Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, January 18, 2018

KAINE GATANA- hausa novel

adsense here
"Yarinyace matashiyar budurwa wacce bazata wuce shekara sha hudu ba,s "sanye take da wata kod'add'iyar atamfa riga daban zani ma daban, kanta d'aure da d'ank'wali irin mai santsin nan d'uk'un d'uk'un take kayan sunyi Bala'in daud'a sai tsami ne ke tashi ajikin ta, bak'ace sosai, tanada tsawo amman ba sosai ba. Kanta d'auke da bokiti da alamar ruwa ta d'ibo, sai sauri takeyi ruwan cikin bokitin na zubowa yana jik'a mata jiki,

"Sannu da aiki goggo" Dan uwarki sai yanzu kikaga damar dawowo?" tunyaushe kika tafi d'ibo ruwan kinje kin tsaya yawon iskancin naki shine zaki wani shugo kina min sannu!" aikece da sannu  bani ba dan kece agajiye,  anya kuwa kausar kina tsoron yanda k'arshan ki zai zama kuwa?" ace yarinya k'arama dake amman kinsan ki ringa bin maza!?"  kai ni talatu wannan jaraba dayawa take wannan wani irin bala'i ne haka, kai!!" Allah yasauwaka maki. Shegiya munafuka kallo na kika tsaya yi bazaki sauke ruwan ba saikin kwaro minshi ajiki dawannan sanyin iyyee!!"

"Dasauri tafara k'ok'arin sauke ruwan akanta aiko nan bokitin ya subuce yafad'o k'asa dama bokitin roba ne nan ruwan ya malale ak'asa. Ciki da masifa goggo ta mike ta shak'e kausar ta had'a ta da bango tashiga jibga saikace tana bugun k'ato, "dan Allah gaggo kiyi hakuri wallahi bada gangan nayiba fad'owa yayi kiyi hakuri" saida taga jini nafitar mata hanci da baki sannnan ta k'yaleta haka nan taci gaba da d'ura mata ashar, kuka kawai kausar keyi, fice min daga gidannan karki sake ki shigo batare da sabon bokiti naba yar'iska kawai, haka kawai yarinya kinzame min jaraba babu dangin iya babu na baba kullum ina ciyar dake ina shayar dake amman ke kullum burinki ki bakanta min rai kiringa jawo min asara!" to wallahi bazan k'ara yarda ba duk sanda kika min asara saikin biyani wallahi nagaji da adashin da babu k'wasa zaki fice kosai na shake ki kin mutu!" bakar banza da wofi kawai wacce tayi gadon mugun hali, "dagudu kausar ta fice tana kuka abin gwanin ban tausayi..................... KAINE GATANA COMPLETE
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *