow ta dora kanta ta kwanta take bacci yace muje zuwa. A bangaren angon kuwa daidai lokacin da ya jiyo hayaniyar yan kawo amaryar yana zaune a cikin falonshi al'amin yana kwance akan cinyarshi yana koya masa wani littafin hadisi na fawakiha kusan duk hadisan dake ciki saukaka ne kuma gajeru basuda tsayi,jin al'amin yayi shiru ya tabbatar masa da cewar yayi bacci daukeshi yayi ya kwantar dashi akan doguwar kujera ya tafi jikin window ya daga labule ya fara hangen yan kawo amaryar, Baya iya gano amaryar domin an kakkareta sai dai yana hango sauran matan wadanda duk cikinsu mace daya ce mai lullubi ajikinta, yana nan tsaye har suka shiga part din nata suka fito suka tafi daidai lokacin ummu al'amin ta shigo falon tana cewa, "Bari na dauki al'amin saboda naga amaryar ta iso tun dazu, Abu al'amin Allah ya baku zaman lafiya" Danta ta dauka ta saba a kafada ta fice acikin falon ba tareda ta jira amsarshi ba, idan da sabo ta saba da wannan halin nashi na rashin mayar da amsa shi komai wahala yake masa domin bashida zafi ko kadan sanyinsa yayi yawa, Tana fita ya shiga dakinsa ya shige toilet ya yi wanka ya fito ya hau kan gadonshi ya kwanta yana tunani acikin zuciyarshi, "Ya dace naje na kwana a dakin yarinyar nan to amma ni bazan iya ba saboda inada kyankyami shiyasa tun farko banyi murna da auren nan ba, tayaya zan auri macen da idan na kusanceta ba zatayi wanka ba, idan tayi period tagama ba zata yi wanka ba, idan tayi fitsari ba lallai ne tayi tsarki ba" Yafada acikin zuciyarshi duk kuwa da yasan cewa tana da wani babban hakki akansa, kwanciyarshi yayi tareda yin baccinshi, sadaf sadaf ummu al'amin ta leko cikin dakin nasa ta window dinshi ta hangoshi yana bacci a hankali ta sulale ta koma side dinta dama tun lokacin data kwantar da al'amin ta dawo ta labe tana son taga fitarshi amma sai taji shiru wannan ya bata tabbacin cewa bazaije dakin amaryar ba yau. *** Washe gari da safe misalin karfe 9 goodness ta farka daga naunauyan baccin da tayi ta bi dakinta da kallo da alamun babu wanda ya shigo, taba baki tayi ta mike ta cire gown din jikinta ta daura towel ta shiga bathroom wanda shima ya tsaru kamar ba bayi ba, wanka tayi ta fito tazo ta shirya ta saka jeans da t shirt, jeans din blue rigar kuma pink mai gajeren hannu an zana cartoon guda biyu ajiki an rubuta _don't tell my momy_ turaren rocking girl tayi amfani dashi ta dauki wayarta ta fita falo anan ta fara kokarin hada kayan kallonta ta jojjona komai ta kamo wata channel ta music vox Africa sannan channel din suna saka Nigerian films, wakar p square ta fara saurare cikin wakarsa ta _you are my African queen_ volume ta kara yadda zata rinka jiyowa har a kitchen, tashi tayi ta shiga kitchen ta kunna electric stove ta dora ruwan zafi, kamshin turarensa kawai ta jiyo taji ta rikice tuni zuciyarta ta fara harbawa da karfi numfashinta ya ci gaba da fita da sauri da sauri, Cikin diriricewa ta nufo kofar kitchen din ta leko yana tsaye ya bawa kofar kitchen din baya yasha farin yadi mai santsi da bakar hula hannunshi rikeda remote yana rage volume din data kure, Tamkar marar gaskiya ta karaso cikin falon, cikin faduwar gaba tace, "Good morning sir" Batare da ya jiyo ya kalleta ba ya amsa gamida ajiye remote din yace "akwai abinda kike da bukata?" "No sir, but banida brush da maclean" tafada muryarta tana rawa, "Ok za akawo miki" yana kaiwa nan yayi gaba abinshi ba tareda ya jiyo ba kallo tabi bayanshi dashi tana murmushi har yafice, cikin kitchen ta koma tana murmushi amma har lokacin gabanta bai daina faduwa ba, ruwan zafin data dora ta tarar da ya kusa konewa saura kadan, saukewa tayi ta debo acikin cup komai na bukata gashi nan acikin wani dan karamin store, kayan tea ta debo ta koma falo ta hada tea din ta fara kurba tana yi tana kallon wani Nigerian film mai suna _love avenge_ nutsuwa tayi taci gaba da kallon film din har ta shanye ruwan tea dinta domin babu bread. Tana nan zaune har wurin azahar sai lokacin ta tashi ta shiga kitchen ta dafa indomie guda biyu ta dawo falo taci ta kwanta nan wani barcin ya dauketa sai yamma lis sannan ta tashi, cikinya wayam take jinsa hakan ya tilasta mata shiga kitchen ta sake dafa wata indomie din ta fito ta zauna taci rabi ta rufe sauran ta shiga wanka lokacin _6_ saura kwata, yar doguwar riga tasa marar nauyi ta dawo falo dirin tsayuwar motar da taji ya sata lekawa ta window din falonta, hangoshi tayi yana fitowa daga cikin mota daga gani agajiye yake, al'amin ya taho da gudu ya rungumeshi, leda taga ya bawa al'amin yana nuno masa part dinta amma da alama sako zai kawo mata, da gudu al'amin din ya taho wurinta shi kuma Malam jabir ya nufi sashensa, burum taji al'amin ya bude kofa ya shigo, "Gashi inji abbuna, gashi inji abbuna" Juyowa tayi ta amshi ledar tana cewa "thank you good boy, my regard to your abbu" da gudu ya juya ya nufi dakin abbunshi yana zuwa ya tarar dashi tsaye shida ummu, "Abbu tana gaisheka, kaji abbu," "Al'amin naji" yafada yana cire hular kanshi, juyawa ummu tayi ta fita tana tabe baki aranta tana cewa "fi'ilin banza danma dai har yau bai kwana a dakinki ba" tana fita al'amin ya rufa mata baya da gudu, shikam jabir dakinshi ya shiga yaje yayi wanka yafito ya sanya jallabiya ruwan madara yasaka dogon wandon jeans aciki ya saka yar karamar hula irinta larabawa ya dawo falo ya zauna zaman cin abinci. Ita kuwa goodness lokacin da ta karbi ledar da al'amin ya kawo mata zama tayi ta bude ledar brush tagani guda biyu da macleans guda biyu manya sannan da ultra pad guda biyu suma, murmushi tayi ta dauki ledar ta kaita dakinta ta sake dawowa falo ta kunna tv tafara kallo tana nan zaune ta hangoshi hannunsa rikeda na al'amin yana sanye cikin jallabiya wacce tayi mutukar yi masa kyau ahankali ta tashi taje jikin window taci gaba da kallonsa yana tsaye yana yiwa watch man magana wanda bata iya jiyo abinda yake fada amma tana hango bakinshi mul mul yana motsi wani azababben sonshi taji yana ratsata kafin ta ankara har yaja hannun al'amin sun fita daga gidan, _"wow you look so good my cool"_ tafada tana murmushi. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [8/26, 9:00 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _33-34_ ~~~ _"wow you look so good my cool"_ tafada tana murmushi tareda lumshe idanuwanta tana mai hango kykkyawar fuskarshi mai dauke da dan karamin bakinsa wanda yake tsananin bata sha'awa, Matsawa tayi daga jikin window din taje ta zauna akan kujera tayi jugum tana kallon tv wacce itace take zame mata abokiyar hira akoda yaushe, tana nan zaune har _9_ tayi lokacin ta jiyo bude kofar gate tasan ko ba afada mata ba shine ya dawo cikin sauri ta tashi taje ta leka window nan ta hangoshi rikeda al'amin a kafadarshi sannan ya kara waya a kunnenshi da alama call yake amsawa, tana tsaye tana kallonsa har ya shige part din farko, sai da kulewa hangenta sannan ta iya barin jikin window din ta koma falo ta karkashe kayan kallon ta wuce cikin dakinta, kan gadonta ta fada ta rungume _pillow_ tana tunanin mijinta da kyar bacci yayi nasarar daukarta. Washe gari da safe bata tashi da wuri ba sai wurin _8:30_ dan haka wanka kawai tayi tasa mini skirt da yar body hug baka mai hoton lips ajiki yasha jan baki ja an rubuta _cute_,memory din wayarta ta cire ta jona ajikin _DVD_ dinta ta kunna wakar Akon cikin wakarshi ta _I like your style baby_ ita dama can mayyar jin music ce domin yana sanyata nishadi shiyasa yake burgeta, volume ta kure karar sautin ta cika cikin falon har tana iya jiyowa daga cikin dakinta, dama tunda ta tashi part dinta yana rufe ko kofar falo bata budeba, _bedroom_ dinta ta shiga ta fara gyarawa ta dan goggoge shi sannan ta shiga dayan _bedroom_ din ta shareshi sama sama domin shi babu abinda ya batashi dan bata taba kwana aciki ba, fitowa tayi ta shiga kitchen shima ta dan kintsa shi sannan ta fito da mooper a hannunta da bokiti tana dan rawa tana bin wakar _"i like your style baby, heyy baby, ohhh bab.....!"_ cak taja ta tsaya jikinta ya fara rawa zuciyarta ta shiga harbawa cikin sauri sakamakon ganinshi da tayi tsaye ya dafa kujerar falon guda daya yana kallonta, ita fa sam bata ji alamun motsin bude kofa ba kai _in fact_ ma ita ko bude kofar ta yau ba tayi ba amma ai tunda maigida da gidansa bai kamata tayi mamakin ganinsa ba amma dai duk da hakan _"am very astonishe"_ tafada cikin zuciyarta, Cikin sauri ta yar da _mooper_ din ta dire bokitin omon dake hannunta taje ta dauki remote ta rage volume din ta juyo tana cewa _"good morning sir"_ Falon yake bi da kallo sannan ya amsa gaisuwarta yana sanye cikin lallausan farin boyel yasha hula ja mai ratsin fari ajiki, hatta takalmin kafarshi farine _half cover_ yana latsa wayar hannunshi kirar _Galaxy E8_ kamshin turarenshi kamar kullum yana barazanar rusa kwakwalwarta. _"morning"_ yafada yana kara wayar a kunnenshi cikin sanyin muryarshi ya fara magana, "Wa alaikumus salam, ka turashi yaje kawai ni bazan samu damar zuwa ba, a'a yanzu office zanje zamuyi waya" Kashe wayar yayi acikin ranshi yana cewa "mayyar jin kida kodai yarinyar nan tana da aljanune?" Ta gefen ido yadan kalleta tayi tsumu tsumu gabanta sai faduwa yake, acikin ranshi baiji dadiba dan ya fahimci kamar tsoronshi take ji, ba tareda yace komai ba ya nufi kofa zai fita "adawo lafiya sir" "yawwa" yabata amsa a takaice abun mamaki sai da ya murza key sannan ya bude kofar, to da ko ta ina ya shigo? Ta tambayi kanta, bokitinta da mooper taje ta dauka tazo taci gaba da mopping dinta tanayi tana rawa tana bin wakar da take saurare ta _before in love_. Hakace kullum take faruwa da safe yana shiga part dinta amma daga nan baya sake komawa da haka har ta cika one week agidan, yau tun da safe ma ta kirata awaya take sanar da ita tana nan zuwa ita da yan tawagar ta domin gudanar da addu'o'in zaman lafiya _(peace prayer)_ sai da taji gabanta ya fadi amma babu yanda ta iya, zama tayi sukuku har wurin _1_ sai _2:30_ su ma suka zo ita da jama'arta wanda sun doshi su goma ciki harda _pastor_ wasu dauke da ganguna dakyar mai gadi ya kyalesu suka shigo nan ma ta shiga ta fito da ita cikin riga da wando ta kawota waje inda mutanen ke tsaye suna jiranta nan masu ganguna suka saki kida na yan mintuna sannan aka tsagaita pastor ya shiga yin addu'o'i bayan an kammala masu kida suka dora daga inda suka tsaya nanfa gida ya cika da kida jin haka yasa ummu al'amin lekowa cikeda tsoro nan ta hango abinda ke faruwa, Cikin sauri ta dauki wayarta ta shiga kiran jabir yana dagawa tace "Abu al'amin wacce irin amarya ka auro ne? Gashinan yanzu sunzo sun cika gidan nan da kide kide, duk unguwar nan ta kaure da kida kuma an san daga gidan nan kidan nan yake fita yanzu wanne irin kallo mutane zasu yi maka?" Cikin rashin fahimta yace "wanne irin kida? Kida ta kunna?" "Masu kidanne suka zo har gida suke yi, idan ka saurara ma zaka iya jiyowa sautin kidan" cikin sauri ya kashe wayar ya dauki hularshi ya fito yana kiran idi driver, Mintuna kadan sai gasu a unguwar, lallai kam gaskiyar ummu al'amin domin tun daga bakin gate yake jiyo sautin kidan gashi almajirai da yara har sun tattaru a kofar gidan suna son ganin abinda ke faruwa amma mai gadi ya hanasu shiga, cikin sauri mai gadi ya bude musu gate suka shiga nan idonsa ya hango masa goodness tsugunne an lullubeta da wani farin kyalle ga wani mutum tsaye da koko a hannunsa idonsa a rufe yana addu'a yana watsa mata ruwan akanta sauran mutanen wurin suma duk sun rurrufe idanuwansu, Cikin sauri ya fito daga cikin motar ya nufi wurinsu, ganinsa yasa masu gangar dakatawa, sam bai iya masifa ba domin fadan ma bai samu muhallin zama awurinshi ba amma yau dai kam zuciyar maza ta baci hakan yasani komawa gefe dan ganin yanda zata kaya, Cikin zafin nama jabir ya finciko mutumin wanda ke rike da kokon nan take kokon ya fadi ya tarwatse, kafa yasa ya shure goodness wacce ke tsugunne take ta hantsila ta fadi, _"what's kind of this madness?"_ yafada da karfi hakan yasa ma saurin bude idonta tareda sauran mutanen da idanuwansu ke rufe, "Agidana za azo ana yimin shirka? So kuke mutane su daina ganin mutuncina? Kida agidana? To ni ba za ayi min shirka acikin gidana ba, baza a yimin bidi'a agidana ba, idan kafurcinku za kuyi ku tafi can inda kuka saba yi kuje kuyi kayanku amma ba anan ba" Cikin masifa ma ta dubeshi "dama baka san irin matar daka aura bane? Kayi kadan ka hana yarinya gudanar da addininta da al'adarta kanaji? And kazo kana kiranmu da hauka, to you didn't seeing madness har sai kayi kokarin hanata addininta" ma tafada tana huci sauran mutanen wurin kuwa sai zare ido suke yi yayinda goodness ta fashe da kuka, Cikin tsawa ya dubi mutanen wurin _"get out from my house"_ da sauri suka fara tattare nasu ya nasu suka nufi hanyar fita yayinda ma ranta ya baci ya baci ta kalleshi "Tunda baka da mutunci yata ba zata zauna da kaiba, ke kuma goodness now you have find a good lesson in your life, wannan shine abinda na jima ina fada miki and you refuse to understand me, dama nasan you will face some challenges if you married a Muslim saboda ba zai barki kiyi addininki yanda ya kamata ba, he can't allow you to worship your God peacefully and successfully, yanzu gashi kin gani with your own eyes tun ba aje ko ina ba he starting disgracing us, and ya kunyatani on the faces of my people, amma its not his fault, laifinki ne kece kin jawo min da kika nace sai kin auri hausa man" Tana kaiwa nan taja jakarta tayi gaba, yayinda goodness ta sake rushewa da kuka, ko kallonta bai yi ba ya juya yanufi sashensa zuciyarsa a bace, yana shiga ummu tana shigowa domin akan idonta komai ya faru, "Abu al'amin kayi hakuri dan Allah naga ranka ya baci sosai, dama amaryar yare ce?" Hular kanshi ya cire yana kallonta "yare ce asalima bata salla ba musulma bace" ya bata amsa,zaro ido tayi "Au bata salla? To Allah ya sawwake" tafada tana jijjiga kai lallai sai yanzu ta gano dalilinsa na rashin ziyartar dakin amaryar ashe bata salla shikuma mutum ne mai tsananin kyankyami kuma ko ba haka bama shi bashida yawan bukatar mace yanda yake da sanyin nan haka sha'awarsa ma take a sanyaye dan ko ita sai yayi kimamin sati 3 koma fiye da haka ba tareda ya nemeta ba ita kuma kunya tana hanata nuna masa tana bukatarsa sannan tana jin bai kamata a matsayinta na mace tana kai kanta gareshi ba, "Bari nayi wanka" yafada tareda wucewa cikin bedroom dinshi kallo tabi bayansa dashi, "shiyasa kullum baka rabuwa da mura domin ko wacce rana kana yin wanka sama da sau 5 narasa wannan son wanka naka wanne irine" tafada tana murmushi. Goodness kuwa tana durkushe inda aka tafi aka barta tana faman kuka dakyar ta tashi ta nufi part dinta ta shige cikin daki ta kwanta taci gaba da gursheken kuka can taji yayarta anty Bilkisu ta fado mata hakan yasa tayi saurin daukar wayarta ta kirata, tana dauka tasake fashewa da kuka cikin rudewa anty Bilkisu tafara tambayarta meya faru cikin kuka tafada mata ta kare maganar da cewa _"ma want to interrupt my marriage,yana daf da ya sakeni tunda dama ba bawai yana sona bane kawai yabi umarnin mahaifinshi ne ya aureni"_ tafada tareda fashewa da kuka, hakuri anty Bilkisu ta shiga bata sannan tace gobe zata zo gidan tunda yanzu yamma tayi, ajiye wayar goodness tayi taci gaba da faman kuka. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:27 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/26, 9:23 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _35-36_ ~~~Tunda suka gama waya da anty Bilkisu ta kwanta take faman dankarar kuka har dare ya tsala haka ta zauna in banda kuka babu abinda take yi nan da nan kanta ya fara ciwo kamar zai fashe gida dari kukan taci gaba dayi har bacci ya sureta ba ita ta tashi ba sai da gari ya waye, tana nan nade akan gado har wurin karfe _9_ gaba daya komai ya jagule mata saboda tasan yau GM bazai shigo part din taba tunda ta bata masa rai, hakan ce kuwa ta faru bai ko kalli sashenta ba ya fita ya tafi office. Wurin karfe _10:30_ anty Bilkisu tazo gidan, dakyar ta iya tashi taje ta bude mata kofa suka shigo ciki nan anty Bilkisu tabita da kallo duk fuskarta tabi ta kukkumbura gashi idonta yayi luhu luhu kuma yayi ja kamar gauta, cikin bedroom dinta suka karasa suka zauna a gefen gado, "My sister what's happening? Kinga yanda fuskarki tayi kuwa? Me yayi zafi haka?" Anty Bilkisu ta fada tareda kamo hannunta ta rike, "Anty ma want to finish my marriage, and tasa mijina yanzu yana jin haushina kuma dama can ba sona yake yi ba, bai taba sona ba and now ma makes him so upset, jiya tazo ita da pastor suna yimin addu'a har ya dawo ya samesu" tafada idonta yana zubar da hawaye, "Calm down my sister, ni dama ban so kika biyewa ma har tazo gidanki yimiki addu'a ba, saboda kinga mijinki musulmi ne kuma malami wanda mutane suke girmamawa faruwar hakan na iya jawowa raguwar kimarsa a idon mutane, amma don't put it into your mind,saboda abun zai dameki, kiyi hakuri har ya huce kinji tunda naga you are lucky bashida fada sosai mutunne salihi, he's a nice person" Bayan hannunta tasa tafara goge idonta wanda yayi sharkaf da hawaye ta kalli anty Bilkisu "thank you anty amma ya zanyi masa ya huce? Fushinsa na damuna, he's upset makes me to fell unhappy" Murmushi anty Bilkisu tayi "kiyi hakuri zai huce ahankali kinji,yanzu kitashi kije kiyi wanka nasan daga ganinki kwana kikayi kina kuka ko abinci baki ciba" Tashi tayi taja towel ta shiga bathroom ita kuma anty Bilkisu ta shiga kitchen ta shirya musu breakfast ta ajiye a falon ta kunna tv tana kallo acan kasan ranta kuma tana yiwa yar uwarta sha'awar wannan gida data samu dama haka Allah yake ikonsa akan bayinsa, tana nan zaune har goodness ta fito cikin riga da wando, wandon pink ne rigar kuma baka mai gajeren hannu, zama tayi suka karya suna ci suna hira, babu laifi damuwar dake ranta ta dan ragu domin anty Bilkisu ta dage wurin yimata wasu bayanai na yanda zata zauna da mijinta harma da kishiyarta, wuni guda sukayi tareda anty Bilkisu sai yamma ta tafi. Tunda anty Bilkisu tatafi damuwar da take ciki ta sake dawo mata alamun bude gate taji dan haka tayi hanzarin mikewa taje gaban window ta tsaya, akan idonta motarshi ta shigo driver yayi packing ya fito ya bude masa shima ya fito, kamar kullum dai yana sanye cikin farar shadda gazna mai tsadar gaske kansa yasa hula, daga nesa ta hango fuskar nan tashi mai mutukar kyau, kansa tsaye ya wuce part dinsa, tsayawa tayi ta kurawa compound din gidan ido har na tsawon wani lokaci kafin daga baya ta nufi cikin dakinta ta kwanta, kamar wacce aka mintsina sai kawai ta fashe da kuka, kuka tayi kamar wacce aka aikowa da mutuwa, nan ciwon kan dake damunta ya dawo mata sabo fil, kafin wani lokaci zazzabi ya rufeta mai zafin gaske. Da zazzabin ta kwana a jikinta ga wani azababben ciwon kai dake barazanar makantar da idanuwanta, jikinta gaba daya ya gama yin laushi, har gari ya waye bata samu barci ba sai da rana ta fitone bacci ya dauketa nan ta wuni akwance tana bacci sai tsakiyar rana sannan ta farka dakyar ta iya tashi jiri yana dibanta ta shiga bathroom tayi wanka da ruwan dumi ta hada tea tasha ta sake komawa ta kwanta ta tukunkune acikin bargo haka ranar ma ta sake kwana da zazzabin, washe gari ta kama friday ranar kasa tashi tayi sai da jan jiki ta shiga toilet saboda wani irin jirine ke daukarta gashi kwana biyu kenan rabonta da abinci tun ranar da anty Bilkisu tazo, tea kawai take sha. Ranar studay ranar jabir yana gida tunda ya fito falonshi ya zauna yana karanta littafin muwadda malik hankalinsa ya kasu gida biyu daya akan littafin da yake karantawa dayan kuma yana tunanin kwana biyu kenan baiji motsin goodness ba domin da kullum idan tana kallo yana jiyo karar tv din har cikin falonshi haka idan ta kunna music shima yana jiyowa idan kuma a kitchen take to yana iya hangota daga cikin dakinshi ta window saboda window din dakinsa yana opposite da window din kitchen dinta gashi window din ba mai tsayi bane shiyasa yake iya hangota idan tana ciki, amma abinda yafi daure masa kai shine kwana biyu sam baiji ta kunna kallo ba kuma bata kunna wakokin data saba kunnawa ba alhalin kuma a yanda ya fahimceta ma'abociyar jin wakoki ce gashi wani lokacin idan ta kunna kamar a falonsa ta kunna yakeji saboda kure volume take yi shikuma yana makwabtaka da part dinta daga ita har ummu duk wanda ya kunna tv yana jiyowa ko al'amin ne yake kallon cartoon a falon ummun yana jiyowa hakama idan ta kunna karatun alqur'ani yana jiyowa yanzu haka ma da yake zaune yana karatun nan yana jiyo sautin karar tv din ummu amma da alama al'amin ne yake kallon domin kamar cartoon yakeji, Littafin hannunshi ya ajiye domin yasan hakkinsa ne kulawa da lafiyarta koda kuwa laifin da tayi masa yafi haka girma sannan rayuwa babu tabbas jiki da jini akwai rashin lafiya akwai mutuwa, takalmi ya saka ya fita ya nufi part din goodness, ta kofar baya ya shiga falon tsit kamar babu mai rai aciki, gabansa yaji ya fadi saboda komai a karkashe yake tun daga light din falonn har socket da fan din falon, falon yabi da kallo yana tunani aranshi mutum ma fa na iya mutuwa ba tareda an sani ba, cikin bedroom din ya nufa ya duba na farko bata ciki hakan yasa ya nufi dayan anan ya hangota kwance saman gado ta kudundune acikin bargo,karo nafarko da taji ya kira sunanta cikin sanyayyiyar voice dinshi "Goodness" yafada a hankali amma shiru bata amsaba, sake kiran sunanta yayi nanma shiru dan haka ya matsa kan gadon yadan yaye bargon data rufa,ganinta yayi fuskara a kumbure ido yayi hulu hulu saboda kuka gashi da gani bata da lafiya sosai, "Goodness what's wrong with you?, are you well? Are you fine?" Yafada a hankali,bata iya bashi amsa ba sai hawayen dake kwaranya daga idanuwanta suna sauka akan kumatunta, hucin zafin da ya soma jiyowa daga cikin bargon ne ya tabbatar masa da cewa zazzabi take yi ahankali ya soma yaye bargon data lulluba amma duk da bata da lafiya sosai sai da ta rike bargon saboda bata son yaga jikinta,bai kulata ba ya fusge bargon gaba daya nan ya ganta daga ita sai wata yar doguwar riga iya cinya fara mai siririn hannu wacce ta bayyanar da dukkan surar jikinta a fili gashi ko inner wears babu ajikinta, idonshi ya dauke daga kallonta yace, "Tashi muje nakaiki asibiti,bakida lafiya shine kuma baki fada min ba why?" Kankame jikinta tayi tana dan karkarwar sanyi ta tashi zaune da kyar ta mika hannu jikin sif dinta tafara kokarin janyo wani skirt da riga yan kanti, jiri yana dibanta ta tashi tafara kokarin saka skirt din ganin haka yasashi komawa falo ya tsaya ya jirata acan, tana gama saka riga da skirt din ta koma ta sake tukunkunewa, shiru shiru yaji bata fito ba dan haka yasake komawa cikin dakin ganinta yayi tasake kwanciya ta lulluba, fita yayi ya nufi part din ummu ya sameta tana yankewa al'amin farcensa, "Ummu al'amin dan Allah acikin hijabanki bani guda daya aro zan kai yarinyar can asibiti bata da lafiya" Tashi ummu tayi tana cewa "Allah ya bata lafiya bari to na dauko maka" tana fita al'amin ya kalleshi "abbu ka siyo mata chocolate itama tana shan chocolate kamar ni" "To al'amin zan siyo mata" daidai nan ummu ta fito hannunta rikeda dogon hijabi ta mika masa tana cewa "basai an dawo min dashi ba kyauta na bata" karba yayi yafita aranshi yana ganin wannan itace mafita saboda ba zai iya fita da ita babu lullubi ba. Lokacin da ya koma dakin nata tana nan yarda ya tafi ya barta, "Tashi muje" ya fada yana kallonta tana lullube, "Sir bazan iya zuwa ba jiri nakeji, ina ji kamar zan fadi idan natashi" tafada tana shesshekar kuka, tsayawa yayi yana nazari, "Ki daure ki tashi ahankali" "Sir bazan iya ba, i can't, since on Thursday nake kwance anan, and now karfina ya gama karewa,my body becomes so weak, i can't" Bai jira komai ba ya yaye bargon, for the first time yasa lallausan hannunshi ya riko nata wanda duk da tana halin ciwo sai da taji wani irin feelings ya ziyarceta, shima hakan yaji amma ya daure ya tayar da ita zaune tareda mika mata dogon hijabi mai hannu, karba tayi ta saka, hannunta ya sake kamowa a karo na biyu ya mikar da ita tsaye, duhu duhu take ganin gabanta ga uban jiri dake daukarta kamar zai kayarta dole ta runtse idanuwanta saboda bata iya budesu sosai, ganin haka ya sanyashi dole karata ajikinshi yasa dayan hannunshi ya zagaya dashi ya dafe kafadarta dayan hannun nasa kuma yana rikeda hannunta har suka fito daga cikin bedroom din ta,dogon numfashi taja saboda wani irin kamshin dadi da taji yana fita daga jikinshi wanda bata taba jin irinsa ba sai yanzu data rabu da jikinsa, ahankali ta dan bude idonta ta kalli kyakkyawar face dinshi wadda yayi aski ya dan gyara sajensa da dan madaidaicin gemunsa daya tara, yau ma jallabiya ce ajikinsa kalar ruwan kasa da yar mitsitsiyar hularta baka ba karamin kyau yayi ba, "you are good looking my cool" tafada acikin zuciyarta tareda sake lumshe idanuwanta tana jin tattausan hannunsa rikeda nata. _*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:28 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [8/30, 11:07 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _37-38_ ~~~ _"you are good looking my cool"_ tafada acikin zuciyarta tareda sake lumshe idanuwanta tana jin tattausan hannunsa rikeda nata, yana rikeda ita a barin jikinshi har suka fita daga cikin falonta bayan tasa takalmin ta,sake shigewa cikin jikinsa tayi har su kaje harabar tsakar gidan, ahankali take jan numfashi tana shakar daddadan kamshin turaren dake fita daga jikinsa, malam idi driver ya fara kira da sanyayyiyar muryarsa hakan yasata bude idonta ta daga kanta tabi kyakkyawar fuskarsa da kallo ta dire kallonta akan dan karamin bakinsa wanda yafi komai burgeta a tattare dashi, da gudu driver ya karaso ya je ya dauko mota daga ma'ajiyarta yazo gabansu ya tsaya, bayan motar ya bude mata ta shiga shima ya zagaya daya barin ya shiga ya zauna ya kalli malam idi driver a hankali yace asibitin da nake kai al'amin zaka kaimu, nan da nan driver yaja suka fita, duk abun nan da yafaru ya farune akan idon ummu al'amin wacce ta tsaya ajikin window dan ganin abinda zai faru, tunani ta fara yi acikin zuciyarta to ko har amaryar ta fara laulayi ne? Sakin labulen window din tayi ta koma kan kujera ta zauna, to amma ai shi Abu al'amin bashida yawan bukatar mace asalima koda ya bukaceta to baya wuce minti 20 yayi abinda zaiyi ya gama, sannan wani lokacin ya kan shafe fiye da sati 6 bai bukaci mace ba, tabe baki tayi "koma dai menene su suka sani" tafada a hankali. Lokacin da su goodness suka nufi asibitin jingina kanta tayi ajikin kujerar motar idanuwanta arufe amma babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskar mal jabir ahankali ta bude idonta ta juya ta dan kalleshi idanuwansa tar akan wayar hannunsa yana lallatsawa sake mayar da idonta tayi ta lumshesu har suka isa asibitin, bayan motar ta tsayane ya fito yazo ya bude kofar barin da take ya mika mata hannu ahankali ta mika nata ta kama nasa ta zuro kafafunta ta fito, dan kallonta yayi asace babu laifi hijabin da tasa yayi mata kyau sannan ya fito da round face dinta sosai, kamar dazu haka ya karata agefen jikinsa suka shiga cikin clinic din, a reception ya ajiyeta ya karasa wurin da ake bude folder, bayan ya gama bude mata folder dinne ya koma inda take zaune tana ta kallon masu shige da fice amma kuma jikinta kamar wuta yake dan kuna, Ba tareda yayi mata magana ba ya dagota tsaye suka nufi wani office inda za adubata suna shiga likita ya fara checking dinta tareda yi mata yan tambayoyi anan yake tambayarta yaushe rabonta da abinci tace kwana 3,cikin sauri mal jabir ya kalleta ransa ya dan sosu domin hakkinsa ne na tabbatar da yanda al'amuranta ke gudana acikin gidansa, fada doctor ya fara yi akan danme zata zauna bata ci abinci ba alhalin kuma tana cikin yanayi na rashin lafiya,jikinta doctor din ya taba yaji yayi laushi dan haka yace gado za abata saboda sai anyi mata karin ruwa, female ward aka kaita aka jona mata karin ruwa, reception mal jabir ya koma ya fara kai kawo lallai abinda yayi bai kyauta ba sannan ai bai ma kamata yaga laifin goodness ba tunda ba itace takai kanta ba takanas mahaifiyarta ta biyota gidan domin yi mata addu'ar, wata faduwar gabace ta sameshi domin tunowa da wani hadisi da yayi wanda annabin rahma, annabi Muhammad (s.a.w) yake cewa _"dukkaninku masu kiwone, kowa za a tambayeshi dangane da kiwon da aka bashi, shugaba mai kiwone akan jama'arsa, mai gida mai kiwone akan iyalansa sannan mace itama mai kiwoce akan al'amuran cikin gidanta"_ tabbas yasan duk da cewa goodness ba musulma bace to tana da wasu hakkoki akansa wanda har yanzu ya kasa saukesu. Awarsu uku acikin asibitin sai da aka kara mata ruwa leda biyu sannan aka sallamesu bayan an hado mata magunguna kaya guda, hannunsa rike da nata ya sata acikin mota suka nufi hanyar gida, maganar al'amin ce ta fado masa _"abbu ka siya mata chocolate itama tana shan chocolate kamar ni"_ gyaran murya yayi yace da driver ya biya dasu ta super market, wani sabon super market suka je da kansa ya shiga ya kwaso mata chocolates kala kala da sauran tarkacen kayan zaki sannan ya siyo mata take away ya dawo cikin motar inda take jingine idanuwanta arufe. Mintuna kadan suka karasa gida, kayan da ya siyo mata ya debo tareda riko hannunta suka shiga falonta. Akan kujera ya zaunar da ita ya ajiye ledojin dake hannunsa ya dan kalleta kasa kasa idanuwanta a lumshe ta jingina kanta ajikin kujerar da take zaune agaskiya kyakkyawa ce ta karshe kawai matsalar dan ba musulma bace shiyasa ya kasa ganin kyawun nata amma dan kyau tana da kyau na asali, "Kici abincin sai kisha magani kin ji doctor yace ki daina zama da yunwa" yafada cikin cool voice dinshi, "Ok thank you" tafada har lokacin idanuwanta a lumshe suke, "Ina zuwa" yafada tareda juyawa ya fita, idonta ta bude tabi bayansa da kallo har ya fice daga cikin falon, zamewa tayi ta kwanta akan doguwar kujerar tareda lumshe idanuwanta. Yana fita part din ummu al'amin ya shiga, samunta yayi tana shirya al'amin da alama wanka tayi masa, yar karamar jallabiya ta yara fara ta saka masa tareda fesa masa turare, "Ummu idan kin gama abunda kikeyi kije ki duba yarinyar can ashe bata da lafiya sosai bamu sani ba" ya fada yana shafa kan al'amin, "Allah sarki, to bari nagama naje, Allah ya bata lafiya" tafada tana gyarawa al'amin wuyar rigarsa, dagudu al'amin ya fita ya nufi part din goodness, yana fita ta kamo hannun sa ta rike cikin nata, "Meke damunta? Ko laulayi ne?" Kai ya girgiza mata "bana tunanin haka kawai zazzabi ne ke damunta, bari naje nayi alwala naga lokacin salla ya kusa" Sakin hannunsa tayi tana murmushi "to adawo lafiya" fita yayi daga sashen ummu ya nufi nasa. Da gudu al'amin ya shiga falon goodness lokacin tana nan a kwance kamar yadda take dazu, ganinsa yasata tashi zaune ta cire hijabin jikinta tana murmushi, _"sannu anty, yas'alul lahil azim, rabbul arshil azim an yashfiki"_ yafada tareda zama akusa da ita, "Al'amin who taught you this?" Tafada tana jansa jikinta, "Anty abbu nane ya koya min, itace addu'ar da ake yiwa marar lafiya, indai mutum bashida lafiya aka yi masa wannan addu'ar to yana samun lafiya da izinin Allah" _"thank you soo much my dear son, my God bless your life"_ Zaune ta tashi ta janyo ledojin da mal jabir ya ajiye mata ta ciro take away ta ajiye a tsakiyarsu itada al'amin, _"oya chop"_ ta mika masa spoon, girgiza kai yayi, "Alhamdulillah Anty, nakoshi" "To ungo ledar chocolate maza dauki kayita sha kaji good boy" Chocolate din ya dauka ya fara sha yana kallonta, hannun hagu tasa tafara cin abincin da spoon, cikin sauri ya rike hannunta, "Anty bakiyi bismillah ba kuma kin sa hannun hagu" Mayar da cokalin tayi hannun damanta ta kalleshi "al'amin kenan waye yace maka ba acin abinci da left hand?" "Abbu nane kullum kullum idan zanci abinci sai yace min sai nayi bisimillah kuma kar naci da hannun hagu saboda akwai wani sahabi da yake cin abinci tareda annabi lokacin sahabin yana dan yaro sai annabi yake cemasa yakai yaro ka ambaci Allah, kaci da damanka sannan kaci gabanka" Murmushi tayi _"wow al'amin you are such a brilliant boy and talent,komai naka irin na mahaifinka ne like father like son, you take after your father, wow this is wonderful thing oh oh, oya ci gaba da bani labari kana shan chocolate"_ Kafin yayi magana ummu ta bude kofa ta shigo idonta akansu domin ta dade a bakin kofar falon tana sauraren hirar da suke yi. Cikin murmushi ta karasa ta zauna tana kallonsu, "Uwa da d'a" ummu tafada tana murmushi, _"welcome anty"_ goodness ta fada itama tana murmushin domin yaune rana ta farko da fara ganin ummun duk zamanta agidan domin bata samu fuskar shiga wurin kowa ba agidan asalima bata taba shiga wani wuri baya ga part dinta ba acikin gidan, "Sannu ashe bakida lafiya, ayya sorry" ummu ta fada tana kallonta domin yanzu ta danji sassaucin tsanar da tayi mata acikin ranta saboda ta fuskanci tana son danta al'amin sosai kun san kuma bahaushe yace uwar d'a mahaukaciya ce duk mai kaunar danta to itama tana kaunarsa, "Thank you anty, nagode nagode" Mikewa ummu tayi "Allah ya kara sauki,bari nakoma saboda inada aiki" "Ayya anty come and chop please" goodness tafada tana mika mata abincin gabanta, "No thank you am ok" ummu tafada tareda juyawa tafita, har bakin kofa goodness ta rakata sannan ta dawo wurin al'amin dake zaune yanata bare chocolate yana sha dan yasha akalla zata kai guda goma, zama tayi kusa dashi tana kallonsa,yaron komai nasa irin na abbunshi ne amma yafi babanshi surutu sosai amma baya ga haka kamarsu daya sannan wani abun burgewar ma ya dauko halayyar abbun nashi, _"my boy don't full your stomach with this zak'i zak'i"_ Dagowa yayi ya kalleta "anty ai ban koshi ba kuma kece kikace nayita sha har na koshi" Dariya tafara yi harda rike ciki "oh dama so kake sai ka koshi sannan zaka bar shan chocolate din?" "Na'am anty" ya bata amsa yana murmushi tareda bude manyan idanuwansa irin na mahaifinshi yana shirin sake wata maganar abbunshi ya bude kofa ya shigo, Tsumu goodness tayi tareda saurin sunkuyar da kanta kasa, kallonta ya danyi ya kalli al'amin wanda shima shi din yake kallo, "Al'amin lokacin salla yayi maza tashi kaje kayi alwala kazo muje masallaci" "To abbu" al'amin ya fada tareda tashi da gudu ya fita, yana fita ya jiyo ya kalleta har lokacin kanta a sunkuye yake tana kallon abincin dake gabanta gashi ta kasa ci gaba da cin abincin, duk jikinta jinsa take ya takure, "Kinsha maganin?" Ya tambayeta a hankali, "No, yanzu zansha idan nagama cin abinci" ta bashi amsa "Ki tabbatar dai kinsha kar kiyi wasa da wannan magungunan, Allah ya kara sauki" yana kaiwa nan ya juya ya fita, lokacin al'amin har ya fito daga part din ummu ya iyo alwala. Bayan fitarshi ta saki ajiyar zuciya "hmmmm i like u my cool" tafada ahankali tareda tashi tsaye ta kalli window nan ta hangoshi yana rikeda hannun al'amin suna kokarin fita, sai yanzu ta samu damar kallonsa domin dazu da ya shigo kasa kallonsa tayi, ya sake wanka ya sake jallabiyar jikinsa daga kalar ruwan kasa zuwa kalar ruwan madara da yar karamar hula itama ruwan madara, ayanda ta lura bai fiya saka kananan kaya ba daga jallabiya sai manyan kaya amma duk da haka bai hana kyawunsa fitowa ba, komawa tayi ta zauna bayan taga fitarsu, yanzu fes take jinta saboda taga alamun ya huce ya daina fushin da ita dama kuma ciwonta yanada alaka da fushinsa, abincin ta kammala ci tasha magani ta tashi ta shiga bedroom dinta ta kwanta, kamshin turarensa take ta ji ajikinta tamkar itace ta fesa turaren ajikinta, rigarta ta sinsina har yanzu kamshin yana nan kamar yanzu ne ya jinginata a jikinsa. Wayarta ta dauka ta kira anty Bilkisu suka gaisa sannan ta kira babanta shima ta gaisheshi, gabanta yana faduwa ta kira ma domin itama ta gaisheta, dakyar ma ta daga wayar cikin fada tace _"goodness kin daina zuwa church ne? Rabonki da church kin jima ko kin canja addini ne?"_ "No ma, banida lafiya ma yanzune na samu sauki amma may be gobe zan zo tunda gobe sunday" Kwafa ma tayi cikin bacin rai tace, _"thank you goodness for what your husband have done to me last time, but i want remind u,you promised me that you will not change and fellow his religion, dan haka ina mai gargadinki be very carefull with him, kar ki bari ya yaudareki ya jaki cikin addininsa"_ "Am so sorry ma about what he has done, sannan ma tun jimawa nafada miki son da nake yi masa bazai saka na bi addininsa ba, kiyi hakuri ma it will neva happen again" "Don't worry my daughter its pass, but you make sure gobe kin zo church kinji" "Zanzo ma, thank you my sweet mother" Kashe wayar tayi tana murmushi aranta tana tunanin hali irin na ma, ita dai a duniya bata son addininsu abbun al'amin, da wannan tunanin bacci ya dauketa. Har yamma tana bacci bata tashi ba, lokacin da mal jabir da al'amin suka dawo daga masallacin ma bacci take, hannun al'amin ya saki ya nufi part din goodness shikuma al'amin ya nufi wurin ummunshi, yana shiga falon yaga bata ciki amma ga su chocolate dinnan da tasha ita da al'amin duk a barbaje, girgiza kai yayi ya danyi murmushi,"ita da al'amin din banbancinsu kadan ne domin itama yarinya ce" yafada acikin zuciyarta, dakinta ya leka tana kwance tana bacci duk ta hada gumi daga gani zazzabin ya saketa, _air condition_ ya kunna mata ya juya ya fita ya nufi sashensa. Sai wurin karfe shida sannan goodness ta tashi daga baccin da take yi, wanka ta shiga tayi ta fito ta saka wata riga da wando dukkansu jajaye yan kanti _cotton_ masu laushi, falonta taje ta gyara aranta tana jin dadin yanda yanzu abu al'amin ya sauya mata yake bata kulawa, tv ta kunna ta jona DVD ta kunna wakar d banj cikin wakarsa ta _"my woman my everything"_ wani farin ciki yau take ji domin ko wanne lokaci idan ta rufe idonta hangota take yi rungume agefen jikin mal jabir _"my man my everything"_ tafada ta hanyar sauya salon wakar da take ji, nan taci gaba da al'amuranta. Misalin karfe _8:30_ ya shigo gidan hannunsa rikeda na al'amin yakaishi sashen ummu sannan ya shiga nasa part din tun da yashiga falo yaji sautin kida yana tashi kasa kasa, "sauki ya samu kenan tunda naji haka" yafada tareda ajiye littafin da ya shigo dashi na adabul mufrad sannan ya shige cikin dakinsa, ta window ya hangota acikin kitchen dinta tana aiki wanda bazai iya fahimtar abunda take yi ba amma kamar girki take yi dan hancinshi ya fara jiyowa kamshin wainar kwai, ajiyar zuciya ya saki domin tunowa da yayi bai taba shan koda ruwa ba acikin part dinta ba,saboda shi kyankyami gareshi, jallabiyar jikinsa ya cire ya shiga wanka ya fito lokacin tabar cikin kitchen din, turaren _right man_ ya fesa yasa karamar jallabiya riga da wando ya koma falo nan ya tarar da al'amin hannunsa rikeda hadisi yana bitar karatun da ya dora masa, "Al'amin yau ba za muyi karatu ba dare yayi kaje ka kwanta maza, sannan kar ka manta kayi addu'a kaji, yama addu'ar kwanciya bacci?" "Abbu bismikallahumma amutu wa ahyana" "Yawwa yarona maza tafi kayi bacci" littafinsa ya dauka ya fice yatafi wurin ummunsa yayinda shi kuma mal jabir ya zauna yafara cin abincin da ummu ta ajiye masa, bayan ya kammala ya kunna tashar huda tv ya fara kallo har _10_ tayi alokacinne ya mike ya nufi sashen goodness. _*Ummi Aisha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:28 PM] ‪+234 810 100 9022‬: *WANI HASKE* _NA_ *_UMMI A'ISHA_* _39_ ~~~Sashen _goodness_ ya nufa, tun akan hanyarsa yake jiyo alamun karar tv wadda daga ji babu tambaya kallo take yi, Ahankali ya kama handle din kofar falon ya bude ya shiga, ganinta yayi ta yiwa tv kuri da ido ko kiftawa ba tayi tana kallon wani Nigerian film _its my life_,agogon falon ya kalla karfe goma da yan mintuna, "Goodness you have to go to sleep now" ya fada cikin sanyayyiyar muryarshi, arazane ta jiyo ta ganshi dan bata san ya shigo ba domin hankalinta gaba daya ya tattara ga kallon da take yi, "Yes sir, ina son ne nagama kallon wannan film din yanzu zai kare" tafada tareda sakin ajiyar zuciya, "Alright, sai da safe" ya fada gamida juyawa zai fita daga falon, "Sir ina son gobe nafara zuwa church pls" Dam ya danyi ba tareda ya jiyo ya bata amsa ba amma kuma bai fita ba, to shi yanzu zai hanata zuwa church dinne ko kuma zai kyaleta taje? "Dole babu yadda zakayi tunda itama addininta zata je tayi" zuciyarsa ta bashi amsa, "Shikenan kije" ya fada a takaice tareda ficewa daga cikin falon ya nufi hanyar komawa nasa sashen, fuskarta ta maida kan tv taci gaba da kallon da take yi. *** Washe gari da safe tun misalin karfe 7 na safe goodness ta dau wanka tasha wasu English wears riga pink colour da yar top dinta baka, tasha bakin jeans mai beza daga kasa, ta kawo hill ta dora bayan ta fente fuskarta da kwalliya, part dinta ta kulle ta fita mai gadi ya bude mata gate ta tari abin hawa ta tafi church a lokacin su mal jabir ko tashi daga bacci ba suyi ba, Sai around 9 sannan ya tashi kasancewar weekend ne, tunda yaji shiru babu alamun tashin sautin kida yasan goodness bata gidan tayi sammakon zuwa church, wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya ya fita falo lokacin ummu al'amin har ta tanadar masa abin karyawa, yana zama al'amin yana shigowa dan haka da gudu ya fada kansa yana dariya, "Abbuna yau anty bata nan" "Taje unguwa ne al'amin" "Abbu muma za muje unguwar nida kai?" "Eh za muje bari mu gama cin abinci" Wani tsalle ya sake yi ya fada kan abbun nashi yana murna yayinda shi kuma mal jabir yake tunani acikin ranshi oh yanzu shi kuma haka Allah ya doro masa ana zuwa church a gidansa. Wuni su goodness suka yi acikin church, kuma gashi ta samu fuska sosai awurin ma dan tayi murna da ganinta ba kadan ba gashi duk da ba wata kulawa take samu daga wurin mijin nata ba duk da haka tayi kyau kumatunta sun dan kara cika, basu bar church din ba sai wurin karge uku na yamma, ma tabi zuwa gidanta. Suna tafe suna yan hirarrakinsu ma tana ta shan cikinta kan zamantakewar ta da mijin nata, wani ta fada wani kuma tayi shiru da haka har suka karasa cikin gidan, Suna shiga tayi ido hudu da mahaifinta acikin falo yana karanta jarida, "Allah sarki my papa" tafada acikin zuciyarta, "Ah papa goodness you dey here?" Ma ta fada tana ajiyewa Bible dinta, Da sauri goodness taje ta durkusa ta gaida babanta wanda rabonta dashi tun bikinta, "I dey here mama goodness" ya bawa ma amsa wacce ta shiga kitchen ta fara kokarin hado musu abinci, teba miyar kubewa ta zubo ta kawowa goodness bayan itama ta zubo nata, "Ehem goodness ina son za muje okene, za muje nida ke zaki gaisa da family wanda baki sansu ba suma basu sanki ba" Cikin sauri mahaifin goodness ya kalleta, "Mama goodness why are you always .....?" Da sauri ta katse shi "papa goodness always what...? Kana nufin bazan kaita wurin dangina ba saboda kai ka fita acikin addininmu tun jimawa?" "Mama its ok,kiyi hakuri papa baice komai ba ai" Mikewa baban nata yayi ya fita shi har yanzu ya kasa gane kan Maman goodness tun lokacin da ya musulunta ta saka masa karan tsana adole take zaune dashi, Yana fita ma ta kalli goodness "you made a big mistake my daughter, kinyi kuskure da kika yarda kika auri hausa man saboda su komai sai suce babu kyau, sannan sai ki samu 1 man yana auren 4 wives, gashi sun iya divorce kamar me" Jijjiga kai goodness tayi tana ci gaba da cin tebar da take yi "hakane ma amma shi wannan man din da nake aure bashida wani problem" "To naji amma kin san dai yanzu kullum zaki rinka zuwa church ko?" "Eh ma shiyasa nake sauri na koma gida da wuri saboda gobe ma ina son zuwa da yamma" "Yawwa my daughter duk yadda zaiyi dake kar ki yarda kibar addininki" Nan ma taci gaba da yi mata hudubar tsiya har ta gama ta yimata sallama ta tafi gidanta, lokacin da ta shiga gidan Ummu al'amin tayi bakuwa ta rakota compound din gidan suna sallama sai gata ta shigo, Daga nesa suka gaisa da ummu ta wuce part dinta, nan bakuwar ta kalli ummu "wannan kuma wacece?" "Itace amaryar abu al'amin din ai" Rike haba tayi "oh lallai yanzu duk yanmatan garin nan hausa fulani masu addini ace malam ya tsallakesu yaje ya debo ahlul kitabi? Allah ya kyauta to" "Amin dai" Ummu al'amin tafada tareda yi mata sallama ta koma sashenta. Goodness kam tana shiga daki ta sauya kayan jikinta zuwa wata yar karamar riga mai karamin hannu da wando tied red colour iya gwiwarta, aikin gyara sashen nata tafara domin yau kasancewar bata zauna agidan ba babu abinda tayi ta fita, tana ta ffaman aikin tana yan wake wakenta al'amin ya shigo wanda dawowarsu kenan shida abbunsa daga unguwa, "My boy ina abbunka?" "Anty yana falonsa" "Oya maza kaje kace masa nace i love you" Dagudu al'amin ya fita yana nanata kalmar a bakinsa gudun kada ya manta yana shiga falon abbun nashi ya same shi zaune shida ummun sa da karfi yace "abbu anty ta aiko ni wai i love you". _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:29 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/1, 7:05 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _40-41_ ~~~Shi kam ma abun dariya ya bashi, dan murmushi yayi gamida shafa dan kyakkyawan gemunsa, ba tareda yace komai ba, kallonsa ummu tayi ta na murmushi, "Ya an aiko maka da sako amma ba kace komai ba?" Kallonta yayi da sexy eyes dinshi ya sakar mata lallausan murmushi, "To ai naji ba shikenan ba" Murmushi tayi ta mayar da idonta kan al'amin Wanda yake tsaye yana kallon tv, shi kuma mal jabir acikin ransa yana mamakin wannan yarinyar goodness shifa daidai da rana daya bai taba jin yana sonta ba kai asalima bazai iya cewa ga yanayin halittarta ba amma dole yaci gaba da zama da ita babu yadda ya iya. Ita kam goodness aikinta take yi hankalinta a kwance har ta gama gyara ko ina na bangaren ta, kitchen ta shiga duk da ba wani yunwa take jiba sosai amma tana da bukatar tasha ruwan lipton, lokacin da ta shiga kitchen shikuma ya fito daga bathroom din dakinsa cumb ya dauka ya je gaban mirror ya fara gyara sumar kansa da gemunsa, daga kan da zaiyi ya hangota acikin kitchen tana kaiwa da komowa, kasa ci gaba da abinda yake yi yayi yaci gaba da kallonta har ta fice daga cikin kitchen din shi dai bazai iya fassara yanayin da yake jinta acikin ransa ba na so ko k'i, turaren right man ya fesa ya saka yar hula ya fito domin tafiya masallaci, part din ummu ya shiga ya kama hannun al'amin suka fita. Karfe 9 da yan mintuna ya dawo gidan shida al'amin, part din ummu ya kaishi sannan ya fito ya shiga part din goodness wacce a lokacin take bararraje akan center carpet tana shan iska tana kallon wani Nigerian film, ahankali ya bude kofar ya shiga cikin falon, motsin da taji ya sata saurin juyowa, tsayawa yayi daga bayanta yayinda ta tashi zaune amma ta kasa juyawa ta kalleshi saboda nauyinsa da taji tana ji yanzu, "Naji sakon ki awurin al'amin" ya fada da sanyayyiyar muryarsa, shiru tayi babu amsa, "Ko ba kiji abinda nafada ba? Nace naji sakonki awurin al'amin" Nanma shirun ta sakeyi sannan bata iya juyawa ta kalleshi ba, "Sai da safe to" ya fada tareda juyawa ya fita, bayansa tabi da kallo tana murmushi ashe dai al'amin ya fada masa sakon, "hmm kana burgeni sosai, i like your style" tafada tana murmushi wanda ji take yi tamkar tabishi ta rungumeshi dan so. Washe gari bata tashi da wuri ba saboda dare ta raba tana kallo sai wurin 2 ta kwanta, shiyasa ta makara, tana tsaka da bacci kamar a mafarki ta jiyo cool voice dinshi yana kiranta zumbur ta tashi tana mutsuttsuke idanuwanta da bayan hannunta tsabar gigita ta manta ma da kayan baccine ajikinta, karo suka yi a daidai kofar shigowa dakin nata shi ya sako kai da nufin shigowa ita kuma tasa kai da niyyar fita falo tana daga labule da niyyar fita taji ta ci karo dashi take ta jita acikin kirjinsa, wayar hannunshi ce ta silmiye ta fadi hakan yasata saurin durkusa dan dauko masa cikin rashin sa'a shima hakan yayi niyya take suka sake yin wani karon, Mikewa yayi yayinda itama ta dago hannunta rike da wayar tashi, idonta a kasa ta mika masa wayar tana cewa _"am sorry sir"_ Jikinta yabi da kallo wanda ke saye cikin wata hadaddiyar rigar barci armless, kalarta yellow marar nauyi tsawonta bazai wuce iya gwiwa ba da dan karamin wandonta iya cinya, kallonsa ya maida kan fuskarta har yanzu idonta kasa yake kallo takasa kallonsa, jin shiru bai amshi wayar ba yasata dagowa caraf suka hada ido dashi, manyan idanuwan nan nashi cikin nata, ahankali ta sauke idonta tabi kafarsa da kallo, takalminsa farine half cover, kamar kullum farin lallausan yadine ajikinsa da jar hula, kamshin turarensa na _explore_ da _right man_ sun taru sun bada wani daddadan kamshi na musamman, fuskar nan tashi tamkar ya shafa farar _powder_, Hannunsa ya mika ya karbi wayar,"morning sir" tafada a hankali "Morning, how was your night?" Ya fada ahankali, shiru tayi bata amsa ba, ganin haka ya sashi juyawa zai fita, "Excuse me sir" cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba, "Am hearing you" yafada yana kallon agogon azurfar dake daure a hannunsa, "Sir zanje saloon ne anjima sannan ina son zuwa church in the evening" "You can go" yafada tareda ciro 1000 ya miko mata ba tareda ya jiyo ba, da sauri ta karasa ta mika nata hannun da niyyar karbar kudin nan ta hado da yan yatsunsa biyu ba tareda ta saniba, wani shock taji cikin sauri ta matsa baya, bai sake cewa uffan ba ya fice ya barta tsaye tana kallonsa, gaskiya ita dai yana mutukar burgeta gashi yauma ya tafi ya bar mata sanyayayyen kamshinsa a cikin hancinta, juyawa tayi ta fada kan gado taci gaba da tunaninsa acikin ranta. Wurin misalin karfe 12 tabar gida ta tafi shagon wata yar church dinsu mai suna blessing dama tun asali awurinta take yin kitso da saloon, gyaran gashi aka yi mata sannan aka jona mata attach nan ya zubo har gadon bayanta, ba atsaya a iya nan ba sai da aka yi mata gyaran farce gamida fenteshi sosai, sai wurin 3 suka gama ta dauki jakarta ta nufi church. Karfe shida daidai ta taso daga church din ta nufo gidanta, lokacin da ta karaso an kusa shiga masallaci, sauka tayi daga kan machine din da ta hawo ta bude yar karamar jakarta ta mikawa dan acabar kudinsa ta juya ta nufi hanyar shiga gida, a kofar masallaci taga mutane wasu zazzaune wasu kuma na yin alwala, haka ta wucesu zata shiga cikin gidan, tana zuwa bakin gate taga wasu mutane su biyu da mal jabir yana tsaye yana yi musu bayanin da bazata iya gane ko na menene ba, kallo mutanen suka bita dashi har shi kansa jabir din sai da ya rakata da ido, tasha riga da wando ga gashi har gadon bayanta ko dan kwali babu akanta hannunta daya rike da Bible dayan kuma rikeda yar jakarta, tana wucewa daya daga cikin wadanda ke tsaye kusa dashi yace "Malam wannan fa? Me zataje tayi agidanka kodai tayi batan kai ne?" Shiru yayi tsabar takaice bai iya bada amsaba saboda yasan ko bai fada ba idan sun bar wurinshi dole ne suyi zancen amma yau yayi damarar takawa goodness burki akan wannan sakarcin nata, shi bazai yarda da wannan banzar dabi'ar ba. Bayan ta shiga gidan part dinta ta bude ta shiga, ko zama ba tayi ba ta shiga wanka ta fito, three quarter da yar body hug tasa ta shiga kitchen ta dafa indomie ta debota ta kawo falo ta kunna tv taci ta koshi, kwanon ta ture ta mayar da hankalinta kan film din da take kallo a tashar _African magic_ mai suna _the present time_ hankalinta duk ya tattara akan wannan film din domin ganin tirka tirkar dake ciki, bude kofar da akayi ya sata bin kofar da kallo dan ganin waye zai shigo, Shine ya shigo amma daga gani yana cikin fushi "goodness as from to day kar ki kuskura na sake ganinki da riga da wando a waje, are you crazy? Who told you wadannan kayan da kike sakawa na mutumcine? Kina son ki bata min sunane a garinnan ko me? Daga yau sai yau kar ki bari naganki da irin kayan dazu awaje, sannan its compulsory ki rinka daura head tied, wannan ai zancen banza ne kullum ki ringa fita gashinki awaje jikinki awaje, i can't tolerate this" Tunda ya fara fadan bakinsa kawai take kallo wanda yayi tsananin bata sha'awa, "am sorry sir" tafada cikin kalar tausayi, "Hold your sorry, sorry for yourself" Juyawa yayi ya fita bai sake cewa komai ba, ajiyar zuciya ta saki tare da rike kanta "hmmm to plan for you how to love me is my headache now, problems neva finish in this house oh oh" tafada tana kallon agogon falon wanda ya nuna karfe 10 saura minti 5,tv din ta kashe ta tashi ta shiga dakinta ta kwanta yau duk yanda taso ta ga karshen film dinnan amma yanzu taji ya fita daga ranta gaba daya, juyi tayi tareda jan dan karamin tsaki,juyi tayi ta mika hannunta kan bedside drawer dinta ta dauki Bible dinta tafara dubawa, ganin bata gane komai yasata ajiyeshi ta tashi tafita taje ta rurrufe ko ina na part dinta saboda bata son gobe jabir ya shigo dan tasan haduwar ba zai yi mata dadi ba, dawowa tayi ta kwanta amma kuma ta kasa baccin akalla sai da takai karfe 1 kafin bacci yayi nasarar daukarta. Bata iya tashi ba sai karfe 11 nasafe lokacin kam tasan abu al'amin ya dade a office, sabgoginta ta shiga yi amma yau bata da niyyar zuwa church, tana falonta tana gugar kayan sawarta al'amin ya shigo hannunsa rikeda chocolate, "My dear son i miss you so much, where did you hide?" "Anty ummu na tace nazo na gaisheki" yafada yana kokarin bare chocolate din hannunsa, "Oh al'amin clever boy, abbuna, ummuna, every one na your own ba?" TV din da take kallo ya kalla, "anty zan kalla carton" "Oya carry that remote and change the channel, al'amin ina abbunka?" "Ya tafi office baije dani ba" "Ayya sorry my dear, na kawo maka wani chocolate din ta kara akan naka?" Girgiza kai yayi "abbuna ya siyo min jiya da yawa da yawa yace in tasha nawane ni daya" Murmushi tayi tana son hirar al'amin domin yaron akwai kwakwalwar daukar abu gashi komansa irin na abbun shi ne shiyasa yaron ya shiga ranta, biye masa tayi yayita yi mata labari har tsawon wani lokaci kafin ya fice ya koma wurin ummunshi. Zama tayi shiru bayan fitar al'amin taci gaba da gugar ta har yamma saida ta goge kayanta tsaf kafin ta tashi ta dora girki taci tayi wanka ta fito bayan ta shirya cikin wasu riga da skirt blue masu adon stones ajiki. Falo ta dawo ta rufe kofar falon sannan ta nutse cikin kujera ta fara kallon channel din _music plus_ tashar zallar wakoki kawai ake nunawa, tana nan kwance har ta jiyo dirin motar jabir alamun ya dawo daga office, bata tashi ba taci gaba da kallonta har duhu yayi, tunani ta fara yi acikin ranta lallai ya kamata taje ta sake bashi hakuri tunda itace tayi masa laifi kuma gaskiya ya fada mata wadannan kayan da take sawa na iya janyo zubewar mutumcinsa a idon jama'a, da wannan shawarar ta zuciyarta ta aminta cewar anjima taje ta bashi hakuri. Misalin karfe 9:30 ta nufi part dinsa wannan shine karo na farko da zataje sashensa domin bata taba shiga kowanne sashe agidan ba baya ga nata, kofar falon ta murda ta shiga babban falo ne wanda yasha kayan alatu amma gaba dashi ma wani falon ne dan madaidaici, ahankali ta tasamma falon sai dai tana saka kai ta hangoshi rungume da matarsa ummu al'amin suna soyewa nanfa gabanta ya fara dukan uku uku zuciyarta ta shiga harbawa da karfi da karfi, dan karamin bakinsa dake sakata cikin wani yanayi ta hango yana cusawa cikin na matarshi sai juyi yake da ita tamkar wata yar baby kasancewar a tsaye suke, wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri akan kumatunta wanda ita kanta bata san ko na menene ba, kamar wanda akacewa bude idonka yana budewa ya hangota tsaye tana kallonsu kafin yayi yunkurin sakin ummu har ta juya cikin sauri ta fice daga falon, tana tafe tana hawaye tamkar wacce aka aikowa da mutuwa, zahiri yau ta yarda jabir bai sonta ko kadan domin tunda tazo gidansa bai taba nuna yasan da ita ba amma yanzu jibi irin soyayyar da yake nunawa matarsa wacce yake so, kukane ya kwace mata ba tareda ta shirya ba lallai wannan shi ake kira da SON MASO WANI. A bangaren malam jabir kuwa tun da yaga fitarta sai baiji dadiba domin yasan kowacece dole sai taji bacin rai musamman ma ita da bai taba gwada mata so ba, sai da ya samu nutsuwa sannan ya fara tunaninta, yasan dan so tana sonshi to amma shi rashin musuluncin da bata yine kawai ya hanashi nuna mata so. Kwana tayi tana kuka ga damuwa da tayi mata yawa dan kowanne lokaci idan ta rufe idanuwanta shi kawai take gani yana romancing din Ummu, kuka tayi mai isarta sannan ta iya hakura amma akoda yaushe bakinsa da take muradi take ganowa cikin na ummu, bacci barawo ne yayi nasarar saceta da misalin karfe 5 nasafe amma 9 tana yi ta farka a furgece, wanka ta shiga tayi ta fito duk ranta babu dadi, zuciyarta ta cika da kunci, tana daure da towel tana shafa mai taji knocking tashi tayi taje ta bude, ganinsa tayi tsaye yana rikeda hannun al'amin, bata iya cemusu komai ba ta juya zata wuce dakinta, "Good morning anty" ta jiyo muryar al'amin, juyowa tayi ta kakaro murmushin dole tace, "Morning my dear son" Kallo mal jabir yabita dashi daga gani tana cikin damuwa amma yayi damarar share mata hawayenta a daren yau duk da ba wai yana sonta bane kuma yasan bazai iya sakin jiki ba domin kyankyami gareshi, "Anty nima kinga za muje unguwa nida abbuna" "Adawo lafiya my son" tafada ta shige cikin dakinta, kallon kofar dakin jabir yayi to wannan me kenan? Ko itama fushin take yi dashi? "Goodness" ya kira sunanta a hankali, Fitowa tayi batare data amsa ba, "Babu abinda kike bukata?" "Babu" tafada atakaice tareda juyawa ta koma cikin dakinta, Hannun al'amin yaja suka fita daga cikin falon suka nufi inda mal idi driver ke jiransu. Goodness dai wuni tayi cikin bacin rai abunku da wanda baya salla, tana ganin 3 tayi ta dauki bible dinta ta tafi church,koda taje church dinma tana tare da damuwa gashi yau ma ba tajeba morning service taje, zama tayi jugum tayi tagumi bata farga ba hawaye suka fara bin kumatunta, "Hello goodness what's happening?" Ta jiyo muryar promise tsohon saurayinta, cikin sauri tafara goge hawayen dake fuskarta gudun kada yagani amma kuma ya rigada ya gani, tsugunnawa yayi agabanta yana kallonta, "Goodness what's wrong with you?" Yafada yana kallon fuskarta,bible dinta ta dafe ta kalleshi amma ta kasa magana to ma me zata ce masa shin zata fada masa cewar mijin data aura baya kulawa da ita ko kuma za tace masa mijinta baya sonta? Ganin bata da amsar bashi yasata yin shiru domin shi idan yaji wannan maganar ma dariya zai yi mata tunda ta kishi a baya gashi yanzu kuma tun ba aje ko inaba tafara korafi, hannunta taji promise ya kama ba tayi kokarin hanashi ba domin tana cikin damuwa dayawa, "Goodness i know kina cikin damuwa because i saw your face symbolised this, but you know am your true lover i can't hold my hands watching you feeling unhappy, so yanzu ki taso muje wurin birthday party din Moses kinga after idan aka tashi sai ki tafi gida by that time i know you can get some relief" Kallonsa tayi ta mike suka tafi duk ranta a jagule, wani dan madaidaicin club sukaje inda ananne za a gudanar da party din, Kujeru suka samu suka zazzauna suka fara kallon yanda bikin partyn zai gudana, nan kuwa aka fara gudanarwa ita dai goodness bin kowa take da kallo amma ta dan ji sauki acikin zuciyarta, suna nan zaune anata chasu har gari yayi duhu, tashi promise yayi yace "I dey come goodness, make i go and bring us some cool minerals" "Ok but don't be long pls kaga ina son nakoma gida in the right time" "Don't worry dear yanzu zan dawo" yafada tareda juyawa yana murmushin mugunta domin shi kadai yasan muguntar da ya shiryawa goodness wadda ita bata san da ita ba, wurin da ake bayar da drinks yaje aka zuba masa juice mai sanyi acikin cups guda biyu, ahankali ya zaro wata yar karamar roba daga cikin aljihunsa ya bude ya zuba abinda ke ciki acikin daya daga cikin juice din ya mayar robar ya rufe ya sata cikin aljihunsa. Goodness na zaune tana jiransa sai dan waige waige take, nan ta hangoshi ya taho yana zuwa ya mika mata wanda ya tsiyaya wannan abun aciki, hannu tasa ta karba ta dan fara kurba ahankali ji tayi lemon yayi mata dadi domin har wani tsami tsami yake yi kamar anhada da lemon tsami amma kuma ta kasa tantance yanayin taste dinshi, "Promise what's kind of sweet juice is this?" Ta tambayeshi tana lumshe ido, "Kedai ki sha sai akaro miki" ya fada yana murmushin mugunta, shanye juice din tayi take tafara jin hajijiya tana daukarta gashi ta fara ganin mutanen wurin bibbiyu bibbiyu, "Hey promise make you carry me and bring me back to my house" tafada cikin maye, "Now now kuwa" yafada yana dariya, hannunta ya rike ya jata zuwa waje, da motar Moses yayi amfani ya sakata aciki ya ja ya fita daga club din yayinda ita kuma goodness ke cikin yanayi na maye domin sai shirme take yi irin na wanda ya bugu. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:29 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/1, 11:02 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _42-44_ ~~~Gidanta ya nufa da ita domin bashida niyyar yin raping dinta domin a tunaninsa ba budurwa bace yanzu tunda tayi aure, a kofar gate din gidan ya sauketa ta debi takalmanta ta rike a hannu ta dauki bible dinta da jakarta, ga dan kwali shima ta rike a hannu tana layi, "Hey promise thank you, till we meet tomorrow in the church" Tafiya tafara yi tana layi tana harhada hanya, Wani mugun bugu take yiwa gate din gidan kamar zata karyashi wanda har sai da mal jabir ya fito daga sashensa ya tsaya a compound din gidan dan ganin waye me yin wannan bugun kofar, Dagudu mai gadi ya zo ya bude mata domin dama bayan gida ya dan zagaya, ganinta cikin maye ya sashi bata hanya, "Don't worry dear, am not angry... Don't worry baba" ta fada cikin magana irinta bugaggu, Takalminta da jakarta da Bible dinta da dan kwalinta a hannunta ta makale wasu a hammatarta tana tafe tana hada hanya, Cikin razani mal jabir ya bita yasha gabanta kallo daya yayi mata ya gane acikin maye take "innalillahi wa inna ilaihir raji'un" shine kawai abinda ya iya furtawa tareda cakumar wuyan rigarta yana karewa jikinta kallo, Sanye take cikin riga t shirt mai dogon hannu da skirt ta jeans blue, "Have you drunk alcohol? Am asking you, tell me the truth" yafada yana jijjigata, Wata dariya ta saka ta kalleshi ta kai hannunta kan fuskarshi tana shafawa, fusgarta yayi ya figeta yayi sashenta da ita shidai mai gadi yana tsaye yana kallonsu, Kankameshi tayi ta gefensa tana dariya "am lucky, you are good looking, i love you soo much" haka taketa furtawa har ya shigar da ita falonta bayan ya bude kofar, Tureta daga jikinsa ya shiga yi yana kallonta, "Goodness me kika sha? Ki fada min abinda kika sha, alcohol kika sha?" Yafada da karfi wanda shi kansa bai san lokacin da ya koyi magana da karfi irin haka ba, Gemunsa taja "i love you my dear, you are such a nice....!" Tsawa ya daka mata "shut up your mouth, you better tell me what...!" "Shhhhh" tafada tareda dora yatsanta akan bakinta "keep silent" Hannu tasa ta shafo kumatunsa zuwa lips dinsa "i like you i swear, am in love" "Goodness bakida hankaline ne? Ki fada min abinda kikaje kika sha" yafada cikin fada "Alcohol nasha..!" Bata karasa rufe bakinta ba ya dauketa da mari tareda hankada ta kan kujera ya juya ya fice domin no need ya tsaya yaci gaba da westing din time dinshi a banza akan shirmenta. Yanda ya fita ya barta haka ta zauna har wani bacci mai nauyi ya dauketa. Yana zuwa dakinsa ya dafe kansa tareda zama a gefen gadonsa, wannan wacce irin rayuwa ce ya samu kansa aciki? To ko dama yarinyar nan bata gari bace? Ya tambayi kansa, tashi yayi ya fara zagaye dakin shi bai san da wacce kalma zai fassara wannan abun ba, yarinyar nan zuwanta cikin gidansa duk ta zubar masa da kimarsa wacce jama'ar gari ke kallonsa da ita, Yanzu in banda kaddara taya za ace ansha giya agidansa? Bayan duk halaccin da yayi mata ya kyaleta take zuwa church daga gidansa hakan bai wadatar ba har sai ta hada da shan giya? Ya zama dole ya rabu da yarinyar nan tun kafin ta shigar dashi cikin wani hali,tabbas a gobe zai sallameta ta tafi gidansu tun kafin mummunar halayyarta ta shafi iyalan gidansa, _bathroom_ ya shiga yayi alwala ya fito yazo kan dadduma ya fara sallolin nafila kamar yadda ya saba gudanarwa ako wanne dare. Tunda goodness ta kwanta bacci bata tashi ba sai da gari ya waye tamgararu rana ta fito, zaune ta tashi ta kalli jikinta take abubuwan da suka faru jiya suka fara dawowa cikin kwakwalwarta tun zuwansu club da promise har dawowarta gida hatta marin da jabir yayi mata duk sai da ta tuno, "I can't pardone you promise, you kid me, you have cheating me, you deceive me promise, i can't forgave you" wasu zafafan hawaye ne suka shiga sintiri akan kumatunta, sai da tasha kukanta ta koshi sannan ta tashi ta shiga cikin dakinta, wanka tayi bayan ta fito ta shirya cikin doguwar riga pink colour mai gajeren hannu rigar roba ce dan haka ta kamata sosai, kitchen ta shiga ta dora ruwan zafi. Shi kuwa mal jabir da bacin ran abinnan ya kwana dan haka koda gari ya waye bayan ya shirya yayi breakfast daukar al'amin yayi suka tafi gidan mahaifinsa wato takwaran al'amin din, Lokacin da suka je yana zaure yana zaune yana lazimi, da gudu al'amin yaje ya dale shi yana dariya, jiyowa shima yayi yana dariyar yana cewa "ja'iri dama nasan babu wanda zaiyi min wannan aiki sai kai, yanzu kuke tafe?" Karasowa jabir yayi ya zauna agaban mahaifin nasa tareda gaisheshi cikin girmamawa, bayan sun gaisa ne yake sanar dashi cewar zai sallami goodness ta tafi gida saboda ga irin abubuwan da take yi masa, "Haba jabiru ina hakurin naka ya tafi? Ina tunaninka da basirarka suka tafi? Idan ka sallameta me akayi kenan? Bukatar tamu bata biya ba kenan tunda ka kasa zame mata *wani haske* acikin rayuwarta, kayi hakuri jabir ban aura maka wannan yarinya ba har sai da nayi bincike akanta, sannan duk wadannan abubuwan laifinka ne yasa suka faru,saboda ka kasa janta ajikinka, ka kasa sake mata fuska ka kasa bata damar da zata zauna dakai ta fuskanceka ka fuskanceta har ta fahimci menene musulunci har taji ya kwanta mata arai, duk ba kayi wannan ba, meyasa?" "Malam insha Allahu zanyi kokarin kwatanta hakan" "Kayi kokari ka kwatanta jabiru saboda ko dan lahirarka domin yarinyar nan tanada wani hakki na musamman a wuyanka muddin ka danne daya daga ciki saboda kaga ita bata salla to wallahi babu ruwan Allah dole ne ya tambayeka yanda ka gudanar da rayuwarka tareda iyalinka, muddin ka fifita daya akan daya saboda ita ba musulma bace to wallahi kasani ranar gobe kiyama zaka tashi gefen jikinka a shanye domin haka annabi yacewa sahabbai duk wanda suka ga rabin jikinsa ya shanye ranar alkiyama to karsu tambayi kowa shine Wanda baya adalci a tsakanin iyalansa, sannan ya kamata ka kyautatawa yarinyar nan domin annabi yace mafi alkairunku shine wanda yafi kyautatawa iyalansa amma ni nafiku alkairi saboda nafi kowa kyautatawa iyalai na,ka zauna da matarka da aminci taji dadin zama dakai ka sake mata fuska kayi wasa da ita kayi dariya da ita kayi mata duk wata hidama wacce zata ja ra'ayinta zuwa gareka" Ajiyar zuciya jabir ya saki tabbas yasan duk wadannan abubuwan da Malam ya fada gaskiyane kuma tun farko hakan ya kamata ace yayi amma bai yi ba, "Nagode Malam Allah ya saka da alkairi kuma in sha Allahu zanyi aiki da abinda ka fada min" "Allah yayi maka albarka, agaida iyalin" Tashi jabir yayi yana kallon al'amin "to za mu tafi ko anan zan barka wurin malam?" "A'a daukeshi ku tafi dan ba zama zaiyi ba kana tafiya zai tada rikici yace shi abbunshi shi umminshi" Mikewa al'amin yayi yana dariya "ni abbuna zanbi" Sallama suka yiwa malam suka tafi, Gida suka koma suna shiga part din goodness yayiwa tsinke al'amin yana biye dashi, acikin dakinta ya iskota ta takure a karshen gado, Har bakin gadonta yaje ya zauna abunda yayi mutukar bata mamaki, "Goodness nazo ne domin muyi wata magana dake, abinda kikayi jiya banji dadinsa ba domin kin wulakantani kin wulakanta kanki a idon duniya, alcohol haramunne a musulunci duk da cewar nasan ke a addininku halal ce, tunda farko ban san kina shan alcohol ba da zan yi miki gargadi akanta domin ba ashanta agidana, sannan zancen zuwa church ni bazan hanaki zuwa ba but zaki rinka zuwane once in a week, amma daily service babu shi yanzu i have called up it at all,did you get me?" "Yes sir but am so sorry, honest to God i have Neva take alcohol before, i swear jiyama deceiving dina suka yi suka bani but it will neva happen again" ta fada tana goge fuskarta, "Don't worry i pardoned you,but you have to maintain it next time" Tashi yayi ya juya ya fita yabar al'amin azaune awurinta, jin baya fushi da ita yasata sakin jikinta ta kamo hannun al'amin suka koma falo, "Clever boy" tafada tana murza hannunsa, "Anty farcenki yayi tsawo dayawa ki yanke ranar juma'a" "Meyasa sai ranar friday? Yanzu ma sai in yanke my boy" "A'a anty abbuna duk ranar juma'a yake yanke farcensa dana tambayeshi sai yace min yanke farce ranar juma'a tana daya daga cikin sunnonin ranar juma'a" "Nagode my boy nima ranar juma'ar i will cut my pinger nails" "Yawwa anty kinga nima zan samu lada saboda annabi yace duk wanda yayi nuni da aikin alkairi to zai samu kwatankwacin ladan wanda yayi aikin" Baki ta rike tana kallonsa yanda yake magana kamar abbunshi har lumshe idanuwansa irin nasa ne, "Al'amin waye annabi? Naji komai sai kace annabi yace kaza yace kaza" "Anty annabi shine annabi Muhammad (s.a.w),dan Abdullah, yazo da addinin musulunci, Allah ya aikoshi ga dukkan mutane baki daya, kuma shine na karshen annabawa, shugaban manzanni, mutum bazai taba zama cikakken mumuni ba har sai ya soshi kuma ya yarda dashi" "Okey i understand now, nagane al'amin thanks for the explanation, let me go and cook indomie for us" Tashi tayi ta shiga kitchen kafin ta fito shi kam al'amin ya koma wurin ummunshi. Indomie ta dora tana aikin tana rera wakarta "am waiting my love love, no body can love it the way i do, am waiting my love love" Jiyo sautin wayarta da tayi a falo yana tashi yasata kwallawa al'amin kira, "My son pls help me with my phone" tafada da karfi, daidai lokacin mal jabir ya shigo cikin falon, sake kwallawa tayi da karfi, "Al'amin can't you hearing me? I said make you bring me my phone" Daukar wayar yayi ya bita cikin kitchen din, daga inda take tsaye tana zuba indomie din acikin tukunya ta miko hannu dan ta karba duk a tunaninta al'amin ne amma kuma ta jiyo sanyayyen kamshinsa sai dai duk da haka bata kawo shi bane domin a iya saninta yanzu yana office babu abinda zai dawo yi agida, tsal ruwan indomie din ya fantsalo mata a fuska hakan ya sata saurin ja da baya da sauri tana fadin, "Ohh God", jinta tayi ta fada jikin mutum ta baya nan ta sake tsorata ta jiyo da sauri take ta kara fadawa kirjinsa da sauri ya tareta, "Oh sorry i didn't hear your step, banji lokacin da ka shigo ba" "Oya take your phone, dazu nayi mantuwa acikin dakinki, bari na dauka" mika mata wayar yayi ya juya ya fita tana biye dashi har cikin dakinta, A inda ya tsaya dazu anan ya fara dube dube, "Sir me ka yar?" Ta tambayeshi tana kallonsa ta bayanshi kasancewar ya bata baya, "Bari gashi ma nagani" nuno mata wani dan karamin key yayi wanda daga gani na safe dinsa ne wato drawer din office dinsa Wanda yake ajiye documents masu muhimmanci, Bashi hanya tayi ya juya ya fita, "adawo lafiya" ta fada tana kallonshi, "Allah yasa" ya fada ahankali tare da ficewa, komawa kitchen tayi taci gaba da hidimominta. Karfe _5_ daidai ya taso daga office ya dawo gida, sashensa ya shiga anan ya iske ummu da al'amin suna zaune acikin babban falonsa, Mikewa ummu tayi ta amshi jakar dake rike a hannunsa tana yi masa sannu da zuwa yayinda shi kuma al'amin ya tashi ya rungumeshi yana cewa, "Sannu da zuwa abbuna, abbu na me ka kawo min?" Kansa ya shafa, "al'amin ya kamata muje muyi aski nida kai anjima ko?" Kansa ya daga "na'am abbu" "Yawwa yarona, bari nayi wanka naci abinci sai muje" Sakin hannun al'amin yayi ya shiga bedroom dinsa, a kofar daki suka yi clashe da ummu, hannunta ya riko "me kika tanadar min?" "Komai my dear" tafada tana zare masa hular dake kanshi, "To nagode bari nayi wanka" Rakashi cikin dakin tayi sannan ta fito ta kyaleshi. Karfe _6_ ya kama hannun al'amin suka fita domin zuwa aski, part din goodness yayi niyyar zuwa kafin su fita, adai dai kofar falonta yaji ana kiransa a waya hakan ya sashi tsayawa domin amsa wayar yayinda shi kuma al'amin ya wuce cikin falon, Al'amin na shiga ya sameta kwance tana kallo, sadadawa yayi yaje ya rufe mata ido duk a zatonshi wai bata ganshi ba, Murmushi tayi ta kyaleshi, tana ji ya dauki bakin dankwalinta dake ajiye agefe ya daure mata fuska, "Al'amin if i catch you ko? Hmm i know you are the one ai, bari natashi" Dagudu ya zura bayan labule yana cewa "anty don't interrupt the game pls, ki nemoni gashi nan na gudu" "I will find you now now al'amin" tafada idonta a daure, da gudu al'amin ya tafi bayan kujera ya boye, yayinda ita kuma ta fara lalubensa sai karo take ci da center table, kujera da kuma bango, Jin an bude kofa ya sata saurin nufar wurin saboda ta zata al'amin dinne zai fice, jabir ne ya shigo ya bude baki kenan da niyyar kiran al'amin sai suka hada ido da al'amin din a bayan kujera inda ya boye, cikin sauri al'amin yayi masa nuni da hannu wai yayi shiru kar anty ta kamashi, Jabir maganar ya hadiye ya tsaya yana kallon ikon Allah, da saurinta ta taho tana cewa "oh yes i will catch you now now al'amin, i have hear your match beside my door" ahankali ta nufi kofar gadan gadan tana mimmika hannu dan ta cafkoshi, Tana zuwa ta mika hannayenta ta dadumo jabir wanda ke tsaye yana kallonsu, wata runguma yaji tayi masa, cikin sauri ta yi baya tareda sakinsa nan ta fara kokarin kwance daurin dake fuskarta, Ihu al'amin yasa "yes oh anty you didn't catch me" Dagudu ya tafi wurin abbunshi yana dariya, kunyace duk ta kamata saboda rungumar da ta yiwa jabir bata wasa bace ta gaske ce sosai, "Al'amin i will catch you next time" "Abbu mutafi tunda na yiwa anty wayo ta kasa kamani" Murmushi jabir yayi ya kama hannunsa suka juya suka fita, zama tayi sharafff akan kujera "oh oh this clever boy make me to fell shy". Tunda suka fita jabir yaji goodness ta dan burgeshi saboda yadda ta saki jiki da yaronshi kwallo daya tal a duniya,gashi tana biye masa suyita wasa kamar wani sa'anta hakanne ya sashi niyyar bata wani dan karamin muhalli acikin zuciyarsa dalilin soyayyar da take yiwa gudan jininsa al'amin. _*Ummi Aisha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/3, 3:29 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _45-47_ ~~~Koda suka je shagon askin ma tunani ne fal acikin zuciyarsa gameda goodness duk da yasan ba wani sonta yake ba amma yasan baya jin tsanarta yanzu acikin zuciyarsa saboda soyayyar da take yiwa al'amin. Ana kiraye kirayen sallar magrib suka dawo gida, a masallaci suka tsaya ba tareda sun shiga cikin gidan ba har sai da aka idar da sallar isha sannan yaja al'amin suka shiga cikin gidan domin yau babu karatu, Lokacin da suka shiga misalin karfi _8:30_ ,kansa tsaye part din ummu ya shiga shida al'amin kamar kullum tana zaune akan abun salla da alama salla ta idar ga tashar sunnah tv tana kallo, Zama yayi akan kujera yayinda al'amin yaje ya dale bayanta wai ta goyashi, "Ummu al'amin ina tunanin fa nan da three weeks zaki bar kasar nan zuwa madina saboda admission dinnan naki ya fito fa gashi komai sunyi shi acikin kurarren lokaci" Kallonsa tayi lokacin da take mikewa da al'amin a bayanta tana ninke abin sallarta, "Abu al'amin dagaske? Shine baka sanar dani ba? To ya zamu shirya tafiyar?" "Eh zan fara kaiki idan munje nayi miki registration nagama zan taho nabarki saboda lectures zaku fara nanda sati ukun wannan session din basu fitar da admission din da wuri ba, idan kika fara karatun sai ki bincikawa al'amin makaranta anan kusa dake sai na kawo miki shi, amma yanzu tafiyar ba zata yiyu dashi ba domin gaskiya visa tana wahala, ni dinma ba lallai ne nasamu ba kinga idan ban samu ba sai dai ki tafi ke daya" Murmushi tayi tana jijjiga al'amin dake bayanta wanda yake shirin yin bacci, "Ai kuwa nima bazan je ba indai babu kai" "Da wasa kike ummu, ai tafiya ta kamaki ko ke kadai ce tunda karatu zaki je" "Haka dai kace" daki ta shiga domin kwantar da al'amin shi kuma ya tashi ya fita ya nufi sashensa. Bai sake fitowa ba sai da gari ya waye, bayan ya shirya yayi breakfast ya fito domin tafiya office, falon goodness ya shiga, hangota yayi tana yin mopping din tiles din dining area dinta gashi kuma kamar kullum yau ma ta music dinta tana sauraren wakar p square cikin wakarsa ta _"teaching me how to love you"_ Daga ita sai wani gajeren wando baki iya cinya da _vest_ baka tana faman bin wakar da take sauraro, _Remote_ ya dauka ya fara rage volume din tv din gamida juyowa ya kalleta, ita dinma juyowar tayi nan suka hada ido, "Ke wannan k'arar bata damunki ne wai?" "Morning sir" tafada tana sunkuyar da kanta k'asa, "Morning how you?" Ya fada yana gyara zaman hularshi akanshi, _"wow! This dress suit you my cool"_ tafada ahankali domin yau ba fararen kaya ya saka ba, wata hadaddiyar shadda ya sa kalarta ruwan toka dinkin samfarin boda sannan yasa hula ash colour mai digon baki ajiki, takalmin kafarshi _half cover_ shima kalar ruwan toka ga wani agogon fata da ya daura shima kalar kayansa ga wani irin kamshi mai dadi da yake fita daga jikinsa, gemunsa da sajensa ya gyarasu ya tajesu sai sheki suke, nikaina ummi nace lallai malamai yan gayune ga iya kwalliya, Kallonta yayi yana balle clips din hannun rigarsa "me kike cewa?" "No sir bance komai ba" "Ok naje office" juyawa yayi ya fita nan tabishi tana lek'enshi ta window har sai da taga shigarshi mota taga fitarsa daga gidan sannan ta koma taci gaba da aikinta tana yi tana murmushi "he's good looking" tafada tana murmushi. Tun ranar da promise yakai goodness club tun lokacin bata kara zuwa church ba hakan ba k'aramin tayarwa da mamanta hankali yayi ba nan ta shiga nemanta a waya dakyar ta samu layin goodness din, lokacin ita goodness ma kwance take a falonta tana karanta Bible dinta, "Hello ma, good afternoon" "Goodness hold your greetings i didn't want it, yaushe rabonki da church? Goodness yaushe kika zama strong headed? Goodness ki dawo cikin hankalinki fa tun kafin mijinki yayi deceiving naki" "Am sorry ma, ba wai nadaina zuwa church bane, kinga yanzu tafiyar daga gidana zuwa church is too long, how many kobo will i spent for the transport from my house to that church? Shiyasa nayi deciding zan rinka zuwa duk ranar Sunday kuma tunda there is one church near my house zan rinka zuwa can daily service" "Ok yanzu nagane, so kiyi kokari kina zuwa ranar Sunday din" "Don't worry ma, i shall come by God willing" "Thank you my daughter, bye bye take care" Tana katse wayar ta saki nannauyar ajiyar zuciya dan ba karamin sa'a tayi ba da ma ta amince da abinda ta fada. Tun daga lokacin goodness take zuwa church sau 1 a sati saboda dokar da jabir ya kafa mata, yayinda ita kuma ummu al'amin keta shirye shiryen tafiya madina garin manzo domin gudanar da karatu, a bangaren jabir shima hakan take domin har ya karbo musu visa dinsu,yanzu baifi kwana 6 ya rage su tafi ba. Goodness zaune a falonta bayan ta kammala taje gashin kanta, agogo ta kalla karfe 9:30 nadare agogon bangon nata ya nuna yanzu tasan jabir ya dawo gida daga wurin karatu dan haka ta mike ta dauki dan siririn mayafinta domin so take taje ayi mata kitso a shagon _blessing_ shiyasa take son yanzu taje ta dauki _permission_ awurin oga, Riga da wando ne ajikinta, rigar milk colour marar nauyi shikuma wandon samfurin _pencil_ kalarshi ja, Ahankali ta bude falon ta shiga, a babban falo ta dan tsaya tana lekewa ahankali, al'amin ta gani zaune kusa da jabir, hannun al'amin rike da wani littafi mai yatsu guda uku ajiki, "Abbu banyi fassara ba, ka tambayeni fassarar" ta jiyo muryar al'amin yana fada, "To al'amin yi min inji, waye ubangijikinka?" "Allah ne ubangijina wanda ya halicceni,ya reneni, da ni'imominsa" "Da wanne abune kake sanin ubangijinka?" "Ina sanin ubangijina da alamomi masu yawa, daga cikinsu akwai dare da yini, da rana da wata" "Waye ya halicci sammai da kassai,da rana da wata?" "Abbu Allah shine ya halicci kasa wacce muke tafiya akanta, ya halacci sama wadda rana take cikinta, ya halicci wata da taurari wanda suke acikin sama, ya halicci mutane,da duwarwatsu, da bishiyoyi,da dukkan komai,Allah shine yake saukar da ruwan sama, yake fitar da tsirrai,yake azurta bayinsa, yake basu lafiya, Allah shi kadai ya cancanta a bauta masa ba tareda kowa ba" "Jayyid, jamilun jiddan al'amin, to yanzu ina zan dora maka?" Sak'are goodness tayi tana kallonsu amma kuma wadannan abubuwan fa da suka fada abin dubawa ne, tabbas wannan addinin nasu akwai *wani haske* acikinsa tunda gashi har al'amin ma yaro karami yana iya fadarsa, Kanta ta kutsa cikin falon tana kallonsu, "Weldon sir" tafada tareda dan rissinawa, "Yawwa" yafada yana kallonta, domin bata saba shigowa sashensa ba, "Sir ina son zanje kitso ne gobe" "Which place?" Ya tambayeta yana kallonta, "Sir near unity bank, unguwar sarki" "Ok Allah ya kaimu goben, zan baki kudin kitson before i left" "Ok thank you sir" "Anty zan rakaki" al'amin ya fada yana murna, "To al'amin zanje dakai" Juyawa tayi ta koma sashenta taje ta cigaba da kallon tv. Washe gari kafin ya fita kamar yadda yace ya shigo ya bata kudin kitson ya tafi, dan haka tana gama abubuwan da zatayi tayi wanka ta tafi kitson wanda tun safe sai daf da magrib aka gamashi, kitson attach aka yi mata yifi yifi mai yawan gaske, lokacin da ta dawo gida su al'amin na shirin fita masallaci shida abbunshi. Bayan sun fito daga sallar ne misalin karfe 8:30 suka shiga sashenta anan suka sameta tana shan ruwan lipton daga ita sai towel a daure ajikinta, kitson nan nata yayi asalin yin kyau kamar bada hannu aka yi ba, "Sai yanzu kika dawo?" Jabir ya tambayeta yana kallonta, "Eh wlh sir kitsonne dayawa shiyasa" ta bashi amsa tana kallon al'amin wanda ya kura mata ido yana kallonta. "Anty babu kyau k'arin gashi, kidaina domin annabi ya la'anci matar da take kara gashi da wadda ake karawa, da mai yin wushirya,ko abbuna? Ai kaine ka koya min hadisin ko?" Ya fada yana girgiza hannun jabir, "Zan daina al'amin kaji? Zan daina" tafada tana murmushi, juyawa jabir yayi yaja hannun al'amin suka fita daga daki zuciyarsa cikeda mamakin yaronshi al'amin hakika yaron nan wayonsa yayi yawa gashi da iya rike abu sam bashida mantuwa girgiza kai yayi koda yake ai annabi yace "karatun yaro kamar rubutune akan dutse, karatun babba kuma tamkar rubutu ne akan ruwa" Tabbas wannan magana haka take domin al'amin duk abinda aka koya masa to ya daukeshi kenan acikin kwakwalwarsa shiyasa har yanzu bai daina bashi zamzam da Zuma yana sha ba. *** Acikin "yan kwanakin ummu har ta kammala shirinta na tafiya haka shima jabir duk ta harhada masa nasa kayan wanda zai bukata acan duk da shi ba wani jimawa zaiyi ba sati uku kacal zaiyi ya dawo, Ana i gobe zasu tafi ya dauki al'amin ya kaishi gidan malam mahaifinshi daga can yayi sallama dasu ya dawo gida, aranar da daddare ummu ta shiga wurin goodness take sanar mata da batun tafiyarta gobe wanda idan ta tafi zata dade bata zo ba may be ma sai ta shekara 2 ko 3 kafin ta zo gida, Duk da ba wani zama suka yi mai yawa ba sai da goodness taji babu dadi, tareda yi mata fatan alkairi anan ummu ta tashi ta koma sashenta wurin jabir. Washe gari bayan sun kammala shirinsu an fito musu da kayayyakinsu an saka acikin mota mal jabir da ummu suka shiga wurin goodness tana kitchen tana shirya breakfast dinta taji motsinsu, da sauri ta fito ta gaishesu, "Za muyi tafiya da ummu al'amin amma ni sati uku zanyi nadawo, al'amin ma yana nan sai daga baya zan kaishi idan ta sama masa school din da zai yi acan, ga wannan ki ajiye saboda ko zaki bukaci wani abu, sannan daga karshe banda fita rampantly, ranar Sunday kawai na yarda ki fita kije Church amma baya ga wannan ko menene indai ba halin rashin lafiya ba ban yarda ki fita ba" Kudi ya mika mata rafa biyu yan dari bibbiyu, hannu tasa ta karba duk jikinta yayi mata wani irin sanyi, "Idan akwai abunda nayi miki kiyi hakuri ki yafe min, nima na yafe miki" ummu al'amin ta fada tana kallonta, "No maman al'amin honest to God you didn't done anything wrong to me, i pardoned you if there is something wrong" Tafada ranta duk babu dadi domin zaman gidan tasan bazai yi mata dadi ba ita kadai gashi ko al'amin dinma ba abarshi awurinta ba, "Sai na dawo" yafada tareda juyawa ya fita ummu na biye dashi, ajiye kudin tayi tabi bayansu tana sanye da kayan bacci _cotton_ riga da wando da hula akanta baka, Bakin motar da zasu shiga ta tsaya anan kuma ta fara hawaye, kuka tafara sosai marar sauti, yana hangota lokacin da yake kokarin shiga cikin motar, har ya shiga sai kuma ya fito yazo inda take tsaye tana faman kuka ya kama hannunta da tattausan hannunshi mai laushi, Part dinta ya nufa da ita yayinda ita kuma hawaye ke cigaba da zarya akan kumatunta, har cikin falonta ya shigar da ita, manyan dara daran idanuwansa ya daga ya kalleta,idonta arufe suke tana hawaye shar sharrrrrr, Hannuwansa biyu yasa ya dafe kumatunta for the first time da yaji tausayinta acikin ranshi har yaji wani abu wanda bai san ko menene ba yana yawo acikin jijiyoyin jinin jikinshi, Bakinsa yasa akan goshinta yayi mata wani zazzafan kiss, cikin sauri ta bude idonta ta dagasu ta kalleshi har lokacin bakinsa nakan goshinta bai dauke ba ga hannunshi duka biyu akan fuskarta, Lumshe idonta ta sake yi take wasu hawayen suka sake kwaranyowa akan kumatunta, amma kuma tana cikeda tsananin farin ciki saboda yau ya nuna kulawarsa agareta, Bakinsa ya cire daga kan goshinta,ahankali cikin cool voice dinsa yace "ki daina kuka kinji, daga ni har ummu zamu dawo kamar yaune, sannan idan nadawo zan dauko miki al'amin kuci gaba da wasanku tunda naga abokin wasanki ne" Dariya maganarshi taso bata wai al'amin ne abokin wasanta lallai ma ashe kallon yarinya karama yake yi mata, har alokacin hannayensa na kan kuncinta ya dago kanta, Saura k'iris maganarshi ta sata dariya, dago da kanta ya sake yi ya manna mata wani kiss din a habarta ya saketa ya juya ya fita, Gaban window ta karasa ta tsaya tana hangoshi har ya shiga mota inda ummu ke zaman jiransa amma bata damuba dan tasan sallama yake yi da goodness din, Akan idonta motarsu ta fita daga harabar gidan, wani farin cikine ya lullubeta marar misaltuwa duk da ta kasa gano dalilinsa na rashin yiwa bakinta kiss sai habarta da goshinta da yayiwa, hakanma ba karamin dadi ya sata ba domin ko babu komai for the first time in history dan karamin bakinsa da take kwadayi ya taba jikinta, lumshe ido tayi ta soma tuno yanayin da yasata aciki dazu. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/3, 9:51 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _48-50_ ~~~Tana cike da damuwar tafiyarshi har yamma tayi lokacin tasan may be sun sauka agarin _madinah_ ko kuma sun kusa isa, Raba dare tayi da daddare tana kallo gashi tana son jin muryar nan tashi mai sanyi amma ta kirashi wayar tashi bata shiga dole ta hakura taci gaba da kallon wani Nigerian film atashar African magic mai suna _life partner_ ,har wurin 1 takai na dare tana kallon kafin taje ta kwanta. Da safe ma haka ta tashi sukuku gidan shuru kamar babu kowa, duk sai taji ranta ya b'aci sa'arta daya da misalin karfe 11 nasafe sai ga yayarta anty bilkisu tazo nan suka bata da adaki suna shan hira. "Yanzu matar tashi zata dade bata dawo ba kenan?" Anty Bilkisu ta tambayeta, "Eh tace min zata kai 2 years ko 3 years bata zo ba" Jijjiga kai anty Bilkisu tayi "am advising you ki rike mijinki ki kyautata masa babu maganar kunya, kinga su matan hausawa kunyace dasu basa iya zagewa su bawa mijinsu kulawa yadda ta kamata shiyasa wasu mazan hausawan sunfi son auren yare domin sunfi basu kulawa ta musamman" Huduba sosai anty Bilkisu tayi mata wadda ita dai goodness har kunya taji domin batun babu sauki acikinsa anty Bilkisu bata komai take abude babu rufi, har dare suna tare sai wurin karfe 9 sannan mijinta yazo suka tafi. Cigaba da al'amuranta tayi har su mal jabir suka kwana 8 da tafiya yanzu abinda yafi damunta shine rashin jin muryarsa da kuma rashin ganinsa, mai gadi ta aika gidan malam wurin Baban mal jabir ya amso mata phone number dinshi ta can. *** Kwanansu biyu da sauka agarin madina mal jabir yayiwa ummu duk wani shige da fice na karatunta, ya gama mata registration yayi komai yanzu lectures kawai zata fara zuwa gashi ya samar mata gidan da zata zauna ita da al'amin Wanda kusa yake da jami'ar da zata rinka zuwa gashi dama gidan na females students ne zalla, Kwance yake adakin yayinda ummu ke kwance ajikinshi ta gefensa yana yi mata tausa ajikinta, lumshe idonta tayi domin jabir akwai iya soyayya sai dai bashida yawan bukata amma kula da mace kam ko sharukhan nan ya ganshi ya barshi, Tunani yake yi aransa yau kwananshi 9 a madina amma bai san halin da goodness take cikiba al'amin kuwa kullum sai sunyi waya dashi awayar Malam, "Yakamata na nemi number yarinyar nan dan jin halin da take ciki saboda ko kazarka ka daure ka tafi wani wuri ka barta ya kamata ace kana bibiyar yanayin da take ciki bare mace mai bukatar a kula da ita" yafada acikin zuciyarsa, karar shigowar text massage yaji awayarshi dan haka ya mika hannu ya dauko ya duba, number Nigeria ce kuma daga gani goodness ce tayi masa text din dan ga abunda tace: _"Some people have a nice smile, some have a nice face and some have a nice eyes, you, you have all of them and nice heart, you are such a special one to me, i can't explain how i fell so lonely during your absent, I MISS YOU....!"._ Sake maimaita karanta text din yayi sannan ya tashi zaune ya fita falo domin ummu tayi bacci tun tuni, dialling number din goodness din yayi, Tana kwance tana kallo kiransa ya shigo cikin wayarta, Da sauri ta tashi zaune ta kara wayar a kunnenta, "Hello sir" "Goodness how you? Ya gida?" "Everything moving fine sir, ina maman al'amin?" "She's sleeping, nima nakusa dawowa nanda 12 days" "Ok sir adawo lafiya idan ta tashi send my regard to her pls" "I shall, babu wani problem ko?" "Sir babu komai" "Alright sai anjima" Katse wayar tayi tabita da kallo tana murmushi har na tsawon wani lokaci. Shi kam daki ya shiga yaje toilet yayi wanka ya fito ya shirya ya fita cikin gari, kasuwa ya shiga ya fara yiwa al'amin siyayyar tsarabar da zai kawo masa, Itama goodness doguwar bakar riga mai zubin after dress ya siyo mata guda biyu sannan ganin mayyar english wears ce ita yasashi siyo mata su wurin set shida, riga da wando da skirt, sannan ya siyo mata takalma guda hudu. Zamansa a madina yasashi bawa ummu kulawa sosai har ana sauran kwana daya ya tafi, kasuwa ummu taje ta yiwa mutanen gida tsaraba ciki harda goodness domin kayan bacci ta siya mata kala biyar masu shegen kyau amma araha banza da yake a madina ne,sannan ta kwaso mata turarruka masu dadin kamshi da sure wurin kala goma goma, A washe gari jirginsu mal jabir ya d'aga daga madina zuwa Nigeria bayan sunyi sallama da matarsa wacce suke jin kamar karsu rabu da juna. Tun yana cikin jirgi ya turawa da goodness text massage cewar yau zai dawo kafin sallar isha ko kuma bayanta, Lokacin da taga text din nasa sashensa ta nufa ta shiga ta shareshi ta gyaggyara ta goge ko ina ta fesa room freshener ta jawo ta rufe ta koma sashenta domin dora masa girki duk da cewar tasan ba lallai bane yaci, Fried rice tayi ta yi masa yan soye soyen tareda chicken pepe, wanka ta shiga tayi bayan ta gama harhada komai, Bayan ta fito daga wanka ne ta shirya cikin wata body hug ash colour mai zanen eyes ajiki, daga tsakiyar rigar an rubuta _Dream again_,bakin wando jeans tasaka tareda daura bakin dan kwali bayan ta daure kitson attach dinta da red colour din ribbon. Misalin karfe 8:30 na dare jirginsu ya sauka, malam idi driver ne yaje ya dauko shi daga airport, goodness na zaune a falonta tana sauraren zuwansu, Tana zaune tana sauraren music wakar p square acikin wakarsa ta _lifes is so sweet_,alamar bude get din da tajine ya tabbatar mata da cewar sun karaso, bakin window ta tashi taje ta tsaya, ahankali ya bude motar ya fito yana sanye da farar doguwar jallabiya da yar karamar hula fara tas, wani kyau na musamman taga fuskarsa tayi ko kuma dan ta dade bata ganshi bane oho, Kamar ya shiga part dinta sai kuma ya wuce nashi saboda ko salla bai yi ba, lokacin da ya shiga part din nashi ba karamin dadi yaji ba domin komai a gyare yake tsaf, dakinsa ne dai kawai bata gyara ba shima dan ba a bude yake ba shiyasa, Alwala ya shiga yayi ya dawo falo ya fara ramuwar sallolin dake kansa yana kan yin sallar ne goodness ta shigo hannayenta dauke da food flaks wadanda ta zuzzuba girkin da tayi mishi aciki, Akan dining table ta jere masa su ta koma kan kujera ta zauna tana kallon yadda yake yin sallarsa a nutse har tana iya jiyo kira'ar karatun da yake yi cikin sanyayyiyar muryarshi gashi ko wanne harafi dalla dalla yake furtashi, Tana nan zaune ya idar da sallar ya fara zikirin da ake yi bayan kowacce sallar farilla, yana gamawa ya daga hannayenshi sama ya fara kwararo addu'o'i, zuru tayi da ido tana kallonsa har ya gama ya tashi daga kan abun sallar. Juyowa yayi ya kalleta, yayinda ita dinma shi take kallo, "Welcome sir" "Ya, gida? Ya zaman kadaici?" Ya tambayeta lokacin da ya wuce domin kunna tv, huda tv ya kamo ya tsaya yana kallon programme din da suke yi mai suna _learn how to correct your Qur'an recitation_,channel din ya bari ya koma kan kujera ya zauna wacce take nesa da ita. "Sir ga abinci can ko na kawo maka nan?" Tafada cikin sanyin murya, Kunyar gwasaleta yaji yace "eh kawo min nan" tashi tayi ta nufi dining table dan debo abincin, nan yabi bayanta da kallo yanda ko wanne bangare na jikinta ke juyawa yayinda take tafiya ga uban hips kaya guda kamar ita ta ajiyewa kanta gashi tanada mazaunai tubar kalla, Ahankali ta kawo abincin gabansa ta ajiye ta koma kan kujerar ta zauna, faratanta ya kalla sai ya gansu a yanke ba irin zako zakon nan bane nan ya danji alamar cewar zai iya cin cooking din nata, K'asa ya sauko ya dan zuba abincin baifi cokali biyar ba ya saka dan soye soyen agefe, ya dauki cinyar kaza guda daya, ahankali ya fara tsakurar abincin yana ci, kallonshi kawai take tana mamakin inda al'amin ya gado surutu domin shi mal jabir sam bashida yawan magana ga sanyi kamar me komai nasa a sanyaye, Wayarshi ya dauka ya fara laluben number din ummu, tana shiga ta dauka kamar dama jira take, "Abu al'amin ka tafi ka barni da kewarka" "Kiyi hakuri, ai nakusa kawo al'amin" "To ya ka sauka? Ina antyn al'amin?" "Gata nan lfy lau, sai munyi magana anjima" Katse wayar yayi ya dan kalli goodness kadan yace "ummu al'amin tana gaisheki" "Ina amsawa ta fada idonta akan tv" zama tayi har ya kammala cin abincin sannan ta kwashe kwanukan ta nufi sashenta, Shirin kwanciya tayi tabi lafiyar gado daga nan bata iya tashi ba saboda ayyukan da tasha sai wurin karfe 11 nasafe wannan dinma al'amin ne ya tasheta tana tsaka da bacci, "Anty wake up, ki tashi kiyi min wanka" Idonta ta bude guda daya "my boy zo muyi bacci kabari idan natashi sai inyi maka" "Nidai ki tashi kiyi min wanka" dole babu yadda ta iya haka ta tashi taja hannunsa zuwa cikin bathroom ta hada ruwan zafi tayi masa wankan, akwatin kayansa ta dauko daga falo tasa acikin dakinta ta dauko masa kayan da zata saka masa, riga da wando yan kanti, tana gama shiryashi ta tuna da ba tayiwa abbunshi breakfast ba, "Al'amin kai da wa kuka zo?" "Abbuna ne yaje ya dauko ni" Hannunshi taja zuwa cikin kitchen ta kunna wuta ta fara shirya abin karyawa, sanye take da rigar bacci iya gwiwarta, kanta babu dankwali rigar tata kalarta kalar ruwan hoda, Dankali da kwai ta soya ta dafa ruwan zafi ta zubawa al'amin nasa ta dauki na abbun nashi ta fita bayan ta daura zani a saman rigar tata, lokacin da ta shiga part dinshi yana zaune da kaya agabansa yana waya, tiren kayan ta ajiye ta juya zata futa, da hannu yayi mata alamar ta tsaya. Zaman jiransa tayi har ya gama wayar, gaisheshi tayi ya amsa fuskarsa babu yabo babu fallasa, jakar gabansa ya miko mata "Ungo kayanki wannan na cikin ledar kuma Ummu al'amin ce ta bada akawo miki" Amsa tayi tace ta gode sannan ta fita ta koma wurin al'amin tarar dashi tayi yanata kokarin kunna tv nan ta tsaya ta kunna masa ta kamo masa spacetoon arabic tashar cartoon ta larabci ta shiga wanka, Tunda al'amin ya dawo taji gidan gwanin dadi, tsarabar da aka kawo mata ta dauko ta duba kayane masu kyau musamman ma dogayen rigunan da jabir ya sai mata gashi kayan baccin da ummu ma ta bayar a kawo mata suma sun hadu, cikin drawer taje ta ajiye kayan ta fito ta koma kitchen ta dora abincin rana. Zama tayi awurin al'amin suka fara wasa, biye masa tayi kamar wata sa'arshi har abbunshi yazo kiransa dan su tafi masallaci, "Anty ke meyasa bakya salla?" Ya soko mata wannan tambayar wacce bata zata ba daga ita har abbunshi sai da suka yi mamaki, "Ka tashi kaje kayi alwala kazo mu tafi salla kar ashiga muna nan" Dagudu ya wuce bathroom dinta yayi alwala yazo ya dale hannun abbunshi suka tafi, yayinda suka barta da tunani lallai al'amin wayo ne dashi wato har ya lura da ita bata salla kenan. Wunin ranar tayi shine tareda al'amin shi kuma jabir yana sashensa, sai bayan sallar isha lokacin sun dawo daga masallaci ta kama hannun al'amin suka je part dinsa, yana zaune yana karanta wani littafin larabci, Anesa dashi suka zauna suka fara kallon tv, "Anty kece tom nine jerry" al'amin ya fada yana dariya, "Ni ba tom bace" ta bashi amsa, "Lah anty tsaya kiga keken wasa na da abbuna ya kawo min" kwasa yayi da gudu ya shige bedroom din abbunshi Jim kadan sai gashi ya fito akan keken yana dariya, "Anty zo ki hau mu tafi" Dariya tayi ta kalleshi "wa zaka dauka a wannan keken naka? Zan tafi na barka yanzu ni kallo zanje nayi, sai ka taho" tashi tayi ta fita shi kuma yaci gaba da wasa da kekenshi har ya gaji ya sauka yaje kan cinyar abbunshi ya kwanta. Karfe 10 ya dauko shi akan kafadarsa ya nufi part din goodness lokacin tana zaune a falo tana kallon Nigerian film, "Gashi zo ki karbeshi yayi bacci" yafada a hankali, tashi tayi taje ta mika hannu zata karbeshi, hannunsa taji ta kama wurin karbar al'amin din, kankame abbunshi yayi idonsa a rufe,gashi ita kuma an matse mata hannu ajikin hannun abbunshi sai wani irin shock take ji ajikinta, "Al'amin jeka wurin anty ka kwanta maza" Dakyar ya yarda yasaki abbun nashi ta juya dashi ta kaishi cikin dakinta ta kwantar dashi, ta dawo falo taci gaba da kallonta. Haka zaman nasu ya kasance har na tsawon sati daya lokacin mal jabir ya koma aiki ya fara zuwa office, Bayan ta yiwa al'amin wanka ta shiryashi ya tafi falo ya zauna ya fara yin game (tvgame),bathroom ta shiga domin yin wanka, daga cikin dakinta ta fara yiwa al'amin magana, "Al'amin you should stay there, don't enter this room, don't come inside this room, did you hear me? "Na'am anty" ya bata amsa domin shi komai sai dai yace na'am amma ko eh bai fiya fada ba, Labulen dakin ta gyara ta shiga wanka tabar kofar toilet din a bude ba tare da ta rufe ba, Mal jabir ne ya shigo ya samu al'amin yana game a falo "ina antyn ka al'amin?" "Abbu tana daki" ya fada yaci gaba da yin game dinsa ta super Mario, Kansa tsaye ba tare da tunanin komai ba yasa kai cikin dakin tareda kara wayarshi a kunnensa ya fara kiran secretary dinsa na office, Yana shiga ya bude baki kenan da niyyar ya yi magana awaya ya hangota tana wanka nicked, kofar bathroom din a bude, Duk jikinta kumfa ta jiyo kamshin turarensa cikin sauri ta karo kofar amma ina ya rigada ya ganta, "Goodness wannan sakarcin fa? Ya zaki bar kofa a bude kuma kina wanka idan al'amin ya shigo fa?" Kwara ruwa tayi ta dauraye jikinta ta fito, "Sir nafada masa wanka zanyi, ni bana rufe toilet wallahi tsoro nake ji" Juyawa yayi "natafi office sai na dawo" Ficewa yayi ya tafi yana mamakin sakarci irin nata,yayinda ita kuma takoma gaban mirror don shiryawa. Sai yamma wurin 5 sannan ya dawo, sashensa ya wuce kai tsaye, anan ya samu goodness ta ajiye masa abincinsa a shirye akan dining, Dagudu suka fito ita da al'amin suka nufi part dinsa yana kallonsu ta window, daidai kofar falon al'amin ya riketa ya wuce da gudu yana yi mata gwalo, a bayan kofa ta labe dan tasan zai sake fitowa yanzu yanzu, Tashi jabir yayi dan zuwa wurin driver dinsa saboda yana son aikinsa cikin gari ya siyo masa watermelon, Yana zuwa saitin kofar taji alamun tafiya da saurinta ta fito ta cafkoshi, caraf ta cafko hannun jabir, "Sorry i thought al'amin ne" Baice da ita komai ba ya wuce yayinda ita kuma ta shiga ciki tana neman al'amin din. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/5, 12:25 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _51-53_ ~~~Lokacin da ya wuce da sauri ta shige falonshi neman al'amin, hangoshi tayi hannunsa rikeda littafi yana karantawa da karfi, "Lah yadkulul jannata lammamun, annamimi bazai shiga aljannah ba, rawahul bukari wa muslim, bukari da Muslim ne suka rawaito, "Hey al'amin you dey hear" "Anty abbuna ne yake koya min karatu" "To maza ka iya before he come back" "Na'am anty" Cigaba da karatunshi yayi ita kuma tana zaune akan kujera tana sauraronsa har abbun nashi ya shigo hannunsa rikeda ledar kankana, Mika mata yayi dan ta je ta yanyanka, amsa tayi ta fita taje kitchen dinta ta samu filet mai fadi ta dauki wuka ta fere kankanar tayi mata yanka mai kyau heart design, Fork ta dauka tasa wani filet din daban ta rufe ta tafi kai masa, shi aduk yayan itatuwa yafi son kankana saboda yasan ko musulumci tana da amfani ajikin mutum, Agabansa ta ajiye farantin kankanar ta koma saman kujera ta zauna, budewa yayi ya dauki fork din ya fara sha, matsawa kusa dashi al'amin yayi ya zubawa kankanar ido na tsawon yan sakannin da basu wuce biyu ba, "Lah abbu kaga anty ta rubuta maka i love you acikin kankanar" Wata dariya ce ta tahowa mal jabir wacce ta kusa sakashi kwarewa, cikin sauri ta kalli al'amin kafin tayi magana yaci gaba, "Abbu dama kullum kullum sai naji anty tana cewa i love you abbun al'amin" "Al'amin when did you started telling untruth?" "Anty wlh ba karya nake ba kullum idan kina bacci ina jinki kina fada" Shiru tayi kamar ruwa ya cinyeta, shidai abbun nashi jinsa yake yana kallonsa bai iya cemasa komai ba saboda ya kula wayon al'amin yawane dashi, Tashi tayi ta fice ta koma sashenta ta kunna kallo ta zauna domin shi jabir kullum daga labarai sai sunnah tv sai huda tv yake kunnawa ita kuma ba kallonsu take ba dan haka ta kunna Nigerian film dinta ta soma kallo. Karfe 9 da yan mintina al'amin ya shigo lokacin tana kwance tana kallon film din _lover boy_, "Anty i am sleepy, ki kaini inyi bacci" Mikewa tayi "woh al'amin your problem neva finish oh oh" Hannunsa taja zuwa cikin dakinta taje ta kwantar dashi ta kunna masa fan ta juya da niyyar fita maganarshi ta dawo da ita, "Anty abbuna ma dey love you" "Oh God, al'amin kayi baccinka pls" "To anty sai da safe" komawa yayi ya kwanta ita kuma ta fita daga dakin aranta tana tunanin ai jabir ba ya sonta baya kaunarta kawai dai yana zaune da itane a matsayin zaman kaddara, tunda duk ta gama ganin alamun hakan a tattare dashi, Kallon film dinta taci gaba dayi har wurin 11 alokacin jabir ya turo kofa ya shigo cikin falon, kallonshi tayi kansa babu hula yana sanye da jallabiya kalar ruwan madara, Tamkar wani dan saurayi haka taga ya zame mata domin ko kadan baiyi kama da magidanci ba indai ba wanda ya sani ba babu wanda zai kalleshi yace yana da mata harda yaro, Dan yatsanta tasa acikin bakinta tana kallonshi, "Abokin wasan naki yayi bacci ne?" "He dey sleep inside my bedroom" "Oya take this" Wata bakar leda ya mika mata mai dauke da wani ganye aciki kamar ciyawa, "Sir what's this?" "Ki dafa min yanzu amma kisaka Lipton aciki, lemon grass ne" "Ok sir" tashi tayi shikuma ya shiga bedroom dinta inda al'amin yake kwance yana bacci, addu'o'i yayi masa ya shafa masa ajikinsa sannan yaja blanket ya lullubeshi ya fito, Part dinsa ya koma, yana zuwa ya shiga wanka. Cikin mintuna kadan goodness ta gama dafa masa shayin ta dauka ta nufi sashensa, a falo ta ajiye masa amma baya ciki hakan yasata karasawa kofar dakin nasa ta murda ta leka daidai lokacin ya fito daga bathroom daga shi sai gajeren wando wannan shine karo na farko da ta taba ganinsa ahaka. Cikin sauri taja kofar tana fadin "i sorry sir" Ji tayi yaja kofar ya bude da sauri ta sauke idonta kasa harda saka hannuwanta biyu ta rufe fuskarta, Murmushi yayi acikin zuciyarsa yace "lallai ma yarinyar nan ba gwara ni ba akan ke tunda ke kullum barin kofa kike abude idan zaki yi wanka" Ciki ya koma ya ziro doguwar riga ya fito har lokacin idanuwanta arufe suke da tafukan hannunta, "Have you add sugar inside that thing?" "No sir" tafada tana bude idanuwanta, "ok let me check i think i have a little honey here" Wata drawer yajawo wacce ke ajiye acikin falon nashi, kwalbar Zuma ya dauko amma babu ta kare ko ba afada ba yasan al'amin ne ya shanye sauran, "Go and bring sugar pls" yace da ita, "Ok" fita tayi taje sashenta ta dauko masa kwalin sugar guda daya ta kawo masa yana nan zaune inda ta barshi yana goge kunnensa da abin goge kunne,idonsa a lumshe yace ta ajiye sugar din, ajiyewa tayi ta fita ta koma part dinta. Washe gari da safe bayan ta shirya al'amin ta gama hada abin karyawa tayi wanka, abincin jabir ta dauka ta tafi sashensa ta kai masa, lokacin da ta shiga baya falon yana bedroom dinsa ya shiga wanka, Part dinta taje ta zubo musu break din ita da al'amin suna ci yana bata labarai tanata dariya, suna kammalawa ta shiga kitchen ta fara kiciniyar hada abincin rana, jallop din cous cous tayi niyyar yi, kayan miya ta zuba a turmi dan jajjagawa, daga falo tana jiyo hayaniyar cartoon din da al'amin yake kallo, Turmin ta dauka ta kai corridor ta ajiye, anan dama take duk wani abu da ya shafi daka saboda shi wurin ba tiles bane siminti ne, Jajjaga kayan miyan ta fara sai daf da zata gama wani cukurin attaruhu ya taso ya fantsalo mata a fuskarsa nan yayi tsalle ya watsu cikin idanuwanta, "Ahhhhhhhhhh! My eyes, al'amin come and give me hand, come and aid me pls, pepe done enter my eyes oh oh" Shiru taji wannan ya tabbatar mata da cewar al'amin ya fice daga falon, "Oh God! My eyes, my eyes! Laluben hanya tayi dan taje ta wanke fuskarta, tana kokarin shigowa falo jabir ya shigo cikin shirinsa tsaf na zuwa office, Ganinta yayi idanuwanta arufe kamar wata makauniya tana neman hanya, "goodness what's happen?" "Sir my eyes, Pepe done enter my eyes" Tafada tana dafa bango, wani karo tayi da dan karamin stoll din dake ajiye gefen kujera ta tafi tagal tagal zata fad'i cikin zafin nama yayi saurin tarota ta fada kirjinsa, Wani irin yanayine ya ziyarcesu gaba dayansu wanda ba zasu iya fassara shi ba, "where are you going now?" Ya tambayeta tana rik'e acikin kirjinsa" "Sir i dey go bathroom to wash my face" Bai sake magana ba ya juya da ita ya nufi cikin bedroom dinta da ita har lokacin yana rik'e da ita akan kirjinsa, wani kamshi mai dad'i take shak'a daga cikin jikinsa wanda yau taji ya banbanta da sauran da tasan yana shafawa, Cikin bathroom ya kaita ya dauki hannunta guda daya ya dora ajikin fanfo ya kunna mata, cikin sauri ta fara wanke fuskarta, "Sir pls give me soup" tace dashi tana mutsuttsuka idonta, Sabulun yana kusa da ita amma bata ganshi ba, dauka yayi ya dora mata akan hannunta, karb'a tayi ta soma gogashi akan fuskarta, "Washhh this pepe want to blinded my eyes" Juyawa yayi ya fita daga bathroom din har yaje tsakiyar dakinta ya jiyota tana fitowa, "Sir bai fita ba wlh it dey inside my eyes especially this one" ta nuna idonta na dama, "Sir pls hure min, yana ciki" Yana nan tsaye cak har ta karaso gabansa, kanta ya d'ago ya bude idonta daya yasa bakinsa ya fara hure mata, tabbas dagaske take ga kwayar cikin attaruhu nan guda daya acikin idonta yana gani, nan yaci gaba da huhhure mata amma fur kwayar attaruhun nan taki fita ita kuma goodness ji take kamar za tayi hauka dan zafin da take mata acikin idonta, Hannunta yaja ya zaunar da ita abakin gado yaci gaba da hure mata idon, gaba daya idonta yayi ja bau kamar me yin afolo, Dakyar kwayar nan ta fice ta can gefen idonta, dan yatsansa yasa ya cirota murza idon taci gaba dayi domin wani radadi yake mata, "Kin ganta" ya mika mata yatsansa dan ta gani, "Abbu na ashe kaima kana son anty na ko?" Suka jiyo maganar al'amin daga bakin kofa, da gudu ya karaso ciki, "sannu anty, abbu me kayi mata take kuka?" "Al'amin babu abinda nayi mata yajine ya shiga idonta shine na cire mata" "Ya salam, sannu anty, taso muje falo ki kalli cartoon" hannunta yaja ta tashi tabishi, murmushi mal jabir yayi yabi bayansu, kyalesu yayi ya tafi office saboda yaga hankalinsu ya tafi kan wasan yaran da suke kallo a tashar mbc 3,sai da taji saukin idon nata sannan taje ta karasa girkin amma har alokacin tana jin zafin yajin ga wani irin ja da idon yayi tasan dama dole ne zai zame mata eye ache. Misalin karfe 5:30 mal jabir ya dawo gida, sashenta ya fara zuwa amma basa ciki, nan yayi tunanin to ko suna cikin falonsa, can dinma da yaje basa ciki, mamaki ya yi to ko ina yaran nan suka tafi? Agurguje ya shiga yayi wanka ya fito sai alokacin yajiyo hayaniyar su abayan part dinsa,ta window ya lekasu, goodness sanye cikin green din t shirt da blue din jeans idonta daure da bakin k'yalle tana neman al'amin, wanda ke tsaye a bayanta sai faman ja mata riga yake suna dariya amma ta kasa kamashi, Murmushi yayi na jin dadi domin al'amin ya sake sosai da goodness saboda yadda ta sakar masa fuska takoma yarinya karama kamar age mate dinshi yasan ba dan goodness ba da tuni al'amin ya addabeshi ya kaishi wurin ummunshi amma yanzu ko zancenta baya yi iyakaci su gaisa a waya, Kaya ta taka ta saki yar kara "oh God" "Anty ba oh God ake cewa ba, annabi ya kasance idan wani abun da yake k'i ya faru agareshi sai yace Alhamdulillahi ala kulli halin, idan kuma na farin ciki ya zo masa sai yace Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihatu, anty kema kiyi koyi da annabi sai ki samu lada" "Thank you al'amin zanyi nima" Sakin labulen window din yayi yakoma cikin falo yaje ya zauna akan dining ya zuba cous cous din data dafa ya dan ci, bayan ya gamane ya tashi ya zagaya baya inda su goodness ke wasa ita da al'amin, Lokacin da ya karasa wurin yanzu al'amin dinne fuskarshi adaure da kyallen ita kuma goodness sai dariya take yi masa itama tana rama abinda yayi mata dazu, "Welcome sir" tafada tana jan rigar al'amin, "Abbu na kadawo? Har kai zan kama yanzu ba iya anty kadai zan kama ba" "Thank you, al'amin nikuma daga zuwana za ace harda ni?" Dagudu al'amin ya taho,cikin sauri goodness ta matsa tabar wurin, "Abbu in dai na kamaka to kai za adaurawa" Da sauri ya matsa ya koma jikin karfen tanki ya tsaya, ita kuwa goodness tana bayan wata kujerar karfe dake ajiye awurin, bayan karfen tankin ya nufa ganin haka yasa goodness fara yiwa malam jabir dariya ta hanyar toshe bakinta da hannunta, Fitowa yayi da niyyar sauya waje, caraf al'amin ya rikeshi yana cewa "yes na kama wani tsakanin anty ko abbu" Cire kyallen yayi yana ganin abbunsa ya fara dariya, "Abbu yanzu kai za adaurawa" "Ya na iya al'amin tunda na kawo kaina, nidai kawai tsautsayine ya fito dani har nazo wurinku" Karbar kyallen yayi ya daure fuskarsa ya fara lalubensu, da gudu al'amin ya arce yayi bayan dakin abbunshi ya tsaya, ita kuma goodness ta labe agefen karfen tanki, Lalube yake tayi amma baiji ko daya daga cikinsu ba kamar basa wurin, al'amin ne ya sadado yazo yaja rigarshi ta baya ya kwalkwale da gudu, da aka sake jimawa kadan ya sake dawowa ahankali yace "Abbu ga anty can agefen karfen tanki kaje ka kamata saboda ni ba iya kamani zaka yiba duk nifiku gudu" Yana gama fadin haka yaja gefen rigarshi ya zura da gudu, Shawarar al'amin yabi dan yasan bazai iya kamashi ba kam, gefen tankin yabi yana tafiya ahankali ganin haka yasa al'amin daukewa goodness hankali daga can inda yake yafara yi mata rada wacce bazata iya jiyo abinda yake fada ba. Hankalinta ta mayar kansa tana tambayarshi da hannu wai me nene? Dariyar mugunta al'amin yayi mata saboda dama yayi hakane dan abbunshi ya kamata, Juyowar da zatayi taji jabir ya taka kafarta daya, daurewa tayi batare da tayi motsi ba har zai juyawa ya wuce sai yaji alamun fitar numfashinta, kansa ya dan matsar nan ya tabbatar da cewa itace, cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai k'asa. _*Ummi Aisha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/13, 5:16 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _Assalamu Alaikum masoya masu karanta wannan littafin na wani haske, ina mai baku hakuri na dan jina shiru da kuka yi kwani biyu da suka wuce hakan ya farune sakamakon abubuwa da suka sha kaina amma insha Allahu yanzu komai ya daidaita zaku rinka jina akoda yaushe har labarin ya kare, ina yi muku barka da sallah da fatan Allah ya maimaita mana amin._ _54-56_ ~~~Cikin sauri ya fisgota da karfi, nan ta fada jikinsa wanda saura k'iris su zube su kai kasa, Fuskarshi na daure da bakin kyallen ya fara yi mata magana a hankali cikin rad'a rad'a, "Pls remove this thing from my face" Daga kanta tayi ta kalleshi ya matseta sosai Wanda har tana iya jiyo bugun da zuciyarshi keyi ahankali, Ahankali take jin saukar numfashinsa akan goshinta, dan motsi tayi ta fara kokarin kwace hannuwanta dake rike a hannunsa, "To ka sakar min hannuna mana" "Idan nasake ki guduwa zaki yi i know" Sake take kafarta yayi, "ohhh..!" Tafad'a ahankali, "ki kunce min daurin fuskata sai na sakeki" "Sir you have match your leg on the top of mine" Tafada tana sake k'ankameshi, "Oh sorry" sausauta rik'on da yayi mata yayi ya dan sake hannunta kadan amma har lokacin yana rikeda su, ahaka ta kunce masa bakin kyallen dake fuskarsa, Sakinta yayi, dagudu al'amin ya garzayo yazo ya dale abbunshi, "Abbu nayiwa anty wayo nasa an kamata" "I already know you are the one who plan this al'amin,but i will take revenge next time" ta fada yayinda take daura dan kwalinta, "Sorry anty i know what i will do so that you can't take avenge" Tsaye yayi yana kallonsu, sauke idanuwansa yayi akan al'amin yace "Al'amin muje kayi alwala lokacin salla ya kusa" Hannun goodness al'amin ya kama yana dariya "anty let's go" Binsu a baya jabir yayi suna tafiya al'amin yana lilo ajikin goodness har suka je sashenta ya shiga ya dauro alwala ya fito wurin abbunshi suka tafi masallaci. Yau ta Kama ranar juma'a, karfe 1 mal jabir ya taso daga office, lokacin da yazo gidan goodness ta yiwa al'amin wankan juma'a tana shiryashi, "Anty fararen kayana zaki samun saboda ummu na duk ranar juma'a fararen kaya take samun kuma kinga ai abbuna ma duk kayansa farare ne saboda annabi yace mu yawaita dinka kaya farare" "Tom bari nasaka maka wannan farar shaddar" "Yawwa anty dama irinta abbuna ce, shima yana da irinta" Yana tsaye a bakin kofa yana kallonsu har ta sakawa al'amin kayan,ajikinta taji alamun ana kallonta hakan ya sata saurin juyawa hada ido tayi dashi yasha farar shadda sabuwa kar, ya gyara sajensa da gemunsa fes sai zuba kamshin turare mai sanyi yake, "Hmmm you are always cool, even your perform is like the way your are" tafada ahankali, "Anty me kike fada? Da abbuna kike?" Al'amin ya fada yana mika mata hularshi dan ta saka masa, "No bada abbunka nake ba da kaina nake, have you get me?" "Na'am anty" hularsa ta saka masa ta dauki turare gaban mirror dinta ta feffesa masa, "Anty baki bamu carpet ba" "Zo nan da akwai abun salla acikin mota" ya fada yana gyara zaman agogon hannunshi, hannunsa yaja suka fita nan ta rakasu da ido, al'amin ba karamin kyau yayi ba shida abbunshi tamkar ta sacesu ta gudu dan kyau. Da yamma tana corridor dinta tana wanke inner wears dinta al'amin yazo yana tsalle "anty nima zanyi wankin" "No bari kar ka bata kayanka" "Nidai anty zanyi" ganin zai dameta yasata tura masa bocket daya ya fara jagwalgawalawa, Mal jabir ne ya shigo jin hayaniyarsu acikin corridor yasa shi binsu can amma falon k'ure yake da wakar akon cikin wakarsa ta _black girl_, Yana zuwa corridor din ya kallesu "me kuke yine? Naji banji motsinku ba gashi kuma ina son fita" "Abbu kayan anty muke wankewa kaga irinsu" bra daya da pant daya ya kwaso da gudu da niyyar kai masa dan ya gani, da sauri goodness ta rikoshi, "Hy give me my kaya" karbewa tayi ta mayar cikin bokitin, wata uwar kunya taji ta rufeta yau kuma da wanne ido zata kalli abbunshi yaga bra da pant dinta alhalin ita kuma tanada kunyar wadannan abubuwan shiyasa ko a toilet bata shanyasu gudun kar yagani ko shi ko al'amin din, "Bari naje wurin malam" yafada yana kallonta ta baya, "Abbuna zan bika ko? Muje wurin malam" "Adawo lafiya, agaida shi" tafada ba tareda ta juya ba, tana ji al'amin ya kwashi takalmansa ya bishi suka tafi, girgiza kai tayi yaro dai yaro ne. Ranar Saturday da safe bayan ta shirya breakfast ta yiwa al'amin wanka, kitchen ta shiga ta dan gyaggyara shi saboda ta dan kwana biyu bata yi masa gyara na tsanaki ba, digirgire tayi ta bude drewar din sama tana zuba dinner set, cikin tsautsayi tana dora wani kofi ashe bai zauna ba, dawowa kofin yayi ya fadi akan babban dan yatsanta na kafa taratsatsa kaje ji ya fashe akan yatsan nata, take ya yankata kamar ansaka wuka an yanka gun kun san dinner set da uban nauyi, Wata kara tasaka da karfi, da gudu al'amin yazo daga falo inda yake zaune yana kallon cartoon a mbc 3, "Anty" ya fada tareda zaro ido, ganin jini yana malala a k'afarta ya sashi fashewa da kuka tareda juyawa da gudu yayi hanyar sashen abbunshi, yana zaune yana karanta jaridar _weekly trust_ al'amin ya shigo da gudu yana kuka yazo ya fara girgizashi ya rike hannunshi, "Abbu jini da yawa a kafar anty... Abbu zo muje ka gani" Ajiye jaridar yayi ya saka silifas dinshi yabi bayan al'amin wanda keta faman kuka, tsoro da mamakine suka kamashi a lokaci guda, to ko menene ya faru? Tambayar da yaketa nanatawa kenan acikin zuciyarshi, Suna shiga ya ganta ta jawo kafar tana zaune akan kujera amma jini duk ya b'abbata wurin gashi tun daga kitchen din jinin yake zuba, "What's happening? Goodness what's happen?" Ya tambayeta gamida bin jinin da kallo, kitchen ya leka anan ya hango kofin da ya fashe ga uban jini awurin, Dawowa yayi inda take, yana kallon fuskarta yasan dauriya kawai take amma tana jin jiki saboda gaba daya naman wurin gashi nan awaje yana gani kai kadan ma ya rage dan yatsan ya rabe biyu, "Am coming" ya fada ya juya ya fita, sashensa yaje ya dauko hydrogen acikin kwalba da farar audiga, har ya dawo al'amin yana kuka, Hydrogen din ya dan tsiyayo acikin murfin kwalbar ya dauki audiga ya zuba akan dan yatsan nata, wani uban tsalle goodness ta daka ta sauko kasa ta kankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinsa, "Sir pls stop it, pls sir wlh da zafi" hawaye ta fara yi tana rirrike hannunsa tana kokarin janye kafarta, Kallonta yayi nan yaji tausayinta tana sanye da rigar bacci _maroon colour_ mai siririn hannu da dan buje din wandon rigar iya cinyarta, kanta sanye da hula baka, "Sorry kadan zan saka miki saboda jinin ya tsaya kinga har yanzu jinine yake zuba ko kina son jinin jikinki ya kare gaba daya?" "No sir but pls don't put it again" Hannunsa ta sake kankamewa, tana kuka, ga al'amin shima agefe yana nasa kukan, rikeshi tayi gam taki sakinsa har shi kansa sai da yayi mamakin karfinta ita kuma ganin haka ya sata mamakinsa har aranta tana cewa "ashe ma bashida karfi nafishi, he's not strong see him like a woman" Bata karasa zancen zucin da take yi ba taji ya zame rikon da tayi masa yasa hannunsa daya ya rike hannayenta duka, auduga ya dauka ya sake zuba hydrogen ajiki zai saka mata, Wani kuka ta saka "ohhh...! Sir i beg u pls don't put it, pls sir, pls, pls" Kankameshi tayi ta cukwikwiyeshi tana kuka hawaye nabin kumatunta, "abbu ka kyaleta kar ka sake saka mata dan Allah" ya jiyo muryar al'amin yana rokonshi, Biris yayi dasu duk da yasan akwai zafi amma haka ya danneta ya sake saka mata, Shure shure ta fara har tana yaye rigar barcin dake jikinta ba tare da ta sani ba, birgima taci gaba da yi tana kuka, kallonta yayi duk ta kwaye rigarta takaita kirjinta, gaba daya cikinta yana waje dan har yana iya hango ash colour din bra din dake jikinta, "Tashi muje chemist ayi miki dressing din wurin" Jijjiga kai tayi tana kuka "no sir abarshi haka zai warke" "Ba komai zasu yi miki ba kawai dressing ne tunda na rigada na wanke miki wurin" Tashi tayi ta dingisa ta shiga dakinta yanzu jinin ya tsaya ya daina zuba, shi kam al'amin yana zaune gefe ya hada kai da gwiwa yanata kuka, gabanshi yaje ya kamo hannunsa, "Al'amin daina kuka kaji, kaga antyn ma ai ta daina alamun ta warke" "Abbu yau babu wanda za muyi wasa tare tunda anty bata da lafiya" "Waye ya fada maka? Za kuyi wasa mana, ai ta warke" Tashi yayi yana share hawayen fuskarshi, dai dai lokacin ta fito sanye da doguwar rigar da ya kawo mata tsaraba lokacin da ya dawo daga madina. Rigar ba karamin kyau tayi mata ba gashi tayi rolling wanda indai ba saninta kayi ba babu abinda zai hana ka dauka bahaushiya ce ita, Dagudu al'amin yaje ya kama hannunta "sannu anty kin warke? Ya daina yi miki ciwo? Yanzu babu jini ko?" "Wannan antyn naka al'amin ai Raguwa ce tunda tana yiwa hydrogen kuka" ya fada da niyyar zolayarta, Kallonsa tayi yanda yayi maganar yaso bata dariya amma sai ta dake bata yi ba, "Muje ko, ko har yanzu baki daina jin tsoron hydrogen din bane?" Murmushi tayi ita gaba daya yau abbun al'amin mamaki yake bata yanda ya sake yake janta da wasa, ashe dama haka yake? Ya iya jan magana ga iya soyayya kamar wanda ya zauna a class aka koya masa,sai dai ita tanada masaniyar baya sonta kawai yana karanta matane saboda danshi al'amin sannan yana zaune da ita ne a bisa k'addara wacce masu iya magana kance ta riga fata, Hannun al'amin ta kama suka fita yana biye dasu a baya har tsakar gida, mal idi ya kira ya karbi key din mota yace zaije chemist din baya ya dawo, Da kanshi yayi driving, goodness na zaune agaba al'amin na kan cinyarta, sautin kira'ar karatun al'qur'ani tana tashi sama sama cikin muryar sheikh Ahmad Sulaiman kano inda yake karanta suratul taubah, Bayan layinsu ya zagaya sai gasu a wani chemist (Al haq medicine & cosmetics store),dan satar kallon fuskarshi tayi yayi bala'in yi mata kyau. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/28, 9:30 PM] ‪+234 810 100 9022‬: [9/9, 9:17 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _Sak'on gaisuwa da godiya ga"yan k'ungiyar fik'ira writers group 1and 2,bisa jinjinar da kuka yimin akan wannan littafi da nake rubutawa na wani haske, hak'ika nayi mutuk'ar farin ciki ganin akwai littattafai bila adadin amma acikinsu kuka zab'i nawa k'waya daya kuka yabeshi tare da yimin jinjina, ummu abdul naga sak'onki kuma nayi murna da ganinsa Allah yabar zumunci, ummi A'isha tana sonku._ _57-58_ ~~~Zuba masa ido tayi bata ko k'iftawa tana kallonsa yana kokarin zare key din motar, "muje ko" ya fada ahankali, dan mitsil din bakinsa ta kalla yanda yake motsawa da k'yar idan yana yin magana, Al'amin ta sauke ta fito tabi bayanshi har zuwa cikin chemist din, Suna shiga suka samu wani nurse yana dan rubuce rubuce nan jabir yayi masa bayanin ciwon da goodness taji, tashi nurse din yayi yazo inda take zaune ya kalli d'an yatsan nata wanda har ya kumbure yayi suntum, Kayan dressing ya d'ebo yazo inda take zaune ai tana had'a ido da hydrogen ta mik'e tsaye, "Any problem?", jabir ya tambayeta, "Sir hydrogen, pls kar asa min shi" ta fada kamar wacce zata yi kuka, Nurse din ya fad'awa cewar ya saka mata hydrogen agida yanzu dressing kawai za ayi, Take aka d'an goggoge mata d'an yatsan nata aka yi mata dressing suka fito, cikin motar suka koma ta dora al'amin akan cinyarta, shigowa ciki yayi yana kallonsu ita da al'amin din, "Abbu kaima kana tsoron hydrogen ko kamar anty?" D'an k'ayataccen murmushi yayi wanda ya k'awata fuskarshi sannan ya kalli goodness ta gefen ido, "Ga mai yiwa hydrogen kuka nan antyn ka" Ya bawa al'amin amsa, kallonshi tayi gaba d'aya ya mayar da hankalinsa akan driving din da yake yi, bata yi magana ba sai shida al'amin ne keta hirarsu har suka koma gida,suna shiga tafito hannunta rike da na al'amin suka shiga part dinta, doguwar rigar jikinta kawai ta cire ta dawo falo ta gyara inda jinin da ya zuba dazu ya babbata, tana gama gyaran wurin ta koma kitchen ta dora abincin rana,tuwon alabo miyar ganye ta yi tana kammalawa ta shiga wanka kamar kullum k'ofar bathroom din a bude ta barta, tana wankan jabir ya shiga dakin domin dawowarsu kenan daga masallaci sallar azahar shida al'amin, "Wai ba zaki daina wanka toilet a bud'e ba" ya fada tare da juyawa zai fita daga cikin d'akin, "Sorry sir i have finish, yanzu zan fito" Ba tareda ya jiyo ba ya fice ya nufi sashensa, yana zuwa ya zaunar da al'amin a kusa dashi ya fara koya masa wani hadisi. Tana fitowa daga wanka ta shirya cikin riga da skirt ta dauki abincin jabir ta nufi part dinsa, tana shiga tun daga babban falo ta jiyo muryar al'amin yana karatu, "An abi hurairata, an karb'o daga abi huraira radiyallahu anhu, Allah ya k'ara masa yarda,k'ala yace, k'ala rasulullahi sallallahu alaihi wassalama, manzon Allah yabo da amincin Allah su tabbata agareshi yace, man la yashkurun nasa, duk wanda baya godewa mutane, la yashkurullaha, baya godewa Allah" Saka kai tayi ta shiga cikin falon nasa tana murmushi domin tsarin irin yadda jabir ke bawa al'amin tarbiya abin yana burgeta she like his fathering, Hannunta dauke da food flasks ta karasa kan dining table ta ajiye tareda dawowa wurinsu, Zama tayi ta zubawa jabir ido yana zaune hannunsa rike da littafin _sahihul bukhari_ yana dubawa, ido ta ware taci gaba da kallonsa har tsawon wani lokaci,babu zato ya dago kansa caraf suka hada ido dashi, "Akwai damuwa ne?" Ya fada yana kallonta, "Me ya faru?" Ta tambayeshi, mayar da kansa yayi kan karatun da yake yi ba tareda ya kara yin magana ba hakan ya sake bata damar ci gaba da kallonsa, "Abbu anty tanata kallonka tun d'azu" al'amin ya fada yana girgiza abbunshi, D'agowa yayi ya sauke idonsa akan goodness wacce ta mayar da kallonta ga tv, Murmushi yayi ya tashi ya shiga _bedroom_ dinshi domin yin wanka, yana tashi ta jawo al'amin, "Al'amin me yasa baka jin magana? Uhum? Am asking you? Yaushe ka ganni ina kallon dad dinka?" "Anty naganki mana sai kallonshi kike yi, ko ya zama tv ne?" Murmushi tayi tajashi jikinta tana dariya, "ohh al'amin you are talkative" "Anty ina jin yunwa" "Oya tashi muje muci abinci to" Mikewa suka yi suka koma sashenta anan ta kunna wak'ar _if do me i do you..._,zaunar da al'amin tayi ta kawo musu abincin ta ajiye suka fara ci, "Anty me yasa kike yawan jin kid'a?" Al'amin ya tambayeta, "Al'amin yana sakani cikin nishad'i ne that's why" Ta bashi amsa tana jinjina basira irin ta al'amin domin komai mutum yake yi yana haddane dashi, "Anty yawan sauraron kid'a yana sanya munafurci acikin zuciya, amma sauraron karatun alqur'ani yana sakawa zuciya nutsuwa da farin ciki" Spoon din hannunta ta ajiye ta tsurawa al'amin ido tare da kama hannunshi, "al'amin a ina kake koyan wadannan abubuwan masu ban mamaki?" Dariya yayi irin tasu ta yara, "anty abbuna da ummuna ne ke koya min, kema idan kina so abbuna zai koya miki" Murmushi ta saki tana wani tunani acikin zuciyarta, "al'amin ina son abbunka sosai, abbunka ya zame min wani bangare na rayuwata, i can't do without him, he's parts and parcels of my life, i like him soo much" Lokacin da take yin wadannan maganganun jabir yana tsaye a kofar falon yana saurarensu, kuma duk maganganun da tayi yajisu acikin kunnensa but shi matsalarsa guda daya ce bazai iya nuna mata soyayya acikin wannan yanayin da take ciki ba domin bata da tsarki shi kuma mutum ne shi mai tsananin kyankyamin kazanta komai kankantarta, "Anty abbuna ma yana sonki soo much" al'amin ya fada yana dariya, Bude kofar yayi ya shiga cikin falon suna zaune suna cin abinci ga _music_ nan yana tashi k'asa k'asa, Gefenta ya wuce ya zauna yana kallonsu, "abbu yanzu anty take zancenka" "To al'amin ka manta idan ana cin abinci ba a magana har sai an kammala?" "Abbu na manta ne" ya fada yana rufe bakinshi da hannunshi, Wani sanyayyen murmushi jabir yayi tareda kallon goodness wacce take ta sussunkuyar da kai k'asa domin bata son had'a ido dashi saboda akwai wani sirri a k'unshe cikin idanuwansa wanda ita bata iya jurewa, "Goodness zan fita ina son zanje wata unguwa da aka gayyaceni domin bud'e wani sabon masallaci" "Abbu zan bika nima" "A'a al'amin ka zauna awurin antynka kaji, bazan jima ba zan dawo" "Adawo lafiya sir" goodness ta fada tana kallonshi lokacin da yake mikewa domin fita, "Abbu ka siyo min chocolate" al'amin yayi tsagal ya fada, "Zan siyo maka,antynka fa me zan siyo mata?" Yana tsaye a bakin k'ofa ba tare da ya jiyo ba, "Sir alewar tsinke" goodness ta bashi amsa, murmushi yayi acikin ranshi kuma yana mamakin k'uruciya irin tata shiyasa lokuta da dama yake danganta yarintarta da irin ta al'amin, bud'e kofa yayi ya fita ba tare da yayi magana ba, Yana fita goodness ta kalli al'amin "al'amin meye ambition dinka a rayuwa?" "Anty ina son idan na girma na zama kamar abbuna nima ina tara mutane ina koya musu karatun alqur'ani saboda annabi yace '''mafi alkairin cikinku sune wadanda suka san alqur'ani kuma suka koyar dashi"' kinga abbuna ma yana koyawa mutane" "Good boy, ina sonka my boy" mikewa tayi ta shiga cikin bedroom dinta tabar al'amin yana k'arasa cin abincin. Tunda jabir ya fita bai dawoba sai misalin k'arfe 8:30 bayan sallar isha ko al'amin ma ranar sai agida yayi salla baije masallaci ba saboda baya nan,yana idar da sallar taji ya fara karatunsa kamar kullum annabi yace "'sallu kama ra'aitumuni usalli, kuyi salla kamar yadda kuka ga ina salla"'. Lokacin da ya shiga gidan basa part din goodness hakan ya sashi tunanin k'ila suna sashensa ai kuwa hakan take domin yana shiga ya hangosu suna wasa goodness tana yi musu after money amma da yake wayon al'amin yawane dashi sai runto yake yi mata, Sallama yayi ahankali ya shiga, da sauri suka d'ago suka kalleshi yayinda al'amin ya tashi da gudu yaje ya rungume shi, Ciki suka karasa yana rikeda hannun al'amin, "welcome sir" goodness ta fada tana kallonsu, "Yawwa anty" ya fada ba tareda ya kalleta ba,murmushi tayi ta kalli dan mitsitin bakinsa wanda ya iya fadar magana sannan yayi fuska,in banda haka taya zai kirata da anty, Ledar hannunshi ya bawa al'amin "maza kaiwa anty ta baka naka" Ledar ta karba sautin sune ita da al'amin, alewar tsinke da chocolate manya manya, jan hannun al'amin tayi suka koma part dinta suka zauna suka fara shan kayan zakin da ya kawo musu, mintina kadan al'amin yayi bacci dan haka ta kwantar dashi kan cinyarta taci gaba da tsotsar alewar tsinkenta, tana kallon tv, Ahankali ya bude kofa ya shiga hangota yayi zaune tanata tand'ar baki da loly pop a hannunta kan cinyarta kuma al'amin ne kwance yana bacci ta dage ta zubawa tv ido, ahankali yaje kusa da ita ya mika hannu zai dauki al'amin nan tayi wata zabura har tana tuttuje bandejin dake kan yatsanta wanda aka nad'e mata ciwon kafarta, "Oh Sir ka tsorata ni banji shigowarka ba" tafada tana mai sauke ajiyar zuciya, "Kawo na rage miki aiki na kaishi daki" mika hannu yayi ya daukeshi nan jikinshi da nata ya hadu wanda yayi sanadiyyar haifar musu da wani yanayi na musamman, daukarshi yayi ya nufi dakinta dashi yaje ya kwantar dashi tare da yi masa addu'o'in kwanciya bacci, bargo yaja ya rufa masa ya fito daga cikin dakin, agogo ya kalla 11 daidai, "Ba zakije ki kwanta ba sai dare ya sake yi?" "Sir sai anjima ina son na karasa kallo ne" Jijjiga kai yayi, ya juya ya fita acan kasan ransa yana tunanin anya kuwa yarinyar nan bata da aljanu? Saboda kullum bata da aiki sai sauraron kida da kallon TV, Komawa sashensa yayi yaje ya kwanta. Washe gari da safe bayan ta kammala yiwa al'amin wanka ta shiryashi cikin wata jar riga wacce ajiki aka rubuta Good boy da bakin wando, "Oya take this, ka kaiwa watchman kace yaje ya siyo min ya baka ka kawo min kaji? Yawwa my boy" kudi ta bashi da yar karamar takarda wacce tayi rubutu ajiki, Da gudu ya fice ita kuma ta shiga wanka, bakin gate yaje amma mai gadin baya nan sannan kofar gidan akulle take, da gudu ya juya ya shiga part din abbunshi,acikin dakinsa ya sameshi yana kwance akan gado, "Sabahul khair abbuna, gashi inji anty na tace asiyo mata" Karb'ar takardar jabir yayi ya bude ya tashi zaune, always ta rubuta ajikin takardar, Drawer din gadonshi ya jawo anan yaga akwai saura guda biyu kasancewar yana siyowa ummu al'amin kuma anan yake ajiye mata sannan itama goodness din yakan siyo mata duk lokacin da yayi mata provision na kayan amfanin gida wannan watanne kawai ya manta, Dauka yayi da kansa ya tafi kai mata shikuma al'amin ya haye gadonshi yana wasa, lokacin da ya shiga ta fito daga wanka tana daure da towel ta kwanta rub da ciki akan gado tana jiran al'amin ya kawo mata Aiken da tayi masa, "Gashi" ya fada lokacin da yake mika mata ledar, zumbur ta tashi tana kallonsa, "Thank you Sir" "Kar ki sake aiken watchman siyo miki wannan abin, ai ina siyo miki wannan month dinma mantawa nayi" "Sorry sir, bazan sake ba" Kudinta ya mika mata da yar takardar ya juya ya fita Cikin sauri ta shiga shiryawa tana wani dan kasaitaccen murmushi ita kadai, tana kammalawa ta shiga kitchen ta fara harhada abincin karyawa da abincin rana domin church zata tafi kuma ba zata dawo ba sai yamma, Sai da ta gama kammala komai sannan ta debi kwanukan abincin ta nufi sashen jabir, lokacin da ta shiga yana tsaye a tsakiyar falonsa yana latsa wayarshi, kan dining ta wuce taje ta shirya komai ta nufi wurinshi da niyyar sanar dashi cewar zata tafi church, tana tsayawa al'amin na shigowa aguje, da gudu yazo ya banketa ta tafi ta fada jikin jabir, ko tsayawa al'amin baiyi ba yayi cikin dakin abbunshi da gudu, Tana rungume ajikinsa ta dago kanta tana kallonshi shi dinma ita din yake kallo zuciyarsa dauke da tambayoyi kala kala na dalilin da yasa duk lokacin da ya tabata sai yaji wani sabon yanayi yana ziyartar shi koda kuwa dan yatsanta ya tab'a. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [9/11, 10:50 AM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _59-60_ ~~~Kasa sakinta daga jikinsa yayi yana rike da ita yabi jikinta da kallo kanta ta daura bakin dan kwali wanda yana iya hango tarin tulin gashin kitson attach din dake kanta wanda ya sauko har kan kafadunta, blue din body hug ce ajikinta tareda bakar skirt ta jeans wacce tayi mata dadas ajikinta, "Anty, abbuna kuyi hakuri fitsari ne ya matse ni shiyasa na shigo da gudu" Suka jiyo muryar al'amin yana fada daidai lokacin da yake fitowa daga cikin bedroom din jabir, Cikin sanyinshi ya saketa ta matsa daga jikinsa kanta yana kasa, "Sir zanje church" ta fada ahankali, "Ok sai kin dawo" yafada tareda juyawa zuwa kan kujera ya zauna, Kan al'amin ta shafa "my boy sai na dawo ko?" "Sai kin dawo anty kinga nima gurin abbuna zanje muyi wasa tunda ke tafiya zakiyi ungunwa ki barni" "Yawwa al'amin maza kayi wasan kafin na dawo kaji good boy" Kumatunsa ta shafa ta juya ta fita ta koma sashenta agurguje tayi breakfast ta dauki katon Bible dinta da yar karamar jakarta ta fita daga gidan. Lokacin da goodness ta fita daga falon jabir, ido ya zubawa al'amin yana tunanin irin shakuwar dake tsakanin al'amin din da goodness gashi Ummu ta fara yi masa maganar cewar ta samowa al'amin din sch akusa da inda take dan haka nan da d'an wani lokaci kankani zai kai mata shi, "Abbu kaga anty idan zata yi addu'a sai ta rufe idonta kuma ko abinci zata ci wani lokacin sai ta rufe idonta sannan bata yin bisimilla" Muryar al'amin ce ta dawo dashi hayyacinsa, hannun al'amin din ya kama yana fuskantarsa, "Al'amin addininmu da addinin antynka ba iri daya bane, dan haka duk abinda kaga tayi irin na addininsu to kar kayi koyi da ita" "Abbu to itama ka koya mata karatu ka sanar da ita ilimin addininmu saboda ka samu lada da yawa tunda annabi yace idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa suna yankewa in banda abubuwa guda uku, sadaka mai gudana, ko ilimin da ake anfanuwa dashi ko kuma d'a na kwarai wanda zai rinka yi masa addu'a" "Nasani al'amin, insha Allahu zan fahintar da antynka addininmu" "Yawwa abbu jazakallahu khairan" Hannunsa yaja suka koma dining table domin karyawa,Amma acikin zuciyarshi ya dauki niyyar koyar da goodness dukkanin kyawawan dabi'u wanda addinin musulunci yazo dasu kuma zai fahimtar da ita menene musulunci cikin salo da dabaru irin na d'a namiji. Goodness bata samu damar dawowa gida ba sai wurin 6,tana shiga dakinta ta ajiye kayanta ta nufi sashen jabir a falo ta samesu sun baje al'amin yanata rubutu acikin exercise book shi kuma jabir yana rikeda littafin _fiqhul aulawiyyat_ yana nazarinsa, Ahankali ta shiga idonta kan jabir tana kallonsa, "Sannu sir" tace dashi tareda zama akusa da al'amin, "Yawwa" yace da ita a takaice, "Anty kin dawo? Nima kinga abbuna ne yasani rubutu" "Dakyau my boy" Dunkufar da kansa yayi yaci gaba da rubutun yayinda ita kuma ta fara kallon jabir kasa kasa tana nazarinsa acikin ranta, dan mitsitsin bakinsa dake burgeta akoda yaushe ta kalla ta lashi lebenta. Suna nan zaune kowa yana abinda ke gabansa har lokacin salla ya gabato, hankalinta ta mayar kan tv din dake kunne tana faman aiki, "Al'amin tashi maza kaje kayi alwala kazo muje masallaci". Ta jiyo muryar jabir yana yiwa al'amin magana cikin muryarsa sai dan karen sanyi, "Na'am abbu" al'amin ya bashi amsa tareda rufe exercise book din da yake rubutu aciki, Tana zaune tana kallo suka fita masallaci ganin zaman baya yi mata dadi ya sanyata mikewa ta koma sashenta ta shiga wanka ta fito ta shirya ta saka wani wando tied da rigarsa mai gajeren hannu purple colour, tana tsaka da fesa turare al'amin ya fado dakin, "Anty kizo inji abbuna" "Yana ina?" "Yana falonshi yana kallo" Tare suka fito ta kunna masa cartoon ita kuma ta wuce sashen jabir. A falo ta tarar dashi yana jan cazbaha ga tv kuma ya kunna yana kallon din huda tv ya mayar da hankalinsa sosai wurin sauraron program din dasuke gabatarwa a lokacin mai taken _missing ingredient_ wanda sheikh Muhammad salah yake gabatarwa, "Excuse me sir" ta fada ahankali, manyan idanuwansa ya dago ya kalleta kanta babu ko dan kwali ko yar hular ma da take sawa yau bata saka ba, "Dauki wannan grass din ki dafa min da Lipton" "Ok Sir" Na'a na'ar ta dauka wacce ke ajiye akan center table ta juya ta fita, bin bayanta yayi da kallo tabbas dan sura tana da cikakkiyar surar da duk wani da namiji yake bukata a wurin mace,domin yar duma duma ce ita sam bata da rama, singalalinta kuwa cikarsa za tayi cinyar wata siririyar, idanuwansa ya dauke daga kallon kofa ya mayar dasu kan tv yana sauraron dawowarta. Part dinta ta koma ta iske al'amin ya nutsu yana kallon cartoon dinsa, wuceshi tayi ta shiga cikin kitchen ta dafawa jabir na'a na'a ta juyo acikin dan karamin tea flask ta fito, "Anty nima zan sha shayin" al'amin ya fada yana tashi zaune, "Oya zo muje abbunka ya san maka" Tashi yayi yabi bayanta, a yanda ta tafi ta barshi dazu yanzun ma haka ta dawo ta sameshi, hannun al'amin ta kama suka koma sashenta bayan jabir ya tsiyaya masa shayin a kofi, "Wash anty na kona bakina" "Ka ringa fifitawa da bakinka kafin kasha" "Lah anty annabi ya hana hura abinsha da baki" Kallonsa tayi ta jinjima kai "al'amin kenan kai kam komai kasani, ko wanne abu yana ajiye acikin brain dinka, maza kasha kazo muje muyi bacci yau bazan yi kallo ba". *** Watan Ummu al'amin uku da tafiya ta kira jabir ta sanar dashi ya kai mata al'amin tun lokacin yaji babu dadi domin zai rabu da al'amin gashi uwa uba yasan goodness zata shiga wani hali na rashin abokin wasanta amma dole ne shi yanzu ya zame mata abokin wasan domin karta shiga halin zaman kunci acikin gidansa. Sashenta ya shiga dawowarsa kenan daga office misalin karfe _5:30_ na yamma, part din nata tsit da alama babu kowa aciki hakan ya sashi komawa nasa, a falo ya jiyo hayaniyarsu sunata kokawa ita da al'amin yana kokarin sai ya saka mata kadangaren roba ajikinta ita kuma tsoronshi take, tana ganin jabir ta nufi wurinshi da gudu, "Yawwa Sir kaga al'amin wai sai ya saka min lizard" ta fada tana haki, "Abbu wlh na wasane fa bana gaske bane, anty tsoron kadangare take yau ko throughout bata zauna a falonta ba saboda da safe kadangare yabi ta corridor ya shiga falonta" "Ai yanzu ya dade da fita bazai yi ta zama acikin falon ba" "No sir, yana ciki bai fita ba idan munje zaka gani" "Muje Nagani" yace da ita yayinda yayi gaba ta juya tabishi a baya, ta bayansa ta tsaya take tafiya ahankali har suka shiga cikin falon, al'amin yana bayanta ya sadada ya jefa mata kadangaren robar yace "anty gashi nan ajikinki" Wata kara ta saki ta kankame jabir ta baya tana faman shassheka irinta wanda ya tsorata, "Wasa nake anty" har lokacin bata saki jabir ba tana rike da rigarsa ta baya, ahaka suka shiga dakinta ya dudduba ko ina tana makale dashi har ya gama caje dakin ya dawo falo nanma baiga komai ba, kofar falon ta Baya yaja ya rufe ya jiyo yana kallonta yanda ta wani rikeshi tamau kamar wacce za akwace mata shi, "To ki sake ni mana tunda kinga babu komai ai aciki dama na fada miki bazai zauna ba ya dade da ficewa, kuma ki daina barin kofar baya a bude kina rufeta dan ta nan zai rinka shigowa" "Yes Sir" ta fada tana mai sake rike rigarshi al'amin kuma yana binsu yana yi mata dariya, Bata sakeshi ba har suka fita daga falon duk ta yamutsa masa rigar sa, sashensa suka koma gaba dayansu, a falo ya barsu ya shiga bedroom dinsa yayi wanka ya sake kayan jikinsa daga shaddar dazu zuwa doguwar jallabiya fara, kansa babu hula ya dawo falon ya hau kan dining ya fara cin abinci jalop din shinkafa da kifi, yana ci yana kallon su sunata kiriniya suna yin puzzle game, sai da ya kammala sannan ya dawo inda suke, "Goodness ki fara hadawa al'amin kayanshi domin nan da sati biyu zan kaishi wurin ummunshi" Kanta ta dago zuciyarta babu dadi tace "to sir" Shi kansa al'amin din yayi wani irin sabo sosai da goodness din wanda ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu, kamar wadanda aka zarewa laka ajiki haka suka dawo. Tun daga lokacin ta wankewa al'amin kayansa gaba daya ta harhada masa dukkan abubuwan da tasan nasa ne sa'arta daya mamanta ta kirata a waya tace ta sanar da mijinta zasu tafi okene nan da sati biyu tunda hakane tana ganin tafiyar tasu zata zo lokaci daya da tasu al'amin amma duk da haka tasan zata yi missing din al'amin sosai. Lokacin da ta sanar da jabir maganar tafiyarsu okene ita da mamanta bai hanata ba saboda yana ganin itama zata samu damar rage damuwar da zata shiga na tafiyarsu shida al'amin, kudi ya bata _50_ thousands yace tayi duk wata hidimarta ta tafiyar domin daga can har Lagos zasuje ita da ma da yayarta Bilkisu. Ranar da su jabir zasu tafi ta shirya al'amin tayi masa kwalliya cikin shadda fara riga da wando harda hula shi kuma jabir ya shirya cikin yadi kalar ruwan madara da hula itama milk colour, hatta takalminsa milk colour ne hannunsa daure da agogon azurfa fari, "Al'amin zanyi missing dinka sosai, idan kaje ka gaida ummunka, ka zama good boy kamar yanda na sanka" tafada hawaye suna kokarin zubo mata, "Nagode good anty, abbuna yace bazan dade ba zan dawo kuma yanzu tare zaku nayin wasa kafin na dawo" ya fada cikin surutunshi irin na yara, Hannunta jabir ya kama "menene abin kukan? Sai kace wanda za a mutu? Kiyi hakuri pls, sai na dawo" Yana gama fadin haka ya saki hannunta ya kama na al'amin suka fita zuwa harabar gidan tana tsaye tana hangosu har suka shisshiga mota, motar ta harba tabar harabar gidan. Komawa tayi ta zauna tana kuka marar sauti domin ta shaku da al'amin sosai, yaron ya shiga ranta saboda basirarsa gashi komai nasa irin na mahaifinsa ne, haka ta zauna ranar kamar wata marar lafiya har dare yayi, koda taje makwancinta ma al'amin taketa tunawa musamman irin wannan lokacin idan tazo ta kwantar dashi sai taji yana addu'a, _"Da sunanka ya Allah nake mutuwa, kuma nake rayuwa"_ Idan kuma Safiya tayi abinda yake fara fada shine _"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya rayani bayan ya karbi rayuwata kuma gareshi tashi yake"_ irin wadannan yan guntu guntun addu'o'in da yake yi duk ta rikesu, gashi wani abin burgewar ko bandaki zasuje idan zata yi masa wanka sai yayi addu'a kafin ya shiga hakama idan zai fito sai taji yana fadar wata kalma. Haka ta kasance cikin kewar al'amin da jabir har bacci yayi nasarar yin gaba da ita, washe gari da asubar fari ta tashi tayi wanka ta shirya ta dauki jakar kayanta ta tafi gidan ma lokacin har Bilkisu yayarta ta karaso dan haka babu bata lokaci suka dunguma suka tafi tasha anan suka samu mota suka dauki hanyar okene. Tun safe basu suka isaba sai bayan sallar isha, gaba daya goodness ta gama gajiya likis, basu jima da sauka ba jabir ya kirata, gaisawa kawai suka yi ya bata al'amin suka fara hira, sun jima suna shirmensu tana biye masa kafin suka yi sallama tun daga lokacin kullum sai jabir ya hadasu a waya ita da al'amin yayita bata labarin _madina_ da labarin ummunshi ko kuma abbunshi ya siyo masa kaza yau sunje wuri kaza. Satinsu daya a okene suka tafi Lagos tunda suka shiga Lagos taga kayayyakin da suka burgeta na maza nan ta zage ta siyawa mr cool dinta domin ta dauki aniyar mayar dashi niga acikin gidanta, underwear na maza ta sissiya masa Sannan ta sai masa short trousers kala kala wurin kala biyar ta koma ta kwaso masa body hug irin ta samari wacce tasan zata yi masa kyau mutuka sannan ta debar masa jeans,da hadaddun kayan bacci na maza masu ado na burgewa da bada sha'awa wanda tasan zasu karbeshi iya karba, akwati medium size sai da ta cikashi da kayan jabir, _"no more wear any doguwar riga or jallabiya inside my house again my cool"_ta fada tana muskilin murmushi, kulewa suka yi acikin daki ita da yayarta tana mai sake bata wasu dabaru na kulawa da mai gida wanda ba duk macece ta sansu ba, zan kawo muku su a shafi na gaba. _*Ummi Shatu*_πŸ‘ŒπŸ» [10/11, 2:52 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [9/12, 1:07 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE............!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _61-63_ ~~~Dabarun kulawa da mai gida wanda ba duk macece ta sansu ba yayarta ta fara bata, dafa kafadarta anty Bilkisu tayi tace da ita, "My dear sister hak'ik'a nasan a zaman da kikayi ko kuma ki keyi agidan aurenki baki taba sanin mai ya kamata kiyiwa mijinki ko kuma ki aiwatar gareshi ba dan haka to ga shawarwari ko kuma ince hanyoyi guda goma sha biyar wanda suka kamata ace ko wacce mace ta sansu kuma ta kiyayesu domin samar da zaman lafiya tsakaninta da mai gidanta da kuma tabbatar da dankon kauna a tsakaninsu, ina so ki bude kunnuwanki sosai ki saurare ni da kyau domin fahintar karatun da zan koyar dake a halin yanzu, Abu na farko da ya kamata ki sani kuma ki kiyaye shine daraja mijinki da kuma ganin girmansa da kimarsa, anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar auratayya kar wai dan kina ganin ya zama kamar abokinki ki rainashi, a'a anfi so mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban acikin zuciyarta da kuma fili, Na biyu kuma shine ki girmama iyayensa da yan uwansa tamkar yanda zaki girmama naki iyayen da yan uwan kar ki kuskura kiyi aiki da wannan karin maganar wacce hausawa ke cewa "'ba a iya musu ya dangin miji"',duk namiji yana son a girmama iyayensa da yan uwansa, Abu na uku shine ki zama mai mutukar hakuri da juriya agidan aurenki domin zaman aure zama ne na hakuri da kawaici, ki k'i ji ki k'i gani sai ki zauna lafiya da mijinki, Abu na hudu kuma shine kar ki zama d'aya daga cikin matan nan masu bayyanar da sirrin mazajensu da sirrin gidan aurensu ga kawaye ko kuma abokan gaisawa hakan haramun ne, Sai abu na biyar shine ki kasance mai tattalin dukiyar mijinki ma'ana banda almubazzaranci da kayan miji, ki kasance mai tattalin dukiyarsa da kayansa domin kowanne namiji yana k'in jinin yaga yasha wahala ya nemo abu sannan an wulakanta, Abu na shida shine kar ki zama mai yawan bin k'wakk'wafin mijinki, komai yake yi idonki da kunnenki akai, kar ki zama haka domin maza basu kaunar mace mai bin diddigin abubuwan da suke yi, Abu na bakwai shine binciken wayar miji ko kuma abubuwan da ba su shafeki ba, kar ki zama mai yawan binciken al'amuran mijinki wanda bai saki aciki ba domin duk namiji baya son bincike da tuhuma, Sai abu na takwas shine kula da abincin mijinki, ki zama macen data kware wurin iya girki domin hakan yana sawa miji yaji kin kara shiga cikin ransa, Abu na tara shine ki zama macen da ta iya furtawa mai gidanta maganganu masu laushi da taushi, kar ki zama daya daga cikin matan da basu iya magana ba duk kalmar da tazo bakinsu sai su kwabawa mai gida ita,kar ki zama daga cikinsu, Abu na goma shine kar ki yarda ki rinka daga muryarki sama da ta mijinki, akoda yaushe idan kina magana da mijinki to ya zamana muryarki ce a kasa tasa a sama, Abu na goma sha daya shine ki zama mai iya kallon soyayya domin kallon da zaki yiwa mijinki ana so ya banbanta da kallon da zaki yiwa sauran mutane, idan kina kallon miji anfi son ki karkada idanuwanki ki sauya musu launi su koma tamkar kina jin bacci yanda zaki ja hankalinsa gareki, Sai abu na goma sha biyu shine kula da tsafta, mata da yawa suna sakaci wurin kulawa da tsabtar jikinsu da ta muhallinsu, to agaskiya ya kamata su gyara saboda duk namijin duniya baya son mace k'azama yafi son kullum yaga gidanki a tsaftace jikinki a tsaftace, Abu na goma sha uku shine ki zama macen data kware wurin iya kwalliya, maza suna son macen data iya kwalliya sosai kar ki zama irin matan nan da sam kwalliya bata damesu ba sai dai su zauna kullum fuskarsu a kod'e wannan kuskure ne babba domin maza da dama abinda ke sakasu kara aure shine matansu basa kwalliya kullum jiya iyau alhalin kuma ita mace "yar kwalliya ce koda yaushe ana son aganta dadas kamar fulawa, Sai abu na goma sha hudu kar ki zama mai tsananin kishi domin zafin kishi baya haifar da zaman lafiya tsakanin mata da miji, Abu na karshe nagoma sha biyar shine ina so ki bani aron hankalinki kiji abinda zan fada miki, abu na karshe ki zama yar soyayya, ki zama macen da ta kware a fagen soyayya sannan ki nunawa mijinki so da kauna, ki rinka zama kina shiryawa mijinki kalamai na kauna da soyayya wadanda zaki rinka tararshi dasu da zarar ya dawo gareki, ki nuna masa shi kadai kikeso acikin maza sannan shi kadai ne namijin da yake burgeki, ki kula da duk wani motsinsa da abinda yafi kauna atare dake, kar kiyi sakacin kasa gane yanayin da yafi sha'awar ganinki atare dashi da irin sutturar da yake son ki rinka sakawa aduk sa'ilin da kuke tare, Ki nazarci abubuwan da suka fi sakashi nishadi atare dake sannan ki kasance akoda yaushe mai nuna son kasancewa dashi kar ki nuna gajiyawa dashi kuma kar ki rinka hanashi kanki aduk lokacin da ya nuna bukatarki domin maza suna tsanar mace mai irin wannan halin, Ina so ki lak'anci gyara jikinki da kayan gyara wadanda ko a lafiyar jiki basa cutarwa kamarsu kankana, madara, zuma, da sauran yayan itatuwa, sannan ki tabbatar kullum jikinki yana fitar da kamshin dadi yanda mijinki zai rinka dokin zama kusa dake, Sannan ya zama wajibi ki gane yanayin mijinki a makwanci domin mata da dama sunada matsala sai ka samu mace tafi shekaru goma da mijinta wata ma fiyeda haka amma bata taba samun gamsuwa atare dashi ba dalili shine tana jin kunyar ta sanar dashi ko kuma ta nuna masa hakan, wata matar kuma zaka samu mijinta sam bashida yawan bukata ita kuma tana bukatarsa to ba zata iya nuna masa ba haka zata hakura ta danne har sai lokacin da shi yaji yana bukatarsa dan kansa saboda ita tana kunyar nuna masa cewar tana bukatarsa to duk wannan kuskure ne, ita mace ana son ta zama mai kunya acikin mutane amma kuma acikin dakin mijinta anfi son ta zama fitsararriya wacce bata da kunya kuma hakika maza sunfi son irin wannan matar domin itace take gamsar dasu take yi musu duk abubuwan da suke so, Ta cikin kissa da dabara zaki nunawa mijinki kina son kasancewa dashi wanda ta sanadiyyar haka shima zaiji yana bukatarki ba tareda ya shirya ba amma rashin wayewa ne da iya zaman aure mace ta shafe sama da sati uku ba tareda mijinta yaga wani abu a tare da ita yayi sha'awarta ba, (masu karatu kar kuce ummi A'isha ta cika rashin kunya bari nayi shiru haka amma agaskiya matan hausawa muna yiwa kanmu illa da yawa, kunya tana cutarmu sosai), Dafa kafadar goodness anty Bilkisu tayi tana murmushi, "yanzu abinda nake so dake shine ina so ki zauna ki nutsu ki gane mijinki wanne irine a ta fannin rayuwar auratayya domin ki san irin abubuwan da ya dace kiyi masa dan ganin rayuwar aurenku ta inganta", Jijjiga kai goodness tayi duk tana cikeda kunyar yayar tata "thank you anty" Tun lokacin ta zauna da niyyar yin duk wasu abubuwan da yayarta ta koyar da ita, satinsu daya a lagos suka dawo gida, gidanta ta wuce bayan sun gaisa da mahaifinta, tana zuwa gida ta ajiye kayayyakinta tabi lafiyar gado ta kwanta sai da ta sha bacci ta more sannan ta tashi ta kikkintsa gidan tayi wanka tana tunanin jabir aranta domin yau ba suyi waya ba kwata kwata. Kitchen ta shiga ta dafa indomie ta je falo ta zauna ta kunna tv tafara kallon Nigerian film, tana nan zaune har jabir ya kirata, Murmushi tayi ta dauki wayar ta lankwashe murya "hello sir" wani yar yaji ajikinsa saboda yanda tayi maganar yau ya banbanta da na kullum, "Ya gida?" Ya fada cikin muryarsa mai mutukar sanyi da dadi, "Am cool sir but am still missing you" ta fada bayan ta sake kasa da muryarta, "Gobe zan dawo ai, me zan siyo miki? Koda yake nasan abinda zan siyo miki" ya fada shima muryarsa kasa kasa, "Sir what? Me zaka siyo min? Chocolate?" Ta ce dashi tana mai tausasa harshenta ta yanda muryar tata zata sake zaki da taushi, "No,i will buy u hydrogen, so that kinga next time idan kika sake jin ciwo sai asaka miki" ya fada yana mai yin murmushinsa mai sanyi, "No Sir, i don't like it, pls don't buy me hydrogen, chocolate nake so" Wani irin shock yaji tun daga babban dan yatsan kafarshi har zuwa cikin kwakwalwarshi saboda yanda tayi maganar cikin shagwaba da kuma wani irin salo na daban. "Where is my boy?" Ta sake fada ahankali domin jabir ya kasa sake magana, "Gashi" ya fada dakyar, al'amin ya bawa wayar wanda yake kwance akan ruwan cikinsa domin ummu ta fita cikin gari, yana jinsu sunata shirmensu ita da al'amin, sunfi rabin awa sunata surutu kafin suyi sallama, karbar wayar yayi ya kashe yana kallon al'amin amma acan kasan ranshi tunani yake yi shin wanne abune yake shirin faruwa dashi ne yanzu akan goodness? Shi dai har yanzu he didn't believe that he's in love with her, sannan yasan yanzu dai bashida burin yin rayuwar auratayya da ita,ya shafe tsawon lokaci yana tunani amma ya kasa gane cewar ya kamu da soyayyar goodness ko kuma akasin haka. Daren ranar yaje supermarket shida al'amin ya fara debowa goodness tsarabar chocolate din da take so amma yana son ya siya mata wani abu mai muhimmanci sai dai ya rasa abinda zai sai mata, tunowa yayi duk lokacin da yazo umarah ummun al'amin tana bashi sautun farin almiski duk da bai san abinda take yi dashi ba amma yasan dai yana da amfani agun mata, hakan da ya tuno ya sashi siyawa goodness farin muskin har guda goma sha biyu, wato dozin daya, Wasu kayan bacci ya hango masu mutukar kyau da daukar hankali ajere a wani bangare, sai kawai ya tsinci kansa da son siyawa goodness kayan saboda yasan ba karamin kyau kayan zasu yi mata ba duk da ba wai zai bata su yanzu bane, Wurin kayan yaje ya zabo guda biyu daya pink colour ce yayinda dayar kuma milk colour amma kayan sun tafi da hankalinsa domin shara shara ne sosai kuma masu santsi ne ba masu laushi ba, daga kirji anyi yar karamar bra ajiki sannan ga dan siririn hannun nan irin na bra, tsayinta bazai wuce iya cinya ba gashi yadin jikin rigar kamar net yake, Gurin biyan kudi yaje ya biya kudin rigunan kowacce guda daya kimanin naira dubu biyu ta kama, "Abbu Anty ka siyawa ko ummu na?" Al'amin ya jefo masa wannan tambayar, "Antynka na siyawa" ya fada atakaice, "Shukran abbu i know this dress will suit my anty" Murmushi yayi yaja hannun sa suka fita, koda suka je gidan ma bai bari ummu ta gani ba boyesu yayi cikin wata jakar kayanshi domin yasan idan ta gani ko bata fada masa ba sai taji bacin rai tunda ya fuskanci su mata komai abin yiwa kishine awurinsu. *** Goodness kuwa ba karamin farin ciki ta shiga ba domin jabir bai taba yin doguwar hira da ita ba makamanciyar wannan tabbas yanzu ta kara samun karfin gwiwar nuna masa soyayya zalla gashi ta kara samun dama tunda yanzu su biyu zasu kasance agidan babu al'amin babu ummu al'amin. Tunda anty Bilkisu ta fada mata kayan gyaran jiki ta fara hadawa da kanta, yau kwakwa da dabino da kankana da zuma da peak ta ruwa ta bawa mai gadi ya siyo mata a kasuwa, gaba daya hadasu tayi tai blending dinsu acikin blender ta saka zuma ta juyo peak gwangwani daya ta ruwa ta saka acikin fridge, ita ta wuni tana sha har dare kasancewar da yawa tayi. Washe gari ma ranar da jabir zai dawo sai da ta sake hadawa cikin babban jug sannan ta shiga kitchen ta shiryawa jabir farar shinkafa da miyar hanta wacce tasha kayan lambu duk da dai bai kirata ba amma yayi mata text cewar karfe _4_ zai sauka. Tana gama dukkanin ayyukanta ta shiga wanka ta sillo jikinta ta fito, kwalliya tayi ta gyara fuskarta sosai tasha jan baki dau akan lips dinta kusan kwalliyar da tayi yau tafi ta kowacce rana da ta saba yi tun bayan zuwanta gidan, Doguwar riga roba ta saka baka mai layi layin kaloli ajiki kama tun daga blue, pink, red, white da sauran kaloli daban daban, rigar tsayinta har kasa yake sannan tanada gajeren hannu amma mai kama jiki ce sosai, kasancewar tayi gyaran gashi tun a lagos ya sata daura dan siririn bakin dan kwali akanta, kamar kullum yauma turaren _rocking girl_ ta fesa bayan ta shafa roll on kala daban daban, agogon dakinta ta kalla karfe 3:58 na yamma hakan ya sata komawa falo ta zauna ta fara kallon wani Nigerian film da ta tarar ana nunawa a tashar _African magic_ mai suna _ladies without borders_ kallonta take yi cikin nishadi har lokaci yaja sosai ba tare da ta sani ba, tana nan zaune taji alamun shigowar mota cikin harabar gidan, daga kai tayi ta duba lokaci,karfe _5_ saura minti _9_ ,zumbur ta mike ta leka _window_ jabir ta hango yana fitowa daga cikin mota yana yin waya hannunsa kuma dauke da littattafan addini wanda bata san ko na menene ba yana sanye cikin bakar doguwar riga ta jallabiya haka kansa ma kamar kullum yasa yar mitsitsiyar hula baka, cikin sanyinshi yake tafiya yana magana a waya, Sai da ya bacewa ganinta sannan ta koma kitchen taje ta kwaso kayan abincin da tayi mishi ta zuba cikin wani katon _basket_ ta kinkima ta nufi sashensa, yana kwance sambal akan doguwar kujera kansa yana kallon sama har yanzu wayar yake yi bai gama ba amma ayanda ta dan fuskanta da ma'aikatan office dinsa yake wayar, kallonsa tayi ahankali daidai lokacin da taje wucewa ta gabanshi, "my cool ba dai tsayi ba" ta fada acikin zuciyarta domin gaba daya kujerar ya dan zartata kafafuwansa sun wuce hannun kujerar. Kan dining ta wuce taje ta fara jera flaks din abincin, binta da kallo jabir yayi rigar jikinta gaba daya ta gama bayyanar da surar jikinta,kallonta yaci gaba dayi yana waya yana karewa halittar jikinta kallo a karon farko ya fara kissima yanda halittar ta take, doguwa ce ba can ba amma tanada kiba dan har tsayin nata ya buya ata sanadiyyar kibar tata, tanada dantse masu kauri gata da cikar kirji sosai, hips dinta da mazaunai kuwa abin ba acewa komai, fatarta baka ce dan har ya dan fita haske ma duk da cewar shima bakin ne, tanada round face ma'ana fuskarta a kewaye take mai dauke da fararen idanuwa madaidaita zagayayyu masu zubin k'wai, tana da yalwar gashin ido dana gira, sannan tanada zankadeden dogon hanci tamkar ummi A'isha ta sammata, bakinta shima zagayayye ne ba mai girma ba sannan ba dan tsul ba sai yar hab'arta wacce ta sake kawata fuskar tata domin harda dan beautiful point a tsakiyarta, Idanuwansa ya sauke daga kallonta ya mayar dasu kan carpet, tana kammala jera masa abincin ta koma inda yake ta tsaya tare da zuba masa ido, zara zaran yatsun hannunshi ta kalla na tsakiyar da na kusa dashi duk sanye suke cikin zoben azurfa, yan yatsun nashi yake lank'wasawa suna k'as k'as, yayi kyau sosai yau dinnan, Tana tsaye har ya gama wayar ya tashi zaune yana kallonta, "welcome sir" "Yawwa thank you, ya hanyar okene kun dawo lfy?" "Yes Sir lfy lau, ina al'amin?" "Al'amin yana gaisheki shida ummunshi" "Ina amsawa sir" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya shiga cikin bedroom dinshi, kujera ta samu ta zauna, mintuna goma sha biyar sai gashi ya sake fitowa cikin wata farar doguwar jallabiya bisa dukkan alamu wanka yayi, Kan dining table ya wuce ya zauna ya zuba abincin data jere masa yaci, sai da ya k'oshi sannan ya dawo falon ya zauna ya dauki remote ya kunna tv ya kamo huda tv, hankalinta itama ta mayar kan tv din wurin kallon program din da suke gabatarwa a lokacin _(financial crisis and Islamic analysis by sheikh Muhammad Akbar India)_,shima jabir hankalinsa duk ya tattara ga program din, suna nan zaune basu sake magana ba har lokacin sallar magrib yayi domin shi jabir mutum ne shi marar surutu, kallonta yayi yace, "Bari naje salla nadawo" "Adawo lafiya Sir" tace dashi, mikewa yayi ya fita ya tafi masallaci ita kuma taci gaba da zama awurin. Sai misalin karfe 8:30 jabir ya dawo gidan har lokacin goodness na zaune a inda ya barta tana kallo amma ta canza channel daga huda tv zuwa mbc 3 abin ma dariya yaso bawa jabir lokacin da ya shigo ya ganta tana kallon cartoon, "Kin zama al'amin ne?" Ya fada yana tsareta da manyan idanuwansa, "No sir" ta bashi amsa, "Koda yake naga kema banbancinku da al'amin din kadan ne" ya fada tareda zama akan kujera, "No,nidai nafi al'amin sosai kadaina cewa mate dina ne shi" tafada cikeda shagwaba tareda tsuke dan madaidaicin bakinta, kallo ya bita dashi shidai shagwabar da take yi mishi ba karamin burgeshi take yi ba, "To in banda yaro ki fada min wanda yake bada sautun chocolate" ya fada ahankali da niyyar sake zolayarta, "Dan na bada sautun chocolate shine zaka cemin nima small girl ce? Am not small girl" tafada cikin wata shagwabar, murmushi yayi ya cire hular kanshi ya fara shafa sumarshi. _*Ummi A'isha*_πŸ‘ŒπŸ» [10/11, 2:52 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [9/12, 9:59 PM] Ummi A'ishaπŸ‘ŒπŸ»: *WANI HASKE........!* _*NA*_ _*UMMI A'ISHA*_ _64-66_ ~~~ Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *