Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 27 July 2017

ABUN SIRRI NE

adsense here ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com *ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* COMING SOON!!!!! Na ‘yan uku MUNAYSHAT HANEEFAH USMAN STYLISH BCH *MHS* ®NWA ☆☆☆☆☆☆☆☆ Parking tayi adaidai lokacin da wata motar ta paka a kusa da ita acikin farfajiyar wani matsakaicin gida mai kama da guest house, kusan atare suka fito daga motarsu. Kallo d’aya zaka musu ka gano irin manyan mata ‘yan bokon nan ne, murmushi suka sakar ma juna sannan suka nufi ‘kofar da zai sada su da asalin cikin gidan. Ajiye handbags nasu sukayi gami da zama a kujera na zaman mutum biyu. Farar ce ta fara magana “Hajiya Rahma, yau dai nasha mamaki” Haj. Rahma tace “Me ya baki mamaki har haka Haj. Hafsat?” “Ya akayi yau muka iso lokaci daya bayan kusan kullum sai na jiraki kusan minti talatin kafin kizo?, ko yaran basunan ne?”, cewar Hajiya Hafsat Dariya Haj. Rahma tayi sai tace “Wallahi yau wani dabara na tsiro, inaga kuma da hakan zan dinga fakewa daga yau tunda y’ay’an nawa basu ta’ba barina nasha iska” Gyara zama Haj. Hafsat tayi tace “Haba tawan?, gayamin ya kikayi?” “In gayamiki, ina gama shiri nah nafito parlour sai tambaya na sukayi wai ina zanje?, zama nayi akan kujera nace akwai wani organization da muke so mu fara ne don taimakawa marayu da marasa ‘karfi, duk suka jinjina kai cike da gamsuwa da kuma tausayawa sai Rafee tace “Allah sarki, in kun fara nima zan bada tawa gudunmawar, marayu abun a tausaya ma ne”. Nan fah Leena da ta fisu ustazanci ta dinga zuba maganganu irin dai na masu tsoron Allah, ni dai jinjina kai na dinga yi don ban so ta d’au lokaci tana jawo min ayoyi, daga ‘karshe ma sai cewa tayi zata bini, bakiga yanda na rikice ba amma cikin ikon Allah sai naci sa’a dabara ta fad’omin nace “Nan da wata biyu dai maybe mun gama komai, ki bari sai lokacin duk zamu dinga zuwa” Haj. Hafsat tace “Wata sabuwa inji d’an chacha, toh yanzu ke in wata biyun sun cika ya zakiyi da ita in tace zata biki?” Haj. Rahma tayi murmushi tace “Na samu abun fakewa in zamu had’u muyi soyayyar mu, kinga yanzu zasu bar damuna akan ina zanje don zasuyi tsammanin abubuwan bud’e ‘kungiyar ne yake sani rashin zama sosai ba wai yawo nah nake tafiya ba, in watannin da na gaya musu ya cika kuma abu mai sau’ki ne, zan dinga ce musu abubuwan ne sun kasa had’uwa, kinsan dai zasu yarda tunda 9ja muke inda abubuwa suke zama long procedures” Dariya Haj. Hafsat tayi tace “K’awata kanki yana chaji, zamu sake kamin su gano ‘karya kika musu” “Kamin su gano zamu ‘kir’kiro sabon plan, bazan ta’ba yarda su sa katanga tsakanin mu ba” inji Haj. Rahma Kashe ido d’aya Haj. Hafsat tayi tana murmushi ta nufi wani d’an ‘kofa sai wani rangwad’a takeyi, mi’kewa Haj. Rahma tayi itama tabi bayanta suka kule a d’aki. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Haj. Rahma tana barin harabar gidanta Rafee da Sofy suka tafa sannan suka kwashe da dariya. Rafee tace “Sister mun iya saka matar nan acikin duhu fah wlh” Sofy tace “K’warai kuwa, ita a tunaninta agida fah muke yini, batasan….” “Tana sa ‘kafa ta fita mu ma muke tamu hanyar ba” Rafee ta ‘karasar Wani dariya suka sake sawa sannan Sofy ta mi’ke tace “Barin tashi na shirya don Bash ya kusa isowa, har na ‘kosa na ganmu a wajen partyn” Rafee ta d’auki wayarta tana dannawa tace “Nima yanzu zan mi’ke na shirya don Nazee zatazo ta d’auke ni muje wani waje” Bayan dukkansu sun fita kaman ba musulmai ba cikin tsinannun kayaki ba ko d’ankwali balle gyale ne Leena ta zabga uban tagumi tana mai tausaya ma rayuwar yayyunta guda biyu, ita dai tafi ganin laifin Momy wato Haj. Rahma don a tunanin Leena da ace momy tana zama agida dasu, da Rafee da Sofy basu ‘bata tarbiyar su ba, amma ina!!, momy ba abinda tasa agaba sai yawo, bata ta’ba yini agida, yau tana meeting anan gobe ta tafi wani biki ko suna, haka dai rayuwar yake tafiya. Wani lokacin kuma Leena tafi ganin laifin mahaifinsu don da ace ya damu dasu da bazai ta’ba nisa dasu har tsawon watanni ba, daddy ba abinda ke gabanshi irin harkokin business nashi wanda ya fifita akan matarshi da ‘ya’yanshi yanmata guda uku, sam bai damu da sanin halin da suke ciki ba, momy haka zata wuni yawo shiko ko a jikinshi, in mutane sun mishi magana sai yace shi bai son takura ma familyn shi, hawaye ne ya sulalo daga idanunta, a fili tace “Ya Allah ka shiryar da yayyu na ka kuma karkato da hankalin daddy zuwa garemu, ya Allah ka nitsar da momy ta bar yawo ta dinga zama damu agida”. ☆☆☆☆☆☆☆☆ “Haba Fu’ad, abinda kakeyin nan aganinka ya kamata?, mesa abubuwan da bakayi a 9ja in mun zo nan kakeyi?, kana ganin don iyayenmu basu nan sabida haka basu san me kakeyi ba sai kayi abinda kaga dama?, wato kana tsoron yi agida Nigeria don bakason iyayenmu su sani amma baka tsoron azaban Allah?, kana tsammanin baya ganinka ne?, haba Fu’ad, kullum abu d’aya?, don Allah ka chanja hali ko kuma na kira gida na gaya musu” Fu’ad ya kama ‘kafafun Suhal yace “Im sorry bro, bazan sake ba, na tuba, kar ka gayama Abba, kasan halinshi, zai iya hanani cigaba da karatuna, Ammi kuma kasan tanada ciwon zuciya, ka rufamin asiri, daga yau bazan sake ba” Suhal ya girgiza kai yace “Allah yasa, kullum kana cewa zaka daina amma sai abinda yake ‘karuwa”. Tohh fah jama’a, ku biyomu ‘yan uku MHS kuji yanda wannan labarin yake, muna fatan za ayi amfani da abinda zai koyar. Sai kun jimu ba da dad’ewa ba. *MHS* ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 5-10 *ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *(MHS)* ®NWA *5-10* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Leena ce cikin motar ta blue mai suna matrix, cikin natsuwa take tu’kin, gate d’in makarantar su (Northwest University, Kano) tadanna kan motar, kowa yaga tu’kin da takeyi sai ta burge shi, gaban department dinsu ta tsaya, jakarta tabud’e taciro ni’kaf d’inta ta d’aura a saman hijab d’inta sannan ta fito ta kulle motar. Lecture room ta nufa cikin tafiyarta mai cike da nutsuwa, gab shigarta lecture room d’in wayarta tad’au ruri “Sis Rafee” tagani jikin screen d’in wayar, murmushi ne yasauka saman fuskarta, a fili tace “Oh my swt sis, me kuma yafaru?”, sannan tayi picking ta kai wayar kunnenta. Daga d’ayan ‘bangaren ba ko sallama Rafee tace “Leena, mum tadawo ne?” Leena cikin kulawa tace “Sister, wai tun jiya ina kika shiga ne?, lafiya ‘kalau kam ko?” Tsaki Rafee taja, cikin masifa tace “Amsa zaki bani ko tambayata zaki tsaya yi?” “Sorry sis, har na bar gida d’azun nan nazo school bata dawo ba, ban sani ba dai ko bayan fitana ta dawo”, ta ‘kara da cewa “Ina Nazee take?” Leena ta fad’a cikin sanyin jiki “Bansani ba, ki kirata in kinaso”, Rafee tabata amsa cikin masifa sannan ta kashe wayar. Leena ta ciro wayar daga kunnenta tana ‘ko’karin maida shi hand bag nata tana tunani “Oh ni Leena, ko yaushe yayyena zasu shiryu oho”, ‘dayan bangaren zuciyarta yabata amsa “Sai lokacin da mum da dad suka fara zaman gida”. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta shiga aji don duba hand-out nata kamin lecturer ya shigo. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Hajiya Rahma ne ke d’aura d’ankwalin ta agaban dressing mirror dake guest house da suke zuwa da ‘kawayenta, tana gamawa ta d’auki jakarta ta rataya, daidai lokacin Hajiya Hafsat tafito daga toilet tana tsane jikinta da towel. Haj. Hafsat ta kalleta sannan tace “Har kin shirya zaki wuce kenan” “Gwanda na tafi yanzu don kinga asali ma ba da niyyan kwana nazo ba gashi har na kwana, nasan yaran nan zasuta tunani ko wani abu ne ya sameni ko kuma na bazama wani wajen, barin je na shirya ‘karyar dalilin kwanan da nayi” Haj. Rahma ta fad’a tana murmushi Haj. Hafsat ta tako zuwa inda Haj. Rahma take tsaye sai tayi pecking nata gami da rad’a mata a kunne “Daren jiya yayi dad’i, sai mun sake had’uwa” Haj. Rahma ta rungumeta tace “Kwana biyu nasan da ‘kyar na samu damar fitowa, koma yaya dai zamuyi waya” Ahaka Haj. Hafsat ta rakata har ‘kofar parlour sannan suka d’aga ma junansu hannu alamar bye-bye. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Haj. Rahma tana danna kan motarta cikin gidan taga Sofy jingine ajikin motar sanye da riga da wando tana hira da Bash. Afusace tayi parking sannan ta nufosu. Sofy bata lura da ita ba saida ta iso daf dasu, Bash yana ganinta yace “Sannu da dawowa” gami da rusunawa kad’an. Ta amsa mishi ba yabo ba fallasa sannan ta watso ma Sofy wani uwar harara sai tayi ‘kwafa ta wuce cikin gida. Jiki na ‘bari Sofy tace ma Bash “Barina je wajen mummy, naga like she is in a bad mood” Matsowa kusa da ita yayi yana faman rungumeta amma sai tayi saurin ja da baya tana waigawa, a rikice tace “Not here, don Allah ka rufamin asiri, kai kanka kasan halin mummy kuma kasan ba son maganarka takeyi ba, yanzu in ta ganmu rungume da juna Allah ne kad’ai yasan masifar da zan sha, in banci sa’a ba ma har marina sai tayi, katafi, sai munyi waya”, tana kaiwa nan ta juya ta nufi parlour ba tare da ta sake waiwayan Bash ba. Tana bud’e ‘kofa taga mummy sai kai komo takeyi a tsakar parlourn, da ganinta ansan tana cikin ‘bacin rai. Cikin babban murya tafara magana “Sofy, mesa bakijin magana?, wato bazaki rabu da d’an iskan saurayin kin nan ba ko?, me kike samu a wajenshi da kika li’ke mishi haka?” Sofy da ta gama tsurewa tace “Mummy ina sonshi, yace kuma zai aureni” Wani ashar ta duruma sannan tace “Ni kike gayama wai sonshi kikeyi?, wallahi kinji na rantse miki, karki kuskura na ‘kara ganinshi a gidan nan, in ba haka ba zaki yaba ma aya za’kinta” Sum-sum ta nufi d’akinsu tana mamakin hali irin na mummy, ita bata zama dasu, bata bincikar halin da suke ciki, batasan shige da ficensu ba, batasan me suka sa gaba a rayuwarsu ba, bata damu da sanin me suke shukawa a doron ‘kasa a bayan idonta ba, ba, ba, ba, ba, mara adadi don ita kullum yawonta take tafiya amma abun mamaki abun dariya wai in ta ‘kyalla ido taga sunyi abu guda d’aya mara kyau to fah ranar ta dinga bala’i kenan. Tana zama akan gado taji knocking na ‘kofa. Mi’kewa tayi ta nufi parlourn, mummy ta tafi d’akinta, bud’e ‘kofar tayi, cikin mamaki tace “Rafee, jiya da dare muka yita trying numbarki ni da Leena amma ya’ki shiga don munaso mu rufe ‘kofa bamu san ko zaki dawo ko……” Da sauri Rafee tasa hannu ta toshe bakin Sofy, murya ‘kasa-‘kasa tace “Ke yi shiru, naga motar mummy a garage, muje d’aki kar taji ba a gida na kwa…na….ba”. Da ‘kyar ta ‘karasar da sentence d’in sakamakon ganin mummy da tayi rungume da hannuwanta a ‘kirji, wani yawu mai d’aci ta had’iye sannan tayi ‘ko’karin fuskewa gamida cewa “Mummy ina kwana?” Mummy tace “Wato don bananan shine kuke abinda kukaga dama ko?, don ubanki gidan ubanwa kika kwana da har bakiso naji?” Cikin in-ina Rafee tace “Gi…dan…su Na…zee…na…kwa…na” Batayi aune ba taji saukar mari akan fuskarta, cikin masifa mummy tace “Gidan ‘kawarki mara kunyar nan?, wanda batada tarbiyya, wacce bata san ta gaida ni a matsayin uwarki ba?” Cikin sanyin murya tace “Im sorry mum, bazan sake ba” Mum tayi tsaki ta nufi d’akinta tanata kumfar baki. Rafee kuma d’akinsu ta nufa, nan ta samu Sofy ta ‘kurama ‘kofa ido, tana ganin Rafee tace “Sis, kiyi ha’kuri, wallahi yau nan ko ni sai da nasha masifa da bala’i daga shigowarta sanadiyar ta ganni tsaye da Bash, kinsan ta tsane shi” Rafee tayi ya’ke tace “Ba komai, in tanaso tayita marina daga yau har gobe amma bazan fasa huld’a da Nazee ba” Sofy tace “Ko ni nan bazan rabu da Bash ba, abinda zamuyi kawai shine mu chanja takun mu, mu toshe duk wata hanya da zai sa ta ganomu” Rafee tayi murmushi tace “I have an idea” Matsowa daidai kunnen Sofy tayi ta rad’a mata wani abu sannan suka tafa suna ‘kara tsara yanda takunsu zai kasance. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Bayan kwana biyu “Fu’ad ka hanzarta mana, ka fa san jirginmu na 12:30 ne koh?, gashi yanxu har 11:35 amma ko wanka bakayi ba ka tsaya chatting, saisa yaushe ma zaka samu lokacin karatu?, mutum kullum waya na hannu yana danne danne” Fu’ad ya kalli Suhal yace “Haba Suhal, wai mesa baka da hakuri ne?, shiri na sharp sharp ne kasani” Tsaki Suhal yaja yana ‘kara duba agogon hannunshi yace “Daga yanzu dai na huta da ‘bacin ranka tunda ni na gama makaranta nah na huta, kai in kaga dama ka cigaba da shashancin da ka saba, its your future you’re ruining, not mine” Fu’ad ya mi’ke tsaye ya nufi toilet yana sambatu “Ka cika takura da masifa wallahi, its my life, nasan me nakeyi tunda ni ba ‘karamin yaro bane” Ko kallon inda yake Suhal baiyi ba ya sa’bi trolley d’in shi da niyyar jiran Fu’ad a motar sannan yace “Na baka 10 minutes, in baka fito ba sai mun had’u a gida don bazan zauna ina jiranka kasani missing na flight nah ba”. Minti goma bai cika da Fu’ad ya fito shima ri’ke da trolley d’inshi. Ba wanda yace ma d’an uwanshi ‘kala har sukayi boarding. Washegari jirginsu yayi landing a International airport dake Abuja. Wani ajiyar zuciya Suhal ya sauke sannan ya kalli Fu’ad yace “Alhamdulillah, daga yanzu na huta da rashin kunyar da kakeyi” Murmushi Fu’ad yayi yace “Ai kam ni ne da hamdala don yanzu na huta da masifa da mitarka” Suna d’an tsokanar junansu suka fito, bayan sunyi claiming luggages nasu sai suka nufi inda suka hango iyayen nasu tsaye bakinsu har kunne. Da gudu-gudu ko wannensu ya rungume iyayenshi suna masu matu’kar farin ciki. Ku biyomu don yanzu ne labarin ya soma. Mu ‘yan uku muke cewa “We love you masoyan mu wherever you are, Allah yabar zumunci, Ameen”. www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com ***MHS*** ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 11-15 ​​​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *REAL MHS* *11-15* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Murnar wannan family aranar bazai misaltu ba, bayan sun d’an nitsa ne sai Suhal ya d’an fara dube-dube kaman yana neman wani abu, ganin haka yasa ummi tambayarshi, cike da kulawa tace “Son ya dai?, akwai abinda kake nema ne?” Murmushi yayi ya shafi kanshi sai yace “Something is missing, banga lil sis ba, ina take?” Abba ya bud’e baki zaiyi magana sai ummi tayi caraf tace “Tana gida, tana wani abu ne” Jinjina kai Suhal yayi, daga nan basu tsaya ‘bata lokaci ba suka dunguma zuwa motoci biyu da sukazo dasu. Gidan ‘katon gaske ne, tun daga garage Suhal da Fu’ad suka fara jin tashin kid’a kad’an-kad’an. Kallon junansu sukayi kowannensu bakinshi yana cike da tambayoyi. Suna dosan main house suka hango wasu bulbs masu wal’kiya an rubuta “WELCOME HOME SUHAL AND FU’AD”, cike da jin dadi Fu’ad ya kalli iyayen yace “Wow!!, ashe dai anyi missing namu tunda gashi har party an had’a mana”, duk suka sa dariya. Wata matashiyar budurwa da bazata wuci 17-20 years ba ta rugo da gudu ta nufi wajensu. Suhal yana ganinta ya sake trolley d’inshi da yake ja, shima da gudu ya nufeta, rungume juna sukayi suna masu nuna tsantsar farin ciki, haka taje ta rungume Fu’ad ma wanda shima murmushin yakeyi. Nan ne Suhal ya d’an harareta da wasa, kaman zaiyi kuka yace “Namanta ma ina fushi dake” Zaro ido tayi ta dafe ‘kirji tace “Ni???, ya Suhal meh na maka?” Jan kumatun ta yayi yace “Baki ji dad’in dawowar mu ba tunda ko airport bakije don tarbar mu ba” Dariya tayi tace “Toh ai inada dalili” Fu’ad yaja guntun tsaki yace “Dalilin me?, ke dai kice bakiso mu dawo ba don koma me kikeyi ai ya kamata ki ajiye shi tunda kinsan da dawowar mu” Ta wani marairaice fuska tace “I’m sorry brothers” sai ta ruga ta shige ciki da gudu tana sharar hawaye. Kasake suka bi bayanta da kallo, muryan Baba sukaji yace “Gashi kun sa daughter na kuka, maimakon ku tsaya kuji dalilinta amma sai kuka yanke mata hukunci” Suhal yace “Meh dalilinta Baba?” Baba yace “Mu ‘karasa ciki, duk zakuga komai” Ba tare da musu ba suka cigaba da jan trolleys nasu har suka isa inda akayi decorations sosai in Blue and White, ga dogon table cike da kayan ciye-ciye kama daga snacks, drinks, cookies, cakes da dai sauransu. Juyawa sukayi suna kallon iyayen nasu, Umma ta girgiza kai tace “Kun ga duk wad’annan abubuwan?, Ilham ce ta had’a muku musamman don tarbanku” Daga Suhal har Fu’ad jikinsu yayi sanyi sosai. Bayan sun ajiye bags nasu a d’akunan su sai suka nufi d’akin lil sis d’in nasu, da sallama suka shiga, tana kwance akan gado tayi ruf da ciki tana kuka, amsa musu tayi ba tare da ta d’ago ta dubesu ba. Suhal ya zauna ta damanta, Fu’ad kuma ta hagu, kallon juna sukayi sai Fu’ad ya mishi alama da ido akan ya fara magana. Cikin lallashi Suhal yace “Lil sis, tashi don Allah muyi magana kinji?, kiyi ha’kuri ki bar kukan nan, we are sincerely sorry” Batayi musu ba ta tashi zaune, nan suka sa ta a tsakiya. Fu’ad yayi magana, Suhal ma yayi har dai suka samu ta bud’e baki tace musu “Nafi kowa murna da d’okin ganinku amma da kukazo sai kuka nunamin wai sam banso ku dawo ba” Suhal ya kama kunnenshi yace “Munyi laifi babba, bamu san kin tsaya shirya mana abubuwa bane” Fu’ad ma ya ‘kara da “Ni har kunya ma naji wallahi, ki yafe ma brothers naki masu sonki” Murmushi tayi sannan ta mi’ke daga zaunen da take, fad’awa jikinsu tayi ta rungumesu tace “I love you so much brothers, welcome home” Ajiyar zuciya suka sauke kusan lokaci d’aya, dariya tasa sannan ta sakesu tace “Ya kukayi wani ajiyan zuciya sai kace kunyi gudu?” Dariya dukkansu suka yi sannan Suhal yace “Mun ji tsoron fushin lil sis ne, mun tsamman bazaki yafe mana ba”, nan fah hira ya kaure tsakanin su ukun. Chan sai Fu’ad yayi hamma yace “Lil sis, yunwa nakeji sosai” Kama baki tayi tace “Sorry bro, na sha’afa ne, muje nayi serving naku”. Jan hannunsu tayi suka nufi inda ta shirya musu abincin, basu kujera tayi sannan tace su jirata bari ta kira iyayen nasu. A hanya ta gansu, nan suka iso wajen table d’in suka zazzauna. Sunci, sun sha sunata raha gwanin sha’awa, duk wanda ya gansu ko ma’kiyinsu ne sai yaji sun burgeshi don yanda suke masifar son junansu. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Hajiya Hafsat ce ke ta knocking a ‘kofar parlourn gidan Haj Rahma, Leena ce tafito dagudu tana cewa “Wayene?” Daga bakin ‘kofar Haj Hafsat ta amsa “Bud’e ki gani” Tsaki Leena ta ja don ta gane mai muryar, bud’e ‘kofar tayi ta bata hanya don ta wuce sannan ta gaisheta, amsawa tayi tana wani ‘kare ma Leena kallo. Leena duk takaici ya cikata, dama ita sam batason Haj Hafsat d’in nan, tasha gayama mummy amma watarana har mari takesha sakamakon hakan, ita tama rasa mesa mummy take ‘kawance da matar da duk wani mai ilimi bazaiso huld’a da ita ba don kuwa a ganinta Haj Hafsat tana abu kaman karuwa. Ta juya zata koma d’aki kenan Haj Hafsat ta jefa mata tambaya “Ke, ina mamanki?” Ba tare da ta juyo ba tace “Tana d’aki, ai ba yau kika soma zuwa ba so ke ba ba’kuwar gidan ba ce” Tsaki Haj Hafsat ta ja sannan ta nufi d’akin mummy. Rufe ‘kofa mummy tayi, ko gaisawa mai kyau basuyi ba suka afka duniyar da shaid’an ke buga musu gangarshi(Ya Allah ka karemu daga fad’awa halaka, Ameen). Haj Hafsat ta fito daga wanka tayi combing na kanta sai ta nemi ribbon nata ta rasa. Cikin takaici tace “Ohh ni Hafsa, yau kuma ina ribbon nawa ya shiga?” Haj Rahma tace “Inaga wajen cire riga ne kika ko’be harda ribbon d’in” Neman duniyar nan sunyi amma ba ribbon ba alamarshi. Haj Hafsat ta nufi ‘kofa tana cewa “Bari naje d’akin yarannan su bani”. Bata jira cewar mummy ba ta fice. Tana shiga daidai lokacin kuma Rafee ta fito daga wanka sanye da towel multicoloured wanda ko guiwarta bai kai ba, wani mayunwacin kallo Haj Hafsat ta bita dashi, nan take taji ta kwad’aitu da ita amma sai tayi ‘ko’karin danne maitarta, ‘kwa’kulo murmushi tayi ganin Leena dake kwance akan gado tana binta da kallon tuhuma. Cikin wani irin yanayi tace “Rafee, bani ribbon naki mana don Allah, nayi neman sama da ‘kasa banga nawa ba” Rafee sai lokacin ma ta lura da Haj Hafsat ta shigo d’akin, batace komai ba ta bud’e drawer ta d’auko sannan ta mi’ka mata. Tasa hannu zata ‘karba sai tayi magana kaman rad’a “Kinada jiki mai kyau, dirinki mai d’aukar hankali ne” Rafee yi tayi kaman bata jita ba, ta’be baki Haj Hafsat tayi ta juya tabar d’akin cike da sha’awar Rafee. Fitarta ya bama Leena damar yin tunani “Wai ma ya za ayi ribbon ya ‘bata a nemeshi a rasa daga zuwanta?, sai kace wacce ta cire tayi wasar ‘kasa?, toh ita dai ba wasa tayi ba tunda dai babba ce, amma a wani dalili yasata cire ribbon har ya ‘bata?” wad’annan tambayoyin tana neman ansarsu kuma tasha alwashin da yardar Allah sai ta samo su koma a ina ne. Haj Hafsat kuwa tana komawa d’akin Haj Rahma ta d’auki jakarta ta sallameta tabar gidan. Da dare ma kasa bacci tayi sai juyi takeyi akan gado, chan sai ta kira wani layi, jin an d’auka ya sata magana “Inaso nasaka aiki ne, ka nemomin number Leena ‘yar gidan Haj Rahma” Bansan me aka gayamata daga d’ayan bangaren ba, nadai ji tace “Ni nafika sanin wannan, kawai dai na kwad’aitu ne kuma ko ta halin ‘ka-‘ka ne sai na mallaketa, ka samomin, zaka samu tukwuici mai tsoka”. Shin su wayene duk wad’annan mutanen?, ku biyomu don jin tushen labarin. Sorry fans, kuyi ha’kuri damu, In Sha Allah zamuyi ‘ko’kari mu dinga kawo muku akai-akai. We love you all. www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com *MHS* ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 16-20 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *REAL MHS* *16-20* TUSHEN LABARI ☆☆☆☆☆☆☆☆ Marigayi Alhaji Modibbo yanada ‘ya’ya guda biyu dukkansu biyu maza; Abdulaziz ne babba sai Murtala. Sun taso cikin soyayya da kulawa had’e da ingantaccen tarbiya daga wajen mahaifiyar su marigayiya Haj. Habiba. Iyayen sun rasu ne a cikin had’arin jirgi na dawowar su daga India inda dama Haj Habiba ta raka Modibbo ne don annual check-up nashi, alokacin kuma Abdulaziz yana shekarar shi ta ‘karshe a jami’ar Bayero wato Bayero University Kano, yana karantar Business Administration, Murtala kuwa yana 300L don ba wani tazaran shekaru tsakaninsu, Abdulaziz ya bama Murtala shekaru d’aya ne kacal. Cikin ikon Allah Abdulaziz ya gama makarantar shi ya cigaba da juya tarin dukiyar da babansu Modibbo ya bar musu. Kaman kiftawar ido aka wayi gari Murtala ma ya gama tashi makarantar inda ya karanci Infotech. Lokaci d’aya Abdulaziz da Murtala suka tada zancen bikinsu, bappansu wato ‘kanin Modibbo shi ya jagoranci komai har izuwa ranar d’aurin aure. Abdulaziz ya auri Hasiya, Murtala kuma ya auri Maimuna, ba tare da ‘bata lokaci ba aka kai amaren dan’kararren gidan da angwayen suka gina, gini ne da yaci kud’i fiyeda tsammani don zana gidan ma daga ‘kasar waje suka d’auko architect, furnitures ma duk sunce sun hutar da iyayen amaren nasu amma iyayen sukace ina!!, bazai yiwu ba. Haka dai aka kawo furnitures kowanne daga gidan iyayensu aka jera musu, gida yayi kyau Masha Allah. Zaman mutunci da girmama juna Hasiya da Maimuna sukeyi, sun sha’ku har suka zama tamkar ‘yan uwan juna. Bayan shekara d’aya Hasiya ta haifi d’anta kyakkyawa son kowa ‘kin wanda yarasa, ranar suna yaro yaci sunan Suhal. Suhal yanada shekaru biyu Maimuna itama ta haifi d’anta namiji mai suna Fu’ad, Fu’ad da Suhal sun taso cikin soyayyar junansu, ba wanda zai gansu yace ba iyayensu d’aya ba don iyayen nasu ma basu nuna banbanci tsakanin yara biyun, duk abinda Baba(baban suhal) da ummi(maman suhal) zasuyi ma Suhal to sai sun yi ma Fu’ad, hakazalika duk abinda Abba(baban Fu’ad) da umma(maman Fu’ad) zasuyi ma Fu’ad to tare da Suhal sukeyi. Daganan duk matan basu sake haihuwa ba, mazan ma sam basu nuna damuwarsu ba don sun gode ma Allah da ya basu yara d’ai-d’ai, wasu mutane ko d’ayan Allah bai basu don haka basuda dalilin nuna matsawar su akan haihuwa. Suhal yanada shekaru 9, alokacin kuma Fu’ad yana 7 kwatsam sai aka wayi gari Ummi tanada ciki, zo kuga murna, gaba d’ayansu sun d’ora son duniyar nan akan cikin. Wata tara cif ta haifi ‘yarta kyakkyawa wacce taci suna Ilham. Ilham ta zamo musu hasken idaniya, komai Suhal da Fu’ad suka samu to akan Ilham yake ‘karewa, in sunga abu kuma sunada kud’in saya toh fah dole su sayamata. Itama Ilham komai Ya Suhal da Ya Fu’ad, abun nasu gwanin burgewa. Dawowarsu gida yanzu Suhal yayi graduating inda yayi university a Turkey ya karanci Pharmacy, Fu’ad kuma saura mishi shekara biyu ya kammala had’a degree d’inshi a fannin Banking and finance. Suhal kyakkyawa ne gashi yanada zubi irin na jaruman maza, baya shiga harkar mata ko kad’an don aganinshi yayi ‘karami da aure duk da yanzu he is 26, Fu’ad on the other hand kuma ya mafi Suhal kyau saidai matsalarshi shine-Shaye-shaye da bin abokan banza, abinda yake had’ashi fad’a da Suhal kenan don ba garin da zai waye har dare yayi ba tare da Suhal ya mishi wa’azi akan abinda yakeyi ba saidai kuma sam Fu’ad baya ji. Tohh gashi yanzu Suhal ya kammala ya dawo gida Nigeria, Fu’ad shi kad’ai zai zauna, ba mai sa mishi ido balle asan me yake ciki har anemi nutsar dashi, ko ya zai kasance??. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Alhaji Kabeer Mansur babban d’an kasuwa ne a jahar Kano. Auren saurayi da budurwa sukayi shi da matarshi Haj Rahma, afarko zaman nasu cike yake da tarairaya da kuma kula da ha’k’kin junansu, saidai fah tun lokacin da ta haifi ‘yarta na fari mai suna Rafee’at sai labari ya chanza don alokacin ya bun’kasa harkokin business nashi zuwa ‘kasashen waje, da yake shi mutum ne da sam bai had’a aikinshi da komai ba sai ya share watanni bai waiwayi gidanshi ba. Zaman da dad’i ba dad’i har Mummy ta haifi ‘ya’ya biyu bayan Rafee’at masu suna Safiyya da Yaleena. Sun sha’ku da uwar tasu sosai amma uban kam gaba d’aya ma in yazo gida yin kwana biyu sam basu sakewa dashi, d’ari-d’ari zasu dingayi har ya tafi, shi ko daddy tun hakan yana damunshi daga baya kuma ya tattara su ya watsar. Tsakanin shi da yaran shine suce “Ina kwana?”, shikuma yace “Lafiya”, sam babu irin sha’kuwar uba da ‘ya’yanshi a tsakaninsu. Daidai gwargwado yaran sun samu tarbiyya daga wajen uwar tasu saidai ba nan gizo ke sa’ka ba, mace ita kad’ai bazata iya tarbiyyar yara har uku ba, gashi dukkansu mata. Kowa dai yasan tarbiyyar namace sai da tsawatar war uba, anasu tasowar ina ma suka ga uban balle har ya tsawatar musu?. Mummy macece mai matu’kar ha’kuri da juriya duk da ko wani dare da kukan rashin mijinta take samu tayi bacci amma ahaka take ‘ko’karin kare kanta daga fad’awa hala’ka. Kwatsam wata rana taje shopping sai ta had’u da wata mata inda suka gaisa har sukayi exchanging numbers, wannan shine kuskure mafi girma da tayi a rayuwarta sannan shine mafarin zubda duk makaman tsaronta. Wannan matan ba kowa bace illah Haj Hafsat, Haj Hafsat gogaggiyar ‘yar duniya ce, tayi aure amma zaman auren ya gagara sakamakon bin maza da takeyi, tanada yaro guda d’aya namiji mai suna Abdulyassar. Hafsat bata tsaya akan harka da maza kawai ba, ita d’in tana cikin manyan mata masu mad’igo. Tunda ta ‘kyalla ido taga Haj Rahma tsigar jikinta suka tashi, hakan yasa taje suka gaisa ta fake da cewar tanaso su zama ‘kawaye. Had’uwar Mummy da Haj Hafsat ba ‘karamin ‘barna yayi ba, shige mata takeyi sosai, tun mummy tana shashshareta har dai ta sake suka soma zumunci. Bayan watanni sai ta soma nuna mata asalin halinta wato lesbianism, da farko mummy sam ta’ki amma da yake shaid’an yana nan yana wasa da zuciyarta sai ta yarda suka fara harka, ba a d’au lokaci ba mummy ta tsinci kanta dumu-dumu acikin harkar don tun asali dama mummy irin matan nan ne masu yawan sha’awa, acewarta Haj Hafsat tana rage mata zafi tunda mijin ba zuwa gareta yakeyi ba sai bayan watanni. Da girma yazo ma ‘yanmata ukun ne kowaccen su tayi nata halin. Rafee ita ‘yar hayaniya ce, abarta da harkar ‘kawaye, asa wannan kayan, a saya waya mai tsada, aje wani waje ahuta sannan tana d’an harkarta itama na lesbianism a ‘boye shiyasa ita tun tasowarta bata huld’a da maza, ko saurayi yazo saidai ta koreshi, tun mummy na fad’a har daga baya tayi tsammanin ko aljanu ne, malami ta kira don ayi ma Rafee ru’kiya. Malami yata zuba ayoyi amma Rafee ko gezau, bayan ya gama ne yake ce ma mummy ai lafiyarta ‘kalaw, ba aljanu bane so tabar damuwa, aure kaman mutuwa yake, in ya iso ba makawa sai an yishi, nan fah mummy ta zuba ma Rafee ido har halin yanzu da take da shekaru 29. Sofy kuma ‘yar party ce da saka matsatstsun kaya, tana d’an d’aga kwalba irin na yanmatan zamani wato codeine saidai nata baiyi yawa ba, in tasha yau toh sai bayan wata d’aya zata sake sha. Duk iskancinta bata ta’ba zina ba, ba wanda zai ganta yace ‘yar musulma ce in tayi wani shigar. Saurayinta guda d’aya ne; Bash, sun dad’e tare kuma tun ba yau ba yakeson tabarshi su dinga aikata zina amma ta’ki bashi fuska, iyakacin abinda ke shiga tsakaninsu shine romance. Leena itace wanda suke kira “Ustaziya”, Leena sam batayi halinsu ba. Tanada kamun kai, bata tara ‘kawayen banza sannan bata shiga harkar da ba nata ba. Itama dai batasan halin da Rafee take ciki ba, iyaka abinda tasani shine rawar kai da sukeyi wanda ba yanda ta iya dasu saidai ta zuba musu ido tunda duk sun girmeta, ta ma isa tayi magana?. Tsakaninta dasu shine addu’ar shiriya wanda bata gajiya da musu ba-dare-ba-rana. Mummy daga baya ta tsiri fita yawo, sam bata zaman gida, hakan ba ‘karamin gudunmawa ya bayar wajen ta’bar’barewar tarbiyyarsu ba. Tohh gashi yanzu Haj Hafsat ta ‘kwallafa rai akan Rafee sakamakon ganinta da tayi da towel, ko ya zai kaya???. Ku biyomu ‘yan uku don jin cigaban labarin. www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munay, Hanee da Stylish. *MHS* ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 21-22 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *21-22* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Cigaban labari Washegari Suhal ne zaune akan kujera a ‘karkashin shade na tree da ke tsakar gidan, ya d’ora ‘kafafunsa akan wani plastic chair, gefenshi d’an ‘karamin table ne wanda yake d’auke da glass cup da kuma juice. Sanye yake da black jean trouser had’e da farar riga, jarida ne a hannunshi yana d’an dubawa, sipping na juice d’in yakeyi cike da aji. Ilham ce tafito daga side nasu da saurinta ta nufi side nasu Suhal. Yi tayi kaman bata ganshi ba, shi ko mamaki ne ya cikashi ganin yanda ta wani fuske tana tafiya kanta a sunkuye, a zuciyarshi yake rayawa tabbas ta ganshi ne yasa tayi hakan, toh amma me dalilinta?. Har tasa hannu zata bud’e ‘kofar parlourn Suhal ya ‘kwala mata kira, amsawa tayi sannan ta tura baki, idonshi ‘kyam akanta yace “Zo Ilham” Kaman kar taje sai kuma ta fasa, fuskar nan ba ko murmushi sai ma bakin da ta tura ita adole wai tayi fushi. A gabanshi ta tsaya sannan tace “Gani ya Suhal” Sau’kar da ‘kafafunshi ‘kasa yayi sannan ya nuna mata kujerar alamun ta zauna, juya kai tayi kaman bata san body language da yayi mata ba. Ahankali yace “Sit down mana” Ba don batason mishi musu ba da bazata zauna ba, jan kujerar tayi tana wani tuttura baki ta zauna. Dariya ne ma ya kamashi wanda ya kasa dannewa sai da ya dara, nan fah Ilham ta kuma ‘kulewa, murya na rawa tace “Ya Suhal ni fah ba mahaukaciya bace da zaka kirani kasani a gaba sannan ka tsaya kanamin dariya” Da ‘kyar yasamu ya tsaida dariyar sannan ya saita kanshi, in a serious tone yace “Lil sis, are we fighting?, jiya fah nadawo garinnan gashi yanzu kinganni sai kika wani kawar da kai kaman kinga ma’kiyinki, me na miki haka da ko sannu bazaki iya ce min ba?” A shagwa’bance tace “Toh…toh…ba kaine kabar sona ba” Zaro ido yayi had’e da nuna kanshi yace “Who?, me?, noo ba ranar da zan bar sonki, bansan dalilinki na tunanin hakan ba so inajinki, gayamin, wani laifi namiki?” Gyara zaman ta tayi tace “In ba kabar sona ba toh mesa baka bani tsaraba ta ba?, ya Fu’ad kam tun jiya da dare ya kirani ya bani, kai kuma baka kawo min ba don baka sona wata’kila ma har fata kakeyi namutu” sai ta fashe da kuka Tsayawa kallonta yayi cikeda mamaki, bakinshi ya kasa furta ko wacce irin kalma, ohhh Ilham akwai rigima, yasan ta d’ora mishi laifi ne kawai don rikici irin nata amma don dai bai bata tsaraba ba ai bai zama reason da zata ‘ki mishi magana ba kuma har tace mishi watakila yana fata ta mutu. Dafa hannunshi yayi a ‘kar’kashin ha’barshi sai ya ‘kura mata ido kaman yasamu tv, itako sabon kuka ta shiga rerawa kaman wanda aka mata mutuwa. Fu’ad ne yafito da plastic chair don shan iska, ganin yanda Ilham ke kuka sannan Suhal ya zuba mata ido sai abun ya bashi mamaki, nufan wajensu yayi ya ajiye kujerar shi a tsakiya inda sukayi kaman triangle. Ya kalli Suhal ya kalli Ilham, chan dai yace “Kai lafiyarku wai?, ke kinzo kin zauna kina kuka, Suhal kuma ya wani saki agaba kaman yasamu tv, me ya faru?” Share hawaye Ilham tayi ta maida dubanta wajen Fu’ad sannan tace “Ya Fu’ad kar kaji mamaki ko da wu’ka kaga ya Suhal yazo zai chakamin, ya Suhal yabar sona” Suhal ya sake baki yana jinta, azuciyarshi yake rayawa lallai Ilham ta cika ‘yar duniya, tas ya kwashe komai ya gayama Fu’ad. Haba, meh Fu’ad zaiyi in ba dariya ba, yi yakeyi sukuma suka bishi da kallo. Bayan yayi shiru ne sai yace “Ke fah wawiya ce ashe bansani ba, yanzu fisabilillahi Ilham don bai baki tsaraba ba shikenan yabar sonki?, ke dai kawai kina neman reason na kuka ne gashi kin samu, toh ko da yake zai iya yiwuwa yabar sonki ne sabida kin zama tsohuwar yayi, yau dai na ganku a rana, Ilham tana holding grudge against Suhal” ya ‘karasa maganar yana tafi harda bubbuga ‘kafa alamun yaji dad’i. Ganin haka yasa Suhal cewa “Wai kai Fu’ad wani irin shed’an ne?, ganinka anan na tsamman zaka tayani lallashinta amma tsaba ka nuna kanada horns harda tail yasa kazo kana neman ‘kara ‘kwa’bawa kana ‘kara ma wuta petur, malam ka tashi ka kama gabanka tunda ba amfani zakayi ba” Fu’ad gyara zamanshi ma yayi had’e da d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya bai ce komai ba. Ba irin lallashin da Suhal baiyi ba amma atapir Ilham ta’ki ha’kura. Mi’kewa yayi yasa hannunshi a cikin aljihu yace “Tashi ki shirya nima barinje na chanja kaya sai nazo in kaiki shopping ki za’bi duk abinda kikeso”(ya fad’i hakan ne don yasan ko wani irin fushi tayi inhar ance za akaita shopping to za a nemi fushin arasa) Nan take hawayen suka tafi kaman anyi ruwa an d’auke, murmushi ta fara yi, cikin jindad’i tace “Ai daman nasan kana sona ba kaman ya Fu’ad mai shegen ma’ko ba, ka ma san meh yabani as tsaraba?” Girgiza kai yayi yana murmushin mugunta yace “Gwanda da kika gane da kanki, Fu’ad ai sai addu’a, ma’konshi yayi yawa, gayamin wani tsiyar ya baki?” Cikin yatsina fuska tace “Wasu jewelleries ya kawo min wanda nasan ba masu tsada bane, ina tunanin ma irin masu fading nan ne da turare guda uku irin cheap ones wanda ‘kamshin su ba dad’in nan sai wani agogon M&S” Suhal da kanshi ya jinjina ma Fu’ad don yasan kud’in da ya narkar ba kad’an bane amma gashi Ilham don tsaba iskanci wai kushewa takeyi. Jinjina kai Suhal yayi yace “Ohh ke kinji mamaki ne?, kad’an daga ma’ko irin na Fu’ad kenan ai, in gaya miki, ranar da ya siya miki abubuwan nan har zazza’bi sai da yayi” Dariya Ilham tasa tace “Ya Fu’ad Allah ya shiryeka, inaga kud’inka sai sun ru’be wataran” Duk maganan da sukeyin nan Fu’ad bai tanka musu ba don yagane manufar Suhal na son ya ‘kular dashi amma yanzu sai yace “Lallai Ilham kincika ‘yar air, yanzu kuma kaina kika dawo?, ba damuwa, gobe ma rana ne” Murgud’a baki tayi tace “Koma me dai, ga ya Suhal mai sona wanda bai ‘kiuyan kashemin kud’i” sai ta juya wajen Suhal da ke ta faman danne dariyarshi tace “Mutafi ya Suhal kar ya ‘kara shiga tsakaninmu”. Basu jima a d’akunansu ba suka fito cikin shirin fita, motar suka shiga sannan sukayi ma Fu’ad gwalo suka fice daga gidan. Sahad stores sukaje, shopping sosai tayi ya biya kud’i suka juyo gida. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman AUGUST 24, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 23-24 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *23-24* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Gida ne mai kyau da tsari duk da ba wani girma yake dashi sosai ba, madaidaicin gida ne mai ‘kunshe da flats guda biyu. D’aya wanda shine na Haj Hafsat yana d’auke da d’aukuna uku had’e da kitchen da store sannan ga parlour babba. D’ayan flat d’in kuma na tilon d’anta ne mai suna Abdulyassar wanda ta d’auki son duniya ta d’aura akanshi. 11:24AM Wayar Haj Hafsat da ke hannunta ne yasoma ruri, ajiyar zuciya tayi daga bisani ta d’aga “Haba Garba, tun jiya ka ajiyeni ba bayani, me ake ciki?, ka samo ne?” Cikin muryar tantiran ‘yan iska yace “Eh to hajiya, saidai fah dole ki ‘karo kud’i don aikin yayi wahala, da ‘kyar…..” Katse shi tayi da cewa “Ban nemi sanin yanda akayi ka samu ba don ba damuwa na bane, kud’i kuma kai da kanka zaka yanka nawa kakeso nikuma nayi al’kawari ko nawa ne zan baka, answer d’aya nake bu’katar ji, ka samu?” Cikin jindad’i yace “Nasamu” Murmushi ta saki sannan tace “Turomin number d’in yanzu” “Hajiya toh kud’in fah, kinsan business nan ba ahaka, cash in hand akeyi, ki bani kud’i sai na baki abinda kike so” Wani tsaki taja sannan tace “Kai bansan yaushe zaka amince dani ba wallahi, ka tuna ba fa yau muka soma abun nan ba, ko akwai ranar da ka ta’ba min aiki ban biyaka ba?” “Babu amma hajiya kiyi ha’kuri, bazan iya bayarwa ba in har kud’i bai shigo hannu na ba” ya fad’a cike da gadara Takaici ne ya lullu’be Haj Hafsat, ba don dole ba me zai kaita cigaba da harka da Garba?, ba yanda ta iya ne don shi yafi ‘kwarewa sannan aikinshi babu ‘bata lokaci yakeyi. Cike da ‘kosawa tace “Naji, nawa kakeso?” Dariya yayi sai yace “Dubu d’ari” Dafe ‘kirji tayi tana nadamar bashi izinin yanka kud’in da tayi, a firgice tace “Haba Garba, me haka?, dubu d’ari?, ba fa kashe rai nasaka ba, number ne kawai, zan daure nabaka hamsin” Dakatar da ita yayi yace “Shikenan tunda bazaki bayar ba, ki ri’ke kud’in ki sannan kiyi bankwana da samun number d’in nan” Cikin hanzari tace “Yi ha’kuri mana mu sasanta, ya na iya?, barin turo maka, yanzu zakaji alert” “Yauwa ko kefa hajjaju makkatu, saisa nakeson business dake don akwai sakin ‘ya’yan banki, ina jin alert zakiji text mai d’auke da number d’in” Bayan ta tura mishi kud’in ko minti d’aya baiyi ba taga ya turo mata da number ‘din. Dad’i ne ya cikata don ganin ta samu number d’in cikin sau’ki, bata ma yi tunanin duba lambar a wayar Mummy ba don basu ta’ba wayar junansu sabida sunyi al’kawarin respecting each others’ privacy. Saving tayi sannan ta tsaya jujjuya wayar a hannunta, wani zuciyar na cemata ta kira wani kuma yana mata hani da kirar, da taga tunanin ba inda zai kaita sai ta ajiye wayar ta shiga wanka, chan ta fito cikin shirin fita, lace tasaka wanda da ganinshi mai tsada ne, tafito fes da ita kamar wata kamilalliya don har wani kashka babba ta yafa. Har zata shiga motarta sai wani saurayi mai matu’kar kama da ita ya fito daga d’ayan flat d’in, ganin shi yasa ta dakata da shiga motar da tayi niyya, takowa yayi har ya iso gabanta sannan yace “Morning mum” Side hug ta mishi sannan ta shafi kanshi, cike da kulawa tace “Morning, how are you my dear?” Yatsina fuska ya d’an yi sannan yace “I’m good, fita zakiyi ne?” “Ehh, i have some business i need to attend to, breakfast naka yana kan dinning , zan dawo nayi mana abincin rana so karka damu” “Gaskiya mum yawan fitan kin nan ya fara damuna, haba mum, don Allah ki dinga zama agida, kullum saidai abokai na su ce min sun ganki anan sun ganki achan, gaba d’aya hakan bai min dad’i wallahi, please mum, can you do me this favour dan Allah?” Ya ‘karasa maganar yana marairaicewa Murmushi tayi sannan tace “Abdulyassar, duk fitan da nakeyin nan sabida kai nakeyi, ba abinda nafiso kaman naga rayuwarka ya inganta, inaso kullum ka kasance cikin wadata, bana fatan Allah ya nuna min ranar da zaka nemi abu ban baka ba, kabar damuwa kaji?” “Nasan ‘ko’karin da kikeyi wajen ganin kin wadata ni da komai and i’ll forever be grateful to you mum, nasan ke d’in mai sona ne har ‘karshen rayuwar mu amma yanzu na girma da zan iya kula da kaina har ma na kula dake, u have done more than enough for me tunda kikasa nayi karatu in one of the best colleges har nayi graduating, don Allah mum kiyi ha’kuri ki bani chance da zan kula dake fiye da yanda kika kula dani tun ina yaro” Jim tayi sannan tace “Shikenan, yanzu dai ina sauri ne, kaje kaci abu kasan banson ganinka da yunwa, we will talk in na dawo, take care” ta d’an mishi murmushi shima yayi ‘ko’karin mayar mata sannan ta shige motarta tabar gidan. Bata tsaya a ko ina ba sai a shoprite, shopping sosai tayi wanda tasan abun amfanin yaran zamani ne, daga nan gidan Haj Rahma ta nufa, da ‘kyar ta iya tattara ledojin ta nufi cikin gidan dasu. Knocking tayi a ‘kofar parlour, Haj Rahma alokacin tana zaune tana kallon tv don haka sai ta tashi ta bud’e, mamaki ‘karara ya bayyana akan fuskar mummy amma sai tayi ‘ko’karin dannewa ta hanyar yi ma Haj Hafsat sannu dazuwa gami da tayata shigar da kayakin cikin parlourn, anan suka yada zango suka gaggaisa sama-sama. Mummy mamakin da takeyi bai wuci akan zuwan bazata da ‘kawartata tayi mata bane sannan ga uban kayan da tazo dasu wanda batada masaniyar ko na wayene su, itako Haj Hafsat damuwarta taga Rafee ko hankalinta zai kwanta. Hira suka hau yi sai chan mummy ta kasa daurewa ta jawo ledojin gami da jefo ma Haj Hafsat tambaya “Haj wannan kayan kuma daga ina haka?, ko yau shopping akamin ne?” Ta ‘karasa maganar cikin sigar zolaya Dariya Haj Hafsat tayi sannan tace “Wallahi shopping nayi ma Rafee, ina take ne ma?, barin bata” Wani kallon tuhuma mummy tabi Haj Hafsat dashi, hakan yasata kwaskware maganar da tayi ta hanyar cewa “Don in nuna godiyata akan bani ribbon da tayi ne fah ba wai wani abu ba, naga kin wani watso min mugun kallo” Mummy tama kasa magana don takaici, ita dai bata yarda ba amma za dai tabi komai a sannu har ta gano manufar Haj Hafsat gameda Rafee , murmushi tayi tace “Ayyah, shine harda wahala haka?, kwata-kwata ribbon d’in nawa ne shine harda jibgo mata wannan uban kayakin?” Haj Hafsat ta d’an yi fuskar tausayi tace “Kiyi ha’kuri, ni aganina ba komai bane don na kashe ma yaranki fiye da haka ma, na d’aukesu tamkar yaran da na haifa tunda ni Allah bai bani ‘ya mace ba” Mummy tuni taji tausayin Haj Hafsat ya tsarga mata zuciya, girgiza kai tayi tace “Ba komai, nima ba nufina kenan ba, barina kirata tazo”. ‘Kwala ma Rafee kira mummy ta hau yi, da sauri Rafee ta fito tace “mummy gani” Mummy ta nuna mata ledojin had’e da cewa “Gashi Haj Hafsat ne tamiki shopping, ki mata godiya” Daman Rafee uwar son kayan ‘kyalli ne, nan take ta soma murna har bata san lokacin da ta rungume Haj Hafsat ba. Wani sanyin dad’i ne ya ziyarci zuciyar Haj Hafsat wanda bata ta’ba jin irinshi ba, take ta ‘kara raya ma kanta tabbas dole ta ‘kara jan Rafee ajiki ta hanyar kyauta tunda ta gano lagonta na son abin duniya, murmushi tayi azuciyarta tace “Rafee, kin kusa zama tawa”. www.gidannovels.blogspot.com Munay, Hanee da Stylish *MHS* Skip to content haneefahusman AUGUST 29, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 25-26 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *25-26* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Suhal da Ilham daga shopping suka zarce shan ice cream, daganan suka dinga yawo suna labaran su sunata kwasar dariya, in mutum bai sansu ba zai tsamman lovebirds ne. Daf maghrib suka dawo gida, inda suka bar Fu’ad nan sukazo suka tarar dashi. Ko gama parking Suhal baiyi ba Ilham ta ‘balle murfin motar ta fito, da d’okinta ta isa wajen da yake zaunen tareda jan kujera ta zauna. Sighing mai ‘karfi tayi alamun ta gaji sannan ta mi’ka mishi leather da take ri’keda had’e da cewa “Ya Fu’ad mun dawo, ga tsaraba nan na kawoma” Sai sannan ya d’ago da kanshi gamida galla mata wata uwar harara, dafa kafad’an shi tayi tana tura baki, ture hannunta yayi har ta kusan fad’uwa ‘kasa da ita da kujerar da take zaunen. Ranta ya sosu don ba abinda ta tsana kaman ayi ignoring nata, cikin muryar shagwa’ba tace “Meh kake wani ciccin magani kaman wanda muke gaba?, ni ne fah ur one and only lil sis ba wata budurwa da zaka ja ma aji ba” ta ‘karasa maganar tana wani fari da ido. Dariya ta bashi amma sai ya danne yace “Ni don Allah ki rabu dani, d’azun nan kika gama kusheni yanzu kuma kin wani zo zaki cikamin kunne” Shiru tayi tana tunanin me tayi ma ya Fu’ad, sai lokacin ta tuna yanda suka rabu, dariya tayi tana rurrufe fuska alamun taji kunya daga baya tace “Wasa fah nake maka wallahi, nasan expensive abubuwa ka siyomin, I’m sorry kaji?, will u forgive me?” ta ‘karasa maganar tareda had’e hannaye waje d’aya alamun ban ha’kuri. Murmushi yayi don yanason ‘kanwar tashi, dama haka suke, su ‘bata su shirya, cikin wasa ya zungure kanta yace “Ya na iya?, Allah ya had’ani da mara kunyar ‘kanwa ai dole nata ha’kuri” Zaro ido tayi tace “Laa!!, ya Fu’ad yanzu kallon mara kunya kakemin?” Jinjina kai yayi yace “Dama ya kike tunani?” Ta bud’e baki zatayi magana Suhal ya iso wajen da ledoji a hannunshi, ajiyewa yayi a gabanta, harararta yayi yace “Ke waye kika ajiye da zai shigar miki da kayan nan?” Marairaicewa tayi tace “Ya Suhal yi ha’kuri, in baka shigarmin ba waye zai shigar min?, kaga ku biyu ne fah kawai yayyuna amma sai kuna min rashin mutunci don kunga inasonku, ba damuwa, zan nemi wasu yayyu” tana kaiwa nan ta mi’ka ma Fu’ad leather’n tsarabar shi sannan ta fara tattara nata ledojin waje d’aya. Suhal da Fu’ad suka had’a ido sai suka sa dariya, sukam sun gamu da ‘kanwa, ita zata sossollesu ba ruwanta amma ita suna mata abu d’aya sai ta fara maganganu kaman tazama wata abun tausayi mara gata. Fu’ad yana dariyar halinta a zuciyarshi, ko in sun ‘bata bata wuce awa d’aya zata manta tazo tana musu magana, saisa duk su biyun(Fu’ad da Suhal) basu iya zama agida in babu ita. Kusan lokaci d’aya Fu’ad da Suhal sukasa hannu suka d’auka mata ledojin, d’agowa tayi taga still dariya suke mata, murgud’a musu baki tayi aikuwa Suhal ya cafke bakin. Ihu ta tsala tana basu ha’kuri, sake mata yayi sannan yace “In kika sake murgud’a mana baki sai na yanke da wu’ka, ba kyau, ki daina kinji?” Murmushi tayi tace “Toh”. Sai ta wuce gaba tafara tafiya kaman ta samu ‘yan aiki tace “Brothers muje ku kai min d’aki ko?” Basu ce mata komai ba kawai suka bi bayanta, a tsakiyar d’akinta suka ajiye mata sannan suka juya. Kirar sunayensu tayi “Ya Suhal, Ya Fu’ad” Cak suka tsaya gamida juyowa, basuyi aune ba kawai sukaji ta rungumesu had’e da kai ma kowannen su peck a kumata. Sakesu tayi tace “Thank you sweet brothers, I’m the luckiest girl on earth, I love you Ya Suhal Ya Fu’ad” ta ‘karasa maganar tana fad’ad’a murmushinta. Murmushin suka mayar mata sannan Suhal yace “We love you too lil sis” sai suka juya zasu fita. Bubbuga ‘kafa ta hau yi tana gunaguni, juyowa suka sakeyi don tambayar dalilinta na haka. Kaman zatayi kuka tace “Ya Fu’ad kai baka sona shine bazakace iya cemin love you too ba ko?” Dafe kanshi yayi yace “Rikicinki is too much wallahi, naga Suhal ya amsa mana mubiyu saisa ni nayi shiru amma i love you too” Tsalle tayi cikeda murna kaman ‘karamar yarinya, girgiza kai Fu’ad da Suhal sukayi suka bar d’akin basu ‘kara cewa komai ba. Alwala sukayi sannan suka nufi masallaci, a hanya ba abinda sukeyi sai hirar hali irin na Ilham sunata dariya zuciyoyinsu cikeda son tilon ‘kanwar tasu. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Abdulyassar yana shiga side na mummy ya wuce dinning ya karya sannan ya zauna a parlourn yana kallon tv amma a zahirin gaskiya hankalinshi gaba d’aya ya tafi akan tunanin irin rayuwar ‘kazanta da maman tashi ke yi, ba ma abinda yafi cimishi tuwo a ‘kwarya kaman fitan da takeyi ba dare ba rana, da yanada ikon natsar da ita da ba abinda zai hanashi rufe gate ya hanata fita gaba d’aya saidai baida wannan matsayin. Bazaice yana jin haushin kasancewarta mahaifiyarshi ba don “uwa uwa ce” ko da kuwa mahaukaciya ce, shi yasan mummy bata had’a sonshi da komai ba don haka shima yake matu’kar ‘kaunarta, ko mahaifinshi bai kashe mishi kud’i kaman yanda ita take mishi. A kullum yanason tsamota daga rayuwar da takeyi saisa in har yaga tana zaune tana kallo toh yana yawan zuwa wajen da cd na wa’azin malaman sunnah ya saka yace mata su gani, haka mummy zata zauna tayita gani, wani lokacin in ana fad’an irin azaban Allah har hawaye takeyi amma abun mamaki wa’azin yana ‘karewa imanin yake tafiya. Yayi fad’an, ya nuna fushin, ba ranar da bai jefa mata magana d’aya-biyu don ta shiryu amma Allah bai nufa ba. Tunani ya dinga yi har dai daga baya ya yanke shawarar cigaba da addu’a kaman yanda ya saba mata har Allah zuwa da Allah zai ganar da ita. Daga ranar nan Haj Hafsat ta fara kirar Rafee awaya su sha hira wanda sam Haj Rahma batasani ba don Haj Hafsat ta haneta da fad’a ma kowa. Afarko Rafee taji abun bambara’kwai, har tana tambayar kanta “akan meh haj zatace kar na gayama momy?”, daga baya kuma ta watsar da tunanin ta amince akan bazata fad’a ba. Bayan sati d’aya ma same thing, shopping Haj Hafsat ta sake yi ma Rafee. Awannan lokacin ne saida momy tace tanason magana da ita, d’aki suka shiga sannan Haj Rahma ta fara cewa “Haj, akan wani dalili kike ‘ko’karin jan Rafee jikinki?” “Sabida naga ‘ya’yanki ai kaman ‘ya’yana ne” Haj Hafsat ta fad’a confidently Jijjiga ‘kafa momy tayi tace “Ban miki katanga da yarana ba saidai inaga yanzu zanyi, maganar wai yarana yaranki ne nayarda, hakan kuma yana nufin abinda zakima Rafee haka ya kamata kiyima Leena da Sofy tunda ba Rafee bace kawai ‘yata. Kinga kin nuna banbanci in har da gaske nufinki na alheri ne, sannan kuma bazan yarda da hakan ba don zai raba min kan yara. In har kinsan bazakiyi ma sauran ba to karkiyi ma Rafee” Sosai ran Haj Hafsat ya ‘baci ganin momy na shirin ruguza duk wani plan da take shiryawa, dole ne ma ta chanja takunta, kuka sosai tasa harda sheshshe’ka, sam momy bata hanata ba, ganin haka yasa Haj Hafsat mi’kewa da niyyar barin gidan. Har takai ‘kofa momy batace komai ba, zata bud’e kenan wani abu ya tsirga ma momy a zuciya, bata fatan rabuwa da Haj Hafsat don tana son harka da ita. Kirar Haj tayi, da farko Haj taso ta d’an ja class amma tunawa da tayi in tayi wasa da damarta fah to tabbas ta rasa Rafee har abada hakan yasa ta tsaya chak tareda juyowa tana share hawayenta. Mi’kewa momy tayi ta isa gaban Haj Hafsat gamida kama hannunta ta jata suka zauna akan d’aya daga cikin couches dake d’akin, nan ta hau sharema Haj Hafsat hawayen dake zuba daga idonta. Haka tayita lallashinta har tabar kukan ‘karyan da takeyi daga bisani momy ta hau rarrashinta tana bata ha’kuri “Kiyi ha’kuri, rai na ne ya ‘baci ganin yanda kike kashe ma Rafee kud’i, sam banson wata ta ra’beki ballantana Rafee da take ‘yar cikina wacce banaso ta fad’a wannan harka don ba abu ne mai kyau ba, ko ni da nakeyi ina fatan watarana na tuba na koma ga Allah” Haj Hafsat ta jinjina kai mai nunin ta gamsu amma chan ‘kasar zuciyarta cewa takeyi “Dole ‘yarki ta shiga tsundum cikin wannan harka ba tare da saninki ba, nasha alwashin tattara ma kaina mabiya baya a wutar jahannam”. Abinku da masoya masu ‘kaunar junansu, nan take suka yafi juna bayan Haj Hafsat ta ‘kara convincing momy akan pure intentions nata gamida Rafee, daga nan suka lula duniyarsu da suka saba zuwa. Bayan kwana biyu Haj Hafsat ce kwance akan gado tana waya, daga gani ansan tana enjoying conversation d’in, juyi tayi sannan tace “Rafee, inaso nayi wani magana mai muhimmanci dake, ina fatan zaki saurareni da kunnen fahimta?” Rafee da yanzu sun saba sosai da Haj Hafsat ta amsa “Hajiya ina jinki, wace magana ce?” Haj Hafsat tayi jim tana neman hanyar da zata fara tunkarar Rafee da bu’katar ta, chan dai tayi gathering liver tace “Inasonki, nasan zakiji mamakin jin kalaman nan daga bakina, tun ranar da na ganki da towel hankali na ya tashi, sam na rasa sukuni na, kullum da sha’awarki nake kwana nake tashi, don Allah….” Rafee ta katseta ta hanyar cewa “Hajiya kenan, ai ni tun ba yau ba nagane take-takenki akaina, zan yarda dake amma abisa sharad’i” Cikeda zumud’i Haj Hafsat tace “Ina jinki, ko menene zanbi in har zan sameki yanda nakeso” Wani dariya Rafee tayi sannan tace “Zaki iya don ba abune mai wahala a gareki ba, kud’i, ina bala’in son kud’i, kin yarda zaki iya bani duk adadin kud’in da nace inaso aduk lokacin da na bu’kata?” Ba tare da wani tunani ba Haj Hafsat ta amsa mata da “Ehh, na yarda” “Good” shine abinda Rafee tace. Haj Hafsat cikeda murna tace “Ki shirya ki fito bakin hanya zanzo na d’aukeki ki saya duk abinda kikeso amma ko da wasa karki bari mamanki taji wannan batun” Rafee ta kwashe da dariya gamida cewa “Ba sai kin gayamin haka ba, nima dama ba gayamata zanyi ba”. Daga haka sukayi sallama kowaccensu zuciyarta cikeda burika kala-kala akan junansu. Da ‘kyar da sud’in goshi momy ta bar Rafee tafito daga gida, sunyi yawo sosai sun kuma yi sayayya ba adadi. Wani hotel sukaje suka kama d’aki don kore ‘kishin ruwan junansu(wa iyazu billah, Ya Allah ka shirya masu irin wannan hali). Ba su suka dawo hankalinsu ba sai bayan awa biyu, dukkansu murmushi ne d’auke akan fuskokinsu, cikeda gamsuwa suka zarce toilet sukayi wanka. Hirar batsa suka dingayi a motar har Haj Hafsat ta sauketa a bakin layi inda Rafee ta kira Nazee tazo ta tafi da kayan akan in momy tafita zata mata waya ta kawo mata don yanzu in ta shiga da kaya ni’ki-ni’ki sai momy ta cikata da tambayoyi. Nazee da kanta taji mamaki har wani kishi-kishi tafara ji amma sai bata nunama Rafee ba, ta dai sa kayakin a motarta ta kama gabanta. Wannan rana itace mafarin ‘kara kwa’bewan abubuwa. Sosai Rafee da Haj Hafsat suke fita yawonsu suje su aikata mad’igo ba tare da sanin momy ba. Ku cigaba da ha’kuri, gobe ma zaku gani In Sha Allah, bama zama ne saisa muke muku bayan kwana uku-uku amma daga yau zaku dinga gani kullum da yardar Allah. We love you all www.gidannovels.blogspot.com *REAL MHS* Skip to content haneefahusman AUGUST 30, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 27-28 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *27-28* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Abba da Baba sun had’u da Suhal da Fu’ad bayan an idar da sallar isha don haka tare suka tako daga masallacin zuwa gida don ba nisa tsakanin masallacin da gidan nasu. A side nasu Suhal yau za ayi dinner don haka Umma(maman fu’ad) taje taya ummi(maman suhal) girki, dama su haka tsarin gidan yake, yau ayi girki aci a side nasu Suhal gobe kuma ayi a side nasu Fu’ad sannan aci a wajen. Iyayen da samarin suna shiga suka samu sai sintirin jera kuloli da abubuwan bu’kata akan dinning ummi da umma ke yi, sannu suka musu sannan suka zazzauna akan kujerun dinning table d’in. Sai da suka gama komai sannan Ilham tafito daga d’akinta da ke side nasu Suhal(d’akuna biyu take dashi agidan, asalin nata a side na iyayenta da kuma na side nasu Suhal d’in), dinning table ta nufa taja kujera ta zauna tana hamma alamun ta kwaso yunwa. Gaishe da iyayen tayi tana bubbud’e warmers na wajen, Fu’ad ya sake baki yana kallonta, da ‘kyar ya iya danne mamakin shi ya bud’e baki yace “Ilham, yanzu fisabilillahi abinda kikeyin nan abu mai kyau ne?, mesa kike haka?, rashin hankali ko kuma rashin sanin-ya-kamata?” Ba tare da tabar bud’e bud’en ba tace “Meh nayi?” Buge hannunta yayi ya kama ta ya zaunar akan kujera, tuni idanunta sun cicciko da ‘kwalla, iyayen kuma ba abinda sukace, sun dai zuba ma Fu’ad ido don jin laifin da yake i’krarin Ilham tayi. Cikin nutsuwa yasoma magana “Ba tun yau ba na lura, kullum umma da ummi ne ke yin duk girkin gidannan, bana ganin ko da shadow d’inki ne a hanyar kitchen, iyakaci abinda kika iya shine in an fito cin abinci zaki fito kina wani hamma kaman zaki had’iye mutane sannan ki hau bud’e-bud’e, wato kin iya ci amma baki iya dafawa ba ko?, baki sha’awar koyan girki?, ke fah macece ce lil sis, watarana aure zakiyi and ba namijin da zai iya jure zama da wacce bata iya abinci ba ko da kuwa yanasonta wane ranshi, ki gyara kinji?, daga yau ki dinga shiga kitchen kina ganin yanda sukeyi har nan gaba ma suhuta in kin iya” Dukkansu jinjina kai sukayi alamun they are in support of abinda yace don kuwa abinda ya fad’a d’in gaskiya ne, Ilham tayi rau-rau da ido tana jiran taji iyayen sun kareta amma sai tajisu tsit kaman ma basu wajen. Hawaye ne ya zubo mata sharr, sharewa tayi sannan tace “Na fa iya girki ya Fu’ad, kabar cewa ban iya ba, yin ne kawai banaso” “Kin iya girki?, meh da meh kika iya dafawa?” Fu’ad ya tambayeta Tunani ta hau yi tana lissafi da yatsunta, chan tace “Na iya dafa indomie, na iya had’a quaker oats, na iya dafa su macaroni, spaghetti, frying na dankali da soya egg” tayi maganar tana washe ha’kora irin tayi abun kirkin nan. Ran Fu’ad in yayi dubu toh ya ‘baci, in ba Ummi da ta d’aure mata gindi ba ya za ayi ace yarinya shekararta 18 iya abinda ta iya kenan, masifa ya hau yi kaman zai cinyeta “Ilham yanzu ko kunya bakiji ba kika lissafo min wad’annan shirmen wai ke kin iya girki?, a ganinki wannan ne girki?, an gayamiki kowa kamanki ne?, wad’annan tarkacen banza ne, wallahi gwanda ki nitsu kisan me kikeyi don wannan ba gata bane, ba namijin da zai aureki in har kika cigaba da tafiya ahaka”. Dinning area d’in tsit ba wanda yace ‘kala, tabbas maganar Fu’ad gaskiya ne, Fu’ad ya cigaba “Kinsan Allah, in nasake ganin ummi da umma suna girki bakya wajen wallahi…..” Suhal ne ya katse shi ta hanyar d’aga mishi hannu don aganinshi bai kamata su taru su juya ma Ilham baya ba duk da gaskiya ake gayamata, murmushi kad’an yayi ya mi’ka ma Ilham hanky don ta goge hawayenta, ‘karfa tayi tana share hawaye kaman wacce aka mata shegen duka. Gyara zamanshi yayi sannan yace “Fu’ad, daga yau kar ka sake d’aga ma Ilham murya, in zaka mata magana kamata yayi ka kirata ku zauna ku tattauna ba ahaka ba, its embarrassing, in kai akayi maka haka zakaji dad’i?, oya apologise to her” Umma(maman Fu’ad and Ilham) tace “Suhal kabar d’aure ma ‘karya gindi, bakasan kalan sangartan yarinyar nan bane, sam ba abinda ta iya, ban isa nayi magana ba nan ummi zata hau ni wai na cika takura ma yarinya, barshi ya ladabtar da ita ko zatayi saiti” Fu’ad ya saki murmushi yana wani rubbing na palms nashi irin yaji dad’in nan. Ummi ta kama hannun Ilham tace cikin sigar lallashi “My dear yi shiru ki barsu, girki ne bazakiyi ba, wannan da kika iya ma ai wasu dewa basu iya ba, miji kuma kin samu kin gama, stop crying kinji?, haushi sukeji” Suhal ya juya ya harari Fu’ad yace “Bazaka bata ha’kuri ba ko?” Fu’ad ya wani d’aga kafad’a yace “Bazan bada ha’kurin ba, daga an gayamata gaskiya sai ta wani fara kuka kaman na duketa, ta had’iye zuciya ma in tanaso” ‘Kwafa Suhal yayi yace “Zamu had’u dakai” sannan ya hau lallashin lil sis nashi. Sam ta’ki shiru har sai da Abba(baban Fu’ad and Ilham) ya daka mata tsawa sannan ta nitsu tabar kukan. Serving na abincin ummi da umma sukayi ma kowa a plate, nan fah wajen yayi tsit sai ‘karan spoons da fork akeji. Acin abincin ma dafarko Ilham mi’kewa tayi zatabar wajen wai ita tayi fushi ta fasa ci, baba ne yayita bata baki har ta ha’kura ta dawo ta soma ci, abba da umma kuwa haushi ne ma ya cikasu da yanda sam iyayen Suhal basu ganin laifin Ilham ko da kuwa ta chanchanci a tsawatar mata. Bayan dinner suka baje a parlour suna kallon 9pm news a NTA, Ilham kam daman d’akinta ta wuce don har yanzu fushi takeyi da iyayen nata(Abba da umma) da kuma yayanta Fu’ad. Chan sai Suhal yabita d’akin, kan gado ya sameta tayi ruf da ciki tana kuka, zama abakin gadon yayi sai yace “Lil sis bar kukan nan haka please, wipe ur tears ki tashi muyi magana” Batayi gardama ba ta share hawayen had’e da dawowa bakin gadon ta zauna a gefenshi. Kama hannunta yayi sannan ya soma magana “Fushi kikeyi da su Umma?” Jinjina mishi kai tayi alamun eh, girgiza kai yayi yacigaba “Kibar fushi dasu, ba kyau fushi da iyaye” D’ago jajayen idanunta tayi tace “Ai sun bar sona ne tunda har tsawa Abba ya min” “Don sun miki fad’a ba wai sun bar sonki bane, in bakisani bama toh don suna sonki ne yasa sukayi hakan” Suhal ya fad’a cikin lallami, Ilham kuma ta wani tura baki kaman zata fashe. Ganin tayi shiru yasa Suhal cewa “And about girki, ya kamata ki koya, kinga in kinyi aure bazaku dinga samun problem da mijin ba, iya girki shine mace sannan the best way to a man’s heart is through his stomach, maza basu wasa da cikinsu, promise me daga gobe zaki dinga shiga kitchen kina koyan girki gun su ummi da umma” Sai sannan ta d’an saki fuskarta tace “Ya Suhal kaima kanason matarka ta iya abinci?” Ba tare da ya kawo komai a ranshi ba yace “Sosai ma lil sis, abinci, snacks, inaga ma before bikin zan sata a catering school ta ‘kara koyo wasu abubuwa” Cikeda jindadi Ilham tace “Ya Suhal nice matarka ai ko?, saisa kakeso na koya girki” Dum!! Yaji maganar ta daki zuciyarshi, wayancewa yayi, yayi kaman bai gane maganarta ba yace “Yanzu dai ba wannan ba, kinmin al’kawari zaki fara koya?” Rungumeshi tayi tace “I promise Ya Suhal, i will do it for you, sannan kuma kacema Ya Fu’ad kar ya sakemin tsawa” ‘Ko’karin ‘ban’bareta daga jikinshi yayi yana cewa “Zan yi warning nashi karki damu, lil sis sakeni, kin girma kinyi nauyi, zakisa na kasa numfashi ai” Sakeshi tayi tana dariya tace “Wani nauyi ne dani da in na rungumeka zaka kasa numfashi?, ko bakason matarka tayi jiki sosai ne?, in bakaso zan soma slimming” ta ‘karasa maganar pure-heartedly. Girgiza kai kawai yayi yabar d’akin don yazama speechless, yanzu kam maganar Ilham yafara bashi tsoro da mamaki, akan wani dalili zata fara tsiro da sabbin abubuwa a tsakaninsu?, mesa zata dinga kiran kanta matarshi?, shi dai sha’kuwansu yana mata kallon ‘kanwa ne ba da wata manufa na daban ba, sannan aure fah, anya ma ilham tasan me take fad’a kuwa?, damuwan shi ma kar watarana ta kira kanta matanshi agaban iyayen nasu, ina!!, sam bazai iya auren Ilham ba, ba wai don batada kyau ko bata cika mace ba, Ilham ta wuce duk inda akeson kyakkyawar mace takai, bai mata kallon da ya wuce lil sis wacce ba aure tsakaninsu gashi kaman labari yanaso ya chanja. Fans, ku cigaba da biyomu don jin ya wannan labarin zai kasance. www.gidannovels.blogspot.com Munayshat.mywapblog.com Munay, Hanee da Stylish *REAL MHS* Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 4, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 29-30 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *29-30* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Bayan sati d’aya Rafee, Sofy da Nazee ne suna zaune a parlour suna kallon “The vow” a zee world, momy tafito daga d’akinta da shirin fita sai ‘kamshi takeyi. Kallonsu tayi sannan tace “Zan d’an fita anguwa, make sure kunyi girkin dare don zankai bayan Isha, Rafee da Sofy karku kuskura ku fita daga gidan nan, Leena dai banda damuwa da ita don batada rawar kai irin nakun nan, in kun fita ma nasa mai gadi ya gayamin, kunsan halina sarai”. Sofy ta wani marairace fuska tace “Haba momy, wannan ai rashin yarda ne, kenan Leena ne kawai mai jin maganarki?”. Rafee ta ‘kara da “Bar momy fah Sofy, tana mana kallon marasa kunya bayan mun mafi Leena sanin-ya-kamata”. Momy ta girgiza kai tace “Meh amfanin sanin-ya-kamata’n ku bayan baku amfani dashi?, Allah ya shirya”, ta maida kallonta wajen Leena tace “Auta kina bu’katan wani abu ne?”. Leena tayi murmushi tace “Momy zan tura miki as text message, naga Sisters sai harara nah sukeyi” Dariya momy tayi, ‘kasar zuciyanta cike da son yaran nata, ta d’auki key’n motarta sannan tace “Toh shikenan, ni na tafi” Kusan atare sukace “Sai kin dawo”. Tana tayar da motar ai kaman jira sukeyi har suna rige-rige wajen le’ka window da ke facing tsakar gidan, sai da suka tabbatar ta bar gidan sannan suka koma kan kujerun da suke zaune. Rafee har jikinta yana rawa don dad’i, wayarta ta d’auka ta danna ma Nazee kira kaman yanda tayi al’kawari. Tana jin Nazee ta d’auka tafara magana “Nazee kizo min da kayaki nah yanzu, kiyi sauri, momy tafita” Nazee ta amsa da “Okay, bani minti goma” “Toh sai kin iso” shine abinda Rafee ta fad’a sai ta katse wayar zuciyarta wasai. Sofy kuwa kiran Bash tayi akan yazo don kwana dewa momy ta kasa ta tsare ko bakin gate bata barinsu suje. Shima cikin jindad’i yace mata gashinan zuwa. Kallon juna sukayi ita da Rafee sannan Sofy tace “Ya zamuyi da mai gadin nan ne?” Rafee tana karkad’a ‘kafa tace “As usual, had’a kud’i zamuyi tunda shi mayen kud’i ne, mu bashi yabar su sushigo, kamin momy tadawo dai sun tafi” Mi’kewa alokaci d’aya sukayi suka shige d’akinsu, jim kad’an suka fito da kud’i a hannunsu, basu tsaya ako ina ba sai a ‘kofar d’akin mai gadin gidansu. ‘Kwala mishi kira Rafee tayi “Tijjani!, Tijjani!”. Da saurinshi ya amsa “Na’am hajiya” gamida fitowa yana ta rawar jiki. Had’a ido sukayi sannan Rafee tayi nodding mata kai alamun tayi magana, Sofy ta le’ka bakin gate sannan tafara magana “Tijjani, alfarma muke nema a wajenka”, tana ‘karasa maganar ta karkad’a mishi sabbin 500 naira notes dake hannunta Washe baki yayi yace “Toh toh, me za amuku?” Rafee tayi wani murmushi tace “Dad’ina da kai akwai gane bayani, abunda mukeso da kai shine zamuyi ba’ki saidai bamuson ko da wasa Momy tasani” Jim kad’an yayi yana nazari, chan sai yace “Amma dai hajiya bazasu dad’e ba ko?, don in tadawo ta gansu zan iya rasa aikina” Caraf Sofy ta kar’be “Kai tsoronka yacika yawa don Allah, bazasu wuce bayan maghriba ba” Jinjina kai yayi yace “Shikenan, meh zan samu?” Kud’in suka mi’ka mishi, ‘kirgawa yayi yaga dubu biyar-biyar ne, yatashi da dubu goma kenan. Assuring nasu ya ‘karayi kan baza asamu matsala ba su kwantar da hankalinsu, cike da jindad’i suka nufi parlour kowaccensu da tunanin da takeyi. A ‘bangaren Leena kuwa suna fita ta bisu da ido tanata sa’ka da warwara, wannan wani irin ‘kazamiyar rayuwa ne?, da taga hakan ba abinda zai haifar mata sai ba’kin ciki kawai ta mi’ke ta nufi kitchen don d’aura girkin da momy tace ayi don tasan yayyun nata bayi zasuyi ba. 15 mins later Sofy ce tasha wanka cikin riga da wando ta hard’e akan kujera sai duba time takeyi a cikin wayarta. Horn da taji a gate ne yasata tashi dasauri ta nufi tsakar gida, mai gadi yana wangale gate motar Bash yashigo. Yana parking yafito daga motar ya nufota, itako dagudu ta ‘karasa wajenshi, wani wawan runguma sukayi ma junansu kaman zasu had’iye juna. Bayan sun d’an nitsu sai suka koma motar suka shiga gidan baya, wasu abubuwa ya fara mata wanda yasa tafita hayyacinta cikin lokaci ‘kan’kani dama kuma sunyi missing na junansu, ganin haka yasa muka tattara yanmatan ‘kafafunmu muka bar wajen. Rafee tsaki take taja, sai faman kiran Nazee takeyi amma numbarta ya’ki shiga, tsaba ta tafi duniyar tunani har bata ji shigowar Nazee parlourn ba saida ta ta’bata, a firgice ta dubeta, wani ajiyan zuciya ta sauke gamida watsa mata harara. Cikin masifa tace “Nazee wani irin iskanci ne wannan?, tun yaushe kika cemin zakizo?, da kinsan ba a lokacin zaki taso ba da baki ce min nan da minti goma zakizo ba” Zama a gefenta Nazee tayi tace “I’m sorry luv, hold-up ne ya tsaidani wallahi, kinsan bazan ta’ba ‘kin zuwa akan lokaci da gan-gan ba” ‘Kir’kiro murmushi Rafee tayi gamida mi’kewa tace “Shikenan yawuce, ina abubuwa nah?” Nazee ta nufi ‘kofa tace “Muje, yana motar”. Jido kayakin suka hau yi, sunyi ‘kafa uku-uku sannan suka samu suka ‘kare kaiwa. Jin ana shigo da abubuwa yasa Leena dake kitchen le’kowa parlour amma bataga komai ba sai muryar Rafee da takeji daga d’akinsu. Rage gas cooker d’in tayi tanufi d’akinsu don ganin ma idonta wainar da ake toyawa. Har tasa hannu zata bud’e sai ta tsaya sakamakon taji Nazee na tambayar Rafee “Love, yanzu duk wannan kayan Hajiya ce ta baki?, tsaya ma tukunna, meh gaminki da ita?, mesa ta narkar da wannan uban dukiya a kanki?, meh dalili?”. Rafee tace “Meh kike tsammani?” Nazee tayi shiru sannan tace “There most be something, ba yanda za ayi haka kawai tayi wannan uban shopping nan a banza, ni gaskiya nafara zarginta ma” Rafee tayi guntun tsaki tace “Ki bar zargin komai, Allah ne kawai yasa jininmu ya had’u, tana kyautata min ne bada wata manufa ba” Nan ta murd’a hannun ‘kofar don ‘kara ma ‘kwanyanta haske akan abinda kunnenta suka jiyo mata, tana shiga tafara cin karo da tarkacen kayaki, baki bud’e ta ‘karasa shiga, tsayawa tayi tana bin kayakin da kallo, da ‘kyar ta iya cewa “Wai wai!!, ya Rafee irin wannan kayaki haka?” Rafee sai lokacin tasan Leena ta shigo d’akin don ta bama ‘kofa baya tana jera kayakin acikin wardrobe, kallon uku saura kwata tamata sannan tace “Ehen, meh yasamu kayan?, meh gaminki dasu?” In-ina Leena ta hau yi tace “Babu, naga sunyi kyau ne, waya miki wannan uban shopping haka?” A fusace Rafee tace “Ubanki ne yayimin, ke naga kwanan nan kanki yana fizga ko?, in baki bar shiga sabgana ba sai na gyara miki zama” Maganar yamata ciwo sosai amma saita danne tace “Allah yabaki ha’kuri, naga ke yayata ce, banga wani abu ba don naga kinsamu alheri har na tambaya waya miki” Nazee taji haushin yanda Rafee tayima Leena, ita dai Allah ya d’ora mata son Leena kaman ‘kanwarta uwa d’aya uba d’aya, cikin nuna ‘bacin rai ta mi’ke tace “Rafee what is this?, why are you always rude to her?, itama fah ‘kanwarki ce kaman Sofy, u should treat her with love kaman yanda kikema Sofy, meh Leena tayi da har zagi zageta?, kuma ma wai akan wancan shegiyar tsohuwar, meh ma sunanta?, haj hafsat ne ko mene?, akanta kika zagi ubanki don bakida hankali”, taja wani dogon tsaki tana huci, sosai ranta ya ‘baci don ya had’u da kishin da takeji wata haj hafsat tana faman ‘kwace mata Rafee. Das’karewa Rafee tayi ta kasa cewa komai, bata ta’ba ganin ran Nazee ya ‘baci irin haka ba, sai lokacin ta gane sam bata kyauta ma ‘yar innocent ‘kanwarta ba. Juyawa Nazee tayi da niyyar barin gidan, dasauri Rafee ta kamota tace “Yi ha’kuri, bansan me ya hau kaina ba” Nazee ta maida kallonta wajen Leena da ke raku’be a jikin ‘kofa tana zubda hawaye, addu’a takeyi Allah yasa ba haj Hafsat ‘kawar momy ba ce, zuciyarta sai raya mata abubuwa da dama yakeyi. Batayi aune ba taji Rafee ta kama hannunta ta fara cewa “Lil sis kiyi ha’kuri, bansan mesa namiki magana in a rude way ba”. Leena batace komai ba sai binta takeyi da ido wai yau itane Rafee take bama ha’kuri akan rude behaviours nata, bata ‘kara jin mamaki ba sai da Rafee ta d’auko wasu dogayen riguna guda uku tabata kyauta. Godiya tamata sannan tace “Bari momy tadawo na nuna mata” A firgice Rafee tace “No, no, wannan tsakanina dake ne, karki gayamata” Dama Leena ta fad’i haka ne da nufin buga cikinta, jinjina kai tayi tace “Okay, bazan gayamata ba”. Tana kaiwa nan ta bud’e drawer d’inta ta ajiye gowns d’in aciki sannan ta koma kitchen don ‘karasar da girkinta da kuma yin shawara da zuciyarta. www.gidannovels.blogspot.com *REAL MHS* Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 4, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 31-32 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *31-32* ☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Da fitan Leena daga d’akin Rafee ta rungumo Nazee tana bata ha’kuri har dai ta ha’kura. Ba ita tabar gidan ba sai maghriba shima bawai don sun gaji da juna bane sai don gudun kar momy tadawo ta sameta. Sofy da Bash kuwa holewa sukayi sosai har saura ‘kiris tabashi kanta, ko meh ta tuna kuma oho saita tureshi tana kakkare jikinta. A wahalce ya dubeta yace “Baby dont do this to me, aurenki fah zanyi, ki kwantar da hankalinki ki bari muji dad’in rayuwar mu kamin muyi aure” Girgiza kai ta hau yi tana cewa “Im sorry Bash, bazan iya baka kaina ba duk da i love you more than my own self, lets just keep it this way, mu tsaya a romance da mukeyi, shi kad’ai ma ya ishi ya cire mana kwad’ayin juna whenever the need arises” Jikin Bash rawa yafara yi don yasa rai sosai, jingina yayi da jikin window na motar yana maida numfashi sama-sama, ya d’au lokaci ahaka sannan yasamu ya saita kanshi, azuciyar shi ya raya ma kanshi dole ne ma yasan hanyar da zaibi har ya cimma burinshi akanta ko da kuwa ta ‘karfi ne. Da ha’kuri da banbaki ta samu ya sauko daga dokin fushin da ya hau, hirar su suka cigaba da yi wanda rabi hirar batsa ce. Bashi yabar gidan ba sai bayan Nazee ta tafi shima saida mai gadi yazo yace mishi “Yalla’bai kayi ha’kuri katafi kar hajiya tadawo na rasa aikina”. Shigan Sofy gida tasamu Leena da Rafee suna hira kaman basu ba, ada kullum Rafee hantarar Leena takeyi amma abun mamaki yau gashi har dariya sukeyi suna labarai, shiga cikin d’aki tayi tashiga wanka sannan tasa wani short gown ta d’aura zani akai tayi sallar maghriba da Isha don lokacin Isha ma har ya shiga, da ta idar ne ta cire zanin ta ninke sannan tafito parlour suka sa abinci su ukun suna ci suna kallo. Ahaka momy tazo ta samesu, mamaki taji sosai wai yau y’anmata ukun sunacin abinci a plate d’aya, rabon da taga hakan tun kamin su girma su mallaki hankalin kansu. Sannu da dawowa suka mata, amsa musu tayi gamida fad’awa kan kujera a gajiye, bayan tasha ruwa sai tace “Yanzu kam kun fara abun kirki, tun da nafita har nadawo Tijjani yacemin ko tsakar gida baku fita ba kuna cikin parlour” Da yake dama ance “A criminal is always afraid” sai suka fara exchanging glances tsakaninsu wanda sam momy bata lura da hakan ba don a gajiye take. Leena ne tayi ‘karfin halin cewa “Momy ko akawo miki abinci ne?” don kawar da maganar. Momy ta tashi da jakarta tace “Bari na watsa ruwa, zanzo naci”, bata jira cewarsu ba tayi shigewarta d’aki. Atunaninta yanzu yaran nata sun fara shiryuwa don yanda mai gadi ya dinga yabonsu, batasan sun manna mata hauka bane. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Suma bayan sati d’aya. Yanzu Ilham ta dage da shiga kitchen don tun ranar da Suhal yace mata shi yanason matarshi ta iya girki bata sake missing na shiga kitchen ba, ba laifi ta fara picking na wasu girke-girke saidai har yanzu da sauranta kad’an. Tsakaninta da Fu’ad kuwa tuni sun koma normal, haka iyayen nata ma taje ta basu ha’kuri sun kuma ji dad’in chanjawan halinta farat d’aya. Tun daga nesa Suhal yake ‘kwala ma Fu’ad kira amma bai amsa ba, hakan yasa yanufi d’akin da saurinshi. Yana bud’ewa yaga Fu’ad du’kun’kune acikin bargo yana ri’ke da waya, lura da yayi sam Fu’ad bai san yashigo ba yasa yayi amfani da wannan dama don sanin meh ya d’auke hankalinshi har bai ji duk kiran da yake mishi ba. Tsugunnuwa yayi ya bud’e blanket d’in a hankali ta baya, aikuwa idonshi suka sauka akan Blue Film da Fu’ad yake gani. Tsaba ya rikice har bai san lokacin da ya fizge wayar ya had’ata da bango ta tarwatse ba, a firgice Fu’ad ya mi’ke tsaya don ganin waya fasa mishi waya, zaro ido yayi ganin Suhal tsaye a gabanshi sai huci yakeyi. Stammering yafara “Su…ha..l….yau…she….ka….shi…go?” Suhal kama kanshi yayi yana tunanin yaushe Fu’ad ya fad’a wannan hali na kallon batsa baisani ba. Kallon Fu’ad yayi up and down sannan yace “Fu’ad, meh ya kaika fad’awa wannan hanyar?, are you out of your mind?, abinda kake ganin nan kai da kanka kasan haramun ne, mesa kake gani?, bakasan zunuban da kake kwasa ba ko?”. Tsuru-tsuru Fu’ad yayi, gashi red-handed Suhal ya kamashi ba halin yin denying, ganin yayi shiru yasa Suhal magana cikin d’aga murya “Ba da kai nake magana bane?!!!!, answer me!!!” Fu’ad ya bud’e baki zaiyi magana kenan sukaji Abba yana knocking na ‘kofar gamida cewa “Ya dai Suhal?” Ido Fu’ad ya ‘kwalalo kaman zasu fad’o ‘kasa, takawa Suhal yayi ya tattara pieces na wayan ya mi’ka ma Fu’ad sannan ya bud’e ‘kofar. Abba yana shigowa yasake tambayar Suhal “Suhal meh ya faru naji muryanka har waje?, Fu’ad yayi wani abun ne?” Tausayin Abba ne ya kama Suhal, yasan da ace zai gayama Abba abinda yakama Fu’ad yakeyi da matakin da zai d’auka Allah ne kad’ai yasani, mai da kallonshi wajen Fu’ad da ya zuba mishi pleading eyes yayi, harara ya watsa mishi sannan ya maida dubanshi wajen Abba, murmushi ya ‘kwa’kulo sai yace “Ba komai Abba” Abba ya bishi da kallon karka maidani ‘karamin yaro mana, atake Suhal ya had’a ‘karya yace “Dama Ilham ne tacemin ya mareta bata mishi komai ba, nazo ina tambayar shi sai yamin shiru shine raina ya ‘baci, amma ba wani abu bane Abba” Abba ya dai girgiza kai kawai ya sa kai yafice daga d’akin ba don ya yarda ba. Yana fita Fu’ad ya sauke wani wawan ajiyar zuciya don ya tsamman Suhal bazai rufa mishi asiri ba. Dur’kushewa yayi a kan gadonshi, Suhal kuwa waje ya nufa batare da ya sake waiwayan Fu’ad ba, har yakai ‘kofa yaji Fu’ad yana cewa “Wallahi sharrin shaid’an ne kuma bazan sake ba, don Allah ka rufamin asiri kar ka gayama iyayenmu, natuba” “Ina tausaya ma rayuwarka in ka koma Turkey ba mai kwa’bar ka, gwanda tun wuri kayi ma kanka fad’a sannan ka ri’ke ro’konka, da naga dama da tuni na gayama Abba abinda ya faru, banyi don kai ba, don banason tayar mishi da hankali yasa na had’a ‘karya na gayamishi” duk maganan nan yayi sune batare da ya kalli Fu’ad ba, yana gamawa kuwa yabar wajen. Fu’ad da kanshi yasan lallai yayi sa’an yaya yakuma shaida cewa ba ‘karamin so Suhal ke mishi ba tunda har ya iya ‘karya don kawai ya kare shi. Sim card nashi kawai yacire daga wayar sannan ya saka wayar a dustbin don in yace zai gyara ma kud’in da zai kashe ba kad’an bane, gwanda kawai ya siya wani tunda yanada kud’i a account nashi. Fita yayi ya d’auki motarshi yaje ya siya latest waya wanda ake yayi a lokacin. Suhal ya fita harkar Fu’ad, sannu-sannu kawai yake had’asu wanda agidan sam ba wanda yagane. Har d’aki Fu’ad ya sameshi ya dinga bashi ha’kuri yana cewa yatuba, har kuka sai da yayi sannan Suhal yace mishi shikenan yawuce amma in ya sake kamashi da laifi irin haka ba abinda zai hanashi gayama iyayen nasu. Da wannan doka suka koma normal lives nasu kaman basu ba. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Tana cikin driving motarta ta tsaya, ba yanda batayi ba amma ya’ki tashi gashi wajen ba mutane, d’ai-d’aikun motoci ne suke wucewa jifa-jifa. Wayarta ta ciro don kiran mechanic shikuma wayarshi ya’ki tafiya, matsalar network. Ga uban rana da ake tafkawa, tun tana tare motoci har ta gaji don ba wanda ya tsaya, tana mamaki yanda na ‘kwarai sukayi kad’an a zamanin nan. Ranar ya shiga jikinta sosai don takai kusan minti talatin a wajen, number momy da duk sisters nata kaman had’in baki suma sun’ki shiga. Ganin haka yasa ta kasa daurewa kawai sai ta fashe da kuka abun tausayi, chan taji ana mata horn amma bata d’ago ba don kukan da yaci ‘karfinta. Mutumin yafito ya iso jikin motar inda ta kifa kanta tana kuka. Sallama yamata ta amsa batare da ta d’ago ta kalleshi ba, chan sai yace “Meh ya sameki kikazo tsakiyar hanya kika hau kan motar kina kuka?” Sai sannan ta d’ago fuskarta, idanunta duk sun rine sun zama jawur, share hawayenta tafara yi tana cewa “Motar na ne ya ‘baci tun dazun, na kira mechanic da ‘yan gidanmu amma duk bai shiga, duk motar da na tsayar don in nemi taimako kuma ba wanda ya tsaya” tana ‘karasa maganar wani sabon kuka ya ‘kwace mata. Tausayin ta yaji a lokaci d’aya kuma shagwa’barta ya burgeshi, cikin sigar lallashi yace “Yi ha’kuri ki sauko ki rufe motar in yaso sai na maidake gida, daganan sai ki kira mechanic d’in yazo ya d’auki motar don ni banda number mechanic nah” Kallonshi tayi tana ‘ko’karin karantar shi, wani zuciyar yana ce mata ta bishi kawai don kaman ba mugu bane, wata zuciyar kuma yana ce mata MUGU BAI DA KAMA(Book by kausariyya). Daga ‘karshe dai kawai ta sada’kar akan zata bishi, sau’kowa tayi ta rufe motar kaman yanda yace mata sannan ya bud’e mata motarshi tashiga, da kwatance har ya kaita gidansu. Godiya ta mishi, har ta bud’e motar sai yace “Sorry, ya sunan mai kukan?” Kunya ne ya lullu’beta tunawar da tayi yanda ya ganta tana kuka shar’be-shar’be, sunkuyar da kai tayi tace “Sunana Yaleena amma ana kirana Leena” Jinjina kai yayi yana mouthing na sunan, murmushi yayi yace “Nice and unique name, ni sunana Suhal”. Tohh readers ku cigaba da biyomu www.gidannovels.blogspot.com Munay, Hanee and Stylish *REAL MHS* Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 8, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 33-34 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *33-34* ☆☆☆☆☆☆☆☆ “Thank you Suhal, Allah ya saka maka da alkhairi” Leena ta fad’a sannan ta fice daga motar. Wani gentle smile ya sakar mata, bai ce komai ba yaja motarshi, bin motar tayi da ido har saida ya ‘bace mata sannan ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya ta nufi cikin gida. Tana shiga parlour taga Momy, Sofy da Rafee zaune suna hira, ganinsu yasa taji wasu zazzafan hawaye suka fara zubo mata. Duk sun rikice ganin yanayin da ta shigo cikin gidan, a kid’ime suka hau tambayarta me ya faru. Hawayen nata ta share gamida ‘karasawa ta zauna a kusa da Momy ta kwantar da kanta a jikinta sannan ta soma gayamusu irin wahalar da tasha har daga baya wani bawan Allah ya taimaka mata kuma shi ne ma ya kawota gida. Dariya sosai Sofy da Rafee suka farayi jin har kuka Leena tayi, Momy ma dai abun dariya ya bata amma ganin yanda Leena tayi rau-rau da ido kaman zatayi kuka yasa ta danne nata, hararar su Rafee tayi tana shafa bayan Leena alamun lallashi. Sai da tabar sheshshe’kar kukantan sannan Momy tace “Yi ha’kuri auta na, bari zan kira mechanic yazo ya kar’bi key d’in in yaso sai ki mishi kwatance yaje ya d’auka” Jinjina kai Leena tayi, cike da shagwa’ba tace “Kinga sai dariya suke min ba?” Momy tayi murmushi tace “Barsu suta yi tunda su dariyar mugunta suke ma auta nah, ki shirya gobe zamuje ki za’bi kowanne irin motar kikeso” Wani ihun dad’i Leena tayi tana ‘kara ‘kan’kame uwar tasu. Su Rafee da Sofy kuwa kaman d’aukewan ruwa dariyar su ya tsaya, mamaki ne ya cikasu har basu san sanda suka wangale bakinsu ba. Sofy ne ma tayi ‘karfin halin cewa “Momy gaskiya baki mana adalci ba indai hakane, yaushe ne muka miki maganar munaso ki chanja mana motar amma kikace bakida kud’i?, yanzu kuma kwatsam sai kice zaki d’auki Leena ta zabi duk wanda takeso?, kuttt!!” Rafee ta kar’be “Wallahi da sakel, bazamu yarda ba, wannan ai nuna bambanci ne, don Allah Momy karki mana haka” Sofy tace “Kuma ma Momy last year fah kika saya mata wannan, nawa yanzu yakai shekaru uku, na Rafee kam yakai hud’u ma if i’m not mistaken” Rafee ta wani marairaice tace “Please Momy….” Duk protesting da sukeyin nan Momy batace dasu ‘kala ba sai murmushin da take binsu dashi, Leena kuwa gwalo take ta musu. Da sukaga ba sarki sai Allah sai suka mi’ke suka nufi kujeran da Momy da Leena suke zaune gamida tsugunawa bisa guiwowinsu. Momy ta kallesu tace “Wayace kuzo kuyi kneeling?” Leena ta gyara zamanta tace “Momy barsu, ha’kuri sukazo bayarwa” Harara Sofy da Rafee suka watsa mata sannan suka maida dubansu wajen momy, kama kafafunta sukayi sai Rafee tace “Momy we are sorry, don Allah dont punish us this way, ki taimaka ki chanja mana motar muma” Momy tayi jim sannan tace “Naji, naji, amma on one condition” Bakunansu har kunne suka had’a baki sukace “Ko menene zamuyi momy” Dariya tayi tace “Ku bata ha’kuri, in ta ha’kura fine, zan saya muku” Sofy tace “Waye kenan?” Momy ta nuna musu Leena tace “Leena mana, dariya kuka mata don motarta ya ‘baci, in ta ha’kura sai na saya muku” Wani dakewa Leena tayi ta tsare ita adole tana jira abata ha’kuri, Rafee taja tsaki tace “Wannan ai zubda girma ne Momy, ‘kanwar mu ne fah ita” Sofy tayi jim tana tunani, chan sai tace “Auta kiyi ha’kuri kinji?” Cike da mamaki Rafee take kallon Sofy jin ta bada ha’kuri ba tare da gardama ba, zungurarta tayi tace “Ke fah wawiya ce, wannan jinjirar zaki bud’e baki kina bama ha’kuri?” Leena tayi murmushi tace “Rise Sofy, kin samu kyautar motar” Tsalle Sofy tayi tana rawa tasamu motar, tsugunnawa tayi daidai kunnen Rafee tace “Sis, ki rufa ma kanki asiri ki bata ko kuma kiyi bye-bye da chanja motar this year” Momy kam me zatayi in ba dariya ba, kirar mechanic tayi yace gashinan zuwa. Rafee kuwa ta wani dake ita batason raini, chan sai ga mechanic kam ya iso, har ‘kasa ya dur’kusa ya gaida Momy, kwatance Leena ta mishi sannan ta bashi car key d’in. Har zai fita sai Momy tace “In ka gyara inaso kayi painting nashi don kyautar wa zanyi” Mechanic ya amsa “Toh” sannan yasa kai ya bar parlourn. Yana fita Leena ta saci kallon Rafee, tana dariya ‘kasa-‘kasa tace “Momy ina laifi abama Rafee tunda ita bazata samu sabo ba?” Momy ta kwashe da dariya tace “Kin kawo shawara mai kyau auta, hakan za ayi, ita zan bama” Rafee ta mi’ke tace “Whatt??!?, ni za abama kwancen motar?, wallahi bazai yuwu ba” Momy ta gimtse fuska tayi ‘kwafa tace “Kina tsamman wasa nakeyi ko?, karki bama Leena ha’kuri, zakisha mamaki gobe” Ganin kaman Momy dagaske takeyi yasa Rafee shafa ma kanta ruwa ta isa wajen Leena tana wani cin rai, dagewa tayi tace “Yi ha’kuri” Leena ta juya kai kaman bata jita ba, hakan yasa Momy cewa “Open your mouth and speak in an audible tone ba ki tsaya kina wani cin magani ba” Ba don taso ba ta bud’e baki ta ‘kara sautin magananta tace “Auta kiyi ha’kuri” Murmushi sosai Leena ta sake, kallon Momy tayi tace “I forgive her momy” D’aga mata kai momy tayi alamun “Noted” Leena ta maida kallonta wajen Rafee da ke tsaye a gefenta tace “Go and sit down, kin ci sabuwar motar gal a leather” Murmushi Rafee tayi takoma kujerar da take zaune. Hira suka hau yi sunata tsokanar junansu gwanin sha’awa, sai sautin dariyarsu ke tashi. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Suhal yana sauke Leena ya wuce Pharmacy da Abba da Baba suke gina mishi, duba cartons na drugs da akayi ordering yakeyi don kar a manta ba a siya wani ba amma sam ya kasa maida hankalinshi. Da yaga ba abinda zai iya tsinanawa sai kawai ya sallamesu yace bai jin dad’i zai dawo daga baya. Yana driving sai tunanin Leena yakeyi, nutsuwar ta ya burgeshi, shagwa’barta, kukanta, idanunta sunfi komai d’imauta shi. Ahaka har ya isa gida, ya dad’e a garage sannan ya samu ya saita kanshi yafito yana Allah yasa kar ya had’u da kowa har ya isa d’akinshi don yasan duk wanda yaganshi zai gane akwai abinda ke damunshi. Cikin rashin sa’a yana wucewa zai shiga d’aki Ilham dake jiran dawowarshi taga giftawar shi, sam bai ma lura da ita ba don hankalinshi bai wajen, mi’kewa tayi ta kira sunanshi “Ya Suhal” Wani takaici ne ya ziyarci zuciyarshi, ahalin yanzu ba abinda yake bu’kata kaman ya zauna shi kad’ai yana tunanin Leena. ‘Ko’karin mazgewa yayi had’e da juyowa yana kallonta, a gajiye yace “Lil sis, lafiya kam ko?” Matsowa kusa dashi tayi tana karantar fuskar shi, lura da abinda take faman yi yasa shi saurin sunkuyar da kanshi, murmushi tayi tace “Tun dazun nake jiranka anan ai, ka dawo kuma bakama lura dani ba” Kanshi a sunkuyen yace “Sorry, kaina ke ciwo saisa ban lura ba” Cikeda kulawa ta kama hannunshi tana ‘ko’karin mi’kar da ‘kafanta don jin temperature na kanshi da yace yake ciwon, yaci sa’a kuwa kan nashi da d’an zafi kad’an, hakan yasa Ilham bata kawo komai a ranta ba. Jan hannunshi tayi tace “Muje ka kwanta sai in kawo ma magani kasha” Murmushi ya ‘kir’kiro gami da bin ta, key ya bata ta bud’e d’akin nashi, zaunar dashi tayi akan kujera sannan ta juya da sauri tace tana zuwa. Hulan da ke kanshi ya cire ya ajiye sannan ya cire rigan ya rage dagashi sai vest, fad’awa kan kujera yayi yana ajiyar zuciya. Bayan kaman minti biyu sai Ilham tadawo da magani da ruwa, bashi tayi, ba musu kuwa ya kar’ba ya sha don ya ma kasa gane kanshi, kanshi a ‘kulle yake, baya tunanin komai sai Leena. Ilham ta zauna a ‘kasa tana wasa da hannunshi ba wanda ke magana a cikinsu, chan dai ya mi’ke ya kalli Ilham sai ta bashi tausayi, shafar fuskanta yayi yace “Lil sis barina shiga d’aki na kwanta, ina jin bacci” Itama mi’kewan tayi tace “Toh muje in kayi baccin sai na tafi” Da sauri yace “Kije kawai bakomai, in na tashi zan shigo cikin gidan” don so yake ya zauna shi kad’ai Ba don taso ba ta fice daga parlour’n idanunta duk hawayen tausayinshi, atunaninta ko ciwon kai d’in ne yake damunshi sosai. www.gidannovels.blogspot.com Munay, Hanee and Stylish *REAL MHS* Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 12, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 35-36 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *35-36* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Kwance yake yanata juyi akan gadonshi, sonta yayi mishi mugun kamu gashi bai ta’ba soyayya ba saisa yake ganin kaman soyayya wahala ne tsantsa, zuciyarshi da ‘kwa’kwalwarshi sun toshe, shi har abun ma tsoro yafara bashi, daga baya kuma yaja tsaki yace afili “Yarinyar da ban sani ba tana neman birkita min lissafi, I have to get her out of my mind don bana ra’ayin soyayya, ban shirya yin soyayya yanzu ba”. Da ‘kyar yasamu ya lallashi zuciyarshi har yayi bacci. Kiran sallar maghriba ne ya tayar dashi daga baccin da yakeyi, da ‘kyar yasamu ya shiga toilet yayi wanka yasa wani short sleeve shirt da three-quarter. Masallaci ya wuce don yin sallah, tare suka dawo da iyayen nasu as usual. Ilham suka gani tana jera abubuwan da zasu bu’kata wajen cin abinci, sannu da shigowa ta musu sannan taje ta kira umma da ummi daga d’akunansu. Dama wajen zamanta a tsakiyan Fu’ad da Suhal ne, tana zama ta d’an karkato da kai daidai kunnenshi tace “Ya Suhal ya headache naka?” Murmushi ya mata yana wasa da cokalin hannunshi yace “Da sauki lil sis, thanks to you” Fad’ad’a murmushinta tayi tace “Kafi ‘karfin haka a wajena” Kallonta yayi ta gefen ido ya girgiza kai kawai ya cigaba da caccakula abincin yana ci bawai don yana jindad’inshi ba sai don kar iyayen su hau tambayarshi, shi kuma bai shirya answer da zai basu ba. Da suka gama suka zauna don kallon news amma Suhal ya musu sai da safe, cikeda mamaki Abba yace “Lafiya dai ko?” “Lafiya lau Abba, nagaji inajin bacci ne kawai” Baba yace “Toh Allah yasa hakan ne” Bai son jan magana sai kawai ya sallamesu ya fice daga sashen. 10:20PM Duk iyayen sun nufi d’akunansu don shirin bacci amma Ilham hankalinta yana wajen Suhal, sosai takeson sanin halin da yake ciki, tashi tayi tabar Fu’ad zaune yana chatting a wayarshi. Ba tare da knocking ba kawai ta bud’e d’akin, ganin wuta a kunne a bedroom nashin sai kawai ta kutsa kanta ciki. Kwance ta sameshi idanunshi suna kallon ceiling amma hankalinshi sam bai wajen don ta kira sunanshi sau hud’u ba tare da yasani ba. Ta’bashi tayi, firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, baki wangale yake kallon Ilham, chan dai ya fuske yace “Yaushe kika shigo?” Zama tayi a bakin gadon tace “Tun dazu, ya Suhal meke damunka?, tunanin me kakeyi?” Daburcewa yayi yace “Amma meh ya hanaki yin sallama?” Da mamaki take kallonshi don ita tun tashinta indai zata shigo d’akinshi bata damuwa da knocking ko wani abu, shiga kawai takeyi, hakan yasa tace “Naga kullum haka nake shigowa amma baka ta’ba magana ba, mesa sai yau kake ganin laifi na da banyi sallama ba?” Murmushi yayi yace “Ba laifinki nake gani ba, ina dai gayamiki ne sabida nan gaba, daga yau ki dinga sallama ko knocking kinji?, its not proper ace gatsau kawai ki shigomin d’aki” Jinjina kai tayi tace “Yi ha’kuri ya Suhal, bazan sake ba” Zama yayi ya jingina da jikin gadon yana mai fuskantar ta yace “Ya wuce, akwai abinda kikeso ne?” Girgiza kai tayi tace “Babu, nazo na duba ko headache d’in ne yasake dawowa saisa ka bar parlour dawuri sai kuma nazo nasamu kana tunani?, is something bothering you?” Jim yayi yana tunanin me zai ce mata, daga baya yayi murmushi yace “Nothing to worry about, kawai sungullan bud’e pharmacy d’in nan ne ya hau kaina, im stressed out” Cikeda tausayawa tace “Ayyah sannu Ya Suhal, ko na dinga rakaka in yaso sai na tayaka wasu abubuwan?” Da sauri ya katseta yace “No dont bother, zai wuce kwanan nan” Hayewa kan gadon tayi, shiko binta yayi da ido yana ganin ikon Allah. Baiyi aune ba yaji ta rungumeshi tana hawaye, bubbuga bayanta yayi yana tambayarta me ya faru. Cikin muryan kuka tace “I cant take it ya Suhal, bazan iya ganin kana wahala ba, zuciya na bazai iya d’auka ba, please let me help you” Zuciyarshi ya hau dukan uku-uku don yanzu kam ya gama tabbatar ma kanshi inda Ilham ta dosa amma sai ya shashantar da maganar ya d’ago kanta yace “Shine harda kuka?” Zuba mishi idanunta tayi tace “Bakasan matsayinka a wajena ba ko?, Ya Suhal ko kaina banaso kaman yanda nake son….” Katseta yayi ta hanyar cewa “Shhhh, its okay, shikenan ki bar zubda hawayenki akaina kinji?” Rungumeshi ta ‘kara yi kaman zata shige jikinshi tana sauke ajiyar zuciya, tunani sosai Suhal ya farayi “Ilham why me?, bakisan kallon ‘kanwa nake miki ba ko?, mesa zuciyarki zata wahalar dake haka?, ina tausayinki sosai don ban jin ko da d’igon soyayyarki a raina saidai i cant bear seeing u hurting, bazan iya ba, gashi Leena tazo tana neman shiga rayuwana ba tare da na sani ba, bazan ta’ba nuna bansonki ba Ilham don ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com acikin zuciyata”. Bayan ya gama sa’ke-sa’kenshi sai ya janyeta daga jikinshi cikin dabara, hannunta ya ri’ke yace “Cry no more okay?” Jinjina kai tayi sannan ta sauko daga kan gadon ta mishi sai da safe gamida pecking nashi a kumatu. Har takai ‘kofa sai ta juyo ta kalleshi, murmushi yamata sai tasa kai ta fice daga d’akin. Tana fitowa suka kusa cin karo da Fu’ad, wani kallon tuhuma yabita dashi don shi yanzu sam hankalinshi baya kwanciya yanda Ilham take shishshige ma Suhal duk da yasan Suhal will never hurt her. Sunkuyar da kanta tayi kaman mara gaskiya ta wuce ta gefenshi, shiga d’akin yayi don yi ma Suhal sai da safe. Nan ya tarar dashi a tsakiyan d’aki sai pacing to and fro yakeyi, gyaran murya da yayi ne ya fargar da Suhal akan Fu’ad ya shigo d’akin. Fu’ad ya ‘kare mishi kallo sannan yace “Dama nazo na maka saida safe ne” Suhal ya d’an sosa ‘keya yace “Okay, Allah ya tashemu” Jinjina kai Fu’ad yayi yabar d’akin batare da yace komai ba. Daren nan Suhal bai samu ya runtsa ba, har hawaye sai da ya zubar don tausayin halin da ya tsinci kanshi aciki rana tsaka, soyayyar Leena yana azabtar dashi har yana ganin bazai iya jure rashinta akusa dashi ba, soyayyanta ya mishi mugun kamu da bai ta’ba zaton akwai irinshi ba duk da dai shi bai ta’ba soyayya ba. Ya mi’ke, ya zauna, ya kwanta, chan kuma sai ya sake mi’kewa har dai ya gaji ya yanke shawarar yin nafila don samun sau’kin abinda yakeji, alwala yaje ya d’auro ya dinga jerosu yanata kai ma Allah kukanshi, daf da asubah bacci ‘barawo ya saceshi. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Washegari kamar yanda Momy ta musu al’kawari kaisu su za’bi duk kalar motar da sukeso ta kuwa cika musu, motoci masu kyau suka za’ba;Leena wani chevrolet ta za’ba, Sofy ta za’bi wani Corolla, Rafee kuma Peaugeot ta d’auka. Kowanne daga cikin ukun bazai kasa million goma ba don sabbi gal a leather ne sannan su ke trending. Komawa gida kowaccensu da motarta ta koma, murnar da ke cikin zu’katansu baki bazai iya fad’a ba, agida suka rungume Momy suna ta zuba mata godiya suna shaida mata yanda suke bala’in sonta and they are lucky to have her, murmushi take ta zubawa tace musu “Ba ni kad’ai zakuyi ma godiya ba don ba da kud’ina kawai na siya ba” Basuyi mamakin jin furucin nan daga bakinta ba don sun san tabbas kud’in daga wajen Daddy yafito, dama shi duk da bai zama dasu hannunshi bud’e yake;ma’ana yana tura musu kud’i ta hannun momy fiyeda misali. Rafee da Sofy suka wani gintse fuska alamun ko oho, ganin haka yasa Momy tace “Ni ku bar wani gintse min fuska, ku kirashi ku mishi godiya tunda da kud’inshi ne kuma ba yanda kuka iya, shine ubanku” Leena murmushin ya’ke tayi tace “Okay Momy, saidai inaso nasan mesa daddy bai kula damu?, mesa bai damuwa da sanin ya muke?, ko hiran kirki fah momy baiyi damu, ni tsoronshi ma nakeji wallahi” tayi shiru, duk suka zuba mata ido suna jiran ta cigaba. “Watarana wallahi I cant help but think, asking myself some stupid questions; ko dai daddy ba asalin ubanmu bane?, in ko asalin ubanmu ne toh tabbas bai ‘kaunarmu, ya….” Da sauri Momy ta katseta “Kul!!, kar na sake jin wannan maganar daga bakinki, batun so kuma I can assure you babanku yana ‘kaunarku fiye da tunanin mai tunani don haka kibar ganin kaman baisonku ne, abinda yasa yake nisantarku kuma ku kanku kunsan he is a very busy man, duk wannan sungullan yanayi ne don ku, don ya tara muku dukiya da bazaku ta’ba neman abu ku rasa a duniyar nan ba, ku mishi uzuri” Momy ta fad’i hakan ne don batason yaran su tsani ubansu tunda bai basu duk wata kulawa da uba ke ba ma ‘ya’yanshi, shi a ganinshi kud’i, material things sune rayuwa, ya manta cewa kowanne mutum koman girmansa yana bu’katar UBA ko don neman shawara da sauransu, ba ranar da in sunyi waya bata mishi ‘korafi akan hakan amma dayake shi mutum ne mai bahagon tunani…har yau ya kasa fahimtar ta. Hawaye Leena ta share tace “I’m sorry Momy amma don Allah ki fahimtar da Daddy munfi bu’katar fatherly love and care daga gareshi akan miliyoyin kud’in da yake turawa don mu, bawai nuna rashin godiya akan hidima da yakeyi damu bane, a’a, sai don kud’i baya ta’ba sayan farinciki, Momy akullum zuciya nah acikin ‘kunci yake na rashin daddy akusa damu, ko irin abu ya shigar min duhu tsoron tambayarshi nakeyi don tamkar wani stranger nake ganinshi” ta ‘karasa maganar muryarta yana rawa mai nuni da zuciyar tata a raunane yake. Momy ta kalli Rafee da Sofy da tunda Leena tafara magana suka ja jiki suka zazzauna akan kujera ba tare da sunce komai ba. Kama hannun Leena Momy tayi tace “Kibar damuwa indai akan wannan ne, I’ve always been here for you ko ba haka ba?, ni mai baku shawara ne aduk lokacin da kuke da bu’katar hakan and whenever you need someone to talk to” Leena tayi jim sannan ta shiga girgiza kai tace “Ke daban daddy daban Momy, each one of you yanada role da yafi iya playing, nasan kullum kina tare damu and banda bakin da zan nuna farinciki nah akan hakan” tayi shiru, sai kuma ta cigaba “We need a father, Momy ki taimakemu ki sa daddy ya zama uban da yake tarairayan mu, uban da zai yi mana holo idan munyi ba daidai ba, uban da zamu sha’ku dashi wanda bazamuji shakkarshi ba” da ‘kyar ta iya ‘karasar da maganar don yanda kuka ya taso mata. Sofy da Rafee ma saida suka zubda hawaye, Momy tayita basu baki tana encouraging nasu akan su dage da addu’a Allah ya karkato da hankalinshi zuwa gida, daganan tasa su kiranshi don su mishi godiya, as usual, daga ya amsa gaisuwar da lafiya saikuma da suka mishi godiya yace bakomai, batare da wani hira ba suka mishi sallama. ☆☆☆☆☆☆☆☆ 3 days later Suhal komai ya kunce mishi, ya zama kalar tausayi, duk surutun Suhal yanzu ya zama shiru-shiru. Yanason ko da kallonta ne yayi don ya fallasa mata sirrin zuciyarshi yakuma shaida mata tun ranar da suka had’u zuciyarshi ya kasa sukuni. Around 4pm ya sha wanka cikin wani Blue shadda wanda aka mishi zubi na fitan hankali, ko mu MHS sai da muka ce “WOW” don iya had’uwa ya had’u, hularshi ya karya irin na samari masu ji da kansu, wankan turare yayi ma jikinshi don ya fesa kusan kala biyar, ‘kamshin suka had’u suka bada wani scent mai bala’in sanyi da dad’i, agogo ya d’auka ya d’aura a wrist nashi, ya ciro takalma “Bertozzi” ya sa, ‘kare ma kanshi kallo yayi a mirror yaga komai yayi sannan ya d’auki wayoyinshi da makullin motar ya kulle d’akin. Har ya shiga motar ya tayar, juyawar da zaiyi sai yaga Ilham ta fito dagudu daga sashen su tana waving mishi hannu alamun ya tsaya. Saukar da glass d’in motar yayi lokacin da ta iso, ganin tanata ha’ki yasa shi cewa “Ya da uban gudu haka?” Daidaita numfashinta tayi tace “Ya Suhal zan bika ne” Girgiza kai yayi yace “No Ilham, meeting zanje ba wani waje ba, kinga ba yanda za ayi naje dake” “Ba sai na zauna a motar ba?” Ta fad’a cikin marairaicewa Tura hulanshi yayi zuwa gaban goshi yana sosa ‘keya yace “Please lil sis zakisa na makara, kingane ne ba?, wajen maza sunyi yawa ba yanda za ayi naje dake”(daman ance in namiji yana sosa ‘keya toh baida gaskiya ne, no be so??;)) Ilham ta zura mishi idonta, chan ko meh ta tuna sai tayi wani fari da ido tace “Ho!!, Ya Suhal does that mean kana sona?” Cikin rashin fahimta yace “Bangane ba” Du’kowa tayi daidai window d’in tace “Kana kishina, it means kana sona” Zaro ido yayi yace “Wa ya gayamiki?” Dariya tayi tace “Kai ka fad’a yanzu batare da ka sani ba, kace bazakaje dani ba don akwai maza sosai awajen” Dafe kai yayi, ‘kasa-‘kasa yace “Oh my God”, shi ya rasa Ilham nan wace irin mutum ce mai negative tunani, shi yace akwai maza awajen so bazai tafi da ita ba don kar ta dage zataje ta kopsa mishi son ganin Leena da yakeyi, gashi bahagon tunaninta abinda ya bata daban, soyayya. Murmushi ya ‘kir’kiro yace “Hmmm, kina ‘bata min lokaci da surutunki nikuma na tsaya ina biye miki, na wuce” Matsawa tayi daga kusa da motar tanata murmushi tana d’aga mishi hannu. Eid mubarak to you all, Allah ya maimaita mana. Love❤ www.gidannovels.blogspot.com *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish. Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 17, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 37-38 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *37-38* ☆☆☆☆☆☆☆☆ A motar yana driving yana d’an tapping na steering wheel yana tunanin yanda zai tsara Leena, murmushi kawai yake sakewa kaman wanda aka mishi albishir da gidan aljannah. Minti goma yakaishi ‘kofar gidansu, parking yayi batare da ya kashe motar ba yana tunanin wa zai samu ya kira mishi Leena daga cikin gida, sai juye-juye yakeyi amma har yayi minti shabiyar bai ga alamun yaro ko d’aya ta wajen ba dayake anguwan shiru yake, kowa yana cikin makeken gidanshi. Da yaga ba sa’a sai kawai ya fito daga motar yanufi gate d’in su yafara knocking, chan sai maigadi ya le’ko yace “Wanene?” Mi’ka mishi hannu Suhal yayi don suyi musabaha, cikin tsoro Tijjani ya bashi hannun suka gaisa sai yake tambayarsa “Y’alla’bai wajen waye kazo?” Suhal yayi murmushi yace “Don Allah ko zakamin sallama da Leena?” “Leena?, Leena?” Tijjani ya maimaita, chan dai yace “Malam da ma kar ka wahalar da kanka don ita wannan bata tsayawa da samari, ko na kirata ma ba zuwa zatayi ba” Suhal ya jinjina kai, yana ‘kara girmama kamun kai irin nata yace “Amma dai da ka taimaka kaje kace don Allah tafito inason magana da ita” Tijjani yayi jim sai yace “Toh amma dai ka gayamin sunanka don banaso nayi ‘kafa biyu” Kai tsaye ya amsa mishi “Kace mata Suhal ne” Kujera ya bama Suhal ya zauna sannan yanufi cikin gidan don kiran Leena. Tana kwance tana kallon MBC2 taji Tijjani yana kwad’a sallama, amsa mishi tayi absent-mindedly don movie da akeyi ya d’auke hankalinta. Bud’e ‘kofar parlourn yayi gamida rusunawa yace “Ana sallama dake awaje” A d’an firgice ta mi’ke tana kallonshi, harara ta watsa mishi tace “Sau nawa zan gayama kar ka sake zuwa kirana cewa wani yana sallama dani?” In-ina yasoma yace “Umm…eh…yi ha’kuri, wannan d’in ma don naga alamun mutunci a tattare dashi sannan yata had’ani da Allah saisa nazo na gayamiki” Guntun tsaki taja tace “Mtchww, sai kaje kace mishi bana nan ai tunda kaud’inka yayi yawa” Mi’kewa yayi ya nufi ‘kofa saikuma ya juyo yace “Aff!!, yace nace miki Suhal ne” Shiru tayi tana tunanin ina tasan sunan don sosai sunan yamata sounding familiar, ta jima sannan ta tuno inda tasan sunan, nan take ta mi’ke tace ma Tijjani “Okay nasanshi, je kace ina zuwa”. Daganan ta nufi d’akinsu don chanja kaya don riga da wando ne a jikinta, a gurguje tasa atamfa gamida yafa gyale sannan ta feshe jikinta da turaren “Victorious”. D’akin Momy tanufa ta gayamata Suhal yazo, Momy tace zata iya zuwa amma karta dad’e. Tun da maigadi ya gayama Suhal ga Leena tana zuwa sai ya tsinci kanshi da fad’uwar gaba, rubbing na palms nashi ya hau yi daga baya kuma yafara jujjuya agogon dake wrist nashi. Sallamarta da yaji akanshi ne yasa shi saurin d’aga idonshi ya saukesu a kanshi, zama tayi ta gefenshi akan kujerar da Tijjani ya ajiye mata. Murmushi tamishi tace “Sannu da zuwa” Zuciyarshi yasoma bugawa fat-fat kaman zai fito daga ‘kirjinshi, da ‘kyar ya iya furta “Yauwa, na sameki lafiya?, yagida?”, yama rasa me zaice mata don bai ta’ba soyayya ba kuma baisan ya akeyi ba. Cikin sanyinta tace “Alhamdulillah, ina ‘kara mi’ka godiyata zuwa gareka bisa taimakona da kayi few days back” Murmushi yayi yana kallonta yace “No ba komai” Tana d’ago idonta yayi saurin kawar da dubanshi daga gareta kaman wani mai tsoro ko kuma ince cikeda jin kunyarta. Shiru sukayi na mintuna, Leena ta lura kaman akwai magana a bakinshi don sai ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma ya had’iyeta, hakan yasa tace “Ko akwai abinda kakeson cewa ne?” Diriricewa yayi, sam ya kasa furta komai, sai da ya dad’e sannan yace “Akwai kam, ko zaki ban number d’inki?, inaga ta waya zaifi” Dariya ne ya kusan ‘kwace mata ganin gashi dai iya had’uwa ya had’u amma kaman tsoronta yakeji, darawa kad’an tayi tace “Meh zai hana?” Wayarshi ya mi’ka mata tasa mishi number d’in, tana bashi ya mi’ke kaman wanda aka mintsila. Gyara hulanshi yafarayi yana cewa “Barina wuce, zan kiraki awaya” Rakashi tayi har ya shiga motar sannan ta koma gida. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Abdulyassar zaune akan kujera Haj Hafsat kuma tana zaune a kujerar kusa dashi, hira sukeyi wanda yake nuni da irin sha’kuwar da ke tsakanin uwar da d’an nata. Jefi-jefi takan fakaici idon Abdulyassar ta d’auki wayarta tayi d’an danne-danne sai ta ajiyeshi, sam bai nuna mata ya lura da abinda takeyi ba amma chan ‘kasar zuciyarshi is full of curiousity don yanda Momy takeyi kaman tana ‘boye mishi wani abu. Yanaso yace mata ta ara mishi wayar tata amma yasan ko ya fad’a ba bayarwa zatayi ba don sun sha yin hakan, ko da wasa Momy bata gangancin ajiye wayarta ako ina, ko kitchen zataje da wayar take zuwa. Hamma yafara yi kaman yana jin yunwa, kallonshi Mummy tayi tace “Ya dai?” Wani hamman ya sake sannan yace “Mummy I’m hungry” Cikeda kulawa tace “Ga abinci a dinning ai, je kaci mana” Girgiza kai yayi kaman ‘karamin yaro yace “Mummy ni miyar da kikayin ne sam bana sha’awar cinta, snacks nakeso” “Haka zakata zama da yunwa kenan Abdul?, kaje ka saya tunda ba nisa sai kazo kaci” Langa’bar da kai yayi yace “Allah ‘kiuya nakeji Mummy, ki taimaka kije ki siyomin kar yunwa ya illata ni” Da saurinta ta tashi ta nufi d’aki don ba abinda tafi so a duniyar nan kaman d’an nata saisa bata iya jure ganinshi cikin wani hali. Bata jima ba tafito tana yafa gyale, cikin sauri ta suri key d’inta ta sallameshi akan zataje ta siyomishi, don saurin da takeyin ne yasata mantawa da wayarta akan kujera batare da ta lura ba. Yana jin ‘karar tashin motarta ya isa kujerar ya d’auki wayan gamida zama, kan chat na Rafee ta tsaya inda tayi saving as *Baby*, haurawa sama yayi nan yaci karo da wasu pictures da aka tura ma mummy wanda yarinyar ta d’aukesu tsirara haihuwar uwarta, nan take kanshi yamishi nauyi, yama rasa wani irin tunani zaiyi, chats d’in ya fara karantawa daga daidai wajen, duk hirar batsa sukayi wanda har mummy take cewa tayi missing na laushin jikinta. Bashiri ya mi’ke yana nanata “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”, jirin da yaji yana faman kwasheshi yasa ya tsugunna akan guiwowinshi hawaye suna zubowa daga idanunshi, ajiye wayar yayi ya dafe kanshi da hannunshi duka biyun, ya dad’e ahaka yana kuka kaman ranshi zai fita, zuciyarshi ne yake raya mishi “Does this mean Mummy tana lesbianism??, nooo!!!, this cant be, innalillahi”, ya kasa gaskata abinda idanunshi suka gano mishi, wani irin takaici ne ya lullu’be shi har baisam time d’in da ya runtse idanunshi yace cikin kuka “Ya Allah!!!!, noooo!!!, ya Allah!!!, Allah…..” A firgice ya bud’e idanunshi don ta’bashi da akayi, share hawayenshi yafara yi yana ‘ko’karin hana kanshi abinda zuciyarshi ke raya mishi yayi, ahankali yace “Mummy….” Cikin razana da ganin halin da ya shiga daga fitarta yasa zuciyarta a ‘kunci balle da taga yana kuka tsakaninshi da Allah. Kama hannunshi tayi taja shi suka zauna akan kujera, bubbuga bayanshi tayi sannan ta tambayeshi “Meh ya sameka?” Rinannun idanunshi ya d’ora akanta, danne zuciyarshi yayi, nan take ya d’au ma kanshi al’kawarin bazai ta’ba nuna mata yaga wani abu ba har sai yabi komai a hankali ya ‘kara tabbatar ma kansa zargin da yake mata gaskiya ne. Da wannan tunanin yayi murmushin ya’ke yace “Bakomai Mummy, kaina kawai ke ciwo… ” Da sauri ta katse sa “Karka min ‘karya Abdul, nazo na sameka kana kuka kaman wanda aka aiko mishi da sa’kon mutuwa sannan kace min kanka ke ciwo?, ni fah uwarka ce, nafi kowa sanin halinka, tunda na haifeka baka ta’ba kuka irin haka ba sabida dauriya irin naka, ka gaya……” “Mummy bani snacks nah naci, I’m starving” ya fad’i haka ne don guje ma conversation d’in. Mi’ka mishi tayi, yana kar’ba yayi hugging nata kad’an yace “Thank you” sannan ya saketa ya mi’ke yabar side d’in. www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish. Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 19, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 39-40 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *39-40* ☆☆☆☆☆☆☆☆ **SUHAL** Yana barin layin gidansu Leena yayi parking na motarshi, hannunshi ya aza dukka biyun ya dafe kanshi cikeda jin haushin kanshi. Tunani ya dingayi “Meh matsalana?, mesa before naje gidansu bakina yake cike da magana amma ina ganinta na nemi hankali nah narasa?, why?, or was i scared?.” Buga kanshi yayi yace afili “No i’m not scared, toh wai ma tsoron meh zanji?, tsoron mace?, noo!!, ba girmana bane na kasa furta mata inasonta”. Sa’ke-sa’ke ya dingayi yanason gano mesa ya kasa koda kallonta da kyau balle ma ya sanar da ita abinda ya kaishi. Ya dad’e yana soki burutsu har saida duhu yafara mamaye garin sannan ya kama hanya. Ko gida bai ‘karasa ba yasamu nearby masallaci ya sauke farali don lokaci yariga yayi, addu’a ya dingayi kan Allah ya mallaka mishi Leena yakuma sauwa’ke ma Ilham sonshi da takeyi. Bashi yadawo gida ba sai 8:30pm, sai sannan ya duba wayarshi da tunda yayi saving number Leena bai duba ba, nan ya tarar da missed calls na Ummi, Umma, Ilham da Fu’ad wanda sun kira ne daga magriba zuwa 4 minutes ago, yama rasa ya akayi yamanta da wayarshi a cikin motar yashiga masallaci. Jiki amace ya kashe motarshi sannan ya nufi sashen su Ilham don achan zasuci abinci yau, yana shiga iyayen suka nufeshi fuskokinsu d’auke da d’imbin damuwar dad’ewar da yayi awaje, abinda bai ta’bayi ba gashi sun ta kiranshi bai d’auka ba. Tambayoyi suka shiga jero mishi: Abba yace “Ina ka shiga haka?” Baba yace “Lafiya kam dai ko?” Ummi tace “Meh ya sameka kayi dare haka?” Umma tace “Ina ka tsaya har warhaka ba tare da ka sanar damu ba, kasamu cikin damuwa” Fu’ad yace “Suhal are you okay?, mesa bakayi picking na calls namu ba?” Ilham kuwa rugawa tayi ta rungume shi, tana kuka tace “Ya Suhal ina fatan ba abinda ya sameka?, I was so worried, zuciyata ta kasa sukuni, i thought something bad happened to you” Kallon Ilham yayi yana shafa kanta yana lallashinta “I’m okay kinji?, kibar kukan haka, ba gani ba?” Jinjina kai tayi sannan ya janyeta daga jikinshi hannunsu sakale da na juna, kai sunkuye cikin ladabi yace “Kuyi ha’kuri nasan nayi laifi amma muzauna tukunna” Ba wanda yace ‘kala acikinsu, haka suka ja jiki suka zazzauna akan kujeru suna sauraren bayanin da zai musu. A raunane yasoma magana “Naje gidan wani abokina ne munata hira don mun dad’e bamu had’u ba, daf maghriba nabar gidansu, ganin in nace sai na iso gida zanyi sallar lokaci zai ‘kure shine na nemi wani masallaci a hanya nayi Maghriba da Isha sannan na taho gida. Rashin d’aukar waya kuma nabarshi a motar ne nikuma nashiga masallaci, sai da na iso gida ne ma na duba wayar naga missed calls naku, kuyi ha’kuri d’aga muku hankali da nayi” Kusan atare iyayen sukayi ajiyar zuciya, nasiha suka mishi akan kar ya ‘kara kai dare awaje haka, in ma yakama dole toh ya kira ya sanar dasu. Ha’kuri ya ‘kara basu sannan yayi excusing kanshi don ya watsa ruwa, yana mi’kewa Ilham tayi saurin dam’ke hannunshi tace “Ya Suhal kaci abinci mana tukunna” Shi sai sannan ma yatuna rabonshi da abinci tun 1pm don ko yunwar bai ji, murmushi yayi yace “Bari nayi wankan zanzo naci”. Bai jira cewarta ba ya sake janye hannunshi ya fice daga parlourn, iyayen duk sun lura da wata irin kulawar da Ilham take bama Suhal wanda hakan yana musu dad’i, saidai matsalar da suke gudu kaman yana shirin tasowa, hakan yana matu’kar fad’ar musu da gaba don in dai tunaninsu na Ilham tanason Suhal daidai ne toh abunda suka binne acikin zuciyoyinsu shekara da shekaru ne za a tono shi. Sha re maganar kowannensu yayi suka cigaba da hirarsu ta yau da kullum. Fu’ad kuwa Suhal yana fita yabi bayanshi, lokacin da yashiga Suhal ya cire jumpa d’inshi ya rage daga shi sai farar vest da short nicker, towel ya d’auka da zummar shiga bathroom don bai san Fu’ad ya shigo d’akin ba sabida tunanin Leena da ya d’auke hankalinshi. Gyaran murya Fu’ad yayi, a d’an firgice Suhal ya juyo yana kallon Fu’ad da yake tsaye yana wani shu’umin murmushi, kallon “me ya kawoka?” Suhal ya mishi. Dariya Fu’ad yayi ya zauna akan sofa dake tsakiyar bedroom d’in sannan yace “Guy, zo kawai muyi magana” Suhal yayi jim sannan yace “Maganar meh zamuyi?” “Maganar wacce kaje wajenta d’azu” Suhal a zuciyarshi mamaki ne ya cikashi ya akayi Fu’ad ya ramfoshi haka?, fuskewa yayi yace “Wata kuma?, wajen abokina naje ba wani waje ba, kaga Malam ni bansan me kake nufi ba, as u can see wanka zan shiga so excuse me” Saurin shan gabanshi Fu’ad yayi ya wani tsare yace “Kabar ‘boyemin don nariga da na ganoka, whats there in ka gayamin?, snatching zan ma?” Ya ‘karasa maganar had’e da daga gira d’aya sama Dafe kai Suhal yayi yana murmushi ya bugi kafad’ar Fu’ad yace “Okay you got me, naga wata yarinya inasonta shine naje gidansu, kai fah shege ne, wai ma ya akayi ka gane?” Murmusawa Fu’ad yayi yace a gadarance “Ka manta waye ni ko?, duk ‘boye-‘boyenka saidai in banga daman ganewa ba don ganewar shine abu mafi sau’ki” Harararshi Suhal yayi sannan yace “Ni bance ka tsaya kanamin bragging ba, just tell me, ya akayi kagane?, or nayi wani abu na rashin gaskiya ne?” Zama sukayi sannan Fu’ad yace “Kai bakama iya ‘karya ba wallahi” Had’e fuska Suhal yayi yace “Bangane ‘karya ba, waye nama ‘karya?” “Dazun da yamma nadawo ina nemanka sai Ilham ke ce min ka tafi meeting, yanzu kuma kace kaje gidan abokinka saisa nagane ba kaje ko d’aya daga cikin biyun ba, wani waje daban kaje” Tunani Suhal ya lula, shi har ga Allah ya ma manta yayima Ilham wani ‘karya, ahankali ya furzar da iska yace “Wallahi namanta ne, amma ai daga kai sai ni mukasan ‘karya nayi so please ka rufamin asiri” Girgiza kai Fu’ad yayi yace “Ilham ma zata gane ai tunda ita ba yarinya bace” Murmushi Suhal yayi yace “Bar maganar Ilham, zan san yanda zanyi da ita” Wani kallo Fu’ad ya watsa mishi sannan yace “Kaman ya?, i hope dai ba toying da feelings nata kakeyi ba?” “Feelings?, wani irin feelings?” “Kabar yi kaman bakasan me nake nufi ba, kasan Ilham tana sonka ba tun yau ba so no need denying it, nidai dont break my sister’s heart, Allah zamuyi rikici sosai” Had’e fuska Suhal yayi yace “What do you mean?, an gayama im heartless ne?, banyi toying da feelings na wasu ba balle Ilham da take da babban matsayi a wajena, inason Ilham but bazan ‘boyema ba, soyayyar wa da ‘kanwa nake mata ba na wani abu daban ba” “Why?, mesa bakasonta?, meh kake nema da bata dashi?, ‘yar uwanka ce ta jini?, mesa?” Dafa kafad’ar Fu’ad Suhal yayi yace “Im so sorry Fu’ad, zuciyata ta kamu da son Leena ba Ilham ba, I cant help it, karkaga laifina, narasa ya zan taushi zuciyata tasota, Ilham tacika mace, infact batada makusa, but…….” Cikeda tausayawa ‘kanwar tashi Fu’ad ya katse Suhal, mi’kewa yayi yace “Fine, ni bazanyi forcing naka ka sota ba but bazan d’auki kayi hurting nata ba, i can do anything for her, if you dont love her kayi ‘ko’karin janye jikinka daga gareta har sonka yafita daga ranta, please just dont hurt her don zamu samu matsala” yana kaiwa nan yabar d’akin kaman yaje yakama Ilham yayita duka bisa son maso wani da takeyi. Jiki sanyaye Suhal yashige toilet yayi wanka sannan yafito yayi shirin bacci cikin pyjamas. Parlour yanufa ya kunna tv amma ba kallo yakeyi ba don ya zurfafa atunani sosai, sallamar Ilham ne yadawo dashi hankalinshi, amsa mata yayi, ahankali ta shigo ri’ke da tray mai d’auke da warmers a hannunta. Sorry lovelies, ku cigaba da biyomu. www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish. Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 21, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 41-45 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *41-45* www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Gidan Hajiya Hafsat*** Binshi kawai tayi da ido don bakinta ya kasa furta ko da kalma d’aya ne duk da zuciyarta cike yake da tambayoyin da take bu’katar amsa daga wajen d’an nata. Jingina da jikin kujerar tayi, nan taji alamun ta zauna akan abu, tashi kad’an tayi gamida zaro abun, aiko tana ganin wayarta ne ta zaro ido cikeda tsoro, nan take zufa suka soma tsatstsafo mata, ba shiri ta danna home button wuta ya kunnu akan screen na wayar, tana swiping yayi unlocking, akan chat na Rafee da ta bari yake har yanzu, nan taji hankalinta ya kwanta don batayi tsammanin Abdul ya gani ba, atunaninta in ya d’auka ba chat na Rafee zai tsaya ba don zai shiga na wasu ma, da wannan tunanin ta saukar da wani nannauyar ajiyar zuciya gamida sakin murmushi ta tattara wayarta tayi d’aki tacigaba da hira da lesbians ‘yan uwanta. Abdulyassar yana isa d’aki ya bud’e d’an madaidaicin fridge nashi yasaka leather da Mummy tashigo mishi dashi sannan ya hau tunanin mafita da hanyoyin da zai bi don ku’butar da uwar tashi daga mummunan halin da take ciki. Wani tunani ne ya fad’o mishi arai, dama MD na company da yakema aiki ya gwada mishi yanason Mummy amma da MD d’in ya mata magana sai mummy bata bashi fuska ba, alokacin yaji wani iri da mutumin ya tinkareshi da maganar don yaga MD’n kaman ya raina mishi wayo ne yazo yace mishi yanason uwarshi, yanzu dai baida choice don haka zai danne zuciyarshi ya yarda yafara cusa ma Mummy ra’ayin mutumin har dai ta amince a d’aura musu aure, sa’ka da warwara ya dingayi yana ambaton duk wata addu’a da tazo bakinshi yana kuma ro’kon Allah ya bashi ikon cin jarabawar nan da ya d’ora mishi na uwa mai mad’igo. Da dare wani irin zazza’bi mai zafi ya ri’keshi, a daddafe yaje masallaci yayi sallah yadawo gida. Momy shiru-shiru har ‘karfe tara bataji d’uriyar d’an nata ba sa’banin kullum da yana dawowa daga Isha around 8pm zai shigo su ta hira suna kallo har 10pm ko 11pm, tunowa da yanayin da ta sameshi dawowarta daga siyan snacks da yace yakeso ta fara, nan fah tasoma WAS-WASI(Book by Mermue my grandmother) acikin zuciyarta “Anya Abdul baiga wani abu a waya nah d’azu da rana ba?” Tsaki taja tana mai jin haushin kanta yanda akayi ta manta da wayarta agida ta fita, chan kuma tace ma kanta “Kai bai gani ba, Abdul da shegen bin diddigin shin nan bazaiyiwu yagani sannan yayi shiru bai min maganar ba”. Mi’kewa tayi tanufi side nashi, sallama tayi har sau biyu bataji ya amsa ba sai kawai ta shiga. A ‘kasa ta ganshi sai wani rawa jikinshi yakeyi, dagudu ta ‘karasa wajenshi tana jijjigashi tana kiran sunanshi, kuka tasoma tana salati tana tatta’ba jikinshi da yayi zafi jau kaman wuta. Dagudu ta fita ta fara ‘kwala ma maigadi kira don ya taimaka mata su sa shi a motar, cikin ‘kan’kanin lokaci ta isa dashi asibiti sabida gudun da tayi, nan fah likitoci suka kar’be shi suka wuce dashi A&E(Accident and Emergency). Awa biyu sukayi suka fito, wasu nurses suka turashi ward sannan Dr yace ma Mummy tabiyo shi office yanaso yayi magana da ita. Jiki asanyaye tabishi har office nashin gamida zama akan kujeran da yake facing nashi, batare da ‘bata lokaci ba yasoma koro mata bayani kamar haka “Meh relationship naki da patient nan?” “D’a na ne” ta bashi amsa Jinjina kai yayi yace “Ba wani serious abu bane, ciwon kai ne ya kamashi har ya kai ga sumar dashi sannan heart nashi is beating more than normal, ko akwai wanda ya ‘bata mishi rai ne ko yanason wani abu?” Jim tayi tana tunani sannan ta girgiza kai tafara magana cikin rawar murya “Shi kad’ai ne d’ana, ba abinda ya nema ya rasa a duniyar nan, don Allah doctor save my son’s life, I cant afford to lose him” “He’s out of danger saidai dole ki kiyaye abinda zai sake jefashi cikin hali irin wannan don kar abun yayi worsening” Share hawayen da ya zubo mata tayi tace “In Sha Allah zan kiyaye” Jinjina kai yayi yace “You can go” Har ta tashi sai kuma ta juyo ta kalleshi tace “Zan iya shiga na ganshi?” Batare da ya d’ago ya dubeta ba yace “Zaki iya shiga but no noise don ba ason ya farka sai alluran ya sakeshi” Cikin rawan jiki ta fita daga office d’in ta nufi d’akin da Abdul ke kwance ga ‘karin ruwa a hannunshi. Daf asubah ya farka, yana motsi Mummy ta mi’ke tana shafa kanshi don ko runtsawa ta kasa yi, cike da kulawa tace “Sannu son, ya jikin?” Bin d’akin yayi da kallo, nan yagane asibiti yake, ahankali ya bud’e baki yace “Da sau’ki, meh ya kawoni asibiti?” Murmushi ta mishi tace “Shhh, dont stress yourself, yanzu barin taimaka ma kayi sallah tukun, in kaci abinci sai muyi magana kaji?” Ba don yaso ba yace “Okay mummy, zan iya tashi da kaina” Mi’kewa yayi a daddafe ya bi gini ya shiga toilet sabida jirin da yake damunshi, cikin ‘karfin hali yayi alwala yazo ya tada sallah. Yana idarwa Mummy ta had’a mishi tea ta bashi sannan itama ta kabbara nata. Da gari yayi haske doctor ya shigo ya dubashi had’e da bashi shawarwari, aciki har yake tambayarshi meh yasa a zuciyarshi da har yake neman barazana da rayuwarshi, sai anan ne Abdul ya gane abinda ya sameshi, bai bama doctor amsa ba, ganin haka yasa dr d’in share zancen kawai yayi murmushi ya bar d’akin. Da yamma aka sallamesu don jiki yayi sau’ki. Bayan kwana biyu Kwana biyun nan Mummy tayi-tayi da Abdul ya gayamata meh yake damunshi amma fafir ya’ki, yanzu ma rikicin da suke tafkawa kenan. Ta sa shi agaba har tana neman mishi kuka, shiru yayi yana tunanin ya zaiyi, shawara da zuciyarshi yahau yi har ya amince ma kanshi da shawara d’aya. Kama hannun Mummy yayi yace “Im sorry Mummy, na rasa ya zanyi ne don bansan ya zaki d’auki maganar ba” Idanunta jawur ta kalleshi tace “Abdul hankalinka d’aya kuwa?, kana wasa da ranka akan tunanin yanda zan d’auki maganar da kakeson gayamin?, you are my only son, ina sonka fiye da yanda nakeson kaina, ka gayamin ni kuma nama al’kawarin zanyi maka shi ko da kuwa it will cost me my life, Abdul kaine komai nah, don Allah ka taimakamin kabar wasa da lafiyarka, bazan iya jure ganinka cikin rashin lafiya da yake barazanar d’auke min kai ba” Wani son uwar nashin ne ya tsirga mishi zuciya, yasan ko menene ya gayamata zata yarda balle yanzu da zuciyarshi ya d’an ta’bu saidai shakkar tunkararta da maganar yakeyi. Share mata hawaye yayi shima yana hawayen yace “Mummy kiyi ha’kuri, bazan sake ba, kibar zubda hawayenki akaina please Mummy” Shafa fuskarshi tayi tace “Shikenan Son, gayamin meh kakeso” Kawar da kanshi yayi daga kallonta ya maida kallonshi gefe don bai jin zai iya kallon idonta yamata maganar. Murya na rawa yace “Mummy aure nakeso kiyi, ganinki ahaka yana matu’kar damuna, i dont mean to disrespect you amma wallahi mummy k’awayenki sam ban yarda dasu ba don basu min kama da masu mutunci sannan inajin wasu maganganu akanki da suke ‘batamin rai, anguwan nan maganarki ake tayi wai kina harka da manya sabida yanda suke ganin abokan business naki suke yawan zuwa nan gidan(shi baisan tana harka da maza ba don bai ta’ba gani ba, da ya dawo daga london after graduating from college sai yaga yanda maza suke sintiri agidan ba dare ba rana, da ya tambayeta sai tace ai business partners nata ne, shikuma haka ya yarda har yau don daga baya kam ma sun rage zuwa gidan sai ‘kalilan nasu don guest house da Mummy ta gina achan suke zuwa suyi harkarsu ba tare da Abdul ya gane ba), aure shine only abun da zai sa subar maganganun da sukeyin duk da dai ban ta’ba yarda ba don nasan halinki, bakya haka, mummy aure zai siya miki mutunci har ma dani, please Mummy” ya ‘karasa maganar kanshi a sunkuye yana zubda hawaye. Mummy da ranta yayi mugun ‘baci jin ya ambaci aure tuni idonta yarufe har batasan lokacin da ta mi’ke ta wanka mishi wani wawan mari ba, ji kake tassss!!!!! A firgice ya d’ago kai yana kallonta don tun yana ‘karami ko da marin wasa ne Mummy bata ta’ba mishi ba amma sai gashi yau ta wankeshi da marin da yaji har kunnenshi saida ya amsa, cikin rawar murya mai d’auke da tsantsan mamaki yace “Mu….m….my……..” ☆☆☆☆☆☆☆☆ Tsugunnawa tayi ta ajiye tray d’in, batace dashi komai ba ta jawo plate da tazo dashi ta zuba mishi abinci sannan tasa mishi drink a cup, stool ta tura zuwa gabanshi ta d’aura plate da cup d’in akai. Komawa gefe tayi tace “Ya Suhal ga abinci kaci, karka kwana da yunwa” Mi’kewa zaune yayi yace “Thank you lil sis” Murmushi ta mishi sannan ta maida hankalinta zuwa kallon tv har ya gama cin abincin. Kwashe kwanukan ta fara yi tana maidasu kan tray d’in da tashigo dashi, mamaki ne ‘karara kwance akan fuskar Suhal ganin yanda Ilham yau tazama shiru haka bayan ba haka take ba. Saukowa yayi daga kan kujeran ya kama hannunta da take faman d’aukan tray, ahankali ta sauke idanunta akan hannunshi da ya d’aura akan nata sannan ta kalli fuskarshi. Kallon cikin idonta ya shiga yi yana faman karantar halin da take ciki, har ta bud’e baki zatayi magana ko me ta tuna kuma oho sai ta girgiza kai tace “Ya Suhal sakeni barin tafi” ‘Kin sakin hannun yayi sai ma ya jawota jikinshi yace “Laifin meh nayi ake fushi dani?” Cikeda masifa tace “I dont know!!, ka sakeni ya Suhal” sai kuma tasa kuka tana tutture shi tana naushin shi a ‘kirji, shiko sai ‘ko’karin kamata yakeyi har dai ta gaji ta bar tureshin ta fashe da wani sabon kuka. Shafa kanta yafara yi yace “Lil sis bansan me na miki ba but I’m sorry” Sai da tayi ya isheta sannan ya sassauta ri’kon da yamata, ahankali ta janye jikinta tana share hawaye, cikin sigar lallashi yace “Don girman Allah ki gayamin meh na miki” Kallonshi tayi da rinannun idanunta tace “Ya Suhal bakamin komai ba, laifi na ne” Cikin rashin fahimta yace “Laifinki kuma?” Jinjina kai tayi tace “Yes, laifina ne da na koyi sonka tun ina ‘karama, laifina ne da na fara sonka tun bansan ma meh soyayya ba, its all my fault, kai ba sona kakeyi ba amma na nace da sonka, Ya Suhal don Allah mesa baka sona?, akwai abinda nakeyi mara kyau ne?, ka gayamin wallahi bazan sake yi ba na rantse ma, don Allah…” ta kai ‘karshen maganar tana kuka sosai. Tausayinta ne ya mugun kamashi, cikeda damuwa yace “Ilham meh ya kawo wannan maganar kuma?, wayace miki bana sonki?” Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace “I know, ko yau ma na ‘kara tabbatar ma kaina hakan, alokacin da kace min meeting zakaje baza kaje dani ba farinciki na shiga yi marar misaltuwa don a tunani na kana sona ne har kake kishin wasu su ganni, unfortunately ashe ba haka abun yake ba don da dare da ka dawo kace gidan abokinka kaje, ya Suhal at that moment my conscious whispered to me cewa ka je wajen wata ne bakaso nasani, Ya Suhal nasan bakasona kawai kanayi kaman kana sona ne don kar nashiga damuwa, hakan da kakeyin kuwa wallahi baka sani ba cutata kakeyi……” kuka sosai takeyi fiye da tsammani, kukan nadamar fad’awa son wanda bai sonta. Suhal yama rasa ya zaiyi da ranshi don ganin yanda Ilham take kuka kuma shine sila, rungumeta gam-gam yayi ajikinshi yace “Ilham inasonki, kibar cewa bansonki sannan kibar ganin laifin zuciyarki” Da sauri ta zame daga jikinshi tana dariya, hawaye suna kwararowa daga idanunta don jin Suhal ya furta yana sonta, kama hannunshi tayi tace “Kana sona ya Suhal?, dagaske?” Suhal ji yayi kaman yasa hannu akai ya rafsa ihu, ba don yaso ba sai don fitar da Ilham daga halin da take ciki yace “Eh” Share hawayenta tayi tace “Toh ya Suhal zaka aureni na haifa maka babies masu kama damu ko?, Allah ya Suhal zan maka duk abinda kakeso” Maganar yajishi bambara’kwai, azuciyarshi yana Allah wadai da soyayya tunda gashi ya maida Ilham mara kunya ya makantar da ita tana ganin komai tayi daidai ne, shi kunya ma maganar ya bashi, daurewa yayi ya d’an kalleta yace “Aure Ilham?, kinsan me aure kuwa?” Tura baki tayi tace “Wani irin tambaya ne wannan?, I’m 18 fah, nasani mana” Kaman gunki ya tsaya yana kallonta yana tunanin yanda zai shawo kanta tabar maganar auren da take mishi, murmushi ya ‘kir’kiro yace “Aure ba yanzu ba kinji?, kibari sai kin ‘kara girma” Kaman zatayi kuka tace “Sai na ‘kara girma?, yanzu ban girma bane toh?” Gyara maganarshi yayi yace “Sorry I mean sai kinyi nisa a university, kinga yanzu kike neman admission, aure sai nan gaba kinji?” Jim tayi tana tunani akan maganarshi sai tace “Eh kuma hakane fah, amma dai kace zaka aureni naji” Ba tare da wani tunani ba yace “I promise you zan aureki”, saida ya ‘karasa maganar ya shiga salati a zuciyarshi, shi harga Allah bai san ya akayi bakinshi yafurta kalmar al’kawari ba. Innalillahi yashiga nanatawa tunawa da girman al’kawari da yayi. Ilham tayi wani tsalle tana ihu, Suhal hankalinshi bai wajenta yana chan yana jajanta ma kanshi wannan furucin da yayi, pecking nashi tayi don bata lura da halin da yashiga ba, cikeda jindad’i tace “Toh Ya Suhal sai da safe, dream of me kaji?” Bai ko iya amsa mata ba haka tafita tanata jindad’i Suhal ya mata al’kawarin zai aureta. Tana barin d’akin bashiri Suhal ya mi’ke tsaye yana salati afili, shi kad’ai ya soma surutu “What was I thinking?, meh ya kaini?, al’kawari?, al’kawarin zan auri Ilham??, la ilaha illahi, meh ma yakai bakina furta wannan babban maganan?, Nooo ina!!, there must be a way, dole na nemi mafita, Leena ne kawai zan iya aura don ita nakeso sannan bana sha’awar auren mata biyu, toh ma idan na auri Ilham inyi meh da ita?, a matsayin ‘kanwa nake ganinta, kai ko gado bazan iya had’awa da ita ba balle wani abu yashiga tsakaninmu, ina!!”. A wannan daren dai ba abinda yake yawo a ‘kwanyar Suhal sai takaicin kanshi da yakeji. Washegari duk wanda yaga Ilham sai yasan tana cikin wani irin farinciki. Tun daga ranar kuwa take ‘kara shishshige ma Suhal tana tarairayar shi, shi ko kawai biye mata yakeyi ba wai yana jinta a ranshi ba. Bayan sati d’aya Kullum sai Suhal yayi dialing na number Leena sai ya fasa kira, shahada yayi ya danna mata kira. D’auka tayi suka gaisa sannan yace mata Suhal ne. Murmushi tayi tace “Suhal ya kwana biyu?” “Lafiya lau, ya school?” “Kalau wallahi” “Okay dama nace bari mugaisa ne” “Ayyah nagode, bye” Yana cewa “Bye” ya katse wayar, kwanciya yayi danne da saitin ‘kirjinshi da yakeji kaman zai faso waje, chan kuma sai yafara jin haushin kanshi na yanda bai iya magana da Leena, magana yakeyi da zuciyarshi “Mesa nake kunyar gayamata ina sonta ne?, dole ne ma na nitsu na dinga dagewa ina kiranta muna hira kar wani yamin shigan sauri”. Two weeks later Zuwa yanzu Suhal ya rage tsoron Leena da yakeji don yakan kirata su sha hira kaman friends sabida yakasa gayamata sonta yakeyi, da yake Leena tanada son raha haka zata biye mishi suta hira suna dariya kaman daman chan sun saba, Suhal kuwa sai ‘kara nitso a cikin kogin sonta yakeyi wanda ita da alama bata ma san yanayi ba. A ‘bangaren Ilham ita dai hankalinta kwance yake, gata da ya Suhal nata, haka zataje d’akinshi suyita hira, shi dai yi kawai yakeyi don bai son ya gayamata shi baya sonta ta fad’a ‘kunci, saidai fah saitace mishi “I love you” sau goma shi baice mata sau d’aya ba, hakan kuwa bai ta’ba damunta ba tunda yamata al’kawarin zai aureta ai shikenan. Thursday 10:00pm Fu’ad ne janye da trolley d’inshi ya iso tsakar gida inda iyayen dasu Suhal suke tsaye suna jiran fitowarshi. Motar biyu suka d’auka suka dunguma sai airport, achan iyayen suka ‘kara d’ora mishi wa’azi akan wanda sukata mishi agida. Baba yace “Fu’ad yanzu kai kad’ai ne zaka koma chan inda ba wanda zai kwa’beka in kayi ba dai-dai ba, abinda nakeso dakai shine ka ri’ke mutuncin kanka ka kare kanka ka kuma ji tsoron Allah, in mu bamu ganinka toh shi yana ganinka, Allah ya bada sa’a” Abba yayi murmushi yace “My son, nasan bakada matsala, ka cigaba da ri’ke addininka da kyau, Allah ya kare” Umma da Ummi da suketa hawaye kaman yau ne zai soma tafiya yabarsu suma suka mishi Allah ya taimaka ya amsa jiki a sanyaye don wa’azin da Abba da Baba suka mishi ya matu’kar razana shi ya shiga jikinshi sosai. Shan hannu sukayi da Suhal, Suhal yace cikin dauriya “Take care bro, all the best, Allah ya kaiku lafiya” Fu’ad yayi mishi side hug yana murmushi, daganan ya rungume Ilham da ke ta shar’bar kuka, lallashinta yayi sannan sukayi sallama. Iyayen basu bar airport d’in ba saida jirginsu Fu’ad ya tashi misalin 11:30pm. Sai muce Fu’ad a isa Turkey lafiya. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Toh anan zamu dakata yau amma you guys should ponder upon these questions: -Shin mummy tana yarda da abinda Abdul yace akan tayi aure ko yaya?, in ta yarda ya zai kasance?, in bata yarda ba kuma ya?. -Suhal yana cika ma Ilham al’kawarin aurenta da yayi ko kuma yana zama mai karya al’kawari?. -Suhal yana iya furta ma Leena cewa yana sonta ko sai lokaci ya ‘kure mishi?. -Momy, Rafee, Sofy, Leena da daddy kuma ya abun yake zama?. Sannan a ‘karshe ya rayuwar Fu’ad yake kasancewa a Turkey?, yana shiryuwa ko kuwa rayuwarshi tana ‘kara zama abun “Allah sarki”?. Muna jiran ra’ayinku ta blogs namu ko kuma ta WhatsApp. We love y’all. Don samun wad’annan amsoshin ku cigaba da biyomu *MHS*, zamu fere muku biri har wutsiya In Sha Allaah. *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 24, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 46-50 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *46-50* Ga masu so sai su duba: www.gidannovels.blogspot.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Mummy cikin kakkausar murya tasoma magana “Abdul meh kake nufi?, aure?, baka yarda dani bane ko kuma meh kake zargi?” Sai kuma ta sassauta murya tacigaba “Aure Abdul?, kasan meh ya hanani aure tun bayan rabuwana da babanka?, toh yau zan gayama, na’ki aurene saboda banaso na rasa baka lokaci nah, na’ki nayi aurene don kar nayi yazamana mijina watarana ya bigeki ko wani abu don ni bazan d’auki a dukeka nayi shiru ba, na’ki aurene sabida kar naje da kai wani gida akiraka da sunan agola, sunan da bazan juri jin an kiraka dashi ba ko da wasa, Abdul na’ki aurene saboda kai, for your own happiness, nayi sacrificing jindad’i nah saboda na baka kulawa ta musamman nakuma baka dukkan lokaci nah, saboda wani dalili yanzu zaka tasomin da batun aure Abdul?, mesa?” Hawaye ne ya zubo ma Abdulyassar a fuska, mi’kewa yayi dafe da ‘kuncinshi ya isa gabanta ya dur’kusa yace “Ki yafemin Mummy, ki gafarceni, nayi suggesting hakan ne don inaga shine zai ‘kara kare martabarki” Kallonshi tayi tace “No Abdul, saboda ka girma ne kake gayamin magana, saboda yanzu kana ganin ka kai shekarun da zaka iya rayuwa batare dani ba, saboda….” Mi’kewa yayi yasa hannunshi ya toshe bakinta yana girgiza mata kai “Mummy I’m sorry, don Allah kiyi shiru kibar wad’annan maganganun, in batun aure ne namiki al’kawari daga yau bazan sake d’agota ba” Daga nan ya juya ya fice daga parlourn ba tare da ya sake waigowa ya kalleta ba duk da irin kiran sunanshi da takeyi akan ya tsaya. Yana fita ta tsugunna bisa guiwowinta tana kuka kaman meh, nadama ne ya dirar mata, sai sannan take jin haushin kanta akan meh ya kaita marin d’anta ‘kwara d’aya tal, wanda takeso fiye da kanta, tama kasa yarda wai yau itace ta d’aga hannunta ta saukar da yatsunta biyar a fuskar d’an nata wanda bashida laifin komai. Laifinshi d’aya ne da ya kawo mata maganar aure bayan ita hakan bai cikin tsarin rayuwarta kwata-kwata. Abdul tun fitarshi daga sashenta misalin ‘karfe sha d’aya bai sake ko kallon wajen ba. Shiru-shiru har bayan la’asar bataji d’uriyar shi ba don ko abincin rana baifito yaci ba, a birkice ta nufi sashen nashi don ta tuna kashedin da dr yamata akan karta barshi cikin damuwa ko ya ‘kan’kantarsa. Kusan cin karo sukayi don alokacin Abdul yafito da niyyar zuwa wajen amininshi ko zai bashi shawara sabida kanshi ya kunce, bai iya tunanin komai gashi yana neman mafita cikin gaggawa. Sunkuyar da kai ‘kasa yayi ya ra’ba ta gefenta yayi wucewarsa, baki bud’e ta bishi da ido don sam bai nuna ma ya lura akwai wata halitta awajen ba, “Allah sarki Abdul, marinka da nayi ba da sona nayi hakan ba” take rayawa acikin ranta. Bata farga ba taji ya bud’e motarshi, gudu tasa takuwa isa lokacin har ya kunna motar yana faman rufe ‘kofa, kama ‘kofar motar tayi, d’agowa Abdul yayi ya kalleta ya sunkuyar da kai yace “Mummy fita zanyi, sakemin ‘kofar please” Bata sake ‘kofar ba tace “Abdul ka fito inaso muyi magana” Batare da ya kalleta ba ya fara tapping na steering wheel yace “In na dawo mayi, please mum i have to go” Rau-rau tayi da ido kaman mai shirin kuka tace “Shikenan tunda yanzu ko maganata ka bar ji, kaje sai ka dawo” tana ‘karasa maganar ta sake murfin motar ta juya da zummar komawa gida amma sai tafara tafiya ahankali, atunaninta zai tsaidata amma sai taga sa’banin haka, har ta isa d’aki ta rufe yana nan yanda tabarshi, bai rufe ‘kofar ba sannan bai kashe motar ba. Fad’awa kan kujera tayi tana hawaye, ita tsoronta ma kar Abdul yayi accident sabida ta hango ‘bacin rai shimfid’e akan fuskarshi. Chan kaman minti goma taji an ta’bata, a firgice ta bud’e baki har zatayi ihu sai taga Abdul tsaye a kanta. Ajiyar zuciya ta sauke tace “Yaushe ka shigo?” Don ita harga Allah bataji ‘karar bud’e ‘kofa ba, ko don ta lula duniyar tunani ne oho. Bai bata amsa ba sai ma tsugunawa da yayi akan carpet, kanshi a ‘kasa yace “Mummy kiyi ha’kuri, banson kina zubda hawaye saboda ni, bazan ta’ba yafema kaina ba” Share hawayen fuskarta tahau yi sannan ta d’ago shi yadawo kan kujerar da take zaune, cikin muryar da yasha kuka tafara magana “Ka yafemin marinka da nayi, wallahi bansan lokacin da zuciya ya kwasheni nayi hakan ba, im so sorry my son” ta ‘karashe maganar tana share hawayen da ya zubo bisa fuskarshi Kama hannun nata yayi ya ‘kir’kiro murmushi yace “Ba komai mummy, bansan maganar zai ‘bata miki rai bane da ban yishi ba” Girgiza mishi kai tayi tace “I totally understand you, zanyi nazari akan maganarka” Cike da mamaki yake kallonta, bakinshi har yana rawa yace “Mu…mmy da…gask…e kike??” Nodding mishi kai tayi tana murmushi, dad’i ne ya ziyarci zuciyarshi wanda bazai iya misaltawa ba, da haka suka sasanta har ma yaci abinci, fitar da baiyi ba kenan don bashi yabar sashen ba sai da aka fara kiran sallar maghrib. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Three months later Saturday morning, 9:30am Ilham da Suhal ne zaune a tsakar gida sai hira sukeyi, suna cikin haka sai wayarshi da yake hannun Ilham alokacin tanata d’aukansu selfies ya shiga ruri, mi’ka hannu yayi da niyyar kar’ba amma sai Ilham ta mi’ke tana dariya, dariyarta ne ya tsaya cak sabida sunan da idonta yayi arba dashi ‘baro-‘baro akan screen na wayar “BAE”, wani kallo ta watsa ma Suhal da saida ya d’an ja baya. Hannu yasa ya kar’bi wayan daga hannunta don das’karewa ma tayi awajen kaman an dasata sai wasu hawaye da ke zuba daga idanunta, yana kai dubanshi kan screen na wayar yaga sunan. Wani murmushi ya sakar yayi picking yana cewa “Hello, yanzu kuwa nake shirin kiranki” ya juya ya nufi d’akinshi don yama manta da Ilham a wajen. A d’ayan ‘bangaren Leena tace “Kai dai kawai kanason kare kanka ne don tun safe baka kirani ba sai kaga na kiraka” Murmushi yayi da saida Leena ta jiyo sautin shi yace “Allah kuwa kina raina, kawai ina d’an abu agida ne” “Tohh shikenan, ya yau d’in?” “Kalau fah, kin tashi lafiya?” “Lafiya lau, umm dama zan tambayeka ne” Daidai lokacin ya isa d’akinshi, kishingid’a yayi akan kujera sannan yace “Inajinki” “Inaso ka rakani wani waje ne don Allah, wallahi ‘kiuyan driving nakeji” Dariya yayi sannan yace “So…. ni nazama driver’nki right?” Da sauri tace “A’a, ni na isa?” Dariya sukasa dukkansu sannan yace “Kin isa mana har kin wuce ma” “Thank you, yaushe zakazo d’in?” “Ke zan tambaya ai your highness, just say the time nikuma zanyi iya ‘ko’karina na iso on time” Dariya kad’an tayi tace “Kai kacika zolaya wallahi, around 4:30 haka if you are free” “Free?, ai ko yau nan i’m the most busy man dole nayi squeezing time nazo” D’an murmushi ta saki don har cikin ranta taji dad’i sannan tace “I’m honoured, sai anjuman kenan ba?” Cikin sauri ya katseta da cewa “Ina ne zamuje d’in?” Dariya ta kwashe dashi tace “Sayarda kai zanyi” Shima dariyar yayi saiyace “No, gayamin kar nasa kayan da bai dace ba” “Bank zamuje sannan zanje na siya wasu abubuwa a mall” “Okay shikenan, bye” “Bye, in zakabar gida sai ka kirani” “Okay I will” Da haka sukayi sallama kowannensu murmushi ne shimfid’e akan fuskarsa. Kukan da yaji da ‘karfi yasa shi kai dubanshi bakin ‘kofa, Ilham yagani, sai sannan yatuna da suna zaune ne Leena ta kirashi shikuma yamanta da akwai ma wata mai suna Ilham a duniyar nan. Tashi yayi ya nufeta, saka hannu abakinta tayi tanata faman toshe bakinta don kukan da yake neman fin ‘karfinta, ganin ya nufota yasa ta ruga da gudu ta banko ‘kofar. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Sofy kwance a jikin Bash a wani club nasu, wine kawai suketa d’irkawa cikinsu hankali kwance, hannu ya d’aga ma waiter da ke wajen akan ya ‘karo musu, cikin ‘kan’kanin lokaci ya kawo musu wani kwalba ya dire musu sannan ya ‘balle murfin yabar wajen. Sofy dai duniya ta mata dad’i, sai jijjiga kai takeyi kaman kad’angare, ahaka cikin sau’ki Bash ya faki idonta ya jefa wani tablet da ya ‘ballo daga wani sachet acikin aljihunshi, da sauri ya d’aga kwalbar wine d’in ya zuba acikin cup da tablet d’in yake. Ta’bata yayi tajuyo ya mi’ka mata cup d’in da tablet d’in yake ciki yace “Cheers” Yamutse fuska tayi tace “No, I’m full, ya isheni, in nasha wani cup zan iya amai” Ranshi ya ‘baci amma haka ya danne yace “Just one more, daga wannan shikenan” Kar’ba tayi suka kara cups d’in sannan suka kafa kai suka shanye tas, kusan lokaci d’aya suka dire cups d’in akan table gamida sakarwa junansu murmushi, hirarsu suka cigaba da yi. Chan sai Sofy ta duba wayarta da ke cikin handbag nata, 2:55pm tagani, a rikice ta tashi ta fara gyara jikinta don dama ‘karya tayi ma Momy akan zataje gidan wata ‘kawarta, Momy kuma tamata kashedin kar ta yarda ta wuce la’asar gashi yanzu la’asar kam har ya doso. Kama hannunta Bash yayi yace “Babe, ina zakije kike gyara jiki haka?” Ba cikin nutsuwarta ba tace “Bash I have to go, Momy zata min fad’a” Wani makirin murmushi yayi da shi kad’ai yasan ma’anar shi sannan yace “Ki d’an tsaya kad’an mana” Ta bud’e baki zatayi magana taji kanta yafara juyawa, batasan lokacin da ta fad’a jikinshi ba. Murmushi yayi cikeda jindad’i don ya lura maganin da yasa mata ne yafara aiki, shafa jikinta yasoma yi ahankali kaman tafiyar maciji yace “Hey, are you okay?” Lumshe ido tayi don tuni tabar duniyar nan tamu, inaga ma har ta isa pluto, shafata da yakeyi ya ‘kara saurin aikin maganin a jikinta. Kasa magana tayi sai wani nishi takeyi kaman zata shid’e, aikam Bash yasamu abinda yakeso, hannun rigarta yafara sa’bulewa saikuma yayi saurin tashi don yatuna a club suke. Jan hannunta yayi ya d’auki handbag nata da ta yar, biyan kud’i yayi sannan ya ri’ke hannunta suka nufi hotel da ke manne da club d’in, neman yaga mishi riga tafara yi, dasauri ya biya kud’i a reception aka bashi key, cak ya d’agata, bai direta ko ina ba sai a cikin d’akin da ya kama musu. Yana kwantar da ita yajuya don kulle ‘kofar d’akin amma Sofy ta cafko wuyarshi, idanunta jawur kaman garwashin wuta wanda Bash da kanshi sai da ya tsorata, da ‘kyar ya janye jikinshi yaje ya sama ‘kofar key. Juyowar da zaiyi yaga har Sofy ta cire rigar jikinta tana wani gantsarewa tana numfashi sama-sama, kayanshi ya cire sannan ya haura kan gadon, ai Sofy irin rikicewar da tayi har ya wuce tsammanin Bash. Da zafi-zafi suka fara shafa junansu har suka tafi mai gaba d’ayan, ihu takeyi dayake its her first time amma da yake maganin yana aiki sai ma wani ‘kara haukace mishi takeyi. A ranar nan duk sun sha wahala musamman ma Bash don saida yayi nadamar drugging nata da yayi, sai kusan maghriba maganin ya saketa, duk yayi mata kacha-kacha ba ko kyaun gani, bedsheet fari da ke shimfid’e akan gadon ya koma ja kamar an yanka babban kaza an zuba jinin akan bedsheet d’in. ☆☆☆☆☆☆☆☆ *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish. Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 28, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 51-55 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *51-55* www.gidannovels.blogspot.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Guntun tsaki Suhal yaja ganin Ilham ta tafi tana kuka, shi kad’ai yake magana “Kishi takeyi kenan ko meh?, lallai ashe nan gaba sai zuciyarta yakusa bugawa don bazan had’a son Leena da kowa ba”. Shareta yayi yafara danne-danne da wayarshi sai kuma wani zuciyar ta lurar dashi rashin dacewar hakan, mi’kewa yayi ya ja ‘kofarshi sai ya nufi sashen su Fu’ad(asalin sashen su Ilham) don yanada ya’kinin chan ta nufa. Sallama yayi yaji shiru ba a amsa ba, haka yasa ya shiga kawai ya nufi d’akin Ilham da yaga ‘kofa a bud’e. Tsayawa yayi ganin Umma tasa Ilham agaba sai faman tambayarta takeyi, sallamar da yayi ne yasa duk suka kai dubansu wajen ‘kofar, ganin Suhal sai Ilham ta fad’a jikin Umma had’e da saka wani sabon kuka. Cike da damuwa Umma ke tambayar Suhal “Ko kasan meh ya sameta?” Girgiza kai yayi ya ‘karasa shigowa cikin d’akin sannan yace “Bansani ba Umma” A sanyaye Umma tace “Bansan daga ina tafito ba, d’azun nan ina zaune a parlour kawai naga ta shigo a birkice ba ko sallama, da farko har zan tambayeta ya batayi sallama ba sai naga ta ruga da gudu tashiga d’aki tana kuka, da sauri na biyota nafara tambayarta meh yasata kuka amma kaga har yanzu ta’ki cemin ko uffan, ba abinda takeyi sai kuka” Zama a bakin gadon yayi ya kalli Ilham sannan ya kalli Umma, murmushin ‘karfin hali yayi sannan yace “Umma d’an bamu minti goma, maybe in mu biyu zatamin magana” Jinjina kai tayi ta janye Ilham daga jikinta sannan takoma parlour tazauna tanata faman tunani. A d’akin kuwa Umma tana fita Ilham ta mi’ke zata bita, saurin shan gabanta Suhal yayi ya tare hanya sannan yace “Ina zaki?” Kallonshi tayi ta watsar sannan tace “Ya Suhal ka matsamin a hanya kar kasa na gayama magana” Baice komai ba ya tura ‘kofar d’akin ya rufe sannan yace “Ilham I’m sorry” Ji tayi ya ma raina mata wayo, meh ya maida ita, toy ko meh?, ko kawai ya maidata abun debe mishi kewa whenever he is bored?, ji tayi gwanda kawai ta amayar mishi da maganganun da ke cikin zuciyarta, wata’kila taji sau’ki ko kad’an ne. Share hawayenta tayi tace “Ya Suhal meh ka maida ni?, wawiya?, wacce zaka juya yanda kaga dama?, wacce zaka azabtar don ka lura ina sonka fiye da kaina?, ya Suhal abinda kamin yau shi yafi cimin rai, muna zaune ka d’auki call na wata har kana wani lankwasa murya… agabana fah, sannan hakan bai isheka ba, tafiya d’aki ma kayi ka barni kaman wata trash, I cant take it anymore” ta ‘karasa maganar zuciyarta a raunane don muryarta har yana rawa kaman zata sake ‘barkewa da wani sabon kukan. Kasa cemata komai yayi kawai ya jawota jikinshi ya rungume, nan ta shiga sau’kar da wani ajiyar zuciya. Suhal ya riga yagama gano lagonta, ko wani irin fushi ta d’auka dashi yana rungumeta had’e da lallashi sai taji ta yafe mishi, wani irin mahaukacin so take mishi da bata ta’ba tsammanin akwai wacce tayi ma saurayinta irinshi ba. Saida yaji bugun zuciyarta ya d’an dawo daidai sannan ya d’an janyeta daga jikinshi ya ri’ke hannunta yana kallon fuskarta, tausayi sosai ta bashi har yaji zai iya bata ko da rabin-rabin zuciyarshi ne don ya tsani yaga Ilham tana kuka. Kanta a sunkuye tana hawaye d’ad’d’aya, d’ago kanta yayi ya ciro hanky daga aljihun shi ya fara goge mata hawayen, da ‘kyar dai hawayen ya tsaya don gogewan da yakeyi kaman ‘kara ma hawayen ‘karfin guiwan zuwa yakeyi. Kissing na forehead nata yayi, a d’an rikice ta kalleshi da idanunta dake cike da mayen sonshi, coolest smile nashi ya sakar mata wanda ya ‘kara narkar mata da zuciya har tanaji ko mata goma ne zata iya zama dasu in har Suhal ya aureta, ita ya auretan shine babban burinta. Murmushi ta sakar mishi itama, nan yace “Yanzu muje muyi ma Umma bayani ko?, kinga yanda hankalinta ya tashi sosai” Bai jira cewarta ba ya bud’e ‘kofar, hannunshi ri’ke da nata suka fito parlour suka zazzauna. Umma mamaki ne sosai ya cikata don ko minti goma Suhal baiyi da shiga d’akin ba gashi har Ilham tabar kukan da takeyi. “Ilham zo” Umma tace da ita Sai sannan Suhal ya sake mata hannu, jikin Umma ta kwanta, Umma tace “Dama meh yasa kike kuka d’azun har ina tambayar baki gayamin ba?” Kallon Suhal tayi taga ita yake kallo, sunne kai tayi tace “Umma komai ya warware, dama misunderstanding ne kawai muka samu” “Ke da wa?” Umma ta kuma jefa mata wata tambayar “Ya Suhal” ta fad’a tana nunashi da yatsa Umma taso ta sake tambayarta sai kuma taga in tayi hakan tayi wauta, fasa tambayar tayi da niyyar samun Ummi, Abba da Baba su tattauna akan abinda take zargi akan Ilham da Suhal sannan su sa ido don kar abun yayi nisa. Murmushi kawai Umma tayi tace “Ai shikenan tunda ni barè ne baza a iya gayamin sirrin ba” Dariya Ilham tasa tace “Allah bakomai Umma”. Suhal kuwa murmushi kawai yayi, Umma ta girgiza kai ta bar su a parlourn. Tana fita Ilham ta dawo kujerar da yake zaune ta dafa kafad’arshi tace a shagwa’bance “Ya Suhal ni fah nagaji da ‘boye-‘boyen da mukeyin nan” Zaro ido yayi yace “Ilham hakan shine yafi for now, kibari sai nan gaba in yaso sai mu gayamusu” Tura baki tayi tace “Ni fah Allah aure nakeso muyi dawuri, Ya Suhal inasonka fiye da komai nah, ina fatan Allah ya nuna min ranar aurenmu” Mamaki kwance a fuskarshi ya gyara zama yana kallonta sosai, chan sai yayi murmushi yace “Meh kike sauri ne?, mene kikeso da bana baki?, yanda muke yanzun haka zai zama in munyi aure so banga meh amfanin damuwa ba” Cikin rashin fahimta tace “Bangane after aure da yanzu rayuwa d’aya zamuyi ba” Kama hannunta yayi yana murzawa yace “Ilham i dont want to hurt you saisa banson ayi auren yanzu” “Kaman ya?” Ta tareshi da sauri Daurewa yayi ya cire kunya yace “What I mean is bazaki iya d’aukar nauyina ba, bazan kuma iya yin komai dake ba don gaskiya sai kin ‘kara girma, gwanda kar ayi auren wannan nasan ko tunanin wani abu dake bazanyi ba, in anyi aure fah?, you know ba yanda za ayi ace na zuba miki ido nata kallonki alhalin lafiya na lau, Ilham ha’kuri zamuyi, banso na jimiki ciwo ko wani abu so please mubar maganar aure for the mean time” Hawaye mai zafi ne ya gangaro daga idanunta zuwa kumatun ta, cikin kuka tace “Ya Suhal wallahi zan iya d’awainiya da kai da komai naka, Allah kuwa ni ba yarinya bace, akwai wasu da na girma amma ahaka suke zaman aure lafiya lau har ma su haihu, please ya Suhal ka yarda, ni zanje na samu su Baba na gayamusu in ma kunya kakeji” “Toh fah, lallai Ilham tayi nisa” yace a cikin ranshi. Afili kuwa cewa yayi “Understand me, a ra’ayina banso na auri yarinya ‘karama, saisa nafiso in kin kai ko 23 haka sai mu fara batun aure, that time kin ‘kara zama cikakkiyar mace” Hawaye ta dinga yi tana mishi magiya amma duk ya’ki, da ‘kyar yasamu ta amince akan zasubar soyayyar tasu as sirri. Girki ta wuce kitchen ta d’aura shikuma ya koma d’akinshi ya d’an kwanta. 4:00pm Daidai wannan lokacin Suhal yake faman d’aura agogo ba’ki mai wal’kiya a tsintsiyar hannunshi, sanye yake da black jean trouser sai t-shirt fari mai d’an blue ajiki, ‘kafarshi kuma bertozzi ne ba’ki, ya dai fito fes, daga nan ya feffesa turare har duk d’akin ya gauraye da ‘kamshin, gashinshi da yake kwance wanda yama askin “low cut” ya ‘kara tacewa ya shafa hair oil. Key ya d’auka sannan ya d’auki wayarshi ya danna ma Leena kira. “Hello Dear” tace dashi “Hey yanmata, yanzu nake barin gida, i hope dai kin shirya?” Dariya tayi don ita lokacin ne ma take faman shiga wanka sannan tace “Ehh kai nake jira” “Yauwa ko ke fa?, da baki shirya ba Allah fasa rakiyar zanyi don banson na shirya sannan na zauna zaman jira” Murmushi tayi tace a zuciyarta “Ai kuwa kayi gamo da asalin mai african time anan baka sani ba”. Afili kuwa cewa tayi “In ka ison dai just flash me sai na fito” “Toh sai na iso” yace da ita sannan suka yanke call d’in kusan lokaci d’aya. ☆☆☆☆☆☆☆☆ *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman SEPTEMBER 30, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 56-60 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *56-60* www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com ☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Shafa sajen da ya kwanta luf-luf a fuskarshi yayi yana murmushi, ahaka har ya shige motarshi yaja yabar gidan. 4:12pm ya iso gidansu Leena, fitowa yayi ya gaisa da mai gadi as usual sannan ya danna mata kira amma har ya tsinke bata d’aga ba. Bayan kaman minti goma bata d’auka ba sai ya tura Tijjani akan ya duba mishi ita, Tijjani yadawo yace “Tana shiri ne, tana zuwa” Ba ita ta fito ba sai quarter to five, Suhal yayi Allah wadai da soyayya yafi a ‘kirga, da ba don sonta da yakeyi ba…ba abinda zai sa shi zaman jiranta kusan rabin awa, ya tsani a mishi african time shiyasa shima he is always on time. Daga nesa ya hangota tasa wani dubai gown sky blue mai ado, tayi kyau sosai, duk haushin da yaji sai ya nemeshi ya rasa. Tana isowa inda yake zaune ta sakar mishi murmushi tace “Tuba nake ranka ya dad’e, na ‘bata maka lokaci ko?” A d’an rikice ya dubeta yace “Ba komai, muje ko?” Waje suka nufa inda yayi parking na motarshi kamin gate nasu, a hanya suna hira sosai don yanzu Suhal yana ma ‘ko’karin hira da ita duk da still yana tsoron bayyana mata sonta yakeyi, bawai yana tunanin zata mishi ‘kusa bane, a’a, matsalar bai ma san yaya zai fara tunkarar ta da maganar soyayya ba. Bank suka fara zuwa ta ciri kud’i daga ATM sannan suka nufi sahad stores. Sun kusa isa kenan Suhal ya kalleta ya kawar da kanshi, tun da yaganta yakeson ya yaba kwalliyarta amma ya kasa, kanshi akan titi da ‘kyar yayi gathering courage yace “You look amazing” Kallonshi tayi disbelievingly, tama kasa yarda wai comment d’in daga bakin Suhal ya fito, murmushi tayi ganin yama ‘ki yarda su had’a ido don tun da yayi maganar bai sake cire idanunshi daga kan titi ba. “Awwwn, Thank you, you look good too” tace dashi “Dont flatter me” yace mata nervously Dariya tayi tace “Im serious, ba wani batun flattering aciki, its the truth, you always look good” Murmushi yayi ya dubeta amma sai ya kawar da kanshi da wuri ganin ta zuba mishi manyan idanunta masu birkita mishi lissafi, ajiyar zuciya ya sauke ahankali sannan yace “Ina godiya” Daidai nan suka isa mall d’in, bud’e ‘kofofinsu sukayi suka nufi cikin mall d’in. Jerawa sukayi ta fara za’ban abubuwan da zata saya shima ya fara za’ba ma kanshi inda shi yamafi za’ban perfumes akan komai, Leena shopping sosai tayi, duk inda tayi Suhal yana tare da ita kaman wani bodyguard, ahaka har sukazo counter. Bayan anyi lissafin komai sai Leena ta fara ‘ko’karin bud’e bag nata don ciro kud’ad’en, da sauri Suhal ya mi’ka ATM card nashi yace su cire. By the time da ta gama lissafo kud’in tana mi’ka musu daidai lokacin matar ta mi’ko ma Suhal ATM card nashi tana cewa “Thank you for shopping with us sir” Jinjina kai yayi ya kar’bi ATM d’in ya mayar aljihu sannan ya fara tattara ledojin kayakin da suka saya yana kai su motar. Har ya gama Leena tana tsaye ko motsi ta kasa kaman statue, ko kud’in haka ta ri’keshi a hannunta tana bin Suhal da ido. Dawowa mall d’in yayi ya hura mata iska a fuska, wani had’a fuska tayi tace “Suhal what’s this?” “Babu, in akwai abinda kikeson ‘karawa ma ki ‘kara nayi settling sai mu tafi” Mi’ka mishi kud’in tayi tace “No, bazan yarda da hakan ba, ni fa nace ka kawoni zan saya abubuwa, *with my money* ba wai nace ka biyamin ba, in da nasan haka ne da tun farko bance ka kawoni ba” Marairacewa yayi yace “Im sorry Leena, bansan ranki zai ‘baci haka ba, don Allah karki maida hannun kyauta baya, please I beg you” Karkad’a kud’in tayi tana kallonshi, zatayi magana kenan ya girgiza mata kai yace “In ba cewa zakiyi kinyi ha’kuri ba please dont say anything” A sanyaye ta mayar da kud’in cikin bag nata, ita gani take laifinta ne, gashi tasa ya kashe wannan uban kud’in a banza, tunanin yanda zata iya repaying nashi kawai takeyi. Muryarshi ta tsinkayo “Kin gama?” “Eh” ta amsa mishi blankly “Ina zuwa” yace da ita sannan ya bata key na motar akan taje ta jirashi. Kar’ba tayi ta fita waje shikuma ya nufi wajen teddy bears da ya hango, tsayawa yayi yana duba wanda zai siya ma Ilham don yasan tana matu’kar son teddy. Wani ‘kato wane mutum ya za’ba, da yaji kud’in sai da ya girgiza amma haka ya cire ya bayar. Awaje kuwa Leena tana fita bata shiga motar ba sai ta jingina da jikin boot tana jiranshi, sallama taji, d’agowa tayi gamida amsawa. “Sannu ko, ko zan iya sanin sunanki?” “Sunana?” Ta fad’a tana neman ‘karin bayani “Eh, sunanki?” Ya bata amsa “Leena” ta bashi amsa a ta’kaice Murmushi yayi yace “I’m Salees, can I have your number?” ‘Kare mishi kallo tayi, fari ne, yanayin gemunshi irin quarter million d’in nan, yanada jiki saidai ba sosai ba, hancinshi yanada tsawo, baida tsayi sosai kuma baza asashi a layin guntaye ba. “Tohh fah, malam lafiya dai ko?” “Lafiya lau, taimakamin da number d’in don Allah, ina d’an sauri ne saisa” Kaman tace bazata bayar ba saidai kuma ganin kyakkyawa irinshi yazo yana neman numbarta ko ita mahaukaciya ce bazata ‘ki bayarwa ba, bashi number d’in ta fara shikuma yana dialing a wayarshi. Daidai ta kira number’n ‘karshe “2” Suhal ya iso wajen, godiya Salees yamata yajuya, saura kad’an suyi karo sai Salees yayi saurin dakatawa yace “Sorry, ban ganka bane”. Bashi hanya Suhal yayi ya wuce bai ce uffan ba. Shiga motar yayi ya mi’ka mata hannu alamun ta bashi key, ba musu ta bashi, ta lura kaman ranshi a ‘bace yake. Zagayawa tayi ta shiga sannan tayi gyaran murya tace “Suhal are you okay?” Guntun tsaki yaja yana jin zuciyarshi na wani irin tafarfasa saboda tsantsan kishi. “Karki damu” ya bata amsa Jan bakinta tayi bata sake magana ba, sunyi nisa da tafiyar sai kawai taji ya taka birki kaman mahaukaci. Kallonshi tayi a razane tace “Suhal, meh ke damunka?” Jajayen idanunshi ya zuba mata, dafe kanshi yayi don shi kad’ai yasan yanda zuciyar shi ke bugawa duk lokacin da ya tuna yaga Leena tana bama wani number’nta. Hucin da yakeyi yasa Leena bashiri ta kama hannunshi tace “Talk to me” Cikin ‘bacin rai yace “Waye naga kuna tsaye d’azun sannan akan wani dalili kika bashi numberki?” “Yace min sunanshi Salees….” “Ba sunanshi na tambayeki ba, mesa kika bashi numberki nakeson ji” ya katseta da sauri “Ya tambayeni ne nikuma naga bai kamata na wula’kanta shi ba tunda bansan da wani magana yazomin ba, na bashi saboda naga kaman ba mutumin banza bane” Kallonta yayi yace “Ana gane mutum ta fuska ne?, mugu bai da kama Leena, mesa kika yarda dashi har kika bashi??!!” Jin yanda yayi maganan cikin d’aga murya yasa bakinta yana rawa tace “Mugu bai da kama kace ko?, you are also a stranger to me Suhal, kana tsammanin in da nayi nazari da wannan kalmar ko sannu zanyi da kai ne balle mu tsaya mutunci?, kenan ma I’m the fool, ni wawiya ce da na yarda da kai, ni wawiya ce da har na kiraka kazo ka rakani ba tare da nasan daga ina ka fito ba, bansan da alheri ko sharri kake bina ba, haka kake nufi Suhal?” Ta ‘karasa maganar tana hawaye Ganin hawaye yana zubowa daga idanun Leena yasa Suhal rikicewa sosai, ba abinda yake cemata sai “Thats not what I meant Leena, wancan had’uwan mu is a different case, karkiyi ma magana ta mummunar fahimta” Share hawayenta tayi tana magana ita kad’ai “Its all my fault, da tun farko ban yarda da kai ba da ko da wasa bazaka fara d’aga min murya ba, tsawa?, abinda nafi tsana a duniya” Nadama ne ya dirar mishi a zuciya, tambayar kanshi yakeyi meh yasa yayi ma Leena haka. Cikin lallashi yace “I sincerely apologize, raina ne ya ‘baci” “Akan meh ranka zai ‘baci?, don na tsaya da wani?” “Yes Leena, I got jealous wanda har nayi over-reacting na saki kuka” ya fad’a kai tsaye gamida cigaba da driving Kallonshi tayi cikin rashin fahimta tace “Jealous?, jealous?, of what?, why?” Murmushin gefen le’be kawai yayi yace “All this questions, reserve them, nan gaba zan answer miki all, yanzu dai tell me kin ha’kura” Murmushi tayi tace “Na ha’kura amma sai ka min al’kawarin u will never shout at me again” “Ohh ohh, wannan d’in ma I was mad saisa, will learn to control myself next time, sannan karki ‘kara tsayawa da wani don anything can happen in na ga hakan” “Lafiyanka?, kar na tsaya da wani fah kace, kai zaka bani miji ne?” Dubanta yayi sannan ya maida hankalinshi kan titi yace “Eh, zan baki miji that I trust, wanda nasan bazai ta’ba hurting naki ba, he will take care of your every need, wanda yake sonki fiye da kanshi” Zatayi magana ya d’aura hannunshi akan nata yace “No more questions”. Da haka suna hira har ya sauketa a gida ya kira maigadi yazo ya shigar mata da ledojin cikin gida, godiya sosai ta mishi har sai da ya gaji yaja hannunta ya kaita cikin gidan sannan yabar gidan da sauri ya shige motar ya tayar. Dagudu tafito kaman zatayi kuka tana d’aga mishi hannu, dariya yayi shi kad’ai yace afili “I love everything about you” ☆☆☆☆☆☆☆☆ Sofy ta farka daga bacci taji jikinta ba komai, gefenta ta duba taga Bash sai shar’ban bacci yakeyi. ‘Ko’karin mi’kewa tayi dafe da kanta sabida yanda yake sara mata kaman zai tsage biyu, gashi ta rasa gane meh ya kawota hotel da Bash har gata a tu’be. Ihu sosai tayi wanda ya tayar da Bash daga wahalallen baccin da yakeyi, rarrafawa yayi ya isa ‘karshen gadon ya rungumeta ta baya yace “Baby kwanta muyi bacci” Hankad’e shi tayi murya yana rawa tace “Bash meh ka min?, ina ka kawoni?, mesa ka kawoni nan?” Sake rungumeta yayi yace “Baby you know I love you….” Tureshi tayi da iya ‘karfin da ya rage mata ta fashe mishi da kuka tace “Bash tell me!!!, meh kamin?!!” Jingina da jikin gado yayi yace “I had sex with you” ‘Kwalalo ido tayi duk da bataji mamakin furucin shi ba don tayi zaton hakan ne saidai tanaso ta gaskata saisa ta tambayeshi, saka hannu akai tayi tana kuka tana salati “Innalillahi, Bash ka kasheni, mesa kamin haka Bash?, sakayyar da zakamin akan irin son da nake maka kenan?, Bashi mesa?, mesa bazaka bari sai munyi aure kayi koma meh ba?, ka cuceni ka cuci rayuwata, yanzu meh zan gayama Momy in na koma gida?” Kamo hannunta yayi ya jawota jikinshi yace “Dont you trust me?, zan aureki Sofy, inasonki, sonki ne yasa na aikata miki hakan, Momy kuma ba sai kin gayamata gaskiya ba don ma ba ganewa zatayi ba, yanzu tashi muje muyi wanka sai na maidake” ‘Kan’kame blanket da ke jikinta tayi tana kuka sosai tace “Mesa ka samin ‘kwaya?, sabida kasan ba yarda zanyi ba shine kayi drugging nah ko?” “No baby, ki yafemin, ba wanda zai gane saidai in ke zaki fad’a” Tashi yayi ya janye blanket d’in daga jikinta, kallonta da yayi ahaka sai ya ‘kara ji dole ne ma ya sake wani round, haurawa gadon ya sakeyi yafara shafata ahankali har yafara yi da sauri-sauri. Ganin abinda yake shirin yi yasa Sofy ta fara kokuwa dashi amma ‘karfin su bazai had’u ba, tanaji tana gani ya sakeyi har sau biyu, tana kuka har ta koma ajiyar zuciya tsaba azaban da takeji, ko motsi ta kasa yi har ya gama abinda zaiyi ya wuce toilet. Bai jima ba yafito d’aure da toilet a ‘kugu, gadon ya hau ya janyota jikinshi yana faman lallashi da mayaudaran kalamanshi. Mi’kar da ita yayi ta tsaya da ‘kafafunta amma meh?, ta kasa sabida ba ‘karamin ciwo yaji mata ba. Cak ya d’agata ya kaita toilet, bai gasata ba baiyi komai ba don shi bai ma san ana wani gashi ba, wanka kawai ya taimaka mata tayi sannan ya dawo da ita d’akin. Sai sannan ta lura da yanda bedsheet d’in yazama jawur, tausayin kanta taji sosai da wannan yanayi da take ciki. Kaya yasamata ya bata wani pain killer sannan ya ri’ko hannunta suka fito daga wajen tana takawa a hankali. Sai da suka shiga motar ne ta tuna da kashedin momy na kar ta kuskura ta kai la’asar. Jiki na ‘bari ta ciro wayarta taga 8:47pm, ga missed calls na Momy, Rafee da Leena sunkai tamanin, rufe bakinta tayi tana kuka don itakam yau tasan kashinta ya bushe. Da lallashi da lallamin SABON SALON D’A NA MIJI ya sa tabar kukan da take yin, yace mata tace ma Momy ta raka ‘kawartata gidan sistanta ne sannan wayarta ta manta yana silent. A ‘kofar gidan ya tsaya, zagayowa yayi ya bud’e mata ‘kofa, fitowa tayi tana cije le’be, rungumeshi tayi tana hawaye tace “Bash, Momy zata gane, tafiyana nasan ya chanja, wallahi zata gane” “Kiyi ‘ko’karin saita tafiyarki yanda bazata gane ba, zan kira wani friend nah likita ne sai na tambayeshi ko akwai abinda zai rage miki zafin, ko ma yaya dai zan kiraki” Jinjina kai tayi tace “Toh zan gwada saitawa” Kissing nata yayi yace “Wannan ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com a tsakaninmu, only the two of us, zakiji sau’ki so stop crying” Sai da yaga ta shiga gida sannan ya shige motarshi yabar wajen, zuciyarshi cike da farin cikin yau ya kar’bi abinda yayi sha’awar kar’ba daga wajen Sofy shekara da shekaru amma ta hanashi, yau yayi yanda yakeso da ita, rayawa yakeyi a zuciyarshi tunda yanzu yasamu yayi disvirgining nata ai yayi mai wuyan, duk lokacin da yake bu’katar ta zai san yanda zaiyi yasa ta yarda ta hanyar mayaudaran kalamai. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Leena tashiga ta nuna ma Rafee da Momy abubuwan da ta saya takuma gayamusu cewa Suhal ne ya biya, ba ‘karamin mamaki sukayi ba, har Momy tace zata kirashi tace bai kamata ya kashe kud’i dewa haka ba amma Rafee ta dinga bata ha’kuri har ta ha’kura amma duk da haka saida ta kirashi ta mishi godiya takuma ce mishi bai kamata ya shiga wahala har haka ba, murmushi yamata yace bakomai. Shiru shiru suna zaune har akayi maghrib ba Sofy ba labarinta, kiran duniyan nan sun mata amma bata d’auka, hankalinsu yayi mugun tashi, su tsoron su ma kar wani abu ne ya sameta a hanyar dawowa tunda tun La’asar ya kamata tadawo. Ko abinci sun kasa ci, suna wannan halin ne har past 9, daidai lokacin Sofy ta bud’e ‘kofa gamida sallama a hankali. Rige-rigen isa wajenta sukayi, tambayarta Momy ta hau yi “Sofy, lafiya?, meh ya tsaida ke har yanzu?, ba abinda ya sameki?” Hawayen da take ma’kalewa ne ya zubo mata, rungume Momy tayi tace “Kiyi ha’kuri Momy, ki yafemin, bazan sake ba” Kama hannunta Momy tayi tajata suka zauna akan kujera sannan tace “Shikenan, ba abinda zan miki, ina kikaje sannan meh ya tsaidake har warhaka?, wayarki kuma mesa baki d’auka?” “Da naje gidan ‘kawata d’in sai mamanta ta aiketa gidan sistanta shine tace muje tare, da mukaje kuma sistanta d’in tana son mutane sosai, ta hanamu tafiya wa sai mijinta ya dawo zai dawo damu, mijinta bai dawo ba sai wajen takwas, muka jirashi yayi wanka yaci abinci shine ya dawo damu, har yace ma zai shigo yabaki ha’kuri yakuma miki bayani don yanda yaga na rikice amma sai nace mishi yabari kawai, in namiki bayani you will understand. Wayana kuma bansan yana silent ba sai da muka kamo hanya ne nagani” Sofy ta fad’a cikin kuka Rafee da Leena zuba mata ido sukayi suna jin labari, Momy ta sauke ajiyar zuciya tace “Shikenan, in zaki sake dare irin haka ki kiramu ki gayamana, kinsa duk hankalinmu ya tashi, na tsamman wani mugun abu ne ya sameki” Jinjina kai tayi tana share hawayenta tana kuma godema Allah da ‘karyar ta ya kar’bu a wajen Momy. *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman OCTOBER 8, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 61-65 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *61-65* www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Yana isa gida ya hango Ilham zaune akan kujera a tsakar gida ta sa ‘yar three quarter da top, kunnenta toshe da headphone, fuskarta saitin sama saidai idanunta a lumshe suke wanda hakan ke nuni da ko ma mene takeji a kunnentan yana ratsa jikinta sosai. Har yayi parking bata ma san ya shigo gidan ba, a hankali yafara takawa yana dosan inda take. Cire headphone d’in yayi daga kunnenta, a d’an firgice ta bud’e idanunta, ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya tace “Ya Suhal you startled me” Murmushi yayi yace “Meh kikeji kika nitsu haka?” sawa a kunnenshi yayi yaji karatun Qur’an ne. Gyara zamanta akan kujerar tayi tace “Daman meh kake expecting?, a song?” “Yeah, na tsamman wa’ka ne” “Na tuba ai ya Suhal, wallahi wani wa’azi naji inda ake cewa duk wanda yaji kid’e kid’e a ranar al’kiyama za a zuba mishi ruwan dalma a kunnuwa, bakaga yanda naji tsoro ba, tsoron azaban Allah” Murmushi yayi yana mi’ka mata headphone d’in yace “Good girl, gwanda da kika bar ji, Allah ya shirya masu ji” Tace “Ameen”. K’are mishi kallo tayi ta rungume hannuwanta a ‘kirji tace “Daga ina kake haka?” ‘Karya yamata yace “Na d’an je yawo kad’an ne” don yasan ko da wasa yace yakai Leena shopping ne ba ‘karamin rikici zasuyi ba “Are you sure??” Ta sake tambayarshi “Kina doubting ne?” Ya jefa mata tambaya batare da ya amsa mata wanda ta tambayeshi ba Rau rau tayi da ido tace “Yeah, Allah ni tsoro nakeji ya Suhal, kar wata ta ‘kwace min kai, da zan samu ma ko fita hanaka zanyi don kar wasu matan su ganka” Basar da maganar yayi don baison su ja conversation d’in. Jan hannunta yayi yace “Ni ba wannan ba ma, i have a gift for you” “A gift?” Ta tambayeshi cikin murna Bai ce da ita komai ba itakuwa sai faman sake tambayarshi takeyi, ‘kofar baya ya bud’e ya ciro teddy d’in ya mi’ka mata. Wani irin ihu tayi wanda sai da ya toshe kunnuwanshi, tsalle tayi ta rungumeshi tana ‘kara ihun murna tanata zuba mishi godiya kaman ya bata aljannah. Da ‘kyar yasamu ta sauka daga jikinshi, murmushi yamata yace “You will never grow up naga alama” Tura baki tayi tace “Kai fah ya Suhal kana son zagina wallahi” “No ba batun zaginki bane, in ba yarinta ba yanzu wannan ihun da kikayin nan ba sai a tsamman saceki akazo yi ba?” Rufe bakinshi ke da wuya suka ga iyayen nasu a tsaye da gani aguje suka fito Baba yace “Ya dai?, lafiya kam ko?” Suhal yaja guntun tsaki yace “Wallahi lafiya lau Baba, kaga yanzu fad’an da nake mata kenan, ihun da tayi ko ni sai da na firgita” Umma tace “Meh yasata ihun?” Ilham cikin murna tace “Ihun murna ne fah umma, bakiga teddy da Ya Suhal ya bani bane?” Ta ‘karasa maganar tana rungume da teddy da yama fita jiki Dariya kawai sukayi don shirmen Ilham sai ita. Ummi tace “Ni wallahi na tsamman ma wani abu ne ya sameta” Dariyarsu suka dinga yi suna fad’an irin tunanin da yashiga ransu lokacin da sukaji ihun. Kiran sallah da aka fara ne yasa Abba, Baba da Suhal suka wuce masallaci, iyaye matan da Ilham kuma suka shige cikin gida. Daga bayan Isha Ilham ta dami Suhal akan suyi game, sunkai sha d’aya da rabi na dare suna game sannan a gajiye suka kakkashe electronics na parlourn. Suna cikin sallama da Ilham sai wayarshi yasoma ringing, dubawa yayi yaga Leena ce, satar kallon Ilham yayi ta gefen ido yaga ta ‘kura mishi mayun idanunta. Sakawa a silent yayi ya mayar aljihu yace “Goodnight” Matsowa kusa dashi tayi da niyyar pecking nashi sai gyaran murya sukaji a gefensu, da sauri Suhal yasa kai yabar sashen. Ilham kuwa kunya kaman ta nutse ‘kasa ganin Abba ya kamasu ahaka, isa gabanta yayi ya kira sunanta “Ilham” Batare da ta d’ago ba tace “Na’am” “Meh ke tsakaninki da Suhal?” Dubanshi tayi da sauri, wani abun da bata ta’ba gani ba yau ta ganshi a idon Abbanta, ‘bacin rai ne kwance ‘karara a fuskarshi, a rikice tafara in-ina “Ba….bu” “Babu?” Ya maimaita “Eh, ba…bu?” Iska ya furzar yace “Kince min babu, karki kuskura na ga akasin hakan” Jiki na rawa tace “Toh, In Sha Allahu” “Je ki kwanta, sannan daga yau ban yarda kina yawan had’a jiki dashi da wata manufa ba, ki mishi kallon wan ki wanda kuka fito ciki d’aya kin jini?, ko da wasa karki fara tunanin sonshi don mun riga mun miki miji” Zaro ido tayi tana kallon Abba, da ‘kyar bakinta ya iya cewa “Miji abba?” Cikin tsawa yace “Eh!!, ko gardama zakiyi ne?!!” Kuka tasa mishi tace “Amma Abba…..” D’aga hannu yayi zai kwasheta da mari amma Umma da fitowarta kenan tayi saurin kama hannunshi tana girgiza mishi kai. Kallon Ilham tayi tace “Ba komai, je kiyi bacci, baza amiki auren dole ba kinji?” Dagudu ta nufi d’akinta tana hawaye. D’aki Umma da Abba suka shiga, ko zama yakasa yi, tunaninshi yana neman guje mishi, zama abakin gado Umma tayi tace “Abban Fu’ad, meh kake shirin yi?, ba dai sirrin da muka binne acikin zuciyoyinmu shekara da shekaru ne kakeson tonawa ba??” Girgiza kanshi kawai yayi yace “Nafiki son abar sirrin nan arufe saidai inaga hakan bazai yiwu ba, dole nan gaba zamu tona” “Mesa za a tona?” Ta tambayeshi tana shirin kuka Zama yayi akusa da ita yace “Maimuna, yazama dole ne yin hakan, yaran nan ni da Yaya muna zargin soyayya sukeyi, ko ba ke bace kika kawo mana maganar tun farko?, ke kika fara lura don dukkanmu bamuyi tunanin hakan ba a lokacin da muka bar ABUN SIRRI a cikin zuciyanmu” “Ehh, amma ai zargi mukeyi, ka bari sai mun gaskata hakan tukunna afara batun d’aukan mataki” Murza hannunta yayi yace “Kinsan girman laifin hakan in ya faru, tun farko gwanda muyi ma tufkar hanci, kar sai abu yayi nisa mu rasa bakin zaren” Kallonshi tayi tace “In Sha Allahu ma ba abinda muke zargi bane”. Tattaunawa suka tayi akan sirrin da suke ‘boyema yaran nasu, duk iya d’auko rahoton mu mun kasa gane menene wannan sirrin, ba abinda suke ce mana sai *”ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com”* ☆☆☆☆☆☆☆☆ Hira suka zauna yi kaman kullum, anan sukaci abinci, duk yanda akaso Sofy ta tashi ta rage kayan jikinta ta’ki, acewarta ta gaji abarta ta huta, gaskiyar magana dai batason Momy taga tafiyarta ya chanja ne. 10:15pm Momy tashi tayi tace “Ni na shiga, sai da safe”. Amsa mata sukayi sannan ta nufi d’aki don call na Hajiya Hafsat da taga ya shigo wayarta. Fad’awa kan gado tayi had’e da picking, cikin wani salo tace “Hello” Hajiya Hafsat daga d’ayan ‘bangaren tace “Yagida Hajiya?, wallahi sai kewarki nakeyi” Momy tace “I miss you more, ina kika shiga ne kwana biyu bama had’uwa saidai muta phone call?” “Hajiya abubuwa ne suka sha min kai, kinsan abu da business, rikicin wani kud’i nah naketa faman yi duk kwanan nan” Haj Hafsat ta bata amsa “Allah sarki, in kud’i kike bu’kata ai zan iya baki ba sai kin dami kanki ba” “A’a Hajiya, a harkarmu ba a haka, bazan d’auki liability nah na d’aura miki ba alhalin inada tawa business d’in” “Toh shikenan tunda haka kike ganin yafi” “Ya yarana?” “Suna parlour, Sofy ne yau takai dare awaje sai yanzu tadawo” Da sauri Haj Hafsat tace “Ina taje haka?” Yanda Sofy ta gayamata haka ta mayar ma Haj Hafsat wacce kawai jinta takeyi, tariga tasan ‘karya Sofy ta shirga don taga fitowarsu daga hotel alokacin da take faman shiga da wani Alhajinta. “Allah ya kiyaye, a dai cigaba da saka ido kar ta fad’a hanyar banza” Murmushi Momy tayi tace “Abinda nakeyi kenan kullum tunda ubansu bai damu dasu ba” Daga nan hirar tasu ta chanja zuwa nasu na ‘yan duniya, mudai MHS muka tattara biros namu muka bar d’akin ☆☆☆☆☆☆☆☆ Momy ta tashi ba da dad’ewa ba Sofy ta d’auki jakanta tafara takawa ahankali tana cije le’be ta shige d’akinsu, Leena dai bata lura da yanayin tafiyar Sofy ba don kallon TV da takeyi, Rafee ce dai ta lura. Bin bayanta tayi da sauri ta maida ‘kofar ta rufe, a firgice Sofy ta dubeta tace “Rafee lafiya?” Jan hannunta Rafee tayi suka zauna akan gado sannan tace “Sofy meh ya sami tafiyarki?” Sunkuyar da kai Sofy tayi tace “Nothing” Tsaki Rafee taja tace “Kibar min ‘boye-‘boye” “Babu nace miki” Tashi tsaye Rafee tayi tace “Fine tunda kinfison Momy tasani, zanje na sameta na gayamata in yaso sai ta tambayeki, ita kam ai baki isa ki ‘ki gayamata ba” Da sauri Sofy ta tsugunna akan guiwowinta tace “Don Allah karki gayama Momy, zan gayamiki” “Ehen?, ina jinki” Tashi tsaye tayi tace “Bash ne” “Bash yayi meh?” Rafee ta tambayeta “Yayi drugging nah sannan yayi raping nah, he did it more than once duk da yasan yajimin ciwo, ya rabani da virginity nah” ta ‘karasa maganar tana kuka Kan Rafee ne ya sara sosai, duk iskancinta tafiso ya tsaya a ita kad’ai, kar ‘kannenta su fad’a iskanci kaman yanda ita tayi tsundum aciki. Rungume Sofy tayi tace “Shhh, yi shiru kar momy ko Leena suji” Shiru tayi sai sheshshekar kuka da takeyi, bubbuga bayanta tayi sannan tace “Shikenan, muje kiyi wanka ki gasa jikinki da ruwan zafi sai kizo kisha magani” Jinjina mata kai tayi, toilet suka shiga, Rafee ne ta tayata gashin, Sofy sai kuka takeyi tana rufe baki don kar ajita duk da irin zafin azaban da takeji. Tayi gashi sosai sannan Rafee ta kamo hannunta suka dawo d’aki, sallah ta rama tukunna tasa kayan bacci. Rafee ta ‘ballo wani capsule ta bata da ruwa akan tasha, duk da Sofy ta tsani magani haka yau tasha ba ko gardama, bata jima da sha ba wani baccin gajiya ya d’auketa. Rafee zama tayi a bakin gadon tana hawaye, ita kad’ai tasan irin turirin da zuciyarta ke yi akan budurcin Sofy da Bash ya kar’ba. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Ku cigaba da ha’kuri, yau d’in kuyi managing don bai da yawa. Don nayi al’kawari ne saisa na dage nayi squeezing time nayi. Love *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman OCTOBER 8, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 66-70 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *66-70* www.gidannovels.blogspot.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Bari mu waiwayi ya Fu’ad yake all this while achan school. Turkey Lokacin da Fu’ad ya sauka a ‘kasar Turkey yakira gida ya gayamusu sannan ya tari taxi ya wuce gidan da suke zama ada shi da Suhal. Bud’ewa yayi yashiga ya fad’a kan couch yana sauke ajiyar zuciya, take wani kewan Suhal ya maimaiye zuciyarshi, ada dai in sun dawon nan su zauna su ta hira suna raha, su tsokani juna sannan in yayi ba daidai ba Suhal sai ya zaunar dashi ya mishi wa’azi, ciro wayarshi daga aljihu yayi ya danna mishi kira. Suhal yana picking yace “Hello” Fu’ad yace “Wallahi gidan so dry, I miss you bro” Dariya Suhal yayi yace “A hankali zaka saba, abinda nakeso da kai dai shine please ka kama kanka, banda shashanci” Dariya kad’an Fu’ad yayi yace “Sannu babban yaya, daman bana shashanci, I just have fun” Suhal yaja guntun tsaki yace “Fun a shaye-shaye?” Dariya Fu’ad yayi yace “Toh naji naji, Bye” ya katse wayar gamida mi’kewa don kintsa gidan. Haka rayuwarshi ya cigaba da tafiya a Turkey inda ya du’kufa sosai akan abinda ya kai shi, da farko-farkon komawarshi yabar shan komai saidai sabida abokai suna buga muhimmin rawa wajen gyara mutum ko ‘batawa toh hakan ya ‘kara tabbata akan Fu’ad. Ruwa tsundum ya fad’a har ma yana faman nitso, wa’azin da iyayen suke mishi in sunyi waya duk ya tattara ya watsar, suna magana yana shiga ta right ear yana fita ta left. Sunday 11:00pm Ayau anyi inviting na Fu’ad wani party wanda students neh suka had’a, ya gama shirin shi tsaf sannan yakira friends nashi wanda suke asalin indigenes na chan ne sukazo suka d’aukeshi a motarsu, circle nasu su biyar ne: Desmond, John, Frey, Rilwan da kuma shi Fu’ad in. Wani club achan bayan school nasu suka je, suna shiga wani table suka nufi inda daman duk anyi arranging nasu as six seats per table. Kid’a ke tashi sosai da wasu irin haske different colours da suka ‘kara taimakawa wajen had’ar da wajen da kuma fitar da kyaun decorating na wajen da akayi. Beer aka kawo musu suka fara sha suna hira, DJ yayi announcing cewa yanzu za a fara rawa, wasu maza uku wanda turawa biyu ne da kuma black guda d’aya, hawa kan stage suka yi suka fara rawa, ahankali suka fara stripping suna jifa da kayan jikinsu. Fu’ad da tun da akace za afara rawa ya sunkuyar da kai yana d’an danne-dannenshi a waya bai d’ago ba, ihu yaji sosai a wajen ana tafi, d’ago kan da zaiyi idanunsa sukayi arba da wad’annan maza guda uku tsindir haihuwan uwarsu suna ta kissing na juna da dai wasu ‘kazaman wasanni. Afirgice ya fara dube-dube acikin makeken club d’in, zuciyarshi ne ya bada sautin “Dum!!!!” lura da yayi ba mace ko d’aya awajen, waiters ne duka, ba mace ko d’aya, ba ma alamun mata a arean wajen. Ta’bashi John yayi, a tsorace ya dubi John d’in yace “What the f*ck is this?” John yace “Calm down man, its interesting, enjoy yourself” Tsaki Fu’ad yaja yace “I should enjoy myself??, I dont see any girl here” Desmond ne ya sako baki cikin hirar tasu yace “We dont deal with girls” “What do you mean?” Fu’ad ya jefa mishi tambayar “You mean all this while you’ve never notice anything strange about the four of us?” Frey ne yayi maganar don yanzu dukkansu sun dawo da hankalinsu wajen Fu’ad Fu’ad yace “Something strange about you guys?, only thing I know is none of you date girls, you dont like girls as you told me” John yayi murmushi yace “And what do you think is our reason for not dating?” D’aga kafad’a Suhal yayi yace “Probably cos you are all broken or maybe tired of being betrayed and played around by girls, I dont really know” Dariya Rilwan yayi yace “You are wrong buddy, we are homosexual” Wani irin razana yayi har da zaro ido yace “Ho…mo….se…xual???” “Yeah” suka fad’a kusan lokaci d’aya suna gyad’a kai Kallonsu yafarayi d’aya bayan d’aya disbelievingly, tura kujerarshi baya yayi ya juya da niyyan barin wajen amma sai Rilwan ya ri’ke hannunshi. Kallon tara sauka kwata ya sakar mishi sannan yace “Let go of my hand” Rilwan da yake shi d’an Niger ne so yana jin hausa kad’an-kad’an sai ya juya harshe yace “Ka tsaya ka sauraremu, tun da kazo school nan ka shiga ranmu, sonka mukeyi, abin nan fah mu kad’ai zamuyi harkar mu, ba wanda zai sani don *ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com*, a tsakaninmu ne kawai mukasan halin mu, meh zakayi da namace?, mata fah liability ne kawai da kuma dirt” Buge hannunshi Fu’ad yayi yace “Rilwan kai dabban ina ne?, luwad’i?, ni a club na luwad’i?, haba saisa mana tun da nashigo banga mace ko d’aya ba, wannan ne yasa kukata kururuta min wai party d’in will be fun?, wannan ne fun d’in?, meh ma dad’i aciki?, kai namiji ni namiji, uban meh zamuyi ma juna da za ace akwai dad’i?, sirrinku kuma ku ta masha’a ku-e-ku, count me out kagane?” Da sauri ya juya yabar wajen zuciyarshi yana ‘kunan ‘bacin rai. Rilwan zai bishi amma Desmond ya kamashi yace “We should give him some time to cool off” Zama yayi sannan ya gayamusu abinda Fu’ad yace, dukkansu ransu bai so ba amma haka suka bama junansu ha’kuri akan su ha’kura, za su san yanda zasuyi har ya amince musu. Fu’ad yana barin club d’in ya tari cab sai apartment nashi. Kwanciya yayi akan gado yana tunanin wannan hali irin na abokan shi, sai sannan ma yake ganin wautar shi na aminta dasu bayan bai san halinsu ba illa shaye-shaye da sukeyi wanda kowa ma ya sani, ya ji haushin kanshi da sam bai ta’ba tsammanin su da wannan halin ba, shi dai yasan sam basu harkan mata, basu ma shiga sabgar da ya shafi mata, asali ma ko magana da mata basu cika yi ba sai in ya kama dole, tambayar kanshi yakeyi mesa tun farko da ya lura da hakan bai ta’ba tambayarsu dalilin hakan ba?, tunawa yafara yi yanda in sun ganshi ma’kale da namace suke nuna rashin jin dad’insu. Buga kanshi yayi da tafin hannunshi yana cewa “Ohhh nooo!!!, Mesa banyi tunanin wannan abubuwan ba sai yanzu da nagane abinda sukeyi?”. Daga ranan avoiding nasu ya shiga yi, yabar zaman gidanshi don kusan kullum sai sunzo suna ‘kara jan ra’ayinshi, in ya gansu a hanya ma gaba d’aya sai ya bar bi. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Suhal yana barin sashen su Ilham ya wuce d’akinshi yana cike da jin kunya, call na Leena da ya kuma shigowa ne ya katse mishi tunaninshi, bai d’auka ba haka kuma bai katse call d’in ba, yana gama ringing ya danna mata kira. Picking tayi tace “Suhal ya dai?, tun d’azun ina kiranka baka d’auka” “Ina cikin gida ne, Ilham ta sani agaba sai da mukayi game, yanzu ma dawowa nah d’aki” “Allah sarki, ni inaso naga Ilham nan” “In ta yarda watarana zan kawo miki ita” “In ta yarda?” Ta tambayeshi “Lil sis d’in akwai bori ne, amma dai in na gayamata nasan zataso ganinki” “Next time in zakazo try your best kazo min da ita don Allah” Jim yayi yana tunanin yanda zai fara d’aukan Ilham ya kaita wajen Leena, yasan ba ‘karamin bala’i Ilham zatayi ba in tasan son Leena yakeyi, chan sai yace “In Sha Allaah zan kawota” Call ne yashiga waiting a wayar Leena da take shirin ba ma Suhal ansa, dubawa tayi taga sabon number, Suhal da ya ji beep d’in sai ya tambayeta “Call ne?” “Eh, amma bansan waye ba”. Ta ansa shi Share call da yaketa shigowa sukayi sunata hirarsu, da Suhal yagaji da jin call yana shigowa sai yace “Leena just pick the call” “Okay toh ka kashe in yaso in nagama sai na kiraka” “No, ki had’a conference call” “Conference call?, bansan waye ba fah, in wani ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com fah?” “Ki sa kawai, ko bakida enough credit ne?” “Inadashi” “Okay, had’a” Batace dashi komai ba ta d’auka sannan ta had’a call d’in tana mamakin wannan irin iko da Suhal ke nunawa akanta. “Assalamu Alaikum ‘yanmata” wani muryan namiji mai matu’kar dad’i ya daki dodon kunnenta “Wa’alaikum salam” ta bashi ansa cikin muryarta mai sanyi “Amm tun d’azun naketa kira naga call waiting, yakike?” “Eh wallahi, ina call ne, lafiya lau” “Toh ba matsala, ni ba damuwa ta wajena ai, ko sau dubu ne zan kiraki ko da kuwa every single time zanji yashiga waiting sannan baki d’auka ba” Murmushi tayi tace “Saidai bangane wake magana ba” “Leena ce ai ko?” Zaro ido tayi ita kad’ai tana tunanin wannan kuma waye haka, ga yanda ya kira sunanta har zuciyarta sai da taji shi. “Itace” ta bashi amsa “Well, ni Sunana Salees, naganki ne nace inaso, zaki aure ni?” Ya tambaya cikin wani irin salo Maganar tashi har dariya ya bata, da jin sunanshi ta gane shine ta bama number a mall cikin dariya tace “Malam daga had’uwa sai kace na aureka?” “Ba ahaka ne?” Ya tambayeta “Ba ayi mana, ba ka ma sanni ba fah” “Na san ki mana, kyakkyawa, calm, modest, reticent, hankali, tarbiyya,…..” Katse shi tayi “Tohh fah, baka sanni ba kam” Dariya yayi yace “Ina gane yanayin mutum ko da sau d’aya na ta’ba kallonshi so karkiyi denying kice bahaka bane” “Lallai kam, sannu psychic” “You can say that again, ina ne gidanku?” A zuciyarta tace “Wannan anyi d’an duniya da renin hankali, oga sharp sharp”. Afili tace “Meh zakayi da gidanmu?” “Zuwa zanyi” “Kazo kayi meh?” Dariya yayi yace “In nazo zaki ga meh nazo yi, aurenki zanzo nema” Yanda yayi maganar acikin wasa sai ta bashi answer “Toh ba damuwa”. Kwatance tamishi, da ‘kyar yagane wanda hakan yasa tagane shi ba asalin d’an Kano bane don anguwan nasu ba ‘batacce bane. “Nagode, kar na ajiyeki na hanaki bacci, sai da safe” “Sai da safe” ta mayar mishi sannan ta yanke call d’in. “Hello, hello, hello” taketa fad’a amma shiru. Dubawa tayi taga call kam ya tsinke, sunan Suhal ta danna taga call duration d’in, buga lissafi tayi tana rayawa a ranta “Ya katse call d’in tuntuni kenan, ko mesa?, oho”. Wayarshi ta fara nema, takira yakai sau goma amma bai d’aga ba har Leena ranta yafara ‘baci. Sake kira tayi, this time around kam ma rejecting yayi, “Whattttt!!!!!???” Leena ta fad’a cikin jin haushin wannan kalar wula’kanci na Suhal. *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish Skip to content haneefahusman OCTOBER 9, 2016 ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com 71-75 ​*ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na ‘yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *71-75* Haneefahusman.wordpress.com Stylishbichi.mywapblog.com Munayshat.mywapblog.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ Tsaki Leena taja tayi hurgi da wayan ta wuce d’aki abunta, alokacin tuni Sofy tayi bacci sai Rafee dake kwance akan gadonta tana chatting da ya zame mata jaraba, yi takeyi ba dare ba rana. Wanka tashiga tayi agurguje don dare ya tsala, nafila tayi sannan ta kwanta baccinta peacefully. A’bangaren Suhal kuma da ta had’a conference call d’in kasa kunne yayi sosai don jin wayene ya kirata, yana saurarensu tiryan-tiryan, ko wani magana da Salees ya furta sai zuciyarshi ya tsananta wajen bugawa, dannewa yatayi. Abinda Leena bata sani ba shine lokacin da Salees yace zaizo neman aurenta har ta bashi answer da toh ba damuwa Suhal yaji bazai iya cigaba da zama ba, ji yayi kaman ya shiga ta waya ya ma’kure wuyar Salees ya aika shi lahira, yasan in ya cigaba da jin maganan wannan mai d’an banzan surutun zuciyarshi bazata iya ha’kura ba, yasan komai zai iyayi, yaso yayi magana amma girman kai da kuma rashin liver ya hanashi magana, shi aganinshi in ya tanka da masifa toh girmanshi ya zube, gani ma yakeyi ba girmanshi bane yayi chachan baki da wani akan mace, bawai zai ce son Leena kad’an yakeyi ba, no, wani irin jarababben so yake mata wanda ko Laila majnun(ku nemi labarin Laila majnun, its heart touching) ya bashi hanya. Ita Leena bata ji beep na fitar shi daga call d’in ba sabida she was carried away by shirmen Salees. Yana kashe call d’in ya had’a wayar da gini, da ba don anti-breaker da ke kare wayar ba da ba abinda zai hana wayar tarwatsewa. Dafe kanshi yayi wasu hawaye suka fara kwarara daga idanunshi, yana cikin haka ne yaji call yashigo amma ko damuwa ya duba waye ne baiyi ba, da yaga ba barin kira za ayi ba sai kawai ya mi’ke ya d’auki wayar ya cire battery duk da yana kyautata zaton Leena ce amma takaici da kishi yasa ko muryarta bai son ji adaidai lokacin. Tunani ya dinga yi akan matakin da zai d’auka, bazai ta’ba yarda Salees yazo ya aure mishi Leena ba, macen da ya kamu da soyayyarta daga kallo d’aya, sa’ka da warwara ya kwana yi har aka fara kiran Asubah. A masallaci Abba yake gayama Baba matsalar da ke ‘ko’karin kawo kai acikin gidansu, Baba ya firgita sosai da kuma tsoron abinda yaran nasu suke aikatawa a cikin RASHIN SANI. Da Suhal yadawo gida wajen 6 lokacin ya d’an ji sau’ki a ranshi, wayarshi ya d’auka daga kan kujera ya mayar da battery gamida kunnawa. Missed calls na Leena da ya gani sam baiji mamaki ba, danna mata kira yayi inda itakuma alokacin suna fama da Sofy da ta tashi da wani mugun zazza’bi, ya gaji da kira bata d’aga ba sai kawai ya shige d’akinshi don bacci ya fara damunshi. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Jikin Sofy yayi zafi tamkar wuta, Momy ba ‘karamin tsoro taji ba, sai kuka takeyi abun tausayi. D’agata sukayi suka kaita motar sannan suka wuce asibiti, atake aka shigar da ita wajen likita inda ya du’kufa da dubata don gano matsalar. Bayan ‘yan dube-dubenshi sai ya kalleta yace “Meh yake damunki bayan zazza’bin?” Cikin zafin ciwo tace “K’asana doctor, zafi nakeji sosai” Likita yayi shiru yana tunani sannan yace “Meh ya sameki a wajen?, ciwo kikaji ko meh?” Hawaye ta share sannan tace “I had sex for the first time shine inaga naji ciwo” Kallonta yayi sannan yace ta gyara bari ya dubata, bayan ya dubata sai ya zaro wani allura yamata gamida yin rubutu. Girgiza kai yayi ya kalleta sannan yace “Ina mijinkin?” Cikin in-ina tace “Ban…da…mi…ji” A d’an razane ya dubeta, zamanshi ya gyara yace “Okay, toh koma wayene dai wanda kukayi abunku, call him kice inason magana dashi” Du’kawa ‘kasa tayi tace “Doctor don girman Allah ka rufamin asiri, karka gayama mamana wannan maganan, it should be between the two of us, yazama private matter ne tsakanina da kai please, nasan bala’i zatayi ba kad’an ba in har tasani” Batare da ya kalleta ba yace “Shikenan, amma ki kira min shi if zai yiwu” Marairaicewa tayi tace “Dole zai yazo ne?, in ma tambayoyi ne zaka iya tambayana kawai ba sai yazo ba” “Ya akayi yaji miki ciwo haka?, shi dabba ne ko kuma ya haukace ne?” Had’iye ba’ka’ken maganganun wannan dr mara dariya tayi tace “Ba acikin hayyacinshi yake ba saisa” “You can go, kije ki kar’bi magungunan nan a pharmacy” ya fad’a yana mi’ka mata wani farar takarda mai d’auke da tambarin asibitin. Amsa tayi tamishi godiya sannan ta juya tana tafiya ahankali har tabar office d’in. Dr binta yayi da idon tausayi “Wannan wani irin rayuwa ne ‘yanmata suke sa kansu aciki?, mesa sukeson zubar da mutuncin su tun awaje?, ko basu san budurcin mace shi zai siya mata mutunci da kuma ‘kara mata matsayi awajen mijinta ba?, toh ma iskancin ai bai mata rana ba don gashi yanda ita ta ‘kare, yayi disvirgining nata in a rough way kaman dabba sannan haka ya watsar da ita yabarta ba wani kulawa balle ya damu da halin da take ciki” duk wannan tunani Doc ne keyi, a ‘kasar zuciyarshi kuwa tausayin mahaifiyar yarinyar(Sofy) yakeyi don gashi ‘yarta ta lalace batare da saninta ba. Knocking da akayi a ‘kofa ne yasa ya kawar da tunanin yace “Come in” Momy ne tashigo daganinta ansan tana cikin damuwa, ko zama batayi ba ta jefa mishi tambaya “Likita meh ke damun ‘ya ta?” Gyara tie da ke wuyarshi yayi sannan yace “Nothing to worry about, zazza’bi ne ya kamata sosai amma bakomai, na rubuta mata magunguna sannan namata allura, In Sha Allahu ba da jimawa ba zataji sau’ki” Ajiyar zuciya Momy ta sauke had’e da hamdala, murmushi tamishi had’e da godiya sannan ta juya tabar office d’in. A cikin motar ta riskesu(daman har zasu tafi sai kuma taji bazata iya tafiya batare da ta nemi ‘karin bayani akan abinda ke damun ‘yarta ba, tanason taji bayani daga bakin likita don hankalinta zaifi kwanciya, ba da son Sofy ba Momy ta bar su a motar takoma wajen likita). Ajiyar zuciya Sofy ta sauke tana godema Allah da likita ya rufa mata asiri don tasan in da ya gayama Momy asalin abinda yafaru da rai ‘bace zata dawo. Leena ne tayi driving ta mai dasu gida, bayan sunyi breakfast ne sai Momy ta kira daddy take gayamishi gashi fah Sofy ba lafiya, Allah ya ‘kara sau’ki yamusu sannan yace shima cikin satin zai zo. Murna sosai Momy tashiga yi don zataga mijinta bayan watanni kusan takwas da tafiyarshi, awajen yaran kuwa ba za ace suna farinciki ba sannan baza ace suna masu ba’kin ciki ba. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Turkey** Yanzu Fu’ad wani irin rayuwa ya fad’a wanda ko amafarki in an ce zaiyi haka to tabbas saimunyi denying sabida yanda ya nuna ya ‘kyamaci abun… ‘kyama mai tsanani, cikin dabaru irin na tantiran ‘yan duniya suka samu Fu’ad yashiga cikinsu. Yayi watsi da abinda ya kaishi ‘kasar wato karatu, holewar shi yakeyi son ranshi. Ba wai kuma ya bar harka da mata ba, harka da matanshi ma sai dai ‘kara yawaita da yayi, yayi da mazan yayi da matan(Wa’iyazubillah). Wad’anda suka san shi tun lokacin da Suhal yakenan kuwa sai dai su bishi da ido suna masu tausaya mishi a ransu akan irin rayuwar da ya za’ba. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Leena sai wajen 9am ta waiwayi wayarta, ganin missed calls yasa ta zauna tafara calling back, numban Suhal ne last one da ta kira, alokacin shikuma yana shan baccin da bai dad’e da d’aukar shi ba. Ringing na wayarshi ne ya tayar dashi, idonshi arufe yayi answering sannan ya kara akunne yace “Hello” sleepily Duk da taji muryarshi bacci-bacci bai sa ta fasa abinda tayi niyyan fad’a ba “Hey, sannu fah, sannu da rejecting min call, godiya nake” Jin muryar Leena yasa baccin da ke idonshi watsewa, cikin hanzari ya tashi ya zauna akan gadon yana duban agogo. “Will call you back, ina zuwa” ya fad’a mata sannan ya katse call d’in Dogon tsaki Leena taja don yanzu kam Suhal yana neman kaita bango da murd’ad’d’en halinshi, bata sake bi ta kan wayar ba ta shige toilet tayi wanka sannan ta sa d’an kayan shan iska ta kwanta akan gado tana chatting. Suhal kuwa yana kashe call d’in ya dafe kanshi da ke sara mishi wanda yana ganin kaman don rashin bacci ne ya jawo mishi, wankan shima yashiga yayi, wani plain long sleeve shirt yasa da wando, d’aukar wayarshi yayi yafara neman Leena yana fita zuwa parlour. Zama yayi, ya kirata bata d’auka ba sai a na ukun, shirun da yaji yasa yace “Hello, good morning” Had’e fuska tayi kaman yana kallonta tace “Ka ri’ke good morning naka, I dont want it” “Hey…Im sorry okay?, d’azun kin kirani ina bacci ne saisa” “Ni ba ma wannan kawai ba, sabida meh kayi rejecting na call nawa jiya da dare?” Kishi ne ya sake taso mishi sabo fil, iska ya furzar yace “Rai na ne ya ‘baci” “Toh ni na ‘bata maka rai ne da zaka sauke zafin ranka akaina?” “Akanki ne raina ya ‘baci Leena, that conference call” “What about it?” Ta tambayeshi “Wancan mutumin na mall chan ne ko?” “Ehen…sai akayi yaya?” Ta tambayeshi a tsiwace “Ni ba arguing nakeso muyi ba kingane?” “Just go straight to the point, kanamin magana a murd’e” Iska ya hura a bakinshi yana iyaka ‘ko’karinshi na ganin yayi keeping calm nashi sannan yace “Meh yakeso da ke?” “Ba kaji komai ba?, ba na had’a call d’in ba?” “Answer me Leena, banson masifa” Murmushi tayi tace “Surutun shirme ya dinga yi, he’s so funny I tell you, wai fah aurena yakeso yazo ya nema” “Leeeeena” ya kira sunanta yana jan sunan “Na’am” ta amsa mishi “Kinsan meh nakeso da ke?” “Nop, what?” “Gaskiya ni hankali nah bai kama guy nan ba, he talks alot, irin guys haka wallahi had’ari ne, and daga jin yanda yake magana in a flirty way mutum zai gane he’s used to talking to girls, ba ma magana kawai ba, ya saba neman mata, and I’m quite sure kanshi yana d’an banzan rawa, ya…..” Katseshi tayi tace “Suhal ya zaka yi ma mutum mugun zato haka?” “No Leena, understand what I’m trying to say, kingane ba?, just in ya sake kira karkiyi picking call d’in, he’s not a good match for you” Shiru tayi tana tunani kala-kala, da ba don tasan Suhal as a friend ya d’auketa ba da sai tace yanasonta ne don wannan maganar da yayi kaman da kishi aciki. “Toh Suhal bazanyi aure bane?, kuma ma ni yanda guy d’in yake da surutu da wasa sai naji ya kwanta min arai” ta fad’i haka ne don tanason gaskata ma kanta zaton da takeyi Murya asanyaye yace “Leena please don’t, karkice zaki aureshi, u barely know him, baki san mugu ne ko wani abu ba, I assure you wanda yafi dacewa da ke yana hanyar zuwa, just do as I say, block him” Shiru bata amsa shi ba, lan’kwasa murya ya sake yace “Kinji?” “Naji, zanyi tunani akai” Wani murmushin jin dad’i ya sake sannan yace “Yauwa ko ke fah, so yakike?” “Lafiya lau, ya weekend d’in?” “Alhamdulillah, ban ma samu enough bacci ba wallahi” Cikin tausayawa tace “Ayyah, kaje kayi breakfast sai ka kwanta kawai, zaka ji normal” “Thank you my dear, will do just that, take care” “Alright, bye” Kusan lokaci d’aya suka katse call d’in kowannensu da tunani a ranshi. Kaman yanda tace haka yayi, cikin gida yashiga, a parlourn Ummi ya tarar da Ilham tana kallon wani movie, gaishe dashi tayi ya amsa mata cikin sakin fuska sannan ta kawo mishi abin karyawa, yana ci suna hira har ya gama ya sallameta akan bari yaje ya d’an kwanta. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Bayan kwana tara Ayau Daddy zai dawo gida, tun asubah y’anmatan da Momy suka fara shirya abinci kala-kala don tarbanshi, Leena tanada lectures amma haka tayi cancelling don tanason taga daddy’nta, tana mai addu’a Allah yasa ya damu dasu kaman yanda kowanne uba yake damuwa da lamuran ‘ya’yanshi. Misalin ‘karfe sha d’aya suka tarkata sai airport, ba tare da wani ‘bata lokaci ba aka gama mishi komai da komai dayake business class yashiga, inda ya hango suke tsaye ya nufa janye da wani d’an madaidaicin trolley ba’ki mai kyau, duk sunaso suje su rungumeshi kaman yanda sukaga sauran ‘yanmatan wajen ke yi ma iyayensu awajen amma shakka, tsoro da kuma rashin sabo dashi yasa suka daskare ba tare da motsi ba har ya iso wajensu. Momy ne tayi saurin ‘karasawa murmushi shimfid’e a fuskarta ta rungumeshi tana mishi barka da dawowa, mai da dubanshi wajen yaran nashi yayi bayan Momy ta kar’bi trolley’n shi. Jiki na ‘bari, murya na rawa suka had’a baki suka d’an sunkuyar da kai sukace “Daddy sannu da dawowa” Karo na farko da yaji rashin sakewarsu dashi ya ‘bata mishi rai, tun daman haka kullum suke tarbanshi, a d’ari-d’ari kaman sunga wani stranger, ranshi ya sosu sosai yanda ya lura duk ‘yanmatan wajen suna rungume iyayensu da suka dawo, murmushin dole ya ‘kir’kiro sannan ya isa gabansu, bud’e hannunshi yayi alamun suzo ya rungumesu. Kallon-kallo suka fara tsakanin su ukun, wani murmushi mai ciwo yayi sannan ya janyo su jikinshi ya d’an bubbuga bayansu yana cewa “Na sameku lafiya?” Sun kasa yarda wai yau daddy ne harda rungumesu, bazasu iya tuna when last yamusu haka ba. “Lafiya lau” suka amsa mishi uncomfortably “Alhamdulillah” yace sannan ya kalli Momy yace “Muje ko?, nagaji sosai wallahi” Motar suka shiga, Momy ke driving daddy kuma a passenger seat, su uku kuma a baya. Zaman kurame sukayi har suka isa gida. *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish [11/12, 9:07 PM] ‪+234 812 202 4749‬: *ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na 'yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *81-85* Haneefahusman.wordpress.com Stylishbch.wordpress.com Munayshat.mywapblog.com Masoya littafin nan bamusan da wani baki zamu baku ha'kuri bisa jinkirin typing da aka samu ba, please bear with us. Allah ya bar 'kauna, lots of love♡♡ ☆☆☆☆☆☆☆☆ Daga Suhal har Ilham mi'kewa tsaye sukayi cikeda fargaba da kuma tsantsan mamakin jin wannan magana da suka fito daga bakin Ummi. Ilham ta taka dagudu ta isa wajen da Ummi take ta fad'a jikinta tana jijjigata tana girgiza kai tafara cewa "Noo Ummi, ya zakice aure ya haramta a tsakaninmu?, don meh kukeson haramta abinda Allah ya halarta?, saboda meh bakuson Ya Suhal ya aureni bayan duk munsan aure bai haramta a tsakaninmu ba tunda dai shi ba muharramina bane, why Ummi?, mesa kuka za'bi ku fad'a fushin ubangiji?" Duk maganar da Ilham ke yi Ummi batace komai ba, parlourn yayi shiru sai sheshshekar kukan Umma, Ummi da Ilham ke tashi, mazan kuma duk idanunsu yayi jawur mai nuni da tsantsan tashin hankalin da suke ciki. Bayan kaman minti biyar Baba yayi gyaran murya ya dubi Ilham sannan ya kira sunanta yace "Ilham" sannan ya kalli Suhal yace "Suhal" A raunane ta d'ago tana kallonshi sannan ta amsa "Na'am" Suhal samun kujera yayi ya zauna da 'kyar, yanaji kaman 'kafafun shi bazasu iya d'aukar shi ba, ahankali shima yace "Na'am" "Inaso ku saurari abinda zan gayamuku ayau wanda duk duniyar nan ba wanda yasan da hakan sai mu hud'u(Abba, Umma, Ummi da shi Baba), tun da mukayi maganar kuwa muka binneta acikin zu'katanmu, muka bar ABUN SIRRI a cikin zu'katanmu, ko da wasa bamu ta'ba tunanin tonashi ba, ba don komai ba sai don ni halak malak na badake ma bappanki" ya fad'a yana nuni da Ilham sannan ya cigaba "Tun daga lokacin da aka haifi yayyunki Allah bai sake sa sunyi ciki ba har suka d'an yi wayo don time d'in Suhal yanada shekaru tara, Fu'ad kuma yanada bakwai, Allah cikin ikonsa ya sa suka d'auki ciki kusan lokaci d'aya, munyi farinciki sosai ganin zamu samu 'karuwar haihuwa acikin familynmu. Daf da zasu haihu sai Suhal da Fu'ad suka matsa mana akan zasuje gidan 'yan uwa achan bichi, mun so mu hanaso don bamuso iyayenku su haihu basanan amma da suka ishemu da rikici sai kawai mukasa aka kaisu chan don suyi kwana biyu akan kashedin ko washegari ne d'ayan su ta haihu toh za aje a d'aukosu. Maimuna(Umma) ita tafara haihuwa amma sai 'yar batazo da rai ba, tayi kuka na fitan hankali don ta sa ranta sosai akan babyn, har wani zazza'bi tayi wanda hakan yasa bamu gayama kowa ga abinda ke faruwa ba har washegari inda Hasiya ta haife ki, wani abun mamaki kuwa tun da aka haifeki kina kama da Maimuna sosai. Maimuna tana d'ora idonta akanki sai ta tuno da nata babyn da batazo da rai ba, ta 'kara shiga 'kunci, ganin haka yasa Hasiya ta kirani tace min in zan yadda tanaso mu bada ke ma Murtala da Maimuna, halak malak, na yaba mata da wannan kaifin tunani nata don ko ni dafarko nayi tunanin hakan amma bansan ta yaya zan fara tunkararta da shi ba sabida tsawon shekarun da ta d'auka bata haihu ba. Samun Murtala da Maimuna mukayi muka sanar dasu hukuncin da muka yanke, kukan farinciki Maimuna tayi sosai ta dinga mana godiya da sa albarka, ba mu bar asibitin ba sai da muka bari a tsakaninmu cewa ko dangi kar mu sanar musu cewa 'yar Maimuna ce ta rasu ma'ana mu ce musu 'yar Hasiya ce ta rasu sannan ko ku bazamu gayamuku ba sai dai in fad'an yazama dole. Da muka koma gida dangi suka fara zuwa barka har aka d'auko Fu'ad da Suhal da kullum suna cikin d'akin maijego suna jin dad'i sun samu 'kanwa, Hasiya kuwa sai dai azo ayimata jaje da ta'aziyar Allah yasa babyn mai ceto ne" Baba ya 'karasa maganar yana jin wani abu a zuciyarshi, kaman alokacin abun yafaru. Tashi tsaye Ilham tayi tana share hawayenta tace "Ya za ayi ace muna uwa d'aya uba d'aya da Ya Suhal?, wallahi 'karya ne" Suhal da tunda aka soma maganar yayi shiru sai lokacin ya d'ago jajayen idanunshi ya kalli Ilham sannan yace "Ilham wani irin maganar banza kikeyi haka?, abinda muka yi abaya cikin rashin sani mukayi, bai kamata muyi kunnen uwar shegu akan gaskiyar magana ba Ilham, gaskiya d'ayace" Kan kujeran da yake zaune ta isa tazauna gamida dafa shi, kaman zautacciya tace "Ya Suhal do you believe them?, akan meh zaka yarda da maganar da ko a tatsuniya da 'kyar ake samun irinshi?, wannan 'kir'kirarren labari ne don kawai anaso a hanamu aure ya Suhal, don Allah kace musu baka yarda ba, su barmu muyi aure please...." Wani irin tausayinta yaji ganin yanda ta fita hayyacinta, rungumeta da yayi ne ya bata damar yin kukan da ya ma'kale mata, bai hanata yi ba har ta gaji ita da kanta sannan ta rage sautin kukan. Wani irin kallo tayima Baba sannan tace "Aure dai sai munyi aure da ya Suhal, saidai in kasheni zakuyi" tashi yayi dasauri ya nufeta cikin 'bacin rai da niyyan dukanta, har rige-rige Abba da Ummi da Umma sukeyi wajen tareshi, masifa yashiga yi akan su bar shi ya koya mata hankali, batada hankali ne da zatace zata auri yayanta wanda suke uwa d'aya?. Umma da Ummi suka kamata suka shige da ita d'aki don lallashinta. A parlour kuwa saida Baba ya gama bambamin bala'in shi sannan Suhal yace "Wallahi Baba an cucemu da ba a gayamana hakan tun farko ba sai yanzu da muka girma har nayima Ilham al'kawarin aurenta, soyayya fah mukayi da ita, soyayya ba tare da mun san ciki d'aya muke ba...." Baba zaiyi magana amma Abba ya girgiza mishi kai don shi yafi Baba sanyin hali, Baba yanada zafi sosai don abu kad'an ke 'bata mishi rai. Tausasa murya Abba yayi yace "Mun san mun muku laifi Suhal, aganinmu hakan da zamuyi shi zai 'kara dauwamar mana son junanmu, munyi ba dai-dai ba da muka 'boye muku gaskiyar lamarin, sam bamuyi tunanin zaku fara soyayya bane da tun farko munyi ma tufkar hanci, duk wannan abun da ya faru sam bamuga laifinku ba sai ma mu da mukayi sanadi har kuka aikata haram(Suna soyayya bayan ciki d'aya suka fito)" Idanun Suhal jawur yake kallon Abba, girgiza kai kawai yayi batare da ya 'kara cewa komai ba ya bar sashen, kanshi kaman zai rabe gida biyu tsaba yanda yake tunani da kuma tafarfasa. Yana shiga d'aki ya jawo wayarshi ya danna kiran Fu'ad don shi kad'ai zai iya tayashi jimamin wannan batu, ringing na farko Fu'ad ya d'aga yana cewa "Bro yau antuna dani kenan" Zama akan kujera Suhal yayi ya lumshe idanunshi gamida dafe kanshi, alokaci guda kuma ya furzar da wani iska mai zafi. Jin haka yasa Fu'ad yagane ba lafiya ba, daidaita nutsuwarshi yayi ya 'kara cewa "Meh ya sameka ne haka?, wani abu yafaru ne?, ko gida ne ba lafiya?" Sai sannan ya bud'e idanunshi da suka 'kara rinewa sannan yace "Fu'ad, yau nan ba 'karamin tashin hankali nake ciki ba wallahi, can you imagine wai......" muryarshi ne ya sar'ke ya kasa 'karasa maganar don yanda maganar yake mishi d'aci. Hankalin Fu'ad ya 'kara tashi, cikin in-ina yace "Meh....ya...fa...ru?" Hawaye ne suka zubo daga idanun Suhal, bai damu da ya sharesu ba yace "Uwa d'aya uba d'aya nake da Ilham" Fu'ad da ke kwance akan kujera bai san lokacin da ya mi'ke tsaye ba har yana neman fad'uwa tsaba yanda yaji maganar kaman saukar aradu a kunnenshi. "What are you trying to say Suhal?, lafiyanka 'kalau kuwa?, tukunna ma, waya gayama wannan maganar?" Murmushin ya'ke yayi yace "Wallahi Im serious Fu'ad, yanzu su Abba suka fad'a mana a parlour" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Fu'ad ya shiga nanatawa yana ta zagaye tsakanin bedroom da parlour. Sai da ya d'an had'iye maganar sannan yace "No, it cant be, ya za ace Ilham Ummi ce ta haifeta bayan da girmanmu aka haifeta, karka manta fah ana haifanta mukaje asibitin, ya akayi hakan ya faru?" "I still cant believe it Fu'ad, I just cant, bansan ya zanyi ba, ni kad'ai nasan how I'm feeling right now...." "Calm down kamin explaining yanda abubuwa suka faru" Shiru yayi na seconds sannan ya kwashe duk yanda sukayi a parlour ya gayama Fu'ad. Tashin hankali sosai Fu'ad ma yashiga har yanajin wani bell yana bugawa a 'kwa'kwalwarshi, buga kan yayi da tafin hannunshi sannan yace "You mean all this while 'boye mana sukayi?, mesa sukayi haka?, akan dalilinsu na banza har kuna soyayya ba tare da kunsan uwa d'aya kuke ba" "Soyayya da 'kanwata uwa d'aya uba d'aya" shine sentence da ke ta yawo akan Suhal. "Abunda yafaru ya riga yafaru, we can't change that" Cikin d'aga murya Fu'ad yace "Ilham!!, Ilham ne damuwa na Suhal, nasan wallahi maganar nan sai ya nemi tarwatsa mata rayuwa, irin son da take maka is extra-ordinary, ga....." Katse shi Suhal yayi ta hanyar cewa "Look Fu'ad, Ilham will get over it eventually" "Yaushe kayi developing wannan banzan I dont care attitude d'innan ne?, Ilham is our only sister, ONLY SISTER, in kai baka damu da ita ba ni ina jin ta har cikin raina as my baby sis...." "I care about her Fu'ad, I really do saidai yanzu da abubuwa suka kwa'be dole naja jiki da ita for our sakes, both of us, in ina 'kara kulata baza ta iya yakice ni daga zuciyarta ba" "Hmmm" Fu'ad yace sannan ya 'kara da "Suhal kenan, I know baka ta'ba sonta ba, baka ta'ba damuwa da ita ba so mu manta da maganar kawai" Ajiyar zuciya Suhal ya sauke sannan yace "Ba zaka gane yanda nakeji bane, had it been yanzu hakan nan da kai yafaru wallahi im 100% sure reaction naka will be worse" Guntun tsaki Fu'ad yaja yace "Kai dai share kawai, yanzu ya ake ciki?, how's she?" "She will be okay, ta dai tafi tanata kuka wai ita bata yarda uwa d'aya muke ba, gani takeyi kaman su Abba sunason hanamu aure shine suka 'bullo tahaka" "Zan kirata, will try to make her understand, ta cire sonka daga ranta don ba aure tsakaninku, kar ta kwasan ma kanta zunubi abanza" Haka dai suka dad'e suna tattauna abinda iyayen suka bayyana musu ayau. ☆☆☆☆☆☆☆☆ Few days later "Rafee!, Rafee!!" Momy ce ke ta 'kwala ma Rafee kira, sai da ta kirata ya kusa baki hud'u sannan ta tsinkayo muryarta tana amsawa "Na'am" "Zo mana, tun d'azun kinaji inata kiranki kinyi shiru" "Ganinan zuwa" Rafee tace da ita sannan ta fito hannunta ri'ke da wayarta da gani chatting takeyi. Zama tayi akusa da Momy tace "Momy akwai abinda zan miki ne?" "Eh, je ki wajen Tijjani maigadi ki tambaya min shi ko an kawo min wani sa'ko" Mi'kewa tayi tana cigaba da danne-dannenta har saura kad'an ta taka 'kafar Momy batare da ta sani ba. Tsawa Momy ta daka mata "Lafiyanki Rafee?, meh kikeyi a wayar da ya d'auke miki hankali haka har kina nema ki karya min 'kafa?" A rikice Rafee ta kawar da wayarta gefe tace "Im sorry Momy, bazan sake ba" Harara Momy tamata sannan tace "Bani wayar" "Momy?, ai nace bazan sake ba fah, kiyi ha'kuri" Rafee ta fad'a tana 'boye wayar a bayanta tana kuma ro'kon Allah ya rufa mata asiri don in Momy ta kar'bi wayar nan yanzu, kashinta ya bushe. "Bani nace!!, in kin dawo kya kar'ba" Momy ta fad'a in a serious tone Ba shiri Rafee ta mi'ka mata wayar ganin yanda Momy ta had'a rai. Juyawa Rafee tayi tafara tafiya amma tana waigowa tana duban Momy, itako ba abinda tamata sai hararar da ta galla mata a 'karshe, daga nan bata sake juyowa ba har ta fita daga parloun zuciyarta yana bugun goma-goma. Seconds kad'an da barin Rafee cikin parlourn wayar yayi beeping sau biyar alokaci d'aya, bin wayar Momy tayi da kallo sai ta sharé, wasu messages d'in ne suka kuma shigowa kusan lokaci d'aya, tsaki Momy taja tace afili "Sai uban chatting kaman wacce tasamu aikin lada, ko wasu asararrun ne suketa mata messages haka oho?" Cigaba da duba magazine da ke hannunta tayi amma duk 'karar da wayar yayi sai ta waiga ta dubeshi. Ana cikin haka ne wayar ya d'auki ruri, d'auka Momy tayi tana duba sunan, 'baro 'baro idanunta sukaci karo da "H babe", tunani tafara yi, itadai tasan Rafee ba kula samari takeyi ba, toh wayene wannan H babe d'in?, taso ta share don respecting privacy na Rafee amma part of her got curious, tanaso tasan wayene. Wayar yana gama ringing ta shiga gallery, yana rufe da lock hakan yasa ta gwada typing "hbabe", cikin sa'a kuwa ya bud'u. Camera pictures da yake shi ke sama so shi tafara bud'ewa, hotunan Rafee ne dai gasunan birjik, wasu daga ita sai bra, wasu kuma ta d'aura towel soko-soko, wasu kuma ba kaya ma...ta dai kare 'kirjinta da tafin hannunta, hotunan dai gasunan dewa ba kyan gani. A firgice Momy ta mi'ke sabida abinda ta gani mai matu'kar rikitarwa, wanda yayi mugun razana da firgitata, wanda yayi sanadin d'aukewar numfashinta na kusan da'ki'kai biyar, wani irin tashin hankali tashiga wanda bata ta'ba shiga irinshi ba tunda tazo duniya, ko amafarki bata ta'ba tsammanin zataga abu mai muni makamancin haka ba. Hawaye ne ya fara ambaliya daga idanunta kaman an bud'e famfo, jikinta har 'kyarma yakeyi tsaba tashin hankali, wani irin kuka ne ya ku'buce mata mai cikeda 'bacin rai da takaici, kuka mai d'auke da ma'ana daban-daban. Rafee daskarewa tayi a 'kofar falon don daman isowarta kenan taga Momy tashiga wannan halin, jikinta ya mugun yin sanyi don ta gama sada'karwa Momy taga abinda take 'boyemata tun watanni dewa abaya. Kaman ba jini a jikinta tafara 'karasowa cikin parlourn, kanta a sunkuye jiki yana rawa ta ajiye ma Momy leather bag da ta kar'bo mata daga wajen maigadi, murya yana rawa cikin rashin gaskiya tace "Mo...my...gashinan" Ko kallon Rafee Momy ta kasa yi har tazo ta ra'be ta gefenta zata wuce, tsaida ita Momy tayi ta hanyar cewa "Ban gama dake ba, zo ki zauna!!" Firgita sosai Rafee tayi, tunani kaloli kaloli sai zuwa mata 'kwanya sukeyi, ta kasa d'aga 'kafarta balle ma tajuyo ta kalli momy har saida Momy ta 'kara maganar cikin d'aga murya. Tsugunnawa a 'kasa Rafee tayi don yau tasan nata ya 'kare, Momy ta rungumi hannayenta a 'kirjinta tanata safah da marwa a tsakiyar parlourn. Cikin kakkausar murya Momy tafara magana "Rafee, meye gaminki da Hajiya Hafsat?" B'ari jikinta yafara tana zuzzura idanu kaman 'barauniya, in-ina tafara "Umm...um...ba...." "Dont you dare!!!, karki kuskura kimin 'karya, wallahi tallahi in kikayi 'karya sai na karyaki a gidannan!!" "Kallon Momy tayi sannan ta sunkuyar da kanta dasauri, zufa tafara sharewa tace "Da...gas...k...." Wani wawan mari da Momy ta kwasheta dashi ne yasa ta kasa 'karasar da maganar da ta fara, tuni bakin ya fashe yafara zubda jini, hawaye Rafee tafara tana yarfe hannu ta kasa 'kara magana. Jefa mata wayar kan cinyarta Momy tayi tana cewa "Still kinaso kiyi denying ko yaya?!!!, zakice min baki san dasu bane ko sharri aka miki bayan acikin wayanki suke?" Ko d'aga wayar Rafee bata iya yi ba, hawaye ne kawai take zubarwa akan carpet da ke shimfid'e a tsakiyar parlourn. Wani tsawa Momy ta kuma dakawa har saida duk gidan ya amsa wanda hakan yayi sanadiyyar fitowar Sofy, Leena da Daddy daga cikin d'akunansu. Yanayin da suka riskesu aciki duk ya razana su, cikin sauri Daddy ya isa wajen Momy ya kama hannunta yana cewa "Rahma!!, lafiyarki?, meke faruwa haka?, meh ta miki?" 'Ko'karin fizge jikinta daga ri'kon da yamata tafara amma takasa, hakan yasa ta kuma fashewa da wani sabon kuka tana bugun 'kirjinshi tana nuna Rafee had'e da cewa "Ka tambayeta, ka tambayeta menene acikin wayarta?, ka tambayeta meke tsakaninta da Haj Hafsat" *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish [11/12, 9:09 PM] ‪+234 812 202 4749‬: *ABUN SIRRI NE www.gidannovels.blogspot.com* Na 'yan uku *MUNAYSHAT* *HANEEFAH USMAN* *STYLISH BCH* *NWA* *86-90* Haneefahusman.wordpress.com ☆☆☆☆☆☆☆☆ "Hajiya Hafsat?, wacece hajiya Hafsat kuma?" Daddy ya tambayi Momy cikeda son jin 'karin bayani don dai sun sa shi a duhu "Wata k'awata ce" Momy ta fad'a still bata dawo hayyacinta gaba d'aya ba "K'awarki?, meh kika gani da yasa kike tuhumar Rafee akanta?" Sai sannan Momy ta fara dawowa taitayinta, kwapsawa tasan ta kwapsa don sam Daddy bai ma san da wata Hafsat ba. "Ba wai 'kawata har chan-chan bane sannan ni ban gama yarda da ita ba" Jinjina kai daddy yayi yace "Bakisan halinta ba daman kuke 'kawance?, a ina ma kika santa in the first place?" "A mall muka had'u har tace tana sona da 'kawance" Momy ta fad'a ba da son ranta ba "Tanada wani halin Allah wadai ne?, and menene kika sani akanta?" Runtse idanu Momy tayi tana kukan zuci, ita kad'ai tasan yanda takeji a zuciyarta; fargaban irin hukuncin da Daddy zai yanke mata in ta gayamishi asalin labarin 'kawancenta da Haj Hafsat da kuma tsoron Allaah da irin azaban da ya tanadar ma masu irin halin da ta tsinci kanta aciki, sanadiyyar haka kuwa gashi 'yarta ma ta lalace...a dalilinta. Wani irin haushin kanta tashiga ji sosai, da kaman zata kare kanta ta'ki gayamishi ala'karta da Hafsat saidai kuma taji gwanda kawai ayita ta 'kare, she can't live a lie anymore. "Ya kikayi shiru?, ina jinki" maganar daddy ne ya katse mata tunaninta Bud'e idanunta tayi hawaye suna 'kara zubowa tace "Tana harka da manyan mutane sannan tana lesbianism" Salati ne yafara tashi a parlourn daga bakin Daddy, Sofy da kuma Leena da yake sunji abun wani bambara'kwai. Rafee kuwa kuka ta fashe dashi tayi rarrafe ta kama 'kafar Momy tace "Momy don girman Allah ki yafemin, bazan sake ba nayi al'kawari" A razane duk suke kallon Rafee harda Momy, d'agota Momy tayi tana girgiza kai tace "Whattt???!!, na yafemiki Rafee?, meh hakan ke nufi?, kina harka da Haj Hafsat?, yaushe kika fad'a harkar nan Rafee?" Jinjina kai Rafee tashiga yi tana cewa "I'm sorry Momy, wallahi itace ta jani, wallahi bani naje wajenta ba....." Kuka sosai Leena ke yi, ta ma kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiyo mata "Lesbianism". Jijjigata Momy tafara tana magana "Why Rafee?, meh kika rasa?, tun yaushe kika fara harka da ita?, me.....". Momy bata samu damar 'karasa maganarta ba Rafee ta fasa ihu sakamakon sau'kar wire a jikinta, Daddy ne ya ciro extension wire yana huci yana dukanta, kana ganin yanayinshi kasan zuciyarshi a cunkushe yake. Ihu Rafee takeyi tsakaninta da Allah amma daddy sai cigaba da dukanta yakeyi kaman an aikoshi, gashi duk sun kasa kar'bota, ko tunkararshi ma sun kasa don tabbas duk wacce ta nufi wajen itama bulalar sai ya shafeta. Momy ba irin kuka da ro'kon da bata mishi ba amma bawan Allahn nan bai ma san tanayi ba, lura da tayi in fah bata dakatar dashi daga dukan da yakeyin nan ba tsaf Rafee zata iya mutuwa don har jini ya 'bata mata jiki sakamakon faffasa mata jiki da extension wire d'in yayi. Shahada Momy tayi ta isa inda Rafee take ta 'kan'kameta suna kuka dukkansu biyu. Cikin masifa daddy yace "Rahma!!, ki sake yarinyar nan ki 'bacemin daga nan, ni zata zubarwa mutunci agari?, ni takeso a dinga yima kallon banza ace 'yata tana mad'igo?, ni takeson ta tozarta?, so take ace ban bata tarbiyyar da ya dace bane ko yaya?, ki saketa nace!, yau sai tayi nadamar shiga lesbianism" Momy cikin 'karfin hali da tsananin 'bacin rai tace "Sai dai ka had'amu ka kashe don wallahi bazan bari ka kashemin 'yata ba, 'yar da kake i'kirarin ka bata tarbiyya mai kyau yaushe ma kakeda lokacinta?, yaushe ka zauna da ita for a month?, yaushe ka saba da ita har ka iya kwa'barta?, kama san WACECE ITA(book by Jaboncy) kuwa?, yarinyar nan laifin ta kaso arba'in take dashi kaikuma kaso sittin don kai ka nuna halin ko in kula akan abinda take ciki tun tasowarta, ba ma ita kad'ai ba, dukkansu uku baka damu dasu ba, Mustafa ayau zan gayamaka ka riga ka lalata familyn nan, ka ruguza shi, ka sa mun fad'a cikin wasu halaye wanda da ace kana tare damu hakan bazai faru ba. Ka had'a da ni ka duka don a sanadiyyar rashin kulawarka gareni nima na fara lesbianism...." Tsananin firgita Daddy yayi har extension wire d'in ya su'buce daga hannunshi ya fad'i a 'kasa. Leena sulalewa 'kasa tayi ta dur'kusa a kan guiwowinta tana cewa "No momy, mesa zaki ma kanki sharrin nan sabida ki kare Rafee?, haba momy, in zaki kareta bai kamata ke ma ki d'aura ka kanki laifin da baki aikata ba" Kallon Leena Momy tayi cikeda so da kuma tausayawa, hawayenta ta d'an share sannan tace "Ba sharri nayima kaina ba Leena, gaskiyar maganar kenan, nashiga lesbianism a dalilin babanku, nasan ni mai laifi ce ako ina amma shima yanada nashi kason don....." Daddy da tunda Momy ta fara magana ya nemi kujera ya zauna don yanajin kanshi yana juyawa yayi saurin katseta cikin tsawa "Menene bana muku?, akwai abinda kuke bu'kata da ban baku ba?, meh kuka rasa a duniyar nan da sai lesbianism ne zai iya baku?, anya kuna tsoron Allah kuwa?, kuna tsoron had'uwa dashi da irin zunubin ku?" Girgiza kai Momy tayi cikin takaici sannan tace "Maganar kenan kullum, kud'i...kud'i, kai a tunaninka kud'i ne komai?, ka fifita aikinka akan mu, familynka ne mu amma bakada lokacin mu" D'aga mata hannu yayi yace cikin d'aga murya "Karki gayamin maganar banza!, don waye nake neman kud'in?!!, ba don ku bane?!!, duk abinda nake nema is for you" Cikin d'aga murya Momy ma tace "Zan gayamaka Mustafa!, daman ance the truth is always bitter, your money is not enough!, kud'in banza kud'in wofi, ni banga amfanin kud'in ba wallahi sai ma takaici da 'kuncin da yasa kullum nake ciki, ba wai ina cewa na raina efforts naka na bamu a comfortable life bane...no, inaso na gayama ne kud'in bai da amfani tunda yayi mana katanga da kai, yayi mana katanga da farin cikinmu, in dai ni yanzu zan bama mace shawara akan za'ban mijin aure wallahi tallahi zance akam ta za'bi mai kud'i wanda baida lokacinta gwanda ta za'bi mai daidai rufin asiri don zai tarairayeta ya riritata, mai rufin asirin kullum zai dinga bata kulawa, zai san meh take ciki akowani rana, zai san meh take bu'kata, bazai ta'ba bari tashiga yanayin kad'aici ba sannan zaiyi iya bakin 'ko'karinshi ganin ya sauke duk ha'k'kokinta dake kanshi, masu kud'i kuwa akasarin su basuda lokacin familynsu, you dont have our time, you dont value us, sai ka share watanni baka waiwayemu ba, ina matarka amma sai muyi wata shida-bakwai bamu ga juna ba saidai muyi magana a waya, bazaka zo ba sai in kai da kanka kaji kana bu'katar zuwa, ka manta da ha'k'kina da yake kanka, nima fah inada bu'kata tunda dai ni ba dutse bace amma haka zaka manta ka ajiyeni agida kai kana chan uwa duniya. A dalilin rashinka kusa dani shaid'an da son zuciya suka rinjaye ni na fara rage ma kaina bu'katarka ta hanyar mad'igo " *REAL MHS* Munay, Hanee and Stylish adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *