Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, January 18, 2018

farar haihuwa

adsense here
[8/22, 2:48 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWA💰1

Bismillahir Rahmanir Rahim



Kai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin halin da kanwarta take ciki. Inna Uwale dake zaune a kan tabarma ta daga hannu sama idanunta duk sun ciko da hawaye tace Ya Allah ka bani farin jika ko wanne iri ne. Ya Allah fari kyakkyawa kamar ni. Zulai aminiyarta tace amin amin Uwale ai ranar sai munyi sadaka. Tani dake kai kawo da sauran matan da 'yan uwansu ke cikin dakin haihuwar suka zuba mata ido. Ta kuwa cigaba da adduar farin jika kamar yadda ta saba. Cikin kunar rai Tani tace amma Uwale baki da mutumci ko kadan. Kanwar tawa tana ciki rai a hannun  Allah kina wani fatan a haifa miki farin jika. Farin jikan yaci.....bullowar mal Yakubu yasa tayi shiru ta share hawayen bakin cikin da ke shirin sauko mata. Ita kuwa Inna Uwale tace ashe baki da kunya Tani? Ban girmi uwarki Baraatu ba? Ita dai Tani shiru tayi don tana gani mutumcin Mal Yakubu mijin kanwarta. Yayi gumi sharkaf saboda tafiyar da yayi zuwa asibitin a kafa bayan dan Tani din ya bishi gona ya sanar dashi halin da ake ciki. Ramlah da Sadi suna ganinsa suka mike suna murna suka tsaya a gabansa. Daukar Sadi yayi itama Ramlah tasa kuka sai an dauketa. Tana kukan bata sani ba ta taka kafar Inna Uwale. Wata kara ta saki kafin ta hankade ta ta fadi kasa. Matsa can gun yar uwarki, shegiya baka mummuna. Mal Yakubu yace haba inna a nan din ma. Tani ta dauke ta tana goge mata bakinta da yasha kasa. Yarinya sai kuka take. Yo ba kaine duk ka cuceni ba dan nan. Mata aka sami abin kallo jin yadda Uwale ta bude murya. Ta cigaba dube ni nan ga fari ga kyau haka Allah Yayi ni tun kuruciya don ma girma yazo. Ta daga siririyar kafarta ta hagu wadda shan inna ya shanye tace da wannan Allah Ya ragewa aya zakinta duk kyan dire na ban sami mijin arziki ba sai ubanka. Allah dai Ya jikansa. Babu irin adduar da banyi ba da cikin ka don ka fini sanin baki ne. Allah Ya taimake ni na haifo ka fari tas ga kyau. Sai hawaye shar suka sauko mata ya durkusa kasa don Allah Inna kiyi shiru. Sauran matan dake wurin suna ta kallo an sami labarin kaiwa gida yau. Yaron nan da yake mai bakin kashi ne ya rasa wadda zai aura sai yar maiduguri. Wallahi kunga wannan yayar tata ta nuna Tani har ta fita haske. Kalarta fa kamar dauda yadda dai kuka ga 'ya'yan nan. Ba yadda banyi ba har da kwanciya a asibiti duk don a fasa auren yaki jin maganata. Ga haihuwar balai duk shekara. Yanzu wannan cakurkurar, ta nuna Ramlah  zaayiwa kani na biyu. To ni mijina ba arziki har ya mutu shima dan babu. Ni kuwa kafin na mutu sai naje makka da kudin jika ko na mijin jika. Haka kawai yadda nake da kyan nan bazan bar baya bakikkirin ba. Mal Yakubu ya share hawayen idanunsa. Inda sabo ya saba da halin innarsa amma irin wannan a cikin mutane ta gama zubar masa da mutumci. FARAR HAIHUWA COMPLETE
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *