Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 20 October 2018

AGOLAH Complete Hausa Novel!!!

adsense here
AGOLAH Complete Hausa Novel!!!

AGOLAH Complete Hausa Novel!!!

[5/24, 10:02 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»  AGOLAH!!!nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABIU ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)
     
SADAUKARWA!!!
 Zuwaga dukkanin yan uwa da abokan arziki, ina me nuna farincikina gareku, Allah yabar zumunci, ameen.

Bismillahir Rahmanirrahim.

Part 1.....5

Agarin kaduna, cikin unguwar Sarki. Awani katon gida, nashiga domin dauko maku labarin cikin gidan.
    Alhaji Abba Bala, hamshakin me kudine, yanada mata daya da ya,ya biyu mata, Sunan matarshi Hajiya Zarah, takasance yar garin zariya, diyace agurin Malam Garba da matarshi Asabe, kishiyar mamanta, ce, tana kiranta da inna, Asabe takasance mace me kissa, hakan yasa take zaune da Zarah tamkar ita ta haifeta, babu wanda yasan dalilinta nayin haka, talakawa ne acikin danginsu kaf Zarah ce kadai tayi sa,ar auran me kudi, dalilin haduwarsu kuwa lokacin da Alhaji Abba yaje zariya acikin unguwarsu Zarah, yaziyarci wani abokinshi, ahanyarshi ta dawowa yahadu da Zarah tadawo daga aiken da Innarta tayi mata, lokaci guda yaji yakamu da sonta, ahaka. Bayan sungaisa yanemi data nuna mashi gidansu, yayi mata godiya yatafi.

Tundaga ranar soyayya tashiga tsakaninsu, kai tsaye yanemi izinin aurenta agurin mahaifinta, babu bata lokaci ya amshi bukatarshi.
Zarah Allah yayi mata son kudi, babu abinda ta tsana irin talaka, duk da Allah yayita acikinsu amma bata son su, ko taron danginsu akeyi bata shiga, hatta da iyayenta hakuri sukeyi da ita, tasha yin mafarkin ta auri me kudi, segashi Allah ya amsa mata addu,arta tasamu me kudin, 
   Zarah bata damu da ilimin addini ba, ko sallah bata damu dayiba, amma tunda suka hadu da Alh, Abba taboye duk wani halinta marar kyau, shi kuma duk farin ciki ya isheshi yasamu diyar gidan mutunci, duk da azahiri iyayenta suna da mutunci amma bata gado suba.

Ahaka akayi aurensu, aka kaita kaduna cikin unguwar sarki akaton gidanta, haka suka cigaba da rayuwarsu cike da so da kauna, hankalinta ya kwanta, arzikin mijinta se karuwa yakeyi, hutu ya zauna mata tuni fatarta, ta murje tayi kyau sosai, tuni ta manta da iyayenta da danginta, tunda akayi bikin bata zuwa garinsu sosai, sede idan mijinta ya matsa mata, shima sede suje tare kuma bazata kwana ba, ko bikin dangine bata cika zuwa ba,  idan ma yabata kudin gudummuwa ko kwatar abunda yabada bata basu, gashi Allah yayi mata rowa.

Ahaka ta haifa mashi diyarta ta farko me suna Hauwa,u sunan mahaifiyarshice yasa dan duk iyayenshi sunrasu, dama shi kadai suka haifa, sede danginshi, hakan yasa aka sama diyarshi sunan mamanshi, ana kiranta da JIDDAH.

Bayan sunanta ne Alhaji Abba yabama Zarah kudi masu yawa yace tafara bussiness, kuma shine yayi mata jagora zuwa dubai domin fara kasuwanci, daga haka harta fara zuwa ita kadai, ahaka ne tahadu da wata mata me suna Hajiya Karima, itama babbar yar kasuwace, halinsu ne yazo daya dan danan suka kulla kawance, itama anan kaduna take. Kawancensu sukeyi sosai, Karima takara nuna ma Zarah duniya anan idonta yakara budewa takara koyon duk wata kissa, sede ita karima bata bin bokaye sede duk wata kissa ta iyata, shiyasa Zarah take zaune da mijinta lafiya, tana yimashi biyayya, saboda yana sakar mata duniya, ita kuma babu abinda takeso kamar kudi, tun bayan haihuwar Jidda taso tayi planing amma Karima tahana ta, acewarta tabari tahaifi namiji.

Bayan shekara biyu da haihuwar Jidda takara haihuwar diyarta mace, har kuka seda tayi, saboda bata samu namiji ba. Ranar suna yarinya taci sunan maman Zarah Saratu, ana kiranta da JALILA.
   Tun daga lokaci Karima tarakata aka tsaida haihuwar acewarta karta tsufa dawuri. Haka yara suka taso cike da kulawa, sudukansu suna da kyau, sede Jalila tafi Jidda kyau, Ahaka suka shiga makaranta, Jidda na P. 1 aka saka Jalila, haka suka cigaba da karatunsu, harsuka girma, alokacin Jidda tana da shekara 18 Jalila tanada 16, alokacin Jidda tana ss 3, Jalila tana ss 1. Halinsu kwata kwata bezo daya ba, Jidda gab daya irin halin Umminsu tadauko, Jalila kuwa irin Halin Dadynsu gareta, tunda suka gama Primary Jidda tafita daga islamiyya, Jalila ce kadai take zuwa, sede Dadynsu besan bata zuwa ba, kasan cewar aiyuka sun mashi yawa, ga tafiye tafiye dayakeyi. Ita kuma umminsu bata damu da ilimin addini ba. Tun Jidda tana ss 1 tafara kula samari, duk wanda zekirata yabata kudi to zata iya binshi duk inda yace, so dayawa Jalila tana kawo kararta amma Umminsu bata daukar maganarta abakin komai, karshema sede takoreta, ahaka harta shiga ss3 alokacin tahadu da kawaye yan duniya tuni suka maida bin maza aikinsu, sede kawarta. Ameera tafisu duniyanci, hakan yasa takaisu asibiti domin suma ayimasu planing. Tun daga lokacin suke sheke ayarsu, kudi suke samu sosai, dayake Jidda tana bama Umminsu kudi hakan yasa tarufe mata baki, takuma zama yar gaban goshinta. Kullum Jalila setayi kuka idan taga halin da yayarta tasa kanta, amma sanin kotayi magana babu wanda ze kulata yasa tayi shiru , saboda Zarah taja mata kunne akan idan har tafada ma Dadynsu wata magana akan Jidda seta tsine mata. Addu,a kawai takeyi mata, sannan ta maida hankalinta akan karatunta na boko dana islamiyya.

Alh. Abba ne yafito cikin shirinshi na tafiya sokkoto. Matarshi da yaranshi biyu, suka rakoshi har bakin mota. Alh, yace to Hajiya nizantafi akula da gida, insha Allah gobe zandawo, kallon yaranshi yayi yace ku kula da karatunku ina fatan babu wata matsala ko? Jidda tayi saurin fadin dady kayan kwalliyarmu sun kare, dariya yayi yace toga dubu 20 nan ai sun isa ko? Karba tayi tana dariya, Jalila tace dady mungode Allah yakara budi. Allah yatsare hanya, sosai yakejin dadin addu,ar da Jalila takeyi mashi aduk sanda yatashi yin tafiya, ita kuwa Jidda tuni tajuya tanufi gida tana murnar samun kudi, daga nesa take fadin dady seka dawo ayo mana tsaraba. Murmushi yayi ya girgiza kanshi yace toni zan wuce, Zarah ta rungumeshi tana fadin seka dawo mijina, Ganin haka yasa Jalila tayi mashi sallam itama ta juya, kiss yayi mata agoshinta yana kara rungumeta, anan yakara mata bandir guda na 1k yace kozata nemi wani abu kafin yadawo. Godiya tayi mashi sannan yashiga motarshi yawuce.

Dayake tafiyar batayi mashi sauri ba, kasancewar tsaye tsaye dayayi kuma dama befito gida dawuru ba, hakan yasa beshiga sokkoto dawuriba segurin karfe 8 na dare, kaitsaye yawuce gurin wadda yazo, dan agobe yakeso yakoma, shiyasa seda yaje yagama abinda yakawoshi sannan yawuce masaukinshi, misalin karfe 9: 30, dayake awajen gari masaukin nashi yake, yafito daga cikin gari tun daga nesa yaga kamar ana tsaidashi, sede beda niyar tsayawa, dan yasan halin yan, fashi babu abinda basayi inde suna son sutareka, haryawuce yaga kamar mata guda biyu ne abikin titin wadanda suke tsaidashi, gani yayi sunata waigen bayansu gashi daya daga cikinsu ta tsugunna kasa kamar tana kuka ganin yawucesu.
    Cikin sauri ya taka burki yakoma baya, suna ganin ya tsaya da gudu daya takama hannun dayar suka nufi gurinshi, tambayarsu yafarayi, amma cike dasauri suka bude bayan motar suka shige. Dakyar take magana, dan Allah bawan Allah katemakemu kayi nisa damu daga gurin nan, wlh sunbiyo mu zasu kashemu...... Ai dajin haka yatada mota yafisgeta suka bar gurin, lokacin damasu binsu suka iso ko alamarsu basu gani ba, haka sukaita dube dubensu, ganin dare nayi suka juya domin komawa gurin Ogansu.

Urs
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/25, 11:51 AM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 5.....10

 Parking yayi adede wani karamin gida, inda yakasance masauki agareshi aduk lokacin dayazo sakkoto, fita yayi suma suka, fito, tsayawa sukayi suna kallonshi, ahankali yace bansan ina zan kaiku ba, kuma gashi dare yayi, duk da kunce infitar daku wajen gari, agaskiya bazan iya kaiku ba, saboda dare yayi kuma gashi ku mata ne, idan harkun yarda dani kushigo ciki ku kwana idan Allah ya kaimu gobe semusan abinyi, domin nima ba,a garin nan nake ba, wani aiki yakawoni yau, kuma nagama gobe zankoma kaduna acan nake da iyalina.

Kallonshi babbar ciki tayi nawani lokaci sannan tace bakomai munyarda da kai. Bude masu gidan yayi bayan sunshiga yakoma yakwaso kayan cikin motar daya siyo, yashigo ya kulle gidan, zaune suke afalo, shima zama yayi sannan yace. Ga dukkan alamu kuna dauke da yunwa, sede abinci beda yawa kaza ce da lemu nasiyo se biredi, kucinye kawai gobe idan nafita nasamo mana abinda zamu karya dashi, matar tace mungode sosai, amma yanzu abinda kedamuna bamuyi sallar magriba da isha,i ba, murmushi yayi yajinjina irin addini na wannan matar, daganinsu kasan suna tare da yunwa, amma duk da haka take maganar sallah.
      Dakinshi ya nuna masu yace akwai bandaki aciki idan sungama ga abin sallah nan, bayan sunshiga shi kuma yazauna afalo yana tunaninsu, yakosa sugama abinda sukeyi ya tambayesu labarinsu.

Babbar matar takalli yarinyar dasuke tare, da alama diyarta ce saboda tsanin kamar dasukeyi, tace kishiga ciki kiyi wanka sannan kiyo alwala, zama tayi tajirata, har tagama tafito sanye da kayan data cire, daukar hijabinta tayi ta kabbara sallah,ita kuma uwar tashiga domin yin wanka.

     Motsi yaji yasashi saurin dagowa, ganinsu yayi sunfito tsaf dasu, anan take ya iya hango kyawun dake tare dasu, duk da akwai alamun walaha atare dasu hakan be hana kyawunsu fitowa ba, musamman dasukayi wanka suka fita daga cikin dattin dasuke, duk da basu canja kaya ba.

Abinci yadauko masu yamika masu lemu da ruwa harda biredin, murmushi babbar tayi tace da alama kaima bakaci komai ba, kuma gashi kabamu duka, kadebi kazar semu hada biredin, yace a,a kude kuci ku koshi tace Allah bazamu iya cinyewa ba, bata jira abinda zece ba, ta deba mashi kazar dan tana da girma ta mika mashi da biredin, amsa yayi yana mata godiya, murmushi kawai tayi takoma kusa da diyarta suka fara cin tasu, shide ci kawai yakeyi amma hankalinshi yana kan wannan matar, addu,a kawai yakeyi acikin ranshi Allah yasa bata da miji, dan tunda tafito yaji wani irin yanayi akanta.

Bayan sungama takwashe kayan tasa aleda ta kaisu cikin dustbin tasaka, kalon diyarta tayi taga tana gyangyadi, Alh, yace yan mata bacci kikeji kije ki kwanta, murmushi tayi tace to Dady, sosai yaji dadin yanda takirashi da dady, tashi tayi tamasu seda safe tashige daki, matar tace Alhaji kai kuma a ina zaka kwana? Murmushi yayi yace bakomai anan ma ya isheni, zama tayi akasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsunta.

Shima kasa yasauko dan nesa da ita kadan, yace duk da bansan sunanku ba, daga ke har diyarki kiyi hakuri kifadamun labarinku dan bazan iyayin bacci ba idan har banji dalilin dayasa akeso akasheku ba. Idan har babu damuwa inasonjin labarinku, dan Allah.

Hawayen dake idonta ta goge tace tabbas Alhaji ka cancanci kaji labarinmu, domin katemakemu kuma nayarda da kai.
    Nide sunana HAJARA amma anfi kirana da HAJJO kasancewar mudin fulanine, Wannan kuma diyata ce sunanta FALAK, kuma ita kadai Allah yabani, mijina Allah yayi mashi rasuwa yau wata 5 kenan. Ajiyar zuciya yayi aranshi yana fadin Alhamdulillah.

Asalin labarin HAJJO...............
    Ita kadai Allah yabama iyayenta, kuma su fulanin daji ne, basu da taka maiman garin zama, ako da yaushe suna. Canza gurin zama daga wannan guri zuwa wannan, tun bayan auren Baffanta da Innarta suka bar garinsu wanda yake acikin niger, dan sunkasance fulanin niger, haka suka rika yawo gari gari tare da Shanunsu, duk inda sukaje sukan kafa bukkarsu agurin suzauna har zuwa wani lokaci, idan sun gama sesu tashi zuwa wani gari, acikin haka har suka haifi Hajjo, wanda sunan innar Baffantane aka samata.

Lokacin da Hajjo tayi girma har takai sheakara 10 alokacin suka yada Zango acikin garin gusau, acan bayan gari suka kafa bukkarsu tare da wasu yan uwansu fulani dasuka hadu ahanya, koda sukaje gurin sunsami fulani dayawa agurin, anan Baffa yaji dadi, dan tunda suke yawo basu taba haduwa da fulani dayawa kamar wannan ba, anan suka zauna suka cigaba da kiwonsu, inda Inna yakeyin fura da nono tana dora ma Hajjo tana bin sauran sa,anninta zuwa cikin gari sukai talla.
      Baffa dakanshi yayi sha,awar saka Hajjo makarantar boko kasancewar yaga wasu daga cikin yaran gurinsu suna zuwa, ahaka wani abokinshi jauro yayi mashi jagora zuwa makarantar da diyarshi take, shima yasaka Hajjo.

    Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya gwanin dadi, su Hajjo suna zuwa makaranta, ranar da babu karatu kuma sutafi cikin gari talla.

Ahaka harsuka gama primary alokacin Hajjo tana da shekara 16, kyawunta yakara fitowa sosai, kowa sonta yakeyi, watarana suntafi kasuwa ita da kawayenta domin aranar kasuwa takeci, sunje kai talla
    Tunda sukaje kasuwar ta lura dawani yanata kallonta, ahaka harsuka saida suka siyi abinda zasu siya suna shirin tafiya gida. Sallama taji anyi mata, amsawa tayi tare da juyawa domin ganin me mata sallama, wannan wanda tagani yana kallonta shine de tare da abokinshi.

Sannunku yanmata yace yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, bayan sun gaisa yake tambayarta sunanta, tace Hajjo, murmushi yayi yace Hajara kenan, amma sunan akwai dadi, ni sunana Bashir, kuma ni dan sakkoto ne, ina zuwa nan duk ranar kasuwa, amma Allah betaba jadamu ba, se yau, murmushi tayi tace zanwuce abokan tafiyana suna kirana kada dare yayi, kallon abokinshi yayi yace to abokina nima tafiya zanyi dan banason dare yayi saboda barayin hanya, dan Allah kabisu Hajjo kaganemun gidansu idan nadawo sati mezuwa kwana zanyi seka rakani. Godiya yayi masu sukayi sallama.

Tundaga wannan lokacin soyayya tashiga tsakanin Bashir da Hajjo, har iyayenta sun san dashi,  Baffane yace ma Hajjo idan Bashir yazo yanason ganinshi.

    Zaune suke abisa tabarma, anan Baffa yake tambayar Bashir asalinshi, Yace nide sunana Bashir, kuma ni dan asalin sakkoto ne, iyayena sun rasu tun ina dan shekara 20, banida kowa se kawuna, agurinshi nake kuma gida daya muke dashi, kasuwanci shine sana,ata ina zuwa garuruwa kasuwanci, kuma a sakkoto gidana yake wanda mahaifina ya mutu yabarmun.
    Baffa yace Alhamdulillahi, anan shima yafadamashi alabarinsu, sannan yace tunda naganka naji hankalina ya kwanta da kai, kuma nabaka Hajjo, ko yaushe kake so adaura maku aure zaka iya zuwa, sede inaso dan Allah karike mana Hajjo bisa gaskiya da amana, ita kadai Allah yabamu, kuma kaga bamuda kowa anan, gashi ba gari daya zamu zauna ba, kasan mudin makiyaya ne, inaso karike mani ita, kuma dan Allah karika kawo mana ita duk sanda zaka zo kasuwa, kafin mutashi daga nan, duk da gaskiya bayanzu zamu tashi ba, dan naji dadin zaman gurin nan.

Bashir yace insha Allahu Baffa zaka sameni me riko da amanar daka bani, kuma insha Allah sati mezuwa tare da kawuna zamuzo se adaura mana aure, banaso ku wahalar da kanku, Hajjo kadai nake so, saboda haka kada kusiyi komai. Godiya Baffa yayi mashi sannan yatashi yakira mashi Hajjo.


Bayan sati guda Bashir yazo da kawunshi Wanda yake kanin mahaifinshi dasuke uba daya, sunanshi Lado, amma mutanan gari suna kiranshi da Figo. Kasancewarshi cikenken dan duniya, danshi haryanzu beyi aure ba,sede lalata yaran gari, beda wata sana,ar data wuce shaye shaye da sata, shine oga acikin group dinsu, dan har yara gareshi. Bashir hakuri kawai yake dashi, tunda agida daya suke, sede shi kawu Figo adayan part din yake.

Bayan andaura aure aka shirya Hajjo cikin dinkunan da Bashir yakawo mata, sosai tayi kyau ahaka sukayi sallama da iyayenta suna kuka tafito, kawayenta suka rakota, harbakin mota suka kaita, suma kukan sukeyi ahaka suka tafi, ita kada abaya Bashir da kawu agaba, Bashir ke tuka motar. Tunda Kawu yaganta yake hadiye miyau yana murmushi aranshi yana fadin tsuntsu daga sama gasashshe.

Bayan sunje gida ya aje kawu sukuma suka shige gidan, gidan yayi kyau sosai, komai yasaka aciki kayan more rayuwa masu kyau yasa mata.

Ahaka sukaji gaba da rayuwarsu cike da so da kauna, komai najin dadi Bashir yanayi mata, sosai yake taka tsan tsan da gidanshi, saboda kawu, dan yafikowa sanin halinshi, ko abincin da Hajjo take bashi be bari takai mashi shine yake bashi da kanshi, idan kuma tafiya takamashi sede yakai Hajjo gidan abokinshi Saddik ta kwana, duk yanda kawu yaso kebewa da Hajjo Bashir yahana, idan yashigo gidan sede idan Bashir yana nan. Duk sanda zeje gusau cin kasuwa tare da Hajjo yake zuwa, sosai Hajjo tayi kyau, takara girma.

Bayan shekara biyu da aurensu tahaifi diyarta me kama da ita sede Allah yayima yarinyar kyau sosai, tun tana jaririya, ranar suna Bashir yasa mata FALAK, dan yace yana son sunan sosai.

Tunda FALAK ta girma yasata a primary, ranar dazeje gusau tare suka tafi, kwnansu 2 sannan sukafara shirin dawowa, Inna tadauko wasu awarwaro masu kyau guda biyu ta bama Falak, kasancewar sun mata yawa yasa Hajjo ta amsa tasaka a hannunta, haka taji kamar karsu tafi, Baffa yakara tunama Bashir akan rikon amanar daya bashi, haka sukayi sallama suka tafi.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/25, 1:02 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 10.....15

Ahaka rayuwarsu taci gaba da tafiya, Falak tagama primary tashiga secondary school, kyawunta sekara fitowa yakeyi, Hajjo har tsoro takeyi idan Falak zata fita, shiyasa bata barinta zuwa ko ina daga makarantar boko seta islamiyya, haryanzu Kawu besamu damar biyan bukatarshi ba, sede ya matsa ma Bashir lamba akoda yaushe cikin karbar kudi yake, da Bashir yabashi jari zecinyesu, yakuma dawowa, tunda yaga Falak tafara girma kwadayinshi yakoma kanta, sede yakasa samun hanya.

Lokacin da Falak tagama Jss 3 suka shirya domin zuwa ganin gida, tare da Bashir suka tafi amotarshi.
   Mamaki ne yakamsu lokacin dasuka isa bukkokinsu Baffa, babu komai agurin, yakoma fili, kasar gurin duk tayi baki. Kuka Hajjo tafarayi Bashir yanata lallashinta, haka yajuya yanufi cikin gari gurin abokinshi.

   Bayan sungama gaisawa abokinshi yace ai wata rana ne da dare yan fashi suka sauka a bukkokinsu Baffa, suka kwashe masu Shanunsu da duk wasu dukiyarsu, sannan suka tarasu aguri guda suka samasu wuta, babu wanda ya tsira acikinsu.

   Kuka sosai Hajjo da Falak sukeyi, Bashir ma duk dauriyar shi seda yayi kuka, sosai ya tausaya ma Hajjo, ahaka yayi ma abokinshi sallama suka juya, tunda sukaje gida yake aikin lallashin Hajjo, kuma yayi mata alkawarin bazatayi kuka dashi ba, da haka yasamu ta hakura.
    Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya, arzikin Bashir se kara habaka yakeyi, dan yanzu yadena zuwa gusau Lagos kadai yake zuwa, tunda suka Haifi Falak basu kara samun haihuwa ba, Hajjo taso suje asibiti amma Bashir yace a,a haihuwa ta Allah ce tunda sun samu daya ma ai sungode.

    Falak tana ss 2 ayanzu, bangaren islamiyya kuwa gab take da saukewa
 Awannan lokaci tana da shekara 16, takara zama budurwa, komai natana yafito, hakan yasa iyayenta suka kara saka matakan tsaro akanta, dan kawu yace arika bata abincinshi tana kai mashi amma Bashir yahana.
  Acikin yaranshi akwai babban yaronshi me suna Idi ana kiranshi da Jungle, shine yake bama Kawu shawarar yasa su sato mashi ita yabiya bukatarshi kawai. Kawu yayi murmushi yace kabari akwai tarkon danake dana ma Bashir saboda yanzu yaga yayi iyali shiyasa yamaidani abaya, duk wasu kadarorinshi yasaka sunan yarinyar nan ajiki, ka kyaleni dashi, yacemun zeje lagos, kuma nayi mashi magana akan inason wasu kudi masu yawa, inaso yabani su sannan in aikata mashi. Dariya suka sa gaba daya.

Zaune suke adaki Bashir yace Hajjo wlh kawu ya matsamun, gani yake kamar wasu kudade gareni, shiyasa yake tambayata kudi akai akai, mika mata wasu takaddu yayi da check na banki yace wannan takaddun gidan nan ne, wannan check din kuma na bankin Falak ne, domin aciki nake ajiye duka kuda dena,inaso kiyi masu boyo sosai, dan nayi alakawrin bazan kara bama kawu kudi masu yawa ba, koda yaje yaduba account dina baze samu komai ba, dan besan da wannan account din na Falak ba, tunjiya dana dawo daga Lagos yakeson ganina ni kuma boyewa nakeyi, se dazu yamun maganar kudi nace mashi banda kudi nayi asara sosai, yanzu mota ta ma zansa kasuwa insamu inbiya mutane kudinsu.
   Haka yatashi yatafi yana bambami, tashi Hajjo tayi taboye. Abinda yabata sannan tadawo kusa dashi tazauna tace Dadyn Falak hakuri zamuyi da halin kawu, ni kaina ina tsoron shi wlh, kana ganin irin yanda yake sakama Falak ido, banaso wata rana yayi mata.......... Bata karasa maganar datakeyi ba, sukaji an banko kofar dakin, wasu mutanene suka shigo , kuka Hajjo tafara tana fadin shikenan munshiga 3. Marin da,aka yimata ne yasata yin shiru, anan suka kama Bashir suka daureshi da Igiya, kukan Falak suka jiyo abakin kofa, dasuri tafada jikin ummanta tana kuka, abinda suka ganine yanasu mamaki, Kawu ne yashigo yana dariya.

     Bashir yace kawu me muka yimaka arayuwa? Duk irin yanda nake yimaka biyayya amma baka gani, dariya Kawu yayi yace dama ai nafada maka, sbd haka yanzu zankashe ka kuma inmaida matarka da yarka dadirona, dan kasan tunda ka aurota nakejin kishinta, amma ka tare komai, ahaka har ta haifi yarinya me kyau, wadda naji bazan iya hakura da ita ba. Kuka sosai Bashir yakeyi sbd abinda yaji Kawu yana fada, ahankali yace kawu dan girman Allah kayi hakuri, wlh kome kakeso zanbaka kada kayimun haka, Kawu yace aikin gama ya gama, Bashir, yanzu da dukiyarka da iyalanka duk sun zama mallakina.
   Zeyi magana kenan, Jungle yakwantar dashi, hanin yafiddo wuka yasa Hajjo da Falak suka matsa kusa,da kawu suka kama kafarshi suna kuka suna rokonshi, karar dasukaji ne yasasu juyawa. Kwance suka ga Bashir cikin jini Jungle yayi mashi yankan rago.
    Anan take Hajjo tafadi kasa asume. Kanta Falak tayi tana kuka,
   Anan kawu yasa su Jungle, suka dauki gawar Bashir yace suje can cikin daji su gina rami su rufeshi, bayaso subarshi batare da sunrufe shiba. 

   Bayan awa 2 su Jungle suka dawo, afalo suka iske Hajjo da Falak adaure se kuka sukeyi, anan kawu yace masu suje su kwaso mashi kayanshi su dawo mashi dasu nan, yace kasan yanzu nine megida, anan zan zauna har Hajjo tagama iddarta sannan na aureta, ita kuma Falak sa daka zanyi da ita. Dariya suka sa gaba daya, Jungle yace Oga tunda kadauki uwar dani kabama diyar ai. 

Hade fuska kawu yayi yace banaso kana kawomun wasa acikin iyalina. Dariya suka kara sawa. Kawu yace jungle gobe kaje gurin malamin can katambayomunshi Shekara nawa macen da mijinta ya mutu takeyi kafin takara wani auren.
     Dariya jungle yayi yace haba Oga ai sekasa ayi mana dariya kamata inje ina tambayar yanda ake idda, kasanfa nima nayi islamiya. Kawu yace yauwa, shikenan ma, fada mana muji, dan data gama zamuyi aure, kasan komai inaso inyishi yanda Allah yace kada inyi aure akan aure.
[5/25, 3:20 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah 
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 15.....20

 Dariya sauran sukayi, kowa yana sauraron abinda Jungle zece, Hajjo ta kalli Falak wadda idanuwanta harsun kumbura saboda kuka, kai ta girgiza hawaye suna kara zubo mata a idonta, jin irin rashin mutuncin da Kawu kemasu.
    Jungle yace ai Oga bata wuce shekara 1. Murmushin jin dadi kawu yayi yace haka nakeson tafiya damasu ilimi, ina ganin idan zamuyi aure kaine waliyina.
     Kallon Hajjo kawu yayi yace daga ranar dakika gama iddarki aranar zaki zama matata, kuma inaso kije kidauko mun takaddun gidan nan, idan bahaka ba wlh agabanki zan keta mutuncin diyarki. Dasauri Hajjo tace wlh zan dauko maka akwanceni dan Allah kada kataba mun Falak. Kome zakamun inde bazaka taba Falak ba, nayarda. Sawa yayi aka kwanceta ta tashi tanufi dakin Bashir tana waigen Falak.

Check din daya bata tafitar tadauko wata karamar jaka wadda tasa awarwaron Falak aciki tasaka check din sannan tadaura ta akugunta tayi saurin fitowa, tana zuwa tabashi, amsa yayi yana murmushi, yace saura kudi, tace kawu kasan Bashir beda kudi, dazu yake cemun zesayar da motarshi ma, kawu yace anyi haka, Jungle daga yau munyi mota.

Tashi yayi yacema su jungle zaku iya komawa gidana nabaku, nikuma ina nan, ke Hajjo keda diyarki ku koma dakin ki dazama ni kuma zankoma dakin Bashir, Sawa yayi aka kwancesu, yace wlh duk ranar da kikayi kokarin guduwa sena kasheki diyarki kuma tazama tawa, ke babu ba hanyar tazaki fita sbd zansa tsaro me kyau. Garama kun kwantar da hankalinku munyi rayuwar jin dadi. Tashi yayi ya sallami yaranshi shi kuma yawuce dakinshi domin kusan karfe 3 saura. Haka su Hajjo suka koma dakinta suna kuka, Falak tace shikenan yanzu umma haka zamuyi ta zama kawu yaci bulus kenan? Hajjo tace inaso kada ki daga hankalinki muyi hakuri komai yayi farko zeyi karshe, insha Allahu bazamu dawwama ahaka ba. Tashi tayi ta dauko duk wasu takaddun Falak da zinaranta dana Falak taciro jakarta tasakasu ciki ta maidasu akugunta . Falak tace Umma meyasa kika dauresu anan? Tace insha Allahu zamu fita daga gidan nan, koni banfita ba, ke zaki fita, nasan wadan nan kayan zasuyi maki amfani. Falak tace Umma kidena fadar haka, idan har kina gidan nan to tare zamu zauna , tashi sukayi suka dauro alwala suka fara nafila.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya, kullum Hajjo ita da Falak zasuyima kattin Allah girki, Hajjo tahana Falak zuwa makaranta, sbd harin da yaran kawu suka taba kawo mata ranar data dawo islamiyya.
Kullum kawu cikin kirga watanni yake,  alokacin har Hajjo tagama iddarta besani ba, danshi kirgen shekara yakeyi, ita kuma taki tafada mashi, ko dan kunne daki sakawa dan bataso yagane ta. Kullum cikin tunanin hanyar dazasu gudu take, amma ina, kawu yasamasu matakan tsaro.
    Aranar da Bashir yacika wata 5 da mutuwa, aranar su kawu suka fita wani aiki da dare,suka bar mutum daya domin yayi gadinsu Hajjo, Jungle yace Oga kana ganin babu matsala abar mutum daya? Kawu yace ayanzu Hajjo ta hakura dazaman gidan nan, tasan idan ta tafima bata da gurin zuwa, kada kadamu muje kawai.

Bayan tafiyarsu da awa1 Hajjo taleka, murnace takamata ganin megadin yana bacci, komawa tayi tadauko wani karfe, tazo kusa dashi, tadaga karfen ta kwada mashi akai, nan take yayi kara yafadi asume, komawa tayi tacema Falak tadauko hijabinta takama mata hannunta suka fita suka fara gudu.
     
   Alokacin dasu kawu suka dawo asume suka samu megdin, cikin sauri yashiga vikin gidan, babu inda be duba ba, amma begansu ba, fusace yafito alokacin har megadi yasha ruwa ya farfado, shakoshi kawu yayi yace suna ina? Megadi yana zare ido yace wlh nima ina. Kwance naji saukar wani karfe bankara sanin inda kaina yake ba, se yanzu. Kawu yace kufita nasan duk inda suke basuyi nisa ba, ku kamomunsu.


Gaji labarina Alhaji, kuma ina me tabbatar maka babu karya ko daya acikin labarin dana baka, idan har karya nake maka kada Allah yamun......saurin rufe. Mata baki yayi, yana me girgiza mata kai, shikanshi wahaye ne suke fita acikin idonshi.
      Hannunshi yacire yace wlh Hajjo nayarda dake dari bisa dari, bakiyi kama da marar gaskiya ba. Hakika labarinki abune me girgizawa, dole duk wani me imani ya tausaya maku, lallai kunga rayuwa wadda ba duka mutum bane ze iya daukar kaddarar da Allah yadora maku.
     Nayi alakwarin rikeku bisa gaskiya da amana. Hajjo inason infada maki wata magana sede ina tsoron kimun wata fassara, ko kuma kice sbd na temakeku ne yasa zance haka. Hajjo ta goge idonta tace wlh babu abinda zaka nema agurina bnyi maka shiba, kafadi abinda ke ranka.
   Shiru yayi sannan yadago kai yana kallonta yace Hajjo bazan iya boye maki ba, agaskiya tun bayan mushigo gidan nan nadora idona akanki Allah yasakamun sonki araina. Idan harzaki amince dani ashirye nake dana aureki kuma inrike Falak tamkar diyata. Matata daya Zarah da yarana 2 mata, Jidda da Jalila, inaganin Jalila zasuzo sa,anni da Falak.

Murmushi takeyi kanta akasa haryagama bayaninshi. Yace Hajjo kinyi shiru bakice komai ba, kada kidamu idan har bakida ra,ayin aure yanzu na amince zan zamo yayanki kuma mahaifin Falak wlh babu damuwa. Kai tadago tace bakomai Alhaji inaso kabari zuwa gobe zanyi shawara da Falak. Murmushi yayi yace badamuwa Allah yakaimu goben, kije ki kwanta dare yayi natsareki nikam yau babu barci, tace sbd mene? Yace yau kam ai buzu zan hau naneman sa,ar gobe. Dariya tayi tashige daki. Murmushi yayi yakwanta bisa kujera, hakanan yakejin wani farin ciki yana shigarshi , godiya kawai yakema Allah daya bashi ikon temakonsu Hajjo.

Washe gari dasafe bayan sunyi sallah sukayi wanka, anan Hajjo takalli Falak tafadi mata duk yanda sukayi da Alhajin daya temakesu, Murmushi Falak tayi tace wlh Umma ki amince mashi, kinga zamuyi nesa dasu kawu, bazasu taba tsammanin muna kaduna ba, kinga hankalinmu ze kwanta sosai. Hajjo tace Falak amma fa yana da mata hada yara 2, ina tsoron tashin hankali. Falak tace  Umma kowafa da halinshi ze zauna, mude muyi kokarin zama da duk wanda Allah yahadamu zama dashi tsakanin mu da Allah. Hajjo tace hakane, Allah yazaba mana abunda yafi zama alkhairi.
    Fita sukayi afalo suka sami Alh. Har yadawo daga cikin gari yakawo masu abin karyawa. Bayan sungaisa Alh, yamika masu abincinsu shima yaja nashi suka faraci. Falak tafara tashi takoma daki, kamar jira yakeyi yasauko kasa yace Hajjo wlh banyi bacci ba jiya amsarki kawai nake jira. Fuskarta ta rufe da hijabinta tana murmushi, yace kin amince? Kai tadaga mashi, godiya sosai yayi mata, yace sufito sukama hanya.

Zarah ce take tafaman gyara gida sbd megidanta zedawo, Jalila da me aikinsu Mairo suna kitchen suna hadamasu abinci. Jidda kuma tana dakinsu tana wanke bandakunan gida. Misalin karfe 2 na rana kowa yashirya suna jiran zuwan Alhaji. Jidda tace wlh nakosa Dady yadawo nasan zemana tsaraba sosai. Zarah tayi murmushi tace ai kunsan kowace tafiya idan Alhaji yayi tsarabata tafi takowa girma. Jalila tace kai Umma yaude tamu setafi taki tsoka, dariya suka dukansu, anan sukaji karar bude gate, da gudu suka fita domin taroshi, Zarah tashige daki domin kara gyarawa.

Mamakine yakamasu ganin Dadynsu dawasu mata, hakade suka yimashi sannu dazuwa suna kallonsu Falak, Jidda aranta tace kai ammade wadannan sunada kyau, tsayawa sukayi domin karbo tsaraba. Se sannan Alh. Yatuna bema yimasu tsaraba ba sbd tsabar farincikin amincewar Hajjo. Alh, yace mushiga cike yau babu tsarabar ci sede ta mutane, ciki suka wuce kowa da irin abinda yake rayawa aranshi.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(  Nabeelert Lady)
08028525263
[5/25, 10:48 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani 
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 20.....25

Da sallama suka shiga cikin gidan, cike dasauri Zarah tafito tayi kyau se kamshi takeyi zuwa tayi ta rungume megidanta tana dariya, shima dariyar yakeyi.
   Janshi tayi zuwa daki, su Hajjo suna tsaye bakin kofa, Jalila ce tajasu zuwa wani daki, bandaki ta nuna masu sannan tashimfida masu abun sallah tafita domin kawo masu abinci da ruwa, bayan sunyi sallah sukaci abincin da Jalila takawo masu.

Atare suka fito bayan yayi wanka, yafito cin abinci, zuba mashi tafarayi, saurin tashi yayi yana kiran Jidda da Jalila, bayan sunzo yace ina bakin da mukazo tare? Jalila tace suna dakin baki sunyi sallah suna cin abinci, ajiyar zuciya yayi yace yau Jalila nagode.
    Ya mutsa fuska Zarah tayi tace Alh, wane irin baki ne suka shigomun gida bansan da zuwansu ba, zama yayi yafara cin abincin shi yana murmushi. Zamatayi kamar zatayi kuka tace ina magana amma kayi shiru, haba hajiya, ai komenene kinbari ingama cin abinci ko.

Zaune suke afalo suduka, ayayin da su Hajjo suke zaune kasa. Zarah se cika take tana batsewa, Hajjo duk jikinta yafara sanyi ganin irin kallon da Zarah take yimasu, ko gaisuwarsu da kyar ta amsa, dama Zarah batason mutane, bare kuma dataga kyawawan mutane suzo tare da mijinta.

Gyaran murya Alh, yayi anan yayi masu bayani akan su Hajjo, har labarinsu seda yabasu. Jalila se kuka takeyi, gaba daya tausayinsu yakamata. Jidda da Zarah kuwa yatsuna fuska sukayi, zuciyar Zarah kamar zata fashe dan haushi.

Alh, yace sbd haka nakawosu gidan nan inafatan kuma zaku rikesu tamkar yan uwanku.... Zarah tace dan Allah Alh, dakata, kayi mani bayani yanda zanfahimta, idan ma masu aiki ne ka kawomun ni banida bukatarsu, inada me aiki, dan gaskiya wadan nan sadakar yallan bazasu zauna mun agida ba, idan ma temakonsu zakayi kabasu kudi sukama gabansu.

Murmushi Alh, yayi yace Zarah ai baki tsaya kika gama jin abinda zance ba ko, kinrufeni da fada kamar kinsami wata Jidda ko Jalila, kuma dan rashin mutunci agaban mutane zaki rufe ido kina fadamun abinda kikaga dama.
   Ina fatan acikin bayani na danayi bakiji nace zan ajesu agidanki ba. Agidana nace zan ajesu ko? Dan haka ki kula da kalamanki. Kuma wannan dakike gani Hajjo, insha Allahu cikin satin nan za,a daura mana aure, Falak kuma zanriketa kamar yanda zanrike Jalila ko Jidda.
    Bana son inkara jin wata magana kuma Jidda ku kiyaye, dan haka wancen part din acan zasu zauna, bance ku hada girki ba, kowa nashi zeyi, abinda nakeso asamu zaman lafiya acikin gidana, kinfi kowa sanin halina banason tashin hankali ahakan yasa bamu taba samun sabani nida ke ba, seyanzu. Dan haka ki kiyaye.

Jalila ga key din wancan part din nan zanyi magana da megadi kuje keda Mairo ku tsaya ya gyara idan nafita zansa akawo kaya azuba aciki dan yau nakeso su koma.

Murmushi tayi tace angama Dady, tashi yayi yace Hajjo kutaso muje. Fita sukayi suka shiga mota. Kasuwa yanufa dasu.

   Wasu irin zafafan hawaye ne suke zarya afuskar Zarah, tunda take da Alh, betaba yimata koda tsawa bace bare fada. Amma yau gashi sbd wasu banzaye yana fadi mata maganganu. Jidda tamatso kusa da ita tace haba Ummi meyasa sbd wannan maganar zaki daga hankalinki, tunda nataso agidan nan bantaba ganin kukanki ba seyau, tayama za,ayi inso wadan nan mutanen masu kama da aljanu.
   Wlh Ummi kinfi karfin yin kishi da fillo, ki kyalesu zaman gidan nan seya gagaresu, naso ace acikin part dimmu zasu zauna wlh damun samu. Masu aiki, amma bakomai idan sunsan wata basusan wata ba.

Jalila tace haba Yaya Jidda, da bakinki kike fadin wannan maganar, kada kimanta fa suma mutane ne kamar kowa, kuma ko ba komai duk abinda Dady yakawo gidan nan ai yakamata mudaukeshi da daraja, kuma ai...... saukar marin dataji ne yahanata karasa maganar datakeyi.
     Zarah tace dama batun yauba nasan bakida kishi akaina, nadauka kune masu goyamun baya aduk halin danake ciki, amma segashi dabakinki kike fadin wannan maganar. Wlh idan kinaso mushirya kifita aharkar wadannan mutanen, idan bahaka ba, kuma zamusa kafar wando daya dake. Tashi tayi tashige daki taci gaba da kuka, aduniya babu abinda ta tsana kamar kishiya, seyanzu take ganin wautar ta narashin mallake Alh, tuntuni ta biyema shawarar Karima, gashi nan duk irin kissar datakeyi mashi be hanata yimata kishiya ba. Lallai wannan tafiya ni akaimawa, kuma nasamu tsaraba me tsoka. Amma wlh duk yanda zanyi matar nan bazata dade agidana ba.

Kafin sudawo har angama gyaran part dinsu, masu kaya sunkawo ansaka aciki, komai yayi dede tun daga labule , kujeru, gadaje da kayan kitchen babu abinda ba,a saba, dakin Falak kadai ya isa ya burgeku, komai na bukata seda aka saka aciki sannan driver yashigo da kayan abinci yasaka a store ya kulle gidan, yatafi.

Se yamma suka gama siyayya lefe sosai yahada mata. Itama Falak babu abinda be saya mata ba, Hajjo har kuka tayi sbd murna, gidan abokinshi yawuce dasu, anan yayi mashi bayanin komai, matarshi Zainab mace me kirki ta tausaya masu sosai. Alh, yace inaso kuje muje gurin telanki domin abashi dinku nansu dan dawuri nakesonsu.
    
Farouk yace bakomai Dauko hijabinki muje nima inyi rakiya, abokina kace nanda kwana 5 zaka angwance, lallai wannan tafiya tayi riba. 
     Seda ya gwadasu sannan Alh, yabashi kudin dinkinshi yace nan da kwana 2 azo akarbi kala 5 na amarya kala 3 na Falak zeyi kokarin kara wasu kafin biki, idan yaso sauran zuwa bayan biki se azo akarba. Godiya sosai, suka yimashi suka tafi. Basune suka koma gida ba se karfe 7 na dare, makulli ya amsa gurin driver suka nufi part dinsu yabude. 
    
Mamaki ne yakama su ganin irin kayan da aka zuba agidan, duk da ba baki bane aganin irin kayan amma sunji dadi sosai. Bayan sunzauna. Hajjo tace Alh, bansan dawane irin. Baki zanmaka godiya ba, kagama mana komai arayuwa sede inroki Allah yabamu ikon saka maka da mafificin alkhairin daka yimana.

Murmushi yayi yace Hajjo basekin godemun ba, domin kingama mun komai tunda kika amsa zaki aureni, nima Allah yabani ikon kamanta gaskiya atsakaninku. Abinda nakeso dake ki kasance me hakuri, banason tashin hankali, kuma nasan baki dashi, kiyi hakuri da duk abinda zaki gani, daga gurin Zarah, nasani sarai bata da son mutane, shiyasa ma na ajeku anan, koda banida wannan part din bazan iya hadaku agida daya ba, dan haka kuyi hakuri dasu.
    Kuma insha Allah bayan biki Falak zaki cigaba dazuwa makarantar su Jalila. Nasan aji daya za,a saka ku tunda kince a ss 2 take , itama Jalila haka. Kome kukeso akwaishi akitchen, Falak inaso kidaukeni kamar mahaifinki, kada kiboyemun damuwarki dan Allah, kuma kizauna da yarana kamar yan uwanki. Godiya suka kara mashi sannan yayi masu seda safe yace su kulle kofar,

Adaki yasamu Zarah kwance, kusa da ita yaje yajawota yana fadin haba my luv yau kuma ni ake sharewa haka. Kinsan fa bamuyin haka dake, dan Allah kada kibari shedan yashiga zuciyarki yabata mana zaman lafiyar damukeyi na tsawon shekaru da dama.
    Murmushi tayi data tuna shawarar da Karima tabata, dazu fasuka gama waya, tace Zarah maza yan lallashine, idan harkinaso kimallake zuciyar namiji kozakiyi mashi asiri dole sekin hada da biyayya da kuma kissa, idan bahaka ba, kina zaune wata zatazo ta kwace maki miji, kawai ki kwantar da hnklinki ayi biki agama idan yaso da kssa ki koreta, amma idan kina tada hankalinki kome yafaru da ita ke za,a ce.

Kara rungumeshi tayi tasaka kukan kissa, tana fadin dan Allah Alh, kayi hakuri nayi nadamar yimaka abunda bantaba yimaka arayuwata ba se yau, kuma agaban ,ya,yanka da bakinka. Allah yasa haka yazama alkhairi, nide fatana kayi adalci atsakaninmu.

Sosai yaji dadin abinda tafada, dama yasan kishine yasata fadin abinda tfada dazu, goge mata hawayen idonta yayi yace nagode sosai matata, Allah yabiyaki, insha Allahu zaki sameni mecika alkawari, bazan taba juya maki baya ba, kema kinsan aduk duniya kece mace ta farko dana fara so, kece uwar yara na, babu abinda ze rabamu. Tashi sukayi tarakashi zuwa bandaki yyi wanka sannan suka kwanta.

Washe gari bayan yashiga sun gaisa dasu Hajjo yanufi gidan kawunshi, anan yafada mashi abinda ke tafe dashi, sosai kawunshi yaji dadin maganarshi, dan suma sungaji da halin matarshi narashin son mutane, yace bakomai Allah yakaimu asabar din, amma waye ze zama waliyinta? Yace abokina Farouk shine yace ze zama waliyinta. Yace to Allah yakaimu, kuma sekayi kokarin rike amanar marayun Allah daka dauko, yace insha Allahu kawu, anan yayi mashi godiya yatafi.

Ana saura kwana 2 biki komai ya kan kama har dinkunansu ankawo saura wadanda ba,a dinka ba, sosai sukayi kyau acikin kwanakin dasukayi, bakamar Falak, kyawunta yakara fitowa, Jalila kadai take shigowa part dinsu dan ita hakanan takeson Falak, amma Jidda da Zarah tunda sukazo basu kara sakasu aido ba, dan Hajjo macece wadda batason wulakanci shiyasa ta tsorata da irin abinda Zarah tayi masu, hakan yasa bata kara shiga part dinsu ba. Duk yanda Alh, yaso tashiga amma tace itade tsoro takeji yabari bayan biki tashiga.

Sallama aketa kwadawa acikin falon, da kyar Zarah tafito tana yatsina ta amsa sallamar. Ahankali tace tofa yau kuma Inna Asabe ce agidanmu, washe baki tayi tace wlh Babanki ne yace kwana 2 bakizo ba, shine yace inzo inga ko lfy. Zama tayi tace tokema Inna banda abunki tunda kukaji shiru ai kunsan lafiya ko, amma kinwani kwaso kafa kintaho.

Ran Inna yabaci dajin maganar Zarah, amma dayake ita Allah yayita da shegen kwadayi yasa tace ayi hakuri hajiya. Anan tasa Mairo takawo mata abinci da lemu, zama tayi tanata zubi tana zuba surutu.

Zarah tace Inna namanta banfada maku ba, Alh, aure zeyi fa. Cike da mamaki tace haba Hajiya wace irin magana kike fadi haka, kamarki ace wai za,ayi maki kishiya kuma kizauna kina fada ma mutane, aini atunanina mutanen kauye wadanda basu waye ba, sune akema kishiya, yanzu duk cikin kawayenki wakika gani da kishiya? Gaskiya bazata sabuba ayima yata haka. 
   Matsowa Zarah tayi jin irin maganar da Inna take fada. Asabe tace wlh na dauka tuni kingama da Alh, seyanda kikace yakeyi shiyasa bandamu davkawo maki maganin mallaka ba, kina tunanin duk son dayake maki idan matarshi tafara haifa mashi namiji agida baze manta dake ba. Gaskiya bazata yuwu ba.

Zarah tace yauwa Innata dan Allah kifadamun abinda yakamata inyi, dama neman abunyi nake, segashi Allah yakawoki, wlh konawa zan iya kashewa inde za,a fitarmun da wannan fulanin agida na. Murmushi Asabe tayi aranta tace anzo gurin, tunda baki badawa dan Allah yanzu kam lokacina yayi nima dazanyi arziki, wlh sena ta tseki kamar me.

Asabe tace kada kidamu acan zariya kinsan munada manyan bokaye, dan haka akwai kawata Dije tana da wani hamshakin boka, inaso bayan biki kizo muje gurinshi kome kikeso za,ayi maki. Godiya sosai Zarah tayima Asabe harta manta da irin abunda takeyimata dazu, Zarah tace yauwa Innata ainasan koda nayi rashin Uwa bazanyi kuka ba tunda ina dake, amma de anan zaki kwana zuwa gobe se insa driver yamaida ke ko. Mamaki sosai Asabe tayi jin yau tasamu matsayin kwana agidan Zarah. Anan suka cigaba da firarsu

Urs 
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/26, 2:17 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 25.....30

Ayau asabar aka daura auren Alhaji Abba da Hajara akan sadaki naira dubu 30, mutane dayawa sunsami halartar daurin aure.

   Acikin gida kuwa babu wanda yazo ta bangaren Zarah daga Karima se Inna Asabe, dan yanzu sosai Zarah take mutunta ta, sbd zata kawo mata mafita amatsalarta. Tare da kawarta tazo wato Dije, sunci sun sha sunkuma kwashi ganima.

Jidda kuwa alokacin bikin ma bata kwana gida ba, tana can gidan kawarta Ameera bayan sundawo daga party suka wuce gidansu Ameera acan suka kwana.
   Jalila ce itada mairo me aikinsu suka shiga bangaren su Falak suka tayasu aiki, matar farouk ma tazo, sekuma yan uwan Alhaji.
   Hajjo tayi kyau sosai, idan kaganta bazaka ce Hajjo daga sani bace a wata 5 dasuka wuce, ita kanta tasan rabonta da farinciki irin na yau tunkafin mutuwar mijinta.

Haka akayi biki kowa ya watse aka bar amarya da diyarta agida, Jalila ce ita da Falak zaune adain Falak. Jalila tace wlh Falak nakosa asakaki makaranta nima insamu abokiyar tafiya, musammamma islamiyya, banida kawar tafiya, dan Yaya Jidda tadena zuwa kuma Ummi tahanani infadama Dady. Falak tace ai gara kada kifada mashi, addu,a kawai zaki tayata, kinsan kowa da irin tashi kaddarar. Jalila tace haba Falak, ko kinsan jiya ba,a gida yaya ta kwana ba, wlh ina matukar jin bakincikin halin da yaya tasa kanta, wlh ko sallah ba sosai takeyi ba, idan namata magana karshe zagine zebiyo baya.
    Falak tace tabbas Yaya Jidda tana cikin jarabawar ubangiji, sede muyi ta mata addu,a Allah yashiryeta, kuma kada kibari Dady yafara jin maganarta abakinki tunda kinsan abinda Ummi tace. Jalila tace nagode Falak bara intafi kada Ummi tanemeni.

Zaune suke gaba dayansu a falon Alhaji, Zarah tana zaune akusa dashi, bakaramin dauriya tayi ba, wajen boye damuwar dake zuciyarta. Hajjo ko gaba daya tsoro yahanata sakewa ta kosa takoma part dinta.
   Alhaji yayi gyaran murya yace, Alhamdulillahi, Allah yanuna mana wannan rana damuke fatan zuwanta.
Zarah takanki zanfara, kece Babba, inaso dan Allah, kamar yanda nasanki bakida fitina acikin gidan nan, haka nakeso kicigaba dazama ayanda nasanki, ku hada kanku, kidauki Hajjo tamkar kanwarki, kuma kirike Falak tamkar Jidda ko Jalila, abanson kubari wasu suzo susamu damar tarwatsa farin cikin damuka gina shekara da shekaru acikin gidan nan. Allah yabaki hakuri akan wanda kikeyi, banyi auren nan dan bana sonki ba, ko kuma da niyar in wulakanta kiba,nayi ne domin ina bukatar hakan, kuma dan inraya sunnar Manzon mu.

Kema Hajjo, inaso ki saki jikinki acikin gidan nan, kidauki Zarah kamar yar uwarki, da yayanta amatsayin naki, banason wata fitina, duk abunda baki ganeba nacikin gidan nan zaki iya samun Zarah ki tambayeta, ko kuma ni kitambayeni.
    Maganar girki kuma dama nafada maku, kowa nata zata rikayi, Hajjo idan kina bukatar me aiki Zarah kisa Mairo tasamo mata, ko kuma idan zata iya tarika yimaku ku biyu, ko ya kikace Hajjo? A,a bakomai Alhaji, ai aikin ma bawani meyawa bane, zan iya yi nidaya, tacigaba dayima Umminsu Jalila, idan ina bukatar wani abu zansa mairo tayimun.

Zarah tace haba Alhaji ai base anakara kawo wata me aiki ba, Mairo ma ta ishemu, Fatana Allah yabamu zaman lafiya, kuma Hajjo dan Allah kiyi hakuri da abinda nayi maku farkon zuwanku, sharrin shedan ne. Hajjo tace lah, ai babu komai.
    Muemushin jindadi Alhaji yayi yace, to Zarah yakike ganin za,a yi gurin raba girki? Zarah tace bayan kagama kwana 3 ina ganin muyi kwana 2 ko hajjo? E duk yanda kikace yayi hakan. Alhji yace to Allah yabani ikon kwatanta adalci atsakaninku. Bara muje mukwanta naga dare yayi, tashi Hajjo tayi tamata seda safe tawuce, jawo Zarah yayi ya rungume, kwallar data ke boyewa ce tazubo, saurin kifa kanta tayi bisa kirjinshi. Kara rungumeta yayi yana lallashinta, da kyar yasamu tabarshi yatafi.


Haka rayuwa tacigaba datafiya cike da kwanciyar hankali, ansaka Falak makarantar su Jalila,inda aka sata a ajinsu Jalila SS 2, alokacin su Jidda suna shirin gamawa, sosai take gane karatun, dama Falak bade kokari ba, cikin lokaci kadan tazama zakaran ajin, hatta da malamai sun santa. Babu abinda ke hadata da Jidda, dan bakaramin Tsanarta Jidda tayi ba, sbd kyan datake dashi, ko magana tayi mata bata amsawa, amakaranta idan akaje daukarsu tarinka fadama kawayenta ga AGOLAR gidansu nan, abun yana matukar damun Falak, kullum sede Jalila tarika bata hakuri, duk irin cin mutuncin da Jidda takeyi mata bata taba fadama Ummanta ba, sbd tasan Ummanta dasaurin damuwa.

Zaman gidansu Zarah zamane na kissa, domin baka taba gane Zarah batason Hajjo, duk da bawani shiga part din juna suke sosai ba, amma tana nuna mata so.kuma Alh, yana iya kokarinshi akansu, babu abinda suka nema suka rasa, duk irin kudin da yake basu Hajjo bata siyan komai, sbd acewarta babu abinda suke bukata. Hakan yasa taroki Alh, dasuje ta duba account din Falak, tanaso ayi mata ATM, sannan tacigaba da ajiyar kudi aciki.
     Tare sukaje akayi mata komai, sannan tasaka dukan kudin datasamu abiki da kuma wanda yake basu, 


Bayan wata daya da bikinsu, Hajjo tafara laulayi, zazzabi me zafi takeyi, hakan yasa Alh, yaduketa suka tafi asibiti, suna zuwa awon farko akace tana da shigar ciki na sati 3. Murna agurin Alh, kamar ba,a taba yimashi haihuwa ba, bayan sundawo gida yawuce part din Zarah. Anan yake fada mata cikin Hajjo, Da kyar Zarah ta dedeta kanta sbd wata irin faduwar gaba ce tazo mata jin Hajjo tana da ciki, murmushi tayi tace kai amma naji dadi, ai gara mukara samun yara agidan, amma wadan nan ,yan matan dasunyi aure shikenan gidan ze koma shiru. Alh, yace wlh kuwa, Allah de yasa tahaifa mana aboki. Dif murmushin fuskarta yadauke, shi bema kula da yanayin data shiga ba, haka yayi ta zuba, daga karshe yakoma part din Hajjo.

Wata irin zufa taketo mata, daki tashiga, tarasa abunyi kawai tasaka kuka. Lallai namiji ba abin riko bane, wai yau Alh, dakanshi yake maganar ahaifa mashi yaro, wato sbd yaga niban haifa mashi ba. Wlh dole gobe inje Zariya, nadena kaima Karima kuka na, dan naga idan nabiye mata zata kaini tabaroni, yanzu lokacin kissa da biyayya sunkare dole se boka yashigo cikin al,amarin nan. Allah yakaimu gobe da safe.

Washe gari dasafe ko abinci Zarah kasa ci tayi, haka su Jalila suka gama shiri sukayi mata sallama, tace masu zataje zariya kilama ta kwana. Sukansu sunyi mamakin jin kalmar zuwa zariya abakin umminsu, kuma ma har maganar kwana takeyi, ganin kamar suna yimata wani kallo yasa tace masu Inna ce bata da lafiya. Sukace Allah yabata lafiya, idan kinje kiduba ta.

Segurin karfe 9 Alh, yashigo, alokacin Zarah harta shirya jiranshi kawai takeyi, sanin Alh, bame hana zuwa unguwa bane shiyasa bata damu da seyanzu zata fada mashi ba.

Bayan sungaisa yace waini Zarah ina zuwa naga kinfito da jaka da gyale? Murmushi tayi tace wlh jiya bayan kafita akamun waya daga gida cewar Inna batada lafiya, to ganin dare yayi shiyasa banfada maka yau zanje ba.

Ashsha, meyasa meta? Tace gsky basu fadamun abinda kedamunta ba, amma idan naje zanji,sede gobe nakeso nadawo. Mamaki ne yakama Alh, sede yaboyeshi dan bakaramin dadi yaji ba, dayaji Zata kwana agidansu, acewarshi kila tafara canza halinta ne. Shikenan babu damuwa Allah yakiyaye hanya, kinga akwai inda zanje aida muntafi tare, amma idan nasamu lokaci zanje indubota. Zarah tace ai bakomai idan najema yawadatar, zanhadaku awaya. Yajikin Hajjon? Murmushi yayi yace jikinta dasauki ai tasha magunguna. Daki yashiga yadauko mata kudin naira dubu 100 yace tarikesu ahannunta ko za,anemi wani abu, godiya tayi mashi, yawuce yafita, tace gata nan zuwa ta duba Hajjo. Mairo ta kwala ma kira kasancewar anan take kwana, dan dattijuwa ce. Bayan tazo tafada mata zataje gida se gobe zata dawo. Ita kanta mairo tayi mamaki, duk abinda zasu bukata ta bata sannan tawuce part din Hajjo.

Bayan ta dubata ta tashi zata tafi, Hajjo tashiga daki tadebo sabulan wanka dana wanki masu yawa tace akaima Inna, godiya Zarah tayi mata sannan tafita aranta tana fadin abanza wlh, babu abinda zesa naji tausayinki, haka nan daga zuwanki keda waccan shegiyar AGOLAR taki kunaso ku mallakemun miji.

Murna duk tacika Inna da Baban Zarah ganin yau Zarah ce agidansu kuma harma zata kwana, Inna tace Malan ai yakamata ka koma kasuwa hakanan kazo ka tsaya acikinmu kamar mace, jiki na rawa yace wai da zama zanyi mugaisa da Zarah ta, tunda taxo ai yau babu batun kasuwa kuma. Zarah tace Baba kaje kawai ai anan zan kwana yanzu akwai inda zanje. Inna tace idamma kazauna mezaka bata, yace shikenan to sekun dawo, haka yafita Inna tana binshi da harara aboye, abinda baku sani ba, Asabe tadade da mallake Baban Zarah, dama kuma tahanyar asiri tashigo gidan, dan Asabe muguwar yar tasha ce dan ba,a cikin Zariya take ba,yawon iskancinta ne yakawoya zariya harta hadu da Baban Zarah, Kawarta Dije ta tsaya mata har ta aureshi, kuma tayi sanadiyar mutuwar uwar Zarah ta mallakeshi take zaune agidan, ko Zarah tarasa yanda zatayi da ita ne shiyasa take zaune da ita, dayake ta iya kissa, hakan yasa mutanen gari suke ganinta kamar ta kirki. Ganin Zarah ta auri me kudi yasa ta saduda tamaida kanta sakarai agurinta saboda itama tayagi rabonta
Se gashi Allah yakawo mata hanyar sauki dazata ci kudinta aruwan sanyi. 
   Bayan Zarah tabata sabulan da Hajjo tabada akawo mata, Asabe tace kinga irin kissar tata ko, ina nan dake idan alh, yazo seta fada mashi abinda tabada aka kawomun,tashi muje gidan Dije, wannan bazesa mukyaleta ba. Alh, baze kara haihuwa da kowa ba, sede ke. Murmushin jindadi Zarah tayi tace shiyasa nake sonki Innata, yauwa ga waya ma nataho maki da ita, nasaka maki layi aciki sbd idan inason wani abu basena nataso nazo ba, banason Alh, yafara zargin wani abu, tunda yasan bazuwa nakeyi sosai ba. Asabe tace dama Hajiya tunda kinada mu agari ai kinwuce kije gurin boka da kanki, aisede kibamu umarni muyi, godiya tayi mata, sannan suka nufi gidan Dije, daga can suka wuce gurin boka, dama Dije ba miji gareta ba.

Abakin bukkar bokan Dije tace sujirata tashiga akwai maganar dazasuyi dashi, kashe ma Asabe ido tayi sannan tashiga, dayake boka natane, anan tayi mashi bayanin abinda takeso yacaji Zarah, dakuma kasanshi idan tabayar, da abinda zasu dauka ita da Asabe.

Fita tayi suka shigo tare. Bayan Zarah tagama yimashi bayani, Boka yayi dariya yace cikin kikeso alalata ko kuma akasheta gaba daya? Fiddo ido tayi, tace boka bazan iya kashe mutum ba, kawai a lalata cikin, idan yaso daga baya da kaina, nasan yanda zanyi inkoreta. Boka yace aikinki yana da tsada, amma sbd wadan nan zanyi maki sauki. Zarah tace boka kudi badamuwata bane, konawa zanbiya inde za,a cire cikin. Boka yace kije can kidaga wancan kwaryar kisaka dubu 150. Tashi tayi jiki na rawa taciro kudin tasaka. Wata diyar roba yadauko hannunshi yasa abisa cikinta yarika wasu surutai, yana murza cikin, wata kara sukaji anyi, Zarah takama Asabe tarike, aje diyar robar yayi yace matso nan ki gani, wata kwarya me ruwa aciki yadauko nan take hoton Hajjo yafito, tana kwance se juyi takeyi akasa, kafafunta kuma jini yana fita. Boka yace cikinne yake fita, angama da wannan matsalar, se nakara ganinki. Tashi sukayi suna mashi godiya.zasu fita boka yace Dije ke kitsaya. 
   Bayan sunfita, boka yace gaky Dije kun kawomun matar dazan ci kudi kuma kuci, lallai bayanzu zan sallami wannan matar ba, semunci kudinta, sosai, kudin yadauko yadauki dubu yadauki dubu 80 yabasu 70, godiya Dije tayi mashi tace semun sake dawowa.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/27, 2:50 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 30..... 35

Falak ce tayi sallama tadawo daga makaranta, kaitsaye dakin Ummanta tanufa, cikin sauri ta ajiye jakarta takarasa gurin Ummanta, ganinta kwance cikin jini tana nishi.
   Kiran sunanta tafarayi tana kuka, ganin takasa amsa mata tayi waje da gudu domin kiran driver, fitar ta yayi dede dashigowar Alh, tsaya wa tayi haryayi parking, dasauri ta isa gurinshi, tana kuka.
   Fitowa yayi yana tambayarta lfy? Tace Umma ce batada lafiya. Ai bejira ta idasa ba, yayi hanyar part dinsu. Yana zuwa yaga halin datake ciki , hijabinta yasa mata yadauketa, Falak tana biye dasu, mota yasata, Falak na kokarin shiga sega Jalila. Alh, yace yauwa Jalila zamuje asibiti Hajjo ba lfy, ku kula da gidan. Shiga yayi yaja suka tafi.

Suna zuwa aka wuce emergency da ita, Alh, se zagaye zagaye yakeyi, Falak ko se kuka takeyi, shikan shi Alh, tabashi tausayi. Seda suka dauki minti 30 sannan aka fito da ita abisa gado aka nufi, dakin da aka bata da ita, bin bayanta Falak tayi, shikuma yabi bayan likitan.

Zaune suke a office, Dr, yace Alh, sede kayi hkr cikin dake jikinta yazube. Sede bamu samu wani dalilin daze nuna mana abinda yayi sanadiyar zubar cikin ba. Amma alhamdulillahi, babu wata matsala atare da ita, anyi mata wankin mahaifa, kuma anyi mata allurai, insha Allahu zuwa dare ma zaku iya tafiya, semunce Allah yakawo wani me amfani. Zufar data fitoma Alh, agoshi yagoge, sannan yace ameen, Dr, nagode. Sosai yaji ciwon zubewar cikin sede babu yanda zeyi dole yayi hkr da hukuncin Allah, tashi yayi yanufi dakin da suke.

Zauns suke adakin Asabe, Zarah tace gaskiya Inna nagode maki, yanzu nakara tabbatarwa banida sama dake, dana tsaya bin shawarar Karima dayanzu ina can ina tagumi. Kome kenan idan akwai wata matsala, zanyi maki waya sekuje gurin bokan, basena zoba, idan kuma takama dole senazo se inzo din.
Wayarta ce tayi kara, ganin Alh, ne yake kira yasata saurin dagawa, jin muryarshi cikin sanyi, yasa tace lfy de Alh, naji kamar wani abu yana damunka, naji muryar kasa kasa.
   Anan yafada mata abinda yafaru, salati tafarayi cike da damuwa kamar zatayi kuka tace Alh, gani nan tahowa, tunda ko la,asar ba,ayi ba. Yace aa kibari se gobe, tunda itama Inna bata da lafiya. Tace a,a ai taji sauki, nide bazan iya zama ba, Hajjo tana da bukatata akusa yanzu, kasan su Falak yara ne, dole asamu wata babba akusa da ita, tunda Mairo aiki yayi mata yawa . Sosai yaji dadin yanda Zarah ta nuna kulawarta akan Hajjo.
    Bayan sunyi sallama tayi murmushi tace lallai aikin boka na kyau, Asabe tace meyafaru? Dije tace ai base an fada maki ba, kema kinsan cikin yabi ruwa. Dariya suka sa suduka. Zarah tace dani kike magana Hajjo. Bara intashi intafi, kada yamma tayi. Kudi tafiddo dubu 2000 tamika masu tace ga wannan asayi magi, godiya sukayi mata, suka rakata har mota, tazo shiga kenan Babanta yadawo, yace a,a Zarah ina kuma zaki? Tace wlh yanzu Alh, yamun waya abokiyar zamana tana asibiti, shine nace gara intafi. Baba yace wayyo Allah yabata lafiya, amma kin kyauta. Allah ya kiyaye hanya kidubata idan kinje. Dubu 1 tamika mashi tace Baba ga wannan anyi cefane, godiya yayi mata yanata shimata albarka, har ta tafi. Asabe tace malam kawo indauki kudina najiya, kasande ai baka baniba ko? Kamar zeyi kuka yace haba Asabe wlh koda naje kasuwa babu abinda nasamo, kuma idan nabaki dari 500 dama kuma meshago yana bina dari 300, kinga kudin sunkare, dan Allah kiyi hkr zanbaki. Dije tace a haba malam kabarshi wasa take maka bakomai tabar maka. Godiya yashiga yimata, anan yawuce masallaci, sukuma suka nufi gida.

Dije tace wlh wani lokacin bakida tausayi Asabe, duk irin kudin da kika samu yau, wanda rabon da ki rike irinsu harkin manta amma saboda dari 500 kinemi sama dan bawan Allah hawan jini. Asabe tace kinsanni akan kudi banida mutunci wlh, tunda harna iya kashe mazajena 2 saboda kudi, kinsan banida mutunci akan kudi, shiyasa bazan daga ma Zarah kafa akan kudi ba wlh, kina ganin sabida tsabar rowa dubu 2 tabamu duk irin wahalar damukasha, amma dayake biyan bukatar tane 150 taba boka. Dije tace ki kwantar da hankalinki, ai tunda de zata iya bada ko nawa ne ayimata aiki, mukam kakarmu ta yanke saka. Kinsan konawa boka yadauka yabamu sauran?  80 yadauka wlh, dariya Asabe tayi tace kai amma wannan boka yanada kirki, gaskiya naji dadi, dauko kibani kasona in adana.

Tunda Zarah ta isa gida wanka kawai tayi, taci abinci tawuce asibiti, lokacin dataje, har Hajjo ta farfado. Tea ta hada mata, takamata suka je bandaki. Seda tayi wanka tagyara jikinta sannan, Zarah tamika mata kayan da Alh, yakawo mata, sawa tayi tafito. Falak ce tashiga bandakin domin wanke kayan data cire.
   Bayan tasha tea taci abinci sannan tasha magungunanta. Zarah tace sannu Hajjo, Allah yabaki lfy, ya kuma kawo wani me amfani. Hajjo tace ameen. Zarah tajuya taga Falak bata nan, kuma Alh, yaje yin sallah. Tace amma Hajjo meze hana kibari sekin warke sosai sannan ki kara samun ciki, ina nufin kizo inraka ki gurin likitana asa maki robar hana daukar ciki, amma kada kibari Alh, yasani kinga seki huta sosai, daga baya se acire maki, nasan Alh, beda hkr ko baki warke ba, yana iya zuwa karbar hakkinshi, kinga niyanzu na huta. Hajjo takurama Zarah, ido harseda ta tsargu.
    Zarah tace kinyi shiru, murmushi tayi tace ai likita ma yace kozan kara samun ciki senan da shekaru sbd barin dana samu. Ajiyar zuciya Zarah tayi, batasan lokacin da murmushi ya kwace mata ba, tace wayyo gaskiya na tausaya maki, amma ai bakomai wata rana zaki samu. Kallonta kawai Hajjo takeyi, aranta tace ai idan mutum yanuna baya sonka daga farko, koyazo daga baya yace yana sonka kada kayarda dashi.

Segurin karfe 8 aka sallamesu. Bayan sunkoma gida, Alh, yace mairo tarika shiga tana taya Hajjo aiki kafin tasamu sauki. Zarah tace ai bakomai ma taje tayi mata sati 2 harta warke, Hajjo tace a,a Ummin Jalila ai za,a barki da aiki, idan tagama maki tunda nawa babu yawa setazo tamun. Alh, yace shikenan hakan ma yayi.

Tundaga wannan ranar Mairo take shiga part din Hajjo tana taya ta aiki, sosai mairo takejin dadin aiki agurin Hajjo, sbd tana da kirki, kuma bata kyamarta kamar Zarah, gashi tanayi mata alkhairi akai akai, harcewa takeyi dama Alh, yasamoma Zarah wata ita abarta anan, idan ta tuna aikin sati 2 kawai zatayi takoma can dazama batajin dadi, Sosai suke zama da Hajjo suyi ta fira, shiyasa ma seta gama aikin Zarah take tahowa gurin Hajjo. Duk wani labari na Hajjo babu wanda bata sani ba, sbd hakanan Hajjo taji mairo ta kwanta, mata gatade dattijuwa, amma tana bata girma, shiyasa ma bata iya kiranta da mairo sede tace mata Baba mairo, hakan bakaramin dadi yakema Mairo ba, Falak da Jalila ma haka suke cemata, amma banda Jidda.

Jidda ce kwance adakin saurayinta Al,amin, bayan sungama aikata masha,arsu, Al,amin yace Dear nah yakamata fa kitashi kiyi wanka inmaida ke gida, kinga ankusa tashi daga islamiyya, tunda nagama dora maki nawa karatun. Murmushi tayi tace wlh, dande Dady yana gari da anan zan kwana, banason tafiya inbarka. Al,amin yace nafiki son haka Jidda, shiyasa naso ace kinbari nazo gidanku muyi aurenmu mu huta kikace bakison aure yanzu. Jidda tace wlh, Al,amin rayuwar aure takura ce, duka yanzu shekarata nawa dazanyi aure, ai gara inbarai sena kai irin 27 ko 28 haka, yauwa lokacin nakara girma. Amma kawai yanzu da kuruciyata inshiga sahun manya. Murmushi Al,amin yayi yace shikenan ai nima bawai auren ne yadameni ba, tunda de inada kudi na nasan bazan rasa yan mata ba, duka Jidda ta kaimashi yana dariya yace, kemafa bani kadai kike kulawa ba, abinda nasani de nida ke muna son junanmu sosai, amma kowa yana kula duk wanda yasamu, ko kin manta da kaina ina hadaki da aboka naina masu kudi, kuma ni seki hanani kula wasu, aikinsan harakar bariki kowa yanada yanci. Jidda tace naji de amma aikasan kai na dabanne tunda kaine kafara sanina ,ya mace, yace wlh Jidda akanki nafara wannan sana,ar. Shiyasa nake bala,in sonki Jidda na. Murmushi tayi tace bara inyi wanka.

Haka rayuwarsu tacigaba datafiya, hanakalin Zarah bakaramin kwanciya yayi ba jin Hajjo bazata haihu yanzu ba, arizikin mijinsu sehabaka yakeyi, shiyasa yabiya ma Hajjo da Falak da su Jalila hajji, yace ma Zarah tabari tunda ita taje wata shekarar se sukara tafiya tare, baya son abrshi shi kadai. Bakaramin dadi taji ba, za,a barmata mijinta.

Lokacin da Mairo tacika sati 2 tana aiki agurin hajjo, ranar data dawo bangaren Zarah sallama takeyi amma jin shiru yasa tawuce dakin Zarah, taje zata kwan kwasa taji Zarah kamar tana waya, har zata juya taji Zarah tana dariya tana cewa, ai wlh, Inna Asabe, yanzu hankalina akwance yake, tunda mukayi nasarar zubar da waccan cikin na hajjo likita yace kozata kara haihuwa senan da shekaru, shiyasa nace dole inyima boka babbar kyauta sabida yabiyani, yanzu Alh, yabiya mata hajji ita da yara, harda wannan AGOLAR banzar akabiya mawa, narasa meyasa Alh, yake son maidata kamar kowa agidan nan. Ai kede kibari da sannu zankoresu subar gidan nan, toshikenan sekinjini. Mamaki ne yakama mairo jin abinda Zarah take fadi, saurin komawa tayi tanufi dakinta, tana tunanin hanyar dazata bi domin. Kare Hajjo daga sharrin Zarah.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[5/27, 4:03 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (  H,O,N,A)

Fita Mairo  tayi tashiga kitchen tacigaba da aikinta, tana tunanin maganganun Zarah, hakade ta barma cikinta, danbazata so afara jin wata magana abakinta ba, amma tayi alkawarin zata sa ido sosai aharkar Zarah, tunda tagano tacanza halinta.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, harsu Hajjo sunje hajji sundawo, sosai tayima Zarah da Baba mairo tsaraba, bayan kwana biyu suka shirya zuwa Abuja ita da Alh, domin kaima matar farouk abokin Alh, tsara barsu, dan bayan bikinsu akayima Faruok transfer yakoma can. Kwanansu 2 acan, bakaramin bacin rai Zarah tashiga ba, anyi tafiya banda ita.

Bayan dawowarsu, Mairo tashiga part din Hajjo, tana zuwa ta isketa abandakin falo tana ta amai, temaka mata tayi, bayan tagama suka dawo falo, mairo tace sannu Hajiya, amma inaganin kamar ciki ne dake ko? Hajjo tace nima haka nake tunani, dan tunkafin muje hajji nadena ganin al,ada ta, sede yaune nafara amai. Mairo tace aikinsan yanzu ba cikin farko bane, kila ma yayi wata 2 shiyasa baki fara laulayi dawuri ba.

Amma zankawo maki wani magani, inde kinsha zaki dena amai kuma zakiji kwarin jikinki. Hajjo tace aiko nagode Baba mairo, wlh bansan da abunda zan saka maki ba, Allah yasani nayi rashin uwa, amma gashi yanzu Allah yabani ke, inajinki tamkar uwata, babu abinda zan iya boye maki. Kwallan da mairo take boyewa suka zubo mata, Hajjo tace Baba mairo meyafaru kuma?  Mairo tace bakomai, kawai naji dadin kalamanki yata, tunda nake bantaba haihuwa ba, banida me kirana mana, segashi yau kinbani babban matsayi wanda bakowa ne yake amsa shiba. Hakika yau ina cikin farin ciki wanda. Nadade banji ba. Allah yayi maki albarka keda diyarki Falak.

Sede inaso infada maki wata magana, ada ina shakkun infada maki, sbd bansan yazaki daukeni ba, kila bazaki yarda da maganata ba. Amma ayanzu dakika bani matsayin uwa agareki, nasan zaki yarda da abunda zan fada maki, dan kinsan uwa bazata fadama yarta karya ba.

Inaso kiboye cikin dake jikinki har lokacin da zaki haifeshi, ko Alh, banaso kifada mashi kina da ciki harse yayi girma, nasan shi baza,a iya boyemashi ba. Hajjo tace meyasa kikace haka Baba mairo, nasan dole akwai dalilin dayasa kikace haka, dan Allah kifadamun koma menene, nayi maki alkawarin bazan bafadama kowa ba.

Anan mairo tafadama Hajjo duk abunda taji Zarah tana fadama Asabe awaya. Hajjo tagoge kwallan idonta, tace wlh jikina yabani Zarah ba sona take ba, kawaide tana yimun fuska 2, lokacin da aka kwantar dani asibiti take cemun wai inzo tarakani asakamun robar hana daukar ciki.

Anan jikina yabani wani mugun nufi take nufi dani, kawai sena fada mata likita yace kozan haihu senan da shekaru, wlh Baba mairo ina gama fada mata bakiga wani murmushi datayi ba. Tun daga nan nagane abinda take nufi dani.

Kuma insha Allah Zarah bazatasan ina da ciki ba sede taji haihuwa ta. Shima Alh, bazan fada mashi ba harse yayi kwari, shima sena rokeshi kada yabari kowa yaji, Mairo tace bara inje inkawo maki maganin.

Haka Hajjo tacigaba da renon cikinta babu wanda yasani daga mairo se Falak, su Jidda anyi graduation duk da bawani kokari tayi ajarabawarsu ba, su Falak kuma sunshiga ss3 karatu sukeyi sosai dan sunaso sucigaba da karatunsu idan sungama.

Jidda yanzu duk inda Al,amin zeje tare suke zuwa, ko da kwana nawa zeyi tunda Alh, baya zama gida yanzu sosai, Zarah kuwa tunda Jidda tana wadata ta da kudi babu abinda yadameta, abinda Jidda tagane ma Zariya tamaida gurin zuwanta, tunda taga Asabe bata kwaba mata duk inda taje kotayi dare bata cemata komai, kuma Baba bashida katabus agidan, hakan yasata yanzu tafi zama Zariya akan gidansu, koda Alh, yaji tana zuwa Zariya dadi yaji saboda yaga umminsu ita bata zuwa.

Lokacin da cikin Hajjo yacika wata 7 aranar Alh, yagane tana da ciki, yace lallai ma Hajjo yanzu nikike boyema abun farin ciki?  Dariya tayi tace wlh banso kagane ba, naso kawai kazo kaga jariri ko jaririya, shiyasa ko zanje awo nake cemaka zanje wankin kai. Amma kayafemun da karyar danayi maka. Jawota yayi yace bakomai, aikinsan dama ni ina baku damar fita duk lokacin da kukeso koda bana nan.

Amma gaskiya naji dadi sosai,  Allah yasa rayayyene, tace ameen. Amma dan Allah banaso kafadama Kowa har ummin Jalila, nafiso inbata mamaki tunda kai kaganoni.
    Yace shikenan angama daukarta yayi suka nufi daki.

Su Falak suna third term a ss3 Hajjo ta haifi yaronta me kyan gaske, babu wanda yasan tahaihu, dan cikin dare nafara nakuda kuma taci sa,a Alh, agurinta yake, haka suka hada kaya suka nufi asibiti, Falak kawai tasan suntafi, gurin karfe 8 suka dawo, bayan ya kaita part dinta yawuce part din Zarah, yanashiga yahadu da Mairo, yace tabar abinda takeyi taje Hajjo ta haihu, sosai mairo taji dadi, tace me aka haifa, yace namiji, barka tayi mashi sannan tawuce part dinsu.

Farin ciki kawai Alh, yakeyi, dakin su.  Jalila yaje yace tafito tacigaba da aikin da mairo takeyi, dan taje gurin Hajjo ta temaka mata ta haihu. Jalila cike da murna tace Dady meta haifa?  Yace kunsamu kani Jalila bakaramin dadi taji ba, fita tayi tawuce kitchen. Dakin Zarah yashiga, ganin yana cikin farin ciki ga bakinshi yaki rufuwa, tace Alh, yaude lafiya kake kamr wanda aka yima bushara da gidan, aljanna? Yace aidole kiganni haka, Hajjo ta haihu kuma tasami namiji me bala,in kama dani. Dariya Zarah tayi tace amafarkin yau ne kaga haka? Yace wlh da gaske nakeyi, tun dare muna asibiti. Zarah tace karbo yaron kukayi kome, nide nasan Hajjo bata da ciki. Ganin zata bata mashi lokaci yajata zuwa part din Hajjo.

Mutuwar tsaye Zarah tayi ganin Alh, yamiko mata yaro me bala,in kama dashi, kamar an tsaga kara, wata irin zufa ce tarika keto mata ta ko ina, tama rasa mezatayi, takasa karbar yaron, hawayene suka taho mata tayi saurin juyawa takoma. Falo, mamaki ne yakama Alh, ganin abinda Zarah tayi, amma su Hajjo sun harbo jirginta.

Urs,
 NABILA RABI,U ZANGO
(  Nabeelert Lady)
08028525263
[5/27, 9:48 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani 
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 40.....45

Afalo yasamu Zarah tana goge kwallan idonta, Zarah meyafaru haka? Fitowa Hajjo da Mairo sukayi suna kallonta domin jin abinda zata ce. Haba Alh, ai wlh bekamata ma indauki yaron nan ba, me kuka daukeni acikin gidan nan, ni na dauki Hajjo kamar kanwa agurina amma ashe ita ba haka bane, 

Kaima kabiye mata kun maidani agefe guda, wai yanzu ace har Hajjo tayi renon ciki agidan nan amma bansani ba, wlh da ace yaron nan baya kama da kai bazan taba yarda Hajjo ta haifeshi ba. Kuma har ace ina gidan nan nakuda takama Hajjo ai komin rashin matsayina amatsayina na ,ya mace za,a iya kirana inrakaku asibiti amma kai me mata zaka dauketa kutafi ku biyu.

Gaskiya baku kyauta mun ba, kuma yau nagane matsayina agurinku, kuyawa tayi tafashe da kuka zata tafi, jikin Alh, yayi sanyi sosai, seyanzu yake ganin rashin wayon dayayi daya biyema Hajjo akan kada afada ma Zarah tana da ciki, gaskiya shima beji dadi ba.

Aje yaron yayi yafita yabi bayanta, Hajjo tayi murmushi tace Xarah kenan, tabbas dan kyautawa bamu kyauta ba, amma Allah yaga nufinmu, dan haka ko kinyi fushima nide tunda nakare lfyr yarona ai shikenan. Mairo tace kukan munafunci ne takeyi, tasan idan bahaka tayi ba, Alh, ze iya gano bata farin ciki da wannan yaron, ki kyaleta tunda ba akan gaskiya take fushin ba, zata sauko, kema kije kiyi mata ta ,yan duniya.

Adaki yasameta tana ta kuka, wanda azahirin gaskiya kukan bakin cikin haihuwar yaron da akayi ne, na 2 kuma rashin sanin Hajjo tana da ciki, da taje an zubar dashi.

Jawota yayi yarungumeta yafara aikin lallashi, shima kamar zeyi kukan, dan har ga Allah beji dadin abinda akayi mata ba, shi sam beyi tunanin zataji haushi ba. Sallamar dasukaji abakin kofa ne yasashi tashi yaduba ko waye, tare da Hajjo suka shigo, zama tayi abisa gefen gadon,

Ahankali tace. Ummin Jalila dan Allah kiyi hakuri, nasan ban kyauta maki ba, amma atunanina keda Alh,naso inbaku mamaki, naso ace kuduka Jariri kawai kuka gani, sede shi yafara ganewa, shiyasa narokeshi akan kada yafada maki, nafiso inbaki mamaki kawai kiga yaro,

Nasan zakifi kowa murnar hakan, saboda irin damuwar danaga kinshiga danayi bari, amma kiyi hakuri, ga yaron nan, nabaki dama kiyi mashi huduba da duk sunan dakika ga yayi maki, domin danki ne.

Murmushin dayafi kuka ciwo tayi ta tashi zaune, tace shikenan Hajjo na hakura, amma kada kisake, kuma nahakura ne, saboda wannan damar da,aka bani. Alh, ka amince inyi mashi huduba?

Dariya yayi yana mejin dadin irin hadin kan da matanshi sukeyi, yace ni na isa inshiga tsakanin yaya da kanwarta, gashi kiyi mashi huduba muji abinda kika sa mashi

Karbarshi tayi acikin kunnenshi tarika dura mashi zaki tana fadin nice ajalinka, magana takeyi tana murmushi, kamar gaske. Dagowa tayi tacenayi masa huduba da sunan marigayi Bashir, ( mijin Hajjo baban Falak).  Za,a rika kiranshi da Amir, inafatan Alh, ban bata maka raiba, kada kace nasaka sunan abokin tarayyar ka? Matsowa yayi ya rungumeta yace gaskiya Zarah kina da tunani me kyau, wlh naji dadi sosai, kuma nagode daya kasance kece kikayi wannan hudubar, dan dani nayita da sunan mahaifina zansa, amma hakan da kikayi, naji dadi sosai, domin anyima Falak da Hajjo kara, idan Allah yasa takara haihuwa zasa sunan Babana.

Wani shu,umin murmushi Zarah tayi aranta tace nima naji dadi da aka bani damar zaben suna nasan dama sunan Babanka zaka sa, wlh, bazaka taba saka sunan Babanka akan ya,yanta ba.

Matsowa Hajjo tayi, ta rungume Zarah tana yimata godiya. Duk da aranta takasa yarda da wannan abun da Zarah tayi, kuma murmushin dataga tayi yakara tabbatar mata da akwai wani abu azuciyarta. Amma koma menene Allah yamaida maki nufin ki.

Tashi sukayi suka fita, bayan taje tafada ma, Mairo abinda yafaru. Mairo tace dole sekin dage da addu,a domin Allah ne kadai yasan irin mugun nufinta akanki, Allah yamana tsari da sharrinta. Ameen.

Haka akayita hidimar zuwa barka, yan unguwa, kudi sosai Alh, yakashe a haihuwar yaron, Zarah hakuri kawai takeyi, dan tace bazataje Zariya ba, sebayan suna, damma dadin datakeji Alh, yabata kudi masu shegen yawa, Yara ma duk yabasu, kasancewar Jidda bata nan, sede yabama Zarah nata.

Su Falak sunata hidima, ranar suna yaro yaci sunanda Zarah tasa mashi.

Fadi irin kudin da aka kashe bata lokacine. Harsu Asabe da Dije seda suka zo suna, wani filin Alh, daya zagaye yayima Ameer kyauta, sede be bari Zarah taji ba, saboda yasan halin mata.

Zaune suke adakin Zarah suna magana. Zarah tace wlh sena sa boka ya korar mun wannan matar, ita da yayan ta acikin gidan nan. Dije tace ai kinyi mata me sauki, baki tunanin idan kika koreta wata rana asiri yakare yasake maido ta? Ai kawai idan zakasha giya kasha ta dubu.

Ina baki shawara ki kasheta kawai, Zarah tace ni nafijin zafin yaron wlh. Asabe tace lallai bakida wayo, idan kika kashe maciji mabi sare kan ba ai kinyi aikin banza. 

Kawai kifara kashe Hajjo daga baya seki kashe yaron, idan kinsamu nutsuwa kizo muje gurin boka.
Haka suka ci gaba da tattaunawa,

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[5/28, 3:42 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 45.....50

Bayan suna da sati daya, Zarah tashirya tanufi zariya, tana zuwa suka tafi gurin boka, bayan tagama yimashi bayani akan tanaso akashe mata Hajjo da yaronta, hada ido Dije tayi da boka ta kyafta mashi ido.
Dariya yayi yace Hajiya ni banayin aiki 2 alokaci guda, musamman idan yakasance na kisa ne, sede zanyi maki wani temako daya, nafarko dole kizabi wanda za,akashe acikinsu,

Zarah tace akashe yaron, Asabe tace lallai bakida wayau, idan aka kashe yaron ai zata iya kara haifar wani. Zarah tace hakane afara kashe Hajjon, dariya boka yayi yace bazamu kasheta lokaci guda ba, dole zamu samata ciwo nawani lokaci gudun kar azargi wani abu.
Shikuma yaron zanmaidashi dolo, kafin shima yabi uwarshi.

Amma wannan aikin naki zeci kudi, tace kamar nawa za,a bada? Naira dubu dari 200 zaki bada, anan take tadauko ta ajesu a inda tasaba ajewa,

Wani allon karfe yadauko yayi wani rubutu akai, sannan ya hura wuta yadora allon asaman wutar, yace yanda allon nan zeyi zafi haka jikinta zerika zafi, ko wane irin magani aka bata bazata taba jinsaukin zafin jikinta ba.

Dasannu zata mutu, garin magani yabata yace ta murzashi ahannunta alokacin data dauki yaron seta shafa hannunta akan yaron, shima idan uwar tamutu ki aiko su Dije suzo sukar ba maki maganin da akashe shi dashi. Godiya sukayi mashi suka tashi suka fita. Dije kuma ta tsaya karbar masu kason su, dubo 60 yabasu, tayi godiya tace naji dadi dabaka bata maganin duka ba, nafiso karika raba aikin yanda za,afi samun kudi. Dariya yayi yace Dije naga alama kinfini son kudi.

Kwance Hajjo take tana bama Ameer nono, kamar daga sama taji antsikareta, tashi tayi, se kuma taji jikinta wani irin sanyi yana shigarta, tashi tayi tajawo bargo, duk da lokacin zafine, amma haka takejin wani irin sanyi, shiga tayi cikin bargon, kafin minti 20 kuma gabadaya jikinta da bargon sunyi wani irin zafi.

Cire bargon tayi tarasa inda zata sa kanta, rigar jikinta tacire shima de basauki, tashi tayi da kyar tanufi bandaki, wanka tayi, sede data zuba ruwa ajikinta kamar ruwan zafi tazuba, haka tafito tasamu riga marar hannu tasaka.

Falo ta fito ta kunna A,C ta kwanta, duk da haka zafi takeji ajikinta, wasu irin hawaye ne sukarika zubo mata saboda ciwon kan datakeyi, ga Falak tana makaranta sunfara waec bata dawowa da wuri.

Kamar daga sama taji sallamar Mairo, kasa amsawa tayi, dasauri mairo tashigo jin Ameer na kuka amma bata daukeshi ba.
     Daukarshi tayi tana fadin Hajiya lfy, kasa magana tayi sede kwalla, kusa da ita tamatsa,ta dora hannunta ajikin Hajjo, saurin cirewa tayi jin wani irin zafi kamar ze kona mata hannu, tace Hajiya ai zazzabi kikeyi, bara inkira driver yazo yakaimu asibiti tunda Hajiya bata nan,

Suna zuwa asibiti aka karbesu domin anriga da ansan Alh, wayar Hajjo mairo tadauka takira Alh, anan take fada mashi suna asibiti, yace gashi nan zuwa, goye take da Ameer yana ta kuka tana jijjigashi, da kyar yayi bacci.

Alh, ne zaune a office din Dr, yace mashi zazzabi ne kawai me zafi takeyi amma anyi mata allura kuma ansa mata karin ruwa insha Allahu zata samu sauki. Godiya yayi mashi ya amshi takardar maganin daze siyo yafita.

Zaune suke duka gidan har Zarah domin ta dawo, Jidda ce kawai bata nan, dan suna Abuja ita da Al,amin. Zarah tace oh, sannu Hajjo, wannan irin zazzabi haka, ace tundazu yaki yasauka, sema kara hawa yakeyi.

Alhaji yace gaskiya nima nafara tsorata da wannan zazzabin, Allah de yabaki lfiya, Hajjo. Zarah tace Mairo kawo Ameer kije gida keda su Falak da Jalila kushiryo abinci ko, naga dare haryafara yi, Falak da tun dazu take kuka tace. Ummi da kinje kin huta yanzu kika dawo daga unguwa fa, ni zan zauna agurinta.

Zarah tace a,a kuje kuda kuka dawo daga jarabawa, ai yakamata kuje kuyi wanka kuci abinci, bakomai nizan zauna, idan kundawo anjima senaje ni. Alh, yace kuje kawai idan kundawo taje.

Suna fita Alh, yace bara yaje yadawo, Ameer na hannuna Zarah, ita kuma Hajjo tana bacci, Saurin fiddo magani tayi ajakarta tashafa a hannunta takama Ameer tashafa mashi akai, wata irin kara yayi wadda har Zarah seda ta tsorata tayi saurin mikewa, Hajjo datake bacci seda tafarka.

Turo kofar dakin akayi, wasu nurse ne 2 suka shigo, ganin Ameer yana wani irin abu farin miyau yanata fito mashi, yasa sukayi saurin karbarshi suka fita, Hajjo tace mekika yimashi Zarah?

Akideme tace wa ni? Nima bansan abinda yafaruba, kina bacci inason inshiga bandaki sena ajeshi kusa dake,nashiga bangama abinda nakeba naji kararshi, ina fitowa naganshi akasa kwance. Wasu hawayene suka fitoma Hajjo, ido kawai ta rufe tanajin wani irin zafi ajikinta.

Bin bayansu Zarah tayi, tana sauke ajiyar zuciya, karo taci da Alh, yana kokarin shiga dakin, yace lafiya de? Anan tafada mashi abinda yafaru, shima binta yayi, koda sukaje Ameer haryayi bacci, nurse tace wai meyafaru dashine? Zarah tafada masu abinda tace ma Hajjo, suka ce Allah yakara sauki, sunyi mashi allura zejisauki, dauko shi tayi suka fita.

Bayan su Mairo da Falak sundawo, Jalila kawai suka bari agida, da kyar suka samu Hajjo taci abinci, se alokacin Ameer yatashi, tunda yatashi yake zubar da miyau abakinshi, ga kanshi yawani langabe,

Karbarshi mairo tayi tana kare mashi kallo, Zarah tace tunda kunzo nizan wuce, dare yayi, Allah yakara sauki.
Alh, yace nima anjima zantaho, tace to. Hajjo tace anya yaron nan faduwar dayayi beji ciwo ba kuwa, kalli yanda yakeyi Alh, karbarshi yayi yace bara inkaim likita shi yaduba shi.

Bayan Dr, yagama dubashi yace aini Alh, banga wata alama data nuna mani faduwa yayi ba, kuma naduba jikinshi lafiy lau babu wani abunda ke damunshi, da faduwa yayi dayatashi da kuka, kasan dama ba,a raba jarirai da miyau abaki, kanshi kuma dayake langabewa dama kasan ai jikinshi beda kwari, tunda ko sati 2 beyiba. Kada kudamu bawata matsala bace, godiya yayi mashi yafita.

Bayanin abinda likita yace yayi masu, itade Hajjo jikinta yakasa yarda da abunda akace, dan kawai tana kunyar Alh, yasa tayi shiru dan ita macece me kauda kai akan abu, yadade har gurin karfe 11 sannan yayi masu sallama yatafi.

Mairo tace Hajiya wai meyafaru har Hajiya tace Ameer faduwa yayi? Anan tafada mata duk abinda yafaru. Mairo tace wlh hajiya batada gaskiya, nikam yanzu tsoronta nakeji, amma bakomai Allah yafita, ni tunda tace zataje Zariya jikina yake bani wani mugun abun zekaita.

Mucigaba da addu,a insha Allahu bazatayi nasara akanki ba, Falak tagoge kwallan dake idonta tace Umma gobe idan naje islamiyya zan tambayi malam wace irin addu,a zanrika tofa maki, dan wannan zazzabin yayi yawa. Mairo tace gaskiya kam nima naga alamar dole semun hada da addu,a.

Washe gari ciwon Hajjo kamar karashi akeyi, sukansu likitocin sunyi mamakin irin zafin zazzabinta, duk wani test anyi mata amma babu koda maleria ce ajikinta, duk wani temako sunyi mata amma zafin jikin yaki sauki, haka suka cigaba dayi mata allurai da magunguna.

Bayan Falak tadawo daga islamiyya tadauko ruwa akofi tayi addu,oin da malaminsu malam Sameer yabata, tayi, tabama Mairo kama Hajjo tayi tace tayi bismilla tasha, tana gama sha tarika atishawa , karbar rowar ruwan tayi ta wanke mata fuska zuwa wuyanta, sannan ta kwanta.

Cikin mintuna kadan zafin jikinta yakoma sanyi, jitayi kamar ancire mata kaya ajiki, Hamdala sukayi, Mairo tace aini nasani wannan ciwon naki akwai aikin asiri aciki, Alh, yazo mukoma gida kawai acigaba dayi maki addu,a. Falak tace shima Malam Sameer haka yace idan har tasha kuma zazzabin yasauka to tabbas akwai sihiri ajikinta. Mairo tace ke duniya, anya mutane suna tsoron Allah kuwa?

Bayan Alh, da Zarah sunzo suka sami Hajjo azaune tana bama Ameer nono, Alh, cike da jindadi yashigo yazauna kusa da Hajjo yana fadin jiki yayi sauki kenan, tace gaskiya Kam jikinta yataba, yaji sanyi yace Alhamdulillah bara inje Dr, yabamu sallama, Mairo tace nimade haka nace, dan suma sunkasa saukar da zafin zazzabin amma Falak tana amso addu,a agurin malaminsu aka bata tasha ko minti 10 ba,ayiba yasauka.
     Kwarewa Zarah tayi, nan take zufa tafara fito mata, tagefen ido suke kallonta, da kyar ta dede ta kanta tace Alh, gara de abarta takara samun sauki, yace A,a suma kansu sunkasa yimata magani tunda addu,a tanayi mata, fita yayi Zarah tabishi dakallo.

Hajjo tace Ummin Jalila yagajiyar jiya? Murmushi tayi tace haba ai gajiya tabi lafiya, yajikinki? Tace dasauki.
   Tare sukazo da Dr, yakara duba jikinta, shima yayi mamakin saukar da zazzabin yayi lokaci guda, shima shawara yabasu akan sucigaba dayimata addu,a. Sallama yabasu suka nufi gida,

Hankalin Zarah bakaramin tashi yayi ba ganin Hajjo tawarke, sede Ameer da haryanzu yana zubar da miyau, kuma kanshi baya tsayawa, shima addu,a sukeyi mashi. Waya Zarah tayima Asabe tace taje gurin boka tafada mashi abinda yafaru, idan zata turama Jidda kudi a account tunda  kince jiya tadawo ko,

Falak ce tare da Jalila suntaso daga islamiyya, sallama sukaji abayansu, juyawa Falak tayi, murmushi tasaki sannan ta amsa sallamar, jalila tace lah Malam Sameer ashe kaine? Yace wlh, kuwa inata sauri naga harkun taho, dama tambayarku zanyi yamejiki, Falak dasauki Malam dan tunda nayi mata wannan addu,ar shikenan bata kara zazzabi ba. Yace Alhamdulillahi kicigaba dayi mata addu,ar dakinga tafara irin zazzabin, tace to malam mungode, tare suka tafi harseda yakaisu kofar gida Jalila tayi mashi sallama tashige, Falak tace nagode sosai malam, bansan da mezan gode maka ba, Murmushi yayi yace dan wannan ai bawani abu bane, Allah yakara bata lafiya. Ya Exam dinku? Tace dasauki ai mungama Waec ma ranar monday zamufara Neco, yace to Allah yatemaka adage ayi karatu, nima dama hutu nasamu kuma yakusa karewa zankoma last semister dina.
Falak tace lah Malam ashe baka gama karatu ba, yace emana, tace wace makaranta kake to, yace a A,B,U Zariya nake, Falak tace amma baka dade dafara zuwa makarantar nan bako? Yace na dade mana, amma aikinsan makarantar 2 ce akwai ta yara data manya, toni da nafison koyama yara, shiyasa nake acan, to shugaban makarantar ne yace indawo nan, amma nibanaso, 

Tace meyasa malam? Yace kinsan halin yanmatan yanzu basuda kunya shiyasa nafison yara, kuma gashi makarantar ba,a dukan manya kinga dole su raina malamai ko, Falak tace to aide ajinmu basa raina ka, ko? Murmushi yayi yace mace daya ce tagama rai nani , zaro ido tayi tace wacece? Yace Falak ce, da gudu yashige gida tana dariya. Shima dariyar yakeyi, shide harga Allah yanason Falak, sede yana tsoron yafada mata abinda ke ranshi taki amincewa.

Wanene SAMEER? 

Sameer dan asalin garin kaduna ne, suna zaune a tundun wada, shi kadai Allah yabama iyayenshi, tunda yagama secondary school mahaifinshi yarasu, daga shi se ummanshi Halima suke zaune agidan, yan uwan babanshi bawani karfi garesu ba, hakan yasa suka kasa daukar nauyin karatunshi tunda result dinshi yafito, duk da mahaifinshi bawani kudi gareshi ba, amma yanada rufin asiri, tunda yanada gidan kanshi, dan karami, aciki suke zaune da Ummanshi, tanayin kosan saidawa da kuma markade, dahaka ta tara kudi tabiyama Sameer kudin makarantar dayasamu A Zariya, cikin ikon Allah yafara karatu cikin sa,a hankalinshi kwance, yake karatunshi, domin Sameer beda hayaniya,mutum ne me natsuwa, ga kokari.

Idan anyi hutu yana koyawa a islamiyya kuma yana zuwa shagon wani abokin babanshi yana aiki, da haka yake tara kudin komawa, Ummanshi tahada mashi da nata.

Dahaka haryakusa gama karatunshi, yanzu haryana shekarar karshe a jami,a wannan karin ne daya dawo bangaren yanmata da koyawa aka bashi ajinsu Falak, tunda yadora idonshi akanta yaji yana sonta sosai, sede ganin daga gidan fatake fitowa yasan tafi karfinshi, amma duk da haka yakasa cire sonta aranshi, Sameer kyakkyawane nakarshe yanmatan makarantar dayawa suna nuna suna sonshi, sede yaki basu fuska, baya magana da kowa, dalilin fara maganarsu da falak akan ciwon Ummanta ne, tundaga nan yasamu damar yimata magana.

Wannan kenan.

Bayan sati biyu da samun saukin Hajjo takara tashi da wani zazzabin, haka kullum Falak take yimata addu,a data sha ciwon yake sauki, bayan kwana 2 kuma yadawo, Ameer kullum ciwonshi kara fitiwa fili yake yanzu kowa yagane Abnormal ne, Hajjo duk tarame tayi baki, Falak ma tarame saboda abu 2 yahade mata, ga ciwon Ummanta ga Exam, damma sunkusa gamawa, 

Alh, yarasa yanda zeyi gaba daya beda nutsuwa, sbd ciwon Hajjo, Zarah ma afuska kullum cikin damuwa take, hakan yasa tace ma Mairo takoma gurin Hajjo harseta warke, koda yaushe cikin turama Asabe kudi take domin akaima boka.

Ameer ma yarame saboda baya shan nono sosai, hakan yasa Alh, yace adena bashi nonon sbd zafin zazzabin datakeyi, madara yasiyo mashi Mairo tana bashi, abin yayima Fakak yawa ga malam Sameer takoma makaranta, ko no wayanshu batada.
    Ahaka ciwo yayita cin Hajjo addu,a kam tana shanta, Aranar da su Falak zasu zana jarabawar karshe, dasafe tafito cikinshirinta, tashiga dakin Hajjo, kwance taganta, sede ayau setaga tayi haske, sosai.

Zama tayi akusa da ita tace Umma zantafi, kuma yau zamu gama makaranta, kinga se indawo inrika kula dake sosai, kinga Baba mairo aiki yayi mata yawa. Murmushi Hajjo tayi, kamo hannun Falak tayi ahankali tace, Falak bazan dena fada maki akowane hali kika tsinci kanki kiyi hakuri da irin rayuwar da tasameki, kuma inaso duk rintsi kada kijuyama Alh, baya, kome zeyi maki kidaukeshi tamkar mahaifinki, kamar yanda ba,a iya canza uba, haka nakeso kirike Alh, ko bana gidan nan banbaki ikon kibar gudan nan ba, sede aure ko mutuwa, ki kula da kaninki, banaso koda wasa rashin kunya tashiga tsakaninki da Zarah, ko Jidda, nasan aduk gidan nan sune basa sommu, amma Jalila Allah yayi mata albarka, banaso kirabu da ita, itace kawarki kuma yar uwarki.

Kiyi hakuri da rayuwa Falak, zakici ribarta wata rana, inaso kirike Baba mairo, domin nadauketa amatsayin uwa, banida abokin shawara se ita, kema inaso kidauketa haka, nasan bazata iya cutar dake ba. Allah yayi maki albarka, tashi kije kada ki makara.
   Hawayen dasuka zuboma Falak tagoge tace Umma insha Allahu zanyi aiki da duk abinda kika ce, kuma zaki samu lafiya kidena fadar haka. Hajjo tace bani biro da takarda, bayan ta aje mata tajuya harta kai bakin kofa takara juyowa, kallonta daga Hajjo nayi, kwalla nafita daga idonta. Shigowar Jalila yasa Hajjo tagoge idonta, Jalila tace Umma yajikin, tace dasauki, Harzakutafi? Tace E, to Allah yabada sa,a.

Kama hannun falak tayi suka fita, biro tadauka tacigaba da rubutu a takardar, tana gamawa mairo tashigo. Hajjo tace Baba mairo duba cikin drowar can zakiga wata zaka baka kimiko mun.

Bayan tabata ne tamika mata takardar data rubuta tace tasaka ciki. Baba mairo, inaji ajikina ciwon nan bana tashi bane, zantafi inbar yarana 2 agurinki, duk da nasan kema bakida karfin rikesu, sede inaso Ameer da Falak sucigaba daza agidan nan, matukar ba, Alh, ya koreta ba, dan Allah ki kularmun da Falak marainiya ce, inaso wannan jakar kiajemun ita harse ranar da aka kai Falak dakin mijinta sannan kibata, idan Allah yasa tayi dacen miji kice kada tazama meboye sirrinta agurinshi.

Duk abinda Zarah zatayima Falak Kibata hkr, tashi kilekamun ko Alh, yashigo, goge kwallan idonta mairo tayi tace Allah yabaki lafiya Hajiya ciwo ba mutuwa bace, tashi tayi tafita.
    Tare suka dawo da Alh, danshigowar shi kenan gidan. Kwance suka sameta tana  kallon silin bakinta dauke da murmushi, kusa da ita Alh, ya matsa, hannunta yakamo gani yayi yakoma, dasauri yadora kanshi bisa kirjinta, nan ma babu numfashi, jijjigata yashiga yi yana kiran sunanta, amma ina rai yayi halinshi.
Kuka yasa kamar karamin yaro, mairo ma kukan takeyi tana fadin shikenan Hajiya wayyo. Yadade ahaka, kafin yadauki waya yafara kiran kawunshi sannan yakira Farouk da sauran mutane, fita yayi domin kiran Zarah.

Tunda driver yakaryo kwanar gidan taji faduwar gabanta ta karu, tunaninta ne yatsaya alokacin dasuka tsaya kofar gidan taga taron mutane, wasu sunata alwala, da gudu tafito tanufi cikin gidansu, ita da Jalila.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/29, 11:36 AM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(  Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

 Part 50....... 55

 Alh, tafara karo dashi yana goge idonshi, zeshiga part dinsu, kusa dashi ta matsa tana kuka, tace Dady shikenan narasa Umma ko? Kasa kallonta yayi saboda wani irin tausayinta dayaji, wani sabon kuka yaki yataho mashi.

Kamota yayi, suka shiga ciki, kwance tasamu Ummanta anshiryata cikin lakafani se kamshi takeyi, gefenta Mairo ce da Zarah, se Ameer abisa cinyar Mairo yana ta kokarin jan zanin da,aka rufe Hajjo, kowa kuka, yakeyi, Zarah kamar uwar ta ce ta mutu.

Fadawa tayi bisa gawar Hajjo tana wani irin kuka neban tausayi, seda tabama kowa tausayi, bude fuskarta tayi, gani tayi kamar tana mata murmushi, ahankali tace Allah yajikanki Ummana, shikenan ni kuma haka Allah yashiryomun rayuwata zankare cikin maraici.

Kuka sosai takeyi, Jalila wadda itama kukan takeyi tamatso takamata tana bata hakuri, Alh, yace ku gyara za,a shigo adauketa domin yimata sallah akaita makoncinta,

Daki Falak tashige dan bazata iya ganin tafiyar Ummanta daga cikin gidan ba, haka aka fita da gawar Hajjo, akayi mata sallah, sannan aka kaita makabarta. Tunda suka tafi Falak tafadi asome, su Mairo suka samata ruwa da kyar ta farfado, kafin sudawo Asabe, Dije, Baban Zarah da Jidda suka iso.

Zaune suka samesu afalo, Falak tana gefe guda zaune ita da Jalila hawaye kawai ke fitowa daga idonta, bayan sungaisa sukayi masu gaisuwa. Jidda ta matsa kusa da Falak, tunda ta kalleta, hawaye suka cika mata idonta, bata tabajin tausayin ta ba, seyau, gaisuwa tayi mata, ta tashi tana kuka tawuce part dinsu, dan ita tunda take bata taba ganin abinda yabata tausayi kamar Falak ba, dan zata iya cewa rabonta da ta zubda kwalla tun tana yarinya, batasan zafin mutuwa ba, tanade jin anayinta, shiyasa takasa zama agurin tawuce part dinsu.

Haka aka cigaba dazaman gaisuwa, gaba daya kulle part dinsu Falak akayi, Alh, yasa Jalila da Mairo suka kwaso duka kayan Falak dana Ameer takoma dakin Jalila, Ameer kuma yana gurin Mairo.
Seda akayi sadakar 3 sannan su Asabe suka koma, ita ko Jidda cewa tayi bazata koma ba, don tunda akayi mutuwar gaba daya hankalinta yatashi, ko Al,amin yakirata da sauran samarinta bata dauka, gaba daya tsoron mutuwa takamata, sallah ma yanzu akai akai takeyi, wanda rabonta dayin hakan harta manta.

Bayan sadakar 7 ne Alh, yatarasu afalonshi, Kallon Zarah yayi yace to Hajiya, kema nauyi yakara hawa kanki, duk dade Falak tayi wayon dazata rike kanta, amma duk da haka, dole se anrika nuna mata yanda rayuwa take, inaso kamar yanda kika dauketa ada yanzu ma ki kara daukarta fiye da haka, saboda yanzu, tadawo gurinki, banaso ki nuna bambamci tsakaninta da su Jalila.

Shikuma Ameer tunda Baba Mairo tace abar mata shi, shikenan Allah yabaki ikon rikeshi, amma duk da haka inaso shima kirika lura dashi,  Allah yabamu ikon rike marayunshi.

Kema Falak banaso kisaka wani tunani azuciyarki, dan kinrasa Ummanki bayana nufin kinzama marainiya bane, idan baki manta ba, tunda nadauko ku, nayi alkawarin rikeki amatsayin diyata, to haryanzu kina nan amatsayinki na yata, duk wata damuwarki banaso ki boyemun, ko Hajiya, kuma insha Allah idan jarabawarku tafito, zakucigaba da karatunku kafin Allah yakawo maku mazaje, dan bazan ce sekun gama karatu zakuyi aure ba, dakun samu miji zan aurar daku, Jidda tunda Exam dinki batayi kyau ba, naso inbiya maki kiyi acikin su Jalila, kika nuna bakiso, ina tunanin kila aure kikeso, sekiyi kokarin fitar da miji.

Ina fatan kuma zaku cigaba da zuwa islamiyya dan nasan wasu dasunyi candy shikenan sunyaye islamiyya, kunga gab kuke da sauka, sekudage ku hada karatunku gaba daya, Jidda kedama tunkafin kigama makaranta naji labarin kindena zuwa islamiyya agurin shugaban makarantarku.

Inaso infada maki duk wata tarbiyya nabaki amatsayina na uba, duk da naksance ba mazauni ba, amma nasan hajiya zata iya, kula daku, sede nasan yaran zamani, ina shawartarki dakiji tsoron Allah, kina ganin de yanda muka rasa Hajjo, agidan nan, kuma shikenan, bazata kara dawowa, ba sede alahira, naso ace mata suna zuwa makabarta kai gawa, dakunga yanda aka gina rami dan karami aka saka Hajjo aciki, babu komai acikinshi, daga ita se halinta zasu zauna aciki, idan tayi hali mekyau, Allah zekara buda mata kabarinta, idan kuma sabanin hka , Allah zesa kabarin yakara matseta, har hakarkarinta suna shiga cikin yan uwansu.

Wlh babu abinda yafi kabari duhu, sallarka ce kawai zata zama haske acikin kabarinka, idan kana yinta da kyau, ina kara tunatar daku kuji tsoron Allah, domin duk abinda mutum ya aikata zeje yasamu abinsa yana jiransa. Alhamdulillahi, ina kyautata zaton Rahma agurin Hajjo, saboda takasance mace tagari, kuma tana ibada sosai, batada abokin fada, bata taba batamun ba, aduk zaman damukayi.

Allah yajikanta da rahma, Allah yasa sanadiyyar mutuwarta yazamo mana shiriya akan halayen mu marasa kyau. Zaku iya tafiya, hawaye ne kawai suke zarya afuskar Alh, shima yakasa tsaidasu, kowa agurin kuka, yakeyi, Jidda kuwa jitayi kamar tafada ma Dadynsu abubuwan datakeyi yaroka mata Allah shiriya,sede tanajin kunyar fadar irin laifinta agaban mutane, sede tayi alkawarin komawa islamiyya, domin neman ilimin dazata tuba dashi.( ni kuma nace Allah yasa ba tubar mazuru zakiyi ba Jidda, nasan dan adam da mantuwa).

Haka suka cigaba dazamansu acikin gidan gwanin ban sha,awa, Baba Mairo tana kokrin kula da Ameer dan yanzu yayi wayon sede kullum doloncinsa kara fitowa yakeyi, haryanzu ko zama befara ba, sbd kanshi baya tsayawa.
      Falak da jalila sukeyi taya Baba mairo aiki dan surage mata wahala, Jidda kuwa dama bata iya girki ba sede gyran daki da falo, kuma shine aikinta. Zarah kullum cikin jin haushin irin yanda Alh, yakeyima Falak da Ameer take, gani take yanzu ,ya,yanta ma sune wararru agurinshi, kome yasamu yace Ameer, akwai wani katon mall daya bude. Suna Ameer yasa, bakaramin jin Ameer yake acikin ranshi ba, gani yake kamar yajawo girmanshi koze fara fita dashi yana tayashi aiki, 

Hakan dayakeyi bakaramun kara wutar kiyayya yakeba azuciyar Zarah, kuma tayi shiru ne, kawai tana jiran dan lokaci, mutuwar takara nisa. Jidda andage dazuwa islamiyya duk da ba ajinsu daya dasu Falak ba, amma batajin kunyar shiga cikin kannanta.

Duk abinda bata ganeba, su Falak suke nuna mata agida, bata zuwa ko ina daga makaranta se gida. Al,amin bakaramin shiga tashin hankali yayi ba, saboda rashin Jidda, duk cikin yan matanshi, ita kadai yakema so metsanani, idan yakirata bata dauka, gashi dama can tahanashi zuwa gidansu,yarasa yanda zeyi yasameta, har kawarta Ameera yasa taje ta dubo mashi ita, amma koda taje tasamu Jidda ta tuba, tafara kawomata maganganun banza seda sukayi fada da Jidda, Haka tafito ranta abace. Data fadama Al,amin shima beji dadi ba, yasan tunda Jidda tadena yin harka shikenan bazata kara sauraronshi ba, haka yacigaba da kiranta, amma shiru.

Jidda ce zaune adaki, tadauko jakarta zata bama, Jalila kudi tasiyo mata, kati, murmushi tayi aranta tace wai yau nice dasiyan kati, lallai mata sunyi sanyi, dubawa tayi sede babu ko sisi aciki, tashi tayi taje gurin Umminsu tace Ummi dan Allah bani 500 Jalila tasiyomun kati.

Wani mugun kallo Zarah tayi mata, batasan dama cike take da ita ba, saboda wannan sabon halin data sake, gashi yanzu ko kudin datake samu hartana bata yanzu babu, gashi yau dan tabewa kudin kati ma suna gagararta.

Ummi ina magana kinyi shiru, Bazan bada ba, ko dole ne? Tunda rayuwar da kika daukarma kanki kenan, talauci ma yanzu kika fara, wata rana ma se kufin siyen turare sun gagareki, tunda dole se Alh, yazo gari sannan yake baku, suma kuma bawasu masu yawa ba, tunda yace bayason saba maku da kashe manyan kudi wai saboda gidan wani zaku.

Wlh kwandalata bazan baki ba, fita kibani guri. Amma Ummi bekamata kifadamun haka ba, kinmanta abunda nayi maki ada, amma yau saboda nace kibani 500 kike fadamun magana,,, saukar marin dataji ne yasata yinshiru.

Fita tayi tabanko kofar tanufi dakinta tana kuka, lallai tayarda sekana dashi kake zama wani abu agurin kowa. Wanka tashiga, sabulun nata ma yakare, ita kuma tafisonshi, dan Jidda babu abinda ta tsana irin taga jikinta yana baki, duk da bawata fara bace amma da tsiya takoma fara, haka tayi wanka da sauran sabulun daya rage tafito, manta ma saura kadan turarukanta duk sun kare, gashi bata saba da shafa turare daya ba.

Gaskiya bari Dady yazo gobe yabamu kudin siyan kayan shafa, bazan iya zama babu kudi agurina ba, wlh.

Saye suke akitchen suna girki, jalila tace wai ni Falak naji ko maganar Mal. Sameer bakiyi, kode harkin manta dashine? Hararta Falak tayi tace meye tsakanina dashi dazan tambayeshi.
    Jalila tace ai naga kedin tadaban ce agurinshi, kozakicemun bakisan mal. Sameer yana sonki ba? Falak tace kede makaryaciya ce wlh, kawai daga muna mutunci dashi zakice yana sona, shida babu ruwanshi, da kowa, kilama yanada budurwarshi yar jami,a mezeyi dani. Jalila tayi dariya tace uhm kede fadi gaskiya gashi nan harkin fara kishinshi, ruwan dake hannunta akofi ta watsa mata, fita tayi tana mata dariya. Rufe ido Falak tayi, ita kanta tasan tayi missing mal. Sameer, ta dade da fara sonshi, sede bata son tafara fada mashi ya wulakantata hakan yasa tahakura.

Zaune suke afalon Alh, suna fira, jidda tace yauwa Dady wlh kayan kwalliyarmu sunkare, dariya yayi yace to Mamana yanzu kuwa za,a baku, koda yake kekadai zanba tunda nakine yakare, jalila da Falak sukace a,a Dady hadamu. Wata irin harara Zarah ta watsa ma, Falak jin yanda take wani zakewa kamar ba AGOLAH ba. Tsaki taja har seda yafito fili, kara gyarama Ameer zama yayi akan cinyarshi, ya kalleta yace yade da tsaki, murmushi tayi tace Allah Alh, kai ke kara shagwaba, yaran nan, yan matane fa amma ace haryanzu kaine zaka rika basu kudin kayan kwalliya, ai gara ma abama Ameer dina shine yaro.

Dariyar jin dadi yayi yace a,a ki kyaleni da yarana, suma agurina yarane, kuma hakkin uba baya sauka daga kan yayanshi harse ranar daya aurar dasu, hakan yake hana mata karbar abun hannun samari, wanda yawanci shine yake jansu zuwa ga halaka, kuma da wannan damar samari suke amfani gurin yaudarar yan mata. Dubu goma goma yabasu, yace suje su siyi abinda sukeso, dubu goma ya mikama Jalila yace ansa ki kaima Baba mairo, na ameer ne, shima asiya masa kayan dadi, wata 5 yaciro yace tabata itama tasiyi abunda takeso.

20k yamika ma Zarah yace kema uwargida ganaki,  hadiye bacin ranta tayi, ganin yan kudin da yabata, bam bancin 10k ne tsakaninta da AGOLA, da kuma dan karamin yaro, wanda ada Alh, seyabata 50k kawai na kayan kwalliya, gaskiya dole ma tasake tsari, seta cire Falak Da Ameer azuciyar Alh, shima sena maidashi rakumi da akala.

Jidda ce tafito zata kasuwa dan su Jalila sunce se gobe zasuje, gashi driver bayanan, ita kuma bazata bari se gobe ba, tafiya take zataje bakin titin domin tarar abun hawa, se sababi takeyi, yama za,ayi 10k ta isheta siyan kayan shafa, to mema zansiya, 10k ai basu kai kudin man datake shafawa ba ma, bare akai gurin sabulai, da turaruka. Gaskiya dasake wlh,,,,, karar horn dataji ana yimata ne, yasata tsayawa, Al,amin ne yafito har yana tuntube ya iso gurinta fuskarshi dauke da murmushi. Bayan sungaisa yace haba Dear meyasa zakimun haka? Jidda tace muje cikin mota muntsaya bakin titi kada Dady yagammu.

Tafiya sukeyi hannunshi cikin nata, tawani lumshe ido, ita kanta tasan tayi missing Al,amin. Yace ina zakije haka cikin rana? Tace. Wlh kasuwa zanje siyan kayan kwalliya. Murmushi yayi yace haba ba girmanki bane zuwa kasuwa, ina laifinma kije mall aizefi. Aranta tace idan kudina sunkai shiga mall ko. Karya kan motar yayi zuwa wani babban mall, suna tafiya yana fadimata irin yanda yayi missing dinta, har suka isa.

Siyayya yayi mata takusan 100k, duk abinda batada shi seda tadauka, azuciyarta fadi take Allah nagode maka daka kawomun Al,amin dabansan yanda zanyi da 10k ba wlh.    Haka suka fito suka shiga mota yakalleta yace Baby muje gidana mana nayi missing dinki fa, kallonshi tayi tace Dady na gari fa, kashe mata ido yayi yace just 1 hour plsssss, yana kamo hannunta, murmushi tayi tace ok badamuwa muyi sauri. (  Wa iyazubilla, Allah katsaremu daga sharrin zuciya, dason kudi, domin abinda yake faruwa kenan azamanin nan, rashin godiyar Allah, mutane basa taba godema Allah, daga abinda yabasu duk mun kadan dinshi, hangen nawasu shine yake kara dulmiyar damu zuwa ga halaka. Allah kacire mana son zuciya, ameen.)

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/29, 2:15 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ ( H, O,N,A)

Part 55.....60

 Tundaga ranar Jidda takoma ruwa, fiye da baya, sosai Al,amin yake kashe mata kudi, dan shide Allah yajarabeshi da son Jidda, itama haka tana masifar sonshi, dan danan Zarah takara jawo Jidda jikinta ganin yanzu tana samun kudi fiye da da. Haka tafara zirya zuwa Zariya, itama kanta Asabe tayi murnar dawowarta, dan tasan zata cigaba da cin dadi, dan ita tasan abinda Jidda take aikatawa, kuma bata damuwa, dan itama tsohuwar yar duniya ce. Jidda har kasar waje tafara fita ita da Al,amin sbd yanzu arzikinshi yakara habaka, har waje yake zuwa saro kaya, kuma duk sanda zeje tare suke zuwa da Jidda, dan Jidda akwai gayu da gyara, bata wasa da kayan mata.

Zarah ce zaune adakin Asabe, tagama fadamata abinda takeso bokayayi mata. Asabe tace ai dama kyaleki nayi mutuwar tadanyi nisa, sannan inzo maki da irin maganar nan, segashi kinrigani, bara inkira Dije muje, amma ai baje yuwa ba ace AGOLA tafi masu gida. Kuma wlh wannan yaron damuke rainawa, idan har bakiyi da gaske be, wata rana zesaki kuka daga shi har AGOLAR.

Bayan Dije tazo ne suka fada mata abinda suka shirya, murmushi Dije tayi tace meyasa kukeson yin abu bakwa tunawa da mutanen gari, kunsan fa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, akwai matsala 2 dazaku fuskanta idan har kuka aikata abinda kukace. Tafarko de idan kuka sa aka kori Falak da Ameer daga gidanki, mutane babu wanda zasu zarga seke, har Mijinki keze zarga.

Matsala ta 2 kuma idan har kuka kashe Falak da Ameer, wlh ina me tabbatar maki da kotu seta daureki, dan nasan mijinki baze taba yarda dakeba, dole yasa yan sanda su bincikeki, 
Asabe tace wlh shiyasa nakesonki kawata, yanzu me kike ganin za,ayi?  Gyara zama Dije tayi tace zanbada shawara 1 amma fa idan tayi maku, Zarah tace wlh kifada zatayi, 

Nafarko de za,a kashe Ameer, amma ta hanya mafi sauki wanda babu wanda zeyi zargin kasheshi akayi.
Na biyu kuma, dole zaki mallake Alh, za,a kawar da kanshi daga Falak, tayanda zemanta da ita acikin gidan kome zakiyi mata baze ce komai ba, sauran yan gida kuma ke keda iko akansu, bakamar wannan tsohuwar munafukar, wadda kika yarda da ita sosai.

Se kuma Jalila, ita kuwa diyarki ce kinsan yanda zaki tafiyar da ita. Falak kuwa kada kiyi mata komai, hakan zesa kifita daga zargin mutane, Ameer dama kowa yasan beda lafiya. Amma Falak kimaida ta ita da almajira basuda bam banci, duk wannan dadi datakeji kihanata, Mairo takoma girki kawai, sauran aikin gidan sukoma kanta. Wannan kyawun nata kimaidashi muni, kuma kirabata kwana daki daya da Jalila, 

Kimaida ta store tarika kwana ita da kwari sucinye wannan shegen jikin nata, duk wani kayan more rayuwa ki anshe su, kayanta ma zanbaki wasu tsofaffin kayana ki kaimata, tarika sawa, ko aike kasuwa yatashi daga kan driver yakoma kanta.

Kuma kicema Mairo tamaida rikon Ameer hannun Falak bazaki iya cin abincinta ba, tana renon yaro me zubda miyau. Daga karshe kuma kisamu dan kwaya ki aura mata shi, idan bahaka ba kina gani masu kudi zasu aureta, dan kinsan tafi yayanki kyau.

Shiru Zarah tayi, Asabe tace yanaji kinyi shiru, tobari infada maki, wlh ba,a samun duniya da tausayi, idan baki sani ba, nidin nan seda nakashe mutane 2 saboda kudi, kuma duk mazaje nane, nakuma gudu da dukiyarsu, Babanki ma........ Saurin hadiye maganar tayi tuna dawa take magana tayi. Babanki ma saboda irin Son danake mashi ne, yasani zuwa naroki ya aureni, kinsan tunda nake bantaba son wata halitta kamar Babanki ba. Shiyasa gashi nan muna zaune lafiya abummu. Murmushi Dije tayi jin irin saurin kwaskwarimar da Asabe tayi.

Dije tace idan har kika iya aikata abunda nace maki, kawai kihangoki cikin jerin manyan mata masu fada aji akaduna, yanzu ina kawarki Karima, bakince tunda mijinta yamutu ba, tabar garin tana can Abuja gidan kudi, batada aiki sefita kasashe, ina da bakinki kikecewa yanzu ko wayarki bata dauka saboda tayi kudi, wani lokacinma sese me aiki tadauka tace tana bacci.  

Haba Hajiya kalleki fa, yanda kike da kyan nan rashin samun kudi masu yawa ne da hutu yarage maki kyawunki, yanzo dan kasuwancin dakikeyi ma kudin duk sushige gurin boka, yanzu haka kila bakida wanda zamuje gurinshi yanzu, dan kinsan aikinshi kamar yankan wuka ne shiyasa yakeda amsar kudi masu tsoka.

Zarah tace wlh, ashirye nake da inyi abinda yafi hakama matukar zansamu kudi, kuma arayuwata babu wadda na tsana kamar Falak, zanyi duk yanda zanyi in kunta tama rayuwarta, bazata taba fin yayana ba, ita Kuma Jalila nasan yanda zanyi da ita, kunsan babu abinda ta tsana kamar fushi na, ko kuma ince zan tsine mata, bakaramun shiga tashin hankali take ba, idan taji furucina ba.

Saboda tana zuwa islamiyya, kuma suna aiki da abinda ake koyamasu sosai, Mairo kuwa kubarni da ita, akarkashin ikona take, kome zanyi bazata iya fadama kowa ba, Alh, ne kawai zata iya fadamawa kuma shima zan mallakeshi. Dariya sukayi gaba daya. Suka tashi zuwa gurin boka.

Wata irin dariya boka yayi yace lallai Hajiya kinzo da babban aiki, kuma aikinki zeci kudi sosai, dan wannan karon zakisani karya maganata dan banayin aiki 2 alokaci 1, amma idan har zaki saki kudi bakida matsala.

Zarah tace boka kamar nawa ne kudinka? Aikin Alh, mesauki ne, zaki bada 150, shikuma Ameer nashi 200 ne, sekizabi 1 idan bakida kudi.

Zarah tace atemaka mun boka yanzu babu kudi sosai, amma ga na Alh, afara yimani aikinshi, se abani na Ameer dana koma bayan kwan 2 nayi maka alkawarin zanturoma Inna Asabe, kudin aikin Ameer takawo maka.

Dije tace boka atemaka mata, kasan yanzu munzama daya. Magani 2 yadauko yabata 1 yace wannan zaki saka ma Alh, acikin abinci, dazaran yaci kingama dashi, wannan kuma wuta zaki samu ko garwashi kifita waje kizuba kamar yanda hayakin nan zetashi sama baze kara dawowa ba, haka tunanin Falak zefita daga zuciyar mijinki, ko yaganta baze tuna amfaninta agurinshi ba.

Wani dan butum butumi yadauko yakama wuyanshi yasa zare yashake wuyan, yace wannan kuma Ameer, tundaga yau babu abinda zekara shiga cikinshi, kome yaci iyakarshi makoshi zedawo, nabaki nan da wani lokaci zemutu. Kuma daya mutu Alh, zemanta dashi, zakici duniyarki da tsinke, sauran kuma sekinje gurin me hukunci. Dariya yasa yace kutashi kutafi, Dije kije sebayan anbaku kudin kwa dawo, Zarah de bata fahimci abinda yake nufi ba.

Baba Mairo itadasu Falak suna zaune adakinta suna fira, ita kuma tana bama Ameer abinci abaki, Jalila tace wai gashi har yamma tayi amma Ummi bata dawoba, bansan meyasa yazu Ummi yawan  zuwa Zariya ba, wanda ada batason zuwa.

Baba mairo tace keko tunda tana da mahaifi araye ai dole tarika zuwa. Aranta kuwa tana fadin Allah yasa bawani mugun abun bane yakaita...... bata karasa ba, Ameer yashiga amayar da abunda yakeci, cikin sauri ta dagashi tana sannu ka kware ko,

Ruwa Falak tamika mata tana fadin aishine yacika cin tsiya, ke kuma Baba mairo kita bashi abinci, karbar ruwan tayi tana fadin tunda beda baki aidole inrika bashi abinci akai akai, kodan ke abincin beda meki ba ne, Jalila tace kyaleta Baba mairo sotake shima yazama kamarta yar siririya,,,,,,,, ruwan Baba mairo tabashi, yana amsa yasake amayoshi.

Tadashi zaune tayi takara bashi, abun tunbe basu tsoro har yafara basu, jikinshi Bab mairo ta taba taji babu zafi, tace tomeke damunka Ameer haka? Jalila tace Baba kawai akira driver yakaimu asibiti tunda dady nenan nasan gobe zedawo.

Shiryawa sukayi suka kulle gidan suka ba megadi key din suka tafi, kafin su kai duk yajike Baba mairo da miyau, dan har miyan baya iya hadiyewa. Sunazuwa suka wuce gurin Dr, bayani Jalila tayi mashi, ruwa yadauko yabashi amma yamaidoshi.

Abu kamar wasa jikin yaro yafara rikicewa, tun likita yana daukar abun wasa, shima yafara shiga damuwa, daki yabasu aka kwantar dashi aka samashi karin ruwa da allurai, sannan yayi bacci.

Baba mairo babu wadda take zargi se Zarah, dan tariga data lura duk lokacin da taje Zariya sewani abu marar kyau yafaru akansu Hajjo, yanzu gashinan ta kauda Hajjo takoma kan danta, duk da tasan cewar itace tayi sanadiyyar maidashi dolo, yanzumma bata debe tammanin tanada sa hannu acikin wannan ciwon nashi ba.

Jalila takira dadynsu awaya tafada mashi, yace gashi nan yanzu zetaho, haka sukacigaba dazama,  Falak se kuka takeyi, Jalila tana lallashinta, duk itama hawayen takeyi.

Koda Zarah tadawo, megadi yabata key, yace mata sunje asibiti kai Ameer, murmushi tayi aranta tace boka aikin ka nakyau, saurin shiga cikin gida tayi, kayanta kawai ta aje tadauko gawayi tadorashi akan electric  burner seda yayi ja, sannan takashe, dauka tayi tanufi gurin part din Hajjo daga baya ta ajeshi, maganin tadauko tazuba aciki, nan take hayaki ua turnuke, sama yayi tayi har yacinye, kakkabe hannunta tayi tana fadin su AGOLA anzama baiwa. Saura kai Alh, Allah yamaidoka gobe.

Ciki tashiga tayi wanka tana saka kaya taji horn din. Alh, murmushi tayi tace wato kai game da anayi maka waya harkataho, nasan Jalilan banzan nan ce zata fada maka, kema zaki dawo kisameni ne,

Da sallama yashigo yace ah, Hajiya bada ke aka tafi asibitin ba? Yatsina fuska tayi tace nim yanzu nadawo daga Zariya, megadi yake fadamun, wanka nayi nake shirin tafiya, ok fito mutafi gaba daya. Falak ce takiraka ko? Shiru yayi yana kallonta, jin ankira sunan Falak seda kanshi yasara.

Murmushi tayi tace yanaji kayi shiru, Fala...... tsawar daya daka mata ce tasa ta yin shiru, meye haka wacece kuma wata Falak, kada inkara jin wannan sunan agidan nan, kema kika santa, Jalila takirani amma kirika fadamun wani suna, banaso, kiwuce mutafi.

Suna zuwa office din likita yawuce, bayan sungaisa Dr, yace agaskiya Alh, nakasa gano wace irin cutace ajikin Ameer, duk wani gwaji munyi mashi amma bamu sami wata cuta dazata nuna mana asalin ciwon shiba.

Abinda nake ganin zefi kumaidashi gida acigaba dayi mashi na hausa, dan gaskiya ina ganin ciwonshi kamar akwai aljanu aciki. Alh, yace hakane, nikaina nafara tunanin haka, tun sadda yafara zubar da miyan bakinshi, da kuma kanshi da baya zama, haryanzu fa Ameer baya iya zama. Bakomai nagode bara naje mutafi, dr, yace nacire mashi karin ruwan ma dan naga jikinshi baya bukatar ruwa, sede matsalar rashin cin abincin shi, idan har kuka koma gida yacigaba da mayar da duk abinda yaci, zan iya zuwa gidan, ko insa azo arika samashi karin ruwa. Godiya sosai, yayi mashi yatashi suka fita.

Tunda yashiga dakin Jalila da Falak sukayi mashi sannu dazuwa, ya amsa yace Jalila yagidan, tace lfiya lau dady, ko kallon inda Falak take beyiba. Baba mairo tagaisheshi ya amsa yana tambayarta Ameer da jiki.

Zarah farin ciki ne aranta, fal, ganin yanda yayi ma Falak, sukuwa basu kawo komai aransu ba, ganin halin da ake ciki, Alh, yace sutashi sutafi gida, ansallamesu, anan yayi masu bayanin da Dr, yayi mashi. Baba mairo tace idan ko haka ne, Alh, se akaishi gurin Malami. Zarah tace koma de menene kuwuce muje, gida. Kallon mamaki Baba mairo tabita dashi, haka suka wuce da driver ita kuma tabi Alh, aranta tana fadin dole yau kaci maganin nan ko aikina zefara dawuri.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[5/29, 10:23 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah,
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@(  H,O,N,A)

Part 60..... 65

Suna zuwa gida Baba mairo ta kwantar da Ameer, su Falak kuma suka wuce daki domin yinsallar magrib. Wucewa kitchen Baba mairo tayi domin dumama masu abinci tayi, shikuma Alh, tadora mashi abinci mesauki, daki takoma tayi sallah.

Bayan tafito ta koma kitchen tana hadama Zarah abincin Alh, Zarah ce tashigo kitchen, din, tace yau mairo jeki dakina kidauko mun wayata bisa gado, tana fita tayi saurin bude cooler din Alh, taciro magani tazuba, kokarin maidawa tayi azaninta, juyawar dazatayi taci karo da mairo tana kallonta mamaki dauke afuskarta.

Cike da duniyanci Zarah tace shigo mana Mairo naga kintsaya kina kallona, Mairo tace dan Allah Hajiya wane irin magani ne kika sama Alh, kinga duk abinda yasame shi ni za,a zarga tunda ni nayi girkin.

Murmushi Zarah tayi, tace bazan fada maki ko maganin menene ba, idan yaci kome yasameshi aka kamaki, zakiyi bayani, ido waje Mairo tace kirufa mun asiri dan Allah hajiya.
Zarah tace naji. Amma da sharadi, banaso kowa yaji wannan maganar, kuma daga yau duk abinda zance maki banason gardama kinsan de ni nakawoki gidan nan ko?  Saboda haka kina karkashin ikona, banason shishshigi, ki tsaya amatsayinki na me aiki, daga yau banaso ki kara fitowa daga dakinki matukar Alh, na gidan nan.

Kuma daga yau, zaki maida Ameer hannun Falak, dan baze yuwa kina girki kuma kina renon kazamin yaro ba, aiki yanzu ze koma girki kawai, naruwanki da wanke wanke nasamu wadda zata rikayi mani harma da wankin kayana.

Inafatan kingane menake nufi, idan kinbi umarnina kicigaba dazama agidan nan, idan kuma kinki, zaki tafi kuma kibar amanar da Hajjo tabaki, dan nasan kafin tamutu tamika amanar yaranta agurinki.

Zabi yarage naki, kuma wlh idan kika kuskura kika rika shiga harkar Falak sekin barmun gidana. Zaki iya tafiya. Fita Baba mairo tayi tana kwalla, wannan wane irin sabon yanayine yashigo gidan nan, anya Hajiya bata fara shaye shaye ba? Ya Allah katsare bayinka kuma marayunka, tabbas Falak nasan rayuwarku zata shiga, kunci, sede bazan bari inyi abinda za,a koreni daga gidan nan ba, nasan idan natafi zakifi shiga damuwa sosai, kuma nasan wasiyar ummanki bazata bari kibar gidan nan ba, dasemu tafi tare.

Abincin tadauka takaima Alh, yana shirin zuwa yaga Ameer tashiga, tace ina kuma zakaje Alh,? Yace Ameer. Zan dubo, tace daga can nake yasamu bacci, kuma yaci abinci, kabarshi yayi bacci tunda yasamu yayi. To Alhamdulillah, Allah yakara bashi lfiya, wlh har hankalina ya kwanta, banason ciwon yaron nan.

Abinci tazuba mashi tana ta janshi ta wasa, sewani shige mashi takeyi, shi kuma duk ya rude, abaki tadebo zata bashi, ganin yana niyar yin bismilla, yasata fadawa jikinshi, dariya yasaka yana shirin yin magana tayi saurin saka mashi abincin abaki.

Taunawa yakeyi yana fadin Hajiya yaude naga alamar amarci kikeso musha, ko? Kara debowa tayi tasaka mashi yakarba, tana ta yimashi kwarkwasa, shikuma duk ya rude. Ahaka haryagama ci beyi bisimilla ba.

Yana gama ci yasha ruwa, ana take yai kanshi yayi mashi nauyi, rike kanshi yayi, kamoshi tayi ta dorashi bisa cinyarta tana shafa bayanshi, da haka haryaji kan ya lafa. Shiru yayi nawani dan lokaci, sannan yatashi yace zanyi wanka idan nafito se inje inga jikin Ameer. Bata fuska tayi tace nace bazaka jeba, kabari se gobe. Nan take yace to hajiya, inje inyi wankan ko?

Wani murmushi Zarah tayi, aranta tana fadin wlh dagaske maganina yaci, kai amma dole incika ma boka alkawarinshi. Kara daure fuska tayi tace zauna inason magana da kai, zama yayi yace inajinki. Kudi nakeso zansaro kaya. To to kamar nawa kike bukata? Dubu dari 5 nakeso. 
    Yace toshikenan yanzu na hannuna basu kaiba, tace ina check dinka? Yace yana nan, to kadauko karubutamun gobe se inje incira. Tashi yayi jiki na rawa yadauko ya rubuta mata, yamika mata, tace haba Alh, atsaye zaka bani kamar wata yarka, yace yi hakuri Hajiya, dukawa yayi yabata. Tace tashi kaje kayi wanka idan kafito kuma bance kafita ko ina ba, sallar isha,in ma kayita agida, idan kagama katsaya afalonka kayi kallo, idan kanajin bacci kayi kwanciyarka. Yace to Hajiya sekin shigo.

Fita tayi tana me cike da fari ciki tana shiga dakinta tace wlh, Alh, sekayi dana sanin yimani kishiya, sena maidaka abun tausayi arayuwa, daga yau bakai ba Ameer da shegiyar AGOLAR KA.


Juyawar dazatayi taci karo da Jalila tana gyara mata gadonta. Cike da firgici, tace Uban waya kawoki dakina? Jalila da tunda taji kalaman Umminta jikinta yafara rawa, kafin tayi magana hawaye sun wanke mata fuskarta.

Jawota tayi ta kwada mata mari tace ina magana shine zakimun shiru, wato labe kikemun ko, Jalila tace dan Allah Ummi kiyi hakuri, nibanji abinda kika ceba, kawai nashigo inamaki gyaran dakine.

Zarah tace idan ma kinji, bakiji karya ba, kuma zauna kibude kunnuwanki da kyau kije abinda zan fada maki, nasan sarai kinji maganar danayi, to haka yake bakiji karya ba, tunda Babanku ya auro uwar su Falak naji natsanesu, gashi nj bantaba haihuwar naminj ba, amma tana zuwa tahaifa.

Saboda haka idan harkina kishina, kuma kindaukeni amatsayin uwa, wadda ta tayi renonki tunkina jini harkika koma tsoka, akasa maki kashi, kika girma acikina, ki hanani bacci, kocin abinci, kika hanani sukuni, sannan nasha wahalar haihuwarki, seda nadauki tsawon awa 1 ina nakudarki kafin kika buda jikina kika fito.

Nashayar dake daga jinin jikin, suk dare duk rana kina tare dani, bana bacci sekinyi, kimun fitsari da kashi in wanke, har kika girma ina dawainiya dake harzuwa yanzu. 

Shin akwai wani umarni dazan baki ki kasa binsa? Kai tashiga girgizawa tana kuka, jin yanda Umminta tasha wahala akanta. Murmushi Zarah tayi ganin yanda jikin Jalila yayi sanyi.

Tace Jalila amatsayina na mahaifiyarki, inaso duk abinda zakiga ya canza agidan nan kada kiyi magana ko kuma kiyi tambaya akanshi.
    Daga yanzu tarayyarki da Falak tazo karshe abanason ina ganinku tare, bazata kara zuwa isilamiyya ba,  kuma ayau zata bar dakinki, zata koma store itada kaninta dan renonshi yakoma hannunta, kuma daga yau itace sabuwar me yimun wanke wanke da wanki, harma dazuwa kasuwa.

Idan harkika kara yima Dadynku maganar Ameer ko Falak, sena tsine maki, dasauri Jalila tadago kanta tana kuka, tace Ummi dan Allah kada kitsine mun, wlh wuta zanshiga, nayarda zanbi duk abinda kikace, amma kijanye maganar tsinuwa.

Murmushi Zarah tayi, tace bazan janyeba harsenaga kinbi umarnina, ko Alh, yamaki maganar makaranta, nasan naze saka da Falak ba, danshima yamanta da ita, bance kimashi maganarta ba. Kinji abida nafada maki ko? Tace E Ummi, kiyi hakuri dan Allah, tace shikenan nayi tashi ki kiramun Falak.

Fita tayi tana wani irin kuka, tana zuwa takalli Falak gaba daya tausayinta yakamata. Falak tace Jalila lafiyarki kike kuka? Tace bakomai kije Ummi nakira, fita tayi tana murmushi tace yanzu haka laifi kikayi mata ko, bara inje inji mekikai mata, idan har bata mata rai kikayi kisani nima baruwana dake. Wani sabon kuka ne yazoma Jalila, tanajin tausayin Falak sosai.

Tana zuwa tayi sallama tace Ummi hala Jalilace tayi...... Saukar marin datajine yahanata karasa maganar datakeyi, zaki tsugunna ko kuwa sena takaki agurin nan, munafuka me kama da Uwarta. Mamaki ne yakama Falak jin yanda Ummi take zagin Ummanta, zama tayi akasa, taan fitar da kwalla.

Zarah, tace kibude kunnuwanki da kyau kiji abinda zan fada maki, daga yau rayuwar gidan nan, tacanza. Babu ke babu sauran jin dadi, dake da shegen kaninki, inaso kije kicire kayan jikinki daga yau kin koma yar aiki agidan ana, zaki rika wanke wanke, da wankina.

Kuma daga yau zaki koma store da kwana, koda wasa naga kafarki ta taka falon Alh, ranki seya. Baci, ga kaya nan kidauma ki kai store domin shine dakinki, tashi kibani guri.

Fitowa tayi tana kuka, tanufi dakinsun haka tazauna taci kukanta dan Jalila tana dakin Baba mairo,  haka falak ta cire kayan jikinta tana tunanin wasiyar da ummanta tayi . Mata, akan kada tabar gidan harse aurenta. Wani irin kuka tashigayi.

Kayan jikinta tacire tadauki wanda Zarah tabata tasaka, kayan sunyi mata yawa, gashi duk sun kode, kuka kawa Falak takeyi, haka Tanufi store ta gyara shi sannan ta aje kayanta. Agurin domin yayi mata kadan.

Jidda ce kwance abisa kirjin.  Al,amin yana wasa da gashinta. Al,amin yace baby na akwai wani friend dina bature ne ahi dazu muna chrt, yaga pic dinki akan fp na, yace mun gaskiya yana sonki, kuma zeso kije mashi hutu, a london yake dazama, me kudine na karshe, idan kikayi harka dashi zakizamo Babbr Hajiya.

Ammafa kisani bawai dan banasonki nace zakije ba, kawai abokina ne sosai, kuma yamun mutunci lokacin muna school, koyanzu ma yana temaka mun sosai, idan banida kudi, shine yake bani, nayi mashi alkawrin wata rana zan kawoki wajenshi kiyi mashi koda wata 1 ne.

Ammafa bayanzu ba, bamma saka rana ba, amma kowane lokaci zaki iya tafiya, yakika ce. Murmushi tayi tace da gske zan samo kudi? Yace sosai ma, kinga dakin dawo semuyi aurenmu ko? Tace hakane, insha Allah zamuyi aure dana dawo. Dariya yayi yajawota yarungume.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/30, 2:45 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO 
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 65.....70

Tun daga wannan rana Falak takoma me aikin Zarah, Alh yamanta da Falak, ko Ameer yadena tambayarshi, tunda Zarah tace mashi ya warke, kuma tana kula dashi, gashi yanzu baya zama sosai, 

Kudi sosai Zarah take samu agurinshi, yazama matar dazama mijin, Baba mairo da Jalila kuwa sunzama yan kallo, sosai suke tausayin Falak, aboye Baba mairo take temaka mata,ga aiki ga renon Ameer, kusan kullum seyayi suma tafi 3 saboda baya iya cin komai.

Damma Falak tana yimashi addu,a shiyasa yake dan samun sauki,  Baba mairo tace mata idan zata bashi abinci tarika yin addu,a, dahaka yake samu yana cin loma 3 ko 4.

Falak duk ta rame tayi duhu, gashi bata samun bacci sosai, dan store din wasu kwari ne, suke cizonsu, kullum cikin dare Ameer kuka yakeyi, se idan ta goyashi ne kadai yake bacci, ita tahakura da bacci, wani lokacin a kitchen take samu tayi bacci, idan Zarah bata leko ba.

Jalila kanta tayi rama, saboda bakaramar damuwa tashiga ba, datayi nufin temakon Falak seta tuna kalaman Umminta, gashi tana tsoron fushin Umminta, saboda a islamiyya anfada masu muhimmancin Uwa.

Akwai ranar da Alh, yadawo cikin dare yarika jin kuka kamar na yaro, tashi yayi yace Zarah kamar kukan Ameer nakeji, tashi tayi tace wane Ameer kuma, bacin ya dade dayin bacci, kila de makwafta ne,

Alh, yace yaushe harzamu iyajin hayaniyar makwafta agidan nan, muda mukeda da nisa dasu, Zarah tace to karya nakeyi, kasan ai nasaba yinta. Alh, yace Allah yabaki hakuri bahaka nake nufi ba, tace zauna bara inje inlekosu.

Fita tayi tana surutai, store tanufa, Falak tagani se kuka takeyi Ameer kuma yana hannun Baba mairo yanata suma, Zarah tace wai meye haka, dan iskanci zaku fito ku hanamu bacci, Baba mairo tace Haba Hajiya kalla fa kiga yanda yaron nan yake suma, ki kira Alh, mukaishi asibiti, tundazufa beci koma ba.

Zarah tace wlh babu inda za,a kaishi, daukarshi kushiga dakinki kiyi mashi wanka ze farfado, kuma ki kulle dakin banason karajin kukanshi, wlh idan kuka bari Alh, yafito sekinbar gidan nan gobe, wucewa tayi tana zage zage.

Dakin Baba mairo suka wuce, ruwan sanyi Falak tadauko suka samashi da kyar yafarfado, kuka yasaka, haka sukayita lallashinshi Falak tana mashi addu,a se can suka samu yayi bacci. Kwantar dashi Baba mairo tayi,

Kuka Falak tasa tace shikenan Baba mairo shima kila tafiya zeyi yabarni, nashiga 3 ni kuma rayuwata haka zata kare, wlh gara mutuwa ta da rayuwata, rufe mata baki Baba mairo tayi itama tana kuka.

Tace Falak kiyi hakuri, duk tsanani yana tare dasauki, kuma duk wanda yayi hakuri yana tare da nasara, ninasan wata rana komai zewuce, Falak tace Baba mairo kina ganin yanzu ko Dady baya nemammu.

Ina alkwarin daya dauka akan rikemu da amana, gaskiya Dady yazama butulu. Baba mairo tace Falak, akwai abinda nasani wanda baki sani ba, banyi niyar fada maki ba, amma dole infada maki kodan ingoge bakin panting da Zarah tayima Alh, agurinki.

Anan Baba mairo takwashe komai tafada ma Falak, kuka sosai, Falak takeyi, Baba mairo tace ko tan tama banayi wannan maganin da Zarah tasama Alh, maganin mallaka ne, domin rannan inajinsu tana yimashi tsawa, shi kuma duk yarude, yana bata hakuri, bakiga yanzu kamar itace mijin shine matar ba?

Kiyimashi uzuri, wata rana asiri zetonu, Jalila ma tana cikin damuwar halin dakike ciki, babu yanda zatayine, dan Zarah tace idan har tarika shiga harkarki zata tsine maki, shiyasa tace makarantar kwana zata tafi bazata iya cigaba dazma tana ganinki cikin damuwa ba.

Falak tace yanzu Baba mairo haka zamu zauna da Ameer babu magani, tace kiyi hakuri gobe idan zakije kasuwa zanbaki kudi kitsiyo mashi magani, haka Baba mairo tayita lallashin Falak, harta hakura, kuma tayi alkwarin saka Alh, cikin addu,a. Dahaka suka kwanta, rabon datayi bacci medadi kamar na yau harta manta.

Washe gari bayan tagama aikinta, taci abinci tayi wanka, tasaka kodaddar atamfarta, ta amshi kudi agurin Baba mairo dan zataje kasuwa, dakin Zarah tashiga da sallama tace mata tashirya, kallonta tayi tace dauka ga kudin nan, kidauka, saura kije kidade,

Fita tayi taje yima Baba mairo sallama, tace Baba mairo natafi, kudi Baba mairo takara bata tace amsa, Falak tace nameye Baba? Tace idan kinje kisiyo turare naga naki yakare, kwallan idonta tagoge, tace nagode Baba mairo, tace haba Falak ai bakomai, yisauri kije kidawo ki amshi Ameer inshiga kitchen kafin Zarah tafito. Kallon Ameer tayi yana bacci, duk yarame,fita tayi tana goge idonta.

Abakin gate taci karo da Alh, yana kokarin shiga mota, binta da kallo yayi, Zarah wadda take gefenshi tace lafiya de naga kana kallonta?  Yace naga bansanta agidan nan ba ne shiyasa, murmushi tayi tace oh, sabuwar me aikina ce, mota yashiga yace yatafi.

Bayan Falak tagama siyen abinda zata siya, taje chemist tasiyoma Ameer maganinshi, sannan taje gurin siyen turarenta. Bayan tasiya, tajuya kenan taji kamar ana kiranta. Haka tawuce batare data juya ba.

Malama Falak, yau kuma babu magana inata magana, juyawa tayi domin taji muryar malam. Sameer, ido suka hada dashi, yana cikin wani yadi mekyau yakara haske, duk se kunya takamata ganin kayan dake jikinta,gashi duk tayi baki.

Bayan sungaisa yace Falak yagida, nima jiya nadawo, shine yau nafito shago, ashe dama kina shigowa kasuwa, ke kadai, yau ina Jalila ne? Shiru tayi kanta yana kasa tana wasa da ledar hannunta, idonta har yafara kawo kwalla.

Yace Falak lafiyarki kuwanaga kamar kina cikin damuwa, gashi naga duk kin rame, inafatan de lafiya? Hadiye kwallanta tayi, tace malam, rana tanayi kada ajirani agida, zanwuce. Murmushi yayi yace shikenan, tunda bazaki fadamun ba, kodan nan kasuwa ce, amma anjima zamu hadu a islamiyya ko? Shiru tayi, yace Falak bani no wayarki mana, tace aikam banda waya, yace tobani ta Jalila, tace barade Inbaka ta Baba mairo, kallonta kawai yakeyi hartagama saka mashi, tamika mashi, amsa yayi yace sena kiraki ko.

Godiya yayi mata ta tafi, kallonta yacigaba dayi, jikinshi yana bashi kamar tana cikin damuwa, ammade bari anjima zan tsareta seta fadamun koma meke damunta, ko intambayi Jalila, haka yajuya yana me farin cikin ganin abin sonshi, dan tunda suka gama makaranta yake dokin dawowa yaganta, kuma wannan karin yayi alkwarin fada mata abinda ke cikin ranshi.

Tun daga nesa tafara ganin mutane akofar gidansu, haka takarasa, gabanta yana faduwa, da kyar tasamu tashige cikin gidan, Jalila tagani tana kuka, saurin matsawa tayi tana tambayarta meyafaru, hannunta Jalila taja suka shiga cikin gida, dakin Baba mairo suka shiga.

Yarda ledar datake hannunta tayi, tasaka wani irin kuka ganin Ameer shimfide akasa bisa tabarma, duk ya mimmike, kuma anrufeshi da zani. Baba mairo shikenan shima ya mutu ko? Kamata Jalila tayi suka zauna, tana bata hakuri.

Baba maito tace kidena magana Falak kada kiyi sabo, kinsan Allah yafimu sonshi tunda har ya amshi abunshi, addu,a yakamata kiyi mashi, kuka kawai Falak keyi, dahaka wadda zatayi mashi wanka yashigo, komawa gefe Falak tayi tana kallon yanda akeyima Ameer wanka ko motsi. Bayayi.

Bayan angama Alh, yashigo shima yana kuka, hankalinshi duk yatashi da kyar yadauki Ameer yafita dashi akayi mashi sallah sannan suka kaishi makwancinshi. Zarah kuwa tana falonta, tarufe fuskarta. Da hijabi duk wanda yashigo gaisuwa seya dauka kuka takeyi,  haka yan unguwa suka rika shigowa yin ta,aziya.

Washe gari Falak ta tashi da zazzabi me zafi, bata iyama tashi ga ciwon kai, Baba mairo duk tashiga damuwa, Jalila cetasamo mata magani adakin Zarah, haka akayita karbar gaisuwa har kwana 3, su Asabe da kawarta Dije ma sunzo.

Jidda kuwa batama san abinda akeba dan suna Lagos ita da Al,amin.   Bayan sadakar 7 su Asabe suka koma suna cike da farin cikin abinda Zarah tayi masu dan tabasu kaya da kudi masu yawa saboda tana cikin murnar aikin boka yayi.

Malam. Sameer zaune a dakinshi yana tunanin kome yahana Falak da Jalila zuwa makaranta, gashi no da Falak tasa mashi yakira harya gaji tun aranar amma bata shiga, jawo wayarshi yayi, yaduba agogo yaga karfe 9 n dare.

No yakara kira, cikin sa,a kuma tashiga, zaune au Baba mairo da falak suke adakinta, dan tunda Ameer yarasu adakin Baba mairo take kwana, wayar Baba mairo ce tayi kara, dauka tayi da sallama,  bayan sun gaisa yace Baba mairo dan Allah ko Falak tana nan? Cike da mamaki tace e tana nan, wayene, yace Malaminsu ne na islamiya Sameer.

Washe baki Baba mairo tayi, dan tanajin labarinshi agurin Falak da jalila,hartake tonan Falak tana cewa kode siriki tasamo mata. Baba mairo tace e gata nan bari abata, mika mata wayar tayi, bayan sungaisa, yace haba Falak tunda kika bani no kuma bansake ganinki a makaranta ba, gashi idan nakira ma bata shiga.

Na tambayi yan ajinku sunce wai kindena zuwa Jalila ce kadai take zuwa itama ba sosai ba. Meyafaru dan Allah, kinsan tun rannan naga kamar akwai abunda kedamunki.

Shiru tayi saboda wani kuka daya taho mata,  Baba mairo kallonta kawai takeyi, tama karajin tausayinta. Hello Falak kinajina kuwa, sautin kukanta kawai yaji daga nan takashe wayar, tafada bisa katifa tana kuka

Kara kiran wayar akayi, ganin harta kusa katsewa yasa Baba mairo ta dauka. Sameer yace hello Falak kinajina, dan Allah kiyi shiru, bana son jin kukanki wlh, yana tadamun hankali, tunranar damuka hadu akasuwa naga kamar kina cikin dakuwa nima nashiga damuwa. Kiyi hakuri idan akwai abinda yake damunki. Wlh ashirye nake da intemaka maki.

Hawayen idonta Baba mairo ta goge aranta tana mejin dadin yau Falak tasamu wanda yake damuwa, da lamuranta. Hello Falak kiyimun magana. Baba mairo tace yaro kanajina, yace e,e Baba inajinki ina Falak din?

 Tace Falak bazata iya maka magana yanzu ba, dan kamata fami akan abinda kedamunta, sede bansani ba, kawai naji ka kwanta mun arai, dama kuma inajin labarinka agurin su Jalila, tun lokacin daka bama Falak addu,a tayima Ummanta sanda batada lafiya.

Agaskiya Sameer bazan iya boye maka abunda yake damun Falak ba, saboda inaji ajikina, kaine zaka temaketa, idan harkaji labarinta, idan harzaka iya sauraron labarin Falak, kabari se gobe idan kasa kudi awaya kamar irin wannan lokacin seka kira inabaka labarinta.

Sameer yace a,a Baba mairo wlh inada kudi awayata zasu isa inji labarin Falak, bazan iya hakuri xuwa gobe kamar yanzu ba. Gyara kwanciya Baba mairo tayi, tace zanbaka labarinta, amma inaso kazam merikon gaskiya da amana idan kaji labarinta.............  Anan Baba mairo tafara bashi tarihin Falak.

Urs, 
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[5/30, 9:17 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 70.....75

Kuka kawai Sameer yakeyi, yana sauraron Baba mairo, hartagama bashi labarin Falak, be iya magana ba, yace nahode Baba, Sautin kukanshi kawai takeji,da haka yakashe wayar.

Tunda yake arayuwarshi betaba jina labari me firgitarwa kamar na Falak, jiyake kamar a film akayi abun, da ace ba Baba mairo bace tafada mashi, labarinta ba, naze yarda ba.

Wata irin soyayyar Falak ce take shigarshi, gatausayinta daya ke shigarshi jiyake kamar yaje yadaukota tadawo kusa dashi, kuka kawai yakeyi, yana jin zuciyarshi kamar zata fito, aranar kasa bacci yayi, sede yayi alwala yafara nafila, har asuba tayi, seda yayi sallar asuba sannan ya kwanta, saboda ciwon dayaji kanshi yana yimashi.

Falak ma haka ta tashi da ciwon kai me tsanani, da zazzabi, da kyar tayi sallah ta kwanta, Baba mairo tana gama sallah taji Zarah tashigo ta watso kayan wanki tace idan wannan AGOLAR tagama sallah kice mata tayi mani wanki, saura kuma tabari gari yawaye infito bata gama ba.

Fita tayi takoma dakinta ta kwanta, Kallon Falak Baba mairo tayi wadda batama san me akeyi ba, saboda bacci me nauyi yadauketa, saurin tashi Baba mairo tayi tadauki kayan tashige bandakin dake cikin dakin tafara wankesu. Dayake bawani yawa garesu ba, kuma basuda datti, cikin minti 20 tagama, cikin sando tafita taje ta shanya, tadawo.

Kitchen tawuce tayi wanke wanke sannan takoma daki ta kwanta ganin haryanzu gari be ida haske ba, kuma dama bata fara girkin safe se karfe 7. Kwanciya tayi tana tunanin hanyar dazata bi Falak tabar gidan, sede tana tunanin Falak bazata yarda tabar gidan ba, inde ba aure tayi ba, saboda tana riko da wasiyar da Ummanta tabar mata. Addu,a tashiga yi Allah yasa Sameer yace ze auri Falak, da cikin lokaci kadan zatace yafito, sede bata sani ba ko Zarah zata yarda Falak tayi aure yanzu.

Har karfe 10 Sameer be fito daga daki ba, ummanshi Halima data gama saida kosanta harta gama aikinta, tajishiru, kuma besaba yin haka ba, dakinshi tashiga da sallama. Tsaye tayi ganinshi zaune yabuga tagumi yana tunanin, ga kuma hawaye suna fita daga idonshi.

Kusa dashi tazauna jikinta duk yayi sanyi ganin danta yana kuka, dan tasan kila mahaifinshi yatuno. Sameer lafiyarka kuwa, kake kuka? Goge idonshi yayi yace Umma ina kwana, kiyi hakuri yau natashi banajin dadi shiyasa banfito dawuri ba.

Lafiya lau, Sameer amma bawannan na tambayeka ba, rashin lafiyar ce tasa kuka kome? Tashi yayi yace Umma bara inyi wanka zan fada maki damuwata, waje yanufa domin yin wanka.

Seda Falak tayi wanka sannan Baba mairo takawo mata abinci, fa kyartaci tasha magani, dan tadanji sauki datayi bacci sosai, kallon Baba mairo tayi tace Baba mairo yaushe aka wanke ma Ummi kayanta harnaga kina linkewa? Anan Baba mairo tafadima Falak abunda yafaru da tana bacci, kwalla ce tacika idonta, tace bansan da abinda zan saka maki ba, Baba mairo, Allah yabani tsawon rai nima inyi maki wani abu wanda zakiji dadi arayuwarki.

Murmushi Baba mairo tayi tace ai keda Ummanki kungama mun komai tunda har kuka daukeni amatsayin uwa, kinga ko babu abinda yafi wannan dadi, nide fatana Allah yabani tsawon rai in kaiki dakin mijinki. Murmushi Falak tayi tace Uhm Baba mairo kenan, aini bana sa rai zanyi aure, dan nasan Ummi bazata barni inyi aure ba, tunda batason cigaba na.

Baba mairo tace insha Allahu sekinyi aure Falak, kuma ni harna zaba maki miji ma, Allah yasa zakiyi na,am da zabina. Dariya Falak tayi tace lallai Baba mairo kinkosa kirabu dani, to afadamun wanda aka zaba mun, ina fatande ba tsoho bane?

Dariya Baba mairo tayi tace a,a wanda kike sone kika boyema ranki na zaba maki, fiddo ido Falak tayi tace kai Baba mairo, yaushe mukayi haka dake, ni babu wanda nakeso. Har Malam. SAMEER din?  Rufe fuska Falak tayi tana murmushi, tace yaushe nacemaki inason malam. Sameer kuma? To inma baki sonshi ni shina zaba maki. Kai Baba mairo shifa bece yana sona ba,

Yace mana, jiya ai naji abinda yace, da kika aje waya nadauka, haka yayita surutai, yadauka kece awayar. Dariya Falak tayi tace nide banyarda ba, Baba mairo tace Allah Falak a aje batun wasa agefe, dama inaso muyi magana dake akan Sameer, nide tabbas nayarda dashi, shiyasama jiya nakasa boye mashi labarinki.

Inaso Falak ki nutsu kigane mesonki, kada kiyi la,akari da Sameer malamin makaranta ne, kice bakisonshi, nide nayarda dashi , kuma nasan zerikeki da amana, inaso insamu lokaci inganshi koda awani gurine, ko kuma yazo yakaini gidansu muyi magana dashi. Allah yasani inaso inga kinbar gidan nan. Falak tace to Baba mairo Allah yazaba mana abinda yafi zama alkairi. Amma kisani duk ranar dazan bar gidan nan kafata kafarki, idan bahaka ba, sede na hakura da auren dan kowa zan aura, seya yarda zaki bini. Dariya Baba mairo tayi tace ti naji insha Allahu ma bakida mijin daya wuce Sameer. Murmushi Falak tayi tadauki kayan Zarah tafara gogewa.

Zaune suke afalo Alh, yakalli Jalila, yace Alhamdulillahi gashide na amso maki, admission dinki, kuma nabama wani abokina yayi maki registration ana A,B,U tunda de kince bazakiyi karatu anan kadunaba, wato kinfison makarantar kwana ko?  Dariya Jalila tayi tace ai Dady anfi yin karatu acan, amma nan kila inacikin yin karatun wani abun yadaukemun hankali.

Zarah tayi murmushi tace can dinma ai gidane, damma tace bazata zauna agida gurin Inna asabe be, tafison hostel, me suka bata ne? Biological science ne suka bata, to Allah ya bada sa,a seki dage.

Alh, yace Hajiya watodesu Inna su kwace mana Jidda ko? Yanzu ko lekomu batayi, naso ace tadawo insa ayi mata exam ta kudi itama tafara karatun tunda taki fidda miji, dazama haka nan, amma gaskiya banajin dadin rashin zamanta agida kusa damu. Zarah takalleshi fuska ahade tace to mekake nufi? Tunda yarinya tace batason karatu abarta mana aiba dole bane, ni karatun nayi dakake zaune dani. Kuma menene bana yi maka, wama ze kalleni yace secondary kawai nayi, itama ta gwamnati, ina laifi ma ita tayi makarantar kudi tasan yes tasan no.

Nifa banason takura wlh, kuma dakake maganar tadawo gida tazauna, kana nufin gidanmu ba gida bane kome? Inma kyamarsu kake nima acan nataso harka ganni kace kanaso, idan tadawo nan, mezatayi maka, kaima da bazama kakeba, kuma acan tana taya Inna zama tunda ita kadai ce.

Allah yabaki hakuri Hajiya wlh ba haka nake nufiba, kawaide nafada ne, amma kiyi hakuri ba za,a sakeba. Kallon mamaki Jalila take bin Umminsu dashi, ganin yanda takema Dadynsu fada, wanda ada ko gardama batayi mashi, amma wai yau shine yake bata hakuri, har muryarta tana fin tashi yin sama. Tunowa tayi da wa,azin da malam Sameer yayi masu akan hukuncin matar datake daga ma mijinta murya. Wasu zafafan hawayene suka rika fiyo mata, saurin gogesu tayi.

Alh, yace Jalila zaki iya tafiy, amma kizama cikin shiri nan da sati mezuwa zaki tafi, anjima kizo ki amshi kudi seki siyo abunda kike bukata. Tashi tayi jikinta duk amace, tafita.

Halima tace Sameer lallai akwai abinda yake damunka, kuma ba karamin abu bane, kallifa dan abincin daka ci. Sameer yace wlh Umma banajin dadin abincin ne. Rufe kwanon tayi tace inajinka fadamun damuwarka.

Gyara zama yayi, ya kwashe duk abinda Baba mairo tafada mashi yafada ma Ummanshi. Kasan cewar Halima mace me tausayi, bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba.

Tana goge idonta tace wai Sameer wannan labarin ba ta tsunniya bace kake bani kuwa. Wlh Umma ni kaina faba Babbar mace bace tabani labarin Falak ba, dabazan yarda ba, kuma nima naga wasu alamomi agurinta lokacin damuka hadu kasuwa, bakiga kayan jikinta ba, bazakice daga gidan masu kudi tafito ba.

Umma tace tabbas nima bantaba jin abinda yabani tausayi da tsoro irin labarin Falak ba, agaskiya Sameer ina yimaka sha,awar aurenta, koda bakace kana sonta ba, nizanyi maka umarni da aurenta kodan kafidda ta daga rayuwar datake ciki, dan wannan mata batada imani zata iya kasheta wlh.

Kuma naji dadi, dakace kana sonta, tunkafin kaji labarinta, hakan zesa nayarda bawai tausayinta ne yasa zaka aureta ba, dama nafison ace akwai soyayya atsakaninku kafin kuyi aure, hakan zesa auren yafi dadewa.

Tunda baze yuwu kaje gidansu ba, meze hana kadauko Baba mairo kuzo nan muyi magana ba. Yace shikenan Umma zanyi yanda kikace. Yauwa Sameer amma dan Allah kacire damuwa aranka, insha Allahu bakada mata se Falak, zantayaka da addu,a har Allah yadoramu akan wannan muguwar mata. Sameer yayi murmushi yace ai damuwa takare, dama ina tsoron kiji labarinta kice bazan aureta ba. Dariya tayi tace haba Sameer ai yakamata kamun sheda mekyau, Allah kada yakawo ranar dazan tauyemaka hakkinka, kamar yanda kakemun biyayya dolene nima inso abunda kakeso, matukar baze cutar da kaiba.

Sameer yace amma Umma anan gidan zamu zauna ko? Kinsan banason nisa dake, tace a,a kada ma kafara, bazan zauna da surika agida daya ba, gara de muna nesa, idan kata fima akwai A.isha diyar yaya Zainabu tagama makaranta kuma dama tace mun zata bani ita, tunda tana da yan mata, seta dawo nan mucigaba da zamammu.
Sameer yace to umma ina zan zauna? Tace bade ka gama karatunka ba, haya zaka kama kafin Allah yabude se kafara gina wancan filin naka. Amma Allah bazamu zauna tare ba. Dariya yayi yace toshikenan Umma ai base kinrantse ba, yanzu de bani abincina incinye. Dariya tayi tace oh baka koshiba kenan.

Sati yana zagayowa Jalila tagama hada komai, nata, dakin Baba mairo tashiga, zaune ta iskesu suna fira, mikama Falak takaddu tayi, idonta yana kallon kasa, saboda gab take da fashewa da kuka, ita kadai tasan abinda takeji. Falak tace nameyene Jalila? Budawa tayi tafara dubawa, cike da farin ciki ta rungume Jalila, ganin result dinta ne ta amso mata kuma gaba daya tacinye both waec dan Neco.

Kuka sosai Jalila tasak tana kara kankame Falak, cikin muryar kuka tace Falak kiyi hakuri nasan Ummice tasakaki cikin halin da kike ciki, gashi yanzu zantafi makaranta batare dakeba, wlh saboda ke nazabi intafi boarding saboda bazan iya kallonki cikin damuwa ba, ki kara hakuri akan wanda kikeyi.

Kuma dan Allah ki amince da malam. Sameer yafito kuyi aurenku kema kibar gidan nan, dan wlh koni bansan lokacin dawowata ba, banason gidan nan, gara inzauna amakaranta yafi mani zaman gidan nan. Nizan tafi, inada no Baba mairo zamu rika waya, Kudi masu yawa tasaka ma Falak ahannu sannan ta bata wata leda wadda kayan shafa ne, aciki masu yawa. Tasiyo mata.

Kuka sukeyi sosai, harseda Baba mairo itama ta tayasu, seda suka gaji sannan sukayi shiru, kufi Jalila tamika ma Baba mairo,godiya sukayi mata. Har bakin kofar dakin Baba mairo suka rakata da kyar Baba mairo taja Falak suka koma ciki ita kuma Jalila tafita tana kuka tasamu su Alh, da zarah suna jiranta awaje, dan sune zasu kaita.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[5/31, 7:55 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 75.....80

Washe gari Falak ta tashi da karfin jiki, haka tagama aikinta, sannan tashirya ta nufi kasuwa.

Yauma tana gama siyayyarta tahadu da Sameer, bayan sungaisa yajata zuwa cikin shagonsu, zama tayi kanta akasa duk kunya takeji saboda kayan dake jikinta.

Falak, taji yakirata. Amsawa tayi amma bata dago takalleshi ba, hakika naji labarinki wanda yafirgitani, gaskiya inga rayuwa, koma ince kina cikin ganinta, abinda nakeso dake ki kara hakuri abisa wanda kikeyi, babu wani rai daze rayu aduniya, face se Allah jarabceshi, da duk abinda yayi niya.

Kuma bakowane yake iya cin jarabawar da Allah yayi mashi ba seme imani. Falak akwai abinda nakeso infada maki, kuma inafatan zaki fahimceni, banaso kidauki maganar dazan fada maki kamar saboda tausayinki ne yasani fadamaki ita.

Wlh Falak tun ranar dana fara ganinki arayuwata Allah yajarabeni da sonki, ina maki son daban san irinshiba, alokacin danaji labarinki sonki da tausayinki suka kara shiga raina. Dan Allah Falak kada kice bazaki amshi roko naba, kiyi hakuri nasan natsaidaki kilama ayi maki fada, bansan inda zanganki ba, idan ba nan ba. Amma bazan matsa maki dajin amsarki yanzu ba, ga wannan wayace nasiyo maki sekirika boyeta kada akwace maki.

Ina Jalila fa? Se asannan tadago kai tana kallonshi, tace ai ta tafi A,B, U Zariya, jiya, yace tasamu admission ne? Tace e tasamu biological science suka bata. Yace yayi kyau, kema kiyi hkr insha Allah wata rana zakiyi naki kinji. Murmushi tayi tace Allah yasa. Wayar yabata da kyar ta amsa, tayi mashi godiya, sannan suka fito yarakota.

Harkusa da gidan yakaita, sannan yamika mata wata leda yace gashi tace ta meye ne, yace idan kinje kiduba zaki gani, idan kuma bakiso sekiba Baba mairo, dariya tayi tace toshikenan, nagode Allah yasaka da alkhairi, yace ameen, amma fa dakinje ki kunna wayarki nasamki ita charji, haka sukayi sallama tashige gida, sa,arta daya Zarah bata nan.

Da dare Zarah tana daki tana waya da Asabe, Baba mairo tazo domin kawo mata abincin da tace akawo mata. Harzata shiga taji Zarah yana wata magana, kara labewa tayi domin sauraron abunda take fada.

Wlh Inna Asabe sonake da inkori yarinyar nan, banaso tana zaune gidan nan wata rana Alh, ze iya ganeta, dan kinsanta dashegen tsaro da addini, kuma tanada addu,a banaso ta karya mani shirina, amma idan nakoreta tabar gidan shikenan nahuta.

Tsayawa tayi alamun sauraron Asabe, Can tace toyanzu Inna wakike ganin za,a aura mata, nifa kinsan bawani sanin yan iskan unguwar nan nayi ba, da se insamu wani yazo ni ko kudi zan iya bashi ya aureta, kona shekara daya ne bayan yagama wulakanta ta, imma da rabo yayi mata ciki sannan yakoreta, dazanfi jindadi.

Banaso yarinyar nan tabar gidan nan batare da wani mugun tabo arayuwarta ba, kibari kawai zan nemi duk dan iskan danaga yayi mun nakirashi inbashi ita kawai, damma kada yan unguwa su zargj
[5/31, 9:22 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH


Cigaban. Part 75..... 80.  AFUWAN BANGAMA TYPING5 BA YAYI SAVING BY MISTAKE, GA CIGABAN
NAN.

Banaso yan unguwa su zargi wani abu wlh da acikin kwana 2 za,a daura masu aure yadauketa duk inda ze kaita ma yakaita. Shikenan Inna nagode, a,a wannan aiki ai base munkaima boka ba, nima zan iyayi kinsan Alh, atafin hannuna yake kome nafada mashi zeyarda. Toshikenan kibani nan da kwana 2 idan har ban samuba, zan maki magana idan yaso seki samomun anan, ti nagode, idan Jidda tadawo kigaishemun ita, nakira wayarta bata shiga.

Komawa da baya Baba mairo tayi saboda wani tashin hankali dataji yana shigarta, ta dade afalo kafin naga cikin sauri tanufi dakin Zarah, da sallama tashiga, Zarah tace shigo mairo, shigowa tayi tace Hajiya ga abincin nan, Baba mairo tafada tana goge kwalla.
Zarah tace Mairo lafiyarki kuwa naga kamar kina kuka? Kara rushewa tayi da kuka tasamu guri tazauna, tashi Zarah tayi tace dan Allah Mairo kifadamun ko wani naki ne, ya mutu? Fyace majina tayi tasa zaninta tagoge, sannan tace Hajiya da irin abunda akamun aigara ace mutuwa akayi mani zan iya hakura akan cin mutuncin da wannan yarinya tayi mani.

Ace yanzu duniya babu gaskiya, duk yanda karike mutum da gaskiya da amana shi kokari yake yaga bayanka. Wlh, danasan haka yarinyar nan take simi simi da ita da bandauki amanar da mamanta tabani ba. Amma koyanzu nafada mata najanye rike amanar da aka bani, kuma nace tafitarmun adaki bazan iya zama da ita ba.

Zarah tace aini mairo baki fadamun dawa kike ba kinzauna kina ta kuka. Dawafa nake idan ba wannan Banzar AGOLAR gidan nan ba, wlh, Hajiya kinyi gaskiya tsintartar mage bata mage, wani irin murmushin dadi Zarah tayi tace Mairo wani abu Falak tayi maki ko?

 Haba Hajiya, ashe yarinyar nan yar iska ce bansani ba, shiyasa damatunda kika fara aikenta kasuwa takejin dadi,kullum bata dawowa dawuri, kuma idan tadawo sekiga tadawo da kaya masu yawa, Inazuwa bari kiga wani abu dan kada kice sharri nayi mata. Fita tayi domin dauko abun.

Wani irin tsallen murna Zarah tayi tafada bisa gado tana fadin wlh, karyarki tasha karya Hajjo kice zaki hada kanki kishi dani kizauna lafiya, nayi nasarar kaudaki keda yaronki, yanzu gashi cikin sauki diyarki zata zama karuwa. Gaskiya naji dadi da Mairo tagane gaskiya, kinga yanzu nakara samun yar uwar dazamu huro maki wuta.

Shigowa Baba mairi tayi hannunta rike da Leda, zazzageta tayi sega kayan shafa masu kyau da tsada. Zarah tace ey! Wannan kayan duk natane? Baba mairo tace sosai ma. Kuma waini ina ganin kamar na isa da ita, shine dazu nayi mata magana akan ina take samo kudi haka, se cemuntayi yawon karuwanci takeyi tana samowa kamar yanda nima nakeyi.

Wlh, hajiya kinji abinda yasani kuka wai kamar ni Falak zata kalla ta fadamun wannan maganar. Gaskiya hajiya nadawo rakiyar wannan yarinyar, gata nan duk abinda zakiyi mata kimata, babu ruwana aciki, idan ma kina da bukatar temako na domin akoreta daga gidan nan ashirye nakw da inbaki gudummuwa.

Dariya Zarah tayi, tace aini nasani Mairo, komin dadewa zakidawo gurina, domin ke renona ce, tunda nazo gidannan muka hadu dake, nasan dole kidawo gareni, nasan dama tausayine yasaki temakawa Falak, bade So ba.

Agaskiya naji dadin zuwanki adede lokacin danake neman temakon yan gari irinku, kuma maganar iskanci datakeyi wannan ita tasani, aure ma zanyi mata kowa yahuta, sede ba irin auren da kika sani ba. Anan Zarah takwashe komai tafada ma Baba mairo, sannan tace yanzu Mairo kenake ao kibani shawara ina zamu samo dan iskan dazan bashi auren Falak?

Murmushi. Baba mairo tayi tace haba Hajiya wannan aikin ai semu, kafin infara aiki agidan nan nayi sana,ar saida abinci atasha, nasan yan iskan tasha sosai, bakida damuwa, akan wannan matsalar.

Zarah tace yauwa, mairo amma naji dadi sosai, da Allah yasa kikazo awannan lokacin, yanzu yaushe yakamata ace kinkawo mani shi inganshi? Baba mairo tace kada kisamu damuwa gobe da safe zanje tasha, akwai wani mugun da shaye shaye ne dan shine ogansu atasha, babu irin aiki da baya yi, sede aikinshi kudi ne. Zarah tace karkisamu damuwa, abinda yafi wannan ma nakashe kudi akanshi, kawai kigada mashi duk abinda nake bukata, ni kuma zan damka komai agurinki, dan abanaso Alh, ya fahimci wani abu, kije kugama komai, sede zuwa jibi inason ganinshi. Baba mairo tace angama Hakiya, kada atausaya mata ko kadan, bara inje inga kota kwashe kayanta. Zarah tace a,a mairo kiyi hakuri ki kyaleta. Ai takusa barin gidan

Zaune adaki Baba mairo tasamu Falak suna waya da Sameer, zama tayi tana kallonta cike da tausayi, Baba mairo tace Falak nasan Sameer ne,  idan kungama kice masa gobe yazo dasafe gurin karfe 9 yadaukeni zamuje gidansu akwai maganar dazamuyi.

Kwanciya tayi tana jiran su gama,  haka sukasha fira kafin sukayi sallama, kamar kada surabu, Falak tanajin aon Sameer aranta sosai.
   Baba mairo tayi dariya tace kaga masoya, amma idan nace kina sonshi sekice a,a Falak tace to nadeji yanzu ai kingane abinda muke ciki ko.

Baba mairo tace e nagane shiyasa ma nazo maki da albishir medadi, sede kuma akwai wata matsala, wadda sekinyi hakuri kafin mudace da abinda mukeso, Falak tace lafiya meyafaru kuma? Kiyi hakuri da abinda zan fada maki Falak dole ne nima tasani zabar wannan hanyar, dan ita kadai ce zata bulle mana, 
 Anan Baba mairo ta kwashe duk abinda taji Zarah tana fada, da kuma. Shawarar data yanke tajetasamu Zarah sukayi magana.

Kuka kawai Falak takeyi dataji irin tsanar da Zarah tayi mata, da kuma yanda Baba mairo take kokari gurin kareta aduk halin data shiga. Kwanciya tayi bisa cinyar Baba mairo tace bansan dame zan saka maki ba Baba mairo, badan keba da rayuwata tagama shiga matsala.

Bakomai Baba mairo, duk abinda kika yanke akaina yayi dede, nasan bazaki taba yimani abunda ze cutar dani ba. Baba mairo tace gobe zanje gidan au Sameer zamuyi magana da Mamanshi, da kuma shi, duk yanda mukayi zakiji. Amma dan Allah kiyi hakuri da irin yanda naci mutuncinki agurin Hajiya. Falak tace Baba mairo banaso kina bani hakuri, akan irin wannan abun, haka rayuwata take, dole se anyi irin haka inde anaso insamu abinda nakeso, babu komai, Allah yashige mana gaba kuma yabamu sa,a. Baba mairo tace ameen, haka sukayita fira, sannan suka kwanta.

Jidda ce kwance adakin Al,amin suna waya da Zarah, Jidda tace Ummi dan Allah kisan yanda zakicema Dady, banaso yakira wayata yaji bata shiga nasan yana iya zuwa zariya, nemana, kuma kinga kawata zan raka london zata hado kayan lefenta, bazamu wuce sati 2 ba.

Zarah tace waini Jidda ke haryanzu bazakiyi kokarin kawo mijin aure ba, sede kirika bin kawayenki, kina masu wahala ke kuma kin kasa fitar da gwani, gaskiya nima nafara gajiya, nima inason inga jikokina. Jidda tace haba Ummi, duka yanzu shekarata nawa dazanyi aure, kina ganin yanda mazan zamanin suke fa yanzu, dazaran sun aureka shikenan duk wata hidima dasukeyi maka awaje sundenata. Wani lokacin ma kudin siyan anko seya gagari mutum, kuma kinga ni ba karatu nayi ba, idan ban tsaya natara kudi ba, kinsan karshenta bawani me arxiki bane zezo aurena.

Nide gaskiya Ummi kibari ayanzu inasamun kudi masu yawa dazaran nagama samun kudina zanyi aure, kinga alokacin nima nazama bussiness woman ko? Zarah tayi murmushi tace yauwa Jidda ta, kokefa, aigara kema kitara kudi kozaki fara zama cikin mata masu aji,  to Allah yabada sa,a Allah yasa daga can kena kisamo Alhjin, london kinga semu kaiki can kawai. Shi kuma Alh, kibarni dashi nasan yana zanyi dashi, kije kawai sekun dawo. Amma dan Allah kada kiwuce sati 2, kinsan Alh, dason ,ya,ya.

Damma nima. Bana daga mashi kafa, ai dayanzu yana takani son ranshi. Jidda tace waini Ummi ina Falak da Ameer kuwa? Zarah tadaure fuska tace meye kuma ana maganar arxiki zaki sako mana ta wasu banzaye. To Ameer yajima da mutuwa, Ita kuma Falak tana nan tazama karuwa, shiyasa zanyi mata aure kowama ya huta. Jidda bataji dadin abinda Umminta tafada ba.

Tace Ummi wazata aura? Tace dede da ita ne, zata aura, kewai yanzu bakiga yanda Falak tazama yar duniya ba, har zagin Mairo takeyi fa. Jidda tace dan taga tana da kyau ne shiyasa, ai garama kiyi mata aure kowama ya huta.  Ana. Mn sukayi sallama .

Al,amin ne yashigo zama yayi yace baby wlh nagaji nasha wahala, sosai yau, garin samun visa , amma gashi anan nasamo mana, ina fatan kinga kashe boss na gidanku? Dariya tayi tace tunima, yanzu de karfe nawa jirgin zetashi? Yace karfe 7 na safe. Dariya tayi tajawoshi yafado kanta tana fadin nagode sosai my luv.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/1, 3:37 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»  AGOLAH!!! Nah 
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Naneelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 80.....85

 Washe gari bayan Baba mairo tagama aikinta gurin karfe 10 kamar yanda Falak tafadama Sameer segashi yakirata yace mata yana inda yatsaya.

Sallama Baba mairo tayi mata, tawuce dakin Zarah tace Hajiya nagama zantafi, dan tunjiya nakira wata kawata damukayi aiki atasha nace mata idan Asid yazo ta tsaidamun shi. Murmushi Zarah tayi tace gaskiya nagode Mairo, Allah yasa amince da bukatarmu.

Baba mairo tace ameen, kudi har dubu 10 Zarah tabama Baba mairo tace tafara bashi kafin sauran suzo, dubu 1 tabama Baba mairo tace tahau abin hawa. Godiya tayi mata tace ta tafi.

Akusa da wani shago Baba mairo taga Sameer duk da bata sanshi ba, amma tana zuwa gurin yace Baba mairo ko? Dariya tayi tace ka canka dede, yace ai tunda kika taho jikina yabani kece. Ina kwana, tace lfiya lau, Sameer, yace muje ko, hawan mashin din tayi suka wuce.

Zaune suke abisa tabarma Sameer kuma yana zaune abisa kujera, bayan sun gama gaisawa, Baba mairo tafara magana. To Halima, nasan de bakisanni ba, amma kuma kinsami labarinmu agutin Sameer.

Bawani abu bane yakawoni se akan maganar da nasan Sameer yafada maki. Halima tace kwarai kuwa yabani labarin Falak me cike da tausayi, kuma yayi mun magana akan yana son aurenta, kuma nima nayi na,am da maganarshi.

Sede yanzu bansan wace magana zakiyi ba. Baba mairo tace hakane, kuma naji dadin yanda kika amshi maganar, babu abinda zamu ce maki sede muce Allah yabiyaki. Kamar yanda kika sani nide ban hada komai da Falak ba, Allah yahadani dasu, tunbayan da Alh, yakawosu gidan danake aiki.

Munyi zama na mutunci da Maman Falak, wadda itace takawomun yanci agidan danake aiki, ada babu wanda yakemun daukar uwa agidan, duk da na a haifena haifi ita kanta Hajiya ba ,ya,yanta ba. Amma suduka mutum 1 ce take bani girmana, wato Jalila. Zuwan Hajiya Hajjo tasakamun Baba mairo, dan ita tace bazata iya kiran sunana kaitsaye ba, hakan yasa tundaga kan Alh, har ,ya,yanshi suka koma kirana haka, sede Hajiyace kadai take kirana da mairo.

Bayan mutuwar Hajiya nacigaba da rikon yayanta, har Allah yadauki dayan, sede Falak kawai tayi saura. Kuma itace Hajiya ta maidata kamar baiwa agidan, datana da ikon kasheta kamar yanda tayima mamanta da kaninta itama da tuni takasheta. Nadade ina tunanin hanyar dazan bi inga Falak tabar gidan, sede kafin mutuwar hajiya tabar mata wasiyar komin rintsi kada tabar gidan Alh, har se idan aure tayi.

Nima haka tabani wannan wasiyar, duk da yanzu Falak ba abakin komai take agurin Alh, ba, kuma ba aikin kowa bane sena Hajiya Zarah, kwata kwata yanzu Alh, yamanta da wata Falak agidanshi, shi kanshi yazama shanyayye agidan.

Ina cikin neman mafita segashi Allah yakawo mana Sameee, tun ranar da yafara temakon Falak naji inama ace yazo yanemi auren Falak, alokacin hajiya bata lafiya anrasa wane irun ciwo take, Sameer yabama Falak wata addu,a cikin ikon Allah ana fara yimata ita tasamu sauki, hakan yasa muka dawo gida akacigaba dayi mata addu,a.

Sede alokacin da ciwaonta yakara tsanani Sameer. Yakoma makaranta, kuma wannan ciwon shi yazama ajalinta. Ajiya naje kaima hajiya abincinta naji wata magana data firgitani,.........   Anan Baba mairo tafada masu irin wayar dataji Zarah tanayi ajiya.

Ina gama jin wayar nan narasa yanda zanyi intemaki Falak, kawai senayi amfani da abinda nafada maku nashiga gurin hajiya da maganar, cikin ikon Allah tayarda da abinda nafada mata, kasancewar mafita take nema, kuma dama hajiya duk wani makiyin Falak to ita masoyinta ne.

Shine nataho domin infada maku shawar danazo da ita. Goge kwallan idonta Halima tayi, shima Sameer tunda yaji irin abinda akeson ayima Falak dinshi yafara kuka. Halima tace lallai wannan mata batada imani, kuma zata iya kashe Falak, damane kawai bata samuba.

Yanzu wace shawara kika kawo? To kamar yanda mukayi da ita, azuwan nataho tasha ne insamu Asid wanda haka kawai nafada mata sunan, domin acan garinmu akwai wani dan kwaya haka ake cemashi, toganin sunan yayi kama dana marasa da,a yasa nima nace mata sunanshi kenan.

Sameer kaida Falak duk sekunyi hakuri idan har kunaso mucima burinmu, Halima cewa nayi meze hana Sameer yayi basaja yazo amatsayin Asid danace zankawo. Ammafa seka canza shigarka, dole kasamu kaya irin na yan iska, da kuma sarkar dazakasa awuya, domin hajiya tayarda kayi dede dawanda takeson bama Falak, kaga idan har Allah yasa mukaci nasara, shikenan Falak tazama taka, kada kadamu da maganar hajiya dan tace shekara 1 kawai takeso Falak tayi agidan aure asaketa. Mude burinmu tabar gidan, kaga idan har igiyar aurenta tazo hannunka, kaine kake da saki, kuma nasan duk inda za,aje babu mesaka kasaketa, tunda ba ita ta haife taba.

Halima tace agaskiya Baba mairo wannan shawara tayi, koko yakace Sameer? Goge idonshi yayi yace hakane Umma , ashirye nake dayin duk wani abu daze fitar da Falak daga rayuwar datake ciki. Insha Allahu gobe zanzo gidan amatsayin Asid kamar yanda kikace Baba mairo. Allah yayi mana jagora.

Suka ce ameen. Halima tace toyanzu Sameer dole mufara shirin biki, dan nasan baze dau lokaci ba, anjima zansamu kawunka, infada mashi halin da ake ciki, nasan shima zebamu goyon baya, danshima mutum ne me gaskiya kuma gashi malami. Bab mairo tace Kada ku takurama kanku kuyi abinda zaku iya, daga baya komai zeyi dede, nasan ai anan gidan zata zauna ko?

 A,a gaskiya Baba mairo nide nafison yaje yakama masu haya mesauki suzauna, idan Allah yasa yasamu aiki ko kuma kasuwancin dayakeyi ya kara kwari tunda yanada filinshi se yafara gini, wlh, banason zama gida daya da sirika, kinsan ance yau da gobe se Allah.

Sosai Baba mairo taji dadin abinda Halima tafada, tace toshikenan Allah yatemaka, kai kuma Sameer banason katakura kanka, kasamu gida mesauk, badole sekunj dadi alokacin da kukeso ba, da sannu wata rana rayuwa take canzawa, kuma duk kudin da hajiya tabayar abaka kayi amfani dasu ka kama haya kuma kayi hidimar bikin dasu.

Sameer yace to Baba mairo, bazace zanki amsar kudin ba, sede kisani bazan yi amfani dasuba, yanda kika bani haka zanba Umma ajiyarsu, banaso in auri Falak da kudin haram, kuma nasan wata rana dole Hajiya zatayi mani gorin abinda tamun duk ranar datasan gaskiya, kuma aranar zanbata kudinta.

Baba mairo tace gaskiya wannan yaron kacika da halak, Allah yayi maka albarka. Ni bara inzo intafi, tunda Allah yasa nasamu abinda nakeso, kada taga kamar na dade. Halima tace to Baba mairo mungode, kema Allah yabiyaki irin jihadin da kikayi. Sameer yayi dariya yace au BabaMairo namanta fa Falak tace idan har badake zamu tafi ba, bazata aureni ba. Dariya sukayi Baba mairo tace haka kullum take cewa. Halima tace ai wannan haka yake, banga abinda zaki zauna kiyi agidansu ba, dama zaman Falak kikeyi, tunda tayi aure ai shikenan. Sede nima ina da tawa shawarar. Baba mairo anan gidan zata dawo da zama,ba gidanku ba. Sameer yace a,a gaskiya Umma kingafa munrigaki. Baba mairo tace kyalesu dama koda tafada nibanyi niyar zama ba, niyata bayan aurenta inkoma garinmu.

Halima tace a,a Allah baza,ayi haka ba kinga babu kowa anan gidan dama diyar kanwata ce nace zata dawo nan idan Sameer yayi aure, tunda kuma gaki ai setayi zamanta, dama ina da almajiri memun aike aike, Allah babu wani abu kidawo nan dazama. Baba mairo tace toshikenan. Allah yamana jagora. Sameer yace wato de anyimana kwace da rana tsaka ko? Sukace ai haka yafi gara abarku kukadai kusan zaman aure kukeyi. Da haka Baba mairo tayi masu sallama tare da bama Halima dubu 10dan tafara ajewa.

Haka Baba mairo tajema Zarah da albishir medadi. Zarah bakaramun dadi taji ba, tace kuma acikin sati daya za,ayi bikin. Baba mairo tace a,a yace yafison nan da sati 2. Zarah tace shikenan, idan Alh, yadawo zanyi mashi magana yabada kudi asai mata kayan aure amma tsofaffi za,a siya mata suma dan kada mutanen gari suce bamu rike amanar da,a bamu ba. Kema zanba kije gurin dillalan nan mata kisiyo mata gado da katifa, se kujeru da yan kayan kitchen, zance mashi cikin kudin dazan bashi yasiya mata kaya kala 3 wanda zatasa da biki.

Haka Baba mairo dashigo daki tasamu Falak tafada mata duk yanda sukayi da Sameer da kuma Zarah yanzu. Sosai Falak taji dadi tajiba, jitake kamar anyi mata albishir da gidan aljanna, itade idan harzata bar gidan nan to ko inama ta tafi.

Jalila tana karatunta hankali kwance, sede akai akai suna waya da Falak, amma Falak bata fada mata labarin aurenta da Sameer ba, da Baba mairo tahana tafadama kowa har Jalila, saboda tace tsakanin da da Mahaifi se Allah, tabarshi idan komai yayi dede taji. Ko maganar auren daza,ayi mata ma sede agurin Zarah Jalila takej, aranar dataji bakaramin kuka tasha ba, tana tunanin wace irin zuciya Umminta gareta.

Jidda kuwa aranar dasuka isa london kwanan Al,amin 2 yayi mata sallama yadawo nigeria, har kuka seda Jidda tayi haka yayita lallashinta, yace nan da sati 4 zezo yadauketa su koma. Tun bayan tafiyarshi suke more rayuwarsu itada abokin Al,amin Joseph, bakananan kudi Joseph yake bama Jidda ba, seda takai har Sallah Jidda tadena yi, rayuwar turai kawai takeyi, idan kaganta sekace baturiya ce, dan takara zama fara sosai.

Yawo sukesha ita da joseph, suk inda takeso yana kaita, domin sosai yakejin dadin harka da Jidda, har fada yakeyi tafi sauran yanmatanshi komai, shiyasa tunda tazo ya sallami yan matanshi, ita kadai yake harka da ita. Duk kudin dayake bata betaba barin takashe koda gwandala ba, shine yake mata komai, shiyasa ma take adana su acikin akwatinta.

Sameer yazo gidan su Falak cikin irin shigar da babu wanda zeganshi yace mutumin kirkine, sosai Zarah taji dadin ganinshi haka, kuma tabashi kudi masu yawa, tace idan Alh, yadawo nan da jibi zata kirashi yazo sugaisa. Amma inaso aranar kadan saka manya kaya, idan ma baka dasu ka aro, duk da zancema Alh, me aikina ce zatayi aure kuma shine ze zama waliyinta, kaga bazeji dadi yaganka cikin irirn wannan shigarba. Anan sukayi sallama yatafi.

Halima tasamu kawun sameer tayi mashi duk bayanin abinda akeciki agame da auren da Sameer zeyi, shima ya tausayama Falak sosai, kuma yace babu damuwa zeje yayi yanda sukace.
     Bayan Alh, yadawo Zarah tayi mashi bayani akan auren dazatayima me aikinta, dakuma abinda takeso yayi, babu gardama ya amince, kudi yabata naira dubu dari 500 yace gatashi gudummuwar asaya mata kayan daki, godiya tayi mashi, sannan tace anjima Sameer da kawunshi zasuzo gaisheshi. Alh, yace sunan yaron sameer tace E, dan shima haka yafada mata, amma yace ba,a kiranshi da sunan, sede Asid, dan Sameer cewa yayi bayaso adaura auren Falak dawani sunan banashi ba. Alh, yace Allah yakawosu lafiya.

Haka su Sameer da kawunshi sukazo suka gaisa da Alh, sosai kawun Sameer ya tausaya ma Alh, gashide cikekken mutum amma yana ganinshi yagane akwai sihiri ajikinshi, dan kawu malamine sosai, haka su kawu suka bada kudin aure da kayan sa rana akasa biki sati 2.

Zarah tabama Baba mairo dubu dari da hamsin  tace tayima Falak siyayya, daga can awuce dasu gidan dazasu zauna bataso akawo matasu, Baba mairo tace hajiya bazakije ganin gidanba? Zarah tace Allah yakyauta, ai naji dadi tunda kina nan, sekiyi komai.

Sameer yasamu dan karamin gida yakama haya, har fenti seda yasa akayi, sannan su Baba mairo suka kawo kayan daki akayi jere, gado ne da kujeru, se katifa dukansu tsofaffine, sede basosai suka tsufa ba, dan hada kudin Baba mairo aka hada akayimata siyayya, kayan kitchen ma, ansai mata rishow da tukunya 2 se kula 2, jug 2 da plate da ludduwa se cokali. Gidan balaifi yayi kyau. Ana saura kwana 2 daurin aure aka kawo kayan da Falak zatasa , suma acikin bakar leda ne, kala 3 kananan atamfofi se takalmi 1. Zarah kamar zatayi rawa dan murna, su asabe da Dije duk sunzo, amma babu abinda suka kawo.

Aranar asabar aka daura auren Falak da Sameer akan sadaki dubu 20, ba laifi mutane sunzo yan unguwa, dayake Alh, yasa anyi sanarwa amasallaci za,ayi daurin aure agidanshi, yan uwan Sameee ma sunzo.

Da dare gurin karfe 7 aka kawo mota daya somin daukar amarya, Zarah tacema Dije da Mairo suje sukai amarya se sudawo. Haka aka fita da Falak, dan babu wani fada da Zarah tayi mata, Falak taso taga Alh, amma Zarah tahana, dan boka yace duk ranar dasuka hada ido da Falak da Alh, asirin ze karye. Haka Falak tafita tana kukan rashin Uwa. Mutanen unguwa se gulmar Zarah sukeyi suna cewa takasa rike amanar da,a barmata. Su Baba mairo basu dade ba, suka juyo, Falak kuka kawai takeyi. Bayan tafiyarsu Jalila ta kirata awaya, tana kuka tana bata hakuri, tace. Wlh Falak bazan iya zuwa inga irin auren da Ummi tayi maki ba, kiyi hakuri Falak, insha Allahj wata rana komai zewuce. Falak tace bakomai Jalila nagode, haryanzu de kinkasa zuwa gida ko? Jalila tace Falak banason abinda Ummi takeyi agidan nan, shiyasa nafison zama. Makaranta akan gida. Falak tace banason Haka Jalila, da kunsamu hutu kidawo gida, ko kin manta wa,azin da Malam Sameer yayi mana akan muhimmancin uwa? Kome Ummi tayi dole kibata hakkinta amatsayintana Uwa, idan har kinaso mushirya to da kunyi hutu kizo gida. Jalila tana kuka tace shikenan Falak zanzo, nagode da tunin da kijayi mani. Allah yabada zaman lafiya, yasunan mijin naki?  Falak tace nimade Ummi tace mun sunanshi Asid. Jalila tace dan Allah jiwani suna, kiyi hakuri Falak nasan Ummi tasakaki kowace rayuwa kika shiga. Sallama tayi mata takashe wayar. Murmushi Falak tayi tace Jalila Umminki tabiyani tunda hartayi sanadiyyar sama mun farin cikina.

Urs, 
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[6/3, 12:52 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)

Part 85.....90

Zaune take ita kadai tana ta tunanin irin rayuwar da tayi, addu,a tayi Allah yasa aurenta yazamo karshen yankewar wahalarta. Sallama taji anyi, Sameer ne yashigo bayan ya kulle gidan sannan yanufi dakin da Falak take.

Zaune take da ganin idonta taci kuka, harta gaji, zamayi kusa da ita tare da cire mayafin data rufa, hannu tasa tarufe fuskarta, murmushi yayi yace Falak yau kuma rowar fuskar akemun? Ai yanzy munzama daya, nazama ke kin zama ni. Cire hannunta tayi tana kallonshi tana murmushi.

Falak nagaji dayawa, tashi muje muyi wanka, kafin muzauna ko? Aini nayi wanka sede kaje kayi, uhm bawani nan banyarda ba, to koma kinyi zaki sakene, ai bance kiyi ke kadai ba, tashi tayi tashiga bandaki ta hada mashi ruwan wanka sannan tafito, kokarin cire riga yake yana fadin da gaske fa nake tare zamuyi, ai tun kafin yakarasa fadi tayi waje.

Dariya yayi yace matsoraciya, wata rana zamuyi ne, shiga yayi bandakin yayi wanka, seda yagama shiryawa sannan tashigo itama tawuce bandakin, daga cikin dakin yake mata magana, kiyo alwala kafin kifito fa.

Bayan tagama tafito tadauki diguwar rigarta a durowa takoma bandaki tasaka sannan tafito, turare kadai tashafa tashimfida masu abin sallah, shiyajasu sallah har suka, gama, sannan yayi mata tambayoyi akan addini, dayake Falak akwai kokari duka ta amsa tambayar da yayi mata,

Tashi yayi yadauko ledar daya shigo da ita, kitchen ya koma ya dauko plate sannan yazuba masu, shiyarika bata shima yana ci, harsuka koshi, Falak de kunya takeji takasa sakin jikinta. Kwashe kayan yayi ita kuma takoma bandaki tayo brush, abandakin yasameta tana shirin fitiwo, hannunta yakama, seda yagama sannan suka fito tare, rigar jikinshi yacire dagashi se gajeran wando da vest, saurin rufe idonta tayi, jitayi itama yana kokarin cire mata riga, tace sanyi fa nakeji.

Dariya yayi yace ai bargo zamushiga, haka yacire mata riga daga ita se under wear da vest yabarta, bisa gado yajata, bayan aun kwanta yajawota yadorata bisa kirjinshi, yanata shafa mata kanta, tuni jikin Falak yafara rawa. Murmushi yayi yace Falak sarkin tsoro, ni babu abinda zan maki, magana zamuyi, kuma nafiso injiki ajikina shiyasa.

Ajiyar zuciya tayi dataji kalamansa. Falak, Sameer yakirata, na,am. Dole mugodema Allah daya nuna mana wannan rana, bazan iya kwatan tamaki irin farin cikin danake ciki ba, Allah yasani duk da ga yanda akayi aurenmu. Wlh banajin haushi kokadan, nasan dayawa mutane suna gulma akan aurenmu, amma ni beda meni ba.

Nasan Falak zakiji haushi da irin yanda na aureki, kiyi hakuri, komai ze canza, duk da kinfi kowa sanin yanda aurenmu yakasance amma dole inbaki hakuri, insha Allahu gobe tela zekawo maki dinkunanki, akwatinanki kuma suna gurin Umma, suma gobe zan daukosu.

Nayi hakane saboda banaso Umminku ta fahimci wani abu, shiyasa nakawo kaya marasa kyau, inaso kidaukeni abokin rayuwa na har abada, banida niyar cutar dake, kuma insha Allahu zan zamo maki abin alfahari, idan komai yayi mana dede zaki koma makaranta kema kiyi karatu kamar kowa,

Banaso idan kina da damuwa ki boyemun, yanzu bakida kowa seni, Baba mairo tayi maki nisa, yanzu nine makusancinki, idan har muka gina rayuwarmu ahaka, tabbas zamuji dadi kuma wani abu baze shigo ya tarwatsa zamammu ba.

Kamar yanda Umma tace nan da kwana 2 Baba mairo zata koma gidanta, itama bazata kara zama amatsayin me aiki ba, shikuma Dady insha Allahu zamu sa shi acikin addu,a kawu ma yace zetayamu da addu,a domin tun ranar daya ganshi yagane yana cikin yanayi na asiri.

Allah yanbani ikon rike amanar dana dauko, kuka sosai Falak takeyi, jawota yayi yakara rungumeta yana lallashinta, shiru tayi tana maida numfashi. Dagowa tayi ahankali tace Bansan dame zan gode maka ba, Allah ya..... bata karasa ba, jin yahade bakinsu guri daya, kissing dinta yake sosai, tuni jikin Falak yafara rawa, jin irin abubuwan dayake mata. Daga haka labari ya canza.

Zaune suke adaki suna ta faman dariya, Zarah tace yakukaga irin aikina, ai nafada maku bazan taba barin Falak tayi rayuwa me dadi ba, haka zata kare daga karshe tayi mutuwar wukakanci. Dije tace gaskiya hajiya kema kin iya aiki, yanzu dasunyi shekara 1 ze saketa?

 E haka nace mashi, daga farko, amma daga baya nace mashi dayaji ta isheshi ze iya koromun ita, kuma nace mashi yatabbatar yayimata raga raga, kada ya saukaka mata dede da kwana 1, kuma nace karyayi mata riko mekyau, kinsan dangiya akwai dukan matansu, haka ze maidata kamar jakarshi, ga aiki ga duka, kafin tadawo gidan nan setakoma kamar me kanjamau.

Asabe tace, amma inafatan idan tadawo ba,anan zata cigaba dazama ba ko? Zarah tace haba de, nikam mezanyi sa wannan yarinyar, ai dama burina ta wulakanta, idan da halima sonake tafito da ciki. Dije tace duk da haka idan tafito kada kibarta tashiga duniya haka, kinsan mutane akwai tausayi, wasu zasu iya daukarta su temaka mata rayuwarta zata iya yin kyau nan gaba.

Kawai itama ayi mata yanda akayima uwarta, asamata ciwo me tsanani kinga kota tafi acan zata mutu. Zarah tace kwarai kuwa wannan shawara taki tayi, zanjira fitowarta, sekuje gurin boka yayi mata aiki. Haka sukayita fira daga nan Zarah tayi masu seda safe tawuce gurin Alh,.

Jidda da Joseph suna nan suna cin duniyarsu, Jidda tayi kyau hartagaji, lokaci zuwa lokaci suna waya da al,amin shima idan yakirata seta ga dama take dauka, ayanzu yanda takejinta cikin daula, gani take tafi karfin Al,amin, shiyasa yanzu take mashi wulakanci. Tunbaya damuwa haryafara damuwa, ganin abin nata yana kara gaba, yasa yayima Joseph magana akan zezo yadauketa.

Dayake agaban Jidda sukayi wayar tun kafin Joseph yabashi amsa ta anshi wayar, cikw da masifa tace wai kai Al,amin ana so dole ne? Nifa yanzu babu wanda zetakuramun nima inada yancin dazanyi rayuwar danakeso, saboda haka dan Allah ka sauraramun kafita ahanyata, wlh yanzu nafi karfin ace wai kai saurayinane, ko ada rashin wayo neyasani biye maka, amma yanzu kasani ni Jidda nafi karfinka, bani ba kai.

Kashe wayar tayi tacema Joseph kada yakara daukar wayarshi, ita baruwanta dashi, anan zata zauna idan taso tafiya gida zata tafi ita kadai. Wani irin mugun murmushi Joseph yayi, dama yana lallaba tane saboda idan Al,amin yadauketa, idan yakara neman tazo zata iya dawowa.

Al,amin kuwa mamaki ne yakamashi, tsayawa yayi yana kallon wayar hannunshi. Wasu irin zafafan hawayene suka rika zubi mashi, har ga Allah yaso ace Jidda ta saurareshi, yanaso tadawo kodan yafada mata shiyanzu yatuba, yanaso itama ta tuba kuma shize aureta, tunda dama shine farkon lalata ta.

Tunda yaga wani abokinshi agabanshi yarasu, tundaga ranar tsoron Allah yakamashi, kuma yayi alkawarin baze kara aikata zina da duk wani laifi marar kyauba. Hakan yasa yakira joseph dan yaje yadauko Jidda amma tayi mashi rashin mutunci. Kuka sosai yakeyi yana fadin why Jidda, meyasa zakimun haka, kinsan ina sonki, tsautsayi ne, da rudin shedan yasa harna iya bama wani banzan arne ke yake kusantarki kamar matarshi, nayima Allah laifi megirma da har na iya amincewa da makiyin Allah.

Tashi yayi yashiga bandaki yayo alwala yafara sallah, bayan yagama yakira wani abokinshi yace mashi   yanason visa zuwa ummrah idan ze samu, yace mashi babu damuwa yazo gobe. Al,amin yace gara intafi inje inemi yafiyar Allah shine abinda yafimani. Ke kuma Jidda zancigaba dayi maki addu,a insha Allahu ko ban aureki ba, yanda na kaiki nine zan daukoki, nasan Allah baze yafemunba matukar ban raboki daga gurin kafirin Allah ba.

Washe gari dasafe Sameer yatemaka ma falak tayi wanka yagyra gurin bayan sunyi sallah suka koma bacci, rungume yake da ita kamar ze maidata ciki, se albarka yake samata. Segurin karfe 10 sukatashi, alokacin Ummanshi ta aiko masu da abinci, haka suka ci , ya gyara gurin, fita yayi yace zeje gida daga can yawuce kasuwa gurin me dinki.

Shatara ta arziki Zarah tayi masu Asabe, Godiya sukayi mata tasa driver yamaidasu. Komawa tayi daki tadauko wayarta domin takira jidda, dan jiya Alh, yake tambayarta ita, harcewa yayi tadawo gida hakanan, duk da yana tsoron Zarah amma bayajin tsoron yimata magana akan yaranshi, sede idan ta taso mashi da masifa ne, yake rudewa. 

Itama Zarah hankalinta yafara taahi ganin haryanzu Jidda bata dawo ba, tsaki taja ganin haryanzu wayar taki shiga, hakan ya tabbatar mata basu dawo ba. Oh ni Zarah kada fa yarinyar nan tajawo mani abun fadi agari, daga zuwa hado kayan aure shikenan. Kuma gashi ko sunan kawarta ta bansani ba, bare insan gidansu. Danaje na tambayo ko lafiya. Gaskiya nima nayi sakaci, kuma Inna Asabe ai tacemun babu inda Jidda take zuwa kullum tana gidanta. To ina tasamo wannan kawar?

Baba mairo ce tayi sallama harya zauna Zarah batasan tashigo ba, seda ta tabata sannan taji shigowarta, Hajiya lafiya kike irin wannan tunani haka? Ai nadauka bakida sauran damuwa yanzu, Murmushi Zarah tayi tace nikam damuwar mezanyi yanzu, kawai ina lissafin wasu kuda dene.

Murmushi Baba mairo tayi, dan taga alamar Zarah batasan duk abinda take fadi afili tafadeshiba. Hajiya dama zuwa nayi ince maki inaso zanje ganin gida, kinga na dade banjeba, amma wannan karon gaskiya zan jima, kila ma zanyi kamar wata 5. Waro ido Zarah tayi tace haba mairo, wata 5 fa? Yanzu yakike so inyi da aikin gidan, to hajiya gashi bansan inda zan sama maki wata ba, sede ki bincika nasan zaki samu.

Toshikenan, yaushe zaki tafi? Gobe nakeson tafiya. Allah yakaimu, bara zanfadama Alh, anjima seya sallameki, godiya tayi mata ta fita.

Falak tana zaune ita kadai afalo gashi babu kayan kallo, sede game kawai takeyi da wayarta. Sameer ne yashigo da sallama yana fadin yi hakuri baby na, nabarki gida ke kadai, wlh ina kasuwa tundazu. Murmushi tayi ta taso takarbi kayan daya shigo dasu tana fadin sannu dazuwa.

Komawa yayi yadauko sauran kayan, ruwa takawo mashi, sannan takoma tadauko abincin da aka kawo masu daga gidansu Sameer. Jawota yayi yana fadin kinzauna shiru ko? Kiyi hakuri zamu sa kayan kallo kinji. Abinci tamika mashi abaki tana fadi bakomai wata rana ai bazan zauna shiruba ko? Yace hakane, karbar cokalin yayi yacigaba da bata shima yana ci.

Bayan sungama takwashe kayan ta kai kitchen, seda ta wankesu sannan tafito, zama tayi yafara fiddo mata kayan dinkinta, sosai kayan sukayi kyau, ga kuma sauran daba,a dinka ba, acikin akwati da kayan shafa, akawatina 3 da kit yayi mata, kayan sunyi kyau sosai. Haka yasata tayi ta gwada dinkunan.

Washe gari. Da safe Baba mairo tashiga yima Zarah sallama, dubu 5 tabata tace inji Alh, yace tahau mota, se kuma kudin aikinta na watan tabata dubu 15, ita kuma takara mata dubu 2. Duk da dubu 50 Alh, yabata yace tabata hada kudin aikinta sauran kuma tayi tsaraba da kudin mota. Amma seda tarage. Godiya tayi mata tadauki kayanta tafita tana fadin nida aiki agidan nan har abada, Allah yatoni asirinki ke kuma.

Nima nace Ameen.

Urs,

NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[6/5, 3:11 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah 
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 90.....95

Zaune Baba mairo take adakin Falak kasancewar Sameer yafita, bayan tagama cin abincin da Falak takawo mata, takalli Falak tace, akwai sakon da ummanki tabani, tunkafin tarasu, kuma tacemun inbaki shi bayan kinyi aure.

Alhamdulillahi yau zancika wasiyar data bani, bude wannan jakar kifara ganin abinda ke ciki, wannan kuma wasika ce tabani ita aranar dazata rasu. Karba Falak tayi tabude jakar.

Awarwaro ne tun wanda kakarta tabata, lokacin tana yarinya, se kuma takardun makarantar ta, da takardun filin da Alh, yabama Ameer. Se A,T,M.  Bude wasikar tayi zata fara karantawa afili Baba mairo tace a,a Falak ki karanta aranki tunda wasiyace. Goge kwallan data zubo mata tayi tace, haba Baba mairo nifa ina maki kallon Ummata ce, kinga ko babu abinda zan iya boyemata, saboda haka kada kiyi tunanin zan iya boye maki wani abu. Murmushi Baba mairo tayi tace nagode Falak.

Fara karantawa tayi kamar haka......Falak nasan alokacin da wasikar nan zata iskeki nadade dabarinku, inaso kiyi hakuri da duk yanayin rayuwar da kika tsinci kanki, dukkan tsanani yana tare da sauki. Inaso kirike kaninki kada kibarshi yayi kukan rashin Uwa, duk da nasan shima da kyar zeyi tsawon rai.

Ga awarwaronki nan kisakasu ahannunki, saboda kirika tunawa dameshi. Nasan bakisan kowa nawa ba, yan uwan mahaifinki ma bawani yawa garesu ba, Kawunki kadai kika sani, kuma bana fatan ki kara ganinshi arayuwarki.

Nikaina bansan yan uwana ba, nare inyi maki kwatancen inda zaki samesu, kuma ba,a nigeria sukeba, a niger suke, sede bansan a inda zaki nemesu ba. Inaso kiyi hakuri ninasan Allah ne yakawo mana Alh, domin yazame mana dan uwa, kuma yazama Uba agareki, nasan kobayan babu raina, Alh, ze iya rikeki kamar nice narikeki. Kiyimashi biyayya kamar mahaifinki.

Banyarda ko bayan raina kibar gidanshi ba, kowane hali zaki shiga, gara kizauna agabanshi yafi kishiga duniya, nasan Zarah batasonmu, amma tunda Alh, da Jalila suna sonki kiyi hakuri kizauna dasu, kowace irin rayuwa zaki gani agidan kiyi hakuri wata rana zaki zamo haske agaresu.

Aure ne kadai nayarda idan kinyishi kibar gidan Alh, Falak dan Allah ki kula da Ameer, nasan beda lafiya amma kiyi hakuri dashi, insha Allah zakici nasara arayuwarki, idan kuma shima ya rasu, inaso kiyi hakuri, kirike Baba mairo tamkar nice agabanki.

Nima kaina namaidata uwa agareni, kema kiriketa zata zamo haske arayuwarki, kobayan kinyi aure idan har kina da hali inaso kidauketa zuwa gidanki, idan kuma mijinki be amince ba, acikin kudinki kisiya mata gida tazauna, kicigaba da kula da ita kamar ni.

Banyarda kirika boyema mijinki komai ba, shine gatanki, nasan In Allah ya yarda zaki samu miji nagari, wanda baze taba cutar dake ba. Kibashi dukiyarki, yakula maku da ita, dake da kayanki duka mallakinshi ne, kada kizamo me rowa arayuwarki, kuma kizama me temako, saboda temako shine yakawoki halin da kike yanzu.

Ga takardun makarantarki nan idan har kinyi aure baki karatu ba, inaso kinemi yardar mijinki kiyi karatu dan nasan burinki ne, idan har ya yarda, kiyi idan kuma beyarda ba, ki hakura. Kuma koni zan baki shawara zance kiyi hakuri da karatu, domin dukiyarki zata isheki kiyi kasuwanci.

Gara kizauna kirike mijinki zefi maki dakirika fita kina zuwa makaranta, 
     Kiyi hakuri da duk irin mijin dakika samu, kada kizama me tona sirrin gidanki agurin kawayenki, domin hakan ze bata zamanku da mijinki, kuma banaso kizamo meyawan kawaye,duk wata shawara dazakiyi kada yawuce Baba mairo da mijinki.

Ga takardun filin Ameer nan, idan har yarayu, wannan filin nashi ne, amma banyarda kimaidasu agurin Alh, ba harse idan shine yanema dakanshi, nasan Zarah tanajin haushin Ameer idan har tasan da Filin nan zata iya amshe shi. Idan kuma yarasu, toki mikasu zuwa ga Alh, dan yanada iko akansu.

Akwai A,T,M acikin jakar, wannan gadonki ne na Babanki, tunkafin yarasu yarika ajiye kudi aciki, kuma da sunanki aka bude accaount din. Bayan aurenmu da Alh, yayi mani kyautar kudi dayawa, kuma da wanda nasamu, hakan yasa nace mashi yarakani inje insaka abanki, kuma akayi maki A,T,M. 

Haka narika tara duk wasu kudi da Alh, yake bamu, bantaba cin komai ba, dan bana bukatarsu alokacin. Kuma nasan zasuyi maki amfani wata rana, kudine masu yawa, kibama mijinki yajuya makisu, kada kidamu da cewar ze iya cinye makisu, insha Allahu babu abinda ze samesu zakici moriyarsu.

Daga karshe kimikamun gaisuwata ga duk mijin da kika aura, Allah yayi ma rayuwarku Albarka, ya tsaremun ku, kada kuncin rayuwa yasaki ki sabama Allah, kiyi hakuri aduk halin da kika tsinci kanki.

Nabarku lafiya. UMMANKI HAJJO.😭😭.

Bisa cinyar Baba mairo Falak tafada tana kuka, jitake kamar yanzune Ummanta ta rasu, itama Baba mairon kuka takeyi, haka suka dauki lokaci suna kuka, har Sameer yashigo basu saniba.

Zama yayi kusa da Baba mairo hankali tashe yana fadin lafiya de Baba mairo, ko wanine yarasu? Se alokacin sukansan yashigo. Gyara zama Baba mairo tayi tana goge kwallan idonta, Falak kuwa kwanciya kawai tayi ajikin Baba mairo tana maida numfashi.

Bayan sun gaisa da Sameer Baba mairo tamika mashi wasikar hannun Falak, zama yayi yashiga karantawa, har yakai karshe, shima hawaye ne, suke fita a idonshi. Baba mairo tace ina fatan ka karanta abinda ke cikin wasikar?

Saboda haka Sameer inaso kabude kunnuwanka kaji abinda nakeso infada maka. Da farko de kai ba yaro bane, kuma malami ne na addini, nayarda da kai, hakan yasa nadauki Falak na baka, nasan bazaka iya cutar da ita ba, saboda marainiya ce, kuma nasan kasan hukuncin cutar da maraya.

Duk da ummanta bata sanka ba, amma hakan behana ta mika amanar Falak agurinka ba, kuma harsakon gaisuwa tayi maka. Tunkafin tasan wanda yarta zata aura tabashi amanar dukiyrta, dan haka inaso kadubi girman Allah karike amanar da aka baka.


Nasan kanada zuciyar nema, kada hakan yasa kace bazaka iya amfani da kudin matarka ba, nasan wasu mazan suna yima mata kudin goro suce gori garesu, dan Allah ka auri Falak, baka taba tunanin tanada dukiya ba, ita kanta batasan dasu ba, dan haka inaso amatsayinka na miji, uba, wa, dangi na Falak,ka karbi kudin nan karikesu tamkar naka.

Kada kaji shakkar daukarsu kayiwani amfani dasu, inaso ka gina filinka dasu, kuma ka kara jari kabude shagonka kaima katsaya da kafarka, kada kace zaka jira aikin gwamnati, itama Falak kabata tayi sana,a acikin gidanta, kasiya maku komai na rayuwa, banaso kuzauna cikin kunci, domin Allah ne yakawo maku sauyin rayuwa.

Banaso wani yaji wannan maganar se Ummanka, itama nizanyi matabayani da kaina, dan Allah banaso kace wani abu acikin maganar danayi idan har kadauki Falak amatsayin yar uwarka, to kada kayi duba ga dukiyarta. Allah yabaka ikon rike gaskiya da amana, kuma ya albarkaci dukiyarku.


Sameer yace amen Baba mairo, agaskiya kinbani aiki me matukar wahala, sede yanda nayarda da Falak nasan macece ta gari, da ace wata ce bazan iya amsar dukiyarta ba, domin gaskiya ni mutum ne meson tsayuwa da kafarshi, sede Allah yaga zuciyata, zanrike kudin Falak da amana, kuma insha Allah bazanyi almubazzaranci dasu ba, zanyi amfani da abinda kika ce, amma se idan Umma ta yarda.

To Sameer gaskiya naji dadin abinda kace, kuma dama yanzu zantafi can gidan dan nabaro gidan Zarah, seku tashi mutafi gaba daya ayita takare, dan gaskiya ina mejin haushin inshigo gidan nan inga wai kayan auren diyata ne, haka, ada danasan babu halin yi na hakura, amma yanzu tunda Allah yakawo mana canji dole ne, komai ya canza.


Jidda ce kwance adakin Joseph, tana hutawa, shigowa yayi tashi tayi tarungumeshi, dama bawasu kaya bane ajikinta, shima cire kayanshi yayi, yafara sarrafata, ahaka harsuka fada gado, wani irin salo yake mata, can tayi saurin tashi jin yana kokarin shigarta ta baya, cike da tsoro tace Joseph kanada hankali kuwa, wane irin abune haka, angaya maka ni namiji ce dazaka so yin amfani dani ta abaya? Wani irin wawan mari yadauketa dashi, jawota yayi, tana kuka tana bigeshi, dayake Joseph irin manyan mazan nan ne ana take ya murdeta ya hayeta. Kuka da ihu tasa amma takasa kwacewa, tanaji tana gani yayi amfani da ita ta baya. Kaca kaca yayi mata sannan yatashi yafita, kuma yasa key ya kulleta tabaya.

Kukan ma da kyar yake fita, wani irib azaba takeji ajikinta. Ko tashi takasayi, haka ta kwanta har barci yadauketa. Se can ta farka, dawani irin ciwon kai, da kyar da rarrafa tashiga toilet tayi wanka, seda ta gasa jikinta sosai, sannan tafito, riga kawai tasa takoma ta kwanta.

Can cikin baccinta taji anbude kofa, Joseph tagani shida abokanshi har 2, saurin tashi tayi tana kokarin saukowa dag gadon, hannunta yarike yana murmushi, cikin turanci yake magana, Baby ga friends dina nakawo maki sutayaki bacci.  Kallonshi tayi tana kuka tace dan Allah kayi hakuri wlh banason kudinka ka maidani gida plsssss.

Dariya suka dukansu, ya shafa fuskarta yace Baby keda gida har abada, zatayi magana ya fincike rigar jikinta, abokinshi yana ganin kaya, shima yamatso, abinka da bature babu kunya, agabansu yayi amfani da Jidda ta ko ina, tun tana kuka har takasa, yana gamawa shima dayan yayi, haka suka yimata kaca kaca, sannan suka fita suka barta asume, kara kulleta yayi suka tafi.

Lokacin data farka, gari yawaye, rarrafe tayi tashiga toilet, dan bazata iya tashi ba, jikinta duka ciwo yake mata, wanka tayi sannan tayi wankan tsarki, tayi alwala, wanda rabonta datayi wankan tsarki bare sallah tunda tazo london.

Da kyar tasamu tahada kayanta suka rufe mata jiki, dan batada wasu kayan kirki,rasa inda zata kallatayi sallah tayi, hakanan tayi sallah, rokon Allah tafarayi akan yakawo mata dauki. Byan tagama taje bude kofa domin samun abinci da yunwa takeji, amma taji kofar arufe, kuka tasaka tana kiran Al,amin.

Seda aka dade sannan aka bude mata kofa joseph yashigo da plate na abinci da kuma glass cup, ashe giya ce aciki yaxuba wasu kwayoyi aciki. Kusa da ita yaje yamika mata abincin, krba tayi tafaraci, tana gamawa yamika mata cup din, sha daya tayi taji warin giya, saurin zubar dana bakinta tayi, tace Joseph, nizaka ba giya? Mari yadauketa dashi, shake mata wuya yayi yadauki cup din yamatse bakinta, ya dura mata duk giyar, seda taji tana niyar mutuwa sannan tashanye. Bakinta yarike dan kada tayi amai.

Cikin lokaci kankani idanuwanta auka juye, wata irin sha,wa ta taso mata, ashe mganin daya samata na sha,awa ne. Nan take tajawoshi suka fada gado.
    Tundaga wannan rana joseph yamaida Jidda yar kwaya, da giya, batada abinsha se giya, tun bataso har tazamar mata jiki, ga kwayoyi tayake bata, duk ta inda yaso yake amfani da ita. Kuma abokanshi babu wanda baya hadawa da ita, gaba daya Jidda tafara lalacewa, idanuwanta sunkoma jajaye.

Al,amin kuwa yana Umarah, banda ibada babu abinda yakeyi, kullum cikin tunanin Jidda yakeyi, duk da yanzu yadena sonta, amma cike yake da danasanin kaita london yake, idan yakirata ma bata dauka, wata rana yakira wani abokinshi makwabcin joseph ne, shine ma yake fada ma Al,amin halin da Jidda take ciki. Sosai Al,amin yatausaya mata, yace ma abokinshi ze iya dauko mashi ita. Yace ai Joseph baya barinta fita, kullum kulle gidan yakeyi. Al,amin yace yana nan zuwa cikin sati insha Allah ze daukota, abokin yace shikenan nima zantemaka maka, dan Joseph mugune.

Haka Baba mairo tayima Umman Sameer bayanin komai, da kuma neman yardarta akan abinda tace, itama ta amince da maganar Baba mairo, kuma takara yina Sameer nasiha akan yaji tsoron Allah, tasan kudi yana iya canza mutum.


Cikin kankanin lokaci aka fara gini filin Sameer, kuma yashayi wani babban shago an kara gyarashi yaxuba kaya aciki, yayi yar karamar plaza, wadda aka sa sunan Ameer Plaza, sosai Falak taji dadin abinda Sameer yayi. Dayake gini ne nasamu kudi ahannu dan da nan yakeyin sauri, har kayan da za,a sa agidan Sameer yasiya, sun ajesu agidansu, komai na more rayuwa seda suka siya. Zama suke me cike da so da kauna. 

Baba mairo da Halima ma sauna zamansu lafiya, wanda ayanzu tadena kosan saudawa, abinci sukeyi me kyau, har cikin gida ake zuwa siye, almajirai sunafiddawa.

Jalila ma gab take dagama makarantar ta, hakan yasa taroki Falak data bari seta gama sannan taxo gida, Falak tace shikenan, Allah yabada sa,a.

Zarah kuwa hankalinta kwance yake babu abinda ke damunta, tasamu wata me aiki Jummai, batayi komai sede taci tasha, takara kyau, tayi kiba, ta maida Alh, saniyar tatsa, har dukiyarshi tafarayin kasa, sabodayawan kudin dayake bama Zarah, sosai ta tara kudi a account dinta. Bata da wata damuwa sena rashin dawowar Jidda, wata rana har kuka takeyi, takasa fadama kowa se Jalila, itama dataji haka seda tayi kuka, dan tasanyawon duniya kawai Jidda ta tafi, kullum cikin yimata addua, take.

Al,amin kuwa yana gama Umarah yakira abokinshi yace gashinan, ze taho, jirgin karfe 8 yabi yawuce London yana me addu,ar samun nasara akan Joseph.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/6, 3:30 PM] Nabeela lady: πŸ™‹πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™‹πŸ» AGOLAH !!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 95..... 100

Al,amin yana sauka london suka hadu da abokinshin yana jiranshi a air pot. Direct gidan shi suka wuce, bayan yayi wanka yayi sallah, yaci abinci. Anan suka fara tsara yanda zasu dauko Jidda. Duk da abokin Al,amin ba musulmi bane amma yana da riko da addininsu, kuma yanada gaskiya, sunanshi Daniel, kum makwabcin Joseph ne, sede halinsu kwata kwata badaya bane. Kwanan Al,amin 2 suna lura da duk wani shige da ficen Joseph. Jiran lokaci kawai sukeyi su shiga gidan, ko so daya bega Jidda ba, hakan ya tabbatar mashi baya barinta fita.

Ginin su Sameer har ankusa gamawa, fenti kawai akeyi, Sameer beda lokaci kullum yana plaza ko gurin masu gini. Falak tayi kyau sosai, idan kaganta baza kace Falak din daka sani bace, takara girma, kyawunta yakara fitowa. Yanzu babu abinda kedamunta, se tunanin Dadynsu Jalila, kullum cikin yimashi addu,a take.

Kuma Baba mairo tace kada suje gidan se nan dawani lokaci. Zamansu da Sameer zamane na mutunta juna, suna bala,in son junansu, Sameer bayasan ganin bacin ran Falak, itama haka, kasancewarta mace me hakuri kuma tasamu miji me hakuri. Haryanzu akwai sauran kudinta a account, ko naira Sameer yafitar seyayi mata bayanin abinda akai da ita, har fushi tayi mashi akan abinda yake mata amma yaki bari, yace haka shine gaskiya. Dole tahakura badan taso ba.

Ajikin gidansu yasa akayi shaguna guda biyu, yace na Falak ne ze zub mata kaya asamu me tsare mata, musamman da unguwar basuda irin shagon saida kayayyaki haka.
    Baba mairo da Umman Sameer hankalinsu kwance suke sana,arsu cike da girmama juna, dan Baba mairo ta girmi Halima sosai, dan ita Halima bawani tsufa tayi ba, kawai de halin rayuwa ne yamaidata babba, amma yanzu da kwanciyar hankali tafara zuwa masu tuni tafara maida jikinta. Duk wata shawara dazasuyi Baba mairo suke kawo ma ita, idan kuma abun yafi karfinsu, Kawun Sameer suke kaima ita.

Zarah ce zaune adakin Asabe, bayan sungama gaisawa, tace waini Inna haryanzu shiru babu Jidda, nifa hankalina yafara tashi, kawai ina cikin kwanciyar hankali yarinyar nan zata sani cikin damuwa, aduniyar nan babu abinda ke damuna se rashin sanin inda Jidda take, tun Alh, yana tambayata ina mashi karya har nafara gajiya.

Jiya yake cemun zezo har nan yatafi da ita, kuma idan har bata fitar da mijin aure ba, duk wanda yasamu zebama ita. Shine nazo dan Allah kirakani gurin boka yaduba mun inda take, kotana raye, kuma arufema Alh, baki yadena maganarta, kota dawo kada yatambayeta inda taje.

Asabe tace gaskiya ni kaina abun yana damuna, kuma kinga idan haryagane bata gidan nan muze zarga, gara muje arufe mashi baki kawai. Ita kuma nasan duk inda take zata dawo. Malam dayake bakin kofa yana jinsu yashigo, ya kalli, Asabe, duk da yanajin tsoronta, amm wannan karon seda yayi magana.

Yanzu ke Asabe kina ganin abinda kikesa yarinyar nan tanayi dede ne? Na dade ina jin duk wani abu da kukeyi akan bawan Allan nan, wai seyaushe zaku tuba kudena abinda kukeyi? Kadafa ku manta akwai wata rayuwa bayan an mutu, kum kowa ze tsaya agaban Allah yafadi abinda yayi, wanda aranar baki baze iya magana ba, saboda shima makaryaci ne. Ke kuma Zarah abinda nakeso dake kiji tsoron Allah, kina ganide tun aduniya yafara nuna maki ishara, akan diyarki, yanzu Allah kadai yasan inda take, kuma duk inda take, ba halin kwarai take aikatawa ba.

Nasha ganinta da manyan mutane suna sauketa kofar gidan nan, amma dayake baku daukeni abakin komai ba, bakwajin maganata, yaude nafada maku iya gaskiyata, idan harkunji to, idan kuma bakuji ba, wlh inaji maku tsoron ranar danasani, ranar da babu lokacin gyara barnar da kukayi.

Zarah ta zunburo baki tace wai kai Baba mekaga munyi? Nifa wlh banason takura, dama naga duk sanda nazo gidan nan labe kake mana, kuma kana nufin Inna Asabe ita zata cuceni ne, ko gorin haihuwa zaka mata? Kuma ni nasan babu abinda Jiddata take aikatawa se alheri, kawai de kanamun bakin cikin yanda na auri me kudi, itama tasamu. Kuma mekaji munce zamuyima Alh?

Inna Asabe tace ai gara ke dayake diyarshi ce kifada mashi, wato Malam yanzu duk irin rikon danayima Zarah beyi maka ba? Lallai nayarda da,akace namiji ba dan goyo bane, to ai kadeji da kunnanka, abinda diyar taka tace. Kuma wlh wannan shine karo na karshe da zakaji muna magana kashigo kasa mana baki. Wuce kabani guri, namiji da akai kana halin mata. Allah yabaki hakuri ammade Zarah kiji tsoron duniya, kuma ni kike fadama magana. Kije duniyace ta isheki komai, wanda bezo bama jiranshi takeyi.

Dallan can kawuce kabamu guri, fita yayi yana matsar kwalla, wai yau diyar daya haiface take fadamashi magana. Asabe tace aikinyi mun dede, maza zuma ne, dole seda wuta. Shiyasa nace kada ki saurarama mijinki, kina ganinde duk irin biyayyar danakema Babanki amma yau yayimun gori. Kukan munafurci tasa, anan Zarah tashiga bata hakuri. Asabe tace tashi muje inrakaki dan Dije bata nan tayi tafiya. Tashi sukayi suka wuce gurin boka.

Tundaga ranar da Zarah tasama Alh, magani a abinci bekara maganar Jidda ba, shiyasa hankalin Zarah yadan kwanta, duk itama bata bacci sosai, dan tanason Jidda, tamafi sonta akan Jalila, dan halinsu daya da Jidda. Saukinta daya boka yace mata Jidda tana raye kuma yakusa dawowa gida.

Yau Jalila tagama final exam dinta, kuma ayau tagama shirya kayanta domin tafiya gida, driver take jira. Yana zuwa yadauketa, seda tafara biyawa cikin kasuwa inda kakansu yake. Dan ita bata zuwa gidansu, kwata kwata jininta be hadu dana Asabe ba, shiyasa tunda tafara karatu so 1 taje gidan.

Abakin shagon dayake zama tasameshi, tasowa yayi yana fara,a ganin Jalila, dan yana sonta sosai, tana temaka mashi, da yan kudi duk sadda tazo gurinshi, har bakin motar yakaraso, bayan motar yashig, bayan sungaisa da driver, Jalila tace ma driver yadan jirasu awaje.  Gaisawa sukayi take fada mashi batun tafiyarta yau, dan tagama karatu, sosai yayi mata murna, sede beji dadin tafiyar taba zedena ganinta, dan itace abokiyar shawararshi. Jalila tace ai kaka kona tafi zanrika zuwa, kuma baga waya nan nabaka ba, zamu rika gaisawa, idan akwai wani abu seka fadamun tanan, idan yakama inzo senazo, ai babu nisa daga Kaduna zuwa Zariya.

Goge kwallan data zubo mashi yayi, Jalila tace kaka akwai abunda ke damunka, bantaba ganinka cikin damuwa haka ba. Murmushi yayi yace Jalila akwai abunda kedamuna sosai ma, kuma akan mahaifinki ne, da kuma Zarah,,,,,,,, anan yafada mata duk irin firar dayaji su Asabe sunayi da irin cin mutuncin da Zarah tayi mashi.

Seda Jalila tayi kuka, jin irin abinda Umminta keyi, hakuri tayi ta bashi, tace Kaka nima nasan akwai abubuwa da dama wanda Ummi takeyi, kuma bakowa bane yake zugata se su Inna Asabe da Dije. Amma Ummi tayi mani kashedi babba akan idan taji ina shiga maganar da babu ruwana aciki, har cewa tayi zata tsinemun, hakan yasa ma tunda nataho karatu ban koma gida ba, Dady ne kuma yanazuwa muna gaisawa.

Addu,a kawai nake masu, amma Kaka yaya Jidda tayi nisa batajin kira sede addu,a. Yace kikara hakuri insha Allah wata rana gaskiya zata fito, mucigaba dayi masu addu,a, kuma kamar yanda Zarah tafada maki, banason kishiga abinda babu ruwanki. Allah yayi maki albarka, kuma dan Allah Jalila kinga kingama karatu, kada kitsaya ruwan ido, kifitar da miji kiyi aure, banason zamanki agidan nan, kinga Falak tayi aurenta tahuta,kema Allaj yabaki miji nagari. Haka sukayi sallama takawo kudi tabashi, suka tafi.


Ayau Al,amin suka shirya yanda zasu dauko Jidda, Daniel yace kabari zan shiga gidan tunda yau munci sa,a shidaya yadawo, zanje muyi fira, zan bashi wiky nahada mashi da maganin bacci, dayayi zankiraka seka taho. Al,amin yace to amma megadin gidanfa? Daniel yace kabari nasan yanda zanyi dashi, kaide kazama cikin shiri, kadauki visa dinku da kayanka, nayima me taxi magana yanzu zezo yajiraka kuna fitowa kushiga yawuce daku. Godiya sosai Al,amin yayi mashi kuma yayi mashi alkawarin idan yasamu dama zezo surika gaisawa.

Zaune ya iske Joseph afalo yana kallo, bayan sungaisa Daniel yace joseph kaboye yanzu kaja kaya ko. Murmushi Joseph yayi yace haba ogana kaine bana ganinka, ya labari? Daniel yace lafiya lau, wata sabuwar whisky nakawo maka jiya wani abokina yabani ita, amma kasan bana shan irinta, shine nakawo maka. Katabar kwalbar Joseph yayi yace wow amma nagode, budewa yayi yafara sha, Daniel yace yauwa bama gateman dinka yasiyomun, irin whisky danake sha acan bakin titi.

Karbar kudin joseph yayi yafita yana tangadi yafita, bayan ya aiki megadi yadawo yacigaba da shan whisky dinshi suna fira, cikin lokaci kadan yafada bisa kujera bacci yadaukeshi.

Cikin sauri Daniel yadaukeshi yakaishi daki, yakira Al,amin. Jidda tana kwance adaki tasha giya da kwaya summata yawa tana bacci, Al,amin be tsaya bata lokaci ba yadauketa daga ita se riga da dogon wondo, kanta babu dankwali yasha tsohon kitson attache, fita sukayi ko tsyawa daukar jakarta beyi ba, ga uban kudin da Jidda ta tara aciki haka yabarsu suka fita, me taxi suka samu dan nan suka shige yadaga ma Daniel hannu suka nufi air pot, shima Daniel yafita. Tun acikin mota Al,amin yaciro jallabiyar daya siyowama Jidda yasa mata, yakama gyalen yadaura mata, sede duk abinda akeyi bacci take. 
   Suna zuwa ya sallami me mota suka jira aka kira sunansu yakamata suka shiga, ko acikin jirgin kwantar da ita yayi bisa cinyarshi tacigaba da baccinta. Suna isa yayima wani abokinshi waya yazo yadaukesu suka nufi gidanshi.


Ayau su Falak suka tare. Asabon gidansu daya keru, yayi kyau sosai, duk da bawani ginin karya akayi ba, amma yayi kyau, duk wanda yashiga ciki seya burgeshi, anzuba kaya masu kyau, dakin Falak yasha kaya masu kyau, kitchen dinta kamar nawata diyar me kudi.

Kwance Falak take akan cinyar Sameer suna fira, wayarta ce tayi kara, dauka tayi tace habawa Jalila nikam nayi fushi, yau satinki nawa da dawowa, amma kinkasa zuwa kiganni. Jalila tace dan Allah kiyi hakuri wlh banaso Ummi tasan gidanki zanzo, amma yanzu kiran danayi maki ma kwatancen gidan nakeso kimun ganinan ina shiryawa.

Falak tace to Allah yasoki, bara inturo maki da address din yanzu. Jalila tace Allah sa de mijinki baya nan dan wlh tsoran masu shaye shaye nake. Dariya Falak tayi tace ai babu abinda zemaki, kuma bayama nan, Jalila tace Allah Falak dande kinmatsamun inzo banason zuwa inga halin dakike ciki. Falak tace nide banason wani dogon surutu sekinzo. Kashe wayar tayi tana dariya, ta tura mata da address din.

Sameer yace keda Jalila ne hala? Tace emana, kasan metace, yace a,a wai cewa tayi Allah sa baka nan tsoron yan shaye shaye take. Dariya yayi yace ai zanso inga irin mamakin da Jalila zatayi idan tagammu amatsayin ma,aurata.

Au, kinga namanta tundazu inaso infada maki, dana fita shago nahadu dawani babban abokina Saleem, tare mukayi Zariya dashi amma shi yasamu aiki, awani kamfani na babanshi. Dama kuma bussiness yakaranta, nikuma nayi Pharmacy. Yarigani gamawa da shekara 1 danmu shekara 5 ne sukuma 4.

Bayan mungaisa yake tambayata menakeyi anan, nace mashi ai shago nane, shine yace meyasa ban bude chemist ba, natsaya bude shago, shine nace mashi kasan bude chemist ba sauki bane dole sekana da hanya shiyasa kawai na bude plaza.

Yace mun bana aiki ne, nace mashi wlh na nema harnagaji bansamuba, shiyasa kawai na hakura. Shine yace anjima da dare zezo yasameni ashago muzo nan gida ze amshi takarduna ya bama babanshi yanemamun aiki, kinsan babanshi babbane dan a Abuja ma yake aiki.

Falak tace kai amma gaskiya naji dadi sosai. Allah yasa asamu, yace Ameen. Tace bara intashi inshiryama Jalila abinci kafin tazo, yace to nide ina daki bacci zanyi idan tazo kitadani.

Jalila tafito cikin shirinta tace ma Zarah Ummi nagama shiryawa, zantafi. Zarah tace kijira driver yazo ya kaiki mana, yanzu zedawo. Jalila tace a,a Ummi kawai kibarshi zantafi sauri nakeyi kuma kawata tana tajirana. Kudi tamika mata tace gashi nan sarkin sauri, kigaisheta, amma kada kiyi dare fa. Tace to Ummi nagode.

Fita tayi tahau taxi tayi mashi kwatancen inda ze kaita, yace yagane gurin. Tafiya suke tana tunanin halin dazata iske Falak aciki. Dede wani hadaddan gida suka tsaya yace mata hajiya mun iso seki kirata kiji wane gidanne aciki. Jalila tace malam anya nanne unguwar kuwa, nifa duk cikin gidajen nan babu wanda yayi kama da irin gidan da,aka cemun Falak tana ciki. Yace tonide sauka kibani kudina ki kirata mana idan bata fitoba seki nemi wani ko. Sauka tayi tabashi kudinshi taciro wayarta takira Falak.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/12, 3:25 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH !!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 100.....105

Lekawa kofar gida Falak tayi domin ganin inda Jalila take, tana fita suka hada ido kasancewar akusa da gidan take tsaye. Mamaki ne yakama Jalila ganin daga inda Falak ta fito, kallo daya tamata tagano kyawun datayi.

Falak tace tokishigo kosena daukoki? Murmushi tayi tanufo gidan, fuskarta dauke da mamaki. Suna shiga, mamakinta yakara yawa ganin irin yanda cikin gidan ya tsaru. Falak tace bismilla mana. Jalila tace Falak bazaki kasheni da mamaki ba, zo zauna ki amsa mun tarun tambayoyina, kafin ayi komai.

Dariya Falak tayi tace a,a zauna inkawo maki abun sha idan muka gaisa zan amsa maki. Bata jira mezata ceba tawuce kitchen, da kallo Jalila tabita, tana mejin farin cikin ganin halin data isketa. Hamdala kawai takeyi acikin zuciyarta.

Bayan takawo mata kayan motsa baki, tazuba mata zobo a cup, tace ina zuwa, kai tsaye dakin Sameer tawuce, tsaye tasameshi yana shiryawa, da alama daga wanka yafito, amsar man tayi tacigaba da shafa mashi tana murmushi.

Sameer yace daga ganin wannan fara,ar nasan Jalila ta iso, Falak tace tanama falo, nace bara inzo inkiraka ta idasa cika da mamaki kafin inbata labari nafiso kana zaune agurin. Kayanshi tamika mashi, ya amsa yasa yace nima zanso inga fuskar Jalila ai. Turare yafesa yace muje ko, hannunta yakama suka fita.

Jalila dake zaune afalo tana cin abinci, se kalle kalle takeyi, duk da gidansu yana da kyau amma tsarin falon Falak ya burgeta. Zumbur tamike ganin abinda batayi zatoba. Malam Sameer, Jalila tafada cike da mamaki. Murmushi yayi yajawo Falak suka zauna akujera, zamewa tayi daga jikinshi ta zauna sosai.

Sameer yace Jalila kizauna mana kada kuda yashige maki baki, zama tayi tana kallon Falak. Dan Allah kufitar dani aduhu, duk da na dade dasanin kana son Falak amma banyi zaton kaine zansama amatsayin mijinta ba, kuma ni Ummi ba irin auren da tace tama Falak bane, nagani agidanta.

Sameer yace to Jalila sede muce Alhamdulillahi, kuma inaso kamar yanda nasanki me gaskiya kici gaba da zama ahaka, kuma inaso infada maki ba,ayima Uwa biyayya inde gurin sabon Allah ne, kuma hakan bayana nufin kamata rashin kunya ba,  duk yanda mahaifiyarka takai ga aikata sabo, tana nan amatsayin Uwa agareka, sede kayita nema mata shiriya agurin Allah.

Tabbas nasan Umminki tana aikata abubuwa dayawa marasa kyau, amma adalilinki da kuma Dadynki yasa dole muma mubata darajar Uwa, kuma inaso duk abinda zakiji kiyi kokarin barinshi amatsayin sirri, kamar yanda mukayi, nan da wanj lokaci komai ze zama dede bara infada maki yanda akayi nazamo mijin Falak..............


Sautin kukan Jalila kawai akeji falon, Falak kam hawayene keta zubo mata. Da kyar Jalila tayi shiru, goge idonta tayi ta matso kusa da Falak, har kasa ta duka tace Falak tabbas nasa Ummi na bata cancanci afuwa agareki ba, amma duk da haka iname baki hkr akan irin abubuwan da tayi maki. Insha Allah wata rana zata gane gaskiya, nide kam banyi sa,ar uw..... dasauri Falak tarufe mata baki tana girgiza mata kai.

Sameer yace a,a Jalila kada inkara jin wata kalma me muni akan Umminki, laifi nede ta aikatashi, abinda yarage agareki, addu,a zakiyi mata, Allah shine maji rokon bayinsa, idan yasota da rahama seya shiryar da ita, amma kada kikara cewa zaki aibanta ta.

Jalila tace nagode Malam, kuma insha Allah nazan kara fadar haka ba, kuma kusani bazan taba fadin wani sirri naku ba, nime kaunar kuce, ina daukar Falak tamkar Jidda agurina, Falak takamata takoma bisa kujera ta zauna, Falak tace to ya isa haka, yanzunde komai yawuce, inafatan yanzu bakijin tsoron mijina ya iskeki agida ko? Dariya suka su duka. Sameer yace toni bara infita munyi alkawari da Saleem zamu hadu a plaza, Jalila kijira indawo ba dadewa zanyi ba, tace to ammade kayi sauri Ummi tace kada inyi dare. Haka sukayita fira da Falak.

Har cikin gate din Al,amin abokinshi yashiga dasu, bayan yayi packing Al,amin yafito yana tallafe da Jidda, wadda haryanzu bata ida dawowa hayyacinta ba, jakarshi yadauka yayima abokinshi godiya, sukayi sallama yashiga gida. Afalo ya kwantar da ita, yawuce daki, toilet yafada domin wanka dan duk jikinshi warin giya yakeyi, bayan yafito yasaka jallabiya yayi sallolin da beyi ba, sannan yafito falo, azaune ya iske Jidda tana ta yan kalle kalle, sede haryanzu idonta ba dede yake ba. Kitchen yawuce yadauko madara pick yazubota akofi, yazo kusa da ita yamika mata, amsa tayi takafa kai seda ta shanye tas tabashi kofin.

Yace Jidda kinaji na? Kai tadaga mashi, yace tashi kije kiyi wanka nasan zakiji karfin jikinki, sekidawo muyi magana, da kyar ta tashi amma seta koma tazauna, ganin haka yasa yakamata suka nufi daki, har toilet yakaita sannan yafito, kitchen yakoma yadora masu indomie, cikin minti 20 yagama hada masu komai, yazauna jiranta.

Da karfi Jidda tabanko kofar dakin tafito, cak ta tsaya ganin Al,amin afalo, kara kallon falon tayi, hawaye suna fita a idonta tace Al,amin ina muke nan? Tasowa yayi yace Jidda ki kwantar da hankalinki a nigeria muke, kinsan nayi maki alkawari zan daukoki. Ya isa haka. Meyasa zakamun haka, kuma ina jakar kayana naduba banganta ba. Al,amin yace Jidda nida name kokarin cetoki daga halaka ina zan tsaya daukar wata jakar kayanki, wadda nasan kayan ciki ma bana mutunci bane.....tasssssss yaji tadaukeshi da mari.

Cike da mamaki yadafe fuska yana kallonta. Wani irin kuka tasa tare da rike mashi kwalar riga. Kacuceni Al,amin, kasan irin walahar dana sha kafin intara kudadena dasuke cikin jakata. Wlh nasan ko zaka saida duka kadarorinka bazasu kai yawan kudin da Joseph yabani ba, harma da wadanda na daukar mashi bada saninshi ba. Sannan ace duk irin azabar dana sha ace nayita abanza. Ina ruwanka da rayuwata, kaine Uwata ko Ubana?...... Kuka yaci karfinta tazube akasa.

Tausayi Jidda tabashi, dukawa yayi yace Jidda kiyi hkr, nasan bankyauta maki ba, amma hakan danayi maki wlh shine gata, kuma kudi bazasu taba biya maki wata bukata agidan Joseph ba, sede ya illataki daga karshe ma Ya kasheki abanza. Ni nasan waye Joseph, kiyarda dani bazan taba cutarki ba, kozaki cemun haryanzu Joseph yana zama dake acikin mutunci?

Kiyi hakuri ki koma gida kema kituba zuwa ga Allah kisake sabuwar rayuwa kamar kowa, haryanzu kinada sauran lokaci tunda Allah be amshi ranki ba. Tashi yayi yadauko abinci yazauna yazuba mata yace dauka kici nasan kinajin yunwa, lemu yazuba mata akofi. Ba musu tadauki abincin tafara ci dan yunwa takeji sosai, kallonta yakeyi tanaci tana kwalla. Shima zubawa yayi yafaraci.

Lemu tadauka tasha, sede kagaba daya test dinshi beyi mata ba, kallonshi tayi tace Al,amin bakada whisky ne, gaskiya bazan iya shan wannan kemun ba. Mamaki ne yakamashi jin abinda Jidda tace, girgiza kai yayi yace Jidda yau kuma kece kike shan giya? Amma ai kinfi kowa sanin bana shanta, asalima bana zama tare da meshanta, saboda haka hakuri zakiyi tunda kindawo gida ki aje duk wata dabi,a da kika dauko acan kicigaba da rayuwarki kamar da. Kinsan gara mutum ya aikata kowane laifi ze iyayin daraja agurin mutane da ace yazama mashayin giya, aduk lokacin dakika shata bakisan da wanda zaki haduba, zaki fita daga cikin hankalinki,saboda haka iname shawartar ki tunda de nasan baki dade dafara shanta ba, kiyi hakuri kidena.

Kuka tasaka mashi tace bazan iya ba, Al,amin, Giya tazama tamkar ruwan shana bana iya minti 5 batare dana shata ba, katemaka mun dan Allah. Tausayinta yakamashi yatashi yadauko mata Lime drink a kitchen, karba tayi tafara sha, duk da bataji dede ba amma garashi da dayan.

Bayan sungama suka koma bisa kujera, tasowa tayi daniyar fadawa jikinshi yayi saurin matsawa, Jidda lafiyarki kuwa? Nifa yanzu rayuwata ta canza ba Al,amin din da bane yanzu, duk da ban fada maki ba, amma yanzu haka daga saudiya nadawo shine nawuce london domin daukoki. Wlh Jidda yanzu natuba m, nakoma ga Allah, babu abinda na tsana kamar Zina. Ke duk wani laifi na sabon Allah nadenashi, saboda haka kema ina rokonki daki tuba kizo muyi aure, amma kafin nan inaso kibani labarin yanda zamanki da Joseph yacigaba datafiya.

Kuka tasaka mashi, anan takwashe komai tafada mashi, sosai yaji tausayinta, duk da hada laifinta, da sin kudinta suka jamata. Girgiza kai yayi yace Lallai Jidda kinga rayuwa, sede agaskiya naso in aureki, tun abaya amma kika gwada a,a ko alokacin da nayi maki waya zanzo indaukeki nayi niyar muna dawowa in aureki, amma kikamun rashi, mutunci. Gaskiya Jidda bazan boye maki ba, bazan iya kara hada shimfida dake ba ahalin dakike yanzu, saboda Joseph yagama cutarki yayi amfani dake ta ko ina dayaga dama, bashi kadai bama harda wasu kazamai, wadda gaskiya ina tsananin kyamarsu, da ace Joseph ne kadai yayi amfani dake, zan iya aurenki, saboda nasan halinshi. Amma kincemun tunda yakawo abokanshi suka fara lalata dake yadena kusantarki. Hakan yanuna cewar akwai muguntar daya shirya maki.

Kiyi hakuri da abinda zanfada maki, kidaure kije asibiti ayi maki duk wani test daya kamata, domin tabbatar da lafiyarki, ni kaina nasan naje asibiti da yawa, ke har saudiya naje anduba ni. Kuma Alhamdulillahi banida cuta ajikina, kinga dole inji tsoron aurenki.
    Jidda tayi murmushi tace nima haka babu abinda kedamuna, saboda haka babu wani asibiti dazanje, kuma dama ai nafada maka nafi karfin na aureka, dan bakada kudin dazaka rikeni, shiriya kuma ai ta Allah ce, kamar yanda yashiryaka nima nasan watarana tawa tana nan zuwa. Murmushi yayi yace Jidda....... Hannu tadaga mashi tace ya isa, kabar wa,azinka banaso, idan kashirya kazo kamaidani gida. Kai ya girgiza yatashi yaname cike da tausayinta.

Doguwar rigar datasaka dazu ita tamaida, gaba daya ta rame, se uban hasken bleaching dayayi mata yawa, duk ta fita hayyacinta. Haka yafita yadauko mota yaja suka tafi. Adede kofar gidansu ya ajeta, kudi yadauko masu yawa yamika mata yaceto Jidda ina maki fatan alkhairi, nide daga yau bazaki kara ganina ba, se ince Allah yasadamu da Alkhairi, abu na 2 kuma ina rokonki daki yafemun, nasan nabada gudummuwa gurin lalacewar tarbiyarki, dan Allah kiyafemun. Murmushi tayi ta amshi kudin tace bakomai Al,amin nayafe maka, Allah ya yafe mana baki daya. Idonshi suka ciko da kwalla, yayi saurin dauke fuskarshi daga kallonta, yanaji tafita tana fadin bye, amma ya kasa kallonta, tabbas yasan Jidda tayi nisa batajin kira, sede addu,a. Haka yaja motarshi yatafi.

Bata shiga gidan ba seda takoma wani chemist tasiyo wasu kwayoyi sannan tawuce gida. Megadi da driver tagani zaune suna fira, wuce su tayi, megadi yace baiwar Allah daga ina zakizo kiwuce mu ko sallama babu, wani kallo tayi mashi tace ina ba gidan ubanka bane bare kadamu da rashin sallamata, driver yace tofa meyakawo nazagi kuma, amma naga kamar Jidda ko? Oho koma wacece badamuwarka bace tunda inda gado agidan, mamaki yakamasu sukayi shiru sukallonta hartawuce. Driver yace ikon Allah, wai yaushema tadawo? Megadi yace yanda kaganta haka naganta, tagaji dayawon duniyar ne. Amma insha Allah zataga bacin rana yanda ta iya bude baki tazageni. Driver yace kayi hkr Baba, Allah yashirya.

Zarah tana zaune afalo tana kallo, taji sallama saurin tashi tayijin kamar maganar Jidda, cak ta tsaya ganin Jidda cikin wani irin kama. Jidda tace Ummi yanaga kintsaya kamar baki farin ciki da ganina ba. Zarah tace Jidda lafiyarki kuwa? Wucewa tayi tazauna tace lafiya lau Ummi. Kusa da ita Zarah tazauna tace a,a ba lafiya ba, naga kindawo kamar wadda aka koro, ko jakar hannu banganki da ita ba se bakar leda, bare jakar kaya. Jidda tace kede Ummi kawai ki godema Allah nadawo lafiya, bakiji ankasheni ba. Zarah tace Jidda kisa kuma meyafaru? Tace Ummi kwanan mu 10 agidan yan fashi, babu abinci me kyau, se wahala dasuke bamu, intakaita maki ma, kawata damukaje london tare sunkasheta, nima da kyar wani yaji tausayina yafito dani yabani wannan kudin ya sakoni motar kaduna, amma sun kwace mana komai, bakiga ko dan kunnena na zinari babu ba. Gaskiya munsha wahala, gashi bamusan garin da,a kaimu ba. Lokacin damuka taho daga air pot dayake da dare muka sauka ashe me taxi din barawone, yafesa mana wani abu, bamu kara sanin inda muke ba, amma nasan ba,a kaduna muke ba, dan kafin na iso nan munyi tafiya me nisa.

Kuka Zarah tasa tace shikenan yanzu baki samo komai ba, duk irin zaman dakikayi haka suka rabaki da komai? Amma de Allah ya isa wlh, ina nan ina jiran samun kusi masu yawa amma wasu sunfini so. Jidda tace wlh kuwa Ummi dana dawo da jakata, dakeda talauci har abada. Zarah tace Allah ya isa wlh bamu yafe ba. Jidda tace Ummi Ina Jalila fa? Taje gidan kawarta, kinsan ai tadawo tagama karatunta. Jidda tace lallai kam tayi kokari, ina fatan de bata barinki cikin rashin kudi? Zarah tace wannan yarinyar idan da ace ita zata rika ciyar dani ai dana mutu, babu inda take zuwa, ko saurayi bantaba jin yayi sallama da ita ba. Duk yanda akayi tagogo kashin tsiya agurin waccan AGOLAR. Dariya Jidda tayi tace ni wlh Ummi harna manta da ita, ashe tana duniyar. Kince tayi aure ko? Emana, takusa fitowa ma. Jidda tace haba keko Ummi tunda de kinmata aure kawai kibarta tayi zamanta agidan mijinta, idan yagaji yasaketa, amma yanzu mezatayi maki idan tadawo? Babu komai, kotadawo ma korarta zanyi, to kingani ai babu amfani mugunta ko,,,, ke tashi kibani guri banason wannan shirmen surutun naki. Dariya Jidda tayi tace nide nawuce daki bacci zanyi kuma kada atadani.

Zaune suke bayan sunyi sallar magriba sun gama cin abinci. Jalila tace wlh Falak tafiya zanyi banason mijinki yajamun fadan ummi, damma Dady baya gari. Falak tace yanzu zedawo kiyi hkr,,, sallama sukaji, Sameer ne, yashigo yana fadin afuwan Jalila wlh Saleem ne ya tsaidani yanzu hakama tare muke. Jalila tace aiko yanzu nake cema Falak zantafi. Sameer yace Dear dauko hijabinki ga Saleem nan zeshigo kugaisa, tashi tayi tashige daki shi kuma yafita.

Atare suka shigo da sallama, Falak ta amsa, tana fadin manyan baki garemu yau ashe, Saleem yace gaskiya kam, kuma masu laifi ba, tunda gashi seyau muke zuwa ganin amarya. Zama yayi bayan sungaisa Falak tace Jalila kawo masu ruwan mana,  Jalila tafito dauke da tray tayi sallama tashigo. Tunda tashigo Saleem yakafeta da idanu harta aje tray din ta gaidashi amma bemasan tanayi ba. Dariya Sameer yayi yabugi kafadarshi yace abokina ina katafi ne ana ta gaidaka kayi shiru. Murmushi yayi yace lafiya lau Jalila ya gidan?

Jalila tayi murmushi tace lafiya lau, Sameer yace to kode.... amma de bari inyi shiru. Falak tace a,a kadeyi shiru zamuji koma menene, Jalila tace Uhm nide zanwuce. Saleem yace tonimade tafiya zanyi tunda mungaisa. Sameer yace ina yunwar ta tafi kuma? Kai ya sosa yace ai nakoshi ma, idan naje gida nasha tea. Muje sena saukeki ko tunda nima fita zanyi. Sameer yace kamade yi magana, idan kadawo nasan dole kabiyo tanan sekaci abincin. 

Jalila tace a,a kabarshi nagode, sameer yace a,a kanwata ai abokinane bakomai kije ya kaiki, kinsan mu bamuda mota ammade tana hanya zuwa jibi zata iso. Dariya sukayi, tace to Allah yakawota, daki Falak taje tadauko mata turaruka , har kofar mota suka rakasu, Sameer yaciro 5k yabama Falak yace tasaka mata ajaka, kama jakarta tayi tace gashi inji megidan yace abaki. Jalila tace haba dan Allah kubarshi, Sameer yace ashe dama kanwa tana kin karbar kyauta daga yayanta? Murmushi tayi tace a,a nagode, to. Haka suka tafi suna tayima Saleem tsiya.

Dije ce da Asabe zaune adaki suna fira, Asabe tace  waini Dije kina ganin yanzu Zarah tafara juya mana baya, wlh jiya 500 takaina banida ita, yanzu ko awaya nakirata bata cika dauka ba, gashi tadena zuwa gurin boka bare musami rabon mu. Dije tace ai dole musake dabara, ammafa idan zaki iya, Asabe tace haba Dije, kode kin manta ko wacece Asabe ne? Tunda na iya kashe rai saboda abin duniya babu abinda bazan iya ba, kawai fadi shawararki. To asabe nafarko de dole kibar mijinki, dan garin zamu bari. Mtswwww Asabe taja tsaki tace danna bar mijina shine wani abu, kema kinsan dayana da maiko da tuni yazama gawa nakara gaba, amma tunda zamuci tajikin diyarshi ya huta, yakikeso ayi?

Urs, 
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/15, 3:15 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 105..... 110

Dije tace Asabe, agaskiya munyima Zarah hidima, kuma tasamu duniya fiye da yadda baki zato, amma acikin kudin datasamu, babu wani abun arziki data yimaki bare kumani. Dan haka lokaci yayi dazamu nuna mata asalin halinmu, kinga damun samu sa,a kawai semubar garin, munufi lagos.

Akwai wata kawata datake zaune acan, zata bamu masauki, kinga semu kama sana,a me kyau, muma mushigo gari. Asabe tace gaskiya kawata kinkawo shawara me kyau, kibari zuwa sati mezuwa zanje kadunan, kibar sauran aikin ahannuna.

Bayan Saleem ya,aje Jalila agida sukayi sallama ya amshi numberta, dan tun ahanya yagabatar mata da abinda yake ranshi, itama agurinta hakan yake, dan tunda taganshi ita taji ya kwanta mata, babu bata lokaci ta amshi tayinshi, dan itama ta kosa tabar gidan, dubu 20 yabata, da kyar ta amsa, sannan yawuce.

Tana shiga gidan tagaishe da megadi tawuce ciki, adaki tasamu Zarah tafito daga wanka, tace Ummi sannu da gida, yauwa Jalila harkin dawo? Tace wlh kam. Zarah tace to albishirinki, tace Ummi goro, Jidda tadawo dazu fa. Kai Ummi da gaske? Emana, tana dakinta bacci takeyi dan kosallar magrib batayiba, tace kada atadata, batajin dadi.

Kai amma naji dadi wlh, Allah sa kada Yaya Jidda takara tafiya tabarmu, ai itama tace babu inda zata kara zuwa, domin tsautsayine asamesu, har kawarta dasuka tafi ankasheta..........
    Anan tabama Jalila labarin da Jidda tabata, Jalila harda kwallanta, sede akasan zuciyarta bata yarda da labarin ba. Wayyo Ummi yaya jidda taci wuya, Allah yakara tsarewa. Kudin da Saleem yabata tamika ma Zarah, washe baki tayi tace Jalila wannan kudinfa daga ina? Ummi agidan kawata danaje gurin dawowa muka hadu dawani Saleem, shine yadauko ni yamaidoni gida, shine yabani kudi.

Kai amma naji dadi wlh, motarshi ce yadaukoki ko? E Ummi tashi ce, to aikin meyakeyi haka? Shine manager a kamfanin babanshi. Toshi baban nashi aikin meyakeyi? Eto yacemun yana aiki aAbuja kuma yana cikin manyan gwamnati.

Kai amma wannan yarinya Allah yayi maki albarka, gaskiya yau kinfaranta mani rai sosai, daam nace inde ina raye ,ya,yana bazasu auri talaka ba. Sosai Jalila taji dadin addu,ar da Zarah tayi mata, dan rabon da tasa mata albarka harta manta, godiya tayima Allah dayasa Saleem yafito daga gidan masu kudi, duk da ita ba burinta kenan ba, amma gashi ta dalilinshi Umminta tana saka mata albarka.

Idan yakara zuwa, ai seki kawoshi mugaisa ko, idan Dadynku ma yadawo zanyi mashi maganar, bazamu tsaya sanya ba, tunda dama kingama karatunki kawai yafito ayi bawani daukar lokaci za,ayi ba. Dama nakosa nima inga nayi biki agidana, tunda waccan sakarar yayar taki taki maida hankali tafiddo miji ai gara kiyi ki kyaleta. Murmushi Jalila tayi jin yadda kudi suka sa Umminsu saurin juyama Jidda baya. Ummi bara inje inyi isha,i idan ta tashi semu gaisa. To Jalilata idan kingama akwai abinci akitchen idan kuma bakisonshi se indafa maki wani. A,a Ummi naci abinci ma. Fita tayi tana mamakin hali irin na Umminsu.

Har tagama sallah tayi duk abinda zatayi, takara fita domin dubo Jidda amma haryanzu bata farka ba, harzata fita taga wani magani abisa side drawer zuwa tayi tadauka, mamaki ne yasauka akan fuskarta ganin sunan kwayar dake jikin maganin. Wasu irin zafafan hawayene suka rika sauko mata, kara kallon Jidda tayi, se anan taga irin ramar datayi da kuma wani irin haske, daukar kwayar tayi tafita da ita, ballesu tayi duka tazuba amasai ta yarda ledar maganin abolar waje. Zama tayi tana ta tunani, can wayarta tayi kara, murmushi tayi ganin wanda ke kira, kwanciya tayi suka shiga firarsu ta sababbin masoya.

Bayan kwana 2 soyayya me karfi dashiga tsakanin Saleem da Jalila, duk wani tarihi na gidansu Jalila babu abinda Sameer da Falak basu fada ma Saleem ba, kuma hada goyon bayan Jalila dan aganinta be kamata taboye mashi wani abu daga gidansu ba, dan tasan wata rana dole zeji.

Sosai Saleem ya tausaya ma Jalila ganin irin uwar da Allah yabata amma gata ita daban acikin gidansu, jin labarinta be rage komai na sonta aranshi ba, sema karuwa dayayi, kuma yasan baze samu matsala agurin Abbanshi ba, dan Mamanshi tarasu.

Har gida yaje yagaida Ummin Jalila kuma sanin halinta nasan kudi yasa yayi mata kyauta me tsoka, sosai taji dadin zuwanshi, Jidda kuwa tunda taganshi takasa dauke idonta akanshi, sede sanin yafi karfinta, yasa ta maida kwadayinta ciki, sede takasa fita su gaisa sema fita datayi tabar gidan. Zarah tace ma Saleem nan da kwana 2 idan Alh yadawo zatayi mashi maganarsu seyadawo sugaisa.

Jidda abin duniya yafara isarta, babu abinda takeso kamar namiji, gashi bata da no saurayinta ko daya, kullum seta yi wanka tafita kozata samu dan hannu sede haryanzu bata daceba, har gidan su kawarta Ameera taje amma tayi rashin sa,a akace mata suntashi daga unguwar, gashi kuma bata da no dinta. Ahanyarta ta dawowa ce tahadu dawani dan bayan unguwarsu, irin yan iskan unguwane, mashayine na karshe, waishi Viju, saboda tsabar bin mata abokanshi suka samashi Viju.

Kamar da wasa yayi mata magana babu bata lokaci Jidda ta amince dashi, anan sukayi exchanging no tawuce gida tana murna. Tun daga ranar suka fara soyayya, da farko be nuna mata dan hannu bane, amma ganin dayayi idan harsuna fira batajin kunyar kama hannunshi tayi ta wasa dashi hakan yasa yayi mata tayin zuwa shagonshi, babu bata lokaci ta amince.

Daga ranar suka fara aikata masha,a sosai sukejin dadin junansu , tunda Viju yasamu Jidda yadena kula kowace mace, dan Jidda tana gamsar dashi sosai, kuma tanuna mashi yayi amfani da ita ta ko ina, dan Joseph ya saba mata da hakan, shima Viju tunda yafarayi yaji dadi daganan shima yacigaba duk ta inda yaga dama, wani lokacin har kwana jidda takeyi adakinshi, sede babu wanda yasan bata kwana agida se Jalila, kuma tayi shiru bata fadama Zarah ba. Gashi yakara koya mata shaye shaye hardasu Sigari takesha, sede bata sha agidansu, gashi taba bashi kudi sosai, dan idan batada kudi na Zarah take sata, dayake itama Zarah kanta batasan yawan kudin ba, hakan yasa bata gane ana diba.

Aranar da Alh, yadawo da dare Zarah tayi mashi maganar saurayin Jalila, sosai shima yaji dadin maganar, kuma yace tafada mashi gobe yazo yanason ganinshi, koda yadawo Jidda ba,a gida ta kwana ba, hakan yasa basu haduba. Jalila tafada ma Saleem, yace mata to zasu zo shida Sameer.

Washe gari sukazo, har cikin falo suka shiga, bayan sun gaisa da Alh da Zarah, ta tashi tabasu guri, anan Sameer yayima Alh bayanin Saleem, ashema yasan Babanshi abokinshine, nan take yakirashi awaya suka gaisa yayi mashi bayanin komai, shima yaji dadi sosai, jin yarainyar da danshi yafada mashi ze aura yar abokinshi ce. Anan yace cikin week end zasu shigo domin atsaida magana. Sosai Saleem yaji dadi yakusa mallakar Jalilanshi, daga haka sukayi masu sallama, anan Zarah tafito sukayimata sallama suka ajemata bandir din kudi.

Zaune suke agidansu Baba mairo, Falak se cin kwadon zogala takeyi suna labari, Baba mairo tace lallai wannan jikan nawa yana da kwadayi, waiko Sameer kunje asibiti kuwa? Sosai kai yayi yace munje Baba, to wata nawa ne, cikin? Watanshi 5. A lallai Allah yaraba lafiya. Murmushi Halima tayi tace ameen.

Falak tace Baba dan Allah inaso inje ingaida Dady nide kobaze amsa ba, wlh inason ganinshi, kwana 2 ina yawan mafarkin Umma tanacemun meyasa nabar Dady kibarni naje naganshi, koda hakan yana nufin Ummi zata dauki mataki akan aurena. Ta goge kwallan data zubo mata.

Baba mairo tace kinyi gaskiya Falak, nima nayi wannan tunanin bakomai, gobe zaku iya zuwa keda mijinki. Sameer yace Baba sede mubari ranar lahadi, domin gobe Zanje inter view kinsan nafada maku Abban Saleem ya bada takarduna toshine ake nemanmu gobe anan genaral hospital, kuma ranar asabar iyayen Saleem zasuje neman aure gidansu Jalila, shiyasa nace mubari se ranar lahadi.

Baba Mairo tace to Allah yakaimu ko kuwa Halima? Tace hakane Baba duk abinda kikace yayi, Allah de ya tona asirin wannan mata. Baba mairo tace Ameen. Sameer yace nizan tafi shago Baba mairo tace zoka dauki matarka kutafi, Falak tace kai Baba mairo tsakani da Allah fa yanzu mukazo, kuma yace seda dare zamu koma. Dariya yayi yace kema de kinsan halin Baba mairo, yizamanki tunda inada mota anjima zanzo indaukeki. Baba mairo tace ohode tunda bazaka iya barinta ta kwana ba, dariya yayi yafita.

Jalila ce da Jidda zaune afalon Umminsu, Jalila tanayima Jidda kitso, Jidda tace waini Ummi ina Mairo tunda nadawo banganta ba? Uhmm wama yasan inda take kota raye kota mutu, tunda tacemun zataje ganin gida bankarajin labarinta, amma Ummi ai da kinsa an tambayo maki ko lafiya ko, kai dalla can rabu dani, daga temako se intsaya ina nemanta, ita tasani idan bata dawo ba, har bikin Jalila wata kwai zandauka, dama na daga mata kafane kozata dawo, amma tunda bata dawoba shikenan. Murmushi Jalila tayi batace komai ba.

Zarah tace Jidda kinga kema dakin fiddo miji da se ahada bikinku tare dana Jalila. Jidda tace nifa Ummi banaso kinamun wani maganar aure, itama data samu mijin ai ba rawa tayima Allah yabata ba, nima kuma zansamu. Tsaki tayi tace ke Jalila tashi muje daki ki karasamun kitsona. Zarah tace E lallai Jidda kingirma, yanzu ni kikema tsaki? Ke kika sani wlh kije duniya ce zak...... saurin toshe mata baki Jalila tayi tana kwalla tace haba Ummi, dan Allah kidena saurin yima Yaya Jidda baki, addu,a yakamata kiyi mata. Hannun Jidda Jalila taja suka bar dakin. Zarah tace aikin banza, kawai kizo kizaunamun agida baki anfana mani da komai, ni narasa wane irin abu akayi mata ma, ada yarinya ta taso da farin jini, amma yanzu kamar wadda akama asiri, gaba daya samarinta sun dauke kafa, dole inje gurin boka kema kisamu kiyi aure.

Aranar asabar iyayen Saleem sukazo, kuma an tsaida rana wata 1, kudin neman aure suka bada naira dubu 100, Zarah kamar zata zuba ruwa akasa tasha, saboda farin ciki, bayan suntafi tace ma Alh, yabata kudi taje dubai tahado ma Jalila kayan daki. Alh yace amma ai dakin bari an siyamata anan ina ganin zefi. Zarah tace to matsolo wlh baka isaba, kawai bikin diyar tawa zakace wai anan za,a mata kayan daki, da kudinka da komai, ko waccan AGOLAR BANZAR FALAK dazatayi aure nawa kabada. Kanshi yadafe jin abinda Zarah tafada, kallonta yayi yace wane suna naji kinfada yanzu. Dif Zarah tayi jin irin katobarar datayi, dan bata manta kashedin boka ba, yace kada takira sunan Falak agabanshi, idan tana kiran sunanta ze iya tunawa da ita, bare kuma su hada ido da ita.
     Cikin sauri tace ina nufin ko sadaka akazo nema agurinkana kayan aure ai yakamata kabada kudi masu yawa bare ace auran diyarka na farko. Tonaji, yanzude kamar nawa kike ganin zasu isa? Murmushi tayi tace Eto kagade gidan masu kudi Jalila zatayi aure, idab bamu zuba mata kaya masu tsada ba, kaima kasan rainamu za,ayi kawai kabada million 6 ina ganin zasu isa. Shiru yayi bece komai ba. Cike da tsawa tace kobaka jini ba? A,a najiki waida inaga kamar sunyi yawa ne, dan duka million 10 ce a account dina kuma wasu kaya nakeso insiyo. To wlh seka badasu, idan yaso kasiyo kayan dasauran kudin. To to naji yanzu check zanrubuta maki ko kuwa transfer zan maki? A,a kamun transfer kawai, kuma yanzu zakamun tavwayarka tunda gobe babu aiki. Anan take yatura mata million 6, sosai taji dadi dan ta aiyana aranta 2 zata raba tadauki rabi.

Washe gari Asabe ta dira gidan Zarah, a yamutse ta karbeta, sewani shan kamshi take mata da kyar ma ta amsa gaisuwarta, Jalila cema ta kawo mata ruwa da abinci. Asabe tace waini kam hajiya kinajin labarin Falak? Yamutsa fuska tayi tace niharna manta ma da ita amma de ai batayi shekara da aure ba ko? E gaskiya batayi ba, yauwa, dan ina jiran lokaci yayi, kinsan Itama Jalila ankawo kudin aurenta.
Asabe tace kai amma naji dadi, amma ina fatan gidan maiko ne ko? Se alokacin Zarah tayi murmushi tafara sakin jiki suka fara magana, anan tafadi mata komai, cikin kissa Asabe tasaka ta tafada mata hada yawan kudin da Alh, yabata. Tunda taji yawan kudin tace lallai muma wahalarmu takusa zuwa karshe.

Haka sukayita fira har la,asar Zarah tace Inna yakamata kitashi kitafi kada dare yayi maki, sakin baki Asabe tayi tana kallonta, dan ita da shirin kwana tazo, hadiye bacin ranta tayi tace toshikenan hajiya bara intafi. Dubu 1 tabata tace tahau mota, atare suka fito waje, dede lokacin megadi yana bude gate, Asabe tace ko Alh, ne yadawo ma, Zarah tace bashi bane, dan yacemun seda dare zedawo, kuma bema da irin wannan motar. Tsayawa sukayi suna kallon motar harta tsaya, ganin wasu kyawawa sunfito daga motar yasa Zarah tace kai yau kuma wane irin yan gayun baki ne mukayi haka, har suka iso kusa dasu basu sani ba.

Falak tace Assalamu Alaikum sannunku da gida, Zarah tace yauwa sannunku, mushiga daga ciki mana, Asabe tace tonima bara muje mugaisa ko, Zarah tace to shigo. Bayan sungaisa, Zarah ta kalli Falak da sameer tace sede bangane kuba. Sameer yayi murmushi yace Hajiya dasauri haka ko shekara ba,ayi ba, kice baki ganemu ba, aiko ita yakamata ki ganeta.

Zarah tace idan da naganeku ai bazan tambaya ba. Sameer yace hakane, to sirikinki ne, Sameer, wato Asid, da matarshi Falak....... zunbur Zarah da mairo suka mike tsaye jin kalaman Sameer.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[6/16, 12:55 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH !!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@(H,O,N,A) 
Part 110..... 115

Cike datashin hankali Zarah tace Asid yaushe ka koma haka? Dama ba dan iska bane kai? Meyasa Mairo ta munafunceni? Zubewa kasa tayi tana kuka, Murmushin mugunta Asabe tayi, sannan tadauki kayanta tace tofa, Allah ya kyauta, nizan wuce hajiya kada dare yayi mun.

Saurin kamota Zarah tayi tace haba Inna kibari ki kwana mana, ai yanzu yamma tayi. Komawa tayi tazauna tana dariya aciki ciki, Sameer yace Ummi kiyi hakuri Baba mairo bata munafunceki ba, tayi abunda yadace ne, domin kinkasa rike marainiyar Allah shiyasa tayi kokarin kubutar da ita daga sharrinki.

Anan Sameer yafadama Zarah komai, kuka kawai takeyi. Falak tace Ummi dady bayanan ne? Dadyn Ubanki, ke awa dazaki tambayeshi? To wlh tunkafin inkirga 3 kubacemun daga gidan nan, cuta ce kun cuceni, bakomai amma wlh duk ranar da kika bari kafarki takara taka gidan nan sede adau gawarki.

Kuma duk ranar dakika zo neman mijina Allah ya isa, dan idan har ina raye bazan barki ki kara hada ido dashi ba. Kutashi kubarmun gidana, kai kuma nabaka daga yau zuwa gobe kamaidomun kudina dakasan nabaka, idan bahaka ba, wlh kotu zata rabamu.

Murmushi Sameer yayi yace haba Ummi meyayi zafi haka? Ni dama can bantaba kashe ko kwandalarki ba, wata jaka yadauko agefenshi yamika mata yace wannan kudinki ne, tundaga dubu 10 da kika fara bama Baba mairo har kudin sadakin da kika bani, babu kwabonki dayayi ciwo. Hannun Falak yakama wadda take ta kuka, suka fita, abakin kofar falon suka hadu da Jidda wadda tundazu take tsaye tana sauraronsu.

Da kallo tabisu harsuka wuce, mamaki kawai takeyi wai Falak ce da mijinta, harma ga alamar ciki ajikinta. Baki ta tabe takalli Umminsu datake ta kuka ta kalli jakar kudin dake gabanta tayi murmushi tajuya tayi waje.

Asabe tace hajiya kitashi mukoma daki kada Alh yazo ya iske ki haka, muje inada mafita cikin sauki. Jakar kudin tadauka suka wuce daki. Seda Zarah tagama kirga kudin tsaf taga sun cika, sannan tasakasu cikin drawer tadawo tazauna.

Inna kenake saurare, banida sauran wata dabara, dolene muje gurin boka babu bata lokaci kashe Falak zanyi, shi kuma mijinta da Mairo wlh bazan kyalesu ba, tunda suka munafunceni, haba dama biri yayi kama da mutum.

Nayi mamakin yanda Mairo tayi saurin canzawa daga son datakema Falak zuwa tsana, duk yanda akayi aranar da mukayi waya dake aranar taji duk wani plan dina, saboda inagama wayar babu dadewa tashigo tana kukan munafurci. Kuma gashi bayan bikin Falak babu dadewa itama tace zataje ganin gida, gashi haryanzu bata dawoba.

Asabe tayi dariya tace aini dama nayi zargin wani abu agame da Mairo, kawaide nayi shirune. Toyanzu duk ki kyale wannan maganar, akwai mafita sede tana da wahala, na manta danazo ban fada maki ba, Boka ya mutu.... zunbur Zarah tayi ta mike taname dafe kirjinta, tace nashiga 3 ni Zarah, boka yazakamun haka seda bukatar nemanka tayi sannan zaka mutu.

Asabe tace kwantar da hankalinki wannan badamuwa bace, duka shekaranjiya Dije tadawo daga tafiyar danace maki tayi, dama ban fada maki bane, kasar yarbawa taje wata mata ta aiketa gurin wani babban boka, domin bakaramin hatsabibi bane, yashafe bokan dakika sani, dan aikinshi alokacin dakika fadi bukatarki alokacin take biya, kuma shi aikinshi beda makari.
Sede bakananan mutane yakema aiki ba, daga matan gwabnoni shugaban kasa, sarakuna se manyan yan kasuwa da yan siyasa, sabida aikinshi ba dubunnai yake amsa ba, miliyoyi ne. Ko Dije Matar sarkin Zariya ce ta aiketa.

Zarah tazauna tace yauwa Inna wlh harnaji dadi, yanzu yaushe za,aje? Asabe tace kina ganin zaki iya harka dashi, kinsan fa bawasu kudi gareki ba, kada yayi maki aiki ki kasa biyanshi aiki yadawo kanki. 
    Zarah tace wlh Inna kozanyi yawo tsirara bazan bari Falak tacigaba da rayuwar jindadi aduniya ba,( wa iyazubillah). Zankashe konawa ne domin ganin burina yacika akanta, kuma aikin ba ita kadai za,ayi mawa ba, hada Alh, inaso ta karbomun maganin mallakar zuciya tayanda beda makari, kuma bazanji shayin suhadu da ita ba.

Asabe tace kinga kudi sunkaru tunda aikin mutum 2 ne, kawai hotonsu zaki bada atafi dashi sekuma kudi, amma bari inkira Dije ince takirashi taji yawan kudin. Amma hajiya inazaki samu kudi masu yawa haka? Uhm kede bari Inna, kinsan Allah yana temakona aduk lokacin danashiga matsala, jiya Alh yabani million 6 na kayan auren Jalila, dama niyata inkashe mata million 3 indau 3,  kuma gashi yanzu wani aiki yashigo, inaganin kawai zanyi mata siyayyarta anan kinsan Alhjn atafin hannuna yake bawani abu zece ba.

Asabe tace hakama yayi, inaganin kisiya mata na million 2 kirike 4 kinga kome aka bukata bakida sauran damuwa. Zarah tace haka za,ayi Inna shiyasa nake sonki nasan idan har kina raye, Allah yabarmunke.

Bara inje insa Jalila tadora abinci ki kira Dijen kiji konawane nafison ayi komai cikin sauri. Tana fita Asabe takira Dije tafada mata komai, nan take Dije tafada mata yanda zata ce.
     Bayan Zarah tashigo Asabe tace uhm, aiki game kareka, kinsan Dije da mutane, muna gama waya takira bokan harsungama magana, tafadi mashi matsalarki, harya yanke mugun hukuncin dazeyima Falak, danshima yanajin haushin masu cin amana. Dariya Zarah tayi tace kai amma naji dadi, gaskiya Dije kawace tagari. Nawa yace kudin aikin?

Uhm aini hajiya abunne naji dayawa, kodayake biyan bukata yafi dogon buri, boka yace maganin dazeyima Alh, zaki mallakeshi, dayanda shine zerika aiki amma kudi suna gurinki, ko naira 1 baze iya kashewa ba, seda izininki, daya samu kudi kece ze kawomawa. Kara washe baki Zarah tayi tace kai, kice nazama babbar Hajiya, kawai fadimun kudin konawa ne, nasan nan da dan lokaci zanmaida mafiyansu.

Uhm na Falak de yace kibada million 2, na Alh kuma 1 da rabi, se kuma kudin da Dije zatayi kudin mota dasu dubu 50 sena abinci dan kwana 2 zatayi. Zarah tace kai kudinma babu yawa tunda acikin million 4 ina da saura, bakomai zan bata dubu 100 gaba daya nasan zasu isheta, gashi ku kuma ba accounta gareku ba bare intura maku.

Asabe tace mene account, kai mude munfi gane murike kudi ahannu, barema Dije ai tasaba tafiya da manyan kudi, haka kawai kitura mata kudi a banki taje cirowa ma aikatan suga batayi kama da wadda zata fidda kudi masu yawa ba, su kira mata yansanda. Kawai asamu. Babbar Gana, ashirya mata su aciki, seta dora kayanta asama babu wanda zece kudine aciki.

Zarah tace toshikenan ai tunda aikinta ne, yanzu kibari gobe monday, se inje banki da Ganar su shiryamun su acan idan nazo gida se tasaka kayan asama. Asabe tace nima gobe zankoma dawuri semu dawo tare da ita jibi idan narakata tasha se inwuce, amma bake zaki kaimu ba, kisaka driver saboda idon mutane. Zarah tace toshikenan, kema kinada dubu 20. Asabe tace ah, lallai nagode.

Zaune suke adakin Baba mairo Falak tanata kuka, Baba mairo tace dan Allah kidena wannan kuka, babu abinda ta isa tayi maki wanda Allah neyi maki ba, tabbas dole munemi temakon Kawunka Sameer, kasan ance idan kana da kyau ka kara da wanka. Halima tace ai baza,a bari se gobe ba, kutashi kawai muje, tashi sukayi suka nufi motar Sameer.

Azaune suke afalonshi bayan sungama gaisawa Baba mairo tayi mashi bayanin komai. Shiru yayi nawani lokaci sannan yace toku baku fahimci komai ba agame da rashin son Falak ta hadu da Alh? Inaganin koma wane asiri ne akayimashi to makarin yana jikin Falak, kuma dole sesun hadu zamu iya temakonshi, idan har mukayi nasarar karya asirin jikinshi tosemu fara bashi temako, domin idan har babu tsari ajikinshi komun karya asirin zata iya yin wani.

Yanzu a ina yakamata kiganshi? Eto dazude damukaje baya gida sede bansani ba, ko yakoma, amma zan tambayi Jalila idan haryana gida se ince tafada mun.  Malam yace hakane, amma banaso kifada mata dalilinki nason ganinshi, kawai kice kinason gaidashi ne, kinsan tsakanin da da Mahaifiya. 

Zamu dage da addu,a kuma zanbaku wanda zakurikayi kullum kafin ku kwanta bacci, insha Allah komai zezo dasauki. Godiya sukayi mashi suka tafi.

Jidda ce tashiga dakin Zarah tadebo kudi masu yawa, tazo fida suka hadu da jalila, Jalila tace wai dan Allah meyasa Yaya jidda kika canza hali ne? Kinsan fa duk wasu halaye marasa kyau dakike aikatawa agidan nan nasansu, wai yau kece da sata, kuma kudin Ummi, haba meyayi zafi Haka, ni wlh banga abinso ajikin wannan saurayin naki ba, kum....saukar mari taji afuskarta shiya hanata karasa maganar datakeyi. Inaso intuna maki nice yayarki bakeba, kuma inada ikon yin duk irin rayuwar danaga dama banason sa ido, zanyi mugun saba maki idan kikace zaki rika samun ido. Tunda har Allah ya rufamun asiri babu wanda ya isa yatonamun.

Dan haka kifita a idona idan harkinaso incigaba da kallonki amatsayin yar uwa. Shikenan yaya dan Allah kiyi hkr insha Allah bazan kara shiga harkar kiba, inde hakan zesa bazaki cireni amatsayin yar uwarki ba, kinsan banida kamarki. Juyawa tayi tafita tana kuka. Jidda tafita tanufi dakin viju.

Tanazuwa tasameshi yagama shirinshi dama yace mata tafiya zeyi ta kwana 2 shine yace yanason kudi dubu 100 daya dawo zabata, shine tadauko mashi na Zarah. Kallonshi tayi kamar zatayi kuka tace haba Viju yanzu harka shirya ai seka bari mudan huta kona bankwana muyi ko, kasan zanyi missing dinka kwana 2. Haba Baby kada kidamu abakon tafiya ta sun shirya nikadai suke jira kibari idan nadawo ai muna tare ko. Dakyar ya lallabata yafita, yahau mashin aranshi yana fadin nidake har abada, hakawai yarinya kinkoma kamar kwanko, mezanyi dake, ta ko ina kinzurma haka kawai kirika morata nikuma ina wahala, gara inkara gaba, dama kudin hayata sunkare.

Bayan kwana 1 su Asabe sukazo dashirinsu natafiya, kwana 1 sukayi duk wani shiri sungama, anshirya kaya asaman kudin Zarah tabasu hoton Falak da Alh, wanda tunkafin Hajjo ma tarasu suka dauka lokacin graduation din Jidda, dayake Jalila tanada na Falak ita kadai, shine Zarah tadauko. Acikin jakar Dije aka saka hotunan, sukayimata sallama tasa driver yakaisu tasha. Asabe tace to sena kara dawowa ko.


Alhamdulillahi Sameer yasamu aiki A Genaral hospital na kaduna, abangaren pharmacy sosai su Falak da Halima sukaji dadi, suma rayuwa zata canza masu, wani abokinshi malamin islamiyar dasuke koyarwa tare yamikama amanar plaza dinshi, komai yana tafiya dede.
Suna zaune afalo Jalila takira Falak tafada mata Dadynsu yana gari, sosai taji dadi tayimata godiya tace gobe sunanan zuwa..

Kwance tasamu Jidda akasa tana ta faman amai, cikin sauri Jalila takarasa shiga dakin tana fadin dama Yaya jidda nace maki bakida lafiya tun kwanakin baya kikacemun lafiyarki lau, saboda bakison zuwa asibiti, kalli yanda kika koma jikinki kamar baki cin abinci, dan Allah kiyi hakuri muje asibiti, Jidda tace Jalila banason zuwa asibiti kisiyomun magani kawai. Jalila tace wlh a,a yaude tunda Dady yana gida semunje asibiti. Fita tayi domin kiransu Zarah.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/3, 3:47 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 115..... 120

Atare suka shigo dakin da Jidda take, kwance suka sameta gaba daya tagama galabaita, Zarah da Jalila duk sun rude, Alh yace su gyarata bari yafiddo mota a kaita asibiti. Cikin lokaci kan kani suka gama shiryata suka wuce asibiti.

Suna zuwa suka nufi gurin likita, anan yafara dubata, duk tambayar dayake mata bata bashi amsa, ganin haka yace masu sudan jirashi awaje. Matsowa yayi yace Jidda inaso ki kwantar da hankalinki kibani amsar tambayar dazan maki, jikinki yayi laushi sosai, idan har baki fadi abinda kike jiba zaki shiga matsala.

Kwallan dake idonta ta goge, takalleshi, ahankali tace, Dr. dan Allah kowace irin cuta ka gano ajikina inaso karufamun asiri kada kabari iyayena suji. Murmushi yayi yace Jidda waya fada maki kina dauke da wata cuta? Nide Dr, kawai inaji ajikina dole asamu cuta ajikina.

Shikenan zansa ayi maki test duk abinda result yabada zamu gani, a,a wlh idan har Dady yasan za,a yimani test dole yaga result din dan Allah kada kabari amun test. Kada kidamu. Bazasu san anyi maki ba, zan temakeki. Fita yayi yakirawosu.

Alh, agaskiya jikin Jidda yayi sanyi dole zamu kwantar da ita asa mata ruwa, sbd maleria tayi mata kamu sosai, gashi tayi amai ruwan jikinta yayi kasa, amma insha Allah ko zuwa gobe zata samu sauki, dan bawani babban ciwo bane, kawai aman datayi ne yasa jikinta yayi laushi. Alh, yace babu damuwa Dr, kayi duk abinda yadace bamusan bata da lfy ba, se Jalila ce take fada, kasan Jidda batason magani shiyasa ta hana Jalila tafada. Allah yakara sauki.

Nurse yakira suka kaita daki aka saka mata drip, Alh yace sukoma gida tunda tayi bacci seku shiryo kafin ta tashi, Jalila tace a,a nide zan tsaya anan, Dr, yace kije kada kibar Hjya ita kadai, tunda tayi bacci harzaku dawo bata farka ba, akwai allurar baccin da aka zuba adrip din ai. Sallama sukayi mashi suka tafi. Suna fita tabude ido, Dr, yasa nurse suka turata zuwa dakin daza a dauki jininta.


Mamaki ne, yakama Dr, ganin result din da wata nurse takawo mashi, duk da dama yayi zargin hakan amma yayi mamakin ganin yadda cutar tayi nisa ajikinta amma ba,a dauki wani mataki ba, duk da yasan laifinta ne bataso asan tana dauke da cutar. Kallon Jidda yayi itama shi take kallo. H,I,V gareni ko Dr? Uhm dama nasan dole hakan zata faru dani, duk da laifina ne, da nazo an aunani dawuri da bankai wannan matakin ba. Dr, yace hakika Jidda kinyi wauta da har kikasan kina dauke da wannan cuta amma kika ki zuwa asibiti kifara karbar magani, gashi yanzu tayi karfi ajikinki. Amma kada kidamu idan har zaki kiyaye dokokin dazan baki zakicigaba da rayuwarki, tunda baki kai last stage ba.

Zaki sha magunguna kuma babu tsallake, kuma zaki dage da cin duk wani abu megina jiki insha Allahu zaki samu sauki kuma jikinki bazeyi saurin nuna kina dauke da cuta ba. Zan baki maganin wata 1 idan kika shanye sekidawo ki karbi wasu amma idan kika dawo zan hadaki da wanda zaki rika amsar maganin agurinshi cikin sauki, kuma zanzuba makisu acikin wata roba, babu wanda zegane wane irin maganine sewanda yasanshi, nide fatana ki kiyaye. Godiya sosai Jidda tayi mashi se kuka takeyi, aranta tana fadin wlh tunda aka sakamun cutar nan nima sena saka ma wasu.

 Asabe yana zuwa gida tasamu mijinta tayi tamashi bala,i adole seya saketa, takaji dazama dashi garin zata bari, dayake dama umarninta yake bi, nan take yasaketa, yana sakinta yaji kanshi ya sara, yaji kamar yadauke mashi wani abu me nauyi, dan danan ya kwanta saboda jiyake kamar ze fadi, ganin haka yasa Asabe shigewa daki tahada duka kayanta tafita domin samun dillaliyar dazata siya, malam Garba yafi minti 30 akwance, yana tunanin abubuwa da dama, dayaji kanshi ya lafa yayi hamdala yatashi yadauro alwala yafara nafila, dan jinshi yake kamar kamar duk wata damuwarshi ta kau, saboda yarabu da Asabe.

Gidan Dije taje suka kara tattaunawa, sbd gobe zasu tafi, Asabe tace kinsan daga gidan Tabawa nake dillaliya, anjima zatazo tasayi kayana, dan babu abinda zanyi dasu muda zamu bar gari. Dije tace nima de sayar danawa zanyi, dama bawani yawa garesu ba, ni har na kosa gobe tayi wlh mubar garin nan nahangomu a Lagos cikin daula. Dariya sukayi suka kashe.

Bayan sunkoma asibitin dayake dare yayi suka dan zauna dan jikin Jiddan yayi sauki tasha drip, Zarah tace Alh, kutafi kaida Jalila nizan kwana da ita, Jalila tace a,a Ummi kibari inkwana. Alh, yace aike yarinya ce Jalila jinya kuwa ai se babba. Kibarta takwana tunda kwana daya ne gobe zasu dawo gida ai. Sallama suka yimasu suka tafi, ganin suntafi Zarah tafita takirawo Asabe, tafada mata abinda yafaru, tace amma goben zanciro kudin bana son Alh, yagane, nasan dawuri zasuzo duba Jidda zansa likita yabar sallamar se da rana, suna zuwa sena barsu nadawo gida amma fa kutaho dawuri. 

Washe gari dasafe Dr, yashigo anan Zarah tafada mashi bukatar ta, yace toshikenan babu damuwa dama akwai saura drip 2 daza,a samata zuwa azahar nasan sun kare seku tafi.

Gurin karfe 8 Alh da Jalila suka shigo, hamdala Zarah tayi, bayan sungaisa, suka tambayi jikin Jidda, Zarah tace dasauki sosai ma, dan tadena aman kuma taci abinci sosai jiya. Alh, yace Allah yakara sauki, bara inje gurin Dr, inji yaushe za,a sallameta. Zarah tace ai yashigo dazu, yace seda rana sbd akwai drip 2 da za,a samata. Amma kuzauna bara inje gida inyo wanka bazan iya yin wanka anan ba, idan nadan huta se indawo. Alh yace hakane gsky nasan bakiyi bacci sosai ba, jiya, bakomai kitafi nima zuwa 9 zan wuce office akwai abinda zanyi tunda ga Jalila nan seta zauna agurinta,  Jidda tashi kici abinci kinji. Sallama Zarah tayi masu ta amshi makullin motar Alh, tace idan taje seta bama driver yakawo mashi.

Tana zuwa gida ta iske su Asabe har sunzo, farinciki ne, yakamata tabude gidan suka shiga tabama driver key din motar tace yakaima Alh, wanka kawai tayi tace sukirata taje takarbo kudin, tace suduba kitchen idan akwai abinci suci idan kuma babu sesu dora kafin tadawo.

Tana zuwa banki babu bata lokaci dayake akwai wanda tasani dan danan aka shirya mata kudin acikin jaka, tadawo gida, duk da tadan dade, tana zuwa gida tasau driver yadawo, tasashi yadauko mata kudin. Kaya aka dora asaman kudin babu wanda zece kudine aciki, takirawo driver tace yadauka zekaisu tasha, yana fita ta dauko hoton Alh, dana Falak wanda tasamo adakin Jalila tabasu, Dije takarba tasa ajakarta, Zarah takawo dubu 30 takara ma Dije tace tarike ahannunta. Asabe tace nima ai tare zamu tafi senaga tashinta daga can nima inwuce dan nace ma Babanki bazan dade ba, Zarah tace toshikenan Allah ya tsare nima asibiti zankoma. Sallama sukayi mata suka fita, itama tashiga motarta tawuce asibiti.

Suna zuwa sukaci sa,a mota takusa cika, seda driver yatafi sannan suka se su 2 ne zasu tafi, Dije tace wannan jakar asata abayan mota kayane aciki amma dan Allah aturata ciki sosai kayan sana,ata ne, drivern mota yace karkiji komai madam kawai shiga mota muware, seda suka biya kudin motar sannan suka shiga, Wata inyamura suka samu akusa da ita Asabe tazauna Dije dazauna kusa da Asabe, suna jiran mutum 1, Asabe baki yakasa rufuwa sun sami duniya. Dije tace gsky Kawata nayi farin cikin haduwarmu gashi ta sanadiyarki zanzama babbar hajiya. Asabe tace kede bari wlh idan muka isa Lagos dole muyi kara,in yanmatancin mu baruwana da harka da tsofaffi, yara zansamu masu jini ajiki tunda inada kudi inkashe masu surika biyamun bukatata. Dije tayi dariya tace ashede kema kina irin tunani na. Kinsan hanyar Lagos batada kyau shiyasa nace asaka mana kudinmu abayan mota nace masu kaya ne, sbd kada wani yasan akwai kudi masu yawa acikin jakar, kinga baruwanmu da tunanin yan fashi. Asabe tace gsky kina da dabara. Dahaka mota tacika suka daga zuwa Lagos.

Sameer ne da Saleem da Falak, amota suna hanyar zuwa asibiti dan Falak tayi waya da Jalila take fada mata suna asibiti Jidda ba lfy shine suka wuce dubata dan tadafa mata Dady yana asibiti shima.

Waya takira Jalila tafito tayi masu jagora, Saleem se kallonta yakeyi yana murmushi, Sameer yace kun tsaya sewani sunne sunne kukeyi sekace bakin fulani, mude bamuson kilibibi. Saleem yace ina ruwanka sa ido, kasan kowa datashi kalar soyayyar. Falak tace Allah baka hkr kada kacinyemun miji, dariya suka saka baki daya.

Da sallama suka shiga dakin, Alh, yana zaune abisa kujera ya amsa sallamarsu, har kasa suka duka suka gaishe shi, ya amsa da fara,a suka tambayi jikin Jidda yace dasauki. Falak tace Dady ina kwana, mikewa yayi yana kallonta cike da mamaki, dede lokacin Zarah tashigo da sallama, cak ta tsaya ganin abinda yake faruwa, kowa hankalinshi yana kansu, babu wanda ma yasan da shigowarta. Ganin babu wanda yakula da ita yasa tayi saurin juyawa tafita, mota tanufa tayi gida dasauri hankalinta tashe.

Alh, yace Falak, tace na,am Dady, komawa yayi yazauna yadafe kanshi dan jiyayi yana juya mashi, Sameer ya matso kusa dashi yana fadin Alh, lfy de? Yace kiramun Dr, dasauri. Fita yayi shida Jalila suka kirawo Dr, yana zuwa Alh, yace bayajin dadi kanshi yana juya mashi, nan Dr, yace ya kwanta bisa dayan kadon yafita yakawo mashi magani yabashi yasha sannan ya aunashi, yace Alh, babu abinda yake damunka kila de rashin bacci ne yasama ciwon kai, amma ka kwanta kadan huta zaka samu sauki, godiya yayi mashi sannan yafita.

Ruwa Sameer yadauka yayi mashi adduo,i sbd dama kawunshi yafada mashi akwai asiri ajikin Alh, hakan yasa ya tofa mashi addu,a dan yasan ganin Falak ne yasa mashi ciwon kan. Cikin ikon Allah yana shan addu,ar yasamu sauki.

Zarah tana zuwa gida tashiga daki kamar zatayi ihu sbd tashin hankali,  durowarta tabude tafara binciken sauran maganin mallakar da boka yabata tasama Alh, a abinci dayake tarage kadan. Ajiyar zuciya tayi dataganshi.

Kitchen tanufa domin doramashi abinci farinciki duk ya rufeta tana fadin wlh karyarki tasha karya kitonamun asiri, kai kuma Alh, zanga bakin dazaka samu damar yimani maganar Falak, dakaci abincin nan zaka dawo hannu, Dadi nama dayane, tana gidan mijinta bazasu samu damar zama su dade tare ba, kafin sukara sabawa nasan Dije ta isa gurin boka daga ranar kungama yawo. Kwance maganin tayi tajuyeshi acikin plate tayarda ledar ta ajeshi tadauko tukunya takunna famfo zata daurayeta. Maganin tazuba acikin tukunyar tazuba ruwa, tana fadin gara kutafasa tare nasan zefi jikuwa kuma zefi aiki, dauko tukunyar tayi zata dora bisa gas, juyawar dazatayi silbi yajata tafadi tukunyar tafadi ruwan yazube.

Wani irin ihu tasaka tana fadin nashiga ukku, shikenan tawa tasameni, tashi tayi takashe gas din tafita tana kuka, daki takoma tazauna tabuga tagumi tarasa meke mata dadi, wayarta ta dauko takira Asabe, amma akashe, wurgi tayi da wayar tasa kuka. Ganin kuka baze mata ba, yasa ta tashi tashiga wanka tana fadin ai nasan yarinyar tanada Imani bazata iya fadama Alh, abinda namata ba, kawai zan gwada mashi komai lafiya kafin wani lokaci aikin boka yafara, da wannan tunanin tasamu kwarin guiwa tashiga wanka.

 Alh, yakalli Falak abin mamaki yaga hada ciki ajikinta, wasu hawaye yaji suna zubomashi yagoge yace Falak se kuma yayi shiru, tashi yayi yace haryanzu Zarah bata dawoba, kila bacci yadauketa, nara inje office inbada sako, daga can zanwuce gida banajin dadin jikina, tunda ruwan yakusa karewa zancema Dr, kutaho gida idan yakare kusameni agida.


Zaune suke afalo Alh, yace ma Jalila kirawo Umminku najita shiru, Cike da karfin guiwa Zarah tashigo tace a,a Alh, harkun dawo kunganni shiru wlh, kaina naji yana ciwo ina gama wanka nasha magani nakwanta kawai ina farkawa naga lokaci yatafi, sannunku.

A,a yau kuma amare ne agidan namu, ai dama nasan da kunji Jidda ba lfy zaku taho, hala Jalila ce tafada maku, zama tayi kusa da Alh, wanda yaketa kallonta cike da mamaki, danshi yaji ana fadin Falak amarya, kuma gata da ciki towai yaushe ma tayi aure? To tama gama karatunta?  Shi yadade beji ankira sunanta agidan ba, bare kuma yasata a ido. Zarah takatse mashi tunaninshi tace Alh, munkusa samun jika agidan nan fa. Sameer, Saleem, Falak, Jalila harma da Jidda kallon mamaki sukema Zarah.

Alh, yace dan Allah kufitar dani duhu, naji kuna wasu maganganu wanda bansan dasuba. Zarah tayi murmushi tace Alh, kana nufin baka gane Falak ba? Yace a,a ammade nasan Ameer yarasu, Falak da Jalila sungama makaranta, nayi masu alkawarin wucewa wata, kuma gashi Jalila ce kadai tayi karatu ya akayi Falak batayi ba, hartayi aure nibansaniba?  Zarah tace lallai Alh, da badan nasanka ba da se ince kasamu tabin hankali, kabada auren Falak da hannunka, kuma kazama waliyinta kabani kudi nayi mata siyayya sannan kace kamanta, haba Alh, kode ciwon mantuwa yafara samunka? Falak fa da bakinta tazo tace tasamu mijin aure bazatayi karatu ba, har na hana kace bakomai tunda mijinta yanada hankali setayi agidanshi.

Dafe kai Alh yayi sbd rudun daya shiga, ganin Zarah tana iya sakama shi ciwon kai yasa Sameer yamatso kusa dashi yace Alh, kada kasama kanka dogon tunani ba,a son irin wannan yana iya yawo maka matsala, addu,a yakama kayi hakane Ummi batayi karya ba, nine mijin Falak kuma kaine kabani ita kazama waliyinta idan katambayi mutanen unguwar nan zasu fada maka anyi haka. Alh, yagoge kwallan idonshi yace shikenan nagode Sameer, tabbas nasan akwai abinda yasameni, sede bansan komenene ba, amma naji dadi sosai tunda Falak tasamu miji nagari, Allah yabaku zaman lfy. 

Falak inaso kiyafemun kada ace nakasa rike amanar da Hajjo da barmun, idan har akwai wani abu dana yimaki kiyafemun bansan awane yanayi nake ciki ba, sede zanyi yanda kace bazan tsananta bincike ba, sema ingodema Allah daya yayemun abinda nakeji. Nagode. Sosai. Gashi ankusa bikin Jalila kema Jidda naso ace kinsamu miji dase ayi tare, amma bakomai Allah yakawo maki mafi alkahiri.

Zarah tayi murmushi tace ameen, Alhn yace wai ina Baba mairo ne, haryanzu bata dawo bane? Zarah tace e kasan ai tadade bataje gidaba, dama tace zata kwana 2. Anan suka cigaba da fira sosai Falak taji dadi yau tana fira da Dadynsu wanda rabonta da haka tadade, tashi su Sameer sukayi suka masu sallama yace zedawo anjima yadauketa. Jalila tace tashi muje daki, Alh, yace a,a kuzauna anan munyi fira kinga anjima zata tafi. Zarah ta maka mata harara, tace Jidda tashi muje kiyi wanka kici abinci ki kwanta nasan kingaji. Haka suka zauna suna tafira cike da jindadi.

Tafiya sukeyi duk sungaji sunyi bacci harsuntashi, gashi magriba hartayi basu isa ba, Asabe tace kai, gsky Lagos akwai nisa, aini tunda nake bantaba tafiya menisa haka ba. Dije tace kede bari, sede dana tuna rayuwar jindadin dazamuyi idan muka isa se inji banajin gajiya. Asabe tace.........Innalillahi wa inna ilaihir raji,un shine abinda sukaji driver yana fadi, hakan yasa Asabe tahadiye maganarta suka maida hankalinsu ga driver. Meyafaru mukaji ana salati? Driver yace to jama,a Allah yahadamu da yan fashi kowa yafara addu,a. Tunkafin yagama maganarshi yataka burki ganin ansetasu da bindiga, parking yayi gefen hanya. Dije tace ma Asabe anshi wannan dubu 15 ne idan akace mubada kudi kibasu nima. Zan basu na hannuna, kada kifada masu akwai kudi ajaka, nasan dasun duba zasuga kaya tunda sauri sukeyi dare beyiba bazasu tsaya dubawa ba.

Kowa yafito, sukaji ana fadi, haka kowa yafito suka fara karbar kudi suna binciken motar, inyamura ana bude jakarta aka samu dubu 50, suka anshe nan tasaka kuka tana fadin nabani kuyi hakuri Oo, yarona beda lafiya zankai masi kudin magani, daya daga cikinsu yace kimana shiru ko in fasa kanki, aka zo kan Asabe ana buda jakarta aka samu 15k, suka dauke, ana zuwa kan Dije aka samu 20k itama suka kwashe, ganin sunsamu kudi agurin kowa yasa wani yace ya isa haka kuzo muware kunsan oga yana jiranmu gashi dare biyi sosai ba, kutashi ku bace mana anan, suka fara shiga mota, Inyamura ce tafara shiga se kuka,takeyi, sannan Asabe tashiga

Asabe ta kalleta ganin yadda take kuka yabata dariya tace inbanda abunki darashin dabara inrin taku yaushe zakitaho Lagos da kudi ajaka har dubu 50. Kinga sunyi maki hankali gobema seki kara tafi baki boye kudiba. Muyanzu wazece muna da miliyoyi acikin boot? Kuma gashi an anshi kadan zamu wuce abunmu. Driver yace wai mekuke jira ke ki matsa masu su shiga muwuce mana. Dije tace ai bansan wane irin surutu Asabe takeyima wannan matarba duk kintare hanyar.

Dasauri Inyamura ta ture Dije tayi waje tana fadi wallasi akwai kudi a boot. Cak kowa yatsaya yana kallonta. Dan fashi ya ce wane boot, tace amota. Dariya yayi yace kowa yafito, nan take jikin Asabe da Dije yafara rawa, Asabe tace nashiga 3 bakina yajamana. Anan aka fiddo kaya, aka ciro jakarsu, yace suwaye keda wannan jakar, su Dije suka ce mune, yace tokuzo nan, kai driver daga ina kuke, yace Kaduna, to kusauran kowa yashiga mota, suna bude jakar suka cire kayan sama anan suka ga makudan kudi, nan take suka maida ma kowa kudin shi suka ce sutafi subar su Dije anan, 

Haka suka tafi suka barsu suna ta kuka, haka suka tasa keyarsu suka nufi gurin Ogansu, suna zuwa suka zazzage duka kudin, Ogan yace shegu, ina kuka samo wadan nan kudin haka? Wlh Oga wata inyamura ta temakemu muka samesu agurin wadannan, Yace sake dubamun jakar hannunsu, ana duba jakar Dije, aka ciro hotuna, yace Oga babu komai se hoto, yace mugani. Cike da mamaki yamike tsaye yana kara murza idonshi yace Hajjo, dama kina Raye??????

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/5, 5:29 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
 Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 120.....125

Wani irin murmushi Ogansu yayi, yace nadade ina tunanin wata rana zamu hadu, segashi cikin sauki nasameki ahannu. Kai, ya daka masu tsawa, a ina kukasan wannan matar tajikin hoton nan, mesuna Hajjo? Cike da fargaba Asabe tace wlh ba ita bace amma de itama mamarta sunanta Hajjo, kuma tarasu da dadewa, wannan sunanta Falak.

Murmushi yayi yace tabbas yarinya kingirma, harkin kai minzalin aure, kinzo adede dama ina bukatar abokiyar hutawa. A wane gari suke? E to dama de AGOLAH ce agidan diyar mijina, kuma bayan mamanta tarasu itama tayi aure. Mene? Aure? Wlh dasake, kinsan koni wanene agurinta? Kai Asabe tashiga girgizawa tana hawaye.

Kawun Babanta ne ni, kinga ko inada hakki akanta, to wai ku inama zakuje da makudan kudi haka, kuma mezakuyi da wadan nan hotunan, kode wannan shine mijin nata? Dan Allah yallabai kayi hkr, wlh muma bamu akayi mukaisu gurin boka shine mukuma mukace bazamuje ba, shine mukayi kokarin guduwa da kudin.

To waya aikeku? Diyar mijina ce, itace kishiyar Maman Falak, wannan kuma mijinta ne, shine takeso amallake, ita kuma Falak akasheta. Hahhhhh, kawai kicemun kuma maciya amana ne. Lallai tunda hadaku za,a hada baki akashemun jinina, lallai kuma zaku amshi rabonku, danni bana yafema wanda yashiga gonata.

Dije tace kawa Allah kayi hkr, mude kudauki koda rabin kudin ne, kubamu sauran mutafi, wlh dama can bamuyi niyar zuwa gurin wani boka ba, muma muna tausayinsu ai..... Saukar marin datajine yasata yin shiru, ke harkin isa kizo gabana kina fadin indauki rabin kudi inbaki sauran. To bara kiji, ko wadanda suka kawo kudin basuda hurumin karbar rabin kudin bare kuda muka kama, wanda lokaci kadan yarage maku aduniyar gaba daya.

Wayyo Allah nashiga 3,ni Asabe, ina zamana Dije kinja mani, gashi nan nibanyi kudiba,  zan rasa raina abanza, nide Allah ya isa tsakanina dake, duk kece kika sakani cikin wannan bala,i. A,a kada kidoramun laifi, dama can da bakin halinki kikazo garinmu, keda kika kashe mazajenki har 2, kuma kike fadin nina koya maki bakin hali.

Ya isa,,,,,,,., Ashe de kuma kananan yan ta,adda ne. Lallai kunyi kokari. Duk ku saurara, banida lokacin batawa, ke a ina zan iya samun Falak? Wlh nima bansan gidansu ba, amma de nasan gidan diyar mijina. Ok, fadamun dan sauri nakeyi.

Idan kaje Unguwar sarki kaduna duk wanda ka tambaya Alhaji Abba Bala, yasan gidan. Da kyau, kai mugu gama masu aiki kasan ni bana barin baya da kuurah. Tasssss kakejin karar bindiga andauke Asabe da Dije. ( se ince karshen Asabe da Dije kenan, dama duk wanda ya gina ramin mugunta, wata rana shine ze fada. Allah yatsaremu, sunyi 2 babu).

 Mazaje, kowa yafara shiri, gobe da asuba zamu dauki hanyar kaduna, bansan ranar dawowarmu ba, harsena cika burina na tahowa da Falak, tunda munsamu isassun kudi bamu da damuwa, kudauki jakar kudin muware, lallai yau munyi babbar sa,a. Daukarmun hoton fuskarsu awayata, hakan zemun amfani idan naje gidan, diyar mijinta.

Sedare Sameer yazo yadauki Falak suka wuce gida, Zarah ko sallama bata bari sunyi ba, har mota Jalila da Alh, suka rakosu, Alh, wani irin farin ciki yakeji. Sameer yace Alh, gobe zanzo indaukeka a office kawuna yana son ganinka, yace lallai muje tare akwai wani temako dazeyi maka. To to babu komai, Allah yakaimu, bara insamaka no ta idan kazo seka kirani, yauwa gata, zantura maka da address din office din. Sallama sukayi masu, Falak kamar kada ta tafi takeji.

Kwance Jidda take abisa gado tana tunanin halin datake ciki, gashi cike take da bukatar namiji idan takira Viju akashe, tarasa yanda zatayi, murmushi tayi, tace wlh bazan tausaya ma duk wanda yanemeni da bukataba, yanda aka likamun cuta kowama yasamu badamuwata bace, Allah yakaimu inkara samun sauki, dole insamo me biyamun bukatata, meza,a fasa, tunda harnazo gargara, ai gara kawai incigaba da shakatawa ta. (Lallai kinyi kuskure Jidda, Allah yashirya). Tashi tayi tabude jakarta tadauko maganinta tasha sannan ta kwanta.

Zarah kuwa aranar kasa zuwa dakin Alh, tayi adakinta tayi kwanciyarta sbd batason yawan tambayar da Alh, yake mata, ga abin duniya yafara isarta, takira no wayar Asabe yafi akirga, amma bata shiga, gaba daya ta gama shiga tashin hankali, addu,a kawai take Allah yasa lfy. Amma ta kudira aranta dole gobe taje Zariya. Da wannan tunanin tasamu bacci yadauketa.

Kuyi hkr da wannan.
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/6, 12:15 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@(H,O,N,A)

Part 125.....130

Karfe 9 na safe Zarah tagama shiryawa tasami Alh, afalo yagama cin abinci yana shirin fita. Bayan sun gaisa, tace Alh, dama zuwa nayi infada maka inaso inje gidan, dan jiya mafarki Baba nayi wai beda lafiya, shine nace gara inje indubashi na dade banje ba. Mamakin kalamanta yayi, dan a iya saninshi Zarah bata taba cewa zataje taduba Babanta ba, sede idan wani uzurinta ya tashi, yace tofa, ai mafarki ba gaskiya bane Zarah, insha Allahu zaki sameshi lfy. Shikenan sekin dawo, amma dan Allah kada kiyi dare kinsan banason tukin dare. Kudi yabata yace tayi mashi siyayya, yakaramata wasu yace idan taje tabashi kuma tace yana gaisheshi. Godiya tayi mashi yatafi itama tayi masu Jalila sallama ta tafi.

Alh, yana zuwa office bayan yagama abinda yakeyi, yaji kiran Sameer, nan yahada kayanshi yafita yasameshi awaje, bayan sun gaisa, Sameer yace ina ganin ka aje motarka semu tafi atawa, haka akayi suka nufi gidan Kawu.

Bayan sungaisa, Kawu yafara magana, agaskiya Alh, ka tsallake rijiya da baya, tun ranar da mukaje neman auran Falak na ganka, nasan akwai abinda yake damunka, gaskiya Alh, kana sakaci da addu,a kasan ita makamin mumunice, duk wanda yariketa, to koda wani abu zesameshi yakan zomashi da sauki. Hakan yasa asirin da akayi maka yayi tasiri akanka. Amma alhamdulillahi yanzu babu komai ajikinka, sede muce Allah yakara karewa, kuma kaima kadage da addu,a.

Alh, yanisa yace tabbas Malam nima naji alamun haka tunbayan da muka hadu da Falak a asibiti, kuma naji labarin da bansan ya akayi ba, adaren jiya sam banyi bacci ba, duk da nace bazan tsananta binciken halin dana shiga ba, amma ajiya nayi nazari sosai, kuma zuciyata tafara zargin wani abu, sede kasan ance zargi beda kyau koda yakasance gaskiya ne, hakan yasa nabar abun kuma nima nayi alkawarin dagewa da addu,a tabbas nasan nayi sakaci abaya, amma yanzu hakan yazamar mani darasi.

Kuma ina baran addu,a awajenka, Malam yace babu damuwa Alh, muna temakon wasu ma, bare kuma nagida, kuma nima shawarar dazan baka kamar yanda kace kana zargin wani abu, to kabarshi ahaka, kada kayawaita bincike, kasan kome mutum yakeyi Allah yana ara mashi rana ne, wata rana dole asirinshi ze tonu.

Abu nafarko dazaka farayi shine karika tashi cikin dare kana sallar dare, kasan Allah yace yana saukowa akowane karshen dare kuma yana amsar addu,ar duk wadanda suka rokeshi a wannan lokacin, ka yawaita karatun alkur,ani, da sadaka suma suna temakon mutum, yawan ambaton Allah safe da yamma, azkar dinka kullum dummin saurin da kakeyi kada kabari suna kubucemaka, koda kana tafiya amota ne, idan ka haddacesu to kasamu kafin ka isa inda zakaje kayisu. Allah shine mafi sani, wannan ruwan addu,a ne danayi maka tunjiya, kashanye yanzu, wannan kuma idan ka koma gida kazubashi aroba kawanke jikinka duka, insha Allah zakaci nasara akan duk wani menemanka da sharri.

Godiya sosai Alh, yayi mashi hada kukanshi, yakawo kudi yace gashi ayi sadaka, daga nan sukayi sallama Sameer yamaidashi office, yana zuwa ya dauki motarshi yanufi gida. Yana zuwa yashiga yayi wanka da ruwan maganin da aka bashi yadauro alwala yazauna yana karatun qur,ani.

Zarah kuwa tana zuwa gidansu taci karo da Babanta yana shirin kulle gida. Tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki, danshi har yamanta rabon daya ganta, tana fitowa daga mota tace Baba ina kwana, yace lfy lau Zarah ashe kina duniyar? Dukar da kanta tayi tana wasa da makullin motar tace wlh kuwa Baba kasan aiyuka ne sukamun yawa. Yace e gsky kam naga alama.
Yanaga kana shirin kulle gidan ina Innar take? To shigo daga ciki tukunna.

Bayan sunzauna, ya kalleta yace Asaben bata fada maki abinda yafaru ba? Saurin kallonshi tayi tace aini rabona da ita tun ranar litinin, kai ya jijjiga yace to ai tundaga ranar nima bankara ganinta ba, dan yanzu bama tare da ita, aranar lahadi tazo tace insaketa zata bar garin, nikuma na sawake mata tundaga nan bankara ganinta ba. Wata irin zufa ce tarika keto mata, tafara fifita tace nashiga 3 yanzu Baba bakasan inda ta tafi ba? Murmurshi yayi yace ai kunfi kusa ni ina zansan inda taje, dama ni asama naganta, bansan kaddarar data kaini aurenta ba, kuma gashi Allah yarabani da kaya, bana fatan musake haduwa da ita.

Shiru tayi tafiddo wayarta tana kara kiranta amma haryanzu shiru. Abinda bata saniba, tun atasha Asabe ta karya sim dinta tace setaje Lagos zata sayi wani. Baba kuma wayarta kullum akashe, dariya yayi yace toni Zarah yakikeso incemaki, kowa yasayi rariya ai yasan zatayi zuba, saboda haka kije gidan kawarta Dije kozata fada maki garinsu. Ai Baba Dije bata nan, kuma bansani ba kota dawo, gashima ni bansan gidanta ba. Kanshi yagirgiza yace waini Zarah me Asabe zatayi maki ne kike nemanta? Babu komai Baba, kawaide ina nemanta ne, kasan banida wata. Uwa data wucemun ita shiyasa hankalina yatashi danaji kace bata nan. Seda yaji kwalla tacika mashi ido jin kalaman Diyarshi, tabbas tausayinta yashigeshi, sede Asabe tayi mata mummunar huduba. Share kwllar datazubo mashi yayi, yace shikenan Zarah, amma de inaso kisani Asabe ba macen kirki bace, kada kicigaba da nemanta babu abinda zaki saku agurinta se halaka, kiyi hkr kamar yanda Allah yarabani da ita kema kidauka rabuwarku alkhairi ce.

Kallonshi tayi cike dajin haushi tace Baba nide kasa wani yarakani gidan Dije sauri nakeyi zankoma. Murmushi yayi yace Zarah kibi duniya ahankali wlh ina tausaya maki duk ranar da duniya zata juya maki baya. Tashi tayi tace nide zantafi, dubu 1 taciro tace ga wannan kayi cefane, yace A,a kirike kudinki zasuyi maki amfani ahanya niyanzu bana bukatar komai, Allah yayima Jalila albarka, tabbas yarinyar nan yar halak ce, tayi mani abinda wadda na haifa takasa.

Tashi muje innuna maki gidan, kudinta tamaida jaka tana gungunai tayi gaba, har kofar gidan Dije yarakata, ya hadu da wani abokinshi makwabcinta, shi yatambay ko tadawo. Yace ai malam Garba Dije da kawarta sunyi hijira bazasu dawo garin nan ba, dan harta saida gidanta da komai nata, nima kiya medakina take fadamun tashiga gida tasamesu suna ta shiri, suke fada mata sukam sunci gaba. Zarah jitayi kafafuwanta suna rawa, zufa kawai take fito mata, da kyar tace to Baba nizan koma, yace to yayi kyau, Allah ya kiyaye kigaishemun da Jikanyata Jalila, haka tanufi mota yana binta da kallon tausayi. Da kyar taja motar ta tafi, ikon Allah ne kawai ya kaita gida, tana zuwa tashige dakinta ta kulle tafara kuka.

Karfe 4 na yamma su Figo kawun Baban Falak suka shigo kaduna, cikin shiga ta mutunci, idan kagansu sekadauka irin manyan yan shiyasa ne, hotel suka nema suka kama daki 2 shi yadauki daya yabasu daya su 3.

Se karfe 6 suka fito shida babban yaronshi Jungle suka tari taxi suka fada mashi inda ze kaisu, suna zuwa unguwar suka sami wani suka tambayeshi gidan Alh, Abba Bala, nan take yanuna masu gidan, godiya sukayi mashi, Figo yaciro wayarshi yasa akunne kamar mekiran waya, can kuma yacire yace wayarshi akashe take kawai muje ma dawo gobe, banason shiga baya gida kasan matarshi bazata barni infito ba, zatace sena jirashi. Kallonshi Jungle yayi Figo yayi mashi signal da driver, murmushi yayi yadaga mashi hannu, suka koma hotel, bayan sun sallami driver Figo yace kasan bana aikina da ka, haka kawai muje guri da driver kuma mu tambayi gidan mutum ana nuna mana kawai mujuya ai kowaye ze iya zargin wani abu. Jungle yace gsky Oga aiki da kai akwai karuwa.

Zaune suke afalo Falak tayi matashi da kafar Sameer, shi kuma yana wasa da cikinta, yace dear idan kika haifa mun mace sunan Ummanki zansa, Idan kuma na kiji ne, sunan Babana zansa, shiru yaji tayi batace komai ba, dukowa yayi yana kallon fuskarta, gani yayi hankalinta baya gurin, girgizata yayi, tayi saurin kallonshi. Meye haka kikeyi Falak, bakisan yanzu bake daya bace, kike irin wannan tunanin, kuma ko ke dayace ma aikinsan banason dogon tunani ko. Murmushi tayi tace kayi hkr wlh ina tunanin Dady ne, ina tausayinshi, nasan Ummi bazata kyaleshi haka ba. Babu abinda zata iya kara yimashi, domin yanzu yafi karfinta, kawai mucigaba dayi mashi addu,a. Shikenan, Allah yakara tsaremu, yace yauwa kokefa, ameen, tashi muje kibani abinci dagata yayi suka nufi daki suna dariya.

Washe gari da misalin karfe 10 nasafe, Jungle da Figo suna daga gefe suka ga motar Alh, tafita. Figo yace yauwa, yatafi muje, suna zuwa suka kwankwasa kofar, megadi yabude, bayan sungaisa, Figo yace ni suna Lado, munzo gurin Alh, ne. Megadi sewashe baki yakeyi yaga manyan kutane, yace yanzu kuwa yatafi office, amma ku kirashi mana. Aa, barshi kawai idan hajiya tana ciki kafada mata zamu bata sako seta aje mashi, yace toshikenan kushigo ga banci nan kuzauna, dasauri yanufi cikin gidan, Karo sukaci da Jalila bayan sungaisa yace tayima Hajiya sallama wasu mutane suna son bata sako ta ajema Alh.

Adaki tasameta kwance tana tunani, tace Ummi wai kizo wasu kutane zasu baki sako ki ajema Dady, tace kash nifa banason yawan damuwa kije kawai subaki, tace a,a Ummi idan kuma sakon kudine fa, ai kinga keyakamata subama, saurin tashi tayi jin ance kudi, gyalenta ta dauka tafita.

Bayan sungaisa Figo ya matsa kusa da ita ahankali yace bagurin Alh, muka zoba gurinki mukazo kuma munzo da magana me mahimmanci amma idan kinasonji zamu iya matsayawa daga nan, harararshi tayi tace nikuma a ina nasanka, murmushi yayi yace amma idan baki sanni ba, kinsan Asabe da Dije ko?

Cike da fargaba tacee kushigo, murmushi yayi yace abokina muje ta matsa semunsha ko ruwane, megadi yace ai gaskiya ne, sekunfito. Bayan sunzauna afalon baki tace dan Allah ina kasan Asabe da Dije? Wayarshi yaciro ya nuna mata hotonsu yace kobasu bane wadannan, jiki narawa ta amshi wayar tafara dubawa, dasauri tace bade sun mutu ba, to ina jakar dasuke tare da ita? Yace tonide bansan wata jaka ba, munshiga mota atare dasu zamuje Lagos, se yan fashi suka tare mu, suka kwace mana kayanmu da kudinmu duka, to ita Dije tana kusa dani, alokacin da aka bude jakarta senaga wasu hotuna sunfado, ina dauka naduba senaga macen jikin hoton nasanta, ita da mamanta, garinmu daya dasu, kuma masu laifine, sunan mamarta Hajjo ko? E ita kuma Falak, haka suke, to bazan boye maki ba, agaskiya mutanen banza ne, mijin Hajjo abokina ne, yanada kudi, shine ita da niyarta suka hada baki suka kashe shi suka gudu. 

Nayima yan sanda alkawarin nizan nemosu aduk inda suke, na dade ina nemansu bangansu ba, harna hakura, segashi Allah yakawomun su cikin sauki. Bayan natambayi Dije a ina suke tacemun Hajjo tarasu, ita kuma Falak tayi aure, shine nace tayi mani kwatancen inda zanganta, shine take cemun ai kekika san inda take, kema kinso akasheta kika basu kudi sukaisu gurin boka, shine sukuma ashe karya suka maki guduwa sukaso suyi da kudinki shine yan fashi suka kamamu. Ita ta fadamun sunan mijinki da unguwarku.

To dayake ansamu kudi agurin kowa sune suka boye nasu da kaya, koda yan fashin suka gano kudin suka tambayi masu su, shine suka kashesu, mu kuma suka maida mana kudinmu, nikuma nadaukesu hoto dan innuna maki. Yanzu nazo kitemakeni ki nunamun gidan Falak domin hukuma tayi saurin cafketa.

Bakin ciki tare da farin ciki ne, suka hadema Zarah, jin za,a kashe Falak cikin sauki.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/9, 1:12 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 130.....135

Wani murmushin farin ciki Zarah tayi takara kallonnshi tace tabbas nima sun cutar dani, kuma bazan taba yafe masu ba, dan haka zan nuna maka gidanta, amma sena tambayi Jalila danni bansan gidanba.

Amma zan hadaku da ita tarakaku gidan. Murmushi yayi yace a,a hajiya baza,ayi haka ba, kinsan halin mata, banason kowa yasan zamuje gidanta, abinda nakeso dake kawai kisaka diyarki taje gidan, mukuma zamu bita abaya, damunga gidan shikenan. Zarah tace babu damuwa, bara inshiga ciki inyi mata dabara. Amma gaskiya tsakanina dasu Asabe Allah ya isa, dama duk munafunci sukemun bansani ba. Gashinan ai tun aduniya Allah yasakamun, kudina kuma duk wanda yacisu Allah ya isa, Jungle yayi dariya yace hajiya aisede ki kiyaye gaba, amma kudi suntafi.

Fita tayi tanufi cikin gida, Jungle yace gaskiya Oga aikinka yana kyau, yace nidin nawasa ne, kasan yau ko shekarata nawa ina dabanci, kasan kuwa dole nakware aharkar.

Adaki tasamu Jalila tafito wanka tagama shiryawa, tace yauwa Jalila wani guri zakije ne? Tace a,a Ummi babu inda zani, tace yauwa dama aikenki nakeson yi yanzu gidan Falak, dasauri Jalila takalleta cike da mamaki, tace ko kema bakisan gidan ba? Tace nasani Ummi.

Yauwa naga kunfi shiri da ita shiyasa nace bara in aikeki kije gurinta amadadina, wlh kunyarta nakeji kije kice mata dan Allah tayi hkr da duk abinda tasan nayi mata, sharrin shedanne, kuma nima zanje inbata hkr da kaina. Murmushin farin ciki Jalila tasaki jin Umminta tasauko daga halinta, cike da zumudi tace kai amma wlh Ummi naji dadi, yanzu kuwa zantafi Allah ya yafe maki, tace ameen.

Fita tayi tana fadin zanyima driver magana idan kingama seya kaiki, tace to. Zarah tayi murmushin mugunta tace aini har abada bazan taba kaunar AGOLAR yarinyar nan ba, wlh senaga karshenta kamar yanda naga na Uwarta.

Afalo tasamesu tace angama zaku iya fita kujirata yanzu zata fito tare da megadin gidan, godiya sukayi mata suka fita. Me taxi suka samu dede lokacin dasu Jalila suka fito, Figo yace yauwa gashi nan yafito, shiyasa nace mashi muyi gaba yace a,a mujirashi yafison yashiga gaba, dan Allah driver wancan zakabi bayanshi, yace to yallabai.

Tafiya sukeyi harsuka isa kofar gidansu Falak, Jalila tace mashi yatafi anjima zata dawo da kanta, yace toshikenan. Figo ya daga waya kamar yana kira yace wai kai dama tare kuke da mace shine kasamu jiranka, toshikenan bazamu tsaya jiranku ba nasan mata da nawa, kawai kasamemu amasaukin mu. Toshikenan sekazo. Yauwa driver muje gaba wancan drivern matan ze bata mana lokaci. Driver yayi dariya yace wlh Alh, haka mata suke, shiyasa bana son mace tadaukeni drop. Jungle yayi dariya yace anbugar dakai. Figo yayi murmushi suka wuce.

Hawaye ne, suketa zuba afuskar Falak, Jalila tace dan Allah kiyi shiru hakanan, nasan Ummi tayi maki abubuwa da dama wanda bakowane ze iya yafewa ba, amma ki kalli girman Allah da zumuncinmu kiyafe mata, kuma itama tace zatazo dakanta. Falak tace shikenan Jalila kodan saboda ke da Dady zan yafe mata sauran laifin kuma tanemi yafiya agurin Allah. Murmushi Jalila tayi tace gsky nagode Allah yabar kauna, tace ameen.

Falak tace biki fa yanata matsowa ko? Jalila tace wlh kuwa, jiyama Saleem yake cemun gobe za,a kawo lefe, kuma wai dame dame nashirya, nace mashi babu abinda zanyi se walima, kinsan bawasu kawaye gareni ba. Falak tace dama yanzu aure ai kayi walima kawai ta isheka, Allah yasade agama lafiya, tace ameen. Falak tace muje mudora abinci to.

Bayan kwana 2. Figo yashirya shi kadai cikin shiga ta mutunci yanufi gidan Falak, akofar gidan ya tsaya yafara kwankwasa masu, Sameer yana waje kasancewar week end ne, yana goge motarshi, yaji kara buga kofa, fita yayi, yaga babban mutum me cike da kamala, yayi saurin karasowa yace sannu dazuwa, yace yauwa, bayan sungaisa yace dan Allah tambaya nakeyi, yace to, konanne gidan Falak? Sameer yace i nan ne, yace Alhamdulillah, yaro yau kwanana 7 agarin nan ina neman gidanta, harnace daga yau zan koma garinmu segashi naci sa,a dayake nima kwatance akamun.

Sameer yace Allah sarki wa za,a cemata? Yace kace dan uwanta ne yazo daga sokoto, yace ato bismillah shigo, abakin kofar falo ya tsaya yace kashiga kafada mata sannan inshigo ai zefi ko. Sameer yace hakane, yana shiga besameta afalo ba yawuce ciki yace mata dauko hijabinki kifito falo muna da bako, komawa yayi yamashi iso.

Kitchen yawuce yadauko mashi ruwa , Falak tashigo da sallama tazauna har kasa taduka tagaisheshi ganin babban mutum, seda yahadiye miyau sannan yakara washe baki yace ikon Allah, lfy lau, Falak kece kika girma haka, da alama baki ganeni ba ko? Saurin dago kanta tayi, ai suna hada ido tayi saurin mikewa cike da firgici, tana nunashi da yatsa, Kawu, meyakawo ka gidana? Shikenan nima kazo ka kasheni kamar yanda ka kashe Abbana.

Sameer yataso yariketa yana fadin mekike fada ne, haka Falak? Tana kuka tace meyasa kashigo dashi gidan nan, kasan koshi waye? Toshine Kawun Abbana danake fada maka,, kuka yaci karfinta ta durkushe kasa, Sameer yayi saurin kallonshi. Shima kasa yasauka yasaki kuka kamar da gske,

Yace dan Allah Falak kiyi hakuri kiyafemun, nasan ban can canci yafiya daga gareki ba, amma tabbas nayi nadamar abinda na aikata, sosai ma, kuma nayi bakin cikin mutuwar Hajjo, bannemi yafiyarta ba, shiyasa nace zanzo gurinki koda zaki kasheni inde zaki yafemun hakan zefi mani.

Sameer yayi shiru yarasa wnda ze lallasa, kusa da Falak yamatsa yajawota yace ya isa haka Dear, Allah yanason mutumin da,aka zalunta, kuma yana da ikon ramawa, amma yayi hakuri inaso kema kiyi hakuri, kalli yanda babban mutum ya duka agabanki yana kuka kidaure kiyafe mashi. Kara kwanciya tayi ajikinshi tana kuka.

Yace kawu kayi hkr katashi kazauna muyi magana, nasan Falak zata yafe maka. Tashi yayi yazauna yana goge kwalla ta malum malum dinshi. Sameer yace kawu ya akayi kasan inda Falak take? Nan yafada masu duk yanda yafada ma Zarah har karshe, sede yanuna cewar yayima Zarah wayau yace shima soyake akamata.

Yace tunda nasan cewar tabada kudi akaiku gurin boka nasan cewar batasonki, hakan yasa nima naje mata da irin fuskarta. Amma nadade ina rokon Allah yanuna munke, kuma gashi yau naganki, koyanzu kikace kinyafemun ayau zankoma dan nabaro iyalina kwana 7. Kuma inaso kisan zaman dazakiyi da Zarah neman hanyar dazata kasheki kawai takeyi, kome zata cemaki to karya takeyi.
Falak tagoge kwallanta tace shikenan Kawu nayafe maka, Allah ya yafe mana gaba daya, yace Ameen. 

Sameer yace Allah yayi maki albarka, yanzu kawu katsaya kaci abinci semuje can gidanmu kugaisa da Baba mairo, dan itace matar data rike Falak da gaskiya. Yace a,a ni akoshe nake, kuma na tsaida abokin tafiyata amma abinda zefaru gobe zanzo semuje tare. Sameer yace toahikenan. Tashi yayi sekara kallon Falak yake yana hadiye miyau, yace to Falak nagode sosai, senazo goben. Tace to Kawu.

Har kofar gida Sameer yarakashi sannan yadawo, Azaune yasamu Falak tana ta kuka, yace haba Falak kukan ya isa haka, tace wlh jikina yaki yarda da abinda Kawu yafada, sam bakasan wayeshiba, beda imani yama za,ayi ace wai shine yazo neman yafiyata. Sameer yace nima jikina yakasa yarda dashi, sede mucigaba da addu,a koma menene Allah zekaremu, kitashi muje musamu Kawu dasu Umma mufada masu halin da ake ciki.

Tafiya yakeyi yana kara tuno Falak, aranshi fadi yake dole inhuta da yarinyar nan koda hakan yana nufin tonan asirina, zansa su Jungle sudauko mun ita, bazan iya hkr da ita ba, haryawuce wata tsaye abakin wani shago seyayo baya, yace sannu yanmata. Jidda da dama tunanin wanda zetaya takeyi tace yauwa, sede ganin babban mutum ne hada furfura yasa tadan bata rai, yace idan bazaki damu ba, kozaki dan bani minti 2? Tace inajinka, yace to mudan bar kofar shagon ko, kallonta yayi yana lashe baki yace yasunanki kene? Tace Jidda, yace da kyau, nima bakone ina zaune a hotel nadan fito shakatawa kuma sena ganki, shine nace kozaki rakani masaukina mudanyi fira? Shiru tayi can kuma tace shikenan babu damuwa, murmushi yayi ya tsaida masu mota suka wuce.

Sallallami Baba Mairo takeyi tace kai, Sameer koni banyarda dashi ba, kasanfa mutane basuda gsky, kawai abinda zefaru, gobe kafadama yansanda yana zuwa su cafkeshi, amma batun tuba bata taso ba. Kawu yace a,a baza,ayi haka ba, akullum idan mutum yace yatuba, to ku karbeshi da zuciya daya, sbd bakusan abinda ke cikin ranshi ba, idan har karya yakeyi, to Allah yafimu sanin hakan, semudage da addu,a Allah ze tona asirinshi. Amma kada ku kai maganar gurin kowa kubarshi, abinda nakeso daku gobe dasafe kutaho nan, kuma kafadama me shagon kusa daku cewar zakayi bako, idan yazo ace mashi kunje unguwa yadawo jibi. Halima tace kai duniya babu gsky, Allah yasa mudace, suka ce ameen.

Ankawo lefen Jalila, kaya sunyi kyau sosai, zarah tarasa inda zatasa kanta dan farinciki, diyarta tasamu abin duniya, itama tayi kokari tasaya mata kayan daki masu kyau. Bayan suntafi Zarah takira Jalila tace to kirawo Jidda kuzo kuga kayan tunda suntafi. Jalila tace wlh Ummi bansan inda ta tafi ba, tunda safe naga tayi wanka ta fita. Zarah tace kyaleta ita tasani kila bakin ciki takeyi dan taji ance yau za,a kawo kayan ki. Jalila tace kai Ummi banason kinama Yaya Jidda haka, seta rika shiga damuwa harkisata tashiga wani hali. Zarah tace keni kyaleni tunda de yawon banza tasa agaba ai babu inda zekaita.

Kwance suke akan gado bayan sungama aikata masha,arsu Figo yakalli Jidda yace gsky na dade bansamu mace irinki ba, dole kisamu kyauta meyawa, ina fatan zaki rika zuwa tayani fira kafin intafi? Jidda tayi murmushin mugunta tace inde da kudi babu abinda za,a fasa. Dariya yayi yace to bari inyi wanka infito, pillow tajawo tarungume tana fadin kaima daga yau kashiga layi sekaya nemi magani. Hannu tasa tadauko wasu hotuna data gani akasan pillown data daga tayi.

Mamaki ne yakamata ganin hoton Dadynsu da na Falak, tace to meya kawo hotansu nan? Karar bude kofa taji, yace mekike kallo haka? Murmushi tayi tace wasu hotuna nagani shine nake kallo, zama yayi yajawota jikinshi yace wannan bansanshi ba, amma wannan nasanta,,,,,,,,, Nan yabata labarin yanda yasamu hotunan agurinsu Asabe.

Yace dama nadade ina neman Falak segashi naganta, yau har gidan naje kuma tayarda da karyar dana mata, amma gobe da dare misalin karfe 10 zansa yarana suje sudauko mun ita, dan narantse sena sha zumarta.

Wannan mutumin kuwa matarshi batasonshi, sotake ta mallakeshi segashi itama wasu sunci amanarta, shi baruwana dashi mantawa nayi ban yaga hotonshi ba ma. Jidda da zufa tagama jikata tace uhm, ammade bazaka kasheta bako? Yace a,a sena gama jindadi na, sannan insa amaidata daga nan kuma inkara gaba. Tace aigara akayi mata haka, tunda suka gudu suka barka. Nizantafi kada anemeni agida. Yace bazakiyi wanka ba? Tace idan naje gidan zanyi, yace tobani no wayarki mana, ai zaki dawo gobe ko? Tace emana, amma kuma banda waya, jakar kudi yadauko yabata subu 50, sannan yabata 30 yace tasayi waya, yarubuta mata no barshi tace to baka bada kudin kati ba. Yace ah lallai yarinya kema kinada son kudi. Dubu 10 yabata, tayi mashi sallama tafita.

Jikinta se rawa yakeyi, aranta tana fadin tabbas Falak bantab yimaki wani abu na alkahairi ba, amma yau dole inyi maki, bazan bari wani yacutar dake ba, yagoga maki cuta, dole insanar da Jalila tarakani gidanki infada maki. Mota ta tare tanufi gida.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

08028525263
[7/11, 3:29 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!!Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 135.....140

Cike da sauri Jidda tabama me taxi kudinshi tashiga gida, da Zarah suka fara cin karo tace ke lafiyarki naganki kamar arikice? Harzata fada mata, se kuma ta tuna da maganar da Figo yafada mata, akan tabada kudi akai dadynsu gurin boka. Murmushi tayi tace wlh Ummi ba komai ina Jalila? Baki ta tabe tace tana ciki, kinsan yau za,a kawo lefenta amma kika ki tsayawa akarba.

Uhm wlh Ummi wani uziri ne, yataso mun, shine nafita dawuri nadauka bada wuri zasu zo ba. Ai shikenan kishiga ciki sunan ki kalla, Jalilan ma tana falo, yauwa Ummi, da kallon tausayi tabita, aranta tace dole insama maki mijin aure kema, damma Asabe ta munafunceni ai da naje gurin boka asama maki miji medan maiko, ita de Jalila Allah yasota batare dana kashe kudina ba tasamu me kudi.

Jidda tana zuwa falo tasamu Jalila tana kara duba kayanta, cike dasauri takamo hannunta har seda Jalila ta dan tsorata, lfy de Yaya Jidda? Lfy lau kede kawai biyoni muje daki muhimmiyar magana ce bata bukatar bata lokaci, daki suka nufa Jidda ta kulle dakin taja Jalila saman gado.

Ita de Jalila kallonta kawai take cike da mamaki. Inajinki Yaya Jidda Allah de yasa lfy. Uhm Jalila inaso kibani aron hankalinki, ayau inaso infada maki wata magana wadda babu wanda yasan da ita, kuma inaso idan kinjita ki temaka mun domin insamu inyi aiki alkhairi guda daya nima arayuwata. Jalila tace inajinki.

    Tun daga farkon shigarta harkar banza harzuwanta London da irin wahalar data sha,  har zuwa haduwarta da Viju da irin yanda ya yaudareta, ta cutar datake dauke da ita, harzuwa haduwarta da Figo da abinda yafada mata, seda tafadama Jalila. Kuka sosai sukeyi ba kamar Jalila wadda tausayin yar uwarta yakamata, jin irin abubuwan data aikata. Jidda tace wlh Jalila tun lokacin da Umman Falak tarasu naso intuba, amma rudin duniya tare da irin halin da Ummi take nunamun yasani komawa ruwa. Tabbas Al,amin masoyine nagari, yaso inbar London indawo muyi aure amma nakasa fahimtar abinda yake nufi, seda narigada nakamu da cuta sannan yace baze iya aurena ba, tunda shi beda ita, yanzu haka bansan inda yake ba, ko no shi nakira bata shiga.

Nayi nadamar abinda na aikata, nacuci kaina da kaina, kuma hakan yasamo asaline dalilin Uwa dabamu samu tagari ba. Ko kinsan cewar Ummi dasu Inna Asabe sune silar mutuwar Umman Falak da Ameer, kuma itace ta mallake Dady, yarika yin duk wani abu dayake ma Falak. Gsky nide tsakanina da Ummi sede ince Allah ya....... Saurin rufe mata baki Jalila tayi tana kuka tana girgiza mata kai. 

Kada kice haka Yaya Jidda, Uwa Uwace koda kuwa yar mafiyace bamuda wadda tafita, domin itace tayi sanadiyar kawomu duniya, dataso lokacin fitowarmu data kashemu, dataso tun muna jini datayi barinmu. Da jinin jikinta muke rayuwa acikinta, dole mudauki duk wani abu dazata mana, dan bekai rabin rabin wahalar datayi damuba. Ayanzu ko zama mu tsareta na awa 3 tayi bacci bazamu iya ba. Amma ita takan hana kanta bacci domin mu muyi. Saboda haka kada bacin rai yasa kifadi wata mummunar kalma akan Ummi, Allah ze iya kamaki da laifi akan hakan.

Addu,a itace abinda yakamata muyi mata wadda itace nake mata kuma gashi tafara canzawa, yanzu haka neman yafiyar Falak ta aikeni rannan nayo mata. Jidda tace Uhm Jalila ke yarinyace bakison kissa irinta Ummi ba. To wlh yaudararki tayi tayi amfani dake tanunama wadan nan mutana gidan Falak. Dan haka yanzu ba lokacin labari bane, kitashi muje mufada masu halin da ake ciki. Kuma akan labarina dana baki banason kowa yaji, kibarni ni nasan tawa tazo karshe, dan haka zankarbi duk wani hukunci da Allah zemun.

Jalila tace amma Yaya Jidda kinashan maganinki kuwa? Yamutsa fuska tayi tace wannan duk wahalar banza ce, tunda de ba,a iya ciremun ita gaba daya ba, babu amfanin shan wani magani, ada nafara sha daga baya kuma naga beda wani amfani, gara kawai incigaba da rayuwata haka har mutuwa ta tasameni. Jalila tace amma dakin cigaba da shan magani koba komai zaki samu lfiyar dazaki nemi yafiyar Ubangiji. Mikewa Jidda tayi tace kitashi mutafi banason dogon zance.

Adaki suka sami Zarah tabuga tagumi tana tunani, Jalila tace Ummi tunanin me kikeyi kuma? Murmushi tayi tace bakomai kawai ina dan tsare tsare akan bikinki ne, kinga saura sati 2. Hakane Ummi amma banason inga kina tunani. Yauwa Ummi zamuje mukai dinki nida Yaya Jidda.
Zarah tayi murmushi tace amma naji dadi dazaku tafi tare, sekun dawo, driver yana waje kusashi ya kaiku, to Ummi amma sede ya ajemu yadawo dan akwai inda zamu wuce. Tace toshikenan sekun dawo.

Suna zuwa gidan Jalila taga motar Saleem, tsayawa tayi Jidda tace muje mana, tace Motar Saleem nagani. Jidda tace to menene, bazaki shigaba kome? Nifa banason gulma. Jalila tace bahaka bane, inajin kunyar yaji labarinki sede idan bazaki fada masu yanda kikaji za,a dauko Falak daga gurin Figo ba. Murmushi Jidda tayi ta goge kwallan dasuka zubo mata, tace babu sauran jin wata kunya, kuma ni nadaukesu abokana shawarata, kada kidamu kobasu ji labarina ba sun riga da sunsan koni wacece sbd sunsan abinda nake aikatawa. Nasan Saleem yana sonki dan yaji labarina baze taba son dayake maki ba. Kuma dole nasan Sameer yafada mashi halin Ummi, tun kafin asamaku rana, kuma tunda kikaga bedena neman aurenki ba, ai yasan kinada hali me kyau. Kasancewarmu nida Ummi marasa hali me kyau baza,a ce dole kema ki kasance haka ba. Kinsan Allah yana fitar da shiryayye daga wanda ba shiryayye ba. Jalila tagoge kwallan idonta tace shikenan muje.

Kuka kawai Falak takeyi, Sameer kuwa gaba daya zufa ce tarufeshi, hankalinshi bakaramin tashi yayi ba, jin wai wani banza yanason zina da matarshi. Kallon Jidda yayi yace tabbas yanda kika kwatan tamana shi shine kawun Abban Falak, kuma daga gidan nan yake, Lallai biri yayi kama da mutum, tunda yatafi muma bamu yarda dashi ba, kuma aniyarmu gobe da safe zamu tafi gidanmu, sede yanzu dole mubar gidan nan, sbd meson abunka yafika dabara, yana iya canza shawara.

Jidda tace dan Allah Falak kiyafemun da duk irin abinda nayi maki, tabbas rayuwa takoyamun darasi, kuma kwadayi yakaini yabaroni, babu abinda nake nema daga gareku se addu,arku kobayan raina. Sameer yace meyasa kike fadar haka Jidda? Cikin kuka suma tafada masu labarinta.

Duk irin dauriya ta maza seda Sameer da saleem sukayima labarin Jidda kuka. Falon ya dade shiru kukan matan kawai akaji, sukam mazan sede hawaye a ido. Jidda tace narokeka Saleem kada labarina yasa wani abu yashiga zucuyarka na game da auranka ko soyayyara da Jalila. Wlh ko Qur,ani zan iya dafawa akan shedar halin kirki irin na jalila, Allah ya shiryata, duk irin yanda Ummi take nuna mata halin ko inkula lokacin da ina kawo mata kudi hakan besa ko samari Jalila tafara kulawa ba. Duk da bansan rayuwar datayi a makaranta ba, amma zan iya cemaka kaine mutum nafarko da Jalila tafara kulawa.

Dan haka inaso kada jin labarina da kuma halin Ummin mu yasa wata rana ka goranta mata. Saleem ya goge idonshi yayi murmushi yace Yaya Jidda kada kidamu. Allah ne yahadani da Jalila, bantaba son wata halitta ba kamar yanda nakeson Jalila, bayan Uwata da mahaifina zan iya cemaki Jalila itace mutum ta 3 datakeda muhimmanci arayuwata. Kima dena tunanin zan goranta mata, har abada, kuma wannan labarin naki insha Allahu daga nan yagama zuwa wani guri. Kuma batun maganinki dole zaki cigaba da shan shi, sbd rayuwa da mutuwa agurin Allah suke, idan yaso seyabarki da cutar harzuwa wani lokaci. Kifadamun idan baki shan magani kuma taci karfinki harta kaiki last stage wanda ko likitoci bazasu iya maki komai ba. Gashi Allah yaki yadauki ranki yazakiyi da wahalar dazaki sha? Alokacinne seme kaunarki sosai zeiya zama dake.

Dan haka kimun alkawari daga yau zaki cigaba da shan maganinki. Shikenan Saleem insha Allahu zancigaba dasha, dama na wata 1 aka bani kuma yana nan. Sameer da tundazu seyanzu yayi magana yace insha Allahu kema zakiyi tsawon rai harkisamu lokacin tuba zuwa ga Allah. Jidda tace Falak kinyi shiru bakice komai ba. Dan Allah kiyafemun.

Falak tagoge idonta wanda yayi ja sbd kuka, tace babu komai Yaya Jidda, niban rikeki da komai ba, kecema zanyima godiya, badan keba bansan yanda rayuwata zata kare ba. Saleem yace kutashi mutafi gidan Umma seku kwana acan, kai kuma Sameer daga can seku wuce gurin abokina D,P,O ne dan musan yanda zamu bullomasu, banason gobe tayi haryazo besameku ba, ze iya tunanin wani abu. Kema Yaya Jidda dake zamu tafi dan dole dake zamuyi amfani musamu mu cafkeshi. Tacebabu komai, ashirye nake dabada gudummuwata dama ina da no shi. Sameer yace Allah yadoramu akan sa,a sukace ameen.

Falak tace amma inaso kafin kutafi kusami Dady kuyi mashi bayani dan bazeji dadi yaji abun daga sama ba, dan yafi kowa sanin labarin Kawu. Saleem yace kinyi gsky, idan muka aje ku semu sameshi mutafi tare dashi ma.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[7/12, 3:35 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 140.....145

Kaf suka fadama Alh abinda yafaru, sede sunboye abinda yashiga tsakaninsu da Jidda, sunfada masa saurayinta ne, yarage mata hanya shine taga hoton Falak amotarshi har yake bata labarin abinda zeyi mata. Kuma basu fada mashi abinda Zarah tayi ba.

Sosai Alh, yayi mamkin jin wannan al,amari, yace lallai dole mudauki mataki cikin gaggawa, dan akowane lokaci ze iya aikata abinda yayi niya, dan beda tausayi. Allah sarki Hajjo babu rabon kiga wannan rana, banyi tunanin wannan mutum yana nemansu haryanzu ba.

Abinda zefaru kai Sameer kuyi gaba zuwa gurin abokin shi Saleem kome kenan kuyi mani waya, amma dole ayau za,a je aka mashi, tunda Jidda tanada no shi kutafi da ita nasan zatayi maku rana, nima dana gama abinda nake zanzo.

Kwance Zarah take, hawayene kawai suke zuba a idonta, zumbur tayi saurin tashi lokacin data kara tuna maganar dasukayi da boka ta karshe lokacin dataje karbar maganin mallakar Alh........... πŸ‘Ή Ina me tambatar maki da duk lokacin da mijinki yasan irin halinki marar kyau, wato asirinki yatonu agurinshi daga ranar zaki haukace. Tace babu damuwa boka bazan taba yarda yasan halin danake ciki ba, inde inada kai ai baxetaba dawowa cikin hankalinshi ba.

😭 Komawa tayi bisa gado tacigaba da kuka, saboda tarasa yanda zatayi tasamu wata hanya dazata temaketa kada Alh yasan halin datake ciki. Seyanzu take danasanin rashin yin kawaye, dayanzu tasan dole tasamu wadda zata kaita gurin wani bokan. Hannu tadaga sama tace ya Allah katemakeni ka rufamun asiri, kada Alh, yasan halin danake ciki.

Zaune suke aOffice din D,P,O bayan sungama kora mashi bayani. Kallon Jidda yayi yace awane hotel yace maki yake? Tace a Hamdala hotel. Kince kina da no shi ko? E gatanan, good, kirawoshi yanzu kinsan de irin kissar dazakiyi mashi yabaki damar zuwa anjima da dare. Shiru tayi tana wasa da wayarta. Saleem yace Yaya Jidda kidan fita daga waje kuyi wayarku nasan kunya kikeji ko? Murmushi tayi tajuya tafita.

D,P,O yace insha Allahu acikin daren nan zeshigo hannu dashi da yaranshi abunma yazo dasauki ai, tunda mayen mata ne.  Wani guri Jidda tasamu sannan takirashi, yana dagawa tace Jidda ce, washe baki yayi yace Jidda kamar kinsan kenake tunani wlh, tundazu nake jiran kiranki, gashi banda no dinki naso inkiraki ince anjima kidawo bazan iya hakurin gobe ba.

Murmushin mugunta tayi tace kamar kasan abinda nakira infada maka kenan, nima tunda nadawo gida nake tunaninka, da na hakura se goben amma naji nakasa shiyasa nace bara inkiraka insheda maka anjima zanzo. Kara washe baki yayi yace kai amma naji dadi, gaskiya kinada kyauta me tsoka sbd wannan albishir din da kikamun. Tace shikenan nagode, karfe nawa zanzo? Yace ni wlh koyanzu ma kitaho dan amatse nake. Tace a,a kaide kawai kayi mana babban tanadi anjima karfe 8 zanzo ana ma zan kwana. Dariya yayi yace kai amma nagode, kinsan dama gobe ina da abokiyar kwana, yau semu kwana tare. Tace yauwa ni namanta room no, ok room 102 dakinzo kawai ki kirani. Sallama tayi mashi tana me hararar wayar.

Tana shiga tafadi masu yanda sukayi dashi, sosai sukayi farin ciki. D,P,O yace yauwa zansa yarana suzama cikin shiri anjima semu tafi. Godiya sukayi mashi. Sannan suka tafi. Ahanya Sameer yakira Alh, yafada mashi duk yanda sukayi, yaji dadi sosai yace Allah yakaimu daren.

Jungle ne yashiga dakin Figo, yana shiga Figo yayi saurin zuge jakar kudin daya daga, yamaidata, Jungle ya washe baki yace Oga ko kudin kake kara kirgawa? Ya daure fuska yace a,a wani abu nadauka abayan jakar. Zama yayi yace wlh Oga dama zuwa nayi infada maka ko cikin kudin nan zaka dan bamu wani abu munaso mudan shiga gari muyo siyayya.

Wani irin kallo Figo yayi mashi, yakara hade rai yace, kaga malam sauraramun, tunda mukazo kaga nadauki kudin nan nayi amfanin kaina dasu? Kuma duk abubuwan da kukeci ai acikin kudin ake maku, shine yanzu zasu turoka, kai me baki kazo ka amsar maku kudi ko? To babu wanda zanba ko sisi harsemun gama abinda yakawomu sannan aduba abinda yayi saura se abama kowa kasonshi. Sbd haka katashi kabani guri, kuma kafada masu gobe,  akwai aikin dazan turaku kuzama cikin shiri. Tashi Jungle yayi ranshi abace yafita. Figo yace ashema wahalar danakeyi abanza indauki kudi inbaku.

Baba mairo tace kai duniya, lallai idan baka mutu ba, zakaga abubuwan mamaki dayawa, wai wannan tabewa dame tayi kama ace Kawu mahaifinka yake nemanka, ada yaso yanemi mamanka yanzu kuma yadawo gurin 'Ya. Sameer yace wlh kuwa Baba, nima kaina abun yana damuna, shiyasa ana kamasu baza,a bata lokaci ba, za,a turasu kotu. Saleem yace wlh da za,a barni da dukansu kashe su zanyi. Umman Sameer tace a,a ka kyalesu shari,a ma ta ishesu. Allah de yabaku ikon kamasu. 

Kawun Sameer yace duniyace yanzu babu gaskiya, shiyasa komai ya lalace mana, tunda har aka iya samun Uban da yayi zina da yarshi babu abinda baza,a iya samu ba, mude mudage da addu,a akan yayanmu. Allah yakara tsaremu baki daya. Suka ce ameen.

Jungle yace wlh wannan karon hakurina yazo karshe, kutumar....., yama gama raina mana wayau, dazu fa inajinshi zanshiga dakin naji yana tare da mace, sena tsaya kusan dubu 100 yabata, kuma acikin kudinne. Shine muda mukasha wahala baze bamu ba, ti wlh sede kowa yarasa, amma bazan barmashi kudin ba. Suduka sukace ai dama Jungle kaine kake hanamu, da tuni mun gama mashi aiki, dammu munfison kazama Oga da wancan tsohon maci amana ne, mukam babu wanda yataba cin amanar wani nashi, wama yasani ko abinda yayi ma dan yayanshi ne alhakin yake binshi shiyasa kome muka samu baya zama, amma shekarar mu nawa muna fashi ace haryanzu ko yar mota babu wanda ya mallaka.

Kana ganin wadda muka siya akayi hadari da ita, tundaga ita bamu kara samun wata ba, sede musami kudi shikuma yabama mata. Jungle yace ka kyaleshi kawai wlh shima tashi tazo karshe, ayau zamuyi mashi abinda yayima yaron yayanshi. Ayau zesan zafin cin amana, kuma mu dauke kudin muyi tafiyarmu, babu wani gidan dazamuje, dama can rashin tausayi ne irin nashi amma ace wai diyar danka ita zaka nema saboda yana dan akuya. Kuzama cikin shiri, karfe 8 zamu dirar mashi, kuma ayau zamu bar garina nan.

Da misalin karfe 7: 30 D,P,O yagama tara yaranshi yayi masu bayanin komai, su Sameer kawai suke jira, basu dade ba, segasu sunzo hada Alh, da Jidda, bayan sun gama gaisawa yayi masu bayanin yanda suka shirya komai. Alh, yace amma kasan dole semun fara samun Manager na hotel din sbd aka ida bekamata police su shiga gurin mutum babu izininshi ba. D,P,O yace wannan Alh,  ba matsala bace, nasan manager din damunje se yaran su tsaya awaje mufara samunshi, nasan baze bamu matsala ba. Tashi sukayi kowa yashiga motarshi suka nufi Hamdala Hotel.

Sede ince Allah yabada sa,a.
Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525268
[7/13, 11:54 AM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 145..... 150

Kwance yake daga shi se kajeran wando, wayarshi yadaga yakira Jidda, bugu 2 tadaga, Haba yan matana naga har 8 takusa amma najiki shiru kada de kicemun kinfasa. A'a ban fasa ba, ina hanya. Toshikenan sekinso.

Turo kofar dakin da akayi ne tasashi saurin kallon kofar. Jungle lafiyade zaku shigomun daki haka? Abinci ne, nasa ankawo maku, idan kuma aikin danace zansaku ne, bayau bane se gobe. Wai lafiya inata maku magana amma kun mani shiru? Hahhhh Oga Jungle yimashi bayani. Oga? Waye kuma wani Oga? Akwai Ogan daya wuceni? 

Ada ba, amma yanzu Jungle muka sani da Oga. Jungle wai meye haka kamun magana mana. Kafa yasa yataka saman gadon da Figo yake kwance yayi, sannan yaciro sigari daya daga cikinsu yayi saurin kunna mashi ita. Seda yazuketa ya fesa mashi hayakin sannan yamikama na bayanshi hannu, wata sabuwar wuka mesheki yadora mashi ahannu.

Ganin wannan wuka bakaramin tsoratar da Figo yayi ba, lokaci guda yatashi zaune yace haba Jungle kasan fa bama irin wannan wasan, daga magana kuma meyako afito da wuka? Murmushi Jungle yayi yace aikai ba abokin wasa na bane bare inyi wasa da kai, kawai munzo muyi maka abinda kayima dan uwanka ne.

Zufa ce tafara keto mashi tako ina, yace dan Allah kuyi hkr haba jama'a yau shekararmu nawa muna tare amma ace rana daya kuzo mani da wannan magana. Idan ma matsayina kakeso wlh yanzu zan sauka inbaka, Jungle yace a,a kawai mungaji da tafiya da kaine, kuma ashekarunka yakamata ace kaima kana kabarinka yanzu kasamu ka kwanta kahuta.

Dariya suka sa, Jungle yace ina jakar kudinan take? Da hannu yayi mashi nuni, dan bakinsa yakasa magana, daukota yayi ya bude. Lallai kam kaci kudi dayawa, to bara kaji wlh kaci rabonka, mikama nakusa dashi yayi yace aje mana ita, yanzu zamu bar garinma. 

Su Sameer suna zuwa bakin hotel din sauran yan sandan suka tsaya daga waje, su D,P,O da Alh, dasu Sameer ne suka shiga ciki, tambaya sukayi ko manager yana nan, akace yana ciki, kaitsaye suka nufi office dinshi. Bayan sungama gaisawa anan D,P,O yayi mashi bayani. Cike da tashin hankali manager yace ikon Allah, wlh bansan dasu a hotel din nan ba. D,P,O yace kada kadamu, kasan ba'a gane mugu afuska, mugodema Allah daya tona asirinsu ma. Manager yace amma gsky naji dadi, kuma nagode. Awane room kukace suke?102, Ok babu damuwa zaku iya zuwa. Godiya sukayi mashi suka fita.

Kafa Jungle yasa yatake cikin Figo, sunsa kyalle sun kulle mashi baki, hawaye kawai suke fita a idonshi. Hannu yahada alamun suyi hakuri. Wani yace Jungle muna bata lokaci fa, kawai aikata mashi shima. Yauwa abokina yama wannan AYAR danaji wani malami yana fadama wasu? Wace kenan? Kaini larabcin ne yakemun wahala, abinda kayi za,ayi maka ko? E e hakane, nima namanta Larabcin. Kuka sosai Figo yakeyi sede babu sauti.

Wuyanshi Jungle yakama babu tausayi yasa wuka yayi mashi yankan rago, jini yafara zuba, dede lokacin wayarshi tafara kara, daukarta Jungle yayi yace Hahhhhh mace ce, kashewa yayi yace kawai muware.

Suna murda kofar suma su Sameer suna tsaye, saurin komawa ciki sukayi, nan D,P,O yayi ma sauran yan sandan waya yace sushigo, Rarraba idanu su Jungle suka fara zarowa. Kwance suka sami Figo acikin jini, nan sukayima manager waya, shima yazo, bed sheet sukasa suka rufeshi.

Jidda kuwa kasa shiga dakin tayi haka tajuya takoma cikin motarsu, se kuka takeyi tana kara danasanin irin rayuwar datayi. Cikin lokaci kankani aka tasa keyarsu aka nufi station dasu, shikuma Figo aka nufi asibiti dashi, gaba daya mutanen Hotel din mamaki sukeyi kowa yana Allah wadai da halinsu.

Gaba dayansu zaune suke a babban falon dayake kusa da office din D,P,O sukuma su Jungle suna tsugunne, D,P,O ya kallesu yace banason mubata lokaci, kunsande munkamaku dumu dumu acikin laifi ko? Dan haka banaso kubama kanku wahala muma kubamu, kai, yanuna Jungle, inaso tsakaninka da Allah kayi mana bayanin abinda yakawo garin nan, da kuma bayani akan wanda kuka kashe.

Jungle yace tabbas yau nasan asirinmu yagama tonuwa, saboda haka bazan tsaya batama kaina lokaci ba, nine nan nakashe shi, kuma tare muke dashi shinema Oganmu............. Anan Jungle yafada masu komai da Figo yayi ma Baban Falak, sannan yafada masu yanda akayi suka san inda Falak take, da kudin dasuka samu, har yanda akayi sukaje gidan Alh, da abinda Zarah tayi. Kuma yasheda masu ita tabada kudi da hotonsu akaisu gurin boka.

Nan take Alh, yaji wata zufa tana fito mashi. Jungle yace muma yaci amanarmu shiyasa muka kashe shi, kuma ashirye muke damu amshi duk wani hukunci daza ayi mana. Kowa agurin seda yayi mamakin irin halin rashin tausayi na Figo. D,P,O yace to Alh, kunje de abinda yafaru, dan haka bazamu bata lokaci ba zamuturasu kotu, wannan kuma tunda yarasu, kawai zamuje ayardashi. Wadannan kudi kuma Alh, Allah ne yamaido maka da abunka, dannasan nakane, babu ta inda matarka zata samesu haka, amma zaka iya kaimata seta fada maka inda tasamesu. Sauran hukunci kuma yana gurinka, sede muce Allah ya kyauta.

Gabadaya Alh, kunya takamashi gashi agaban sirikanshi har 2 duka sunji bakin hali irin na matarshi, nan take yai tsanarta tashiga zuciyarshi, fita yayi batare dayace komai ba, yanufi motarshi yanufi gida zuciyarshi tana zafi.

Sameer da Saleem sukayima D,P,O godiya yabasu jakar kudin sukatafi, amota suka sami Jidda se kuka takeyi, Saleem yace dan Allah yaya Jidda kukan nan ya isa haka, keme yayi zafi maganinshi Allah. Sameer yace zakija ma kanki ciwo, kiyi hakuri hakanan. Tace haba Saleem, yanzu idan Dady yaji abinda na aikata nasan kasheni kawai zeyi, gashi zamu hada mashi zafi 2, dole yanzu yasan abubuwan da Ummi ta aikata, ina zesa kanshi? Wannan tashin hankali dame yayi kama? Kaiconmu, Dady beyi sa'ar mata da diya ba, gashi yarinyar dana raina na tsana yanzu itace zata zama abun alfahari agurin Dadynmu bani ba. Jalila kam taji dadinta dabata bari shedan yayi mata hudubar banza ba. Suduka seda sukaji tausayinta. Sameer yase ya isa haka......

Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga Alh, ne yake kiranshi yana dagawa yaji muryarshi tana rawa, yace hello, Alh, yace yauwa Sameer kadauko Falak da Kawunka, kuduka de kutaho gidana inason ganinku, yace to.
    Sameer yace Saleem muce gidanmu tunda mota ta tana can se indauketa Alh yace mutaho dasu Umma , Falak da Kawu. Jidda tace innalillahi Wa inna ilaihir raji'un. Shikenan watan tonan asirinmu yakama😭😭😭.

Urs, 
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/14, 3:00 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ»AGOLAH!!! Nah 
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)

Page 150.....155

Hannu bibiyu Alh yasa yadafe kanshi, gabadaya jiyake duniyar tamashi zafi, wani abu ya tsaya mashi a makoshi, wanda daze samu yawuce dayafi jin dadi. Kuka yakeso yayi amma sam hawayen sunki zuwa, tabbas kuka ma rahamane.

Zarah data shigo falo tace a,a Alh yaushe kashigo banji shigowarka ba? Shiru yayi bece komai, dan yanda yakeji idan yabude baki komai ze iya fada mata. Zama tayi kusa tashi tace magana fa nakeyi amma kayi shiru ka kyaleni. Ko baka da lfy? Wani ne ya mutu? Duk tambyr datake mashi hakan besa yadaga kai ya kalleta ba. Cike da masifa tace wai Alh, mekake nufi......

Sallamar da akayi ne, yasata hadiye sauran masifarta. Juyawa tayi tana kallon kofa jin sallamar bata mutum daya bace, baki ta saki ganin mutanen dasuke shigowa. Mamakinta be karuba seda taga Baba Mairo tashigo gata tayi kyau cikin shiga me kyau.

Samun guri sukayi gaba dayansu suka zauna, yaran kuma suka zauna akasa, haryanzu kan Alh aduke yake, guri Zarah tasamu tazauna, gaba daya jikinta yayi sanyi. Wata irin zufa tafara keto mata. Baba Mairo tace Alh ina wuni.

Dago kai yayi cike da mamakin ganinta, ahankali yace Baba Mairo. Tace na,am, dama kina garin nan? Murmushi tayi tace wlh kuwa Alh. Gaisawa sukayi dasu Kawu, Alh ya kalli Jidda wadda taketa kuka har idanuwanta sun kumbura saboda kuka. Yace Mamana lafiya kike kuka?

Kara sakin wani kukan tayi ta tashi tamatso kusa dashi tazube bisa guiwowinta, hankalinshi dana Zarah yatashi ganin irin kukan datakeyi. Jalila da Falak suma duk kuka sukeyi dan sun san abinda Jidda takeyima kuka. Dago kai tayi tace Dady dan Allah kayi hakuri kayafemun, tabbas banzamo diya tagari ba, na cuceka na cuci kaina.

Nasan Allah baze taba yafemun ba idan har baka yafemun ba. Nayi dacen Mahaifi nagari amma rashin samun Uwa tagari yasani nima nazama wadda bata gari ba. Alh, yace Mamana wai mekike fada haka ne? Zarah kuwa da cikinta yafara yamutsawa jitake kamar ta nutse dan kunya, agaban sirikinta Jidda take fada mata wannan maganar, jitayi kamar tashakota.

Alh yace ya isa haka mamana, kidena kuka kifadamun wane irin laifi kikamun haka. Zarah tayi saurin fadin a,a Alh, kabarta tashiga ciki tasamu ta kwanta tayi bacci ta huta kasan batada lafiya. Jidda tace, a,a Ummi ya isa haka, kibarni nafadi abinda aka dade ana boyewa agidan nan, garake Ummi kinada lafiyar dazaki iya tuba zuwa ga Allah, nifa? Ina cikin cuta, wadda ko ayanzu Allah ze iya amsar raina.

Tundaga auran Hajjo da fara shigarta cikin halin banza, da abunda Zarah dasu Asabe sukayima Hajjo da Ameer, harsukayi sanadiyar mutuwarsu, dazuwanta London, da irin hudubar da Zarah takeyi mata, zuwa auren datayima Falak da Sameer, da yanda tabama su Asabe kudi, zuwa yanda Zarah ta temaka ma su Figo har cutar datake dauke da ita seda Jidda tafada masu. Gaba daya falon yayi shiru, kukan Jidda, Jalila da Falak kawai akeji.

Zarah kuwa zama tayi kasa kamar meshirin hawa bori, takasa kuka kuma takasa magana, Alh, kawai ta kurama Ido, hatta da Kawun Sameer seda yafitar ma Jidda da hawaye, su Baba Mairo da Umman Sameer suma Kuka, kawai sukeyi. Sameer da Saleem da dama sun san da labarin amma jin sauran labarin seda yasasu kuka.

Alh da haryanzu yarasa gane wai mafarki yakeyi ko gaske gashi haryanzu hawaye sunkasa zuba a idonshi, zuciyarshi jiyake kamar ansamata wani katon dutse. Tabbas daza,a gwada jininshi babu abinda zesa aga be hau ba.

Zarah yakalla da idanunshi dasuka juye tamkar garwashi, kallonta kawai yake amma yakasa magana, Zunbur Zarah ta mike tace a,a wlh kadena kallona Alh, ka tsaya nida kaina zanyi maka bayanin duk abinda nayi, kai tafara sosawa, da jikinta, can kuma tafashe da dariya, tace.

Yo aike Jidda bakima san komai ba,,,,,, nan itama tashiga fada masu irin abubuwan datayi, komai seda tafada, tanayi tana dariya tace Mairo aike baki iya munafunci bama, gashinan kina ganin AGOLAH hada ciki, ai wlh rantsuwa nayi senaga bayanta. Hauka de tuburan Zarah tafarayi, kowa salati yakeyi yana kallon ikon Allah.

Kawu yace Alh,ai inaganin bekamata abarta haka ba, a kamata ayi mata addu,a Alh daseyanzu yayi magana, yace Malam babu abinda zankara yima wannan azzalumar matar, tsakanina da ita sede alahira. Ta cutar dani, taso tasani inkasa rike amanar marainiyar Allah dana dauki alkawari.

Babu abinda banyi mata ba, amma tarasa abinda zata sakamun dashi se wannan rashin mutuncin da cin amana, tabbas ko hakkin mahaifinta kawai ya isa ya tambayeta, bare kuma na baiwar Allah Hajjo, da karamin yaro wanda ko agurin Allah ba,a bude mashi littafin rubuta lada da zunubi ba. Kai!!! Agaskiya bazan boye maku ba Zarah tacutar dani, Allah shine zemun sakayya, kuma gashi tun aduniya tafara gani, idan da tasamu sa,ata dayanzu nakara zama rakumi da akala. Dan haka ni babu abinda zan mata.

Ke kuma Jidda bazanyi maki baki ba, sbd ba laifinki bane, duk da kema kina da laifi, meyasa Jalila batayi abinda Zarah tasakiba? Yanzu ai kinga karshe da kuma illar bariki ko? Ko ahaka Allah yabarki yahadaki da babban aiki, kuma wannan cuta taki idan har bakisha mata magani ba, zakizamo abin kyama agurin mutane. Abu daya ne zesa nazauna agidan nan, shine auren Jalila, amma iname tabbatar maki ina aurar da ita nima zanbar maku garin, bazan iya zama bakin cikinku yakasheni ba. Tashi yayi yana hada hanya, da kyar yashige dakinshi sbd jirin dayake gani.

Zubewa Jidda tayi agurin tana wani irin kuka me tsuma zuciyar me saurare, Jalila ta matso kusa da ita tariketa itama tana kuka, Falak kuwa jitayi cikinta yawani murda kamar alokacin zata haifi abinda ke ciki, kwantawa tayi tasaki wata irin kara tana kara rike cikinta, dasauri su Baba Mairo dasu Sameer sukayi kanta, jini ne yafara bin kafarta, nan take ta sume.

Cike da tashin hankali Sameer yadauketa Saleem da sauran suna binshi abaya, mota yanufa da ita suna shiga Saleem yaja suka nufi asibiti. Gaba daya hankalin Kawu yagama tashi, su Jalila se kuka sukeyi, Zarah tafito kanta ko dankwali babu, se cizgar gashinta takeyi haka tanufi bakin gate. Jalila tace Kawu kate maka mana......

To nimade hawaye sunma fuskata yawa, bara nadan huta😭😭.

Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/17, 1:54 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
 Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)

Part 155.....160

Suna zuwa asibiti aka ansheta aka nufi Emergency room da ita, Sameer hankalinshi bakaramin tashi yayi ba, yakasa zaune yakasa tsaye, Saleem ne yadafashi yace kayi hkrdan Allah, addu,a yakamata muyi mata.

Sameer yace wlh tsoro nakeji kada murasa abinda ke cikin Falak, Saleem yace insha Allah bazamu rasa shiba. Sunfi minti 30 agurin sannan wani likita yafito suka bi bayanshi zuwa office.

Bayan yagama yan rubutunshi yakallesu, murmushi yayi ganin yanda Sameer yayi kamar meshirin yin kuka, yace to alhamdulillahi, munsamu tsayar da jinin dayake zuba, kuma cikin jikinta befita ba. Sede dole ze kara ko sati biyu akan kwanakinshi.

Wani murmushin farin ciki Sameer yayi yace mungode Dr. Yanzu ya jikin nata? Yace dasauki, ansamata karin ruwa tana bacci, zuwa anjima insha Allah zata tashi, sede kada tarika aikin wahala,kuma arika kwantar mata da hankali, magunguna ya basu wanda zasu siyo mata, amsa sukayi suka mashi godiya suka fita.

Zarah kuwa gaba daya tafitar da kayan jikinta, se jan gashinta takeyi, duk tajima kanta ciwo, Jalila se kuka takeyi tarasa yanda zatayi da ita. Kawun Sameer ne yadauko ruwa akofi yayi addu,a ya watsa mata ajiki, nan take tafadi kasa bacci yadauketa. Kamata Jalila tayi takaita dakinta ta kwantar da ita bisa gado.

Wata doguwar riga tasaka mata da kyar, sannan tarufo maka kofar dan kada tafito, dakin Jidda tanufa, dan tunda aka tafi da Falak asibiti bata kara ganinta ba, kwance tasameta ta rufe da zanin gado, numfashinta yana fita dasauri. 

Dasauri tahau saman gadon ta budeta, jikinta zafi taji sosai tace Yaya Jidda bakida lfy ne? Kai tadaga mata, sauka tayi taje tadauko mata maganinta, ruwa tadauko mata ta kamata tabata maganin, tana gama sha tayi saurin sauka tanufi bandaki tafara amai, seda tagama Jalila ta temaka mata ta gyara jikinta suka fito, bayan ta kwantar da ita takoma ta gyara bandakin.

Zama tayi tana kallon yanda take fitar da numfashinta kamar zebar jikinta. Wasu zafafan hawayene suka sauko mata, kai ta girgiza tana me tausayin kanta, akan irin rayuwar datake fuskantota, ga Ummi ta haukace, ga Jidda akwance. Ahankali tace Yaya Jidda kozaki shirya muje asibiti? Kai ta girgiza tace konaje asibiti babu abinda zasu mani, kawai kibarni haka. Jalila tace bara inje inkira Dady, hannunta Jidda tarike tace,

A,a Jalila, ayanzu babu abinda Dady yakeso kamar natsuwa, ayanzu yana cikin tashin hankali bekamata kije gurinshi ba, dan yanzu ma Allah kadai yasan cikin halin dayake, Jalila tace haka ne, Jidda tayi murmushi tace kiyi hkr Jalila, zamu barki cikin kuncin rayuwa, Allah yakareki daga sharrin dangin miji, tabbas nida Ummi munbar abin fadi aduniya, amma insha Allahu bazaki tozarta ba, nide ina rokon addu,arki akullum.

Jalila tace bakomai Yaya tunda har Allah yajarabceni da wannan rayuwa yasan zan iya dauka, kuma kema zaki samu rayuwa me kyau, fatana kawai kirika shan maaganinki. Ummi kuma insha Allahu zata samu lafiya. Jidda tace hadomun black tea.

Alh, kuwa tunda yashiga daki jiyayi kamar zuciyarshi zata fito waje, har ya kwanta sekuma yayi saurin tashi yanufi bandaki yadauro alwala yazo yadauki Qur'ani yafara karantawa, yadade yana karatu harseda yaji zuciyarshi tayi dadi sannan yatashi yayi raka,a 2 yayita rokon Allah akan yadora mashi duriya da dangana aduk halin daze shiga.

Jin falon yayi shiru ne, yatashi yafito, akofar kitchen yaci karo da Jalila, wani sabon tausayinta yakara kamashi, kasa kallon idonta yayi yace ina su Falak? Ana tafada mashi abinda yafaru, yace to ina Jidda take fa? Tace tana daki ita zankai ma tea ma, ze kara magana yaji wani sabon kuka yazo mashi kawai yajuya yatafi.

Da kallo Jalila tabishi itama tana kuka, dan taga lokacin da hawaye suka taho mashi.

Awaya yakira Sameer ya tambayeshi jikin Falak, Sameer yace dasauki yafada mashi duka abinda likita yafada. Alh, yace toshikenan idan naji dama dama zanshigo.

Zaune Falak take gefenta Baba Mairo da Umman Sameer ce zaune, sesu Sameer da Saleem zaune abisa kujera, Baba mairo tace sannu Falak, inaso ki kara hkr akan wanda kikeyi, Allah yana kallonki baze bari kishiga wani hali ba, inaso kidauki duk abinda yawuce yazama tarihi. Kada kisaka wani abu aranki yazo yadameki.

Ita kuma Zarah kome tayi dan kanta, gashi nan tun aduniya Allah yafara nuna mata ishara, sede abu daya nakeso kisani, ana barin halak kodan kunya, wlh tausayin Jalila nakeyi saboda zata shiga wata irin rayuwa. Kallon Saleem tayi tace dan Allah kada abinda yafaru yasa wani tunani yashiga ranka, nasan kasan komai akan Jalila tunkafin abaka aurenta, inaso kaji tsoron Allah, kuma kamar yanda wannan abu yafaru acikin gida inaso kabarta agida.

Saleem yayi murmushi yace wlh Baba babu abinda yaragu akan son danake ma Jalila, sema karin tausayinta danaji, kuma insha Allah babu wanda zeji wannan maganar abakina. 

Sameer yace bara muje muyi sallah damun dawo zamu tafi gida dan banason ta kwana anan, Ummanshi tace a,a idan bataji sauki ba, babu inda zataje, Baba Mairo tace a,a tunda de komai lfy ai gara mutafi gida zefi, nima banason zaman asibitin.

Bayan mintuna 30 Zarah tafarka daga baccin da takeyi cike da firgici, sauka tayi daga kan gadon tanufi hanyar fita, sede taji kofar arufe,komawa tayi tacigaba da daukar duk wasu kayan bisa dressing mirror dinta tana fasawa, hatta da madubin seda tasa hannunta tafasa shi, duk tajima kanta ciwo, jawo sif dinta tayi cikin tsautsayi tafado mata akafarta ta dama, tundaga kwaurinta, wata irin kara tasaki wadda har megadi seda yaji.

Kasa tafadi, tana ihu, gashi takasa cire kafar daga karkashin sif din. Megadi da driver suka shigo suna sallama, Jalila tafito itama lokacin taji ihun Zarah, suka ce lfy? Wlh nima bansani ba, nade barta tana bacci sede naji ihunta, bayanta sukabi.

Tana bude kofar tasaki salati suduka sukabi bayanta, jini ne kwance akasa, Zahar hartayi shiru sbd azaba, dasauri Jalila takarasa gurinta tana kuka, megadi da driver sukayi saurin daga sif din, ai nan sukaga kafarta ta datsa biyu, kamar ansa gatari an fasa, jikin kaurinta shima harkashin ana gani, kafar se reto takeyi.

Jalila tafita tanufi dakin Dadynsu tana kuka, yana ganinta yace Jalila lafiya de? Cikin kuka tafada mashi abinda yafaru, sosai yaji tausayin Jalila, haryayi niyar kyaleta sekuma yatuna mahaifiyarsu ce, yace shikenan kije kicema driver sukamata sukaita mota inazuwa.

Amotarshi yashiga yace suwauce asibitin, Jalila tana rungume da ita, Zarah tayi shiru se hawaye take fitarwa, suna zuwa asibiti aka karbeta aka nufi accident room da ita, ana akayi mata allura tayi bacci.

Likitan yanufi Alh, yace suje office. Bayan sunzauna yace agaskiya Alh, sede ayanke kafar matarka, sbd kashi kafar yariga daya rabe 2, fata ce kawai tarike sauran rabin kafar, amma shi ciwon kaurin za,a iya mata dressing sbd kashin tsagewa ne kawai yayi. Kuma naga kamar tana da matsalar tabin hankali ko? Alh, yace Dr, inaso kuyi duk abinda zaku iya wanda yadace, babu ruwanka da matsalar haukanta, ita tajama kanta, yanzu haka ba matata bace kawai darajar 'Ya'Yanta zataci. So banason yawan tmby. Dr yamika mashi takarda yace yasa hannu, Alh, yace bara inkira diyarta taji da bakinta, sbd yanzu kome zanyi za,aga kamar nayi da wata manufa ne.

Fita yayi domin yakira Jalila.

Urs,
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[7/18, 1:50 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 160.....165

Shiru Jalila tayi tana hawaye jin bayanin da Dadynsu yayi mata. Tace shikenan Dady muje insaka hannu. Shiga sukayi Dr, ya mika mata takardar tasaka hannu. Anan Alh, yabiya duka kudin aikin dana magani. Dr, yace zaku iya tafiya dan aikin zedauki lokaci, Alh, yace to mungode, muje Jalila.

Zaune suke afalo Kawu yagama yi masu bayanin abinda Zarah tayi bayan tafiyarsu. Falak tace wlh tausayin Jalila nakeyi, Allah de yabata lfy. Baba Mairo tace ita tajama kanta, kuma gashi duniya tana koya mata hankali, sbd alhaki nawa Zarah tadauka akanta, harna mahaifinta fa, kwata kwata tamanta dashi arayuwarta.
Nide yanzu Malam abu daya nakeso aduba akalli mutunci irin na wannan yarinya Jalila, atemaka ma Zarah da addu,a tasamu lafiya.

Kawu yace bakomai, bawani abu bane yake dawainiya da ita ba, se aljanu, kuma sihirin datayima wasu ne, yanzu aljanun suka dawo kanta. Bakomai insha Allahu zamuyi bakin kokarinmu, babu abinda ya gagari Allah. 

Saleem yacema Sameer bara inzo inwuce, Falak Allah yakara sauki, sallama yayi masu suka fita shida Sameer. Saleem yace zanje gida idan na huta zanje indubo Jalila dan tundazu nake kiran wayarta bata dauka ba, nasan tana cikin damuwa. Sameer yace shikenan kayi kokarin kwantar mata da hankali plsssss.

Jalila tana shiga daki tasamu Jidda kwance cikin amai, gashi ta bata jikinta da zawo, cike da tashin hankali ta juya tanufi gurin Dadynsu. Atare suka shigo dakin. Kai Alh, yadafe ganin halin datake ciki. Allahumma Ajirni fi musibatihi haza, Wa aklifini khairan minha.

Itace addu,ar da yarikayi azuciyar shi, yace Jalila kiyi hkr kitemaka mata ta gyara jikinta semutafi asibiti, kada kisa damuwa azuciyarki, kirika addu,a zaki samu sauki. Fita yayi yajirasu afalo. Zama yayi yadafe kanshi, yarasa inda zesa kanshi.

Waya yadauko yakira kanin babanshi yana dauka kawai yasa mashi kuka, se alokacin kukan dayake so yayi yazo mashi jin kamar muryar babanshi. Cike da tashin hankali yace Abba lfyrka meyake faruwa kake kuka? Shiru yayi yacigaba da kukanshi, Kawunshi yace shikenan ya isa haka, koma menene tunda ina gari ganinan zuwa.

Kashe wayar yayi ya kwanta bisa kujera yacigaba da kuka sosai, seda yayi me isarshi sannan yaji dadi azuciyarshi, duk wani nauyi dayakeji ada yanzu yaji sauki, tashi yayi yashiga bandaki yayi wanka, yashirya yasamu su Jalila sun fito suka tafi.

Suna zuwa yanda likita yaga jikin Jidda yace dole abata gado, nan aka kaita wani private room sbd yasan matsalarta. Ruwa aka samata da allurai, nan take bacci yadauketa. Alh, yace Jalila muje gida, tace to.

Suna zuwa yasata tayi masu girki yace tazubo yasata tazauna, atare suka ci abincin yana lallashinta, shima daurewa kawai yakeyi, ahaka suka gama cin abincin Jalila ta kwashe kayan, Alh, yace yauwa idan kinyi wanka semutafi ko, dan dare yayi, tace to. 
    Bayan tagama tadauki abincin Umminsu dana Jidda kasancewar asibiti daya suke, suka tafi.
Sadda sukaje har angama ma Zarah aikin ankaita dakin hutu, ana Dr, yafada mashi komai yayi dede amma dole akula da ita sosai sbd karta fama kafar. Godiya yayi mashi yanufi dakin Jidda.

Zaune yasameta Jalila tana bata tea, yace sannu Mamana, kallonshi tayi idonta cike da kwalla, tace yauwa Dady. Zama yayi, Jalila tace Dady ya Ummin take? Yace bacci takeyi kuma komai lafiya angama asa,a zata iya kai gobe bata farka ba, sbd haka kizauna agurun Jidda ku kwana tare. Tace to Dady, yace bara inzo intafi dare yayi kuma Kawu yamun waya yana jirana agida. Sallama yayi masu yakawo kudi yabama Jalila yafita.

Bayan sungama gaisawa Kawu ya kalleshi yace Abba lafiya kuwa nazo gida kuduka bakwanan, gashi kamun waya kana kuka, seyanzu dana ganka nakara tabbatar da babu lafiya dan ayanayin dana ganka nasan bacikin kwanciyar hankali kake ba. Kai Alh ya girgiza yace wlh kawu wani iftila,i ne yasameni alokaci guda, shiyasa narasa yanda zanyi da rai na.............   Anan ya kwashe komai yafada mashi, babu abinda yaboye mashi har labarin Jidda.

Innalillahi Wa inna Ilaihirraji'un. Shine abinda Kawu yaketa fada. Yace lallai Abba ka hadu da wata irin jarabawa wadda bakowa bane ze iya irin wannan dauriya dakayi. Kada kadamu insha Allahu komai ze zama dede, kuma kada kasa abun aranka harya haifar maka da wata matsala, bara inzo intafi dare yayi, kome kenan goben zan sameku asibitin. Yace nagode Kawu, sallama yayi mashi yarakashi bayan yatafi yadawo cikin gida.

Urs,

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/19, 3:55 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ (H,O,N,A)

Part 165.....170

Washe gari tunda asuba Zarah tacika asibitin da ihu, sbd tafarka kuma babu kowa akusa da ita, gashi allurar da akayi mata tasaketa, hatta daurin da aka yimata na kauri tafara cireshi, hauka sosai takeyi.

Duk da zafin datakeji hakan besa ta nutsu ba, abunka da hauka, dakin duk ya baci da jini. Cikin sauri aka shigo dakin, wasu nurse ne guda 2 mata, duk yanda suka so riketa abun ya gagara, nema take taji masu ciwo, daya ce tafita domin kira maza.

Atare suka shigo da wani Dr, tare da wasu maza cleaners 2, kamata sukayi da karfi suka zaunar da ita, Dr, yaduba file dinta, anan yace ma dayar nurse din takawo mashi allura, ko minti 5 ba,ayi ba takawo, amsa yayi tare da zuba ruwan yayi mata, cikin mintuna kadan bacci yadauketa.

Dr, yace wannan matar akwai hauka ajikinta, dama kuma jiya Dr, yafada mani kuma dole se ansamu wadan da zasu rika kula da ita sosai idan ba haka ba, wannan kafar zata bamu matsala, yanzu dole kusake mata wani dressing din. Nurse suka ce to. Yace bara na kira mijinta awaya na fada mashi tafarka dan me kula da ita yazo.

Jalila tace sannu Yaya Jidda kitashi in hada maki ko black tea ne kisha kinga tunjiya kike amai, kalli yanda kika koma acikin kwana 1, dan Allah kidaure kici abinci kisha magani kozaki samu sauki, wlh bazan iya daurema wannan rayuwar datake fuskanto ni ba, kinga Ummi tana can kwance kema kuma kice bazakisha magani ba, ai abun seyayi mani yawa, tunda Dady babu ruwanshi da Ummi.

Murmushin karfin hali Jidda tayi tace wlh Jalila nikaina ayanzu inaso in rayu kodan intayaki jinyar Ummi, inaso inrayu kodan nima nayi aure nasamu yarana, inaso inrayu kodan insamu damar neman gafara agurin Ubangijina. Amma nasan namakaro, domin sama tayima yaro nisa, nasan kwanaki na kadan suka ragemun, fatana Allah yakarbi tubata kafin in mutu. Kuka duka suka saka, babu me lallashin wani.

Jidda tace kinyima Baba na Zariya waya kuwa? Jalila tace na masa, yace yau dasafe zetaho. Kai cona, shima wannan bawan Allah ban daukeshi da daraja ba, na dauki hudubar Asabe, wadda itace tayi sanadiyar fadawar Ummin mu cikin wannan halin, duk da hada laifinta amma Asabe ce Babbar me laifi. Jalila tace bakomai insha Allah Ummi zata samu sauki.

Jidda tace gashi yau saura kwana 5 bikinki Jalila kuma ga halin damuke ciki, tabbas mun saka rayuwarki cikin takura. Jalila tace wlh niyanzu auren yafuta arai na, kuma koyanzu baza,a daura ba, harse kunsami lafiya. Jidda tace wlh kada ma kifara, aure kamar anyishi angama ne, bakison inga bikinki kafi Allah yadauki raina?😭, Shiru Jidda tayi tana kuka, Jalila takara matsowa kusa da ita tace Yaya Jidda dan Allah kibar maganar haka nan, kitashi muje kiyi wanka kiyi brush kisha tea, nasan Dady ze kawo mana abinci sekici.

Jikin Falak yayi sauki dayake agidansu Sameer suka kwana hakan yasa gurin karfe 9 suka shirya su duka suka nufi asibiti, dan Sameer yayi waya da Alh, yafada mashi suna asibiti, tafiya suke ahanya, Baba Mairo tace dole ni nazauna agurin Zarah dan nasan babu kowa agurinta, tunda nasan Jalila tana gurin Jidda, Falak tace toni se nazauna agurin Yaya Jidda. Sameer yace babu inda zaki zauna haka nan kawai ki kwaso mana cuta. Umman Sameer tace gsky kam Falak kiyi hkr zaki rika zuwa dubata amma batun kizauna betaso ba, kema haka nan karfin hali kikeyi amma duka yaushe kika warke.

Kawu yace hakane, kiyi hkr idan yaso ke Halima sekiyi masu kara kizauna agurin Jiddan, kema Allah zebaki lada, amma wlh nima ina tausayin Alh, dole kowaye Allah ya jarabta da irin wannan abu yashiga tashin hankali, kuma sbd shi da diyarshi zan nema mata magani, amma da munbarta duniya ta koya mata hnkli, duk da ayanzu ma tafara gane kuranta, tunda ance anyanke mata kafa. Umman Sameer tace ai bakomai yanzu suma sunzama yan uwanmu. Allah yakara basu lfy.

Malam Garba mahaifin Zarah da Alh, ne suka shigo asibitin, kasancewar ya iskeshi agida shine suka taho tare. Mal. Garba yace dan Allah Alh, kayi hkr da irin abinda wannan yarinya tayi maka. Babu irin yanda banyi da ita ba, amma bataji magana taba, tabbas babu abinda zance tsakanina da Asabe sede ince Allah ya isa, duk da kacemun ankashe su, amma bazan yafe mata ba, ita da kawarta, sun cuceni, gashi seda cutar takai harzuwa diyata, duk da itama da laifinta amma Asabe babbar annobace agidana.

Alh, yace bakomai Baba, Allah yakara basu lfy. Yace ameen, kuma hukuncin daka dauka akanta kayi dede, nima dande kawai zuciyar Imani amma da ko zuwa bazanyi ba, to Jalila tayi tamun kuka, kuma ina son Jalila, shiyasa nace zanzo sbd ita. Amma tabbas idan ta warke sede taje wani gurin tayi haukanta amma ba gidana ba. Alh, yace kayi hkr muje de muga jinkin nasu.

Suna shiga suka wuce Office, anan Dr, yayi masu bayani. Alh yayi shiru dan yana kunyar mal. Garba, ganin yayi shiru Babanta yace to ai ita tasani, kuyi mata abunda zaku iya kawai ku sallameta. Alh yace a,a Baba baza,ayi haka ba, Dr, inaganin abinda ze faru zansamu wani malami zamuyi maganar dashi dan gsky haukanta bana asibiti bane, kome kenan zanzo mukara magana. Dr, yace gsky dayafi, dan tana cikin wani hali, kome tayi kubarta da halinta amma ceton rai zakuyi kuma kamar jihadi ne, koba komai ai Uwar yaranka ce, kai kuma Baba ai diyarka ce, kasan da mahaifiyarta tana nan kome zata zama bazata iya barma duniya ita ba. Jikin Baba yayi sanyi yace haka ne, likita, kuma nagode da tunatarwar dakamun. Allah yamana jagora. Fita sukayi suka nufi dakin Jidda.

Adakin suka sami su Falak harsunzo, bayan sungama gaisawa, Alh, yace Jalila yajikin nata? Tace to Dady dasauki za,a ce, amma kome taci amai takeyi, yakalli Jidda gaba daya tausayinta yakara kamashi yace sannu Mamana, tace yauwa Dady, kidaure kirika cin abinci maganin baze maki amfani ba, idan baki cin abinci. Kuma banaso kirika saka damuwa akanki, mutane nawa suke dauke da irin cutarki gasunan muna hudda dasu wasu ma harsun fimu lfy da kyan fata, babu wanda ze kallesu yace suna da wata cuta. Meyasa suka zama haka? Sbd suna shan maganinsu, kuma suna cin abinci me kyau, dan haka kicire komai aranki, nide nayafe maki, insha Allahu zaki samu lfy.

Baba Mairo tace yanzu Alh, yajikin Zarah? Yace to banje ma naganta ba, dan Dr, yace mun sunyi mata allurar bacci, dan da asuba data tashi haukan yadawo sabo, duk tajima kanta ciwo, kuma ta fama ciwon kafarta, shiyasa yace dole asamu wanda zerika kula da ita.

Baba Mairo tace bakomai Alh, kome zamuyi, zamuyi ne, dan Allah da kai da kuma yaranta. Nizan zauna agurinta ita kuma Halima zata zauna agurin Jidda, tunda Jalila tayi yarinta ace tayi jinya.  Alh, yace to mungode sosai Allah yasa da alkhairi. Baba Mairo tace, ammade bikinta dagawa za,ayi ko? Alh, yace ina tunanin haka, duk da nariga dana gama gayyatar abokanaina, amma tunda lalura ta gifto dole adaga.

Mal. Garba yace a,a baza,ayi haka ba, wannan yarinya ta dade ana shiga hakkinta, acikinsu babu wanda tacema yashiga rayuwar da yayi, dan haka saboda su baza,a daga bikinta ba, acikinmu waye yasan lokacin dazasu warke? To kuma kawai se ashiga hakkin baiwar Allah ace sesun warke za,ayi bikinta. Shima mijin ai anshiga hakkinshi, yagama fada ma kowa nashi, ai  bikin magaji baya hana na magajiya, dan haka abar bikin nan da kwana 5 kmar yanda akasa, Allah yabasu lfy.

Alh, yace shikenan dama gani nayi kamar Jalilan bataso ayi acikin wannan halin shiyasa zan daga, amma shikenan ke Jalila kiyi hkr, nasan bazakiji dadi ba, ace za,ayi bikinki a irin wannan yanayin komai zezo karshe, ranar asabar za,a daura aurenki kuma aranar za,a kaiki. Kuka Jalila tasaka ta tashi tafita, seda tabama kowa tausayi adakin.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/20, 11:43 AM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Part 170.....175

Haka suka wuni a asibiti, Falak da Jalila ne, suka koma gida suka yomasu girki, Kawun Sameer kuwa dakin Zarah yaje shida mal, Garba da Alh, anan yafara yimata addu,oi, shiyasa lokacin data farka batayi wani hauka me yawa ba, Baba Mairo tana gefenta ita tarika bata abinci da kyar taci sbd wasan datakeyi.

Lokacin da Saleem yazo shida Sameer bayan yaduba jikin Jidda yakira Jalila suka fita waje, cike da tausayi ya kalleta yace my dear wlh harkin rame. Murmushi tayi tace ba dole ba, yace haka ne, dazu munyi magana da Sameer har nake cemashi koza,a daga bikinmu ne, yace mun a,a Dady yace baza,a daga ba. Jalila tace nima naso adaga amma Baba na Zariya yace a,a.

Saleem yace babu damuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda ze gagara insha Allah, fatanmu de Allah yabasu lfy, tace ameen. Yanzu mekike bukata, nasande bawani abu kikace zakiyi ba ko? Tace hakane, walima ce kawai zamuyi da yan islamiyarmu, yace shikenan idan nabaku dubu 100 yayi ko? Murmushi tayi tace basuyi yawa ba? Harararta yayi yace bansani ba, anfada maki bikin wasa zanyi, wasu ma a party kadai suke kashe abinda yafi haka, seni daza,ayi walima zakice wai sunyi yawa. Tace tonaji maida wukar, Allah yasaka da alkhairi, yace yauwa ko kefa.

Sameer yafadamun duk abinda yafaru jiya, kuma munyi magana da Abbana sede banfada mashi komai ba, kawaide nace ba,a san abinda yasamu Ummi ba, kuma yakira Dadyn ma sunyi magana, yace zeshigo yadubata se Dady yace a,a yabari tunda saura kwana 4 daurin aure seyayi zuwa daya. Kwallan dasuka zubo mata ta goge, tace nagode, bansan dawane baki zanyi maka godiya ba. Yace bakida bakin yimani godiya sbd kinbiyani dakika amince zaki aure ni. Amma inason inrokeki wani abu 1. Wannan yawan kukan da kikeyi yayi yawa, dan Allah kidena, nasan dole ne, amma inaso kiyawaita fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji'un aduk lokacin da kikaji wata damuwa tadameki. Tace shikenan nagode.

Haka suka cigaba da jinyar Zarah da Jidda, jikin Zarah kam ana samun cigaba, amma jikin Jidda ba sauki, duk ta rame tayi baki, idan kaganta bazaka ce Jiddar daka sani bace, haryanzu aljanun jikin Zarah basuyi magana ba, sede haukan dasauki, tana samun sauki aduk lokacin da ake mata addu,a amma idan har bakowa agurinta haka zakaga kafarta tana fitar da wani irin ruwa marar kyau, kuma aranar se ansake wani gyaran dan ta kafarta suke cutar da ita, shiyasa har yanzu kafarta kamar sabon ciwo ne.

Hakan yasa Kawu yace ma Alh, dole zeyima wani abokinshi Babban malami ne, kuma yana da sani sosai akan harkar aljanu, Alh, yace to amma abari bayan biki seyazo.

Kasancewar bawani cikin keanciyar hankali ake ba, hakan yasa Jalila bata samu gyara sosai ba, sede duk da haka Falak tana kawo mata wasu abubuwan sha tana sha, Falak takaita gurin saloon akayi mata, takira wata me kunshi tayi mata, duk da ta rame amma tayi kyau sosai, duk wani shiri da za,ayi na Walima wata kawarta yar ajinsu ta mika ma komai Bilkisu, tare da wata Farida, duk ajinsu daya, malamansu da Sameer sune suka shirya komai, kuna anan makarantarsu za,ayi walimar.

Ana gobe daurin aure ranar juma,a kenan wanda kuma aranar da karfe 4 za,ayi walimar, zaune suke adakin Jidda, tana kishingide tana shan kankana, fuskarta har wasu kuraje sun fara fito mata, kadan kadan tana goge kwallar datake fito mata. Falak tace Yaya Jidda dan Allah kidena wannan kukan, babu ranar dazata zo bakiyi kuka ba. Jidda tace Uhm Falak kenan, nikadai nasan menakeji araina, da jikina. Kamata yayi ace hadani akae wannan hidimar bikinta Jalila, amma sbd son zuciya da biyema rudun duniya kalli yanda nadawo, ina nan kwance za,ayi bikin Jalila, wanda gashi de da raina amma banida ikon halartar bikin, wannan kadai ya isheni ishara.

Kalli Ummi, duk yanda taci buri da bikin nan, amma gashinan son zuciya da rudun duniya itama ya kamata ahannu, har garani nasan me akeyi, amma ita batasan meke faruwa ba, kuma hakan bazesa adaga bikin ba. Lallai mun ishi duk wani me hankali zama abun kwatance. Jalila tana kuka tace Yaya Jidda kiyi hkr Allah yana karbar tubar me tuba, insha Allahu zaki kasance daya daga cikinsu.

Baba Mairo da Umman Sameer ce suka shigo sun dawo daga dakin Zarah sunyi mata wanka, Baba Mairo tace Falak kuzo kutafi kishiryata kinga har 3 tayi, kada ayita jiranku kunsan taro za,ayi sosai bekamata ace ku tsaida mutane ba. Kuma idan kingama kisamu guri kizauna kinsan jikinki yayi nauyi, tace to. Kama Jalila tayi wadda take ta kuka, tace muje, Jalila tace tomuje inga Ummi sannan. Baba Mairo tace kuje taganta seku wuce. Kara kallon Jidda tayi, Allah sarki Jidda kifar da kanta saman cinyarta tayi, tana wani irin kuka me ban tausayi, seda tasaka su kuka. Haka Falak tajata suka nufi dakin Zarah.

Kwance take tana bacci, gaba daya tayi bakikkirin fuskarta kamar an shafa mata bakin tukunya, kafarta meciwo takoma siririya tundaga guiwarta har dungulmin da aka yanke, babu kyan gani, gashi duk tarame, kamar ba ita bace me kiba da jiki me kyau, shiru Jalila tayi tana kallonta, tace Allah yabaki lafiya Ummi. Falak ta kalleta, seta tuna Ummanta, lokacin tana cikin rashin lafiya, zuwa tayi ta taba jikin Zarah, taji babu zafi, kai ta girgiza tace ai dasauki ma tunda ita batajin zafin jikinta. Saurin fita tayi sbd kukan daya taho mata. Jalila tagane me Falak take nufi, duk se tausayinta yakamata, tace kingani ko Ummi, mutanen dakika cuta kika maida banzaye yau gashi sune suke maki rana, 

Yaugashi Falak da kikaso akashe, itace take amatsayin daya kamata ace kece kikemun abinda takemun. Goge idonta tayi tace Allah yasa kina cikin wadanda Allah ze gafarta ma kura kurensu, sede nasan baze yafe maki laifin bayin dakika cuta ba. Saurin fita tayi tajawo kofar tasamu Falak amota suka tafi.

Jalila tayi kyau sosai tasha hijabinta harkasa, haka tazauna, agefenta Falak ce itama tasha hijabinta da katon cikinta, mutane dayawa sun halarci taron, taro yayi taro sosai aka gayyaci mutane dayawa, kasancewar Jalila tanada kokari amakarantar. Bangaren manyan mutane daban, hatta da Mahaifin Saleem seda yazo shida abokananshi sbd suntaho har daurin aure, Saleem da abokananshi suma sun halarci gurin, Sameer kuwa sune manyan malamai, suna ta hidima da mutane, Alh, da Kawunshi da Mal. Garba dasauran abokananshi daya gayyata duk suna zaune acikin rumfa.

Kanshi yadaga yaga irin mutanen dasuka halarcin gurin kawai seyaji kwalla tacika mashi ido, glass dinshi yaciro yasaka, Kawunshi wanda yana kula dashi yace haba Abba, kayi hkr mana kada kabari mutanen dasuke gurin nan su fahimci halin da kake ciki, nasan kana tunanin babu mahaifiyar Jalila agurin nan, da babu ita akwai wani abu daya ragu? Kalli gefen iyaye mata kagani, ga medakina can da sauran yan uwa waye ze iya cewa babu Zarah agurin? Sede wanda yasanta, kuma kowa ai yasan rashin lafiya ko. Alh, yace shikenan kawu nagode.

Haka aka fara bude taro da addu,a sannan aka gabatar da manyan baki, aka kira Jalila domin ta karanta wata sura daga cikin Qur'ani amatsayinta na wadda akema walima, da kyar tafito, seda Falak ta anshi nikaf din wata tabata tasa, sbd tundazu take kuka. Haka tafara karatu cikin dadin murya, sede dakaji muryarta kasan muryar kuka ce, tana cikin karatun tafara kuka, seda ta burge mutane dayawa, sbd sun dauka karatun ne da murna suka sata kuka, wadanda suka san halin datake cike ne kawai suka san dalilin kukanta. Shikanshi Alh, seda yatashi bada sanin kowa ba yanufi cikin motarshi yazauna yarika kuka kamar karamin yaro, seda yaji dadin zuciyarshi sannan yafito, dayake bakin glass yasa babu wanda yake ganin idonshi. Yana zama Kawunshi yagane meyayi, shima kanshi tausayinshi yakeji.

Ganin Jalila tana kuka yasa Sameer yaje ya amshi lasifikar yayi mata godiya duk da shima jikinshi yayi sanyi. Saleem kuwa seda yayi yan kwalla, har abokananshi suna janshi. Gaba daya tausayin Jalila da Sonta suke kara ratsashi.

Haka aka kira Alh, yazo yayi jawabi, dauriya kawai yayi yafito, yana magana shima muryarshi tana rawa, ahaka yasamu yagama, sannan aka cigaba da. Wa,azi. Se karfe 6:00 dede aka tashi, tare da mika ma Jalila kyaututtuka, haka kuma tasamu kyautar kudi daga gurin bakin dasukazo, aka rarraba kayan ciye ciye kowa ya watse.

Adaran ranar su Baba Mairo sukaje suka bada duk wani abinda za,a girka gobe, ita da Hajiya Fatima matar kawaun Alh, dayake anan gidan yace su sauka, sbd itama tasan komai daya faru, ko kayan gara nasiye suka siya sbd lokaci yakure ba,ayi ba, kuma sunje sunyi mata jerenta, dan dama ansayi kayan dakin, sauran abinda ba,a siya ba, na kitchen suka bari se gobe da safe suje su siyo.

Haka suka tsara komai, da sauran yan uwan Alh, dasukazo, abangaran Zarah kam babu wanda yazo se yan uwan Babanta, shima cewa sukayi sbd Jalila da Alh, sukazo dan ita bata yarda suba, amma ko asibitin babu wanda yaleka. Gida kam yacika ba laifi mutane sun taru.

Adaren ranar jikin Jidda yayi tsanani cikin dare tarika suma, haka Umman Sameer da Baba Mairo suke tsaye akanta da sauran nurse, ganin jikin yaki sauki yasa wata nurse tayi ma Dr, waya acikin daren.

Ur's 
NABILA RABI'U ZANGO 
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/20, 4:06 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 175.....180

Se da asuba suka samu jikinta ya dedeta, haka aka samata oxygen har seda numfashinta yadawo dede, duk abinda akeyi su Jalila basu sani ba, dan Baba Mairo tace kada afada masu tunda dare yayi.

Da misalin karfe 6 nasafe Alh, ya iso asibitin anan yakejin abinda yafaru, cike da damuwa yace amma Baba Mairo ai da kunsanar dani, ko dare yayi ai zan iya zuwa, tace hakane Alh, yace sannunku Allah yasaka maku da alkhairinsa, Baba Mairo tace Ameen ai ba komai, duk munzama daya.

Fita yayi yadubo jikin Zarah, tana kwance kamar gawa sbd allurar bacci ake mata idan dare yayi dan kada ta farka tajima kanta ciwo, haryanzu bata farka ba, tausayinta yakara kamashi, yace kaiconki Zarah, kalli yanda kika jama kanki bala,i ana bikin diyarki amma kina kwance cikin hauka, juyawa yayi yafita, yabiya gurin Dr, anan yake kara mashi bayani akan ciwon Jidda. Alh, yace Dr, kode afita da ita waje, ciwonta yana bani tsoro?.

Dr, yace E to hakan ma yana da kyau, amma gsky matsalar Jidda bawani abu bane kawai cutar jikinta ce taci karfin jikinta, kuma da karfi tasamu nasarar karya garkuwar jikinta bawai dan takai lokacin ba, da farko tayi sakaci batazo asibiti dawuri ba, na biyu kuma tafara shan magani tabari. Na ukku kuma yanzu kwata kwata maganin baya yimata amfani ajikinta, sbd kotasha amayar dashi takeyi.

Karin ruwan da ake samata ne, kadai yake amfani ajikinta, kuma babbar matsalar bata cin abinci sosai, kotaci ma baya zama. Wadannan sune matsalar Jidda, kuma duk inda kuka kaita, basuda abinda zasu mata. Alh, yace shikenan Dr, nagode. Dr, yace se hkr Alh, Allah ya jarabceka da lalura, amma idan kayi hkr wata rana komai zewuce. Karfe nawa ne daurin auren? Karfe 2 ne, toshikenan Allah ya kaimu. Sallam yayi mashi yafita.

Da misalin karfe 2 dede na rana dubban mutane suka sheda daurin auran Jalila da Saleem, wanda akayi abisa sadaki dubu 50. Adede lokacin su Jalila da Falak suna asibiti, dan Jalila cewa tayi bazata zauna agida ba, tasan anjima babu wanda zebarta tazo asibiti, zaune take agaban Zarah, se kuka takeyi. Zarah kuwa tana kallonta tana dariya tana dariya, Falak tana gefe ta kalli Jalila tace haba Jalila kukan ya isa haka, Jalila tace dole inyi kuka Falak, ace ayau ana daurin aure na, amma Ummina da Yayata suna kwance agadon asibiti, kuma su duka babu me ciwon daza,a fada ta dadi, dukansu su suka jama kansu, yakike so inyi? Kinaji jiya agabanmu wasu suke gulmar Yaya da Ummi, sbd kome kake boyewa dole mutane su sani.

Wlh yafi acema banda Uwa za,ayi bikina hakan zefi mani insan cewar bata raye bazan damu da rashin wanda zemun nasiha ba, amma gata araye kuma cikin halin hauka, wanda zuwa yanzu mutane dayawa sunsan cewar ta hauka ce, kuma qai qayine yakoma kan mashekiya, yakike tunani idan dangin mijina sukaji haka? Nide wlh Ummin kin..... Falak tayi saurin rufe mata baki tace haba Jalila da iliminki, da komai, kinsan fa kome Uwa tazama ba,a canza ta ko? Dan haka inaso kitoshe kunnuwanki da duk wata magana dazakiji daga gurin dangin mijinki, kuma duk wanda yatareki da maganar kiyi banza ki kyaleshi shine kawai abinda ze kwaceki daga gurinsu.

Baba Mairo ce tashigo, cak ta tsaya ganin haryanzu basu tafi ba, tace mezan gani haka Falak? Kinsan fa tundazu aka daura auren yakamata ace kuna gida yanzu tasamu takara wanka sannan taci abinci. Falak tace wlh abinda nake fada mata kenan, tonaji kema ai nace kidena yawo dayawa ko, kinsan fa kinshiga watan haihuwarki, dan likita yace zaki iya kara kwanaki ba lallai bane ace kinsan lokacin, kuma wahala ma tanasa mutum ya haihu babu shiri, nide kutashi kutafi.

Jalila tace Baba Mairo yajikin Yaya Jiddan, munje dakin akace antafi da ita za,ayi mata test. A,a jikinta dasauki nabaro Halima agurin suna can gaba yanzu zasu dawo, Falak tace muje driver yana jiranmu.

Fita sukayi suka nufi dakin da aka kai Jidda test, atare suka jero, tana bisa wheel chair ana turata, wasu mata da miji suka wuce su mijin yana dauke da yaronshi, harsun wuce Jidda tace ma Jalila dan kwalama wancan kira kice Al,amin. Jalila tace kinsanshi ne? Tace inaji kamar shine, amma kirashi mugani. Jalila tace Al,amin. Cak ya tsaya atare suka juyo da matarshi, dawowa sukayi da baya, dan danan matar ta bata fuska.
Al,amin yace sannunku yamejiki? Jalila tace dasauki, kuma itace ma tace amaka magana. Kallon Jidda yayi cike da tausayi yace sannu baiwar Allah yajikin? Kuka Jidda tasa, kowa ya tsaya yana kallonta, Matarshi tace dan Allah honey muje kasanfa akwai inda zamu biya ko.

Jidda tace Al,amin, Ameerah, cike da mamaki matar takara kallonta tace ni kuma? A ina kikasanni? Goge kwallan idonta tayi tace lallai duniya kenan, baku ganeni ba? Jidda ce. Gaba dayansu suka zaro ido suka hada baki sukace Jidda Abba Bala? Ta daga kai tace kwarai kuwa. Umman Sameer tace bayin Allah mun tsaya ahanya kumuje dakinta gashi can sekuyi maganar acan.

Al,amin da Ameerah kuka sosai sukeyi dasuka gama jin labarin da Jidda tabasu, tace na cuci kaina, Ameerah kece silar shigata wannan harakar, Al,amin kaine mutumi na farko daka fara sanina 'ya mace amma yau gashi kudayake kunada rabon tsira Allah yatema keku kunshiryu, abun mamaki kuma harkunyi aure hada rabo atsakanin ku.

Ameerah tagoge idonta tace tabbas Jidda na cuceki, sbd nice silar shigarki wannan rayuwar,  sede wlh tun bayan damukayi fada dake akan nazo inaso inmaidake ruwa lokacin da kika tuba, mukayi fada tundaga lokacin mukabar unguwar da muke, kuma nasake waya shiyasa bankara nemanki ba, dan naga kinbar harkar danakeyi, haka nacigaba da rayuwar bariki.

Dalilin shiryuwata shine lokacin da Babana yarasu, tundaga ranar naji tsoron Allah, sbd agabana yarasu, nashiga firgici, dama akullum addu,ar Mamana Allah ya shiryeni, segashi Allah ya amshi addu,arta, nashiga damuwa tunbayan mutuwarshi nakara canza layi, duk wasu kawayena seda narabu dasu, sbd malamin dana samu nafada mashi irin rayuwar danayi kuma nace mashi inason intuba, yace abu nafarko dazan farayi shine inrabu da duk wasu kawayena.

Sbd yace mun idan har mutum yana aikata alfasha, kuma yatuba, matukar berabu da abokanan shiba, tamkar be tuba bane, dan wata rana zasu iya dawo dashi ruwa, alokacin hargidanku nazo sede bansamekiba, Umminku tace mun kina zariya, na amshi no ki amma nakiraki bata shiga, alokacin naso mukulla sabon kawance tunda nasan kin tuba.

Tundaga ranar nikuma bankara tunanin zuwa gidanku ba, haka nashiga islamiyya wannan malamin yatsaya mun sosai nayi karatu me yawa, wata rana nadawo daga makaranta, nahadu dawani dan unguwarmu tare da wani, na tsaya mugaisa kawai senaga ashe Al,amin ne, anan muka gaisa shima yayi mamakin ganina haka, shine ya amshi no ta yace zezo muyi magana, dan bayason muyi agaban abokinshi.

Naji matukar tausayinki lokacin dayabani labarinki, alokacin yayi kuka shima, dan yacemun shine sanadiyar komawarki ruwa, kuma ya kaiki inda kika hadu da matsala, haryake cemun yaso kuyi aure amma kika kiya, alokacin daya temakeki kuma yace yana zargin kina dauke da cuta, yaso kije kiyi gwaji idan baki da ita kuyi aure amma baki yarda ba.

Ganin nima nashiryu, shima yafadamun irin kallar tubar dayayi kuma yace idan zan amince ze aure ni, dama alokacin mijin aure nake nema ni kuma na amince mashi, yanzu haka yaronmu daya Sultan, kuma haryanzu banwuce karatu ba, dan gani nake gara nayi zamana nayima mijina biyayya yafi dan tsoron yan matan Jami'a nakeyi, keni zan iya cemaki kawata daya yanzu ma kwafciyata, itama tadan girmeni.

Al,amin kuwa kasa cewa komai yayi sbd kuka yakeyi tamkar mace, kowa yakasa lallashin shi. Jidda ma kukan takeyi, da kyar tayi shiru tace bakomai Ameerah wlh nayafe maku, duk da kune silar shigata wannan rayuwar amma babban laifin yana gurina da gurin Ummin mu, mekikace yanzu? Mamanki kullum addu,arta Allah ya shiryeki, toni banda wanda yakemun addu,a se kanwata. Kuma kinsan yanda addu,ar Uwa takeda tasiri akan 'ya'yanta, yakike gani idan da ace Ummina ce takemun addu,ar da Jalila takemun?.


Mutum yasamu Uwa tagari ma babban abin alfahari ne, Baban nawa daya kamata shima yatuna dani yamun addu,a bata bari yasan halin danake cikiba, bare yamun addu,a. Asalima tasashi yamanta dani acikin yaranshi.

Wannan Uwa tagari ce? Uhm, nikam ahaka nazo duniyar banci ribar komai ba, kuma gashi zanbarta babu wata riba. Al,amin bakayi laifi ba, dan ka auri Ameerah, laifi nane, fatana kobayan raina kada kumanta dani kurika sakani cikin addu,arku kuma duk wanda zebani sadaka, inarokon daya aje bayan raina agina mun koda rijiyace wadda mutane zasu amfana da ita, koda hakan nasan da kudina nabar abinda wasu zasu amfana dashi, kuma Allah zekai ladar akabarina, amma tabbas ban tara komai na lada ba, wanda zanyi guziri dashi natafiya,,,,,,, kuka ne yaci karfinta.

Shiru dakin yayi sbd gaba daya dakin kowa kuka yakeyi. Al,amin da kyar yace Jidda kiyafemun kiyafemun dan Allah, tashi yayi yadauki Sulta ya aje masu kudi wanda besan yawan suba yafita sbd gaba daya zuciyarshi tayi mashi zafi, Ameerah ta mike tana kuka tamika ma Jidda hannu sukayi musabaha, itama tafita tana kuka, akofar fita suka ga mutum tsaye ya juya baya, da alama shima kuka yakeyi.

Alh, ne yazo tafiya dasu Jalila dan Baba Mairo tace mashi suna nan, tunda yazo zeshiga yaji firarsu kawai ya tsaya akofar dakin. Tausayin Jidda yayi mashi yawa, haka yashiga dakin daka ganshi kasan yasha kuka, bakin glass ne a idonshi amma duk da haka afuskarshi ana ganewa.

Kwance ya iske Jidda tana ta kuka, yace Jalila kumuje kunga har la,asar tayi, Falak kuwuce muje. Jalila ta matsa tarike Jidda sosai, tana kuka, tace Yaya Jidda kiyafemun, zantafi, amma gobe zamuzo, Allah yabaki lfiya. Jidda tace bakitaba yimun komai ba Jalila, nice yakamata inrokeki gafara, na cutar dake, kiyafemun, Falak kema haka dan Allah kiyafemun. Falak tace nadade dayafe maki, Allah yabaki lfiya.

Da kyar aka cire Jalila daga jikin Jidda sunata kukan saurin fita Alh, yayi danshima kukan yakeyi.Jidda kwanciya tayi tana kukan zuci jitake dama Allah yadau ranta yanzu.

Da misalin karfe 7 aka gama shirya amarya, tayi kyau, sede fuskarta ko kwalli bata bari anshafa mata ba, bamaze zauna ba ko anshafa, sbd hawayen dasuke zarya afuskarta, afalon Alh, aka kaita suyi sallama, zaune suke da Mal. Garba, da Kawunshi, anan kowa yayi mata nasiha sannan akace Alh, yayi mata nasiha, kasa cewa komai yayi, sede yace Allah yabaki hkr Jalila, saurin tashi yayi yashige daki sbd kuka, daya taho mashi, itama kukan takeyi, haka matar Kawun Alh, ta dagata suka wuce, Falak kuwa dama tundazu Sameer yadauketa yakaita gidan amaryar dan yace baya so tasha wahala, manyan mata 2 ne suka sakata tsakiya, da yan uwan Kakanta, se dangin Dadynsu.

Sauran mutane suka biyo bayansu. Gidanta yayi kyau sosai, haka suka shiga da ita, bayan sunmikata ga dangin mijinta akayi abubuwan al,ada sannan Sameer yashiga yace sufito amaidasu, dan ance manya bazasu kwana ba, Falak ma Sameer ne yace ta kwana sbd Jalila. Da kyar Falak tasata takara yin wanka sbd gidan kowa ya tafi daga Falak se su Bilkisu da Farida, su 3 ne zasu kwana, lallashinta sukayi taci abinci. Suna zaune Jalila tace wlh Falak gabana faduwa yakeyi, Falak tace badole ba, tunda gobe kamar yanzu kina gaban angonki. Tace ke wlh kincika fassara, nikwai inaji ajikina kamar wani ya..... bata karasa fadi ba, Saleem yayi sallama yashigo shida Sameer, daka kalli idanunsu kasan akwai abinda yafaru. Zunbur Jalila tamike tace Ummi ko? Yaya Jidda ce? Kufadamun waye ya mutu acikinsu? Kamota Saleem yayi yace babu wanda ya mutu kawai jikin Yaya Jidda ne yatashi. Murmushi tayi tace wlh banyarda ba, shikenan kawai, nashiga 3 yazakimun haka Yaya Jidda kinsan banda kowa seke, meyasa zakimun haka,,,, kuka tasa masu, Falak taja Sameer tace meya faru, Yaya Jidda tarasu ko? Share hawayen idonshi yayi yadaga mata kai,

Wata irin zufa taji ta taso mata, mararta tawani murda, saurin dafe cikinta tayi ganin halin data shiga yasa Sameer yayi saurin kamata, yace Saleem muje inajin Falak haihuwa zatayi, kadauko Jalila kawai dasu Bilkisu kasa megadi yakulle gidan bari intafi da ita asibiti. Juyawar da Saleem zeyi yayi ma Jalila magana yaganta kwance akasa ta sume.
😭😭😭😭😭😭😭😭
Washhhhh!!!!! bara inbarku haka, nima najike sekunjini a page na gaba. Tnx alot

Ur's 
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/21, 2:38 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Part 180.....185

Suna zuwa aka nufi labour room da ita, shi kuma Saleem yashiga da Jalila su Bilkisu suna binshi abaya, itama daki aka nufa da ita domin adubata. Sameer gurin su Baba Mairo yanufa, koda yaje ya iske har ansaka gawar Jidda ambulance, za,a kaita gida, Baba Mairo tace lafiya Sameer naganka arude? Alh wanda fuskar shi take jike da hawaye, ya goge idon shi yace lafiya de Sameer? Yace bakomai dama Falak ce zata haihu tana dakin haihuwa.

Alh, yace to ina Jalilan kotana gidanta? Kai yasosa yace a,a nabarta ita da Saleem inaji befada mata ba, yauwa kada kufada mata kawai yadauketa yakaita gida. Baba Mairo kikoma gurin Falak din mucemu wuce da gawar, tunda Halima tana gurin Zarah.

Goge kwallan idon ta tayi tace a,a Alh muje inaso inyima Jidda wanka da kaina, kai Sameer kasamu Halima tunda dazu akayi ma Zarah allurar bacci kace taje gurin Falak din, nizanje can gidan. Yace to nima yanzu zanzo kafin agama shiryata tunda ance yau za,a kaita tunda dare beyi ba.

Haka suka nufi gida da ita kowa yana cikin damuwa. Babu bata lokaci Falak ta haifi kyawawan yaranta guda biyu, Mace da namiji, cikin koshin lafiya, bayan angama shiryasu aka fada masu Sameer, Bakaramin murna Sameer yayi ba, dan betaba tunanin samun yan biyu ba. Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga Saleem.

Dauka yayi yace Saleem ya Jalilan ta farfado? Yace E amma haryanzu kamar bata gama dawowa hayyacinta ba, amma likitan yace zeyi mata allurar baccin dazata kaita har gobe dan tasamu ta huta. Sameer yace toshikenan yanzu itama Falak ta haihu, ansami twins, fito muhadu semuwuce can gidan.

Saleem yayi farin cikin ganin jariran masu kyau dasu, bayan ankai Falak dakin hutu, itama haryanzu kuka takeyi, suka dubata da jiki, suka ce zasuje sukai Jidda, Falak tace Allah sarki Yaya Jidda Allah yajikanta, naso ace nakara ganinta. Sameer yace se hkr addu,a zamu cigaba dayi mata, bara muje semun dawo, nasan se gobe za,a sallameki gara kizauna ana ku huta, tace tosekun dawo ina Jalilafa? Anan suka fada mata abinda yafaru, tace to Allah yabata lafiya, haka suka fita suka bar Umman Sameer agurinta.

Gida mata se kuka sukeyi, Baba Mairo da Matar Kawan Alh, su sukayima Jidda wanka, suka shiryata, babu bata lokaci aka fiddota, akayi mata sallah,aka nufi gidanta na gaskiya da ita.
     Koda sukaje Alh, kasa sakata kabari yayi, sbd kukan dayakeyi, sede su Kawu ne da Baba na Zariya da Kawun Sameer suka sakata, Alh, yabama kowa tausayi agurin, haka aka gama sakata akabarinta aka rufeta, suka dawo.

Aranar haka kowa yazauna masu bacci kadan ne, dan Alh, tunda yashiga daki, yayi wanka yayi alwala yayita nafila da karatun Qur'ani har seda aka kira sallah sannan yanufi masallaci. Bayan sunadawo ne, yake tambayar Sameer yabega Jalila ba, anan yake fada mashi halin datake ciki, da kuma abinda Falak tasamu, yayi murna sosai, yace tobai bazama zamuyi ba, muwuce muga jikin nasu.

Lokacin dasukaje asibitin har Falak tayi wanka Anyima jariran wanka suma, sunyi gwanin kyau, sede daka kalli Falak kasan tana cikin damuwa. Baba Miaro tana kusa da ita dan agurinta ta kwana, ita kuma Umman Sameer ta kwana agurin Jalila ita dasu Bilkisu.

Jalila kuwa tafarka, tunda tayi sallah itama take kuka, se lallashinta sukeyi, haka Alh, yasameta, yana ganinta shima yaji wani sabon kukan yazo mashi, da kyar yasamu yadedeta kanshi yashiga, shima lallashinta yashiga yi, sannan suka nufi gurin Falak, acan ma du lallashin ne, daga can yawuce gurin Zarah.

Zaune suka sameta duk ta kwance bandage din da aka rufe mata ciwon tana ta wasa dashi, cikin sauri Saleem yaje yajira nurse, ana suka riketa aka sake mata wani sabon dressing din. Tagumi Alh, yayi, yana kallonta, yarasa neke mashi dadi aranshi, addu,a kawai yakeyi itace take kara sanyaya mashi ranshi. Fita yayi yace bara yatafi tunda gari yayi haske sbd masu zuwa gaisuwa.

Karfe 10 aka sallami Falak da Jalila, Baba Mairo tace awuce da Falak gidansu Jalila, idan kunje se a bude part dinsu nada tazauna aciki, sbd asamu saukin zirga zirgar. Sameer yace hakan ma yayi, tace nima anjima zanzo sbd nasan babu wanda ze zauna agurinta, idan yaso se Halima tazauna agurin Zarah, anjima se indawo.

Sunzo tafiya, su Bilkisu sukace bara suwuce gida anjima zasu dawo, godiya sukayi masu, Saleem yabasu kudi suka tafi, sun fito kenan suka hadu da Al,amin, Jalila yagane, hakan yasa ya tsaya suka gaisa, kallonta yayi tana kuka yace ina fatan kunshedani? Al,amin ne, yame jikin? Falak tashare idont tace Allah yayi mata rasuwa jiya da dare. Kiyayi kamar ansara mashi icce akanshi, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mashi. Yace shikenan Jidda ciwo ya warke, darabon mugana ashe, sallama yayi masu yace zeje yadauko Ameerah suzo tare.

An gyara part din su Falak na da dama kuma babu abinda aka cire aciki, tunda Hajjo tarasu da aka kulle shi ba,a kara amfani dashi ba, share shi akayi aka goge, sannan Falak da Jalila suka shiga ciki, amma Falak cewa tayi adakinta na da zata zauna bazata shiga dakin Ummanta ba, Sameer yaje yadauko mata duk kayan dazasuyi amfani dasu yakawo, Baba mairo ta dora ruwa takara yima yaran wanka, tasa Falak itama takara yi.

Saleem ne zaune afalo shida Jalila, haka yayita lallashinta da kyar yasamu taci abinci shima kadan taci, yace Jalila inaso ki kwantar da hankalinki yanzu babu abinda Yaya Jidda take bukata daga gurinmu se addu,a. Kirika yawan ambaton Allah da addu,oi zaki samu sauki aranki, nasan dole kiyi kuka amma hakuri zakiyi. Allah yaji kanta, yabama Ummi lafiya, tashi yayi yace zeje waje. Itama shiga gurin Falak tayi, dan batason zuwa bangarensu.

Haka aka cigaba dazaman gaisuwa, Al,amin da Ameerah sunzo gaisuwa, itama tasha kuka, Al,amin yakira Jalila yace yadauki nauyin ginama Jidda rijiya amakarantar almajirai kamar yanda taroka, kuma zeginata ne da sunan ta, amatsayin sadakar daze bata. Sosai Jalila tayi mashi godiya, seda suka jera kwana 7 suna zuwa gaisuwa, ranar da akayi sadakar 7 aranar akayi sunan Falak, bawani taro akayi ba, bayan sadakar 7 akayi radin suna.

Namijin aka samashi sunan Alh, wato Abba, ana kiranshi da Ameer, dan Falak tace tana son sunan, Macen kuma Aka samata sunan Hajjo, Zainab, ana kiranta da Ameerah. Falak tayi mamaki sosai da Sameer besa sunan babanshi ba, har seda tayi mashi magana, murmushi yayi yace haba Dear, Alh, shine mutumin da yayi sanadiyar haduwata dake, kuma ya cancanci abinda yafi haka agurina dake baki daya. Umma kuma dana sa sunanta, kinga tarasu kuma saka sunanta zesa murika tunawa da ita, jawota yayi yace kada kidamu nasan nan da shekara 2 zaki kara sama mana wasu babies din. Murmushi tayi tace nagode.

Ayau ne, Jalila zata koma gidanta, dan Alh, yace sutafi gida zatafi samun sakewa idan tana kusa da mijinta, sauran mutane ma, duk sun watse se yan uwa kawai suka rage, yan Zariya ma yau zasu tafi, Alh, yasa aka kira kowa yace yana son magana dasu, anan falonshi suka taru, hada Kawunshi, da Kawun Sameer, da Mal. Garba dasauran mutanen.

Bayan anbude taro da addu,a, aka kara yima Jidda addu,a sannn Alh, yafara magana, hakuri yakara bama kowa, sannan yace Jalila,Falak, ayau nakeson kowa takoma gidanta, wanda yarasu yariga da yarasu, dan haka addu,a kawai zamu cigaba dayi mata, banaso insamu labarin acan kun kasa sakin jikinku, kowa hkr yakeyi arayuwa, kuma dama dan Adam baya zama haka, har se Allah ya Jarabceshi, dan haka murika daukar kowace kaddara tazo mana da hannu 2, Allah yayi maku Albarka.

Kuma itama Zarah munyi magana da Malam, yace gobe Malaminshi zezo yafara yimata rukiya, dan haka nayima Dr, magana zamu maidota gida yau, idan yaso se arika zuwa gida ana mata dressing, tunda yanzu yakoma bayan kwana 2. Kallon Kawaunshi yayi yace Kawu ko akwai abinda zakace?.

Gyara zama yayi yace hakane, duk abinda kafada yayi dede, sede abu 1 nakeso inkara, Baba Mairo mungode kwarai da irin abunda ku kai mana, daga ke har Halima, tabbas kunzama yan uwa, sede ina rokonki wata alfarma, daga ke har Halima, duk da bata nan, amma ga malam nan, muna neman alfarmar daka barsu sudawo gidan nan dazama, kaga akwai marar lfy, kuma yanzu Zarah ba matsayi matar Abba take ba, asali ma, babu sauran igiyar aure atsakaninsu, idan har kayarda mun rokon alfarmar dasu dawo nan dazama, hakan zeyima Abba sauki dan baze yuwu ace mubama shi mal. Garba ita yatafi da ita ba, duk da tayi mana laifi amma ba,a kallon abinda yawuce, idan ka kalli alherin da mutum yayi maka zaka iya temaka mashi dashi.

Kaima Abba dole kayi hkr da duk abinda Zarah tayi maka, tabbas tacutar da kai da kowa naka amma, ka kalli darajar yaranku kayi hkr, inaso tacigaba dazama agidan nan har Allah yabata lafiya, daga nan kuma seta zaba ma kanta abinda taga zefi mata.
   Amma inaso inji daga bakinka ka amince zata cigaba dazama agidanka harta samu lafiya?.
       
       Se kunjini a next page dina wadda insha Allah shine last page. Nagode da kaunarku gareni.

Ur's 
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/24, 7:53 PM] Nabeela lady: πŸ™†πŸ»πŸ˜­πŸ˜­πŸ™†πŸ» AGOLAH!!! Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

Part 185.....200
   The Last Page.........

Shiru Alh, yayi nawani lokaci, sannan yace shikenan Kawu duk abinda kace yayi dede, Allah yabata lfy. Kuma nagode da abinda kuka yi mani, Allah yasaka da alkhairi. Kawu yace Alhmdll, anjima malamin ze iso, dan haka se kuje kudauko ta. Haka suka tashi kowa yafara shirin tafiya.

Bayan andauko Zarah daga asibiti duk wanda yaganta seya tausaya mata, takoma kamar skeleton ne aka sama fata, tayi baki, ga kafarta da aka yanke tundaga cinyarta har kasan kafar sun shanye tazama siririya, ta yanda bazata kara amfanuwa ba, sede ciwon dake jiki yayi sauki, sbd Kawu yabada ruwan addu,a ana shafa mata akan ciwon, hakan yasa yadena fitar da ruwan dayakeyi, kuma dama aljanun jikinta ne suke sakashi zuba.

Jalila da tunda ta kalli Zarah take kuka, a part dinsu Falak Alh, yace akaita, awani daki dayake farkon shiga daga gefen falon, anan aka saka mata katifa, dayake akwai bandaki aciki, sede dakin bawani girma gareshi ba, bayan su Baba Mairo sunyi mata wanka, suka gyarata aka daureta tana kwanciya tayi bacci.

Saleem ne yazo daukar Jalila, tana kuka haka suka tafi su Baba Mairo se hkr suke bata, Falak ma seda tayi mata kuka, Sameer yace kema shiryawa zakiyi anjima zamu tafi, Baba Mairo tace gsky bazaku tafi ba, dama inaso inga Alh, muyi magana, dama ace yaro daya gareta se kutafi, amma yara har biyu, sannan kai kuma aikinku idan kafita wani lokacin har dare kake kawai, yazatayi da yaran? Kuma kaga muduka muna nan bare ma ace ni inje inzauna mata. Sameer yayi murmushi yace haba Baba yanzu dan Allah so kuke inzama gauron karfi da yaji? Inde haka ne, nima sede indawo nan. Baba Mairo tace nidama ai bance zan hanaka ganin matarka ba, sekaje ka kullo gidan kaima kadawo nan idan sukayi ko wata daya ne, sunyi kwari se ku koma gidanku. Yace shikenan nagode, tace yauwa zanje insamu Alh.

Da misalin karfe , Kawun Sameer suka iso da Malamin dazeyima Zarah karatu, Alokacin shima Sameer ya iso gidan da akwatinshi, dan Alh, yace shima yadawo, a dakin Falak yasauka, su kuma su Baba Mairo suna dakin Hajjo, Alh, shi kadai a part dinsu.

Afalo akayimata shinfida bayan sunyi mata alwala, malamin yazo yafara yi mata karatu, yadade yana karatu amma sunkiyin magana, sbd manyan aljanune, kuma bakake, yasha wahala sosai, kafin suka fara magana.

Wayyo Malam, ya isa zamuyi magana wlh, zufar goshin shi yagoge yace inajinku..... nide sunana Zurkum, kuma nine shugaban bakaken aljanu, wannan matar bata da kirki, sunyi da megidanmu akan duk lokacin da mijinta yagane halin datake ciki, akwai abinda ze sameta, amma haka ta amince, mu kuma dama mune yasa muke mata aiki, kuma dama duk wanda ya kasance yana maka aiki duk ranar daka dena biya mashi bukata, to kanka ze dawo, hakan yasa tundaga ranar da asirinta yatonu muka shiga jikinta.

Mune nan muka fado mata da durowa akafarta, kuma muka shanye jinin jikin kafar da bargon kafar, hakan yasa bazata kara amfani da kafar taba, tabbas wannan mata tayi sa,a tasamu masu yimata addu,a amma munso semun bi duk wani jini dayake jikinta munshanyeshi duka sannan daga karshe mukasheta, amma karfin addu,ar da akeyi mata yasa muka kasa aikata abinda mukayi niya. Amma kusani wannan mata bazata kara ganin haske arywarta ba, sbd tasamu mun cuci mutane, aciki harda karamin yaro wanda besan komai ba.

Dan haka kada ka konamu zamu tafi amma duk lokacin data kara shiga gonarmu tabbas takira ajalinta. Malam yace kuyi mani alkawarin bazaku kara shiga jikinta ba, idan kun fita. E munyi alkawari, amma itama ta gyara rayuwarta, takuma koma ga Allah wanda take bautamawa, hakanne ze kareta daga shrrinmu. To nagode.

Wata irin kara Zarah tasaki tare da atishawa, har so 3 sannan takoma ta kwanta, bacci yadauketa. Malam yace Alhmdllh, insha Allahu data farka zata dawo hankalinta, sede ina tunanin zata iya kaiwa gobe, dan haka zantafi gobe da safe zandawo. Ga wannan asamu wani ya zauna kusa da ita, aduk lokacin data farka abata wannan ruwan addu,ar tasha. Allah yakara sauki, kome kenan sauran bayanin idan nazo gobe zakuji.

Godiya sosai, sukayi mashi, yatashi yatafi. Falak, tana gefe se kuka takeyi, Baba Mairo tace banga amfanin asarar hawayen da kikeyi ba Falak, ace kuka yaki karewa, haba dan Allah, so kike kijama kanki wata cutar. Umman Sameer tace gsky Falak ya isa haka, kin sande kuka baya maganin komai, nasan akwai abubuwa da yawa dakike tunawa, amma kiyi hkr kisama kanki dangana, kinga kinrasa mutane dayawa arayuwarki, kuma duk da haka numfashinki bedena tafiya ba, dan haka kimanta da duk abinda yafaru dake arayuwa, Allah yana tare dake.

Idan kika kalli baiwar da Allah yayi maki ta yara 2 ya isa ki godema Allah, ada kinkasance ke daya, yabaki miji nagari, sannan yazo ya azurtaki da yara, Allah kadai yasan iyakar abinda zaki haifa, kinga wannan ma wata rahama ce daga Allah. Falak tagoge idonta tace nagode, da irin kulawarku gareni, kuma insha Allah, nadena saka damuwa araina. Baba Mairo tace yauwa kokefa, tashi ki kaima mijinki abinci kije daki kidauko yan biyu ki maidasu dakinku.

Bangaren Amarya da Ango kuwa, da kyar Saleem ya lallashi Jalila, taci abinci tayi wanka, yasa sukayi sallah, yajata zuwa gado yacigaba da lallashinta yana kara kwantar mata da hankli, taji dadin irin kalaman dayake fada mata sosai, cikin lokaci kankani taji zuciyarta tayi haske, duk wata damuwa ta gushe, daga lallashi shima ango ya canza tasha, naja masu kofa nace seda safenku.

Washe gari da safe har 8 tayi amma Zarah bata farka ba, mutanen gidan harsun gama karyawa, sunyi wanka, suna jiran tashinta, Baba na Zariya kuwa har yagama shiryawa dan yace shima yau zetafi, jiran tashinta kawai yakeyi da kuma jawabin da malam yace zeyi, se wajen 8:30 sannan ta farka cike da firgici, Baba Mairo tayi saurin riketa tana tofa mata addu,a Umman Sameer tamiko maganin da malam yabasu aka bata, kallonsu kawai takeyi Babanta yace kintsaya kina kalon mutane bazaki bude baki kisha maganin ba? Baki ta daga tasha maganin, sannan tamaida kallonta zuwa cikin Falon, akan Alh, tasauke idonta, suna hada ido yayi saurin dauke kanshi tare da kara daure fuska. Juyawa tayi tana kallon Baba Mairo da Falak, wacce take rike da Ameerah, dan Ameer yana bacci.

Sauke kanta kasa tayi dasauri takara kallon Alh, idanunta suka ciko da hawaye ganin kafarta datayi anyanke, kuma ta koma siririya. Haka falon yayi shiru kowa yana kallonta. Sallamar su Kawu da Malam sukaji, anan Alh, yafita domin ya shigo dasu. Bayan sun shigo aka gaggaisa, suka samu guri kowa yazauna, Sallamar Saleem da Jalila sukaji, dan Alh, yayi ma Saleem waya akan suzo. Falak da tunda taga yanda Jalila ke tafiya tafara dariya ciki ciki, suna hada ido da ita Jalila ta maka mata harara. Sameer ya zunguri Falak ahankali yace kede kincika sa ido. Zama sukayi suka gaida kowa, Jalila se kallon Zarah takeyi wadda kanta yake akasa tana kuka.

    Bayan kowa yayi shiru Kawun Alh, wanda shima yana cikin falon, yayi gyaran murya yafara magana...... to Alhmdllh Allah mungode maka da ka kawo mana karshen wannan iftila'i da muke cike, wanda bakowa bane yayi sanadiyar shigarmu cikinshi seke, Zarah, tabbas kincutar da mutane dayawa arayuwarki, ki godema Allah daya barki harzuwa yanzu da ranki, wanda yabaki damar neman gafarar wadanda kika cuta, sauran kuma da kika kashe, sede ince tsakaninki da Allanki ne, kuma ki kara godema tsohon mijinki,,,, saurin dago kai tayi jin abinda Kawu yafada, wai tsohon mijinta.

E tsohon mijinki, dan yanzu haka babu igiyoyin aurenshi akanki, duka ya sauke maki su, kuma duk da irin abinda kika yimashi besa yayi watsi dake ba, ya tsaya akanki ganin baki wulakanta ba, duk da ke burinki kenan inda Allah yabaki dama, kiga kin wulakanta shi, sede ahi azuciyarshi ba haka bane, asali ma, yahanaki fita kije ki gogu da sauran yan'uwanki mahaukata, kuyi yawo aduniya kuna bin bola, yara suna jifarku, wasu marasa imani kuma suna binku suna maku fyade, kuna haihuwa akan titi, duk wadan nan abubuwan babu wanda Abba yabari kikayi, asalima acikin unguwar nan, bakowa yasan halin dakike ciki ba. Sannan wadan da kike da burin ganin bayansu, sune suka zama gatanki, alokacin da kika rasa wadanda zasu zauna dake,  Falak, yarinyar da kika tsana, kinso ki lalata mata rayuwa, Allah yatsare abinshi, kin kashe mata Uwa, kaninta ma baki barshi ba, amma duk da haka ta tsaya domin ganin kinsamu lafiya,

Baba Mairo dattijuwa me kirki, wadda ahaife ta haifeki, bake bama, Abba kanshi ta haifeshi amma bata isa ki daraja taba, sbd kawai tana aiki a karkashinki, segashi yau tayi maki abinda Mahaifiyarkice kadai zata iya yi maka shi, tazauna dake acikin halin hauka, na tsawon kwanaki, tayi jinyar diyar cikinki, wadda ayanzu bata duniyar. Harma wata daban wadda baki sani ba, kawai ta dalilin yarinyar da kika tsana itama ta amfaneki, kinga kenan kinci darajar Falak, sirikarta gatanan azaune, sbd ke take zaune gidan nan, kuma ita tayi jinyar Jidda.

Saboda haka yanzu shawara tarage naki, dama ni naroki Abba akan yabarki kizauna agidanshi harki samu sauki sannan sekizabama kanki rayuwar data yimaki, mahaifinki ma nine na tsaidashi, sbd baki daukeshi da muhimmanci ba, bare kuma yan 'uwanki, wadan da tunda sukazo bikin Jalila sukace bazasu dubaki ba, sbd kema kin manta dasu, dan haka yarage naki ki gyara rayuwarki, duk wanda ya yarda zumunci to wata rana seyayi dana sani.

Shiru falon yayi inbanda kukan Zarah bakajin komai, sauran masu tausayi sede hawaye, Jalila, kam idanunta harsun kumbura, azuciyarta tana tirrr da irin halin Umminta, yanzu agaban kowa harda mijinta kalli yanda ake fada mata bakaken maganganu, jitake kamar tabar falon.

Malam yayi gyaran murya yace to Zarah, kinji de da kunnenki irin abubuwan da kika aikata, ace wai musulmi ne, da kanshi ya aikata wannan abun, sbd son zuciya da kuma kwadayin abun duniya, gashi nan ta sanadiyar abinda kikayi kalli irin abinda kika jama kanki, yanzu bakida saura daraja agurin kowa, sede idan har kin tuba kuma kin gyara halinki, abinda nakeso dake, idan har kinyarda zaki canza halinki, to dole sekin koma baya kin gyara rayuwarki daga farko, dan kinada karancin addini, kuma dole sekin gyara ibadarki, sannan zaki samu damar neman gafara agurin ubangijinki, sauran mutanen da kika cutar kuma gaki gasu, zaki iya neman gafararsu, saura kuma sede ince Allah ya gafarta maki,amma tabbas kina da kalubale agabanki, kuma duk wanda yayi niyar tuba, to dole seya bar duk wani abu najin dadin duniya sannan ze iya samun lokacin ibada. Daga karshe kuma ina maki ta,aziyar mutuwar diyarki, tare da fatan alkhairi na auren diyarki Jalila.

Kuka sosai Zarah takeyi, jitake dama Allah yadauki ranta, da irin wannan rana daya gwada mata, jan jiki tayi ta matsa kusa da Babanta, wanda shima kanshi yake kasa yana kuka, kafarshi takama tana kuka tana fadin Baba kaine mutum na farko daya kamata infara neman gafararka, tabbas na cuceka, na wulakantaka, ban baka darajarka ta Uba agareni ba, kai cona, daban zama 'ya tagari ba,nahada kai da makiyiyarka munzalunceka.  Dan girman Allah Baba kayi hrk kayafemun, nasan idan baka yafemun ba, raywata bata da amfani, wlh ko haka Allah yabarni naga rayuwa kayafemun ko naga haske arayuwata. Kamota yayi yana kuka yace, ya isa haka Zarah, nayafe maki, duniya da Lahira, idan kina da laifi nima inadashi danayi sakaci da addu,a har wata tasamu galaba akaina, tazo taruguje tarbiyar dana baki afarko, tabbas, yanzu kam naga falalar addu,ar iyaye akan 'ya'yansu. Allah yagafarta mana gaba daya. Kije kinemi gafarar mijinki, shine yafi can canta daya yafe maki.

Matsawa tayi kusa da Alh, wanda shima yake kuka kamar karamin yaro, zata kama kafarshi yayi saurin janyewa, tace nasan banida bakin dazan nemi gafararka, na cutar da kai, na wulakanta ka, naci amanarka, na ha'inceka, nakasa bama yaranmu tarbiya mekyau, amma dan Allah kada kadubi laifukan dana yi maka, ka kalli girman Allah da darajar yaranmu ka yafemun, kaima Allah ze saka maka da mafificin alkhairinsa, kayi hkr da duk abinda nayi maka.

Shiru Alh, yayi yana kuka, Jalila ta matsa kusa dashi tarike kafarshi tana kuka tace, Dady dan Allah kayi hkr ka yafema Umminmu, nasan ta cutar da kai amma idan baka yafe mata ba, zata shiga wata irin rayuwa, dan Allah Dady. Goge idonshi yayi yace shikenan Jalila nayafe mata, ko alahira wani yanacin arzikin wani, haihuwa me rana, kigodema yarki kinci darajarta, nayafe maki.

Komawa gurin Falak tayi tana kuka tama kasa magana, dan muryarta harta dashe, Falak ta tashi ta aje Ameerah, tadawo takama Zarah tana goge mata kwallan idonta, itama tana kuka tace haba Ummi, kintaba ganin inda uwa tadurkusama yarta? Kamar yanda bazaki durkusama Jalila ba, haka nima agurina na daukeki Uwa, kada ki wahalar da bakinki gurin neman gafarata, ni 'yarkice, na dade dayafe maki, kuma har cikin zuciyata nayafe maki, Allah ya yafe mana gaba daya, Zarah jitayi gaba daya kunyar Falak da sauran mutanen falon takama ta, kallon Baba Mairo tayi tace Baba Mairo dan Allah kiyafemun abinda nayi maki, tabbas ke Uwa tagari ce dayakamata ace narikeki amatsayin Uwa, amma sena wulakantaki narike wadda tayi silar shigata wannan rayuwar amatsayin Uwa, gashi ta dalilinki nasamu alkhairi inbadan keba, dayanzu nakarama kaina zunubi me yawa,amma se bakibi son zuciyarki ba, kika kareni daga fadawa halaka. Nagode da irin zaman da kikayi dani da yarana. Baba Mairo tace ai bakomai Hjya. Zarah tace zanso kidena kirana da wannan sunan, dan yanzu nazama diyarki, narasa gatana Uwa, inaso kimayemun wannan gurbin dan Allah.

Kwalla Baba Mairo tagoge tace bakomai Zarah dama can ni amatsayi diya na daukeki, Allah yayi maki albarka,kuma Allah yajikan jidda, kallon Umman Sameer tayi tace Umma duk da bansanki ba, amma kinmun alkhairi, nagode maki sosai, Allah yasaka maki da gidan Aljannah. Tace Kawu kaima nagode kayi sanadiyar samun lafiyata.

Sameer kaima bansan dawane baki zan nemi yafiyarka ba, amma dan Allah kayi hkr da duk abinda namaka, kuma kayafemun, nagode sosai da dawainiyar da kukayi mana kaida Saleem, Allah yabiya ku. Suka ce amin. Zarah tace Allah sarki Jidda Allah yaji kanki, banida rabon neman gafararki, nasan banzamo Uwa tagari agareku ba, amma ina rokon Allah ya yafe maki laifukanki, kema Jalila kiyafemun. Kuka tasaka, kowa seda yatausaya mata.

Malam yace to Alhmdllh naji dadi sosai da kuka zamo mutane masu yafiya ga junanku, kuma dama haka Allah yakeson bayinsa masu saurin yafiya akan laifin da,akayi masu, dan duk mutumin da,aka cuta, yana da ikon daukar mataki amma yayi hkr ya yafe tabbas wannan mutumi Allah zesaka mashi da mafificin alkhairinsa. Allah yakara yafemana laifukanmu, yashiryar damu da iyalanmu, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu. Daga karshe Alh, inason inroki wata alfarma agareka, inaso kamar yanda su Baba Mairo zasu zauna agidanka, inaso itama Zarah kayi hkr kabarta tazauna agurinsu, tunda zatafi samun matemaka, akan idan takoma gidansu, tunda shima babanta ba aure gareshi ba, kaga idan Allah yakawo mata miji setayi aure hakan zetemaka mata tasamu saukin damuwar datake ranta.

Kawun Alh, yace tabbas Malam karigani, nima abinda ke raina kenan, kaima Alh, bazeyuwu kazauna haka ba, amma kome kenan, nan da kwana 2 zanzo akwai maganar dazamuyi. Zarah jitayi kamar ta kurma ihu, wai agabanta ake maganar mijinta zeyi aure, ita kuma gata ta nakasa, kilama bazata kara aure ba. Goge idonta tayi aranta tace kaicona. Jalila ma hakanan bataji dadin abinda Kawu yafada ba, taso ace ba saki 3 Dadynta yayi ma Umminta ba, da tasashi ya maidata.

Malam yace to ai semu rufe taro da addu,a ko? Anan yayi masu addu,a yayi masu sallam Alh yabashi kudi masu yawa, yace baze karba ba, Kawu yace a,a ai ba biyanka mukayi ba, kyauta ce yayi maka, anan ya amsa yayi masu godiya yatafi tare da Kawun Sameer. Alh, da Kawu da Mal. Garba suka fito suka nufi part din Alh, Kawu yace kaima Mal. Garba yakama kasamu kayi aure zama babu mata bakaramin matsala bane, sbd akwai lalurar ciwo kuma ga al,amuran rayuwa.

Murmushi yayi yace wlh Alh, ni tsoron ma matan nakeyi, dariya Kawu yayi yace kada kasamu damuwa, idan har kabani dama nizan zaba maka. Yace haba ai yanzu munzama daya, duk wacce kazaba mun nikuma na amince. Yace dama akwai wata diyar kanina da mijnta yarasu yabarta da yara 2 mace da namiji, yanzu haka tana gidana anan take zaune, idan har ka amince zaka aureta, amma kuma da yaranta zata zauna, to? Malam. Garba yace ai babu damuwa, yaro ai nakowa ne, wlh na amince, sede bansani ba ko ita. Kawu yace kamar yanda mukayi maganan nan da kai itama haka tacemun inzaba mata, nikuma gsky nayaba da kai, shiyasa kuma idan bazaka damuba, zanso kabani dama inmaka gyaran gidanka.

Alh, yace a,a kawu kabarni nizanyi wannan aiki, Kawu yace ai ni narigaka, dan haka kaima seka samu wani abun kayi mashi. Har kuka seda mal. Garba yayi, yace babu abinda zance maku se godiya. Alh, yace shikenan nikuma zanbude mashi babban shago wanda zerika kula dashi. Kawu yace yauwa, dan haka bawani daukar lokaci abun zeyi ba. Yace nagode sosai. Kawu yace kaima kashirya kilama tare za,ayi bikinka dashi. Alh, yayi dariya yace haba Kawu niyanzu ai nagama kallon wata mace ince inasonta, inama zan tsaya kallonsu. Kawu yace ato aini harna kallo maka. Dariya suka sa gaba daya.

Baba mairo se lallashin Zarah sukeyi, tace tashi muje kiyi wanka kici abinci, inaso kisaki ranki kada wata cuta tadameki, kidauka kamar ba,ayi komai ba, Jidda kuma addu,a yakamata kirika yimata. Haka suka kamata suka kaita bandaki dan tayi wanka.

Falak taja Jalila daki tana tayi mata tsiya, Jalila tace wlh ke muguwa ce, koma kimun sannu shine daga shigowata ina kallonki kinamun dariya, wai dan Allah ya akayi kika gane? Falak tace yo daga tafiyarki mana. Jalila tace nashiga 3 yanzo kowa yasan abinda yafaru dani, har Dady ko? Falak tana dariya tace ke kwantar da hankalinki ai babu wanda ya kula dake, kinsan hankalin kowa yana gurin Ummi. Jalila tace wash, harnaji dadi, Falak tace to Allah yasa nan da wata 9 musami yan biyu. Jalila ta kaimata duka tace wlh yan biyu su tsaya akanki, Falak tace toshikenan zamu gani ai. Baba Mairo tashigo tace to meza,a dafa ne agidan yau? Jalila tace a,a Baba kibari tunda ina gida indora, tace a,a Jalila daga ganinki bakijin dadi, kawai kibarshi kizauna kihuta. Dariya Falak tayi tace Baba kawai kidafa komai medadi, Jalila tajuya tana gungunai, Baba Mairo tace waini menace ne? Falak tace rabu da ita Baba, Jalila tadauko pillow tana dukanta dashi, baba mairo tayi waje tana dariya. 

Bayan kwana 2 komai yafara dedeta, sede haryanzu Zarah takasa sakin jikinta agidan, duk da Baba Mairo tana kokarin ganin tana janta ajiki, gaba daya sunkwaso kayansu sun maido gidan, zamansu gwanin ban sha,awa Umman Sameer da Baba Mairo sune suke girkin gidan, Zarah kuwa ansama mata sanda hartafara amfani da ita, kuma kafarta tana kara samun sauki, sede aje ayi mata dressing, kuma jikinta yafara haske. Kullum tana cikin jan carbi tana istigifari, sallah akai akai takeyinta. Sameer yace ze kawo mata malamin daze rika kara mata karatu.

Bayan kwana 2, Kawun Alh, yazo, kai tsaye gurin Baba Mairo yawuce, waje suka fito, wata magana suka gamayi, sannan nga sunnufi bangaren Alh, Bayan sungama gaisawa Kawu yace dama nace maka zanzo bayan kwana 2 togashi nan nazo, kuma tare muke da Baba mairo dan ina ganin maganar zefi ayita tana nan.

Bawani abu bane akan maganar auren danayi maka ne, akwai wadda nagani kuma na yaba da hankalinta, bakowa bace se sirukarka, Zaro ido Alh, yayi yace bangane ba. Yace E sirukarka nace, wato mahaifiyar Sameer mijin Falak, tabbas tana da halin kirki inaso kayi hkr ka karbi zabin damuka yimaka nasan bazakayi dana sanin abun ba.

Shiru yayi Baba Mairo tace gsky Alh, nima ina maka sha,awar auren Halima, nina zauna da ita kuma kasan bazan zaba maka abinda ze cutar da kai ba. Amma me kace? Alh, ya sosa keya yana murmushi. Kawu yace shikenan nagane, kuma naji dadi daka amince, insha Allahu kasamu wadda zata share maka hawayenka, Allah yabada zaman lafiya, kuma insha Allahu nan da asabar mezuwa za,a hada dana mal. Garba, kaga tsohon sirukinka da kai zaku Angwance arana daya. Dariya Alh, yayi yace kai kawu. Godiya yayi masu.

Haka Baba mairo tasamu Umman Sameer da maganar, amma da kyar ta amince, dan cewa tayi tana jin kunyar Zarah, Baba Mairo tace bakomai zanyi mata bayani kuma nasan zata amince. Zarah wadda take jin duk abinda suke fada dan tazo zata shiga falonsu taji suna magana. Kuka kawai takeyi tana kara tsanar Asabe da kuma irin halinta, share idonta tayi, tayi sallama tashiga, bayan tazauna tace Baba Mairo kuyi hkr naji duk abinda kukace, nazo shigowa naji kuna magana amma wlh ba labe nayi maku ba. Umma kada kidamu babu komai, koma menene nina jama kaina, kuma zanfi son ace kece kika auri Alh, akan yaje waje yasamo wata, Allah yabaku zaman lafiya. Fita tayi tana kuka. Baba mairo tace tokinji abinda tace, Halima tace shikenan, Allah yazaba mana abinda yafi zama alkhairi.
     Baba Mairo tace amin, dan haka kinga saura kwana 5 daurin auren kuma da an daura zaki tare, dan haka dole ingyaraki dan bawai tsufa kikayi ba, kawai rashin gyarane, murmushi tayi ta tashi tafita. Kowa yaji dadin wannan hadi da akayi, duk da Jalila bataji dadi ba, amma kuma taji dadin da akace Umma Alh, ze aura dan tasan halinta.

Haka akayita shirye shirye Umman Sameer cikin kwana 5 tayi kyau sosai tafito mace me kyau, dan komai yana son gyara. Sameer se tsokanarta yakeyi yana cewa dama Ummanshi tana da kyau amma batason yin kwalliya, itade sede tayi ta murmushi. Sameer yazo gurin baba Mairo shida saleem yace gsky Baba ana daura auren su Umma nima zandau matata mukoma gida, dan gsky abun da kunya. Saleem yace hakane Baba dan Allah kibarsu su koma. Tace to ai shikenan, dama ita nake tausaya mawa, tunda kace ku koma se kutafi amma wlh karika dawowa dawuri, yace angama Baba Mairota. Dariya tayi, sukayi mata godiya.

Ayau asabar aka daura auren Alh, Abba Bala da Halima kan sadaki dubu 30, se Mal. Garba da Samiyya suma sadaki dubu 30, kuma aranar aka kai kowa gidanta, Kawu yayi kokari na gyran gidan Mal. Garba, gashi Alh, yabude mashi babban provision store, haka aka kai amarya Samiyya sede ance yaranta sedaga baya za,a kawosu.

Halima ma Alh, yasa mata kaya adakin Zarah, ita kuma aka maida mata kayanta can part dinsu, akace idan su Falak suntafi seta koma dakin falak, aranar zarah ko abinci bata ciba, tana dakinta takasa fitowa, kuka kawai takeyi, seda tabama kowa tausayi, amma kuma ita tajama kanta.

Bayan kwana 2 da biki Sameer yadauki matarshi suka koma gidansu, wanda yakara shan gyara kamar wata sabuwar amarya, tayi mamaki sosai ganin irin gyran da yayima gidan, haka suka bude sabuwar rayuwa.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya cike da jindadi Alh, yanajin dadin zama da Halima, shikanshi yasan yanzu yana cikin kwanciyar hankali, har mantawa yakeyi dawata Zarah, dan koyaje gaida baba Mairo bata barin su hadu, shima baya nemanta, yana bama Baba Mairo girma sosai kamar ita ta haifeshi, kuma yahanata yimasu girki, yacika masu store da komai na abinci yace suyi iyakar nasu, bayaso ta wahala. Jikin Zarah kam ya warke, har ancire daurin kafar tazama dungulmi, sede haryanzu bata maida jikinta ba, dan kullum cikin kuka take, da tunani, sede kawai bakin datayi ne yaragu amma duk wanda yasanta ada yanzu baze iya gane taba. Malamin da Sameer yasama mata yana zuwa yana mata kari kullum, tamaida hankali sosai gurin koyon karatu.

Bayan shekara daya Jalila tahaifi yaronta me kyau aka samashi sunan Mahaifin Saleem, suna kiranshi da WALEED.Taro yayi kyau, yaran Falak sunyi wayau sosai, kamar sunfi shekara daya, kuma alokacin ne tafara laulayi, bayan suna sukaje asibiti, likita yace bakomai zata iya cigaba dabasu nono, amma tafara basu abinci, idan cikin yayi girma seta ciresu.

Halima ma tasamu ciki wanda haryayi girma, Alh, bakaramin farin ciki yayi ba, ganin zekara samun haihuwa. Zarah ma jiki yayi kyau, tafara dangana, har tafara kiba, kullum Baba mairo cikin kulawa da ita takeyi.

Ayau Halima ta tashi da nakuda sede har Alh, yafita bata fada mashi ba, sede takira Baba mairo, tana zuwa ta temaka mata, cikin lokaci kankani tahaifi danta namiji, Baba mairo tayi mashi wanka ta gyara gurin itama tayi wanka sannan aka kira Alh, akace yazo an haihu, lokacin dayazo yaga abinda aka haifar mashi seda yayi sujada yagodema Allah, har kwallan farin ciki seda yayi. Zarah ma tayi farin ciki, kuma tazo tayi mata barka, dan bata shigowa gidan idan Alh, yana nan.

Bayan kwana 2 da haihuwarta Samiyya matar Mal. Garba ma ta haifi mace, zarah bakaramin jin dadi tayi ba, haka tashirya ita dasu Jalila da Falak sukaje barka, Aranar sunan halima bakaramin kashe kudi Alh, yayi ba, seda ya yanka manyan raguna Biyar, taro yayi taro, yaro yaci sunan Alh, Abba, dan yace sunanshi zesama yaron za,a kirashi da KARAMEE. Bayan kwana 2 akayi sunan Samiyya, itama tasamu alkhairi sosai.

Cikin Falak yana wata 6 ta yaye yan biyu, aka kaisu gurin Baba mairo, haka suka cigaba darenon cikin Falak, harya kai lokacin haihuwarshi, da dare suka nufi asibiti, suna zuwa ta haifi yaronta me cike da lafiya, nan Sameer yarika kiran waya yana fadama mutane, bayan ta huta aka sallameta, suka dawo gida.

Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Sameer Abdullahi ana kiranshi da SUDAIS, Falak ansha kyau sosai, dan takara zama babbar mace, haka taro yatashi cike da farin ciki.

     Bayan shekara 2 an maido su Ameer da Ameerah gida, har ansasu makaranta, kowa yagansu yana sha,awarsu, domin suna matukar kama, gasu kyawawa, Jalila takara haihuwa tasamu mace, aka samata Zarah, suna kiranta da AMAL, shima   Waleed an saka shi makaranta, hada Karami ma Alhn yasashi makaranta, dan itama Halima wani cikin gareta.

Haka rayuwar Zarah tacigaba da tafiya agidan Alh, kullum jinta takeyi kamar tana kurkutu, idan tayi tunanin komawa gidan ubanta setaga gara tayi zamanta, dan batada daki agidan, gashi de tana cin abinci mekyau, amma kullum kamar ana dibarta, Baba Mairo harta gaji da lalllashi tasa mata ido, shiyasa yanzu idan zatayi kuka seta shige daki sannan, amma duk da haka da baba Mairo ta ganta seta gane tayi kuka sede kawai ta kyaleta. Ga Son Alh, dayake hanata bacci, batason tana sonshi dayawa hakaba seda tarasashi, kuma taga yayi aure, wani lokacin har labewa takeyi idan yashigo tayi ta kallonshi. Zama tayi bisa gado tace Oni zarah, yanzu wai nice haka, lallai rayuwa ta koyamun hankali, Danasani nayi hkr da Hajjo munyi zaman mu Da yanzu nasan nazama wata babbar Hajiya.

Danasani banyima Alh, asiri ba, dayanzu ina nan da kafata lafiya lau, Danasani ban dauki shawarar Asabe ba, dayanzu bnshiga wannan kangin ba. Ya Allah kaji tausayina ka kawomun karshen wannan zaman danakeyi.
   Allah kashirya duk masu irin halina ya Allah. Kwanciya tayi tana kuka me tsuma rai.

     Nikam dariya πŸ˜„πŸ˜„nayi nace Zarah ada kenan, dama ai Danasani keya ce.

Wata bakar jaka Falak tadauko taciro wani abun hannu, tadawo 
kusa da sameer tazauna, yana kallonta, tace Ameerah zonan, hannunta takama tasaka mata abun hannun, Ameerah tace lah, Momy ke kika siyomun? Kwallan idonta tagoge tace a,a Grandmother dinki ce tace inbaki, Ameerah tace toyaushe zan ganta? Sameer yajawota yace kin kusa ganinta kinji. Ameer yace Dady nito ina nawa? Tashi yayi yadauko wani karamin agogo yace kaima ga naka, yace toni wayace abani? Murmushi yayi yace kaima GrandFather dinka yace abaka, tashi sukayi suna tsalle, sukace Thank you Momy and Dady, waje suka nufa suna murna.

 Jawo Falak yayi yace haba my dear kin manta kince bazaki kara kuka ba, tace dole inyi kuka my Luv.

Kawai natuna wani abune, wai yau nida ake kira AGOLAH, nice nake zaune da yarana har 3, suke kirana momy, agaskiya ina tausaya ma duk wata AGOLAH datake AGOLANCI awani gida, Allah yajikanku Umma da Abba, badan narasa kuba da babu wanda ze kirani da AGOLAH, har yau idan natuna sunan nan yanamun ciwo.

Sameer yace banaso kina rike abu aranki, kinmanta kince kinyafe masu? To kibar tuna abun, komade menene yanzu gashi kin daukaka, ayanzu kina sama da ita kuma ita tana kasa dake, kuma kinmata nisa, sosai. Yanzu albishirinki. Tace goro, yace hajjin bana tare za,ayi damu. Tsalle tayi ta rungumeshi tana murna tace wow amma gsky kayimun babban albishir, bansan ma dame zan gode maka ba. Dariya yayi yace ni ai nasan da abinda zaki godemun, kuma Falaka, kinfi haka agurina, kece farin cikina, kin bani kyautar yara har 3 kina kula dani yanda yakamata, nine zance bansan dame zan gode maki ba. Amma yanzu tashi mushiga ciki kibani goron albishir. Tashi tayi tana dariya tashige daki.

ALHAMDULILLAH

Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mesuna AGOLAH.  
   Kuma ina mika sakon gaisuwa meyawa ga dukkanin masoyana nagode da irin kulawarku gareni. Allah yabar zumunci, abinda nafada da kuskure sekuyi hkr dan dan Adam ajizine.

Nasadaukar da wannan littafi ga mahaifina, ALLAH YAJI KANSHI DA RAHAMA AMIN, ALLAH YAJIKAN DUKKANIN MUSULMAI BAKI DAYA, MUKUMA IDAN TAMU TAZO ALLAH YABAMU GUZURIN TADDASU.ALLAH YAKAREMU DAKA SHARRIN ZUCIYA YASA MUFI KARFINTA AMIN.


Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
 (Nabeelert Lady)
08028525263

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *