Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 27 July 2017

AUTAR HAJIYA

adsense here [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [29/07 3:49 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 1-5 _Amincin Allah ya tabbata ga duk wanda ze karanta wannan littafi nawa, duka da ma wanda besamu damar karantawaba_. πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ» ✍🏽 Kwance take kan d'an madai-daicin gadon mahaifiyarta, hannunta ri'ke da waya, kirar tecno H³ wani game take me matukar sanyata nishad'i, Ta tattara hankalinta duka ya koma kan wayar. Muryar Hajiya ta tsinkayo tana kwalla mata kira, da sauri tasanya pause a game d'in domin zuwa kiran mahaifiyar ta. "Hajiya gani, tafad'a bayan ta d'an rissina gabanta, Alamar girmamawa, matar da takira da Ahjiya ta d'ago ta kalleta, tace "ki shirya inaso in ayke ki yanzu, tace "ina? Tace "kije ki shirya mana koma inane ay zakiji. 'Daki tanufa ta cire kayan jikinta, tayi d'aurin kirji, sannan, tafito ta cika bokiti da ruwa ta nufi toilet. Bayan ta she'ka wanka, tafito tanufi d'akin dai daya kasance nan ne na mahaifiyarta Wanda da Alama itama nan take, kwandon kayan shafarta ta d'auko ta ajiye gabanta, Wanda babu abinda babu aciki, tafara d'and'asa kwalliya, takai kimanin awa d'aya tana kwalliya, bayan tagama ne ta tashi' tanufi wadrope ta dauko wata green d'in atamfa, me zanen ganye golden, nd yellow, wacce akayima ado da yellow Codeless d'inkin zamani riga da zani pieces. Bayan tasaka kayan, sun kuma kar6i jikinta, dan ba 'karamin kyau saukayimata ba, sun fiddo da duk wata kya'k'kyawar halitta da Allah yabata. Fara ce, Amma ba irin tass d'innan ba, farinta dai-dai misali, tanada manyan idanu Wanda akoda yaushe idan ta kalleka, sai kayi tinanin kashe maka su takeyi, amma ba haka bane haka yanayin kallonta yake, ga dogon hanci Wanda ya 'kara fito da anaifin 'kyawunta, bakinta d'an karami, hakoranta farare tas, sai wushiryar data 'kara fito da kyawun su, gefen kumatunta ko magana take yana lotsawa, barantana kuma idan tayi dariya, wannan dimple ba karamin 'kara fiddo da 'kyawunta yake ba. Bayan tagama shirinta tsaf, ta dauko hijab d'inta, kalar golden, ta Sanya tiare ta dauko ta feshe jikinta dashi, sannan ta d'auko plat shoes shima kalar golden, ta Sanya, tanada tsayi shiyasa bata damu da takalmi me tudu ba. Fitowa tayi tsakar gida, inda mahaifiyarta ke jiranta, tace "gani Hajiya. Hajiya tace "yauwa dama gidan Maman Ummi zakije, kicemata ya maganar adashi, yanaji shiru, ko har yanzu, ba'a gama had'a kud'in ba?. Kuma kice ina gaisheta, sannan ta d'auko naira Hamsin tabata, Anshi ki hau napep, ta kar6a sannan tafice Daga gidan, Hajiya namata fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya. Taje gidan ayken harta, Isar da sa'kon takuwa yi sa'a dan angama had'a kudin saboda haka aka bata, dama kwasar adashine na Hajiya. Kasancewar hajiyar kud'in zuwa kawai tabata, can kuma gidan dataje, Mmn Ummi tabata, kud'in napep d'in Amma ta'ki kar6a, saboda haka a 'kafa ta tafi, tana tafiya tana zancen zuci, tayi matu'kar danasanin tahowa a 'kafa domin yanda ta lura da duk Inda ta gifta maza ke binta da ido. Azuciyarta tace "Allah ya taimakeni hijab na Sanya, da nabani. ✍🏽Zee Elkasem Mmn khady. [29/07 4:33 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 6-10 ✍🏽 Da sallama tashigo gidan, kitchen ta iske Hajiya, tana faman dafa masu abincin rana, Hajiya tafito Daga kitchen d'in tana mata sannu da dawowa. Ta fiddo da kud'in ta mi'ka mata tace "gashi kuma Mmn Ummi tace tana gaisheki, kuma tace "dan Allah kiyi hakuri wallahi mutanen ne sai Ahankali, Hajiya ta kar6i kud'in cikin farin ciki, ta kirga su dubu tamanin dai-dai, sannan ta kalli Autar Hajiya tace, "to Auta ga kud'in adashi sun samu yanzu ki gaya mani dami-dami kike bu'kata, kinga gobe idan nafita gurin ayki sai in sawo maki. Autar Hajiya tayi murmushi, taji dad'i har cikin ranta, game da yanda iyayenta suke nuna tsantsar so da Kauna da kuma kulawa a gareta, dan ita iya saninta tinda ta taso gidan, bata ta6a neman wani Abu tarasa ba, duk da iyayenta ba masu kud'i bane Amma sunada rufin asiri, domin mahifinta yana ayki, mahifiyarta ma tana ayki. Da misalin 'karfe hud'u na yamma, Hajiya suna zaune tsakar gida itada autarta suna shan iska, kasancewar yau Alhamis ba'a zuwa islamiyya. wani yaro yayi sallama, bayan an amsa Mashi, ya gaida Hajiya, sannan yace "wai ance ana sallama da Zainab a waje, Hajiya tace je kace waye, yaron yaje ya tambayo sannan ya dawo yace, "wai yace ba'ko ne, dan Allah ta taimaka tafito, Hajiya tace jeka kace tana zuwa. Tayi saurin tashi daga kwancen datake, tace dan Allah Hajiya kice baninan, ni wallahi banison wannan kiran, nifa ban ma San ko wayeba, Hajiya tace "to kifita mana sai kiga kowaye, haba zainabu na wulkanci bashida kyau, kifita ko gaisawa kuyi sai ki dawo ba sai kin dad'e ba. Hijab dinta ta Zara, ta Sanya, wacce tsawonta ya kai mata iya gwiwa, sannan ta fita. Jingine yake jikin motarsa, baki ne amma ba kirin ba, yanda 'kya'k'kyawar fuska, yanada saje Wanda ya'ara fito da kyawunsa, gajere ne dan baza'a ta6a sashi sahun masu tsayi ba, zai kai kimanin shekara talatin da takwas a duniya. Tinda ta fito ya zuba mata, idanu yana kallonta, harta 'karaso, ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a, Daga nan bata 'kara magana ba, sai shi yacigaba da magana. "Wato Zainab, hausawa sunce maso tsuntsu shike binsa da jifa, a gaskiya tinda naganki naji kin kwanta min arai, kuma ba kome ya'kara karkatar da Hankalina garekiba illah kamun kanki, da kuma kaywun surar da Allah yayi maki, nidai tafe nake da 'ko'kon barata, idan kin Amice aurenki zanyi dan ba maganar wasa ta kawoni anan ba. "Au sorry nacikaki da saurutu ban ko fad'a maki sunana ba, sunana "Adam kuma ni d'an nan cikin garin katsina ne, ina zaune a Unguwar Al'kali da iyalina, inada mata d'aya da yara ukku, da fatan zaki kar6i soyayya ta. Kafin tayi wata magana ta hango babanta tafe kan mashin d'insa saboda haka bata tsaya bashi amsaba ta shige gida. Nan Baban nata ya Tarar da Adam kofar gida, bayan sun gaisa, yayi Mashi yan tambayoyi. Zee Elkaseem Mmn khady. [29/07 9:30 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 11-15 ✍🏽 Koda ta shigo gidan d'aki ta wuce, ta d'auki wayarta tacigaba da danne-danne, azahiri idan ka ganta wayar take dannawa, Amma zuciyarta cunkushe take da tinani barkatai. Itako a tsarinta babu Auren me mata, saboda ita mace ce me tsananin kishi, yaushe zata yarda ta auri namiji me aure, Amma wannan mutumin yama raina mata yawo, to wallahi, da matar shi hada 'ya'ya ukku kuma sannan yace yana so ya aureta, ya Allah tsareta da aurensa, wani irin mugun hauhinsa taji ya rufeta, itako da beda mata da zata iya daurewa ta Auresa, kidan saboda yanda babanta ya matsa akan yanaso tayi aure. Da sallama mahaifin nata ya shigo, Hajiya dake zaune tsakar gida ce ta Amsa sallamar, sannan tayima me gidan nata sannu da zuwa, bayan ya amsa da "yauwa" d'akinsa ya wuce, Hajiya tanufi gurin ajiye ruwa tacika boket da ruwa takai toilet, sannan ta iske me gidan nata d'akinsa tace "Alhj ga ruwan wanka can na kai ma kewaye, yace "to bari inje inyi wankan, "Amma kafin in Shiga inaso in tabayeki, tace "to Alhj inaji, yace "Wannan yaron dana gani 'kofar gida yazo gurin Zainab tin yaushe yake zuwa, Hajiya tace "yau ne farkon zuwanshi, da Autar ma tace bazata fitaba dan bata sanshiba, nice nace tafita taji me ke tafe dashi, Alhj yace "kin riga kinsan banison inga yarinya tana tsayawa da samari barkatai, saboda haka ki gaya ma ita Zainab d'in idan har tana son wannan yaron to tasanar dashi yaturo da magabatanshi, kafin yacigaba da zuwa gurinta. Hajiya tayi murmushi tace, "Haba Alhj Daga zuwa d'aya sai ace yaturo kamar muna Neman maraba da d'iyar, ay dole dai su samu su fahimci juna kafin a kai ga maganar iyaye, yace " kidai gaya mata idan tana sonshi ya turo magabantashi, idan kuma bata sonshi kada in'kara ganinsa 'kofar gidannan, "kuma da kikace ba Neman maraba ake da itaba, so kike mu tasa ta gaba muyita kallonta, tinda tagama makaranata, kuma islamiyya sunyi sauka ai Alhamduliilah, Aure kawai yarage muyi mata hankalinmu ya kwanta, haka suka gama tattaunawa sannan ya fito yanufi kewaye, dan yin wanka, ita kuma tanufi d'aki inda Autar Hajiya take tana ta tinane-tinane kala-kala. Da sallama ta shigo d'akin, ta isketa kwance, kamar me bacci, amma ba baccin takeba' tinani ne kala-kala acikin zuciyarta, nan Hajiya ta bayyana mata yanda sukayi da babanta, na maganr ba'kon datayi yau. Cikin tsananin firgici, ta dafe 'kirji tace "wallahi Hajiya bani sonshi, ni banma sanshiba, yau ne fa kawai nafara ganinsa, "Dan Allah ki gaya ma baba abar wannna maganar, murya saukaji kamar Daga sama yana cewa, "ba saita gaya maniba inaji, waike zainabu yaushe zakiyi hankali, ki nutsu ki fitar da miji kiyi aure, yaufa shekara biyu kenan da gama makarantarki, Amma ko kad'an bakiso ayi maki maganar aure, to kisani bazan sanya maki ido ba kina zaune, muddin idan nagaji da zamanki zan za6a makin duk Wanda naga ya kwanta min arai. Wasu hawaye masu zafi suka zubo, kan kumatunta, tace dan Allah Hajiya ki gayama baba wallahi banison miji me mata, wallahi zan iya auren Kowa amma banda me mata, Hajiya tacigaba da rarrashunta tana cewa, haba auta, saboda me bakison me mata, mace nawa ta Auri me mata ukku ma itace cikon ra hud'u kuma ta xauna lafiya. Wani kululun ba'kin ciki taji ya tokare mata zuciya. Azuciyarta tace _Ni in auri me mata ukku ay 'kila kafin a kaini zuciya ta buga namace saboda tsananin kishi_ _kome mata d'aya bazan iya aureba_ Wani sabon kuka ta faahe dashi. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [29/07 7:16 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 16-20 ✍🏽 washe gari haka Autar Hajiya ta tashi jikinta sukuku, a zuciyarta tana ma Adam Allah ya Isah, yanzu gashi sanadin zuwanshi, yajawo mata babanta ya tado da maganar tayi aure, Wanda a da ya lafa da maganar, kuma shi gashi yanada mata barantana ta auresa, itako yanda babanta ya matsa mata akan tafito da miji wallahi da Adam bayada mata data auresa, saboda Adam beda makusa, Amma kuma ya cuceta daya furta mata kalmar "So" Alhalin yanada mata, _Allah ya isah tsakanina da kai Adam_ ta Furta afili tare da zubar da wasu guntayen hawaye. Ranar haka ta kasance ita d'aya cikin gida, tinani kala-kala ya addabi zuciyarta, kasancewar yau litinin Hajiya tana gurin ayki, tana aykine a general hospital katsina, yayinda babanta yake ayki, ma'aikatar agric, fannin dabbobi. Da sallama wani yaro ya shigo, ta amsa masa sallamar, sannan yace auta ana sallama dake waje, tanajin haka bata tsaya tamabayar waye me sallamar ba tace kace ina zuwa, ko ba tamabaya tasan be wuce Adam, takoyi matu'kar farin cikin zuwansa dai-dai wannan lokacin, yanzu ko zata fita ta bige masa warning. Hijab ta Sanya, sannan ta zari silifas d'inta na wanka tanufi kofar gida. Shine kuwa, Wanda take tsammanin, jingene yake jikin motarsa, yauma yayi shiga ta musamman, yayi masifar kyau, cikin gadara da tsiwa ta isa gabanshi, yau ko gaisuwa be samu arzi'kinta ba, ta tsaya gabansa tare da d'aure fuska kamar bata ta6a dariya ba. Cikin fara'a yake magana, "sannu da fitowa gimbiyar mata, ina fatan dai ban takura maki ba danazo dai-dai wannan lokacin, wallahi nakasa daurewa ne da rashin ganinki....... Hannu ta d'aga mashi, tare da yimashi magana cikin d'aga murya, "dakata! Adam kake ko waye, inaso in gaya maka ka fita hanyata, dan wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi wacce daga ita babu wata, to ko duniya zata rage daga ni sai kai bazan aure kaba. Cikin tsananin tashin hankali, da mamakin jin kalamanta, Wanda koda wasa beyi, tinanin jin wannan daga gareta ba, a yanda ya d'auketa yarinya, me hankali, da nutsuwa ga kuma uwa uba ilimi, na addini dana zamani. Cikin sanyin jiki Adam yafara magana, yace "Zainab saboda me kika yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kaina,? Ko kinyi bincike ne kingano wani aybu da nike dashi?. "Ko d'aya tafad'a, illah dalili d'aya shine bazan iya auren me mata ba, "idan kuwa ka nace akan saika aureni to wallahi saidai akai gawata gidanka, dan zan iya shan guba in kashe kaina, na tsani kishiya, hakan ne yasa duk Wanda ze zomin da maganar aure bamu dai-daitawa, saboda mafi yawancin masu zuwa Neman aurena masu auren sunfi samarin yawa. Bata jira abinda ze fad'aba tashige gida,zuciyarta cunkushe da abubuwa da dama. Wani kululun ba'kin ciki ya tsaya ma Adam azuciya, yama kasa matsawa daga Inda yake, yakai kimanin minti talatin tsaye a gurin sannan Daga bisani ya shiga motarsa ya tafi, jikinsa ba laka ko kad'an. Tana shiga gida, ta wuce d'aki kan gado ta fad'a ta fashe da wani irin kukan takaici, kuka take baji ba gani. Daga waje kuma anata sallama, amma batajiba, saboda kukan yinsa take tsakaninta da Allah. Jitayi ba'ada niyyar amsa sallamar data dad'e tanayi, saboda haka kutsa kai tayi cikin d'akin, dan tanada tabbacin Hajiya bata nan. Autar Hajiya datayi nisa cikin kuka, sai ji tayi an dafata, da sauri ta d'ago da manyan idanunta da suka canja zuwa ja saboda tsananin kuka, sadiyya tagani wacce batasan lokacin data shigo gidan ba. Cikin tsananin damuwa sadiyya, ke magana, "kawata, meya faru? Naganki cikin wannna yanayin. Bata tanka mataba, illah cigaba datayi da kukanta. Zee Elkaseem Mmn khady [30/07 7:37 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 21-25 ✍🏽 Sai da tayi kuka me isarta sannan ta d'ago ta kalli sadiyya, wacce ta kasance 'kawa ce gareta, tin suna yara kuma bata da wata aminiya data wuce ta. Nan tabata labarin duk abinda yafaru, tin zuwan Adam dakuma Abinda babanta ya fad'a na cewa idan bata fito da miji ba ze za6a mata duk wanda yaga yayi masa. Sadiyya ta numfasa, sannan tace "wallahi Autar Hajiya kinada problem, ni narasa gane kanki, kwata-kwata tinda nake ban ta6a gani ko jin me irin wannan tsatstsauran ra'ayin ba irin naki, be kamata ace kin kartake akan ke bazaki auri me mata ba, ki duba kiga kwanaki yanda kukayi soyayya da Bashir kamar bazaku ta6a rabuwa ba, ba irin tsantsar soyayyar dabaki nuna masa ba, Amma lokaci d'aya kika bad'e ido toka kikace baki sonshi, dan kingano yata6a Aure kuma ya rabu da matar, wai kina gudun kada wata rana yace ze maida ita. Auta ta numfasa sannan tayi wani guntun murmushi Wanda yafi kuka ciwo, tace "hum sadiyya bazaki ta6a ganewa ba wallahi duk lokacin da wani namiji yace yana sona daya furta min yanada aure jinake kamar in kashe kaina, dan na kwammace na mutu dana auri me mata. Sadiyya tace "to Allah kyauta, Allah rage maki wannan zafin kishin naki, tace Ameen ni kaina ina yawan yin wannan addu'ar dan wallahi wani lokaci abin har tsoro yake bani. "Wai ina khaleed ne? shiru naji kin daina zancensa, ko shima yanada matar ne?. Auta tayi murmushi, wanda yasa har kumatunta suka lo6a, tace "Hmm khaleed mutanen Sudan, ay yana can karatu, kawai yasa gaba, ni inaga kila yanzu ya manta dani, shekara hud'u fa kenan rabon da muga juna, kuma tinda yatafi ko waya bamu ta6a yi dashi ba, Amma kuma ni nasan har in mutu bazan ta6a son wani d'a namiji kamar yanda nake sonshi ba. Sadiyya tayi murmushi, tace tabbas kunyi tsantsar soyayya da khaleed, kuma bani tinanin shima ze iya mantawa dake, kuma naji ajikina khaleed shine mijin dazaki aura. Wani farin ciki ya rufe Autar Hajiya, dan tinda take duniya bata ta6a son wani namiji ba, irin son datakema khaleed, Cikin jin dad'in maganar sadiyya tace "Allah ya tabbatar min da hakan, Allah sa khaleed yazama mallakina ni kad'ai batare daya had'ani da wata jaka ba. Sadiyya tayi dariya, cikin tsokana tace au amaryar taki kike kira jaka, Auta ta kaimata duka cikin wasa tace "bani son iskanci, ki dainamin wannan wasan khaleed nawa ne ni d'aya Kedai kawai ki tayani addu'a Allah sa be manta daniba, sadiyya tace "to Allah sa be manta dakeba kuma Allah sa yana dawowa musha biki, su duka suka sa dariya, haka suka sha firarsu, sam Auta ta manta da wani ba'kin ciki datake tattare dashi, jitake kamr har khaleed d'inma yadawo an d'aura masu aure saboda tsabar farin ciki. Sai gab da Hajiya zata dawo sannan sadiyya tayi haramar tafiya, Auta tayimata rakiya, tare dayimata Al'kawarin zuwa gidansu ranar Friday. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [31/07 10:47 am] 😘: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 26-30 *•Bayan Wata biyu•* Kwance take kan tabarma, tayi filo da cinyar Hajiya, yayinda ita kuma Hajiya ke tsefe mata manyan kitson dake kanta, cikin shagwa6a ta ri'ke hannun Hajiya tare da rintse ido Alamar tanajin zafi, tace "Hajiya dan Allah kiyi min Ahankali da zafi, Hajiya tace "to sarkin son jiki tsifar kan shine keda zafi, kitson da be wuce 'kwaya goma ba, cikin shagwa6a tace ni wallahi shiyasa ban fiye son kitson ba ma, dan dai kawai kina matsawa sai nayi. Murmushi kawai Hajiya tayi "Uhm" sannan tacigaba da kwance mata kan, bayan ta 'karasa kwance mata kitsin, tasa masharci ta sharce ta shafe mata shi da mayuka masu kyau da dad'in 'kamshi, sannan ta hade mata shi guri day'a ta d'aure mata shi, yayi gwanin kyau ya zubo har kan kafad'unta, ga gashinta da tsantsi, ga tsananin ba'ki kamar na larabawa. "Assalamu Alaikum, sallama yayi tare da shigowa cikin gidan. saurayine, d'an kimanin shekara ishirin da tara a duniya, kya'ky'kyawa ne ajin farko, ba fari bane, Amma kuma baz'a kirasa ba'ki ba, choculate colour ne, me matsakaicin tsawo, jikinsa kuwa baza'a kirasa me 'kiba ba kuma ba za'a kirasa ramamme ba. Hajiya ce tayi saurin tada, sadiya daga kan cinyarta, tace " a,a,a Bakin sudan ne, saukar yaushe, Auta najin haka tayi saurin kai dubanta ga Wanda aka kira ba'kon Sudan, wani mummunan fad'uwar gaba taji, dan ba Kowa bane tagani sai masoyinta khaleed, Wanda bata ta6a jin son wani namiji aduniya ba kamar shi. Cikin fara'a yace "Yau sati biyu kenan da dawowar mu, Hajiya tace " sannu da zuwa, shigo mana, a falo akayimasa masauki, sannan suka gaisa da Hajiya, nan take tambayarsa, ya momynsa, yace "tana lafiya tace tana gaishe Ku, tace "ina amsawa, ya karatu kuma, yace "karatu angama, yanzu kuma sai maganar ayki, tace "Allah taimaka, yace "Ameen, tace kuma yanzu Baban naka yafita da kun gaisa, yace ay mun gaisa dashi jiya, tace kaga kuwa be fad'a mamu dawowar kaba, yace "Eyyah ina tinanin mantawa yayi. Auta kuwa tun bayan shigowar khaleed, tanufi d'aki ta gyara fuskarta, sannan ta yafa wani karamin gyale ta rufe gashinta, sannan ta nufi pridge ta dauko ruwa pure water da holandia fresh milk, ta d'auko d'an karamin cup na glass ta d'ora kan wani madaidaicin tire ta nufi falo, ta ajiye gabansa, Hajiya tafita waje, tacigaba da yan hidindimunta. Auta kuwa guri ta samu ta zauna, kan kujerar, dake facing d'insa, sannan ta gaidashi, ya tsareta da ido, a zuciyarsa yace _wai Autar hajiya ce takoma haka lallai yanzu nakara tabbatar da gangancin danayi na amincewa da auran fadila_ "sannu da zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta, me kama da ta yara, yace "yauwa sannu na sameku lafiya, tace "lafiya lau, tasowa tayi tazo gabansa, ta zuba Mashi, fresh milk a cup ta mi'ka mashi, ya kar6a ya kur6a sannan ya ajiye, kallonta yaci gaba dayi yanda Kasan yau yafara ganinta. Ita kuwa wani sabon sonshi, taji ya 'kara mamaye zuciyarta, a ranta cewa tace _Allah sa yanda nakejinka a zuciyata kaima haka kakejina_. Zee Elkaseem Mmn khady [31/07 11:49 am] 😘: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 31-35 Saida yagama 'kare mata kallo a zuciyarshi yana cewa _Allah ka mallakamin zainab Amatsayin uwar 'ya'yana, tabbas nayi gangancin Amincewa da Auren fadila,Amma ba kome tinda itama inasonta zan had'a dukansu in auresu_ Ita kuwa auta duk ta tsargu da yanda ya tsareta da ido, gashi ya'ki magana, sun kai kimanin minti goma a haka, sannan yace " Autar Hajiya, kece kika koma haka? Cikin jin kunyar tambayar dayayi mata tayi murmushi kawai, dan batada Amsar dazata bashi, illah tsananin sonshi da 'kaunarshi dake d'awainiya da zuciyarta. Jin dayayi batada niyyar magana, yasashi tasowa daga inda yake zaune, ya dawo kusa da ita, ya zauna kan hannun kujerar datake zaune akai, kasancewar kujerar ta zaman mutum d'aya ce. Wani irin kallo yayi mata, Wanda yasata jin wani yarrr ajikinta, lokaci guda kuma ya kashe mata ido, yace "ya maganar soyayyarmu tananan kokuwa bayan tafiyata kin samu wani?, cike da jin kunya, da kuma jin dad'in zancen daya fito daga bakinsa, itama ta watsa mashi wani kallo, wanda lokaci guda yaji jikinsa yayi sanyi, tace "ai kaine yakamata inyima wannan tambayar, domin tinda katafi ko a waya ka nemeni baka ta6a ba, kaga kuwa kaine zance kasamu wata. Yayi wani 'kyayataccen murmushi, yace "Zainab bazan ta6a had'a soyayyarki da wata mace ba, ina sonki ina 'kaunarki, kuma burina Aurenki, kawai yanzu ki amice in sanar da baba,saboda na matsu na ganki gidana a matsayin matata, ke kinga yanda kika koma kuwa, ai gaskiya nataki sa'a dana iskeki, wani be min shigar sauri ba. Tinda yafara magana Auta jinsa kawai take, a zuciyarta kuwa cewa take _"Khaleed nafika son kasancewa matarka dan a duniya banida wanda nakeso nake 'kauna kamar kai_ Khaleed yace "kinyi shiru Kodai akwai Wanda kukayi al'kawarin aure ne? Tayi murmushi, wanda har saida kumatunta suka lo6a, tace "babu wani bayan kai, kuma na Amince da ka sanar iyaye su shiga maganar, sai Kuma fatan Allah shige mana gaba, yace "Ameen, Amma nayi matu'kar farin ciki, gaskiya auta ina sonki, so irin Wanda be musaltuwa, wani sanyi taji ya mamaye zuciyarta, tare da jin wani irin shau'ki a cikin ranta. Haka suka kwashe kusan awa biyu suna Fira, kafin Daga bisani yayi haramar tafiya, har Bakin mota tayi masa rakiya, bayan sunyi sallama da Hajiya, Wata leda ya Ciro Daga motar ya mi'ka mata, "ga tsarabarki, ta kar6a cikin jin kunya tare dayimasa godiya, Tananan saida yashiga mota yatafi, harya 6ace tana d'aga mashi hannu sannan takoma gida, cikin farin ciki ta tarar da Hajiya zaune falo ta mi'ka mata ledar. Hajiya ta amsa tare da tambayarta "na miye? Auta tace "tasaraba ce khaleed ya kawomin, nan suka zazzage kayan suna cikin dubawa me gidan ya shigo, falon yanufa kai tsaye dayake ya jiyo maganarsu a can. Hajiya tayi mashi sannu, itama auta cikin girmamawa tace "Baba sannu da zuwa, yace "yauwa zainabu, sannan ya kalli kayan dake gaban Hajiya yace "wannan kayan fa, tace "khaleed ne yazo yanzu be dad'e da tafiya ba, yakawoma auta tsaraba. Kayan cosmetics ne masu tsadar gaske, sai takalma kala biyu, suma tsadadadu, sai swiss less guda, sai atamfa super aura, sai turaruruka designer's, masu dad'in kamshi. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 36-40 *Bayan wata d'aya* Soyayya tayi nisa tsakanin khaleed da Autar Hajiya, dan yanzu yanda takejin khaleed a zuciyarta, bazata iya rabuwa dashiba, kome rintsi kome wuya, bata had'a sonshi dana Kowa ba, shima haka yake mata wani matsanancin so. Yanzu dai iyaye sun san da maganar soyayyar khaleed da Zainab, dan har anyi maganar aurensu, ansaka ranar auren nan da wata ukku. Ranar da auta tasan an saka ranar aurenta da khaleed, ranar jitayi kamar anyimata busahara da gidan Aljanna, saboda tsabar farin ciki , shima 6angaren khaleed d'in haka, dan tinda yake beta6a had'a son auta dana wata mace ba, ko fadila yana sonta ne kawai saboda wasu dalilai amma ko kad'an bazaya iya had'a son da yake mata ba da Wanda yakema auta. ***** ****** ****** "Wai ni khaleed bangane me kake nufiba, Cikin gadara da nuna isa take maganar "kana nufin ka raina za6in danayima a matsayina na mahaifiyarka ban isa dakai ba, sai kawai inji labarin wai ansaka ranar aurenka da Autar Hajiya, dan Baku d'aukeni a Bakin kome ba kaida mahaifinka, kun maidani shashasha, to wallahi baka isaba, wato ka za6i 'yar'uwarka shikuma mahaifin naka dan yaga d'iyar d'an uwansa ce shine ya Amince hadda sa ranar aure ba tare da saninaba, sai bayan anyi anyi kome angama ranar aure kawai ake jira tazo sannan aka sanar dani. Tinda matar tafara magana khaleed be ce uffan ba sai da tayi shiru sannan yafara magana cikin nutsuwa, da Alamar rarrashi, yace "kiyi ha'kuri Momy nasan idan na tinkareki bazaki yarda da maganar aurena da Zainab ba, shiyasa na ro'ki daddy akan kada ya sanar dake har sai an tsaida ranar, amma dan Allah Momy kiyi hakuri, badan banison Fadila nayi haka ba, kawai manufata shine bayan na auri Zainab da kamar shekara ita kuma sai in aureta daga baya. Wani irin salati ta kwad'a Wanda yasa 'yan'cikin sa juyawa, sannan tafara magana cikin masifa, Wato khaleed ni zaka cima mutunci ka nuna dangin ubanka sunfi dangina daraja a gareka, to wallahi ban Amince da wannan manufar takaba, sai dai kafara auren fadila sannan daga baya ka auri Autar, dan bazan hanaka aurensuba, dan su duka 'yan'uwanka ne, kuma Addini be hanaka auren Mace biyu ba ko ukku, kai harma hud'u, Amma kasani Fadila, itace ta farko idan kuma ka'ki za6ina to wallahi sai dai kafasa aurensu su duka. Khaleed rasa yanda zeyi yayi, dan yasan halin mahaifiyarsa sarai, zata iya wargaje maganar aurensa da Auta, wacce kuma itace macen daya fara so a duniya kuma har yakoma ga mahaliccinsa baze so wata mace kamar yanda yake sonta ba. Cikin tsoron halin mahaifiyarsa, yace "na Amince momy zanyi yanda kikace, zan fara auren Fadila Daga baya sai in auri Zainab d'in. Bata san lokacin da ta saki wani murmushi ba tace "yauwa to ko kaifa, murmushi yayi na k'arfin Hali dan gabaki d'aya ji yake Momy tagama takura rayuwarsa. Amma dan Allah Momy ina Neman wata alfarma, tace "ina jinka Yace dan Allah Momy idan antashi sa bikina da Fadila, asa wata d'aya saboda baniso a canja lokacin da aka sa bikina da Auta, cikin nuna rashin damuwa tace "wannan kuma matsalar kace, idan ma sati d'aya kace a sanya iyayenta shirye suke,kamar yanda kake shirye. A ranar Momyn khaleed ta sanar da daddynsa, yanda sukayi da khaleed, be musa mataba, ya Amince da duka bayanin datayi mashi. Anje Neman auren Fadila, wacce ta kasanece 'ya ce ga 'Kanwar Momyn khaleed, Fadila kwarkwararrar 'yar duniyace, wacce boko yagama zaunawa jikinta, da kwalwarta, wayayyace ajin farko, zata kai shekara ishirin da biyar a duniya. Cikin sati d'aya aka gama magar auren khaleed dafadila, ansaka ranar biki wata d'aya da sati biyu. _To fah jama'a kunsan dai ba abinda Auta Hajiya tatsana kamar namiji me mata kuma gashi sahibinta wanda tafi 'kauna zaya fara auren wata kafin ita tab, πŸ€” lallai akwai bada'kala_ *kudai kubiyo Zee Mmn khdy dan jin yanda zata kasnce* 08166169254 Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:54 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [01/08 7:32 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 41-45 *Bayan sati Biyu* ✍🏽 "Auta,....... Hajiya ce ta kwala mata kira tana daga kitchen, da sauri ta iso tace "gani, Hajiya ta mi'ka mata wani d'an karamin bokiti, "anshi ebo min ruwa nan in tsame d'an wakennan, sauri nake fita zanyi, da sauri Auta ta kar6a ta ebo ruwan takawo ta ajiye sannan ta d'auko kujera irin ta zaman tsakar gida ta zauna tace "Hajiya ina zaki ne?, Hajiya tayi murmushi tace kai lefe zamu koh, Auta ta kalleta cikin rashin Sani tace waye zeyi aure? Hajiya tace to waye zeyi aure kuwa in banda yayanki, Amma ay nasan dai ya sanar dake, Auta tace "Hmm Hajiya nifa ban gane wane yayana kike nufiba tukun, _kwata-kwata Auta bata kawo khaleed aranta ba dan tasan ita kadaice za6insa kuma be had'a sonta dana kowaba_ Hajiya tace "yayanki khaleed mana, kina nufin be sanar dake nan da sati biyu za'a d'aura auren sa ba, Jitayi kanta na juyawa, zuciyarta tayi mata nauyi, idanunta sun daina ganin haske, kanta yayi wani irin sarawa, lokacin kuma ta nemi numfaahinta ta rasa, Hajiya na daga kitchen kawai sai gani tayi Auta tafad'i kasa ba Alamar numfashi tattare da ita, da sauri tanufi inda ta fad'i tana furta Kalmar *Innalillahi,wa'inna,ilahirrajiun* A d'imauce take gigizata tana kiran *Zainab*....... amma ko Alamun motsi batayi, cikin tsananin rud'ewa ta dauko waya takira me gidanta, ta sanar dashi Auta ce ba lafiya, gata kwance ko motsi batayi, Cikin tsananin rud'ewa suka nufo gidan shida daddyn khaleed, dan lokacin da Hajiya tayi waya ta gaya Mashi suna tare. Kusan minti sha biyar sannan suka iso, har yanzu Auta na kwance ba Alamun rai tattare da ita, Hajiya na tallabe da ita tana faman zubar da hawaye, batare da 6ata lokaci ba aka sakata mota sai asibiti, suna zuwa aka wuce Emergency da ita, kahleed shine likitan daya kar6e ta tare da taimakon wasu abokan aykinsa suke kokarin ceto rayuwarata, Kusan minti talatin Amma Auta bata farfad'o ba, hankalin iyayenta yayi masifar tashi, ba kamar Hajiya wacce saboda tsananin kuka idanunta sun kumbura sunyi jawur, kallo d'aya zakayimata ka gane tsantsar tashin hankali tattare da ita. An akai kimanin awa daya, sannan Auta ta farfad'o Amma duk da haka bata san inda kanta yakeba, haka aka fito da ita Daga Emergency, aka maidata wani d'akin, tare da sanar da iyayenta inshaAllah kome normal data farka, babu wani ciwo dake tartare da ita sumar datayima yanada Ala'ka da wani Abu daya d'aga mata hankali, amma muddin aka kiyaye zata cigaba da samun sau'ki, khaleed ne kema Hajiya wannna bayanin, dakuma daddynsa da Baban Auta Wanda su duka shi suke sauraro. Zee Elkaseem Mmn khady [01/08 8:36 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 46-50 ✍🏽 Hajiya zaune gaban gadon da Auta ke kwance, ta zuba mata idanu tana kallon yanda take maida numfashi, ahankli tafara motsawa alamar farkawa daga baccin datakeyi, Ahankali ta bud'e idanunta ta 'karema d'akin kallo ta tabbatar da asibiti take, sannan Ahankali ta ri'ka tino maganar da Hajiya ta gaya mata, wasu zafafan hawaye suka zubo ta gefen idonta, A zuciyarta tana cewa. _shikenan rayuwata batada wani amfani wanda nikeso yaci amanata ya cuci rayuwata bayan yariga yasan ba wanda nakeso kamarsa, bazan iya mallakama wani namiji kainaba bayan shi, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta_ Da sauri Hajiya ta matso kusa da ita tana yimata sannu, "auta kiyi hakuri ki d'auki 'kaddara, kisani duk me rai ba Wanda kaddara bata fad'amawa, kuma ki d'auki wannan Amatsayin jarabawa ce daga nahaliccinki, kawai sai kiyi fatan cinye wannan jarabawar. Cikin disashshiyar murya, auta tace "Amma Hajiya khaleed ya cuceni yaci Amanata yagama da rayuwata, Allah ya Isah tsakanina dashi. Ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi, ta sauko daga kan gadon datake ta dur'kusa gaban mahaifiyarta, tace "Hajiya dan Allah ki gaya ma Baba bazanyi aureba har Abada, na hakura da aure, dan Allah Hajiya kada Ku 'kara tinkarata da maganar aure. Kama hannunta Hajiya tayi ta mi'kar da ita tsaye, ta maidata kan gadon ta zaunar da ita, sannan tafara mata magana cikin sigar kwantar da hankali, tace "Auta wannan maganar dakikeyi bame yiyuwa bace, ke kanki kinsan halin mahaifinki sarai ba saina sake maimaita makiba, kin San dai baze samaki ido ki zauna ba aure ba, kuma khaleed ba cewa yayi yafasa aurenkiba, maganar aurenki dashi tananan ba Abinda ya canja, ita wannan wacce ze aura d'iyar kanwar momynsa ce, kuma tin yana sudan mahaifiyar ita yarinyar tabashi ita, saboda haka inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki, kisani aurenki da khaleed ba fashi, idan kuma zaki tinkari mahaifinki da wannan maganar to kisani nidai ba ruwana. A hankali aka turo kyauren d'akin, suduka suka maida hankalinsu gurin dan ganin me shigowa, khaleed ne yashigo da sallamarsa, sanye yake cikin milk d'in shadda wacce tasha ayki da zare copee, sai wani daddad'an 'kamshi ke tashi daga jikinsa, lokaci guda kamshin turarensa ya bige d'akin, kallo d'aya auta tayi mashi taji wani masifaffen sonshi ya'kara shiga zuciyarta, lokaci guda kuma ta tuno da cin Amanar dayayi mata, batasan lokacin data tashi Daga kan gadon datakeba taje ta cakumeshi, ta fashe da wani irin kuka, tace "Khaleed ka cuceni kaci amanata, Allah ya isah tsakanina dakai, kuma ka Sani bazan aurekaba koda Kaine auntan maza a duniya. Da hanzari Hajiya ta mi'ke tana 'ko'karin 6an6are hannun Auta Daga jikin khaleed, amma hakan ya gagara dan Auta ba karamin ri'ko tayi Mashi ba, cikin 6acin rai Hajiya ke magana, "ki sakeshi nace auta, saima ta'kara rikeshi tana mashi wani matsiyacin kallo Wanda shi kanshi yakasa gane kona miye. Ji kake tasss, Hajiya ta d'auke Auta da mari, hakan kuma yayi dai-dai da shigowar daddyn khaleed, da kuma babab ita Autar, cikin 6acin rai Hajiya take magana, "waike Auta wace irin shashashar yarinya ce da ina maki magana amma kin raina maganata, cikin sanyin jiki Auta ta saki khaleed tafad'a kan gado ta fashe da kuka, Ko kad'an khakeed beji dad'in marin da Hajiya tayima Auta ba, dan dama yasan duk ranar dataji labarin aurensa zatayi abinda ma yafi wannna dan yanda take gaya mashi batason kishiya, ta tsani kishiya. Zee Elkasee Mmn Khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [02/08 5:24 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 51-55 ✍🏽 "wannan zancen banza ne zancen Wofi, abinda baze ta6a yiyuwa bane, Wato Zainabu kinaso ki maidamu 'kananan mutane ko? ko kinaso ki haramta abinda Allah ya hallata, duk namiji Allah ya halatta mashi Auren mace daga d'aya har zuwa hud'u, saboda haka ke baki isa ki haramta Abinda Allah ya halatta ba. Mahaifin Auta ne keta faman fad'a tinda suka shigo asibitin shida mahaifin khaleed, Hajiya tabasu labarin abinda ya faru tsakanin Auta da khaleed. Cigaba yayi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, Auta kuma banda aikin kuka ba abinda takeyi, kwance take kan gadon asibitin ta juya fuskarta dan bazata iya had'a ido da khaleed ba, dan ita kanta sai daga baya tayi danasanin abinda tayi mashi, cikin zuciyarta kuwa cewa take. _Allah kasa kada Abinda na aikata yazama silar fasa Aurena da khaleed inason khaleed son da bazan ta6ayima wani namij iirinsaba_.... Wani sabon kuka ta fashe dashi lokacin data tsinkayo muryar daddyn khaleed yana cewa, "A'a Alhj baza'ayi hakaba kada fa atakurama yarinya, yakamata atambayeta aji ra'ayinta, tinda ada lokacin data Amince da aurensa ba'ayi da ita ze fara auren wata kafin itaba.... "Haba Alhj ka daina wannan mqganar" Baban Auta yafada' "yaushe zamu zauna yarinya 'karama kamar Zainab tana juyamu, "to kisani cewa aurenki da khaleed ba fashi, ke barima kiji in sanar dake, an sassauto da lokacin bikin yadawo lokaci daya da wanda za'a d'aura mashi nan da sati ukku, inshaAllah lokaci guda za'a kaima khaleed mata biyu, Alabashi kinga idan aka kaiki saiki kashe kanki saboda tsabar kishi, shashasha kawai wacce bata San ciwon kanta ba. Cikin fushi yafita daga d'akin, daddyn khaleed yabi bayansa, Hajiya ma binsu tayi, Harabar asibitin suka tsaya daddyn khaleed yana cigaba da ba d'an'uwansa hakuri " yana cew "Kabi kome a sannu Zainab d'in duka nawa take dazaka ri'ka yimata fad'a kamar kanayi da wata babbar mace, duka bana fa take cika shekara sha takwas, kaga kuwa akwai 'kuruciya tattare da ita. Hajiya dake tsaye tana saurarensu, tace " haba Alhj ai halin Zainab dole sai da haka, idan ba'a tsawata mata haka zata ri'ka mana yawo da hankali, ni kaina naji dad'in haka, kuma 'kara da aka sassauto da bikin ayi a huta. Daddy khaleed yace "Allah sa haka shine mafi Alkhairi, suduka suka Amsa da "Ameen. Cikin d'akin kuwa khaleed na ganin fitar iayensu yafara rarrashin auta, yana nuna mata irin sonda yakemata, Amma ko kallo be ishetaba, Ahankali ya matso ya dur'kusa kusa da gadon datake kwance, ya marairaice, cikin sigar rarrashi yake magana. "Haba Zainab ki yarda dani, ki yarda da son danike maki, duk duniya ba macen danikeso kamar ke,.... A fusace ta d'ago ta kalleshi cikin tsiwa tace "Akwai khaleed, na tabbata kafi son Fadila a kaina, khaleed ka ha'inceni, ban ta6a tinanin ko a mafarki zakayi mani haka ba. Ya salam...ki fahimceni Zainab, Fadila fa bani nace ina sontaba, had'in iyaye ne,kuma ke.... "Dakata khaleed, bakada kalaman dazasuyi tasiri akaina, ka adana kalamanka, wata kila suyima amfani nan gaba.... _(Hmm zainabu kenan halinki sai ke)_ *Zee Elkaseem* *Mnn Khady* [02/08 6:26 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 56-60 ✍🏽 Kwanan Autar Hajiya biyu aka sallamota daga asibiti, duk ta wani rame ta kod'e hancinnan ya'kara tsayi, ga wani haske data 'kara, idan ka ganta sai kayi tinanin tayi ciwon wata biyu ne, dan ba 'karamar rama tayiba, duk tsabar kishine kawai. Ranar sukayi waya da 'kawarta sadiyya, tace dan Allah tazo yau tana son ganinta, sadiyya tace "lafiya dai? Auta tace "lafiya lao kizo mana akwai labari 'kawata wallahi ina cikin tsananin damuwa da ba'kin ciki, cikin rud'ewa sadiyya tace "Damuwa 'kawata?, wace irin damuwa kuma? Auta tace "kedai sai kinzo kome kenan kinji. ••••••••••••••••••••••••••••••••• Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa kalar sararin samaniya, wacce tasha d'inkin zamani, dinkin ya matu'kar kar6ar jikinta, dan ba karamin kyau yayi mataba, bata d'aura d'an kwaliba, sai wani karamin gyale me sharara ta yafa akanta, amma hakan baze hana ka hango madaidaicin gashinta ba Wanda yasha 'kuna, tayi parking dinsa tsakiyar kanta. Wankan tarwad'a ce, amma dayake tana amfani da cream da lotion masu tsadar gaske masu matu'kar gyara fata,hakan ya 'kara fito da hasken fatarta, tanada idanu madai-daita, da dogon hanci, Wanda yayi dai-dai da matsakaicin bakinta, Wanda yasha romantic red colour, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da boko ya zauna jikinta, da kwalwarta, *Fadila kenan*. Da sallama ta shiga falon da akayi Mashi masauki, tafiya take cikin yanga da karairaya, Lokacin khaleed ya d'ago ya kalleta tare da amsa sallamarta, Yanda take tafiya baya birgesa ko Alama, dan tanada 'yar'kiba shiyasa tafiyar bata mata kyau, ga Allah ya hore mata manyan nonuwa kamar me shayarwa. Sannu da zuwa angona, tafad'a tare da zama kan kujerar dake kusa dashi, hannu tasa ta d'auki sauran lemun dayasha cikin cup d'in glass ta kur6a sannan ta ajiye, ta maida kallonta gareshi, tare da tambayarshi, "ya hidima? Yace "Alhamdulillah, My dear lefe yayi kyau amma ka manta, da sarkar gold d'in dana fad'ama ba irin wacce ka sako bace, inaso dan Allah ko zaka musanyo mani ne?....... "Ke Fadila, cikin d'aga murya yafad'a, idan bazaki iya amfani da abinda kika gani acikiba, to ba'ayimaki dole ba, nidai namaki iya 'kok'arina......... Daga mashi hannu tayi, cikin d'aga murya take magana, "Dakata khaleed, bazakaje wata ta 6ata maka raiba kazo ka huce kaina, ko kana tinanin banida labarin abinda ke faruwa, tsakaninka da wannna yarinyar, Auta take ko miye..... A fusace ya mike tsaye, yace ni zan wuce, ba wannan ya kawoniba, zowa nayi inji idan kina bu'katar wani abu, kuma naji bakida bu'katar kome sai anjima, Ya fita Daga falon yanufi harabr gidan inda ya ajiye motarsa, yana niyyar Shiga yaga mamar Fadila, direba ya sauketa, ta dawo daga Unguwa, nan ya gaisheta, ta tambayeshi momynsa, yace tana lafiya, sannan ya shiga motarsa ya wuce. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [03/08 10:20 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _Page_ 61-65 *_Bayan sati biyu_*• ✍🏽 Yau sauran sati d'aya bikin khaleed da Autar Hajiya da kuma Fadila, duka 6angarorin guda ukku shirye-shirye suke, ko'ina ka gani suna cikin farin ciki. Amarya Fadila ansha gyara anyi fresh, dan tin ana saura sati biyu bikin take faman gyara kanta, duk wani Abu datasan yana da amfani a jikin mace tana amfani dashi, tin Daga kayan gyaran jiki zuwa kayan tsumi ba Wanda batayi. 6angaren Autar Hajiya kuwa kullum ba abinda take sai tinani, duk tabi ta rame ta kod'e tayi wani irin fari, idanunta sun kara fitowa, a haka dai aketa shirin biki, 6angaren Hajiya kuwa ba irin rarrashin da batayima Auta ba, haka babanta tin yana mata fad'a har ya dawo yana rarrashinta yana mata nasiha, da haka dai aka samu tad'an saki jikinta, aka cigaba da hidima. A 6angaren khaleed kuwa shima hidima yake sosai shida abokaninsa, zuciyarshi fal da farin ciki, dan jiya yaje gurin Autar Hajiya ta saki jiki sunyi magana ta fahimta, wacce rabon daya samu haka tin ranar da tasan ze auri Fadila. Ana saura kwana biyu d'aurin aure sadiyya tazo gidan su Auta, da sallama ta shigo, gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, bayan ta gaisheda mutanen dake tsakar gidan, sannan ta wuce kitchen inda ta hango Hajiya tana faman had'a wasu kaya, tace "Hajiya ina wuni, Hajiya ta amsa da "lafiya lao sadiyya, ya mamarki, tace "lafiya lao tace a gaiaheki, kuma tace abaki hakuri bazata samu zuwa yau ba sai zuwa gobe, saboda tayi ba'ki, cikin fara'a Hajiya tace "ba kome wallahi Allah kaimu goben, sadiyya ta amsa da Ameen, sannan ta tambaya, "ina Autar take? Tana d'aki ki isa, tana ciki. Kwance take kan godo ta juya fuskarta ta kalli bango, tayi lamo kamar me bacci, muryar sadiyya taji tana cewa "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida...... Auta tayi kamar bata jita ba, dan ko motsi batayiba, daga inda take kwance, sadiyya ta matso kusa da ita ta zauna gefen gadon, takara magana karo na biyu, "Amarya......., nan ma shiru Auta tayi mata, sadiyya ta'kara magana karo na ukku cikin jin haushi ta kaimata duka, tare da fad'in Auta banison rainin wayo, ya inata maki magana zaki wani sahareni...... Da sauri Auta ta tashi zaune tana Sosa inda sadiyya ta doketa, tana murmushi, tace "ina jinki wallahi, abinne naki yabani haushi da kika kirani amarya, aini nafi 'karfin amarya sai uwar gida, sadiyya tayi dariya tace to ai kinsan dai Fadila ta girmeki saboda haka itace babba, kuma itace uwar gida kekuma amarya, Auta tace "tab wallahi bazan yardaba, badai ance d'akin wacce yafara kwana ba itace uwar gida, to wallahi d'akina ze fara kwana. Sadiyya ta kyalkyale da dariya, dan ita yanzu rigimar Auta dariya take bata,tace "to yanzu ba wannan ba kitashi muje gurin gyaran jiki, Auta tace "ke nifa na gayamaki ba wani gyaran da zanyi, a kaini haka yanda nake, wallahi sadiyya konayi niyyar yin wani Abu da natuna ba nikad'ai za'a kai gidan khaleed a matsayin matar saba sai inji duk na sire, Sadiyya tayi murmushi, tace "Hmm auta kenan, to ay yanzu yakamata ki gyara, dan na tabbata ita waccan bazata zauna hakaba, kema dagewa zakiyi, ki gyara kanki yanda koda kin jera da waccan aga kamar sarauniya da baiwarta. Suduka suka kwashe da dariya, haka sadiyya ta rarrashi 'kawarta harta yadda sukaje gurin saloon, Daga nan suka wuce gurin 'kunshi, Basu dawo gida ba sai gab da magrib, suna dawowa, sadiyya tayo Alwala ta kabbara sallah, ita kuma sadiyya wanka tashiga, bayan tafito Daga wankan ta haye gado tayi kwanciyarta, kasancewar tana fashin sallah, bayan sadiyya ta idar da sallar ne suka cigaba, da tattauna yanda party da za'ayi gobe ze kasance, dan kuwa partyn Baki d'aya za'a yishi da fadila da Auta, kuma kowace da 'kawayenta. Zee Elkaseem Mmn khady [03/08 11:57 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _*Page*_ 66-70 ✍🏽washe gari ana gobe d'aurin aure, yau ne aka shirya wani 'kawataccen party Wanda Za'ayi a liyafa parlance dake cikin garin katsina, duka a 6angarori guda ukku, kowane yana cikin shiri, khaleed da abokaninsa da 'yan'uwansa, Autar Hajiya ma da 'yan'uwanta da 'kawayenta, haka ma Fadila, tana cikin shiri itada 'kawayenta da 'yan'uwanta. Da misalin karfe hud'u za'a fara aiwatar da partyn, sabida haka kafin lokacin Fadila ta gama shiryawa, wani tsadadden material ne red colour tasanya dinkin riga da siket, kayan sun matseta sosai, abinka game jiki, kirjinnan kamar ze fasa rigar, kanta kuma golden gwagwaro ta d'ora takalmanta masu masifar tsini, wanda suka taimaka gurin 'kara mata tsawo, suma golden colour, sai wata 'karamar jaka dake hannunta itama kalar golden, kallo d'aya zakama Fadila kasan amarya ce, fuskar nan tasha make-up, dan me kwalliya ta d'auko ta musamman ta gyara mata fuskarta, ta biyata kud'i me yawa. A 6angaren Autar Hajiya kuwa zaune take itada 'kawayenta, anata labari anata shewa, ko kad'an Auta batada niyyar yin wanka barantana ta shirya, sadiyya ce ta duba agogon wayarta sannan ta kalli Auta tace, Auta kinsan kau 'karfe nawa yanzu? amma ko niyyar shiryawa bakiyiba, kafin tayi wata magana, taji 'karar wayarta, tana dubawa taga sunan Ahmad, wani abokin khaleed ne, hannu tasa ta d'auki wayar sannan ta dannan OK ta kara a kunne tare dayimashi sallama, a d'ayan 6angaren Ahmad yace Ku fito gamu kofar gida muna jiranku, Tayi saurin tashi tsaye tare da dafe 'kirji tace kuna waje fa kace, yace "eh tace "gashi kuma bangama shiri ba, yace owk bari muje gidan su Fadila, idan kingama mundawo, bejira abunda zata fad'aba ya tsinke wayar. Da sauri tashiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta d'auko wani lotion me dad'in 'kamshi ta shafe jikinta dashi, sadiyya ce ta 6ata lokaci gurin yima Auta make-up, tin nan Auta tafara yin kyau, fuskar nan kamar wata balarabiya, ga kunshinta Wanda yayi masifar kyau, manyan Flowers ne yayi bakikirin sai Jan ranin daya 'kara 'kawata kunshin. Wani tsadadden farin Swiss less ne, Wanda yasha ado da flowers silver colour ta sanya dinkin doguwar riga, rigar ta kar6i jikinta dan ba 'karamin kyau tayimata ba, sannan ta sanya, takalmi silver colour, sai yar post d'in hannunta itama silver colour,kanta kuwa gwahgwaro me ta d'ora shima kalar silver, tayi masifar kyau, sannan ta d'auko turarurruka masu dadin 'kamshi ta feshe jikinta dasu. Sadiyya ta kalleta tace Amarya kinsha 'kamshi, Auta ta harareta, cikin wasa tace "kin manta, sadiyya tayi dariya tace "oh sorry tuba nike Amarya uwar gida, Auta tayi dariya tace "ki karani kirani Uwar gidana Kawai, Sadiyya tace "to uwar gida sarautar gida, suduka suka kyalkyale da dariya. Suna cikin wannan sukaji tsayuwar motoci, Ahmad, yakirasu yace su fito gasu a waje, nan aka fafa d'ibar 'kawayen amarya ana kaisu. Daga karshe kuma aka d'auki Auta da wasu sauran 'kawayenta dasuka rage. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [03/08 9:43 pm] Zee Elkaseem: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 71-75 ✍🏽 Hall d'in cike yake ma'kil da 'yan'uwa da abokan arziki, tun daga kan 'yan'uwan khaleed da abokaninsa, har zuwa 'yan'uwan Autar Hajiya da kuma 'kawayen Fadila da kuma 'yan'uwanta, Kowa yayima kansa mazauni, ana jiran shigowar ango da Amarensa, Autar Hajiya da Fadila. Bayan hall din yayi shiru, sakamakon Mr DJ daya fara magana cikin speaker's dinshi, Kowa ya maida hankali ga yanda yake jawabi. Can na hango Ango khaleed da Amarensa sun jero, tsakiya suka sanyashi, Auta na gefen damarsa yayinda Fadila ke gefen hagu, suna tafiya ahankali cikin nutsuwa, kallo d'aya zakayima Auta ka fahimci tana cikin wani yanayi, dan yanda taga Fadila ta wani shishshigema khaleed ta kama hannunshi ta ri'ke abin ba 'karamin takaici yayi mata ba, tin nan tafara tinanin me zatayi ta ba'kantama fad'ila rai, kamar yanda ta ba'kanta mata. Sun Isa high table inda nan ne yazama masaukin Ango da Amarenshi, tsayawa khaleed yayi yayima fad'ila nuni akan ta wuce tafara zama kujerar can, yayinda shi tashi kujerar take tsakiya, Bayan Fadila ta wuce ta zauna kan kujerar ta, khaleed na niyyar zama kan tashi kujerar kawai sai ganin Auta yayi kan kujerar, yana shirin yimata magana ne yaji, ta kamo hannunsa, ta wani kashe Mashi manyan idanunta, tace "ka zauna mana my dear, tare da nuna mashi kujerar da itace zata kasance gurin zamanta, ba yanda zeyi haka ya zauna, sai tsarin zaman ya canja, ya kasance Autar Hajiya itace tsakiya, yayinda Fadila ta koma gefe, cikin 'kawayenta. Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama Fadila a wuya, ta rin'ka cika tana batsewa, fuskar nan tata ba annuri ko kad'an duk 'ko'karin datayi na taga ta share da abin ta nuna be dameta ba kasawa tayi, Itako Auta sai fara'a take, ta dan du'ko da Fuskarta saitin fuskar khaleed har sunaiya juyo numfashin junansu, Labari tari'ka bashi shikuma dama abinda, yake nema, sabkda haka ya biye mata, dan tin lokacin da Auta tasamu labarin ze auri Fadila maganr ta minti goma bata 'kara had'asuba, Shiyasa ya biye mata sukayita labari suna sakarma junansu wani 'kawataccen murmushi. Can zuciya ta 'kule Fadila, batasan lokacin data tashi, cikin tsananin masifa, da bala'i ta fito daga ida take zaune, ta tsaya gaban tebur d'inda aka cika da kayan ciye-ciye da lemuka kala-kala, tasa hannu tafara watsi da kayan, 'karar fashewar kofunan glass d'in gurinne ya maido da hankalin duk illahirin mutanen dake gurin. Cikin tsananin mamaki Auta ta nufi Fadila, wacce idanunta suka rufe saboda tsabar masifa, ta ri'ke hannunta tana fad'in "Haba Fadila lafiya, ya muna taron arziki zakizo ki 6ata mana, cikin tsananin fushi Fadila ta bankad'e Auta, abinka ga marar jiki ta tafi taga-taga zata fad'i dai-dai lokacin khaleed ya iso gurin yayi saurin tarbeta, ta kuwa fad'a jikinsa tana kukan shagwa6a, tana fad'in "my dear menayi mata zata tureni? 'Kara rungumeata yayi jikinsa yana rarrashinta, ita kuwa sai wani 'kara narkewa take. A fusace Fadila ta nufi hanyar Barin hall din tana zubar da hawayen ba'kin ciki, Ahmad ne yabita yana cewa, "Fadila ki tsaya mana a gyara, ai bekamata kiyi hakaba, wallahi muna cikin maganar zamuyima khaleed magana agayara tsarin zaman kawai sai gani mukayi kin tashi kina wannan d'anyen ayki, cikin dusashshiyar murya tace " Ahmad ka taimakeni ka maidani gida kada zuciyata ta buga bazan iya ba. Bayanda Ahmad beyiba akan tayi ha'kuri ta koma ta 'kiya, dole tasa ya d'auketa a motarsa dan kada yabarta tatafi yanda ranta yake 6ace wani Abu yaje yafaru da ita a hanya. Haka aka tashi partyn Kowa na jimamin abinda ya faru, wasu na ganin laifin Fadila, wash na ganin laifin khaleed,wad'anda kuma suka fahimci yanda abun yake laifin Autar Hajiya suke gani. Mmn khady [03/08 10:51 pm] Zee Elkaseem: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 76-80 ✍🏽 washe Gari da misalin karfe biyu na rana, dubban mutane suka sheda d'aurin Auren khaleed da Amarensa, Zainab _(AUTAR HAJIYA)_da Fadila. Da misalin 'karfe hud'u na yamma aka fito da Auta dan kaita gidan mijinta, bayan an kaita d'akin mahifinta yayi mata nasiha me ratsa jiki, da kuma yimata nuni da tayi ha'kuri, dan duk Wanda yayi ha'kuri duniya baze ta6a ta6ewa ba. Bayan an fito da ita daga d'akin mahaifinta aka wuce da ita d'akin Hajiya, itama Hajiya tayi mata nasiha me ratsa jiki, 'karfe hud'u da rabi aka fito da Auta aka sakata mota, ba abinda take sai kuka, da kyar aka rabata da hajiya, A unguwar lay out dake cikin garin katsina, misalin 'karfe biyar suka isa gidan, can suka iske 'yan'uwan khaleed dana Fadila dan ita tin 'karfe hud'u aka kawota. Bayan sallar magrib ne aka fara gabatar da walimar da 'yan'uwan khaleed suka shirya, wanda aka gayyato shahararriyar malama wacce zata gabatar da wa'azi kan zaman aure da kuma nasiha ga Amare, wato malama *AMINA ALIYU MOHM'D (BINTUSH~SHEIKH)* Bayan malama ta bud'e taro da Addu'a, tayi wa'azi akan ha'kuri sanna tafara nasiha ga Amare kamar haka: "Alhamdulillahi Allah Kaine abin godiya, daka azurtamu da rai da lafiya, bayan wa'azi da nayi akan ha'kuri yanzu kuma inaso inyima Amare nasiha akan zaman Aure, Wanda shima dai ha'kurin akeyi, yaku wad'annan Amare ina ro'konku da kada kuyi kishi irinna jahilai, kada kuyi kishi irinna wad'anda basu san ciwon kansuba. Kuyi kishi irinna matan Annabi Muhammad _(S.A.W.)_ Kada kuyi kishin da ze tada hankalin mijinku, kuyi kishi Wanda kullum burinku Ku kyautatama mijinku, kunsan shi rai yana son me kyauatata mashi, sannan daga 'karshe na horeku da tsafta, Ku zamto masu tsafta kada ku yarda mijinki yaga wata 'kazanta ajikinki ko ya sha'ki wani abu a jikinki sa6anin daddad'an kamshi. Haka dai malama tayi nasiha me ratsa jiki, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a Kowa ya tafi gida, bayan an raba sadakar Qur'an Kowa izif sittin, Ana Allah shima malama Albarka, Akan wannan wa'azi datayi. Da misalin 'karfe takwas na dare, gida yarage daga Auta sai 'kawayenta guda biyu sadiyya da Zahra'u sune suka tsaya suka gyagayara mata kome suka share ko'ina suka kunna turaren wuta, ko'ina na sashen ya bige da 'kamshi sannan sukayi bankwana suka tafi. Itama Fadila 'kawayenta ne suka tsaya sukayimata 'yan gyare-gyaren daya dace, sai misalin karfe tara da rabi suka bar gidan, *TO FAH MASU KARATU GIDA YA RAGE DAGA AUTAR JAJIYA SAI FADILA• πŸ€” SAI ALLAH YA KAIMU GOBE MUJI WACE IRIN WAINA ZASU TOYA*πŸ˜‚ Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [04/08 8:00 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _*Page*_ 81-85 ✍🏽Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar gidan akwai 'kofa waccce zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a 6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida khaleed da yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake. Fadaila ce ta kalli agogon dake manne jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar amma bataji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta d'auko wani tsadadden less ta sa, bata tsaya d'aura d'ankwaliba, bayan ta tsara make-up yafa d'ankwalin kawai tayi a kai, sannan ta fito general falo ta zauna jiran shigowar angonta. Auta kuwa itama tana d'akinta ta gaji da jiran shigowar ango, saboda haka, itama wanka tashiga, bayan ta she'ka wanka, ta fito, ta tsaya gaban dressing mirror tana tinanin me ma zatayi, yanzu dai kam batada lokacin yin make-up da wannan daren, lotion kawai tashafa me d'adin kamshi, sannan ta feshe jikinta da turarruka masu kyau, tanufi wadrope ta d'auko rigar baccinta, ta Sanya, tsayawa tayi tana kallon kanta, yanda rigar tayi mata, sharara tamkar batasa kome ba, dan duk illahirin surar jikinta bayyane take, tayi niyyar canja riga saboda tana kunyar khaleed yashigo ya ganta haka, amma kuma tana jin zafi-zafin da ake a garin, saboda haka tace bari ta d'an sha iska, idan taji shigowarsa sai ta caja, gado ta haye,ta kwanta lamo, zuciyarta cike da tinani kala-kala, daga nan bacci yayi awon gaba da ita. Karfe sha d'aya da rabi khaleed yayi horn Bakin get d'in gidan me gadi ya bud'e mashi yashiga,. Fadila na zaune Falo saboda haka, da sauri tanufi d'akinta ta 'kara shafa humra, me dad'in 'kamshi sannan ta dawo falon ta zauna. Da sallama ya shigo falon, cikin kashe murya Fadila ta amsa salamar, tare da mi'kewa ta rugomeshi tayi Mashi sannu da Zuwa sannan ta kar6i ledar daya shigo da ita ta ajiye gefe. d'akinsa ya nufa tabishi, acan ta had'a mashi ruwan wanka, sannan ta taimaka Mashi ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka, bayan ya fito daga wanka, wasu 'kananan kaya ya sanya masu sakai-sakai, sannan ya umarci Fadila da ta tashi suje falo. Bayan sundawo falo sun zauna, khaleed ya umarci Fadila data d'auko ledar daya shigo da ita, ta tashi tana wani yanga tana karairaya, ta d'auko ta ajiye, sannan ya umarceta ta d'auko plate da cup's, kitchen tanufa ta d'auko duk wani Abu datasan zasu bu'kata. Tana fitowa daga kitchen d'in taga ba khaleed, bata kawo kome a ranta ba, tana tinanin yana d'a'kinsa, saboda haka zama tayi tana jiran fitowarsa, amma har kusan minti talatin be fitoba, saboda haka d'akinsa tanufa, da sallam ta Shiga d'akin amma saitaga ba Kowa ciki, sai tayi tinanain koyana toilet ne, Bakin 'kofar toilet d'in ta kanga kunnenta bataji alamar mutum aciki ba, Ahankli ta tura 'kofar toilet d'in nan ta'kara tabbatar da baya ciki. Take zuciyarta ta ayyana mata inda khaleed yake, a fili ta furta *~Wallahi bazan yarda ba~* Zee Elkaseem Mmn Khady [04/08 11:19 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_page_* 86-90 ✍🏽 khaleed kuwa a lokacin daya umarci Fadila data d'auko plate kitchen, tana shiga kitchen d'in da sauri yanufi d'akin Auta , dan tunda yashigo hankalinsa na gun d'akinta ko zata fito amma shiru bata fitoba. Ahankali ya tura 'kofar d'akin kwance ya hangota kan katafaren gadonta wanda yasha shimfid'a da wani 'katon bedsheet, da manyan filo da 'kanana. Baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ahankali ya isa Bakin gadon ya tsaya yana k'are mata kallo, kaf surar jikinta bayyane take, ga fitila d'akin kunne haske fayau ko'ina, lokaci guda yaji jikinsa yafara kyarma, besan lokacin daya hau kan gadon ba ya rungumota jikinsa baki d'aya yafara shafata, yakai hannunsa kan kirjinta yafara wasa da dukiyara fulaninta. Cikin bacci tajita jikin mutum, gashi kuma anata romancing d'inta, cikin firgici ta bud'e idonta khaleed tagani ya 'kura mata ido baya ko 'kiftawa, ta bud'e baki tana shirin yin magana, ya had'e bakinsa danashi yacigaba da kissing d'inta, lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi, itako auta 'kara narkewa tayi jikinsa, tana mashi shagwa6a shikuma sai kara matseta yake jikinsa kamar wani ze kwace mashi ita, Ji yayi anturo 'kofar da 'karfi, a firgice yakai dubansa ga 'kofar, Fadila yagani tsaye tana cika tana batsewa, shi kwata-kwata yama manta da ita, wani irin haushinta yaji dan ta yankemashi jin dad'insa, cikin d'aga murya yace, "Fadila meya shigo dake nan? Bata bashi amsa ba kuma bata motsa daga inda takeba, cike da jin haushin abinda tayimashi yace "get out, ki fita nace maki ganinan zuwa. Ita kuwa Auta ganin Fadila yasa ta'kara narkewa jikin khaleed, ta dauki hannuwanta duka biyu ta sa'kalosu a wuyanshi, tana mashi wani shu'umin kallo wanda ya'kara rikitar dashi, tace "haba my dear, meyasa ka shigo baka sallameta ba, kamata yayi ka sallameta kuyi sallama kafin ka shigo, kaga yanzu tazo muna cikin jin dad'in rayuwarmu ta mana cikas. Da gudu Fadila ta juya tabar d'akin dan jin hawaye na niyyar zubo mata saboda tsabar takaici, falo ta zauna tana share hawayen ba'kin ciki, a zuciyarta tana cewa *_Lallai yarinyar nan ni zata gwadama duniyanci, to wallahi sai nayi maganinta cikin gidannan saina nuna mata nafita iya duniyanci_* Nan suka isketa zaune suma suka zauna, Auta yanda take haka tafito, bako d'an kwali kanta, gashin kanta ya zubo kan kafad'unta, saboda haka hankalin khaleed yana kanta duk wani motsi nata sai ya had'iyi yawu, Da kanshi ya d'auko ledar ya d'auko plate ya juye dankwala-dankwalan kajine guda hudu, sai fresh milk daya ajiye masu gefe, da ruwan roba na swan. Nan ya Uamrcesu dasu zo su ci, Auta dama ta kwanta da 'yar guntuwar yunwarta saboda haka matsowa tayi taci me isarta, sannan ta kora da fresh milk tasha ruwa, shima khaleed yaci sosai, sannan yasha ruwa, Fadila kuwa kasa cin kome tayi saboda zuciyarta cunkushe take da ba'kin ciki. Bayan sun kammala ne khaleed yayi masu basiha akn zaman tare, sannan daga 'karshe, ya sanar dasu abubuwan dayake so da wanda bayso, dan su kiyaye. Sannan ya kallesu yace idan akwai me magana zata iyayi, Fadila tace "babu, Auta tace ni maganata kawai itace duk abinda kakeso shi nakeso wanda bakaso kuma shine baniso kaga ra'ayimu yazo d'aya kenan. Nan suka cigaba da fira sam-sama, yawancin firar ma tsakanin Auta ne da khaleed, Fadila duk takaici yahanata magana. Saida suka kai 'karfe sha biyu da rabi suna falo, lokacin khaleed yafara jin bacci dan dama akwai gajiya tattatare dashi, saboda haka yace to yakamata mu kwanta hakanan dan dare yayi saosai, Fadila tace "Eh gaskiya nima baccin nakeji, kazo mutafi dan nima gajiyarce a jikina, Fadila ta tashi tanufi d'aki tana lumshe ido alamar bacci, ganin Auta bata tankaba yasa khaleed ya tashi yabi bayan Fadila, Auta tayi saurin shan gabanshi tace "Ai d'akina zamuje ko, Fadila najin haka ta juyo tace "kamar ya d'akinki, amma kinsan ay na girmeki, kuma niyakamata ace anba girmana, Auta tayi murmushi tace "ay nan gidan aure ne ba maganar girma, saboda haka kazo muje kawai, nan rigima ta kaure tsakaninsu, wannan tace d'akinta za'a fara kwana wannan tace nata za'a fara kwana, khaleed yarasa yanda zeyi dasu kawai sai ya koma falon ya zauna kan kujera three seater ya zauna, suma suka biyoshi suka zauna, kowace da abinda take sa'kawa a zuciyarta. Shikuwa khaleed daya gaji da zama kwantawa yayi kan kujerar, tin yana kallonsu yana mamakin halinsu, har bacci yayi awon gaba dashi. Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tasheshi daga baccin dayake, zaune yagansu, suduka sunyi shiru, da Alama ba wacce ta runtsa cikinsu, tashi yayi yanufi d'akinsa yashiga toilet yayi wanka sannan yayo Alwala ya kabbara sallah. Sai lokacin sukuma kowace tanufi dakinta dan gabatar da tata sallar. Zee Elkaseem Mmn khady. [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [04/08 6:34 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 91-95 ✍🏽 Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a gidan khaleed, yau kimanin kwana ukku kenan kullum kwanan zaune sukeyi a falo, dan Auta ta kafe ita a dole sai anfara kwana d'akinta, ita kuma Fadila tace Sam bata yardaba, hakan ke sawa khaleed yayi kwanciyarshi kamar yanda ya saba, wato falo kan kujera three siter sukuma haka zasu zauna su tasashi gaba sunata hararar junansu. Yauma kamar kullum, zaune suke babban falon gidan, da musalin 'karfe biyu da rabi na dare, shikuma khaleed yana kwance yanata sharar baccinsa hankalinsa kwance, yau ma atakaice haka sukayi kwanan zaune, asubah nayi ya wuce d'akinsa dan gabatar da sallah suma kowace tanufi d'akinta. Khaleed abin na damunsa yarasa yanda ze 6ulloma Al'amarin, saboda haka bayan yayi break fast ya shirya cikin 'kananan kaya, wandon jeans ba'ki da jar T-shirt yayi matu'kar yin kyau. 'Dakin Auta yashiga, zaune ya isketa tsakiyar falonta, kan carpet hannunta ri'ke da waya tana game, da sallama ya shiga d'akin bayan ta amsa ya'karso inda take ya zauna kusa da ita, ta d'ago da manyan idanunta ta kalleshi tace "barka da kwana, yace "ku zanyima barka kuda ke kwanan zaune, Kafin tayi magana yaci gaba da cewa, yanzu Zainab rayuwar da kuka za6ar mana agidannan kuna ganin ya dace, ace ku duka ba wacce zatayima 'yar'uwarta hakuri, Amma Auta kinga kece 'karama yakamata kiyi hakuri nafara kwana d'akin fad'ila duka fa kwana biyu ne zan dawo d'akinki, haba Auta bakison kwanciyar hankalina ne? Wani irin kuka ta fashe dashi, cike da mamaki khaleed ke kallonta, cikin maganar dayayima Auta miye abin kuka. Kuka tacigaba dayi tana cewa "shikenan khaleed ka nunamin kafi son Fadila akaina, kaje ka kwana d'akinta d'in wallahi nikuma idan har ka kwana d'akinta ranar zan bar gidannan, kuma idan natafi kada kayi tinanin gidanmu zanje, a'a zan tafi inda ba'a sanniba inda bansan kowaba, incigaba da rayuwata acan. "Idan abin gaskiyane it's kace ta hakura ta barmin mana. Haka khaleed yayi rarrashin duniyar nan amma Auta ta kafe akan sai dai ya fara kwana d'akinta, haka khaleed yabar d'akin Auta yana mamakin rigima irin tata. A d'akin Fadila ma haka yasha daga da ita yana rarrashinta akan ta ha'kura ya fara kwana d'akin Auta, amma tace sam ita bata San wannan ba, aiko abin ya 6ata ransa nan ya balbaleta da fad'a ta inda yake shiga ba nan yake fitaba, yace "shikenan kuyi duk abinda kuka iya, yanzu ke Fadila bazakiyi hankali ki ri'ke girmankiba ki kawo 'karshen wannan kwanan zaunen da kukeyi, Cikin masifa itama take magana "Wallahi bazan yardaba, yanda ita bakace ta hakura ta barmin ba nima wallahi bazan barmataba, ai ba fina sonka tayiba. Cikin fushi khaleed yafita, a harabar gidan yanufi gurin ajiye motoci ya hau motarsa ya kunna, me gadi ya bud'e mashi get yadau hanya, Gidan abokinshi ya wuce Ahmad, a ranar can ya wuni be baro gidan ba sai bayan magrib, daga nan kuma gidansu ya wuce be dawo gidaba sai 'karfe tara da rabi na dare. Zee Elkaseem Mmn khady [04/08 8:04 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 _*Page*_ 96-100 ✍🏽 Da sallama ya shigo falon, Abin mamaki yau bega kowa a falon ba kamar yanda yasaba kullum nan yake iske matan gidan zaune suna jiran dawowarsa, A hankali take tafiya dan bayaso suji karar dawowarsa, su fito su sashi kwanan falon nan, d'akinsa yanufa toilet ya shiga ya she'ka wanka sannan ya saka jallabiya marar nauyi, a hankali ya fito daga d'akin yanufi d'akin Fadila, kwance ya isketa kan katafaren gadonta tayi dai-dai tana sharar bacci. Dalilin baccinta kuwa shine, bayan fad'an da khaleed yayimata yana fita ta fashe da kuka, a zuciyarta tana cewa _(Shikenan ni dama nasan khaleed ba sona yakeba, hakanan su Momy suka ma'kale akan sai ya aureni, kuma nima ina masifar sonshi, sai yanzu na tabbatar da son maso wani nakeyi, dan kuwa kome Auta zatayi khaleed baya ganin laifinta, dama hausawa sunce so hana ganin laifi)_ Haka tasha kukanta ta gaji, Nan take kuwa kanta yafara ciwo, dama ga rashin bacci na kwana ukku, bayan magrib taji ciwon kan yayi tsanani tasamu magani tasha, da misalin karfe takwas na dare tad'an kwanta aikuwa bacci yayi awon gaba da ita. Nan khaleed ya 'kare mata kallo, yayi murmushi, sannan ya fito daga dakin, cikin hankali yakeyin kome dan kada 'yar rigimar tajiyoshi, aiko yana fitowa daga d'akin Fadila ita kuma tana fitowa daga d'akinta. Da sauri ya 'karaso inda take ya had'a jikinsa da nata yayi mata ky'k'kyawar runguma, ita kuwa ganin ya fito daga d'akin Fadila yasata jin wani irin ba'kin ciki, ta bud'e baki zatayi magana yayi saurin had'e bakinshi da nata, hot kiss yake mata, yana romancing d'inta lokaci guda ta mance duniyar datake ciki. 'Daukarta yayi kamar wata jaririya, bezame ko'ina da'itaba sai bedroom d'inta ya kwantar da ita kan gado yacigaba, da aika mata da sa'konni, a ranar dai saida khaleed yasan Auta a matsayin mace, aiko Auta tasha wahala ba kad'anba, shikuwa khaleed banda rarrashinta ba abinda yake,yanata shimata albarka, sai gurin 'karfe d'aya da rabi bacci yayi awon gaba dasu Auta tana jikin khaleed duk ta wani shagwa6e mashi. Kiraye-kirayen sallar asubah ne ya tashesu daga baccin da suke, khaleed ne yafara tashi yashiga toilet d'in dakinta yayi wanka, sannan itama ya ha'da mata ruwa me dumi da Kansa yazo ya d'auketa yakaita toilet yayi mata wankan tsarki tare da gasa mata jikinta, sannan yasa sabulu ya wanketa ya d'aura mata towel ya d'aukota, kan gado ya direta sannan ya d'auko mata doguwar riga ta atamfa, simple ta sanya sannan suka gabatar da sallar asuba, bayan sun gama suka koma kan gado suka kwanta. Wani sabon bacci yayi awon gaba dasu me cike da nisha'di da tsantsar 'kaunar juna. Zee Elkaseem Mmn khady. [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [09/08 11:12 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page````111-115``` ✍🏽 Ahaka Fadila tayi kwana biyu tana masu girki, kullum daurewa kawai khaleed keyi yana cin abincin ba dan yana jin dad'insa ba, Auta ma daurewa kawai take dan ta lura da yanda shi kanshi me gidan yake cin abincin yana 6ata rai kamar yana cin magani, amma beta6a bud'a baki yace beyi dad'iba, saboda haka itama bata ta6a nuna kome ba. 6anagaren Fadila kuwa tayi mamakin yanda khaleed ke daurewa yana cin abincinta, wanda ko ita kanta data girka shi bata jin dad'insa. Da misalin 'karfe shidda na yamma Auta ta shiga kitchen ta d'ora girki, kasancewar yau Fadila ta cika kwanakinta biyu. Cikin tsari da tsafta da 'kwarewar girki Auta take aiwatar da girkinta, jalouf din shinkafa da makaroni ta dafa, Wanda yaji kayan lambu da kayan kamshi, da kayan d'and'ano na girki, hanta zallah tayi girkin dashi maimakon tasanya nama, cikin 'kan'kanin lokaci 'kamshin girkinta ya gauraye gidan. Fadila na d'akinta taji k'amshin girkin Auta ya daki hancinta, take ta had'iyi wayu, dan tasan yau zasu debi girki, πŸ˜‹ ```{Kaji fadila iyayen kwadayi ansan aci da dad'i amma ba'asan a girka da dad'i ba 😜}``` Haka Auta tagama girkinta ta kammala kome ta jera kan dining table, gefe kuma ga kunun ayar data had'a Wanda yaji dabino da kwakwa tun a gurin markad'en ayar, sannan ta zuba mashi sugar dai-dai kima saboda bataso yayi za'ki da yawa, ga kamahin flavor mai d'andanon ayaba, sai 'kan'kara data jefa ciki lokaci guda jug d'in yayi ra6a. Da misalin karfe takwas da rabi suka hallara kan dining domin cin abinci, Auta ce ta zuba ma kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda suka d'ebi abincin suka kai bakinsu, Fadila taji dad'in abincin har cikin kwanyarta, khaleed kuwa lumshe ido yayi, yana taunar abincin cikin nishad'i ya kalli Auta yace " Zainab amma bayan kinyi candy kin shiga makarantar koyon girki koh?, Auta ta tuntsure da dariya tare dasa hannunta ta tallabo bayanshi, tace "bari ayima waigi kada ka fad'i daga kujerar, shima dariyar yayi yace "Allah kuwa da gaske tambayar ki nake, indai ba makarantar koyon girkiba yaushe mace zata iya tsara abinci haka wanda ko hotel baze kama 'kafarsaba, lokaci guda ta rage dariyar datake tare da gyara zama tace "wannan makarantar Hajiya ce, domin itace ta dage gurin ganin na iya girki kala daban-daban, tin daga na zamani har zuwa na gargajiaya, cike dajin dadi da nishad'i khaleed yakara kai abincin bakinsa, yace "Amma gaskiya Hajiya ta kyauta mana Allah saka mata da Alajannah Firdausi, Auta tace Ameen ya rabbi. Fadila kuwa wani irin kishi ne ya tokare mata zuciya, lokaci guda taji bata iya cin abincin duk da dad'insa datake ji haka tabarsa. Bayan sun kammala cin abincin, Auta ta zuba masu kunun ayar suka sha, nan ma saida khaleed yayi wani santin, Auta kuwa dayayi saita tareshi tace bari ayimashi waigi. Fadila kuwa Auta tagama 'kuleta wani irin haushinta takeji, Auta kuwa ta lura da yanda Fadila ta 6ata ranta saboda haka, ranar dad'i har cikin ranta, basu wani dad'e suna fira ba Auta ta nuna tana jin bacci, haka suka tashi suka nufi d'aki tare dayima Fadila saida safe, itama d'akinta tanufa tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka, cikin ranta tana ganin laifin momynta da bata koya mata girkiba, kodayake itama Momyn tata ba dakanta takeyiba masu ayki ne kemata koda kuwa dahuwar ruwan zafine. Haka tacigaba da tunani kala-kala, daga 'karshe bacci 6arawo yayi gaba da ita. Zee Elkaseem Mmn khady [09/08 1:02 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```page``` 116-120 ✍🏽 washe gari da safe Auta ta had'a break fast, nan suka zauna sukaci kamar yanda suka saba, bayan sun kammala khaleed ya tashi tare da d'aukar makullin motarsa, yace "nizan wuce gurin aiki saina dawo, Fadila tace Allah kiyaye hanya ya kuma bada sa'a yace "Ameen, sannan ya kalli Auta yace "zan tafi amma zan dawo da wuri, inaso kiyi mani girki me dad'i wanda zesa kunnena ya tsinke, wani tattausan murmushi tayi mashi tace "zan yi maka girki me dad'i, amma ba wanda ze tsinka kunnenka ba, sai dai Wanda zesa kayi santi wanda yafi Wanda kayi jiya, yace to shikenan nizan tafi, ita ta d'aukar Mashi jakarsa tarakashi har bakin mota saida taga tafiyarshi tana daga mashi hannu harya fice daga gidan sannan takoma zuciyarta cike da farin ciki. Fadila tariga ta gama 'kulewa da yanda koda yaushe khaleed ke yabon girkin Auta, amma ita idan girkintane yanaci yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta. Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba. Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da sauransu, ga kamshin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake. Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa. ```{ πŸ˜„kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}``` Da karfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya, wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan dining, Auta cike da nishad'i da jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya cokali, sannan ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido. ```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa``` Lokacin itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan komin dauriyar mutum baze iya cin saba. Cikin tsananin rud'ewa Auta ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta *Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka, yaushe na zabga gishiri cikin abincina har ya wuce misali. Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya bu'katar a can-cana maganar. Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har gidan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special coaking 😜. Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wani sabon d'and'ano a zo6on wanda beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata motsawa daga inda take, Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi ya wuce d'akinsa, Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa, Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6aci, nan tashiga rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o. Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Auta dani kike magana```~ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [06/08 10:33 pm] .: [06/08 9:42 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 101-105 ✍🏽 A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada khaleed ya dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba. Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan tabbatar ma idonta abinda ta gani gaskiya ne, Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba, safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta tura 'kofar d'akin tashiga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki. Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale 'kasan d'akinba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta take cewa: *_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_* Shiru tayi na kimanin minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi wani shu'umin murmushi, tace *~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~* : Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi wanka sannan ta d'auro Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan turarrukanta masu dad'in 'kamshi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa ajikinta. Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin, Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sallamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya kwana, shima wani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani sabon sonta ya shiga zuciyarshi. Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata kya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man. Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu break fast, Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu English wear riga da siket, siket d'in farine har 'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu, sai wani siriri kamar na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak. Zee Elkaseem Mmn khady [06/08 11:42 pm] .: [06/08 11:10 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 *_Page_* 106-110 ✍🏽 Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin, dan kuwa Auta ba daga baya ba gurin iya girki, ita kanta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel abinci baze wuce wannan dad'i ba. Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da wannan dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa, domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina. Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana d'akinta kinga kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu. Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta. Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata ku fidda, sai lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi. Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita haushi ke hanata magana, dan ita kome Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila. A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura, kuma kullum girkin Autar takeci, dan kuwa tare suke cin abinci su duka, •••••••••••••••••••••••••••••••••••• Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare, Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin abinci, Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi. Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace " ~_Salmanu!...... kada inga salame idan haka take_~" Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda yaushe yana yaba mata kan iya girki. Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba yanda za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki. Bayan sun kammala sun d'an ta6a fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka ba. Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka wuce d'aki. Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya wata doguwar riga ta bacci ta haye gado da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata. Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagayen d'akin zuciyarta nata tafarfasa, falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo yayi awon gaba da ita. Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [10/08 11:29 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page```121-125 ✍🏽 Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki tun kafin ta kai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa ba ita ta zuba gishiri haka ba, ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba dad'in ji. **************************** Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan swan, abin gwanin ban sha'awa. Da misalin 'karfe biyu da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da murna, Auta kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce d'akinsa, Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace kullum mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe ma haka za'ayishi, babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne. Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wuce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya, koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani juya mazaunai. Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo, dining suka sauna dan cin abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shigewarsu d'akinta tanufa tafad'a kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta dauko man le6e ta shafa, wadrope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen duwatsu daga gabanta ta Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba. Kan dining ta iske Fadila da khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da fadilar suka fahimci halin datake ciki ba. Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare dayin hanyar toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta, khaleed kuwa binta yayi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure dan bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya, Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa ```lallaima yarinyar nan nizakima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da kifin akwai dai inda kika dosa```. Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake tayi filo da cinyar khaleed, Shikuwa sai wani rarrashinta yake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba. Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, cikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici. Zee Elkaseem Mmn khady [11/08 11:44 am] .: [11/08 10:19 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 126-130 *_BAYAN KWANA BIYU_* ✍🏽 Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin tsayawa tsayin daka tayima mijinta abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta duk wani 6acin rai na baya, kuma ya dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata. Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau ta fere ta d'ora kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta d'auko abarba domin yau *(pineapple juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu datayi lemun da ita. 'Dakinta tanufa ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba me gadi ya siyo mata Abarba, Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba musu ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit. Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata da kitchen d'inta kai tsaye, tazo dai-dai window kitchen dinta kamar ance tayi duba gurin, Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta. Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka zallah tayi amfani da ita gurin yin miyar. Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah, Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali ta juye, saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa cokali ta motse, Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in. Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in, 'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan ta d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai 'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta kulle kitchen d'in ta tafi da makullin d'akinta. Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar hannunsa tayi gaba zuwa d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito zuwa falo Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya mamaye falon, Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalli khaleed tace "my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara yaci ba dad'i. Auta tayi murmushi tace "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma matsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah. Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in dazeji, Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwanyarsa. Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata da kuma addu'ar da mijinta yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya tsakaninmu, yace "Ameen my wife. Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya, batasan lokacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su 'koshi, Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in yau bare na gobe Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa, Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta. ```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata nuna 6acin ranta ba``` *_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta da Fadila_* Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [12/08 3:00 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 131-135 ✍🏽 "Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna dani, Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima mutum yawa sai ahankali, Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali, Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu, "Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambayata ma kike, duka yaushe mukayi waya dake na gaya maki. Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina uwar gidanki? Tunda nazo ban gantaba, "Auta ta harereta tare da kaimata duka cikin wasa tace "Uwar gida fa kikace, kodai amarya' ay nice uwar gidan kamar yanda nad'au Alwashi, nan auta tabata labarin yanda sukayi ranar da aka kawosu da kuma kwanakin da suka kwashe suna kwanan zaune. Sadiya tayi dariya sosai sannan ta kalli Auta tace "kai Auta bakida dama gsky rigimarki tafiki 'karfi, khaleed d'in kuka samu shiyasa kuke yanda kukaga dama, idan nice shi wallahi sai in za6i d'akin danikeso kawai inyi kwanciyata kuma dole wacce ban za6a ba ta hakura. Auta tayi dariya tace" Ay koda hakan yayi nasan d'akina ze za6a dan na dad'e da fahimtar irin tsananin son da khaleed kemani, shiyasa bani yarda inyi abinda zai 6ata ransa, Sadiya tace Yauwa 'kawata haka yakamata kiri'kayimasa shine zesa ya'kara jin sonki da 'kaunarki, kuma kada ki yadda koda wasa kiyi fad'a da abiyar zamanki wanda ze d'aga hankalinsa randa duk haka ta kasance sai son dayake maki ya ragu a cikin zuciyarsa. Auta tace "ina ay bazan yarda haka ta faru ba, dan nayi al'kawarin babu ranar daza'ayi kace-nace dani a gidannan, amma kuma naga take-rakenta tana Neman ta ragemun son da mijina yakemin ta haryar 6atamin duk wani Abu dana girka dan na faranta ransa. Nan Auta ta kwashe labarin yanda Fadila tari'ka zabga mata gishiri cikin abinci, Wanda sanadin haka khaleed yafara juya mata baya, Sadiya tace "tab ammafa yarinyar nan makira ce, wato ita nata ba dad'i shine ta 6ata maki, tsabar ba'kin ciki kawai, amma kin kyauta da kika kyaleta, kawai ki ri'ka kaffa-kaffa da duk wani Abu wanda kikasan zata iya 6ata maki. "Tab wallahi bazan 'kyaletaba, Auta ta fad'a cikin d'aga murya, Sadiya tayi saurin sa hannunta ta rufema Auta baki, tare da cewa "ki rufamin asiri kada kiyi wani Abu ace nice nazo na sakaki, kuma kinsan fa yanzu haka tana jinmu, Sai lokacin Auta tayi 'kasa da murya tace "wallahi bazan 'kayletaba dole sai na rama abinda tayimin, sadiya tashiga bata hakuri akan ta hakura ta 'kyaleta ai dai tasan tafita, Auta tace "Hmm Sadiya inaga kin fara manta ni, sadiya tayi murmushi tace "ina zan manta da rigimarki Auta, amma ai yanzu yakamta ki rage wasu abubuwan saboda yanzu gidan aure kike ba gidan iyayenki ba. Auta tasan halin Sadiya idan ta biyemata tsaf zata sage mata gwuyawu taji bazata iya aiwatar da kome akan ramuwar abinda Fadila tayimata ba, Yawarta ta d'auka dake ajiye kan bedsite ta duba, sannan ta kalli Sadiya tace "kinga rana tayi har karfe sha d'aya da yan mitoci, bari nashiga kitchen na samo maki abinda zakici, nasan bazaki iya cin abincin waccan matar ba, Sadiya tayi murmushi tace "wallahi da kin barshima dan tafiya zanyi yanzu, Auta tace wallahi bazaki tafiba sai kinci abinci, kinsan me zan dafa maki, bata jira abinda zata fad'a ba tace taliya da manja da yaji zan dafa, nasan ke mayyar tace, suduka suka sa dariya. Tare suka shiga kitchen d'in, cikin minti talatin suka gama girka taliyar suka zuba a flate, sauka zabgo uban yaji, amma duk da haka saida Auta ta taho da wani Yajin cikin wani 'karamin vowel wai zata 'kara gabanta. Sai gurin karfe sha biyu da rabi Sadiya tayi haramar tafiya gida, tare suka fito daga d'akin a babban falo suka had'e da Fadila ta fito daga d'akinta zata shiga kitchen, nan suka gaisa da Sadiya kowanensu ba yabo ba fallasa, sannan suka wuce, har kusan get Auta ta rakata sukayi bankwana, tare da mi'ka mata wata yar 'karamar leda wacce ta had'amata kayan make-up aciki. Auta na komawa d'akinta, toilet ta fad'a ta she'ka wanka, bayan tafito ta zauna gaban mirror ta d'and'asa kwalliya, sannan ta d'auko wasu 'kananan kaya riga da wando ta sanya, Rigar ta d'an sauko dan ta rufe mata rabin cinyarta, amma ta matseta sosai, sai wando pencil, sannan ta dauko wani karamin gyale tayi rolling, lokaci guda ta tashi daga jinsin Hausa zuwa na larabawa, dan idan ba magana tayiba sai kace bata ta6a jin yaren hausa ba. Fadila kuwa itama lokacin tagama tsara kome na abinci kan dining, sannan takoma d'aki ta she'ka wanka shigar doguwar riga tayi ta atamfa, itama tayi kyau gwargwadon nata. Da misalin 'karfe biyu da minti arba'in khaleed yadawo gidan, suduka falo ya iskesu, sukayi mashi sannu da zuwa, hankalinshi duka nakan Auta, kallonta kawai yake yanajin wani feeling tattare dashi, Saida Fadila ta lura da irin kallon dayakema Auta sannan tayi dabarar zuwa kusa dashi tace, "muje ka watsa ruwa ko, ga kuma abinci yana jiranka. Beyi mata musu ba suka wuce d'akinsa, amma cikin ransa jiyake inama Auta ce suke tare da ba abinda ze hana su kashe arna kafin su futo. Zee Elkaseem Mmn khady [12/08 4:14 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 136-140 ✍🏽 Zaune suke kan dining sunyi shirin cin abinci, kamar yanda suka saba duk wacce ke girki ita ke zuba ma kowa ta ajiye masa gabansa, yauma Fadila ce ta zuba masu ta ajiye masu, lokaci guda Auta ta ebi abincin takai bakinta, Dadai lokacin shima khaleed ya ebo abincin yakai bakinsa, Wani irin zafi yaji ya ziyarci 'kwalwarsa, ya mamaye duk illahirin Kansa, har cikin kunnuwansa yakejin bala'in yajin da aka zambad'a cikin abincin, Wani mugun attaruhu aka zabga irin me yajin nan, Kalmar innalillahi kawai yashiga furtawa, dan shi mutum ne wanda be shiri da yaji ko kad'an, Robar ruwan dake gabanshi yayi saurin jawowa, ya tsiyaya ruwan cikin cup ya shanye, ya kara cika cup d'in ya shanye ko zeji sau'kin rad'ad'in yajin dayakeji amma abanza dan ko alamar zebar jin zafin beyiba. Dai-dai lokacin kuma yaji Auta ta fashe da wani irin kuka, yanda kasan wata 'karamar yarinya ta tashi tsaye, duk ta wani gigice tanata yarfa hannu, ta bud'e baki tana sha'kar iska tana fad'in yaji, lokaci guda fuskarta tayi jawur, abinka ga farar mace, ga hawaye share-share. ```{Niko zee da nike tsaye ina kallon ikon Allah ri'ke baki nayi ina mamakin Auta dake kukan yaji, kamar ba ita bace tagama cin abinci da 'kawarta suka zabga yaji amma ita saida ta 'kara kan wanda suka zuba}``` Khaleed kuwa koda yaga yanda Auta ta fita hayyacinta, tanata kuka saboda yaji, besan sanda yayi saurin zuwa inda takeba ya rungumota jikinsa, ya nufi kujera three saater da ita ya zauna ya d'orata kan cinyarsa, yana rarrashinta kamar wata 'karamar yarinya, ruwa ya d'auko ya zuba cikin cup yabata ta shanye amma yana cire cup d'in daga bakinta saita fashe da wani sabon kuka, Lokaci guda khaleed ya rud'e yarsa yanda zeyima Auta taji sau'kin yajin. Bakinsa ya d'ora kan nata tare da tura harshensa cikin bakinta yashiga tsotsar bakin nata kamar yasamu wani sweet 🍬, wai a dole ze tsotse mata yajin, Dama abinda auta ke nema, itama tacigaba da kissing d'insa tana 'kara shigewa jikinsa, lokaci guda khaleed ya susuce ya manta da maganar wani yaji dayakeji, yacigaba da aika mata da sa'konni masu wuyar fassarawa, ita kuma sai wani 'kara shigewa take jikinsa tana shagwa6ewa, Abu yayi nisa hannuwan khaleed kan 'kirjin Auta yanata wasa da dukiyar fulaninta, itako batayi 'ko'karin hanashiba saima 'kara mi'ka mashi kanta datayi. Wani irin kukan ba'kin ciki Fadeela ta fashe dashi, dan duk abinda sukeyi gabanta sukeyi, kallonsu kawai take takasa magana saura kad'an zuciyarta ta buga, wannan kukan dayazo mata shine samun sau'kin takaici da ba'ki cikin da Auta ta 'kunzuga mata. Da sauri ta tashi tanufi d'akinta, minti biyar batayiba da Shiga, sai gata ta fito, sanye da gyale, da takalmi a 'kafarta, sai yar poss a hannunta, Sai lokacin ta iske khaleed ya sake Auta, amma suna zaune kusa da juna kowanensu yana cike da sha'awar d'an'uwasa saboda wasanni da sukayi, abin ba'a cewa kome πŸ™ˆ. Bata ko kallesuba tanufi 'kofar fita daga falon, fuuu kamar zata tashi sama, khaleed ne yayi saurin tashi yabi bayanta yana tambayarta "Fadila ina zaki? Bata ko saurareshiba tayi gaba abinta. Tana fita get d'in gidan takoyi sa'a wani me napep ya ajiye wata mata wani gida kusa dasu, nan tafad'a mashi inda ze kaita, tashiga. Khaleed na fitowa napep d'in na barin 'kofar gidan, "ya salamm ya furta, can kuma sai yayi wani guntun tsaki yace ```"kinyi laifi kuma kifi wanda kikayiyamawa zuciya``` Gida ya koma ya iske Auta zaune inda yabarta, nan take tambayarsa, "Lafiya kuwa saboda me Fadila ta tafi, be bata amsa ba sai rungumota dayayi jikinsa yafara shafata ta ko'ina, Auta batayi 'ko'karin hanashiba saida taga yana neman wuce gona da iri, sannan tayi saurin tureshi, ta tashi zaune, nan khaleed ya marairaice mata yayi kalar ban tausayi yace (please Auta help me) ki taimakeni nariga na shiga wani yanayi, cike da tsoro Auta ta kalleshi taga yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja, Lokaci guda ta langa6e tana bashi ha'kuri "kayi ha'kuri my dear kaga ba aykina bane, yanzu idan nabaka kaina mun shiga ha'k'kin Fadila, kayi hakuri kada kasa kanka cikin maza masu rashin Adalci tsakanin matayensu. Haka Auta ta rarrasheshi har ya hakura, nan ya wuce dakinsa, ya shiga toilet yasake watsa ruwa sannan ya dawo yabi lafiyar gado. Itako Auta yana shiga d'akinsa, itama nata d'akin tanufa tana ahiga ta she'ke da dariya tace ~_(Fadila dani kike magana)_~ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [13/08 7:03 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 141-145 ✍🏽 Da sallama Fadila ta shiga gidan, falo ta tarar da momynta tana zaune hannunta rike da (newspaper) jarida tana dubawa, Cikin fara'a ta kalli Fadila ta amsa mata sallama, dai-dai lokacin Fadila ta tsinci kanta da tinanin yanzu idan momynta ta tambayeta meya kawota me zatace, Muryar momynta ta katse mata tinanin datake, "Ina me gidan naki na ganki ke kad'ai? Fadila tayi saurin dawowa daga tinanin datake ta kalli momynta tayi murmushi, dan bataso ta gane tana tattare da wata damuwa, tace "shine ya saukeni yana sauri ne yanada meeting a office d'insu shine ya wuce, yace idan yadawo d'aukata ze shigo, Momy tace "owk" Sukayi shiru na 'yan wasu mintittika, Fadila kuwa tunani tashiga yi, a zuciyarta tana cewa: *_Yanzu wannan 'karyar danayi idan khaleed ya'ki biyoni ya zanyi, kokuma idan yazo yace bada izininshi na fito ba , Allah dai yasa ya rufa min asiri_* "Fadila lafiya naga kinyi shiru kamar kina tunanin wani abu, kodai akwai abinda ke damunki ne? Da sauri Fadila ta washe ta tashi tana murmushi tace "lah ba kome Momy, tanufi hanyar kitchen tana fad'in me kuka dafa wlh yunwa nakeji, Bata jira amsar Momy ba tashige kitchen tazubo tuwon shinkafa da miyar d'anyar ku6ewa, sannan ta d'auko lemu a pridge ta dawo falo ta zauna tafara ci, Momy kuwa kallonta kawai take azuciyarta tace *Anya Fadila* "Fadila yanaga kinatacin abinci haka kamar wacce ta kwana bataciba? Fadila tayi saurin kai dubanta ga momynta tace " banci abinciba na fito saboda ina d'okin ganinki Momy, tafad'a tana murmushi, Itama Momyn murmushin kawai tayimata tacigaba da duba jaridar dake hannunta. Har misalin 'karfe shidda da rabi na yamma khaleed bezo d'aukar fadila ba, momy ta kalleta tace "khaleed shuru kodai ya manta dake ne, Fadila taji gabanta yafad'i tace "a'a Momy yana zuwa, inaga har yanzu begama abinda yake bane. Fadila tashiga damuwa hankalinta yafara tashi ganin har angama sallar magrib amma khaleed bezo d'aukar taba, gashi bataso dadynta ya tarar da ita kuma tasan ana gama sallar isha'i ze dawon gidan. Karar tsayuwar motarahi ce ta dawo da ita daga dogon tinanin datakeyi, Da sallama ya shigo gidan, Momy ta amsa tare da yimashi sannu da zuwa, falo akayimashi masauki, bayan sun gaisa ya kalli fadila wacce dama on ready tagama shirin tafiya zuwanshi kawai take jira, yace "ki taso muje ko kinga dare yafara, Wani sanyi fadila taji cikin zuciyarta, da khaleed be fad'i dalilin tahowarta ba. Haka suka bar gidan, Fadila, nata godema Allah daya rufa mata asiri, dan yau da Momy tasan da yanda ta taho gida da ranta idan yayi dubu sai ya 6aci. Haka suka shiga mota suka d'au hanya, tinda suka fara tafiya ba Wanda yacema d'an uwansa kome har suka isa gida. Koda fadila tafito daga motar kasa shiga tayi gidan saida tajira khaleed sannan suka shiga tare, Falo suka iske Auta zaune kan kujera, sanye take da wata riga me hannun bes da wani d'an 'karamin siket iya gwiwa, hannunta ri'ke da remote tana canja tasha zuwa *ZEE CINEMA* dayake ita meson kallon Indian film ce, kanta babu ko d'an kwali gashin nan ya zubo 'kan kafad'unta, cike da murna ta taso ta rugume khaleed, "sannu da zuwa mijina, murmushi yayi tare da bata kiss a kumatu yace "yauwa matata. Fadila kuwa tana tsaye tana kallon ikon Allah, sai lokacin Auta ta kalleta tace "Andawo lafiya, Bata amsa mataba illah wata uwar harara data buga mata sannan taja dogon tsaki "mtswwwww ta wuce d'akinta. Khaleed ma d'akinsa ya wuce, Auta kuwa dariya tayi, dan ganin tagama 'kule fadila, ta koma ta zauna taci gaba da kallonta, canja tasha tayi zuwa *STmusic* aiko ta iske an sanyo wa'kar *justing viiver* cikin wa'karshi me taken _(Love me love, kiss me kiss me)_ dama tana masifar son wa'kar duk ta iya ta, saboda haka taciga da bi, tana 'yar rawa daga inda take zaune. Lokacin Fadila tafito daga d'akinta tanufi kitchen, ta kai dubanta ga Auta wacce tayi kamar batasan da mutum a falon ba, wani 'kululun ba'kin ciki ya tsaya mata tayi tsaki Mtsww "Aykin banza tafad'a sannan tawuce kitchen din. Zee Elkaseem Mmn Khady [13/08 8:10 am] .: [13/08 7:40 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 146-150 ✍🏽 Washe gari, Fadila tagama had'a musu break fast, kunun gyada ne ta she'ka musu, yayi gwanin kyau, dan ta masifar iya kunun gyad'a dan duk cikin abinda take girkawa a gidan shi kad'ai ne takeyi susha cikin kwanciyar hankali, kuma wani lokaci har khaleed ya yaba. Yauma shine ta she'ka masu, tare da soya masu dankakali da kwai, bayan tagama ta jera kome kan dinning ta koma d'aki dan yin wanka. Auta kuwa dayake ba itabace meyin girkin tuni ta dad'e da yin wankanta ta shirya cikin Riga da siket na material tayi kyau sosai. Tana jin shigewar Fadila d'aki, sai tafito tana tafiya ahankali, sad'af-sad'af yanda ba Wanda ze iya jiyo 'karar takun ta, hannunta ri'ke da wani 'karamin cup, dining tanufa inda fadila tagama jera kayan break fast d'insu, ta bud'e, plask d'in dake d'auke da kunun gyad'a wanda yaji peak milk yayi fari 'kar, ta zuba abinda ke hannunta cikin cup, ta d'aga plask din tad'an jijjiga yanda ze gauraye kada a gane anzuba wani abu daga baya, tayi saurin komawa d'akinta. Zazzaune suke kan dinning kowane da cup me d'auke da kunun gyad'a a gabansa, dankalin da kwai suka fara ci saboda kunun akwai zafi, Khaleed ne yafara d'aukar cup din gabansa yakai baki, dan yana sauri yafita aiki dan yau yanada patient's dayawa a hospital, Wani irin d'and'ano yaji na daban, cikin kunun Wanda ko a mafarkin baya tinanin jinsa cikin kunun, Cike da 6acin rai ya kalli Fadila, ya daka mata harara tare da Jan wani irin dogon tsaki "Mtswww, Fadila bata kai ga fara shan kununba saboda haka batasan yanda testing d'insa yakeba, cike da 6acin rai tatashi tafara magana tana d'aga murya "gaskiya khaleed nagaji da cin mutunci da cin zarafi dakakemin cikin gidannan, shikenan ni kullum nice abin wula'kantawa dan kana ganin wannan kod'dad'iyar yarinyar tare da kai..... Kafin ta ida rufe baki, sai jin abu tayi ajikinta, wata irin 'kara ta saki dan kunun yanada sauran zafi, zuciya takai khaleed ya watsa mata shi, cike da masifa yatashi yana cewa "ke har kinada bakin dazakice anyi maki rashin adalci, kenan adalcinne yasa zaki zambad'a mamu uwar kanwa cikin kunu, wannan kanwar da kika zabga ko kunun kanwa aka zubamawa baze shawuba, barantana kunun gyad'a wanda beda had'i da kanwa. Sai lokacin Auta tayi magana, tace kayi ha'kuri mijina, kayimata uzuri, wata 'kila da kunun kanwa zatayimana, kasan shima yanada dad'i sosai. Bebi takansuba suduka, cike da 6acin rai ya d'auki makullin motarsa yafita, Har yabar falon Fadila na tsaye gurin kamar an dasata, ba abinda take sai zubar da hawaye, Auta ta tashi ta kalli fadila, datayi tsaye da kunu ajiki, har ga Allah tabata tausayi, amma kuma koma miye ita ta fara, Dariya tayi, tace *"Kije ki wanke*, tashige daki tana cigaba da dariyarta, har Fadila na jiyo sautin dariyar. Haka Fadila ta tattare rigar tanufi d'akinta, tacire, sannan tafad'a toilet ta sakarma kanta showar, bayan ta gama wankan ta dad'e toilet tana kuka. Bayan tagama wanka ta sake shafa lotion me dad'in 'kamshi, ta saka wasu kaya. Auta kuwa tana d'akinta ta kwanta ruf da ciki kan gado, tana danne-danne cikin wayarta, kawai jitayi kamar alamar mutum a kanta, da sauri ta d'ago takai dubanta kan Fadila wacce ke tsaye tana cika tana batsewa. Take wani irin mugun tsoro yakama Auta,dan ganin Fadila yau har cikin bedroom d'inta, tasan idan za'a barta da Fadeela sai dai taci na jaki. *_innalillahi'wa,inna'ilaijirraji'un_* tashiga furtawa duk illahirin jikinta kyarma yake, gashi ba kowa gidan daga ita sai Fadila. ```Su Auta anbani ga tsoro ga jan fad'a πŸ˜‚ nidai zee barin gidan nayi dan bazan raba wannan fad'an ba, tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka``` πŸ˜„ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [13/08 5:47 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 151-155 ✍🏽 Tafiya yake a mota amma zuciyarsa cunkushe da tinani kala-kala, saida yakusa kaiwa asibiti, ya tuna da ya manta wasu muhimman takardu wanda yau ne yakamata yaje dasu, Juya akalar motar yayi, ya koma gida, me gadi yatashi da Sauri ze bud'e mashi get, amma sai ya tsaidashi, yace" kabarsa kawai zan ajiye anan dama wata yar mantuwa nayi zanshiga na d'auko, me gadi ya russuna yace "to ranka ya dad'e. Shiru ya iske falon alamar matan gidan kowace na 'dakinta, sallama yayi sannan yashiga, d'akinsa ya wuce kai tsaye, Auta kuwa tana kan gado ido ya raina fata, ga fadila na tsaye bata dai tankamata ba, kuma batada niyyar barin d'akin, Cikin sa'a Auta tajiyo sallamar khaleed a falo, wanda ko kad'an fadila bata jiba, kodan tana cikin 6acin raine, oho πŸ€” Saukowa tayi daga kan gado, tazo gaban fadila ta kama wuyan rigarta tacimata kwala, sannan ta kwanta kasa ta fasa ihu tana cewa "dan Allah kiyi hakuri, wayyo nashiga ukku zata kasheni, menayimaki zaki kama dukana, wayyo Hajiya kizo zata kasheni, iya karfinta take maganar cikin murayar kuka tana kuma buga 'kafarta jikin gado da bedside, sannan kuma takama wuyan rigar fadila ta ri'ke sosai, hakan yasa dole fadilar ta duko yanda idan kagani sai kace dukanta takeyi da gaske. Fadila kuwa mamaki ne yagama rufeta, tanata kokarin 6am-6are wuyar rigarta daga hannun Auta amma ta kasa, saboda Auta ba 'karamin ri'ko tayi mataba. Khaleed na d'akinsa yana tattara takardun dayazo nema, yajiyo ihun Auta tana Neman taimako, aiko da hanzari yanufi d'akinta dan ganin abinda ke faruwa. Fadila yagani duke kan Auta, itakuma tana kwance 'kasa tana Neman taimako, da sauri ya Isa gurin ya jawo fadila da iya karfinsa, wadda ganinsa yasa Auta tasaketa daga sha'karar datayimata, Wani lafiyayyen mari ya d'auketa dashi, Fadila tayi saurin dafe gurin daya mareta, zatayi magana ya'kara d'auketa da wani lafiyayyen mari, yana huci yace "bakida hankali fad'ila zaki kama 'yar muatne da duka haka, so kike ki kasheta. Lokacin kuma Auta ta tashi daga Inda take kwance tayi wujiga-wujiga, fuskar nan sharkaf da hawaye, idan ka ganta saika rantse kace mugun duka akayi mata. Fad'awa tayi jikin khaleed tana kuka, shikuma ya rungumeta yana rarrashinta kamar wata yarinyar goye, sannan ya maida dubansa ga Fadila wacce ta dafe kunci tana zubar da hawayen takaici, Yafara bal-baleta da masifa, ta inda yake shiga batanan yake fitaba, iya tsawon rayuwar Fadila bata ta6a sanin khaleed nada fad'a haka ba sai yau. Bayan yagama zazzagamata bala'i sannan ya nuna mata Kofa yace *(Get out)* ki fita nace daga d'akinnan tin kafin inyimaki mugun bugun dazaki kasa tashi, sha-sha-sha wacce batasan girmantaba, in banda sakarci me zaki daka jikin Zainab, Ki duba girmaki ki duba nata, kin kai biyunta, duk maganar nan dayake Auta na rungume jikinsa tana kukan shagwa6a. Haka fadila tabar d'akin cike da takaici, tana mamakin yanda Auta ta Jamata sharri cikin 'kan'kanin lokaci. Babban falo ta zauna tana sharar hawayen ba'kin ciki, Kusan kimanin minti talatin Fadila na zaune falo tana kuka, sannan khaleed yafito shida Auta,yana mata magana wacce fadila batajin me suke cewa amma dai taga Auta na dariya hadda kyalkyatawa, Saida sukazo gab da ita khaleed ya kalleta ya buga mata wata uwar harara, yace "gatanan zan tafi gurin ayki, idan kin isa' kin haihu ga iyayenki, kuma kin isa marar mutunci to in dawo in iske gawar Auta a gidannan, yabuga wani dogon tsaki "mtswwww sannan ya wuce, tare da ba Auta lafiyayyen kiss a kumatu yace saina dawo matata, *(Tak care of your self)* ki kulamin da kanki, wani lafiyayyen murmushi tayi mashi tace *(never mind my husband)* karka damu mijina. Haka tarakashi har bakin get saida taji 'karar tashin motarshi Alamar yatafi, Sannan takama hanyar komawa cikin gidan. Saida tazo 'kofar shiga falon tatsaya tana tinani, "{```Yanzu idan nashiga Fadila takamani ba abinda ze hana ta rama marin da nasa akayimata, me sau'ki kenan idan batayimin d'an banzan duka ba}``` Tsayawa tayi tana shawarar yanda zata shiga d'akin, ga kuma fadila zaune. Ta dade nan tsaye kafin ta yanke shawarar ta wuce d'akinta da gudu kada tabari Fadila ta kamata. Haka kuwa akayi da gudu, tashigo falon da niyyar ta wuce d'akinta ta kulle kanta, bazata fitoba sai khaleed ya dawo, amma ina, tariga ta makara, dan ko kusa da 'kofar d'akin bata kaiba Fadila ta dam'kota. Zee Elkaseem Mmn khady [13/08 6:54 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 156-160 ✍🏽 Auta tagama tsorata da yanda Fadila ta dam'kota, tanayimata wani mugun kallo, Lokaci guda 'yan cikinta suka motsa saboda tsoro, harta hangoma kanta irin dukan dazatci gurin Fadila. Amma a fili saita nuna dakewa, ta kalli Fadila Alamar ba tsoro ko 'kadan a tartare da ita, tace "dallah malama sakeni, kin wani kamani kin ri'ke ko nayimaki satane, tafad'a tana wani hararta. Wani guntun murmushi fadila tayi mai d'auke da takaici, ta kama hannun Auta ta kaita kan kujera ta zaunar da ita, sannan itama ta zauna kusa da ita, ta kalleta tace "Yanzu Auta abinda kakayimani kin kyauta, ki duba kiga yanda kika shiga tsakanina da mijina, menayimaki dazaki saka mani da wannan, Wani sanyi Auta taji cikin zuciyarta, dataga Fadila bata nemeta da fad'aba, danko da dafarko tafara tinanin yanda zasu kwashe, amma sai taga Alamun Fadila na Neman sulhu ne. Har cikin ranta taji tausayin Fadila, yakamata, dan ita dama tincan mutum ce mai matu'kar tausayi. Cikin sanyin murya Auta tafara magana, "ni dama ba da niyyar wani Abu nayiba, naga kin shigone kamar zaki dakeni, nikuma kinga dole in nemarma kaina mafita. Fadila tayi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin Zuciyarta tace ```{"Da kinsan abinda nazo dashi lokacin da baki sakamin da abinda kikayimaniba}``` "Koda kikaga na shigo ba da niyyar tashin hakali Nazo ba, nazo ne kawai muyi magana. Auta tace "To ayni bansaniba, da saikiyimin sallama kafin ki shigo, tunda naga kin shigo ba sallama sai inyi tunanin ba arzi'ki yakawokiba, "Amma kiyi hakuri, tafad'a tare da juyar da fuskarta gefe, tana wani turo baki. Fadila ta 'kara zama tare da matsowa kusa da Auta, Auta tad'an matsa, dan ita har yanzu da d'an sauran tsoro tattare da ita, gani take fadila nada wata manufa cikin zuciyarta Fadila tace "Amma miye yasa kike 6atamin duk wani abu dana dafa, a gidannan? Auta ta turo baki tace "to ay ke kikafara, dan rannan da kaina na kamaki, kina zubamin gishiri a binci, kawai kyaleki nayi a lokacin, idan bazaki manta ranar danayi sakwara da miyar agushi. Fadila tayi murmushin takaici, mai cike da nadamar abinda ta aikata tun farko, *_(Dama ance farau batada zafi sai ramau)_* "To yanzu dai nazo neman sulhu, yakamata mubar duk wannan abun damukeyi, kinga bekamata ace mun zauna muna yima kanmu abunda be daceba. Auta tace "ni dama ban d'auki abun da zafi ba, kawai dai kinsan hausawa sunce _*"Ramuwar gayya tafi gayya zafi*_ Amma kome ya wuce Allah shige mana gaba, Fadila ta Amsa da "Ameen. *```To you my namesy Autar Hajiay```*πŸ’ƒπŸ» _ina mi'ka gaisuwa ga masoya a duk inda kuke_ ~kibiyo *Zee Mmn khady* akwai sauran labari~ Zee Elkaseem Mmn khady. [10/16, 7:55 PM] ‪+234 816 616 9254‬: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```page``` 171-175 ✍🏽 koda Hajiya ta farfad'o daga dogon suman datayi, doctor ya'kara dubata ya tabbatar da lafiyarta, sannan yace za'a iya tafiya da ita, amma ari'ka kula da kiyaye abinda ze jefata cikin tashin hankali. Daga asibitin gidan khaleed aka wuce da ita kai tsaye, dan an riga an wuce da gawar a can. Cikin likaffaninsu ta iskesu, hankalinta yayi matu'kar tashi, ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa. *shikenan zainab kin tafi kin barni bayan kinsan banida wani d'a ko d'iya sai ke, Allah kai ka bani zainab kuma kai ka kwace abinka badan baka sonta ba, ya Allah ka ji'kan zainab ka kai haske cikin kabarinta* Haka tacigaba da kuka tanayima Auta addu'a nan mutane aka shiga rarrashinta ana kwantar mata da hankali. A asibiti kuma momyn khaleed da momyn Fadila sunacan suna jiran abasu dama su shiga su duba me jego da babynta, sai bayan magrib aka basu izinin Shiga, Haka suka shiga jikinsu ba 'kwari ko kad'an, Zaune take kan gado, ga baby gefenta, kuka take kamar zata fitar da ranta, idanunta sun kumbura fuskarta tayi ja, tayi face-face da hawaye, jin motsin shigowar mutane yasa ta d'ago da fuskarta wadda ruwan hawaye yagama wankewa, takai dubanta garesu. Momyn fadila itace gaba, tana zumud'in ganin fadila da babynta, ```Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un``` Ta faurta lokacin da idanunta suka sauka kan Auta, Zaune kan gado ga babynta kusa da ita. Momyn khaleed ce ta dafe, 'kirji Alamar mamaki tace *"Auta dama ba ke bace aka cemana kin mutu ba* .Auta ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa, Momy fadila.....fadila.... ce tatafi ta barni, wani sabon kuka ya kwace mata. Momyn fadila najin haka tanemi numfashinta ta rasa, nan tafa'di sumammiya, Momyn khaleed tarud'e da ganin yanda 'yar'uwarta ta suma, Da sauri ta ebo ruwa ta yayafa mata, nan ta farfad'o, Zaunar da ita Momyn khaleed tayi tana rarrashinta, tana gaya mata, irin Rahamar da Wanda yamutu gurin haihuwa yake samu, tace "kawai yanzu Addu'a Fadila take nema garemu ba kuka ba. Wani sabon kuka Momyn Fadila ta fashe dashi, dan rarrashinma da akemata jitake kamar ana zuba mata garwashin wuta cikin zuciyarta, shiru suka d'anyi nawasu yan mintittika, bakajin kome sai sheshshekar kukan Auta, Momyn khaleed ta maida hankalinta kan Auta tana rarraahinta, sai jin fad'uwar Momyn Fadila tayi, A hanzarce tajuyo gareta, tarin'ka jijjigata tana kiran sunanta, amma ina ba maganar lumfashi tattare da ita, cikin tsananin rud'ewa momyn khaleed tafita tana Neman taimako, wasu leburori ne mata suka taimaka mata, suka d'ora momyn Fadila kan gadon da ake tura marassa lafiya aka nufi Emergency da ita, nan fa lokitoci suka taru anata Abu d'aya amma numfashi ko Alamarsa babu jikin momym Fadila, amma kuma da an Auna sai aga zuciyarta na bugawa Alamar akwai rai tattare da ita. Oxygen aka sanya mata *(Abin jawo numfashi)* Sai lokacin Momyn khaleed ta buga waya ta sanar da daddyn fadila halin da ake ciki, aiko cikin tsananin rud'ewa ya iso asibitin, dan shima yayi tinanin Auta ce ta rasu amma yanzu ance Fadila ce d'iyarshi wacce yakeso, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonshi, yasa hannu ya goge. Sai 'karfe hud'u na asuba Momyn Fadila ta farafad'o, da misalin 'karfe takwas doctor yabata sallama dan ganin jikin nata da sau'ki sosai. Lokacin kuma aka sallami Auta, bayan likitan ya tabbatar da lafiyarta data babynta. 'Karfe tara dai-dai suka isa gida, lokacin an fito da gawar Fadila data babynta, Aiko da gudu Auta ta fito daga motar, tana goye da babynta, yayinda momyn khaleed ke goye da 'diyar da fadila ta bari. Bata ko kalli yawan mutanen dake gurinba tabi tacikinsu ta isa gaban makarar ta ri'ke tana cewa ```Wayyo sister fadila kada ki tafi ki barni, fadila ki dawo mu zauna mucigaba da gina rayuwarmu yanda muka tsara.... Fadila kin manta munce zamu rike yaranmu mu had'a kawunansu su tashi tsin-tsiya mad'aurinki daya, wayyo sister fadila ki dawo garemu....``` haka tayita surutai tana kuka, nan aka kakkamata ana bata ha'kuri aka shige da ita cikin gida, Hajiya tana cikin gida tanajin hayaniya daga waje, sai kunnuwanta suka ri'ka jiyo mata kamar muryar Autar ta, amma saita share tacigaba da istigifari tana nemar ma Auta rahamar ubangiji, dan tariga tasan Auta ta mutu kuma Wanda yamutu baya dawowa. Da sauri ta taso dan ganin anshigo da Auta tana kuka, wasu mata sun rirrekata, Cike da mamaki ta isa gareta tace Auta dama bake bace kika mutu, bata bata amsaba sai wasu zafafan hawaye dasuka 'kara ganagarowa daga idanunta. Hajiya batasan lokacin data rugume Auta ba tana wani irin kuka me wuyar fassara, na farin cikine kona ba'kin ciki. Da misalin 'karfe sha d'aya yan kai gawa suka dawo, Allahu Akbar ankai Fadila makwancinta. Lokacin Kuma akayi addu'a aka shafa, gidan yayi tsit bakajin kome sai sheshshekar kukan mutane 'kasa-'kasa. πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ“Ώ πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ ```Kulli nafsin za'ikatul maut, dukkan mai rai mamacine " fadila tarigamu gidan gaskiya``` πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ˜­πŸ˜­πŸ“ΏπŸ“Ώ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:56 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [15/08 9:39 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 161-165 ✍🏽 Alhmdulillahi dan kuwa yanzu ansamu jituwa tsakanin Fadila da Zainab ```{AutarHajiya}``` yanzu kowace tarage jin haushin 'yar'uwarta, Saidai fa maganar girki idan fadila tayi, basu iya ci sai dai su d'an yafuta su tashi badan sun 'koshiba, Auta kuwa kalaluwan girki takeyimasu masu dad'in gaske. Watarana Auta na zaune falo tana kallon wani tsohon Indian film mai suna *(Maharaja)* ta maida hankalinta tsaf kan TV sai jitayi an rufe mata ido ta baya, takama lalube tana dariya, takama hannun da aka rufemata fuska ta ri'ke tana dariya, tana cewa "dan Allah ko waye ayimin afuwa kada ayi wani Abu a film dinnan ban ganiba, Sakin fuskar tayi ta zagayo ta zauna kusada ita, tana dariya itama Auta dariyar take, takai kallonta ga Fadila tace "Kai sister yanzu abinda kikayimin kin kyauta, kinja an wuce banga wani wurinba, Fadila tayi dariya tace "to ay sai kiyo tariya, cike da nishad'ia Auta ta mi'ko mata remote d'in tana dariya tace "kar6i tariyo min, dan tasan ba maganar tariya tunda ba kaset bane ta sanya. Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon, murmushi kawai Auta tayi tacigaba da kallonta. Kusan Awa d'aya da yan mintoci Fadila na zaune tana taya Auta kallo, saida film d'in ya'kare ana shirin sanyo wani, Auta takai dubanta kan agogon dake manne jikin bangon d'akin taga har 12 ta d'an gota. Auta ta kalli fadila tace girki fa? Kinsan fa rana tayi baki d'ora mana ba, gaskiya ki tashi kada kiyi mana horon yunwa, fadila tayi dariya tace wace ni in horaki da yunwa, kinaso me gidan ya d'aga min yellow card kenan abani hutun sati biyu, Auta tayi dariya tace ayko baze fara ba, kinsan kuwa irin son dayake maki, ai ko hutun kwana biyu baze iya bakiba baranatana sati biyu, dariya sukayi su duka. Bayan shiru ya ratsa na yan wasu mintittika Fadila takai dubanta ga Auta tace "Niko Auta me zaihana murin'ka yin girki tare, ranar girkinki muyi tare nima idan nawa yazo muyi tare. Auta tayi dariya, tariga tagama d'agowa da fadila, so kawai take tari'ka tayata dan itama tasamu girkinta yayi armashi kamar nata. Tare suka shiga kitchen suka fara girki, farar shinkafa suka dafa me had'e da makaroni, sannan sukayi miya mai rai da lafiya, cikin 'kan'kanin lokaci suka gama suka jera kome kan dining sannan suka gyara kitchen d'in tsaf sukayi moping, kafinnan kowace tawuce d'akinta ta sheka wanka suka fito falo suka zauna zaman jiran me gidansu, sunyi kyau suduka shar dasu abin gwanin ban sha'awa. Khaleed ne yashigo gidan da sallama suduka suka tashi suka tarbeshi sunayimashi sannu da zuwa, fadila ta kar6i jakar dake hannunsa ta wuce mashi da ita d'akinsa, Saida yaba Auta lafiyayyen kiss sannan ya wuce d'akinsa, ya tarar har fadila tagama had'a mashi ruwan wanka, Wanka yashiga, bayan yafito ya sanya kananan kaya marassa nauyi, sannan suka fito suka zauna kan dining, sunfara cin abinci gwanin ban sha'awa sunata fira suna dariya,. khaleed ya kai dubansa ga Fadila yace waini fadila kodai kema kin Shiga makarntar koyon girkine bansaniba,? Auta tayi saurin tashi ta d'auko filo daga cikin filon kujerun daka zagaye a falon ta mi'koma Fadila tana dariya tace "kar6i sister yimasa waigi kada yafadi ace mune muka kadashi, suduka suka sanya dariya hada kyalkyatawa, Fadila tad'an tsagaita da dariyar datake tace "bawata makaranta nashiga ba illah makarantar sister d'ita gata zaune kusa dakai, ta nuna Auta. Cike da jin dadi, khaleed yad'aga hannunsa sama, yace "Allah nagodema daka bani mata nagari masu sona masu 'kaunata masu son kasancewata cikin farin ciki koda yaushe, ya kallesu su duka yace Allah yayi maku Albarka suduka suka amsa da "Ameen. Ranar dai haka suka wuni cikin nushad'i da annushuwa, dan ranar khaleed be fita ko'inaba, saboda jin dad'in zaman gidan dayayi. ************************* *_BAYAN WATA TAKWAS_* Ahankali take takawa zuwa d'ankin Auta saboda nauyin da cikinta yayimata, tura kyauren d'akin tayi sannan ta shiga da sallama, Auta dake kwance kan kujera 3seater itama da 'katon cikinta, idanunta rufe kamar me bacci, jin shigowar Fadila yasa ta bud'esu takai dubanta gareta, sannan takai dubanta ga cikin Fadila, har cikin ranta take tausayama Fadila yanda take fama da ciki, dan tinda tasamu cukin take ta rashin lafiya, yau zazza6i, gobe ciwon kai, ga kuma rashin 'karfin jiki, babban abin ban tausayin shine tinda Fadila tasamu ciki bata iya cin abincin kirki, ga wani irinkumburi datayi, danma koda yaushe khaleed na kula da lafiyarsu itada Auta. Duk da itama Auta tana d'an ta6a rashin lafiyar jefi-jefi, amma idan ka kalli fadila sai kace Auta ba ciwo take ba. Tare suka fito falo suka zauna suna firar duniya, duk rabin firar tasu ta yanda zasu tsara rayuwarsu ne nan gaba, da yanda zasu had'a kan 'ya'yansu sutashi kansu a had'e. Zee Elkaseem Mmn khady [15/08 11:11 am] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page``` 166-170 ✍🏽 Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar ze 6are saboda azabar ciwo, Daga khaleed har Auta sun rud'e sun rasa inda zasusa Kansu, cikin tsananin rud'ewa khaleed yakira Momynsa yasanar da ita halin da fadila take ciki, nan ta umarceshi da sutafi asibiti gatanan zuwa asbitin, tare da taimakon Auta aka kai Fadila mota sai asibiti, An wuce da ita labour room, nurses sun taru kanta anata faman amma, har 'karfe 3 na rana bata haihuba, lokacin Momyn Fadeela ta iso asibitin cike da tashin hankali, nan ta iske Momyn khaleed sai kai komo take cikin asibitin, kallo d'aya zakayimata ka gane tana cikin tsananin damuwa, khaleed kuwa tagumi yayi yarasa me kemasa dad'i. Lokacin wayarsa tayi ringing, hannu yasa ya dauka, sunan Auta yagani yana yawo kan screen d'in wayar, da Sauri ya d'auka ya kara a kunneshi, muryar dayaji Auta tana magana da itace ta d'aga mashi hankali, cikin tsananin ciwo take maganar _"kha....khaleed kazo ka taimakeni zan mutu_...... Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun ajiye motarsu inda yadace. Bedroom suka isketa cikin jini male-male, ba Alamar numfashi tattare da ita, Cikin tsananin rud'ewa suka d'auketa suka nufi asibiti, khaleed kuwa banda kyarma ba abinda yakeyi, dan ko tu'kin yinsa kawai yakeyi, amma besan inda kansa yakeba, da taimakon Allah suka isa asibitin, labour room itama aka wuce da ita. Nan fa likitoci suka taru akanta, amma abin sai du'a,i Wasa-wasa har karfe shidda na yamma basuji wani dadd'an kabari ba, lokacin kuma Hajiyar Auta ta dad'e da zowa asibitin, zazzaune suke sunyi jugum-jugum Kowa Allah-Allah yake yaji ance d'anshi ya haihu, yayinda khaleed ke cikin matsanancin tashin hankali. Can gurin 'karfe shida da rabi dictor yafito daga d'akin duk yahad'a gumi, duk illahirin jikinshi ya 6aci da jini, suna ganin fitowarshi sukayimashi caaa, suna tambayarshi "Yaya dai doctor sun haihu kuwa, wata nannauyar ajiyar zuciya likitan yayi sannan yace "ina mijinsu yake?, khaleed yace "gani, biyoni office, Momyn khaleed tace dan Allah doctor kayi mamu bayani anan Kowa yaji halin da suke ciki, ko hankalinmu ya kwanta, nan da kake gani muduka iyayensune, ba wani abu ka fad'i kawai. Doctor ya share wani gumi daya tsatstsafo mai a goshi, yace " ina farin cikin sanar daku cewa su duka sun haihu, Fadila ta haifi yara biyu mace da namiji, sai kuma Zainab ta haif d'a namiji. Lokaci guda fuskokinsu suka washe cikin farin ciki suka fara yima Allah godiya, Sai lokacin likitan yacigaba da magana "amma inaso Ku Sani Allah shi ke badawa kuma shine me kar6ewa a duk lokacin dayaso, saboda haka ina me ba'kin cikin sanar daku d'a namijin da aka Haifa ya rasu, kafin daga bisani itama uwarsa tabishi, Allah yafiku sonsu, saboda haka kuyi hakuri addu'a kawai zakuyi masu sai Ku d'auki gawar kuje gida ku shiryasu dan kada akaisu matuary, ```Innalillahiwa'inna,ilaihirrajiun``` Suka furta lokaci guda suka shiga matsanancin tashin hankali, khaleed kuwa jiyayi 'kafafunsa bazasu iya d'aukarsaba zaman dirahan yayi yana zuabar da hawaye, yana cewa "shikenan Zainab kin tafi kiin barni ina zan saka raina, yakama 'kafafun momynshi yari'ke gam yana cewa Momy kicema Auta kada ta mutu ta barni, sosai Momy ta taasayama d'anta ganin yanda yake aurutai marassa kan gado, itama hawayenne suka gangaro kan kumatunta. Hajiya kau tinda likitan yafad'i rasuwar taji kanta yayimata wani Jim, tana tsaye dafe da kai, kawai sai jinta sukayi 'kasa ta fad'i sumammiya. Da sauri sukayi kanta, suna salati, nanfa aka shiga wani sabon tashin hankali, dan Hajiya an yayyafa mata ruwa amma ba Alamar numfashi tatare da ita. Nan aka d'auketa Emergency aka nufa da ita, likitoci ne suka taru dan ganin an ceto rayuwarta, akalla ankai awa biyu kafin asamu numfashinta yafara dawowa. Nan aka sanar da Baban Auta da baban khaleed abinda ke faruwa asibitin, lokaci guda suka iso hadda mahaifin fadila, nan aka d'auki gawar jaririn data mahaifiyarshi aka nufi gida dasu, tin daren a kayi masu wanka, aka shiryasu, sukayi kwanan keso. πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ“Ώ ``` Allahu Akbar, kulli nafsin za'ikatul maut" dukkan me rai mamacine```πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ˜­ Zee Elkaseem Mmn khady [10/16, 7:56 PM] ‪+234 816 616 9254‬: [15/08 8:13 pm] .: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š *AUTAR HAJIYA* πŸ’ƒπŸ» πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š ®NWA πŸ‘‡πŸ» _ZEE MMN KHADY_ 😘 ```Page```176-180 ✍🏽 Bayan kwana bakwai da rasuwar Fadila, kuma ranar aka rad'ama yaran suna, d'an gurin Auta yaci sunan Baban khaleed, Ana kiransa shaheed, sai kuma babyn Fadila wacce yanzu haka tana hannun Auta ta had'a da yaronta tana shayar dasu, ita kuma sunan Mahaifiyarta aka maida mata *_Fadila_* mashaAllah anyi suna lafiya lau, duk da ba wani taro akayiba, amma 'yan'uwa da abokan arzi'ki sunzo, Auta tasha kyaututtuka ita da baby's daga gurin danginta da dangin khaleed, 'yan'uwan Fadila kuwa sha tara na arzi'ki suka had'oma Auta, abinda yakara d'aga hankalinta tari'ka sharar 'kwalla tana tuna sister d'inta Fadila. momyn khaleed ce tasamo wata dattijuwar mata wacce zata zauna da Auta dan ta tayata rainon yan biyunta. *************************** Bayan kwana arba'in su Auta sun gama wanka, suduka suna cikin 'koshin lafiya itada yaranta, sunyi 6ul-6ul dasu yarinayar Fadila kya'kyawa kamarsu d'aya da mamarta, sai dai ta d'auko farin babanta. shaheed kuwa babansa ya biyo, fari tas dashi, kamar d'an larabawa. Haka yaran suka taso cikin kulawar iyayensu, dan khaleed kullum idan yataso ayki be'kara fita zama yake suna raino tare. *_BAYAN SHEKARA BAKWAI_* Wasu kyawawan yara na hango a harabar gidan khaleed suna wasa da ball, cike da nishad'i. Can kuma sai suka kama rigima bansan kome ya had'asuba, macen ce ta rugo da gudu, tashigo gida, namijin na biye da ita, jikin Auta tafad'a tana cewa "Ammi kice kada ya dakeni,suanan dasuke Kiran Auta dashi kenan _*Ammi*_ Auta ta'kara rungumeta, tace"kai shaheed kada ka doketa, miye ya had'aku? "Ammi wai dan munyi ball naci 3 itakuma taci 1 dan nayi dariya shine ta dokeni ta rugo. Auta ta rungumoshi jikinta tace yi ha'kuri kaji shaheed d'ina bazata 'karaba. Ya kalli Fadila wacce ta'kara narkewa jikin Auta yace "kuma yarinya idan kika 'kara saina doddokeki. Ta kalli Auta tace "ai dai Ammi bazaki bari ya dokeniba ko? Auta tace Bazan bariba mana, aiko Fadila najin haka sai ta kyalkyale da dariya tayima shaheed gwalo, 😜 Aiko yabiyota da gudu ze doketa ta ruga tana kiran Ammi... Ammi kice kada ya dokeni, Auta ta tashi tana 'ko'akrin raba rigimar ne khaleed ya shigo da sallama, aiko da gudu suka ruga suka rungumeshi suna fad'in _welcome my daddy_ 'daga Fadila yayi sama yana dariya yace welcome my baby, sannan ya ajiyeta ya d'aga shaheed yace "welcome my dady, sannan suka wuce ciki, nan suka zauna yana tambayarsu karatun dasuke a school suna bashi amsa, dan yaran badai 'ko'kariba, Auta ce tagabatar masu da abinci, suka zauna sukaci sunata nishad'i, bayan sun gama khaleed yace su shirya zasu fita Unguwa, aiko nan suka kama tsalle suna murna, Sun fito cikin shiri, sunyi shar dasu gwanin ban sha'awa Fadila sanye cikin wata had'ad'diyar doguwar riga, milk me zanen Flowers pink, sai takalminta masu tudu suma pink colour, kanta kuwa yasha gyara, kamar na yan indiya, yazubo har bisa 'kafad'unta, shaheed kuwa fararen jacket ya Sanya, sai farin takalmi cover yayi kyau abinsa, haka suka shiga mota gidan Momyn khaleed suka fara zuwa, cike da murna ta tarbesu, tanata ji da yan jikokinta, har daddyn khaleed yadawo suka gaisa sannan suka wuce,... Gidan su fadila suka sauka, da sallama suka shiga gidan, da gudu shaheed ya Fad'a jikin Momyn fadila yana Fad'in momyna gani nazo, cike da fara'a tace "a'a yau megidanne da kansa, to sannu da zuwa, nan suka shigo suka gaggaisa, sunjima anan kafin daga nan su wuce gidan Hajiya. A gidan Hajiya suka 'karasa wuninsu, sai bayan ishsha'i suka tafi, yaran sunata kewar Hajiya, da Fadila da kyar ta yarda aka tafi da ita wai ita a dole nan zata kwana, saida akayima wayo akan gobe za'a kawota tare da kayanta duka, sannan fa ta yarda aka tafi da ita tanata murna gobe za'a maidota gurin hajiyarta, Shaheed ya harareta yace, yarinya nima idan aka kaiki nima sai an kaini gurin Hajiyata (Momyn Fadila) Khaleed yace duka gobe zan kaiku, aiko suka shiga murna. *_Anan inso inyi amfani da wannan damar inyi kira ga 'yan mata masu kafewa akan su bazasu auri me mataba, shin bakusan tin kafin kazo duniya Allah yariga ya tsara yanda yakeso rayuwarku yakeso ta kasanceba_ *Kawai ku ro'ki Allah yaza6a maku mafi Alkhairi* ```Alhmdulillahi anan nakawo 'karshen littafina me suna Autar Hajiya, Ina mi'ka dumbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke Allah bar 'kauna, nagode``` πŸ™…πŸΌ *Sadaukarwa* Na sadaukar da wannan littafi ga 'kawata, kuma 'kanwata, kuma takwarata *Zainab* ```(AUTAR HAJIYA)```πŸ’ƒπŸ» 🏻Allah bar mu tare 😘 Kyakyawar gaisuwa gareku group member's d'in πŸ‘©πŸ» *CIWON YA MACE* πŸ’ž *ZEE MMN KHADY FAN'S* Allah 'kara hada kawunanamu. Daga marubuciyar πŸ’ž *siyasa ko soyayaya* 🌎 *Duniya juyi* πŸ‡ *Halin girma*πŸ‘πŸ» πŸ•Š *Autar Hajiya* πŸ’ƒπŸ» Sai kunjini a buk dina na gaba πŸ‘‡πŸ» ```ALHINI```😭😭😭😭 Kya'ky'kyawar gaisuwa ga All writer's ✍🏽 Lokaci baze isa in lissafo kuba, amma kuna raina akoda yaushe. Love u All 😘😘😘😘 [16/08 3:35 pm] .: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ 😭 *_ALHINI_* 😭 πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡ ®```NWA``` _written by_ *_Zee Mmn khady_*😘 ```Fatima shine asalin sunanta, amma ana kiranata da balaraba, Balaraba yarinyace yar kimanin shekara 14,yarinya me farin jini da kwarjini a fad'in karakararsu duk wani namaiji me ji da kanshi a 'kauyen yana so Balaraba tazama mallakinsa, samari suna gasa akanta, kowa yanaso yazama mijinta, Amma matsala da Balaraba ta fuskanta itace duk wanda ta tsaida matsayin mijinta, da lokacin biki yagabato sai ya mutu, Hakan yasa Balaraba tashiga cikin matsanancin tashin hankali. Suakuma muatnen 'Kauyen gain haka yasa suka fara gudunta. Har abin yakai duk Inda doshi mutane sai kaaga suna gudu, 'kawayenta kuwa duka gudunta suke``` Shin waye ze Auri balaraba, da wannan matsalar ? Kuma miye matsalar ta wadda duk Wanda yanemi aurentayake mutuwa? *shin me ya jawo ma fatima (Balaraba) wannan?* _Amsar wannan tambaya tana cikin littafin *ZEE MMNK HADY* me zuwa kada kubari abaku labari 😭ALHIHI 😭 labari mai ban tausayi ban Al'ajabi da kuma ban mamaki da tsan-tsan soyayya gami da nishad'antarwa da ilmantarwa, kudai kubiyoni dan jin yanda zaya kasance_ ```COMING SOON COMING SOON COMING SOON``` Zee Elkaseem Mmn khady adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *