Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, July 7, 2018

ABINDA AKE GUDU hausa novels world

adsense here
ABINDA AKE GUDU hausa novels world
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup an
d cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239


ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1

Batul Mamman💖

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM





Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi. Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin nishadi.

Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado cike da damuwa ta soma magana.
" don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai san tayi ta kashedi akan African time".

Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace  "kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito".

"Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana dube dube.

Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin tamkar babu irinsa a duniya.

Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk kirjinki ya fito ta sama".

Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa da kawayenta na dakin suka maido da kallonsu gareta. Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba ce....

******
Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna sai kamshi ke tashi.

Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta suka fito suna taku daidai.

Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da na waya suka fara aikinsu. Haka suka rinka tafiya har suka karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan ma ya kayatar da mutane.

Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren 'ya'yansa ba bare yaga jikokin da suka fara tarawa.

Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya. Nasan sarai Abubakar zaki turawa".

Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto". Dariya duk suka yi sannan aka cigaba da biki.

******
Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta gaji sosai. Dakinta suka nufa ita da kawayenta suka yi  tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci, kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar hotunan kamu.

A lokacin yana tare da abokinsa Qasim. Shi dai Qasim gani yayi Abubukar ya dan matsa ya fara waya. Murmushi yayi don yasan da wa ake wayar. Hira suke yi sosai yana fada mata yadda tayi kyau da kuma rashin jindadinsa da aka hana shi zuwa wurin kamun.

Karshen gado ta koma ta rungume waya suna ta hira. Tun ana cewa ta sauko ga abinci har suka gaji suka dena. Ba su suka gama wayar ba sai da ya fara jin kiran sallar isha daga masallacin gidansu wanda suma su Asma'u shi din suke ji. Sallama suka yi tare da alkawarin zai kirata anjima.

Tana saukowa daga kan gadon ta dafe cikinta "yunwa nake ji kamar na kwana ban ci abinci ba"

Walida ta dan harareta "abincin ai ba jiranki zaiyi Juliet. Ni nayi tsammanin a irin soyayyarki da Romeo din naki baku san yunwa ko kishiruwa ba idan kuna tare".

"Nasan ba wani abu ke damunki ba sai tafiyar da rabin ranki Babangida yayi gashi ba kya samunsa a waya sosai" Asmau ta fada cikin tsokana ai kuwa Walida ta jefeta da pillow tana fada. Babangida yaron gidansu Walida ne irin almajiran nan marasa kunya gashi ya kware wurin kaiwa matar babansu gulmar duk abinda take yi shiyasa ta tsane shi. Har kusan daya na dare 'yan matan suka kai suna hira sannan bacci ya dauke su. Wasu akan gado wasu a katifun da aka shinfida a kasa.

Cikin bacci Asma'u taji wayarta na kara ta dauka cikin magagi. Tana ganin sunan mai kiran ta wartsake.

Cikin taushin murya yace " Asmy na tasheki daga bacci ko?"

Sai a lokacin ta kula karfe hudu da kwata na dare sunfi wata daya yana tashinta a irin wannan lokacin dama.

Ta dan shafa idanu "babu komai Yayana yau mun so mu makara ma".

"To a tashi ayi a nemi kusanci da Allah. I love you Asmy."

Murmushin da yake so a gareta tayi sannan tace "me too Yayana".

Bayan ta ajiye wayar tashi tayi ta fita ta tafi bandaki ta dauro alwala. Nafila tazo ta fara yi sannan ta dukufa istigfari kamar yadda suka sabarwa kansu ita da Abubakar har aka kira assalatu. Sake kira yayi ya tabbatar idonta biyu sannan ya tafi masallaci ita kuma ta tashi 'yan matan dakin ta tayar da tata sallar.

*****
Yau ta kama alhamis babu wani taro da za'ayi a gidan sai karfe bakwai da rabi da za'ayi dinner da daddare.

Qasim yazo har gida ya sami Abubakar tare da takardar da aka bashi ta canjin wurin aiki da karin matsayi. Abin takaici ana bukatar lallai yaje ya gabatar da kansa a sabon ofishin da aka tura shi a Zamfara kafin litinin mai zuwa. Abubakar ya taya shi murna sai dai sunyi bakincikin bazai sami dinner da daurin auren abokin nasa ba. Abubakar duk ya shiga damuwa Qasim ya rinka kwantar masa da hankali.

Abubakar yace "yanzu tunda ka zama ACP Qasim to sai ka nemo mana mata musha biki."

Dariya Qasim yayi "wace mata zan nemo bayan kasan albashin dansanda har yanzu bai taka kara ya karya ba."

"A dai rinka godewa Allah" Abubakar ya fada yana saka takalmi. Har bakin mota ya raka Qasim. Dukkaninsu basu ji dadin zuwan  canjin aikin a wannan lokacin ba.
******

Kwalliyar Asma'u ta yau har tafi ta jiya. Kawaye da 'yan uwanta kowa yayi irin nasa adon. Anti Shema'u, 'yarta Mimi da Aina'u  kayansu iri daya. Mazan gidan su biyu suma shadda suka saka iri daya.

Suna gama shiryawa motar ango tazo daukar amarya. Shima kayansa ya dace da nata. Tun a gida ake daukarsu hotuna haka a wurin dinner din. Abin ya kayatar saboda komai anyi shi cikin nutsuwa irin na 'yan boko. Duk motsin Asma'u idon Abubakar yana kanta suna hada ido sai suyi murmushi. Soyayya ce da ta samo asali tun farkon tarewarsu Asma'u a unguwar su Abubakar shekaru tara da suka wuce.

Sai wurin shadaya da rabi aka tashi daga taro kowa ya tafi gida. Wani abokin Abubakar ke tuka motar suka ajiyeta a gida sannan suka wuce.

******
Washegari Juma'a gidan commissioner kamar yadda duk 'yan unguwa suka sakawa gidansu Abubakar sun tashi a makare saboda gajiyar da suka kwaso a wurin dinner da kuma sanyin da aka tashi dashi.

Mahaifinsu Alh Adamu Matawalle tsohon dan sanda ne har commissioner ya taba yi. Da taimakonsa Qasim ya sami aiki ma. Matarsa daya Yalwa wadda suke kira Mama. Su shida ta haifa. Babban danta sunansa Abdulhalim yana da mata daya da 'ya'ya biyu sai mai binsa Nasiba itama tana gidan nata mijin. Abubakar ne na uku amma kannensa mata biyu Sadiya da Suwaiba duk sunyi aure. Su biyu suka rage shi da autansu Umar.

A gaggauce suka tashi domin baifi awa daya da rabi ya rage musu ba lokacin daurin auren ya yi. Mata suka tashi aka shiga kitchen saboda abokan Baba kamar yadda suke kiran mahaifinsu a gidan zasu ci abinci idan an taso daga wurin daurin auren. Ga samari 'yan uwa da suka kwana a gidan su ma shiyasa aka yi ta layin shiga wanka a bandakuna biyun dake bangaren maza. Da gangan suka ki barin Abubakar ya fara shiga a cewarsu shi ango dole a jira shi.

Baifi minti talatin ya rage ba Umar ya fito daga bandaki kumfar jikinsa bata gama fita ba Abubakar ya shiga ya rufe kofar da mukulli.

Sauran samarin babu wanda ya tsaya cin abincu suka fita dama wurin daurin auren babu nisa daga gidan ko a kafa zasu iya karasawa kofar gidan kakan Asma'u tunda bayan layi ne.

Duk an gama taruwa iyaye suna daga cikin katon soron gidan sauran mutane suna daga waje duk an cike layin. Alh Adamu ya kira Abdulhalim yana tambayarsa ina Abubakar. Abdulhalim yace "inajin yana waje kasan halinsa da kunya karshenta ya ki shigowa."

A waje kuma abokansa ke tambayar juna ko ya shige ciki ne domin basu ganshi ba.

Babu wanda ya saka damuwa a ransa har aka gama daurin auren kowa yana tunanin yana wani wurin.

A can gidansu kuma Haj Yalwa ce ta kira wata yarinya cikin 'yan uwansu tace ta duba mata kowane bandaki na gidan ta dauko bota a cika su da ruwa a ajiye a waje saboda abokan Baba. Idan sunci abinci zasu yi shirin sallar Juma'a.

Yarinyar tayi ta zagaye tana dauko buta. Kofar bandakin dake cikin dakin Umar ce ta kasa budewa sai ta koma ciki ta fadawa Nasiba. Tare suka dawo suka yi ta kokarin budewa suka kasa ga ruwa kuma ya fara fitowa ta karkashin kofar bandakin. Nasiba ta saka kunne jikin kofar taji alamun famfo yana zubar da ruwa. Mama suka sanarwa tace a samo wani ya balle kofar saboda kada ruwan bangaren ya kare tunda tanki ne. Abu ya hada da mata suka kasa budewa ga ruwan yana yawa.

Dole suka hakura har Allah Yasa aka fara dawowa daga wurin daurin auren. Lokacin duk sun tsince kayan dake kasan dakin saboda ruwa. Umar na shigowa Mama ta hau shi da fada shi bai ma san laifin da yayi ba sai da tace yaje ya bude kofar bandakin shi. Yayi mamakin jin kofar a rufe ya saka iya karfinsa ya soma dukanta. Babu kowa a dakin sai shi kadai don Mama tace  babu mai taya shi gyarawa. A bugu na hudu kofar ta bude yayi tozali da abinda yayi matukar razana shi.

Abubakar ne kwance cikin ruwan da ya hade da jini daga kasan kansa ga sabulu can a gefen kafarsa ta hagu alamun zamewa yayi.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 2

Batul Mamman💖



Lokaci guda Umar ya gigice jikinsa ya hau bari.  Da sauri ya shiga bandakin ya zauna cikin ruwan kusa da Abubakar sannan ya daga kansa ya dora a kan cinyarsa. Da kyar ya iya cewa "Yaya".
Babu wata alamar motsi a tare da Abubakar. Umar ya shiga jijjiga shi yana kiran sunansa. Duk da haka Abubakar bai motsa ba. Iyakar tsorata Umar yayi don ji yake kamar zuciyarsa zata buga. Wasu zafafan hawaye ya soma yi a hankali yace "Yaya Abubakar ka tashi an daura auren."

Nan ma dai shiru yaji. Tunaninsa gabadaya ya kulle ya rasa me zaiyi ya taimakawa dan uwansa. Da sauri ya tashi ya fara kokarin daga shi ya fitar dashi daga cikin ruwan, amma yayi masa nauyi domin duk jikinsa a sake yake. Ya sake gwadawa yaji tabbas bazai iya ba sai ya tashi ya fita tare da rufe dakin da mukulli.

Duk wanda ya ganshi da kaya a jike ga alamun jini a gaban sabuwar shaddarsa da tasha dinki sai ya tambaye shi ko lafiya. Babu wanda ya bawa amsa ya wuce dakin Mama.

A tsaye ya ganta a gaban mudubi tana saka sarka. Kafin yayi magana ta juyo da sauri saboda ganinshi da tayi ta mudubin. Gaban rigarsa ta nuna tare da zuwa gabansa ta tsaya "Umar me ya faru? Ciwo kaji garin gyaran bandakin? "
Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeta yana kuka mai tsuma zuciya.
*****

Duk akwatunan kayan Asmau an gama hadasu a wuri guda. Daya daga ciki ta bude ta dauko wata atampa zata saka Aina'u ta shigo dakin da gudu sai haki take yi.

"An daura auren. Daga yau dakin nan ya zama nawa ni kadai" ta fada iyakar karfinta tana murna. Tana gama fadar abinda ya kawota ta sake ficewa da gudu.

Su Walida suka soma guda suna yiwa Asmau tsiya. Harda masu yi mata wakar ta zama dauko riga....ta zama dauko hula....ta zama dauko wando....

Duk baki irin nata jikinta sai da yayi sanyi ta kasa biye musu kamar yadda ta saba. Ji tayi zuciyarta tana bugawa da karfi har abin ya bata tsoro kawai sai ta soma kuka. Hankalinsu ya fara tashi. Walida ce ta rungumeta maimakon ta bata hakuri itama sai ta fara kukan. Wata 'yar kanin baban su Asmau ce tace "haba Walida maimakon ki bata hakuri sai ki biye mata. Yau ai ranar farinciki ce ba kuka zakiyi ba. Ki tashi kiyi nafila ki godewa Allah da Ya nuna miki wannan rana."

Jiki a sanyaye Asmau ta saka kayanta ta dora hijab ta tayar da sallah.
*****

Gaban Mama ya fadi ta dan ture Umar daga jikinta. Ta soma kokarin daga masa riga ta ga ko ciwo yaji ya zubar da jini da yawa haka.

"Mama jinin Yaya Abubakar ne".

Jin maganar tayi har tsakiyar kanta. Jinin Abubakar kuma? Abubakar din da ta tabbatar yana tare da abokansa yanzu suna shirin zuwa wurin reception din da zasuyi. Cikin rashin fahimta tace "wane irin jini? A ina kaga Abubakar din?"

Umar yace "yana toilet dina ya suma".

Mama bata jira ya sake magana ba ta fita daga dakin da sauri yana binta a baya. Matan dake cikin gidan suna ta tambayar abinda ke faruwa. Ganin basu tsaya basu amsa ba suka bi bayansu.

A kofar dakin Umar suka tsaya ya saka mukulli zai bude kofar Abdulhalim ya shigo yana fadan Abubakar ya bar mutane suna ta cigiyarsa har Baba sai da yayi ta fada. Umar dai bai kula shi ba ya bude kofar Mama ta ture shi ta shiga da gudu. Inda ya barshi a kwance  suka sake samunsa.

Abdulhalim ya karasa gabansa da sauri yana tambayar Umar me ya faru. Da taimakon Umar suka dora shi a kan gado daga shi sai dogon wando a jikinsa. Mama ta fada kanshi tana jijjiga shi tana kuka.

Matan dake kofar dakin suma suka soma kukan. Nan da nan aka kirawo 'yan uwansa mata. Abdulhalim ya kira wani abokinsa likita da yazo wurin daurin auren ya bukaci ya karaso gidansu da gaggawa. Dakin duk ya rude da kuka duk da har yanzu basu san ainihin me ya same shi ba. Sai da Abdulhalim yayi da gaske ya iya sawa suka fita.

Cikin mintuna kadan likitan ya karaso. Yayi mamakin ganin angon kwance jini har ya soma jika zanin gadon. Umar ne yayi masa bayanin yanayin da ya tsince shi a ciki. Abdulhalim yace "bari mu saka shi a mota mu tafi asibiti. Bana so mutane su ganmu. Zanyi kokarin kawo motata baya sai a fita dashi." yana gama magana ya fita.

Kabiru ya duba kan Abubakar inda ya fashe sannan ya taba kirjinsa da tsintsiyar hannunsa. A razane ya dago kai Mama ta kalle shi da jajayen idanu tace "ya cika ko?"

Yadda ta tsare shi da idanu bai isa yayi mata karya ba. Sunkuyawa yayi ya sake bincika shi sosai sannan cikin murya mai rauni yace "Mama sai dai muyi hakuri....".

A take ta zube a jikin Abubakar a sume. Su Suwaiba sai kuka suke yi suka dagata. Kabiru ya fara kokarin taimaka mata. Kuka kowa na dakin yake yi sosai. Tun kafin Abdulhalim ya karaso yaji sautin kukan ya shigo a guje. Umar ya fara hangowa durkushe yana kuka ya shigo ya tarar Kabiru yana danna kirjin Mama. Wani irin numfashi taja sannan ta bude ido da kyar.

Mikewa tayi tana kuka ta koma bakin gadon inda har ansa gefen zanin gadon an rufe Abubakar. "Allah Ya jikanka Abubakar. Na yafe maka duniya da lahira. Allah Ya sa mutuwa hutu ce gareka."
Ana amsawa da amin kuka yana karuwa.

Duk dauriya irin ta Abdulhalim shima kukan yake yi ya kama hannun Kabiru suka fita. Suna fitowa ya fara hango kawunansa da sauran abokansa da na Abubakar. Wurinsa suka taho suna tambayarsa ina ango. Bai iya cewa komai ba sai hawayen da yake zubarwa. Kabiru ne ya iya basu amsa ya sanar dasu halin da ake ciki. Gabadaya farfajiyar gidan ta rude da addu'a. Tashin hankali mara misaltuwa aka tashi dashi. Abubakar ya rasu daidai lokacin daurin aurensa.

Maza sai kai kawo suke yi cikin dan kankanin lokaci labari ya isa kunnem Alh Adamu wanda dama suna hanyar shigowa gidan da abokansa. A gigice ya shigo ya wuce dakin Umar inda su Yalwa suke da sauran 'ya'yansu. Suna ganinsa kuwa su Nasiba suka rungume shi suna kuka. Duk wanda yake gidan sai ya tausaya musu wannan tashin hankali da suke ciki. Shi kanshi Alh Adamun da kyar yayi ta maza da taimakon dattijai abokansa suka sa duka matan suka fita domin a yiwa Abubakar wanka idan sun sauko daga sallar Juma'a sai a kai shi.
*****

Jafar shine wanda yake bin Shema'u ita kuma Asmau take binsa. A gabansa Kabiru yake fadar rasuwar Abubakar. Saboda firgice bai san da yadda kafafunsa suka kawo shi gida ba.

Masu kidan kwarya ya hango suna ta jera kayan kidansu. Zuciyarsa ta sake tsinkewa da ya tuna halin da kanwarsa zata shiga. Dama tun a bakin gate ya goge hawayensa saboda gudun tambaya. Yana shiga falo aka fara tambayarsa ko 'yan daurin auren sun watse ana son kai Asmau wurin kakarta tayi mata nasiha kafin 'yan yini su kara cika gidan. Jafar yace akwai sauran mutane sannan ya nemi jin inda Umma take.

A bayan gida ya ganta suna magana da kanwarta Anti Bintu. Umma na ganinshi tace "baban Yaya har kun dawo? Ka ce zaku reception ko kaya ka dawo canzawa?"

Jafar ya ji kamar ya fasa fada sai dai kuma babu yadda zaiyi. Idanunsa suka kada sukayi jazur yace "Umma Allah Yayiwa Abubakar rasuwa".

Daga ita har Anti Bintu a tare suka ce "Me?"

Jafar yace "yanzu muka dawo daga wurin daurin aure Yaya Abdulhalim yake fada...." maganar tasa makalewa tayi saboda kukan da ya zo masa.

Suma kukan suka fara. Wannan tashin hankali da yawa yake. Fuska sharbe da hawaye tana salati Umma ta shiga ciki ta tafi daki. Anti Bintu ta daure ta leka dakinsu Asmau ta kirata.

Tun da ta taso gabanta ke matsanancin faduwa tana ta karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil.

Kafin ta shiga dakin Umman taji muryoyi suna cewa Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.....a razane ta shiga Shema'u ta taso ta rungumeta. Kokarin ture yayarta tayi bakinta har rawa yake yi tace "waye ya rasu?"

Bazata iya tuna muryar wadda tace "sai dai  hakuri Abubakar ya rigamu gidan gaskiya" ba.

Kamar saukar aradu haka Asmau taji zancen sannan numfashinta ya fara kokarin daukewa. Daga nan bata sake sanin inda take ba sai farkawa tayi a gadon asibiti.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽3

Batul Mamman💖

_Afuwan Qasim Inspector ya zama ba ACP please_

*GA MASU NEMAN BOOK IDAN AN WUCE KU SAI A DUBA www.fikrahwriters.com.*


Kusan minti biyar kenan da ta farfado amma ta kasa bude idonta. Tsoro take ji idan ta bude za'a sake fada mata wannan mummunan labarin da take tunanin taji a mafarki.

Kasakasa take jin muryar su Umma a dakin ana ta tambayar ya jikin nata. Wannan ya tabbatar mata ba mafarki take yi ba. Lallai ta rasa Abubakar har abada. Ji tayi inama daga wannan kwanciyar itama mutuwar ta dauketa. Ya zata yi da rayuwarta ba tare dashi ba? Ita da Abubakar masu rikon sirrin juna ne. Mutuwarsa komai daren dadewa zata fallasa sirrin da suka boye. Sirrin da ya kara musu soyayya da mutunta juna saboda rashin gudun juna da suka yi. Hawaye ne ya zubo ta gefen idonta. Walida ce ta lura da hawayen tace "Umma ta farfado".

Haj Bara'atu ta dawo gefen gadon ta zauna tare da rike hannun Asmau.
"Ki bude idonki Asmau kinji. Ko ruwa ne ki tashi ki sha. Kin dade a kwance gashi har la'asar ta wuce".

Subhanallah! Ta tabbatar ta rasa Abubakar kenan. Garin yaya aka barta a kwance har ta kai yanzu ba'a bari ta sake ganinsa ba? Ko bata tambaya ba tasan tuni Abubakar yana makwancinsa. Sake runtse idonta tayi. Gara ta cigaba da kwanciyar har nata lokacin ya yi.

Umma ta kalleta da tausayawa kwalla ta cika mata ido tace "kiyi hakuri Asmau. Shima ba gaggawa yayi ba. Mu kuma da kike ganinmu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda hakuri da tawakkali ya bari."

Maganganun Umma suka sake saka mutanen dakin kuka. Asmau kuwa taki bude idon. Duhun da take gani ido rufe ya fiye mata akan hasken da babu Abubakar a cikinsa. Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude idonta balle ta tashi zaune.

Suna haka suka ji sallamar Haj Yalwa da Abdulhalim. Ita da Umma suna hada ido sai kuka. Suka rungume juna suna yi ana basu hakuri. Umma tace cikin kuka "Mama Yalwa me yasa kika fito? Allah Ya jikan Abubakar....Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Dakin ya sake rudewa da koke koke. Bayan sun dan nutsu ne Mama ke tambayar ya jikin Asmau.

Umma ta dan tabe baki "tana jinmu tun dazu ta farfado amma taki bude ido.  Mama Yalwa ni dai banso fitowarki yanzu ba. Mutane zasuyi ta cigiyarki a gida. Da zamu samu ta tashi muma duk gidan zamu taho yanzu."

"Zamana a gidan bazai dawo dashi ba Umma. Komai na gani ji nake kamar karya ne Abubakar yana nan."

Tashi Mama tayi ta koma gaban gadon da Asmau take kwance tana hawaye. A hankali Mama ta tayar da ita zaune ta rungumeta a jikinta tana shafa mata baya. Abdulhalim yana tsaye daga bakin kofa zuciyarsa cunkushe da bakinciki.

Cikin nutsuwa Mama ta soma magana "Asmau kuka ba soyayya bane tsakaninki da Abubakar. Kiyi masa addua da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Da iliminki   amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba."

Jin haka Asmau ta bude idonunta da suka kumbura da kyar. Dai dai ta rinka kallon mutane kafin ta sake fashewa da wani kukan mai shiga rai aka shiga tayata. Babu mai bawa wani hakuri sai Abdulhalim. Shima da ya gaji fita kawai yayi daga dakin.

Likita yazo ya sake duba Asmau ya tabbatar musu cewa zasu iya tafiya da ita gida. A haka suka tafi  ko da suka iso gate din gidansu Abubakar da yake shine a farko kafin nasu wani kukan ta sake fashewa dashi. Mutanen da suka zo daurin aure sun koma zaman makoki. Duk a nan suka sauka suka shiga gidan. Gaban Asmau sai faduwa  yake balle da taji ana cewa ga amaryar nan ta shigo. Mutane da dama suka taso ana kallonta. Kowa na fadin albarkacin bakinsa na dangane da tausayawa gareta.

Bayan sun shiga gidan dakin Mama aka wuce da ita. Ko zama batayi ba Umma tace mata taje tayi alwala saboda batayi azahar da la'asar ba. Jiki kamar wadda bata da laka haka ta shiga bandakin jiri na dibarta ta dauro alwala tazo ta biya sallolin dake kanta. Tana sallar tana zubar da hawaye. Bayan ta idar ta dade tana kuka da addu'a.

Sadiya ta hado mata tea mai zafi ta mika mata. Kai ta girgiza alamun bazata ta karba ba.

Kusa da ita Sadiyan ta zauna " ki daure ki sha ko yaya ne sai kici abinci. Kowa da kika gani dauriya kawai yake yi Asmau." Nata hawayen ta share sannan ta dubi Shema'u  tace "Anti Shema'u kisa baki ta sha ko kadan ne".

Taruwa akayi ana lallabata tasha tea din amma taki har Umma da Mama suka dawo daga waje inda suka karbi gaisuwar wasu maza 'yan unguwar. Suma suka saka baki har Asmau ta karbi tea din. Bai fi rabin kofi tasha ba ta fara kwara amai saboda tun jiya rabonta da abinci. Haka ta rinka amai ta baki ta hanci abin tausayi.

Ta galabaita sosai. Bayan ta gama aman Nasiba ta dagata zata shiga da ita bandaki ta gyara jikinta ta fadi kasa a sume. Nan da nan aka taru a kanta ana mata fifita. Aka shafa mata ruwa a fuska tare da sauke mata zip din rigarta don tasha iska amma duk da haka bata tashi ba.

Mama tace aje a kirawo mata Baba a waje. Ita Umma gefe kawai ta koma tana kuka. Gani take yi kamar Asmaun ma ta cika.

Shi da wasu suka shigo suka ga halin da Asmau ke ciki. Jafar aka kira da Abdulhalim suka sakata a mota aka kaita wani asibitin mafi kusa dasu. Su Mama suka biyosu a wata motar kowa bakinsa da addu'a.

Bayan an bata gado wata likita da nurse suka zo suka tsaya a kanta ana ta kokarin ceto rayuwarta. Allurai kala kala kam tasha su. Likitar tace jininta ne ya hau ga kuma rashin kuzari a tare da ita. Gwajin jini ta umarci ayi mata don su gani ko akwai wani ciwon a tare da ita.

Har wani likitan ne yazo suka taru ana ta abu daya sannan suka samu ta farfado. Su Umma sai godiya suke ga Allah. Mama na zaune a kusa da Asmau tana sake bata baki akan tayi hakuri kuma duk da ana mata karin ruwa ta daure taci abinci sai ga nurse din ta shigo.

Shema'u ta tashi da kyar Anti Bintu tace " kema kina bukatar hutu tun dazu baki zauna ba. Kada kafarki ta kumbura". Murmushi Shema'u tayi sannan ta tambayi nurse din tana fata babu wata matsala a tare da Asmau.

Nurse Ngozi ta washe baki cikin hausarta irin da inyamuran da suka zauna a Kano tace "babu wani masala sai abin murna...." ta mayar da kallonta ga Asmau "...congratulations ashe ciki ne yana baka wahala."

Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci har maganar nurse Ngozi ta gama shiga kwakwalwarsu.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽4

Batul Mamman💖




Kallon kallo suka fara yiwa juna. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin Asma'u ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki.

Mama ce tayi karfin halin kallon Ngozi  tace" 'yar jakar uba bakinki ne cikin ai, dama Hausa bata gama zama ba dole kiyi shirme. Bari likitan tazo da kanta muji daga bakinta. Kila ma ciwon ciki kike son cewa kika ce ciki zaki karasa tsorata mu."

Nurse Ngozi tace "Madam ina jin Hausa sosai fa. Yarinyarki is pregnant zata haihu shine abinda nake nufi."

Takardar hannunta Umma ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Shema'u ta karbi takardar suka hada kai ita da Nasiba da Anti Bintu suka karanta. Gabadayansu Asmau suka zubawa ido da tsantsar mamaki a fuskokinsu. Mama dake tsaye a gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar.

Jafar ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan inda Abdulhalim yake tsaye tana masa bayanin magungunan da aka rubutawa Asmau. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Abdulhalim ya tambaye shi ko jikin Asma'un ne. Jafar yace "ai gara ace jikinta ne da abinda mahaukaciyar nurse dinnan ta rubuta. Wai ciki? Asma'u ke da ciki kamar a tatsuniya...." likitar ya kalla "...ki taso muje ki sake gwadata don kada ku karasa gawar da ba taku ba."

A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ta karbi report din daga hannun Nasiba ta karanta. Ita ma abin ya bata mamaki domin kuwa Abdulhalim yayi mata bayanin dalilin suman Asmau. Ta bukaci kowa ya fita suka fice babu musu. Sirinji ta dauko daga aljihun rigar asibitinta ta sake daukar jinin Asmau. Bayan ta gama tace "Asmau yaushe ne lokaci na karshe da kika ga al'adarki?"

Tun dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi tace " biyu ga watan da ya wuce na gama".

"Yanzu kuma gashi ana karshen wata na gabansa. Yau kinga ashirin da takwas ga wata." Likitan ta fada tana rubutu a wata takarda. Fuskarta na kan takardar tace " ki fada min gaskiya kin taba tarayya da namiji?"

Kasa bada amsa tayi sai jikinta da ya kara mugun yin sanyi. Fatan mutuwa kawai take yi akan bala'in da yake tunkaro ta. Da taki magana likitan ta fita su Umma suka dawo har yanzu babu mai cewa uffan kowa zuciyarsa na sake-sake. A haka likitar ta dawo kana ganin fuskarta kasan labarin da ta kawo bashi da dadi. Ita kanta ta tausayawa mutanen ta dan sunkuyar da kai "a bisa binciken da nayi da kuma amsar da Asmau ta bani ya nuna tana da CIKI na kusan wata biyu."

La haula wala quwwata illa billah....a rana daya duk wani farincikin gidajen biyu ya koma kishiyarsa. Umma tayi kan Asmau wadda dama tasan haka zata faru.

"Asmau me nayi miki zaki yi min muguwar sakayya irin wannan? Uban waye yayi miki ciki? Har kinsan ki kebe da namiji ba tare da aure ba a tsakaninku?" Tana magana tana dukan Asmau ko ta ina. Su Anti Bintu ne suka yi kokarin riketa tana fada tana kuka.

Shema'u ma gefe ta koma tana nata kukan. Wane irin abin kunya ne wannan Asmau ta janyo musu a wannan halin da suke ciki?

Umma na dukanta duk da rashin lafiyar da take ciki amma ta kasa yin kuka. Biyewa son zuciya na 'yan mintuna ya wargaza dukkan wani farinciki da ta taba sani a rayuwarta. Irin ABINDA AKE GUDU kenan. Yau asirinta ya gama tonuwa. Sirrin boye ya fito fili bata da abinyi sai yadda Allah Yayi da ita. Mama ta rike hannun Umma da take shirin sake dukan Asmau "ba da duka zamu tambayeta ba Bara'atu. Kada ki bari bacin rai yasa kiyi aikin dana sani."

Muryar Umma har ta dashe tace "akwai wani dana sani daya wuce haihuwar wannan yarinyar? Fyade aka yi miki ko kwaya kika sha da har zaki yarda da namijin da ba naki ba?"

A hankali Asmau ta sakko daga kan gadon har allurar da ake yi mata karin ruwa ta fita daga hannunta bata sani ba jini ya rinka zuba daga hannun. Ranar wanka ba'a boyon cibi. Sai a lokacin ta soma kuka ta durkusa akan gwiwoyinta a gabansu Umma.
"Tsautayi ne da sharrin shaidan. Don girman Allah ku yafe mana. Wallahi sau daya ne kawai. Idan har ina da ciki na Abubakar ne".

Cikin tsawa Mama tace "kin ma isa ki dora masa. Wallahi nasan karya kike yi saboda kinga kasa ta rufe masa ido shine zakiyi masa irin wannan mummunan kazafi?" Magana take tana haki saboda bacin rai, sai kuma hawaye.
"Yanzu kinyi masa adalci kenan? Ko kwana baiyi a kabarinsa ba kike binsa da mummunar shaida bayan kinsan mala'iku suna tsayawa karbar shaida akan mamaci. Allah Ya isa tsakanina dake. Har yaushe kika ga Abubakar din ma? Mutumin da sau biyu yake zuwa Kano a wata. A can makarantarku dai kika hadu da wanda yayi miki"

Anti Bintu ta kama hannun Asmau ta tayar da ita tsaye cikin jin haushin maganar Mama gashi Umma taki cewa komai "wannan magana bata asibiti bace. Mu bari idan an sallameta sai ayi a gida. Amma kowa yasan bata da wani saurayi bayan Abubakar."

"Babu wata magana da zamuyi a gida. Kai, ku wuce mu tafi." ta fadawa Abdulhalim da Nasiba. Dukkaninsu an rasa mai bakin magana. Tabbas Abubakar ne kadai saurayin Asmau. To amma kowa yayi shaidarsa wurin kyaun hali. Mutum ne mai kawaici da kunya. Ita kanta Asma'un ba don a gabansu aka yi komai ba sai su karyata saboda itama ko 'yan unguwa  zasu shaideta da kyaun hali.

Abdulhalim yaso ya tsaya domin a kare maganar a nan Mama ta daka masa tsawa dole yabi bayanta suka fita tana ta bambami. Bude kofar dakin kenan suka hadu da mata sun kai shabiyar daga gidan rasuwar suke sun taho jin halin da Asmau take ciki. Kana ganinsu kasan duk abinda ake yi a cikin dakin sun gama ji. Mama ko kallo basu isheta ba tayi gaba su Nasiba na bin bayanta. Matan dai tunda har an gansu dakin suka shiga suna tambayar ya mai jiki. Anti Bintu tace da sauki suka tashi ko minti daya cikakke basu yi ba suka fice ana ta mayar da zance.

Bayan fitarsu Anti Bintu tace "Yaya Bara baki ce komai ba kina jin abinda Maman Abubakar take fada."

"Me zance Bintu? Kin taba ganin cikin shege yayi uba kai tsaye a kasar musulmi? Duk abinda Mama Yalwa ta fada tayi min daidai. Nima da namijin ne nawa bazan yarda a kakaba masa cikin shege ba." Hada ido suka yi da Asmau Umma ta sakar mata wani mugun kallo. Abinda yafi wannan ma tasan zata gani tunda haka ta faru. Kusa da Umman ta dawo ta sake durkusawa a kasa ga wani irin jiri da take ji, kirjinta kuma kamar ana hura wuta.

"Umma ki yafe min. Wallahi sharrin shaidan ne kuma muna ta istigifari kullum. Wallahi bazan kara ba wannan ma kaddara ce. Umma...."
Ture ta Umma tayi ta dubi inda Shema'u da Jafar suke tsaye suna hawaye "Jafar fita ka samar mana abin hawa mu koma gida."

"Asma'un fa?" Anti Bintu ta tambaya. Tamkar da dutse tayi maganar haka Umma ta shareta. Bayan Jafar ya dawo Umma ta rike  hannun Shema'u saboda kafarta data rike suka yi hanyar fita. Asmau na ganin haka ta tashi tabi bayansu Anti Bintu na kiranta bata tsaya ba. Haka suka fice daga asibitin ga dare suka shiga tasi din da Jafar ya tsayar. Har suka isa gida babu mai magana a cikinsu.

Abin mamaki nasu gidan a cike suka same shi bayan tunda aka yi rasuwar aka koma gidansu Abubakar. Bacin ran Umma ya sake karuwa don tasan labari ya riga  ya iske duka umguwar. Sai cewa akeyi ya jikin Asmau. Aka rasa me amsa musu tunda sun san ainihin abinda ya kawo su.

A cikin falo Umma zata wuce dakinta taji ance "Ke Bara'atu dakata." Ta gane muryar mai maganar ta san ba karamin rashin mutumci yazo yi mata ba. Alh Rabe ne kanin marigayi. Kin tsayawa tayi sai da taji muryar Hajjo mahaifiyar maigidanta sannan ta juyo. Kuka ne ya kwace mata yadda taga duk 'yan uwan mijinta a wurin mazansu da matansu ga kuma mahaifiyarsu. Allah Yasa itama akwai nata 'yan uwan wadanda suka zo biki daga Wushishi ta jihar Niger. Dangin mijinta basu taba kaunarta ba gashi Asmau ta sake shafa mata kashin kaza.

Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse. Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u suka shige ciki.

Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh Rabe ya zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki."

Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu ta cuce ta.

Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin wai tana ciwon wuya.

Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar 'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye uban ba?"

A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba."

Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali."

Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta. Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye.

Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata gujeta ba a wannan yanayin.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽5

Batul Mamman💖




Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba? Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta shafi cikin zuciyarta na kuna.

"Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani.

Gari na wayewa ta rinka jin muryarsu Umma a kitchen ana dafa abincin da ta fuskanci na sadaka ne da za'a kai gidan Kwamishina. Tana son fita amma tana tsoron abinda zai biyo baya. Duk wannan tashin hankalin wata muguwar yunwa take ji sai dai ko zata mutu bazata  fita neman abinci ba.

Sai wurin karfe goma taji gidan ya danyi shiru. Tana nan zaune Anti Bintu ta shigo dakin. Itama dai ba sakin fuska tayi ba, ta shigo dauke da plate din abinci da ledar pure water. A gaban Asmau ta ajiye ta juya ko gaisuwar da take mata bata amsa ba.

Sai da ta fita ta fashe da kuka. Rana daya Asma'u ta zabge idanu sunyi ciki kamar ta shekara a kwance. Tana jin tausayinta sai dai dole a nuna mata kuskurenta. Abincin da ta kai mata ma babu wanda yasan ta kai. Kuka tayi sosai sannan tabi bayansu Umma da suka riga suka tafi gidan rasuwar.

Su Umma zasu shiga gidan taji Mama Yalwa tana cewa alajirin da ya kawo abincin ya mayar musu da abincinsu bata so. Dama tasan tun faruwar al'amarin jiya dole Mama ta canja mata. Sai dai mutuwa ta kori komai shiyasa ta daure tazo. Sallama tayi suka shiga sai tayi kamar bata ji abinda Mama ke fada ba. Itama kunyar ganin Umman tayi sai ta bar gaban kulolin abincin. Haka suka gaisa kowa fuskarsa a cunkushe su Umma suka sami wuri suka zauna. Babu mai cewa komai dama gidan rasuwa ne. Mutane  'yan kallo suka taru suka zuba musu ido.

Haka ce ta kasance kullum Umma zatayi abincin sadaka kuma su je gidan su zauna sai anyi la'asar su koma gida. Tsakaninsu da Asmau kuwa ko kallonta batayi duk da tana fitowa ta gaisheta. A rana ta shida ne da daddare wata dattijuwa cikin 'yan uwan Umma tace ya kamata su zauna suyi magana akan lamarin Asmau.

Umma tace "kayya dai Gwaggo, me ya rage mana kuma banda zubewar mutumci."

Gwaggo tayi dan murmushi "Bara'atu nayi tunanin ke mace ce mai hangen nesa da tawakkali. Me kike tsammani ga yarinyar da take cikin yanayi na Asmau ace kowa ya juya mata baya? Idan abin ya isheta dole tayi tunanin nemawa kanta mafita koda kuwa mafitar halaka ce fiye da halin da take ciki yanzu. A 'yan kwanakin nan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin damuwa kuma muna fatan ta yi nadama. Kamata yayi a sake tambayarta lallai ta fadi gaskiya game da cikin sai a san matakin dauka."

Kowa a dakin yayi na'am da shawarar. Shema'u dama mijinta yayi mata fada akan rashin kula Asmau da suke yi ba shine mafita ba. Umma tace aje a kirawo Asma'un.

Gabanta na faduwa ta shiga dakin kowa ya zuba mata ido. A can gefe ta zauna idonta a kasa.

Anti Bintu tace " Asmau ki dubi girman Allah da halin da kike ciki ki fada mana gaskiya game da cikin jikinki."

Kai a sunkuye ta sake nanata musu cewa na Abubakar ne. Ran Umma a bace tace ta tashi ta fita. Ji take inama Asmau tace fin karfi aka yi mata. Da ta tausaya mata amma da jin bayaninta kasan abin ba haka bane.

Shawara aka yanke jibi bayan anyi kwana bakwai da rasuwar suje su sanar da iyayen Abubakar. Haka kuwa akayi. Da yawan 'yan bikin sun koma Wushishi sai kadan suka rage saboda abinda ya faru. Babu wanda ya sake zuwa daga gidan Hajjo dama basu sa a ka ba.

Umma da Anti Bintu suka je sai Gwaggonsu da Asmau. Mama na ganinsu ta hade rai Umma ta daure ta bukaci ganinsu ita da Alh Adamu.

Harda Abdulhalim da Nasiba suka zauna a falon. Gwaggo ta gabatar musu da dalilin zuwansu.

Alh Adamu yayi gyaran murya ya soma magana "duk wannan bayanin naji shi tun a ranar da Abubakar ya rasu. Ina sane nayi shiru har sai an share makoki. Bazan boye miki ba Haj Bara'atu wannan labari yayi matukar muni garemu baki daya. Sai dai kuma tsakani da Allah wanda ake abin a kansa yanzu baya raye. Maganar Asmau kadai bazata sa mu karbi cikin jikinta a matsayin nasa ba. Yau da yana nan ne sai ya karba ko ya kare kansa."

Tunda ya fara magana Umma ta soma zubar da hawaye..
" Alhaji duk mun shaida Asmau babu wanda take sauraro sai Abubakar. Idan kuka gujemu a wannan lokacin bansan inda zanyi ba. Dangin babansu dama ba kaunar mu suke yi ba, kune dai a garin nan kuka tsaya mana tamkar 'yan uwa....."

Mama ta katseta  "maganar 'yan uwantaka da cikin shege fa bata taso ba. Kamar yadda Baba ya fada da Abubakar yana raye sai muji ta bakinsa. Amma babu yadda za'ayi mu karbi cikin nan kawai don Asmau tace nasa ne."

"To a bari ta haihu mana sai a gwada a tabbatar da zancenta." Abdulhalim ya fada yana kallon Asmau. Shi tausayinta yake ji.

Mama tace " zanci mutuncinka wallahi. Idan an  bari ta haihu ya dace da dan uwanka zaka karba ka rike ne? Shashasha tashi ka fita."

Baba yace "ina zaunen kike irin wannan abin Yalwa?..." ya juya ga su Umma
"kiyi hakuri Haj Bara'atu amma babu yadda zamuyi saboda babu kwakkwarar shaida. Idan har kina bukatar taimako kinsan ni mai taimaka miki ne kodayaushe." Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki Mama tabi bayansa. Nasiba ma ta tashi babu wata magana da suka ji mai dadi.

Umma da Asmau sun sha kuka. Suka tashi suka tafi gida jiki babu kwari. Asmau tana tausayin halin da ta jefa mahaifiyarta.  Suna zuwa gida hawan jinin Umma ya tashi aka kaita asibiti. Kuka dai yaki karewa a gidan.  Kuma aka ki tafiya da Asma'un asibitin. Sai bayan isha suka dawo Yasar yazo dakinsu Asmau ya kirata fuskarsa babu walwala. Tana tashi yayi mata wani kallon banza " idan kika kashe mana Umma wallahi sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. "

A razane ta kalli yaron da ta bawa shekara hudu wanda tsakaninta dashi kullum girmamawa ce. Indai Yasar zaiyi mata haka kowa ma dole ya tsaneta. A sanyaye tabi bayansa.

Yanayin da taga Umma ya bata tausayi sosai tace "Umma yaya jikin?"

Maimakon ta amsa sai tace "munyi magana da wata ma'aikaciyar asibiti tace gobe mu kaiki karfe goma na safe a cire cikin".

A tsorace Asmau ta mike tsaye tana kuka "Umma kada zunubin yayi min yawa. Ga laifin ciki ga na kisa. Don Allah ki janye..."

Saukar mari taji mai zafi a kumatunta daga Jafar, marin bai gama shigarta ba yace
"banza ana son taimakonki zakiyi mana shirme. Waye zai sake kallonki idan aka bari kika haihu? Dubi yadda kika tarwatsa mana gida Asmau. Ki bari a cire indai ba kuma neman karasa zubar mana da kima kike son yi ba."

Shema'u ta taso ta rike kafadar Asmau
"cire cikin nan shi kadai ne maslaha garemu baki daya. Waye zai dauki dawainiyarki data abinda zaki haifa? Haba Asmau, ki bari muji da bakinciki daya mana."

"Ku kyaleta ta nuna min iyakata. Asmau da kinsan irin radadin da nake ji a zuciyata da baki soma bude baki ba ma. Wallahi nayi nadamar haihuwarki, ina ma barinki nayi tun kafin ki zama mutum da dai naga irin wannan bakar ranar a dalilinki." Umma ta fada kuka mai sauti.

Hankalin Asmau ya sake tashi sosai da jin abinda Umma dake matukar kaunar 'ya'yanta take fada yanzu. Durkusawa tayi a gabanta tana ta kuka da rokon ta yafe mata. Anti Bintu mai jin tausayinta tace ta fita ta basu wuri. Tana bakin kofar taji Jafar yana cewa ko ta karfin tsiya sai sun kaita asibitin ko a kira likitan har gida a cire. Umma dai bata sake magana ba amma sauran sun amince. Har Gwaggo na cewa akwai wasu saiwoyi da basu fada a asibitin ba sai tasa a kawo daga Wushishi a bata tasha cikin zai zube.

Kasa tsayuwa tayi a bakin kofar ta koma daki. Ita da Abubakar sunyi kuskure babba amma tabbas zubar da cikin nan karin laifi ne. A yadda ta janyowa gidansu bacin suna a duniya bazata so ta zama silar karin zunubi a garesu ba a lahira. Da wannan tunanin ta janyo akwati daya cikin na lefenta ta hada 'yan kayayakinta ta zuba a ciki. Dan kudin da ta samu na biki  da dan sauran kudinta ta saka a jakar hannu mai girma sannan ta ciro wasu sarka ,dankunne da awarwaron daga wata drawer duk ta saka a ciki tare da wasu kayan kala uku. Ko kadan bata runtsa ba a daren. Asubar fari Jafar da Yassar suka bude gate suka tafi masallaci. Suna fita Asmau ta lallaba ta fice daga gidan tayi hanyar titi.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽6

Batul Mamman💖




Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci. Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma titi ta tare dan sahu.

Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi magana
"Hajiya ina zuwa?"

"Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume jakarta da akwati.

"Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda zaki je"

Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya
" kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?"

Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace "kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai"

Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe fuskarta da hijabinta.

Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin labarin komai, idan taje wurinsu ba ta tsira ba. Tana cikin wannan tunanin taji ana cewa,

"Azare mutum daya
Azare mutum daya"

Ko dogon tunani batayi ba ta nufi motar da sauri. 'Yan kamasho har sun fara baibayeta ana tambayarta ina zata je. Da shigarta motar dreban yazo suka gama surutansu da 'yan uwansu drebobi ya tada mota suka harbi titi.
*****

Har karfe tara babu motsin Asmau. Anti Bintu da Jafar ne zasu kaita asibitin duk sun shirya. Umma tace aje a tashe ta idan batayi wanka ba su tafi a haka ta yi idan sun dawo.

Aina'u aka tura taje ta dawo tace bata ganta ba. Shema'u tace kila tana bandaki kije kice mata tayi sauri ita ake jira.

Da gudu Aina'u ta dawo tace "Anti na duba bata daki kuma bandakin a bude yake".

Umma na jin haka tace a tashi a dubota karshenta buya tayi saboda kada aje asibitin. Da farko Yassar da Aina'u kadai ne suka duba dakunan  da bayan gidan suka dawo basu ganta ba. Hakan ya soma tsorata Umma kowa ya tashi a rude suka shiga nemanta. Ganin babu alamun za'a sameta a gida Shema'u ta kira wayarta. Tayi mamaki jin muryar Walida. Bayan sun gaisa Walida tace wayar na hannunta. Tun ranar da abin ya faru zance ya fara bazuwa mahaifinta har gidan yazo ya dauketa da kansa lokacin da aka sake mayar da Asma'u asibiti kuma ya haramta mata sake zuwa gidan.

Shema'u tayi kasake har Walida ta gama bayani sannan tace zata turo Yassar ya karbi wayar. Tana juyowa Umma ta kalleta a tsorace
"Kada kice min an sace wayar ne".

"A'a Umma tana wurin Walida."

"To ina Asmau ta shiga, ni Bara'atu daga wannan sai wannan".

Da gudu Jafar ya dawo falon da takarda a hannunsa wadda ya gani a tsakiyar gadon dakin su Asmau. Jiki babu kwari ya mikawa Umma ta karba hannu na rawa.

_Umma ina mai rokon gafararki a lokacin da kike karanta wannan takardar nayi nisa da gida. Nayi nadama da bakincikin halin da na saka ku na kuma jefa kaina. Sai dai na dauki komai a matsayin kaddara. Na tafi ne saboda bana son ku daukarwa kanku zunubin kashe rai. Zan haifi abinda ke cikina da izinin Allah zan kula dashi batare da na fada mummunar rayuwa ba. Ki yafe min kuma ki cigaba da yimin addu'a. Allah Ya hadamu cikin aminci. Sannan ina mai kar tabbatar muku cikin nan na Abubakar ne. Ku yafe mana._
                _Asmau_

Kuka mai sauti Umma ta saka wanda yasa Shema'u saurin karbar takardar ta karanta. A take itama ta fashe da kukan. Umma sai sumbatu take saboda tsabar tashin hankali.

"Asma'u ki dawo wallahi babu mai cire miki cikin. Ki dawo na yafe miki. Ina zaki je ke kadai a wannan duniyar da amana tayi mana karanci?"

Duk wanda yake wurin sai ya tausayawa Umma. Dama da mayafi a jikinta tace Jafar ya dauko mukullin motarta yazo su fita neman Asma'u. Nan da nan kowa ya fita suka fara karade unguwar. Daga nan sune gidajen kawayenta da tashoshin mota tare da hoton Asmau suna tambayar ko an ganta.

*****
Karfe goma na safe tayiwa Qasim a kofar shagon mai gyaran waya. Mai shagon a wurin ya sameshi a ransa yace dan anace ya iso. Allah Ya taimake shi ya gama gyaran shiyasa da fara'arsa yace "ranka ya dade ai yanzu nake shirin kiranka idan na bude shagon."

"Baka da abin da zaka fada min. Gyaran waya sati guda kuma na biyaka. Kawai sai ka zauna kana ja min rai."

Gefe ya matsa mai shagon ya bude. A cikin wata drawer ya dauko wayar Qasim wadda screen dinta ya fashe tun ranar alhamis da ya iso garin Zamfara. Duba wayar yayi ya tabbatar tayi sannan yayi sallama da mutumin ya fita.

Bakin titi ya koma inda ya ajiye motarsa. Yana shiga ya kira mahaifiyarsa bayan sun gaisa ya sanar da ita wayar ta gyaru zata rinka samunsa. Dama ta wani yake ara a ofishinsu ya saka sim dinsa ya kira. Karamar wayarsa tana wurin kanwarsa da ya bawa kafin ya taho.

Bayan yayi sallama da ita ya kira numbar Abubakar. Kullum idan ya ari waya sai ya gwada  amma a kashe yake samunta. Dariya kawai yake yi yace ango ya dau hutun waya kenan. Sai da aka fi kwana uku a haka ya fara damuwa ko sace wayar aka yi. To da yake data aro yake amfani shiyasa bai matsa ba sosai. Yau kuwa yayi sa'a gwaji daya ta shiga. Sai da ta kusa tsinkewa yaji an dauka. Ko magana bai jira anyi ba yace

"Haba mutumina, daga aure sai ka yar dani. Nayi ta kira bana samu gashi tawa wayar ta lalace. Ya madam? Ina fata duk kuna lafiya."

Shiru yayi saboda yaji ba'ayi magana ba.
"Hello, Abubakar ko baka jina ne?" Ya dan cire wayar yana dubawa ko gyaran ne baiyi ba.

Daga daya bangaren yaji ance "Qasim".

Muryar tayi kama da ta Abubakar sai dai ya tabbatar bashi din bane.
Rike wayar yayi yaji an sake kiran sunansa sannan ya amsa
"Ango me ya sameka ne? Naji muryar taka taso ta canja min."

Abdulhalim ya hadiyi yawu sannan ya shafa kansa yana tunanin da yadda zai fadawa Qasim abinda ya faru.
"Qasim nine Abdulhalim, dama Abubakar ya fada min anyi maka transfer a wurin aiki da karin girma".

Sai a lokacin Qasim yayi ajiyar zuciya da ya gane mai maganar
"Wallahi kuwa baban Yaya. Kuma da yake ko wata ba'ayi da bani query ba shiyasa dole na tafi kada nayi laifin da za'a koreni. Daga karin girma ace na fara wasa da aiki" Yana dariya yake maganar sannan ya tambayi ina amininsa ango Abubakar.

Shiru Abdulhalim yayi na dan lokaci sannan yayi ajiyar zuciya yace
"Qasim Allah Yayiwa Abubakar rasuwa a ranar daurin aurensa".

Wani duhu-duhu Qasim ya fara gani da kyar ya iya cewa "kai, karya ne Wallahi. Abubakar din? Abubakar fa nake nema kaninka mai wannan layin".

Abdulhalim yasan za'a rina. Abubakar da Qasim abokai ne tun aji daya a firamare. Cikin nutsuwa ya labartawa Qasim abinda ya faru.

Tamkar karamin yaro haka Qasim ya rinka kuka. Har wani zazzabi yaji ya kama shi a lokacin. Ya dan gyara murya yace "ina Asmau?"

"Tana gidansu" Abdulhalim ya bashi amsa a takaice. Qasim yayi alkawarin zuwa Kano a satin idan ogansa ya bashi dama. Mahaifiyarsa bata sami zuwa bikin ba saboda ciwon kafa kuma kanwarsa wadda su biyu ne dama ita take jinyarta. Kila shiyasa basu ji zancen rasuwar ba tunda a Shanono suke.

Daga nan suka ajiye wayar Qasim ya tafi office. Duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali. Koda yaje wurin ogansu da hawaye a fuskarsa ya fadi bukatarsa. Labarin ya taba zuciyar ogan ya bashi damar tafiya a ranar ya dawo wata lahadin.

Gidan da aka bashi yaje ya canja kaya cikin kankanin lokaci ya kama hanyar Kano.
*****

A can Kano an bazama neman Asmau. Umma tayi kuka har ta gaji. Hajjo da 'ya'yanta  suka zo har gidan suka yi mata abinda suka saba. Har cewa sukayi ita ta turata yawon karuwanci.

Da zance ya kai kunnen Mama Yalwa ko kadan bata ji dadi ba haka ma Baba da sauran 'ya'yan gidan. Sun tausayawa Umma sosai Baba yace zai sa a bada cigiya a kafafen yada labarai.
*****

Shiru Asmau na zaune a cikin mota banda addu'a babu abinda bakinta yake ambato. Tana daga gefe ta ja hijab dinta ta rufe rabin fuskarta. Sunyi nisa sosai taji wani daga gaba yana tsaki da zage-zage. Na kusa dashi wanda da alama abokinsa ne yace "ya dai kake tsaki kai kadai Bala?"

Wanda aka kira Bala ya nuna masa wani hoto a wayarsa "ka duba don Allah yadda ake rashin imani a duniyar nan. Dubi fuskar yarinyar nan kai kace idan aka saka mata hannu bazata ciza ba...."

Hankalin sauran 'yan motar ya koma jin jawabin Bala. Shi kuwa ya cigaba da magana cikin bacin rai "....wai yarinyar nan ce ranar aurenta ta kashe mijin saboda ya gano tana da ciki kuma yace ba nasa bane. A cikin gidansu fa aka tsinci gawar tasa a bandaki ta buga masa guduma a keyarsa bayan an kai ta, ance a halin yanzu tana hannun hukuma. Shegiya Allah Yasa su harbeta ma"

A hankali Asmau ta daga kai ta kallo hoton da duk 'yan motar sai da suka karbi wayar suka gani. Gabanta ne ya fadi sosai da taga hotonta ne. Cikin dan lokaci an canja labarin gabadaya. Ba karamin mamaki tayi ba da taga hoton da ita kanta yanzu bata dashi a wayarta. Mutane kamar jira sukeyi abu ya faru sai ayita yayatawa ana ta kara gishiri da maggi a zancen. Kafin ka ankara zancen ya sauya daga ainihin yadda yake. Shiyasa ake so mutum ya kiyaye me yake saurin turawa mutane a kafafen sada zumunta (social media).

Sake rufe fuskarta tayi don kada su ganeta. Wani daga kujerar baya yace "nima ina da wani hoton nata daban da wannan harda mijin" wayar tasa ya miko shima da hotonsu na dinner ita da Abubakar.

Mutumin ya cigaba da cewa "ni a yadda aka turo cewa akayi kafin a daura auren aka tsinci gawarsa a bandakin hotel shine aka kalawa yarinyar. Ana tunanin wata yayiwa ciki ta kashe shi."

Har zuciyarta zancen yayi mata daci sai dai kafin a gama ganin hoton wata tace itama taji labari amma cewa akayi rasuwa yayi a gidansu kuma a ranar aka gane amarya nada ciki. An rasa gane ko cikin waye nasa ne ko na yayansa don amaryar tana bin maza.

Duk masu bayani na matar ne yayi kama da gaskiya. Duniya kenan, kowa da abinda zai ce ba tare da yasan gaskiyar lamari ba. Asmau tana ji motar ta kaure da tsine mata ita da Abubakar ga wadanda suka yarda ciki yayiwa wata. Rufe ido tayi kamar mai bacci tana kukan zuci har suka shiga tashar Azare ta jihar Bauchin Yakubu.
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽7

Batul Mamman💖




Ba karamin gudu Qasim yayi ba a hanya. Allah ne Ya kawo shi Shanono lafiya. Kai tsaye gidansu ya nufa. Gida ne irin ginin gargajiya amma yasha gyara ciki da waje ga sabon fenti. Duk shiririta irinta Qasim baya wasa da lamarin iyayensa. Shiyasa albashinsa duk wata a hidimar gidan yake tafiya ko tunanin aure baya yi duk da shine babba. Kanwarsa daya Jamila wadda ada yaso Abubakar ya nemi aurenta.

A soro ya tarar da mahaifinsa Mal Musa zagaye da dalibansa samari da magidanta wurin su goma. Da dai-dai Qasim ya gaisa dasu sannan ya gaishe da mahaifinsa. Yana durkusawa gaban Malam sai hawaye ya kufce masa. Ganin haka daliban suka tashi gabadayansu suka yi sallama da malaminsu.

Hankakin Mal Musa a tashe yace
"Baba wata matsalar ka sake samu a wurin aiki ne?"

Qasim ya girgiza kai. A lokacin Jamila ta fito zata je makota inda Inna ta aiketa. Ganin yayanta yana hawaye yasa ta koma ta sanar da Innar abinda ta gani. Kokarin tashi tayi da kafarta daya da tasha dori sakamakon karayar da ta samu a kafar bayan ta zame a bandaki. Kafadar Jamila ta dafa ta kaita soron. Suna shiga suke jin Qasim yana sanar da mahaifinsa mummunan labarin da ya dawo dashi gida.

Inna ta saki kuka hade da salati "Abubakar din da na sani ko dai wani kake nufi Baba".

Ido fal hawaye ya fada musu abinda ya sani dangane da rasuwar amininsa. Inna da Jamila sai kuka. Ba tun yau Abubakar yake dan gida a wurinsu ba. Yadda Qasim ke zuwa Kano hutu haka Abubakar yake zuwa Shanono. Lokacin da Mal Musa ya sami mutuwar barin jiki ba karamar hidima iyalin Kwamishina Adamu suka yi musu ba. Lalurar iyayensa da canjin aiki da ya samu yasa basu je wurin bikin ba. A can Kano kuma tashin hankalin cikin Asmau yasa basu tuna da sanar musu ba.

Bayan sun gama koke-kokensu suka shirya duk da yamma tayi Qasim yasa kujerar guragun da ake tura mahaifinsa a ciki a bayan mota sannan suka kama hanyar Kano. Ana gab da magariba suka isa kofar gidan Kwamishina. Maigadi ya sanar dasu cewa gabadaya 'yan gidan  suna makota wato gidansu Asmau. Gaba Qasim yayi da motarsa suka karasa can gidan. Ya taimakawa mahaifinsa ya fito jingine da jikinsa suka shiga gidan.

Jigum suka tarar da Umma da Mama Yalwa kamar basu sami sabani sakamakon jin batun cikin ba. Baba Kwamishina yana gefe shi da Abdulhalim suna ta bige bigen waya. Kowa ka gani da abinda yake yi. Sallamar Qasim ta sa hankalinsu ya koma ga kofa. Kuka sosai ya zowa Mama saboda ganin Qasim. Shima bayan ya zaunar da mahaifinsa gabanta ya koma yana kukan.

Mutuwar Abubakar ta dawo musu sabuwa. Da suka dan nutsu ne Qasim yace " Umma ina Asmau ne?"

Kamar yace a fara wani kukan suka sake dasa sabo. A gigice yace " ba dai itama ta rasu ba?"

Jafar ne ya bashi amsa da cewar ba'a ganta ba tun safe. Qasim ya share kwalla "amma me yasa Asmau bazata yi tawakkali ba. Ina ta tafi haka?"

Boye- boye bashi da amfani shiyasa Shema'u ta sanar  dasu abinda ya faru. Idan ma basu fada ba a waje wasu zasu fada musu.

Labarin yayi matukar razana Qasim da iyayensa. Lallai iyalan biyu suna cikin tashin hankali. Jikinsa duk babu kuzari ya dubi wurin da Malam da Baba suke zaune "ko da ba a gabana akayi ba, ni shaida ne cikin Asmau na Abubakar ne."

Mama ta dago jajayen idanunta tana kallonsa " Qasim abokinka fa ya rasu, yanzu ka kyauta kenan kana binsa da wannan mummunar shaida".

"Mama na san inda yaje nima a ko wane lokaci zan iya tafiya. Fadin gaskiya shine adalcin da zanyi masa." Daga nan ya basu labarin abinda ya sani dangane da Abubakar da Asmau wanda babu wani mutum da ya sani. Shi  kadai ne yasan wannan sirrin.

Falon ya sake rudewa da kyar Baba da Malam suka samu aka yi shiru sannan suka ce a tashi ayi sallar magriba zasu karasa maganar idan sun dawo daga masallaci.

*****
Tun kafin azahar mota ta sauke su Asmau a tasha. Kowa na ciki ya dauki kayansa yayi gaba, ban ita. Sai yanzu take tunanin inda zata je kuma bayan nan. Bata taba zuwa Azare ba kuma bata san kowa ba. Wurin da taga an kebe domin sallah taje tayi sallah sannan ta karasa wurin masu abinci ta sayi wake da shinkafa da pure water. Yunwa take ji sosai. A gefen wurin sallar ta zauna taci abincin. Da akayi la'asar ta sake yin sallah ta kuma samun wuri ta zauna. A nan dai magariba da isha suka riske ta tayi sallolinta cikin fargaba. Ga dare yana yi gashi bata da wurin zuwa.

Bayan tayi Isha ne hankalinta ya kai kan akwatinta. Dama jakar na kafadarta. Akwati dai babu shi babu dalilinsa wani ko wata ya dauke batare da ta sani ba. Bakin cikinta ya karu ta soma kuka. Ita ga tsoro bare tayi cigiya. Tana kallon yadda mata ke fada a cikin tashar da maza amma bazata iya ba. Tayi sa'a ma akwatin babu kudi a ciki.
Tana wannan kukan ne taji muryar wani daga gefenta yace
"Gani  nazo sai kizo mu tafi."

"Mu tafi ina?" Ta fada a tsorace ga wurin babu wadatar haske.

Wata dariya mutumin yayi. Babba ne don a kalla zai shekara hamsin. Yasa riga da wando na yadi ga taba a hannunsa. Bakinsa kuwa hakoran Makkah ne har biyu daga sama. Tsoro ne ya sake shigarta ta dan matsa baya.

"Kinga ki kwantar da hankalinki yarinya kinzo gida. Irinku sunfi a kirga da nake taimakawa a tashoshin garin nan." Ya dan zuki tabar sannan ya sake kallonta. " ki taho mu tafi idan ba a tashar nan kike son kwana ba 'yan iskan gari su danneki anjima kadan.."

Asmau ta manne jikin bango zuciyarta na dukan uku-uku
"Don Allah ni dai ka kyale ni."

Mutumin ya girgiza kai alamun ya saba jin irin haka.
"Kinga 'yata ta kaina. Ni dinnan da kike gani ba cutar dake zanyi ba. Billahillazi masauki zan kaiki."

Cikin tsiwa tace "bazani ba"

Ya dan tabe baki "kinyiwa kanki, irinku- irinku yawa garesu. Ku fito daga gidan iyayenku duk garin da kuka ga mota zata kuje. Sai kun sauka a tasha kuke gane kunyi kuskuren barin gida. Irina kuma sai mu nuna muku cewa ku kadai zaku iya rayuwa batare da iyaye ba. Akwai gida na mata zalla dama can nayi niyar kaiki saboda kwanan tasha ga zukekiyar mace irinki ba karamin hatsari bane."

Maganganunsa kara tsorata Asmau suke yi sai dai haka kawai bazata bi mutumin da bata sani ba. Dauke kanta tayi ya gaji da tsayuwa ya juya abinsa bayan ya bulbuleta da hayakin taba.

Ajiyar zuciya ta saki bayan ya tafi sai dai kafin ta motsa daga wurin da take taji wasu maza na tahowa wurin da take. Tana jin su suna tattaunawa a tsakaninsu waye zai fara amfani da ita. Abin nasu kamar fada mutum biyu suka dage harda zage-zage. Kafin su karaso da sauri Asmau tabi bayan mutumin da ya gama yi mata magana dama baiyi nisa ba. Tana kankame da jakarta tace ya tsaya zata bishi.

Wani shu'umin murmushi yayi yana kare mata kallo. Shiyasa yake son aiki da su Shoki yaran da ya biya suka tsorata ta.

Addu'a kawai take yi tabi bayansa suka mike wata hanya da tayi kudu da tashar.

*****
Su Umma sun sake taruwa a falon gidanta inda Malam Musa ya bada shawarar a dage da addu'a da binciken mutanen da take da alaka dasu. A cewarsa babu wani abu yanzu mai mahimmanci a gabansu sama da sanin inda Asmau take. Sannan ya ce
" a gaskiya dukkanku kunyi kuskure akan yadda ku ka karbi al'amarin yarinyar nan. Dukkan dan Adam ajizi ne, Allah da Ya haliccemu mai gafara ne da jinkai. Idan mutum ya aikata ba daidai ba musamman abu irin nata dolene mu nuna mata kuskurenta sannan kuma mu jata a jiki don gudun sake faruwar makamancinsa. Mu nuna mata mahimmancin tuba da karbar kaddara. Amma idan muka watsar da lamarin 'ya'yanmu saboda sunyi laifi hakika muna tura su ne ga aikata wanda yafi shi. Wani lokacin idan hantara da kyama tayi yawa sai kawai yaro ya fandare gabadaya yace bari yayi ta laifin tunda bashi da sauran gata.

Mu kula sosai idan mutum yayi laifi fada, nasiha da jankunne yakamata muyi ba sharesu ba har su bi hanya mara kyau. Allah ma muna masa laifi Ya yafe mana duk girmansa indai ba shirka bane balle mu 'yan Adam. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama izina ga sauran mutane.

Kuma na tabbatar yadda kuka nemi tilasta ta akan a cire cikin shi ya koreta. Sannan ta fiku gaskiya domin cire ciki ba tare da wata lalura ba bashi da muhalli a addininmu. Allah Ya tsare mana ita a duk inda take."

Jikin kowa kuma sai yayi sanyi da jin bayanin Mal Musa suka ce Amin.

Haj Bara'atu dai babu abinda ke damunta sai irin yadda ta rinka fadar maganganu marasa dadi ga 'yarta cikin bacin rai. Da ta sani bincikar ta tayi taji yadda al'amarin ya faru domin a kiyaye faruwarsa ga sauran yara.

Bacin rai da fushi dole ne amma yin komai cikin hikima da ilimi shine daidai. Da ta sani fada tayi mata wanda ta tabbatar halin da take ciki ma ya isheta abin kunya. Daga nan sai a kiyayi gaba,yanzu kuwa tana iya zuwa inda rayuwarta zata iya gurbacewa gabadaya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽8

Batul Mamman💖




Tafiya su Asmau suke yi a inda tafi tunanin kasuwa ce saboda yawan shaguna da ta gani da mutane suna kai kawo kamar ba dare ba. A bakin kofar wani gida suka tsaya mai kofa daya. Sai da suka shiga ta ga ashe gidan yana da girma ta ciki. Dakuna ne birjik ta bangaren hagu , dama da tsakiya. Ga 'yan mata kamar ba dare ba suna ta bidirinsu babu mai shigar arziki. Harda masu daurin kirji. Tun daga nan Asmau ta fara dana sanin biyo mutumin.

'Yan matan taga suna gaisawa da mutumin da ta biyo suna tambayarsa bakuwa ya kawo musu yace eh. Tafiya suka cigaba da yi har sai da suka je kofar wani daki daga gefe. Dan mukulli yasa ya buga kofar dakin wata budurwa ta fito a fusace. Wani mugun kallo ta watsa musu shi da Asmau sannan ta matsa gefe wata babbar mata ta fito. Doguwa ce da gani shekaru sun ja, jikinta kuma yayi jaja-jaja alamun anci bleaching lokacin da ake ji da sauran kuruciya. Ganin su Asmau yasa ta washe baki tana murmushi.
" Bulayi kaine a daren nan? Bakuwa ka samo mana ne?"

Shima murmushin yayi "a bamu wurin zama mana sai muyi magana a nutse".

Yarinyar da take ta hararsa a kofar dakin matar ta kalla ta koma ciki ta dauko musu tabarma aka shimfida a wurin. Sauran 'yan matan gidan kowacce harkar gabanta take yi.

Mutumin da ya amsa suna Bulayi yace
" ina shirin fita daga tasha nayi gamdakatar. Dubi tsaleliyar da na gano. Ina ganinta nace wannan taki ce don duk garin nan gidanki ne gidan kyawawa."

Matar ta maida kallonta ga Asmau " yarinya ina miki barka da zuwa. Ni sunana Uwargida haka kowa yake kirana. Kuma tunda kika zo gidan nan zamu taru mu sharewa juna hawaye. Babu ruwana da abinda ya fito dake bariki indai zaki kiyaye dokar gidana shikenan."

Asmau ta mike tsaye domin ta gano wane irin gida aka kawota. Jakarta a hannu tace "Hajiya kiyi hakuri ni ba yawon bariki na fito ba. Bazan iya zaman gidan nan ba. Nagode".

Takalminta ta fara kokarin sakawa ta dan hada ido da yarinyar dake tsaye a wurin. Ga mamakinta murmushi sosai yarinyar tayi mata.

Uwargida tayi dariya sosai "duk yaran gidan nan da kika gani babu wacce take yarda karuwanci ta fito yi sai babu ta sakata a gaba. Ni bazan matsa miki ba. Akwai daki na haya dubu goma duk wata. Idan kina so a jona injin gidan nan dake ki rinka samun wuta idan babu a gari duk sati zaki biya dari biyar. Ci, da sha da sutura kuma kowa ta kansa yake yi. Zabi ya rage naki. Zaki zauna ne ko zaki fita ki kwana a titi".

Shiru Asmau tayi tana tunani. Yanzu idan ta fita ina ta nufa.

Matar ta katse mata tunani " bana tilasta mace tayi sana'ar da bata so amma indai ba kina da jari ko wurin zuwa fa to nan ne gidan da kowace 'ya da bakincikin rayuwa ya korota zata kira gida."

Bulayi yace "kuma gata da jikin sana'ar ba. Fatarta har wani sheki take yi tayi luwai-luwai. Ni da na matsa kusa da ita ma har kamshi naji tana yi shiyasa nace da shirinta ta fito."

Dan murmushi Uwargida tayi sannan ta zaunar da Asmau a kusa da ita
" ke amarya ce ko?" Ta fada tana daga gira.

"Irinku yawanci mijin ne bakwa so sai ku gudu. Shiga duniya ba da ka ake yinsa ba. Dole ki fara ta wani wurin. Kamar yadda na fada miki ko wurin zama ki samu nan gaba idan kika shafa kika ji babu abinda zaki ci nasan zaki fara sana'ar da bata tsufa. A lokacin zan taimaka miki da kayan aiki wato maganin mata sannan na hadaki da kilayen(client). A tsarin gidan nan duk wadda tayi ciniki a gida ko a waje zata bani kaso goma a ciki. Sauran bayani dai sai kin shigo hannu. A lokacin kuma zan saka miki suna. Ni nan babu ruwana da sunan kowace yarinya na gaskiya."

Yarinyar dake tsaye a gefe tayi tsaki "haba Mama tace ba abinda ya fito da ita ba kenan ko dole ne?"

Bulayi ya kalleta yana dariyar shakiyanci "ustaziya Zubaida kenan, kina nan da halinki na korar mana alheri".

Baki ta murguda masa Uwargida tace " yanzu ma fadan da nake mata kenan ya kamata ta ajiye girman kai ta rungumi sana'ar da na haifeta kuma na raineta a ciki shine ta fara min rashin kunya na bige shegen bakin."

Asmau ta sake kallon yarinyar sai taji tana sonta. Murmushi tayi mata yarinyar ta mayar sannan Uwargida ta umarceta da ta nuna mata daki daya cikin wanda babu kowa. Babu yadda Asmau ta iya dole ne ta nemi muhalli kafin tasan yadda zata fara gudanar da rayuwa. Shiyasa ta bi bayan Zubaida. Wani daki ta bude duk yayi kura. Zubaida tace bari na kawo tsintsiya. Bata dade ba ta dawo da yake akwai wutar nepa ta kunna fitilar dakin. Sai da ta taya Asmau shara da goge kura suka karkade yamushasshiyar katifar dakin da babu zanin gado. Bayan sun gama Zubaida ta fita sai gata ta dawo da tuwo wanda aka fara ci da ruwa a kofi.

Tana murmushi tace "Allah Yasa ki iya ci dazu na fara ci Mama ta fara damuna na barshi. Don girman Allah da Ya haliccemu kada kiyi karuwanci. Gidan nan har mace ta nemi mace anayi."

Asmau ta karbi tuwon da murna taci tayiwa Zubaida godiya sannan ta kara tabbatar mata da cewa da zarar komai ya daidaita barin gidan ma zatayi.

Zubaida tace "idan babu damuwa ki fada min abinda ya raboki da gidanku".

Ajiyar zuciya Asmau tayi "in sha Allahu gobe zan fada miki tarihin rayuwata".

Zubaida sai murna take. Har ta fita ta dawo da sauri "ina kara tuna miki kada kiyi sana'ar matan gidan nan. Mata da yawa da farko haka suke cewa sai an kwana biyu su fi kowa lalacewa. Ni ma ba don bani da wurin zuwa ba da tuni na bar gidan nan."

A haka suka yi sallama. Da Zubaida ta koma dakinsu har ta kwanta addu'a take yi Allah Yasa bakuwar nan kada tayi halin matan gidan. Bata da wani ilimin addini amma tasan cewa sana'ar da ta tashi taga mahaifiyarta tanayi bata da kyau..

Washegari shayi da bredinta ta dauka zata fita daga dakinsu Uwargida ta kalleta tayi murmushi.
"Zuby tawa kenan, da kinga bakuwa kin rinka rawar kafa kenan ke a dole sai kinsa ta koma gidan iyayenta. Rayuwar duniyar nan ta wuce tunaninki fa. Ki sani duk wadda kika gani a nan to abinda ya korota yafi nan muni."

Zubaida ta gallawa Uwargida harara ta fita. Kai tsaye dakin Asmau ta wuce. 'Yan matan gidan suna ta mata dariya don sun saba ganin irin haka a wurinta idan taga bakuwa.

Da sallama ta shiga dakin. Asmau na gyangyadi a zaune. Kyamar katifar yasa bata kwana a kai ba. Kusan kwana tayi tana koke-koke da addu'o'i. Cike da farincikin ganin Zubaida ta amsa mata sallama.

Zubaida na zama ta mika mata abincin ta karba da godiya taci. Sannan ta tambayeta inda ake samun ruwa domin taimama tayi da asuba tayi sallah.

"Meye kuma taimama?" Zubaida ta tambaya.

Asmau tayi mata bayani. Zubaida ta gamsu sannan ta sanar da ita kowa a gidan siyan ruwa yake yi. Dole sai ta siye duk wani abin amfani sannan ta tanadi kudin hayarta domin anjima kadan Uwargida zata bukaci ta kawosu. Bayan duk ta gama jin bayanin gidan ne Zubaida tayi mata tuni akan alkawarinsu na jiya.

Asmau tayi murmushi mai ciwo sannan ta fara sanar da Zubaida dalilin watsewar farincikinta.

*FARKON LABARI*

Alh Shu'abu Yahaya sunan mahaifinsu Asmau. Iyayensa duk 'yan Kano ne kuma a nan cikin Kanon suka tashi. Su biyar ne a gidansu shine na biyu. Babbar yayarsa suna kiranta Yaya Abu sai shi sannan mai binsa Rabe sai Lami da Garzali.

Babansu mazan kawai yake sawa a makaranta. Saboda haka Shu'aibu yayi karatu har matakin digri inda ya karanci Agric Science harkar aikin gona. Shi mutum ne mai saukin kai da kirki shiyasa mahaifinsu yake ji dashi. Sauran 'yan uwansa kuwa kusan duk halin Hajjo mahaifiyarsu suka debo na fada da sa ido.

Lokacin bautar kasa aka tura shi makaranta a wata karamar hukuma a jihar Niger mai suna Wushishi. A can ya hadu da Bara'atu tana ajin karshe na sakandire. Farkon haduwarsu duk da baya koyar da 'yan ajinsu soyayya ta kullu a tsakaninsu. Abu kamar wasa har lokacin komawarsa gida yayi inda yayi mata alkawarin turo iyayensa. Dama a hannun kawunta take ita da kanwarta Bintu marayu ne ko kadan basa jindadin zama da matar kawun.

Da ya koma Kano ya sanar da iyayensa Hajjo ta dage indai tana da rai danta bazai auri banufiya ba. Duk 'yan Niger mayu ne a cewarta. Ita a son ranta ya auri 'yar kanwarta. Akayi ta jan zance ita da mahaifinsu shi kuma ya dage Shu'aibu sai ya auri wadda yake so. Rigima sosai akayi sai bayan wata biyu iyayensa suka je Wushishi. Lokacin Bara'atu har ta fitar da rai. Ba wani dogon lokaci aka saka bikin ba gashi ko aiki bai fara ba. Wurin hada lefe yasha wahala Bara'atu ta bashi kudi cikin kudin gadonta ya cika ya siya mata kaya masu kyau. Haka aka yi biki aka kawo amarya Kano ita da kanwarta Bintu saboda bazata iya barin kanwar a hannun matar kawunsu ba ta cigaba da azabtuwa.

Wani bangare aka gyara musu a cikin gidan iyayensa suka tare a ciki. Zaman lafiya sosai suke yi da mijinta sai dai a wurin Hajjo da 'yan uwansa tana ganin wulakanci mara misaltuwa. Daga ita har kanwarta basu da sunan da ya wuce Mayya. Gashi dama duk suna da idanuwa Tubarakallah.

Duk wani aiki na gidan ya dawo wuyansu amma bata taba korafi ba. Kullum Shu'aibu sai dai ya bata hakuri lokacin yana ta fafutukar neman aiki. A haka ta samu ciki har sau uku yana barewa saboda aikin wahala.

A karo na ukun ne da safe Hajjo ta shigo taga Bara'atu bata sha kunu da kosan da ta aiko mata dashi ba wanda babansu Shu'aibu ne ya tilasta mata dama.

Fuska babu walwala tace "Au baku karya ba har yanzu saboda ki jawo min fada wurin Malam yace bana kula dake?"

Daga kwance inda take saboda rashin kuzari Bara'atu tace "Kiyi hakuri na koshi ne".

Hajjo tayi dariya "yo ba dole ki koshi ba, kunyi kalaci da jikana ke da kanwarki. Ai Shu'aibu ya gama janyo mana masifa. Nan gaba kadan ma mu zaku bi ku lamushe."

Bayan ta gama fadanta ta fita Bara'atu babu abinda take yi sai kuka. A wannan yanayin Shu'aibu yazo ya sameta. Hakuri ya bata kamar kullum tare da kyakkyawan albishir na cewa ya sami aiki a jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria a matsayin lecturer matakin farko. Kuma har da gida aka bashi. Murna a wurin Bara'atu ba'a magana.

Kafin su tattara su koma Zaria ne mahaifinsa ya fara cuta yana ta ramewa. Hajjo tasha kuka tana rokon Bara'atu akan ta sakar mata kurwar miji.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽12

Batul Mamman💖



*BAYAN SHEKARA DAYA*

Anti Bintu tazo Kano wurin yayarta yawon arba'in. Tunda tazo kullum sai sun fita kasuwa siyayyar kayan amfanin gida. Duk wani kudin Bara'atu na albashi, kasuwanci da abinda ta samu na gado ta hada shi a gini da zuba kayan bukata a sabon gidan. A lokacin falo da dakuna biyu kawai ta gama sai kitchen amma bahaushe yace da babu gara ba dadi. Hatta sutura da Hajjo ke yi mata gorin bata siyawa yaranta duk ta siya. Dama tara kudin take sai ta gama da abinda yafi mahimmanci.
Sai da ta gama shirinta tsaf sannan wata juma'a bayan su Asmau sun dawo daga makaranta tasa sukayi wanka duk ta basu sababbin kaya sannan ta hada sauran 'yan kayansu suka tafi dakin Hajjo. Duk yaran mamaki ya ishe su ina Umma zata kaisu sun kwashe duka kaya.

Kwadon zogale take ci yaran Rabe suna zaune suna wasa a gefenta tana dariya. Shigowar Bara'atu da 'ya'yanta yasa ta hade rai.

Dan Rabe na biyu sarkin gulma ya ruga ya fadawa babansa ga Anti Bara da su Jafar zasu fita yau sunyi kwalliya. Daga shi sai dogon wando haka ya fito da sauri jin kwaf.

Bara'atu na dauke da jaririyar Bintu tace
" Hajjo albarkacin zaman tare a yafemu Allah Yayi zamu tashi"

Zaro ido sukayi ita da Rabe. Shi a son ransa idan Bara'atu ta gaji da takurata da akeyi ta yarda da aurensu. A ranar ma zai saki Sagira.

"Ina zaki kai min yaran da kike cewa zaku tashi? Idan tafiya zakiyi ke kadai dai ga hanya nan."

"Ba nisa zanyi ba Hajjo, nan layin gidan sabon kwamishinan 'yan sanda zan koma. Cikin ikon Allah na kammala gini na."

Ashar Rabe ya fara saki sannan yace "kika kammala wane ginin? Waye ya baki filin da kudin ginin?kada ki raina mana wayo wani saurayin kika yi kuke zaman....."

Katse shi tayi kafin yayi barambarama gaban yara.
"Fili dai tare muka siya da wannan da kuke ciki ni da babansu Yassar. Ina sana'a ina aiki. Allah Ya buda min gashi nayi gidan kaina. Wannan da kuke ciki kuma har abada ku sani cewa gidan marayu ne. Allah SWT kuma Yace wanda yaci dukiyar marayu tamkar yana ciwa cikinsa wuta ne."

Hajjo ta bata rai "nufinki mune 'yan wutan..Bara'atu ki kiyayeni wallahi. Kuma idan kika fita da yaran nan to ki sani babu ni babu su."

"Ai aikin gama ya gama. Yara dai ke kika haifi babansu saboda haka jininki ne. In Allah Ya yarda zasu rinka zuwa gaisheki tunda ba nisa mukayi ba."

Daga haka suka fice Rabe yana binsu a baya yana kiranta.
*****

*Sabuwar Rayuwa*

Wannan tashin nasu shine ya kara kiyayya tsakanin iyalan mariyayi Shu'aibu da gidan Hajjo. Kamar yadda ta fada duk juma'a bayan masallaci take tura yaran gaishe da Hajjo. Manyan kullum sai sun dawo rai a bace ko da hawaye a idonsu. Amma hakan baisa ta dena turasu ba saboda tasan su din dai suka rage musu dangin uba.

Rayuwa sabuwa suke yi cike da 'yanci da jindadi. Bara'atu ta dage wurin bawa yaranta tarbiya. Sannan tana nuna musu soyayya irin wadda bazata sa su sangarce ba. Shakuwa mai karfi ce a tsakaninta da 'ya'yanta.

Washegarin tarewarsu suka shiga makota domin gabatar da kai. Lokacin da suka shiga gidan Kwamishina Mama Yalwa tayi musu tarba ta karramawa. Dama sun saba da Umma. Duk yaranta suna gida ta kirasu ta gabatar dasu ga 'yan uwansu kamar yadda ta fada musu. Abdulhalim, Nasiba da Abubakar dai duk sun girmesu amma suma sunyi kokarin jansu a jiki.

Bayan 'yan kwanaki ne Mama Yalwa taje gidan Umma take sanar da ita Baba yace ta rinka turo su Asmau ana yin magariba masallacin gidansu akwai Malamin da yake koyar dasu Sadiya karatun Qur'ani zuwa karfe tara.
Umma taji dadi sosai,duk da suna zuwa islamiyya amma wannan ma zai taimaka kuma ba nisa suka yi da gida ba.

_Asmau S. Yahya_

Ranar farko da zasu je makarantar kowa yana doki banda Asmau. Haka take da tsoron mutane. Duk gidansu ita ce ta kasa sakewa da yaran Mama.

Kowa ya shirya ta kwanta ciwon cikin karya saboda taji ance kowa karatunsa shi kadai malam zai biyawa. Yadda zata yi karatu a gaban su Suwaiba ne yake kara tsorata ta. Umma na ganinta tasan ciwon karya ne. Da rarrashi ta lallabata suka tafi suna idar da sallar magriba.

Cikin gidan suka fara zuwa suka gaishe da Mama sannan suka fito waje. Suwaiba 'yar Mama ta hudu ita ce kusan sa'ar Shema'u amma duka ita da Sadiya sun zama kawaye da Shema'un. Tare suka fito zuwa masallacin Asmau na bin bayansu rike da hannun  Aina'u.

Malam Hadi yana zaune tare da Abdulhalim, Abubakar da Umar. Suna zuwa gaishe shi suka yi kowa ya sami wurin zama. Sai da ya gama da manyan sannan yaji karatun su Suwaiba. Daga nan ya fara jin inda su Asmau suka tsaya yace kowa sai ya biya surar karshe inda ya tsaya.

 A nan ake yinta ana zuwa kan Asmau da ta fuskanci idanu sun dawo kanta tana yin Bismillah sai hawaye. Malam yace ta barshi ya gama da sauran .Shema'u tayi tsaki tace " malam wallahi ko a islamiyya haka take yi sai taji bulala take kawo hadda."

Murmushi yayi "ni bana duka kinji Ma'u. Bari na gama da kannenki sai ki biya min."

Hatta Aina'u sai da ta karanta suratul Ikhlas amma ana dawowa kan Asmau sai kuka. Jafar yace Ummansu tace a zaneta idan bata yi karatu ba.

Tunda ta fara kukan farko Abubakar yake kallonta. Dariya abin ya bashi sai da yaga taki denawa ta soma bashi tausayi.

Malam Hadi yayi har ya gaji taki karatu sai kuka da rawar murya. Yace  kowa ya fita banda manyan yayye. Suna tafiya ya nuna mata Abdulhalim da Abubakar
"Waye a cikinsu kika yarda zakiyi karatun a gabansa tunda kin kasa a wurina."

Tana daga kai suka hada ido da Abdulhalim ya hade rai. Da shine malamin zaneta zaiyi fes baya daukar rainin hankali. Da sauri ta nuna Abubakar. Malam Hadi yace "to Sadiq ka kwatanta gaskiya ka ji karatun. Ke kuma gobe ki tabbatar zakiyi a gabana ko na samo bulala".

Da haka suka fita saura ita da Abubakar.
Fuskarsa a sake ya fara tambayarta "shekarunki nawa Asmau?"

"Shahudu"

"Ashe ma kin girmeni da shekara takwas"

Ta dan saki fuska amma muryarta bata dena rawa ba "so kake kace ka girmeni da shekara takwas dai"

Yayi murmushi  dama so yake ta saki jikinta "Haka ne,  ni yanzu ina level two a BUK ina karanta computer science. Ke fa?"

"SS1 nake a science class. Likita nake son zama" yadda take maganar yasan ba karamin son hakan take ba.

"Very good, sai dai bakiyi kama da likita ba saboda tsoro yayi miki yawa. Likitoci kuma basu da tsoro".

Yana kallon  bata ji dadin maganarsa ba ya sake yin murmushi.
"Kada ki damu akwai maganin tsoro. Shine ki daure ki rinka magana a cikin mutane. Babu mai yanka ki. Iyaka idan kinyi kuskure a gyara miki. Karatun Qur'ani karfin zuciya yake sawa ba ragwanta ba."

Shiru tayi tana sauraronsa yana ta janta da zance. Sai karshe yace ta biya masa yaji.

Da kyar ta daure hawaye wani na bin wani ta karanta. Kafin tayi rabi kukan ya dauke sai karatun ake ji.

Tana kaiwa karshen surar yayi kabbara sannan ya sake karfafa mata gwiwa wurin bude baki a gaban jamaa.

Da murmushi ta fito suka tafi gida ran Shema'u a bace saboda tasa sun dade.

Tun daga wannan lokacin ko ta fara kukan idan Abubakar yana masallacin sai ta daure. Karshe dai sunanta ya koma Idon kuka saboda kullum sai tayi. Gashi ta tsani sunan.

Haka rayuwa ta cigabar musu har lokacin bikin Nasiba. Gidajen biyu suna ta shiri duk da su Umma basu fi shekara daya a unguwar ba. Haka suka yi bikinsu lafiya kalau kamar dangin juna.

Su Asmau an  kara zama 'yan mata. Yanzu tana dan sakewa har ayi hira da ita. Wani lokaci da Umma zata Wushishi  gashi basu yi hutu ba a nan gidan Mama Yalwa ta barsu.

Abdulhalim ya tafi bautar kasa Jos yanzu Abubakar ne babba a gidan. Duk da yanayin karatunsa bai hana shi cigaba da zama daukar karatu a wurin malam Hadi ba. Duk cikinsu yafi kowa mayar da hankali akan karatun  addini shiyasa Baba yake matukar ji dashi.

Watarana an gama karatu kowa ya fita daga masallacin sai Asmau dake zaune tana kokarin kammala aikin da malam ya bata na fitar da hukuncin (NUUN saakina) a thumunin da ya biya mata ranar saboda washegari test gareta a makaranta karatu take son yi. Abubakar yana can wurin zaman liman yana tilawa aka soma iska mai karfi alamun ruwa zai iya sakkowa a kowane lokaci.
Da dan gudunta ta tashi zata rufe tagogi kafin ta fita saboda kurar dake shigowa. Har ta gama rufewa Abubakar baiyi yunkurin tashi ba. A take kuma aka dauke wuta saboda wata tsawa da akayi mai karfi. A dan tsorace tace
"Yaya Abubakar kazo mu fita kafin ruwan nan ya sauko"

Shiru taji sai numfashinsa da ya kara karfi. Gabansa ta karasa sai dai duhu yasa bata ganinsa sosai. Wayarsa da ta taka ta dauka ta haska shi. Kwance yake numfashinsa yana sama-sama da kyar yake fita. Hannunsa daya kuma yana nuna mata aljihun wandonsa.

Asmau duk ta rikice ta kuma fahimci abu yake so ta miko masa daga aljihunsa. To kuma Umma tayi musu gargadi sosai akan taba maza wannan yasa ta kasa tabashi ta fita da gudu a cikin ruwan ta shiga gidansu ta fadawa Mama Yalwa.

Tare suka dawo har da Suwaiba dauke da irin filtilar nan mai batir. A kwancen dai suka same shi ya hada gumi idanunsa harda hawaye. Mama ta daga kansa ta dora a cinyarta a rude tace "ina inhaler dinka?"
Aljihunsa yayi kokarin nuna mata. Tasa hannu ta dauko ta shaka masa. Asmau da Suwaiba suna tsaye suna yi masa sannu.

Duk da haka numfashin bai dawo daidai ba. Mama tace a fadawa dreba yazo su tafi asibiti. Bayan fitarsu Asmau ta tafi gida ta sanar da Umma abinda ya faru.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽11

Batul Mamman💖




Rabe ne ya fito yasha sabuwar shadda sai kyalli take yi. Idonsa a kan Bara'atu da yanayin da ta shiga yayi dariyar mugunta. Don tsabar wulakanci yace
"A'a bazawara kune a garin? Ya hanya?"

Hawaye take yi wani na bin wani ta durkusa a gaban Hajjo
"Nasan har mijina ya rasu baku taba kaunata ba amma Hajjo wallahi cin dukiyar marayu haramun ne. Gidan nan baku da hakki a kansa to a wane dalili zaku zo ku tare batare da izini ba".

"Eh, lallai wuyanki ya isa yanka Bara'atu. Ni da gidan dana kike gaya min maganar banza." Hajjo ta amsa itama rai a bace.

"Ko kinki ko kinso zama dole muyi a gidan nan. Idan bazaki iya zama damu ba sai ki bar min yaran ki kama gabanki."

Yusuf mijin Anti Bintu yace "Anti kada ki sake cewa komai. Ai basu fi karfin hukuma ba. Kuma rabon gado ba hauka bane. Ki bari mu kwana yau gobe sai mu san abinyi."

Mikewa tayi cikin zafin nama tana kallonsu daidai. Garzali banda taba babu abinda yake busawa. Rabe da amaryarsa suna tsaye suna mata kallon banza. Hannu tasa ta share hawayenta
"Dama can saboda marigayi nake raga muku to amma wallahi yanzu an wuce wurin. Mu zuba ni daku shege ka fasa."

Yaranta ta dakawa tsawa duk suka tashi daga gaban Hajjo suka bita cikin gidan.

Hajjo da su Rabe kowa yayi tsit suna mamakin wai yau Bara'atu ke mayar musu da martani haka.
*****

A cikin gidan dakuna biyu ta samu a bude ita da Yusuf da su Shemau suka rinka shiga da kayansu. Sai cikin dare tana zaune tana kallon 'ya'yanta na bacci ta rinka kuka.

Washegari ko karyawa batayi ba suka fito ita da yaran suka hadu da Yusuf zasu tafi ofishin 'yan sanda.

Rabe yana tsaye a waje yace " kinga basai kun wahala ba a bayan layin nan akwai gidan wani babban dan sanda. Maza ku tafi ku kai kara kada kuda ya rigaku."

Basu kula shi ba suka wuce. Duk wani bayani sun gabatarwa 'yan sandan. Mutum hudu aka hado su dasu suka zo aka bukaci  su Rabe su fita.

Wannan muguwar dariyar yake yi ya dauko takardun gida sai gashi sunansa ne dana Shu'aibu a jiki a matsayin tare suka gina.

Kuka sosai Bara'atu take yi tana karyata shi. Sai dai kuma bata da shaida. Bata san yadda akayi ya sami takardun gidan ba wanda a hannunta suke har akayi canje canje haka.

Dole 'yan sanda suka tafi domin basu da wata shaida.

Yusuf ya nemi ta bishi su koma Zaria daga nan ta koma garinsu da zama.

Tana kuka tace "ko zasu kashemu babu inda zamu je. Gidan nan namu ne kuma duk rintse sai ya dawo hannun masu shi."

Babu yadda Yusuf ya iya dole ya tafi ya barta. A dakin kwanansu ta sayi risho mai kai biyu da kayan abinci. Kullum suna daki tana saka yadda zata bullo musu.

A karshen sati ne abokan marigayi biyu suka zo. Anyi ta kai ruwa rana Hajjo da Rabe da sauran 'ya'yan gidan suka hade musu kai. Magana dai har wurin dan sandan dake bayan layinsu,  Adamu Matawalle ashe abokin daya daga cikinsu ne. Shima ya gamsu da bayanansu sai dai ga shaida kurukuru suna gani gida na Rabe da Shu'aibu ne. Shawara suka bata akan ta koma gida kawai tace babu inda zata je.

Wani katon fili wanda gida daya ne tsakaninsa da gidan dan sandan ta nuna musu. Rabi nata ne ta siya da kudin kasuwancinta daya rabin kuma Shu'aibu ne ya siya mata. Takardun ta bawa dan sandan ta roke shi ya rike mata amana zata gina kayanta a hankali sannan su tashi daga can gidan. Duk ta basu tausayi. Wani cikinsu ne yayi cuku-cukun nema mata aiki a kamfanin sadarwa na MTN , duk wannan abu batare da sanin su Rabe ba. Tayi musu godiya kamar ta ari baki.

Cikin dan lokaci ta saba da iyalin Adamu sai dai kullum a gida take barin 'ya'yanta idan zata je wurinsu. Tana tsoron surutun yara kada su fada a gidan. Makaranta ta samar musu a nan cikin unguwa. Saboda yanayin aikinta ta koyawa Shemau da Jafar girki ko da bata dawo da wuri ba. Zagi da surutu har su Hajjo sun gaji da yi wai tana yawon bariki. Bata kula su ba sai dai bata bari 'ya'yanta sun raina kakarsu ba.

Wata rana ta fito suna sauri zata kai yara makaranta ta wuce wurin aiki ta nemi motarta bata gani ba. Rai a bace ta koma ciki ta tambayi Sagira. Sai da ta gama yaukinta sannan tace ban sani ba. Itama Hajjo amsar data bata kenan.

Tasan aikin Rabe ne sai tayi kamar ta hakura. Har wani gadara yake yi yana cewa motarsa. Na tsawon sati biyu ta dauke kanta daga kan motar sai dai a bayan idonsa ta sami wani abokin aikinta ya samo mai siya.

Ranar Juma'a Rabe na kwance a daki mai siya yazo yaga mota aka gama ciniki ta bashi mota da takardunta. Shi kuma yayi alkawarin kawo kudin ranar litinin.

Sam Rabe bai san me ake ciki ba sai washegari ya gama shirin zuwa daurin aure. Ganin babu motar kuma yasan Bara'atu nada mukulli ya tafi kofar dakinta yana ta bugu iya karfinsa. Yaranta duk bacci suke yi ta fito da dogon hijab a jikinta tana murmushi don tasan me ya kawo shi.

"kinga ba wasa bane ya kawoni ina kika kai min mota"?

"Hmmm, karfin hali barawo da sallama." Ta fada tana tafa hannuwa.

Hajjo da Sagira suka fito suka sakata a gaba.

Bara'atu ta yatsina fuska "mota dai tawa ce kuma na sayar na cinye kudin. Shikenan ko."

Ran Rabe a bace ya zabga mata mari. Hajjo tace kayi min daidai.
Bai ankara ba Bara'atu ta kwashe shi da mari shima tana harararsa.

"Dani daku a gidan nan daga yau an shata layin rashin mutumci. Na gaji na kai wuya duk abinda zakuyi kuyi. Banda rashin tsoron Allah komai na gado sai mun raba ni daku? To mota dai tawa ce ni kadai"
Tsaki taja ta shige dakin ta banko kofa.

Hajjo ta kalli Rabe a dan tsorace." Anya yarinyar nan bata shan kwaya kuwa? Kada tasa a koremu fa."

Rabe ya dafe kunci "barni da ita Hajjo sai na nuna mata bata da wayo". Sai dai har kasan ransa bazai iya ba saboda son da yake mata.

Haka suka cigaba da zaman doya da manja a gidan. Tsakanin Bara'atu da su sai kallo. Yaranta kuwa ta wajabta musu zuwa gaishe da Hajjo safe da dare duk da bata amsawa. A haka har suka shekara daya da rabi tana ta gininta a hankali, sannan duk da tana aiki bata dena kasuwanci ba.

Wata ranar lahadi tana daki ta jiyo hayaniya a falo. Yaya Abu ce da Lami suka zo yini da 'ya'yansu. Su Shemau na son zuwa wurin sauran yaran suna tsoron Ummansu. Murmushi tayi tace su je amma banda tsokana.

Da gudu suka fice tunda da sauran kuruciya basu gama bambamce masu sonsu ba. Iyayen dai babu wanda ya amsa musu gaisuwa da 'yan uwansu yara suke ta wasa.

Kamilu babban dan Yaya Abu ne ya shigo ya soma rungumar kannensa kamar yadda ya saba. Yana rungume da Shema'u yana tsokanarta Bara'atu ta fito idonta ya fada kansu. Mantawa tayi da mutane a wurin tace
"Kamilu wane irin wasa ne wannan? Shema'u ban hanaki wannan rungume rungumen ba?"

Dena hirar su Hajjo suka yi suka tsaya kallon Bara'atu tana yiwa dansu fada.

Lami ta watso mata harara "To kinibabbiya kin fito ne ki fara rashin da'ar taki? Menene aibu don ya taba kanwarsa, yaro da muharramarsa ma sai an nuna musu iyawa" mtws.

"Bani da matsala don Kamilu ya taba kanwarsa sai dai Shema'u ba muharramarsa bace shiyasa na hana. Daga shi har ita babu karamin yaron da ba'a budewa littafi ba".

"Ya Sayyada manya....indai Yaya Shu'aibu ne uban Shemau to baki isa ki rabata da Kamilu ba domin kuwa iyayensu uwa daya uba daya suke. Kinga sun zama muharraman juna".

Kallon Lami kawai Bara'atu tayi ta girgiza kai zata koma ciki Hajjo ta dakatar  da ita.
"Sai kin fada min dalilin son raba min kan jikoki tunda kin gama fetsare kafafunki".

"Hajjo ni ba rashin kunya nazo yi miki ba. Wannan abu ba fadata bace. Da yawa mutane muna jahiltar abinda ake nufi da muharrami. A musulunce duk mutumin da ko ku kadai kuka rage a duniya aure ya haramta tsakaninku shine muharrami."

Yaya Abu tace "to ina kuma alakar jini da take tsakaninsu? Ita kuma an datse ta kenan?"

Bara'atu ta fahimci neman kureta suke yi sai dai kuma tana da hujja ba da ka tayi magana ba.
"Alakar jini bazata hana aure tsakaninsu ba wannan yasa ya zama ba muharraminta ba. Mutanen da suka amsa wannan suna a garemu sune kaka(namiji),'yan uwansa wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Haka kuma yake ga bangaren   kaka(mace), sai 'yan uwan uwa da na uba suma wanda suka hada uwa, uba ko uwa daya uba daya amma banda 'ya'yansu. Sannan sai 'ya'yan kanne maza da mata. Babban misali shine Sayyadina Ali RA kani ne ga Annabi Muhammad SAW domin iyayensu wa da kani ne. Nana Fadima bazata iya auren Abu Dalib ba saboda kawun babanta ne amma ta auri dansa duk da cewa kani ne ga mahaifinta.
Sannan ko a gidan nan Rabe da ya auri Sagira ai kanwarsa ce tunda Hajjo da babar Sagira shakikan juna ne.
Muna yawan yin kuskure sai muce 'ya'yanmu 'yan uwa ne mu bari suna taba juna ko suna shiga dakin juna kai tsaye da sunan 'yan uwan taka.( A labaranmu na soyayya muna yin wannan kuskuren duk mu  saka cousins ko 'ya'yan riko sun gama tabe taben jikin juna duk da sunan 'yan uwan taka sannan daga baya mu kulla soyayya tsakaninsu). Aya ta ashirin da uku a suratun Nisa'i ta iyakance mana su waye muharramai. Kuma
_An karbo daga Ma'qal ibn Yassar yace Manzo SAW yace: ya fiyewa dayanku a buga masa kusa a kansa da ya taba jikin macen da ba muharramarsa ba.At-Tabarani ya rawaito shi, Sheik Nasiruddeen Albani ya inganta shi a Sahih Jaami'."_

Wani kallon raini suka rinka binta dashi tunda dai ga hujja ta basu. Yaya Abu tace  da Kamilu " Kai, daga yau babu ku duka babu wadannan 'ya'yan gwal din."

Bara'atu dai kyalesu tayi ta wuce tana addua'ar kammala gininta su huta da wannan masifa.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽13

Batul Mamman💖



Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi.

Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin.

Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana ba.

Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki amsawa har sai da Qasim yayi masa magana.
"Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba"

Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa Qasim ba.

Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke ce Asmau ko?"

Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace "eh" tare da mikewa ta tafi masallaci.

An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa.

Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai  ba ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da kanta.

"Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai"

Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne kuma duk lissafi ko daya bata yi ba.
"Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin duka yake yi."

"To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido, uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics. Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero shikenan" ta fada da dariyarta.

Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin.

Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan science a gidan Mama."

"Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya amsawa idan naje nasan bazai kulani ba"

"Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?"

"Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba".

Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani rashin fahimta suka samu. Ko ma dai meye bazata bari yayi nisan da zai shiga tsakaninsu iyaye ba. Wayarta ta dauka ta kirashi. Tayi sa'a yana gida tace yazo tana son ganinsa.

*****
Dakin Mama yaje ya fada mata Umma na kiransa. Plate din da take shan kankana ta ture ta tashi.
"Jirani muje tare jiya naji Aina'u tana ta tari. Tun dazu nake tunanin zuwa duba ta."

Tare suka tafi suna 'yar hira a hanya. Umma taji dadin ganinsu su biyun. Sun dan taba hira ta kwalawa Asmau kira.

Tana fitowa da taga Abubakar sai da gabanta ya fadi...ba dai Umma kiransa tayi akan abinda ta fada ba?

A kasa ta zauna ta gaishe su. Umma ta lura tabbas bai amsa ba. Kuma bai dade da gama tsokanar Aina'u ba.

Idon Umma akan Asmau tace "dazu da nace kije Abubakar ya koya miki assignment me kika ce min"?

Cikinta har wani kullewa yayi ta daga kai suka hada ido ya harareta. Da sauri ta sauke kanta
"Uhmm, uhmm, babu komai".

Mama ta kallesu duk su biyun. Asmau a tsorace, Abubakar ya hade fuska.
"Ni kun batar dani Umma, me ya faru?"

Umma ta sanar da ita abinda Asmau ta fada da kuma wanda ta kula dashi a wurin. Duk su biyun Abubakar suka zubawa ido suna jiran amsarsa.

Dariya suka bashi ya mike tsaye " ni bata yi min komai ba. Bari na koma gida dama aiki nake yi."

Mama ta daure fuska "kaga abokan wasanka a nan ne, zauna ka fadi me ya hadaka da kanwarka. Ni bazan lamunce da gaba cikin 'ya'yana ba. Ku da su Asmau duk matsayinku daya a wurinmu."

Ita dai Asmau sai satar kallonsa take yi a tsorace.

"Mama kin tuna ranar da na sami attack har na kwanta a asibiti? Yarinyar nan fa tana cikin masallacin. Na kasa dauko inhaler a cikin aljihun wandona saboda yadda nake ji nayi ta nuna mata kuma ta gane wai sai ta fita kiranki. Da baki zo da wuri ba shikenan fa".

Umma da Mama sai dariya shi kuwa da gaske yaji haushi ya dubi Asmau itama shi take kallo.
"Da na mutu a lokacin idan ba fatalwa zan rinka yi miki ba."

Wannan karon itama sai da tayi murmushi ganin ya dan saki fuska.

Mama ta janyota jikinta "Me yasa baki bashi inhaler din ba Asmau?"

Idonta ne ya cicciko da hawaye. Umma tace " oh ni Bara'atu yarinyar nan ko baure bazai nuna mata zuba ba. Ke baki da aiki sai na kuka daga tambayar fatar baki."

Mama ce ta lallaba Asmau muryarta na rawa ta kalli Umma.
"Ba cewa kika yi haramun bane mace ta taba namjin da ba muharraminta ba. Har a islamiyya duk ana fada mana. Da na taba shi nasan fada zaki yi min sannan a rubuta min zunubi shiyasa na kira Mama".

A take Abubakar yaji wani irin yanayi game da Asmau. Shi kan shi yasan bai dace ace yana fushi da ita ba amma abinda ta fada yasa yaji ta sami wani matsayi a wurinsa. Ashe abinda tayi, tayi shi ne don bin umarnin addininta. A yadda yake matashi mai tsantseni wurin addini yana son mutane masu kiyayewa.

Yanayin kallon da yake mata ya canza zuwa sakin fuska "dauko littafin muje na koya miki kinji kanwata Idon kuka."

Sai da suka dara gabadaya sannan Umma tace "Asmau addinin musulunci yayi mana iyakokin da musulmin kwarai bai dace ya tsallakesu ba. To amma akwai sassauci akan abinda ya zama lalura. Kinga a lokacin da ya sami attack bashi da wani mataimaki sai ke kadai a wurin. Rashin taimakonsa kuskurene tunda yana cikin mawuyacin hali. Da ace akwai wani namijin to dama bai kamata ki taba shi ba. Komai na addininmu yana da sauki. Duk abinda ya zama lalura wajibi ka taimaki mutum koda kuwa baki sanshi ba. Ku tashi Allah Yayi muku albarka".

Shi Abubakar har kunya yaji. Yarinya ta fishi hangen nesa. Can gefe suka koma a cikin falon wurin wasu kananan kujeru da dan tebur a tsakaninsu. Littafin ya karba yace ta dauko text book dinta na P.N Okeke

Mama ce ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta maida hankalinta ga Umma.
"A gaskiya Umma ina yaba miki wurin kokari a tarbiyantar da yaran nan. A zamanin nan da kananan yara sun san meye mace ko namiji amma har a irin wannan yanayin Asmau bata manta da hudubarki ba. Allah Ya kara taimaka mana wurin basu tarbiya. Shiyasa nake jinki kamar kanwata ta jini wallahi."

Murmushi kawai Umma tayi.

Mama ta cigaba da magana " inama dai yaran nan su hada kansu? Wallahi ba karamin dadi zanji ba. Ji nayi Asmau ta kara shiga raina. Ni daga yau ma ta kwace matsayin auta Umar."

Wannan karon dariya Umma tayi.
"Anya wannan dan shagwabar zai yarda? Maganarki kuma akan ita da Abubakar ba tun yau ba nima nake sha'awar hakan. Allah Ya zaba mana abinda yafi alkhairi."

A can gefe inda suke yin aikin kuwa ko yaya suka hada ido sai su sakarwa juna murmushi.

Wannan murmushin sai da ya zame musu jiki. Ko karatun dare suka zo sai Abubakar yayi ta kallon Asmau har sai sun hada ido anyi murmushin nan. Ita yanzu kunyarsa take ji sosai. Shi kuma duk irin basarwar nan tasa da rashin kula mutane indai suka taru suna hira ko a gidan Mama ko gidan Umma to sai yasan yadda yayi Asmau tasa baki.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽14

Batul Mamman💖





Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji uku a jami'a sannan ansa bikinta wata hudu masu zuwa. Asmau tayi murna don lokacin ta gama jarabawa.  Karatu take yi sosai saboda don cika burinta na zama likita. Har gidan su Abubakar yaje da laptop dinsa yayi mata registration din JAMB. Anan ne ya cike mata medicine a matsayin zabin farko sai pharmacy a zabi na biyu.

Duk abinda ya shige mata gaba tana tambayarsa ya koya mata.

Gab da fara jarabar  tasu ne posting din su Abubakar ya fito an tura shi jihar Ebonyi bautar kasa. Da yaje fadawa Umma yana kula da yadda fuskar Asmau ta nuna rashin jindadi sosai. Shi kuwa hakan yayi masa don yanzu ya tabbatar ba shi kadai ne zuciyarsa ta kamu da sonta ba. Jira yake yi ta kammala makaranta sannan ya fada mata.

Watansa biyu da tafiya watarana tana dawowa daga makaranta sun gama practical din food and nutrition yamma tayi sosai wani saurayi ya tareta a hanya. Tunda ta fito daga makaranta bayan sunyi sallama da Walida kawarta yake binta a baya. Tsoro ne ya cika mata zuciya bare da yayi mata sallama ya bukaci ta tsaya. Yana bayyana mata soyayyarsa tace yayi hakuri tana da mijin aure  har ansa mata rana. Saurayin ya gamsu ya tafi. Ita kuwa a ranta gani takeyi kamar taci amanar Abubakar ne ma idan ta tsaya da wani duk da bai taba cewa yana sonta ba.

Alhamdulillah sun gama jarabawarsu lafiya sai jiran sakamako. Ranar da ta gama tana dawowa gida Umma na kitchen ta kwala mata kira. Ko kayan makaranta bata cire ba taje amsa kiran.

Umma na murmushi tace "Asmau yau an gama jarabawa ko? To ki dage da addu'a kamar yadda kullum nake yi muku. Allah Ya bada sa'a Yasa ku gama lafiya."

"Amin Ummana".

"Kije dakina akan gado duk abinda kika gani naki ne na tayin murnar gama exams. Sauran kyauta sai naga result mai kyau."

Dadi ya kama Asmau tana ta godiya ta ruga dakin Umman.

Kwalin waya ta gani akan gadon hannunta har yana rawa ta dauka tare da yin ihun murna.

Daga kitchen Umma tace "Asmau babu hamdala sai ihu ko? Kin kyauta."

Dena ihun tayi ta fara godiya ga Allah sannan ta fito falo wurinsu Jafar. Sun tayata murna Yassar yana rokonta ta rinka bashi yana yin game. Shema'u da Jafar kayansu baya tabuwa.

Jafar ya bude kwalin harda sabon sim na mtn. To dama Umma yanzu ta kara samun matsayi don har mota ta siya. Masu abu da abinsu. Duk wanda ta sayawa waya dole yayi sim din mtn.

Suna gama murnarsu ta saka hijab ta fadawa Umma zata je ta nunawa Mama. Umma tace "babu inda zaki sai kinyi wanka kin canja kaya. Kin yini da uniform kuma kice dasu zaki fita?"

Komawa tayi ciki tayi wanka ta canja kaya ta. Tare da Aina'u da Yassar suka tafi. Umma ta girgiza kai kawai tana dariya.

Da sallama ta shiga ganin Nasiba tayi a falon da danta Amir. Asmau ta karasa ta rungume Nasiba tana murna sannan ta karbi Amir.

"Tun dazu nazo fa, naje munsha hira da Umma tace kina makaranta. To ya exams din?"

Maimakon amsa wayar ta mikowa Nasiba bakin nan yaki rufuwa. Ta tayata murna suna duba wayar Mama ta fito "yau Idon kuka ce take ta murna haka kamar an baki takardar karatun likita."

"Haba Mama na dena fa. Kinga wayar da Umma ta bani."

"Masha Allah, Allah Ya tsare. A kula sosai don Allah banda yin abinda bai dace ba kinji ko. Ni zaki fara bawa numbar kuma" .

Dariya suka yi Umar yazo shima yana nacin a bashi ya gani. Kamar daga sama aka ziro hannu aka karbe wayar a hannun Umar. Da sauri tabi hannun da kallo.

Abubakar ne tsaye yana mata wannan murmushin. Yayi kyau wata uku da rabi da bata ganshi ba har kiba yayi. Ga gemu dan madaidaici ya tara shi. Fuskarsa sai tayi mata kyau.

Nasiba ce tayi dan tarin gulma wanda yasa Asmau tayi firgigit ta dauke idonta daga kansa. Mama sai ta basar kamar bata gani ba ta tashi ta bar falon.

"Bazaki gaisheni bane?" Ya fada yana zama kusa da yar uwarsa.

Kunya ta kama Asmau tace "ina wuni?"

"Tunda sai da na roka na yafe. Ni da na taho musamman saboda tayaki murnar gama makaranta ".

Nasiba ta soma dariya ganin yadda Asmau tayi kamar ace kyat ta tashi a guje. Mikewa tayi "bari naje na fara shiri ana magriba Baban Amir yace zai zo daukana."

Aina'u ta kinkimi Amir tabi bayanta. Yassar da Umar ne suka rage. Abubakar ya dan kallesu "baku da abinyi ne a ciki kuka tsaya a nan?"

Ba shiri suka tashi suka bi bayan Nasiba. Itama Asmau tashin tayi zata bisu taji muryar Abubakar yana mata magana a hankali
"not so fast Mrs A.A Matawalle. Zance zamuyi. Ko kinfi so nazo gida anjima?"

A kidime take sosai. Tana dago kai ya kashe mata ido daya.

Yau kuma me ya sami Yaya Abubakar tayi tambayar a zuciyarta.

"Soyayyarki ce ta sameni Asmy. Kuma nayi missing dinki da yawa."

Hannu tasa ta rufe bakinta don bata san maganar ta fito ba. Shi kuwa dariya ta bashi ma. Bata saba ganinsa yana nishadi kamar haka ba, sai take ganinsa kamar ba wanda ta sani ba. Duk ya canza.

Ya kula duk bata da nutsuwa kuma shima dai bazai sake ba a falon gidansu inda ake ta shige da fice.
"Ki koma gida anjima zan zo in sha Allah."

Kanta a kasa tace to ta juya zata fita. A takure take dama kamar wadda tayiwa sarki karya.

"Asmy..." sabon sunan da ya rada mata taji ya fada. A hankali ta juyo amma bata iya daga kai ta kalle shi ba.

A tsaye yake shima "dama fuskarki nake son kara gani. Sai na shigo anjima".

Bata iya yiwa kowa sallama ba ta fita da sauri. Ko wayarta bata nema ba wadda tana kallo yasa a aljihun wandonsa.

Har taje gida ta kasa gaskata maganganun Abubakar. Wai ita ya kira Mrs A.A Matawalle. Murmushi ta saki saboda sunan yayi dadi. Kai tsaye daki ta shige ta tarar Shema'u ta dawo daga makaranta.

Itama murna ta fara taya kanwarta ta sannan tace ina sabuwar wayar ta gani.

Asmau ta danyi yake "Yaya Abubakar ne ya karba zai duba amma yace zai kawo min anjima."

Shema'u tace to Allah Ya kaimu. Daga nan hira suka cigaba wadda duk akan shirye shiryen bikin Shema'un ne.

Sai bayan sallar Isha Abubakar yazo. Dayake  ranar babu karatun dare saboda Malam Hadi ya danyi tafiya.

A falo ya same su suna cin tuwo ita da Aina'u a plate daya. Yana sallama Asmau ta tsame hannunta don yadda take jin kunyarsa yanzu ko kallon inda yake ta kasa. Binta yayi da ido yana murmushi har ta shige kitchen.

Shema'u da Yassar suka yi masa sannu da zuwa ya tambayi ina Umma. Yassar ne ya kirata suka gaisa tana tambayarsa ya Ebonyi. Sun sha hira har yake fada mata bazai koma ba sai bayan bikin Shema'u. Makarantar secondary aka tura shi service kuma sun yi hutu.

Asmau tunda ta shiga kitchen ta kasa fitowa. Yana ta kallon hanya yaji shiru. Gajiya yayi ya tashi yayi musu sallama sannan yace Shema'u tazo zaiyu mata magana.

Wurin da Umma ke ajiye mota suka tsaya ya dan shafi fuska "nifa wurin Asmau nazo amma na kasa sanarwa Umma kamar yadda nayi niyya tun a gida."

Dariya Shemau tayi cike da jindadi "Allah Yayi lokaci yayi. Mun dade muna jiran lokacin nan da zaku dena satar kallon juna ayi kowa ya sani".

Ya dan daure fuska yana harararta "Ke nifa yayanki ne kike min dariya. Amma seriously ke da waye 'yan sa idon?"

"Tabdi, Yaya Abubakar kowa fa ya gano ka tuntuni. Su Umma ma duk jira suke hasashensu ya zama gaskiya. Yanzu ma da ka kalli kofar kitchen sai Umma tayi murmushi."

Kunya yaji sosai "kice kawai na dena zuwa gidan nan. Ga wayarta ki bata, ni yanzu kunyar ganin Umma nake yi ma."

Shema'u dai dariya tayi ta masa da tsokana har ya tafi. Tana shiga gida ta bawa Asmau wayarta sannan ta sanar da Umma yadda suka yi da shi. Kasa boye farincikinta tayi saboda sun jima suna jiran hakan ita da Mama. Asmau ta kira ta bata izinin zata iya tsayawa da Abubakar tunda ko yanzu za'a iya aurar da ita a shekara shabakwai. Sannan  ta ja mata kunne sosai game da kare mutumci duk da dai ta yaba da tarbiyar Abubakar.

Asmau kamar ta shige kasa don kunya wai ita Umma ke yiwa nasihar fara zance. Bayan ta koma daki missed calls ta gani da numba an sa _Mine_. Duk tunaninta tasan batayi saving numbar kowa da wannan sunan ba. Tana kallon wayar aka sake bugowa ta dauka. Muryarsa taji mai dadin sauraro musamman idan yana karatu. Ya ce
"My Asmy"

A hankali tayi magana "Yaya Abubakar?"

"Sunan da kika gani kenan da aka kira ki?"

"A'a" ta amsa tana dan murmushi

"Wane suna kika gani?"

Lallai ma Yaya Abubakar so yake ta fadi sunan da ta gani yaji dadin cewa tayi rashin kunya. Shiru tayi har kusan minti biyu babu wanda yayi magana.

Ya numfasa har tana jin sautin "idan na dameki ne bari na ajiye wayar."

Da sauri ta ce ba damunta yayi ba.
"To ki fadi sunan da kika gani don shi kadai zan rinka amsawa daga gareki idan har kin yarda nan gaba kadan ki zama matata."

Wani irin dadi taji yana ratsa zuciyarta. Bata taba sanin soyayya ba sai akansa. Muryarta kamar mai rada yaji ta ja kalmar
 "Mine"

Ji yayi kamar yafi kowa nishadi a wannan lokacin. Bai ja ta da hira sosai ba sai dai duk abinda ya fada mai tsayawa ne a rai. Da suka yi sallama wata hirarsu ta tuna da Walida inda take ce mata babu wanda ya kai ustazai wadanda suka koshi da boko kuma suka dauki koyarwar Al'Qurani da hadisi a matsayin jagoran rayuwarsu iya soyayya. Kafin tayi bacci yayi mata text ya kai biyar duk na kalamai masu ratsa zuciya.

Cikin dan lokaci kowa ya san soyayyar Abubakar da Asmau. Mama ta kara nuna mata so tamkar 'yar cikinta. Duka gidajen biyu babu wanda alakarsu bata burge shi. Ya zauna a Kano har akayi bikin Shema'u da sati daya sannan ya koma Ebonyi. Waya kam shi da Asmau kullum ne sai sunyi. Soyayya suke yi mai tsafta saboda dukkansu sun fito daga gidan tarbiya. A can garin ma shine Amir din Muslim Students' Society (MSS) dinsu suna kiransa Young Ustaz.

*****
Admission ya fito Asmau bata sami medicine ba sai pharmacy. Abubakar yace ta karba ta godewa Allah domin zabinSa a kodayaushe shine alkhairi. Haka kowa tayi registaration dinta tayi sa'a Walida ma shi aka bata saboda haka kullum suna tare.

Yana dawowa Abdulhalim yayi aure Mama tace gidan nata duk ya daye saura su biyu shi da Umar. Shima aiki yake nema ido rufe saboda a fara maganar aurensa da Asmau. Baba yayi musu gini duk su uku mazan a wuri daya gate ne ya rabasu. Amma yace daga nan kuma mutum ya nemi aiki ko sana'a sannan a fara batun aure.

Itama Umma a nata bangaren sai siyan kaya take tana ajiyewa kada biki ya tashi batayi tanadi sosai ba. Da bikin Shema'u dangin babansu na nesa sune suka bata gudummawa. Hajjo da 'ya'yanta da suke makusantansu babu abinda sukayi mata. Daurin aure dai Alh Rabe ne ya karbi sadaki...su Rabe an zama Alhaji sakamakon  kujerar Makkah da shugabar kamfanin da yake aiki Haj Rufaida ta biya masa. Shiyasa wannan karon Umma ta kara dagewa don fita kunya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽9

Batul Mamman💖




Mal Yahaya dakansa ya rinka yiwa Hajjo fada amma ta takura Bara'atu. Lokacin Shua'aibu yaje gyaran gidan da zasu koma a Zaria. Yana dawowa ya tarar da mahaifinsa a kwance shine suka kaishi asibiti shi da Rabe. Likita ya duba shi aka ce malaria ke damunsa. Magunguna kawai aka rubuta suka dawo gida.

A tsakar gida Hajjo tayiwa mijinta shimfida suka kwantar dashi yana shan iska shi kuma Shu'aibu ya tafi siyan magani. Fitarsa keda wuya Rabe ya karasa kusa da Hajjo yace
"Hajjo likitan fa yace basu gane kan cutar dake damun Baba ba. Idan bakiyi wani abu ba duk sai mayun nan sun cinye mu."

Hankalin Hajjo ya kara tashi. Rabe yaji dadin hakan. Bashi da burin da ya wuce asa dan uwansa ya saki Bara'atu shi kuma ya aura. Tun farkon haduwarsu yaji yana sonta. Duk wasu alamu ya nuna mata inda tayi masa tatas shine ya koma zuga Hajjo suna muzguna mata. A dalilin bata son hadashi da dan uwansa ne yasa bata tona masa asiri ba tunda dama babu mai kaunarta sai mijinta. Ko ta fada kila bazasu yarda ba.

A fusace Hajjo tace "Bara'atu fito nan muguwa mai mugun nufi".

Bara'atu tana kitchen ta fito da sauri ta durkusa. Lokacin bacci ya fara daukar Baba amma hayaniyar Hajjo tasa ya farka.

Sai da ta gama harararta sannan ta dubi Rabe "fita ka nemo min abokanka majiya karfi koda biyu ne"

Murmushin mugunta yayiwa Bara'atu sannan ya fita. Ba jimawa suka dawo su uku. Hajjo ta tashi ta nuna musu Bara'atu da Bintu "gasu nan, so nake ku sa su tsallake Malam sau bakwai ko na samu su saki kurwarsa. Bari naje na debo garwashi na kunna turaren mayu."

Bara'atu tayi matukar razana ta soma rokon Hajjo tayi hakuri. Ko kallonsu bata sake yi ba tayi gaba abinta tana masifa. Ganin haka yasa ta kama hannun Bintu zasu shiga daki su rufe Rabe ya fizgota. Suna ihu da kuka ya rike Bara'atu wani kato ya daga Bintu yana tsallaka Malam Yahaya da ita a kafadarsa.

Mal Yahaya jiki babu kwari ya kasa tashi sai daga kwance yake kokarin yi musu magana amma babu mai sauraronsa.

Bayan sun gama da Bintu suka ajiyeta sannan Rabe da dayan suka kama hannu da kafafun Bara'atu suna shillata ta saman Malam. Kuka dai tayi har muryarta ta dashe. A karo na biyar da shilla ta da suke yi Shu'aibu yayi sallama ya shigo.

Abinda da ya ga kaninsa yana yiwa matarsa yasa yaji wani mugun daci a wuya. Shi kanshi Rabe ba karamin tsorata yayi ba suka yar da Bara'atu yayi ciki inda Hajjo take tahowa da kasko fal garwashi.

Ko tunanin daga Bara'atu, Shu'aibu baiyi ba. Kan Rabe yayi da gudu ya damko shi. Dukansa yake kamar ba jininsa ba yana zaginsa. Hajjo tayi iya kokarinta amma bai sake shi ba sai da ya gaji don kansa ya koma ya daga matarsa yana haki.

Hajjo ta durkusa ta daga Rabe. Baki da hancinsa duk jini. Rai a bace tace " yanzu saboda wannan yarinyar kayiwa dan uwanka irin wannan dukan? Meye laifinsa don yana son ceto rayuwar mahaifinsa. Kuma ni na saka shi".

"Yanzu saboda Allah Hajjo ko Bara'atu ba matata bace abinda akayi mata yayi daidai kenan? Duk abinda akeyi ina dauke kai darajar Baba amma na rantse duk wanda ya sake shiga sabgar iyalina sai hukuma ce zata raba mu."

Da hannu Mal Yahaya yayi masa alama ya durkusa a gabansa. Hakuri baban nasu  ya sake bashi da alkawarin idan yaji sauki zai dauki mataki.

Bayan kwana uku ciwonsa ya kara tsanani suka je wani asibitin aka ce typoid ce taci hanjinsa ma. Dama irin abinda ake gudu kenan. A kai mutum asibiti babu  gwaji su hau dirka masa magani. Washegari Malam Yahaya ya cika. Iyalinsa sun sha kuka sosai. Bayan wata daya Shu'aibu ya hada nasa iyalin suka koma Zaria. Hajjo dai ta kullaci Bara'atu don ta yarda dari bisa dari su suka kama Malam.

Tunda suka koma Zaria suke samun budi. Bara'atu har kiba ta soma yi kuma ya samar mata gurbin karatu a ABU Zaria tana karanta Public Administration. Duk sati Shu'aibu yake zuwa Kano amma baya tafiya dasu. Da tayi magana yace babu amfani tunda ba kaunarta sukeyi ba. Itama Hajjon don neman magana ta tambayeshi yace hakan ya fiye musu kwanciyar hankali.

A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah. Shekara bata zagayo ba Bara'atu ta haifi Shema'u. Danginsu na Wushishi sun zo sosai tunda mijinta yana bari taje ganin gida. Daga Kano ma su Yaya Abu sun zo sai dai ba'a rabu lafiya ba.

Bayan shekara daya da rabi ta haifi Jafar sannan Asmau. Shu'aibu yana kula dasu sosai. A lokacin Bintu ta gama secondary akayi bikinta.

Haka suke zamansu lafiya ga jari ya bawa Bara'atu tana sayar da kayan sawa na mata a cikin gida. Sai lokacin sallah kawai suke zuwa Kano ko idan wani abu ya faru. Basu da wata matsala a lokacin. Asmau nada shekara hudu aka haifi Yassar.

Wata rana da yamma Shu'aibu yana zaune a falo tare da iyalinsa Rabe ya zo. Shi da matarsa ne Laraba da yaransa biyu. Baraatu bata nuna wata damuwa ba tayi musu tarba mai kyau. Laraba mace ce mai mutumci shiyasa basu dauki lokaci ba suka saba a dan zuwan da suke yi Kano.

A can falo kuma Rabe yake sanar da yayansa yazo ne zasu dan kwana biyu shi da iyalinsa. Ko kadan Shu'aibu bai so hakan ba sai dai ya kyale yaga iya gudun ruwansa.

Shiru basu da niyar tafiya ita kanta Laraba har kunya take ji. A sati na uku Shu'aibu ya dawo daga makaranta zai shiga dakinsa yaji muryar Rabe yana rokon Bara'atu da ta amince masa wannan zuwan ma duk nata ne.

Daga murya tayi tana fada tace cikin kuka "idan baka fita ba sai nayi maka tonon asirin da bazaka kara mutumci ba a duniya. Matarka fa tana gidan nan. Ko don kaga tuntuni ina rufa maka asiri?"

Murya kasa kasa yace "ki amince Bara ko ba a gidan nan ba. Ni sau daya ma kawai ya isheni. Ki taimaka."

Ihu ta kurma a tsorace ganin yayo kanta Shu'aibu ya bude kofar ya shigo. Yau ma iya karfinsa yasa yana duka Rabe. Abu yayi tsanani har Laraba ta jiyo su ta fito. Korarsu yayi a yamman yace ya fice masa daga gida.

Laraba na fahimtar abinda ke faruwa ta tattara ko jiransa batayi ba ta kwashi yaranta suka tafi. Shu'aibu yayi kukan bakinciki sosai sannan yayi mata fadan rashin sanar dashi da wuri.

Washegari da safe yace mata zai je Kano ayi maganar a gaban Hajjo don yasan Rabe yanzu yanzu zai juya zance. Haka kuwa akayi Hajjo tace sai ya saki Bara'atu ko ta tsine masa. Jiya Rabe ya dawo gidan jina-jina saboda sharrin data kulla masa. Duk yadda Shu'aibu yayi Hajjo taki yarda. Laraba ma data bada shaida akan Rabe a take Hajjo tasa ya saketa.

A kan hanyarsa ta komawa ne Shu'aibu yayi hatsari. Bacin rai ne ke damunsa saboda Hajjo tace idan har bai saki Bara'atu ba sai dai ya sake wata uwar.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽10

Batul Mamman💖

www.fikrahwriters.blogspot.com


Bara'atu ta gama girkinta tayi wanka sannan tayiwa yaranta. Albishir gareta ga maigidanta idan ya dawo wanda take tunanin zai rage masa bacin rai. Ciki ne da ita har wata biyu. Dayake ranar babu islamiyya su Jafar sai wasansu suke yi a gida.

Sallamar maza taji a kofar gidan ta dauki mayafi ta fita. Ga mamakinta har da 'yan sanda biyu. A tsorace ta  gaisa da su sannan guda cikin 'yan sandan ya miko mata ID card ko ta gane wanda yake jiki.

Tana ganin hoton jikinta ya fara rawa "ku fada min abinda ya same shi"

Wani mutum a gefe yace "Hajiya sai dai hakuri a hanyar shiga gari muka ga motarsa yayi hatsari. Allah Yayi masa rasuwa".

Kuka Bara'atu ta saka har yaranta suka fito. Ganin Ummansu na kuka suma suka fara. Bare Shemau da Jafar masu wayo sosai.

Cikin dan kankanin lokaci sauran abokan aikinsa suka zo. Bintu da mijinta ma duk sun zo da makotansu. Karfe uku suka kama hanyar Kano.

Basu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan Marigayi Mal Yahaya a unguwar  kofar mazugal. Hajjo tayi kuka sosai na rasuwar danta sai fadin irin halinsa na hakuri da kawaici take yi. A nan aka yi masa sutura aka kaishi.

Bara'atu duk ta rame a cikin 'yan kwanakin nan saboda tashin hankali. Saukinta daya shine canjin data gani a tattare da Hajjo. Mutuwar ta daketa sosai shiyasa duk tayi sanyi. Sabanin yadda ta saba yanzu tana jan su Shemau a jiki. A da kuwa sai dai tace su dena kallonta da kwala-kwalan idanunsu na mayu.

Bayan sati biyu da rasuwar gabadaya 'ya'yan Hajjo suka taru da Kawun Bara'atu tare da wani malami da Rabe ya kira akan rabon gado. Kafin malamin ya fara jawabi Bara'atu ta sanar dasu cewa tana da ciki.
Ran Rabe yayi matukar baci ita kuwa Hajjo abin yayi mata dadi. Dole aka hakura da rabon gado sai ta haihu.

Da amincewar Hajjo ta koma Zaria saboda makarantar yara.  Tausayin Bara'atu ne kawai ya kamata tun bayan rasuwar Shu'aibu.

Bayan wata shida ta haifi 'yarta mace Hajjo da kanta ta zaba mata suna Aina'u. Yarinyar duk tafi sauran 'yan uwanta kama da mahaifinsu shiyasa ta shiga ran Hajjo sosai. Kano suka dawo lokacin kafin tayi arbain. Kwana goma da haihuwar Bara'atu Rabe ya sake dawowa da Malamin rabon gado. An gabatar masa da dukkan kadarar Shu'aibu wanda ya hada da motarsa guda daya da kuma makeken gida da ya gama ginawa a unguwar Hotoro sai 'yan kudade a banki da kuma wanda wurin aikinsu suka bawa iyalinsa sai kuma wata gona a Zaria. Malam ya gyara zama
"Tunda mamacin yana da 'ya'ya da mata sannan mahaifiyarsa tana da rai duk 'yan uwansa basu da gadon shi."

Rabe yaji kamar an kwada masa guduma "Malam ya zaka ce bamu da gado? Dukkanmu fa uwa da uba daya muke. Ni nan da kake gani shi ya saki nono na kama ko ba haka ba Hajjo?"

Malam yayi murmushi "Alh Rabe ai shi rabon gado ba'a yi masa katsalandan. Allah SWT da Kansa Ya raba saboda haka babu wani son zuciya a nan. Zan nemi 'yan uwana malamai kamar mutum biyu sai muyi abinda ya dace. Allah Ya jikan Alh Shu'aibu".

Malamin na fita Rabe ya soma fada ya dubi 'yan uwansa. Babu wanda yace masa komai. Dama Garzali karamin cikinsu baya shiga sabgarsu sosai shaye shayensa ne a gabansa. Yaya Abu da Lami ma basuyi magana ba ganin Hajjo tayi shiru. A haka taron ya watse Bara'atu na mamakin wannan hali na Rabe.

Har daki Rabe yabi Hajjo tana daga kwance akan gado ta tashi zaune.

Ya numfasa yace "Hajjo kina jin malamin nan. Yanzu banda sharri yace bamu da gado. Nufinsa wannan gidan da Yaya yake ta shirin komawa Bara'atu da 'ya'yanta ne kadai zasu tare?"

Hajjo tace "banda abinka Rabe ai haka rabon gado yake. Da so kake ace kaima ka shiga gidan ko yaya? Dubi fa yadda ya sake gyara gidan nan. Ni bana son tashin hankali. Kada na sake jin zancen nan ya taso". Da haka ta kashe maganar.

Kwanaki biyu a tsakani Malamin ya dawo aka zo akayi rabo daidai da sharia. Gida da mota duk sun fada rabon Bara'atu da 'ya'yanta. Gonar Zaria an sayar aka fitarwa Hajjo nata sauran duk na 'ya'yansa ne. Bakin cikin Rabe baya misaltuwa. Ya kwallafa rai sosai akan gidan. Bara'atu ta koma Zaria suka fara shirin dawowa Kano gabadaya.

*****
Rabe zaune gaban wani malamin tsibbu ya gabatar masa da bukatarsa ta son a toshe bakin Hajjo duk abinda ya fada ta amince.

Dariya Malamin yayi sannan ya karbi kudin aikinsa. "Indai wannan ne matsalarka an gama."
*****

Bayan sati daya Hajjo ta zaunar da Rabe fuskarta cike da damuwa " idan baka fada min matsalarka ba wa kake dashi wanda ya fini?"

Kansa a kasa yayi dan murmushin takaici "Hajjo ko na fada bazaki amince ba. Gani kike yi kamar cutar da iyalin dan uwana nake son yi".

"Ko kadan Rabe, fada min abinda ke ranka".

"Dama nayi tunani ne bai kamata na bar zuri'ar Yaya ta wulakanta ba. Kinga matarsa tana da sauran kuruciya. Idan tace zatayi aure waye muka sani da zai kula da ita da 'ya'yan da zuciya daya? Ni a tunanina ta bani su tunda mun rabo da Laraba sai na kara aure na rikesu gabadaya. Ko kuma....."

"Ina jinka, ko kuma me?"

Dan murmushi yayi mai nuna yana jin kunyar abinda zai fada "nace ko zaki yi mata magana ta amince na aureta. Kinga sai mu zauna tare gabadaya da yaran. Babu zancen a rabata da 'ya'yanta."

Shiru Hajjo tayi yana tunani.."yanzu matar da ko wata uku batayi da haihuwa ba kana ganin ba'ayi wauta ba idan aka bijiro mata da zancen aure?"

Dadi yaji batayi fada ba "nima ba wai yanzu yanzu zan ce ayi auren ba. Kawai dai tasan da maganar ne".

Hajjo ta kada kai "shawararka tayi kyau , ranar asabar zata zo su fara kawo kayansu sai kayi mata magana a lokacin.

Asabar da yamma Bara'atu na shayar da Aina'u a tsohon dakinsu Rabe ya shigo babu ko sallama.

Da sauri taja rigarta ta suturta jikinta rai a bace. Wani kallon kasa kasa yake mata yana murmushi.
"Mutum da kayansa meye kike wani rufe jiki"?

Maganarsa ta bata mata rai tayi yunkurin tashi yace ta zauna magana zasuyi. Zama tayi a nan ya sanar da ita bukatarsa. Hade rai tayi tana kallonsa a wulakance.

"Rabe bahaushe yace in maye ya manta uwar da bazata manta ba. Duk irin cin kashin da kukayi min a gidan nan don rashin kunya zaka ce kana son aurena. To ni ba shashasha bace,  nasan sarai abinda kake nema a gareni. Gida ne ya tsokale maka ido kake son mu koma daga nan dani da yaran da abinda kake ganin sun samu mu koma mallakinka. To wallahi kayi kadan. Ko mazan duniya sun kare bazan aureka ba."

Hajjo ta shigo tana kallon yadda Bara'atu take fadawa danta magana. Tuni ta rufe ido ta fara fada.

" yanzu saboda yana son rufa miki asiri kike masa wannan rashin mutumcin? Idan har baki aure shi ba to ki sani dole ki bashi yaran nan."
Fada sosai Hajjo tayi Bara'atu bata tanka ba. Washegari ta koma Zaria suka karasa hada kayansu wata mai zuwa zasu taho idan sun karbi takardun yara na makaranta.
*****

A nasa bangaren Rabe yayi ta zuga Hajjo akan ta bari ba sai ya auri Bara'atu ba kawai ta amince ya zauna a gidan da nasa yaran sai ya hada duka ya kula dasu. Itama Hajjon ta zo a tare da ita tunda gidan akwai dakuna.

Yaci galaba domin Hajjo ta amince. Sannan tace ya nemi mata yayi aure. Ita ya barwa zabi ta hadashi da 'yar kanwarta. Bayan sati uku aka daura aure amarya ta tare a sabon gida a Hotoro. Ba ayi mata kaya da yawa ba saboda kusan komai na amfani Shu'aibu da Bara'atu sun saka.

Kwanan amarya biyu su Bara'atu suka iso Kano. Kayansu ta kwatantawa masu mota aka kai hotoro ta wuce kofar mazugal. Makota ke sanar da ita su Hajjo sun tashi. Tayi mamaki sosai to ina suka koma?  hotoro ta wuce da sa ran zata je gidan Lami a kwatanta mata inda suka koma.

Suna isa gate din gidan Jafar ya fita ya budewa mijin Anti Bintu da ya tuko su a motar da yanzu ta zama ta Bara'atu ya shiga. Yaran Rabe su biyu ta gani suna wasa a waje ga Hajjo zaune karkashin bishiyar goba tana shan iska.

A sanyaye Bara'atu ta karasa kirjinta na dukan uku uku. Hajjo ta washe baki tana yiwa jikokinta maraba. Bara'atu ta gaisheta tana kallon kofar gidan a bude.

Hajjo tayi tsaki "ya naga duk jikinki yayi sanyi ne? Ki kwantar da hankalinki nayi tunanin bai kamata na matsa miki ki auri Rabe ba shine muka dawo gabadaya a taro a kula da marayu. Kuka ne ya tasowa Bara'atu sai dai kafin ya kai ga fitowa ta ga Sagira yar kanwar Hajjo ta fito Garzali yana binta a baya yana tsokanarta.

Hajjo ta saki murmushi "ga amaryar Rabe fa shekaranjiya ta tare. Bari tazo ta nuna miki dakunanku ke da yara. Daki har biyu Rabe yace a baku. Su Jafaru dakinsu yana nan kusa da na kawunsu Garzali"

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Bara'atu ke fada saboda tsananin bacin ran da take ji a wannan lokacin.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽16

Batul Mamman💖




Wannan karshen satin tun alhamis Abubakar yazo. Kullum sai yaje wurin Asmau sunyi hirarsu yadda suka saba. Ranar asabar ya wuce Shanono wurin Qasim suka je daurin auren wani dan uwan Qasim din. Daga nan suka koma gidansu sai zuwa yamma yayi niyar komawa cikin Kano.

Zaune suke a dakin Qasim suna kallon ball wayar abokin nasa tayi kara. Rage sautin TV din yayi ya amsa wayar. Ya dan jima suna hira d wadda Abubakar ya fuskanci mace ce sai daga baya yaji akalar hirar ta canja. Qasim yana tambayar yarinyar wane irin kaya ta saka.

Murmushi yayi bayan ta bashi amsa "me kika saka a ciki?"

"Ni kwance nake a daki da shorts(gajeren wando) ina shan iska ina tunaninki" (karya yakeyi. Kufta da wando ya saka).

Irin wannan hirar ya kusa rabin awa suna yi da budurwarsa. Abubakar sai kada kai yake don takaicin wannan hali na Qasim. Yayi fadan da nasihar har ya gaji gashi ya kasa rabuwa dashi saboda shakuwarsu. In dai hirar banza ce a waya to Qasim ya ciri tuta. Sai ance ya fidda matar aure yace duk mata babu tagari.

Mugun kallon da Abubakar yake jifansa dashi yasa ya katse wayar yana dariya.
"Ya Ustaz irin wannan harara haka. Ni fa bance ka tsaya jin hirar ba duk ka wane hade rai."

"Yanzu bazaka dena wannan muguwar dabi'ar ba? Ina jiye maka tsoron kada watarana kayi me gabadaya. Kasan zuciya bata da kashi".

Kujerar kusa da Abubakar ya dawo ya zauna.
"Kaima kasan duk abuna bazan yarda nayi lalata da 'yar mutane ba. Irin wannan hirar dai da dan abinda ba'a rasa ba shi muke yi don mu rage yawa.

Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma matan suna so. Sai a taimaki juna".

Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA SAA'A SABILA*
(ISRA' 32)

Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_

Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu azo ana cizon yatsa."

Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai shaidan bai barshi ba.
"Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take. Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse."

Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka".

Qasim ya dubi abokinsa. Tabbas Abubakar ba tun yau ba baya cikin maza masu kallon mata. Shiyasa ake masa kallon mai kunya sosai shi kuwa yana yi ne don ya kare zuciyarsa.

"In Allah Yaso zanyi kokarin denawa sai dai fa abin sai a hankali. Bazan maka karya ba wallahi na saba sosai. Allah mun tuba."

Da haka hirar ta kare bayan la'asar Abubakar ya koma gida.

*****
Washegari lahadi Umma ta tafi da Aina'u yinin 'yar wata kawarta sai Asmau da Yassar a gida Abubakar ya kirata a waya zai zo suyi sallama don yau da wuri yake son tafiya.

Sauri tayi ta karasa girki sannan tayi wanka ta canza kaya. Kwalliya tayi sosai irin yadda take karantawa 'yan matan littafi na yiwa samarinsu. Ta saka wata doguwar rigar atampa maimakon ta daura dankwali tasa hijab ko mayafi mai mutumci yadda ta saba sai ta dauko wani karami a kayan Aina'u ta yafa rabin kanta da yasha sabon kitso duk a bude ta gaba. Falo ta koma ta zauna sai taji kunyar ya ganta a haka. Ta tashi ta koma zata canza wata zuciyar tace tayi zamanta abinda sun kusa aure kuma dai haka ake yi yanzu don ita duk abinda ta karanta har ranta gani take yi daidai ne saboda a yadda ta dauki marubuta masu buga littafi da online komai suka rubuta basa kuskure.

Sake shafa hoda tayi ta dawo falon. Tana zama Abubakar yayi sallama tare da neman izinin shigowa ta amsa masa.

Gabansa ne ya fadi da yaga Asmau. Tayi kyau sosai gashi tana da 'yar kiba sai rigar ta kamata a kirji da kugunta. Ba wai bai taba ganin yanayin jikinta ba saboda yau da gobe yakan ganta babu mayafi  amma sai bisa kuskure. Yau kuwa shigar ta tsaya masa a kokon rai har ya kasa dauke idonsa daga gareta.

Murmushi tayi na nasara saboda yadda taga yanayinsa ya canza. Tunda ta fara karance karance da hirarsu da Walida taji ta matsu ko hannunta ne ya dan rike itama taji yadda ake ji.

Wani juya ido tayi duk sauran kunyar suka bace "Mine ka zauna mana."

Wani jan numfashi yayi "Asmy kinyi kyau"

Tayi masa murmushi "nagode"
"Kaci abinci ko na kawo maka? Bana son ka tafi da yunwa".

Abincin ya bukaci ta kawo masa. Ta tashi tana tafiya mai daukar hankali. Har ta shige kitchen ya kasa dena kallonta. Sai da ta bace yace _Astagfirullah_ tare da kudurta niyyar zaice ta suturta jikinta sosai.

Tana dawowa kujerar gefensa ta zauna kamshin turarenta ya bugi hancinsa sai ya fasa cewa ta rufe jikin. Yana matukar son Asmau amma yau harda wata muguwar sha'awarta ce ta taso masa. Yana cin abinci suna hira kadan kadan domin duk hankalinsa ya koma kan halittar jikinta.

A nata bangaren ta lura da canjawarsa kuma taji dadi a ranta. Da ya tashi zai tafi dubu biyu ya miko mata kudin motar makaranta. A da sai ya bata sau uku bata karba ba har suyi fada wani lokacin. Amma yau kawai don taji hannunsa a nata ta mika hannun a kunyace tana kallon kasa. Tana sane tayi hakan hannunta ya kai kan nasa maimakon kudin.

Saurin dauke hannun tayi  saboda wani yanayi na daban da taji (dama shaidan komai kankantar haram dada mata dadi yake fiye da yadda take don kawai a cigaba da aikata ta)
"yi hakuri ban kula ba"

Abubakar yaji dadi fiye da yadda taji domin tana taba hannunsa ji yayi kamar ya janyota jikinsa. "Dama ina zaki kula kina wani sunkuyar da kai kasa. Ni zan tafi sai friday in sha Allah. Ki kular min da Asmy na".

Tana murmushi tace
" nima  ka kular min da Yayana. Allah Ya tsare Ya kaika lafiya."

Haka Abubakar ya tafi surar Asmau tana yi masa gizo. Sawa yayi a ransa idan sunyi waya zai fada mata ta dena irin shigar nan har sai sunyi aure. Sai dai yana isa bayan sallar magriba wasu hotunanta suka shigo wayarsa. Duk babu wanda tasa dankwali kanta wasu ma rigunan sun dameta fiye da rigar dazu.

Bai iya yi mata maganar da yayi niyya ba ya rasa dalili.

A haka suka kwashi wajen wata biyu. Asmau ta dena jin kunyar fita gabansa da shigar bayyana jiki indai tayi sa'a yazo Umma bata gida. Mayafin nan kullum a kafada an baza gashi ta kasan dankwali. Tun yana tsanar kansa idan suka rabu har ya saki rai yana jindadin hakan tunda yasan aurensu yana kusa. Kusa da juna suke zama yanzu ana hira sai su rinka neman hanyoyin taba hannun juna kowa yana nuna kamar ba hakan bane a ransa.

Sai yanzu Asmau ta yarda suna soyayya domin tafi jindadin alakarsu. A zuciyarta ta kwantar da hankali tunda tana da yakinin aure zasuyi kuma dai ana aure komai ya wuce. Ita yanzu babban burinta yayi kissing dinta ko sau daya ne yadda take karantawa. Ayi kiss amma sai a nuna kamar bisa kuskure ne ko kuma a nuna na komai yin hakan a addini da al'adarmu.

A nasa bangaren shima ya dena damuwa. Kullum  sha'awarta karuwa take yi a ransa hakan yasa ya soma rasa nutsuwarsa. Bashi da aiki sai azumi kamar mai kaffara amma wasu ranakun shi kansa yasan a irin tunanin Asmau da yake yi na tsantsar sha'awa azumin nan baya kaiwa ko ina.
*****

Su Asmau an gama jarabawa kuma wannan karon suna dawowa makaranta idan aka sake hutu za'ayi bikinta.

Ko sati ba suyi ba da fara hutu Anti Bintu tazo Kano ziyara. Kwananta biyu mijinta yazo da zasu koma tace da Asmau zata tafi. Umma bata musa mata ba ta umarceta da hada kaya. Murna tayi sosai Aina'u kuwa ansha kuka gashi ba'ayi hutu ba.

Abubakar yaji dadin komawar Asmau Zariya wani satin da ya zagayo ko Kano bai je ba. Mama Yalwa tace ta gane dama zuwan ba nasu  bane na Asmau ne.

A gidan Anti Bintu yake zuwa su sha hira wadda a hankali ya fara rungumarta da sunan zaiyi kewarta idan ya tafi. Su biyun duk sun san haramcin abinda suke yi amma sunyi nisa. Suna haduwa duk yakin da suka shirya da wannan sabuwar dabi'ar tasu sai ya rushe.

Anti Bintu ko kadan bata san me suke yi ba. Falonta take bar musu idan yazo. Nutsuwa da tarbiya irin ta Asmau da Abubakar babu wanda zai taba zargin haka tsakaninsu.

Wata rana bayan asuba karamin dan Anti Bintu Haidar yana toilet bayan ya gama ya fara kiran Asmau tazo tayi masa tsarki. Lokacin ko bakwai na safe bata yi ba duk baccin da take ji taki komawa saboda an turo cigaban wani labari da take karantawa. Ko yunkurin tashi bata yi ba tace masa tana zuwa.

Haidar ya kirata yafi sau biyar tana cewa gata nan har Anti Bintu ta fito daga kitchen tayi masa tsarkin lokacin har ya fara kuka. Duk abinda suke yi da Asmau ta ji.

Dakin nasu ta shiga Asmau tayi nisa a duniyar labari sai ganin Antin tayi a tsaye a gabanta. Da sauri ta tashi a tsorace zata fita.

"Dawo indai tsarki zaki yiwa Haidar nayi masa"

Duk sai taji kunya sannan ta gaisheta. Anti Bintu ta dauki wayar da ta ajiye akan gado ta bude ta dan karanta wani bangare na labarin. Tayi scrolling sama kuma irin sakon nan ne na kwanciyar aure.

Jikin Asmau kamar mazari don tsoro ta gama rudewa. Anti Bintu ta kama hannunta ta zaunar da ita a bakin gado sannan taja kujerar gaban mudubi ta zauna.

"Kin bani mamaki Asmau. Wannan wane irin text ne kike karantawa? Yanzu kwanciyar aure har sai wata can da baki sani ba ta koya miki? Wannan abu halitta ce wadda idan lokacin yinta yayi baka bukatar malami. Idan kuma har akayi rashin sa'a mace ko miji suka  matsala ta fannin gamsar da juna to ba duniya zaki fadawa matsalarki ba. Mutum daya zaki samu cikin 'yan uwa ko abokan arziki wanda zaki iya bawa amanar sirrinki sai ki fadi matsalar a baki shawara. Amma me ya kaiki karanta irin wannan post din wanda ko matar aure ce ta karanta da wuya idan bai karya mata alwala ba saboda yadda ake bayani 6aro-6aro. Kada ki bari kawayen banza suce ya kamata a koya miki irin wannan tunda kin kusa aure. Komai yana da lokaci. Kodayake masu rubutawa sunfi kowa laifi tunda kayi rubutu ne baka san iya idanunwan da zasu karanta ba. Wayar nan yarinyar da bata fara jini ba ma tana da ita kuma akan same su a groups din manya suyi ta sakin baki a gaban 'ya'yan cikinsu. Wani lokacin sai su tura yara masu karfin sha'awa su karanta a tayar musu da hankali su fara neman mafita. Ki rufawa kanki asiri ki dena karanta abinda bazai amfaneki ba.

Abu na biyu wannan novels din da kike karantawa. Nima babarki ina karantawa amma ki sani akwai wanda har ki gama babu wani darasi da zaki dauka sai bata lokaci da tabarbarewar tarbiya. Uwa uba kuma wannan mugun son da muke yiwa labaran yana sawa mu manta da al'amuran da suka fi bukatar hankulanmu.

Tun zuwanki gidan nan na fuskanci kin canja sosai. Kina idar da sallah ko azkar baki gama ba sai ki janyo waya. Har akwai wani labari da zaisa ki kasa hakurin minti biyar ki bautawa Allah cikin nutsuwa? Mata irinki da yawa gasu nan. Sau nawa girki yake konewa ko mace ta yini cikin kazanta saboda karatun labari wanda a ciki tsafta da kula da miji ake koyarwa? Wata ma bata girkin akan lokaci sai taji mijinta ya kama kofar gida zai shigo ta ruga kicin. Wata ta bar yaro da kazanta har sai ta gama karatu. Wata kuwa da wayar zata shigo bandaki tana biyan bukatarta tana karanta labari. Idan hakane karatun labaran masu dauke da darussa bai amfanemu da komai ba sai kasala, ganda da kazanta.

Ki zama mace mai tsari a rayuwa komai kiyi shi a lokacin  da ya dace. Babu abin takaici sai kinga mace da tsakar dare ko asubar fari tana cigiyar novel ga mijinta a gefe bawan Allah kila yaso ta bashi hakkinsa na aure ma amma ya hakura don kada ya takurata. Idan mara hakuri ne ayi ta samun sabani.

Asmau nasan Yaya Bara tana kokarinta a kanku. Gashi aiki yayi mata yawa duk don biya muku bukatu. Kada ki watsa mata kasa a ido da dabi'u marasa kyau kinji ko".

An tuno da Idon kuka ana mata fada tana sana'arta. A take tayi nadamar daukar shawarar Walida wanda yasa take yin abubuwan da a da can tasan basu dace ba. Kukanta ya tsananta da ta tuna tabbas irin yadda suke gudanar da soyayyarsu yanzu yana da alaka da canjin da ya fara tasowa daga gareta. Wai ita ce suke rungumar juna da Abubakar. Abubakar dinta mai riko da addini ta zama sanadiyar da suke munafuntar kawunansu da iyayensu.

Anti Bintu ta cigaba da yi mata nasiha mai ratsa zuciya sannan ta tashi. A ranar ta ga canji sosai a wurin 'yar tata. Asmaunta ta da ta dawo.
*****

Abubakar na kwance a daki yana kallon wasu hotunan Asmau. Tun daren jiya da ta turo ko baccin kirki ya kasa yi. Yau da ciwon mara ya tashi irin wanda ake samu idan sha'awa tayiwa mutum yawa. Ya rasa abinda yake masa dadi ko office ya kasa zuwa. Shawara ya yanke zaije Zariya a ranar ko dan yaya yayi dan abinda zai kwantar da kwadayinsa. A yadda yake sonta bazai iya neman wata matar a waje ba. Ita dinma bashi da niyar ayi mai gabadaya ta bakin Qasim. Dan dai abinda ba'a rasa ba yadda sai samu yaji dadi. Da wannan shawarar ya tashi yayi wanka ya hau shirin zuwa Zariya.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽17

Batul Mamman💖




Kafin ya fito ya kira Asmau a waya ya sanar da ita zai zo. Jikinta a sanyaye ta amsa masa don ita yanzu kunyar ganinsa take yi. Ko ba'a fada ba daga nasihar Anti Bintu tasan cewa duk abinda ya faru laifinta ne.

Har daki taje ta sanar da Anti Bintun zai zo kamar yadda ta saba.
"Ki dora abinci dashi amma ki bar dan waken sai gobe don bazan bawa suriki dan wake ba"

Ita da Asmau duk dariya sukayi sannan ta wuce ta dora shinkafa da miya.

Wuraren karfe uku ya iso Anti Bintu tazo suka gaisa sannan ta basu wuri.

Yau Asmau hijab ta saka dogo har kasa fuskarta babu kwalliya sai hoda da kwalli. Jikinta duk babu kwari tayi nadama sosai. Abubakar kuwa tamkar ya hadiyeta da kallo. Anyi sa'a yaran gidan suna ta gilmawa a falon. Da laasar suka tafi islamiyya  shi kuma yaje yayi sallah.

Ana idarwa ya dawo ya kalli Asmau dake zaune a can gefe.
"Asmy dawo nan kusa dani nafi jindadi". Ya nuna kujerar gefensa.

Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Tana zama ya kama hannunta ya rike yana lumshe idanu. Can kasa take jin muryarsa
"I love you so much Asmy. Ina ma anyi aurenmu kiga irin abinda nake nufi."

A kwanakin baya har so take ya rike mata hannu amma yau sai taji ta tsani hakan. Tana son nuna masa kuskuren abinda tasan ya fita sani amma dole tabi lamarin a hankali kada yayi mata mummunar fahimta ko yace ta mayar dashi dan iska.

Har lokacin tafiyarsa yayi bata iya sakin jiki dashi ba. Shi kuwa gabadaya ya kasa samun nutsuwa. Bakin motarsa da ya ajiye a wajen gate ta raka shi ai kuwa yana bude motar ya rungumota jikinsa. Dama layin ba mutane sosai  saboda unguwar bata gama cika ba ga duhun dare.

Wasu hawaye masu zafi Asmau taji sun taho mata ta hadiye. Dole ta sami lokaci suyi magana da Abubakar akan wannan abin. Rungumar da take jindadi daga gareshi yau bata so. Tana wannan tunanin taji yayi mata abinda bai taba yi ba. Abinda take ta mararin faruwarsa. Bakinsa ya hada da nata yayi mata rikon da bazata iya kwatar kanta ba koda tayi niyya.

Hawayen da take boyewa ne suka sakko ganin Abubakar tamkar baya cikin hayyacinsa. Abubuwan da yake  mata sun fara wuce gona da iri. Ba shi ya saketa ba sai da don kansa yaji hankalinsa ya fara dawowa gareshi.

Ganin tana kuka ya soma bata hakuri.
"Asmy kiyi hakuri please. Na rasa dalilin da yasa nayi miki hakan. Ki sani ina sonki tsakani da Allah kuma in sha Allah bazan sake kwatanta miki haka ba sai munyi aure".

Yadda yake maganar sai ya bawa mutum tausayi. Tabbas baya son abinda yake yi sai dai karfin sha'awarsa da tsananin rudin shaidan yasa ya kasa hakuri.

A hankali ta share idonta "Yaya Abubakar don Allah mu dena irin wannan abin kaga babu kyau."

"Na sami Asmy, ni kaina na rasa gane yadda akayi muka fada ga  wannan masifar. Ki share idonki kinji matar Abubakar".

Kafin ya tafi sai gashi ta sake sosai hankalinta ya kwanta. Suka rabu zuciyar kowa tana nata sake saken.
*****

Abubuwan da suka gudana tsakanin Abubakar da Asmau su suka rinka yi masa yawo a kwakwalwa. Yayi tunanin zaiji saukin sha'awar dake damunsa sai abin yayi tsanani sosai. Kullum cikin mafarkinta yake yi. Baccin kirki ya gagare shi sai tunanin yadda zaiyi ko dai a matso da aurensu ko ya kashe yunwarsa ko sau daya ne.

A nata bangaren hatta hirar da suke yi a waya yanzu tana kame bakinta daga hirar da bata dace ba. Ta tarkarta tunaninta kaf zuwa lokacin aurensu ko sa sami nutsuwa da kwanciyar hankali saboda tasan duk su biyun yanzu a matse suke da ganin wannan lokacin.

Bayan kwana biyu ya sake zuwa wannan karon ko waya baiyi mata ba. A hirarsu da Anti Bintu ya nemi izinin ranar asabar da Asmau zata tafi zai zo ya kaita da kansa a cewarsa baya so ta shiga motar haya.

Anti Bintu tayi shiru na dan lokaci saboda ba haka sukayi da yayarta ba. Dama tasha za'a kaita ta tafi saboda motar Kawu Yusuf tana gareji wurin makanike. A duk dan tunaninta bata hango wata matsala ba duba da irin siffa ta kamala da suke dashi su biyun.

Asmau kanta bata ji komai ba saboda yau hirarsu duk irin ta da ce. Cikin nutsuwa da kiyayewa. Soyayya mai tsafta irin wadda masu yinta basa son rabuwa da juna.

Kwanaki ukun da suka zo kafin tafiyarsu Abubakar yaji babu dadi. Har wani zazzabi ne ya kamashi saboda ji yake tamkar ana hura masa wutar sha'awar kasancewa da mace. A yadda yake ji ko ba Asmau bace wannan karon zai iya nema.

Ranar da zasu tafi wurin karfe goma ya iso. Asmau da yaran harda dan kukansu na rabuwa.

Suna mota ita da Abubakar babu wata hirar kirki don basu taba kadaicewa a mota haka ba na tafiya mai nisa.

Hanyar cikin gari ya nufa ya kashe motar a gefen titi.  Asmau ta kalle shi zata yi magana sai ta kasa ganin idanunsa sunyi wani iri kamar wanda yake cikin tashin hankali.

A raunane yake dubanta har sai da tsigar jikinta ta tashi don tsoro da ya dora hannunsa a kan nata.

"Asmau"

Yaushe rabon da ya kirata da sunanta haka. Gabanta na dukan uku-uku ta amsa.

"Idan na rokeki alfarma zaki yi min?"

Ita fa Yaya Abubakar tsoro yake bata da yanayinsa na yau.
"in sha Allahu idan baifi karfina ba".

Gwauron numfashi ya ja.
"Asmy ina cikin matsala kuma ke kadai ce zaki iya yi min maganinta. Ko sati ba'ayi ba da muka amince mun dena taba jikin juna.."

Bugun zuciyarta ne ya karu tana ganin kamar ta fara fahimtar inda zancensa ya dosa.

"Ni mutum ne mai yawan bukata, ina tsammanin baki san me hakan yake nufi ba."

A ranta kuwa tace sai dai na fadawa wani. Rabe-raben mutane ta fannin sha'awa tuni ta san shi a posts din waya. Muryarsa wadda take rawa taji a kusa da ita.

"Ina cikin tashin hankali da son kasancewa tare dake. Wallahi bazan iya kaimu Kano ba a yanayin da nake ji yanzu musamman da kike zaune kusa dani. Ki taimakeni ko sau daya ne na kawar da wannan masifaffen tunanin."

Kofar motar ta kama a gigice hawaye na wanke mata fuska jin ya saka lock. Sanyin AC bai hanata gumi ba.
"Yaya Abubakar ka rufa min asiri ka mayar dani gidan Anti Bintu. Duk ni na jawo wannan matsalar da na rinka saka kaya masu matse jiki ina zama kusa da kai. Sharrin shaidan ne da na zuciya don Allah kayi hakuri nan da wata hudu zamuyi aure fa".

Magiyar da take masa jin muryarta yake kamar tana masa busa. Wannan wace irin masifa ce??? Shiyasa tun a da yake nisanta daga duk abinda zai jawo masa sha'awa tunda ya gane yanayinsa.

Hawaye ne ya zubo a idonsa wanda bai san dalilinsu ba.
"Ke kadai nake so kuma da ke kadai na amince Asmy. Idan baki amince ba wallahi nayi miki rantsuwa zan nemi wata. Bani da lafiya duk a dalilin sonki da son kusantarki. Ko kinsan satin nan ko sau daya banje wurin aiki ba saboda halin dana tsinci kaina a ciki".

Kuka Asmau take yi sosai gashi tausayinsa ya mamaye zuciyarta.
" Yaya kada mu aikata haram. Kuma idan ka rabani da abinda duk budurwa take takama dashi yaya zanyi?"

Hannuwanta duka biyun ya rike. "Asmy kinsan dai nine mai aurenki ko? Kuma ni ba wai zanyi miki yadda zaki tashi daga budurwa bane. Akwai yadda zanyi babu wanda zai ce namiji ya kusanceki. Ki taimake ni.

Har bincike nayi wasu malaman sunce kudin aure daidai yake da sadaki. Ko baki ga iyayenmu maza ke zuwa ba ayi a gaban shaidu. Al'ada ce kawai sake taruwar da ake yi a daura aure. Amma yanzu ma a haka ni da ke matsayin mata da miji muke." Shi da yake fada mata hakan ya tabbatar karya yake yi amma babu yadda ya iya da zuciyarsa.

Roko da rarrashi haka ya rinka yiwa Asmau tana kuka haka ta amince saboda tausayin da ya bata da tsoron kada ya nemi wata.

Wani hotel ya sama musu kuma da yake duk sunyi shigar mutunci babu mai cewa ba ma'auratan gaske bane. Haka ya karbi mukullin dakin zuciyarsa tana kwabarsa da abinda yake shirin aikatawa amma gangar jikinsa bazata iya hakuri ba.

A kofar dakin da kyar Asmau ta shiga. Yana rufe kofar ta kara fashewa da kuka. Abubakar yayi nisa duk da yana tausayinta hakan bai hanashi biyan bukakarsa ba. Alkawarin da yayi mata na yin dabara kada ta rasa budurcinta tuni ya manta dashi.

Sai da komai ya kammala yaji kamar tashin hankalin duniya duk ya kare a kansa. Gefen gado ya koma ya dafe kai ya rasa inda zaisa kansa.

Asmau tana kwance sai sautin kukanta ke tashi. Ga ciwo ga bakinciki.

Sun kusa awa daya sannan yayi wanka ya umarceta da itama tayi. Wannan masifa da yawa take...Ya Allah Ka tsare mana imaninmu.

Haka suka fito babu wanda yake yiwa dan uwansa magana. Ya biya kudin hotel suka wuce Kano yana ta zabga gudu a hanya.

A bakin gate din gidansu ya sauketa zuciyarsa tana kuna. Ya rasa me yake ji game da Asmau. Ko kayanta bai taimaka mata da dauka ba haka ta fito dasu ta shige gida fuska a kumbure.

Su Umma sai murna suke yi ta dawo amma ganin yanayinta Umman ta tsorata tana tambayarta abinda ya faru.

Asmau ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta. Yau taci amanar addininta kuma taci amanar Umma.

Taruwa suka yi a kanta Jafar ya taba jikinta. Zazzabi ne sosai a jikin hatta kanta ya dau zafi.
Ya danyi murmushi "Umma wannan 'yar taki ta fiye shagwaba da raki. Daga zazzabi kuma sai kuka?"

Sai a lokacin tayi dan murmushi ganin cewa idan ta cigaba da kukan zata tonawa kanta asiri.
"Yaya Jafar ji nake kamar kan zai tsage biyu"

Umma ta tasheta tsaye
 "Ki dena tsorata ni irin haka Asmau. Baki ji yadda gabana ya fadi ba. Muje ki dan watsa ruwa sai kici abinci kisha magani. Ina Abubakar din?"

Har zuciyarta ta razana jin an ambaci sunansa.
"Ya tafi gida amma yace zai shigo ku gaisa anjima".

"Babu komai ai kun sha hanya ga rana. Allah Yasa ba kukan nan naki kika rinka yi masa ba saboda baki jindadi."
*****

Har washegari Asmau tana kiran wayar Abubakar saboda bai zo ba kamar yadda tayi tsammani. Babu waya babu text. Nata kiran kuma yaki dauka. Hankalinta yayi matukar tashi. Yanzu idan ya fasa aurenta saboda abinda suka yi yaya zata yi da ranta.

Shima a gida kwana yayi kuka. Idan yaga wayar Asmau ji yake kamar yasa ihu. Zuciyarsa ta kasa rabe masa haushinta yake ji don ta bashi kanta ko kuwa haushin kansa da ya tilasta mata.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽18

Batul Mamman💖




Bacci barawo ne ya sace Asmau ba don taso ba. Ta raba dare tana kuka wanda ya haddasa mata mugun ciwon kai ga jikinta da yayi tsami. Washegari wurin karfe takwas da rabi ta fito daga dakinsu zata shiga kitchen dora ruwan tea ta tarar Umma har ta dama kunu tana buga kosai.

 Gaishe da Umman tayi sannan ta yunkura zata karbi aikin ta karasa Umma tace ta bari ya jikin nata. Kafin ta amsa Umma ta dakatar da ita
"Asmau ki fada min gaskiya meye yake damunki? Ji yadda fuskarki ta kumbura ga wata tafiya kina yi kamar me tatata".

A dan tsorace Asmau tace "zamewa nayi a toilet da zanyi alwala."

Umma ta bita da kallo na rashin gamsuwa.
"To fuskar taki fa? Kinsan bana son boye-boye idan rigima kuka yi da Abubakar jiya ki fada min tun wuri ayiwa tufkar hanci."

Murmushi Asmau ta kalalo "Umma lafiya kalau muke. Kaina ne har yanzu yake ciwo sosai kamar bansha magani ba".

"Idan anyi breakfast sai Jafar ya kaiki asibiti tunda dai kin sha magani jiya bai warke ba gara kiga likita sosai. Allah Ya sauwake. Bari na soya kosan sai kici kiyi wanka."

Jikinta a sanyaye ta fita ta koma daki tayi wanka.  Zuciyarta ta gama raunana amma cigaba da kukan bazai amfaneta da komai ba sai tonon silili.

Umma kuwa sai tattalinta take yi har daki ta kai mata abinci tana ta sannu. Wannan ya kara sawa taji ta tsani kanta. Ji yadda mahaifiyarta ke kula da ita bayan ciwon nata baya bukatar tausayawa daga kowa.

Sunje asbiti tasha allurai saboda zazzabi sannan aka bata magunguna.

Da suka koma gida Umma ta sanar da ita Abubakar yazo amma ya wuce Kaduna ana nemansa akan wasu takardu da ya kulle a office. Kai kawai Asmau ta gyada ba don ta yarda ba. Daga dawowarsu zuwa wayewar gari tayi masa text yafi goma banda waya da ba'a kirgawa. Gani take yi kawai zai gujeta ne kamar yadda take yawan jin labarai na samari da suke yaudarar 'yan matansu.
*****

Kafin azahar Abubakar ya isa Kaduna. Jiya ko kadan bai runtsa ba sau tunani da ya addabi zuciyarsa. Ji yayi Kanon tayi masa zafi shiyasa ya dawo saboda baya son yawan tambaya akan me yake damunsa.

Kwanansa biyu da dawowa  baya zuwa ko ina daga office sai gida sai ko masallacin unguwar da yake. Rabonsa da abincin kirki ma ya manta. Yana kwance ya kurawa fanka dake juyawa ido wayarsa tayi kara.

Sunan Qasim ya gani shiyasa ya dauka. Qasim ya sanar dashi wani aiki zai kawo shi garin yanzu zai kamo hanya. Addua Abubakar yayi masa sannan ya dan gyara dakin da ko shara baya samu.

Tun zuwan Qasim ya kula da canjawar da abokinsa yayi. Yayi tambayar har ya gaji babu amsa. To me zai fada masa?

A nata bangaren Asmau ji take yi kamar tayi hauka. Tayi wayar har ta gaji. Hawayenta ma ya kafe jira take kawai azo ace Abubakar ya fasa.
*****

Ranar juma'a da safe Abubakar ya gama shirin tafiya office Qasim yace
"Karfe nawa zamu tafi Kanon?"

"Wannan satin bazan je ba ayyuka sunyi min yawa" Abubakar ya bashi amsa.

Kayan da yake sawa a 'yar jakarsa ya ture ya koma kallonsa "Abubakar nayi nayi ka fada min abinda ke damunka kaki na rasa dalili. Ni mai sonka ne da alkhairi idan ka fada min ko addua sai na tayaka".

Kwalla yaji ta cika masa ido ya dan dake "na fada maka babu komai bari naje na dawo mu tafi. Shikenan ko".

Qasim dai bai gamsu ba. Yana nan zaune aka kawo wuta ya saka wani CD na wa'azi da ya gani a kusa da tv din dakin. Ko minti goma ba'ayi da farawa ba Abubakar ya shigo lokacin shabiyu saura.

Zamansa ke da wuya aka yiwa malamin dake wa'azin tambaya akan ZINA. Malamin yace
"Lallai zina tana daga cikin manyan kaba'ira da Allah SWT Yayi hani dasu. Ban da lalacewar zamani yanzu da muka dauketa ba a bakin komai ba zaka ga yawanci duk addinin duniya yayi hani da zina saboda muninta da kazantar dake cikinta. A cikin suratul Furqan ayoyi na 69 zuwa 71 Allah Yana cewa
*WADANDA BASA DAUKAN WANI BAYAN ALLAH A MATSAYIN UBANGIJI KUMA BASA KASHE RAI BA BISA SHARI'AH BA, KUMA BASA ZINA WANDA DUK YA AIKATA HAKA ZAI SAMI ZUNUBI DAIDAI AKIN DA YAYI*.
*ZA'A NINKA MASA AZABAR RANAR ALKIYAMA KUMA ZAI KASANCE A CIKINTA HAR ABADA*.
*SAI WANDA YA TUBA KUMA YAYI IMANI KUMA YA AIKATA AIKI MAI KYAU, WADANNAN SUNE ALLAH YAKE CANZA MUSU ZUNUBANSU ZUWA GA LADA. ALLAH MAI RAHMA NE MAI JINKAI* Abin duba a nan shine an lissafa zina da ayyuka masu matukar muni wato shirka da kisan rai ba tare da hakki na shariah ba"

Haka malamin ya cigaba da janyo ayoyin AlQurani da hadisan Annabi SAW wadanda suka yi hani da zina ko azabar dake jiran masu yinta.

Ya kawo aya ta 32 a cikin Sural Isra' wadda Allah Madaukakin Sarki Ya umarce wadanda suka yi imani da kada su kusanci zina.

Sai aya ta 2 a cikin suratun Nur wadda Allah SWT Yake cewa: *MAZINACIYA DA MAZINACI IDAN SUKA YI ZINA KU BULALI KOWANE DAYA DAGA CIKINSU BULALA DARI. KADA KUWA WANI TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA TABBATAR DA HUKUNCIN ADDININ ALLAH IDAN KUN KASANCE KUN BADA GASKIYA GA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA LALLAI NE WATA TAWAGA DAGA MUMINAI SU HALARCI WURIN YI MUSU HADDIN*

Abubakar da Qasim duk hankalinsu yana ga bayanin wannan malami. Duk su biyun jikinsu yayi sanyi musamman Abubakar da yasan abinda ya aika.

Malam mai wa'azi cikin bayaninsa ya kawo hadisin Bukhari wanda Annabi SAW yake cewa _MAZINACI BA SHI DA IMANI A LOKACIN DA YAKE AIKATA ZINA...._

Da wani hadisin na Abdullahi ibn Mas'ud  wanda yake cewa _MUN KASANCE TARE DA ANNABI SAW MATASA MARASA KOMAI NA DUKIYA_. _SAI ANNABI SAW YACE DAMU_:
_YA KU SAMARI, WANDA YA SAMI IKO A CIKINKU YAYI AURE DOMIN YAFI AKAN KARE KALLO DA MUTUMCI. WANDA BAZAI IYA BA SAI YAYI AZUMI SABODA ZAI ZAME MASA KARIYA._

Kallon kallo ne ya koma tsakanin Abubukar da Qasim a lokacin da malamin ya soma bayanin lahira da tanadin da Allah SWT Yayiwa bayi masu biyayya da masu sa6o. Ya karanto ayoyin Suratul Haaqqa wurin da Allah SWT Yake fadan irin farincikin da masu aikata aiki nagari zasu shiga idan sun karbi littafinsu da hannun dama da tanadi mafi kyau da Yayi musu a aljannah. Da kuma tashin hankalin ma'abota sabawa Allah a lokacin da suka karbi nasu littafin da hannun hagu(Ya Allah Kasa bama cikinsu. Amin) da azabar da zasu tarar.

Duk da Qasim ya shiga tashin hankali da jin wadannan bayanai saboda abinda yake aikatawa na shafa jikin 'yan matansa saboda gusar da sha'awa, yayi matukar mamaki ganin Abubakar ya fashe da kuka. Dafa abokin nasa yayi yana cewa
"Ba kaine zaka yi kuka ba Abubakar. Ni ne ya kamata nayi kuka saboda nasan na sabawa Allah sosai. Irin wannan abin da na fada maka akalla nayi da mata wurin biyar."

Abubakar ya kalle shi hawaye na kwararo masa." Qasim nawa sabon yafi naka. Na cuci kaina na aikata zunubin da bana hangowa kaina komai sai azaba."

A tsorace Qasim ya dago kan Abubakar dake kallon kasa" ban fahimceka ba, kada dai kace maganarmu ta rannan tasa kaima kaje kayi romancing wasu. Na shiga uku, ai ni ne cikin matsala tunda duk wanda yayi umarni da mummunan aiki yana da zunubi kwatankwacin na wanda ya aikata kamar yadda yake ga mai umarni da kyakkyawa".
Dafe kansa kawai yayi yana tunanin wannan sabon tashin hankali da ya saka kansa a ciki.

Zuciyar Abubakar cike da danasani yace "Qasim zina nayi"

"What??? Abubakar garin yaya? Da wa?"

Sai da ya hadiyi yawu da kyar ya iya amsawa "Asmau".

Qasim yana girgiza kai yana karanto La haula...
"Marainiyar yarinya, wayyo Abubakar ni ne sila ko? Tun yaushe ne? Garin yaya ka aikata hakan kai da ka kusa aure? Idan aka gane fa? Ga mahaifiyarta mutuniyar kirki."

Tambayoyin da Qasim keyi shima Abubakar din sune suke masa yawo a kansa. Yana hawaye ya sanar da Qasim abinda ya faru da irin kunya da bakincikin da ya sami kansa a ciki. "Yanzu shikenan nima da hannun hagu zan karbi littafi na ranar lahira. Lallai Annabi SAW yayi gaskiya da yace a hadisi na hudu cikin arba'una na Annawawi wanda aka karbo daga Ibn Mas'ud yake cewa ..
_......Hakika dayanku zaiyi ta aikata aiki irin na 'yan aljannah har sai ya kasance tsakaninsa da ita bai wuce zira'i ba sai littafinsa ya rinjaye shi sai ya aikata aiki irin na 'yan wuta sai ya shigeta...._

Qasim ya soma hawaye " in sha Allahu bazamu shiga wuta ba. Ka manta Allah Yayi alkawarin yafe zunubin masu tuba.?"

Sai da suka sha kukansu sannan Abubakar ya bawa Qasim wayarsa ya karanta wasu cikin sakonnin text da Asmau ta turo masa.

_Yaya Abubakar ka dubi girman Allah ka daga wayata. Kada ka gujeni a wannan lokacin_

_Idan ka rabu dani rayuwata bazata kara wani amfani ba. Me zan fadawa duniya nan gaba._

_Kai kadai ne zaka iya taimakona a wannan halin. Ka daure kada ka fasa aurena._

_Na amince ko washegarin aurenmu ne ka sakeni wallahi bazan yi korafi ba. Amma yanzu idan ka kini duk wanda ya aureni zai iya tona min asiri._

Kasa kara karatun Qasim yayi saboda tausayin Asmau da ya kama shi. Sun dauki wasu mintuna babu mai magana sai muryar malamin nan kawai suke ji yana kara tsorata mutane game da aikata zina.

Qasim ya tashi tsaye yana kashe kayan wuta na dakin dake kunne "ka tashi mu tafi ka bawa yarinyar nan hakuri sannan mu san yadda zamuyi su Baba su amince a matso da bikin nan zuwa wata biyu tunda kace mai hayar naka har ya gama ginin da wuri."

"Kana ganin zasu amince? Wata hudu ya rage da 'yan kwanaki yanzu nace a maido shi baya?"

"A nawa ganin hakan ne zai kara kwantarwa Asmau da hankali tasan cewa da gaske bazaka gujeta ba. Wallahi Abubakar ban taba zaton   zamu wayi gari mu ga rana irin wannan ba. Ba don da bakinka ka fada min ba Allah bazan taba yarda ba."

Rufe dakin suka yi sannan suka fita zuwa motar Abubakar. Qasim ne zai tuka su. A hanya suka sami masallaci sukayi sallar juma'a sannan suka wuce Kano suna ta tattauna yadda zasu bullowa su Baba domin su yarda a dawo da bikin baya. Kafin su rabu sai da Abubakar yasa Qasim yayu masa alkawarin wannan zancen zai zama sirri a garesu har mutuwa.

*****
Ko gida Abubakar bai shiga ba yana sauke Qasim ya tashar unguwar kabuga zai wuce Shanono, gidansu Asmau ya wuce kai tsaye. Lokacin Umma na wurin aiki ita kuma tana daki tana sana'ar kuka. Ta gama sawa ranta Abubakar ya gujeta kenan yanzu abinda ya faru matsalarta ce ita kadai. Jafar ne ya buga mata kofar daki ya sanar da ita zuwan Abubakar.

A zabure ta tashi ta lulluba mayafi ya rufe mata rabin fuska ta fita ta same shi a wurin da Umma ke ajiye mota.

Tana zuwa gabansa bata yi la'ari da cewa wani zai iya ganinsu ba ta zube gwiwoyinta a kasa tana kuka mai sauti.
"Don Allah Yaya Abubakar kada kace kazo rabuwa dani. Gara na mutu da in ga ka juya min baya a wannan yanayin."

Waigawa yayi ya tabbatar babu mai ganinsu sannan yayi mata alama da ta tashi. Shima hawayen yake shirin yi.
"Asmy kiyi hakuri ki yafe min. Naci amanarki na cutar dake. Amma ina so kisan cewa bazan gujeki ba. Wannan tsautsayin ni ne na tilasta miki saboda haka tare zamu fuskance shi. Idan kin amince zanyi magana a gida a dawo da bikinmu nan da wata biyu".

Wani hawayen ne ya sakko mata ga dariyar farinciki duk a lokaci daya.
"Da gaske? Wallahi na amince. Na yarda. Nagode Yaya Abubakar."

"Ki dena yimin godiya. Ni dake duk bamu fi karfin kaddara ba. Kuma kowane bawa akwai irin jarabawarsa a duniya. Dama Annabi SAW yace _Shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake yi._
Kinga ashe bamu fi karfin fadawa tarkonsa ba. Sai dai Ubangijinmu mai rahma ne da gafara. Idan muka tuba sai kiga kamar ba'ayi ba."

A sanyaye yake maganar ciki da nadama.

Daga wannan lokacin suka fara azumi da tashi cikin dare neman gafarar Allah. Yaso samun matsala da su Baba amma daga baya sun amince an matso da auren. Tun daga lokacin Asmau take bashi girma fiye da na da, tsoro take yi kada ta kuskure yace ya fasa asirinta ya tonu.

Haka lokaci ya tafi har zuwa bikinsu da abinda ya faru bayan nan.

*****
*CIGABAN LABARI*

Asmau ta share hawayenta bayan ta gama bawa Zubaida labarinta. Ita ma Zubaidan kukan take yi na tausayi ga bakuwar da kwanansu daya da haduwa amma jininsu ya hadu.

"Tabbas kinga tashin hankali a rayuwarki Asmau. To amma abinda ya daure min kai shine yadda kuka tuba amma duk da haka kika tsinci kanki a irin wannan rayuwar".

Dan murmushi Asmau tayi "Zubaida kenan, tubanmu ba shi zai hana faruwar kaddarar rayuwarmu ba. Komai da kika gani ya faru ga bawa rubutaccen al'amari ne tun kafin zuwansa duniya. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama darasi ga wasu don su kiyaye. Ni bana bakinciki da ikon Allah. Nasan bazai barni na tabe ba albarkar Annabi SAW."

Zubaida ta gyada kai ta gamsu da bayanin Asmau.
"Allah Ya jikan Abubakar"

Asmau tace "Amin " tana share kwalla.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽20

Batul Mamman💖




Wani mugun fitsari ne ya tashi Asmau daf da kiran assalatu. Ta fito zata je bandaki amma ko ruwan tsarki bata dashi. Haka ta koma daki tana ta matse shi da adduar Zubaida ta fito da wuri ko dan yaya ne ta sammata. Har aka idar da sallah a masallaci Zubaida bata fito ba. Zuwa lokacin Asmau sai gumi take yi tana cilla kafa. A hankali taji ya fara zubowa dole ta tafi bandakin da gudu tayi batare da tayi tsarki ba. Haka ta dawo dakinta ta shafi kura tayi taimama sannan tayi sallar asuba.

Batun jin yunwa dama ba'a magana. Wannan yanayin da ta tsinci kanta a ciki hakurinta ya fara karewa. Ace tayi fitsari ko ruwan tsarki babu gashi tana gani amma gidan nafsi nafsi (kowa na ta kansa)kawai ake yi.

Yau Zubaida bacci sosai take yi don har tara ta wuce bata farka ba. Asmau ta gaji da jiran tsammami ta duba hijabinta wanda yafi kowanne dauda ta saka ta fita bakin titi. Ga rana ta kwale haka ta daure zuciyarta ta zauna duk wanda yazo wucewa tace.

_Sadaka fisabilillah_

Mutumin farko da ya bata naira goma yana yin gaba ta saka kuka. Wai ita da watanni kadan da suka wuce take cikin rayuwar jindadi tare da masoyinta da iyayenta, ita ce take bara tamkar mara galihu. Bara sana'ar da take tattare da kaskanci da mutuwar zuciya. A ranta addua take yi Allah Yasa mufi karfin zukatanmu Ya nesanta mu da kaddara mai muni irin wannan.

Ita kenan ma da tayi nadama amma Allah Ya zabeta don gwada imaninta da kuma nuna aya ga sauran mutane. To ina masu aikata zinar duk da sun san laifine amma basu dauketa a bakin komai ba. A ganinsu suna da sauran lokaci. Ina masu bada muguwar shawara a baki ko a rubuce batare da yin la'akari da tasirin da hakan yake yi a zukata masu rauni ba. Da Abubakar bai tuba ba shikenan haka mutuwa zata riske shi yana halin sabawa Mahalicci.

Taci kuka har ta godewa Allah a wurin. Har rana ta take naira hamsin da biyar ta hada. Ga jiri na dibanta saboda tsabar yunwa. Tashi tayi ta kama hanyar gidan da yanzu shine matsuguninta. A hanya ta sayi fanke na naira hamsin din da pure water guda daya.

Dakinta ta wuce wanda ko jawo kafar batayi ba. To me zata rufe bayan bata da komai. Fanken nan ta janyo tana ci hannu baka hannu kwarya. Ko uku bata ci ba sai amai ya taso mata. Dole ta hakura ta dan jingina da bango tana adduar kada ya fito don ta dan ji kwarin jikinta.

Ba don tana gudun mutuwar kafirci ba gani take yi a wannan lokacin gara ta mutu ta huta. Tana jin shigowar Uwargida ta tashi ta bita daki. Bazata iya cigaba da bara ba gara kawai tayi abinda zai fishshe ta a nata ganin.

" 'Yar Da6as yau tun safe kina ina?"

Asmau ta dan waiga bayanta tana dube dube.

Uwargida tace "indai Zubaida kike nema na kaita wurin uwargijiyata a wannan sana'a. Girma ya fara kamani dolenta ta nema mana kudi. Yaya Babba zata koyar da ita ta karfin tsiya sannan ta dawo gidan nan ta taimaka wurin dago darajarsa kamar da."

Tausayin Zubaida ya kama Asmau. Yarinyar da bata kaunar zaman gidan ma bare sana'arsu ace wai mahaifiyarta da kanta take son lalata mata rayuwa. Sai dai babu taimakon da zata iya yi mata yanzu. Kanta a kasa tace "idan kina da maganin zubar da cikin ki bani".

Wata shewa da tafi Uwargida tayi cike da murna. Tasan za'a rina. Wannan yanzu idan ta fara bawa Asmau abinci na sati tuni zata murmure ta fara caskar kudi da ita.
" kin taimaki kanki kuma na tabbatar bazaki yi dana sani ba muddin kika fara jin jakarki da nauyi. Bari na dauko miki wani jiko da na bawa Darling kwanaki."

Uwar dakinta ta shige ba jimawa ta fito da wata robar swan da ta dafe da datti. Ruwan ciki kore ne fatau ga wasu 'ya'yan ball suna ta shawagi a ciki. Asmau na ganin robar taji amai na yunkurin fitowa. Toshe bakinta tayi ta karbi robar ta fita bayan Uwargida tayu mata bayanin yadda zata sha.

Tun da ta ajiye robar ko kallon wurin bata sake yi ba. A matsayinta na wadda take da ilimi daidai misali tasan shan wannan kazantar babbar illah ne gareta.

Washegari wurin karfe goma ta tashi ta shiga cikin kasuwa. Tasha yawo sannan Allah Ya sa taga abinda take nema wato chemist(kemis). Daga saman an rubuta *SADA AND SONS CHEMIST*.

Mutane ne suke ta shige da fice a wurin ta rakube daga can gefe tana jira suyi sauki ta je ta roki mai kemis din ko zai taimaka mata da maganin zubar da ciki. Sama da awa daya bata ga alamun mutanen zasu yi sauki ba har ta gaji ta soma gyangyadi a gefen wani benci da aka ajiye a wurin shagon.

Cikin bacci taji an soma kiraye kirayen sallar azahar ta bude ido tana hamma sannan ta dan kalli kofar shagon ta ga akwai mutum daya a ciki har yanzu. Daga can nesa  ta hango wani yaro da kayan makaranta da flask din abinci ya nufo wurin shagon. Ta tashi ta kade jikinta da niyyar idan ya iso zata roke shi ko ya rage abinci ya bata.

Yana zuwa kuwa ta dan sauke murya.
"Don Allah in ka rage abincin makarantar ka bani in ci".

Yaron da zai kai shekara goma yana da dan jiki ya kalleta yayi murmushi
"Kwanon abincin makarantana na mayar gida. Wannan na babanmu ne na kawo masa".

Daga haka ya shige cikin shagon. Ba dadewa suka fito wurin 'yar rumfar kofar shagon inda bencin yake. Yaron ya ce "Baba kaga almajirar da tace na bata abincin naka".

Mal Sada mai kemis ya dan kalli Asmau. Tabbas babu wanda zai mata wani kallo daban da na almajira. Dogon mutum ne mai dan haske da kiba. Fuskarsa kadai zata nuna wa mutum yana da kirki.

Da hannu ya yafito wata mai awara yarinyar ta karaso da gudunta don kada 'yan talla 'yan uwanta su riga ta zuwa. Ya zira hannu a aljihu ya dauko naira dari ya mika mata.
"Zuba wa matar nan ta sittin sai ki bata canjin. Abba miko mata ruwa a cikin fridge dinnan guda biyu."

Mai awara da Abba suka yi yadda Mal Sada ya saka su. Asmau na karba ta rinka yi masa godiya da fatan alkhairi sai ka zata ta dade tana sana'ar bara.

Mal Sada ya dan daure fuska "nan ba wurin zaman almajirai bane kinji ko. Idan kin gama ci ki tafi."

Ta gyada kai ta koma gefe ta zauna. Da ledar ruwa daya ta wanke hannunta ta fara cin awarar cikin jindadi. Rabonta da abincin kirki ta kwana biyu. Tana gamawa tasha ruwa sannan ta dauki daya ledar ruwan tayi alwala ta shimfida dankwalinta tayi sallah. Lokacin tuni Abba ya tafi. Sada yana kallonta sai ta burge shi da bara bata hanata ibada ba.

Bayan ya dawo daga masallaci yana bude shagon kafin kowa ya shiga ta bi bayansa. Sai kuma kunya ta hanata fadin abinda ya kawota.

"Kina bukatar wani abu ne?"

Kamar mai rada tace "nawa ne maganin zubar da ciki?"

Cak ya tsaya yana kallonta. Wato ban da bara har jikinta take sayarwa. Ransa a bace yace "idan baki fice min daga nan ba ranki zai baci. Ku baro gidajenku kuna bara saboda mutuwar zuciya karshe almajirai da marasa zuciya irinku su rinka yi muku ciki. Ko ina dashi bazan bayarba."

Asmau ta soma kuka tana rokonsa ya taimaka mata.

Daga hannu Sada yayi kamar zai maketa shiyasa ta fita. Amma a kofar shagon nan ta zauna har taran dare lokacin da yake rufewa. Ko kallonta baiyi ba da zai wuce tana ta masa magiya.

Washegari tun kafin yazo shagon ta iso. Yinin ranar da ta ga babu mutane sosai sai ta shiga ta roke shi. Tun yana mata fada ta fita har ya dena kulata sai ta ga wani zai shigo ta fice a sanyaye.

Dansa Abba ya sake kawo masa abinci amma yau bai bi ta kanta ba. Yana ciki yana cin abincin ne ya jiyo kakarin amanta. Tun awarar jiya bata sake samun wani abincin ba.

Kamar ya share sai ta bashi tausayi ya dauko flask din ya mika mata. Idanunta sun kara fitowa waje sai hakora gayau kamar ta shekara tana jinya. Kusan fizgar flask din tayi ko wanke hannu bata yi ba ta soma cin abincin. Abinda bata taba ji bane ya faru a wannan lokacin. Motsi taji a cikinta wanda ya kara tabbatar mata lallai ba ita kadai take rayuwa ba. Yanayin da ta shiga da jin motsin yasa ta farinciki ta dafe cikin. Tunowa da Abubakar da halin rayuwarta kuma yasa ta koma yin kuka. Abincin da bata iya cinyewa ba kenan.

Da Sada zai tafi ta mika masa flask din yace ta rike ya bar mata. Yana kallonta ta tafi har ta bace masa.

*****
Sau biyu kenan Rashida tana fadawa maigidanta ta kai masa ruwan wanka sai yace to ina zuwa. A karo na uku ta zauna kusa dashi cikin damuwa.
"Baban Abba me ya faru ne? Allah Yasa ba laifi nayi ba."

Dan murmushi Sada yayi yana kallon abar kaunarsa.
"Ko kadan Maman Abba. Bari nayi wankan dai."

Sai da ya gama cin tuwo sannan ya bata labarin Asmau mai zuwa kofar shagonsa.
"Ni bansan daga ina take ba sai dai ta bani tausayi. Muna ganin kanmu kamar marasa arziki amma wallahi cikin rufin asiri muke akan wasu. Tsorona daya kada taje wurin wani mara imanin ya bata maganin."

Rashida tace "to ai dama kaine kullum kake ganin kamar shagonka kadai baya wadata mu. Amma gashi yara hudu duk suna makaranta kuma bama rasa abinci.
Idan bazaka damu ba gobe sai na kawo maka abincin da kaina na ganta. Kila idan  na bata shawara ta hakura da zubar da cikin ta koma gida".

*****
Asmau ta dauko robar da Uwargida ta bata. Tana son sha kuma har ranta bata son zubar da cikin. Dama gudun zubarwar yasa ta fito daga gida. Dan motsin nan da taji ya sa ta kara son abinta. Robar ta dauka ta zubar da kadan a bakin rariya sannan ta mayarwa Uwargida. Bakin Uwargida a washe tace
" nan da wayewar gari ma yana iya zubewa. Kinyi kyan kai 'Yar Da6as."

Yau ma ta riga Sada zuwa shagonsa. Ita kanta bata san me ya dawo da ita ba. Da yazo har kasa ta durkusa ta gaida shi. Ya amsa mata fuskarsa babu yabo babu fallasa. Yayi mamaki da ko sau daya bata sake batun maganin ba. Tana dai zaune ne kawai a gefe guda.

Wuraren shabiyu wata mace ta sha katon mayafi ta iso kafar shagon da flask din abinci. Matar tayi mata murmushi Asmau ta gaisheta. Sada ya fito daga cikin shagon yace "wannan ce yarinyar".

Rashida taji tausayin Asmau ba don komai ba sai don yanayin da ta ganta. Har wani wari take yi saboda rashin wanka. Sada yace su shigo ciki ya dan kara kofar alamun ko anzo kada a shiga.

Asmau na zaune a kasa a gabansu Rashida tace ta fada musu daga ina take kuma ina uban dan dake cikinta.
"Kada kiyi mana karya domin kuwa Allah Yana kallonmu".

Karo na biyu kenan tana bada labarinta. Kafin ta gama Rashida tayi ya6e ya6e da hawaye don tausayi. Mata da yawa idan an tambayesu game da ciki a irin wannan yanayin sai suce fin karfi aka yi musu. Amma wannan yarinyar ta zabi ta fada musu abinda suka fi tunanin gaskiya ne. Wato biyewa rudin shaidan da son farantawa masoyi. Shi kansa Sada yaji tausayinta matuka. Lokaci guda tarbiyarta ta wargaje a dalilin kawa da kafafen sada zumunta.

Waje suka ce ta fita ta jira su. Muhawara sukayi inda yace su mayar da ita gida Rashida tace kada ta koma sai ta haihu ta yiwu iyayen su yafe mata idan suka ga dan a hannu. Duk da suna tsoron halin Dan Adam yanzu. Kayi masa rana yayi maka dare amma zukatansu sun amince da taimakonta musamman ma suna jin tsoron kada ta zubar da cikin ta fada sana'ar banza.

 Sada ya rufe shagon suka ce ta biyosu. Babu musu tabi bayansu tana adduar Allah Yasa alkhairi ne a tattare da mutanen.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽22

Batul Mamman💖




Zahra 'yar Rabe ta biyu ke zaune tana waya da mahaifiyarta Laraba wadda Raben ya dade da saki. A hirarsu ne take fadawa Laraban zancen haihuwar Shema'u wadda akayi kwanaki goma da suka wuce. Tun ranar da akayi haihuwar Yassar yazo ya sanar sai akayi rashin sa'a Rabe da Zahran ne kadai a falon. A wurin ya ci mutumcin  Yassar  sannan yace da Zahra kada ta fadawa Hajjo babu mai sake zuwa gidan Bara'atu.

Laraba duk ta gama sauraren 'yarta tace mata su kara hakuri da babansu. Dama ita ta bata shawarar dagewa taje bikin Asmau. Tace idan ta shigo Kano zata zo tayiwa Umma jajen abinda ya sami Asmau da barkar Shema'u.

Hajjo tana tsaye a bakin kofa ta fahimci duk hirar Zahra da Laraba. Ko kwanaki uku da suka wuce sai da ta cewa Rabe wai har yanzu Shema'u bata haihu bane yace wa ya sani ne. Bara'atu da bakin hali kuma. Ta rasa gane irin wannan tsana da yake nunawa iyalin dan uwansa.

Dakinta ta koma jiki a sanyaye ta dauko mayafi ta fito. Karnukan Garzali ne suka yo kanta ba shiri ta koma ciki. Dakinsa ta je yana bacci ta daka masa duka a baya. Shi babu arabi babu boko sannan auren ma ya gagara. Sai dai yaje yawo ya dawo gida ya kwanta bacci.

A zabure ya bude ido ganin wace ke kansa ya turo baki "haba Hajjo yau kuma me nayi zaki doke ni? Na rantse jiya ban sha komai ba. Sansana bakina kiji".

Ta kau da fuska "Allah Ya tsareni na kai hancina bakinka. Ni tashi ka daure karnukan ka fita zanyi. Ka mayar mana da gida kamar dandalin 'yan daba. Motsi kadan sai haushin karnuka."

Dariya yayi tare da zuro kafafunsa zai sauko daga kan gadon. Daga bayanta taji ance "ina zaki je?"

Gabanta sai da ya fadi don firgici ta juya tana kallon Rabe wanda bata san ya dawo gida ba. Murmushin da bai kai zuci ba ta kakalo
"Yaushe ka dawo Alhaji?"

Ya basar da tambayar. "Naji kina cewa zaki fita".

Kamar ba mahaifiyarsa ba duk ta kidime tace "uhmm dama gidan waccan mara kunyar zani. Ashe Shema'u ta haihu shine ko ta aiko mana. Ai bata isa ta rabamu da 'ya'yan Shuaibu ba ko?"

Rabe ya soma jin tsoron yawan ambaton su Bara'atu da take a kwanakin nan sai ya dan dake.
"Yanzu a kanta zaki fita cikin ranar nan? Ki kyaleta kawai da halinta. A ce har 'yar dan uwana ta haihu bamu ji ba kawai don bata daukemu a bakin komai ba. Ni daga yanzu na kafa doka babu mu babu su. Tunda haka ta zaba kowa yayi ta kansa."

Hajjo ta jinjina kai tama mamakin yadda yake gilla mata karya haka. Ta tabbatar maganar da Zahra keyi a waya ba karya bane. Ta sake gwada sa'arta ta hanyar cewa
"Wai dama nace muje ko tare da kai ne mu dan zagesu mu huce haushi"

Juyawarsa yayi don kada ta sake jan zancen.
" Koma daki kiyi kwanciyarki ki huta Hajjo".

Tana kallo ya tafi itama ta juya zata koma dakinta. Hawaye ne ya sauko mata wanda bata san dalilinsa ba ta goge da habar zaninta sannan ta koma daki.

Garzali da bai tanka musu ba yaji tausayin mahaifiyarsa ya ratsa shi. Ya rasa dalilin da yasa dukkansu har Yaya Abu da Yaya Lami basu da katabus sai abinda Rabe yace. Amma zaiyi kokari ko yaya ya kai Hajjo taga jikokinta tunda wulakancin da suke musu yasa suka dena zuwa gidan.

A daki Rabe ya kasa sukuni. Sagira na masa magana ya daka mata tsawa. Dama ba wani matsayi gareta a wurinsa ba. A duniya babu matar da yake matukar so kamar Bara'atu duk da girma ya kamasu. Sai kuma batun Malamin tsibbunsa. Dama lokaci lokaci yake sake biya a toshe bakin Hajjo da 'yan uwansa. Yanzu idan asirin ya karya yasan Hajjo cewa zata yi su tashi daga gidan Bara'atu ta dawo. Matsalar idan suka tashi basu da wurin zuwa. Ya riga ya sayar da gidansu na kofar mazugal ya mutstsike kudin batare da sannin kowa ba.
*****

Baaba Ta Annabi tana zaune kofar wurin girki tana tsintar wake taji sallamar yayarta Hassana wadda suke kira da Yaya Tagwai. Farantin waken ta ajiye ta tarbo su cikin farinciki.

Ta Annabi ta kalli 'yar daya yayan nata Usaini tace "auta ba kya laifi kullum kina kuturin Yaya Tagwai. Naga alama idan anyi bikinki  tare za'a kaiku."

Yaya Tagwai tayi murmushi tana kallon Harira autar dan uwanta . Ita Allah bai bata haihuwa ba shine ya bata Harira take ruko duk da a gida daya ma suke da zama.

Tabarma Ta Annabi ta dauko Harira ta shimfida musu suka zauna aka gaisa. Ta tambayesu ya suka baro mutanen Misau.

Sai da suka ci abinci ne Yaya Tagwai tace ina sauran yaran gidan. Ta Annabi ta fada mata sunje biki ne a dangin Babansu. Ita ma girki zata karasa ta tafi.

Yaya Tagwai tace " gara da nayi sa'ar ganinki. Ke Harira tashi ki tafi gidan yayarki kafin nazo na sameta ita ma."

Fitar Harira ke da wuya Yaya Tagwai ta kalli kanwarta rai a bace "kin kyauta Ta Annabi, wato don ni ban haihu ba shine kika kira Usani kina sanar dashi katobarar da 'ya'yanku suka yi. Allah Yasa ina labe a bakin kofa naji duk abinda kika fadawa Ado ya sanar dashi. Don shashanci sai ji nayi yana sanya musu albarka. Sai da na kare masa tanadi na taho. Duk tsiyarku nice babba dole kuyi yadda nake so daga ku har 'ya'yan naku."

Ta Annabi ta dukar da kanta. Yaya Tagwai akwai rikon zumunci sai dai bata da hakuri. Hakuri ta bata sannan tayi mata bayanin yarinyar da Sada da Rashida suke riko.

Sada da Rashida auren zumunci suka yi. Shi Sada dan Ta Annabi ne ita kuma Rashida 'yar Kawu Usaini. Tun farkon zuwan Asmau yayiwa mahaifiyarsa bayani a kanta kuma ta nuna amincewarta. Daga baya ne ta yanke shawarar sanar da Usaini don yasan me yake faruwa.

Bayan ta gama bayanin Yaya Tagwai taja dogon tsaki.
"Ina tsammani yarinyar dai da asirinta tazo gidan. Idan ba haka ba waye zai ajiye mace mai ciki a gidansa ba dangin Iya ba na Baba. Ni zanje gidan na same su. Lallai ne su koreta ko don tsare lafiyarsu da ta yaransu. Wa ya sani ma ko mayya ce ko kuma duk abinda ta fada musu karya ne."
ABINDA AKE GUDU🙆🏽23

Batul Mamman💖




Hanjin cikin Rashida sai da ya kada da Harira ta gama fada mata dalilin zuwansu.
"Bari na kira Baban Abba na fada masa kafin ta karaso gidan nan."

Ta dauko wayarta sai dai tayi ta kira Sada bai dauka ba.

Harira tace "kema Yaya me zaisa ki amince ku ajiye matar da baku sani ba. Wallahi yanzu duniya babu gaskiya."

"Na sani Harira. Sai dai karki manta mu musulmai ne. Idan har zamu biyewa halin mutane yanzu ko sadaka bazamu bayar ba. Kamar yadda Baban Abba ya fada kayi komai saboda Allah. Idan mutum ya cutar da kai yayiwa kansa kuma dama faruwar hakan rubutaccen al'amari ne. Asmau bata da matsala ko kadan,sai kin zauna da ita zaki gane hakan".

Suna hirar Asmau su Abba suka dawo daga makarantar boko. Dama jira tayi su dawo ta basu mukulli ta tafi gidan bikin da su Baaba Ta Annabi zasu je. Yanzu dole ta hakura tunda Yaya Tagwai ta zo gari.

Sai biyar da rabi Yaya Tagwai ta iso gidan tun daga bakin kofa take fada.

Rashida tayi tsuru tsuru da ita har ta shigo ciki. Gaisuwar ta ma bata amsa ba sai fadan rashin hankalinsu da ta gani sun ajiye matar da basu san asalinta ba. Tana wannan fadan Asmau ta shigo a gajiye tana jan kafa saboda tsufan cikinta.

Sallama tayi ta shigo ganin baki ta durkusa da kyar ta gaishe da Yaya Tagwai. Kamar gaske ta saki fuska "maraba da tsintacciyar mage. Babu kunya kike yawo da cikin shege a cikin gari."

Asmau tayi shiru tana kallon Rashida wadda kunya duk ta lullubeta. Rasa abin cewa tayi ita kuwa Yaya Tagwai ta cigaba da magana
"Rashida yanzu wannan mai kwalakwalan idanun kika ajiye a gidanki da sunan taimako. Kina kallon yadda jikinta ya mulmule babu mai cewa daga gidansu ta gudo."

"Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Idan kika ji labarin yarinyar nan sai kin tausaya mata. Kaddara ce ta afka mata. Adduarmu Allah Ya kare 'ya'yan musulmi daga fadawa makamancin halin da ta tsinci kanta a dalilin sharrin waya."

Hannu Yaya Tagwai ta kai zata doke Rashida "yi min shiru shashasha. Sai iya bayani rai-rai-rai kamar wata zabiya. Zabgegiyar mace kamar wannan kika sani ko barauniya ce, ko kuma rufeki Sada yayi cikin ma nasa ne".

Kukan da Asmau take yi ta tsayar ta dago kai da sauri tana kallon Yaya Tagwai.
"Wallahi duk abinda na fada ba karya nayi ba. Kuma ban taba ganin Kawu Sada ba sai a garin nan da ya taimake ni. Kiyi hakuri don Allah idan zuwana ya bata miki rai".

Rashida ma hawaye take yi tace "na yarda dake Asmau nasan amana ce a tsakaninmu.
Yaya Tagwai don Allah kiyi hakuri. Da zarar ta haihu zamu mayar da ita gaban iyayenta".

Ta juya wurin Asmau da take ta zubar da hawaye.
"Tashi ki koma dakinki. Bani mukullin Kemis din nasan ya kusa dawowa ya karba."

Su biyun Yaya Tagwai ta ke bi da kallo cike da mamaki." Mukullin wane kemis din ne?"

Rashida tayi shiru ita kuma Asmau ta tashi ta tafi dakinta.

"Nace mukullin wane kemis din ne?"

Rai a bace Rashida tayi mata bayanin tsarin da suke yi na zaman kemis da Sada.

Hannuwa ta shiga tafawa tana salati.
"Aahaf, ni nasan ba a banza ta barku ba. Yanzu hanyar samun naku ma tare kuke yin komai da ita. To na rantse sai ta bar gidan nan ko kunki ko kunso. Bazan koma Misau ba sai naga abinda ya turewa buzu nadi."

Asmau tana daki tana jin fadan Yaya Tagwai da muryar Rashida da Harira suna bata hakuri. Kuka take yi sosai tana cike da fargabar abinda zai faru a gaba.

Har kusan  magariba Sada bai dawo ba. Dole Yaya Tagwai ta tashi ta koma gidan kanwarta saboda idan duhu yayi sosai ba gani take da kyau ba.

Gidan shiru har Sada ya dawo Rashida ta fada masa abinda ke faruwa. Ko zama baiyi ba ya wuce gidansu sai dai shima babu sa'a. Fada yasha sannan tace ya tashi ya bata wuri.

Haka suka kwana gidan kamar babu mutane. Asmau tasha kuka ga wani ciwon kai da ya kama ta.

Da safe Sada ya kirata suka kara kwantar mata da hankali yace zasu je gidan su sake bata hakuri. Har Kawu Usaini sun kira yace yana hanya zai zo a taru a bata baki. Batun zuwa kemis kuwa ranar babu ita.

Adaidaita sahun ya karbo bayan yaran sun tafi makaranta sannan suka fita shi da Rashida da Harira da ta kwana a gidan.

Ba suyi minti biyar da fita ba Yaya Tagwai ta shigo tare da kanin Sada mai suna Habu. Asmau na daki taji sallamarta. A tsorace ta fito ta bude mata kofa ta bata hanya ta wuce.

Yaya Tagwai ta soma kiran Sada, Asmau ta fada mata sun fita.

"To tunda saboda ke dama nazo ki fada min iyakar gaskiyarki. Shin cikin nan na Sada ne ko wani wanda ya sani?

Asmau ta girgiza kai tana hawaye.

"Alhamdulillahi tunda ba cikinsa bane ina so yanzu yanzu kafin su dawo ki fita ki bar gidan nan."

Gwiwa a kasa Asmau ta durkusa tana rokonta. Yaya Tagwai ta dubi Habu
"Kai da nazo da kai meye amfaninka ne? Ja min ita ka datse kofar gidan. Wallahi idan kika sake dawowa gidan nan sai na kirawo miki 'yan sanda. Haka kawai kin tsaface min yara basa jin maganar kowa sai taki. Kin gama karuwancinki zaki nemi bayin Allah ki  hadasu da wahala. In dai cikin nan ba na dana bane to ki kama gabanki".

Asmau tana kuka tace "ki taimakeni don girman Allah. Bani da wurin zuwa idan na tafi."

Yaya Tagwai ta harareta "daga bishiya kika fado da zaki ce baki da wurin zuwa? Tun wuri ki koma gaban iyayenki."

Ta sake cewa Habu yaja Asmau sai ya kasa saboda tausayinta da yaji. Yaya Tagwai tace
"Idan baki fita ba zan sa iyayensu su zare hannuwansu daga kansu. Idan baki sani ba ina so kisan cewa ina da wannan ikon da kannena".

Jin haka Asmau ta juya zata shiga dakin ta debo 'yan kayanta. Yaya Tagwai ta tsare kofar dakin. "Bazan bari ki sake shiga ba bare ki kunna wani tsafin nima naji ina sonki. Fita tun kafin nayi yekuwa a unguwar nan nace ke mayya ce".

Habu ma sai da yasa baki akan ta bari ta dauko kayanta amma taki. Haka ta ja hannun Asmau daga ita sai kayan jikinta Allah Yasa da mayafi tayi waje da ita ko takalmi babu. Kuka take yi sosai amma a haka Yaya Tagwai ta ja hannunta har suka bar layin. Sai da suka yi nisa ta jefa mata naira dari biyu.
"Matsiyaciya sai ki dauka ki kara gaba wasu masu tsautsayin su dauke ki amma ba gidan 'ya'yana ba. Allah Ya isa idan  kika dawo."

Kukan Asmau ba karamin tausayi ya bawa Habu ba amma yana kallo tayi gaba Yaya Tagwai ta kama hannunsa suka koma gidan Sada.

*****
A gidansu Sada ne Baaba Ta Annabi ta fada musu tun dazu Yaya Tagwai ta tafi gidan nasu. Suna jin haka suka kama hanyar gida hankali a tashe. Suka yi rashin sa'a titin da ya biyo wata mota ta lalace ta hada uban goslow.

Kusan tsalle Rashida tayi da suka iso gida ta fito daga dan sahun. Tana shiga ta tarar da Yaya Tagwai tana yin boli boli da kayan Asmau. Kuka ta saka tana tambayarta ina take Habu yace ta tafi.

Sada na jin haka cikin fada ya tambaye shi hanyar da tabi ya kwatanta masa. Tare suka bi hanyar ko zasuyi sa'ar ganinta. Sai dai sunfi awa biyu suna nema daga baya wani yace ta shiga wata bus amma bai san inda bus din tayi ba.

Da suka dawo gida Rashida ya gani a tsakar gidan ta rungume kayan jariran da Asmau take tarawa tana ta kuka. Yaya Tagwai tace "idan kin gaji kya yi shiru. Irin wannan kuka da kike yi sannan ace ba aikin asiri bane."

Ayatul Kursiyyu ta shiga karantawa tana tofawa Rashida a ka wai maganin sihiri. Sada ya dagata ya shigar da ita daki tana ta kuka. Habu da Harira kuwa sai kallo. Yaya Tagwai ko a jikinta. Tasan komai daren dadewa zasuyi mata godiya saboda ta rabasu da masifa.

*****
Yaya Babba ke bacci harda minshari Zubaida ta samu ta lallaba da kyar ta fito daga gidan.

A iya watannin da tayi duk shegantakar karuwanci 'yar tsohuwar nan ta koya mata. Tun tana nuna bata so har ta hakura tana biye mata saboda a rage matakan tsaron da aka saka mata. Bata taba yarda wani yayi amfani da ita ba. Tace sai ta koma gidan Uwargida. Yaya Babba bata damu ba ita dai aikin da aka sakata tayi.

Tunda tazo gidan sai yau ta samu damar fita. Kullum tana tunanin Asmau. Bata sani ba ko ta haihu yanzu.

Gidan Uwargida ta tafi da niyyar idan Asmau tana nan su gudu tare. Daga bakin kofa ta hadu da wata cikin matan gidan.

"Zuby kin dawo?" Ta fada tana kallon irin shigar Zubaidan da yadda ta kara cikowa.

Zubaida ta rage murya
"Shiga ki kirawo min Asmau bakuwar nan. Don Allah kiyi sauri ga wannan kada ki fadawa Mama kin ganni." Dari biyar ta bawa matar ta karba sannan tace "wannan bakuwar baki dade da tafiya ba ta gudu. Har an sami wasu bakin biyu bayan tafiyarta."

Zubaida tayi wani murmushi cike da jindadi."Alhamdulillah nasan taji shawarata ta koma gidansu."

Daga nan ta dauki jakar kayanta ta juya ita ma. Matar ta biyota tana tambayar ina zata je Zubaida tayi gaba ko kulata bata yi ba.

Daga nan bata zame ko ina ba sai tasha ta nemi motar Kano. Basu dade ba motar ta cika suka hau titi. Indai bata manta ba Asmau tace sunan umguwarsu Hotoro layin kwamishina Adamu. Gidansu zata nema don tasan in Allah Yaso yadda Asmau ke bata labarin Umma zasu riketa har ta sami mijin aure. Ta dan yi murmushi "ko me Asmau ta haifa" ko meye ma zata tayata raino tunda dai taji shawararta ta koma gida. Allah Yasa dai ta gane gidan.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽24

Batul Mamman💖





Zuciyar Asmau banda zafi babu abinda take yi. Ji take kamar ta haye tsakiyar titi mota tayi gaba da ita kowa ya huta. A tunaninta babu sauran mai kaunarta a duniya. Tana wannan jan kafar ne taji kwandastan wata hayis yace Hajiya zaki hau? Kai ta gyada tare da shiga motar da bata san inda suka nufa ba.

Sunyi tafiya mai dan nisa wasu na sauka wasu na hawa kwandastan nan yana ta tambayarta kudin mota hankalinta baya wurin saboda kukan da take yi. Wata mata ce a kusa da ita ta dan taba ta sai ta kula da yadda kafafun Asmau suka yi futu-futu ko takalmi bata dashi. A tsorace matar ta ja jikinta gefe ta karewa kodaddun kayan jikinta kallo. Daga murya tayi iya karfinta tace
"mahaukaciya ce"

Nan da nan hankalin jama'a ya dawo kanta aka fara cewa za'a sauka. Dreban hayis din ya hau yiwa kwandasta fadan ya dauko musu mahaukaciya. Tsayawa yayi suka janyo hannunta aka fitar da ita daga motar. Bakincikin da take ji ya hanata magana. Wai yau ita ake yiwa kallon mahaukaciya.

Tana kallo motar tayi gaba sannan ta kula da cewa inda take ya danyi wajen gari babu gidaje sosai. Ga wani irin ciwon baya da mara da ya taso mata lokaci guda. Runtse idonta kawai tayi tana tafiya zafin kwalta yana kona mata kafa sai ji tayi an taka burki da karfi motar tayi wata irin kara.

A razane ta bude idonta. Wata mota ta gani mai kyau ashe da tana tafiya ta dan hau titi bata sani ba. 'Yan samari biyu ne suka fito suna ta zaginta ta uwa ta uba. Dukkansu bata jin akwai wanda ya shekara ashirin sai tsayin kafa kawai. Kayan jikinsu sun nuna yaran sun fito daga gidan arziki sai dai daga yanayin maganarsu ta kula a buge suke.

Wanda ya danfi tsahon yayo kanta kamar zai doketa dayan yayi saurin rike masa hannu
"Haba Annur, duba da kyau mahaukaciya ce. Tunda Allah Yasa bamu tabata ba kawai zo mu ware".

Mai suna Annur ya ja tsaki "da ka barni na mareta. Haka kawai zata janyo mana makara a wurin party din. Sai an gama zabe fine chicks din"

Ciwo ne ya sake kwasarta tayi kasa tana rike baya. Jajayen idanunta da suka rine don kuka ta daga tana kallonsu tace
"don Allah ku taimaka min"

Wanda ya hana a mareta yace "kai Annur it seems matar nan haihuwa zata yi".

"Gaddafi bazan tsaya a wurin nan ba. Kaima kasan yanzu haka an fara nemanmu a gida. Allah Ya kawo wani amma ba mu ba. "

Da sauri yaja hannun abokinsa suka shiga mota. Gaddafi ya leko da kansa ta taga yana kallon Asmau kwance a kasan gefen titi. Motoci basu da yawa saboda har lokacin goma na safe bata yi ba. Gashi titin fita gari ne.

Annur ya fizgi motar da gudu Gaddafi yana rokonsa da su taimaka ko wane gari suka gani su sauketa a nan wani ya kaita asibiti. Tsaki da zagi Annur ya rinka yiwa abokinsa kafin ya juyo da motar suka dawo inda take. Ransa a bace yace Gaddafi ya shigo da ita. Kuma ya zauna a baya tare da ita saboda kada ta kai masa duka. Shi duk saurinsa ya isa party din abokinsa da za'ayi a Jos batare da sun sami matsala a hanya ba domin kuwa ko license na tuki basu dashi.

Da sauri Gaddafi ya taimakawa Asmau ya shigar da ita motar. Ciwo ya fara tsananta a gareta sai gumi take yi. Annur ya soma yiwa Gaddafi magana da turanci
"Tun farko da nasan haka zaka yi min da ban ce ka raka ni Jos dinnan ba. Amma babu komai zanyi maganinka. Hmmm yau 'yan matan Jos suna da manyan baki" ya karasa maganar yana wata shu'umar dariya.

"Kayi hakuri Annur ni kaina bansan meyasa ta bani tausayi ba. Ji fa yadda take gumi ko magana bata iyawa. Allah Ya tsinewa wanda yayi mata cikin nan dai"

Ciwon taji ya lafa mata ta kallesu tayi dan murmushi. Ga dukkan alamu Yassar zai girmesu duk su biyun. Ita ma turancin tayi musu wanda hakan yasa hankulansu dawowa gareta
"Wanda yayi min ciki ya rasu fatana Allah Ya jikansa. Ku kuma ina yi muku fatan shiriya daga Allah kada ku fada mummunan hali nan gaba."

Annur ya juyo kamar ba shine yake tuki ba yana kallonta da mamaki dan sauran mayen da yake duk ya tafi "wai dama ke ba mahaukaciya bace. Gaddafi kaga ka dauko mana masifa ko? Ke police ce ko 'yar mafiya?"

Kasa bashi amsa tayi saboda ciwo. Yana maida kansa titi saura kadan ya bugawa wani. A haka ya cigaba da tukin Gaddafi yana yi mata sannu. Sun isa wani gari yayi kokarin tsayawa su sauketa sai ya kula da 'yan sanda a gefen wurin. Dolensa ya sake taka mota yana ta sharara gudu. Basu tsaya a ko'ina ba sai da suka shigo garin Jos. A wannan lokacin ba karamin tausayin Asmau duka su biyun suke ji ba. Wai dama hake ake nakudar gaske ba ta fim ba. Idan taji ciwo tana addua sai taji suna tayata suna yi tare. Idan ka matso kusa da motar sai ka zata duk su ukun suke nakudar, sai sharba gumi suke yi kamar babu AC a motar . Bakin gate din wani asibiti da yayi musu kama da na gwamnati suka tsaya. Sai da Annur ya taimakawa Gaddafi suka fitar da ita daga motar. Tsoronsu daya kada a kamasu ayi tunanin ko sato ta sukayi ko suna da alaka da ita.

Cikin tsananin jin ciwo Asmau ta tambayi sunansu suka fada mata.
"Bansan daga ina kuke ba amma ina muku fatan alkhairi da shiriya don nasan iyayenku ba rayuwar da suke yi muku fata ba kenan. A duk inda kuke ku rinka tunanin lahirarku. Nagode sosai."

Daga haka ta lallaba ta karasa bakin gate din. Wannan karon sai da Gaddafi yayi da gaske Annur ya ja motar suka tafi.

Kasa daga kafarta tayi taji kamar zata fadi wata mata mai uniform din masu shara da wanke bandaki ta tareta daga baya tana yi mata sannu. Daga nan bata san da yadda aka shigar da ita asibitin ba. Ko awa daya bata cika ba Allah Ya taimaketa ta haihu.

Tana jin wannan kukan na jarirai taji gabadaya damuwarta ta gushe burinta kawai taga abinda ta haifa. Nurse din da ta karbi haihuwar tace mata kin sami 'ya mace. Asmau tayi murmushi tare da dago kai ta kalli kyautar da Allah Yayi mata tana hamdala. Gata da 'yar Abubakar sai dai babu shi kuma babu iyayensu. Kaddara ta riga fata a kansu. Ba don haka ba da yanzu iyayensu za'a mikawa jaririyar.

A wani dan zani aka nade 'yar aka miko mata. Ta zuba ido tana kallonta. Sai kuma kuka ya kwace mata da ta tuna bata da wata hanyar kulawa da 'yar. Ko suturar da zata saka mata bata da ita. Wannan mai sharar tayi mata Allah Ya raya sannan ta fita daga dakin. Ba jimawa ta dawo da wasu tsofaffin riga da zani amma a wanke ta bawa Asmau fuskarta a sake.
"Ga wannan akwai ruwa a bandaki ki gyara jikinki sai ki saka. Idan kin fito sai ki fadi wa za'a kirawo a danginki."

Asmau kamar kada ta bata yarinyar haka take ji. A rayuwarta bata taba son wani kamar yadda take jin son jaririyarta ba. Tayi godiya ta karbi kayan ta wuce bandakin.

Bata dade ba ta fito aka kaita dakin hutu. Wani likita yazo ya dubata yace babu wata matsala amma sai da safe zasu sallameta. Ya bata takardar magungunan da zata siya. Bayan fitarsa mai sharar ta kara dawowa wurinta ta sake tambayarta ina 'yan uwanta saboda a bakin gate ta ganta ita kadai. Ya kamata a sanar dasu ko don su kawo mata abinci da kayan baby.

Asmau bata da amsar da ta wuce kuka. Matar sai ta kyaleta ta koma bakin aikinta. Ita kuma ta cigaba da kallon jaririyarta tana bacci. Ikon Allah, yarinyar kama take yi da Mama Yalwa. Asmau sai ta rantse duk 'ya'yan Mama babu mai kama da ita kamar wannan yarinyar. Dama duk sunfi kama da Alh Adamu. Da namiji ta haifa dama sunan Abubakar zata saka masa. Amma tunda mace  ce zata saka sunan mahaifiyarsa kamar yadda suka yiwa juna alkawarin sai sun sakawa 'ya'yansu sunayen iyayensu. Da wannan tunanin ta danyi murmushi. Babbar matsalarta  yanzu  bata san ta ina zata fara ba? Bata da komai bata da kowa. Sannan bata san irin tarbar da za'ayi mata ba idan ta koma gidansu.

Wannan tunanin ya isheta ga kudin asibiti duk da na gwamnati ne tasan ko yaya za'a bukaci ta biya kudin wani abin. Hakan ne yasa tana ganin duhun dare yayi ga cikinta kamar anyi mata yasa don yunwa ta kwance dankwalinta ta goya jaririyar da shi sannan ta zura hijab dinta tayi waje. Gara ta gudu tun kafin ace ta kawo kudin da tasan bata da su. Ta kusa karshen barandar da zata kaita bakin gate ne taji muryar mai sharar nan tace "ba dai guduwa zakiyi ba".

*****
Hajjo ce ta farka daga bacci a gigice ta rinka juyi akan gado har ta tabbatar dai a dakinta take. Hawaye ne kwance a fuskarta sakamakon mafarkin da tayi da jikarta Asmau. Kuka ta ganta tana yi tana kiran Hajjon da ta taimaketa. Duk yadda taso ta kama hannun Asmau ya gagara har ta farka. Jikinta sai karkarwa yake ta tashi ta dauko mayafinta a gefen kujerar dakin ta tafi dakin Garzali. Ko agogo bata duba ba tayi sa'a ta same shi yana fesa turare da alama fita zaiyi.

Tsayuwar kirki ta kasa cikin tsawa tace yazo ya kama karnukansa zata fita.

"Hajjo ina zaki je da yamman nan. Biyar da rabi fa".

Harararsa tayi fuska a murtuke don kada ya kawo mata wargi "inda ka aike ni zani. Kaga kada ka bata min lokaci wuce muje".

Suna fitowa yayiwa karnukan fito suka yo kansa Hajjo ta samu ta fice. Don sauri kafarta har zafi take yi mata taji takun mutum kamar ana binta da gudu. Duk da a tsorace take haka ta dake bata juya ba take magana
"Rabe wallahi yau ko me zaka ce sai naje wurin Bara'atu. Ba kai ka haifa min Shu'aibu ba shiyasa baka san ciwon iyalinsa ba."

Garzali yayi yar dariya
"Ni ne Hajjo. Raka ki zanyi. Nima rashin mu'amala dasu ba karamin damuna yake yi ba."

Tayi murmushi "Allah Yayi maka albarka" daga nan ta bashi labarin mafarkin Asmau da tayi suna tafiya.

*****
Tun kafin azahar Zubaida ta iso garin Kano ta samu mai tasi suna ta yawo a unguwar Hotoro basu gane gidan ba. Gajiya yayi ya sauketa bayan ya karbi dubu biyu a hannunta. Har zai tafi sai ya dawo saboda ta bashi tausayi yace ta sami mai adaidaita sahu sunfi sanin layukan cikin unguwa.

Tayi sa'a kuwa ta sami wani ta fada masa inda take nema. Da ya kula bakuwa ce a garin ya tsula mata kudi sai dai bata damu ba. Biyan bukata yafi dogon buri. Kusan dubu talatin ta dauko a cikin kudin da Uwargida ta bawa Yaya Babba.

A cikin layin mai adaidaita sahun ya nuna mata gidan kwamishina. Tayi masa godiya ta bashi kudinsa. Daga nan tasan Asmau tace gidansu babu nisa. Wata tsohuwa ta hango da wani mutum a bakin gate din wani gida tayi saurin karasawa kafin su shiga.

Sallama ta rinka yi musu suka juya suna kallonta a tare. Riga da siket ne a jikinta sun dameta sosai ga katuwar jakar kaya sai wani siririn mayafi da ta rataya a wuya. Da murmushi a fuskarta ta dan rissina ta gaishesu sannan tace "don Allah gidan Umma nake nema. Umman Asmau".

Garzali ya sake kallon Zubaida sannan yace "nan ne".

Ko jiransu batayi ba ta shige ciki tana kwalawa Asmau kira. Yassar da yake shanya ne ya fara ganinta bai san lokacin da ya saki wandon da yake kokarin dorawa a igiya a kasa ba ya nufota. Zubaida na ganinsa ta saki murmushi.
"Tabbas nan ne gidan don naga kamarku. Kai ne Yasir ko?"

Kallon rashin sani yake mata yace "a'a sunana Yassar"

Zubaida tace "hakane kaini wurin Asmau".

Hanyar falon ya nuna mata sai ya kula da Hajjo da Kawu Garzali. Har dan tsorata yayi sai yaga Hajjo tana hawaye
"Zo nan Yassar, zo naji duminka a jikina"

Ji yayi kamar mafarki yake ya fara tunanin gudu Garzali ya damko wuyan rigarsa ya hada shi da jikin Hajjo. Kuka ta fashe dashi na takaicin yadda jikanta yake nuna tsoro da fargabar ganinta har yana neman gudu.  Tana rike da hannuwansa tace "kuyi hakuri Yassar. Ku yafewa wannan tsohuwar".

Shima kukan ne ya zo masa ya kankameta. Ashe akwai ranar da Hajjo zata nuna masa so? Tana rike da hannunsa suka shiga cikin falon.

Umma suka gani da Aina'u da kuma Jafar sun saka Zubaida a gaba suna kallonta jin tace daga Azare  tazo wurin Asmau.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽25

Batul Mamman💖





Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai biyoni mu koma ciki".

Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin albashinta.

Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya. Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan."

Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare. Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da yaso kwarai ta kai washegari.

Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya nazo muje gidana tunda dare yayi".

Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda babu ta dauko tabarma ta shimfida mata.

Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh. Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora"

Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki.

Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi. Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda suka yi masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane. Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace
" Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara kuka".

Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon.

Wata dattijuwa ce rike da wani mutum yana ta tangal tangal kamar zai fadi. Daga bakin kofa ta tsaya tana jifan Zulaiha da harara "yau kuma wani sabon iskancin ne ya tashi kina jina ina fama da Gidado bazaki zo ki taimaka mu kaishi daki ba?"

Idonta ne ya sauka akan Asmau ta daure fuska
"Wannan kuma fa, daga ina?"

Zulaiha tana saka hannuwan mutumin a kafadarta tace " 'yar haya na samo dazu a asibiti. Zata karbi hayar daki daya a gidan nan, kinga kudin ko cefane sai mu kara dashi".

"Cefanen banza, ni zan rinka karba ina karawa a jari na."

Asmau ta dan duka ta gaishe da matar ko kallonta bata yi ba ta fara tambayar ina abincinta. Shi kuwa mutumin da Zulaiha ke ja surutai yake marasa kan gado. Da suka zo wucewa ta gabanta wani irin wari yake fitarwa.
A falon ta jira Zulaiha ta kaishi daki sannan ta nuna mata wurin da zata kwana. Tana kwance rungume da 'yarta tana jin wannan dattijuwa tana masifar anyi kaza anyi kaza ba daidai ba. Can kuma taji mutumin wanda ta tabbatar mijin Zulaiha ne ya soma zage zage bata bashi abincinsa ba zata kashe shi da yunwa. Har Asmau tayi bacci babu abinda take ji yana fitowa daga bakin Zulaiha sai "kuyi hakuri".
*****

A can Kano kuwa lokacin da Yassar ya shigo ciki rike da hannun Hajjo sai da gaban Umma ya fadi. Aina'u tayi saurin labewa a bayan Umma a tunaninta daukarsu tazo yi.

Hankalin Umma ya bar Zubaida ya koma wurin Hajjo. Cikin sanyin jiki ta gaisheta sai dai sabanin da sai taji Hajjon ta amsa cikin kuka. Har inda Umma ke tsaye taje ta kama hannuwanta tana hawaye "Bara'atu nasan ke mai hakuri ce da kawaici. Ki dubi girman Allah ki yafewa wannan tsohuwar banzar hakkinku da ta dauka."

Umma ta saki baki cike da mamaki. Me kunnenta yake jiye mata ne? Hajjo ta cigaba da magana tana kuka "nayi nadamar abinda nayi miki tsahon shekarun nan. Ni kaina bansan dalilin yin hakan ba. Bakiyi min komai ba na dora miki tsana da tsangwama."

"Alhamdulillah" Umma ta fada a fili itama da nata hawayen. Hajjo ta cigaba da rokon gafara Umma tace ai zuwanta kadai yasa komai ya wuce. Hajjo ta mika hannu "zo nan autar Bara'atu. Taho wurin kakarki kinji 'yar albarka. Jafaru baka ce komai ba. Ku yafeni ko don darajar babanku"

A darare Aina'u ta matsa jikin Hajjo. Garzali ma a kunyace ya gaishe da Umma ta amsa bakinta yaki rufuwa don murna. Jafar ma murna yake yi sai dai hankalinsa yafi karkata ga Zubaida dake tsaye tana kare musu kallo.

Sai da aka dan sami nutsuwa a falon sannan Jafar yace "Umma  bakuwar nan fa tana jiranki"

Hakuri Umma ta bata ko wurin zama basu bata ba suna farincikin fara daidaituwar al'amuran danginsu. Aina'u ta kawowa Zubaida lemo da abinci tana ci suna kallonta. Jira suke yi ta gama ta fada musu abinda ta sani game da Asmau.

Da ta gama ne Umma ta fada mata Asmau tayi wata bakwai rabonta da gida. Zubaida ta dan cije lebe fuskarta ta nuna rashin jindadi "nayi tunanin gida da dawo da na koma aka ce min bata nan. To ina ta tafi?"

Hajjo tace "kinga yarinya, bayani zakiyi mana yadda zamu fahimceki sosai. A ina kika ga Asmau'un?"

Zubaida ta fada musu komai game da zamansu da Asma'u. Umma da Hajjo sai kuka jin Asmau ta zauna a gidan karuwai. Tace hatta yadda ta sami cikin duk ta fada min.

Umma ta share hawaye
"Ta fada miki sunan wanda yayi mata cikin?"

"Eh tace sunansa Abubakar".

Umma ta toshe bakinta da hannu tana wani kukan. Dama Qasim ya tabbatar musu cikin Abubakar ne amma basu bawa wacce abin ya shafa damar bayani ba. Yassar ta nuna "tashi maza kaje ka kira Mama Yalwa. Ka fada mata bakuwa ce tazo daga Azare wadda tasan Asmau".

Ba'a dade ba sai ga Mama suka zauna Zubaida ta fada musu duk labarin da Asmau ta bata na waya da yadda al'amarin ya cigaba. Falon sai salati suke yi ana jimamin wannan abu. Ace tarbiyar shekara da shekaru wasu can da basa kishin addini suyi ta fito da samfurin yada alfasha salo salo suna turawa 'ya'yan musulmi.

Hajjo tace "to shi shegen giruf (group) din aje a tarwatsa mana kowa ya huta. Haka kawai an janyowa marainiya fadawa mummunar rayuwa. Kada na kaiku da nisa ko mu da babu waya a zamaninmu waye ya koya mana yadda ake yi tsakanin mata da miji. Gashi mun rayu dasu cikin kwanciyar hankali mutuwa ce ta raba. Duk wannan shaidancin kuma da ake yadawa ai bai hana mutuwar auren yara kanana ba."

Mama da batasan yadda akayi Hajjo ke nuna damuwarta akan Asmau ba tace " ai group din a waya ake bude shi. Ni abinda ya fi damuna bai wuce yadda zakiga yara da matan aure a dauki waya tun safe har dare ki rasa me ake gani. To ashe duk harkar lalacewa ce duk da dai ana samun karuwa ta wani fannin. Yaranmu da sunyi waya sai kiga basu da lokacin komai sai nata."

Zama sukayi ana ta mayar da zance kowa na tofa nasa. Kawu Garzali a fusace yace "ita wacece wannan Walidar ne? Tayi fatan kada mu hadu don wallahi sai nayi mata rauni. Kawaye da abokan banza sunfi saurin lalata tarbiya. Ni ba daga abokin bane muka kare a haka."  Ya dubi Jafar da Yassar
" yanzu kuna da uba saboda haka duk yaron da na gani baiyi min ba kafin na kore shi ta kanku zan fara".

Umma tayi murmushin jindadi. Duk da tasan Garzalin kansa baya sahun mutanen kirki amma dai taji dadin kulawarsa ga 'ya'yan dan uwansa.
"Walida kawar Asmau ce tun primary. Kuma itama nata mahaifin yana kokari. Don ranar da abin ya faru kafin mu dawo daga asibiti yazo ya dauketa."

Hajjo taja tsaki wanda har Zubaida da Aina'u sai da suka yi dariya "anyi ta baya ta rago. Shi da 'yarsa ta bata ta wani ai ya jira nasa lokacin. In Allah Ya yarda sai ta dauko masa abin...."

Mama da Umma suka dakatar da Hajjo daga yin mummunar addua. Daga nan suka yanke shawarar washegari da sassafe zasu tafi Azare neman Asmau. Anti Bintu da Shemau duk an sanar dasu haka Abdulhalim da Qasim.
*****

Annur da Gaddafi tunda suka isa masaukinsu ko abinci sun kasa ci. Abokin da suka zo wurin party dinsa yayi ta damunsu da su tashi suyi wanka a tafi sai su kalli juna su sunkuyar da kawunansu kasa. Gabadayansu dana sanin baro gidajensu suke yi. Sun baro iyayensu musamman matan cikin tashin hankali domin sun san yanzu ana nan ana nemansu. Yau da suka ga yadda mace ke wahala wurin haihuwa kowannensu shiriya ta saukar masa. Sannan ga adduar da tayi musu bayan taimakonta da suka yi. Suna kallo aka shirya duk 'yan samari sa'aninsu suka fice sai su kadai. Karshe ma shawara suka yanke gobe zasu koma asibitin neman wannan matar daga n[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽26

Batul Mamman💖




Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".

Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa.

"Wane suna zaki saka mata?"

Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.

"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".

Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?"

"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."

Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki".

Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa.

"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu".

Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.

"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?"

Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."

Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?"

Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa.

Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."

Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"?

"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri."

Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.

Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin.

"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.

A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba."

Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya."

A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan."

Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"

"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri".

Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba.

*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho.

Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan.

Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau."

Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"

"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.

Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.

Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba.

Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta.

Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.

Ai tunda matan gidan  suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa.

Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?"

Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..

Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".

Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."

Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta.

Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje.

Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."

Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke.

Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka.

Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.

Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki."

Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah."

Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."

Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.

Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce  dai shikenan."

Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau.

*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada.

Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna."

Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."

Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan.

Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"

Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.

Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."

Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa"

Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba"

Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru.

Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?"

Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽26

Batul Mamman💖




Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi
"Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba".

Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa.

"Wane suna zaki saka mata?"

Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani.

"Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne".

Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?"

"Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu."

Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi.
"Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki".

Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa.

"Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu".

Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa.

"Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?"

Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi."

Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?"

Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa.

Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki."

Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"?

"Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri."

Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan.

Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin.

"Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar.

A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba."

Zulaiha ta share hawaye
"A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya."

A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai
"Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan."

Asmau taji tausayin Zulaiha sosai.
"Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya"

"Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri".

Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba.

*****
Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho.

Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan.

Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau."

Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?"

"Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa.

Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali.

Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba.

Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta.

Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta.

Ai tunda matan gidan  suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa.

Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma.
"Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?"

Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take"..

Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba".

Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki."

Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri.
Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta.

Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje.

Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...."

Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke.

Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka.

Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida.

Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki."

Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito.
"Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah."

Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta."

Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti.

Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce  dai shikenan."

Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau.

*****
Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada.

Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa.
"Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna."

Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...."

Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na"
Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan.

Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?"

Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau.

Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba."

Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa"

Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba"

Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru.

Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?"

Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽27

Batul Mamman💖





Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya ake ciki.

Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi musu rakiya aka karbi numbar wayar juna.

Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai ya duba ko za'a dace.
*****

Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita. Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa".

"Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo".

Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna"

Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi.  Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau sannan tace da Zulaiha
"Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan sami irin naki sai nayi".

Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin makusanci kafin zuwanki."

"Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa makaranta ba saboda rashin kudi."

Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta sami aikin itama.

Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma. Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da yaran a gida.

Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita.

Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director (shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana samu sosai a dalilin Amatullah.

Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru. Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta. Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya iya boye son da yake yiwa Asmau. Ya sha nemanta sai dai taki bashi hadin kai kuma kullum haka ta faru sai ta fadawa Zulaiha don gudun matsala. Tayi ta yiwa Zulaiha nasihar rabuwa dashi sai dai tayi murmushi kawai. Wannan ya tabbatar mata da cewa har yanzu Zulaiha na son mijinta. Sai ta kyaleta suka cigaba da zamansu.

*****
Annur yana kwance a daki bayan ya dawo daga makaranta yana dan danna wayarsa aka turo masa wani text da hoto. Da farko baiyi niyar bude hoton ba sai da ya karanta labarin yarinyar a matsayin wadda mijinta ya rasu ranar aure kuma aka gane tana da ciki. Tsaki yayi sannan ya bude hoton don shi da Gaddafi yanzu karatu suka saka a gaba.

Matar ya gani kyakkyawa da ita har ya ajiye wayar sai ya sake daukowa ya duba hoton. Hannunsa na rawa ya turawa Gaddafi yace ya duba ko ya gane ta. Ba jimawa Gaddafi ya kira yace sai ya ga kamar matar nan mai ciki da suka taimakawa mai suna Asmau. Matar da suka je nema a asibiti basu sameta ba.

Tausayinta suka ji musamman da suka tuna halin da suka tsinceta da irin nasiharta garesu. A cikin sati daya suka yi ta bincike da tambaya ko akwai wanda ya santa har suka dace da samun wani dan makarantarsu da yace a unguwarsu abin ya faru a Kano. Yaron har gidan Umma ya kaisu suka sanar da ita labarin haduwarsu dai Asmau. A wannan ranar an sha kuka sannan Umma tace ita ta hakura zata cigaba da yi mata addua. A duk inda take Allah Ya tsareta kuma Yasa ta dawo gida da kafarta.


*BAYAN SHEKARA BIYAR*

Idan kaga Asmau bazaka ce itace tazo garin Jos a rame da tsohon ciki ba. Duk da bata da jiki kamar da amma ta dan samu nutsuwa. Ita da Zulaiha kuwa ko 'yan biyu bazasu nuna musu kusanci ba. Tana tuka tuwo Zulaiha na tsinke zogale taji sallamar Amatullah da Aliyu.

Da gudu Amatullah tazo ta rungumeta ta baya
"Ummina tuwo kike yi?"

Asmau ta bata rai "Ama so kike na kone zaki fado min haka. Me ya dawo daku yanzu bayan ba'a tashi ba?"

Zulaiha tayi dariya "tunda kika ji ta kiraki da _Ummina_ kema kinsan akwai abinda take so".

Amatullah ta kama kasan dan hijab dinta tana wasa dashi, Zulaiha ta dubi Ali "kai da kayi mata rakiya sai ka fadi me ya dawo daku ai"

Ya ja baya da sauri "Umma nifa fitsari tace zata yi na rako ta".

Asmau ta nuna hanyar bandaki "wuce kiyi kizo ku koma".

Sum-sum Amatullah ta wuce bata dade ba ta dawo ta sake tsayawa a bayan Asmau. Zulaiha ta kula akwai abinda take so ta janyota jikinta
"Amatullah ta Ummi me kike so ne, fada min naji"

Dan turo baki tayi wanda duk lokacin da tayi sai Asmau ta ga kamarta da babanta ta fito sosai  Nabila ce take shan kafi kaza kuma Ummi ta hanamu roko shine nazo ta bani biyay na siyo".

Zulaiha ta kwashe da dariya "bakinki ne biyay din ai"

Amatullah ta dan buga kafa "Umma biyay nace fa ba biyay ba".

Wannan karon Asmau ma tayi dariya. Amatullah bata iya fadan duk kalma ma harafin *r*, idan ka fada yadda tayi kuma tace sam ba haka ba.

Zulaiha ce ta basu naira biyar biyar ita da Ali suka tafi. Asmau tace
" da baki basu ba. Sun baro makaranta takanas saboda kwadayi. Yanzu gobe idan taga wani abin sake dawowa zatayi."

"Na sani, rokon ne bana so tayi. Idan suka dawo sai a kwabesu akan hakan. Amma da ban bayar ba karshenta nan gaba bazamu sani ba sai da su roka a makarantar.

Asmau ta dage sosai kullum tana yiwa yaran lesson musamman na turanci da larabci. Duk wanda yake da homework zata zauna ta koya masa. A makarantunsu 'ya'yan gidan sun fita daban saboda kokarinsu. Ita kam Zulaiha zuwan Asmau ya janyo mata alkhairi.  Manyan yaran Humaira, Muhsin, Amina da Habib duk makarantar gwamnati suke yi. Anisa, Aliyu da Amatullah kuwa a makarantar kudi mara tsada irin ta cikin unguwa suke. Gabaday Asmau ta tattara hankalinta ga 'yarta. Burinta a rayuwa yarinyar ta sami kulawa sosai ta kuma san addininta don gujewa [truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽28

Batul Mamman💖




Da yamma Asmau ta dawo daga wurin aiki tun kafin ta bude gate din taji kukan Amatullah. Ji tayi kamar an tsikareta. A duniya babu abinda ta tsana kamar a taba mata 'ya da rashin adalci domin kuwa indai Amatullah tayi kuka a cikin gidannan baya wuce aikin Zinaru. Su Humaira ji suke yi da ita balle tace anci zalinta.  Da sauri ta shiga ta sami Zinaru tsaye da bulala ta daga zata sake dukan Amatullah ga Ali da Anisa a tsaye suna nasu kukan. Asmau tayi saurin dauke 'yarta bulalar ta sauka a bayanta. Don ma da mayafi amma ba karamin shigarta tayi ba. Bata damu ba ta duba jikin Amatullah sai ga shati lafcece a bayanta tana ta kuka da sheshsheka.
Kawar da kan da take yiwa Zinaru yazo karshe. Bazata zuba ido a kashe mata 'ya ba. Cikin tsananin bacin rai ta dago ido tana kallon Zinarun da ko a jikinta an kamata tana dukan karamar yarinya haka.
"Me tayi miki kike mata irin wannan dukan?"

"Lallai Asamau wuyanki yayi kauri. Ni kike tsarewa da ido haka kamar wata sa'arki. Ko zaki rama mata ne?"

Amatullah sai wani irin kuka take yi, Asmau ta tambayi su Ali me suka yi.
Zinaru tace "jikokina babu abinda suka yi. Ba su nake duka ba. Wannan afiruwar yarinyar da har yau ba'a san ubanta ba ita na daka ehe. Na fada na sake nanatawa ta dena kiran Gidadona da Baba taki ta dena. Kun zo kun tare mana a gida kamar tare muka gina shi daku"

Rai a bace tace "akan wannan kike neman kashe min ita. A iya zamanmu ban taba tanka miki ba idan kina cin zalinta. Zulaiha ke shiga kullum. To ina so ki sani wallahi kika kara taba min 'ya za'a ji kanmu dake. Na baki girman da zan baki a matsayinki na uwa amma tunda hakan baiyi miki ba zan zauna dake yadda kike so. Kuma da kike cewa ba'a san babanta ba don Allah ki nuna mana naki dangin ko na baban Gidado. Mtsww, gida kuma yanzu na fara zama tunda kema ba naki bane."

Zinaru taji zafin maganganun Asmau "ni kike fadawa haka saboda baki da mutumci. Ita Zulaihan ce ta fada miki bamu da 'yan uwa?"

Asmau bata tsaya ta karasa sauraron Zinaru ba ta shige daki. Da kyar ta rarrashi Amatullah tayi shiru har bacci ya dauketa tana ta ajiyar zuciya. Kuka ne yazo mata da ta tuna irin rayuwarta. Yau da a gidan aure ta haifi Amatullah babu abinda zai fito da ita daga cikin danginta har wani ya sami damar fada musu magana irin haka. Ta tabbatar har ta mutu duniya bazata taba mantawa da cewa a zina tayi cikin 'yarta ba. Ta cuci karamar yarinya saboda soyayya.

Su Humaira sun dawo daga makaranta suma kannensu ke fada musu abinda Zinaru tayiwa Amatullah. Duk sun zo sun dubata har lokacin bacci take yi.

Bata farka ba sai bayan magriba da zazzabi mai zafi jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata mutu."

Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta. Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata ta cika.

Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta. Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har wani sama yake yi.

A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama kirjin yara).
Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane."
Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka. Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar, Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah."

Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin babana?  Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta dokeni. Sai ya yama min ko."

Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar addini kin tara yara da yawa".

Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi. Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai mu tafi namu gidan ko?"

"Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin. Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo. Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen.

A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko musu kayan kwana.

Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi. Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da kura don tana ganin alamun asthma gareta ba pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan 'yarsa tayi. Amma irin halin da  taga yana shiga ga kashe kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali.

Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar gudan jininta ba.

*****
Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta fada mata ranar da ta zane Amatullah
"Wato Kande maganganun  sun kona min rai. Yarinya kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman mata ya iya."

Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa 'yar masu kudi".

"Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya.  Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya suka yi."

"Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko."

Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a sayi kayanta.
*****

Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare  Asmau ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta. Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi.

Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren jari da ita."

Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita ma sonta nake yi."

"Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen 'yar masu kudi. Yanzu dai ko da safe ne sai kayi yadda nace."

Asmau ta jinjina bakin hali irin na Zinaru. Gashi Zulaiha laulayi take yi babu wanda ya sani sai ita. Har kuka tayi saboda bata son cigaba da haihuwa ga talauci da rashin gata. Sauri tayi taje dakin Zubaida ta fada mata abinda taji sai tayi tuntube da kwaftareren takalmin Gidado. Zinaru ta fito da sauri taga ko waye suka hada ido da Asmau. Ta dan ji tsoro da farko sai kuma ta dake ta soma kwalawa Zulaiha kira.

Cikin bacci taji kiran da Zinaru ke yi mata ta fito tana murza ido. Zinaru tace "munyi magana ne da Gidado akan yadda Asamau ta raina ni da irin rashin jituwar dake tsakaninmu shine yace zai koreta. Ni kuma sai na tuna masa cewa gidan nan ba namu bane. To yanzu yake fada min wai ko dai ki sallameta da kanki ko kuma ya sakeki mu tafi mu bar miki gidan."

Zulaiha ta rude "me yayi zafi Gidado har da zancen saki? Zinaru ki bashi baki don Allah."

Asmau tace "wallahi karya take yi Zulaiha. So take ya sakeki ki bar musu gidan".

Zinaru ta kalli Gidado
"Ince dai kaga irin yadda take yi min. Ni bazan zauna a gidan nan ana wulakanta ni ba".

"Zinaru kiyi hakuri indai Zulaiha ce yanzu zan saketa mu tafi"

Yaransu duk suna kallo  ita Asmau har ta soma jindadi sai kawai Zulaiha ta durkusa a kasa ta rike masa kafa tana kuka"ka rufa min asiri Gidado kada ka sakeni. Ina zani da yaran nan."

Muhsin ya dagata tsaye "Umma kawai ki bari ya sakeki kema kya huta da duka da wankin amai. Dama don ke kike yi ne nake tayaki amma daga yau sai muga mai wanke masa"

Bakin Muhsin din ta daka "waye ya saka bakinka. Ku bar wurin nan kafin na bata muku rai."

Suna tafiya ta cigaba da rokonsu shi da babarsa. Zinaru ma tasa kukan karya ita dole su bar gidan. Ganin haka Asmau tace "indai saboda ni ne to in sha Allah da safe zan tafi. Zulaiha ki tuna da gatan da Allah Yayi miki ki koma gaban iyayenki. Gobe nima gidanmu zan tafi na roki nawa iyayen gafara".

Daga haka ta bar wurin. Wannan wane irin so ne Zulaiha ke yiwa Gidado. Tausayi take bata don wannan ba karamar jarabawa bace. Mutum ya mayar da kai bolarsa amma ka kasa rabuwa dashi.

Da kuka Zulaiha ta biyo bayan Asmau."kiyi hakuri Asmau ki zauna gobe zan sake rokonsu."

"Zulaiha a kaina bazan so kiyi ta zubar da mutumcinki a gaban su Humaira ba. Ni dai shawarata ki koma gida ki roki gafarar su Inna".

Zulaiha tayi shiru. A yadda zuciyarta ta karaya bata jin zata iya zuwa gaban iyayen da ta yiwa rashin kunya harda kaisu kara.
*****

Karfe goma na safe Asmau ta gama hada 'yan kayanta da na Amatullah. Tayi mata wanka suka shirya tafiya. Daga kan Humaira har Ali kuka suke yi basa son tafiyarta. Itama kukan take yi amma gara ta koma gida. Kewar iyayenta ta dameta gashi duk inda ta zauna sai wani dalili ya koreta.

Kamar bazasu rabu ba ita da Zulaiha kowa kuka ta rike hannun Amatullah suka fita.

Tasha suka je bata dade ba motar Kano ta cika suka fito. Sunyi tafiya mai dan nisa sun wuce wani gari Saminaka ba jimawa suka ga wani mutum yana daga hannu alamar neman taimako. Gefensa mace ce babba da dogon hijab sai wata 'yar budurwa da bazata kai shekara ashirin ba. Dreban  farko kamar kada ya tsaya sai kuma yaji tausayin dattijuwar suka tsaya. Motarsu ce ta lalace ga makanike yana dubawa amma yace injin ya buga sai an sauke shi. Su Asmau suka marmatsa matar da yarinyar suka shigo. Aka bar dreban da makanike.

Sallama tayi musu suka gaisa tare da yi musu godiya.

Ta kalli Amatullah da ke zaune a cinyar Asmau tayi mata murmushi.
"Yan mata yaya sunanki"

"Safinatu Abubakay. Amma Ummina Amatullah take ce min ko Ummi"

Asmau tayi dan murmushi kawai. Fargabar zuwa gida ce fal a zuciyarta. Ita kuwa dattijuwar tace "Safinatu Abubakay ko Abubakar" tana yar dariya.

Amatullah tace "Abubakay nace ba Abubakay ba"

Mutane da yawa a motar sai dariya. Can ta dan taba matar nan "kema aljannah zaki je? Ni da Ummi can zamu wurin Babana. Ban taba ganinsa ba, Zinayu zai zane saboda tana duka na."

Asmau ta dan kai mata duka saboda suruta sannan ta share hawaye. Matar nan tana kallonsu sai taji tausayinta ya kamata. A hankali yadda Asmau zata ji tace "Allah Ya jikansa"

Asmau ta dago kai tace "Amin" wani hawayen yana fita a idonta.

Sun iso Kano garin da hadari ga kura. Tana kokari daukar kayansu ne ta ga Amatullah ta dafe kirji numfashi baya sauka. A gigice ta saki jakar ta rungumota tana kuka. Yau kam ta tabbatar asthma gareta saboda yadda take kokarin numfashi yaki sauka.

Wannan matar da wasu maza suka taho wurinta. Dreban da yazo daukar matar yana zuwa tace Asmau ta tashi su tafi asibiti. Kuka take yi kawai ga Amatullah ta sandare.

Wani asibitin kudi suka je aka karbi Amatullah. Tana ji matar tana waya tana sanar da wani inda suke.

Bayan kamar awa daya an samu Amatullah ta dawo hayyacinta suna wani daki Asmau sai godiya take yiwa matar taji an turo kofar dakin tare da sallama. Wani daddadan kamshi ne ya mamaye dakin kafin ta kula da mutumin da ya shigo cikin shigar sojoji masu babban mukami.
Amatullah dake kwance ta tashi zumbur tace
" Ummi wannan ne baban nawa?".
ABINDA AKE GUDU🙆🏽29

Batul Mamman💖



Dan tsayawa yayi yana kallon kyakkyawar yarinyar. Tana daga zaune harda ware hannuwa ta dan bata rai "Baba bazaka yi min oyoyo ba? Nima bazanyi maka ba. Shine ka taho aljannah ka barmu ni da Ummi."

Asmau kunya ta isheta ta kai hannu zata hana Amatullah sai matar ta girgiza kai.

Taku yake mai cike da kamala da kuma kwarjini ya karasa daya barin gadon ya zauna yana murmushi. Asmau ta kasa daga ido ta kalle shi. A kan gadon ya zauna ya janyo Amatullah ya dorata akan cinyarsa.
"Oyoyo baby din Baba. Kiyi hakuri bazan kara tafiya na barki ba kinji"

Amatullah ta kankame shi ya dago kai ya kalli mahaifiyarsa yana murmushi. Juyowa yayi inda Asmau take zaune suka hada ido ba shiri ta kara sunkuyar da kanta. Mutumin ba karamin kwarjini yayi mata ba. A kalla zai kai shekara arbain. Kayan jikinsa sun kara masa kyau. Shi kuwa mayar da hankalinsa yayi ga Amatullah yana shafa mata kai. Girmansa da matsayinsa bai sa ya kyamaceta ba. Muryarta ya sake ji tace "Baba idan anje aljannah ba'a zuwa gida ne. Kullum ni da Ummi bamu ganka ba. Kuma Zinayu sai tayi ta dukana baka zuwa ka yama min".

Sake hada ido suka yi da Asmau ya kula da kwallar da ta cika mata ido. Wani tausayinsu ne ya shige shi a lokaci daya. Ko ba'a fada ba yasan baban yarinyar nan ya rasu. Wannan ne dalilin da zaisa yarinyar ta rinka ambaton an tafi aljannah an barsu.

Tana daga jikinsa yace "daga yau duk wanda ya sake tabaki sai na rama miki kinji."

Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta kanta. Tun dazu ake kawo kararta."

Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba".

Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda.

Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai da na turo mota daga Jos din."

Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi."
Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a san halin da kuke ciki kada suji shiru"

Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan zasu kira idan suka ji shiru."

Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane layi gareki?"

Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba tace "MTN".

Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka"

Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan dawo"

Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma ya isa.

Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni"

"Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?"

Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun.

Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya don karfin hali harda kwatancen asibitin.

Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta.

Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya Lubabatu wannan jikata ce."

Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar sunansa"

Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki maganinta."

Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da dan nata.

Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi"

"Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu"

Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani numbarki saboda kira ko da akwai wani abu."

Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya.

Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu tawa numbar a wayarta ko."

Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma zan saka chaji idan an kawo wuta"

Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki lafiya kinji".

Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci. Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa.
*****

Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne saboda kada tayiwa mamanta rigima.

Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi. Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka dagawa babarta hankali."

"Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya"

Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo"
Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani.
*****

Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau take yi mata.
"Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba aljannah bane kuma na fada miki yana can. Bude bakinki ki karbi abincin...."

Sallamarsa ta sake ji cikin muryar da ta gama ganewa yanzu. Amatullah na ganinsa ta matsa daga kusa da Asmau har allurar da ake yi mata karin ruwa ta soketa ta tsala ihu. Kukanta yaji har ransa ya matsa da sauri ya gyara mata ya bi Asmau da harara, ita kuwa ta matsa gefe rai a bace.
Rarrashin Amatullah yayi sannan ya bata abincin kamar ba soja ba ya mayar da kansa yaro a gabanta. Ko sau daya bai yiwa Asmau magana ba har sai da Amatullah tayi bacci sannan ya tashi.

Wayarsa ya miko mata fuskarsa babu alamun wasa ta dan ja da baya.
"Karbi mana, numbarki zaki saka min"

Tayi kicin kicin da fuska
"Na bawa Hajiya"

"Na sani, ina son karba saboda na kira 'yata anjima".

"Da ka barshi ma, saurin mantuwa gareta kana fita zata mantaka"

Ya dan daga gira "ke kadai kike son faruwar hakan banda ni da ita. Nasan bazata manta ni ba."

Duk da haka Asmau taki karbar wayar tana adduar ya fita kawai. Tunda an biya musu kudin asibitin ba yau ta fara ba, guduwa zatayi idan dare yayi.

Ya tsareta da ido "na fa san ba numbar daidai kika bawa Hajiya ba. Kuma nasan baki kira kowa ba dazu. So ki bani numbar tun girma da arziki kafin na fara bincike a kanki."

Duk da ta tsorata harararsa tayi tana magana a dan tsorace
"A wane dalili zaka yi bincike a kaina? Daga taimako, dole ne na bada number?"

Yadda ya kalleta yasa tayi shiru. Wayarta ya dauka daga kusa da Amatullah ya kunna sannan ya saka numbarsa ya kira tasa wayar.

Mayar da wayar yayi inda take ya kama hanyar fita "saura kuma kiyi tunanin cire sim din. Na bar sojoji biyu zasuyi min gadin 'yata don kada ki gudu cikin dare".

Gabanta sai da ya fadi da ya fadi haka. Ji tayi kamar yana karanta abinda ke ranta. Ba'a fi minti biyar da fitarsa ba taji wayarta na kara. Da sauri ta dauko a tunaninta Zulaiha ce sai ta sake jin muryarsa.
"Baban Safina ne, Colonel Ishaq Muhammad Jikamshi. Na bugo ne don na tabbatar baki cire sim din ba." Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar yaja motarsa yayi gaba.

Asmau ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. Tsoro ne ya kamata don da gaske ta yarda ya bar masu tsaronta kada ta fita su bindigeta a banza. A hankali ta sake maimaita sunan nasa. Dama a jikin rigarsa ta ga inda aka rubuta I.M Jikamshi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽30

Batul Mamman💖




Sau biyu Asmau na leka waje amma bata ga soja ko daya ba. Ga tsoro kada sai ta fita su tsareta. Haka nan ta hakura zata zauna don dole. Dadin dadawa tana so Amatullah ta kara samun sauki.

Sallah tayi ta ci abinci itama sannan ta saka kati daya a wayar ta kira Zulaiha ta fada mata inda suke. Sauran ukun kamata yayi ta sayar dasu ta fada a ranta.
****

Col. Ishaq gidansa ya wuce dake Tudun yola. Gidan da a yanzu baya son zama cikinsa saboda abubuwa da dama da yake tuna masa dasu. Dakinsa ya shiga ya dauko wasu takardu ya jira akayi har sallar isha sannan ya tafi gidan Hajiyarsa.

Babu kowa a falon lokacin da ya shiga shiyasa ya wuce dakin kaninsa wanda yayi aure kwanakin baya inda yanzu ya mayar nasa. Yayi wanka ya saka kananan kaya sannan ya hau gado ya kwanta. Tunanin Amatullah yake yi yana dan murmushi. Yarinyar ta tsaya masa a rai. Sai kuma ya koma tunanin mamanta. Ji yayi yana son sanin ko ita wace ce. Tunani kala kala ya rinka yi game da ita. Da ya gaji wayarsa ya dauko yana karanta sakonnin da aka turo masa  wasu ya share wasu ya bada amsa.

Sunan da baiyi tunanin gani bane ya dauki hankalinsa da sauri ya bude sakon. Sallama tayi masa sai hoton baby da ya biyo baya. A kasan hoton ta rubuta _Alhamdulillah mun sami baby boy_.
 Da kyar Ishaq ya iya hadiyar yawu don tashin hankalin da ya tsinci kansa a ciki. Har wani guntun zazzabi ne ya nemi rufe shi. Ya tashi ya fita zai je wurin Hajiya a daki sai yaji muryarta a falo.

Labarai take kallo ita kuma Bilkisu tana zaune a kasa suna hirar sanyin Jos da mai aikin gidan Hinde. Motsinsa yasa Hajiya kallon kofa tace "yaushe ka shigo gidan ban sani ba?"

"Dazu ne bayan Isha"
Ya zauna akan kujerar kusa da ita tare da mika mata wayar. "Kin gani Badar ta haihu"

Hajiya ta kalli su Bilkisu "ku dan bamu wuri"

Tashi suka yi Bilkisu sai da ta waiwayo ta kalli Kawunta tana mai tausaya masa.

Bayan sun wuce Hajiya ta karbi wayar ta kalli hoton jaririn tayi guntun murmushi "Allah Ya raya" ta gyara zama sosai tana fuskance shi
"Mai sunan Alhaji, nasan irin damuwar da kake ciki amma ina so ka sani ba'a yiwa Allah dole. Duk yadda kaso Allah bai nufa zaku kare rayuwarku da Badariyya ba. Duk kuma yadda kuka nemi haihuwa kasan wani baya haifar dan wani."

Kansa a kasa yace "na sani Hajiya. Yanzu na tabbatar mun rabu har abada kuma kamar yadda Mami take yawan fada ya tabbata nine bana haihuwa" a yadda yake ji a wannan lokacin gara yayi kuka ko zaiji sauki a ransa. Tausayi ya bata sosai.
"A matsayinka na musulmi ka sani cewa babu abinda bawa zai samu a rayuwarsa sai wanda Allah Ya kaddara masa. A bisa tsari da hikimarSa *Yake azurta wasu da 'ya'ya mata, wasu da 'ya'ya maza, wasu Ya hada musu duka biyun, wasu kuma Ya barsu haka* duk inda Allah Ya jarabceka da fadawa kasan babu wayo ko dabararka. Ka zama mai hakuri wata rana zaka ci ribarsa".

Ajiyar zuciya yayi ya gamsu da bayananta wanda ya sani dama.
"Nagode Hajiya, bari naje na kwanta"

"Abinci fa"

"Bana jin yunwa. Sai da safe"

Tasan halin da zai shiga kenan shiyasa tun tana Jos shekaranjiya da maman Badariyya tayi mata waya ta sanar da ita haihuwar bata fada masa ba.

*****
Sake kwanciya yayi yana tuno rayuwarsa ta baya. Auren soyayya suka yi da Badariyya suna zamansu lafiya. Har suka shekara biyu da aure ko batan wata bata taba yi ba. Gashi Allah Yayi shi da son haihuwa tun bata fara damuwa ba ya matsa su je asibiti. An duba su aka tabbatar musu duk lafiyarsu kalau su jira lokaci.

A haka har suka yi shekara shida babu labari. Maman Badariyya duk ta damu. Magunguna har da na gargajiya kawo musu take yi amma shiru. Ishaq ya tayar da hankalinsa sosai gashi ko ina suka je sai ace babu matsala. A wani asibitin Jiddah ne ma aka ce kwan haihuwarsa bashi da karfi. Ya shiga damuwa sosai sai gashi Badariyya ke bashi baki.

Sun sami shekara goma da aure Mamanta taje har gidan Hajiya ta roketa arzikin asa Ishaq ya saketa tunda anfi tunanin matsalar daga gareshi. Hajiya Lubabatu tayi ta rokonta akan tayi hakuri sai tace to nan da wata shida idan ba'a saki canji ba dole ya saketa.

A wannan wata shidan Ishaq yaje asibitoci sunkai takwas. Magani kuwa duk wanda aka bashi sha yake yi. Lokaci na cika har gida Mami tazo ta bukaci ya saki 'yarta. Badariyya kanta tace ko waye da matsalar a cikinsu zasu hakura tunda suna son juna. Mami ta dage abu har kunnen manya a danginsu duka. Ganin al'amarin yana neman lalacewa dole ya yi mata saki daya suka rabu ba don suna so ba. Tana gama iddah da wata biyu yaji labarin  aurenta, gashi yanzu har ta haihu ko shekara bata cika ba. Ya amince bashi da rabon ganin dansa. Kannensa duka sun haihu hatta autansu matarsa ciki gareta.

A haka bacci ya dauke shi zuciyarsa cunkushe da tunani.
*****

Da safe likita yazo ya duba Amatullah yace jikin da sauki amma zasu barta sai gobe a sallamesu. Asmau masa tayi godiya sannan ta tashi tayi wanka ta gogewa Amatullah jiki ta canja mata kaya.

"Ama zan fita na siyo miki abinci kinji. Duk wanda ya shigo ki ce masa ina bandaki"

"Ummi kayya ko, ashe kema kina yi kika ce na dena"

Kafin ta iya bata amsa taji tace "yeeey Babana ya dawo"

Asmau ta dago kai a kunyace. Karshenta yaji abinda Amatullah ta ce. Yau ma kayan sojan ne a jikinsa sai dai babu fara'a kamar jiya. Duk da haka yayi kyau ga cika ido.

Gaishe shi tayi ya wuce bai amsa ba. Wani mutum ne ya shigo da kwandon abinci ya gaisheta ya ajiye a gefe ya fita.

Col. Ishaq yana zaune akan kujera yana yiwa Amatullah wasa da tambayar ya jikinta. Asmau duk ta takura ta rasa abin yi.

"Ki zuba mata abinci mana idan ke baki jin yunwa."

Wai mutumin nan ina ruwansa da ita ne. Me yasa ya kara dawowa ma. Ta danyi tsaki a hankali sannan ta hada abincin ta zauna a daya gefen zata bawa Amatullah ya miko mata hannu alamun ta bashi plate din. "Kema ki zuba kici".

Gefe kawai ta ja tana kallon ikon Allah. A baki ya rinka ciyar da Amatullah tana ta yi masa surutu. Asmau tana satar kallonsa.
"Abinci nace ki zuba ba kallona ba"

Ya Salaam! Ba karamar kunya taji ba ta tashi da sauri ta zuba abincin ta dawo tana tsakura da cokali.

Ya tashi saboda ya fuskanci kunyarsa take ji. "Safina bari na je naga likitan da ya dubaki na dawo"

Fita yayi ko waige babu. Asmau ta tuttura abincin kada ya dawo ya sameta.

*****
Tambayoyi ya yiwa likitan game da ciwon Amatullah. Da ya fito ya tsaya bata lokaci don ya bata damar gama cin abincin. Gara da Allah Yasa yayi tunanin kawo musu abincinsa da yake tafiya office dashi ba don haka ba don ganganci fita zata yi ta bar yarinya ita kadai a daki. Wasu na nema ido rufe ita ta samu bata rike da kyau ba.

Kafin ya dawo ta gama ta dauke plates din ta dauraye a toilet. Ya shigo yayi mata alama da ta fito waje.

Darajar girmansa da take gani da tsoronsa da take ji a yanzu yasa ta fita. Ta tsaya can gefe ta sunkuyar da kanta.

"Da ban zo ba sai ki fita ki Safina ita kadai a daki? Kuma shine harda koya mata karya. Allah kadai Yasan me kike koya mata kafin yanzu"

Taji haushin maganarsa ta dago kai zata yi masa rashin kunya "ina ruwanka da abinda nake koya mata".

Yanayin kallon da yayi mata kadai yasa ta kawar da kanta gefe
"Ni kike fadawa haka?"
Da wadanda ke karkashinsa zasu ji abinda ta fada kila idan ta fara tsallen kwado sai kafarta ta kumbura. Lallai tana da tsaurin ido. idan kayan jikinsa basu yi mata kwarjini ba ai shekarun da yake jin zai bata shabiyar ko sama da haka ya isa yasa taji kunyar idonsa.

Da yake rashin kunyar ba dabi'arta bace sai taji babu dadi "kayi hakuri wallahi nagode da taimakon da kuka yi min. Abinda kaji na fada mata ma don babu wanda zai zauna min da ita ne"

"Its ok, zan aiko muku da abinci anjima saboda haka kada ki fita ki barta ita kadai."

"Nagode"

"Har yanzu baki kira kowa a gidanku ba?"

"Uhmmm sun ce zasu zo anjima".

"Maman Safina kin iya karya" ya fada yana shafa kansa.

Asmau taji kamar ta nutse a wurin. Kai wannan mutumi da bin kwaf yake.

"Ance gobe za'a sallameku. Na fadawa likitan kada yayi sallamar sai nazo"

Ta dan bata rai "saboda me"?

"Saboda na kamaki da kyau. Ina son sanin inda zaki kai min 'ya idan kin fita daga nan"

Cikin dakin ya koma ya cewa Amatullah zai je office ya dawo. Har da kukanta ita zata bishi. Asmau ta kalleta bayan ya fita a ranta tace ki gama ganinsa da kyau kafin ki dena ganinsa.

Da yamma Haj Lubabatu ta saje dawowa har take tambayar Asmau ina iyayenta. Tace mata yanzu suka tafi za'a kawo musu abincin dare. Hajiya tace "ai mun zama daya nasan zamu hadu ko ba yau ba".
A zuciyarta tana kokonton ko da gaske sun zo. Babu wani alamar kayan dubiya ga akwatunansu Asmau a gefe wanda ya kamata ace an tafi dasu gida. Da Ishaq ya koma gida da daddare sai da ta fada masa. Yace shima yana son bincike ne a kanta ko don yarinyar da take tare da ita.


*****

Sai wurin karfe tara na safe Col. Ishaq ya dawo washegari amma sau biyu yana aika musu da abinci har da kayan kwalama na yara.  A lokacin aka basu takardar sallama da magani. Sauran kudin da ake binsu duk yaje ya biya mutumin da ya kawo musu abinci ya kinkimi akwatunanta.

Asmau ta dakatar dashi yace Yallabai ne ya saka shi. Dauka kawai yayi zai fita Ishaq ya shigo yace ya wuce dasu gidan Hajiya zasu biyosu a baya.

"Bangane ba" Asmau ta fada a tsorace. "Nima namu gidan zam wuce don Allah kace ya ajiye min kayana"

"Kinga ki wuce muje akwai tambayoyin da nake so nayi miki daga nan nayi alkawari zan kaiki gidanku da kaina."

"Ni bazan bika ba, haka kawai na sani ko....ko..."

Yayi murmushi "karasa mana. Ko satar mutane nake yi. Nima tsoron da nake ji kenan ko sato Safina kika yi".

Idonta har ya ciko da hawaye tace "wallahi 'yata ce, don Allah ka barmi mu tafi."

Fita taga zaiyi daga dakin tace cikin kuka  "zanyi maka ihun barawo"

Col. Ishaq yayi dariya ya kalli Amatullah  "Safina ina babanki?"

Ta sake lafewa a jikinsa "ga ka"

"To kinji, idan kina son 'yarki ki biyoni. Taimakonki nake son yi albarkacin wannan yarinyar"

"Bana son taimakon ka bani 'yata...." tafiyarsa taga yayi dole tabi bayansa tana dan gudu gudu saboda yadda ya soma yi mata nisa.

Gaban wata mota mai kyau suka tsaya baka ya bude gaba ya ajiye Amatullah wanda dadi ya isheta sannan ya zagaya ya zauna a wurin dreba. Babu yadda Asmau ta iya dole ta bude baya ta shiga. Suna hada ido ta mudubi ya kashe ido yana murmushi ita kuwa ta murguda masa baki.

Shi da Amatullah suke ta hira tana bashi labarin gidansu Umma Zulaiha. Gidan Hajiya ya wuce dasu zuciyar Asmau tana ta daridari.

Duk kunya ta dameta haka tabi bayansa suka shiga gidan. Haj Lubabatu  ta tarbeta cikin fara'a aka kawo musu abinci. Col. Ishaq yace Bilkisu taje ta yiwa Amatullah wanka. Asmau tabi bayansu da ido yarinya sai murna takeyi ta sake dasu.

Hannunsa ya dan kada a gabanta ta dawo daga tunanin da take yi. Yace "Malama Asmau ina ganin ya kamata ki sanar damu ko ke wace ce. Hajiya ma ta fahimci akwai abinda kike boyewa shiyasa na kawoki nan ki fada mana a gabanta."

Asmau ta soma hawaye "naso ace yadda muka hadu cikin mutumci mun rabu a haka batare da na tonawa kaina asiri a duk inda na tsinci kaina ba"

Hajiya tace "kada kiga kamar mun takuraki, rayuwar Safinatu muke dubawa shiyasa. Idan har baki da wurin zuwa ga yarinya mai lalura lallai kina bukatar taimako"

"Ina da iyaye da 'yan uwa. Kuma a garin nan muke"

Col Ishaq yace "to me ya rabaki da gida har kika kasa fada musu kuna asibiti"?

Asmau tayi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin rayuwarta. Tun Haj Lubabatu tana kada kai ha[truncated by WhatsApp]
ABINDA AKE GUDU🙆🏽33

Batul Mamman💖




Gidan suna dai ya koma wurin zuwa kallon Asmau da 'yarta. Bayan anyi sallar la'asar ne ta tuna da Col. Ishaq da ya kawo su. Dafe kai tayi saboda tasan bata kyauta ba. Ganin su Umma yasa ta manta da kowa. Shema'u ta fadawa cewa dan matar da suka zo tare shi ya kawosu kuma yana waje. Haj Lubabatu tana jinsu sai dai kunya ta dan fari ta sanya taki tuna mata dashi. Kuma tasan yau rana ce mai matukar mahimmanci a wurin Asmau. Ta hadu da iyayenta da 'yan uwa bayan tsahon lokaci. Shema'u ta sanar da Umma. Nan da nan aka samu food flasks aka hada masa duk wani na'uin abinci na gidan sunan. Jafar aka kira akan su wuce gidansa domin bako ya samu yaci abinci ya huta.

Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah. Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho. Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su taho kawai.

Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban motar ya mika masa hannu suka gaisa.

"Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba"

Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?"

Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki, ya nuna Asmau "ai sunanta kenan."

Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai "sunan ya dace da ita"

Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare da rokonsa. Yayi yar dariya

"Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin yayanki baki ba?"

Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada "nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka gaisa da duk 'yan uwa."

Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban Safina"

Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan nan"

Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce kawai take kiransa babanta. Sunansa...."

Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga motarsa.

Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota suka tafi ta koma ciki.

Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo.
*****

Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana mita yadda masu hankali zasu fahimta
"Kai jama'a ace anzo  taron suna anci tatsotse dinnan anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe gamo ya gagara".

Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya janyo musu.

Basu samu gidan yayi daidai ba sai bayan karfe tara. A falo suka zazzauna. Duk 'yan uwan Asmau makusanta suna wurin har da Kawu Garzali ga kuma Haj Lubabatu da danta. A nan aka shiga bada labarin abubuwan da suka gabata. Kowa jikinsa yayi sanyi musamman da suka ga Asmau tana ta kuka da rokon a yafe mata. Suka yi ta kukan wannan kaddara da ta riga fata.

Mama Yalwa tace "ai wannan bala'i na waya sai an dage da addua sosai. Akwai alkhairi tattare da ita amma sharrinta a bayyane yake. Kuma kullum kara samar da sabuwa akeyi mai saurin hada mutane da barna."

"Haka ne" Haj Lubabatu ta amsa mata. " Sai kiga yara kanana sun yini da waya a hannu ki rasa me suke tattaunawa. Wani lokacin a haka ake haduwa da mutane babu sanayya idan kika yi rashin sa'a ba nagari bane sai su bata maka tarbiya ba tare da ka lura ba. Kwanakin baya jikata dake karatu a nan wurina Bilkisu na fuskanci ta soma nacewa waya fiye da yadda ta saba. Kullum suna hira da wata yarinya da suka hadu a irin group dinnan na waya. Kunsan yanzu tsakanin mace da mace ko maza ma babu abinda ba'ayi. Na kula kawancen ya soma yawa bata da zance sai nata. Abun ya fara bani tsoro. Shabiyun dare sai kiji suna waya sai da nayi mata tas akan hakan."

Hajjo tace "ni idan babu hali ba sai a hakura da wayar ba. An fara abu da gaisuwa da sada zumunci a hankali waya ta zama tamkar kana dauke da duniya a tafin hannu. Idan kaki bawa danka waya ma zai fita ya gani a ta wasu."

Tattaunawa suka yi ta yi a game da tasirin waya ga al'umma yanzu. Babu babba babu yaro kowa yana da ita kuma ya iya amfani da ita. Jankunne sosai manyan suka yi garesu akan su dubi yadda rayuwar Asmau ta kasance su kula da kawunansu da na yaransu. Kasancewarsu masu aure duk bashi bane domin yanzu hatta mata da mazan aure suna fadawa tarkon waya. Daga group sai kaga matar aure tana mu'amala da 'yar uwarta mace ko namiji mai aure ko mara shi wanda a da ba halinta bane.

Sun jima suna hira har shadayan dare tayi basu kula ba sannan Haj Lubabatu da Col. Ishaq suka tashi tafiya. Sun sha godiya a wajen dangin Asmau sosai tare da neman a cigaba da zumunci don yanzu sun zama daya.

Fitowa suka yi har bakin mota rakiya Amatullah na makale jikin Col. Ishaq tana bacci. Tashin da yayi zasu fito yasa ta farka ta soma rigimar binsa. Shi kan shi baya son rabuwa da ita. Ana ta lallabata taki yin shiru sai da Asmau ta karbeta ta karfi tana mata fada. Hakura tayi amma bata dena kukan ba. Col. Ishaq ya bata rai sosai saboda fadan da tayiwa Amatullah. Kallon da yake mata ya nuna rashin jindadinsa sai kawai ta sunkuyar da kanta.

Bayan tafiyarsu Umar ya tafi kai Mama Yalwa gida shi kuma Abdulhalim ya dauki matarsa da yara suka wuce. Dakin Umma suka koma Amatullah tana ta kuka har sai da Asmau ta goyata duk girmanta don taki yarda da kowa. Daga nan aka soma wata sabuwar hirar har aka zo kan Kawu Rabe Asmau tace shi kadai ne bata gani ba . Shema'u tace "hmmm Asmau mutum babu kyau. Ashe duk tsahon lokacin nan Kawu Rabe wurin wani malami yake zuwa ana rufe bakin Hajjo da su Yaya Abu. Bayan tafiyarki Hajjo tazo ta nemi gafarar Umma har ta bukaci lallai ta dawo gidannan dasu Aina'u idan har ta yafe mata. Shi kuma tace ya soma gyara musu gidan kofar mazugal su koma. A nan aka ji ashe ya dade da siyar da gidan. Ya kuma dage wannan nasa ne. Sai ga ainihin takardun gida Hajjo ta fito dasu, ke magana har za'a shiga kotu don duk su Kawu Garzali sun ce sai ya biyasu kudin gidansu da ya sayar. Wurin aikinsu ma suka kore shi yaci kudin kamfani bai biya ba. Sai da yaga abu ya kure masa ya roki gafarar Umma suka tashi. Yanzu haka yana kauyen Dakasoye can ainihin kauyen babansu Anti Sagira. A nan baban nata ya bashi gona da gida suka zauna tunda bashi da wurin zama. Yanzu da wuya yazo cikin Kano. Zahra dai tayi aure tana Jigawa"

Asmau tace "har ya bani tausayi. Da ma Umma ta barshu kawai a nan din"

Aina'u tace "tabdi, ko yanzu fa ba wani rissina yayi ba. Tsoron hukuma yaji don da gaske su Yaya Abu sunso a kama shi sai ya biyasu kudin shiyasa ya bada hakuri ya tattara yayi gaba"

"To Allah Ya kyauta" duk suka ce Amin.

Kan katon gadon Umma suka kwanta su uku sannan aka shimfide yaran akan bargunan banda baby Asmau wadda suke kira Husna.

Sai wurin daya da rabi na dare Umma ta baro dakin Hajjo inda su Anti Lami suke. Su ma sum gama tasu hirar. Wani hawaye taji yazo mata da taga 'ya'yanta mata kwance su uku a wuri daya sun takure alamun daya gefen nata ne. Kasa kuma ga yaransu duk sunyi bacci. Maimakon ta kwanta alwala ta dauro tazo tayi sallah tana mai mika godiyarta ga Allah tare da adduar dadin shiriya ga zuri'arta da sauran musulmi.
*****

Col. Ishaq yana kwance amma ya kasa bacci. Ya rasa abinda yasa yake ta tunanin Asmau. Can kasan zuciyarsa yace tausayinta ne kawai da kuma son Amatullah. Sai dai kuma ko rufe ido yayi murmushin da tayi bayan komawarta gida yake tunawa sai kawai ya tsinci kansa da yin murmushin shima.
*****

Washegari  karfe takwas na safe sai ga Jafar da Sabira dauke da kwanunkan abinci. Dankali ta suya da plantain da kwai. Duk da tasan dai a gidan ma za'ayi. Umma ta nuna jindadinta sosai. Shiyasa take son Sabira, barta dai da surutu amma mace ce mai ladabi da sanin ya kamata. Sauran matan masu jini a jika irin su Shemau da Rashida suna kitchen ana ta soye soye. Aina'u ma ta tashi duk da hanata aikin komai ita da Zubaida mai ciki. Asmau kuwa kamar wadda aka saukarwa bacci tana yin sallar asuba ta koma. Ji takeyi rabonta da bacci mai dadi cikim kwanciyar hankali har ta manta.

Amatullah ce ta tasheta tana kiran Babanta. Cikin bacci Asmau ta janyota jikinta ta soma rarrashi
"Ama nan ne gidanmu fa, na rasa inda kika koyi rigima. Amma idan kika cigaba zan mayar dake wurin Zinaru"

Shiru tayi ta kwanta a jikin Asmau daga baya tace "Ummi to zaki kaini naga Babana sai mu dawo?"

Asmau ta shafa kanta tana murmushi "in sha Allah zan kaiki kinji. Tashi muje muyi brush a gaishe da su Hajjo"

Suna fitowa falo suka tarar da kowa a zaune har su Jafar. Rike take da hannun Amatullah sai suka basu sha'awa. Ita kuwa kallon da suke mata yasa taji kunya ta saki hannunta. Yanzu tunda anzi gida sai ta koyi kara kada ace bata da kunya. Suna zama suka gaishe da kowa Anti Bintu ta cikawa kowannensu plate da abinci. Amatullah ta ware ido sai ta tashi taje tayiwa Asmau rada a kunne. Duk ana kallonta sai suka ga tana share hawaye. Hankalinsu ya tashi Umma tace me ya faru.

Kunya tasa Asmau ta kasa fada da wayo Umma tace "Safina zo ki fada min abinda kika fadawa Ummi. Kinga gashi har kin sakata kuka"

Duk aka zuba mata ido ita kuwa tace "Ummi in fada?"

Murmushi kawai Asmau tayi tace "tambayata tayi taci ko kuwa"

Amatullah ta cafe "idan naci Ummi zata ce nayi kwadayi. A gidan Babana ma sai tace naci. Mu a gidan Zinayu koko da kosai muke ci, ko byodi da tea, ko tuwon safe ko Ummi"

Kasa cin abincin Asmau tayi ta fashe da kuka. Sunga rayuwa ita da Amatullah. Dan kudin da take samu a kudin makaranta yake tafiya. Abinci kuwa sai dai aci garau garau. Su Umma suma kukan suke tayata. Abinda tafi karfi a da shine yanzu yafi karfinta. Anti Bintu tazo ta rungumeta "komai ya wuce Asmau. Kuka bazai dauke shekarun baya ba sai dai ya tuna miki da bacin rai."

Hajjo tace "haka ne ki dena kukan haka. Rayuwace kowa da irin tasa duk da dai komai yana da sanadi. Naji dadi da kika koyawa yarinyar nan tarbiya mai kyau."

A haka suka ci abincin ana taba 'yar hira har Asmau ta sake. Kafin su tashi Amatullah ta sake cewa "Ummi daga yau a nan zamu zauna ne?"

"Eh mana ai kun dawo gida kenan" inji Shemau

Tare duk suka tashi aka kwashe kwanukan suka fara layin wanka.

Wurin shadayan safe Asmau na saka kaya don kuwa Mama Yalwa tace yau a gidanta zasu yini taji wayarta na ringing. Ko da ta dauka bakuwar number ta gani har tayi zaton ko Zulaiha ce tace "tuba nake maman 'yan biyu ban samu na kiraki ba"

Shiru taji daga daya bangaren tace "Zulaiha ko kinyi fushi ne. Ni da ke fa ba'a ji kanmu ba"

"Ashe kin iya hira Idon kuka" ji tayi gabanta ya fadi. Muryar da ko cikin bacci yanzu tasan zata gane taji. Kamar yana gabanta ta dan russuna a kunyace ta gaishe shi.

"Har kin gane mai magana, ko kuwa dai wayancewa kika yi?"

Tana murmushi tace "Na gane"

Col. Ishaq ya gyara kwanciyarsa. Shi bai ma san dalilin da yasa yayi mata waya da safe haka ba.
"To waye?"

"Baban Amatullah"

"Uhmm uhmm, a wurinta kadai nake baba. It seems ko sunana baki sani ba. Shiyasa jiya kika kasa fadawa yayanki"

Asmau taji muryarsa kamar baiji dadin hakan ba tace "na sani kuma na fada masa ma"

Magana yake kamar maganar aiki ce mai zaman kanta yace "me kika ce masa? I am sure ba Baban Safina kika ce ba".

Ita fa kunyarsa take ji. Ganinsa take yi babban mutum mai matukar kwarjini da cika ido shiyasa bata tsawaita hira dashi. Sake maimaita tambayar yayi tace "Col I. M Jikamshi"

Wani iri yaji yadda ta fadi sunan a hankali kamar bata so yaji.
"I. M Jikamshi yana rokon alfarmar ayi saving din numbarsa saboda kada ki sake kirana Zulaiha. By the way ina princess dina?

"Ana yi mata wanka"

"To zan sake kira anjima ki hadani da ita. Ina fata kinji request dina. Idan kika sake kirana da sunan mata zamu kulleki ni da Safina. Ki gaida da Umma."

Amsa masa tayi da to...tana 'yar dariya ta ajiye wayar.

Mimi babbar 'yar Shemau ce ta shigo tana kiranta Umma tace tazo falo. Hijab ta saka ta fito daidai lokacin da Qasim ya dago kansa. Suna hada ido nata ya ciko da hawaye shi kuma nasa suka yi ja sosai.

Ya kura mata ido yana kallonta "Asmau ke ce?"

Ta fashe  da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni.

Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye
"Yaya Qasim ai bazan ganeka ba"

Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din Abubakar ta dawo gaban iyayenta.

Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata kama wata sabgar.

Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa fuskarta, muryarsa na dan rawa yace  "yaya sunanki"?

Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay"

Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa. Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen rayuwarta. Yana shafa kanta yace
"Safinatu nine babanki"

Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu ne"?
ABINDA AKE GUDU🙆🏽37

Batul Mamman💖





Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido
"Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai mu bi Yaya Yassar mu koma Kano"

"Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau tana bata hakuri
 "Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa magana"

Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan tunanin.

Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu  sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba.

Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk don ta nuna musu bata tare da damuwa.

Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo ganin Amatullah.

Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko uwar 'yar"

"Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi sau da kafa".

"To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da Asmau ta yaba dashi.

"Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana"

"Ita yayar taku tasan da zuwansa?"

"Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum yayi tafiya irin wannan saboda danka"

Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren yayarsa. Yana fita ta shiga ciki  suna daki ana ta wanka saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna Islamiyya.

Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi.

Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a kasa.

Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal-tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta kamar wadda aka kafe a wurin yace
"Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?"

Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya don dadi. Ji tayi kamar ta make shi.

Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta.
"Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga shigowata"

Da sauri Yassar ya nuna masa kujera. Anti Bintu ta karaso ta zauna suka gaisa amma har lokacin idonsa na kan Asmau da ta tsaya kawai tana kallonsa. Bata taba kawowa da gaske zai zo ba kamar yadda ya fada a wayar. Ji tayi ya sake shiga ranta har abin yana bata tsoro.

"Yaya hanya? Yassar na shirin tafiya yace ka shigo gari"

Sai sannan ya maida hankalinsa ga Anti Bintu yana magana da alamar damuwa a fuskarsa
"Waya muka yi da Ummin Safina sai naji kamar tana kuka kuma taki fada min abinda ya sameta. Shine kawai nayi deciding na taho don ko na zauna bazan iya aikin ba"

_Subhanallah_ ta fada a zuci. Shi kuwa me yasa yake haka ne. Baya jin komai idan ya fadi magana a gaban mutane. Kallonta Anti Bintu tayi sai taji kunya. Kada tayi tunanin ko ta fada masa abinda ya faru ne. In'inar karfi da yaji ce ta kamata
"Uhmmm...dama...da.....lokacin...kai" ta rasa karyar da zata yi ma. Shi kuwa ya zuba mata ido kamar bai san da mutane a wurin ba.

Anti Bintu tayi gyaran murya don ta kula hankalinsa yayi gaba. Hasashensu ita da Yassar ya tabbata. Wannan kallo da yake yiwa Asmau indai ba na soyayya bane to bata san dame zata kwatanta shi ba. A iya saninta dai yasan komai game da Asmau shiyasa ta fada masa magana ce surikarta ta fada da batayi mata dadi ba shine dalilin kukan.

Bata so aka fada masa ba tana tsaye a inda take tun dazu ta soma hawayen da ta rasa dalilinsu. Karshe ciki ta shige kawai ta koma daki. Sai da yaga shigewarta yace "ita Asmau haka take ne da saurin kuka? Na zata a yadda taga rayuwa by now ta zama jaruma wadda zata iya daukar duk abinda yazo mata"

Yassar ya bi bayanta zai lallabata ta dawo wurin bakonsu don maganar komawarsa Kano yanzu kuma tabi iska.

Anti Bintu tace "tun da can Asmau mace ce mai raunin zuciya. Faruwar wadannan al'amuran sun sa ta kara samun rauni dole ne sai muna binta a hankali har Allah Yasa ta iya sakin jikinta kamar da. Dazu munyi mata nasiha sosai akan toshe kunnuwanta game da irin wadannan  maganganun da zasuyi ta tasowa"

"Allah Ya kara rufa asiri. Kiyi hakuri I just can't help myself when it comes to Asmau"

Tayi dariya "babu komai, mu hakan muke so ma. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"

Da yake yasan bazata girmeshi sosai ba sai yayi murmushi "ko Yayata? Kada kice kin gano ni "

"Na nawa kuma" tayi dariya.

Sai ya rufe fuskarsa da hularsa "amma kuwa har naji kunya."

Anti Bintu me zatayi banda dariya ta tashi "haka kake da abin dariya"

Dan dakewa yayi shi a dole babu wasa "don dai kawai a gaban in-law nake. Amma ni serious mutum ne. Soja ai baya abin dariya"

"Uhmmm naga alama, sai dai ban rike sunan wannan sojan ba"

"Call me Ishaq"

"To Ishaq kanina Allah Ya bada sa'a. Bari na turo maka ita. Ga abinci nan don Allah ka ci"

Daga shi har ita dariya suke yiwa juna sannan yayi mata godiya ta tafi. Da taje dakin Yassar ta gani yana faman bawa Asmau dake kuka hakuri tana yi masa fadan me yasa ya kawo shi gidan.

Ta shiga dakin ta zauna a gefen gado "bana son shirme Asmau, meye abin kukan ma. Idan  mutum ya nuna kina da mahimmanci a rayuwarsa bai cancanci wulakanci daga gareki ba. Dan gyara fuskarki kije ku gaisa."

Ta tashi zata shiga bandaki ta wanke fuskar Yassar yace "Antinmu kema kinyi mubaya'a ne. Naga kin shigo kina dariya"

Ta kalli Asmau da ta juyo tana kallonsu " ina wasa da kai ne. Tashi ka bani wuri kazo ka zauna a cikin mata" fita yayi yana dariya kawai.

Asmau ta wanko fuskarta ta fito "mubaya'ar me Yassar yake tambayarki?"

Ainau da tun dazu bata saka musu baki ba tace "nima abinda zan tambaya kenan"

"Ku kyale shi shashancia ne kawai" ta bagarar da zancen ta fita.

Ainau tace "ko dai baban Amatullah yana ciki ne"

"Kinga ki kiyayeni. Ya isheku daga ke har Yassar"

Tana jiyo dariyar Ainau har ta kai karshen korido din da zai kaita falon.

A zaune ta same shi yana waya ta zauna a wata kujerar daga can gefe. Yassar yana daga kusa dashi. Sai da ya gama yace "Yassar dan bamu wuri ina son siye zuciyar yayarka"

Ya tashi yana dariyar da ta soma bawa Asmau haushi ita kuwa ta bata rai. Ya dan mike kafafunsa
 "yunwa nake ji"

Fuskarta babu wata fara'ar kirki tace "ba ga abinci nan a gabanka ba"

"Kince naci ne?"

"Au sai nace?"

Ya gyada kai yana murmushi wanda yasa ta dan saki fuska.
"To ga abinci nan kaci"

"Nagode" ruwa ya fara sha sannan ya bude plate din da aka hada masa abincin zai ci.

Asmau ta tashi "bari na baka wuri kaci abincin"

"No yi zamanki please"

Kasa kallonsa tayi yana cin abincin. Shima kadan yaci ya rufe plate din. Haka yake abinci bai dame shi ba.

"Asmau kalleni nan"

Dan kadan ta iya daga kanta ta dube shi

"Ina so ki zama jaruma mai hakuri da dukkan abinda zata ji ko ta gani a wurin mutane. Babu wani abu da bazai wuce ba a duniya saboda haka yawan zubar da hawaye akan magana ba naki bane. Ke uwa ce dole ki jajirce wurin zama macen da ba raguwa ba ko don kada 'yarki tayi koyi da hakan"

Yana magana ta soma hawaye har ya kai karshe. Girgiza kansa kawai yayi
"Don nace ki rinka barin kukanki kiyi a gabana shine zaki yi kuma. To share hawayen ko na share miki da kaina"

Habar mayafinta tasa ta goge hawayen da sauri
"Ko ke fa...yanzu ace nazo tun daga Kano amma fuskarki duk a kode"

Ta dan turo baki "don zaka zo sai nayi kwalliya?"

"Sosai ma kuwa, ko ba kya so ki kara samun karbuwa ne. Yanzu haka zan kama hanya har na koma gida kodaddiyar fuskar nan zanyi ta gani. Da na sani driver nasa ya kawoni"

Asmau tace "nifa..."

"Ke fa me?  Kinga mu bar wannan zancen sai kin koma gida. Wai ina princess dina ne banganta ba"

"Sai yanzu ka tuna da ita? Tayi bacci"

Ya kwantar da kansa a saman kujera "duk laifinki ne. Kin wani kasheni da ido kinsa bana tunanin komai sai naki. Kije ki tasheta magriba ta kusa kada ki koya mata baccin yamman nan"

Asmau ta tashi tana tafiya tana waigensa. Duk juyawa sai yayi mata murmushi sai ta kawai da kai. A na ukun ta kusa karo da bango ya soma dariya "yi a hankali ba yanzu zan tafi ba sai kin koreni da kanki"

A kunyace ta shige tana mamakin yadda ya gama da zuciyarta cikin dan kankanin lokaci.
******

Bayan tahowarsu Mama Yalwa taje gidan Umma. Suna zaune harda Hajjo take fada musu yadda suka yi da Qasim a daren jiya kafin ya tafi da kuma amsar da Asmau ta bashi.

Hajjo tace "ki ji min yarinyar nan fa. Ita banda abinta ai ba saka mata ido zamuyi ba. Kuma yaron nan Qasimu ya cancanci yabo wallahi. Bari ta dawo muyi magana amma aure ai shine rufin asirinta."

Umma tace "nima na yaba da halayensa sosai. Nasan duk abubuwan da take tunani har yasa take tsoron yin aure. Amma ko kadan ba hujja bace. In sha Allah zamuyi mata magana. Ni kaina ban hango mata rufin asiri ba kamar a gidan Qasim. Allah Yayi masa albarka".

"Amin" Mama ta amsa. "Kar kiso kiga yadda naji dadin labarim nan. Yarinya ce mai biyayya nasan bazata watsa mana kasa a ido ba.
*****

Da yamma ne bayan tafiyar Mama  Anti Bintu ta kira Umma tana bata labarin zuwan Col. Ishaq da hirar da suka yi. Cike da murna tace "Yaya Bara wallahi na yaba da yadda ya damu da Asmau. In  Allah Yaso shine zai share mata hawayen dukkan damuwarta."

Umma bata iya bata amsar kirki ba saboda tunani da ta shiga yi akan maneman 'yarta.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽36

Batul Mamman💖




Ba karamin damunsa rashin daukar wayarsa da Asmau take yi yayi ba. Sai dai kuma ya kuduri niyyar bazai barta ba. Murmushi yayi....yana son mace mai jan aji, amma bazai bari ta ja masa aji da yawa ba saboda yadda yake ji da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu. Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa kansa yana murmushi ya tura mata da text
"Asmau Ummin Safina  ki shirya, don Jikamshi da gaske yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt"
*****

Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din. Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana wannan  tunanin ne bacci ya kwasheta.

Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta da tunanin da ta kwana ta tashi dashi.

Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo washegari.

Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take son yi kenan.
"Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman haka."

"Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba. Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara."

Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana" ta kare maganar da kuka.

Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin shaidan da mukarrabansa.
"Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da bayinSa."

Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu.
*****

ASP Qasim zaune gaban mahaifiyarsa ya gabatar mata da zancen Asmau wanda ta dade da sanin kudurinsa akai.

"Baba ni bazan hanaka aurenta ba. Babanku ma yace ya amince da auren. Abu daya nake so da kai shine ka tuna dukkan abubuwan da suka faru. Naso kwarai kayi aure kafin yanzu ta yadda ko ka auri Asmaun zaka hadata da wata matar"

"Inna kenan, kina gudun ita kadai ta kasance surika a gareki saboda tana da 'ya kafin tayi aure?"

"Dan nan yau da gobe sai Allah. Mutane da bakinsu bazasu fasa surutu ba"

"Amma Inna nasha fada miki ina gudun zamansu da kishiya yaki dadi saboda gori. Da bata dawo ba kamar yadda kika bukata a shekarar nan zan nemi aure. Ku cigaba da yi mana addua."

Ta kada kai "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Haj Yalwa tace zata zo dasu su gaishe da Malam. Allah Ya kiyaye hanya"

Qasim ya tashi ya leka dakin mahaifinsa har lokacin bacci yake yi. Shiryawa yayi cikin wani yadi mara nauyi ruwan toka yayi kyau sosai ya kama hanyar Kano daga Shanono.

Ana magariba ya iso. Gidan Mama ya fara zuwa suka gaisa sannan ya kira Asmau ya fada mata zai zo idan an idar da sallar isha. Umma taje ta sanarwa.
"Allah Sarki Qasim, gaskiya ya rike amana. Ji yadda yake kokarin kula daku duk da ba a garin nan yake aiki ba. Allah Ya biya shi da mafificin alkhairi."

Asmau ta amsa da amin tana gyara goyon Husna da tayi.

Suna cikin hira Qasim yayi sallama Umma tayi masa izini ya shigo. Cike da ladabi ya gaisheta ta amsa fuska a sake. Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma dakin Hajjo. A nan ta sanar da Amatullah zuwan Qasim daya baban nata ta fito gaishe shi.

Qasim ya ajiye kofin lemon dake hannunsa yana maida hankalinsa Asmau.
"Asmau magana nazo muyi, ina fata zaki saurare kuma ki fahimceni."

"Ina jinka Yaya Qasim"

"Asmau kinsan irin shakuwa da abotar dake tsakanina da marigayi Abubakar"

Ta gyada kai tana tuno masoyin da bazata taba mantawa ba a tarihin rayuwarta.

"Duk abinda ya gudana a rayuwarku na sani na kuma san nima akwai sa hannuna a ciki. Bazan gaji da rokon gafararki ba saboda ance karfe daya baya amo. Kamar yadda kawa ta ribaceki haka nima nayiwa Abubakar, ga kuma sakamakon hakan duniya ta gani. Asmau tun kafin ki dawo na yanke shawarar aurenki ko a wane yanayi na sameki. Cikin ikon Allah yanzu na tsinci kaina da tsananin kaunarki"

A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya
"Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Abubakar bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki na kuma zama uba ga 'yata Amatullah."

Wannan shine ana wata ga wata. Ita fa ko kadan bata son maganar aure ma yanzu. Qasim wani babban jigo ne a rayuwarta saboda yadda ya damu da lamarinta da na Amatullah. Ya rike amanar Abubakar ba da wasa ba.
"Yaya Qasim bani da abinda zance maka sai godiya da fatan alkhairi amma don Allah ka janye maganar aure a tsakaninmu. Maganar aure ba ta mace irina bace. Duk yadda zan so bani da wani mutumci da kima da zan kai gidan aure. Amatullah ko naki ko naso 'yarka ce amma don Allah mu bar maganar aure."

Dama yasan da wuya ta amince kai tsaye.
"Ba cewa nayi ki bani amsa yanzun nan ba. Zan baki lokaci kiyi tunani. Amma ki sani kamar yadda aure yake zama garkuwa ga kowace mace kema shine mutumcinki. Zamanki a haka shine zai janyo miki duk abinda kike gudu wato surutun mutane."

"Ni dai....."

Hannu ya daga mata alamun tayi shiru ya tashi tsaye "kiyi tunani nace kuma kiyi shawara da duk wanda kika san zai baki shawara tagari"

Rasa abin fada tayi kawai ta sanar dashi batun tafiyarsu a washegari yayi mata addua sannan yace zai zo idan ta dawo yasan lokacin tayi duk wani tunani da zata yi.

Bayan tafiyarsa Asmau ta shiga tashin hankali. Ko zata yi aure ba dai da Qasim ba.  Idan ta amince tamkar taci amanar Abubakar ne. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa ta tafi daki da niyar kwanciya wayarta ta soma kara.

Sai da gabanta ya fadi da taga sunan mai kiran. Kwana biyu tun ranar da taki amsa wayarsa bai kara kiranta ba sai yau. Zuciyarta ce ta rinka bugu da sauri da sauri amma ta kasa amsa kiran. Text taga ya turo mata
_Idan Safina batayi bacci ba ki hadani da ita. Taki muryar ma ina son ji amma ba a waya ba, so wayar ba taki bace._

Wani dan murmushi ne ya subuce mata. Sai kuma ta dan dake tana yiwa zuciyarta tuni da cewar ta manta da maganar aure. Babu wani namiji da zai aureta a yanayin da take ciki komai tsahon lokaci ace wata rana bai goranta mata irin rayuwar da tayi a baya ba.

Dakin Umma taje ta bawa Amatullah dake aikin wasa da Husna wayar da ya sake kira. Kusan minti ashirin tana ta yi masa hira sannan mikawa Asmau. Da ta karba sakawa tayi a kunnenta tayi shiru tana so taji ko ya ajiye.

Yanayin yadda take saukar da numfashi ne ya tabbatar masa ta karbi wayar. Murmushi yayi kamar tana kallonsa yace
"Ana so ana kaiwa kasuwa"

Da sauri Asmau ta kashe wayar tana dariya. Me ya kaita saka wayar a kunnenta ne. Umma tace "ke lafiyarki kuwa?"

Tayi saurin daidaita kanta. Yanzu fa ta gama cewa babu zancen aure a sauran rayuwarta. Me yasa take jin wani daban idan al'amarin ya shafi Jikamshi.
*****

Col. Ishaq yana zaune ya saka abinci a gaba bai ci ba ya soma wayar. Dariyar da yake yiwa Asmau ce tasa Hajiya kallonsa.
"Yaya dai kake dariya kai kadai? Kwana biyu na fuskanci wani nishadi kake ji."

"Hajiyata babu komai" abincin yaci dan kadan ya sa Bilkisu ta kwashe kwanukan. Wai shine tunanin mace ya mayar haka. Abin da mamaki, duk dakiya irin ta soja yanzu baya jimawa sai Asmau ta fado masa.
******

Da wuri suka tashi aka karasa shiri saboda Yassar yana son dawowa a ranar. Kafin karfe goma na safe sun hau hanya bayan sun biya gidan Mama sunyi mata sallama.

Aina'u tana gaba Asmau na zaune a baya da baby Husna da Amatullah. Sunyi nisa Qasim ya kirata. Har kunya taji saboda yace ta kirashi kafin su fito taki kira, a cewarta kada ta sa masa rai yayi zaton zata amince nan gaba. Adduar neman tsari yayi musu sannan ya gaisa da Amatullah. Ba dadewa kuma  Col. Ishaq yayi mata text. Lokacin bai dade da shiga office dinsa ba.
_Zan kira ki yanzu ki fara dauka kafin ki hadani da princess dina._

Ya zata yi ne da Jikamshi. Duk irin wannan abubuwan da yake yi mata kara kashe mata jiki yake yi. A daya bangaren kuma tana ganin gangancinta da har ta bari yake tasiri a zuciyarta haka. Idan har aure ya zama dole a kanta ma bashi ya kamata ta aura ba. Qasim yafi kusanci da ita, yafi sanin dukkan matsalarta. Amma Jikamshi shine a ranki zuciyarta ta tuna mata kafin wayar ta fara ringing.

A kasalance ta daga wayar ta kara a kunnenta kamar tana jin tsoron amsawa.

Shi kadai ya sauke ajiyar zuciya da yaji ta dauka.
"Just wanted to let you know how much I miss you."

Muryarsa da komai nasa daban take jinsa. Ga wani girmansa da take gani a kullum. Lumshe ido tayi batare da tayi koda gyaran murya ba.
"Idan kin janye yajin aikin yi min magana ki fada min zan zo na ganki. Ina Princess dina?"

Mika mata wayar tayi ta fara bashi labarin tun dazu suke cikin mota suna ta tafiya. Ina zasu je da safen nan ya tambayi kansa. Sai kuma ya tambayeta waye yake tuka motar tace Uncle Yassay ne. Yana son jin inda zasu je amma kuma baya son tilasta Asmau tayi masa magana. Karshe yace tace masa ya kirashu idan sun tsaya. Bata ajiye wayar ba ta fadi sakon. Yassar yasa Ainau ta danna speaker a wayar. Gaisawa suka yi ya fada masa inda zasu je. Col. Ishaq yace to a kula masa da 'yarsa.

Sai da ya ajiye wayar ya hau tunanin ko kwana nawa zasuyi. Kwana biyun da baiji murya ko yaga Asmau ba baya jindadi.
*****

A gidan Anti Bintu yau tun safe suke kitchen ita da 'ya'yanta. Yadda kasan bata ga Asmau ba bayan dawowarta haka take ji. Maman mijinta Kawu Yuduf tana gidan ana gyara a nata gidan. Tun da taga suna aikin nam take tabe baki tana kananan surutai. Bata tashi yin magana sosai ba sai da taji tsayuwar mota taga duk sun fita tarbarsu Asmau. Suna shigowa ta ganeta don dama ta santa. Yar tsohuwa tace
"Yanzu duk wannan doki da murnar na ganin shegiya ne da uwarta, banda lalacecar zamani yaushe 'ya zatayi zina sannan a rinka rawar jiki don ta dawo kamar wadda tayi wani abin arziki"

Anti Bintu ta rasa me zata ce don tsabar kunya. Asmau kuwa tuni ta soma zubar da hawaye. Babbar 'yar Anti Bintu da ake shirin aurarwa bata rai tace "haba Gwaggo"

"Wane irin haba, barni nayi magana son raina. Ba 'yar zinar bace ko kuwa uwarta bata bar mata abin kunya ba na 'ya'ya da jikoki?"

Ba Asmau ba hatta Aina'u sai da tayi kuka. Allah Ya rufa musu asiri ma Kawu Yusuf yana gidan ya fito daidai sanda babarsa ke yabawa Asmau maganganu.

"Gwaggo me ya kawo wannan maganar kuma. Kaddara ce wacce bata wuce kan kowa"

"A'a wallahi irin wannan kaddarar sai 'ya'yan da basu da tsayayye a kansu. Nawa jikokin Allah Ya tsare min su. Kowacce zata kai budurcinta gidan miji"

Kuka wiwi Asmau take yi. Kukan nata ba don abinda Gwaggo ta fada bane ai duk abinda tace gaskiya ne. Gaskiya kuwa akwaita da daci. Lallai sun tafka babban kuskure a rayuwarsu kuma muddin tana numfashi tasan wannan abu bazai taba gogewa daga zukatan mutane ba. Mutumci madara ne idan ya zube ba'a taba iya kwashe shi gabadaya.

Anti Bintu ta kaisu dakinta tana ta rarrashi da bata baki. Yassar ya kasa zama ya fice ya koma mota rai a bace. Allah Kadai muke yiwa laifi yafe mana baki daya amma indai dan adam ne to a kowane lokaci ya sami dama sai ya tuna mana da laifinmu ko da bisa kuskure ne. Hakika shaidan dole yayi murna idan yaci galaba ya sanya mutane suka aikata zina domin tabonta baya taba kankaruwa a duniyar mutane dai.

Yassar na zaune ransa sai suya yake. Ko kadan abinda aka fadawa yayarsa baiyi masa dadi ba. Mutane basu san laifi indai Allah akayiwa kuma aka tuba Shi mai yawan gafara ne da jinkai. Yamadidi da mai laifi bashi daga cikin kyawawan halayen musulmi. Tsaki yayi ya dauki wayarsa ya kira Col. Ishaq dama ya karbi numbar a wurin Asmau. Ya sanar dashi sun iso lafiya sai dai tuni ya gano akwai abinda yake damun Yassar din. Yayi ta tambayarsa me ya faru ya dage babu komai. Hankalinsa ne ya tashi ya kira Asmau.

A lokacin Anti Bintu har da mijinta sun gama bata baki sun fita akan sai tayi hakuri domin zata yi ta cin karo da irin haka.
Tana ganin wayar batayi tunani komai ba ta dauka.
Wannan muryar mai dadi taji yace "Ummin Safina"
Fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya wanda ya sashi saurin tashi daga zaman da yayi.
"Asmau me ya ya sameki?"

Shasshekar kukanta ya cigaba da ji ya sake kiran sunanta har lokacin bata amsa ba. Hankalinsa a tashe yace "Asmau please ki amsa mana"

"Naam" ta fada cikin muryar kuka.

To me aka yi mata haka?duk yadda akayi abin ya shafi 'yan uwanta tunda yaji Yassar ma ransa a bace.
"Kina son ganin Jikamshin ki?" Ya fada cikin wata irin murya.

"Naam" ta sake fada da alamar tambaya duk da kukan da take yi.

"Kinji me nace fa ni bana son gulma. In zo ki ganni ki fada min damuwarki?"

Sake kankame wayar tayi tana jindadin maganarsa harda dan murmushi.

"Kinyi shiru ko ba kya son gani na?"

"Eh" sai tayi saurin cewa "a'a" tun kafin ya sake magana.

"Ban san abinda ya saka min ke kuka ba amma ki rinka jira sai ina wuri kiyi kuka don na rarrasheki. I will see you soon in sha Allah"

Bai jira tayi magana ba ya katse wayar ya tashi ya tafi office din abokinsa.


SADAUKARWA GAREKU
*MATAN KWARAI NA SAMI SAKON GAISUWA
*UMMUL DIHYAH, HASSANA, USAINA, AMINA DA RUQAYYA.

SAURA MASU GAISUWA DUK BAN MANTA DAKU BA. NAGODE
ABINDA AKE GUDU🙆🏽38

Batul Mamman💖






Har karfe tara na dare ta wuce Col. Ishaq bashi da niyar tafiya. Hira suke yi da Anti Bintu da Kawu Yusuf kamar sun dade da sani juna. Sai ko Amatullah da ta tare a falon tana jikinsa tun bayan tashinta daga bacci. Hatta masallaci da ita suka je da Yassar. Maman Kawu Yusuf kuwa tana daga daki tuni tayi bacci bata san wainar da ake toyawa ba.

Asmau tana tare da 'yan uwanta suna tasu hirar amma tana tunanin yaushe Jikamshi zai tafi ne. Gashi a dalilin zuwansa Yassar yayi biris da zancen komawa Kano.  Ainau ta dauki waya zata kira babbar Yaya wato Shemau ta tsegumta mata abinda ke faruwa a Zaria Asmau ta hanata.
"Naga alama sai da ya tofeku tas ya shigo gidan nan. Kowa sai wani kokarin kyautata masa yakeyi"

Ainau tayi dariya "ki ce hakan baya miki dadi duk sai mu daure fuska"

"Yaya Asmau mu dai kada ki cucemu ki hanamu zuwa bikin sojoji. Kinsan babu abinda ke bani sha'awa kamar su hada takubba amarya da ango su wuce ta tsakiya." Dijah ta fada tana hango ranar bikin.

Daga nan suka shiga tsara biki harda irin kayan da zasu saka. Tun Asmau na hanasu har ta koma sakin baki tana jin yadda suke bayani kamar gobe ne daurin aure. Da ta gaji tace "to amarori sai kuyi hakuri zan bata muku show amma ni bani da niyar aure, dadin abin ma ba cewa yayi yana sona ba kuke ta rawar kai"

Ainau tace "jiran *I love you*kike sai kace wata matar da. Yanzu ai alama kawai ta isheki. Dazu fa da na fito falo ba karamar kunya naji ba yadda yake yi miki ga Anti Bintu a wurin."

Bata da abin cewa da zai hanasu abinda suke yi sai kawai ta kyalesu.
*****

A falon Col. Ishaq yace zai nemi wurin kwana gobe da sassafe ya kama hanyar Kano don ba da niyar kwana yazo ba. Yassar yaso binsa masaukin da zai nema sai dai yadda Anti Bintu ke kallonsa ya gane rashin dacewar hakan ko don kada ya dora masa nauyi. Tace ya daure ya biyo ta gidan yayi breakfast sannan ya wuce. Ya tashi yana yi musu godiyar irin karramawar da suka yi masa, suma suna masa godiyar ziyarar da ya kawo musu.

A waje ya tsaya da Amatullah wurin motarsa ya tura Yassar ya kirawo masa Asmau. Daga shiga sallar magriba bata sake fitowa ba. Gabadaya kewarta ta dameshi. Don kada aga rashin kunyarsa tayi yawa ne da tuni ya nemeta saboda ziyarar ma don ita yayi.

Tasha tsokana a dakin kafin ta fito. Yassar ne mai yi musu jan ido su dena damun matar ubangidansa. Yana fadin haka ta dage ta kai masa dundu a baya tana cewa duk sun raina ta amma zatayi maganinsu.

Tana sakkowa daga matattakalar kofar wajen yana ta kallonta har sai da ta kusa faduwa saboda yadda kafarta ke hardewa. Yayi saurin zuwa inda take yana mata sannu ta dan daure fuska. Yayi murmushi
"ashe dai kema kina jin yadda nake ji Asmau."

"Nake jin me?"

"Dazu garin kallona kika kusa bugewa da bango, yanzu kuma gashi kina neman faduwa" yayi mata murmushi "idan muka yi aure anya zaki bari na rinka zuwa aiki?"

Tafa hannu tayi tana girgiza kai sannan tace "ni bansan me zan ce maka ba ma."

"Babu abin fada ne tunda kinsan gaskiya"
Ya bawa Amatullah ledar alawa yace ta shiga ciki yana zuwa. Sai da ta nunawa Asmau tayi masa godiya sannan ta shiga ciki.

Yace "gara ta koma cikin gida kada ki koya mata soyayya tun yanzu"

Dan cije lebenta tayi tana murmushi. Har kasan zuciyarta ta amince tana son Col. Ishaq. Bata san lokacin da ta kira sunansa ba a can ciki tana mai jan sunan.
_Jikamshi_"

Wani irin sonta yaji yana kara shigarsa. Bai taba damuwa da sunan garinsu ba amma saboda dashi Asmau take kiransa har wani dadi yake ji na daban.
"Yes dear"

Ta sunkuyar da kanta kasa "wai so...so"

"Ki fadi abinda zaki fada bana son jan rai. Ko don kinga ina son muryarki. Hmmm? Sai ki rinka kara hargitsani da ita."

Murmushi ta sake yi shima yayi. Yana jindadi idan yaga ta saki jikinta tana fara'a kamar kowa. Tace
"Wai soyayya muke yi"?

"A'a a filin yakin duniya na uku muke" ya bata amsa yana daga gira.
"Kina so nayi miki gwari gwari ne sai ki fi fahimta?"

Ta kawar da kanta gefe cike da kunya da fargaba. Muryarsa taji yace "Ina sonki Asmau Ummin Safina. Babban burina yanzu bai wuce na aurenki ba da kasancewa tare daku har karshen rayuwata. Kuma zuciyata tana bani kema abinda ke taki zuciyar kenan. Right?"

 Hawaye taji sun taho mata. Wannan mutumi da ya santa cikin kankanin lokaci kuma yasan sirri mafi muni a rayuwarta shine yake fada mata kalaman so har yake batun aure. Dole taji sonsa yana kara shigarta sai dai kuma bata manta alkawarin da tayiwa kanta ba. Duk irin son da take yiwa Jikamshi bazata iya aurensa ko waninsa ba. Tana kuka tace
"Nagode Jikamshi, kaine mutum na farko da ya fara sona da gaskiya tun bayan kaddarar da ta sameni. Ka kyautata min kuma ka kyautatawa Amatullah. Allah Ya saka maka da alkhairi. Amma kayi hakuri da maganar aure. Kasan komai game da rayuwata me zai sa ka...."

Bai nuna damuwa ba ba fuskarsa sai ma murmushi da yake yi mata a yayin da take zubar da hawaye.
"Asmau, Asma'u na. Kina ganin idan nace na janye zaki ji dadi?"

Sai da taji faduwar gaba sannan ta gyada masa kai.

"Hmmm kamar gaske. Ina so kisan cewa bazan taba janyewa ba. Ni ba karamin yaro bane. At the age of 42 nasan meye so ko kishiyarsa. Kuma a naki idon so nake gani....infact kamar ki hadiye ni"

"Lahhhhh" ta iya fada hawaye na sintiri a idonta. Wallahi tana son Col I.M Jikamshi amma dole ta hakura indai ba so take ta daukarwa kanta dala ba gammo ba. Tana da yakinin ko Hajiyarsa bazata lamunce danta ya aureta ba.

"Rufe bakin mana"

Ta kuwa hade bakinta kamar yadda yace.

Dan kara matsowa yayi amma da sauran tazara a tsakaninsu.
"Kafin haduwarmu na ajiye batun aure a gefe tun bayan rabuwarmu da matata ta shekara kusan shadaya. Yanzu da na hadu dake sai nake jin rayuwata bazata kara min dadi ba idan babu ku. Ki manta da komai na bacin rai ki rungumi mai sonki. Ni fa nake nufi"

Murmushi ne yazo mata babu shiri.  Sannan tace
"Kasan dalilina na gudun aure. Gori nake gudu ko a ni ko Amatullah. Sannan kaima duk inda kaje za'a nuna ka"

Hamma yayi alamun baya son maganar "duk kin tsareni da zance kin hanani na tafi na kwanta."

"Maganar fa tana da mahimmanci"

"Bacci na ma yana da mahimmanci. Ina fatan haduwa da Asmau ne muyi hirar arziki batare da tayi min kuka ba."

Jikinta ya kula yayi sanyi. Duk abinda take gudu ya riga ya hangosu amma ko da aure ko babu abinda ya faru ya riga ya faru a baya. Wucewarsa sai a hankali idan Allah Yaso. Indai ya sami amincewar Hajiya wanda baya tunanin zata ki to duk abinda mutane zasu fada sun dade basu fada ba.
"Zan baki lokaci daga nan har ki gama zamanki. Yassar ya fada min zaku je Niger so duk zan baki damar yin tunani kiji ko zaki iya zama batare da kina ganina ba. Ranar da kika dawo a ranar zanzo naji amsarki. Kada kiyi tunanin gujemin Asmau."

Kanta a kasa har ya shiga mota yana tausaya mata. Ba don kaddara ba ace tana son abu amma wani kuskure da ya riga ya wuce yasa tana gudunsa. Bata dago kanta ba har ya saita motar zai tafi sannan suka hada ido. A hankali ta karanta lebensa ta gane abinda ya fada wanda ba'a ji sai motsin bakinsa kawai.
_Love you_
******

Bayan tafiyarsa gida ta shiga tana ta juyayin zancensa. Dakin Anti Bintu ta nufa tayi sa'a bata dade da fitowa daga wanka ba. Cike da damuwa ta zayyana mata yadda suka yi da Jikamshi.
"Ko baki fada ba Asmau idanuwanmu sun gane mana. Ki godewa Allah da Ya dubeki da rahma Ya kawo miki mai share miki hawaye"

"Anti ba kya ganin rashin dacewarmu. Karshenta  danginsa bazasu amince ba. Kuma ina tsoron wulakanci da gori nan gaba duk da ni na janyowa kaina." Ta fashe da kuka

"Haba Asmau. Har yaushe za'ayi ta maimaita abu daya. To bari kiji in fada miki. Indai bakiyi aure ba wallahi sa ido sai yafi a kanki. Ko takalmi kika canza sai an sami masu yi miki muguwar fassara. Gara kiyi aure ki samu garkuwa da rufin asirin da kowace mace take nema."

Tasan gaskiya ake fada mata amma gaba take ji. Ranar da miji zai goranta mata. Ranar da zai nuna mata alfarma yayi mata da ya aureta. Anti Bintu tana ta nuna mata ta karbi kyautar Allah hannu bibbiyu ta fada mata yadda suka yi da Qasim.

"Ikon Allah, wannan yanke shawara ba zai yiwu da gaggawa ba. Duk mun shaida irin neman da Qasim ya rinka yi miki. Amma banyi zaton abin zai kare a soyayya ba. Ga kuma Ishaq da kuka hadu lokaci guda ya kamu da sonki da na Amatulllah. Kuma kema nasan shi din kike so. Ki bari ku koma Kano nima sai nazo ayi magana da su Hajjo da Yaya Abu. A yanzu dai ki dage da neman zabin Allah. Amma ki sani aure shine gatanki. Kada na kara jin kince bazaki yi ba"
*****

Sati dayan da suka yi sunji dadin zaman garin idan ka cire maman kawu Yusuf. Soyayyar Jikamshi kuwa kullum karuwa takeyi a ranta. Duk da basa waya don yace zai bata lokaci tayi tunani batare da ya dagula mata lissafi ba. Ga Qasim kullum yana waya amma baya mata zancen soyayya. Shima yace sai ta dawo zasuyi shawara.

Al'amura duk sun cakude mata. Ranar da suka cika sati Umma, Yassar da Jafar suka iso harda Sabira. Mota biyu suka yi.  A ranar suka wuce Wushishi. 'Yan uwa da abokan arziki sunyi musu tarba mai kyau. A gidan Kawun su Umma aka yi musu masauki. Mutane suna ta zuwa ganin Asmau da 'yarta. Kowa da abinda zai fada. Wasu su fadi mai dadi wasu kuma sai dai a kawar da kai idan sunyi magana. A nan ma sati guda sukayi suna zaga dangi sannan suka kamo hanyar Kano.

Tun a hanya Qasim ya sanar da ita zai zo washegari da daddare idan sun huta saboda jin amsarta. To kawai tace tana tunanin abinda zata fada masa. Gashi Umma tace sai sun dawo Kano zasuyi maganar sosai don duk su biyun babu na yarwa amma dai zukatansu sunfi karkata ga Qasim da suka sani tuntuni.
*****

Kamar yadda yayi alkawari a gidan Isha tayi masa ma. Bayan sun gaisa da Umma suka fito waje da Asmau suka zauna kan wasu kujeru daga gefe.

Bayan fitarsu Col. Ishaq ya rinka kiran wayarta. Yasan jiya tace zasu dawo saboda haka lokacin jin amsarta yayi. Da yaji shiru saboda tun kafin magariba ta jona  chaji  ta barta a daki sai kawai ya shirya ya taho.
******

Suna zama Qasim yace "Ya naga kamar kin rame ne? Ko duk rashin hutu ne kuna ta ziyara."

"Kai kuma kayi kiba Yaya Qasim kamar ba dansanda ba. Anya zaka iya bin barawo da gudu kuwa yanzu?"

Tare suka soma dariya yana kallonta yana jindadi. A daidai wannan lokacin Col. Ishaq ya shigo gidan da motarsa. Bisa rashin sani ya haskosu suna dariya ransa yayi matukar baci saboda kishi.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽39

Batul Mamman💖





Tsabar bacin rai yasa yayi wani irin cin taya sannan yayi parking din motar. Duk jikinsa tsuma yake yi, zai iya rantsewa bai taba jin kishi makamancin wannan ba duk tsahon rayuwarsa.

Asmau ma tuni ta hadiye dariyarta gabanta na faduwa. Duk da bata ganshi ba amma ta gane motar. Sai taji ta tsani kanta da har tayi abinda zai bata masa rai. Amma laifinsa ne don ranar da suka dawo yace zai zo shiyasa yau ta fito wurin Qasim da kwarin gwiwarta. So take yi ta fara sallamarsa sannan shima wanda yayi nasarar samun soyayyar tata ta nemi su rabu. Duk iya tunaninta karatu ne kawai mafita garesu ita da Amatullah.

Qasim bawan Allah ya kula da yadda ta canja lokaci guda har ya fara tunanin waye a motar. Motar ya rinka kallo da Asmau.
******

Kamar ya juya haka ya rinka ji sai dai kuma hakan ba girmansa bane tunda har ya shigo gidan. A zuci ya karanta *Hasbunallahu wa ni'imal wakeel*har yaji bacin ran ya ragu sannan ya fito yana zuba _kamshi_. Taku yake daidai har ya iso kusa dasu. Kamshin turarensa da yake sanya Asmau nishadi ne ya fara ziyartar ta. Taji bugun zuciyarta ya tsananta. A iya saninta da Jikamshi baya boye magana ko gaban waye. Bata san me zai ce a gaban Qasim ba, mutumin da bai cancanci wulakanci ko kadan ba daga gareta.

Yana karasowa ya saki fuska duk da ta ciki na ciki ya mikawa Qasim hannu yayi masa sallama.

Qasim ya karbi hannun shima cikin fara'a ya tashi suka gaisa. Sai kuma suka kalli Asmau suna jira ta gabatar dasu. Tsuru tayi da ido kamar wadda tayiwa sarki karya.

Da kyar ta saita kanta tace "Yaya Qasim ga baban Amatullah da nake fada maka. Col. I M Jikamshi."

Sake kama hannunsa Qasim yayi yana murmushi "naso ace har gida nazo na sameka domin kara mika godiya bisa taimakon da kayi mana. Allah Ya saka da alkhairi Ya bada lada. Ashe manyanmu ne masu tsaron kasa. Bari na baka girmanka yallabai."

Gyara tsayuwa Qasim yayi ya daidaita kafafunsa sannan yayi saluting Jikamshi. Shima murmushi yayi ya tsaya a attention ya mayar masa da salute din duk suka yi dariya banda Asmau.

Col. Ishaq yace "ka kirani Ishaq kawai. Asmau bata iya kiran sunana kai tsaye ne shiyasa kaji tana maka kwana kwana ko" ya fada yana mata kallon da ke kara kashe mata zuciya. Ta sunkuyar da kanta kawai. Abinda take gudu kenan ya bata kunya a gaban Qasim.

Ta daure tace "ga Yaya Qasim shi dan sanda ne"

"Allah Sarki, its a pleasure meeting you. Ai ta bani labarinka. Kune manyan ai muna bayanku. Baka ji ana cewa abokin kowa dan sanda" Col Ishaq ya fada yana kara kallonsa zuciyarsa fal kishi yana ta kokarin dannewa.

"Nima ta fada min yadda ta hadu daku. Muna kara godiya."

"Kada ka damu ai yiwa kai ne. Amma me kuke yi a waje haka ga kura? Ina tsammanin damuna ta kusa tsayawa dai" yadda yayi maganar Asmau ce ta fahimci da biyu yake yi.

Shi kuwa Qasim ya dan sosa kai yana dariya. Ko babu komai Jikamshi ya girme shi "Yallabai kenan. A tayamu addua dai muna nema ne"

Wani abu ne ya tokarewa Col Ishaq makoshi yaki sauka kasa. Wai ya taya shi addua. A zuciyarsa yace (Allah Yasa kada ta taba yi maka soyayya irin ta mace da namiji.). Abu daya ke yi masa yawo a ka shine kada Asmau ta juya masa baya. Wannan Qasim din wani sanyi ne gareshi mai sa mutum yaji dadin mu'amala dashi.

A fili kuwa murmushin yake yayi "ah to bari naje naga Amatullah sai na tafi. Dama ita nazo gani kewarta ta isheni" daga nan gefe ya matsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya shigar dashi ciki. Ransa a bace da ya hango Asmau da Qasim yana taya Jikamshi kishi.

Bayan sun shiga ciki Qasim yayi ta yabon saukin kai irin na Col. Ishaq "kamar ba babban soja ba, ji yadda yake jana kamar ya dade da sanina"

"Uhmm" kawai Asmau tace a sanyaye.

"Asmau wace shawara kika yanke mana?"

Ta dago kai a hankali "Yaya Qasim ni dai da mun bar maganar nan"

"Kinga Asmau duk abinda kike gudu baki da tabbas a kansa. Yana iya faruwa ko kuma kiga bai faru ba. Haka nan ma masu aure na fuskantar matsaloli musamman mata daga dangin miji. Bance komai zai tafi mana daidai ba amma nayi alkawarin tsaya miki har karshen rayuwata"

Tausayinsa ta kara ji. Banda tsoronta na aure ko kadan bata jin son Qasim sai tausayinsa saboda yadda yake mata.

"Ka dan kara min lokaci, ban samu nayi maganar da Umma ba"

"To babu komai, shi garaje ai bashi da alkhairi. Duk yadda kuka yi ki sanar dani. Sannan zan kiraki idan na koma gida in sha Allah. Akwai keke da na siyowa Amatullah bari na dauko yana bayan mota"

"Nagode"

"Wai kin gode, mutum da 'yarsa? Shiga ciki bari na dauko"


Da sauri sauri tayi shige.
*****

Daga kallon kofa sai agogo Col. Ishaq yake yi tunda ya zauna hankalinsa baya tare dashi. Ji yake kamar ya koma wajen ya hana zancen. Hajjo ce take kokarin janshi da hira sai Amatullah tana bashi labarin Wushishi. Yassar kuwa kamar yaje ya dauko Asmau yake ji. Da ta shigo Jikamshi ya kafe ta yayi da ido ta kasa kallon inda yake kawai sai ta shige dakin Umma inda suke ta hada kaya ita da Ainau zata koma gidanta washegari.

Qasim ya shigo da keke mai kyau na yara. Amatullah sai tsalle da murna. Tana ta cewa ta gode kamar yadda Umminta ta koya mata. Hajjo ta dubi Col Ishaq "da kai da Qasim kuna shagwaba yarinyar nan da yawa. To ni ina nawa keken?"

Suna dariya Yassar yace "kada ki damu ni zan siyo miki irin mai katuwar tayar gaban nan na zamaninku"

Umma ta fito tayi godiya sannan Qasim yayi musu sallama ya fita. Sai da suka ji tashin motarsa Col Ishaq shima ya tashi yace da Amatullah ta kira Umminta su gaisa. Umma ta jinjina kai tunda ya shigo dazu ta kula ransa a bace yake yana dannewa. Gaskiya akwai matsala nan gaba sai dai fatan Allah Ya zabawa Asmau mafi alkhairi cikinsu.
*****

Tana kwance akan gado har wani zazzabi ke neman kamata saboda tunani Amatullah ta fada mata sakon babanta. Ta dan zaro ido "Baba Qasim ya tafi?"

"Eh ya tafi kuma ya kawo min keke mai kyau"

"Kinyi masa godiya ko"

"Nayi masa Ummi"

"Muje kiyi wasa kafin lokacin bacci yayi"
******

Baya falo da ta fito sai ta saka takalmi ta fita waje.

Tsaye yake a jingine da motarsa yana danna waya ta hasko fuskarsa. Kamar mai taka kwai haka Asmau ta karasa gabansa.

"Ina wuni"

Muryarta tana masa dadi, wani irin sonta yake kara ji yana shigarsa. Sai dai kishi yasa ya kasa amsa gaisuwar.

"Asmau wallahi ina da kishi sosai. Kada ki bari na kara ganinki a yanayi irin na yau. I can't take it"

Ta kara sunkuyar da kai da jin furucinsa.

"Kinga ki dago kanki ki kalleni magana zamuyi"

Mayafinta tasa ta rufe fuskarta gabadaya. kunyarsa take ji.

"Kina so na bude fuskar ne da kaina?"
 Ta girgiza kai da sauri

"To ki bude da kanki kafin hakurina ya kare"

Hannu tasa ta bude fuskar tare da dagowa a hankali. Fuskarshi ta bata tsoro saboda babu digon wasa

"Jiranki da nayi a falo dazu yana cikin lokutan da bazan manta ba a rayuwata. Zuciyata bazata juri ki hadani da wani ba"

"Don Allah kayi hakuri" tace idonta na kawo ruwa.

"Ki fada min ni dashi waye ya fara nuna miki so"

"Kai ne" ta amsa masa jiki a sanyaye. Bata son bata masa rai ko kadan saboda yadda take sonsa.

"Alhamdulillah, da ya rigani zan ci girma na bar masa ke don bazan iya tarayya da wani akanki ba. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai yau. Amma tunda na riga shi sai dai shi ya hakura. Ina sonki kuma bana jin zan iya hakura dake."

Shiru tayi tana kallon kasa. Tun bayan rasuwar Abubakar ta cire rai da sake samun soyayyar wani da namiji sai gashi yanzu har mutum biyu ne suke sonta. Mutum biyun da take matukar son daya, dayan kuma take ganin girmansa. Duk su biyun kuma tana jin kunyar nuna musu bata sonsu a yadda take ganin ba karamin darajata suka yi ba da suke sonta da aure.

Col Ishaq yana kallo  yadda ta shiga rudani. Kamar yadda ya fada mata da ace Qasim ya rigashi to zai hakura ne indai ya tabbatar da gaske yake sonta. A yanzu kuwa yana da yakinin shi Asmau take so kuma ya riga saboda haka yana nan daram sai yaga abinda ya turewa buzu nadi. Shi kishin kara masa so da kaunarta yayi ma.

"Kamar kwana nawa kike bukata na baki ki sallame shi"

Ji karfin hali ta ayyana a ranta. A fili tace "bangane ba"

"Kin gane, karin bayani kike nema dai. Bansan iya matakin da kuka kai ba ke dashi shiyasa zan baki lokaci kuyi rabuwar arziki. Shima don na fahimci kamar yana da halin kirki ne."

"Ya kake so nayi? Kaima na fada maka babu zancen aure a raina shima kuma hakan na sanar dashi"

"Idan babu zancen aure a ranki kin tanadi yadda zakiyi da soyayyata wadda yanzu ma na fara nuna miki ita. Idan bakiyi wasa ba nan gaba kadan saboda yadda zan rinka yakin neman sonki da kanki zaki ce gobe a daura mana aure"

Dariya tayi, shi a komai sai ya saka wasa tace"kai Jikamshi"

"Allah kuwa Asmau" shima ya mayar mata da murmushi.

"Ni da ban taba cewa ina sonka ba. Amma kana da confidence a kaina"

Kansa ya shafa yana kallonta. Baya gajiya da kallon Asmau ko kadan.
"Asmau kina sona. Nima ina sonki. So  bana bukatar sai kinyi ta maimaitawa da baki. Akwai lokacin da zaki rinka fada da kanki"

Ita kam Jikamshi yana bata mamaki. Sai ya fadi magana ya kuma dake abinsa.

"Ki shiga ciki bana son kina shakar kurar nan. Kada ki manta da abinda nace. Idan kin sallame shi zan turo iyayena a fara maganar aurenmu"

Magana taso yi ya sanya yatsansa akan lebensa alamun tayi shiru.
"Idan rokona zakiyi akan Qasim kada ki bata bakinki. Nan da sati biyu idan baki sanar dani yadda kuka yi ba ki zaki ga magabatana sunzo. Ki kula min da kanki da princess dina. Yau duk kin rikita min lissafi na kasa bata kulawa yadda ya kamata"

"Ni babu ruwana."

"Harda tsakinki. Sai da safe"

"Allah Ya bamu alkhairi"

Tana kallo ya shiga mota ya zauna sannan itama ta juya.
"Matar Jikamshi"
Cak ta tsaya amma bata juyo ba sai murmushi da take yi.

"I love you"

Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cike da kunya tayi hanyar gida a kunyace.
******

Daurewa kawai Col. Ishaq yayi har suka karashe hirar cikin wasa. Da ya rage shi kadai yana tuki tunani yake kada iyayen Asmau su bawa Qasim ita saboda sunfi sanin shi sannan abokin Abubakar ne. Saurin kawar da tunanin yayi daga ransa.  A zatonsa ya gama soyayya akan Badar sai gashi lokaci guda Asmau ta wargaza masa tunani.

Yana zuwa gida dakin Hajiya ya wuce. Bayan sun dan taba hira ya sanar da ita zancen Asmau. Tayi mamaki sosai don bata taba hasko hakan ba. Bilkisu da tayi niyar fada mata kuma ranar tun a hanya yaja mata kunne. Shiru tayi na dan lokaci kafi tace

"Kai yanzu kana tunanin  sai ka aureta ne kawai zaka iya kyautata rayuwarta da ta Safina?"

"Hajiya nifa ba don in kyautata musu kawai nake son aurenta ba. Ina sonta ne tsakani da Allah"

Ko kunyar yace yana son mace baiyi a gabanta. Tayi iya kokarinta wurin nuna masa kunyar dan fari amma duk baya biye mata. Yanzu me ya kawo zancen soyayya a gabanta.

"Bazan zama irin iyaye marasa karbar kaddara ba musamman da na san komai game da ita. Kai ba yaro bane da zan ce  baka san abinda ya kamata ba. Amma ka jira nayi shawara da 'yan uwana dana mahaifinka. Kasan zancen duniya baya buya. Gara su sani tun kafin ayi auren sabo gudun gutsiri tsoma"

Murmushi yayi ya nuna mata tsantsar farincikinsa. "Hajiya nagode da kika fahimce ni. Ina fata ko sun nuna rashin amincewa don Allah kada ki hanani aurenta don wallahi bakiji yadda nake jinta a zuciyata ba"

Haj Lubabatu ta kawar da kanta gefe a kunyace. Ya cigaba da cewa "idan tayi murmushi ji nake kamar...."

"Kai tashi ka bani wuri zancen ya isa haka" ta fada amma kafin ya tashi ita tayi gaba. Dariya yayi dama tsokanarta yaso yi.

Sai da ya gama shirin bacci ya dauko wayarsa zai kira Asmau yaga missed calls da bakuwar number har uku. Ya kira numbar ga mamakinsa sai yaji muryar Qasim. Sun sake gaisawa yace ya karbi numbarsa a wurin Yassar ne don su rinka gaisawa. Hira suka dan taba cikin mutunta juna. Suna yin sallama ya kira Asmau.

Ta dauka kafin tayi magana yace cikin muryar shagwaba "Matar Jikamshi kin cuce ni"

Gyara zama tayi a dan tsorace."  Me nayi kuma"?

"Wannan dan sandan saurayin naki wallahi yana da mutumci. I feel guilty nace ki rabu dashi gashi har yana min waya."

Ta dan murmusa "to ko na barshi kai ka janye"

"Ba haka nake nufi ba fa. Kawai dai naji babu dadi ne. Da kin sani wani dan caburus kika nemo wanda zanji kwarin gwiwar yiwa rashin....." ya dan toshe baki "wai shekarunki nawa ne? Kinsan dole na kula da abinda zan fada a gabanki saboda kada na bata yarinya"

"Nice ma yarinyar. Shekarata ashirin da takwas fa"

"Kai, kai ,kai...kada azo a kamani ina soyayya da 'yar yarinya"

Asmau sai dariya take yi tana juyi akan gado, Ainau daga gefe tace "love in Tokyo"

Pillow ta jefeta dashi ta cigaba da dariyarta saboda yadda Jikamshi yake mata shagwaba yau "shiyasa nace ka hakura ka janye kawai ka barwa yaro"

"Ai baki isa ba yarinya. Bayan duk kin gama kashe min jiki da wadannan idanuwan naki. Na dai fada miki ina tausayinsa ne amma bance ki tausaya masa ba. Ki gaggauta sallamarsa kada ya janyo zuciyarki da kirkinsa"

"Jikamshi"

Sai da ya gyara kwanciya ya amsa mata "mene ne?"

"Babu komai, sunan kawai nake son fada"

"Shi mai sunan ba kya son shi?"

"Ina so"

Da sauri ta tashi zaune da ta gane abinda ta fada. Ta rasa dalilin da yasa idan tana tare dashi take manta komai tayi ta sakin baki. Ko dai ta fara zama irinsa ne???
*****

Washegari Malam Musa ya zaunar da iyalinsa ya fada musu cewa nan da sati mai zuwa zai tura masu wakiltarsa a nemawa Qasim auren Asmau. Ya gaji da ganin dan nasa gwuaro. Da Qasim yace basu gama shawara sa Asmau ba, Mal Musa yace babu komai sunyi magana da Alh Adamu yace zaije ya sami Umma da Kawu Garzali a tsayar da magana ayi aure kowa ya huta. Murmushi Qasim yayi na jindadi don yasan Asmau bazata bijerewa iyayensu ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽40

Batul Mamman💖




Washegari su Asmau basu sami zaman gida ba. Sun hadu da Shemau, Sabira da su Nasiba an sake gyara gidan Ainau kamar masu shirin kai amarya. Da yamma Umar yaje ya daukota. Kana ganinsa kasan yau yana cikin farinciki. Kusan wata uku bata gida don tun kafin ta haihu aka bata bedrest shine Mama tace ya kaita gida zata fi hutawa.

Ranar Jikamshi ya kirata yafi sau shida kuma sai anyi hira akalla ta rabin awa. Yana kira sai ya tambayeta ko Qasim ya kira kuma wayar minti nawa suka yi. Sai da ta gama dariya sannan ta zolaye shi tace
"baya ajiye waya sai wata wayar ta shigo min."
Shima dariyar yayi mata kawai yace "ba zan damu ba don nasan tawa hirar ce kawai take burgeki koda kuwa ta minti daya ce. Amma zancen gaskiya ki dena kashe masa murya yadda kike yi min. Kara sonki kawai zaiyi ni kuma ba hakura zanyi na bar masa ba"

Tayi dariya sosai hakan ya sanya shi nishadi.

"Haba Yaya Ishaq, kai fa Yayana ne  kuma Yayan Qasim. Kaci girma kawai"

Kamar tana gabanshi ya dan daure fuska cikin wasa "ki kiyaye ni fa matar Jikamshi. Ni ba yayanki bane na fada miki. Kina magana da  baban Safina mijin Asmau in Sha Allah"

Ta danyi shiru tana jin inama hakan ya tabbata.

"Baki ce amin ba"

"Amin" ta amsa ba don yana tunanin ganin ranar aurensu a gaba ba. Addua zata yi masa Allah Ya bashi mace ta gari. Amma tasan bazata je komai ba a bikin.

Daga haka suka yi sallama kowannensu yana kara jin son dan uwansa.
*****

Bayan sati daya kullum Col. Ishaq da Qasim sai sun kirata a waya kowanne yana kara jaddada mata irin son da yake mata. A wannan kwanakin da Jikamshi bai zo ba ita kanta abin ba karamin damunta yayi ba. Har mamaki take yi da take masa so irin wannan duk da tana kokarin dannewa. Ranar alhamis ta kira Zubaida ta sanar da ita zata zo yini washegari. Zubaida sai murna don tun dawowarta sau daya ta samu taje gidan, basu zauna sunyi hira yadda suke so ba. Ita kuma Zubaida saboda cikinta ya tsufa babu batun fita.

Kafin shabiyun rana washegarin Asmau ta gama girkin rana tayiwa Amatullah wanka sannan itama ta shiga. Tana fitowa taga Umma ta dawo duk da ranar aiki ne. Har daki ta bita tana tambayar ko lafiya.

"Babu komai yau dai na gaji ne. Kinsan kwana biyu bamu huta ba. Kema da kin hakura da zuwa gidan Zubaidan sai wani satin. Yarinyar nan kina ta yawo da ita 'yan kwanakin nan"

"Umma Yaya Jafar yace zai kaini ba adaidaita zan hau ba."

"To kiyi maza ki karasa shiri kinsan baya son jira."

Asmau ta tashi ta koma daki ta karasa shiryawa sannan ta zauna jiran Jafar. Ko rabin awa ba ayi ba ya iso. Suna shirin fita taga Kawu Garzali shima ya shigo. Gaisawa suka yi yace mata Zubaida tun asuba take jiranta. Yanzu Kawun nasu kamar wani kaka haka yake musu wasa. Shima dai tayi mamakin ganinsa don ance mata Umma ce ta sama masa aiki a inda take wato MTN office.
*****

Suna fita Umma tayi ajiyar zuciya ta tafi dakin Hajjo ta sanar da ita wayar da suka yi da Mama tun tana wurin aiki. Shine ma dalilin dawowarta gida da wuri da zuwan Kawu Garzali. Alh Adamu ne yake son ganinsu don yace gidan zai zo idan ta taso aiki. Kasa hakura tayi saboda Mama tace mata batun auren Asmau da Qasim ne zai kawo shi. Shiyasa ta fada Garzalin suka dawo gida kawai. A cikin satin da tayi magana da Asmau akan manemanta biyun ta nuna mata ita karatu kawai zatayi duk zata sallamesu batare da bacin rai ba. Sai dai kuma tuni Umma ta gano inda zuciyar 'yarta tafi karkata. Matsalar dai bai wuce abinda itama Asmau take jiyewa tsoro ba na dangane da gori ko rashin amincewa daga dangin mazan.

Bayan ta gama bayaninta Hajjo tace "yaron nan da gaske yake da rike amanar amininsa. Allah Ya tabbatar da alkhairi." Ta danyi shiru kamar mai tunani sannan tace
"Amma idan banyi kuskuren fahimta ba sai naga Ishaq shima kamar fa sonta yake yi. Kinsan mu idonmu idon soyayya. Muna ganinta muke ganewa"

Umma tayi dariya sannan  ta fada mata wayarsu da Anti Bintu  da kuma yadda suka yi da Asmau
"Bazamu zuba mata ido ba duk da muna jin tsoron surutun mutane auren shine rufin asirinmu. Duka su biyun ni bana kin kowa amma Hajjo kinga Qasim muka fi sani kuma gashi har maganarsa ta kai kunnen manya. Garzali ma ya shigo ina tsammanin a falo ya tsaya. Shine namiji dole ayi komai dashi "

"Kinga wancan mutumin banzan shi ya kamata ace zaiyi komai akan lamarin yaran nan amma kafin a ganshi ma aiki ne"

Umma ta fahimci da Kawu Rabe take. Murmushi kawai  tayi "kada ki damu Hajjo, Garzalin ma ai babanta ne kuma na fadawa su Yaya Abu don su san me ake ciki. Saura kuma sai yazo munji"

Kawu Garzali sallama zai shigo dakin yaji Hajjo tace "Kinsan Allah Bara'atu kada ku yarda kuce kun amince ba tare da munji ta bakin Asmau ba, bazan yarda kuyi mata auren dole ba. Idan bata so ya hakura kawai"

Umma tace "Hajjo mu har mun isa muce bama so? Kada ki manta duk abinda ya faru da Asmau. Yanzu duk wanda yazo neman aurenta ai alfarma yayi mana"

Hajjo ta danyi shiru tana tausayawa jikarta "kuma fa haka ne. Allah Ya rabamu da mummunar kaddara"

Tashi Umma tayi "dama yanzun ma ina jin shawara ce dai yake son bamu a matsayinsa na uba gareta."

Kawu Garzali ya gaishe da Hajjo sannan tace su fito falo Alh Adamu yazo.
*****

Sun zazzauna an gaisa da Alh Adamu da Mama Yalwa da bata dade da shigowa ba itama.

Yayi dan gyaran murya wanda ya janyo suka fuskance shi "Nasan Yalwa ta fara sanar dake dalilin zuwan nan. Mal Musa ya kirani a waya ya sanar dani yadda suka yi da Qasim akan auren Asmau. To shi a son ransa nan da lahadi su zo ayi magana ta iyaye a tsayar da lokaci. Shine ya bukaci lallai in fara sanar daku domin ayi shawara"

Hajjo ce ta soma magana "hakika Alhaji kai uba ne ga dukkan 'ya'yan Bara'atu. Ka rikesu tsakani da Allah tun lokacin da mu da suke dolenmu muka wofantar dasu. Duk shawarar da ka yanke akan yarinyar nan muna da tabbacin bazata cutar da ita."

"Duk da haka Hajjo me kuka gani? A basu dama su zo ko akwai wani tanadi da kuka yi mata".

Kawu Garzali yayi saurin cewa "haba haba  Alhaji akwai wani tanadi ne da ya wuce aure. Amma Haj Bara'atu me kika gani?"

Idanu suka koma kan Umma. Daga yadda Alh Adamu yake magana ta tabbatar yana so su amince tunda har ya zo gidan da da kansa. Mutumin nan yayi musu gata fiye da tunanin  mutane. Ta dauke shi tamkar dan uwanta bazata iya bijere masa ba balle kuma Asmau.
"Nima dai bani da zabi sai abinda kuka yanke. Wannan aure idan ya yiwu ba karamin dago mata martaba zaiyi ba a idon jama'a sai dai muyi fatan alkhairi. Shi kuma Abubakar Allah Ya gafarta masa" ta kare da guntun hawaye. Da yana raye duk wannan abin bazai taso ba.

Mama ma sai ta soma kuka duk kuma zukatansu suka raunana. Alh Adamu yace "zaku fara ko?"

Da yaga sun nutsu ya ce "tsakani da Allah ni naso nasa Abdulhalim ya nemi aurenta domin kare martabarmu gabadaya. Sai na bari ta dan kara kwana biyu ashe rabon Qasim ce. Zan sanar dashi su zo jibin. Idan yaso sai mu kira dangi na kusa azo ayi komai da wuri. Iyalin Mal Musa sunyi mana abinda bazamu manta ba tunda suka bari dansu ya nemi auren tamu 'yar."

Sunyi ta tattaunawa akan maganar karshe mazan suka yi shirin zuwa masallaci. Aka bar su Mama suna kara shawara akan kamar yaushe ya kamata asa auren idan dangin Qasin  sun nemi asa rana da wuri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽41

Batul Mamman💖




Asmau tana can gidan Zubaida suna hirarsu bata san wainar da ake toyawa a gidansu ba. A cikin hirar ne ta fada mata zancen Qasim da Col. Ishaq.

Zubaida taji dadi sosai "kinga yadda Allah ke juya lamarinSa ko. Shawarar  zan baki ki yarda kiyi aure amma ki zabi wanda zuciyarki tafi so. Ni shaida ce akan irin abinda Qasim yayi da kika bata to amma nafi danganta hakan da rike amanar Abubakar da yayi. Bansan gaskiyar lamari akan menene a zuciyarsa ba yanzu. Ma'ana soyayya ce ko tausayi. Shi kuwa sojan nan dole na yaba masa. Duka duka yaushe ya sanki amma yake sonki da aure"

"Ba kya tunanin nan gaba matsala ta taso ko a kaina ko akan Amatullah"

"Hmmm Asmau kenan, ke kike da goben da har kike tunanin matsala? Yadda Allah Ya daidaita miki lamura yanzu, idan har wani abin ya taso a gaba Shi din dai zai mana magani. Kada ki manta nima ba 'yar aure bace amma Allah Ya hadani daku gashi babu wanda ya taba yi mim gori. Auren ma Hajjo ce ta hada. Zamana nake lafiya na manta da kazantar da na taso cikinta. Yadda na hadu daku da yardar Allah itama zata hadu da mutane nagari a rayuwarta"

Asmau ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na taho mata. Duk matar da tayi zina ta gama cutar abinda ta haifa. Sai dai idan an hadu da mutane na kwarai. Kuma duk da haka haifewar itace tafi akan zubar da ciki wanda yake daidai da kisa idan an busawa jaririn rai. Mace sai ta sami rahmar Allah idan ta rungumi kaddararta ta bawa abinda ta haifa tarbiyar da ta dace da addininmu.

"Ki kara hakuri da rayuwa Asmau. Haka Allah Ya tsara miki. Ke kika zama ishara ga masu hankali wadanda idan sunji labarinki zasu san cewa biyewa sharrin yanar gizo da son zuciya halaka ne. Uwa uba babu wani alkhairi da yake tattare da shiga groups din nan na whatsapp ko facebook masu yada alfasha."

"Nagode Antina ta kaina. Allah Ya raba lafiya mu sha suna"

Dadi Zubaida taji da taga Asmau ta dan sake. Amatullah tana tsakar gida suna wasa da yaran Zubaidan.

"Tashi mu soya wainar fulawa"

Asmau ta zaro ido "yaushe muka gama cin abinci?"

Cikinta ta shafa "bani nake so ba kaninki ne ko kanwa"

"To kala masa sharri saboda bashi da baki. Ina fulawar take na hada?" Ta fada tana tashi.

Ranar dai sun wuni suna hira kuma taji dadin shawarar da Zubaida ta bata. Duniya kenan, Zubaida da ta tashi a matsayin 'yar magajiyar karuwai gashi Allah Ya sauya mata rayuwa. Sai bayan magariba Asmau tayi shirin tafiya. Dama Jafar yace zai dawo daukarta sai ya kira yace ayyuka sun masa yawa. Nan kuwa bata san suna can gidansu ana maganar aurenta bane.

Zubaida ta sake yi mata tuni akan lallai kada ta bari dama ta kubuce mata. Ta amince tayi aure
"Ni na kula sojan nan ba dai iya nuna kulawa ba. Zuwanki nan kunyi waya sau uku."

Murmushin Asmau ya tabbatar mata da zarginta na cewa shi take so. Har kofar gida ta rakata suka tafi titi suka shiga adaidaita sahu ita da Amatullah suka tafi gida..

Abin mamaki tana zuwa ta tarar da Anti Bintu tazo da yaranta wai zasuyi weekend. Tayi murna sosai. Amatullah ma ta ganesu saboda haka ta saki jiki ana hira. Umma tace idan  ta huta tazo dakin Hajjo tana son ganinta. Anti Bintu Asmau ta kalla tana dan murmushi, ko dai ta fadawa Umma zuwan Jikamshi Zaria ne. Karshenta maganar aure ce. Ta riga ta kudiri niyar bin shawarar Zubaida. Zata tsananta addua ta amince da Col. I M Jikamshi.
*****

Ko kayanta bata cire ba da ta shiga daki Jikamshi ya kirata kamar yasan tunaninsa take yi a wannan lokacin.

Daukar wayar tayi tare da yin sallama.

Shima lokacin yana gida ya tasa laptop a gaba yana kallon wasu hotuna da ya dauki Amatullah. Yana son yarinyar nan, ko babu komai ta dauke shi uba sannan gashi tayi sanadiyar hadashi da Umminta. Safinansa akwai shiga rai.

Sallamar Asmau ce ta katse masa tunani ya amsa mata cikin daddadar muryarsa.
"Matar Jikamshi kun dawo gida lafiya?"

"Lafiya kalau"

"I miss you so much"

"Duk wayar da muke yi tun safe?"

Yayi yar dariya "yanzu ke hirar waya ta isheki. Ni nafi son na ganki a gabana. By the way lokacin da na baki fa yayi. Anyi sati daya ya kuka yi da Qasim?"

Shiru tayi domin kuwa bata sami biyan bukata ba. Tayi kokarin nuna masa ya hakura da zancen aure sai ya rinka danganta abin da ko tana gudun aurensa saboda tunanin Abubakar ne. Karshe yace mata ta jira nan da lahadi komai zai zo karshe.

Col Ishaq yace "ya kika yu shiru? Kada kice min bakiyi komai ba."

Sautin muryarsa kamar baiji dadi ba tace "ka kara hakuri yace na jira zuwa ranar lahadi idan yazo kamai zai zo karshe"

"Ban fahimceki ba, komai zaizo karshe kamar yaya?"

Asmau kanta bata gane abinda Qasim yake nufi ba "nima dai haka yace min"

Col. Ishaq ya tashi daga kashingidar da yayi "look Matar Jikamshi, ni mutum ne kaifi daya. Idan kina jin nauyin fada masa saboda kusancin families dinku ni zan fada masa da kaina. Tunda naga ya cigaba da yi min text da waya nasan bai san alakarmu ba. Kinga kashe wayar kawai bari na kira shi na fada masa Ishaq da Asmau suna son juna don Allah ka nemi wata"

Bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba "yanzu don Allah sai ka fada masa haka"?

"Kin dauka wasa nake yi, yara ne suke da lokacin wasa da soyayya."

Tace "kayi hakuri zuwa lahadin please"

Yadda take magana duk ya kashe masa jiki. Zai iya hakuri amma zuwa sunday kawai. Daga nan kuwa to sai dai ayita ta kare. Shi ba don yana ganin mutuncin Qasim din ba tun ranar da ya gansu da Asmau da a lokacin zai fada masa.

"Yarinya dake duk kin rikita min lissafi. Amma zan rama ne, sai kin shigo gidanki"

"Nima fa ka rikita min"

"Me kika ce?"

Zancen zuci ne ya fito fili tayi saurin toshe bakinta. Ta rasa inda zata sa kanta don kunya. Tana ji yana mata dariya don yasan bata so yaji abinda ta fada ba.
"I love you Matar Jikamshi. Nasan bazan kara samun nutsuwa ba idan ba aurenki nayi ba. Na riga na fadawa Hajiya amsarki nake jira a fadawa iyayena maza. Idan kika zabi Qasim zan tayar da yaki a zuciyarki"

Wani dadi ne taji yana ratsata. Ashe tana da rabon samun farinciki a rayuwarta. Ita ma tana son shi kuma ta shiryawa duk wani nau'i na gori da zai iya zuwa daga danginsa. Abinda ake gudu ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba.
" 'yarka da Yassar ma bazasu barni ba idan na zabi wani ba kai ba. Da ka tashi sai ka hada da zuciyata data Amatullah kuma harda ta kanina."

Da tasan irin yadda yake ji a ransa da ta rage  yi masa magana ko don ta sassauta masa. Ajiyar zuciya yayi har tana jin sautin
"Say you love me please" ya fada cikin sanyin murya.

Yau daya zata sakaya kunyarta ta farantawa mai faranta mata "I do love you _Jikamshina_"
Kafin ya kara magana ta kashe wayar gabadaya don tasan zai sake kira. Kwanciya tayi akan gado tana juyi ita kadai zuciyarta kamar an wanke mata.

Shi kuwa rike yake da wayar a hannu yana murmushi. Hmmm bari dai ace an daura musu aure. Ranar Asmau zata san tana da masoyi. Zaiyi iya kokarinsa wurin nuna mata soyayya da cewar itama har yanzu tana da darajarta a cikin mata. Abinda ya wuce a baya sai ayi ta addua da fatan Allah Ya yafewa musulmi  kurakuransu.
*****

Tana ta maimaita hirarsu a kwakwalwarta tana dariya Amatullah ta shigo
"Ummina Umma tana kiyanki"

Ai da sauri ta sauko daga kan gadon. Shaf ta manta Umma tace tana son ganinta.

Saurin da take yi yasa Amatullah tace "Ummi guduwa zamuyi ne? Me nene akan gadon?"

Asmau tayiwa kanta dariya sannan ta dauki Amatullah tana juyi da ita. Soyayyar Jikamshi ta zame mata wani bangare mai mahimmanci a rayuwarta. Tana juyin tana dariya.

Amatullah tana tayata duk da bata san dalilin murnar Ummin ta ba
"Ummi abin dadi ne ya fayu?"

"Shine zai faru in sha Allah Ama, muma Allah zai bamu rayuwa mai tsafta kamar kowa"

"In ce Alhamdulillah?" Amatullah ta tambaya

"Fadi kinji Aman Ummi"

Sai da ta gama murnarta ta kama hannun Amatullah suka fito. A falo ta barta ta karasa dakin Hajjo. Kafin ta shiga taji muryar Anti Bintu tana magana sama sama da ji kasan ranta a bace yake
"Yaya Bara wallahi Asmau tana son Ishaq. Don ta fada miki zata sallamesu duk su biyun kawaici ne kawai. Ita a tunaninta bata da wata kimar da namiji zai aureta. Don Allah kada ku shiga tsakaninsu. Hajjo kiyi mata magana "
Hajjo tace "Bintu nima ba wai naki Ishaq bane. Ki tuna wacece Asmau, tana da tabon da babu ruwan da zai wanke shi duk duniya. Qasim da iyayensa sun san komai game da ita kuma dazu muke ji ashe saboda ita yaki aure tuntuni wai kada kishiya tayi mata gori ko habaici"

Anti Bintu tace "to duk abinda yayi ai ba wai sunyi da ita zata aure shi bane. A yadda na kula da irin son da Ishaq yake mata ba zai hakura kai tsaye ba."

Umma kanta tasan wanda Asmau take so amma bazata iya yiwa Alh Adamu musu ba kamar yadda shima yaji nauyin Mal Musa. Idan ta biyewa Bintu jan zancen kawai za'ayi ta yi azo zumunci ya sami rauni.
"Bintu don Allah ki bar zancen nan. Komai ya kure tunda ranar lahadu zasu zo kawo kudi. Itama sai tayi hakuri ta karbi kaddara"

A fusace Anti Bintu ta mike "ni bazan zuba ido ina kallo a cuci yarinyar nan ba. Ba kwa tunanin kada *abinda ake gudu* ya sake faruwa? Don kaddara ta fada mata shikenan kuma bata da damar zabar wanda take so"

"Abinda ake gudu ya riga ya faru kumq shine yasa dole duk muyi hakuri. Kina jin da hakan bata faru da rayuwarta ba zan amince da auren nan ne? Yanzu kuwa bamu da bakin magana tunda mu za'a taimakawa. Ki dena bata bakinki akan maganar nan. An gama yanke shawara tun dazu"

Hajjo ta rasa yadda zatayi da su biyun. Kowacce ta kafe har suna neman yin fada "don Allah kuyi hakuri. Bintu kece karama, mu taru kawai mu tayata addua."

Hawayene kamar an kunna famfo yake saukowa daga idanun Asmau. Dama shiyasa Qasim yace ta jira zuwan lahadi? Yanzu shikenan tun ba'aje ko'ina ba an datse mata samun farinciki daga wurin Jikamshi. Duk maganar su Umma kuma gaskiya suke fada. Ita din tana da tabo a rayuwarta. Wannan yasa a komai shawararta zata zamo ta karshe. Iyaye zasuyi ta ganin kamar komai suka yanke shine alkhairi gareta.

A sanyaye ta shiga dakin ta zauna a kasa.
"Umma indai auren Qasim kuke gani shi yafi dacewa dani na amince"

Anti Bintu ta taso ta tayar da ita tsaye.
"Asmau wace irin magana ce wannan. Ishaq kike so kuma na shaida yana matukar sonki. In Allah Ya yarda shine mijinki"

Umma taji tausayin Asmau har ranta amma yadda abin yazo musu ne basu da yadda zasuyi "Bintu na dauka mun gama maganar Ishaq dinnan"

"Yaya Bara'atu bazan bar maganar ba sai naji daga bakin Ishaq ko shi din ya hakura"

Cikin kuka Asmau tace "Anti Bintu ki bar maganar kawai. Allah Yasa hakan shine mafi alkhairi"

Tashi tayi ta fita jikinta duk babu kwari. Gobe in Allah Ya yarda zata kira Jikamshi ta bashi hakuri. Bata san wace irin rayuwa kuma zatayi da Qasim ba. Mutumin da bata taba jin sonsa ko kadan a ranta ba.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽42

Batul Mamman💖




Sallar isha kawai tayi ta kwanta sai kuka. Ganin bazai fishsheta ba yasa ta tashi ta dauro alwala ta soma nafila. Yi take tana kuka tana kara istigfari. Rokon Allah take Ya yafe musu kuskuren da suka aikata wanda har yau yake bibiyar komai na rayuwarsu. Daga nan tayi adduar fatan samun nutsuwa da dukkan wanda Allah Ya kaddara zata aura. Tana sallar Anti Bintu ta shigo da niyyar sake bata baki ta tarar tana sallah. Gefen gado ta samu ta zauna tana jiran ta idar. Tunanin wannan al'amari ne ya rinka damunta. Idan akace *abinda ake gudu*to ba faruwar laifin ake ji ba. Abubuwan da zasu iya biyo bayansa. Asmau ta dade tana ganin tasirin hakan a rayuwarta tun ranar da Abubakar ya rasu. Miji ya rasu ranar daurin aure sannan a sami amarya da ciki. Ai ko a iya nan aka barta ta kafa tarihi a rayuwa wanda duk mutumin da ya santa idan suka hadu sai ya tuna. Ga 'ya ta haifa itama nan gaba tana kara wayo zata iya bukatar jin waye ainihin babanta. Idan kuma marasa tausayi cikin mutane suka goranta mata yanayin haihuwarta ko na sakan daya ne sai ta tsani mahaifiyar da ta sha wahalar rayuwa don ta haifeta. Babu dan da yake son jin shi shege ne. Sannan ga soyayyar wani Allah Ya dora mata amma saboda abinda ya faru a baya idan tace zata bijire ma kallon mara kunya kuma mara godiyar Allah za'ayi mata. Allah Sarki Asmau da matan da suka sami kawunansu a yanayi shigen nata. Tuba da tawakkali shine kawai kwanciyar hankali garesu.

Anti Bintu tana ta tunani har bacci ya kwasheta a zaune Asmau bata idar da sallah ba. Itama sai gabanin asuba ta soma baccin. Ana kiran assalatu ta tashi dama baiyi nisa ba. Ta shi Anti Bintu da 'yan matan da suka shigo dakin kwanciya tun tana sallah. Sai wurin bakwai na safe bacci mai nauyi ya dauketa.
*****

A kitchen Umma ta rabawa kowa aikinsa na taron gobe. Gidan Mama zasuyi meatpie da doughnut. Nan kuma cake zasuyi da pepper chicken sai lemuka da za'a siyo. Har dakin Yassar  taje ta bashi kudin abubuwan da zai siyo a fara aikin yace mata da zazzabi ya kwana. Yassar da bashi da kyuyar aike yau kirikiri ya nuna mata bazashi ba. Dama tun jiya ta kula yana wani cin magani ta rasa dalili. Bata san Col. Ishaq yake tayawa kishi ba tun kafin ya fara nasa. Dayake Shemau zata zo sai kawai ta kirata a waya ta fada mata abubuwan da zata taho dasu.

Ta fito tana mitar tasan Yassar kalau yake Anti Bintu tayi dariya.
"Indai Yassar ne ranar daurin auren ma yana iya kirkiro ciwo. Don baki san irin shakuwarsu da Ishaq bane."

"Ke kuma naga alama abin yayi miki dadi. Ni duk a yaushe ya tara masoya a gidan nan ne ban sani ba?"

"duk abinsa ai dole yaji kunyarki. Don baki ga yadda mukayi dashi a Zaria ba. Hatta babansu Dijah sun sha hira sosai. Tamkar 'yan uwansa haka ya dauke mu. Gashi yanzu kun zo kun raba"

Umma ta rike haba tana kallon kanwarta. Da gaske Bintu ta zama 'yar kamfen "kun mayar dani wata boss dai. Gani kuke yi kamar bana son Asmau. Bari ayi auren ku gani idan suka fara zaman lafiya. Yau fa ko gaisheni bata fito tayi ba."

Anti Bintu tace "bacci take yi, jiya kwana tayi tana sallah da kuka"

Hajjo dake tsaye a bakin kofa tana musu dariya tace "ta kwana sallah kika ce, to ni dai babu ruwana Bara'atu da Garzali ne suka yanke shawarar. Allah Yasa dai bata ambaci sunana a adduar ba. Ko dai na tasheta na tambayeta ne. Kunsan addua ba abin wasa bace"

Duk su biyun dariya suka yi. Daga falo suka ji shigowar Zubaida da Sabira. Har kitchen din suka zo aka gaisa suna yiwa Zubaiba fadan dalilin zuwanta tace "Umma jiya banyi bacci ba tunda ya fada min gobe za'a kawo kudin Asmau. Mu dan shiga ciki akwai wani sirri da nake tsammanin bata fada miki ba"

Anti Bintu tace "fadi a nan kawai, ba zancen Ishaq bane"

Zubaida tace "wannan sojan ko. Ashe kun sani, to meyasa za'a hadata da Qasim?"

Hajjo tace "kinga matar auta, jeki ki bawa 'yar uwarki baki kawai. Maganar nan an gamata tun jiya. Allah Ya sanya mana alkhairi"

Jikin Zubaida duk sai yayi sanyi. Mata nawa ta gani a gidan Uwargida wadanda suka ce auren dole ne ya fito dasu daga gidan iyayensu. Allah Yasa Asmau ta iya hakuri dai.

Ko sau daya Asmau bata fito daga daki ba. Abinci ma Dijah ce ta kai mata. Amatullah da bata iya komai idan Umminta bata walwala itama a dakin ta zauna. Har su Shemau suka zo yara sun cika gidan amma taki fita sai nanikar jikin Asmau take yi. Col. Ishaq yayi ta kiranta ta daure ta dauka tace masa baki ne a gidan yau duk ya cika. Har su Anti Bintu sun zo.

"To bazan takuraki ba kije kuyi hira zuwa dare sai muyi magana. Ki gaishe min da Yayata Bintu"

Tana ajiye wayar sai kuka. Yanzu da tasan za'ayi mata katanga dashi tafi jin sonsa ma a zuciyarta. Duk bayan dan lokaci kadan sai tayi mata text mai cike da kalamai masu ratsa zuciya. Shemau tazo tayi ta rarrashinta akan ta hakura ta karbi wanda Allah Ya zaba mata. Gudun kada su dameta yasa ta dan sake tana amsa musu idan an sakota a hira.

Sunyi aikinsu sun gama zuwa yamma. Washegari kawai ake jira mutanen Shanono su iso. A daren ranar Ainau da bata sami zuwa tayasu aiki ba ta kirata harda kukanta. Ta kira Umma tana rokon kada a hana yayarta wanda take so. Umma dai ta rasa yadda zata yi. Duk sun hade mata kai. Jafar ne ma bai nuna ga wanda ransa tafi so da Asmau ba.

Uban gayya ASP Qasim shima sai dare ya kira Asmau. Kana jinsa kasan yana cikin farinciki yace
"Asmau kinga ikon Allah ko. Ina sanar da su Baba maganarmu suka ce kawai azo ayi komai. Ina fatan hakan zai karan kwantar miki da hankali kisan cewa komai ya wuce."

Zuciyarta har wani zafi take yi don bacin rai ta daure tace  "babu komai Yaya Qasim, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi"

Yaji dadin furucinta "Amin Asmau, goben zanzo nima. Idan sum gama nasu sai mu fara tsara bikin. Sai da safe ko gimbiyata"

Ta kakalo murmushi tayi "to sai da safe" ta ajiye wayar ido na cikowa da kwalla.
*****

Washegari da wuri gidan ya cika kamar masu shirin biki. Yaya Abu da Anti Lami sun zo, Mama da 'ya'yanta mata harda matar Abdulhalim. Sai Aina'u da Shemau da Sabira. Falon aka share aka tura kujerun baya aka shinfida wani kafet din ko da wurin zaman zaiyi kadan. A bangaren maza ma akwai masu zuwa ta bangaren Hajjo da maigidanta sai Kawu Garzali da abokansa biyu. Ga mazansu Anti Lami da na Anti Bintu. Banda kuma gayyar Alh Adamu. So suke su nunawa dangin Qasim suna son 'yarsu kuma ita din 'yar dangi ce.

Tun safe Asmau ta kashe wayarta don bata san me zata cewa Jikamshi ba idan ya kirata. Adduarta kada yazo ana tsakar taron. Yau ma a daki ta zauna sai dai 'yan uwanta su shigo tayata hira.
*****

Ana la'asar mutanen Shanono suka iso gidan Alh Adamu. Daga nan suka dunguma zuwa gidansu Asmau. Mota biyu suka ciko da nasu 'yan uwan. Qasim dama ya rigasu zuwa ya sai zauna a cikin gidan idan taro ya watse zaije ganin Asmau gimbiyarsa.

Kafin su iso Umma tace Asmau ta tafi gidan Jafar tare da wasu cikin 'yan matan tace kanta na ciwo bazata iya fita ba. Umma tayi murmushi kawai ta rabu da ita.

Sauran suka tashi aka jera komai a falon sannan suka koma ciki suna hira a dakin Hajjo saboda yafi fadi.

Asmau na kwance zazzabin dole ya rufeta taji hannuwan Amatullah sun rike mata wuya ta baya. Tun jiya taki sakewa itama. Idan ta korata tayi wasa bata dadewa take dawowa wurin Umminta. Murmushi tayi tana kokarin cire hannunwan don rikon ya danyi karfi
"Ama sake min wuya mana"

Jin tayi shiru yasa ta juyawa sosai. Amatullah ta gani tana kokarin numfashi bakinta a bude.
"Subhanallah" ta fada a rude tana dagata.
"Ama ki rufa min asiri, wayyo Allah"

Gabadaya ta manta da inhaler din da aka basu a asibiti ta dauketa sai dakin Hajjo. Kuka take yi sosai tun kafin ta shiga su Umma suka fara fitowa saboda muryarta da suke ji.

Ganin Amatullah na numfashi da kyar Shemau ta karbeta Sabira kuma ta kira Jafar a waya. Lokacin Umma har ta dauko mukullin tata motar. Yassar baya gidan shi tun safe ya fice.

Sabira na fadawa Jafar ya tashi da sauri. Lokacin an gama gaisawa da dangin Qasim kenan. Abdulhalim ya tambayeshi abinda ya faru ya fada musu.

Kowa sai salati suka tashi  don ta nan su Umma zasu wuce.

Kafin kace meye wannan suna mota Asmau ta cire dankwali sai hijabinta kawai tana yiwa Amatullah fifita. A can gidansu kuma Alh Adamu ya gama gigicewa. Yana matukar son jikarsa shiyasa hankalinsa ya tashi. Karshe yace don Allah suyi hakuri zai bisu asibitin. Idan komai ya lafa sai su karasa abinda ya tara su. Duk da wasu basu ji dadi ba to amma lafiya tafi komai. Haka suma aka samu wasu cikinsu suka bi bayansu aka tafi asibiti.

Ainau ce ta kira Yassar ta fada masa. Kafin ya karasa asibitin ya kira Col. Ishaq ya sanar dashi da kuma sunan asibitin. Shima hankalinsa a tashe ya tafi. Dama yayi ta kiran wayar Asmau yau baya samu. Niyarsa bayan magariba yaje gidan.
*****

Emergency suka kaita nan da nan likitoci suka fara aikinsu. Sun tabbatar musu ba abin damuwa bane asthma dinta ce ta tashi amma abin baiyi tsanani ba.

Ana ta rarrashin Asmau ta kasa shiru. Dama can hankalinta ba a kwance yake ba. Suna nan aka canza mata daki lokacin numfashin ta daidaita ta sami bacci. Qasim ya shigo dakin aka gaisa ya duba Amatullah ya fita. Bai dade da fita ba Jafar yace taje waje Qasim na kiranta.

Bata son nunawa mutane rashin son auren shiyasa ta fita ta same shi. Kokarin kwantar mata da hankali yayi tace ta gode. Suna nan tsaye Col. Ishaq ya iso. Tunda idonsa ya gano masa Asmau da Qasim yaji wani bacin rai sai dai jikin Amatullah ne a gabansa. Daya karaso suka gaisa da Qasim. Itama ta gaisheshi  sai ya shareta kawai. Tana kallo Yassar ya fito ya kaishi dakin ya duba Amatullah.

Kasa nutsuwa yayi ya fito ya dawo inda suke. Gaban Asmau sai faduwa yake yi. Yana zuwa yace
"Naga dakin a ciki da mutane da yawa. Tun yaushe ta fara ciwon ban sani ba?"

Qasim ne ya bashi amsa "ko awa daya ba'ayi ba. Mutanen ciki 'yan uwana ne dana Asmau. Kayi hakuri naso sanar da kai ma abin ne yazo a kurarren lokaci."

Idon Col. Ishaq akan Asmau yace "wane abu kenan?"

Da dan murmushi Qasim yace "kawo kudi aka zo sai ciwon Amatullah ya tashi"

Guntuwar fara'ar fuskar Col. Ishaq tuni ta bace "kudin aure??? Na wa?"

Kirjin Asmau sai bugu yake da karfi don tsoro. Gashi yq tsareta da ido.

Qasim yace "kin barni ina ta magana ni kadai ko, wallahi daga fadawa iyayena kawai sai suka yanke shawarar gara ayi komai lokaci guda. kudin *aurenmu* aka zo kawowa."

Sabanin bacin ran da tayi tunanin gani a fuskar Jikamshi sai taga yayi dan murmushi
"Kasan mata da kawaici da kunya. Musamman ma dai _Matar Jikamshi_. Asma'una baki fada masa muna soyayya bane?"

Qasim ne yaji kamar an sauke masa guduma a kansa. Sai ya kalli Asmau da tayi mutuwar tsaye sannan ya kalli Col. Ishaq wanda yake binta da kallo mai nuni da tsantsar soyayya kamar ya sanyata a jikinsa.

Daga bayansu Yassar ne yazo kiran Asmau ya fada mata Amatullah ta farka. Jin abinda Col. Ishaq ya fada yasa shi daka tsalle ba shiri.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽43

Batul Mamman💖




Shiru suka yi gaba dayansu sai Col. Ishaq da yake murmushi kamar bai san abinda yayi ba. Shi kuwa Qasim nema yake maganar da yaji ta gama shiga kwakwalwarsa. Ihun tsallen Yassar ne yasa duk suka kallo inda yake. Baiyi wani dogon tunani ba don kada a gano shi ya durkusa kasa tare da rike kafarsa ta hagu
"Wayyo Allah wani abu ne ya cije ni"

Asmau tayi kansa da sauri dama neman hanyar da zata bar wurin take yi don ji take kamar idan ta kara minti daya itama sai dai a bata gado kusa da Amatullah saboda irin bugun da zuciyarta take yi.

"Mu gani a ina ne?"

Ya dago kansa yana kallonta, duk sai ta bashi tausayi. Karyar kafar ma saboda ita yayi
"Barshi kawai bari na cire takalmin. Kije Amatullah ta tashi tana kuka"

Kamar an harba walkiya haka ta bar wurin ko waigowa baya bata yi ba. Qasim da Col Ishaq suka dawo kusa dashi suna tambayarsa abinda ya sami kafar.
"Ji nayi kamar abu ya cije ni. Ku shiga ciki Amatullah ta tashi."

Qasim ya dawo hayyacinsa daga abinda Col. Ishaq ya fada har ya yiwa Yassar sannu harda kokarin cire masa takalmin zai taya shi duba kafar. Yassar yayi saurin jan kafar yana mai jin kunyar karyar da yayi "ya dena ciwon, zan karasa motar Umma ina da silifas a ciki ina jin cinnaka ne ya shiga."

Daga haka ya samu Qasim ya shige. Kafin ya mike tsaye yaji an kama wuyan rigarsa an tayar dashi. Ba don yasan wanda ya rike shi ba sai yayi ihun gaske. Col. Ishaq yayi 'yar dariya yana kallonsa "ka kyauta da ka taimakawa yayarka don sauran kadan ta suma a wurin nan. Har na fara tunanin me zan fadawa su Umma"

Shima Yassar dariyar yayi yana murza wuyansa "haka kawai kun sata a tsakiya. Ga soja ga dan sanda da wanne zata ji"

"Laifinta ne da tasa duk muka kamu da sonta. Allah Yasa kada ta kwaso mana lauya ko alkali kuma."

Murmushi Yassar yayi tare da jin kunyar amsar da aka bashi. Shi dai komai na Col. Ishaq yana burge shi. Ina ma ace shi zai aureta. Ba kuma don baya son Qasim ba sai dai wannan maganar aure ce.
*****

Asmau na shiga dakin Amatullah ta dena kuka. Kan gadon taje ta zauna tana yi mata fadan dalilin kukan don bata ganta ba kamar bata san sauran mutanen wurin ba.

Mama tace "kiyi mata a hankali Asmau. Yarinyar nan taji jiki. Haka muka sha fama da Abubakar da yana yaro. Idan ta kara wayo zata san yadda zatayi ta rinka kiyayewa sai kiga attacks din basa zuwa sosai."

 'Yan uwan Qasim suka ce zasu tafi sai dai su dawo wani satin. Alh Adamu yayi ta basu hakuri yace tunda Amatullah taji sauki suna iya komawa a karasa. Hakan ya razana Asmau sosai ta shiga rarraba idanu taji me Jikamshi zai ce. Sai tayi sa'a yayi kamar baya jinsu. Su din ma sun nuna babu damuwa tunda yamma tayi zasu sake saka rana.

Ita dai Asmau ko kallon Qasim din ta kasa. To da wane idon zata kalle shi bayan abinda Jikamshi ya fada masa. Shi a rayuwarsa ta kula baya jin shakkar fadin magana ko a gaban waye indai yana tunanin akan gaskiyarsa ne. Gashi yau ya fadi maganar da tasan dole Qasim ya kullaceta a ransa.

Shima a nasa bangaren gani yayi gara ya kyaleta saboda asibiti ba muhallin maganar bane. Sannan ga Amatullah babu lafiya yanzu ko me zata fada masa zai zamto babu nutsuwa a tare da ita. Tare da su Alh Adamu suka fita raka 'yan uwansa zasu biya gidan Umma su dauko sauran. Kayan ciye ciye da aka tanadar musu Umma tasa Sabira da Shemau su bi bayansu sai su hada a basu su tafi dashi.
*****

 Suna zaune har akayi magariba sannan su Umma suka tafi aka bar Hajjo da Asmau. Kayan kwana za'a hadu musu sai Mama ta dawo su kwana tare. Col. Ishaq yana dakin amma shima yaki kallon inda Asmau take, shima bata da abin fada masa. Ba don ciwon Amatullah ba da yanzu an gama magana tsakaninta da Qasim sai batun saka rana. Biyewa Amatullah yayi tana ta shagwaba son ranta, sai Hajjo dake dan yi masa hira itan ma kunyarsa take ji tunda tasan komai. Duk yadda Asmau taso su hada ido yaki. So take ta bashi hakuri tunda tasan yanzu bata da sauran mafita. Karshenta kafin sati ya zagayo ma mutanen Shanono su sake dawowa.

Shigowar Jafar da Qasim yasa shi tashi yayi musu sallama ya fita.

Damarta kenan ta bashi hakuri a yau tunda wayarta tana gida. Bai dade da fita ba tace zata je tambayar likita ko zata iya bawa Amatullah abinci. Jafar yace ta bari yaje ta wayance "barshi Yaya Jafar so nake na dan fita na gaji da zaman wuri daya"

Shi kuwa Qasim tuni ya gane inda take son zuwa sai kawai ya dauke kansa. Yana kallo ta fita cikin sauri don kada ya bar asibitin kafin ta karasa wajen.

Tana fitowa ko alamunsa babu ta kara sauri harda dan gudunta. Tsoronta bai wuce kila daga yau yaki dawowa ba. Garin sauri tabi wata hanyar da zata kaita wurin ajiye motoci ta kusa karo da mutum har sai da taji tsoro saboda rashin wadatar haske a wurin. Tsaye yake ya sanya hannuwansa a aljihun wando yana kallonta. Kallo ne na tuhuma wanda har ranta sai da taji babu dadi don bata kyauta masa ba. Bai motsa daga inda yake ba yace  "me yasa kika wahalar da kanki da yin gudu bayan kinsan dole zan jira fitowarki. You have alot of explaining to do"

Fuskarsa yau babu fara'ar nan da take kara saka mata sonsa. Yau a sojansa ya fito sai ta daburce ta rasa ta ina zata fara bayani.

"Kinyi shiru, na tafi ne?"

"A'a don Allah kayi hakuri" sai ta soma kuka.

"Matar Jikamshi" sai yanzu ta danji sanyi a ranta saboda yadda ya kirata. A hankali ta dago ido ta kalle shi.

"Why?" Ya tambaya shima duk dakewarsa yana jin babu dadi. Idan ya rasa Asmau gani yake bazai taba samun madadinta ba. Yana mamakin irin wannan so da yake mata wanda ya shige shi lokaci daya.

Idanunta cike da hawaye ta soma fada masa yadda abin ya faru." Kayi hakuri da ban sanar da kai ba. Babu yadda zanyi ne tunda duk iyaye sun amince"

Ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar ta "ki dena kukan nan kinji ko. Idan nace miki everything is ok nayi karya because it is not. Kinji kunyar sanar da Qasim da wuri kinga abinda hakan ya janyo. Magana kuma tunda ta hada da iyaye zan hakura kamar yadda kike so. Dazu ma naga ya kamata ya sani ne shiyasa na fada masa."

Wani kukan ne yazo mata sai zubar da hawaye take. Tana sonsa fiye da yadda take tsammani a baya.
"Jikamshi to yaya zanyi?"

Tausayi ta bashi. Asmau ta fuskanci abubuwa da dama a cikin 'yan shekaru.
"Da ace babu ni a cikin manemanki sai na baki shawara. Amma tunda ina ciki bana so a zargeni da son kai. Shawara tana gareki Asma'una. Idan Allah Yayi Qasim ne mijinki alfarma daya nake nema kada ku rabani da Safina. Atleast ko school fees  dinta ku bari ya zama responsibility dina."

Meyasa Qasim bai sanar da ita iyayensa zasu zo da wuri ba. Ji tayi gabadaya auren ya fice mata a rai. Kuka kawai take yi mai ciwo. Muryarta a shake tace "To yanzu shikenan?"

Murmushi yayi mata, sai da taji shi har ranta. "Shikenan Matar Jikamshi. Maybe daga yau bazan kara kiranki da wannan sunan ba. Ki rike duk abinda Allah Ya kaddara miki da hannu biyu. Qasim mutumin kirki ne a yadda na fahimce shi. Ban taba ganin mutum mai kokarin rike amana kamarsa ba"

"Na sani wallahi, shiyasa na kasa fada masa gaskiyar abinda ke zuciyata. Ina gudun bata masa rai saboda nasan duk abinda yake yi don ya kyautata mana ne."

"Kada kiyi ja in ja da iyaye akansa. Idan shine alkhairin rayuwarki bamu da zabi da ya wuce karbar kaddara."

Juya mata baya yayi zai tafi. Yana jin sautin kukanta ya karu. Yasan yana sonta ba da wasa ba, amma duk abinda aka ce iyaye sun shiga ciki a matsayinsa na babba bai kamata ya nuna mata bijerewa alkhairi bane. Duk da kuwa yana ji a ransa kamar gobe ya turo nasa iyayen. Asmau ta wuce a kirata wani bangare na jikinsa. Shine ita, itace shi. Da haka kawai zai iya kwatanta kaunar da yake mata.

A sanyaye yaji muryarta yadda bata zaton zai ji tace "Jikamshi ina sonka" a hankali

Wannan kalmar ta tsaya masa sosai a zuciya har ya fasa tafiya. Sake juyowa yayi ya ganta durkushe tana kuka. Shima durkusawa yayi a gabanta suna fuskantar juna "Matar Jikamshi kina so na hakura dake"?

Girgiza kai tayi tana fitar da hawaye mai dumi.

"To bazan hakura ba. Jikamshi yana son matarsa. Ki tashi ki koma ciki. Gobe in sha Allah zanyi magana ta fahimta da Hajjo tunda ita ce babba. Zan fada mata bazaki iya rayuwa da kowa ba sai Ishaq. Nima da ke kadai nake son karashe rayuwata. Duk shawarar da ta bayar da ita zanyi amfani."

Tana hawayen amma murmushi take yi tana kallonsa. Yayi dariya "to dena kallona haka kada ki cinyeni kafin a daura auren"

Ta sunkuyar da kanta kasa cikin kunya. "Ba fa kallonka nake yi ba."

"Kallo na nawa kuma, a ciki ma ko kunyar Hajjo baki ji ba kika rinka satar kallona. Anya yarinyar nan baki fi karfina ba. Da ina yi miki kallon saliha amma yanzu ajinki daban ne"

Murmushi kawai tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta tace "zama da kai ne"

"Indai nine baki ga komai ba. Kinga koma kada a fara cigiyarki. An saba maza ke zuwa zance amma yau kin kasa hakuri kin biyo ni. "

Sai da ya rakata har kusa da dakin sannan ya dawo. A daidai inda suka gama magana yaga kamar  alamar mutum. Ya dan juya yaji shiru sai kawai ya tafi.

Qasim ne a wurin kuma duk yaji maganganunsu. Tun bayan fitowar Asmau ya biyo bayanta a zatonsa Col. Ishaq ya riga ya tafi. Rasa inda zaisa kansa yayi saboda a yau ya tabbatar ko kadan bata yi masa soyayya irin wadda yake fata. Duk wani tunaninsa ya kulle a yanzu shiyasa kawai ya shiga motarsa ya bar asibitin.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽44

Batul Mamman💖






A daren nan Qasim ya wuce Shanono. Abin duniya duk ya ishe shi. Dama wani lokacin baka sanin kana son abu sosai sai kaga alamun zaka rasa shi. Da gaske yake jin kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi.
*****

Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya.

A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar.
"ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare?

"Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka"

"Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu."

Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa"

Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa
"Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?"

"Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?"

Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau.
"Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye."

Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba"

Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa.
"Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna"

A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne."

Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka"

"Goro maigadon zinare"

Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo"

Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna farincikinsa.

Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna mamanki zata zo ko?"

Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba"

Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba"

Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya. Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta kuma kanwarta"

Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi. Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu.
******

Washegari litinin su Asmau sun kwana a asibiti. Da sassafe Umar yazo ya kai Mama gida ta yi wanka sai ya taho da Ainau ta taya Asmau zama. Ko goma bata yi ba suka ji sallamar Col. Ishaq. Asmau na jin muryarsa taji wani irin dadi a ranta. Soyayyarta da Jikamshi kullum jinta take sabuwa. Cikin khakinsa yake na sojoji yayi kyau ta bishi da ido a lokacin da yake shafa kan Amatullah dake kwance tana bacci. Ya amsa gaisuwar Ainau sannan ya juya yana kallon Asmau. Saurin sunkuyar da kai tayi tana jin kunyara tan cigaba da yiwa Husna dake hannunwa wasa. Bai dauke idonsa daga kanta ba yace
"Ainau dake ake shirin kai Matar Jikamshi gidan wani?"

Ainau ta zaro ido "wallahi babban yaya nima har kuka na tayaka. Ba don kada kuga wautata ba sai nace asthmar Amatullah tayi min daidai."

Wani wawan dundu Asmau ta kai mata harda harara. Ainau tace "ba fa har raina naso ciwon ba." Ta dan juya " kaga tana hararata ko"

Col. Ishaq ya karbi Husna daga hannun Asmau yana dariya "nima harararki nayi a zuciya. Ya zaki ce asthma tayi. Duk da dai na dauketa a matsayin tazo hanawa a raba Jikamshi da matarsa"

Irin kallon da yake yiwa Asmau yana wani lumshe ido yasa Ainau jin kunyar kasancewa a wurin. Sai murmushi suke yiwa juna. A ranta tace ba dole Yaya Asmau taso shi ba. Shi kuwa Yaya Qasim bata ga alamar ya iya nunawa mace soyayya ba. "Allah Ya baku hakuri to. zan fadawa Baba Amatullah ta warke ko gobe Yaya Qasim ya kawo kudi"

"Kinga kina jego shiyasa nake tausayinki. Idan aka aura mata wani ranar zaki kwana a guardroom don nasan adduarki ce taci" Col Ishaq ya fada suka yi dariya sannan ya yiwa Asmau alama da ta biyo shi.

Sai da suka je bakin motarsa yace "Matar Jikamshi kin tashi lafiya, ya jikin princess dina?"

Tana kallon kasa saboda kunyar tunowa da yadda jiya ta nuna masa tana sonsa tace "lafiya kalau Alhamdulillah"

"Yau 'yan kunyar sun zo ne zasu hana ace min I love you" ya karashe maganar yana kwaikwayonta.

Bata san lokacin da ta soma dariya ba yace "jiya duk bana cikin hayyacina ne sosai nima bance miki Matar Jikamshi ina sonki ba. Amma yanzu na fada. Zan wuce office sai an taso zan dawo ko kuma bayan magrib. Ki kular min da matata da 'yata"

"Allah Ya tsare Ya bada sa'a kuma Ya kareka daga dukkan sharri"

Kasa bude motar yayi ya kalleta "Matar Jikamshi"

"Naam Jikamshi _na_"

Yana murmushin jin dadi yace "komai naki ina sonsa, ki rinka yi min adduar nan kullum don Allah. Kuma idan zamu rabu ki kada ki rinka kirana Jikamshina. Sawa kike naji kamar kada na tafi"

Tayi dariya ta sake cewa "Jikamshina"

Ya dan marairaice mata "don Allah ki bari"

Ta sake bude baki zata maimaita tana dariya yace "kina fada zan wuce wurin Umma na fada mata irin kalaman da kike yi min wanda yasa nake so a daura mana aure a yau dinnan"

Ba shiri ta rufe bakinta. Ko dai bai fadi hakan ba tasan zai iya kwatantawa. Dan gefe ta matsa ya shiga motar ya dago mata hannu sannan yaja ya tafi.

Ciki ta koma Ainau tana yi mata tsiyar yadda duk su biyun yanzu basa iya boye sirrin zukatansu a gaban juna. Sai shabiyu su Umma suka zo ita da Hajjo da Mama. A nan suka yini don likita yace sallama sai gobe idan numfashin Amatullah ya daidaita yadda ake so"
*****

Daga wurin aiki gida Col. Ishaq ya wuce. Bazai iya zuwa wurin Asmau ba sai yayi wanka ya canza kaya. Idan Mami ta iso kuma su je da ita dasu Hajiya.

Tun a waje yaga motoci a cikin gidan na kannensa da wata da yake tunanin a cikinta aka kawo Mami. Hakan ya bashi tabbacin yau duk sun zo a tare. Mara motar dama daya ce mai bin auta. Dadi yaji saboda yawanci suna zuwa ne kafin ya taso aiki basu fiye haduwa ba. Ya shiga falon yaji shiru sai daga dakin Hajiya yaji ana magana ana daga murya. Karasawa yayi kofar dakin ya tsaya yana karewa 'yan uwansa kallo.

Mami ke binsa sai Ismail, Dahiru, Safiyya da auta Musaddiq.

Mami ce take magana cikin matsanancin bacin rai harda hawaye a idonta "wallahi tallahi Hajiya bazamu yarda Yaya ya bata mana suna ba."

Ismail yace "meye na rantsuwa Mami, kema kinsan babu mai zuwa cikin su Kawu nema masa aurenta. Idan basu san karuwa bace yarinyar ni...."

Tsawa mai karfi Col. Ishaq ya daka masa. Duk sai da suka razana don sun san halinsa sarai. Kirjinsa ke bugu da sauri da sauri saboda bacin rai "ko da wasa kada ka kara kuskuren kiranta da wannan sunan"

Safiyya tace "ayi hakuri Yaya, Sayyada zamu kirata ko ustaziyya?"

Dariya suka yi dukkansu banda Hajiya ta sha kunu "ban taraku a nan don ku zagi Asmau ba. Yarinyar nan kaddara ce ta fada mata wadda babu wanda ta wuce ta a cikinku. Kuma ni ba amincewarku na nema ba. Na dai fada muku tana da 'ya ne saboda bana son kananan zance nan gaba"

Musaddiq yace "haba Hajiya wannan ai ba zancen da ya kamata Yaya zo dashi bane ki karba. 'Yar shege da uwarta bazasu sami karbuwa ba a danginmu."

Col. Ishaq yayi kansa ya cakumi wuyansa yana huci. Musaddiq sai kakari yake yi don wahala. Hajiya tana ta cewa ya sake shi amma yaki. Cikin zafin rai yace "Musaddiq kada ka kaini bango. Dukkanku nan babu zaman wanda nake yi. Idan na aureta don Allah kada wanda yazo gidana."

"Dama waye zai zo" Safiyya ta fada cikin tsiwa. Ya juyo kama ya mareta.

Daga nan suka tararwa yayansu ana ta musayar magana. Hajiya taji babu dadi saboda yaranta akwai hadin kai. Yau daya sai fadawa juna magana suke yi akan Asmau. Ita da tayi laifi shekarun baya amma a yau sanadiyar wannan kuskuren 'yan uwa duka magidanta suna fada.

Col. Ishaq yace "an fada muku duk matar da ta haihu ko tayi ciki a waje karuwa ce jikinta ta sayar.?"

"Yaya ka fada mana gaskiya fyade aka mata ko me? Ni wallahi gara ka auri gurguwa da wannan yarinyar. Kila ma asiri tayi maka duk ka kasa fahimtar mu " cewar Mami

Yau duka 'yan uwan nasa haushinsu yake ji "ba fyade aka yi mata ba Mami. Idan su basu fahimce ni ba yakamata ace kin gane inda na dosa."

"Tausayinta kake ji?" Dahiru ya tambaya

"ina jin tausayin Asmau saboda irin wannan abubuwan naku ma tun farko taki amincewa da aure. Amma ba don tausayi zan aureta ba. Sonta nake yi so you all should better learn to live with that."

"Wai Yaya da kake maganar nan hala ka manta cewa baka *haihuwa* ?"

Ismail ne yayi maganar wadda tasa kowa yayi shiru. Hatta Col. Ishaq jikinsa yayi matukar sanyi. Hajiya ta taso rai a bace "Ismail wace irin magana ce wannan? Dan uwan naka kake fadawa magana haka" ta daga hannu zata mare shi

Col. Ishaq ya rike hannun idanunsa sun kada sunyi jawur. A sanyaye yake magana "Hajiya gaskiya ya fada. Lokaci daya na manta ina da lalura har nake tunanin yin aure."

Ya kalli kannensa daya bayan daya "in sha Allah daga yau na bar zancen auren Asmau. Ismail nagode da ka tuna min da waye Ishaq, ni mutum ne da Allah Ya tsarawa yin rayuwa ba tare da  naga nawa dan ba. Alhamdulillah tunda duk kuna da yara bazan ce na rasa gabadaya ba. Allah Yayi musu albarka. Bari na shiga nayi wanka zafi nake ji"

Hankali a tashe Ismail yace "Yaya"

"Kada ka damu kasan gaskiya daci gareta. Na da dan lokaci idan tayi aure zan manta da ita in sha Allah. Fatana Allah Ya tabbatar da aurenta da Qasim ko wanda ya fishi alkhairi gareta."

Yana fita yaci karo da Bilkisu. Hawaye take yi sosai ga tray din abinci a hannunta. Tana jin shigowarsa taje ta hada masa abinci don tasan tunda su Mami suka zo bazai fito da wuri ba. Duk zantunkansu taji komai. Ganinsa baisa ta tsorata ta bar wurin ba. Shima baiyi mata magana ba ya wuce abinsa.

Tana nan tsaye taji Hajiya tace "kun bani kunya da mamaki. Ban taba zaton zaku iya juyawa dan uwanku baya ba. Ina cewa Asmau tana da 'ya kuka hau surutu babu wanda ya tambayi garin yaya tayi cikin kafin aure."

Cikin nutsuwa ta basu labarin Asmau kamar yadda taji kuma ta gani. Safiyya uwar tsiwa sai ta fara kuka
"Mun shiga uku. Hajiya kuji wata muguwar kaddara. Allah Sarki"

Mami kuwa cewa tayi "duk da haka Hajiya ai bamu tabbatar da cewa a garuruwan da ta zauna bata taba karuwanci ba. Nima ta bani tausayi amma a bar maganar auren tunda ya fasa shima. Kinsan shi  baya magana  biyu"

Suna ta magana akan halin da Asmau ta tsinci kanta wanda ya girgiza tunaninsu ya kuma basu tausayi. Ace har rubutun cikin waya ya isa ya sa mutum aikata zina. Abin da ban tsoro da firgici saboda babu wanda ya isa ya tserewa kaddara sai dai komai akwai sila. Hajiya Lubabatu tace tunda zata je dubo Amatullah tana so dukkansu suyi mata rakiya.

Kukan Bilkisu suka ji Hajiya ta tashi da kanta sai dai kafin ta fito Bilkisu ta koma dakinta tana kuka. Bata taba sanin wannan labarin ba.  A iya tunaninta baban Amatullah ya rasu ne ko ya saki Asmau. Tsoro ne ya kamata saboda akwai wani saurayinta da suke chatting a facebook. A hankali ya fara sako mata zantukan banza tun bata amsawa har ta dan fara sakewa yanzu. Wai har ya iya tambayarta ta kwatanta masa kayan baccinta da daddare. Tayi saurin dafe kirji, yanzu idan da abin yayi nisa kila itama ta shiga sahun masu bawa samari jiki. Kuka take sosai tana tausayawa Asmau kuma har ranta tana fatan Uncle Ishaq ya aureta ko don ya rufawa rayuwarta asiri. Sabon saurayin da suke dan satar kallon juna dashi ta kira a waya tana sheshshekar kuka. Numbar ma a wayar Uncle ta dauka batare da saninsa ba. Da sallamarsa ya dauka cikin muryar da ta dashe da kuka tace "Yassar ne?"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽45

Batul Mamman💖




Mamaki ne ya kama Yassar, kamar ya san muryar amma bashi da tabbas.
"Da wa nake magana don Allah?"

"Bilkisu ce"

Tsorata yayi, shima yana neman numbarta amma yanzu da ta kirashi da alamun kuka sai yaji hankalinsa ya tashi.
"Bilkisu me ya faru?"

To me kuma zata ce masa? Tausayin kawunta take yi amma tana tsoron yi masa shishshigi. Uncle Ishaq yana da dadin  sha'ani amma babu mai son ganin bacin ransa. Fasa maganar tayi na son ta roke shi ya lallaba yayarsa kada ta ki Uncle dinta tace "babu komai, anjima zamu zo duba Amatullah" tayi masa sallama ta ajiye wayar.

A ransa yasan don zasu zo ba shine dalilin kiran ba. Tashi yayi ya shirya ya tafi asibitin. Zai jira su zo ya sami damar tambayarta. Ko dai ta lura da yawan kallonta da yake yi ne? Yayi murmushi, tun zuwansa gidansu na farko ranar da kare ya biyo Asmau ya fara jin wani abu game da Bilkisu. Sai dai duk hayaniya ta Yassar bai taba yin budurwa ba. Ta nan bangaren tsoro ne dashi kamar farar kura.
*****

Col. Ishaq na shiga dakinsa ya fada kan gado ko takalmi bai tsaya cirewa ba. Kansa ne yake wani irin ciwo kamar ana buga masa kusa. Ga zuciyarsa ta gama tafasa da bacin rai. Wai yau shine kannensa har da Mussadiq dan karamin cikinsu suke fada masa magana son ransu. A gidansu akwai tsari na girmama na gaba sosai. Sun tashi da so da kaunar juna. Lalurar kowa tare suka haduwa suyi maganinta. 'Ya'yan Ismail biyar duka maza karamin ma bai shekara ba. Amma saboda yadda suke bashi girma duk shi yake sakawa yaran suna. Haka yaran Dahiru guda uku. Gidansu gwanin sha'awa baka ce babansu ya dade da rasuwa ba. Amma yau akan auren Asmau duk sun ture wani girmamawa da shakuwa kowa ya fadi son ransa. Da akanta kadai suka tsaya ya tabbatar da har yanzu yana dakin suna cacar baki. Sai gashi saboda irin rayuwar Asmau ta baya har gori Ismail yayi masa. Gori da abinda yafi so a rayuwarsa, haihuwa. Shi da kullum yake kwantarwa da yayansa hankali. Kafin rabuwarsa da Badariyya ma yaransa biyu manyan a wurinsa suke. Dumi yaji a idonsa yayi saurin mayar da hawayen dake neman zubo masa. Duniya ta Allah ce kuma ba wurin tabbatar bayi ba. Da ace babu lahira sai yace rayuwar Asmau ta wuce abinda ake gudu domin komai daren dadewa sai an ambaceta ko 'yarta a matsayin mazinaciya ko 'yar zina. Ya tabbatar ko shugabar malaman duniya Asmau ta zama sai kaji mutane suna cewa
"Wance kamar ba ita ce tayi cikin shege ba"
"Ji yadda take nuna mana ita ta Allah ce kamar bamu san tarihinta ba"

Amatullah kuwa ita ma bazata tsira ba. Komai kyawun rayuwarta sai an ce "kaga wance kamar ba shegiya mara uba ba" "wance fa da kuke gani babu aure aka haifeta"
Irin haka da maganganun da suka fisu zafi mutane zasu fada a kansu. Babu ruwan kowa da yaya tsakaninta yake da Allah. Shin  ta tuba ko kuwa. Zina ta zama mugun tabo mara gogewa.

Tashi yayi ya zauna tare da daga hannuwansa sama. Hawayen da baya son yi ne suka zubo masa
"Ya Allah Ka karbi tuban baiwarKa Asmau da sauran al'umma da suke cikin hali irin nata. Allah Ka basu rayuwa mai albarka su ji dadin tuban da sukayi bisa laifukansu, Ya Allah Ka bata miji nagari wanda zai zame mata alkhairi kuma mai wanke mata bacin rai da bazata taba dena fuskanta ba a dalilin kuskurenta na baya. Ya Allah Ka karemu da sauran musulmi daga fadawa alfasha kowace iri ce. Amin"

Sai yanzu yaji saukin kuncin zuciyarsa ya tashi zaiyi wanka kafin a kira magariba. Abu daya ne a ransa yanzu, shine hakuri da Asmau da zaiyi. Ba karamin so yake mata ba amma dole ya barta ta auri wanda zata iya haihuwa dashi. Zafin soyayya ya rufe masa ido har ya manta yana da nakasa a rayuwarsa. Tunda baya haihuwa bazai cutar da kuruciyarta ba ta zauna da 'ya daya.

Wanka ya shiga ya fito ya sanya riga da wando na  yadi mara nauyi. Ya saka hula kalar adon rigar ya sha turare sai gashi ya fito a Jikamshinsa. Idan ka ganshi bazaka ce yana da damuwa ba saboda tunda yayi adduar nan babu abinda yake sai tasbihi ga Allah. Wannan ne ya saukaka masa damuwarsa yaji kwarin gwiwar niyarsa ta rabuwa da Asmau idan suka koma gida. Kafin ya fito text dinta ya shigo wayarsa. Yaa budewa yaga ta rubuta _missing Jikamshina_. Wani sabon sonta yaji ya ratsa shi. Kasa yi mata reply yayi ya tura wayar a aljihu.

Yana fitowa ya tarar da kannensa jugum a falo domin kuwa Hajiya tana gama basu labarin Asmau tace su fice mata daga daki. Da ya fito duk da ransa babu dadi haka ya basar ya dubi mazan
"Kuzo mu wuce masallaci"

Suka tashi jiki a sanyaye. Mami tace "Yaya don girman Allah kayi hakuri da abinda Ismail ya fada. Wallahi duj don bama so ka auro wadda zata gurbata mana dangi ne"

Suma sauran suka soma bashi hakuri. Ismail kuwa ko kallon yayansa ya kasa yi. Murmushi yayi wanda dukkansu sun san irinsa yake idan ransa ya baci
"Magana ta wuce, bazan auri Asmau ba kamar yadda kuke so. *Amma ba don kun nuna rashin amincewarku bane, don baku isa ba*. Saboda kaddara ta fada mata ba zan ce sai na aureta ba duk da ni din bana haihuwa ko Ismail?"

Ismail ji yayi kamar yayi kuka. Idanunsa tuni sun canja launi. Yayansu yana da kirki matuka, bai san yaya akayi shaidan yaja shi yayi wannan katubarar ba.
"Yaya ka yafe min, wallahi Hajiya yau har zagina tayi bayan fitarka. Yanzu ma cewa tayi zamu rakata asibiti duba yarinyar Asma'un daga nan kowa ya fice mata daga gida. Hatta Mami Hajiya tayi rantsuwa bazata kwana a gidan nan ba."

Col. Ishaq ya kara murmusawa "to ai babu damuwa Mami ga kannenki nan sai kibi daya daga cikinsu ki kwana a gidansa"

Mami ta saki baki don batayi tunanin haka zai ce ba. Tayi zaton zaije ya bawa Hajiya hakuri. Duk sun san bacin ranta yafi karfi akan gorin haihuwar da aka yi masa ne.
"saboda Allah ya zaayi naje gidan kannena na kwana da girmana"

"To bari mu dawo daga masallaci sai na baki key din gidana. Babu datti sosai saboda karshen sati maigadi yana min shara. Sai ki tafi da taki 'yar Bilkisu ta tayaki kwana" yana gama magana yayi gaba kamar bashi ya fada ba. Sun san sun tabo soja yau sai yadda ta yiwu kuma. Bayan fitarsu masallaci Mami da Safiyya suka zauna suna ta magana akan lamarin auren Asmau da kuma karin laifin da Ismail ya janyo musu.

Bilkisu dai shiryawa tayi a daki ta fito ta zauna jiran zuwa asibiti don tasan dole aje da ita tunda mai aikinsu bata nan.

Tare suka dawo daga masallacin su Dahiru suna ta bashi hakuri ya nuna musu komai ya wuce. Wurin Hajiya ya je ta shirya ita ma tace motarsa zata shiga su tafi.

Suka fito falo Bilkisu tabi bayansu suma sauran suka fito. Bilkisu na gaban motarsa Hajiya a baya Safiyya tazo ta kama daya kofar zata bude ya juyo ya watsa mata harara ba shiri ta saki kofar.
"Ki koma kibi motar 'yan uwanki masu haihuwa. Ni Hajiya zan dauka da 'yata."

Tayi saroro tana kallonsa. Dahiru da yaji ya dan matso wurin motar "Yaya don Allah kayi hakuri ka manta da zancen nan. Kuma ka yarda ta biku ko Mami ta shigo. Kaga sai ayi saving din mai mu tafi da mota biyu"

Col. Ishaq ya wani kankance ido ya kalli Bilkisu "toshe kunnenki kinji mai gadon zinare" ta kuwa tura yatsu a kunne tare da sunkuyar da kanta.

Hajiya tasan karshenta wata maganar mara dadi zai yabawa kaninsa tace "a gaban 'yarku zaku nuna min hali ko, kai kuma Dahiru kusan yadda zakuyi ku taho"

Col. Ishaq ya mayar da kansa ciki albarkacin Hajiya suka ci. Dole mota biyu suka yi don daya zata matsesu saboda Dahiru da Safiyya duk akwai jiki.

Yana soma tuki Hajiya tace "kai"

"Naam"

"Kayi hakuri da abinda suka yi maka don Allah kada kuyi min gaba. Aure kuma da kaina zan sami kakar Asmau muyi magana in sha Allahu. Tun farko na fada maka dole zaka fuskanci kalubale ta ko'ina saboda wannan abu fa ba wanda ake iya saurin kawar da kai bane a kansa. Ni dai ina sonta kuma na baka goyon baya ka nemi aurenta. Allah mai yawan gafara ne da jinkai. Idan bama iya kawar da kai ga kuskuren mutane to bamu san da wane laifi mu kuma Allah zai kamamu ba"

Allah Sarki Hajuyarsa akwai zurfin tunani.
"Hajiya nagode sosai amma ki bar maganar auren. Asmau bata cancanci ta kare rayuwarta bata haihuwa ba. Nima daga yanzu bana fatan kara neman aure. Mu bari kawai tabi shawarar iyayenta a zauna lafiya."

Sosai Haj Lubabatu taji tausayin Ishaq. Duk sallah bata fasa yi masa adduar samun rabo saboda yadda yake son yara. Da suna kanana har goya masa kannensa tana yi saboda yadda yake mata nacin zaiyi raino. Sai ayi goyon ya zauna a falo ko baki tayi baya jin kunya.
"Dole kayi aure shine cikar dan Adam. Kayi addua kamar yadda nake maka. Allah Ya kawo maka mace tagari" ya amsa da amin amma ba don yana tunanin zai kara son wata bayan Asmau ba. Shi fa bashi da raayin auren da babu soyayya. Kuma soyayyarsa ta kare a wurin Matar Jikamshi.

Ya kai hannu kan giya zai canja yaji Bilkisu ta dora nata a saman nasa ta kankame. Ya dan kalleta ya kula kuka take yi a hankali. Yace "nine ko, nasa Maminki kuka"

Muryarta na rawa tace "a'a Uncle don Allah kada kaki auren Ummin Amatullah"

Murmushi kawai yayi yana kwanar shiga asibitin motar Musaddiq tana bayansa.
"Allah Yayi miki albarka kinji. Ki cire duk abinda kika ji dazu daga ranki.... Wai ma wa ya koya miki labe? Bari mu dawo yau sai kinyi tsallen kwado"

Da guntun hawayenta tayi murmushi. Hajiya ma murmushin tayi. Taji dadi da fushinsa bai shafi 'ya'ya ba.

Boot dinsa ya bude ya fito da ledoji biyu cike da tarkacen kayan kwadayi na yara sai katon din ziza. Yana tasowa daga office ya siyo kafin ya wuce gida. Bilkisu tazo taya shi dauka sai ga su Ismail da sauri kowa ya dauki abu daya cikin su mazan. Ya kawar da kansa gefe don yasan suna neman shiri ne. Abinda bazasu samu kenan a nan kusa ba.
*****

Shi da Hajiya ne a gaba sai Bilkisu da ta jero tare da Mami da Safiyya tana tambayar Mamin kannenta. Sun kusa zuwa dakin suka ga wata mace ta fito daga wani daki da hijab dinta har gwiwa tana kuka. Col. Ishaq bai san lokacin da ya isa gabanta ba da sauri ba hankali a tashe yace  "Matar Jikamshi menene?"

Asmau kuka take yi kawai "Amatullah ce ta sake samun attack. Likita zan kira"

Shima a rude yake yace "koma wurinta bari na kira likitan"

Kasa komawa dakin tayi tabi bayanshi da gudu tana ta zubar da hawaye. Duk sunji tausayin Asmau da yadda ta gigice. Dakin da suka ga ta fito Hajiya tace "mu shiga mu jirasu"

Mami ta bude kofar suka shiga da sallama. Mama Yalwa ce a tsaye kan Amatullah tana ta kakari. Safiyya na jin yadda take kakarin ta matsa kusa da gadon da sauri tace "wannan ba attack din asthma bane. Ba kuji yadda take numfashin ba, majina ce a kirjinta"

Mama Yalwa tana jin haka ta saka bakinta a hancin Amatullah ko kyama babu ta rinka zuke mata tana tofarwa.  Tana kaunar Safina fiye da sauran jikokinta sosai saboda yarinya ce mai tattare da tabo mai muni a rayuwarta. Bayan zina mace aka fi gani da nason zunubin duk da cewa dole idan anyi akwai namijin da suka yi tare. To amma namijin sai ya tsira daga aibatawar mutane saboda shi ba'a ganewa a jikinsa. Idan ya karyata babu yadda za'ayi dashi. Sharrin zuciya ya cutar da Abubakar wanda yayi sanadin cutar da Asmau. Gashi a karshe Safina ita ce abin ya kare a kanta. Mama ta dan share hawayenta sai ga Amatullah ta ware saboda hancinta ya bude.

Sai a lokacin suka gaisa dasu Haj Lubabatu. Mama tace "Hajiya duk wadannan yaranki ne? Masha Allah"

Hajiya ta dan murmusa "ya mai jikin?"

Mama tace " gata nan duk ta ruda mu." Ta kalli Safiyya "nagode miki kinji. Ya sunanki ne?"


Safiyya ta fadi sunanta kenan su Asmau suka shigo tare da likita. Ga mamakinsu a zaune Amatullah take ta jingina da pillow. Asmau taji wani sanyi a ranta sannan ta matsa kusa da Amatullah tana mata sannu. Likitan ya dubata ya tabbatar harda mura tayi mata mugun kamu. Magunguna yace zai turo nurse ta kawo musu.

Bayan fitar likitan Asmau ta gaishe da su Mami. Cikin su babu sa'anta duk sun girmeta. Sun amsa mata fuskokinsu babu yabo babu fallasa. Col. Ishaq yana tsaye daga wurin kofa. Idonsa kyam akan Asmau har 'yan uwansa suka fuskanci yadda suke jifan juna da kallo.  Ita duk kunya ma take ji musamman saboda su Hajiya da Mama.

Amatullah ce ta kurawa Ismail ido tace "kai da Babana iyinku daya. Kaima sunanka Jikamshina?" saboda irin kamaninsa da Ishaq.

Ya Salam, Asmau ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige. Allah Ya taimaketa ma Amatullah bata ce irin yadda Ummia ke fada ba. Don kadan daga aikinta ne yin hakan.Col. Ishaq kansa yau yaji kunya karo na farko a rayuwarsa game da fadin magana a gaban kowaye batare da yaji komai ba.

Su Musaddiq sai kallon kallon kallo ana dan murmushi. Ismail kuwa yace mata "nima babanki ne 'yan mata" ya karasa wurin gadon da murmushinsa.
Ta kalli Col Ishaq tayi masa gwalo " Babana kaga nayi sabon baba ko. Ni yanzu na dena yin baba da kai"

Yace "subhanallahi me nayiwa princess dina haka. Kai Ismail tashi ka bani wuri mu sasanta ni da 'yata"

'Yar dramarsu tasa mutanen dakin dariya. Amatullah tayi saurin rike hannun Ismail  tace "yanzu baka wasa dani sosai sai da Ummi na. Nima ga sabon Baba nayi" 

Asmau ta rasa abin cewa. Tsiyar yaro mai surutu fa kenan. Yau Amatullah ta gama bata kunya.

Safiyya tace "amma da baban nan naki da Ummi basu kyauta ba. Yanzu ga sabo nan mun baki. Amma kiyi hakuri Babanki so yake ku koma gidansa sai ku rinka wasan tare kullum shiyasa yake yi da Umminki"

Kana gani kasan Amatullah taji dadin wannan zancen tace "Ummi kuje kuyi wasa da Babana to idan kun gama mu koma gidansa."

Yau kam ta kai karshen jin kunya, shi kuma Col. Ishaq saboda shawarar da ya yanke ta rabuwa da ita shiyasa yau bai bada amsar da zata karasa bata kunya ba.

Hajiya da Mama Yalwa sai sunkiyar da kai suke. Ita Mama harda mamakin dama son Asmau sojan nan yake bata sani ba.

Ismail ji yayi ta shiga ransa. Dama yana son 'ya mace gashi duk maza gareshi.
"Ki kyale wancan Baban kawai kinga a gidana zan siyo miki kayan wasa da alawa"

Tace "ai Ummi ma tana siya min. Ta hanani kwadayi. Kuma bana yi sai tace min Allah Yayi miki albayka"

Yarinya karama sai basu sha'awa take yi. Mami kallon Asmau take yi. Yanzu mace mai kamannin kamala irin haka ace a waje ta haihu. Kai wannan duniya mai rudin bayin Allah.

Amatullah ta sake cewa "sabon Babana in kayanta maka Allahu?"

Dahiru yace mata "karatu ake cewa ba kayatu ba"

Tuni ta bata rai "kayatu fa nace ba kayatu ba"

Daki ya kaure da dariya. Col. Ishaq yana kallon yadda 'yan uwansa duk suka mayar da hankali gareta. Murmushi yayi yana fatan ko nan gaba idan ya roki alfarmar a bari tazo gidansu ta yini wurin Hajiya bazasu yi mata gori ba. Ido suka hada da Asmau tayi murmushi sai taga ya dan sunkuya kamar zai duba waya. Bata kawo komai a ranta ba.

Ismail ya samu shiga wurin Amatullah yace "karanta min a kunnena ni kadai kada su ji"

Ta fito da ido da mamaki "Ummi fa tace mai yada mai yada dan wuta, mai ji mai ji kafiyi." Nan dariya aka yi suka ce to sai ya kiyaye yarinya tasan rada babu kyau.

Daga kai yayi ya kalli Asmau ta danyi murmushin jin kunyarsa. Su Mami suma mamakinta suke yi. Ga dai ta yadda ta haifi 'yar nan amma ga dukkan alamu tana da tarbiya sosai. Tunda ta bude baki ta fara karanto sunayen Allah gudu biyar da tsallake. Musaddiq ji yayi inama 'yarsa ce. Ga muryarta akwai dadi tana yi kamar da addu'a
"YA RAHMANU YA ALLAH-AMIN
YA RAHIMU YA ALLAH-AMIN
YA MALIKU YA ALLAH-AMIN...."

Haka tayi ta yi har karshe. Mami ta y kurawa Asmau ido, yarinyar bata da makusa sai abinda tayi a baya. Idan har aurenta zai sa dan uwanta ya dawo mata kamar da, to zata amince da auren nan. Sai dai fa dole su shirya da jin surutu da gorin 'yan uwa da sauran mutane.
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
   Arewa hausa novels
       Novels villa
     Duniyan novels
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And
Cool novel, makeup and cooking)

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239

ABINDA AKE GUDU🙆🏽46

Batul Mamman💖





Surutun Amatullah ke tashi a dakin da masu biye mata. Tsakani da Allah ta shiga zuciyar Ismail. A ransa ji yake ina ma yarinyar nan ta cika 'ya kamar kowa. Ta tashi har karshen rayuwarta bazata taba jin wata magana mai muni game da haihuwarta ba. Col. Ishaq kuwa Asmau har ta gaji da kallon inda yake tsaye. Duk iya yinta ta kasa yin sa'ar kallonsa a daidai lokacin da yake kallonta. Shi kuma yana sane yake dauke kansa daga gareta idan yaga ta dago nata kan. Duk son da yake mata dole ya rabu da ita indai tsakaninsa da Allah yana son farincikinta. Duk wani tanadi da yake yi mata da Amatullah maganar Ismail ta rusa komai. Zaiyi kokarin taimakonta ta kowane fanni na rayuwa musamman karatu da tace tana son komawa. A shirye yake ya dauki nauyin hakan idan bazai kawo matsala tsakaninta da wanda ta aura ba. Ko kawai ya hada kudi ya bata a matsayin gudunmawar aure. Shi kadai yake ta tunaninsa har su Umma suka shigo ita da Anti Bintu da Shemau.

Ba haka su Mami suka tsammaci ganin dangin Asmau ba. Gashi dai suna da rufin asiri sannan ga hadin kai. Wani abin mamaki wai harda babar wanda yayiwa Asmau ciki ake jinyar Amatullah. Mamakinsu bai karu ba sai da Alh Adamu ya shigo. Mutum mai fara'a jan mutane a jiki. Ya gaisa da kowa sannan ya zauna yana tsokanar Amatullah. Lokacin dakin ya cika sosai shiyasa Haj Lubabatu tace su tashi su tafi.

Tun daga kan Mami har Musaddiq sun yaba da 'yan uwan Asmau. Kaddara kam babu inda bata giftawa. Kuma idan ta ratso kamata yayi dukkan musulmin kwarai ya karbeta hannu bibbiyu. Ashe ba daidai bane idan 'yar mutum tayi ciki ko zina a kyamaceta a koreta. Hakan ba komai zai kara musu ba sai bushewar zuciya idan basuyi sa'a kamar ta Asmau ba. Ba'ace a nuna musu sunfi kowa ba ko a shafe girman laifinsu a mayar dasu kamar komai bai faru ba. Amma a jasu a jiki ta hanyar nuna musu kuskurensu da wajibcin tuba da nesanta daga aikin dana sani. Asmau ta zama babban misali. Duk da iyayenta sun yafe mata kuma ta tuba amma fa har abada da gaban abada idan akwai baza'a taba mantawa ba.  Ita da ta manta da haka a rayuwarta sai ranar da taji ance *shiga aljannah cikin aminci*. Ya Allah Kasa mu dace.

Ita da Anti Bintu suka fito rakiya. Sai a lokacin suka hango Bilkisu da Yassar a wurin wani benci. Kusan kowa ya manta dasu ma.

Duk abinda taji daga bakin iyayenta da kakarta ta tambayi Yassar ya tabbatar mata da haka ne. Bilkisu tayi kuka sosai taji tausayin Asmau. Ta fada masa shawarar da kawunta ya yanke na rabuwa da Asmau saboda matsalarsa. Nan fa hankalin Yassar ya tashi. Bai ga wanda ya dace da yayarsa ba kamar Col. Ishaq. Suna wannan tattaunawar ne suka hango fitowar su Ismail. Bilkisu ta rasa inda zata saka kanta don kunya. Kada ayi zaton ko Yassar saurayinta ne duk da kuwa hakan take fata. Amma bata riga ta faru ba. Yanzu kokarin daidaita Kawunta da yayarsa suke yi.

Allah Yasa hankalinsu baya wajen. Asmau da Anti Bintu ne suka gansu. Anti Bintu sai ta tsaya wurin Col. Ishaq saboda dama tana son ganinsa. Sauri zatayi suyi magana kafin Hajiya ta fito don Alh Adamu dasu Umma sun dan tsaya hira da ita. Ita kuma Asmau ta karasa wurin su Bilkisu.

Suna hangota suka tashi sai dai ta kula da hawayen da Bilkisu ke gogewa da sauri. Tsorota tayi ko Yassar yayi mata wani mugun abin. Tsaresu tayi da ido tana kallonsu daya bayan daya
"Me kuke yi a nan tun dazu?"

Yassar ya dan sosa kai yana murmushi "babu komai Ummin Amatullah"

Tayi dan tsaki "Bilkisu fada min kinji. Me yayi miki kike kuka?"

Itama murmushi tayi "Allah babu komai, abu ne ya shigar min ido"

Ko kusa bata yarda dasu ba. Daga ganin yanayinsu tasan basu da gaskiya.
"Tunda bazaku fada min ba bari na kira babanki, shi nasan zaku fada masa"

Zata juya Yassar ya riko hannunta da sauri "don Allah kada ma ki fara. Bari su tafi wallahi zan fada miki duk abinda kike son ji.

Suna kallo motocin su Ismail da Dahiru suka fita daga asibitin. Bilkisu tace "bari naje, Anti Asmau sai da safe."

Asmau ta dan bata rai cikin wasa "bazan amsa ba sai naji bayani."

Murmushi kawai Bilkisu tayi ta kama hanyar motar Col. Ishaq.
******

Tana karasawa taji Anti Bintu cikin tashin hankali tana cewa  "wace irin magana ce wannan Ishaq? Haihuwa ta Allah ce. Yanzu saboda wannan zaka ce ka fasa. Wallahi baka ga yadda na shiga damuwa ba da naji zancen Qasim"

Rabin hankalinsa yana kan Asmau da yake hangowa suna magana da Yassar. Ba a nan inda 'yarta ke kwance tana jinya yake so taji zancen ba. Bilkisu ya kalla babu fara'a a fuskarsa.
"Kin gama kai gulmar? To kije ki fada masa nace kada ya kuskura ya fada mata komai yanzu"

Hanjin cikinta har wani kullewa yayi don tsoro ta koma wurinsu da sauri sosai. Ya mayar da hankalinsa ga Anti Bintu.
"Rashin haihuwa ba karamar matsala bace. Ke shaida ce ina sonta amma yaushe zan tauye mata hakkinta ta zauna dani babu haihuwa"

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Asmau tana ganin jarabawa kala kala a rayuwarta. Tunda ta dawo gida ban taba ganin farincikinta ba kamar idan tana tare da kai. Ishaq wallahi tana sonka. Kada kayi mata haka. Yarinyar nan taga taskun rayuwa. Yanzu kuma zata rasa masoyi" Anti Bintu tana magana ita kanta kamar zata yi kuka.

Ji yayi zuciyarsa har wani zafi take masa. A jiya ya yanke shawarar ko me zai faru bazai rabu da ita ba. Amma magana daya tasa ya tuno da rashin dacewarsa da ita.
*****

Kafin Bilkisu ta isa wurinsu Asmau tayo gaba. Yassar yayi mata alkawarin sai sun koma gida zai fada mata komai, ita duk tunaninta ma ko soyayya sukeyi a boye. Bata matsa masa ba tace shikenan. Cikin nutsuwa ta taho wurin da Jikamshi yake tsaye da Anti Bintu. Ita dai Anti Bintun tana ganinta ta bar wurin zuciyarta tana kara karaya. Bata san halin da Asmau zata shiga ba idan taji abinda Ishaq yake tafe dashi. Gashi lamari na haihuwa ba'a daukarsa da wasa. Ita bata isa tace dole ayi auren ba tunda da kansa ya fada mata aurensa na fari shekarunsu goma shadaya da matar. Gashi suna rabuwa ta haihu.

Da zata bar wurin suka hada ido da Asmau tayi saurin sunkuyar da kai a kunyace. Shima ba dadewa zatayi a wurinsa ba saboda kada Hajiya ta fito.

Yaji dadin ganinta amma yanayin da zuciyarsa take ciki ya hana ya bayyana mata duk kokarinsa na boyewa. Da murmushi a saman fuskarta ta gaishe shi.

"Matar Jikamshi"

"Uhmm"

"Yau nafi sonki akan kullum, ji nake kamar yau na fara sonki ma" yadda yake furta kalamansa a hankali yasa taji wani dadi a ranta.

Mukullin motar yake dan kadawa yace "baki amsa min ba."

A zuciyarta tace zai fara sakata jin kunyar da ya saba. Kasa take kallo tace "to me zan ce?"

"Au baki ma sani ba, to bari na fada miki tunda ni nake son jin amsar. Ina ji idan baki fadi abinda nake so ba bazan iya kaimu gida ba." jikinsa duk a sanyaye yake. Daga yau baya jin zai kara furta mata kalmar so. Kallo kuwa tamkar ya cinyeta da idonsa. Jin soyayyarta yake sabuwa a zuciyarsa.

Dago kai tayi "don Allah ka dena fadin haka bana so"

"Nine bakya so ko maganar da nayi"

Kwabe masa fuska tayi tana shirin kuka yaji ta kara shiga ransa"kasan me nake nufi. Ka dena cewa bazaka iya zuwa gida ba"

Yayi dariyar karfin hali "to bani amsar da ta dace"

Rufe fuskarta tayi da mayafi sannan tace "I love you Jikamshina" da sauri ta juya zata gudu ya dakatar da ita ta tsaya amma bata juyo ba.

"Matar Jikamshi ki rike mijinki da gaskiya kinji ko. Allah Ya albarkaci rayuwarki"

Duk ya kashe mata jiki da kalamansa amma ko kadan bata kawo komai a ranta ba. Ita a zatonta shi yake nufi a matsayin mijin nata shiyasa tace
"Amin" sannan ta shige cikin asibitin.

Allah Ya taimaketa domin kuwa a hanya ta hadu da Umma da Mama sun rako Haj Lubabatu. Gashi babu damar canja hanya haka tayi mata sallama ta wuce su kuma suka rakata har mota.

Har su Umma suka zo tafiya Anti Bintu bata ga wani sauyi a tare da Asmau ba. Wannan ya sa tayi tunanin Ishaq bai riga ya fada mata ba. Duk su biyun tausayi suke bata, zata saka su a addua don ita bata san wace shawara zata basu ba.
*****

Bayan kwana biyu aka sallami Amatullah. Duk kwanakin da Mami tayi a Kano a gidan Col. Ishaq tayi su don kuwa da gaske Haj Lubabatu ta hanata kwana a gidanta. Ranar da zata tafi suka taru ita da kanneta suka sake bawa Hajiyan hakuri. Shi Col. Ishaq tuni ya ware dasu. Fushin bazai kaishi ko'ina ba yanzu tunda akwai gaskiya a maganarsu. Mami ta tafi akan duk shawarar da ya yanke su duka zasu bashi goyon baya.

A wannan lokacin ya rage kiran Asmau. Idan ta kira sai taji wayar a kashe. Nambobinsa biyu gareta duk bata samunsa sosai sai idan shi ya kirata. Shima din hirarsa tafi yawa da Amatullah. Idan ta karbi wayar daga gaisuwa sai yace mata zaiyi aiki ko zai kwanta. Tun bata dauki abin komai ba har dai ta fara tunanin akwai wata a kasa.

A bangaren Qasim ya matsa mata sosai da waya yanzu. Yazo sau daya ya koma bakin aikinsa. Nunawa yayi bai san da maganar Col. Ishaq ba. Ita kuma taki sakar masa jiki tana jira taji daga bakin Jikamshi tukunna.
*****

Haka tayi sati daya duk abubuwa sun cakude mata. Jafar ya karbi takardunta na SSCE zai sake nema mata admission. Amatullah tunda taji sauki Abdulhalim ya zo wata litinin da safe ya tafi da ita makarantar da yaransa suke yi. Makaranta ce mai tsada sosai domin kuwa ana arabiya da boko tun bakwai da rabi sai hudu da rabi  ake tashin yara.
Ga karatun Qur'ani ba kama hannun yaro. Ita dai Asmau sai son barka. Kowa na kokarin kyautata musu. Shemau taso ace a makarantar da nata yaran suke zuwa aka saka Amatullah. Da yake saura sati daya hutun makaranta gwaji kawai aka yi mata suka bata aji, kayan makaranta da litattafai. Karatu sai an dawo zata fara sosai. Abdulhalim ya biya kudin komai. Alh Adamu ya kara masa kudi don kada ya shiga matsi tunda yana da nasa yaran. Amma yaki karba Amatullah 'yarsa ce baya bukatar taimakon kowa.

Da ya dawo da ita gida kuwa an sha labarin sabuwar makaranta. Tana ta zuba zance akwai lilo da wurin computer irinta Uncle Yassar. Hajjo da Umma kadai ke amsa mata. Asmau na rike da waya a hannu tana ta kiran Jikamshi ta kasa samu. Bata jima da ajiye wayar Qasim ba yace mata iyayensa suna so a sake basu ranar da zasu dawo.

Umma ce ta lura da yadda take ta tsaki ga waya a hannu tana ta dannawa.
"Asmau wa kike nema ne haka? Kinsan dai wani lokacin network sai yaki dadi amma duk kinsa abin a ranki sai tsaki kike faman yi."

Amatullah tayi caraf tace "kuma ni ta hana ni yi, wai tsaka ce yake yi"

Ran Asmau yayi mugun baci ta kai mata duka ta sameta a gefen fuska  "ban hanaki idan manya na magana ki saka baki ba. Tashi ki bar wurin nan kafin na kara miki"

Kuka sosai Amatullah take yi don har dankunnenta sai da yayi tsalle. Umma da Hajjo har suna rige rigen janyota jikinsu. Umma itama ta harzuka tace "wane irin rashin hankali ne wannan Asmau. Daga tayi magana sai duka."

Hajjo tace "kuma dukan ma a fuska, tayi kuskure don ba'a so a koyawa yara saka baki a zancen manya. Amma ya zaki mata hukunci irin wannan. Ji yadda dankunne ya karce ta"

Suna kokarin jan Amatullah amma taki tsayawa. Da Hajjo ta saketa jikin Asmaun ta koma tana kuka "Ummi kiyi hakuyi na dena"

Kuka Asmau ta saka, tasan bata kyauta ba don fushinta ta saukewa Amatullah. Ga zuciyarta dama ta gama rauni. Bata samun Jikamshi shima baya kira sosai sannan Qasim yana jiran amsarta na ranar da zasu dawo. Amatullah ta sake cewa "Ummina kin hakuya?"

Cikin kuka ta rungumeta sosai a jikinta "na hakura Ama"

"To ki dena kuka nima na dena"Amatullah ta fada tana share hawayenta.

Wannan ya kara karyarwa Asmau zuciya ta cigaba da kukanta bilhaqqi. Umma da Hajjo suka tsaya kallon ikon Allah. Sai da tayi mai isarta ta dauki Amatullah suka shiga ciki.

Suna tafiya Hajjo ta rike baki "Bara'atu anya yarinyar nan bata da mutanen boye?  'yan kwanakin nan na lura tana cikin damuwa. Wannan kukan ma da biyu ko uku ma zance take yinsa."

"Nima haka nagani, bari naje naji ko menene"
*****

Dariyarsu Umma ta fara ji Asmau tana bin Amatullah tana  cewa zata shafa mata dettol a wurin da dankunne ya karceta ita kuma tana zagaye gado da gudu. Umma ta rike baki kawai. Asmau da Safinanta sai Allah. Tare suka ga wahalar rayuwa shiyasa shakuwarsu take bawa mutane sha'awa.

Sakin fuska tayi ta shiga ta daga Amatullah.
"Gudu wurin Hajjo kinji yarinyar kirki."

Ta fice kuwa a guje tana dariya. Asmau kunya ta kamata ta ce "Umma kiyi hakuri don Allah".

"Bakiyi min komai ba Asmau. So nake ki fada min abinda yake damunki. Ba'a so damuwa tasa iyaye su rinka hucewa akan 'ya'yansu. Amatullah bata kyauta ba da tayi magana amma ba da haka zaki tsawatar mata ba. Ko don gaba ki kiyaye"

"In sha Allah Umma. Nagode"

Wuri Umma ta samu ta zauna  tace "zauna Asmau, magana zamuyi"

Murmushi ta kirkiro "babu komai fa Umma, haushi ta bani ne"

"To na tashi kenan tunda kina da wanda zaki fadawa matsalarki bayan ni"

Daga magana kamar ance fara kuka kawai ta kwantar da kanta a cinyar Umma ta soma kuka. Tausayi ta bawa Umman ta fara rarrashinta "komai yayi tsanani maganinsa Allah. Yakamata ace kece mai fadawa wani hakan. Wa kike nema a waya har abin ya bata miki rai haka"

Muryarta har ta dan shake tace " idan mutum ya dena nemanka a waya sosai alama ce ta ya hakura da kai ko, ko kayi masa laifi"

Duk da Umma tasan wa Asmau ke so sai tace "waye baya kiranki a waya"

Rufe bakinta tayi da sauri. Maganar ce take cinta amma bata yi niyar fada ba.

Dan murmushi Umma tayi. Tun ranar da suka hadu da su Hajiya a asibiti kafin Anti Bintu ta koma Zariya ta fada mata yadda suka yi da Col. Ishaq. Ta sauke ajiyar zuciya
"Ishaq ne baya kiranki?"

Sake sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa. Umma tace "ki yawaita addua da neman zabin Allah nima zan tayaki."

Abinda yake ta cin ranta ta kasa boyewa "cewa yayi zaiyi magana da Hajiya, ina jin saboda Amatullah bata amince ba. *Umma nayi kuskure ne da ban zubar da cikin ba na haifeta*?

Wannan karon Umma ma sai hawaye "ko kadan Asmau. Haihuwarta shine maslaha gareki damu baki daya. Mun so bin son zuciya da muka dage sai kin zubar da cikinta. Ki duba ki gani yadda Allah Yayita mai kokari da ladabi. Kema kinsan ba iyawarki bace kawai tasa kike da yarinya mai tarbiya kamarta. Mata da yawa da iyayensu sukan gujewa kunyar duniya su zubar da ciki ko a yar da jariri. Sai anje lahira kuma ido ya raina fata. Ga laifin zina ga na zubar da ciki ko kashe jinjiri. Ko ki sami miji ko kada ki samu ki sani cewa rayuwarki ibada ce. Hakuri da tawakkali shine ginshikin farincikin dan adam. Batun Ishaq kuma kada ki damu zai nemeki da kansa ku kare magana. Da shi da Qasim wanda duk Allah Ya zaba miki ko waninsu sai mu ce Alhamdulillah.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽47

Batul Mamman💖


*Maman Farida mai Hanyar Ruwa. Ina gaisuwa da fatan alkhairi. Ga naki shafin yar uwa*

*Amina Yau, Jikamshi yana gaisheki da kyau.*

*Shafaatu mai masaukin baki a gidan Batul ina godiya*

*Masu sakonnin gaisuwa bazan taba mantawa daku ba. Allah Yayi mana jagora*


Sai yanzu Asmau ta dan sami nutsuwa a ranta. Tun da Jikamshi ya dena kiranta sosai ta fara tunanin ko Hajiyarsa ce bata amince ba. Amma yanzu Umma ta kwantar mata da hankali. Zata sake nemansa daga yau zuwa gobe. Idan taji shiru to zata bar komai ga iyayenta. A yanzu dai Umma da Mama Yalwa sun riga sun san da maganar Col. Ishaq. Mama har fada tayi da basu fada da wuri ba sai a asibiti ta ganewa idonta. Asmau ta san bazata bar maganar ba dole ta fadawa Baba.

Bayan fitar Umma tashi tayi ta dauko Al-Qur'ani tana karantawa. Neman sauki kawai take a zuciyarta da ke kitsa mata abubuwa da yawa. Adduarta bata wuce idan Jikamshi bazai aureta ba zata mayar da hankali ga karatu, idan kuma iyayenta sun zaba mata Qasim duk da a yanzu sun san bata son shi to bazata yi musu ba. Fatanta bai wuce ta sami juriya wurin karbar duk wata jarabawa da tazo mata ba.
*****

Washegari Umma ta gama shirin zuwa gidan Mama suyi magana ta karshe da Alh Adamu sai ga Garzali ya shigo yana ta fara'a suka hadu a bakin kofa. Umma tace "kanina mijin 'yata irin wannan fara'a haka. Ko dai Zubaida ta haihu"

Yana murmushi yace "yanzu daga asibitin nake. Ko awa daya bata yi ba. An sami namiji."

Umma sai murna ta koma ciki tana mita akan me bai fada musu ba tun lokacin da suka tafi asibitin. Sai da suka je dakin Hajjo bayan ta fada mata kyakkyawan labari tace "ina kuka kai su Walid?"

"Kai Yaya Bara'atu sai faman fada kike yi. Tsakar dare fa ta fara nakudar. A makota na ajiyesu muka tafi."

Asmau ce ta shigo dakin daga kitchen bayan taji muryar Kawu Garzali. Tayi murna sosai tace bari ta dora ruwan zafi sannan ta hada abinci. Kawu Garzali yace ta barshi makociyarsu duk tayi wannan. Yana jin bazata dade ba za'ayi sallama. Tace to bari tayi wanka sai su tafi. Tana tafiya Umma ta soma fada masa halin da suke ciki ga Qasim kuma da yake jira a sake basu lokaci. Hajjo tace
"Allah mai iko, wallahi idan aka ce min yarinyar nan zata sami manemin aure sai in karyata. Gashi yanzu an samu har an rasa na zabe. Ni dai shawarata kada ayi mata dole. Yaron nan Qasim dan mutumci ne gaba da baya amma bana son ayi auren dana sani. Asmau ba kankanuwar yarinya bace da zaa ce bata san me take yi ba. Kai Garzali mu zamu je asibitin. Kaje ka sami Alhaji kuyi magana. Idan za'aji ta bakin Ishaq din ne ya kamata a hanzarta. Idan kuma da Qasim din ne ma duk yadda akayi babu matsala."

Umma ta dan sassauta murya tace "Bintu fa ta fada min shi Ishaq din yace ya janye saboda baya haihuwa."

"Baya haihuwa?" Hajjo ta fada tana daga murya.

Umma tace "Asmau bata sani ba. Yace zai fada mata da kansa. Nima ban nuna mata na san wani abu ba"

Kawu Garzali ya shiga jimami. Zubaida ta fada masa irin yadda ta ga Col. Ishaq da Asmau suna son juna ranar da taje yini a gidan. Anya akwai ranar da Asmau zata ga haske a rayuwarta kuwa. Daga wannan matsalar sai wannan.
"Wai ya taba aure ne ko tuzuru ne shi Ishaq din"

"Kaima dai Garzali in bai taba aure ba yaushe zai san da matsalar rashin haihuwar. Shekararsa shadaya da matarsa ta farko"

Gefen gado Hajjo ta samu ta zauna "ni dai kaina duk ya kulle. Haihuwa ba abin wasa bace duk da mutum baya bawa kansa amma kowa yana so. Muje dai wurin maijegon, kai kuma duk yadda kuka yi da Alhajin ka fada mana. Ai ita shawara tana da dadi. Bana son azo ana cizon yatsa nan gaba shiyasa cikinsu babu wanda zan ce lallai sai ta zabe shi."
*****

A nan suka bar zancen su Umma suka wuce asibiti daukar Zubaida. Kawu Garzali ya tafi gidan Alh Adamu.

Bayan sun gaisa ne Alhajin yace "ina Hajiya Bara'atun? Tace zata zo. Ashe tare ma kuke"

"Ni kadai ne Alhaji. Sun tafi asibiti mai dakina ta sauka dazu bayan asuba"

Barka Alh Adamu yayi masa sannan suka fara tattauna abinda yake gabansu. Zancen Col. Ishaq ma sai da Alh Adamu yayi ya ce Mama ce ta fada masa. Ashe shiyasa yaga shi da mahaifiyarsa da 'yan uwansa sun zo duba Amatullah. Daga Shanono kuma jiya ya sami waya suna bukatar a sake basu lokaci.

"Alhaji wannan abu duk mai sauki ne. Yanzu nake ji cewa shi Ishaq din yace zai janye saboda yana da lalura ta rashin haihuwa. Idan haka ne kaga Qasim ya kamata ta aura"

"Banki taka ba Garzali. Duk abinda aka riga aka sani yafi sauki idan za'a tunkare shi. Amma menene tabbacinmu na cewa shi Qasim yana haihuwa ko ita Asmau zata sake haihuwa? A zahiri nafi sonta da Qasim saboda kusancinsa da Abubakar. Gani zanyi kamar dana ne ya aureta. Sai dai kuma bana son mu saka son zuciya a cikin al'amarin nan. Tana gida ne yanzu?"

"A'a tare suka fita dasu Hajjo" Garzali ya bashi amsa.

"Idan ta dawo kace ina nemanta jibi bayan azahar in sha Allah. Zan je daurin aure ne gobe Gashua. Tambayarta zanyi don kada abin yazo da daukar alhaki. Wanda ta zaba sai mu duba mu kuma muga dacewar hakan. Aure ai ba'a yi masa garaje. Rashin karasa karbar kudin wancan karon ma daga Allah ne."

"Shikenan Alhaji, Allah Ya zaba mata mafi alkhairi." Daga nan suka yi sallama Kawu Garzali ya tashi ya tafi.
*****

Inna mahaifiyar Qasim ce ta saka shi a gaba suna magana akan aurensa.
"Baffanka yace sunyi magana da Alhaji Adamu yace a dan kara musu lokaci zasu sanar da ranar da za'aje kai kudi"

"Eh munyi maganar. Dama Asmau nace ta fada musu da farko to ashe ma Baffa ya kira shi"

Rai a bace Inna tace "yanzu ita Asmaun har sai an bukaci lokaci kafin ace an yarda a kai kudin? Naga dai ita ce ma me abin bincike a kanta. Yarinyar da ta bar gidansu tsahon shekara biyar."

Murmushi kawai yayi. Inna bata son auren nan nasa duk irin yadda zaiyi mata bayani tace su rayuwarsu ba irin ta birni bace. A nan duk wanda yaji Asmau tana da 'ya sai ya tambaya mijinta rasuwa yayi ko sakinta yayi. Wasu ma suyi ta cewa mai zai sa Qasim ya fara da auren bazawara. Babu yadda za'ayi su boye gaskiyar lamari. Wasu ma sun dade  da sanin rasuwar abokin Qasim da cikin da yayiwa budurwarsa. Gulma da kananan maganganu sai yawo suke. Ko kadan Inna bata jin dadin hakan duk da tana kokarin yiwa Malam biyayya ta nuna ta amince da auren.
"Sai anyi magana kayi ta murmushi kamar wani bazawari. Ya dai kamata kafin komai ya kankama kuje ayi mata gwajin 'yan cututtukan nan na zamani musamman kanjamau"

"Inna ba fa karuwanci taje tayi ba. Aikin asibiti tayi duk tsahon lokacin nan"

Tabe baki tayi "haka dai ta fada muku ku kuma kuka hau kuka zauna. Mace babu mai kwabarta ai sai ta mike kafa. Ni dai ba wani abu nace ba. Ayi mata gwaji ko don taka lafiyar. Gurbacewa ce dai ka gama gurbata mana dangi. Ko me kuka haifa nan gaba sai ance yayarsu shegiya ce"

Har ransa Qasim baiji dadi ba. Innarsa ta lura da yadda ya hade rai tayi murmushi "Baba kenan, kada ka daukeni muguwar uwa wadda bata son danta yayi aikin neman lada. Duk wata uwa komai shedancin danta tana son ya auri mace tagari. Abubuwan da kaga suna ta faruwa da yarinyar nab kadan ne daga *abinda ake gudu* a zina. Bana muku fata amma wata rana idan kunyi aure zata iya yin abu da zuciya daya amma saboda sanin da kayi na rayuwarta  ta baya kawai sai shaidan ya kitsa maka zargi ka hau kai ka zauna. Karuwai da yawa sun yi aure. Wasu ma a gidan mijin suke sheke ayarsu. An sani amma da yake aure rai gareshi sai kaga ba'a sake su ba. Kasan halina bana boye abinda yake raina. Idan ka auri Asmau kayi mata halacci kuma ka rike amanar abokinka. Ka gyara abinda ya bata. Sai dai bazan fasa nanata maka ba ina so ka kara aure a gaba."

Duk maganar Inna yasan gaskiya ne. Idan Asmau zata taba mantawa da juyin da rayuwarta ta samu sai dai idan an goge wannan bakar ranar da tayi sanadiyar tarwatsa mata rayuwa.
"Akwai wadda kike so na aura ne? Da niyata bazan kara aure ba bayanta."

"Yo dan nan kasan me gobe zata haifar ne da zaka ce haka? Zabin wata matar yana daga gareka don kada ma a sami matsala nan gaba kace nice na zabo matar. Bari na shiga wurin Malam naga la'asar ta kusa"

Da Inna ta tashi Qasim dogon tunani ya zauna yi game da auren Asmau da ya takurawa kansa lallai sai yayi. Burinsa ya kyautata rayuwarta ba ya zama sanadiyar kunci da bacin ranta ba. A yadda ya fahimci hirarta da Col. Ishaq kwanakin baya ba karamin so suke yiwa juna ba. Addua ya rinka karantowa a zuciyarsa
"Ya Allah, na sani ina daga cikin mutanen da suka batawa Asmau da Abubakar rayuwa. Allah Ka yafe mana baki daya. Ka zaba mata miji nagari tsakanina da Ishaq. Idan aurenta ba alkhairi bane garemu Ka kaita gidan da za'a so ta dominKa."

Tashi yayi yayi shirin masallaci. Yana ganin janyewa kawai zaiyi amma zai tsaya mata sosai idan ta tashi aure. Dole mijin da zata aura ya kasance mutum da za'a iya yarda dashi. Mai amana. Shi kadai yayi murmushi da ya tuno irin kalaman da Col.Ishaq yake fadawa Asmau. Hmmm dole ta so shi ma. Shi kam ya manta rabonsa da tsara mace irin haka. Tun zamanin yana Qasim mai shafe 'yan mata. Rasuwar Abubakar tasa duk tunanin soyayya ya fice masa a rai. Kila harda rashin wannan yasa Asmau bata sauraron shi sosai. Mata da son soyayya kuma....
*****

Haj Lubabatu ke faman fifita an dauke wuta saboda hadarin da ya hado. Ta kira Bilkisu da ke zaune wurin taga tana ganin haske tana karanta littafinta na makaranta saboda test da zatayi washegari.
"Bilkisu ina babanki ne? Na zata ya dawo amma naji shi shiru tun dazu."

"Ya dawo Hajiya, na kai masa abinci ma"

"Duba min kiga me yake yi a ciki tun dazu. Kwanakin nan sai kace wata amarya bashi da aiki sai zaman daki"

Dariya Bilkisu tayi "Hajiya ita amarya zaman daki take yi?"

"Ban sani ba. Wuce ki duba ga magariba ta kawo kai."

Da sallama Bilkisu ta shiga dakin. Duhu ta gani duk labulayen a sauke ga zafi. Daga kan gadon ta hango shi a kwance ya rike kansa. Saurin karasawa tayi bakin gadon
"Uncle Ishaq" ta kira shi a hankali.

Da kyar Col. Ishaq ya iya bude idanunsa. Kansa ke masa wani azababben ciwo kamar zai tsage. Kwana uku kenan yana fama amma na yau yafi tsanani.
"Uncle baka da lafiya ne, bari na fadawa Hajiya."

Ta tashi zata fita wayarsa tayi ringing. Bata yi niyar dauka ba sai da yace "dauki wayar nan Safiyya ce take kira tun dazu. Idan kin amsa ki kasheta kawai. Ga dayar can a kusa da tv itama ki kashe"

Muryarsa da kyar take fita. Hankalin Bilkisu a tashe ta dauki wayar ta fita. Karawa tayi a kunnenta tace "Anti Safiyya bashi da lafiya Uncle din. Kamar ciwon kan nan da yake na bari..."

Gaban Asmau ne yayi mugun faduwa. Baki na rawa tace "Bilkisu nice Asmau. Tun yaushe ne bashi da lafiyar?"

Dan sauke wayar Bilkisu tayi daga kunnenta ta duba sunan. MJ ta gani wanda ta gane yana nufin Matar Jikamshi saboda ta taba ji Uncle din nata ya fada.
"Anti Asmau yi hakuri ban san kece ba. Yanzu na shiga dakinsa na ganshi a kwance. Zan fadawa Hajiya ne ko za'a kai shi asibiti. Dama yana yi idan baya samun hutu sosai."

Idanunta har sun ciko da kwalla , duk abinda tayi niyar fada masa na bacin rai tuni ta manta. Sake rike wayar tayi da kyau tace " Bilkisu don Allah ki kai masa wayar kinji."

Ta san baya son komai idan yana wannan ciwon musamman surutu. Amma kuma bazata iya cewa Asmau a'a ba. Juyawa tayi ta koma dakin. Yana nan inda ta barshi a kwance ta dan kara masa wayar a kunnensa tayi saurin fita kafin yayi mata fada.

Asmau ji tayi kamar tayi tsuntsuwa ta ganta tare dashi. Allah sarki Jikamshinta. Ashe bashi da lafiya shiyasa kwana biyu ta dena jinsa. Haushin kanta taji da har da tayi niyar nuna masa fushinta saboda baya kiranta kuma baije gidansu ba.

Yanayin canjin numfashin da take iya ji yasa ta gane an bashi wayar. Mamakin karfin halin Bilkisu yake da ta kawo masa a halin da yake ciki. Bari ya warke zata fada musu. Rashin Asmau yasa shi shiga damuwa sai yayi ta dadewa wurin aiki. Hakan ya tayar masa da ciwon kai. Sai kuma ga text da tayi tana fada masa yadda suka yi da Qasim akan zasu sake turowa. Tsabar kishi ne da rashin sanin me ya kamata yayi ya kara kwantar dashi. Kamar ba soja ba ya kasa daurewa zuciyarsa yaje ya fada mata ya janye. Dena kiranta a waya din ma ba karamin juriya yayi ba.

Muryarta mai sanyi yaji tace "Jikamshina me ya sameka?"

Bugawa zuciyarsa tayi da karfi da yaji muryarta babu zato babu tsammani. Ba karamin dadi yaji ba ya ratsa shi har ya dan manta da ciwon kan na 'yan dakiku. Bai iya ce mata komai ba sai manna wayar da ya sake yi a kunnensa. Ita kuma ta sake rudewa ko ciwon yayi tsanani ne
"Jikamshina nice, matarka ce, kayi min magana don Allah."

Shiru da ta cigaba da ji ne ya sakata kuka. Dama kullum haka take kamar tana jiran kiris.

Kukan nata murmushi ya saka shi babu shiru. Idon kuka kenan ya fada a ransa kamar yadda yaji a gidansu.
"Its ok ki dena kukan"

Cikin shagwaba tace "Kaji sauki? Ina da ina ke yi maka ciwo? Me yasa baka fada min ba kawai naji ka shiru"

Ta so saka shi dariya yadda yake jin muryarta a hankali amma tana rawa alamun kukan nata bai kare ba
"I miss you too" taji yace a wahale saboda ciwo.

"Uhmm?"

"Duk wannan tambayoyin nan nasan abinda kike son cewa kenan. Kinyi missing dina. But I miss you more Matar Jikamshi. Kin hana Ishaq sukuni."

Jin kanta take kamar anyi mata wani babban albishir da taji muryarsa har ya fara tsokana yadda ya saba. Ta kara kashe murya
"Nima ka hana ni. Har dan wuya nayi. Kasa naji ina kara ....uhmm....na fasa fada"

Sautin dariyarsa taji. Dama Asmau ce ciwon kuma ita ce maganin. Ajiyar zuciya yayi yana gyara kwanciya
"Yanzu ina kwance babu lafiya ma sai kinja min rai. Ki tausayawa patient."

"Kasha magani ne?"

"No, muryarki kadai ta isheni magani. Yau ki shirya zamuyi ta waya har sai kunnenki ya gaji"

Kamar yana gabanta tayi dan fari da ido "bana fatan gajiya da kai Jikamshina. Baban Ama _da kannenta_"

Yaji dadin furucinta amma kalmar karshe ta dawo masa da tunanin da yake addabar zuciyarsa.
"Matar Jikamshi ina son ganinki. Akwai magana mai mahimmanci da zamuyi kinji"

Tunanin maganar aurensu ne yazo mata tace "to Allah Ya kaimu. Ka bari sai kaji sauki sosai. Dama duk na damu ne da naji ka shiru."

"Ki kular min da kanki." Ya iya cewa zuciyarsa babu dadi ya ajiye wayar.

Motsi yaji a wurin kofa ya juya. Hajiya ce a tsaye bai san tun yaushe take a wurin ba. Abin mamaki sai yaji 'yar kunya kadan ba da yawa ba. Itama basarwa tayi ta shigo ciki kamar bata ji komai ba.
"Zaka je asibitin ko kaji sauki? Ni a yadda Bilkisu ta fada min na zata ciwon sosai ya kamaka"

"Sosai ne mana Hajiya. Kamar kan zai tsage haka nake ji"

Tayi dan murmushi kawai "ai naga kamar ka sami magani."

Dariya ta bashi ya tashi zaiyi alwala. Fita tayi tace idan anyi magriba lallai yaje asibiti don tasan ciwon kan baya masa da wasa.
*****

Bayan isha Asmau da Amatullah suna gwada sabon dinkinsu da Yassar ya karbo musu taji waya. Ringtone din Jikamshi daban yake shiyasa ta gane shi. Da fara'a ta dauka don tun wayarsu ta dazu hatta su Umma sun ga canji a tare da ita. Kafin tayi magana yace "fito ina jiranki"

Har wani faduwar gaba taji. Tayi kewarsa sosai amma tana jin kunyar hada ido dashi kuma. A waya ta iya nuna masa soyayya sai an hadu bakin ya mutu. Ga mamakin zuwansa shi da bashi da lafiya. Amatullah ta tura wurin Yassar tace ta fada masa suje babanta ya zo. Ita kuma ta zauna ta gyara fuskarta ta sami mayafi ta yafa sannan taje ta fadawa Umma. Addua tayi mata tace ta gaishe shi. Da ta fita Umma tace ashe ga dalilin sauyin da ta gani a tare da ita. Allah Yayi mata zabi mafi alkhairi. Mai son naka dole ka so shi.

Tunda ta fito daga cikin gidan yake kallonta. Samun kansa yayi da yin godiya ga Allah da ya hada jininsa da Asmau. Yarinyar akwai nutsuwa da kamala. Tana bukatar miji nagari saboda samin ingantacciyar rayuwa da nutsuwar zuciya idan aka yi laakari da kaddarar da ta fada mata. Kuma tana burge shi saboda ta karbi jarabawarta hannu biyu. Har ta iso wurin da yake zaune a gefen mota shi da Yassar da Amatullah kanta na kasa tana murmushi.

Da sallama ta karaso ta dan rissina ta gaishe shi. Ya amsa yana kare mata kallo. Tayi kyau sosai. Shi kuma ta lura ya dan fada.

"Yassar ka shigo dashi falo"

Yace "kiji min mata, ni gurgu ne?"

Ita da Yassar suka yi dariya sannan suka koma falon. Da kyar Yassar ya yiwa Amatullah wayo suka shige ciki.

Daga inda take zaune Asmau ta dan dago kai suka hada ido da Jikamshi. Karuwa sonta yake a zuciyarsa amma dole yayi abinda ya kawo shi. Tattaro duk nutsuwarsa yayi yace......
ABINDA AKE GUDU🙆🏽48

Batul Mamman💖





Ta kagu sosai taji abinda zai fada shi kuma nauyin maganar yake ji. Idan ya fada shikenan yayi musu katanga daga wannan lokacin. Ganin babu amfani yayi ta jan abin yasa yace
"Banda sunan sunan matata ta fari baki san komai game da ita ba ko"?

Asmau ta dan turo baki kishi na cinta duk da bata san matar ba.
"Ni sunan nata ma na manta. Kawai kazo bayan sama da sati daya ka fara min da hirarta"

Yadda take hade rai ya bashi dariya. Ya gyada kai  "kishi gareki haka, mun dade da rabuwa fa har ma tayi aure".

"To ai kaine sai ka rasa hirar da zaka yi sai tata"

Ya gyara zama tare da harde kafafunsa "saboda abinda zan fada miki yana da alaka da ita. Ina so ki saurareni da kyau ki fahimci abinda zan fada miki."

Hankalin Asmau ya fara tashi. Wani abu ne ya darsu a zuciyarta ta soma hawaye babu shiri tace cikin murya mai nuna rauni  "ba ma sai kace komai ba na gane abinda kake son fada. Aurenta ya mutu zaka mayar da ita ko. Babu komai zan iya zama da kishiya. Don Allah Ka kwatanta adalci a tsakaninmu" ta kare tana jan hanci.

Col. Ishaq bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Ita kuwa Asmau tayi kicin kicin da fuska. Hankici ya dauko daga aljihun wandonsa ya bata "kinci sunanki Idon kuka. Daga fara magana ji yadda fuskarki ta kumbura. Ai dai kya bari na fadi abinda ya kawoni kafin ki soma zubar da hawaye. Mata na gidan mijinta zaki kashe mata aure da baki"

Dan sanyi taji a ranta kila ba abinda zai fada ba kenan. Har tayi  murmushi sai kuma wani tunanin yazo mata "maganar aurenmu ne?"

Ya daga kai yana kallonta. Tausayinta yake ji sosai a ransa.

Murmushi tayi mai ciwo "Hajiya bata amince ka aureni ba ko? Dama nayi tunanin haka zata faru. Ba kowace uwa bace zata iya daure zuciyarta ta bari danta ya auri mace irina. Ko nice kila nayi sama da haka ma. Abinda kayi mana na kyautatawa Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai wallahi. Ko a haka  ma nagodewa Allah da Ya hadani da kai har ka nuna min so ka zama cikin masu nuna min na kara hakuri da kaddarar rayuwa"

Hawaye ke zubo mata tana magana bata ko tunanin tare shi. Dago kansa yayi daga cikin kujerar ya dan matso gaba.
"Ya Salaam, Matar Jikamshi haka kike? Lokaci daya duk kin rikita kanki. Kada ki dauki alhakin Hajiyata wallahi ta amince da aurenmu"

Jikinta duk da haka a sanyaye yake tace "sauran 'yan uwanka ne basu amince ba?"

"A duniyar nan Hajiya ce kadai zata hanani aurenki na hanu. Banda ita babu wanda ya isa. Yara kanana akeyiwa haka ba ni ba. Kamata kowa yasan ina da hankalin da zan san abinda ya dace da rayuwata. Ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada. Kamar yadda na fara magana kafin ki katseni da dan bakin nan naki mai bani shaawa..." ya fada yana kashe mata ido.

Kunya taji sosai harda rufe fuska da hannuwanta. Yayi murmushi ya cigaba da magana "na taba aure, shekarunmu shadaya da Badar babu haihuwa. Munje asibitoci da dama ana cewa bamu da matsala. Har maganin gargajiya mun sha. Daga karshe mahaifiyarta tasa na saketa kuma cikin ikon Allah a shekarar da tayi aure ta haihu"

Asmau ta dan girgiza kanta "Allah sarki, dama haihuwa ta Allah ce. Wani baya haihuwar dan wani"

Kallonta yake da mamaki kamar bata fuskanci inda ya dosa ba
"haihuwar Badar ya tabbatar min da inda matsalar take. *Matar Jikamshi, bana haihuwa*. Saboda haka kiyi hakuri da na bata miki lokaci amma na _janye maganar aure a tsakaninmu_."

Tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi haka taji saukar maganarsa ta karshe. Shiru tayi na dan lokaci yana ta kallonta yana jiran ta fara kuka sai yaga idanunta ko alamar hawaye babu banda wanda ta zubar dazu. Shirunta tsorata shi yayi yace "kice wani abu mana."

Murmushi take yi kamar bata ji abinda ya fada ba ma.
"Jikamshina"

Jiran amsarta yake na nuna masa bacin rai da bai fada mata tun da wuri ba.

"Lokacin da ka fara sona tausayina kake ji ko kuwa sona kake fisabilillah"

"I love you Asmauna, and I will always do"

Tayi sassanyar ajiyar zuciya "duk macen arziki bata da burin da ya wuce idan zatayi aure ta kai budurcinta gidan miji. Jikamshina na rasa wannan damar har abada. Na fada tarkon shaidan har ya zamana ina da shaidar da duk wanda ya kalleta bazai manta da cewa Asmau ta taba bayar da jikinta ga mutumin da babu aure a tsakaninsu ba. Ni abar gudu ce da kyama a cikin mutanenmu. Bani da sauran daraja da kima a idon jama'a sai dai kawai ayi min kara. Da wannan ciwon nake kwana nake tashi kuma dashi zan koma ga Mahaliccina. Idan aka kallemu sai an sake. Ga wadda tayi cikin shege nan. Amma duk da wannan nakasar ta rayuwata kake sona saboda Allah. Ka rike 'yar da bata da uba na aure a matsayin taka. Ka nuna min ina da sauran darajar da zaka iya zama dani. Shine yanzu zaka ce zaka barni saboda rashin haihuwa.?"

Sai da yayi tunanin haka zata iya faruwa. Ba yanzu yake jiye musu ba. Kada ayi aure hakurinta ya kare musamman da yake tana da kuruciya.
"Matar Jikamshi, haihuwa ba abin wasa bace nakasa ce mai girma. rashinta ya kashe aure da yawa. Ya bata soyayyar shekaru da dama. Ya hana zaman lafiya tsakanin kishoyoyi"

Innalillahi wa inna ilahi rajiun take karantawa tun da ya fadi  maganar don ta sami kwarin gwiwar magana. Kada tayi kuka ya tursasa mata amincewa da bukatarsa.
"Sayar da jiki a waje ko haihuwa babu aure shine babbar nakasa a rayuwar musulmi. Amma rashin haihuwa ta sunna ba nakasa bace. Jarabawa ce daga Allah Madaukakin sarki. Shi kadai Yasan ladan da Ya tanadarwa masu hakuri da rashi. Ita fa aba ce da duk kudin duniya bazai siyeta ba kuma marasa ita su kadai suka san halin da zukatansu ke ciki sai Allah. Amma mutuncina da ba fin karfi akayi min ba wurin rabani dashi kaga bani da uzuri. Taka jarabawar kenan, hakuri da ita sai yasa Allah Ya yafe maka dukkan zubunanka Ya baka aljannah. Ni kuwa fa? Ni na jawowa kaina. Bani da masaniya Allah Ya yafe min ko kuwa...."

Sai yanzu ta soma kuka mai cin rai. Wayyo Allah son zuciya. Babu wanda yayi musu dole ita da Abubakar suka biyewa shaidan. A rayuwa bazata taba manta groups da ake hira ko litattafan da ake rubutawa ba masu sanya mace budurwa taji bukatar namiji, mai aure idan mijinta na nesa taji ta kasa hakuri. Duk su biyun idan shaidan na kusa ga kaddara sai su fada ga halaka. 'Yan mata nawa ne a sanadiyar karamce karance irin wannan suke burin samarinsu su dan taba wani bangare na jikinsu ko don su rage musu shaawa? Da yawansu sun koshi da tarbiya kuma suna kokarin kamewa. Rana daya tsautsayi zai sa suci karo da irin wadannan masu yada alfashar shikenan komai nasu sai ya lalace.

Col. Ishaq ji yake kamar ya tayata kuka. Tausayi tare da son Asmau ke karuwa a zuciyarsa. Bude baki yayi zaiyi mata magana ta riga shi
"Jikamshina idan kaki aurena saboda rashin haihuwarka ka cutar dani kuma ka raina son da nake maka. Idan so kake ka rabu dani saboda Allah zanyi hakuri. Amma idan wannan ne dalilinka to ka sani *wallahi*  bazan taba rabuwa da kai ba. Har zaka iya son auren mace irina sai nice kake tunanin zan gujeka"

Dafe kansa yayi saboda ta daure shi da zantukanta. Ya kara yarda Asmau mace ce tagari wadda kaddara ta gifta mata. Yana jin kukanta har ransa. Saukowa yayi daga kan kujerar da yake ya zauna a kasa dan nesa kadan da ita.
"Look at me please"

Babu musu ta dago kanta. Wannan idan su Umma suka ganta sai a zata wani mugun abin yayi mata ai.
"Har mamaki nake yadda kika shiga zuciyata Matar Jikamshi. Ban taba jin zafin so da tsoron rabuwa  kamar akanki ba. Ina tsoron muyi aure ki kasa hakuri da lalura ta. Kada son da muke wa juna ya koma zaman hakuri kawai a nan gaba. Kada kiga kamar saboda abinda ya wuce a baya dolenki ki zauna dani duk yadda nake. Kiyi tunani sosai, bani da niyar cutar dake."

Idonta cikin nasa abinda bata yi ko bisa kuskure suka hada ido tana saurin dauke nata.
"Gobe Baba yace yana son ganina kuma nasan so yake yaji wa na zaba cikinku. In sha Allah sunanka zan fada masa. Idan kaki amincewa zan hakura nasan Allah bai kaddari aurenmu ba. Amma bazanyi aure ba har abada. Bazan yarda na kara son wani ba balle na kara haduwa da irin ciwon da nake ji a zuciyata yanzu."

Tana gama magana ta tashi tayi hanyar da yasan zata kaita cikin gidan sosai. Kasa motsin kirki yayi sai daga baya ya tashi duk jikinsa babu kwari. Wannan ciwon kan ne ya sake dawo masa ya tashi jiri na dibarsa. Yana son Asmau amma yana tsoron kada Allah Ya kamashi da tauye mata hakki. Da kyar ya iya zuwa bakin motarsa. Duhu duhun da yake gani yasa ya dauko wayarsa ya kira Yassar.

Bai dade ba ya fito ya tsorata da halin da yaga Col. Ishaq. Mukullin motar ya bashi yace don Allah Ya kaishi asibiti daga nan ya ajiye shi a gida amma kada ya fadawa su Umma balle Asmau. A rude Yassar yaje yace da Umma zai raka Col. Ishaq unguwa tace to sai sun dawo.

Asmau kuwa daki ta wuce ta fada kan gado tana kuka. Bata da abinda zata sakawa Jikamshi dashi sai aure da yi masa tsantsar biyayya. Zata aure shi ta nuna masa haihuwa ba ita kadai bace aure. Ita dai tana karawa maaurata jindadi ne. Amma idan Allah Ya hanaka to bai hanaka saurin jindadin rayuwa ba. Bai hanaka lafiya da arzikin ibada ba. Ko yanzu kukanta na tsoron kada yaki amincewa ne.

Da Umma taji shiru bata fito ba tace karshenta tana can tana kuka Ishaq ya gaya mata ya fasa.
*****

Da Yassar ya kaishi gida yaso tambayarsa abinda ya faru amma ya kasa saboda yanayin da yake ciki. Sunyi sallama ya bashi kudin mota yaki karba ya tafi gida da wasiwasi.
*****

Washegari Asmau tayi wanka da wuri tana jiran zuwan Shemau da Jafar. Tun bayan asuba ta tura musu text tana rokon su zo kafin taje gidan Baba. Umma dai addua take yi mata a zuci da fatan Allah Ya kawo mafita cikin sauki. Tayi mamakin ganinsu Shemau suka ce Asmau ce ta neme su. Suma hankalinsu ya tashi.

Hajjo na bacci lokacin suka shiga dakin Umma bayan ta hada Amatullah da kayan wasa don kada ta dame su. Duk yadda sukayi da Col Ishaq ta fada musu. Babu wanda yayi mamaki domin kuwa duk sunji komai a wurin Umma. Maganarta ta karshe ce ta dauki hankalinsu da tace shi zata cewa Baba ta amince ta aura.

Shemau tace "Asmau baki da hankali ne. Rashin haihuwa da kuruciyarki ba abu bane da ya kamata ki bari soyayya ta rufe miki ido a kai."

"Yaya Shemau ki tuna shi fa da 'yata ya ganni kuma yace yaji ya gani. A irin rayuwata ko 'ya'ya yazo dasu yanzu ai dole na hakura na aureshi tunda nima ina da ita. Duk yarinyar da ta tafka kuskure irin nawa wallahi zabinta ya zama ragagge a rayuwa. Dole idan tana son jindadi ta hakura da wasu abubuwan. Sharrin zina kenan. Yanzu ko auren mai duka nayi indai ina son rufawa kaina asiri dole na hakura na zauna dashi ko na fito duniya ta zageni ace kila ma halin da nayi a baya ya sake kamani dashi."

Umma tace "yanzu ke kina ganin zaki iya zama dashi a hakan. Bai fiye miki ba ki amincewa Qasim."

"Umma ba karamar alfarma yayi mana ba da yace yana sona. Babu wata alaqa da ta hadamu fa. Rana tsaka ya ganni kuma yace yaji ya gani duk da abinda ya faru dani. Sai nake ganin bai dace ba naki shi saboda rashin haihuwa. Abinda bashi yayiwa kansa ba. Yaya Qasim kuwa nafi alakanta da tausayinmu yake ji "

Jafar ji yayi Asmau ta burgeshi ba kadan ba. Kanwarsa ta ga rayuwa ta kuma hankalta da ita. A yanzu tasan so ba shine samu ba. Duk yadda ake son haihuwa a aure indai tana son kanta da arziki dole ne ta ajiye son ranta ta karbi abinda Allah Ya azurta dashi
"Umma ni dai ina ganin indai tana sonsa kuma ta amince da lalurarsa a barta ta aureshi. Wallahi shi da Qasim bazamu manta dasu ba har abada. Duk da sun san komai game da ita suke son aurenta. Umma mu akayiwa alfarma ba mune zamuyi musu ba. A matsayina na yayan Asmau na bawa Col. Ishaq ita har abada" ya fada da murmushi.

Shemau ma ta fahimci kanwarta yanzu ta kai masa duka a baya "to sannu waliyyin Asmau. Ai dai akwai manya gaba da kai"

Nasiha mai ratsa jiki Umma tayi mata tare da bata goyon baya. A karshe tace "bamu ba wasu ma zasu hankalta idan suka ji labarin rayuwarki Asmau. Auren Ishaq zai iya rage miki gori da surutan mutane saboda  wasu zasu ga kema kinyi masa hallaci. Shi Qasim sai a bashi hakuri tare da godiya domin ba karamin mutuntamu yayi ba.  Allah Yayi muku albarka. Allah Ya kara kare mana zuria daga fadawa ga tarkon shaidan Ya yafe mana kurakuranmu baki daya."

"Amin" suka amsa su uku. Bayan azahar kuwa da Asmau taje gidan Baba bata yi nauyin baki ba ta sanar dashi wanda ta amince wa. Sai da yayi ta tambayarta zata iya zama dashi babu haihuwa. Amsarta ko sau daya bata canja ba tace eh. Addua yayi mata shima da fatan alkhairi. Da rayuwarta bata zama yadda take yanzu ba bazasu yarda da wannan aure ba. To amma yanzu sun san cewa ba karamin arziki Allah Yayi musu ba da ya bata manemi kamar Col. Ishaq Muhammad Jikamshi. Zai rufa mata asiri itama ta rufa masa. Allah Mai hikima ne kuma Masani akan komai. Zuwa Shanono ya kama shi dole zai je yasan irin dabarun da zaiyi a warware maganar Qasim batare da zumunci ya sami rauni ba.
*****

Su Asmau na zaune a tsakar gidan Kawu Garzali suna hira ta dauki waya ta turawa Jikamshi text.

_Na zabi Jikamshina a matsayin miji. Na yarda na bashi amanar sauran rayuwata. Na amince babu wanda nake so sai shi kadai. Ina fata zaka amince ka karbi soyayyata. Kuma ina so ka sani cewa ba tausayinka nake ji  ko auren alfarma nake nema ba. So ne kawai, Matar Jikamshi sai da Jikamshinta_
*****

Zaune yake gaban Hajiya tana yi masa nasiha saboda damuwa da tayi masa yawa yaji shigowar text din. Yana karantawa ya dago kai ya kalli Hajiyarsa yana murmushi mai burgewa "Hajiya ki fadawa su Kawu su shirya zuwa nema min auren Asmau"
ABINDA AKE GUDU🙆🏽49

Batul Mamman💖





Bayan tayi text din duk da hira suke mintuna kadan sai ta duba wayar ko ya aiko mata da reply. Ganin babu bai sa taji komai ba. Naci zata kafa masa har sai ya amince don dole. Wannan shine abinda ta yankewa kanta zata yi masa. Haka kawai bazata bari Jikamshinta ya kasance cikin bacin rai da sadaukarwa ba shi kadai saboda wata lalura da bai isa ya yayewa kansa ba. Wani guntun murmushi tayi ta sake daukan waya. Kafin ta fara rubuta text din taji an kwashe mata da dariya. Shemau da su Sabira ne a wurin. Asmau ta dago kai tana kallonsu. Maijego Zubaida da Ainau shayar da yaransu suke amma suna tayawa wurin yi mata dariya. Ta dan ware ido
"Me aka yi?"

Sabira tace "me kuwa akayi banda kallonki da muke yi. Gaskiya wannan sojan ya cancanci a kira shi da gwarzon namiji."

Ainau ta amshe "ai baku ga komai ba ma. Sai suna tare wallahi, abin sai ya baki shaawa. Shiyasa tuni na canja takuna wurin Yaya Umar. Muma mun zama Laila Majnu"

"Lallai yaran nan kun koshi, a gaban nawa ko" Shemau ta fada amma fuskarta a sake.

Sai yanzu Asmau ta gano wai da ita suke dariyar. Ta murmusa "to me nayi yanzu"

Wannan karon Zubaida ce tayi magana "ke kadai kike ta kallon waya kina murmushi kamar yana kusa dake. Don Allah a bawa Qasim hakuri idan ya rabaku karshenta ku kamu da ciwon zuciya."

Aka sake yin dariya. Shemau tace "da dai Asmau akwai kunya amma yanzu sai a hankali. Akan _Jikamshinta_bata gane su waye a kusa. Allah Ya kaimu lokacin buki a kaiki tun asuba kafin mu laluba muji amarya ta kai kanta.

Suna dariya Asmau ta turo baki "amma kun gama dani wallahi. Kuma har yanzu da kunyata fa. Daga yau na dena magana ma"

Sabira tace "Yi abinki Asmau, idan mutum na sonka kaima ka nuna masa baka da tamkarsa. Bari nima na kira Abban Abid mu dan taba hira. Yau tunda muka fito banji muryarsa ba" sai da ta gama magana ta tuna da Shemau. Tashi tayi da gudu ta shige daki. Tsakar gidan kuwa sai dariyar su Asmau.

Sai yamma suka tashi tafiya gida. Hankalinta kwance kamar an cire mata dutse a zuciyarta. Duk da bata ga amsarsa ba ta gama yanke shawarar jurewa har sai ta shawo kansa ya amince. Ainau da Shemau tare suka tafi. Ita kuma ta bi Jafar da yazo daukar Sabira suka ajiyeta a gida.

A bayan motar tana zaune da waya a hannu Amatullah tana wasa da Abid. Text din da bata sami damar yi ba dazu ta rubuta ta tura masa.

_Don Allah kace kana sona....zanyi kuka fa._

Daga bakin gate suka sauka don lokacin har anyi magariba suna hanya. Tana tura gate din ta ga wata bakuwar mota a kusa da ta Umma. Bata damu da sanin mai motar ba ta shiga ciki tana sauri taje tayi sallah. Amatullah tace "Ummina muyi yige yigen shiga falo"

Ta bi 'yarta da murmushi "idan na riga me zaki bani?"

"Zan siya miki mota idan na giyma. Kuma zan kaiki Makkah da Madina"

"Idan kuma kika rigani me kike so?"

Amatullah tayi dariya harda alamar tunani "zaki goyani yau har nayi bacci."

"Kin girma fa Ama ga nauyi"

"to bazan ci abinci daye ba. Don Allah Ummi ki goyani" ta karashe da buga kafa.

Asmau tace "naji shirya 1, 2....." kafin ta kai 3 Amatullah ta kwasa a guje. Dariya tayi kawai tabi bayanta. Yarinya sai son goyo bata san ta girma ba. Kyaleta tayi sai da ta kusa shiga sannan ta bita da gudu. Tana sane ta bari ta rigata.

Da dariyarsu shiga falon Amatullah tana cewa ta riga. Asmau ma ta shigo da dariya sai tayi turus daga bakin kofa. Kamshin turarensa ta fara ji kafin idanunta su sauka akan Jikamshi. Shadda ce ruwan kasa a jikinsa ga hula tayi masa kyau. Ganinsa tayi kamar an kara masa girma, ya gyara sajensa da gashin baki. Shima din ita yake kallo sai da suka hada ido tayi saurin sauke kanta a kunyace. Ko kadan bata yi tsammanin ganinsa a gidansu ba. Balle da taji shiru bai amsa sakonninta ta hanyar waya ko text ba.

Dan gyaran murya taji sannan aka ce "muna kusa fa" ta  kalli wurin da sautin ya fito. Subhanallah...
Umma, Hajjo da Ismail ne zaune a wurin.  Daburcewa tayi gabadaya tace "uhmm sauri nake banyi sallar magariba ba."

Bata jira amsar kowa ba ta shige ciki gabanta na tsananta bugu. Tana jiyo dariyar Ismail din yana tsokanar yayansa.
*****

Bandaki ta fada ta watsa ruwa da sauri tayi alwala. Sai da tayi sallah sannan ta koma gaban madubi ta shafa mai da gyara fuska. Ba kwalliya ta tsananta ba amma tayi kyau. Ta rasa kayan da zata saka kada su Umma suce kwalliya tayi saboda ganin Jikamshi. Sannan kuma bata son mayar da na jikinta don a gaskiya tayi suyar nama dasu. Karshe wata jallabiya ta dauko baka mai adon duwatsu pink. Tana son rigar sosai, Anti Bintu ce ta siya mata da taje Zaria. Mayafin rigar tasa tayi nadi sannan ta sami wuri ta zauna tana tunanin yadda zatayi ta fita.

Umma da kanta ta shigo ta danyi murmushi ganin Asmau na kallon kasa. Allah mai iko, sai  Ya sanya musu son juna duk da lalaurar dake tattare da kowanensu. Wannan ma kadai ya ishi bawa aya. "Asmau kije ku gaisa mana kin barmu da baki kuma kinsan naki ne"

A kunyace tace "ni bansan zasu zo ba."

"Bari na sallame su to. Ina jin gaishemu suka zo gara su tafi tunda mun gaisa."

Dago kai tayi da sauri amma bata ce komai ba. Umma tayi murmushi kawai ta godewa Allah. Cikin ikonSa 'yarta ta sami farinciki a rayuwarta. "Gulma to tashi kada waccan akun ta cika su da surutu"

Sai da Asmau ta jira Umma ta bar dakin sannan ta fito falon. Da sallama ta shiga. Ai kuwa Amatullah ta gani tana ta zuba zance tana bawa Ismail labari yana biye mata suna dariya. Hajjo kuma da Jikamshi suke tasu hirar.

Tana shiga Ismail yace "yauwa ga amaryar tamu. Hajjo ke fa an sallameki. Daga yanzu duk abinda zaki fada ba ganewa zaiyi ba"

Wayyo Allah, ji tayi kamar ta juya da gudu. Ismail na tsokanarta shi kuma gogan ya wani zubo mata idanu yana kallonta yana lumshe ido kamar mai jin bacci.

"Babu inda zani, ni har akwai masu nuna min soyayya ne. Allah Ya jikan Malam amma muma a zamaninmu fa ba'a cewa komai"

Ismail yace "Allah Hajjo?"

"Hmmm kaidai bari dannan." Ta fada tana jinjina kai. Yau fa tunda ta tuno Malam to wanda bai sanshi ba zai sha labari. Allah Sarki Malam Yahya. Hajjo baki shi kuma shiru shiru. Shiyasa akayi zaman lafiya duk da rigimarta.

Daurewa Asmau tayi ta gaishe su. Ismail ne kawai ya amsa, Jikamshi tashi yayi yana dubanta. "Muje na baki amsa ko"

Hajjo tace "'yan nema kuyi a gabana mana."

Da muryarar nan tasa me sa Asmau jin tafi kowa dace yace "ga Ismail nan ya fini iya hira da tsofaffi. Ni ga tawa nan." Ya nuna Asmau.

Amatullah ta taso tana kumburi "Babana kace fa yau da ni zaka yi wasa banda Ummi"

"Duk yau taki ce. Yanzu ma sako zan bata kinji princess. Zauna a wurin sabon Baba kafin na dawo"

Asmau na kallonsa ya fita. Ismail yayi mata alama da hannu tabi bayansa. Sai da tayi dariya a hankali sannan ta fita. Hajjo tace "oh, yaran zamani baku da ta ido. Wannan yayan naka Sama'ila yana wani mici mici da ido sai kafirin iya saye zuciya."

Ismail sai dariya "ko dai za'a koma da ne ki zabe shi ki bar Malam"

"A'a fa, Malam yafi kowa. Wannan alakoro ne Asmau ta samu. Ni kuwa nawa shine gangariya"
*****

Wurin motar Ismail da suka zo da ita ya kaita. Barin dreba ya bude ya nuna mata kujerar yace "zauna"

Zata tambaye shi ina zai zauna ta ga ya tafi  hanyar kofa inda wasu kujerun roba suke farare ya dauko daya. Sai a lokacin ta zauna kafafunta a waje shi kuma ya dasa kujerar daga gabanta ya zauna kafarsa daya kan daya.

Ji tayi kamar wadda aka rufe a cikin keji duk ya cike wurin. Ta kasa kwakkwaran motsi.

Wayarsa taga ya dan turo gabanta ta karanta abinda ke rubuce a ciki. Text dinta ne na biyun da ta tura masa kafin su iso gida.

"Ina sonki Matar Jikamshi, don Allah kada kiyi kuka. Hawayenki yana da tsada. Ba a gaban kowa zaki zubar dashi ba. Amsar ta gamsar dake ko na kara wata?"

Murmushin da yake so daga gareta take yi amma ta kasa dago kanta. Kunyarsa ke karuwa sosai a zuciyarta. Ga wani nishadi da take ji kamshin turaren Jikamshinta ya baibaye wurin gabadaya.

Dama yasan irin wannan kalamai sai a text. Tana ganinsa take komawa bebiya. Ranakun da take ajiye kunyarta kuwa sai taga alamun zata rasa shi ne.

"Dago kanki na baki amsar sakonki na farko. Shine babban dalilin zuwana"

Dan kadan ta iya daga kan tana sauraronsa.
"Matar Jikamshi Allah Yayi miki albarka. Bani da wata kalma da zan iya nuna miki matsayinki a zuciyata. Sakonki ya shigo a lokacin da komai ya rikice min. Haduwata dake zuwa yau hadi ne daga Allah. Har abada nasan cewa kinyi min abinda mata da yawa bazasu yi ba. Ni kuma saboda son kai na amince maimakon na dage na rabu dake ki auri wanda zaki haihu dashi..."

Bude baki tayi zata yi magana ya sanya yatsansa a saman lebensa "shhhh, kada kiyi magana. Text dinki yace komai. Ki barni nima na fadi nawa. Banyi miki alkawarin cewa idan munyi aure shikenan duk wani bacin rai da damuwar da kike dasu zasu kau dari bisa dari ba. Amma Matar Jikamshi zanyi kokari naga na kare hakkinki kuma na kyautata rayuwarki har karshen rayuwata. Abinda kike gudu tun farkon da na gabatar miki da soyayyata bance bazai taba faruwa ba. Kowane mutum yana da damar fadin son ransa duk da kiyaye bakin shi yafi akan fadar magana mara alkhairi. Ki sani a dangina ko naki, makota ko abokan arziki dole watarana sai anyi miki gori a gabanki ko bayan idonki wannan bani da haufi akansa. To ina so duk lokacin da aka fada miki maganar da ta shafi rayuwarki ta baya kuma bana wurin bare na kare miki ki sani cewa Ishaq yana son Asmau. Ki sakawa ranki akwai wanda zaki zo kiyi kuka a gabansa ya rarrasheki, akwai wanda yake kaunarki saboda Allah yake fatan kasancewa abokin rayuwarki har a aljannah."

Ba sai na fada ba Asmau kuka take yi sosai saboda yadda kalaman Jikamshi ke ratsata. Shi kanshi a raunane yake idan ya tuna cewa duk su biyun suna da abin fada a rayuwarsu.
"Abu na karshe Matar Jikamshi ina so don Allah kiyi hakurin zama dani. A duk lokacin da kika ji anyi haihuwa zuciyarki ta kwadaitu da son ina ma kece maijegon to ki tuna cewa samu da rashi na Allah ne. Da kudi na bayar da haihuwa da wasunmu sun sayar da komai nasu don suji kukan jariri a gidajensu. Ki godewa Allah kina da wadda zaki kalla a matsayin tsatsonki. Ni bani da wannan kuma na yarda na karbi kaddarata. Ina fatan hakurin da nake da wanda zaki zo ki tayani muyi ya zama silar samun rahmarmu a wajen Allah"

Da gaske Asmau take kuka. Abinda ake gudu ya riga ya faru. Allah Ya kara kare sauran 'yan uwa musulmi. Ji take duk duniya idan ba da Jikamshi ba bazata taba iya rayuwar aure da wani ba. Shi kanshi idonsa yayi ja amma sai ya daure yace "kinsan dai ba'a daura mana aure ba don Allah ki dena kukan nan. Nafi so ki tara shi sai ranar da idan kinyi zan daukeki na...."

Da kukan nata da jikakkiyar fuska ta dago kanta tana murmushi tare da dora hannunta irin yadda yayi a lebenta "shhhhh Jikamshina kada ka karasa ko na gudu"

Yayi murmushi "ina sane na turaki cikin motar don kada kice zaki gudu. Share hawayenki kinji Matar Jikamshi. Kada Umma ta hanani aurenki, kullum nazo sai kinyi kuka."

Tissue din gaban motar ta zara tana goge hawayen yana fada mata wuraren da kwalli ya bata. Tace zata duba madubin motar yaki yarda. Haka ta goge suna kallon juna suna dariya.

Sun danyi hira yake ce mata sunyi magana da Umma yana ganin nan da wata uku za'a saka musu rana. Umma tace akwai bikin Dijan Anti Bintu wata biyu masu zuwa wanda shima lokacin yaso ayi aurensu. Yasan kafin nan ya gama gyaran gidansa.

"yanzu da Umma kayi zancen saka rana?"

"Na lura kin mayar dani mara kunyan karshen zamani. To Ismail ne ya fada musu. Ni shiru nayi ina ta sunkuyar da kai irin yadda kike yi"

Dariya take yi wanda hakan yake sanyaya masa zuciya. Yana jindadin ganin ya faranta mata. Sun fi awa daya a wurin batare da sun san lokaci ya wuce ba. Ismail ne ya fito da Amatullah a bayansa. Haka nan Allah Ya dora masa son yarinyar nan. Shi bai ki ba wallahi Asmau tace ta bar masa ita.

Suna zuwa gaban motar Amatullah tace "Ummi kinga sabon Baba ya goyani."

Col. Ishaq ya tashi tsaye ya sauko da ita daga bayan Ismail sannan ya dorata a cinyarsa.
"Idan banyi da gaske ba naga alama zaka yi min kwacen 'ya"

"Colonel ai na gama da kai. Ka taho nan sace zuciyar Umminta da dadadan kalamai ni kuma ina nawa yakin a kanta da kayan kwadayi. A takaice dai yanzu nine baban"

Asmau ta rufe ido tace "Yaya Ismail kada muyi haka da kai"

Jikamshi yace "gara ki kira Musaddiq yaya da wannan. Shifa bai san ya girma ba. 'ya'ya biyar amma idan yana barkwanci kamar mara iyali."

"Kada ka zubar min da girma mana soja. Yanzu dai gaskiya Madam ta damu ban koma gida ba tun fitar safe. Ummin Amatullah taimaka ki sallame shi mu tafi. Don ma na fada mata Yayanta na rako zance yau da an hanani tuwon dare"

Ta fuskanci da gaske Ismail mutum ne mai barkwanci. Jikamshi ya katse mata tunani da cewa "haka suke daga shi har matar tasa. Gidansu kamar gidan wasan yara"

"Allah Sarki kace ina gaisheta"

"Fada mata da kanki dai" Ismail ya ciro wayarsa ya kira Aisha matarsa. Da gaskiyar Jikamshi kuwa don da gaske Aisha tayi ta janta da hira da wasa kamar ta santa. Karshe tayi ta jaddada mata ta rike amanar yayansu. Ita dai Asmau sai dariya kawai. Bayan sun gama wayar sukayi sallama dasu. Jikamshi kamar kada ya tafi. Ba don dare yayi ba kuma dai yakamata Ismail ya tafi gida yau da Umma sai ta koreshi da kanta.

A hanya ne ya dubi kaninsa yace "nagode Ismail da yadda kake yiwa Asmau da Amatullah "

Idonsa na kan titi yace "Colonel nine da godiya da ka yafe min maganar da nayi maka rannan. Duk da bana ganinsa amma na tabbatar shaidan ne irin masu hada fada tsakanin 'yan uwa ya murde min harshe na fadi abinda banyi niyya ba"

Murmushi dan uwan nasa yayi "zaka fara ko, kada ka damu komai ya wuce a wurina in sha Allah. Ka fadawa su Dahiru idan zasu sami lokaci karshen sati sai muje Jikamshi ayi magana dasu Kawu"
*****

Ranar Juma'a da yawancin ma'aikata ke tashi da wuri Col. Ishaq da kannensa maza suka tafi garinsu, Jikamshi a Katsina garin Dikko...Katsinawa kunya gareku ba tsoro ba. Kafin tafiyarsu dama Hajiya ta riga ta fadawa Yayanta da kuma kanin mijinta komai game da Asmau a waya. Kamar yadda yayi tsammani bai sami goyon baya sosai daga garesu ba. Wani kawunsa ma cewa yayi indai saboda rashin haihuwa ne yasa zai auri karuwa, karuwar ma mai 'ya to akwai zawarawa a gari masu yara ya zaba a cikinsu don Allah Ya aura amma kada ya gurbata musu dangi. Su da suka je yin kwana biyu basu sami dawowa ba sai litinin. Col. Ishaq sai da ya taba rashin kunya aka sami daidaito tsakaninsa da Kawunan nasa da manyan Gwaggoninsu. Daga karshe ma dai harda wa'azi da nasiha ya hada. To anyi sa'a da yake ana ganin girmanshi gashi kuma da dan abin hannunsa sai suka gama fadansu suka amince zasu taho Kano nan da sati biyu. Kamar yadda ya saba ya hadasu da alkhairi kafin ya tafi. Wannan karon harda kari don kada su bashi kunya ma.
*****

A bangaren su Asmau kuma washegarin da Jikamshi yaje gidansu Qasim yazo. Ya nuna mata ya janye batun aurensu kuma yana mata fatan alkairi a zamansu da Col. Ishaq. Taji kunya sosai tace "Yaya Qasim kayi hakuri da hukuncin da na yanke a matsayin zabin Allah. Bazan taba mantawa da abinda kayi mana ba. Duk da kaine babban abokin Yaya Abubakar amma hakan ba shine yake nufin sauran su gujemu ba. Tun ranar da ya rasu ban kara jin duriyar kowa ba sai taka. Nagode Allah Ya baka mace tagari kamilalliya."

Yayi mata murmushi "babu wata godiya mata zaki nemo min kawai."

Itama tayi murmshin ga dan hawayenta "to In sha Allahu zan nema maka kuwa"

"Kada ki dauka wannan abin zai shafi zumuncinmu Asmau. I am always here for you. Ki daukeni dan uwanki wanda zaki iya fadawa matsalolinki. Shi kuma soja tunda yayi min fin karfi ki fada masa aure bazai yiwu ba sai ya kama kafa dani."

"An gama ranka ya dade" ta fada zuciyarta wasai. Alhamdulillah dama bata so su rabu ana jin haushin juna.
ABINDA AKE GUDU🙆🏽50

Batul Mamman💖




Tun daga wannan lokacin tsakanin Matar Jikamshi da Jikamshinta wata sabuwar soyayya ke tashi da shakuwa. Duk wani labarin rayuwarsu da basu sani ba a da yanzu sun fayyacewa juna. Komai nasu abin shaawa sannan suna soyayya a tsaftace. Irin hirar nan da zata jawo budurwa da saurayi su fara sakin layi har a kai ga jin sha'awar kusantar juna sun nesanta kansu da ita. Kuma duk da haka idan kaga yadda suke sai sun burgeka. Wannan ita ce soyayya ta gaskiya. Duk wata hira mai tado sha'awa sunanta batsa kuma tana cikin jerin abubuwan da suka kusanci zina indai ba ga ma'aurata ba wanda Allah SWT  Ya umarcemu da mu nisanta kawunanmu da ita. Allah Ya kara shige mana gaba.
*****

Bayan sati biyu kamar yadda suka yi alkawari kawunnan Col. Ishaq suka zo daga Jikamshi. Haj Lubabatu ta shirya musu tarba mai kyau sai da suka ci suka koshi sannan sauran kannensa maza suka yi musu jagora zuwa gidan Umma. A nan din ma tun safe ake shirin zuwan nasu. 'Yan uwa da abokan arziki sun taro. Alh Adamu ma da tasa gayyar duk don a taru a rufawa juna asiri. Baki kam sun ga karamci kuma sun yaba. Matsalar dai itace haihuwar Asmau kafin aure. Amma tunda dan nasu yace yaji ya gani dole su bi yarima su sha kida. Dubu dari suka bada wanda yasa su Baba nuna a rage. Wani cikinsu dan tsoho yace ko kwandala bazasu rage ba. Dansu yace lallai abinda zaa bayar kenan ko sama da haka. Kawu Garzali sai murna yake. Allah Yayi Asmau zatayi aure kuma zata auri wanda yake matukar sonta. Adduarsu Allah Yasa soyayyar  ta zarce har gidan aure. Taro ya tashi cikin mutunta juna aka yi sallama suka tafi.
*****

Asmau kuwa da wuri ta fita amma ta bar Amatullah a gida. Hankalinta a kwance wannan karon kana ganinta zaka san amarya ce mai murna da dokin lokacin aurenta. Da kwatance saboda sababbin gine gine ta isa gidansu Walida tsohuwar aminiyarta. Har kofar gidan adaidaita ya kawota. Tana sauka a kofar gidan Walida ta fito daga makotansu. Hada ido suka yi sai suka tsaya kallon kallo kowacce tana zubar da hawaye. Duk su biyun abubuwa da dama suke tunawa wanda suka wargaza musu rayuwa. Asmau ce ta fara yunkurawa kafin ta karasa itama Walida ta taho cikin sauri suka rungume juna. A bakin kofar gidan suka fashe da kuka sosai suka rike da juna. Mutane kuwa sai kallonsu suke yi. Sai da suka dan nutsu Walida ta ja hannunta suka shiga ciki. Antin Walida matar babansu na zaune tana yankan farce suka shigo. Murna ganin juna suke sosai. A firgice ta tashi tana nuna Asmau.
"Wa nake gani kamar Asmau?"

Walida tace "ita ce Anti"

Ta karewa Asmau kallo sannan ta tabe baki "to ina abinda kika haifa. Ai na jima da jin labarin kin dawo Kano da dane ko 'ya ni ban rike ba. An gama yawon ta zubar an dawo gida."

Murmushi Asmau tayi, irin wadannan maganganun 'yan uwa da yawa da Jikamshinta sun fada mata dole ko taki ko taso sai tayi hakuri dasu. Kuma sanin halin Antin na kwarewa wurin rashin mutunci yasa bata dauki abin da zafi ba. Walida ma da a da tasan cewa bata shiru, idan matar nan tayi mata ramawa take suyi ta cacar baki kamar kishiyoyi shiru Asmau taga tayi. Ta kama hannunta suka shiga dakinta. Kan wata kujera suka zauna Walida tace
"Ashe rai kan ga rai 'yar uwa? Na fidda rai da sake haduwa dake wallahi"

"Kiyi hakuri Walida. Na dan jima da dawowa amma na rasa me zamu cewa juna idan muka hadu. Har ga Allah abinda ya faru dani shekarun baya kika gujeni yasa ban kara nemanki ba"

Walida ta share kwalla "ki yafe min Asmau, na cutar dake da na zama sanadiyar koya miki dabi'un da ba naki ba. Ba haka kawai na gujeki ba amma..."

Asmau tace "kada ki damu. Yaya Qasim ya fada min kema duk abinda ya faru dake. Mu kuma haka Allah Ya rubutu mana tama jarabawar" da kuka ta karashe maganar. Suka taru su biyu suna yi babu mai rarrashi. Asmau na tuna rasuwar Abubakar da cikin da aka gane tare da ita a ranar da ya rasu. Ita kuma Walida tana tuno ranar da mahaifinta ya kamata da saurayi ya zura hannuwansa cikin rigarta. Wa'iyazu billah wadannan 'yan mata bazasu manta da sharrin social media ba.

Da suka gama kukan ne suka bawa juna labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Walida tayi murna da jin zancen auren Asmau sannan tayi ta kallon hotunan Amatullah a waya tana mita ba'a zo mata da ita ba. Itama ta bawa Asmau labarin irin takunkunmin da babanta ya saka mata saboda jin labarin  cikin Asmau. Karshe ma ko karatun jami'ar bai bari ta kammala ba yace sai tayi aure. To gashi shekaru shida babu auren babu karatun sai zaman gida da zuwa islamiyya. Matar gidan ta sami yadda take so wurin fadawa Walida maganganu sai dai ta dena ramawa saboda yanzu babanta bai damu da lamarinta ba. Indai ba aure tayi ba shi baiga amfaninta ba. A wannan zaman gidan kannenta biyu 'ya'yan Anti sunyi aure har sun haihu. Bata yawo daga islamiyya sai gida sai kuma abinda ya zama dole. Samari kuwa kamar anyi ruwa an dauke. Babu mai zuwa yanzu.

Asmau tace "dukkanmu munga irin abinda ake gudu a waya da social media. Allah kara rufa mana asiri duniya da lahira."

"Amin Asmau, amma ai kinfini ganin tashin hankali. Kullum ina miki addua Allah Yasa kada rayuwarki ta lalace da kika bar gida. Da farko a social media na fara watsa hotunanki cigiya kafin Baba ya karbe wayar. Rabona da wayar arziki na manta"

Yini suka yi suna hira sai bayan laasar lokacin da Asmau ta tabbatar an gama taron gidansu tayi haramar tafiya. Jikamshi yayi mata waya yace to ta fara shiri sauran kadan fa ta karasa zama matarsa yana fatan za tayi shiri mai kyau kafin zuwan lokacin. Yaso zuwa daukarta ma da kansa amma kamar yadda suka faro da bin komai yadda ya kamata sai ya hakura. Wani lokacin ko babu social media idan budurwa da saurayi suka kebe su kadai a mota sanyin AC yana dan ratsasu sai shaidan ya fara kawo musu hari. Ko kadan babu burgewa kice wai duk inda zaki saurayinki shine yake kaiki ya dauko ki. Ki duba da kyau kiyiwa kanki adalci watarana ko dan yaya sai anyi abinda bai dace ba ko da kuwa taba hannu ne. Yau da gobe ai tafi karfin wasa.
******

A cikin wata daya Col. Ishaq ya dage sosai ana ta gyaran gidansa. Duk inda yake bukatar canji kamar kayan cikin toilet irinsu baho da sink an canza an saka komai sabo. Haka ma a kitchen da su kofa. Ga fenti sai da ya kira Asmau ta fadi irin kalar da take so. A bangarensu ma Umma ta tashi tsaye sosai. Daga Asmau yanzu babu kowa a gabanta sai Yassar. Su Shemau ne suka je suka gano gidan aka zo aka fara siyayya. Dole ita ma ta dage ta fito da 'yarta ta. Gado ma ready made ta siya guda biyu tare da sauran kayan gida. Shemau, Jafar, Kawu Garzali da gidan Mama duk ba'a barsu a baya ba. Kowa akwai abinda ya dauki nauyi don ganin cewa Asmau ta sami nutsuwa a rayuwarta. Ita kam sai son barka da yi musu addua.

Saura kwanaki biyar su tafi Zaria bikin Dijah. Umma da Anti Bintu basa zama kullum sai an fita siyayya saboda ana gama na Dijah da sati hudu za'ayi na Asmau.

Jikamshi yazo yiwa Asmau sallama tafiya ta kamashi Warri zaiyi sati uku. Zaune yake ya dora hannuwansa akan cinyarsa sannan ya tallabi fuskarsa dasu yana kallon Asmau. Kallon ya takurata tace "Jikamshina zan tashi fa idan baka dena kallona na ba"

"Tashi ki tafi ban hanaki ba. Amma ki sani zan je na sami 'yan matan Warri na kalla son raina"

A shagwabe tace "don Allah ko da wasa ka dena fadin haka. Kada kasa na kasa bacci yau"

"Shine kike son hanani baccin? Daga gobe fa zanyi sati uku ban sakaki a ido ba. Ji nake kamar a daura auren nan na tafi dake. Idan mun dawo sai ayi bikin, kada kice wani abu nasan kema haka kike so ko Matar Jikamshi" wannan lumshe idon yake mata. Ita kuwa ta soma dariya.

"Wane irin aure ne amarya da ango zasuyi tafiya bayan an dawo ayi biki."

Yace "to kawai idan mun dawo mu wuce gidanmu ko. Tsayawa bikin duk bata lokaci ne."

Dariya Asmau take yi kawai. Jikamshinta yau sai wani marairaicewa yake.
"Kada ka damu ni dama ba wani biki nake so ba. Zuwa za'ayi ayi ta kallona. Na fadawa Umma ayi komai a rana daya. Bayan daurin aure mata kadan su zo a kaini."

Col. Ishaq ya gane sarai dalilinta na yin haka. Yadda mata ke son biki amma tace bazatayi komai ba saboda surutun jamaa. Dena wasan yayi yace "Matar Jikamshi ko me kika yi na fada miki dole za'a sami masu magana. Bakiji ance Dan Adam mai wuyar gane hali ba. Idan kinyi biki ace baki da kunya ko makamancin haka, idan kin ki biki ace ko dan bikin nan batayi ba don kada mutane su je. A wurin Dan Adam bazaka taba fita ba. Saboda haka biki da akeyi abu na lokaci daya zukatan masoya suji dadi na makiya su fashe...."

Da har ta fara kwalla sai yanzu tayi dariya. Shima biye mata yayi.
"I am a soldier Matar Jikamshi. Dole nayi aure irin na sojoji. Su Safiyya suna can suna tsare tsare kamar yadda su Ainau suke yi. Zamuyi aure da biki kamar kowa kinji ko. Duk wanda ya fada miki mara dadi ki rinka tuna ranar asabar din da zaki tare a gidana. Ranar da Jikamshinki zai nuna miki matsayinki a rayuwarsa. Wannan ya isheki maganin duk wani bacin rai. Look forward to being Mrs Jikamshi a zahiri." Gyara zama yayi bayan ya gama maganar yana son ganin yanayinta. Kasa take kallo tana wannan murmushin da ta saba idan tana jin kunyarsa. Bai barta haka ba sai da ya tabbatar mata lallai bikinsu za'ayi taro kamar na kowa. Masu farinciki da 'yan saka ido kowa ana gayyatarsa. Addua zasu cigaba Allah Ya kare duk wani tashin hankali da abin ki har ayi a gama lafiya.

Da zai tafi Asmau harda kuka. Tana ta cika masa baki sati uku ba komai bane zata iya jurewa ko basu hadu ba akwai waya. Hoto ya rinka daukarta fuska a kumbure saboda kuka. Da ya shiga mota ya tayar tace "Jikamshina don Allah kada ka kalli kowace mace. Ai ni kadai na isheka ko?"

Ya murmusa "anya kuwa? A haka kinsan bazan tabbatar ba sai nan gaba. Idan rabon na hadu da kishiyar matar jikamshi ne a can sai ki tayani addua"

Ranta a bace ta zamo dankwalinta ta kasan mayafin da ta lullube kanta ta jefe shi dashi. Dariya yayi mata ya dauki dankwalin ya dora akan fuskarsa tare da rufe idanu. Muryarsa can kasa yace
"Ina son kamshinki"

Kunya taji ta mika masa hannu "don Allah ka bani"

"Haba yarinya, dama ba roka nayi ba kika bani. Yanzu kuma yazo kenan. In sha Allah ke dashi sai a gidanki. Love you, kiyi min adduar tafiya"

Tana kallo ya rataya dankwalin a wuyansa yaja mota kamar baya jin magiyar da take masa. Dafe kai tayi tana tunanin me zata ce idan aka tambayeta dankwalin. Tayi sa'a babu wanda ya kula. Kafin ta kwanta ya turo mata hotunansa ya ware dankwalin akan fuskarsa ya rungume da hannuwansa. Ranar har tayi bacci shi take tunani.

Da sassafe ta kira shi bayan sun gaisa tayi ta jero masa addu'o'in neman tsari da sa'ar tafiya. Dadi kamar me haka ya rinka ji yana saka mata albarka. Haka suka yi ta waya yana hanya har suka isa.
*****

Kwanci tashi sun je Zaria an sha biki lafiya. 'Yan uwansu na Wushishi sun zo sosai suna cewa saura zuwa Kano bikin Asmau.  Bayan an kai amarya Kaduna da suka dawo da daddare kafin su kwanta Anti Bintu ta kirata dakinta. Ita dama bata je kai amarya ba kamar yadda al'adar bahaushe take. Wata jarka karama ta dauko ta bawa Asmau.

"Ga wannan zuma ce da aka yi mata hadi mai kyau. Kullum a kalla kisha cokali biyu. Kada ki sakata a gaba kiyi ta sha da yawa. A hankali zata ratsaki." Ta hado mata da wasu kullin magani duk na sha ne. Tace da kanta ta hadasu kayan amfanin jiki ne.

Tunda ta fara bayani kan Asmau a kasa. Da farko kunya take ji daga baya sai hawaye. Anti Bintu ta rude "menene kuma Asmau?"

"Anti yanzu a matsayin budurwa fa zanyi aure amma ....."

Fadawa tayi jikin Anti Bintu ta rungumeta tana kuka. Itama ta biye mata tana kukan tana rarrashi. Umma dake bakin kofa tana jinsu itama da nata hawayen. Babu wani abu a duniya da zasu bawa Asmau ya dawo mata da budurcinta. Shi kam idan ya tafi ya tafi kenan. Shiyasa ake so mata mu kiyaye. Kada ki sayar dashi a waje wasu suci kudinki da sunan zai dawo. Halittar Allah da 'yan dabaru na mutane basa taba zama daya.

"Ki dena kuka Asmau. Shima Ishaq din yasan komai ba yaudararsa kika yi ba. Amma dole ki gyara jikinki saboda rayuwar aure zakiyi yanzu. Ki cire yawan tunani don Allah. Bashi da fa'ida. Yawan kukan nan tamkar baki godewa Allah ba da ya ni'imtaki da samun masoyi. 'Yan mata da zawarawa nawa ke kwadayin irin wannan sai gashi ke Allah Ya kawo miki don Ya saukaka miki matsalolinki na baya."

Haka ta dauki jakar da magungunan jiki a sabule. Yadda 'yan mata ke rawar kafar shan magani idan bikinsu yazo sai gashi ita jin abin take kawai wani iri. Yanzu haka za'a daura auren budurwa mai 'ya. Allah abin godiya.
*****

Sun fi sati da dawowa Kano sannan Col. Ishaq ya dawo. Yana zuwa gida wanka kawai yayi tunda yayi sallah ko abinci ya kasa nutsuwa yaci ya fice. Hajiya ta girgiza kai, Allah Ya kara hada kawunansu su zauna lafiya.

Asmau ta zauna ta hada abinci mai rai da lafiya wanda ya dace da tarbar bako. Bata taba yi masa abinci ba. Idan yazo lemo kawai take bashi da snacks saboda tana kunyar irin wannan. Yau ma Umma ce ta bawa Yassar kudi akan a siyo abubuwa na abinci yau kwadayi take ji. Tasan yau Ishaq zai dawo amma saboda kunya Asmau bazata yi yunkurin yi masa wani abu daban ba. Itama kuma hakan yafi mata. Bata taba bawa 'ya'yanta kofar idan saurayi zai zo ayi ta girke girke kamar maigida ba. Sai kaga 'ya'ya basa kunyar iyayensu. Bayan ta gama Umma tace "ki dibarwa Ishaq mana kinsan matafiyi kila yayi sha'awa." A kunyace ta diba ta ajiye masa nasa.

Da ya iso Amatullah ta dafe shi tana ta murnar ganinsa. Yayi musu tsaraba ta doya da sauran abubuwan kudancin kasarmu. Idonsa kyam a bakin kofa har Asmau ta fito. Ji yake inama dai anyi auren. Yayi kewarta sosai, ga wani haske da kyau da ta kara saboda mayuka da sabulun gyara jiki da Zubaida ta hada mata da kanta. Itama ganinsa ba karamin dadi yayi mata ba. Tana zama yace
"Yi a hankali kada na narke da wannan kallon da kike yi min"

Sam ta kasa boye murnarta shiyasa yake ta tsokanarta. Da ta gaji da kunyar ta soma ramawa. Yaci abinci ya kuma yaba da iya girkinta. Daga nan ne suka dasa hira har ta fada masa cewa ita dasu Umma zasu je Azare da Jos nan da sati daya.

"Wannan tafiyar dani za'ayi in sha Allah. Dole naje har gida na godewa mutanen da suka taimaka wurin kare min martabar iyali."

"Kuma har gidan Uwargida zamu je. Umma tace dole Zubaida ta ga mahaifiyarta"

"Tabbas uwa komai munin halinta ba'a canja mata suna. Kila kiga rabon shiriyarta ne idan taga 'yarta tayi aure har da 'ya'ya. Ki fada min da wuri ranar da aka yanke yin tafiyar sai na shirya da wuri."

Ta danyi ajiyar zuciya "Yaya Qasim ma yace zashi"

Murmushi Jikamshinta yayi "Matar Jikamshi bazan taba rabaki da Qasim ba. Ina son halayensa kuma nasan mutum ne nagari. Ko jiya munyi waya dashi. Yasan Asmau matar Jikamshi ce wannan ya isheni kwanciyar hankali. Ke dai Allah Ya kaimu muje mu dawo a fara biki "
ABINDA AKE GUDU🙆🏽51

Batul Mamman💖





Shirin tafiya sosai suke yi. Umma ta nemi Shemau da Jafar su kawo abinda ya sauwaka wanda zasu kaiwa mutanen Azare da Jos tsaraba. Duk da bata san Zulaiha ba amma ta yaba da taimakon da tayiwa Asmau. Sune suka rufawa 'yarta asiri ba don haka ba Allah kadai Yasan irin rayuwar da zata tsinci kanta a ciki yanzu.

Shemau dai katan din taliya hudu ta kawo da maggi. Shi kuma Jafar galan din mai da katan din macaroni bibbiyu. Suna zaune a falo ana ganin kayan tana saka musu albarka. Idon kuka sai da tayi sana'ar tata kafin tayi godiya. 'Yan uwanta sun rufa mata asiri. Bata san mata nawa bane irinta a duniya wadanda kyama da hantara ta dangi ta kara tura su ga aikata sabo. Umma tace "na bawa Yassar ya siyo min buhun shinkafa biyu sai a bawa su Rashida daya ita ma Zulaiha daya."

Asmau ta kara yi musu godiya "nima zan duba cikin kayan da kuka bani wanda ban dinka ba na daukar musu."

"Hakan yayi kyau" inji Hajjo "kai Yassar ina naka ne? Ka zauna sai washe baki kake yi ban ga wani abu daga gareka ba"

"Hajjo ni da ban fara aiki ba ina ni ina gudummawa. Ai ma na kyauta tunda zan tuka mota." Sai ya kara fadada murmushinsa "ashe da Yayanmu za'ayi tafiyar."

Shemau tace "haka Umma ta fada min. Ni fa har kunyar Qasim nake wallahi. Nutsuwarsa tayi yawa. Gashi dai bashi zata aura ba amma ko kadan bai bari hakan ya zama sanadiyar bacin zumunci ba"

Yassar ya dan tabe baki "au shima zuwa zaiyi? Ni da mutumina nake yallabai baban Amatullah"

Umma ta rike haba "oh ni Bara'atu, nagode Allah a namiji kazo Yassar da ina tsammanin sai kunyi fada da yayarka. A take takenka da gani zaka iya kwacen saurayi. Idan Ishaq  yazo gidan nan aka yi rashin sa'a kana nan kayi ta rawar kafa kenan. Jiya ina jin ku kana mita wai Asmau taki fitowa da wuri"

Dariya suka yi, Yassar ya sosa keya "wallahi Umma burgeni yake yi. Nifa gaskiya idan an gama bikin nan zan nemi short service nima na zama soja. Baki ga ba idan yana tafiya ko magana....kai"

Hajjo tace "anya Bara'atu kin tabbatar yaron nan namiji ne ba mata maza ba?"

Su Jafar sai dariya Yassar ya tashi yana tura baki. Shi ba'a kyauta masa ba. Yabonsa fa kawai yayi saboda ya burge Asmau. Da taga anyi masa taron dangi sai ta koma bayansa tana kare masa. Yace "rabo dasu sai sun ga matar da zan aura ma sis. Kowa sai ya yaba harda tsohuwa mai ce min mata maza" aka sake dariya.
******

Lokacin da Col. Ishaq ya fadawa Hajiya zaiyi tafiyar nan dasu Asmau ta dage itama sai taje.

"Ke da kike fama da kafa Hajiya"

"Kada kaga laifina. Ba wai na karyata abubuwan da Asmau ta fada mana bane amma ance gani ya kori ji. Kai sonta kake da aure ni kuwa son 'ya nake mata. Ina so idona ya gane min inda ta rayu kafin haduwarku. Ina son samun hujja ga mutanen da tuni suka fara kawo min sukar auren nan. Da yawa cewa suke karuwanci tayi lokacin da ta bar gidansu. Bazan tura kowa a dangi ba bare a sami na gutsiri tsoma. Kai dai kawai ka hadani da dreba idan motarka ta cika"

Ji yayi jikinsa yayi sanyi. Mutum ba'a iya masa. Mahaifiyarsa kuma da gaskiyarta. Da yana da yayye kila su zata wakilta tasan bazasu yi mata karya ba. Kuma gara taje din akan ta tura wani.
"Shikenan Hajiya Allah Ya kaimu. Bilkisu sai ta koma gidan Safiyya ko su Dahiru"

"Tare zamu je kasan rabonta da gida tun haduwarmu da Asmau. Ita ma gara taje ta kwana biyu kafin bikin tunda ta gama jarabawa"

Da ya kira Asmau ya fada mata ko kadan bata nuna damuwa ba. Har zuciyarta dadi taji ko babu komai idan akwai wani zargi da yake ransu zasu ganewa idanunsu cewa ba karya tayi ba.

Ranar da zasu tafi sammako suka yi. Yaran Shemau duka ta kawosu gidan Umma zasu zauna da Amatullah da Hajjo. Asmau da ita taso tafiya Shemau tace gara ta barta ta fara sabawa da rashin ganinta saboda idan anyi biki sai kamar bayan sati biyu ko uku za'a kawo mata ita. Ta dai amince don babu yadda zatayi ne. Basu saba rabuwa da juna ba. Wani abin ma sai sunje kwanciya  ta mayar da kanta yarinya ta biyewa Amatullah suyi ta hira tana sauraron shirmenta. Burinta ta dasawa kanta babban matsayi a zuciyar Amatullah yadda nan gaba yarinyar bazata nuna mata kyama ba idan taji tarihin haihuwarta. Soyayya kuwa zata nuna mata hadda wadda take tunanin da Abubakar yana raye shima zaiyiwa 'yarsa. Allah Sarki bai ma san da cikin ba bare haihuwarta.

Sun gama loda kayansu a motoci aka fara shiga. Asmau, Bilkisu da Zubaida suna motar Jafar da yaran Zubaidan. A motar Umma kuma kawu Garzali ne a gaba Yassar zai tuka. Baya ita da Mama ne. Shi kuma Col.Ishaq drebansa ne zai tuka su. Yana gaba a baya kuma Hajiyarsa da Shemau.

Tun zuwansu gidan ya samu Asmau ta dan fito kafin a fara shiga mota "yanzu ina kallo zamu je wuri daya amma ba motarmu daya ba? Wannan tsarin baiyi ba gaskiya ki dawo motarmu Shemau ta koma ta Jafar. Wa zan rinka satar kallo ta madubi"

Zaro ido tayi "sai na zauna kusa da Hajiya don rashin kunya kai kuma kana kallona?"

Yace "to meye a ciki? Naga auren danta zakiyi karewa."

Ta kawar da kai tana murmushi "ni dai kayi hakuri don Allah kada a fito ka fara cewa na dawo motarku. Kada ka sani jin kunyar da ban shirya ba".

"Dama kina da kunyar ne? Ana shirin tafiya kin kasa hakuri kin fito ki ganni"

Asmau ta rasa me zata ce sai bude baki kawai da tayi cikin mamaki. Shine fa yayi mata waya yana magiyar ta zo ya ganta.
Dariya yake mata don yasan ya kureta "rufe bakin kada ya makale a haka"

Ta dan juya ido "gara ya makale kowa ya huta"

"Tuba nake Matar Jikamshi, shi bakin nan naki da kike gani ba karamin mahimmanci gareshi ba. Idan ya makale an cuce ni."

Ta soma dariya ganin yadda ya kara marairaice fuska "meye amfanin bakin banda cin tuwo. Idan ya zauna a haka kaga na dena shan wahalar bude shi"

Yace "da gaske kina so na fada miki kadan daga cikin mahimmancin bakin Matar Jikamshi"

Wani jan zancen yake yana  kallonta kasa kasa. Ko baa fada ba tasan ko me zai fada karshenta sai taji kunya shiyasa ta saka hannuwanta biyu ta toshe kunnenta tana ja da baya.
"Ka barshi kawai na yafe. Wani ilimin ba sai na sani ba"

Yayi murmushi mai kyau "kaji min yarinya. To ba abinda kike tunani zan ce ba. Shiyasa nace kinfi karfina dama"

Sosai Asmau taji kunya ta koma ciki da sauri tana jiyo dariyarsa.

Yanzu da suka shiga motocinsu zasu tafi ji yake ina ma motarsu daya. Ko yaya suka juya su kama juna suna kallon junansu.
*****

A titin Zaria road suka hadu da Abdulhalim da Qasim a motar Qasim din. Daga nan suka mika sai Azare.

Tun fitowarsu Zubaida ana ta hira a mota amma jikinta yayi mugun sanyi. Ba don Umma tayi mata nasiha sosai ba ita ko kadan bata son tuna asalinta. Yanzu duk mutanen nan kowa sai ya ga a irin kazantar da ta tashi. Addua take Allah Yasa kada su je su tarar da irin tsofaffin yan tashan nan da basa tsoron Allah masu zuwa wajen Uwargida a dakin. Sai su zo suce wai banda tsufa ya fara zuwar mata duk tafi yaranta iya aiki. Wani sa'in ma idan taji kudi sosai komai kuruciyar mutum bata jin komai take bashi dama. Koda yake ina wata kunya ga mace irin wannan.

Motarsu ce a gaba Zubaida tayiwa Jafar kwatance. Su Asmau ma jiki ya mutu suka dena hirar saboda ganin yadda yanayinta ya canja. Asmau tana zancen zuci tace kada Allah Ya kawo ranar da Amatullah zata kyamaceta irin yadda Zubaida take yi a yanzu.

Gidan yana nan yadda yake ko fenti ba'a canja ba. 'Yan bakin kasuwa suna kallon abin mamaki. Motoci irin wadannan a kofar gidan Uwargida. Kuma gashi harda mata bare ace wasu kadangarun barikin ne suka zo neman 'yan matan gidan.

Asmau da Zubaida aka rasa me fara shiga. Ita Zubaida ma hawaye take yi har Kawu Garzali ya gani. Da sauri yazo ya karbi baby dinta mai suna Shuaibu suna kiransa Aiman sannan ya rike hannunta suka fara shiga. Zuciyar Asmau ta tsinke, yanzu haka Jikamshi zai shiga gidannan. Allah Yasa kada shi ko Hajiya wani yace a fasa auren.

Zuga guda suka shiga da sallamarsu. Matan a gaba maza a bayansu. Kaya ne tarkace kala kala a tsakar gidan. Wasu matan na wanki wasu suna girki. Kowacce da sabgar gabanta. Kadan a ciki Asmau ta gane. Duk barin abinda suke yo suka yi kallo ya dawo kan baki. Daga kofar dakin Uwargida Bulayi ya fito. Mutumin da ya fara kawota gidan nan. Dama can a dattijo ta san shi. Yanzu kuwa tsufa ya kara bayyana a tattare dashi. Yana kokarin zura takalmansa ne idonsa ya sauka akan Zubaida. Fuskarsa ba karamin mamaki ta nuna ba yace "Zuby???"

Ranta a dagule yake dama ta harare shi "Zubyn uwarka" a duniya yana cikin mutanen da ta tsana. Duk yarinyar da aka kawo gidan sai yayi amfani da ita kafin kasuwarta ta bude.

Maimakon ta ga bacin rai a fuskarsa sai ya washe baki cike da fara'a yace
"Shegiya ita ce kuwa, kina nan da bakinki kamar reza"

Cikin dakin ya koma da sauri har yana tuntube. Suna jin muryarsa yana kiran Uwargida tazo ga Zuby ta dawo. Zubaida ta ji muryar mahaifiyarta tana cewa "Bulayi kada kayi min wasan da zai tayar min da hawan jini"

"Yasin da gaske nake, bari na kamaki muje wajen"

Kunya ta kara kama Zubaida, yanzu haka zasu fito hannu da hannu kamar wasu mata da miji a gaban mutanen  nan masu daraja a idonta. Dukkansu kallon kofar suke zasu ga wannan Uwargidan ga wadanda basu taba ganinta ba. Bulayi ne ya fara fitowa hannunsa rike da sanda yana cewa "yi hankali da matattakalar kofar"

Rike da sanda ta fito wacce Bulayi ya daga mata daga waje yana mata jagora. Tana nan da tsayinta fuskar nan tayi wani irin dabbara dabbara saboda mayukan bleaching da taji a baya. Sanye take da tubarau baki wuluk irin na makafi. Tana mika hannu cikin iska alamar lalube tace
"Zuby kina ina?"

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zubaida bata san lokacin da ta saki hannun Kawu Garzali ba ta tafi wurin babarta tana kuka
"Mama makancewa kika yi? Wayyo Allah na, kinga ni fa jikokinki na kawo miki nayi aure. 'Ya'yana hudu. Mama ki bude ido ki gansu don Allah"

Uwargida tayi dan murmushi tana rungume da 'yarta. Hawaye ya zubo mata tana ta shafa fuskar Zubaida tace "Ashe zamu gana kafin na mutu Zubaida. Allah nagode Maka. Ina yaran? Wane dan albarkan ne ya rufa min asiri ya aureki? Kinga yadda Allah Ya mayar dani ko. Karyar karuwanci ta kare bani da wani mataimaki sai Allah sai Bulayi da bai gujeni ba"

Zubaida ta kalle shi sai taji kunyar zagin da tayi masa. A yadda taga mahaifiyarta ta kara tsufa da yankwanewa sai ta godewa Allah da Umma ta dage lallai sai tazo. Bulayi ne yace "Uwargida tare da baki take fa. Ina jin surukanta ne mu shiga daga ciki ko kuma ina zuwa dai" dakin ya koma ya dauko tabarmi gudu uku. Kamar hadin baki Qasim da Col. Ishaq suka ki zama. In da sabo tsayuwa ba komai bace wurin soja da dan sanda. Sai akayi dace kyamarsu tazo daya basa son zama a tabarmar da ta fito daga dakin matar.

Sauran dai sun zauna sannan Zubaida ta fara yi mata bayanin kowa. Yaranta kuwa sai da Uwargida tabi tana shafasu tana binsu da kiss a fuska. Manyan biyu mace da namiji dai kyankyaminsu suke. Tana yi suna gogewa duk ta yaba musu yawu. Da Zubaida tace tare suke da Asmau Uwargida ta mika hannu zata kamata. Balayi yace "Yar dabas kin canja Yasin. Jikinki duk ya murje kinyi fresh. Dama naso naga kama to kuma sai naga ta yanzu tafi ta da kyau da daukar ido."

Wani mugun kallo Col. Ishaq ya sakar masa wanda ya girgiza har hanjin cikinsa. Ba arziki yayi shiru. Asmau ta dan matsa gaba Uwargida ta kama hannunta.
"Nayi sanadiyar lalacewar 'ya'yan mutane da yawa Yar dabas, iyayenki har nan sun zo nemanki. Nagodewa Allah da baki kama sa'a kamar yadda naso ba. Hakkin wadancan shegun kadai ya isheni. Ni shaida ce akanki har kika bar gidannan namiji bai taba zuwa kofar dakinki ba. Ke kam kinji dadi 'yan uwa basu kyamaceki ba har Allah Yasa rayuwarki ta koma kan layi. Me kika haifa?

Tausayi Uwargida ta rinka basu. Asmau ta soma kuka saboda yadda ta tuna Uwargida da iya gayu duk girmanta. Yanzu kuwa sai da dauriya zaka iya zama kusa da ita saboda warin jiki. Su Umma sun gama gaisawa da Uwargida sai Haj Lubabatu ta dan yunkura zata tashi. Col. Ishaq yace "Hajiya kafar ce?"

Bata bashi amsa ba sai matsawa da tayi gaban Uwargida ta zauna kusa da Zubaida tana kare mata kallo. Kuka sosai ya kwace mata tace "Habiba"

Uwargida ta fara mika hannu inda taji kira. Rabonta da amsa wannan sunan tun ranar da ta baro garinsu. Hannunta har rawa yake tana ta mika shi ko zata kama mai kiran tace "wace ce don Allah, babu wanda yasan sunana sai 'yan garinmu"

Hajiya sai kuka ta kara shigewa kusa da Uwargida. Col. Ishaq ji yake kamar ya janyota. Me ya hadata da wannan matar. Hannuwanta duka biyu ta rike
"Lubabatu ce, Luban gidan Sarkin dorin Jikamshi"

Salati sosai Uwargida ta saka kafin ta rungume Hajiya. Babu kyama Hajiya ta rungumeta itama suka barke da kuka. Kowa sai kallosu yake. Matan gidan sun fito ganin kwaf Qasim ya daka musu tsawar da ta kidimasu suka bar wurin suna karo da juna.

Uwargida ta share majina da kasan zaninta tace "Allah mai iko, ashe zan sake ganin na gida. Luba ina Baba da Inna, ina 'yan uwana?"

Cikin kuka Hajiya tace "Liman da Inna sun dade da rasuwa. Yayarki Indo ma babu ita. Sauran 'yan uwanki duk suna nan an tara 'ya'ya da jikoki"

"Allahu Akbar, Allah Ya jikanku Baba, Allah Yasa sun yafe min kafin su rasu"

Tana kuka ta labarta musu yadda almajirin Liman yayi mata ciki ashe ma fyade ne yayi mata kuma ya gargadeta kada ta fada har ciki ya bullo. Babu uzuri ko neman ba'asi iyayenta suka tsine mata. Wannan kuskure ne babba. Yana da matukar amfani jurewa wajen kula da yara idan sunyi kuskure domin a toshe kofar gaba.  Tunda ta fiti take aikatau da ayyukan wahala domin taci abinci. A haka cikin ya bare tana yawo a gari. A wani gidan aikinta ne a Bauchi maigidan ya kuma yi mata fyade da ta fada matarsa tayi mata duka duk da lokacin shekarunta sunyi gaba don da jima tana rayuwar kunci da wahala. Maigida ya karyata kamar yadda aka saba ji. Shine da ta fito ta sami uwardaki. Bata zubar da cikin ba ta haifi Zubaida. Da girmanta ta fara sana'ar karuwanci kuma tace ta gwada rashin imani kamar yadda mutane suka gwada mata. Sai shekaru biyu da suka wuce da ta kamu da lalurar ido tayu nadamar rayuwarta. Duk matan gidan sun dena bata kudin haya ga rashin abinci. Ta kare da bawa mutane shawara da su rinka taimakawa masu raunin imani da wadanda ke cikin matsanancin hali don gujewa samuwar karin mugayen dabi'u a cikin jamaa.

Su Mama duk anyi kukan tausayin labarin Uwargida da kuma dadin handala da Asmau tayi dacen haduwa da mutane nagari. Wannan kuma zamu iya cewa harda adduar da suke yi mata ba tsinuwa ko zagi ba. A gidan aka bar Zubaida da Kawu Garzali. Sun yanke shawarar idan zasu koma Kano a tafi da ita sai a kaita Jikamshi taga 'yan uwanta ko da basa maraba da dawowarta.
*****

Daga nan gidan Rashida suka wuce. Dama tasan da zuwansu. Sada ma yana gida yana jira ga su Abba duk an zama samari. Cikin gidan aka yi musu shimfida mazan kuma suna dakin nan da Asmau ta taba zama. Tana shiga gidan sai kuka da ta tuna lokacin da ta zauna ga ciki ga rashin iyaye a kusa. A falo taga Sada ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yace
"Asmau kece kuwa?"

Tana kuka ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Sada ne mutum na farko da ya fara taimakonta a rayuwa sosai bayan Zubaida mai bata shawarar kada ta zabi gurbatacciyar rayuwa. Wurinsu Abdulhalim yaje inda aka ajiye musu kayan abinci. Sai da suka yi sallah suka ci abincin.

A ciki suma matan sallar suka yi aka ci abinci. Nan hira ta barke ana tuna baya ana kuka da dariya. Rashida tace "yakamata watarana muje kiga Yaya Tagwai fa"

Asmau tayi murmushi, Yaya Tagwai ai ta janyo mata kara shiga garari. Cikin yaran kuwa babu wanda ya tuna ta sai Abba. Sai da suka yi laasar a ranar dai suka kama hanyar Jos. Rashida da Sada sai lokacin biki zasu taho Kano.

Sun sha tafiya jiki kuma ya fada saboda zaman mota. Duka matan a gidan Mami akayi musu masauki sai gari ya waye zasu gidan Zulaiha. Asmau ta damu sosai da ita saboda dena samunta da tayi a waya. Col. Ishaq ne ya samarwa mazan masauki a cikin barikinsu na sojoji dake garin. Shi da Matarsa sai dare suka sami damar yin waya aka biya bashin soyayyar da ba'a yi ba a ranar.

Mami da yaranta sunyi kokarin karrama bakin Kano. Bilkisu sai murna anzo gida. Da safe wurin shadaya suka gama shiri aka dunguma zuwa gidan Zulaiha. Motarsu na tsayawa Asmau ta hango Humaira da karuwar roba a kanta cike da ruwa. Da sauri ta fito ta kira sunanta. Ai tuni Humaira ta saki robar ruwan ya kware a jikinta ta rugo da gudu ta dafe jikin Asmau. Sai ga kannenta suma duk ruwan suka. Yara sai murna suke suna tambayarta ina Ama. Kusan janta cikin gidan suka yi tawagarsu Umma suka biyo baya suna mamakin yadda yaran ke murna haka.

A durkushe bakin murhu tayi tozali da Zulaiha tana ta hura wuta tana tari. Tsaye a gefenta kuma Zinaru ce ta harde kafa tana masifa "malalaciyar banza, tun dazu hada wuta ya gagareki. Yanzu idan suka fito da me zasuyi wanka. Kinsan Gidado baya son ruwan sanyi...."

Zulaiha tace "Zinaru kiyi hakuri itacen ne mai danshi"

Tun a bakin kofar Asmau ta soma hawaye. Rayuwarta ta gyara ga Zulaiha cikin matsanancin kunci har yau. Duk ta kara figewa sai dan wuya kamar kazar mayu. Cikin sauri ta karasa shigowa tace "Zulaiha"

Tashi Zulaiha tayi da sauri itama ta nufo Asmau cike da murna da mamaki. Rungumar juna sukayi suna kukan yaushe gamo. Zinaru babu bakin magana saboda yadda gidan ya cika da mutanen da Asmau tazo dasu. Borin kunya ta soma da taga su Shemau na binta da mugun kallo.

"Haka ake tarbar baki kin tsareta a hanya kuna kuka. Ke Humaira maza shimfida tabarmar nan a rumfar babanku. Kai kuma Ali jeka ka taso babanku. Yau Asmaun da yake ta jira ta dawo"

Wata mace ce wadda da kadan zata girmi Humaira ta fito tana yatsina fuska.
"Hayaniyar me nake ji haka? Zinaru wannan banzar ta dafa min ruwan wankan ko kuwa?".

Zinaru ta galla mata harara zata bata musu harka. A yadda taga mutanen da shigar  Asmau tasan akwai maiko. Har ta fara nadamar barin Gidado da tayi ya auro 'yar mutumin da ya bashi shago a kasuwa.

Zulaiha sai murna take ta shimfida musu tabarma da zannuwanta wankakku biyu don babu abinda zata basu su zauna. Basu zauna ba sai tausayinta da suka rinka ji. Zulaiha tana cikin mawuyacin hali. Yaranta kaf babu mai zuwa makaranta yanzu. Duk abinda ya rage mata dashi Gidado yayi aure. Watarana ya sha giya ya bugu yayi mata duka cikin jikinta ya bare. A yanzu haka babu irin wukakancin da basa gani ita da 'ya'yanta a wurin Zinaru da amaryar Gidado. Yi sukayi kamar basa ganin su Zinaru suka shiga hirarsu da Asmau da yan uwanta.

Col. Ishaq ba karamin haushinsa yaji ba bare da ya fito yana tangadi alamun mayen jiya bai sake shi ba. Ya dubi Zulaiha da take gaishe da su Umma. Wahala ta mayar da ita wata iri. Idan za'a bashi dama daga Gidadon har uwarsa sai ya kullesu.

Zulaiha tace "Ummi kinji dadi iyayenki  sun yafe miki. Ji yadda kika koma nayi miki murna"

Hajiya ce ta ce "kema in sha Allah bazamu tafi ba sai mun hadaki da naki iyayen. Asmau ta fada mana komai game da rayuwarki"

Zibaru ta cafe "to tace muku tana bukatar taimako ne? Yarinya tana zaman auren soyayya da mijinta zaku shiga tsakani"

Qasim ya taso mata "idan baki kiyaye bakinki ba wallahi idan nasa aka rufeki babu wanda ya isa ya fito dake"

"Kaiiiiii, babar tawa kake yiwa tsawa" Gidado ya fada.

Darajar 'ya'yansa tasa duk mazan nan su Jafar, Yassar, Abdulhalim ga soja da dan sanda basu rufeshi da duka ba.

Zulaiha tana kuka tace "nasam bazasu yafe min ba. Shekarun da yawa. Kara na kaisu na zabi wannan rayuwar akan su"

Asmau tayi ta bata baki ta amince da shawararsu ta zuwa gida. Zinaru tace "idan kika fita a bakin aurenki"

Yau da Zulaiha ta sami masu tsaya mata bata ji maganar Zinaru ba tayi gaba 'ya'yanta na binta. Tana ji Zinaru tace Gidado ya sake ta. Dama me ya rage mata a auren nasa. Suna kallo duk suka fita. Zinaru tasan sun gama yawo domin kuwa korarsu zaayi daga gidan.

Zulaiha ke kwatance har suka iso bakin gate din wani makeken gida. Gida ne babba na gani a fada. Asmau tace cikin tsantsar mamaki "nan ne gidaku?"

"Nan ne Asmau" su Humaira ma duk mamaki suke wai daga nan mahaifiyarsu ta fito amma suke ganin kuncin rayuwa. Daga bakin gate kenan ma. Maigadi yayi musu iso akan cewa bakin mamanta ne. Jikinta a sanyaye suka shiga. Gidan ya kara fadi gashi ya dace da zamani.  A wurin ajiye motoci ta hango kaninta da Alhajinsu. Zuciyarta tana dar dar Alhaji na hangota ya taho wurin da suke yana kallon Zulaiha. Shekarunta sha bakwai rabonta da gida. Ana jiran aji da wacce zai tarbi yarsa.

A hankali yace "sai yau uwata? Sai yau kika iya tunawa kina da iyaye?"

Abin tausayi Zulaiha ta fada jikin mahaifinta. Saboda yadda ta kode sai ka zata wa da kanwa ne ba uba da 'ya ba. Farinciki yake ji mara misaltuwa. Allah Ya karbi adduarsa 'yarsa ta dawo. Ba karamin fushi yayi da ita ba a da amma daga baya ya hakura sai dai yayi alkawarin babu mai zuwa gareta idan bata kawo kanta gida ba. A ciki ma wurin Innarta sai murna da kukan farinciki. Ga 'ya'yanta duk aka taru ana kallonsu. Duk 'yan uwanta suka taru ana murna. Alhajinsu yayi ta godiya ga su Umma da suka dawo da ita gida. Zama suka yi ana jajanta irin wannan hali da yara ke jefa kansu a dalilin soyayya sun yarda su rabu da kowa.

Asmau da Zulaiha sun zauna suna ta mayar da zancen halin da suka tsinci kawunansu a ciki. Ta yanke shawarar nema takardarta a wurin Gidado. Ita da aure kuma sai a aljanna. Asmau tayi dariya tace "zaki yi ne tunda na sami miji kema zaki samu in sha Allah" ta bata labarin Jikamshinta da bikinsu da za'a fara nan da sati biyu. Zulaiha tace biki kam da ita za'ayi komai in sha Allah. Ranar ma a gidan Mami suka kwana washegari sai Kano ta Dabo tumbin giwa. Biki ya gabato ana ta rabon kati
ABINDA AKE GUDU🙆🏽52

Batul Mamman💖




Daga 'yan uwan Asmau har na Col. Ishaq kowa shirin biki yake yi sosai. Ita har mamaki suke bata. Hala sun manta wace ce ita suke son yi mata biki irin wannan. Mutanen da zasu zo karshenta duk 'yan kallo ne wadanda zasu tafi da ita a baki. Sake yiwa Jikamshi korafi tayi akan haka yace shi bai taba damuwa da biki ba sai yanzu. Idan suka yi abin shiru shiru a gida shine mutane zasu sami na magana ace dama ansan dole ayi abin kamar na marasa gaskiya. Yanzu kuwa biki zasuyi su nunawa duniya farincikinsu da ni'imar Allah garesu. Dama tasan tuni yabi zugar su Shemau da Ainau shiyasa batayi mamakin amsarsa ba. Kwanansu biyu da dawowa Walida tazo gidansu har ta rakata karbo dinkunanta na fitar biki. Kokari suke su ajiye komai su mayar da kawancensu na da. Bata da niyar gayyatar sauran kawayen makaranta don basu nemeta ba a baya kuma dama bata dasu da yawa. Yanzu ma bata san ina yawancinsu suke ba. Duk wadda tazo bazai wuce bawa ido hakkinsa ba. Dinkuna sunyi kyau sosai. Kayan Amatullah ma ba'a magana. Musamman da yake kayan yara akwai daukar ido. Ita da su Mimin Shemau da Nanan Kawu Garzali mai sunan Hajjo duk anko akayi musu.

A bangaren gyaran jiki da abinda ya shafi lalle kuwa takanas Nasiba yayar Abubakar tayiwa aminiyarta ta Nijar magana. Massouda kenan, matar da a Nijar din ma ji suke da ita. Taji labarin Asmau kaf a wurin kawarta kuma ta tausaya mata shiyasa tayi mata hadin kayansu masu kyau da tsada sosai don tace Asmau dole a gyarata a saya mata kima a wurin mijinta. Shi kanshi mijin wani girmansa take gani. Duk mutumin da zai iya auren mace kamar Asmau lallai ya cancanci yabo da jinjina. Dole a taya shi da adduar Allah Ya saka masa da alkhairi bisa wannan kyakkyawan aiki da yayi. A wannan lokacin idan kaga Asmau zaka so sake kallonta. Duk da dama can ita bata sahun farare amma fatarta ta kara kyau sosai tayi haske. Kuma duk wahalar nan ta baya da tasa ta rame yanzu cima ta canja ga kwanciyar hankali. Shiyasa jikinta ya dan dawo ta ciko. Idan Umma ta kalleta sai dai tayi godiya ga Allah. Bata ma so tayi tunanin halin da Asmau zata fada da bata hadu da mutanen kirki ba ko ta dawo gida.

A dan tsukun lokacin Col. Ishaq ya damu sosai da rashin ganin Matarsa. Massoudan Nijar ta saba da irin wannan aikin na gyaran amare ta taho har gida ta murjeki da kyau. Saboda haka gidan Umma akayi mata masauki. Safe, rana, dare daga wannan turaren sai shafa wancan abin. Sau uku yana zuwa ana ce masa bazata iya fitowa ba. Ransa a bace a karo na hudu yace da Yassar idan bata fito ba wallahi bazai tafi ba komai dare.

Yassar yayi murmushi wannan soyayya tana daukar hankalinsa sosai "ka bani dan lokaci zan fito da ita. Umma da matar da Anti Nasiba ta kawo ne basa bari ta fita. Yau kwana biyar ko kafar gidan nan bata fito ba"

Fuskarsa sam babu walwala yace "Ka fadawa matar zan kara mata kudi amma gobe tayi shirin komawa garinsu aikin ya isa haka"

Yassar ya kalli yadda yake magana kamar bashi yayi ba ya wani hade rai. Shi dai ya sosa keya ya tafi. To Col. Ishaq ba irin wanda zaiyiwa tsiya bane da ya sha tsokana.

Yana komawa dakin Anti Bintu tace "Allah sarki bawan Allah, ya tafi kuwa?"

"Ya ce komai dare zai jira a gama"

Umma ta dan sha kunu "kaje kace ina wurin ka kasa fadin sakon, haba yayi hakuri mana. Nan da kwana hudu za'a fara bikin sai ya ganta. Kema da laifinki da baki fada masa lokutan da kuke farawa ba"

Asmau ta rufe ido kawai. Ba karamin kewarsa take yi ba ita kanta. Gashi tasan abubuwa sunyi masa yawa tunda bikin ya matso amma kullum kokarinsa ya ganta ko yaji dadi. Sai ake rashin sa'a idan yazo an fara shafe shafe ko turara mata jiki. Da daga ita sai Massouda ne kawai yadda suke wasa da matar ficewa zatayi ba'a sani ba. Amma kullum ba'a rasa babba da take jin kunya.

Har Yassar ya juya Hajjo ta dakatar dashi. Tace a goge jikin ta fita "gyaran nan ai saboda shi ake yi ko. Kwana nawa kullum yazo amsa daya ai babu dadi, sai kun sa ta fita a ransa. Ko dai ku barta ta fita ko kuma naje na kawo shi har dakin nan muga karshen gyara"

Umma kunya ta kamata ta fice daga dakin su Anti Bintu suna dariya. Auduga ake tsomawa cikin ruwan wani humra mai bala'in kamshi ana goge mata jiki. Sai da aka gama tas ta zura dogon hijab akan rigar jikinta ta fita don ko kwalliya an hanata sai ranar kamu.
*****

Tayi zaton yana waje sai ta ganshi a falo yana waya ga Yassar da Amatullah suma suna zaune. Cikin nutsuwa ta shigo falon Yassar ya dauki Amatullah a wuyansa suka fice.

Col. Ishaq ko sallama baiyi ba a wayar ya kashe  yana kallonta. Ya ciri tuta a iya kallo mai kashe mata jiki. Ashe ita ma tayi missing dinsa sosai. Sai yanzu da ta ganshi taji sauki a ranta. Ko hoda babu a fuskarta kuma iya abinda yake iya gani kenan amma tayi masa kyau. Ga wani kamshi mai sanyi da bai san da yadda zai fasalta shi ba yana fitowa daga jikinta.

Kujeru biyu ne tsakanin wadda ta zauna da tashi ta gaishe shi amma da kai ya iya amsawa babu magana. Shirun nasa ya dameta tace "Jikamshina yaya, ko kayi fushi ne?"

Yayi sassanyar ajiyar zuciya "Matar Jikamshi harda muryarki ma gyarata ake yi? Tunanin nawa zan karawa matar da take gyara min ke nake. I just love the way you look. Matsalata daya ce hanani ganinki da ake yi"

Tayi murmushi "to kayi hakuri kaji _Jikamshina_ .

"Na fada miki idan zan tafi ki dena kirana da sunan nan amma kinki ji ko?"

Wani kalar tausayi yake mata tayi dariya sannan ta fara magana da shagwaba "haba Jikamshina yanzu fa na fito. Ko rabin ganinka banyi ba kake zancen tafiya"

"Kina wasa dani yarinyar nan. Nace ki dena kin cigaba. Kada kice banyi warning dinki ba dai. Bari na tafi, da na sani ban matsa sai na ganki ba yau"

Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace
"Me yasa kace haka"

Kallon da yake mata na  ido cikin ido ne yasa tayi saurin kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada miki nan gaba. I love you. Sai da safe"

Kasa amsa masa tayi tana kallonsa ya fita. Ta koma ciki duk tana jin babu dadi. To me tayi masa haka da ko minti shabiyar batayi ba da fitowa ya tafi. Ko dai yayi fushi ne da gaske? Bazata iya jurewa hakan ba kwanaki kadan kafin aurensu. Dakinsu ta koma ta dauko wayarta zata tura masa text don bata son kira yana tuki. Hakuri zata bashi idan ma tayi laifi ne. Tana dauko wayar ta ga sakonni a whatsap dinta. Idan ba 'yan gidansu dasu Rashidan Azare ba babu wanda take chatting dashi sai Jikamshinta. Budewa tayi zata tura masa text sai taga nashi ne a sama alamun yanzu ya turo sakon.

_Allah Ya kaimu ranar aurenmu Matar Jikamshi. Ranar zaki san irin matsayin da Allah Ya baki a zuciyar Ishaq. Kada ki fassara tafiyata da komai, idan na dade tare dake *kamshin matar jikamshi zaiyiwa jikamshinta illah* Ji nayi kamar na tafi dake._

Asmau ta karanta sakon yafi a kirga tana murmushi ita kadai. Ko a yanzu ace zaiyi mata kishiya ta tabbatar zuciyarta zata iya bugawa. Duk wannan kalaman nasa da iya nuna kulawa ace ya nunawa wata matar bata san inda kishi zaiyi da ita ba. Adduar son kai tayi a zuciyarta. Allah Yasa Jikamshi nata ne ita kadai....
*****

Washegari da azahar sai ga Zulaiha a Kano ita da su Humaira, Muhsin da sauran 'ya'yanta. A bakin kofa suka rungume juna suna tsalle kamar wasu yara ita da Asmau. Yara na murnar ganin Amatullah. Gida mai dadi ba Zulaiha ba hatta yaranta sun dan murmure. Kayan jikinsu kuwa ya isa ya fada maka cewa babanta wani ne. Don ko gidan Mama da Asmau take yiwa kallon arziki sosai bai kai na mahaifin Zulaiha ba. Kaddara da rabon 'ya'ya ya kaita auren Gidado. Dreba mahaifinta yasa ya kawosu tare da kanwarta itama sunanta Asmau suna kiranta Ma'u.

A tsarin bikin ranar Juma'a za'ayi Kamu da walima wanda gidan amarya ne suka dauki nauyi. Washegari asabar a daura aure sannan bayan magriba ayi Sword Crossing sai kuma ranar lahadi ayi yini a kai amarya.

Yadda su Shemau suka ci burin kawata kamun ayi biki mai kayatarwa wasu mata suka dauko masu shirya biki da duk wani abu na bikin kamar abinci da harkar decoration. Ya da kanwa ne  Aisha da Zainab Maiturare. Tunda suka ji sunan ango har ragin kudi suka yi musu sun ce ai su  kannensa ne wannan biki na yayansu ne saboda haka zasu zage damtse wurin yin abinda za'a yaba.

Rashida tazo itama da yaranta da kanwarta Harira. Yaya Tagwai ma ba'a barta a baya ba. Da ta shigo gidan harda kukata tana bawa Asmau hakuri da bata tausaya mata ba ta koreta. Sai a lokacin suka daidaita da Hajjo. Mutanen Wushishi da amarya Dijah wadda ta kafawa mijinta naci duk sun zo. Gida kam yayi albarka don ya cika da 'yan uwa da abokan arziki. Asmau gidan Jafar ta koma ita da Zulaiha. Rashida tana tare da Zubaida a nata gidan inda take kula da Uwargida. Sai bayan biki zasu je Jikamshi.

Sabira ce ta kai Asmau wani salon aka gyara mata kai gashin nan yana ta kyalli sannan aka gyara kafa da hannu. Ta kalli Sabira tace "yanzu banda iyayi har hannu ma ana gyara shi. Na zata sai masu saka farce ake yiwa"

"Ummin Amatullah yanzu gyara ai ko'ina ake yiwa. Matan da ake cewa suna kwacen miji a waje ba wata tsiya suka fimu ba sai gyaran da rashin kunya. Mu kuma Hausawa komai sai mu ce Allah Ya sauwake nayi kaza bayan kuma gidan mijinki kike"

"Kuma fa gaskiya ne, shiyasa naga Yaya Jafar indai abu ya shafeki wallahi baya kyashi ko kadan. Ashe gyara ne da sauran sirrikan da zanzo ki bani. Muma Allah Yasa mu dace"

Suka yi dariya, Sabira tace "ai dacewa dai kin gama. Wallahi ki rike baban Amatullah tsakani da Allah. Irin yadda yake sonki kadai ya isa ya nuna miki cewa Allah Yana jin adduar bayinSa. Abinda ya rage kawai ki bi duk wata hanyar kyautata masa yasan cewa shima ya auri mai sonsa."

Ummy mai salon tana mata gyara tana nade shawarar da Sabira ke bata itama zata gwada a nata gidan.
*****

Ranar da daddare Col. Ishaq ya dawo gida a gajiye saboda ya tsaya karasa wasu ayyuka kafin hutunsa na aure ya fara washegari. Har wani aiki za'a turo shi Liberia ya samu aka bawa wani. Suna magana da Mami da ta iso a ranar ne yaji waya. A zatonsa Asmau ce don yau aiki yasha masa kai tun wayar safe bai kara kiranta ba. Da ta kira ma bai ji ba sai daga baya ya gani ya aika mata da text.

Bakuwar numba ce ya dauka tare da sallama. Muryar da yaji ko bata fadi sunanta ba bazai taba mantawa da ita ba.
Badariyya...


Ko aurenta ya mutu ne????
ABINDA AKE GUDU🙆🏽53

Batul Mamman💖




Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace

"Uhmm Ishaq dama dazu  naje yini gida ne aka bani katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari"

"Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards nasan zaki ji labari"

Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan murmushi. Wayar  ma sai da ta nemi izinin mijinta dama ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki.
"Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai naji wani labari a gida da ya tada min hankali...."

Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar. Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting.
"Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko? Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi"

Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?"

Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata maganar da zata dade tana mata ciwo a rai.
"Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki gaida mijinki"

Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin Asmau kafin ya yanke muku hukunci."

"Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane baka iya ba a wurin wasu."

Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki ce sannan ta kwanta.
*****

Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba. Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan. Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu. Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi dai shine da laifi amma yafi kowa fushi.

Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai dangi ba'a canza su.

Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima ana cin amarci.

Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke. Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba.  A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi wasu daga ina suka zo.

Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce
"Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai fara'a kike yi."

Allah Yasa dreban motar ya fita sai AC da aka ware musu. Walida tace "baki ga komai ba ita da Col. Ishaq nasu salon daban yake"

Asmau tayi fari da ido kawai tana murmushi. Motar tasu mai tint ce ta waje ba'a ganinsu sun jiyo kida daga wurin bikin yana tashi ga mata suna ta shige da fice.  Wurin cike yake da sojoji masu gadi. Da farko ma taron ba'ayi niyar yi da maza ba. Sai Mami ta roka akan cewa ango zai zo da abokansa suyi hoto da amarya ya tafi. Shima da kyar ya yarda da zuwan. Shemau ce ta fada mata kalar kayan da amarya zata saka suka yi gaggawar nemawa ango wanda zai dace.

Bugu zuciyar Asmau ne ya karu da ta hango motar Jikamshinta. Wurin motoci bakwai ne suka shigo tare. Wai bikin da akace babu maza kenan. 'Yan kashe kwarkwarar ido da abokan arziki duk sun biyo shi.

Saitin motar da take Dahiru da ya tuko motarsa ya daidaita tasu yadda zasu fito tare. Ya hakimce a baya yana waya. Sai da ya gama ya fito ko'ina ya dauki kamshi.

Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar Jikamshi. Duk abinda kake so kuwa dole kaga kyaunsa. Indai haka ne Jikamshi da Asmau sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden lace ne peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali purple mara turowa akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar daurin nata da pin. Takalminta mai tsini da jaka duk kalar mayafin ne. Ango ma shaddarsa irin mayafin nata ce amma fa ba mai kyalli ba. Ga hula har wani dan karkacewa tayi. Asmau tana gama fitowa aka fara daukar hotuna kamar me. Safiyya da Shemau ne masu tsari suka jera su MC din taro S.Kilishi ita ce ta sanar da shigowar ango da amarya. Suka taho suna taku daidai. Wuri ya kaure da sowa.

_Qamshi qamshi yana tashi, 'yan mata zamu kamun amarya_

_Yaune muke shirin kamu...amarya_
_Asmau amarya zo gamu...amarya_
_Ki hakuri da zancenmu, kinsan aure yana kanmu_

Kafin mai wakar ta karaso gaban ango da amarya tuni 'yan mata sun fito ana ta rausayawa. Jajimaji kenan, idan ta bude baki ko Sangandali sai dai taja baya. Haka ta cigaba da waka har amarya da ango suka zauna.

Bayan Hajiya YBK ta bude taro da addua aka shiga biki da gaske. Su Bilkisu da tawagar gidan Hajiya Lubabatu da 'yan Jikamshi ankonsu iri daya ne da nasu Ainau. Ga su Amatullah yau anyi kwalliya itama ta fito sosai. Yaran su Shemau da nasu Sadiya 'yan uwan Abubakar kowa fa yayi kyau.

An bukaci dangin ango su fito fesawa amarya turare sai gasu mata biyar ne harda Mami kowacce da tsadadden turare a hannunta suka zo a rinka fesawa. Biki yayi biki mata sun sha rawa. A cikin taron  mata 'yan taya ango da amarya murna sun gwangwaje. Saboda yawansu ba sunan kowa zaka iya kamawa ba. Akwai su Maman Afrah, Tash, Jatma, Zahida, Mrs G, Sadiya Jegal, Ibtihal, Shukriya, Ummu Rauda, Maman Sadiq, Ummu Aslam, Mrs Ambursa, Hauwa Ag, Mum Little, Farha, Jammu, Mardiya, Shafa, Ruqayya, Tafeesu, Ummi BK, Didi, Mjay, Zahra BB, Biebie Isah, Temseey, Khadija Candy.....(wai abin da yawa ni mai rubutu naji hannuna zai tsinke nace wallahi sauran ma duk ina sonku har raina).

Taro kam ya kayatar. Anci an sha an kuma rausaya. Ana cikin daukar hotuna ne Mama Yalwa tazo zasu dauka ita da Asmau da ango. Suna hada ido da Asmau suka tuna abu daya suka fara kuka  lokaci guda. Duk wanda yasan wadannan matan yasan kukan me suke yi. Allah Ya jikan Abubakar, mutuwarsa ce tasa har aka zo rana irin wannan. Suna yi ana tayasu har su Umma. Suwaiba karamar kanwarsa ce ta iya daurewa tana basu baki. Col. Ishaq duk kishi  irin nasa ya dauke kai a yau. Abubakar wani bangare ne na rayuwar Asmau da bazai gogu ba.
Haka aka kare taron kowa ya tafi gida cikin farinciki da annashuwa. 'Yan gulma basu sami abin fada ba sai san barka domin taro ya burge kowa.
*****

Washegari sai shabiyun rana zaa daura aure. Asmau tun dare ta kasa baccin kirki. Yaushe zata manta ranar aurenta na farko da ango ya rasu. Ji tayi gabadaya bata da kuzari har gari ya waye.

Col. Ishaq kuwa jin kansa yake kamar anyi masa wani albishir mai kyau. Farar shadda ya saka harda babbar riga. Anyi mata aiki da zare ruwan goro saboda haka hularsa da takalmi harda agogon hannunsa ruwan goron ne. Masallacin Hotoro ya dauki jama'a wadanda suke son shaida wannan babbar rana. Su Jafar da Yassar suna kan gaba, ga Kawu Garzali da wani abin mamaki Kawu Rabe yazo yana ta ra6e ra6e. Bisa amincewar Hajjo da sauran 'yan uwansu Alh Adamu Matawalle shine waliyin amarya. ASP Qasim ma gayya guda yazo da ita daga abokan aiki zuwa makusantansa a Shanono. Ga su Sada suma ba'a barsu a baya ba.

Ango sai faraa yake yana gaisawa da jama'a. Har hoto suka yi da Qasim suka gaisa a mutunce. Shabiyu nayi Liman ya bukaci wakilin angon da waliyin amarya. An daura auren Col. Ishaq Muhammad Jikamshi da Asmau Shu'aib Yahya akan sadaki dubu sittin.
*****

Asmau na zaune kowa yayi wanka ana ta shirin tafiya gidan Umma inda zasu zauna saboda baki masu son ganin amarya. Tamkar wadda aka zarewa laka haka take jin jikinta. Ga faduwar gaba da ta kwana dashi. Tana kwance text ya shigo wayarta ta dauka a firgice. Kalma daya ta gani daga Jikamshi wadda ta saka ta kuka sosai.
*Alhamdulillah.*

Su Sabira suka zuba mata ido har dakin ya fara cika da su Ainau da Zulaiha suna ta tambayarta me aka yi mata. Shemau rai a bace tace "ku kyaleta tayi kukan nan. Tun daren jiya take neman yinsa. Ni nayi mamaki ma da kika jira sai yanzu. Ace mutum bashi da sana'a sai ta zubar da hawaye."

Tana kukan tace "Anti Shemau an daura fa"

La'ila ha ilallah....shine abinda Shemau ke fada tana tafa hannuwa.
"Amaryar zamani da kanta take sanar da aurenta"

Wani hawayen ne ya zubowa Asmau bata ji haushin yayarta ba tace "na zata shima mutuwa zaiyi, tun jiya gabana ke faduwa"

Jikin Shemau yayi sanyi bata san abinda ke ran kanwarta ta ba kenan taje ta rungumeta. Ainau ma ta matso ta rungumeta suka soma kuka. Sabira da Zulaiha aka bari da rarrashinsu.

Sai da suka saka Asmau yin nafila godewa Allah sannan tayi wanka ta shirya suka tafi. Shigarsu gidan ke da wuya Yassar ya shigo yace ga ango a waje zasu dauki hoto da amarya. Umma tana cikin mutane ta girgiza kai tana murmushi. Wannan ango bashi da dama. Bare an daura aure ai shikenan kuma.

Dakin da suke zaune da su Rashida Mimi taje ta kirawota. Yawanci sallah masu rakata sukeyi sai ta  nemi takwararta Ma'u ta rakata. Mayafi tasa ta rufe fuska haka suka fito. Ashe tawaga guda ce domin harda su Jafar da Qasim. Ita dai duk kunya ta isheta haka akayi hotunan ta kasa sakewa. Shima bai matsa mata ba. Ko don idon mutane ya raga mata.

Qasim tun fitowarsu idanunsa suka fada kan Ma'u. Yarinya ce kyakkyawa suna kama da Zulaiha sosai. Itama ta kula da kallon da yake mata sai ta sunkuyar da kanta cike da kunya. A take yaji wani abu a ransa game da ita. Sun gaisa da Asmau zata shiga ciki ya kalli Col. Ishaq. "Ango don Allah a bani dama zan roki amarya alfarma. Ta dan daga kai suka hada ido da Jikamshi yace "bari na matsa ga mutane can zamu gaisa. Idan kun gama sai kuyi mana jagora mu dauka dasu Hajjo"

"Godiya nake yallabai, idan tarkona ya kama zan fada maka don kune masu nema"

Col. Ishaq na matsawa Qasim ya tambayi Asmau game da Ma'u. Tayi murna sosai ta masa bayani game da ita harda bashi numbar waya. Tana tafiya wurinta ta fada mata. Ma'u tayi murmushi kawai. Asmau tace alamun nasara kenan.

Har cikin falo aka shigo da angwaye aka dauki hotuna da iyaye da kakanni sannan suka tafi.
*****

Bayan magariba aka shirya tafiya Meena event centre inda za'ayi Sword Crossing. Wasu sun saba yi ido na ganin ido amma wannan karon tsarin na dare ne. Fili suka kama ba hall ba saboda shi zai dace da irin abinda suka shirya.

Kayan Asmau na yau har sunfi na jiya. Wannan ango da kansa ya aiko mata dashi dinki kawai ta kai. Material ne light green sosai. Riga da siket aka yi mata. A bisa umarnin ango ita da Amatullah suka dinka kayan. Wani irin dauri Najah mai kwalliya tayi mata da sauran material din wanda ba'ayiwa shafi ba. Kowa sai cewa yake tafi jiya yin kyau. Komai da ta saka ya dace da kayan sai daukar ido take. Amatullah ma Najah sai da tayi mata kwalliya kada da ta dace da yara aka daukesu hoto da Umminta. Ana fara tafiya ango yazo daukar amaryarsa. Drebansa ke jan motar sai wani abokinsa a gaba. Ko kadan ba haka yaso ba amma wannan tsarin na Mami ne. Kasa dena kallon Asmau yayi tunda ta zauna. Itama yayi mata kyau sosai domin kuwa korayen kayan sojoji ne irin wanda suke sawa lokutan taro a jikinsa. Sai yau ta kara jin soja yayi. Fuskar nan tasa ya gyara saje ya kara haske da kyau. Ji yayi inama daga wurin dinner sai gidansu. Ya mika hannu mai sanye da farar safar hannu mai santsi zai riko nata da yasha lalle suka ji kukan Amatullah. Kuka harda ajiyar zuciya wai Umminta da Babanta zasu tafi su barta. Ana ta rarrashinta akan suma can zasu je yarinya taki amincewa. Col. Ishaq yace a miko masa ita. A tsakiyarsu ta zauna ta hana ruwa gudu don har suka isa wurin surutu kawai take yi. Gata a tsakiyar iyayenta duniya tayi mata dadi.

Da suka je wurin ya fara cika. Duk masu cewa zasu sword crossing dinnan kowacce ta je. Gashi dai card admit ne amma haka wurin ya cika sai san barka.

Iyaye ma ba'a barsu a baya ba. Hajjo da Yaya tagwai ma duk tsufansu sunce basu taba ganin bikin sojoji ba dole ne ayi dasu.

Tare da sauran yara aka hada Amatullah sannan MC ya sanar kowa ya zauna ango da amarya zasu shigo. Yace a zauna ne saboda a tsaye dogaye zasu karewa marasa tsaho. Duk sojojin wurin cikin uniform din occassion suke. Dole su burge mutane. Sannan babu hargitsi don biki ne na manyan kasa da kowa baya son tsokano su.

Layi ne sojoji suka yi hagu da dama mutum goma goma. Kowanne ya rike hularsa a hannu daya sannan suka hada takubbansu ta sama inda amarya da angi zasu wuce. Kida ne mai taushi yake tashi aka umarci amarya da ango da su taho su wuce. Babu masu daukar hoto ta waya don ance kowa ya zauna. Masu daukar hoto biyu ne kawai wadanda aka hayo su suke binsu. Sun zo inda zasu shiga karkashin takubban hularsa na makale a hannunsa ya lankwasa hannun damansa yayi mata alama da ta rike. Duk da tana jin kunya haka ta zura hannunta ta cikin nasa suka fara tafiya. Jama'a kuwa sai tafi har suka wuce suka zauna.

Duk taron da akayi da tsari dole ya bada sha'awa. Irin wannan taron akayi a bikin Ishaq da Asmau. Tana daga mazauninta ta hango Qasim table dinsu daya da Ma'u suna ta hira. Ta nunawa Jikamshinta yayi murmushi "Allah Yasa shima tashi Asmaun mace ce tagari kamar tawa"

"Amin" ta amsa tana 'yar dariya masu hoto suka sami na yi.

Yaya Tagwai tace da Hajjo "wai ku a bikin Kano tsufaffi basa takawa ne? Tunda muka zo kidin yara ake sakawa suna ta rawa."

Hajjo tayi dariya sosai sannan ta yafito  Yassar da hannu tace aje a saka wakar da zasu iya takawa kuma a fada filin nasu ne tsufaffi. Ango da amarya dole su sauko.

Yassar ya rinka dariya yaje ya fadi sako amma don shakiyanci wakar da yace a saka bata dace da Yaya Tagwai da Hajjo ba da sauran irinsu masu kashin kafa yayi laushi.

Sai da suka fito tsakiyar fili ga ango da amarya kawai aka soma wakar Uban Duma ta Ali Dawayya. Hajjo ta karkace itama Yaya Tagwai ta gotar da kafa daya zasu fara taku suka ji sautin yafi karfinsu. Kunnen Yassar ta jawo yace "wallahi Hajjo tsohuwar waka nace ya saka kuma ita ya saka."

'Yan taro suna ta dariya Yaya Tagwai ta gwangwaje abinta. Ango ma sai gashi yana juyi da abokai. Asmau dai kunya ta hanata rawa sai dariyar tsufaffi dake cikinta.

Iyaye ma sunyi tasu da amarya da ango asa ta turanci asa ta hausa. Da taro yazo karewa su Hajjo sunyi hanyar fita aka saka Mata ku dau turame. Dafa juna sukayi ita da Yaya Tagwai suka koma fili suka sha rawa. Su Ainau sun sha dariya kamar cikinsu zai kulle. Hajjo tace ita ba don amarya tayi ba. Dole ta taka idan aka ambaci sarki.

Sai wuraren shadaya da rabi wurin yayi saukin mutane anata tafiya gida. Col. Ishaq ya dubi Asmau wadda duk ta gama gajiya. Ga tsinin takalmi. Drebansa yace ya bashi key din mota ya bi wasu ya tafi gida. Abokinsa da suka zo tare yana wurin yace "ango duk tsiyarka fa tare zamu tafi. Naga kana sallamar dreba nasan ni zan biyo baya. Kasan  Mami...."

"Mamo ba Mami ba. Ka fita idona Captain. Wai Baraka ba tazo ba. Don Allah ka dauketa ku tafi dare yayi"

Saluting dinsa yayi yana kyakyata dariya. "Na barku lafiya angon Asmau."

A can  gefe daya kuma su Mami ke neman Bilkisu a tafi gida an rasa inda tayi. Tana can ita da Yassar a wurin wasu kujeru. Abinci yake ci yunwa ta dame shi yaji sallamarta. Har kusan kwarewa yayi don baiyi zaton ganinta ba. Tayi murmushi ta zauna a kujerar dake kallon tasa. Yassar ya ajiye cokalin yana kallonta. Tace "ci abincinka mana"

"Bazan iya ba. Ni bana iya cin abinci a gaban mutane shiyasa ma kika ganni a nan yanzu"

"Ni kuma kaga so nake kullum ka rinka ci a gabana"

Sauran abincin bakinsa ne yasa shi kwarewar da yake gudu da yaji abinda tace. Tayi masa sannu amma tarin yaki tsayawa. Da tayi magana sai ya sake yin tari.

Bilkisu ta dan harare shi "dama saboda ni kake tarin? To aiki ya sameka don bazan dena yi maka magana ba"

Yassar ya rasa me zai ce mata. Haka yake da kunyar mata tuntuni. Babu wanda zaice ga budurwarsa. Ta dan sassauta kallonsa tace "ni na gaji da kallon kallo da muke yi fa, sai yaushe zaka ce kana sona?"

Wannan karon da ya fara tari har sai da ya sauko daga kan kujera. Yana dafe da kirji tana yi masa sannu yace "ke haka danginku suke ne, basa jin kunyar magana"

Turo masa baki tayi "to ba wani bane a cikin 'yan biki yace yana sona ba. Kuma har cewa yayi zaiyiwa Uncle magana shima soja ne a karkashinsa yake"

Yassar ya ware ya koma ya zauna yana kallonta babu zancen wasa "don Allah kada ki amsa masa. Nima zanyi sojan nan har Yaya Ishaq ya karbo min takarda zanyi short service"

"Uncle Ishaq nake ce masa fa" tana magana kamar zata yi masa kuka

Duk ya rude da tayi zancen wani soja yace "to nima Uncle Ishaq kinji"

Ta juya masa ido "to kana sona kenan na sallami wancan"

Kai ya sunkuyar kasa da gaske kunyarta yake ji ya gyada kai a hankali.

"Ni da baki zaka fada"

"Kiyi hakuri zanyi miki text ko na kiraki"

Shan kunu tayi "zan cewa wancan ya turo kawai"

Yassar ya sake rudewa "me yayi zafi kiyi hakuri. Ina sonki mana ai ko ban fada ba kin sani"

Sai yanzu yaga alamu taji kunya ta rufe kuskarta da mayafi ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka kirani fa"

Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata"

Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace "Yassar"
Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba.
******

'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col. Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi. Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu. Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin yanayinta a ransa yace baki ga komai ba.

Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai biyo baya.

Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo kirjinta don tsoro.

"Tunanin me kike yi ne"

Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a salihance take fita.

"Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?"

Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya kallon bangaren da take.
"Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana cewa"

Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi.
"Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari  ko kiss ne nayi masa"

"La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya taji har bazata iya misalta ta ba.

Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta Asmau.
" ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata ni?"

Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka nace ba fa"

Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi wannan tunanin?"

Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda haka kake so nace"

"Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau."

Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan bakin ya sha janbaki
"Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun isa gida. Naga alama kin fini zumudi".

Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake hankali kwance. Tace "Jikamshina"

"Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi"

"Zan rama ne."

Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama yanzu?"

Ta gyada kai "I want to hug you"

Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka"

Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan alamun sun dawo.

Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata
"Kiyi  hakuri kiyi min magana please"

Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na baki kada ki bude kofar nan"

Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai  da ta ziro kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a hankali.
"Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki ne kice wata tayi miki tausa a kafa?"

"Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana idonta na kan kofa.

"Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi mata daukar  jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya nufi hanyar kofar gidan da ita.

Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka saukeni"

"Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni"

Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa"

"Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan bakiyi shiru ba"

Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko waye sai dai taji kunyarsa sabanin da  wani namijin ne kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke yiwa kallon burgewa.

Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba.
"Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani dazu"

Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta.

Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha"
.
Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi"

"Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta.
"Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki da kayanki gobe"

Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan mun hadu a dakinki" a goshinta yayi mata wani kiss din ya tafi ya barta a tsaye tana numfashi da kyar.

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *