Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 27 July 2017

AMEEN DA AMEENA

adsense here [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [12:00, 7/28/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜ *AMEENA DA AMEENU* ®NWA ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com 1-10 *AZAMANIN MAN,AKW'AI MASU KI'DAN DAMUKE D'AUKOWA LOKACIN BIKUNKUNANMU SUNA NE BIKI NE, DA DAI MAKAMANTANSU AKW'AI WAD'ANSU MASU KI'DA D RAWA A GURIN BIKI WAD'ANDA SUN KASANCE YARAN DJ N* *SOMETIMES ZAKIGA MASU D'J SUNZO DA Y'AN MATA GURIN BIKI SUNAMUSU RAWA* *TA BURGEWA DAN KAWAI SU BASU ABIN HANNUNSU, DAGANAN WASU* *ZAKIGA SUN LALACE TARBIYYARSU TA TAB'ARB'ARE,* *HARMA KIGA BAASAMU DAMAR YIN AURE BA.* *SABODA WANNAN SANA'A DA WASU Y'AN MATAN SUKA D'ORAWA KANSU, DUK KUWA INDA* *KIKAGA MUTUM NA RAWA GABAN MAZA DA MATA* *KINSAN BABU* *KUNYA A GURIN.* *ALLAH SA* *MUDACE AMEEN* Tafiya nake akan titi kamar yadda nasaba dan in samo muku labarai, aikuwa kw'atsam naci karo da wata nuts'atstsiyar yarinya cikin k'atoton hijab, daga gani makaranta zata ko kuma ta taso? oho nidai Foulani haka nayi ta mamaki, da jaka a rataye a kafad'arta, tafiya take cikin kw'anciyar hankali a natse. Madaidaiciya ce, daga kallon danayi mata daga baya, binta na cigaba dayi a baya har naga ta tsayar da me keke napep(adaidaita sahu) banji inda tace masa xataje ba amma naga ta sh'iga, nima da saurina na ts'ayar dawani nace yabimin bayan waccen matar, adai-dai gidan wani party naga ta sauka, tabiya d'an keke napep kud'insa ta fito,. mamaki na zaro ido ganin da hijab ne ajikinta yanzu kuma naganta tafito da mayafi, hmm dad'inta d'aya kayan jikinta ba matsatstsu bane, kuma mayafin bawani babba bane can, tayi rolling dash'i ta sh'ige. Kid'ane ke tash'i sosai,. Ta sh'iga ga matanan a zazzaune akan fararen kujeru, daga can kuma gamasu kid'a nan, yana tash'i wajen naga ta nufa, tayiwa wani magana yazoko har inda take, ahankali naji tana masa magana yace to ta sh'iga ta ajiye jakarta , aka ware kid'a tafito tafara dancing kamar baajikinta ba, aikuwa nan danan mutanen dake wajen suka dinga zuwa sunayi mata lik'i, kud'i kuwa se zubar mata ake saboda yadda ta iya rawar sosai, 6:00 ta kalli agogon hannunta, jakarta ta d'auko, wannan wanda naga tayiwa maganar sh'idi'nne ya biyota a baya, a d'an wani waje suka samu suka tsaya, kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'o mata yace"ga kudin ladar rawarki, "Ok nagode ta karba tana hucewa atake kuma wasu zafafan hawaye suka ziraro mata, a ranta tace"Allah kazama gatana ka fitardani daga rayuwar danake,. Tash'are hawayenta ta ts'aida wani me keke napep ya kaita har k'ofar wani madaidaicin gida, ta fito da hijab d'in d'azu ajikinta t bash'i kud'i ta sh'ige gida da saurinta. Da sallama ta sh'iga gidan, wata matace a zaune tana tsefewa wata yarinya kai, "Mama sannu da gida "yawwa y'ar kirki har kindawo "eh wlh Haleema ma tana gaish'eki gash'i tace ma abaki ta ciro kud'i ajakarta ta mik'a mata Mama ta karb'a tana irgawa, ta lissafa dubu biyar ne cif "duk ita tabaki wannan d'in Ameenah? "eh ita tabani ta fad'a tana sh'igewa d'aki. Yarinyar da akewa tsifarce ta juyo ta kalli Mama tace"Mama kinga sai ki biyamana kud'in makaranta nida Asleem "Insha Allahu Tasleem mugodewa Allah da yakaho mana kud'in nan dan dakinga gobe baki da zuwa makaranta. A d'aki kuwa Ameenah ce zaune tana ninke kayanta tasa asif ta fito dawata doguwar riga ta saka sannan tafita tayo alwala tayi sallah, bayan ta idar ta d'aga hannunta tana rok'on Allah ya kaho musu mafita a rayuwarsu, Allah ya fitar da'ita daga cikin halin data jefa kanta na zuwa gidan biki tayi rawa dan kawai abata kud'i tasamu na taimakawa Mamanta domin.......... ~HOPE DA DAD'I INAJIRAN RA'AYINKU~ Maman triplet ce๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEENU* ®NWA ©FOULANI CERDIYYA 10~40 Maraicin da suke ciki ya jaho musu haka, ga mats'anancin son Ameen datakeyi, wanda besan tanayi ba hasalima gani take kamar ya tsaneta, saboda k'azamar rayuwar data d'aukarwa kanta dan ta taimaki mahaifiyarta, Amma tana tunanin wannan zuwan datayi gidan party Insha Allah sh'ine zuwanta na 'karsh'e, badan komai ba sai dan ta samu soyayyar Ameen kamar yadda Haleema tash'a gaya mata takance da ita"Friendy kin d'auki rayuwa me wahala gash'i kin fad'a son Yah Ameen kina tunanin zai soki a haka ne? sh'awarata a gareki itace ki hak'ura da wannan yawace-yawacen gidan rawar. Hawaye ya k'ara zubowa a Fuskar Haleema wanda hakan yayi dai-dai da sh'igowar Tasleem k'aninta da gudu, yana zuwa ya fad'a jikinta yace"Aunty Sayyada sunan da suke kiranta dash'i a dalilin kasancewar sunan Mama ne akasa mata, sh'iyasa k'annen nata ke kiranta da Sayyada Wacece Ameenah(Sayyada))? Amina muhd Abdullahi sh'ine asalin sunanta y'ace wurin Alhaji Muhd yakasance d'a d'aya agurin iyayensa wato Alhaji Abdullahi d'an kasuwane na hak'ik'a inda yake ordern kaya daga waje yana turowa nigeria domin a sayar Alhamdulillah sana'ar ta karfesh'i dan nan danan yafara gini, ana haka ne Allah ya had'ash'i da Ameenah wato Mama Mama ta kasance itama y'ace d'aya a gurin iyayenta bayanta basu k'ara haihuwa ba Alhaji Muhd ya auri Mamanta har dai bayan auren nasu basu haihuba sai da suka d'an jima dayin Aure lokaci d'aya Allah ya basu haihuwar yarinya mace wato Ameenah Ameenah ta taso cikin kulawa daso da k'auna har makw'aftansu ma suna son Ameenah sakamakon yarinyar ky'akyky'awa ce data fara hankali kuma ta kasance nutsatstsiya ce bata da hayaniya bata da girman kai duk kuwa dacewar Alokacin Mahaifin nata me kud'i ne Bayan y'an sh'ekaru sunja har ansa Ameenah a makaranta ta boko da islamiyya, tunda suna primary take da wata k'awa me suna Haleemah'Haleema irin yaran nanne masu kok'ari a makaranta kamar dai Ameenah itama babu ruwanta hakan ce tasa suka saba da'ita kuma itace k'awarta har yanzu, Mama ta haifi yara biyu bayan Ameenah wato Asleem da Tasleem sune ma suka samata suna Sayyada wato Aunty Sayyada Mahaifinta ya rasu; bayan yayi jinya inda tacinye masa rabin dukiyar daya tara.Watarana da daddare bayan mutuwar Mahaifinsu Ameenah b'arayi suka sh'igo musu suka musu satar kaf abinda suke dash'i, kuma Alokacin ne Ameenah ta gama secondary school daganan rayuwa ta sauya musu,babban gidan dasuke cikima suka sayar dash'i dan asamu na cin abinci da biyawa yara makaranta, Ameenah tana zuwa islamiyyar dake bayan gidansu wacce itama Haleemah tana zuwa,. Bayan anyi hakane ta yanke sh'awar dayaya xata ringa taimakawa Mamanta? hardai wata rana taje bikin wata frnd d'inta taga wata tana rawa a gidan biki kuma ta fuskanci kud'i aka biyata sh'inefa taje tayiwa masu Dj mgana su kuma ganin ky'akyky'awa yasa sukayi saurin amince mata data dinga zuwa tana musu rawar sudinga biyanta, kullum ran asabar da lahadi zakiga Ameenah baa zuwa Islamiyya, Halema takan tambayeta" wai ke Friendy ina kike zuwa ran weekend ina monitoring d'inki saboda nash'a zuwa idan antash'i Mama tacemin kinje makaranta while ni bakizo ba, ki gayamin ina kike zuwa? kuka ne ya kufcewa Ameenah adalilin yaudarar Mamanta datakeyi, "Kiyi hak'uri Friendy wallahi ba inda nake zuwa, but.......sai kuma tayi sh'iru tarasa abin cewa"but what? tell me bekamata ki boyemin ba' nan dai Ameenah ta gaya mata abinda yake faruwa na zuwa gidan party tayi rawa a biyata. Salati Haleema tasa tace"talauci haukane Friendy? kinyi Kuskure, yanzu ni bazaki iya gayamin mats'alarki na? sh'in ni bazan iya taimakonki ba,? nandai Haleema tayi Fush'i da k'awartata hardai tayi mata alk'awarin baxata k'ara xuwa guri Party tayi rawa ba. anan nema Haleema take sanar mata bikin Yah Ameen saura sati d'aya,"yaush'e ya dawo ne Friendy, "ya dad'e da daho wa anyi anyi ya futo da mata yak'i to akw'ai wata y'ar k'awar Mumy shine aka had'asu duk da yace sh'i baya sonta ita kuma tana sonsa sosai, "Allah ya kaimu mush'a biki Ameenah ta fad'a tana faraa a fuskarta. Yau takama Friday taje wajen Dj khaleed tana tambayarsa koda wani party a week d'in nan? "Yes akw'ai wani zafaffen Party dazamuje wannan partyn nasan zamu samu kud'i, murmush'i tayi tace"ok yaush'ene "gobe ne "aina ne? ya fad'a mata sunan gurin "Allah ya kaimu ta fad'a tana juyawa tace "sai nazo a hanya tunani take ga bikin Yayan Haleema ya zatayi? data tuna jiya basu wani ci abinci ba yasa tace afili" sorry Friendy bayan ta koma gidane, Haleema tazo, lokacin Ameenah na d'aki tana gogewa su Asleem unifoam d'in school d'insu, Tasleem ce ta sh'igo tace"Aunty sayyada ga Aunty Haleema, da gudu ta fito tana fadin"oyoyo my Friendy, murmush'i mamatayi tace"saketa karki karyata, tayi dariya ta sh'ige d'aki itama ta bita, Haleema ta dubi Ameenah tace"ke gobe zaa fara bikin Yah Ameen, dummmm gaban Ameenah ya fad'i saboda bazata samu damar attending ba dalilin gobe zataje rawa kuma...... "ke ina miki magana, karb'i wannan, ash'obenki "woww yayi ky'au but Friendy ya....Haleema ta rufe mata baki tace"noh karkice komi kedai kizo, "ok alot of thanks Friendy harara ta galla mata tace"ke kika san thanks d'in ai suka tuntsire da dariya. Ameenah ce taketa sh'irin fita tayi kw'alliya harta gaji, tada yayin bikinta na less golden, dan daga wajan rawarta zata zarce gurin bikin su Haleema, duk da Haleeman tace ta ts'aya zata biyo ta d'aukets su tafi, itakuwa bata kaho komai ba ta yanke sh'awarar d'aukar wayar Mamanta ta tafi da ita in yaso in tafifo daga can saita kirata ta gaya mata wajen. "Cab Aminah ta fad'a ganin wajen partyn dabata ma tab'a zuwansa ba, gaskiya gurinfa yayi ky'au anyi decoration na k'ayatuwa tunda take zuwa party bata taba zuwa irin wannan ba, Mutane sai sh'igowa suke suma y'an gayu, sai dai tunda Ameenah ta sh'igo gurin gabanta keta fad'uwa ganin irin kayan dake jikinta, sh'ine na ragowar mutanen dake sh'igowa, *"Tash'in hankali*Ameenah ta fad'a a fili, bayan an zazzauna akan chairs dake wurin amarya da ango suka sh'igo aka bisu da tafi masu camera sai d'aukar photo suke, itadai jikinta yanata rawa gabanta nata fad'uwa, bayan anyi wasu jawabe -jawabe, aka ware Dj kid'a ya fara tash'i, babu yadda zatayi dolenta ta sh'iga tayi musu abinsu ,amma badan haka ba da bazata sh'igaba, tambayarta d'aya wai sh'in bikin nan nasu waye? itafa jikinta yana bata kodai bikinsu Haleema ne? "Nash'iga uku idan sh'ine hawa tayi kan stage tafara rawa normal, rawarta ta burge kowa da kowa, masu waya suka fara vedio, Ango Ameen sani muhd yaji gaba d'aya yarinyar ta burgesh'i, besan ta akai ya tsinci kansa da kallonta ba har ya tash'i yayi mata lik'i "woww handsome Ameenah ta fad'a a ranta dan yayi mata mugun ky'au inama mijintane, gaskiya ta burges'hi sai dai daya tuna rash'in kunya ce da fitsara yasata yin rawar sai yaji ta bash'i haushi zuwa yayi yasanarwa da masu magana cewar a daina d'aukar vedio, aiko aka sanar gab'a d'aya suka koma suna kallo amma sundena d'aukar vedion, "wannan familynmu ce? ko kuma yaya? tambayar dayakewa kansa kenan, kamar daga sama ta hango Haleema tana tahowa, Innalillshi wa'inna ilaihir rajiun, na sh'iga uku!!! can wata dabara ta fad'o mata ta sauko tana tafiya a hankali sh'ikuwa angon kallonta kawai yake taburgesh'i kuma ta bash'i haushi tana isa inda take ta rungumeta tace" nama rugaki zuwa, "Friendy kinyi bala'in ky'au "kema kinyi ky'au, Sh'ine kika taho, to aina kika san gurin? "uh....ai..hm kinga, tun kafin ta k'arasa fad'a Haleema tagane rawa tazoyi, tsaki tayi ta jaho hannunta suka hau kan stage d'in, ta rik'o hannunta ,suka fara rawa tare itada Haleeman, nanfa aja k'ara tagi raf rafrafraf, tasowa yayi ya musu lik'i yace ya kamata ku fita daga wajen rawar nan, yana fad'a ya kalli Ameenah data kulash'i ya harareta, a dai*dai lokacin k'arfe sh'idata nuna, aiko tayi dariya suka fita itada Haleema, Me dj ne ya taso yabiyota ya bata wasu uban kud'ad'e wanda bansan adadinsu ba, amma fa sunkai kudan dubu tal..bara dai inyi sh'iru kar ace na zuk'ata. Bayansu Ameena sun dawo daga dinner ne tazo kw'anciya bacci but baccin yak'i zuwa idonta , ta juya nan ta juya can tarasa mekeyi mata dad'i abu d'ayane ya ts'aya mata arai hararar da yayan Haleema yayi mata, murmush'i tasaki ita kad'ai, "dama zaka aureni *Ameenah da Ameen* what a mach!!! sai kuma ta tuna auren sa akeyi take taji fad'uwar gaba, tayaya ma za'ai ya aureta? yana da wannan matar? "ze aureki mana Ameenah kina fa da ky'au idan sh'i yakewa Ameenah fara ce amma ba k'al ba, doguwace dai-dai misali, k'irjinta cike yake fam, gata da hips , tana fa shape me 8 tana da fuska me ky'au wacce take d'auke da dara-daran idanuwa d'auke da zara-zaran bakin gash'in ido(eyelashes), gata dawani irin hanci me ky'au bawai dan yana da tsini ba, hancinta yayi ky'au a fuskarta, bakinta me ky'au d'an k'arami, gash'im giratta mara yawa y'ar siririya, gata maabociyar kw'alliya, idan tad'au makeup ke sekace khareena kapoor, idan tayi murmush'i dimples d'inta su lots'a, idan tana tafiya kese ki rantse tana sani take girgiza jikinta, amma ba haka bane, hasalima itabata so takeyi, woww takoina tayi. *Ameenah* Bayan sati d'aya, Ameenah na zaune ita kad'ai, tayi uban tagumi, ga lokacin islamiyya yayi, amma tana zaune tana sana'ar tata wato tunani, tarasa meyasa idan ta rufe idonta take ganin Ameen a ciki? bata san soba amma dase tace kosh'i ne? hawaye suka gangaro kan fuskarta, dai*dai nan Asleem ya sh'igo ,"Aunty me akayi miki? "bakomi Asleem i just need your prayer....... sallama tajiyo wacce kobaa gaya mataba tasan Friendy c, sh'igowa tayi da sallamarta, Ameenah ta goge fuskarta ta amsa, tun kafin Haleema ta zauna tace"mekuma akayi miki kike kuka? seko ta fad'a jikinta cikin kuka tace"i don't know Friendy tunani yamin yawa just pray for me pls, fad'amin abinda ke damunki? da ky'ar ta gaya mata komi, tana gama fad'a ta ky'al ky'ale da dariya tace" You feel in love, brother na , don't worry Friendy muyita addu'a dan kinsan sh'aamin Yah Ameen sai sh'i, but dole yasoki ai. Maman triplet๐Ÿ˜˜ *Wanene *Ameen*?? sh'i irin mutanen nanne miskilai ga zafin kai, da nuna isa gash'i bayada yawan magana, sh'i i irin chocolate colour d'in nanne fatarsh'i very smooth yana da ts'ayi da zati, Fuskarsh'i d'auke take da dara-daran idanuwa hancinsa dogo, gawani saje daya kewaye Fuskarsa"Wow Ameen kenan wanda y'an mata suketa kaho masa hari Amma basa burgesh'i saboda sh'i har yanzu bega macen datayi masa ba dan sh'i ya kasance yana son mace me ilimin addini bawai dole sena boko ba, sannan yana son Mace nutsatssiya mai hankali da kamun kai wacce tasan mutuncin kanta. Yayi aure da matarsa khadeeja wacce ta kasance zab'in mumynsh'ice, dan sh'i bama yasonta , ko gado ne yadda sun had'aba, Khadeeja irin y'ayan masu kudin nanne wadanda basusan sunemu abu su rasa ba. Sedai abinda take buri da Ameen ya kw'anta da'ita gash'i sh'ikuma yak'i dan yace jikinsa bame arha bane, yana nan yayiwa macen datasan kanta , wacce bakowani karene yake kallon surarta ba ita ba irin macen dayake burin samu bace, yanason nutsatstsiya wacce zata bawa y'ayansh'i tarbiyya me ky'au ba ky'alekyalen abinda wasu mazan suke dubawa ba, yanason mace me dauriya bame raki ba wacce bazata iya d'aukarsh'i a sh'infid'a ba, dan sh'i d'in ingarmane, totally khadeeja batayi masa ba, ita sedai ky'au a fuska amma k'irjin a sh'afe yake, har garama hips d'innata ba laifi. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 40~42 Abinda yafisa Ameena taji gaba d'aya rawar da takeyi tafita daga ranta sh'ine, Watarana taje gidan party, kamar yadda tasaba takansa kayanda ba matseta sukayi ba, tayi kw'alliya a fuskarta tunda dama itad'in sarkin kw'alliyace, bayan tasa hijab d'in makaranta tafito, Mama ta tarar a ts'akar gidan, tayi mata sallama tace mata ta tafi islamiyya, anan Mama tayi mata nasiha da cewa"Ameenah ki kula da kanki, kar kiyadda ki biyewa rud'in rayuwa kiyi abinda duk inda kikaje zaa samiki albarka ayabeki,kar kiyi abinda zaayi Allah wadai dake". "To Mama nayi miki alk'awarin kare mutunci na,insha Allah daganan tasa k'afa ta fice, tana zuwa titi ta tari me keke napep(Adai-daita sahu) ya kaita gidan party, ta fito cikin tafiya ta k'asaita wacce dama asalin Ameenah a haka take, jikinta yakan d'anyi rawa kamar tana girgiza sh'i while ba haka bane. Gurin partyn ya had'u ga maza da matanan, sunata dancing anata rawar sh'oki. Tak'arasa gurin y'an uwanta y'an D'j tamusu magana suka gaisa, alokacin me magana yayi umarni da kowa yakoma gurinsa ya zauna zasu fara nasu programm d'in, wato Mace da namiji su fito suyi rawa kamar yadda akasaba a wajen D'j. Aka fito aka fara rawa, nanfa Ameenah ta fara zuba rawa iri iri ta 'iya, mutane akafiffito akayi mata lik'i . Ana cikin rawarne tasamu y'ar uwarta wato y'ar rawa itama ta sh'igo cikin fili, "Woww rawar nan sun iyata kugunsu kamar ya cire gash'i komi a tare sukeyi, ke kyace zama sukayi aka koyamusu amma ina babu d'aya ballantana k'anwar biyu. Agogone ya nuna kansa 6:00 tafito, tana fitowa aka mik'o mata kud'inta ta karb'a, _SHOKI AH SHOKI_ wak'ar data daki kunnenta, amma ta fuske tasakud'inta ajaka, wanda adai-dai lokacin ne y'anmata da samarin gurin suka tash'i suna taya iblis iblish'sh'i a kw'aso a kuma rufe ido d'aya, *WA'IYAZUBILLAH* _SHOKI AH_ tana kaiwa nan tafad'i ak'asa *TUIM* kallo sai yadawo kanta, da gudu mutanen gun sukayo gurin a dai-dai nan tace ga garinku ne . Wata gigitacciyar k'ara taji a lokacin da akace bata numfash'i, "Ni Ameenatu baiwar Allah, ubangiji na tuba kayafeni" Ameenah ta fad'a tare da saurin ficewa daga hall d'in, tana ta jimamin yanzu mofy ta rasu? agurin rawa,? yanzu taje tace da Allah me? "Yasalam har Ameenah ta dawo gida da jimamin abun aranta, sukuku tazama, Mama ta tambayeta ko lafiya? tace da ita bakomi Abinci ma ta kasa ci, balle wani abu ruwa, itadai istigfari take yi da salloli tana rok'on Allah ya yafemata. *Y'AN UWA MUGANE WANI ABU, ITA RAWA BA'ACE HARAM BACE, AMMAADINGA SANIN A'INDA ZAAYI,* *SABODA YANZU* *DUK BIKUN KUNAN DAMUKEYI ZAKIGA* *MATA DA MAZA AN HAD'U ANCUD'E* *ANA RAWA A GURI D'AYA*. *IDAN DA'ACE A IYA* *GURINE PERSONAL WANDA BA MAZA IYA ZALLAN* *MATANE TO BABU WANI ABU,* *AMMA IDAN KAJI ANCE ZAAYI BIKI BABU D'J* *SAI KIJI ANA* *FAD'IN AI BIKIN WANCE LAMI BA* *DAD'I WAI SABODA* *BAAYI D'J BA HMMMMM* *ESPECIALLY IDAN AKASA* _SHOKI_ *WLH MATA DA MAZANE ZAKIGA SUN CURE GURI D'AYA ANA KW'ASO SHOKI* *ALLAH SA MUDACE* ~Maman Triplet~ Ga ha'intar Mama datekeyi, tunda bata san aina take samo kud'inba tana dai cemata Haleema ce ta bata, da farko Mama fad'a tayi mata akan me Haleema zata na bata kud'i ita gaskiya bataso at the end dai wataran Mamynsu Haleema tazo ta kahomata kayan provision tayi mata godiya, to tundaga lokacin ne Maman take yarda da hakan. Haleema takan rufawa Ameenah asiri saboda sau tari tash'a zuwa taga Ameenah bata nan koda kuwa Mama tace ai Ameenan tatafi sai kiji tace" May be sab'ani mukeyi Mama bari inje makarantar" koda wasa bata tab'a nuna mata bata zuwa makaranta ba. Kuma koda Maman tayi mata godiya akan wani abu da Ameenan ta kaho tace inji Mamynsu Haleema bata tab'a nuna mata ba itance ta bayar ba, dan wani lokacin idan taje ta dawo kud'in da'aka bata takan sayo kayan Abinci da kayan dazaa nema ta kaho mata azuwan Mamyn Haleema ce ta bayar. Koda tafad'a mata cewar Ameen takeso Haleema tayi murna da farin ciki sai dai ta k'ara gargad'inta da dole ne ta sauya halinta, ta dawo Ameenarta data sauya kanta da wannan banzar rayuwar. Ta zuwa gidan biki yin rawa, hirarsu ta k'arshe da Haleema ranar dataje gidan party ta dawo tayi sallah tana addu'ar Allah ya kaho musu d'auki cikin rayuwarsu, Sallama tayi ta sh'igo suka gaisa da Mama, ananne Maman take mata godiyar kud'in data bayar akaho mata. Murmush'i kawai tayi tace"ai Mama yiwa kaine," "kish'iga tana ciki" "to Mama Haleema ta fad'a tana sh'igewa cikin d'akin. tunani take ita kad'ai ta tuno hararar da Ameen yayi mata a farkon ganinta dash'i face to face, dan bata tab'a ganinsa a fili ba sai a hoto, afili ma yafi ky'au....... "sannunki juliet sarkin soyayya kinwani kish'ingid'e da alama tunanin romieo n kike ko?" Haleema ta fad'a cike da zolaya "Eh yason ranki y'ar sa eyes?" "Wai hmmm wai wayaga kuma fa ko kundace wallahi," But Friendy kinsan Yah Ameen d'an uwana ne, dole tilas ki gy'ara halinki ki dena zuwa gidan rawar nan dan Allah badanni ba" "kina tunanin wani zai aureki ne idan yasan cewar kina zuwa gidan biki yin rawa? sam-sam baze yuhuba, bawai akan Yah Ameen ba, kinsan kowanne uba burinsa samawa y'ayansa uwa tagari? why not bazaki zama haka ba?, ko kinaso nan gaba y'ayanki su taso ace Uwarsu kafin tayi rawa y'ar D'j ce? bafa haka kike ba Friendy You have to change your bad behaviours, pls You know har baiko akaiwa Benazir an kusa bikin but da saurayin yaji tana yimawa y'an D'j rawa ya fasa aurenta? pls nd pls Friendy ki sauya. Tana kaiwa nan tayi sh'iru "Insha Allah bazan k'ara koda rawa a gidan biki ba har indai ba iya y'an uwana mata ne zalla ba." "Yawwa k'awas har naji dad'i, nagode da k'arba'ar sh'awarata da kikayi" "nice da godiya ai"Ameenah ta fad'a da faraa a fuskarta. "ina romieo na??" "Hahhhhhh yana gurin matarsa daga aure wata d'aya hartafara kaho k'ara, sh'i yace mafa ya gaji da ita, dan halinta be masa ba. Itama kuma Mamy ta gaji da kaho k'arar da Aunty khadeejan ke kahowa,. danfa rash'in kunya wai ta iya cewa Mamy wai betab'a kw'anciyar aure da ita ba Mamy taji haush'i ranar nan wallahi. Haleema ta k'arasa maganar da bacin rai "Allah yasa mudace Ameen, Ameena ta fad'a tana mik'ewa ta kahowa K'awarta ta abin sh'a. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 43~45 Ranar asabar da misalin k'arfe hud'u ta sh'irya zataje gidansu Haleema kw'alliya tayi tak'in k'arawa tasaka riga da skirt na atamfa ta d'auko hijabinta har k'asa tasaka ta fito tayiwa Mama sallama tafita. Ak'ofar sh'iga falon gidan taci k'aro dash'i gabanta ne ya yanke ya fad'i ta dafe k'irjinta, "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun " ta fad'a tare da cigaba da tafiya cikin nuts'uwa, sanye yake cikin skyblue d'in sh'adda taji aiki, ga hular sa _zanna bukar_ ya kafa itama me rats'i rats'in skyblue, sanye yake da agogo a jikin hannunsa, ga gash'in nan ya kw'anta da alama ansh'afa masa man k'ara fito da ky'an gash'i na maza. Tana zuwa daf dash'i tad'an russuna tace cikin rawar murya"in.........ina..yini...? d'ago da idonsa yayi ya mata wani kallon sh'ek'ek'e ya amsa da "klau" hanjin cikintane ya kad'a rugugugu da wannan kallon dayayi mata sonsa ya k'ara dira a cikin birnin zuciyarta ta sh'ige ciki. Haka ta lallab'a ta sh'iga ciki kamar wacce kw'ai ya fash'ewa a ciki. bakowa a falon dan haka ta nufi d'akin Friendy, tana kw'ance tana sana'ar tata wato karanta _Hausa novel_ Hadeeza Deeza Dije take karantawa littafin ;U Fadeela FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com nd hauwa'u damary. D'ala mata duka tayi, firgigit Haleema tasaki wayar hannunta ta kw'alla k'ara saboda ta tsorata ainun. [8:32AM, 8/12/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Hatta nima Foulani da nike rubutoo muku labarin sai da wayar hannuna ta subuce saboda razana. "Gaskiya badan kebace da nace Allah ya......kafin ta k'arasa Ameena tasa hannu ta tosh'e mata baki "sorry Baby herly kinsh'iga shauki ko"Allah dai ya sh'iryamin ke Friendy, "Lah yanzu Yah Ameen yafita "Ai nagansh'i sarkin miskilanci kinga wani kallo dayamin? "hmmm ki dad'a hak'uri" "wai ina Mamyne?banjita ba "tana sama tash'i muje "ok "kinsan Yah Ameen fa girki yasani in masa wai baze iya cin abincin aunty khadeeja, bayan sungaisa ne suka fito, suka nufi kitchen suka fara had'a masa delicious food Haleema sai zolayarta take wai dayake girkin Yah ameen ne ta dage sai fama take. Dai-dai sh'ida da rabi suka gama suka fito da ga kitchen sun gama girkin, suna fitowa falo sukaci karo dash'i zaune akan kujerar dake zagaye da falon, "cab lallai wannan 'yan gayu ne sh'i, yanzu daga fitarsa daga gidan har ya sauya kaya, yanzun sanye yake cikin k'ananun kaya sun amsh'i jikinsa, gash'in nan ataje luf-luf. "Sannu da hutawa Yah ameen," Ameenah da Haleema suka fad'a suna had'a baki "sannu" kawai yace ya cigaba da kallon Tv. Toh bayan Ameenah tayi sallar maghrba ne ta fito zata tafi gida, Mamy na falon ita da Yah ameen suna magana banaisan me suke cewa ba, ganin fitowar Ameenah yasa Mamy ta tash'i tana fad'in " badai tafiya zakiyi ba ko? "wallahi Mamy tafiya zanyi, "toh tsaya ina zuwa Mamy ta fad'a tana hayewa bene, sh'iko gwanin kallo d'aya yayi mata ya 'dauki remote yakamo tash'ar _Music plus_ga d'an kwando na kayan marmari yana d'auka yanaci. sa kin baki tayi tana kallonsa yadda yake taunarma abin burgewa ne, wayyo jitakeyi kamar tafad'a jikinsa ta rungumesh'i ta fad'a masa cewar tana sonsa sedai hakan bazata yuhuba, dan ita d'in mecece me aji. Mamy ce ta sakko da leda a hannunta ta bata, "aa Mamy kibarsh'i dan Allah "noh bazamuyi haka ba karb'i a matsayin y'a kike gurina. Hannu tasa biyu ta russuna ta karb'a tace"Nagode Mamy daga nan tayi mata sallama ta fice. "Dama yarinyar nan tana da nutsuwa? "gata dai a haka kamar ta Allah "nan kuwa ko dujal nan yaganta ya ky'ale saboda rawa. "Mtswww yayi ts'aki a fili dan sh'i a ganinsa Mace ta sh'iga filin biki tayi rawa gurinda maza da matan suka gauraya gani yake kamar rash'in _class ne_ "lafiyarka kuwa Son naji kana tsaki? sosa gash'in kansa yayi yace"Noh bakomi Mamy. "Yawwa Mamy wai wannan y'ar waye?(Littafin granny khairat up" "Kawar Haleema ce tana da kirki sosai ga nutsuwa da hankali wallahi yarinyar ba ruwanta. "Hmmmmm ya d'an k'ara girman idonsa alamar mamaki , yarinyar dabata kunya ina wani hankali. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 45~50 BAYAN SATI D'AYA Anyi hutun islamiyya ya kama yanzu su Ameenah suna gida hutu. Idan Haleema batazo gidansu Ameenah ba to ita Ameenah zataje, suna sh'irya planing ta yadda zaa jaho hankalinsa, but duk ta inda suka bu'lllo sai suga da akw'ai matsala. Yau takama Alhamis, Haleemace tazo gidansu Ameenah, lokacinma Mama tana kitchen tana dafa musu abinci, ita kuma Ameenah tana d'aki tana yiwa Asleem da Tasleem home work d'in da'aka basu a school. Haleema ta sh'igo ta sallamarta bayaj sun gaisa da Mama ta ciro kud'i a jaka ta bata tace inji Mamyn su, godiya Mama tayi mata sosai, Naso in gano muku ko nawane amma Mama ta soke a zaninta lol, ganin Ameenah na aiki yasa ta fita tsakar gida tana taya Mama aikin datake. Bayan duk sungama aikinne Mama tazubo musu abinci dama _dambu_ sukayi ita dama masoyiyar sace sukacinye abinci bayan sungama Haleema ta kalli Ameenah tace"Friendy kinsan dame nace" "aa ta fad'a tare da girgiza kanta "kizo muje gidan Yah ameen pls kirakani bawai dan wani abu ba kema ai kya gansh'i ko? Haleema ta fad'a tana d'aga mata gira, ba musu tace"to bari na sanarwa Mama, bayan ta fad'a matane tace "sai kun dawo ku kula da kanku banda kula kowa a hanya _pls_ "Insha Allah ta fad'a tana sh'igewa d'aki tasanja kaya sanan suka tafi. Tash'in hankali wanda baasa masa rana suna zuwa gidan kafin su sh'iga parlour sukajiyo ihun kukan mutum, kuma daga ji na mace ne sai dai in ka k'ara sa kunnenka sai kaji kamar harda namiji ma ke kukan, kallon-kallo sukayi ts'akanin Ameenah da Haleema "Friendy meke faruwa ne? anya kuwa mush'iga?, bamu sani ba ko wasu ne suka sh'iga gidan" Ameenah ta fad'a tana narai-narai da ido. "Ah no kizo mu sh'iga, karkiji tsoro bakomai" Haleema taja hannunta suka sh'iga ciki , zazzaro ido sukayi waje ganin Aunty khadeeja(Matar Ameen) ce ke kukan Yah Ameen sai jibgart yakeyi ita da wani, ya had'a kansu ya gwara har jini ke fitowa ta bakinta, " _kije ki tafi ki tash'i ki barmin gidana ki tafi gidanku ki cigaba da neman maza da bin mazan da kika fara yanzu kin matsa kince bana kw'anciya dake, bakisan rufa miki asiri nayi ba ,mahaifita kinje kin gayaa mata bana saduwa dake duk meyayi zafi, ko duk saboda masifarki sai kin kahomin kw'arto cikin gidana kitash'i nace na sakeki, ya jahota ya danganata da waje inda damatuni kwarton nata ya d'ibi kafafuwansa ya arci na kare sai dai ya kw'afsa dan tuni y'an sanda suka kama s'hi suka fice dash'i station_ "Friendy dan Allah ki taho mutafi kinga kar ya had'a daku jibifa yadda yake kallonmu," kus-kus ta fad'i mata "aa tsaya dai" "muts'aya muyi me? juyowa yayi yaga mutane abayansa, huci yake kamr tsohon zaki yakallesu yace" ku kumafa?" Haleemace tayi kok'arin bash'i amsa da cewa "uhm dam...ma cemukayi bari muzo mugaisa da Aunty khadeeja kuma.......kuma......mhmm "kuma me? "go out munafukan banza. Aiko da gudu -gudu sukayo waje, fitsarine kawai ya ragewa Ameenah bata saki na, amma ta tsorata ainun. Gidansu Haleema suka huce, suna zuwa suka baje a parlour suna numfash'i Haleema dariya kawai takeyi, tana tuna yadda suka tsorata. Jiyo dariya yasa Mamy ta sauko" ku kuma lafiya dan Allah? "Mamy daga gidan Yah ameen muke wallahi ya zane Aunty khadeeja, ita dawani, "duka fa kikace Haleema?, "eh kamar dai kwarto ya kama a gidan, "Innalillahi wainnailaihirrajiun!!! Abinda yarinyar tayi kenan?, "yamace yasaketa, sukadai kwashe kaf labarin suka gaya mata,. Baa dade'ba sukajiyo sh'igowar mota koba'a fadamusu ba sunsan shi ne ai da y'ar rige-rige suka tsere d'aga tayi kitchen d'aya tayi d'aki. Bayan yash'igo ne kuma yama Mamy bayani tayi masa fad'an akanme zedaki y'ar mutane? ai haku'ri akeyi ta lallab'ash'i nan da nan ya dawo normal, "ni zan k'ara nema maka wata macen, "what Mamy Ameen ya fad'a yana zare ido, inda Ameenah dake kitchen itama d'in ta zaro ido tare da cewar"what na sh'iga uku, kqmar zeyi kuka ya marai-raice ya sakko k'asa ya tsugunna a gabanta, ya had'a hannu biyu yana rok'onta. "Mamy pls ki barni wallahi Mamy mata basada gaskiya, ki barni in zab'o wata me mutunci da hankali y'ar tarbiyya, Mamy ba cikin y'ayan k'awayenki ba wad'anda aka sangarta ba, ba irin wad'anda basu san ilimin addininmu ba sai na yahudu, Mamy masu qualities danakeso , ba wad'anda basa cikin tsarina ba, Mamy wacce zata haifamin y'an biyu , ta basu tarbiyya me ky'au ba ky'ale- kyalen zamani ba Mamy, hawaye ne ya zub'owa da Ameenah yadda Ameen yayi ya matuk'ar bata tausayi, "Son duk wad'annan qualities d'in yarinyar ta had'a, sedai tunda bakaso anfasa sh'ikenan ko? "ohhh sweet kill me ooooo that's why i proud of you Mammy, "da akw'ai abinci Mamy? "eh jeka kitchen da akw'ai" da murnarsa ya nufi kitchen dan samun abinda zesa a cikinsa, turus yayi ganin mutum a tsugunne yana hawaye, ...."keee..... Ameen ya kirata. ~Maman triplet~๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘ง๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [1:56PM, 8/15/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 50~52 In'ina Ameenah ta fara, dacewa"Uhm bakomi.......bah....abinda nake......yi" "tambayarki me kike yi? "munafuka dallah fice kibani guri," ai tun kafin yakai k'arsh'e ta kw'asa da gudu ita wallahi kw'arjini yake mata tarasa meyasa,? _hm ai dole yayi miki kw'arjini dan Ameen ko baki sansh'i ba kika gansh'i sai kinji sh'ayin yi masa wani abu_. "Au kece kika sh'iga kitchen dama? Mamy ta tambayeta "eh Mamy nice wallahi, tana fad'a ta sh'ige d'akin Haleema, dariya Haleema keta ky'akyatawa saboda taga k'awartata ta sh'igo a kid'ime kuma duk abinda suka tattauna tsakanin Mamy da Yah ameen duk taji. "Friendy romeo ne ya tsoratar da juliet d'insa"? "kefa muguwa ce wa billahillazi ko? ina tausayin randa kema zaki fad'a tarkon son wani".... Tv suka kunna suka kamo tash'ar _Mazzika_ kid'a yafara tash'i, mussaman da Ameenah taji wak'ar datayi matane, ta d'au remote ta k'ara volume, ta tash'i ta cire hijab d'in jikinta, ganin kid'an zai wuceta yasa ta tash'i ta fara rausayawa tana karkad'a k'irji k'ugu da kai rawar larabawa kenan wani lokacin. Haleema kuma itace me temaka mata da tafi"woww woo wannan rawar sai ranar bikinku keda Yah Amee...... "Kuwai bakuji ana muku magana kun mayar mana da gida sai kace gidan biki?, kun cikamana kunne da wak'a?... duk wannan maganar Ameen ne ke yinta but kawayen nawa basusan yanayi ba saboda sh'auk'in dasuka sh'iga. Bugo k'ofar da akayine da k'arfi yasa suka zuba ido ga bakin k'ofar dan ganin wake sh'igowa, "Inye????? lallai tayi muku ky'au, inata muku magana kun karad'e gida da kid'a hmmmm." Ameen ya fad'a cikin masifa, mutuwar tsaye Haleema tayi, tace "yi...hak'uri..bamuji bane, "kedai wannan, ya nuna Ameena da yatsa yacigaba da cewa"in baki wasa ba akan wannan Raye-rayen da kike sai kinje kin kw'asowa kanki jinnu. "Ke kuma Haleema, itama ya kira sunanta "kici gaba da biyemata kuna zama d'aya banzaye ku fito kumin girki kuma kala biyar nakeso, a cikin minti 30 juice kala uku, aciki zan zab'i d'aya inci, ragowar kunyi asarar hannunku da lokacin da zaku b'ata, wannan shi ne punishing naku" kuma a ciki idan d'aya bemin ba sai kunsake. Cab Kallon kallo akayi tsakanin Ameena da Haleema, "munsh'iga uku suka had'a baki su ka fad'i a tare. "ai Allah gida zantafi Friendy, "kut....ke kinma isa? wallahi baki isaba. [5:32PM, 8/15/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: "Bake ce kika jaho mana ba? "to ke in bandake da abunki tayaya zakice zaki tafi ki barni ni kad'ai? sai kace me hannun Gizo-gizo?, Haleema tayi maganar cikin tsiwa. "to mu computer ne dazamuyi masa girki kala biyar? me zamu dafa masa? ga juice har kala uku, dan Allah ya zamuyi, Ameenah ta fada da tunanin nemo mafita, zaman bori sukayi suka zub'e a k'asa, Ameenah tayi facing Haleemah kowacce tayi uban tagumi suna tunanin mafita, lokaci d'aya suka had'a baki da cewar"Menene Mafita? me zamu girka masa acikin 30minute????. Jin sun tafi tunani ne yasa nima Foulani na d'anyi plugging wayata kafinsu dawo daga tunanin. *Toh Masu karatu, ko zaku iya basu sh'awarar abinda zasu girka a cikin 30minutes? inkece ko in kune mezaku girka masa,? me zakiyi??.* ~Maman triplet~๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘ง๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 52~54 "Ki tash'i muje muyi masa white rice nd spaghetti with soup, sai muyi masa pineapple nd coconut juice , sai mu bash'i hak'uri Ameenah ce me wannan maganar "Cab duk acikin 30minute d'in?"ni aganina mu soya masa indomie da k'wai sai kuyi masa fara mu zuba mai, sai muyi masa jallop d'inta kinga hud'u kenan, sannan sai muyi masa d'an wake ko? Ameenah ta fad'a "sai muyi masa pineapple juice dana watermeloon, mu markad'eta musa madara da sugar sai musa a fridge dan yayi sanyi, biyu ko? "wai ke Haleema bazaki bada taki idea ba kinwani kafeni da ido kina kallo?, "Dalla ni gyalen...... Bazaku fito ba? kunacin time d'inku fa, Yah ameen ne yayi maganar yana daga falo, atare suka fito suna zuwa suka zub'e akan centre carpet dake d'akin, "Dan Allah Yah Ameen kayi hak'uri bazamu sake ba, ko Haleema ko Ameenah? suka fad'a a tare suna kallon juna, dariya suka so bash'i amma sai ya k'ara had'e rai yace"oya maza-maza kutash'i kumin abinda nasaku ko yanzu ranku ya ba'ci, Mamy tana sama dan haka batasan wainar da ake toyawa tasauko da niyyar d'aukar abu a k'asan ta tarar da y'ara a durk'ush'e duna bada hak'uri. "Meyake faruwa kuma? ka dawo gidan zaka takurawa yara, da ita k'anwar taka da wacce ba k'anwartaka ba,? sedai dan mutunci da zumunci ta zama k'anwarka, amma ai bahaka ake rayuwa ba mesuka maka? "Mamy ina musu magana sunmin banza, sun ware kid'a, suna rawa" "to sh'ine me? "punishment na basu, "name? "sumin girki, "au girkin ne ku kuma bazaku iyaba kuka zube kuna bash'i hak'uri? da kun tash'i kunyi da kun huta ai ko? Mami ta fad'a tana kallonsu sunyi wani zuru zuru da ido. Haleema ce me kok'arin cewa"Kal...kala biyarfa yace muyi masa kuma wai da juice kala uku a cikin 30minute . Hangame baki Mamy tai tana kallonsa tace"kala biyar kuma duk zaka cinye a cikinka? "zasuyi maka amma fa kaima duk sai ka cinyesh'i ku tash'i kuje babban kitchen ku d'ora masa duk abinda kuka so. Damurnarsu suka tash'i , Halema tayi niyyar dariya amma tak'i saboda tsaro. Suna zuwa daya ta d'ora ruwan zafi, tayi masa tea ta juye a plask, d'aya ta soya indomie da k'wai, sannan suka yi masa d'anwake, suka yi masa white sphagetti nd soup, bayan sh'i suka fara juice kamar yadda Ameenah ta fad'a haka sukayi, kuma duk yafi k'arfin cikinsa. D'auke da tire suka sh'igo suka ajemasa kan dining "Food is ready romeo, Haleema ta fad'a cikin siririyar murya daky'ar ma inyaji abinda tace, tunda be d'auki wani action ba. Ameenah ce ta kalli Haleemah tace "Nidai Friendy gida zantafi wallahi, "driver ne ze kaiki, coz ban yadda adinga kallemin matar yaya baa, eyye Haleema tafad'a tana d'aga mata gira, duk a ta da'ala mata tace"ke dallah rabu dani, wannan yayan naki yana wahalar dani ni bazan iya jurar wannan wulak'ancin ba, in mukayi aurenma haka ze dinga sani girki kala goma. Ta fad'a da fuskar tausayi . Har gida driver ya kaita, tash'iga da sallamarta, Mama ta amsa mata, Asleem da Tasleem suka rugo da gudu sula rungumeta"We miss you big sis" Missing you more ta musu peck, suma sukayi mata ta sh'ige d'aki. Mama tana alfahari da y'arta saboda kasancewar bata tab'a jahomata magana ba, gash'i tana taimakawa k'annenta wajen karatunsu, sai dai tace"Masha Allah. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [8:52AM, 8/19/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 54~55 BAYAN WATA D'AYA. Yanzu in kaga Ameenah gaba d'aya ta sauya, ko hira ake sedai tayi sh'iru saboda tunanine yake addabarta, kai ko a hanya ta taho zata iya bigeka ma bata sani ba. Agida kuwa su Asleem da Tasleem suyi ta damunta da"Ya sayyada wai meyake damunki? yanzu baki mana tatsuniya, kindena zama kiyi hira da Mama, meyasa? takance tasu "bakomai Twins d'in Mama. Mamar matayi tambayar har tagaji, takaita asibiti a duba ko bata da lafiya ne? amma lafiyarta k'alau dan haka da tagaji sai kawai ta kyaleta. Acan gidansu Ameen kuwa, kullum Mamy zatayi masa zancen yarinyar nan, seyayi kamar zemata kuka ita kuma tasan had'in dazatayi masa bana sh'arri bane dan ta yadda da tarbiyyar yarinyar da zata bash'in, Haleema y'ar sa ido, sedai kiji ta lallab'o tace"Mamy wai wacece wannan d'in ne? kigayamin inji mana. Haleema tanayin hakan ne dan kar k'awarta ta rasa zab'in ranta, tanaso taji wacece dan tasan hanyar dazata bullowa da abun, but Mamy tak'i gaya mata. Yau Alkhamis da misalin k'arfe takw'as na dare, Ameena ce zaune ita da Twins d'in Mama, tana k'aramusu karatun Alqur'ani sakamokan an basu hadda a islamiyya. Yaro ne ya sh'igo da sallama yace"wai ana sallama da Ameenah, "What??, Me?, Ameena ta fad'a tana nuna kanta da hannunta, da sauri tace "kace batanan." "kace tana zuwa" Mama fad'aa tana kallonta, kitash'i ki fita, jik'aki zamuyi mush'a koyaya? sai ayita zuwa gurinki fira amma sai kik'i fita, to yau sai kinfita. Tash'i tayi taja hijab d'inta Fuuuuu ta fita. Tana zuwa ta taddash'i tsaye jikin motarsa ash, cikin sh'adda milk, ya kafa hularsa _Zanna bukar_ sai tash'in k'amsh'in turare yake. Tsayawa tayi k'ik'am bata masa sallama ba. "Barkanki da fitowa yake gimbiyar mata" "barkanka" abinda ta iya cemasa kenan ta d'inke bakinta tayi masa sh'iru "To dafari nidai sunana Haruna ina zaune a garin abuja inda anan nake aikina, nazo biki nan kano naganki, kuma naji kin burgeni har nayi sh'aawar mu had'a halak'a ta soyayya fatan zaki karb'a?." tunani ta tafiyi a gidan biki wajen rawa anan yaganta kuma yace yana sonta? Anya?? katse mata tunanin yayi da cewar"Haba yadai naji kinyi sh’iru ne,? kobanyi miki ba? "Aa bakomi hira yadinga yimata sedai ta bish'i da uhm eh aa. daga k'arsh'e dayaga ba wata hira kawai yayi mata sallama tare da mik'o mata kud'i tak'i karb'a, se cayayi ba abinda zakiyi min wanda zesa im nakoma gida in dunga tunaninki? "mezan maka? Ameenah ta tambaya, "Haba baby Meenah ko d'an irin hugging da kissing ai nasamu ko,? ya fad'a yana k'ok'arin kami hannunta, sauri tayi ta janye tace"ya haka Malam?? "mekake tunani? ni y'ar iskace? ko kuka me? mtswww to kasanja tsar...."ke dalla saurara kina y'ar rawar D'j dan nazo namace inasonki sh'ine zakimin shauting? "Kaicona!!! ta fad'a da gudu tayi cikin gida. [5:11PM, 8/19/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Kafin ta k'arasa cikin d'akin tasaita kanta dan kar su Mama sugane wani abu. Koda ta sh'iga bata musu magana ba ta sh'ige d'akinta tayi kw'anci tana tunanin halin Wash'egari Mama tana zaune tana yanka salad taji tsayuwar mota a k'ofar gida. Sallama tayi tayi ta sh'igo "Lah Mamyn Haleema? sannu da zuwa Mama ta fad'a da mamakin ganinta dan ta dad'e batazo gidan ba. Ameenah Dafara'arta tafito tana "oyoyo Mamynmu Mama ta dafata suka sh'ige d'aki bayan an gaggaisa Mama take cewa"kin d'auke k'afarki daga gidanmu ko Daughter? "aa wallahi Mama ba haka bane" "To aini gani nabiyoki " Ameenah ta sunkuyar da kanta alamar kunya. ta tash'i ta aiki Asleem ta sayo mata lemo me sanyi ya kahomata, taji yaron ya burgeta sosai. Bayan tash'ane suka fara hira da Mama ganin haka yasa Ameena ta fita tabar musu d'akin domin bedace tasasu a gaba tana kallo ba. Bayan tafita ne Mamy ta kalli Mama tace "dama nazo miki da wata magana ne, kuma inafatan zakiyimin alfarma, Gaban Mama ya fad'i dajin wannan abu amma sai tace "menene Mamyn Haleema? Mama tafara da cewa dama............ Ayya wayata ba charge ๐Ÿ˜ซsorry Fans ~Maman triplet~๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘จ‍๐Ÿ‘ง๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [8:05AM, 8/21/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 56~57 "Dan Allah Maman Ameenah kimin alfarma, " "wace abune wannan Mamyn Haleema? kifad'amin mana, kinfi k'arfin komi a gurina". "Dama so nake kibani y'arki, so nake ki yadda in had'a *AMEENA DA AMEEN* aure, ammafa sai in kin amince kin yadda tunda kece mahaifiyarta." Gumine yake ketowa Maman, dan maganar tazo mata a bazata, coz batayi expecting hakan ba but why?, tayaya zata had'a y'arta da yaron da taji Haleeman da Ameenan suna cewa yafiye fad'a da miskilanci, Mamy ce ta katseta daga tunanin datake tace"Maman Ameena yanaji kinyi sh'iru ne? ko kin bayar da ita ne? "Sh'in Ameen yana son Ameenah? sh'i yace miki ki nemo masa aurenta? inke kika zab'a masa ya amince?"Mama ta tambayi duka dantaji amsar da Mamyn zata bata. To itama Mamyn ta tafi tunanin amsar bawa Mama, "ki kwantar da hankalinki na isa da Ameen , bash'i yace in nemo masa ba, ni na duba dacewar hakan, ina ganin Aurensu zai kaho sauyi a rayuwarsa, ki yadda in had'auren *Ameena da Ameen* pls Maman Ameenah, Tayaya? babbar mace kamar wannan tazo ta nemi abu agunta ta hanata? matar da take taimakonsu a rayuwa, sai dai abinda ta nema d'inne kamar da wuyar bayarwa, Y'afa?.... "Maman Ameenah in kinga bazaki iyaba sh'ikenan Mamy ta fad'a cikin fuskar tausayi, "yaron nan matar dana bash'i a farko bata masa adalci ba, bata juri duk abinda yake mata ba, bata rufa masa asiri akomai ba, Hankali da nutsuwar Ameenah da tarbiyyarta su suka jani suka saminsh'aawar had'a *Ameena da Ameen* itace dai-dai sh'i". Amma idan kinga bazaki bayar da itaba s'hikenan. Maganar ta sh'igi Mama sosai kuma taji tausayinsa tunda beyi dacen mata ba. "sh'ikenan Mamyn Haleema Allah yasa hakane yafi alkhairi. [8:40AM, 8/21/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Da sauri Mamy tajuyo cikin farin ciki tace"da gaske? da gaske kin yadda Maman Ameenah? "eh na yadda mu had'asu, " "Insha Allah zamuga alkhairi tunda da niyyar hakan mukayi Allah sa albarka acikin auren *Ameena da Ameen*" "Ameen ya rabb" suka fad'a a tare. Kowanne da tsantsar farin ciki a zuciyarsa. Bayan Mamy tafuto zata tafi ne, take cewa Ameenah" yaush'e zaki zo? kink'i gidanmu yanzu, "aa Mamy ba haka bane zanzo soon" "Allah yasa. Daganan sukayi sallama da cewar sai Abbansu Ameen d'in yadawo zasu tsaida magana dan baya gari. [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [13:56, 8/23/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 58~59 Bayan fitar Mamy ne Mama tayi kiran Ameenah, take cemata"Ameenah Mamyn Haleema tazomin dawata Magana.Daganan ta kw'ash'e duk yadda sukayi da Mamyn amma bata gayamata cewar da Ameen zaa had'asu ba. Tunani sosai ta sh'igayi saboda zancen yazo mata a bazata, ita dawani d'an nata Mamy zata had'asu?, ya zatayi, ita datake son Ameen yanzu idan bash'i bane fa? idan k'aninsa ne shi'kenan an mata yankan k'auna da abin son zuciyarta, sai dai data tuna hirar Mamyn da Ameen, sai take tunanin to kodai shi'ne? Allah yasa haka to. D'aki tash'iga jiki asalub'e, ta haye gadonta tafara tunanin yadda za'ai a had'ata aure dawani wanda baya sonta cab jink'iri mak'ari. "Yah Ameen "Yah Ameen ka tash'i Daddy yadawo yana ta kiranka kazonan sai sh'ar bar bacci kake". Haleema ketash'insa, amma saboda jiya ya d'auko Abbansu daga airport kuma cikin dare ne dan Haleeman ma tayi bacci a lokacin, shi'yasa batasan ya dawo ba sai da safe data ganshi' sh'i ne har take tuna masa yataa'shi. Bargonsa ta janye, ta jaho d'an yatsan k'afarsa "ka tash'i.Tafa'da da k'arfi, tafice da gudu, dan dole ya tash'i ya sh'iga toilet yayi brush,wanka da alwala saboda besamu sallah asuba ba. Bayan yagama yayi addua sosai sannan ya tash'i, yayi cikin gida. kodash'igarsa cikin gidan a dining ya taddasu sunfarayin breakfast, sallama yayi sannan ya nemi guri yazauna. Gaida iyayen nasa yayi,suka amsa ckin sakin fuska, daga nan ya jaho flat d'in abinci yayi serving kansh'i. Bayan sungama cine Abbansu yayi gy'aran murya, sannan yafara magana kamar haka "My son! kaga dai be kamata mubarka haka ba, duk ka tsufa sh'ekara tafiya take, kwara ka amfani kurciyarka, kai yanzu ba yaro bane, kana da y'an uwa k'anne kuma suna koyi da abunda kakeyi ne, inso samune inaso kayi aure, kuma nasa Mahaifiyarka tayi maka zab'i na hak'ik'a, ba irin wancen ba."Inafatan zaka amince da duk wacce aka kaho maka amatsayin mata". Shi'ru falon yayi, kasancewar kowa yayi tsit yana saurar Abban. Duk kansu inka kalli fuskokinsu da farinciki, banda Yah Ameen wanda yake ta faman had'a uban gumi dukko da sanyin Ac dake ratsasu. Tunani yake sh'idai yanason matar daxai aura ta kasance dawasu qualities wanda yake burin samun mace dasu, yanzu idan ba haka take ba yaya zaiyi, wallahi aure ze k'ara.Haka yaketa tunani kafin Abban ya katseshi da cewa"nasan kana da biyayya da hak'uri, kayi hak'uri ka tallafi kowacece insha Allah zakaga Alkhairi." "toh Abba insha Allah zanmaka biyayya domin farantawa MAHAIFINA zan auri koma wacece" "Allah yayi maka albarka"Mamy ta fad'a tana faraa. "Allah yabaku zaman lafiya" Abba ya fad'a. A'inda ba abar Haleema y'ar sa eyes ba sai da tace"Allah yasa ku haifo y'an uku masu kama dani da Abba da Mamy ko?. Duka aka tuntsire dariya amma banda Yah ameen wanda ya kad'a bujensa yafita. Abba ne ya kalli Mamy yace" "Aise akahomin Y'artawa in ganta ko? duk da dai naaganta a photo inason naganta; dan intabbatar da banyiwa d'ana zab'in banza ba, duk da nasan Haleema bazatayi k'awar da bata kirki ba." "Abba k'awata kuma? Haleema ce tayi tambayar tara da k'arawa eyes d'inta girma. [14:13, 8/23/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Mamy ce ta tare ta da fad'in "eh k'awarki Ameenah saura ki bari yaji yasan kowace ranki zai ba'....."Wayyo Allah sweet kill me woooo,"Mamy Haleema tayi gunta da murna ta rungume ta ta k'ara kallon Mamyn tace"Mamy are you serious? kafin ma Mamy ta bata amsa tayi gun Abba sh'ima ta rik'e masa hannu tace"Abbana da gaske *Ameen da Ameena* kuka had'a? sh'ima be bata amsa ba sai murmush'i kawai dayayi ganin y'ar autar Mata na farinciki ,ta mik'e tana tsallen murna" Dole inyi murna da celebration, kunsan daga jin sunan ma Abba couples d'im sun had'u? aiko? kuma sun dace da juna? ko? *Ameenah da Ameen* woww perfect match wayy.... Bata k'arasa Mamy wacce Haleema ta cika mata kunne da ihu tace "Ke dallla kincika mana kunne dawannan sh'ash'ancin naki, sh'iyasa tunda wuri nak'i gayamata dan nasan sh'irme zatayi mana. "Aaa Mamyn yara banson fad'a yazakice bazatayi murna ba? barta tayi, yayanta take tayawa murna. "Autar mata(sunan da Abba yafi kiranta dashi) tash'i kije ki sh'irya kije gidansu y'artawa ki tahomin da ita". "Yee ok Abbana.Da gudu tafita daga parlon tayi d'akinta, tana mejin dad'in wannan abu burin k'awarta Aminiyarta, Sister ta zai cika. By; ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* BY;FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 62~64 Ameen ne ya juyo yana hararar Haleema yace" "Mamy ga driver nan a zaune, aikin meyake?". Haleema ce tayi saurin cafe zancen ta k'irkiro k'arya tace. "Uhmm, ai sh'i driver aikensa za'ayi," Mamy koma kin aikesh'insa? "Aa dai yanzu nake sh'irin kiransa,". Ameen ne ya kalli inda Haleema ke zaune yace "Hmmmmmm!! zan kama yarinya ne duk randa Abba ya tafi, yasa kai ya fice," Sai kina hak'uri fa y'ata, d'annawa akwai kirki" "uhm" murmush'i kawai tayi, itadai so take sud'an bar parloun sukoma d'akin Haleema dan takasa sakewa, duk kuwa da yanda su duk suka sake da ita, musamman Abba dayake jin kamar 'yar daya haiface. Yarinyar ta burges'hi saboda nutsuwarta da kunyarta. Kiran sallar maghriba aka fara, sh'ine dalilin dayasa suka tash'i Abba yayi masallaci, Ameenah da Haleema ma sukayi d'akin Haleeman, suka d'auro alwala suka fito sukayi sallah kowacce ta roki' ubangiji buk'atunta. Tv dake parloun suka kunna suka fara kallon Mbc bollywood, suna wani film ne wanda Ameenah ke mugun so, wato *vivah* murmush'i ne d'auke a fuskarta, dan intana kallon, sai taga Ameen yayi yanayi da jarumin film d'in _Shaheed kapoor_ sai dai ya nuna masa hasken fata, amma gani take ma yafi _Shaheed kapoor_ d'in ky'au. Masoyan sun burgeta, dan tana kallonne ma, Haleema taga tension d'in Ameena baya kanta dan haka ta kalleta da tsokana tace"Ah su juliet tunanin romeo akene? "hmmmmm" Ameenah ta harareta batace mata uffan ba. Mamy ce ta kira Haleema tace ta kira Yah ameen, ai tana zuwa d'akinsa ta sh'iga a bud'e amma bayanan, ta sh'iga bedroom, bata gansh'iba,. Bata kuma ji motsin ruwa ba bale ta lek'a toilet d'insa. Dan haka kawai ta fita. Ashe sh'ikuma yana ciki, Haleemah na fita, ya d'auko Key d'in motarsa zai fita. Haleemah na sh'iga ta sh'aidawa Mamy bayanan, ganin dare na k'arayi tace"jeki kira driver yazo ya maidata, "Daughter bari nazo ko? Mamy ta fad'a tana d'an dafe da kafad'ar Ameenah, stair d'inta ta hau, Haleemah ta dawo tace ma Ameenah tazo ga driver nan zai kaita. Mamy ce ta sauko dawata bag me ky'au, daga gani kayan kw'alliya ne a ciki dasu turare dan naji k'amsh'i sosai. Haleema ce ta ruk'omata ledar da Abba ya bata ta tsaraba, da bag d'in da Mamy ta bata. Tayiwa Mamy godiya, tayi mata sallama inda Mamy tace"kicewa Mamanki sai nazo ina gai'sheta" "to" sannan suka fito. Karaf idon Ameenah cikin na Ameen ya fito sai uban k'amshi yake, ya sauya kaya zuwa dark blue sh'adda taji aiki,. K'amsh'i kawai yake bugawa, Ameenah ce ta tab'o Haleema "ke ina zash'i? da daddaren nan,! yawani ci wanka?, "oho masa, koma ina zash'i ki barni dash'i, kar kice masa uffan ki tsaya kiyi kallo. "Toh" kawai tace da ita. "Yah ameen so kake Mamy tai fush'i dakai ne? cataifa ka kai Friendy gida sh'ine zaka fita, Hararta yayi tukun kafin yace"Baga driver can ba nifa unguwa zani, "Driver Mmy aikensa zatayi gidansu Aunty khadeeja,(Tsohuwar matarsa idan baku manta ba). Sai dai in drivern yakaita gida kai kuma kaje aiken da drivern, gidansu Aunty khadej. ................"Shut up, muje, abinda kawai ya isa cewa kenan, dan bayason ya tuna da khadeeja taci amanarsa sai dai Allah ya isa . Hannu ta d'aga Jinjina Ameenah tayi mata, kin iya suburbud'o k'arya. Sukayi dariya tabud'e mata mazaunin me zaman banza, ta zauna, kallo kawai yabisu dash'i, danya fuskanci yaran halinsu yafi k'arfinsh'i. S'higa ya kunna mota, zai juya yafita, Haleema tace"Au Yah Ameen, Mamy tace ka sh'igar mata da wannan", ta mik'o masa Ledar nan da bag, "wai daganan sai ku gaisa da Mamanta. Karb'a kawai yayi yako d'orasu asaman cinyar Ameenah, yaja motar yabar gida,. Har ya fita titi, besan inane gidansu ba, besan wacce unguwa take ba, yanason ya tambayeta amma baison yimata magana,. Dan haka kawai ya zaro phone nash'i ya kira Haleema, yana tambayarta inda zai kaita,. "Ah yah Ameen ka tambayeta mana". Abinda tace kenan ta katse wayar. "Mtsww" Parking yayi kawai yaci gaba da danna wayarsa, tanason yimasa magana amma tanajin tsoro, gash'i har anfara kiran ish'ai. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [06:17, 8/28/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* BY; FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 65~66 Zaman sh'irunne ya ish'eta, tanason tayi magana amma tana gudun kar yamata wulak'anci yayi banza, itakuma babu abinda ta tsana sama da wulakanci, sh'iyasa ma ta gudurce aranta bazatayi masa magana ba har sai lokacin da yaga dama yayi mata maganar. Wak'arsa kawai yakeji ko a jikinsa, amma fa so yake yayi yakaita ya dawo saboda akwai abinda zaijeyi yanzun, so yake tagaya masa inda zai kaita bawai alallai sai yabud'i baki yayi mata magana ba. Lokaci d'aya yaja tsaki"Mtswwww" yayi sh'iru bece uffan ba, ita kuwa Ameenah sai ta juya fuskarta gefe tana ta zumb'urar baki ganin har nine 9 ta kusa, ita batason Mama tayi mata fad'a ne sh'iyasa. Ameen ne ya k'ara jan tsaki ana biyu, tare da cewar"Ke dallah tash'i ki fitarmin daga mota tunda bakisan inda zaa kaiki ba" Kinwani yi sh'iru sai kace mutuniyar kirki, nanko a shaid'ananci inajin sh'aid'anma ya fiki iyawa". Daurewa tayi, tayi magana kamar zata fash'e da kuka tace cikin inda- inda. "Ni........ai baka.....tam..bayen inda...zaka kaini ba, kawai jinayi kayi parking basai in tunanin wani abun zakayi gunba". "to tash'i ki fita kinemi keke napep _D'an sahu_ kihau inyaso sai sh'ima kimasa sh'irun karki fad'a masa inda zai kaiki kigani in be je yasayar da kanki ba". "G/k'aya ne" "G/k'ayan ma nan da nan kusa kusa mtsww iyayin banza kawai". ya fad'a yana wani harare - harare. Motar ya figa, dasuka sh'igo tadinga nuna masa hanya har suka. bud'e motar tayi ta fita, tabar masa kayan daya d'ora mata a cinya akan kujerar data tash'i, bayadda zaiyi ya d'auko ledar da bag d'in aransa kawai dan dai Mamy ce tace ayi amma wallahi da bata isa ya kahota ba, ballantana har yawani sh'iga gidansu"mtsww" ya k'ara jan tsaki a karo na uku. Bayan ta fita ta sh'iga gida tasanarwa da Mama zaa zo gaish'eta tace to. "Bismillah ka sh'igo mana" lums'he idonsa yay sannan ya d'ora k'afarsa cikin gidan, wayarsa tafara ruri, ya d'auko ya duba ganin My only Mum yasa sh'i saurin d'agawa"Hello Assalamu alaikum" Mamy" daga ciki wayar kuwa Mamy ce tace"ka kaita gidan?, "Aaa yanzu zamu sh'iga dai." Tace"ok ka d'an bawa Mamanta wanii abun mana,"toh Mamy" yace tana kash'e wayar. Domin a rayuwarsa yana girmama duk wani abu dazata sash'i, bata tab'a sash'i abu yak'iyi koda ace kuwa bayaso, yasan bazata sash'i abinda ba dai-dai ba. Ciki suka sh'iga a parlour ya tadda inda Mama take, kai a k'asa yagaish'eta kamar kuwa yasan surikarsa ce. Bayan sun gaisa yayi mata sallama tare da ajiye mata y'an d'ari -d'ari bandir uku, da ky'ar Mama ta karb'a, tayi masa godiya sosai sannan ya fita. Dayafito a ransa yake cewa"A haka kamar masu tarbiyya hmmm amma y'arsu agun rawa kamar jiki ya karye. Yawani yatsina fuska tare da sh'iga motarsa. [08:37, 8/28/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Har zaija motar kuma sai yaji kamar tsayuuwar mutum a gefensa dan haka ya fito ya duba, turus yayi ganin ta tafito d'auke da jug na ruwa. kallonta yayi da mamaki yace"yadai?? kw'arjini yayi mata sh'iyasa batason ganin tayi masa kallo cikin ido. "Aa dama Mama tace bakash'a ruwa ba zaka tafi sh'ine na biyoka dash'i. "Ok nagode ya fad'a yana ciro jarkar ruwa daga cikin motarsa, "ina dash'i in zansh'a basai kin kahomin ba ? right?, ya fad'ayana wani d'age gira dan haka sai anjima" yaja motarsa yabar gurin, wani malolon bak'in ciki ne ya cikata ganin yamai da'ita like statue, tafi minti uku agurin kafin daga baya taja matattun k'afafunta wanda da kyar suka iya d'aukarta tayi cikin gida, amma kafin tash'iga tasamu tad'an zubar da ruwan, dan kar Mama tasan besh'aba domin bazata ji dad'i ba. BAYAN SATI BIYU. Lokacin da zaa tsaida magana yayi, gash'i suna so acikin dangin babanta wani yazo domin ayi maganar dash'i, kowanne akaje gidansa sai ya nuna ai kawai su hak'ura, wani in sunje masa da maganar yakance a week d'in zebar k'asar haka dai har sukaje gidan wani kawun baban Ameenah, to sh'i dayake bawani me kud'ine sosai ba, sai ya yadda, amma da wajewar bazai yimusu kayan d'aki ba. Sukuma sun yadda saboda dai ayi abu cikin mutunci yafi. BAYAN WATA D'AYA. Antsaida bikin *Ameena da Ameen* nanda wata uku masu zuwa. Awata ranar alhamis da yamma Mamy tazo gida itada Haleema, aka dunga sh'igo musu da buhuhhunan sh'inkafa da macaroni da taliya su maggi gish'iri, doya dadai sauran tarkace wanda Abba ne yasa akaho musu, anannema Mamy take sanar dasu karsu bawa kansu wahala akan kayan d'aki d'annesu yace subarsh'i, sh'i zai musu komi, Godiya sosai sukayi, saboda sunji dad'i domin suna cikin zullumin kayan d'akin dama. Kai kuyi hak'uri nagaji da typing wlh Masoyana ina sonku aduk inda kuke kuma Foulani na amsar gausuwarku, Samee tawa Sameen Munay ina jin sak'on gaisuwarki sosai kuma ina amsawa, Allah yabar k'auna. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [19:06, 8/30/2016] "Yar Fara๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 67~68 BAYAN WATA BIYU. Lokacin biki yagaba to, ankaho lefe nagani na fad'a, duk wanda yazo yaganin kayan saiya yaba domin kyawunsu kuma kana gani kasan Naira tash'a kuka. Dan da Mamy da Haleema ne takanas sukaje dubai suka had'o mata kayan lefen sannan da furnitures dazaasa a d'akin. Me gyaran jiki takanas Mama ta d'auko mata daga sakkoto, tazo tana mata gyara, ko giftawa zatayi tawaje sai kinji k'amsh'i, haka ko zama tayi na d'an lokaci a wajen in ta tash'i, sai ta bar maka tsarabar k'amsh'i. A wata ranar alkhamis ana ya saura sati d'aya bikin Mamy ta sauko daga stairs, tayi d'akin Haleema dash'igarta tace"Haleema ko zakije gidansu Ameenah ki kai mata wannan, turarene me ky'au wanda na sayo mata a dubai. "Aa Mamy kingafa Yah ameen betab'a zuwa gidan nasu ba tun bayan zuwan dayaje kaita, kawai yanzu kice yaje yakai mata, "ok bari insa a kirash'i. "Mamy gani" Yah ameen ya fad'a yana tsugunnawa. "dama canai kaje gidansu Ameenah kakai mata wannan". Mamy ta fad'a tana mik'amasa ledar. Wani fad'uwar gaba yaji, yarasa meyasa indai zaa ambaci sunan Ameenah sai yaji gabansa ya fad'i..... "Ungo mana son" "ok" ya fad'a yana karb'a. Part d'insa yanufa yaje ya ajiye jakar a kan bed d'insh'i yash'iga d'aki, yayi wanka ya fito ya zauna a parlour yakunna Tv yana kallon tash'ar larabawa. Wayarsh'i ce tafara ringing yana dubawa yaga k'aninsa Habeeb ne me biyemasa wanda yake karatu a egypt, d'agawa yayi ya kara a kunnensa "Hello" "Hello ang"... Bek'arasa fad'ar abinda zaice ba ya katsesh'i "Dallah karka cikan kunne malam" Ameen ya fad'a da y'ar tsawa. "Kai Yah ameen wallahi kasauya hali, nifa inkayimin nayi hak'uri ita kuma fa?," " itawa?" Ameen ya tambayesh'i. "Amarya mana," Habeeb ya bash'i amsa. Nakusa dawowa fa Yah, i think on friday zandawo saboda I can't wait to see........Bye bye Yah . Habeeb ya katse wayar. Ai sai Yah ameen ya sh'iga tunanin maganar k'aninnasa Habeeb, " Yah mu in kayi mana mun hak'ura.....itafa wa?.....Amarya.... can't wai to see.........What?? "Mmtswww ya doka tsaki tare da jaho d'an fruit d'in gabansa yasomaci yana ta tunanin abubuwa da yawa. Sai da dare yayi bayan anyi sallar maghriba sannan yafita yayo wanka ya sh'irya cikin wata sh'adda dakakkiya tayi masa ky'au, am mata d'inkin boda. [19:07, 8/30/2016] "Yar Fara๐Ÿ˜˜: Hula ya kafa abunsa, ya fesh'e jikinsa da turare me d'an karan k'amsh'i sannan ya fito. Direct parking space ya nufa yad'auki motarsa har ya kunna ta ya tuna aiken da Mamy tayi masa "Mtsww yaja tsaki, sannan ya kash'e motar ya koma ya d'auko ledar, aransa yana mitar kamar sh'i wai zaa aikesh'i gurin k'anwarsa? yanzu inda zaice bazai jeba Mamy tayi fush'i, itakuma y'ar sa ido Haleema ta zuga"Mtsww ya k'ara jan tsakin, adai dainan ya hau motarsh'i yayi gidansu Ameenah. Kodayaje layin bakowa kuma babu yaron da zai aika, kawai sai yayi zamansa cikin motar, giftawar yaro yagani kamar ya huce, da sauri ya fito yana magana "Hi boy" "Hello" yaron ya amsa masa tare da mik'o masa hannu suyi musabiha, mamaki ne ya cika Ameen yaro k'arami kamar wannan yasan yayi musabuha da d'an uwansa musulmi lallai. "Yadai Yaya naji kayi sh'iru?" D'an yaron ya tambayesh'i cikin siririyar muryarsa. Murmush'i Ameen yayi najin dad'in ganin yaro k'arami me tarbiyya haka yakeson sh'ima ace yana da y'ay'a masu tarbiyya da hankali sh'iyasa yakeson yasamu y'ar mutunci da tarbiyya domin rayuwar y'ayansu ta inganta. "Dama aikenka zanyi nan gidan," Ameen ya fad'a yana nuna masa gidan. Dariya yaron yayi sannan yace"Ok gidanmu ne ai menene?, da mamaki Ameen yace "Gidanku?" "Lah eh mana" yaron ya bash'i amsa. Hmmm "Karb'i wannan ka kaima yayarka kace Mamy tace a kaho mata" Ameen ya fad'a yana mik'o masa ledar . Karb'a yayi sannan yace"Sunana Asleem" kaifa?, "Ameenullah" Ameen ya bash'i amsa fuska asake. Sh'iga gidan Asleem yayi yabata tare da gayamata yadda sukayi, tash'i tayi da sauri tayo waje dai dai zai sh'iga mota ta k'araso. Magana tafara cikin sark'ewar murya tace"Ka....cema..Mammyn. Nagode" Kallonta kawai yake yadda tayi wani haske gash'i jikinta sai wani sh'ek'in kyau yake, ga wani sihirtaccen k'amsh'i daya bugi hancinsa, k'amsh'in me sanyi sanyi, me dad'i, yakasa tantance wannan wami irin k'amsh'ine. Basarwa yayi yakalleta yawani yatsina hanci yace" Nid'an aikenki ne?,. "dan ita ta aiken kema cemiki akai kin isa ki aiken?............ Kuyi hak'urin rash'in typing wlh mun fara hidimar bikin sister ta.Shiyasa zaku dinga jina sh'iru. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:34, 9/1/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 69~70 Ameen yacigaba da magana da cewar"Koma wane ya gayyatoki nan gurin,? oho. Ya kad'a kansa ya sh'ige motarsa yabarta kamar statue. Itadai tana ganin ikon Allah, yanzu ace a haka za'ayi rayuwa? Mijin tanefa idan Allah yanufa, tunda baa d'aura auren ba. Amma yake mata haka. Gash'ita kuma kasa cemasa uffan take, saboda sh'e like the way dayake accting, yana matuk'ar burgeta sosai sh'iyasa sai dai tasaki baki, tana kallonsa. Murmush'i kawai tayi a lokacin dayaja motarsa yayi gaba. Gida ta sh'iga, taga turarene guda uku aciki kamfaninsu d'aya sai dai different na k'amshi ammafa turaren nan yahad'u iya had'uwa. "Kai Friendy nace miki babu komai wallahi ai i think Mamy tayiwa Mama bayani right,?, so kinga kar ki damu, wallahi its nothing, ai d'an lokacine pls kar kiyiwa Mamy maganar nan remain 5 days a auren nan fa. Ni inaganin better idan anyi auren amasa bayani tunda Iyayenmu sun san Good and kuma sun san Bad." Ameenah ce duk take wannan maganar ita da Haleema, akan wai Haleema tace kar Mama ta fuskanci wani abu tunda Yah ameen baya zuwa, gash'i koda bikin ya k'arato sai dai in da aike Mamy ta aika Haleema takai mata. Wai zatayiwa Mamy maganar kawai ya sani ya dunga zuwa fira. Amma ita Ameenah tace kar tasake tai maganar. Ahaka suka bar zancen suka sh'iga yin abinda zai fish'sh'esu. Biki ya k'ara k'aratowa. Komai anayinsa cikin mutunci da dattako, Event uku aka had'a d'aya namata zalla, d'aya ta iyaye ce, 'daya kuma ta ango da abokan ango d amarya da Family su. Randa aka kaho mata invitation Card tayi mugun mamaki ita yanzu ranar dinner zataga yadda zaayi, Ameen zaizo kuwa? Tayaya tunda besan amaryansa bace.? Anyi kamu inda aka kira Wata malama wato Aunty YBK tazo tayi lecture akan zamantakewar Aure, lecture d'in ta fad'akar sosai, matan aure wad'anda basa bin mazajensu jiki yayi sanyi. Aunty Ybk ta zuba bayani, sai dai muce Mamala Allah saka da alkhairi. Anyi party inda k'awayen Ameena sukazo sosa tayi mmaki, ash'e duk Haleema tasanar musu kuma sunzo. A yaune zaayi dinner da daddare, inda Aka sh'irya amarya cikin wani d'an ubansun kaya, fuskarnan tash'a gyara ga wani uban k'amsh'i datake zubawa, jikin nan ya d'au jan lalle da baki, gash'i tawani dad'a cika k'irjinta ya k'ara cikowa Mash'a Allah. "Mamy hidimar me ake a gidan nan ne? Ameen wanda yake zaune kusa da ita yana tambayarta. ®NWA [08:35, 9/1/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: "Biki muke"Kawai ta bash'i amsa. "Bikinwa"? ya k'ara tambaya. "Ta d'ana mana aa Ameen kar kayi disturbing d'ina fa okay," Mamy tabash'i amsa cikin zafi zafi, sh'iru yayi yana nazari to wane d'anta kodai Habeeb ne tunda dama yaji yace masa zai dawo? but be k'are karatunsa ba how,? kaf maganar da sukayi da Habeeb ta k'ara fad'o masa arai, to s'hifa be gane komai ba, actually dayagaji sai yabar tunanin. Ya d'ago ya kalli Mamy yayi fuskar tausayi yace" Yanzu Mamy a gidanan nine babba amma bazaki iya gayan komai ba. Kuma koma bikin wakike ai yakamata ace kin fad'amin mana, Yak'aresa yin maganar kamar wani maraya. "Ameen nasan halinka ne, sh'iyasa kaga ban fad'amaka ba, aiko lefe kamata yayi ace kai nabawa but dakaina naje saboda sanin halinka." "Haleena Mamy?" ya tambayeta da mamaki. [08:36, 9/1/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: "Eh to tambayar ta isa haka dan kai ba d'an jarida bane ehhe". Misalin bakwai dai-dai Haleema ta fito taci kwalliya tayi kyau cikin ashoben biki, d'akin Yah ameen ta nufa a bud'e yake tayi sallama ta sh'iga. "Yah Mamy tace tana son ganinka yanzu yanzun nan". "Ok" ya fad'a yana kash'e tv. "Mamy gani". "Yawwa Darling son kasan meye?" girgiza mata kai yayi alamar aa. "Dama yau ne Dinner d'in d'ana so kuma bazai samu damar zuwa ba saboda yayi tafiya, to shi ne nakeson cin arzik'in kaje dinner a matsayin kaine angon, kaga bedace ace anbar amarya ba ango ba ko?". Sh'iru yayi yana tunanin wannan rainin hankalin da akeson yi masa, yazaai amarya bata saba kawai yawani je dinner yayi replacing ango?, "cab I can't wallahi" ya fad'a a zuciyarsa. Mamy ta kallesh'i tare da cewar"kai nake saurare Darling son". Numfash'i yayi kafin yake cewa" I'm sorry to say gaskiya Mamy bazan iya.....zu.......waba. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:27, 9/6/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 71~72 "Son yanzu amatsayina na Mahaifiyarka insaka abu kuma kak'i yimin? "Ni Mamy bawai nak'i yimiki bane, wallahi Mamy ni bazan iya zuwaba kawai nawani yi replacing ango,? da sh'i angon yasan da Dinner d'in amma yak'i dawowa koma inayaje oho masa. Mamy ce ta k'ara magana da cewar" d'an uwanka nefa? yanzu bazaka iya sh'aremasa hawaye ba? "wane d'an uwan nawa to? Mamy tanason yaje dinner dan haka data tuna Habeeb zai dawo kawai sai catayi masa"Amaryar k'aninka Habeeb cefa?. da sauri Ameen ya juyo yana zare ido yace"yanzu ni.........Ni....Zaku aurar da k'anina ban sani ba....?Amaryar k'anina kuma zanje in replacing haba Mamy ai ta rainanima wallahi, kuma ma ai bansan da bikinba dan Haka Allah sanya alkairi amma bazani ba. Aransa kuwa tunanin rash'in kunyar Habeeb yake gani? watakan dan zaayi masa aure sh'ine ya kirash'i yana masa wannan fitsarar lallaima. Mamy ce ta katseshi dan ta fuskanci idan tayi masa sh'iru wallahi tunda yace bazash'inba bazash'i ba dan tasan halin d'an nata "Darling Son umarni nake baka kayi maza-Maza ka tash'i kaje d'akinka ka sh'irya zansa akaho maka kayan da zakasa." Tana gad'in haka ta wuce stairs tayi d'akinta ta barsh'i anan. Babu yadda yaso dolensa ya tash'i jiki asabule yaje yayi wanka yafito, akan kujerar parloun sa yaga an ajiye masa sabbin kaya masu mugun ky'au. Ya da'auka yayi d'aki dasu, mai kawai ya sh'afa ya gyara sumar kansa tayi luf-Luf, ya kafa hularsa zuciyarsa nata k'una. Haka yaje gaban mudubi ya kalli kansa "Woww nayi ky'au kamar nine angon(Hmmm nidai Foulani ina ganin ikon God)". Fitowa yayi yash'iga ciki yace mata ya fito, wata sabuwar motace fil aka fito da'ita, Driver ne ya bud'emasa motar, Mamy danjin dad'i har parking space d'in tabiyosh'i tana fesa masa wani irin turare me sh'egen k'amsh'i. Hannu take d'aga masa alamar Bye bye, but gogan naka sai yayi gefe da kansa a dole fush'i yake da takuramasan daakai. Driver gidansu amarya ya nufa, sh'iko Ameen bece masa k'ala ba sai binsa da ido dayayi. Ada-dai nan aka fito da amarya, ga motoci sai d'iban mutane takeyi wad'anda zasuje dinner, dama su Haleema tuni sunnyi gaba. Dan haka Aka fito da ita drivern ne yafito ya bud'emata bayan motar, tash'iga ai bata ida zama ba taji dumm rass gabanta ya fad'i amma sai ta fuske tazauna driver yakoma mazauninsa yaja mota. [12:34, 9/6/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Kod'agowa Ameen beba inbanda danne-danne dayakeyi a phone d'insa, K'amsh'intane yafara damunsa duk k'amsh'in yacakud'e danasa da nata, sai suka had'a suka bada wani sihirtaccen k'amshi ne me kwantar da hankalin wanda yajish'i. Zuciyarsace ta bash'i daya kalli fuskar matar k'anin nasa, wacce ko gaisuwa bata iyaba, tasan ba angonta bane amma ta kasa koda gaidash'i,?. Azuciyar Ameenah kuwa tunani take tayaya yazo dinner? dan a iya saninta besan bikinsa akeba, to kodai yasanima tunda gash'i zaiyi attending dinner d'in? Tanaso ta koda gaidash'ine amma tana tsoron balainsa kar ya gwale ta sai taja bakinta tayi tsit bace kala ba. Juyowa Ameen yayi da niyyar kallonta amma sai yafasa, turarentane yake addabarsa dan wani iri yakeji ajikinsa, ta maza yayi, yad'an saci kallonta, ita kuma kamar tasan abinda yake ta juya kanta gefe tana kallon titi, don haka bewani ganeta sosai ba" auxubillahi munashshaidanirrajim kawai yake fad'a aransa dan yaga sh'aid'an nason angazash'i kallon matar da batasa ba matar k'aninsa Habeeb. To you all my fans ina baku hak'urin rash'in typing dabanayi, hakan yafaru dasanadin bikin damukayi, kuma bayan mun gama wallahi rash'in lafiya takamani but nafara jin sauk'in jikina yanzu zakudinga jina ko yayane Tnx u all๐Ÿ˜˜ ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:08 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [15:47, 9/7/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 73~74 Aransa yake tunanin ai duk laifin na Mamy ne tada tilasta masa zuwa dinner k'aninsh'i abinda bemasan anayiba, kenanma da Habeeb d'in zeyi attending dinner d'in bazai san ana bikinsa ba? kenan sai daima kawai yaga anayi kamar yadda yanzun yaga anayi, dan dai ansan yana da amfani sh'iyasa ma aka fad'a masa."Mtswww" yaja tsaki a fili. Juyowa tayi dan ganin dalilinsa nayin tsakin, karaf tana juyowa suka had'a ido, ido cikin ido yake kallonta yad'an k'arawa idonsa girma da mamaki k'arara a fuskarsa, itakam saroro tayi tana kallonsa, tunda anata tunanin yasan komai tunda gash'i zayaje dinner amma kuma ya'akai taga mamakin ganinta dayayi?. Ameen ne yayi wani kw'akwkwaran numfash'i ya nunata da yatsa yace"da.....Ma..Kece Habeeb ze aura?"lallai ya girgiza kansa alamar mamaki. Aransa tunani yake tayaya,"how"suka fara dating juna da brothern sa anyama kuwa Habeeb yasan meyake? dazai zab'i wannan mara kunyar yarinyar amatsayin mata? uwar y'ay'a? yarinyar da ba y'ar gidan *NAGARTA* ba (Littafin y'ar uwa). Itad'inma tash'iga duniyar tunani sai dai bata zurfafa tunanin ba akazo gurin partyn. Driver ne yayi masa maganar an iso. Kasa fitowa yayi inda itad'inma tak'i fita tayi zamanta. Ana hakane masu ashobe suka fiffito a'inda Haleema tayi wajen motar ta bud'e wani k'amsh'i taji ya daki hancinta ga wani irin ky'au da Amarya da angon sukayi,batasan sanda tace"Woww so cute". Tajaho hannun Ameena tafito, sannan ta jaho hannun Ameen, bamusu yabiyota. Masu ashob'en ne wasu a gabansu akasa su a tsakiya sannan wasu a bayansu. Kamo hannunsa tayi ta kamo hannun Ameena ta had'asu guri d'aya"Wayyo Allah zo kuga yadda Ameen ya watsawa Haleema wata sh'egiyar harara, Sarai tagansh'i memakon tabar abinda take ina ai saima tayo saitin kunnensa tace"Pls Yah kasaki jikinka kar agane ba kaine angon ba". Wak'a aka saki me taush'in dad'i. Daga kan stage d'in dazasu zauna wajen da d'an duhu amma suna zuwa haske ya haska sai ga Welcome dara-dara daga bayan decoration haske ya haskaka koina tuni aka fara Dinner. [15:47, 9/7/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Haleema ce tafito tabada tarihin ango kuma tabada na amarya kuma tace Ameen da Ameena soyayyace me matuk'ar gaske a tsakaninsu kamar laila da Majnoon ko kuma ace romeo da juliet. Inda ta k'ara da cewar basa tab'ayin nesa da junansu, saboda tsabagen soyayya da k'auna da kulawa. A k'arsh'e tace Dan Allah kowa ya tafawa wad'annan couples d'in. Aiko tuni aka d'au tafi Raf raf raf. Cake aka nemi yankawa aikuwa zo kuga Ameen yadda yawani had'e rai ya yanka ta bud'e bakinta duk tsoro ya cikata yasa mata, itama ta yanko tazo sa masa memakon yaci iya Cake d'in sai ya had'a harda hannunta. Camera tafara haskawa ta koina anata uban tafi masu d'aukar vedio nayi masu camera ta waya suna d'auka. In banda harararta ba abinda yakeyi, itadai duk ta tsani kanta a gurin, ankira ango da amarya wajen rawa hannunta yana cikin nash'i suka fito, y'ar rawa tafara a hankali, saboda kar tasaki jiki taji duka dan ze iya dukanta ma ayadda yake aikamata da sak'on harara. Haleema ce ta hayo ta musu lik'i duk da ba rawa suke ba. "Ke yau nefa kinsan sai kinyi rawa wallahi duk wannan rawar taki bazata tash'i a banza ba." Haleema ce tayi wannan maganar. Inda tasanarwa dame kayan sauti akan ya sauya kid'a, atake kuwa yasa wakar nan me tsuma zuciya me taken Wayyo mijina k'aunarka na tsumani". Wak'arnan ta narkar da zuciyar Ameen yadda take bin wak'ar tana d'an juyawa tana kallonsa dan yasan dash'i take. Aiko camera sai tak'aru, lik'i yayi mata da kansa saboda ta burgesh'i but tafa bash'i haush'i. Yajaho hannunta duk da yasan ba Matarsa bace hasalima matar k'aninsa ce Habeeb. Dawannan zanyi amfani in taya y'ar uwata k'awata Ummul Fadeela gama littafinta me suna NAGARTA. Tabbas littafin nan yayi dad'i uwa uba ya fad'akar tawajen dogara da Allah da kama addua ako wani Hali mutum yake. Baabinda zance sai dai ince Allah ya k'ara baseera Foulani na miki jinjina ๐Ÿ‘๐ŸปFoulani's Fans sun baki kyautar............. "toh nasan har su"oo da "oo sun zuba kunne dan suji bazan fad'a ba๐Ÿค”. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [10:31, 9/8/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 75~76 Hotuna aka sh'igayi Haleema tajaho sh'i akayi musu tare sannan suka sash'i a tsakiya aka d'auka. Ransh'i ya b'aci amma bayadda zaiyi gash'i Haleema sai nanik'a jikin Ameenah take dana Ameen anayi musu hoto, haka dai akaita budiri inda na hango Y'an K'ungiyar Nagarta sunata sh'aani, cima kala-kala, kowanne yana ta sh'aaninsa haka na hango y'an Excellent Hausa Writers suna ta hira dan kunsan su sarakan surutune, hakama baa bar Y'an group d'in Foulani's Fans sai da suka halarci gurin, ni kuwa Foulani ina Manne da Haleema duk inda tayi dan in kwaso muku labari ku biyoni. A haka dai Dinner ta wats'e ainda tun kafin atash'i Ameen ya yatash'i da niyyar tafiya dan ya gaji kuma gurin ya gunduresh'i, ai yana tash'i Ameenah itama ta tash'i tare da yin saurin rik'e hannunsa, kallo kawai yabita dash'i a ransa yana Allah wadai da halinta tasan bash'ine mijinta ba amma ta'iya rik'emasa hannu eh lallai bata da kunya. Fitowa sukayi Driver na ganinsu yabud'e musu k'ofa suka sh'ige cikin motar jan motar yayi yabar gurin Partyn. Ahanya ne wayarsa dake hannunsa yanata latse latsensa wanda da alamar chatting yake. Duba sunan yayi sannan ya ja Little broo tsaki"Hello" "Big broo gaskiya naji dad'i dakayi replacing d'ina wajen dinner na gode so........"Dallah can yimin sh'iru wallahi kafin ranka ya bac'i." "Aha sorry broo kayi hak'uri yanzu dai ina Amaryar .tawa" Habeeb ya tambayesh'i da tsokana. "Nasayar da ita kawai yace tare da katse wayar. Agidansu Ameen kuwa Haleema ta koma gida tana ta bawa Mamy labari had'i da nunnuna mata photon da akayi gurin dinner, Anan Mamy take bata labarin plan d'in da suka had'a akan auren Habeeb akeyi, sai dai kawai yaji an d'aura aure dash'i idan ya tambayi ya haka Abbanku sh'i zaibash'i amsa." [10:31, 9/8/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: "Wow Mamy kinyi a rayuwa kinsan idan yasan aurensh'i ake bama zai yadda ba kwata-kwata" . "Wallahi kuwa". Wash'egari d'aurin aure inda Ameenah tana d'aki gabanta sai fad'uwa yake an mata kw'alliya cikin wata dakakkiyar sh'adda taji aiki, aka d'aura mata d'an kwali yayi kamar Head, Abangaren Ameen kuwa tun bayan da yayi sallar asuba yakoma ya kwanta yayi ta bacci, Inda da Misalin k'arfe Tara da rabi Habeeb ya sauka a nigeria, Ameen nata bacci Habeeb ya sh'igo d'akin ya taddash'i sai bacci yake zubawa aransa yace wai ango ne har tara da rabi be fara sh'irin d'aurin aure ba. Duka yad'an d'ala masa tare da fad'in Ango ka tash'i" mana" Gyara kwanciyarsa ya k'arayi, Habeeb ya k'ara sakar masa duka yace"Big broo ka tash'i yau nefa d'aurin aurenk.....Kafin ya k'arasa ya tuna da maganar da Mamy ta fad'a masa sai yafasa k'arasa fad'ar abinda yayi niyya. Motsi Ameen d'in yafara da salati ya tash'i a bakinsa ganin k'anin nasa yasa yaja tsaki saboda sh'i duk haush'ima yake bash'i ya rasa matar da zai aura sai wannan yarinyar da bata da kunya ko kad'an. Tash'i yayi sannan ya fad' toilet yayo wanka ya fito d'aure da towel, sh'ima Habeeb d'in fitowarsa daga wankan kenan, Wani bowel ne me ky'au da tsada Ameen yasa ya fesh'e jikinsa da turare kamar yadda ya saba. Habeeb sh'ima yafara sh'iryawa sannan yaciro yasa, ya juyo saitin yayan nasa yanason yayi masa maganar ya sauya kaya tunda aurensa ne, amma yanajin tsoro kar yaji kuma Mamy ma taja masa kunne, hikimace ta fad'o masa wasu kaya ya d'auko y'an ubansun kaya kuma sunyi mugun ky'au, d'inkin babbar rigane yayi ky'au ga takalmi da agogo komai yayi matching yace"Big broo a matsayinka na yayan ango ai kamata yayi kasa wad'annan ko? ya d'age masa gira, Mik'o masa yayi ya ajiye kan mirror. "Kai karfa ka takuran, wallahi na fasa zuwa ma d'aurin auren," "Aa broo kar ayi haka ai kaga irin a baka girman nan ko? babban yaya guda haba pls kasaka mana". "Mtsww" yaja tsaki sannan ya bud'a kayan Woww sunyi ky'au ya fad'a aransa to ko yasa? "Kai nifa ba ango ba bazan sa kayan nan ba," "Aa broo irin babban yayan nanfa pls kasamana kaga goma fa yanzu kuma goma da rabi zaa d'aura". Ameen ya fuskanci idan besa kayan nanba to sai ya sh'iga uku a wajen Habeeb, dan haka kawai yajaho kayan yana tsaki yasaka badan yaso ba. "Woww wannan wanka yafita fit wallahi" Habeeb ya fad'a da dariya a fuskarsa. Mudubi yakalla yaga yayi kyau ba k'arya, amma sai cayayi"Meye wani abin ky'au anan,? "Eh dai"Habeeb yayi masa gwalo. Sh'ima Habeeb wasu kayan yasaka sun masa ky'au, turare ya d'auka ya fesh'esu da turare ya kamo hannun Ameen suka jero a tare cike da so da k'aunar junansu. Ameen yana son Habeeb, kamar yadda sh'ima Habeeb yake sonsa, sunayin komai cikin had'in kai da y'an uwantaka. Wata sabuwar Mota Habeeb yaja, ya bud'ewa Ameen gidan gaba ya sh'iga sh'i kuma Habeeb ya zauna sit d'in driver yaja motar sukabar gidan. Am sick Need your prayers pls. ~Maman triplet~ [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 77~78 Wak'a me dad'i ce ke tash'i daga cikin motar, Ameen ne ya kash'e wak'ar yanawa Habeeb fad'a akan yawan jin wak'e-wak'en dayake. Adai dai nan sukazo gurin d'aurin auren, inda mutane sukayi taron dandazo, yawanci abokan Abba ne na kasuwanci, da kuma abokan Ameen wanda yayi matuk'ar mamakin ganinsu tundash'i beyi inviting ko d'aya a cikin Friends d'insa ba. D'aurin aure aka fara inda Ameen yayi wajen abokanansa, me Camera ne yamusu hoto, bayan nan yake tambayar ya akai sukasan da auren? "Ango Ango kash'a k'amsh'i" wani Abokin Ameen wanda yake best friend dinsh'i yake tsokanarsa. Ameen yabud'i baki kenan zaiyi magana ya juyo wani marok'i yana fad'in"Alhamdulillah Ranar tazo Lokaci yayi, An d'aura Auren *AMEENU DA AMEENA* akan sadaki Naira........ai Ameen jiyayi kunnensa ya dod'e ganinsa yana kok'arin d'aukewa, da sauri yabar gurin abokanan nasa yayi wajen da Abba yake, ai Abba yana ganosa yataho a sukwane, da sauri ya had'e rai, yana k'arasowa ya bud'i baki da niyyar magana Habeeb dake tahowa ya wulla masa Sweet a baki yace"calm down sh'a alawar aurenka," Jaho wuyan rigar Habeeb yayi yace"Little broo me kakejin marok'an nan na cew???.....Ai Ameen be k'arasa magana bama kunnensa ya k'ara juyo masa tare da tabbatar masa cewar An d'aura auren *AMEEN DA AMEENA* "Why? hawaye ya cikomasa idonsa Habeeb dake tsaye yayi saurin jansa yasash'i a mota yash'iga yaja motar suka bar gurin. Gida suka nufa, suna zuwa Ameen yayi sash'en Mamy, kaf y'an bikin ya iya hucewa ya tsatstsalakesu, wasu daga cikin tsoffin sunata tsokanarsa amma kota kansu be biba. Mamy na zaune gaban Mirror tana d'aura d'ankwalinta Ameen ya sh'igo a hargitse idon nan yayi jajir, sai uban gumi yake tafkawa, gefenta yazauna ya rik'o hannunta, yafara magana cikin sh'ashsh'ekar kuka"Mamy Why???"Why Me? "Why always Me?? . Ya fash'e da kuka tare da kifa kansa jikin Mamyn. Yayi matuk'ar bawa Mamyn tausayi, ganin jarumin d'anta yana kuka ya matuk'ar tsorata ta. kunsan uwa da tausayi cikin siga ta lallash'i tafara magana tana sh'afa gash'in kansh'i da yayi luf-luf "Son"My Darling Son banason ganinka cikin yanayi na damuwa kozan iya sanin meyake damunka? meya tash'i hankalin gwarzon d'ana?. Kar kamanta agurin Mahaifiyarka kake me sh'are maka kukanka, ka gayan meyafaru." Jikinsh'i yayi sanyi dajin abunda Mamyn ta fad'a, ya d'ago runannun idonsa yace"Mamy waye Ameenah?? Aurenwa aka d'aura?." Numfash'i dasaki dan tasan k'arsh'en zancen kenan dan haka ta d'an kalli fuskarsa da damuwa a tata fuskar tace"Son Matar mutum kabarinsa, babu yadda zamuyi, Abbanku sun fita da niyyar d'aura auren Habeeb da Ameenah, amma cikin ikon Allah sai Abbanku yake ganin kwata-kwata Habeeb be isa aure ba kaga ko karatunsa be k'are ba sh'iyasa kawai ya yanke sh'awarar d'aurawa dakai tunda kaima ba auren garekaba, kuma Abbanku beyi haka ba sai dan yasan zakayi masa biyayyaya". "Habeeb fa Mamy yanason yarinyar nan itama tana sonsa meyasa zaku rabasu kuce kun had'ata dani Alhalin ba tsarina bace," yana kaiwanan yajiwani bak'inciki ya danfare masa zuciya. Lallash'insa Mamy tayi tayi har tasamu yadaina kukan, sannan tasa aka kahomasa abinci tasash'i a gaba da ky'ar yaci rabi yash'a ruwa. Part d'insa yakoma inda ya tadda abokansa sunata sh'aaninsu tsaki yaja yayi d'akin Habeen yaci saa bakowa ciki dan haka yash'iga yakulle kansa a ciki. Acan gidansu Amarya kuwa sh'aani ake tayi, amarya tana murna kuma tana fargabar zaa kaita gidan mijin da bayasanta hasalima ya tsaneta tana tunanin irin zaman da zasuyi. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* By FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 79-80 Ameena kam kuka take kamar ba gobe lokacin da aka kaita wurin Mama domin yi mata haduba. Mama ma tana jin wani abu a rai amma ta dake don kada ta kara dagama Ameena hankali. Sai da ta dan kai-kaice idanun mutanen dake dakin sannan tasa habar zaninta ta share kwallan da ya fito mata. Ameena kam kanta a doke yake gyalenta ya rufe fuskarta. "Maman Ameena ki ce wani abu don Allah, ga 'yan gidan ango can na jiran a basu amarya" Fadar wata daga cikin kawayen Mama. Sai da ta numfasa sannan ta ce "Yi bari na bari da biyayya ga miji shine cikon zamantakewa na aure. Hakuri kuma shine jigon rayuwa, tsaftar jiki da ta muhalli Ameena ya zamo koyaushe kina yinsa. Amina kiyi hakuri da mijinki duk runtsi kada ki kawo kararsa haka kuma kada ki bari ya kawo taki, ki zamo mai hakuri a rayuwar aurenki, don Allah ki rike ibadarki da addininki duka...." Muryar Mama ta sarke saboda kukan dake son kwace mata. Tada Ameena aka yi da niyar tafiya, ai kuwa ta rirrike Mama tana kuka tana fadin "Mama ba zan iya tafiya na barku ba....." Na kara rushewa da kuka. Haka aka lallasheta aka sata mota zuwa gidan angonta. Haleema kam ta kasa daurewa dole sai da ta koka. A Lamido crescent aka kaita, inda gida yasha tsari mai kyau, aka zuba kayan furnitures masu dan karan kyau. Dakin da aka ware mata aka kaita cikinshi, kan gado aka yi mata nuni da ta zauna. Masu huduba da masu zolaya duk suka shiga yi mata tareda lallashinta. Tayi shiru sai dai sheshshekar kukan ne har yanzu, abu biyu idan ta tuno yake sata kuka wato rabuwa dasu Mama da makomar auren Ameen. Gidan tsit kowa ya watse an barta ita kadai, ta saka wannan ta war-ware wancen, zancen zuci ya dabaibayeta. Ji tayi an shigo hakan yasa tayi saurin gyara zamanta tareda kara jawo gyalenta. Shiru kuma taji, sai ta fara ambaton Allah a zuci, ita kam tasan wulakanci har na saidawa sai ta same shi wurin Ameen amma ya ta iya tunda kaddarar aurenta ne haka. Likowa yayi ya ganta a zaune, wani bacin rai yake ji a zuciyarshi, wani wawan tsakin da yaja sai da tayi saurin dago kanta. Wata uwar harara ya aika mata sai tayi saurin kai kanta kasa, ledojin da kawayenshi suka sawo domin amarya ya jefa mata su ya wuce yana jan tsaki. "Buduwar Habeeb ce wai yau aka aura masa? Yarinyar da bata da kunya.... Mtsw" Ya karashe maganar yana tsaki. Kan doguwar kujera ya kwanta idanunshi na kallon sili. Ameena kam wani babin kuka ta bude, tayi ta gaji ta tashi ta sauya kaya zuwa kayan bacci sannan ta hau gado ta kwanta saboda zazzabin da taji ya rufeta. Ameen wanda ke kwance kan kujerar parloun tunani yake tayi barkatai, tunanin maganar Abbansa ne suka dawo masa kwanya lokacin dayasa aka kira masa Ameen d'in cewar; Auren dayayi masa bayayi dan ya k'untata masa bane, sai dan ya faranta masa. Yakuma k'ara bash'i hak'uri akan rash'in saninsa na d'aura auren sh'ima abin yazo masa a bazata ne. Abinda yake k'ara k'onawa Ameen rai lokacin da Abban yasa aka kira Habeeb sh'ima yayi masa nasiha da yayi hak'urin rabash'in da akayi da budurwarsa wacce yake tunanin aura. Habeeb kuwa yayi k'asa dakai kamar gaske,. Daga k'arsh'e Abban yak'ara cewa da Ameen beyadda yaji wani abu na tash'in hankali yafaru tsakaninsa da Matarsa ba. Ko yaji wata magana ta saki to wallahi sai yayi mummunan sab'a masa. Daganan yayi musu addua yace su tash'i su tafi. Tsaki Ameen yaja tare da tash'i ya d'auko ruwa a Fridge ya kurb'a ya k'ara komawa kan doguwar kujerar da yake kai, a ransa yana sak'a irin rash'in mutunci da wulak'ancin da zatash'a, Matar da K'aninsa keso? Ace wai yau itace matarsa, "God Forbid" ya fad'a a fili. Nikuwa Foulani danake a lab'e nace"Daga baya kenan๐Ÿ˜›". ~Maman triplet~. [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* By FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 81~82 Tunani da ya ish'esh'i ya kunna Tv dake jikin d'akin tash'ar larabawa ya kama tun yana kallo har 'barawo me iya sata ya sacesh'i. Zazzab'in yatakura mata amma dataja blanket ta rufa sai ta ragejin sanyin, itama d'in tunani ya addabeta daga haka bacci yad'auketa. Guraren k'arfe 4:50 ta tash'i, jikinta yad'an rage mata daga zazzab'in datske. Toilet ta sh'iga tayo alwala tazo ta sh'imfid'a sallaya, ta tada sallah tayi rakaatal fajiri, sannan tayi asubah bayan ta idar ta duba ta d'auko qur'an d'inta tayi izif d'aya sannan tayi adduo'i. 7:45 Ameenah tana Kitchen tana had'a musu breakfast, tuni gidan ya d'au k'amsh'in abincin. Bayan ta gama ta d'ebi nata ta kaiwa Ameen nasa Dining ta jajjere masa ta koma d'akinta, tunda dai bataji motsin mutum a gidan ba bayan ita. Tunda ta sh'ige d'aki bata k'ara fitowa ba sai da Azahar lokacin wasu y'an uwan Mama sunzo. Koda taje da niyyar musu girki ta tadda breakfast d'in yadda ta barsh'i babu abinda ya tab'asu. D'aukowa tayi ta kawa bak'in sannan ta kaho musu lemuka da ruwa. Bayan sun tafi takoma Kitchen d'in ta wawwanke kwanukan sannan ta d'ora na dare tunda itadai yau bataji koda motsin miskilin mijin nata ba. Bayan tagama kamar 'dazu ta jere kan dining takoma d'aki. Sh'iru-sh'iru babu mutum, tunani ne ya dabaibayeta, kowani ango ranar aurensa yana murna, wash'egarin aurensa yanajin wani nish'ad'i dajin dad'i amma banda ita danata angon,. Wanda tun bayan daya jefomata leda bek'ara bi takanta ba, hasalima bata k'ara jin d'uriyarsa a gidanba. Zaman sh'irun ne ya ish'eta gash'i duk ta gaji da kwanciya dan haka ta fito Parlour, kafin ta k'arasa takejin Tvn d'akin nayi da mamaki ta fito. Turus taja ta tsaya jitake kamar ta koma da baya, amma sai ta dake tak'araso cikin tsakiyar parloun d'aya daga cikin kujeran ta zauna tace" Barka da yamma" Sh'iru ba amsa sema juya kansa da yayi gefen da baya kallonta, Murmush'i tayi ta k'ara da cewar" Breakfast yayi ta jiranka Lunch yadad'e da jiranka, sannan ga Dinner d'inka can sh'ima yana jiran........ Ai bata k'arasa ba Ameen ya daka mata wata wawar tsawar dani kaina Foulani sai da phone d'ina ta kusa fad'uwa . "Ke Shut up!!! "duk waya baki damar yimin wad'an nan maganganu?", "sh'egen surutun banza. "Tash'i ki bani waj, ai be k'arasa Ameena tafara turje turje sai ta fash'e da kuka da gudu tabi d'akinta. Mamakine ya cikash'i, lallai yarinyar nan ta isa, cab aiko zan gyara miki zama, jibi yadda tawani fash'e da kuka kamar ya daketa, zan sh'iga dukanki inyaso kiyi kukan da hujja "Mtsww". Oh Ni Foulani Wlh kayi a hankali da wannan tsakin, wataran sai kaje ka tsinka bakinka da kanka". Happy Happy Happy Sallah to you All My Fans Wannan page d'in na sadaukar dash'i ga duk meson Wannan novel kuma Ameena da Ameen suna yi muku barka da sallah, dan har sak'o Ameen ya bani yace in sanardaku kuci Nama a Hankali, 'yan ukuna ma baa barsu bayaba sunce Aunties d'insu sucimusu Naman Sallarsu๐Ÿ˜ŠHappy Sallah to All Muslims Ummah๐Ÿ‘๐Ÿป Ayi salh lafiya. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* By FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 83~84 Wash'egari da Misalin takwas tagama breakfast tajere dining, tayo wanka wani riga da skirt tasa na Atamfa d'inkin yahau jikinta ta yafa wani mayafi d'an ziriri, tafesh'e jikinta da turare musamman ma da akamata wannan gyaran na turare, sai turaren yabada wani daddad'an k'amshi, fitowa tayi tayo parloun ta zauna tana kallon Mbc Bolly wood suna film d'in Agnipath. Dawowar Ameen kenan daga gida domin kuwa bama a gidansa ya kw'ana ba yana gidansu a part d'insa yayi bacci yana tashi yayi wanka yafito wajen gate dan anan yabar motarsa, ya dauki abarsa yayo gida. "Ina Kw'ana" Ameena ta gaidash'i. Ko kallon inda take beba, itakuma tayi tunanin ko beji bane tak'ara cewa"Ina kwana" "Mtsww daban kwana ba kin ganni". Yana fad'ar haka ya sh'ige d'akinsa ya kulle. Ganin har tara befito cin abinci ba taje k'ofar d'akinsa tayimasa knocking "Waye ne" Ameen ya fad'a da balai. Ameenah tayi sh'iru kamar bazatayi magana ba sai kuma tace"Dama..c...nai breakfast zaka zo muyi". "Waye zaici jakwal kwalanki wallahi kibar nan ko infito in zane ki". Duka??? wallahi baka isaba kuma ba inda zani Ameenah ta fad'a a ranta. Jin bud'e k'ofar yasa ta kwasa da gudu tay d'akinta tasa Key dan kar yabiyito yadaka. Bayan Sati d'aya. Kwata-kwata Ameen baya kwana a gida, in dare yayi sai yatafi gidansu yaje part d'insu ya kwanta, in safiya tayi yatafi office, idan ya dawo ya d'an zaga gari sannan in dare yayi sai yataho gidansu ya kwanta. Koda Ameena ta duba ba motarsh'i, d'akinsa kuma a kulle yake, kwata-kwata ma batajin motsinsa ko kad'an, Hakan ya bata damar sakewa a gidan tana fitowa sosai, wataran kuma ta kunna tv tash'ar Music Plus ko Mazzika su tafi sawa kawai saboda tanason wakokin larabawa da rawarsu . Yauma zaune take kan kujera ta d'ora kafa d'aya kan d'aya ta kurawa Tv ido kamar me kallo amma ina kwata- kwata bawai tana kallon abinda take ganin bane, tunani take ina yake zuwa? tasan dai ba a gidansu yake kwana bato ina yake zuwa?, "Allah ka karemin mijina a duk inda yake Allah ka karesh'i daga sh'arrin matan zamani" Addu'ar datayiwa mijinta kenan. Bud'ewar gate taji da sauri ta lek'a" Ameen d'ina" ta fad'a a fili tare da zubowar wata y'ar kwalla kallonsh'i take a hankali komai nasa burgeta yake"Inason wannan bawan Allah" Ameena ta fad'a a fili. Komawa tayi ta zauna sakamakon sh'igowarsa. ya sh'igo tsakiyar parloun tace"sannu da zuwa" be kalleta ba in banda kallon Tv dayayi ya girgiza kai, tare da d'aukar remote ya sauya channel d'in ya sh'ige d'akinsa. Yunwace ta damesh'i dan baison cin abincin waje, kuma Mamy bazata yadda yaci mata abinci ba cazatai ina matarsa, kullum sai dai yash'a tea da biscuit, yau kuwa yunwa ta damesh'i ga kulolin abinci a ajiye dan koda Ameen baya nan kullum dash'i take girki, sai dai baa d'auka hasalima baya kwana a gidan. Cikinsh'i ne ya fara ciwo, yarasa abinyi, idan yayi mata magana ajinsa ya zube matar da k'aninsa keso? budurwar k'aninsa zaiwa magana, ya gayamata matsalarsa, wallahi aa sai dai ciwon cikin ya kash'esh'i. Sosai cikinsa kemasa ciwo, nish'i yake a hankali,. Ameenah take k'ofar d'akin tanason yin knocking ta tambayesh'i ko akwai abunda yake so? amma tana tsoro gash' tazo tadda yana nish'i kamar mara lafiya. "Yah ameen"Yah ameen" whats wrong? sh'iru ba amsa ga nish'in sai dad'uwa yake. "Whats wrong? are you ok?? noh?? pls open the door. "Yah ameen" hankalinta duk ya tash'i batason taga wani abu ya samesh'i. Gawani uban nish'i dayake, tabbas jikinta ya bata baya da lafiya. "Mezanyi inceci mijina?". ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:09 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [06:00, 9/16/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* By FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 85~86 Buga mush'i k'ofar take 'karayi, "Ameen ka bud'emin " Ameena ta fad'a da tausayi. Nish'i yake sosai saboda cikinsa . Zunbur tayi ta tash'i kamar wadda ta tuna wani abu, d'akinta taje tajaho sabuwar wayarta, alokacin ta had'ata Allah yaso da charge, ta daddanna number Haleema. Kira tash'iga yi amma baayi picking ba"kai Friendy bazata sauya tsarin nan nata ba in batasan number ba sh'ikenan bazatayi picking ba". Ameenah ta fad'a tare da komawa bakin k'ofar Ameen, tana zuwa ta taddash'i ya bud'e k'ofar da sauri ta sh'iga ciki a bakin k'ofar ta tarar dash'i rik'e da ciki. "Yah ameen" "sorry ina maganinka yake in baka". Sh'iru yayi mata, in banda nish'i dayake. Aransa yanason ta taimaka masa amma miskilanci bazai barsh'iba. Wayarsa yake nuna mata da hannu, tace"Mene? tare da d'aukar wayar aranta tace ko doctor zaa kira? bata tsaya sanya ba tashi'iga dubawa aikuwa taci karo da Family doctor kamar yadda akayi saving, kira tayi bugu biyu ana uku aka d'aga, "hello" aka fad'a daga d'ayan b'angaren, "Hello doctor pls kazo gida Yah ameen bayada lafiya, "Haleema ce" ya tambaya. "aa pls unguwar lamid'o crescent zaka zo, tafad'a masa sunan layin, baafi mintunoni ba taji bell d'in gidan tana k'ara bud'emasa tayi ta kaish'i har d'akin. Bayan ya dubash'i ya tabbatar mata da yunwace a dinga kula da abincinsa, to kawai ta iyaamsa masa dan tasan abincin kullum sai an ajiyemasa baya da niyyar cine kawai. Bayan doctor ya tafi tash'iga kitchen ta had'omasa tea me xafi dan ya warware masa cikinsa. dawo wa tay taga yana had'a gumi, tea d'inta ajiye sannan tazo kusa dash'i tace"ka cire rigar sai inbaka tea kash'a kaga gumi kake had'awa," sh'iru yayi mata ganin haka yasa ta fara b'alle maballin rigar tasa "Alhamdulillah ta fad'a a ranta, tana mejin kunyar abinda tayi. Tea d'in ta d'auko tasamu hankerchf ta goge masa gumin fuskarsa sannan ta tallafosh'i tafara bash'i, da farko gefe yayi da fuskarsa yawani had'e rai, sai data k'ara tallafosh'i ta d'uramasa sannan ya sh'a. 'kin kallonsa take saboda tas kofin zai iya zubewa dan jikinta har rawa yake. Bata kyalesh'iba sai da yajish'i dam sannan ta k'ara goge masa gumin, ta ballo masa maganin ta bash'i yash'a. Sh'ikam yasaki baki kawai yana kallonta, mamaki ta bash'i sosai. gy'aramasa kwanciya tayi ganin yafara gyangyad'i, tazuba masa ido tana k'arewa halirtarsa kallo wanda idan ido biyune bata isa tayi ba(dama kika samu kalleshi son ranki) sh'idai wannan a kama da sh'iru sh'irunsa inda kasan wani jarumin india Abishshek, babu inda suka banbanta sai ta abunda baa rasa ba, amma suna tsananin kama. Dawannan tunanin bacci ya d'auketa itama, a gefensa. Inda garin dad'in bacci yasa hannayensu suka manne da juna batare da sanin suba. [08:11, 9/16/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Sai kusan 12:30 Ameen yafara tash'i, yaji dad'in jikinsa sosai kuma cikin ya lafa masa daga ciwon dayake. Gefensa ya kalla yaganta kwance tana bacci, sosai yayi mamaki, me yakahota bacci har d'akinsa,? kallonta yayi kyakykyawa ba kyan hali,. "Mtsw Ke dalla tash' ki fita d'akinki, ko an gayamiki nan d'akin baccinki ne? Mik'a Ameenah tafara tare dayin salati, gefe Ameen yayi da kansa abun haush'i wai matar k'aninsa?. Murza ido take tana kok'arin tash'i amma Ameen ya k'ara daka mata tsawa "bazaki tash'i ba?" Watstsakewa tayi sosai ta kallesh'i da mamaki, mara lafiyan ne ya warke, yake mata tsawa? "badake nake ba? tash'i ki fita ko in ball dake". Murgud'a baki tayi tana kallonsa ta gefe, ni kike murgud'awa baki?, jahota yayi yasa hannu ya matse bakin sannan yasa hannunsa yadinga d'illan bakin da hannunsa d'ayan. "zaki k'ara murgud'an baki"? "uhm uhm"Ameenah ta fad'a tana girgixa kai alamar aa. "Tash'i ki fita yasaki bakin tare da hankad'ata. "uhm uhm Ameenah tafara alamar kuka tare da turo baki gaba. "Allah Allah ya.....i.s.... bata k'arasa ba ya biyota da gudu aiko itama tuni tazubawa k'afarta mai ta kwasa a million.......... Kuyi hakuri wayatace ta samu matsala. Love you all my Fans๐Ÿ’‹ ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [08:27, 9/17/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _By_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 87~88 D'akinta ta nufa sh'ima kuwa ya mara mata baya, tana zuwa ta danna kof'a ta sh'ige ta rufe ruf, Bugawa yake amma tayiwa k'ofa lock ta ciki, haka ya hak'ura ya wuce ya koma d'akinsa. Toilet ta sh'iga tayi wanka tare da d'auro alwala, sallah tayi sannan tad'anyi makeup tasa wasu pakistan kalarsu blue black, ta gyara gash'inta tazuba dash'i dadai kafad'arta Masha Allah gaskiya Ameena tayi kyau. Fitowa tayi ta lek'a parlour, bayanan ta salallab'o a hankali tazauna akan kujeran d'aki. Kallo ta kunna tash'ar Zee aflam suna film d'in _Rajkumar_ "Wow"tayi tsalle tare da fad'in "My Best actor kenan". kallonta take cikin kwanciyar hankali film d'in yanayi mata dad'i sosai. Dan har d'ankwalin data d'an yafa ya sab'ule Sh'igowa yayi yana ganinta yayi kwafa, ya kalli tv ya kalleta yadda take tawani jin dad'i, kawai sai yaji haush'i ya d'auko remote d'in ya sauya channel d'in zuwa Mbc action. Juyowa tayi dan ita batasanma ya sh'igo ba, mamakine ya sauka a fuskarta tayaya film d'inta yad'au dad'i sannnan kuma ya sauya mata?. Har zatayi sh'iru sai kuma meta tuna oho mata ta kallaesh'i tawani buntsuro baki ta sauko daga kan kujerar ta zauna kan centre carpet, tace cikin yanayin sh'agwaba"Haba haba itafa rayuwa ba haka take ba kawai anzo an sauyaea mutane tash'a mu me zamu kalla da wannan k'azaman horayan". Sakin baki yayi yana kallon ikon Allah, sh'ida gidansa dan yasauya abinda yaga dama har zaayi masa complain?, Bece mata uffanba illa kallo daya bita dash'i. Tayi ky'au amma fa baky'an hali tunda ba ilimin addini balle asamu kunya. Ameen ke wannan tunanin a zuciyarsa. Mik'ewa Ameenah tayi tash'iga kitchen tad'anyi preparing simple abunci dai-dai cikinta bata wani dad'e ba ta fito, samunsh'i tayi ya sauya channel d'in ya koma zee aflam d'in. Dad'i taji sosai harda fad'in"Lah me takwaran sunana komawa kayi kaga basu gama ba ma." Tafad'a tare da zaunawa plate d'in abincinta ta ajiye dan yad'anyi sanyi. Ganin tana murmush'i yasash'i saurin sauya channel d'in alhalin kuma sh'ima yanason ganin film d'in, kawai saboda itane bazai kalla ba. Ga girkinta k'amsh'insa ya bud'ad'e masa hanci, jiyake kamar ya d'auka yaci dan yanajin yunwa sosai, wayo yayi mata yace"ke jeki kitchen ki had'amin tea". Had'e rai tayi, tsabar ya rainamin hankali na kunna kallo ya kash'e sannan yanzu yazo yawani sani aiki, "ko bazaki tash'iba". [08:50, 9/17/2016] FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com๐Ÿ˜˜: Tash'i tayi tana bubbuga k'afa tana gunguni. Tana sh'iga kitchen d'in ya d'auki plate d'in abincin yaje fridge ya d'auko ruwa ya sh'ige d'akinsa. Abincin ya kalla ya had'iyi yahu kawai yayi bismillah yafara ci, "woww delicious". ci yake yana tand'ar baki har ya gamaci ya kora ruwansa sannan ya d'an huta yanason fita parloun yana jin kunyar abinda zaice mata. Ameenah kuwa ta had'o tea tafito bata gansh'iba kawai sai ta ajiyemasa. Plate d'in abincinta tash'iga nemowa amma bata gansh'i ba. Yunwa sai cinta take, ta k'ara lek'awa k'ark'ashin kujerar amma still bataga plate d'inba, sai tayi tunanin ko kitchen ta barsh'i? bata fito dashi ba dama. Dan haka ta koma kitchen d'in ta duba amma wayam babu plate d'in abincin ta. Ameen ne ya lek'o ya tarar bata nan dan haka kawai ya sh'ige kitchen d'in anan ya sameta, turus tayi data ga plate d'in a hannunsa, "Takwaran sunana ina abincin? Ameenah ta tambayesh'i. "Uhm ke dallah kinga bawai wani abun nayi dash'i ba, kinsan doctor yace adaina barina da yunwa so nad'auka naci, sai kije kish'a tean" Ya fad'a cikin masifa tare da ficewa a kitchen d'in. Tsorata Ameenah tayi sosai, dan catake zaneta zaiyi. Ameen yana komawa d'aki yafara tunane-tunane, "a gaskiya dole nabar k'asar nan, matar da k'anina keso, an auramin, matar da ba itace zab'ina ba"Afili yake wannan zancen. can ya tuna inda yayi karatu suna nemansa tun bayau ba, dan haka atake anan yabud'e laptop tash'i yafara sh'irye sh'irye, visa ne ta rage masa, dan haka dazarar komai yayi settle tafiya zeyi ko in sungaji sa sallameta su dasuka aurota, amma sh'i tafiya zaiyi ugenda. Toh fa kunji kuma wata sabuwa. Zanyi amfani da wannan dama in mik'a sak'on ta'aziyyata gareku Futhatulkhair inai miki gaisuwa Allah jik'an kaka. Aunty sis kema ina miki gaisuwa Allah ya jik'anta yayi mata rahma. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [14:40, 9/21/2016] 08106619411๐Ÿ˜œ: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 91~92 Ita yanzu a haka rayuwarta zata cigaba babu so da tattalin miji. Haleema ce ta tash'i tash'ige d'aki domin ajiye jakarta, sannan ta d'an watsa ruwa. Tunani tash'igayi, tunanin ko yaush'e zai dawo itama bata sani ba, gash'i bata da numbern sa, to ko tana da ita ma ai bata k'asar bace"Ohh My God!! Need Your Assistance Ya rabb" . Ameenah ta fad'a a fili, tare da zaro envelop d'in da yabata ta bud'e ta fara karantawa. Bawani abu bane a ciki illah kud'i masu yawa in zata buk'aci wani abun. Abinda yafi bak'anta mata rai sh'ine inda yace"In tagaji da zaman zata iya sanarwa da wad'anda suka ajiyeta." Bak'in cikine sosai ya ziyarceta, watakan bama zamansa take ba lallai, hawaye ne suka sh'iga zubomata ainda Wani zazzafan zazzab'ie ya rufeta, atake a gurin , Haleemah ce tafito ta taddata tana rawar sanyi, tsoro taji ta zaro ido tace"sannu Friendy zazzab'i?. "Eh" Ameenah ta fad'a tana b'oye takardar a k'asan kayanta. 'Dagota Haleema tayi, kud'i taga ya zubo, ta tsugunna ta harhad'a mata tazura cikin envelop d'in sanan ta k'ara rik'ota suka sh'ige bedroom. Kw'antar da ita tayi tare da kash'e mata Ac sannan taja mata blanket, tayi mata sannu sannan ta fita daga d'akin. Kitchen taje ta had'a abinci tafito. Wash'egari Ameenah tad'anji dad'in jikinta, dan har Asleem da Tasleem sunzo sunyi kwana uku, da suka ga ta wartsake yasa suka tafi. Mama da Mamy duk sun d'auka ciki ne da ita, amma ita tasan ba haka bane. "Friendy wai yaush'e cikin nan zai fara d'agawa ne". Haleema ce ta fad'a a lokacin da suke zaune a palour suna kallon Film d'in Salaam Namaste... "Hmm Friendy kenan kina ban dariya waike waya fad'a miki cikine dani?," Ameenah ta fad'a tana harararta. "Aa bakiga bane kinyi wani haske, gash'i kin d'an rame laulayin da ya saki a gaba". "Hahhh kyayi ki gama dai"kanki akeji". *Ugenda* Toh tun bayan saukar Ameen ya sauka a hotel, bayan ya huta ya watstsake, sannan yatash'i ya sh'iga cikin gari, wani dad'ine yake sh'igarsa jiyake kamar ya yarda kwallon mangora ya huta, amma a d'aya b'angaren zuciyarsa jiyake kamar yayi Missing wani abu. Bayan zuwansa da kamar sati d'aya yafara aiki a gash'i alhamdulillah yanata aikinsa yadda ya kamata. Wata ranar Monday da yamma Ameen ya fito daga aiki kenan rik'e da briefcase ya gaji ga yunwa, saurin dayake yasa yabugi wata matash'iyar yarinya wacce bazata fi sh'ekara ash'irin da uku ba, Jakar dake hannunta ce ta fad'i a k'asa.... "Am sorry" Ameen ya fad'a yana d'auko mata jakar ya mik'a mata, kallonsa tayi sosai ta rasa aina tasan fuskarsa, sh'ima kallon sani yake mata a makarantar da yayi karatu, "Bakomi" Budurwar ta kats'e masa tunaninsa. "Nagode" Ameen yafad'a yana k'are mata kallo. [14:42, 9/21/2016] 08106619411๐Ÿ˜œ: "Don't Mind" matash'iyar ta fad'a tare da hucewa. Sh'ima tafiya yayi domin yayi matuk'ar gajiya, yana buk'atar ya huta. ~Maman triplet~ [10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* _By_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 89-90 Tundaga wannan rana Ameenah bata k'ara sakash'i a idonta ba sai da akayi kusab sati biyu sannan ne ta gansh'i. Data gaidash'ima k'in amsawa yayi, dan ko kallonta ma baya sonyi, domin a ransa yanajin wani irin ba dad'i da zararar ya d'aga ido ya kalleta. Yau dai Ameen ya gama had'a komai nash'i, tafiya ce kawai ta rage masa. Kodayaje gidansu da zancen Mamy tak'i, Amma sai cayayi dasu An kirash'i wani taro ne a school d'insu, dan haka ba yadda suka so Abba ya bawa Mamy hak'uri tare da fad'in tayi hak'uri yaje ya dawo badai wata biyu yace ba. Bayan sati d'aya. Ameenah zaune kan kujerar dake parlourn, kallo take tajuyo daddad'an k'amsh'insa na tash'i, lumsh'e ido tayi sannan ta bud'e a lokacin da yake k'araso saitin ta, d'agowa tayi ta kallesh'i yayi ky'au cikin k'ananun kaya, sumar kansa tayi luf luf fuskar nan bayabo ba fallasa sh'i wani irin mutum ne befiya dariya ba, sai dai murmush'i, murmush'inma sedai kiga hak'orinsa biyu yad'an fito, itadai Ameenah ji take kamar taje tayi hugging d'insa tight ta hanash'i fita duk inda zaije, amma ina bata isaba. "Ke yadai naga kin wani k'ureni da ido haka". Kunya taji ta dabai bayeta ya kamata tana kallonsa, "Ahm gani nayi kunyi kama..." "kama dawa" Ameen ya tambaya. Tunanin wa zatace masa takeyi saboda tayi hakanne dan ta kare kanta. "Da sh'i". Kawai ta bash'i amsa. Tsawa ya daka mata"Dawa nake kma". "Habeeb". Kawai taiya fad'a tunda d'an uwansa ne. Numfash'i yayi sannan yace"ohh dan ina kama da saurayinki sh'ine zaki tsireni da ido kina kallo?." zaro ido Ameenah tayi a ranta tana fad'in innalillahi wai sh'i wannan wani irine? nifa Habeeb ba saurayina bane nafad'i hakane dan na tsira ash'e bab tsira ba, katsemata zancen zucin yayi dacewar"K'arb'i," hannu tasa kawai ta karb'a batare data k'ara kallonsa ba . Jaka taga yaja yafita daga Parloun yayi wajen motoci, lek'awa tayi ta tagar d'akin tana hangosh'i har ficewarsa, Ko ina zash'i haka harda su jaka?,. Komawa tayi ta d'auko wayarta, tafara game taji takun mutum, tsalle ta daka tare da fad'in" oyoyo oyoyo Friendy nahi fush'i. "Ke Amaryar yaya kinga yadda kikayi ky'au gaskiya abubuwan sun amsh'eki," Haleemah tafad'a da zolaya. "Wasu abubuwan fa" Ameenah ta tambaya da son jin amsar. "Dalla kina nufin baki gane ba, kinga jakata haka kawai Mamy wai inzo in tayaki zama kar kad'aici ya dameki". "Kad'aicinme?" "Ba Yah ameen yatafi ugenda ba," Mamaki k'arara a fuskarta tace"Ugenda? yaush'e?. "Ohhh yanzu ai yatafi ma" Ameenah ta fuske ta fad'i haka saboda kar Haleema tasan abunda ke tsakaninsu,tunda ita be gaya mata zaiyi tafiyaba dan bata ma isaba. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ [10/24, 7:10 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [13:06, 9/25/2016] Foulani Cerdia๐Ÿ˜˜: *AMEENA DA AMEEN* _BY_ FOULANI CERDIYA www.gidannovels.blogspot.com ®NWA 95~96 Kira ya k'arayi, "Mtsw"Ameena tad'anja tsaki kafin take kallon wayar tace a fili"Kai koma waye wanan zai dameni". Zumb'uro baki tayi kamar yana kallonta "Hello" ta fad'a tana kara wayar a kunnenta, "Pls kozan iya sanin dawa nake magana?,"Ameen ya fad'a. "wai ba nace maka mutum bace,?" Ta fad'a da tsiwar da da batasan da itaba. "Uhm"Ameen yasaki numfas'hinda har cikin kunnen Ameenah,.. "kiyi hak'uri kifad'amin mana, sunanki pls". Tunani tayi nad'an muntuna sannan tace"After na fad'a maka sunana kaima zaka gayan," "? "ok" d'an jim kad'an tayi sannan tace "Sunana Fanteka,". Dariyace ta sub'uce masa, yad'an dara sannan yace. "Toh fa sorry to say, amma sai nake ganin kamar fanteka wani abun amfani ne ko?," Ameen ya tambaya. "Eh haka na taso ana fad'amin agida, kaima sai kagayamin sunanka yanzu". "Ok......Suna......A.." Ameen be k'arasa fad'aba wayarta ta mutu sakamakon rash'in charge,. "Hello.hello"Ameenah ke fad'a sai data duba wayar taga ta mutu ba charge,. "Mtsww"Ameenah taja tsaki tare da ajiye wayar, ta janyo pillown dake kan kujerun ta sa kanta,tare da rufe idonta, tana tunanin waye wannan medad'in muryar haka?, gaskiya ba Ameen bane,dan muryarsh'i batakai wannan zak'i ba, amma dagaji guy d'in nan ya had'u. Idonta ta bud'e dai-dai yasauka akan pic d'in Ameen dake manne jikin gefen bangon 'dakin yayi d'an murmush'i a jiki, tunanin datake ta tsayar dash'i da fad'in"Auzubillah minashshaidanirrajim" inada aure ina tunanin wani"astagfirullah". Toh ab'angaren Ameen d'inma haka abin yake, dan gaba d'aya yatafi duniyar tunanin wannan muryar da kuma memuryar, ji yake ajikinsa kamar muryar watace wacce yakejin yayi missing, kai bama ita bace, any way in na koma 9ja zanga wannan fantekar. [13:32, 9/25/2016] Foulani Cerdia๐Ÿ˜˜: Abba da Mamy na zaune, Mamy takecewa Abba" Abban yara kaga fa yaron nan har wata na Biyar ya sh'igo gash'i be dawo ba kuma ma ko ya kiramu yayi mana bayani inwani abunne ya tsaresh'i." Numfasawa Abba yayi tare da kurb'ar juice d'in dake hannunsa yace"Nafu tunanin wani abunne ya rik'esh'i amma karki damu, duk randa yaga dama ya kira". "Allah ya sh'irya ya kuma kare mana sh'i" Mamy ta fad'a. ~Maman triplet~๐Ÿ˜˜ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *