Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, June 4, 2018

Birnin matsafa complete hausa novels

adsense here
Birnin matsafa complete hausa novels

Under: Birnin Matsafa
Firgigif,nayi natashi dalilin mafarkinda nayi nayo
yafi na kullum, saboda kyakkyawan saurayinda
nake mafarki kullum nesa dani yana kirana yau
na isa gurinshi, kuma sai gashi yacanja
halittarshi ta sauya daga mai kyau ya koma
kamar dodo.
Salati nadinga yi nan nasamu na mike koda
nadiba ago go karfe biyar da rabi na safe,take
naje na dauro arwallah nagabatarda sallah.
sanannan naroki Allah daya kareni da wannan
mummunann mafarki danayi,ina gamawa na
shirya najawo trouly dina dana kimtsa kayana, na
tafiyarda xamuyi nida yan uwana. falo nasamu
kowa suna break fast, cikin ladabi nagaida
mahaifana, sannan najuya gurin yan uwana,
salma da khadeeja suma nagaidasu, sukakarba
ba yabo ba fallasa.bandamuba sabida nasaba da
haka,daddy yafara yimun dariya as ikram kice kin
matsu harda trouly kin jawo, murmushi nayi,
nace
daddy bana son nakoma ne shiyasa nafito
gabadai, nan mummy ta amsa da to meyasa
sameki naganki wani shuru, lah mummy ba
komai, aa ikram keda idan xakije kano gurin
gwagwanki kowa sai sai ya sani hatta makota
amma yau kin wani kakkame ko bakyada lpy,
haba daddy ai ita ba yarinyace balle ace idan
batada lpy bata saniba,salma ce ke maganar tana
hade fuska, uwaki nace ina ruwanki, karkisake
shiga xancenda baa sakakiba. shuru tayi tana
kunkuni,murmushi nayi ina mamakin wannan
kiyayyar dake tsakanina da yan uwana sai kace
ba ciki days muka fitoba.daddy ba komai kasan
halin rauyawa amma ni lpy na qlw, to shikenan
iki
na,
Idan kungama Ku tafi Allah ya kaiku lpy sai dai
ina gargadinki ke khadeeja ki bi hanya mai kyau
kinji, kuma bana son biyebiye, saboda badan aiki
daya mani yawaba,isah driver bayanan gashi
tafiyar taxama dole da babu abinda xaisa na
barku kutafi har kano Ku kadai, sobada haka Ku
kiyaye,khadeeja bands gudu a hanya, to daddy
tace. sannna a kula mani da autata, mummuyn
yara mexakice masu aa banda nacewa duk kace
kawai dai su kula, sannan k salma kar ki yadda ki
takurwa autata,turo baki tayi komai auta auta
saikace wani gold ai tafi ma gold inji daddy marar
kunya to inji kinmata wani abu, nidai komai
banceba sibada Allah yasani duk jikina ya mutu
da tsfiyarnan, amma bayadda na iya tunda
gwaggwo ce ba lpy dole mije mu dubata,
Da haka dai mukayi sallama da iyayenmu ni
harda
kuka nayi muka dauki hanyar kano, jikina duk a
mace. a hanya haka su anty salma suka dinga
xagina ba ko kakkautawa amma nayi shuru ban
tanka masuba
Asali
Alhaji mustapha mutun ne mai dukiya sosai, duk
dawainiyar yan uwanshi dake kano shike
masu,shikadaine ga mahaifansa,mahaifinshi
malam idi yarasu tun mustapha nada shekara
8 ,sai mahaifiyarshi tacigaba da kula dashi
sunsha gwagwarmayar rayuwa amma daga baya
suka mike dama ance mahakurci
mawadaci.saboda gwaggwao tadage yayi karatu
inda yafito egenaer babba. yana kula da gwggwo
sosai, yayanshi 3mata khadeeja ce babba sai
salma sannan ikram. mahaifyarsu yar agdez ce,
shiyasa suka dauko kyanta amma kuma ikram,
tafisu kyau sosai, sabida komai ikram nada.
farace tasa ga hanci, d dan karamin bakinta ga
hips d dukiyar fulani. abin baa cewa komai.
Ikram mutunce mai saukin Kai batada tsiwa bata
d fada batada rowa ballae jijji dakai, sabanin su
khadeeja da keda jidakansu babu abinda ke mata
haushi dasu irin wulakanci kowaye kai komai
girmanka xasu wulakntaka su cimaka mutunci
wanda shine sanadinda suka sakamu cikin
rayuwa mai wahala wacce bantaba ganiba ko jin
labari a rayuwata. su ddady sunyi iya kokarinsu
amma abin nasu axxemun ne, shiyasa bama shiri
dasu basa sona akan INA gaya masu gaskiya
saidai kullum suta xagina. Kokadan bansan dadin
yanuwaba idan dai banaje kano ba gashi banada
kawaye.amma duk da haka banada damuwa.
Damuwata dayace mafarkinda nake.kuma narasa
wanda xanije ingayawa.
Tafiya muke suna firar su ni kuma na lumshe
idanuna INA sauraren kiraar sudex danasa a
kunne na,baya naji munyi wanda saida na nayo
gaba kuma INA salati.Ban Ankara naji salma su
anty salma na xunduma ashar, koda nafito inga
meya faru dayake sun rigani fita, tsohuwace
durkushe tana makyarkyata, tana basu hakuri
amma basudaina xagintaba nan nace haba anty
khadeeja kudaina zaginta mana tafayi kama
kunne daku amma akan dan abu kalilan kudinga
zaginta.eyyeh to uwarmu yimana fada inji anty
khadeeja itakuwa anty salma cikina tayi tana
duka an mata fadan, tunda dabbce ita bata san
metakeba daxata xo ta hau titi sai kace hanyar
ta ubantace baki narufe INA subuhanallahi anty
meyayi xafi haka,anfada dama ni nadanne kan
kaxamar dattijuwarnan, inji anty
khadeeja,kamama tsohuwar nayi ta tashi INA
bata hakuri
Murmushin karfin hali tayi tace bakomai
yarannan
indai duniyace, k tsohuwa kama bakinki kanji ko
karki mana maganar banxa da bikini mai doyi inji
salma uwar rashin kunya hanji suka dade suna
dariya,ji ita waccan kaxamiya harta iya ma
tabata MTS WWW salm taja tsaki ,k salma mije
dan Allah idan baxato shigo mu wuceba nahada
da ita na take, nkm bayan kuka babu abinda
nake,
NaNtshuwar tajaye daga hanyar tana magana
badai ni kuka wa rashin kunyaba to xaku ga
karshenku, ba abinda xamu gani sai alkhairi. NaN
nakara bata hakuri muka wuce saida khadeeja ta
tattara kura ta xuba mata, INA hangota tana
kakkabewa har nadaina hangota,
NaN suka dawo kaina suna xaxxagamani masifa
shuru nidai nayi, har Allah yakaimu kano lpy,
kowa sai murnan ganinmu yake, hardai ni dayake
duk anfi shiri dani dan kuwa Nice mai kulasu,
sarakuna tsiwa kam yatsine yatsine kawai suke.
Gwggwo dai taji sauki alhmdlha nan muka
haufira dayake tana sona sosai kullum addua
take mini Allah ya bani miji nagari, nan xanyi
dariya ince ameen
Muna haka anties din suka shigo NaN gwaggwo
tahau masu masifa, waiku yaushe xaku fitarda
maxaje kuyi aure, tab gwwggwo aurefa eh
meneneto ko baku isabane ,nan salma tacigaba
wlhy ni kimadaina duwata dan bayanxu xanyi
aureba saidai ko kila anty khadeeja ita ta
fashion,ido anty kahdeeja ta xaro wa tab Allah y
kiyaye.
Baki gwaggwo tarike lallai yaranan rashin
kunyarku yafi karfin tunanina to ko ubanku bai
isaba balle Ku kananan kwari, cenake ko wacenku
ta kammala karatunta amma kememe kunki
aure.
NaN na amsa amm gwaggwo kinfasan aure
lokacine dashi da lokaci yayi xasuyi, naji iki amma
ai daniya kuma to futsararrun yaranan basuda
niya barni nacimusu mutunci.mtsswww sukayi
suka bar falon gwaggwo sai fsman jidalin take.
Da kyar dai muka yi satinda muka xo da niya
muka dauki hanyar abuja domin komawa
gida,bamu ankarba ba muka sake cin karo da
tsohuwarnan da muka tashi kadewa, NaN
gogayen suka fito da niyar sumata duka amma
mexamu gani canja wa halittarta tayi tadawo
yarinya kyakykyawa take muka shiga kaduwa
sarakunan tsiwa sun kusa su suma dan tsoro
nice ma nake ta addua cikin tsawa take magana
duk wuri sai amsawa yake kuma cikin ikon Allah
ba ko motarda tabiyo. Dama nagaya maku
xakuga karshen rsshin kunya, mu baa mana
rashin kunya a gama lpy ,saboda haka
kushiryawa abinda xai biyo baya.
NaN take iska ma karfi ya taso, ga wani haske
duk ya rufemu su anty salma sai kuka suke suna
bata hakuri nikuma kwalla kawai nake ina
addua,amma INA abu sai karuwa yake bama
ganin komai illah dariyarta da muke ji mai
raxanrsuwa. take duk muka xube bamusan inda
muke ba.
Da salati na Mike amma jikina duk ciwo yake duk
nakasa motsawa, maexan gani wani irin dauri aka
yimana, su anty suna kwance kamar matattu,
suma daddaure.
Salati nadingayi ina kuka meyasamemu ne nan
natuna abinda y faru, innalillahiwainnailahirrajiun
nace shikenan mun mutu bamuyi bankwana dasu
daddy ba, nan nakara fashewa da kuka,nan su
anty suka tashi, ashe ma ni nawa mai saukine
dan kuwa su harda shureshure suke suna kiran
su mummy.NaN wani kato ya fito yana mana
tsawa, take muka kama bakinmu, jan mu ya
dinga yi,har muka isa wani babban birni wanda
muka kasa gane inane dan kuwa kamar ginin
turawa kuma kamar na chaines,
Janmu kawai yake har muka isa bakjn gate din
wanda akayi da luuluu sai kyalli yake, mutun
kusan ashirinne suka bude gate din mukuwa sai
kallo muke, kowanmu yarasa bakin magana kawai
xaxxarw idanu muke,mutanen sai kallonmu ake,
sturarsu ma dabance mai kyaun gaske suma
haka suke da kyan,ko ina kaduba mutanenne, d
yayansu, ga dabbibbi halitta iriiri saboda daga
cikin dabbarsu hadda mai tashi sama akwai, irin
wanda muke gani a film.................

Zahraddeen shomar
Whatsapp 08168575100


Birnin Matsafa 2
Posted by ANaM Dorayi on 05:42 AM, 21-Jul-15
Under: Birnin Matsafa
Wasu suna tshi sama akwai, irin
wanda muke gani a film, ga takobi da wukake
iriiri kai ince maku shigarsu da komansu kamar
wadanda sukyi marlin, sabida irin kayanda
kejikinsu kenan haka Kuma gininsu, sai
harkokinsu suke, ga makera nata kere krensu ga
kuma mata na harkokinsu saidai komai da suke
da tasfi sukeyinshi,sabida duk aikinda suke alama
kawai sike da hannunsu sai kaga akin yana yin
kan shi.
Wata mata mukagani tana wanki amma kuma
hannuta ne kawai take juyawa tana magana saiga
wankin yanayi,wani mutun Shikuma magana
kawai yake ga kifi gabanshi da wuka amma kifin
yana gyara kanshi,kaikomai bada tabawa amma
kuma aikin yanayin kanshi ido nabude nasake
budewa INA kallon ikon Allah anty salma kuwa
suma tayi nan kawai mukaji yayi wata magana
saiga keji irin wanda ake saka tsuntsaye yafito
ankada anty salma mukuma sai janmu ake muna
tafiya.
Abinda yafi tayar mani da hankali shine yadda
maxa ke saduwa da mata akan hanya kuma
tsirara, matane kwance ko ina kan abubuwa
masu
taushi da matsahi masu kyau ga yayan itatuwa
kusa da su, amma matan tsirara suke ko wacce
tana shafar alaurarta da xarar namiji yabiyo idan
tamashi sai ya auka mata, haka suketayi ni
runtse idanuna nayi INA addu tare da ambaton
Allah,INA mai tambayr kaina ina ne nan, ai kuwa
nan kuka yadawo mani sabo amma mutunnen
juyowa kawai yayi yayi watamagana saiga salatef
yarufe bakina.anty
khadeeja kuwa sai kukan xuci da nadama
take.duk mun fita hayyacin mu,haka mukayita
tafiya inda muka kai wani guri mai masifar girma,
ga dawaki harda masu fika fikai farare tas, maxa
ne kawai gurin ke koyon fada kowa da takobinshi
yana sarar dan uwanshi,abinda yabani mamaki
shine da ansari mutun saikaga ya taba gurin sai
ciwon ya bace kamar baa sareshiba,hmmmm
babbar magana nace cikin raina kenan basu
mutuwa shinwai inane, badai lafiraceba, dan
kuwa
lafira baa xina, kuma baa tsafi, nanan natuna
karshen kalaman matannan da takecewa xan
turaku wata duniya ta dabam kutafi BIRNIN
MATSAFA""""" dam gabana ya fadi, INA maimaita
sunan a xuciyata.,
NaN muka isa wani bangare wanda naso ace nim
nayi irin na anty salma wato insuma da irin
halittarda nagani, narasa gane menene shin
dabbace,mutunne, tauntsu oho, sai wani yawu
suke fitarwa mai yauki gasu da kanxanta tuni
amai ya taso mun, ga bakina kulle, aikuwa dana
yunkuroshi saiga abunda aka rufemani baki dashi
kasa take nadinga kwarara aman.
Su kuwa halittar sai hauka suke sun cixon junan
su.
INA gamawa,muka ci gaba da tafiya baa jimaba
itama anty khadeeja tafara nata aman, take ta
xube itama takasa tafiya, cikin inda yasa anty
salma itama ya sakata.
Haka muka cigaba da tafiya, ga yunwa gajiya ga
kallon abubuwan mamaki.NaN muka kai wani
tafkeken gini wanda ni ko a film bantaba ganin
irinshiba domin baka iya hango karshenshi gashi
kuma duk gold ne ajikinshi, shiba samaba shiba
kasa ba, wata sanda muka hau ta tashi sama ta
kaimu daidai kofa,abin mamaki tsuntsaye ne keta
waka. kofar ita t bude kanta muna shiga ta
kulle,NaN wani sabon kallo y tashi dan kuwa
guren kyanshi har ya wuce misali ga kamshi mai
dadin gaske,matane kyawawa kowace tana
aikinta amma d tsafi., muna kallonsu suna
kallonmu,har muka wuce,,babu abinda ni ke
tasuwa mani da hankali irin xinarda suke a fili ga
alamu waddan mutanen ko aure basayi kottara
yasamune, hmmm Allah yasa mudace, bumu yi
tafiya mai nisaba sai gamu kusa ga wani kogi,
ruwanshi fresh ne sosai, ga wasu fure masu kyau
acikinshi,abinda yabani tsaoro shine flowers din
suketa gyaran kansu inda yayi yawa su rage ni
runtse idanuna nayi dan tsoro,sai gashi nagi
antabani koda naxabura nabude ido ina salati
naga flower ce ta debo wani bangare nata mai
kyau tabani, cikin ikon Allah kuma sai na amsa,
INA amsawa sai ga hannu na da kunshi mai kyau
na xanen fulawa nan nakara tsaorata inata gugan
hannuwana amma abin yaki fita dole na hakura.
Da haka har muka isa wani katafaren gini shima
wanda yafima na farko kyau ga kaya irin na
sarakuna dawaki masu yawa kuma farare, sai
faman wanka sukewa kansu, tab mamaki, sai
gamu cikin wani kasaitaccen guri wanda naba
sunan falo, ga wani mutun mai kyan gaske da
kayan wadanda bantaba ganin irinsuba,yana
saman wata kayatattar kujera mai kyau,mutunen
dattijone amma dagani hutu ya ratssshi da
kyau,gefenshi kuwa wata kyakykyawar
matace,itama cikin shiga mai kyau ga kayan
fruits kusa dasu kuma su fruit din kowane kusada
iccenshi yake, wasu kuma cikin kwanoni na gold
suke ciki,da sun kare sai su sake xuba kansu
hmmmmm"""""".ga mutane kewaye da su mata
da
maxa saura kuma nacan na sanaarsu dana fi
tsana wato xina. muna isa gabansu mutunnen ya
kwancemu, muka xube kasa,saigashi yaxo kusada
anty salma yana tabata sai gata ta farka, ai kuwa
tana farkawa tafara xare idanu tana kuka tana
fixgefige nan suka dauki dariya, anty salma ke
fadin ina ne muke wai dan Allah nashiga uku ina
kika kawomune kigayaman cikin daga murya take
maganar, take mutunnenda yakawao mu ya daka
mata tsawa aikuwa ta nutsu mu dama zuciyarmu
ta bushe,
NaN yashiga yiwa mutune bayani ""wai yaga mun
fado daga bokanya kufana ta kawomu nan
sanadiyar rashin kunyarda biyu daga cikinmu
suka mata, nan diyan hanjinmu suka kada, muka
shiga kallon kallon wato bokanyace muka hadu
da ita, nan nadinga kuka itakuwa dan me xata
mana haka bayan tasan mu ba irin halittarsu
bace dama kashemu tayi muka huta yafi wannan
wahalar.
Nan yacigaba dayake cikin turanci yake maganar,
tace xata bayyana domiin ta yanke masu hukunci
saboda sun bata mata rai sosai,duk maganr nan
dayake gaban kingrda yake yana gurfanene gaban
dattijonan wanda naji yana Kira king laihanu,
wato sarkine wanan, hmmm"""yana gama fada
saiga wani irin haske take ta bayyana tana sauka
kamar tsuntsuwa,take gurin yadauki kuwa
kufana"kufana"kufana".har ta sauko tana
murmushi, taje gaban king laihanu tana gaisuwa,
nan tashiga basu lbrn yadda ta hadu damu da
irn
walakancin da su anty salma sukayimata,
Take aka fara jifarmu, nan tayi umarni d
hannunta ban anakraba sai gani gabanta sukuwa
su anty khadeeja aka cigaba d jifansu duk
anfitarmasu da jini,ni kuwa sai kuka nake ina
rokan suyi hakuri amma INA, dole na durkusa
gaban kufana INA rokonta da tayi hakuri naci
SAA kuwa ta saurareni tayi umarni da sudaina
jifansu aikuwa da guduna na isa gurinsu duk sun
galabaita jikinsu da fuska duk jinine, hmmm yan
gatan su mummy ne wai haka. rugumesu nayi
INA shafemasu jinin fuskokinsu, INA kuka anty
khadeja ce tayi karfin halin magana iki kiyi hakuri
da irin halinda muka sakaki nasan mu tamu
takare idan kika samu komawa duniyarmu ki
rokamana su daddy su yafe mana kanji, yaune
irin ranarda suke mana gudu, ashe wulakanci
bashida kyau wani k kewa ka gama lpy wani
kam""" shuru tayi takasa karkare maganr saboda
Adana,itakuwa anty salma banda kuka ba abunda
take idonta cike d nadama,nikuwa sai rubxarkuka
nake ina baxaku mutu kubarniba tare xamu
mutu
daku nima duk takshe Ku saita kasheni, baxan iya
jurar ganinku cikin wahalaba,.
Y Allah kamana mafita ta alkahairi da karfi nake
fadar haka duk abunnan da muke kallonmu
kawai
suke,
NaN kufana taci gaba da cewa xani hukuntasu
hukunci mafi muni duk da mu a duniyar bamu
horon kisa amma xan ladabbtasu tayadda baxasu
sake marmarin wulakanta waniba, saboda haka
na diba masu shekara talatin, INA hukuntasu,
sannan na maidasu duniyarsu, kekuma xan
maidaki duniyarku domin kikai labr, da guduna
naje gurinta narike kafarta mai taushin gaske INA
rokonta da ta barmu mutafi amma INA taki nan
nace nikuwa baxanje ko ina ba ina nan tare da
yan uwana haranan da shekara talatin idan Allah
ya kaimu, da kyar ta amince nan su khdeeja
sukayi sukayi da inje ta maidani naki,kije iki
kinsan iyayenmu xasuyi rashinmu amma wata
kila idan suka ganki xasu rage wani abu, ba llalle
ne mukai shekara talatin da rayuwaba, koda
munkai kina ganin nanda shekara talatin xamu
isake yan uwanmu da rayuwa,anty salma ko
shekara darine xan tsaya koda ko xan rasa
rayuwatane baxan iya tafiya nabarkuba baxan
iyaba,nan nakara fashewa d kuka, ikin daddy
kibarmu muda muka ja ruwa su jamu karki lalata
rayuwarki yadda tamu ta lalace,anty khadeeja ke
maganar,itakuwa salma cetake Allah sarki
gwaggo dama mundauki shawarta, nan fa
mukayita kuka har akaxao aka wuce dasu anty
..

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



Birnin Matsafa 3
Posted by ANaM Dorayi on 09:27 PM, 23-Jul-15
Under: Birnin Matsafa
Har akazo akawuce da su Aunty salma tofa nan
sabon kuka yatshi, nikuwa
kyakykyawar matanna wacce naji suna kirada
princess ikahala ita taxo tace xata je dani gurinta
da haka aka rarrabamu,akatafi dasu nima
princess
ikhala tawuce dani, nan ma nasha kallo amma
dayake tunanin yanuwana na raina ban tsaya
wani kalle kalleba, gashi su daddy su inata
tunosu ko wane hali xusu shiga idan suka
nememu suka rasa, sabon kika nasake rusawa,
nan ikhala taxo tana lallashina dayake kufana ta
gaya mata ta kula dani sosai, hannunta mai
laushi ta axa a kafadana tana lallashina nan na
ture hannunta ina kuka.kibarni nayi kukana idan
har baxaku sake yan uwana ba ki kyaleni.
Duk abunda na fada taji dayake turanci nayimata,
Hakuri tacigaba da bani, cikin harshen turanci
take maganr sunana ikhala kamar yadda kika ji ni
yar sarki ce, kuma inda Yaya prince kameer,
gwarxon namijine gashi kyakykyawa, yanxu haka
yanacan gurin yaki da wadansu dodonni dake
mana barna anan garin, wannan garin dakike
gani
babban garine ya samo asaline daga mutun biyu,
matsafane na gaske aka korosu daga birnin sin
sai suka yi tafiya mai nisa sannan suka kafa
wannan birnin har xuwa yanxu, nan nadago na
kalleta cikin mamaki nace mata shin yanxu dai
dai wani garine birnin nan naku na matsafa
yake,murmushi tayi sai da tsdade sannan tace
yana gaba ga birnin sin, ido naxare tareda dafe
kirjina INA salati ikhala kina nifin yanxu muna
kusaga bangon duniya.kwarai kuwa hakane,NaN
nashiga rero sabon kuka, kinga kiyi shuru kigaya
mani duk abinda kk so xan maki idan baifi
karfinaba, saboda naji kawai INA kaunarki da
tausayinki, ajiyar xuciya nayi, nace nidai abu daya
xakimun nasan kina tausayina kuma kina kaunata
ki maidamu duniyarmu nida yan uwana baxamu
iya rayuwa da kuba,fusakrta daure take magana
baxai yuba yan uwanki sunyi laifi kuma xaa
hukuntasu, dole kuma ni ingaya maki ban isa
naja
da maganr kufanaba sabida itace sugabar
matsafan birninmu ko bababna baya tsallake
umarninta.
Allahumma ajirni fi musibati,Rabbana atina min
ladunka rahama wa hayyilana min amrina
rashada, haka nadinga fada ina kuka ita kuwa
ikhala kallona kawai take, tarasa wane yarene
nake dan bata taba jin irinshiba. NaN nace yanxu
ikhala taimako daya nakeson kiyimun kigaya
mani INA xaa kaimun yanuwana, ajiyar xuciya
tayi, sannan naga ta jawo wani mirrow na gold,
tayi yan surutanta saiga su anty salma nagani
daure sai dukansu ake ana saka Kansu a ruwa,
NaN nafashe da kuka INA kiran su mummy,
Take natuno kiransu mummy baxai amfaneni da
komaiba, da sauri nace Mata ina xan sami ruwa
dariya tayi tana fadin birnin matsafa fa duk
abinda kk keso shike kawo kanshi,nan tayi
tsafinta saiga ruwa cikin wani dan dogon Kofi
mai kyau na gold,naga kamar baxasuyi arwallaba
amma sai natuna Allah yasan cikin irin halinda
nake saboda haka xaimin uxuri.
Arwalla nafara harnagama, nadauki wani mayafi
daga cikin kayanda kufana ta kawomun na
suturce jikina dashi mayafin maabuci laushine d
kamshi nidai na kwatanta alkibla na fara sallah
yinake ba kakkautawa har naji nafara gajiya
sannan nadaga hannuna sama INA rokon mai
samaniya da ya bayyanarda gaban iyayenmu
cikin gaggawa.itadai kufana sai kallona take dana
gama take tambyata wai menene nayi,murmushi
nayi na karfin hali duk dai nasamu natsuwa
sallarda nayi,amma bai hanani tuno yan
uwanaba
ikhala wannan itace ake Kira sallah, kuma itace
alamun musuluci,sallah tana dai daga cikin
rukunnan musulunci,
Ikhala kuwa sai kallona take kamar ta fahimci
abinda nake fada, NaN naci gaba da cewa
addinina musuluncine ikhala kuma addinina ya
horemu da duk lokacinda muka tsinci kammu a
cikin mummunan yanayi to muyi imani da
qaddararda ubangiji y nufe mu da ita.
Menene ubangiji ikhala ta tambayeni, murmushi
nayi
Nacigaba da cewa ikhala ubangiji shine wanan da
ya haliccemu yayi dabbobi, duwatsu, itace, sama
da kasa, ke duk wata halitta da ke cikin duniya
dama duniyar baki daya, mallakinshine, shine
mai
biyamana bukatunmu batare da munbiyashiba
kuma yana ganinmu duk inda muke a sarari ko a
boye, baya angaje baya bacci, duk lokacinda
muka kaimashi kukanmu yakan share mana
yanxu haka nakaimashi kukana kuma nasan xai
sharemun.
Ajiyar xuciya ikhala tayi dan randa take bata taba
jin irin wannan surutunba amma ga alamu abin
yashiga xuciyarta tofa,
Da haka dai ikhala tacigaba da kula da ikaram
kuma killuma saita nuna mata su salma da irin
wahalarda ake basu babban abinda ya tasuwama
ikram ha hankali shine yadda ake saduwa da yan
uwanta duk wanda yaga dama xuwa yake ya
sadu dasu ga kuma uwar wahalarda sukesha, duk
sunyi baki sun lalace saikace ba big girls ba
duniya kenan,
Ikram kam tayi kuka harta godewa Allah,har
rashin lpy tayi itama duk ta rame dik da
kulawarda take samu, amma baisa tadaina
tsanarsu ba akan wahalda yan uwanta da akeyi.
Banda sallah ba abinda take duk da basanin
lokacin sallah tayiba takan kwatanta kawai
tayi,tayi bKincikin rigar mutuncinda aka yagawa
yanuwanta duk irin tarbiyarda aka yi masu amma
yau ta tashi abanxa kaxxaman mutane wadanda
basuda ko wane irin addini bayan tsafi sun
ruguxa masu rayuwa
Yanxu takai inda ko kukan bata iya yi saidai
tayita fama da bakin ciki,
Tasaba da ikhala sosai dan har dan fita sukanyi
tare kuma kullum tana bisa cusawa ikhala
addinin
musulunci takan bata misalai da dama saboda ta
fahimciikala nada saukin Kai, xaune take bayan
ta ida sallah tana karanto abinda ta haddace na
qurani wato hixib hamsin dayake takusa haddace
qurani ne abinyafaru easy.
NaN taji wani irin bushi mai karfi kamar ana busa
kaho ko INA yadau kara sai kuwa ake,tsuki taja
MTS WWW mahaukata kawai nan taci gaba da
karatunta, saiga ikhala tashigo da saurinta taja
hanunnunta biye take da ita kawai harsuka isa
waje inda ake kuwa.wai ikhala INA xki je danine
muje kawai xaki gani, suna isa aka bata wuri
tawuce wasu mutanene majiya karfi sun riko
wadansu halittu masu Kama da dodo da sauri na
boye kaina bayan ikhala INA salati, da kyar
nasamu nutsuwa na dago kaina, aikuwa sai na
Kara rikicewa dan kuwa wanda nagani yayi balain
tayar mani da hankali shikenan mafarkina,ya
xama gaske, take nafadi bansan inda nake ba
INA
farkawa naganni kan rantsatstsen Gado mai
laushi, da kyar na mike INA salati take ikhala
tamatso kusa dani tana tambayana mai
yasameni,kamin inyi magana sai gashi ya shigo
cikin shiga mai kyau kanshi yasha crown na gold
sai haske yake sumarshi kuwa kamar ta mata ya
daureta baya kaini tinda nakebantaba ganin
mutim mai kyhauba irimshi.
Tafiya yake cikin kasaita har ya iso kusa dani
gabana sai dikan uku uku yake, xama yayi kan
gadonda nake ita kuwa ikhala sai murmushi take,
nikuwa runtse idona nayi dan kar Inga sanda xai
dawo mun dodo kamar yadda nayi mafarki
darenda xamu tafiya.
Ikhala ta katseni da fadin ga yayana nan ikram
dana ke baki lbr yaje yaki gashinan yadawo kuma
yayi nasara dama nagaya maki kameer jarumine,
dariya naji yayi meyasa kawar taki batason
ganina ne naga ta kulle idonta, sai lolacin nabude
idona duk ni suke kallo nikima banda tsoro ba
abunda nake ji, to wai meke shirin faruwane
Wanda nake mafarki yau gashi kusa dani.
Mehakan ke nufi, nikadai ke xancen xuci. ikhala
ce take mashi bayanina,dalilin fadowata birninsu,
yayi mamaki sosai NaN dai sukaita surutunsu
bancemasu komaiba har sika tafiyarsu, nikuwa
fadawa nayi nacigaba da sanaata kuka,
Haka rayuwarmu takasance a birnin matsafa
babu dadi musamman su anty suda ake
axabtarsuwa, abinda kebani mamaki shine yadda
ikhala da kameer suke kusantar junansu wato
xina saidai su adakin kameer sikeyi saida nakara
tambayrta da gaske yayanta ne tace eh banansu
d mace daya yayi muamala wato mamarsu harta
haifesu sannan ta rasu, abin yabani mamaki ace
Yaya na neman kanwarshi,ashe halyyar ta garin
ce haka kamr dabbobi suke. Allah y tsaremu d
irin wannan kaxamtacciyar rayuwaa.
Yanxu takai inda naxama kamar yar gari dankuwa
bana tsoron komai dan har wani tsuntsuu nake
hawa INA yawo mai suna kumash inason kumash
saboda yanada kyau sosai farine tas fikafikanshi
masu ado, kumash yasaba dani ko INA nakeso
yana kaini, kuma har nashaku da wannan flawer
mai kyau har gurinta nake xuwa tasamun
ganyanta kushi yafito hannuna muyita wasa da
tsuntsaye hmmmm
Sukuwa su anty salma suma har wahala tabi
jikinsu sun saba kuma yanxu nakan hadu dasu
muyi kuka mu watse.........


Xaharaddeen shomar
Whatsapp   08168575100


Birnin Matsfa 4
Posted by ANaM Dorayi on 09:55 PM, 23-Jul-15
Under: Birnin Matsafa
Sukuwa su anty salma suma har wahala tabi
jikinsu sun saba kuma yanxu nakan hadu dasu
muyi kuka mu watse.
Shikuwa kameer sai faman shigemun yake amma
INA nesa dashi wani lokaci haka kawai xan
ganshi ya fito mun ta gina wai yaxo gaidani nace
nagode.yagaji ya tafiyarshi, idan kuka ganni
xakuce aljance ni saboda tsabagen kyanda nayi
duk da ko inacikin damuwa ta tunanin iyayena
da
rayuwarda yanuwana suke ciki.
Fari nakara nayi kyau sosai ga gashina sai sheki
yakeyi, gashi nima ana bani irin kayanda ikhala
ke
sakawa wato gwan masu kyan gaske da kuma
crown na gold da takalma suma masu kyau.
Haka dai muke ta rayuwar
Yadda ikhala ke gayamun wai munada shekara
daya kenan da xuwa
To bari mukoma duniyar iyayensu ikrama muji
sukuma wace waina suke toyawa.
. BIRNIN TARAYYA
Tunda sati yacika su mummy suka shirya tarbon
yayansu, saboda sun masu waya sun taso,
mummy ta matsu bataga autarta ba saboda itake
debe mata kewa.
Amma shuru basu gansuba sunyi kiran wayoyinsu
amma takowacensu a kashe take, suka kira can
mutan kano aka gaya masu tabbasa sun taso,tofa
hankalinsu yayi balain tashi,, suka shiga damuwa,
har sati daya baa gansuba saida daga baya aka
samo motarsu da wayoyinsu xube babu kuma
alamar hatsari sukayi, mummy tayi kuka matuka
kamar xata rasa ranta daddy shima tamaxa daine
kawai, amma shima ba karamar damuwa yayi
based,duk inda ake saran xaa gansu anduba
amma shuru, anyi cigiyar gdn radio shima kamar
anshuka dusa babu su babu lbrn su.
Daddy har kudi ya axa ga wanda ya samesu ai
kuwa gari ya dauka ko INA lbrn batansu ake
amma shuru kakeji.
Ko yaushe idan mummy ta tuna irin yadda
autarta ta tafi sai ta fashe da kuka wato ashe
abin ne take ji ajinkinta shiyasa tayi shuru shuru.
Daddy kuwa lallaban mummy kawai yake idan
yashiga dakinshi yy ta kuka shima,
Anyi sauke alqurani yafi akirga duk sun lalace
sunyi baki mummy kuwa abin sai yaxamemata
kamar tabin hankali da mutun yashigo sai
tasheka ta cabe wuyanshi wai INA yakai mata
yayanta saida daddy yafita da ita waje da kyar
aka samu lpyr ta NaN dai daddy ya dauko mata
ta yarinya mai debe mata kewa.
Mummy kullum cikin addua suke Allah y nuna
mata yayanta kamin y dauki ranta gashi har
shekara daya tayi amma ba lbrn su,
Haka gwaggwo tashiga damuwa killum kuka take
har hawajinta yatashi d kyar itama aka samu
kanta
Dole daddy ya maidata kusa dashi domin kulawa
da ita. hankalin daddy dik ya rabu shin rashin
lpyr matarshi xaiji dashi kona mahaifiyarshi ko
kima batan yayanshi har uku.
Haka dai rayuwa t dinga masu daci.to bari mu
koma birnin matasafa muga su ikram sukuma
yaya sike dan nadan jima ban lekasuba.
kwance take tana karatun alqurani saboda shine
aikinta kullum, ba karamin kyau tayiba tana
sanye
da wata gwan mai kyan gaske saikace itace diyar
sarkin,kamin naganeta nima bebeelo saida nayi
da gaske sannan nagane ita daice ikaram saboda
kyanda tayi. da kaganta kasan tana cikin damuwa
dukda kuwa hutunda take samu, saiga abokinta
kumash yaxo ta window gini ya tsaya tana
ganinshi tayi murmushi tayi,tacigaba da karatunta
kumash yariga yasaba da idan yaxo su fita sai
tagama abinda take.
Haka ya jirata har tagama sannan ta hau suka
shuda sararin samaniya wannan abu shikadaine
kesata nishadi, bayan sungama yawonsu suka
sauko bata dire ko inaba sai wurin kawarta wato
flower hmmmm abin mamaki ashe ana kawance
da fure sai a birnin matsafa nagani.
Bayan ansaka mata GB sabon kunshi ta dauko
hanya dan komawa fada,
udai mutannen basuda dabiaa xinarda ma
Allah ya haramta itace abin yinsu kuma ma a
bayyane sukeyinta MTS SSW tawuce saboda ita
bata ma kallonsu yana daya daga cikin abinda
yasa bata fita kullum dan batason kallon tsiraici,
Tana cikin haka taji an sharbota wasu gungun
maxane majiya karfi suka suka yi kadi da ita sai
kan wata shinfida inda suke masharsu, kuka take
tana kiran ubangiji ashe itama bata tsiraba
dukansu take amma ko a jikinsu kuma wani abin
mamaki ba wanda yadamu balle ya kawo mata
dauki, kuka take da karfinta amma saida suka
rabata da rigar jikinta, Ana hakane taga da dai
dai
dinsu anayi sama dasu ,ikhalace tsaye sai faman
axabtardasu take sanan ta kyalesu ,jikina duk ya
mutu saida ta chanja mani kaya da magic dinta
sannan tarika hannuna sai gashi muntashi kamar
tsuntsaye sai cikin dakinda nake bacci
Bayan kuka ba abunda nake nan tashiga
rarrshina saboda ikhala ta lura duk cikin
abubuwanda suke ba abinda na tsana kamr
xinarda suke kuma nayi mata bayanin illar
abinda
suke shiyasa taki bari amun,
Bamu anakraba muka ga kameer ya fado a
fusace, fincikeni yy ya yar duk d magic yayita
dukana dayaga nayi lubus sanna y koma kan
ikhala wacce tayi kokari ta kareni amma takasa
saboda magic dinshi yafi karfin nata, fada yaketa
yi wai danme xataje tawahalarda mutanenshi
akan
wata banxa,nan dai sukayita masifa nikuwa sai
kuka nake dan naji jiki sosai saida y fitata taxo
tana bani hakuri,
DA kyar natashi nasamu nayi arwallah nayi sallah
babu yadda batayi daniba tayi mani tsafi naji
saukin jikina naki cemata nayi Allah xaimun
magani, dole ta kyaleni dan kuwa ni duk abinda
ake bani jira sumun tsafi subani d hannunnan
nake abina,
Kamar diban fruits, wanki, gyran bed room,da
sauran ayuka,
Bayan nayi sallah na roki Allah yayi gaggawar
fitardamu daga wannan halinda muke cikin,
sannan na dora d karatu.
Har bacci y kwasheni.Da safe ikhala takawo mani
abinci da kanta, ta kara bani hakuri, nan nace
mata ba komai,ya wuce.
Bayan naci abinci take gaya mani ta gargadi
kowa ne namiji akaina cewa duk wanda ya sake
ya tabani saita kashe shi, naji dadin abinda tace
saidai INA fargabar kameer sosai.,
Tunda akayi abin nadaina fita ko INA iyaka
kumash ya daukeni nayi yawo sama ya maidani
inda ya daukeni,, su anty salma kuma ikhala nasa
taci gaba da nuna mani halinda suke ko yaushe
nagansu sai nayi kuka akan irin axabarda ake
masu,
Duk sun canja kamar basuba,
Nakan yi kuka INA tambayar ikhala INA kufana
tashiga ne, inaso naganta nasake rokonta koxata
hakura ta maidamu duniyarmu,
Ikhala ke gayamun ai baxata sake waiwayarmuba
sai sanda waadinda ta diba mana ya cika,
Nakanyi murmushi ince shin ita tasan tana da
tabbacin rayuwarta xata Kai wannan lokacin balle
har ta diba irin shekaru haka masu yawa, duk dai
inda likhala ta bullo saina kamota dole ta kyaleni
tayi tafiyarta.
Shiko gogan tun lokacin ya tsaneni daya ganni
sai ya bani wahala har nadaina fita waje ma
daga daki sai daki dayaga haka sai yakama
biyana har daki yana bani wahala, saboda wani
lokaci tsafi yake ya kaini ga bango ya matse
kuma shi yana gefe umarni kawai yake da
hannunshi,
Gashi mai taimaka mani batanan tayi tafiya xuwa
wani gari cikin birnin sin wato chaina.
Haka tafaru ranar INA shirin shiga nayi wanka
kameer ya fado duk na firgice sai makyarkyata
nake, shi kuwa wani shuumin kallo yake mun,
ban ankaraba naji yayo cikina yana shafata duk
kokarinda nayi na kwace kaina nakasa, sai kuka
nake INA kiran ubangiji amma baifasa abunda
yake ba,
Idona na runtse INA addua, can naga y wurgani
gefe ya tashi yayi tafiyarshi batare da yako
kalloniba, nikuwa dagudu naje narufe kofa amma
sai na tuna shuumaine harta bango shigowa
suke, kara nasaka mai karfi duk abinda k dakin
saida nayi mashi raka raka,
Danaga bata fishsheni naje na dauro arwallah
nafara sallah ba ko kaklautawa bansan iya rakaa
nawa nayiba har bacci ya kwasheni,
Shikuwa kameer kasa bacci yy yana tunata komai
nata burgeshi yake amma kuma haushi take
bashi,bai gama rikicewa da alamarinta ba saida
yaga surarta, gashi kuma yaji ya kasa yimata
komai.Da haka har bacci ya same shi,
Da safe kai tsaye dakinta y wuce bacci take saida
ya tsaya yagama kalleta tsaf wani abu yaji yana
ratsa zuciyarshi, sai sannan yakai kallonshi ga
dakin komai ya farfashe,
NaN take yashiga aikinshi na tsafi take ya gyara
ko INA ya saka sababbin abubuwa masu kyau
take dakin ya dauki kyalli,
Maidata yy kan gado sakamakon kasanda take
kwance sannan yayi ficewarshi,
Fadar mahaifinshi ya wuce yy gaisuwa sanan ya
wuce gurin motsa jikinshi.,
Bayan ta tashi taga komai ya koma tsaf sabani
yadda ta hargitsa komai ita kanta sabon tsarinda
aka mata yy mata kyau, amma tsaki taja sannan
ta tashi tayi wanka,ta shirya kanta tunda tayi
sallarta.
Haka dai sukaci gaba da rayuwa bata sake
sakashi a idoba shikuma sai tayi bacci yake xuwa
ya kalleta sanan ya wuce,
Cikin lokaci kankani kameer ya kamu da son
ikram fiye da tsammanin ku so yake mata bana
wasaba, itakuwa bata masan yana yiba.
Yauma kamar kullum kumash ne yaxo daukanta
tana murna ta hau suka cillah sararin samaniya,
tunani tashiga yi wai yau itace kan tsuntsu
yatashi da ita suna tafiya sama sunata taji ankira
da wani lafaxi na koyo alamun mai kiranta bai iya
sunan ba tayi mamaki d taji ankira sunanta
saboda tasan ikhala kadaice tasan sunanta har
ta iya sunan,itama da kyar ta iya. tana waigowa
taganshi shima yana tashi sama sai kace tsuntsu
cikin riki cewa ta sake igiyarda take rike da ita ai
kuwa take tayi kasa da saurinshi ya tare ta sai
gata ya matse cikin kirjinshi duk ta rikice tama
rasa mexatayi,umurni yaba kumash ya tafi
Shi kuwa bai xarce ko INA da itaba sai gurinda
yake hutawa gurin akwaishi da kyau, ga furanni d
tsuntsaye masu kyau,ga korama ruwa sai malala
suke abin gwanin ban shaawa a hanakli muka
sauka duk INA makale a kirjinshi.
Bayan munsauka kuma duk sai na tsorace indai
baya kawoni neba nan yaksheni aikuwa sai nahau
kuka, dariya yakama yimun wai me meyasa kk
son kukane komai kuka daya fahimta tsorunshine
yakamani sai yajani dai dai koramar yace idan
INA bukata nashiga nayi wanka sanan shi bai
kawoni dan ya cutardaniba dan haka na
kwantarda hanaklina,
Banshiga ruwanba gefe nasamu nayi xamana
shikuwa ya fada yana wanaknshi har ya fito yaxo
kusa dani ya xauna, duk sai naji jikina ya mutu,
kallona ya dainga yi wanda saida na tsargu, wani
fure naja sai naji furen yayi Kara alamun wai yaji
xafi nikuwa ban san sanda nafada cikin kirjin
kameer ba dan tsoro, da karfi ko na makaleshi
shi
kuwa sai dariya yake mun sai daga baya kuma
naji kunyar shige mashi danayi dole na matsa
nesa dashi bai damu ba illah fira ya shiga yimun
yana mani wasa iri iri wasu naji tsoro wasu kuma
nayi dariya, da haka dai har muka dibi lokaci nan
nace mashi xan koma saboda inaso nayi sallah
amma ban cemashi ga abinda xanyiba saboda
ikhala ta gargadeni da kada na bari asan INA yin
sallah nima xan iya fuskantar matsala idan aka
sani,
Bai musaba ya dagani muka dauki hanya har
dakina ya ajeni sanann ya tafiya, mamakinshi
kawai nake ashe yanada saukin Kai shima kamar
ikhala.
Tundaga lokacin kullum sai kameer ya daukeni
munje jeji muyita wasa tun INA dari dari har
nasaba dashi har dakina yake xuwa muna fira da
wasanni, sai kuma y dawoshine k nuna mani yan
uwana, idan nafara kuka ya dinga lallashina,
Haka dai rayuwarmu tacigaba sai kace wasu
masoya idan banga kameer ba bana jin dadi
shima haka. ....

Zaharaddeen shomar
Whatsapp
08168575100




Birnin Matsafa 5
Posted by ANaM Dorayi on 11:43 PM, 25-Jul-15
Under: Birnin Matsafa
yau dakanshi ya kaini
gurin su anty salma, kuka nayi sosai saboda
ganin anty khadeeja danayi da ciki, rugumeta
nayi
INA kuka,
Baxakace suneba saboda duk sun sauya Kama
akan wahala.
Kameer ya tausaya muna sosai saboda dan
xamanda mukayi dashi yasan komai nawa gashi y
kamani INA sallah daya ke kameer yana tafiyae
tafiye sosai sai yagane abinda nake dan kuwa
yataba ganin wasu nayi a birnin dubai daya
tamabya menene suke aka cemashi sallah kenan
kuma musulmai keyinta abin yabashi shawa sosai
sai gashi yaga inayi ranar naji tsaoro sosai dan
naxata xai kasheni,
Amma saima yace wai nayi mashi cikakkaken
bayani akan addinina nan kuwa nashiga yimashi
tare da bashi missalai, kuma nakara nunashi illar
xina.,
Abubuwanda Nagaya mashi sun shigeshi
soasai,amma ba yadda xaiyi, but amma addinin
yabashi shaawa, musamman akan xina dan kuwa
shi bacika maamala yake da mataba illaa
kanwarshi kumabai taba saduwa da itaba a
gaban jamaa, gashi yaji kuma ubangijinda yake
saran shine na gaske wato ubangijin ikram ya
haramata xina balle ma har ka nemi wacce kuka
fito ciki daya da ita,. tunda daga lokacin ya dauki
alkawarin baxai sakeba, amma bai gaya munba.
Bayan mun koma yake gaya mun ya kafa dokar
kar wanda yasake saduwa d su anty khadeeja Kai
ba karamin dadi naji ba, har bansan sanda na
rungumeshiba shikuwa wani hali ya shiga da kyar
ya iya komawa side dinshi nikuwa sallah nashiga
yi INA godewa ubangiji akan canjinda muka fara
sank
Kameer y soma fuskantar matsala akan dokarda
ya kafa amma, dayake akwaishi da iya tsara
magana take ya tsarawa babansu wato king
laihanu, magana, cewa bai dace su dinga hada
jikinsu da bakinda basu san inda suka fitoba,
kilama sunada wata cuta a jikinsu kar suxo su
saka masu a birninsu,laihanu yy naam,d maganar
danshi da kuma kara yaba mashi akan tunaninshi
mai kyau d yy yi,baisan cewa da walakinba goro
cikin miya.
Ai kuwa sarki laihanu dakanshi yakara jaddada
maganar danshi, sukuwa mutane basu ji dadiba
dan kuwa su basu taba jin niima irin ta su
khadeeja d salma ba shiyasa suke yawan
kaimasu hari.
Angaya masu mu hausawa irinsune hala salaf
salaf kamar anyi miya d ruwan kan dan isaka
Tofa ni bebeelo mamaki ya isheni ganin kameer d
ikram sun buge sai rafka soyayya suke
hmmm,dan kuwa ita ikram bata masan sanda ta
fadaba kawai dai taganta cikine, to balle ni da ke
labe INA samun na rubutawa kunga kuwa ba
dogon motsi xanyiba kar taji ta koroni gashi na
dauko bayani.,
Dawowar ikhala sunyi rikici sosai da kameer dan
kuwa duk yanda taso ya biya Mata bukatarta yaki
sai kauracemata yake tayi mamaki sosai meye
wai dalili, sai nan ta xargo kodai ikram ta mashi
irin waaxinda tamata cewa subar neman junansu,
dan kuwa ita yanxu kallonsu kawai take dan
tagama hango jirginsu amma babu yadda xatayi
dan kuwa kameer yafi karfinta gashi kuma
tanason ikram bata son abinda xai cuta mata
dataje ta sanrda sarki., amma dole tasaka masu
nagani
Sukuwa rayuwarsu kawai suke, basu damu da
kowaba
Ana haka ne birni matsafa yatashi hargitse
saboda dodonninda suka xo daukar fansa, nan fa
akashiga kururuwa fada ya kaure,ikram duk
tashiga tashin hankali saboda dodonnin sum
masu xuwan ba xata kashesu kawai suke nan
kameer ya fito cikin shirinshi na yaki,
Amma me rikeshi ikram tayi wai baxaije ko inaba
d kyar ta sake shi y tafi sai kuka take, kufanama
ta tafi filin daga, aikuwa jikake kamas
kamas"""""karar takubba itakuwa ikram tana
saman bene tana hangosu sai addua take, gabaki
daya ta rufe idanunta, shikuwa tun da ya isa
yafara aikinshi kasancewarshi gwarxo sai gashi
ya yita kashinsu ga kuma adduarda ikram k
mashi take suka samu Saar dodonnin,
Sukuwa dodonni dasukaga ba nasara suka fara
gudu, amma daya mexaiyi tuma yy y cafko
ikrama dake sama, bude idonda xatayi sai
taganta cikin hannun wanan halittar mai bakar
kama ga doth,ai kuwa take tabuga kara sai kuma
ta suma,kameer yashiga tashin hanakli take
yasake shiri yabi bayansu suna gudu yanayi
shima, saida suka jashi a jeji tukun sanan suka
tsaya NaN aka fara fada nikuwa INA some
bansan wainarda ake toyawaba, kameer ya
galabaita soasai kamin yasamu ya kwacene gashi
sun mashi rauni wanda tsafinshi baxai iya
warkaddashiba da kyar yasamu y dawo dani.
Aikuwa,yana dawowa ya xube. nikuma da kyar
aka samu na farka INA farkawa nadinga
tambayar INA kameer d kyar lkhala ta kaini inda
yake yy rauni soasai kuma anyi tsafi har angaji
amma yaki ya warke,
NaN naci gaba da kula dashi, INA addua a ruwa
INA bashi sai kuwa gashi ya samu lpy rauninda k
jikinshi duk saura kadan su warke,bakaramin
dadi
najiba kuma nayi godiya ga Allah saboda nasan
karfin addua ne kawai y warkarda kameer.,
Da safe bayan nayi wanka sai na xarce dakin
kameer koda naje na riski ikhala, INA shiga tace
xata wuce saboda tana son taje wani guri nan dai
nashiga aikina nagyara dakin sanan nace yaje yy
wanka,
Bayanyayi wankane INA cikin gyaran gado jinayi
kawai nafada kangadon dagani harshi, wani irin
kallo yake mun nayi nayi na tureshi nakasa sai
faman shafata yake ban ankarba naji bakinshi
cikin nawa duk yafita hayyacinshi nikuwa sai
kicirniya nake amma nakasa ko motsashi daga
jikina da haka har ya rabani da rigana sai kuma
ya koma kan kirjina yana wasa dasu, xuwa wanan
lokacin duk jikina ya mutu komai nakasa yi shi
kuwa kameer sai sarrafani yake abinda naji yana
shirin yine yasani na buga wata irin
Kara INA kuka dole yafasa
abinda yy niya pant dina ya mayarmun, y
mannani a kirjinshi sai faman ajiyar xuciya yake,
ikram Yaushe ne wai xaki yarda dani kibani kanki
inasonki inasonki sosai,cikin daga murya nake
magana babu lokaci saboda kuwa addinina ba irin
nakuneba, addinina ya hanani dana aikata xina
saboda haka dan inasonka kameer bashi xaisa na
sabawa maha liccinaba,.
Dagoni yy yana kallona sanan yace kina nufin
addininki bai hallatta namiji y kusanci maceba,ya
halatta yaxance bai halattaba to idan nace
hakane ya akeyi ana hayayyafa, addinina ya
halatta namiji ya kusanci mace amma idan ya
biya sadaki kuma antara shaidu sun shaida ,
Kallona yadinga yi dan kuwa baisan menake
nufiba, nan nashiga Kara yimashi bayani har ya
fahimta, Sunanana ya kira, amma nakasa dagowa
saboda yy kalar tausayi idan naci gaba da
kallonshi xan iya tausayawa mashi,.
Ikram yasake kirana na amsa mashi kiyi hakuri
kinji, to nace mashi,d saurina nabar dakin, kuka
nayi mai isata sanan nayi bacci dan gajiyarda
nayi.
Tundaga lokacin ban sake sakashi a idonaba ko
INA nadubashi amma banganshiba har akayi sati
daya, duk na takura saboda banida Wanda xanyi
fira dashi inji dadi, ikhala batanan tayi tafiya,
gashi bana son fita ko INA.
Kullum sai kumash ya kaini inda muke xuwa nida
kameer amma kuma bana jin dadi kasancewar
baya kusa dani.
INA kwance sai famana tunani nake naji kamshi
turarenshi da sauri na mike INA kallonshi tsaye
yake ya rungume hannayenshi cikin kirjinshi, da
sauri naje na fada kanshi INA kuka danme xaka
tafi kabarni,bayan kasa bana iya rauyawa idan
bada kaiba,
Murmushi yy sanan ya dago kaina, muka fuskanci
juna, ikram xaki aureni dam gabana ya fadi, sake
maimai tawa yy nace xAKI AURENI """eh nace
amma kameer, shhhhhhhh yace mani tambayarki
nayi xaki aureni ko kuwa nan nasake amsa mashi
da eh, but ta yaya,
Baicemun komaiba illah takalmi yasaka mun
sannan ya ja hannuna muka fita,
Kumash ya daukemu bai dire mu ko inaba sa
cikin wani babban gini, mukashiga ciki wata
matace xaune ta saka wani madubi gefenta,.
Muna isa tayi gaisuwa sannan ta tambayeshi INA
xamuje nan yace mata Dubai xaya koma.
Ba a jimaba tafara surutanta saiga wani abu
kamar haxo ya mamayemu ni duk tsoro
yakamani
hannunan y Kara matsewa sai kawai wani haske
yaxo ya dagamu sai ganin mu nayi a wani guri,
mutane sai safa da marwa suke ko INA hasken
lantarkine.
Ba xame ko INA daniba sai wani bababn guri
kamar ansan da xuwan mu sai naga dattijawan
sun fara shirye shirye, saiga wani dattijo ya
mikowa kameer wani mayafi ya lillube mani jikina
dashi.,aka bamu guri muka xauna,
NaN wani dattijo yace wai shine wakilina, dayan
kuma shine wakilin shamsideen, nayi mamaki
wannene shmsdn sai daga baya nagane kameer
suke nufi.
To yaushe yaxama shmsdn kuma, nan naji an
yanka mashi sadaki ya bayar kuma, aka axa
mashi hakkokina yace ya amince nima haka nace
na amince nan suka fara daura aurena d kameer
hawaye ne keta yimani kwarara,
Dan kuwa iyayena na tuno yau ace gani andaura
aurena amma basu Saniba. cikin xuciyata nake
magana kuyi hakuri iyayena dolece tasa haka
xaifimin sauki dana aikata sabon Allah.idan da
rayuwa watarana xaku gannmu amma nasan
baxakuji dadiba kuyi hakuri kuyafe mana nida
yan
uwana, naxata duk maganarda nake a xuciya
nake yinta ashe harta fito fili,
Rungumeni yy yana lallashina, ikram ko bakya
son aurenne kigaya mani baxanso na takura
makiba,Kara shigewa jikinshi nayi, INA kuka inso
kameer inaso.........kawaidai na tuna iyayenane
ace nayi aure amma basu saniba.
Kaina yashafa xusu sani d sannu ki kwantarda
hankalinki kawai to nace sanan yabani lbrn yadda
akayi, harya musulinta kuma y shirya aurennmu,
Nayi mamaki matuka kuma naji dadi, kuma y
tabbata mani tsakaninshi da Allah y musulunta
koda y rasani baxai daina musulunciba.
Nayi murnan sosai da haka muka koma LAND OF
MAGIC"""""wato birnin matsafa.
Bamu xarce ko inaba sai dakin baccin kameer
duk hakalinta a tashe yake, arwallah yasata
sukayi sannan yaja masu sallah tayi mamakin
acewai kameer ne ya iya sallah haka duka duka
yaushene y musulunta ta jinjina mashi gaskiya,
hmmm lallaima ikram yo musulmai nawane
yanxu basu iya sallarba kuma cikin musulunci aka
haifesu ai komai sa kaine, naso na gaya mata
haka amma dole naja bakina nayi shuru tunda
batasan cewa ni bebeelo INA nan biye da itaba,
kunga kuwa idan tasani baxata barni nacigaba da
samun lbrn ta ba,gashi inaso naga yadda first
night dinta xai kasance tunda naga duk ta wani
tsorace .
Bayan sun idarda sallah, kuma sai taga yana
mata addua duk mamaki abin k bata, suna
gamawa sukaci abinci,. NaN tashiga tambayrshi
yaxaiyi da yan uwanshi to, mtseta yy a jikinshi
sannan yace badamuwa baxasu san abinda k
tsakaninmuba sai nan da wani lokaci ,wanda
nasan dole su sani iyaka duk wacce xaayi ayi,,
Kara marairaicewa yy ikram inaso kimani
alkawarin duk halinda xamushiga kada ki
rabudani, saboda ni duk abinda xaa yimun baxan
taba rabuwa da keba,. Nayi maka alkawari
kameer inanan tare dakai baxamu rabuba. Kara
mtseni yy saida nayi wata yar kara
Tofa daga nan salo y canja dan kuwa shafata
yadingayi ta ko INA nikuwa jikina duk bari yake
wani tsoro y xiyarceni, NaN fa nadinga kwalla
amma baimasaninayiba yana wata duniyar, haka
ya dinga sarrafani dole na kyaleshi tunda kuwa
yanxu naxama mallakinshi babu wani abinda xan
ce mash I,
Duk yadda naso na daure kasawa nayi dan kuwa
nayi kuka sosai, nikaina dai bebeelo na tausaya
mata dan kuwa fita nayi daga dakin, saida safe
nadawo .
Da safe dakanshi y mata wanka ya shiryata yaji
dadi sosai dan kuwa ita daban yajita ba kamar
sauran mataba. Aikuwa wani irin sonta ya karaji
na shigarsa, ita kuwa duk kunyarshi takeji,
dayagane nan ya dauketa sukaje inda suke
hutawa NaN kuma sabuwar soyayya ta balle,
Nidai bebeelo abin baya barin bani mamaki
hmmm
Dakanta taje ta sanarda yan uwanta abinda take
ciki cewa kameerfa y musulunta y aureta sunyi
mamaki matuka, amma kuma ba abin
mamakineba idan da abin mamaki bai wuce
xuwansu birninba,sunyimata fatan alkhairi,
Khdeeja kam cikinda tasamu y lalace taji dadi
sosai kuma,axaba kam basudaina cintaba saima
abinda y karu.
Bayan takoma gida tafada tayi wanka, tana
shiryawa taji an Kama kugunta sai kan gado, INA
kk jene kk barni nikadai,
Murmushi tayi ai kasani mana INA madubinka na
magic, au abin yarxolayace kuma, to bari in nuna
maki inda na boye madubin, kicirniya tashiga yi
amma INA takasa kwatan kanta dole ta biye
mashi,
Xaman kam alhmdlh soyayya baa ma magana,
gashi yanxu kmaeer yadaina magic komai ikram k
mashi,
Bayan lkhala tadawo ba fargaba yagaya mata
abinda ake ciki cikin ikon Allah bata yi
gardamaba illah ma cewa tayi itama tanason
tashiga addinin, suduka sunyi murna dajin haka
bada jimawaba suka bata kalmar shahada,
sannan suka dage har ta iya sallah ta iya komai.
Soyayyarsu na bata shaawa sosai,amma kuma
tana guje masu randa sarki xai ji hmmm, nimadai
shinakewa gudu kar a hada dani mai rahoto.


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100



Birnin Matsafa 6
Posted by ANaM Dorayi on 11:52 PM, 25-Jul-15
Under: Birnin Matsafa
Haka dai mikaci gaba da rayuwa gwanin
ban shaawa d dadi.
Lokacinda muka fara fuskantar matsala shine
sanda ciki y bayyana a jikina, mun shiga tashin
hankali dan kuwa rashin lpy nayi yakira aka
dubani sai aka gaya mashi juna biyune dani, bai
gayawa kowa ba illah ikhala,
Saida cikina yakai kusan wata takwas yafito dole
aka san dashi,
Anan sarki laihanu y tara jamaarsa dani da
yayanshi akan cikinda k jikina,
Bayani yake akan cewar yy mamaki y kafa doka
amma ace baa daukaba, cewa wai yace kar
wanda yasake tarayya damu amma baa dainaba
tunda gashi har anmun ciki,.
NaN yaci gaba d cewa xaiyi maganinsu.
NaN saiga kufana ta bayyana, duk hankalina y
tashi sai kuka nake INA neman tsarin ubanhiji
shikuwa gogan xuciyarshi tariga t bushe shirye
yake,
Bayan kufana taxo tana shirin bayyanawa sarki
ko menene, sai kameer y mike take yashiga
bayanin cewa shine main cikin shikadai ya taba
tarayya dani, sarki yy mamaki ganin cewa shida
kanshi y kawo mashi korafi amma ace shiya
karya dokar kuma,
Sarki laihanu harya hakura nan kufana tagaya
mashi cewa yabi addinina tambaya sarki keyi
harda wani addini daya wuce tsafi ,ran sarki y
baci sosai nan yace aje dani a kulle dan na sauya
mashi rayuwar danshi aikuwa akayo cikin aka
Kama duk yadda yaso y taimaka mun yakasa
kasancewar bashida magic ya daina kuma nace
karya yasake yace xai taimakeni da tsafi,
Ihkala ma kuka take tanaba sarki haukuri amma
yaki ko kulata, shikuwa kameer dakinshi ya koma
yana neman mafita,
Dole nasamu mafita Dole hannunshi yaketa
noshin bango yana maganar da kyar ikhala ta
samu kanshi.
Nikuwa tunda aka je dani aka ajeni sai wahala
ake bani sunan Allah kawai nake kira nasan kuma
xai karba Mani.
Har dakin mahaifinshi yaje ya bashi hakuri amma
kememe yaki, yace idan dai basu koma yadda
sukeba suka sake addininan n musulunci to xai
kasheni kowa ya huta, Kara kameer ya saka
kamar ya shake mahaifinshi yake ji, na rantse
maka da ubangijin gaskiya duk wanda yasake ya
tabamun matata saina halakashi nima, sanan
baxan taba barin addinin musulunciba, huuu yayi
tafiyarshi
Sarki km ya tsorata d halinda yaga danshi dole
ya dauki mataki.
Nidai banda addua,ba abundanake .Yauma
xaune
nake INA kuka INA rokon Allah, ga yunwa gashi
kuma abinda ke cikin cikina sai motsi yakemun
kila shima yunwar yake ji,
Jinayi andafani koda nadaga naga kameer idonshi
yy ja,duk y rame, rungumeshi nayi INA kuka, kiyi
shuru ikram, saida mukayi kuka mai isarmu
sanan yace ikram bamuda lokaci kitaso muje, ban
tsaya komaiba binshi nayi kawai yana rike da
hannuna, koda muka fito waje naga wadanda ke
tsare dani kwance jinajina kallonshi nayi, shima
haka yagane kallon tuguma nake mashi nan yace
bani bane aikin lkhalane yanxu haka tana can
tareda yan uwanki kixo muje, bai rufe bakiba
saiga kumsh y sauka muka hau sai inda muka
taba xuwa nida kameer sanda aka daura mana
aure, NaN naga yan uwana muka rungume juna
muna kuka,
Ikram lokaci yy daya kamata Ku koma gurin
iyayenku, idonaxare INA kallonshi, eh ikram
yaune
mahaifina y yanke shawar xai kasheku keda yan
uwanki, nikuwa baxan iya ganin wanan ranarba
nafi gwammacewa ni ya kashe ni akan y kasheki
saboda haka kuje xaa maidaku gida ki kula mani
da dana kinji kuka nafashe dashi kameer
baxanjeba akai yan uwana kawai amma ni
baxanje ko INA nabarka ba,
Aa ikram baxaiyuba kecefa kullum sai kinyi kukan
iyayenki yau ga dama ta samu kije kawai wata
kila watarana xamu sake haduwa kuka nake
sosai lkhala taxo tajani kije ikram idan da rai
xamu sadu kinji amma dan Allah kije kodan ki
tsratarda abinda ke cikinki,
Kara kankame kameer d ikhala nayi INA kuka
suma haka haka su anty salma suma kukan suke
suna jana, amma hannuna na makale d na
kameer shima ya kasa sake hannunan Nan muka
tsinko mutanen sarki dole muka sake juna
NaN ilkhala tashiga tsafi sai ga haske y
mamayemu sai kuma mukaga dif,koda mutanen
sarki sikaxo mun cilla, gashi kuma ikhala takashe
mai tsafin tafiya kuma bayan ita matar ikhalace
kawai ta iya tsafin tafiya.
Dole suka juya, da kyar ikhala ta ja kameer suka
wuce, koda kufana taji ,sai taxo sarki yacemata
ya xaayi tace babu dan kuwa bata san inda suka
kaimuba, taji haushi sosai, haka sarki shima
Aikuwa wahala yasa kufana tadinga basu dayake
tsafinta yafi nasu amma kememe suka ki yarda
su bar musulunci.
Mukuwa bamu fado ko inaba sai bayan asibitir
abuja lokacinda muka fado bawanda ya gani
kawaidai angamu xube kasa.
NaN aka kwashemu aka kaimu emerjamcy aka
kwantar, kwanan mu biyu bamu farfadoba, gashi
ba asan daga INA muka fitoba nannan wani
mutune yace shidai INA mashi kama da wadan
akayi cigiya shekaru biyu d suka wuce sai dai
biyu dinne baisaniba.
Haka ya kawo hutunmu inda mukayi mu uku,
dactan yace tabbas mune, aikuwa aka dauki
lamabar daddy aka kirashi cewa yaxo babban
asibitin abuja ga yayanshinan angani waib.
murna
gurinsu daddy da kuka baa magana.
kuka biyu, nafarko da Allah yasake hadani
d iyayena, na biyu kuma RABUWA DA MASOYI
littafin bebeelo nagaba.
Iyaenmu kamar su ciyenmu irin kularda suka
nuna amma,musaan ni mai ciki, kokadan
mahaifana basu xargeni akan aurena ba hasalima
tausaya mani suke saboda CeCe Ku Ku cecen da
jamaa ke yadawa a gari
Ai kuwa kwana biyu duk na lalace banda tunanin
masoyina ba abunda nake,
A raina kulumm tunani bai wuce naga sahibinaba
kameer ko wani hali yake ciki ai kuwa sai nafashe
d kuka,mummy tafito kitchen kenan taganni INA
sanaar,
Gurina taxo tayi xaune tana fuskantata saida
tabari nayi mai isata sanan tafara lallashina,
Ikaram kiyi imani da kaddara mai kyau da marar
kyau ,shin kina tunanin Ubangiji bai maki
adalcibane, AA mummy bantaba kawo hakaba a
raina kawai dai INA dubin yadda mutane k
fassara abinann ne kidubafa ko fita nayi anfar
nunani kenan duka duka yaushene abin sati daya
ammma har wasu garuruwa ansan d xancennan
kuma kalilan na suka yarda da KADDARAR MU.,
shima littafin bebeelone da xai fito,
Autana inaso kidaina sa xancen mutane a rank
I,shin inace shi Allah masanine sannan mu
iyayenku mun yarda menene banaso kina saka
damuwa a ranki, to mummy nace
Da sama mukaji maganar gwaggwo dasu anty
salma suna saukowa, barta so take ta wahalar
mani da jikallena,
NaN anty salma tace tabs da kuwa kinyi rashin
miji mai kyau dan kuwa babanshi kamar aljani
yake saboda tsabagen kyau, aikuwa baxan yarda
ba dama ko gashi gwarancin ya isheni shiyasa
take mani bakinciki dan taga mijin nawa
kyakyawane, dariya kowa yasaka harda daddy
daya shigo yaji xancenda ake,
Aikuwa take naji nafara samun sukuni, haka yan
uwana d mahaifana suka cigaba d kwantar suwa
mani d hanakali
Nakan ji dadi amma ban daina tunanin
masoyinaba.
Watanmu daya da dawowa na sulbulo dana
mai kyan gaske kyanshi har yafi na mahaifinshi
nikaina kyan yaron har tsoro yake bani nakan dai
yi addua kullum, mutane kuwa har xuwa
kallonshi
ake,
Mutan gidanmu kuwa kamar su cinyeshi akan
sonda suke mashi,
Anyi suna yaro yaci sunan kakanmu wato kabeer
amma an aje xaa dinga kiranshi da khaleefa.
Daddy yakashe naira gurin bikin y nunawa duniya
yanason jikanshi fiye da yadda ake tsammani.
Nikuwa ranar nayi kuka ganin yau na sauka lpy
amma ba uban yaro balle shima naga irin farin
cikinda xai nuna.
An watse taro lpy, naci gaba d renon yarona,
kullum gwggwo k mashi wanka mummy t
shiryashi. kai sunaji d yaron.
Khaleefa nada wata shidda akayi bikinsu anty
salama sun samu maxaje masu kirki ga kudi
saidai duk magidantane, anyi shagali aka Kai
amare gidajensu,duk anan cikin garin abuja.
Dayake ni daddy yaje gurin malamai yy tanbaya
akan cewa MENENE MATSAYIN AURENA, shima
wagon littafin bebeelone,
Sunce tunda aurene akayi daidai yadda addini
yace to dole abi ka ido dinshi.dan haka ajira
daidai lokacinda wacce mijinta yatafi yabarta,
agani wato shekara bakwai idan bai xoba inyi
wani auren, su mummy sun tausaya mani amma
b yadda suka iya.
Ni dama auren baya a raina dan kuwa baxan iya
xama d waniba bayan landed
Karatu na nemi alfarmar su daddy su samani,
haka kuwa akayi
An nemani bangaren unguwar xoma, nafara
karatuna, bansha wahalaba dan kuwa dankuwa
inda ilimina sanan kuma khaleefa bayyada fitina
nono ma baxaifi sha so ukuba a yini,
bAYAN SHEKARA6⃣
Na kammala karatuna cikin sauki d jindadi na fito
likita kwararra, su daddy ranar mur baa ma
magana,
Koda nadawo gida na iske yan uwana d yaransu
d
maxajensu duk ancika falon mu,anty salma
yayanta uku kasancewar tayi rurrutasa ita Kuwa
anty khadeeja danta daya Ismail,anty salma kuwa
habib da fauxy d kuma yar karamarsu
Fatima,yaran kyawawa dasu,
Sai wasa suke d khaleefa dayake ya girmemasu
shiketa jansu, khaleefa har fita aka hanashi
saboda tsabagen kyanshi daga schools sai
schools yake xuwa, islamiyya ma malami daddy y
dauka mashi.
Da murnata na iso yaran kuwa duk suka
keawayeni, mum INA sweet dina d kk CE,inji
khaleefa o sorry dear namanta aiki yamun yawa
duk nagaji,but amma bari nayi wanaka sai muje
d
su Ismail mu siya ko,yes dat y I luv you mum,y
manna mani kiss ya gudu,
Kowa abun yabshi shaawa dan kuwa sun san
soyayyace mai tsanani k tsakanina d dana.,
NaN muka gyasa dasu cikin farin ciki, sannan
nawuce nayi wanka muje siyaen sweet din.
Bayan mun kammal mun fito kenan sai mukaga
anyi accident, nan nasa su khaleefa moto ban
kulleba nace kar su fito nayi gurin koxan iya
bada taimako.
INA xuwa gurin an hana kowa katina na shedar
xama likita na nunawa police dinda ke gurin.
Ai kuwa cikin girmamawa suka barni na isa Turin
INA isa nunfashina ya fara daukewa waxan gani
nan.Kameer ne kwance jinajina, aikuwa cikin kuka
na isa gurinshi na rugume INA kuka,
Haba dakta ke dakanki, rinannun idanuna nadago
na watsawa police din harara kasan shi ko
wayene gareni aa yace to luminance yau
shekaran
shidda rabona d shi. duk wanda ke gurin ya
tausaya mani
DA sauri nace a taiamaka mani nasashi moto
haka kuwa akayi,,police din ya tafi tare dani
shiyayi drvn har asibiti dan kuwa ni bayan kuka
ba abunda nake,
Muna isa aka amsheshi emgency aka hau mashi
taiamkon gaggwa, yarana ko suma kuka sike dan
sunga inayi musamman khaaleefa yy tamabayana
nan nacemashi khaleefa daddynn kane,
NaN ya fara jindadi dan nace daddyn shi saboda
kusan kullum sai y tambayeni INA daddynshi
yakaishi schools yasaimashi choculata, kamar
yanda akewa yan schl dinsu.
Dayake n gayawa iyayena cikin gaggawa suka
iso, suma su anty salama sunxo da
maxajensu,NaN aka hau lallashina
Datka yaxo yace yana bukatar jini saboda jininshi
y xuba sosai,
NaN take mijin salama usaman yace agwada
nashi anko ci saa yy aka saka mashi.,
Bayad baayi naje gidaba amma naki nace nan
xan kwana danida mummy aka bari d anty
khadeeja, har safe bayan munyi sallah ne saiga
kameer y farka sunana ya dinga kira da guduna
naje kanshi,
Cikin mamaki yakaganar d yaen turanci ikram
kece da gaske, kara kankeshi nayi INA kuka,
dayaga tabbasa ikram dinshi ce sai y dinga
godewa Allah ,ikram taji dadinda har yanxu
kameer bai bar musulunci ba.
NaN dai daddy yy gyran murya sannan suka
ankara d dakin cike yake d jamaa,
NaN yake tabayarta hala sune mahaifanta tace
eh kamama mashi tayi y mike batun saukowa
yake kasa wai yagaida su daddy, d sauri daddy y
rikeshi aidashi xaune, anan y fara gaidasu cikin
girmamawa, su mummy sunji dadi sosai, ganin
hanaklin kameer a matsayinshi na wanda bai
dade d karbar musuunciba.,
Su ikram baki yaki rufewa
Kameer yasamu kulawa sosai dankuwa harsu
daddy ba a barsu bayaba kuladashi suke sosai
hmmm balle uwar aikin,
Gaban kowa soyayyrsu suke su mummy har
mamaki suke duk irn kunyar ikram amma take
haka gabansu. hmmm nimadai nayi mama kin
Satinshi biyu aka sallameshi, suka koma gida tab
nan yakara samun wata kulawar ta musamman
har lokacin su salma basu daina kaimashi cimaba
iriiri.
NaN yabada lbrn cewa bayan tafiyarsu ikram
sarki dakanshi yadinga sawa ana masu axaba
amma sukaki barin musulunci, Ana hakane ranar
ikhala tasamu kubutarda su, taje ta hada magic
din tafiya, tace yaje ya bidi matarshi, ba yadda
baiyi da itaba tace baxata jeba suna cikin haka
ne mutanen sarki suka harbo kibiya dan kuwa
sarki yace dasubi musulunci gwara y kashesu,
ana dai kihala ta rasu bayan kalamar shahada da
tayi.
Shi kuwa yy rokon Allah d y sa yaga matarshi
batareda bata lokaciba sannan ya fado, sai kuwa
yy dadai da wata mota ta kwasheshi.
Kowa y tausaya mashi, itakuwa ikram kuka t
dingayi kananufin ikhala t rasu, t rasu ikram,
Allah yama boyar Allah rahama saboda ikhala ta
taka rawa a rayuwata baxan daina mata adduaba
har karshen rayuwata.
Malammai sunyi bayanin cewa auranmu d
shamsideen kamar yadda y dawo ynxu, dan haka
daddy ya gyaramana gidanshi dake kusaga
wanda muke ciki, bkki akayi sosai na tare da
dana wanda bama xan iya gaya maku irin sonda
mahai finshi k mashiba.
""""""""Karshen labari""""""""
Daddy yasa kameer cikin businesses dinshi
hasalima shiya damkawa komai shiko ya xauna y
huta,
Kowa nason kameer saboda kirkinshi d kyanshi,
Ga kwarjini,mummy kanta itama tayaba d
hallayyar shi,mutane yan gulma akayi tsit, su
anty salama suma hankalinsu y kwanta tunda
ada gani suke sune sanadin halinda nashiga,ashe
alkhairine agurina.
Bayan shekara biyu nasake sulbulo yan biyu dina
kamal da Sumayya masu kyan gaske
suma,jekaga farin ciki gurin babansu anyi biki na
kece raini, lokaci bakina har wuya su gwaggwo
har tsokanta suke, yan biyu dina nada wata uku
su anty salma suka haihu dai rana anty salam d
safe anty khdee kuma d dare,nan kuma wani
farincikin y tashi
Ranar suna yara sukaci umar d Hafiz.
Soyyarmu da shamsideen baa cewa komai
tattalina yake saikace kwai, nukiwa sai shagwaba
nake xuba mashi.Koda aka sake wasu shekara
hudu inada yayana biyar, khaleefa ,Sumayya
kamal da hanifa. lokacin khaleefa na jss, 2saboda
kokarinshi gashi d jikin girma yaron akwai kyau g
ladabi,d haxaka, duk wani talla d xaa nuna shike
yinta saboda masu sanar idan suka sakashi sunfi
samun ciniki.kameer kuwa lokacin hausa kamar a
bakinshi aka samota, yasamu ci gaba sosai
dukiyar daddy takara habaka ta dalilinshi yasa
daddy yy suna sosai hmmm abin baa cewa komai
dan kuwa naira t xaunu.
Masallataynda shamsideen y gina basu kirguwa d
isalamiyya,
Yauma kamar kulluma bayan munyi shirin
kwanciya nida sahibina, sai muka kunna talabijin
nan mukaci karo d tallar da khaleefa kewa
kamfanin clouse up, hakoranshi kuwa fes dasu
abin gwanin ban shaawa,
Bayan sahibina yakashe TV din sai y jiyo inda
nake,bebina kinfa iya haihuwar yara, murmushi
nayi nace INA ai kaine xaa ce ka iya dankuwa Kai
k bada ajiyar, wata irin dariya yy Allah ko eh
mana nace to gashi kuwa kinga kuwa yakamata
ace hanifa tasamu Kane kullum saitamun korafi,
dariya nayi nace adai ragawa yaya suma su
samu, au ita karyar da karfi nake dariya lah
ashema kasan kayi karya, eh naji to adafe kawai,
nan kuma muka shiga wata duniyar wacce baxan
iya fadiba, nukuma bebeelo yarrahota naso na
gaya maku idan ita baxata iyaba amma me kawai
sai suka kashe haske, dole nayi sauri nafito dan
kuwa bana shiri da duhu, to kuma gashi gurin
mtsinda nake taganni kuma da safe dana dawo
tace ya isa haka kar nakara dawo mata gida d
sunan daukar lbr, banji dadiba amma yaxanyi
dole nayi hakuri
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *