Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 4 June 2018

MAJNOON hausa love novels

adsense here
MAJNOON hausa love novels
MAJNOON
      THE MAD MAN   

              _A love story_💝
   *BISMILLAH*

" MAHAUKACI !! MAHAUKACI!!! "  Shine sunan  da dandazon yara kekiransa yana tafiya suna binsa a baya
       Wasu daga cikin yaran dake biyarsa  har rigarsa sukeja

      Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30,  gashin kansa duk ya kudun dune,
   Launin fatarsa ya chanza saboda  dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage,
      Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake**
     Tafiya yakeyi yaran kuwa sai binsa sukeyi suna masa ihu, wani lokaci idan yagaji da ihun yakan dan juyo yabi yaran da gudu sai su zura da gudu..

Hakadai yaci gaba da tafiya, idan yaga bola a gefen titi yakan tsaya yayi tsince2 sa kafin yaci gaba da tafiya,

Wata waka naji yaran sun fara masa suna cewa "ga maj nun uban tanbele,  ga maj nun uban tanbele  " shikuwa sai dukawa kasa yakeyi yana tsintar ledojin pure water, yana kwasar rawa ga alama wakar tanai masa dadi..

***        ***      ***
A hankali take  taku kamar batason taka kasa, matashiyar budurwace yar shekaru 20 cikin shigar kamala tufafin hausawa  atamfa da zani sai kuma katon hijab data saka har kasa.
   Hannnun rike da 'Yar karamar kula ta abinci...
     Dai dai kwanar wani layi ta kunnu kai Tun daga nesa ta hangi yara sunai masa waka, "Ga maj nun uban tanbele"
     Wani zarr taji jikinta yadauka, dasauri takarasa  gurin duk ta  watse yaran sannan ta  dubesa ta saukar da murya tace "haba ! Haba  meye haka katsaya yara suna mai maka waka kana rawa" sai tayi shiru tana kallonsa kafin yadago kai ya kallesa, sannan tace "ko so kake na fasa aurenka kane ?"

Maj nun yayi saurin girgiza mata kai "a a nadaina " yana gama fada yayi sauri yazauna ya langwabe kansa 

Murmushi tayi tadawo kusa dashi tazauna ta mika masa kular datazo dashi "ga abincika maza ka cinye kabani kular na wuce gida, tun kafin Abbana yadawo "

Da karfi ya firgi kular yana kokarin budewa, da kyar yasamu ya iya  budewa shinkaface da namomi akai, karkade hannunsa kawai yayi ya fara aikawa cikinsa sako.

Kura masa ido tayi tana kallosa cike da tausayi, bata ankaraba tafara hawaye, wani iri takeji a zuciyarta  akansa, tarasa sanin ko meye wata zuciyar tace mata sona wata zuciyar kuwa tace mata tausayine... ita kanta takasa baya kanta amsa, *so ne ko tausayi*
Tana zaune tana tunani harya  kammala canye abinci ya miko mata kula "ungo" maganarsa tafitar da ita daga  duniya tunanin datake ciki, tadan zabura kadan, sannan ta kirkiri murmushi tace  "harka cinye " yace "eh " yana wasa da tsunmar rigarsa,
Mikewa tsaye tayi shima ya tashi ta dubesa tayi murmushi tace "nizan wuce gida sai nazo da dadare"

Maj nun ya hada kansa da kafada yace "nibanason  kitafi kitsaya, muyi fira " yakarasa maganar yana gunguni
    Dariya tayi kafin tace " to shikenan idan nazo dadare zamuyi firar yanzudai zan wuce gida"
"Tohm.. toh yaushe zamuyi aure" maj nun yafada yana cizon rigarsa

Murmushi tayi tana kalloso tace "gobe "

Tsalle yayi yana ihu cike dajindadi yace "idan mukayi aure a jirgi zan daukeki nakaiki india"

Dariya  tayi sosai, saida taga yafara kuluwa sannan ta tsayar da dariyarta  tace "tohm shikenan  nidai na tafi sai anjima" tana gama fada ta fice tabar gurin, saida tayi nisa kan dashu saikuma tatuna da maganar daya fada takara saka dariya.. sai kace itama haukar takee
  Saita fara tafiya ta juyo ta kalle sa tagansa sai tsalle yake wani irin mugun tausayinsa  takeji,
    Hakadai taci gaba  da tafiya cike da tausayin maj nun daidai kwatar layinsu  ta hangi wata bakar mota da karfi taja da baya gabanta ya fadi sosai "innalillahi wa inna ilaihin raju un " itace kalmar data subuce daga bakinta.

Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka, nan ta fara salati harta samu na tsuwa tadan wani lokaci sai kuma taci gaba da tafiya

Takai dap da Motar taji ankira sunan " *Rumaisa* !!!" Gabanta yafadi ko juyowa batayiba taci gaba da tafiyar  ta ..

Da sauri yafito daga cikin motarsa ya tari gabanta sukayi ido hudu, ya marairaice fuska kmar zainyi kuka yace "haba rumaisa meyasa bakijin tausayin zuciyatane, plx kitsaya ki saurareni dan Allah koda na minti biyune "

Hawaye sunka  cinciko a  idon rumaisa, a duk lokacin data gansa wani irin bakin ciki takeji ya ziyarci zuciyarta,

Muryarta tafarasa rawa   kalilan abu zai iya sakata kuka, bude bakinta kuwa sai kuka "wai menai maka kake bibiyana kahanani jindadin rayuwata dan Allah ka fita harkata"

*Fahad* yayi shiru yana sauraron kukanta, zuciyarsa na masa kuna, kwata2 bayason ganin kukan rumaisa, idan tana kuka shima jiyakeyi kamar zai tayata,  muryarsa na rawa yace " sonki nake rumaisa zuciya ta tsunduma a cikin kogin sonki, iduwana basa muradin ganin kowa saike, a koda yaushe kece a mafarkina, plx rumaisa dan Allah kisoni"

Hawayenta ta share ta sakar masa wani irin  tsaki tace " ko  kai kadaine namiji a duniya bazan sokaba, daidai da dakika daya bantabajin ina sonkaba" kafita daga harkata, kabano hanya na wuce " tanakarasa maganar tana kokarin turesa, shikuwa sai binta yake a duk gefen dataje yana fadan plx rumaisa,

Da taga bayada niyar bata hanya taturesa ta wuce,

 A karo na biyu yakara shiga gabanta yana fadan plx rumaisa, wlh ke kadaice a raina, nayi miki alkawarin zan chanza halina idan har kika amince da soyayya ta, kiduba fa kigani wannan ma kadai ai kinyi jahadii...

Bata jira yakarasa kalmarsa ta jahadi ba ta wanka masa wawan mari tas kakeji kafin tace "bana son, kuma natsani ganinka " takarasa maganar tahuci ta zagaya ta gefensa ta fice..

Tsayi yayi a guri daya sai kace bushanshiyar bishiya
Dafe gefen  kumatunsa  yayi yana mai jin zogin marin da rumaisa tai masa,

 Hartayi masa nisa kadan  yak'wala mata kira tajuyo ya saukar da hannunsa akan kuncesa ya share hawayensa yace " bazan iya hakura dakeba, domin kece muradina, tunda nabiki ta laluma amma kinki aminta dani dan haka yau zan saceki"

Yana gama fadan hakan yajuya ya shiga motarsa yabar unguwar

"Mahaukaci" rumaisa tafada fuskarta a ya tsune sannan taja Tsaki taci gaba da tafiyarta harta isa bakin gidan su gabanta faduwa yake akan maganar daya fada mata nacewa  nasaiya saceta...

Tana isa kofar gidansu tatura kofar tashiga a harabar gidan taga motar abbanta a gefe yayi parking, cak ta tsaya guri daya, gabanta yayi mummunan faduwa, bugun zuciyarta yakara karfi, duk tsoro yakamata, domin tasan dacewa da suci karo da Abba akan maganar majnoon to gwanda ta fada rijiya zaifi mata sauki, da kyar ta iya taka kafafunta takarasa bakin kofar falo,

A hankali take  tura kofar falo  tashiga tare dayin sallama, jin sallamarta yasa ya mike tsaye yana jiran shigowarta..

A tsaye ta samesa fuskarsa a murtuke

Sau daya tadaga kai suka hada ido da sauri ta sauke kanta kasa, sum sum  take tafiya kamar ba lanka ajikinta, gabanta sai faduwa yake tanufi dakinta...

RUMAISA!! Cikin hargowa yakira sunanta saida ta kusan faduwa akan tsoro

Hawaye suka soma zubo  mata a hankali takarsa gurinsa, tas tas yadauketa da mari biyu kyawawa saida tasaki kara  tayi baya tadafa kan kujera,

Da gudu umma tafito daga dakinta cikin baccinta tajiyo karar mari,

Alhaji lafiya" itace kalmar da umma take fada tana kokarin karasowa gurinsu, rumaisa najin muryarta ta tamike  da gudu ta rungumeta  tana kuka, cike da  masifa yafara mata magana "bana hanaki zuwa gurin  majnoon  dinnan ba, wato kin maida maganata maganar banza, nizaki mayar karamin mutum, wannan shine karo na biyar kenan danayi miki a kansa amma kinki jih, to wlh kisani yau kinyi kuma kinkai karshe, gobe gaben nan zan daura miki aure da *faisal*, tunda nalura dacewa bakida hankali, meye abinso acikin mahaukaci, shashashar yarinya"

Rumaisa takara fashewa da  kuka jin yakira sunan faisal, kuma da furucinsa na cewa gobe zai daura mata, batajin zata iya rayuwa da wani da namiji a duniyar nan idan ba majnoon bane, tana manne a jikin umma tafito ta gurkusa  a gaban abba tana kuka ta rike masa kafa  " dan Allah abba kayi hkr wlh banason faisal"

A fusace abba ya dukar da kansa kasa yana kallonta yace "idan bakya sonsa idan na aura masa ke ki  kashesa" yana gama fada  ya firgi kafarsa yabar falon yanufi dakinsa..

Durkusawa tayi kasan cafet tana kuka sosai, a lokacin umma takaraso gurinta fuskarta  ba annuri tadafata tabaya " rumaisa"
Dasauri tatashi ta rungume umma tana kuka tace "umma nashiga ukku, abba zaimun aure da faisal, kuma wlh umma bana sonsa" .....


Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka, nan ta fara salati harta samu na tsuwa tadan wani lokaci sai kuma taci gaba da tafiya

Takai dap da Motar taji ankira sunan " *Rumaisa* !!!" Gabanta yafadi ko juyowa batayiba taci gaba da tafiyar  ta ..

Da sauri yafito daga cikin motarsa ya tari gabanta sukayi ido hudu, ya marairaice fuska kmar zainyi kuka yace "haba rumaisa meyasa bakijin tausayin zuciyatane, plx kitsaya ki saurareni dan Allah koda na minti biyune "

Hawaye sunka  cinciko a  idon rumaisa, a duk lokacin data gansa wani irin bakin ciki takeji ya ziyarci zuciyarta,

Muryarta tafarasa rawa   kalilan abu zai iya sakata kuka, bude bakinta kuwa sai kuka "wai menai maka kake bibiyana kahanani jindadin rayuwata dan Allah ka fita harkata"

*Fahad* yayi shiru yana sauraron kukanta, zuciyarsa na masa kuna, kwata2 bayason ganin kukan rumaisa, idan tana kuka shima jiyakeyi kamar zai tayata,  muryarsa na rawa yace " sonki nake rumaisa zuciya ta tsunduma a cikin kogin sonki, iduwana basa muradin ganin kowa saike, a koda yaushe kece a mafarkina, plx rumaisa dan Allah kisoni"

Hawayenta ta share ta sakar masa wani irin  tsaki tace " ko  kai kadaine namiji a duniya bazan sokaba, daidai da dakika daya bantabajin ina sonkaba" kafita daga harkata, kabano hanya na wuce " tanakarasa maganar tana kokarin turesa, shikuwa sai binta yake a duk gefen dataje yana fadan plx rumaisa,

Da taga bayada niyar bata hanya taturesa ta wuce,

 A karo na biyu yakara shiga gabanta yana fadan plx rumaisa, wlh ke kadaice a raina, nayi miki alkawarin zan chanza halina idan har kika amince da soyayya ta, kiduba fa kigani wannan ma kadai ai kinyi jahadii...

Bata jira yakarasa kalmarsa ta jahadi ba ta wanka masa wawan mari tas kakeji kafin tace "bana son, kuma natsani ganinka " takarasa maganar tahuci ta zagaya ta gefensa ta fice..

Tsayi yayi a guri daya sai kace bushanshiyar bishiya
Dafe gefen  kumatunsa  yayi yana mai jin zogin marin da rumaisa tai masa,

 Hartayi masa nisa kadan  yak'wala mata kira tajuyo ya saukar da hannunsa akan kuncesa ya share hawayensa yace " bazan iya hakura dakeba, domin kece muradina, tunda nabiki ta laluma amma kinki aminta dani dan haka yau zan saceki"

Yana gama fadan hakan yajuya ya shiga motarsa yabar unguwar

"Mahaukaci" rumaisa tafada fuskarta a ya tsune sannan taja Tsaki taci gaba da tafiyarta harta isa bakin gidan su gabanta faduwa yake akan maganar daya fada mata nacewa  nasaiya saceta...

Tausayi tabawa umma,

 Umma tarika shafar bayanta tana cewa " kiyi hakuri nasan zafin zuciyane kedibarsa a  yanzu, kije daki nizanje namesa, zamuyi magana dashi "

"Tohm" kawai rumaisa tafada tana shanshekar kuka ta wuce dakinta

Tana tsaye tana kallonta harta shige dakinta, sannan ta girgiza kai ta ya tsune fuska tace " wayuwar banza, aini banki ace an miki auren  kin mutuba, d'an kishiya ai ba da bane, yadda mahaifiyarki ta mutu akan bakin ciki kema haka nekeson kimutu, niba inda zanje dakina zan koma insah bacci na, Allah yasa gobe ai miki auren ni ina ruwa kije cen ki karata mtsw" tsaki taja tanufi dakinta kan gado ta koma tayi kwanciyarta sai bacci

*Fahad*kuwa yana barin unguwar  gidan sa yazar ce, wani irin katon gidane mai fasalin gaske, shekin glass kawai ke walwalniya a cikin harabar gidan,

Abikin kofar shiga falon bodyguard ne tsaye fuskarsa a murtuke yana gadin kofar, ganin faisal yasa  yayi saurin bude masa kofa yashiga ciki, yana zuwa yafada dakinsa, zuciyarsa cike da kuna yakasa zaune yakasa tsaye sai safa da marwa yakeyi a tsakiyar dakin, tunani yakeyi ta wace hanya zaibi ya cimma burinsa akan rumaisa, dasauri yakarasa bikin telephone din da kecikin dakin  wata number naga ya daddan sannan yadora telephone din a kunnensa, kiran yana shiga aka dauka, baijira wadda yakira yayi maganaba yayi sauri   cewa "akawomin giyi kwalba ukku, yanzu ina jiranku" bai jira aka bada amsaba ya kashe wayar zuciyarsa cike da bakin cikin akan abinda rumaisa tai masa, tunda yake a duniya ko mahaifinsa bai taba marin saba amma yau za ace macce tamaresa, wani irin haushi yakeji, dakye ya iya kai zaune  ya dafe  kansa ya rufe idonsa, dai dai lokacin da rumaisa ta wanka masa mari yakegani,  da karfi ya bude idonsa yana huci idonsa sunyi ja sosai,

A lokacin yaji anfara knocking na kofar dakin, da kyar ya iya bude bakinsa yace "yes com in"

Ma aikacin gidan ne  yashigo da uniform dinsa na aiki, da kwalabe guda ukku a faranti,

Bai masa maganaba yakara saman dinner table ya ajiye masa kwalaben akai, sannan yafita yamayar da kofar dakin ya rufe,

Dasauri faisal ya cire rigar dake jikinsa ya jefar akan gado sannan yakarasa bakin dinner table din yadauko kwalba daya ya bude yafara zukar giyar a hankali yana lumshe ido, tunanin marin da rumaisa tai masa kawai yake yana karajin zuciyarsa nai masa zafi,

*Bayan minti 20*
Saida yayi mankas da giyar sannan yafara sabbatu, magana yakeyi cikin muryar mashaya giya yadaga d'an yatsansa daya  yana cewa "ni kika mara, koh..zakiga mezan miki" yana karasa fadan hakan ya mike tsaye yana tangadi kamar zai fadi sai kuma ya bushe da  dariya yana cewa "Zan saceta Allah saina saceta" sai kuma yayi taku kadan sannan yadaga hannusa dayake rike da kwalbar giyar kamar yana ganin mutum kusa dashi yace "ni kika mara koh Allah saina kasheki"

Duka yakai da hannun nasa ai kuwa nan kaji kamass kwalbar ta fashe,   ginin dakin yadaka, dariya yayi yace "ah...ah... sai kuma maganar ta kasa fita, saida makwogaronsa ya sarke sannan ya iya cewa " nakasheta, ke kin isa ke mareni ne ai dole saikin mutu  " yakarasa maganar yana nuna ginin dakin,

Hakadai  yaci ga sabbatunsa duk abinda yazo masa arai fada yake,

A hankali dai ya sulale kasan cafet din dakin sai bacci,
******       *****  ******
*Bayan wasu a wanni*
Sai magriba sannan rumaisa ta iya fitowa daga cikin dakin bayan tagama sallah masu aiki suka kawo mata abincinta,

Abinci tadauko  tasamu tafito daga cikin dakinta, tafito falo cikin sand'a takeyin tafiya  tana kokarin sulalewa taje gurin majnoon, kamar daga sama taji an k'walla mata kira da sauri ta juyo abbanta tagani ransa a bace da gudu tajuyo takoma dakinta tasa keys ta kulle...


Da sauri abba yakarasa bakin kofar dakin yana dukan kofar dakin akan ta bude,  amma taki bude wa, sai kukanta yakeji,

Saida yayi mata barazana dacewa  idan bata budeba yanzu zaije ya dauko sepia  key yabude dakin kuma idan yabude zaiyi mummunar saba mata

Sannam tatashi tazo tabude kofar, jikinta na rawa, ta shunkuyar da kanta kasa,

Abba  yashigo dakin ransa a bace yake kallonta " wlh idan kika fita a gidan nan bada saninaba, banyafe miki ba, kuma wlh zan iya  tsine miki, akan wannan *Majnoon* din, kehar kin isa nahaifeki kuma kikibin umurnina"  da sauri rumaisa tadago kanta a lokacin har hawaye sun fara ambaliya akan fuskarta, tana kallon abba takara fashe da kuka "kayi hakuri abba bazan jeba  wlh bazan je dan Allah karka tsinemun" da sauri ta ajiye kolar dake hannunta takarasa bakin gado ta kwanta sannan tadago kai tana dube abba, muryarta na sarkewa saboda kuka tana cewa "kagani abba na kwanta wlh ba inda zanje yanzuma zanyi bacci, sannan  ta hada hannayenta guda  biyu tace "Dan allah abba karka tsinemin" takarasa maganar tana kuka,  sannan ta noke kanta cikin filo,

Abba yana huci yace " nidai na fada miki karkibar gidan nan bada saninaba"  yana gama fada yajuya yafita yabar dakin

Kuka take  sosai zuciyarta har wani zafi take  edonta duk sun kunbura,  yazatayi da soyayyar majnoon datake sabuwar fill a cikin zuciyarta.. haka dai taci kukanta  har aka  kira sallar isha sannan tatashi taje tayi alwala, tazo ta dora sallah, bayan tagama sallar tafara kwararo adu a, saida tayi hawaye kafin takarasa adu' ar,  tana kammala adu'ar sannan tanade sallaya ta takoma saman gado ta kwanta zuciyarta cike da tunanin majnoon komai zaici yau cikin darenan, a dai dai lokacin hawaye suka sauko kan kumatunta,  koda tagama tunaninsa hawaye sharkaf a fuskarta, a hankali take fitar da sautin kukanta, tarasa gane wane irin sone takeyiwa mahaukacin nan,

Sai a lokacin tatuna da bata rufe kofar dakin taba, da kyar ta iya tashe taje ta rufe dakin sannan tadawo tayi shirin bacci sannan takara  komawa kwance,  tana  cikin tunaninsa bacci ya kwasheta...

*2:39am Na dare*
Majnoon yana kwance a gefen layin wata unguwa mai mota yabiyo layin, ga alama mai motar nan yayi mankas da giya  tun daga nesa yake masa hoh amma Majnoon yaki ko motsawa dominshi baccinsa yayi nisah, mai motar na karasa wurinsa yatakashi ya wuce ....

*Majnoon* ta furta Da karfi rumaisa ta farka daga mummunan mafarkin  datake, da salati a bikinta, kuka yasoma zo mata, tayi jim tana tunani mafarkin, karde ace hakan tafaru da Majnoon, saitaji tanason ganin Majnoon a yanzu amma kuma saita tuna da maganar abbanta, hawaye suka sauko kan fuskarta a hankali ta sulale takoma kwance, tundaga lokacin bata kara komawa bacci ba sai sake2 take a zuciyarta..

*Asuba tagari*
Bayan Rumaisa tayi sallar asubah  tashiga bandaki tayi wanka sannan tafito har a lokacin bata dawo normal domin gaggar  jikinta ce kawai a tare da ita amma zuciyarsa zakatakaf tana gurin tunanin Majnoon,

Bayan taga shirinta tadauko littafanta tanufi dakin abba, zaune tasame  saman kujera, nan ta durkusa har kasa ta gaidashi sannan tace "abba kayi hakuri da abinda yafaru jiya, kabani izini na fita, zanje makaranta"

Abba yadago kai ya kalleta har yanzu fushi yake da ita  yayi jim, sannan yace " ai fita kije makaranta yazama dole nabarki kije amma kisani bazan barki kitafi ke kadaiba zansa driver yakaiki, domin banason wata alaka takara hadaki da waccen mahaukacin, wai shin meyake dashi da sauran maza basa dashi, yaja nunfashi kafin yace " kuma maganar aurenki munyi magana da abban faisal yace na kara masa kwana biyu domin yanason yayi shirya2 amma badan hakan ba da yau dinnan zan daura miki aure, yasa hannu yaciro kudi ya mika mata yace "kije waje kicewa drive yakaiki makaranta kuma idan aka tashi yaje ya daukoki"

Koda ta dago kanta idonta sunyi ja sosai takarbi kudin sannan tatashi tafita...


Tana zuwa tasanar da baba driver cewa abba yace yakaita makaranta, ba musu bb driver  ya shiga mota suka lula makarantar,

Yana ajiyeta a harabar makarantar  ya juya, tun a cikin mota ta sanar dashi cewa idan suka tashi zata kirasa yazo yamaidata" tohm kawai yace,

Bayan bayar makarantar Rumaisa tayi tsaye tana kallon makaranta kafin tad'aga kafarta tafara tafiya cike da yanga take tafiya harta karasa cikin aji,  ganin kawayenta yasa takirkiri murmushi nan dai tadan waye fuska suka gaisa kafin malami yashigo a fara lecture,

1:30pm na rana Suka karasa lectures dinsu baki daya, kowa yafito nan tayi saida safe da kawayenta sannan tafito waje takira bb driver, bada jimawaba kuwa saigashi yakaraso..

Shiga motar tayi suka dauki hanyar gida,
Rumaisa ta dube bb driver tace "baba dan Allah inaso naje nan layin kusa da namu wurin wata zanje" bb driver yace "tohm shikenan ba matsala"

Bata kara maganaba saida suka kusa karasawa kusa dayin sannan tafara nuna masa hanya,  dai dai inda  tasan majnoon yana zama ta tsyar da bb driver sannan  tafito tana dubinsa amma bata ganshi,  danmm taji gabanta yafadi..

Mafarkin datayi jiya akansa shiya fado mata a zuciya gabanta yayi mummunar faduwa, hawaye suka cicciko mata edo, a zuciyarta take fadan kar dai ace abinda tayi mafarki yazamo gaskiya,

Shiru tayi tana kallon gurin kafin tajuya
 A hankali take kokarin juyawa, ta gefen edonta tasoma hangosa yana d'aga mata hannu, da dasauri ta juyo batasan lokacin data kasance cikin murmushiba, da gudu yake zuwa gurinta, yana karasa yaja birki saida kura tatashi, yana cizon rigarsa yace " ke kuwa shine jiya baki zoba koh, saida nayita kuka"

Rumaisa tayi kuru da ido tana kallonsa cike da tausayi, tabbas taga alamun hakan a idonsa domin gasunan duk sun kunbura nunfashi taja kafin tace "kaci abinci yau" ya girgiza mata kai, alamar a a

Tayi shiru tana kallonsa tace "jiya dadarefa " haka yakarasa girgiza mata kai a a"

Wani irin kallon tamasa saida hawayen dake cikin Edonta suka zubo, da sauri tashare sannan takasa hannunta cikin jakarta ta ciri kudi har zata bashi sai kuma ta makale hannu  tace  "nabaka kudi zaka iya sayen abinci  da kanka"

Ya girgiza mata kai yana Murmushi yace "eh zan iya, idan naje wurin talatuwa mai abince sainace tabani, nikuwa saina mika mata kudi"

Rumaisa tayi murmushi tace yawwa, gashi kaje kasiya " tamika masa kudin,

Karbar kudin yayi yana wasa dasu yace sannan yadago kai yana kallon rumaisa yace "kinsan wani abu, Rumaisa tace "a a saika fada "

Ya sunkuyar da kai yace  " jiya ina bacci wata mota tatashi takani"

Dam taji gabanta yafadi, mafarkinta yafara dawo mata a kwakwalwa da sauri  tace "amma dai bata taka kabandai koh"

Ya girgiza mata kai yace " eh, yana gama fadan haka sai kuma yayi shiru yana wasa da kudin dake hannunsa,

Rumaisa tace "kaje kasiye abincin nizan wuce nakoma gida"

Majnoon ya tsuke fuska bayason tatafi  yace " yanzu yaushe zaki dawo" rumaisa tace " sai gobe  irin wannan  lokacin"

Majnoon ya kalleta saikuma ya sunkuyar dakai yace " bazakizo dadare "

Rumaisa  tayi ajiyar zuciya tace  "bazan zoba Majnoon domin abbana yahanamun zuwa gurinka "

Dasauri Majnoon yadago kansa yana kallonta yace " abba baya sonane"

Rumaisa ta girgiza masa kai tana murmushi tace " yana sonka mana, kaida zaka aure 'yarsa mezai hana yasoka, tana kallonsa tace " kodai ka fasa aure nane"

Da sauri majnoon ya Girgiza kai  yana dariya yace "a a, ina sonki sosai" yana gama fada ya sunkuyar da kansa kasa yana wasa da yatsunsa, shi ala dole yaji kunya,

Yanayinsa yabawa rumaisa dariya,

Baba driver yana a mota sai mamaki yake me rumaisa takeyi a gurin mahaukaci gashi yaganta sai Murmushi take, ta mirror motar ya hangi wata mota a bayansa wadda tayi sanadiyar sakashi firgita fiye da kima, bakinsa na rawa ya iya furta "alhaji"

Da sauri yafito daga cikin motar, yana kiran rumaisa, domin tayi sauri tazo sutafi, tana juyowa yayi daidai da lokacin da abbanta yafito daga cikin motarsa, sukayi edo hudu ko kashe motar bai tsaya yiba,  yanufi gurinsu,

Rumaisa kuwa tuni tayi mutuwar tsaye,

Fuskarsa ba annuri kwata kwata, yakarasa gurinsu, kafin yayi magana saida yadauke Majnoon da wani irin wawan mari, rumaisa ta kanne edonta domin bazata iya ganin ana duka Majnoon ba,  a  dai dai lokacin Hawaye suka sauko kan kuma tunta, 
Kafin ta bude idonta itama taji saukari mari tas tas,  saida ta ja da baya kamar zata fadi,

Yana dafe da kumatunsa Ganin an mari rumaisa yasa yayi ihu cikin sigarsa ta marasa hankali yayi kan abban rumaisa ya kamo  kwalar rigarsa, ya ware hannu zai mazga masa mari rumaisa tayi saurin rike hannunsa tana kuka tace " karka maresa abba nane "
A hankali Majnoon yasaki wuyan abba yana huci,

Abba kuwa gabaki daya ya tsorata, ganin yadda majnoon ya damkesa, indai baibar gurinsaba to komai zai  faruwa,

Majnoon ya rike hannun rumaisa, wannan shine karo na farko dataji majnoon yataba jikinta, wani zar taji, ta lumshe ido, tayi mamakin jin hannunsa da laushi,

Abban rumaisa yagyara rigarsa yana huci yace "sakarmun 'ya"

Uffan Majnoon baice dashiba, rumaisa kuwa kuka kawai take, tana fana dan Allah abba kayi hkr wallahi bazan sakeba,

Da karfi da yaji abban rumaisa yashiga Firgar rumaisa daga hannun Majnoon shikuwa Majnoon yariketa gam saikace abarsa,

Nan take mutane suka taru a gurin, da kyar aka iya b'amb'are rumaisa daga hannun Majnoon, mutane suka rirrikesa..

Abba rumaisa ya fincikota  tana kuka, yanunawa majnoon yatsa yace "kaiiii dani kakee sa insa" sannan  yayi kalci yaja hannun Rumaisa dakarfi yanufi mota da ita,

Janta yake amma tana juyowa tana kallon Majnoon, wanda mutum sama da biyar duk sun rirrikesa,

Rumaisa kuka take sosai,

Abba na karasa bakin mota ya bude kofar motar ya jefata a ciki, sannan ya zagaya ya shiga  motar  yabar unguwar.

Baba drive duk ya tsorata,
 tsoro yakeji kar ya rasa aikinsa...


Bb driver kuwa Cike da fargaba abinda zai tarar a gida yashiga motar yatada yabar unguwar..

****      ***     ****
*FAISAL* yana kwance saman gado ya tayar da edonsa sama yana kallon ginin dakin, edonsa sunyi ja sosai, da duk kan alamu kuka yayi sosai, kaman nunta yafara zayyanowa mai kyauce da fasali, bayajin zai iya rabuwa da ita,

Kofar dakinsa yaji anturo da sauri yashare hawayensa,  yana kallon kofar,
Abbansa yashigo cikin shigar kamala, da jikar aiki makkale a kafadarsa,

Basai an fada masa yasan halin da yaronsa yake ciki, domin  zai iya kasan  cewa shine silar matsalar,

Kallo daya faisal yayi masa ya kauda  kansa gefe,

Karasowa abba yayi kusa dashi yana kallonsa, tabbas faisal yana cikin damuwa sosai, murya kasa2 faisal yace "daddy ina kwana"  daddy yace "lafiya lau" yadan shiru nadan wani lokaci kafin yayi ajiyar zuciya  sannan yace "meyasa baka fito mukayi break fast ba"
"Daddy banajin yunwa" faisal yafada yana kokarin komawa kwnace,

Daddy ya nisa yace " jiyafa bakaci abinciba  yau ma haka zaka wuni, kawai aka na hanaka auren rumaisa, nifa cetonka ne nake akan bakin cikin da zaka shiga bayan anyi aure domin yarinyar nan ba sonka takeba, kayi hakuri kacire yarinyar nan a ranka domin ni banzan yarda ka aureta ba"  Faisal yayi saurin tashi yana hawaye "daddy dan Allah kayi hakuri, wlh nakasa cire son rumaisa acikin zuciyata, ban taba tunanin zan iya bijirewa umarninkaba amma a yanzu zuciyata takasa hakura daddy" yakarasa maganar kamar mai shirin yin kuka ,

Daddy yayi ajiyar zuciya yana kallon tilon d'ansa faya susuce akan soyayya,

Daddy ya furzar da iska yace "rumaisa bata sonka danme dazaka cewa dole saika aureta, nifa badan MAhaifinta yana amininaba da tuni na dade da tarwatsa wannan lamarin, look faisal, daddy yadafa kafadarsa sannan yaci gaba dacewa "hakuri shine jigon komai kasawa zuciyarka salama insha Allah wata rana zaka manta da ita, kaji faisal" yakarasa yana kallonsa ido cikin ido

Shiru faisal yayi nadan wani lokaci kafin yace " daddy wlh inasonta plx dan Allah kabari na aureta, nikobata sona zan iya zama da ita plx daddy" yakarasa maganar cike da magiya

Daddy ya girgiza kai yana mamakin almarin faisal shi ana gaya masa magana amma ko dauka bayayi, baice dashi komaiba, ya mike tsaye sannan yace "shikenan zanyi shawara akai tashi kaje kaci abinci, saina dawo zamuyi magana"  bai jira me zai furtaba daddy yafice yabar dakin, sai a lokacin faisal yaji sanyina zuciyarsa, sannan ya mike tsaye.. soyayyar rumaisa itace a cikin kowanne  bugun zuciyarsa a koda Yaushe. ..

*_Waye faisal_*

Faisal d'a daya tilo a gurin mahaifinsa Alhj nura(wato daddy)Yataso cikin gata da azriki, iyayensa suna matukar sonso domin shine kadai d'ansu daya tsaya a duniya, sun haifi wasu yaran kusan hudu amma duk sun rasu, faisal ne kad'ai yatsaya,

Hakan yasa suka dauki son duniya suka daura masa, sun bashi tarbiya akan tsarin addinin musulunci..

Mahaifiyar faisal haj cima yar asalin mali ce, alhj nura kuwa dan 9ia ne, aikine yakaisa mali acen kuma yagano haj cima  yanemo aureta kuma aka bashi, bayan andaura aurene yadawo  da ita 9ja,

Faisal farine amma ba iri  farin nan sosaiba yanada tsayi daidai misali, yanada gwarjini sosai a gurin wadda baisaba dashiba, sannan kuma yanada fara 'a,

Wata rana  yaje karbar sako a gurin mahaifin rumaisa a lokacin yaganta kuma yaji yana sonta kuma yanaso takasance matarsa, bayan yakarbi sakon yadawo gidane yasanar da daddy cewa shifa yaga matar aure gidan amininsa, bakaramin jindadi daddy yayiba, domin ya kosa faisal yayi aure,

 Washe garin ranar tunda  safe daddy  yaje yasanar da mahaifin rumaisa cewa d'ansa yaga 'yarsa ynaso, abban rumaisa yajidadi sosai tun a gurin  yace yabayar  da ita ga Faisal kuma tana kare karatu za a daura musu  aure,

Daddy yayi godiya sannan  yadawo gida yasanar da  faisal cewa anbashi rumaisa,  bakaramin jindadi faisal yayiba, yayiwa daddy godiya  sosaii,

A daren Ranar da faisal yafara zuwa gurin rumaisa babu abinda yaganewaa domin taki sake masa fuska, kuma taki yi masa magana, 

Shine daya dawo gida yasanar da iyayensa yadda  sukayi da rumaisa, daddy ya tsorota sosai dominshi bayason dansa ya aure wacca bata sonsa, domin yasan illar auren dole

Washe gari daddy yaje gidan abban rumaisa domin yaji gaskiyar lamari shin rumaisa nasaon yaronsa ko bata sonsa,
 Bayan yakarasa gidan a bakin  kofar falon  yajiyo hargowar abba yana yiwa rumaisa fada akan acewa dole saitaso faisal kuda kuwa ranta zaifitane,

Hankalin daddy yatashi makura, baijira abba yazo yasamesaba yayi saurin dawowa gida yasanar da faisal komai dayaji tare da bashi shawarar cewa yadaina tunanin rumaisa a ransa domin shi bazai barshi ya aure wacca bata sonsa ba, Momyn faisal ma tabiyewa daddy akan itama bata yarda ya aure wacce bata sonsa ba..

_Wannan kenan_
**** **** ***
Yajima a tsaye kafin yakarasa toilet yayi wanka sannan yafito ya kammala shirinsa yakarasa falo  yagaida momynsa kafin yafara breakfast...

**** ***** ***
A harabar wani dankararen gida yaja parking ma'aiktan gidan sukawo kansa da gudu suka bude masa kofar motarsa, yafito cike da kasaita wani farin  dattijone fuskarsa amurtuke, alamun tsufa sun bayya a fuskarsa makura,

Farar shadda ce a jikin dakuma babban riga ga hula fara hakama takalmi farare, sai wata yar gajeruwar sanda dake rike a hannunsa,

A hankali ya kalli ma aikatan yace  "where is my son" daya daga ma'aikatan  ya sunkuyar dakai domin sunsan halinsa ba a maganani dashi ana kallonsa "alhj wlh tun jiya daya shiga cikin dakinsa bai sake fitowaba kuma yahanawa kowa shiga cikin dakinsa, yanzu haka abincinsa na nan a kichin, sai kira yakeyi yace a akawo masa kayan maye"

Farin dattijon yace "what!! Yakara kalon ma'aikatan ya rafka musu tsawa"kuna aikinme, meye amfaninku a gidan, dabazaku kirani kusanar daniba, wlh duk wani abu yasami d'ana saina kasheku baki daya, yana ina yanzu"

Muryar ma'aikacin tasoma rawa domin ganin yadda ya tambayesa a hnakli yake cewa "yana ciki "

Baijira yakara maganaba ya yanufi cikin gidann....


Dakinsa ya wuce direct, ya bude kofar dakin warin giya da hayakin taba ya ziyarci hancinsa saida yayi tari sannan yakarasa shiga dakin,

Zaune yasa mesa a tsakiyar gado komai na maye akwai agabansa hurar tababrsa kawai yake idonsa sunyi jajir haryanzu baidana tunanin marin da ta masa ba a duk lokacin daya rufe edonsa karar marinn kawai yakeji tasss,

A hankali farin dattijon ya furta "FAHAD" yana kokarin  karkade hayakin tabar daya mamaye dakin, dasauri yakarsa gurin yana kallonsa "son meyake faruwane, nasan baka shiga cikin irin halam sai idan antabaka, uban waye yatabaka a duk cikin fadin garin nan gaya munshi dan gidan waye"
 Hawaye suka sauko a edon fahad zuciyarsa na tafasa a hankaki ya iya furta " papa ba wani bani, wata ceee"

Papa yayi saurin cewa "wataaa ce !! Kalmar yafada cike da mamaki kafin ya karbe tabar dake hannunsa ya jiye gefe sannan yatattar kyan mayen dake gabansa ya turasu gefe shikansa papa edonsa sunyi ja domin ga hayakin dakin kuma yanzu gashi yaji antabaa yaronsa, " wacece ita kuma  meta maka"

Fahad yace "  banason kadau matakin komai akanta papa, kabarni da ita wlh saina koya mata hankali, zansa asakceta"

 bacin rai sosai papa yake, cikin fada yake  furta "ba ita kadaiba harda iyayenta domin duk waadda yatabaka a garinan to wlh sai yasan yataba dan gidan Alhaji babba" papa yadaki kirjinsa

Fahad yashare hawayensa sannan yace " a  a papa karka kama kowa nata bana maso su san nina saceta, domin satar har  abada zan mata, kabarmin komai a hannunna"

 Zuciyar  papa tayi matukar baci domin bayason abinda yataba fahad jiyake dashi, bayason yamusa masa, hakan yasa yabar komai a hannunsa, yayi lallashinsa sosai kafin yabar gidan saida yasashi gaba yaci abinci sannan yayi wanka ya shirya, sannan papa yabar gidan,

Waye *FAHAD*

Alhj sani babba shine mahaifin fahad hamshakin mai kudine, yana da kudi sosai , asalinsu ba haisawa bane yarobane, amma zuwansu kasar hausa yasa sukejin hausa sosai kamar su suka kirkireta,

Saida Alhj sani babba yakai shekara 10 da aure bai samu haihuwaba, yayi maitar haihuwa kamar ya mutu har malama da bokaye saida yabi kafin a samu cikin fahad,

Kwatsam kamar daga sama matarsa haj kubura ta samu ciki, ai kuwa  je kaga murna a gurin alhj babba, ya kula da haj kubura sosai lokacin data sami cikin fahad haslima 9ja yabari da ita domin afad'arsa 9ja hayaniya tayi yawa, American yakaita acen ta haife masa yaronsa, ranar bikin anyi almubazanci domin kowa  yasami naira lokacin bikin fahad,

A American fahad ya girma domin duk dabi unsa yadauko, acen yafara karatunsa harya kammmala,

Yanzunma sunzo ganin gidane a 9ja daman duk shekara suna zowa sau daya,

_Wannan kenan_

**** **** ***
Abban rumaisa kuwa yana karasawa da ita gida ya jefota a falo har alokacin kuka take tana bashi hakuri, baice da ita uffanba yannufi dakin umma a bikin kofar dakin yatsaya domin yaji tana waya, a cikin wayar datake yaji tana fadan "keni ina ruwana da yarinyar  ni wlh bankibta mutuba domin ni natsanima naganta" hakadai taci gabba da fadan munanan kalama akan rumaisa, Abba yana labe a kofar dakinta yana jinta..

Abba yayi saurin barin bakin kofar dakin domin basau dayaba yashajin irin wad'an nan kalaman daga bakin umma, amma yakasa daukar mataki,

 dakinsa yanufa yadauko wata zankadeediyar bulala yadawo  falo gurin rumaisa, tana zaune a gefen  kujera tana kuka tana ganinsa da bulala ta mike tsaye domin tasan yau kashinta ya bushe, kuka take tana fadan dan allah abba kayi hakuri bazan sakeba" 

Idon abba sunyi ja sosai sai kokarin matsawa yake kusa da ita gadan gadan taga ya nufo gurinta, ihu ta saka tana kuka yafara auka mata bulala,

Da gudu umma tafito daga dakinta "alhj lafiya kuwa" dasauri takarasa gurinsa tana kokarin  kwatar bulala daga hannunsa, wata  irin tsawa yadaka mata saida taji tsoro, ai kuwa dolenta gaja baya,
 daman dai bason kwatar bulalar take ba duk abinda takewa rumaisa na munafuncine, dadin dukan takeji har cikin ranta,

Saita kintaci baya ganinta ta kauda kanta gefe tayi gwalo itakam yau anyi mata abinta takeso ,

Cike da munafunci take cewa " haba alhaji kadaina dukanta yarinyacefa  "

Abba ko sauraront baiba saida yayiwa rumaisa lilisi sannan yasauke bulalar yajuyo ya kalli umma yana huci "kekuwa wlh kikyayeni" yana gama fada yabar falon,

Umma tayi shiru duk da bataso  rumaisa amma tayi matukar bata tausayi, karasawa tayi kusa da iya ta rikota tun tana kuka harta daina kuka abu daya bakinta ke furtawa shine "ummata!!!ummata!!"

Umma tamikar da ita tsaye da kyar ta   iya kaita dakinta takwantar da ita kan gado, bata ce mata uffanba domin wani irin haushi takeji a lokacin dataji taba fadan ummata, tana ajiyeta tabar dakin....


Rumaisa ta kwanta saman gadon duk jikinta ciwo, fatarta harta kunbura , idonta sun fito bulla2,

Tunanin ummanta kawai take, tasan da  ace yau ummata nan da bazata bari ayi  mata  wannan dukanba, sai a lokacin tasamu tayi kuka,

Sosai takeyin kuka,  bata ankarabba bacci yadauketa, zuciyartaa cike da bakin cikin halin datake ciki,

Abba kuwa daki yakoma yayi wanka yagyara jikinsa domi duk yayi gumi a kan dukan dayaiwa rumaisa,

Sannan yafita police station yanufa yafadawa yan sanda cewa yanaso akama majnoon, sukam sukace bazasu kama mahaukaciba, haka yayita musu magiya amma sukace sufa bazasu iyaba,

Dolensa  ya hakura yabar station din amma zuciyarsa takasa hakura akan abinda majnoon yamasa, kawai yayanke shawara aransa zaisa 'yan daba su narkawa majnoon dukan tsiya  cikin dare... haka  kuwa ya ajiye a ransa..

Sai 4 na yamma rumaisa tafarka, jikinta duk yayi tsami da kyar ta iya tashi taje tayi wanka d ruwan dumi, koda zataji saukin ciwon dake damunta, bayan tagama wanka  tayi alwala sannan tafito, tadan shafa mai,, sannan takarasa bikin drower tadauko hijab, komai datakeji ba kama jiki,  a hakan  tayi salloli biyu azahar da la'assar, bayan taggama taci abinci, sannan taka dawowa saman gado ta kwanta,

A hakadai ta yuni bawani kuzari a jikinta.

Misalin karfe 9 nadare rumaisa kwance a  tsakiyar gadonta, sanye take  da rigar bacci,tunani kawai take tana hawaye, dukta fita hayyacinta, a yuni daya dukta soma ramewa,

Majnoon dinta take gani a duk lokacin data rufe idonta, hawaye fal a idonta, ummata ta tuna sai kuka, kuka tasomayi sosai cikin  kukan take fadan "haba umma meyasa zaki tafi kibarni, meyasa nakasa binki, umma na nisan nan kusa zanzo gareki cikin yan kwanakinnan domin nagaji da duniyarna... ummana zan mutu...." takarasa maganr tana kuka abin tausayi Allah sarki rumaisa, tayi rashin mahaifiyarta tun tana tanada shekara 12, tun daga lokacin da mahifiyarta ta rasu bata kara samun farin cikiba sai lokacin da ta hadu da majnoon,  to gashi shima ana kokarin rabasu, 

Haka dai taci kukanta mai isarta har dare yafara nisa sannan tayi adu'ar bacci tabi lafiyar gado, har bayan bacci yafada daukarta tatuna bata rufe kofar dakintaba, Taso ta tashi amma saita kasa, hakura kawai tayi tashiga sharar baccinta...

Karfe 2:00am nadare mutun biyu cikin baka ken kaya suka dirko ta ginan gidan su rumaisa a hankali suka karasa cikin falon bakowa hakan yabasu damar shigewa dakin rumaisa kai tsaye, kwance suka sameta saman gado tana bacci,

Dayan yakarasa inda take yafitar da wata porda ya zuba mata a hanci, kadan tayi kara saikuma takomaba bacci haka suka daukotaa suka fice da ita daga gidan babu wadda yasani,

_Washe gari_

Misalin karfe 8:30  nasafe abba yayi shirinsa zai fita aiki, amma yaji shiru yayi dubin rumaisa tafito zuwa skull amma sai yaji shiru,

tashi yayi yanufi dakinta, yaduba bata ciki, sunanta yashiga kira a tunaninsa kotana cikin toilet hakan ma yaji shiru, tiolet din yanufa ya bude yaduba bata ciki fitowa waje yayi zuciyarsa cike da sake2 kala2, yadaisan rumaisa bazata guduba, yafi zargi saceta akayi,  da karfi ya kalawa umma kira, dasauri ta kara gurinsa "gani alhj lafiya kuwa "

Ina rumaisa " itace kalamar daya fara fada fuskarsa a murtuke

Umma ta kallesa da mamaki tace " ni ina zansan inda rumaisa take rabona da ita tun jiya dadare "

Cikin fushi abba yace " bazaki fito da itaba kenan, inafa sane daduk wata kisisina  da kike shiryawa, jiyama najiki kina waya wato kinsa aje akasheta koh"  abba yakarasa maganar yana kallon umma wacce tuni tafita hayyacinta tana mamakin kazafi, cikin tsawa abba yace "zaki fito da ita ko sai kin sha bakar wahala"

Nan Umma tashiga yi masa rantsuwa akan wallahi bata san inda take ba,  amma cewa yayi wlh bai yarda ba ita tasa ta aka dauke masa rumaisa, dan haka tajirashi yana  zuwa

Fita yayi yabar gidan yana huci, sai bayan yafita sannan  umma ta tuntsure da dariya, tana fadan ruwa su iza harda matuka jirgi, ace akarata ... rumaisa anshiga duniya, tafada tana dariya..

***      ***

A hankali take bude idonta tana kallon yanayin dakin wadda ya chanza mata  kamanni kamar ba dakin taba,

Da karfi tatashi  zaune, caraf idonta yasauka kan fahad dake zaune a gefe yana kallonta yana murmushi,

Firgita tayi ta tallatsa ihu mai matukar kara

Dariya taga yanayi mata saida tagaji sannan  tadaina ihun sai ta saka kuka tana fadan " dan allah kayi hkr kamaidani gida "

Murtuke fuska yayi, yana kallonta yake fadan  "aikuma keda fita daga gidan saikin haifemin yarana domin kinshigo kenan bake  ba fita, naso ace munyi harkar azriki dake kishigo gidan nan amatsayin amarya amma sai kikaki, amma yanzu gaki  kinshigo gidan nan a tsayin karuwa kuma bake ba fita, ya mike tsaye sai kuma yasaka dariya sannan yace "barka da zuwa sabowar alawa " yana gama fadan haka yafita yana dariya yamayar kofar  dakin yarufe....


Tana manne a jikin ginin dakin tafara sulalewa kasa tana kuka hartakai zaune kuka take sosai ta d'aga idonta sama sannan ta d'aga hannayenta masa tana kukan take fadan "Ya Allah kaine gaitana, kaine wadda zai iya kubutar dani daga khairin wannan mutum, Ya Allah karka barshi ya cika mummunan kudurinsa akaina, Ya Allah kafitar dani daga cikin gidan nan...." takarasa maganar tana kuka cikin murya mai matukar ban tausayi,

Da sauri tatashi takarasa bakin kofar dakin tana dukan kofar tana kuka, hadi da ihu kamar wadda tasan anajinta,

Dakarfi taji a turo kofar dakin taja da baya, wani irin katon mutum tanagani baki wulik idonsa sunyi ja sosai ya dallah mata harara saida ta firgita tana kokarin rufe idonta saboda muninsa cikin wata kakkaurar murya yace " keee!! Karki dame mutane da ihu, a gidan nan  mata da yawa irinki sunyi ihu harsun gaji wasuma anan suka mutu, idan kinshe karra ihu anan to ihunki banza ne domin bawanda zaiji, dan haka kisaurara mana" yana karasa maganar yafita,

Rumaisa takara fashewa da kuka tana fadan Ya Allah kakubutar dani daga shairin wadan nan mutane...
****           ****            ***

Bayan a wanni kadan Abba yasake dawowa gidan har a lokacin babu annuri a fuskarsa, zaune yasami momy  a falo tana kallon tv hankalinta kwance,

A gabanta yazo yatsaya fuskarshi a murtuke, tana ganinsa ta mike suna kallon juna " ina Rumaisa," Abba yafada yana kallo momy

Murmushi kadan momy tayi kafin tace "wlh ni gaskiya nake gaya maka, bansan inda tatafiba, shin waima idan na boyeta ina zankaita, dama dai tuncen yarinyar bata sanu tarbiyaba" takarasa maganr tana ya tsine fuska

Abba ya yi kalci yana huci yace "shikenan kina ganin kamar bazan iya komai a akai bako, shikenan karki fito da ita, wlh nabaki daga nan zuwa gobe da safe idan baki fitomun da 'yataba, zakiga mezan miki "  yana gama fadan maganar yabar falon

Cike da masifa umma take masa magana "to saime, mezaka iya yi, wlh ni ko kwana dari kabani bazan iya dawoma da iyaba dan Allah kaje kayi duk abinda zakayi, tana kokarin komawa zaune tace aikin banza yiwa kare wanka, kawai azo a mannawa mutum batar budurwa" mtsw taja tsaki sannan taci gaba da kallonta....


Rumaisa kuwa Kuka tayi 
harna fitar arziki itakam tata kaddarar a haka tazo mata,

Data daiga kuka bazai  kara sheta da komaiba hakan yasa   tadan tsagaita kuka, tatashi tashiga neman bandaki a dakin, cen ta hangi kofa takarasa gurin kofar ta bude, taga ban dakine shiga tayi ta watso  ruwa sannan tayi alwala tafito, kayan baccine kawai a jikinta tarasa yadda  zatayi tayi sallah, duban dakin take gefe da  gefe edonta duk  sun  kumbura,

Babu abinda tasamu wadda zai suturtata a dakin, fara  bincike  daken tayi  a  kasan gado taleka tana dube2,

 wani farin kyalle tagani dasauri  ta dauko tana kokarinn  warware kyalle,

Ware ido tayi tana mamaki a hankali bakinta  ya iya furta "HIJAB" mamaki take  meya kawo hijab din macce anan, gbanta yayanke ya fadi kardai ace fahad da gaske yake yana wiwa   mata fyade, 
Hawaye  tasoma  tana tunanin makomarta, a tsorace ta karkade hijab din tasaka sannan ta karkade kasan cafet din dakin tafara sallah, bata jimaba tagama sallar sannan tarafa kwararo adu'a akan Alllah ya kubutar  da  ita yasa fahad yakasa aikata komai akanta, adu'a tayi sosai kafin tagama  saida tayi kuka,

Bayan tagama sallar tayi zamanta akan sallayar tana kallon dakin, yunwa takeji kamar yan hanjinta zs su fito,

Tashi tayi tashiga nemi abinda zataci, kaf dakin bata samuba hakan yasa ta koma kan gado ta kwanta tana kuka,
****     ****   ****
Tunda Abban rumaisa yafita gidan daddy  yanufa yasanar dashi komai dake faruwa, lamarin yayi matukar girgiza daddy,  saidai yanajin yadda zai fadawa faisal wannan lamari,

Daddy ne zaune a falo shida momy sunyi jugum2 suna jimamin abinda yafaru da rumaisa, sake sake suke kala kala,

Faisal yafito daga cikin  dakinsa cikin shirinsa na fita office, farin yadine a jikin filtexs  irin mai shara2 dinnan yayi matukar yimasa kyau, 
Cikin ladabi da biyayya  ya durkusa yagaida momy da daddy,

Ganin yanayinsu kamar da dadamuwa a tattare dasu yasa yakasa hakura saida ya tambaya, duk da shima kuwa tun yafarka yau da safe yakejin  gabansaa  na faduwa,

"Daddy meya farune naga kamar kuna cikin damuwa" faisal yana kallon daddy yana jiran yabashi amsa , nunfashi daddy  yaja yanajin nauhin yadda zai gaya masa maganar, daddy ya kalli momy, momyma haka daddy take kallon sai kuma sukayi shiru,
Faisal kasa fahimtar komai yayi  duk ya soma tsorata domin yanaji a  jikinsa akwai abinda yafaru,

Ya juya yakalli momy yace "momyna tambaya nake amma kuyi shiru meyake faruwane" momy taja nunfashi kamar zatayi magana saikuma tafasa, daddy ya dubeta yace "fada masa mana"
Momy tayi jim kafin tace "Faisal, rumaisa ta bata, yanzu haka nemanta ake" wani irin tashin hankali yaji ya ziyarci duk ila hirin jikinsa, tuni hawaye suka soma fita a edonsa, kasa yadda da maganar yayi, ya dube daddy yace "daddy idan bazaka amince da aurena da  rumaisaba  basai kasa ammin karyaba domin karya bata kama cekuba, momy kufa iyayena meyasa bakoson  farin cikina"

Daddy ya sunkuwar dakai, wani irin bacin rai yakeji,  koda yadagonkansa eedo sa sunyi ja sosai, ya daga hannu ya wankawa Faisal mari, yanaa huci zuciyarsa har wani zafi take cike da masifa yake fadan "so haukane, ko kuka so zai iya  sakaka kafada iyayenka magana,  idan mun maka karya meye ribarmu...to.to" daddy yakasa yin maganar domin wani irin bacin rai yakeji, Faisal yana dafe da kumatu, yana mamakin wai yau daddy ne yadaga hannunsa ya maresa hawaye kadai ke fita a cikin edonsa, ya dube daddy da momy, muryar na  rawa  yasomma magana "yaune karo na farko daka fara dukana daddy,  badan komaiba sai  dan  akan innason rumaisa, yadanyi shiru kamar zaiyi kuka, sai kuma yafasa sannan yaci gaba da cewa  "bazan hanaka dukanaba domin kai mahaifinane kuma kanada incin dukana aduk lokacin dakasoz, amma bazaka iye cire  soyayyar rumaisa a   cikin zuciyata  ba, idan kuwa kukayi yunkurin rabani da rumaisa ts karfi da yaji to tabbas kuna kokarin rabani da rayuwata ne,  kuka yasomayi sannan yamike har a lokacin dafe yake da  kumatunsa, kamar  zai tafi saikuma yatsaya ya juya musu baya yana fda "idan har kuka rasa wani farin  ciki  a cikin gidan  nan ni zanyi duk yadda zanyi  nadawo  muku dashi,, ammani abu daya  kalilan kukasa cikamun, da kunsan irin yadda nakeji akan son rumaisa da bazaku  hanani auren tabs, da kunsan yadda zuciyata  kemun zafi a yanzu dabazakuyi yunkurin fadamun wannan maganarba, amma bakomai bazanga laifin kuba amma dai zance kunyi sonkai" yanaa  gama fada yanufi hanyar fita,

Momy tani zuciyarta tayi snyi,  hawaye take cike da tausayin d'anta daya kasa fahimtar  abina suka fada masa, daddy kuwa edinsa sunyi ja sosai yama rasa  mezaiyiwa faisal,

Faisal kuwa tunda   yatashi tsaye yakejin jiri, yana dibarsa yana kai daf da kofor fita yaji bugun  zuciyarrsa yasoma karfi, dafe kirrjinsa yayi yana jan nunfashi da karfi, a hankali ya sulale ya fadi kasa...


Cike da firgita momy da daddy suka karaso gurinsa, momy harta soma kuka tana kiran sunansa, daddy ya yadago kansa yana jinjigawa, yaga baya motsi hannu yasa yarika danna kirjinsa yana kiran sunansa,  amma shiru ba nunfashi, daddy yacewa momy "daukomin ruwa a firij"

Girgiza masa kai  kawai momy tayi tana kuka, da  gudu  taje tadauko gorar ruwa a firij takawowa daddy ya kwara masa,

Da karfi faisal yaja nunfashi yana  tari, daddy yaci gaba da danna kirkinsa yana kiran sunansa,

Da kyar faisal ya iya furta "daddy" sannan yarike hannun daddy gam,jikinsa duk yayi zafi, daddy ya kara rike  hannunsa yana hawaye zuciyarsa cike da danasanin kin amincewa da kudurin d'ansa,

 A hankali faisal yake kokarin tashi daddy yatayashi, ya mikar dashi,

Suka mike a tare, muryarsa na rawa yace "daddy kaini daki, zaciyata zafi, bazan iya zuwa gurin aikin nanba" yana karasa maganar ya langwabe kai a kafadar daddy

Yabawa momy tausayi sosai,
Daddy yarikashi suka nufi Dakinsa, ya kwatar dashi akan gado sannan ya janyo bargo ya rufe masa jikinsa,

Daddy yashafa kansa yana hawaye, faisal ya rike hannun daddy shima hawayen yake, muryarsa na rawa yace "daddy da gaske rumaisa ta bata"
Daddy ya girgiza masa kai " tabbas rumaisa ta bata"

Faisal yace "innalillahi wa innalillahi raju au" saikuma ya fashe da kuka, daddy yashiga lallashinsa, momy kam bayan kuka babu abinda take,

Jitakeyi komai yafaru da faisal laifinsune, sosai daddy ya lallashesa, ya kwantar masa da hankali, sannan suka fita sukabar dakin,

 faisal yayi kuka sosai, kafin yasamu bacci yadaukesa, zuciyarsa takamu da son rumaisa matuka ta yadda bazai iya jurar rashin taba..
*** *** ***
Abba rumaisa kuwa bayan yajima daki yanata sake2 akan lamarin rumaisa, yadai gaza gane komai, amma yafi zargin umma da ita tasa aka saceta,  fitowa yayi  yakara samun  umma zaune  tana kallo babu abinda yadameta, yakara jaddada mata cewa tafito masa da  'yarsa, umma tace ita wlh batasan inda takeba,
Ransa a bace yace "wallahi komai yafaru akanki ke kikajawa kanki.zakiga mezan miki"  yafita yabar gida..

Oho ma komai zakayi ga hanya" umma tafada sannan taci gaba da kallonta zuciyarta fal da farin ciki, Adu' a take Allah yasa kar aga rumaisa..

Bayan wasu 'yan mintuna kadan abba yakara dawowa gidan amma a wannan karon shida 'yan sanda police yazo, umma tana zaune tana kallo jikawai tayi abba yace "yallabai kushigo gatanan kukamata kuje da ita karku saketa saita gayamin inda takaimun rumaisa ta"

Da sauri umma tatashi tsaye tana zare ido hakan yayi daidai da lokacin shigowar  police din cikin  falon,

Umma tana kallonsu cike da tsoro ta rosa kuka tana fadan " wlh bansan inda takeba" abba yana cewa "karya take, itace tasa aka sacemun 'ya, daman tunba yauba nasan tana bakin cikin rumaisa"

Kuka mai sauti umma takeyi tana rokon abba amma ya kyankyashe kasa yace shifa,sai anje da ita idan tafada masa inda  'yarsa take to zaisa a saketa,

Haka kuwa akayi 'yan sanda suka jata suka tafi da umma tana kuka,

Kafin dare maganar tabi gari abba rumaisa yasa aka bazama nemanta duk inda ake sarar aganta amma ba a gantaba, bakaramin tashin hankali yashigaba. Akan rashin rumaisa..

A zuci nace ina ruwana shiya jawa kansa


A daren ranar rumaisa, tana zaune a bakin gado, kuka take sosai , duniya duk ta isheta, jitakeyi dama ace mutuwa tayi datafi mata, akan rashin ganin majnoon kwana daya tana cikin tunani,

Jitayi anturo kofar dakin da karfi saida tadan zabura,

fahad ne yashigo, da legoji a hannunsa tana ganinsa tadaina kuka ta mike  tana ja da baya, fahad yayi murmushi "kidaina jada baya ba abinda zan miki, ya ajiye ledojin a kasan carfet sannan yace "ga abincin kinan kizo kici, amma kisani daga yau bazan kara kawo miki abinciba domin nasaka akawo kayan  abinci a gidan nan kirika fita kina dafawa da kanki, saboda yanzu ke matar gidan nan ce"

Yana karasa maganar yafita yabar dakin yana dariya ya janyo kofar dakin yarufe,

Rumaisa kuwa daman yunwa takeji, da sauri tazo ta bude ledojin tana dubawa, abincine da lemon mai sanyi,

A dayan ledar kuwa dogayen rigunane guda biyar a ciki kala2,

Abinci tafara ci kamar wacce tayi sati daya bataci abinciba, dasauri takeci,

Tana cikin cin abincin tatuna da majnoon, yanzu mezaici, ta tausaya masa sosai, saida tayi hawaye,  a haka ta kammala cin abincinta sannan tatashi tashiga bandaki tayi wanka....


Tana fitowa daga ban dakin ta saka doguwar daya daga cikin dogayen rugunan daya siyomata,

Sannan tadawo gefen gado ta zauna ta sunkuyar dakai tana hawaye,

Tana zaune fahad yasake shigowa dakin, da sauri tatashi tana ja da baya, tana shirin yin kuka,

Fahada yayi tsaye yana kallonta yana murmushi, taku yafara kadan ganin tana ja da baya yasa yadan tsaya yana kallonta yayi murmishi yace "ikon Allah yau naga mata na gudun mijinta, tsorona kike,"

Rumaisa ta marairaice fuska "dan Allah karka matso kuka dani, kaji tausayina kamaidani gida, karka cutar dani, wallahi..." bata karasa maganar ba yadaka mata tsaya "ya isa..." saida rumaisa ta tsorata, idonsa sunyi ja sosai, yana kallonta saikuma yayi murnushi "ke kina tunanin zan barnikine a cikin gidan nan kawai ina kallonki, a ina kika taba ganin haka, ace lafiyan yen namiji kamata da kuma lafiyan yar macce kamarki, yanuna ta da dan tsaya sannan yaci gaba dacewa, "suka kebe a guri daya batare da wani abu yashiga tsakaninsuba, Rumaisa  kidai tunanin bazan miki komaiba domin ko kinki ko kinso saina kusanceki"

Rumaisa ta fashe da kuka tana fadan "na shiga ukku, menai maka ne kake nema kasaka bakin ciki a cikin rayuwata, niban isa na hanaka abinda kakeso kayi  daniba amma nasan dacewa Allah bazai barka kacutar daniba" tana kuka sosai,
Fahad yayi dariya "hmm rumaisa kenan, bakece macce tafarkoba data fara shigowa gidan nan ba, mata barkatai sunzo kuma sun fita salin alin babu wadda yaji mu dasu, amma ke dinnan ina ganin bazan sameki a saukiba, kinada masifar taurinkai"

Hannayensa yasakada cikin aljihu yana murmushi yanufi gurinta, tana ganinsa tafe takara saka kuka adu'oi kawai take karantowa, tana ambaton Allah,

Daf da ita yatsaya ta yadda harta najin fiter nunfashinsa ta kunnenta, kura mata ido yayi yana kallon kirjinta a kullum kara burgeshi take, hannunsa daya yadaura a ginin dakin yasaka a tsakiyar kirjinsa, kirjinta na zuzar nashi, yayi wani lumshe ido,
Cikin kuka rumaisa tace "karkayi haka fahad, Allah fa yana ganinka, wannan abin dakake shirin aikatawa zunubine, kusantarsama zunibeni, dan Allah kaji tausayina kakyaleni"

Edonsa a lumshi suke yanajintane kawai amma wani irin nishadi yakeji yana ziyartar jikinsa,

Tunda yazo daf da ita ta rufe edonta domin batason hada ido dashi,
 Jin shiru datayi yasa tadan bude edon kadan, tana shanshekar kuka, ganinsa tayi daf da ita  edonsa a rufe, da sauri takara rufe edonta tana fadan innalillahi wa inna ilaihin raju un,

Kallar  taci gaba da maimai tawa kenan,
Kokarin kai bakinsa  yake a  cikin nata, sai alokacin yafarajin abinda take fada,  jin kalmar datake fada yasa ya bude edonsa, yana kallonta, a lokaci daya yaji tausayinta yakamashi,

Murmushi yayi yajanye jikinsa daga nata yaja da baya,

Rumaisa ta nan sai kara nanata kalmar take, jin babu motsi a gabanta yasa takara bude idonta,  a lokacin har yakai bakin kofar fita, 

Juyowa yayi sukayi ido hudu dasauri takara kanne edon,

Fahad yayi murmushi wutar sonta yakeji tana kara shiga zuciyrsa, yace "kibude edonki kiyi kwanciyarki, nizan wuce saida safe, amma kisani gobe saina cimma burina akanki" yana gama fada ya janyo kofar dakin yarufe yafita, wani irin ajiyar zuciya tayi tana kara godewa Allah..

Daya kubutar da ita daga shairin fahad..


Tana tsaye a gurin tana kuka, a hankali ta sulale kasan carfet, Tana rokon Allah daya kara tsareta daga shairin fahad,

Cike da mamaki Fahad yabar dakin, baitaba jin tausayin macce ba idan yazo kosantarba sai Rumaisa, 

Dakinsa ya wuce, ya cire  rigarsa, daga shi sai singlet da wandon rigar daya cire, yayi zaune bkin gado, yana maida nunfashi, telephone kawai yakira yasa a odo masa giya, bada jima waba kuwa ma'aikacin gidan yashigo dakin da kwalabe a hannnunsa,

 ya zubesu a gabansa  sannan yafita,  fahad yabude kwalba daya yafara korawa yana lumshe edo, kamannin rumaisa kadai kemasa gizo, yarinyar kara shiga ransa take...

Giyar yasha yayi mankas har kusan karfe 2 na dare baiyi bacciba, tunain rumaisa yahanashi bacci, tashi naga yayi yana tangadi kamar zai fadi, yana sambatu yafita, yana tafiya kamar zai fadi yanufi dakin rumaisa,  yana zuwa ya tura kofar dakin yashiga..

A inda yabarta a tsaye anan ta sulala kasa, tayi bacci, tayi sharkar kasan carfet, yakarasa gurinta yayi tsaye a kanta, yana kallonta yana tangadi kamar zai fado mata,

 kakin amai yasoma yi hakan yayi sanadiyar tashin rumaisa daga bacci taganshi a kanta, da karfi ta zabura ta miki tana fadan innalillahi wa innalillahi raju un,

Amai yafara kwararowa tana tsaye tana kallonsa, wani irin tashin zuciya takeji kamar itama zatayi aman wani irin kyankyami, tayi mamakin ganin fahad yanashan giya, a take cewa   lallai kuwa wannan yana cikin bala'I ga nema mata kuma ga shan giya,

Saida yagama kwara amansa sanna ya kalleta yana murmushi cikin salon murya irin ta mashaya  yake fadan "rumaisa nakasa bacci saboda ke,  com to me plx" yana kokarin fado mata da sauri takauce masa tana kokarin gudu, ya riko hannunta gam, kuka tasaka  tana dukan hannun amma yaki sakinta, cizo takai masa, da sauri yasaki hannun yana wash,

Tasamu tabar gurin, yakara daga kasan ya hengeta acen gefe tana kuka tayi wani kakkame jiki,

Yanufi gurinta yana tangadi, yana fadan rumaisa com plx, com an hug me, I need u , rumaisa,
Kokarin kai ga jikinta yake da karfi tasa hannu taturesa, rakafff  kakeji yafadi kasa kansa ya daki gefen gado, jini kadan yafito, shiko ajikinsa bai damuba, kokarin tashi yake sai kuma yakasa,

Rumaisa tayi tsaye tana kallonsa, lallai giya bala'ice, ace mutum yajiciwo amma shi baimasan anyiba,

Kasa tashi yayi a gurin ya sulale ya kwanta a hankali bakinsa ke furta rumaisa, I need u rumaisa, " har bacci yadaukesa,

Rumaisa tayi tsaye akansa tana kallon  jinin dake fita akansa, tausayi yabata sosai, a hankali ta durkusa gurinsa cike da tsoro jikinta na rawa, ta kira sunansa cikin siririyar murya, taga ko motswa baiba, hannunta na rawa takai a jikinsa tadan dakesa kadan taga bai motsaba,

 gabanta yafadi, kardai ace ta kashe dan mutane,

Sai kuma ta lura da kirjinsa na harbawa, hakan ya tabbatar mata da cewa  yana raye,

Mikewa tsaye tayi tarasa yadda zatayi, gajini yana fita a kansa,

Jitayi tanason tataimaka masa , a hankali tashiga neman tissue, tsumma a dakin,  tazagaye kaf dakin bataga komaiba,

 Rigarta ta bacci datazo da ita daga gida  ita tatuna, dasauri tadaukota ta yaga sannan tadawo gurinsa har a lokacin jikinta rawa yake, ta daga kansa kadan tasa tsumman ta dauremasa kansa, sannan ta mayar dashi a kwance...

Kamar daga sama taji ya cafki hannunta..


Cike da firgita taja hannun da karfi ta mike tsaye jikinta sai rawa yake,
 Hannun fahad kuwa ya sulalel kasa yafadi, har a lokacin bakin sa yana furta I need you rumaisa,

Tajima a tsaye tana kallonsa, kafin taje tadauko sauran tsumman rigar data daure masa  kansa, ta share aman dayayi, takara kallonsa ta girgiza duk tausayinsa takeji, sannan tajanye daga gurin, takoma gefe daya acikin dakin ta takure, jikinta sai kyarma yake, a hankali hawaye kefita a cikin idonta,  tana tsoron kartayi bacci fahad ya farka ya farmata, soboda  haka ta hana idonta bacci  sai shanshekar kuka take,

gangad'I tafarayi sai kuma ta farka da sauri,  a haka dai bacci yagarara zomata  tana zaune tafara jin kiran sallah, nan tamike tashiga toilet tayi alwala sannan tafito,

Ba sallaya a dakin, ta karkade kasan carfet tafara sallah,

Bayan tagama, tayi adu a sosai sannan tafara karanto alqur'ani mai girma a daidai inda ta hadda ce, reroshi takeji cikin murya mai dadi gaske,

Sautin yakeji yana shiga masa kunne yarasa ko  meye, jinsa yakeyi kamar ana rairai masa  waka, amma dai ba waka bace, a hankali yasoma bude idonsa, a lokacin har gari yasoma wayewa,

Kadan ya iya furta wash, a lokacin yadafe kansa, domin ciwon dayaji yanai masa,  a  hankali yake kokarin tashi yasa hannu yadafe kansa gefen da yakejin zafin,

 mamaki yake meya jimasa ciwo,  kuma waya daura masa tsumma a kai,  juya yayi gefen daya kejin sautin na fita, idonsa suka sauka kan rumaisa, baki ya saki yana kallonta ita kuwa cike da mamaki ita kuwa  wannan  metakeyi haka yafada a zuci,

Kamar mai kowon tafiya yafara taka kafarsa yana kokarin karasa gurin Rumaisa,  .

Jin motsin mutum a bayanta baisa ta tsayar da karatun da takeba, idonta sunyi ja sosai sakamakon rashin bacci dabata samuba,

Gabanta yazo yayi tsaye yana kallonta, kamar zaiyi magana saikuma yakasa, zaunawa yayi ya kura mata ido yana kallonta,  sai yaji ta kara shiga ransa,

Gaban rumaisa duka yake tara2 kanta a sunkuye ta kanne idonta, sai karatunta take billahakki,

Ganin takai karsher sura yasa tadakatar da karatun, a  hankali take bude idonta, tadago kanta sukayi ido hudu, tagumi taga yayi yana mata murmushi,  cike da tsoro ta iya furta "ina kwana" sai kuma ta sunkuwar da kanta, tana jiran taji mezaice,

murmushi yayi "lafiya lau, sai kuma ya tambayeta meya kawoni dakin nan"

Duk da batason hada ido dashi amma  a hakan tadaure ta daga kanta ta kallesa, tayi mamakin tambayar da yayi mata, sai kuma tatuna da cewa kodafa yazo dakin cikin maye yake, ajiyar zuciya tayi sannan tace "cikin maye kazo dakin nan"

"Oh god, Allah yasa ban dakekiba" fahad yafada yana kallon rumaisa, 

Sai a lokacin tayi masa murmushi "bakamun komaiba, hasalima nicee..." saita kasa karasa maganar tana kallonsa , fahad yace ihum karasa maganar mana,

Rumaisa tace " a a kabarshi kawai katashi kaje kayi sallah"

Fahad ya zare ido da mamaki "sallah kuma, lokaci yayi ne"

Cike da mamaki rumaisa tace "au bakamasan lokacin salla ba"

Fahad yafada a kasale "nibanma iya sallarba, domin rabona da salla tun ina dan shekara 15. Amma tunda nagirma na daina" yana gama fada yamike yana kokarin fita daga dakin,  rumaisa ta bishi da kallo harya fita, sannan tayi ajiyar zuciya tana mamakin rayuwar fahad ace mutum dan musulmi amma bai iya sallah ba, sai taji tanason zama dashi domin takowa masa sallah dakuma addini koda Allah zai saka mata da tukuicin abinda takeso wato majnoon,  ( nace kekuwa rumaisa meya ganoki, nacewa saikin kowar  dashi addini ko kin manta satoki yayi ) nidai nayi shiru naci gaba da rubutuna

Yunwa tasoma addabarta a  hankali ta mike tsaye, tanufi kofar fita tana leken falon, batasan gidanba, ai kuwa tana leka kanta sukayi ido hudu da wani bodyguard fuskarsa a murtuke ba imani, dasauri ta koma cikin dakin ta jingina jikinta a ginin dakin tana jan nunfashi...


Fahad nakarasa dakinsa yasa hannu ya warware daurin da rumaisa taimasa akai, sannan  yaje yayi wanka, bayan yafito ya dauko wasu sabanbin kaya yasaka dominshi baya yiwa tufafi sawa biyu,

Yadan zauna a bakin gado  yana nazarin kalaman rumaisa, sonta yakeji yana kara shiga masa zuciya, bayajin zai iya rabuwa da ita, 

Ajiyar zuciya yayi
Sannan Tashi  yanufi dakinta yana shiga dakin yasameta manne a jikin ginin dakin ta sunkuwayar da kai,

 kallonta kawai yayi yana murmushi sannan yajuya zai fita, murya kasa2 rumaisa ta furta "yunwa nakeji"  fahad ya juyo ya kalleta "to basai  kije ki girkaba abinciba, aina gaya miki bazan kara siyo miki abinciba, domin ke matata ce"

 rumaisa ta tsuke fuska "to ai bansan inane kichin dinba"
Yadda tayi maganar yabashi dariya, yace "muje nanuna miki "

Rumaisa tazo gurinsa
Tayi tsaye, riko hannunta yayi yana murmushi da sauri ta firgi hannunta cike da tsoro, fahad yace miye haka,

"haramun me namiji yataba jikin macce idan har ba matarsa bace" rumaisa ta fada saikuma taja da baya,

Mumrshi fahad yayi yakara kai hannusa "oya lez go"  yana kokarin koma rikota, ta janye daga gurin, tasoma hawaye kuka na kokaron kubce mata, ganin zatayi kuka yasa  fahad yadaga mata hannu "ya isa haka muje" fita yayi tabi bayansa tana share hawayenta,

Nan yaje yanununa mata ko ina a gidan duk inda ta daga ido bodyguard take gani, a zuci tace wannan gidan ba wurin fita saidai taimakon Allah ko ina da mai tsaronsa,

 haka dai ya gama nuna mata ko ina sannan, yace shizai fita, sai ya yadawo,

Kai kawai takada masa,

Yana fita takoma kichin tafara dafa abinci...
****    *****    **
Tun wayewar  ake tursasawa  umma akan tafadi inda takai rumaisa amma  umma tace ita wallahi batasan  inda rumaisa tajeba"   tasha duka iya duka, duk jikinta ya kumbura,

Abban rumaisa yana zaune a cikin police station din, domin anan yakwana tare dashi ake  ganawa umma wahala, dominshi a yanzu yama daina jin sonta a zuciyarsa,  baya mason ganinta, shidai kawai Rumaisa yakeson gani ko a raye ko a mace,

Edonsa sunyi ja sosai domin bai samu bacci ba jiya,  daya daga cikin police din ne yaoi gurinsa yana fadan "alhj wlh matar taki fada, nifa ina ganin kamar ba Hannunta a cikin batan wannan yarinyar"

Abba yadago janjayen Idonsa ya kalli police din  yace " taya akayi kasan babu hannunta aciki, kaine mijinta, ko kuma kaike tare da ita, ninasan matata kuma nina baku izinin kamata, dan haka idan zaku iya bincikenta ku binciketa idan kuwa bazakuniyaba tokubarta anan har sai zuwa lokacin da akacemun anga 'yata sannan kusaketa" police din zaiyi magana Abba yadaga masa hannu yana huci "karka kara mun magana, bana bukatar jin kowa a yanzu"

Police din ya girgiza masa kai kawai ya fice yabar gurin, abba yajima a gurin yana tunani kala2 sannan yatashi yaje yaja motarsa yabar station din..

**** ****  ****
 Nikaina bazan iya misilta muku iya kukan da faisal yayiba, a yunin jiya domin yunin jiya yakasance masa kamar ranar mutuwarsa, yakasa cin komai a haka yuni har dare, a daren ma  bai samu isanshen bacciba, domin daya kwanta zai fara tunanin rumaisa, dolensa ya mike..

Wayewar gari

Daga wanka yafito yana goge kansa da tawol, jikinsa duk ba kwari, yakarasa bakin mirror yana kallon kwayar idonsa sunyi ja sosai,

 Fusakar rumaisa ta soma  yimasa gizo a bayansa tana masa Mumrshi ta jikin mirrorn yake ganinta,  da sauri ya juya baya saikuma yaga bakomai, hawaye suka sauko masa, a hankali yasa hannu yashare sannan yakarasa gurin shirinsa, kananun kaya yasaka sunyi masa kyau sosai, sannan yasaka ta kalmi cover,  ya janyo jakarsa saida ya kallmasa  shirinsa na fita aiki sannan yafito waje....

Kwata2 fuskarsa ba annuri, a falo yasami momy a zaune tayi jim tana tunani,  a lokacin daddy yafita suna cen gurin fafutukar neman rumaisa, faisal ya durkusa ya yagaidata, ba yabo ba fallasa momy  ta amsa tana murmushi "har ka shirya fitar ne "
Yace "eh, banason nayi late ne"

Momy tace " toh amma ai baka karya ba, mutum na fita baici abinciba"

Mikewa faisal yayi yana wunkurin barin wurin yana cewa "bana jin yunwa" yana kallon momy, momy tace "to shikenan Allah yakai lfy"

Faisal ya amsa da ameen, sanna yasa kai yafita yabar gidan yanufi gurin aiki,

Katuwar office ce mai matukar kamshi turaren airfrshn yake a  ciki ga takardu birjin akan table,

 Faisal yana zaune akan wata lallausar kujera, tana juyi dashi, yayi kuru yana kallon kofar office din, edo sa sunyi ja sosai, tunani rumaisa yake, a ranar daya fara gininta, ba zato ba tsammani hawaye suka soma gaggarowa a fuskarsa, yarasa meyasa son rumaisa yakama zuciyarsa har ta yadda bazai iya mantawa da itaba, son rumaisa yazame masa wani irin tabo a cikin zuciyasa wadda bazai iya warke waba, amma duk da haka yana zargin kansa, ayya soyayya baso take ta horar dashiba, ayya ba alhakin soyayyane yake fita akansaba,

Hawaye suka kara saukowa kan kuma tunsa, a zuci yake fadan DAMA HAKA SO YAKE  lallai kuwa akwai babbar matsala da wadda yakamu da son maso wani, hausawa nacewa son maso wani, koshin wahala, a hankali naji sautin kukansa yafara fita, da karfi ya daki table dinda ke gabansa, yana kuka yake fadan " why! Why! Why lov, meyasa kamun haka, meyasa ka ingizani gurin da baa sona, plx lov I accpt my fault,  nasan nayi kuskure plx...! Yakarasa maganar yana kuka, ya saukar da kansa akan table din yana kuka,

Yajima yana kukan kafin yaji an fara knocking kofar office dinsa, da sauri yake kokarin share hawayensa tare da  kokarin gyara kansa,

Saida ya tabbatar daya saita  kansa sannan yace "yes com in" murya a raunane,

Tunda aka bude kofar kamshin turaren almiski yadaki hancinsa, yaji wata irin ni'ima tasaukar masa a jiki, ya lumshe edo, sannan yadago kai ya kalli kofar a lokacin da take kokarin shigowa, caraf suka hada edo tana murmushi,  takaraso cikin office din ta zauna a kan kujerar dake duban tashi, kyankyawar maccice ajin farko ga kyau ga murmushi mai kyau, (to wacece wannan) nakasa bawa kaina amsa..

Shikuwa ya kura mata edo, gizon fuskar rumaisa yake gani akan fuskarta,
Tayi shuri tana kallonsa, cike dajindadi  taga yau ya kura mata edo yana kallonta, ashe dama akwai ranar da faisal zai kalleta haka, a zuci take fadan Allah yasa dai yafara sona, cike da farin ciki tayi gyarar murya, yadan zabura a sannu sannan  yadawo hayyacinsa, cike da jindadi tace "kwalliyar ta maka ne"
 Sai a lokacin faisal yagane cewa ba rumaisa bace a gabansaba, janjayen edonsa yadago ya kalleta sai kuma ya sunkuyar dakai ya tsuke fuska, uffa bai furta mata ba,

Murmushi tayi tana kallonsa tace " nasan haryanzu cikin tsanata kake, amma dan Allah kayi hakuri, yaufa kwanana ukku kenan  bangan kaba, kullum sainaso gurin aiki nayita nemanka, lafiya dai kuwa meke faruawa?"

 Shiru yayi mata yamaa kasa dago edonsa ya kalleta,

Yanayin fuskarsa take nazari ga alama kuka yayi cikin salon kisisina ta furta " meke damunka ne dear?, ko anmaka laifine?"

A hankali bakin faisal yasoma rawa yasoma fadan "ZARAH plx liv my office, bana bukatar kowa a yanzu inaso na huta"

murmushi naga wadda yakira da zarah tayi kafin  tace "aini dama a kullum baka bukatar zuwana  gurin ka, nikuwa gashi nadake sai zowa nake, kuma ni bana ganin  laifin kaina domin nasan wannan ba komai bane face  sonda zuciyata take maka... tadan marairaice fuska kamar zatayi kuka "dan Allah faisal ka aminta da...."

Da sauri yadaga mata hannu yana huci, kalamanta haushi suke bashi, ya nuna mata kofar fita yace "ki fita nace"
Zarah tayi murmushi takara gyara zama, tana kokarin yin magana,

Faisal ya mike tsaye yadaka mata tsawa, I said liv my office"

Da sauri zarah ta miki a lokacin harta soma hawaye muryata narawa kuka yasoma zomata, hannusa yana nunin kofar office din , tana kuka take furta " zan fita, amma wlh zandawo, kai wane irin marar tasaurayine wadda baisan darajar wadda yake sonsa ba, a kullum burinka bai wuce kaga kawulankatani a gaban kowa, amma ni zuciyata a kullum burinta shine na kyautata maka,  kai ne muradina amma kakasa fahimtar haka... ina sonka faisal, takarasa maganar tana kuka tana fadan I love you faisal,

yaji tausayinta sosai,  domin a yanzu duk ciwonsa daya, amma yakasa nuna mata haka, kara tsuke fuska yayi "kifita nace " yafada yana hawaye, 

Zarah ta firgi kofar office din dasauri ta fita tana kuka, jin karar  rufe kofar kakeji  da karfi gaff,

A hankayi yake sulalewa akan kujera yana kuka yadafe kansa,  wannan wane irin sone yake a zazzalar zuciyarsa, son rumaisa yana kokarin haukatar dashi

A haka dai yawuni a office din ba wani aikin kirki da yayi har yamma tayi baici komaiba,

Karfe 6:00  na yamma time din tashinsa yayi, yatashi yabar office din yakoma gida, koda yaje gida yasami daddy zaune a falo yana kallon news, anan yake tambayarsa anga rumaisa kuwa ?" Daddy yace a a ba a gantaba,
Bai kara furtawa daddy komaiba yatashi yabar falon  yanufi dakinsa,

  Yana karasa ya cire tufafinsa yafada toilet yayi wanka, sannan yafito ya chanza kaya, yazaune yana jirar a kira sallar magriba,

Baijima kuwa a zaune ba aka fara kira nan yatashi yaje yayi alwala, yafita yaje masallaci, bayan sungama sallar magriba yayi zamansa a masallaci saida aka kira isha sukayi sallah sannan yadawo gida, jikinsa duk ba kwari, yana kokarin saka jallabiya yana shirin bacci  momy tashigo dakin"kafito kaci abinci"

Faisal  ya mutse fuska " banajin yunwa momy naci abinci a waje"

 Momy ta girgiza kai kawai tafita tabar dakin...
*****       *****    ****

Rumaisa kuwa kaf yunin ranar bacci tasha abinta, mai isarta, bawani kuka tayiba, amma aduk lokacin da ta tuna da majnoon saita zubar da kwalla,

 Tunda fahad yabar gidan bai kara dawowaba yana cen  gurin sharholiyarsa, tayi jira yadawo amma taji shiru hakan yasa tabi lafiyar gado sai bacci, 

Misalin karfe 12 dare fahad yashigo gidan, yana  tangadi da kwalbar giya a hannunsa, duk kofar daya karasa ma aikata ke bude masa,  harya karasa cikin falo, dakinsa ya nufa haryakai bakin kofar shiga  sai kuma ya fasa shiga dakin,  yajuya yanufo dakin rumaisa,

A hankali yatura kofar dakin, tana kwance a kan gado tana bacci ya kura mata ido, tayi bala'in burgesa, takara shiga zuciyarsa, sha'awarta ta kara yaduwa a jikinsa, cikin tangadi yakarasa bakin gadon, tunga kafarta yasoma kallo har zuwa kirjinta anan yatsalar da edonsa yana kallonta yana hadeye yawu,

A hankali yakai hannunsa yafara taba kafarta, yana shafawa hankali.....


A cikin baccinta takeji kamar ana mata sosa a kafa, dadin abin taji hakan yasa takara lafewa,

Fahad kuwa sai karayin  gaba yake, harya hauro ta saman jikinta, hannunsa na rawa yasoma kai ga kirjinta, yana kai hannunsa ta zabura da karfi suka hada edo, ganinshi tayi akanta, ihu tasaka tana kokarin turesa amma ta gagara, kuka tasomayi shikuwa a lokacin yake kokarin kai bakinsa acikin nata saboda yanin budewar bakinta tana kuka shiya bashi shaawar, bashiri taji saukarsa shi a jikinta lamkwaf, yana kokarin fara shafar jikinta, ihu take a daidai lokacin  taji saukar bakinsa a cikin nata, uhim uhimm kawai kakeji, alamar tana ihu amma sakamakin bakinsa yana cikin nata ihun ya garara fita,

 hawaye kawai kemara sintiri akan kumatu, yaukam tashiga ukku,

Fahad kuwa tuni yafita hayyacinsa, daddan ne mata hannaye yayi yana kissing dinta da karfi da yaji, wani irin nishadi yakeji, sabanin itakuwa rumaisa wani irin zafi takeji,

Da karfi takai masa cizo a lips dinsa, saida yayi kara  sannan yasaki hannayeta tayi saurin turesa gefe ta mike tsaye tana huci tana kuka,

har a lokacin kwalbar giyar tana rike a hannunsa, ya soma saukimowa aka  gadon yakasa tsayi guri daya sai tangadi yake, ya nunawa rumaisa dan yatsa " kifa tsayafa, domin naga kin rabemin gida ukku"

Rumaisa sai bin ginin dakin take tana kuka, shikuwa sai binta yake yana kokarin kamota,

Cikin muryar 'yan maye f yake fadan 'kifa tsayafa, Allah zan illataki"

Kuka sosai rumaisa keyi tarasa yadda zatayi dashi a lokacin tafara karanta adu o inta,  a cikin zuciya,

Sai zagayar dakin suke ita dashi, harta soma gajiya,

A angle daya na ginin dakin tasamu ta rakube tana kuka,

Fahad yakai dubansa a gurin yaga ta rabe masa gida ukku, kallonta yakeyi kamar baisan taba, harya karasa gurin,

Hannunsa daya rike da kwalbar giya, dayan hannun kuwa yadaga ya nuna rumaisa data rabe masa gida ukku,

Cikin murya irin ta masu maye yace "yaushe kika zamo mutum ukku, wacece ta kwarai a cikinku"

Rumaisa tayi shiru sai karanto adu oninta take, tasa hannu ta toshe bakinta domin kar saurtin kukanta yafito,

Fahad yazo daf d ita yace "bari na fitar data kwaran a yanzu"

Yad'aga hannusa dake rike da kwalbar yakai duka a gurin,

Saukar kwalbar kawai taji akanta rakwasss , tunganan bata kara ihuba, ta sulale a gurin tafadi,

Fahad ya kuramata da ido yana kallon ta,

ya yarfa hannunsa "au bacci kikayi, toh shikenan bari nima na tayaki"

A kusa da ita ya kwanta, hannunsa yadora akan cikinta....


Yana sambatunsa har bacci yayi ayon gaba dashi,

5:30Am na safe,
A hankali naga fatar idonsa  tasoma motsi sai kuma naga yana kokarin bude idon a hankali har idon suka yashe,

Nisji yake kamar wadda yayi wani aikin wahala, har a lokacin rabin  kwalbar giyar na hannunsa, dayan kuwa yana kan cikin rumaisa,

A hankali yakai dubansa ga hannunsa dake rike da kwalbar giya, yaga kwalbar a fashe, da sauri ya zabura yatashi domin yasan yayi aika aiki baisaniba,

 Caraf edonsa suka sauka kan rumaisa dake kwance sharkar tamkar gawa, goshinta ya fashe kadan,

Cike da firgita yakai hannusa yana jinjigata, yana kiran sunanta cike da hargowa, yaga ko motsi batayi, muryarsa na rawa ya furta "OMG ,  nakashe 'yar mutane, rumaisa!!!!" Yakara kiran sunanta cikin hargowa a daidai lokacin kuka yazo masa,

Yadafe kansa ya gurfana a gabanta yana kuka sosai, ya riko hannunta ya murzawa a hankali " plx rumaisa karki tafi kibarni, dake na tsara rayuwata, ceke silar farin cikina, plx rumaisa com back 2 meeeee,( cry)...."

Dubasa yakai  gurin rabin Kwalbar giyar dake gefensa  yakara dauka cike da jin zafi yakara tarwatsata a kasa duk tafashe a dakin, karar fashewar  kwalbar yasa rumaisa taja nunfashi da karfi, tana tari, saikuma tayi shiru,

Fahad dake kuka yakara kiran sunanta cikedajin dadin bata mutuba, da sauri ya ciro wayarsa yakira Doctor. .

Yana rike da hannunta yana shanshekar kuka, akayi knocking din kofar dakin, da hanzari ya mike yakarsa bakin kofar ya bude, bodyguard dinshi yagani a tsaye, " likitane yazo, yana falo " bodyguard din yafada,

Fahad bai furta masa koh uffanba, yajuya da sauri ya koma wurin rumaisa,  hannunsa yakai yana kokarin daukoto, sai kuma ya tuna da magabar data  masa jiya, (HARAMUN NE NAMIJI YATABA MATAR DABA TASHIBA)

Yayi jim yana nazarin maganar ya kalleta, hawaye suna fita a edonsa, a koda yaushe kara jinson rumaisa yakeyi a zuciyarsa

A hankali bakinsa ya iya furta "kai bazai yuyuba, noo" hannunsa yakai ya tallabo rumaisa,

wani irin nishadi yaji ya ziyarcesa, da sauri ya lumshe edo, sai kuma ya bude,  edon sunyi ja sosai, ya nufi waje da ita akan kujera  ya saukar da ita, likita yafra dubata ....

Tare dashi ake aikin domin tsaye yayi yana kallon duk abinda  likitan keyi, duk ya fita hayyacinsa, zuciyarsa cike da takaicin giya data sakashi yayi wannan aika2, gashi yanzu yayi yunkurin kashe a bar sonsa a banza da wofi,

Dafe kansa yayi kafarsa sai rawa take yakasa tsayuwa guri daya,

Bayan Likita ya kammal mata dressing,  sannan ya juyo ya kallo fahad yace "ogaa komai ya kammala insha Allah nan bada jima waba zata sami sauki"

Fahad ya girgiza masa kai, yana hawaye, nan likitan yayi sallama dashi yatafi,

Da kyar ya iya karasa bakin kujera wadda take duban tata shima ya kwanta yana kallonta... jira yake ta farka,

7:52am
Har safiya tafara bayyana, rumaisa ta bude idonta, zafi taji a kanta hakan yasa tasa hannu ta dafe kanta tana wasshh, jin bandeji a goshinta yasa tafara tuna abina yafaru jiya, da sauri ta mike tana kokarin tashi, nan kuma jiri yakara d'ibanta, tangal-tangal tayi zata fadi a lokacin fahad yakaraso gurin da sauri ya rikota tafada kirjinsa tana mayar da nunfashi, shikuwa ya kura mata edo, yana kallonta, 

Ita kuwa edonta a rufe yake domin ida ta bude edon gani take dakin na juya mata,

Tajima a kirjinsa, kafin ta fara bude edon a hankali, caraf edonta suka sauka akan nashi, da karfi ta mike tana kallonsa, ranta a bace, wani irin haushinsa takeji,

Harara ta auka masa sannan tanufi hanyar dakin datake,

biyota yayi yana kiran sunanta amma ko juyosa bata yiba, tana karasawa bakin kofar dakin tashiga sannan  ta turo kofar da karfi kamar zata game da hannunsa da sauri yaja baya, tasaka key ta rufe kofar,  ta jingina jikinta a jikin kofar, kuka ta somayi mai sauti a hankali take sulalewa kasa tana kuka hartakai zaune,

Fahad kuwa sai knocking kofar yake yana kiran sunanta amma taki budewa, jin sautin kukanta dayake yakara tayar masa da hankali,

A hankali ya ke furta "plx rumaisa kiyi hakuri, wallahi bada sanina komai yafaruba, dan Allan kibude kofar"
rumaisa  tayi bnza dashi kuka kawai take,

Fahad yaja nunfashi yace " nayi miki alkawarin daga yau nadaina shan giya, dan Allah kibud'e kofar"

Duk da kukan datake amma saida tayi murmushin karfin hali, jin kalaminsa nacewa zai daina shan giya,
Amma kuma saita gagara tashi ta bude masa kofar, 

Fahad yayi jim, yajita shiru, hakan yasa yajuya ba'ason ransaba zaibar kofar,

Sautin karar budan kofar yatsayar dashi, yatsa cak guri daya, yana kallon kofar,  

Tana bude kofar takoma bakin gado tazauna ta dafe kanta tana hawaye,

A hnkali ya turo kofar dakin  yashigo, yakarasa bakin gadon, kusa da ita yazauna, yashare hawayensa, ya kalleta yace " wai garin yayi wannan abin yafaru, ni bnsan lokacin dana aika hakan agarekiba"

Rumaisa tayi bnza dashi ko uffan tagagara ce masa, a lokacin ta tuna da batayi salla ba,

Tana yunkurin tashi Fahad yace " talk mana" harara ta dalla masa tamike tanufi toilet, 

 dasauri yatashi yabita baya,

Takai bakin kofar toilet din taga yana kokarin binta hannu ta daga masa " karka kuskura kabiyoni"

Tana gama fada bata jira yayi maganaba, tafada toilet din tamayar da kofar ta rufe,....


Shiru yayi yana kallon kofar ban dakin  kafin yajuya yadaki ginin dakin, yana yajan nunfashi  sannan ya koma bakin gado yazauna, yana tunanin rayuwarsa wai yau shine kebiyar macce, shida bai mayar da mace komaiba, amma yau gashi macci na wahalar dashi,

A lokacine yaji kamar kafarsa na masa ciwo, kallon kafar yayi yaga jini, kwalbar giyar daya fasace yataka kuma harta fasa kafar, yadago kafar yana kallon, zafi yakeji sosai,

A daidai lokacin rumaisa tafito daga ban dakin, yana jin fitowarta yayi saurin sauke kafarsa yana murmushin sai kaice wadda babu abin kedamunsa,

Bata kulashiba, yana kallonta ta karkade kasan cafet din tafara sallah, yana zaune yana kallonta tana salla,
Jiyayi yana sha'awar yayi sallah,

Amma ya gagara tashi, yana zaune har rumaisa ta kammala sallar, sannan tazauna tayi adu oi,  tana gamawa ta soke kanta kasa tana hawaye,

"Harkin gamane " fahad yafada cike da fargaba,

Rumaisa ta dago kanta amma bata juyo gurinsaba tace "meya dameka da sallana, aikai bakayi" tana gama fada saikuma tayi shiru, .

Fahad yayi murmushin, yaji dadin data amsa masa maganar mike wa yayi yakarasa gurinta yazauna kafarsa namasa zafi sosai ya dubeta yace "fushe kike dani Rumaisa" yafadi maganar a marairaice ,

Sai a lokacin rumaisa tadago edota ta dubesa, ta share hawayenta sannan tace " dole nayi fushi dakai domin kasauka akan tafarkin addininka kakama addinin yahudu da nasara, Fahad takira sunansa, ths is th fst tmy data kira sunansa, sai yaji abin wani daban, the way yadda takira sunan yamasa dadi, yace "yes "
Rumaisa tace "baka sallah, sannan kuma baka tunanin lahirarka, kadauki duniyar nan kamar wani gidan jindadi, kamanta cewa a koda yaushe zaka iya mutuwa kuma kakoma ga Allah, mezaka fada masa idan kaje garesa, zaka fada masa cewa shan giya da neman mata shiya hanaka yin salla, bazaka iyaba, a ranarma bakinka bazaiyi magana domin baki zai iya shirya karya, sassan jikinka sune zasuyi magana wadanda kasan dacewa kana aikata barna dasu, fahad kaiba yaro bane, kamallaki hankalin kanka, yakamata kagyara zamanka da uban gijinka"  nadai tashiga karoro masa nasihohi daban-daban...

Jikinsa yayi sanyi sosai, ajiyar zuciya yayi sannan yace "shikenan naji, zan daina komai, indai har hakan zai sakaki farin ciki, ya kara kallonta yana murshi kafin yace "amma namanta komai  kikoyamun yadda zanyi"
Dadi sosai rumaisa taji,

Acen kasar zuciyarta tace yes my mission started,...

kallonsa tayi tay murmushin tace "shikenan zan koyama"

Shima murmushin ya mata,

Zafin kafarsa yakai masa ko ina yayi yunkurin tashi, sai a lokacin rumaisa ta lura da jinin dake fita a kafarsa,

Tace "subhanallah, jin ciwo kayine" ya girgiza mata kai,

Oh sorry" tafada tana kokarin taba masa kafa, da sauri ya janye yana  kallonta yace "babu kyau macce tataba kafar daba ta mijintaba"

Rumaisa ta kallesa tayi murmushin tajidadin maganar har cikin ranta tace "babu shamaki gaduk wadda zai tamakawa musulmi dan uwansa a duk lokacin da yake cikin neman taimako, dan haka idan har taimakonka zanyi babu laifi idan natabaka"
Fahad yayi dariya yace "ok shikenan" ya miko mata kafar ta kama ta matse jinin daya taru a ciki sannan tamike taje toilet ta dibo ruwam zafi a heater tazo tana gasa masa kafarshi,  tana dan kara yimasa bayanin akan addini,

Haka dai harta kare,  sannan tatashi taje tashirya musu breakfast, bayan sun gama suka dawo falo suka zaune tafara kowayar  abubuwa, ranar tasaki jiki sosai dashi,

A ranar babu inda yafita yana gidan har yamma tayi, kuma ya koyi abubuwa dadama daga gurin rumaisa,
******    *****    ****
Allah sarki majnoon,
Majnoon nagani a rakube a gefen tati yana kakkarwar sanyi, duk ya rame yakara fita hayyacinsa,

Duk da babu hankali a tatare dashi amma dai yaji rashin zuwan rumaisa gurinsa, yashiga da muwa sosai amma babu wadda yadamu dashi balle yasan damuwa sa, yanzu yama soma daina yawan wasar nan da yara, burin shi kawai shidai yaga Rumaisa.

*Bayan kwana biyu*

Zarah ce zaune akan gado, tadafe kanta tana hawaye, edonta duk sun kumbura, tasha kukanta mai isarta,

Turo kofar d'akin nata akayi akashigo da gudu, bata d'ago kantaba ballema tasan waye yashigo, illadai taji shigowar mutum,

Yarinyace yar kemanin shekaru 10 tashigo d'akin tana murna, tafada kan gado inda zarah take, "anty zarah, kingafa abbanmu yasayimun game boy" tafada tana nunawa zarah game din,

Zarah ta d'ago edota ta kalleta tace "Feena kije nagani banason damuwa" tafada a kasale

Feena tana kallon zarah, tagane kuka take tadan bata fuska tace "anty zarah kuka kike, me akayi miki, mamace ta miki laifi ko Abby"

Zarah ta share hawaye ta  tadan langawabe kanta kadan tana kallon feena "basu bane, kidai nace kije kibari anjima zamuyi magana"

"Faisal ne koh?" Feena tafada tana kallon zarah, zarah ta zare ido tana kallon feena cike da mamaki, tayadda akayi tasan faisal, saikuma ai bazatayi mamakiba domin tana yawan bata labarinshi, bata san lokacin da data girgiza mata kaiba, feena ta tsuke fuska "waishi faisal dinnan duk lokacin da kikaje gurinsa saiya sakaki kuka, ni gaskiya anty zarah kidaina zuwa gurinsa, kima rabu dash.." bata karasa maganar ba zarah ta toshe mata baki, tana girgiza mata kai a lokacin har hawaye sunzo mata ta dora kanta akan feena tana fadan "bazan iyaba feena, wlh bazan iya rabuwa dashi ba, kee bakisan MIYE SO ba, shiyasa kike fadan na rabu dashi, I lov him feena, I lov him...." takarasa maganar tana kuka,

Feena  ta tausaya mata sosai.  tasa hannu ta share mata hawaye sannan tace "anty zarah malamin islamiyarmu yace duk abinda mutum keso toh yakai kukansa a gurin Allah insha Allah allah zai shere masa hawaye, anty zarah mezai hana kifadawa Allah damuwarki"
Zarah tayi murmushin yake tace "ngode sister na, nagode sosai, tashi kije inason na kwanta"

 feena ta mike daga kan gado tanufi hanyar fita tana tana juyo tana kallon antynta, harta fita tabar dakin, zarah takara fashewa da kuka....

**** ****   **** ****
Kwanan umma biyu kenan a station tayi baki dukta kode, tasha wuya sosai,

Yanzu dai kam abba yagane ba umma bace ta sace rumaisa, domin da ace ita tasaceta data fito da ita kodan wahalar datasha,

Abba duk ya fita hayyacinsa, 'yarsa k'waya daya tilo tabata, anyi nema har an gaji, dole akaje aka bawa malamai adu'a akan sutayasu da adu'a ko Allah zaisa aganta,  tafito a duk inda take ,

Abba kullum yana station idan baya station to yana gida amma kwata2 yadaina aikin komai, komai nasa yatsata cak, tashin hankali yashiga sosai, zuciyarsa cike da danasanin abinda yayiwa rumaisa,

Yauma Yana zaune a station yana tunani2

Zunbur ya mike  kamar wadda aka tsigala, dasauri yafita yabar office din, yashiga motarsa, ya kunna yahau hanya gudu yake sosai, harya karasa unguwar da ya saba ganin rumaisa....


Unguwar da majnoon yake zaune, daidai gurin daya zo yasami rumaisa ranar anan yaja birki, yana tsaya yana kallon unguwar, yana jan nunfashi,

A gefen wani gida ya hangi majnoon a rakube, yayi wani irin zama kalar tausayu..

 Dasauri abba yafito daga cikin motar yanufi gurinsa, yana karasawa ya gurkusa yazauna kusa dashi edon abba sunyi ja sosai, yadube majnoon sai kuma yasaukar da kansa, yanayinsa yabashi tausayi cikn sanyi murya yace " ina rumaisa"

 majnoon yayi saurin dago kansa yana kallon abba, saikuma ya mike tsaye yana kokarin barin gurin, abba yayi saurin shiga gabansa " magana nake maka ina rumaisa" majnoon ya ture abba daga gabansa yacigaba da tafiyarsa, ran abba yasoma baci kara shiga gaba majnoon ya runtumo kwalar rigarsa  yadaga murya sosai yace "kai inaima magana ka kashareni, ina kakaimun rumaisata, wallahi saika fito mun da ita saboda komai yafaru da rumaisa kaine sila, abba yakara jinjiga kwalar rigar majnoon yana fadan " ina rumaisa..." yafada yana hawaye,  nan take mutane suka taru a gurin suna kokarin babbare majnoon daga hannun abba, shidai majnoon uffa baiceba, sai mazurai yake da  edo, abin tausayi duk ya rama,

Abba yana kuka yake fadan " karku barshi yatafi wlh 'yata yasacemun, 'yata tana wurinsa kuce masa yabani 'yata" mutane suka rirrike abba, wasu kuma wasu kuma suka rike majnoon..

daya daga cikin mutanen yace " haba Alhj yazakace mahaukace yasacemaka yarinya, meyasani waddama koshi kansa baisaniba ballema harwata 'yarka, kaidai kaje kanemi wadda yasacema 'yarka amma ba wannanba"

 nan kaji mutane gurin sunce "gaskiyane wannan bazai iya sace maka 'yaba " wani matashi yana rike da majnoon yace " wannan mahaukacin yau kwanansa biyu kenan ko wasa yadainyi da yara, kullun yana rakube a gefen titi ko agefen unguwa, gaskiya wannan bashi yasace maka 'yarka ba, kaje cen kanemi wadda yasace maka 'ya"

Abba yace "wlh shine.. wannan ne " yanuna majnoon, mutane suka ce a fa bashi bane, abba kuwa  yayi juyin duniya suka koki bashi gaskiya, mutane suka rikesa suka kaisa har bakin motarsa suka sakashi, sannan ya kunna motar yabar unguwar yana kuka, soyayyar  'ya da mahaifi kenan....

**** ***   *****
Faisal kuwa duk ya rame abincima kadan yakeci bai wuce a yuni yaci abinci saudayaba, koshi dandai momy na matsa masa ne, ammashi kwata kwata bayajin dadin abinci,

Faisal yana zaune a falo yana kallo bayan dawo daga gurin aikinsa dagashi sai singlet da 3cutr yadora kafarsa kan dani table dake tsakiyar dakin ya jingina jikinsa a jikin kujera, kallo yake amma hankalinsa kwata2 baya gurin yana gurin tunanin rumaisa, gaggar jikinsa ce kawai zaune a gurin amma zuciyarsa bata tare dashi,

Momy ce tafito daga cikin  dakinta, ta ganshi saune yayi kuru da edo yana kallon tv, tayi murmushi sannan takarasa gurin tazauna tana kallonsa  takira sunansa har sau biyu taji yayi mata shiru, bubbuga kujerar tayi sannan ya zabura yana kallonta " momy" yakira ta yana kikarin yin murshi, yaushe kikazo nan "

momy tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace " taya za'ayi kasan nazo, tunda kadauki damuwa kasaka kanka aciki, wai mekakeson kazamane faisal akan soyayya duk kabi ka susuce, jibi yadda karame sai kace bakaiba"

Faisal ya tsuke  fuska, shiko yawan magana yanzu bayaso, shidai yafison kummul abarsgi alone, yace " menayi kuma umma, nifa ba ita nake tunaniba, kawaidai ina kallone"

Momy taja nunshi tace "duk yadda kaso kaboye damuwarka, bazaka iyaba domin fuskarka da jikinka zasu bayyana hakan, kiyi kokarin saita kanka faisal"

Faisal yasaukar da kafafun daga kan dani table di  yana kokari  saka takalminsa, yace "nifa babu abinda ke damuna momy, ni baccima nakeji " yamike tsaye momy ta bishi da kallo haryabar falon, ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin yaronta, akan soyayya duk yabi ya susuce...
******     ********    ******
_One day later_

Rumaisa ta koyawa fahad abubuwa sosai kuma sun shiga kansa, yanzu yasan yadda zaiyi sallaj aduk lokacin dayaji ankira sallah,

 hankalinsa yasoma dawowa kansa, rumaisa tasakashi harda siyo littattafan addini, (kujimun samun guri irin na rumaisa) yanzu kam tasake dashi sosai,

Yauma suna zaune a falo, tana koya masa adu'oi, tasaki jikinta da gidan kamar gidansu, daman cen a gidan nasu  ba wani farin ciki take samuba, yanzu kuwa tasamu freedom, 

Kallonta yakeyi kamar zai hadiyata ita kuwa kanta na kasa tana karan ta masa littafin dake gabansa,

Saidai ta lura da hankalinshi baya gurin sannan ta dago kanta tana kallesa taga ita yake kallo,  ta kida masa masa hannu da sauri ya zabura, yana murmushi, itama murmushin tayi tana kallonsa tace " littafi zaka kalla baniba"

Fahad ya girgza kai "tohm malama" murmushi tayi sannan taci gaba da karanto masa,

Shidaikam yagaga daina kallonta domin akoda yaushe kara shiga masa rai take, sha'awarta makil take a duk wani sassa na jkinsa..


Da yamma fahad yakira duk wani ma aikacin gidan suka taru a falon, rumaisa tana zaune a gefen kujera tana jiran taji maizaice, kowa a falon yayi tsit yana jiran yaji me fahad zaifada,

Fahad yayi gyaran murya yace "daga yau nabawa rumaisa damar shiga ko ina agidan nan amma banda fita, dan haka karkowa ya hanata zagaya gidan nan, yana kallonsu yace " ina mai gadi " mai gadi ya leko.kansa daga cikin taron ma aikatan  yace "gani oga "

Fahad yace "toh kaji abinda nace ba, karka kuskura kabarta tafita" mai gadi yace "toh"

 fahad yanisa yace  "toh shikenan kowa yatashi yakama gabnsa"  nan falon ya watse rumaisa dake zaune duk tasha jinin jikinta, a zuci take fadan watoshi wannan  baya mada niyar sakina nan , lallai kuwa akwai matsala, bazan dawwama anan ba yazama dole inje inga majnoon, shima wannan zaman danake dan kaina nakeyi, kuma domin in gyarawa fahad rayuwarsa ta yadda zaiji dadin rayuwa koda bama tare dashi..

Maganar sace ta katse mata tunani yana fadan "yanzu kinsamu freedom a gidan nan dan haka saikiyi abinda kikeso"

 kai kawai rumaisa ta daga masa sannan tatashi tanufi dakinta yabita da kallo, tafiyartama burgeshi take,

Sai da tashige dakin sannan ya furzar da iska, yatashi yanufi dakinsa, yazauna bakin gado zuciyarsa cike da wasu wasi kalla2 , dafe kansa yayi sha'awar rumaisa tasoma fin karfinsa ta yadda bazai iya hana kansa aikata abinda yaso akan taba,

Yana zaune cikin wannan yanayin yaji anturo kofar dakinsa, dasauri yadago kansa yana kallon kofar,  rumaisa ce tashigo dakin da littafi a hannunta, murmushi ta sakar masa suns kallon juna tace  " kamanta da littafin nan ne a dakina shine nace bari nakawoma ko zakayi bitarsa, murmushi yayi yace "ok kawomin"

Taku takeyi tana kokarin karasowa gurinsa, shikuwa edonsa na akan kirkijinta, tana karasowa ta mika masa littafin, da sauri ya cafki hannunta, ya lumshe edo, yana sosar hannun
Jikin rumaisa yadau rawa, taga edonsa sun fara rikidewa, murya na rawa ta furta " sakeni na wuce daki "

Fahad ya dubeta a lokacin duk tsigar jikinsa tatashi, dasauri ya mike ya tsaya daf da ita kamar zasu hade fuska  yace " rumaisa kinunamin soyayya mana, a koda yashe kece muradain raina"

Yafada yana kokarin sanyata jikinsa, rumaisa ta na kokarin kwatar kanta tana fadan "meye kuma haka Fahad ko kayi haukane"

Fahad yace " eh rumaisa nayi hauka indai akan kine, rumaisa I need you,  plcxx" k'akk'ameta meeta sosai yayi a jikinsa yana shakar nunfashin ta, rumaisa ta soma kuka " dan Allah kasakeni natafi"

fahad yan nishi yace " rumaisa bazan iya bane sha'awarki zata illatani rumaisa kiyi helping dina  plx dan Allah kosau dayene muyi sex"
 rumaisa ta tureshi daga jikinta,

Tana kuka take fadan  "bazan iyaba fahad, nayi zaton karatun damuke da zaman da mukayi dakai yasa kacanza halinka ashe bahaka bane, makeson zamane fahad, nidai wlh bazan iya baka kainaba amma nasan banada karfi dazan iya hanaka abinda kake sonyi dani, a duk yunkurina so nake naga na gyaraka koda Allah zaisa sonka yashiga zuciyata, amma kai baka gani wlh fahad tir dakai" ta tofar da yawu tana kuka,

fahad yayi tsaye yana hawaye, bazai iya gujewa sha'awar dayake yiwa rumaisa ba, cikin muryar kuka yace " sau dayafa rumaisa, daga wannan wlh bazan karaba sai idan munyi aure plx"

Rumaisa ta dafe kanta tana mamakin wannnan wane irin mutum ne, baya tsoron Allah ko kadan, baya tunanin makomarsa a gobe jiyama,  cike da hargowa tace "bazan aminceba fahad,  kuma walh bazan aureka matukar baka gyara halayen kab.. kuka ya hanata karasa maganar, kuka take sosai, cikin kukan taci gaba dacewa " matukar ina raye bazan barka kakusanceniba, ta nuna kanta da dan yatsa tana kuka tace " kazo kakasheni fahad, kazo kakashine dan ka sami abinda kakeso a gurina" takarasa maganr tana kuka sosai,

Fahad ya fa juye2 a cikin dakin  kamar wani mahaukaci yayi ihu yadaki ganin dakin yana fadan " bazan iyaba rumaisa, bazan iya kashe kiba Rumaisa, kece hasken idanuwana"

  yana gama maganar ya juya gefen gado ya hangi makullan motarsa karasawa yayi yaje yadauko makullan sannan yafice yabar dakin yana hawaye,

Baifi minti biyu da fitaba taji kukan motar sa yafita yabar gidan, dasauri tatashi tana kuka tanufi dakinta, tashiga tamayar da kofar dakin ta rufe  tasa key, saboda  tana tsoron kar yaje yasha giyarsa yazo yasameta,

Sannan tafada kan gado tana kuka, Zuciyarta cike da bakin ciki yanzu duk abinda ta koyawa fahad tayi abanza kenan, lallai kuwa wannan bazai taba shiryuwaba, yazama dole ta dauki mataki, tayi kokarin barin gidan tun kafin ya cimma mummunan kudurinsa akanta,

Tambayar kanta take to ta inama zata fara ...

A ranar kaf har dare fahad bai dawo gidan ba, haka ta kwanta tayi baccinta cike da fargaba,
Washe gari
Tatashi bataji motsinsaba,  tafito taje har dakinsa bata ganshiba, hankalinta yasoma tashi, ta zurawa lamarin Allah edo,

Haka har yamma tayi baidawo hankalinta yatashi sosai duk ta sukukuce, takasa yin komai, sai taji gidan duk baya mata dadi saboda baya nan,

Misalin karfe 10:03 na dare  tana rakube akan kujera cikin falo  tana jiran dawowar fahad, amma taji shiru, gangadine yafara dibarta, bata ankaraba bacci yayi awon gaba da ita,

11:00 fahad ya dawo gidan, yanayin  bude motarsa kawai nagani nace akwai matsala domin kuwa da karfi tsiya ya turo kofar,

Sai kuma naga yana fitowa a hankali,  yana tangadi kamar zai fadai ko ba a fadamin ba nasan giya yasha yayi mankas domin ko tsayi gagara yi yayi yana tangadi yafadi sai kuma yagagara tashi,

Bodyguard dinda ke tsaye a bakin kofar suna kallonsa sukazo gurin, " oga lfy"

Cikin murya irin ta yan maye fahad yace " kudaukeni kukaini ciki"

 Yadago musu hannayensa, ba musu suka rika hannayen suka dagashi sama suka sark'afahi suka nufi cikin gida dashi, 

A falo suka sami rumaisa tana bacci,  duk da acikin maye yake amma hakan bai hanashi ganin rumaisa a kwanceba, yacewa bodyguard din "ita wannan metakeyi anan" dayan  bodyguard din yace "bacci take oga" fahad yayi gyatsa kamar zaiyi amai  sannan yace " bacci,,, bacci, ya fada cikin salon kasala, sai kuma yace "to kuma kuje kuyi bacci, ni kubarni anan nima anan zan yi bacci"

 sukace "toh oga" suka karasa dashi bakin kujera daya suka ajiyesa sannan suka fita suka wuce dakinsu, koba komai yau zasu Huta da tsaron wannan mashayin...

Yadade a kwance kafin yayi yunkuri iya karfinsa sanna yasamu ya mike,
tangadi yake sosai da kyar ya iya yakarasa gurin rumaisa,  yayi gyatsa kamar zaiyi amai,

Sautin gyatsar yaratsa kunnen rumaisa da sauri ta farka ta ganshi a kanta, yana mashalo, cike da zafin nama ta mike, edonta duk suncinciko da kwalla, tana kallonsa,  wannan bazai taba shiryuwaba, a zuci tafad'a,  duk ta firgita, yazu kam tsoron fahad take  domin yazamo ibilis, mutum bayajin nasiha,

 fahad dake tangadi yace "zonan Rumaisa" rumaisa ta makale kafad'a tana shirin yin kuka,

Fahad yace" bazaki zoba, toshikenan bara nazo ni" yayi taku daya zuwa biyu yana kokarin karasawa gurinta tangadi ya hanashi sandin cafet din yajasa yafadi  rakwassss a gurin daidai dani table din da ke tsakiyar falon  yafadi, dani table yarabu gida biyu,
Rumaisa ta toshe bakinta takara tsorata ganin fahad kwance cikin glass,

 A hankali takira sunansa, taji shiru, dafe kai tayi ta rosa kuka tace na shiga ukku"

Dasauri ta nufi hannyar fita domin yanzu ba bodyguard ko daya agurin, takara bakin gate tana kuka a lokacin mai gadi yafito, da fitila a hannunsa" hajiya lafiya,  yana fada yana dalla mata fitilar

Rumaisa tace " fahad zai mutu yana ciki" takarasa maganar tana kuka,

Mai gadi ya tsorata sosai,  dasauri yace " hajiya yana ina" rumaisa ta nuna masa kofar shiga falon " yana ciki"

Mai gadin baijira takara magana ba ya zura da gudu yanufi cikin falo,

 harta daga kafa zata bisa, saikuma ta tsaya cak, zuciyarta na harbawa tara2, yau gata a bakin gate, kuma ita kadai, ai kuwa bazata watsar da wannan damar ba, dole tabar gidan da sauri takarasa wurin key din kofar tana kokarin budewa, cikin sa'a kuwa yabude, ta tura kofar tafita waje, unguwar shiru kake jinta, tsoro yakata jitakeyi kamar ta koma cikin gidan, wata zuciyar tace "ina ai komai tsoron da zataji gwara tatafi" tayi tsaye a bakin kofar tana kuka.

 tambayar kanta take, to ina kuwa zata je, kalaman mahaifinta ta tuna nacewa zai mata aure da faisal kotanaso kobataso, hakan yasa taji batason zuwan gidan, toh ina zataje,

 Kakarta tafadi mata a rai, mahaifiyar abba, gurinta zataje domin tana da tausayi sosai kuma tana son rumaisa,

  Tohm amma kuma ba'a garin takeba a sokoto take, taya za a yi tasamu motar sokoto a yanzu cikin daren nan, ta tsaya tana nazari...

 jin mai gadi yafito yana kiran hajiya! hajiya!! a cikin gidan ta kara firgita, mai gadine yana kokarin fitowa waje..

Rumaisa tace kafa menaci banbakiba, nan ta famtama da gudu tsiya tabar kofar gidan ta ratsa unguwar cikin duhun dare...

Mai gadi na fitowa yaga babu hajiya,  kuma kofar gidan  a bude abin,  yadafe kansa yafashe da  kuka, domin yasan dacewa gudu tayi, yafito waje yaleka yaga babuta babu alamarta, kuka yafarayi....

"Nashiga uku, yanzu idan oga yatashi yasan dacewa hajiya ta gudu wlh zai iya illatani,wlh bazan zauna a gidan nan ba, dole inje innemota, idan kuwa ban sameta bazan dawo gidan nan ba" mai gadi yafada, Dasauri yashiga dakinsa yafara hada kayansa yana kuka,

 saida yagama hada kayan  kaf sannan yafito,  cike da tsoron kar wani yagansa,  ya sulale yafita yabar gidan,

Rumaisa kuwa sharara uban gudu kawai take, ita kanta batasan inda takeba, ballema harta samu hanyar zuwa sokoto,

Daidai wani layi ta karyo kwana, karnuna na kwance a gurin sunaji gudun mutum, suka tashi suka fara haushi,  a daidai kwanar tayi kicibus dasu,
 Cike da tsoro da fargita ta famtama ihu, daman dai tuncen rumaisa tsoron kare take,

 karnukan sukaji ihu ta,  ai kuwa  nan suka biyota, cab bata mayi guduba yanxu tafarashi domin wani masifaffen gudu danaga rumaisa nayi,  nikaina banzaci zata iya yinsaba, gudu take tana kuka, Wani irin sabon karfi yazo mata, su rumaisa anga mutuwa.

Karnukan na biye da ita suna mata haushi, ita kuwa tana gudu tana kuka ratsa unguwar kawai take bata masan inda takeba,  tana cikin gudun kawai jitayi tafada ciki wani rame  fancamm!!! saida bakinta yadaki gabar ramen, bakin ya fashe da jini, duk jikinta ya goge, ta duke a kasan ramen  tana maida nunfashi,ta toshe bakinta duk da zafin dayake mata amma a haka tadaure, saboda batason  karnukan suji kukanta,

Karnukan sukazo gurin sai haushi suke amma basu gantaba, suka yi tsaye a gurin suna sintiri, saida suka gama zagayensu sannan suka bar gurin, saida  taji gurin yayi shiru sannan ta saki bakinta shanshekar kukanta kakeji sannu2,

Sai a lokacin tasamu natsuwar duba ramen data fad'a, da kyal ta mike tsaye tana hawaye, duk jikinta ciwo,

Irin ramun nanne na gefen titi, (lamba 2)  tana daga kanta kuwa sai taga titi, wata irin ajiyar zuciya tayi tana nishi,

Da gyar ta iya kama bakin ramen, tafito tahau titin tayi tsaye, tana kallon titin  gefe da gefe, tsif kakejin tati babu ko motsin lade, a hankali tafara tafiya tana tangadi tare da hawaye, zafin ciwon yasakata kasayin kuka, ta dafe kafarta dai dai gurin dake mata ciwo, tadan jima tana tafiya kafin tafara jin kukan wani ubu a bayanta kamar motace ke shirin zuwa  gurin, da sauri ta juyo, tana juyawa kuwa saitaga hasken fitilar mota, tayi tsaye a gurin ta d'aga hannu tana yiwa motar alamar ta tsaya,

Motar bus ce taxi, tundaga nesa driver ya hangi mutum namasa hannu, hankalinsa yatashi  duk jikinsa yadau rawa a tunaninsa irin yan fashin nan ne wadanda zasu nemi  taimako,  idan katsaya kataimaka musu sai kuma suyi maka fashi, tsoro yakashi sosai, yanayinta bai nuna tana cikin natsuba sannan  kuma sai yaganta tana hawaye hakan yasa wata zuciyar tace masa yatsaya,

Daf da ita dirver yazo yatsaya, ya kura mata edo yana kallonta,  rumaisa tana kuka take fadan "dan Allah malam katai makamun walh saceni akayi" shidai yayi kuru yana kallonta kyankyawar gaskice,  a zuci yake fadan "wannan ba mutum bace Aljanace" nan yafara kwararo adu'oi, naneman tsari

Ganin baice mata uffan ba yasa tafara Taku takaraso kusa da motar, a lokacin driver ya dube bakinta yaga duk jini, yakara tsorata sosai, azuci yace "wayyo Allahna yau hadu da aljana mai cin mutane"  muryarsa narawa yake furta "kukuke ganinmu bami muke gani kuba, dan Allah karki cutamun wlh ni taimakonki natsayayi"

Rumaisa tace "wlh ni mutum ce kamar kai, idanma baka yardaba ga hannuna kataba kaji" ta zura masa hannun tana kuka,
Jikinsa narawa yakai hannunsa saman jikin Rumaisa,  sai yaji laushi,

 Yadubeta  yayi  ta maza yace "malama lafiya meya fito dake cikin wannan tsohon daren,"

Rumaisa ta fashe da kuka tana fadan "dan Allah kataimakeni kakaini sokoto, wanine ya saceni,na samu kubuta daga hannunsa, shine na gudu"

Har a lokaci bai yarda da rumaisa ba leko kansa yayi ta glass din motar yana kallon kafar Rumaisa ko zaiga kofato, sai yaga kaface  irin tasa a lokacin ya kara  tabbatar dacewa itama mutum ce kamar sa, ajiyar zuciya yayi  sannan  yace "kwantar da hankalinki, Allah ne yakawo miki ni, domin ni yanzu haka Sokoto zan nufa,  ya bud'e mata kofar motar sannan yace "shigo muje"
Bakaramin dadi rumaisa tajiba, tace "nagode, nagode" tashare hawayenta sannan ta zagaya tashiga motar suka lula zuwa sokoto,

A cikin motar yadauko wani tsumma ya mikawa rumaisa yace " ga wannan ki goge jini dake jikinki, kafin zuwa gobe idan mun sauka sai mu nemi clinic agubaki"

Ba musu rumaisa ta karba, ta goge jikinta sannan tasa tsumman ta toshe bakinta dai dai gurin dake fitar da jini,

Divern yadan kauda kansa daga tukin dayake ya dubi rumaisa yace " kekuwa garin yaya aka saceki daga sokoto zuwa abuja"

Nan Rumaisa tashiga kwararo masa bayani, amma saidai tamasa karya, saboda bata gaya masa gaskiyar cewa ita yar Abuja bace,

Bayan tagama gaya masa,  Driver yayi ajiyar zuciya sannan " Allah sarki, sai kuma yayi shiru sai cen sannan yace " Allah yaka kareki daga shairinsa"

Tace "ameen" sai kuma tayi shiru, bata mason yawan surutu saboda ciwon dake bakinta, dama zai kyaleta da yafi mata,

Driver yace " nikuwa kinga lodi ne yakawoni garin nan, kuma nasauke shine zan kara komawa na dauko sannan  kuma nadawo"

Girgixa masa kai kawai rumaisa tayi,
Nan dai yaci gaba da xuba mata suturu, sai kace bbc,

Rumaisa kuwa banda toh da him babu abnda take ce masa,

Daya lura dacewa bata son yawan magana, dolensa yakyale ya maida hankalinsa ga tukinsa

Gudu suke tsalawa kamar sutashi sama koda akace maka asuba takusa  sun kusa karasowa sokoto..

Karfe 8:30, na safe suka karasa sokoto,  lokacin har rumaisa tayi bacci,

Mutumen yatadata, tatashi yace " gamu munzo sokoto, ni a nan zan tsaya cikin  gareji domin baza a barni na fita ba"

Rumaisa Tace "tohm " tana kokarin fitowa daga cikin motar,

Driver yasaka hannunsa cikin aljihu yaciro naira 200 ya mikawa rumaisa " ungo wannan kyasamu ki hau keke napep"

Rumaisa ta karba tayi masa godiya, sannan yace "toni zan wuce "
Rumaisa ta kada masa kai cikin yanayin tausayi, sannan ta sauko daga cikin motar, shikuwa ya rufe motar yafice yabar gurin, yabarta  tsaye a gurin  Zuciyarta tashiga harbawa 9-9, nan tafara zancen zuci yanzu gata cikin garin sokoto saidai kuma btasan inda zata jeba, daman duk zuwan dasuke a motar abba suke zuwa, kuma idan sukazo basa wuce wuni daya, sai kuma sukoma, hakan yasa ko sunan unguwar da kakar tata take bata saniba, shiru tayi tana kallon garejin, sai taga kowa harkar gabansa yake babu wanda yadamu dawani,  a hankali tafara taku  ta sami wani gefen acikin  garejin ta rakube tana cizon labba duk ciwo takeji a jikinta,

***  **  

Wata babbar motace bus  irin wadda tasauke rumaisa yanzu taja birki a cikin garejin, mutane sai fitowa suke,

Yafito daga cikin motar zuciyarsa fal da farin ciki, a hankali bakinsa yake furta " alhamdulilla"

Kallon daya nayiwa mutum daya fito daga cikin motar yanzu, naga kamar nasansa,

tsaye yayi yana kallon garejin gefe da gefe, 

Caraf edonsa yafada kan rumaisa datake rakube a gefen gereji, zare edo yayi cike da mamaki, yakara furta " alhamdulilla" cikin sanda yake tafiya, kamar barawo yazo sata, ta  yadda bazataji hayaniyar zuwan saba har ya  karasa gurinta, da zuwansa ya cafki hannunta, cike da tsoro da firgita rumaisa ta daga kanta ta kallesa, gabanta yayi mummmunar faduwa, taje zatayi ihu ya toshe mata baki.....
Mai gadi yace "karki kurkira kimun ihu anan, tashe muje" yafada yana kokarin tadata,

Rumaisa ta kwabi hannusa daga bakinta, tana kokarin yin magana,
Tun bata karasa maganar ta fashe da kuka" dan Allah karka maidani gurinsa, wlh azzalumin Mutunne zai cutar dani"

Maigadi yadube tabashi tausayi, hannuta yasaka sannan ya gurfana a gabanta yayi ajiyar zuciya yana kallonta yace  " ai ko banada imani, bazan iya mayar dake gurin saba, domin nikaina nagaji da zama dashi, na gwanmaci zana cikin talauci da zama tare da fahad, ya nisa sannan yace "mekikazoyi sokoto"

Rumaisa ta share hawayenta tana shanshekar kuka tace  "gurin kakata nazo kuma nibansan unguwar da takeba, a kullum idan mukazo, a mota muke zuwa, shine yanzu nakasa gane gidan, ni sunanta kawai nasani "

Mai gadi yayi ajiyar zuciya "ya sunan kakar taki, ko Allah zaisa nasan ta"

Rumaisa tace  " sunanta hajiya luba mai tuwo"

Mai gadi yayi shiru yana nazarin sunan kamar yasan mai sunan a hankali bakinsa yake maimata sunan "hajiya luba mai tuwa, kamar nasan mai sunan, domin akwai wata mai irin wannan  sunan, kusan  unguwar mu daya da ita, saidai ita yanzu tadaina yin tuwo"

Dasauri rumaisa ta girgiza kai " eh itama tadaina kawaidai inkiyace ake mata"

Mai gadi yace " to shikenan tashi muje zan kaiki gurinta, idan Allah yasa itace kinga shikenan idan kuwa ba ita bace, saimu shiga neman kakar taki"

Rumaisa tace "nagode Allah yasaka da khairan" 
Nan suka mike a tare suka shiga napep sukabar garejin

 Uguwar suka shiga suna zuwa aka saukesu, suka fito, har mai gadi zai biya kudin napep rumaisa tace " kabarsu kawai akwai farar dari biyu hannuna zan bashi" bata jiraba  ta zaro dari biyu ta mikawa mai napep,
   Mai gadi yace "ayi haka kuwa" yafada yana murmushi"

Rumaisa tace bakomai, ai kaima katai makeni, ta juya tana kallon gidajen unguwar kamar ta soma tuna gurin, saida tabasar ta dube mai gadi  dake kokarin fitar da jakar tutafinsa a cikin keke napep  tace " inane gidan"

Saida yafitar da jakar sannan ya juyo ya kalleta yace " ga gidan nan mushiga" ya nuna mata gidan, suka shiga

Wata bakar dattijuwa zaune tana tsintar shinkafa, tajiyo sallama a zaure, da sauri ta amsa tana lekon zaure domin taji ana kokarin shigowa, a dai dai lokacin su rumaisa suka shigo gidan, damm gabanta yafad'I. suna hada edo da matar  rumaisa tace "wlh itace, " da gudu ta karasa gurinta ta rungumeta tana kuka"

Haj luba takara rungume tana fadan "Allah sarki yau saiga rumaisa a gidana, ina abban naki yake "

Mai gadi yayi tsaye yana kallon ikon Allah, ashema yasan kakar rumaisa,

Batayi maganaba hakan yasa Haj luba ta dube mai gadi tace "habu lafiya kuwa, ko tare kuke da Rumaisan ne"

Mai gadi data kira da habu yakaraso gurin ta yazauna, sannan yashiga kwararo mata bayani duk abinda yafaru tundaga farkon  zaman Rumaisa a gidan fahad har zuwa yanzu,

Ba karamar girgiza haj luba tayiba, tayita yiwa mai gadi godiya,

Sannan ta fitar da rumaisa daga jikinta ta kalleta, har a lokacin rumaisa kukan farin ciki take,

Haj luba tace "aikin me baban naki yakeyi dahar  yabari akasacemin ' yar jikar tawa kwaya daya tak, kuma shine baizo yagayamunba"

Rumaisa tana kuka tace "wlh inna komai yafaru, shine sila..." zatayi magama sai kuma  kuka ya hanata karasa maganar

Haj luba tace " kobaki fadaba nasani domin nasan munafukar matar nan tasace koh"

Kasa magana Rumaisa tayi sai kuka take,

Inna tayi ajiyar zuciya sannan takara juyo gurin habu mai gadi tace " habu nagode, Allah yasaka da khairan" habu mai gadi
Yace amen, hajiya nizan wuce, saina jewawo anjima" yana gama fada yafita yabar gidan,

*****    ******       *******
Koda ma'aikatan gidan suka tashi, suka karasa cikin falon suka tarar da fahad  kwance cikin glass jikinsa duk jini,

Cike da firgita suka daukesa suka sakashi a mota suka nufi asibiti dashi, sai bayan sunkarasa asibitni sannan suka kira mahaifinsa suka sanar dashi..

Tsorata sosai abban fahad yayi a lokacin da aka sanar dashi cewa fahad yana asibiti,  Bayama 9ja suna American shida umman fahad amma a ranar suka hawo jirgi suka shigo 9ja,

Karfe 10:30 na safe jirginsu yasauka a airport dake garin abuja, tun a cikin jirgin mahaifiyar fahad take kuka, abban fahad sai lallashinta yake, da kyardai yasamu ta saurara,

Suna saukowa cikin jirgi motoci suka dira a airport din, daman abban fahad yasa a kawo musu moter, nan suka shiga motar suka suka wuce asibiti,

Suna karasawa bakin asibitin abban fahad ya dubi asibitin ya tsuke fuska "wht anan aka kawomin yaro" yafada a sanyaye, ransa a bace ya shiga asibitin a wulakance yake kallon mutane,  yakarasa dakin da fahad yake, a kwance suka samesa duk ansaka masa bandej a jiki, umman fahad takarasa gurin fahad tana kuka, tarike masa hannu,

Abban fahad kuwa ma'aikatan yahau da masifa, fada sosai yayi musu ransa ya bace daga karshe yake cewa "wannan wane irin kauyancine da gigadanci, zaku kawomin yarona wannan karamar asibitin me suka sani, asibitin da kowane talaka zai iya kawo d'ansa,  abban fahad yayi huci ya dube ma'aikatan, duk sunkuyar da kansu kasa, sannan yace "duk na koreku daka aikin tsaron yarona, domin naga bazaku iyaba" ma'ai katan suka shiga bashi hkr, amma sam yaki hkr, mahaifiyar fahad itama fada tamusu sosai itama ta goyi bayan maganar mijinta,  sannan abba yafita yaje yasami likita yace yanaso ya bashi transfer zai dauke yaronsa daga asibitin zuwa wani babban  asibiti, ba musu likitan ya yanka masa,  yakarba suka dauki fahad suka bar asibitin dashi, wata babbar asibiti suka kaisa, saboda har a lokacin bai farka ba.
Duk glass yayanke masa jiki,

Likitoci sukayi masa aiki sosai sannan suka bada yakinin cewa insha Allah daga nan zuwa gobe zai farka,

Abban fahad yace "toh shikenan" anan suka wuni asibiti suna jinyarsa, mahaifiyar fahad ta tambayi abban fahad "waishin meya faru da fahad ne"  abban fahad yace " nikuwa ta ina zan sani, bayan nidake duka bama kasarnar, mudai jira yafarka sai ya gaya mana da kansa"

Haka suka zauna ko wannesu cike da bacin rai da kuma jimamamin rashin lafiyar yaronsu, basason komai yasami fahad...

*****       *****         *****
Wani irin katon falone, yasha ado da kamshin turare, wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru 45  ce zaune tana kallon tv cikin nishadi da kwanciyar hankali,

Zarah tafito daga cikin dakinta tayi shirinta nafita tana kamshin, fuskar nan tasha make-up tayi kyau abinta sai murmushi take, takarasa bakin kujerar da matar take zaune ta zauna kusa a ita tana murmushi, ummana kallo kike"
Matar data kira da umma ta dubeta tana murmushi " ey, ina zuwa kuma haka aka chaba wannan adon haka"

 Zarah ta sunkuyar dakai, tana sosar kanta, kamar marar gaskiya "umma gidan su maryam zance kinsan yau ake bikin antyn ta "
Umma tace " haka nefa, toh shikenan amma dai kirki dade a gidan domin kinsan halin  mahaifinki baya son fitar nan dakike, idan yadawo bak'ya nan babu ruwana"

 Zarah tayi murmushi tace " insha Allah bazaima dawo ba yatarar bana nan, da wuri zan dawo, nidai zan tafi saina dawo"

Harta mike zata tafi umma tace "zarah naga kwana biyunan  kindaina fita aiki lafiya kuwa"

Zarah tadan langwabe kai tana kallon umma tace "ummana banga ribar fita aikin nan ba domin kona fita bana samun natsuwar zuci, ummana kawai kitayani da adu'a Allah yasa na iya jure bakin cikin dazan shiga nan  gaba"

Umma ta dube tadan zare ido da mamaki " wane irin bakin ciki kuma 'yarnan, meke damun kine a gurin aikin"

Zarah tayi murmushi a lokacin duk kwalla sun cika mata edo, tana sauri tabar gurin kar umma ta gane kuka take shirinyi tana fadan " saina dawo zan fada miki umma " dasauri ta fice daga falon tafita harabar gidan,

Umma ta tabe baki "toh" sai kuma tayi shiru tana kallon kofar da zarah tafita, sannan tace " Allah yakauta, ina jiran dawowarki" ita kadai take maganar sai kuma tajuya taci gaba da kallonta,

Zarah na fita hawaye suka sauko mata, dasauri tashige motar ta,ta daura kanta kansitari, tana hawaye, zuciyarta har wani zafi take mata, rashin faisal a gareta ba karamin tashin hankali bane, a duk lokacin da suka hada edo dashi wani irin sonsa yake kara shiga zuciyarta, saboda ta sami salamar zuci yasa tadaina zuwa gurin aikin domin tagaji da irin wulakanci da faisal kemata, amma duk da haka haryanzu zuciyarta cike take da kaunarsa,

Sitarin motar ta daka tana hawaye sannan tadaki kirjinta daidai gurin zuciyarta tana fadan "laifin kine zuciyata, kece kika sakani komai, kece kika ingizani inda ake wulakantani, inda aka daukeni marar zuciya mai nacin soyayya... kuka takeyi cike da tausayi, cikin kukan take fadan "meyasa kika kamu dason maso wani, tabbas kuwa  kin sakani a koshin walaha,..." kuka ya kubuce mata, takasa karasa maganar  ta saukar dakai kan sitiri, ta jima a hakan kafin ta dago kanta, tatsayar da kukanta sannan  tashare hawayenta,  ta sai-sai ta kanta, ta kunna motar tayiwa mai gadi hoh ya wangele mata kofa sannan tafice tabar gidan...

*Wacece zarah*

Zarah heesham shine asalin sunananta, black beauty ce ga diri ga k'ira sonkowa kin wadda yarasa,

Zarah ta kammala karatunta na degree yanzu haka tana aikine a wani company,  a company ne suka hadu da faisal, tun farkon haduwarsu da ita tafara nuna masa so amma shi saiya rika basarwa,

 Hakan yasa tanace harsaida takai data furta masa, tun da ta furta masa cewa tana sonsa kuwa  a take a gurin ya yi watsi da maganar tare da dayima wulakanci, ko da gargadin cewa karta kara bijiro masa da irin wannan maganar,

Amma duk da haka zarah bata daina binsa ba tanayi masa magiya akan yakarbi soyayyarta amma faisal yaki, kullum wulakancinsa kara karuwa yakee. Zarah tayi masa kuka har ba iyaka amma kwata2 yakiji tausayinta, shi ace warsa baya kaunarta, shi bata yimasa baki daya, duk wulakanci na duniya faisal yayiwa zarah akan yaga yacire mata sonsa a cikin zuciyarta amma ina yakasa...hakadai zarah taketa hakuri dashi, tana kara lallashin  zuciyarta akan ta dage wata rana zatayi nasara akansa,  ( wace rana ce wannan ) oho

Iyayen zarah ma'aikatan kwainatine, mahaifinta da mahaifiyar duk aiki suke, mamarta doc ce, mahaifinta kuwa librarian ne a wata university, 

Su biyune a gurin iyayensu daga ita sai kanwanta Nafisat wacca suke kira da feena...

_Wannan kenan_

*****    *****    ******

Haj lubace zaune a daki tasaka rumaisa gaba tana tambayarta akan tagaya mata yadda wannan abin yafaru kuma ta sanar da itada meye silar faruwarsa, rumaisa kuwa bayan kuka babu abinda take, hajja luba tace  "to nidai nagaji da wannan kukan naki, tunda bazaki fadamunba, ni zan koma waje idan kingama kukanki saiki kirani kisanar dani" tana gama fada ta mike tsaye,

Rumaisa  tayi saurin riko hannunta, tana shanshekar kuka tace "zan fada, dan Allah kizauna wlh zanfada "

Haj luba tayi ajiyar zuciya sannna ta zaune tace "fadamun ina jinki, meye silal faruwar komai" ta fada ta kallon rumaisa edo cikin edo, 

Muryar rumaisa na rawa tafara fadawa hajja luba, komai daya faru, harda dukan da abbanta yamata akan saita aure faisal,  tun bata karasa gayawa  hajja luba,

Hajja luba ta dakatar da ita, zuciyarta tadau zafi zanta yabace sosai cike da masifa take fadan "shi  Usman (abban rumaisa) shine zai miki auren dole, harda duka, wato kenan badan Allah yasa kinzo nanba , dasaidai kawai naji auranki daga sama, to wlh bai isaba, yadda yake nuna ikonsa akanki nima haka inada iko akansan domin nice na haifesa, hajja luba tayi shiru tana huci, sannan ta kara kallon rumaisa tace "kikace kinada wadda kikeso koh" Rumaisa tace "eh inada"
Haj luba tace "ya sunansa kuma d'an gidan waye" gab rumaisa ya tsinke yafadi, domin acikin labarin data bawa hajja luba bata sanar da ita cewa mahaukaci take soba, rumaisa tayi shiru tana kallon hajja luba, batasan sunan majnoon ba ballema hartasan sunan iyayensa,  a wane gari yake oho, itama bata saniba, tsoro takeji karta fadawa hajja luba cewa wadda yakeso mahaukacine ne, domin tasan dacewa, zata dauki maganar tata ashirmen banza,

Tayi shiru hajja luba ta tsureta da edo, bakinta na rawa ta soma furta " bansan..."

 Hajja luba ta dakatar da ita domin duk zuciyarta tadau zafi, wani irin haushin abban rumaisa takeji, tace " bana mason kifadamun sunansa ko sunan iyayensa, wlh babu makawa shizaki aura kuma nayi miki alkawarin indai ba mutuwa nayiba saikin auresa" sai kuma ta koma fada " maganar banza maganar wofi yanzu ai zamani ya chanza andaina yiwa mata auren dole, 'yar jikan tawa kwaya daya tak, za'a nemi amata auren dole salon idan aka kaita gidan mijin bakin ciki yanemi kasheta, toh bai isaba wollah"

Rumaisa tayi shiru sauraronta kawai take, tasoma ganin nasara acikin lamarinta da majnoon, amma saidai tana fargabar ya Hajja luba zata dauki abin idan har taji labarin cewa mahaukaci takeso"

Dafa kafadunta Hajja luba tayi hakan yayi sanadiyar fitowarta daga duniyar tunanin data shiga Hajja luba ta dubeta tace "kitashi kije kiyi wanka, kizo kici abinci, insha Allah gobe zamu koma abuja, kuma ina mai tabbatar miki dacewa zaki aure wadda kikso"

Rumaisa ta rungumeta tana kuka " nagode inna" kukan farin take,

Sannan A hankalin tafito daga jikin Hajja luba  tana share hawayenta sannan ta mike tafita tabar dakin tanufi ban daki,

Wanka tayi tafito koda tafito Hajja luba ta ajiye mata abinci, zaunawa tayi taci ta koshi, sai alokacin tasamu natsuwa,

Daki takoma takwanta saman gado, tunina barkatai suka rika zomata, yanzu ya fahad yake oho itama bata saniba, sai dai har yanzu akwai sauran tausayinsa a zuciyarta, wannan me yake nufi *so'ne ko tausayi*,

Majnoon dintafa yanzu wane hali yake ciki, tabbas tayi kiwarsa sosai,  kalaman Hajja luba suka rika dawo mata a kwakwalwa nacewa dole saita aure wadda takeso,

 murmushi tayi cike dajindadi, a zuci tace "Allah yasa hakan nee" nan dai taci gaba da tunani kala kala, har bacci yazo mata...

*Washe gari*
Tunda sassafe hajja luba tazo tatashi rumaisa,  tun agurin ta sanar da ita cewa, idan tagama salla tayi wanka tazo tasameta, domin motar safe zasubi suwuce abuja,

Haka kuwa akayi bayan rumaisa tayi salla sannan tayi wanka ta shiya, tazo tasami hajja luba zaune a harabar gidan itama ta shirya, karin kumallo kawai sukayi, suka wuce tasha, basu dad'e sosai ba a tashar  suka sami mota nan suka hau hanyar zuwa abuja,
*****     *****    ******
A *Abuja*

Fahad yana kwance kan gadon asibiti  edonsa suka fara motsawa, sunana kokarin budewa,  a hankali har edon suka yashe, kallon dakin yakeyi gefe da gefe, firgir ya mike zaune, yana mamakin wannan  dakin inane, juyowar dazaiyi  suka hada edo da ummansa, cike da farin ciki take kallonsa,

Shikuwa mamaki yacikashi, abubuwan da suka faru jiya yarika tunawa, muryarsa na rawa yace " ina rumaisa"
Abba yana tsaye ya kura masa edo  cike da rashin fahimta, maganarsa, wace rumaisa kuma? Abba ke tambayar kansa,

 umma takaraso gurinsa ta rike hannunsa tace "wacece kuma rumaisa"

Abba shima yakaraso gurin yana cewa "wacece kuma  Rumaisa son"  duk mamaki yacika su,

Fahad ya dafe kansa dake masa zafi yana kokarin tashi tsaye abba ya zaunar dashi, tuni hawaye suka cinciko masa edo, nan yasoma kuka yana fadan "kubarni natafi gurinta abba, wlh banzan samu salamar zuci ba  matukar banga Rumaisa ba, itace farin cikina, dan Allah kubarni natafi"

Umma ta dube abba, abba ya dube umma sudukansa mamaki yacikasu, wace irin rumaisa ce wannan data rikita musu yaronsu,

Ganin basuce dashi komaiba yasa Fahad yakara fashe da kuka yana cewa  " nacuce kaina, na cuce zuciyata, ya dube abba sannan yaci gaba dacewa "abba daga yau nadaina shan giya, wlh duk abinda rumaisa bataso zan daina, zan dawo mutumen kirki sabida ita, dan Allah abba kanemamin aurenta, idan bansamu auren  rumaisa ba wlh  bazan iya rayuwaba, dan Allah abba kanemamun auren rumaisa..." yakarasa maganar yana kuka sosai duk ya fita hayyacinsa,

Umma duk ta rikice, tunda take bata taba ganin kukan fahad ba akan macce sai yau,

Abba kuwa tuni edonsa sunyi ja sosai, yana tunanin wannan wacece ita kuma 'yar gida waye, tabbas zai nemota kuma zai nemawa yaronsa neman aurenta koda kuwa dukiyarsa zata kare kaf akan  wannan matsalar,

Abban fahad ya sunkuwo  yadafa gadon da Fahad yake zaune yana kallon fahad edo cikin edo yace "waye mahaifinta kuma a ina take"

Fahad ya yashare hawayesa yana cewa "A nan garin take, bansan sunan mahaifinta ba amma nasan unguwarsu da kuma  gidansu"

Abba yace "toh shikenan mujira zuwa gobe idan kakara samun sauki, zamuji musami iyayen nata"

Umma tana zaune tana kallonsu sai a lokacin tasamu damar cewa "bazamu jiraba har zuwa gobe, domin bazan iya jurar ganin yarona cikin damuwaba, sannan kuma banason yarona yayi asa'rar wannan yarinyar muje gidan nasu a yau kuma a yanzu "

Abban fahad yayi ajiyar zuciya sannan yace "toh shikenan muje "

Nan suka shiga hada kayansu, bayansun gama hada kayan, sukaje karbar takardar sallama a tare suduka ukku, 

Bayan sun karba suka fita motar suka shiga suka, abban fahad ne yaja motar har sun fara tafiya abba yace "mezai hana mutsaya mukarya kafin mukarasa, domin kunsan ni bana iya zama yunwa yanzun nan ulcer ta zata iya tashi"

Umma tace "hakanefa, muje mukarya kafin muwuce" toh kawai abba yace suka wuce wata katuwar restaurant, 
Shidai Fahad ko uffan baice dasuba, shidai burinsa kawai yaga abar sonsa wato rumaisa,

Nan aka ordo musu abinci kala2 suka fara ci... (ganin zasu batamin lokaci gurin kallon cin abincinsy yasa, nabar gurin, nace idan sun gama cin abinci nasu na 'yan gayu, ma hadu a gidan su rumaisa, nan na fece nakarasa tashar mota)

*****       ******    ******
*TASHAR MOTA* _A Abuja_

A tasha mai  motar ya jibgesu, bayan sun fito suka tare mai napep suka shiga, yakaisu har unguwar, suka biyasa sannan suka shiga cikin gidan,

Abban rumaisa yana zaune a falo, lamarin duniya duk ya ishesa, duk ya kara ramewa, 

 Sallama yajiyo a waje ana kokarin shigowa falon, ya kura kofar falon edo yana jiran yaga wazai shigo,

Ummansa yagani saida gabansa yafadi, ya mike tsaye cike da mamaki, a zuci yace "kardai ace tasamu labarin cewa rumaisa tabata"

Ganin yanayin fuskarta a murtuke, yaji tsoro sosai domin yana matukar tsoron ummansa,

Abinda yakara firgitashi saida yaja da baya jiyake kamar mafarki yake, ganin rumaisa da yayi a bayan hajiyarsa,

Hannusa yadaga yana nuna rumaisa cike da mamaki bakinsa ke furta "RUMAISA!!"

Hajja luba tayi saurin karbe maganar, cike da masifa take fadan "eh rumaisa ce wadda kukayi yunkurin kashewa, to ta Allah bata kuba, ina muguwar matar nan taka take, toga rumaisa tadawo gidan ubanta saiki mutu, kina inane " hajja luba  tashiga kiran sunan umma,

Abban rumaisa wadda tuni murmushi ya mamaye fuskarsa, cike da farin ciki da jindadi yaga 'yarsa,

Hajja luba taji shiru, bataji motsin ummaba , ta dube abba tace "ina matarka take"

Abba ya sauke hannunsa ya dube hajja luba yace "barka da zuwa Hajiya, ya hanya " yafada cike dajin kunya,

Hajja luba ta dalla masa harara "ni ba wannan na tambayeka ina matarka domin ni danta nazo garin nan"

Abba yace "hajiya kiraso kuzauna mana sai muyi magana, ya dube rumaisa yana murmushi yace "rumaisa ta zoki zauna kinji"

 Rumaisa ta tsuke fuska, hajja luba taja hannunta suka karasa bakin kujara suka zauna

Bayan sun zauna abba yayi dariya yace "bari nakawo muku ruwa" da sauri ya mike yaje yadauko ruwa a firij yakawo musu, rumaisa sai kallon abbanta take taga duk ya rame, saida yabata tausayi, kallon gidan take duk taga ya canza mata komai na gidan a hisgitse,

 Abban rumaisa shima ita yake kallo duk ta koma masa bakuwa,

Hajja luba ta katse musu tunina da cewa " wai ba magana nake maka ba nace ina matarka, ko kafita yawon iskancin nata  ne"

Yanayin fuskar abba ya chanza zuwa bacin rai sannan yace "tana police station" saida  rumaisa ta furzar da ruwan dake bakinta saboda razana akan maganar da abbanta yafada,

Cike da mamaki hajja luba tace "meta keyi a police station"

Abba yace "tun lokacin da rumaisa ta bata nasa aka kamata domin ni nayi zaton cewa akwai hannunta acikin wannan matsalar"

Rumaisa tuni hawaye suka sauko kan kumatunta cike take da tausayin umma duk da ba itace ta haifetaba amma tanajin sonta har cikin zuciyarta, rumaisa ta marairaice fuska ta dube abba tace "Dan Allah abba kaje kazo da ita, wlh babu hannunta a ciki"  sai a lokacin tayi magana,

Abba yadube yaga yata hawaye tausayi ta bashi, yace "toh shikenan"  da sauri ya mike, yanufi hanyar fita,

Hajja luba tace "ina kuma zakaje"
Abba yajuyo yace " zanje station din ne nazo da ita tunda rumaisa ta bukaci ganinta"
Bai jira hajja luba tasake maganaba yafita yabar gidan,

*Bayan minti 30*

Falo ya cika umma da Abba Hajja luba da kuma rumaisa,   duk suna zazzaune, sunyu jugum2, umma dukta galabaita tayi baki, ta wahala sosai,

Abba yana zaune yana kallon hajja luba,

Umma tatashi tazo gurin rumaisa kwalla duk sun cika mata edo tace " Dan Allahki rumaisa kiyafemin, Alhakinkine  ke fita akaina, nasan dacewa na  cuceki, na hanaki jindadi a gidan nan, amma wlh yanzu nayi nadama sosai, dan Allah kiyafemin"
Kuka rumaisa takeyi  ta d'ago umma ta rungumeta tana fadan " nayafe miki ummata, wlh nayafe mike har cikin zuciyata"

Umma tana kuka tace " nagode rumaisa"  suka kara kakkame juna, suna kuka,

Duk haushi umma take bawa hajja luba,
Hajja luba  taja tsaki  sannan tayi gyaran murya, domin ita har yanzu bata sauka daga dokin zuciyar data hauba,  tace " ni ba ruwan da kukanki, kukan munafinci, mtsw,
Hajja luba ta juya gurin abban rumaisa tace " kai kuma bara kaji, maganar auren dole  dazakayiwa rumaisa na janye wannan maganar, kabawa rumaisa wadda takeso, idan kuwa ba haka wlh nida kaine"

Cike da mamaki abban rumaisa yake kallon Hajja luba, wai kodai batasan wadda rumaisa takeso bane, mahaukacine fa, taya zai aurar da diyarsa ga mahaukaci,
Cikin sanyin jiki abba yace "hajiya waddafa takeso dinnan mahau..." bai karasa maganarba sukaji an turo kofar falon aka shigo tare dayin sallama,

Fahad ne shida da iyayensa...
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *