Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, 3 September 2017

Amadu

adsense here

Amadu 1 page 1
Posted by ANaM Dorayi on 02:21 PM, 31-May-15
Under: Amadu
"INA SONKA"Itace kalmar da nafi tsana a
rayuwa,ba don komai ba sai saboda na ji ta yafi
sau nawa daga bakin mata mayaudara maciya
amana,basa taba rike alqawari. Daga kammala
karatuna zuwa wannan lokacin,shekara daya
kenan amma na kasa samun mace wacce zata
soni tsakani da Allah ba don kyawun halittana ba.
Na hadu da 'yan mata kusan su goma amma
gaba
daya babu mai yimin so don Allah,na rasa
wannan dalili gashi ni din dai ba mai kudi bane
asalima ni din maraya ne mara uwa da uba
sannan dan riko a hannun wan mahaifina Alhaji
Mudi.
Cinyata naji an dafamin,na dago kaina ina mai
duban Badamasi. Jikinsa yayi sanyi ganin yanda
gaba daya yanayina ya chanja. Na daure na
qaqalo
murmushi"Au ai na dauka ka wuce." Badamasi ya
quramin ido yana nazarina,na dauke
kaina"Wannan
kallon fa malam?" Ya saki ajiyar zuciya yana mai
girgiza kansa"Ina tsaye fa kazo ka wuce ni baka
ko
lura dani ba,wai meya faru? Yanzu yanzun nan
muka
rabu kana cikin walwala amma har ka chanja a
lokaci
daya,me akayi?" Na share gumin goshina,na daga
kafada kadan"Babu wani abu,cin fuskar da aka
sabayi min ne akayi." Badamasi ya dan ja
tsaki"Allah Ya kyauta,gaskiya ya kamata kaima
kayi aure ka
hutarwa kanka da zaman gidan nan tun kafin
takaicin matan Alhaji ya kar ka." Nayi 'yar
dariya"Mutumina kenan,kana tunanin auren shi
kadai zai rabani da gidan Alhaji sai kace wani
mace?
Ai banajin zan daina zuwa gidan Alhaji koda nayi
aure,ni da ko aiki bani dashi a hannu kake
maganar
aure? Toh idan ma auren ne ina naga
budurwar?"
Badamasi ya harareni"Haba dai Ahmad,kai da
'yan
mata suke bi domin ka kaunacesu ya zaka dunga
fadin haka? Kawai dai baka ga dama bane." Na
girgiza kaina"Ba haka bane,kai shaidane,mata
nawa suka yaudareni? Kai kanka kasan na tsani
muna
soyayya dake ke kuma ki na kula wasu bayan ni
anan wurin bazamu jitu ba,idan nayi maki
gargadi
har fin uku baki ji ba toh zan rabu dake ne
domin
tun
anan zan gane ba sona kikeyi tsakani da Allah ba.
Bar batun aure Badamasi,an taba yin aure babu
sana'a? Idan na auro dame zan ciyar da iyalina?
Kai
bama wannan ba,nifa bana jin zanyi aure yanzu
sai
na samu aiki,na gina muhalli. Nasan zakayi
tunanin
meyasa bazan nemi aiki a qarqashin Alhaji ba
ko?"
Nayi 'yar dariya mai ciwo na girgiza kaina ina mai
duban qasa"Tun kafin na kammala karatuna
Alhaji ya so hakan,kodayaushe idan zaije ofis tare
muke
tafiya,akan hakan ba qaramin rikici aka tafka ba
tsakanin Yaya Usman(babban dan Inna,kuma
tilon
'da namiji babba ga Alhaji Mudi,mazaunin garin
Lagos a yanzu) da Inna dasu anti amarya,wai
don me
Alhaji zai ce ni zai dora kan harkokinsa,haka Yaya
usman yayi ta zuga su har suma suka bijire,ran
Alhaji
ya baci ainun,shi kuma yace bazai fasa dorani ba.
A
ranar saida ya mari yaya usman saboda jin zafin
yanda yake shiga harkar mata kamar wani mace.
Kasan dai bama jituwa da yaya usman tun muna
yara
domin kishi yakeyi dani kamar me. Wannan ya
qara bata ran su inna,kai a ranar fa nayi kwanan
wahala
domin a zaure na kwana yaya usman hanani
kwanan dakinsa yayi. Saida asuba ne Alhaji ya
ganni,banso hakan ba domin saida ya batawa
yaya
usman rai,yace ya tattara kayansa ya koma Zaria
inda
yake karatu,kada ya qara dawo masa gida tunda
bashi da mutunci. Dakyar dai Alhaji ya haqura,a
ranar
haka na wuni cikin azababben yunwa babu
wanda
ya bani abinci. Zahra ce kadai me tausayina,toh
abun
daya daure min kai tashi daya Alhaji ya sauya ya
daina kirana mu tafi ofis dinsa. Kai ko na shirya
na zo
bakin motar sai ya dakatar dani yana mai cewa
na zauna na huta na maida hankali ga karatuna.
Su
kuwa hakan ba qaramin dadi yayi musu ba,tun
daga
lokacin na daina shiga harkar duk wani abu na
kasuwancin Alhaji. Wallahi badamasi babu
abunda
nakeso face na nemi na kashin kaina,banaso na
dogara da cewa Alhaji ne mai yimin nafiso nima
nasan zafin nema. Na tallafi kaina da 'yan uwan
mahaifina dana mahaifiyata masu kaunata.
Wallahi
nasan inda Allah Yayisu masu arziki wallahi
bazan
wahala ba,toh duk cikinsu babu mai wadata
kamar
Alhaji,shiyasa wasu sukemin kallon jin dadina
kawai
nakeyi a gidan,daidaiku ne suke da sanin irin
wahalar dana ke sha,daidaikun ma mata ne
domin
mazan basu fiye zuwa gidan Alhaji ba." Badamasi
ya
jinjina kansa"Gaskiya kayi tunani mai kyau
Ahmad,Allah Ya taimakemu,Ya buda mana.
Rayuwarce ta zama abun tsoro,dan uwa bai
damu
daya kula da dan uwansa ba. Ballantana kuma a
kai ga bada hakkin makotaka,Allah Yasa mu
dace. Sai
hakuri Ahmad komai lokaci ne." Daidai nan Wayar
badamasi tayi qarar shigowar saqo,ya dauka
yana
dubawa. Murmushi kawai yakeyi,sannan ya
dubeni,nima nayi murmushin"Sarkin
soyayya,halan
dai mutuniyar taka ce?" Badamasi ya dan shafi
kansa"Atoh,meya fi raina?" Ya mike tsaye yana
mai
tura hannu daya aljihu"Ya,zaka rakanin?" "Insha
Allahu,bari nayi wanki na kafin magriban."
Mukayi
musabaha yayi gaba nima na nufi kanti don siyan
omo.
Na dage ina tiqar wankina,ina yi ina sauraron
muryar shahararren mawakin nan wato Alan
waka
a
cikin waqarsa ta Ummina. Ina son waqar a duk
lokacin da nake saurare sai na dunga tuno tawa
uwar,duk da cewa bansanta ba ta mutu tun ina
rarrafe amma na samu labarinta a wajen kakata
wacce ta haifeta. Tana yawan labarta min irin
soyayyar da ummina ta nunamin bata da buri sai
na
ta ganni na girma. Allah Sarki duniya,kana naka
Allah
Yana nashi. Yau gashi babu ran iyaye na,ina
rayuwa
cikin wahala,wanda koda wasa nasan bazan
dandani hakan ba inda suna da rai. Har waqar ta
qare bansani ba,sai maganar Baba maigadin
gidan
wani makocinmu ce ta katseni"Sannu
Amadu,wanki
akeyi?" Na mike daga durkuson da nayi ina nishi
da
share gumi,na dubeshi"Wallahi Baba,kaga ma har
na
kusa qarewa. Kayan salihu ne ba dai datti ba."
Baba
maigadi yayi 'yar dariya"Yo kayan salihu ai dole
suyi dauda,yaron da bashi da aiki sai wasan
qasa. Nan
zaka ganshi ya fito yana zubawa akan rigarsa."
Nayi
dariya alokacin da nake matse rigar"Yara
kenan,basu da wata matsala data sha musu kai a
rayuwa,su dai suyi wasa kawai shine
damuwarsu."
Baba maigadi ya jinjina kai"Kwarai kuwa,ai su
yara basu da wata matsala,rayuwarsu abun so da
sha'awa ne." Na jinjina kai"Hakane,yanzu baba a
rayuwa za'ayi iya samun manyan mutane
wadanda
basu da damuwa?" Baba maigadi yayi 'yar
dariya"Haba Amadu,a duniyar nan ai babu wanda
zai
rasa damuwa,saidai na wani yafi na wani. Wani
yana da tawakkali da daukar komai na rayuwa
cikin
saukin,yana daukar komai ya faru dashi daga
Allah
ne kuma yana yarda da kowacce QADDARA ta
Ubangiji hakanan yayi imani babu wanda Ya isa
yayi
masa ko ya hanashi face Ubangiji. Wanda baiyi
imani
ba kuwa kodayaushe bashi da kwanciyar
hankali,hakika Ubangiji Yana son bayinSa
wadanda
suke yarda da QADDARA kowace iri ce mai kyau
da
mara kyau. Don haka Amadu inaso na qara nusar
da
kai muhimmancin haquri. Ka cigaba da haquri a
duk
inda ka tsinci kanka,insha Allahu Allah mai alheri
ne
ga bayinSa." Na jinjina kaina,shiyasa nakeson
zama da baba maigadi saboda akwai shi da
hangen nesa.
Na zubar da ruwan kumfar ina fadin"Gaskiyane
Baba,Allah Yasa mu dace." Baba maigadi yayi
murmushin jin dadi"Amin Amadu." Ya mike"Ga
motar
Alhaji ya dawo bari na bude masa." Na daga
kaina
ina kallon motar,Alhaji Sunusi ne hakimce daga
baya,yayinda direbansa "Bala" yake tuqashi. Da
sauri
baba maigadi ya qarasa don budewa,motar ta iso
ta
gabana,nayi saurin dagawa Alhajin hannu cike da
girmamawa,ya dago hadi da jinjina kansa yana
murmushi. Alhaji Sunusi yana burgeni,mutumin
bashi
da girman kai ko kadan,ina fatan yin koyi da
halayensa a duk randa na zama wani nima. Na
kammala daurayar kayan sannan na nufi ciki
domin
shanyawa. A ciki nayi ta waige waige ko zan ga
Zahra,amma babu ita ba alamunta,hakan ya
tabbatar
min tun shigarta dakin bata fito ba. Na zagaya
baya
na shanya kayana dana Salihu da Abubakar sai
usmanu,'ya'yan Anti amarya daga nan na nufi
dakina. Kaya na sauya sannan na dora alwala na
nufi
masallaci.
Koda na idar,gida na koma. Sallama nayi a tsakar
gidan,Zahra wacce fitowarta kenan daga kicin
hannunta rike da plate ta amsamin. Na dubeta
ina
mai murmushi a hankali nace"Zahra kinyi
homework
din?" Idonta ya ciko da kwalla,a dan razane
nace"Subhanallah,me kuma ya faru Zahra?"
Hawayenta ya qarasa sauka akan kuncinta,na kai
hannu zan goge mata sai kuma naga rashin
dacewar
hakan,da sauri na wayance ta hanyar yarfe
hannu"Zahra please sanar dani me ya faru? Anti
ta
dokeki ne?" Ta girgiza kai jiki a sanyaye ta
dubeni"Yaya Ahmed wai don Allah meyasa 'yan
gidan nan basu kaunarka? Babu mai
tausayamaka
duk a cikinsu,kowa kansa ya sani dana
'ya'yansa.
Akan batun homework dinnan saida anti ta kusan
dukana wai kada na qara nemanka domin ka
koyar
dani,idan ma ya zama tilas naje gidan su
Badawiyya
ta koya min. Na rasa dalilin wannan tsanar da
suke yi maka Yaya Ahmed." Nayi murmushi mai
ciwo,ina mai
qara jin kaunar 'yar uwata a raina. Ba komai ya
jawo
hakan ba sai irin yanda take tausayamin,duk
gidan
daga ita sai Alhaji ne masu kaunata. Don na
kwantar
mata da hankali nace"Haba Zahra meyasa zaki
damu
kanki har ki zubda hawayenki a kaina? Wallahi
wannan ba wani abu bane ki daina damun kanki
don Allah. Duk tsanani yana tare da sauki
wannan
fada ce ta Ubangijin Talikai,ki tayani da addu'a
komai
me wucewa ne a rayuwa kinji my sister?" Ta
gyada
kai tana share hawayenta,na dan yi kasa da
kaina
ina leken fuskarta"Yauwa Zahra,danyi murmushin
nan naki mana mai kama da na larabawa." Sai
ma
maganar tawa ta sanyata dariya. Nima dariyar
nayi,kiran da anti ta kwala mata ne ya katsemu.
Tuni
Zahra ta rude,ta dubeni"Yaya Ahmed ga abincin
ka a
kicin,kada ka qi ci don Allah." Na gyada mata kai
ina
murmushi,ta maida min martani sannan tayi
hanyar dakinsu,kallo na bita dashi ina murmushi
a hankali
na dawo da kallona ga kicin din na saki sassanyar
ajiyar zuciya. Kwanano na sunguma nayi
waje,wayata naga tana blinking na wuta,na
dauka
na duba kiran Badamasi na tadda har sau
hudu,hakan ya tabbatar min ya iso,abincin na
dire,na ja kofata na fita. Yana tsaye a jikin
motarsa na
qarasa,kafin nayi magana yace"Kaidai wallahi
kana
da rainin hankali,ina ka shiga ne bayan munyi
dakai
zakayimin rakiya?" Nace"Yi hakuri mutumina,na
shiga gida ne." Ya sauke ajiyar zuciya ya juya
yana
kokarin bude motar"Muje kada ran gimbiya ya
baci." Nayi dariya na zagaya na shiga ciki. Ina
mai kallon
motar cike da mamaki nace"A'a,ban gane ba.
Yaushe
ka chanja mota kuma?" Na qarashe tambayar ina
mai
dubansa,dariya ya danyi sannan yace"Motar
Abba
ce
fa,baisan ma na dauko ba." Nayi murmushi"Kace
dai
bakason murja ta rainaka." Mukayi
dariya,Badamasi yace"Atoh,yaushe zan bari ta
rainamin aji? 'Yan
matan yanzu fa sai kana hada musu da
qarya,gujewa
raini." Nayi dariya ina mai girgiza kai"Badamasi
kenan." Ya kalleni"Toh kai ya ka gani?" Na jinjina
kai"Hakane." Haka mukayita hirarraki har muka
isa
unguwar Sharada. Bamuyi dogon tafiya ba a titi
muka gangara layin gidansu Murja,gida na uku
daga
hannun dama naga yayi fakin,ya dubeni"Toh fa!
Mun
iso ga gimbiya." Nayi 'yar dariya"Ai saika kira
ta." Ya
dauki wayarsa,ya lalubota. Yanda yake magana
yana
kashe murya kamar mace ne ya ban dariya,duk
da
cewa ba yau na saba jin badamasi na rage sautin
murya ba ga 'yanmatansa ta waya ba,hakan
baisa na
dara ba. Ya dubeni bayan ya ajiye wayar"Toh dan
duniya me kuma akayi?" Na dubeshi"Irin wannan
kashe murya naka yana ban mamaki
Badamasi,kana
yi kamar mace." Yayi dariya kadan"Ai gwara ni
tunda
muryar tawa akwai dadin sauraro,wata budurwar
fa idan kaji muryarta a zahiri tamkar ana buga
rodi
wallahi." Muka kwashe da dariya gami da
cafkewa.
Daidai nan wata budurwa ta fito daga gidansu
sanye
da riga da zani na atamfa da wani yalolon mayafi
taci
kwalliyarta dai irin na 'yan matan zamani. Babu
tantama itace murja,ba shakka Badamasi yayi
gaskiya domin kuwa farar ce ta bugawa a jarida
saidai fa bata da wani kyau na azo a gani.
Murmushi
kawai nayi,Badamasi ya fita ya qarasa gareta.
Ina
zaune daga mota ina dubansu,sai wani rausaya
idanuwa takeyi kamar sa fado kasa. Kamar bazan
fito
ba ganin yanda abokin nawa ya manta dani
saboda yana gaban gimbiyar tasa,saidai kuma
naga rashin
dacewar hakan na bude murfin mota na fito.
Sallama nayi musu,suka juyo gaba daya suka
dubeni. Na harari Badamasi,yayi dariya kadan
yana
dafa kafadata"Afuwan abokina,kinga ganin
fuskarki
tasa ni mancewa da babban aminina a mota ko?"
Ya
qarashe yana mai duban murja. Ita kuwa dariya
ta
danyi sannan ta dubeni"Ina yini?" Babu laifi
muryarta batayi kama da an buge rodin
ba,"Lafiya
lau Murja,ya gida? Me kika yiwa abokina haka ya
mance da batuna sai naki?" Tayi dariya tana mai
rufe
fuskarta,nima dariyar na danyi ina maida kallona
ga
Badamasi wanda bakinsa ya gaza rufuwa idonsa
a
kanta na girgiza kaina na dubeta"Hakane
mana,kada kiso kiga irin dokin daya dunga yi,ji
yake kamar ya
tashi sama ya ganshi a gidanku. Ashe ba'a banza
ba,balarabiya kike." Mukayi dariya ita kuwa kanta
ya
qara fasuwa ta ja gyalenta tana mai qara rufe
fuskarta,muka dubi juna da badamasi ya daga
min
gira alama dai zancena ya burgeshi. Nayi 'yar
dariya kawai,nace"Bari na baku waje kada na cika
ku da
surutu ko?" Badamasi yace"Ok."Na juya na shiga
mota. Wayata na ciro na bude Facebook,saqo na
tarar har guda biyu,na bude na duba,daga Hafsa
ne.
"Salam,Ahmed ya gida? Kwana biyu ban ganka
online ba fatan kana lafiya?"" Hafsa kenan,wato
tana lura dani?" Banyi sanya ba na maida mata
amsa,domin duk wanda ya kula da lamarinka ai
mai
kaunarka ne."Amin wslm Hafsa,gida
Alhamdulillah.
Wallahi lafiya lau,nagode fa." Daga haka na
danna
send ya tafi. Ina shirin sauka ne naga ta bada
amsa,hakan ya tabbatar min tana online."Babu
komai wallahi,dama wata tambayace dani ina
fatan
samun amsata?" Mamaki ya kamani,na qara
kishingida jikin kujera"Insha Allahu zaki samu,ina
jinki." Sai ta qara turowa"Don Allah kasan wata
Zahra'u Mudi Yakasai?" Kwarai Zahra take
nufi,toh ya
akayi ta santa? Banyi wata wata ba na tura mata
amsa"Ni kuwa nasan Zahra'u,she's my
cousin,amma
ke a ina kika santa please?" Ta aiko min da
smiley na
murmushi mai bayyana jin dadinta,sannan
tace"Aminiyata ce a makaranta,idan kaji Zahra na
ambaton Hafsa toh ni take nufi bayan haka kuma
na
duba album dinka naga hotonka kuna dibar
kama,hakan yasa na kasa daurewa har saida na
tambaya." Dadi ya lullubeni ganin ina tare da
aminiyar 'yar uwata mai kaunata amma kuma
ban
sani ba."Kai amma naji dadi,ashe ina tare da
kanwata
kice." Ta aikomin da amsa"Hahaha,hakane
yayanmu
Ahmed." Nima dariyar nayi a fili sannan a
rubuce,"Hakane kanwata,please ki kularmin da
Zahra kinji? Banda wasa a dage wajen
karatu,kodayake naga ke chatting yafi daukar
hankalinki ko?" Tayi dariya"A'a wallahi yayanmu
ina
karatu,idan kaga na hau facebook toh bana
komai
ne." Na gyada kai kamar tana ganina"Masha
Allahu." Haka mukayita hira da Hafsa tana bani
labarin Zahra
a makaranta,da rashin yawan maganarta da
mu'amalarta da mutane har badamasi ya
kwankwasa gilashin motar ban sani ba. Saida ya
bude murfin kofa sannan na dubeshi,cike da
nishadi
nace"Ya akayi?" Yayi dariya"Toh wa kake
tsarawa? Zo kuyi sallama zamu wuce." Nayi
dariya na fito ina
cewa"Haba dai,ina ni ina tsara mace?" Na dubi
murja"Toh malama murja,sai gani na biyu. A rike
amana don Allah,abokina yana da kishi sannan
yana
da zafi a kula ina mai tabbatar maki daga gareshi
bazaki samu wata matsala ba." Ta dubeni"Anya
bakayi son kai ba malam Ahmed?" Mukayi dariya
gaba daya"Wane ni na so kaina? Gaskiya ce dai
nake
fadi sanin halinku na mata." Tayi dariya tana mai
jinjina kanta"Hakane,amma ai ba duka aka hadu
aka
zama daya ba ko,kuma kafin mace ta yaudari
namiji,wallahi namiji ya yaudareta." Muka bude
baki ni da Badamasi na dubeta"Haba dai Malama
Murja,ai
kuwa mun fiku rike alqawari. Domin idan muka
ce
muna son mace mun sota kenan ba qarya,da
wuya
mu kula wata a matsayin budurwa." Murja ta
jinjina
kanta tana mai murmushi ta dauke kanta tana
duban
hanya,kamar bazata yi magana sai kuma ta juyo
tace"Shikenan,zamu gani. Allah Ya bawa
kowannenmu ikon rike alqawari." Mukayi dariya
ni
da Badamasi,nace"Yauwa ko kefa." Nayi mata
sallama na koma mota,na duba wayata,hafsa har
tayimin sallama ta sauka. Nayi murmushi kawai
nima
na sauka bayan nayi mata addu'ar tashi lafiya.
Ina kallo Badamasi ya rakata har qofa sannan ya
zagayo
ya shiga mota ya ja. Na dubeshi"Hankali ya
kwanta
an ga murja ko?" Yayi dariya ba tare da ya
dubeni
ba
yace"Kaidai bari,abun ba'a cewa komai. Amma
tayi
fa." Ya mikomin hannu muka cafke muna
dariya"Allah ko?" Ya jinjina kai"Kwarai ma
kuwa,tana da dabi'u masu kyau,kan yarinyar a
waye yake
amma fa ba wayewar banza ba." Nayi
dariya"Kaidai
ka sani." Sai anan ya dubeni"Au baka yarda ba?"
Na
qara yin dariya"Allah Ya barku tare toh." Ya jawo
amin har sau uku. Dariya nayi sannan na maida
kaina ga kallon
titi,komai Badamasi yayi akan mace bana wani
mamaki domin babu abunda namiji bazaiyi ba
akan mace. Na dandana soyayya nasan zaqinta
kamar yanda nayiwa dacinta farin sani,budurwata
ta farko Zaliha,ta yaudareni. Aisha,mun jima
muna soyayya karshe tazo min da labarin an
kawo kudin aurenta. Jamila,ta rabu dani dalilin
samun Alhajin birni. Sa'a,tayi bankwana dani
saboda samun wani. Kai suna da yawa,ban
manta da Hadiza ba wacce tafi kowacce
budurwata shiga raina,nayi zurfi a sonta rana
daya na sameta da wani Alhaji suna hira,koda na
isa gareta baqaqen maganganu nayi arba dasu.
Toh tayaya zan rasa sanin zaqi da dacin soyayya.
Rashin masoyiya ta gari babbar asara ce. Na
ayyana hakan a raina. Maganar Badamasi ce ta
katseni"Ya akayi mutumina,ina magana ka
shareni?" Nayi firgigit na dubeshi,na saki
nannauyen ajiyar zuciya"Me kake cewa?" Ya
girgiza kai"Allah Yasa ba matsalar gidanku ke
damunka ba,nasha sanar dakai muhimmancin
wanda yayi hakuri Ahmed,ya kamata ka dunga
daukar lamura..." Na dakatar dashi ta hanyar
daga masa hannu,kasancewar yana tuki bai kula
ba,saida na hada da furucin baki"Ba tunanin da
nakeyi ba kenan." Ya kalleni"Tunanin me kakeyi
toh?"Na sauke ajiyar zuciya na jingina kaina jikin
kujerar ba tare da na ce komai ba. A sanyaye
Badamasi yace"Haba Ahmed,meyasa kayi
shiru,kodai akwai abunda kake boyemin? Idan ba
ni ba kana da wanda zaka fadawa?" Nayi
murmushi na dafa kujerarsa"Ko kusa babu
abunda nake boye maka,kawai tunanin
'yanmatan
da suka yaudareni nakeyi." Badamasi yayi
dariya"Wallahi kada wannan ya dameka,ba irinku
'yan mata ke gudu ba Ahmed. Duk wacce ta
gujeka bata da rabo ne." Dariyar nima nayi ba
tare da nace komai ba,ya cigaba da jana da hira.
Nima nake labarta masa yanda mukayi da Hafsa
har dai muka isa gida. Ya dubeni a sanda ya faka
motar"Facebook kenan,sai ka hadu da 'yar
cikinka ma baka sani ba." Mukayi dariya na bude
kofar na fito shima ya fito na dubeshi"Kaima dai
ka fada,yanzu mutane sun ganewa facebook." Ya
jinjina kai"Gaskiyane." Nayi murmushi"Shiken
an,Allah Ya bamu alheri." Na juya yace"Tsaya
mana." Ban tsaya ba sanin halin Badamasi,bai
fasa biyoni ba sai ji nayi ya sanya min kudi
acikin tafin hannuna. Na juyo a fusace nace"Meye
haka ne badamasi? Banason haka please,ga
kayanka bazan amsa ba." Na daga hannu zan
jefa cikin motar ya rike hannun"Haba
Ahmed,yaushe ka fara maida hannun kyauta
baya? Ashe bamu zama 'yan uwa ba har yanzu
da ni da kai ba? Wallahi idan ka maidomin
wallahi daga yau bazaka qara ganina ba a
gidanku." Ya daure fuska tamau,jikina yayi sanyi
nace"Kayi hakuri,wallahi ba wani abu yasa na qi
karba ba illah ganin yanda kake wahala dani.
Kodayaushe kazo sai ka min kyautar kudi,me na
taba yi maka Badamasi? Amma kai kodayaushe
cikin hidimata kake..." Ya katseni ya dafa
kafadata"Ahmed kenan,kada wannan ya dameka
na fi kowa kusanci dakai duk cikin abokanmu
nasan halin da kake ciki wallahi nayi imani inda
Allah Ya yika mai wadata zakayimin fin abunda
nake yi maka. Kada ka qara qin karbar abun
hannuna please. Sai da safe." Ya juya da sauri
yayi gaba,nabi bayansa da kallo ina murmushi,a
ko'ina bawa baya rasa mai kaunarsa don Allah.
Kaina na girgiza,sannan na juya nayi ciki ina mai
cike da tunanin Badamasi. Na tuno farkon
haduwarmu dashi,da yanda yake daukar kansa a
makaranta shi dan mai kudi. Rana ce da bana jin
zan manta da ita.
Ina zaune bayan fitowa daga aji,ina jiran wani
abokin karatuna,Bukar,ya kawomin wasu
takarduna
daya karba. Na hangi motar Badamasi ta faka,ya
fito
yana wani takun isa yayin da abokansa kuma ire
irensa 'ya'yan masu hannu da shuni suka isa
gareshi
ana cafkewa. Yana sanye da wata tsaddadiyar
riga da wandon jeans,ga wani arnen agogo daya
manna
a hannunsa,daidai da takalmin Badamasi abun a
kalla a yaba ne. Hakanan abokansa
suma,kowanne
da irin shigar da yayi. 'YA'YAN HUTU shine sunan
da
mafi yawanci daga daliban makarantar ke
kiransu.
'Ya'yan hutu basu damu da suyi zaman aji don
daukar lectures ba,barsu dai idan jarabawa ta fito
zakayi mamaki idan kaga sakamakonsu yayi
kyau.
Hakanan basu yarda wani ko wata ya taba su ba
a
makarantar face sai sun dauki mataki kwakkwara
akansa. Babu abunda ke hadani dasu face
wulakancinsu da na tsana,domin kuwa ko kai
waye baka isa su shiga harkar ka ba matukar ba
kai ka
nemesu ba. Toh dayawa masu kwadayin abun
hannunsu suna kai kansu garesu,hausawa na
cewa
inda kwadayi da wulakanci. Hakan bai sasu jan
jikinsu ba. Hakanan zaka ga 'yan mata kala kala
suna
giftawa ta gabansu duk domin su yaba,marasa
kunya daga cikinsu ma ga da ga suke tunkararsu.
Ina mamakin yanda a yanzu mata basu kunyar
furtawa namiji suna sonshi,ai ita 'ya mace duk
inda
aka santa toh 'yar kunya ce. A'a,badai a wannan
zamanin ba. Hayatu,Imam,Haidar da Kabir sune
abokan Badamasi. Gaba dayansu babu na arziki
acikinsu,naji ance ma shaye shaye shine abin
yinsu,Badamasin ne dai ban taba ji ance yayi ba
amma ina zaton shima bazai rasa yi ba tunda
abokin
dan iska dan iska ne
Maganar Bukar ce ta katseni"Kayi hakuri don
Allah Ahmed,na zaunar dakai ko? Wallahi wata
Fatima na arawa,tayi photocopy,gashinan." Nayi
murmushi"Babu komai." Na karba na sanya a
'yar
jakata sannan na mike,na yiwa Bukar sallama na
qara gaba. Babu zato mukayi karo da mutum,na
dago da sauri ina mai furucin ban haquri. Banyi
aune
ba,naji an daki kafadata nayi taga taga kamar zan
zube a wajen,Allah Ya taimakeni ban zube ba.
Raina
ya baci,ba wani bane illa daya daga cikin 'ya'yan
hutu,Badamasi."Me yayi zafi haka malam? Inaji
dai na
baka haquri don me zaka tureni?" Ya dubeni
fuska
a murtuke"Kai don Ubanka kai dan gidan wanene
da
zaka bangajeni na kyale?" Ubana kace?" Cikin
bacin
rai Badamasi yace"An fada..." Kafin ya qarasa na
cire
hannu na wanke shi da mari. Da sauri su hayatu
suka
yo kaina,ya daga musu hannu cikin tsawa
yace"Babu ruwanku!" Suka ja baya suna mai huci
kamar su na mara. Ya dago jajayen idanunsa,ko
ba'a
fada ba nasan ran Badamasi ya baci,toh ya kai
ya ni?
Mahaifina ya taba wanda ya jima a
gushewarsa,ta
yaya zan kyaleshi? Mutane suka zubo mana ido
suna
jiran ganin abunda zai faru,daga masu kama baki
sai
masu jinjina kai. Rai a bace muke duban juna,na
kauda shirun ta hanyar nunashi da yatsa"Kayi na
farko ka yiwa kanka fatan zamtowarsa na karshe
domin duk randa ka sake katarin zagin mahaifina
zanyi maka abunda yafi mari." Daga haka na
gyara
zaman jakata na giftashi zan wuce,naji muryar
abokansa suna zage zagensu,raina ya qara
baci,na tsaya cak na juyo,da sauri Bukar ya ja
hannuna. Na
dubeshi babu shiri ya sakarmin hannu ganin
yanda
fuskata ta sauya,a sanyaye yace"Haba
Ahmed,bansanka da haka ba kayi hakuri don
Allah
ka tafi." Haidar ya hayayyako"Kai rabu dashi,yazo
mana muga abunda zai iya!" Badamasi ya daka
masa tsawa"Ya isa Haidar!" Haidar rai a bace ya
dubi
Badamasi,sai kuma ya jinjina kai a fusace yayi
wajen
motarsa,su hayatu ma suka watse. Na tabe baki
na
juya muka jera da Bukar mukayi bakin gate.
Bukar
ya dubeni"Gaskiya Ahmed wallahi ka burgeni
kuma
ka bani mamaki yanda ka iya daukar mataki akan
Badamasi nan take. Saidai ina tsoron matakin da
Badamasi ke shirin dauka akanka,domin shirunsa
banajin alheri ne gareka." Nayi murmushi mai
ciwo"Bakomai Bukar,babu abunda zai iya yimin.
Na
jima da imanin komai ya faru da bawa daga
UbangijinSa ne,toh waye Badamasi? Idan
takamarsa kudi,ni na dogara ga Allah. Kada
wannan ya
dameka. Sai gobe." Muka qara yin musabaha
nayi
gaba,ina hangen masu nuno ni da yatsa daga
mun
hada ido sai su waske,murmushi kawai nayi.
Babu
zato naji ruwan dake kwance a qasa na dauda ya
fancalo min a jikina,da sauri nayi baya ina mai
duban hanya. Motar Haidar ce,sai motar
Badamasi dake
binta a baya. Ya tsaya daidai saitin da nake
tsaye,ya
jima yana dubana a hankali kuma ya zuge glass
dinsa ya qara gaba. Gayun nan fa sun mugun
batamin rai,mutane sai kallona suke,na ciro
handkerchief dina na share fuskata da sauri na
bar harabar makarantar.(Kai masu kudi! A daina
wulakanta dan adam!).
A ranar nayi yinin bacin rai. Wani abun haushin
kuma ina shiga gida don daukar abinci na tadda
kofar tsakar gidan nasu a kulle hakan ya
tabbatarmin babu kowa a gidan. Zafi biyu ya
hademin a lokaci guda,na ja tsaki na fito. A bakin
kofa na jingina ina mai tunanin mafita. Na hau
laluben aljihuna,na ji karar takarda ai da sauri na
ciro
cike da farin ciki saidai ganin naira ashirin yasa
jikina
yin sanyi hakan baisa na karaya ba na nufi kanti.
Biskit na siya sai pure water,na zauna anan
gaban
kantin ina ci muna hira da idi har na qare. Ga
mamakina dago kan da zanyi na hangi mota irin
ta Badamasi sak ta fice ta gabanmu,toh ko dai
shi
dinne?" Ashe a fili nayi tambayar sai naji idi
yace"Wa
kenan?" Na maida dubana gareshi"Kasan
Badamasi
Tukur?" Idi yace"Dan gidan Alhaji Tukur Daula?"
Na
daga kafada kadan"Bansan sunan mahaifinsa
cikakke ba." Idi yace"Inaji dai shi kake
fada,zakaga badamasin wani fari dogo mai
yawan sanya sarqa a
hannu ko?" Da sauri na jinjina kai"Kwarai kuwa
shi
fa." Idi ya danyi tsaki lokacin da yake karbar
kudin
wata yarinya mai siyan sabulu"Yaron ai bashi da
mutunci ko kadan,baya shiga harkar kowa a
unguwar nan saboda yana jin babu wanda ya
isa." Furucin da yayi na unguwar nan yasa ni
hadiye biskit
din bakina wanda bai gama taunuwa ba,hakan
ya
janyomini kwarewa,idi yana min sannu,na kurbi
ruwan hannuna sannan na qara dubansa"Me
kake
nufi? Kace unguwar nan kana nufin a unguwar
nan
suke? Ya akayi bansani ba?" Idi yayi dariya ya
miqawa yarinyar chanji ta ruga da gudu tabar
wajen,ya samu kusa dani ya zauna"Ai kai kifin
rijaye
ne amadu,kai da baka fita ko'ina? Ni har
mamakinka
nake,idan ba yunwarka ce ta kwaso ka ba ko
kuma
siyan wani abu baka taba zama anan muyi
hira,gwara gwara dai Baba maigadi naga taku
tazo daya dashi. Kaga ba abun mamaki bane ace
bakasan
yaron dan unguwarnan bane,kaga kwanar can ta
dama. Nabi kwanar da kallo,itace ta qarshe daga
hannun dama take ta jikin jerin da gidanmu
yake,na
gyada kaina kawai. Yace"Toh kana shan kwana
da
tafiya kadan zakaga wani gida mai fenti ruwan
madara,katon gida ne kamar a turai." Na tare
shi"Nasan gidan kwarai ma kuwa ina wuceshi
saidai
ba kasafai na fiye bin layin ba." Idi yayi
dariya"Toh ai
nan ne gidan Alhaji Tukur din,matarsa daya,kuma
Badamasi ya kasance 'da namiji tilo a gidan,sai
yayarsa mace mai aure a can Misra,da kannensa
mata hudu. Suma dai karatu sukeyi anan
garin,autar ce ma
naji ance tana can Misra wajen yayartasu." Na
jinjina
kaina gami da sakin ajiyar zuciya. Idi ya
dubeni"Toh
kai a ina ka sanshi?" Nayi murmushi na sanar
dashi
abunda ya faru. Sai ga idi na salati,cikin rashin
fahimta na dago na dubeshi ina neman qarin
bayani,sai gashi a tsugunne a gabana,ya rasa me
zaice. Daga ya dora hannu aka sai ya ciji yatsa.
Hakan
yasa na dubi gefe da gefena amma banga komai
ba,na dubi hanya ban hango wani ya taho ba,a
firgice nace"Lafiya kake kuwa idi?" Ya jinjina
kai,ya
hadiyi miyau ya dago kamar zaiyi magana sai
kuma ya fasa sannan ya qara dago kansa zanyi
magana ya
rigani"Amadu,meya kaika fada da yaron Alhaji
Tukur? Kasan waye ubansa kuwa?!" Na daure
fuska
tamau,domin na dauka wani abun zaice na
girgiza
kaina"Ko dan shugaban qasa ne banajin zai zagi
ubana na rabu dashi,matakin dana dauka shine
daidai,kuma na gargadeshi akan kada ya qara
idan
kuwa ba haka ba wallahi sai na yi masa abunda
yafi
mari." "Idan kana da tsawon ran kenan." Idi ya
fada,kai yanda idi ya rude sai ma ya bani dariya
sosai,na shiga kyakyatawa. Ya harareni"Kaifa
baka
tausayin kanka Amadu,bakasan irin wahalar daka
jajibowa kanka ba wallahi. Bari na baka labarin
wani
malami na islamiyya daya taba zane 'yar Alhaji
Tukur
da irin wulakancin da akayi masa.
Wallahi da labarin ya isa ga Ubanta,saida yayi
sanadin korarsa daga makarantar,kai da malamin
ya
kawo masa rashin kunya har ya zo nan kofar
gidansa yana zage zagensa saida yasa aka
daureshi
yayi kwana uku a hannun hukuma. Saida
mahaifinsa
yazo da kansa ya bawa uban hakuri,toh kasan
malamin yaro ne,saurayi inaga ko aure bashi
dashi.
Kuruciya na dibarsa,mahaifinsa yace ya bawa
Alhaji
hakuri yaso yayi gardama,saida mahaifinsa ya
bude
masa wuta sannan ya rusuna ya bada hakurin.
Makarantar da bai qara komawa ba kenan. Kuma
a
gaskiya laifin yarinyar ne,rashin kunya tayi
masa,yace tayi shiru ta qi ji ya daka mata tsawa
ta
murguda masa baki wai ai shi tsaron aji aka basa
amma ai ajin kananun yara yake koyarwa. Ya
fusata
ya zaneta da dorina." Na jinjina kaina"Amma ya
burgeni,saidai inda ya kuskuro kawai,cin
mutuncin
da kace yayi a kofar gidan Alhajin. Bai kamata
ba,ai da sai ya bada haquri kawai,kodayake su
zuri'ar
gidan inaga basa jin ban haquri domin nima dana
bayar ba tsira nayi ba." Mukayi 'yar dariya,mun
jima
sosai muna hira da idi sannan na koma gida.
Takarduna na cigaba da dubawa saboda
jarabawar
da muke shirin farawa. Shiru shiru naji anzo
tafiya dani amma ko tsayuwar mota banji ba a
kofar gidan
namu. Kasancewar mun wayi gari lahadi,na hada
kan wankina na zauna a kofar gida kamar yanda
na
saba ina yi,hankalina gaba daya yana kan aikina
lokacin ko wayar hannu ban mallaka ba,toh waye
zai
ban? Tsayuwar mota naji a gabana,ban damu
dana dago kaina ba saboda sanin da nayi babu
mai mota a
gidanmu,don lokacin Alhaji baiyi arzikin siyan
mota
ba. Har dai mai motar ya gaji ya fito don kansa
ya
tsaya agabana gami da yin sallama. Anan ne na
dago
kaina ina mai amsawa. Cike da mamaki na mike
tsaye
ina dubansa,toh me ya kawoshi wajena???????
Badamasi ne yana sanye da wata dakakkiyar
shadda getzner,ta sha aiki. Na daure fuska bance
komai ba na sunkuya na cigaba da wankina
amma a
raina ina cike da matsanancin mamakin ganin
Badamasi. Daga can shagon idi zaune yayi yana
hangenmu,ido waje kamar ace arr ya ruga aguje.
Maganar Badamasi ta katseni"Dan uwa wajenka
nazo fa." Na tsayar da wanki na qara dagowa har
lokacin ban saki fuska ba"Ina fatan dai lafiya?"
Sai
naga yayi murmushi"Wallahi lafiya lau,dama tun
ranar da sa'insan nan ya shiga tsakaninmu
hankalina
ya kasa kwanciya ina ta neman hanyar da zan
hadu da kai,ban samu ba. Har na hakura na
fawwalawa
Allah zuwa ranar litinin mu hadu a makaranta sai
kuma kwatsam yanzu nazo wucewa na hangeka
anan,don Allah kayi hakuri kwarai nayi tunani na
gano rashin kyautatawana." Na sauke ajiyar
zuciya,sai a sannan na dan saki fuska"Babu
komai ya wuce,na yafe maka kada wannan ya
dameka." Ya
fadada fara'arsa"Yauwa nagode sosai." Nayi
murmushi kawai na gyada kaina,shima ya
maidamin
martani sannan yayi min sallama ya shige
motarsa ya
qara gaba. Na bi motar da kallo kawai domin
ganin
lamarin nake kamar almara wai yau daya daga
cikin 'ya'yan hutu ne ya kaskantar da kansa yana
mai
bada haquri akan laifinsa?" Lallai" Abunda na
ambata kenan sannan na sunkuya na cigaba da
wankina. Muryar idi naji a kusa dani"Amadu
meya
faru ne kai da mutumin naka?" Nayi dariya na
dago
na kalleshi"Ho idi gulma." Yayi dariya shima. Na
maida masa yanda mukayi shima kansa yayi
mamakin hakan. Nan muka maida zance sannan
ya
koma bakin aikinsa nima na cigaba da abunda
nasa
gaba. Toh haka ma dana je makaranta ran
litinin,har
inda nake zaune Badamasi yazo muka
gaisa,wannan
ya bawa mutane da yawa mamaki musamman
ma wadanda suke nan abun ya faru. Hatta
abokansa
sunyi mamaki,ni kuwa ko a jikina qarqari dai yayi
min sallama na amsa na cigaba da abunda
nakeyi.
Haka badamasi ya soma shigemin,tun ina dauke
kaina har dai nazo na saki jiki. Abokansa kuwa
basu
shiga sha'ani na,barshi dai bini bini zai taho
wajena,har mukayi sabo dashi. Ya zamana har
gidanmu sun sani,inna ta sha gayamin magana
wai
kwadayi ne irin na uwata yasa na rasa wanda
zaiyi
abota dashi sai Badamasi wanda ya keta aji na a
komai da komai. Bana ce mata kala. Abu na biyu
daya daure min kai sai irin karbar da Alhaji Tukur
yayi min farkon zuwa gidansa,ya jani a jiki sosai.
Ya
nuna min kauna,hakanan yayi tamin godiya
domin
yace tun haduwata da 'dansa ya ga chanji sosai
daga
gareshi. Hakanan Ummi,mahaifiyar badamasi
itama
kanta bata nunamin komai ba. Jama'ar unguwa
aka
fara tsegumin kwadayine ya kaini,abun haushin
ma yanda suke fadin ai hatta 'yan gidanmu sun
san
hakan. Inna ga da ga takeyi min fada wai ruwa
ba
sa'an kwando bane na rabu da Badamasi,idan
ma
abotar ne ai usmanu shine daidai dashi tunda ko
banza ubansa yana da rufin asiri. Maganar ba
qaramin ciwo tayimin ba saidai kawai na share.
Kai kananun maganganu basu qaru ba,sai
sa'adda
Badamasi ya dawo daga Umrah ya kawo min
jallabiyoyi har uku tsadaddu,da agogo da waya
tsadaddiya mai kyau. Ina nunawa Alhaji ya hau
fada,saida na nuna masa irin turjiyar da nayiwa
Badamasi wajen qin amsar kayan da kuma fushin
da ya nuna sa'annan ya sauko. A lokacin ne
Yaya
Usman ya dawo hutu gida,shima haka muka rayu
dashi da dadi babu dadi,inda a zuwan ne akayi
rigimar fita dani aiki,har Yaya usman ya koma.
Haka
zumuncina da Badamasi yayi ta ginuwa har Allah
Ya
kawo muka kammala karatun mu nake zaune
babu aiki,gwara gwara shi Badamasi ganin dama
ne baiyi
ba domin kuwa yana da hanyar samun aikin
sosai.
Yayi karatu ne a fannin Masscom,ni kuwa na
karanci
Accounting ne. Ina shiga dakin na dubi kudin da
Badamasi ya bani,dubu uku ne. Kaina na girgiza
ina
mai jinjinawa Badamasi yanda baya gajiya da
hidimta mini,ko kadan baya yarda na zauna bani
da ko sisi. A
duk sa'adda ya fahimci bani da kudi nan da nan
yake
min kyautarsu,duk sa'adda yayi kuwa sai mun
kusa
yin rigima dashi kafin na yarda na karba. Na
sanya a
'yar dirowata sannan na yi tsakar gida na dauro
alwala na koma na gabatar da isha'i.
Washegari da safe naji ana kwankwasamin
kofa,na mike ina salati. Sannan na bude,Zahra ce
tsaye cikin uniform. Sai kuma naga ta juyamin
baya
da sauri,na dan tare gira ina dubanta cikin rashin
fahimtar dalilin hakan,sai kuma na dubi jikina.
Daga
ni sai gajeran wando,na juya a lokacin da
nace"Kanwata ya akayi?" Tace"Abba ne yace
kazo
ka kaimu makaranta,hassan bai zo ba." Daidai
nan
na zura jallabiyata nace"Ok muje." Da sauri ta
bar
wajen,na matsa toothpaste a cikin brush na fito
nan
tsakar gidan na wanke baki sannan na dubi inna
wacce ke zaune a cikin kicin,qarasawa nayi na
tsugunna domin gaisheta hararar data maka mini
yasa na mike a sanyaye na bar wajen. Dakin
Alhaji na
nufa,shima yana falonsa yana jan casbaha,na
rusuna
a gabansa,domin mun gaisa dashi da asuba.
"Abba
gani." Yace"Yauwa Amadu,kai kannenka
makaranta,bansan mai ya hana Hassan isowa
ba." "Toh Abba,ina makullin?" Ya sanya hannu
kan
kujera ya dauko ,na karba sannan na mike. Na
fito,dakin anti amarya na leqa. Rusunawa nayi na
gaisheta,ta amsa babu yabo babu fallasa. Na
dubi
usmanu autan anti amarya,mai shekaru bakwai
dan
aji daya a primary yana karyawa"Toh usmanu ayi
da sauri kada ayi latti. Anti amarya tace"Karfe
nawa
yanzun da zaka ce yaro yayi sauri?" Na dubi
agogon
dake manne a dakinta"Anti takwas ta kusa fa."
"Toh
ai saika jira shi,yaro idan bai koshi ba wane
darasi ne
zai shiga kwakwalwarsa?" Mikewa nayi ina mai
fadin"Shikenan,ku sameni a mota." Na fice da
sauri,a bakin motar na tadda Zahra gaba daya a
rude take.
Ta gaisheni na amsa ina murmushi"Zahra
kenan,kun
kusan makara ko?" Tayi narai narai kamar zatayi
kuka"Wallahi Yaya Ahmed English teacher ne ya
bamu assignment,a qa'idarsa idan har takwas
tayi
bamuyi submitting ba wallahi bazai karba
ba,shikenan mun rasa maki goma." "Insha Allahu
bazaki rasa ba kanwata,shiga da sauri ki fito da
kannenki." Da gudu gudu ta shiga gidan,ni kuwa
tuni na tada motar,can babu jimawa sai
gasunan,sai
titse qeyar Usmanu take tana fada"Kai a kullum
kai
ne mai sanyamu latti ko? Toh wallahi yau idan
nayi asarar maki sai na zaneka. Ya turo baki
yana
kunkuni. Ta rufe musu kofa sannan ta zagayo ta
shiga gaba na ja. Gudu na shiga yi har saida
muka isa
makarantarsu Usman,bayan mun saukesu,na
miqa
Zahra,lokacin saura minti biyar takwas ta cika.
Cike
da farin ciki Zahra ta dubeni"Kai Yaya Ahmed
nagode sosai,Bye." Ta dagomin hannu tana
murmushi
wanda ya bayyana fararen haqoranta da
wushiryarta. Nima na daga mata,ina tsaye ta
shiga da
sauri da saurinta. Nayi ribas ina shirin jan
motar,na
hangeta zata shiga makarantar littafi a hannu
yayin
da take rataye da jakar makaranta. Ita dince dai
Hafsa Beauty. "Masha Allah" nayi furucin a
fili,ashe
dai ganinta a zahiri yafi hotonta kyau? Kayan
makaranta ne mai farin riga da wando ruwan
hoda,sai dan qaramin farin hijab mai hula. Ta
sanya
farin agogon hannu. Bata lura dani ba,ina tsaye
har
ta shige ciki,saida ta kai kofa,kamar a shirin film
ta juyo caraf idanunmu suka hadu sai kuma ta
dauke ta
shiga da saurinta. Bana zaton ta gane ni,na dan
tsurawa kofar makarantar ido kamar zata qara
fitowa,sai kuma na saki ajiyar zuciya na ja motar
nayi
gaba. Bansan taqamaimai abunda nakeji game da
Hafsa ba,kawai dai yarinyar na BURGENI.
Ina komawa,Alhaji yace na karya nayi wanka zai
aikeni. Na amsa da toh sannan na juya na nufi
kicin.
Na leqa banga komai ba,hakan yasa na qarasa
tura
kaina na daga flask,nan ma wayam. "Toh me
kuma
kakeyi?" Naji muryar anti,na waiwayo da sauri na
dubeta fuska a sake"Yauwa anti,banga kayan kari
na bane shiyasa..." Harara da take watsomin ce
tayi
sanadin tsukewar bakina nayi shiru. "Wa kake
ganin
ka ajiye da zai yi maka wannan wahalar Amadu?
Toh
yau mai yin bata ga damar yi dakai ba ai sai ka
fice
ko?" Na jinjina kaina na fito jiki a sanyaye,ashe
Alhaji
yana ji. Kawai sai ganinsa mukayi,fuskar a daure
ya dubeni"Zo nan amadu,zo mu karya tare." Ran
anti ya
baci amma bata iya tankawa ba,hararta yayi ba
tare
da yace uffan ba yayi ciki na mara masa baya.
Inna
tana ganina ta hade rai,"Oh ni Amadu,wannan
wane
irin kiyayya ce haka suke yimin? Ni maraya gaba
da
baya har akwai wani abu da nake dashi da zasuyi
kishina? Ban qara sanin abun ya girmama ba
saida
naga inna ta mike tsam ta nufi daki. Na sunkuyar
da
kaina kawai,Alhaji yaji mugun tausayin 'dan dan
uwansa. Babu zato naji ya dafa kafadata"Kada
ka
damu Amadu,rabu dasu wataran sai
labari,tsiyaya
ruwan shayin." Na dan saki fuskata domin
kwantarwa da Abba hankali,na tsiyaya. Sannan
na
soma kurba,Alhaji ya dubeni"Wai Amadu kana
gwada zuwa neman aiki kuwa?" Na ajiye kofin na
dubeshi"Wallahi Abba ina zuwa,satin nan ne ma
gaba daya banje ba saboda na nema har na gaji
ban
samu ba." Cike da tausaya ya dubeni"Toh amma
Amadu me zai hana ka gwada kasuwanci,tunda
wancan bai samu ba,idan yaso ko jari ne sai na
baka." Dadi ya lullubeni,jin batun nayi kamar a
mafarki,wuf kamar an jefota ta fito daga dakin.
Gaba
daya muka dubeta,sai huci takeyi ta dubi
Alhaji"Haba
Baban Kubra(Babbar 'yar hajiya inna a cikin jerin
'ya'yanta mata uku wadanda duk ta aurar
dasu,akwai Abida da Mariya),amma yanzu fa
nake yi
maka batun chanjawa Mariya kayan daki kace
min
baka da kudi,shine kake ikrarin bawa dan karo
kudin jari?" A fusace Alhaji ya nuna kirjinsa"Dan
dan
uwana kike cewa dan karo Salamatu? Ko bakisan
yaya muke da Muttaka ba har kike ambaton dan
sa
da wannan suna a wajena? Toh bari na
fadamaki,Amadu 'dana ne,duk randa kika qara
gigin
kiran sa dan kaaro wallahi sai na saba maki. Idan
banda ku mata shashashai ne,Mariyar ko shekaru
goma tayi da aure ne? Toh bazan chanja ba haka
nan baki isa ki hanani kudurina ba kinji ko?!" Ya
ja tsaki
sannan ya mike domin ransa a bace yake bazai
iya
cigaba da karin ba. Nidai gaba daya jikina yayi
mugun sanyi na dubi inna idanunta sunyi jawur
hannunta har rawa yake ta nuno ni"Akanka Alhaji
ya tozarta ni ko Amadu? Lallai zan dauki mataki!"
A fusace ta fice daga dakin gaba daya ta yi
hanyar
dakinta. Anti amarya dake labe tayi saurin
komawa
dakinta da sauri,dadi ya isheta,domin ita kam taji
dadin fadan da Alhaji ya yiwa gimbiyartasa wacce
yake ji da ita,duk da cewa a bangare daya tana
cike
da bakin cikin fifikon da Alhaji ke nunawa
Amadu,amma hakan baisa taji dadin yanda
akayiwa
KISHIYA ba!" Nima din dai kasa qarasawa nayi,na
mike nayi dakina. Zama nayi ina mai nanata
furucin
inna"Akanka Alhaji ya tozarta ni ko Amadu? Lallai
zan dauki mataki!" Me take nufi toh? Duk iya
tunani
na na kasa gane ma'anar hakan,karshe na tuno
Alhaji yace zai aiken,nayi saurin fadawa wanka
na
shirya cikin Shadda fara qal na fesa turarena,na
dauki wayata mara chaji da niyyar na miqa ta
CallCenter a sanya min. A zauren mukayi kicibus
da
Alhaji,na rusuna cike da ladabi ya dubeni har
lokacin
yanayinsa bai dawo daidai ba kamar yanda ni
dinma zuciyata babu dadi yace"Muje kawai ka
saukeni a
kasuwa daganan sai ka wuce gidan gwaggonku
ka
amshi katin magungunanta na ciwon kafa ka siya
ka
kai,ungo wannan.(Ya mikomin kudi har dubu
uku)
sauran chanji ka rike. Cike da ladabi nayi
godiya,muka fito yana sanar dani Hassan ya
kirashi ya sanar dashi cewar matarsa ce take
nakuda yau
kwana biyu kenan. Don haka ni zan koma na
dauko
su Zahra. Na amsa tare da yiwa matar hassan
addu'ar
sauka lafiya.
Da sallama na shiga wajen gwaggo. 'Yar
tsohuwar tana zaune akan tabarma a tsakar
gida,sai
jikokinta 'ya'yan kanwar Mahaifina(Dije) suna ta
wasansu. Muka gaisa da mutan gidan wadandsa
suka kasance matan 'yan uwan su Abba da suka
hadu ta wajen Uba. Gidan mai dakuna biyar
kowanne da bangarensa,bayan bangaren gwaggo.
Sai kawu murtala,kawu shamsu,kawu lawal da
kawu
hamza. Gaba daya a gidan suke zaune da
matansu,bangaren da gwaggo take shine inda
mahaifina yake a baya kafin Allah Yayi ikonSa
akansa. Na qarasa ga tabarmar da gwaggo ke
zaune nima na zauna ina dariya"Allah Ya ja da
ran
amaryata." Ta dan harareni"Amaryar da ba
kasafai
ake zuwa a ganta ba,tuni na jima da sakin ka."
Na
kame baki ina dariya"Ah haba dai,kice na koma
da
zobena." Mukayi dariya,na gaidata,ta amsa tana
mai
dubana"Ya wajen matan uban naka? Su dai sun
daina nemana ko?" Nayi murmushi zanyi magana
matar Kawu Lawal,Larai ta cafe"Yo ke kuwa
gwaggo
yaushe zasu tuna da kin haifa musu miji? Ai
kansu
kadai suka sani." Na girgiza kaina kawai ina
murmushi domin kuwa nasan Larai nasan
halinta,akwai shishshigi da son tsegumi. Na tare
zancen"Ko kusa ba haka bane,ai su kansu sun
san
Gwaggo tana da daraja saidai wani dalilin ne ya
hanesu da zuwa." Ta tabe baki gami da sunkutar
yaronta mai rarrafe"Ai sai kayita tare
musu,amma
ba
yau nasan Salame da Jummai ba." Na dawo da
kallona ga Gwaggo wacce tayi shiru kawai tana
sauraron mu,itama ni din ta kalla,cikin basar da
zancen nace"Bani katin magungunan naki." Ta
daga
kasan tabarmar da take ta ciro wata leda ta
mikomin"Gashi ka duba,katinan yawa ne dasu. Ni
na
rasa wannan dalili na asibitoci,katin ma sai an
bawa
mutum kusan goma ko duk anan kudin namu ke
tafiya?" Na kwashe da dariya ina mai duba
takardun
nace"Kai gwaggo kowanne ai da amfaninsa wani
receipt ne,kati ai guda daya ne matukar ba wani
asibitin kika je ba toh shine nan ma saikin yanki
wani. Kin gane ko?" Ta tabe baki"Kai ni rabu dani
da
wannan bokon naku,sai ku gama karatun amma
ku zauna babu sana'ar toh meye amfaninsa? Tun
farko
saida na qi bokon nan taka,na shawarci 'dannan
(Alhaji,kasancewar 'danta ne na fari)ya kawo nan
gabana ka dunga yimini tallah amma ya kafe ya
nuna
shi yafi,toh yanzu meye ribar? Ya ci ace a yanda
kake
dinnan kana da sana'a da aure,yanzu wa kake
tunanin zata aureka babu sana'a Amadudu?" Na
mike bayan na mika mata ledar ina fadin"Shiyasa
fa
banason zuwa yanzu sai ki cikani da batun aure."
"Ungo wannan." Tayi min daquwa,nayi dariya
kawai.
Bahijja ce ta shigo 'ya ga Kawu Shamsu mabiyin
mahaifina,sa'ar Zahra. Ta miko min hannu tana
dariya,mukayi musabaha"Oyoyo yaya Ahmed,yau
kuma kai ne a gidan namu?" Nayi dariya"Ke
kuma
yau din mai ya hanaki zuwa makaranta?" Salatin
gwaggo ya katsemu,kuma yayi sanadin fitowar su
Larai da Nafi matar Kawu Murtala,gaba daya
muka
dubeta muna tambayar lafiya. Ta kalleni idonta
sun firfito"Gidanku,yau naga wani al'adar banza.
Idan
banda haukan yaran zamani me zaisa Amadudu
da
Bahijja suyi musabaha?" Gaba daya muka sanya
dariya,na hada hannuwana waje daya"Allah Ya
baki
haquri gwaggonmu,dan ba qara!" Tace"Yo ka
qara
ma ka gani idan ban hadaka da uban naka ba."
Na fice ina dariya,Bahijja ta dan daga
murya"Yaya
Ahmed tafiyar kenan?" Na dago mata hannu"Ina
nan dawowa,ko zakimin rakiya?" Ai kuwa sai ta
taho,larai tace"Au Bahijja ciwon cikin kenan?" Ko
kulata bamuyi ba muka fice daga gidan,a mota
na
dubeta"Ashe ciwon ciki kike?" Ta kwantar da
kanta jikin kujera tana dubana"Wallahi ko daya
Yaya
Ahmed,nifa makarantar ta isheni shiyasa na fake
da
ciwon ciki. Toh dayake na saba ciwon ciki mai
azaba
shiyasa suka yarda da hakan babu wanda ya
takuramin." Nayi dariya"Allah Ya shiryeki
Bahijja,ke
dama tun kina qarama fitinanniya ce." Mukayi
dariya. "Ina Yariman naki? Ko ba haka kike
kiransa ba?" Na
qarashe ina mai dubanta,ta kyalkyale da
dariya"Wallahi yana nan,ko jiya ma yazo." Nayi
murmushi"Ke dai inaga kina gama secondary
zamu
aurar dake,domin bakison karatu,kinga Zahra
dayake tana so ban taba ganin ta kula wani ba."
Bahijja tayi dariya"Hm lallai,kuma wallahi kada
kaso
kaga masoyanta,tace wai tunda ta lura kanason
karatu sai ta gama kaf sannan zatayi aure." Nima
dariyar nayi. Har muka je Chemist din muna
kwasar
hira ni da Bahijja,domin jininmu ya hadu da ita
sosai,bata jin kunyar bani labarin samarinta.
Hirar gaba daya akan yarimanta ne da kuma
abunda ya
shafi zumunci. Saida na sauketa,na bata
magungunan ta mikawa gwaggo saboda bazan
samu shiga ba,lokacin dauko yara yayi. Na ja
motar
na harba titi ina mai dokin sakin cin karo da
Hafsa.
Nayi parking a kofar makarantarsu
Usman,bayan na daukesu nayi makarantar
su Zahra. Sune basu tashi ba sai karfe biyu.
Dalibai suka fara fitowa,na hangi Zahra da
Hafsa sun jero,hakan yasa na fito daga
motar na jingina tare da zuba mata ido. Tafiya ce
ake yinta tamkar ba'ason taka
qasar,hira sukeyi ita da Zahra,jefi jefi ta
kan murmusa wanda hakan ke qara mata
kyau. Na rasa yanayin da nake shirin
shiga,na kasa dauke ido daga kanta,ganin
da nayi Zahra na nuno inda nake yasa nayi
saurin dauke kaina daga garesu gami da
sakin ajiyar zuciya. Ta gefen ido nake satar
kallonsu har suka qaraso da sallama. Sai
anan na sauke idona akanta ina mai
amsawa. Ta nunoni tana dariya mai
bayyana haqora"Lah Yaya Ahmed." Nima dariyar
nayi"Hafsa beauty." Muka sanya
dariya,ta rufe fuska cike da kunya. Zahra
tace"Yaya Ahmed baka sanar dani ba,ashe
kun hadu a facebook?" Na dubi Zahra"Sorry
kanwata,na sha'afa ne naso sanar dake na
manta." Hafsa ta dan rusuna"Ina yini." Cikin
murmushi na amsa"Lafiya Beauty,ya
karatu?" Ta dan rausayar da idonta
kadan,ai baki na saki ina dubanta,tace"Ga
shinan muna fama Yaya Ahmed." Na
jinjina kai"Allah Ya taimaka." Tayi
murmushi tana mai dubana,nima sai na maida
martani,a hankali lebbanta ya
motsa na gane amin ta furta. Ta dafa
kafadar Zahra"Toh 'yar uwa sai mun hadu
gobe,don Allah kizo min da Textbook din."
Zahra tace"Insha Allahu,bye." Ta
dubeni"Yayanmu sai gobe." Nayi murmushi"Ok
Beauty ki gaida gida." Tayi
dariya tana mai rufe fuska da
hannayenta"Oh no Yaya don Allah daina
kirana hakanan." Mukayi dariya gaba daya
nace"Toh ai ke kika laqabawa kanki,ko
don kinsan kina da kyan?" Tayi gaba tana
cewa"Gaskiya Yayanmu ka sanya naji
kunya,bye bye." Bata qara juyowa ba tayi
wajen motarsu,na yi dariya na bude motar
na shiga,Zahra ta zauna a gaba muka nufi
gida. "Zahra kawarki tana da kyau." Ta
juyo ta dubeni cike da zargi sai nayi saurin
chanja magana"Tana da mutunci,meyasa
bakwa ziyartar juna?" Tayi murmushi tana
duban titi,ta gama dago inda ya
dosa,amma sai bata nuna komai
ba"Hum,Yaya kenan,kasan Abba bayason
yawace yawacen nan zuwa gidan qawaye,ita
kuma ta taba zuwa wajen sau
biyu shine taga bana zuwa gidansu tayi
fushi ta dauke kafa har sai randa na je."
Na jinjina kaina ba tare da nace uffan ba.
Bayan na dauko Alhaji,da la'asar ina zaune
a gaban shagon idi muna hirar duniya tare da shi
da wasu samarin unguwa,motar
Badamasi ta tsaya. Ya fito ya qaraso inda
muke aka gaggaisa,sannan ya zauna muka
cigaba da hirar dashi. Idi ya gyara zamansa
ya cigaba"Ai ku kadan ma kuka
gani,domin ni din nan na sha bata kudina wajen
kaiwa Zinaru kudi kai bana ce ga
yawan adadin dana kai mata ba,domin
wallahi daidai da ribata da nake samu sai
na gutsirar mata nata kason amma tashi
guda naji 'yar kaza kaza ta zo min da
zancen banza wai mahaifinta yace ta rabu dani
me zatayi da mai qaramin shago? Toh
fa! Ai baisan ya tabowa kansa bala'i da
masifa ba sai yayinda naje na sameshi
zaune a kofar gidansa,kai kuma fa wai
Ubanta malami ne yake wannan tsiyar. Ai
ina gaya muku rusunawa nayi a gabansa muka
gaisa,yace bai gane waye ba.
Nace"Malam ni ne saurayin Zinaru,idi mai
qaramin shago,nazo domin a biyani
haqqina ko kuma a aura min ita." Nan
abokansa dake zaune suka fara kallon
kallo,har dai Alaramma 'dan delu ya dubeni"Kai
idi kasan da wa kake maganar
nan kuwa? Duba dakyau Malam Dalhatu ne
fa." Ai na fadamuku qeya na juya
nace"Kwarai kuwa Alaramma na sani. Nan
na zayyano qarya da gaskiya,kai har cewa
nayi yana aikota ta karbar masa sikari a
kyauta,nan kowa ya fara salati,malaminka
ya soma gumi,ya nunoni da yatsa"Kaji
tsoran Allah idi ka fadi iyakar gaskiyarka."
Ahaf! Ai sai kuma yayi domin na gama
magana,akayi akayi nace hakan akayi
babu dadi babu ragi. Malam ya taso kamar zai
dokeni,nan na durkusa ina neman
afuwa ina fadin"Daga fadar gaskiya
shikenan sai kuma ace za'a
hukuntani,yanzu wannan ai yaudara ce
akayimin." Kai na fadamuku saida malam
da abokansa suka hadamin Dubu uku sannan na
bar wajen. Toh wallahi duk
budurwar data yaudareni,bana barinta
hakanan sai na ci ubanta,ko ta biyani
kudina ko na kullawa iyayenta da ita
sharrin da bazasu fita ba." Nan wasu daga
cikinmu suka sanya ihu,masu dariya nayi ciki
kuwa harda Badamasi. Daga mai cewa
idi yayi daidai sai mai qara tunzura shi. Na
dubi idi a tsanake"Yanzu kai kana ganin
kaci riba kenan idi? Ashe kenan bazaka iya
haqurin da nayi ba? Wallahi 'yan mata
goma sha sun yaudareni kuma babu wanda ban
gafartawa ba. Idi ya rike baki"Lallai
Amadu,ai kai dama daban kake,amma
irinmu ai sai yanda ta yiwu don bazamu
kyale ba."Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100Amadu 1 page 2
Posted by ANaM Dorayi on 02:22 PM, 31-May-15
Under: Amadu
Na jinjina kaina ina dariya kawai."Toh kai Amadu
ai kai din dan gayu ne ka hadu ta ko'ina,kana
zaton akwai macen da zata gujeka ka damu? Ai
kai wannan ba matsalarka bace domin kanta ta
yiwa,naga ko 'yan matan unguwarnan so suke ka
kulasu,kai akwai wata Maryam data tareni take
tambaya wai kodai kai kurmane,domin bata taba
ganinka kana magana ba." Na rike haba jin
abunda Abba yake fadi,su kuwa dariya suka
sanya. Badamasi yace"Ai mutumin nawa akwai
shan kamshi ga mata." Nidai jinsu nake kawai,har
suka qare duk wani iskancinsu sannan muka mike
tare da Badamasi. A gefen motarsa muka
tsaya,ya dubeni"Kai daddy fa ya bude wuta." Na
zaro ido kadan"Toh fa! Me kuma kayi? Ko yanzun
ma su Haidar ne suka ja ka yawon?" Ya shafi
sumar kansa yana murmushi"Eh toh hakan ne
ma
silar jawo maganar,tun safe dana bar gidan nan
dasu sai uku na koma. Daddy yasan ni din ba
ma'aikaci bane ballantana nace aiki naje,ya kirani
yace ina naje? Na rasa me zance,karshe dai nace
muna tare dasu haidar. Wallahi Ahmed na sha
fada maka tun a baya dama daddy baya kaunar
mu'amalata dasu domin su banda shaye shaye
da neman mata babu abunda suka sanya a
gaba,toh yau dinma kirana Haidar yayi wai don
Allah nazo ko sau daya ne,Jamcy ta jima bata
ganni ba hankalinta a tashe yake." Nace bazanje
ba ya matsamin dole dai na mike naje. Wallahi
babu abunda ya shiga tsakaninmu saidai..." Ya
hau sosa qeya"Abunda ba'a rasa ba,toh shine
daga nan na maidata gida. Toh ashe sa'adda na
shiga toilet daddy ya kira kuma yaji muryar
mace,ina komawa ya hau fada ta inda ya shiga
ba tanan yake fita ba har dai ya yanke min na
nemo matar aure nan da wata biyu idan ba haka
ba ya zabamin a 'ya'yan abokanansa. Hankalina
fa ya tashi." Raina ya baci na dubi Badamasi"Ka
bani kunya Badamasi,nayi zaton ka chanja ka bar
duk wani sabon Allah da kukayi a baya tare da
abokanka,ashe still kana tare dasu?" Badamasi
yace"Haba Ahmed kasan dai bana shaye shaye."
"Sai neman mata ko? Nasan da wannan,amma
ina jin ba tun yau ba ka tabbatar min ka tuba?
Wai Badamasi a zamanin nan meke damun
samarin yanzu da suka dauki soyayyar banza a
matsayin wayewa? Wallahi wannan ba wayewa
bace,jahilci ne. Jahili ne kadai zaiyi wannan
iskancin,wannan ba addini bace ko kusa babu
kamata a wannan. Mutum ya kasance mai tsoron
Allah a duk inda yake,saboda haka ne Allah Ya
sanyo aure tsakanin namiji da mace. Amma duk
da haka mutane sai sun saba masa?! Toh wallahi
ka tuba tun kan mutuwa ta riskeka,Daddy yayi
min daidai daya yanke wannan hukunci a gareka.
Ni wallahi yanzu duk ka bani kunya,na
tabbatarwa da daddy yanzu badamasi ya chanja
ashe dai baibai yake rufeni? Allah Ya kyauta." A
zuciya na juya zanyi gida,ya sha gabana,fuska a
marairaice kamar zaiyi kuka,hannuna ya riko"Don
Allah Ahmed kayi hakuri,wallahi sharrin shaidan
ne. Na rasa yanda zanyi da jamcy ta sanyamin
kahon zuqa,mace shaidaniya ce Ahmed,wallahi
tun a baya wani abu bai qara shiga tsakanina da
ita ba sai wannan jiqon,amma insha Allahu na
daukar maka alqawarin bazan qara ba." Na
dubeshi domin tabbatar da furucinsa,sai na
hangi
iyakar gaskiyarsa har cikin kwayar idonsa sannan
na gyada kaina ina mai sakin ajiyar
zuciya"Shikenan ,Allah Ya dada kiyayewa." Sai
anan ya saki fuska"Amin,amma har ka tayar da
hankalina,kasan banason nayi asarar amintaccen
aboki." Mukayiwa juna murmushi. Muka koma
wajen motarsa na labarta masa yanda mukayi da
Hafsa,ya dubeni haqora a bayyane"Ashe dai
kanwarmu ce,lallai abu zaiyi armashi." Na dan
tare gira"Ban fahimceka ba." Ya dan harareni da
wasa gami da dukan kafadata"Haba
mutumina,yau na sanka?" Dauke kaina nayi ina
mai murmushi,daidai nan Zahra ta fito sanye da
hijabi da alama aikenta akayi. Ganinmu yasa ta
nufomu tana murmushi,ta dan rusuna ta gaida
Badamasi. Ya amsa yana mai zolayarta"'Yar
kauye,kina nan ashe?" Ta dan harareshi tana mai
narkar da fuska"Gaskiya Yaya Badamasi
banaso,wannan budurwar taka ai itace 'yar
kauyen." Mukayi dariya,cikin dariya ya rike
hab'a"Lah Zahra haka kika koma? Au budurwata
ko? Toh ba shakka zan samo miki miji 'dan
kauye futuk!" Dariya kawai nake ban sanya musu
baki ba,domin Zahra da Badamasi ba yau suka
saba zolayar juna ba. Na dubeta"Ina zaki ne?" Ta
nuna min kudin hannunta"Anti ce ta aiken kantin
idi siyo mata kalanzir." Na daure fuska"Yanzu ke
don rashin hankali sai ki ratsa maza haka ki
shiga kanti? Miko kudin ki jirani anan." A sanyaye
ta mikomin,na karba ba tare dana qara kallon
Badamasi ba saboda wani irin kallo da yakemin
yana murmushi. Na dawo na mika mata"Yauwa
shiga ki kai ga chanjin." Ta karba tayi
ciki,badamasi ya sanya dariya"Mutumina anya
babu wata a qasa?" Da sauri na kalleshi"Kamar
yaya fa?" Ya dauke kansa cikin dariya yace"Ko
'yar gida za'ayi?" A razane na dubeshi.
Gaba daya na dauke wuta na rasa me ya
janyowa Badamasi wannan tunanin? Kodai
yau ya taba shaye shaye ne a wajen abokan
nasa? Dakyar na samo abun fada"Amma
yau dai ka shawo ta?" Ya kyalkyale da
dariya har da jijjiga kafada sannan yace"Babu
abunda na sha,gaskiyar
kenan,kai baka hango dacewarku ba?" Na
ja qaramin tsaki"Dan iska kawai,kada ka
qara tara ta da wannan batun,ina baka
labarin hafsa kai kuma kana wani shiririta.
Please barmin batun nan,me zanyi da Zahra?
Wacce na gama ganin fitsari da
kashinta,nasanta mun zauna tare."
Badamasi yace"Toh ai aminina hakan shine
daidai,meye laifin Zahra? Toh wallahi duk
kyawunka Zahra ta fika,don dai kawai
kwalliya bata dameta bane..." Na daga masa
hannu"Barmin batun,Allah Ya hada
kowa da rabonsa. Ina ni ina zama surukin
mace irin Anti Amarya? Kodayaushe tana
sanya min ido akan 'yar ta,kiris zata jira ta
ci min mutunci." Muka sanya dariya.
***************************************
Tana
kwance akan gadonta tayi ringingine
a lokacin data tsurawa hotonsa ido,ba
qaramin kyau yake mata ba. Ita tunda take
bata taba ganin wanda farat daya ya shiga
ranta ba irin AHMED,babu macen da
bazatayi alfahari da kasancewarsa mijinta ba. Ta
lumshe ido tana murmushi a yayinda
idonta ya hasko mata sa'adda yake dariya.
Ahmed fari ne tas,fulani sak. Yana da
dogon hanci daidai misali,ga gashin
bakinsa luf luf gwanin kyau,sai dara daran
idanuwansa ga dogon gashin ido baqi wuluk.
Daidai da hannunsa gashine a
kwance. Ba ma anan kadai ba,Allah Yayi
Ahmed mai kyawun dabi'a ne,a yanda
Zahra take yawaita bata labarinsa. Da irin
wahalar da yake sha a gidansu,tana yawan
nuna mata zafin da takeji akan abunda akeyiwa
Ahmed. Hafsa ta saki ajiyar zuciya
ta qara bude idonta akan hoton Ahmed
dake wayarta a fili tace"Insha Allahu ni
zan kasance FARIN CIKIn ka,ni zan jiyar
dakai dadin rayuwa. Bazan bari ko kadan
ka shiga damuwa ba Yaya Ahmed." A hankali
takai bakinta jikin hotonsa dake
wayar ta sumbata sannan ta qara kalla
tana murmushi. Kiran da mahaifiyarta ta
kwala mata yasa tayi saurin jefa wayar
qasan filo gami da mikewa.
Tun sa'adda mukayi maganar kasuwanci da
Alhaji banji ya qara tada zancen ba. Shiru shiru
har
dai akayi sati babu labari. Babu abunda yafi
daure
min kai sai yanda gaba daya idan naje gaisheshi
yake amsawa a dakile kamar bayaso. Hakan ya
sanyayamin jikina kwarai,toh wane laifi kuma na
yi masa? Rannan dai ina cikin share zauren
dakina naji
sallamar Mariya. Na dago ina mai amsawa,ta
dubeni
babu laifi fuskarta a dan sake yake ba dai kamar
yanda ta saba yimin ba. Nima sai na fadada
fara'ata"A'a mariya,yau kece a gidan?" Ga
mamakina
sai ta murmusa"Eh wallahi Ahmed(Kasancewa ba
wani girmana take gani ba),abun alheri ne ya
kawoni." Nima murmushi nayi mai bayyana
haqora"Toh Masha Allahu,Allah Ya tabbatar."
Tayi
dariya tana mai shigewa ciki"Ai ya tabbatar din
ma."
Na bita da kallo har cikin raina naji sanyin yanda
ta
dan sakemin,na tattara shara na wanke hannu
sannan na fada wanka. Saida na shirya tsaf cikin
riga
blue da wandon jeans shima blue na sanyawa
dakina mukulli,sannan na nufi cikin gidan.
Lokacin
sha biyu da rabi na rana,Abba yana gida
kasancewar
rana ce ta hutu,Lahadi kenan. Da sallama na
shiga,yana zaune akan carpet dake shimfide a
falon,inna tana kusa dashi daga saman kujera
tana
girgiza kafa fuskarta cike da walwala. Yayin da
Mariya ke kusa dashi a zaune,sai anti amarya
dake
gefe fuskar ba yabo ba fallasa sai kuma su Zahra
dake gefe. Zahra,Abba da mariya kadai ne suka
amsa,shi dinma fuska a daure. Gwuiwa a sake na
rusuna domin gaisheshi,ya dauke kansa ya
cigaba
da lissafin kudaden hannunsa,a gaban idona ya
mikawa Mariya"Gashi sai kije ko ita Kubrar sai ta
rakaki amma ki zabi masu kyau,don a yanzu
akwai
katakwayen banza." Ta karba fuskarta farin ciki
fal,nima din murmushi nake saboda na jiye mata
dadi"Abba nagode Allah Ya qara rufin asiri." Ya
amsa
yana murmushi,inna ma ta shiga yi masa godiya.
Anti
amarya tace"Toh Alhaji ya batun siyayyar dana
ce
zanyi?" Alhaji ya sanya hannu aljihu yana
cewa"Ho
Jummai akwai ki da gajen hakuri,ai saiki tsaya ki
gani
ko?" Sai a sannan ta saki fuska tana dariya,inna
ta dubeni da wani irin kallo wanda na kasa gano
fassararsa. Na dauke kaina na qara cewa"Abba
ina
yini." Ya dubeni fuska a daure"A'a me kuma kake
jira? Inace tun farko ka gaidani?" Na shafi kaina
na
mike a sanyaye na fita. A sanyaye na jingina da
bangon zaure gami da dafe kaina,kai wallahi na
gaji da rayuwa haka. Nifa namiji ne,ina da qarfin
neman
na kaina akan wane dalili zan tsaya sai wani ya
ciyar
dani? Wata irin zuciya tazo min,dakyar na danne
na
leqa kicin domin daukar kwanona nan ma dai
wayam babu komai a cikinsa. Kamar na sanya
hannu
aka na rusa ihu saboda tun safe ban sanya komai
a bakina ba. Cike da takaici na fito daga
gidan,ina
shirin fita kanti naji hon din mota. Na juya muka
hada
ido da Badamasi,ya dagomin hannu. Tsayawa
nayi
har yayi parking,ya dubeni"Ina zuwa?" Na dan
tare
gira"Nan shago zan shiga." "Shigo mana kayi min
rakiya,daddy ne ya aikeni." Na dan yamutsa
fuska"Yanzu fa nake kokarin karyawa,ban jima da
tashi ba.""Kaidai shigo babu matsala." Na zagaya
na
shiga. Ya dubeni"Ya akayine? Kamar kana cikin
damuwa ko?" Na qaqalo murmushi na qara
jingina
kaina jikin kujerar"Kaidai bari amma rashin aikin
nan
ya soma damuna. Kasan me ya faru kuwa?" Ya
girgiza kai"Saika fada." Na sanar dashi yanda
mukayi
da Alhaji tun wancan satin da irin sauyin dana
tarar a
tattare dashi." Yayi shiru sai kuma yace"Lamarin
akwai daure kai saidai kada ka sanya komai a
ranka,Allah Ya shige maka gaba. Ba lallai ne
hakan
ne hanyar samunka ba." Na saki ajiyar
zuciya"Hakane,ai Badamasi ina samun aikin nan
da
kuma muhallin zama zan soma neman aure,ko
bakomai zan dan rage wani kewar akan zamana
karkashin Alhaji,matansa suna juyani."
"Gaskiyane,nima dai daddy yace dole na nemi
aikin
yi,zaiyiwa wani abokinsa dake da gidan rediyo
magana,idan yaso sai ya turani. Nifa wallahi
bana son
wahala." Na gyada kaina a raina nace lallai masu
kudi basu san wata aba wai wuyar neman aiki
ba,ni
da nake nema ido rufe ban samu ba sai gashi
Badamasi wanda bai damu da aikin ba ana nema
masa yana zillewa,lallai iyaye ma suna da rana.
Badamasi dai Allah Yayo shi da gatansa,toh
muma
Allah Ya zame mana gata,amin." Na
numfasa"Allah
Sarki." Ya juyo ya dubeni daidai sa'adda danja ta
tsayar damu"Ya akayi mutumina?" Nayi
murmushi
gami da girgiza kaina"Bakomai,gaskiya Badamasi
ka
dage domin da ayi kiranka 'dan mai kudi gwara a
kira ka mai kudin. Kaima ya zamana kana da
naka
sunan. Ka cire kwuiyuwa ka tsaya da
kafarka,kada
ka biyewa rayuwar gata da kake dashi ka
sangartar
da kanka kodayake Allah Yayiwa daddy albarka
domin na lura ko kusa baya yarda da wannan
rayuwar ta sangartar da yara.(Matsalar daddy
daya,bai yarda wani ya hukunta ya batawa dansa
ko
'yarsa rai ba ya kyale matukar labarin yaje
gareshi inji
rufaida)" Badamasi ya ja motarsa yayi fakin a
Yahooza suya spot"Gaskiyane,insha Allahu zanyi
aiki
da maganarka,muje ko?" Na fito muka
shiga,nama
ya siya da yoghurt sai kuma ruwa. Muka koma
mota,saida muka ci mukayi nak sa'annan ya ja
muka
qara gaba. Gidan da zamuje babu nisa da
nan,yayi
kwana,a wani tafkeken gida ya tsaya ya shiga
hon.
Nidai bude baki nayi ina qarewa gidan kallo
saboda
haduwarsa,fili ne babba sai kace na ball,ya sami
can
wata rumfa na parkin ya faka motarsa. Ya
dubeni"Kasan gidan su waye?" Na girgiza kaina
ba
tare da na iya furta uffan ba,ya dauke kansa
yana
dariya"Gidansu Haidar ne,Daddy ne yace nazo na
amso masa saqo wajen babansa. Sauko mu
shiga."
Na girgiza kai"Jeka kawai." Ya dan
harareni"Wallahi
baka isa ba,sauko please." Yayi yayi nace bazan
shiga ba har dai yayi fushi ya fice ya kyaleni.
"Sauka
lafiya,bazan je haidar ya wulakantani ba." Na
fada
gami da dora qafa daya kan kujera ina mai duba
facebook wanda na samu messages har uku daga
mutane daban daban ciki har da Hafsa. Ban bi
takan
sauran ba na bude nata,sallama ce da gaisuwa
sai kuma tambayar lafiyata.
Na aika mata da reply"Wa'alaikissalam
kanwata,lafiya Alhamdulillah. Kema ya kk?"
Kasancewar bata online,yasa ban saka ran ganin
reply ba,na bude daya saqon. Daga Bukar
ne,shima
dai gaisuwa ce,na maida masa amsa.
Kwankwasa
glass din motar da akayi ne yasa na dago kaina.
Haidar ne yana doka min murmushi. Nima na
maida
martani sannan na sauke glass din gami da miqa
masa hannu"Salamun Alaikum." Cikin dariya ya
amsa
min ya qara da cewa"Haba abokina,me nayi da
zafi
da ka kasa shigowa gidanmu? Ai yaci ace komai
daya faru ya wuce,shekaru sun ja sai a manta
rayuwar baya." Mukayi dariya,ya budemin motar
yana cewa"Don Allah zo mu shiga." Dole na fito
na
rufe motar,muka jera ciki. Lallai na yarda haidar
ya
chanja tunda har ya iya fitowa da kansa tarbata.
"Tsarki Ya tabbata ga Ubangiji mai azurta wanda
yaso,Godiya ta tabbata a gareShi wanda ya
horewa bayinSa ni'ima da rahmarSa."Kirarin da
nayiwa
Ubangiji kenan a sa'adda na ganni a wani
hadadden
falo babba,daga can loko akwai dinning table,sai
kuma tsakiyar falon akayi wani dogon bene mai
fadi
inda zai sadaka da sama. Daga falon idan ka
daga kai
kana hangen hanyoyin da suke daga sama,nayi
zaton anan falo daya ne sai naga munbi wata
hanya
daga can kusa da dinning area anan naga Haidar
ya
bude wata kofa,wani benen ne dan qarami
daban
muka hau ya bude kofar yana cewa"Shigo mana."
Na shiga da sallama,dakin sanyi kwarai toh
dayake
ni ba baqon hakan bane yasa banyi kauyanci
anan ba saboda na saba jin hakan a motar Alhaji
idan na
hau ko kuma idan munje gidan su Badamasi ko
motarsa. Wani dattijo ne zaune akan kujera,sai
wata
Hajiya wacce bana tantama sune iyayen
Haidar,tana
zaune kusa dashi,daga can gefen dattijon naga
mutumin nawa a zaune suna kwasar hira da
dariya. Shigowarmu ce ta katsesu,gaba daya
suka
kalloni,duk sai naji kunya ta kamani wallahi.
Dakyar
na iya qarasawa na durkusa gefen Badamasi ina
mai
gaishesu cike da girmamawa. Suka amsa fuska a
sake,Dattijon wanda ko ba'a fada ba shine Alhaji
Musa uba ga Aliyu Haidar Musa ya dubeni
yace"Kaine mai gadin mota?" Sukayi dariya yayin
dana sunkuyar
da kaina ina mai murmushi. Alhaji Musa ya
cigaba"A'a toh,idan bacin gadi me kakeyi da ka qi
shigowa 'dana? Na girgiza kai ina
murmushi"Babu
komai Abba." Da alama yaji dadin yanda nayi
kiransa,yayi murmushi. Ya maida dubansa ga
Haidar"Kai jeka dakina ka dauko min envelop a
cikin
jakata ta ofis." Haidar ya mike yayi hanyar wani
corridor. Na bi bayanshi da kallo a raina
nace"Kamar
mutumin arziki idan yana gaban iyayensa."
Maganar
Abban haidar ta katsemin tunani"Badamasi ya
akayi
bansan wannan ba? Shima abokinku ne?" Cikinn
ladabi yace"Eh tare mukayi karatu dashi." Ya
jinjina
kai yana qara dubana"Kaga kuwa shi baiyi kama
da
taqadiri ba kamar ku." Mukayi dariya gaba dayan
mu.
Daidai nan Haidar ya dawo rike da envelop. Ya
miqawa Abbansa,ya karba ya bawa
Badamasi."Toh
gashi zamuyi waya dashi." Ya karba,muka mike
muna masu yi musu sallama,Abba ya zaro kudi
har
dubu goma ya miqowa Badamasi"Gashi kai da
abokin naku." Cike da jin nauyi ya qi karba,saida
Abba yace"Kuji min yaro,ni da Tukur ba daya
bane?"
Hakan yasa ya karba yana mai 'yar dariya,godiya
mukayi masa sannan muka fito. A kofar gidan ma
saida muka qara tsayuwa da Haidar,ya
dubeni"Abokina ina fatan zumuncinmu zai
daure?"
Nayi dariya"Insha Allahu." Badamasi ya dafe
kuncinsa biyu yace"Amma ka kula kada ka sha
mari
fa,hannun Ahmed kamar karfe." Muka kyalkyale
da
dariya. Na yi qaramin tsaki"Amma kaidai wallahi
dan'iska ne." Badamasi ya hada hannayensa waje
daya"Afuwan." Muka qara sanya dariya,haidar ya
dubi Badamasi"Kai mutuniyar taka fa bata garin
nan." Jin haka yasa na matsa na basu waje na
shiga
mota,bansan me suka tattauna ba sai dai naga
Badamasi ya bude ya shigo muka qara yin
sallama da
Haidar sannan yayi ribas muka tafi. A kofar
gidanmu
ya faka,yayi daidai da fitowar Yaya Usman daga
gidan,toh yaushe kuma ya iso? Na tambayi
kaina,abunda Badamasi ya tambayeni
kenan"Yaushe
yayan naka ya dawo?" Daidai nan Yaya usman ya
watsomin wani kallon raini sannan ya kada kai
ya
hau mota yayi gaba. Nayi murmushi,mai hali dai
baya
chanja halinsa,na dubi Badamasi"Ni kaina bansan
da
zuwansa ba. Shikenan sai mun kuma haduwa
ko?" Daga fadin haka na murda kofar,ya dakatar
dani"Tsaya mana,ga naka kyautar Abban." Ya
mikomin dubunnai,na karba na fito mukayi
sallama
ya ja ya tafi. Jiki a sanyaye na shiga gidan
lokacin
biyu ta kusa. Kai tsaye na dora alwala na nufi
masallaci. Na tada sallah,ina idarwa na nufi
gidan. A tsakar gidan nayi sallama,anti amarya ta
dubeni tana
mai yatsine fuska ta nunoni"Kaidai wallahi Amadu
baka ji dadin rayuwarka ba,ace ka maida kanka
'dan
maula,tir! Amma Safiya tayi asarar haihuwar 'da
mara
zuciya!" Raina idan yayi dubu toh wallahi ya
baci,bansan lokacin dana dago jajayen idanuwana
ba na watso mata mugun kallo. Kirjina har
dagawa
yakeyi don bacin rai,ta dafe kirji da zaro ido"Au
Amadu ni kake yiwa wannan kallon? Eh lallai ba
karya,abokan naka ai 'yan shaye shaye ne babu
tantama sun koya maka. Nan gaba dukana
zakayi."
Na runtse ido,na bude. Zahra naji tace"Haba anti
me yayi maki?" Ai sai ta kai wa bakinta
duka,Zahra ta
durkushe ta sanya kuka. Na kasa jurewa na fice
da
sauri nayi dakina bayan na datse kofar da
mukulli.
Hawaye naji suna sauka akan kuncina,jikina
kuwa sai kakkarwa kamar mai jin sanyi. Wannan
wane irin bala'i ne? Na zaro kudin da suke
aljihuna
wanda Badamasi ya bani,nayi kamar na yaga sai
kuma na fasa na jefar dasu anan tsakar dakin.
Innalillahi wa'inna ilaihir raaji'un! Dole na tashi
na qaryata batun anti amarya,dole ne na nemi
na
kaina!
Ni ake kira uwata tayi asarar haihuwata?! Wane
irin
zafi maganar zaiyi mata idan yau ace da ranta!
Ashe
har yau ana yimin kallon makwadaici saboda
tarayyata da Badamasi! Na buga hannu jikin
bango,kaina ya soma sarawa,da karfi na rike na
koma gefen gado na zauna. Wayata tayi
ringing,kamar bazan dauka ba sai kuma na sanya
hannu na dauka. Ganin lambar Badamasi yasa na
kashe wayar gaba daya. Ranar dai haka na yini
zuciyata babu dadi. Har wajen la'asar ina kwance
kaina yana matsanancin ciwo,naji ana buga kofar
kamar za'a ballata"Kai dallah budemin tun kafin
na
balla,dan kaza kaza kawai!" Hakan ya ganar dani
cewa Yaya Usman ne,na mike jiki babu
kwari,bayan
na dafe kaina da hannu daya na bude masa. Ya
bangajeni na dafe bango gudun faduwa
qasa"wash"
na ambata. Ya dubeni fuska a daure"Kai meye
zaka kulle kofa? Ince dai ba sata kayimin ba?" Na
girgiza
kaina kawai,ya juya yana rage kayan
jikinsa"Kodayake mu yanzu ai saidai ka
bamu,saboda kayi kudi. Ka koma akwadaita,mai
yawo da 'ya'yan hutu dole ne naira ta zauna
maka,kai a dadinka ma ko aure ka tashi yi baka
da matsala." Takaicin maganarsa yasa ban ce
masa
uffan ba na sanya kai na fita domin shaf na
mance da
na zubar da kudi a kasan dakin. A qafa nayi ta
tafiya
har dai na tsallaka gidan wata kanwar
mamana,sau
da dama idan takaicin gidan Alhaji ya isheni nan
nake zagayawa. Anti Aisha sunanta,saidai ita tun
da take Allah bai taba bata haihuwa ba,ta taba
cemin
shine dalilin da tayi magiyar a bar mata ni ta
raineni,amma saboda son da Alhaji yake yiwa
dan
uwansa yace tayi hakuri bazai iya ba,haka ta
haqura
saidai da fari tana zuwa dubani ina yaro amma
ganin
wulakancin da su inna keyi mata yasa ta dauke
kafarta gaba daya,jefi jefi dai a sa'adda nake
zuwa
islamiyya takan biyo ta bani 'yar naira biyar. Nayi
sallama tana tsakar gidanta tana daka,ta amsa
tana
kallon hanya,ganina yasa ta fadada fuskarta"Toh
Ahmed kaine tafe? Sannu da zuwa." Na qaqalo
murmushi murya a dashe nace"Yauwa anti,kina
lafiya?" Tayi murmushi ta dan tabe baki tana
duban
turmi"Uhm lafiya lau Amadu,ai har na fidda rai
da
zuwanka a wannan satin,ganin wancan ma daya
wuce ko qeyarka ban gani ba." Na lumshe ido ina
murmushi sannan na bude"Anti kenan,ban manta
dake ba,lafiya kalau wallahi. Kawai dai ban shigo
bane,kiyi haquri." Ta tsayar da abunda takeyi ta
dubeni"Ahmed idanunka sunyi ja kaima gaka duk
wani iri ko baka da lafiya?" Na gyada kai cike da
dauriya"Wallahi anti kaina ke ciwo." Cike da
tausayawa tace"Assha,ka sha magani?" Na
girgiza
kaina,ta mike tana fadin"Haba Ahmed kamar
yaro
qarami,kana ciwon kai baka ko nemi magani ba?"
Ta
shiga kicin sai gata da flask,tayi hanyar falonta
tana
cewa"Maza shigo kaci abinci ka sha magani."
Kamar
kuwa tasan har da yunwar,na mike jikin babu
kwari
na bi bayanta. Daidai lokacin da nake zama a
kujerarta wacce taci gidansu saboda
tsufa,nace"Uncl e bayanan ne?" Tace"Ya fita tun
safe,can ringim ya
tafi daurin auren qaninsa." A hankali nace"Allah
Ya
dawo dashi lafiya." "Amin." Ta fita sai kuma gata
dauke da ruwan randa mai sanyi,da paracetamol.
Ta
ajiyemin"Bari na kammala dakan yajin nan kafin
ka
ida." Nace"Toh." Dambun masara ne yaji kabeji
da gyada. Babu fargaba na ci sosai domin kuwa
Anti ba
daga nan ba wajen girkin gargajiya,ina gamawa
na
kora magani da ruwa. Sannan na jingina kaina
jikin
kujerar idanuna a rufe ina tunane tunane.
Sallamar
anti ta katseni,na amsa ta zauna tace"Sannu
Ahmed."
Na danyi murmushi"Yauwa Anti." Tayi shiru
kamar bazatayi magana ba sai kuma tace"Ahmed
ya batun
neman aikinka?" Ta tabo inda yakemin qaiqayi
nace"Anti gashi sai faman lalube mukeyi bamu
samu
ba,wallahi anti lamarin har tsoro yake bani duk
inda
naje a baya kamar abun zai yiwu har a sanya
ranar
da ake bukatar na dawo sai kuma kiga abu ya
dagule an maidomin takarduna. Kuma wallahi
anti
kada kiso kiji yanda ake yabon takardun a
kowane
ma'aikata da nake zuwa amma duk da haka ba
nasara." Na qarashe ina mai sunkuyar da kaina
yayinda naji kwalla ta tahomin.
Tausayin yaron ya mamaye Anti Aisha,itama sai
ta
tsinci idonta da ruwan hawaye tayi azamar
sharewa
gudun kada ta karya masa zuciya. Ta daure duk
da
cewa muryarta ta raunana tace"Haba Ahmed,ka
zamo mai tawakkali. Idan kaga abu mai tabbata
ba
lokacinsa ne baiyi ba. Kada ka cire rai da samun
rahmar Allah,Shi masani ne akan gaibu. Allah
Sarki
rayuwa,'dan adam da buri yake. Lokacin da
mahaifiyarka na raye babu irin burin da bata
dashi
na ganin Allah Ya nuna mata girmanka. Ban taba
ganin uwar data so 'danta na fari ba ba tare da
kunya irin na al'ada ba kamar yanda
mahaifiyarka
ta kaunaceka Amadu. Wallahi Amadu a yau inda
iyayenka na raye zakaji dadi,toh yanzun ma ba
wai
baka jin ba,a'a ka qaddara lokacine kawai
baiyiba.
Idan lokacin yayi Allah zai dubeka da tarin
ni'imarSa.
Ka cigaba da haquri da lamuran duniya,kayi
haquri
ka qara haqurin. Shi Ubangiji ba'a yi masa
dole,ka cigaba da gaskata cewa komai ya faru na
daga
matsalolinka jarabtace ta Ubangijinka a
kanka,kayi
qoqarin cin jarabawarnan ta hanyar haquri da
miqa
kukanka a gareShi. Bakomai Amadu kada wannan
ya dameka har ka karaya,na sha fadamaka duk
wani
abu da kake nema duk da kasancewata ba wata
wadatacciyya ba kayi min magana insha Allahu
zan
taimakeka. Shi Alhaji bai qara yi maka batun aiki
ba?"
Na ja majina na goge hawayen kan fuskata
wadanda
suke zuba ba tare da sauti ba,ban dago kaina ba
na
zayyane mata yanda mukayi da Alhaji gaba daya
da
kuma yanda ya chanjamin a 'yan kwanakin nan.
Sai naga tayi murmushi"Bakomai Amadu,bakomai
rabu
dai da makircin mata. Allah zai shige mana gaba.
Kada duk wannan ya dameka,Alhaji yana sonka
Amadu,na gani kuma ni din shaida ce babu irin
soyayyar da Alhaji bai gwada maka ba. Wallahi
Amadu ba don Alhaji ya isa da gidansa ba,da
ayau bakayi karatun arabi ba balle boko. Babu
irin
gwagwarmayar da ba'asha ba kai kanka ka san
da
hakan,kada ka damu fadar Allah ce"Hakika
Tsanani
yana tare da wani sauki" saboda haka ka kwantar
da hankalinka,ka isa aure Amadu,ka kammala
karatunka,koda babu wancan kayi ta addu'a
Allah
Ya dafa mana ko ni ai sai na baka jari. Daga nan
kuma ba sai muje daukar matar amadu ba." Sai
ma ta
bani dariya na murmusa,itama ta dara. Mun jima
muna hira da anti ban bar gidan ba sai da aka
soma
kiran la'asar sannan nayi mata sallama bayan ta
bani
naira dari a cewarta nayi hakuri na karba. Ni
kuwa banason rabata da 'yar darinta wanda
nasan idan
ance shi kadai ta mallaka ba qarya. Ai kuwa
zillewa
nayi zan gudu dasauri ta riko hannu"Au Amadu
rainawa kayi ne?" Ganin har tayi fushi dole na
karba
nace"Gaskiya anti inda nasan saikin matsamin
karbar
'yar darinki wallahi da ban zo ba." Ta kawo min
duka na zille ina dariya tace"Ja'iri kawai." Mukayi
dariya na
fice daga gidan,saida nayi sallah a masallacin
dake
kallon gidansu sannan na qara gaba.
Na shiga dakinmu,Yaya Usman bayanan. Wayata
na sunkuta na kunnata,message din Badamasi na
soma cin karo dashi"Ahmed na kira baka dauka
ba,hope lafiya?" Na saki ajiyar zuciya,sai alokacin
na
tuna da kudin dana bari,sama da qasa babu su a
dakin mamaki kwarai ya kamani daidai nan Yaya
usman ya shigo yana wake wakensa na turanci
na
dubeshi fuska a sake"Don Allah baka ga kudade a
tsakar dakin nan ba?" Ya dan dubeni sannan ya
kauda kansa yace"Ban gani ba." Daga haka bai
qara
cewa komai ba,haka na haqura na mike na fito.
A
kofar gidan nayi kicibus da Zahra,muka dubi juna
baiwar Allah har goshinta ya dan tashi. Ta dan
langabar da kanta tana dubana take idonta ya
ciko
da kwalla"Yaya Ahmed don Allah kayi hakuri da
abunda anti tayi maka." Nayi murmushi
kadan"Haba
Zahra,kina zaton zanyi fushi da anti ne? Bakomai
kinji
komai ya wuce kuma inaso aduk sa'adda Anti ke
yimin magana kada ki qara sanya bakinki kinji
ko?"
Ta gyada kanta tana share kwallar da suka zubo
mata,"Daina kuka mana,gashi kin janyowa kanki
kumburin goshi." Ta shafa wajen sannan tayi
murmushi a hankali tace"Wallahi Yaya Ahmed
indai a
kanka ne anti tayimin abunda yafi haka bazan
damu ba." Nayi mata wani irin kallo mai alaman
tambaya
domin maganar da tayi na buqatar qarin bayani.
ta
dauke idonta daga kaina ta sauke ajiyar
zuciya"Zan
wuce." Kamar na tsayar da ita sai kuma na fasa
na
bata hanya,ta shige da sauri na bi bayanta da
kallo"Zahra ta damu dani." Na ayyana a
raina,lallai kaunarta a gareni mai yawa ce. Nayi
murmushi
sannan na nemi wuri na zauna akan bencin.
Banyi
wata wata ba na share tunanin maganar Zahra
wacce
na kasa nema mata fassara,na shiga
facebook,direct
chat na gangara na duba,sassanyar ajiyar zuciya
na
saki ganin Hafsa na online
Banyi qasa a gwuiwa ba,na aika mata da
saqo"Salamun Alaiki ya ma'abociyar kyau hafsa."
Saqon ya isa ga hafsa a lokacin datake zaune a
barandar dakinsu tana sauraron waqa a Mp3
player,ta ware sauti earpiece manne a kunnen.
Yayinda hannu daya rike da waya,dayan kuma
rike da kankana tana sha. Ganin mutumin nata
online
yasa ta fiddo ido waje. Da sauri ta bude saqon
hannunta har yana rawa. Kasa gaskatawa tayi ba
mafarki take ba,MA'ABOCIYAR KYAU fa yace? Ta
lumshe ido a hankali tana mai jin wani dadi yana
ratsa zuciyarta,sai tayi saurin maida masa
reply"Amin wa'alaika assalam Yayanmu,wallahi
sai naji kamar
zolayata kake,bana cikin jerin kyawawa idan har
aka
jerani da kai." Wani irin dadi ya ziyarceni,na
manta da
duk wani bakin cikin dake zuciyata na bata
amsa"Wayyo ni! Kada kice haka mana,kefa
BEAUTY
ce,wallahi ba qarya kuma kina da kyan saidai
beauty kinsan me?" Ta aikomin amsa"Hm
yayanmu
kenan,shikenan tunda kace haka. A'a yayanmu
saika fada." "Ya kamata ki cire hotonki daga
facebook,ko bakya tsoron samari 'yan bana
bakwai?" Ta lumshe ido kamar yana ganinta a
lokacin data ajiye kankanar ta kashe mp3 din,toh
meye amfaninsu alhalin tana tare da mafi
soyuwa
a
ranta? Ta bashi amsa"Wallahi yayanmu zan cire
tunda har ka nuna baka so,yanzu kuwa." Kafin
na
bata amsa tuni har ta cire"Lallai tafiyarmu zatayi
daya
da Hafsa." Na ayyana a raina,sannan nace"Kai
hafsa
amma nagode,toh bani labari mana." Sai ta qara
aikowa"Ba godiya tsakaninmu,wane irin labari?"
Kai
abu fa yayi dadi,ai sai gani jingine da
bango,qafata
daya akan bencin ina murmushi"Bani na
samarinki."
Sai ga Hafsa har da kwanciya da dafe kai da
gwuiwar hannu"Har naji kunya wallahi,ina
student
zan kula samari yayanmu? Bana kula kowa."
Wani
dadi ya ziyarceni na aika"Haka akeso beauty,kina
whatapp?" Hafsa ta jima tana son taji yayi mata
wannan tambayar,da sauri tayi replying"Eh
yayanmu ina 'dan tabawa." Haka nakeson ji,na
qara tura mata
saqo"Yauwa bani lambar taki,kinga ba
kodayaushe
nake hawa facebook ba,sai mu dunga gaisawa ko
ya
kikace?" "Ba damuwa." Ta aiko min da
lambar,nayi
saving sannan na duba contact dina na whatapp
sai
kuwa gatanan ta bayyana,nan dinma wani
hotonta ne sanye da gown anyi masa kwalliyar
baqi da
orange sai duwatsu. A hankali na sauke wata
sassanyar ajiyar zuciya,na gyara
zamana"Tubaraka
llah." Shine furucina,na sauka daga facebook
sannan
nayi mata sallama a whatapp bayan da nayi
saving
profile pic dinta. Mun jima muna hira da
Hafsa,na
shagala tana bani labarin wani qaninta Noor mai
abubuwan dariya kawai sai naji an warce wayar.
Na
dago don ganin waye mukayi ido hudu da
Badamasi. Fuskartasa a daure,na gyara zama ya
zauna kusa dani,jiki a sanyaye nace"Kayi hakuri
please,wallahi na manta ne banyi kiranka ba." Ya
gyada kansa a lokacin da yake duban chat dina
daga
nan ya mikomin wayar yana murmushi"Bakoma
i,watakila gajiya kayi dani ne." Na dan bude
baki"A
haba dai? Ni na isa? Wallahi ko kadan." Ya
dubeni"Shikenan abar zancen,wacece wannan
kuma?" Nayi murmushi"Hafsa." Ya sanya dariya
yana mikomin hannu muka cafke"Shegen
sama,har kayi
nasarar samun lambarta kenan." Dariya nayi nim
din
ma,na labarta masa yanda mukayi. Muka qara
cafkewa,"Dakyau yayanmu kana da wayo fa.
Kaga
ma kada na sha'afa Murja tace na gaisheka,wai
yaushe zaka kuma zuwa?" Ban kawo komai ba
nayi dariya"Ah haba dai? Ai laifinka ne,nasan
lokacin da
kake satar jiki ka tafi? Ai ya dace ka sanar dani
ko
gaisuwa na aika gareta." Yayi dariya"Shikenan
toh,ni
din ma na kwana biyu banje ba,zuwa gobe sai
mu
leqa,amma bazan sanar da ita ba zuwan bazata
zanyi." Nace"Toh kada kuma muje batanan." Ya
girgiza kai"Bata fiye yawan fice ficen nan
ba,nasan
dai da wuya mu tarar bata gidan." Na jinjina
kaina"Ai
shikenan." Wayata tayi ringing,na duba Hafsa
Beauty ce,na
wangale baki kawai ina mai duban screen din.
Har ta katse banyi yunkurin dauka ba,badamasi
ya sanya kafadarsa ya daki tawa"Na juyo bakin a
bude nake dubansa. Ya daga min kai da
gira"Wacece? Dauka mana." Sai a sannan na kai
wayar kirjina na jingina da bango ina sassanyar
ajiyar zuciya tare da murmushi. Badamasi ya
zubamin ido a mamakince ya dan dunguri kaina
na dubeshi"Kasan wacece kuwa ta kira?" Ya
girgiza kansa yana mai zubamin ido,na gyara
zama sosai na sauke wayar na nuna masa. Kafin
yace wani abu ta qara kira,banso hakan ba da
sauri na katse sannan nayi kiranta. "Hello beauty
inajinki." Na fada cikin rage sautin murya
kadan,Hafsa ta mike zaune ta gyara tsayuwarta
bayan ta rage sautinta sosai kamar mai mura
tace"Yayanmu naji kayi shiru ko gajiya kayi?
Sorry na cikaka da surutu ko?" Lumshe ido nayi a
hankali na shafi sumar kaina"Ba gajiya nayi ba
Beauty,wani aminina ne ya iso. Kiyi haquri kada
kiyi fushi,ya zan gaji dake,ko ba'a taba fada maki
kin iya hira ba?" Wani sanyi ya ratsa
zuciyarta,me yafi hira da masoyi? "Dagaske
yayanmu?" "Ba karya beauty." "Hm,nagode toh."
Na jinjina kaina ina murmushi"Nima nagode,sai
mun hadu anjima kinji?" Ta gyada kai kamar
yana
ganinta"Ok ba matsala." Ta kashe wayar,ai sai ta
saki ihu da tsalle don farin ciki,kaninta Faruk
wanda ke shigowa ya bude baki yana
kallonta"Toh,ke kuma lafiyarki kuwa?" Ta
harareshi cikin murmushi"Ina ruwanka? Dan
sa'ido kawai." Ya tabe baki"A'a hah,me ruwana
dake? Yayi gaba yana waqar Fall in Love na
D'banj. Ta bishi da gudu,shima ya qara qarfin
gudunsa suna dariya domin ya dagota tunda dai
Faruk ba wani yaro bane tsakaninsu watanni
goma. Toh ni din ma kasa nutsuwa nayi bayan
mun gama wayar,na dubi badamasi,muka sanya
dariya a lokaci guda. Na dan daure fuska"Kasan
dai ni din bazan yi soyayya a yanzu ba kamar
yanda na sanar dakai." Ya harareni yana
dariya"Ai fa shiyasa naga kana kiyayya." Muka
qara sanya dariya,daidai nan Yaya Usman ya fito.
Kallonmu yayi,badamasi yace"Yayanmu ina
yini,ashe ka iso?" Ya washe baki"Na iso
wallahi,ya kake?" "Lafiya lau." Ya dubeni"Kai kana
da Dubu biyu ka rantamin?" Ji nayi kamar na
dora hannu aka na kurma ihu,meyasa Yaya
usman zaiyi min haka? Kafin nayi magana
Badamasi ya zura hannu a aljihunsa ya miqo
masa dubu uku"Gashi Yayanmu." Babu kunya
yasa hannu ya karba yana dariya"A'a kai,da son
wahalar da kanka kake,wai fa 'yar riga nakeson
siya,kasan a matsayina na ma'aikacin gwamnati
ya kamata na dunga chanja shiga kada a
rainani." Badamasi yayi dariya kadan"Gaskiyane."
Ya dubeni"Shikenan sai na dawo." A ciki ciki na
amsa masa. Bayan tafiyarsa ma raina babu
dadi,wani irin kunyar Badamasi nakeji. Shine ya
katseni"Gaskiya ka yarda ko kada ka yarda ka
kamu da son Hafsa." Jin abunda yace yasa na ji
'dan sanyi,jiki a sanyaye na murmusa batare da
nace masa komai ba.
Sai wajen magriba muka rabu da Badamasi. Nayi
sallama na shiga gida bayan na dawo daga
masallaci,karo muka kusan yi da Zahra zata fito.
Ta
dakata,mukayiwa juna murmushi nace"Abba yana
nan ne?" Ta gyada kai ba tare data iya furtawa
ba.
Nayi hanyar dakin,yana zaune kan kujera yana
amsa waya,samun waje nayi na zauna. Shiru ya
gama
waya maganar dai akan kasuwancinsa ne,daidai
nan
anti amarya ta shigo tana yatsine yatsinen
fuska,harara ta maka min kafin tace"Ai saika fita
waje
ka jira tunda waya yakeyi,ka sanyashi a gaba."
Na
mike a sanyaye zan fita sai gashi ya ajiye
wayar,na dawo na zauna cike da ladabi
nace"Abba barka da
dare." Bai dubeni ba ya gyada kai,mikewa nayi
kawai na bar falon har na kai kofa anti tace"Ka
turomin Zahra." Na amsa da toh sannan na fita.
Dakinsu na shiga,lokacin ta dawo tana zaune
tana
koyawa qannenta homework. Tana sanye da jar
atamfa,kan babu kallabi,gashinta tufke da ribbon
sai
fada take zabgawa Abubakar"Ai saika nemo
cleaner,don iskanci abunda na siyo yanzun har
kaje
ka batar? Toh wallahi tashi ka nemo ta da
kanka." Ya
turo baki yace"Cabdin." Ta dungure masa kai,nayi
saurin cewa"A'a haba Zahra,ki dunga binsa a
hankali mana." Sai anan suka ankara dani,sai
kuma ta ja
dankwalinta tana mai daure kanta cike da jin
kunya
a sanyaye tace"Wallahi Yaya Ahmed abubakar
dinne
bayaji ko kadan,kaga yanzu fa na siyo cleaner har
ya
batar." "Sorry,kada ki dokeshi,Abubakar biyoni ka
amsa,ke kuma kije anti tana kiranki. Nayi
waje,Abubakar ya biyoni bayan ya cewa Zahra
Allah
Ya isa." Da gudu kuwa ta biyoshi na rike
hannun"A'a
kiyi haquri Zahra,tafi kiran Anti,kyaleshi zanyi
masa
magana." Tayi kwafa sannan tayi dakin Abba. Na
ja
hannun abubakar mukayi kanti ina cewa"Haba
abu,kaida yayarka,meyasa kake mata rashin
kunya." Ya turo baki kadan"Ina ruwanka?"
Mamaki ya
kamani,lallai rashin kunyar abubakar takai inda
takai
ban qara tankawa ba,na tsaya a shagon idi na
siya
na bashi"Toh gashi ka kai wa Zahrar." Ya karba
ya
ruga gidan. Tana kwance ta mike zaune,duk da
hakan zuciyar bata bar yin radadi ba,dole saida
ta
dangana da mikewa tsaye. Ta sanya hannu a
bango
sannan ta dora kanta kan bangon. Na shiga uku!
Meke faruwa?!! Wayyo zuciyata kada kiyimin
haka!
Wa kike tunani? Wa kike zaton kin kamu da so?!!
Abokin Saurayinki!! Subhanallah. Ta zame anan
tana
mai dafe kirjinta,hawaye masu zafi suka
kwaranyo mata. Ta dubi fuskar wayarta,hotonsa
ne wanda tayi
nasarar dauka a wayar saurayin nata. Kamar
wata
tababbiya sai kuma tayi murmushi,ita kanta ta
gaza
tantance ainahin abunda take ji game da shi. SO
ne
ko kuwa SHA'AWA?!!
MURJA ke wannan tunanin ita kadai a dakinta. A
hankali ta dubi agogon dake manne a
dakinta,wanda ya nuna karfe daya da rabi na
daren
yau. Sai kuma ta sauke a hankali tana duban
hoton
tace"Kana wahalar dani AHMED,meyasa ka hana
bacci uhm? Ko so kake na zautu ne?
Murmushinka na burgeni." Ta fada a yayin data
shafi lebbansa ta
hoton. Haka dai Murja tayi ta sumbatu har bacci
yayi
nasarar daukarta. ***************
********************************Washegari
da
asuba tashi nayi cike da walwala,saboda mafarkin
da
nayi wai gani ni da Hafsa,muna zaune a bakin
ruwa muna cilla duwatsu. Tana yimin hira mai
sanya
nutsuwa don haka a kunnena akayi kiran
sallah,na
dan bugi kafar yaya usman,ya juyo a fusace"Wai
me
akayi?" "Ka tashi anyi kiran sallah." Yace"Toh
qanin
liman,naga dai kiran farko ne ko assalatu ba'ayi
ba,please kada ka takuramin." Ya juya yana mai
qara kudundunewa cikin bargo,sai ma ya bani
dariya wai
mutumin da ake shirin bikinsa nan da 'yan
watanni
shine har yanzu bai gama yin wayon qarfafa
ibada
ba. Na mike ina mai salati sannan na fito na dora
alwala. Haka na zauna nayi ta tilawar al'qur'ani
har
saida naji an kira sallah,sannan na mike nayi
masallaci. Da safe kuwa cike da sa'a(domin a
wajen
sa'a ne) hassan bai iso ba,Abba ya umarceni
dakai su
Zahra makaranta. Naji dadin hakan,ko a hanya
sai
labarin Hafsa nake bawa Zahra ina mai
cewa"Zahra
qawarki akwai mutunci,kada kiso kiga yanda take
girmamani kamar na kasance yayan nata a
gaske." Muryarta ciki ciki tace"Ai Hafsa tana da
mutunci
sosaima." Na gyada kaina,batare da hankalina
yakai
ga tsinkayen wani abu daga chanjawar muryar
Zahra
ba. Har muka sauke su Abubakar muka kama
hanyar makarantar su Zahra,ban bar yi mata
maganar Hafsa ba. Zahra ta cika tayi fam,kai!
Inda ace Yayanta Ahmed yasan yanda zuciyarta
ke tuqiqi da
wallahi da ya dakatar da batunsa. Ai ita ba
yarinya
bace da zata kasa gano cewa yayan nata son
aminiyarta yake. Ya akayi hankalinsa ya kasa
hasko
masa KAUNARTA a gareshi? Ashe duk yanda
takai ga
fahimtar dashi ta hanyar idanuwanta,furucinta da
kulawarta agareshi bai kai ya gano ba? Ashe ita
kadai take kidanta take rawanta? Toh wane irin
kallo
ne dauke a kwayar idonsa a kodayaushe idan
suna
tare? Wannan wane irin kallo yake mata? Toh
kodai
haka kallonsa yake ga kowa amma soyayyar da
take
masa yasa take zaton ko ita kadai yake yiwa?
Dakyar ta iya hadiye damuwarta amma duk da
hakan saida
kwallar data taho mata ta kusan tona mata asiri
babu
shiri ta shanye. Na tsaya daidai kofar,saidai nayi
rashin sa'a ban ga hafsa ba a waje,a sanyaye
nace"Kice ina gaisheta kinji? Ayi karatu dakyau."
Zahra bata juyo ba ta gyada kanta da sauri tayi
cikin makarantar.Zaharaddeen  Shomar
Whatsapp   08168575100
Amadu 1 page 3
Posted by ANaM Dorayi on 03:23 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
Koda na dawo daukarsu,burina kawai nayi tozali
da sanyin idanuna. Na fito na tsaya jikin motar a
lokacin da dalibai suka soma tururun fitowa. Cike
da
sa'a mukayi ido hudu da ita a lokacin data sanyo
kai
ta fito. Murmushi mukayi a lokaci daya,ta
qarashe
nata da sunkuyar da kanta. Zahra na biye da
ita,amma can qasan ranta ji take
kamar ta komar da
Hafsa baya saboda irin kallon da taga yayan nata
ya
tsareta dashi. Babu yanda ta iya haka nan ta
daure
zuciyarta. Suka qaraso,gaba daya suka gaisheni.
Na
juya na bawa Zahra baya ina magana da
Hafsa"Beauty ya garin?" Ta sunkuyar da kanta
tana murmushi"Gari ai yana
wajenku yayanmu." Baiwar
Allah Zahra,tuni ta shige mota zuciyarta na
zafi,kwalla
ta cika mata ido domin ita kadai tasan abunda
takeji.
Lallai tana tausayawa ire irenta masu fama da
SON
MASO WANI. "Ai kune da gari,ko yau din ma noor
ya
sanyaki kuka?" Muka sanya dariya tana mai rufe
fuskarta gami da langabar da kai
a shagwabance
tace"Kaii yayanmu,ashe baka mantuwa?" Na tsare
da
kallon da nasan dole taji a jikinta,ta sauke
hannuwanta a hankali,muka kalli juna sai kuma
ta
dauke idonta da sauri. Na saki ajiyar zuciya ina
murmushi wani irin yanayi yana shigata"Ta yaya
zan manta? Wai ke yaushe zaki
kawo mana ziyara ne?
Zahra yaushe....." Sai kuma naga wayam a
lokacin
dana juya don neman Zahra,sai na hangeta
zaune a
motar ina 'yar dariya na maido dubana ga
hafsa"Ashe qawar taki ta shige,inajinki yaushe
zaki
zo?" Tace"Lallai ma yayanmu,ai aminiyartawa
zakayiwa fada,tambayeta sau nawa
naje ita ko
qeyarta ban gani ba. Har a gida ana min dariya
wai ni
kadai ke kida da rawana,Zahra bata kaunata." Ta
qarashe tana mai shagwaba murya,muka sanya
dariya. Tunawa da nayi akwai su Abubakar a
motar
kuma kwarai zasu iya fadi a gida cewar ni na
tsayar dasu yasa na dubeta"Kada ki
damu,nayi maki
alqawarin zaki ganmu watarana,bari mu wuce."
Ta
dan matsa daga jikin motar tana
murmushi"Shikenan
tunda daga bakinka ne na yarda,zan zuba ido."
Na
kasheta da kallo"Kin yarda dani har haka?" Ta
lumshe ido tana mai gyada kai"Fiye da hakan." Ai
ji nayi kamar kada na tafi dole
dai mukayi sallama ta
leqo ta window"Toh 'yar uwa sai tomorrow."
Zahra
ta daga mata hannu tana mai murmushin da yafi
kuka ciwo. Na shiga motar cike da annashuwa
zuciyartawa fari tas,na dubi su Abubakar ta cikin
glass wa'yanda suke ta cin gurasa hannunsu rike
da Vanilla sannan na ja motar
nayi gaba.**********
**************************************Da
magriba muka shirya tsaf ni da Badamasi kamar
yanda mukayi muka nufi gidansu Murja. A mota
na
labarta masa yanda mukayi da Hafsa,yace"Kai
amma
na jiye maka dadi,Hafsa ta hadu amma bata kai
murjata ba. Ta fita fari wanda
anan Hafsa ta
kuskuro." Na dan ja tsaki"Ba don larabawa farare
bane da na zagi kalar fari. Bayan fari babu
abunda
Murjar taka zata nunawa beautyna." Badamasi ya
tabe baki"Toh ai kaji ni farin nakeso. Ta haskaka
gidana." Mukayi murmushi a lokaci daya,sai kuma
muka sanya dariya na girgiza
kai"Allah Ya kyauta."
Ya cafe"Amin toh." Daidai nan muka isa kofar
gidansu Murja. Ya dauki wayarsa"Bari na kirata
nasan zataji dadi sosai idan taji ina qofa." Nidai
dariya
kawai nayi ina mai daddane wayata. Ina ji suka
gama
wayar ya sanar da ita,sai kuma naji yace"Assha
dama baki da lafiya? Daure ki fito
na tabbata kina ganina
zaki warke." Sai kuma ya kashe wayar,muka dubi
juna"Gatanan zuwa." )Murja kuwa cike da takaici
ta mike,wata cousin
dinta wacce tazo gidan hutu,Aimana,ta dubeta"Ya
dai? Badamasin ne yazo?" Ta ja tsaki cike da
bacin rai
tace"Shine mana,dan takura kawai baisan tuni na
dawo daga rakiyarsa ba." Aimana ta mike
zaune"Wai
Badamasin shine wanda na ganku rannan a
tsaye?" Ta gyada kai tana mai cigaba
da gyara
fuskarta,aimana ta bude baki sannan taja
tsaki"Gaskiya ke dinnan wata sakaryace
wallahi,duk
haduwa irin ta Badamasi kice bakya sonshi,yaron
da
kudi suka riga suka zauna masa? Ai ina shan
labarinsa a wajen classmates dina da suke BUK a
baya amma ban taba ganinsa
ba,yana daya daga
cikin 'YA'YAN HUTU. Kinsan kuwa waye Alhaji
Tukur?
Lallai 'yar nan kina wasa. Toh wa kike so idan ba
shi
din ba? 'Dan gidan waye kuma?!" Murja ta ajiye
jan
baki ta juyo ta nufi cupboard daukar mayafi
bayan ta
gallawa Aimana harara"Aboki kuma
amininsa,Aimana duk kyawu irin na Badamasi
wallahi bai taka sahun Ahmed ba,bansan dan
gidan
waye ba,amma a yanda nake ganinsa da yanayin
fatarsa nasan cewa kudi sun zauna. Gayen fa ya
hadu,wawiya itace zata ganshi ta kyale." Aimana
ta
jinjina kai tana mai mamakin 'yar uwarta kuma
abokiyar shawararta"Aminin
Badamasi? Lallai murja
kin sanya kanki cikin babbar matsala! So kike ki
hadasu rigima ne? Please kada ki soma wannan
danyen aikin." Murja ta ajiye turaren data fesa
ajikin
mayafinta tana mai murmushi ta dubi kanta a
madubi"Ahmed ya cancanci sanya mace a
matsala,ke Ahmed is my everything zan
iya komai a kansa ciki
kuwa har da murje kunyata ta 'ya mace na
bayyana
masa sirrin zuciyata. Da Ahmed zai bani dama
wallahi
komai yake so ni mai yi masa ce. Na jinjinawa
wanda
a sanadinsa na hadu da Ahmed,kinga ko banza
Badamasi yayi min rana. Kada na cikaki da
surutu,kinsan bana gajiya da batun
Ahmed,sai na
dawo. Idan mama ta sauko ki sanar da ita." Ta
juya ta
fita tana dariya,Aimana kuwa cika tayi da
tausayin
Badamasi ganin dagaske qawartata take koda
dama
tasan Murja zata
aikata.***********************
************************Na shagala ina hira
da Hafsa ne sai naji Badamasi
yace"Bismillah,gatanan."
Na dago kaina na dubeta. Yau dinma ta ci
kwalliya
cikin doguwar riga na shadda ta sanya qaramin
mayafi. Na dauke kaina. Ita kuwa murja wani
sanyin
dadi ne ya ratsata ganin Ahmed. Cike da
rangwada ta
qaraso wajenmu. Ta rankwafo ta jikin glass saitin
da Badamasi yake,a yangance
tace"Salamun Alaikum."
Muka amsa a tare muna murmushi. Ta zuba min
ido
tana murmushi sai kuma tace"A'ah ashe harda
Malam
Ahmed,toh bismillah ku shigo." Ta budewa
mutumin
nata kofa,ya fito yana mai cike da farin ciki,nima
na
fito tana gaba muna biye da ita har saida ta
sadamu da falon baqi. Bayan mun
zauna ina daga can
gefe,yayinda take zaune a kujerar dake
fuskantarmu. Ta gaida Badamasi nima ta waigo
ta
gaisheni,cikin 'yar dariya na gyara zama ina mai
dora
gwuiwar hannu akan ta qafa"Malama murja,ya
garin? Ya akaji damu?" Ta wani yi far da ido
muryarta kamar mai jin bacci
tace"Gari yana hannun manya ire
irenku ai,yanzu muka fara ji daku Ahmed." Na yi
murmushi a raina ina cewa"Lallai wannan yangar
tata tayi yawa,wato har ta zame mata dabi'a?" A
fili
kuwa nace"Toh Madallah,ince dai an rike
alqawari."
Tayi wani murmushi dana rasa gane fassararsa ta
dubi tsakar idon
Badamasi"Saidai idan abokin naka
ne ya karya,amma na daura alqawari daku har
sai
sa'adda burin nan ya cika." Badamasi ya dubeni
mukayi dariya gami da cafkewa,wani dadi ya
ratsa
zuciyarsa yace"Na gaya maka mutuniyartawa ba
dai
iya kalami ba,shiyasa nake kasa tafiya duk lokacin
da nazo." Murja ta dan yi
qaramin tsaki a ranta
tace"Wawa kawai." Daga karshe dai na mike tsaye
ina murmushi"Toh ka sameni a mota." Ga
mamaki ina
mikewa murja ma ta mike"Nima tafiya zanyi,na
sanar
daku bana jin dadi ne." Badamasi cike da sanyin
jiki
yace"Haba dai babyna,bakya bari mu dan yi
hira." Murja ta dan hasala"Au yanzu
da na zo din ma duk
da rashin jin dadina banyi maka ba?" Yayi saurin
tarewa"A'a wallahi ko kusa." Ganin yanda ta bata
fuska nace"Haba malama murja ayi haquri a
tausayawa abokina,bakisan rawar kafar da ya
dunga yi ba,ko da mintuna kalilan ne ki bashi
kuyi hira." Ta dan kashe min ido
hakan ya bani
mamaki"Shikenan Ahmed tunda kasa baki zan
tsaya,Ahmed bani lambarka mana sai a dunga
zumunci,kaga koda na kama abokinka da laifi sai
na
kawo qara." Bamu kawo komai ba,muka sanya
dariya gaba daya,nace"Alhalin ma bazaiyi ba,ke
don bakisan yanda kike a
zuciyarsa bane." Na fada gami
da zayyano mata lambata,tayi saving fuskarta
cike da
annuri,nayi musu sallama na fita. Har na zauna a
mota ina mai cike da mamakin kallon da murja
ke
jifana dashi,saidai na dauki haka akan kissimawar
shaidan shiyasa nayi azamar watsar da batun don
bana son na cika zargin wani
abu. Domin ni ai ba yau
na san mata ba,abu kadan zasuyi na fahimci
manufarsu,toh zuciyata ta bani a kallon da murja
ke
watsamin akwai wata a qasa wanda bana fatan
zatona ya kasance gaskiya.*******
************************************Da
daddare nayi shirin kwanciya,Yaya usman
yana waje
zaune tare da abokansa lokacin karfe sha daya
da
rabi. Toh kasancewar su maza ba wani dare suke
gani ba domin lokacin ma chatting nake da
friends,Hafsa tuni ta sauka,wayata tayi qara.
Lamba
ce babu suna,iya tunani ya gaza bani wanda yake
kirana a lokacin nan. Ban qara
mamakin kiran ba sai
da naji muryar mace. Na boye mamakina na
amsa sallamarta. Ta qara
da cewa"Ahmed kenan,baka ganeni ba ko?" Naso
na dauki muryarta saidai banason gaskata hakan
sai
nace"Kwarai kuwa domin yau ne karo na farko
dana
fara ganin lambar nan." Murja ta qara rungumar
filo
tana murmushi,a gefe Aimana ce ke sharar bacci
bata san ma me ake ba.
Tace"Zakayi mamaki idan na ce
maka MURJA ce ko?" Da gasken kuwa mamaki ne
ya
kamani,na dan gyada kai kamar tana ganina"Au
murja,ince dai lafiya?" "Lafiya kalau
Ahmed,muryarka
kawai nake son ji." Innalillahi,nayi ta ambata a
raina,kada fa zargina ya tabbata. Na rasa ma
amsar da zan bata,dakyar na hadiyi
miyau gabana yana
faduwa"Bangane hausarki ba." Tace"Ai nasan
bazaka gane ba,a sannu zan fahimtar dakai
manufata Ahmed,yanzu dai na bugo domin naji
muryarka ko bacci zai zo mini. Wallahi Ahmed
bazaka
gane ba,ni murja ni nasan me nakeji akanka!" Da
karfi na runtse ido ina salati a
fili,raina ya soma
baci,ba shakka ta shayar dani mamaki,aminina
ne ya
fadomin a raina,wayyo Badamasi baiyi sa'ar
budurwa ba. A hasale nace"Kinga please kada ki
cikani da surutan banza,gudnyt." Na kashe wayar
gaba daya,mikewa nayi gumi yana zuba daga
fuskata,dakin na shiga zagayewa ina
yin salati a
bayyane. Na shiga uku ni AMADU! Wannan wane
irin
bala'i ne? Murja tana cikin hayyacinta kuwa?
Tasan
me takeyi? Budurwar abokina? Sakayyar da zata
yi
masa kenan? Ina tarin kaunar da yakeyi mata?
Ashe
dama butulu ce? Na toshe kunnuwana domin har
lokacin muryarta da kalaminta na
yawo a cikinsu,I
just cn't believe it! Murja da kanta? Ya
subhanallah!
Inama ace mafarki nakeyi? Motsin Yaya Usman
naji
yana rufe gidan,hakan yasa nayi azamar kwanciya
bayan na juya bayana na fuskanci alkibla. Ranar
yini
nayi zuciyata babu dadi,tausayin aminina ne fal a
zuciyata qarshe na fawwalawa
Ubangiji na kwanta.
Koda safe haka na tashi jiki a sanyaye,Yaya
usman
yana ta shirye shiryen tafiya abunda ya kawoshi
daman har da batun aurensa da za'ayi nan kusa
babu jimawa. Ni na kaishi tasha ya hau mota
babu
laifi a motar ya sakar min fuska,mukayi rabuwar
arziki saida naga tashin motarsu
sannan na koma
gida. ******************************
**************A ranar Hassan ne yakai su
Zahra
makaranta. Da misalin sha biyu ina zaune abun
duniya duk ya dameni,lamarin ma tsoro yake
bani ni
Ahmed,rai daya amma gani da tarin matsaloli
birjik. Babbar matsalar dake a
gabana yanzu bai wuce
wannan sabon salon na Murja ba,idan Badamasi
yaji
wane irin kallon zaiyi min?***********
*************************************Da
yamma na isa gidan gwaggo domin gaisheta. A
kofa
muka hadu da kawu murtala da kawu lawal suna
hira,na durkusa cike da ladabi na
gaishesu. Kawu
murtala cikin murmushi yace"Amadu mun kai
kudin
yayanka,yaushe zamu miqa naka?" Ina murmushi
na
sunkuyar da kaina ban iya furta komai ba. Kawu
lawal cikin dariya yace"Ko 'yar gida za'ayi maka?
Tunda naga kai tsoron matan kake." Mukayi
dariya nan ma dai kasa furta komai
nayi. Kawu Murtala ya
kauda wasa"Ya dai kamata ka nemi matar aure
koda
ba'a hada naka da na dan uwanka ba sai ayi
nakan
daga baya." Kawu lawal yace"Yaya kenan,yaron
nan
fa ko sana'a bai kama ba." Kawu Murtala cike da
mamaki ya dubeni"Ikon Allah! Mudi yace ya baka
jari,me kayi dasu amadu?"
Mamaki ya cikani,na
hadiye nace"Eh toh yace zai bani mai yiwuwa dai
mancewa yayi." Kawu Murtala ya girgiza kai cike
da
al'ajabi"A'a amadu,jiya jiyan nan fa da yazo nan
shi
da usmanu yake sanar dani hakan." Sai nayi
saurin
chanja magana"Eh kawu yace zai bani a jiyan
yace nazo na karba toh sai kuma ya
manta amma nasan
yana sane." "Yauwa yanzu naji batu,kaga ko
qaramin shagone ai saika bude da kadan kadan
hardai Allah Ya albarkatar maka tunda aikin bai
samu
ba ko?" Ya qarashe yana duban kawu lawal,muka
gyada kai"Gaskiyane." Saida muka jima anan
muna hira dasu kawu sannan na
mike na qarasa cikin
gidan. Na qarasa ina mai mamakin yanda mutum
babba
kamar Abba ya fadi abunda bai faru ba,amma
bansan qudurinsa ba ko yana da niyyar
aikatawar."
Da sallama na shiga,muka gaisa da matan
gidan,nace"Mutuniyata kina ina?" Daga daki
Bahijja
ta amsa"Inanan zuwa Yayana." Nayi dariya ina jin
Badariyya 'ya ga Kawu Hamza
na fadin"Wato Yaya
Ahmed ita kadai ka sani ko?" Raliya 'yar Kawu
Shamsu dake wanki anan bakin famfo tace"Rabu
dashi Badar dama ina rannan har katin waya ya
turo
mata amma mu kam ko oho." Nayi dariya"Ku dai
kishi kukeyi,toh kwalelanku,ni da 'yar kanwata
mutu ka raba." Iyayensu dai dariya
sukeyi,na shige dakin
gwaggo ina cewa"Kanwata ina nan ina jiranki
akwai
labari." Ta daga murya"Yauwa yayana ganinan
zuwa
nima akwai magana a bakina." Nayi dariya
kawai,na
qarasa tura kai dakin ina jiyo Mama Ladi
mahaifiyar
Raliya tana tare min"Ku dai gulma na cinku,meye
ruwanku da zumuntarsu?" Nidai
na shige wajen 'yar
tsohuwata,na dubeta tana zaune tana taunar
goro"Tsohuwa amaryata." Ta harareni tana mai
cigaba da taunar goro"A'a ai na fadamaka ni
bana
auren dakai,ko 'yar ledar nan ta kaza baka taba
zuwarmin da ita ba." Nayi dariya"Amaryata kada
ki damu wataran sai kinci kin
ture." Tayi
murmushi"Allah Ya nuna mana amadu." "Yauwa
amin gwaggo." "Ai jiya baban naka yazo nan shi
da
Manu." Na gyada kai"Eh hakane." "An qara
tattaunawa game da bikin nasa,yace a can
ma'aikatar
da yake an bashi gida qarami acan zata zauna ita
Fiddausin,toh iyayen naku ma
suna batun za'a hada
dana kannenka." Nace"Toh nasu Raliya kenan?"
Ta
gyada kai"Ita da Badariyya ba,naso ace kai din
ma a
hada da naka amma ka gaza samo matar aure."
Nayi
murmushi ina mai shafa sumata"Gwaggo
kenan,ai
shi aure lokacine,kada ku damu kuyi tamin
addu'a har dai nayi dacen samun aiki.
Aure ai sai kana da
muhalli da sana'a ko kuwa?" "Gaskiyane 'dan
nan,toh Allah Yayi maka arzikin,Ya jikan
mahaifanka." Naji dadin addu'arta"Amin gwaggo."
Bahijja tayi sallama ta shigo fuskarta a
sake"Yayana
ina yini." "Lafiya lau kanwata,ya karatu?" Tayi
murmushi"Mun gode Allah." Ta
matsa ta bude
kwanon gwaggo,gwaggo takai hannu zata janye da
sauri tayi baya rike da kwanon tana dariya
tace"Kedai tsohuwarnan saidai kiyita cin dadi kina
kyalemu,toh wannan kuwa sai na ci shi." Ina
dariya
nace"Kanwata meye shi?" "Dambun nama mai
dadi ne fa yaya suwaiba ta aiko
mata shine ta makale tana
ci abinta ita kadai." "Matso kizo nan mu ci." Ta
zauna
muka hau ci,gwaggo tace"'Yar qaniya,kada ku
cinyemin,shiyasa nake kaffa kaffa kada ki fado
dakin
nan tun dazu naqi bacci ashe kice idona biyu ma
zaki
iya kawo masa hari." Muka tuntsire da
dariya,nace"Kai amma yayi dadi,gaskiya a
qulla min
na tafi dashi." Gwaggo tace"An hana,ku miqomin
ai
kunci da yawa." Muka diba sannan ta rufe ta
maida
ma'ajiyarsa. Muka fito tare da Bahijja nayiwa
gwaggo
sallama,a kofar dakin muka tsaya,nace"Bari na
fara
jin naki domin ni nawa bamai dadi bane
kanwata." Sai naga itama jikinta yayi
sanyi"Haba dai yayana?
Toh ai ni dinma kusan hakan ne. Matsalar daga
iyayen yarima ne,sunce su sam bayan aure basu
yarda na cigaba da karatuna ba. Gashi ni
ra'ayina ina
kaunar karatun shi kansa ya yarjemini yace za'ayi
hakan yanzu ya zanyi?" Nayi shiru ina mai cike da
tausayinta,sai kuma nace"Kada
ki damu,kiyi hakuri.
Idan har kina sonshi ki nuna masa ke mai
biyayya ce
ga iyayensa ba ma shi ba,a hankali idan kika yi
sa'a
bayan auren naku kina binsa sau da qafa kina
kyautatawa iyayensa sai kiga sun sauko,tunda
kansu a waye yake 'yan boko ne." Ta gyada kanta
zuciyarta na sanyi"Shikenan
yayana insha Allahu
zanyi aiki da shawararka." "Yauwa kanwata kuma
ki
dage da addu'a." Ta jinjina kai"Ina yi zan qara
insha
Allahu." Ta dubeni"Toh yayana kai kuma meye
damuwarka?" Na sanar da ita batun Hafsa,na
qara da
cewa"Ni wallahi na rasa ma ta yanda zan soma
bullo mata da batun soyayya naga
yarinyar tana
girmamani gashi ina nuna mata kada ta kula
samari."
Sai naga Bahijja ta sanya dariya sannan
tace"Haba
Yaya Ahmed,kana tunanin akwai macen da zata
qi
ka? Haba yayana sai kace yau ka fara yin
budurwa?
Kawai ka sanar da ita kada ka kwari kanka,ko
kuma ka sanar da Zahra ita sai..."
Nayi saurin dakatar da
ita"A'a haba dai so kike girma ya fadi? Zan dai
gwada
sanar da itan." Haka mukayi sallama da
Bahijja,kowannenmu ya bawa dan uwansa
shawara
na gari,na bar gidan na kama hanyar komawa. A
zahirin gaskiya ba wannan nayi niyyar sanar da
Bahijja ba,naso nayi mata batun
Murja ko zata bani
shawara sai kuma naga kamar hakan bai dace
ba,na
bar abun a zuciyata,ina mai addu'ar kada Allah
Yasa
ta qara kirana. Tayi lamo akan cinyar yayarta
hawaye na zuba. A
hankali Abida ta ja tsaki"Wai meye haka Zahra?
Meke
damunki ne? Tun zuwanki baki da sukuni kuma
nayi
magana kin kama kuka anyi wani abune?" Zahra
ta
dago kanta ta share hawaye,tayaya ma za'ace ta
sanar da Abida sirrin zuciyarta alhalin itama tana
cikin masu kiyayya ga yayan
nata? Gaskiya bamai
yiwuwa bane,ta wayance"Nifa anti cikina ke ciwo
tun
zuwana." Abida ji tayi kamar ta bugeta,ta ja tsaki
gami da mikewa"Allah Ya sauwake maki
Zahra,don
kina ciwon ciki shikenan sai ki zauna kina hawaye
kamar wata yarinya qarama? Tayi hanyar daki
tana mita"Meyasa kika zo kinsan
baki da lafiya toh?"
Zahra dai bata ce uffan ba ta jingina kanta jikin
kujera
a hankali tana sharar hawaye. Inda ace akwai
wanda
zata iya sanarwa damuwarta bai wuce
aminiyartata
ba amma babu dama tunda ta zama kishiyarta.
Ina
ma tun farko ta sanar da Yaya Ahmed sirrin
zuciyarta? Inama ta sanar dashi
dalilinta na qin kula
kowanne saurayi,ga samari da yawa masu
kaunarta
ciki har da 'yan uwan Abba dana Antinta,amma
bata
taba amincewa da ko daya a cikinsu ba saboda
zuciyarta Yaya Ahmed kadai take so. Ta lumshe
ido,a
dalilinsa ta baro gidan saboda ganinsa da takeyi
na qara hura mata wutar
kaunarsa. 'Dan Abida ne,khalil
ya katsemata tunani"Lah anti zahra yaushe kika
zo?"
Ta dago kanta da sauri tana mai share
hawayenta ta
riko hannun yaron tana murmushi ta shafi
kansa"Khalil yanzu na iso,ina ihsan?" Ya nuna
hanyar waje"Tana waje tare da daddy." Ta gyada
kai,gami da jan majina ta bude
jakarta ta dauko
alawar bigbom guda biyu ta miqa masa"oya gashi
dauki daya ka kai mata daya." Da gudu ya fice
yana
murna,anti abida ta fito rike da magani a
hannunta,gashi ki sha. Zahra ta karba domin dai
da
gasken cikinta na dan ciwo,ta sha da ruwa. Abida
tace"Wai yaya usman ya koma
ko? Shine ma ko yazo
gidana?" Zahra ta dan murmusa"Ai kuwa naji
yana
cewa zai zo watakila dai wani abun ya hanashi."
Anti
abida ta kyabe baki"Shi dai ya sani." Sai la'asar
Zahra
ta baro gidan zuciyarta babu laifi ta dan saukaka
domin kuwa Abida badai hira ba,tana da mutunci
idan taso matsalarta dai
kwadayi. Toh anan kuma sia
muce uwartasu suka gado.**********
**********************************A ranar
gaba daya ban yarda mun hadu da Badamasi ba
domin gani nakeyi kamar fuskata kadai zai kalla
ya
gane wani abu. Da yamma ina zaune akan benci
wajen Baba maigadi,naji qarar
shigowar saqo
wayata"Ina neman gafara idan har na kasance
mai
takura maka,banji dadin kashe wayar da kayi ba
a
jiya domin hakan ba qaramin shiga hakkina yayi
ba.
Na kasa runtsawa,ka barni da kokwanto,nidai na
gama aminta babu namijin da ba zaiso
kasancewa dani ba,ganin yanda ka
nunamin yasa na soma
kokwanto akan hakan. Kai din namiji ne alfaharin
kowacce mace Ahmed,yanzu na fara sonka. Kada
kayi qoqarin sanar da abokinka da kaina wataran
zan furta masa,ko banza shi yayi sanadin
haduwata
dakai. I love you." Na maimaita yafi sau biyar
gabana ya cigaba da faduwa,na
murza idanuwa na qara
dubawa sosai. Wai anya murja bata shaye
shaye,kasa
zama nayi na mike da sauri nayi cikin gida har
muna
kusan karo da Zahra. Ta bani hanya,ina rike da
waya
na sanya a kunne kamar wanda ke amsa kira
saboda bana son ta ga yanayin da nake dauke
dashi na rudani. Zahra ta bishi da
kallo,wani daci ya qaru a
zuciyarta,bata tantama Hafsa ya kira. Da sauri ta
shige
gidan tana mai kokarin hadiye kwalla.


Zaharaddeen  Shomar
Whatsapp  08168575100


Amadu 1 page 4
Posted by ANaM Dorayi on 03:31 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
Zaman nayi gefen gado,kirjina har rawa yakeyi
saboda zafi. Me zan yiwa Murja ne? Dabara ta
fadomin
kawai sai na kirata,ita kuwa suna tare da 'yan
uwanta ana hira da sauri ta mike tayi gefe guda.
Ta
daga"Hello." Rai a bace na soma magana"Wai
murja
wane irin rashin hankaline kike shirin aikatawa?
Ban taba ganin mara tunani kamar
ki ba. Ina warning
dinki,ki fita daga harkata tun kafin na dauki
kwakkwaran mataki akanka,nonsense!" A
tunanina
furucina zai tsoratar da ita sai ma naji tayi dariya
kadan"Ahmed kenan,ni wallahi bazan iya fushi da
duk wani abu da zakayimini ba,nice fa da kaina
nace ina sonka,toh ai duk abunda
zakayimin ni din mai iya
jure wa ce. Akanka na yarda bani da hankali,na
yarda ni mahaukaciya ce. Wallahi Ahmed ina
tsananin bukatar ganinka,ka tallafawa mai
kaunarka
mu hadu batare da sanin abokinka ba,na daukar
maka alqawarin faranta maka. Hakan ne kadai
zai sa na rabu dakai,sannan na qi
sanar da abokinka
dangartakarmu,zai kasance sirri tsakanina
dakai,kaji?" Innalillahi,ai gaba daya sai na rasa
abun
cewa ji nake inama kusa nake da ita na dauketa
da
mari,tsawa da daka mata"Shut up!" " Ahmed
kenan,wai kai bakasan a komai ma muryarka
dadi gareta ba. Toh wallahi Ahmed
kada ka wahalar da
kanka idan kana so na rabu dakai kawai ka yarda
da
soyayyata,muyi ta koda a boye ne,idan ka
amince ka
kira ka sanar dani zan baka address na inda
zamu
hadu. Sai anjima." Ta kashe wayar ta barni rike
da
waya ciki matsanancin fargaba,kai ban qara
rikicewa ba saida na dago kaina naga
Badamasi tsaye a jikin
kofa.****************************************
*******Fargabarta ta qaru da irin kallon da take
binta dashi,ta hadiye wahalallen miyau ta rasa
amsar
da zata bawa antin nata. "Wai Zahra yaushe kika
zama haka? Yaushe kika soma boyemini
damuwarki? Ki fito ki sanar dani,idan ma
ciki ne dake
mu dauki mataki,saboda wannan ramar taki da
yawon ciwukan nan ban yarda dasu ba." Zahra ta
zaro ido a firgice tana mai dafe kirji"Anti wallahi
a'a,kawai dai kwana biyu banajin dadin jikina
ne."
Antin ta tabe baki"Ki kiyaye dai da samarin
zamanin nan don bana tantama akan
saurayi kike wannan
laulayin." Zahra dai ta lallaba tayi dakinta domin
ta ji
da abunda ya dameta. Gumi ya karyomin,shi
kuwa ido ya zubamin. Na
rasa gane irin kallon da yake min,ji nake kamar
na
saki fitsari. Ga mamakina sai naga yayi murmushi
yace"Wai kai da wa kake waya naji ana kiran shut
up?" Ya qarashe yana zama gefen gado. Na
lumshe
ido gami da sakin ajiyar zuciya ganin bai ji sauran
zancen ba,nima na juyo bayan
na chanja yanayin
fuskata zuwa murmushi cikin rawar murya
nace"Uhm..um.m..Bukar ne dan rainin
hankali,shareshi kawai,ya na ganka yanzu da
magriba?" Ya dan tabe baki gami da daga
kafada"Gobe Daddy yace naje naga abokin nan
nasa akan batun aikina amma
wallahi banason
zuwa,wallahi abokina sai nake jin babu dadi ace
zan
fara aiki kai kuma kana zaune hakanan." Na saki
ajiyar zuciya na dafa kafadarsa ina dan
murmushi"Haba abokina,ka bar fadin haka ai sai
kasa zuciyata ta karye,ban fidda rai ba
Badamasi,Allah zai dafa min please kada ka
damu.
Allah Ya taimakeka,Yasa ka fara a sa'a."
Badamasi
cike da tausayi yace"Haba Ahmed nace ka bani
takardunka na nunawa daddy amma...." Na daga
masa hannu"Daina batun nan please,kaidai tunda
nace maka haka kada ka damu,nagode da
kyakkyawar niyyarka." Badamasi yayi
shiru baice
komai ba domin har ya rasa dalilin da yasa
ahmed
baya kaunar taimakonsa a duk sanda yayi
yunkurin
yi. Na katseshi"Muje muyi sallah ko?" Ya mike
yana
dan qaramin tsaki"Kaidai wani sa'in kana da
matsala,sai ka dunga sanyawa nayi tunanin
kamar bamu zama daya ba." Nayi 'yar
dariya kawai bance
komai ba. A hakan ma da bana neman taimakon
Badamasi da iyayensa akan lamurana ya aka
qare da
munafukai da 'yan sa ido,ballanatana kuma aji
na
samu aiki daga gurinsu? Hakan ba mai yiwuwa
bane,a daidai lokacin da muke shirin alwala
wayata tayi qarar shigowar saqo,na
duba daga murja ne da
sauri na kashe wayar gaba daya na dubi
Badamasi
yana wanke fuska hakan ya tabbatar min bai gani
ba. Na sauke ajiyar zuciya,Mata wani sa'in
shu'umai
ne. Yanzu ina zaman zamana yarinyar nan tana
neman sanyani cikin matsala. Ko bayan tafiyar
Badamasi ina zaune a daki Zahra
ta kwankwasa min.
Na mike na fito ina mai amsa sallamarta. Bata
dubeni
ba hakanan fuskar babu wannan murmushin
data
saba yi a duk yayinda mukayi arba ta miqo min
kwanon tuwona"Gashi." Na karba ina mai
dubanta,ta qara da cewa"Abba yace kazo yana
son ganinka." Nace"Toh." Zata tafi
nayi saurin kiran
sunanta. Ba tare data juyo ba ta tsaya,nayi qasa
da
murya saboda kada wani ya ji"Haba Zahra me
nayi
kika chanjamin haka? Fadamin mana." Ta runtse
ido,idan da ace Ahmed yasan yanda zuciyarta ke
dawainiya da sonsa da bai tsayar da ita har yayi
yunkurin tausasa harshe wajen yi
mata magana.
Hawaye taji sun zubo babu zato. Ba tare da kula
da
yanayin data shiga ba na cigaba"Lovely sister ya
kikayi shiru?" Murya na rawa tace"Babu komai
yaya
Ahmed kwana biyun nan bana jin dadi." Cike da
tausayi nace"Ya salam,meke damunki?" Ya isheta
hakanan kawai sai tace"Ciwon
ciki." "Allah Ya baki
lafiya,amma ki daure ki dawomin da walwalarki
please." Kawai sai ta tsinci kanta da
murmusawa,nayi
dariya yauwa my sister ko kefa." Ta girgiza kai
kawai
ta yi ciki,na juya nima na shiga dakin. Ta juyo ta
bi
bayanshi da kallo,sannan ta share hawayenta
tana murmushi"I love you." Ta fada
a hankali sannan ta
juya da sauri ta shiga ciki zuciyarta na qara sanyi
ba
kamar da farko ba. Kai tsaye falon Abba na shiga
da sallama,yana
zaune shi kadai ne. Domin indai akayi magriba
toh
Abba baya son mace ta zauna domin lokaci ne da
yake nafilfilunsa,yanzun ma yana shirin tadawa
na
shiga da sallama har na juya zan koma
yace"Shigo
Amadu,zauna kayi jirana."Na samu gefe na
zauna,har dai ya idar da sallarsa yayi
addu'oinsa
sannan ya dubeni"Amadu kajini kuma shiru ko?
Abubuwane sukayimin yawa shiyasa.Dama inaso
nayi maka maganar aure,ka kai munzalin da ya
kamata ace kaima kana da aure. Munyi magana
da
yaya murtala,yayi min magana akan hakan nima
na nuna masa amincewata da
batunsa. Yanzu dai daga
yau zuwa 'yan watanni biyu ya kamata ka nemi
matar aure,kada ka damu da batun sana'a da
muhalli,insha Allahu wannan ba matsala bace.
Fatana
dai ka samu macen arziki ta gari wacce zata
daraja
iyayenka,ta bawa 'ya'yanku tarbiyya ta gari. Allah
Yayi maka albarka,Ya jiqan
iyayenka." Gabana ya fadi
sannan kuma wani irin farin ciki ne ya cikani. Ji
nake
kamar bayanin nan na Abba a mafarki ne,lallai
Allah
mai yanda Yaso ne. Na qara sunkui da
kaina"Amin
Abba,insha Allahu." Yayi murmushi
yace"Madallah,k
ana iya tafiya." Na mike bayan na yiwa Abba
godiya na fito. Caraf muka hada ido
da inna wacce ke shirin
shigewa daki,kallona tayi ba tare data ce komai
ba,na sanya kai na fita daga gidan. Koda na isa
daki
sai na mance duk wani bacin rai dake
gabana,wani
farin ciki ne ya mamayeni,ashe dai gobe akwai
zuwa
gidan Anti Aisha,zatayi farin cikin jin wannan
labari. Qarar da wayata ta qara yi ne
yasa na farga. Na
rarumo ta na bud'a,gaba daya dai daga murja ne
dauke da kalamai na nuna tsantsan bege,tsaki na
ja
na gogesu ina fadin"Shashasha kawai." Sai na
duba
whatapp dina naga wani saqon daga
masoyiyartawa,nan na shantake na shiga maida
mata amsa. Ya zama dole na
sanar da Hafsa sirrin
zuciyata tun kafin wani ya riga ni. Don haka na
quduri a niyyar sanar da ita. Nace"Beauty yaushe
zan
zo naga qanin nan nawa da ake yawan bani
labarinsa?" Hafsa ta sanyo smiley na
dariya,sannan
tace"Dagaske yayana zaka zo kaga noor? Toh
yayanmu idan kaga noor shikenan ni
ba zaka ganni
ba?" Nayi murmushi"Beauty kenan,ai saboda ke
zanzo,akwai magana a bakina." Hafsa ta danyi
ihu
kadan na murna ita kadai akan gado sannan
tace"Ina marhabun dakai." Nace"Nasan da
hakan,zan zo naga beautyna." "Toh yayanmu
ranar yaushe zaka zo?" Shigowar
wannan saqon nata yayi
daidai da shigowar saqon murja ta
whatapp,domin
nidai banyi saving lambar ba amma ina tuni na
rike
lambarta,gabana ya fadi shikenan fa tsiyar
whatapp,babu dama mutum yayi saving lambarka
in
har yana whatapp sai kayi appearing. Mtsw,na ja
tsaki,ban ko kulata ba na bawa
Hafsat amsa"Idan
nace gobe ban takura ba?" Cab! Toh ai ita haka
take
so,don haka tace"Yayanmu baka takura ba ko
kadan." Naji dadi nace"Toh shikenan,ina jiran
address." Kafin tayi reply ne na duba saqon
murja,smiley ne na dan bakin nan mai alamun
kiss,sai kuma ta qara da
cewa"Sweety ashe kana
whatapp." Ya zama dole na dauki mataki akan
murja
wallahi,na ayyana hakan a raina. Har zanyi
blocking
dinta sai kuma na fasa na aikata da reply"Ke
shashasha wacce bata san abunda take ba,ki fita
harkata tun kafin na dauki tsatstsauran mataki
akanki. Ke idan ana soyayya ma
waye zai soki?
Banza wacce batasan abunda take ba." Na aika
mata
sannan na koma ga masoyiyata na kwafi address
din
data aikomin tare da fadin"Sai kin gani" Saqon
murja
ya shigo"Hm,sweety kenan. Baka jin magana ko
kadan wallahi,na fadamaka nifa bazanyi fushi da
abunda nakeso ba koda zaka
tsireni amma kai gani
kake ci min mutunci shine ribar da zakaci don mu
rabu,toh ko kusa wallahi,na sanar dakai ka yarda
kawai da haduwarmu hakan zaisa na janye
qudurina
na sanar da cewa abokinka kai nake so ba shi ba.
Kafi kowa sanin Badamasi mai shiga wani hali ne
idan babu ni tare dashi,kai kasan
ai irin son da yake
mini. Bana son hadaku fada da amininka shiyasa
nakeso muyi abun mu a sirrance Sweety."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un" Itace kalmar
dana hau maimaitawa,gumi na shiga yi. Sai ga
sallamar Badamasi a whatapp,gabana ya fadi,na
amsa ya sanyo smiley mai nuna kuka
yace"Abokina
tayani jimami,na yiwa murja magana shiru,na
kira
wayarta tana ringing ta qi dauka,tayi fushi dani."
Toh fa! Ai sai na gigice da sauri
na tambaya"Me ya
hadaku toh?" Amsar da ya bani ta kusa sanyani
mutuwar zaune" Cewa tayi ta haqura dani wai
kuma
na nemi wata ba ita ba domin taji labarin ina
kula
wasu bayan ita,please taimakanni kayi mata
magana
wallahi har kaina ya soma ciwo hankalina ya
tashi,I love her with all my hrt,help
me friend." Ya sanya
smiley na kuka. Kwalla ta cikamin ido,ni Amadu
naga
abunda yafi qarfina,sai ga tanan ta qara yin
magana,"Hahahaha! Abokinka ya labarta maka
abunda ya faru sweety?" Haushi ya
isheni,"Meyasa
zakiyi masa haka? Wai murja meke yawo a
kwanyarki? Ki nutsu ki dawo hayyacinki
wannan
Mugun Butulcine. Ina hadaki da Allah ki bari."
"Hmm,sweety kenan,dama nayi hakan don na
nuna
maka ni din ni ce farin cikin amininka,wallahi
Ahmed
idan har na rabu da Badamasi ban kyauta masa
ba ni
kaina nasan da hakan,mafita daya ce ka ceci
rayuwata ka amince dani da bukatata
ka bani hadin
kai ni kuma nayi alqawarin farantawa amininka
bisa
qarqashin inuwar aure." Wayyo ni Ahmed,na
shiga
tsaka mai wuya! Ya zanyi da wannan baqin
al'amarin? Ta qara turowa"Kwantar da hankalinka
sweety,nayi masa magana. Bar batunsa zan
kwantar da hankalinsa,sweety ina
muradin ganinka aikomin
hotunanka,wadanda nake dasu sun zamemin jiki
ina
bukatar sabbi." Wayar na kashe don bakin ciki na
cilla kan gado,ina mai dafe kaina"Ya zanyi ne?
Menene mafita anan? Allahu ka kawomin
dauki,na
mike na fita jiki babu laka domin gabatar da
sallar isha'i. Koda na idar na jima
zaune cikin masallaci dafe
da kaina ina mai tunane tunane,baba maigadi ya
dubeni"Amadu,Amadu." Firgigit nayi ina dubansa
da
jajayen idanuwa,ya bude baki"Subhanallah,meke
samunka ne?" Na dan sauke ajiyar zuciya
nace"Bakomai Baba,kaine ke ciwo ne."
"Assha,shine zaka zauna haka cikin
masallaci Amadu? Tashi muje."
Na mike a hankali ji nake kamar na zube a
wajen,damuwa tayimin yawa har na rasa wanda
zan
dauka nayi tunani akai. Muna fitowa ya
dubeni"Kana
da maganin ciwon kan?" Na gyada kai"Ina dashi
baba,yanzu zan je na sha." Yace"Toh Allah Ya
sauwake,a samu ayi bacci
Amadu,Allah Ya baka
lafiya." "Amin baba nagode." "Bakomai." Na shige
gida shima yayi gidan da yake aiki,ina kaunar
tsohon
domin yana kulawa dani kamar 'dan daya
haifa,ya
damu da kowace damuwata. Na bi umarninsa na
sha
magani,na kwanta amma fa ba don nayi baccin
ba domin a lokacin idanuna sun
bushe
kyamas.***********************
***********Washe gari wajen karfe goma sha
biyun
rana,lokacin munyi waya da Badamasi ya sanar
dani
yana can wajen abokin daddynsa kamar dai
yanda
ya sanar dani zaije batun aikinsa. Nima na fito na
nufi gidan Anti Aisha,wayata tayi
qarar shigowar saqo
daga whatapp,nan ne na tuna da batun
Murja,gabana ya fadi,a tsorace na ciro sai naga
ashe
mutuniyartawa ce ke gaisheni,nima na bata amsa
da
tambayar lafiyarta. Daga nan na rufe babin chat
da
ita,kamar a film na hangi hotona maqale a jikin
profile din Murja,a status kuma ta
qara da cewa"My
love for you is real!" Na gigice,na duba dakyau ni
din
ne dai jikin profile pic dinta,na duba Badamasi
rabonsa da whatapp tun jiya da daddare bayan
mun
yi magana,na gigice,gashi itama bata online,dole
na
kirata a waya kenan,ya zama dole ta cire. Murja
bala'i ce,tana neman hanani
sukuni. Cikina har wani kugi
yakeyi. Na kira wayarta yayi ta ringing bata dauka
ba,na
qara rudewa. Ina shirin kuma kira sai ga kiranta.
"Hello sweetyna,kayi hakuri kaji ban dauka
ba,wallahi banison ka wahalar da kanka da
aljihunka wajen kirana nafiso ni na kiraka. Kana
lafiya?" Murya a shaqe nace"Ina mai roqonki ki
fidda hotona daga profile dinki,wai
me kike nema dani
haka?" Tayi murmushi mai sauti"Uhm sweetyna
kenan,kayi hakuri ban fiye son maimaici ba. Mun
riga
munyi magana dakai na sanar maka da buqatana
don me a kodayaushe kake neman dawo da
hannun
agogo baya? Kawai ka amince mu hadu wallahi
zan janye komai." Na runtse ido
ina mai matse yatsuna
waje daya,na datse haqorana,sannan na shiga
nuna
yatsa kamar tana gabana"Kiyimin shiru,na gaji da
jin
wadannan zantukan naki marasa ma'ana,wallahi
ki
kiyaye. Kuma ina mai tabbatar maki idan baki
cire
hotona ba sai na bata maki rai!" Ta tare
shi"Banason bacin ranka sweetyna zan
cire yanzu wallahi,amma
don Allah sweetyna ka tausayamin ina cikin wani
hali,wallahi idan baka zo ba zaka ganni a
gidanku."
"Allah Ya isa murja!" Furucin da nayi kenan a
zuciyata,idanuna suka kada,masifar nan ta soma
isata,anya bazan sanar da Badamasi ba? Toh
amma ta yaya zai amince da haka
din? Yanda murja ta iya
shirya magana kwarai zata iya tsarashi,ya zanyi
ne?
Sai dabara ta fadomini da sauri na tare
ta"Shikenan!
Naji zan zo! A ina zamu hadu? Ki fada,ko ma a
ina ne
ki sanar dani murja! Amma sai kinyi alqawarin
zaki
cika alqawari! Zaki rabu dani daga lokacin." Murja
dake kwance jikin wani
saurayinta daga ita sai
wando iya gwuiwa da 'yar vest ta mike ta nufi
jikin
windon dakin tana dariyar jin dadi,ta kashe ido
tace"Na amince sweety idan har kaima zaka
yarda da
bukatana,gobe wajen qarfe biyar mu hadu anan
zoo
road,idan kazo daidai Sahad store kayimin waya
zan maka kwatancen inda zaka
sameni. Sai anjima" Ta
kashe wayar,ta juyo tana dariya har da 'dan
tsallenta.
Saurayin yayi murmushi lokacin da yake kunna
karen sigarinsa"Wa kuma aka samu? Manyan gari
ko
qananan kwari?" Tayi wani murmushi ta qaraso
tana
mai bin umarnin Ahmed wato chanja porfile
pic,sannan ta zauna kusa dashi"Kasan
bigi sai
bigi,babban goro sai magogin qarfe! Ina ganin biri
bazan ci dila ba." Yayi wani dariyarsu ta 'yan
duniya
yana mai jinjina kai a lokaci guda kuma yana
buso
mata hayakin sigarin a fuska,ta hau yamutse
fuska
tana tari ta mike ta dubeshi gami da jan qaramin
tsaki sannan tayi hanyar toilet
tana cewa"Na sha
fadamaka ban fiye son hayakin nan
ba."*****************************************
*******Gama wayarmu na sauke ajiyar zuciya
ina
mai share gumi,"Allah Kayimin tsari da sabonka."
Na
fada a fili,sannan na kashe wayar gudun kada
muna tare da Antina,murja ta qara
kirana. Kallona kawai takeyi,duk qoqarina na
boye
damuwar dake dauke akan fuskata na
gagara,tace"Wai Ahmed meya faru na ganka a
birkice?" Nayi qoqarin saita kaina,nayi murmushin
yaqe ina mai ajiyar zuciya"Me kika gani anti?
Babu
komai dama...." Na zayyane mata yanda mukayi
da Abba na qara da cewa"Toh ni yanzu anti
tsoron
matansa nakeyi wallahi.." Ta dakatar dani tana
dariyar farin ciki"Kai kuwa Ahmed wannan ai
abun
murna ne,sai kayi wa Allah godiya. Babu abunda
matansa zasu iya yi insha Allahu,amma Alhaji ya
burgeni,wallahi sai yanzu naji sanyi,amma tun
sa'adda mukayi zancen nan da kai bana cikin
kwanciyar hankali,nema nake Allah Ya horemin
na
baka ka ja jari kayi aurenka,kai amma naji
dadi,kenan dana usmanu za'a hada?" Na girgiza
kaina"Kayya bana tunanin hakan,domin su nasu
ai
yazo daf saboda wata daya da kwanaki ya rage
musu,ni kuwa da ko matar ban gama nema ba
ina ni
ina aure yanzun?" Tayi dariya tana rike baki"Ba
shakka,ah lallai Alhaji yayi magana mai
dadi,rannan
koda kawunka na brigade yazo saida ya qara
tuhumata akan batunka yana cewa kwana biyu
ma
baka leqa can brigade din ba,nace masa komai
lokacine,insha Allahu kana kan hanya,batun zuwa
kuma nace mai yiwuwa dama ne baka samu ba
amma ai kai kam akwai qoqarin sada zumunci."
Na
shafi sumar kaina ina murmushi a sanyaye
nace"Gaskiyane,kwana biyun nan ne bani da
nutsuwa amma Abba ya sanyaya min raina,insha
Allahu zan leqa ko zuwa jibi ne." Tayi
dariya"Yauwa
ko kaifa." Nayi murmushi,nidai kam nafiso naji da
damuwata,domin bana wani dokin maganar Abba
a
yanzu,Murja tana neman kawomin matsala. Haka
na
zauna a gidan har saida ta gama shinkafa da
wake
da salad ta zubamin,itama ta diba,muna zaune
muna ci mijinta ya shigo. Shima ya zauna muka
dasa
hira,saida aka kira Azhar sannan nayi mata
sallama
na fito tare da maigidanta muka nufi
masallaci.*****
******************************
*********Yanzun ma tana zaune kan gado ta
qudundune waje daya tana kuka,uwarta ta shigo
a fusace ta janyota ta miqar tsaye"Don qaniyarki
ki
fadamin matsalarki tun kafin na lakada maki
tsinannan duka wallahi." Zahra ta share
hawayenta
tana 'dan dariya wanda kana gani kasan ta dole
ce ta
shiga girgiza kai"Ni anti bani da matsala..." Ta
daga
mata hannu"Idan baki daina min qarya ba sai na
daukeki da mari wallahi,ki sanar dani matsalarki,
(Ta
sanyaya murya) ni mahaifiyarki ce Zahra,idan
baki
fadamin ba wa zaki fadawa? Usman ya sha
fadamin
da daddare kuka kikeyi,ki sanar dani ko meye
shi,ke
ko da wani kikeso ni din mai sanin yanda za'a
shawo
kansa ne." Kwarai furucin karshen da anti
amarya
tayi ya bawa zahra mamaki,ya akayi ta gane
akan
namiji ne? Amma na bazata so Ahmed ya aureta
a
dole ba face da son ransa,ta daure tace"Anti
wallahi
Yaya Ahmed nakeso,shi kuma ashe....." Tas!! Taji
mari
a kuncinta,kafin tayi qoqarin kallon antin nata ta
hau
jibgarta tana fadin"Gwara na kasheki da dai naga
wannan abun bakin cikin." Zahra ihu take tana
bata
hakuri,toh itama dai ganin Zahra na ihun kuma
bataso uwargidan nata tasan meke faruwa yasa
ta
dakata tana huci kamar ta shaqeta takeji,tayi
kwafa"Yanzu ke banda iskanci ki rasa wanda zaki
yi
laulayin so akansa sai wannan matsiyacin wanda
bai ajiye ba bai bayar ajiya ba? Ta rike
kunnenta,Zahra
tayi 'yar qara tana mai cigaba da
sheshsheqa"Ashe
ke soyayya kukeyi dashi bansani ba? Toh wallahi
bada ni ba,nafi qarfin zama sarakuwar 'dan
talaka,talakan ma tsinanne irin Ahmed,toh tun
wuri
ki bar wannan bahagon tunanin tun kafin na
kasheki na huta. Shashasha wacce batasan
abunda
takeyi ba." Fuu ta bar dakin,zahra ta fashe da
kuka
dama tana mai cike da fargabar irin daukar da
anti
zatayi wa lamarin nan. Batajin zata daina kaunar
Yaya
Ahmed,ta saba da sonsa tun batasan manufar so
ba,meyasa zata daina tunaninsa? A gefe guda
kuma tana tausayin kanta yanda ta fada cikin
kogin son
wanda bai san ma tanayi ba.


Zaharaddeen  Shomar
Whatsapp   08168575100Amadu 1 page 5
Posted by ANaM Dorayi on 04:07 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
Washegari misalin karfe biyar,kamar yanda
muka
shirya da murja. Na shirya,na fito gaba daya a
gigice
nake. A kofa muka ci karo da Zahra,ta dubeni
daga
sama har qasa,ta danyi murmushi duk ta dan
rame"Yayana sai ina haka?" Na danyi murmushin
nima da wasa na ja karan hancinta"Zance zani
ko zaki rakani?" Sai naga ta sauya fuska tace"A'a
Yayana,a gaidamin antin tawa." Nayi 'yar dariya
ba
tare da nace komai ba na fito. A raina kuwa ina
fadin"Inama ace haka dinne hira da masoyiyata
zanje ba wannan tashin hankalin ba." Titi na fita
na
sami adaidaita na hau,na sanar dashi inda zai
kaini. Muna isa na sallameshi sannan na tsaya
wajen store
din na kirata. Ringing daya biyu bata dauka
ba,har ta
katse,na ja tsaki tunawa da nayi da abunda tace.
Sai
kuma ga kiran nata,na dauka a fusace nace"Gani
kina ina?" Ta danyi dariya"Wow sweetyna,kada ka
damu bari na zo da kaina." Ta kashe wayar,na ja
tsaki na tsaya gabana na faduwa,ina maimaita
sunan
Allah a raina. Ba'a fi minti goma ba sai ga mota
camry
baqa wuluk ta tsaya a gabana,kallo daya na yiwa
motar na dauke kaina,daidai saitina take,aka
zuge
glass gami da yin hon,na juyo na dubi motar.
Murmushi ta sakar min,wanda a wajen wasu
yake
da ban sha'awa amma a gareni tamkar an
zubamin
garwashin wuta ne. Ta sanyo hannunta ta
budemin
gidan gaba fuska a daure na bude na shiga,ta
kawo
hannu zata rufe na dakatar da ita ta hanyar daga
mata hannu"Zan rufe." Ta janye hannunta tana
murmushi har lokacin ni din take kallo,na rufe
motar,na dubeta rai a bace kafin nayi magana ta
rigani"Kada ka damu,koma meye zamu tattauna
idan
mun isa ga muhalli." Daga haka tayi ribas ta juya
muka shiga kwanar kusa da Sahad. Bamuyi
doguwar tafiya ba tayi kwana,a daidai wani
falthouse tayi hon,maigadi ya bude muka shiga.
Gabana ya tsananta bugawa ina ambaton
Ubangijina.
Ba zato naji muryarta kusa da kunnena"Fito
mana
sweetyna." A fusace na juyo,sai kuma muka
kusan
karo,na ja tsaki na juya na fito gami da buga
kofar.
Raina idan yayi dubu toh ya baci,ji nake inda ina
da
dama da sai na babballata. Falo ne dan
qarami,sai dinning area daga gefe
da
kayan kallo,sai kuma kofunan dakuna guda
uku,ga
daya can daga wajen dinning area wanda bana
tantama kicin ne. Na zauna fuska a hade,ta
kwala
kira"Ladi! Ladi!" Da sauri wata tsohuwa ta fito
daga
daya daga cikin kofofin nan. Ta rusuna cike da
ladabi tace"Na'am uwar dakina." Murja ta zauna
a kan
kujera kusa dani ta dora qafa daya kan daya"A
kawo masa ruwa da lemo." Ladi a ladabce ta
gaisheni,na amsa mata. Bayan fitar ta na dubi
murja
fuska a daure"Malama ki hanzarta sanar dani
abunda
kike bid'a ba zama ya kawoni ba ina da
abubuwan yi." Tayi murmushi ta taso bayan ta
sauke mayafinta
wanda ba wani na kirki bane ta ajiyeshi gefenta
na
dauke kaina daga kallonta domin wani shegen
dinkin atamfa ne a jikinta babu tsari. Ta durkusa
a
gabana bayan ta dafe hannunta gefe da gefen
kujerar da nake kai. Na kauda idona da sauri na
mike tsaye,itama ta mike. Na nunata da yatsa
zanyi
magana sai mukaji sallamar Ladi hakan yasa na
fasa
na juya baya raina a bace. Ta dire kayan
hannunta
sannan ta mike ta bar falon. Kafin na juyo naji
hannun murja a kafadata,bansan sa'adda zuciya
ta
kwasheni na juyo na dauketa da mari ba.
Idanuwana sun sauya launi na nunota da
yatsa"Ina
mai gargadinki kada ki kuma gangancin tabani ko
kuma ki raina kanki wallahi!" "Kut!" Shine furucin
da
Murja tayi,na zuba mata ido ina jiran ganin
abunda ta
taka,shiru ya biyo baya sai kuma na dago ta
kalleni
fuskarta dauke da ruwan hawaye,sai ta zube ta
qanqame kafafuna"Haba Ahmed,ina laifin wanda
ya
nuna yana kaunarka? Meyasa kake nema kayimin
haka? Wallahi Ahmed kaunace ta sanya har na
nemeka,don Allah ka tausayamin Ahmed." Ta
mike
tana mai qoqarin riko hannuna,nace"Dakata
murja!
Ke meyasa bakya aiki da tunani? Haba murja
wallahi kin bani mamaki,abokina bai kamaci
wannan
butulcin daga gareki ba! Ya kamata ace ki cika
alqawarin da kika dauka kada ki ci amanarsa.
Toh
bari na fadamaki na gane buqatar da kike ikrarin
na
biya maki,hakan ba mai yiwuwa bane ko
kusa,kuma
duk randa kika qara gangancin yin wani abu da
zaki batamin zumunta da aminina wallahi zaki
raina kanki
sosai. Bana yiwa mutum mai kyan zuciya irin
Badamasi auren mace watsatstsiya irinki. Tur da
mata
masu hali irin naki!" Daga haka na fice na nufi
qofa.
Saidai jin da nayi qofar a qulle yasa jikina ya
saki,innalillahi! Na juyo ina kallonta,tana zaune
hannun kujera ta dora qafa daya kan daya tana
shan
lemon kwali tana bina da wani murmushi fuskar
har
lokacin dauke take da hawaye,a hankali ta shafi
kumatunta ta dagamin gira"Sweetyna." Ta
ambata a
shaqiyance. Ta taso tana rangwada ta iso gabana
ta
tsaya,kirjina har dagawa yake don tsananin
bugawa,a hankali ta kai hannunta fuskana,na
kauda
fuska gefe cike da tsananin bacin rai,ta sanya
yatsanta manuni ta shafi gefen fuska zuwa
wuyana,na rike hannunta gam,tayi dariya mai
hade da kukan iskanci"Please sweetyna kada ka
karyamin
hannuna,bai kamata ace rikonka na farko a
gareni
ba ya kasance na mugunta ne,amma bakomai
nayi
maka uzuri bana tunanin kasan yanda nakeji. Na
yarfar da hannun nata tayi murmushi ta girgiza
kai
sannan ta juya tana karairaya kamar zata
balle."Malama ki budemin kofa kafin qarfina ya
kwatar min." Ta daga gira ta nuna kirjinta"Koda
anan
mukullin yake?" Na runtse ido ina mai kauda
kaina,ban taba cin karo da tantariyar 'yar bariki
ba
sai a yau. Wayata tayi qara,na ciro ganin sunan
Badamasi yasa gabana yayi matsanancin
bugawa. Na dubeta tayi murmushi tana mai nuna
min wayar tawa
da ido,na maida kallona ga wayar,a hankali
nace"Ki
rufamin asiri kiyi shiru." Ta tabe baki ta yarfa
hannu
tana mai girgiza kanta. Gabana na faduwa na
dauka,"Hello,dan uwa ina ka shiga ne? Nazo da
labarai amma baka nan?" Na dago na dubeta
hankalinta kwance tana kallona,murya na rawa
nace"Um.m.m..kai dai bari,nazo nan Brigade
ganin su
Kawu,amma zuwa bayan magriba zan shigo gidan
naku." Yayi dariya"Ashe yau za'ayi ruwa da
qanqara,bari na hanzarta sanar da mami tana da
babban baqo." Muka danyi dariya na katse wayar
da sauri,na dubeta ina miqa hannu"Bani
mukulli!"
Tace"Zan baka Ahmed,amince da buqata kawai."
Innalillahi! Dabara tazo min"Haba murja kinga dai
yanzu ina sauri ne,ki amince na tafi yanzu nayi
maki
alqawarin dawowa gobe insha Allahu." Ta zaro
ido
cike da farin ciki"Dagaske sweetyna?" Nayi
murmushi"Alqawari ne,bana barinsa ba tare da
na
cikashi ba." Ta matso daf dani sai ji nayi ta
rungumeni,da sauri na fisgeta nayi baya"Haba
murja,ki bari wannan duk mai afkuwa ne idan na
dawo gobe,for now kinga munyi dake badamasi
ba
zaiji komai ba kuma kinga yana can yana jirana
yanzu idan na dade zai sanya min alamar
tambaya."
Ta jinjina kai"Haba sweetyna ko kaifa? Please
kada
ka qi zuwa idan ba haka ba wallahi Ahmed zaka
ganni a gidanku." Gabana ya fadi,nayi
yaqe"Zanzo
Murja,kada ki damu,ban iya saba alqawari ba."
Ta
jinjina kanta,ta zaro mukullin daga rigarta ta
budemin qofar,na dubeta ina murmushin
yaqe"Shikenan ko?" Ta riko hannuna,tana mai
daga
yatsa"Haba sweetyna,amince min koda kiss nayi
maka don Allah." Ba yanda zanyi tayi min sumba
a
lebba,sannan ta rakoni. Tace"Ko nazo na kaika?"
Da
sauri nace"A'a barshi zan tafi." Tayi dariya"Kai
sweetyna akwai ka da tsoro,koda yake muje zuwa
dai." Murmushi kawai nayi a raina
nace"Shashasha
kawai." Toh haka na samu da wayo na kubuta
daga
tarkon murja
Koda na isa gida ana kiran magriba ne. Saida
nayi
sallah na roqi Allah Ya nema mini mafita akan
wannan bala'in da ya afkomin na kuma roqi
gafararSa akan sab'a masa da nayi sannan na
fito na
nufi wajen Badamasi. A bakin gate muka gaisa
da
maigadinsu nace"Yana ciki ko?" Cike da fara'a
ya
amsa"Eh yana nan." Na sanya kai na
shiga,direct
sashensa na nufa. Yana zaune tare da abokan
nasa
su hudu,hayat,da haidar sai imam da kabir.
Nayi
musu sallama,gaba daya suka juyo,babu wanda
yayi
min kallon raini,na miqa musu hannu muka
gaggaisa. Cike da zolaya hayat yace"Mazaje ya
garin?" Nayi murmushi kawai,Badamasi
yace"Nidai
nace ku bi a hankali da abokina domin ba
abokin
wasan ku bane if not zaku jawa kanku." Ya
shafa
fuskarsa,suka sanya dariya. Imam yace"Ai kai
kam
kayi kwana biyu kana jinya." Nan ma dai dariyar
akayi,haka mukayita hira dasu har dai suka
mike
zasu tafi,muka rakosu muka qara yin musabaha.
Bayan motarsu ta tashi ya dafa kafadata"Ai sai
muje
ka gaida daddy." Nayi murmushi nidai har
lokacin
jikina a sanyaye yake. Yace"Ai na fadamaka
mutanenka kuma an tuba,shima hayat kwanan
nan
zai wuce Abuja zai ja ragamar kamfanin
abbansa,shi kuwa imam shirin aure yake,toh
shima kabir din har
an kai kudi,ya zama doctor anan wani private
hospital na abbansa,haidar ne dai zaiyi auren
gida,wata cousin dinsa Muhibba. A lokaci daya
zamu
angwance dai." Sai a sannan ne na sake na
labarta
masa batun da mukayi da Abba,ai wani tsalle
yayi
yana mai miqomin hannu muka cafke muna
dariya a
daidai lokacin da muka qarasa kofar falon
gidan"Gaskiya naji dadin wannan magana,Allah
Ya
qara rufawa Abba asiri,Allah Ya taimaki angon
Hafsa,rana daya zamu angwance nawan,amma
nasan mu zamu haska taro,fara da fari." Saima
naji ya bani dariya na girgiza kai"Allah Ya
sauwake maka
kaidai." Yace"Amin." A raina ina mai tausayinsa
domin na yarda Badamasi yana mutuwar son
Murjanatu. A falon gidan mami ce zaune da
qannen
badamasi suna kallo. Tana ganina ta rike
baki,fuskarta a sake tace"Toh yau kuma Ahmed
ne a gidan namu? Lallai yau babban rana ce."
Nayi dariya
cike da jin nauyin furucin mami,na durkusa har
qasa
na kwashi gaisuwa,suma suka gaisheni. Mami
tana
dariya tace"Halan batan hanya kayi Ahmed?"
Nayi
dariyar nima ina mai girgiza kaina"Ko kusa
mami,shigowa nayi dai na gaidaku." Ta jinjina
kai
tana murmushi"Gaskiya kam,ka kyauta."
Badamasi
ya dubeta"Mami Daddy yana ciki?" Tace"Yanzu
zai
fito." Muka zauna tana jana da hira ina amsawa
babu
jimawa sai ga daddy. Ya iso ya zauna kan kujera
shima cewa yake"A'a Ahmed,kaine a gidan?" Na
gaida Daddy a ladabce,ya amsa yace"Ya Alhajin
naka?" "Lafiyarsa kalau." Ya jinjina
kai"Madallah,ai na
dauka ka bata a rububi." Nayi dariya,yace"Kayi
dariya mana Ahmed,amma yaushe rabonka da
kazo
gaishemu?" Mami ta cafe"Yanzu na gama yi
masa
batun,ai Ahmed tunda zumunci ya hada sai a
dunga
kokarin sadarwa." Na jinjina kai"Gaskiyane mami
insha Allahu zan gyara." A tare suka ce"Yauwa."
Daddy ya qara da cewa"Kokaifa." Na fito ni da
Badamasi,muka tsaya nan wajen muna hira har
dai
nace zan tafi yace babu inda zani sai na ci
abinci.
Haka dole na bi bayansa,lokacin duk an hallara
a
dinning,nima na ja na zauna. Bamu rabu dashi
ba
sai wajen takwas da rabi.**********
***************
*******************Washegari ban tashi ba
sai
wajen sha daya na rana,dakyar na mike domin
kuwa
a daren jiya mun yini muna hira da abar
kaunata
duk
da cewa har lokacin ban furta mata komai game
da
sirrin zuciyata ba amma a siyasance nakan jefa
mata kalaman soyayya. Nayi miqa hadi da salati
sannan na
ja qaramin tsaki na fada wanka. Shigata babu
dadewa naji muryar badamasi,ya kwankwasa
qofar
bandaki,nayi gyaran murya,hakan yasa yace"Dan
iska,da gani baka jima da farkawa ba." Daga
fadin
haka ya zauna,hankalinsa ya kai ga wayar
abokin
nasa dake blinking na shigowar saqon
whatapp,ya
kai hannu ya dauka yana rayawa a ransa bari ya
duba yanda aminin nasa ke hirar soyayya. Ya
kai
minti goma sha biyar yana karanta saqonnin da
suke
turawa juna shi da hafsa,caraf ya hangi
lambar,ya
karanta ya qara karanta,ita dince ba wata ba.
Gabansa ya buga,ya dauka hannunsa har rawa
yake
ya duba. Kusan minti biyar yana karanta hirar
data
wanzu tsakaninsu,daidai nan na murza kofar
bandaki na fito ina goge fuska da qaramin tawul
din
wuyana,ina cewa"Kaidai bari,yau a gajiye na
tashi,jiya na kwana hira da sahibar shiyasa ina
sallah na....." Sauran zance ya maqale a
harshena
sakamakon ganin badamasi rike da wayata yana
gumi,jikinsa har rawa yake,gaba daya baiji
abunda
nake fadi ba. Ta faru ta qare!!" A hankali nake
tahowa na iso gareshi,amma
na
kasa furta komai. Miqewa yayi ya dubeni,wani
irin
duba. Idanunsa sun sauya launi,baice komai ba
ya
ajiye wayar ya ficewarsa. Na shiga uku! Murja ta
rabani da Badamasi! Abunda na ayyana
kenan,da
sauri na zira kaya,na bi bayansa amma ina! Sai
qurar motarsa. Ba shiri na sanya takalmi ban bi
takan
karyawa ba na fito. Na isa wajen idi mai
shago"Ina
kaga Badamasi yayi?" Ya nunamin hanyar
gidansu,ban nemi sauran bayani ba na tafi da
saurina. Dakyar na saita kaina na amsa gaisuwar
da
Baba maigadi yayimin na sanya kaina ciki.
Sashensa na nufa kai tsaye na hau buga
kofar,amma kamar
baya ciki. "Ka taimaka ka bude dan uwana nayi
maka bayani." Amma ko motsi hakan yasa na
juya
na koma gida jiki babu qarfi. Shikenan murja
tayi
nasara,bana zaton zan yafe mata idan tayi
sanadin
rabuwana da aminina. Gaba daya yinin ranar
babu dadi,wayata na kashe gaba daya saboda
damuwar
da nake dauke da ita,babu abunda ke min dadi.
Wajen karfe uku na rana,ina zaune na kasa fita
ko
kofar daki,Zahra tayi sallama,nayi mata iznin
shigowa. Ta shigo hannunta dauke da kwano,ta
tsugunna ta ajiye ta dubeni sai naga ta
rikice"Yayana meke faruwa dakai?" Na mike
zaune dakyar ina
murmushi mai ciwo,na dago na dubeta sai naga
kamar tana shirin kuka"Kanwata banajin dadi
ne."
Ta karyar da wuya"Sannu yayana,amma gaskiya
banji dadi ba ai kamata yayi ka fada kaje
asibiti."
Na
danyi murmushi nace"Ai ke ya kamata kiga likita
Zahra,kin rame kamar ba wacce na sani ba?" Ta
mike
cikin son basar da zancen"Yayana kenan,ka ci
abincin don Allah,Allah Ya baka lafiya." Tana
fadin
haka ta fice da sauri. Dakyar na qoqarta nayi
loma
biyar na rufe. Sai la'asar na fito daga daki,har
idi
na
tsokanata wai yau na zama mace. Dariya kawai
nayi bance komai ba na nufi masallaci bayan
mun idar
ne,muna fitowa na hangi motar mutumin nawa
a
kofar gidanmu. Wani sanyi naji ya dirar min,da
sauri
na qarasa,ya dago ya dubeni,idonsa sun
kode,saida
na tsorata ganin irin tashin hankalin dake kan
fuskar
aminina. Hannu yasa ya budemin gaban motar
ba tare dayace komai ba,na gane nufinsa na
shiga
na
zauna. Na dubeshi"Haba dan uwa,don Allah ka
tsaya
nayi maka bayani,wallahi na rasa ta yanda zan
tare
ka da wannan maganar ne,amma...." Ya juyo ga
mamakina naga yana murmushi wanda nasan
na
dole ne ya girgiza min kai"Kada ka damu dan
uwa bana zaton zaka ci amanata,kai din
aminine
na gari
wallahi Ahmed baka batamin rai ba." Ya jingina
kansa jikin kujera ido a runtse"Bani labarin
yanda
abun ya soma Ahmed." Ni kaina nasan aminina
yana
cikin yanayi mai wuya,amma ya zama dole na
sanar
dashi komai. Ban boye masa ba tun kiran murja
na farko har yanda mukayi da ita jiya. Na qara
da cewa"Wallahi dan uwana bani da
niyyar cin amanarka,ko kusa babu wannan a
zuciyata. Wallahi wannan dinma don na rasa
hanyar
sanar maka ne,yanzu haka zancen da nake
maka
murja tana nan tana jiran zuwana. Idon
badamasi
ya
kada jawur,jikinsa ya shiga rawa,wata murya ce
da ban taba sanin badamasi yana da ita
yace"Shiga ka
dauko wayarka please." Na dubeshi idonsa na
kan
sitiyari,na fita na dauko na shiga,bai qara
sauraron
komai ba ya figi motar,zan yi magana naga
babu
dama na zubawa sarautar Allah ido. Bai tsaya
ko'ina
ba sai a daidai Sahad Store,na dubeshi,shima
anan ya dubeni yayi murmushin da nasan na
qarfin hali
ne"Zaka gane gidan?" Na gyada kai,ya dauke
kansa
gefe yace"Kirata a waya ka sanar da ita gaka
nan,goslow ya tare ka." Na kunna wayar na
danna
kiranta,bayan na kunna loudspeaker,har ta
katse
bata dauka ba,sannan ta kira"Hello sweetyna."
Badamasi ya runtse ido yana murza yatsun
hannunsa saboda ji yayi kamar an watsa masa
wuta,toh ni kaina saida naji wata irin kunya ta
kamani duk da cewa bani da laifi,jin nayi shiru
yasa
ta qara cewa"Sweetyna ya akayi ne na jika
shiru?
Hello kana jina kuwa?" Sai anan Badamasi ya
juyo yayi min alama da hannu wato na nutsu,na
hadiye
miyau nace"Sorry murja,go slow ne ya rike
ni,tun
safe kuma wayar babu chaji ballantana na sanar
maki ina tafe. Ban jima da karbowa ba,amma
gani a
hanya." Tayi dariyar farin ciki"Shikenan sweetyna
sai
kazo,I love...." Da sauri na katse wayar saboda
banason batawa Badamasi,shi kuwa murmushi
kawai yayi yace"Wane layi zamu shiga?" Na
kwatanta masa ya ja motar,kafin mu kai kwanan
gidan yayi fakin"Sauka ka qarasa Ahmed,kada
ka
nuna komai ka saki jikinka,zan shigo daga baya."
Na
jinjina kai a sanyaye nace"Please dan uwa ka
nutsu." Ya girgiza kai yana murmushi duk da
sanyin AC
amma gumi yake"Kada ka damu,jeka,wannan
shine
gidan ko?" Ya nuna da hannu kasancewar muna
hanga,na gyada kai"Kwarai shine." "Ok,you can
go."
Na bude na fito nayi gaba. Motarsa ya ja ya
faka
a can
qasan bishiya kirjinsa nayi masa quna. Yana jin
ana wai wai cewa wasu matanbasu da amana
mayaudara
ne bai taba yarda ba sai a yau da hakan ta fada
kansa. Murja! Ashe murja haka take! Toh maza
nawa
take kulawa?! Kai murja ba macen arziki
bace,lallai ya
godewa Allah da Ya nuna masa tun bai aureta
ba
ma.


Zaharaddeen   Shomar
Whatsapp    08168575100Amadu 1 page 6
Posted by ANaM Dorayi on 04:15 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
Na shiga gidan muka gaisa da maigadi
sannan kai tsaye na nufi ciki. Kida na fara ji yana
tashi,ina cike da fargaba amma a kashi dari na
yanda nakeji a baya ya ragu kasancewar
Badamasi yasan komai. Na kwankwasa,ta bude
kofar. Na qaqalo murmushin dole ina jifanta
dashi,tayi wani far da ido,ta ja hannuna"Sannu
da
zuwa." Muka shiga ciki,ta rufe kofar ina ta
addu'a
kar ta sanya key ai kuwa Allah Ya taimaken bata
sanya ba. Na zauna,ta zauna kusa dani tana
kallona fuskar dauke da murmushin da ke qara
mata muni a wajena."Wallahi sweetyna har na
dauka ko yaudarata zakayi ka qi zuwa." Nayi
murmushi ina mai dubanta"Ai na fadamaki,bana
saba alqawari." Tayi dariyar farin ciki"Dama
nasan sweetyna ba mutumin banza bane."
"Amma ga
mutuniyar banza a gabana ba." Na ayyana a
raina,ta mike tace"Bari a kawo maka ruwa." Ta
juya tana karairaiya ta bar wajen. Tir! Da mace
irin
murja mara sanin kamata.Babu jimawa sai gata
dauke da faranti an jera
kayan marmari,biye da ita mai aikinta ce dauke
da
wani plate din. Ta ajiye,na gaisheta maimakon ta
amsa sai ta qara gaisheni,dole na amsa mata.
Murja ta
zauna ta dauki ayaba ta bare ta nufi bakina. Na
amsa
na soma ci,cikin dabara nima na dauka na shiga
bata. Dadi kamar tayi me,ta lumshe ido tana
murmushi"Lallai sweetyna na yarda na hakikance
kai
din masoyine a yanzu." Nayi dariya kadan"Toh
murja
kema kinsan kin kai a soki." Tayi dariyar farin
ciki,har
muka gama,a raina kuwa Allah Allah nake
Badamasi
ya shigo ganin tana ta shishshigemin. Cikin ikon
Allah sai gashi an turo qofar an shigo. Ya rufe ya
sanya qafa daya jikin bango,ya rungume
hannayensa a kirji,fuskar nan tasa babu annuri.
Cak
ta tsayar da hannunta akan kirjina,bata motsa
ba.
Kwarai tsabar firgici ne,da sauri na fisgeta na
mike.
Badamasi ya dan dagamin gira,kwarai na gane
me yake nufi,na dubeta a fusace ina nuna ta da
yatsa"Ashe abunda kika shiryamin kenan? Ba
kince
min bazaki sanar da Badamasi komai ba! Murja
ta
koma kurmar karfi da yaji,sai jujjuya hannu
take,naji
dadin hakan,da sauri na isa ga Badamasi"Wallahi
wallahi...." Ya dakatar dani ta hanyar dagamin
hannu,murya a kausashe yace"Baka da abun
cewa
Ahmed,da idona naga chat dinku a wayarka,baka
da
laifi ko kadan. Ya taka a hankali ya isa gareta,ai
tuni
ta tsorata,hawaye ke malala daga idonta dakyar
ta
iya hada abun cewa"Wal..wal.wallahi honey
sharri."
Ya daka mata tsawar da har saida mai aikinta ta
fito a guje,hannu na rawa ya nunata"Kin
cuceni,kin min
mugun butulci. Ashe ke din 'yar bariki ce?
Nagode
Allah da Yasa ban kai ga aurenki ba,lallai ke ba
matar
aure bace domin duk namijin dake son 'ya'yansa
su
tarbiyyantu toh bazai aureki ba. Daga yau kada ki
nuna kin sanni koda akan hanya ne! Kina zaton
zaki iya hadani da Aminina?" Ya girgiza kai yana
murmushi a lokacin da hawaye suka zubo
masa"Ko
kadan murja,bazaki iya rabani da Ahmed ba. Baki
isa
ba kinyi kadan,ke a banza! Ahmed munyi
shaquwar
da mace bata isa ta rabamu ba murja,inda ke
mutuniyar arziki ce,kika nunamin kina son Ahmed
ni mai iya sadaukar da ke gareshi ce. Amma
wannan
bata dace da matar Ahmed ko Badamasi ba! Jeki
ki
nemi dan iska irinki! Nikam na fasa aurenki!"
Daga
haka ya juya a fusace ya fice,ban jira komai ba
nabi
bayan abokina. Murja kuwa bata taba zaton haka
ba,bata taba zaton akwai abunda zaisa zuciyarta
ta karaya ba,kawai sai ta zube ta fashe da wani
irin
kukan bakin cikin rashin da tayi na masoyi kamar
Badamasi.Ko sanda na isa,tuni yana motar.
Zaune na
taddashi a mazaunin kusa da direba,bance komai
ba
na zagaya na shiga. Shiru ya ratsa babu wanda
yace
wani abu sannan kuma naji muryar
Badamasi"Muje
Ahmed." Na juyo na dubeshi jin yanda muryarsa
ke
rawa amma sai na rasa abun cewa kawai na
tashi motar nayi ribas muka bar unguwar. Toh
haka har
muka je Yakasai babu wanda yace uffan. Ya
dubeni"Ahmed kaini gida please sai ka wuce." Sai
anan nace"Dan uwa baka da lafiya ne?" Ya runtse
ido
yana rike kai"Kaina ke dan sarawa." Allah
Sarki,sai
ya bani tausayi nace"Allah Ya sauwaka,don Allah
ka daure kada ka sanyawa kanka damuwa,please
ka
kwantar da hankalinka." Yayi murmushi a lokacin
daya shafi sumar kansa"Kada ka damu ya wuce."
Muka iso gidansu nayi fakin a farfajiyar,muka fito
na
mishi sallama na juya don tafiya,yace"Bazaka
bari
kayi sallah ba?" Na juyo ina murmushin qarfin
hali domin gaba daya tausayi yake bani"Ba wani
abu
nayi idan na qarasa,agaida su daddy." Ya gyada
kai
sannan ya juya ya nufi sashensa,na bishi da kallo
sannan na juya na bar gidan. A ranar nayi bacci
mai
dadi babu fargaba,domin rabona da baccin kirki
tun
shigowar murja rayuwata. A gefe guda kuma
tausayin aminina ce fal nasan da wuya idan yayi
wani
baccin kirki. Haka na wayi gari zuciyata
wasai,nagodewa Allah. Gaskiya mace shu'uma
ce,haka kawai na rasa kwanciyar hankalina na
kwanaki saboda wata murja can.
***************
******************** A makaranta Zahra ce ke
Allah Allah ta shige motarsu bayan an tashesu
domin
gujewa Hafsa saidai ta makaro kafin ta isa taji
takunta
da sauri tana tahowa gami da kiranta"Zahra
Zahra
please ki tsaya." Dole ta tsaya ta juyo fuskar
babu
walwala sosai tana dubanta,Hafsa taji jikinta yayi
sanyi ta dafa kafadar aminiyarta"Zahra sanar
dani idan nayi maki wani laifin mana,gaba daya
kin
chanjamin a kwanakin nan why? Haba aminiyas
bansanki da gaba ba." Zahra ta kauda kanta
daga
duban Hafsa,lokacin babu laifi ta dan saki
fuska"Ke
babu komai fa,kwana biyun nan banjin dadi ne
shiyasa..." "Yanzu Zahra don bakijin dadi
shikenan sai kuma ki sauyamin meyayi zafi don
Allah? Nidai
iyaka tunanina na kasa gano abunda nayi maki
har
haka,please ki sanar dani." Zahra taji bata kyauta
ba,toh akanme zataji haushin hafsa? Idan ma ta
nuna
tana kishi da ita shi wanda take kishin dominsa
ya
san tana yi ne? Babu hujjar da zata kama tayi
fushi da aminiyarta don haka tayi dan
murmushi"Ke dallah
babu wani abu sarkin zargi,kada wannan ya
dameki,sai mun hadu goben. Idan kuma kin bari
har
8 ta shige goben babu ke babu maki goma na
english." Sai anan hafsa taji sanyi,sukayi
dariya"Ina
zanyi wannan saken? Ai tun bakwai zan iso insha
Allahu,kedai zakiyiwa kanki fada." Nan ma dariyar
sukayi sannan sukayi sallama ransu wasai.
Badamasi yakai sati yana fama da damuwa har
dai Allah Ya yaye masa ya watsar da batun murja
gaba daya ya dukufa ga aikinsa. Ko kusa
badamasi
ya chanjamin ba,asalima yana iyaka kokarinsa
wajen
boyemin damuwarsa idan muna tare nima nakan
yi
duk abunda zai faranta masa a lokacin.
******************************
****************Wataranar juma'a da yamma
muna waya da hafsa nace"Beauty wallahi inason
ganinki." Tayi 'yar dariya tace"A'a yayanmu
bakason
ganina." Na dan zaro ido kamar tana
ganina"Haba
dai beauty meyasa kike wannan tunanin?" Ta
marairaice murya"Haba yayanmu ka manta na
jima
da baka adireshina?" Nayi murmushi ina mai
sauraron muryarta mai kamar an busa
sarewa"Hakane,toh ai baki bukaci ganina bane
beauty." Da sauri tace"Haba yayanmu,inda bana
bukata meyasa zan baka adireshina? Ai baka zo
ba ballantana kasan ko inayi ko a'a." Nayi
dariya"Shikenan toh,sanya min ranar zuwa kada
nazo ranar da kike tare da saurayinki." Hafsa tayi
dariya"Uhm,wallahi bana kula kowa. Ashe har
yanzu
baka yarda ba?" Nayi dariya"Na yarda mana
amma
bansani ba ko kin fara yanzu." "A'a wallahi bana
kula kowa yayanmu." Na sauke ajiyar
zuciya"Shikenan toh beauty,insha Allahu zuwa jibi
zaki ganni." Hafsa tayi tsalle kan gadonta"Ok
yayanmu,ina nan ina jiran ganinka." Nayi
murmushi
mukayi sallama zuciyar kowannenmu cike da jin
dadi. A daren yaya usman ya iso kasancewar biki
na matsowa,za'a kai lefensa a satinnan. Ya qara
kiba,daga ganinsa kasan yana jin dadi a Lagos
dinnan,har dai saida na fadamasa"Yaya usman
kayi
kyau kayi jiki wallahi." Duk da fuskarsa a daure
take
saida ya dan saketa kadan"Allah ko?" Nayi
dariya"Kwarai ma." Ya gyada kai"Toh nagode."
******************************
******************Inna ta dubi 'dan nata
bakinta
ya qi rufuwa"Toh kai yanzu nufinka bayan ka auri
fiddausin duk da haka Alhajin zai baka diyarsa?"
Usman shima cike da nishadi yace"Kwarai ma
inna,ai
Alhaji Mahdi yace muddin na ceto ran diyarsa
data fada tarkon sona toh ba shakka zai min
kyautar gida
sannan ya bani jari mai tsoka." Inna tayi dariyar
farin
ciki tana jinjina kai"Lallai ba shakka mun kusa
keta
raini shiyasa auren 'yar mai arziki yake da
amfani. Ai
inda ace tun farko ita Hamidar ta nuna tana
sonka ai
da ba'a fara batun aurenka da fiddausi ba." Ya
dan hade fuska"Batun gaskiya inna ina kaunar
fiddausi,kuma zan aureta a hakan,nifa hamidar
nan
ba wani kyau ne da ita ba wallahi duk rashin
kyau
irin na fiddausi,hamida tafi ta. Kawai ita auren
arziki
zanyi. Yanzu ma tahowar nan da zanyi jirgi na
biyo
wallahi har dubu talatin Alhaji ya bani. Yana son
hamida sosai ita kadai ce mace a cikin 'ya'yansa
hudu." Sai kuma ya danyi sanyi ya dubi innar
tasa"Kina ganin Abba zai barni na aureta kuwa?
Munyi da Alhajinta nan zuwa hamidar ta gama
secondary,sauran mata nan da 'yan watanni
shida
tafiyarsu daya dasu Zahra." Inna ta washe
baki"Kai madallah,kada kaji komai,nace maka
za'ayi ka yarda
dani kawai,ta Alhaji mai sauki ce." Usman yaji
dadi ya
shiga dariya,sannan suka cigaba da batun shirye
shiryen kai lefen da za'ayi nan da kwana biyu.
Ya kama ranar lahadi ne kai lefen yaya
usman,tun
karfe hudu gidan yake a cike da mata daga 'yan
uwan inna har can gidansu gwaggo. Na shirya
tsaf
cikin shadda ta fara qal,na fesa turare sannan na
sanya baqar hula,na fito. Ina tsaye ina kulle kofa
ne
Bahijja dasu Raliya suka zo wucewa. Raliya ta
rike baki tana dariya"O'o,irin wannan kwalliya
haka yaya
Ahmed,sai ina?" Nayi murmushi ina harararta
cikin
wasa"An gayamaki ku kadai ke da masoya."
"Aahhh." Suka fada suna dariya,Badariyya
tace"Eh
lallai,wace gimbiyar aka samu?" Bahijja na dariya
tace"Wai ina ruwanku? Yayana kada ka
fadamusu,ashe dai akwai labari ko?" Na daga
mata
babban yatsa alamar hakan ne"Kada ki damu
kanwata,akwai labari bari dai naje na dawo
kinsan
mu 'yan yamma ne ba dare ba." Na qarasa ina
mai
nuna Badariyya da ido. Sukayi dariya tace"Au
lallai
ma yaya ahmed mu ne 'yan dare ko? Toh ai dai
mun kusa bar muku filin gidan." Nayi dariya ina
rike
baki"Au au,haka kika koma badar? Kema kin
fitsare
ko?" Da gudu sukayi ciki suna dariya,nima dariyar
nayi,na fito cike da nishadi." Direct yaya usman
na
nufa dake zaune akan benci tare da abokinsa
Abdulhamid. Ganin da nayi yana cikin fara'a yasa
naji sanyi,muka gaisa na roki alfarmar ya bani
mukullin
motar Abba. Ya dubeni daga sama har qasa"Ina
zaka
ne?" Na shafi sumata ina murmushi,Abdulhamid
yayi
dariya"Ai baka bukatar qarin bayani man." Ga
mamakina kuma naga yayi dariya,lallai aure da
dadi
yake domin kuwa ya fara chanja halayen yaya
usman tun ba'a kai ga bikin ba. Ya zaro mukullin
ya
mikomin,cike da mamaki nasa hannu na karba
ina
godiya kai ai ban qara mamaki ba saida ya zura
hannu aljihu ya zaro kudi har dubu biyu ya
miqomin.
"Toh!" Abunda ya subuto daga bakina kenan,suka
kalleni,usman cike da rashin fahimta yace"Da
akayi me?" Nayi murmushi na girgiza
kai"Bakomai,nagode
yaya. Sai na dawo." Abdul yana fadin"Toh a
gaisheta." Nayi dariya kawai.
Unguwar hotoro na nufa kai tsaye,a nutse na
shiga kwanar maggi. Har kofar gidansu Hafsa
sannan na faka. Na dauki wayata dake ajiye
gefena
na danna kiranta. Ringing biyu ta dauka tana mai
sallama. Na amsa"Beauty gani a kofar gidanku."
"Ok
yayanmu ganinan." Ba'a fi minti hudu ba sai gata
ta fito. Tasha kyau cikin leshinta orange,ta yafa
mayafi
kalar kayanta. Kasa dauke idona nayi daga kanta
har
nabude motar na fito. Ta kalleni tana
murmushi"Bismillah." Na maida mata martani,ta
dauke kanta cike da kunya tayi gaba nabi
bayanta
har farfajiyar gidansu,wani qaramin falo ta
saukeni na saukar baqi. Bayan na zauna ta
dubeni"Ina
zuwa." Har takai kofa nace"Ji mana." Ta juyo
tana
murmushi,na kalleta ina jin wani wutar kaunarta
na
qara ruruwa a zuciyata,sai ma na kasa magana.
Ta
dan langabe kai"Yayanmu kayi shiru?" Na danyi
firgigit na shafi kaina ina murmushi"Ki taho min
da noor." Tayi dariya har haqoranta suka
bayyana
sannan ta juya ta fita. Babu jimawa sai ga yaron
yayi
sallama yana tsalle tsallensa,na amsa ina
dubansa.
Yana dariya ya qaraso"Anti hafsa tace nazo kana
nemana." Na janyo shi jikina ina masa
murmushi"Fine noor hakane,ka sanni ko?" Ya
sanya yatsa daya akan hab'ansa yana kallona
alamar
tunanisannan sai yayi dariya yace"Eh na taba
ganin
hoton mai kama dakai a wayar anti hafsa." Nayi
dariya daidai nan ta shigo hannunta dauke da
plate,na qara dubansa"A wayar kaga hoton?" A
razane naga ta dago ta dubeni,na tsareta da
ido,sai kuma tayi kasa da kanta cike da kunya.
Noor
yace"Eh mana,kullum tana nuna min tace
wannan
shi
zai zama mijinta ko aunty hafsa?" Ya maida
maganar
gareta. Wani dadi ya ratsa ni,ta kalli noor a
fusace
tace"Tashi ka tafi sarkin surutu kawai." Nayi
dariya a
lokacin da noor ya sanya gudu saida yaje kofa ya
juyo da karfi yace"Kuma har magana takeyi da
hotonka." Ya sanya gudu,na qara sanya
dariya,itama
rufe ido tayi tana dariya. Na dubeta murya kasa
kasa
nace"Haka ne beauty?" Ta kasa cewa komai,nayi
murmushi nace"Kiyi magana mana,hakane?" Nan
ma
bata ce komai ba. Na share zancen"Toh na
sameki lafiya?" Ta kawar da hannunta daga kan
fuskarta
tana murmushi bata yarda mun hada ido ba
tace"Alhamdulillah,ya su Zahra da Abba?" "Duk
lafiyarsu kalau,ya su faruq da mamanmu?" Ta
amsa
min sannan nace"Bakiyi mamakin gani na ba?"
Ta
girgiza kai"Meyasa zanyi mamaki? Ai munyi dakai
dama zaka zo din." Na jinjina kai ina
murmushi"Gaskiyane,toh kinji dadin ganina?" Tayi
shiru ta kasa magana,nace"Haba beauty ki dunga
amsamin please,kinyi magana da hotona ma toh
meyasa bazakiyi dani a zahiri ba? Fadamin ma
me
kike cewa hoton nawa?" Tayi dariya ta ja mayafi
tana rufe fuskarta. Nayi dariya"Toh ko sai a
whatapp zaki
fadamin uhm?" Ta gyada kai da sauri."Na gamsu
da
wannan,naji noor yana cewa kina ce masa ni
mijinki
ne,dagaske kina fatan haka?" Wayyo wata irin
kunya
ta cika hafsa toh me zata ce? "Ko karya yake?"
Na
tambayeta,ta kasa amsawa. Na sauke ajiyar
zuciya na qara dubanta"Hafsa." Jin da tayi na
kirata da sunanta
kai tsaye yasa ta amsa min. "Kinsan meya
kawoni?"Ta girgiza kanta tana mai qara jan
mayafi."So da
kauna." Na bata amsa. Sai tayi dariya kadan
tace"Yayanmu kenan,to wa kake so?" "Au baki
ma
sani ba?" Ta gyada kanta duk da cewa ta sanin
tana
dai son jin ta bakinsa ne. "Wata Hafsa
nakeso,'yar
hotoro kwanan maggi." Dadi ya cikata ta kalleni
na sakar mata murmushi ta dauke kanta da
sauri. "Don
Allah Hafsa ki saki jiki muyi hira mana,batun
gaskiya
nake fadamaki hafsa,sonki nakeyi da aure,idan
har
kin amince kina sona." Shiru ya ratsa ni kuwa
banaso
naji ina mana anyi shiru,nace"Kiyi magana please
kada na tashi nayi tafiyata." Nan ma shiru hakan
yasa naji raina ya dan sosu,duk da cewa ina da
tabbacin
tana sona amma nafiso ta furta da bakinta,sai
nace"Toh ko zaki sanar dani ta chat?" Ta gyada
kai
da sauri. Nayi murmushi"Beauty kenan,kunyarki
na
burgeni,gashi kinci kwalliya kuma kin hanani
ganin
fuskar sosai,kada ki zama marowaciya mana."
Tayi dariya,a hankali kuma ta saki mayafin,tana
satar
kallona mukayi murmushi sannan ta zuba min
lemon
data kawo a kofi ta miqo min. Na karba ina
godiya na
sha. Tun hafsa na dar dar har ta dan sake
mukayi
hira sosai,har naji banason tafiya,hakan yasa
bamu
ankara ba sai gani mukayi gari ya soma duhu
alamun dai rana ta fadi. Hakan yasa na mike ina
duban agogon dake daure a hannuna"Kinga kin
maqalar dani gashi har magriba ta kawo kai ko?"
Tayi dariya"Wallahi nima ban ankara ba sai
yanzun."
"Toh meyasa?" Na watsa mata tambayar,tayi
kamar
zatayi kuka a shagwabance tace"Oh yayanmu ka
fiye tambaya wallahi." "Waya koya maki
shagwaba ne?
Tun haduwarmu dake kike a hakan." Na qara
watso
tambayar,ta dubeni mukayi dariya,nace"Kiyi
hakuri
dani wani sa'in akwai ni da tambaya kamar dan
jarida." Tayi dariya"Na yarda." "Yauwa,toh sai
yaushe
kuma?" "Nan da sati biyu." Na dan zaro ido
kadan"A haba dai ke kuwa? So kike na mutu ko?
Nan zuwa
juma'a zan dawo bazan iya ba." Mukayi dariya ta
taka
mini,anan farfajiyar gidan muka hadu da faruq
shima
ya dan rusuna ya gaisheni na amsa fuska a
sake,yana satar kallon hafsa wacce take maka
masa
harara tana murmushi. Ya jinjina kai yana dariya
sannan yayi cikin gidan da sauri." Na
dubeta"Shine
faruq ko?" Ta gyada kai"Eh,ya akayi ka ganeshi?"
"Kamar da kukayi." Mukayi sallama da ita
kowannenmu zuciyarsa wasai. Cike da nishadi
nake
tuqi,wayata tayi ringing na dauka,badamasi
ne"Ya
dai mutumin,kana ina ne?" Nayi dariya"Ganinan
dawowa gida daga wajen hafsa." Badamasi yayi
dariya"Eh lallai kace kana can kana soyewa ka
barmu tsaye kofar gidanku." Cikin rashin fahimta
nace"Har kai da wa?" Yayi dariya a karo na
biyu"Ni
da Haidar ne. Har mun juya ma." "Ok kuyi hakuri
yau
hafsa ta kwace muku hirar." Yayi dariya"Dan iska
sai ka dawo." Ya kashe wayar,sai kuma ga kiran
yaya
usman a fusace ya soma fada wai na dade yana
son
fita da mota idan anyi magriba." Na bashi hakuri
nace
ganinan. Sannan ya kashe. Sanda na isa na kai
masa
mukullin har daki ya karba yana tsaki"Kai haka
ake
sai kace kayi zamanka?" Na shafa kaina"Ayi
hakuri." Ya mike,shima dai kwalliyar shadda
yaci,dariya ta
ciyoni na gimtse,ya harareni a lokacin da yake
gyara
zaman hularsa"Me ya faru kake dariya ciki ciki?"
Na
girgiza kai da sauri"Haba babu komai." Nayi wuf
na
fada toilet don yin alwala,shima nasan dai hirar
ya
nufa. Ai babu abunda yakai hira da masoyi
dadi,akodayaushe burin masoya su gansu tare
suna
hira.****************************************
*****Jin da tayi antin nata ta shigo dakin yasa
tayi
saurin mikewa tsaye,fuska daure ta dubeta"Wai
tun
dazu da nace ki shirya uban me kikeyi? Gashi har
faisal ya iso." Zahra ta hadiye kukan da ya taho
mata ta soma shafawa fuskarta hoda,antin ta
tayi
tsaki"Kya dai ji da kumbiya kumbiyarki,duk
abunki
na rantse maki duk ranar da naji koda wai kina
soyayya da dan iskan yaron nan sai na cire
hannuna
akanki,shashasha kawai. Ga dan uwanki nan
Faisal,da ace ki so wani na gwammace shi yazo
ya nemi aurenki tunda ko ba komai ciki daya
muka fito
da uwarsa,amma ba wannan wanda bai tara ba
bai
bawa wani ajiya ba. Idan kuma kika qara
mintuna
goma baki fito ba wallahi sai na sab'a maki."
Daga
haka ta fice,kwalla suka cikawa zahra ido,toh
idan
antin nata ta kwantar da hankalinta ma ai ita
kam ta haqura da yaya ahmed. Ina amfanin
wannan son
maso wanin? Yaya Ahmed din ko kusa bata
gabanshi toh kenan ita kadai take kidanta da
rawarta. Saidai tasan har abada batajin zata
daina
son yaya ahmed wanda asalinsa tausayin da
takeyi
masa ne ya juye ya koma so. Ta shirya bata ko
chanja kaya ba,ta dauki mayafin baqar abayar
dake jikinta
ta yafa. Fuskar a hade ta fito,yana falon suna
hira da
antin nata yayinda su Salihu ke kallon MBC3,ya
zubo
mata manyan maganansa,ta qarasa ta durkusa
ta
gaisheshi. Fuska a sake ya amsa mata,sannan ya
yiwa anti sallama ya fito. Antin ta dubi
zahra"Sauran kuma ki qi sakin fuska." Zahra dai
bata ce komai ba
ta bi bayan faisal a sanyaye. A jikin motarsa ya
tsaya
ya dubeta"Zahra nasan kinsan dalilin zuwana
amma
bari na fada da bakina domin ki tabbatar cewa
ba
wai matsanta mini akayi na kawo kaina gareki
ba,a'a
gaskiyar lamari dama can ina kaunarki toh sanin
yanda zamanin nan yake a yanzu yasa naji tsoron
tunkararki musamman ma yanda kike da rashin
magana sai nake tunanin kamar idan na kawo
kaina
zaki wulakantani." Zahra ta danyi murmushi ta
girgiza kai"Haba dai yaya faisal,ai kasan koda ba
wannan ba kafi qarfin wulakanci a wajena a
matsayinka na dan uwa,ka kauda wannan ma."
Yayi
murmushi"Hakane zahra." Nan dai yayi ta sakin
maganganu da kalaman soyayya sakaka ita dai
Zahra tayi shiru tana jinshi,kasancewarsa yana da
ban dariya wani sa'in duk da bada son ranta ba
takan yi dariyar idan ya fadi wata maganar.
Daidai nan nazo zan wuce cikin gida dawowata
kenan daga
masallaci na hangi wata budurwa tsaye tare da
wani
a gaban gidanmu. Mamaki ya kamani har ina
cewa
toh yau kuma wacece take zance kofar
gidanmu,sai
da na matso sosai sannan na hangi zahra. Ai sai
na
qara bude baki ina dubansu,kamar a mafarki
nake
ganin lamarin,wato zahra har ta isa tsayawa da
saurayi? Nayi musu sallama,ta juyo muka hada
ido da
alama dai a firgice take ni kam ko a jikina na
shige
daki. Saidai har lokacin ina jin wani yanayi a
jikina,toh banda ma rigima irin tawa ai zahra kam
ta
isa aure ma ballantana tsayawa da saurayi. Na
dan ja tsaki"Toh koma meye dai Allah Ya zaba
mata miji
nagari." Sannan naja wayata na hau danne
danne,saidai zuciyartawa babu dadi bansan dalili
ba,duk sai naji chatting dinma ya ficemin daga rai
na
ajiye wayar na fito a sanyaye,har lokacin dai suna
tsaye"Dan iska zai lalatamin kanwa da soyayya."
Na fadi a raina,sai kuma na yiwa kaina dariyar
qarfin
halina kamar wani tababbe. A shagon idi na yada
zango,muka gaggaisa da samarin wajen sannan
nima na nemi waje na zauna. Idi da baya gani ya
kyale ya dubeni"Amadu yau kuma 'yar gidanku ce
tsaye da saurayi?" Na dan ja tsaki ina dariya 'yan
wajen suna tayani"Idi kaidai tsiyata dakai kenan
akwai son shiga abunda bai shafeka ba,ina
ruwanka
toh?"Samarin sukayi dariya,idi yace"A'a toh ai
abunda
baka saba gani bane ka ganshi a yau,dama
tsaleliyar
budurwa kamar Zahra ace ta qi kula samari ai
ansan
da walakin. Ashe tsalelan saurayi take dashi." Sai
ma
ya bani dariya duk da cewa raina ya dan sosu,na
qara waigawa har lokacin suna tsaye sai naji
raina babu dadi. A daddafe dai na tsaya har
saida
naga
Zahra ta koma gida sannan nayi sallama dasu idi
na
shiga ciki. Da sauri na cimma zahra a zaure,na
dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Ta juyo
tana
dubana na lura dai har yanzu a firgice take,fuska
ba
walwala nace"Waye wannan da yazo gurinki?" Ta
dukar da kanta qasa a sanyaye tace"Yaya Faisal
ne
'dan gwaggo mariya." Gabana ya fadi nayi
murmushi"Oh ai na dauka wani ne daban,kice dai
dashi za'ayi." Zahra sai ma ya bata haushi tayi
shiru
bata ce komai ba. Ganin da nayi ta share batun
sai
nima nace"Shiga gida toh." Ta wuce da sauri
sannan na bude dakin na shiga. Kwanciya nayi a
gado,toh
wai meyayi min zafi da batun nan? Ina ruwana?
Nima
ai soyayyar na gama yi,kuma banda haka ma
Zahra
takai matakin da za'a ce ta shiga gidan miji. Sai
na bar
zancen na kunna wayata. Kai tsaye whatapp na
shiga. Cikin sa'a na tadda mutuniyartawa online
har da message daga gareta,na bude na duba"I
LOVE
YOU." Na maimaita yafi sau nawa na mike daga
kwance ina murmushi wani sanyi yana ratsamin
zuciya. Nayi mata sallama ta bada mintuna
kusan uku
har nayi zaton ko bata gani bane sai kuma naji ta
amsa min. "Hafsa naga sakonki,nagode." Ta aiko
da kan aljan mai murmushi sannan tace"Nima
nagode,ya kaje gida?" Na maida mata martanin
murmushin sannan na amsa"Alhamdulillah,kema
na
barki lafiya?" "Alhamdulillah yayanmu." "Har
yanzu
ban kai a canzamin suna ba beauty?" Tayi
murmushi"Me kakeso na kiraka toh?" "Kirani da
yanda kikejina a ranki,ma'ana daidai sunan
daidai
matsayin da kika ajiyeni." Hafsa ta gyara
kwanciyarta
tana mai jin dadin hira da masoyinta tace"My
heart
yayi maka?" Na saki ajiyar zuciya ina mai jin
dadi,sai
naga bata lokacine ma tsayawa hira a whatapp
kawai sai nayi kiranta. Kamar ba zata daga ba
sai kuma ta daga,shiru bata ce komai
ba"Hello,kina jina
beauty?" "Eh ina jinka." "Wa kike ji?" "Kai mana"
"Ni
bani da suna?" Hafsa ta mike tana mai narkar da
fuska tana mai jin haushin tambayoyin ahmed,ala
dole dai sai ta fadi abunda yake ra'ayi. Sai na
tsinci
muryarta"My heart." Nayi dariya saboda jin yanda
ta kira kalmar kamar an shaqeta,daga ji dai dole
ce ta
sanya"Sorry beauty na takura maki ko?" Tayi
murmushi mai sauti tace"Ko kusa,kawai dai
tambaya
ce banasonta wallahi." "Amma kin manta
tambaya
akace mabudin ilimi ce?" "Gaskiyane." Nayi
murmushi"Naga saqon da kika turo,saidai kamar
yanda kika rubuta please ki furtamin da bakinki
naji." Hafsa dake zaune ta sanya hannu ta rufe
ido
tana dariya kamar yana gabanta. "Au dariya ma
na
baki?" Dakyar ta furta I love you. Naji dadi,haka
mukayi ta hirar soyayya da Hafsa,motsin da naji
na
shigowar yaya usman yasa nayi sallama da
ita.Muna kwance naji an kira yaya usman a
waya.
Na dan muskuta ina murmushi a raina nakeji
inama
zan iya kiran hafsa muma mu soye. Ga mamakina
kuma sai naji ba da fiddausin tasa yake waya ba
wata ce kuma a Lagos take don har na sanar da
ita
gobe zai taho. Abunda dai babu ruwanka sai ka
ja
bakinka hakan kuwa nayi domin banason shiga
abunda babu ruwana. Wasu mazan ma
hadamammu
ne,basu taba tsayawa a mace daya,ga dai
wannan
har ana shirin aure nan da satittika amma yana
nan
yana sha'aninsa da wata. Saima fiddausin ta bani
tausayi,tun inajin hirar sa har dai bacci yaci
qarfina. BAYAN SATI UKU, BIKI BUDURI
A kwana a tashi cikin hukuncin Allah har bikin
yaya
usman dasu badariyya ya iso. Gidanmu ya fara
cika
da 'yan uwa 'yan nesa. Hatta su kubra gidan
suka
tare da 'ya'yansu sai an gama biki. A gidan
gwaggo
aka yanke yin taron bikin tunda dama ai kirjin
bikin duk suna gidan. Nima shadda har kala biyar
Abba ya
dinkamin kamar nine angon. Ranar da akayi
daurin
auren muka dunguma raka angwayen ciki domin
gaida iyaye. Aka gaggaisa sannan aka fito aka
nufi
nan kofar gidanmu,aka shiga fito da abinci,daki
muka shige tare da Badamasi muka zauna muna
ci. Na dubi badamasi ina dariya"Kai mutuniyar fa
tazo."
Ya jinjina kai bayan ya hadiye abincin bakinsa
yace"Ya akayi ka sani?" Nayi dariya"Wallahi
kuwa,waya mukayi da ita." Yana murmushi ya
dubeni ya jinjina kai"Kace yau ba kanta." Muka
cafke
muna dariya.
Da yamma muna tsaye jikin motar Badamasi tare
dasu Haidar,hatta Bukar ya sami halartar daurin
auren ana ta hira sai ga Zahra da Hafsa sun fito
sai
kuma wata lubna kanwar faisal. Na kallesu,gaba
daya zahra ta haskakasu saboda ita din fara ce
tas,tana sanye da shadda ruwan hoda itama ta
wajen nawa tayi kyau cikin leshinta baqi mai
kwaliiyar
fulawoyi jajaye. Ga wani dan qaramin faringlass
dake
manne a idonta ai sai hankalina yafi karkata
kanta,kafin na samu bakin magana tuni
Badamasi
yasa baki yayi kiransu. Suka iso inda muke suka
gaishemu,muka amsa. Badamasi ya dubi
Zahra"Kanwarmu ya hidima? Kwana biyu ba'a
ganinki?" Zahra wacce take satar kallon Yayanta
Ahmed wanda gaba daya hankalinsa yana ga
aminiyarta,ya sha kyau kamar wanda aka ciro
daga
kwali ta hadiye kwallarta ta daure ta qaqalo
murmushi"Wallahi Yaya badamasi ina nan,sai a
hankali ne kawai." Nidai duk kishi ya cikani
domin
gani nake kamar dukansu sun zubawa hafsa ido
ne,da sauri na dubi Zahra"Ina kuka nufa?" Ta
daure
tace"Can gidan bikin zamu koma." Na dan zaro
ido"Haka zaku fita da wannan uban kwalliyar?"
Lubna tayi dariya domin ba laifi tana min
mutunci
idan tazo gidan"Oh yaya Ahmed kai kuwa ai
kasan
biki akeyi." Haidar ya cafe"Yauwa 'yar gari
fadamasa,kuma kai Ahmed 'yan mata idan basa
kwalliya ai sai a hankali,kaga waccan mara
maganar
ma ta fisu iya kwalliya." Hayatu yace"kaidai kayi
shiru
baka san hanzarin Ahmed ba." Sukayi dariya,nayi
murmushi na dubi badamasi zo muyi rakiya.
Imam
yace"Au banda mu? Ke ta tsakiya sai mun hadu
wajen dinner ko?" Ya qarashe yana dariya nasan
tsokana ce don su qular dani domin dai Hafsa ce
a
tsaki,na juya ina harararsa. Suka sanya dariya,a
hanya ni da hafsa muna daga baya yayinda
badamasi ke gaba tare da zahra wacce yake yiwa
zuba ita kuwa duk jikinta a sanyaye yake tana
fata
inama akwai randa yayanta zai sota koda ya
kasan
awa ashirin da hudu ne kawai,da taji dadi domin
ko
banza ta samu ya kalleta a mace. Na dubi
hafsa"'Yan
matana meyasa kika fito da wannan mayafin?"
Hafsa cike da rashin fahimta ta dubi mayafinta
don taga
inda aibunsa yake,babu laifi ya rufe mata jikinta
tsaf,ta dubeni a raunane"Haba my heart ina
laifin
mayafina?" Na dan daure fuska"Amma meyasa
aka
fiye kallar min ke? Wato ko a gida ma haka kike
fitowa ko?" Da sauri tace"Wallahi ni bana yawan
fita ma,bikin nan ma ai na fadamaka don dai
Zahra taje
da kanta ta kaimin IV ne da babanmu bazai barni
ba." Nayi murmushi"Toh ya zaki dinar?" Tayi
dariya"Zanje my heart amma bazan jima sosai
ba,babanmu baison na kai dare a waje." Nayi
dariyar
farin ciki"Gaskiya Allah Yayi wa Babanmu
albarka,naji dadi da yake kularmin da tarbiyyarki.
Yaushe zaki gayyatoni na gaidashi?" "Duk sanda
kazo zan yi maka jagora har falonsa." Na jinjina
kai"Sai nazo din." Daidai nan muka iso kofar
gidan,zahra bata tsaya ba tuni ta shige ita da
lubna,Badamasi yace"Malama hafsa Allah Ya baki
ikon rikemin amanar dan uwa." Hafsa ta
murmusa"Amin." Bahijja ta fito rike da
leda,saboda
tsabar hankalinta ya tafi wani wajen bata ko lura
da
mu ba,cafke ledar nayi na kwace,hakan yasa dole
ta
juyo a fusace zatayi fada ganin ni ne sai tayi
dariya"Lah Yayana ashe kai? Ina yininku." Muka
amsa,nayi dariya"Halan hankalinki baya nan?"
Tace"Uhm wallahi yayana Yarima ne yazo yana
can
gidan gwaggo dije(dayake dan yayan mijinta
ne)shine zan tafi." Badamasi yace"Wai ni sai naji
kodayaushe kina Yarima Yariman ina ne haka?"
Muka tuntsire da dariya harda Hafsa. Bahijja ta
tsaida dariyarta cike da wasa take hararar
badamasi"Kaji
min yaya badamasi da neman rigima,yariman
zuciyata ne kaga kuwa yafi kowane yarima."
Badamasi yace"Eh lallai da gaskiyarki." Wayarta
tayi
qara ta dubeni a marairaice"Don Allah bani
yayana
bana haka dakai." Na miqa mata alokacin da take
duban hafsa"Hafsa kenan,kuna budurinku,ki dai
kula da yayana domin babu irin lauye lauyen so
da
bai kwantar dashi ba zamanin....." Nayi kanta zan
janyo da gudu ta qara gaba tana dariya,mu
dinma
dariyar muke. Na dubi hafsa"Sai anjiman ko?" Ta
gyada kanta sannan ta shige muka juyo muka
taho. Badamasi yace"Bahijja ba dai 'yar tsokana
ba." Nayi
murmushi"Kaidai bari yarinyar ai ta gama
rainani."
Koda muka isa wajen su imam,hira sosai aka
shiga yi
suna mana iskanci wai tadi mukaje. Nan dai
muka
cigaba da hirarmu har saida magriba ta kawo kai
muka rabu dasu bayan na bawa kowannensu
katin gayyata dinner.Zaharaddeen   Shomar

Whatsapp   08168575100


Amadu 1 page 7
Posted by ANaM Dorayi on 04:16 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
Bayan sallar isha'i nima nayi wanka na shirya
cikin gogaggiyar shaddata kalar sararin
samaniya,kamar dai yanda aka ce zai kasance
shigar maza. Na sanya bulun hulata,Bukar kuwa
wanke fuska kawai yayi ya murza farar hoda ina
yi masa dariya"Kaidai sai kace wata mace,meye
na sanya hoda kuma?" "Au kai baka san wasu
mazan ma har jan baki sanyawa suke ba? Toh ai
yawanci 'yan film sai an shafa musu hoda ire iren
finafinan india har jan baki ake sanya musu. Da
'yar jagira." Mukayi dariya nace "Toh Allah Ya
kyauta." "Amin dai,saida muka gama shiri sannan
na rufe kofar domin dai ango gidan abokinsa
Abdul ya tafi shiryawa daga nan zai fito. Motar
Abba na karba,muka nufi can babban gida.
Motoci ne birji ga 'yan mata anyi kwalliya cikin
pink din leshi mai adon bulun fulawoyi. Kowacce
na ji da kanta,muka tsaya a lokacin ne na kira
Badamasi"Ya ka taho?" Yace"Gani yanzu nake
shiri." "Ok sai ka fito." Na ajiye wayar,Bukar
yace"Don Allah ka taho mana da wannan kanwar
taka ta zo nan mu tafi da ita." Na dan
harareshi"Me kake nufi toh?" Yayi
murmushi"Haba abokina ai kaima dai kaje
gano,wallahi yarinyar ce tana burgeni ko don
nustuwarta." Nayi murmushi raina ya dan
sosu"Toh an mata miji a gida sai hakuri kuma."
Yace"Kaine mijin kenan." Na ja tsaki"Idan ma
hakan ne bazan qi zahra ba saidai kasan so
daban yake idan kana yi kanayi idan baka yi
bakayi,toh ni aminiyarta nake so." Bukar yayi
murmushi"Ni kuwa sai nake gani kamar ita din
ma kana sonta ganin yanda ka damu da
lamuranta." Na harareshi"Idan damuwa da
lamuran mutum shine so toh bahijja ma sonta
nake. Don Allah kada ka dameni." Yayi
dariya"Allah Ya baka hakuri mutumina." Na zaro
wayata na kira hafsa,ta dauka"Beauty kuna ina
ne?" Cikin sanyin murya tace"Gamu mun fito." Na
dan wur wurga ido sai na hangota tsaye,tun daga
nesa take haskemin ido nayi murmushi"Na
hangeki,taho gaba gani kusa da bishiyar nan."
Muka hada ido da ita ta kashe wayar. Na dubi
Bukar"Malam sai ka koma gidan baya." Bukar
yace"Au abun 'yar haka ce?" Nayi dariya"Hakane
mana,waye bazai so zama da masoyiyarsa ba?" A
can kuma hafsa ta dubi Zahra wacce itama tayi
kyau har ta gaji"Ga yaya ahmed can yace muje."
Zahra ta tdan yamutse fuska"Kuje motar yaya
faisal zan hau." Hafsa da lubna sukayi
dariya"Lubna tace"Eh lallai soyayya dadi,ashe
haka yaya faisal ya samu shiga amma ake wani
sha masa kamshi." Zahra harararta kawai tayi ta
dauke kai domin duk haushinsu takeji,wani irin
kishi ke addabarta,hafsa tana dariya taja hannun
lubna"Toh ai shikenan sai kin taho." Zahra itama
tayi gaba saboda hango motar faisal da tayi yana
kokarin fakin. Bukar yana dariya bude ya fito
daga gaban motar daidai lokacin hafsa da lubna
suka iso. Na bude mata gaba ta zauna lubna ta
zagaya ta shiga baya,numfashina ne ya dan
dauke na 'yan sakonni ina duban Hafsa,itama sai
ta saci kallona ta sakarmin murmushin nan nata
mai qara mata kyau,ai sai naji na fara fita
hayyacina. Bukar ne ya katseni"Malam muje
mana,wayarka ma tana ringing ka tafi uwa
duniya." Muka sanya dariya harda lubna,ita kuwa
hafsa kunya ce tasa ta rufe fuskarta. Badamasi
ne ke sanar dani ya kama hanya,nace nima
ganinan. Sai bayan na ajiye wayar na lura babu
Zahra,na dan daure fuska"Lubna ina Zahra?"
Lubna na dariya tace"Hum,yau tana motar
masoyinta." "Wa kenan?" "Yaya faisal mana."
Nayi shiru sai kuma na ja tsaki. Na ja muka tafi
bayan na ware mana waqar nan ta hausa"jinin
jikina."
Wajen a cike yake taf da 'yan uwa da abokan
arziki. Toh shagali ne bana mutum daya ko biyu
ba,a'a har mutane uku. A babban dakin taro na
Afficent ne,gayu kala kala sun cika wajen. Can
gefe
na hangi Badamasi tare da mutanensa,na qarasa
garesu bayan nace hafsa tayi jirana. Muka qara
gaisawa,lokacin angwaye da amaren basu iso ba.
Muka dunguma sai dakin taron. Kowa ka gani ya
cakare cikin anko,gaba daya mazan wajen kalar
bulun shadda ke garesu yayin da mata akayi
shigar
pink lace mai adon bulun fulawoyi. Can na hangi
Zahra tare da faisal,cikin sa'a muka hada ido da
ita,ita ta fara janye idanunta,sai ma na qara
mamakinta,wai
zahra ce ta dauke kanta daga kallona? Na lura
ma
kamar tana cikin damuwa ne,maganar Hafsa ta
katseni"My heart ya ka tsaya?" Na juyo ina
dubanta
ina murmushi muka jera muka shiga sai kace
couples. Bayan an zauna babu jimawa sai ga
angwaye sun iso,suma kalar shigarsu kenan
saidai
nasu tsadaddu ne. Kowannensu ya haskaka tare
da
da amaryarsa. Ana cikin gabatar da shirye
shiryen da
akayi hafsa tace"My heart kaga baba ya kira har
sau
uku,zan tafi." A tsorace ta mike,nima na mike ina
mai
chanja fuska cike da tausayin kaina nace"Yanzu
haka zaki tafi ki barni maraya?" Tayi dariya
tace"Ai
kaine abin ji kada ka samu wata ka manceni."
Nayi
dariya"Ai ni da kaina zan kaiki kada ki damu.
Banga
wacce zata iya tsonemin ido ba bayan ki." Tayi
murmushi a lokacin da muka iso daidai saitin su
Zahra ta sunkuya"Qawata zan wuce,ina yini." Ta
gaida faisal,ni kuwa na mika masa hannu yana
wani
dauke kai,na watsar dashi gefe ko ita zahra ban
kalla
ba nayi gaba na barsu tare da hafsa. A mota
suka
iskeni,na budewa hafsa ta zauna,Zahra
tace"Nagode
Hafsa sai mun hadu a school." Na dubi Zahra da
sauri"Kanwata zo muje kiyi min rakiya mana."
Tayi shiru,hafsa ma ta sanya baki sannan ta
bude gidan
baya ta shiga,daga fuskarta na gane cewa bata
so
ba. Ko a jikina domin dai hakan ya fi min da dai
ta
koma wajen faisal. Na ja muka tafi,a mota ma
shiru
kamar bata ciki,ni da hafsa muna ta hirarmu.
Zahra
takaici ya isheta,kuka kawai takeyi ciki ciki
batason su ji ta,dama tasan wulakantata yaya
ahmed yayi
niyya shiyasa ya matsa sai ta biyoshi. Zuciyarta
sai
tafarfasa takeyi,ta kwantar da kanta jikin kofar
motar
tana kallon titi kirjinta na zafi. Haka har muka
iso,nan
ma na dubi Zahra"Kanwata minti biyu please."
Ban
jira amsarta ba na fito,saida mukayi sallama da
hafsa sannan na shiga na dubi zahra cike da
wasa nace"Au
kanwata dawo gaba mana,kada a tashi taro
muna
nan kinji?" Ta shareni,na kuma magana sannan
ta
fito ta shiga. Na ja mota cike da nishadi,na juyo
ina
cewa"Saurayinki zai nemeki ya rasa bazaiji dadi
ba
fa." Tayi murmushi batace komai ba. Sai lokacin
na lura da yanayin fuskarta,kafin nayi magana
wayata
tayi qara,Badamasi ke tambayar ina nake?
"Ganinan
tafe dallah,na sauke hafsa gida ne." Mukayi
sallama,sai lokacin na dubi Zahra"Kanwata meya
faru
tunda muka taho na lura kina tare da damuwa?"
Zahra tayi shiru,a gaskiya bazata so ya gano
halin da take ciki game dashi ba don haka
tace"Bakomai
wallahi yaya ahmed kwana biyun ne banjin dadi."
Nayi murmushi"Allah Sarki,Allah Ya baki lafiya."
Ta
amsa a hankali. Koda muka koma ana ta cin
abinci,ina ganin faisal yana watso min wani
mugun
kallo. Na dauke kaina ina murmushi domin ko
banza na nuna masa isata,na nufi can wajen su
Haidar. Sai
na hangi Badamasi da wata budurwa ana ta
hira,na
zauna ina dubansu"Ashe mutumin nawa Allah
Yayi."
Sukayi dariya,Kabiru yace"Atoh,mu kam bazamu
kula kowace budurwa ba kada labari yaje kunnen
'yan matanmu suce sun fasa auren." Muka qara
yin dariya. Haka aka watse daga taro kowanne
yana mai
jin nishadi. ******************************
************ Antin a fusace ta dubeta"Don
ubanki
bana gargadeki da kada ki qara shiga harkarsa
ba?
Shine har da barin dan uwanki ki hau motarsa?
Toh
uwar ina kuka je?" Zahra ta dago kanta ta dubi
antinta"Hafsa muka kai gida." Anti ta
harareta"Wallah
i idan baki fita hanyar yaron nan ba sai na koya
maki
hankali. Duk kaffa kaffar da nakeyi kada ubanki
yaji
batun nan yace zai muku auren zumunci amma
ke
don iskanci sai kin nuna wa duniya kina sonsa
ko?!
To kiyi azamar chanja tunani wannan ba mai
yiwuwa bane wallahi." Zahra dai kuka takeyi
kawai
Kwana uku da bikin yaya usman,ya koma Lagos
da matarsa. Ranar alhamis wajen karfe uku nayi
niyyar kaiwa Kawu na brigade ziyara. Brigade
shine
ainihin unguwarsu mahaifiyata. A can danginsu
suke
da zama,mahaifinta wato kakana Malam Illiya ya
jima
da rasuwa tun mahaifiyata na raye,hakama
kakata wacce ta haifeta da kuma kakana wanda
ya haifi
mahaifina. Malam Yahaya shine sunan mahaifin
babana,malam muttaka. Yana da mata
biyu,Uwargidansa Gwaggo basira tana da 'ya'ya
biyar,dan ta na farko Murtala,sai
Lawal,shamsu,ha
mza da kuma autarta Yahanasu ake kiranta Yaha.
Sai kuma amaryarsa gwaggo fatima tana da
'ya'ya uku
Abba(mudi)shine babban danta sannan
mahaifina
Muttaka sai autarsu dije. Malam yahaya
malamine
babba a fannin addini shine headmaster a wata
makarantar islamiyya. Ya bawa 'ya'yansa
tarbiyya
daidai gwargwado. Babban dansa kawu murtala
ya kasance mai son kasuwanci,hakan yasa koda
malam
yahaya yayi shawarar sanya yaransa maza kadai
a
boko yace shi sam bazaiyi ba. Ba'a takura masa
ba ya
fada harkar kasuwanci inda yake tsaron shagon
wani bayarabe anan sabon gari. Shi kuwa Abba
yafisu murna da wannan magana ta malam
domin bashi da burin da ya wuce ya ganshi a aji
yana
daukar darasi. Gaba dayansu sunyi murna ba
kamar
dai Abba ba wanda ya fisu kaunar karatun.
Iyayensu
kuwa basu damu ba domin basu takura akan
lallai
sai sunyi ba idan suna so suna iya yi idan kuwa
basu
ra'ayi shikenan,malam yahaya baida ra'ayin
'yarsa mace tayi karatu a cewarsa aure shi yafi
ga 'ya mace
wanda zata samu ma a fannin arabi ya wadatar.
Gaba
daya aji daya na primary aka tura su,karatu
sukeyi
sosai,saidai da kwanaki suka soma ja,shima
kawu
hamza ya tubure ya bar zuwa don ko an turashi
saidai ya gudu can wajen wani abokinsa mai
aikin kanikanci ya zauna. Toh shima sai malam
yahaya ya
tsigeshi aka barshi. Kawu lawal da shamsu da
kuma
mahaifina da Abba sune suka bada himma wajen
koyon karatu. Cikin hukuncin Allah har suka
gama
primary suka shiga secondary,amma sai Abba
yafisu
kyakkyawar takarda hakan yasa aka sanyashi aji
biyu a secondary yayinda suke a aji daya.
Alokacin
ne aka aurar da gwaggo yaha da gwaggo dije.
Gwaggo yaha tana da shekaru goma sha uku ita
kuwa dije tana da shekaru goma sha biyu. Babu
dadewa shima Kawu murtala yayi aure da Nafisa
(Nafi) anan babban filin tsakar gidan aka gina
musu daki falle daya da 'yar tsakar gida kicin
kuwa daya
ne a gidan na kowa da kowa. Bayan bikin da
wata
bakwai ciwo ya kama gwaggo basira,hankalin
kowa
ya tashi domin kuwa an rasa gane kan
ciwon,magungunan gargajiya ake ta dura
mata,Abba ke yawan cewa a kaita asibiti amma
malam yace sam baza'a je ba ai ba zasuyi
abunda
Allah bazaiyi ba. Don kanta gwaggon tace ta gaji
a
gwada zuwa asibitin a gani. Gwaggo fatima ta
dubi
malam yahaya"Toh malam tunda mai ciwo tace
aje
sai aje mana a dubata ita kadai tasan me take ji
a
jikinta." Sai a sannan ya amince aka je likita yace
ciwon qoda gareta har ya ci qarfinta,nan yayi ta
fada
akan me ba'a kawota da wuri ba daga karshe dai
ya
bata gado,gwaggo fatima ke kwana a wajenta sai
wata kanwar gwaggo basira, satinta daya Allah
Ya
karbi abarSa,sun ga tashin hankali kwarai da
gaske
koda yaushe gidan idan kaje yi musu gaisuwa
kamar a ranar ta mutu. Gwaggo fatima kanta ta ji
mutuwar
kasancewa zama sukeyi na aminci da gaskiya
tsakaninsu,malam yahaya shima har rashin lafiya
yayi domin mutuwar uwargidan tasa ta girgizashi
kwarai. Toh har dai akayi watanni uku sannan
suka
samarwa kansu nutsuwa suka aminta cewa
wanda ya mutu ya mutu ba zai dawo duniya
kenan ba. A
kwana a tashi babu wuya wajen Mai Tsara
lamura,
Abba ya kammala karatun secondary
dinsa,malam
yahaya yaji dadi musamman ma yanda abba ya
sha
yabo a wajen malamansu na makaranta saboda
tsabar hazaqarsa,da farko malam yahaya ya qi
amincewa da cigaban karatun Abba,amma ganin
yanda kowane malami ke cewa kada ya hana
abba
cigaba yasa ya yarda ya kyaleshi. Ya wuce BUK
yana
karantar Bussiness. Shi kuwa mahaifina shima
daga
sakandire yace bazai iya cigaba ba,kamar hadin
baki
su kawi lawal suma suka dire karatun
kowannensu ya fada kasuwanci. Shekara uku da
fara karatun
Abba,ya auri Inna salamatu. Itama 'yar garin
kano
ce,ta gama karatunta na sakandire a ra'ayin
mahaifinta saidai tayi aure. Sun hadu da Abba
sanadin wani yayanta Alhaji Yusuf wanda ya
kasance
abokinsa. Soyayya sukayi sosai da Abba toh a
lokacin kuma sai mahaifinta ya bullo da batun
aure,Abba yaso ya bari sai ya qare
karatunsa,amma
yanda mahaifinta ya bude wuta aurar da 'yarsa
yake
son yi idan bai shirya ba ya barwa wani ya aura
yasa
hankalinsa ya tashi ya samu malam da
batun,malam
ya bashi shawarar ajiye karatun yayi
kasuwanci,hakan kuwa yayi domin a lokacin
yanda
yakeson inna gani yake komai zai iya bari. Allah
Ya
dafa masa ya soma kasuwancin saro dan kunne
da
sarqa anan cikin kasuwar kano yana
siyarwa,shima
dai nan aka yanka akayi masa gini irin na kawu
murtala ya sanya inna salame. A lokacin matar
Nafi ta haifi 'yan biyu duk mata amma Allah baiyi
sun kai
wani lokaci ba suka rasu. Ta qara samun wani
cikin
shima tayi barinsa yana da wata hudu. Gwaggo
tana
kula dasu gaba daya ta daukesu abu daya,bata
bambantasu da 'ya'yan cikinta,hakan yasa suma
suka dauketa tamkar uwa. A shekarar da aka
auro inna salame ta haifi yaronta namiji wato
yaya usman.
Yana da wata hudu a duniya akayi bikin
mahaifina
da mahaifiyata safiya wacce itama ya hadu da ita
anan brigade. Ita ce babba a mata a gidansu
sannan
anti aisha sai babban yayansu kawu buhari da
masu
bi masa kawu hasan da kawu husaini. Lokaci
daya aka hada dana kawu lawal da matarsa
kubra(larai),
sannan kawu shamsu da ladi da kawu hamza
shima
da matarsa sadiya. A lokacin sai Malam yahaya
ya
tashi daga gidan gaba daya ya koma wani gidan
haya dake kallonsu saboda yace da kunya ya
zauna
dasu. Aka maida gidan mai bangare biyar
kowannensu da nashi. Zama ne sukeyi da dadi
babu
dadi,mahaifiyata ta kasance mai hakuri sosai ko
kadan bata da hayaniya. Tun zuwanta tana
matukar
kokari wajen yin biyayya ga matan yayyan mijinta
wato inna salame da nafi amma su kam da gayya
suke sanyata aikin wahala. Sai ta yini tana
aiki,su larai kuwa basu da ikon sanya hannu nan
inna salame
zata hau sababi,kyawunta duk shi yafi tsone
musu
ido da iya girki da tsafta. Domin a ranar girkinta
idan
ta gama komai na wajen zaka ganshi fes kamar
dai
yanda dije ta labarta mini. Jininsu sam bai hadu
da
inna salame da nafi ba. Nafi tana shigewa inna
salame saboda kwadayin abun hannu kasancewar
ita din mahaifinta yana da rufin asirinsa daidai
gwargwado. Toh shima mahaifina bai fiye sanya
baki
a maganarsu ba,wataran ma yana ji zasuyi mata
amma ko uffan baya cewa saboda a ganinsa me
zaisa shi shiga harkar mata? Saidai ya zauna
yayi ta bawa mamana hakuri. Haka ta shanye
komai,abun
Allah har mahaifiyata tayi shekaru biyu bata
haihu
ba,lokacin su larai sun haihu. Toh anan din ma
sai
suka sanya mata kahon zuqa,ba dama ta motsa
zasu
bita da habaici,larai kuwa sai ta zama munafukar
cikinsu. Idan mamana batanan ta zauna suyi tayi
da ita idan ta dawo ta nuna ai ta mamana takeyi.
Mamana duk tasan da hakan amma ko kusa bata
damu ba,ladi kuwa bata da yawan magana sai ta
yini
a daki bata damu da fitowa tsakar gidan hira
ba,ita
kuwa sadiya sai ta zama aminiyar mamana
kowace
shawara tare suke yinta. A lokacin ne kuma Allah
Ya dauki ran malam yahaya sakamakon hatsari
da yayi
a hanyarsa ta dawo daga makaranta. Nan ma
anyi
jimamin mutuwar kwarai dagaske kafin hankali
ya
natsa.
Haka lamura sukayi ta tafiya,Inna salame ta qara
haihuwar 'ya mace,kubra,yayinda Nafi ta haifi
'da
namiji aka sanya masa sunan malam,wato
yahaya
suke ce masa baba karami.
Rayuwar mamana ya kasance cikin matsi daga
inna
salame. Sai kuma Allah Yayi ta budawa Abba har
ya yi gininsa na zamani sosai. Flathouse ne mai
bangaren
mata biyu sai kuma bangarensa,sannan dakin
zaure,kicin daya ne a gidan. Kowa yayi masa
murna,inna salame aka shiga ji da kai ana
dagawa.
Habaici kala kala take watsawa,a lokacin hatta
da
nafi da suke mutunci bata ragawa ba,alokacin ne
jikin nafi yayi sanyi sai ta ja baya da ita. Suka
tashi
daga wannan gidan. Saidai ta sha jinin jikinta da
taga
Abba yayi ginin mata biyu. Koda ta tambayeshi
bai
boye mata ba ya sanar da ita aure zaiyi. Ai fa
farin
cikin komawa sabon gida ya gushe a wajen inna
salame,haka tayi ta ruwan bala'i ga tsohon cikin
Abida da take dashi,amma ko tunanin hakan
batayi
ba. Karshe dai Abba ya korata gida yace ta tafi
ya
gaji. Bakin ciki kamar ya kasheta to da yake
lokacin
fushi take yasa tayi zuciya ta bar gidan abinta.
Bayan
tafiyarta ne kuma da kwana biyu akace ya rasa
sukuni yabi ya rame bashi da walwala. 'Yan
uwansa suka damu sosai,ya shiga zarya gidansu
inna
salame,tace fir bazata koma ba. A gefe kuma
dadi
take ji yanda take gasa shi,akwai sa'adda ya turo
dije
ta roqeta tayi murmushin mugunta tace"Dije
kenan,kina zaton dan uwanki ya isa ya rabu dani
ya
zauna lafiya har ya samu damar auren wata?
Wallahi wannan qarya ne,ni kadai ce zan zauna
da
mohd,banda kuma wata 'yar iskar data isa ba.
Wannan shine furucin da dije tace inna salame
tayi
gareta a lokacin,ai kuwa gaskiyarta domin kuwa
koda kawu murtala yayi maganar batun kudi da
za'a
kai gidan wacce yake so 'yar wani mai
unguwa'Maijidda' cewa yayi ya fasa bazaiyi ba.
Dakyar dai suka shawo kan inna salame tace idan
ta
haihu zata dawo,yaya usman yana hannun
gwaggo
yayinda kubra ke wajenta. Tana haihuwar da
kwana
arba'in ta dawo gidan tana mai jin dadi tayi
nasara.
Haka zancen aure ya watse abba ya manta da
batun aure sai hakuri aka bawa iyayen maijiddan.
Cikin
hukuncin Ubangiji,Mamana ta samu ciki. Zo kaga
murna wajen ta da baba,haka ya kasance ko ofis
yaje hankalinshi yana gareta. Cikin na da watanni
bakwai,babana ya rasu,lafiya lau ya bar kasuwa a
hanya zai shiga mota ya dawo aka ga kawai ya
kife a wajen ashe rai har yayi halinsa. Allahu
Akbar!
Mahaifiyata ta shiga matsanancin tashin hankali
sosai,gwaggo kuwa saida tayi rashin lafiya na
kwanaki itama har an fidda rai cikin hukuncin
Allah
kuma ta warware. Abba ma ya shiga wani hali na
rashin dan uwansa wanda ya kasance kamar
amininsa,domin duk wani abu da zaiyi yana
neman
shawarar babana yana cewa Muttaka kanina ne
amma kamar yafini hankali da hangen nesa.
Mamana
duniya tayi mata zafi taso ta koma gida,gwaggo
tace
sam ta zauna tayi takaba a dakinta. Anti Aisha ce
tazo
ta zauna a wajenta har ta fita takaba. Nan ma
dai gwaggo ta roqi arzikin ta zauna wajenta har
ta samu
mijin aure.
Haka mamana ta zauna tana rainon cikinta,duk
ranar
da inna salame tazo gidan kuwa ai ta shiga uku
domin iyayi kala kala take yi tana jefa habaici.
Mamana bata taba tanka mata ba,sai kuma wata
sabuwa,abba ya soma kula da lamarin mamana
sosai,duk sa'adda yazo gidan. Nan ma dai aka
samu
wata munafukar ta sanarwa inna salame,ya
rantse
shi ba son mamana yake ba,kulawa ce kawai
saboda
kwadayin yaga gudan jinin kaninsa. Wannan ma
ta
qara sanyawa inna tsanar mamana. Gwaggo ce
ta shiga zancen tace ya bar zuwa. Domin kuwa
abun ya
soma isarta,duk sauran 'yan uwansa babu wanda
ake jin wani abu akansa shi da iyalinsa,kamar
yanda
ake jin tashin tashina ana Abba. Mamana tana
yawan
kebewa tayi kuka ta koshi,ita dai gashi dangin
miji
na kaunarta amma bata san me ta tsarewa
facalarta ba. Anti Aisha tayi aure a lokacin,tana
yawan zuwa
wajen mamana tana debe mata kewa.
Kodayaushe
mamana bata da buri sai ta haihu lafiya taga mai
kama da mijinta. Anti Aisha ta kanyi mata dariya
da
addu'ar sauka lafiya. Ana haka wataran ta tashi
da
nakuda azababbiya,har ta galabaita,ganin dai ta
dauki lokaci bata haihu ba suka yi asibiti da ita.
Bayan haihuwata Allah Ya dauki ranta. Babu
wanda
baiji mutuwar nan ma.daidai da inna dake
maqiyarta
saida jikinta ya danyi sanyi.
Bayan an share makoki,Anti Aisha tace zata
daukeni,nan Abba ya tubure yace sam,shi zai
rikeni. Dakyar aka rarrasheshi ya yarda ta karbeni
ta shayar
dani har nayi wayo. Ta tambayi iznin mijinta ya
amince da hakan. Ina da shekaru uku Abba ya
karbeni,inna salame bataso hakan ba domin qiri
qiri
take nuna tsana a gareni. Wataran ma kwanan
waje
zanyi ga sanyi da ake fama dashi a garin amma
ko kusa babu tausayi. Yaya usman shima haka
na zame
masa bawa komai ni nake yi masa,sharar dakinsa
ne
da sauran su lokacin ina da shekaru goma. Ga su
Anti Abida itama haka zasu sanyani aiki,ban isa
na qi
yi ba,ni ne boyi boyinsu. Cikin ikon Allah mai
Mulkar
bayinSa,rana daya Abba yace aure zaiyi,toh
fa,Abba ya ballowa kansa ruwa sosai,amma
karfin addu'a da
gwaggo ta yawaita yiwa dan ta da kuma rabo da
ya
rantse inna batayi nasarar hana Abba aure ba. Ya
auro Anti Amarya ya kawo gidan.
Zuwanta bai sa na samu sauki daga wannan
halin
matsin rayuwa da nake ba. Sai abunda ya
qaru.Akayi
auren kubra da Abida suna aji daya a sakandire
basu
qarasa ba suka ajiye saboda kwadayi irin na
innarsu
ta aurar dasu ga 'ya'yan masu rufin asiri.
Shekaruna
sha daya a duniya aka haifi Zahra. Tun sadda aka
haifi yarinyar ta shiga raina haka kawai naji ina
kaunarta ko don babu wani yaro a gidan? Oho.
Duk
a shekarar ne Abba ya chanjamin,sai ya zamana
ina
gama primary inna ta hana na koma a cewarta ni
yaro ne har yanzu ban kai a sanyani a sakandire
ba.
Ita kuwa mariya tana aji biyu a primary. Abba ya
bada goyon bayan haka,lokacin sai abunda inna
ta
gindaya a gidan toh dashi kowa zaiyi aiki. Ko anti
saida ya kasance tana tsoranta shiyasa bayan
haihuwa ta tattara ta tafi gidan iyayenta don
wanka.
Na zama maraya na sosai,duk wani aikatau ni
nake
yayin da kanwata mariya ke zaune. Toh a lokacin
kuma sai nake zuwa wajen baba maigadi,nan
nake
zama wani sa'in tare muke cin abinci idan gidan
sun
hanani. Wataran ma da kuka zanje masa ina fada
idan inna ta dokeni,ko kuma anti amarya idan na
taba mata 'yarta. Haka baba maigadi zai
rarrasheni ya
bani hakuri ya nuna min su iyayena na dunga
hakuri da duk abunda zasuyimin. A haka
rayuwata ta
dunga gagari a gidan nan. Akwai sanda bazan
manta ba inna ta aikeni na zubda kudin,a ranar
yini
nayi ban ci abinci ba ga baba maigadi baya nan
ya
tashi aiki saboda a lokacin su biyu ke gadi,sai
gidan
kakarmu naje na ci. A lokacin ne cikin hikima irin
tasu ta manya ta tambayeni yanda nake zaune a
gidan,nan na zayyane mata komai. Sai kawai ta
fashe
da kuka tana salati,hakan ya jawo hankalin 'yan
gidan. Nan suma sukaji kowannensu ya shiga
tofa
albarkacin bakinsa. Cewa suke ai daga gani zasu
aikata. Gwaggo ta kira Abba ta bude masa
wuta,nan kwallah tazo masa ya nuna shima abun
na damunsa
ya rasa hanyar da zai bi ya magance ne. Takaici
ya sa
gwaggo tace ya bar mata gidan kuma nazo kenan
bazan koma gidansa ba tunda bazai iya rikon
'dan
dan uwansa ba. Yayi ta bata hakuri har su kawu
suka sanya baki amma tace sam bada ita ba. Har
saida nayi shekaru uku a hannun gwaggo,inna na
mulkar Abba yanda taso sai abunda tace
akeyi,kai a
lokacin Abba har daina zuwa gaida mahaifiyarsa
yayi,takan yawaita kuka tace yau mata sun
rabata da
'danta. Zamana a gidanta ya fimin kwanciyar
hankali
ma domin kodayaushe ina bin kawu murtala
shagonsa ina tayashi saye da siyarwa. A cikin na
goma sha hudu ne kuma sai rannan kwatsam
mun
dawo daga kasuwa tare da kawu sai muka ga
Abba
a gaban gwaggo ya durkushe yana rafsar kuka.
Gwaggo kuwa ko kallon inda take batayi ba,nan
yace kawu ya sanya baki ta yafemasa kada ya
fada wani hali,shi wai a kwanakin baisan
damuwarsa ba
kawai ya tsinci kansa da mantawa da lamuran
'yan
uwansa. Ita kuwa gwaggo cewa take yaje ta
barwa
inna da anti tunda su ya zaba akanta. Dakyar dai
gwaggo ta sauko ta bar fushi. Abba yace indai ta
sauko toh ta bashi ni,gwaggo tace sam zan
cigaba da zama a hannunta. Hankalin Abba ya
tashi yayi ta bata
hakuri nan ma saida akayi mata taron dangi har
dasu
Gwaggo Yaha sannan ta yarda bayan tace indai
irin
haka ta qara faruwa toh zaiji ba dadi a wajenta.
Tun
da na dawo zamana yayi dadi a gidan,ba laifi
Abba
ya dauki kwakkwaran mataki akan takuramin da
akeyi da aikace aikace. Inna itama tayi sanyi da
wannan ikon nata domin a yanda na lura Abba
ya
daina shakkar kowa a cikinsu,idan ya zartar da
umarni dole a bi. Ya maidani makarantar
sakandire
na cigaba da karatuna. Zahra ta fara karatunta
daga
nursery one tana da shekaru biyar,yakasance
mun
shaku da ita a lokacin,anti amarya ta sha marina
idan
ta ganni da Zahra,maimakon nayi kukan sai
zahra
tayimin,kodayaushe ina nuna mata babu komai
kada
ta damu. Yaya usman shima ya kusa kammala
karatunsa. Mariya ma dai ko sakandiren bata
shiga
ba tace bata son karatu,kasancewar inna mai son
'ya'ya ce sai ta biye mata Abba zai matsa tace ai
aure
sunna ce tunda ta nuna shi takeso sai a
kyaleta,shima ai yayansa ko karatun baiyi ba
balle
yace wajibi ne. Wannan shi ya kashe bakin
Abba,yace shikenan. Akayi auren mariya tana
'yar
shekaru goma sha hudu. Haka rayuwa tayi ta
miqawa har na gama sakandire na tafi
jami'a,zahra
kuma aka zama 'yan sakandire. A lokacin ne na
qara
shaquwa da anti aisha,ya zamana kodayaushe
ina
gidanta,domin tausayi take bani bata da 'da ko
daya
gata da son jama'a kodayaushe zaka ganta da
yaran
maqota. Alokacin yaya usman ya samu aiki a
Lagos ta hanyar Yayan inna kuma abokin
Abba,Alhaji
Yusuf. Wannan shine tarihina a takaice.*******
Ko gidan ban shiga ba na fito,yayi daidai da
tsayuwar motar Abba,na tsaya har ya faka. Na
durkusa cike da girmamawa na gaidashi,ya amsa
fuska a sake sannan yace"Au baka tafi ba?" Na
shafi
kaina nace"Yanzu zan wuce dai." Yace"Toh
madallah." Sannan ya zura hannu cikin aljihun
wandonshi ya miko min kudi yace"Gashi a bawa
kawun,ace ina gaisheshi." Na karba nayi godiya
sannan yace"Karbi mukulli wajen hassan sai kaje
ko?" Cike da jin dadi na amsa nace"Allah Ya qara
girma." Yayi murmushi"Amin,sai ka dawo."
Nace"Toh." Ya shige ciki,hassan ya miqomin
mukullin yana dariya"Allah Ya ji kanka bazaka
sha rana ba."
Nima dariyar nayi ina kallon sararin
samaniya"Kaidai
bari ai yau garin sai godiyar Ubangiji."
Yace"Hakane."
Mukayi sallama ya leqa gidan domin amsar abinci
ni
kuma nayi ribas na bar layin. Farin ciki wajen
bayin
Allahn nan kamar me,suka rasa inda zasu
sanyani. Matar kawu Buhari nan ta shiga hidima
dani,koda
kawu ya dawo ya ganni shima yayi mamaki
kwarai
ya zauna muka gaisa yace"Oh Amadu ashe rai
kan
ga rai?" Sai ma ya bani kunya,nayi dariya"Wallahi
kawu lamura ne suke boyeni." Kawu yace"Toh
amma amadu komai girman lamuran ai bai kai
zumunci ba ko?" Na jinjina kai da
sauri"Gaskiyane
kawu kuyi hakuri." Yayi murmushi"Toh ya wajen
Alhajin naka?" "Alhamdulillah,yace a gaisheku
ma."
Na fada ina mai zura hannu aljihu na zaro kudin
da
Abba ya bani wanda bansan adadinsu ba na
mika
masa. Ina cewa"Gashi ma yace a baku." Na miqa
masa kudin ya karba yana godiya sannan ya
sakomin batun aure da sana'a shima dai bayani
nayi
masa na yanda mukayi da Abba. Ya nuna farin
cikinsa da hakan,amma sai yace" toh kai kuwa
Amadu don kawai Mudi yace haka shikenan sai
ka
zauna haka bazaka cigaba da kokarta nema ba ko
Allah zaisa a dace? Kada ka zama ragon namiji
fa
amadu." Na qara ladabtar da muryata jikina
kuma sai
yayi sanyi,ina kishin kaina da nake cewa inayi?
Ina
ikrarin da nake yawan yi na neman kaina? Na
tsayawa da kafafuna? Amma dai Allah shaida na
nema na neman ban samu ba."Kawu nayi iyakar
qoqarina wajen neman aikin nan amma har Allah
baiyi zan samu ba hakan yasa na tattara
takarduna
na ajiye gefe." Kawu yace"Haba Amadu,bai
kamata
ace ka karaya har haka ba,ka cigaba da
nema,ance
mai nema yana tare da samu kaji ko?" Na gyada
kai"Insha Allahu Kawu." Yayi murmushi"Toh
madallah." Sai da mukayi la'asar sannan na baro
Brigade.


Zaharaddeen  shomar

Whatsapp  08168575100Amadu 1 page 8
Posted by ANaM Dorayi on 04:24 PM, 01-Jun-15
Under: Amadu
A daren tare muka yini da Badamasi yana labarta
min batun budurwar da yayi mai suna Jamila
qawar Raliya. Ya cigaba da cewa"Gaskiya na
yaba da nutsuwarta sosai,tana da hankali da
sanin ya kamata." Nayi murmushi"Gaskiy
ane,jamila halayenta nada kyau." Ya saki ajiyar
zuciya yayi shiru,nace"Ya akayi?" Ya girgiza
kai"Ina tsoron kada itama ya kasance..." Na tare
shi"Please ka bar wancan maganar,ai ba duka
aka hadu aka zama daya ba Badamasi,nima dubi
yanda nasha wuya akan mace kafin na samu mai
kaunata tsakani da Allah. Nasan jamila a gun
Raliya babu ruwanta ina yawan jin suna
maganarta kada wannan ya dameka insha Allahu
da ita za'ayi." Mukayi dariya yace"Ai yanzu ma
daddy fushi yake dani wai na zama ragon namiji
tunda na kasa tunkarar mace,dama yaji sanda
nayi rayuwa a jami'a 'ya'yan hutu ake
kiranmu,toh bazai dauki iskancin nan ba,kada
naga yana da gudun bacin ran 'ya'yansa,wannan
daban ne sai wani ya tabasu amma bazai dauki
wannan ba." Mukayi dariya nace"Ai da
gaskiyarsa,ya kamata ace mu ma munyi auren
nan." Badamasi ya dan tabe baki"Lallai fa,mudai
Allah Ya yafe mana zunubanmu." Sarai na gane
abunda yake nufi,na amsa da amin. Amma ai a
baya badamasi sun yi harkar 'yan mata sosai.
Haka muka jima tare dashi har isha'i sannan na
rakoshi ya wuce gida. Na bi shawarar kawu na
shiga neman aiki,kodayaushe idan naje banki
babu sa'a. Wataran ma saidai naje idan layi yazo
kaina ace lokaci ya kure. Toh yau dinma haka
naje na gama zamana na gaji na taho. Na kare
rana da 'yar jakar dana sanya takarduna ina
tafiya a gefen titi. Hon naji ta bayana. Ban juyo
ba saboda ban dauka dani ake ba sai can kuma
naji shiru. A hankali naji wata murya tayi min
sallama,hakan yasa na juyo. Ai kasa amsawa
nayi na zuba mata ido a firgice,sanye take da
Katon mayafi ta rufe ko'ina na jikinta,ta zubamin
ido a sanyaye tana murmushi.MURJA?? Na
ambata cike da mamaki,sai naga
hawaye sun zubo mata tana murmushi a sanyaye
tace"Ni ce Ahmed,ina yini?" Har lokacin mamaki
da
fargaba ne suka mamayeni,dakyar na iya
amsawa"Lafiya." Tayi 'yar qaramar dariya tana
mai
share hawayenta"Allah Sarki Ahmed,don Allah ka
saki jikinka wannan ba murjar daka sani bace a
baya,wannan murjar kamilalliya ce,wacce ta tuba
ta
bar duk wani aiki na sabo da tayi a baya,wallahi
yanzu haka murjar da kake gani tsaye gabanka
aure
take shirin yi Ahmed,har an kai kudinta,na dade
ina
neman hanyar da zan ganka kai da amininka na
roki gafararku amma Allah baisa na samu ba.
Don
Allah
Ahmed ka yafemin don girman Allah." Sai gata
tana
shirin durkusawa,da sauri nima na dan rusuna
nace"Haba murja kada kiyi haka don
Allah,bakomai
magana ta wuce kada ki damu kanki wallahi."
Tayi
dariyar farin ciki,nima sai alokacin na saki
sassanyar ajiyar zuciya ina murmushin jin dadi.
Tace"Yauwa
nagode Ahmed,ina kuma ka nufa yanzu?" Na dan
daga kafada"Gida nayi daga banki." Tace"Ko
zamu je
na rage maka hanya?" Na juyo ina girgiza
kaina,tace"Don Allah kada kayi min haka." Tayi ta
roqona dole tasa na shiga motar ta ja muka tafi.
Tace"Ahmed nasan kayi mamakin hakan ko?"
Nayi
'yar dariya"Gaskiya nayi mamaki,domin wallahi
har
yanzu gani nake kamar a mafarki murja." Tayi
dariya
ta dan girgiza kai a lokacin da take shan
kwana"Hakane,bari na labarta maka.""Tun
lokacin
da muka rabu daku naji wani
mugun tsanar kaina Ahmed,ya kasance tun
tafiyarku
ina ta kuka a nan. Nan din dana kaika gidan
yayana
ne sunyi tafiya ne da matarsa,a sanadin zaka zo
ne
yasa naje har gida na dauko Ladi mai aikinsu na
bata
mukulli ta gyaramin ko ina saboda kai,wallahi
Ahmed ko a gidanmu babana bai san ina wannan
mugun halayyar ba,mamana kuwa babu abunda
bata sani ba amma bata taba nuna min aibun
abubuwan da nakeyi ba. Wallahi Ahmed na kasa
nutsuwa kodayaushe cikin damuwa nake tun
bayan
tafiyarku,sai kuma gashi a kwanan labari yaje
kunnen babana wani makowabcinmu ya sanar
dashi
yawace yawacen da nakeyi idan baya gari,dukan
tsiya baba yayimin ya sanyamin dokar daina
zuwa
ko'ina ya kwace mukullin motata,kai har takai ya
daina kula ko mamana yace ta tafi gidansu.
Dakyar
ya sauko ya barta ta zauna nan dinma saida ta
sanar da yayansa." Ta danyi ja numfashi,sannan
ta nemi
gefe tayi parking ni kam kallonta kawai nakeyi
domin hatta muryarta ta chanja ta koma ta
nutsatstsu. Kanta na duban yatsunta da take
wasa
dasu ta cigaba hawaye na diga akan
hannunta"Ahmed naji kunyar babana sosai cewa
yake ya daukeni mai hankali ashe dai ni mai
fuska
biyu ne a gabanshi na nuna ni din nutsatstsiya ce
ashe a bayan idonshi ina zubar da kimarsa ne a
unguwa,yana yabona yana kaunata duk cikin
'ya'yanshi. Ahmed tun daga lokacin babana ya
daina
shiga harkata,sai nayi kwana uku bani da kudi,ko
da suna cin abinci nazo zanci zai dakatar dani
yace na
koma za'a kawomin nawa. Suka ware ni,wallahi
da
kansa ya nemo min miji dan kanwarsa,yace dole
idan
inaso ya yafemin sai na bi umarninsa na yarda
na
auri tahir. Babu musu na amince,shine har aka
sanya
mana rana bayan na watsar da shashanci kuma
yace babu ni babu kowace irin kawa ga 'yar
uwata nan
ummu aimana ta isa nayi kawance da ita." A
daidai
nan tayi shiru,nima har lokacin kallonta nake ina
mai
jin dadin wannan hukunci na baban ta,ta dubeni
tana murmushi bayan ta goge hawayenta"Nagode
Ahmed babu abunda zan iya ce maka,har yau
idan na tuno da yanda na zubar da mutuncina
na
'ya
mace ina bibiyar maza babu ko kunya nakanji
haushi
da takaici sun cikani,ina mai matukar
nadama,nakanji kunya." Ta runtse ido ta dauke
kanta,nace"Allah Sarki,Allah Shine abun godiya.
Murja kenan,ki kwantar da hankalinki,ina tayaki
murnar auren da zakiyi. Allah Yana son bayinSa
masu
neman gafara. Komai ya wuce murja,Allah Ya
qara
kiyaye gaba,Ya baki zaman lafiya da maigidanki.
Kiyi
hakuri da kowace irin rayuwa zaki tsinci kanki
koda
nan gaba ne ina mai tabbatar maki dan uwanki
zai
rike ki bisa amana da gaskiya ki tsoraci Allah ki
rike aurenki. Babanki yayi gaskiya,a zamanin nan
duk
wani batanci daga kawaye ake daukarsa,kiyi
hankali
da wadanda zaki aminta dasu. Allah Ya bada
zaman
lafiya." Tayi 'yar dariya ta dauke idonta
akaina,lallai
na yarda ta shiryu domin bata fiye kallona tsakar
ido
kamar a baya can ba. Ta tashi motar"Nagode
Ahmed,insha Allah zan bi shawararka,ina zanga
dan
uwanka shima na roki gafararsa,duk da nasan da
wuya ya saurareni." Nayi murmushi"Zai saurareki
insha Allahu ma." Ta jinjina kai a lokacin data
harba
motar titi,wayarta tayi qara ta ciro ta daga. A
yanda
take wayar na gane da Tahir ne ta tabbatar masa
da lafiyarta kalau sannan sukayi sallama.
Tace"Tahir
kenan,yana sona kamar me,tun zamanin da nake
kan ganiya ta na iskanci bai taba yimin kallon
mara
mutunci ba kodayaushe burinsa na kaunace shi
amma sam bai min ba. Nayi dariya"Yanzu ai zai
yi
maki ko?" Mukayi dariya. Na kira badamasi na
tabbatar yana gida nace yayi jirana. Ya amsa
min. A
kofar gidansu mukayi fakin na dubeta"Ki jira nayi
masa magana." Ta gyada kanta na lura da sanyin
jikinta,nayi murmushi"Kada ki damu Murja
kwantar
da hankalinki." Tace toh. Yana zaune a falonsa
yana
kallo ga jakar ofis a gefe hakan ya tabbatar min
bai jima da dawowa ba.Na zauna kusa dashi ina
fadin"Kaga manyan
newscasters,kace hutu akeyi." Badamasi ya shafi
gashinsa yana dariya"Wane hutu? Ai aikin nan
bisa
dole nake yinsa wallahi don babu yanda zanyi
ne."
Nayi dariya ina mai jinjina kai"Kaidai wallahi rago
ne
na karshe." "Eh naji dai." Mukayi dariya yace"Toh
ya meye labari?" Nace"Akwai kuwa labari babba
kuwa,ga murja a gidan nan." Ai wani irin firgita
yayi
nan da nan ya mike tsaye a zafafe"Haba Ahmed
ya
zakayi min haka? Meyasa ka rakota gidanmu? So
kake daddy ya ci gidanmu kenan? Don Allah ka
hanzarta dakatar da ita ta bar gidan nan please."
Gaba daya na lura ya rikice,na dafa
kafadarsa"Cool
down dan uwa..." Ya dakatar dani ta hanyar daga
hannu,a fusace yace"Ya isa hakanan,nidai nace
kaje
kace ta bar gidan nan." "Haba dan uwa,wallahi
idan
kaga murja a yanzu zakayi mamakinta. Ta chanja
gaba daya,yanzun ma zuwa tayi ta nemi
gafararka." Ya harzuka"Ina ruwana? Dole ne sai
naje na ganta?!
Taje babu ruwana da tubanta." Sai a sannan
nima ya
bani haushi a fusace na bashi amsa"Ok,ka nuna
kai
din baka san ka yafewa wanda yayi maka laifi ya
nemi gafara ba. Allah kanSa yana yafewa
bayinSa,ka
kyauta bari naje na bata hakuri." Na giftashi rai a
bace na fito daga falon nasa,na sameta tsaye
jikin
kofar motarta tana waige waige,tana ganina sai
ta
dan gyara tsayuwarta. A sanyaye na qarasa
gareta,ta
dan yi hangenta bayana amma bata ga alamun
Badamasi ba. Ta dubeni a gajiye tayi
murmushi"Ahmed ya qi fitowa ko?" Zanyi magana
sai mukaji muryarsa"Me zai sa ni qin fitowa?"
Muka
juya muka dubeshi,fuskarsa a sake ya qaraso.
Murja
tayi dariya kadan tana mai sunkuyar da
kanta"Badamasi kenan,ina yini." Tun daga
yanayin
shigarta ya soma mamakinta,dakyar ya daure ya
iya
amsawa"Lafiya lau murja,ya garin?" "Gari
Alhamdulillah Badamasi,nasan Ahmed ya
fadamaka
dalilin zuwana ko?" Yayi dan murmushi ya dubeni
sannan ya maida kallonta gareshi"Ya fadamin
saidai
na hankalina ya gaza daukar hakan amma waqa
a
bakin mai ita tafi dadi ko ba haka ba?" Muka
danyi
dariya,ta jinjina kanta"Gaskiyane,toh hakika
abunda ya fadamaka hakane Badamasi. Wannan
ba murjar
da kuka sani ce tsaye a gabanku ba,halayen
waccan
da wannan sun bambanta. Na tafka babban
kuskure
a rayuwata ina neman afuwarka don Allah." Ta
fada
a lokacin da idonta ya qara cikowa da kwalla.
Badamasi shima a sanyaye yace"Bakomai
murja,na yafe maki wallahi,Allah Ya qara kiyaye
gaba." Ta
amsa da amin. Cike da jin dadi nace"Amma dai
za'a
gayyacemu auren ko?" Badamasi yace"Au ashe
aure
zakiyi?" Ta sunkuyar da kanta cike da kunya
bakinta
yayi nauyi ta kasa amsawa,nayi dariya nace"Eh
mana
ko kana kishi ne?" Gaba daya mukayi dariya daga
karshe dai mukayi sallama ta shige motarta ta
wuce.
Muka bi motar da kallo,na juyo na dubeshi,sai
kawai
na tuntsire da dariya ina mai dukan
kafadarsa"Yane
mutumin? Ko za'a koma gidan jiya ne?" Ya
harareni
yana murmushi"Barmin batun nan ni din sai
Jamcy."
"Lallai wayaga Jam." Muka sanya dariya sannan
muka koma ciki. Bayan mun zauna ya dubeni"Wai
ma a ina kuka hadu?" Sai a lokacin na tuna da
yunwar dana kwaso,na dan tabe baki"Na dawo
daga banki ne." Ya dago zaune da sauri yana
dubana"Kace ka samu aikin?" Nayi murmushin
takaici"Uhm,aiki yanzu kuma ai sai masu hanya."
"Haba kana nufin shiru kenan?" Na dafe kaina
saboda sarawar da yake yi"Kaidai bari kawai sai
a
hankali.""Kaima Ahmed ai ina ganin ko stores ne
ka
gwada ka gani ko Allah zai sa ka samu a can."
Na
dago kaina na dubeshi"Toh anan dinma kana
ganin
akwai sa'a ne? Har nawa naje ban samu ba? Kai
nifa
bari kaji kallon wulakanci na tsana wallahi,akwai
inda na taba zuwa manager na wajen ya shiga
yimin kallon tara saura wallahi ban kai ga amsa
tambayar
da yayi min akan matsayin karatuna ba na mike
na
bar wajen. Na tsani wulakanci ne ko kadan,amma
su
mutane a zamanin nan bansan me suke daukar
kansu ba,gani sukeyi kamar wayonsu ne ya kai
su
wannan matsayin ba Allah ba." Badamasi
yace"Gaskiyane,Allah dai toh Yasa ka samu
kwanan
nan." Na danja qaramin tsaki alokacin da na mike
tsaye"Amin dai,bari ni zan wuce." "Ah haba dai
ka
jira mu ci abinci mana don Allah." Toh dama da
yunwar na koma na zauna,ya dauki wayarsa ya
kira
kanwarsa siyama. Ya dubeni"Ina labarin Hafsa?"
Nayi murmushi"A soyayyarmu sai abunda yayi
gaba,yanzu ma jira nakeyi na samu na zauna da
Abba a nutse na sanar dashi." Muka cafke muna
dariya daidai nan siyama ta shigo,ta gaisheni ta
qara
da cewa"Yaya Ahmed shine baka shigo wajen
mami
ba?" Nayi murmushi"Zan shigo siyama."
Badamasi yace"Mutumin da har ya mike zai tafi?"
"Toh ai
niyyata daga nan na shiga kafin na wuce."
Siyama
tace"Nidai zan fadawa mami kazo kuma kace
zaka
shigo."Na gyada kai"Ba matsala."
***************
**********************************Bayan
rabuwarmu da Badamasi na dawo gidan. A zaure
muka ci karo da Zahra sanye da hijabi,mukayiwa
juna murmushi"Sai ina?" Ta dan jingina gefen
kanta
da bango"Islamiyya." Na kura mata ido ina
dubanta
kafin nace"Zahra meke damunki please,kin rame
gaba daya kamar ba ke ba,kodayaushe a sanyaye
kike. Wannan itace kanwata da na sani kuwa?"
Ta dubeni da alamar sanyi a idanunta shiru bata
ce
komai ba sai kuma dukar da kanta"Bakomai."
Jikina
ya bani akwai din tunda har gashi bata iya
boyewa,na dan matso kusa da ita a hankali na
ambaci sunanta a karo na biyu"Zahra." "Na'am."
"Idan har kin yarda ni yayanki ne mai kaunarki
mara son damuwarki toh ki sanar dani meke
faruwa dake
a kwanakin nan. Ko nayi maki wani laifin ne?" Ta
girgiza kai bata ce uffan ba,naji babu dadi na
hade
rai"Shikenan kina iya tafiya tunda ba zaki iya
fadamin
ba." Sai kuma naga ta gotani zata tafin da sauri
na
riko hannunta ta juyo,na razana da ganin hawaye
akan fuskarta. Kafin nayi magana mukaji salatin
Anti
amarya daga bayana. Na saki hannun Zahra na
juya
ina dubanta,gaba daya a zatona hannun dana
rike
mata shine dalilin razanarta ashe rabon naji
abunda
zai hargitsamin tunani ne."Dan banza
munafuki,wannan halin na uwarka
ne ka gado ba shakka. Bayan ka gama asirce
min 'ya
tace nan duniya kai take so ashe burinka ka
lalata
min ita? Toh wallahi kayi da 'yar halak,kuma
zanyi
maka gargadi babu kai babu Zahra,idan na qara
ganinku tare wallahi sai na hada maka tuggun da
har ka bar duniya bazaka mance dani ba." Ta
juya ga
Zahra idonta cike da masifa,Zahra kuwa tuni ta
firgita,kafin tace wani abu da gudu Zahra ta fice
daga
gidan. Ta gallara min wani mugun harara"Dan
iska
kawai,dangin matsafa." Ta ja tsaki ta bar wajen.
Kaina ya daure,na kasa tunanin komai,jiri naji
yana qoqarin dibata,dakyar na iya bude kofar
dakin na
shiga. A kasa na zauna bayan na yarda jakar
takarduna a kofar dakin,innalillahi! Me kalaman
Anti
suke nufi? Tace Nan duniya Zahra tace ni take
so?
Kamar ya? Wani salon makircin ne ko kuwa me?
Zahra sona takeyi?? Anya hakane? Wata zuciyar
ta tabbatar min wannan kawai fadi ne na anti
don ta
kulla min sharri. Toh amma ai Zahran shiru tayi
karshe ma guduwa tayi daga gidan,wai me hakan
ke
nufi? Amma idan har haka ne Zahra tana sona ba
shakka ina cikin hadari. Na runtse idona na qara
dafa
kaina da sarawarsa ta qaru,a hankali na shiga
tunano yanda abubuwa suke ta kasancewa tun
sa'adda muka fara soyayya da Hafsa,da yanda
Zahra
take daure mana fuska har na tuna sadda Hafsa
ke
sanar dani Zahra ta bar kulata a makaranta ko
sallama tayi mata bata amsawa. Da yanda ta
daina
sakar min fuska ba kamar a baya ba. Ya Salam!
Shine furucin da nayi a bayyane,fatana kada
hakan ta
tabbata domin kuwa muddin ya kasance hakan
na
shiga matsala babba. Ta tuno sa'adda nace mata
hira
zanje haka nan ta daura fuska,da yanda ko
kallona
batason yi,kai abubuwa dai barkatai da suka
wuce
suna qara tabbatar da zargina. Ya zanyi ni
Amadu idan wannan maganar ta fito? Allah
shaida bazan qi
Zahra ba,kuma bana jin tsanarta kamar yanda
bana
yi mata so na aure bayan na zumunci. Ya zama
dole
nayi azamar tunkarar Abba da batun Hafsa
kamar
yanda mukayi da babanta. Yayi min iznin turo
magabatana idan har da gaske ne ina son 'yar
sa. Na mike a hankali na fada toilet domin watsa
ruwa har
lokacin ina cike da mamakin Zahra a yanda ta iya
danne komai gefe guda kuma tausayinta nakeji
kwarai,lallai Zahra tana wahalalliyar soyayya.
Inama
ace zan iya barin Hafsa na so Zahra ko don
halaccin
da tayimin,inama zan iya biyanta ta hanyar
aurenta? Saidai hakan ba mai yiwuwa bane
musamman idan
na hangi tarin matsalolin da suke cikin wannan
al'amari indai akace zai tabbata.
Wajen biyar da rabi ina zaune can wajen baba
maigadi,yana ta hira da wasu dattijai biyu suma
aikin
gadi suke,hankali ko kusa baya tare dasu kalle
kalle
kawai nakeyi. A zahiri sai ka rantse nasan
abunda
nake kalla amma a badini hankalin nawa yana ga
tunanin wannan jarabar dana fada. Cike nake da
damuwa,tausayin Zahra fal a zuciyata gefe guda
kuma ina mai bakin cikin yanda ta tsinci kanta da
sona alhalin ni din banajin zan kaunaceta.
Maganar
Baba maigadi ta katseni"Amadu wai lafiya kayi
shiru?" Na dubi Baba maigadi ina murmushin
yaqe"Bakomai baba." Yayi 'yar dariya sannan ya
juya suka cigaba da hirarsu. Na hango Zahra
kanta a
duke sun taso daga makaranta zata shiga gida.
Na
bita da kallo har ta shige sannan na dauke kaina
cike
da tausayinta,gaba daya ta rame ji nayi kamar na
tashi naje na kwantar mata hankali da sanyayen
kalamai saidai ko kusa bazan soma hakan ba,na
yanke yin nesa nesa da Zahra. ***************
***********************************Kwana
biyu da yin haka na rasa kwanciyar
hankalina,abun
ya dameni kwarai. Na yanke tunkarar Abba da
batun
Hafsa. Na sameshi zaune a falo shi kadai yana
kallo,da sallama na shiga ya amsa yana mai
dubana fuska a sake. Nima na dan sake fuskata
duk
kokarina na danne damuwata. Na qarasa na
zauna
kasan kujerar da yake. Yana murmushi yace"Ya
akayi Ahmed?" Na dukar da kaina cike da ladabi
nace"Eh Abba dama maganar da mukayi kace na
nemo matar aure,na samu yanzu haka ma
iyayenta sunce na turo magabatana ne." Abba ya
tashi daga
kishingidar da yayi yana mai washe haqora"Kai
madallah,haka ake so,ita yarinyar a ina take?"
Naji
dan sanyi a raina na qara dukar da kaina ina mai
jin
nauyinsa"Hafsa ce qawar Zahra,'yar gidan Alhaji
Rabi'u Zango." Abba yace"Lallai kaje gidan
karamci,zamuyi maganar da Yaya(Kawu murtala)
idan yaso sai a yanke ranar da ya kamata aje sai
a
sanar musu ko?" Nayi murmushi na dan gyada
kaina
kadan,sannan yace"Shikenan,Allah Yasa ta zame
maka mace tagari." A ciki na amsa sannan na
mike
na tafi. Wani farin ciki ne ya mamaye min
zuciyata,sai yanzu hankalina ya kwanta. Wayata
na sura na kira
Hafsa. Ringing biyu ta dauka tana mai yimin
sallama,"Amin wa'alaikissalam beautyna,ya
garin?" A
shagwabance tace"Haba my heart kaima kasan
garin
yayimin zafi yau fa gaba daya baka kira ba,nayi
maka
magana a whatapp baka bani amsa ba nasani ko
isarka nayi." Na dan buda baki kadan"Haba my
beauty wane ni na gaji dake? Sorry yau gaba
daya
bana jin dadi ne amma yanzu garau nake
Alhamdulillah." Tayi murmushi mai sauti"Allah
Sarki
my heart,Allah Ya qara maka kwanciyar hankali."
"Amin beautyna,kin shirya jin wani daddadan
labari?" Ta tareni da sauri"Eh my heart." Nayi
'yar
dariya kadan"Toh sai kin ce kina sona." Ta
shagwaba murya"Haba My heart,ai fadi kamar
rage
matsayin sonka ne wallahi son da nake maka ya
wuce tunaninka,amma don faranta maka zan
fadi,I
love you I love you and I love you." Na sanya
dariya itama ta shiga tayani"Beauty kada fa kisa
nazo
yanzu." Tayi dariya tace"Har ka bani kunya."
"Haba?"
"Wallahi gashi ma ina rufe fuska da tafin hannu."
Na
dan lumshe ido ina murmushi"Ashe kenan bazaki
iya
sauraren labarin ba." "Zan iya mana." "Ok toh
bude
fuskar." "Na bude.""Yau naje munyi magana da
Abba za'a turo nema
mini aurenki." "Don Allah dagaske?" Nayi
murmushi"Gaskiyar kenan beauty,Allah Ya kusa
mallaka min ke." Tayi 'yar dariya"Uhm Allah Ya
tabbatar mana da alheri,naji dadin labarin nan."
"Hakane." Muka cigaba da hirar soyayya kamar
bazamu rabu
ba,karshe dai bacci ya soma cin qarfina nayi
sallama
da ita. Da safe ni zan kai su Zahra makaranta
kasancewar Hassan yaje kauyensu daurin aure.
"Ahmed,Ahmed!" Naji muryar Usman karami yana
ta
kwalamin kira lokacin ina tsaya ina zura
jallabiya,"Ya akayi Usman ganinan." "Kayi sauri
zaka sa muyi latti."
Na girgiza kaina sam yaran gidan nan basu yi
tarbiyya mai kyau ba,laifin duk na iyayensu ne.
Amma haka yaran ke kiran sunana gatsal,Zahra
ce
kadai tasan tayi kirana da Yaya. Allah Sarki
Zahra. Na
fada a raina,sai kuma na kauda tunaninta na fito.
Na dubeshi"Shiga gurin Abba ka amso mukullin
motar.".
Ya turo baki yana gunguni a haka ya tafi nayi
murmushin takaici na juya na fito ina mamakin
halin
yaran anti. Ko kusa Abba baiyi sa'ar mata ba su
dukansu babu macen arziki. Zahra da su Salihu
suna
tsaye a wajen motar tana qarasa mai homework
da tsaye na zura mata ido,bata ko yarda ta dago
kanta
ba ballantana nasa ran zata dubeni. Zanyi
magana
muryar usman karami ta katseni"Gashi."
Na karba na bude,yau din gidan baya ta zauna.
Bance mata qala ba,kannenta dama inhar ni ne
zan
tuqa toh gidan baya suke zama wai ai idan
hassan ne shima a baya suke zama gaba
daya,tun farko Zahra
ke nuna musu ni din dan uwansu ne kada su
maidani direba sai kuma gashi da kanta itama ta
zabi
gidan baya akan na gaba. Na tsaya ban tafi ba
ina
mai dubanta ta madubi,na lura daga mun hada
ido
sai ta dauke kai karshe dai ta daure fuska tamau
sannan ta fito ta shigo gaba. Murmushi kawai
nayi na
ja motar.
Bayan na sauke yaran motar tayi shiru sai
labaran
duniya dake tashi a rediyo,na sanya hannu na
kashe.
"Zahra." Na kira sunanta,bata kalleni ba ta
amsa"Na'am." "Yimin qarin bayani akan abunda
anti ta fadi jiya,tace kina sona da gaske ne?" Na
qarashe
ina dubanta,ta dauke kanta murya na rawa
tace"A'a." Na gane batason bada kanta ne,sai
naji na
qara tausaya mata na share zancen da
cewa"Shikenan dai,amma na lura kina boyemin
wani
abu Zahra." Shiru tayi bata bani amsa ba kanta a
qasa,na dai gane batason zancen mai yiwuwa
zuciyarta ce babu dadi. Har muka isa babu
wanda ya
qara magana,ina fakawa ta rataya jakarta da
sauri ta
fita,na bita da kallo har ta shige sannan na
kwantar
da kaina a jikin kujerar saidai na rasa kalar
tunanin
da ya dace nayi.Kwankwasa glass naji anyi,a dan
firgice na kai
dubana ga waje. Hafsa ce,ta sakarmin murmushi
ta
daga min hannu,na gyara zamana nima na daga
mata ina mai murmusawa daga haka ta shige
makaranta." Na bita da kallon so sannan na
maida
hankali na tashi motar na qara gaba raina fari sol
ina sauraron waqar nan ta "Masoyiya kece tawa."
**************************************** A
ranar nakai Abba can gida na ajiye. Ya shiga har
wajen gwaggonsa suka gaisa,ya tambayi lafiyarta
daga nan kuma ya dubeni"Jeka ka kira iyayen
naka." Na mike a ladabce na isa ga sashen su
kawu murtala na sanar dasu gwaggo na
nemansu,gaba
daya suka je banda Kawu lawal domin shi baya
gidan yana can kasuwa bai dawo ba. Abba ya
dubeni"Ai sai ka ka dauko kannen naka,ni na
koma.
Na amsa cike da ladabi sannan na bar gidan
zuciyata
cike take fal da farin ciki nasan komai ya kusa
yanke min. Wayata tayi qara na dauka,Badamasi
ne. "Ya
kana ina ne?" Nayi murmushi ina mai mikewa
daga
kofar gidan"Kaidai bari akwai labari,kana ofis
ne?"
Yayi dariya"A'a na dawo gida yanzu dai nake
shirin
zuwa wajenka." "Ok toh kazo sai muje
makarantar
su Zahra tare ko?" "Ok." Na tashi mota na nufi
kofar gidan su Badamasi,hon biyu nayi masa
babu jimawa
sai gashi ya fito ya bude ya shiga na ja. Bayan
gaisuwa ina murmushi nace"Kai da labari fa." Ya
dubeni"Haba dai?" Na jinjina kaina,na labarta
masa
yanda mukayi da Zahra da kuma batun auren
hafsa
dana yiwa Abba." Na qara da cewa"Agaskiya ina
matukar tausayawa Zahra wallahi inda zan iya
daukar soyayyar da nake yiwa Hafsa na maida
kan
Zahra da nayi,amma dan uwa na riga nayi nisan
da
bana jin kira akan Hafsa,I love her a lot."
Badamasi ya
girgiza kai"Allah Sarki Zahra,dama wallahi na
jima ina
zargin yarinyar nan sonka take amma na lura kai
din baka gane hakan ba,yanzu Ahmed ba zaka
iya
tallafar 'yar uwarka ba ka aureta?" Na saki ajiyar
zuciya ina murmushin takaici"Dan uwa kenan,da
ma
ace abunda kake hange mai yiwuwa ne. Inda ace
ya
tsaya a sadaukarwar kawai da zan iya kokartawa
duk da nasan mai wuya ne,amma baka hango
tarin matsalar da akwai ba? Na sanar dakai fa ta
hanyar da
naji maganar ko daga nan baka fuskanci matsalar
ba?" Badamasi ya jinjina kai"Gaskiyane
wannan,kai
lamarin akwai tausayi wallahi,Allah Ya zaba mata
miji
nagari toh." "Amin dai." Muka iso makarantar su
usman karami,na shiga na daukosu sannan muka
qarasa makarantar su Zahra. Suna tsaye tare da
Hafsa,na faka a saitinsu. Zahra ta dauke kanta
fuskar
a daure na lura ko wanda ke gaban motar bata
lura
dashi ba,badamasi cikin rada yace"Ka kula please
kada ka bata mata rai." Na gyada kaina. Hafsat
ta
budewa Zahra gidan gaba"Shiga kanwarmu sai
ina lallabaki." Sai kuma suka ga Badamasi,kunya
ta
kama Hafsa saboda furucinta. Zahra ta dan saki
fuskarta"Ina yini yaya badamasi." Yayi
murmushin
shima"Lafiya lau kanwarmu." Tayi murmushi
kawai
ta bude baya ta shiga,inason yiwa Hafsa magana
kuma ina gudun Zahra kada ranta ya sosu
saboda kunya ma ai wani abu ne,ya kamata na
rage mata
zafi ba wai na qara mata ba. Badamasi ya amsa
gaisuwar da Hafsat ke masa yana
zolayarta"Amary
armu kenan ashe kina da baki?" Tayi dariya tana
rufe
fuskarta"Hm ai bansan tare kuke ba." Ya jinjina
kansa"Hakane." Na dan dubeta na sakar mata
murmushin da tace tafiso a tare dani"Sai munyi
waya,ki gaida min noor da mama da Faruq." Ta
gyada kai lokacin da take dago mana hannu"Ok
my... Sai kuma ta tuna a harabar school take tayi
shiru ta waske da duban zahra"Sai next week
kuma
kawalli." Zahra ta daga mata hannu itama,na lura
da yanayin fuskarta bata nuna wata alama ba ta
bacin
rai,na sauke ajiyar zuciya a raina nace"Ta daure
kenan." Na ja muka tafi,a mota yaran nata hira
da
Badamasi duk da cewa shine yake jansu nikuwa
ban
sanya musu baki ba,haka madam din kamewa
tayi
tana cigaba da karanta wani novel dake
hannunta. Har dai mukaje suka sauka muka dubi
juna da
Badamasi yace"Zahra fa na lura ko kallonka
batason
yi." Na daure fuska"Toh meye ruwana a ciki? Ni
hakan ma yafi min wallahi saidai kasan me?"
"Saika
fada." "Naso ace ko gaisuwa na mutunci irin
yanda
muka saba mu cigaba da gudanar dashi,amma ta
daina wannan din ma." Badamasi yace"Wallahi
Ahmed tana matukar kaunarka,kai nifa ji nake
inama
ita din...." Na dakatar dashi a lokacin da nake
qara
daure fuska"Please kada mala'iku suce amin."
Yayi
dariya"Lallai ma,toh Allah Ya zaba abunda yafi
alheri." Na dan saki fuska"Yauwa amin,ko kaifa
amma ina zan iya da masifar Anti amarya?"
Mukayi
dariya.


Zaharaddeen  Shomar

Whatsapp  08168575100Amadu 1 page 9
Posted by ANaM Dorayi on 10:43 PM, 12-Jun-15
Under: Amadu
Bayan kwana biyu Abba yace na sanar cewa za'a
je ranar juma'a. Dakyar na iya danne farin cikina
a gaban Abban,na fito. Allah Allah nakeyi yamma
tayi na samu ziyartar hafsat domin nafison muyi
maganar ido da ido. Na fito na nufi gidan Anti
Aisha. Tana zaune tare da 'yan uwan mijinta da
suka zo. Bayan mun gaisa dasu ta dubeni ganin
yanayin fuskata yasa ta murmushi"Shiga ciki
Ahmed ina zuwa." Na shiga na zauna kasan ledar
dakin saboda kujerun sai a hankali duk sun lalace
sun gaji da wahala. Na shiga qarewa dakin kallo,a
kwana biyun da banzo ba gaba daya ya qara
lalacewa,tausayinta ya kamani ina mai burin
Allah Ya azurtani na kyautatawa antina. Daga
karshe na ciro wayata na kunna,Hafsat tana
online. Nayi murmushi "Sarauniyar kyawawa
kenan." Na aika mata,ta aiko da 'dan aljani mai
murmushi a idonsa zanen heart ne"Sarkin
kyawawa na Hafsa ka wuni lafiya?" Naji sanyin
maganarta"Lafiya lau my beauty,ya gidan?"
"Alhamdulillah heart,ina aminiyata?" Sai lokacin
na tuno da Zahra,gaba daya a kwanakin nan ban
qara sanyata a ido ba,dayake yau dinma ba ni na
kaisu makaranta ba,Hassan ne,gashi har sun
dawo bamu hadu ba. "Tana nan lafiya." "Eyya,ya
kan nata ya daina ciwo?" Na dan dakata,ashe
kuma bata da lafiya? Nayi shiru har ta qara
aikowa"Hello." "Hy,ina jinki,da sauki."
"Alhamdulillah." "Nima yau zani tad'i da
kanwarki." Ta sanyo aljani mai zare ido da mai
kuka"Haba my heart tun kafin ka mallakeni har
ka tanadar min kishiya? Toh ni na bar mata kai."
"Hahaha sorry beauty wasa nake miki fa,ai ke
kadai nake so." "Dagaske?" "Sosaima,anjima
insha Allahu zaki tabbatar da hakan." "Toh Allah
Ya nuna mana." Maganar Umma kanwar mijin
Anti Aisha ne ya katseni"Toh Ahmed mun wuce."
Na dan daga murya"Ok umma ku gaida gida."
Anti tayi musu rakiya sannan ta dawo ta zauna
tana fuskantata na gyara zama sosai ina
murmushi"Antina ina yini?" Ta amsa"Lafiya lau
'dana,ya gidan naku?" "Suna lafiya." Ta qara
dubana tana murmushi mai bayyana haqora"Yau
dai na lura kamar kana cikin nishadi
Ahmed,meya
faru?" Nayi dariya kadan ina mai shafa sumata
na
sanar da ita yanda mukayi da Abba." Tayi dariyar
farin ciki"Kai madallah,abu yayi kyau,Allah Ya
tabbatar mana da alherinsa,ka sanar da 'yan
brigade?" Na girgiza kai"Haba anti ai ke zaki
sanar musu idan an sanya." Tayi 'yar dariya"Ai
shikenan Allah Yasa ayi damu." Na amsa da
amin. Mun jima muna hira har la'asar tayi nayi
mata sallama na bar gidan.
Ana idar da sallar magriba,na nufi gidansu Hafsa
bayan na dau wanka. Motar Abba na dauka
dayake
mukullin yana gurina na nufi unguwarsu Hafsa a
hotoro. Ina isa na kira wayarta bayan sallama na
sanar mata na iso. Ta fito fuskar nan tasha hoda
da
jan baki,tana murmushi ta dan rankwafo kanta
jikin windon"Sannu da zuwa my heart." Na
kasheta da
murmushi"Yauwa beautyna." Mukayi murmushi
lokaci daya,ta dan matsa"Bismillah." Na bude na
fito
tayi min jagora har sittingroom dinsu sannan ta
zauna muka gaisa. Mun jima muna hirarmu
sannan
nace"Kinsan me?" Ta dan dubeni"Saika fada
heart." Nayi murmushi ina mai jin dadin sunan
nan da take
kirana dashi"Ranar friday za'a zo nema mini
aurenki." Ta rufe ido da sauri tana murmushi a
hankali tace"Dagaske?" "Kwarai kuwa." Bata ce
komai ba,nayi dariya"Au bazakiyi magana ba? Ko
addu'a ma?" Itama dariyar ta danyi ta cire
hannunta tana mai kauda kanta"Allah Yasanya
alheri." "Amin."
Ban bar gidan ba sai bayan isha'i.
***************
*******************************An sanya
ranar
aure da zarar Hafsat ta kammala SS3 dinta
ma'ana dai
tayi candy da wata daya. Gaba daya dai za'a nan
zuwa watanni uku masu zuwa ne. Ranar mun
kwana muna murna da hirarmu ta masoya.
Bayan sati daya
da yin haka,Abba yace na sameshi a kasuwa.
Wajen
daya da rabi Hassan ya saukeni a titi ya nufi
makaranta don dauko yara ni kuma na hau
adaidaita
sahu na qarasa kantin kwari. Muka gaisa da
yaran
wajen,sannan na tambayi daya daga cikinsu inda
Abba yake ya tabbatar min yana dan qaramin
ofis
dinsa dake shagon wanda anan yake sallah da
cin
abinci. Na qarasa lokacin yana zaune yana amsa
waya,na cire takalmi na zauna gefen carpet din
da
yake kai. Yana gama amsa wayar cikin sakin
fuska ya
dubeni,na qara gaidashi ya amsa sannan
yace"Amadu,ka kai munzalin da ya dace ace kana
cin
gashin kanka. Gashi har kana shirin ajiye iyali
amma
babu aikin yi." Nayi shiru bance komai ba,shima
yayi
murmushi ya cigaba"Inaso ne kaje ka zauna nan
da
kwana biyu kayi nazarin sana'ar da kake ganin
zaka
iya yi ka sanar dani. Ka tsaya sosai kayi tunanani
mai kyau kaji ko?" Hamdala kawai nakeyi ga
Ubangiji Mai
yankewa bayinSa wahala a lokacin da basu taba
tsammata ba." Ina dariyar farinciki na hau godiya
ga
Abba yayi dariya yana mai dafa kafadata"Haba
Amadu,kai din ai 'dane a wajena,babu laifi kana
iya
tafiya kaji?" Na gyada kai"Nagode Abba,Allah Ya
qara rufin asiri." "Amin Amadu,idan kaje ka cewa
Hassan yazo yanzu mu tafi,ga wannan ka hau
mota."
Ya mikomin kudi har dubu daya na qara godiya
sannan na fito. Na rasa inda zan tsoma raina don
dadi sai yanzu nakejin zuciyata tayi wasai.Ranar
duk wanda ya ganni zai tabbatar ina cikin
farin ciki. Da la'asar na nufi can wajen Badamasi
saidai nayi rashin sa'a baya gida. Haka na juyo
na
taho,na biya call center na karbi wayata na
kunna,anan na tsaya na kira wayarsa. Ya
daga,bayan
sallama nace"Kana ina ne naje ban sameka ba?"
Yace"Wallahi yau gidan granny nayi yinin
nawa,daga
ofis na wuce,amma idan na dawo zan biyo ince
dai
labari mai dadi zaka bani?" Nayi dariya"Kaidai
bari
dadin nasa ma har yaso yayi yawa." "Kai haba?!"
Na
qara darawa"Kaidai zakaji idan kazo." Mukayi
sallama na saki ajiyar zuciya cike da farin ciki ina
waige waige kafin na taka qafa na bar wajen na
isa
ga Idi mai shago na zauna. Ya dubeni"Ikon Allah
Ahmed,yau kuma ka tuno ni? Kaida saidai muga
kana giftawa?" Nayi dan qaramin tsaki ina
murmushi"Kaidai idi akwai ka da mantuwa wani
sa'in inace jiyan nan ma na shigo fa na sayi Omo
kodai har ka manta?" Ya dafe goshi"Af ai kaji irin
bala'in matan,duk indo ce ta janyomin wannan
uban
mantuwar wallahi,kodayaushe idan zan fito sai ta
bini da masifa." Nayi dariya ganin yanda ya
qarashe
yana waige waige,ya saki ajiyar zuciya shima
yana
dan dariyar"Ai na dauka kaninta na kusa kasan
shi bashi da aikin daya wuce kai mata rahoton
abunda
nakeyi. Matar nan duk wata ribar da zan
samu...." Bai
qarasa ba na katse shi"Haba kai kuwa idi kada
ka
tona sirrin matarka gareni mana,ka cigaba da
haquri
da ita ka kuma yawaita addu'a." Idi ya jinjina
kansa
yana dariya"Bakasan mata ba,wallahi duk yanda
ka kai da kauda kanka wataran sai sun kai ka
bango.
Murmushi nayi"Kaidai ka cigaba da hakuri kai
wani zubin ma ai mazan suma suna da laifi sune
suke
musgunawa matan nasu." Idi yace"Bari na fada
maka nifa bazan juri tsayawa tarairaiyar mace
ba,ai
an shani na warke wallahi. Idan kana
tarairaiyarsu
rainaka suke su ci ubanka. Duk 'yar iskar da tace
zata kawomin raini saidai na ballata." Nayi
dariya"Toh
kuma ya akayi ka kasa da masifar indonka?" Yayi
dariya ya soma kirari"Indo masoyiyata abun
alfaharina,zama dake dole ne koda akan bola
zani
kwana." Mukayi dariya,daidai nan sai muka ji
muryar yaro
wanda mai wuce shekaru goma ba,yace"Lalalala
sai
na fadamata." Ai da sauri idi ya taro shi"Kai
Yunusa
kai zo ka amshi alawa kaji?" Yaron ya dawo yana
dariya,idi ya miko masa biskit da alawa,ya shafi
kansa"Kada ka sanar da ita kaji dan qanina?"
Yayi dariya ya dubeshi"Wasa ma zan tafi." Yayi
hanyar
inda yara suke wasan qasa,dariya na shiga yi"Ho
idi
mai tsoran mata." Idi dai kunya ta kamashi
murmushin yaqe kawai yakeyi karshe ma sai ya
shige shago yana fadin"Kai dallah ka cikani da
surutu kada na rasa masu ciniki." Mikewa nayi
ina girgiza kaina cikin dariya nace"Kaga ma
tafiya."
Na juya na kama hanyar gida,shi kuma ya taho
da
mota saura kadan ya makeni nayi baya da sauri
ina
duban motar. Faisal ne yayi fakin ya fito,kallon
wulakanci ya bini dashi ta saman gilas din dake
kan
idonsa"Sorry guy." Daga haka ya sanya kansa
ciki,na bishi da kallo yanzu wannan mara
tarbiyyar akeson
hadashi da kanwata Zahra? Wani daci ya
ziyarceni,ji
nake kamar na bishi har dakin na kula da ita
kada ya
kawo mata maganar banza amma babu hali
bakin
rijiya ba wurin wasan yaro bane.
Ina ni ina shiga dakin anti har nayi zaman hira?
Na nufi dakina a sanyaye,dadin mahaifiya kenan
wacce
kowace matsala gareka zaka tunkareta,zata share
maka hawayenka da daddadan shawarwarinta,z
ata
kwantar da hankalinka ta hanyar tuna maka
ni'imomin da Ubangiji Ya tanadarwa masu
hakuri,zata kula da kai zaku zauna kuyi hira.
Koda yaushe kana da ikon shiga dakinta ka
zauna kayi
abunda kake so. Na fada kan gadona a hankali
na
furta"Allah Sarki Mahaifiya." Lallai mutum duk
yanda
yakai a shekarunsa yana jin dacin rashin
iyaye,wasu
kwalla naji sun tahomin da sauri na hadiya.
Inama
ace koda daya daga cikin matan Abba sun damu
dani,haka na taso a hannunsu wala na tambade
na
zama dan kwaya,wala na zama mai tarbiyya oho
musu,babu wanda ya taba kirana ya bani
shawarar
Amadu kada kayi kaza babu kyau,kada kayi kaza.
Nayi murmushin takaici,sallamarta ce ta katseni.
Na fito da sauri ina mai amsawa,ta kauda kanta.
Ta gyara fuskarta sai kamshin turare takeyi,a
sanyaye
tace"Anti tace ka tashi inji Yaya Faisal najin zafi."
"Tashin hankali!" Abunda na furta a zuciyata
kenan,nayi murmushi ina duban agogon dake
daure
a hannuna"Kinga saura mintuna ma a kira sallar
magriban,a bari tunda ana idar wa ake tashinsa
sai a tasar,yanzu idan na kunna Abba zai tambayi
dalili."
"Ai dama nasan sai kayi gardama shiyasa na biyo
sahu bayan haka dole na dunga kula da takunka
akan 'yata. Ka fini kusa da Abban ne? Kai a
suwa? Ka
wuce ka bi umarnina bana ciki da iskanci kaji
ko?"
"Allah Ya baki hakuri anti." Na fada a lokacin da
nake zura takalmina,ta ja tsaki ta
titsa keyar Zahra suka koma ciki,tausayin Zahra
ya
kamani nasan duk domin a nesantata dani ake
mata
haka,anya ba abun kunya bane ace na qi Zahra?
Toh
idan naso Zahra ya zanyi da masifaffiyar suruka?
Na
shiga cikin gidan,zanyi hanyar gidan injin,naji
muryar inna"Kai me kake shirin yi?" Na dubeta
tana tsaye ta
kicin,daga windon ta hangeni"Anti ta umarceni da
tada inji." Ta gallaramin harara"Tafi ka bar wurin
nan
babu uban da za'a tadawa inji matukar ba
lokacin ne
yayi ba." Na wuce ni kaina naji dadin abunda
inna
tace saidai nasan akwai matsala. Zanyi dakina
anti ta cimmani"Me kuma ya dawo dakai?
Kada kace ba mai domin dazu Hassan ya dire
jarkarsa." Zanyi magana inna ta fito rike da
cokalin
miya hannu a qugunta"Uwargidan ce ta
hana,babu
wanda ya isa ya tashi inji fashe lokacin tadawar
ne
yayi." Anti ta harareta ta ja dogon tsaki"Aikin
banza,wani power kike dashi a gidan da har kike
ganin zaki iya sanyawa ko ki hana? Toh wallahi
ni
kam baki isa ki juyani ba,kai Ahmed kaje kabi
umarnina tun ban wanke ka da mari ba wallahi."
Da sauri na juya hararar inna tasa nayi ribas
sannan
ta dubeta fuskarnan a daure tamau"Yau zan
nuna
maki isata jummai,zaki gane isata. Ke babu
abunda
kika sani sai wasa da arziki,ai duk son kudina
wallahi
bana almubazzaranci kamar naki,kodayake babu
mamaki tunda ubanki mai ajiye ba ballantana ya
bawa wani ajiya." Toh fa! Fada ya soma
zafi,faisal ya
fito ya rike Antinsa wacce ke neman kaiwa inna
duka"Please anti bar batun,naji na hakura zan
zauna
hakanan." Inna ta daka masa tsawa"Dallah yi
mana
shiru dan iskan yaro bai ci arzikin gidansu ba
yazo
yaci gadon wasu,idan baka bace daga nan ba
wallahi zaka sha mamaki,shege dan talaka." A
fusace
faisal ya dubeta"Da jikin biredin zaki dukeni,ai
kece banza wacce batasan abunda takeyi ba
katuwar
kawai."
Da sauri na isa ga faisal a fusace na nunashi da
yatsa"Kai ba mace bane,ka kiyaye kada ka ci
zarafin
matarAbbana." "Kai dallah ware,Abban bogi
ba,shege kawai. Ko an fadamaka bamu da
labarinka! Dan karu...." Kafin ya qarasa na fidda
hannu na
wankeshi da mari,ban sauke ba nima anti ta
wanka
min. Yayi daidai da shigowar Abba wanda
kalaman
faisal yaji da marin da nayi dana anti,baiyi wata
wata
ba shima ya fidda hannu zai wanketa,na ankara
da
sauri na dakatar dashi,hannunsa yana rawa a
zuciye yake fadin"Barni Amadu barni,masifar nan
ta isheni
hakanan. Ashe Jummai baki da mutunci,nagode
da
wannan tozarcin da kike shirin yimin." Ya dubi
faisal"Kai kuma daga yau kada na qara ganinka a
gidana idan ba haka ba wallahi komai zai iya
faruwa,fice min!" Faisal sum sum ya fice yana
fadin"Toh sai me? Meye a gidan naka da mutum
zaiyi
kwadayin zuwa?" Anti tana faisal faisal,Abba ya
dakatar da ita a zafafe"Muddin kika keta zauren
gidan nan wallahi kema binsa zakiyi,shashshar
banza! A haka kike so ki hada aurensa da 'yarki."
Ta
yamutse fuska"Toh meye? Ai dan uwanta ne yafi
bare." "Ai da wani dan uwan gwara bare
wallahi,me
za'ayi da fitsararre." Ai sai ta sanya ihu da
kuka"Wayyo Alhaji ka zagi dangina,wayyo ni
jummai." Abba ya ja tsaki yayi shigewarsa
daki,ga
mamakina naji muryar inna"Amadu tafi ka rabu
da
ita kaji ko?" Na dubeta don gaskatarwa,murmushi
tayi wanda ya taimaka na gani sanadin hasken
farin
wata,muryar Abba ta katseni yana fadin ta tayar
masa da inji. Nan na tashi injin,nazo zan fita anti
ta
cakumi wuyar rigata"Dan iska dan shege,na fada
din
ayi abunda za'ayi." Zahra na kuka tazo ta kama
hannun antinta"Anti don Allah kiyi hakuri,meye
haka?" Abba ya fito ya daka mata tsawa"Sake
shi!"
Ta sakeni tana jijjigar jiki tana duban Abba"Eh ai
shi
da Salame sun gama da kai,sun gama za
'yata,dole ka
qi ganin laifinsu,toh wallahi baku isa ba sai na
dauki
mataki." Abba ya fidda hannu ya wanke ta da
mari,na shiga bawa Abba hakuri dakyar ya koma
dakinsa yana zuba mata fadan rashin
hankalinta,nima na dubi Zahra dake kuka amma
na
kasa cewa komai saboda idon Anti wacce ke
watsomin harara hawaye na zuba daga idanunta
na
tabbata ji take kamar ta shaqeni. Na bar gidan
gaba
daya na nufi masallaci,wannan masifa dame tayi
kama?
A hanyar dawowa daga masallaci ne na hadu da
Badamasi. Mukayi musabaha,ya dubeni a
tsanake"Ya
akayi ne na ganka duk wani iri?" Nayi murmushin
takaici"Kaidai bari rayuwar wani sa'in sai a
hankali.
Yau kuma 'yar qafa ce?" Yana dubana yace"Na
bar
motar a gida gwara mu dunga motsa jikinmu."
Nayi murmushi a karo na biyu,yace"Gaskiya har
ka sanya
jikina yayi sanyi,munyi waya dakai lafiya lau
amma
har ka chanja yanzu." Na dan saki fuska"Kai bafa
wani abu bane dan qaramin hargitsi akayi amma
komai ya wuce." Badamasi dai ya lura kamar
banason batun ya share"Toh Allah Ya kyauta."
"Amin." Muka qarasa dakina tun kafin mukai ga
shiga sai ga Salihu"Ahmed kazo inji Abba." Nayi
shiru
domin nasan bazai wuce batun wannan matsalar
ba,na dubi badamasi ina mai murmushin kauda
masa
damuwa"Ganinan zuwa,ka shiga." "Ok." Nabi
bayan
salihu wanda tuni yayi ciki,nayi sallama na shiga.
Abba yana zaune shi kadai a falon yana tare da
matsanancin damuwa,na durkushe kusa dashi a
hankali nace"Gani Abba." Cikin sanyin murya
yace"Ahmed inason ka sanar dani abunda ya
kawo
wannan rikicin." Ban boye komai ba kamar yanda
banyi qari akan zahirin abunda ya farun ba,na
sanar dashi tun daga farko har karshe. Ransa ya
qara
baci,ya shiga girgiza kai"Alhamdulill
ah,Alhamdulilla
h,Alhamdulillah,lallai Ubangiji Shi ke jarabtar
bayinSa
jarabta. Allah Ya hadani da mata har biyu masu
butulci,burinsu su ganni kodayaushe cikin bacin
rai
da tashin hankali,nagodewa Allah da abun ya
tsaya a iyakar su,nagodewa Allah da wannan
jarabawar ina
mai roqon ya bani ikon cinyewa." Tausayin Abba
ya
kamani ganin yanda yake maganar kamar mai
shirin
kuka,ya dubeni"Kayi hakuri Amadu,kai din 'dana
ne
nasan yanda ka wahala a hannunsu,kayi hakuri
komai mai wucewa ne. Basu isa su rabani dakai
ba Amadu,kai din dan danuwana ne rabin jikina
babu
dalilin da zaisa na juya maka baya koda da ran
muttaka ni mai iya rikonka ne har aurenka.
Abunda
zanyiwa Zahra zanyi maka,abunda zan yiwa
Usmanu
kaima zan maka,ka cigaba da hakuri ina roqa
maka
Rahma da ni'imar Ubangiji ta hanyar neman kudi
da aure,Allah Ya baka na gashin kanka
Amadu,kaji ko?"
Idanuna sukayi ja,na jinjina kai murya a shaqe
nace"Amin Abba,don Allah ku rage damun kanku
kuma." Yayi murmushi"Toh Amadu ka cigaba da
yiwa abbanka addu'a kaji?" Daidai nan Zahra ta
shigo da sallamarta muka hada ido itama duk
idanunta sun kumbura ta durkusa gaban
Abba"Abba gani." Ya maida dubansa
gareta"Babata
banason na qara ganinki da faisal,kiyi hakuri ki
rabu
da soyayyarsa Allah zai fito maki da wanda ya
fishi
kinji ko?" Zahra ta gyada kai tana mai hawaye
har
nayi zaton ko haushi maganar Abba ya
bata,tace"Insha Allahu Abba,dama anti ce ke
sona
dashi." Abba yayi murmushi"Antinki bata san
abunda ya dace da kamilalliya kamar ki ba,kiyi
hakuri Allah zai baki miji nagari insha Allahu
domin
so nake na aurar dake lokaci daya da yayanki. A
razane muka dubi juna da ita,sai kuma ta dauke
kanta na cigaba da dubanta kafin nima na sauke
idona,gabana na faduwa,yanzu Zahra batayi
qanqanta da aure ba? Nida nakeson ganin ta tafi
jami'a? Amma toh meye nawa a ciki? Muryar
Abba ta
katseni"Kuje Allah Yayi maku albarka,ku dai
cigaba
da hada kanku babu ruwanku da haukan
iyayenku
kunji ko?" Muka amsa sannan ya sallamemu,na
lura
har lokacin Abba na tare da damuwa. Da muka
fito
na dubeta"Zahra." Ta juyo ta kalleni a hankali
nace"Ke kika cewa Abba kinason aure yanzu?" Na
lura tambayar ta bata mamaki amma ta danne
tace"Me ka gani?" Sai nima na share batun na
girgiza kaina"Bakomai,shikenan." Na juya nayi
waje na
barta tsaye bansan lokacin data bar wajen ba.
Muna
cikin cin abinci da Badamasi ya dubeni"Wallah
kallo
daya za'ayi maka asan kana tare da damuwa,wai
meya faru?" Nan na labarta masa komai har
kiran
da
Abba yayimin a yanzu na qara da cewa"Kai nifa
bansan meyasa ba banason naji ana kirawo wa
Zahra aure yanzu ba wallahi." Badamasi ya
zubamin
ido cike da zargi,na kauda kaina ina mai kai
lomar
tuwo"Me kake nufi? Kada dai kace ka kamu da
sonta?" Na harareshi"Ko kadan,kaima dai kasan
inason Zahra da karatu." Badamasi ya tabe
baki"Kaidai ka sani,amma Zahra ta isa aure,kuma
ai
aure baya hana karatun zata iya cigaba da
yinsa,saidai idan wani abun ne a ranka." Na
daure
fuska kadan"Shikenan abar batun,muyi wanda na
kiraka dominsa." Saida muka qare cin tuwon
muka
wanke hannu badamasi yace"Matan Abba sun iya
abinci duk da masifarsu." Mukayi dariya,nace"Wal
lahi
kuwa,da zasu samawa kansu lafiya da sun zauna
daram da Abba domin shi bashi da hayaniya da
tauye hakki." Badamasi ya ajiye ledar ruwan daya
zuqe"Ai mata basu da wannan tunanin burinsu
dai
su ganka a rana su a inuwa." Nayi ajiyar
zuciya"Allah Ya shirya toh." "Amin." Na sanyo
masa maganar da
mukayi yau da safe da Abba. Ya tayani murna
sosai
sannan ya dubeni"Yanzu kai wace sana'a
hankalinka
yafi kwanciya akai?"Na saki ajiyar
zuciya"Agaskiya nafi sha'awar
bude store qarami na zuba kaya na ciye ciye da
sauran na amfanin gida haka." Badamasi
yace"Kwarai kayi tunani mai kyau abokina,Allah
Yayi
maka jagora,hakan ma yayi nima tunanin da nayi
maka kenan wallahi." Nayi murmushi,yace"Kai
nima dai na je da batun Jamila wajen
daddy,kwanan nan
za'a kai kudin aure." Na bude baki ina
mamaki"Kai
haba dai?" Yayi dariya"Wallahi kuwa,kasan yanzu
sai
da iyalin." Mukayi dariya,daga karshe muka bar
gidan muka nufi can majalisar idi. Har wajen tara
muna tare kafin daga bisani yayi mana sallama
ya tafi. ******************************
***************Cikin dare hayaniyar Anti ta
tasheni,na fito da sauri hankali tashe na nufi
tsakar
gidan. Tana ta balbalin masifa wai yau sai ta
qona
gidan kowa ma ya mutu. Abba yana tsaye yana
fadin"Jummai mene haka kikeyi kamar wata
yarinya qarama? Kina da hankali kuwa?" Sai ta
qara
harzuka"Eh din nayi,ai kai ka ja,wallahi Mudi ka
cuceni! Ka cuceni daka hadani kishi da wannan
tsohuwar banzar,ita wacece? An gaya mata
zatayi iko
dani ne? Wallahi bata isa ba don kaza kazanta.
Inna
ma ta fusata ta matso"Don Allah Alhaji barni da
ita! Barni da ita na koya mata hankali." Ta
matsar da
Abba ta fuskanci Anti wacce ke faman jijjiga tana
zaro jajayen idanunta"'yar iska wacce bata taso
cikin
tarbiyya ba sai ki dokeni nace,taba lafiyar tawa
kiga
yanda ake cin uban kishiya anan. Ai ke fadan
naki
ma na karya ne,wallahi ni Salame jikar dan indo
nafi karfinki,ke kin sanni kuwa?" Anti tayi kukan
kura ta
cakumi wuyan inna,da sauri na qarasa,Abba ya
shiga
tsakani,ya daka musu tsawa"Kai! Banason
iskancin
banza,ke Salame koma daki tun ban dauki mataki
akanki ba!"Inna tayi baya tana huci"Ni kika
cakuma?
Wallahi kinyi da 'yar halak Jummai." Zahra a
gigice itama ta fito tana mutsitstsika ido,ranar
anyi kata'i
dakyar Abba ya danna Anti daki,ya juyo ya dubi
inna
a fusace yace"Shige ciki." Inna taja tsaki fuu tayi
dakin Abba,Ya dubeni kamar zaiyi kuka"Jeka ka
kwanta Amadu." Na juya jiki a sanyaye na koma
daki. Tausayin Abba ne ya fi komai damuna,ranar
bazan ce wani a gidan ya runtsa ba,domin kuwa
ina
jiyo hayaniyar Inna da Abba. Abba kam baiyi
sa'ar
mata ba. Da asuba muna idar da sallah,abba ya
shigo
ya nufi dakin anti,can sai gashi ya fito,ta biyo
bayanshi tana kuka"Nagode ai dama dan adam
butulu ne,duk zaman da mukayi tare yau
sakayyar
da zakayimin kenan,nagode." Ta dubi dakin inna
cikin daga murya tace"Ke kuma tsohuwar kilaki ki
bar murna,wallahi sai na dauki mataki akanki."
Ta
koma dakinta,banji dadin hukuncin Abba
ba,inajin
sa'adda ta fito,ta shiga bugamin kofa kamar ta
karya,na fito ta bankamin harara"Eh ai kayi
murna mana,Dan shegiya tunda ka sanya an
koreni."
Nace"Anti don Allah..." "Dallah rufe min baki,ga
gidan nan sai ku cinyeshi,daukarmin jaka muje ka
nema mini mota." A sanyaye na dauki jakar,Abba
ya
fito ya dubeni"Kai ajiye,babu inda zakaje idan
taga
dama ta dauka da kanta." Na ajiye,ta fisge
jakarta tana tsaki ta bar gidan tana fadin"Aikin
banza
kawai." Abba ya bita da kallo sannan ya dubeni
ganin da yayi kamar banji dadin hukuncinsa ba
yace"Hakan shine daidai Amadu,na gaji da
wannan
rashin hankalin na jummai." Nace"Amma Abba
baka
duba yaran...." "Nasan da haka Amadu,nasani,ka
da ka damu ai ba sakinta nayi ba,nace taje ne ta
huta
kaji ko?" Na gyada kai ya juya ya koma ciki,nima
nayi
dakina zuciyata babu dadi.
Yinin ranar gidan babu dadi. Na fito wajen karfe
tara na safe na jiyo kukan Usman Qarami da
Salihu,na qarasa dakin da sauri ina mai sallama.
Zahra ta amsa,ita din ma durkushe take a qasa
hawaye shabe shabe a fuskarta. Na qarasa ciki
na riko hannun Usman qarami ya warce ya ja
da
baya"Usman,Salihu meye kuke kuka? Zahra ya
kika biye musu maimakon ki rarrashesu?" Zahra
ta share hawayenta cikin sheshsheka tace"Ya
zanyi dasu Yaya Ahmed? Nayi nayi suyi shiru
sun
qi ko karyawa basuyi ba wai su dole wajen Anti
zan kaisu." Tausayinsu ya kamani,nace"Amma
sai kema ki shiga kuka Zahra? Baki lallabasu?"
"Nayi iyakar qoqarina Yaya Ahmed,amma sun qi
shirun." Na girgiza kaina cike da tausayi na
dubesu"Haba Abubakar kaima babba dakai kake
kuka? Anti zata dawo tayi 'yar tafiya ne." Budar
bakin Abubakar sai cewa yayi"Karya kakeyi,ai
Abba ne yace ta tafi ta barmu." Zahra ta kai
hannu zata buge bakinsa na tare
hannun"Kyaleshi
." Tayi kwafa,na saki hannunta na dubeshi ina
murmushi"Da gaske nake Abubakar Antinku zata
dawo ku bar kukan nan ku ci abincinku." Nan
ma
dai basu kulani ba,na dubi Zahra itama lokacin
ta
bar kukan. Ta ja hannun Usman karami"Daina
kuka kaji 'dan anti,zata dawo nan bada jimawa
ba." Ya dubi Zahra"Dagaske kike anti zata
dawo?" Zahra tana murmushi ta gyada kai tana
goge masa hawayen. Yayi dariya"Toh ta dawo
yanzu mana." Zahra tayi murmushi"Zata dawo
dagaske ma,bari na dauko maka alawar data
siya
maka jiya ma." Ta mike ta nufi daki can ta fito
da alawoyi,ta mika masa daya,ya karba,suma
su
Abubakar suka amsa. Sai ga yaran sun sake,ta
hada musu shayi suka zauna zaman sha,na
dubeta mukayi murmushi sannan na mike na
fito
bayan nayi mata alama data zo. A zaure muka
tsaya,na dubeta"Zahra ki cigaba da rarrashin
kannenki kinji ko? Anti zata dawo." Hawayen
data
danne ya zubo"Anya Yaya Ahmed a yanda Anti
ta
yiwa Abba zai dawo da ita? Wallahi Yaya Ahmed
ina mai jin dacin wannan hali na Anti,ina
tausayawa Abba. Yanzu Yaya Ahmed kana ganin
akwai ranar da Antina zata bar wadannan
halayen nata?" Kawai sai ta qara qarfin
kukanta,ta bani mugun tausayi nace"Haba
Zahra,kin manta cewa Allah Shine mai
shiryarwa?
Ki cigaba da yiwa Anti addu'a,ita din takobi ce
ga
mumini ina mai tabbatar maki wataran Allah zai
amsa mana,wallahi idan har da qarfin addu'a
wataran Allah zai shiryi Inna da Anti." Zahra ta
gyada kanta"Hakane." Nace"Yauwa kinga ki
daina
yawan damuwa,ki kula da kannenki dakyau kinji
ko?" Ta gyada kanta. "Toh bakiyi min murmushi
ba?" Sai ma tayi 'yar dariya,nima na tayata ta
juya ta koma ciki na bita da kallo kafin na juyo
na koma daki ina mai tausaya mata.**********
*************** ********************Wajen
kwana
biyu da faruwar lamarin nan sai ga Anti ta
dawo,maman faisal,Hajiya Tamasar. A zaure
mukayi kicibus dasu,na gaishesu babu wanda ya
amsa,na basu hanya suka wuce nima nayi gaba
abina kada ayi wani rikicin kuma a gaban idona.
Kwana uku da dawowar anti,na lura yanzu bata
fiye magana ba musamman ga ni da inna. Saida
na bari hankalin Abba ya natsa sannan na
sameshi har kasuwa,nayi masa bayanin sana'ar
da na zaba,ya dubeni yana murmushi"Kwarai na
yarda 'dana ya girma." Nayi murmushi ina
dukar
da kaina yace"Toh Madallah,kayi tunani mai
kyau."Sati daya da faruwar hakan,abba ya bani
makudan kudi har dubu dari biyar domin na
zuba
kaya a shagon da ya bani dake nan titin
yakasai,ya
bani takardun shagon da komai. Bansan lokacin
da
hawayen farin ciki suka zubomin ba,ina mai
yiwa
Abba godiya da addu'o'i. Abba ya dafa ni"Haba
Amadu,kada kaji komai ka ji ko? Allah Ya ji kan
mahaifanka,nidai fatana shine ka tsaya ka nutsu
banda shashanci,ka rike sana'arka da kyau,ka
zamo
mara tsawwalawa a kasuwancinka kaji ko? Ka
riki
gaskiya Allah Yayi maka albarka." Nace"Amin
Abba,Allah Ya qara muku tsawon rai da lafiya."
Yayi dariyarsu ta manya(wai ya take ne?)sannan
yace"Amin Amadu." Na mike na tafi bayan na
sanya
kudin wanda ke cikin leda a aljihuna. A satin da
taimakon mijin anti aisha dana Badamasi muka
kammala komai na gyaran shagon,muka zuba
kayan
ciye ciye da amfanin gida na mata da
sauransu,muka hada shago babba. Na sanyawa
shagon"Alheri
Store." Tsayawa nayi daga jikin motar Badamasi
ina
duban shagon wai wannan mallakina na ne?"
Badamasi ya dan bugi kafadata"Ya akayi?" Nayi
murmushi ina mai girgiza kai"Babu komai,Allah
Ya
qara rufawa Abba asiri." Badamasi yace"Amin
Alhaji Ahmed." Mukayi dariyar zolayar da yayi
min,sannan
nace"Tukunna dai,ai kune manyanmu."
Badamasi
ya
girgiza kai"Ahmed kenan,ai abun Allah ba haka
yake
ba,sai kaga ya maida Sarki talaka,Ya maida
talaka
Sarki." Nace"Hakane,amma ina roqarwa kowa
budin
Allah." Badamasi yayi murmushi"Toh Allah Ya
dafa mana." "Amin." ***************
***************
***************Cikin ikon Allah shagon ya
soma
ciniki,na samu Tasi'u daya daga cikin
amintaccen
almajiran kawu murtala,yake tayani zama a
shagon
idan bana kusa. Sai ya zamana na rage yawan
chatting tunda dama zaman banza ne ke
sanyani,amma yanzu aiki ya samu. Saidai aikina
baya
hanani waya da sahibata. An sha rigima sosai da
Abba da matansa,wai akan me zai bani shago?
Dakyar dai maganar ta kwanta bayan Abba ya
sanya
musu doka akan duk wacce ta tada maganar a
bakin
aurenta. Haka yasa suka bar batun,amma tsana
qarara da hassada suke nuna min ya zamana ko
gaidasu nayi basu amsawa,Zahra kuwa har
dakina ta
iso tana mai fara'a,na mike daga kishingidan da
nayi
ina dubanta"Ya akayi kanwata?" Tayi murmushi
ta
dukar da kanta"Babu komai yaya,dama cewa
murna
nazo tayaka,Allah Ya qara daukaka." "Amin
kanwata,nagode sosai." Ta jinjina kai ta mike ta
bar
dakin. Na bita da kallo ina mai mamakin yanda
ta
sauyamin,sam ta daina daure min fuska,kodai ta
daina sona ne? Shine tambayar da bani da
amsarta.
Na sauke ajiyar zuciya na mike zaune,wayata
dake
gefe tayi ringing,sunan Beauty na gani a kai,na
dauka ina mai sallama ta amsa. A yanayin da
naji
muryarta na gane babu lafiya,nace"Beauty baki
da
lafiya ne?" Sai ma ta fashe da kuka,gabana ya
yanke
ya fadi. Mu hadu a AMADU kashi na biyu.
RUFAIDA UMAR IBRAHI

Amadu 2 Page 1
Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 13-Jun-15
Under: Amadu
Hankalina ya tashi,sai na tsinci kaina da daka
mata tsawa"Shut up Hafsa! Sanar dani meke
damunki,kukanki yana hargitsamin tunani." Dif
naji an kashe wayar,mikewa nayi na zari rigata
na
sanya na fice ko dakina ban kulle ba. Allah Ya sa
mukullin motar Abba yana gurina,tashinta nayi
kawai na bar unguwar. Gaba daya a rikice
nake,fatana kawai na ganni a gaban hafsa.Ta
dauke kanta daga kallona ta nemi kusa da
kujerata ta zauna. Noor ya sauka ya fita a
guje,na
maida hankalina kan hafsa. Muryarta a sarqe
tace"Ina kwana." Na dubi agogo shida ta kusa,na
jinjina kai lallai hafsa bata da cikin
hayyacinta,akwai
damuwa tare da ita. "Beauty shida na yamma ya
kusa kina kiran kwana?" Ta dan daga gira tana
murmushin yaqe"Oh wallahi na manta ne,ina
yini."
Na saki ajiyar zuciya ina mai dubanta sannan na
girgiza kai ban amsa nace"Beauty kin tayar mini
da
hankali,yanayin fuskarki kadai ya tabbatar mini
ba lafiya ba,sanar dani abunda ke damunki duk
kin
tadamin hankalina wallahi." Ta share hawayen da
suka taho mata murya a dashe ta soma
magana"Yaya Suleiman ne ya dawo daga turai."
Cikin
rashin fahimta na dan daga kafada"Sai akayi me?
Kuma ma waye shi?" Ta dubeni na dan wani
lokaci
kafin ta dauke kanta tana wasa da yatsunta"Yaya
Suleiman 'da ne ga wan Babana,Alhaji Sagir. Tun
muna qanana muke tare da shi,har girmansa.
Babana ne ya rike shi,mun shaqu dashi,gaba
daya
gidanmu babu wanda baya ji dashi. Toh yau
kwanansa uku da dawowa sai.....sai....." Ta kasa
magana muryarta ta dashe,nidai kam nasha jinin
jikina,na qara daure fuskata ina qoqarin kauda
tunanin da ya zo mini akan abunda hafsa ke son
sanarmin. "Ina sauraronki beauty." "Sai Yaya
suleiman yazo da wani sabon rikici wai sona
yakeyi,tun dawowarsa ake abu daya,har taron
family
anyi ance ya hakura yace shi sam a'a ai tun ina
qarama yake sona don me za'ayi masa haka?
Yanzu
har mamina ta soma yarda da batunsa,abbansa
kuwa har rigima sukayi da babana akan yana
son
hana danshi aurena. Ina cikin tsaka mai wuya my
heart,tun lokacin komai ya chanja,kakarmu wacce
ta
haifi babana haka take cin mutuncin baba tana
fadan wai ya hana 'dan dan uwansa zai bawa
bare,hankalina a tashe yake fargabata kada na
rasa
ka." Ta fashe da wani irin kuka mai tsuma
zuciya,ban
taba tsintar kaina a matsanancin tashin hankali
ba
akan soyayya sai yau,sai a yanzu na gane lallai
wuyar da nake ikrarin na sha akan soyayyar da
nayi tayi a baya shafar mai ce akan wannan.
Idanuna suka kada,kukan zuci kawai nakeyi,na
zubawa
Hafsa ido ina mai ambaton sunan Allah a raina
amma
na kasa furta komai. Karshe ma kawai mikewa
nayi
na bar dakin,hafsa a rude ta biyoni tana kirana
amma
ina ji nake kamar sai na bar gidan zan dan sami
nutsuwa. Motata na shiga ina shirin tayarwa sai
gata
a guje ta bude ta shigo gidan gaba. Dole na fasa
na dubeta,itama cikin kuka take dubana ta girgiza
kanta"Haka zakayimin? Anya son da kake min ya
kai
inda a kodayaushe kake ikrarin ya kai? Meyasa
zaka
tafi ka barni Yaya Ahmed? Kada muyi haka da
kai don Allah. Ka tausayamin Yaya
Ahmed,banason
yaya
suleiman kai nake so."Na yi saurin juyowa ji nake
kamar na rungumota sai kuma na fasa murya na
rawa nace"Beauty ya kikeso nayi? Zuciyata zafi
take,wallahi bazan iya bari ki kubucemin ba,na
soki
ina tsananin sonki. Ban taba son wata irin son da
na maki,nidai ina zaton bani da sa'a a rayuwa."
Na kifa
kaina jikin sitiyari a yayin da naji hawaye zafafa
sun zubomin.Hafsa itama kukan takeyi harda
sheshsheka kafin
tace"A'a yaya ahmed,idan kaima ka karaya ya
kakeso nayi? Don Allah ka bar hawaye,wallahi
kana
qara tada min hankalina." Hakan yasa na dago
ina
murmushin da yafi wuta radadi a wajena"Kina
zaton
nima ina kaunar ganin naki hawayen ne?" Tayi
saurin sanya hannu ta goge"Shikenan ko?" Na
jingina kaina jikin kujera ina duban Hafsa,itama
ni
din
take kallo kafin daga bisani ta kauda kanta gefe.
Na
saki ajiyar zuciya ina hadiye wahalallen miyau
cikin
nutsuwa nace"Hafsa." Dakyar tace"Na'am." Na
girgiza kaina"Kallona zakiyi." A hankali ta juyo
tana dubana"Kin yarda ina sonki?" Ta dan yi
murmushi
hade da dan nishi"Haba Yaya Ahmed,tun yaushe
kuma? Na jima da gaskata hakan." Na yi
murmushi ina mai jin dadi"Toh Alhamdulillah,h
afsa aurena
dake
babu abunda zai hanashi face ikon Ubangiji. Na
yarda mutum baya auren matar wani kamar
yanda mace bata auren mijin da ba nata ba. Mu
miqa lamuranmu ga Allah,muyita addu'a wataran
sai
labari
kinji ko? Kada wannan maganar ta firgitaki ko ta
sanya ki damuwa. Alhamdulillah tunda dai har
yau
baba yana bayanmu ko?" Ta gyada kanta na lura
hankalinta ya soma kwanciya,nace"Yauwa toh
kin gani,babban tashin hankali ya zamana shima
baban
yace dole sai dan uwan naki,mu yawaita addu'a
komai zai wuce insha Allahu. Ina ji a jikina Hafsa
matata ce,bata da miji sai Ahmed." Mukayi
murmushi,nace"Amma shine wanda naga ya fito
dazu ko?" Ta yamutse fuska"Shine yazo yayi yayi
na fito daga daki na qi qarshe dana ji motsin zai
shigo
na fada toilet." Wani kishi ya kamani,nace"Wato
har dakinki ma yake shiga?" Tace"A'a wannan ma
don
na qi fitowa ne. Meyasa ka tambaya ko wani abu
ya
faru ne? Na girgiza kai ina daga kafada"O'o ni me
yayi min zafi? Abunda banma sanshi ba,kawai dai
na masa magana bai amsa ba na lura hankalinsa
baya
tare dashi." Hafsa ta tabe baki"Shi ya sani." Nayi
murmushi"Nidai ki kularmin da kanki." Ta
sunkuyar
da kanta tana murmushi. Nan muka share batun
wani suleiman muka more hirarmu ta masoya,har
sai
gashi zuciyarmu tayi fari qal daga bisani mukayi
sallama saboda kiraye kirayen sallar magriba da
aka
soma.
Tun a hanya nake tunanin wannan
lamari,na
tabbata akwai rikici kwarai da gaske toh amma
tunda baba bai bada goyon baya ba komai zai
zo
da
sauki idan Allah Ya yarda. Kai tsaye shagon
alheri
na nufa,na tadda tasi'u zaune a bakin shagon
yana
hira
da wasu samari su uku. Mukayi musabaha,na ja
buta a gefen shagon nayi alwala. Ciki na shiga
na
shimfida
darduma na tada sallah. Tasi'u ya shigo ya
zauna,ina
idarwa na dubeshi"Zahraddeen ya zo kuwa?"
Tasi'u
yace"Eh yazo,ya bada saqo ma na baka." Na
gyada
kaina a yayinda tasi'u ya tafi ma'ajiyar kudi
domin dauko saqon. Ya miko min na kirga na
mika masa
ina cewa"Shiyasa gayen ke burgeni,akwai
hankali,sai ya
amshi kaya ko na nawa ne kuma ya kawo
kudin."
Tasi'u yayi 'yar dariya"Wallahi kuwa,yanzun ma
daya
kawo saida yace na baka hakuri bai kawo maka
da
wuri ba." Na girgiza kaina"Babu komai,ai na
yaba
da
hankalinsa. Mikomin littafin lissafi." Ya miko,na
shiga duba kayayyakin da suka kusan
qarewa,ina mai
tambayarsa,yana min lissafin kudade. Muryar
badamasi ce ta katsemu"A'a kaga manyan
alhazawa." Na dago na dubeshi mukayi
dariya,ya
ja kujera ya zauna,tasi'u ya gaidashi ya fita. "Ai
kune
manyanmu,ku da kuke ma'aikatan rediyo.
Bakasan kuna da farin jini ba?" Yayi
murmushi"Ina zamuyi
farin jini mu da ba ganinmu ake ba sai sauraro?
Muryar mu mai kama da an buga mandiri."
Muka
qara darawa,nace"Ai kuwa ko don iya turancinka
kayi farin jini." Ya dan tabe baki kafin ya
dubeni"Kai
kaga zanyi mantuwa ko?" Ya sanya hannu
aljihun
wandonsa ya ciro katin gayyatar daurin aure har
biyu ya miqomin. Na karba ina mai
dubawa,daya
na
kabir ne dayan kuma da imam." Ina dariya na
dubeshi"Kai haba,har abun yazo?" Badamasi
yace"Gashi kuwa,shi imam sati na sama,shi
kuwa
KB
wannan juma'ar da zamu shiga,jibi kenan dai
za'a ce insha Allahu." Na jinjina kaina"Abu yayi
kyau,Allah
Ya sanya alheri mu ma Allah Ya kawo namu.
Toh
sauran gaurayen sai yaushe kuma?(Hayatu da
haidar)." Badamasi yace"Shi kasan Hayat na
fadamaka yana Abuja,acan shima dai ya samu
matar
aure har iyaye sun shiga maganar,toh nan zuwa
bayan sallah qarama insha Allahu za'ayi
auren,shi
kuwa haidar na fadamaka auren zumunci zaiyi
da
cousin dinsa Muhibba,yanzu an tsaida rana nan
da wata shida dayake tana karantar law acan
Malaysia.
Sai ta gama zasu angwance." Nayi
murmushi"Allah
Ya nuna mana,nima dai nafiso da zarar Hafsa ta
qare zana paper ayi komai domin lamarin ya
soma
tsoratani." Cikin rashin fahimta Badamasi
yace"Kamar
yaya fa?" Na sauke ajiyar zuciya na labarta
masa
yanda hafsa tayimin bayani. Ya dafe kai"Oh
God!
Akwai matsala babba kuwa." Nace"Ni kuma
kasan
me? Ban fiye hangen girman matsalar ba
saboda
baba bai basu goyon baya ba." Badamasi yayi
wani
irin murmushi yana juya kai"Ahmed
kenan,kaidai
ka cigaba da addu'a kawai." Nayi murmushi mai
ciwo,nayi shiru cike da damuwa wajen kimanin
mintuna uku kafin nace"Kasan me?" "Saika
fada."
"Bana jin idan na rabu da Hafsa zan qara kula
wata budurwa wallahi." Badamasi yace"Daina
fadin haka,insha Allahu ba zata kubce maka
ba."
Nayi
murmushin takaici nace"Allah Yasa,kaji labarin
Aisha
ko?" Badamasi yace"Ba dai tsohuwar
budurwarka
ba da tayi aure?" Na gyada kaina"Ita fa,a bakin
idi nakeji,dayake a nan layinsu tayi auren. Wai
ta
fito
saboda mijin ya gane kudinsa ta aura,yanzu da
Allah
Ya jarabceshi da karayar arziki wulakanci iri iri
take
gasa mishi shi kuma ya sallamata." Badamasi
yayi 'yar dariya"Allah Sarki 'ya mace,mata suna
bani
tausayi wani sa'in Ahmed. Toshewar basira na
hanasu gane mai kaunarsu don Allah,wallahi
wata ba kyau ne da ita ba haka kawai sai kaga
Allah Ya
sanya maka kaunarta amma haka zata dunga
gasa
ka tana wulakantaka fite da tsammani. Kuma
wallahi
idan ta barka ka tafi da wuya ta samu mai
kaunarta
don Allah kamar kai din. Kai bama zata gane ba
kudin wani ya rudata sai bayan wasu lokuta
sannan zata ciji yatsa." Nayi murmushi"Gaskiy
ane,ai mata
suna wahalar damu." Badamasi ya zaro wayarsa
yana dannawa"Ai shiyasa yanzu na horu,bana
zurfafa kaunar mace a raina har sai na gama
gaskata
kaunarki agareni. Yanzu wallahi jamila ladabin
da
take yimin kai ko aurenta nayi sai haka. Tunda
na
ganta tsaye da wani saurayinta na nuna mata
fushina
harda kukanta,karshe ma alqawari ta daukar
min
ta
bar kula wani idan bani kadai ba. Shiyasa ba
shiri
na
tada maganar kai kudin nan." Mukayi
dariya,nace"All
ah dai Yayi mana kyakkyawan zabi." "Amin."
Mun
jima tare da Badamasi har bayan sallar isha'i
sannan ya bar shagon,nima nayi zaman lissafi
ina
gamawa
na qulla shagon lokacin karfe goma da rabi,tare
muka tafi da tasi'u bayan na dan yi masa alheri
na
saukeshi kofar gidan maza,inda suke kwana da
sauran almajirai sannan na nufi gida.
A satin muka sha bikin imam dana kabir,komai
wanda ya danganci angwaye damu
akayishi,daidai
da Dinner sun gayyaceni. Bayan mun rakasu
dakunan amaransu mukayi sallama dasu. Cikin
hukuncin Allah lokacin kuma su Zahra suka
kammala jarabawarsu,aka fara shirye shiryen
yaye su daga makaranta. A lissafe yayi sauran
wata daya
da sati biyu bikinmu,nan fa babu zama,duk
kudin
dana samu dama ba kashewa nakeyi ba,na
dunga
damqawa Anti Aisha tana ajiyemin saboda hada
lefe
da sauransu. A lokacin ne Abba ya kirani ya
bani
mukullin wani flat house dinsa dake a goron
dutse yace nan zan sanya amarya,idan da wani
gyare
gyare na sanar dashi. Bansan lokacin da na
shiga
sharar hawaye ba,abba ya dafani"Haba
Amadu,meye
abun kuka? Da kai da usmanu na daukeku
daya,abunda zan yi masa zan maka Amadu. Ka
manta ciki daya muka fito da mahaifinka? Ashe
idan mahaifinka yayi maka wannan kyautatawar
saika
sanya masa kuka? Haba amadu,komai nayi
maka
ai
tamkar shine yayi maka,ka bar hawayen
nan,fatana
bai wuce Allah Ya albarkacin auren nan naka
ba,Ya
kauda maka sharruka da fitina,Yasa hanyar farin
cikinka da kwanciyar hankalinka ne." Na share
hawayena ina mai shan majina"Amin
Abba,nagode
Allah Ya ja nisan kwana. Ya raya zuri'a." Abba
yayi
murmushi"Amin Amadu." Nan aka soma gyara
gidan
da Abba ya bani,ya zamana hankalina ya rabu
gida biyu,ga kula da shago ga kula da
ma'aikata.
Watarana da yamma na dawo daga wajen masu
aikin gida,kai tsaye ban tsaya a gida ba gidan
gwaggo na
nufa,ina cikin tafiya naji ana min hon,ban juyo
ba
har saida naji muryar idi yana fadin"Amadu kai."
Na
juyo
na hangeshi zaune gaban motar,cike da mamaki
na
tsaya motar ta tsaya daidai inda nake,idi ya riga
mai motar fitowa"Kai ana maka hon baka
ji,wannan
bawan Allahn ne yace yana son ganinka,nace ya
jira
zaka dawo yanzu ya matsa saidai mu bi bayanka
indai nasan inda kaje,dole tasa na rufe shagona
na rakoshi. Na dubi saurayin da ya fito daga
motar,na
qara cika da mamaki,SULEIMAN?? Me yazo
nema
a
guna,ya kauda kansa daga dubana,cikin sakin
fuska ya miqawa idi kudi yana fadin"Nagode
sosai bawan Allah,kana iya tafiya." Idi ya washe
baki ya juya
yana
godiya ya nufi shagonsa. Ya miqomin hannun
dakyar na iya daga hannuna na miqa masa cikin
daurewar kai,mukayi musabaha.Fuskar
kowannenmu idan ka kalla kasan cike muke da
kishin juna,amma babu wanda ya nuna
a
zahiri. Cikin murmushi nace"Bawan Allah neman
me
kake yimin? Gashi kuma ban ganeka ba." Na
qarashe cikin murmushin nawa,ya kauda kansa
yana mai
'yar
dariya"Gaskiyane abokina,sunana Suleiman
Sadisu Zango dan uwan Hafsat Rabi'u Zango."
Nayi dariyar
nima wacce bata kai zuci ba ina mai dan
rusunawa
kadan cike da wasa nace"Ashe da surukina nake
tsaye bansani ba?" Yayi min wani irin kallo
sannan ya
kauda kansa gefe yayi shiru yana murmushi
kafin
yace"Lallai fa,amma wannan da kake gani ba
surukina bane." Na gane inda ya dosa amma na
nuna ban fahimci komai ba ta hanyar nuna
mamakina akan fuskata"Toh kamar ya kenan?"
Suleima ya dubeni tsakar ido"Alfarma babba
nazo
nema a wajenka Ahmed,amma me zai hana mu
shiga daga mota?" Na fara gane take takensa da
dalilin
zuwansa wanda hakan ba mai yiwuwa bane,na
daga
kafada kadan ina mai dan tabe baki"Ba
matsala."
Ya
gyada kai sannan ya zagaya ya shiga mazaunin
direba,nima na bude na zauna. Shiru ya ratsa
kafin
yace"Ahmed ni din na girma ne a hannun
Baba,wato
mahaifin hafsa. Mun taso tare da hafsa,mun
shaqu
da juna fiye da zaton duk wani mai zato. Mun
rabu da ita
a dalilin fitar da nayi abroad don karatuna. Na
tafi
ina
mai tsananin so da kaunar Hafsat saidai Allah
bai
sa
na budi bakina na sanar da ita ba dalilina
kodayaushe bai wuce na ganin da nake mata na
yarinya ba. Ashe da rabon hafsa ta subuce min
ne,ashe da rabon na dawo na tadda hafsa ta
kusa
zama mallakin wani ne." Yayi shiru yana mai
sauke
ajiyar zuciya kafin ya jingina kansa kan sitiyarin
motar. Raina tuni ya baci,wani irin zafi nakeji a
zuciyata,harararsa nayi ba tare da yasan ina yi
ba
saboda ya rufe idanun,a zuciyata nace"Kayi ka
gama suleiman,amma na fika bukatar Hafsa."
Ya
dago
kansa sai ga hawaye,ko a jikina domin indai
hawayene kan ya zubda akan mata na riga shi.
Ya
dubeni"Nazo ka taimakeni Ahmed,wallahi
Ahmed
ko
nawa kake so zan baka,amma don Allah ka ceci
rayuwata ka bar min Hafsat,zan iya rasa raina a
rashinta." Zuciyata har rawa takeyi wani irin
radadi
nakeji,tsikar jikina tashi ya dunga yi ina mai jin
wani
irin takaicinsa. Na dubeshi da jajayen idanuna
kafin
nace"Bana tunanin ka kaini son hafsa,sannan
ban
gaskata batunka na cewa kana son hafsa ba.
Duk
masoyi yana burin yaga masoyinsa cikin farin
ciki
koda bashi ne silar sanyashi ba. Suleiman inda
ace
kai din masoyine na hakika ga Hafsa wallahi da
zaka
so abunda take so. Ni Ahmed ina mai tabbatar
maka
a yau inda Hafsa zata cemin kai take so ba ni
ba,wallahi ni mai hakura da ita ne na bar maka
ba
don bana sonta ba a'a sai don nasan idan har
kai
tafiso kuma ta sameka zata fi farin ciki fiye da
ace
ni
din da ta guda." Na juyo na dubeshi,shima ni
din
yake kallo da alama yana jin dacin maganata a
yanda
yake wani huci yana kallona kansa na
rawa,"Kayi
hakuri bazai iya rabuwa da Hafsa domin farin
cikinka
ba. Bazan iya rabuwa da hafsa ba saboda baka
fini bukatarta ba Suleiman,kuma ina roqonka
kada ka
qara tara ta da magana makamancin
wannan,domin
banajin zan iya jurewa kalamanka. Sai anjima."
Daga
haka na bude motar na fita. Cikin zafin nama
shima
ya bude ya fito ya sha gabana,rai a bace ya
nunoni
da yatsa"Kai waye da har zan nemi alfarma a
wajenka ka qi? Toh wallahi zan nuna maka
karfin
zumunta na kwaci hafsa daga gareka,kada ka
manta
ita hafsa 'yar uwata ce,ciki daya iyayenmu maza
suka
fito,ban ga wanda zai hanani auren Hafsa ba. Ni
suleiman ni ne mijin Hafsa,bazaka taba samun
Hafsa
ba Ahmed,bazaka taba ba." Daga haka ya juya
da
sauri ya fada motarsa ya figeta itakar qarfinsa.
Na bishi da kallon mahaukaci sabon kamu,kafin
na
cigaba da tafiya raina idan yayi dubu ya
baci.Ji nayi kamar na juya na koma gida saboda
yanda nakejin qunar zuciya,lallai suleiman ya
batamin rai fiye da tsammani. Toh amma nasan
ko
naje gidan baifi na qara haduwa da wani bacin
ran
ba saboda yanzu matan Abba ko abinci an daina
bani a cewarsu nayi kudi,na yagi rabona gurin
Abba ya ci ace na fara ciyar da kaina. A kofar
gidan na
hadu da kawu Hamza zai fita,har qasa na
durkusa na
gaidashi. Ya amsa fuska a sake yana
zolayata"Ango
ango,ashe abun ya matso ko? Toh Allah Yasa ayi
damu." Cikin murmushi na qara duqar da kaina
ina
mai amsawa ciki ciki. Daga nan na shiga ciki.
Sallama nayi,matan gidan suna zaune suna hira
abinsu,Bahijja ta taso"Oyoyo oyoyo yayana,har
mun
so muyi fushi ka bar leqomu." Na harareta da
wasa
bayan na gaida mutan gidan nace"Kinji wannan
'yar?
Ke yaushe rabon da kizo gidanmu?" Larai uwar
surutu ta cafe"kayya,ka manta halin matan
Abban
naka? Ta je su korota?" Mukayi
dariya,nace"Haba
dai? Ai ba zasu raba zumunci ba." Nafi ta tabe
baki"Ai
fa gashi suna rabawa,wai Amadu dagaske
bikinka
ya matso ko?" Da sauri na nufi wajen da gwaggo
ke
zaune kasan rumfa ina dariya,bahijja na dariya
tace"Wallahi kunya yake ji,amma biki ya matso."
Nafi kasa kasa tace"Nasani dama son jin ta
bakinsa
nake." "Tsohuwata mai ran qarfe,kina lafiya?"
Tace"Lafiya lau 'dan nan." Bahijja ta qaraso tana
dubana"Yayana da wani abu kamar ko?" Nasan
dama koda wani bai fahimci damuwata
ba,bahijja
zata fahimta. Nayi murmushi"Me kika gani dear
sis?" Na qarashe ina mai nuna mata gwaggo da
ido hakan
yasa ta waske ta bar batun tana mai mikewa.
Saida
na gama hirata da gwaggo tana min fada akan
kada
na bari zumunci ya lalace na dunga zuwa akai
akai,na tabbatar mata zan gyara na sallameta
da
bata
dubu. Sannan na mike nan ma matan
kawunnaina
na basu dari bibbiyu suna masu jin dadi da shi
min
albarka. Bahijja ta taso"Au yayana ni fa?" Ina
dariya
na nufi waje"Ki zo ki karba."Ai kuwa sai
gatanan,muka tsaya a zaure. A sanyaye
tace"Yayana
meke damunka ne?" Nayi murmushi,bana
boyewa
bahijja damuwata kamar yanda itama bata boye
min,na zayyane mata halin da nake ciki. Itama
sai
naga ta bata rai,ta ja qaramin tsaki"Amma
wannan
dan rainin hankaline,a zatonsa kudi zai rudaka?
Wallahi yayana kada ka yarda da batunsa kome
za'ay. Ai ita hafsar kai takeso,kuma duk
taqamar
da
yake na shi din zuri'asu daya ba lallai sai shi
din
ne mijinta ba. Gaskiya yayana kana bukatar
addu'a
sosai wallahi." Ta qarashe cike da tausayamin.
Na
jinjina kaina"Hakane kanwata,ki dunga tayani
addu'an kinji ko?" Tace"Insha Allahu
yayana,yanzu
kasan me?" "Sai kin fada kanwata." Ta girgiza
kai"Wallahi kada ka qara saurarar sa." Nayi
murmushi ganin da nayi ta fini damuwa
ba"Haba
kanwata ni ne fa? Ko kin manta ni? Ai koda
wasa
bazan qara tsayawa naji batunsa na banza ba."
Tayi
'dan murmushi"Yauwa yayana. Nima fa yarima
yace
muna yin celebration din candy dinmu na
makaranta
za'a yi biki." "Lokaci daya dai zamuyi auran
kice."
Mukayi dariya,tace"Naji ma fa abbanka yana
fadawa
gwaggo har da Zahra za'a hada saidai yace har
yanzu ta kasa fitar da tsayayye." Nayi shiru
kadan ina
mai tunawa ko rannan sai da wani gaye nan kan
layinmu ya zo yana sallama da ita tace ita fir
bazata
fita ba,amma ai da laifin anti amarya tunda ita
ke
hanata zuwa a cewarta dole sai faisal zata aura.
Abba
kuwa yace sam bazai bawa faisal mara tarbiyya
'yarsa ba."Kayi shiru yayana." Nayi firgigit na
dubeta"Toh kanwata muna dai yi mata addu'ar
zabin
Allah." Ta dubeni sosai kafin tace"Amma yayana
sai
nake gani kamar zahra kai take so wallahi." Da
sauri nace"Meyasa kika ce haka?" Gabana yana
faduwa
nayi wannan tambayar,banaso wani a gidan ya
gane
abunda ke ran zahra,nasan za'a iya cewa auren
zumunci! Tayi 'yar dariya"Wallahi kawai haka
nake
gani." Na harareta"Ita ta fadamaki?" Ta girgiza
kai"Kawai duba da yanda take kaunarka ne
kamar
ya zarta na 'yan uwan taka?" Na qara harararta
ina
mai qoqarin barin zauren"Kya ji da
gulmarki,amma
zahra tana da saurayinta." Ta biyoni da
sauri"Haba
yayana ina nawa kyautar?" Cikin dariya na zaro
dari
biyu itama na bata,tayi godiya ta koma ciki.Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100Amadu 2 Page 2
Posted by ANaM Dorayi on 06:41 PM, 13-Jun-15
Under: Amadu
Tun
daga nesa na hangi wata
tsaleliyar mota fake a kofar gidanmu. Mamaki ya
kamani na qarasa ina mai tunanin motar waye? A
kofar gidan na tadda abubakar ya fito zai tafi
shago,da sauri na dakatar dashi"Kai abu zo nan."
Cikin kunkuni ya zo,nace"Waye yazo?" Ya sanya
gudu yana mai daga murya"Yaya usman ne." Na
bishi da kallo sannan na qarasa ciki ina mai jin
dadin
zuwan yayan nawa duk da cewa ba shiri muke
sosai
ba. Har cikin gidan na shiga na jiyo muryarsu a
falon
Abba,nima na nufi ciki. Yana zaune ya sha
manyan
kaya,ya koma wani Alhaji,fatar sai sheki
take,matarsa fiddausi itama tana can gefe zaune
a kasa ta dan
dukar da kanta kasancewar Abba yana falon. Na
wangale baki ina mai qarasawa kusa da yaya
usman"Yaya ashe kana hanya? Barka da sauka."
Yayi dan murmushi"Yauwa Alhajinmu." Nayi 'yar
dariya ina girgiza kaina"A'a kune manyanmu."
Shima dariyar yayi,nace"Baka ga yanda ka yi kiba
bane
yaya." Da sauri inna tace"Tubarakallah." Na
dubeta ta
maka min harara,na sauke kaina. Abba na dariya
yace"Usmanu anya kana aikinka?" Falon akayi
dariya gaba daya,yace"Wallahi Abba muna aiki
sosaima." Shi dai abba kai kawai yake jinjinawa.
Da dare ga mamakina muna kwance,naji yaya
nata
soyewarsa a waya,na lura sam ba da matarsa
yake
waya ba,saidai abunda babu ruwanka toh naka
kallo da saurare. Na yi addu'a na kwanta bacci
ya
sureni,wajen biyu da rabi na farka domin gyara
kwanciya,nayi mamaki kwarai ganin yaya har
lokacin waya yake. "Ikon Allah." Kalmar ta subuto
daga bakina,yaya ya dubeni duk da cewa mun
kashe fitila amma haske wayarsa ta haskamu,ya
dubeni yana murmushi a lokacin da yace"Bebi
shikenan sai da safe ko?" Ya qara cewa"Kada ki
damu zan zo a mafarkinki." Daga haka ya kashe
wayar yana dubana fuskar dauke da
murmushi"Ya
akayi ne? Kasan aure zanyi nan kusa,yanzun ma
maganar ce ta kawoni wajen Abba." Na
razana,aure?! Na tambayi kaina,amma a fili
nace"Tooh,Allah Ya sanya alheri." Ya saki ajiyar
zuciya"Amin." Na gyara kwanciyata na juya na
cigaba da baccina,karfin baccin dake idona bai
bari
na tsaya tunanin maganar yaya usman ba.Misalin
goma na safe na shirya tsaf domin tafiya
shago. Yaya usman ya dubeni yana mai
murmushi"Alhazawa shagon za'a tafi?" Nayi 'yar
dariya"Wai alhazawa? Ai kune manyanmu." Ya
jinjina
kai yana mai dan tabe baki"Za dai mu zama
manyan
muddin burinmu ya samu cika." Na dubeshi"Allah
Ya tabbatar da alheri." Cikin sakin fuska
yace"Amin
amin,aure fa zanyi." A mamakince na dubi yaya
usman kafin nayi magana ya rigani"Mamaki ko?"
Na
kasa magana ina dubansa,ashe dai dazu ba
qarya
naji ba hakan ya sanar dani,ya juya yana goge
kansa
da tawul"Tun kafin na auri fiddausi,Alhaji Mahdi
wanda nake aiki a qarqashinsa ya bani 'yarsa
Hamidah,yanzu lokaci yayi kuma da zan
aureta,maganar ce fa ta kawoni yanzun." Nayi
jim,'yar alhajinsa? Sai kuma nace"Toh Allah Ya
sanya
alheri." Yayi murmushi"Amin." Na dauki wayata
na
zura a aljihu tare da handkerchief dina na fito ina
mai jinjina batun yaya usman. Cikin gidan na
nufa,a
tsakar gidan na tadda fiddausi ta fito ga tsohon
cikinta ya fito,tana rike da kayan kari. Ta dubeni
nima
fuska a sake na gaidata,tana murmushi
tace"Lafiya
lau Ahmed,yayanka yana ciki ko?" "Eh yana ciki
antinmu. Ko na taimaka na kai maki?" Ta
harareni tana 'yar dariya"Allah Ahmed ashe
kaima
kana da
tsokana,barni naje da kaina." Nayi dariya na fice
ina
mai sallama a kofar dakin Abba. Yana shirin fita
shima ya shirya,na durkusa na gaidashi,sannan
na
gaida inna ta dauke kanta tana mai amsawa
kamar
dole,ba don Abba na wajen ba nasan da wuya
ma
ta amsa min. Abba yace"Yanzu zaka tafi ne?"
Cikin
ladabi ina mai shafar kaina nace"Eh." "Toh
madallah,ka karya ko?" Nayi jim,na lura Abba
baida
labarin an bar bani abinci a gidan nan a dalilinsu
na
wai nayi arziki,na gyada kaina"Eh nayi." Ina ganin
sanda inna ta sauke ajiyar zuciya,nayi murmushi
kawai. Yace na jirashi a waje su ragemin hanya
na
fito. Dakin Anti amarya na leqa na gaisheta,ko
kallona batayi ba balle nasa ran amsawa,na mike
na
fita.****************************************
***Da misalin uku da rabi ina zaune a shago naji
wayata tayi qara,ba tare da nasan ko lambar
waye ba na dauka. Bayan nayi sallama,aka amsa
min daga
can sannan aka ce"Ahmed baka shaidani ba ko?"
Ina murmushi kamar mutumin na gani na
nace"Gaskiya ban gane ba." "Baban Hafsa
ne,Alhaji
Rabi'u Zango." Ai bansan lokacin dana sauka
daga
kujerata ba na durkusa kamar yana ganina,ban
damu da 'yan matan dake tsaye suna siyayya
ba,nace"Baba an wuni lafiya?" Yayi 'yar
dariya"Alhamdulillah Ahmed,dama lambar Alhajin
naka nake so ka turomin kaji ko?" Gabana ya fadi
na
daure nace"Toh baba,insha Allahu yanzu zan
turo."
Mukayi sallama yana mai samin albarka. Daga
bisani na mike na koma mazaunina ina mai sakin
ajiyar
zuciya. Na daga kaina sai lokacin na lura da 'yan
matan nan suna dariya gami da satar
kallona,nasan
bai wuce russunawar da nayi ne ya basu dariya
ba.
Nayi murmushi kawai ina mai cigaba da lalubo
lambar Abba,sai bugun zuciya nakeyi bansan me
wannan neman da baba ke yiwa Abba ke nufi
ba.Na zurawa wayar ido a lokacin da computer ta
tabbatar min saqon ya isa ga Baba.Na buga na
tambayeshi,ya qara tabbatar min ya gani,mukayi
sallama. Na sauke ajiyar zuciya ina mai jingina
kaina
jikin kujerar,na zubawa tasi'u idanu,ina jinsa
yana
hirarsa da 'yan matan nan,kallonsu kawai nake
amma gaba daya hankalina baya tare dasu,na
tafi
tunanin abunda zai faru. Karshe ma naji gaba
daya
zaman ya gagareni,na mike jiki babu kwari na
dubi
tasi'u"Ka kula sosai don Allah,zanje na dawo."
Tasi'u
ya gyada kai"Toh,sai ka dawo." Kai kawai na iya
gyadawa na fice ba tare da ko waiwaye ba. Kai
tsaye ban zarce ko'ina ba sai gidansu
Badamasi,baba
maigadi ya tabbatar min yana cikin gidan. Na nufi
sashen mami,a falo na tadda ita zaune,tare da
Badamasi,cikin dariya yace"Au dama kana
hanya?"
Nayi 'yar dariya a lokacin dana durkusa ina gaida
maminsa. Ta amsa fuska a sake,tace"Ahmed
kwana biyu saidai ka zo a ji sautin muryarka na
tashi daga
dakin abokin naka ko? Baka son qarasowa
gaisheni." Na sunkuyar da kaina ina mai jin
kunya,cikin murmushi nace"Ba haka bane Mami."
"Hakane mana Ahmed,don Allah a kula da
zumunci.
Ya kasuwa?" "Alhamdulillah." "Toh Allah Ya
taimaka." "Amin mami." Daga haka na koma
gefen
Badamasi na zauna,ya dubeni"Yane
mutumina,na
ganka wani iri fa." Na shafi kaina,daidai lokacin
da
mami ta mike tayi sama,"Kaidai bari sai a
hankali. Na
kasa samun nutsuwa,yanzu baban hafsa ya kirani
yake tambayar lambar Abba,na dai tura masa
amma ina fargabar abunda zai biyo baya."
Badamasi shima
yayi shiru yana tunani kafin yace"Ikon Allah toh
neman me kuma yake masa?" Na daga kafada
kadan"Ni kaina ba zance gashi ba,amma na
tabbata
akwai wata a qasa,fatana ya kasance alheri. Kai
ba na
manta ban sanar dakai yanda mukayi da wannan
dan iskan ba." Badamasi ya tashi daga
kishingidar da
yayi,yana dubana cikin rashin fahimta"Wa
kenan?"
Na zayyane masa yanda mukayi da suleiman,ai
sai ji
nayi Badamasi ya gundumo ashar. Na rufe masa
baki,ina mai nuna masa kafar bene alamun
mami
zata ji,ya cire hannun yana dariya,nima dariyar
nake,yace"Kai wallahi rainin hankalin ne yayi
yawa
bansan sa'adda na zundumota ba. Gayen nan
dan
iskan karshe ne,wato kai ka hakura ka bar masa?
Dan....." Sai kuma ya fasa yayi kwafa"Bar dan
iska,insha Allahu ba zai sameta ba." Nayi
murmushi
kafin nace"Kai ni yanzun ma na kasa samun
nutsuwa har sai naji dalilin neman Abba da baba
yayi."
Badamasi ya jinjina kai"Gaskiyane,kada ka damu
kanka,muyi fatan alheri dai." Daidai nan mai
aikinsu
ta sauko daga saman mami,badamasi ya
umarceta
data kawo min ruwa. Sai la'asar muka rabu da
Badamasi yana mai qara kwantar min da hankali.
Na kira Hafsa mukayi hirarmu kamar da,na lura
bata da
damuwa,idan ma akwai wata matsalar da neman
da
baba ke yiwa Abba toh bata da masaniya. Kai
tsaye
shago na koma ko gida ban leqa ba,anan na
tadda
tasi'u yana fama da masu siyayya. Na taimaka
masa
sai bayan an ragu ne,ya dubeni yana
murmushi"Oga kaji mutanenka ko?" Cikin rashin
fahimta na dan
daga kafada"Su wa fa?" Yayi dariya"Wadannan
'yan
matan daka bari,tambayana sukeyi wai don Allah
kana da aure ne? Nace musu ka dai kusa. Sai
suka ce
ko zan basu lambarka nace wayata babu
chaji,sunce
dai zasu dawo." Na ja qaramin tsaki ina dariya
hadi da girgiza kaina"Mata basu da kunya ko
kadan. Ai da
ka shina kace musu nayi auren,yanzu idan suka
dawo sai kasan yanda zakayi dasu don babu
yarinyar da zan saurara." Tasi'u yayi
dariya"Wallahi
oga daga ganinsu kuma 'yan duniya ne." Nayi
murmushi a lokacin da nake kakkabe kayan da
sukayi qura"Atoh 'yan matan yanzu suna zubar
da
qimarsu da mutuncinsu,basu jin kunyar bude
baki
suce suna son namiji. Mace duk inda aka santa
tana
da kunya da kamun kai,amma banda na yanzu.
Inda
hafsat ke burgeni kenan." Tasi'u yayi
murmushi"Gaskiyane oga,sai du'ai." Nima
murmusawar nayi na juya ina mai cigaba da
aikina.
Koda na komo gida bayan tashina daga
shago,kasancewar yau banjin dadin yanayina,da
wuri na tashi tun karfe takwas,a zaure na hadu
da
Zahra zata fita taci kwalliya. Na tsaya cak kamar
yanda itama ta tsaya tana jira na wuce kafin ta
samu shigewa,sai kamshi ke tashi hakan ya
tabbatar min
baqo tayi. Na girgiza kaina a zuciyata na ayyana
yanzu haka zahra ta zama? Wai itama har tasan
ta ci
kwalliya ta fita wajen saurayi? Jin da tayi shiru
ban
motsa ba yasa ta dago kyawawan idanunta ta
zubamin tana murmushi wanda na ganshi wani
daban kamar ba zahra ce tayi ba,muryarta cike
da
sanyi tace"Yaya Ahmed zan wuce." Sai ma na
jingina
da bango ina mai harde hannuwana guri daya
cikin
kwaikwayon muryarta nace"Aunty Zahra nima
wucewar zanyi." Tayi 'yar dariya tana mai sanya
hannu a fuskarta,nayi murmushi"Saurayinki ne
yazo ko?" Bata ce komai ba,na tabbata ko zamu
kai awa
nawa anan bazatayi magana ba,dole na bata
waje
ta
fice da saurinta. Zuciyata ta fara gayamin lallai
zahra
ta daina sona,kawai sai na tsinci kaina da sanyin
jiki,toh amma meye zan damu tunda ni din ma
hakan
nafiso? Na watsar da batun kawai na shiga daki.
Yaya usman baya nan ya fita,na fada kan gado
ina
mai cike da tunani. Hankalina ya kasa kwanciya
damuwa tayi min yawa,dole na mike jiki babu
kwari
na fito. Na wuce zahra tsaye a gaban wata baqar
siena,wani saurayine ya sha gogaggiyar shadda
sai
zuba yake yi kamar wani radio,babu nutsuwa,ita
kuwa tayi shiru kawai tana sauraronsa. Duk
wannan
kallon na yi a 'yan sakanni,na shige na nufi wajen
baba maigadi na na zauna,bana bukatar
hayaniyar
surutu hakan yasa na qi nufar wajen idi na
tabbata
zai takura min da gulmarsa ta banza kamar wani
mace. Baba maigadi yana zaune tare da tsofaffi
su uku suna hira nayi musu sallama sannan na
zauna,ya
dubeni"Malam Amadu ya siye da siyarwa." Nayi
murmushi"Wallahi Baba sai godiyar Allah." Tun
daga
haka ban qara cewa uffan ba,gaba daya
hankalina
ya koma ga su Zahra,har karfe tara ta buga suna
tare,takaici duk ya isheni,ni ba wani abu nake
tunani ba kawai dai yanda take wani doka masa
murmushi
sai kace wani mijinta. Mtsw idan banda kayan
haushi
irin na 'ya mace meye zata biyewa wannan
gajan?
Haka nayi ta saqe saqena dole dai na mike na
koma
cikin gida bayan mun hada ido da zahra na
harare ta
ta dauke kai kamar bata gani ba ta cigaba da
zancenta. Na qara jan tsaki na fada
dakina,wayata na
duba har sau uku hafsa na kirana. Hakan yasa
na
bi
bayanta,amma na tarar wayar a kashe. Toh ko
lafiya
kuma? Nake tambayar kaina a daidai lokacin da
nakejin faduwar gaba.Tsabar gajiya bansan
lokacin da bacci ya
kwasheni ba ina tunane tunane. Mafarkaina duk
akan hafsa ne,kuma marasa dadi. Hakan yasa na
tashi ina mai cike da dacin zuciya. Yanayin gaba
daya
babu dadi a gareni. Dakyar na mike na shiga
toilet,yaya usman baya dakin kodayake nasan
yana cikin gidan domin rana ta soma fitowa. Na
fito daga
wanka,na dauki wayana na qara gwada lambar
Hafsa har lokacin a kashe take. Jikina ya qara
yin
sanyi,koda na shirya tsaf na fito cikin gidan na
shiga.
Falon Abba na tunkara ina mai sallama,bana
zaton ya
ji saboda fadan dana ji yana yi wanda babu
tantama da yaya usman yake. "Yaushe kayi
auren
da har kake
batun yin wani? Anya kana da hankali kuwa?
Matarka da tsohon ciki kana batun qara aure
usmanu?" Banji abunda yaya usman yace ba,na
juya
na koma baya da zummar sai ya fito na shiga.
Toh ai
Abba da gaskiyarsa,ni 'yan uwana maza suna
bani mamaki,ace su dai sai kwadayin jaraba? Sai
kaga
wani namijin ma bai ajiye wani abun azo a gani
ba,kai wani ma aurensa na farko a gidan haya ya
sanya matar,amma don bala'i ya jajibowa kansa
wani
auren,na gida bai koshi ba amma yana qoqarin
qarawa kansa nauyi. Allah Sarki na tabbata
matarsa batasan wannan auren da yake shirin
jajibowa
kansa ba,tun jiya ta tafi gidansu yin kwana biyu.
Yanzu idan taji ko yaya zata dauki lamarin?" Ban
ji
fitowarsa ba sai takunsa naji,hakan yasa na bishi
da
kallo ban lura da yanayin fuskarsa ba kasancewar
ya
juyamin baya dakin innar tasa naga ya nufa. Nayi
sallama na shiga wajen abba,da alamun baya
cikin
walwala. Ganina ya dan saki fuska kadan,na
gaidashi,ya amsa yana mai dubana,ina shirin
tashi ya
kira sunana"Amadu." Na juyo"Na'am Abba." Ba
tare
da ya dubeni ba yana mai duban qasa yace"Zo
ka
zauna akwai maganar da zamuyi." Gabana sai
dukan tara tara yake,na dawo na zauna ya soma
magana"Mahaifin hafsa ya kirani a jiya da
yamma,yace yana son ganina. Ince dai Amadu ba
wani laifin ka aikata ba?" Na girgiza kaina tsabar
kidimewar da nayi murya na rawa na samu
damar
furta"Wallahi Abba banyi laifin komai ba." Abba
ya sauke ajiyar zuciya"Shikenan Amadu,na sanar
dashi
zan je yau da yamma idan Allah Ya yarda. Muyi
fatan
alheri naga kamar hankalinka ya tashi kada ka
damu
nasan Alhaji Rabi'u bashi da mugun hali,babu
abunda zai faru kaji ko?" Na dan sami nutsuwa
na
gyada kaina"Toh Abba." Yayi murmushi yana
shirin magana sai ga sallamar inna,daga jin
yanda sallamar
ta fito kasan muryar cike take da masifa. Na
amsa ina
maido dubana ga Abba,ya gyadamin kai alamar
in
tafi." Na mike jiki babu kwari,na russuna na gaida
inna,ta maka mini harara ta ja dogon tsaki,na
sanya
kai na bar mata falon tun kan na qarasa dauke
qafata daga dakin ta soma fada"Alhaji akan wane
dalili zaka ce yaron nan bazaiyi aure ba?" Abunda
na
iya ji kenan na shuri takalmana na bar tsakar
gidan.
Cikin sa'a dama ina tunanin yanda zan samu
ruwan
zafi domin yin kari,kasancewar na sayi madara
peak
na leda har biyar da milo biyar sai kullin sigari na
na ajiye,biredi kuwa tun dare idan zan dawo
daga
shago nake shigowa dashi,na hangi zahra a kicin
tana juye ruwan zafi,anti kuwa tun safe ta tafi kai
Salihu asibiti babu lafiya,banyi qasa da gwuiwa
ba na
qarasa bakin kofar kicin din,ta dubeni tana
murmushin nan nata,ta dan rusuna kadan ta
gaisheni,cikin murmushin nace"Lafiya kalau
kanwata,ya jarabawar taku? Yau baki da paper
halan?" Zahra fuska a sake tace"Eh yau bani da
paper,hafsa ce dai take da Geography amma sai
wajen hudu." Na gyada kaina"Ok,Allah Ya
taimaka,kawartaki ma tun jiya wayarta a kashe."
Ta min wani kallo dana kasa fassarashi,tana mai
fasa
kwai cikin bowl,tace"Uhum,ai inaji bata jin dadi
ne,domin jiya da safen munyi waya da ita ta
sanar
dani ciwon kai take fama dashi." Nima sai naji
babu
dadi"Allah Sarki,Allah Ya bata lafiya." Tayi
murmushi"Amin,a zuba ma lipton dinne?" Na
gyara tsayuwa"Kai kanwata kina da saurin
fahimta,zuba
min,ko na kawo kofina?" Cike da tausayawa ta
dubeni muryarta a sanyaye tace"Ka manta kana
da
kofi a kicin dinnan? Yaya Ahmed kayi hakuri don
Allah,naga kaima ka dauki zafi da hukuncin su
Anti.
Wallahi Yaya Ahmed duk sa'adda akayi girki na
saba na dauka na kawo maka naka,a yanzu da
aka daina
baka banajin dadi ko kadan. Akwai sa'adda na
diba
zan kawo maka,anti cewa tayi idan na taka zaure
da
niyyar kai maka abinci bata yafemin ba,shiyasa
dole
na zuba ido." Kwalla har sun cika mata
ido,tsayawa
nayi ina mai qura mata ido,babu tambayar dake
yawo a kwanyata sai guda biyu,Wane Irin So
Zahra
Takemin? Tausayine ko kuwa Tsantsar Soyayyar
ce?
Saidai banason na fiye damuwa da lamarinta,na
kauda wannan tunanin ina mai watsa mata
murmushi wanda zance ban fiye yinsa ba sai ga
mutane masu muhimmanci irin su Hafsa da
Badamasi. A hankali tayi qasa da
kanta,nace"Kanwata."
"Na'am." "Nagode da kaunarki gareni,Allah Ya
baki
miji nagari wanda zai kularmin dake,ya guji
dukkan
abunda zai batamin ranki." Da sauri kuma naga
ta
kalleni lokacin hawayenta sukayi nasarar zuba
akan
fuskarta mai sheki. Matukar tausayi Zahra ta
bani,na daga qafa zan shiga kicin din sai kuma na
fasa,da
sauri na juya ina fadin"Bari na kawo kofin." Ban
bari
na qara jin abunda zata ce ba na bar wajen.
Idanuna
nan da nan suka kada,ba shakka na yarda har
yanzu
Zahra na sona,ta yaya zan iya cirewa Zahra
soyayyata
daga zuciyarta? Inda ace zan iya da na dade da
aiwatarwa,meyasa zuciya bata shawara? Meyasa
zuciyar Zahra zata yaudareta ta hanyar kamuwa
da
soyayyata? Meyasa bata hango tarin hatsarin
cikin
kasantuwar hakan ba? Na runtse ido,abubuwa da
dama suna damun zuciyata,matukar tausayi ina
tausayawa Zahra saidai banajin zan iya karbar
soyayyarta domin bazan iya jure zagin da iyayena
zasu sha a wajen Anti ba. Dakyar na iya daukar
kofi
na koma kicin din,babu zahra saidai na hangi
ruwan
zafi a cikin kofin da ta kira shi da nawa an dora
plate
a kansa. Nayi murmushi mai ciwo,na tabbata
tana
cikin damuwa saidai bazan iya zuwa na
rarrasheta ba. Nabude naga kwai a ciki,nasan
nawa ne,na juye
ruwan zafin a kofin dana kawo na nemi leda
sanya
kwan a ciki,na bar kicin din. Nayi haka don bana
son
karya dokar dasu inna suka kafamin akan taba
kwanukansu. ******************************
************Bayan na gama kari na nufi shago.
Rabin hankalina gaba daya yana ga agogo,bini
bini
na kalla ina mai lissafin awannin daya rage Abba
yaje
ga Baban Hafsa. Da misalin karfe biyar mun
gama cin
abinci a shago,muna zaune da samari a kofa
muna
hira,har lokacin hankalina baya tare dani,wayata
tayi
qara. Na duba naga sunan Abba ya fito. Koma
meye TA FARU TA QARE!
Sallama na yi ina mai karawa a kunnena,Abba ya
amsa ya qara da cewa"Amadu kana ina?" Murya
na rawa nace"Ina shago." "Toh madallah,kazo
yanzu ina son ganinka." Saida naji faduwar
gaba,na amsa mukayi sallama. Na mike,usaini
daya daga cikin samarin nan ya dubeni"Sai ina?"
Nayi murmushi"Kiran Abba." Suka min fatan
dawowa lafiya na amsa na dubi tasi'u"Yanzu zan
dawo ka kula don Allah." Daga haka na fice,a
qafa na tafi ina mai addu'ar fatan alheri ga kiran
da Abba yayimin. Ban tsaye ko'ina ba sai a kofar
falon Abba,tunda na hangi takalma na sha jinin
jikina. Sai naji qafafuna sunyi nauyi,har saida
naga an daga labulen,yaya usman ne zai
fito,hakan yasa dole na shiga da sallama. Kawu
murtala ne da kawu lawal sai Abbana. Suka
amsamin,zuciyata rawa takeyi,na qarasa na
durkushe a kusa da Abba,a ladabce na gaishesu
suka amsa min. Shiru ya dan ratsa kafin na
tsinkayi muryar Kawu Murtala ya soma magana.
"Amadu." Cike da fargaba ba tare dana iya duban
fuskarsu ba na amsa"Na'am kawu." "Ka yarda
cewa komai da Allah Yayi mai kyau ne?" Gabana
ya cigaba da faduwa,ban iya magana ba illa dai
kaina kawai dana gyada. Ya cigaba"Madallah
,namiji baya auren matar da Allah bai tsaga
rabonsa bace,hakanan mace bata auren mijin da
basu da rabo tare. Amadu a yau munje gidan
Alhaji Rabi'u Zango da Abbanka,saboda kiran da
shi Abban naka ya samu daga gareshi. Bayan
munje mun tattauna akan aurenka da 'yar
wajensa. Ya bamu hakuri iya hakuri,ya nuna
mana cewa zai bawa 'yar tasa dan 'dan uwansa
a bisa umarnin da mahaifiyarsu wato kakar ita
yarinyar wacce ta haifeshi ta zartar cewa muddin
bai bawa shi dan uwan ba toh ba shakka zata
tsine masa. Toh kaga tunda har hakan ta shiga
dole idan kuwa shi din ya kasance 'da na gari ya
bi umarnin mahaifiyartasa. Kayi hakuri
Amadu,haka Allah Ya shirya maka,Allah Yayi kai
ba mijin Hafsa bane,ka daure ka sanyawa
zuciyarka hakuri da nutsuwa. Ka yawaita addu'a
domin yayewar soyayyarta daga zuciyarka. Kaji
ko?" Kawu lawan da Abba suka amshe"Gaskiyane
wannan." Abba ya soma magana cikin
dasashshiyar murya"'Dana kayi hakuri ka bar
batun yarinyar nan,kwarai basu kyauta ba da
sukayi mana haka. Kada ka takura zuciyarka
ansan dole ka damu amadu,kayi hakuri Allah Zai
baka wacce ta fita." Anya zan samu? Shin wai su
Abba sun san radadi da azabar dake cikin rashin
masoyi? Na ayyana a zuciyata,ban iya furta
komai ba,miyan bakina ya kafe dakyar na iya
gyada kaina,na mike tsaye. Ina dafe da kirjina,jan
kafata kawai nake,ina mai ji kamar na zube. Ina
daga kaina na hangi zahra tsaye a kofar dakinsu
tana dubana da jajayen idanunta ga hawaye na
zuba,na dauke kaina bance qala ba,ina shiga
dakina na zube a qasa ina mai zuba uban
tagumi.
Kukan ma ya qi zuwa,komai jinsa nake kamar a
mafarki ne. Na kasa gaskata lamarin ko kadan,na
qara jingina kaina jikin gado idanuna a runtse,kai
wannan maganar ba gaskiya bace." Toh waye zai
maka qarya a cikin bayin Allahn nan uku
Amadu?"
Tambayar da na yiwa kaina kenan,amsar kuwa
Babu! Domin babu wanda zai min wasa
makamancin wannan. Ga Zahra ma naga tana
zubar hawaye,kodai sunyi wata maganar da
aminiyarta ne? Ko kuma taji tattaunawarmu? Toh
ya za'ayi na qara gaskatawa? Tuni na tuna da
wayata,na lalubota a aljihuna,cak na tsaya ina
qarewa hoton Hafsa kallo dake jikin screen na
wayata kafin na sauke ajiyar zuciya.
A hankali na rubuta lambarta ba tare dana sha
wahalar lalubowa ba,domin na riga na haddace
lambar hafsa a kwanyata. Ya shiga ringing har
saida
ya kusa tsinkewa sannan naji an daga. Kusan
tare
muka yiwa juna sallama,mukayi shiru,a sanyaye
ta
amsamin nawa. Na lumshe ido ina mai jin
muryarta yana qara tsirgamin jikina,sai a lokacin
hawaye yayi
nasarar zubowa a kuncina. "Beauty." Shiru naji
sai
sheshsheka,zuciyata ta cigaba da yin zafi dakyar
na
daure na qara kiran sunanta. Tace"Na'am my
heart."
Ta fada murya na rawa. "Naji wata
magana,Abbanki
yace zaki auri suleiman hakane?" Ta hau
sheshsheka,nima har lokacin hawayena bai yanke
ba,na qara cewa"Beauty taimaka ki sanar dani."
Cikin
daga murya alamar dai muryar ta shake tace"My
heart ina cikin tashin hankali,a gefe guda ina
matukar tausayawa kaina na auran yayana
suleiman.
Wane hali zan shiga idan na auri waninka?
Wallahi bana jin zan iya biyayya gareshi. Yaya
Ahmed ka
taimakemu mu san abun yi kada mu fada kuncin
rayuwa sanadin wannan lamarin. A baya na yiwa
lamarin kallon sauki kasancewar baba yana
kaunar
aurena dakai,ashe akwai ranar da baba shima zai
amince da batun auren yaya suleiman?" Ta qara
fashewa da kuka ba kakkautawa,na rikici ni kaina
kukan nake. Nace"Hafsa." "Na'am my heart." Sai
kuma na kasa magana,kawai na kashe wayar na
ajiye gefe zuciyata na tafarfasa. Ban taba son 'ya
mace yanda naso Hafsa ba,bana jin zan qara
duban
wata budurwa a matsayin masoyiya bayan hafsa.
Ya zanyi ne? Na qara daukar wayar na danna
kira,ko
ringing biyu baiyiba ta dauka"My heart ya ka
kashe
wayar?" Nayi murmushin takaici"Beauty bazan
juri
sauraran kukanki ba,don Allah ki bar kukan nan.
Ya
kikeso nayi? Kina qara min damuwa."
Tace"Kayya,bana jin zan bar zubar hawaye
matukar ban sameka ba yaya ahmed,a yau baba
ke sanar
dani ya yanke aurena da yaya suleiman,ina cikin
tashin hankali. Har yanzu nafi tunanin mafarki
nakeyi
nan bada jimawa ba zan farka. Na kasa yarjewa
zuciyata cewa da gaske baba ya kirani yayi batun
aurena da yaya suleiman nan da sati uku.
Innalillahi,yaya ahmed kada ka barni don Allah."
Ta
qara sanya kuka,gaba daya ta gama gigitani,ni
kaina
hawayena ya qaru na mike tsaye. "Hafsa a ina
zan
ganki yanzu?" Da sauri ta amsa"Yaya Ahmed mu
hadu a gidan antina,unguwar daya ce ai ka
sani....."
Na katseta"Na gane,ganinan tafe." "Toh." Na
kashe wayar sannan na fito. Ban saurari motar
abba ba
kasancewar mukulli yana gurinsa,har lokacin yana
tare dasu kawu,na miqa nayi titi,na dakatar da
mai
adaidaita sai hotoro.Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100


Amadu 2 Page 3
Posted by ANaM Dorayi on 06:46 PM, 13-Jun-15
Under: Amadu
Har kofar gidan antinta aka saukeni,ina shirin
kiranta na hangota tana tahowa gidan. Saida naji
mugun FIRGICI ganin yanda Hafsa ta koma. Ta
koma
'yar siririya,babu wannan kumatun,gaba daya
kana
ganinta kasan akwai matsanancin damuwa,na
zuba
mata ido har ta qaraso. Idanunta farare tas sun
koma jajawur,ta duqar da kanta a
hankali,muryart
a dakyar
take fita tace"Yaya Ahmed ina yini." Na dubeta
sosai"Au beauty har kin chanjamin suna ko? Na
tashi
daga heart dinki na dawo dan uwa." Ta dago
kanta
tana dubana,hawaye na zuba ta girgiza kanta"Ba
haka bane,na fada ne kawai ba don wani abu
ba."
Nayi murmushi nima kwallah ta cikamin ido,a
sanyaye nace"Beauty,baba bashi da wani wanda
zai
fadamasa ya yarda da aurenmu?" Hafsa tayi
murmushin takaici mai hade da qaramin nishi"My
heart kenan,yayansa fa wanda suke uwa daya
uba
daya bai bada goyon baya ba saboda son
zuciya,eh mana son zuciya tunda 'dansa ya gani
yana so har ya
iya yayi fushi da baba akan ya hana yaya
suleiman
aurena. Toh bama wannan ba,kakarmu har gida
tazo
ta zaneni,ta ci mutuncin ummana a cewarta ita
ke
zugani na qi yaya suleiman,batasan cewa ita din
ma
tafison yaya suleiman ba. Nima na ci duka a
hannunta,baba kuwa tsine masa tace zatayi
muddin
bai yarda da aurena da yaya suleiman ba,hakan
ba
qaramin tashin hankali muka shiga ba. Baba yace
yaji
zai yi tunani tayi hakuri. Haka ta fice sai kuma
yau
baba ya zo min da wannan batun." Ta dago
kanta
muka dubi juna,gaba dayanmu hawaye
muke,murya na rawa tace"Don Allah my heart
kada kaga laifin
babana,wallahi bashi da lai...." Na dakatar da ita
ina
murmushin takaici"Haba beauty,me zai sa na rike
baba? Mahaifiya fa akace? Ko ni kina tunanin zan
sabawa mahaifiyata a bisa wani umarninta a
gareni?
Bansan dadin uwa ba,bansan ya ake ji ba idan
ana da uwa hafsa,ban taba dandanar dadin uwa
ba. Ni
maraya ne hafsa,duk da cewa bansan ya fushin
mahaifiya yake ba,amma nasan dole hankalin
baba
ya tashi muddin ran hajiyarsa ya baci. Biyayya
gareta
wajibi ne hafsa,a bisu a rabu lafiya shine yafi.
Muyi
hakuri hafsa,haka Allah Ya tsara mana. Idan ni
mijinki ne babu wanda ya isa ya hana
aurenmu,idan
ke ba matata bace bazan aureki ba koda nafi
quda
naci Hafsa. Ina mai baki shawara ki bi umarnin
iyayenki. Zan so ki sanyasu farin ciki,zan so ki
kubuto baba daga rantsuwar mahaifiyarsa. Zan
so ki
kasance 'ya mai biyayya hafsa,inason naga
mutum mai kaunar iyayensa,mai son farin
cikinsu.
Banason
mutum mai wulakanta iyaye,mai tozarta su
musamman ma MAHAIFIYA,wacce ta dauki
cikinka
tsawon watanni tara ta haifeka tana mai shan
baqar
wuya,ta hau rainonka duk bata huta ba har saida
ta
taimaka maka wajen samun ilimi ingantacce.
Hafsa ina sonki amma duk son da zan maki bai
kai na
iyayenki ba,wallahi hafsa iyayenki sun fini sonki.
Kibi
umarninsu zaki ga abunda suke maki hangensa
na
daga jin dadin aure. Allah Ya bamu karfin da
zamu
jure rashin juna,ina maki fatan alheri a aurenki
da
suleiman. Allah Yasa ya zamto hanyar farin
cikinki a rayuwa,Allah Yasa muyi hakuri da juna.
Nagode
Hafsa,a rayuwa kin kaunaceni,bayan zahra bana
jin
akwai 'ya macen data nunamin so na hakika da
kuma tausayi irinki,Allah Ya sadamu da alheri."
Daga
haka na juya da sauri na barta nan tsaye,ban
qara
waigenta ba domin banason ganin yanayin data
shiga wanda nasan ba mai dadi bane. Dakyar na
saita kaina na tsaida adaidaita. Murya a dashe
nace"Yakasai zaka kaini." Ban qara magana ba
ya ja
muka bar layin. Tun ina motar naji kaina yana
sarawa,ta dafe da hannu biyu ina mai runtse
ido,ni
kadai nasan me nakeji a zuciyata. Allah kadai
Yasan irin son da nake yiwa Hafsa,ashe
rabuwarmu na
kusa?
Ina isa gida daki na shige. Gado kawai na
fada,har lokacin kaina bai bar sarawa ba. Kafin
wani
lokaci naji zazzabi ya rufeni,na kasa tashi. A
hankali
nake jin hawaye na shatata daga idanuna. Na
runtse
ido,duk jarumtar namiji sanadin soyayya yakan
koma rago. Na kasa sarrafa zuciyata,da zarar na
tuno na rabu da hafsa sai naji wani kunci ya
mamayeni. A
haka bacci ya kwasheni,sai ji nayi yaya usman na
tashina"Kai lafiyarka kuwa,gashi yanzu har an
idar
da magriba kana kwance?" Na bude rinannun
idanuna,na mike zaune dakyar,kaina ya tsananta
ciwo,har wani fat fat gefen kaina yakeyi don
tsananin ciwo. Daidai da hannuna da na shafa a
fuskata saida naji zafin da ya dauka. Na lashe
busassun lebbana dakyar na qoqarta na mike,ina
duban yaya usman wanda ke zaune da abokinsa
Abdul. Ina mutsitstsika ido na nufi toilet. Ba
jimawa
na fito na tada kabbara,da kyar na idar da
sallah,na zauna anan na kasa mikewa ina mai
duban yaya
usman da abdul suna kwasar hira akan budurwar
da
yaya usman zai aura,sam ban fahimci komai ba
hankalina yana ga tunanin abunda ya dameni.
Abdul
ya katseni"Alhaj Ahmed kamar baka jin dadi ko?"
Hakan daya fada yasa yaya usman waigowa yana
mai dubana,yace"Oh baka da lafiya ne? Af! Ashe
fa
naji labarin an hanaka budurwarka ko?" Ya ja
tsaki"Kai ka damu,mata da yawa meye don daya
ta
guje ka? Kai ka wartsake ka nemi kudi
kawai,aure
lokaci ne." Banyi niyyar dariya ba,amma saida
yasa
na murmusa cikin zafin ciwo. Ban ce komai
ba,Abdul yana dariya ya qara dubana"Allah
dagaske Ahmed
bashi da lafiya." Yaya usman ya tabe baki yana
mai
mikewa"Shine zai zauna kamar wata mace,ya
mike
ya je ya nemi magani mana. Idan ka qare
shishshigin
kazo mu ware." Ya fice daga dakin,abdul ya mike
ya
dubeni"Don Allah ahmed tashi kaje ka nemi
magani,Allah Ya bada lafiya,Yayi maka wani
zabin."
Na lumshe ido kadan ina murmushi a ciki na
amsa. Ya
fita nabi bayanshi da kallo,a hankali na mike,ba
shakka raina ya qara sosuwa da rashin hafsa,na
shuri takalmana na fito. Nayi hanyar waje sai ga
salihu,"Ahmed kazo inji abba." Na juyo,tuni ya
koma ciki,na juya nabi bayanshi. Dakyar na
qarasa dakin
da sallama,ya amsa sannan na shiga. Ido ya
zubamin
har na nemi gefe na zauna,yace"Subhanallah
Amadu
baka da lafiyane? Ga idanunka sun kada,meke
damunka haka?" Na sunkuyar da kaina kafin
nace"Zazzabi ne da ciwon kai." "Assha,haba
amadu,meyasa zaka takurawa kanka? Meyasa
hakanan? "Maza tashi ka sami yayanka,kace nace
ya raka
ka asibiti." Na mike ya dakatar dani,ya miqomin
kudi
har dubu biyu,na amsa ina godiya sannan na
juya
na
fito. Har lokacin idon Abba a kaina. Na shuri
takalmana na bar gidan cike da tunanin yanda
yaya
usman zai amince da hakan. A zaune na gansu
tare da abdul suna hira,na qarasa gareshi"Yaya
Usman
Abba yace ka rakani asibiti." Ya dubeni kafin ya
ja
tsaki"Yanzu kai don Allah baka ji kunya ba? Da
girman naka sai an rakaka asibiti kamar wani
qaramin yaro?" Abdul ya dubeshi"Haba kai
kuwa,kamar baka san rashin lafiya ba? Ka dunga
yi masa uzuri mana." Ya cigaba da danna
wayarsa ran a
bace,sai kuma ya qara jan qaramin tsaki ya zura
hannu a aljihu ya ciro mukullin motarsa ya
mikomin"Gashi kaje ni kam bazan iya binka ba
don
gaskiya ina da abun yi,sannan ka kula kada ka
buga
min mota na lura kana fama da ciwon so ne." Na
girgiza kai kawai ina murmushin karfin hali,cikin
ikon Allah sai ga motar Badamasi ta tsaya,ya
faka ya
fito,ya qaraso sukayi musabaha da yaya usman
da
abdul. Ya dubeni"Ya dai mutumin?" Na juya ga
yaya
usman na mika masa mukulli"Gashi Badamasi sai
ya
rakani." Ya karba yana fadin"Ai gwara hakan." Ya
karkata kansa yana mai cigaba da danne
dannensa,abdul ya dubeni"Toh Ahmed Allah Ya
baka lafiya,sai kun dawo." Murya a dashe na
amsa"Nagode." Muka jera da Badamasi har
mota,bayan mun soma tafiya ya dubeni"Naje can
shagonka ban sameka ba,tasi'u ke sanar dani tun
da yamma ka bar shagon gashi nazo na tarar
dakai ba
lafiya,meke faruwa ne?" Kaina na kwance jikin
kujera,jikina yana rawar sanyi,muryata dakyar
take
fita nace"Taimaka ka kashe AC please." Ya
dubeni"Ai
ba'a kunne take ba." Na runtse ido
nace"Ok,dagamin
glass toh." Ya daga ya rufe na saitina,kafin
yace"Sannu." Na gyada kaina,shiru mukayi kafin
na
soma magana cikin azabar ciwo"Na rasa Hafsa."
Cikin
rashin fahimta badamasi yace"Kamar ya kuma?"
Nayi
murmushin da yafi wuta radadi a zuciya"Kamar
yanda na fada,a yau Baba ya kira Abba har gida
yace
ayi hakuri hafsa zata auri suleiman." Wani burki
Badamasi ya taka a lokacin da danja ta tsayar,ya
dubeni a razane"Innalillahi wa inna ilaihir
raaji'un,meyasa Baba zaiyi mana haka? Wato
abun
nasu son kai ne." Na girgiza kaina,a yayin da
idanuna ya cika da kwalla mai dumi"Babu laifin
Baba,shima umarnin MAHAIFIYA yake bi. Ni
yanzu damuwata daya badamasi,yanda zan cire
Hafsa a
raina. Ka tayani addu'a please." Badamasi ya ja
motar
ba tare da ya yarda mun hada ido ba,na lura
shima
jikinsa yayi sanyi,tausayina yakeji. Na qara duban
hanya sannan na dubeshi"Wane asibiti ka nufa?"
Murya a sanyaye yace"International,can wajen
bata." Bance komai ba,ina mai tunane
tunanena,muryarsa
ta qara katseni"Ahmed,duk abunda Allah Ya
tsarawa
bawanSa hakika alheri ne. Ubangiji baya dorawa
bayinSa abunda Yasan ba zasu iya dashi ba.
Ubangiji
Ya qaddara hakan. Kayi hakuri,Allah Ya baka
lafiya,Ya zaba maka wata wacce zata nuna maka
soyayyar da zaka mance ka taba son wata 'ya
mace
ka rasata a rayuwa,wacce zata soka fiye da
zatonka.
Allah Ya baka wacce zata share ma hawayenka,ta
mantar da kai dukkan bakkan ciki." Zuciyata tayi
sanyi,kwarai naji dadin addu'arsa,a hankali
nace"Nagode Badamasi." Amma kwarai nasan da
wuya na qara kallon wata 'ya mace da zummar
soyyaya. Na ayyana hakan a raina.Munje likita ya
rubutamin magunguna,koda mukaje siya ina
qoqarin miqa wa Badamasi kudin ya dakatar
dani,da
kudinsa ya siya. Koda muka isa gida,nayi masa
godiya,ya dubeni alokacin da yake shirin
tafiya"Don Allah ka kwanta ka huta,ni zan wuce
Daddy yana
jirana." Nayi masa godiya ya tafi. Na hada shayi
da
ruwan pure water na sha hakanan ba tare da
biredi
ba,na hadiyi magungunan. Nan na kwanta ina
mai
duban wayata dake ta blinking na haske
yellow,wanda hakan ya tabbatar min babu chaji.
Zuciyata har lokacin bata sake ba,tunanina bai
wuce
yanda zan juri rashin hafsa ba,a ranar gaba daya
duniyar siremin tayi,Allah Sarki iyaye. Su kadai
suka
fadomin a raina,ina son Abba ina kaunarsa
saboda
yanda ya damu da lamura na,amma hakan bazai
mantar dani dadin iyaye ba wanda ban taba
dandanarsa ba,wacce nake sa ran samun
walwala
daga gareta Allah baiyi zata zamto rabona ba.
Haka
nayi ta tunane tunanena har tasi'u yayi
sallama,na
bashi hakurin rashin dawowa da banyi ba,yayi
min
sannu da fatan samun lafiya kafin muyi sallama
ya
wuce gida.
Washegari da safe cikin hukuncin Ubangiji na
tashi garau saidai rashin kwarin jiki. Yaya Usman
tuni
ya fice,ba shakka na jima ina bacci tun bayan
komawata da asubah yanzu har tara da wani
abu. Na
wanke fuska nazo domin hada shayi na tarar
babu
madara gashi jiyan ma ban samu damar siyan
biredi ba. Dole na hakura zan sha ruwan lipton
toh shima
na tarar ya tafi garinsu."Allah mun gode maKa."
Shine furucin da nayi. Na mike a niyyata nayi
wanka
tukun,amma wani jiri ne ke dibana banajin ko
nan
da
can zan iya takawa. Na ja qaramin tsaki ina mai
dafe
kaina,motsi naji za'a shiga gidan. "Waye ne?" Na
fada murya a dage,naji tace"Ni ce." Na sauke
ajiyar zuciya
nace"Oh Zahra ce,zo don Allah na aikeki." Ta
amsa da
toh sannan ta shigo,da alama aikenta akayi
saboda
kudin da na gani rike a hannunta,ta durkusa tana
gaisheni,tana mai tambayar lafiyata,na amsa ba
tare
da na qara dubanta ba domin na lura ni din ma
ba son kallon nawa take ba,hakan bai wuce
saboda
yanayin kayan jikina ba. Na sa hannu kan
akwatin
kayana na janyo wandona na jiya,na lalubo mata
dubu na miqa mata"Gashi ki taho min da madara
da
biredi don Allah." Anan ne ta dago idanunta,na
gansu kamar wanda suke ciwo saboda ja da
kumburi,ta karbi kudin nima ina dubanta da
nawa
idanun wadanda bacci ya rinar nace"Zahra." Ta
dago
tana dubana bata ce komai ba sai ma ta sauke
kan"Kina ciwon ido ne?" Ta girgiza kanta. Na
zuba
mata ido,har ta gaji ta mike"Bari na siyo kada
anti
taga na jima." Bance mata komai ba ta fice da
sauri,na tabbata damuwar Zahra yana da alaqa
dani,ta
burgeni wajen alkunyarta. Tausayinta ya
mamayeni,"Kiyi hakuri Zahra,Allah Ya fito maki
da
mijin da zai baki kowane irin farin ciki na
rayuwa."
Na furta a fili. Na dubi wayata babu chaji da
kanta ta
mutu,ai gwara ma data mutun zan fi samun
nutsuwa fiye da ace tana bude,domin hoton
Hafsa
ne ya
mamaye kan screen dina,dole yanzu na cire ko
banaso tunda tana dab da zama mallakin wani.
Lallai
Suleiman ya ci nasara,amma na tabbata sai yayi
dana
sanin auren hafsa,domin banajin zata taba sonsa.
Koda ace zata so shin,bana jin zai taka rabin
rabin wanda tayi min. Yanzu dole na dakatar da
anti data
fara yimin siyayyar kayan lefe ko? Na tambayi
kaina,na kuma bawa kaina amsa,Eh mana,dole
ma a
tsayar a haka,toh zan yi aurene? Ai banajin zan
qara
duban wata mace matsayin matar aure domin na
gane bani da sa'a a wannan bangaren. Na gama
soyayya,anya kuwa zan qara kallon wata mace da
zummar yinta?" Tayi sallama ta shigo,na dago
kaina
na dubeta,idanunmu suka hadu guri daya,ta
dauke
kanta tana murmushi ta miqomin"Gashi Yaya
Ahmed." Na karba ina dubanta,har saida ta juya
na
iya furta"Nagode." Bata ce komai ba ta wuce rike
da leda a hannunta. Sai kuma ta dawo,"Yaya
Ahmed ina
kofin ka? Ya kamata ko flask ka siya na dunga
zuba
maka ruwan zafi bai kamata ace kana amfani da
ruwan sanyi ba duk da nasan babu aibu a yin
hakan." Nayi murmushi ina duban
Zahra"Gaskiyane
kanwata,amma ina gudun batawa iyayena rai."
Ta dan tabe baki"A'a bakomai,kada
kadamu,bazasu
san na aikata hakan ba." Sai ma ta bani dariya
na
mika mata kofina ina mai cewa"Shikenan,Allah Ya
biyaki kanwata." Ta qara murmusawa lebbanta
na
motsi na gane furucin amin tayi. Ina zaune ina
jiranta
da tunani iri iri a kwakwalwata,sai gata da sauri a
bakin kofa ta dire"Gashi yaya ahmed." Daga haka
ta
fice da saurinta,na janyo ina mai tunanin lokacin
da
anti da inna zasu sauya,ya ci ace mutum yana
girma
yana qara hankali amma su dai kam bansan inda
suka dosa ba. "Allah Ya kyauta" na
furta.********* Da misalin karfe
biyar na yamma,na taka naje gidan gwaggo a
dalilin kiran da na samu daga gareta ta wajen
tasi'u.
Na sameta a dakinta zaune,bayan gaisuwa na ja
ta da
wasa kamar yanda na saba. Tayi dariya sannan
tayi
shiru cikin sanyin jiki kuma ta fara
magana"Amadu
ashe kuma haka al'amarin ya koma?" Murmushi
kawai nake ina kakkabe qasan wandona,ta qara
da
cewa"Lallai mutanen nan basu kyauta ba,sun
nuna
gwara su baiwa yaronsu da su baka kenan,toh
madallah ai kai dinma dan dangi ne,ba daga
sama ka
fado ba." Cak na bar abunda nake na
dubeta,"Toh
me kike nufi?" Ta harareni"Abunda ka
fahimta,kaima auren dangi zamu yi maka mu
nuna musu bawai
babu ce tasa muka fita ba." Maganar ma dariya
ta
bani,na kyalkyale da dariya,tace"Au dariya ma
kake
kenan? Ja'irin yaro,ya jikin naka?" Na bar
maganar
wasa"Na samu sauki,gwaggo don Allah daina
wannan batun naki ma don ba abune mai
yiwuwa
ba indai ba kun gaji da ganina bane a duniyar..."
Ta
dakatar dani"Assha amadu,daina batun
mutuwarnan kaji ko? Insha Allahu sai naga
jikonka.
Kaida mutuwa ba yanzu ba insha Allah." Nayi
murmushi domin gwaggo batason batun
mutuwa,nasan yanzun ma iyayena ta tuna. Sai
gata tana hawaye"Allah Ya jikan muttaka da
safiya."
"Amin gwaggo,kin manta da mijin naki?"
Tace"Toh,shima Allah Yayi rahma agareshi." Cikin
murmushin na amsa,na dora da cewa"Gaskiya ki
bar
hawayen nan kafin su kawu su ganki suce nazo
na
rikita musu uwa." Ta harareni"Ai kai dinne kuwa
ka rikitani,yanzu ma idan kaje ka cewa abban
naka
yazo ina son ganinsa. Sannan kaje ka kira min A'i
itama ko zuwa gobe kace tazo nan zamuyi
magana."
Gabana ya fadi,nayi dum kafin nace"Toh ai
shikenan,nidai kada ayimin auren dole don bazai
yiwu ba." Mukayi dariya tace"Dan nema,kaidai
tafi kaji da lafiyarka koma mene za'a nemeka."
Na tabe
baki,na zura hannu aljihu na zaro goro a kulle a
leda
na mika mata,ta karba"Ai fa saidai goron,amma
baka
iya kawomin mai maiko ba." Nayi dariya"Atoh ni
da
ake shirin yiwa auren dole,a barni naji da
kaina,kada
ku nemeni ku rasa. Inda nasan kiran kenan ai
da.." Sai kuma nayi shiru,"Qarasa mana." Ta fada
tana
bude ledar goro,nayi murmushi"Nayi shiru dai."
Ta
girgiza kanta"Babu mai yi maka auren dole
Amadu,ka kwantar da hankalinka kai dai." Na
tabe
baki kadan ina daga kafada"Hankalina kwance
yake,aure ba yanzu ba gwaggo. Ki huta lafiya."
Na fice daga gidan,Bahijja bata nan wai tana can
bikin
qawarta.

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100


Amadu 2 Page 4
Posted by ANaM Dorayi on 07:24 PM, 13-Jun-15
Under: Amadu
Kai tsaye gidan anti aisha na nufa,tana kwance
akan kujera na shiga da sallama. Ta mike zaune
tana mai amsawa,bayan gaisuwa ta zura min ido.
Na dauke kaina cikin murmushi nace"Kamar ma
baku jin dadi ko?" Anti Aisha tace"Kai zan
tambaya amadu,kaga yanda ka rame kuwa kamar
ba kai ba? Ince dai lafiya." Na sosa kaina"Anti
kenan,mun gode Allah toh. Lamuran ne sai a
hankali." Taqara kallona a yayin da take gyara
daurin dankwalinta"Ka sanar dani Amadu meya
faru dakai,gaba daya ka chanja kallo daya za'ayi
maka a gane kana tare da damuwa." Na
sunkuyar
da kaina kafin na koro mata yanda akayi game
da
Hafsa." Ai sai ga anti aisha na salallami"Au haka
sukayi mana?" Nayi murmushi"Haka Allah Ya
tsara anti." Sai kuma ta bini da duban
tausayi"Banji dadin lamarin nan ba,amma kada
kayi fushi da yin Allah." Nan tayi min nasihohi
kafin mu shiga maganar abunda ya kawoni,na
nuna mata ya kamata asan yanda za'ayi da
lefan. Ta jinjina kanta"Kada ka damu da
wannan,zan san yanda za'ayi." Na sauke ajiyar
zuciya,na sanar da ita kiran da gwaggo ke
mata,tace"Toh saidai goben,nasan malam bazai
hana ba,zan shiga insha Allahu." Daga nan
mukayi sallama.**********************
*****************A daren mun jima da
Badamasi
yana kwantar min da hankali ta hanyar jana da
hirarraki don na mance da batun Hafsa,haka na
bishi yanda yaso na nuna masa ni din ma na
manta mukayita hira,har daga bisani mukayi
sallama ya tafi. Saida nazo kwanciya bacci ya
dauke,tunanin hafsa fal a zuciyata. Rayuwarmu
kawai nake tunanowa,na dubi wayata da har
lokacin ban kunna ba,ji nake kamar na janyo na
ji
muryarta,saidai hakan ba mai yiwuwa bane
domin
tuni Hafsa tayi nisa a gareni. Dole na mike na
dauro alwala,a matsayina na musulmin da yasan
saukin kowane matsala daga Ubangiji yake,na
tada kabbara nayi raka'a biyu,kafin nayi zaman
salati da hailala. ***************
***************
*************Na gaji da shan shayi da
safe,haka
yasa na nemi yaro na bashi ya karbo min
indomie
dafaffe a wurin masu shayi. Ina tsaye muna hira
da hassan direba,yana kakkabe mota,sai ga Abba
shima ya fito. Na rusuna ina gaidashi ya amsa
fuska a sake"Lafiya amadu,ya jikin naka?" Na
shafi qeya"Alhamdulillah abba." Abba ya jinjina
kai"Toh madallah,nima wajen gwaggon taku
zani." Na dago kaina ina shirin amsawa sai ga
yaron dana aika ya dawo dauke da kwano ya
miqomin"Gashi yace babu chanji anjima kaje ka
amsa da kanka wai." Na gyada kai"Ok nagode."
Bayan ya bar wurin Abba ya tsareni da ido kafin
yace"Amadu me kenan aka siyo maka?" Nayi 'yar
murmushi"Abba indomie ne." "Indomie?! Ya
nanata a mamakince. Nayi saurin tare
zancen"Bakina ne babu dadi,nafi sha'awar cinta
ne..." Ya tari numfashina cikin fada"Ko ma meye
inace a gidan akwai indomie? Kai kwana biyu na
lura kamar bana ganinka ka shiga gidan don
daukar abinci amadu,amma koma mene zanyi
bincike. Tashi ka tafi,Allah Ya bada lafiya." Daga
haka ya shige motarsa,na lura ransa a bace
yake,hassan ya ja suka tafi. Jikina yayi sanyi ina
mai nadamar siyo abincin danayi amma ya zanyi?
Na girman ma ba'a bar wahalar dani ba? Bansan
sa'adda hakan zai sauya ba.
Ina shago hankalina yana ga wajen su gwaggo.
Bansan dalilin kiran su Abba da tayi ba,fatana ya
kasance alheri domin na gama gane koma
menene
ya dangance ni tunda har ta hada da anti aisha.
Tasi'u ya katsemin tunani"Oga mutanenka ai sun
dawo jiya." Na dubeshi"Su wa fa?" Yayi 'yar
dariya"Wadannan 'yan matan,na ce musu kayi
aure
shine suka ce ban kyauta musu ba da tun farko
na
basu lambarka ai da haka ba,ita fa wai qawarta
sonka take. Karshe dai haka suka tafi suna masu
fushi." Nayi 'yar dariya"Mata kenan,babu kunya.
Ai
gwara da kayi musu hakan. Sau tari ga da ga sai
su tunkari namiji suce suna sonshi." Mukayi
dariya. A
daren Abba ya kirani falonsa,na shiga da
sallama,inna tana zaune har da anti amarya. Sai
da
naji hanjin cikina sun kada,na dake na qarasa na
nemi guri na zauna. Na gaida su inna,a ciki ta
amsa
ita kuwa anti ko kallo ban isheta ba ballantana
sanya ran zata amsa min. Abba ya dubi bangaren
su
inna"Dazu da safe na ga Amadu ya sayi abinci
daga
waje,shine nakeson jin akan wane dalili baku
bashi
abun kari ba?" Ai saida naji kaina ya
sara,shikenan
Abba ya qara cewa su inna su tsaneni kenan.
Nayi
dana sanin aikawa siyen indomie da nayi. Inna
tace"Ban gane nufinka ba? Akan me zamu
hanashi
abinci? Oh tanan kuma ya bullo? Wannan ai
munafunci ne." Anti amarya tace"Kema dai kya
fada,idan banda salon munafunci banga lokacin
da
ya shigo neman abinci muka hanashi ba,kai Allah
wadai hali irin naka amadu,babba dakai sai
munafuncin tsiya?" Na rufe ido kadan kafin na
bude,abunda nake gudu kenan. Abba yace"Kuyi
min
shiru don Allah,meyasa baku da tunani ne? Da
zarar
an soma magana sai ku sanyo shirme?"Ya girgiza
kai
yana mai juyowa gareni"Kai Amadu,sanar dani
abunda ke faruwa." Nayi murmushin takaici kafin
na qara saukar da kaina qasa"Babu komai Abba."
Yayi
shiru yana nazarina sai kuma ya bude murya ya
kira
Zahra. Ta shigo itama ta nemi gefena ta
zauna"ya
dubeta"Zahra tsakani da Allah sanar dani ko
iyayenki na dora sanwa da dan uwanki." Ina
ganin
sa'adda Anti amarya ta mako mata harara,zahra
tayi qas da kanta,na tabbata ba zatayi karya
ba,ba tun
yau ba nayi mata kyakkyawar shaida,nima kare
mutuncina ne yasa ban sanar da Abba gaskiya
ba.
Zahra tace"A'a Abba. Yaya Ahmed ya jima baya
karbar abinci a gidan nan." Abba ransa ya baci,a
fusace yace"Tun yaushe kenan?"A sanyaya ta
amsa"Tun bude shagonsa." Ai kuwa Abba ya
shiga
bude musu wuta"Nan gidana ne,zan iya rabuwa
daku amma bazan iya rabuwa da Amadu ba.
Jinina
ne,'dana ne! Akan me za'a dora tukunya a
gidana
a
hana 'dana? Kun kyauta kenan? Sai ga Abba ya
soma
haki,can kuma ya shiga tari sosai. Da sauri na
mike idanuna tuni sun sauya na isa gareshi.
Inna ta matso"Dauko masa ruwa mana." Ta daka
tsawa,a rikice na juya na nufi firij,Zahra har ta
riga ni
daukowa,ta miqa masa dakyar ya iya sanya
hannu
ya karba ya sha,a hankali kuma tarin ya tsaya
lokacin
har hawaye ya soma zuba daga idanunsa. Ya yi
shiru,inna da anti sukayi jugum,a sanyaye
kowannenmu ke yi masa sannu bai ce komai ba.
Sai
da ya dauki mintuna,lokacin ni kaina kwallar
nakeyi,zahra kuwa kuka kawai take. Ya soma
magana"Kun cuceni,yau inda ace muttaka shine a
raye,da zuri'ata bazata wulakanta ba. Ina mai jin
kunyar dan uwana duk da cewa ya jima a
gushewarsa,har a dora sanwa a gidana a hana
'dan
sa? Salamatu kun kyautamin kenan? Kun kyauta
da
wannan danyen aikin da kukayi?" Abba ya girgiza
kai"Daga yau duk randa kuka qara dora tukunya
ba
tare da Amadu ba Allah Ya isa! Ban yafe muku
ba
Salamatu da Jummai!" Abba ya cigaba da bude
wuta,ni kaina saida na tsorata da yanda yake
magana murya a sama,gaba daya sukayi shiru
kallo
daya zaka gane ransu a bace yake,na tabbata su
kansu tsoron fadan Abba yasa babu wacce zata
iya
tankawa amma na lura gaba dayansu sun dauki
zafi
sosai. Daga qarshe yace su tafi. Suka mike suka
bar dakin har suna buga labule don kowaccensu
ta
dauki zafi,bayan tafiyarsu Zahra murya na rawa
tace"Don Allah Abba kayi hakuri." Ya daga
hannu"Ya
isa Zahra'u,bakiyi mini komai ba,iyayenki sune
masu
laifi,kada ki biye musu a wannan rashin hankalin
nasu don na lura basu son zaman lafiya,ki qara
zage damtse wajen kula da dan uwanki kinji ko?
Allah
Yayi muku albarka." Muka amsa da amin. "Zahra!
Ke
kuma don iskanci ina kika tsaya? Ni zanyi maki
gugar?" Muryar anti dake wannan sababin a
tsakar
gida ne,Abba ya girgiza kai"Tashi ki tafi kinji? Ki
cigaba da biyayya gareta,mahaifiya ce gareki." Ta
gyada kai"Toh Abba." Ta bar falon kafin ya juyo
ya
dubeni"Kayi hakuri Amadu,kayi hakuri,bani da
masaniya akan wannan lamarin ko kadan,amma
insha Allahu bazai qara kasantuwa ba,kaji ko?"
Nayi
murmushi ina mai share hawayen da na manta
rabon
zubansu,tun rabuwata da Hafsa"Abba babu
komai,nasan dama baka sani ba,ban rikesu a
zuciyata ba,Allah Ya bani ikon binsu sau da qafa.
Na
rikesu iyayena." Abba yace"Allah Sarki,Allah Yayi
maka albarka Amadu,Allah Ya baka jin dadi
duniya
da lahira." Naji dadin addu'ar Abba,na jinjina
kaina
ina mai amsawa da amin.**********
Tun daga
lokacin komai ya chanja,saidai babu mai takowa
ya
kawo mini,Zahra kuwa gaba daya anti ta hanata
ta
ko gaisheni a cewarta bata yafe ba muddin hakan
ta
kasance. Hakan yasa ko mun hadu saidai ta
sakarmin murmushi na maida mata
martani,wannan itace gaisuwarmu. A kicin ake
barmin,da kaina nake
shiga na dauka. Har lokaci yazo aka yaye su
Zahra
daga makaranta,a lissafe sauran kwana goma
bikin
hafsa da suleiman indai har sati ukun da akace
za'ayi
hakan ne. Allah Sarki,sai nayi tunanin da tuni
nawa
ne zai kasance haka saidai hakan bai tabbatu ba.
Saidai a lokacin an gyaramin gidana tsaf,an
kammala
komai babu abunda yayi saura sai kayan daki. Da
kaina mukaje da Abba ya gani,wajen yayi kyau
sosai,ya dubeni yana murmushi lokaci guda kuma
ya
dafa kafadana"Masha Allah 'dana,sai kuma aure
ya
rage,shi din ma bama fatan ya kai wani lokacin."
Dariya ma maganar ta bani,hakan yasa na
dara,Abba
ya tayani,"Kana mamaki ko Amadu? Kada kayi
mamaki,ka zauna cikin shiri nan bada jimawa ba
zaka ga matarka." Da sauri na dubi Abba,lokacin
ya
juya yana murmushi zai koma mota,dakyar na iya
motsawa na bude masa gidan gaba ya
shiga,nima na zagaya na ja motar. Duk da cewa
zuciyata na bugu
don bansan manufar kalaman Abba ba,toh
nufinsa
aure zaiyi min? Yace bada jimawa ba zan ga
matata,'yar ina ce? Suna nufin auren hadi za'ayi
min?
Nidai kam na rasa abun tunani,hakan yasa na
barwa
zuciyata. Koda na sauke Abba haka na nufi shago
ina saqe saqena,tambayata bai wuce son sanin
Me
Abba Yake nufi
ba?"*************************"
Aure zaiyi maka mana." Badamasi yayi wannan
furucin a yayin dana sanar dashi yanda mukayi
da
Abba. Na kalleshi kafin na girgiza kaina na ja
qaramin tsaki,"Ka daina wannan hangen,bamai
yiwuwa bane,babu ni babu kula kowace mace."
Badamasi wanda yake zaune saman motarsa a
nan
bakin shagona yayi dariya"Lallai Ahmed,wallahi
ka
bar wannan magana domin nan gaba zaka yiwa
kanka dariya. Yanzu kai sai ka qi aure don kawai
mata sun yi wasa da hankalinka?"
Na tabe baki"An shani na warke,ban yarda da
kowace mace ba kuma a yanzun." "Har Zahra?"
Tambayar ta daki zuciyata,nayi shiru kamar
bazanyi
magana ba,na rasa irin amsar da zan bashi. Har
saida
naji dariyarsa,"Aminina kenan." Sai lokacin na
dawo
cikinhayyacina,ya qara da cewa"Ya kayi shiru?"
Na daure fuska tamkar ban taba dariya ba,ina
mai daga
masa hannu,a kausashe nace"Please ka san me
zaka
dunga fadi,banison ire iren maganganun nan. Ban
taba yiwa Zahra kallon masoyiya ba ballantana
har
ka dunga hangenta matsayin mata a gareni,na
dauketa 'yar uwa kuma kanwata. Bazan iya zama
da ita a qarqashin inuwar aure ba,bazan iya
ba,ba
don
ina qinta ba,ina kaunarta matsayinta na jinina
please
bar tunanin hakan,so kake na shiga cikin
matsalar
wadannan iyayen nata?" Badamasi yayi wani irin
murmushi"Ka daina fadin haka Ahmed,amma dai
tunda ka nuna bakason batun shikenan Allah Ya
zaba ta gari." Na sauke ajiyar zuciya ina mai
amsawa.***********************
*************Qarfe tara na qulle shago na nufi
gida
sakamakon ciwon kan dake addabata. A nan qofa
mukayi kicibus da Anwar mijin anti abida,cikin
girmamawa na rusuna kadan ina mai mika masu
hannu mukayi musabaha. Cike da fara'a
yace"Kaga
manya,wato dai ahmed kayi wuyar gani ko? Ni
kuwa
tun haihuwar yayar taka daka kawo su hajiya na
qara ganinka a gidana? Lallai baka son zumunci
Ahmed." Nayi dariya"Ba haka bane,al'amuran sai
a
hankali." Anwar yayi dariya"Kwarai kuwa,gashi
sai mulmulewa kakeyi." Muka qara sanya dariya.
Karshe
yace na turo masa ita su wuce. Daga haka na
shiga
gidan,sallama nayi kofar dakin inna,babu wanda
ya
amsa,hakan yasa na tsaya ban shiga ba kamar
yanda
addini ya koyar,a karo na biyu na qara yin
sallama,cikin daga murya Anti Abida tace"Wai kai
ya akayi ne?" Nayi murmushi ganin yanda ta fito
a
fusace"Ina yini anti abida." Ta harareni ta ja tsaki
sannan tace"Me akayi?" "Baban Khalil ke
magana."
Ta juya ta saki labule tana fadin"Dan banza zai
takuramin,na zo gidan uban nawa ma." Banyi
mamakinta ba saboda su kam raina miji ba wani
sabon abu bane a wajensu. ***************
Juyi kawai nakeyi akan gadon saidai duk yanda
naso da bacci ya daukeni hakan ya gagara,babu
abunda yake cin zuciyata sai maganar Abba. Na
rasa
gano inda ya nufa da zancensa na dazun. Toh
itama
Anti Aisha har yanzu akwatunan lefe suna nan
banga tana niyyar fitar dasu ta siyar ba,wai ni
Amadu ko dai auren dole za'ayimin ne? Sai ma
tambayar da
nayiwa kaina ta bani dariya,hakan ko dadin fadi a
baki babu. Haka nayi ta saqa saqe har bacci
barawo
ya saceni.***********************
************Kwana biyu tsakani,aka fara shirin
graduation nasu Zahra,ranar kuwa da za'a
yayesu,hatta Badamasi sai da ya samun katin
gayyata,sai daga baya mukaje. A mota nayi shiru
kamar ruwa ya cinyeni,badamasi dake gefena
zaune
ya dubeni"Wai lafiya na ganka duk a sanyaye?"
Na
sauke ajiyar zuciya"Tunani nake yanda zanga
Hafsa
a yau,ko ta chanja?" Badamasi yayi 'yar
dariya"Allah Sarki rayuwa,Ahmed kenan. Toh ya
kuwa zaka
ganta? Kaima kasan har yanzu dole a samu
burbushin sonka a ranta. Kai Ahmed wani sa'in
fa
mata sun fimu alqawari,kai din sai ka mance 'ya
mace
amma wallahi kafin mace ta manta 'da namiji
musamman ma idan soyayya mai qarfi ta gifta
tsakaninsu abune mai wahala. Ina mai tabbatar
maka har yanzu Hafsa tana sonka." Nayi
murmushin
takaici kafin na ja tsaki ina mai gyara zama
na"Babu
amfanin son tunda buri bai samu cika ba. Amma
zan
iya qaryata batunka Badamasi,don wallahi har
yanzu
akwai soyayyar Hafsa a zuciyata,idan nace maka
na mance ta gaba daya qarya nayi wallahi."
Mukayi
shiru,ina mai jin zuciyata na zafi. A sanyaye
badamasi
yace"Haka Allah Ya so Ahmed,please mu bar
zancen
nan. Allah Yayi maka zabi." Nayi murmushi
kawai.
Mun isa Afficent a qurarren lokaci,waje a cike
damqam da jama'a. Kowanne ka gani cike da
farin ciki,wajen dalibai daban suna daga can
gefe,saida
aka qare duk wani events da aka shirya domin
ranar
sannan muka samu sararin ganin su Zahra. Ido
kawai na zuba mata ina mai dubanta,cak ta tsaya
itama tana mai zubamin nata idanun. A nutse
fuskata
dauke da murmushi na nufota,ban kai ga
qarasawa ba,ya taho ta gabana ya nufeta yana
sakar mata
dariya,hakan yasa nayi saurin juya baya zuciyata
na
zafi. Da sauri na fito daga dakin taron na tsaya
anan
'yar barandar dake hanyar fita. Allah Sarki
Hafsa,ba
shakka na hango wannan kallon na kaunarta
gareni
a cikin kwayar idonta,kwarai na yarda da batun
badamasi har yanzu Hafsa na kaunata. Dafani
naji
anyi,hakan yasa ni waigowa,Badamasi ne. Na
qara
tsuke fuska"Ka ga Zahran?" Ya girgiza kai"Wai
kai
don Allah bazaka daurewa zuciyarka bane? Be a
man please." Maganar Zahra ta katsemu cikin
muryarta mai sanyi"Yaya Ahmed." Na juyo ina
mai dubanta,fararen haqoranta sun gaza
rufuwa,har
hakan yasa wushiryarta bayyana,yau rana ce ta
farin
ciki a gareta,a hankali kuma naga annurin dake
kan
fuskarta ya dauke,a sanyaye ta matso sosai tana
dubana"Yaya Ahmed meya faru?" Nayi
murmushi"Me
kika gani kanwata?" Badamasi yayi
dariya"Kyaleshi kawai,damuwa ya shiga dalilin
bai hangeki ba." Tayi
dariya"Yaya Badamasi kenan,akwai ka da son
zolaya. Mukayi dariya,na hau waige waige"Musty
kuwa ya iso?"(Mai daukan hoto ne). Badamasi ya
waiga"Nima dai ban ganoshi ba,na dubi
Zahra"Ina
su Anti Abidar?" Ta nuna min su da yatsa"Gasu
can suma tafiya suke sonyi,mai hoton ake jira."
Muka
garzaya muka nufi wajensu.
A mutunce suka gaisa da Badamasi,ni din ma
mun gaisa dasu. Anti Kubra tace"Wai ina mai
hoton
ne ahmed? Ba tare kuka taho ba?" Na zura
hannuna
a aljihu na dauko wayata. Ringing biyu musty ya
daga,"Ya kana ina ne?" "Gani tun dazu nake
cigiyarku,kuna daga ina?" "Ka fito muna tsaye
daidai qofa ta biyu na farfajiyar wajen." Jim
kadan sai gashi
nan,aka dauki hoto,na juya ina waigen inda zan
qara
sanyata a ido,can na hangeta tare dasu faruq sai
dariya suke ana daukar hoto,ita kuwa duk a
sanyaye
take,ta juyo muka kalli juna,na sakar mata
murmushi
ina mai daga mata yatsuna. Ta sunkuyar dakai
kafin ta ja hannun noor ta dubi mamanta,bansan
me tace
ba sai kuma gata ta nufomu. Na dauke kaina har
ta
qaraso,murya a sanyaye ta gaida su anti
abida,suka
amsa suna masu fara'a. Mariya tace"Hafsa
amarya,ashe abu ya kusa ko?" Tayi
murmushi,raina
ya dan sosu. Anti Kubra tace"Ai muna jiye maki
dadi,Allah Ya sanya alheri,sai munga katin
gayyata."
Na fahimci don baqantamin ne suke wannan
maganganun hakan yasa na daure fuska ina mai
kauda kaina daga garesu. Dariyarsu naji,Zahra
kuwa
dif tayi. Badamasi ya share batun da cewa"Zo mu
dau
hoto mana Hafsa." Sai a lokacin ta dubeni da
idanuwanta da suka kawo ruwa"Ina yini." Na
gyada
mata kai ina mai murmushin da yafi kuka
ciwo,noor
ya rungume qafafuna yana cewa"Uncle ka daina
zuwa." Ya furta a sanyaye,na sunkuya ina mai
dafa
kansa cikin 'yar dariya nace"Zan zo
wajenka,zuwa na
musamman kana so?" Yayi dariya ya gyada
kansa,nima murmushi na qara yi"Good." Daidai
nan
su faruq suka qaraso,na mike tsaye,ban nuna
komai
ba na mikawa suleiman hannu muka gaisa shima
cikin sanyin jiki ya miko min,sannan faruq ya
gaisheni"Malam faruq ya karatu." Ya dan shafi
kansa"Wallahi muna nan muna fama." Na jinjina
kaina,na durkusa na gaida mama,ta amsa min
itama
jikin a sanyaye. Sannan aka shiga daukar hoto
bayan
qare gaisuwa,akwai wanda mukayi tare da hafsa
da
zahra,sai kuma nayi dasu daddaya. Zuciyata ta
qara
min zafi da quna,tabon da ya jima da warkewa
ya
qara tasowa da ciwo. A hankali na juya nayi
hanyar fita ina mai zaro bakin gilashina dake
cikin aljihun
gaban riga na sanya. Mota na shiga ina mai
tunane
tunanena,naso hafsa ban sameta ba,hakanan zan
hakura domin ba rabona bace. Ganinta yana
tunamin
da rayuwar mu da ita a baya. Ban fi minti goma
ba sai
ga Badamasi ya iso. Ya dubeni"Haba
Ahmed,meyasa ka taho?" Na qara daure
fuska"Sun gama?"
Badamasi ya zubamin ido yana nazari,kafin ya
sauke
ajiyar zuciya yana mai jinjina kansa"Gasunan
fitowa.
Tare zamu tafi ne?" Na bude mota ina bashi
amsa"A
motar mijin anti abida zasu tafi.(Kasancewar ta
iya
tuqi,ita ta kawo su). "Ok" Inji Badamasi,shima ya
shiga,ban jira komai ba nayi ribas,muka qara
gaba.


Zaharaddeen Shomar

Whatsapp  08168575100Amadu 2 page 5
Posted by ANaM Dorayi on 03:19 PM, 16-Jun-15
Under: Amadu
Shiru babu mai magana a cikinmu,kowanne da
kalar tunaninsa,nawa bai wuce akan famin ciwon
da ganin Hafsa ke neman jaza mini ba. Badamasi
ya katseni ta hanyar cewa"Ahmed yane?" Nayi
gyaran muryata dake a toshe ina mai maida
kaina titi"Da akayi me?" "Naji kayi shiru,ince dai
ba sanadin haduwa da hafsa bane? Na dauka
tuni
ka jima da rufe shafinta a rayuwarka." Nayi
murmushi wanda nasan yana qara min kyau da
kwarjini saidai ban ce komai ba,har dai da kansa
yace"Kayi shiru." Na dubeshi ta cikin gilas,sannan
na juya kai"Kana zaton zan mance Beauty a
rayuwata ne? Ko kusa bazan iya mance ta
ba,hakanan sonta har yanzu yana nan a raina
saidai kawai na hakura bisa dole ne,tunda tayi
min nisa. Kai baka ga yanda ta koma bane? Kai
duk soyayyar da nake yiwa yarinyar nan ban
kama koda rabin qafar wanda take nuna min
ba,kaidai kawai ayi sha'ani,abar komai as
past,Allah Yasa hakan shine alkhairi." Badamasi
yace"Amin,gaskiya na ga yanda ta rame kada ka
damu nisantarku da juna shi zai bata damar bin
umarnin iyayenta." Na jinjina kai ina mai share
batun"Wai ya ake ciki da maganarka da jamila?"
Yayi 'yar dariya ya jingina kansa jikin kujera
sannan ya dora kafa daya kan kujerar"Kai a
satinnan za'a kai lefe,nan da sati uku zamu sha
biki." Na bude baki"Ah,kace hakan ta zauna
kenan." Badamasi yayi murmushi"Kwarai kuwa,ai
farko matsalar daga jamilar ce,kasan ita tafiso
wai ta soma zuwa jami'a kafin aure,ni kam ina
da
bukatar auren nan,ko an fiso sai na tsofe banyi
ba? Yanzu gashi matar kabir har ta kusa
haihuwa,kai lamido('dan kanin daddynsa ne
sannan kanine ga Badamasi)kansa yanzu yana da
yara biyu,mtsw,ko jiya da naje gidan ummi
(maman lamido)saida tayi ta min fada,wai gwara
dai nayi auren. Kowa a wajen duk aka sanyo
baki,haka na tattara na baro gidan." Mukayi 'yar
dariya,nace"Atoh yafi dai." Mukayi shiru,ya qara
cewa"Kaima dai nasan su Abba sun kusan aurar
dakai." Cikin dariyar nace"Kamar wani qaramin
yaro,hm." Badamasi yace"Ahmed kenan,ka shirya
dai ranar da zamu kawo maka amarya har
gidanka." Na maida abun wasa daga karshe
muka share zancen.***********************
**************A gida an shiryawa Zahra 'yar
qaramar walima. Qawayenta na islamiyya duk
sun
samu halarta,a kofa muka hadu da Bahijja da
amare(Badariyya da raliya). Na karbi jaririn
Badariyya,Yusuf. "Kaga amare sai kyau kuke
qarawa." Sukayi dariya,suna gaishemu. Muka
amsa. Badariyya tace"Ai yaya ahmed fushi
nakeyi,baka zuwa gidana yanzu inda Bahijja ce da
tuni kana zarya." Raliya wacce ta riga tayi nauyi
da tsohon ciki ta cafe"Ai bake kadai ba badar,ni
kaina na mance rabona da yayan nan namu,don
ba bahijja bace ai." Mukayi dariya ni da badamasi
da bahijja. Bahijja ta rike haba"Oh,ashe dai kuna
matukar kishin zumuntarmu da yayan nawa,har
gashi an kasa boyewa ya fito fili." Muka qara
sanya dariya nace"Rabu dasu kanwata,mu dai
nan gani nan bari babu mai rabani dake kinji ko?
Batun zuwa gidanku kuma ku tambayi 'yan
unguwa har sau nawa na je ban sameku ba,kune
kun fiye yawo." Badamasi yace"A'a Ahmed amma
dai baka kyauta ba,bai dace ba,ke bahijja ai dole
a yi kishi dake." Sukayi dariya,raliya tace"Atoh dai
tayamu ganin wanga lamarin." Bahijja tace"Au
Yaya Badamasi laifinmu ka gani,toh mudai ba
ruwanmu munso zumunci amma yawonsu ya
hana a taddasu gida." Haka mukayita raha har
lokacin da Zahra ta fito don raka wasu
qawayenta. Kallo nake binta dashi,tana sanye da
shadda brown,tayi kyau sosai farinta ya qara
fitowa. Ashe dama zahra kyanta ya kai nan,daidai
lokacin data dubi su bahijja"Kai anty badar ashe
kun zo shine kuka tsaya a kofa? Nayi fushi." Ta
shagwabe fuska,raliya tana dariya tace"Sorry
kanwarmu,ai domin ki muka zo,congratulation."
Tayi murmushi wanda dimple dinta ya bayyana
ya qara fito da kyawun dake fuskarta"Thank you
my sister,Allah Ya saukar mana ke lafiya." Muka
amsa amin. Badamasi yace"Kai kanwarmu irin
wannan kyau haka sai kace an sanya ranar
aurenki?" Tayi dariya,Bahijja tace"Ta Nas bada
kanki asare." Nan da nan ta daure fuska tana
harara bahijja"A'a ba nas ba saura naz,ba
damuwata bace." Bahijja ta rike baki"Au haka ma
zakice? Shikenan ai kuwa kamar a kunnen yarima
ince kince kin daina kaunar abokinsa." Saida naji
dum a zuciyata saidai na share maganar"Ke fa
bahijja da hade hade kike,yanda kika zaba kika
more sai ki kyaleta itama tayiwa kanta zabi."
Akayi dariya,na lura da lokacin da badariyya da
raliya suka kalleni daga bisani suka kalli juna
suna masu murmushi,ban kawo komai ba sai na
dauka ma zancen nawa ne ya sanyasu,hakan
yasa na qara da cewa"Atoh." Zahra dai murmushi
kawai tayi tana mai jan hannun bahijja sukayi
ciki. Na miqawa badariyya yusuf dake bacci suka
shiga ciki na dubi badamasi"Toh ya? Ni shago na
nufa." Badamasi yace"Muje kawai,nikam yau hutu
nake." Nayi murmushi"Ai mu namu sana'ar ba
hutu kodayaushe cikin tafiya muke." Badamasi
yace"Hakane." Ranar Lahadi ne da safe ina shirin
tafiya
kasuwa,na samu saqon kiran Abba wajen Salihu.
Dama ina shirin zuwa gaidashi,na isa yana zaune
yana karyawa,na gaisheshi,ya amsa fuska a sake
kafin yace"Zaka wuce shago ne?" "Eh." Ya jinjina
kansa"Toh madallah,da misalin qarfe hudu na
yamma kaje can gidan gwaggon taku akwai
qaramin
meeting da za'a gudanar." Naji faduwar
gaba,dakyar
na iya tankawa"Toh." "Ka karya ko?" Nayi
murmushi"Eh na karya,sai mun dawo." "Allah Ya
bada sa'a." Na amsa da amin sannan na mike na
fita
zuciyata cike da tunane tunane,meeting din
mene
kuma? Na riga na gama tsarguwa koma menene
ya
shafeni,jiki a sanyaye na dauki hanyar titi bayan
na
dagawa baba maigadi hannu shima ya dago
min,sannan na qarasa zan wuce na hadu da idi
yana
zaune a kofar shago,mukayi musabaha. Yana
dariya
yace"Kaga manyan Alhazawa,wallahi kwana
biyun nan sai chanjawa kakeyi,ga wani sheki da
ke tashi a
kan fuskarka ana ganinka ansan kudi sun zauna
anan." Bansan lokacin dana bushe da dariya ba
ina
mai nuna shi da yatsa"Ho idi,kaidai wallahi baka
rabuwa da zolaya,wato har kalar kudi ma nakeyi
ko?" Shima dariyar yayi"Wallahi kada kaji batun
wasa Ahmed,sai kace ba kai ba,kodayake kullu
yaumin kana cikin shago ba fita kakeyi ba
ballantana
rana ya dokeka,dole kayi haske da kyau. Kai wai
baka da labarin 'yan matan unguwarnan sun
mato
akanka ne?" Nayi dariya ina mai girgiza kai a
lokaci
guda kuma na soma tafiya"Idi kenan,baka rabo
da abun dariya." Shima cikin dariyar
yace"Atoh,kada
kaji zancen wasa gaskiyar kenan. Kaje ka dawo
akwai katuna masu dauke da lambobin waya
daga
'yan matanka." Nayi dariya bance komai ba nayi
gaba,nasan babu karya a maganarsa,domin
nasha
samun aiken 'yan mata wanda ni ko kadan basa
gabana,har mamaki nakeyi yanda 'ya'ya mata ke
zubda mutuncinsu su furtawa namiji kalmar so
bayan basu da tabbacin ko yana sonsu ko
bayayi. Ko
ina suka baro kunya ta bahaushe?
***************
************************** Na idar da
sallah,na
mike ina mai nannade dardumar,na dubi tasi'u
dake fama da jama'a"Zanje yanzu na
dawo,gwaggo na
nemana." Tasi'u yace"Toh sai ka dawo." Na
maida
agogo na na daura sannan na fito. Gidan gaba
daya
'yan uwa ne cike,har da inna delu kanwar
mahaifina.
Gaba daya sun halara. Daga falon gwaggo su
Abba
ne zaune a ciki,har da su anti amarya,nidai kam
na gama shan jinin jikina. Muka gaisa da
kowa,kawu
murtala yace"Toh ai tunda wanda ake jira ya iso
sai a
soma ko?" Gwaggo tace"Gaskiyane,Amadu cewa
'yan wajen nan su shigo ciki." Na mike nayi
kiransu,suka rankayo ciki. Kawu murtala ne ya
bude
taron da addu'a,sannan yayi dogon bayani akan
muhimmancin zumunci da falalarsa. Daga nan
kuma
sai yayi kiran sunana,cike da faduwar gaba na
dubeshi"Na'am kawu." *********
"Zaman nan dai anyi shine dominka." Da sauri na
qara duban kawu,babu wasa a fuskarsa,na hadiyi
miyau ina mai sunkwui da kaina kasa. Ya cigaba
da
nuna mini yarda da kaddara da karfin sunnar
aure
a
musulinci,kafin daga bisani yazo kan tushen
zancen."Munason hada ka aure da 'yar uwarka
Zahra bisa yarda da amincewarku." A razane na
dago na
dubi kawu,sannan na dubi Zahra dake zaune
gefe
kusa dasu bahijja,itama tayi mugun razana. A
lokacin
anty amarya ta mike tsaya cike da tsawa
tace"Bamai
yiwuwa bane,'yata bazata auri Amadu ba
matukar
ina numfashi!" Ai kafin ta qara wata maganar
Abba ya wanke mata fuska da mari da sauri
kawu
hamza
da kawu shamsu suka rikeshi jikinsa har tsuma
yake."Sai naga ta yanda zaki hana,muddin yara
suka
amince baki isa ki hana ba. Shashasha kawai
wacce
batasan abunda ya dace ba." Anty amarya da har
lokacin take rike da kuncinta tana zubar hawaye
ta koma ta zauna tana huci kamar zaki. Ni kuwa
gaba
daya kamar an zaremin lakar jikina,gabana sai
dukan tara tara yake. Miyau kuwa ai kafewa yayi
kamar yanda bakin yayi min nauyi,jina nakeyi
kamar
ba'a duniyar nake ba,a lokaci guda kaina ya
soma
sarawa. Kamar daga nesa na jiyo sautin kukan
Zahra,sannan naji gwaggo na yiwa anti amarya
fada,hankalina ya qara tafiya dogon tunani,ya ma
za'ayi na auri Zahra? Su su kawu sun mance
aminiyar
Zahran na nema ban samu aurenta bane? Ko
kuwa
sun mance Zahra ina yi mata kallon kanwata ne
wacce muka fito ciki daya? Waya ce musu na
taba yiwa Zahra duba a matsayin matar aure?"
Tunanina
ya katse a lokacin da Hashim('da ga kawu lawal)
ya
dan bugi kafadata,na dubeshi"Kawu na magana."
Na
dago kaina,ganin yanayin fuskokin iyayen namu
babu walwala yasa na qara yin kasa da idanuna
wadanda tuni sun kada sunyi jawur. Sai kuma
naji gwaggo ta umarci kowa ya bar falon,aka
barmu
daga ni sai Zahra da su Abba,harda anty amarya.
Kawu murtala ya qara cewa"Kinga jummai,ba
dole
zamuyiwa 'yar ki ba,a gabanki zamu tambayi
ra'ayinsu idan sun amince shikenan,idan kuma
basu
amince ba sai a kyalesu. Zumunci ne ake son a
qulla yayi kyau bamu fatan lalacewarsa,idan
muka ga
abun zai zama akasin haka toh barinsa yafi
alheri. Ki
kwanta da hankalinki." Daga haka ya juyo ya
dubeni"Amadu." Na daure na amsa"Na'am
kawu."
Kana son 'yar uwarka Zahra,ka amince zaka
aureta?"
Nayi shiru,ba shakka qin amincewa da batun
auren nan,zai sa na zama butulu. Iyakar halacci
abba
yayimin,ya daukeni kamar dansa,ya kyautatamin
a
lokacin da mutane ke kyamata,ya darajani lokacin
da
nake ba komai ba kamar yanda ya nuna min
kauna
tsakani da Allah wanda ko mahaifina idan yana
raye
sai haka. Ta yaya zan mance dukkan wadannan?"
"Amadu kayi shiru?" A hankali na soma
magana"Na
amince Kawu." Ai nan da nan farin ciki ya cika
fuskokin iyayen suka soma hamdala,idona yakai
ga
Zahra wacce take dubana a firgice,kafin na
saukesu
kan anty amarya wacce take hararata kamar
idanun
zasu fado sannan na maida kasa. Ni kaina nasan
nayi dakiya ba 'yar kadan ba wajen amsa wannan
maganar,sai kuma kawu ya jefa ma zahra
tambayar,banji maganarta ba saidai naji suna
hamdala hakan ya tabbatar min kai ta gyada. A
fusace anty amarya ta mike ta bar falon tana
maganganunta. Gwaggo kuwa nan ta shiga sanya
mana albarka har da 'dan kukanta. Allah Allah
nake
su sallamemu,suna cewa mu tafi,na mike na
shuri
takalmana na ja kafafuna na bar gidan ba tare
dana
saurari kowa ba. Kai tsaye wajen badamasi na
nufa,yana zaune a falonsa na shiga,na zube kan
kujera. Ya dubeni,nan ya gane ina tare da
damuwa. Idanuna a
rufe,yace"Subhanallah,Ahmed
meya
faru?" Haba abokina,meye abun fushi? Kayi
hakuri
ka saurareni Ahmed. Kasan dai iyaye ba zasu
zaba maka abunda baka so ba,asalima tun farko
kana da wacce kake so Allah baiyi zakuyi auren
ba,idan baka manta ba,basu hana ka ba. Sai
kuma a yau suka so suyi maka gata,bayan sun
nemi amincewarka ka amince kuma ka
yarda,suka shirya hadaka aure da 'yar uwa kuma
kanwarka Zahra. Haba Ahmed,ka tuna fa yanda
Abba ya kula da kai da rayuwarka,anya kuwa ya
dace ace kana mai fushi don zaka auri Zahra?
Toh wai ka manta irin kauna da tausayawa da
Zahra
ta nuna maka? Kai abun farin ciki da jin dadin
ma,Zahra tana sonka,wallahi Ahmed tun soyayyar
da take maka bai kai ga fitowa fili ba na gane a
kwayar idanunta tana sonka. Ai idan baka manta
ba na taba tada maka maganar ko ayi 'yar gida
ka nuna min bakason zancen toh wallahi tun a
sannan na dago yarinyar tana kaunarka,kaima
Ahmed bana jin akwai qiyayyar Zahra a zuciyarka
saidai zan iya yarda koda ace kana sonta toh
baka gane bane. Fatana ka dauki
maganganuna,kayi hakuri ka zauna da
Zahra,Allah Shi Yasan abunda ya boye. Allah
Yasa
ta kasance tauraruwa a gidanka." Jikina yayi
sanyi domin maganganun Badamasi sun ratsani
fiye da zatona. Nayi shiru ina nanata
maganganunsa a raina.
Abunda ya dauremin kai bai wuce cewa da yayi
wai ina son Zahra ba. Ta ina ya gano hakan?
Wannan
kam sharrinsa ne. Na hadiyi miyau ina mai laso
labbana da suka bushe na dubeshi"Naji
bayananka
kuma na dauka,yanzu ka gayamin da wane ido
zan
iya kallon Hafsa?" Na lura na bata masa rai,ya ja
qaramin tsaki ya dafe kansa"Haba Ahmed,kai fa
ba
yaro bane da za'ayi ta maimata maka
magana,yanzu
kuna tare da Hafsa ne? Inace aurenta itama
zatayi?
Auren ma da dan uwanta? Toh kaima sai kayi
hakuri
ka bi umarnin naka iyayen kamar yanda ita da
take
mace tayi,kodayake ka riga ka amince yanzu dai
koma menene kayi hakuri. Insha Allahu zakayi
alfahari da aurennan." Nayi murmushi ina mai
matso
kwallar data cikamin ido tun shigowata. Kafin
kuma
na danyi dariya,shima ya tayani"Ya akayi kuma?"
Na
ja qaramin tsaki"Gani nayi yau ka koma malami."
"Atoh,ai dole na zama qaramin malamin naga
kana neman ka kufce." Mukayi dariya muna
masu
cafkewa,na janyo robar faro dake ajiye akan
tebur
na soma zubawa a kofi"Toh ya akayi ka manta
da
mahaifiyar Zahra? Ita kuwa fa? Ba matsala
bace?" Jin
yayi shiru nima na biye masa,sai kuma muka
soma
dariya. Na dan daure fuska"Kai mene haka ne?
Uwa take fa a gareni,matar abbana ce." Cikin
dariya
yace"Ikon Allah,toh me nace? Ai tambaya kayi sai
ka
saurari amsarka ko?" Nayi murmushi,kaina yana
sarawa,na qara jingina da kujera"Ina
sauraronka,ina
mafita? Yanzu kaga yanda ta tayar da bala'i
wajen
taron nan kuwa?" Nan na zayyane masa,mukayi
shiru muna masu zubawa tv ido. A lokaci guda
muka
sauke ajiyar zuciya"Itama fa matsala ce." Cewar
Badamasi."Babba ma kuwa,fargabar komawa
gidan nake
shiyasa bazan koma ba sai dare." Badamasi yayi
murmushi"Kaidai duk abunda zatace gareka kayi
kokarin toshe kunnuwanka,kada ta chanja maka
ra'ayi. Abba zaka dunga kalla ba wani ba,duk
wani
zage zagen da zatayi kada ka kulata please."
"Hakane,Zahra ma nakeji tausayawa don nasan
da
wuya idan bazata sha fada ba wajen anti."
"Gaskiyane,Allah Ya kyauta." A fili na amsa"Amin
dai." Haka mukayita hirarraki akan maganar,sai
bayan sallar magriba muka rabu dashi. Kai tsaye
shago na nufa ko gidan ban shiga ba don nasan
ana nan ana rikici. A shagon ma rabin hankalina
yana ga
tunani,a daddafe muka kammala na rufe shagon.
Karfe goma da mintuna na shiga gidan,shiru kake
ji
babu hayaniya,nayi hamdala na shige dakina na
rufe. Auren Zahra? Wai ni zan auri Zahra? Ikon
Allah!
Na ciro wayata ina mai bude bangaren hotuna,na
zurawa hotonta ido wanda na dauketa ranar
walimarta,tana tsaye jikin motar abba tana
dariya,ta
rike kugu na dauka,a hankali nake bin hoton da
kallo zuciyata na ayyanamin kyawawan
kamanninta,bana ganin laifin wadanda ke cewa
muna dibar kama da Zahra. Kallonta nake kamar
wata tauraruwa,fuskarta na sheki,dariyar Zahra
mai
wuyar gani yau gashi nan tayi a sanadin ranar
candy
dinta,idanunta dara dara ta maidasu 'yan kanana
cike da gayu a yayin daukarta hoton,bani
mantawa
har Badamasi yana mata tsiya wai irin wannan
farin
da takeyi da ido na menene? Su bahijja na
dariya,hannunta dake rike da kugunta ya sha
lalle
baqi da ja,kasancewarta fara tas sai ya qara
haskuwa. Ina kallo zuciyata na bugawa da sauri
da
sauri,sai kuma lokaci guda na kife wayar a kan
gado,na mike zaune ina jan tsaki,takaici da bacin
rai
suka cikani,wai meye nawa na duban hotonta?
Ashe dai zan iya cin amanar hafsa? Toh meyasa
na kasa
dauke ido daga hoton Zahra? Cike da bacin rai na
mike na soma rage kayan jikina bini bini kuma sai
naja tsaki. Bayan nayi wanka na zura jallabiya na
shimfida darduma sannan na kalli gabas don
gabatar
da shafa'i da wuturi. ********


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100Amadu 2 page 6
Posted by ANaM Dorayi on 05:49 PM, 16-Jun-15
Under: Amadu
Washegari da safe ko ta kan breakfast ban bi
ba,fatana na bar gidan kafin wani a gidan ya
tashi. A
gurguje na zura kayana na fito hulata a hannu
ina
qulle qofa. Na juya zan fita naji qarar wayata,na
ja
tsaki ashe ma garin sauri na barta a dakin,na
bude
na koma lokacin har ta katse,sai kuma kiran ya
qara shigowa na dauka ina mai sallama. Bayan
ya amsa
yace"Amadu idan ka tashi kazo ina son magana
dakai." Nasha jinin jikina,a sanyaye na amsa
da"Toh
Abba." Ya ajiye wayar,na zura ta a aljihu. Abunda
nake gudarwa kenan,sai gashi ya faru,domin karo
na ci da takalmin Zahra a qofar falon Abba. Na
qarasa ciki da sallama,Abba yana zaune sanye da
doguwar
jallabiya da alama ko wanka baiyi ba,ita kuwa
zahra
tana gefe a hankali nakeji sautin kukanta yana
tashi.
Fuskar Abba ta fallasa sirrin zuciyarsa,domin a
hade
take tamau. Duk da cewa da asuba mun gaisa
hakan
bai sa nayi sanya gun qara gaidashi ba. Kai ya
iya gyadawa,Zahra ta dago kanta,hawaye
takeyi,dakyar
ta iya gaisheni,na amsa sannan wajen yayi shiru.
"Amadu." Na dago kaina"Na'am Abba." "Ban taba
samun matsanancin farin ciki irin wanda na samu
a
jiya zuwa yau ba,naji dadin wannan hadi na
Ubangiji
tsakaninka da 'yar uwarka. Kwarai tun farko naso
hakan ya kasance saidai ban fito fili na furta ba
lura
da yanda zamanin nan ya sauya,banason abunda
za'a zo ana dana sani akansa da kuma abunda
zai
kawo lalacewar zumunci. Toh sai kuma cikin
hukuncin Allah kai amadu na baka damar kawo
matar aure,ka zo min da batun Hafsa,hakan yasa
na qara hadiye wannan kwadayin nawa na son
hadaka
da 'yar uwarka itama na bata damar fito da mijin
aure
don nafison aurenku ya kasance tare. Abun Allah
kuma sai gashi bayan rabuwarku da
hafsa,gwaggonku tayi kirana ni da 'yan uwana
akan
hadaku aure,babu wanda bai bada goyon
bayansa
ba amma da sharadin sai kun amince." Ya dakata
kadan kafin ya cigaba"Alhamdulillah,Allah Shine
abun godiya,Shi ke tsara lamura yanda Yaso,cikin
nufin Allah sai gashi kuma anyi sa'a kun amince
da
juna saidai ita jummai da taso kawo matsala." Ya
qara
jinkirtawa kafin ya cigaba"Amadu ka nunamin kai
din jinina ne,'dana 'dan muttaqa,mahaifinka
munyi
shaquwa dashi wanda har takai sai ya sanar min
da
damuwarsa bai sanar da mahaifiyarmu ko
mahaifinmu ba. Amadu ka sanar dani gaskiya
banason ka boyemin komai,dagaske ne ganin
idonmu ne yasa ka amince da aurennan ko
kuwa?" Na qara sunkuyar da kaina,wani mugun
tausayin
Abba ke ratsani,na tabbata wani abun ne ya faru
shine dalilin sanyashi yin tambayar nan a
gareni,ba
tare dana dauki lokaci ba na dago kaina"Abba na
amince domin ina kaunar Zahra ne." Yayi shiru
yana
nazarina,kafin yace"Ka tabbata Amadu?" Na
gyada kaina"Kwarai kuwa Abba,ina kaunarta."
Yayi
murmushi ya qara duban Zahra"Masha Allah,kinji
abunda yace ko?" Zahra ta qara sunkuyar da
kanta
tana murmushi,Abba ya girgiza kai"Ki daina
damun
kanki Zahra,sai kin toshe kunnuwanki,duk wata
magana da zakiji daga bakin mahaifiyarki kiyi
hakuri da ita. Duk wani abu da zata fadi kan
Amadu kada ki
dauka,ki rike dan uwanki,ku hade kanku kada ki
biye mata kinji ko? Mahaifiya ce bance kiyi mata
rashin kunya ba,ki bita sannu ku rabu lafiya
kinji?"
Ta gyada kai,Abba yayi murmushi ya maido
dubansa
gareni"Amadu ga amanar Zahra,bana shakku
akanka,nasan halinka tun kana qanqani kai mai
kulawa ne da 'yan uwanka duk da irin qiyayyar
da
suke nuna maka kamar yanda nasan shaquwar
dake tsakaninka da Zahra'u,sai kunyi hakuri da
halin
iyayenku,Allah Yayi muku albarka Ya kareku." A
lokaci daya muka amsa da amin,ya dan gyara
zama"Madallah kuna iya tafiya." Har mun mike
yace"Ba dai fita zakayi tun yanzu ba gashi tara
bata
ida cika ba." Na juyo ina dafe kaina"Eh Abba fita
zanyi." Ya girgiza kai"A'a ka tsaya tukunna,ke
Zahra'u maza shiryawa dan uwanki abun kari."
Daga
haka muka bar falon,na koma dakina na zauna
cike da tunanin maganganun Abba.
Amma abunda ban gane ba shine,ita Zahrar da
kanta ta sanar da Abba cewa bana sonta ko
kuwa
dai anti amaryar ce ta fadi? Ina ta tunane
tunanena
har saida siririyar muryar Zahra ta katseni,na
dubi
bakin qofa ina mai amsa mata sallamar,caraf
muka
hada ido da ita,na tsinci kaina da sakar mata
murmushi tayi saurin sunkuyar da kanta,sai kuma
naji haushin kaina,a daidai lokacin da ta durkusa
domin ajiye farantin silbar data dora kayan shayi
akai
na ja qaramin tsaki ina mai dan kauda kaina
jikina a
sanyaye. Sai kuma na juyo ga mamakina dubana
takeyi hawaye kwance akan fuskarta,da sauri
nace"Lafiya? Me ya faru Zahra?" Ta sanya hannu
tana
mai sharewa ta girgiza kanta"Babu
komai,gashinan."
Ta mike da saurinta zata bar dakin saidai ni din
ma
bani da karfin dakatar da ita domin gaba daya
jikin
nawa babu kwari,na tabbata tsakin da nayi ne ya
sosa zuciyarta toh ya zanyi? Duk motsin da
zanyi sai na tuno Hafsa,ta yaya zan soma
tunkarar aminiyarta
da sunan so? Wannan bazai taba faruwa
ba,zamuyi
zama ne da Zahra,zama na mutunta juna,amma
bana
jin akwai abunda zan iya yiwa Zahra,mtsw." Na
qarashe tunanin da jan dogon tsaki,na soma
hada
tea,sai kuma kalaman abba suka dawomin inda
yake bani amanar 'yar sa,zuciyata ta qara
cunkushewa da
matsanancin bacin rai,a daddafe na kammala
kurban
ruwan shayin wanda ban iya na hada da biredi
ba,ko
kwan ban iya ci ba,na mike na bar gidan. Lokacin
tara ta buga,a sona na wuce gidan anti aisha
saidai
kuma na tabbatar mijinta yana gida,hakanan
yanzu lokacin bude shagona baiyi ba,na hangi
baba
maigadi zaune yana karyawa akan benci,hakan
yasa
na miqa qafa na isa gareshi,cike da ladabi na
gaisheshi ya hadiye biredin daya lunquma a baki
fuska a sake yace"Lafiya lau amadu,har an fito
kenan
da wuri haka?" Nayi murmushi sannan na zauna
kusa dashi"Na fito baba." Daga haka ban qara
magana ba,ya katsemin tunani"Bismillah." Na
girgiza
kai"Alhamdulillah,na karya baba." Ya jinjina
kansa ya
cigaba da karinsa,hankalina ya tafi duniyar tunani
naji baba maigadi na bubbuga qafata"Amadu,Am
adu kai." Nayi firgigit na dubeshi ina mai sakin
nannauyen ajiyar zuciya,cike da mamaki baba
maigadi yace"Ikon Allah! Kai kuwa meke
damunka
har haka? Ina ta magana baka san ina yi? Wani
abun
ne kuma ya faru?" Nayi murmushin
yaqe"Bakomai
Baba." Baba maigadi ya quramin ido da alama
nazarina yakeyi,kafin ya kai ga juya kansa daga
hagu zuwa dama,dama zuwa hagu"Amadu
kenan,tun kana yaro nake tare dakai,a zatonka
akwai yanayin da zan gani akan fuskarka na kasa
ganewa? Fuskarka na dauke da damuwa ka
sanar
dani koda shawara ce na baka." Gaskiya baba
maigadi ya fadi,nidai dan tsohon yana burgeni
saboda tarin iliminsa,sannan akwai saurin
fahimta,dattijo ne na kwarai,hakan yasa na sanar
dashi batun auren Zahra. Ga mamakina sai naga
yayi
murmushi"Yaro kenan,toh banda abinka Amadu
mene abun damuwa? Wannan ai gata za'ayi
maka,sannan babata(Zahra'u hakanan yake
kiranta) tana da nutsuwa,kodayaushe tazo
wucewa sai ta iso
nan ta gaisheni,babu ruwanta yarinyar,ta fi
sauran
yaran unguwar nan kai babata tana samun
kyawawan shaidu a gun jama'a,ban taba cin karo
da
wanda ya aibunta yarinyar nan ba,gaskiya Alhaji
yayi
tunani mai kyau. Kada ka damu Amadu,toh ai ni
zamanin nan ma mamaki abun yake bani,wai har
sai
yaro ya zabowa kansa matar aure,a lokacinmu da
saidai kawai iyaye sun aura maka yarinya wacce
ko
taba ganinta bakayi ba amma a yanzu sai namiji
da
mace sun amincewa juna. Yanzu dai ka ga ni din
nan,sa'adda na auri matata marigayiya
saudatu,ban santa ba,bata sanni ba har muka
haifi yaro daya
Umaru,amma cikin hukuncin Allah soyayyar da
muke
yiwa juna ko wadanda suka ga junansu sukace
suna
so sai haka. Toh sai mutuwar mai yankan kauna
ta
dauketa. Fuska cike da mamaki na dubi baba
maigadi"Baba dama kana da 'da?" Baba maigadi
yayi 'yar dariya"Ikon Allah! Ina da yaro daya
mana,umaru dai da ka sani dake zaune a gidan
Alhaji
namu(wato maigidansa Alhaji sunusi)." Kaina ya
kuma daurewa,na zaro ido"Baba kada kace min
umar dan gidan Alhaji yaronka ne?" Baba
murmushi
kawai yake,ya jinjina kai"'Dan Saudatu ne,dana
ne,yanzu kuma yake matsayin dan Alhaji
namu,ya
rikeshi kamar 'dan cikinsa yanzu gashi har ya
kusa
hada digirinsa?" Nidai shiru nayi sai a lokacin
kuma
nake hango kammanin umar da baba
maigadi,saidai
shi umar fari ne,babansa kuwa baqi ne,na jinjina
kaina"Allah Sarki." Baba maigadi yayi 'yar
dariya"Amadu kenan,a rayuwa mutum yakan
hadu
da mutanen arziki,wadanda suka san darajar dan
adam,toh wallahi Alhaji da hajiya sun rike umaru
kamar su suka haifeshi,har na kan tsorata idan
naga
irin kyautatawar da hajiya keyi masa,amma
baiwar
Allah tausayinta nake na danganta hakan da
rashin haihuwarta. "Allah Sarki,haka hajiya ke
kaunar yaron nan,kai
daidai da karatunsa na jami'a Alhaji yaso ya
turashi waje,amma fir hajiya ta qi yarda,a
cewarta idan umaru ya barta wa zata kalla taji
dadi? Sai kuma abun Allah,shi kansa umaru yana
kaunar hajiya umma sosai,kai duk da umaru
yasan cewa ni din ne mahaifinsa su Alhaji ba
iyayensa bane hakan baisa ya fasa kyautata
musu ba. Ba yabon kai ba,amma Alhamdulillah
ina alfahari da yarona,domin komai nasa idan su
Alhaji suka yi masa sai yayi shawara dani,daidai
da bangaren karatunsa saida ya nemi shawarata
akan ya karanci likitanci ko kuwa? Toh dama shi
tun fil'azal ya fison karatun likita,hakan yasa na
zaba masa bangaren,yaji dadi yace suma su
Hajiya nan din suke so. Da farko umaru ya nuna
rashin jin dadinsa game da aikin gadin da
nakeyi,na nuna masa babu komai,a son Alhaji
kada nayi gadi,ni din dai na zabi hakan,domin a
baya da muka zo,kasancewar ni almajirin malam
saleh ne,shi malam saleh mazaunin kazaure
ne,dan uwan baban Alhaji ne,toh sai yawan
zuwan da Alhaji yake yi yasa muka saba
dashi,don yakan cewa malam shi dai Aliyu yana
burgeshi bangaren dagewa wajen karatu,kai har
dai nayi aure da saudatu muna tare da
Alhaji,duk
da lokacin yana matashi na dan girmeshi da
shekaru biyu hakan bai sa ba ma zumunci ba,har
Allah Ya kawo lokacin da Alhaji ya nemi na dawo
Kano da zama nima. Farko na qi,saida yaje har
wajen malam saleh akan ya roqi innata ta bari ya
wuce dani,toh nan dinma dai an sha fama dani
don ita ta amince ni kuma nace sam. Har Alhaji
yayi fushi ya koma,daga baya kuma ya hakura
muka cigaba da gaisawa domin yakan jima bai zo
ba,saboda aiki da ya soma yi masa yawa. Har
mukayi shekaru biyu Allah bai sa saudatu ta kai
munzalin da zan dora mata nauyina ba,domin na
aureta tana 'yar qarama mai shekaru goma cif.
Haka har saida ta kai shekaru goma sha biyar
kafin na soma shiga dakinta. Bayan nan da
shekara daya ta samu ciki,lokacin Alhaji yayi aure
bisa yawan qorafin da yake samu wajen iyayensa
akan hakan,a son ransa ya zauna hakanan yayi
ta neman kudi." Baba mai gadi ya dan jinkirta
yana murmushi kafin ya cigaba"Toh tunda Alhaji
ya auri hajiya umma,'yar garin kano bashi da
buri
sai ganin sun haihu. Tafiya tayi tafiya har
shekaru biyar amma shiru,lokacin umaru yana da
shekaru hudu a duniya,abun ya damu Alhaji
kwarai,malam saleh kodayaushe yana yi masa
nasiha,hakanan iyayensa. Qarshe dai ya qara
taso da batun komawata,wannan karon da kansa
ya samu innata,ganin irin kaunar da yake gareni
yasa ta yarda da hakan. Muka dunguma sai
birni,bamu tsaya ko'ina ba sai nan unguwar
yakasai. Hajiya Umma mace mai kirki da sanin
darajar dan adam,ta karbemu hannu bibbiyu. Ni
kaina gidan Alhaji ya burgeni,duk da cewa lokacin
bai kai haka girma ba,domin babu bene saidai
ko'ina yayi kyau,an malala sumunti a tsakar
gidan. Muhalli mai kyau muke kwana mu tashi a
ciki,saidai bamu iya bacci da daddare,domin
lokacin gidan babu maigadinsa,hakan ba qaramin
mamaki yake bani,domin a gurinmu mutan kauye
gida babba irin haka ai ganganci ne ace babu mai
gadi,duk da kasancewar Allah Shine mai tsarewa.
Da safe koda Alhaji ya tambayeni na nuna masa
damuwata da yanda muka kasa samun nutsuwa
har muyi bacci,yayi dariya sosai,yace ai wannan
ba wani abu bane. Toh a haka dai har na soma
zuwa nan ina kwanciya,cikin dare na farka na
dunga kula ko babu wata matsala da kwadon
dake garkame jikin kofar,har dai daga haka na
saba kwana anan. Alhaji babu irin hanawar da
baiyi ba akan zai sanya a nemo wani na bar
kwana a nan amma fir na qi yarda. Kai har dai
na
saba,toh haka umaru ya shaku da saudatu,bamu
yi shekara a garin ba saudatu ta samu cikawa.
Nayi kuka kamar me daga baya na hakura,hajiya
umma ta nuna son rike umaru a wajenta,ban
kawo komai a raina ba domin nayi imanin a
yanda hajiya umma ke son umaru ba zata cutar
dashi ba. Inna ta nemi amincewa ta nace na
amince. Ai kuwa murna wajen bayin Allahn nan
sai wanda ya gani. Toh a lokacin ne Alhaji ya
nuna min na soma gwada kasuwanci,ban iya na
amince ba,a soyayyar da mukayi da
saudatu,mutuwarta ba qaramin girgizani tayi ba
Amadu,gaba daya ji nayi komai na duniya ya fita
raina wallahi,shiyasa yana fada na hade rai,na
nuna masa idan har ba gajiya yayi dani ba toh ya
kyaleni hakanan na cigaba da yi masa gadi,hakan
ba wai yana nufin mun rabu bane,a'a muna tare.
Kai shaida ne wataran Alhaji har nan yake fitowa
ya zauna muyi hira dashi muyi wasa da
dariya,daidai da shawara Alhaji Sunusi yana
nemana dashi. Toh Amadu kaji yanda muke da
Alhaji,ya rikeni dan uwa kamar yanda na
rikeshi,inda ace duniya ce a gabana Amadu bana
shakku zan azartu da arzikin Alhaji,da tuni na
hada gidaje da motoci Amadu,saidai tun bayan
mutuwar saudatu ban qara marmarin duniya
ba,gani nake ko dayaushe mutuwa zata iya zuwa
ta tafi dani a shafe babina daga duniya. Amadu
ita rayuwar nan da kake gani ba komai
bace,wallahi ina mamakin masu daukarta da
zafi,har su samu damar bata lokacinsu wajen
yiwa wani hassada,mugunta,bakin ciki da sauran
munanan abubuwa. Naga qoqarin Alhaji da har
ya
samu abun duniya amma hakan bai sa idonsa ya
rufu ba wajen tsayar da gaskiya ba. Amadu ka
dauki darasin rayuwa anan,kaga ban san Alhaji
ba
saita dalilin malam saleh,bansan Hajiya ba saita
dalilin Alhaji,amma soyayya da kaunar da suka
nunamin da iyalina kamar wadanda suke 'yan
uwan juna. Kalli fa wannan lamari Amadu,a
zamanin nan inda ace ana samun haka ai da abu
bai baci ba. Amadu Alhaji Mudi,mutumin arziki
ne,makocine wanda yasan darajar
makocinsa,yana da qoqari wajen wannan,nidai
tun
da muke dashi ban taba jin yayi fada da wani ba
kamar yanda yake jarumin namiji mai halin
dattako,Alhaji yana yawan yabonsa domin kuwa
wajen lokaci daya suka tare a nan layin. Kayi
kokari kayi biyayya Amadu,rayuwa ba komai
bace,albarkar da iyayenka suke sanya maka bazai
tashi a banza ba kamar yanda addu'arsu ke
bibiyarka kodayaushe. Auren gata za'ayi
maka,babata tana da halayyar kwarai,a sanin da
nayi mata ban taba jin an aibatata ba ta kowane
fanni ba,yarinya ce mai hankali. Allah Shi yasan
abunda ya boye,ka kasance mai kokari wajen
biyayya ga iyaye,dama ba ganin ido ba kana da
wannan kokarin,ka cigaba kaji ko?" Na gyada
kaina ina murmushi"Insha Allahu baba." Shima
murmushin yayi"Yauwa Amadu,Allah Yayi maka
albarka." Na amsa da amin,kafin daga bisani nayi
masa sallama kasancewar goma har tayi. Ina
tafe ina tunanin labarin nan na baba maigadi mai
ban al'ajabi,kwarai dattijon bai damu da duniya
ba,Allah Sarki,rayuwa kenan,Allah Ya jikan
matarsa saudatu. Haka dai har na isa shago cike
da jinjina wannan labarin da baba maigadi.
Duk wanda na tunkara da batun Zahra saidai naji
yana yabo gareta,hakan yasa na miqa lamurana
ga
Ubangiji. Domin ko anti aisha dana je
gidanta,nayi
mata maganar na zaci zata dauki zafi sai ma
wani irin
farinciki da ya bayyana akan fuskarta,tace ai ita
bata
ga abun tashin hankali ba,dama tun lokacin da
gwaggo tayi kiranta ta sanar da ita hakan yasa
ta
cigaba da hadamin lefena da sunan na Zahra.
Nan
itama tayimin dogon nasiha,har take sanar dani
tuni
su kawu sun san da hakan kuma sunji dadi. Toh
haka dai har akayi kwana uku,lokacin ne kuma
aka
sanya ranar aure nan da sati biyu wai ba'a son a
dauki lokaci,har na bahijja da yarimanta za'a
hada.
Ina ganin yanda Badamasi ke rawar qafa,shine
gwanin zaqewar bugo iv,ni kuwa gaba daya bana
cikin kwanciyar hankali,har 'yar rama nayi. Yau
ma
tsareni yayi akan lallai muje na rakashi gidan
bukar
ya damqa masa na classmates dinmu da aka
rarrabu. Ya qara duban agogon dake daure a
hannunsa kafin
ya maido dubansa gareni ya ja tsaki"Amadu
wallahi
zan zageka." Ya bani dariya,cikin dariyar na ajiye
littafin lissafin dake rike a hannuna"Toh me yayi
zafi
hakanan?" Ya harareni,tasi'u shima murya a
sanyaye
yace"Oga kaje mana zan kula da shagon." Nayi
murmushi nasan ganin yanda ran Badamasi ya
baci
ne ya sanyashi fadin hakan,na mike ina sanya
hulata"Kaidai wallahi kana neman shiga
rayuwata."
Badamasi ya harareni amma bai iya yace komai
ba da
alama dai ya qulu. Ya fice daga shagon na bishi
a
baya. A mota ma fisgarta kawai yake,nayi dariya
ina dubansa"Haba abokina,meye kuma na bacin
rai?
Kayi hakuri please." Ya sauke ajiyar zuciya"Ai
lamuran naka ne Ahmed,akwai ban haushi,komai
sai
ka yi kokarin zame kanka,meyasa kake haka
please?
So kake ka bawa mutane damar da zasu fahimci
wani abun? Ya kamata fa kayi taka tsantsan." Na
jinjina kai"Gaskiyane,zan kiyaye." Daga haka
muka
shiga hira,yana sanar dani an shirya dinner,nidai
jinsa kawai nakeyi. Har muka isa wajen Bukar,nan
ma yayi mamakin jin batun aurena da Zahra,ya
dubeni"Ahmed haka kuma Allah Ya tsara?" Nayi
murmushi kawai,yace"Toh Allah Ya sanya alheri."
"Amin." Muka amsa gaba daya. Daha nan
Badamasi
ya damka masa katunan gayyatar daurin aure
yace
ya taimaka wajen rabawa,ya tabbatar zaiyi
sannan
muka rabu. Gida kuwa tuni an qara gyarashi,ana
sauran kwana hudu a soma biki,ina kwance a
dakina cike da tunani,wayata tayi qara,lambar
dana gani yasa na mike zaune babu shiri,na qara
mutsitstsika idanuna amma ina lambar ce
dai,HAFSA????? Tayi sallama agareni na amsa
mata,mukayi
shiru,gaba daya muryarta ta kashemin jikina,na
mance rabon da naji muryar Hafsa a waya. Nayi
ta
maza nace"Hafsa.....Beauty." Cikin rawar murya
Hafsa
tace"Uhum,yayanmu barka da dare." Allah
Sarki,rayuwa kenan,Yayanmu danaji Hafsa ta
ambata ya tunamin cewa yanzun fa ba da
bace,na daure na
qaqalo murmushi mai sauti"Kanwata barka
dai,kina
lafiya?" Ta dauki lokaci kadan kafin ta
amsa"Lafiya
lau yayanmu,dama nace Zahra kwana biyu
shiru,koda na buga layinta bana samu gashi
kuma
inason magana da ita ne." Ta dakata,mukayi
shiru,gabana ya fadi,na tuna ashe fa bata da
labarin
aurena da zahra. Na hadiyi miyau nace"Allah
Sarki,mai yiwuwa ko matsala wayar ta samu bari
na
aika mata kuyi magana." Shiru ya biyu bayan
"Ok"
din da Hafsa tace,na katse shirun"Hafsa ina su
noor
da faruq?" Cikin sauri ta amsa"Suna nan
lafiya,Faruq ne ma bayanan ya wuce Ghana
karatu,noor yana
nan sai yawan maganarka." Nayi murmushi"Allah
Sarki,da ace yana kusa damun gaisa ai." Tayi
'yar
dariya"Ai shi wannan tun magriba yake bacci,tuni
har yayi nisa." Na gyada kaina ina mai jin tsohon
tsumin son yana tashi,"Hafsa." Na kira sunanta
cike da salon da na tabbata zai ratsata,"Na'am."
"Yaushe
za'ayi aurenki?" Tayi shiru,har saida na qara
kiran
sunanta,"Hafsa,kina jina kuwa?" Muryarta ta
nuna
alamun kuka takeyi"Hum,yayanmu gobe za'a
daura
aure,Zahra ce na jita shiru ma shiyasa na bugo
domin
naji ko laifi nayi gareta." Wani irin daci naji ya
mamaye zuciyata,na dafe kaina"Ya Salam!" Na
furta a
fili,shiru kamar babu wanda zai qara cewa
uffan,na
daure nace"Allah Sarki,Allah Ya sanya alheri toh."
Tayi shiru,sai ma ta dan bani dariya,nayi dariya
kadan"Bakice komai ba kanwata?" "Uhum,amin."
Na
jinjina kaina"Madallah,bari na kai mata kina iya
kashewa sai ta kira." "Toh." Ta fada sannan ta
kashe,na zubawa wayar ido,Allah kenan! Shi ke
tsarawa bawa rayuwa,na mike jiki babu kwari na
fito,hanyar shiga gidan kawai nake bi da kallo,ta
yaya zan iya shiga? Ga anty amarya wacce har
lokacin bala'i kala kala takeyi akan wannan
auren,domin kuwa ba don Abba ya tsawatar ba
da
tuni Zahra ta bar kwanan dakinta,don cewa tayi
tunda ta nuna tafison ubanta sai ta bar mata
daki taje
tayi ta auren biyayya wanda bazai amfaneta da
komai ba don bada yawunta ba,shi kuwa Abba
yace
ai gidan na uban Zahra ne,saidai ita ta bar gidan
amma ba Zahra ba. Ni kuwa tsakanina da ita sai
harara da zage zage,hatta mahaifiyar faisal wato
yaya
a gareta saida ta zo gidan tayi cin mutunci kala
kala
sa'arta daya Abba baya gidan,ni kaina ban ko
leqo
ba,inna kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa ta
sha,domin ita duk abunda zai quntatawa amarya
shi takeso. Abba koda ya dawo yaji yanda ta
kasance a
bakin inna ko zama baiyi ba yace na kaishi gidan
Alhaji Garba,mahaifin faisal,ya sameshi ya kuma
gargadeshi akan kada matarsa ta qara takowa
gidansa. Alhaji Garba ya bawa Abba hakuri. Na
gyara
tsayuwa ina tunanin ta yanda zan kira zahra na
bata waya,sai gashi Allah Ya jefo mariya zata
shiga
gidan,kasancewar ta dawo gida wai mijin yayi
tafiya,nace"Yauwa mariya don Allah taimaka ki
bawa
Zahra wayar nan,kice ta kira Hafsa." Ta sa hannu
ta
karba"Hafsa?!" Ta nanata a mamakince tana mai
zubamin ido cike da tuhuma,nayi murmushi ina
dan daga gira"Yes Hafsa,meye abun mamaki? Ai
qawarta
ce ko?" Ta tabe baki tace"Lallai fa,akwai
matsala,hafsa?" Tayi gaba tana maganganunta,na
ja
qaramin tsaki"Yara ayi su sai jaye jayen magana?
Toh
meye don Hafsa ta kirani? Aure aka daura mata?
Mtsw,Allah Ya kyauta. Na bar dakin na nufi
waje,lokacin qarfe takwas na dare,shagon idi na
nufa. Tun daga nesa samarin wajen suka soma
fadin"Kaga ango,barkanka da zuwa." Sai ma suka
bani dariya,cikin dariyar na girgiza kaina"Shiyasa
na
dauke qafa daga shagon nan." Akayi dariya,idi
yace"A'aha,kai kuwa me yayi zafi? Ai murna
muke son taya ka,saura kwana nawa ne?" Na dan
hade rai
ina mai daga kafada"Ina zan sani?" Wani Yusha'u
makwafcinmu yace"Haba dai Ahmed,wasa
kake,kafi
kowa sani kaidai kawai kace bakason a ga
zalamarka ne." Nayi murmushi,su kuwa suka
kwashe da dariya,na dauke kaina a zuciyata kuwa
cewa nayi"Inda ace auren so ne,ba shakka da sai
nafi haka zaqewa."
Kai har saida nayi dana sanin fitowa na wajen
idi,haka sukayita min iskanci kala kala,dole na
mike
tsaye na dubesu"Naga alama idan har ba wurin
nan
na bari ba bazaku kyaleni ba." Sukayi dariya,wani
rabi'u yace"Kai kuwa Ahmed ai da ka jira uztas
aminu ya qaraso yayi maka 'yan nasihu." Na
harare shi ina mai jan tsaki,suka kwashe da
dariya,na bar
wajen. Aminu wani dan unguwan ne saurayi
ne,amma akwai ilimi da yawan nasiha. A dakin
ma
ban iya na tsinana komai ba idan banda tunanin
wannan auren. Wai nan da kwana hudu ni
Ahmed
zan zama mijin Zahra? Hmm,ba shakka komai na
Allah ne. Ba zato naji qarar waya na tashi a
dakin,har
saida na firgita nayi baya,ashe tana nan kan dan
teburi,kenan Zahra ta maidota. Badamasi ne,na
ja
tsaki,shi dinma dai bai wuce ya hau yimin tsiya
ba. Na
sanya a kunne"Me ya faru?" Yayi dariya"Haka ka
dauki zafi? Babu ko sallama?" Na daure
fuska"Salamun Alaika." Ya amsa kafin yace"Ko
kai
fa? Na kira ai naji amarya ta dauka,hakan yasa
na
katse nayi zaton zance ne kukeyi kada na
katsewa
maso...." "Please ya isa." Na dakatar
dashi,"Hafsa ce
tayi kira shine dalilin jin wayata da kayi a
hannunta
wai bata samunta a nata wayar." Badamasi
yace"Kaga dan iska,wato baka rabu da Hafsar
nan
ba ko?" Nayi murmushi mai ciwo"Inda ban rabu
da
ita ba ai da ni kaina naji dadi,saidai ita hafsar
nan
gobe ma za'a daura aurenta ai karshen rabuwar
kenan ko?" Badamasi kuma sai yayi sanyi"Allah
Sarki,kace abu yazo ashe? Allah Ya sanya
alheri,kaima ba gashi ka kusa angwancewa ba."
Na
ja tsaki,yayi dariya"Kai ni ka cikani da tsaki
kamar
wani tsaka,ba wannan ne yasa nayi kiranka ba
dallah." Na muskuta na gyara zamana"Ina jinka
toh,ya akayi?" "Yauwa,batun dinner da za'ayi
ne,toh
mun kama wuri anyi komai bisa tsari,gobe ka
shirya muje ka ga inda aka kama." Nace"Kaidai
kana da
daukarwa kai wahala,ashe batun dinner baku
barta
ba?" Badamasi yace"Ai sai kayi,amma bikin naka
guda kuma sai yazo ya wuce bamuyi wata 'yar
kwarya kwarya ba? Na bugawa Buhari(Yarima)
waya nace ya kasance cikin shiri da qarfe hudu
zamu je." Nayi murmushi"Shikenan toh,Allah Ya
nuna
mana,kai ma muna fatan ganin bikinka haka."
Yayi
dariya"Insha Allahu,kaidai bari ai ba lokaci mai
tsawo bane." Na qara yi masa fatan alheri kafin
mu
ajiye wayar.************************


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100Amadu 2 page 7
Posted by ANaM Dorayi on 06:27 PM, 26-Jun-15
Under: Amadu
Gida ya cika,mafi akasari 'yan
uwan inna ne da wasu daga 'yan uwan Abba.
Mamaki lamarin yake bani,wai inna ce ke nuna
murnarta a wannan auren,lallai na yarda kishi
babu
abunda bayasa mata. Haka inna ke jana a jiki
sosai,abu kadan zata aika a kirani,na ci abinci
nayi
kaza nayi kaza ashe ita duk don ta quntatawa
Anti amarya takeyi. Yaya usman ya turo anty
fiddausi shi
sai daga baya zai taho da amaryarsa,auren dai
saida
yayi shi hankalinsa ya kwanta. Ni naje daukota
daga
airport kasancewar jirgi ta hau na safe,da
fara'arta ta
qaraso,nima na taimaka mata da jaka,ita kuma
taji da
riqon yaronta dan wata biyu mai sunan Abba,ana
ce masa Imam. A mota nace"A'a kinga yanda
kuka
zama kuwa? Wasu b'ula b'ula da farko wallahi
bansan kece tafe ba." Tayi dariya,"Ango
kenan,don
ma baka ga yayan naka ba da kanwar tawa,su
sai
kace iska ake qara musu." Mukayi
dariya,nace"Kod
ayake kinsan bata taba zuwa ba,tun zuwan da
inna taje tayi muku kwana uku toh babu wanda
yaje
daga nan ko? Inna ce kadai ta santa." Anti
fiddausi
tayi wani dan murmushi wanda ko ba'a fada ba
na
yaqe ne"Kaidai Ahmed ayi sha'ani,kai nifa har
tausayin Hamidah,domin wallahi yaudararta
kawai
yayanka keyi,ba sonta yake ba kudinta yake
so,komai yake mata sai ya sanar min,yanzun ma
nuna mata yayi tare zai taho da ita. Wallahi
Ahmed
ina tausaya mata ace babu soyayyarta a zuciyar
namiji,kada kaso kaga yanda ta dauki kanta har
wani gani gani takeyimin a zatonta ta fini a
zuciyarsa." Nayi murmushi ina jinjina lamarin
yaya usman,ashe dai kudi zai iya sanyashi har ya
yaudari
'yar mutane? Na girgiza kaina ina mai sakin
ajiyar
zuciya"Kash,amma yaya usman ya bani kunya,shi
bai
tsoron ma Allah Ya kamashi?" Ta dan ja
tsaki"Rabu
dashi,sau nawa zan zauna nayi kokarin yin nasiha
agareshi ya watsamin qasa a ido? Ya nunamin
kawai dai na sakata mu ci kudi? Toh ai innar
tasa kanta
tasan niyyar dan nata ita da kanta tasha aibata
hamida a gabana,bayan haka kuma ta sha sanar
dani kada na damu kaina da kishin wacce bata
isa
ba,kudi ne kawai za'a ci a wajenta ba wata tsiyar
ba."
Banyi mamakin jin lafuzzan data ce sun fito daga
bakin inna ba,don inna ba wanda baisan irin son
kudinta ba. "Allah Sarki,Allah Ya ganar dasu toh."
"Amin dai." Muka bar wannan shafin muka sanyo
hirar biki,tana mai zolayata iyakacin nayi
dariya,ko
kadan ban nuna mata bana kaunar Zahra ba
asalima
nuna mata nayi nan duniya ina kaunar Zahra.
Har
take dariya tana mai nuna mamakinta,wai ashe
dai
da zamu yiwa kanmu ne daga ni har zahrar
muna
son juna mun qi mu fad'a. Murmushi nayi bance
uffan
ba,har muka isa gida.
A daren anti aisha tayi kirana muka je tare da
Badamasi,ta nuna mana akwatunan data hada
seti,babu kayan raini a ciki,komai yayi kyau,hatta
gwal saida ta samu ta siya da taimakon mijinta
da
kudin da take tarawa don bikina a cewarta.
Komai
yayi kyau,ni kaina komai ya burgeni kuma yayi
daidai da zabina Badamasi yana dariya
yace"Amma
dai antinmu kin iya hade lefe,wannan irin kaya
hakanan?" Tayi dariya"Kai ko Badamasi ai dole
na
hadowa Zahra kayan kece raini,ai mutuniyata ce
kuma koda a fita kunya ai za'ayi." Sukayi dariya
nidai
tunda na gama kallo na koma kan waya ina
danne danne,har saida suka bar hirar aka sanyo
ta auren
Badamasi yake ce mata saura wata daya a nan
ne na
sanya baki,daga qarshe mukayi sallama da ita
tace a
goben za'a kai kaya. ***************
***************************Ana gobe za'a
soma
biki yaya usman ya dira da amaryarsa aunty
hamida,duk da cewa dai na girmeta hakan bai
hanani kiranta da anti ba. Sai wani iyayi take
tana
shashshan kamshi a lokacin da suka iso. Na karbi
jakar hannun yaya usman ina dariya"Barkanku da
zuwa." Ya dafa kafadata yana jijjigawa"Kaga
Alhaji
Ahmed angon Zahra ba shakka angon kake."
Saida ya sanyamu dariya sosai,ita kuwa gwanar
tana gefe
sai latsa wayarta takeyi,jin abunda yaya usman
yake
fadi yasa ta dagowa ta kalleni,duba na raini. Sai
kuma
ta tabe baki tana mai cigaba da danne dannenta.
Sai
nine nace"Antinmu ina yini?" Ta dago tana mai
dan
tare gira"oh,lafiya lau,ya hidima?" Na juya nayi
gaba ba tare dana amsa ba,idan wulakanci ne ni
dinma
wataran ai ba baya bane. Wulakanci abune mai
baqanta zuciya,bashi da dadi,hakanan na
tsaneshi
saboda sanin zafinsa da nayi tun yarintana. Duk
wani
mai wulakanta dan adam baya burgeni,saidai na
tausaya mata domin tana yin abu ne bisa rashin
sanin abunda ke zuciyar mijin nata. Na sauke
kayan
a dakin,dama tuni kayana sun koma sabon
gida,yau
dinma can zan wuce na kwana.*********
*****************************Aka soma biki
saidai ba'a nan gidan ake taro ba,banda ranar
da
sukayi kamu anan sauran shagulgulan duk gidan
gwaggo suka nufa. Nidai gaba daya ma barin
gidan
nayi zuwa gidana,kyau kam ba'a magana babu
abunda zan cewa Abba sai godiya,ko kwabona
baiyi
ciwon kai ba. Yace 'da nake gareshi don haka shi
zai
mini komai. Nidai babu wanda zai ganni ya gane
ina
tare da damuwa idan banda Badamasi. Nayi
kokari na danne komai dake zuciyata har ana
gobe daurin
aure. A daren kuwa na wahaltu,komai yayi min
babu
dadi,shikenan Zahra ta kusa kasancewa
matata,Allah
Sarki Hafsa tuni ta jima a dakin mijinta. Ina
kwance a
dakina ina tunane tunane,badamasi ya dokamin
sallama,na fito mukayi musabaha. Na zauna kan
kujerar zuciyar babu dadi,ya dubeni"Ango
kenan,har yau dai ka qi sakin zuciyarka ko?" Na
shafe kaina ina mai murmushi"Me kuma ka
gani?"
Ya
zuramin ido kafin ya girgiza kansa"Gashi ma yana
faruwa,Ahmed ni kuwa ka kira Zahra a waya
tunda
aka soma bikin nan?" Na tabe baki ina mai dan
daga kafada"Meyasa zan kira ta kuma?" Ya
harareni
sannan ya ja tsaki,ransa ya baci nan ya shiga
budemin wuta kamar wani ubana"Haba
Ahmed,meyasa baka taba daukar nasiha? Toh
wallahi kaji tsoron Allah,kada yarinyar nan ta
shigo
ka wulakantata,bana jin dadin abunda kake
mata!
Wallahi dazu data fito zan basu katunan rabo na
dinner saida ta zubda kwallah,wai ko don yanda
mahaifiyarta ke tsangwamarta akan auren nan
bai
isa ace ka raga mata ba?! Toh ni kam bazan qara
yi
maka maganar nan ba kai da Ubangijinka kuma!
Gobe dai za'a daura maku aure,idan ma gasa ta
zakayi sai kayi!" Ya mike a fusace ya nufi qofa,da
sauri na riko hannunsa,hankalina ya
tashi,idanuna
suka sauya launi,jikina yayi mugun sanyi,ba
shakka
maganganunsa sun shigeni sun ratsani,ya kwace
hannunsa"Barni Ahmed,ban ga amfanin
tarayyarmu
ba tunda har bazan iya fadamaka ka dauka ba."
"Kayi hakuri,tabbas nayi kuskure,amma nayi
maka
alqawarin yau zan kira zahra insha Allahu." Ya
dan
sauko sannan ya nunoni da yatsa"Ba wannan
kadai
nake buqata ba,so nake ka chanja gaba daya ka
zama jarumi wajen rikon aure." Nayi murmushi
na
gyada kaina"Insha Allahu bazan taba wulakanta
Zahra ba." Ya sauke ajiyar zuciya"Shikenan."
Dakyar
dai ya sauko muka dan taba hira ya barni wai
duk
domin na samu sarari nayi hira da Zahra,nidai
na
rakashi na dawo ciki. Lokacin karfe tara da rabi
na
dare,na ciro wayar na lalubo lambar zahra,na
tsaya
cak ina kallon lambar,a hankali na sauke ajiyar
zuciya,Zahra ce fa wannan dana ke yiwa kallon
kanwata,ta soni ta kaunaceni,Zahra bata
kyamaceni
ba. Zahra mai kyawun hali,mai kyan fuska,Zahra!
Zahra!! Zahra!!! Yau ita zan kira ba matsayin
kanwa
ba,amma matsayin wacce zan aura a
gobe,matsayin
wacce zamu dauwwama tare,sannan MASOYIYA.
Da kamar wuya! Saidai kuma tuni ban ankara ba
na
danna kiran layin. Na tsinci kaina da faduwar
gaba,na daure na kara
wayar a kunne,yana ringing sai kuma can aka
daga. Siririyar muryarta ta doki kunnena"Assalam
u alaika." Na lumshe ido kadan,a yau kuma sai
nakejin kamar an sanyawa muryar Kanwartawa
wasu sinadarai don zaqi da sanyin da tayi. "Amin
wa'alaikissalam,kina lafiya?" Ta danyi shiru
sannan tace"Lafiya lau,ina yini." Na
daure"Lafiya,ya hidima?" A sanyaye
tace"Alhamdulillah." Sai kuma shiru ya biyo baya
kowannenmu babu abun cewa,nace"Ok,lafiyarki
na bugo naji dama,Allah Ya tashemu lafiya."
"Amin,nagode." Na kashe sai na bi wayar da kallo
ina mai jin tausayinta,kamar kuma ban kyauta
ba,toh amma me nayi na rashin kyautatawar? Ai
dama hakan dole ya faru tunda babu wata
shakuwa ta soyayya tsakaninmu. Da wannan na
jona wayar a chaji na bi lafiyar gado,iska mai
dadi na fanka dana hadarin da ya hadu a sararin
samaniya ya sanyani bacci mai dadi.**********
*************** ****************Bayan
sakkowa
daga sallar juma'a aka daura aurena da Zahra
sannan na Buhari (yarima) da bahijja. Zo kaga
farin ciki wajensu Abba da 'yan uwansa. Kowa ka
gani farin ciki da walwala yake,ni kaina na dake a
ranar ban nuna wani abu da zai sanya mutane
zargina ba. Haidar da su kabir,kai har hayat dake
a Abuja saida ya halarci taron daurin aurena.
Bukar kuwa da sauran abokaina na makaranta da
aka rabu sun samu isowa suma. Bayan daurin
aure,muka dunguma can gidan gwaggo,aka
kwashi gaisuwa,mata kuwa sai buda sukeyi.
Bakin kowa a wangale cike da nishadi. Badamasi
zai sanya a kirawo Zahra wai ta gaisa da
abokanmu,na dakatar dashi,a hankali
nace"Please
banason wannan al'adar." Badamasi yayi
murmushi yace"Good,haka akeson namiji da kishi
wanda hakan alama ce ta so." Murmushin kawai
nayi,daga nan aka dan dauki hotuna muka fito sai
kuma naga Badamasi na fadin"Maza kuyi sauri
mu isa kada rana tayi don Allah." Na dubeshi"Ina
zuwa kuma?" Yayi dariya"Akwai qaramin liyafa
dana hada mana ne,can gidanmu ne." Na jinjina
kai kawai,a nan bangarensa muka yada zango,ya
shiga ya sanarwa mami mun iso,nan aka shiga
fito da kayan abinci kala kala da abubuwan sha.
Sai bayan an gama ne kuma aka shiga hira,su
bukar gwanaye,aka shiga zolayata. Kai ranar dai
yini akayi ana raha. Sai la'asar aka watse da
zummar sai an hadu wajen dinner wanda zai
kasance bayan isha'i.
Na gama haduwa cikin dakakkiyar shadda kalar
dark brown,qamshi kuwa ba'a maganarsa. Koda
na fito nan na tadda Badamasi tare da Haidar da
wasu da basu riga sun wuce daukar qawayen
amarya ba. Ai kuwa sukayi kaina da ihu"Kaga na
Zahra,ango Ahmed." Murmushi na sakar musu
mai bayyana haqora,Badamasi ya mikomin
hannu
yana dariya,na miqa masa muka cafke"Shegen ka
hadu." Na ja tsaki"Ku dai da wani abu kuke? Sai
kace wasu mata?" Sukayi dariya,Haidar yace"Ai
kuwa kafi wasu matan kyau." Na qara
murmushi,Badamasi yace"A hanzarta dare yana
yi."******************************************Har
kofar gidan gwaggo muka tsaya,na zubawa kofar
gidan ido,duk da cewa dai ba wani kaunar Zahra
nake ba,amma ni kaina naji a jikina sai
kwalliyarta ta burgeni,toh Zahra dama da kwalliya
ya take ballantana kuma yau ranar bikinta?
Badamasi ya dauki waya yayi kiran Bahijja,yace
su fito,jamila ita ta soma fitowa ta nufomu,ta
zubawa Badamasi ido cikin wani salon
murmushi,shima ya sakar mata"Kaga tawan,kin
hadu." Sukayi dariya tana fari da ido"Ai ban kai
ka ba." Ta dan leqo tana dariya"Ango ango,kasha
kyau da qamshi." Nayi murmushi"Jamee kenan,ya
gari?" Ta dan dago"Lafiya lau wallahi,garin yanzu
ai yana hannunku mu kam da saura." Na bude
baki ina mai mamakin yanda ko kunya take fadin
haka a gabana. Suka tuntsire da dariya ita da
badamasi,nayi murmushi"Shiga ki fitomin da
amaryata." Kafin tace wani abun sai gasu sun
fito. Kishingide nake saida na mike na zauna
sosai ina mai qara qura mata ido. A hankali suke
takowa,bahijja tayi kwana ta nufi motar
yarima,Zahra ta qaraso,saida ta iso na samu
qarfin dauke ido daga kanta ina mai saurin kauda
kaina gudun kada ta ganni. Badamasi na janta da
wasa yana koda kyawunta,bansan ya akayi ba sai
ji nayi na sanya hannu na bude mata motar da
kaina,ta shigo ta zauna,wani sassanyar ajiyar
zuciya na saki. Ta dubeni na dubeta,kyawawan
dara daran idanuwanta ta dubeni,ta hade da
leshi
milk,nadin kanta kalar shaddata,ai sai ga ni ina
murmushi agareta,ta maidamin martani tana mai
sauke idanunta qasa a hankali kamar mai yin fari
dasu. Na gyara zama ina mai jin yanayi na daban
game da Zahra,tuni badamasi ya ja
motar,jamilarsa na gaba suna kwasar hirarsu ta
masoya. A fakaice nake satar kallon Zahra,ganin
yanda tayi qasa da kanta yasa na karkato sosai
ina dubanta,a zuci nake nanata sunanta,har
bansan ya akayi na furta cikin salo na daban ba
ba"Zahra."
Ta dago kanta cikin nutsuwa tana mai
dubana,har lokacin fuskarta dauke da murmushi
wanda ke qara mata kyau. Fuskarta sai kyalli
yake,farin nan nata kuwa ai kamar qara mata
akayi tamkar wata balarabiya. Lebbanta ya
motsa hakan ya tabbatar mini ta amsa,na bisu da
kallo kafin a hankali na maida dubana kwayar
idonta wadanda tuni ta daukesu daga gareni.
Saidai kuma na rasa abun cewa,na girgiza kaina
na gyara zamana sosai ina duban waje,kirjina
yana bugawa,na kasa samun nutsuwa jefi jefi
nakan dago na dubeta,itama na lura tunda ta
sanya kanta qasa bata dago ba ballantana ta
dubeni. Kamshi mai dadin shaqa ke tashi a
jikinta,shiru mukayi a hankali badamasi da
jamilarsa ke soyewarsu har muka iso. Bayan mun
fito,su haidar da sauran abokanmu sukayo mana
caa,muka shiga gaba,a hankali na kamo
tattausan
hannun zahra saida tsikar jikina ya tashi domin
sai ince tunda nake da Zahra ko hannu ban taba
rike mata ba idan ba yau ba,koda ace na rike a
baya ba don komai ba saidai yau ni kaina nasan
hannun matata na rike. Muka shiga ciki,aka saki
sauti mai dadi,har muka isa mazauninmu,shima
yarima da bahijjarsa suka zauna a nasu
mazaunin. Nan fa aka soma gudanar da shagalin
bikin,zo kaga yanda 'yan mata da samari ke
cashewa,wasu kuwa bansan fuskokinsu ba saidai
naji Badamasi na fadin abokansa ne dake a DM
na facebook,hakanan ma Bahijja ta gayyato
kawayenta da yawa na DM,lallai kuwa sunyi
kara,kowannensu ka gani fuska a sake tamkar
dama can sunyi mini farin sani,toh abu ne na ba
mutum daya ba. Waje ya cika makil da
mutane,koda muka fito domin mu dan taka
tsayawa nayi cak,hakan yasa kanwar tawa itama
kasancewar rawa baya cikin tsarinta tsayawar
tayi,aka soma yi mana liqi,daga 'yan goma goma
har dubu dubu. Bakinmu ya qi rufuwa,haka
kawai
nima na tsinci kaina cikin wani mugun nishadi ina
maqale da Zahra,karshe kuma da abun naga
zaiyi
yawa na ja abata muka koma mazaunin mu.
Bayan an ci an sha kuma aka zo yanka kek. Nan
dinma saida na riqo qugunta kafin na sanya
mata,ita kuwa saida ta durkusa sannan ta
sanyamin. Kwarai mun burge,nan wajen ya dauki
ihu da tafi. Ga hasken camera na tashi,mai video
ma yana nasa. Haka nan Bahijja da
Yarimanta,nan ma sun bada salo na daban. Sai
kuma kowa ya koma mazauninsa,aka dan qara
cashewa sannan aka tashi. Bamu bar wajen nan
ba saida mukayi sallama da kowa,'yan DM
kuwa,har saida suka jira mukayi hotuna,saboda
yawansu duk da cewa dai na dan ji ana ambaton
su bari'a,engineer,su zee,rabi'a,mary
am,aisha,hafsa,nafisa,kai har su
ahmed,aminu,musbahu,abdul,layuza,da
sauransu
dai da basu qidayuwa amma bazan iya nuna su a
fuska ince ga wance ko wane ba. Kyauta kuwa da
Zahra ta samu daga garesu ba'a magana,wasu
su miqo envelop wasu kuwa kwaline da akayi
nannade shi da leda mai kyalkyali. A mota kuwa
tuni zahra ta langabe jikin kujera alamun gajiya a
tattare da ita,na juyo da sauri"Ya dai Zahra,kin
gaji ko?" Ta dan yamutse fuska tana mai lumshe
ido"Wallahi yaya duk na gaji sosaima." Na matso
ina mai riko hannun ina dan matsawa,cike da
tausayawa nace"Sorry kinji?" Tayi murmushi sai
kuma ta soma gyaran mayafinta,na dubi
Badamasi"Kai dan rage AC yayi yawa mana."
Badamasi yayi dariya yana dubana ta madubi ya
kashe ido ya dubi jamila"Babyna kinaso a rage?"
Tayi dariya"Rage sweetyna,nima sanyin nakeji."
Ya rage,na girgiza kai"Au lallai ma kai dinnan,toh
inda tace kada a rage fa?" Badamasi ya jinjina kai
yana dariya"Wallahi bazan rage ba." Muka sanya
dariya,har Zahra wacce ke qara qudunduna da
mayafinta. Ganin haka na dan ja tsaki,na dauki
babbar rigata dake gefe na rufe ta ina
fada"Kaidai
dan iska ne,wannan soyayya taku ta soma isar
mu gwara a tattara ayi auren mu huta."Sukayi
dariya,ina duban Zahra ta dubeni,muka sakarwa
juna murmushi,ta dauke kanta,hakan yasa na
zauna sosai ina mai sauke ajiyar zuciya. Wai
meke damuna ne hakanan? Ni kaina fa nasan na
chanja. Koda muka isa nan din ma Badamasi ya
dubeni
yana murmushi"Toh ango bari mu barku kuyi
sallama ko?" Ban musa ba don ni kaina zan so
hakan,gyada masa kai kawai nayi,yayi dariya
suka fita shi da jamila suka tsaya daga gaban
motar suna hira. Na juyo na matso daf da Zahra
yayinda qafata daya ke kan kujerar,tana ta
kiciniyar janye rigata zata gyara mayafinta,nayi
murmushi"Zahra kenan,dakata na taimaka maki
duk na lura a gajiye kike." Tayi murmushi tana
mai sauke idonta qasa,na janye rigata a hankali
saidai kuma na tsaya cak ina dubanta,dinki ne na
zamani akayiwa rigarta,ya zauna das kamar
dama can haka yazo a jikin nata. Na lura dai
gaba daya a sanyaye take ganin yanda take
sauke ajiyar zuciya a kai akai,nayi murmushi a
yayin da nakai hannu qasan wuyanta"Meya
sanyaki faduwar gaba? Ko kin dauka yayanki zai
maki wani abun ne?" Ta girgiza kanta da
sauri,alamun tsoro bayyane kan fuskarta,a
hankali
kuma ta motsa lebbanta"A'a." Na hadiyi
miyau,ina mai binsu da kallo,sai ga 'dan muttaka
yana kai lebbansa kan na kanwartasa,na hadasu
guri guda kafin daga bisani na janyesu wato dai
na sumbaceta. Ta runtse ido tamau tana mai
numfarfashi,toh ai ni kaina kamar an jonamin
igiyar wuta nakejina,saidai kuma babu zato naga
hawaye kan fuskar Zahra,na qara ware jajayen
idanuna a kanta,da sauri na dago
hab'anta"Subhanallah,Zahra meya faru? Nine ko?
Don Allah kiyi hakuri kinji." Ta girgiza kai,na
soma share mata hawayen,murya a raunane
tace"Yaya Ahmed sai na dunga tunanin kamar
kan dole ka aureni ne,musamman ganin yanda
kake kaunar Hafsa sai na......." Nayi saurin sanya
hannuna kan lebbanta ina fadin"Sshh." Raina a
bace nace"Banason irin wannan maganar
please,wa yace maki bana kaunarki? Ko kin taba
jin na furta maki?" Ta girgiza kanta jikinta na lura
yayi sanyi ganin yanda na hade rai,nima na
sauko
ina ma riko hannunta gami da qara sunkuyo da
kaina"Toh kada ki qara wannan tunanin kinji ko?
Yayan nan yana kaunar kanwarsa." Tayi
murmushi tana mai juya kanta,na rufe ta da
hakan,nima nayi murmushi"Yauwa,shikenan dai
bari na barki dare na qara yi,sai Allah Ya kaimu
gobe idan an kawomin ke ko?" Tayi 'yar dariya na
tayata,na zura hannu na bude mata kofar ta
sauka. Sannan nima na fito. Har kofar gidan na
taka mata,sannan na juyo,itama jamila tayi ciki
bayan munyi sallama domin dare yayi nan zata
kwana. Muka cafke da Badamasi muna
dariya,yace"Shegen sama,so ko qiyayya?" Na
harareshi ina mai jan tsaki a lokaci guda kuma na
murmusa"Ai ban taba furta kalmar qi ga Zahra
ba." Badamasi ya kwashe da dariya"Kaidai ka ji
da gulmarka." Mukayi dariya,bayan mun shiga
mota nace"Kai ni kaina ina jin wani yanayi game
da zahra a yanzu wallahi ai nagode Allah da
baisa na cika baki ba cewar bana sonta dana sha
kunya." Na qarashe ina mai kauda kaina daga
kallon badamasi wanda ya karkato kansa yana
hararata"Kaji dan iska,ai hatta anti aisha ta ji sai
tayi maka dariya,ni kaina dariyar kake bani. Wane
irin abune baka ce ba game da Zahra? Sai gashi
kana jagwalgwalata yanzun?" Nayi dariya"Kai!
Wato dai idonku na kanmu ko?" Yayi dariya ko
kusa ai na waje baya hangen na ciki,na dai san a
rina irin wannan dadewar da kukayi sai a
hankali." Nayi murmushi ina mai cire hulana,gaba
daya a gajiye nake,Zahra! Na nanata sunan a
raina,lallai ta soma samun gurbi a zuciyata. Koda
muka rabu da Badamasi,ranar dai wuni nayi
kallon hoton Zahra dake a wayana,da kuma
wanda na sanya Badamasi ya daukarmin a wajen
dinner. Murmushi nakeyi ina qarewa matata
kallo,qarshe mikewa nayi na gabatar da shafa'i
da wuturi na roqi kwanciyar hankali da zaman
lafiya cikin aurena da Zahra.
Waje ya hautsine,sai hira mukeyi da dariya. Ni
dasu Bukar da sauran abokanmu
ne,kowannenmu
yayi tsaf babu ma kamar ni da nake angon. Na
gama haduwa cikin fararen kaya na shadda da ya
sha ado. Sai qamshi ta ko'ina ke tashi. Muna
kofar gidansu Badamasi a tsaye ana shirye
shiryen zuwa dauko amarya. Haidar ya dafe
kafadata yana dariya"A'a,kaga ango yau fa har
wani haske haske fuskar taka takeyi." Aka sanya
dariya,Badamasi yace"Ai dole ma yayi abunda
yafi haske,yau fa ranar ce." Nayi murmushi,"Allah
Ya shiryeka." Sukayi dariya,na dubesu"Zaku tafi
daukomin matata ko kuwa?" Sukayi dariya,Hayat
yace"Gwara mu hanzarta muje,yau ba ranar
zolaya bace,kuyi baya baya dashi kada ku fadi
wanda zai kai hannu kuncinku." Muka sanya
dariya har ni,na jinjina kaina kenan dai har yanzu
ba zasu bar tsokanar Badamasi ba dai kan marin
da na taba yi masa farkon haduwarmu. Cikin
dariya Badamasi ya kai wa Hayat bugu a
qafada"Dan iska." Muka sanya dariya,Bukar
yace"Ku dai abu bai wucewa a wajenku." Sai da
takwas ta cika sannan suka fice. Wajen tara da
rabi kuwa kowa ya watse,sai lokacin muka rufa
musu baya tare da Badamasi. Gabana sai dukan
tara tara yakeyi,saida muka tsaya ya sayi lemuka
da kaza sannan ya tashi motar mukayi gaba har
qofar gidan. Babu bata lokaci muka qarasa har
dakin da Zahra take. Saidai kafin mukai ga shiga
tuni 'yan matan sun datse qofar a cewarsu sai
mun biya kafin su barmu muga amarya. Na dan
ja qaramin tsaki ina mai ja da baya kadan,aka
soma fafatawa,'yan matan suka ce sai dubu
hamsin,kasancewar harka ne da 'ya'yan masu
kudi. Nan da nan Badamasi ya zura hannun ya
dauko ya damqawa wata qawar Zahra,baraka
kudi har dubu hamsin,haidar yana murmushi ya
zura hannu ya qara zaro kudi har dubu hamsin
ya miqa musu. Nan suka sanya tafi wata gwanar
ta saki buda. Akayi dariya,suka bude muka shiga.
Na shaqi daddadan qamshin da tun jiya yake
fisgata na daga jikin Zahra. Na lumshe ido na
saukesu akanta,tana lullube da farin mayafi,da
alama dai kuka takeyi. Na qarasa na zauna kusa
da ita. Kabir yace"Toh ai sai a dan bude fuskar
mu gani ko?" Na harareshi,suka sanya
dariya,Haidar yace"Wannan gaskiyane,ya kamata
dai muga fuskar amaryar." Nayi murmushi"Babu
mai gane mini fuskar mata,gwara ku tattara ma
ku tafi." Suka sanya dariya har qawayen amarya.
Gaba daya kukan Zahra ya dameni,fatana su
barni na samu damar rarrashinta,suna tsaye
suna
kwasar hira,can dai nayi gyaran murya"Ya dace
dai ayi addu'a hakanan ko?" Suka kwashe da
dariya,wata makociyarmu hauwa tace"Oh
Ahmed,ko kunya kake korar mu?" Badamasi
yace"Barshi,dan iska kawai,mu ma tafiyarmu
zamuyi." Akayi dariya,Ustaz ya kwararo mana
addu'a aka shafa har wajen na rakasu suka tafi.
Na dawo na rufe qofar. Dakin na nufa har lokacin
dai sheshsheka take,nayi murmushi na durkusa
gabanta,na lumshe ido a karo na biyu kafin na
budesu. A hankali na daga mayafinta,hawaye ke
zuba kan fuskarta,kanta har rawa yake saboda
tsananin kukan da takeyi. A gigice na soma share
hawayenta,"Haba Zahra,ya isa hakanan." Ta
dago idota ta dubeni,sai kuma ta qara fashewa
da kuka,murya na rawa tace"Yaya Ahmed,na
baro
gidanmu mahaifiyata tana mai fushi dani hakan
yasa ko fatan alheri ban samu daga gareta ba,sai
ma zagi da mugun baki data bini dashi. Ina zan
sa kaina? Tace babu ni babu ita." Tsananin
tausayin Zahra ya kamani har bansan sa'adda na
rungumota gaba daya jikina ba,idanuna suka
kada a fili nace"Kiyi hakuri Zahra,a sanadina kike
fuskantar matsala da mahaifiyarki,ki yafe min ina
kyautata zaton akwai ranar da Anti zata gane
manufar Abba,akwai ranar da zata chanja. Nasan
dole hankalinki ya tashi amma don Allah kiyi
hakuri,komai mai wucewa ne wataran kinji ko?"


Zaharaddeen  Shomar

Whatsapp  08168575100Amadu 2 part 8
Posted by ANaM Dorayi on 06:37 PM, 26-Jun-15
Under: Amadu
Ta gyada min kai,na qara hada ta da jikina a
hankali nake shafa gadon bayanta. Sai kuma
lamura suka nemi chanjawa a yayin dana dago
fuskarta na soma aika mata da zafafan saqonni
har saida naji ta qara sanya kuka tana fadin"Kayi
hakuri don Allah Yaya Ahmed." Na ankara da
abunda nakeyi,na sake ta,da sauri na mike tsaye
a yayin da na juya mata baya,toh abunka ga
wanda bai taba kusantar wata 'ya mace ba koda
ta hanyar rike mata hannu ne don farantawa
zuciya,gaba daya ma sia naji kunya ta kamani,na
runtse ido,murya a wahalce nace"Sorry
Zahra,tashi ki dora alwala." Da sauri da sauri na
bar dakin zuwa nawa,gefen gado na zauna ina
mai dafa kaina,oh ni Amadu meke damuna haka?
Ashe zan iya barin batun Hafsa da sauri
hakanan? Sai kuma na tuna a yanzu ita din fa
matar wani ce na ja qaramin tsaki,na mike na
shiga wanka. Bayan na fito na zura jallabiya na
feshe jikina da turaruka,ango nake dole na
zamana cikin qamshi duk da cewa zama ba
turaren ma ba al'adata bace. Na fito falon,na
kashe fitilu,na sunkuci ledojin da muka zo dasu
nayi dakin amarya. Tana zaune a qasa,ta dago
jajayen idanunta wanda ya sha matsa saboda
kuka ta dubeni,na sakar mata murmushi ta
sunkuyar da kanta ba tare data maida min
martani ba. Jikina yayi sanyi,ni kaina sai naji
kunyar kaina wallahi. Yanzu me Zahra zatayi
tunani ne? Wannan kallon da tayimin meye
manufarsa? Anya Zahra zata yarda dani cewa na
soma kaunarta kuwa? Kwarai ya dace kafin wani
abu ya soma shiga tsakanina da ita,So da
shaquwa ya samu a zamantakewar mu. Hakan
yasa ko bayan munyi sallah mun ci abinci na
umarceta data rage kayan jikinta. Ta mike bayan
na zabo mata rigar bacci a jerin rigunan dake
kwabarta,na miqa mata. Ta shige bandaki na bita
da kallo ina murmushi,Zahra kenan. Na kashe
fitila na kunna ta gefen gadon sannan na kwanta
ina tunane tunanena. Har saida naji ta murda
kofa ta fito,a hankali na dago kaina na dubeta,a
minti biyu na qare mata kallo tun daga sama har
qasa sannan na janye idanuna daga kanta ina
mai sakin ajiyar zuciya sassanya. Yau qanwar
tawa ta chanja min,riga ce lylon mai santsi
iyakarta gwuiwa,baqa ce mai qaramin hannu. Ya
zaka ga fara a cikin baqin tufafi? Gashinta yayi
cunkus a cikin ribbon an tufkeshi daga baya,kanta
na qasa ita bata motsa daga inda take ba
ballanta ta taho gareni. Na sauke ajiyar
zuciya,murya na rawa na qara satar kallonta"Ya
kika tsaya?" Ta qara daga qafa ta
matso,murmushi nayi a lokacin dana sanya
hannu na kashe fitilar dakin yayi duhu. Ina jin
motsinta a yayin data hayo gadon,Ya Allah!
Qamshin nan dai na lura a jikin Zahra yake ba
wai turare ne ta fesa ba don tun jiya nake shaqar
shi a yanzun kuwa jinsa nayi yafi na kodayaushe.
Anya zan iya barin Zahra kamar yanda na
daukarwa kaina???
***
Na juya ina dubanta,ban ganin yanayin da take
ciki,na dai ji a jikina ta takure kanta ne. A sannu
na matsa daf da ita,cikin sauri na rungumota ta
baya,duk ta kudundune kafafunta gu daya,nayi
murmushi saitin kunnenta nayi mata rada"Kada
ki
damu babu abunda zanyi maki kinji kanwata?"
"Uhum." Shine furucinta,inajin yanda take faman
sauke ajiyar zuciya akai akai,na sanya hannu na
kunna 'yar fitilar,na juyo Zahra wacce tuni ta
runtse idonta don kunya na qara sakin
murmushi,a hankali na soma hura mata fuskar,ta
danyi firgigit alamun dai ya shigeta,na sanya
yatsa ina mai yawo dashi daga goshinta har
zuwa wuyanta. "Zahra." A hankali ta bude
idanunta ta saukesu a kaina,na tsura mata nawa
rinannun idanuwan wanda nasan ba lallai ta
fahimci yanayin da na shiga ba saboda rashin
qarfin haske. Da saurinta kuma tayi qasa da
idanunta,na saki murmushi"Kinyi farin ciki da
kasancewata maigida uban 'ya'ya agareki?" Tayi
murmushi tana mai qara duqar da kanta,na dago
hab'anta ina mai girgiza mata kai"No Zahra
magana nake so muyi. Wane irin farin ciki kikayi a
lokacin da aka daura mana aure? Please ki saki
jiki ki bani amsa,ni ne fa?" Cikin siririyar
muryarta
ta soma magana"Nayi farin ciki a ranar saidai
rashin sanin matsayina a zuciyarka ya sanya ni
kuka sosai." Sai ta bani tausayi,nace"Allah Sarki
Zahra,yayanki yana kaunarki kada ki qara
tunanin
dole akayi mini na aureki,kinji?" Ta gyada kanta.
Na sa hannu na kashe fitilar,a hankali kuma
zance ya soma sauyawa. Nayi duk abunda zanyi
da ita saidai ko kusa ban yi yunkurin sanin ta a
diya mace ba. Bacci mai dadi ya biyo baya bayan
faruwar lamura masu tsayawa a rai. Koda asuba
da na farka,Zahra na manne da jikina,na bita da
kallo,na gyara mata rigarta na matsar da ita gefe
sannan na mike na nufi toilet. Dana fito na
tasheta ta hanyar mammatsa qafafunta,ta bude
ido a hankali,mukayiwa juna murmushi ta sauke
kanta,"Tashi asuba tayi." Na isa ga darduma na
tada kabbara domin nafila.
***
)Na jima ina kwararo mana addu'o'i na zama
lafiya da kwanciyar hankali da zuri'a nagari. Da
safe kuwa,ban farka ba har saida rana ta fito gari
yayi haske. Hakan yasa na mike da sauri cike da
mamakin irin baccin da nayi. Na duba agogon
jikin bango,karfe takwas da rabi na safe.
Subhanallah! Na furta,babu zahra a shimfida
hakan ya tabbatar min ta rigani tashi. Na fito
falon,motsin da naji ne ya tabbatar min cewa
tana kicin,na nufi dakina. Nima wankan nayi na
hade cikin koriyar shadda. Na sameta tana jera
kayan kari kan tebur,tsayawa nayi kawai na dafe
kujera ina qarewa Zahra kallo,ta gama haduwa
cikin farin leshinta mai adon jajayen
fulawoyi,dinkin ya zauna tsam a jikinta. Ta juyo
kanta a qasa tana murmushi,har qasa ta
durkusa"Yaya Ahmed ina kwana." Ina murmushin
na amsa mata a lokacin dana tako zuwa
gareta"Lafiya lau amaryar Ahmed,ya kwananki a
gidansa?" Tayi murmushi tana mai dan jan hanci
kamar mai mura. Na dubi kan tebur din"Ina can
ina bacci na barki da aiki? Meyasa baki tasheni
na taimaka maki ba?" Ta girgiza kai tana
dariya"uhum,nidai ban taba ganinka a kicin ba."
Mukayi dariya,na ja hannunta lokacin dana
zaunar da ita kan kujera nace"Haka kikace ko?
Toh babu mamaki ma na fiki iya girki." Cikin
dariyar nan nata mai burgewa tace"Kayya,bana
tunanin hakan. Kada ka manta fa gida daya muka
taso,ban taba ganinka a kicin ba." Nayi murmushi
ina mai tsura mata ido,ji nake kamar kada ta
daina dariyar nan,wallahi na hakikance son Zahra
nake. Kai ko yaya ne ma dai ni Ahmed na soma
son Zahra. Na kasa dauke ido daga dubanta,har
saida ta dakatar da dariyarta tana mai sauke
kanta qasa cikin murmushi murmushi na jin
kunya,hakan yasa na sauke ajiyar zuciya na
dauke kai ina mai shafa sumata cike da jin
nauyin
irin yanda na zuba mata ido. Ta soma hadamin
tea,komai tayi burgeni takeyi,gani nake kamar ba
wacce na sani bace,har bansan yanda akayi na
tsinci kaina da subutar baki ba"Zahra." Ta ajiye
flask din dake hannunta ta dubeni lebbanta ya
motsa."Kinyi kyau." Tayi qasa da kanta tana
murmushi. Sai kuma naji kunya ta kamani,oh ni
Ahmed! Kada fa yarinyar nan tayi zaton jikinta
nake so,toh eh mana! A iya sanin Zahra tasan
bani da masoyiya kamar aminiyarta,nasan ko a
baya ta lura da yanda nake shareta tun sa'adda
naji cewar tana kaunata. Dole ne soyayyarta ya
qara samun gurbi a zuciyata kafin wakanar
komai. Wajen sha biyu muna zaune a falo,muka ji
ana sallama. Na mike na dubi Zahra,"Shiga ciki."
Ta mike na bude kofar,su anti abida ne tare da
sauran 'yan uwa,har da su gwaggo delu. A
kunyace na matsa gefe ina musu sannu da zuwa.
Anti kubra ta tabe baki"Oh Ahmed,aure dadi har
yanzu ana gida ba'a tafi shago ba." Nayi
murmushi kadan ina mai shafa kaina,bayan sun
zauna na durkusa har qasa na gaidasu. Jin
muryarsu Zahra ta fito,da gudunta ta isa ga
gwaggo delu ta rungumeta suna dariya. Sai kuma
ta sanya cikin cinyoyin gwaggo delu,anti abida
tace"Kuji mu da yarinya,kunyar me kike toh?"
Gwaggo delu tace"Ina ruwanki toh da ita ke
kuma? Banason sakarci fa." Na mike a kunyace
nace"Gwaggo ni na wuce shago." Anti abida
tace"Ji gulma,farko ai bakayi niyyar fita ba,salon
munafurci saida muka zo sannan zaka tsiri
tafiya?" Nayi murmushi mai ciwo,gwaggo delu
tace"Wai ke abida meyasa kike hakane? Ya ci ace
ki dunga kyautata lafuzzanki ga dan uwanki,shine
zai maki munafurci?" Ta ja tsaki ta dubeni"Tashi
ka wuce Amadu,Allah Ya bada sa'a,na mike na
kai kofa naji tana cewa"Tashi kiyiwa maigidanki
rakiya,banason shiririta." A kofa na tsaya ina jiran
Zahra,sai gata a sanyaye,fuskarta na nuna rashin
jin dadi,nasan bai wuce kalaman anti abida ba,na
janyo hannunta ina dariya duk domin kaudar
mata da bacin rai"Matso nan kiji kanwata? Zanyi
kewarki fa,me kikeso na taho maki dashi?" Na
janyota jikina,murya a shagwabance tace"Yayana
nidai Allah Ya dawomin dakai lafiya,shi kadai
nake bukata." Nayi murmushi"Amin
kanwata,Allah
Ya kiyayemin ke kinji? Sia na dawo,ki kularmin da
kanki please." Na sumbaci goshinta,ta lumshe ido
tana murmushi,muka dagawa juna hannu na nufi
motar Abba wacce ke hannuna tun fara biki. Kai
tsaye gida na soma nufa gun Abba domin na
gaidashi,na faka ina mai cike da fargabar yanda
zamu kaya da anti amarya domin sai ince tun
fara biki bamu hadu da ita ba. Sallama na soma
yi a tsakar gidan kamar dai
yanda na saba,Allah Ya taimakeni babu kowa
tsakar gidan saidai kafin na kai ga shiga dakin
Abba sai ga inna ta fito tana amsawa,ciki daga
murya tace"Kaga angon Zahra,kai ne tafe?" Nayi
murmushi jikina yayi sanyi don rashin sabawar da
banyi ba da irin wannan raha daga inna,har qasa
na durkusa na gaisheta don ni har lokacin dar
dar
nake da inna."Lafiya lau,ya Zahra ince tana nan
dai lafiya?" "Alhamdulillah inna,Abba yana ciki
ko?" Tace"Qarasa yana ciki,idan ka fito ka zo ciki
mu qara gaisawa ko?" Ta qarashe tana mai
kallon dakin anti amarya,nayi murmushi"Toh."
Kawai nace mata sannan na mike nayi dakin
Abba,inna kenan uwar kissa,don na lura kawai
don quntatawa Anti take wannan budurin. Dan
dattijon yana kishingide a kan kujera hannunsa a
gefensa kuma rediyo ce yake saurare,ganina yasa
shi mikewa zaune yana mai fadada
fara'arsa"Sannunka Amadu." Ina 'yar dariya na
qarasa kusa dashi. Cikin ladabi na gaida Abba,ya
amsa yace"Kun kwana lafiya?" Na qara duqar da
kaina"Alhamdulillah." "Toh Madallah,haka
akesonji ai. Sai a qara hakuri da juna,a kula da
wannan nauyi daya hau kai, ka kasance mai
kiyaye dokokin Allah,kaji ko?" Na gyada kai ina
mai amsawa"Insha Allahu Abba zan kiyaye." Abba
yayi murmushi"Masha Allah,Allah Yayi maka
albarka." "Amin Abba." Na zaro mukulli na miqo
masa"Abba gashi." Abba ya zurawa mukullin ido
yana murmushi kafin ya dubeni"Mota kuma ta
riga ta zama taka Amadu,na sayi wata yau zata
iso insha Allahu." Farin ciki ya mamayeni,na qara
wangale baki ina dariya"Abba nagode,Allah Ya
raya zuri'a,Ya Kare ku da iyalinku." Na shiga
kwararo addu'a Abba na amin,har saida ya
dakatar dani"Ya isa Amadu,haba,kaifa 'dana ne."
Nayi murmushi,"Tashi ka tafi wajen aikin
ka,wannan ba komai bane." Na mike na fito,kiran
da na tuna inna tayimin dazu yasa na soma shiga
dakinta kafin qarasawa dakin anti. Na taddata
zaune a falonta,nidai gabana faduwa yake,na isa
na nemi guri na zauna. "Inna gani." Tayi 'yar
dariya"Yauwa Amadu sannunka." Saidai kuma ina
jiran jin abunda zata ce ta soma maganar da
bata shafeni,nan ta shiga bani labarin irin
kudaden da yaya usman ya samu a aurensa da
anti hamidah,nidai mamaki ne ya kamani,toh
meya shafeni? Haka inna ta cigaba da zubamin
hira marasa kan gado,har saida aka dauki wani
lokacin sannan tace ina iya tafiya,har kofar
dakinta ta rakoni tana fadin"Idan ka koma ka
gaida amaryar taka,sai a kula." Yanzu na gane
dai inda inna tasa gaba,tayi duk domin ta cusawa
anti amarya haushi,na lura so take ta janyoni
jikinta. Kai mata akwai kishi,da wuya ayi abu don
Allah. Nayi sallama har wajen sau uku amma
babu amsa,ana hudun ne aka na bankade
labule,anti ce ta zubamin jajayen idanunta"Uban
me kake nema a guna?" Gabana ya fadi,tana
magana cike da bala'i kamar ta mareni,murya na
rawa nace"Nazo domin na gaishe......" "Wake
bukatar gaisuwarka?! Bace ka bani guri!"
Hayaniyarta ya sanya Abba fitowa da
sauri"Lafiya? Meye haka wai?" Inna ma ta fito
tana wani dafe kirji,"Me ya faru ne jummai?" Ta
banka mata harara,ta dubeni"Kai qaramin dan
iska,duk tsagerancinka ya qare akan wasu,tun
kafin nasa qafar wando daya dakai ka gaggauta
rabuwa da 'yata idan ba...." "Binta!!" Abba ya
kira
ainahin sunan anti amarya,ta dubeshi rai a
bace"Eh! Ya sakarmin 'yata muddin yana son
zaman lafiya da kwanciyar hankali wallahi. A rasa
wanda za'a bawa 'yata sai dan iska wanda baiyi
gadon arziki ba!" Kau! Abba ya wanke mata fuska
da mari har sau biyu,inna ta rike
Abba"Subhanalla
h,Alhaji ayi hakuri,ke kuwa jummai meyasa kike
haka? Inace da Amadu da Zahra duk daya ne?
Kada ki manta fa 'yan uwa suke." Abba ya
fusata"Rabu da ita,ki cigaba da yimin rashin
kunya ki gani,kuma muddin na sake jin kinyi
wannan wawan furucin wallahi kafin Zahra ta bar
gidanta ke zaki bar gidan nan! Shashasha kawai
wacce bata da tawakkali! Amadu fice ka tafi
wurin aikinka." Jikina yayi mugun sanyi,na juya
na fice daga gidan. Yaushe zan rabu da wannan
masifa? Anya akwai ranar da iyalan Abba zasu
nunamin kauna tsakani da Allah? Da kamar wuya!
Na bawa kaina
amsa.*************************
*****************A shago ina ta fama da
jama'a
kasancewar alokacin hatta mayafai da takalma
na mata muna dan ajiyewa saboda ana nema.
Ina
ta cinikin wani mayafi da wata mace,Badamasi ya
shigo,na bar wa tasi'u shagon muka fito. Yana
dariya yace"Kaga ango,ai wallahi ban tsammaci
zaka fito yau ba." Nayi dariya"Toh ya za'ayi? Na
bar gida ba don rai ya so ba,rabin hankalina yana
gareta." Muka cafke muna dariya,Badamasi har
yana kwarewa ya duben"Wallahi Ahmed mamaki
kake bani,yanzu don Allah ko kunyata bakaji ba
har kake fadamin kana tunanin Zahra? Anya ka
tuna yanda nasha fama dakai akanta?" Na
harareshi kadan ina murmushi"Ai ban taba furta
kalmar qi gareta ba." Badamasi ya cafe
zancen"Dama can kana sonta gulma ce." Na
sauke ajiyar zuciya yayin da abubuwan da suka
wakana tsakanina da Zahra a jiya suke dawomin
kwakwalwa,na lumshe ido kadan na shafi
sumata"Bazaka gane ba,amma kwarai na soma
kaunar Zahra fiye da tunaninka." Yayi
murmushi"Ai dama Zahra ba matar qi bace
Ahmed,kana sonta saidai baka gane ba,amma
Alhamdulillah data kasance rabonka ba wani ba."
Na jinjina kaina"Saidai kasan me?" Yace"Saika
fada." "Na rasa gane kan lamarin anti amarya,ita
fa da gaske take lallai sai na rabu da 'yar ta."
Badamasi ya ja tsaki"Wannan tana da matsala
wallahi,I am sorry to say amma wallahi Abba
baiyi dacen mata nagari ba. Meyasa har yau
bazasu haqura da qaddara ba?" Na tabe baki"Ai
gaskiya ka fadi,wallahi yau ni kaina saida Abba
ya bani tausayi,kada ka so kaga yanda ta soma
budemin wuta a tsakar gida kai koda Abban ya
daka mata tsawa bata saduda ba har saida ya
kai ga marinta." Na dan ja tsaki"Wallahi lamarin
baiyi dadi ba,Zahra na bani tausayi. Duk soyayyar
da anti ke mata a kan ta aureni ta bar nuna
mata." Badamasi ya dafa kafadata"Kada wannan
ya dameka Ahmed,kaidai kada ka bawa Abba
kunya,ka rike Zahra da amana kada wani abu ya
razana ka. Insha Allahu shaidan bazai nasarar
shiga tsakaninku ba." "Hakane,insha Allahu zanyi
aiki da shawararka." Nan muka hau wata hirar,na
sanar dashi kyautar mota da Abba yayimin,shima
ya tayani murna,yace mami ma tace a gaisheni.
Na amsa da godiya,hakika Badamasi amini ne na
gari,fatana Allah Ya bar zumuncinmu domin kuwa
daddy har dubu dari ya bani a matsayin
gudunmuwar biki,mami ma dubu hamsin. Abba
shima saida ya buga ya yiwa Daddy godiya bayan
na je masa da labarin domin har gidan sukayi
kirana. Babu abunda zance da zumuncin mu ni
da
Badamasi sai Allah Yasa yafi haka. Bamu rabu ba
saibayan azhar,nima barin shagon nayi hannun
tasi'u nayi gida wajen sahibar tawa. Bacci takeyi
tayi rigingine remote yana ajiye
saman kirjinta. Ina murmushin ganin kyakkyawar
fuskar matar tawa,na kai hannu saman gashinta
wanda dankwalin ya zame na soma shafar
gashinta a hankali,ta qara muskutawa tana
murmushi da alama dai na risketa tana wani
mafarkin mai dadi,fuskarta ta burgeni,na
sumbaci
kuncinta. Sai gashi tayi firgigit ta mike
zaune,ganina yasa ta soma qoqarin janyo
dankwalinta. Nayi 'yar dariya na dauka na zauna
kusa da ita ina mai qoqarin dora mata."Amaryata
kin sha qamshi,bacci ko?" Ta sunkuyar da kan,a
sanyaye tace"Barshi zan daura." Na sakar mata
ina murmushi,ta zame a hankali tace"Ina yini."
Na
zuba mata ido kafin na sauke ajiyar zuciya"Lafiya
lau Zahra,ya yininki na barki ke daya ko?
Kodayake kina tare da yayyunki da iyaye." Ta
mike tsaye tana murmushi,na janyo hannunta ta
zauna kan kujerar"Kinyi shiru?" Ta dan kauda
kanta gefe"Sun wuce tun dazu." "Ok." Na kai
dubana kan tebur,kulolin abinci na gani a jere.
Na
dubeta ina murmushi"Kinyi girki kenan?" Ta
gyada kai. Wanka na soma shiga,kafin na fito
Zahra ta daukomin qananun kaya riga da jeans
farare tas saidai babu ita babu dalilinta,na daga
rigar ina mai shaqar qamshinta a sannu na
lumshe ido ina mai sauke ajiyar zuciya
sassanya,ZAHRA! Ashe dai so yakan shiga zuciya
farat daya?! Nidai duk wanda zaiyi musu kan
hakan toh wallahi a yanzu yanda nake cike da
begen Zahra zan iya ja da koma wane. Sai gani
na fada kan gadon ina mai rungume rigar kamar
na rungumi Zahra,tunanin kada ta riskeni hakan
yasa na mike tsaye da sauri na soma zura riga.
Nan dai kujerar na tadda ta zaune,tana ganina ta
mike,na lura da yanda ta zubamin ido,kafin
kuma
tayi azamar daukesu daga kaina,cikin sanyin
muryarta tace"Yaya ga abinci nan." "Ok,muje
mana." Nayi gaba tana mai bina da saurinta
kuma ta dan sha gabana ta janyomin kujera,na
bita da kallo ina mai zama"Nagode." Na furta
gareta,ta soma zubamin,na zuba mata ido ina
dubanta,kanwata ta hadu ashe? Wani irin
kaunarta nake qara ji,yanzu kuwa da wuya a
samu macen da zata bi miji irin haka musamman
ma idan taga gida daya kuka taso tasanka tasan
dariyarka nan da nan raini ke shiga,saidai kuma
zan yabi Zahra tun a baya ma bata da rashin
kunya. Ban ankara ta turomin plate shaqe da
abinci ba saida naji tana kiran sunana"Yaya
Ahmed,Yaya Ahmed." Ba shiri na maido
hankalina
gareta,saidai kuma kunyarta ne yayi min dirar
mikiya. Itama sai ta dauke kanta,"Ga abincin." Na
girgiza kai cikin rashin fahimta na dubeta"Ban
gane ba? Duk wannan ni kadai? Me kika ci?" Tayi
murmushi mai bayyana haqora"Naci abinci tare
dasu anti." Na dan daure fuska"Nafiso mu dunga
cin abinci tare,saidai idan ban sami isowa da wuri
ba kina iya ci don kar ki wahalar min da kanki
kinji?" Ta gyada kai"Toh." Nace"Zauna toh
kiyimun hira,ni ban amince kinci abinci sosai ba
ma,kodayake ke din baki fiye cin abinci ba saidai
ni bazan dauki hakan ba,maza zauna."
***
Saida muka qare cika cikinmu sannan na ja
matata muka zube nan qasan carpet. Na maida
dubana ga tv,tashar zee aflam ce suke haska
wani film wai shi Mujhe Dosti Karoge. Film din ya
soma daukar hankalinmu,a sannu nake nazarin
yanda tsarin soyayyar jarumar film din da
jarumin
yake tafiya. Jikina yayi sanyi a farko farkon,yanda
jarumar ke matukar kaunar jarumin saidai shi
sam hankalinsa ya karkata ne ga 'yar uwa kuma
aminiyarta duk a rashin sani,wane irin ciwo Zahra
ta ji akan irin hakan? Wane irin yanayi ta tsinci
kanta? Ga mamakina ina kai dubana gareta
hawaye na tarar na tsiyaya kan kuncinta. Na juyo
gaba daya ina mai tallafo fuskarta,"Zahra lafiya?
Meya faru don Allah?" Da sauri na soma share
hawayenta,ni kaina zuciyar tawa babu dadi. Na
saki fuskarta,ta duqar da kanta don tserewa
kwayar idanuna wadanda suke binta da kallo,a
sanyaye na kamo hannuwanta duka
biyun"Zahra."
Ta qara dago kanta ta dubeni,na bita da kallon
nan nawa mai tsada"Me ya sanyaki kuka please?
Kada ki boyemin,a yanzun baki da wanda ya fini.
Ni din nine mai share hawayenki kinji ko?" Ta
runtse ido hakan ne ya bawa hawayen dake
maqale damar zubowa,ban gaji ba na qara sanya
hannu na dauke mata dasu. Ta sunkuyar da
kanta na saki fuskarta na janyo remote na kashe
qarar TV gaba daya. "Ba wani abune ya sanyani
kuka ba illa film din nan." Na lumshe ido
kadan,nasan damuwarta,amma ina son qara
tabbatarwa"Meyasa film din ya saki kuka Zahra?"
Ta girgiza kai,saidai kuma tayi shiru,na riko
hannayenta ina murzawa"Look zahra,yanzu ni
dake mun zama daya,sanar dani duk abunda ke
ranki bani so ki boyemin komai,fadamin me film
din ke tuno maki don nasan akwai dalili." Ta
gyada kai a hankali tace"Na tuna ne da baya
sa'adda nake fama da ciwon sonka amma kai din
bama kasan inayi ba." Tausayinta ya
mamayeni,na janyota zuwa kirjina ta kwanta
lamo na rufe ta da hannuwana,a hankali nake
yawo da hannuna a gadon bayanta."Zahra."
Murya na rawa ta amsa min"Na'am."
"Fadamin,tun lokacin da kika soma kaunata,bani
labari kinji?" Ina jin yanda take faman ajiyar
zuciya,na qara riketa gam,saidai ta soma qoqarin
zamewa,hakan yasa na saketa,ta matsa gefe ta
jingina da kujera,hakan yasa nima na matso sosai
ina fuskantarta,ta soma da cewa"Na soma sonka
tun bansan ma'anar kalmar ba,bazan iya ce
maka ga ainahin lokacin ba saidai nasan mugun
tausayin da nake a gareka ne ya janyo so da
kauna." Nayi shiru ina mai sauraronta,ta dan yi
shiru kadan tana wasa da zoben hannunta,kafin
ta cigaba da cewa "Yaya Ahmed ban gane na
kamu da sonka ba sai
sa'adda muna SS1. A lokacin ne na fahimci lallai
na kamu da sonka,har ya zamana ko makaranta
naje burina na dawo na tadda yaya ahmed a
gida,naga fuskarsa na saurari muryarsa,yayimin
dariyar nan tasa. Hakanan ina matukar jin dadin
na ganka zaune kana koyar dani karatu wannan
yana bani dama sosai wurin qare maka kallo ina
ayyanowa yanda zan kasance duk ranar da
yayana ya furtamin kalmar so. Domin zuciyata
bata taba kawomin baka sona ba,yanda kake kula
dani kake kyautatamin yasa nake ganin kai din
ma kana kaunata." Ta yi shiru kadan tana mai
sakin ajiyar zuciya,ni din ma har lokacin kallonta
nake bana ko kifta idona,ta cigaba"Saidai bayan
shekara daya da soma hankalta da irin kaunar da
nake maka,Hafsa ta sameni da batun ai kun
hadu
da ita a Facebook. Ban kawo komai ba,don a
zatona yanda nake yawan yiwa Hafsat hirarka ya
ci ace ta fahimci cewa ina kaunarka,ashe ba haka
bane." Hawayen Zahra suka qaru,ina share mata
da hannu,ta lumshe dara daran idanunwanta
sannan ta bude su tana murmushi wanda nasan
na qarfin hali ne"Allah Sarki,ni ce har da
qarfafawa Hafsat gwuiwa,na qara bude mata
halayenka,na sanar da ita irin mutuncinka da
nake gani,da kuma kyawawan dabi'unka na nuna
mata zata iya cigaba da kula ka kana da mutunci
sosai sannan ka iya zama da kowane mutum.
Haka abubuwan suka cigaba,saidai kuma rana
daya na gane cewa soyayyace kukeyi da Hafsa.
Hankalina yayi mugun tashi,na rasa me ke mini
dadi a rayuwata,shikenan ni Zahra nayi asara. Na
rame na daina cin abinci sosai,kodayaushe ina
maqale da hotonka ina duba. A lokacin ne kuma
anty ta matsamin da tambayar abunda ke
damuna,ganin yanda take kwantar dakai tana
nunamin cewa zata yimin qoqari wajen samun ko
ma waye,koda ta wace hanya ce,saboda son daya
rufemin ido naka,yasa na bude baki na sanar da
ita komai a tsammanina zata taimaka din,saidai
ban qarasa ba ta daukemin fuska da mari ta hau
zagina,tana mai min Allah Ya isa muddin na bari
maganar nan ta fita." Ta dakata saboda kukan
da yaci qarfinta,ni kaina a lokacin hawayen ke
zubomin,ta shaqi numfashi kamar mai mura ta
cigaba da cewa"Babu baqar wuyar da ban sha
ba,anty ta bar kulani,ya zamana ko wane aiki ni
take sanyawa. Salihu su ne ma suke dan
tausayamin,abinci kuwa na ci ko kada na ci bai
damunta tace in har akanka nake ciwo ta
gwammace ma na mutu kada na rayu da dai
wataran maganar nan ta fito a cewarta wannan
abun kunya ne a gareta dole ta dauki mataki.
Hakan yasa babu bata lokaci ta turo Yaya
Faisal,ya shigo rayuwata. Ni dinma bayan biyayya
da zanyi gareta sai kuma don nayi kokarin ganin
na yakice ka a raina ne ko na samu sanyi. Har
dai aka zo kan sanya ranar ka da Hafsa,da sanya
ranar bikinku,haka nayita wahala,a daddafe har
muka kusa candy,da taimakon Allah na zane
jarabawar nan. A lokacin kuma na rage shiga
harkar Hafsa saboda kishin da nake yi da ita,har
Allah Allah nake na bar makarantar kada mu
hadu da ita." Anan ta dakata ta sauke kanta tana
cigaba da zubar hawaye.
. So, kauna, shauki,duk babu wanda bana ji akan
Zahra,cikin zafin nama na matso da fuskata har
muna jin hucin numfashin juna,ban saurari komai
ba na shiga aika mata saqonni masu zafi,can
kuma na janye na zauna sosai ina mai jingine
qeyata da kujera,na juyo a kasalance,na zubawa
Zahra idanuna wadanda abubuwa da yawa suke
yawo a ciki,tuni ta sanya kanta tsakankanin
cinyoyinta,na girgiza kaina kadan"Zahra
dago,magana fa muke,sanar dani ya kika ji bayan
hukuncin dasu Abba suka yanke gami da
auranmu?" Shiru shiru bata dago ba,nace"Kiyi
magana ko kuma nayi maki abunda bakya so."
Da saurinta kuma ta dago kanta saidai bata bari
mun hada ido ba tace"Kamar yanda na
fadamaka,nayi farin ciki banyi ba. Farin cikina
kuwa na murnar Allah Ya cikamin burina ne
wanda na riga na fidda rai da cikarsa,don a
daren
kwana nayi kan darduma ina godiya ga
Allah,rashin farin cikina bai wuce tunanin irin
karbar da zaka yiwa lamarin ba,don a iya sanina
bana gabanka,ko kadan baka so da
kaunata,Hafsa ce a gabanka. Ka makance a kan
sonta,ban shiga tashin hankali na sosai ba sai da
ka soma rashin lafiya duk dai akan Hafsa,nasan
lallai yaya ahmed ya amsawa iyayenmu ba don
har ransa hakane ba. Hakan yasa daga baya
komai yayimin zafi,anti ta dage tana zugani kan
cewa idan ka aureni wulakantani zakayi da
sauransu. Na gaji na sami Abba na sanar masa
ina mai kuka da roqonsa idan har bada son ranka
ba a janye,hakan ne yasa Abba kiranmu da
sassafen nan har yayi mana nasiha." Ta
dakata,na qara jefo mata wata tambayar"Ya
kukayi da Hafsa a lokacin data kira ta wayana
tana nemanki?" Tayi murmushi wanda na lura ya
bambanta da wancan na yaqen datayi,dimple
dinta ya fito sosai,tace"Magana ce mukayi ta
fahimta da ita. Tayimin qorafin rashin zuwa
bikinta da banyi ba alhalin ta aiko aka kawo min
iv? Na bata haquri saidai na tsinci kaina da
rashin sanar da ita batun aurenmu saboda gudun
zargi sannan banason ranta ya sosu. A haka
muka rabu da ita saidai bana tunanin har yanzun
ta san da batun aurenmu duk da cewa dai bani
da
tabbas." Na gyada kaina ina sauke ajiyar
zuciya,na mike zaune sosai ina fuskantar ta,na
janyo hannunta ina kokarin juyo da ita"Juyo sosai
ki dubeni Zahra,zan fadamaki wata magana
fatana ki yarda da abunda zance babu qarya
ciki,bana zuwar maki da batun wasa tun a baya
ballantana kuma a yanzun,dafatan zaki
saurareni?" Muka dubi juna ta gyada kanta a
sanyaye. "Zahra naso Hafsa,so mai yawa sannan
naji
ciwon rabuwa da ita bazan boye maki ba. Ko
bayan rabuwarmu ban taba zaton zan iya kallon
wata 'ya mace da sunan so ba,saidai kasancewar
bawa bashi keda iko da zuciyarsa ba,hakan yasa
rana daya na tsinci kaina dumu dumu cikin kogin
sonki." A razane ta qara bude ido tana
dubana,hakan yasa na qara kafeta da nawa
idanun ina mai qara jaddada mata da yare na
daban,ta sunkuyar da kanta,nayi murmushi
kadan"Bana so kiyi mamaki kanwata,wallahi ni
Ahmed a yanzu babu wata diya mace a gabana
idan bake din ba,wallahi Zahra ina sonki,na soma
sonki tun sa'adda aka daura aurena da ke.
Nasani kin jima kina fama da ciwon sona,kwarai
zanyi kokari na warkar maki da wannan ciwon ta
hanyar samar maki nutsuwa,baki kulawa ta
musamman. Zahra fatana kada ki zargeni da
komai,nidai ki amince ki yarda dani a yanzu ina
sonki ina kaunarki kinji?" Ta qara dago kanta
tana mai jifana da kallo,saida na dauke numfashi
na lokaci kadan domin kwarai bansan Zahra da
wannan kallon ba. Kallo ne mai tattare da
abubuwa da yawa. Na qara murza hannuwanta,a
sanyaye nace"Kin amince da hakan?" Idanunta
suka cika da kwallah,ta sakarmin murmushi tana
mai gyada kanta"Na aminta dakai." Zuciyata tayi
sanyi,na maida mata martanin murmushinta. A
lokaci guda kuma hankalina ya koma kan film din
da muke kallo,jaruma da jarumin sunyi nasarar
auren junansu,na maida dubana ga
Zahra"Kanwata bayan wuya sai dadi,dubi fuskar
pooja(Rani Mukherji wacce ta fito a matsayin
pooja)ta samu abunda take so,tana jin dadi,sai ki
bar zubar hawaye kema ai dama bayan wuya sai
dadi ko?" Tayi dariya tana rufe fuskarta da
tafukan hannunta. Haka muka yini tare da
Zahra,ban qara fita ko'ina ba saidai dole bayan
magriba na bar gidan don amsa kiran Anti
Aisha.****************Zaharaddeen  Shomar

Whatsapp   08168575100


Amadu 2 part 9
Posted by ANaM Dorayi on 07:06 PM, 26-Jun-15
Under: Amadu
Na Rufaida Umar Ibrahim
Na sameta tare da babbar 'yar kawu na
brigade,yaya salma. Ta maido da hankalinta
gareni"Ahmed na kira ba don komai ba sai don
na
qara jaddada maka batun Zahra. Don Allah
Ahmed kada ka bamu kunya,kaga dai da yanda
akayi auren nan naku? Kayi kokarin rike 'yar
nan
da amana,kada ka biyewa mahaifiyarta. Kuma
na
tabbata Jummai bata bar maganar nan ba
nasan
tana nan tana qoqarin daukar mataki...." Na
katseta"Kwarai ma kuwa anti,don ko dazun da
safe zuwana gidan saida ta tsareni akan sai na
saki Zahra." Anti Aisha da yaya salma suka
sanya salati. Ta yarfa hannu tana duban yaya
salma"Kinji irinta ba? Ai dama ni nasan dakyar
idan jummai zata yarda da qaddara,ashe dai
tana
nan kan bakanta." Yaya salma ta tabe baki"Ni
wallahi matan abbanka suna bani mamaki,gwara
gwara za'a ce salame ta tadda mahaifiyarka,toh
jummai fa? Inace labarinta kadai taji,toh akan
me
suke maka wannan qiyayya ta ba gaira ba
dalili."
Nayi murmushi"Ai inaga yanzu inna ta sauko."
Anti Aisha tace"Kada ka soma yarda da ita
dai,bita sannu sannu." Na gyada kaina"Toh anti."
Suka cigaba da bani shawarwari daga qarshe
muka dan taba hira. Sai bayan isha'i na samu
damar komawa gidan.********
Ta gama haduwa cikin riga da skirt na material
baqi mai adon fari. Zahra gwanar iya
kwalliya,fuskar nan kamar matso kyanta ake
qara
yi,tana murmushi ta matsa gefe,na qaraso sosai
cikin falon hankalina yana gareta,ta maida qofar
ta rufe,tana juyowa na hade ta da jikina gam na
matse. Sai gamu muna numfarfashi,murya na
rawa nace"Bebina." Shiru bata amsa ba,na dan
dagota ina dubanta"Bebina." Ta quramin
ido,kawai a hankali kuma lebbanta suka motsa
kadan,nayi murmushi ina mai riko fuskarta da
tafin hannuna"Sunanki kenan daga yanzu,ya
maki
dadi ko?" Ta saukar da idonta tana
murmushi,na
ja qaramin tsaki kadan sannan nayi dariya ina
mai jan hannunta zuwa kujera"Kinga fa ni
banason wannan kunyar wallahi,kodayake ba
laifinki bane nawa ne amma yau zan cire maki
ita." Na qarashe bayan na zauna kan kujera ina
mai janyota jikina,shiru babu alamun
magana."Kin iya kwalliya bebina wallahi." Ta
soma qoqarin zamewa,hakan yasa na saketa,ta
zauna kusa dani tana mai kauda fuskarta
gefe"Ai
ban kai ka ba." Na saki baki ina duban
bakinta,anya kuwa daga bakinta maganar ta
fito?
Ko dayake babu mamaki,ba abunda so bai
sanyawa. Sai kuma ta rufe fuskarta,alamun
kunya,nayi dariya. Hankalina yakai ga tebur,an
jera kuloli,na dubeta"Me aka tanadar min?" Tayi
far da ido"Cima mai dadi." Na gyada kai,"Toh
muje nayi wanka tukunna." Na ja hannunta
muka
nufi daki,ina tsaya ina rage kayan jikina,ta fada
bandaki ta hadamin ruwan wanka. Koda ta fito
bata kalli inda nake ba kanta na qasa ta nufi
hanyar fita. Cikin zafin nama na janyota,"Ina
zuwa?" Ai zuwa zakiyi ki tayani ko?" Ta
marairaice"Kayi hakuri yaya ahmed don Allah."
Nayi dariya"Matsoraciya,na haqura amma gobe
dole ki tayani." Ta gimtse dariyarta sannan ta
gyada kanta. Nayi gaba ina dariya.
Har qarfe goma
da rabi muna zaune falo muna kallo,hankalina
gaba daya ya tafi kan labaran duniya,Zahra tuni
ta soma gyangyadi. Sai jin kanta nayi bisa
kafadata,na waigo,tuni tayi nisa. A hankali na
soma kiran sunanta,shiru na shafi fuskar,ta
mike
zaune,tana amsawa har launin idanunta sun
sauya,bacci ne fal a ciki."Tashi mu tafi." Ta mike
tana dogon hamma,dakinta ta shige,na kashe
kayan kallo da fitilu. Dakin Zahra na nufa kai
tsaye,turus nayi a bakin qofa a yayinda idanuna
suka ci karo da kyakkyawan surar matar tawa
tana shirin zura rigar bacci. Sam bata lura dani
ba har ta qarasa zurawa. Riga pink mai hawa
biyu,doguwa saidai mai tsantsi ce. Sai a lokacin
muka hada ido,kunya ta sanyata sauke kanta
tana mai janyo hular data ciro ta rufa gashinta.
Nidai kamar an jona min igiyar wuta haka na ji
ni.
Duk tsikar jikina ya tashi,babu abunda nake
buqata idan ba Zahra ba. Na qara kallonta,har
lokacin tana tsaye a inda take,na juya kamar zan
tafi saidai ina babu ta yanda za'ayi na iya
haqura
da abar sona alhalin tana matsayin halal
awajena. Na juya na rufe qofa sannan na nufi
Zahra.
.
***
Komai ya tsaya cak,salati kawai nakeyi cikin
raina. Duk na hada gumi duk da wadattacen
iskar
da
fankar dakin ke bayarwa. Na dubi Zahra idonta
a
rufe ruf,na lura ta gama tsorata da abunda
nake
shirin aikatawa. Saidai ba anan gizo ke saqar ba.
Na
mike jiki a sanyaye na dauki doguwar jallabiyata
dake gefe na zura,sai anan Zahra ta bude ido
tana
dubana cike da mamaki. Banason cigaba da
kallonta,da sauri da sauri na bar dakin na koma
nawa. Zama nayi kan gado na dafe kaina da
hannu
biyu,"Ya salam! Ya akayi na kasa maida Zahra
cikakkiyar mace? Ya akayi na kasa aiwatar da
komai akan Zahra. Wannan masifa dame tayi
kama,idanuna
suka kada,wasu zafafan kwallah suka zubo kan
kumatuna,nasan yanzu Zahra tana can cikin
damuwa
saidai ni din na fita damuwa. Toh nidai a iya
sanina
lafiya kalau,wannan wane irin lamari ne haka?
Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! A daren banyi
bacci ba,kwana nayi ina addu'a sai bayan sallar
asuba ne
bacci mai qarfi ya sureni nan kan darduma.
Cikin
baccin naji ana buga qafata,na bude jajayen
idanuna,na sauke akanta. Ga mamakina
murmushi ta
sakar min saidai daga gani baije ko'ina ba,can
qasan
zuciyarta damuwa ce. Sai gaba daya naji
nauyinta,ta ci adonta tsaf cikin kananun kaya
riga da siket,na
mike zaune ina mai kauda kallona daga gareta
duk
kunyarta nakeji,ai abun kunya ne namiji kamar
ni
na
kasa biyawa kaina da matata buqata."Ka tashi
yaya,kada ka makara,yanzu karfe tara da rabi
fa."
Na
dubeta sosai,yarinya mai hakuri ba qaramin
qoqarinta na gani ba wajen boye damuwarta
duk
da
nasan ba kowace mace ke da wannan haqurin
ba.
Nayi murmushi kadan"Ok,hadamin ruwa na fara
wanka." Ta mike cikin sauri tayi hanyar bandaki
na
bita da ido,mace har mace amma na kasa
aiwatar
da
komai akanta,ta gama haduwa ko ta'ina. Allah
Sarki ni Amadu,Allah Ka Yayemin wannan
matsala
da
bansan da zamanta ba." Kwallah suka cikamin
ido,ganin tana niyyar fitowa na mike na soma
rage
kayan jikina,muka hada ido ta sunkuyar da
kanta"Na hada." Na gyada kai ni dinma ban
qara
kallonta ba saboda wani abu dake taso min,ban
qara ce mata komai ba na shige bandaki.
.
.
Shiru sai qarar cokali ke tashi a
falon,kowannenm
u da irin tunaninsa nasan gaba tunaninmu bai
wuce
iri guda ba,duk akan daren jiya. Nasan ba don
ita
din
mai kunya bace tsab zata tambayeni abunda ya
faru.
Hakan yasa na ajiye kofin shayi ina
dubanta"Bebina."
Ta dago dara daran idanunta ta dubeni saidai
bata ce komai ba,na kauda fuska daga
gareta"Kiyi
hakuri,nasan jiya na bata maki rai ko? Wallahi
bansan meke damuna bane." Ta sunkuyar da
kanta
da sauri,na tabbata kunya na bata,kanta kawai
ta
iya
gyadawa bata ce komai ba. Zan qara magana ta
girgiza kanta"Don Allah yaya abar zancen ya
wuce." Na zuba mata ido kafin na mike ina
murmushi"Shikenan bebina an bari. Taso ki
rakani."
Ta mike nayi gaba ta bini a baya,ina gyara karin
hulata na dubeta,muka yiwa juna murmushi
sannan
na sumbaci goshinta"Zan wuce." "Allah Ya
kiyayemin
kai,Ya kawo kasuwa." Nayi dariya ina shafar
fuskarta"Amin bebina zanyi kewarki." Tayi
murmushinta mai burgewa"Nima haka." Ai sai ta
qara burgeni,kamar kada na tafi saidai zaman
nawa
ma bashi da wani amfani tunda babu abunda
zan
iya
aikataw,cigaba da zama a gidan azabtar da
zuciyata
ne kawai,ya zama dole na tashi tsaye na dage
da
addu'a kan lamarin nan. Na juya mata baya"Sai
na
dawo,ki kularmin da kanki." Ban qara sauraron
abunda zata ce ba nayi gaba na hau
mota
Misalin biyar na yamman muna zaune a benci
nan
qofar shagona,Badamasi ya iso ya faka
motarsa,bayan ya qaraso an gaisa muka koma
gefe
dashi. Yana murmushi yace"Ya dai mutumin?
Har
ka
chanja fa." Nayi dariya"Ko?" "Dagaske
wallahi,kayi
kyau Ahmed duk wanda ya ganka yasan ango
kake." Nayi murmushi mai ciwo na tunano
matsalar
dake damuna. Cikin bagarar da zancen
nace"Yasu mami? Yau fa nake tunanin shigowa
wallahi." Ya
harareni"Kamar gaske?" "Bazanyi maka
rantsuwa
kan qarya ba,ai ba wajen ka zan zo ba,iyayena
zan
gaida." Badamasi yayi murmushi"Ya dace
hakan,nima gobe ake sa ran kai lefe." Na bude
baki"Ah haba dai? Abu ya iso ashe?" Ya gyada
kai"Kwarai ma,ai nima nafison nayi na
huta,haba
nayita zama a gauro kenan?" Mukayi dariya.
.
.
"Gwara nima nayi auren naji yanda akeji." Nayi
murmushi,ya dubeni yana mai nazari na"Amma
fa
kamar kana boye wani abu,na ganka so cool."
Na
gyara tsayuwata"Bakomai,tunanin amaryata
kawai
nake." Badamasi yayi dariya"Shegen sama,kai ko
kunyata baka ji ba? Zahra ce fa?" Nayi dariya
ina
mai shafar sumata"Kai dai baka mance abu,toh
abunda ya faru ai ya riga ya faru ko?" Ya jinjina
kai"Gaskiyane,ai komai yayi farko zaiyi
karshe,kai
na hadu da Murja jiya a Shopwell." Na bude
baki"Ah haba dai?" "Wallahi kuwa,har da baby
boy
dinta,yana tafiya sosai idan ka ganshi kamar an
tsaga kara don kama,yaron kamar wani
balarabe."
Nayi dariya"Allah Sarki Murja." "Ai saida ta
tambayeka,nace kana nan kayi aure,ta rike
baki"Kai haba da gaske kake badamasi?"(Ya fadi
yana mai kwaikwayon muryarta.) Nace mata toh
haka za'a zauna ba cigaba? Ke yanzu ba gaki da
yaronki ba meye sunansa ma? tace sunansa
Jabir.
Tace"Kaifa Badamasi yanzu yaranka nawa?" Sai
ma
ta bani da riya wallahi,nace mata ban kai ga
auren
ba na dai kusa." Tace Allah Yayi maka zabi
nagari
toh." A haka muka rabu bayan nayiwa yaronta
siyayyar kayan kwalam." Nayi murmushi"Allah
Sarki rayuwa,ai duk wata diya mace darajarta da
mutuncinta ace tana da aure." Badamasi ya dan
tabe baki"Wallahi kuwa,amma ai su basu
ganewa
kodayake wani sa'in laifin yana ga iyayenmu,a
takurawa mace akan lallai sai tayi karatu ta
gama
kafin a aurar da ita,wata tana son yin auren
amma ina! Iyayenta sun hana,haka sai kaga sun
fada
wani hali daban." Na gyada kaina,wannan haka
yake,Allah Yasa mufi qarfin zuciyarmu."
Badamasi
cikin sanyin jiki yace"Amin dai Ahmed,wallahi
kada
kaso kaga 'yan matanmu da muke sheqa aya
dasu
a baya ba,duk babu wacce tayi aure cikinsu.
Idan
banda shaye shaye da yawon bin maza babu
abunda suka sanya gaba,sune yau an tafi
Abuja,jibi
wance tabi Alhaji wane qasa gaza. Mtsw." Ya ja
tsaki
yana girgiza kai cike da takaici"Wallahi Ahmed
sun
bani tausayi,ba'a fi kwana biyar ba na hadu da
wata Sakina Yusha'u itama duk 'yar club din da
muke zuwa shaqatawa ne tare dasu haidar a
baya,ita duk take sanar dani,akwai wata yasmin
cikinsu ita ta mutu ma sanadin ciwon hunhu da
tayi
fama dashi. Babu amfanin rayuwar
watsewa,wallahi mata da maza inda zasu gane
da
sun bar rayuwar watsewa. Har yau ina mai jin
takaicin cewa na taba kusantar wata diya mace
ta
hanyar haram." Yayi shiru,na dafa
kafadarsa"Haba
Badamasi,ai Shi Ubangiji Gafurur Rahim ne.
Abunda
ya faru ya riga ya wuce,na tabbata Allah zai
yafe
maka. Allah dai Ya shirya,zamani ne ya
chanja,saidai kawai fatan shiriyar Ubangiji." Ya
sauke ajiyar zuciya"Hakane."
Kamar da wasa har dai mukayi sati biyu da aure
amma ban iya na tabuka komai ga Zahra ba.
Hankalina ya tashi matuka sosai,babu irin
maganin
da ban nema ba,har asibiti naje suka ce lafiyata
lau
a iyakar bincikensu,daidai dana gargajiya na
nema
amma nan din ma shiru kakeji,duk wanda ya
ganni yasan ina tare da damuwa. Toh ita kanta
Zahra
nasan ta damu saidai kawai kasancewarta diya
mace mai alkunya bata nunamin ba,asalima ta
kanyi qoqarin kawar min da damuwata ta
hanyar
yi mini hirarraki masu dadi.**********
****************************"Kaga
Ahmed,please
ka sanar dani damuwarka,haba!
Duk ka bi ka rame kamar ba ango ba? Wai
menene
haka?" Nayi shiru bani da niyyar cewa komai,toh
idan nace zanyi magana me ma zance? Na dan
ja
qaramin tsaki"Kai ba wani abu fa,kwana biyun
ne
kaina ke yawan ciwo." Badamasi yayi wata iriyar
murmushi'Hum,Ahmed kenan,qarya bata kyau a
muhallin da ba nata ba,amma shikenan zan
barka
tunda na lura baka son sanar dani. Allah Ya
yaye
maka,dama na matsa ne saboda na sani,ko ba
komai zan maka addu'a,shikenan." Ya harde
hannuwansa a kirjinsa yana mai juye kansa
bangare guda,na sauke ajiyar zuciya a sanyaye
nace"Kayi hakuri aminina,wallahi kwana biyun
nan
ina cikin matsala babba ma kuwa." Hakan dana
fadi
ya sanyashi juyowa cikin rashin fahimta da
neman
qarin bayani yana dubana,na tareshi kafin ya
samu
damar jefo tambayarsa,"Wallahi Badamasi tun
aurena da Zahra na kasa aiwatar da komai
akanta
bansan a ina matsalar take ba,duk wani
kuzarina
sai na nemeshi na rasa I don't know why."
Badamasi yace"Innalillahi wa inna ilaihir
raaji'un!
Haba Ahmed,yanzu wannan babbar matsalar
kake
boyewa haka? Wannan ai ba abune da za'a
boyeshi ba,abu ne da zaka fadi a nemi
maganinsa
tun kan lamarin ya baci." Ya qarashe yana mai
rike
haba baki bude,nayi murmushin takaici"Ya
za'ayi
mutumina? Wallahi ni nauyin fadi ma nake...."
Ya
dakatar dani cike da fada"Nauyi fa kace? Haba
Ahmed,wannan ai kanka zaka kwara,da kuma
matarka,wallahi nayi mamaki,amma yanzun ma
bata baci ba ya kamata mu nemi magani,anya
kuwa ba basir bane Ahmed?" Na girgiza
kaina"Anya kuwa? Na sha magungunan gargajiya
kafin nakai ga nan ma saida naje asibiti bincike
tsaf
ya nuna lafiyata lau Badamasi,nidai lamarin
akwai
ban tsoro." Mamaki ne ya hana Badamasi cewa
uffan,saidai can kuma ya jinjina kai yana fidda
numfashi"Gaskiya lamarin nan addu'a yake
buqata
sosai Ahmed." Cikin sanyin jiki nace"Nima nayi
wannan tunanin wallahi.
Kwana biyu da yin wannan magana da
Badamasi,ya daukeni muka leqa har wajen wani
kawunsa kasancewarshi malami mai bada
taimako ta hanyar Allah bata kaucewa ba. Kawu
Mu'azzam,mun sameshi a gidansa dake gadon
kaya. Bayan mun gaisa ne,Badamasi ya sanar
dashi matsalata,malamin ya dubeni yana mai
nazarina kafin ya tambayeni yanda nakeji,nayi
masa bayanin komai. Ya jinjina kai"Allah Ya
sauwake,insha Allahu zan taimaka maka da
addu'a,kai dinma dai akwai addu'o'in da zan
baka na karya duk wani mugun abu dake
jikinka.
Sannan ka samu ganyen magarya guda 7,
danyu,
sai ka azasu kan dutse ka daddaqesu, sai ka
zubasu cikin ruwan wanka mai tsalki, sai ka
karanta Isti'azah da basmalah sannan: 1. Ayatul
Kursiyu 2. Aya ta 117 zuwa ta 122 cikin Suratul
A'raf 3. Aya ta 79 zuwa ta 82 cikin Suratu
Yunus.
4. Aya ta 65 zuwa ta 70 cikin Suratu Daha 5.
Suratul Kafirun 6. Suratul Tauheed 7. Suratul
Falaq 8. Suratul Nâs Idan ka gama karantasu a
ciki sai ka kamfata da hannunka kyasha sau
uku,
sauran kuma kayi wanka. Insha Allahu koma
menene zai bar jikinka,zaka samu lafiya." Na
dubi
kawu cike da girmamawa"Allah Ya saka da
alheri,amma zaifi na rubuta ko?" Ya gyada
kai"Gaskiyane,ya mikomin takarda da biro,yana
fadi ina kwafa har ya gama,sannan ya bani
wasu
addu'o'in. Mukayi sallama dashi bayan nayi nayi
ya karbi wani abun daga gareni ya qi,a cewarsa
ai ya daukeni tamkar Badamasi don haka naje
kawai Allah Ya bada lafiya." Sati daya da nayi
ina
yin aikin daya bani,cikin ikon Allah ni da kaina
nasan na samu sauki saboda chanjin dana ji a
jikina. Addu'o'in kuwa kodayaushe cikin yinsu
nake ba dare ba rana. Ranar dana yi kwana
takwas da soma maganin,a daren bayan na
dawo
gida na tadda Zahra ta gama haduwa cikin
kananun kaya riga da wando wadanda suka
kama
jikinta har ya zamana ana hangen kirjinta. Da
gudu ta taho ta rungumeni na qanqameta don a
yanzu tuni ta rage kunyarnan tawa,a
shagwabance ta dubeni"Kai yayana don Allah
dubi lokaci(ta fada tana mai min nuni da agogon
dake jikin bangon falon)sha daya da rabi fa
yanzu,nidai gaskiya bazan yarda da kaiwa daren
nan ba." Kallo kawai nake binta dashi,yanayin
da
nake qoqarin dannewa a duk lokacin da muke
tare
shi nake ji yana qara tasomin a yau,na yau
dinma
har yafi na kodayaushe,duk iya qoqarina na
dannewa kamar yanda na saba abun ya
gagara,nayi qarfin hali na yi gaba ina mai
murmushi bayan na riko hannunta,murya a
dashe
nace"Sorry bebina,yau din na tsaya wani lissafi
ne,sannan na biya gurin Abba don kai masa
wani
saqo." "Ok." Abunda tace kenan,koda na fito
wanka tuni ta ciro min kayana kamar yanda ta
saba saidai bata dakin,bayan na zura kayan
baccina na nufi falon. Koda muka qare ta shiga
don chanja kaya. Na wuce daki babu jimawa sai
gata ta shigo,na tsayar da idanuna ina
dubanta,tuni yanayina ya chanja,na lura da
yanda
ta rikice tayi qas da kanta. Koda ta kwanta nayi
niyyar shareta saidai a yau naci alwashin gwada
sa'ata ko Allah zai bani damar sanin
Zahra,hakan
yasa na mike zaune ina bubbuga
qafarta"Zahra."
Ta juyo,"Na'am." "Tashi muyi sallah kinji?" Tayi
shiru sai kuma tace"Bani da sallah ai." Kamar ta
bugamin guduma tsakar kaina,na ja dogon
tsaki,"Kina iya kwanciya." Daga haka na mike
tsam nabar dakin ina mai cike da bakin ciki.
A daren ban iya baccin kirki ba,ciwon mara ya
addabeni,dole saida na jiqa kanwa na kora.
Saidai
hakan baisa ya ragu ba,dole na mike na dora
alwala a bandakin dake falo na tada
iqama,dakyar
bacci barawo ya saceni daf da asubah. Toh
saidai
kasancewar baccin wahala ne kamar a kunnena
naji kiran sallar,na mike ina salati,alhamdulillah
komai ya lafa,na qara shiga bandakin falo na
dora
alwala har na nufi kofar daki domin tashinta sai
kuma na tuno cewar tana fashi,hakan yasa na
juya
na fice zuwa masallaci.********************
***********************Ban shigo gidan ba
saida
gari yayi sha,dakina wayam na taddashi babu
Zahra,jikina yayi sanyi sai kuma nadamar
abunda
nayi mata jiya ya dirar min,toh ya zanyi? Idan
har
zan zauna kusa da ita dole ne kallonta ya
sanyani
shiga wani yanayi gashi babu damar kusantarta.
Ko a bayan ma hakuri kawai nakeyi da
dauriya,toh ballantana kuma a yanzu da nakejin
yanayina yayi
daidai,ai abun ba'a cewa komai. Saidai banason
tunani ya darsu a zuciyar matar tawa,na juya na
nufi dakin nata,tana kwance ta tura kanta cikin
bargo kasancewa lokacin sanyi ne,ina jiyo
sheshshekarta,tausayinta ya mamayeni,na
watsar
da wancan batun,da sauri kuma na haye
gadon,jin
motsina yasa tayi dif,na soma kiciniyar janye
bargon don ganin fuskarta."Zahra." Na kira cikin
siga ta lallashi,"uhm." Abunda ta iya fadi
kenan,na
janye bargon saidai tuni ta rufe fuskarta da
tafukan
hannuwanta,na janyesu,hawayen suka kwaranyo
kan hancinta,na soma sharewa a
gigice"Subhanal
lah,bebina meya faru?" Ta dago idanunta ta
watsamin wani irin kallo,na gane dai fushi take
dani sannan ranta ya baci akan abunda nayi
jiya,sai
naji ma ban kyauta mata ba,na janyota ta
fisge,na
rikice"Don girman Allah bebina kiyi min aikin
gafara,ki tausayamin,a jiya nesanta kaina gareki
kadai ne zai sa na rage jin abunda nakeji,jiya
ban
iya baccin kirki ba,na kwallafawa raina abunda
ban
taba tsammanin bazan samu ba jiyan,idan da
ace
muna tare a shimfida daya zan iya aikata
abunda
zai kasance sabo ga Mahaliccina,dole ta sanya
na bar maki dakin wallahi ba wani abu
bane,kiyimin
uzuri domin Allah." Na lura tayi sanyi,hakan
yasa
na matsa na rungumota kanta bisa kirjina,a
sanyaye tace"Yayana kayi hakuri don Allah."
Zuciyata tayi sanyi,na sauke ajiyar zuciya
hannuna
daya na cikin gashinta"Ya wuce bebina,nima na
sanyaki kuka ko? I am so sorry." "It's ok."
Qarshe
dai muka koma bacci,har bansan lokacin data
tashi
ba,saidai digon ruwan da naji akan fuskata,na
juyo
a firgice,ta ja baya da sauri tana kyalkyale
dariya,tana sanye da gown 'yar kanti irin ta 'yan
matan zamanin nan,hannunta rike da kofi
qarami.
Sai dariya takeyi,na zuba mata ido,ta gama
kashemin jiki,ina dariya na mike daga gadon ina
shirin cafkota ta yi waje a guje na mara mata
baya.
Muka shiga zagaye a falon har nayi nasarar
cafketa"Wa na kama?" Tana dariya tace"Don
Allah
Yayana kayi hakuri." Ina dariya na amshi kofin
ruwan na ajiye kan tebur"A'a wayace ki
zubamin
ruwa? An gayamaki haka ake tashin maigida?" Ta
turo baki"Kayi hakuri don Allah Yayana bazan
qara
ba." "A'a sai kin zo kin tayani wanka." Ta zaro
ido"Kayi hakuri don Allah." Na bita da kallo
bayan
na saketa ina murmushi,cigaba da kallon nata
ma
wani tashin hankali ne,na juya ina daga mata
hannu"Tam shikenan."********************
****************Idanuwanta sukayi kwal kwal
kamar zatayi kuka,na shafi kumatunta"Toh my
baby,rigimar da aka saba ko? Yau dai ki shirya
bayan la'asar zanzo muje wani guri." Ta danyi
tsallen farin ciki"Dagaske yayana?" Nayi
dariya"Sosaima,ki shirya kawai sai munje zaki
gani." Tayi dariya itama"Toh shikenan,Allah Ya
dawomin dakai lafiya." "Amin bebina." Haka
muka
rabu bada son rai ba,na ja motar nayi gaba ina
dago mata hannu hakanan itama............
. Mun gama haduwa cikin shadda,iri daya saidai
bambancin dinki na maza da mata. Shaddar
lemon
green ce,kasancewarmu farare,sai muka hasku.
Na
zagaya na bude mata kofar mota ta shiga
sannan
na rufe na zagaya na shiga nima. Motar ta dauki
kamshi,ta dubeni cikin sigar rigima"Yayana nifa
baka sanar dani inda zaka kaini ba." Nayi
murmushi ina mai yin reverse da motar,"Idan
munje zaki gani." Ban tsaya ko'ina ba sai gidan
Bahijja. Na dubi Zahra wacce ta saki baki tana
kallon gidan domin dai bata taba zuwa gidan
'yar
uwartata ba,kamar yanda itama bahijjar bata zo
ba hakan yasa sam batasan gidan ba. Na rufe
mata
bakin da hannuna ina dariya"Me akayi toh?
Kedai
ki nutsu mu shiga." Jiki a sanyaye ta fito nima
na
bude na fito,ina dubanta a yayin data zagayo
itama
ni din take kallo tana mai washe baki sai kuma
ta
marairaice"Please gidan waye?" Nayi
murmushi"Ikon Allah,abunda gashinan zamu
shiga,ai saiki tsaya ki gani." Na ja hannunta
muka
shiga,da sallamarmu. Bahijja dake rike da plate
tana
niyyar shiga kicin ta juyo tana mamaki,Zahra ta
saki
ihu ta yarda jakarta,itama ta dire plate din
hannunta
tana dariya suka rungume juna farin ciki ya cika
su,ihunsa ne ya fito da Yarima da saurinsa,na
sunkuya na daukarwa Zahra jakarta,ya saki
ajiyar
zuciya yana dariya ya nufoni,"Wallahi sun
tsoratani
matan nan." Mukayi dariya muka cafke. Muna
kallonsu suna kus kus,sai kuma aka cafke,Bahija
na kyakyata dariya tace"Shegiya." Ina murmushi
nace"Toh kun fara ko? Gulmar wa ake? Ke kuma
ko ciki ba zaki shigar damu bane? Haka dama
kike
yiwa baqin naki?" Tayi dariya tana rike da
hannun
Zahra ta taho,"Haba dan uwana na kaina,ayi
hakuri,kuzo mu shiga." Bayan an gaggaisa kuma
hira ta barke,qarshe kuma Bahijja ta ja Zahra
zasuyi ciki,na dakatar da cewa"Ban fa yarda da
qulle kai a
dakin nan ba,bebina idan ta fadamaki ya shiga
ta
nan ya fice ta nan." Na qarashe ina mai
kwatance
da kunnuwana,mukayi dariya gaba daya,Bahijja
tace"Haba dai dan uwana,ai ba wani abun zamu
ce
ba,kaidai kawai uhum." Mukayi dariya,anan na
bar Zahra bamu koma gida ba sai wajen
takwas.***********************
*****************Har dai akayi kwanaki biyar
ina
cikin wani yanayi,ana shida na shigo a gajiya na
ci
karo da Zahra tana sallah a falo. Zuciyata tayi
fari
qal,hakan yasa na juya na fita,can bakin titi na
nufa,ban tsaya ko'ina ba sai wajen Ya'u mai
kaza.
Na sayi har ta dubu daya,na riko sai qamshi ke
tashi na nufi gidan.
.
Ina budewa ta mike tsaye tana duban qofar a
firgice,sai kuma ta dafe kirji tana mai sakin
ajiyar
zuciya da murmushi kan fuskarnan nata da ban
gajiya da kallo"Na tsorata fa wallahi,naga ka
shigo
sai kuma ka juya ka fice,na dauka ko ba lafiya
ba."
Nayi murmushi"Lafiya lau bebina,tsarabarki na
mance ban taho dashi ba,kin ganshi nan." Na
dan
daga ledar hannuna kadan,ta kalla sannan tayi
murmushi tana dubana da alamun tambaya.
Nayi
gaba ina mai ajiyewa kan tebur,dauko flask ki
sanya ciki kafin na fito." Ta amsa da"Toh." Na
tafi
ina waiwayenta,ni kadai nasan yanda nakeji.
Bayan fitowa ta ne na tadda ta zaune tana bin
karatun
alqur'ani da ake sanyowa a tashar Al-majd3. Na
zauna har suka kai qarshen Surar Kahfi,sannan
na
rage murya"Bebina kawomana abinci nan yau
anan zamu ci." Ta mike"Toh." Ta fara shiga kicin
ta
dauko ledar da ake shinfidawa ta malaleshi a
nan
gabana,kafin ta jera kulolin da ruwa da jug
dauke
da zobo. Muna ci ina kallonta,har dai saida ta
gaji ta
ajiye cokalinta tana dariya"Wai yayana lafiya?"
Nayi
murmushi idanuna har lokacin ban iya na
daukesu
daga gareta ba,na ja hancinta kadan"Kyau
kikayimin." Tayi 'dan kara tana mai rike
hancinta"Kai yayana da zafi fa." "Hum,ai kece
da
wani zance,mene idan na more kallonki
matsayinki
na masoyiya kuma sahiba agareni?" Ta sauke
kanta qasa tana murmushi,na dauki cinyar
kaza"Maza karbi ki ci." Ta shagwabe
fuskarta"Nidai
saidai ka bani." Yanda ta narke fuska yasa ta
qara rikitani,na janyota"Oya matso nan kusa
dani
toh."
Ta matso na shiga ciyar da ita,har saida na
tabbatar
ta qoshi,na taimaka mata muka kwashe
kayan,nan
falo na zauna yayin da tayi daki,na bita da kallo
ina
mai jin wani abu. Na zurawa TV ido saidai
bansan
me akeyi ba ban fahimtar komai,tunanina yana
gareta,na mike na kashe kayan kallon da
fitilu,daidai nan ta bude kofar dakinta wanda
nan
dinma ta kashe fitilarsa,hakan yasa ban iya na
hangi irin shigarta ba sai qamshin daya ratsa
hancini,"Yayana har zaka kwanta ke...." Ban bari
ta
kai qarshe ba na lalubota na janyo jikina. Tun
anan hankalina ya soma fita daga jikina,ta soma
shirin
kuka"Don Allah yayana ka hakuri." Na dago
fuskarta duk da duhun da ya mamaye
falon,cikin
wata murya nace"Sorry bebina." Daga haka na
dagata nayi daki,sai a lokacin na gigice da ganin
shigarta,cikin ikon Allah kuma sai batun sallah
ya
fadomin,na dubeta"Tashi kije ki dauro alwala."
"Toh." Ta mike ta soma shiga,bayan fitowarta
nima
na fada na dora alwalar. Munyi nafila raka'a
biyu,sannan na shiga jero mana addu'o'i kafin
na
dafa kanta nayi addu'a bisa sunna. Daren ranar
ban
iya na runtsa ba!.

Zaharaddeen shomar

Whatsapp 08168575100Amadu 2 part 10
Posted by ANaM Dorayi on 11:46 AM, 29-Jun-15
Under: Amadu
Aure rahma ne,kwarai na yarda da hakan. Da
asuba bayan mun idar da sallah,kallo kawai nake
bin Zahra dashi ina sakar mata murmushi,gaba
daya ita kuwa kanta na qasa bata son koda
kallon inda nake,fuskarnan a daure ita a dole
fushi takeyi dani. "Yau ko gaisuwar ba zan samu
ba?" A ciki ciki tace"Barka da asuba." Na amsa
ina murmushi,kafin na mike na dauketa har kan
gado na ajiye tana sussunne kanta. Na jawo ta
jikina"Da kin bar kunyar nan tawa haka
bebina,bazan iya rabo dake ba." Ta soma kukan
shagwaba"Nidai don Allah ka barni bacci nakeji."
Na tura hannuna daya cikin gashinta"Ba abunda
zan maki,baccin zamuyi." A satin dai babu inda
nake fita,tasi'u na bari yake kula da
shagon,iyakaci yazo da daddare muyi lissafi don
yanzu cikin hukuncin Allah komai na qara cigaba.
Soyayya mai tsafta muke gudanarwa,kwanana
shida ina maqale a gidan,badamasi yazo. Bayan
sun gaisa da Zahra cikin wasa yace"Amarya kin
boye angonki ko masallaci baya zuwa ko?" Tayi
dariya,"Kai yaya badamasi,har da zolaya?" Nayi
dariya"Rabu dashi bebina,sharri yake neman yi
mana." Badamasi yace"Ba wani nan,kai don Allah
yaushe rabona dakai?" Na harareshi cikin
wasa"Ko ba komai munyi waya ai." "Wayar da
yaya? Inace ni da kaina na nemeka?" Mukayi
dariya,lokacin Zahra ta bar falon,"Naji,ya isheni
hakanan,kai din ma wa yasan shariyar da zakayi
idan kayi naka auren? Gwara ni wayata a kunne
take kodayaushe." Muka qara darawa,Badamasi
ya shafi sumar kansa"Shege mutumin,wallahi ka
chanja,aure mai dadi." Nayi
murmushi"Atoh,zauna
dai garin kallon ruwa kwado yayi maka qafa."Yayi
murmushi,zai yi magana wayata tayi qara,na
duba sunan Abba ne. Na dubi Badamasi"Toh
fa,kwana biyu banje ga Abba ba saidai
waya,Allah
Yasa lafiya." Na daga ina mai sallama,bayan ya
amsa yake sanar dani cewa nazo yana nemana.
Saida muka ajiye na dubi Badamasi"Ai fita ya
kamani,Abba yana nemana." Badamasi ya
mike,nima na mara mishi baya"Allah Yasa lafiya
toh." "Amin dai." Yayi gaba yana cewa"Ka sameni
a waje." "Ok." Na sami Zahra zaune gefen gado
tana danne dannenta a waya,tana ganina ta dago
fuskarta dauke da murmushi,na sumbacin
lebbanta"Bebina zanje Abba yana nemana." Ta
rike hannuna da alamun firgici tattare da ita"Toh
ina fatan lafiya?" Na sanya daya hannuna na
dora
kan nata ina mai jinjina kaina"Kada ki
damu,khairan insha Allah." Ta mike tsaye,har
qofa tayimin rakiya,"Toh saina dawo ko?" Ta
langabe kanta"Allah Ya dawomin dakai lafiya
yayana." Na lakaci hancinta"Amin bebina,ki kula
dani." Na fada ina shafa cikinta cikin sigar
wasa,tayi baya tana dariya,sannan ta rufe fuska
da hannu"Kai yayana,nidai banda komai." Nayi
dariya"Idan na dawo zakiyi komai ma,sai anjima."
Na fice na barta nan tana dariya. Badamasi tuni
yana cikin mota,na qarasa ya ja qaramin
tsaki"Kaga dama kenan?" "Toh ya za'ayi? Mutum
mai iyali?" Mukayi dariya,ya jinjina kai"Zakayi
bayani? Ya hanyar nayi,zaka zo mu wuce tare
ne?" Na zagaya na shiga muka tafi.**********
Ganin su Abba da kawu muntari a tsaye a tsakar
gidan,gefe kuma inna ke rusar kuka,anty amarya
na daga bakin qofarta itama dai duk bala'inta
jikinta ya nuna alamun sanyi. Na qarasa sallamar
ma ban iya yinta qarara ba lebbana kawai ke
motsi. Na dubi Abba kafin na dubi Kawu
muntari,tun kan na kai ga tambayar abunda ya
shigemin duhu,Kawu muntari ya
katseni"Af,Ahmed
ka qaraso ashe?" Gaba daya hankalinsu ya dawo
gareni,Abba ya dafa kafadata"Kunyi waya da
yayanka a satin nan?" Na girgiza kaina a
sanyaye"A'a ko kusa." Inna ta qara daga
murya"Shikenan dai,maganar fiddausi ta
tabbata,sun kama mini 'da,ya zama dole a dauki
mataki,na shiga uku ni salamatu." Ta dora hannu
aka tana rusa ihu. Na qara rikicewa,"Wai meya
faru Abba?" Abba ya juya ga inna"Haba
salame,kamar ba musulma ba? Don Allah kiyi
shiru,abunda ba'a tabbatar ba? Idan ma hakan
ne ya zamuyi? Dole dai sai hakuri har Allah Ya
fito dashi." Nidai kaina ya qara qulluwa,Abba ya
juyo ya dubeni"Ahmed,yarinyar nan ce(fiddausi)ta
bugo take sanar damu cewa yayanka ya zane ita
amaryar tasa,hamidah,mahaifinta yasa an
tsareshi a police station."
.
.
"Subhanallah! Me ya kai yaya dukan mace?"
Kawu muntari yace"Abunda bamu tabbatar ba
kenan,yanzu dai dole aje can din domin tabbatar
da maganar,shi Alhaji Mahdin ma an kira
wayarsa
ya qi dagawa karshe ma kashe wayar yayi gaba
daya hakan yasa muke zaton akwai kamshin
gaskiya a cikin maganar fiddausi." Banji dadin
wannan maganar ba sam,kodayake dai ance
kwadayi mabudin wahala,anan dai muka shirya
dasu Abba cewa da safe zamuyi sammako muje
Lagos." Ban koma gidan ba saida na biya gurin
anti aisha,tana kwasar tuwo ta juyo ta
dubeni"Ikon Allah,wata sabon gani ahmed." Nayi
'yar dariya"Haba dai Antina,wannan watan na
koyaushe ne." Tayi dariyar itama"A'a
Ahmed,yaushe rabon dana sanyaka a ido? 'Yar
wayar ma tawa ta lalace ballantana nasan ko
kana bugowa ko bakayi." Na zauna kan tabarma
har lokacin dariya nake"Wayyo,shiyasa nayita
gwada lambarki bai shiga ashe bata aiki." Ta
harareni fuskar dauke da murmushi,sannan ta
juya tana cigaba da kwasar tuwo"Ahmed gaba
daya a sanyaye kake fa,akwai matsala ne?" Naja
qaramin tsaki ina shafa kaina"Wallahi wata
matsala ce ta daban ta kunno kai,yaya usman ne
wai surukinsa na can Lagos,ya sanya aka
kamashi akan ya doki 'yar sa." Anti aisha ta
tsaya cak ta bar kwasa,"Toh,innalillah! Shi kuma
abunda ya sameshi kenan? Wane karambanin ne
ya kaishi dukan 'yar mutane?" Na tabe baki
kadan"Tsautsayi ne inajin,dama ita fa yarinyar
nan ba wani mutuncin danginsa take gani
ba,yanzun wayasan meya hada su? Shima dai
kwadayinsa ne ya jaza masa." Anti aisha ta
girgiza kai"Allah Ya kyauta,dama kwadayi shi ke
kai mutum tashar wahala." Haka mukayita
tattauna maganar har daga karshe nayi mata
sallama. Zahra ta budemin qofar,na lura a firgice
take,ta bani hanya na shigo bata barni na furta
wani abu ba ta hau tambaya"Yayana lafiya
kuwa? Wani abu ya faru ne ka dade haka?" Na
sakar mata murmushi na ja hannun muka zauna
kan kujera"Lafiya lau,na biya gidan mamanki ne."
Nasan ta gane wacce nake nufi,ta dafa kirji tana
mai sakin ajiyar zuciya"Toh Alhamdulillah." Na
girgiza mata kai"Kada ki damu ba wani abun
tashin hankali bane,gobe ma Lagos muka nufa ni
da Abba." Ta zaro ido"Kamar yaya?" Na
riketa"Kada ki tashi hankalinki bebina,ba wani
abu bane kinji ko? Yayanki ne dai baiji dadi ba
kwana biyu shine zamu leqashi." Tayi rau rau da
ido,na tallafo fuskar nata"Kada ki damu,jikin nasa
da sauki." Ta jinjina kai a sanyaye
tace"Shikenan,Allah Ya qara masa lafiya,yanzun
gobe da safe zaku wuce?" Na gano tarin
damuwar dake kan fuskarta,nayi murmushi
kadan,ni kaina nasan zanyi kewarta"Insha
Allahu."*************************************
**Tana rike da jakata,bayan na shiga mota ta
bude mazaunin kusa dana direba ta sanyamin
ciki,gaba daya fuskarta ta nuna rashin jin
dadinta. Na riko habarta"Haba bebina,don Allah
ki
saki fuskarki,so kike na tafi hankalina a tashe?"
Ta girgiza kai sai kuma ta saki murmushi"A'a,sh
ikenan toh,Allah Ya kiyayemin kai,Ya kaiku
lafiya." Nayi 'yar dariya"Yauwa bebina ko kefa?
Amin,ki buga ki gaida Abba kinji ko?" Ta gyada
kai tana matsawa gefe,na tashi motar ina dago
mata hannu na bar layin cike da kewar matata.
Abba ma tuni ya shirya,ni kawai yake jira,ya
shiga motar bayan na maida jakunkunanmu
baya,ya dubeni"Mu biya can wajen gwaggo mu
dauki yaya(kawu muntari)." "Toh." Gadan gadan
muka kama hanyar Lagos. Tafiya ce mai
nisa,sallah da cin abinci kadai ke
tsaidamu,bamu muka isa ba sai qarfe dayan
dare. Gaba dayanmu a gajiye muke,saida muka
shigo gari sosai sannan na soma niyyar kiran
fiddausi,Abba ya dakatar dani,yace mu nemi
hotel
kawai. Hakan kuwa akayi,hotel muke nema,daki
biyu muka kama,abba da kawu waje daya,ni
kuma a daki daya. Dakyar na iya yin wanka,na bi
lafiyar gado gabobina kuwa banda ciwo babu
abunda sukeyi,na mike zaune na bude
jakata,kwalbar rub na dauko wanda bana rabo
dashi na shiga mulkawa qafar ina fadin"Ashe dai
tuki akwai wahala har haka? Haba,wannan tafiya
mai sanya ciwon jiki?" Na kai dubana ga wayata
data mutu,dakyar na iya mikewa dauko chaja na
jonata. Na zurawa wayar ido daga kwance burina
ya dan chaju na samu na kira Zahra don nasan
hankalinta ba'a kwance yake ba,saidai kuma
gajiyar dake tattare dani yasa bansan yanda
akayi bacci nannauye ya daukeni ba. Nidai ban
farka ba saida naji ana kwankwasa qofar dakin.
Na mike idanuna cike da bacci,na dubi gari,tuni
ya danyi haske kadan,subhanalla! Kada dai gari
ya waye banyi sallah ba? Na mike a hanzarce na
bude,Abba ne tuni ma yayi wanka ya sauya
kaya,yace"Kayi sallah kuwa?" Na girgiza kai"A'a."
"Subhanallah,ka hanzarta gabatarwa ya akayi ka
makara?". Ya juya ya tafi,nima nayi bandaki.
Karfe takwas da rabi tuni mun kammala komai
na
daga wanka da karin safe mun fito. Kai tsaye
Victoria Island muka nufa inda gidan yaya usman
yake,qerarren gida na gani na fada. Nayi
hon,maigadin wani inyamuri maimakon ya bude
sai ya taho domin yaga ko su waye,Abba ne ya
leko,nan ya shaida fuskarsa,ya dan rusuna ya
gaisheshi,Abba ya amsa,sannan ya wuce ya bude
mana. Bayan na faka,muka fito muka nufi ciki.
Anti fiddausi ce ta fito sanye da hijabi,idanunta
duk a kumbure tana ganinmu ta dan rusuna kai
ta bamu hanya,"Abba sannunku da
zuwa,bismillah." Muka shiga,yaronta dake ta
rarrafe wato imam ya tsaya yana dubanmu
kasancewar bai sanmu ba. Muka zauna,ta qaraso
cike da ladabi ta gaida su Abba,nima na gaidata.
Muryarta a sanyaye tace"Ai na dauka tun jiya
zaku zo da naji ance kun taho." Kawu ya jinjina
kai yana murmushi"Munso hakan,saidai
kasancewar dare yayi muka kama hotel anan
muka kwana." Ta gyada kai. Na ja imam ina
masa wasa,Abba ya dubeta"Ya ake ciki game da
yaron nan?" Idonta ya cicciko da kwallah murya
na rawa tace"Wallahi nima har yau ban samu
ganinshi ba Abba,cewa ma akayi kada na qara
wahalar da kaina da zuwa station din domin ba
zasu barni na ganshi ba umarni aka basu."
Hawaye suka zubo mata ta sanya gefen hijabinta
tana sharewa,muka jinjina maganarta. Kawu
yace"Ah'ah,toh wai meya jawo usmanu ya doki
ita hamidar?"
.
,
Muryarta na rawa tace"Nidai ina zaune a falo,sai
ga hamida ta sauko daga sama a fusace,tana
rataye da jaka ga qaramin gyale ta yafa,shima ya
biyota da sauri yana fadin"Baki isa ki fita daga
gidan nan ba hamida,na fadamaki banason
yawan yawace yawacen nan,ke baki da aiki sai
bin qawayenki ku fita? Qawayen bama musulmai
ba,a'a wasu can masu dangalallen siket,toh
wallahi ba zan dauka ba na gaji,ke ba'a koya
maki tarbiyya bane? Shi aure an fadamaki abun
wasa ne? Kodayaushe daga party sai zaki tafi
birthday na wancan 'yar kirista?" Hakan daya fadi
ya fusata hamidar,ta hau fada masa baqaqen
maganganu wai ai a qarqashin ubanta yake don
haka dole ne ya barta tayi yanda taso,kamar
yanda uban nata zai juyashi da ikonsa,haka itama
tana da ikon juyashi. Kuma bai isa ya hanata yin
yanda ya so ba.gama fadin hakan kenan ta juya
zata tafi bayan ta ja masa dogon tsaki,ya fisgota
ta dawo yace"Babu inda zakije,wannan gidana ne
da kudin albashina na gina shi,ke kuma ikona
ce,dole kibi umarnina ko an gaya maki kudi
hauka
ne? Don kawai kina 'yar ogana shikenan sai ki
watsamin kashi ban dauki mataki ba? Toh
billahillazi kika sake qafarki ta taka qofa sai na
nuna maki waye ni." Ta fusata ta hau masifa,wai
sai taga wanda ya isa ya hanata,hakan yasa ta
tafi a fusace zata fice,shi kuma ya zuciya ya
fisgota ya hau jibgarta duk iyakar kokarina don
na kwaceta na hana,har yana neman hadawa
dani ma,ganin yanda dukan yayi yawa yasa na
fita waje don neman agajin masu aiki,dakyar
muka kwaceta,shi kuma ya koma samansa a
matukar fusace. Dakyar muka dauketa muka
sanya a mota sai asibiti. Bamu fi minti ashirin
ba,sai gashi ya iso shima,nadama ce qarara akan
fuskarsa,sai ga Maman hamida itama ta iso a
gigice. Ta tambayemu ina hamidan,na sanar da
ita tana ciki,saidai kawai muka ga ta fito,ta harari
abban imam,ta dauki waya ta kira baban
hamida.
Bayan ta ajiye tacewa yaya ai ba jaka aka kawo
masa ba,wato shi har ya zama butulu,ashe ya
manta a qarqarshin ubanta yake aiki. Toh daga
nan kuma muna nan wajen,lokacin hamida an
wanke mata raunukan jikinta,yaya yaso ta tsaya
ta saurareshi amma bata bashi damar nan ba.
Haka har mahaifin hamida ya iso da 'yan
sanda,baiyi wata wata ba ya wankawa yaya mari
sannan ya umarcesu dasu tafi dashi. Ina roqonsa
yaya ma yana yi amma bai ko sauraremu
ba,haka
ina ji ina gani suka tafi da yaya,yana cewa na
koma gida bakomai." Daidai nan kukanta ya qara
qarfi sosai,tana girgiza kanta"Wallahi Abba yaya
bashi da laifi,don baka ga zagin da hamida ke
dura masa bane,kuma tun da can din ma wani
sa'in baya biye mata ne,wataran ma qawayen
nata zata gayyato su cika gidan da hayaniya,basu
suke barin gidan ba sai wajen goman dare. Bai
isa ya kwabeta ba,sai abunda take so
zatayi,hakanan yake bin ta." Tayi shiru saboda
kukan da yaci qarfinta,mukayi shiru mu
dinma,kowanne da abunda ke zuciyarsa. Nikam
na dan tausayawa yaya usman,saidai kuma nafi
tausayin anti fiddausi wacce bataji ba bata gani
ba an sanyata cikin damuwa,ai shi kam shine ya
janyowa kansa inda baiyi auren kudi ba duk
hakan da bai faru ba. Kawu ya numfasa"Innalil
lahi wa inna ilaihir raaji'un,Allah Ya kyauta." Abba
a fusace yace"Amin dai,wallahi tun farko ni dama
zuciyata batayi na'am da batun auren yaron nan
ba,tsabar naci irin na uwarsa da nasa yasa na
yarda. Nidai....." "Kaidai me Muhammad? Yanzu
koma menene ya riga ya wuce,kawai dai abunda
za'ayi mu je har gidan Alhaji Mahdin mu bashi
hakuri kawai,shi yafi."
.
.
Babu nisa sosai tsakanin gidan Alhaji Mahdi da
na yaya usman,duk unguwa daya ce,nan da nan
sai gamu mun iso. Qaton gaske ne,gaba daya sai
ma na raina gidan Yaya Usman akan na Alhaji
Mahdin,na sauke ajiyar zuciya ina mai godewa
Allah da irin namu muhallin,na soma hon,wani
ma'aikaci ya fito sanye da kaya irin na masu gadi
yana leqomu."Sannu,daga ina?" Yanda yayi
hausar kasan cewa ba bahaushe bane,nace"Alhaji
muke son gani." Ya dan saki fuska"Oh oga ya tafi
ofis,sai dare zai dawo." Mukayi shiru na dubi
Abba don jin me zasu ce,sai Abba yace"Ok,mun
gode." Ya dauki waya ya kirashi,har ta katse bai
dauka ba,sai ana biyun ne ya dauka,suna ta
magana da Abba,na lura yana magana ne a
sanyaye abban,can kuma yace toh shikenan Allah
Ya kaimu sai anjiman." Bayan ya ajiye kawu ya
tambayeshi"Ya kukayi ne?" Abba ya jinjina
kai"Gaskiya ya dauki zafi da yawa,farko cewa
yayi yana da ayyuka bazai samu ganinmu
ba,amma daga baya kuma yace mu hadu a gidan
nasa da misalin biyar na yamma." Na lura Abba a
fusace yake,ya soma 'yar fada"Duk yaron nan ne
ya janyowa mutane wallahi,dole ma ya tattara ya
bar garin nan,da girmana da mutuncina ya dunga
zubdamin." Abba dai fada yakeyi,muna bashi
hakuri,har muka isa gidan bai daina ba.Anti
Fiddausi ta tambayeni ko lafiya,kawu ya
tare"Bakomai lafiya lau kinji,kada ki damu,yanzu
zaki gane ofishin da mijin naki yake?" Ta gyada
kai"Zan gane kawu." Kawu ya dubi Abba"muje
ko?" Abba yace shi sam bazai je ga yaya usman
ba,yaso mu maidashi can hotel,amma anty
fiddausi ta roki da mu zauna nan tunda akwai
bangaren baqi sai mu zauna. Dakyar Abba ya
amince,muka barshi nan yayinda ta rakashi,ta
dawo muka wuce daga nan zamu biya hotel don
dauko kayanmu. A mota kowannenmu yayi
shiru,kafin kawu ya nisa"Oh Allah,wannan
lamari,Allah Ya shige mana gaba." Muka amsa da
amin. Unguwar Ikeja muka je,sergeant dake
wurin
yana ganin anty fiddausi ya daure fuska"You
again?" Ya fada yana dubanta,ta dubemu a
tsorace,na matsa ina mai gaisheshi,ya amsa a
dakile,na fadamasa wanda muka zo gani,yayi
shiru yana cigaba da rubuce rubucensa,hakan
yasa raina ya soma baci,mun kai minti biyar
baice mana qala ba,kafin ya dago kansa"Kuyi
hakuri,bazaku samu ganinsa ba,wannan umarnin
ogan mune yace kada a bar kowa ya ganshi."
"Haba officer,ka taimakemu don Allah." Mun fi
rabin awa muna magiya,har saida na hada da
sunna masa wani abun,sannan ya dubemu fuska
a sake"Shikenan,yanzu dai oga baya nan,zan
barku ku ganshi na lokaci kadan,amma sai kunyi
da sauri." Mukayi godiya,yace mu biyoshi,har
wani dan daki ya kaimu,sannan ya tafi sai gashi
sun dawo tare da yaya usman wanda gaba daya
fuskar tasa ta kumbura,ga raunuka dakyar yake
tafiya. Muka mike kowannenmu a razane.
Fiddausi kuwa
kuka ta sanya,usman ya qaraso ya sanya
hannunsa daya a kafadata daya ana
kawu,muryarsa dakyar take fita"Kawu,Ahmed
kune? Kawu kunga yanda azzaluman nan
sukayimin ko?" Sai ga hawaye na zuba daga
idonsa,ni kaina saida ya bani tausayi sosai,na
rungume yayana ina hawaye. Kawu cikin dakiya
yace"Kai kuwa Amadu kai me kwantar masa da
hankali amma ace kai ke tayashi kuka? Banson
shiririta,na dago ina dukar da kaina,bana son
qara
duban yaya usman. Duk da ba wani shiri da
shaquwa mukayi ba,amma haduwar jini yasa
yanayin dana ganshi ya bugeni har zuciyata. Tun
mafarin zancen banji tausayinsa irin na yanzu
dana ganshi cikin wannan yanayin ba. Kawu
yace"Usmanu kai kuma iftila'i daya fada kanka
kenan? Kayi hakuri usmanu,insha Allahu komai
yazo qarshe anjima zamu ga Alhajin. Kaji ko?"
Yaya usman ya dake yayi murmushi hawaye na
kwararo masa"Toh kawu,ina Abba?" Mukayi
shiru,kawu yace"Abbanka yana nan lafiya,tare
muke yana can gidan." "Kawu Abba bayason ya
ganni ko? Na bata masa rai? Don Allah ku bashi
hakuri,tsautsayi ne ya kaini bugun
hamida,yarinyar ce ta bata......." "Ku hanzarta fa
lokaci yana tafiya,kada oga ya zo." Maganar
sergeant ta katsemu,yaya usman ya karbi imam
a hannun anti fiddausi wacce ke sheshshekar
kuka na tausayawa mijinta. Ya danyi masa
wasa,kawu yace"Kayi hakuri usmanu,zamu
wuce,insha Allah bazaka wuce yau ba kaji?" Yayi
murmushi kadan"Kawu kenan,Alhaji yana da
tsauri bana zaton zai amince ya sauko da wuri. A
kwanakin nan ba qaramin darasin rayuwa na
dauka ba,nayi dana sanin biyewa son zuciya na
auri wacce tafi qarfina kawu. Na tabbata hakan
ne ya qonawa Abba rai,don Allah kawu ku nema
min gafararsa." Maganar sergeant ta qara
katsemu"Oya oya,kuyi sauri oga yana hanya fa."
Hakan yasa na sa hannu na karbi imam,"Toh
yaya usman zamu wuce,Allah Ya kubuto mana
dakai." Ya gyada kansa"Amin Alhajinmu." Nayi
murmushi kadan sanin ya fadi da niyyar wasa. Ya
matsa kusa da matarsa yana mata magana qasa
qasa,hakan yasa muka fice ni da kawu,can kuma
itama ta biyo bayanmu,mukayi godiya ga
sergeant Olaminde,sannan muka tafi zuciyarmu
cike da tausayin yaya usman. Hotel muka biya,na
biya kudi,muka kwaso kayanmu sai gida. Bayan
mun ci abinci na fito tsakar gidan na zaro
wayata,missedcalls na Zahra har goma sha
biyar,nayi salati. Tana raina saidai ban samu
sukunin kiranta bane. Na kira ai kuwa da saurinta
ta dauka"Hello yayana kana lafiya kuwa? Ya yaya
usman?" Na sauke ajiyar zuciya"Lafiya lau
bebina,kiyi hakuri please,ban samu na kiraki ba."
Cikin raunanniyar muryarta tace"Yayana ashe
akwai abunda zaka iya boyemin? Dama kama
yaya usman akayi shine baka sanar dani ba?"Sai
ta sanya kuka,na rikice"Ya salam! Me akayi
bebina? Me kikaji?" Ta rage sautin kukan nata"Ai
da baka sanar dani ba,abubakar yazo kuma shike
fadamin an kama yaya usman dalilin kenan da
kuka tafi." Na sauke ajiyar zuciya ina lumshe
ido"Kiyi hakuri bana son ki tashi hankalinki
ne,mun samu munga yaya usman,yana nan
lafiya
insha Allahu muna sa ran fitowarsa yau ko
gobe,please ki bar damun kanki,ko so kike nima
ki qaramin damuwa?" A sanyaye tace"A'a kayi
hakuri na daina kukan." "Yauwa bebina ko kefa?
Gayamin me kikeyi?" Na jiyo sautin
murmushinta"Bakomai,ina nan gidan shiru babu
dadi wallahi." Nayi dan jim ina mai tausaya
mata"Allah Sarki bebina,ko zakije gida?" Da sauri
tace"A'a zan iya zama har lokacin da zaka
dawo,ai nasan ba zaku wuce gobe ba ko
yayana?"
Nayi murmushi kamar tana gabana"Insha Allahu
bebina,kedai kiyi mana addu'a." "Toh
yayana,Allah Ya kubutar mana da yaya usman."
"Amin bebina." Daga nan kuma muka shiga
hirarmu ta soyayya sannan mukayi sallama cike
da kewar juna.*************************
***********Da misalin qarfe biyar kuwa muka
dunguma gidan Alhaji Mahdi. Wannan karon
maigadin gate din kawai ya wangale mana da
alama yasan da zuwanmu don harda dago mana
hannu. Wani dan dogon titi ne da ka shiga
gidan,haka muka isa har farfajiyar gidan. Bayan
mun sauka direban ya faka a can wata 'yar
rumfa
da ake fakin,wani dake tsaye ya dubemu"Kune
baqin da Alhaji yace zaiyi ko?" Nace"Eh mune."
"Ku biyoni." Muka bi bayansa,har wani
kayataccen falo wanda ya hada komai na jin
dadin rayuwa. Sanyi ke tashi ta ko'ina. Su Abba
suka zauna kan kujera,ni kuma na samu mazauni
kan carpet din dake shimfide a falon. Shiru zai
fito ba zai fito ba,can sai gashi ya bullo ta wata
qofa dake makure a dan lungu. Ya qaraso,Abba
ya mike sukayi musabaha,sannan ya bawa kawu
hannu. Fuskarsa a sake kamar ba wani abun na
tashin hankali yayi ba,ya zauna a kujerar dake
fuskantarmu,anan nima na gaisheshi ya amsa
yana dubana"Af,kaine Ahmed ince?" Nayi
murmushi"Kwarai nine." "Toh madallah." Sai
kuma Kawu ya numfasa zai soma magana.
.
.
"Nasan abunda ke tafe daku,bai wuce kan usman
ba ko?" Alhaji Mahdi ne ya katse kawu dake
shirin magana,sai lokacin kawu ya numfasa yana
mai jinjina kai"Gaskiyane wannan,munsan
usmanu bai kyauta maka ba,amma don Allah
muna roqon a yafe masa,insha Allahu za'a kiyaye
gaba." Alhaji Mahdi yayi wani irin murmushi
sannan ya girgiza kai"Ai ba sai an kai ga kiyaye
gaba ba,naji zan karbi rokonku,zan sanya a saki
danku,saidai akwai sharadi." Gaba daya muka
dubeshi,munason jin abunda zai ce,Abba
yace"Wane irin sharadi kuma Alhaji Mahdi? A
zatona mun zama daya yanzu? Kada ka manta
fa,ba ta sanadin usmanu muka san juna
ba,saidai
tun zamanin da muke zuwa makaranta na sanka
ka sanni,bai dace ace yara sun shiga tsakani ba.
Kwarai ni kaina naji haushi kan abunda yaron
nan
ya aikata wallahi,toh ya za'ayi? Yaro ne ka haifa
baka haifi halinsa ba." Alhaji Mahdi wanda har
lokacin murmushi yake kamar bashi da wata
damuwa yace"Haba Alhaji Muhammad,kada son
'danka ya rufe maka ido mana,nima fa nasan
abunda nake,ban mance da abubuwan daka
lissafo ba,inda na mance da 'danka bai zauna
qarqashina ba,usmanu yaro ne mai hazaqa a
fannin aiki. Yana da kokari matuka wajen
kularmin da dukiyata,hakan yasa nayi kwadayin
hada aurensa da 'yata hamidah saboda son da
take yi masa. Tun bayan auren yarinyar nan take
kawo min qorafe qorafen abubuwan da yake
mata,ina tausarta ina nuna mata wannan halin
zama ne,dole a dunga samun sabani ta dunga
hakuri,wani abun ma saidai na korata bana
yarda,sai gashi Allah ba azzalumin bawa ba,yayi
mata dukan kawo wuqa,sadda labarin ya riskeni
nayi matukar jin ciwo don da farko naso na
musa,saida mahaifiyarta ta tabbatar min gasu
nan ma a asibiti,a sanadin dukan da har saida ta
rasa cikin dake jikinta." Ba qaramin kaduwa
mukayi da jin jawabinsa na qarshe ba,kusan a
tare Abba da Kawu suka hada baki"Ciki?!" Alhaji
ya jinjina kai"Kwarai kuwa,ashe tana da juna
biyu,toh me yafi wannan ciwo?" Mukayi
shiru,kowanne yana jinjina maganar,tabbas yaya
usman bai kyauta ba. Alhaji Mahdi ya cigaba da
fadin"Kada ku damu,ba wani sharadine
tsatstsaura ba,don fitowar usmanu ba matsala
bane,waya kawai zanyi a sakeshi,saidai kuma
yana fitowa inason ya damka min takardar
'yata,ta bar zama gidansa." Abba zaiyi
magana,Alhaji Mahdi ya dakatar dashi yana 'yar
dariya"Kada ka damu Alhaji,hakan shi zaifi
alheri,ba wai nufina mun bar zumunci ba ko
kuma
usmanu ya bar aiki tare dani,a'a. Aiki daban
family issue daban,don haka muna tare bazamu
rabu ba,saidai dole ya bawa 'yata takardanta.
Idan har kun amince yanzu sai na buga a
sakeshi." Kawu a sanyaye yace"Toh amma
Alhaji....." Abba ya katseshi ta hanyar dafa
hannunsa,suka kalli juna,yayi masa alamar yayi
shiru,sannan ya fuskanci Alhaji Mahdi"Shikenan,
insha Allahu takardar Hamida zata iso gareka da
zarar ya fito." Alhaji Mahdi yayi murmushi"Madall
ah." Hannu yasa ya dauki wayarsa ya shiga
lalube,can kuma ya kafa a kunnensa"Hello,
inspector,you can now release that
boy,everything
is settled." Daga nan yayi masa godiya sukayi
sallama ya dubemu"Alhaji kada ku damu,danku
yau zai fito,kuna iya zuwa ku daukeshi,sai dai ayi
kokarin cika alqawari don Allah." Muka mike a
sanyaye bayan munyi godiya muka fito. A mota
ranmu gaba daya babu dadi,kwarai bamu ji
dadin
yanda Alhaji Mahdi yayi mana ba,saidai a wani
hangen bashi da laifi,Abba ya fusata"Nidai yaron
nan yaja min abun magana,banji dadin lamarin
nan ba,ai shikenan kansa ya yiwa. Kai saukeni
gida babu inda zanje." Kawu yace"Babu
dadi,amma dai muyi hakuri,sai ya kiyayi gaba.
Allah Ya kyauta." Gaba daya suka sauka na juya
domin komawa can police station dauko yaya
usman.

Zaharaddeen  shomar
Whatsapp 08168575100


Amadu 2 part 11
Posted by ANaM Dorayi on 12:12 PM, 29-Jun-15
Under: Amadu
Ko ringing uku batayi ba,ta dauka."Amincin Allah
da rahmarSa su tabbata agareka yayana." Na
gyara kwanciyata ina mai jin dadin muryarta har
tsakiyar kwakwalwata,na numfasa"Kema aminci
da rahmar Allah su tabbata agareki bebina,kin
wuni lafiya?" Na jiyo sautin murmushinta kafin ta
bani amsa murya a shagwabance"Alh
amdulillah,saidai fa nayi missing dinka." Nima
murmushin nayi"Baki kaina ba,kedai kawai ba'a
cewa komai." Ta katseni"Hakane,ya batun yaya
usman?" "Ya fito,yanzu haka ma likitansa ya
dubashi ya bashi magunguna,insha Allahu komai
yazo karshe mun gode Allah." Tace"Toh Allah Ya
kiyaye gaba,don Allah ka gaidashi." "Ok,fadamin
me kikeyi?" Tayi 'yar dariya"Ka ganni zaune kan
darduma na idar da shafa'i da wuturi,yanzu nake
shirin turo maka text mai dadi....." "Oh text kawai
ma? Hm,me nayi da baza'a kira aji muryar gaba
daya ba?" Na katseta. Muryarta kamar mai shirin
kuka tace"Toh ai kudin ne sunyi kadan,gashi bana
so na kira ya katse alhalin ban gaji da jin muryar
ba." Wani dadi ya ratsani jin kalaman da Zahra
ke furtamin,na qara muskutawa akan gadon
nace"Haba bebina,nawa ne dake?" Tayi
dariya"Dari da talatin ne a ciki." Mamaki ya
kamani"Kina nufin sunyi kadan ki kirani?" Ta qara
darawa"Eh wallahi,nidai haka nake gani,sai naji
kamar muna hira shegiyar na'urar nan zata
katsemu,sai nafi bakin ciki hakan yasa na
gwammace na tura maka saqo." Nayi dariya
sosai,wani abu na yawo a jikina har yana tada
min tsikar jiki,"I really love you bebina." "I love
you more." Na lumshe ido kadan ina shafa
sumata"Anya kuwa zaki fini?" Tace"Kwarai kuwa
yayana." Na girgiza kai tamkar tana
ganina"Gaskiya ban yarda ba,don bakisan yanda
nake ji bane." Nan fa musu ya kaure
tsakaninmu,ita tace tafi sona ni nace nafi
sonta,kowanne da hujjojinsa,saidai nata yafi
nawa
qarfi,tace"Ka tuna fa yayana,tun ban mallaki
hankalin kaina ba nake so da kaunarka,na soka
tun bansan ma'anar so ba,na jiku a sonka. Son
da nake gareka ya hanani kallon kowane namiji
dake a doron qasa,kallo na soyayya,kai din dai
kai nake ji,kai ka zamo masoyi gareni,tun baka
san dani ba har kazo ka san dani. Kaifa? Wata
kaso kafin Zahra..."Na katseta ina mai jin bugun
zuciya,ji nake dama ace tana kusa dani dana yi
mata abunda zata jima yana bin jikinta,murya a
dashe nace"Bebina,bar maganar data
wuce,wallahi a yanzu babu wata 'ya macen da
nake so face ke. Babu wata da zata iya shige
maki gaba,I love you with all my heart,ki yarda
bazan iya kuma kallon wata diya mace ba da
sunan so,bana fatan Allah Ya doramin. Na
amince
kinfi sona a baya,amma a yanzu nafi kowa
kaunarki. A bayan ma ina maki so,saidai
makancewa da soyayyar wata ya sanya ban kai
ga ganewa ba. Ke din ce dai ke kadai a ruhina,ke
kike bin jini da jikina,fatima zahra uwargida
amaryata." Shiru ya biyo bayan maganata na
'yan sakanni,na tabbata abunda nakeji shi Zahra
ke ji,abunda ke tadamin hankali,shi ke yawo a
nata jikin,na jima da rinannun idanuna a
rufe,kafin
na budesu ina mai sauke ajiyar zuciya,muryata ta
qi tsayuwa waje daya,dakyar na iya furta
kalmar"Zahra." "Uhm,yayana ina jinka." Na
lumshe ido"Nayi zaton bacci kikayi." "Bacci yanzu
yaya? A'a kawai dai...." Ta kasa qarasawa,nayi
murmushi"Bari na barki haka,Allah Ya tashemu
lafiya kinji?" "Toh." Bata bari na qarasa ba ta
kashe wayar da sauri,a hankali na sauke wayar
daga kan kunnena ina mai bin ta da kallo,har call
duration daya fito ya dauke,hoton zahra dake kan
screen ya fito tar da tar,tana murmushinta,tun
na
ranar walimar candy dinta dana dauka. Na zuba
mata ido,ba shakka nayi mugun kewarta,saida
kyar bacci ya kwasheni lokacin biyu ta kusa.
.
.
Bayan nayi sallah ma,kai tsaye gado na fada na
cigaba da bacci. Nidai ban farka ba sai wajen
tara
na safe. Nayi wanka na tsuke cikin jar riga da
baqin
jeans,sai ruwa ake shararawa,na bude windon ina
kallon yanda ruwan ke sauka,a hankali na fesar
da
iska,ina murmushi sanda iska ta bugo ruwan kan
fuskata,inama ace a wannan yanayin ina tare da
bebina? Na lumshe ido,sannan na janyo tagar na
rufe,ina son weather irin ta Lagos,su dai
kodayaushe cikin ruwa. Garin yana burgeni sosai.
A falon na tadda Abba da kawu suna kallon
labarai
da harshen turanci,Abba na yiwa Kawu bayanin
abunda ake fadi. Sallamata ce ta katsesu,suka
amsa
suna dubana cikin murmushi. Na rusuna na
gaishesu,Kawu yace"Amadu kenan,sannu,kasha
bacci." Nayi dariya kadan,Abba shima haqora a
bayyane yace"Yo ai dole,Amadu yasha zirga
zirga,yaron nan ya wahalar min da da'na."
Mukayi dariya,sallamar da akayi ce ta sanyamu
waigowa
gaba daya. Da sauri na mike na nufi yaya usman
ina
rikoshi,ganin yanda yake daga qafa
dakyar,maigadinsa wanda yake rike da lema ya
rakoshi,ya juya ya koma,kawu ya mike"Ya
Salam,kai kuwa usmanu me yayi maka zafi fitowa
ana ruwa?"Bayan ya zauna a kan kujera,Abba ya
dubeshi jiki a sanyaye,na tabbata ganin yanda
raunuka suka maida fatar dan nasa,"Haba kai
kuwa,baka barin ruwan ya tsagaita,dubi yanda
kake tafiya dakyar,bakayi hakuri har mu zo?"
Yaya
usman yayi dan murmushi kafin ya dukar da
kansa,hawaye suka zubo masa,murya na rawa
yace"Don Allah Abba ina neman gafararku,ku
yafe
mani na san na bata maku rai amma insha Allah
wannan karon bazan qara tsallake umarninku
ba."
Abba ya dafa kafadar Yaya usman"Bakomai,k
omai
ya wuce,Allah Ya qara maka lafiya. Ka kwantar
da
hankalinka." Ya shiga share hawayensa,Kawu
yace"Haba Usmanu ai shikenan kuma,saidai a
kiyayi gaba." Abba ya dubeni"Amadu,maza ga
kayan kari can,jeka ka ci wani abun." Na mike na
nufi tebur,na hada komai na zauna ina karina.
Ina
jin yanda kawu ke ta yiwa yaya usman yanda
sukayi da Alhaji Mahdi. Iya razana yaya usman
yayi,yace"Wallahi kawu bansan hamida na dauke
da ciki ba." Abba yace"Yanzu komai da ya
wuce,sai
kayi qoqari a yau ka rubuta takardan na kaiwa
Alhaji Mahdi da hannuna. Allah Yasa hakan shi
yafi
alheri." Kawu ya amsa da amin. Na lura dai jikin
yaya usman yayi sanyi,sai kuma nayi mamaki a
raina,toh meyasa zai damu don ya bata takardar
hamida? Inace dai ba kauna yake mata ba dama
can na Allah da annabi?" Maganar yaya usman ta
katsemin tunani"Wallahi Abba babu irin hakurin
da
bana yi da yarinyar nan,bata da aiki sai gayyato
qawayenta wadanda ba musulmai ba,su cika
gidan
da hayaniyarsu,hakanan zasu jata su fita wani
wajen,saidai na dawo na tadda bata gidan,a duk
lokacin dana kaiwa Alhaji qaranta ya kan musa
min,yace shi ya bawa 'yarsa tarbiyya,ba zai yarda
tana aikata hakan ba. Toh hamidah fuska biyu
take amfani da,a gaban Abbanta ta kan nuna ita
din mai
biyayya a gareni ce,amma a bayan idonsa ba
hakan
ba. Sannan duk abunda takeyi takan yi
takatsantsan yanda shi din bazai sani ba ko ya
sami
labari,maminta ita kadai ce tasan duk wani shige
da
ficenta,domin tun a gidan ta saba,a rufe Abban
da
cewa ai tana gidan wata qawar mamin. Toh Abba
ace ayi aure da haka?" Abba yayi murmushi"Kai
ka
jawowa kanka usmanu,kai da mahaifiyarka,ka
manta da yacce na yarje da auren nan?" Usman
ya
sunkuyar da kai,baice komai ba. Kawu ya qara
da
cewa"Abar komai dai bisa qaddara,Allah Yayi sai
an kai ga yin auren,yanzu ai magana kuma ta
qare,Allah Ya kyauta." "Amin."********
Washegari
kuwa da safe Abba yayi sammakon zuwa har
gidan Alhaji Mahdi ya damqa masa takardar
'yarsa,sukayi rabuwar mutunci. Da yamma muka
bi jirgi muka taho Kano don Abba yace bazasu iya
qara kwana ba,toh ni dinma dai nafisu jin
dadi,domin har lokacin qafafuna ciwo suke
saboda
dogon tuqin da ban saba ba,yaya usman yace zai
sa a kawomin motar tawa. A jirgi ma haka nayi
ta
tunanin Zahra,wacce tuni tasan da dawowarmu a
yau,fatana na sameta lafiya.
.
.
Sai bayan magrib muka iso,malam hussaini shi
yazo daukarmu. Bayan an sauke su Abba,na
bawa tasi'u jakata ya kai gida,ni kuma na shiga
don gaisawa dasu anti. Inna sai washe haqora
takeyi,tana min godiya sai kace ni na sanya a
fiddo yaya usman. Tayi ta zubamin tambayar ya
suke? Nayi murmushi"Lafiyarsu lau inna,sunce a
gaisheku." Tayi dariya"Kai madallah,ai Alhaji
Mahdi bashi da mutunci,duk tsawon lokacin da
usmanu ya dauka yana masa bauta,arzikinsa na
bunkasa ace karshe ya yi masa wannan diban
albarkar? Meye don ya doki 'yarsa,fitsararriya ce
ai,ko zuwanta nan haka tayi ta......" "Wai ke
salame meyasa baki tauna harshenki? Kai
amadu,tashi ka tafi." Na mike a lokacin inna na
fadin"A'a toh Alhaji me kuma nayi? Ai magana ce
kawai ake mayarwa. Nidai na fito na barsu,kai
tsaye dakin anti amarya na nufa,sallama nayita
bugawa amma shiru bata amsa ba,sai su
abubakar,na sanya kai ciki. Tana zaune
hankalinta yana ga akwatin talabijin,fuskar nan a
daure take tamau,tun daga nan na sha jinin
jikina,na durkusa har qasa"Anti ina kwana?" Idan
dutse ya amsa toh anti ta amsamin. Nakai minti
uku anan bata ko dubi inda nake ba,hakan yasa
na mike na bar dakin. Har naje zaure kuma sai
naji murya usman qarami a bayana"Yaya
Ahmed."
Mamaki yasa na juya da sauri don bai taba
kirana da yaya ba,yace"Ka gaida anti zahra."
Nayi murmushi na dafa kansa"Zataji insha Allah."
********************************************Sai
bayan isha'i na isa gidan. Ina kwankwasawa,ta
bude da saurinta. Na qarasa ban jira komai ba
na
rungumeta tsam. Tayi dariya"Don Allah nidai ka
sakeni zaka ballani fa." Cikin dariyar na sassauta
rikon da nayi gareta"Don Allah nidai ki barni,nayi
missing dinki fa." Mukayi dariya,sannan na
saketa,ina mai zuba mata ido. Ta dauke
idanunta,na lura ko kadan bata jure mu hada ido
na dan lokaci. Na rufe qofar,ina rike da ita na
qarewa kwalliyarta kallo tun daga sama har
qasa,dan fingilin siket ne iyaka gwuiwa sai wata
'yar t-shirt wacce ta fiddo dukkan surarta,na
hadiyi miyau kafin na kauda kaina, gaba daya ta
chanja tayi kiba kadan a kwana biyun da ban
sanyata a ido ba. Saida nayi wanka,nayi
sallah,sannan na fito falon don cin abinci. Na
sameta tana fiddo jug mai dauke da lemo daga
frigde. Na qarasa gareta cikin murmushi na
zauna
kan kujera ina mai tagumi idanuna na kanta,wani
irin kyau ne tayi mani. Ta ajiye jug din ta soma
kiciniyar zubamin abinci"Wai yayana mena zama
kake ta kallona?" "Kin fini sanin me kikayi
bebina,kin tafi dani da
yawa,kowane motsi idan nayi saikin fadomin a
rai,wallahi nayi kewarki fa." Tayi dariya
sosai,fuskarta sai sheki takeyi,ta turomin plate
shake da abinci"Yayana kenan." Na janyota na
zaunar da ita bisa qafafuna"Ba yayana ba,sanar
dani meke bakinki kike boyemin,nasan kema
kinyi
kewata ko?" Tayi shiru,ta kasa magana,hakan bai
hanani fasa abunda na soma ba,na dau wani
lokaci har saida ta mike da sauri taja baya,na
dago idanuna wadanda suka kada na zuba
mata,kallo ne na tambaya,ta dauki kanta tana
gyara zaman ribon data tufke kitsonta,bayan ta
qara gyara muryarta tace"Don Allah ka ci
abincin." Na zuba mata idanu kafin na qara
hadiyar yawu,na maida dubana ga abincin,sam
sai naji ya fita a raina amma saboda yunwar data
taso min yasa ban qara bi takan Zahra ba wacce
ta koma cikin falo ta zauna bayan ta juyamin
baya,na soma ci. A daren dai mu kanmu munsan
munyi kewar juna.*************************
********************Kamar yanda muka
saba,yau
dinma rakoni tayi har bakin qofa,ta
dubeni"Af,yayana kaga na manta,kodayake saidai
ka dawo akwai wani labari da zan baka." Na
dubeta da sauri"Bani yanzu mana bebina,kada
na
tafi ina tunani." Tayi murmushi tana mai harde
hannuwanta a kirji,ta kalleni kallon da nakan jishi
har tsakar kaina"A'a kaidai kaje Allah Ya
dawomin da kai lafiya,zakaji labari." Na sumbaci
kuncinta"Shikenan bebina,amin,saina dawo." Ta
dagomin hannu,nayi gaba ta ja qofar ta rufe.
.
.
Alhamdulillah,yanda na tafi ba fargaba akan
shagona cikin ikon Allah na samu komai yana
tafiya
daidai,tasi'u ya kula da komai yanda ya dace.
Shagon cikin hukuncin Allah Yana ta samun
cigaba
ta bangaren kayayyaki,don a yanzu kudin da suke
a
account dina sun haura dubu dari da hamsin,sai
godiyar Allah. Na gama duba komai,mukayi
lissafi.
Sai da akayi azahar,na dauki waya na lalubi
lambar
aminina. Ringing yayi har ya tsinke bai daga
ba,nayi
masa uzurin baya kusa ko yana ofis. Bayan wasu
mintoci sai gashi ya biyo bayan kiran,bai barni
nayi
sallama ba,ya soma cewa"Dama kana duniya?
Irin wannan tafiya babu sanarwa,ai hakan da kayi
ka
kyautata farko ma banyi niyyar biyo bayan
kiranka
ba Ahmed,hakan da kayi yasa ma tun tafiyarka
ban
nemeka ba." Nayi murmushi"Gaskiyane ban
kyauta
ba mutumina,amma don Allah ayimin uzuri.
Tafiya ce
ta gaggawa bayan mun rabu dakai da naje gida...
(Nan na labarta masa yanda akayi har
dawowata)
yace"Subhanallah,Allah Ya kiyaye gaba." "Amin."
"Toh sai yaushe zaka shigo." Na numfasa"Sai dai
zuwa gobe idan Allah Ya kaimu." "Allah Ya
kaimun,gwara dai ka shigo muyi magana,kasan
fa
biki ya qarato nan da sati za'ayi daurin auren."
Na mike daga kishingidar danayi"Haba dai?" Yayi
dariya"Wallahi." "Kai madallah abu yayi
kyau,Allah
Ya nuna mana,kai ni inaga ma ko na shigo yau
bayan magriba." Badamasi yayi dariya"Ai
shikenan
toh,sai ka iso,kaga kuwa shegen nan haidar yace
zai
shigo shima." Nayi dariya"Ai shikenan,sai mun
hadu." "Ok." Daga nan mukayi sallama. Na ajiye
wayar ina murmushin nishadi,zuciyata sol ina
tunanin rahmar dake ga aure,lallai na taya
aminina
murna. Na lumshe ido na shafi sumar kaina
wacce
nake sa ran ragewa nan zuwa gobe,babu abunda
ke fadomin sai tunanin abar kaunata Zahra.
Hakan yasa na dauki waya na tura mata
text,sannan na
ajiye wayar gefe na cigaba da harkokina. Duk
yanda
naso na biya gun Badamasi Allah baiyi ba saboda
wata irin gajiya data zo min,ga bacci dana ke
jinsa.
Hakan yasa qarfe takwas na daren muka kulla
shago. ******************************
******************Ina kwance kan
gado,yayinda
Zahra ke mammatsamin qafafu. Na dubeta a
gajiye,ina mai jin dadin hakan"Bebina." Ta dago
kanta ta dubeni fuskar dauke da murmushi
kamar
koyaushe,"Na'am." Na miqa mata hannu ta
sanya
nata ciki na janyowa ta zauna gefena,cikin
yanayin bacci nace"Baki sanar dani abunda kike
son
labartamin ba idan na dawo." Tayi murmushi ta
langabar da kanta"Kai yayana,bacci fa kakeji,kayi
hakuri yanzu mu kwanta da safe insha Allahu
zakaji
koma menene." Kasancewar baccin nakeji ban
musa
mata ba,"Ok." Kawai na bita dashi sannan na
kwanta,ita ta mike ta kashe fitilu sannan ta shiga
toilet. Nidai ban qara jin komai ba sai sallar
asuba,hakan yasa na mike dakyar na nufi
bandaki.
Bayan fitowata na tashi Zahra. Nan dinma muna
idarwa muka koma.
.
.
Shiru sai qarar cokali kake ji a falon,muna
karyawa. Zahra ta hadiye dankalin dake
bakinta,ta
karkato ta dubeni"Yayana." Na dago kaina na
dubeta ina amsa mata da ido. Tana murmushi ta
sauke kanta tace"Baka tambayeni abunda
nakeson
sanar maka ba." Na dan dafe goshi"Oh no,sorry
bebina,wallahi gaba daya na manta,sanar dani da
sauri please menene shi?" Ta dan gyada kai tana
langabar dashi tana dubana tsakar ido
tace"Hafsat
tazo gidannan da baka nan." Cokalin dake
hannuna
na maida na ajiye,gabana ya fadi,na saki baki ina
dubanta,shikenan abunda muke boyewa ya fito
fili. Saidai na daure nayi gyara murya ina
murmushin
yake"Kai haba?" Na lura da yanda Zahra ta dan
chanja,na tabbata kishi ke damunta,itama dai ta
daure din tace"Allah kuwa,can gidanmu taje
nemana,shine anti ta sanar da ita nayi aure.
Tasa aka
rakota nan. Dama ina ganinta na sha jinin
jikina,domin nasan anti tayi hakan don tasan
hafsa
batasan waye mijina ba. Hafsa ta rungumeni tana
murna na jata har falo muka zauna,gaba daya
kamar
ba ita ba tayi kyau abinta. Tace min"Amma
qawata
baki kyautamin ba,ace har kiyi aure babu gayya
babu komai,sai yanzu da naji labari daga sama?
Haka alkawari yace?" Hum yayana ina fadamaka
tun
daga nan na soma jin zufa,na daure dai na bata
amsa"Kiyi hakuri aminiya,abun ne yazo min a
bazata,amma ina niyyar idan an kwana nazo har
gidanki na baki hakuri." Tayi dariya"Toh waye
maigidan?" Na rasa me zance,na basar ta hanyar
mikewa tsaye ina fadin"Bari kedai na kawo maki
ruwa." Na mike da sauri banaso ta qara tsayar
dani,"Zahra." Ta kira sunana,gabana ya fadi,dole
na
juya na dubeta,tana daga zaune tana murmushi
tace"Dawo ki zauna." Na zauna ina harararta da
wasa"Toh babata." Amma fa yayana gabana sai
bugawa yake,tayi murmushi"Kada ki damu,na
lura
duk kin rude,wallahi nasan cewa yaya ahmed kika
aura,anti ta sanar dani kafin na zo nan. Kada ki
damu
wallahi a yanzu ina son yaya suleiman,kinsan yau
da
gobe idan mutum yana kyautata maka koda baka
sonshi,toh wallahi dole wataran kaji kana
kaunarsa. A yanzu nan da kike ganina na manta
da yaya
ahmed,kada ki manta yanzu ina da igiyoyi uku a
kaina,wallahi ki saki jikinki babu laifin da
kikayimin.
Saidai banji dadin yanda kika boyemin kaunar da
kike yiwa yayanki ba,Zahra ke din kece kika dace
da
yaya ahmed,ba ni hafsa ba. Karambani ne irin
nawa,kinga kuma abun Allah sai ya kashe ya
baki."
Nayi murmushi,duk ta sanyayarmin da jiki
wallahi,sai
ma na kasa dubanta,ganin da tayi bani da niyyar
magana,ta daki cinyata tana dariya"Dallah
can,meye
na damuwa,wallahi babu komai a zuciyata."
Humm,ai kuwa ta tabbatar mini don
wallahi,bamu
qara tada maganarka ba,sai labarunmu da
mukayitayi,da hirar qawayenmu. Hafsa har da
tsohon ciki,haihuwa ko yau ko gobe." Naji dadin
jin
Hafsa tana cikin kwanciyar hankali,nasan cewa
bata
da damuwa yanzun,duk da cewa dama dole naji
sosuwar rai ko yayane,na dake ina dariya na
mike
na rungumota"Madallah,nayi maki murna da
aminyarki ta fahimcemu,Allah Ya qara mana
kaunar
juna,kema Yasa ki sami naki bebin." Tayi
dariya"Kai
yayana." "Eh mana." Na saketa nayi hanyar daki
ina
murmushi"Maza qarasa kizo kimin
wanka."********
.
.
Da yamma koda na dawo gidan nazo na tadda
tashin hankali. Domin kuwa Zahra na samu a
zaune
tayi tagumi,babu ma abunda yafi ban mamaki
yanda
qofar falon ke a bude,har na zagaya na zauna
batasan nayi ba,hawaye na zuba na ajiye hulata
gefe
na kama hannunta"Subhanallah,meya faru
hakanan Bebina? Ya akayi kika bar qofa a bude?
Waye yazo?"
Ta dubeni kukanta ya qaru"Anti ce tazo." Gabana
ya
fadi,"Me tayi maki?" Ta girgiza kanta"Yayana har
yanzu anti tana fushi dani,yanzu ta zo ta tafi,tace
idan
har ni din 'yarta ce ta cikinta toh ya zama lallai
nan
zuwa sati na bar gidanka,koda ina tsoron
komawa gida saboda Abba,toh zata turani gidan
mama
tamasar(gidansu faisal) sai ace na gudu,dole ka
bada takardana. Dana bijire mata shine ranta ya
baci
har da marina,sannan ta qara tabbatar min bana
tare
da albarkarta muddin na cigaba da zama da kai."
Ta
qara fashewa da kuka,gaba daya na gigice,raina
idan yayi dubu ya baci,wai yaushe anti zata
sauko
tabar wannan fushin? Na tausayawa kanmu,ai a
yanzu babu wanda ya isa ya rabani da Zahra,na
sassauta murya"Please Zahra kiyi hakuri,nidai
fatana
don Allah kada ki barni. Muyi hakuri da anti,mu
cigaba da addu'a ko Abba kada mu fadawa
wannan maganar,insha Allah wataran komai zai
zo
qarshe,anti zata fahimcemu,zata fahimci waye
AMADU? Zata kaunaceshi a matsayinsa na
surukinta,zatayi alfahari da aurensa da 'yarta.
Wallahi
bebina kodayaushe idan na sanya goshina a qasa
sai na roqi Allah akan anti. Allah Ya daidaitaki da
mahaifiyarki." Haka nayita rarrashin Zahra har
dai
saida ta bar kukan,daga haka na dauke mata
hankalinta. Cikin dare na zubawa fuskar Zahra
ido
da taimakon 'yar qaramar fitilar dake gefen
gadon,tana baccinta a nutse,sai numfarfashi
takeyi
da qarfi irin na wanda ya sha kuka. Na shafi
gefen fuskarta wanda zanen yatsu ke
kwance,wajen yayi
jawur,ina mai jin soyayyarta har cikin qoqon
zuciyata,ga wani matsanancin tausayinta da
nake.
Tunanin wannan rikicin na anty ya hana zuciyata
sukuni,wannan ya nuna har yanzu hankalinta
yana
kanmu bata hakura ba,na mike na nufi bandaki
domin dauro alwala,na jima ina kaiwa Allah
kukanmu kafin na kwanta.********
**************(hum,kuma dai
kun san me zansa. Ba saina fada ba.)
.
Da gudu Zahra ta fada kan cinyar gwaggo suna
dariya,na ajiye jakar Zahra dake hannuna a gefe
ina
dubansu cikin dariya nace"Zaki qarasa mana 'yar
tsohuwa ko?" Ta dagata tana dariya,gwaggo
tace"Ja'irar yarinya,kin auremin miji kunzo zaku
qarasani." Mukayi dariya gaba daya,Zahra tace"Ai
so nake qafafun su daina aiki,naga da qafar da
zaki
tako gidana." Gwaggo ta bantali goronta ta hau
tauna"Ja'ira,ai kuwa sai na zo gidan naki,baki
kwace
min mijina ina zaune ina kallonki. Kai dinma
dayake
ja'irin kanka ne yaushe rabon dana sanyaka a ido
Amadu?" Nayi murmushi ina mai zama a
gefenta,muka sanyata tsakiya nida Zahra,"Haba
uwargidana,inace ranar da zamu tafi na shigo?"
Gwaggo tace"Ai dayake dalili ne ya sanya,kazo
tafiya
da babanka inda ba haka ba da babu abunda zai
sa
na ganka." Zahra ta cafe"Kedai 'yar tsohuwa
kishi ke
nukurkusar zuciyarki,shiyasa kika sanyamana
ido." Gwaggo ta daki cinyarta,ni kuwa kallon
Zahra kawai
nake ina dariya. Zahra cikin dariya ta mike"Nidai
bari
na shiga gaida sauran uwayena na gane kedai
baki
murna da zuwana. Nama fasa yinin tare zamu
juya
da yaya." Gwaggo tace"Toh meye ciki idan kin
juya,dama bana bukatar ganinki." Zahra ta bar
dakin,na bita da kallo sannan na maido hankalina
ga
Gwaggo"Allah Ya baki hakuri 'yar
tsohuwata,wallahi
lamuran ne sai a hankali." Jin haka ta kalleni ta
gefen
ido,"Kamar ya sai a hankali? Wani abu ya kuma
faruwa ne?" Nayi dariya kadan"Babu komai sai
alheri,kasuwa ce ta boyeni." Gwaggo ta tabe
baki"Allah Ya taimaka toh,ka dai dunga kula,ga
dai
yayanka nan da irin bala'in da ya janyowa kansa
shi
da uwartasa,ai inda nice Alhajin nan har kudina
sai
ya biyani." Na rike baki"Kai gwaggo,yaya usman
ne
fa." "Atoh,ba kwadayi irin nasa bane,shi da uwar
tasa,ai kaga yanzu sun koyi hankali,munafukar
jiya har tsakar dakina tazo ta gaidani,taji ana
yamudidi
da 'danta a unguwa cewar ya ci kudin baban
matarsa an kamashi,abu ya zame mata abun
kunya a
unguwa. Duk tsawon lokacin data dauka da yaron
nan sai yanzu tasan tayi hankalin zuwa
ziyartana.
Lallai duniya ta fara koyawa salame hankali,ta
godewa Allah ma da abun ya tsaya anan. Naji ita
kuma waccan 'yar tata,'yar bala'in,Abida,mijin
zai
dawo da tsohuwar matarsa da suka rabu kafin ya
aureta. Ita kuwa kubrar mijin sai wulakantata
yake,mariya kuma uwar miji ta matsa mata,toh
duk
wannan me ya ja? Ai dama abunda kayiwa 'dan
wani sai an wa naka,yanzu ai ta soma
ganewa,saura
waccan 'yar fitinar." Nayi shiru,ina sauraron
gwaggo,Allah shaida duk bansan da wadannan
maganganun ba,rayuwa kenan. Na jinjina kaina
na
qara duban gwaggo a mamakince"Toh wai me ya
kawo innar wajenki?" "Wai tazo gaisheni don
munafurci." Nayi dariya"Haba dai gwaggo,wane
irin
munafunci kuma ana zaune kalau?" "Yo idan
banda
munafunci salame ta saba zuwa gaidani? Kajimin
yaro." Shigowar Zahra ta dakatar dani daga
abunda
nake shirin cewa. Hakan yasa muka bar
zancen,na
mike ina dubansu"Shikenan,ni zan wuce sai kuma
da yamma,ga matata nan ki lallabamin ita,a
matsayinki na uwargida na baki amanarta." Na
cewa
gwaggo. Gwaggo tace"Yo ai sai ka sanyata a
aljihu
ka tafi da abarka,ban kulawa da ita din." Ni da
Zahra
mukayi dariya,nace"Allah Ya huci zuciyarki." Na
dubi
Zahra,ita dinma dubana tayi har tsakar ido,muka
isarwa da juna saqonni masu shiga har
zucci,kafin
na sanya kai zan bar dakin. "Yaya." Na juyo,tana
murmushi ta mikomin hulata wacce shaf na
manta
da ita,na qarba"Lallai ganin uwargida yayi
armashi,ashe har mantuwa na kusan yi a rumfar
taki." Mukayi dariya na fice suna min addu'ar
sa'a. Sai da na shiga wajen su inna larai sannan
na fice. Kawu
basu nan gaba daya an tafi neman kudi,hakanan
samarin gidan daga mai zuwa makaranta sai mai
iyali.


Zaharddeen shomar
Whatsapp   08168575100Amadu 2 part 12
Posted by ANaM Dorayi on 01:32 PM, 29-Jun-15
Under: Amadu
. Bayan sati biyu Na dubi Zahra wacce ke zaune
a hannun kujera tana wasa da gefen
dankalinta,ta
turo baki ita a dole fushi takeyi. Na zauna
saitinta ina daura farin agogona a hannu,cikin
murmushi ba tare dana qara dubanta ba
nace"Dama dai kin samarwa zuciyarki sauki kin
bar fushin nan bebina." Ta qara muskutawa gefe
daya ta bar fuskantana,tana mai kukan
shagwaba"Toh ba kai bane kake ta wani kwalliye
kwalliye,salon wata tace tana so...." Na katseta
ina dariya sosai na mike na hada jikina da
bayanta ina mai dora hannuna a qugunta"Bebina
kin fiye kishi da yawa,wai kin manta cewa daurin
aurene ba wani shagali bane da zan hadu da
kanwarki?" Ai sai ta sanya kuka tana mai mikewa
tsaye"Eh ai dama haka zaka ce,wato kanwata ma
ko? Ai dole dai ku shiga gidansu jamila. Nidai
kada ka qara kulani,ka tafi kawai." Tayi hanyar
daki,ina kiranta bata waigo ba,wayata ta soma
ringing a daidai lokacin da nake shirin mara mata
baya,na duba angon ne da kansa,na dauki hulata
dake ajiye kan kujera,ina duban hanyar daki ko
zata fito amma ina,gashi kuma ina neman
makara,zuciyata babu dadi haka na juyo ba da
son raina ba na fice da sauri. Saida na shiga
mota na bi bayan kiran wanda a lokacin har ya
yanke,yana dagawa kafin nakai ga soma magana
yace"Kaifa a komai sai ka bata lokaci,don Allah
ka taho nan gidan yanzu muke shirin fita." Nayi
murmushi"Kayi hakuri ango,gani a hanya ai." Ya
katse wayar,banfi minti biyar ba na isa
gidan,qofar cike take maqil,da 'yan uwa da
abokan arziki. Bayan na gaggaisa dasu na wuce
inda ango badamasi ke tsaye da aminansa,kana
ganinsu kasan sun ci sunansu wato 'ya'yan
hutu,domin ko wannensu yayi shiga wacce babu
raini,toh ni dinma ba baya ba. Muka
gaggaisa,hayat ya soma da cewa"Kai Ahmed
kamar kai dinne angon? Kaga kyallin da kakeyi?"
Na harareshi a wasance"Kai dai ka zageni a
fakaice." Mukayi dariya,badamasi yace"Kaidai a
komai sai ka shanya mutane,auren nan ko naka
ne sai haka." Nayi dariya"Toh kasan abu ga mai
iyali,saida na lallabata." Akayi dariya,haidar
yace"Dadin abun kowa da aurensa." A ranar dai
aka daura auren Badamasi da Jamila,gaba daya
hankalina yana ga Zahra,hakan yasa koda aka
shiga gidansu jamila don gaisuwa,na samu waje
daya na kebe na ciro wayata domin kiranta.
Saidai duk iyakar ringing din da wayar tayi bata
daga ba. Hankalina ya tashi,na soma tunanin
kodai ba kalau ba,domin duk yanda zamu samu
sabanin da bai taka kara ya karya ba da Zahra
toh hakan bai sanyawa ta qi daukar wayata.
Hakan yasa bayan fitowarmu,na dubi
Badamasi"Zanje gida na dawo,Zahra nayi kiranta
ta qi dauka,na tabbata akwai dalili." Badamasi
yace"Kai Ahmed,mu da zamu tafi walima?" Nayi
murmushi"Yanzu zan dawo,zan sameku a gidan."
Ban jira cewarsa ba na juya da sauri na nufi
motata,ikon Allah ne Ya kaini gidan don hankalina
bai tare dani. Koda na shiga babu kowa a
falon,hakan yasa na soma kwala mata kira na
nufi dakin,nan ma bata nan,na juya na koma
dakina,nanma din ban ganta ba,ina shirin fitowa
na hangi zaninta yashe a qofar bandaki,hakan
yasa nayi sauri komawa na shiga
bandakin,kwance na ganta cikin amai,tayi har ta
galabaita. Tana kwance tana numfarfashi. Da
sauri na dagota"Subhanal lah,bebina meya
sameki?" Ta kwantar da kanta a kirjina,cikin
raunanniyar murya tace"Yayana zan mutu,amai
nakeji gashi babu sauran abun amayarwa." Na
taimaka na wanke ta tas,sannan na rufa mata
tawul muka fito. Saida na dauko mata wasu
kayan na taimaka ta sanya sannan na kwabe
rigata da hula,na ajiye agogo gefe,na soma aikin
gyaran bandaki. Bayan na qare nima na chanja
kaya,sannan na dauko mata hijab ta sanya,ina
rike da hannunta na miqar"Tashi muje asibiti
bebina."
.
.
Babu dogon layi kasancewar private hospital ne
sannan cikin sa'a mutane basu cika ba don
mutum
uku ne a gabanmu,na zaunar da ita na
dubeta"Bari
na bude mana file." Ta gyada kanta,na wuce ina
mai
cike da tausayin Zahra,sai na tuno yanda muka
rabu
da ita,yanzu inda mutuwa lokacin saidai ta tafi
tana fushi dani. Jiki a sanyaye na koma na zauna
bayan
an kai file din dakin doctor. Zamana ba jimawa
layi
yazo kanmu. Bayan Doctor taji matsalarta,ta
janyo
wata 'yar takarda ta hau rubutu,sannan ta miqo
min"Kuje Lab a duba fitsarinta." "Ok." Na taimaka
mata ta mike muka fita. Mintuna goma muka
kwashe anan kafin mu amshi result. Bayan likita
ta duba tayi
rubutunta cikin file,sannan ta rufe tana
miqomin,fuskarta dauke da murmushi"Congra
tulation! Your wife is pregnant." Habawa! Ai
kamar
an min albishir da gidan aljanna,hankalina yana
ga
zahra wacce ta sunkuyar da kanta tana
murmushi,na tsinci doctor na qarashe
bayaninta"3months". Har
allura akayi mata saboda aman data kwarara.
Muna
shiga mota na jawo ta sosai jikina na
rungume"Kin
gama yimin komai bebina,Allah Ya qara muku
lafiya,Ya saukeki lafiya." Cikin kasalar jiki ta
tureni"Nidai ka rabu dani,ai ka manta ba munyi
fada ba." Na rike habarta ina murmushi"A'a
bebina ai tuni
mun shirya,kiyi hakuri don Allah bazan sake ba
kinji
bebi maman bebi." Mukayi dariya,ta qara
shagwaba
fuska"Nidai wallahi yayana yunwa nake ji sosai."
Na
dubeta ina dora hannu kan cikin"Ai dole a nema
maki abunda zaki ci bebi,fadamin na wane
restaurant kike sha'awa?" Ta qara sanya kukan
shagwaba sai kuma tayi 'yar dariya ta girgiza
kanta
kafinta muskuta ta jingina da kujera tana mai
lumshe ido"Nidai koma na ina ne,amma ya
kasance
tuwo miyar kuka." Na fashe da dariya a lokacin
dana
harba motar,an gama wannan mai sauki ne ranki
ya dade." Mun soma tafiya wayata tayi qara,sai
da naga
sunan Badamasi na tuno ashe fa yau daurin
aurensa,awa da mintuna da suka wuce muna
tare.
Na danna na kara a kunne,ai nan ya hau ni da
fada,na bashi hakuri na sanar dashi rashin lafiyar
Zahra da kuma qaruwar data sameni,ai nan ya
hau fadin"Assha,Allah Ya qara sauri,Ya sauketa
lafiya,a
tayani yi mata murna." Nayi murmushi"Amin,z
ataji,nagode sai mun hadu anjima." "Ok." Na
ajiye
ina
dubanta daidai lokacin da traffic light ya sauka
kan
jar danja,"Kinga fa na mance da Badamasi,sai da
ya
bugo na tuna,missedcalls dinsa har goma." Tayi
murmushi kadan bata ce komai ba,har ya sauka
kan
Kore na ja mota. Bayan mun tsaya a wani
restaurant
dake nan hanyar yakasai,na siya mata tuwo da
miya,na qaro mata har da romon hanta sannan
muka tafi zuwa gida. A ranar dai yini nayi kula da
Zahra,saida naga ta samu nutsuwa ta warware
sosai sannan na fita domin leqa dinner na
Badamasi da
za'ayi bayan na tabbatarwa Zahra bani wuce awa
daya. Hakan kuwa,duk yanda su Haidar suka so
na
tsaya har a kammala hakan bai samu
ba,Badamasi
kasancewar yasan uzurina yasa bai damu ba.
Haka
na baro wajen dinner wanda su a lokacin nema
kamar aka fara.**** "Haba yayana don Allah ka
barni naje,yanzu idan banje ba wallahi jamila
bazata
ji dadi ba." Na qara muskutawa na juya mata
baya
cikin bacci nace"Babu inda zakije,bakya jin dadi
amma don son yawo kice zaki ki wahalar min da
jiki?" Ta fado kaina tana kukanta na
shagwaba"Don
Allah Yayana kada muyi haka dakai,wallahi babu
dadi." Na juyo sosai domin kuwa jinta a jikina ya
farkar dani. Na dubeta da jajayen idanuna irin na
wanda ya sha bacci,tana daure da tawul,ruwa
yana
zuba daga jikin gashinta,na kalli fuskar wacce ke
ta sheqi tayi bul bul gwanin ban sha'awa. Sai
kuma na
kai dubana ga qaramin bakin Zahra wacce ta
qara
tsukeshi,ita a dole fushi takeyi,idanunta farare
qal
sukayi rau rau,tana shirin yin kuka. Cikin
murmushi
na sanya hannu na fisgota,na shiga yi mata rada
a
kunnenta,ta dan gyara matsowa tana ihun
murna"Eh wallahi na yarda in har zanje." Mukayi
dariya.
.
.
Na dubeta ina shirin tada mota,ta gama haduwa
cikin dakakkiyar shadda ruwan hoda,tana kicinyar
zura wayarta jaka,ta dago ta dubeni"Ya dai?" Na
jingina kaina da kujera"Anya kuwa bebi akwai
fitar
nan? Kinga yanda kika hadu,kada fa kije ayi ta
kallemini ke." Tayi narai narai da ido"Kai haba
don Allah Yayana,kaga fa nayi lullubi har kaina."
Na dan
tabe baki kadan a lokacin dana tashi
motar"Fuskar
taki fa? Nidai please ki kularmin da kanki." Tayi
murmushi"Insha Allah my dear." Na harareta
itama
ta sanya dariya nayi murmushi"Don kina son fita
kenan." "A'a wallahi my dear." Na qara
murmusawa na ja muka bar qofar
gidan.*********
.
Cikin ikon Allah,aka gama biki lafiya,Badamasi ya
tare a can unguwar rijiyar zaki. Koda na dawo
tuni
Zahra tayi bacci,sai ajiyar zuciya takeyi na
gajiya,na
shafi gefen fuskar,a firgice ta tashi zaune na
riketa,ta
hau mutsitstsika ido"Yayana ka dawo?" Na yi
murmushi"Na dawo bebina,bacci ko?" Ta ja
qaramin tsaki"Wallahi kuwa kaga daga idar da
sallah bacci ya
kwasheni nan,ashe kofar ma bude take." Nayi
murmushi"Allah Sarki bebina na tabbatar gajiya
ce
kawai,tashi ki shiga daki." Na taimaka mata,ta
mike
muka nufi dakin,bayan na kwantar da ita nima
na
soma kiciniyar cire kaya don watsa ruwa.
"Yayana ko na taimaka maka?" Na juyo da
sauri"No,wallahi ki
yi kwanciyarki bebina,keda bakijin dadi. Please
kwanta." Ta qara gyara kwanciyarta. Bayan na
fito
ga mamakina na sameta idonta biyu tana duban
sama. Na qaraso na zauna kusa da ita gami da
riqo
hannun ina murzawa,hakan yasa ta juyo ta
dubeni sannan ta wayance"Yayana ka fito?" Cikin
rashin
fahimta na dubeta"Bebina tunanin me kikeyi ne
haka? Don Allah ki sanar dani koma menene ni
dinnan fa nine naki,baki da wani abokin shawara
face ni please." Ta muskuto tana fuskantana ta
qara
dora daya hannunta kan nawa murya a raunane
tace"Yayana yau gaba daya banajin dadin
jikina,ina
tunanin anti,yayana zuciyata nayimin zafi,yaushe
anti
zata yafemin. Yayana gashi ina gabar
haihuwa,antina
tana fushi dani,idan wajen haihuwa Allah Ya
dauki
rai....." Da sauri na toshe bakinta a lokaci guda
na
miqar da ita zaune ta hanyar kama kafadarta
daya,ina mai yin hagu da dama da kaina
nace"A'a
Zahra,a'a kada ki qara yimin irin wannan furucin.
So
kike zuciyata ta fashe? Ga rashin iyaye ga naki?
Oh
no,insha Allah hakan bamai faruwa bane,ki
tausayamin don Allah Zahra ki bar wannan
furucin
har abada,ki taimakeni." Gaba daya na tsinci
kaina a rude,hawaye suka soma zubowa daga
idanuna,ganin haka ta rungumeni itama tana mai
yin
hawayen"Kayi hakuri yayana shikenan ya wuce
wallahi na bar fadi kaji?" Na dago fuskarta ina
share
hawayenta"Mahaifina ya rasu ban taba sanyashi
a
idona ba,hakanan mahaifiyata ta rasu itama ban
taba sanyata a idona ba,haka ban san dadin
mahaifiya ba
Zahra,a yanzu ne na maidaki abokiyar
rayuwata,ke
kike sharemin hawaye,ke kike mantar dani
matsayina na maraya bayan Abba,Zahra. Idan
kina
wannan furucin ya kike so nayi? Na san kwarai
dole
hankalinki ya tashi saboda yanda Anti ta bar
kulaki Zahra,na tabbata fushin MAHAIFIYA abune
mai tada
hankalin duk wani 'da nagari,insha Allah Zahra
anti
zata fahimcemu,insha Allahu akwai randa zata
karbi
auren nan namu da hannu bibbiyu,na tabbatar
maki
wataran zaki sha mamaki." Tayi murmushi tana
qara
goge hawayenta"Hakane yayana,Allah Ya kawo
mana wannan ranar da sauri." "Amin
Bebina." )Tun ranar da mukayi wannan zancen
da Zahra
na lura bata da nutsuwa,bata yawan dariya sai
murmushi wanda shi dinma hakan ba qaramin
damuna yayi ba,ga likita tace a kula da ita
saboda bebinta. Ina tafe a hanya amma gaba
daya hankalina yana ga Zahra har na iso qofar
gidanmu zuciyata cike da tunani. Abba na zaune
kasancewar yau asabar,yakan bar yaransa a
shago can kasuwa,shi kuma ya samu lokacin
hutu. Na fito cikin fara'a na qarasa,ana masa
gyaran farce,na durqusa har qasa"Abba barkanku
da safiya." Shima fuskarsa a sake ya amsa"Kuna
lafiya amadu?" "Alhamdulillah Abba." "Masha
Allahu,kaga antin taku ma kwana biyu bata jin
dadi." Gabana ya fadi,na dubi Abba kafin nace
wani abu yace"Shiga ku gaisa mana." Na miki jiki
babu laka,Zahra ta fado a raina,Allah Sarki waya
sani ma ko taji a jikinta ne shiyasa kwana biyu
take wuni tunaninta. A tsakar gida na samu inna
zaune a kan kujera,yayin da anti Abida ke zaune
kan tabarma kusa da ita tana hawaye,duk ta bi
ta
rame kamar ba ita ba. "Toh ita kuma lafiyarta?"
Na fada a zuciya,suka dago suka dubeni suna
masu amsa sallamata,na rusuna na gaishesu,inna
ce ta iya amsawa,na mike ban qara dubansu ba
nayi hanyar dakin anti. Na shiga da
sallama,saidai babu amsa,tana zaune tana shan
tea. Gaba daya ta chanja,idonta sunyi ciki ciki,ko
dubana batayi ba fuskar a daure,kallo daya
zakayi mata kasan tabbas bata ji dadin jikinta ba.
Murya na rawa na gaisheta saidai yacce kasan da
dutse nake babu kowa a wajen hakane. Domin ko
kallon inda nake bata yi ba. Na qara bude
baki"Ya jik......" Ta dakatar dani ta hanyar
dagamin hannu"Tashi ka barmin daki." Na mike
na fito a sanyaye. Su inna sun koma daki,hakan
yasa na fice daga gidan,a qofa na tadda Abba an
gama gyara masa na hannu an soma na qafa. Na
durkusa"Abba zan wuce." Ya dubeni
dakyau,sannan yace"Ya akayi Amadu,fuskarka da
alamun damuwa." Na qaqalo murmushi"Babu
komai Abba." Yayi murmushin shima sannan ya
girgiza kansa"Amadu kenan,bar wannan uwar
taku,bata da tunani,ku cigaba da addu'a,matar
nan jiya da thypod dinta ya tashi kamar bazata
rayu ba,amma ashe bata saduda ba?" Nayi
murmushi"Bakomai Abba,insha Allah wataran sai
muga kamar bai taba faruwa ba." Ya jinjina
kai"Allah Yasa." "Amin." Daga nan mukayi
sallama,koda na ja saida na dakata wajen baba
maigadi muka gaisa sannan. Na maka
sallama,amma babu amsa. Na shigo
falon sosai,bata nan,na shiga dakin qarar ruwan
dana ji ya fahimtar dani tana bandaki. Na ja
mata
qofar na koma dakina. Har na shafe mintuna na
fito
daga dakin bayan nayi wanka. A dakin dai na
sameta tana shafe shafenta a gaban madubi
saidai ta zura 'yar doguwar rigarta mara nauyi,a
yanzu sam
bata kaunar abunda zai mata nauyi a jiki. Ta
dago ta
dubeni,ta saki murmushi"La yayana dama ka
dawo?" Na qarasa ina mai sanya wuyana kan
kafadarta muna duban juna ta madubi"Bebina na
dawo har nayi wanka baki sani ba,gaskiya ya
kamata a nemo wacce zata taimaka maki da
aikace
aikace,na lura gajiya tana sanyaki mantuwa,kofar
yau ma na risketa a bude baki tsoron azo a tafi
dake?" Ta kwanto da kanta,kanmu ya hadu waje
daya tayii dariya"Kai yayana dama gani da tsoro
kana qara tsoratar dani." Mukayi murmushi. Na
dagata,itama na miqar da ita ina rike da
kafadunta,muka fuskanci juna,na sanya yatsa
nabi
zagayen lebbanta na zagaya dashi,sannan
nace"Koda baki gyara fuskarki ba bebina,kina da
kyanki wallahi kinfi burgeni ma." "Au daman idan
nayi kwalliyar bana burgeka ko?" Na girgiza
kaina"Ko kusa bance ba. Ya bebina?" "Lafiyarsa
lau."
"Madallah." Na daga kaina a hankali na bi bayan
Zahra
da kallo a yayin data tafi maida kwanukan abinci
kitchen,na maido dubana ga TV ina sauke ajiyar
zuciya. Ya dace dai na sanar da ita domin taje
dubo jikin mahaifiyarta. Sai kuma dabara tazo
min,bayan ta
dawo nace"Bebina." Ta dago kanta ta dubeni
bakinta yana mai amsawa."Na lura har yanzu
zuciyarki akwai damuwa ko?" Ta dan daga
kafada
cikin nuna alamu na rashin fahimta tace"Kamar
ya
yayana? Damuwa wace iri? Ni lafiya lau nake
amma meka gani?" Nayi murmushi na karkato
sosai ina
dora k'afa daya kan kujerar"Bebina babu yanayin
da zaki shiga da bazan gane ba,nasan har yanzu
zuciyarki bata sake ba tunanin anty kikeyi a
kowane
dak'ik'a." Tayi shiru kanta a qasa tana murza
zoben
dake hannunta,na cigaba da rarrashinta da
tausasan kalamai har ta kai da zubda
hawaye,abunda nake
gudu kenan. Na shiga goge mata"Why Zahra? Kiyi
hakuri idan na batamaki rai,I am just trying to
comfort you." Ta girgiza kanta tana murmushi
mai
ciwo"Ba komai fa yayana." Na sauke ajiyar
zuciya"Shikenan toh,a bar hawayen nan bana
kaunarsa ko kadan,yanzu dai na yanke,insha
Allah
zuwa gobe zamuje mu gaida antinmu shikenan
ko?"
Tayi dariya sosai,na tsaya ina kallonta"Me kuma
ya
faru kike darawa haka?" Ta matsa gefe kadan
tana
dariyar ta dubeni"Wallahi yayana dariya ka
bani,wai
fa ji yanda kake batun zuwa wajen anti,kamar
inda munje iya kulata zakayi." Nima sai ta bani
dariya,"Bangane ba?" Tayi dariya"Hum yayana
kenan,kadai san halin antin namu kake
mancewa,bana tunanin zata qara kallon Zahra.
Ta
manta dani." Nayi murmushi ina mai jin
tausayinta"Kada wannan ya dameki,uwa bata
taba mancewa da 'yarta,kina nan daram a
ranta."
Zahra
tayi murmushi mai kama da an tabe baki,saidai
bata
ce komai ba. Haka na share batun,na sanyo na
Badamasi akan ciwon bakin da yake na bataje
wajen
jamila ba. "Allah Sarki,gaskiya kam yayana baka
kyauta
ba,ya dace ace munje wajen jamila." Na dan
kama
kunnenta tana 'yar qara"Au ni zaki dorawa laifin
ko?
Kaji yarinya wato kin tsame kanki ko? Amma dai
baki tsira ba tunda gaba dayanmu laifinmu yake
gani." "Hakane." "Yauwa,yanzu dai fadamin me
kika fi buri kiyi a rayuwarki?" Tayi shiru tana mai
danne
dariyar"Yayana me kuma ya kawo wannan
tambayar?" Na dan ja kumatun"Inason na sani
ne,so
nake na kyautatawa Zahra ta." Ta gyara zama
sosai
tana murmushi"Wallahi yayana kaine burina
kuma
na sameka,abu na gaba na ga anti ta bar fushi
dani na karshe kuma na ganni na cigaba da
karatuna."
Nayi shiru ina dubanta,har na lura ta dan
tsorata"Zahra kenan,meye na tsorata baki
batamin
rai ba? Naji burinki,kuma ina mai tabbatar maki
insha
Allah zasu tabbata,batun karatu dama ina da
niyyar
maidaki makaranta amma ba yanzu ba sai kin
sauke." Na shafi cikin mukayi dariya,tayi d'an
tsalle
tana mai rungumoni"Kai yayana,amma naji
dadi,Allah Ya bar kauna." "Amin bebina."
*************
Muna tafe a mota na waigo na
kalleta"Zahra kenan,kada fa ki tsorata,ki sanya a
ranki insha Allahu anti zata saurareki kinji ko?"
Ta
sauke ajiyar zuciya tana murmushin yak'e a
hankali
kuma ta gyada kanta"Toh." Na gyada kai"Ko
kefa."
Na zagayo bayan na faka motar a k'ofar gidan na
bude mata murfin"Fito." A daidai lokacin data
zuro
k'afarta mukaji muryar Abubakar wanda a yanzu
ya girma yana da shekaru goma sha uku"Lah
yaya
zahra." Muka waiga muna dubansa,ya k'araso
yana
dariya,da saurinta itama ta fito daga motar tana
mai
fara'a. Ta dafa kafad'arsa"Lallai abubakar,ka
d'ad'a
tsawon k'afa. Shine ko lek'oni ma bakwayi ko?"
Ya
shafi kai yana dariya"Makaranta ke boyemu
sister." Ta harareshi"Makaranta ko ball?" Nayi
murmushi
bayan na rufe k'ofar"Yanzu ba abubakar din da
kika
sani bane malama,wannan nutsatstse ne."
Mukayi
dariya,abubakar ya gaisheni na amsa. Ita kam
mamaki kawai takeyi. Maganarsa ta katseta"Kice
kinzo duba anti kenan. Ai yanzu jikin ma babu
laifi da d'an sauki ba kamar jiya ba da ta wuni a
kwance." A firgice take dubana,shikenan ai tunda
ta
riga ta ji,bata ce komai ba ta maida dubanta kan
Abubakar tana mai yin gaba"Zo muje." Sukayi
gaba
na mara musu baya. Muka shiga saidai bata
falon,abubakar yace"Mai
yiwuwa tana bacci fa." Na mike"Ok Abba na nan
ko?" Abubakar ya gyada kai"Eh yana nan bai fita
ba
tukunna." "Ok,ina zuwa." Zahra ta gyada kai
sannan
ta mike itama"Muje tare." A falo muka
taddashi,yana
zaune yana ta budewa anti Abida wuta"Ke
wacece da baza'ayi maki kishiya ba? Ina ce
uwarki bayanta
na auri wata? Kuma idan banda abinki
abida,tsohuwar matarsa ce,yanzu ke kina nufin
yaji
kika yo? Toh sam bazan lamunta ba,bazan dauki
shashancin banza ba,kina dai gani yanzu uwar
taki
tayi sanyi,kuma idan ma ita ke zuga ki ki bar
gidan mijinki,ita inace ba'a gidansu take zaune
ba
gidan
aurenta ne. Maza yau ki tattara komatsanki ki
koma
gidan mijinki,zan kira anwar din yazo inason
ganinsa." Anti Abida ta mike sum sum ta fita,duk
a
wannan jawabin babu abunda ya dauremin kai
sai
jin da nayi inna tayi shiru asalima tagumi tayi
tana duban Abba jikinta a sanyaye. Ba shakka
komai
lokaci ne,gashi ta soma ganin ishara kan
'ya'yanta.
Bayan fitar ta Abba ya dan saki fuskarsa,muka
gaisheshi tare da inna,ta amsa tana 'dan
murmushi,kafin ta mike ta bi bayan 'yar ta. Abba
ya
maido dubansa garemu yana mai amsa
gaisuwarmu,gaba daya sai fara'arsa ta
dawo"A'ah
idonki kenan 'yar Abba?" Zahra tayi murmushi
tana
sunkuyar da kanta,"Kin manta da Abbanki,saidai
kuma akwatin ajiye sak'onni na wayata cike suke
da
sak'on gaisuwarki ko?" Mukayi dariya. "Toh kuna
nan lafiya dai?" "Alhamdulillah Abba." "Toh
masha Allahu,haka akeso." Zahra ta mike ta fita
yayi saura
daga ni sai Abba. Muna ta hira har yake sanar
dani
cewar yaya usman yana nan zuwa cikin wata mai
kamawa." Nayi murmushi"Allah Ya kawo shi
lafiya."
"Kuna waya dai da dan uwan naka?" "Eh amma
mun
kwana biyu bamu gaisa ba." Nan ya dan daga
murya"Haba Ahmed,ai ko shi baya kira tunda
kaine
k'arami ka dunga nemanshi kuna gaisawa,a haka
ai
sai zumunci ya lalace. Koda wasa kada ka dunga
la'akari da cewa kai kake kira bai damu da ya
nemeka ba ko wani abu can,shi zumunci abu ne
mai
k'arfi ba'a wasa dashi. Ka kula." "Toh Abba,insha
Allah zan kiyaye." Abba yayi murmushi ya bude
baki
zai k'ara magana muka jiyo ihun Zahra." Da gudu
na
fito,Abba shima ya taho,anti ce rik'e da belt tana
tsaye kan Zahra wacce ta durkushe tana kuka
tana
magiya,hakan ya fito dasu inna ma,saidai ban jira
komai ba na nufi Zahra na d'agata. A fusace take
magana"Kada ki k'ara zuwa gaisheni,na fadamaki
na tsame hannu akanki,kin zab'i wannan(ta
nunoni)
a kaina ko? Toh kije......""Ya isheki!" Abba ya
daka
mata tsawa,sai numfarfashi takeyi,daga gani
k'arfin
hali ne kawai irin na anti amma bata jin
dadi,Abba ya
matso"Nace ya isa,don Allah wane irin zuciya ce
dake haka da ko kadan bata da tawakkali?
Wallahi
ki kiyayeni,duk ranar da na k'ara samunki da
laifin
koda yiwa Zahra'u tsawa sai na koya maki
hankali,shashasha kawai,kina cikin halin rashin
lafiya amma baki saduda ba. Meyasa haka?" Tayi
shiru sai huci takeyi,na daga Zahra dake faman
kuka kamar ranta zai fita,Abba ya ja hannunta
suka shiga
falonsa. Anti ta maka min wata uwar harara gami
da
jan wawan tsaki,sannan ta maida dubanta ga su
inna"Magulmatan banza." Ta bankada labule ta
koma dakinta. Inna ta tabe baki tana rike
baki"Oh
wanda bai da laifin ma abun shafarsa yake?
Hum,Allah Ya kyauta." Ta juya ta koma ciki anti
Abida
ta bi bayanta. Na shiga na samu Abba yana ta
rarrashin Zahra,yana mata nasiha. Har saida ta
tsayar
da kukanta,ganin ta sauko,yasa shi yin
murmushi"Yauwa ko kefa 'yar Abba,Allah Yayi
maki
albarka." "Amin." Nan na rusuna"Abba zan wuce
kasuwa." Ya girgiza kai"A'a,ka maida Zahra
gida,ko
kuma ka kaita can wajen babar taka(Anti Aisha).
Nima fita zanyi,ban yarda da waccan sakarar
ba,yanzu saita k'ara b'ata mata rai." Mukayi
masa
sallama muka fito. A k'ofa na bude mata ta shiga
mota,na tsaya gaisawa da baba maigadi. Na
tsallaka saidai ban sameshi ba sai ma wani
dattijo dana
tarar,bayan gaisuwa na dubeshi"Baba fa?" Yayi
'yar
dariya"Ai ya tafi can kazaure,anyi masa rasuwa
ne."
"Toh waye ya rasu?" Kafin ya bani amsa sai ga
umar
ya fito daga gidan,mukayi musabaha
dashi,nace"Ashe rasuwa akayi maku?" Yayi dan
murmushi"Eh wallahi,matar malamin daya koyar
da
baba ce ta rasu,dama ta tsufa dakyar take
magana."
"Assha Allah Yayi mata rahma." "Amin,shima ai
bana
jin zai dawo,don daddy ya bude gidan gona a
can,yace baba zai zauna can." Na wangale
baki"Kai
madallah,amma nayi fushi da baba ko
shekaranjiya nazo unguwar nan mun gaisa bai
sanar dani ba."
Umar yayi dariya na lura yana cike da jin dadin
yanda na damu da mahaifinsa yace"Allah Sarki
yayana(kasancewar haka yake kirana,ya daukeni
tamkar dan uwansa)kada ka damu,bari na baka
lambarsa." Nayi murmushi"Toh." Bayan na kwafi
lambar a waya,na dubeshi"Nagode,saidai fa
wataran
dole naje kazaure don gaida Babana." "Ai kuwa
nima kwanan nan zanje kazauren nan." Nace"Toh
zuwa yaushe kenan zaka? Idan yaso sai na duba
na
gani ko zan samu lokaci muje tare?" Yace"Eh toh
sai
dai nayi magana da hajiyata,duk lokacin data ce
sai nayi maka magana." "Ok,shikenan sai na ji
ka."
Mukayi sallama na taho,hussaini direba har ya
iso
yana goge mota,muka gaisa sannan na shiga
mota.
Na dubi Zahra wacce ke faman saita fuskarta,na
gane dai kuka takeyi bataso na sani." Tausayinta
ya
mamayeni,na ja motar jiki babu laka muka bar
k'ofar gidan. Tafiyar minti hudu ta kawomu gidan
anti
aisha. Sai anan ne bayan na faka na juyo gaba
daya
ina dubanta,sannan na janyota jikina"Haba
bebina,ya dace ace kinyi shiru hakanan,kuka fa
ba
magani zaiyi ba. Nasan dole kiyi kuka,amma don
Allah ki barshi hakan,insha Allahu wataran sai
labari,na tabbata anti zata sauko. Kedai kiyi ta
addu'a
Allah Ya k'ara mata lafiya kinji ko?" Ta gyada
kai,na
sumbaci kanta sannan na saketa ina d'an
murmushi"Good girl,d'an murmusa na gani mana
tawan." Tayi murmushi kadan." Nace"Yauwa,muje
ko?" Na sanya hannu na bude mata,ta fita nima
na fito.


Zaharaddeen Shomar
Whtasapp 08168575100Amadu 2 part 13
Posted by ANaM Dorayi on 01:39 PM, 29-Jun-15
Under: Amadu
Anti Aisha ta karbemu hannu bibbiyu,a nan na
bar
Zahra na wuce kasuwa,sai bayan magriba na
dawo. A falo na same su suna hira,Zahra sai
tuntsira dariya takeyi. Na harde hannu a kirji ina
dubanta,gaba daya kaunarta nakejin tana
dawomin sabo. Sam basu lura dani ba,ni kuma
yanda naga matar tawa ta saki jiki kamar ba
itace mai damuwa a dazu ba yasa sam bana son
katse ta,anti aisha ta cigaba da bata
labarin,saidai kuma dana lura duk labarine na
'yan matancin ta a baya take bata. Sai can suka
ankara dani,Anti Aisha ta dubeni"Au,kai kuma
yau
babu sallama?" Na k'araso ina murmushi na
nemi
waje na zauna"Ina zaku ji? Hankalinku yana ga
hira." "Hm,kaidai bari ai yau Zahra ta rayamin
gidan nan." "Hakane,toh nidai ku hadani da
abinci
ko zan ga daidai." Anti ta mike"Su Ahmed gajen
hakuri,bari a kawo maka." Ta fita daman abunda
nake jira kenan,da azama na janyo matata na
shiga aika mata da sakonni,tana ta tuttureni,da
kyar ta fisge jikinta tana fidda numfashi ta koma
gefe tana mai hararata. Na bita da murmushi"Me
akayi?" Ta harareni tana kumbura fuska"Haba
yaya,idan anti ta dawo fa?" Cikin yanayi na
dubeta"Ke kika ja ai." Ta dauke kanta tana duban
k'asa jin motsin anti da tayi,anti ta k'araso rike
da plate wanda aka rufe da wani plate din,na
k'arba,ta zauna. Ina ci muna hira,anan har nake
mata batun samar wa Zahra 'yar aiki. Ta jinjina
kai"Gaskiya kam,ya dace a samar mata wacce
zasu zauna tare,yarinya k'arama dai haka. Zan
bincika mata." Bamu bar gidan ba sai da mijin
anti aisha ya dawo,mun gaisa sannan muka
tafi.
*********
Haka rayuwa tayi ta tafiya,yaya usman yazo
baifi sati ba ya juya. Kamar yanda mukayi da
umar cewa in zai je kazaure ya sanar dani. Hakan
kuwa,yana tashi tafiya ya sanar min,da iznin
abba,nayi sallama da iyalina na kaiwa Baba
ziyara har can kazaure,ba k'aramin dad'i baba
yaji da ganina ba,toh sai ince na fishi jin
dadin,saboda yadda suka karb'eni da hannu
bibbiyu. Haka na taho da tsaraba nik'i nik'i. Baba
yayi ta godiya har da hawayensa,na nuna masa
babu komai yanzun mun zama d'aya zumunci ya
riga ya k'ullu Abba ma yace a gaisheshi."
************
A kwana a
tashi babu wuya wajen Ubangijin talik'ai har
Zahra ta shiga watan haihuwar ta,gaba daya sai
komai ya gagareta,dakyar take tashi idan ta
zauna,duk da cewa a lokacin an kawo mata
yarinya k'arama wacce bata wuce shekaru goma
sha biyu ba,amma bata yi mata yanda ta so a
ayyuka sannan ga wani girma da cikin yayi,dole
ta sanya anti aisha tace ta koma gidanta. Ba da
son raina ba haka nan na hak'ura Zahra ta koma
wajen anti aisha,ita kanta tafison hakan. Don
wani sa'in idan naje da buk'atana sai ta
sanyamin kuka wai bana ganin yanda take ne?
Ita yanzu bata iya yin komai. Haka dole nake
hak'ura sai kuma daga baya ta bani hak'uri tace
ta amince. Gidan yayi min fadi babu dadi,hakan
yasa nake binta har can gidan anti aisha mu
wuni tare bayan na dawo daga shago. Wasu
lokutan kuma muna tare da Badamasi ko kuma
Bukar,idan kuma kewa ta isheni nan majalisar idi
nake zama nayi ta cin dariya. Watarana ina
kwance cikin dare wayata ta soma ringing,ganin
lambar anti aisha ya sanyani wartsakewa babu
shiri. Na mike na kafa wayar a kunne bayan na
latsa kore,saidai a nutse ta amsa min
sallamata,sannan tace"Ahmed kazo yanzu ka
kaimu asibiti."Duk da muryarta a nutse take
hakan bai hana ni jin tashin hankali da firgici ba.
Na bude sif na janyo jallabiya na zura na fice.
Har
na kai tsakiyar falo na tuna da mukullin motar,na
dawo na dauko duk na rude na fita..... Unguwa
tayi shiru kamar babu kowa,hakan yasa
cikin minti uku na iso gidan. A gaggauce na
sanya
akwatin kayanta,kawu ya bude suka shiga,yayin
da
muke gidan gaba mu biyu. A rude nake
tafiya,saboda kukan Zahra da nake ji har cikin
kwakwalwata. Anti Aisha ta katsemin
tunani"Ahmed wane asibitin muka nufa? Nayi
zaton inda take awo
zamu?" Na gyada kaina dakyar murya na rawa
nace"Eh nan zamu." "Ba na nan kusa kuke zuwa
ba?" Na girgiza kai"A'a,Get Well take zuwa,acan
janbulo." Gudu nake shatatawa kasancewar dare
duk da dai jami'an tsaro sun sha tsayar damu
amma cikin mintuna goma sha biyar muka iso.
Sun
karb'emu da hannu bibbiyu,aka shiga da Zahra
ciki,anti ta bi bayansu,ni da kawu nan muka
zauna.
Tunanina yana kan Zahra,zuciyata sai dukan uku
uku takeyi,kawu ya dafani"Kayi addu'a
Amadu,kuka
baida amfani,insha Allah zata sauka lafiya." Na
jinjina kai kawai,a zuciya ina fatan hakan. Ya
katseni"Ka
sanar dasu Alhaji." Na hau laluben aljihuna,na
dubeshi"Na bar wayar a mota." Kawu ya ciro
tasa,ya
mike yana mai danne danne,na maida dubana
ga
hanyar da akayi da Zahra. Bazan iya jurewa ba
saboda daga inda nake ina jiyo k'arar ihu da
salatinta. Na mike raina na k'una na sauko k'asa
na
zauna kan kujera a nan waiting room.hawaye
suka
zubomin,duk yanda na kai da dakewa amma ina.
Na
fi minti uku zaune,saidai kuma dole na mik'e na
koma saman bazan iya nesa da Zahra ba. Na
tadda
anti aisha tsaye tana yiwa kawu wasu bayanai.
Da sauri na k'arasa,tana ganina ta boye tashin
hankalin
dana hanga kan fuskarta"Anti meya faru? Ina
Zahrar?" Duk irin yanda take kauda kanta saida
hawaye suka gangaro mata,kafin takai ga
magana,sai ga metron ta fito"Ina mijin nata?"
Muka
dubeta na k'arasa da sauri"Ganinan." Ta gyara
zaman gilashinta tana dubana"Ok,matarka ta
jigata
bata iya haihuwa da kanta ba,dole sai anyi ma
CS. Ku
jira likita tana hanya. Kafin nan muje ka sanya
hannu." Gabana ya fadi,innalillahi!, Zahra CS
kuma?"
Daidai nan su Abba suka shigo,suka k'araso,ga
mamakina har da anti. A rude take
tambaya"Meya faru kuma? Ina Zahrar?" Anti
Aisha ce ta iya yi musu
bayani,sai ga likita ta shigo. Nan sukayi gaba da
metron,can kuma metron ta dawo ta kirani,anti
ta
biyomu. Har ofishin likita,nan na sanya hannu.
Anti
kuka takeyi iya k'arfinta,ni ma dai duk dauriyata
hawaye ke zuba daga idanuna. Likita ta fito cikin
shirinta na shiga CS,ta dubemu"Kuyi hakuri ba
kuka
ya kamata kuyi ba,addu'a zaku bita dashi,Allah
Ya
rabasu lafiya." Na gyada kai,shigarta ba wuya ta
fito"Waye yaya ahmed da anti amarya?" Mukayi
gaba"Gamunan." "Ok ku shigo tanason ganinku."
Da suari muka fad'a d'akin. Zahra gaba daya a
birkice take,hawaye ke fita idonta,gashinta ya
cukuikuiye,gaba daya kamanninta ya sauya kallo
daya zaka gane tana cikin mawuyacin hali. Ta
rik'o
hannuna tamau sai kuma ta saki ta ri'ke na anti
wacce ke ta kuka,murya dakyar take
magana"Mahaifiyata ki yafemin,ki
yafemin,bansani ba ko zan rayu ko zan mutu,ni
mai laifi ce a
gareki,don Allah ki gafartamin." Anti na kuka
tace"Na yafe maki Zahra,kada ki k'ara batun
mutuwar nan,insha Allah zaki fito lafiya." Zahra
tayi
dariyar wahala ta dubeni"Yayana kaima ka
yafemin."
Ina hawaye na dafa kanta"Har abada bakiyimin
komai ba,insha Allah zaki fito ki samemu da ranki
kinji ko?" Ta gyada kai,tana mai sakin hannun
anti
yayin da ta sanya 'yar k'ara,metron ta ja gadon
tana
fadin"Please kuna iya tafiya,kuyi hakuri ku cigaba
da
addu'a." Daga haka suka shige,hankalina idan
yayi
dubu ya tashi,anti amarya ta k'ara fashewa kuka
cike da tashin hankali tana fadin"Oh ni binta,na
cuci
kaina na cuci 'yata. Allah Ka fiddomin da 'yata
lafiya
na nemi gafararta." A gigice na fice,kai tsaye na
zo
zan wuce su Abba,da sauri abba ya rik'o
ni"Amadu
lafiya? Ya ake ciki?" Kawai sai na fashe da kuka
na
fada kafadar Abba"Abba don Allah kayiwa Zahra
addu'a kada ta mutu,bazan iya jure rashinta ba
kamar yanda na rasa iyayena. Ka taimakeni."
Abba
ya rungumi kafadata yana bubbugawa"Ya isa
hakanan Ahmed,ya isa,insha Allahu lafiya lau
Zahra'u zata fito,ka bar tashin hankalinka haka
kaji
ko? Komai na Allah ne. Haba Ahmed kamar ba
namiji ba?" Na dago ina share hawayena,yayi
murmushin
k'arfin hali"Yauwa kokaifa,maza tafi ka daura
alwala
kayi nafila ka kai kukanka ga Ubangiji,Allah Ya
fiddo
matarka lafiya kaji?" Na gyada kai,kaina a k'asa
na
sauka ina mai jin jiri yana d'ibana.*******
hNa shafa mintuna goma cikin sujjadata ina
kaiwa
Ubangiji mai kowa da komai kukana. Sannan nayi
sallama nan ma na dau lokaci ina addu'a sannan
na
shafa. Nutsuwa ta musamman ta zo mani,na
shuri
takalmana na koma cikin asibitin. A nan na dubi
agogon dake manne a bango,uku har da
mintuna.
Sai kuma na sauke kai na soma hawa benen. Su
Abba suna nan sai nasiha yake yiwa anti amarya.
Tayi zugum ta zuba tagumi tana sauraronsa,na
nemi
waje can jikin bango na jingina ina mai harde
hannuwana guri daya,ina duban hanyar da aka bi
da Zahra kamar dai zan ganta. Har aka kira sallar
farko,Abba ya dubeni"Ai sai muje masallaci ko?"
Muka fita nan muka bar su anti aisha da anti
amarya.
Bayan mun dawo bamu samesu ba,can sai ga
anti
aisha ta fito ganin fuskarta kamar wacce aka
yiwa
albishir da aljanna yasa naji wani mugun sanyi ya
ratsani. Ta dubemu tace"Alhamdulillah,an
ciro....." "A'a a'a ke kuwa ya zaki rigani fad'a ni
da nake
bukatar a bani goro?" Muka dubi metron wacce
naji
likita na kiranta da jidda,ta k'araso tana dariya,ta
dubeni"Toh angon k'arni,sai ka bani goro kafin na
sanar maka." Na sunkuyar da kai ina dariya,Abba
yace"Kada ki damu,nayi maki alk'awari,goronki a
hannuna yake." Akayi dariya,tace"Toh masha
Allah,ta sauka lafiya an samu tagwaye mace da
namiji. Sai ka bar kukan ko?" Mukayi dariya,ji
nayi
kamar na shid'e don dadi,su Abba suka shiga
hamdala da tambayar baby. Anti Aisha tace"Maza
Ahmed,ciro akwatin nan daga mota ana bukata."
Na juya na koma a gurguje sai gani na dawo,ta
amsa
tayi gaba. Ina ji Abba yana bugawa abokan arziki
yana sanarwa. Nikam gaba daya hankalina ya
tafi,so
nake kawai nayi tozali da matata. Bamu fi minti
uku
ba,sai ga anti amarya rike da bebi daya,itama
metron
tana rike da d'aya. Farin cikin dake bayyane kan
fuskar anti amarya shi ya tabbatar min lallai ta
saduda. Ta mik'awa Abba,metron ta mik'omin.
Cike
da jin nauyi nasa hannu na k'arba. "Masha
Allah."
Abunda na fada kenan,Yarinya kyakkyawa jawur
da
ita,sai yamutse yamutsen fuska take,"Little
Zahra." Na
ayyana a raina ina murmushi,na yi mata
huduba,sannan na mik'awa kawu,abba ya
mik'omin
namijin,shima sak kamar an tsage kara an karya
da
zahra,kodayake kamannin da nakeyi da Zahra
bazai
sa na gano da wanda tafi kama ba cikinmu.
Shima
nayi masa huduba. Saidai ban k'ara dubansa ba
na
mik'awa kawu wanda tuni ya mik'a babygirl din
ga anty amarya wacce bakinta ya k'i rufuwa har
abba
na tsokanarta wai ta rude ganin jikokinta. Ita dai
kunya ta hanata tofawa. Sai da gari yayi sha
sannan
na samu ganin Zahra. Lafiya lau na sameta,saidai
bacci takeyi na gajiya,hakan yasa muka koma
gida
muka barta da anti aisha da anti amarya. Sai
wajen goma na koma asibitin tare dasu inna da
su inna
larai da inna nafisa. Gwaggo taso zuwa saidai su
kawu suka hana ganin yanda ta kwana ciwon
k'afa.
Ina shiga nayi tozali da fuskarta,duk da ramar
data
d'anyi amma sai naga tayimin wani haske. Ta
saki
murmushi ta maida dubanta ga su inna. Nan aka
shiga gaisawa ana yi mata barka,tana amsawa
murya a dashe saboda bata iya magana sosai.
Bayan
sun fita gaba daya ne na samu damar k'arasawa
gareta,ina rik'o hannunta. Muka dubi juna muna
murmushi,sannan na kai dubana ga kyawawan
yarana da suke bacci a d'aya gadon"Kinga
yaranmu kyawawa,'yan biyu kyautar Allah." Tana
dubansu
itama tayi murmushi saidai batace komai ba. Na
juyo
na kalleta"Allah Ya k'ara maku lafiya,bebina babu
abunda zan yi maki daya wuce addu'a Allah Yayi
maki albarka." "Amin." Jin motsi yasa na mike da
sauri. Likita ce ta shigo,ta k'ara duba Zahra
sannan ta gargademu kan a dunga barinta tana
hutawa a bar
cika ta da hayaniya,na amsa da toh.***********
Sai da Zahra
tayi sati a asibiti aka sallamota. Babu batun
suna,sai
dai kawai rad'i da akayi a masallaci,macen taci
suna"Safiya"(Sunan mamana) shi kuma namijin
yaci sunan Abba(Mahmud). Saidai mata da bidi'a
sun
tsara zasuyi 'yar walima bayan an sallami
Zahra,hakan kuwa,bayan an sallameta da kwana
biyu suka hada gagarumar walima anan gidan
Abba. Ina shago sai yamma na isa gidan,muna
tare
da Badamasi muna kwasar hira cikin motarsa
bamu fito ba. Saidai muna hangen masu shiga da
fice,na
girgiza kai"Mata kenan,su dai komai nasu daban
ne.
Basu hutar da kansu,yanzu haka za'ayita
jagwalgwala yarannan da dauke dauke
Badamasi yayi murmushi"Kai ma banda
abinka,haihuwar fari dole ne dama ayi 'yar
walima. Yanzu ba gashinan ba,kowanne fuskarsa
fal da farin ciki ba." "Lallai kam." Na zaro waya
na kira Zahra saidai har ta katse ba'a dauka
ba,na k'ara dannawa shiru. Na ja tsaki. "Me
kuma ya faru?" "Ai illar kenan,kayi ta kiran waya
a k'i dauka,ita tana mancewa bata da lafiya?
Nasan tana can ta biye musu tana zirga zirga."
Badamasi ya tuntsire da dariya"Ahmed kenan na
Zahra,wai kai baka san sha'anin mata bane? Sai
dai fa ka hak'ura da wayar nan malam yanzu
haka ma ta manta dakai." Na k'ara k'uluwa,ina
mai kwafa"Ai shikenan,nidai in har yarinya ta
bari
aka jagwalgwalamin yara ranta ne zai b'aci."
Badamasi kam dariya kawai yakeyi,ya zaro
wayarsa yana fadin"Bari kaga yanda zamuyi." Ban
tanka mashi ba,sai kuma naji yana magana na
gane jamila ya bugawa,daga k'arshe sukayi
sallama bayan yace su fito tare da Zahra. Jin
hakan na dubeshi"Ka mance fa ba lafiya gareta
ba." Ya harareni yana mai bude motar"Ai
shikenan zauna." Ganin hakan nima na fito muka
nufi bakin k'ofar gidan. Tun tahowarta na kafa
mata ido ba k'akk'autawa ina dubanta cikin
shadda maroon. Don haduwa ta gama yinsa,har
ta tsaya gabana ban bar kallonta ba,tayi
murmushi ta juya tana gaida Badamasi. Ya amsa
yana zolayarta"Maman 'yan biyu." Tayi dariya"Kai
yaya badamasi." "Atoh k'arya ne?" Jamila ta
cafe"Baka k'arya honey." Sai a nan na dauke
dubana ga abar begena na dubesu"Sai dai ya
fada ba daidai ba kenan." Jamila tayi dariya"Eh
mana,kaima ai kasan halinshi." Nayi dariya,suka
matsa gefe,shige da ficen 'yan uwa yasa ban
sake da Zahra ba,ban samu mun gaisa ba
saboda
kowa yazo wucewa sai ya tsaya mun gaisa,hakan
yasa naji babu dadi,takaici ya isheni kenan dai
bazan sake da matata ba,na dubeta itama tana
dubana a raunane nasan tuni ta gane fushin
dake
kan fuskata. A dakile nace"Sai na kira." Ta gyada
kai,na kauda fuska daga dubanta"Saura kuma ki
bar wayar taki nayita kira ki k'i dagawa." "Bazan
bari ba." Tsayuwar mota ce ta sanya ni barin
wurin,ita kuma ta shige ciki don aiken da anti ke
yi na kiranta. Cikin mota na koma saidai k'ofar
bude take. Mai motar ya fito,itama wacce suke
tafe ta fito. Idona yayi tozali da Hafsa rungume
da baby wanda zaiyi watanni biyar. Sai lokacin na
lura ashe Suleiman ne,ta shiga cikin gidan,shi
kuma ya nufo inda nake yana murmushi. Daidai
nan Badamasi shima ya iso. Ya mik'omin hannu
yana mai sallama gareni,na amsa fuska a sake
nima na mik'a masa. Sannan suka gaisa da
Badamasi. Yayi min barka,na amsa na tambayi
iyalinsa."Lafiyarsu lau,ai kun kyauta bamu ji
haihuwar ba sai a jiya." Nayi dariya"Allah
Sarki,gaskiya munyi laifi amma kuyi hakuri." Yayi
dariya,"It's ok,Allah Ya raya mana." "Amin."
Muka amsa ni da Badamasi. Bai jima ba yayi
mana sallama zai tafi,Badamasi ya dakatar
dashi"A'a tsaya kaga yaran naka mana." Yayi
murmushi"Ok." Sai ga jamila rik'e da
baby,nusaiba na biye da ita rike da d'aya. Ashe
yasa ta kawo su. Suleiman ya karbi
daya,badamasi ya karbi daya. Na juya ga nusaiba
ina amsa gaisuwarta cikin fara'a nace"Nusaiba
sai kika b'uya ko? Ina faisal?" Tayi dariya"Yaya
faisal ai yana Dubai,tare da mama nazo. Wallahi
ina nan gidan naku ne dai Allah bai ban ikon
lek'owa ba." Nayi murmushi"Bakomai,amma
yanzu ko don yaranki ai kya dunga shigowa ko?"
Tayi dariya"Hakane." Suleiman ya dubeni"Masha
Allah Ahmed,Allah Ya raya kaga babies
kyawawa." Nayi murmushi,na karb'i bebin da
yake mik'omin,sannan ya amshi na wajen
badamasi. Hakan ya ganar dani macen ce a
hannunsa farko. Na k'ara tsura mata ido,soyayya
irin ta d'a da uba ya shigeni. Na sumbaci
goshinta sannan na mik'awa Badamasi. Sukayita
min dariya suna zolayata wai na tsufa. Nima
dariyar nake,daga karshe mukayi sallama ya tafi
su jamila ma suka koma. Badamasi da yabi
motar suleiman da kallo ya juyo"Ikon Allah,ashe
dai so ya kan maida mutum mahaukaci,dubeshi
kamar bai taba laulayin so ba." Na tuntsire da
dariya sosai"Kai dai dan iska ne,meye kuma
laulayin so?" Cikin dariya yace"Eh toh laulayi
mana,yanzu tunda kwalliya ta biya kudin sabulu
ai kaji shiru." Nayi dariya"Ni gwara da hakan ma
ta faru,ko yanzu na gano mai sona na hak'ik'a."
Mukayi dariya.************Sai magriba na k'ara
shiga gidan amma takaici
kawai na shak'o,Zahra sunyi bacci.
Haka nayita zaman gauranci har sai da suka cika
kwanaki arba'in suna zaman gida saidai kullum
naje
mu gaisa mu d'anyi hira. Ranar da zasu dawo
kuwa ji
nayi kamar an mini albishir da gidan aljanna don
kuwa da wuri na rufe shago na tafi gida. Bayan
ta
bude k'ofa muka tsaya kallon kallo da ita,shigar
da
tayi da kwalliyar kan fuskarta sune suka tafi
dani,tayi
wani irin fari mai kama da an lumshe ido tana
murmushi k'asaitacce"Sannu da zuwa yayana."
Na
k'araso ciki na rufe sannan na janyota sosai na
shiga amsa gaisuwarta cikin wata siga daban.
Har saida
k'afafun mu suka kai ga kasa daukar nauyinmu,a
gajiye na saketa ina fidda numfashi. Ta sunkuyar
da
kanta na ja hannunta muka shigo falon sosai ina
mai
murmushi nace"Yau ango nake,hope an yimin
tanadi mai kyau?" Ta harareni kad'an har ma ta
ban dariya,na saki hannunta ina mai lek'a cikin
gadon
yarana,baccinsu kawai sukeyi babu abunda ya
damesu na sauke sassanyar ajiyar zuciya..... Na
dubi Zahra"Kinga yarana ma sun san yau
mominsu ta daddy ce." Tayi 'yar dariya saidai
bata ce
komai ba. Daren dai munyishi ne cike da farin
ciki. BAYAN SHEKARU HUDU
Rayuwa ta chanja min. Komai ya dawo sabo a
wajena. Gani ga matata abokiyar rayuwata
sannan
ga kyautar Allah dana samu har biyu. Amir da
Amira
kenan,kamar yanda mahaifiyarsu ta zab'i a kirasu
dashi. Sai ya zamto tamkar babu wani bakin ciki
dana tab'a yi a rayuwata,ni Amadu na manta da
wani
abu wai shi MARAICI. Iyalina sune farin
cikina,bani
mantawa da Abba yanda ya zamemin uwa
ubana,addu'a da fatan alheri ga Anti Aisha bazai
yanke ba daga gareni. Na k'ara gyara zamana
kan
kujera ina duban Zahra wacce ke sallah amir da
amira na gefenta suna kwaikwayonta duk yanda
tayi sai suyi saidai wurin sujjada sai su malale
kan
carpet,nayi 'yar dariya cike da farin ciki,ina jin
wani
nishadi a raina. Jin sautin dariyata yasa
hankalinsu
yayo gareni,amira ta soma tasowa a guje ta fado
cinyata,na dagota na dorata sannan na daga amir
shima ina mai hade shi da jikina ina dariya"My
angels
ya kuka wuni?" Amira wacce tafi amir wayo da
surutu ta cafe"Lafiya lau Abba." "Ke bana hanaku
cewa Abba ba? Daddy zaku ce daga yau." Na
dago
na dubeta ashe har ta shafa,cikin murmushi
nace"Sannu Doctor Zahra,har bokon ya soma
ratsaki ko? Wannan idan kika zama cikakkiyar
Doctor ya
kenan? Kada suce daddy sai Papa??" Muka
sanya
dariya ni da ita,yaran ma duk da basu fahimci
komai
ba suka shiga yinta.************************
Na faka mota k'ofar gidan gwaggo. ana ganinmu
kaga happy family. Anko mukayi da Zahra na
shadda koriya mai duhu. Yaran ma sun sha
kyau,da
gudu sukayi cikin gidan,na dubi Zahra muka yiwa
juna murmushi muka bi bayansu. A falon Abba
muka samesu,suna ta yiwa abba hirarsu ta
jagwalgwalo yana dariya yana fadin"Kai dai ka
d'agamin k'afata,so kake ka k'arasamin ne?
Barni da
" Akayi dariya,muka gaishe dasu anti da inna.
Inna
ce ta bashi amsa"Toh banda abinka ai gwara shi
angon namu ya hau da dai wannan kishiyar."
Abba
yayi dariya"A'a,ku dai kishi kukeyi ta fiku kyau da
iya kwalliya,yanzu ke kina k'arama a baya ma
bakiyi
wannan adon ba." Muka k'ara sanya dariya,anti
tace"Rabu dashi dai hajiya,duk wacce zai samu ta
bi
bayanmu." Cikin dariya nace"Anti kudai kawai
kishi
kukeyi." Inna tasa hannu ta dauki amir,anti tana
murmushi tace"Ina fa zamuyi kishi? Dadin abin
mu dinma ai muna da miji." Akayi dariya,gida
yayi
dadi
sosai,koda na tashi tafiya kamar kada na tafi
naji,haka Abba ya matsan dole na mike don zuwa
bakin aikina. Zahra ta yo min rakiya,muna isowa
zauren na matseta a jikina"Zanyi missing dinki."
Ta
harareni kadan tana dariya"Kai yayana,kaida
kodayaushe muna tare?" Na sauke ajiyar zuciya
ina
murmushi"Bazaki gane ba,amma naso ace zuwa
yanzu kin fahimci idan son samun Ahmed ne ya
kasance kowane lokaci yana nan mak'ale da
Zahrar
sa." Tayi murmushi ta dago tana dubana"Ni kuwa
nasan waye yayan nan nawa,wanda nake
damuwa da damuwarsa,nake farin ciki da farin
cikinsa. Ni
kuwa nasan waye yayana uba ga 'ya'ya na.
Fatana
Allah Ya barni dakai har k'arshen rayuwata." Ta
k'ara shige mini na rik'eta gam ina sauke ajiyar
zuciya akai akai,nace"Bebina kin tuna lokutan da
Ahmed dinki ke fama da matsalar cikin gida dana
waje? 'Yan uwa? A yanzu idan kin duba rana
daya
Allah Ya chanjawa Ahmed rayuwa,Ya soma da
mallaka masa ke,sannan Ya gyara zamantakewar
iyayen Ahmed da Zahra. Ya k'ara azurtamu da
yara
biyu masu tarin albarka,ba anan hukuncin
Ubangiji
ya tsaya ba,saida ya shirya Ahmed da yayyensa
wadanda a baya suka daukeshi ba a bakin komai
ba. Yau komai na bakin ciki ya zama tarihi a
rayuwar
Ahmed. Bazan tab'a mantawa da Badamasi ba
domin
shima ya taka rawar gani wajen daukemin
damuwa
ta hanyar nasiha da rarrashi. Allah Ya sauki anti
aisha
lafiya,fatan alheri gareta bazai yanke ba. I love
you so much my baby,shigowarki rayuwata alheri
ne
wanda har gobe ina ganinsa. Allah Yayi maki
albarka." Zahra ta k'ara manne jikinta a nawa
tana
fadin"Amin yayana." Ganin muna shirin fad'awa
wani hali na tuna a inda muke,na matsa"Ke kinga
zanyi abun kunya ko?" Tayi dariya"Nidai kam ba
ruwana." Na ja hancin"Ki shirya daren yau sai
mun
samu little Zahra insha Allah." Ban saurari
cewarta ba
nayi gaba,saidai furucinta dole ya tsayar
dani"Lallai,nikam ba yanzu ba." Na waigo"Ai
kuwa
zan kawo maki 'yar Alhaji ba kowa ku zauna tare
kinga sai ta haifomin 'yan uku." Ta biyoni tana
kukan shagwaba nayi saurin ficewa ina dariya.
ALHAMDULILLAH!


ZAHARADDEEN SHOMAR
WHATSAPP 08168575100
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *