Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, October 20, 2018

abadan complete hausa novel 1

adsense here
abadan complete hausa novel

abadan complete hausa novel

Muhammad kabir
Documentation work shop
08160112181

[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺 *DA 'IMAN*🌺
🌺🌺🌺🌺🌺🌺  *written by safiyya Abdullahi musa huguma*     
💖💖💖💖💖💖💖
           🌺🌺
              🌺



            ⏯1⃣



A hankali ta tsallako tatitin kai tsaye kuma ta shige dogon layin dake gabanta,ta dubi tsahon layin duk da yawan al'ummar da yake da shi a dade yake babu kowa tankar anyi shara,hakan baya rasa nasaba da irin ranar da ake kodawa kamar mutum yaa dora hannu akansa yace wayyo Allah


sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta


babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan na bata haushi


ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’
‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan
hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin tsaki
''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba''
''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa''
cike da masifa hauwa ta qwalalo ido
''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?''



ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto''haba kulu na,wata kai yake a gurina ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?''
duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da tadinsu


sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya cikin farar leda tana lodawa a botiki


bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana'ar tasu wato yada habaici da baqaqen maganganu
''hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin uwa kayi zamanka''
''kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu kai da cewar kyakkya wa,bace 'yarsu?,ai dole su maisheta jari''
''hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za'a dire abun kunya cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa''


duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu


isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace''haba isyaku me yasa baku iya tafiya ne a hankali?''
baki ya murguda ya galla mata harara
''eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin gida''
ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya gaga tana fadin
''ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai kanshi to zamu kwashi 'yan kallo dake wallahi''


bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin
''kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne''
gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin gidan
''kai kai lafiya?''
''yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi yarranmu?''ya katseta da fadin
''to yanzu me kuma ya faru?''
''wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da kaina''


''kai isyaku me yasa haka''
''baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama''
''ke *maryam* bashi haquri''
babu yadda ta iya haka tace kayi haquri
shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura
hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah


ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji maman tace
''na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne cikin gidan nan''wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin
''mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehaving,yanzu mama kamar isyaku fa qanin bayana mama?''
''ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke bane''
cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa lamuranta ga Allah
''to mama''shine abunda ta fada a sanyaye



*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
 💖 *ABADAN*💖
    🌺💖🌺💖🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
    🌺💖🌺💖🌺
         🌺💖🌺
           🌺💖
              🌺


*assalamu alaikum masoya,xaku ga nun canzs sunan littafin mu zuwa ABADAN,haka ya faru ne sakamakon yin wani littafi a baya mai wannan sunan,ina muku fatan alkhairi*


    
          ▶2⃣


Hundatu ce tayi sallama ta shigo rumfar sanye da unifoam ruwan tsamigaye riga da zani sai farin hijabinta kafadarta rataye da jakar makaranta fara,tana cire takalminta hade da socks tace
''anty maryam ya na ganki yau a gida da wuri?''
dan dafe kanta tayi kadan tace''yau da wuri na kammala aikin ne shi yasa,kuma dama bana jin dadi sosai''
cikin nuna damuwa ta zauna saman kujera
''sannu antin mu,ko na karbo miki magani?''
murmushi tayi har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana
''idan banda abun hindu wanne me chamist za'a samu da uwar ranar nan?''
ta dage gira''haka ne fa anty''
''ki duba locker kusa da gadona akwai paracetamol ki dauko ki sha,tuntuni da kika shigo baki gayamin ba har kika tsaya fada da mutane ko?''


ta karyar da kai ''ayyah maman mu ba haka bane,sallah kinga muka gama yanzun ai''
''dawa antin tayi fada mama?,wannan maras kunyan ne isyaku ko?''
''shine mana''
a fusace ta miqe zata fita maman ta yi kiranta
''ina kuma zaki?''
''mama don Allah ki barni naje naci uwar yaron nan don Allah,yayi matuqar raina yaya maryam,dan iska mara kunya kawai''
''ko da wasa naji kinje gurinsu sai na sabarmiki''
ba haka taso ba amma babu yadda ta iya haka ta wuce daki tana kumbure kumbure ta sauyo unifoam dinta ta dawo dan kitchen dinsu wsnda daki ne gudun tashin hankali suka maida shi kitchen ta zubo musu shinkafa da miya da salad da maman tayi a faranti daya,duka suka sa hannu 


hindatu tace''dama zamu samu ruwan sanyi yadda ake zabga ranar nan wlh''
''ai insha Allahu da na dauki albashina,zan siya mana qaramin firji''
cike da doki hindatu tace
''eh wlh yaya''
mama ta dubi maryam din''yanzun maryam ba zaki yiwa kanki fada ba?,bama zancan aure kike ba zancan siyan firji kike ki saka mana,duk yadda mutane ke maganganu tamkar ma ke din baki damu ba maryam?''


duk sai taji abincin ya fice mata a ka,ta sunkuyar da kanta,Allah ne kadai yasan abinda take ji a zuciyarta,itakam tasan ba domin mamanta bata sonta take mata wannan fadan ba,tana yine sabida qauna,ita din ma da za'a tona zuciyarta tabbas babu dadi


🎄🎄🎄🎄🎄🎄

Zaune take cikin rumfar tasu wadda ke da madaidaiciyar yalwa,kujeru ne one sitter two sitter da kuma three sitter masu dan sauqin farashi,falon malale yake da tyles ruwan madara da labulaye suma ruwan madara masu sauqin kudi,sai kayan kallo da suka hada da t.v ta xaune da d.v.d,komai na falon madaidai cine dai dai talaka wanda albashin maryaman ne da qoqarinta ya kai falon ga zama haka


kusan kaf gidan babu muhallin da yakai tsaftar nan,ko yaushe zaka sameshi a goge qal yana qamshin turaren garwashi ko na tsinke,hakan ke qara haddasa qiyayya da kishi mai zafi tsakanin mama *amina* da sauran abokan zamanta


sanye take da pakistan riga da wando wanda rigar tasa ta kai mata har gwiwa,dan kwalin pakistan dinne daure a kanta,duka hankalinta ta tattarashi kacokam kan wayarta da tayi googling din wasu sabbin girke girke,shirun da dakin da ma gidan baki daya da yayi shi ya qara mata nishadi da fahimtar abunda take karantawa,


sallamar da ta jiyo anayi cikin tsakar gidan ita ta ja hankalinta,ta sauke wayar tana amsawa tare da cewa ''a shigo''
mai sallama ta sake maimaitawa lokacin da take shigowa rumfar tasu,da sauri maryam ta sauke wayar a gefanta fuskarta dauke da murmushin farinciki wandayayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta ta miqe
''radiya..saukar yaushe kenan mutanen south africa?''
harara wadda aka kira da radiyan ta cilla mata
''hmmm,babu wani nan,wlh baki da abinda zaki kare kanki da shi,yanzu ma ni ba gunki nazo ba,mama na kawowa jikanta ta ganshi''
''oh ni maryama,laifi baya qaremin,me kuma nayi''ta fada cikin murmushi da dafe kai
harararta dai ta sakeyi''kinfi kowa sanin laifinki maryam,sati na guda da dawowa qasar nan amma ko mai kama da ke ban gani ba,ina dira nigeria kece ta farko da na fara yiwa tex amma ko matsayin reply ban samu ba''


''yanzu dai yo haquri don sonki da annabi ki zauna tukun,don mama bata nan ta tafi kitso''ta fada tana karbe kyakkyawan baby boy din dake sabe a kafadarta,tare suka zauna idon maryam na kan yaron''masha Allah laquwwata illa billah fadil''yana kan kadarta ta shiga kitchen din su ta dauko mata ruwa da lemon sobo cikin fridge din da daqyar ta shawo kan mama da dadin bakin hindatu aka siyoshi suke lemon siyarwa a kuma fita kunyar baqi idan anyi


''bismillah''tace da ita bayan ta tsiyaya mata lemon
''bani dana kawai na wuce''
''haba sister,kada fa ayi mana dariya a ganmu a rana''
''ke kika jawo hakan ai''
''kinsan Allah banga saqonki,ki yarda dani bani da lokaci wallahi yanzu isashshe idan ba weekends ba saboda aiki''
da qyar ta samu ta shawo kan radiya bayan ta mata alqawarin zuwa mata a wannan weekend din wanda daga nan suka fada hirar duniya


radiya ta ajiye glass cup din bayan ta kalli maryam
''maryam har yanzu dai batun aure shiru?''sakin ajiyar zuciya tayi sannan ta tabe baki
''hmmm,barni kawai radiya,samun miji na gari yanzun ya zamo wuya,mazan yanzu duka 'yan garari ne,yawancinsu ba aure ke kawosu gurinki ba''
''anya maryam,bana manta fa yawan samarin da kike da su tun muna school''
''radiya kenan......manta da wannan,na fada miki yawa yawansu ba don Allah suke sonki ba,sun lallabo ne kawai su kwashi abunda suka kwasa na rasa wannan masifa kamar hadin baki?kamar ni kadai sukewa haka,ke dai ki sani kawai a addu'a radiya''ta qarashe maganar muryarta na dan rawa alamun kuka keson zuwa mata
''shikenan maryam,insha Allahu na miki alqawari ba zan fasa sakaki cikin addu'o'ina ba,komai yayi farko yana da qarshe''


a hankali suka fada wasu hirarrakin nasu a haka maman ta cimma su,tunda ta dauke fadil bata dawo da shi ba sai da zasu tafi,sabulai ta bawa radiyar sinqi biyu da turare,hannu biyu amsa tayi mata godiya sannan maryam ta amsheshi ta biyo radiyan qofar gida don raka ta
''ke da nasir fa muka zo''
cikin mamaki take kallin radiyar''amma baki da mutunci,ki bar bawan Allah a mota duka lokacin nan yana zaman jiranki''
fuska ta yatsina''rabu da shi,fada mukayi da shi sulhu yake nema shi yasa''
''Allah ya shiryeki radiya ''abunda ta samu ta iya fada kenan don sun qaraso gaban motar''


gidan gaba ta shige ta dora mata fadil saman cinyarta suna gaisawa da nasir din
''munfa yi fushi maryam gaskiya''
sassanyan murmushinta tayi''to ayi haquri tunda na wanke kaina next week ina tafe insha Allahu ranan sunday''
''to Allah ya nuna mana''
sallama sukayi ta koma cikin gidan radiyan na jaddada mata ta cika alqawari fa




tana cusa kai gidan suka ci karo da *BINTA*
dauke da botikin awara zata fita inda aka fi kaurin,maryam dince ta fara ja da baya don tasan bata qi ta bangajeta ta wuce ba,duk da hakan ma dai bata tsira ba daga tsaki da harar da qanwar bayanta ta saba jifanta da su ba koda zasu hada hanya ne sau miliyan


ta rasa me ra tsarewa yaran da iyayensu,gaba daya anbi an cika zukatansu da qinsu,qannenta ne duka amma babu daya dake ganinta da gashi,saidai duk da haka rashin mutunci wani yafi na wani
ga tsantsar rashin tarbiyya da qin karatu da aka dasawa zucoyoyinsu,ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa suka zabawa kansu,da wannan tunanin ta qarasa  falonsu ta zube saman kujera tana rowon Allah daukinsa kan halin da take ciki



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
 💖 *ABADAN*💖
    🌺💖🌺💖🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
    🌺💖🌺💖🌺
         🌺💖🌺
           🌺💖
              🌺






           ▶3⃣





sanye take da material silk dark pink wanda aka yima ado zane na qaqen flowers manya,yayin da ta yane kanta da mayafi baqi tayi rolling dashi wanda ya maisheta tamkar jinsin larabawa,qaramar jaka ta sagale a gwiwar hannunta sai baqin toms mai kyau,sosai shigar tayi mata kyau tamkar bata da wata matsala a rayuwarta


a rumfa ta tadda mama tayi mata sallama tace mata a dawo lafiya ta gaida fadil da mamarshi,suna zaune a tsakar gidan kamar ko yaushe ko wacce ta maida hankalinta kan kayan sana'arta,wanda da zaki tambayesu suk cikinsu babu wadda zata iya gaya miki taqamaimen inda yaranta suke,sana'arsu ta fiye musu komai


da sauri ta fara qoqarin ficewa daga gidan don bata fatan daya daga cikinsu ta,ganta balle ta jefeta da kalmar da zata bata ranta,saidai duk iya saurinta bata ci nasara ba sai da huwaila ta ganota
''uhmmm,mutanen burtali,an fita kenan''
bata fasa sauri don ta fice a gidan ba kamar yadda bata ko waiwayo ta dubesu ba


cikin soron sukayi kacibus da *AZARA*,qanwar ta ce ta hudu wadda  tayi aure da yaranta uku,ba laifi mijinta na iya bakin qoqarinsa duk da wasu abubuwan bai iya dauke nauyinsu,sai kuma Allah ya hadashi da mace mai izgili izza da rainuwa,azara akwai rainuwa da izgili saidai ba laifi rashin kunyanta da sauqi akan ta sauran yaran,tunda ko babu komai idan sun hada zata tsaya su gaisa koda zata jefeta da habaici a fakaice


yanzun ma hakance ta kasance,fuskar maryam din fadade da murmushi ''maraba da mutanen fanshekara(unguwar da take aure)''ta fadi tana miqa hannu zata amshi yaron axaran yaqi zuwa saboda dan banzar qiwar da yakeyi,azaran tace
''hmmmm,sannunku kuma''
''azara yaron nan qiwa yake haka?''
''ko ba ya qiwa aike yayi miki tunda ba ganinki yake ba,mu ko nsmu gidan ba'a zuwa saboda bamu da komai''
murmushi maryam tayi,don ta fahimci inda tasa gaba
''ko daya ba haka bane azara,kinsan bani da lokaci sai weekends,to su din ma sai wani zarafin ya shigo ya cinye wunin naka duka''ta kawar da maganar don kada tayi nisa ta hanyar cewa
''ina sauran yaran?''
''kunun aya ne bai qare ba na,barsu su qarasa saidawa don kada ya lalace shi yasa ma ban taho da su ba''


wani abu ya tokare maryam,wato irin rainon da aka mata shi zata yiwa nata 'ya'yan,a maimakon ta bata amsa da sun tafi islamiyya don a yanzu lokacinta ne sai tage gaya mata ta barsu gun talla?,du du du yaran nawa suke?,kamar tayi mata magana kuma sai taja bakinta ta tsuke don kada cibi ya zama qari
''sai ina kuma?''azaran ta tambayeta bayan ta gama qare mata kallo
''wallahi zani gidan raliya ne''
''hmmm,babban goro sai magogin qarfe,su ai sun isa ayi da su din,bari na qarasa ciki ko,sai kin dawo''
danne zuciuarta tayi ta murmusa
''to shikenan,idan na dawo na tadda ke to''
''o'o,anya zaki tadda ni kuwa,wannan fitar taku ta manya wa yasan ranan dawowarku''
''to ki gaida gida''
''gida zaiji''


tana tafe a layin zuciyarta cunkushe da tunane tunane,hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta dinga karantawa har ta iso titi,akwai qarqncin motocin haya kan titin nasu ko kuma ace kusan duk wadda tazo cike take da 'yan makarantar boko da suke dawowa gida,kusan motoci uku ne suka tsaya don bata lift saidai ko kallo basu isheta ba,hakan,na yawan faruwa da ita kasancewar unguwar nasu na maqotaka da unguwar nasarawa G R A,duk sanda hakan ta faru takan yawaita neman tsarin Allah,sannan takaici mamaki gami da tsoron maza kan sake yawaita cikin zuciyarta,basu da burin da ya wuce suga sun samu damar da zasu shiga rigar mutuncinki su wuce su barki babu batun aure


da qyar ta samu wata da yara yan makaranta biyu a ciki,ta masa kwatance inda zai ajjiyeta


cikin murna raliya ta tarbeta,cikin falonta suka zube bayan ta cikata da kayan ciye ciye suka hau hirarsu da bata qarewa fadil na bisa cinyarta,
''kinga kawo fadil din na riqe miki shi tunda yayi bacci ki samu kici wani abun,idan ba haka ba bazai barki kici komai ba''
''a'ah qyalemin shi''
cikin haka wayar raliyan ta soma tsuwwa,ta cirota ta duba screen din tana fadin ''abban fadil ne''
magan sukayi ta tsawon minti biyar sannan ta kashe tana duban maryam bayan ta miqe
''yace yana miki sannu da zuwa,bari,na saka miki wani film ya dan debe miki kewa ni shiga kitchen ya kamani,abban fadil ne zaiyi baqi''
''haba kema raliya naji zancan shiga kitchen kuma na zauna,ai kinsan sai anyi da ni''
''sannu uwar madafa''ta fada cikin zolaya
''na karba,ko kin manta kan abinda na samu degree kenan''
''wannan gaskiya ne,bani fadil din to na kwantar da shi sai mu wuce kitchen din ko?''


qarfe hudu da mintina ashirin suka kammala,lafiyayyen girki ne wanda maryam ta gwada basirarta akai,ita kanta raliya komawa tayi gefe tana kallonta don bata zaci qawar tata takai haka ba,biyar saura ta suna falo,ta soma hada kayanta don tafiya gida ''amma diyana(haka suke kiranta wani lokaci a makaranta)ki sake wanka mana wannan aiki da kika sha''
''ai dole ne,amma fa idan na isa gida''
''ai ko wlh anan zakiyi''
murmushi tayi wanda har dashashinta sai da ya bayyana
''kinsan dai bana wanka na maida kayan da na cire,ni kuma ban taho da spare ba''
''tsarabarki ta south africa tana nan,saiki zabi daya a ciki kisa''
duk wayon,maryam sai da raliya ta sata yin wankan ta kawo mata ledar tsarabar ta zabi doguwar riga guda daya da tasha adon jajayen dutsina masu yawa da sheqi


a falo ta taddata''kinga kuwa maryam yadda rigar nan ta miki,Allah ya kawo miji na gari,gaskiya ba qaramar hidima zamu sha ba''
''har yanzu babu abinda ya ragu a surutun raliya''
''haka miskilanci kyau da ajin maryam diyana har yau yana nan''duka sai suka sa dariya,yana daya daga abinda ya sa qawancensu ke ma maryam dadi,raliya akwai vbarkwanc,inda kuma halinsu yazo daya ta bangaren haquri da dauke kai


qarar bude get din gidan ne yasa suka ankara da isowar abban fadil
''kinga har sun iso ina nan a zaune,biyar harda kwata''maryama ta fada tana miqewa
''kinga malama koma ki zauna tunda sun riga sun iskemu tare ai bakya tafi ba,ki bari mu tari baqinmu qarasa ladarmu tare''babu yadda ta iya haka ta koma ta zauna,ta fiddo wayarta tqna yiwa hndatu texs ta sanar da mama tana nan tahowa raliya ce ta tsaidata


tana cikin sending sallamar baqin ta ratsa dodon kunnenta,a sanyaye ta dago tana amsawa,su uku ne abban fadil na hudu,duka sai taji ta a takure gashi raliya ta shiga ciki sako mayafi,sai ta miqe tana daukar jakarta tace
''sannunku da zuwa,abban fadil yanzu raliyan ta shiga ciki bari na mata magana''
dakatar da ita yayi
''a'ah yi zamanki,nasan a gajiye kike kunsha aiki bari na fito da ita,jabir bari na fito da madam''


falon yayi shiru su duka harda baqin,wayarta na hannunta tana danne danne amma sai take jinta a takure,gashi daga raliyan har nasir din shiru kamar an shuka dusa
''madam haka ake kula da baqi?''
tajiyo maganar lokaci guda,ta daga kanta don ganin me maganar,shije zaune opposite dinta,sanye yake da shadda hartin da hula,murmushi ta danyi a taqaice
''ai bani bace matar gidan,ku jirayi fitowarta''
''ke da ita din ai daya ne,don na tabbata yarda ce tasa suka barki da baqinsu''
sai ta maida idonta kan wayarta don bata da abun ce masa,Allah ya taimaketa masu gidan suka qaraso


gaishe gaishe ne suka biyo baya da 'yan hirarrki,saidai duk lokacin da bisa kuskure idonta ya kai sashen da wanda ake ka kira da jabir sai ta tsinci idanunsa na bisa kanta,wanda hakan har ya fara damunta,nasir ya musu jagora zuwa dining domin cin abinci hakan yasa ta cema raliya
''to ai na gama ko,bari na wuce gida''
''tunda ba da mota kika zo ba ki bari mu kammala sai mu wuce tare ko?''
ta jiyo muryar jabir din na fadi
''kasan kuwa kusa da unguwar take ba''inji nasir
''haka,ne fa,shikenan kin huta hawa keke napep''inji raliya
''amma kinsan baxaiyiwu su kaini gida ba,idan mama ta ganni kuma nace mata su waye?''
''indai mama kike ji zan kira tq na gaya mata''inji raliyar


cikin zuciyarta ta ja tsaki,
''wannan jabir dan shiga hanci ne wlh''babu damar musu tunda duka ido na kanta haka ta koma ta zauna tana jira su kammala,yana bisa dining din amma idanunsa na kanta har raliya ta ankara,cike da gulma ta tabota
''ke,inafa tsammanin kinyi tsuntuwa yau a gidannan''
cikin rashin fahimta tace
''ta me fa?''
hararta tayi ''kiji min 'yar rainin sense,kina nufin baki lura da irin kallon da jabir ke miki ba?''
''shine me?''
''wlh sonki yake bisa dukka alamu''
wannan karon ita ta maida nata hararar''kijimin mata,kawai daga kallon sarkin fawa sai miya tayi zaqi?''
''wlh da gaske nake,jabir mutumin kirki ne diyana,kada kice zaki qishi don Allah''
''a'ah,kinji ta da wani guntun wa'azinta,ashe har yace miki ma yana sona ko?''
''ni na gaya miki zai fada miki''


Can saman dining dinma jabirne ke cewa cikin qasa qasa da murya
''kai mutumina nifa nazo gidanka a sa'a,Allah yasa bata da wani''
dariya ya saka''tuni na harbo jirginka ai,indai bilkisu ce a iya sanina ba'a tsaida mata miji ba''
''ai kuwa bazan tsaya kallon ruwa ba,a yau zan kafa kaina''


A bakin layinsu tasa ya tsaida motar,ta bude murfin tana cewa 
''na gode''
''haba madam da sauri haka?''
sai ta juyo cikin mamaki tana dubansa
''eh mana,ya zaki min illa kuma ki tafi ki barni ba tare da kin bani magani ba''
ci gaba tayi da dubansa,sai ya saisaita nutsuwarsa,baiji ko,nauyi ba ya bayyana mata duka manufarshi,da farko ta ja masa yace shikam yace baisan wannan zancan ba,babu inda,zata tafi ta barshi cikin qila wa qala,idan,ko ta tafi to zai tare ne a qofar gidansu har sai ta amsa masa koda zai shekara


maganar da sukayi da raliya ce ta fado ranta
''maryam,wlh indai aure kike so kiyi kada kiqi karbar tayin jabir matuqar yayi miki maganar,jabir bazai taba tararki da maganar banza ba,nasan jabir tuntuni,abokin nasir ne da dewa,halayensu kusan daya,hakan shi ya qara danqon abotarsu''
ita kanta a zahirance bata ga wani aibu ba tattare da jabir din,yana da kyau daidai wanda duk hassada ba zaka kira shi mummuna ba,a iya abinda ta gani da bayanan da raliya ta mata ta fuskanci zata iya amsa tayin jabir,ko don ma ran mahaifiyarta yayi fari,ko don ta samu itama ta zauna a nata dakin kamar sauran qawayenta da 'yan uwanta


ganin shirun nata yayi yawa yasa ya sake marairaice mata ga tsammaninsa zata wofantar da buqatarsa ne
''shikenan,Allah ya shige mana gaba''
''um um maryama,wannan ba amsa bace,kice ina sonka jabir shine magana''
kanta ta girgiza cikin alkunya tace''don Allah ka barni na wuce gida,na tabbata zan sha fada gun mama,don na kai magariba a waje,tunda ka kwaahe min numbers ai sun isa''


fitowa yayi ya zagayo ya bude mata murfin yana cewa''shikenan,kin bani izini na kiraki?''
kai ta gyada masa,kafin ta dauko jakarta yayi sauri ya rigata ya bude zif din ya jefa mata kudi,ta noqe alamun ba zata amsa ba shi kuma yace indai bata karba ba to tana nufin bata sonshi,tilas ta karbi kyautar tasa,sukai sallama amma sai taga ya ja ya tsaya,kallonshi tayi ya daga mata gira
''sai na hango,shigarki gida don tsaron lafiyarki da kuma gane gidan naku koda na tashi zuwa''
murmushi kawai tayi tajuya domin shigewa layin nasu


katsam idonta kan isyaku,kai ya gyada sannan ya kwasa da gudu yayi gida,la'ilaha illa nata subhanaka inni kuntu minaz zalimin,tasan tamkar a idanun iyayenshi tayi,cikin fargaba taci gaba da takawa jabir na mata rakiya da idanu har ta shige gidan



*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📓✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺





              ▶4⃣





sai da tayi dira dira a soron kafin ta gano ainihin hanyar wucewa,saboda cike yake da 'yan zance,can hauwa can binta can maijidda kai abun takaicin ma harda zainabu wadda du du du ba zata wuce shekaru goma sha hudu ba kacal a duniya
ta tsakiyarsu ta raba ta wuce,taji dadi sosai da babu wadda ta tanka mata a cikinsu


cirko cirko ta samesu a tsaye cikin tsakar gidan,inna hadiza ce da baba huwaila sai babansu dake bakin famfo yana daura alwala da alama haramar sallar isha'i yake yi,sai kuma isyaku dake qame a gefe da alama tuni ya gama fesar da abunda ya qunso
''la ha ila ha illallahu,muhammadu dan abdullahi''suka dauko salatin tare yayin da huwaila ta dire ita daya ta kuma dora
''wlh yaya da gaske ne yaro baya qarya,tayani gani don Allah,suturar jikinta ma ai ba da ita ta fita ba,lallai dandi na dada samun gindin zama a gidannan''


inna hadiza dake ta faman gyada kai tana kallon maryamu wadda ke tube takalmanta a qofar dakinsu ba tare da ta dubedu ba tace''qwarai da aniya,ya gama yawon barikin da ita ya kwashi na kwasa ba dole ta canza sutura ba,yo zata shigo mana gida ne da najasa ne''
''ke meramu zo nan''
kiran baban nata da baqin qazafin da suka jefeta da shi ya daki zuciyarta lokaci guda,a sanyaye ta dawo gabansa ta durqusa kanta a qasa
''wanne dan iska ne ya dauko ki a mota har gidan ubanki?''
muryarta a sanyaye tace''ba dan iska bane baba,gidan raliya muka hadu yace yana sona''
''yana sonki?''
huwaila da hadiza suka fadi kusan a tare


bai biya ta kansu ba ya dora da nashi bayanin
''alhmdl dama ni na gaji,na gaji wallahi kullum rana a unguwarnan sai anyi da ni kan na ajjiye babbar mace a gida,saboda haka ki shaida masa matuqar da gaske yake to na bashi kwana goma ya fito ayi kowa ma ya huta''
''yo idan banda abunka malam amadu saurayin qwarai ne zai dinga yayibar yarinya yaro kwararo kwararo kuma yace zai aureta,ai qarya ne dan yaudara ne kawai''inna hadiza ta,cafe maganar
''oho,koma dai meye nidai na gama magana,tashi ki bani guri''


jikinta a sabule ta miqe tayi hanyar dakinsu,har yanzu kunnuwanta badu daina jiyo mata qananun magan ganun da suke yi bq marasa dadi akanta ba,taimakon da Allah yayi mata daya yau baban nasu bai bi ta kansu ba yayi ficewarsa masallaci,wannan wace iriyar masifa ce?,tamkar ita ke da ikon rubutawa kanta qaddararta?,ita ta hana kanra aure ne?,shikenan a rayuwa babu dama Allah ya qaddara maka wani abu sai jahilan cikin mutane su dinga ganin tamkar kai ka jawowa kanka ko da amincewarka hakan ta faru?,


mamanta na cikin rumfar a zaune amma tamkar bata a cikin gidan,wannan dabi'arta ce,tana da dauke kai da yakana akan 'ya'yanta,da wuya ka taba mata yaro kaji bakinta,da wannan damar mutanen gidan ke amfani suke cin karansu babu babbaka a kansu,duk da wasu lamuran hindu na masu tambotsai idan taga cin kashin yayi yawa,don ma mama na kwabarta


yanzun ma baqinciki ne ya hanata motsi da kuma umarnin maman,don tana zaune ne tana karatun waec da fitilar qwai a gabanta,sallamar ta kawai hindun ta amsa ta dora da cewa
''yanzu fisabilillahi yaya maryam haka zaki ci gaba da zama ana miki cin mutunci ba zaki kare kanki ba?''
''kinci gidanku nace hindatu,nace kinci gidanku,da baban nata zatayi sa'insa ko da matan ubanta?,ke maryamu,ina kika samo kayan jikinki?''
kai ita kam dai ta shiga uku,wato ko ina cikin tuhuma take
''mama tsarabar da raliya ta bani ce,na tayata aiki tace bazan taho ba sai nayi wanka,shine aciki na cire nasa wannan''
''madalla,amma daga yau kada ki sake ki sake kaiwa magariba a waje kina jina ko?''
''to mama''


dakinsu ta shige ta ajjiye jakarta saman katifarta,qoqari take ta shanye dukkan wani bacin rai,batason ta barshi yayi tasiri a ranta,tunda idan da sabo ai yaci ace ta saba,sau nawa ake ruwa qasa tana shanyewa,ta zare rolling din kanta ta dawo tsakar gida ta daura alwala,sai da tayi nafila raka'a biyu ta kaiwa Allah kukanta,ta dade saman carfet tana jan,hasbunallahu wa ni'imal wakeel sannu a hankali taki sauqi na zuwar ma zuciyarta


kira ne ya shigo wayarta data duba agogo sai ta tabbatar jabir ne don bata da alaqa da wani da zai kirata a irin wannan lokacin,shi dinne kuwa,awanni kusan biyu sukayi akan wayar har ta soma gajiya don bata saba doguwar hira irin haka waya ba,cikin awanni tayi amanna da kyawawan halayen  jabir,bayan ta,jada da wanda raliya ta gaya mata,a yanzun mafita kawai take nema,koda wanda bai kai jabir din ba zata iya aurenshi matuqar zaya riqeta da daraja


sunayin sallama hindatu ta shigo dakin da tarin litattafanta ta watsasu tata katifar,kasancewar dakinsu daya don maryamu bata da sha'awar raba daki da 'yar uwar tata,doguwar hamma ta ja,maryam ta dubeta tana dariya ''boko wahala''
''mtsw,ke dai bari yaya maryam,yanzu a haka kukayi degree?''
''me kayi da maza inji karya,idan banda abun hindu ke,da sai yanzu ma zaki bar secondry din''
''gaskiya ne kuma fa''ta fada tana fadawa kan katifar tabayan ta ture liattatafan da ta watsa gefe


''yauwaaa''maryayam ta gada tana janyo jakarta ta ciro kudin da jabir ya bata dazu
''ungo irga kiga nawa ne''
''an biya ku salary ne ya maryam?''tace lokacin tame lissafa kudin
''a'ah jabir ne ya bani''
''ya maryam Allah ya tsaida jabir din nan mu sha budiri''murmushi itadai kawai tayi
''ten thousand ne''
''ok...to ko riqesu,zan cika miki kudin rigistration din exam dinku''
''na gode ya maryam,na gode''
''don mind,ni dake duka daya ne,kawai ki tayani addu'a hindu''
''ai babu fashi wannan ya maryam''


🎄🎄🎄🎄🎄🎄

cikin sati,guda kacal sabo ya shiga tsakaninsu da jabir,yana da sauqin kai,fara'a da haba haba da jama'a,yan sonta ji da ita da tattalinta,cikar satin ta isar masa da saqon baban,murna da farinciki tamkar zai goya ta,washegari kuwa magabatansa suka iso,a take aka tsaida magana harda sa rana,farincikin mama bazai misaltu ba duk da tana boye wa,yayin da huwaila da hadiza sukejin kamar an musu transfer zuwa jahannama


🎄🎄🎄🎄🎄🎄

shiye shirye tuni suka fara kankama domin sati biyu kacal ya rage,cikin yammacin gab da sallar magariba jabir yazo gurinta kawo mata invitations kasancewar akan hanya yake yasa bai shiga daga cikin gidan ba,suna tsaye jikin motarsa taga kamar an wulgasu,ta dago kanta don ganin me wucewar,maraqisiyya ce har ta gota su taga ta dawo,da baya,qare musu kallo tayi sannan ta gyada kai ta shige cikin gidan fuuu da uban akwatinta dake rinjayarta



wani faduwa taji gabanta yayi wanda yasanya har sai da ta rufe idonta,duk lokacin da maraqisiyya tazo gida to babu alkhairi a zuwanta,don bata taba komawa inda ta fito sai ta assasa wani bala'in cikin gidan
''lafiya?''jabir ya tambayeta cikin kulawa
murmushi tayi wanda yafi kama da na yaqe ta girgiza kai''babu komai''



*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺




         
          ▶5⃣





Babu sallama sam bisa tsarin maraqisiyya,don kaf gidan tafi kowa lalacewa,jamila ke rufa mata baya,a tsakar gida ta iske uwarta hadiza da 'yar kanzaginta huwaila,basu ga shigowarta ba sai yif kawai sukaji na warbar da akwatinta da tayi da zamanta jabar kusa da su 


inna hadiza ce ta dafe qirjinta''na shiga uku ni dije,kada dai kice min yauma korokin yayi?''
fuska ta yatsine
''yau ba shi ya kore ni ba ni na taho,don na gaji da zama da matsiyaci direban babbar mota kuma mashayi''
''oh ni 'yar nan,auwalu matsiya cine''
''lamba daya''maraqisiyyan ta qarashe mata
huwaila tace
''aini na ma kasa magana,yara duka aure ya zama na tafashi kada,babu daya qwaqqwara?''
matsowa maraqisiyya tayi sosai kusa da su ta ma manta da tata matsalar''wai hadiza ni fa ban gane ba(haka suke kiran iyayen kansu tsaye)idanuna kamar wancan mujiyar nake gani da wani jikin wata qatuwar mota,ko gixo take min''


caraf huwaila ta kama''itace mana 'yar nan,kinga babarku babu yadda banyi da ita ba mu tashi tsaye ko malaman da mata ke shiga muma wannan karon mu fada amma tace bata da kudi,dame zata ji,da matsalolinku ko da kisan kudinta da take nema da qyar?kawai mu qyaleta tunda wancan karon hakanan taqi auruwa to wannan karon ma hakance zata faru''
''hadiza ai ranar biyan buqata rai ba a bakin komai yake ba,ku yanzu ko kunya bakwaji,ai abun kunya ne a tattarw da ku maryama ta auri irin mijin dai da na ganta tare da shi,wlh dukkanin alamu sun nuna mai akwai ne,yaranku suna zaune?,wadanda ma aka aurar din gamu cikin wahala?,kuma ita tahaye?,si wallahi inaaaa,zaman gida bai qarewa maryam ba,ku matso kuji''


shewa sukayi bayan sun tafa kamar wasu,sa'anni wanda yayi daidai da shigowar maryam din
''sannunku,maraqisiyya ya hanya?''babu amsa sai uban tsaki da taja kamar zata cire harshenta


🎄🎄🎄🎄🎄🎄


washegari ta shirya tsaf don zuwa karbo dinkunanta da kuma yin sallama da uwar dakinta wadda take aiki a qarqashin katafaren kamfaninta nayin girke girke da shirya guraren biki,tayi sallama da maman ta,fito tsakar gidan


saiji tayi maraqisiyya na dura ashar,cikin takaici ta,juya don ganin da wa take,ita da hindatu ne ta,sirka ruwanta ta wanke kanta rabi zatayi wanka maraqisiyyar ta,sheqar mata ta,tara wsni don shiga nata wankan
''wannan banzar yayar taki ma bata isheni ba bare ke karan kada miya''
hindatu dama dake qullace da su tace
''dalla gafara can malama,banza a banza kawai,wadda ta kasa zsmsn gidan aurenta,yayar tawa kuma da,kike maganarta kuwa wallahi tako ina ta sha gabanki,aure kuwa nasan bazati irin naku ba auren jeka nayi ka,wanda dashi gwara babu''tofa baki yasan abinda zai fada baisan me za'a mayar masa ba


kamar ta zubawa maraqisiyya ruwan zafi ta,lsilayo wani uban ashar din''wlh zaki san kinyi da huwaila 'yar hadiza,auren da kike taqama ayishi mu gani''
''Allah ya fiki ya fi wanda ya fiki ma''hindatu ta fada wadda maryam ta tura daki tana mata gargadin kada ta sake cewa komai,sai kuma abu ya dawo kanta bata kula kowa ba ta fice inda ta nufa cikin zuciyarta cike fal da tsanar halayensu

🎄🎄🎄🎄🎄🎄

Saura kwana goma biki aka kawo lefe,lefe ne na gani na fada wanda ita kanta maryamu ta yaba qwarai da gaske,qarara rudewar su huwailan ta fito,sumbatu suka dinga yi don duka cikinsu babu wadda ta aurar da 'yar da ta samu lefe kwatankwacin haka,komai sai da suka masa dilla filla suka qare masa kallo



abinda ya bata mamaki ganin dukkan 'yan gida sun shiga shirye shiryen bikin gadan gadan,kada ma inna hadiza taji labari,duk da ba shiga sabgar su maryamun take ba,harda cin bashi da sauya furnitures din daki


maryam na zaune gefan mamanta tana lissafa mata sunayen mutanen da zata tura hindatu takaiwa cingam tana rubuta mata a takarda hindatun ta shigo,hannunta ledar dinkunanta ne da ta door mat da maryam ta bada ta siyo,ta zauna kan kujera tana fadin 
''sannu harkin dawo?''
''eh wlh amma fa na sha wuya''ta fada tana shiga kitchen ta dauko ruwa cikin gorar faro da suke durawa susa a fridhe dinsu,sai da tq shanye sannan tace
''mama''
''na'am''
''nifa abun nan na bani mamaki''
''mefa?''ta tambayeta tan duba rubutun,da maryam keyi
''su hauwa mana da su jamila,gaba daya sai hidimar biki ake yi,kada ma jamila taji labari ita da mamanta,mutanen da aduniya babu wadanda suka tsana kamar mu?''
sai a lokacin maman ta kalleta duka harda maryam din
''to,banda abinki hindatu sai ku godewa Allah,me yiwuwa Allah ne ya ganar da su gaskiya,tunda babu wanda za'ace *ABADAN* zai dawwama a halin da yake,dole watarana akwai sauyi,qila Allah ya ganar da su ne''
''nima dai mama haka nayi tunani,kuma wallahi bakiji dadin da naji ba,Allah yasa silar gyaruwar tsakanin mu kenan''
''ameen''cewar mama,ita dai hindatu tabe baki tayi tace ''to Allah yasa,amma ba girin girin ba tayi mai''


sallamar jamila ce ta katse hirar tasu,dukkaninsu suka bita da kallo,don basu iya tuna yaushe ta shigo dakin na qarshe,koda sun tuna ma ba alkhairi ne ya kawo ta ba
''sannu mama''
''yauwa sannu''
''gurin maryamu nazo''
''to gani''injita
''cewa nayi yaishe zqki lalle,ina son na biki ne muje tare,kinsan qannan amarya dole su fito kamar amaryar''


sosqi maryamun taji dadi har ta saki tattausan murmushin ta
''ai ba damuwa,jibi ne sai mu tafi tare ai''
''to shikenan''ta juya ta fice
hindatu ta kalleta
''haba ya maryam,nidai gaskiya bazan hada tafiya tare da su ba''
''sai ki fasa zuwan ai''inji mama
''don kuwa ni zan biya mata ma kudin lallen,haba hindatu dan uwanka dan uwanka ne fa,kuma ka dinga kyautatawa dan uwanka musulmi zato,ki zama mai tsarkakkiyar zuciya kinji qanwata''dole hindatun taja bakinta ta tsuke



Tare suka je lallen maryam hindatu da jamila,ita biya kudin dukkaninsu


🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

cike gidan yake da mutane kasancewar yaune ranar daurin aure,ga gauyar yan uwa daga bangaren mama da inna hadiza,kusan yawancin danginta na cike a gidan danqam,har ita kanta maman tayi mamakin hakan,amma sai ta share,batun sanin cewa babu yadda Allah baya iya sauya lamarinsa


maryam na maqotansu ita da qawayenta ciki harda raliya,tayi shar cikin atamfa super riga da zani plain,ba qaramin kyau tayi ba,fuskarta cike da walwala da farinciki


guda suka dinga ji tana tashi sosai tamkar a cikin gidan akeyi kasancewar maqota ne gida jikin gidan,raliya ta saki tata gudar tana fadin
''shikenan alhmdlh an daura,tazama tazama,yau diyana ta shigo sahu,Allah yasa wata tara iwar haka mu hadu suna''dariya duka aka saki wasu na cewa amin wadda shigowar hindatu cikin gunkin kuka ya katse musu ita
maryam ce ta soma miqewa tanajin qirjinta na bugawa tun kafin taji me ya samu hindatun zuciyarta ke mata saqe saqen munanan abubuwa


zubewa tayi gaban maryam tana fadin
''ya maryam don Allah me kika yiwa ya jabir?,me kika yi masa da zai miki wannan sakayyar?,me kika yi masa da har ya guje miki ya maida aurenshi kan *JAMILA*?''
dum taji kunnuwanta sunyi,qwaqwalwarta lokaci guda ta gaza yin aikinta,sai ta daina gane komai,meke shirin faruwa d ita?tambayar da taji qwaqwalwarta na mata kenan,kafin bijirowar amsar sai taji tamkar an zare dukkan wata garkuwa da ta sata ta iya tsaiwa da qafafunta,yaraf taji ta zube,daganan komai ya dauke mata dif kamar an dauke wutar nepa adaki mai tsananin duhu........




*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺





           ▶6⃣




''ya maryam,me kika masa da har ya guje miki ya maida aurensa kan jamila?''
maganar da keta amsa kuwwa cikin kunnenta kenan bayan ta farka,sai hawaye ya fara turereniyar fitowa daga runtsatsun idanunta da ta kasa budesu suna bi ta gefan fuskarta su sauka har cikin kunnenta,wani irin yanayi take ji daban cikin zuciya da gangar jikinta
me ta aikatawa jabir da zafi haka wanda har ta cancanci wannan hukuncin?
a iya saninta ba zata iya tuna abu guda ba mara dadi da ya taba hadasu a tarihin rayuwar soyayyarsu ba


hindatu ce ta fara ankara da farkawar tata ta sanadiyyar hawayen fuskar tata dake bi ta gefen kuncinta,da sauri ta taso
''sannu ya maryam,me yake miki ciwo yanzu''
kai kawai ta gyada mata alamar babu komai
mirya can qasa tace
''dagoni hindatu''
a hankali ta taonaka mata ta tashin ta jingina da filo sannan tace bari na kira ''mama''


maman ce ta takurata kan ta tashi hindatu ta rakata asibiti,bata biqatar fita koda falon nasu ne don bata san da wanne iso zata kalli jama'a,hakanan suma batsan da wanne ido zasu dubeta ba,ta tabbatar maganar ta gama zaga unguwar ma gaba daya ba gidan ba,amma ba zata iya misa mata ba don ita don ma so take tadan gusa daga gidan saboda haka ta zura hijabinta hindatun tace bari ta nemo dan adaidaita sahu sai tayi mata magana


bayan fitar hindatun shiru dakin yayi,baka jiyo komai sai hargowa da hayaniyar jama'arsu huwaila da inna hadiza cike da farinciki,mintuna biyar sai ga hindatun ta dawo ita ta riqe maryamun suka fito yayin da 'yan uwan maman nata dake zaune jugum a rumfar tasu suke mata sannu da jaje,don tuni wasu ma soma hada kayansu don komawa inda suka fito


Sun samu ganin likita cikin qanqanin lokaci don private clinic suka je,likitan yace zai riqe ta zuwa magariba ta huta sosai tasha magungunanta,bata musa din ba suka bata gado hindatu na tare da ita


basu bar asibitin ba sai magariba,suna hanya ne hindatu tace''anty raliya ta kira ki har sau biyu kina bacci,tace zaga sake kira,ya nasir ne yayi kiranta tunda kuma ta fita bata dawo ba''
kai ta iya gyada mata kawai don bata jin zata iya bude bakinta
suna shigowa layin gabanta ya dinga dukan uku uku,ji take tamkar ta,canza wani gidan ba nasu ba,ji take kamar ta yanka a guje ta bace a nemeta a rasa,motocine a jere har zuwa qofar gidan nasu,sauka sukayi suka biya shi sannan suka dutfafi gidan wanda har qofar gida jama'a ne 


duhun da garin yayi yasa babu wanda ya shaidasu har suka shige gidan wanda tun daga soron suke jiyo tashin muryoyi cike da hargowa,babu wadda tace da 'yar uwarta komai har suka shigo ainihin tsakar gidan,ga mamakinsu qofar dakinsu ne cike yake da jama'a wanda ya tabbatar musu da koma mene ya shafesu


da qyar suka kutsa cikin rumfar tasu,mamansu ce zaune bisa kujera fuskarta dauke da tashin hankali,sai anty kubra qanwar mamansu,inna hadiza da baba huwaila sai jamila dake gefansu tana zuba ruwan bala'i har daurin zaninta na kwancewa anty kubra na maida mata da raddi
baba huwaila ke riqo,jamilan ta fincike kana ta zabga mata harara
''kinga malama ki qyaleni kawai,wallahi babu inda zani sai da lefena koda motocin daukar amaryar zasu shekare,a qa'ida ai lefe nawa ne kuma sai in zuba ido a take min haqqina,wallahi babu wanda ya isa ko duk duniya gatanshi ne yau sai kun fiddo lefen nan''
''qwarai kuwa haqqinki ne ai''babarta hadiza ta fadi cike da nuna goyan baya,wani abu ne ya tsirga wa huwaila,wato tsiyar ma har da ita a ciki yau


'yan mata biyun dake tsaye bakin qofa cikin 'yan daukar amarya suka hada ido,cikin tashin hankali dayar ta cewa 'yar uwarta,muryarta can qasa''mun shiga uku malika,wacce iriyar mace ya jabir ya kwaso mana''babu mai amsar duk cikinsu,saboda haka jiki a sanyaye suka zame,suka fice daga gidan


hindatu dake jiran qiris ta saki jakar hannunta tana huci ta qaraso gaban jamila 
''rufe mana baki matsiyaciyar banza matsihaciyar wofi 'yan taka hayen arziqi,lefen banza lefan wofi,mj jabir ma yanzu bai ishemu kallo ba balle abinda ya fito daga hannunsa,idan kinsa ranki a inuwa ma zamu fito muku da gayuar tsiuarku ba sai kinzo kina haushi kina ragewa kanki daraja ba idon dangin miji ba''
sai ta,hau ihu
''e hooo,munji dai duka haushin rashi ne ,kaya dai sai kun bada su''
''ai dama zamu bada din amma ba saboda wannan hayagagar taki ba,zamu baku ne saboda mu a gun mu ba yanke talauci jabir ya bamu ba,kune nake tsammanin zai iya zama yanke talauci a gunku''
hannu inna hadiza ta saka zata zabga mata mari,tuni ta tare ta kana ta sake taku uku zuwa gabanta tana huci da nuna ta da yatsa
''kada ki kuskura wallahi,don idan a baya kin saba tabani ina qyaleki ta yanzu babu wannan maganar,idan kuma kika yi gigin aiwatar da hakan wallahi ko kadan bazaji kunyarkk ba daga hannu zanyo nima in nuna miki salon nawa iya marin,tsohuwar banza wadda shekarunt basu dade ta da k.....''


tsawa mamarta ta daka mata''kada ki kuskura kici gaba,zo ki wuce ki debo musu kayansu kawai idan na isa da ke''yarfar da hannun inna hadizan tayi a fusace ta shiga dakin maman inda anan kayan ke ajjiye ta soma fiddo da su tana watsosu falon 
''kada fa ta barnata muku kaya kuyi mata gana''
''ina ruwanki,da muka zo da ke wanne taimako kika iya yi,tunda dai sun fiddosu ai shikenan''inji jamilar
takaici yasa huwaila jiyawa ta bar dakin


a warwatse haka hindatu ta dinga jefomusi su tas tun mama na mata magana har ta gaji da qyaleta,bayan kuma ta gama tace wallahi ian basuyi gaggawar kwashesu daga rumfar tasu ba zasu ga qasqanci,duk iya ikancinsu sun sqn halin hindatu sqrai bata iya fushi ba,don haka cikin rawar jiki suka dinga kwashewa ciki harda uwar amarya inna hadiza


sai da suka gama sannan taji kuka yazo mata cikin dakin nasu da ta shiga da niyyar rage qincin zuciyarta,sai ta tadda maryam nayin nata,kasa lallashinta tayi hala suka hada kai suka dinga risgar kukan da qyar anty kubra ta sha kansu


haka suka kwashi amaryarsu suka kaita gidan da aka shirya shi da sunan maryam din,wanda hatta kayan gado fiye da rabi kudinta ne ta baiwa baban nata ya hada da na gurinsa aka siyesu,abu daya ne inna hadizan tasa aka jado aka dawo musu da shi kayan kitchen,duk da haka sun cire manya manyan warmers masu tsada da maryam din ta siya cikin albashinta


🎄🎄🎄🎄🎄🎄

kwana biyu gidan yayi da ragowar baqin su inna hadiza da basu ida tafiya ba,kwanakin biyun nan daidai suke da shekara goma na tsanani gurin maryam,kallo daya zaka mata ka dauke kai,hatta da mamarta wannan karon ta kasa daurewa zuciyarta sai da ta taya diyar tata kokawa

🎄🎄🎄🎄🎄🎄

ciwon kwana na hudu bayan sallar la'asar raliya ta iso gidan,maryam na kan dadduma bata kai ga tashi ba tunda tayi sallar la'asar,suna hada ido ta soma share qwalla,itama raliyan sai ta kasa daurewa duk da alqawarin da tayi ma nasir din bazata zo su hada kai suyita kuka ba


kusa da ita ta zauna suka soma aikin kuka wanda mama dake dakinta bata ji shigowarta ba sai rishin kukansu,leqowa tayi don ganin waye''ashshsha,haba raliya,abu da ya riga ya wuce kuma,don Allah ya isa haka,tashi ku shiga daki''ta fada tana karbar fadil daga gunta ta fice ta bar musu rumfar


da taimakon ambato Allah da take ta samu zuciyarta ta rage zugin da take 
''raliya me n yiwa jabir haka da zafi?,wace iriuar qiyayya ce wannan ya gwada min,idan yasan tun farko baya sona me yasa bai gayamin ba tunda ba tilas aka mishi ba?''
girgiza kai kawai raliyan take
''maryam,ke kanki idan kika ga jabir sai kin tausaya masa,kallo daya zaki masa ki tabbata ba'a cikin hayyacinsa yake ba,kinsan me ya fafu ne?,lafiya suka zo gurin daurin auren amma kafin a kai ga gama taruwa ana zaune kawai su nasir suka ga jabir ya sume,mintina kadan ya dawo hayyacinsa,kinsan abinda bakinsa ya fara fada?,jamila nidai jamila nake so wallahi,zan iya rasa rayuwata idan ban mallaketa ba wallahi,abbanshi uazo yabi ba'ason maganar sai yace shi wallahi baisan wata maryam b ai tab cewa yana son wata mai suna marym ba,abbanshi ya dauka iskanci ne ya hau maa fada yace  bazai maidashi mutumin banza ba,


abu kamar wasa sai ga jabir ya sake sumewa jin an hanashi jamila,da babanku yaga haka sai yace wa abban nashi ya barshi ai dake da jamilan duka daya ne''ajiyar zuciya maryam din ta ski mai tafe da hawaye,idon raliyan ciki natan tace
''maryama don Allah ki dinga saka abir a addu'o'inki,don ya hadu da jarabta,jiya nasir ya debeni muka je gidan,kinga yadda ake zaman?,yadda kika san bawa da uban gidansa,jabir ya zama abun tasayi,da jamila ta yi magan sai kiga ya zabura,tana saman kujera kwatankwacin bawa da uban gidansa''


a maimakon haushi takaici da tsanar jabir sai tausayinsa ya maye gurbi,take taji fiye da rabin quncin zuciyarta ya tafi,bata jin komai a ayanzu sai tsantsar tausayinsa,lallai ya fada cikin jarrabawa mai girma,sun dade tare da raliyan suna tattuna lamarin har daf da magariba sannan tayi musu sallama ta tafi


Bayan sallar isha'i baban su ya shigo falon nasu,bayanin da yayi musu kusan tishi ne kan wanda raliyar ta musu,ya rife da cewa''dln haka ke maryam sai kiyi haquri ki fidda wani mijin,tunda ke da jamilan duka daya ne 'yar uwarki ce''lamarin baban nasu na daure musu kai saidai ko daya maman tasu bata bari suyi maganar da ita kan yadda yake nuna wariyar launin fata qarara su da sairan yaran gidan,daga haka ya kade rigarshi ya fice yace idan ta samu wani mijin ta sanar masa






*Mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺






        ▶7⃣


*WACE CE MARYAMA?*




Maryama diya ce ga *amina* da kuma malam *mahmud*,za a iya cewa itace diya ta farko da suka fara haifa shi da ita,asalin su fulanin kano ne cikin wani qauye da ake kira da gaya dukkansu shi da amina mazauna garin ne,yanayin nema ya dawo dasu cikin garin kano



amina maca ce mai matuqar haquri da kawaici tsantsar kyau nafulanin usuli,hakan yasa take da farinjinin samari da dama wanda hakan ya kusa haifar da rigima cikin qauyen nasu,dalili kenan da yasa babanta yayi saurin aurar da ita ga mahmuda dan maqocinsa wanda duka cikin samarin nata dama tafi karkata gashi,kasancewarsa shine kadai mai ilimin primary a cikinsu,amina maca ce maison karatu matuqa da gaske saidi a lokacin lokaci ne da ake qamatar karatin boko hakanne yasa bata samu wannan damar ba shi yasa tayi kwadayin auren mahmud din


kusan shekara uku da auren nasu kafin Allah ya azurtasu da samun qaruwa,da namiji ta haifa saidai baizo da rai ba,sosai mamuda yayi takaici kasancewarsa mai son 'ya'ya musamman maza,babu yadda ya iya haka ya haqura


bayan wannan haihuwar saida amina ta sake wata guda biyu duka maza kuma babu rai sai akan maryamu Allah ya tsaida mata,saidai wannan karon mahmuda baiyi wata murnar azo a gani ba kasancewar ba abunda yake so ba ya samu wato namiji,itakam amina hakan yayi mata dadi don a ganinta duka daya ne fatan dai Allah ya kawo mai albarka


bayan yaye maryam ta sake wata haihuwar macen itama babu rai a haka sai da ta haifi hudu dukkan ajajjere tsiran watanni ne ta kuma samun wani cikin duka dai basu zauna ba,lokacin ne mamuda yace ahikam aure zai qara,bata wani tada hankalinta ba tace ''Allah ya sanya alkhairi''
huwaila ya dauko wadda tunda tazo gidan ta fuskanci ba wani girmamawa yake wa amina ba,don haka ta tayashi takata,kusan tuni ya sakar mata duk wata ragamar kulawa da ta rataya tasu a kansa


Ba'a taba yiwa Allah dole,hakan ce ta faru ga mamuda domin huwailan ma da ya qwallafa rai a kanta haihuwarta ta fari da mace ta fara,a haka ahaka saida ta tara yara shida duka mata,ganin ita din ma babu biyan buqata sai ya tafi ya auro hadiza ya kuma zubar da lamarin huwaila kamar yada ya yowa aminatu


to ita din ma hadizan bata sake zani ba,matan ne dai sai da ta haifo bakwai sai daga qarahe ne Allah ya kawo namijin wato *ISHAQ* da suke kira isyaku,sunan mahaifin mamudan ne,to fa,babu zama wai an saci dan barawo,nan fa hadiza aka shiga daga kai an haifi namiji,rashin mutunci babu kalar da bata shukawa cikin gidan,hakkane yasa huwaila boye kishinta ta shige jam'iyyar hadizan suke gallazawa aminatu baiwar Allah wadda a lokacin ta sake samun qaeuwar diya mace shekarunta takwas kenan


Rayuwa tayi da rayuwa,yau da gobe kayan Allah,babu da talauci ta ishi jama'a hakan ce ta sauka gidan malam mamuda,ya taraau ya sanar da su cewa saidai fa kowacce tayi haquri da abunda zat gani don gaskiya bai da abun ci da su,ranar da ya samu ya bayar a dafa,ranar da babu kowa ya ci da kanshi,to dama ko can baya ba abinda yake masu,abinci ne zai baki kudin awo ranar cefanenki sai makaranta mai sauqin kudi ya sanya yaran ita din ma don ya dan san dadin ilimin kadan,to sai kuma salla salla ya dinkawa kowa kala daidai dama maryamu bata cikin duka wani budget nasa,idan akayi magana sai yace ai ita babbace ta dauki girma daga haka babu dadi babu ragi


huwaila da hadiza sukayi tsallen albarka suka ce sukam ba zasu iya ba,dukkan yaran nasu suka fidda su daga makaranta suka hau yin sana'a suna dora musu talla,to yaya lafiyar kura balle tayi hauka,dama can ba tarbiyya yaran suka cika ba balle yanzun da suka zama *'yan talla*,tashin kunya kule kule kulen maza da diban albarka kala kala,tun malam mamuda nayin magana har sai ya saka ido,don bashi da ikon yayi maganar sai gori


kisan hadiza ce ke juya malam mamuda itace mowar mata sakamakon haifar masa namiji da tayi,duk abinda isiyaku ya fada kam baya qarya,sai ya zamanto aminatu baiwar Allah da yaranta sun zama yan kallo cikin gidan,duk da itama huwailar na baqincikin yadda hadiza ke yadda taga dama amma tilas ta bunne cikin zuciyarta don samun damar cin arziqin samun 'yanci a gidan


Amina cire yaranta tayi ta maidasu ta gwamnati,da yan kudaden hannunta tayi masu dukkan abinda ya kamata,ko dama can ita din ba mace ce mai matacciyar zuciya ba,ba'a rabata da 'yan sana'o'i,sune kuwa auka zama marufar asirinta,ita ce kitso,daka,wanki,'yan qulle qullensu kuka daddawa kubewa su lalle ne,da sauransu,da su take samu ake gurgura rayuwar da dadi babu dadi


lokacin da maryamu ta kammala primary taci common entrance G.G.S.C duka wuya ta samu dake qofar famfo,wanda yayi daidai da fitowar manema wa yaransu hadiza wato SHEMA'U,HARIRA FURERA DA RABI,uku yaran huwaila ne daya ce ta hadiza,dukkaninsu basu wuce sha biyu ba sha uku sha hudu,tsabar son aure ne da suka saka aransu ya sasu zama dika dika,ba bata lokaci kuwa aka sa musu ranar aure,malam mamuda ya samu amina da auke kira mama ya sanar mata zai hada ne harda maryamu ya airar da su gaba daya,tunda su gasu qannenta ma sun fidda miji


cikin ladabi da son fahimtarwa tace''amma malam ni a ganina dukkaninsu basu yi girman da za'a aurar da su ba,yanzu haka ita kanta maryamun bata kai sha biuar ba bare su,ba zata fi sha hudu ba gaba daya,ni a nawa ra'ayin malam nafison maryamu tayi karatu,idan ta qara girma tasan  ciwon kanta sai a aurar da ita''
wannan abun ya qullata yace indai bata yarda an aurar da ita ba to babu ashi babu duk wani shirgi nasu,bata damu ba don dama can ba wani abu yake musu ba


tofa,wanna ya sake hura wutar tsanar da sukayiwa maryam wanda dama tun suna qanana aka horesu da ita,don ko wasa bata isa ta shiga cikinsu tayi ba,gashi lokacin bata da 'yar uwa don ba'a haifi hindatu ba alokacin,bugu da qari,kyau da Allah ya bata fiye da duk wata yarinya dake cikin gidan,duk da suma Allah ya basu nasu kyan babu laifi saboda mahaifinsu malam mamuda kyakkyawan bafulatani ne


Allah yayi maryam mai hazaqa da qwaqwalwa,tana da matuqar son karatu,haknne yasa bata yadda ta kula kowanne saurayi wanda su kuma suka fassara hakan da cewa girman kai ne kurum don tana ganin ita kyakkyawa ce,cikin zuciharta ita din tasan ba haka bane tunda ba haka take din ba azahirance


maryam doguwar mace ce wadda Allah ya yiwa baiwar diri da structite na jiki duk da tsahonta hakan bai boye kyawun zubinta ba,fara ce amma ba tas ba,idan kaso ma zaka iya kiranta da ja,don irin farin nan ne mai cakude da ja,gashinta sosai irin na fulani mai laushi da santsi,zara zaran gashin ido da na gira da madaidaicin baki,dimple dinta hagu da dama wanda ko magana murmushi tayi sai ya lotsa,hancinta ba mai tsani ba tafe yake da tsohonsa da kuma tudu,idanunta irin idon nan ne da ake cewa oily eyes wanda zakayi tsammanin qwalla ko ruwa ne suka taru cikin qwayar idon,bata da baqin qwayar ido sosai,sanyin muryarta da zaqinta ke dada bayyana kyawun halittar da Allah yayi mata wanda hakan ya ja mata yawan masoya da maqiya ciki harda 'yan gidansu


haka aka sha bikin yan uwan nata su hudu yayin da ita kuma ta duqufa karatunta,maryam badai qwaqwalwa ba,hakan ne ma yasa bata samu cikas ko ksdan a karatunta ba,cikin nasara komai ke tafiyar mata,janye jiki da masoyanta sukayi a lokacin bai dameta ba don dama bata buqatar wani damuwa karatunta ne kawai damuwarta,cikin nasara ta shige B U K inda anan ta samu shaidar degree dinta kan fannin girke girke


ba jimawa,da kammalawa kuwa ta samu aiki da wani katafaren gurin cin abinci da shirya bukukuwa ,wanda cikin qanqanin lokaco ta samu matsayi mai girma na shugabantar dukka masu girka wani abunda za'aci ko a gurin ko kuma aka basu kwangilar yi na biki,qwazo himma gaskiya da amana su suka jawa maryamua wannan matsayin wanda hatta da wadda ta kafa gurin *HAJIYA ATIKA ABUBAKAR BAFFA* ke qaunarta


ta bangaren 'yan uwanta kuwa saidai ace Allah ya rufa asiri kawai domin dukkaninsu cikin shekara guda babu wadda bata da tabon saki wanda tsantsar rashin tarbiyyarsu ya hanasu zaman arziqi da mazajensu,a haka dai ake gurgurawa har kawo wannan lokaci,hankalin maryamu bai fara tashi ba sai da aka zo auren qannanta zagaye na biyu wato *azara*  *shamsiyya* da *maraqisiyya*,tsantsar gori habaici da baqar magana idan da tana tsiro a lokacin to da tuni ta yiwa maryam,sai Alla ya halicceta mai haquri da kawaici hakanne yasa bata fiya zafafawa kan lamuransu ba,idan suna yi dauke kanta take kamar yadda tun usuli ta tashi taga mamanta nayi


samuwar aikinta ya taimaka qwarai wajen kyautatuwar rayuwarsu,wanda alfanun ilimin da ta gani ya sata jajircewa da tsayawa qanwarta daya tilo don ganin itama ta amfana,duk lokacin da ta daki albashinta bata fasa siyan wani muhimmin abu ta kaiwa mahaifinta ko ta ciri kidin tsaba ta bashi,babu kuma wani jin nauyi zaisa hannunshi ya amsa da sunan ai yarshi ce,haka rayuwar maryamu ta taso cikin tsangwamar *'yan uba* wanda har yau ita take gani ba kuma tasan ranar qarewarta ba


_*WANNAN KENAN*_




*Mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺




            ▶8⃣




Cike da tawakkali da yarda da qaddara ta miqa dukkan lamarinta ga Allah,a yanzu kam ta sanya jabir ne kawai cikin addu'o'inta kamar yadda raliya ta shawarceta,domin tausayinsa ne fal cikin zuciyarta,tana ji a cikin zuciyarta ta sanadinta ne ya afka wannan qaddarar


abu guda ne ta kasa tinsa komawa walwalarta da aikinta tamkar,yadda take yi a da duk da yadda take son aikin,ta barwa ranta cewa ta ajjiye aikin zata kuma jira har lokscin da ubangiji zai musanya mata da da wani mijin ko da baikai jabir dinta ba

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

misalin biyar da rabi ne na yammaci,zaune take a rumfar tasu wadda ta sha mopping tayi fes,dai qamshin turaren tsinke take,mamanta na dakin babansu tana gyarawa don ita ta amshi girki,don sam bata lamunce don ranar girkinta bane ta tura yaranta su share dakin baban nasu ba kamar yafda taga su huwaila nayi tsabar ganda,yayin da hindatu ke makarantar islamiyya


sanye take da maroon din material dinkin doguwar riga da yake ma'abociyar son dogayen riguna ne ko don tsahon da take da shi,yatsunta sunyi kyau da jan lallen da tadan qunsa iya yatsu,a lokaci irin wannan idan bata da abinda duka zatayi,taka duqufa wajen research din girke girke a daga sashukan dake watso kalolin abinci na qasashe daban daban,kadan kadan hankalinta ke rabuwa gida biyu,wani lokaci yayi tsakar gida da yaran inna hadiza keta faman ta'adi cikin falon gyatumar tasu da hayaniya na 'yan fadace fadace atsakaninsu kuma babu wanda ya isa yace zai tsawatar musu


cikin haka ta jiyo sallamar inna hadizar,abu na farko da ya biyo bayan sallamarta shine ashar da ta dura wanda har sai da maryamu tayi ta'awizi cikin zuciyarta
''kaga tsinannun yara shegu,ke balaraba da na bar muku dakin a bude shine kuka maida min shi sansanin fada da kokaye kokaye,kuma saboda tsabar baqincikin Allah yayi maka arziqi a rasa mai tsawatrwa uaran salon su fasa ma abu kosu lalata ma su jawo maka asara,dadin abun ma yanzu kana da arziqin da zaka gyara''


sarai mama tasan da ita take amma kasancewar ko da can ma da jini ajika ba kula shirginta take ba yasa yanzun ma tayi mata dif,saiga huwaila ta fito daga wanka takalleta
''a'a,ina kuma kikaje?''
''yo ina kuwa zanje da ya wuce gidan doyar albarka jamila''ta fada tana shirin shigewa dakinta
sakwatoto huwailan tayi
''amma inace baki tafi ba don wanna wanka da nayi na shirin zuwa ne,tunda munyi tare zamu je''
''kiji hiwaila da wani zance,don,lawai zaka girin naka sai ka jawo bare?''binta wadda tare suka je da innar tata ta maidawa huwaila raddi
''kinga ba dake nake ba 'yar ayi jikar na saba''


''a'a,dakata don ta fadi gaskiyarta,kada kiyi haushin kaza huce kan dami''inji onna hadiza cikin salon tare mata
''au bayanta kike goyo kenan?''
''qwarao,yo akan me?''
baqinciki ya,hanata cewa komai sai qwafa kawai da ta ja ta shige dakinta
qarar wayarta ce ta sata dawowa daga diniyar da su inna jadizan suka shigar da ita,a kullum kwanan duniya sake gasgata zancan raliya takegame da abinda ya faru tsakaninta da jabir,jikinta a sanyaye tabi wayar da kallo ,da kamar ba zata daga ba amma ganin sunan *mama* ya sata babu jinkiri ta daga,cike da,girmamawa take gaidata
''babu abinda zaki cemin maryamu,wa yafi qarfin qaddara a rayuwa?,abun nan ya riga ya wuce addu'a ce kawai mafita,amma anyi anyi ki koma gun aikinki kinqi,na tambayi haj rabi ko wani laifin aka miki sunce babu komai,ko an miki wani abu ne agun?''
cike da girmamawa tace ''babu abinda aka yimin mama wallahi''
''to shikenan,indai da gaske haka ne kizo gobe gida ki sameni da la'asar,da akwai aikin da aka samu kuma gaskiya a iya hasashena babu wadda ta dace da aikin sai ke,don na yaba qwarai da tarbiyya gaskiya da riqon amanarki''
ba zata iya musu da mama ba wato hajiya atika abubakar,banda haka da wata ce zqta ce mata ta gode bata buqata,amma girmanta da qaunar da take gwada mata ta wuce haka a gurinta don haka tace
''to mama,na gode Allah ya saka da alkhairi insha Allahh goben ina hanya''
''to shikenan a gaida mutan gidan''
''zasu ji insha Allah''


ta sauke wayar tana jin wani abu na dan taba zuciyarta,mama da bata kima da shigowa ba tace ''ke da waye?''
ajiuar zuciya ta saki 
''haj atika ce,wai tana nemana gobe''
''to Allah yasa lafiya,ko zancan komawarki ne gurin aikin?''
''a'a,tace wani aiki ne ya samu,amma sai naje goben zanji''
''Allah ya rufa asiri ''ta fada maman tana ficewa dauke da wankakken zanin gado da rigar filo
murmushi maryam tayi tana jinjina kai,wato miji da mata sai Allah,maman ta tana burgeta matuqa,bilhaqqi take kula da mijinta,bata duba komai sai zatin Allah da kalmar nan ta *aure bautar ubangiji*

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

washegari ta shirya tsaf cikin atamfa dinkin riga da skert yaluwa sosai tayi,mata kyau ta qara haske da rama,hakan sai ya sake fidda tsayinta,kasancewar lahadi ce yasa ta nemi rakiyar hindatu ko zata ji dadin tafiyar,don ita kanta bata son tafiya ita kadai,gani take kamar idan ta fita nuna ta za'a dinga yi,tsawon watanni kusan biyar amma tunda abin ya faru baifi sau biyi ta fita ba zuwa uku shima sai dare


babu dadewa suka isa gidan maman,a falon qasa aka saukesu mintina biyar aka haura da su samanta wanda ba kowa take kaiwa ba,cike da fara'a ta tarbi maryam din,ita dai ranta yanason maryam din,natsuwarta na burgeta,
kayan ciye ciye ta sa aka kawo misi ta dan basu lokaci kadan sannan ta dawo
''maryam''abinda ta fara cewa kenan
''kamar yadda jiya na shaida miki a waya aiki ne ya samu,yayi shige da na gurina amma yana da bambanci domin wannan a gida zaki dinga yinshi,zaki samu albashi mai tsoka fiye da na gurina''
ta,dubeta da aily eyes dinta''mama wanne irin aiki ne a gida?''
''kinsan marigayi *alhaji abdulkareem mai nasara*?''
sai da tadan shiga tunani sannan tace
''eh ina jin sunanshi mama''
''yauwa,kinga sanannen mutum ne kuma fitace tun kafin rasuwarshi,yaro daya Allah ya basu wato *Abdallah*duk da cewa yana da wata matar amma Allah abi bata haihuwa da shi ba,saidai ya riqe mata nata uaran da ta taba haifa awani gidan mata ne su biyu da nimiji daya yanzu haka duka suna tare a gidan duk da rasuwan shi alhj abdulkareem din hakan baisa sun raba mazauni ba,mamanshi na matuqar sonshi da kaffa kaffa da lamuranshi,duk da haka ana farautar rayuwarsa don kusan sau biyu kenan ana zuba poising abincinshi,ta rasa daga ina matsalar take,kuma duk lokacin da hakan ya faru idan aka tashi binncike sai a samu da hannun kukunshi,hakan yasa take canza masa kuku kala kala,amma har yau babu wanda hankalinta ya kwanta da shi


abdallah shine shugaban jami'an tsaro na farin kaya wato *S S*na nijeria gaba daya,wanda aikinsa kansa na buqatar ya zamo cikin kulawa da tsaro na musamman


bata da lokacin zama agida kasancewarta cikakkiyar likita kan fannin matsalolin da suka shafi mata,wannan ne yasa ta bayar da cigiyar amintacce ko amintacciya wanda ya qware kota qware afannin girki,to qawarta aminiya ta ce hakan ne yasa ta bani cigiya ni kuma naga ke kika fi cancanta da wanna aikin maryam,ina fatan kin fahimceni abunda kuma ya shige miki duhu kina iya tambaya ta''


shiru tayi domin tana jin abun da kamar wuya,sam bata ji ya kwanta mata ba aikin,tamkar aikatau zata tayi,kenan tunda aikin dafa abinci zata gidan wasu?,anya kuwa zata iya amsar tayin maman,amma tana jin nauyinta ,ba zatq kallon tsabar qwayar idonta tace mata a'a kai tsaye ba,kusan minti biyi sannan ta ajjiye numfashi
''ina ganin mama zanje na sanar da maga batana tukun,idan yaso duk abinda suka yanke akai zan sanar miki''
''yayi kyau,hakan dai dai ne maryam,wannan shike dada nunamin hankalinki da kaifin tunaninki,amma ina fatan bazaki watsa min qasa a ido ba''
''insha Allahu''
ta fada ka a qasa''
a haka sula rqbu bayan ta baiwa hindatu dubu daya tace ta siyi kayan kwalliya


cikin mota hindatu ta isheta da karadin wallahi yaya maryam ki amshi aikin nan
murmushi kawai tayi 
''yarin ya ce ke hindatu har yau baki da hangen nesa''
''to,ya maryam meye aibu a ciki?''
bata amsa mata ba sakamakon jin ringing din wayarta da tayi ta soma kiciniyar cirota dqga aljihun jakar,raliya ce mai kiran
''hello ummin fadil''
''na'am mommyn fadil kina ina ne?''
''kin ganni a hanya na dawo ne a wata unguwa''
''yauwa don Allah ina son ganin ki ne ya za'ayi?''
''babu damuwa bari kawai na qaraso''
''yauwa ta gurina''
dariya ta bata tace ''sai na qaraso''ta maida wayar jaka sannan ta yiwa mai adaidaita bayanin inda zai juya da su''

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

''daga ina kuke da yammacin nan ne?''raliya ta tambayi maryam sanda take dire musu drinks
''hmmm,wallahi kinga haj atika ce tayi kira na,wai ta samamin aiki gidan marigayi abdul kareem mai nasara''
sai taga fuskar raliyan ta sauya ta dan tsuketa
''ba zaki koma wani aiki ba,aure zakiyi maryam''ta gada kai tsaye tana kallon maryam din
ba tare,da kawo komai cikin zuciyarta ba tayi murmushi
''banda abinki qawata ba sai Allah ya kawo mijin ba?''ta fada cikin rashin kulawa
''Allah ya kawomiki miji maryam''sai da taji qirjinta ya wani irin buga
''miji?,wa ya gaya miki,qarya ne ni babu mijin da na samu''
matsowa tayi sosai ta kama hannayen ta
''maryam kin amince da ni kin kuma yarda da amincin dake tsakaninmu?''
''me ya kawo wannan tambayar kuma raliya?''ta tambayeta cikin yanayi na shiga duhu
''maryam so nake ki auri nasir mijina''


a hagunce take kallon raliyan,jo tayi lamar ta doka mata guduma atsakiyar ka,gani take kamar ba'a hayyacinta take ba''raliya,me kika sha yau,ko baki da lafiya?''
murmushi tayi
''nasan zaki fadi haka maryam,amma ras nake,kuma nasan me nake,cewa nayi mijina nake so ki aura nasir''
''shi ya aiko ki lo ke kika aiko kanki?''ta tambaueta tana mata kallon ba a hayyacinta take ba
''ni na aiko kaina tare da amincewarsa''
zame hannayenta tayi ta miqe
''idan kin warke kya kirani muyi maganar da kika rani domin ita,don dai wannan ban daukeshi da muhimmanci ba''
kamo hannunta tayi
''zauna maryam,wallahi a hayyacina nake,kuma lafiyata lau''


wani kallo ta watsa mata''sake ni raliya,ni 'yar halak ce kuma nasan halacci na kuma yi imani da akwaishi,idan haka kike to ni ba haka nake ba,idan kuma nasir din ne ya saka ki to ki gaya masa ni maryam 'yar halak ce''ta zame hannuwanta ta fice yayin da raliya ta bita tana qwala mata kira amma ko waiwayota bata yi ba,hindatu dake farfajiyar gidan tana waya itama wucewar maryam din ta gani sai binta tayi a baya


kuka zata yi ne ko ihu?me kuma yake shirin faruwa da ita?me yasa guguwar rayuwa ke walagigi da ita?,yau wai amiyarta ke gaya mata ta auri mijinta,ta ina ta yaya ma zata iya auren mijin raliya ko su biyu ne suka rage a duniya,ko da suka ke gida mama kasa gane kanta tayi,don tunda ta shigo gidan dakinta ta wuce kai tsaye,cikin damuwa maman ke tambauar hindatu me ya faru da maryam din
''ni dai mama da mukaje gidan hajiya lafiya lau muka fito,kuma iki ta samar mata gida alhj abdulkareem mai nasara,amma dai mun biya gidan anty raliya,to nidaiina waje bansan me suka tattauna ba naga dai ta fito da sauri ma biyo bayanta''
''alhj abdulkareem mai nasara?''mama ta maimata sunan don ba boyayyen mutum bane,mai arziqi ne na gani a fada wanda akayi qiyason duka nigeria babu wanda ya kama qafarshi


''to Allah ya kayuta,indai raliyance ai ba'a ashiga tsakaninsu,idan kuma aikin ne ma zamuji,qyaleta hindatu,nasqn zata min maganar da kanta''don shaquwar dake tsakaninsu yasa maryam bata boyema maman tata duka damuwarta




*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺


          ▶9⃣




kwana guda da yini daya bata ce da maman tata komai ba,itama zuba mata idon tayi bata tambayeta ba


kwana na biyun ne qarfe uku taji sallamar raliya,tana kwanve can cikin dakinsu saman katifarta,don yanzu zaman daki da kwanciya kuma ta aira wanda hakan baya rasa nasaba da yawan tunanin da take fama da shi,sai da gabanta ya fadi lokacin da tqji suna gaisawa da mama ta fadi mata tana cikin dakin


jawo dankwalinta tayi tana dauraqa tare da qoqarin yashi duka a lokaci daya,raliya ta iso bakin katifar ta zauna bayan ta shimfide fadil dake sharar bacci a gefanta
''na gode diyana,na gode''
''ai ni ke da godiya''ta fadi tana sake matse fuska
''wai ni zan ta kiranki maruam amma kiqi dagawa?''
''kadan ma kika gani matuqar kina kan qudirinki,nan da dan qanqanin lokaci zansa almakashi na datse igiyar mu'amala ta dake,tunda ba son Allah da annabi kuke min ba,so kuke ku cutar da ni''
dafe bakinta raliya tayi tana kallon maryam din kamar yau ta fara ganinta,ta sani babu shakka ba qaramin baci ran maryam din yayi ba tunda har ta iya furta mata haka,tafi kowa sanin halinta na rashin son fada da tashin hankali


''sonki muke kuwa maryam,saidai ke dake ahirin juya manufarmu ta alkhairi ki maisheta ta sharri,meyw aobu cikin aurenki da nasir maryam?''kafeta tayi da ido cikin bacin rai tace
''baki bar maganar,nan ba kenan ko raliya?''
''ta yaya kikeso nabar alkhairin da na hango miki ha wofanta kenan a banza?''
''lallai babu shakka kin gaji da hulda da ni.....ina zuwa''sai ta yunqura ta miqe kana ta fice


mintina kadan sai gata sun shigo tare da mama
''wai me ya hadaku ne da raliyan?''maman ta tambaya tana daga tsaye ba tare da ta zauna ba
''mama kinji abunda raliya ke fada kuwa,ba shakka ina tsammanin ta haukace ne,wai mama na auri nasir mijinta fa take cewa''
ba shiri mama ta nemi giri ta zauna,ta dubi raliya sosai
''da gaskene abunda maryama ke fadi?''
cike da tabbatarwa ta girgiza kai
''eh mama haka ne,ni a ganina ni da maryam mun zama daya,na yadda da ita na kuma aminta da kyawawan halaye da dabi'unta,na tabbata ba zata cuce ni ba,to mama laofi ne don na gayyatota tazo mu zauna qarqashin inuwa guda?''


azafafe maryam tace
''kinjifa mama irin abunda take cewa,ro billahil azim indai raliya bata sauka daga kan bakanta ba na miki rantsuwa mama har da Allah daga yau babu ni babu ita har abada''
tsot dakin yayi son su kansu aun sani matuqar maryam ta rantse akan abu to sai ta aiwatar,kuma alamu duka sun nuna irin yadda batun ke taba mata zuciya ba qarami bane,maman ce ta soma magana
''koda maryamu ta amince da maganar ma ni bazan amince ba,haba raliya aisai duniya ta zagemu,jama'a su saka mu a tadinsu,idan banda abunki ma raliya kwata kwata shekarunku nawa da yin auren,banda quruciya haka kawai kuna zamanku gwanin sha'awa ki dinga kira ma kanki kishiya uhm raliya?,na roqeki nima ki bar maganar haka nan kinji?''
qwalla ta cika mata ido ta tausayin maryam don qaunar da take mata ta fisabilillah
''shikenan mama,koda baki roqeni ba zan bar zancen ko don kada na rasa aminiya irin maryam,saidai....maryam na gode,na gode da kika nuna min iyaka ta''
duk da taji rashin dadin batawa raliyan da tayi amma sai taji kamar an tafiyar mata da wani qullutu da ya tokare mata wuya,sai taji damuwarta ta rage farashi zuwa kaso tamanin


durqusawa tayi bayan ta miqe tana qoqarin daukar fadil tace da mama
''mama ni zan wuce''
''kinga malama ajjiye fadil din ni zan daukeshi,tunda ba ke kadai bace ai uwarshi ba''cewar maruam tana yafagyalenta don yi mata rakiya,don ta fuskanci tafiya,zata yi,ta san halin raliya ciki da bai tasan fushinta koda ta tsaidata ma ba hirar atziqi zasu yi ba
''ni kadai ce mana uwarsa tunda kinqi ubansa''ta maida mat martani tana qoqarin ficewa,murmushi kawai maryam din tayi ta saba fadil din ta biyo bayanta


''halan driver ne ya kawoki?''
''ban sani ba,idonki ya baki amsa''tave da maryam din lokacin da auka fito tana gaba ita na binta abaya,mirmuahin dai ta kuma yi har beuty points dinta suka loba
''Allah ya baki haquri,yau kam ai akan gwiwa kike sai lallabe''
''a'ah,akan haba nake''
amsar da ta bata ta sanya maryam tuntsirewa da dariya har itama raliyan ta dan murmusa don fushinta da maryam ba ya wani tasiri
suna isa gaban motar ta ganshi zaune,shi ya kawota kenan,raliya ta bude ta shiga yayin da maryam ta galla masa harar lokacin da suka hada ido,dariya ya tuntsure da ita yana kallon raliya da tayi kicin kicin
''kada kice komai,don babu ruwan nasiru,kinga kanwar nan''
''babu wani nan,waye baisan halinku maza ba,to wllahi bari kaji,idan ka sake ka yiwa aminiya ta kishiya ban yafe ba koda wace ce kuwa,ke kuma kici gaba da nema masa aire kinji ko solobiyo''ta fada harda dan kama kunnen raliyan
dariya abun nata ya basu
''ni don Allah sake min kunne,tunda kin gujemu dai ba shikenan ba''
''indai irin wannan gudun ne raliya am sorry to say....zanta gudunku har abada''ta dan ja da baya ta rue musu qofar tana murmushi sanna ta dan sara mata  shigen yadda sojoji suke
''Allah ya huci zuciyar ranki shi dade,oya kai kuma kaja mini aminiya ta ahankali''
''oho dai abanza tinda yau gaku a rana''ya fadi yana yiwa motar key tare da cillawa raliya gwalo
''wlh a inuwa ka ganmu,kuma duk qwaqwqwafinka ba zaka taba ganinmu a rana ba,ku sauka lafiya,sister am sorry,sai munyi waya''


koda ta koma gidan cikin al'ajabi suke tattauna zqncan da mama,maman ta kuma yabwa qwarai da irin qaunar dake tsakanin maryam din da raliya,ta musu addu'ar Allah ya dorar har tsufansu
sai a san nan ne maryam ta samu sukunin yiwa maman zancan aikin da hajiya atika ta samar mata,shiru maman tayi kamar yadda maryamun tayi tana jirqn cewa maman,shudewar mintina kusan biyu kafin tace
''ke me kike gani game da aikin,tunda kinga azahjrin gaskiya zamanki babu aikin babu dadi,tunda kin riga kin saba,hakanan zai debe miki kewa,baya ga haka harkar makarantar hindatu wa zqi ci gaba da daukar nauyinta idan har kika daina?,amma ke me kike gani mene ra'ayinki?''
''aini mama banida wami zabi sai abunda kika ce''



''kina da zabi mana maryamu zan tauye miki haqqinki ne?,amma dai abinda yafi kawai shine kici gaba da addu'a,Allah yayi miki zabi mafi alkhairi''
''ameen mama''
da haka suka saki maganar suka shiga kuma wani batun daban kuma,haka rayuwarsu take su uku suke yinta,su kashe su binne abinsu babu maiji,hakan ne ke qara haushinsu,cikin zukatan al'ummar gidan


sati guda da maganarsu da haj atika amma har yau ta kasa yanke komai a kai,kwana bakwai daidai da azahar tana sharar tsakar gida ta jiyo sallamarta,cike da mamaki ta yi mata sannu da zuwa sannan tayi mata jagora zuwa dakinsu


ruwan sanyi na pure water da alalen da sukayi ta ajjiye mata sannan ta zauna suka gaisa
''baki da kirki maryamu''haj atika ta fada tana dubanta
murmushi tayi ta dan sunkuyar da kai
''kiyi haquri mama''
''tashi kike abunki da mamanki ma zanyi magana,ko abbanki yana nan?''
''eh,bari na dubo miki''ta fadi tana miqewa,
taci sa'a kuwa yana niyyan fita ta tadda shi,ta sanar da shi sannan ta zura mayafinta ta fita gidan maman fatima maqociyarsu


mintina talatin suna cikin hira isyaku ya shigo yana zumbure zumbure
''ke kije bana yana kiranki''ya juya ya fice abinsa,maman fatima tace
''oh ni Allah,Allah ya kyauta''
''hmmmm,ameen bari naje maman fati sai anjima''maryamu tayi mata sallama ta fice


bata tarad da haj atika ba,sai babanta da mama dake zaune
''baba gani''ya fada bayan ta samu guri gefe da su ta zauna
''maryam''
''na'am baba''
''ki shirya gobe idan Allah ya kaimu ki hada duka abunda kike da buqata hajiya zata zo zaki tafi gidan nan da kukayi magana da ita ta samar miki aiki''
cikin rashin fahimta ta dubeshi
''amma baba ni ina ganin koda zanyi aikin ma ai bani da buqatar tafiya da kaya na,tunda ba wani garin bane ko?''
''ke,bani son sakarcin banza,na riga da na gaya miki,ki hada kayanki,suna da buqatar zamanki ne a can gidan,yo idan kin zauna anan din me zaki tsinana min,illa inyita ganinki baqinciki na ci gaba da damu na?,kije kawai banason kuna sauran qorafi kinji ko?''


kai ta gyada hawaye na layi bisa kuncinta,wannan sam bai dadashi da qasa ba ya miqe ya fice abinsa,kai ta hada da gwiwa ta rushe da kuka,duk yadda taso daurewa zuciyarta ta kasa
''wai me yasa baba baya sona ne mama,me nayi masa?''ta tambaya cikin kuka
''kul maryam,kada na sake jin wannan mummunar maganar a bakinki,mahaifinki ya isa da ke,saboda haka nima bana buqatar wani qorafi kibi umarninshi kawai''
bata iya cewa konai ba face miqewa da tayi ta shige dakinsu zuciyarta na zafi tare da jin tsanar wannan sabon aikin,aikin da zai nisanta ta da mahaifiyarta,zai nisan tata da 'yar uwarta,mama binta tayi da kallo tana jin tausayin diyar tata sosai na sauka cikin zuciyarta,addu'a kawai take mata cikib ranta Allah ya yanke mata wahala,ya kawo lokacin da zata zauna ta huta cikin dakin mijinta

🎄🌲🎄🌲🎄

jikinta duka a sanyaye take shirya kayanta cikin sabon dan trolly dinta mai kyau pink wato ruwan hoda,hindatu ce ta rufe mata sannan ta jawo mata shi cikin parlour don bata da kuzarin da zata iya janshi


tsaye tayi cikin falon ta kasa cewa maman nata komai,don hawaye ne fal cikin idanunta da suya da zuciyarta ke mata,ji take kamar ta bar gida kenan,tana jin tamkar ta bar mamanta kenan,sai maman ce tace
''kuje hindatu jiranta suke,Allah ya bada sa'a,abu guda zan fada miki,ki riqe mutuncinki a duk inda kike,ki tsarw ksnki maryam ki kuma ji tsoron Allah,don babu wani abu da zan iya yi miki a lahira,iya kacin amfani na a duniya ne wajen tunatar da ke bin hanyar Allah,ki riqe amsna ki zauna da kowa lafiya''
kuka ta saki ta fada jikin mama,sai da taci kukanta sannan a sabule ta fice hindatu tabi bayanta da akwatin


sam basu lura da su ba sai shewa suka ji,inna hadiza nw da binta har da tafawa kamar sa'annin juna
''haka dai za'a qare a boyi boyi''inji inna hadizar,hindatu na shirin maida mata martani maryam ta damqe hannunta ta jata suka fice ba tare da ta bata damar tsayawa sun taya yinsu ba



*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺




          ▶🔟




shiru tayi cikin motar tana maida ajiyar zuciya,zugi take jo tana yi mata
har ga Allah da tana da iko ba zatayi aikinnan ba,sam bai kwanta mata ba ko kadan a rai
''maryam,kiyi haquri kinji,na fuskanci baki son aikin nan,amma ni mai sonki ce maryam,na yadda da tarbiyyarkk,ke yarinyace mai hankali da nitsuwa,idan da nasan zaki cutu a gidan wlh bazan gaba kaiki ba,ki kwantar da hankalinki na tabbatar zaki samu nutsuwa da jin dadi cikin gidan *haj hasiya*na da dadin mu'amala,insha Allahu ba zaki samu matsala ba,ki cire damuwa a ranki don Allah kinji maryamu''


ta sake sakin ajiyar zuciyar a bayyane ''to msma insha Allah''ita kanta tasan ta fada ne kawai amma Allah ne kadai yasan ranar daina damuwarta,bata taba rabiwa da maman nata ba sai yau


tafiyar mintina kimanin talatin suka iso unguwar,tun daga farkon unguwar zaka gane cewa ba qananan muta ne ke zaune cikinta ba,daga get din farko allo ne mai dan girma dauke da rubutu kamar haka
*welcome to millonier quaters*


sannu a hankali suke ratsa layukan,layuka ne tsararru tamkar a qasar waje,shuke shuke ne jere reras qofar kowanne gida,hakan sai ya yiwa layin ado ya zamo cike da furanni,layin ya burgeta sosai,duk,da uadda,zuciyarta ke mata babu dadi


qofar wani gida suka ja suka tsaya,dauke yake da madaukakiyar katanga da get mai tsawo da girma,horn tayi har kusan uku kafin wata qaramar qofa ta bude
kallo daya zaka masa ka tabbatar cewa qaqqarfan mutum ne,sanye cikin kaya riga da wando ruwan bula wanda ke alamta unifoarm ne a jikinsa


fuska a hade yake tambayarsu cikin karyayyen turancinsa na brooking 
''wa kuke nema?''
haj atika ce ta amsa masa''gurin hajiya muka zo,ta san kuma da zuwan mu''ya sake tambayarta mene sunanta ta gaya mishi 
bai sake cewa komai ba ya wangale mamakeken get din motarsu ta fada ciki


gurin parking ne wanda yake cike da motoci na alfarma a qalla guda goma,haj atika ta raba tata gefe kana suka fito,sunyi tafiya ta kusan minti biyar kafin su cimma dogon valcony din dake fuskantarsu wanda lullube yake da nau'in furanni kala kala masu qamshi da kyawun kaloli,qofa ce mai fadi cikin valcony din wanda suna shiga ta kaisu ga tafkeken falo wanda ya lamushe rukunin kujeru har set biyar saboda girmanshi


iya qawatuwa an qawata falon iya ganin mai kallo,saidai kawai na barwa mai karatu ya siffanta shi iya yadda zai iya,shiru falon yake sai qamshin freshner da ya gauraye falon da na a.c




_kuyi haquri da wannan don Allah,ku bini bashi gobe uxiri ya riqeni_



*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:50 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺      ▶1⃣1⃣



       tsit falon yake tamkar babu kowa cikin gidan,da ido suke kallon falon tare da  yin sallama koda zasu samu wani a akusa ya amsa musu,saidai har yanzu babu motsin kowa
qofar dake hannun hagu suka ji an murda an bude,duk da 'yar tazarar dake tsakaninsu suna iya jiyo dariyar su,su biyu ne daya a gaba daya abaya
matashiya ce 'yar kimanin shekara ashirin da biyar sai wata agefenta wadda zata iya bata shekaru uku


basu kula da su maryam ba dake tsaye a tsakiyan katafaren falon ba har sai da suka zo daf da su,ta gaban ce mai kimanin shekaru ashirin da biyar din ce ta soma qare musu kallo,kallo ne na qurilla da saka tsarguwa,sai da ta gama tace
''mu je ko jidda na taka miki''ta fada tana kallonsu sama da qasa
har zasu gota haj atika tace
''ji mana''ba tare data dawo ba ta waiwayo tana jirqn me zasu ce
''don Allah ko zaki mana magana da haj bintu?''


cikin halin ko in kula tace''ku zauna ku jirayi fitowarta,may be yanzu zata fito''daga haka tayi gaba abinta tare da jan hannun wadda suke tafiyar tare,haj atika tace ''zauna maryam,bari na kira hajiyar''
maganar second uku fayi da ita ta kashe wayar,cikin minti biyar katafariyar qofar dake hannun dama ta bude,kyakkyawar mace ce 'yar kimanin shekara talatin amma a zahiri ta kai shekara hamsin da uku,kyawun jiki iya ado da kwalliya hade da tsafta ne suka wawashe ragowar shekarun suka boyesu


sanye take da swiss lace ruwan toka da adon orange,sai labcoat da ta dora fara tas a sama,takalmin qafarta hill ne shima fari ne qaf kamar ranar ta fara sashi,ta nade wuyanta da mayafi orange,fuskarta qunshe da yalwataccen murmushi
''sannu hajiya,maimakon ku shigo sai kuma ku zauna anan,ku taso don Allah''ta fada tana nuna masu qofar,gaba tayi suka bita abaya


abun mamaki sai gasu a wani gurin,guri ne mai kama da gurin shan iska,saidai dauke yake da tyles fari qal illa tsakiyar gurin da aka yiwa shafe din cycle aka cika shi da 'yan shuke shuke masu furanni dake fidda qamshi
qofa ce ta glass wanda na waje baya iya ganin na ciki bayan sun shiga ciki ta fahimci hakan,falo ne shima mai dauke da kujeru set biyu,gini ne sama da qasa wato mai bene,wanda matattakalar na acikin falon,tsarinshi abun sha'awa ne matuqa duk iya iya tsarinka sai ya burge ka,komai na cikin falon fari ne da milk,babu alamun qura ko dauda a tattare da shi sai kace yanzu aka bare komai aledarsa aka sanya


''bismillah''hajiya bintu tace musu tana shirin zama
''hajiya ga maryam na kawo miki,kuma bani da haufi a kanta,ke kanki,nasan zaki ji dadin aiki da maryam insha Allahu''haj atika ta fada bayan sun gama gaisawa
murmushi ta sake yi
''ina fatan haka,maryam sannu,ina fata hajiya ta gaya miki komai,girki ne kadai nake so ki dinga yiwa yaro na,kada kiji a ranki cewa wai aiki kika zo,kisa aranki taimako na kika zo yi,ki dauki kanki tamkar diyata,domin dama ina cike da kewar rashin yarinya mace,to ina ji a raina yau Allah ya bani,abu daya kawai nake buqata daga gareki,ki riqe amana don Allah,ki kula ki kuma yi taka tsantsan da abincin yarona,nasan kinsan komai game da abubuwan da ya faru a kanshi,ina son *abdallah* don Allah ki kula min da shi,na rasa babanshi bana son in rasa shi''ta qarashe maganar muryarta na bayyana raunin da zuciyarta tayi


duk sai taji tausayin su ya kamata,sai take jin ina ma ita ta samu wanna gatan,ina ma ita ke da gata har kamar haka
''insha Allahu haj na miki alqawarin ba zaki samu wani abu mai kama da cin amana ba daga gareni''
hakan data fada dukansu yayi masu dadi har haj bintan na murmusawa
''idan kika min haka kuwa maryam kin gama min komaibani da abinda,zan saka miki da shi,gyara guda daya,indai kina son insinga jinki kamar diyar tawa da gaske to kada ki sake kira na hajiya,ki kirani da *mami* kamar yadda *Abdallah na* ke kirana''
sai a lokacin maryam tayi murmushi karo na farko,harga Allah taji dadin karramawar da tayi mata''to,mami''
''yauwa,na gode,hajiya atika na gode qwarai da gaske,bazan iya manta wannan taimakon da kika yimin ba''
''babu komai haj bintu,ai abdallah kamar da yake a gurina,ni zan wuce,maryam.....''
hajiyan ta fada tana miqewa


har waiting parlour haj bintu ta taka mata sannan ta dawo,da murmuahin dai nata ta dubi maryam
''taso,maryam na nuna miki daki,don fita zanyi asibiti ina da C S har mutum uku,Allah ne ma yayi ba zamu samu sabani ba''ta gaya mata lokacin da tayo gaba ta bita abaya,wani labule mai kyawun tsari ta daga daga sashen hagu na falon,saiga gajeran corridor ya bayyana,dakuna uku ne a gun,ta tura daki na uku ya bude tace
''bismillah maryam,ga dakinki,ni,zan fita ki zauna ki huta kafin na dawo mu shirya yadda lamuran zasu kasance,yau dai babu aiki,don Abdallan ma baya gari,amma gobe zai dawo''
''to,mami sai kin dawo''ta fada cikin girmamawa


tabi dakin da kallo bayan mami ta fita,daki ne wadatacce shimfide da carfet mai taushi,sai gado cupboard ta jikin bando da madubi hadi da dressing chair,curtains,dukkaninsu pink da fari,cikin dakin akwai toilet,sai a c daura da window din jikin gado,gefan gadon ta ajjiye kayanta sannan ta shiga toilet din ta dauro alwala ta gabatar da sallar la'asar sannan ta soma jera kayanta cikin sif din


sama sama take jiyo sallama a falon,ta miqe ta maida hijab dinta tayo hanyar falon,budurwar da suka gani ce dazu tsaye tana kalle kalle
''sannu''maryam tace da ita don jawo hankalinta ta fuskanci ta fito
a dage ta kalleta 
''ina mami?''
''ta fita aiki''
bata tanka mata ba ta juya ta fice itama maryam ta juya ta koma dakinta



*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺


         ▶1⃣2⃣




Har gefin magariba tana gyaran kayanta cikin drower din,dakin tsaf yake don haka bashi buqatar wani sabon gyaran na daban,ta maida qofofin cupboard din ta rufe dai dai lokacin ta jiyo kiran sallah sama sama saboda haka ta shige toilet


har isha'i tana kan abun sallarta,sai da ta bada faralin isha'in sannan ta nannade ta,zaman shirun ya mata yawa,sai kewar gida ta soma damunta,ta jawo wayarta ta lalubu number din hindatu ta kira,ba bata lokaci ta daga
''wayyo ya maryam dita,i missed you wlh wuni guda kawai''
ta gatsine fuska tamkar tana gabanta
''hmmmm,ba wani nan,kinyi missing din nawa kika gaza kira na sai da ni na nemeki''
''ayyah anty na,kinsan dai halin student,wayan,ba credit,am sorry ya maryam''


''shikenan,ya gidan ina mama ta''
''gata kusa da ni bari in bata''
kusan minti goma suna hira har aka fara mata warning kudinta sun kusa qarewa sannan sukayi sallama
toilet ta koma ta hada ruwan dumi tayi wanka ssnnan ta sauya doguwar rigarta mai kauri ta bacci ta dora hijab,tsna maida kayan da suka fadl daga cikin sif din ta jiyo sallaman mami


kan kujerar falon ta taddata a zaune tana cire agogon hannunta
''sannu da dawowa mami''cikin fara'ar nan dai tata tace
''yauwa maryama,ya baqunta,na barki ke daya ko,gurin nawa ba yara ni daya ce,gun haj laura kuma basu sanki ba bare ki shiga,sannan na manta ban nuna miki kitchen ba,ina fata yunwa bata takura ki ba''
murmushin itama tayi
''banjin yunwa ma mami''
''a'ah,ban yarda ba,bari na shirya na fito saiki dafa mana wani abun mai sauqi''
''to mami''
miqewa tayi tana nuna mata jakar da ta shigo da ita
''taimaka ki shigo min da brief case din nan''inji mamin ta haura sama maryam din ta bita a baya tana mamakin sauqin kai irin na mamin,tamkar ita ba wata bace,tsabar sanin qima irin ta dan adam


saman ma wata duniyar ce,komai nashi fari ne tun daga parlour har bedroom din mamin sai dan ratsin baqi kafan wanda bai taka kara ya karya ba
''hmmm,wani aikin sai likitoci''maryam ta fadi a zuciyarta


a falon qasan suka sake zama bayan sun kammala cin abincin daren
''gaskiya maryama my son zai morewa girkinki,haka kija iya abinci''a kunya ce tayi mata murmushi
cikin seriouse tone tace
''maryam kamar yadda na fadi miki dazu inason Abdallah so na haqiqa saboda shi kadai Allah ya mallakamin,cikin irin abinciccikan da Abdallah keso akwai irin namu na gargajiya,sannan yanason kayan snacks,aikinki zai kasance ne ranar weekend zaki dinga breakfast lunch da dinner,amma ragowan kwanakin breakfast ne kawai sai dinner,amma idan ke kina da buqatar ci zaki iya dafawa,saidai majority idan da wuri abdallah zai fita yana tafiya ne da breakfast dinshi


sannan anan zaki dinga shirya masa saman dining dina anan yake karyawa,ina fata nima za'a dinga sammin idan an dafa din''ta qarashe cikin sigar tsokana,dariya ta baiwa maryam
''me zai hana mami,ai sai kince ya isheki ma''
''to godiya nake,amma please maryam ki riqe min amana don Allah,na yarda da muta ne da dama akan Abdallah na amma sun ha'inceni,and pls feel free ke 'yar gida ce''
taji dadin bayanin mamin sosai har zuciyarta


kadan kadan mamin ke janta da hira bayan ta nuna mata store da kitchen din nasu,tace ta duba idan da abunda take buqata ta fada zuwa gobe da safe a siyo tunda da yamna take tunanin zuwan Abdallan
girgiza kai tayi
''komai yayi mami''
''to masha Allah,sai waj.....''
maganr tata ta katse sakamakon shigowar kira wayarta qirar iphone 7
murmusho maryam taga tayi har haskrn haqorin makkar ta ya bayyana
''dan halak,yaqi ambato''mami ta fada a bayyane tana shirin daga wayar
''salamu alaikum my son yanxu nake zancenka''
''mami na ke da wa?''
''sabuwan mai dafa abinci nayi maka abdallah''
sai da ya danyi jim 
''anya mami ba za'a haqura haka ba?''
''kada ka damu son,insha Allahu wannan karon ba za'a samu matsala ba kaji,saboda hankali na ya kwanta da ita fiye da wadancan''
''tunda kin aminta mami shikenan''maryam dake tsaye sai ta danji ba dadi,duk da bata jin abinda yake fadi amma ta fuskanta kamar bai marhabin ne da zuwanta gidan


''insha Allahu ba damuwa,yanzun ma muna tare,muna tsara tarbarka gobe''
ya narkar da murya tamkar qaramun yaro
''ayyah mami na,abinda nakw ta fargabar gaya miki kenan tun dazun,aikin ne mami bai kammalu ba sai nan da kwana uku,kinga ya zama dole na qara kwana hudu kenan,bazai yiwu na taho na barsu ba gudun samun matsala,but....i promise mami na nan da kwana hudu a gida zan kwana kiji mamina,kuma pls kada ki saka damuwa cikin ranki''
ta danji a ranta kam don tana matuqar son Abdallah,amma sai ta share
''shikenan my son,Allah ya kaimu ya kuma kare min kai,ya bada sa'a,ka ci gaba da addu'a don Allah banda wasa''
''insha Allah mami na,i love you''
sai da tayi murmushi sannan tace
''i love you too my son''


daskarewa maryam ta kusa yi a tsaye,tana sake jinjina soyayyar dake tsakanin mami da dan nata
''kinji ma maryam,abdallah ya hutashsheki,sai nan da kwana hudu zai dawo''tace da maryam wadda ke duba,cikin wani dan qaramin oven dake gabanta wanda a badini duniyar tuna ni ta tafi,ta dan washe fuska
''ayyah,Allah ya nuba mana''
''ameen ameen,mujeko sai kiyi kwanciyarki abinki''
tare suka fito falon sai suka tadda ta a zaune saman kujera,budurwar dazu ce 
''sannu mami''tace tana dan murmushi hade da kallon maryam da hakanan tun ganin farko taji ta tsone mata ido,ko don kyawun da take hangowa baro baro ne kwance a halittar maryam din oho?
''yauwa sannu zubaida''
''na shigo ai dazu baki nan sai waccar na gani''
mami ta juya tadan kalli maryam
''sunanta maryam....ya akayi zubaida?''
tadan murmusa
''zuwa nayi na amshi key na part din ya abdallah zansa a gyara,naji kamar gobe zai dawo ko?''
'' damuwa jeki abunki zubaida zan gyara miahin da kaina,tunda kinga waccan karon yayi fada''
''to zan gyara da kaina mami''
''kada ki damu zubaida,jeki abunki''raahin,kin dadi qarara ya bayyana a,fuskarta,amma sai ta juya zata fice
''am....zubaida''mami tayi kiranta
ta juyo a sanyaye,kana ta amsa
''ku tafi tare da maryam ta gaida nene,ma'aikaciyar da na daukarwa abdallah ce''
dif zubaida tayi a ciki ciki tace ''to''ta juya tqci gaba da tafiyarta


momy ta kalli maryam''kije ku gaisheta,abokiyar zama na ce tin kafin rasuwan abban abdallah''
to din itama tace kana tabi bayan zubaida da tuni ta fice daga falon nasu har ta isa filin dake cikin bangaren nasu


Tana biye da ita har suka shiga bangaren nasu,ginishi iri, na mamin ne babu maraba sai bambancin furnitures,mutum biyu ne zaune a falon kallo suke na wani american film a M B C ACTION wanda volume dinsa ya gauraye falon,zubaidaida batayi sallama ba sai maryam wadda siririyar muryarta bata wadatar da su sun jita ba,zubaida ta zauna kusa da matar wadda ta kusa ahekara hamsin da biyar tana fitar da numfashi daga bakinta
matar na juya ta dubeta
''um hmmm,ai nasani iska ce ke wahalar da mai kayan kara,ni nasan ba baki za'ayi ba,amma tunda ke kika g....''
''nene ga mai aiki nan mami tace na kawo miki ki ganta''ta katse babar tata don ta lura basu lura cewa ba ita daya ta shigo ba
lokaci daya suka zuba mata ido nenen da daya budurwar dake zaune kusa da ita har maryam din taji faduwar gaba


nenen ta maida kallonta ga zubaida
''mai aiki,kodai baki ji bane sosai''
cikin yamutsa fuska da alamun qosawa tace
''wadda zata dinga wa ya Abdallah girki da ta canza''
nenen ta dawo da kallonta gun maryam,ta dan tara qarfin gwiwarta tace
''ina yini''second kusan biyar kafin tace
''lafiya,Allah ya taimaka''
''ameen,sai da safenku''maryamun ta fada tana juyawa ta fice a bangare nasu,sai da ta fita sannan ta samu nutsuwa,don ta tabbata rakiyar idanu suka yi mata






*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺

         ▶1⃣3⃣




cikin kwanaki ukun da tayi da mami ba qaramin dadin zama da ita taji ba,maca ce mai sauqin kai da iya mu'amala,haba haba da jama'a kowa nata ne,duk lokacin da suka zauna bata da labarin bawa maryam da ya wuce labarin abdallah
halayenshi
me yakeso mene baya so
quruciyarsa da shirmensa
tun maryam na daukar abun qarami har ta maida shi babba,lallai qauna ce mai girma tsakaninsu wanda Allah ne kawai yasan iyakarta


takanyi kuka aduk lokacin da mamin ta gama bata labarin mu'amalarta da Abdallah,tana dadewa kafin tayi bacci
me yasa ita bata ganin irin wannan qaunar musamman daga gurin abbanta?
me tayi masa?
wanne irin laifi tayi masa da yasa take samun rashin kulawa da raahin damuwa da ita daga abbanta?
saidai tana godiya ga Allah saboda uwa ta gari da ya bata mai jajircewa kan lamuranta


duk lokacin da zata fito zata tadda sashen nasu tas,ma'aikatan har sunzo sun gama aikinsu sun tafi,saboda mami gwanar tashi ce da wuei ta saba,sai aka hada biyu don itama maryam din haka saboda yanayin aikinta da tayi a abaya


ita daya take wuni bangaren nasu musamman idan mami ta fita,takanyi mamakin yadda gidan yake shiru kamar babu kowa a gidan,don ita dai tun ranar farko bata qara ganin wani ba,daga ita sai mami idan ta dawo,ta saba gidansu cike yake da jama'a,hayaniya kuwa sai dare ya tsala kake daina jinta,wannan yasa ta kuma maida hankalinta kan wayarta,research kan nai'ikan girke girke ya sake zama abokin ta wanda hakan yake sake bata damar qwarewa da samun experience duk kwanan duniya

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

ta fito kenan dauke da kayanta kala biyu sukayi kacibus da mamin hannunta riqe da maqullai
pakistan ne ajikinta riga da wando sai mayafinsa da ta yane kanta,yana daya daga jikin abinda ke boye shekarun mamin 


tadan rusuna
''barka da warhaka mami,na zaci kin fita da muka gaisa dazu''
fuskarta a sake kamar kullum tace
''ban fita ba maryam,na tsaya gyaran dakunan Abdallah ne,kada ya dawo ya iaheni da mitar na bayar an gyara masa daki''
murmishi itama tayi
''ina fatan diya ta baki mance gobe ne aikinki zai fara ba''
gyada kai tayi
''ina sane mami''
''yayi kyau,kayan meye a hannunki''
ta kalli kayan sanna ta kalli mamin
''waje,zan dan fita ne na wanke su,bana son in tara kayan datti''


dariya tayi
''to wa yace miki bamu da mai wanki maryam?,ajjiyesu,zan baki num din mai mana wanki ki kirashi yazo ya karba,zan fito da nawa duka ya hada''
''to mami''


da la'asar mak wankin yace mata ya iso yana waiting parlour wato falon su na farko,ta jado kayan duka ta sameshi tsaye,yana amsa ya juya zai fice,kafin yakai ga fitar zubaida da zahariyya 'yar uwarta suka shigo,dukkaninsu dogayen riguna ne ajikinsu masu santsi,babu mayafin da suka yafa yana saqale ne agwiwar hannunsu sunyi fashion da shi,kwatan kwacin irin shigar da 'yan matan yanzu keyi espicially gurin dinner din biki(wadda a nasu ganin suke kiranta da iya ado ko wayewa,wanda sam ko kusa,tsabar rashin sanin ciwon kai ne,Allah ya yiki mai tsada amma kin maida kanki mai arha,jikin da sai mutim ya biya sadaki zai gani kin raba shi kyauta kowa yagani,tinda hatta dinkunan da akwyi na fityed gown babu shatin abinda bai bayyana ba,ki sani bakya burge mai ilimi sai jahili,duk wanda yace kina burgeshi da irin wannan shigar to qarya yake,jikinki ne yake burgeshi,aqalla nasan bazai bar qanwarsa tayi irin wanna shigar ba bare 'yarsa,kin fito sak hadisin da annabi ya siffanta irinsu wadanda yace ba zasu shiga aljanna ba baza su kuma ji qamshinta yace kaasiyatin Aariyatin masu tufafi ne amma tsirara suke,maa'ilaatin mumilaat,karkatattu ne masu kuma karkatar da hankalin maza,sadaqa rasulul kareem)


kuma da yaci moriyar ganga zai yada qoranta,tuni zahariyya wadda me qaras qaras da chewing gum ta bangajeshi,sannan ta kuma juyo cikin gatsali da qasqanci
''dalla can malami,saboda ysabar rainin wayo da rashin mutunci kana gani zaka bangaje mutane?''
''Allah ya baki haquri''yace da ita yana sake kauce mata
''wallahi next time idan ka sake ka sake kwatankwacin haka na ranste sai na maka qasqanci,kuma ka tsaya ka jada a namu wankin,aikin banza kawai,mtseew''taja wani matsiyacin tsaki ta wuce,zubaida ma nata tsakin ta ja tabi bayan 'yar uwarta ba tare da ko sun dubi maryam ba


suna tsaye sai ga zubaida ta dawo dauke da kayan ta watsa masa
''kuma kada su wuce gobe na gaya maka''tajuya tayi shigewarta ciki
maryam ce ta tayashi tsince kayan tana bashi haquri,don duk gaba daya jikinta yayi sanyi,bata son taga ana wulaqanci wa dan adam
murmushi yayi
''ai babu komai hajiya,idan da sabo ai mun riga mun saba,banda darajar hajiya mami ma da tuni cin abincinmu ya qare agidannann tun bayan rasuwar alhaji''


ita dai bata fasa bashi haqurin ba har ya fice,a tausaye ta bishi da ido,wato a fayuwa idan dai kai talaka ne to baka to da kai da banza duka daya ne?,mutane daidaiku ne suka san waye dan adam wanne matsayi yake da shi cikin halittun ubangiji
''aikin banza''
taji am fada cikin dan daga murya
da sauri ta waiwayo,zubaida ce tsaye,cikin valcony din benansu wanda aka yishi ta cikin waiting parlour din,dauke kanta tayi don tasan sarai da ita take,itakam idan wannan ne itama ba naqonta bane,idan da sabo ai ya zame mata ruwan shata tun tasowarta cikin sararin duniya bata huta da makamancin wadannan dabi'un ba cikin mutanen da take rayuwa da su

🎄🌲🎄🌲🎄

Washegari tun bakwai mami ta fita tace zata ta nada excuse wa patients dinta don gobe da jibi bazata samu fita ba saboda dawowar dan lelenta wanda ya koma england cheekup bayan dawowarsa ta farko ya sake komawa tun bayan poising din da yasha,mutum ne mai qulafucin aikinsa saboda haka ya jefi tsuntsu biyu da dutse guda,bincike suke kan wani dan nijria tun kafin ya kwanta jinyarsa ta poising din da yaci wanda ake zargi da safarar muggan qwayoyi,a dan binciken da ya fara ne ya gano ya gudu england saboda haka yana gama ganin likita ya kutsa binciken mai laifin,cikin taimakon Allah
gogewa jajircewa da qulaficin iya aiki ya gano shi,abunda ya tsaidashi ya sashi qara kwana uku shine kamo ragowan abokan sana'ar tasa guda uku wanda dukkaninsu ya samu nasarar daqumosu ya aunosu nijeria gaba daya dan su girbi abunda suka shuka


jirgin da zai sauka qarfe shida na maraice ne zai sauka da su don haka tun misalin sha biyu na rana maryam ta shiga kitchen,tun jiya ta gama redy din duka abunda zata biqata ciki kuwa harda qullin waina da sinasir,miyar agushi ta soma hadawa wadda ta wadat ta da busashen kifi hade tantaqwashi sannan ta hada lemuka kala uku


bayan sallar la'asar ta hau suya wainar da sinasir,ta kammala tana shirin wanke kwanukan da ta bata ta jiyo shigowar mami,kan ta fito ta taddata cikin kitchen din,da fara'ar dai tace
''gaskiya an tayarmin da yunwata,qamshin kawai yasa naqagu inji dandanon ya yake,tunfa daga waje maryam nake jiyo qamshin nan,kai yau kice Abdallah da santi kenan''
murmushi tayi
''ko na zubo miki mami?''
sai da takalli agohon dake daure atsintsiyar hannunta sannan 
''a'ah,jirginsu Abdallah ya kusa sauka,sauri zanyi na shirya kafin a daukoshi,idan naci abincina kuma ai masha qorafin don me banyi jiranshi ba''


sallamar zubaida ta ratsa dodon kunnensu,mami ce ta amsa mata tana fadin qaraso kitchen din



*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺

          ▶1⃣4⃣




Sallamar zubaida ce ta katse hirar tasu,mami ce ta amsa mata tace ta qaraso suna kitchen
taci ado ta cake cikin code lace dan ubansu wanda kana ganinshi kasan ba qananun kudi aka kashe wajen siyanshi ba
orange ne don haka ya haska baqar fatarta,tayi kyau sosai
''mami zamu je airphort taro ya Abdallah'' ta fada tana dan sunkui da kai
''Allah ya tsare sai kun dawo''
''ameen''


har ta juya mami tace
''am...zubaida,cikin ayarin su zai iso,ina ganin zaifi idn kika jira isowar a gida ko''kada kai tayi
''mota ta daban da tasu ai mami''
itama kan ta kada ''shikenan sai kun dawo''


sai da ta fice mami ta dawo da kallonta kan maryam
''zan haurq sama maryamu,idan kin kammala kema kije ki huta,sannunki,lallai kin aikatu''
''to mami,sai kin fito''ta fada cikin 
murmushi
sai da ta sake biyawa ta dining din ta tabbatar komai yayi neat kana ta wuce dakinta


wanka tayi ta sauya kayanta zuwa atamfa dinkin riga da skert,gashinta kawai ta kama ta daureshi da qaramin ribbom saboda bata fiya sa babban ribbom ba kasancewar gashinta akwai tsaho da cika,gefan gadonta ta koma ta zauna bayan ta dauko man da zata sjaf ta soma sjafawar a kasalance tamkar mai tausayin kada ta jima fatar tata ciwo,haka kawai take jin wata kasala na saukar mata,ji take kamar ta lwanta abinta tayi bacci


bata kammala shafa man ba ta jiyo jiniya da hayaniyar motoci cikin harabar gidan,a hankali ta miqe ta isa bakin window din dakin ta dan yaye labulen,bata hango komai yadda ya kamata sai dan abunda ba'a rasa baba kasancewar window din ba dirwct harabar gidan yake kallo ba ya dan fi karlata wani sashen,na doguwar valcony dinsu,bugu da qaro jama'ar da auka shigo gidan cikin motocinsu wadanda dukansu yan rakiya ne


tawagar mutanen suka biyo ta cikin valcony din tanan ta hango zubaida wadda fuskarta ke a dinke tsaf da alamu cikin bacin rai take


yana tsakiyarsu,saidai dukansu ya fisu tsaho,tafiya yake cikin hanzari wanda alamu ke nuna cewa cikin kuzari da qoshin lafiya yake,fari ne sol wanda yasa ya zarta duka jama'ar dake tare da shi hasken fata,ko ba'a gaya mata ba ta fuskanci shine *abdallan mami*yawan jama'ar dake baibaye da shi ya sanya bata iya ganin fuskarshi saboda juya kanshi da yayi daya bangaren yana magana da wani saurayi  da sauran jama'ar dake gefan nashi,abu uku zuwa hudu zata iya fadi a kanshi suit ne a jikinsa baqa wul mai sheqi wadda ko da bakasan kudin sutura ba kallo daya zaka mata ka tabbatar bata qananen kudade bace,sumar kanshi cike take kuma akwance luf ba tsayayya tamu irin ta hausawa ba,tafi kama data jaruman fina finan india ko larabawa,sai abunda ke saqale bayan kunnenshi guda daya wanda take gani gurin masu aikin tsaro,saidai wannan mai azabar kyau ne haka nan shima baqi ne


har suka kammala wucewa tana tsaye a gun,ita kanta batasan me ya tsaida ta din ba,sai daga bisani ta saki ajiyar zuciya hade da sakin labulen ta koma ciki ta lalubo hijabinta ta zura ta tayar da sallah don wasu guraren har sun idar


mami na tsaye qofar sashenta harde da hannayenta,duk yawan 'yan rakiyar abdallah bai hanata gano yaron nata ba,yayin da murmushin farin ciki yaqi bacewa fuskarta,daga hannun hagun falon kuma haj nene ce tsaye ita da zahariyya,idonsu tsaye car kan abdallah da zubaida wadda a yanzu ta bar bin bayanshi ta nufo inda suke tsaye
zahariyya ce ta tabe baki''don Allah nene dubeta,aikin banza shegiyar yarinya kawai mahaukaciya,wai har wani murna take da dawowar abdallah,don Allah ki barni da ita nene wallahi sai na gyara zamanta''



dafa kafadar zahariyyan tayi tana wani murmushi da na kasa fassara shi''um...um,kinga matsalarki kenan zahariyya gaggawa,idan bakiti wasa ba zaki bata mana  plan,ki bar zubaida tayi yadda take so loka ci ne fa,kuma ke kanki kinsan nasan me nake yi ko?''
''to amma nene wallahi idan ba muyi taka tsantsan ba zata zame mana matsala''
''ita din ubanta,ni na haifeta ko ita ta haifeni,ki rabu da ita dai a yanzu,akwai lokaci kamar yadda na gaya miki''
''ko tazo kada ki mata maganar''nenen ta fada da sauri ganin zubaidar ta kusa cimmasu,dama mutanen dake falin ne suka hanata isowa da wuri


har isha'i maryam na jiyo sauran hayaniyar jama'a,don haka tana idar da sallar isha'in tayi rigingine abunta bisa gado,kusan goma saura tunanin mamanta ya fado mata,layin hindatu ta shiga nema saboda muryan maman da takeson ji,saidai tayi rashin sa'a is switched off,tsaki taja cikin rashin jin dadi a ranta tana raya cewa da ta dauki albashinta na farko cikin abunda zata yi harda siyawa maman ta waya sabuwa da kuma power bank mai aiki da hasken rana


tana tsaka da tunane tunanen nata taji an turo qofar dakin,mami ce wannan karon cikin kwalliyar atamfa super mai kalan blue maidan turuwa,abunka da fara sai tayi tas
''a'ah maryamu kwanciya akayi?''
''eh wallahi mami''ta amsa mata tana mai miqrwa daga kwanciyar da tayi tana maida daurin dankwalinta da ya zame
''a'ah,yi kwamciyarki abinki,ai kinsha aiki bsna tasheki ba''
tana saka slipper dinta dake bakin gado wanda mami ta bata take amfani da shi tsakanin edroom din zuwa parlour zuwa kitchen
''ba komai mami me kije buqata''



tana shirin amsa mata wayarta ta dau ringing
ta kara a kunnenta kai tsaye tace
''ya akayi abdallah''
cikin kwantar da murya yace
''mami yunwa nakeji,wayyo cikina mami''
dariya tayi
''kajimin shi don Allah,yaron goye ne kai,ka soma ci gani nan fitowa na shigo in taho da maryam ne don muci abincin tunda tare muke ci bayan baka''
''wace haka?''
''sabuwar mai girki kuma diyata''
''ayyah mami,ayyah....,nikam nasan kin rage ji da ni,banda haka daga dawowata mami yau inason musha hirarmu mu biyu kuma saiki yo gayya,nidai mami ki taho  ke daya abinki kamar yadda muka saba ko inzo in taho dake''
''naji ya isa sarkin qorafi,kada ka shigo mana daki gani nan fitowa''
''thank you my mammy,ki sauri na qagu ki fito''
dariya ma ya bata,abdallah kenan,ko yaushe idan yana gabanta daukan kanshi yake kamar qaramin yaro


sai da ta dan kalli maryam ta gefan ido dake zaune gefan gado kanta a qasa tana fatan bata ji ba,ta riga da taji amma sai ta nuna kanar bata ji din ba saboda bata ji komai a ranta ba don itama batason ta shiga tsakanin wannan uwa da dan masu azabar shaquwa
''kinci abincinki e maryam''
''sai anjima,amma dai na shigo da shi''
''to shikenan ki kwanta ki huta,Allah ya huta gajiya,sai gobe idan Allah ya kaimu''
''to mami''
har ta kusa ficewa maryam din tace
''a cewa ya Abdallah ina masa barka da zuwa''



murmushi mamin ta saki don har cikin ranta taji dadin kulawar da maryam din ta nuna kan tsoka daya a miyanta
''zaiji insha Allah''
ta fice bayan ta ja mata qofar
kayanta ta cire ta sauya na bacci ta ja abincinta ta danci sannan ta kwanta baki daya



Qarfe takwas a kitchen tayi mata,tana cikin hade haden abinda zata tanadar musu na bre fast taji an shigo kitchen da sallama,ta waiwayo tana amsawa,mace ce wadda a qiyasce zata doshi shekaru hamsin,ta qaraso kusa da maryam,a ladabce maryam din ta gaidata,itama ta amsa mata cikin fara'a sannan ta dora da cewa,ni suna na uwani,ma'aikaciyar haj bintu ce,naje hutu na ne da take bani na shekara sai yau na dawo,kin ganni da wuri ko?,qauyen mu ba mai nisa bane shi yasa na fito dacwuri gasji Allah ysa na iso da wuri,ni daga qauyen sumaila nake''


murmushi maryam tayi jin cewa suna da maqwaftaka da qauyukansu
''sannu baaba,ni kuma suna na maryam sabuwar ma'aikaciyar data dauka ce saboda kula da girkin yaronta,ni a cikin gari nake saidai asakin mu yan qauyen gaya ne''
cikin jimami da 'yar fara'a tace''Allah sarki kice maqota ne mu,kingawadancan ma'aikatan hajiyan maha'inta ne,da su aka hada baki aka zubawa yaron nan guba wallahi,Allah ne yayi da sauran shan ruwansa a gaba,don Allah mero ki riqe amanar hajiya saboda mutuniyar kirki ce''
dariya baba uwani ta bata jin ta ambaceta da mero


''insha Allahu baba,Allah ya bamu ikon riqe amana''hira baban ta shiga zubawa maryam tana maida mata labarin yadda lamarin ya auku,taso ta karbi wani abin ta taya maryam din amma ta qiya don hirar ma kadai da take mata tana debe mata kewa da sata jin qwarin gwiwar aikin,da haka har ta kammala hada fried plaitain with sauce,ta dafa tea da ya wadatu da kayan qamshi lemon grass,kimba da ginger,ta jada da coconut flour pancakes saboda tea din


da yake ba mai yawa tayi ba duka kadan kadan ne daidaisu hakan ne ya bata damar kammalawa da wuri,ta zubawa bab uwani tana ci tana santi maryam na dariya,cikin haka mami ta shigo suka gaisa itama ta shiga dariyar santin da baaba uwani take bayan ta yi mata sannu da isowa,itama tayi mata barka da dawowar abdallah gida,mami tace ta bar baaba uwani ta gyara kitchen din ta wanke kwanukan don dama aikinta ne


cikin kitchen din ta barsu ta shiga dakinta ta gyarashi kana ta shige wanka bayan ta wadati shi da freshner,koda ta fito karyawa tayi ta kuma kwanciya,babu dadewa kuwa bacci ya sureta,sai sha biyu da rabi ta farka,agogo ta duba da hanzari ta shiga toilet ta wanke bakinta da fuskarta ta zura hijabinta dan zuwa saman mamin ta tambayeta a dora girkin rana ne





*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺
         ▶1⃣5⃣




A qofar falon ta tsaya tayi knocking,daga can ciki taji mamin na tambayar wane,ta amsa mata sannan ta mata izinin ta shigo


A bedroom ta tarad da ita tana gyaran wadrob dinta
''sannu da aiki mami''
''yauwa maryam,sannu''
''mami ai da kin kirani na miki aikin''
''haba,kina bacci maryam ya zan tada ke''
''mami dama cewa nayi me za'a dora,naga rana tana ta yi''
tana zuba wasu kayan cikin sif din tace
''indai don ta Abdallah ne rabu da shi,don ko breal fast din ma baici ba,yana can yana yawon bacci,na yi da shi ua tashi ma ko laruawar ne yayi ya koma kinga yaqi,baqi sai ziwa suke masa sannu da dawowa amma kinga yaqi fitowa wai ramuwar bacci yake,saidai kawai ki dan dafa wani abun ba mai hawa ba saboda ke da baba uwani,ga baqi kuma don nasan yau ba za'a rasa baqi ba''


''to,mami''ta amsa tana shirin juyawa ta fice
''tsaya ki dan taya ni hira,ai yayi wuri a dora shi yanzu mamin ta dakatar da ita tana murmushi
kadan kadan suke hirar tasu har soma taya mamin aikin,tana shirya kayan ta miqa mata ita kuma ta zuba acikin drower din


Bata shirya kallon qofar dakin ba amma tilas tayi hakan,sallama akayi cikin wata murya mai cike da dadi da kwarjini wadda ke bayyana cikar haiba da halittar mamallakinta,second daya da yin sallamar qamshi ya baibaye dakin gadon mamin duk da cewa an dan turo qofar ne kadan an kuma boye a bayan qofar daga waje ba'a kai ga shigowa ba


hannun wanda ya bude qofar mai daure da agogon rolex ne kawai da barin jikinsa zaka hango
''mami na shigo ko na koma?''
''taya zance abdallah ka koma,bismallah qaraso''ta bashi amsa tana kallon qofar fuskarta qunshe da murmushi
ya qarasa turo qofar a hankali ya bada wata 'yar qara kadan,ya sako farar qafarsa mai dauke da zara zaran yatsuda maau qunshe da gargasa saman kowannensu,sanye yake da shadda fara qal babbar riga da 'yar ciki da wandonta,baqar hula ce zanna ahannunsa wanda da alama yana tafe ne yana mata kari bai qara sa ba ya iso dakin,fuska cike da qayataccen murmushi yake fadin
''nayi zaton kinyi fishi saboda banyi break ba''


''banyi fushi ba amma banji dadi ba''
''Allah ya bako yawan rai mami na,nima banso nayi missing daddadane n break fast ba,saboda na tabbata zaiyi dadi kamar abincin jiya''
''to ai ga mai girkin nan,sai ka mata sannu''ta fada tana nuna maryam wadda ke,daskare gu guda,kallo daya ta masa ta kasa yin na biyu,ba don komai ba sai wani kwarjini da cika ido da taga yayi mata,duk kyawun mami da take gani aahe nafila ne,wannan tabbas idan da mace ne saidai a hanata fita zuwa ko ina saboda fitar ba qaramin hadari  bace tattare da ita da ssauran mutane


ya dan dubeta a fisge atill,kanta na duqe yace
''sannu fa''
ba tare da ta dago ba tace
''ina wuni?''
''lafiya''
ya amsa yana diban mami
''uhm,sai ina kuma''
yana ci gaba da karin hularsa yace
''masallaci mami,kin manta yau juma'a''
''haka ne,ka ci wani babban riga kamar gaske''
''kamar ranar daurin aure na ko mami''ya fada yana qarasawa bakin mirror yana dai daita hular a kanshi
''gafara can,mutumin da ya kasa fidda mace shike zancan ranar aurenshi,kaci gaba dai da zama a tuzurunka har a rasa mai aurenka''


murmushi ya fidda mai dan sauti ya dukin turaten mamin yana sake fesawa
''haba mami,ba irinmu kerasa macen aire ba ko shekara sittin sukayi a duniya,ki kwantar da hankalinki ina nan ina duba miki,kinsan sai na zaba na darje''
''garin ruwan ido kuma fa...''
da sauri ya tare ta
''wayyo mami....yi shiru don Allah,you will be suprise in sha Allah''
''hmmm,Allah yasa....maryam ina zuwa?''ta tambaheta ganin ta miqe
''zanje ne na dora girkin mami''


''abdallah maka lunch ne?''
''kai kuci kayanku kawai mami ni zan wuce gidan baffa mu gaisa''
''to yayi kyau,ka gaishe min su da kyau,muje maryam nima saukar zanyi,kada a shigo a yita nema na''


tare suka sauko dukansu abdallah na gaba,mami na bayansa maryam na binsu a baya
''banza a banza kawai,maras kunyar qarya,gidan da kike taqama da shi ina cewa 'yar karo ce ke''
surutan wata matashiya kenan lokacin da take shigowa falon,matashiya ce 'yar zamani wadda shigarta kadai ta isa nuna maka hakan,sanye take da fitted gown wadda tabi lafiyar jikinta,kanta daure da roses sai swagger dinta mai sarqa rataye a kafadarta,takalmin qafarta kuwa kai kace sama take shirin tabowa saboda tsininsa,fuskarta tasha fente fenten kwalliyar zamani
''a'ah salma,ke da wa kuma,hali zanen dutse''inji mami da ta tsaya tana kallonta


''ni da waccar agolan gidan taku mana,duk randa nazo gidan nan sai ta nemi raina min hankali,wallahi abdallah ka ja mata kunne ni ba sa'arta bace,ni na hana ka sota da zata dinga neman huce haushinta akaina,ina ruwan biri da gada,nafsi nafsi kawai''
kafadunshi ya daga yana ware hannayenshi🤷🏻‍♂
''ina ruwan abdallah ya taku,kina da baki kema fa''ya fada cikin ko in kula
ta yamutse fuska
''baka fa da kirki wani lokacin wallahi,watsamin to qasa a ido,mami kina jinsa ko''
murmushi tayi
''bismillahi Allah,ai kun fara kuma kenan''


ya dubi mama
''manta da ita mami,ni zan wuce masallaci''
''ni matsalata da kai waqanci wlh,ka sani fa sarai saboda kai na zo,shine zaka wani fita''ta fadi mishi tana kallonshi bayan ta zauna tana sabule cogen qafafunta
''sai na fasa sallar juma'a saboda sarauniyar matan duniya ta zo''ya fada yana yin gaba abinsa
''a'a,ni bance ba amma sai yaushe zaka dawo?''
''qarfe biyar,bit ban tabbas ina iya wuce hakan,idan zaki iya jira na fine''
''ina jira sai ka dawo''
ba tare da ya amsata ba ya qarasa ficewa
maryam na kichen take jiyo su


tunda ta shiga kitchen din bata fito ba sai da ta kammala girkin,lokacin da ya fito mami bata falon sai baquwar da taji an kira salma dake kwance dai dai kan three sitter,kanta ta dago tabi maryam da kallo,hada idon da sukayi bak sata dauke idonta ba
''sannu maryam,kada dai ace har kin kammala?''
inji mami dake saukowa daga saman bene
''eh na gama mami''ta amsa mata bayan ta tsagaita daha tafiyar da takeyi
''sannunki''ta amsa mata sannan ta juya don shigewa dakinta,tana jiyota tana tambayar mamin wace ita?saidai bata ji amsar da mamin ta bata ba


kiran da mamin ta yi mata ne ya sake fito da ita tun bayan shigarta dakin wanda wanka kawai taui ta saiya kayanta tayi salla,biyi taga 'yan matam sun zama,saidai iya wannan sanhe take da riga da wando wadanda suka bayuana surarta,inda Allah ya taqaita siririya ce sosai,
tadan dauke kanta zuwa sashen da mamin ke zaune
''gani mami''
''yauwa maryam,baki fito kinci abincinki ba,ga baqi yau agodan amma kin zauna a daki''
''mami na qoshi ne sai anjima''
''to zauna muyo hira,bana son kina zaman dakin nan ke daya,na gaya miki nafison ki dinga jin a ranki ke diya ta ce,wannan sunanta salma 'yar qanwata ce,waccan kuma sunanta saddiqa ita kuma 'yar yaya na ce,dukansu sunzo yoma abdallah sannu da zuwa''
''sannunku''ta fada cikin sassanyar muryarta


amsawar ganin dama suka mata tamkar wadanda aka tilasta,wanda hakan sam bai,mata dadi ba,har taji zamansun ma guri daya babu marching,don sam bata son wulaqanci,maca ce ita mai karamci shi yasa ako yaushe take tsammanin karamci daga gurin duk wanda zata mu'amaleshi
''am...mami da wai kitchen zan koma in dora abincin dare''
''baki gajiya maryam,a qa'ida ai kin gama girkinki na yau tunda sau biyu ne a rana ko''
kanta na aqasa tayi murmushi
''ba aikinta kenan ba,ki barta mana mami''inji saddiqa wadda ta dora qafa daya kan daya tana danne danne waya da bai wuce tana charting ne


''ba komai mami,ai ba wani qa'ida tsakanin mu,kuma ko ba haka bama ai kinga baqi aka yi,kuma aikin ya abdallah nake,tunda aikinsa nake kinga ba laifi na giwa wadanda suka zo gunshi abinci''
sosai ta burge mamin,tana son mutum mai sauqin kai,wanda ta fuskanci halin maryam ne
yayin da salma da,saddiqa suka dago kai suka kalleta,salma ta kasa shiru
''hmmmm,lallaikam,dadin abun ma biyanka ake ba''


sai abun ya bawa maryam din mamaki,to meye kuma hadin kaska da kifi,me haka kuma,me tayi mata,gaza bawa kanta amsa taui don ita dai yasan yau ta fara ganin salma,babu kuma abunda ya hadata da su balle tace ko ta mata wani abun ne
''salma,bana so fa irin wadan nan halayyar naki kin sani sarai ko''mami ta fada cikin dan hade gira
''yi haquri mami,nima ba wani abu nake nufi ba''
''jeki maryam ki hutar da kanki kiyi iya cikin abdallah kawai,shima din kiyi simple kada ki dauka da wuya''
''to''
ta gada sanna ta miqe ta shige kitchen dinmami ta nita da kallo,yanayin yarinyar na burgeta,sanyi sauqin kai da kawaic yakanah da danne abu cikin rai





*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺

        ▶1⃣6⃣




jallop din couse couse ta hada mishi wadda ta wadata da carrot grean beans da piece,sai qoda da hanta a madadin nama,qamshin curry da tyme kadai ke tashi a ciki,yayi shar gwanin sha'awa,sannan ta hada banana apple anda strawberry juice,baaba uwani ta barwa gyaran gun ta wuce ta shirya dining,duk suna zube a falon kowacce da abinda take,ko saahen da 'yar uwarta ke zaune bai isheta kallo ba tamkar ba 'yan uwa ba,taji dadi da bata tadda mamin cikin falon ba don haka tana kammalawa ta ahige daki don ko alama bata buqatar zama acikinsu


mutum ce ita mai jan mutuncinta da gudun wulaqanci,


har magariba abdallah bai shigo ba hakanan basu fasa jiransa ba,ana kirayen kirayen sallar isha'i sannan salma fa fara hada tarkacenta tana yima mami sallama,bata kai ga fita ba abdallah ya shigo


sanye yake da jeans baqi da red din t.shirt hannayensa soke cikin aljihun wandonsa,kan sa yasha gyara sai qyalli yake sumar ta masa kyau sosai,ma'abocin qamshi ne hakan yasa turare ke masa rakiya duk ta inda zai gifta


duk yadda salma ta dauki zafi ganinshin da tayi sai taji sakayau tamkar ma bai mata komai ba,ta saki ajiyar zuciya wadda har sai da ta fito fili
''a'ah,yaushe ka shigo gidan?''inji mami
''b fore isha,na shigo nayi wanka ne zan fita sallar isha ne waccar yarinyar ta tsaidani zubaida take ko''
dukansu babu wadda bata shaqa ba,mami ce ma ta dan tare masu don ba dadi
''amma dai kasan ana jiranka tun dazu ko''
ya karuar da wuya yana kallon mami
''hakan ne yasa ma na shigo yanzu mami,don nasan kaskar nan na jirana''


kasa magana mamin tayi salma ko da tasan cewa da ita yake wani abu ya tokare mata wuya,tuni qwalla ta ciko mata ido,cikin rawar murya tace
''abdallah ni kake cewa kaska''
yayo wani dan qaramin murmushi irin na gefan bakin nan
''mene don ance miki kaska,ita ba halittar Allah bace kamar yadda kike''
kai ta girgiza tare da cewa
''na gode abdallah''
fuu ta zagayeshi ta wuce
mami ta soma kiranta tare da yunqurin binta,da sauri ya sha gaban mamin yana murmushi


''qyaleta don Allah mami,indai salma ce zata dawo''
harararshi ta danyi
''saboda ka saba mata haka ko,to saddiqa na daki saura itama ka wulaqanta tan kaji abdallah''yarfe hannu hayi cikin gajiyawa
''again mami?''kafin ta bashi amsa saiga saddiqar ta fito tana sakin hannu rigarta wanda ta tattareshi saboda alwalar data daura
bakinta a waahe take fadin 
''oyo yo ya abdallah''hannu ya dan daga mata
''🖖🏼qanwa,yaushe ke kuma kika zo?''
murmushi ta saki hade da kashe ido daya cikin sigar son jan hankali


''cikin awa ta ta kusan hudu nake da zaman jiranka,kuma naga na kiraka nace maka zanzo''
ya dage kafadunshi
''nayi,tsammanin mami zaki gaida ko qanwata''
''ni gunka nazo''tace cikin salon shagwaba
''kuma kinga yanzun bani da time,time din mami na ne,jiya na dawo kinga baici ace mun gama hirar yaushe rabo ko,da zaki yi tafiyarki next time na baki appointment''yana murmushin mugunta qasan zuciyarsa ya fada,duk da yana jin yadda mami keta zungurinshi amma sai yayi kamar baiji ba


saddiqa gwanar girman kai da ganin ta isa ce,ki tayo tafi qarfin abdallah ya mata haka,son haka ta figi gyalenta wanda shi da babu duk daya
''abdallah....wai da ka fuskanci ina sonka shine ya baka damar takani yadda kaga dama,to wallahi aji na ya wuce nan''
murmushi ya kuma saki wanda ya qarawa kyansa kyau da kwarjini


''ni kaina nasan ke me aji ce''qufula ta sake yi don tuni ta fuskanci magana yake yaba mata a fakaice
''to indai don son da kake taqama ina maka ne daga yau na daina son naka sai me?''
''fine kin huta wallahi,kin kuma burge abdallah''wani zafi taji ranta na mata tuni ta durfafi fita ba tare da ta yima ko mamin sallama ba kamar yadda salma tayi


da sauri mamin tayi yunqurin binta,ya sake shan gabanta da hanzari
''pls mami ki qyaleta itama,wallahi hutu ta zabarwa kanta,hukuncinta yayi dai dai''
wata iriyar harara ta maka mishi
''matsa min abdallah agun tun ban sabar maka ba''
baice uffan ba ya janye gefe ya bata hanya,sai yayi komawarsa saman dining yayi zaune abinshi yana kallonsu


tana cimmata sai ta saki kuka,mamin tadan daddaki kafadarta a hankali
''meye kuma na kuka haka saddiqa da girmanki''ba don mamin bace da sai ta daka mata harara,amma sai ta toge tace
''haba mami,don kawai ana sonshi zai tsaya yana wulaqanta ni,yasan fa koni wace,su waye ke sona,to an daina sonshi din ma''
''ya isa daina kukan haka,ki barni da shi kinji''


da qyar ta lallaba saddiqan ta tafi,ta iso kan dining din inda abdallan ke zaune hankalinshi kwance tamkar babu abinda yayi,kujera ta ja ta zauna
''abdallah so kake kawai ka dauko min magana,kasan Allah akan haka zamu saba ni da kai?''
''ya salaaam....mami me kuma nayi da kike fadin wanna maganar mara dadi?''
''ka sani sarai abdallah yadda muke da yaran nan,ka san kuma irin magan ganun da ake tayi a kanka ko?,to ni na gaji gaskiya,ka zabi wadda kake so acikinsu kawai kowa ya huta abun ya isa haka''


''for god sake mami,ni babu wadda fa na taba cewa ina ina so duk cikinsu,yanzu mami anan kinga matar aure,kinga wadda ta cancanci zama surukarki matar danki qwaya daya abdallah,ni ban gani ba mami kuma kema na san baki gani ba''
ajiyar zuciya tayi don ta sani gaskiya abdallan ya fada
''amma wulaqancin bai da amfani abdallah,gwara arabu cikin mutunci da salama''
''mami ai bani na kawosu ba,kuma ni ba wulaqanci na musu ba,zuciya sukayi suka tafi''


murmushi tayi cikin zuciyarta,idan banda abun abdallah ai kora da hali ka musu,tace cikin zuciyarta
''tunda kace duka basu maka abida fa?,itadai nutsatstsiya ce ai ko''
yadan yatsine fuska
''ai nutsuwa kam akwaita,amma ba kamun kai,itama ina tabbatar miki mami gobe ko jibi zaki ganta da uban tana tana sum sum sum,marabarsu kadan ce ai''
''abdallah
abdallah,Allah ya shirya min kai''
''ameen mami na''


takaici ne ya rufeshi jin sallamar zubaida,ta qaraso tana wani satar kallonshi
''mami barka da dare''
''yauwa zubaida''filet ya zara ya bude warmers ya zuba abincin ya haura saman mamin abinsa 
zubaidan binshi tayi da kallo yayin da ami ta dafe goshinta 🤦🏽‍♀
abdallah na bata damuwa da yawa kan yaran mutane
''ya akayi zubaida?''
maganar mamin ce ta janyo hankalinta daga kallon saman inda abdallan ya haye ya barta


''bab....ba komai mami,cewa nayi dama sai da safe''tace cikin in ina
''Allah y bamu alkhairi,ki gaida nene yau duka bamu hadu ba,insha Allahu zan shigo gobe''
''zasu ji''ta fice daga bangaren cike da takaici


a kwance ta tadda ahi saman three sityer wanda saboda tsahonsa kansa na daya hannun kujerar qafafun na daya hannun har sun zarta sosai
yasan qorafi zata yi don haka yayi saurin riga ta
''nidai,mami banji dadin dawowar nan tawa ba sam,duka yaran nan sun hanani sakewa,gaskiya daga yanzu kada wadda ta sake shigowa indai ina nan har sai na fita kawai''
''to uba na''
dariya yake ciki ciki don yasan tunda ta fadi haka ya quleta ne kuma ba zata sake cewa komai ba

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

a fusace huwaila ta fito daga dakin nata,kai tsaye qofar dakin inna hadiza ta durfafa,a fusace ta saka hannunta ta yaye labulen tana fadin
''fito hadiza,wallahi na gaji na wannan iskancin da ake min cikin gidan nan ni da yara na''
inna hadiza dake kwance kan kujerarta da daurin qirji ta miqe ta soma qoqarin zama tare da jawo dankwalinta tana fagamniyar qulle danqararren kanta tare da fadin


''ai ni na girmewa fitowa saidai ashigo a sameni''
ba tayi wata wata na ta gado falon wanda saura ladan ta take qafar binta dake kwance saqe saqe,tayi saurin janye qafar tata tare da fadin
''Allah ya isa na wallahi''saidai bata ji ba kasancewar cikin masifa take da hayagaga


''hadiza,ki jawa diyarki
binta kunne,iskancin da take cikin gidan nan ya soma isata,haka kawai sai ta kama lubabatu ta dinga jibga,babu dama ta dauki aron wani abu nata''
''ahaf,kince haka kawai sannan kin dawo kin warware maganarki kince tana daukan aron abun ta,to ke da ita ku bude kunnuwanku da kyau,indai lubabatu bata daina daukar aron kayan binta bazan hana binta jibgarta ba,wutsiyar raqumi ai tayi nesa da qasa,mu yanzu cikin gidan nan babu sa'an mu don arziqi ba qarya bane''


kallon tara saura huwaila tayi mata,kana ta saki guda
''aikin banza....hara ra aduhu,arziqin nan fa da kike ta taqama da shi a sa hannuna ya samu,amma da yake butulu ce ke had kina da bakin goranta min,baya ga butulcin da kullum kwanan duniya kike min na hanani morar duka wani abu da jamila ta kawo cikin gidan nan,to bari kiji wallahi ki bini a hankali,don wallahi duk abinda kike taqamar da shi a yau idan naso sai na warware miki zarenki tas ta yadda baki isa ki maidashi ba''


hindatu dake parlour tana yiwa mama tsifa ta dubeta
''mama...kunnenki yana jiyo miki abinda nake ji kuwa?''
duk da cewa,zamcan ya duketa amma sai tace
''ina ruwanki hindatu?manzan Allah yace yana daga cikin kyawun musulincin mutum ya bar abinda babu ruwansa''gilma na cin hindatu amma dole haka ta ja bakinta tayi shiru tana addu'ar Allah ya kawo mata ya maryam,kai qila ma sai ta kira ta ayau din cikas din kawai mama da zata hanata


sai kuwa inna hadiza ta hauro itama huwailan dake kusa ta bi mata,sai fada ua zama hudu,binta nayi da lubabatu,huwaila nayi da hadiza ,mama ta yunqura zata fita bada haquri hindatu ta tareta tace wallahi mama babu inda zaki,lokacin da suke 'yar dadin babu wanda auka dauka abanza ieinki saboda haka yanzun ma ba ruwanki,su kashe kansu''a haka malam mamuda ua sjigo ya tadda gidan nasa


zancan ya bibiya amma daga qarshe sai ya goyawa inna hadiza baya,ko dama can itace mowar,balle yanzu da jamila ke satowa tana kawowa uwarta ita kuma take yagar masa,bayan sun shige daki ba qaramin ciwo abun ya yiwa huwaila ba,ta cizi yatsa yafi  sau ashirin,lubabatu dake tsaye tana taya uwar tata takaici tace
''wallahi huwaila duk ke kika ja mana tun asali,da tuni nice kan matsayin jamila kika tsaya gina wasu kika qi gina kanki,ai da arziqi,a garin wasu gwara a garinku a garinku ma aunguwarku a unguwarma agidanku a gidanku ma adakinku''
''duk banga haka na lubabatu sai yanzu,nayi dana sani wallahi yafk a qirga,tsinanniyar mata ta kuma samun power a gida?''
''ato,shawara dai ta rage ga mai shiga rijiya,saiki zauna ki tuna bunyi''


kamar tayi mata allura ta figo mayafinta dake ajjiye saman qofar falon ta tace
''kinga zauna ki jiremin daki na,ba'a bori da sanyin jiki,bari naje gidan talatuwa''
saman tabarmar dakin ta zube tana fadin
''sai kin dawo''cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa adace,tuni ta fara hango kanta a irin daular da jamila ke ciki,tana yin son ranta wanda tuni an maida jabir wani sususu,aure dai an yishi amma amma fa na cin abinci da cin kayan dadi da dibar kudi






*mrs muhammad ce👑*



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺

        ▶1⃣7⃣

sama sama hadarin ke hadowa yana bajewa tun daren jiya,hakan ne ya sanya har safiyar yau garin yake da lullumi,lullube sama take da hadari mai duhu saidai sanyi sanyi yake bayarwa har yau ruwan bai kai ga sauka ba,qarfe goma ta kammala komai,wankanta tayi ta shirya cikin pskistan riga da wando daya daya daga cikin tsarabar da raliya tayi mata ta south africa,orange ne wanda aka yiwa adon dutsina dark blue daga gaban rigar da qafar wandon

mayafinshi shara shara ne amma yana da dan girma shi ta saka ta yane kanta da shi,tun baiwai yau mami ta fita saboda ta cinye hutunta na kwanaki ukun saboda haka bangaren babu kowa sai ita daya,kusan tunda tazo gidan bata fita ko ina ba saboda hala tayo sha'awar dan zagaya wa,wayarta na hannunta ta saka flat shoes ta fito

iya girma gidan yana da shi,ba ma wannan ba yanayin ginin ya burge maryam,bugu da qari yanayin da gafin yake ya qarawa maryam nishadi,lokaci gida hadarin ya yaso garin yayi duhu sosai,cikin qanqanin lokaci iska ta taso ruwa ya kece

da sauri sauri take nufar hanyar sashen nasu don bata son ruwan ya tabata,su uku me ysaye a waiting parlour din,nene zahariyya sai wani matashi da ya bawa qofa baya yana fuskantar  nene,shigowar tata taji sunyi dif a maimakon sauti sautin maganar da take iya ji duk da cewa baka iya tantance abunda suke fadin,binta sukayi duka su biyun da kallo wanda hakan ya ja hankalin saurayin ya juya shima don ganin abunda suke kallon

har cikin jikinta take jin kallon nasu hade da faduwar gaba,hakanan take jin wani tsarguwa duk lokacin da suka bita da irin wannan kallon,saida ta shige sannan suka dauke idonsu
''nene,wace wannan?''ya tambayeta idonsa cikin nata cikin son jin amsa 
sai da ta kuma tsuke fuskarta kafin ta amsa masa
''yar aikin da bintu ta sakewa abdullahi ce,bana buqatar kuma kace komai,idan ma wani abu kake shirin sawa zuciyarka kayi gaggawar cireshi,don wannan karon babu gudu babu ja da baya sai mun cika burin mu,a shirye nake da kawar da duk wani abu da zai kawo wa plan din mu cikas,kuma ina fatan haka ne cikin zuciyarku''

zahariyya ta tauna chewing gum dinta ya bada sautin qas qaqass
''nifa nene na fiki son cikar burin nan,sabodda haka har abunda ma ke ba zaki iya ba ni tsaf zan aikata shi''
''to balle kuma ni da nake namiji,ina da burika da dama...saidai fa...gaskiya naji yarinyar cikin jini na,tana da fitinannen kyau,any way zan ajiiyeta a side har sai bayan kammaluwar plan din mu''
''ato ya dai fi maka alkhairi''cewar nene tana buda hanci

garam taji taci karo da wani abu wanda tsabar sauri da rudewa yasa bata gane ko meye ba,ga duhu da ya mamaye falon kasan cewar duk wani qwan lantarki ta kasheshi lokacin da zata fita din
tsoro yaso kamata da tabi inuwar abun da kallo dogo ne wanda duk tsawonta ya kereta,yana kuma tsaye qiqam bai ko motsa ba
gabanta yayi mummunar faduwa,bata sake rudewa ba sai da taji muryarsa na fadin
''wannan wanne irin shshanci ne haka da hauka,kina tafiya kamar mai tabin qwaqwalwa,yanzun kuma da kinji min ciwo fa''

haushi maganar ta bata,wato ita ce ma mahaukaciyar?,shi da yake namiji baiji mata ciwo ba sai ita ce,zata ji masa?ita fa bata son rainin hankali shi ya sanya har yau bata bari su hada gu da shi,don ta fuskanci ya raina ajawalin mata saboda yaga yadda suke masa rushing

cikin dan daga murya yace
''kin wani tsaya kamar wata doluwa,ina breakfast din mu yake?''
''tun dazu na dora saman dining ai''
''ok it means ni zan sarving da kaina kenan,haka kika ga mami na na yimin''
kamar tace mishi to ai ni ba mamin ka bace,sai kuma taga bai dace ba,don tana kallonta ne tamkar mamanta
''comone dallah...dole ki dinga showing caring like my mami,babu buqatar nana ta miki aikinki,duk da cewa u can't replace my mami ko da digo daya cikin kaso dari ne,idan kuma ba zaki iya ba the door is opened''

bata ce masa komai ba ta zagayeshi ta wuce bayan ta kunna qwayayen lantarkin din dake falon,ta riga shi isa dining din don haka ta soma hada mishi tea don kafin ta kammala zuba mishi komai zafin ya dan sarara
kujera ya ja ya zauna daidai lokacin da wayarshi ta soma ringing
tamkar wani mace haka yake amsa waya,ba hayaniya ba daga murya

''shi don ubanshi bai san kai wane ba da,zai hanaka shigowa?,to ya bari mintina biyar su cika ya gani,idan ka ahigo ka sameni gefan mami''abinda kawai taji yace kenan ya kife wayan saman table,fuska a murtuke ya ja kofin shayin ya kai bakinsa,tana ahirin dakatar da shi amma tuni ya kai bakinsa,ai kuwa babu shiri ya dawo dana bakinsa ya fesar

''ke wacce iriyan muguwa ce don Allah,haka ake bawa mjtum tea da azabar zafi kamar za'a dafa mishi baki?''
muryarta a narke tace
''ayyah,don Allah kayi haquri,ina shirin dakatar da kai naga har har ka sha''
''mtswee...you are verru stupid''ya fada sannan cikin hanzari ya dauki wayarshi dake bisa teburin ya fara danne danne

''hello abdallah,lokacin aiki ne fa ina tare da patients''muryar mami kenan
''mami yarinyar nan aiki aka kawota ta min ko kisa?''a razane maryam ta dago ta kalleshi,sai kuma ta maida kqnta qasa ta sadda shi,tini oily eyes dinta suka qara sheqi ssakamakon qwallar da ta soma dan taruwa mata
cikin faduwar gaba mamin tace
''me ya faru abdallah?''
''mami zata kasheni da ruwan zafi,tea mai azabar zafi mami ta bani zai qona ni''
ajiyar zuciya ta saki
''oh my god abdallah,kasan yadda ka bani tsoro kuwa?,just ruwan zafi kawai ahine kake wa haka,sau nawa kana shan tea ba tare da ka fifita shi ba,sannan nasan maryam bazata taba baka tea da zafi tana sane ba''
''gaskiya mami bata san aikinta sam''
''enought abdallah....bani maryam din''

qyashin bata wayarshi yake,sai ya saka handsfree kawai ya dan tura ta gabanta kadan
''maryam,ya akayi''cikin rawar murya tace
''wallahi mami ba da niyya bane kaw....''
''manta da abdallah kinji,kici gaba da aikinki,but ki kula da shi kinga bani nan,hakanan sai kinyi haquri da tabarar abdallah don na....''
cikin hanzari ya dawo da wayar gabanshi bayan ya kashe handsfree din yana cewa
''omg mami''
batasan me tace masa ba ta dai ji yace
''ok bye take care''

daga bakin falon ake sallama,bai dubi gun ba yace
''comone guy,idan zaka shigo ka shigo duk ka cikawa mutane kunne da sallama''
matashi ne kusan sa'a,ne ga abdallah
''kaifa baka da mutunci wallahi''
''kai shine da kai ai''
dariya ya saki bayan ya iso ya bashi hannu suka cafke,kujera daua ya ja ya zauna yana leqen flate din dake gaban abdallan

''kai mutumina,irin wannan liyafa haka,rabona ne kawai ya rantse shi yasa na qaraso kenan,da har nayi fushi nace bazan shigo ba''
''kanka ake ji sarkin kwadayi,yi sarving dinshi''yace da maryama wadda ke goge gun da abincin ya taba
sam bai kula da ita ba sai da abdallan yayi magana
''ina kwana''tace masa idonta na kan flaye din da take zuba masa hadin salad
fuakarsa dauke da mayalwacin murmushi ya amsa
''lafiya lau 'yammata ya gida?''
''lafiya''tace masa ataqaice don ta qagu ta kammala ta bar gun,tun dagowar farko ta lura da yadda yake faman kallonta
tana sauka daga stares din dining atea din taji yana tambayar abdallah
''fatabarakallahu ahsanul khaliqin,abokina wanna fa,cikin family dinku take?''

a qufule abdallan yace''dan iska ban sani ba,kaga wannan tayi kamar da 'yar dangin mu ne,dan rainin hankali?''
''pls guy yimin bayani don Allah''
sai da ya gama shan qamshinsa kafin yace
''cook dina ce,mami ce ta kawota''
har wani dan zullo hisham yayi
''wow,gaskiya ta qeru wallahi ba qarya,kai....man ba cook mami ta kawo maka ba,matar aure ce wallahi wannan''
abincin bakinsa ya tofar bayan ya dalla masa harar kamar zai cinye shi
''allah ua,isa tsakanin mu kawai hisham,wanna ai cin fuska ne,house girl fa,ni abdallah,i think ka manta waye abdallah ne ko,ya kamata kayo gaggawar tunawa,har yau ba'a qera matar abdallah ba,ni,mai ysada ne don,haka mace mai tsada ce matar abdallah,ban tsammanin ma zanyi aure cikin jinsin hausa fulani,sai na shiga cikin larabawa,i hope ka fahimceni?''

dariya hisham ya qyalqyale da ita kafin yace
''nasan waye abdallah,d expensive man,amma ina tsammanin man ka makance ko?,bana zato ko cikin larabawa kowa ke da irin halittar babe din nan''
''kaga malam ni ba ganewa nake ba,u know ni ba irinka bane mayan mata,kai da ka gano,sai kaje ka qarata ai ko''
''is ok...is ok,ni na gani to ina so''
cikin i dont care yace
''ok,ba laifi,amma daga ranar ka cire abdallah daga list din abokanka''
''why?saboda me ?''
goge hannunshi da tissue kana ya tire kujerar da yake kai ya miqe yana duba agogon hannunshi
''coz babu mai zubda min class,kaga nifa ina da wani aiki,ina da bincike cikin unguwar tudun maliki,so bana buqatar securities su rakani saboda is screet,idan ka gama zub da mutuncin naka ka fito mu wuce''
daga haka yayi saukanshi,hisham na daroya ya miqe ya bishi
maryam dake saman kujera ta tabe baki

''lallai,Allah ya tsareni da da tarayya da ire irenku,kai din ma baka min ba bare abokanka,mai girman kai kawai,kudi ai ba sune mutunci ba''cikin zuciyarga take zanta hakan,ta jawo wayarta ta kira raliya don kada ma ta batawa kanta rai a banza 

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:51 PM] 80k: *ABADAN*18
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*assalamu alaikum wa rahmatullah,ina miqa godiya ta ga dukkanin mutanen da suka yimin ta'aziyya wadanda suka kira ni da wadanda suka turamin saqo sms da watsapp,na gode Allah ya saka da alkahiri ya bada lada,akwai wadanda suka turomin saqo ta watsapp ban musu reply ba su yimin afuwa wayar ce tayi misbehaving duka saqonnin sun goge na gode Allah ya bar zumunci*
can cikin uwar dakin suke a zaune su biyu rak,a haka idan ka kallesu sai kayi zaton maganar arziqi suke
''huwaila kenan,ai ni na dade da ganin baikenki,kin kima bani mamaki wallahi''uwani ta fada bayan ta dora qafarta daya kan daya daurin dankwalinta a goshi
''abunda ya faru ya riga ya faru uwale,yanzu meye abunyi mafita nazp nema,tunda na fiskanci abun nata ba na mutunci bane''
''abunyi kuwa akwaishi....''
''cewa nayi kawai mu koma gurin boka mai gayya ya warware aikin da yayi mana da farko,tunda ta inda aka hau ta nan ake sauka''ta gada cikin katse hanzarin uwale
bakinta ta kama tana kallonta
''ai kinji irin wautar taki,ina ke ina dosarsa,ko kin manta cewa yanzu hadiza sun fiki kudin da,zasu biyashi ya musu aiki nan take,ai hannu zamu sauya,ina da wani boka na da ya jima yana min aiki,amma fa sai kin shirya,kudadenki zaki fito da su ajjiyayyun nan''
''amma fa uwale na tarin auren lubabatu ne,na fiddo su kuma a kashe?''
''a aha,to zauna mana kiga idan zasu maganta miki,kin manta cewa idqn aiki yaui kyau wanda zata aura din mai arziqi,ne?,shi zai mata komai da komai ba damu bace ai''
baki huwailan ta washe''kuma fa hakane,kinga ke kin fini hangen nesa,to shikenan babu damuwa,yanzu kina ganin idan na raba su biyi rabi zai yi?''
tabe baki uwale tayi
''kinga malama,idan dqi kina son aiki gangariya ko fiddo da kudi kawai,wai tsoron me kike yi ne?ke da,zaki zama surukar mai arziqi,idan kuma kina ganin abar maganar shikenan sai na barki''
da sauri ta tareta
''a'ah,ba za'ayi haka baai,yanzu kina ganin yaushe zamu tafi?''
sai da ta dan nisa sannan tace
''jibi,jibi laraba kenan,ta bawa ranar samu ba,don mu samu dacewa''
dariya huwailan ta qyalqyale da ita
''gaskiya ne fa,kai Allah ya bar min ke qawata,bari na tashi na tafi kada su fuskanci wani abu,sai Allah ya kaimu kenan''
''to shikenan,Allah ya nuna mana''
tana gama ficewa uwale ta sheqe da dariya
''wawiya kawai,sai na gama tatseki tas,kuma naci halas tunda ba aikin Allah bane,idn banda ke cikakkiyar shashasha ce waye yaqi gidan hutu da jin dadi,nima fa 'yan matan nan gareni na hadashi mana da wata daga ciki,ai ba ke ladai ce mai son dadi ba''ta ja dogon ysaki kana ta miqe tana gyara daurin zaninta hadi da cewa
''ai ni kuma na samu sana'a har gida ina kwance kudi zasu dinga shigowa
ta waiwayo hannunta dauke da plate cike da tsiren tukunya wanda ya ji kayan hadi ta miqawa abdallah wanda ke tsaye qiqam a bayanta hannayensa harde bisa qirjinsa yana ta zuba mata surutu
''ungo,ai yanzu kam ka qyaleni na fita ko''
yasa fork guda biyj cikin plate din sannan yace
''kin gama wannan mami na,sauranki ci,don kin sani tare zamu ci''
girgiza kai tayi tana goge hannunta da doster din kitchen
''haba abdallah,me yasa wani lokaci kake da rigima kamar yaron goye?,kace tsiren tukunya kake so nace maryama tayi ma kace baka so nawa kake so,yanzun kuma kace sai na zauna munci tare,kaci naka ka ajjyemin nawa,idan na dawo sai naci,ina da patient da nace yau suzo su same ni''
''yau througout ba inda nake so ki fita,duk sun maida min ke kamar wata engine,weekend din ma ba za su barmin ke ki huta ba,kuma ma ni mami bazan iya ci ba idan babu ke''
''alright,ga maryama nan ta wakilceni sai kuci tare''ta fada tana daukan mauafinta dake saqale kan qofan kitchen din
ya kalli maryama ta wutsiyar ido wadda ke fasa qwai cikin bowl zata hada potatoes bolls sannan ya harareta kadan ya dauke idonshi ya maida kan mamin
''mami kina ragemin matsayi gunki,babu wanda zai iya replacing dinki a guna''
''to tunda ba zaka kaci da maryama ba sai na turo maka zubaida,ita ai na zaka qi ba tunda masoyiyarka ce ko''ta fada tana ficewa a kitchen din
maryam wadda kanta yake sunkuye tana kada qwan bata san lokacin da dariya ta ciyota ba don tuna dramer din da suka gama shi da zubaidan dazun da safe,bata snkara ba dariyar ta subuce ta fito
hannayeshi harde bisa qirjinshi as usual,a hankali ya dora kyawawan qwayar idanunsa gefen fuskarta wanda dimple dinta ya fito radau saboda motsawar fuskarta,sai taji duka ta sha jinin jikinta duk da ba kallonshi take ba,cikin second daya tayi qoqarin mai da fuskarta yadda take
hijabinta taji an damqa hade da jawota wanda har hakan ya haddasa fadowarta jikinshi,cikin zafin nama taji ya ja hijabin ya cireshi sannan yayi wurgi da shi,cike da azama tayi gaggawar barin jikinshi,a tsorace take kallonshi tare da takure jikinta guri daya,sanye take da fitted gown na atamfa wanda yabi lafiyar jikinta,a qa'ida dinkin ya mata kadan amma son da takewa atamfar yasa ta kasa bayar da ita,dalilin da yssa kenan duk lokacin da ta sakata hijabi take sawa
tuni oily eyes dinta suka qara sheqi kan wanda suke da shi a da sakamakon taruwar qwalla cikin idanunta,zuciyarta bugu take wanda a take jin ya wuce qa'ida,tama kasa hada ido da shi kamar yadda ta kasa motsawa,saboda idan tace zata motsa din tofa ko ina na jikinta zai motsa din ne
hucinsa taji a gabanta,a hankali ta dago da kanta don kallin abinda ke gabanta,tafin hannunshi ne mai dauke da zara zaran yatsu bude,tsakiyarshi kuma kunama ce qatuwa,saura kadan nunfashinta ya dauke,da sauri ta ja baya sannan ta daga kai ta kalli fuskarshi
gumi ne sosai yake hadawa yayin da idanunshi suka soma sauya kala bisa dukkan alamu ta hahharbeshi bama sau daya ba,a gigice ta koma gabanshin taci burki ganin yana tsaye qiqam yana kallon abunda ke hannun nashi tamkar ba wani abu bane mai cutarwa,hannunta ta saka ta tankwabe hannun nashi kunamar tayi tsalle ta sauka gefanshi,takalminshi ya sanya ya taketa
batasan ta kama hannunshi ba tana lalubar inda dafin yake ba sai da taji ya fisge hannun yana fadin
''mtswee,sakemin hannu dafi na shigar mutum sai ua masa illa kin tsaya shashanci''
hannunshi ya saka ya riqe inda yake tsammani iya nan dafin ya tsaya
zaune yake a falon tunda ya fito a kitchen din,da alsmu xafin harbin na damunshi sosai,duk da 'yan dabarun da yayi,duk sai ta shiga damuwa tana jin itace sila,ta rasa da me zata taimaka masa,duk sanda ta matso gun da yake sai ta kasa tabuka komai saboda kwarjinin da yake mata,qarshe sai tq koma kitchen din ta dauki wayarta ta kira mami ta sanar mata
sosai mamin ta rude tace ta gaya mishi ya taho asibiti yanzun lallai
kwance ta sameshi saman doguwar kujera
a darare ta matsa kusa da shi kadan cikin sassanyar muryarta
''mami tace ka sameta a asibitinta''
sam bai ji isowarta gun ba sai saukar siririyar muryarta
jin shiru ya sata sake maimaitawa
kusan minti uku kafin yace
''leave me alone pls,bani son naci tunda ni ba kurma bane,sannan bani son gulma,har kin kirata saboda tsaban gulma,bace min a gun''
bata damu ba tunda ta isar da saqon mamin dai,kitchen din ta koma ta fara soya patatoes bolls din duk da rabin hankalinta na ga abdallah wanda bata ji motsin tafiyarshi ba,dalili kenan da yasa taa kammala suyar ta sauke man ta leqo falon,yana kwance abinshi yadda ta barshi,sai 'yar nutsuwar da ta samu tayi qaura,waishi wane irin mutum ne da ciwo ke cin jikinshi amma bai damu ba
cikin dan qwarin gwiwar da ta tattara ta sake nufarshi da nufin tunassr da shi koda qila ya manta,saidai kafin ta qarasa wayarshi dake ruwan cikinshi ta dauki sassanyar ringing alamun shigowar kira
da alamun kasala ya dauki wayar ya duba mai kiran nasa ya amsa bayan ya maidata handsfree ya dorata saman cikin nasa
''abdallah yaya me na jika shiru?,ko maryama bata sanar maka saqona ba?''
cikin murya mai kama da ta mai bacci yace
''ta gayamin mami,kawai....''
''ya isa bana buqatar uziri,na baka minti talatin in ganka a office dina ok?''
''yes mami''ya fada daga bisani wayar ta katse
cikin sanda ta juya don komawa da baya tunda bai ganta ba
''dakata a nan''ya fada cikin kaurara murya,cak ta tsaya din yayin da shi kuma ya miqe a hankali
''sai ki fito amma zan sake maimata miki ni bani son shishshigi''daga haya ya juya yayi waje
motoci hudu ne baqaqe masu azabar kyau a jere,tun kafin ta qaraso taga abdallah tsaye jikin daya,xubaida ce ke fuskantarta bisa alamu magana suke,isowarta ne ya sanyata jin maganar qarshe da abdallah ke fadi
''nacinki kullum sawa yake ina dada tsanarki,bana son shishshigi bana son naci kuma bana son takura,ki tambayi nene tun asali ke ba type dina bace,bazan taba auran macen da bata yimin ba,ba ko wacce irin mace nake so ba,for now ya kamata ki gane hakan''
ya sanya hannunsa ya janue hannunta data tokareshi da shi ya bude bayan motar da kanshi
''naji abdallah,amma atleast dai a yanzun ka barni na raka ka asibitin bai cancanci ka tafi kai daya ba''
ko kallo bata isheshi ba don tuni ya gama maganarshi da ita
ya juya bayanshi yace da daya daga cikin security dinshi su rage biyu daga cikin motocin da biyu za'a tafi,ya rufe maganar da fadin
''ko kun manta muna bincike kan alhj haladu uba mai qusa,kuma banson yasan ina cikin garin nan,ku kiyaye''
''yes,sir''ya fada cikin girmamawa
kusan tare shi da zubaida idonsu yake kan maryama dake tsaye daura da su
''me kika tsaya kina wa mutane a gurin?''
cikin tattausan muryarta tace
''bansan wacce mota zan shiga ba ai''
''saikiyita sanqamewa anan har a tashi qiyama''ya fada yana shirin shigewa motar
''amma abdallah wannan ita kuma fa?''
wani kallon biyu babu ya mata cike da quluwa da tarin tambayoyin da nabu macen da isa ta masa su idan ba maminshi ba,tsaki ya ja mata sannan ya ja motarshi ya bame
sun gama reverse suna shirin ficewa maryama dake motar baya cikin gidan baya a takure saboda su uku ne maza biyu ita ta ukun taji an dakatar da su,abdallah ne ya fito ya qaraso har gaban motar,glass din duka motar yasa suka sauke ya qare musu kallo sannan yace da na gaban motar
''you are verry stupid lawal,oya getout ka koma baya,ke kuma ki fito ki dawo gaba saunar yarinya kin shige cikin maza kin wane qwame''
yana tsaye akayi hakan sannan ya bisu da tsaki ya kona tashi motar duka direbobin suka ja suka fice a gidan
*ABDULLAHI SPECIALIST HOSPITAL* shine abinda ke rubuce jikin wani makeken allo dake maqale a goshin ginin benan asibitin,wanda ko daga ina ka taho zaka gani saboda girman allon da rubutun da kuma tsahon benan,gini ne na alfarma tamkar ba asibiti ba,komai neat bisa tsafta tsari da kuma qwarewa,tun daga parking space ma'aikatan dake cikin harabar asibiti leburori da masu gadi suka soma tururuwar zuwa gaida abdallah,ga mamakin maryam hannu yake basu suna mudabaha cikin fara'a da sakin fuska
a haka suka ratsa cikin asibitin har zuwa sashen da office din mami na musamman yake
''wonderful,abdul dama kana nigeria?''suka ji an fada,wani matashi ne wanda ke nufosu yake fadar haka,sanye yake cikin qananun kaya wanda kallo daya zaka mishi kasan dan birni ne yasan gayu gayu ya sanshi,ba wani mugun kyau ne da shi ba amma iya adonshi ya bashi sunan kyakkyawa
da fara'a sukayi musabaha da abdallah
''idan ban manta ba shekaru biyar rabona da kai abdallah,yanzu laifin kudrat sai ya shafi mansur?''
dan qaramin murmushi ya saki kana yace cikin basarwa
''manta kawai friend ya bayan rabuwa?''sai alkhairi abdul,hala wannan ce madam din tamu?''
wani haushi ya kama abdallah don yasan ba kowa yake nufi ba sai maryam,sai ya zuba mata ido yaga yadda zata karbi maganar,babu abinda ya fuskanta tattare da ita don kanta a sunkuye yake jinta take kamar ta,zura a guje,ta takura matuqa cikin tafiyar nan
maida kallonshi yayi gun mansur
''kada ka sake fadi,cook dina ce,nazo ganin mami na ne ta shigo cikin sahun bodyguard''
murmushi mansur din yayi
''tofa wannan karon babu rabuwa abdul,bani adress dinka,zan sameka har gida,ina da magana da kai''
saboda yanayin aikinshi yasa bai bashi adress din gidan ba kai tsaye sai ya amshi phone num din mansur din yace zai nemeshi duk lokacin da zasu hadun,sukayi sallama kana suka nufi office din mami
duka a waje suka tsaya abdalla ne ya shiga ciki,fitowar mamin kenan daga toilet ta daura alwala
''ina maryam din''ta tambayeshi tana shimfida abun sallah
''suna waje''
''kana nufin har ita din''
''eh mana mami,har da ita''
''koma ka shigo min da ita''
cikin shagwaba yace
''yanzu mami a gabanta za'a min treatment din bayan da zafi kuma salon ta raina ni''
ita dai mami bata kulashi ba ta tayar da sallarta,tilas ya koma yace da lawal ya shigo da ita
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
     🌺💖🌺💖🌺
        🌺💖🌺💖
           🌺💖🌺
               🌺💖
                  💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶1⃣9⃣


teburin mamin yayi zamanshi yaja laptop dinta yana danne danne ya barta nan a tsaye,a haka mamin ta kammala sallarta ta shafa addu'o'inta
''sannu maryama ya akayi kunama ta sami abdallah?''mamin ta fada cikin kulawa tana linke sallayarta
''tsautsayi ne mami''taji abdallah ya amshe zancan yayin da tayi duru duru tana tsaka da neman amsar da zata bawa mamin
''Allah ya tsare gaba to,amma ya kamata ka daina zuwa gun da ta samekan,don nasan bazai wuce cikin garden ba''ta fada tana hada allurai cikin syringe


maryama tsayawa kawai tayi tana kallon yadda abdallan keta marairaita kamar qanqanin yaro,ita abun ma kunya ya dinga bata,amma shikam ta fuskanci ko ajikinshi wai an tsikari kakkausa
''wannan matarshi zata sha fama da shagwaba,mami duka ta sangartashi''tayi gulmarshi cikin zuciyarta,da sun hada ido sai ya maka mata harara hakan ya sanya ta dauke kanta ta maida kan dan wani qaramin frame me masifar kyau dake kafe kan table din mamin,hoton wani yaro ne wanda bazai haura shekaru takwas ba cikin shigar tazarce da hula da takalmi sawu ciki,ko shakka babu wanna hoton abdallah ne lokacin quruciyarshi,kyawunshi ba loka in girmanshi ne kawai ba kyawu ne na tun usuli


ya lura hoton take kallo don haka ya miqa hannu ya tuntsurar da shi,ya dan bada qara sakamakon haduwarshi da table din har sai da mami ta dago ta dubeshi sannan ta dubi frame din,ta fuskanci abunda yake nufi don haka murmushi kawai tayi can qasan ranta taci gaba da abunda take


bayan mamin ta kammala bashi duka wani taimako na kashe radadi da kuma tsaida dafin sai ta hada mishi da magani,minti goma tsakani mami tace ya taahi su wuce amma sai ya marairaice kan cewa bari ya huta,wayarshi dake gefan system din mami ta dauki kida,kamar bazai daga ba amma yana dubawa yayi hanzarin dagwa
''sir,munga alhj haladu uba mai qusa yanzu cikin asibitin nan''abinda aka fada kenan da ya sanyashi hanzarin miqewa,mami ta dubeshi
''lafiya abdallah?''
''mami ina zuwa,just twenty minute''bai tsaya sauraron komai ba ya fice daga office din,yayin da mamin ta bishi da kallo cikin ranta tana masa addu'a,ita kanta mqryam din binshi tayi da ido cikin mamakin me ya sanya masa kuzari haka lokaci guda,mutumin da anyi anyi ya tashi a tafi gida ya qiya?ya tsaya shagwaba


shudewar kusan sa'a biyu har mami ta soma nuna damuwa sai gashi ya dawo,zufa duka ta wankeshi,cikin kulawa mamin ta dubeshi
''lafiya dai abdallah?''ta sake tambayarshi karo na biyu
''mami na samu nasarar kama alhj haladu,saura alhj hamza naira''ya bata amsa yana tsiyaya ruwa mai sanyi cikin tambulan na glass



ba mami ba,hatta da maryama dake zaune can gefe ba qaramin burgeta yayi ba,tana tsammanin dazun nan taji uana zancan neman mutumin amma har ya sami nasarar cafkeshi cikin abunda bai gaza awa daya da rabi ba,fuskarta qunshe da madaukakin murmushi take fadin
''masha Allah masha Allah,lallai dana daya da daya ne,baka tsinta aqasa ba abdallah,fata na Allah ya tsaremin kai yaci gaba da yi maka jagora,ya baka ikon ci gaba da tsayawa akan gaskiua,ya rabaka da aikinka lafiya''


yana kurbar ruwan sanyin yana ratsa qwaqwalwarsa sannan sanyin dadin addu'ar mahaifiya na sake shigarshi
''ameen ummi na,kullum addu'arki ita ce sirrin nasarata a rayuwa''
cikin mintina gona suka bar asibitin harda ummin don lokacin tashinta yayi


Sashensa ya wuce mami ta haura sama itama don kintsawa yayin da maryam kuma ta koma kitchen don kammala masu abincin dare tunda tuni an fara ahirye shiryen kiran salla,fashin sallar da take ne ya bata damar ci gaba da ayyukanta
shigarta kenan ta kunna gas tana shirin aza tukunya samanshi taga kamar anyi wuf an fice daga kitchen din,da sauri tabi hanyar fitan itama tana dube dube,bata ci nasarar ganin kowa ba sai adnan yayan zubaida dake shigowa cikin waiting room,wanda sairan qiris suyi karo da shi tayi saurin ja baya atsorace


kallo yake qare mata hade da wani shu'umin murmushi wanda hakan ya sanyata ta tsargu,ta tsani namini mai kallo don a aqidarta takan fassara mutum ne kawai da dan iska
''yi a hankali mana baby kada ki jiwa wannan kyakkyawan jikin ciwo ko''babu abunda tace da shi sai juyawa da tayi cikin sassarfa ta koma kitchen shi kuma ya mata rakiyar idanu,sai da ta bace ya wani lashe labba kana ya shige bangaransu


nene tayi saurin damqo wuyan rigarshi don ta fuskanci baima gansu ba a inda suke labe ita da zahariyya suna gano farfajiyar waiting parlour wucesu zaiyi,a razane ya juyo
''banza solobiyo kawai,harka wani tsorata,amma ka iya tsayawa kana qarewa jikin yarinya kallo''
kansa ya shafa yana fadin''to ai nene ba laifi bane''
''kaga ni ba wannan ba,kaga alamun yarinyar nan ta fuskanci an shiga kitchen dinsu ne?''
''eh to,ni dai na ganta a gurguje da alamu wani ta biyo''
''hanyar ina kaga tayi?''
''hanyar valcony''
ajiyar zuciya nene ta saki
''Allah na gode maka bata ga ko waye ba,kuma da alamu bata fuskanci komai ba''


''ya?nene?''adnan ya tambaya yana dagawa uwar gira
''mun aiwatar da aikin mu,saidai mu jira sakamako kuma,indai kuwa sakamako yazo da kyau,to mafarkin kowannen mu ya gama cika,don wannan karon indai aikin mu yaje inda ake buqata to babu makawa burinnu sai ya cika''
tsallen murna yayi
''that's why nake sonki nene,amma....''
ya katse maganar jin takun saukowa daga saman bene,zubaida ce,itama dubansu tayi kamar yadda suka dubeta,ganin yanayin fuskartq bai sauya ba ya tabbatar musu bata ji komai ba,gurin t.v ta nufa ta kunna sanna ta kamo tashar da take da buqatar kalla ba tare da tace da su komai ba,haushinsu duka take ji don dazun sun dqn haura sama kan yadda take son abdallah yana yarfata



_kuyi haquri da wannan sakamakon na wuni gurin mama na da bata jin dadi sosai,muna buqatar addu'o'inku,na gode_




*mrs muhammad ce*👑






 📚 📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*20
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
Gab da isha'i ta kammala tuwon semovita miyar busashshiyar kubewa,kan dining ta jera konai yayi net sannan ta barwa baba uwani gyaran kitchen kamar ko yaushe ta shige bedroom dinta,wanka tayi ta shirya cikin atamfa doguwar riga ta haye gadonta don ba salla zata yi ba
research ta shiga yi kamar yadda al'adarta take lokaci bayan lokaci idan ta samu kanta free kamar yanzun
takwas da rabi da mintina hudu kiran mami ya shigo wayarta,a ladabce ta daga
''maryamu an kammala abinci ne?''
''eh mami na kammala''
''ok,taimaka don Allah ki shirya abincin cikin folding basket ki kawo nan sashen abdallah anan zamuci,nazo bashi magani kuma ya ruqeni''
''to,amma mami ban san inda saahen yake ba''
''idan kika fito cikin balcony gefen hannun damanki zaki miqehar sai kinzo qarshenta''
''to gani nan''
tsaf ta shiryasu cikin basket din mai kalan ja da fari,hijabinta ta zura mai hannu ta sanya slipper ta dauki basket din ta fito
a hankali take taka balcony din tana sake qara kallonta don bata taba yin area din ba tunda tazo gidan,sai taji kamar kada tafiyar ta qare saboda dadin da yanayin yayi mata,iskace take busawa mai mai sanyi hade da qamshin qasa wanda hakan ke alamta lallai yau wani sashe na cikin garin kano yana samun saukar ruwan sama,kasancewar shigowar yanayin damina,duk da cewa har yau tasu area din basu samu ruwan ba saidai yawaitar haduwar hadari da bajewarsa
Qiris ya rage ta bangajeta Allah yasa tayi saurin cin burki,zubaida ce tsaye a gabanta tana huci,a zaton maryama bata da case don ita don haka tayi qoqarin gewayeta ta wuce,binta ta sakeyi ta sha gabanta
''lafiya?''maryam ta tambayi zubaidan cikin sanyin nan nata
''kiyi qoqarin kame kanki daga cikin lamuran abdallah,don na fuskanci wani rawa kanki yake,bari in tuna miki idan kin manta,ke ba kowa bace cikin rayuwar abdallah face 'yar aiki wadda bata da maraba da baiwa,babu abunda abdallah zaici dake,gargadinki kuma nake ba shawara bace''
ta mata kallon sama da qasa hade da bangazarta ta wuce,da kallo ta bita harda waiwaye,sai da ta bacewa ganinta sannan ta dawo kallon gabanta
sam abun vai bata haushi ba sai ma dariya wanda hakan ya sanyata murmusawa hade da kada kai ita daya,idan banda abun zubaida ina zata kai abdallah?,me zata ci da shi,sam ko kadan ma ita dai dai da second bata taba qyasta wani abu wai tsakaninta da shi ba
da wannan tunanin ta qarasa sashen,da qyar ta samu ta iya shiga saboda tun daga qofa ta soma ganin bambanci,hamshaqin parlour ne wanda zata iya cewa bata taba tozali da makamancinsa ido da ido ba saidai ko cikin hotuna
kusan shima komai na parlour din fari nesai ratsin maroon kadan da baqi
kujeru set uku ya lamushe don shi din ma ba baye bane gun girma da kuma tsari,kowacce kujera na rukuninta daban,girmanshi baiyi yawa ba haka nan baiyi kadan ba,bisa can dining area din dake daura da matattakalar bene ta hangosu wanda hakan ke nuna mata sunyi ready ita suke jira
a nutse ta qarasa ta soma serving dinsu mami da abdallanta na hirarsu,ta turawa kowa plate din tuwo da miyarshi ta sona kiciniyar bude flask din patatoes balls din
''meye haka?,wani sabon salon raini ne haka,ta yaya zaki raba mana plate ko yau kija fara sanin tare muke cin abinci?''
abdallah ya fada cikin hade gira yana typing saqo a wayarshi
ta saki flask din da niyyar hade masu abincin a plate guda mami tace
''rabu da shi fitananne kawai,kalna mai sauqi kace hada mana sai ka ja wani dogon magana?''
''wallahi mami ke ke shagwaba yarinyar nan da yawa,shi yasa kullum sai ta yima mutane shirme''
''Allah ko,ita ce ma kai''inji mamin
da daidai ta soma jera patatoes balls din cikin plate,saidai duk wanda ta dago ssi taga ya rabe biyu,tayi tsammanin tauri yayi da yawa yssa yake haka,don haka a hankali ta lallabashi ta gama jerawa cikin plate din ta tura musu,tana shirin sauka qasa mami tace ta zauna ta saka hannu suci tare,ce mata tayi taci nata ta qoshi
''kunyanki yayi yawa maryam,har yau kin kssa daukan kanki a matsayin diyata ko?,shikenan tunda ba zaki ci da mu ba zauna muyi hira tare idan na kammala mu wuce''
tilas ta koma ta ja kujera daya ta zauna kanta na sunkuye a qasa,lokaci lokaci mami na jefata cikin hirar don ta sake cikinsu saidai kaifin idanun abdallah ya hanata,duk tunda ta zauna din qurar da ta kwasota ma bai duba ba duka ya tattara hankalinshi kan maminshi da plate din abincinsu
abdalla ne ya soma tsame hannunshi yana fadin
''mami turomin daya plate din''ta tura masan tana ci gaba da cin tuwonta don ita duka wadannan yame yamen basu dameta ba
hannunshi ya saka ua dauki guda daya,lokaci guda wata matsananciyar faduwar gaba da sameta,rashin yarda da patatoes balls din ya kamata cikin tazarar lokacin da bai wuce second biyar ba
kai balls din bakinsa yayi daidai da saukar hannun maryama kan nashi hannun ta buge da qarfi har yaji zafi,ba 6ata lokaci balls din ya fadi saman teburin cin abincin ya wargaje,wani ruwa yellow din ruwa ya soma fita daga tsakiyanshi wanda idan ba sani kayi ba zaka yi tsammani ruwan curry ne,wannan shi ya taimaka daga abdallah har mami basu kula da shi ba
zuciyarta taci gaba da tsananin bugu,tsoro qarara ya bayyana cikin fuskarta,tana tuna giftawar data gani dazu cikin kitchen da ta rasa ta waye?,sa'an nan ta dawo da tunaninta kan dalilin daukota don kula da abincin abdallah,guba ne fa?guba abdallah yaci sau biyu a baya,kada fa ayi amfani da damarta a aikata wani mummunan abu,a zafafe abdallah ya kalleta,ranshi yayi tsananin bacin da har ya gaza tambayarta sai mami ce tace
''a'ah,ya haka maryamu?''
''barta mami,ai dama daga ganin wannan yarinyar bata da kunya,in banda tsabar rashin mutunci ya mutum yana.....''
dakatar da shi tayi tana kallon maryam wadda ke qoqarin daidaita natsuwarta don lalubo dalilin da zata bada wanda har ya kai ta aikata abunda ta aikata din yanzun
ba shiri ta tsinci bakinta na fadin
''mam...mi na manta ne ba gishiri da magi cikin balls din,da muka tafi asibiti ashe ban zuba ba,kada kuma yaci yaji babu dadi a bakinsa''
''amma banda abun maryamu ai sai kice mishi kawai kada yaci,next time ba haka ake gyara ba kin fahimta?''
da sauri take gyada kai tana cewa''eh mami,kayi haquri''
ta fada tana kallin abdallah,fararen idanunshi da ya zuba mata yana kallonta shi ya kuma sakata rudewa har ta rasa me zata aiwatar,ba shiri ta shiga tattara fasashen balls din dake gabanshi tana niyyar kwashewa taji ya riqe tsintsiyar hannunta
a razane ta dago idanunta suka shiga cikin nashi,ta danyi kusa da shi hakan ya sanya yaji kaifin idanun nata har qwaqwalwarshi
''daina kallona da idanu sai kace na mage''maganar ta subuce masa
ya maye gurbinta a dan tsawace da fadin
''qarya kike,wannan bai kai dalili ba,na gano wani abu daban cikin ranki,akwai dalili amma ba wannan ba''
tuni qwalla suka cika mata idanu,cikin son kare kanta tace
''da gaske nake,ba qarya nayi ba ka yadda yaya abdallah''
''akan me zan yarda dake,bayan ire irenki biyu sun so ganin qarshen numfashi na a baya,kema kin biyo sahu ne?''ya fada yana huci
tuni qwallan da ta tara a idanunta suka cika suka zama hawaye,ba b'ata lokaci suka soma gangarowa kuncinta,kuja ta qwace mata,tsoro da rauni suka mamayeta
''me kakayi haka ne abdallah,sakar mata hannu''mami ta fada cikun fushi
''mami yarinyar nan ban yarda da ita ba,baki ga reaction dinta bane?,aikina kenan mami nasan reaction din masu laifi''
''ina ce nan ba a office din SS muke ba,ai kin naka baka gwadashi a baya ba sai akan maryam,comon bani son sakarci sakar mata hannu tun kafin in sabar maka''dolenshi ya saketa amma duk da haka bai barta ba binta yake da ido
''oya maryam,tattara kayan nan ki tafi kije ki kwanta gani nan tahowa''jikknta na rawa ta dinga hada kwanukan,tausayinta fal zuciyar mami tana ganin abdallah ne ya tsoratata
''abdallah,ka saurareni da kyau,ba da ka zan dauko maka maryam a matsayin cook ba,nayi bincike mai kyau game da ita,nasan halayenta gaba da baya,baya ga haka nasha yin istihara game da zamanta da mu jikina na bani alkhairi ce ita,saboda haka ina mai tabbatar maka maryam ba zata taba iya cutar da wani dan adam ba balle mu,ni maminka nake gaya maka wanna maganar ba wata ba ka fahimceni?''a ladabce ya amsa mata
''kada ka sake mata irin haka,gaba daya ka tsoratata,ka kiyaye gaba,''
''insha Allahu bazan sake ba''tafiya taso yi amma ya kasa ya tsare ya hanata,sai da ya sata dariya kana ya mata rakiya har bedroom dinta sannan ya dawo bangarenshi
maryam kuwa jiki na rawa ta isa dakin baccinta bayan ta tabbatar ta yiwa patatoes balls din mugun boyon da babu mai ganinshi sai ita,sam bata qaunar tashin hankaki a rayuwarta,kuka ta zauna tanayi riris a bakin gadonta,lijaci mai tsawo ta dauka a haka kafin ta gane cewa kuka babu abunda zai amfanar da ita,ta tabbatar da cewa rayuwar cikin gidan akwai wani qulli da su su mamin basu san da shi ba,fargabarta daya kada wani abu ya samu abdallah ta sanadinta,idan ta fada wannan shingen wazai fiddata
bata da wannan gatan saidai yadda Allah kawai yayi da ita
har kusan uku na dare ta kasa runtsawa,sai da wayarta ta buga alarm na qarfe uku da rabi wato dai dai lokacin tashibta sallar dare kenan sanna ta shiga toilet ta daura alwala
kusan dadewarta ta yau tana addu'a tafi ta kullum har sai da kiran assalatu ya rusketa,sallar asuba tayi ta dora da azkar zuwa qarfe bakwai ta fita kitchen
sam jikinta babu kuzari kamar yadda zuciyarta babu dadi,fuskarta kadai ka kalla ta isheka amsa saboda ja da ta hada da kuma tasawa da idanunta suka danyi,a kasalance take hada musu break din wanda ya kaita har qarfe goma bata kammala ba saboda rashin qwarin jiki
goma da minti ashirin da shidda ta ji sallamar mami cikin kitchen din,a hankali ta dago tana amsa mata kafin daga bisani ta rusuna ta gaidata bata damu da amsawa ba ta dora da tambayar maryam din cikin fuskar rashin jin dadi
''maryam,lafiya?,me ya samu fuskarki?,kada kice min kwanan kuka kikayi?,abdallah ne ko?''
zuciyarya ta danyi rauni amma sai ta dake,ta dan murmusa kadan hadi da kada kanta
''ko baki fada ba na sani shine,kiyi haquri kinji maryam na mishi fada kuma insha Allahu haka ba zata sake faruwa ba,ni zan fita,ga wannan albashinki ne na wannan watan''ta fada tana zaro rafar kudin daga jakarta sababbi kar da su
hannu biyu ta saka ta amsa sanna ta mata godiya
''nice da godiya maryam,inajin dadin zama dake,kina da kyawawan halaye da mutane da dama suka rasashi a wannan lokacin,fata na Allah ya baki miji na gari maryam wanda zai riqekibisa gaskiya da amana''
kunya maganar ta bawa maryam wanda yana daya dqga cikin halayenta dake burge mami
lura tayi da akwai magana a bakin maryam din
''kamar kina son cewa wani abu ko?''
''dama yau inason inje gida ne''
''hoo,maryamu,wannan din ne kika kasa fada,banda abunki ai kinyi kara ma wata guda baki gansu ba,babu matsala zan yiwa driver magan ki shirya sai ya kaiki idan zaki dawo ki masa waya yazo ya daukeki,idqn baki dawo da wuri ba ma babu damuwa ni da wuri zan dawo gida yau in yaso sai na mana dinner dinko,ki gaishemin da mutanan gidan da kyau kinji,zan ajjiye miki saqo a parlour idan kin tashi tafiya ki tafi musu da shi''
godiya sosai ta yiwa mamin tare da yaba karamcinta,tana kammala breakfast din ta shirya a gurguje cikin baqar abaya wadda ta sake fidda sirrin kyawunta ta kuma haska farar fatarta wadda ta sake fresh saboda zama gu daya da kuma sanyin a.c,kitchen ta koma ta juye duka patatoes balls din cikin leda bag ta daure ta jefa shi cikon jakarta,sai da ta tabbatar ta qulle duk inda tasan idan an shigo shi za'a iya samun matsala gun abinci ko abunsha da zasuyi amfani da shi sannan ta fita,hatta da breakfast sai data nemi alfarmar baba uwani ta kula da shi kafin abdallan yazo yaci
cikin motar ta zaro wayarta ta lalubi number din raliya,har tayi ringing ta katse ba'a daga ba sai da ta sake kira,bugu daya ta daga
''sorry sis,fadil ne ya rudani da kuka na kasa daga kiran''sama sama suka gaisa,tana shirin tsokanarta taji muruarta ba yadda ta saba ji ba sai kawai ta share
tambayarta tayi zata iya samun nasir abban fadil a asibiti ko bai fita ba
''tun dazun ya fita,ina tsammanin ma yakai awa uku acan''godiya ta mata ta kashe wayar,kamar ta tambayeta lafiya?sai kuma taga bai kamata ba,idan da buqatar taji maryam ba mai boye mata bane,a mutunce ta cewa driver din zooroad zasu fara zuwa ya amsa mata sanna ya sauya akalar motar
*mrs muhammad ce
[9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣1⃣




_yar fadakarwa_

_*shin ko kinsan gwalagwalan kwanakin da muke ciki 'yar uwa?,kwanaki ne masu matuqar tsada da daraja har agun Allah madaukaki,kwanaki ne da ayyukan alkhairi suka fi soyuwa agun ubangiji a cikinsu,kwanaki ne mafi daukaka cikin kwanakin shekara,an karbo hadisi daga imamu bukhari r.a,annabi s.a.w yana cewa(babu wasu kwanaki da kyawawan ayyuka sukafi soyuwa agun ubangiji kamar kwanakin goman farko na watan zulhijja,sahabbai suka ce da annabi hatta jihadi saboda Allah?,annabi yace eh har jihadi,saidai mutumin da ya fita jihadi da ranshi da dukiyarshi bai dawo da komai ba),shin me kike aikatawa na neman lada?,kada ki yarda su shude ba tare da kin amfana da komai ba,baki da tabbacin ganin na wata shekarar,Allah ya karbi ibadun mu yasa mu dace ameen*_

🕋🕋🕋🕋🕋🕋🕋


Minti talatin suka isa asibitin da nasir ke aiki,ta taradda marasa lafiya da suka rigata zuwa,hakan yasa tabi doka itama ta hau kan layi,don ta sani indai tace masa ta zo babu makawa sawa zaiyo ta ahiga kawai ita kuma ba zata so shiga haqqin wani ba


ko kafin azo kanta tuni ta qosa,jira ne na tsawon awa guda da rabi kafin ta samu shiga,da mamaki yake dubanta tare da fadin
''yau kuma an tuna da mu kenan''
dan qaramin murmushi tayi kan ta haye kujerar da masu buqatar ganinshi ke zamansa 
gaisawa sukayi yaso ya dan tsokaneta yadda auka saba sai kuma ya fuskanci yanayonta ba yadda ya saba ganinta bane


madaidaiciyar handbag dinta ta zuge ta fidso da leda bag din ta dorata saman table dinshi
''taimako nake buqata daga gurinka nasir ko zaka iya yimin shi?''
''me zai hana maryam indai ba kaucewa addini ba''
''abunda ke cikin nan nake da buqatar a duba min ko akwai poising a ciki?''
ido ya dan zuba mata kamar mai buqatar qarin bayani,gganin bata da niyyar qara masa haske yasa ya kauda idonshi kana yace
''ok,ba damuwa,ga kujera can zauna bari na kira lab azo a dauka''


cikin mintina uku kacal wani matashi ya shigo sanye da farar labcoat ya dauki ledar ya fice


mintina arba'in din da yayi kafin ya dawo jinsu tayi kamar awa arba'in ne,tuna ni babu kalan wanda bata yishi ba,dawowarahin tayi daidai da kammala ganin patiente da nasir yayi,hakan ne ya bawa matashin damar zama tare da miqawa nasir result din ya ajjiye ledar a qasa yana duban fuskar nasir din


nuni ya yiwa maryam din da hannu kan ta taso idanunshi na cikin takardar,a sabule ta iso gaban teburin ta samu kujera daya cikin biyun dake gun ta zauna
''maryama....taya aka samu irin wannan mummunar gubar cikin abinci?,kinsan nau'in guba iri wannan bamu da ita ma sosai cikin qasar nan?,guba ce da ke iya kashe mutum cikin mintunan da basu gaza biyu ba,baya ga haka hatta da gawarka ma bata qyaleta ba sai ta narka duka kayan cikin mutum,dubi yadda ta maida wannan dankalin''ya mata nuni dashi dake cikin ledar da yasa matashin ya bude


A hankali ta maida firgitattun idanunta kan ledar,dankalin ya zagwnye ya koma kamar ruwan kunu,hakanan gabaki daya kalarshi ta sauya zuwa kore da baqi,kumfa ce kawai ke tsattsafa a samanshi tamkar ya ahekara ne da sarrafawa ba kwana daya ba,wani irin tsoro ya sake kama maryam,da sauri ta maida idonta kan nasir,cikin rawar murya tace
''ko zan iya ganinka kai daya?''
''why not?,sadam dan bamu guri''


office din ya rage daga ita sai shi,a hanakli ta zayyana masa dukkan abunda ta sani,ya jima yana jinjina kai kafin yace
''maryam akwai hadari mai girma tattare da gidan,saidai abu guda da ban goyi bayanki ba barin gidan da kike shirin yi,barinki gidan ayanzu dai dai yake da mutuwar abdallah da maharfiyarshi,bayan kin gano matsalar da su basu san da ita ba,shawarar da zan baki shine kawai ki zama mai matuqar kula da takatsantsan,abu na gaba shine ki riqe addu'a,qarfinta da kaifinta ya sha gaban duk wani kaidi da zalunci''


sun shafe fiye da mintuna talatin yana bata shawarwari wadanda syka sa taji hankalinta ya kwanta,nutsuwarta ta dan dawo,da kanshi suka zagaya can bayan asibitin sukayi haqa ya binne ledar patatoes din
''yanzun kuma sai ina?''ya tambayeta bayan sun isa bakin get din asibitin
''gida na nufa inje inga mama''
''gashi wani aikin yanzu zan koma ciki na qarasa kinga ai da na kaiki''
''ba damuwa,zan hau adaidaita sahu yanzun zaka ga naje''


a gabanshi ta hau napep din ya biya mata ta wuce bayan ta masa godiya,murmushi kawai yayi
''kada ki damu,ke da raliya duka abu daya ne''


har qofan layinsu dan adaidaitan ya direta saboda babu damar shiga layin nasu,ba dob matsi ba sai don yawan kwatoci da suke da su budaddu wadanda ke wa ababan hawa cikas gurin wucewa,sannu a ankali take takwa har ta isa qofar gidansu


Ba laifi akwai ahige da ficen al'umma wanda baka rasa gidan da shi sakamakon yawan 'ya'ya da sana'a da auke da shi,musamman a irin wanna lokaci da ake shirin tada sallar azahar masu neman abincin rana nata hada hadar siya,wanda ayanzun huwaila ce kadai keyi don inna hadiza na ganin yanzun ta girmewa haka


da ''zan wuce zan wuce''ta samu shiga cikin gidan saboda yawan mazan dake soron suna dakon a miqo musu abincinsu,can tsakiyar yara ta hango lubabatu da daurin qirji tana zuzzuba abincin a kwano tana mita,alamu dake nuna cewa inna huwaila bata nan kenan ita aka bari da aikin abincin,qofar dakin inna hadiza kuwa labule ne asake qarar music na fita,kada kanta tayi cikin zuciyarta tana fadin''fidan mu,gidan mu kenan,ya Allah ka daidaita shi kamar kowanne gida''ta cire takalmanta tashige dakin mamanta


daidai lokacin da maman ta fito daga dakin da suka maida kitchen dauke da farar roba da ta zuba shinkafa danya aciki,da alama girki take wato yau baban nasu yayi tsiyar kenan kowa kansa yau zai ciyar
murmushi ya subucewa maman kamar yadda ya bayyana fuskar maryamu,wani farinciki dukkansu suke ji wato da da uwa ba wasa ba,ta isa gaban maman tana niyyar amsar robar hannunta yayin da mamar ke cewa
''maraba,yau kece atafe,a'ah barmin kayana yanu zan kammala ai,daga ahigowarki ko hutawa baki yi ba''dole ta qyale maman ta fita waje ta wanko shinkafar ta ta zuba sanna ta dawo ta zauna


hira sosai suke da mamar nata har ta kammala shinkafa da wake da an quli hade da salad tumatir albasa da cocumber,zasu tada sallar kenan hindatu ta shigo,murna kamar ta cinye maryam,cewa tayi itama ba zata zauna ba bari ta fara sallar,ta yada takardun jarrabawarta saman kujera ta fita ta yo alwala


Dari biyar maryam ta fitar ta bawa hindatu da kanta taje ta aiyo musu serdine soyayye suka zauna hankali kwance suna cin abincinsu suna hira,hindatu sai santin maryam take
''wallahi adda maryam kada kiso kiga yadda kika koma,kin zama wata hajiya skin dinki tayi wani freah,qiba ce kawai baki qara ba,kinga kiwa da kin dada qiba tsawon nan naki raguwa ziyi''
dariya ma ta basu mama tace
''to sarkin zance,kiyi a hankali dai kada ki qware''cikin nishadi auka kammala hindatu ta guara gurin ta dawo suka sake bude sabon babin hira,da daidai da daidai take jin matsalolinsu,sai taji dadi jin cewa basu da wata matsala mai yawa,mama tana cikin lemonta sosai don haka sai dan abunda ba'a rasa ba,wanda shina mafi yawa kan karatun hindatu ne


duka albaahinta ta fidso ta damqawa maman tana fadin ta fadi abunda ya dace ayi da su
''um um maryamu,ke din mai hankali ce,na tabbata ko bance komai ba zaki yi duka bunda ya dace din''
tana lissafawa mama abunda takeso tayi din maman na sa mata albarka,ciki harda aiyqn kayan abinci ta ajjiye agidan nasu tunda albaagin nata ya tasamma dubu dari


''hmmm um''hindatu ta fadactana turo baki,maryam ta juya ta dubeta
''ya akayi bakin ki da magana kenan''
''wlh akwai,haka kawai zaki narka albashinki ki siyi abincin gida wanda har wadancan mutanen za'aci,jamila ma da suke qaryar arziqi bata taba siyan gallon din mai ta ajjiye tace kowa yayi amfani da shi ba sai ke da kike nema da guminki,a jikinta kawai zaki ga samunta ita babarta da 'yan dakinsu''


_kumin afuwa kuyo maleji da wannan,a bini bashi_



*mrs muhammad ce 👑*



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*22
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
murmushi maryam tayi
''akwai bambanci tsakanin jamila da maryama,mama ce mu ta haifemu uwa ta gari,mai nuna mana hanyoyin alkhairai da samun dacewa duniya da lahira,yayin da su kuma inna hadiza ce ta haifesu,kowanne mutum da kika gani yana kyauta ne da abunda yake hannunshi yake kuma da shi na alkahairinsa ko sharri,ma'ana duk abunda mutum yayi miki na sharri to abunda ke hannunsa kenan sharrin,ke kuma kada kice za kiyi amfani da abunda yake hannunki na sharri ki maida masa da martani,nuna masa ke alkhairi ne da ke,kada ki damu da sai wani yayi abu zakiyi,idan kina da dama kiyi din,kuma ki qudurce cewa kinyi ne saboda Allah,to sai kiga koda wanda kika yiwa din bai gani ba baki da haufi don kinyi ne domin Allah kuma ahike bada lada da sakamako''
cikin hikima maruam ta ragewa hindatu haushin da take ji na abunda tayi shirin yi a gidan nasu,har ta rakata super market din dake bayan layinsu ta siyi cartoon na macaroni taliya da couse couse,galoon na manja da man quli,dan madaidaicin buhun shinkafa,ta siyawa mamanta kayan tea complete,har da su cornflakes saboda hindatun
ledar da mami ta bata ta atamfofine guda biyar ciki da sabulai masu tsada sinqi biyu mamanta bawa guda biyu hindatu daya ta ware biyu zata bawa huwaila da hadiza,yara suka samu suka dauko musu kayan hindati na biye da su yayin da maryam tayi gaba
sallamarta atsakar gidan tayi arba da baban nata,cikin fara'a ta nufeshi tana shirin tsugunawa tace
''baba,barka da warhaka''yayin da shi kuma ya tareta cikin hade fuska ba kuma tare da amsa gaisuwar ta ba yana fadin fadi
''lafiya ,ya akayi me kika zo yi?''
''ya salam,taya za'a raba mjtum da gidan mahaifinshi koda kuwa aure yayi ballantana ita da bata yi aurenba?''take zantawa ita da zuciyarta
''zuwa nayi na gaidaku baba,kusan wata guda ban ganku ba''
''amma dai maryamu ina cewa.....''maganar tasa ta katse lokacin da yara suka soma ahigo da kayan suna ajjiyewa
''yaya,kai,wannan kuma daga ina?''
''siyayyar adda maryam ce''hindatu ta bashi amsa lokacin da take sallamar yaran da naira goma goma ladan dako
''uwarta ta siyowa kenan?''baban ya fada yana duban kayan
''a'ah baba,na dukka gida ne,ga wannan baba a sa mana albarka''ta ce tana ciro naira dubu biyar ta miqa masa
washe baki ya shiga yi
''ah,lallai haihuwa mai rana,maryamu dukka haka,basuyi yawa ba?''
mirmushi ta danyi zuciyarta fal mamaki
''basuyi ba baba''
''ah lallai wannan gidan aiki ya karbeki,to Allah yayi albarka ya bada miji na gari''ya fada yana irga kudin fuska qunshe da fara'a
ko banza taji dadin addu'ar da yayi mata,tunda dai uba uba ne ba'a canzawa tuwo suna,sai take jin ranta yana mata dadi
ina wuta inna hadiza ta saka maryam,qememe taqi karbar atamfar da ta bata din ai ita tafi qarfin atamfa wallahi,su yanzu atamfa saidai su bayar,ita kuwa huwaila hannu ta saka ta amshe kayarta tana tunanin gobe idan Allah ya kaimu taje kasuwar bakin rimi ta saida barta ko dubu biyar suka bata ta rage son tuni bokan uwani suka soma tatsarta,ita kuwa hindatu ta kalmashe tace gaba ta kaita,
''aikin banza aikin wofi,wa ma yasan daga inda kudin suka fito,an tura yarinya yawon karuwanci tana samo kudi tana kawo muku kuna karbewa an fake da gidan aiki aka kaita,a dai juri zuwa rafi da tulu diban ruwa wata rana zai fashe,ke kuma na dawo gareki munafuka makwadaiciya,an baki abu kinsa hannu kin karbe,to ni nafi qarfin atamfa wlh ehe''
''Allah ko?,Allah sarki,mu gani a qasa mana wai inji kare ance ana suna a gidansu,idan akwai uwar makwadaita ta duniya to kece kakarta,kwadayin ne ya sakk cusa 'yarki inda bata da gurin zama,kuma da sannu unguli zata koma gidanta na tsamiya''ta yaue labulen dakibta ta shige tabar inna hadiza na ci gaba da babatu da sharrence sharrance kala kala
lokacin da maryam ke sallama da mama tana shirin ficewa daga tsakar gidansu zuwa soron jamila ta danno kai zuwa,ta cake ado cikin wata yar ubansun shadda dinkin riga da skert na rashib arziqi,qam rigar ta kamata har boobs dinta na yowa sama,babu zancan mayafi sam atattare da ita sai daurin zamanin nan da ake kira ture kaga tsiya,waya take tana taku cikin isa da qasaita tamkar wata diyar qaruna
''yanzun nan na fito daga gidan mu hadu kawai a ni'ima guest palace din,amma fa gaskiya wannan karon bazan kuna ba gida zan koma,ok sai na iso''daidai lokacib da ta kammala wayar,bangazar kafadar maryam din tayi sannan ta juyo a wulaqance ta qare mata kallo,wata mahaukaciyar dariya ta saki tana ci gaba da kallonta
''sannu adda maryam,ana nan ana fama ko,ko da yake dai....''ta fada tana kuma kallonta daga sama har qasa
''ba laifi naga kin dan canza,ko an fara bin kwalta ne?''
waniabu ne ya tokarewa maryam dim maqoshi,rainin hankalin ya fara isarta dukan ya mata yawa,tayi mata uwarta ta mata,batasan lokacin da ta daga hannu ta zabga mata mari ba,ba ita kadai ba hatta da hindatu tayi mamaki,tsawon shekarun da suka dauka bata taba gwada yiwa wata cikin maraina wayon ta haka ba
''kan can uba,kut,me nayi miki,ko ko tsabar baqin ciki da qyashi ne...''
''kika ci gaba da magana ina mai tabbatar miki zaki kwashi haqoranki a qasa,banza jahila dabba wadda batasan inda yake mata ciwo ba''
tsit tayi da bakinta don taga irin bacin ran da bata taba gani cikin idanun maryama ba,gaskiyar hausawa dake cewa wargi ma guri shika samu
daga haka bata dada ba ta mewayeta tayi wucewarta,dadi kam tamkar maryama ta taka rawa saboda farinciki,mama ma wannan karon bata ce uffan ba,don tsan yau da gobe tafi qarfin wasa,fitarta waje babu inda idanunta suka kai sai kan jabir dake zaune mazaunin direba,idanunshi qur bisa qofar gidan tamkar dama an sanar da shi maryam din na fitowa,mamaki da tausayi suka cika maryam,jabir ne wannan,jabir ne ya koma haka,ina gayu davtsaftar jabir suka tafi?,me yake faruwa da jabir me ya sameshi?,mamakinta bai sake daduwa ba sai da taga ya dauke kansa daga gareta tamkar ma bai taba saninta ba
cikin matuqar sanyin jiki take takawa har ta isa bakin titi ta tari napep tayi gida
lokacin da ta isa gidan tuni anyi sallar magariba duhu ya riga ya shigo,ba haka taso ba taso ne ta koma da wuri ta dora musu dinner din,saidai lokacin ya riga ya qwace mata,kitchen din ta nufa kai ysaye bata ko doshi dakinta ba,mami,ce gaban gas din tana ta hidimar hada abincin,yayin da kuna dan shagwabar nata ke tayata da dauko wannan dauko wancan
''idan banda rigimar abdallah don Allah ina kai ina girki?,nace ka...''sallamar maryam ta katseta
''sannu mami da gida,har kin dawo?''ta fada tana ahirin amsar aikin daga hannunta
''yauwa maryamu ya kika barosu?''
lafiya mami suna gaidaki?''
''kinga maruamu barmin nayi yau dai daya ki huta kema,nima na wasa qwaqwalwata ko?''mami ta fada tana hanata aikin da take qoqarib karba
''ayyah,mami da wuri ma naso na dawo lokaci ne ya qwace min''
tsaki abdallah ya ja hadi da barin miqo albasar da yakewa mami ya koma ya zauna
''ki bata mami aikinta ne,idan baki bata ba ma acikin albashinta na wani watan''
yau ranta abace yake tana jinta daidai da duk wanda ya taba tane,hakan ne yasa ta maida masa raddi
''babu damuwa,mami ina jinta ne tamkar mama na ne saboda haka babu ciniki tsakaninmu,ko ba kudi qimar shekarunta sun biya in mata aiki''
baki ya tabe kamar mace
''gaskiya ne naga kina amsar albashinki,ai da,sai kice kin yafe''
murmushi tayi cikin gatse,sanann cikin qasa da murya ta yadda mami da ta tafi sink wanke albasa ba zata ji ba
''kada ka manta haifata akayi yadda akayi yadda aka haifeka,aiki nake kamar yadda kake wa qasarka aiki da albashi ake biyanka,am not a servant,ciniki kuma ko tsakanin da,da uwa halas ne''
tofa baki yasan me zai fada tuni fuskar 'yan maza ta sake hadewa
a zafafe yayi niyyar maida raddi saidai isowar mami gun ya katse masa hanzarinsa,tilas ya hadiye abunda ya qunso
''zan zuba miki albasar maryamu kafin nan ki shiga daki kin ajjiye kayan hannunki kin sauya kaya ko?''
''to,mami na gode''maryam ta fadi gami da juyawa ta bar kitchen din,abdallah ya bita da kallon zaki san koni waye,yayin da ta daga kafadu alamun dake nuna masa am ready
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣3⃣




*_an karbo daga abu hurairah Allah ya qara yadda da shi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace: kalmomi guda biyu,masu sauqi akan harshe,mafiya soyuwa agurin ubangij,masu nauyi akan mizanin auna ayyuka SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI,SUBHANALLAHIL AZIM_*






su biyu cikin falon misalin qarfe goma na dare,mami na bisa computer dinta tana tsara wata saminer da zasu gabatar yayin da maryam ke zaune gefanta tana tayata hira
''abdallah shiru bai dawo ba,halan yau aiki ne ya tasaahi gaba''cewar mami lokacin da take ci gaba da typing 
''da alama''maryam tace
mami tadan bar abunda take ta juyo da hanklainta ga maryam
''wai ni kam maryam meye matakin karatunki ne?''
murmushi ta danyi
''degre ce''
''ta daya ko ta biyu?''
dan bude baki tayi alamun mamaki
''a'ah mami,ta dayan dai''
''mai zai hana in maida ke makaranta ki samu wata degree din kan fannin kasuwanci?,na fuskanci kina da amfani matuqa atattare da mu,sa'annan ina buqatar mai kula da kamfanonin abdallah mai amana kamar ke,kamfanoni wadanda ya gada da kuma wadanda ya bude daga baya,ya kike gani maryam zaki iya?''


shiru ta danyi cikin shakku,bata son ta fiya zura kanta cikin harkokin masu hannu da shuni, tana gudun wulaqanci,duk da tayi amanna cewa mami sam ba haka take ba,ta yarda da karamci da kuma son jama'a irin nata,to amma shi uban tafiyar fa wanda sam tasu batazo daya ba?
''yaya ne maryam naji kinyi shiru ko baki da sha'awa?''
girgiza kanta tayi
''a'ah mami,duka abunda kika yanke mami dai dai ne,amma zanso na fara sanar da baba da mama naji me zasu ce akai''
''gaskiyarki,wannan dai dai ne,amma duk da haka ki fara hada min takardunki nasan bazasu qi ba,babu wanda zaiqi ilimi wa dansa,ina da qawa a jami'ar b u k sanate ce so insha Allau babu matsala''


''to mami na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma''
''no maryam,diya ta nayiwa kinga babu buqatar godiya''gyada kai tayi fuskarta qunshe da murmushi
sallamar nene ce ta maida hankalinsu bakin qofar,nenen ce kiwa cikin doguwar riga mai zubin buba mai taushi saidai wannan nada hannaye gajeru da alamu shigar barci ce tayi
''maraba da nene''
''yauwa...mami''ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon dake,daura da inda mami da maryam din ke zaune,a mutunce suka gaisa
''zuwa nayi na diba yarona abdallah kwana biyu banjin duriyarsa''nene ta fada tana murmushi


mami ta rufe computer tana cewa
''abdallah na nan qalau aiki ne ya sashi gaba,da wuri yake fita kuma bai shigowa da wuri,yanzun na zancanshi muka gama da maryam''
ta juya ta dubi maryam sai a lokacin ta gaidatakanta na sunkuye a qasa,sam batason kallon idanun natar,haka nan sai taji fargaba ta kamata,second talatin idanunta na kan maryam din tana saqa a kanta kafin ta dauke kabta ta maida ga mami
''lafiyanshi dai qalau ko?''
''lafiya qalau yake''mami ta bata amsa cikin jin dadin tambayar tata,wadda har ga Allah tayi tsammanin ta mata ita ne da zuciya daya


ta miqe tsaye tana cewa
''tiw,ni zan wuce dama abunda na shigo naki kenan,sai da safenku''
''Allah ya bamu alkhairi nene an gode ki gaidamin su zubaidan kwana biyu ma bata leqo min ba,zahariyya dama sai wani abun ya kawota''murmushin yaqe nenen tayi cijin zuciyarta tana cewa
''bintu ki guji ranar gamuwar mu dake,gamon mu dake bazai ma rayuwarki daidai ba''


''abdallah na bani kunya wlh,dubi yadda baiwar Allahn nan ke sonshi take damuwa da shi,amma shi bashi da abun wulaqantawa sai diyarta,idan baiyi wasa ba na kusa masa auren dole''
'yar qaramar dariya ce ta subucewa maryam
''ai mami ba'a yiwa namiji auren dole''
itama dariyar ta tayata 
''to za'a fara kan abdallah''


mintina ashirin basu cika da fitar nene ba abdallan ya shigo,ya sauya shiga ba wadda ya fita da ita bace,indai mami taga hakan to a gajiye ya dawo ya fara shiga sashensa yayi wanka ne
kan table maryam ke serving nashi yayin da shi da mami ke hira jifa jifa,ta kammala tana shirin sauka ta basu guri taji yace
''ke...mene wannan din?''ya fada yana nuna abincin da ido,kafin ta bashi amsa mami ta karbe zancan
''dambun shinkafa ne mana''
ya bata fuska kamar yadda yara keyi ya dubi mami
''gaskiya mami ni bazanci wani abu dambu ba''maryam ta kalli farantin don sake gano aibun dake tattare da dambun da ta bata lokaci a kitchen tana girkawa,dambun shinkafa ne da aka masa hadin vegtables sosai saboda ta sonshi da son gayayyaki,cabbage ne carrot zogale green beans harda gyada da wadatacciyar albasa sai dafaffen nama data yankashi qananu ta zuba a ciki,mamaki tayi cikin zuciyarta duk da bata nuna ba kan fuskarta,ta lura tsirfar da ya tsuro da ita kenan cikin yan kwanakin nan


''amma kaifa dazun kace shi kake sha'awar ci ayi maka?''
''am sorry mami na,dambu ayanzu is too heavy na cishi na kwanta ai sai ya kashe miki ni''
dariya ma ya bata,bata zaci konai ba don yaune ya fara wa marya din a gaban idonta
''is ok,maryam yi haquri kinji taimaka ki sama mishi wani abun mai sauqi da sauri''
''no mami,ni zan zaba akwai abunda nake sha'awar ci''
''uhmm''ta fadi tana kallonshi
''sakwara nakeso miyan agushi''bata fuska mami tayi
''kai lokaci fa ya qure gaskiya ba zata girka ma sakwara a yanzu ba saidai ka barwa gobe''
''tunda kin roqa mata shikenan tamin jallop din supaghetti with serdine''bai qarasa ba ma ta sauka tayi kitchen


girki ba baqonta bane cikin minti ashirin ta kammala ta,tun kafin ta fito qamshi ya soma cika qofofin hancin abdallah amma sai ya dake
''mami,dazu munyi waya da abida,ta ce nan da kwana uku zata zo nijeria''
farinciki sosai maryam ta gani fuskar mami
''masha Allah,gaskiya ta kyauta qwarai kuwa da gaske,kaga ta baka kubya kai da kaqi zuwa''
''to mami me zanje na mata''
''any way dai tunda tace zata zo magaba ta qare,fata na idan tazo din wannan karon konai ya daidaita,canki cankar da kake tayi wa muta ne ta qare''
''haka nake fata,na soma gajiya da qulafucinsu naci da rashin zuciya,inason nima na huta mami na samu peace of mind''


kafadarshi mamin ta buga''ja'iri sai yanzu kasan da hakan...am maryam''
''na'am''
''insha Allahu nan da kwanaki uku zamuyi baquwa abida diyar ambassador muhammad mukhtar kuma idan tazo zata dan zauna da mu na wani dan lokaci,so ya kamata kinga na sanar miki haqqinki ne sa'an nan daura da dakinki zata zauna kinga ke zaki karbi baquncin,ina son kuma a sake tanadin sabbin girki,duk na san ban da matsala dake,ke din ba baya bace''ta qarashe maganar cikin sigar zolaya tana murmushi wa maryam din
murmushin ta maida mata
''insha Allahu mami babu damuwa''


''mami a maida abincin nan kawai kitchen nina qoshi ma''inji abdallah bayan ya gana jagulashi da cokali
harararshi tayi
''baki isa ba ko zaka ci kayi amanshi sai ka ci,maryam tafiyarki kije ki kwanta Allah ya bamu alkhairi,gobe insha Allahu zamu tattauna''sallama ta yi mata tayi shigewarta yayin da mamin ta ja plate din ta soma nado taliyar cikin pork tana cusawa abdallah,shikam ya bude ciki ya dinga diba,dama yana so kasuwa kawai yake kaiwa
''almiri ashe kana ci din kenan shegen girman kai yasa kace baka ci''mami ta fada tana dubanshi
dariya ya qyalqyale da ita ya kanne ido daya
''so nake dama mami ta bani da kanta nasan sai yafi dadi''
''Allah ya shirya min kai abdallah''ta fadi tana murmushi

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

tafiya take bata ko ganin gabanta saboda takaici da baqinciki,wai sai yaushe ne burinsu zai cika kan abdallah?,sai yaushe zasu samu nasarar kau da abdallah daga doron duniya,da wannan tunani ta samu da qyar ta maida kanta bangarensu


adnan da zahariyya dake dakon zaman jiranta cike da buri da fatan jin daddadan labari suka taso
''yaya nene?,anyi nasara kuwa?,rashin ganin nashi nada nasaba da aikin mu kuwa?''saida ta fada jabar saman kujera kafin tace
''mun sake fadu wannan karon ma babu nasara,rashin nasarar kuma yafi na kowanne lokaci''
adnan ya sake matsowa gabanta
''yaci dinne bai mutu ba?''
''ina ma yakai ga cin,ai ko ci baiyi ba,kuma hakan baya rasa nasaba da wannan tsinanniyar mai girkin da na rasa inda bintu ta samota,yarinya sai shegen kwarjini''
''oh shit!''adnan ya fada bayan ya dunqule hannunshi ya daki tafin hannunsa,zahariyta kuwa kasa magana tayi face bin sahun uwarta da tayi ta fada saman kujera


a sukwane ya koma shina ya zauna bayan yayi qasa da muryarshi
''nene,nifa na gaji da wannan shirin kisan ta bayan fage,ki barni kawai na tari abdallah na kasheshi da hannuna''
''kai dalla gafara can''nene tayi hanzarin katseshi
''ashe baka da hankali?,waye ya gyamaka kashe mutum kamar abdalla abune da yaje da sauqi har haka?,ka manta matsayinshi?,ka manta wayeshi a nijeria,bama haka ba,ka mance qirar qarfin da abdallah ke da ita,wanda na tabbatar idan aka barka da shi naushi daya zai maka saidai mu dauki gawarka ba kai din ba''shiru adnan din yayi don yasan haka maganar maman tashi take


zahariyya ta furzar da wani rin huci
''tsinanne matsiyaci,ni da zai amince ya auri waccar yarinyar zubaida ai da kinga komai yazo mana da sauqi,mu kasheahi hankali kwance,idan da rabo ma har sai ta haihu kinga tuwo namu miya ma tamu,to amma shegen girman kai da jin ajinsa bazai barshi yaso zubaida ba,to amma nene mai zai hana mu nemi hadin akn ita kukun tashi ko zata amince kamar yadda na baya suka amince,idan yaso itama musa a mata daurin baki idan ta amshi kwangilar ta yadda koda lamari ya baci zata gaza ambato sunansu kamar wadancan kukun''


ajiyar zuciya nenen ta saki
''hmmm,yaro yaro ne,duka tunaninku babu wanda ya kwanta min,wannan yarinyar tasha banban da wadancan kukun nasu na baya kallo daya na mata jiki na ya gaya min haka,abunda zai faru shine ni da kaina nake so ku bani lokaci zanyi tunanin mafita,na rantse da Allah wannan karon ko bata hanyar guba ba *SAI NA SALWANTAR DA ABDALLAH*


_TOH FA_🤔



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*_daga abu hurairah yardar Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace:ba zaku shiga aljanna ba har sai kunyi imani,ba zakuyi imani ba har sai kunso junanku,shin bana nuna muku abunda idan kuna aikatashi zaku so junanku ba?KU YADA SALLAMA A TSAKANINKU_*
cikin kwana ukun mami ta hana gidan sakat da shirye shiryen tarbar abida,ragowar daki biyun dake maqotaka da nata aka bude,kusan komai irin na nata dakin ne sai dan bambancin abunda ba'a rasa ba,ganin yadda mamin ta dauki zuwan abida da muhimmanci ya sanya maryam itama sake shirya kitchen
Ranar da zata iso din jirgin da yake sauka sha biyu na rana ne zai sauka da ita,tana jin mami na sanar da abdallah ya,haqura da fitar yau yaje a taro abidan da shi
''kai mami barta kawai,fita ta ta yau mai muhimmanci ce,driver yaje kawai ya daukota,ba dai tana gidan ba almost two to three months fa zatayi tare da mu''
qarfe sha daya maryam ta gama kintsa dining da kalolin abincin nijeria africa da kuma qasar da abidan ta baro wato turkiya,dakinta ta shige tayi wanka,don aikin bai barta tayi wankan ba,riga da zani ta zaba ta shirya cikinsu dukkansu normal dinki ne irin na riga da zani plain na asali,ba qaramin fidda sigarta yayi ba yanayin dakin akwai fidda shape din mu ba irin dinkin mu na yanzu ba mai tattara dake cika mace ya badda shape dinki,bata fito a dakin ba sai da ta jiyo surutu sama sama cikim parlour din mami qarfe daya saura kwata na rana
mutum uku ne cikin parlour din harda mami ta hudu,tashin farko zuciyarta ta bada abida cikin su ukun,sanye take da doguwar riga baqa mai azabar kyau da tsada irin mai robar nan dake bin jikin mutum,fara ce qal don har tafi maryam fari duk da dai akwai bambanci,farinta mai dau ne babu sirkin ja aciki ko kadan,zaka iya kiranta gajeriya don bata cika tsawo ba,tana da kyau kam ba laifi don kallon farko zaka kirata kyakkyawa,bata da qiba da yawa saidai jikinta acike yake babu lobawar rama
mami ce ta soma ganinta fitowarta
''yauwa maryam kin fito?''
''eh mami na fito baqin sun qaraso,sannunku da zuwa''
ta fada tana dubansu,daya ce kadai ta amsa sabanin biyun ciki harda abidar wadda ta dago kai ta dubeta,kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace
''nidai kam ba baqiwa bace ina tsammanin kece baquwar''
murmusho maryam din ta danyi
''eh to,kusan haka dinne''ta bata amsa tana kallon fuskarta wanda take bisa screen din tsadaddar wayarta
''maryam kuje da ita ki nuna mata dakinta''
''to mami''ta fadi tana yin gaba
''wa zai daukar miki trolly din?''abida ta ce tana hakimce a zaune tamkar ba ita za'a nunawa dakin ba
bata ce komai ba ta dawo,ta dubi akwatinan da kallo,qwaya biyu ne masu azabar kyau wanda ko ba'a fadi maka ba kasan cewa ba na talaka bane,ta daga dogon sandan dake jikin akwatin wanda zai bata damar janshi akan tayoyinshi ta kwantar da ita ta jata zuwa ciki
ta sake dawowa don daukar dayar,saura mami da abidar kawai yanzun cikin falon still abidan na hakimce,nuni ta mata da handbag dinta big mama tace
''shigarmin da wannan ma''
''barshi,maryam bari baba uwani tazo zata shigar miki da su,aikin maryam a gidan nan girki ne kawai''mami tace da abida,sai ta bar abinda take yi din ta dubi maryam sannan ta dubi mami
''ok,ai duka daya ne mami,dan aiki dan aiki ne da mai girki da mai shara duka 'yan aiki ne''
''to kam anan gidan akwai banbanci,kowa matsayinshi daban''
dan tabe baki tayi sannan ta saki murmushi kana ta canza topic din
''gaskiya mami abdallah bai kyauta min ba,yaushe rabona da nijeria ammayau kawai ya gaza kashe aikin gabansa yaje ya dauko ni''
''kinsan dai halin abdallah sarai tun ba yau ba,aikinshi na da muhimmanci matuqa a gunshi,ba dan qaramin abu bane zai sanya shi qin fita aiki ranakun ayyuka ba''
maryam dake tsaye tana jiran tasowar abida duk ta qosa,ta dan gyara tsaiwarta
''mu qarasa na nuna miki dakin''
''jeki kawai gidan ba baqona bane''
bata kuma tanka ta ba tayi komawarta daki,saida da ta dqidaici lokacin da ya kamata tayi serving nasu sannan ta fito,saita taddasu tuni sunyi nisa da fara cin abincin,son haka ta qarsa ficewa daga bangaren gaba daya,boys quaters ta zagaya inda anan gidan baba uwani yake
da fara'a ta tarbeta
''maraba da maryamu,sai yau Allah yayi za'a zo mana''murmushi tayi har fararen jerarrun haqwaranta suka bayyana
ta gaida baba uwanin da baquwar da ta taras tayi
hirarsu suka sha sosai don bata baro bangaren ba sai da akayi sallar isha'i sukaci tuwon dawar da baban ta girka,don dama tana kewarsa matsalar su mutanen cikin gidan basa cinsa shi yasa ma bata girkashi
ita daya ta taho iskar damuna na kadata,cikin parking space ta jiyo motsi,ta dan juya kadan hisham ne abokin abdallah,a tunaninta basu ganta ba don haka ta kau da kai tayi gaba
''haba 'yan mata irin wannan shan qamshi haka?,a qalla dai ai ko gaisawa kya tsaya muyi ko?,duk da cewa ma zuwan don ke nayi shi''inji hisham wanda ya sha gabanta,qirjnta ne ya shiga dukan uku uku,fatan ta kada Allah yasa ya furta mata kalmar so,don ita tsoro ma take bata,ta jita daga bakunan maza da yawa saidai babu abunda ta tsinana mata
a qagauce ta ce masa
''ina wuni''
''lafiya qalau maryam diya na ya gida ya aiki?''
kai ta dago ta kalleshi jin ya ambaceta da sunan da schoolmate da classmate dinta zuwa friends ke kiranta da shi
''lafiya qalau,ina son ganinki amma bari idan mun gama da abdallah zan kiraki,da fatan ba zaki qi zuwa ba''
''Allah ya bani iko''ta fada da gaggawa tana wucewa don ganin abdallah na isowa gurin
duk da haka bata kasa jin abunda yake fada ba kasancewar sun biyota ne a baya
''hisham,wlh hisham ka fita a ido na,kai me yasa baka jin shawara sai shegen taurin kai?''dariya ya qyalqyale da ita
''kai kuma mai yasa kake da girman kai da kafiya,Allah bai haramtamin harinya ba na gani inaso to kuwa ba zaka hanani ba''
''ok haka kace?''ya fadi cikin huci yana dubanshi
''yes,haka nace,idan kuma kai ke sonta ai sai ka fada sai in janye maka''
a zafafe ya soma fadin
''na rantse hisham zaka jawo mu samu sabani mai girma da kai,in rasa inda zanyi ajiyar soyayyata sai gun house girl kuku?,ina da dukiyar da zata iya bani duk kalar macen da nake so na aura,ko 'yar wane kuma ko awanne qasa take,wanda nake tare da shi ma yafi qarfin auran house girl,indai ko zaka ci gaba kan qudirinka ka tabbatar cewa yana daidai ne da datse igiyar abotarmu''yayi gaba cikin hanzari abunka da qaqqarfan mutum
ko cikin parlour din ma dambarwar da suka dinga yi kenan sai da mami ta shiga maganar
''hisham ka qyale rigimar abdallah,maruam ta cika macen da za'a so,tana da dukkan halaye managarta,uwa uba kyau,don haka babu hujjar da abdalla yake da ita da zai hanaka neman maryama,ni na goyi bayanka saidai idan ita tace bata so''
''toh...nima haka na gani mami,nace masa ya fada idan yana so ne shima sai....''
''dakata hisham,don ina nema maka hanya mai bullewa kake cimin fuska?,to kayi na farko kayi na qarshe,duk lokacin da ka sake cewa inasn waccar abar wallahi sai na fasa bakinka''
ba hisham ba hatta mami abun ya bata dariya,abdallah mai rikicin gangan inji hisham,a haka abida tq fito ta taddaau,wannan karon ma cikin shigar doguwar riga take mai sulbi saidai armless ce,a mutunce suka gaisa da hisham don sunsan juna,ta juya ga abdallah
''soulmate,me yasa kamin haka don Allah,na diro naija da daukin ganinka sai kuna kayi tafiyarka aiki sai yanzu zan ganka?''
''da kika ganni yanzun ma ki godewa Allah,a tsare gobe ne haduwarmu,haka ne?''da sauri hisham ya shiga maganar ganin abdallah nason qarawa kwabar ruwa
''shareshi don Allah,kanshi ne ke hayaqi tun dazun''
tuni abida ta rudevta dawo kukerar da abdallan ke kai tana tambayar wa ya taba mata ruhinta,tsam mami ta miqe ta basu guri,banza ya bawa ajiyarta don haka kawai yake jin ransa na zafi
''wlh abdallah nan naki rigimamme ne sai kinyi da gaske,haka kawai ya haqiqance wai bazan auri maryam ba?''
''wace maryam?''ta tambaya tana duban abdallah
''mai shirya masa abinci kullum yana dirkewa''
ido ta,zubawa abdallan,lokaci guda wani kishin maruam din ya dirar mata,take taji ta tsaneta
''amma soul mate mene hujjarka na hana hi....''
a fusace ya miqe
''ke dakata min,kinsan banson titsiye ko?''yaja tsaki ya juya zai fice a sashen
kuka abida ta saki,wannan wane irin jaraba ce,daga dirarta a qasar ko kwana batayo ba abdallah ya aona bata mata rai,lallai abunda kake so shike wahalar da kai
kukanta bai dameshi ba ya juya ya fice,da sauri hisham yace
''kiyi haquri bari,na sameahi ranshi ne a bace''cikin hanzari ya bi bayanshi
amma da yake gwanin sauri ne tuni ya miqe balcony yayi sashensa
bai damu da hade girar sama da ta qasa da ya sakeyi ba duk don kada ya masa qorafin abunda ya yiwa abida ya hau masa fada tare da cewa yaje ya lallasheta
''wa?,ni?Allah ya tsareni,bani da lokacin lallaahin mace wallahi,ruwanta ta ci gaba da sona ruwanta tace ta haqura,amma babu lokacin rarrashin mace a rayuwata indai ba mahaifiyata ba''
karab cikin kunnen maryamu dake kwance saman gadonta don sun iso saitin window dinta,miqewa tayi ta zauna saman gadon,wani irin haushi da tsanar abdallah suka kamata
wanne irin nau'in mitum ne shi?
taqama da gadararsa sunyi yawa,dukiya?ita ke rudarshi ko kyawun da yake da shi?,haushi da takaici suka kamata tamkar da ita suke maganar,haushinsa ta dinga ji sosai,da tana da iko sai ta masa dukan tsiya ko zata samu sauqin abunda take ji
haushinsu abida ya kuma kamata
don me suna mata da Allah ya yiwa baiwa da ado da kunya su dinga watsi da baiwar,so hauka ne?,ta godewa Allah da bai dora mata wannan masifar ba,gwara da Allah ya bar zuciyarta wankakkiya kuma kubutacciya daga dukkan soyayyar wani
kusan awanni biyu da shigewarsu mami ta turo qofar dakin ta shigo fuskarta qunshe da murmushi
''maryamu diyata,jeki harabar gida hisham abokin abdallah na son magana da ke,duk abinda ya tambayeki kada kiyo nauyin baki ki sanar masa da gaskiya kinji ko?''
ba zata iya musu da mamin ba tilas ta amsa da to sannan ta fito
yana jingine jikin motarshi ta isa gareshi,da fara'arsa yake fadin
''barka da isowa,tun dazun nake jira har ma na fidda rai?''
''uhmmmm''kadai ta iya cewa taja bakinta tayi shiru tana sauraren bayanan hisham,ya rufe da fadin
''ina son inji gaskiyar abunda yake ranki''
tayi shiru kamar ba zata ce komai ba,bata jin ko dis a ranta zata iya hada dangatar aure da duk wani abu da ya shafi abdalla, *MUTUNCI* shi take nemawa kanta, *DARAJARTA* itace mafi muhimmanci fiye da komai a gurinta,har sai da hisham ya sake maimaita tambayarshi
''ya hisham na gode da mutuntawa da karramawar da kamin har ka furta kana sona,saidai ina mai baka haquri tare da addu'ar Allah ya baka wadda ta fini komai da komai,amma bani da ra'ayin soyayya,kayi haquri idan hakan ya bata maka rai''
shiru yayi na wani dan lokaci da alamu baiji dadin,amsar da ya samu daga gareta ba
''babu komai maryam,ita dama harka ta soyayya babu batuntilas,na gode nima da yadda kika mutuntani,amma ina nan ina jira har zuwa lokacin da kika ji jin aminta da soyayya''
murmushin yaqe tayi,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarya,wani irin qunci take mata,kyautar dubu goma hisham din yayi mata,da ta doje tace bazata amsa ba yace shina kam yayi niyya bai fasawa,dolenta ta amsa ta masa godiya sanna ta juya don komawa ciki
tuni an kashe qwayayen waiting parlour babu haske sai wanda ke fitowa daga sashen mami da nene,tazo tsakiyar parlour din taji an fincikota baya,razana tayi matuqa,tuni idanunta suka fito wajevta bude bakinta da niyyar qwalla qara saidai bata samu damar hakan ba,sakamakon hadata da bango da kayi aka saka wani lallausan tafin hannu aka danne bakin nata,qamshin daddadan turare ya mamaye hancinta,qirjinta ya shiga dagawa da sauka numfashinta ya soma tsere,minti kusan daya sannan taga haske kadan ya bayyana atsakninsu ,haaken screen ne na waya,fuskarsa ta fara gani abdallah ne,sanye da t.shirt fara sol cotting mai gajeren hannu wadda ta fito da murdadden damtsensa,kauda da qwayar idanunta tayi ta daina kallon fuskarshi sakamakon yadda take babu alamun rahama ko kadan a cikinta
murya a kausashe kuma qasa qasa yake fadin
''kin taimaki kanki da baki amsa masa kina sonshi ba,wallahi koda wasa kika amsa kina son wani da ya jibanceni kin shiga uku,baki kai ajin da zaki shiga rayuwar abokan huldata ba,ki qara gaba zaki iya samun wanda ke muradinki acan wata rayuwar ba tamu ba,bana aon cusa kai cikin lamura na da katsa landan tun ba yau ba na gaya miki,ki kiyaye don samun zaman lafiyarki da ci gaba da aikinki cikin gidan nan''
kamar jira ake ya kammala maganarshi haske ya mamaye falon,jdanun zubaida suka sauka kansu yayin da nashi idanu suka sauka kan fuskarta da hawaye ya aoma gangarowa,wani abu ne ya riqe mata maqogaro wanda koda an bata damar maida masa martani ba zata iya ba alokacin,saboda baqincikin da ta hadiya ba kadan bane,tsanarsa da tsanar halayensa uka sake linkuwa cikin zuciyarta
''kai din banza,abokan mu'amalar taka ma din banza,baka isa maryama ta soka ba,saboda daraja mutunci da karamci take bida ba tarin dukiya ko kyau ba''abunda take ta son ta amayar masa kenan saidai abundaya tokare tan ya hanata fada
cikin zafi baqinciki da kishi zubaida ta iso gabansu
''abdallah''abunda ta iya ambata kenan cikin karyar da kai hawaye ya soma mata zirya,sam bai damu da ganinta agun ba,duba daya ya mata ya maida idobsa kan maruam ya cire hanunshi yana jan tsaki,ya ja mayafinta ya goge hawayen ta da ya soma taba masa hannu
''indai bakiji abunda na gaya miki ba yanzu kika fara kuka''ya kewayeta da,zafinsa ya fice asashen,ita dinma gyalenta ta ja kawai ta shige sashen nasu,abida ce kawaia falo da tayi zaman kallo tana kuma dakon dawowar abdallah don yace ta zauna ta jira shi batasan gatse ya mata ba lokacin baccinshi yayi,dakinta ta wuce ta danna qofar ta rufe kana ta saki kuka,me tayi masa?,ita tace tana son hisham ne ko kuwa,ahikeban talaka ba komai bane agun wasu masu kudin,talaka bai cika mugum ba,ko talaka baisan ciwon kanshi ba,taqamarshi ta isheta,tana jingidansu zata bar masa shi yafi mata sauqi,ga fargabar yanayin gidansu ga taqama da gadararshi da wanne zata ji?
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN*
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*_Daga abu hurairah yarda Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzan Allah s.a.w yace:yana daga cikin kyawun musuluncin mutum,ya bar abunda babu ruwansa_*
*_a wani hadisin kuma manzan Allah s.a.w yana cewa:jibrilu bai gushe ba yana min wasiyya da maqoci,har sai da nayi tsammanin/zaton maqoci zai iya gadon maqocinshi(saboda girman haqqin dake kan maqoci akan maqocinsa)_*
washegari a makare ta tashi saboda rashin baccin kirki,kitchen ta shiga ta shirya musu breakfast,adana kebabi,tavouk koftesi a abincin turkia sairuwan shayi chips da soyayyen qwai,cikin lkkaci qanqani gidan y game da qamshi,bata bar kit hen din ba baba uwani ta shigo
''af,makara kikayi ne yau maryamu''murmushi tayi tace ''wlh kuwa baba uwani''
gaisawa sukayi sannan ta bar mata kitchen din ta koma dakin
sha biyu na rana ta fito tayi sarving nasu mami ce da abida,cikin mamaki abida ke cin abincin tana tantamar yinsa akayi ko restaurant aka je aka siyo?,abincin yan turkey a nijeria,kusan ma har yafi nasun dadi sakamakon banancin spices da muke da shi
so take ta sanarwa mami qudirinta na barin gidan saidai ta gaza,nauyinta take ji sosai,alkhairan mamin a gurinta na da yawa,da haka har suka kammala cin abincin ba tare da ta ce mata komai ba
kafin ta bar gurin mamin le sanar da ita gyaran gida da canza kayayyakin da suke duk shekara idan ya rage saura kwanaki bakwai azumi
''akwai ma'aikatan dake,zuwa,suna aikin nan da jibi zaki gansu,abunda kawai nake so kimin alfarmarshi shine zaku shiga kasuwa kiyo soyayyar kitchen dukkan abunda ya kamata wanda za'a buqaceshi''
ta dan saki murmushi''diuarki ce ni mami kamar yadda kike fadi,ba alfarma bace umarni zaki bani kawai na bi''
''na gode diyata Allah yayi miki albarka''
wanna halaye na mamin na daya daga cikin abinda ke sata sake jinta cikin zuciyarta
koda ta kammala abincin dare,sashen ta sake bari,gurin baba uwani ta kuma wuni,kiran wayarta da mami tayi da daddare shi ya fiddota ziwa,sashen mamin,a hanya suka ci karo da zahariyya na shirin fita cikin motarta,wani kallo ta jefi maryam din da shi wanda ya tilasta maryam neman tsari da ita
cikin shirin fita ta samu mamin
''maryam yau kwanan asibiti zanyi bazan dawo ba sai gobe idan Allah ya kaimu,ga gidan nan na barshi hannunki''
''to mami''ta fada tana amsar jakar hannunta don yima mamin rakiya zuwa motarta
daidai lokacin abida ta fito sanye da riga da wando,kunnenta maqale da earpiece
''mami ina zuwa?''
''af,na mamce kina cikin gidan''
hara rar maryam abida tayi
''mamee kika manta da ni amma wannan ki kasa mantawa,da ita''bata lura da hararar da take ma maryam din ba tayi dariya
''to ai kece din sarkin kwanciya,klum kina kwance a gado kamar ruwa,zan tafi asibiti ne ina kuma tsammanin kwana zanyi''
''q'nnnn,si kin dawo''ta fadi tana kwanciya saman doguwar kujera yayin da suka fice ita da maryamu
mami na shirin shiga motar taga shigowar abdallah gidan,hakan ya sanya ta dakata har ya iso inda suke ta sanar mishi fitarta ta dora da
''am....abdallah,inason in ganka daman''
''to mami ai gani''
janye jikinta maryam tayi ta koma gefe don basu damar ganawa,daidai duk da hakan tana jiyo abunda mamin ke cewa
''har yanzu banga alamun jituwa tsakaninka da bida ba abdallah me yake faruwa?''
''mami ba komai kawai dai rawan kanta ne yake bani haushi,azarbabi rashin aji da kamun kai,kuma ma ban samu zama bane kinga soaai,kwana biyin cases sun mana yawa a office,bainciken wadanda suka saci kudin talakawa''
''duka naji,saidai inaso ka ajjiye dukka wani uzirinka,ka tabbata kun fahimci juna kai da ita,maganar halayenta kuwa kana da damar canza ta tunda tana sonka,ya kamata ace i yanzu ka ajjiye iyali,don nima ina da buqatar ganin qana nan yara suna gilmawa,ina fata ka fahimceni da kyau abdallah?''
''na fahimta mami,saidai koda jikokin sunzo ta yaya wadan nan patient,naki zasu barki ki sake da family dinki,suna qwace min ke kina kwanan office''ya qarashe maganar cikin sigar zolaya
murmushi tayi don ta san dama sai yayi qorafi,haka take fama da shi duk lokacin da zata kwanan asibiti
'?idan na biye maka abdallah sai ka makarar da ni''ta dan daga murya kadan ta kira maryama,cikin nutsatstsen takunta ta iso,gidan baya mamin ta shige sannab maryama ta miqa mata jakar tana cewa
''a dawo lafiya mami''
''Allah yasa maryama,a kula da gida''
''insha Alahu mami Allah ya bada sa'a''
mamin ta juya ga abdallah dake tsaye yana jinsu,hannayenshi harde saman qirjinshi,har ga Allah yaji dadin yadda ta nuna caring wa mahaifiyarshi
''abdallah sai na dawo,banda tsokane tsokane?''mami ta fada tana dariya
''mami sai kace yaron goye,zaki jawo a raina abdallahnki fa''ya fada yana shigeqa ahima gidan bayan
''a'ah,ya haka?''ta tambayeshi
''zanje na rakaki ne mami''
''yabzun fa kaima ka dawo daga aiki,na uafe ka shiga ciki ka huta,abida na parlour tana jiranka''
''idan ina tare da mami mancewa nake da duk wata mace,a naje asibitin naja masu kunne duk wansa ya barki kikayi aiki duka dare baki runtsa ba ni da shi ne,driver muje''haka drivan yaja sauran securitu dinshi suka dafa musu baya maryam ta dawo cikin gida tana jiniina yawan qaunar dake tsakanin mamin da abdallah
a inda ta bar abida anan ta taras da ita,bata tanka mata ba,tana gab da shiga dakinta taji tace
''ke zonan,''tayi kamar ba zata kula ta ba don ta tsani irin wannan kiran sai kuma taga baquwar mami ce ko ba komai taci darajarta
''wai me kika dafawa mutane?''kafin ta kai ga bata amsa kuma sai taji tace
''jeki kawai,sai abdallah soulmate ya iso kyazo kiyi serving namu''
ta gama shirin kwanciyarta tsaf ta tuna ta manta da littafin addu'o'inta cikin kitchen,hijabinta ta zura ta fito don ta dauko
abdallah ne cikin falon gefanshi abida ce zaune ta sanya ahi a gaba tamkar zasu hade,magana auke qasa,qasa,son bata iya jiyo me suke cewa,tayi kamar ta koma sai kuma ta fasa tayi ahigewarta kitchen,tana qoqarin komawa taji tace
''ke zokiyi serving mutane,kin shige daki kin zauna sai kace baki san aikinki ba''
bata tanka mata ba sai da suka isa teburin,a sanyaye cikin jerartun maganganunta masu cike da nutsuwa
''idan baki sani ba sunana maryam don Allah ba ke ba,aiki kuma ba naki aka umarceni da inyi ba,ba don ke nazo gidan nan ba,so please don Allah mu girmama juna,tunda dukkanin mu 'yan adam ne,halitta mai qima da daraja agun Allah''
''naqi na kirakin da hakan,kuma ni ba sa'arki bace kada ki kuma hada kanki da ni,ki dubeni ki dubeki mana,tundaga sutura ai kinsan da banbanci,kada ki kuma gigin hada kanki da ni''
shiru tayi mata domin ta fuskanci abidan tayi nisa,gwana ce itama gun girman kai,amma bata jin zata iya jurewa shararta ba sam,da iliminta itama da shekarunta,ba jahila bace bare tace zata dinga shiga gonarta tayi mata kashi ta qyaleta,ta kammala zuba musu tuwon semo miyar kubewa danya sai farfeaun kan rago a plate daban,a yatsine abida ke duban abincin
''meye kuma wannan?''tayi tambayar tana duban maryam,banza tayi mata tamkar bata jita ba,don,kanta da ta gaji da shirun tace
''ni wlh soulmate bazan ci wanna abun ba,na manta wanne lokaci ne na qarshe,da na cishi,kinga malama ki ahiga kitchen ki dafa min wani abun''
''awoyin shiga kitchen dina na yau sun qare,amma babu damuwa idan zaki iya jira zuwa gobe''
daga haka ta miqe tabar musu teburin,ahi kansa abdallah dan binta yayi da kallo ganin yadda yai take maida raddi babi kinkiri,fana iya jiyo ihun abida na zage,zage da hausa mixs da,harshen nasara wani lokaci harda turkanci
''oh god,pls don Allah ki yiwa maqogoronki afuwa,baki gajiya da fada?''abdallah ya fada bayan ya tallafe kumatunta ya sanya zazzafar qwayar idanunshi cikin tata,laqwas jikinta yayi,farinciki ya maye gurbin bacin ranta,tuni ta sanya hannu ta aoma kwasar tuwon sai gashi qarshe ta bige da santi
ta cusa kanta cikin pillow ta sake rubtse idanunta akaro na barkatai,har yanzun dai bata daina jiyo tashin hayaniyar ba daga dakin abida
muryar abida ce wani lokaci data abdallah,kuka take tun kusan rabin awa das,uka shuhe,sun hanat a bacci,ta kuma gaza fahimtar meke faruwa
''wallahi abdallah ko baka aureni ba indai ka kwanta da ni burina na duniya ya gama cika,don Allah abdallah ka amince wallahi zan iya rasa raina ayau idan ban samu cikar muradina ba,muna da dama abdallah muna da lokaci isashahe,mami bata nan daga ni sai kai kawi abdallah,pls ka taimaka min''
mamaki baqinciki da takaici suka sake cikashi,gumi ya kuma karyo masa,kimanin awanni biyu yana fama ta rabu da shi amma ta qiya,tun yana lalashinta yana qoqarin fahimtar da ita har ta soma bashi haushi,da ya miqe ta yago shi,har ta rabaahi davtshirt din jikinshi sai singlate kamar tsohuwar mayya,bayason gwada mata qarfi ne amma ya fuskanci sai ya biyo,mata ta hakan
cikin zafin nama ya miqe ta sake yunqurin kamoshi,tuni ya watsar da ita ya fice kana ya maida maqulli ya rufe dakin,dai dai da fitowar maryam kenan wadda tayi niyyar barin dakin nata ta canza makwanci sakamakon hayaniyar da ta hanata sakat tasu
a tsorace ta dubeshi idanunta cikin nashi,ganinshi a jargitse ga sautin kukan abida dake fitowa cikin dakin da ya kulleta,sai ta dan ja baya kadan zuciyarta ta soma harbawa,shi din ma ita yake kallo
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣7⃣


*_ubangiji madaukakin sarki yakanyi duba izuwa filin arfa,sai yace da mala'ika jibrilu,me bayin nan nawa suke nema haka(duk da cewa shine mafi sani),sun fito cikin tsananin zafin rana da qasqantar da kai?,sai mala'ika jibrilu yace''rahamarka da gafararka,sai ubangiji yace na gafarta musu''_*
*_haka ubangiji s.w.a yake rabon irin wanna garabasar a filin idi,annabi muhammad s.a.w yana cewa''kada ku hana bayin Allah mata zuwa masallaci''_*
*_sannan yayi umarni da a fita sallar idi maza da mata yara da tsofaffi_*
*_yake 'yar uwa,kada ki bari wanann garabasa ta wuceki wadda baki da tabbas din ganin wata kamarta,Allah yasa mu dace,ya yafe mana kurakuranmu,yasa mu cikin bayinsa da za'a gafatarwa Allahumma ameen_*


*_wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkanin al'ummar musulmi,Allah ya karbi ibadunmu_*



ci gaba yayi da lallonta kamar yadda take kallonshi,tuni oily eyes dinta suka qara sheqi da sakamakon tsoro da qwalla da ta tarar mata,zuciyarta na raya mata mummunan abu abdallah ya yiwa abida,cikin hanzadi ta juya da nufin komawa dakinta ta banke saidai taku daya biyu ana ukun ya cafkota ya maidota baya,take jikinta ya soma bari,bakinta na rawa ta soma fadin
''don.....d....don Allah kayi haquri,ka fufamin asiri''


galala yake binta da kallo,tuni ya gano manufarta,ganin taqi nutsuwa ya sanyashi daka mata tsawa
''me zayi dake da har kike tsammanin wani abu zan miki?,koyin ma zanyi kin min kadan 'yar tsakuwa,abinda nakeso dake kada ki kuskura wani yaji abinsa kika gani?,ina fatan kin fajimceni?''
kai kawai take gyadawa babu qaqqautawa,burinta kawai ya saketa ta samu ta tsere,yana sakin nata kuwa ta shige dakin jiki na rawa ta murza key


binta yayi da kallo cikin mamkin mummunar fassarar da tayi masa tashi guda,koda ya koma daki sai yaji abun ya tsaye masa a rai,ta tuhumeshi da laifin da bai taba sha'awar aikatawa ba,hasalima ya tsani mai aikata shi,gefe guda kuma tsanar abida ce fal cikin zuciyarshi,yaci alwashin koda zata rasa rayuwarta bazai iya aurenta ba,yana da tsananin kishi ya tabbatar koa ya aureta din bazaya samu kwanciyar hankali ba

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

kusan dukkaninsu kwanan zaune sukayi babu wanda ya runtsa,kowa da abunda ke yawo cikin rai da zuciyarshi,duk da hakan maryam bata kasa tashi yadda ta saba ba ta hada breakfast,saidai babu wanda yaci,bata san da hakan ba sai da mami ta dawo ta hau sama ta kintsa kana ta sake dawowa qasa don yin karin safe,abida qunar zuciya ta hanata fitowa,abdallah yayi sammakon zuwa ofgice saboda wani taron gaggawa da zasuyo wanda shi kansa bai san da shi ba sai da asubahin ranar his excellency mr presdent ya sanar mishi,saboda haka kiegin qarfe shida yabi zuwa abuja


maryama kuwa tsoro da fargabar haduwa da abdallan ne ya hanata fitowa bayan ta samu ta kammala aikin ba tare da sun hadu ba
''shi kam abdallah ai ya jima yanzun a abuja,jeki kiramin abidar dai ta karya,ya zatayita zama bata ci komai ba''
kamar tace da mami ba zata iya zuwa ba don tana fargabar halin da zata je ta taradda abidar,bata da amsar tambayar da mami zata yi mata game da abunda zata ga ya samu abidan


ba zata iya qin zuwan ba don haka ta miqe jiki a sanyaye ta nufi dakin,sai da tayi knocking sau biyar kafin a bada izinin shiga cikin qaqqarfa kuma kausa sashiyar muryar abidar
ga mamakinta sai ta tadda abidar ta fito daga wanka ras da ita,babu wasu alamu dake nuna wani mummunan abu ya faru da ita
''meye kika tsaya kikatsaya kika zuba min idanun kin nan masu zubi da na mage?''
sai a lokacin ta ankara da tsayawa tayi kallon abidar
''mami ke kiranki''tana jinta tana tambayarya ta dawo ne tayi mata banza ta wuce


da daren ranar ta sake shiga wani rudanin,a hanyarta ta dawowa daga sashen baba uwani zahariyya ta sha gabanta ,tace taje nene na kiranta


zaune take gaban nenen cikin falonta na can sama,daga ita sai nenen sai zahariyyar
''maryamu kike ko?,nasan zakiyi mamakin irin wannan kira na bazata,ba komai bane yasa na kira ki wata buqace da ni wadda nake neman taimakonki gurin cikarta,ina fata kuma zan samu hadin kanki gun cikar buri na''
''zan iya taimaka mikin indai bai kauce addini na na ba''
wata dariya nenen ta kece da ita
''idan banda quruciya irin taki ai yanzu kowa ma ba bin qa'idar addinin yake ba,biyan buqata kawai ake nema''nene ta sake qasa da murya kana ta kuma matsowa kusa da maryam
''ba wani abu nake nema agunki illa poising da nake buqata kawai ki diga a abincin abdullahi''
a firgice ta miqe har jiri na shirin kayar da ita lokacin da nenen ta gama zayyana mata buqatarta,bari kawai jikinta yake,addu'a duk wadda tazo bakinta yi take


halin da ta shiga kawai ya ishi nene amsa
''kinga zauna ki nutsu,sai kace wadda aka ce ta diga a abincin ubanta,aikin nan fa ba a kyauta zakimin ba,biyanki zanyi kudi masu yawa da nauyi,zan dauke miki dukkan wani quncin talauci da kike ciki,zan wadata ki zan yalwataki''


hawaye ne ya shiga bin kuncinta,girgiza kai kawai take cikin takaici
takaicin ha'intar managarciyar mace kamar mami
takaicin cin aman ada yaudara da sukewa mamin
takaicin son dasa baqincikin da qunci na har abada da mutanen keson dasawa a zuciyar mamin
wannan cin amana da me tayi kama?,haka mutanen duniya suke


''bazan iya ba,bazan iya cin amanar mami ba ko duniua da abunda yake cikinta zaki bani''abunda ta iya fada kenan ta juya a guje zata bar sashen
''ke,dakata''mamin ta tsaidata,har ta iso gabanta ta kasa motsawa,cikin huci take dubanta
''rashin karbar tayi na yarinya daidai yake da tangal tangal da rayuwarki,arziqi na binki tsiya ta hanaki ki ganewa,kije....ko babu ke sai na cika burina,hanyoyin nada yawa,amma ki tabbata rayuwarki na cikin hadari,kuma wallahil azeem kika bari maganar nan ta fita sai na batar dake''


a sukwane ta bar sashen,da qyar ta kai kanta dakinta cikin mawuyacin hali,fadar irin halin data tsinci kanta bata baki ne
tabbas ta kuma gasgata cewa nene na iya aiwatar da duk abinda ta fada din,ta gani,cikin qwayar idonta
mafita daya take hangowa a gareta shine ta nemi miji tayi aure,ba zata iya kallon qwayar idanun mami ba tace tabar aiki,wata fuskar tafi gaban mari,aure shine zai rabasu salin alin




*_dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki_*

*_ina taya daukacin al'ummar annabi murnar zagayowar babbar sallah da fatan za'a gudanar da bukukuwan sallah lafiya_*

*_insha Allahu daga yau zamu je hutun sallah,littafin abadan zaici gaba da izinin Allah bayan qare hidindimun sallah_*

*_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_*




*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:53 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣8⃣


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*💡


*_wannan page din naku ne,wato mata iyayen gida,ku huce gajiyar sallah,Allah ya qara mana himma da lafiya,ya bamu ladan kula da iyali_*





material ne a jikinta mai baqi da fari,skert din baqine sol babu digon komai,rigar kuma fara ce mai adon baqaqen fulawoyi,irin dinkin nan ne da muke kira three quater iya gwiwa,skert din simple ne mai tsaga a baya,baqin mayafi ne tayi rolling da shi sai farin plate shoes mai igiya data sanya


a kasalance take nunawa ma'aikatan irin kayan da suke so su kuma suna cirowa suna sanyawa cikin keken tura kayan,qarfin hali kawai take,batason nunawa mami wani abun na damunta,duk da tana jin kamar zazzabi na shirin kamata


sannu a hankali suka qurewa bangarwn electronics dake cikin makeken shagon zamanin nan na shoprite dake ado bayero mall,suka juya bangaren warmers da plates cups da sauransu,daya bayan daya take bi tana zaban sababbin design 


''subhanallah''suka fadi a kusan tare suka kuma ja da baya,tuni cups din da ta dauko sukayi nasu guri a qasa sakamakon karon da sukayi,a tare suka duqa suka soma kwashewa


''kiyi haquri madam don Allah ban kula bane''ya fada yana miqa mata guda ukun da yayi nasarar kwashewa,sai a lokacin ta dubeshi,baqi ne ba can ba zaka iya kiranshi da chaculet,dogo ne maras qiba,ya mata kama sosai da mutanen qasar habasha ko kuma baqaqen fulani
''ba komai'' ta fada tana amsar kofunan,kana ta rabeshi ta wuce


''ko am min izini na taya madam din zabar kayan duk da ba bangare na bane?''taji an fada daga bayanta,da sauri ta waigo mutumin dazun ne,tamkar tace a'a sai kuma taga babu buqatar ta fadi hakan
''bismillah''tace da shi
cikin hikima da dabara yake bayyana mata ko shi waye



''ni sunana abdur rahim tasi'u alhasan,ina zaune a unguwar qoqi dake tsakiyan birnin,ni dan kasuwa ne kamar yadda mahaifina yake,ina fata kin gamsu da dan taqaitaccen bayanin da na miki''ya qarashe magana lokacin da yake tura kwandon yana kuma kallon fuskarta
dan qaramin murmushi ne ya subuce mata
''to ni kuma meye nawa da sanin kai waye,daga taya ni siyayya?''


murmushin shima yayi bayan ya tsaida basket din
''ke kuwa kike da ruwa,saboda ina sa ran zamowarki uwar gida na,bazan boye miki ba tunda na ganki naji kin kwanta min,da gaske nake sonki *maryam*aurenki kuma nake so inyi anan kusa''
a mamakance take kallonshi,to ko addu'ar da ta kwana yi jiya ne Allah ya amshi roqonta?,babu shakka Alkah maji roqon bayinshi a kurkusa ko a nesa
''yaya akayi kasan sunana,bayan a iya sanina ban gaya maka ba baka kuma ji wani ya ambata ba?''
murmushi ya sakeyi
''maso dan tsuntsu shike binsq da jifa,sonki nake bada wasa ba hakan yasa nasan komai game dake kafin na iso gareki''


cikin wani mamakin ta kuma dubanshi
''kana nufin ba yau ka fara sani na ba?''
ya dage girarsa sama
''eh,kusan haka dinne''cike da mamakin shigowar abdur rahim cikin rayuwarta lokaci guda suka kammala dukkan siyayyrsu ita da abokan tafiyar tata,har lokacin abdur rahim din na biye da su hqr suka kammala,a bakin motarsu ya dubeta
''yaushe zanzo mu tattuna a nutse''ya tambayeta yana murmushi,dan jim tayi tana tunani a lokacin taji wayarta na ringin,da sauri ta cirota,ta duba,atsammaninta hindatu ce don tace zasuyi waya sai kuma taga baquwar number
''ga number dina nan kiyi serving zan kiraki naji lokacin da zanzo din''


da mamakin karona uku ta sake dubanshi,mamakin ina ya samu num dinta,kamar yasan me take tunani yace
''nasan mamkin inda na sami number dinki nake ko,kada ki manta na gaya miki dazu,na shigo sonki ne bada wasa ba hakan ya sanyani sanin komai game da ke tun kafin na iso gareki''murmushi ta sakar masa,sai taji abdur rahim din ya burgeta karo na farko,wannan wane irin so ne haka?


ko cikin motarma tunani abdur rahim din ta fada,tana gaya wa kanta ta samu mijin aure tabbas,tana kuma qarfafawa kanta gwiwar wannan karon zata shiga dakin aure kamar kowacce mace


bayan mami ta gama ganin kayan ta yaba sosai,don tace basu taba siyan kaya new fashioned and durable haka ba kamar wannan shekarar,kai tsaye dakinta ta wuce don tayi sallar la'asar su fara rage koda gyaran kitchen ne tunda taga da time,biyu daga cikin daki hudun dake rufe ta sake gani a bude,bata ce komai ba don ga tsammaninta baqi mamin ta sakeyi



da taimakon ma'aikatan harda baaba uwani cikin qanqanin lokaci suka fidda tsoffin kayan kitchen din suka fara shirya sababbi,aiki na yiwa maryam dadi sakamakon yadda yake tqfiya cikin tsari,sunayi kuna suna hiransu abinsu,kada ma baaba uwani taji labari,akwai abun dariya
''lamarinku na yaran zamani na bani mamaki''baba uwani ke fadawa maryam qasa qasa 
''me mukayi baaba uwani?''maryam ta tambayeta tana fiddo da wani foodflask daga cikin kwalinshi
''mata su dinga biyo maza gida suna neman aurensu?''
''kamar yaya baaba?''
''hmmm,yaran nan mana dake son yaron gurin hajiya abdullahi,dazu daya yarinyar nan itama tazo da kayanta na satittika,ummm.......salamatu,mu a da ba sai an kaiki daki ba ma kike sanin waye mijin?,idan ma kuwa har kinsan waye shi din kafin a daura aurenku to ko hanyar da yabi baki iya bi saboda kunya,idan kuwa tsautsayi ysda kuka hada hanya to sai kinkusa qamewa a tsaye vaki iya motsi har sai ya wuce''


dariya ce ta kubcewa maryam
''baaba kin iya bata suna,salma ake cewa ba salamatu ba''
''kome me take ne barta,abun nasu sai addu'a,ko kunyar hajiya basa ji,ko fada ne ya kama yi suke a gabanta,abunda mu ko abinci baka iya ci gaban suruka,wannan zamani wannan zamani yazo qarshe,fatan Allah yasa mu gama lafiya''
''ameen''maryam din ta amsa mata da shi,daga haka bata ce komai ba,ita kanta mamaki take,saidai babu ruwanta don bata shiga shirgin da ba nata ba


ana kiran sallar magariba suka kammala aikin duk girman kitchen din yayi kyau ya sake haske,lallai sabon abu akwai kyau inji baaba uwani,ita kanta mamin ba qaramin mamaki tayi ba,ta sallami sauran ma'aikatan tana yabawa qoqarinsu


dakinta ta kuma komawa sanda tafito daga kitchen din abida ce zaune gaban makekiyar t.v plasma tana kallo sanye da matsattsun riga da wando,kusan duka shigarta kenan ta fidda tiraici ko doguwar riga zata sanya sai ta samu mai tighting jiki,wanka tayi ta sauya kayan jikinta,ta daura alwala tayi sallah,tana saman dadsuma tana lazumi ta tuna zata kira fa hindatu,ta laluba wayar bata jita ba hakan ya bata tabbacin ta manto ta a kitchen,ta gyara zaman ijabin jikinta ta fice ta nufi kitchen


su uku ta tadda yanzu a falon abida salma da abdallah da suka saka atsakiya,kallo daya zaka musu ka tabbatar daga abidan har salman ba jin dadin zaman suke ba,shi kuwa hakimin na tsakiya zaune yana ta aikin amsa waya,bisa dukan alamu wani aiki yake shiryawa don taji bada order din yayi yawa cikin fada da fushi


ilai kuwa cikin sabuwan kitchen wear din ta ganta,missed call goma ta taras,hudu na hindatu hudu na abdur rahim daya na raliya,murmushi tayi don dama ta sani bata da masu kiran nata sai su,sai ta rasa wanda zata soma kira a cikinsun,cikin haka kiran mami ya shigo
''kina ina ne maryamu,na shiga dakinki ban tadda ki ba''
''mami ina kitchen''
''baki gajiya ne maryam aiki sai kace inji,already baaba uwani tayi abinci ki huta haka nan don Allah''
tana jin dadin qaunar da mami ke nuna mata qwarai da gaske
''wayata na manta ma nazo in dauka''
''ok,ki sameni a parlour na''
''to''ta amsa mata ta cire wayar daga kunnenta ta fita daga kitchin din


''ke mero''taji an fada lokacin da take qoqarin hawa matattakalar benan
kamar kada ta juyo sai kuma ta waiwayo din don ganin mai mata kiran,abida ce
''meye kika tsatstsareni da idanuwankin nan kamar na?,shawarma nake sonci,ki shiga kitchen yanzun kimin idan kin iya''
rausayar da kai maryam tayi
''batun iyawa na dade da wuce babinshi,saidai lokacin aiki ya qare,zaki iya barwa gobw idan Allah ya kaimu,tunda majority utensils din duka sabbi ne bamu bude su ba''


cikin izza isa da gadara tace
''ke,wai mai kike taqama da shi ne,ki fadi nawa ne albashinki duka a nunka miki bama iya kudin aikin yau ba,ban mance ba rannan haka kika mana wani abu tuwo sunanshi ko me?nace kimin wani kalar girkin kika ban banzan answear irin wannan,kinsan wace ni kuwa?''


sakin makarin silver din da maryam din ta riqe tayi ta juyo ga abidan sosai
''ni ba kowa bace kuma bana taqama da kowa face Allah,kudi kuma ba zaki bani yanke talauci ba har abada,matsayin da Allah ya ajjiyeni ya gamsar da ni sosai na kuma gode masa,gaskiyata na fada tsarin siki na kenan cikin gidan nan,baquwa ce ke ina zato shi yssa kike mantawa,sannan ke din ma ba kowa bace face baiwar ubangiji kamar yadda nike kowa kuma yake''


a hankali abdallah ya dago kanshi daga kallon wrestling a tashar mbc action da yake ya dubeta,sai yaji amsarta ta burgeshi,babu hayaniya cikin raddinta,cikin calmnesses and cool voice,sai ya dan tsaida abunda yake yaga yadda za'a qare
tuni fuskar abida ta canza,cikin bacin rai ta dubi abdallah
''mu sugar kana gani da jin abunda yarinyar nan ke gaya min ko''ta fadatana nuna maryam wadda tuni har ta kusa kaiwa qarshen benan


murmushi ya saki mai hade da yar dariya
''duk bakery din dake garin kano kin raina,kin rasa inda zaki ci shawarma ne?''
''zaka iya kaini ne?'
''a lissafin lukuta na babu wannan,idan kina so akwai direbobi sai wani daga ciki ya kaiki ya dauko''sai ta sake tunzura,ya yrfata gaban salma kenan?,abunda madyam din ta mata ya hadu da wanda abdallah ya mata ya zamar mata zafi biyu
a zafafe ta miqe tana cewa
''tunda kai bazaka iya daukan matakin komai ba to ni zan daukarwa kaina,bazan zauna talaka 'yar talaka wulaqantacciya ta dinga taba mutuncina ba''


wani murmushin ya kuma saki ya kima kashingida
''eh kuma fa,gaskiyarki nima na goyi bayanki,kamarki diyar ambassador guda bai kamata a dinga samun iein haka ba,jeki dauki mataki''
sai ya kuma tunzurata don ta fuskanci kamar gatse yake mata ko kuma jirwaye mai kamar wanka,a haukace ta haye saman


kujera ta samu ta zauna tana fadin
''gani mami''
''yauwa maryam....cewa nayi''maganar mamin ta katse sakamon kiran da ya shigo wayar maryam din,screen din ta duba,sunan abdur rahim ya bayyana,sai ta maidata silent taqi dagawa
''ki daga mana maryamu''inji mami
murmushi tayi ta dan sadda kanta
''um um mami,ina jinki''
cikin murmushin da salon zolaya tace
''kodai suruki na ne maryam?''


sai kunya duk ta kamata tayi qasa da kanta tana murmushi
,ganin tayi shiru yasa mami cewa
''Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,shawarata gareki ki riqe mutuncinki,ka kame kanki,mutuncin mace kunya da kamun kai,duk da nasan duka halayenki ne,idan na samu lokaci zan miki magana yazo inganshi mu gaisa''cikin jin dadi da gamsuwa da maganganun mamin take gyada kai,sai ta kuma tsokanarta
''bari nayi sauri na sallameki kada surukin nawa ya qosa da jirankin ko''sai ta sake bawa maryam din kunya


''kaya ne wadanda aka fitar da kayan firniture da za'a fitar gobe nake son ki zazzabi dukka abunda kike so ki kaiwa mamnki ko zatayi amfani da wasu wadanda bata so ta bada''
tayi mamakin yadda mamin ta bada kayqn,don kaya ne da babu abunda aukayi tamkar yau aka zuba su espicially kayan furniture din,ta wani fannin kuma ba abun mamaki bane saboda halayen mamin ne *karamci* da *kyauta*
sabanin wasu masu hannu da shunin da sun gwammace su saida kayan maimakon 'yan uwanau su amfana furniture ne ko kayan sawa,ko me zasuyi da kudin oho,bayan Allah ya wadata su ya basu arziqin amma suna maida kansu baya


''na gode mami qwarai,Allah ya qara girma''
murmushi mamin tayi
''bakin maryamu ya saba da godiya,nasha fadi miki ba haka tsakani na da ke''
kafin tace wani abu an banko qofar an shigo,abida ce kanta tsaye ta tafi gurin mami
''mami,ki shiga tsakanina da house girl din nan,hala bata san koni wace ba,ta raina ni matuqa,wallahi idan bata kama kanta ba zanyi sanadiyyar qulle danginta kaf babu wanda ya isa ya fito da su,batasan ba'a raina ni ba,bana daukar raini?''
kama kai mami tayi tana kallon abida
''qara kika kawomin ko mataki kika zo dauka?''cikin rashin iya magana tace
''duka mami''
ta riga da tasan abida rainon tabara ce,ta san ita har zuciyarta magana ta fada mai kyau,ta bar ta tata ta juya ga maryam ta tambayeta mai ya faru,a nutse ta gaya mata
''tashi kije maryam,sai da safe Allah ya bamu alkahairi''
''ameen mami''ta fada tana ficewa,yunqurowa abida tayi gurin maryam mami ta dakatar da ita


mamaki ne ya ishi maryam,tana shiga daki kiran abdur rahim ya shigo wayarta,murmushi ta saki ta isa gefan gadonta ta zauna sannan ta daga





*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:53 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶2⃣9⃣


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*💡
*_home of expert and perfect writers_*







Kimanin awanni biyu suka shafe kan layi ita da abdur rahim din,ta fuskanci ya dan san wasu abubuwa game da ita wanda hakan ke qara mata amanna da qaunar da yake iqirarin yana mata din,tuni ta yanke ma ranta abdur rahim na daya daga cikin batutuwan da zasu tattauna a gobe ita da mamanta,bai barta ba har sai da ya fuskanci ta soma jin bacci tukunna ya mata sallama cike da qauna da bege mai yawa

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Abu na farko da ta fara cin karo da ahi cikin gidan nasu bayan yin sallamarta shine dambe tsakanin huwaila da haduza abinda zata iya cewa bata taba gani ba,daga gefan huwaila lubabatu ce da binta ke zuga uwarsu,yayin da kuna gefan hadizar kuma shamsiyya da yasira ne suma ke nasu aikin sai jamila dake zaune bisa dakalin qofar dakin mahaifiyar tata da uban akwati a gaba,idanu jajir wanda ke nuna bisa dukkan alamu kuka take sharba ko kuma take kan sharba din,mamanta ta hango na shirin fitowa daga dakinta hannunta ruqe da dankwalinta tana mai qoqarin daurawa hindatu na biye da ita tana fadin
''don Allah mama ki barsu''


Da sauri maryam ta taya hindatu tarar maman nata
''mama wanna ba sabgarki bace,kin taba ganin suna dambe?,to ki qyalesun kamar yadda hindatu tace Allah ne yasan me ya hadosu,babu ruwanki mamana tunda koma mene lokacin da zasu qulla basu nemi shawararki ba,kiyi addu'a kawai Allah ya warware musu ita ta ruwan sanyi''


da dadin baki suka sanyata a tsakiya suka koma cikin dakin abinsu,har aka gama shigowa da kayan suna bala'i basu sani ba
''amma maryama gini irin wannan namun ai bai cancanci kayan gado na alfarma irin wannan ba''
dariya ma maman ta baiwa maryam
''haba mama,tunda Allah ya baki sun cancanta din kenan,yanzu aikin kawai zamu shiga yi har kitchen din''
hindatu dake tsaye wadda farinciki duka yabi ya cikata tace
''yauwa adda maryam,kinga zuwa gobe mun gama zama 'yan gayu,babu raini wallahi,don duk cikin gidannan babu mai arziqin siyan irin wadan nsn kayan''
dadiya duka ta basu don har yau hindatu shirmen auta bai saketa ba


sai da suka soma fidda na dakin maman suna shigar da wadancan sannan suka ankara,lubabatu ce ta fara gani ta zunguri uwarta dake riqe da habar zaninta daketa kwancewa saboda azabar bala'i tana qoqarin daurawa


''huwaila tayani gani,kinga su kuma wadan nan ina suka samo kayan alfarma haka''
da sauri ta juyo don ganin abunda lubabatun ke nuna mata,idanunta suka sauka kan kayan fadon da buhun shinkafa catoon na taliya mscaroni da couse couse wabda mami ta hada mata da su irin kayan da Abdallah ke rabo na musamman duk azumi sadaka ga mahaifinsa mafigayi alh abdul kareem mai nasara


''kinga inda ake abu,kare ya san ana abu a gidansu,tunda gashi yana gani a qasa''
wannna zancan ne ya dauko hankalin hadiza kan kayan
''mtswew,aikin banza aikin wofi,kayam haram din da aka samu ta hanyar haram har wani abun fariya da alfahari ne?,kwadayi dai ai mabudin wahala ne Allah na tuba nawa akayi''
''kamar ku kenan da ruwan ya qarewa dan kada ko?'' wani irin ashar hadiza ta lailayo ta narkawa huwaila
''ai wallahi qaryarki tasha qarya,tuni na gama fahimtarki dama huwaila,sai kima kinsan cewa ba'a ja da masu kudi''
tsaki ta ja kana ta turo daurin dankwalinta gaba
''yo Allah na tuba ina abun yake,ina qudan yake ballantana romonsa?,game ce anyita kuma yau anzo game over din,sai kusa haquri masu rano su dara daga inda kuka tsaya'ta antaya qeyar yaranta daki ta bar hadiza abakin qofar tana ci gaba da zage zage kamar zata tada jinnu,ta gama da huwaila ta kalli qofar dakin mama ta yi nata,ita kadai ita da yaran nata tamkar wasu sababbun tabi


hindatu kam babu abunda take sai sheqa dariya cikin dakin suna aikinsu maryam ta dan dubeta kana ta kau da kai ta ci gaba da ahimfida zanin gadon dake hannunta kan sabon gadon maman
''ko kema shirin bin sahun nasu kike irin wannan dariya haka''dariyar na ci gaba da cinta tace
''ai wallahi adda maryam ki gode Allah,kinsan wannan bala'in tun jiya ake zuba shi cikin gidan nan''
''amma ina baaba,bai tsawatar ba?''
''ya tafi gaya duba inna gwaggon baba,kuma ko yana nan ma ma zai tsawatar din akai?,mowarshi aka taba fa,jamila ce ta dawo gida jiya wujiga wujiga''


sai da gaban maryam ya fadi,a hanzarce cikin fuskar mamaki ta kalli hindatu
''garin yaya?''
''to yaya jabir yace baya yi ta taho gida har dactakardar sakinta kyawawa guda uku,a kuma karbe duka wani abu na dukiya ko kadara da ya mallaka mata,amma in fada miki baaba hadiza da yake jahila ce ba ilimi a take suka hau dan sahu ta maidata wai zata bashi haquri a daidaita,wallahi in taqaice miki ko zama bata yi ba bayan dawowarta sai ga jamilar ta biyo sahunta,da duka ya koro ta daga cikin gidan da qyar ta qwaci kanta,to kuma bala'i sai ya koma kan inna huwaila wai itace sila tunda dama ta taba cin alwashin sai ta wargaza komai''
hindatu ta sake qasa qasa da muryarta kada mama ta jiyota
''in taqaice miki adda maryam jiya dai har gun bokan da sukaje ya raba tsakaninsku da ya jabir sai da suka tona abinsu,cikin hargagin fadansu''


sai jikin maryam yayi sanyi,ta bar abinda take yin din tayi zaune gefan gadon,tabbas tasan ba'a yi mata adalci ba,saidai rabuwar aure ai ba dadi gareta ba,espicially yaran gidansu da dukkaninsu babu wani mai qwarin gwiwa kan aurenshi kullum cikin jeka ka dawo suke,to ga wata kuma sabuwata samu
''kinga ya maryam,kada kice fa zqki wani damu,sakayya ce Allah ya miki ita da gaggawa haka''ta fadi ita tana ci gaba da dame gadon aikin da maryam din ta saki


''a'ah,maryamu kin gaji ne,idan ba dama sai na aika hindatu ta kiramin laure ta tayamu''
girgiza kanta tayi alamun a'a
''mama haka abu ya faru da jamila kuma dai?''
''uwar asugwi din ta fesa miki din kenan ko''maman ta fada tana qarasowa cikin dakin,ta kama kunnen hindatu ta dan murde har sai da ta saki aiririyar qara tana dafe hannun maman
''don Allah mama kunne na,zaki tsinke kunnen autar taki fa ki rage mata kudin sadaki''
''ai gwara in tsinke kunnen tunda ya iya jiyo gulma ya fadawa addarshi''
da qyar hindatu ta zame a hannun maman


jikinta babu qwari haka suka dinga aikin,har ga Allah bata ji dadin mutuwar auren ba,tunda yau babu wanda,zaiso ace nashi ne kullum a bazawara,sai magariba uka kammala aikin komai yayi neat da shi,ta cire kaya jikinta ta daura zani da hijabi tq fito bandakin tsakar gidansu tayi wanka,tsakar gidan shuru da shi qwal kowa yana daka da mugun abinshi a zuciya,girgiza kai kawai tayi cikin zuciyarta tana fadin Allah ya gyara,sam rayuwar gidan nasu a karkace take kowa da inda ya dasa tasa alqiblar


tana cikin sallar isha'i kiran abdur rahim ya dinga shigowa wayarta,hindatu ce zqune kan kujerar dq wayar ke kai don haka ta daga,bata ankare ba taji sun shiga hira da hindatu,dama gata gwanar surutu,sai da ta idar sannan ta miqa mata wayar,kasa dagawa tqyi saboda kunyar ama dake gurin,itama maman na ankare da ita amma tayi kamar batq gani ba,dn tasan maryq din ba boye mata zata yi ba,cikin zuciyarta take addu'ar Allah yasa mijin aure ne diyartata ta samu


su ukun cikin kwano daya kamar ko yaushe suka ci tuwonsu na masara miyar busashshiyar kubewa,santi kawai maryam ke ti wa mama don tayi missing girkin maman sosai,mama gwana ce ba baya bace gun tsara girki musamman namu na gargajiya


zumudi yasa hindatu ta kasa shiru jin addar tata taqi tada zancan mutumin da ya kira din dazun
''wai adda maryam abdur rahim din dazun fa yace saurqyinki ne,kuma naji shiru baki ce komai ba''
hara rarta tayi
''wannan baki naki hindatu kamar ba'a gasa miki shi ba?''
dariya suka sa su dukka ukun,tilas yanzun ta yiwa mama maganarshin tunda tun ajiyan yake jadda da mata aure yake son yayi bada wasa ya zo ba,a kunyace ta yiwa maman bayani,farinciki fal zuciyar maman
''Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,ya kade dukkan sharri da fitintinu,addu'a ce yanzu kawai abunyi gareki maryam''
''insha Allahu mama,sai a tayamu muma da ddu'ar''ta fada cikin karyewar murya wanda ke nuna raunin zuciyarta,tausayinta ya kama maman


''addu'a ta zama dole akan musulmi,ballantana uwa ga 'ya'yanta,wacce garkuwa kike da ita da zaki basu wadda ta zarce addu'ar,uwar ma irina mai yara mata da take musu fatan samu mazaje na gari nagartattu,babu sallar da zan idar da ita maryama ban muku addu'a ba,ku kadai nake da su fa''
wata iriyar qauna hade da tausayin mahaifiyar tasu suka lullubeta,haqiqa uwa ba wasa bace,wata ni'ima ce daga ubangiji,cikin zuciyarta take fata insha Allahu wannan karon zuciyar mqhqifiyar tasu zata wanke daga dukan wani quncin rashin auren nata,hawayen da suka tqru suka fara sauka a idanunt cikin dabara take sharewa don kada maman ta gqni hankalinta ya tashi


kiran abdur rahim ne ya sake shigowa,wannan karon ba tare da jinkiri ba ta daga don so take ta kaucewa idon amman kada tqyo tozali da hawayen da takeyi
''ranki ya dade lafiya kike kuwa?''ya tambaya a sanyaye
''lafiya nake me kaji?''
''muryarki ce naji tamin kama da ta masu kuka'' 
duk da yanayi da take ciki sai da murmuahi ya subuce mata
''idan banda abun abdul har yaushe kasan muryata da zaka tantance kuka nake yi?''
murmushi ya saki har tana iya jiyo sautinshi
''na dade da sanin muyarki maryam,ke dince baki sani ba,kina gidanku ko?''ya qarashe maganar da tambaya,cikin mamaki da sigar tambaya itama ta maida masa amsa
''wa ya gaya maka?''maryam,kina shakka cikin son da nake miki ko.....any way....naje gidanku ance min baki nan kina gun mamanki''


a wani mamakin ya kuma sakata,son iya saninta babu mai shigowa gidan su mamin ta sauqi
''ya akayi kasan gidan da nake zama taya kuma ka iya shiga da sauqi irin haka?''
''maryam,duka abdul ba mai daukar abunda yake so da sauqi bane,yana bashi muhimmanci ne afili da boye,ina fata kin fahimceni?''
''jinjina ga irin wanna son da abdul yake min''
''jinjina ga zuciyar data sadaukar min da kanta''sai duka suka yi murmushi


''ina fata zuwa yanzu mutanen gida sun san da zama na?''
''tun yanzu abdul,duka duka jiya fa muka hadu''
''ke kika hadu da ni jiya,nikam ba tun jiya ba kika zama wani bangare daga jikin zuciya ta,so inason asan da ni maryam,aure nake so nayi da,wuri idan da ina da iko ma cikin watan nan banqi ki zama tawa ba''
tilas abdur rahim ya bawa maryam dariya
''gaskiya na baka sarkin zumudi na duk duniya''
''na amsa tunda sonki ne ya ja min''


cikin qanqanin lokaci ya cika zuciyarya da farinciki ta mance duka abinda take ciki,ba dadewa da gama wayar tasu bacci yayi awon gaba da ita don tuni mami ta yarje mata tayi kwananta a gida washegari taa dawo

🎄🌲🎄🌲🎄

qarfe tara na safe ta gama shirinta tas,a falo ta taradda hindatu na shirya musu abun kari kan center table daya daga cikin abunda jiya ya zama mallakinsu
cikin girmamawa hindatun ta gaidata ta amsa mata tana tambayarta mama
''mama na gurin baaba''
''ya dawo ne?''
''eh ya dawo dazu da sassafe,kin sanshi da tafiyar asubanci,yauwa tace idan kin tashi ki shiga ku gaisa''
''yanzu kuwa''ta fada tana ciro wayarta dake tsuwwar shigowar saqo tana dubawa
saqon barka da asuba ne aga abdur rahim,zaqaqan kalmomi da suka sanyata mirmushi ita daya tamkar wata zautacciya,tana mamakin yadda zuciyarta ta nutsu wa abdur rahim lokaci guda,sai da ta kammala karantawa ta masa reply sannan ta koma bedroom ta ciro dubu goma cikin kudin da mami ta bita kyautasu jiya dubu goma sha biyar


mamanta inna haule baaba hadiza sai lubabatu jamila da shamsiyya su ta tarar cikin dakin,kallo banza uka suka bita da shi,gefan binta ta matsa zata zauna,cikin rashin mutunci bintan ta janye jikinta tana wani harare harare da kumbure kumbure
gaida su ,bata da isar da zasu amsa mata har gara inna haule ta ama din sama sama,cikin girmamawa ta gaida baaban nata,ba laifi a sake ya amsa mata har yana tambayarta gun aikin nata,shiru ne ya biyo baya na wasu mintina sanan baaban ya dubi jamila
''inatambayarki tun dazu kun min shiru,yaro yace shi baisan lokacin da ya aureki ba,to inason in san ta yaya akayi ya aurekin,tunda shi ya rantse ya mayq bai san ke matarsa bace kuma bazai dawo dake ba''
cikin fitsara da rashin tarbiyya ta zumburo baki
''toni baba....ka tamvayi hadiza mana''
ya juya ga inna hadizan
''to kimin bayani tunda tace a tambayeki''
cikin borin kunya da haqiqancewa tace
''haba malam,wannan wane irin abu ne,ya zaka zo kasuwa ka dinga kwance min zani,sai da ka tara min idon duniya ni da diyata zaka hau bin qwaqwafinmu''


''ke hadiza dubanni nan da kyau,na gaji da iskanci da rashin mutuncin yaran nan,jiya tunda naje qauye fita ta daya na gaza fita,zance na ake ko ina,ance na kasa kula da yaya matan da Allah ya bani,dukkansu babu mai zaman aure ko wacce rabi aure rabi zaman gida,ga wasu kuma sun kasa auruwa''
zuciyar mafuam ta kada don tasan maganar qarshen tata ce
''to wallahi ya isheni haka,kun gama mai da ni mutumin banza ko,baku isa ba wanna karon na gaji ko masu auri suyo zaman auresu marasa aure suyi aure ko inci uban yarinya wallahi''
ba inna hadiza kawai ba hatta da su maama sunyi mamaki,yau baane ke ja in ja da inna hadizar?,lallai a dade anayi sai gaskiya,komai yayi farko qarahensa na zuwa babu shakka,a bangaren inna hadiza kuwa ta gama qullatar huwaila ne dadi bisa dari kan dukkan bala'in da taga ya afko,mata babu shakka ita ta qulla zuwanshi


qasa mama tayi da kanta tana fadin
''Allah ya huci zuciuarka malam,a yi mana afuwa''
sai yaji zuciyarahi ta dan rage zqfihar ya juya ya dan dubi maman,sannan ya maida idonsa gasu hadiza wadanda sjka zuba masa iddo qir babu mai cewa komai,baba hadiza na huci tana jiran ya gaya mata cuta ta fada masa mutuwa
''ke jamila ki tsaida hankqlinki,mahaifinki ne wanna,ki fada masa ya aayi hakan ta kasane don,samun bakin zaren,so ake a gyara lamarin ki koma gidanki kuci gaba da zama,mutuwar aure gun diya mace ai faduwar daraja ne,saidai kuma idan na qaddara ne''cewar mama


jin an sako maganar komawarta gidan jabir ya,sanyata cikin rawar jiki ta bude baki zata yi bayani a wautarta da jahilcinta za'a maidata din,don a yadda ta dandana zaman daula bata jin zata iya zaman gidan nasu kona wata daya ne bare na dindin din
tuni inna hadiza ta katsi numfashin jamilar
''uban me zaki gaya musu,cin fuska yaso yi miki kawai,ya aureki da kansa sanna yace baisan ya aureki ba,kujimin da,ke kuma aminatu banason munafurci da gilma,ina ruwanki?,ina cewa dai jamila bake kika haifa min ita ba,ai na dade da sanin cewa abunda kike nema kenan saboda har yau baqincikin qin aurar diyarki da baiyi ba yana nan cikin zuciyarki,to ahir dinki ki fita sabgata data yara na''
tsawa baban ya daka mata ya kuma ce ta ta shi ta fice masa adaki,koda ta ficen da yake ta riga da ta rainashi sai tayi tsaye abakin window tana eqa dakin tare da kallon jamila tana mata gargadi





*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:53 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺🌺
    🌺💖🌺💖🌺
       🌺💖🌺💖
          🌺💖🌺
              🌺💖
                💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖
*WRITTEN BY*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
💖🌺💖🌺💖🌺
💖🌺💖🌺💖
💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺    ▶3⃣0⃣


*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*💡
*_home of expert and perfect writers_*






dauke kanta tayi tamkar bata ga gargadin nata ba,domin burinta kawai a maidata ga gidan jabir,don ba jabir dinne ma yafi damunta ba tunda bashi daman take aure ba dukiyarshi take aure,tana da abokanan holewarta a waje
a take ta warware musu yadda tayi amfani da sihirtaccen kwalli da turare har sau biyu ta dauke hankalin jabir ya aureta cikin gushewar hayyaci


gumi ne kawai ke ketsatstsafowa maryam,bata sake jin tsananin tausayin jabir ba sai a lokacin,shikam baban nasu shiru yayi ya kasa furta komai,kimanin mintina biyar sanna ya dubi su binta yace su fita adakin,sumi sumi suka fice ya dubi huwaila da tayi tsamo tsamo
''duk abinda kukayi huwaila don kanku,amma ku sani dole ne ku nemi yafiyar maryama don an zalunceta''
ya waiwaya ga inna hadiza dake labe yace
''kije Allah ya isa tsakani na dake,tarbiyyar yara da kika bata min,haqqin maryam kuma ke da ita,kya sake samowa jamilar wani mijin,ku taahi dukkanku ku bani guri''


dama a qagauce suke saboda kunya da nauyi tuni suka fice,saura maryam da mama,miqewa itama maryam din tayi ta ajjiye masa kudin hannunta 
''ba wanna babu yawa amana addu'a,kuma kayi haquri Allah ya huci zuciyarka,insha Allahu zamu gyara dukkan abinda baka so''
''na gode,Allah yayi miki albarka,baki gaji ba maryam baki dade da yi mana hidima ba,har yanzu abincinki ake ci a gidan nan''
''ba komai baba,kunfi qarfin haka ai''


tana shirin ficewa mama tace
''dawo ki zauna ayo maganar yaron nan a qareta''
cikin rashin fahimta baban ya dubeta
''au ta samu wani mijin ne?''
''eh,gata nan ta maka bayani''inji mama bayan ta miqe tana tattare kwanukan da ya karya
kanta a duqe ta gaya mishi iya abinda ta sani game da abdur rahim din
''to,madalla,sai a sanar masa ya turo kawai,ai babu wani bincike da za'a tsananta tunda kina sonshi kuma ma kada muje ya subuce mana garin binike,kinsan wani baya son tone tone''


sai taji,maganar ta mata wani iri taya za'a dauketa adanqata ga mutumin da ba'a binciki wayeshi ba,sanna kuma uwa uba daga haduwarsu jiya sai tace ya turo magabatansa,tilas sai an nuna masa an gaji da zamanta dama
sai ta lanqwashe murya tace
''baaba,ina ganin an dan badakamar wata guda ko fiye kafin ayi masa maganar turowar,sanna baba ka gafarceni ayi binciken inaga haka sai yafi kyau''
''hmmm,karatun boko ya bude miki ido mero''ya fada yana murmushi
bata ji dadin yadda ya fassarata ba,don ita tayi ne da zuciya daya,tayi ne don gujewa auren jeka nayika
''shikenan tunda kin zabi hakam,amma kada kiyo kuka dakowa idan shima ya kama gabansa kafi wata gudan,maganar bincike kuma tunda ya gaya miki unguwarsu na baki wuqa da nama kiyo kinga kin hutashaheni ma''


hawaye ni ya silalo mata,bata taba jin inda 'ya takewa kanta binciken ma'aurinta ba,amma yata iya jaka tata *qaddarar rayuwar* take,ta kuma godewa Allah da bai sata ta kauce hanya ba duk da yadda ta tsinci rayuwar tata cikin tsangwama
''na gode baba,Allah ya gara gima''ta fada aladabce
''ameen ameen,idan kin fita ki turo min iwar taki''



tare suka karya da lafiyayyen qosai da kunun tsamiya wanda yasha lemon tsami,sosai tayi namijin qoqarin fidda dukkan damuwa daga zuciyarta suka karya din cikin wawala
sun tattauna da mama kan atamfofi da take so ta dinga sarowa maman idan tadauki albashinta na wannan watan ko falle bibbiyu ne ta fara saidawa agani idan zasu karbu,albarka maman kawai ta shi mata tare da mata kyakkyawan fata


sai la'asar ta fara shiri tafiya,hindatu tace
''ki jirani adda maryam mu fita tare zanje duba jamb dina,tun jiya naji sanarwa ta fito''
''to kiyi,maza ki shirya don so nake naje nayi abincin dare,jiya duka baaba uwani na dorawa aikin''
''gaskiya kam,don ma muta nene masu karamci da mutunci''
inji mama dake ta hadawa mami su kuka daddawa kubewa man shanu da sauransu


qarfe biyar sukayo sallama da mama ta fito don raka su,jamila ce tsaye a tsakar gidan sanye take dai da swiss lace dinta tun na shekran jiyan,mai tsada ne amma gaba daya ya yamutse yasha squeezing,fuskar nan ta hqutsine kamar dakalin kashi sqboda tsabar bqcin ran da take,ciki da baqinciki uwa uba kwana biyun nan bata saurari wanka ba,gabanta hadiza ce riqe da kwanon da yasha uwar lamba shinkafa da wake da manquli ce aciki da barbaden yaji
''haquri fa zakiyi kici tunda dai na ba gidanki bane,mu bamu da wani miyar nama da zamu zuba miki,kina kallo haka suma qanna naki suka ci''
''idan naci wannam abun Allah ya tsinen hadiza,wai ma meye amfamin kudaden da na ringa satowa ina kawo miki duk ina kika kaisu?,kinje kin rabawa garadan soro sun cinye kuma gashi nan auren da ake ta tattali din ya tsinke....''
da sauri hadizan ta kaiwa bakin kamilar dula kin zata mata tonon silili cikin jama'a
''don ubwnki sharri zakimin''
''ba wani sharri wlh gaskiya ce da bakina sai a hanani fadan gaskiya ta...''


binta ce ta atse cece kucen ta fito dakin,inna hadizan hannunta dauke da wayar jamilan wadda ta tasamma dubu dari biyu da hamsin tana ta digar ruwa
''kinga aikin da kulu ta miki''ta fada tana miqa mata wayar
hannu jamia ta dora aka ta kurma ihu tana fadin kulu ta kasheta,ita kadai ce ta rage mata kadara shine don baqar zuciya zata tsoma mata ita a ruwa wallahi to ba zata yarda ba
kukan kura tayi ta banka dakin nasu da gugu inna hadizar tabi bayanta tana fadib kada ta nakasta mata yarinya amma ina kota kan uwar bata bi ba
tsaki hindatu taja tana fadin
''jarababbu,ku kashe kanku dai''


naira talatin talatin suka biya zuwa caffe din dake qasansu,su taradda gun cike da dalibai masu duba jarabawarsu,hakan ne ya dan janyo musu jinkiri,sai da suka jira har kusan shida sannan suka samu sarari,babu jimawa aka gano result din hindatu,ba ita mai jarrabawar ba hatta maryam tayi farinciki ainun,don makin hindatun ya kai dari biyu da biyar,sai da ta rakata ta samu ota sanna itama ta tari tata ta wuce gidan

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

kamar yadda layukan suke shiru gidan shima yake shiru lokacin da ta isa


tana shirin shiga ita kuma na shirin fita kunnenta maqale da waya,cikin dinkin fitted gown take na material ruwan zuma,dan siririn dankwalin kawai ta nade wuyanta da shi,ganin ta nufota gadan gadan yasa tayi hanzarin matsawa gefe dob ta lura idab batayi hakan ba tsaf zata bangajeta ne ta wuce,saddiqa ce uwar girman kai da dagawa,duk da hakan bata tsira ba sai data yi mata kallon biyi babu taja tsaki bayan ta cire wayar a kunnenta sanna ta wuce


su biyun kuma na kwance cikin kujerun falon wato abida da salma kowa na sabgar gabanshi,abida na charting salma na danne dannen laptop da bata san me tak yi ba,sai t v plasma din falon dake ta zuba aiki babu mai kallonta,babu wadda ta amsa sallamarta cikinsu,bata damu ba sam don ba yau ta soma ganin hakan ba,har zata wuce daki sai ta jiyo motsi cikin kitchen din haka ta sauya akalar tafiyar tata can,baba uwani ce ke wanke kwanuka,ta qaraso kitchen din dafe da bakinta
''ayyah,baaba uwani ayimin afuwa na barki da wahala jiya da yau''murmushi tayi tana taunar goro
''haba 'yar nan ai an zam daya babu komai,ke dai ya kika barosu?''
''lafiya baaba suna gaidake''ta amsa mata tana karbe soson wanke wanken
''to madala muna amsawa,inace yanzu kika shigo gidan?''
''eh baaba''
''to amma shine zaki wani,karbi wanke wabke,bani in qarasa kije ki huta ga kiran sallar magariba can anayi''
''a'ah baaba,haba gaskiya bazan baki ba,ki huta kema nasan tun jiya kike dawainiya''


''hmmm,wallahi ke dai bari 'yar nan,inda ace abdullahi ne sai ni sai hajiya aikin da sauqi,tofa ina wadan can marasa kunyar yaran kawai sun isa su saka ka gaji,ga daya ta dadu,wancan tace ita kaza za'a dafa min waccan tace kaza''
wani takaici ya kama marya
''kuma kika dafa baaba?''
''to ya za'ayi meramu sai haquri''
ta ajjiye kwanon hannunta
''bana jurar raina babba baaba,babu wadda zaki sake dafawa komai saidai idan maami ta saka ki,duk mai buqatar wani abu ta shigo ta dafa ai itama tana da hannu''


sai da suka qarasa komai sannan suka bar kitchen din tare bayan baaban ta gaya mata mami na asibiti da azahar ta fita zuwa bayan isha'i zata dawo,yadda ta barsu a falin haka ta dawo ta taradda su babu wadda ta motsa don tayi salla


tara saura ta fito din ta debi abincinta,zaunen dai suke duka su uku wannan karon kowacce taci ado,abida cikin matsatstsun riga da wando,salma cikin fitted gown,saddiqa kuwawata gown ce wadda bata da hannu duka saman qirjin a waje,mamaki ya cikata tamkar irin matan gidan nan dake tsammin dawowar mai gidansu a lokacib,babu tababa zaman jiran dawowar abdallah suke,takaici ya isheta kamar ta rufesu da duka,duk su suke jawowa abdallan ke daukar kansa on top,yake rage qimar mata,koma meye sune sila


tasa kanta gaba zata wucesu dauke da plate din abincinta
''ke malama a bawa mutane abinci ko su zasuyi serving kansu?''
a nutse ta waiwayo
''su waye mutanen?''ta tambayi salma cikin gatse,amma da yake sam ba ganewa take ba sai tace
''mtseeww,gani kuwa kina kallona''
''ayyah,to ai na dauka a qoshe kuke ko''
ta shige dining area din ta zuba mata ta ajjiye mata


''ni da kika raina sai nayi magana zaki zuban?''inji abida
maryam ta dubi plate din hannunta
''sai kayi magana zansan kana so ai,ga wannan kici na zuba wani''ta fadi bayan ta ajjiye mata shi a gabanta,ba bata lokaci tasa qafarta ta shure shi take yayi dai dai a gun,wanda ba don tayi saurin ja da baya ba har a jikinta zai samu masauki
''lallai ne ba qaramun raini ne tsakanina da baqauyar yarinyar nan ba''cikin qanqanin lokaci ta yar da wayar hannun ta ta miqe tayo kanta,qyam ta tsaya hannayenta harde da qirjinta tana kallon abidan,qarasowarta dab da ita ta daga hannunta saidai kafin ta aiwatar da komai muryar mami ta karade falob
''kai,meye haka abida?''dolenta ta sauke hannun nta cikin hayaniya take fadin
''wallahi mami sai na hora yarinyar nan''


''me ya hadaku kuma yau maryamu?,ban sanki da fad ba fa''hankali kwance ta gaya mata abinda ya faru,girgiza kai kawai mamin tayocikin takaici tace wuce amaryamu''
cike da takaici ta isa dakinta,tayi imani a lokacin da abidan ta taba jikinta ko siyar wace ce ita ba zata daga mata qafa ba,bata ga amfanin alkunya ga mutumin da baisan darajar dan adam ba,cikin ikon Allah abdul ya kirata,shi ya ebe mata kewa har bacci yayi awo gaba da ita

🍃🍂🍃🍂🍃

cikin bacci ta dinga jin yunwa na rage mata dadin baccin wadda ta tilastata farkawa,wayarta da ke gefan pillow dinta ta dauka ta duba lokaci,shabiyu da arba'in da takwas na dare,cikin mutuwar jiki da kasala ta sauko daga adon ta shiga toiket ta dauraye bakinta ta daura alwala ta fito ta tayar a sallah,raka'a hudu ta samu tayi tayi addu'oo'inta ta shafa


a hankali ta bude qofar dakin nata ta fito don samawa kanta abinci a dining,tayi mamakin ganin qwayayen falon duka akunne,ganin laptop da waya kusa da ita yasa ta bayar salma ce qarshen tashi tabar falo a haka


jingine yake da bango falon hannayenshi harde a qirjinshi,idanu kawai ya zuba mata fuskarsa qunshe da qaramin murmushi,yayin ita kuma take gaf da ahi har tana iya sheqar hucin nashi numfashin,hannayenta dafe da bangon kusa da kafadarshi
''fyaden kema zakimin?''ya tambayi salma kanshi tsaye,cikin lumshe idanu ta kada kai
''ko kadan,kawai ina da buqatar inji dumin jikinka ne,dubi kwalliyarnan duk kai na yiwa amma tun dazun nake jiran dawowarka,na hana idanuna bacci don kada ta tashi a tutar babu''
murmushinsa ya qaru fiye da na dazu,yasan kalma daya zaiyi amfani da ita wadda zata sata taji haushi
''sai ance mutum kaska ne yace shi bashi bane''
a maimakon yaga taji haushi kamar kullum sai yaga ko a jikinta,murmushi ta kuma yi
''to meye idan ma kaskar ce,duk akan sonka ne,nidai ko hugging dina ayi kawai na wuce dumin da naji da qamshin turarenka ya isheni''


ya janyeta ya bada nisa tsakaninsu yana fadin
''saboda tsabar raini ma naga sai da kika nemo irin turarena da shi kike amfani ko''
''idan zan kwanta na fesa jina nake kamara qirjinka nake kwance''ta fada tana sake matsowa daf da shi,hannunta ta dauke daga kan makunnin da takeson kashewa wanda hakan ya haddasa motsin awarwarayenta da suka jawo hankalin abdallah,jiki na rawa ta juya zata bar gurin,tuni ya saki briefcase dinshi da ya dawo da ita daga office ya biyo bayanta da sauri,ganin tana niyyar takawa a aguje yasanya shi dada hanzarinsa don ya fuskanci idan ya qyaleta zatq sake masa irin fassarar da tayi masa kwanaki,taku uku ya cimmata tare,da fusgota baya,tayi taga taga ta fadi jikinsa cikin tsoro da daukewar numfashi





*mrs muhammad ce*👑



📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:53 PM] 80k: *ABADAN*31
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*_home of expert and perfect writers_*
jikinsa ta fada qeyarta ta samu masauki a tsintsiyar hannunshi fuskarta na facing tashi fuskar,yabi oily eyes and golden eyes dinta da kallo wadanda suka dada sheqi saboda hasken farin qwai daya mamaye falon ya haska cikinsu,ya kalli dan qaramin bakinta da yake motsi yana tattara kalmomin kayi haquri cikin rudewa
Ranshi ya baci,wai me yarinyar ta maida shi ne?,dan iska?,haka wancan karon tayi masa fa?,tana so tace masa a age dinta bata taba ganin romance tsakanin mutum biyu ba saboda tsabar rainin hankali?idan ma hakanne yau zai koya mata hankali,a hankali ya soma kusantar da bakinsa zuwa nata,numfashinsu ya soma gauraya,tsoro da rawar jikin maryam ya dadu,don tuni zuciyarta ta gama ayyana mata abinda abdallahn ke shirin yi
karon farko tattausan lips dinsa suka taba haduwa da na wata diya mace kamad yadda yake haka a gurinta,baisan yadda akayi ya tsinci kanshi da tsotson lausasan lebunan nata ba cikin rashin sani
''hasbunallahu wani'imal wakeel''kadai take ambata cikin zuciyarta,gudun zuciyarta ya dadu har numfashinta na qoqarin janyewa,hawayen dake malala kan fuskarta ne ya soma taba fuskarshi da sajen bakinsa na quater millon
''abdallah!,meye haka kake yi?''salma ta fada cikin qaraji da wani irin yanayin baqin kishi da bata taba shiga irinshi ba,a nutse ya saki bakin maryamun ya juya yana kallon salmar wanda hakn ne ya bawa maryam qwarin gwiwar hada ragowar qarfinta don ta tsere masa,saidai tana tashi taji ya cafko dantsenta idanunsa na kan salma,kallon 'yan sakanni ya mata ya maida idonsa ga maryam
cikin fada da tsawa yaso yi mata maganar amma sai ya gaza,kasala ce ta saukar masa lokaci guda tamkar mai jin tsananin barci
''gobe ma idan kinganni tsaye da wata kimin kallon dan isaka,zaki ga yadda ake iskanci ra'ayil ain''ya fada yana kallo tsakiyar qwayar idonta da hawaye ya cika yake zuba kana ya cikata,da gudu kuwa ta bar gurin sai ya bita da kallo yayin da salma ita kuma ta tsare shi da idanunta wadanda suma tuni suka kawo qwalla
''haba,haba abdallah,irin wannna cin fuska haka da me yayi kama?cook dinka?''ta fada tana nuna hanyar da maryam din tabi da yatsa ''abdallah ka rasa bakin da zaka tsotsa sai nata,ni me na gaza da shi?just hugging dina kawai nace kayai ka kasa sai gashi ka buge da kissing house girl''
''hey!stop''ya tsaidata cikin hade girar sama data qasa,ya qara taku biyu ya iso gareta ya tsaya agabanta
''kada ki sake ambatar nayi kissing yarinyar can,kaifi tayimin nayi punishing dinta,ina fata kun fahimta''
murmushin takaici ta saki sannan takama qugunta da hannu daya tana girgiza kai
''kada ka maidani jahila mana abdallah,sau nawa ina maka laifi ka taba punishing dina ta wannan hanyar''
har ya juya vaya taba dauke briefcase dinsa sai ya waiwayo
''ita tana showing kanta a matsayin kanta a matsayin mai nutsuwa tana min kallon abinda ban taba aiwatar da shi ba,kinga gwara nayi mai dalili ko?''
girgiza kanta ta sake
''ko jikina kunne ne bazan yadda ba,kayi ne da manufar wulaqantani da nunama duniya iyakata''
''well,idan hakan kika zaba shikenan daidai ne''ya fadi yana kewayeta ya fice daga sashen bayan yasa key dinshi ya kullesu ta baya kamar yadda yazo ya tarar da su,dama abincinshi ya shigo yaci ya sameta zaune ita daya afalon
kamar ta dora hannu aka tayita rusa ihu haka ta ji,hawaye shabe shabe ta shige dakibta bayan ta qudiri abinda zata aiwatar musu a gobe
Qarfe goma ta gama breakfaat di gidan ta shiryashi a dining,Allah Allah take ta kammala komai ta shige dakinta don bata son haduwa da kowa uwa uba abdallah da take masifar jin haushi tsoro da tsanarsa,ta yanke ma zuciyarta abdallan yana layin 'yan iskan maza ne kawai,tuni ta bashi wannan sunan
tana gefan gadobta tana shafa mai bayan sanya doguwar rigar atamfa da tayi mai dogon hannu taji wayarta na b'urari,sunan mami ya soma yawo saman screen din,haka kawai gabanta ya fadi,cikin rashin kuzari ta sanya robar lotion din dake hannunta a gefanta kana ta daga wayar,tana qoqarin gaidata taji tace
''ki sameni yanzun a sama''
''to mami''ta fada cikin rawar murya,kasa ci gaba da shiryawar tayi sai ta zaro blueblack din hijabibta ta ware shi daga gugarsa ta sanya ta miqe ta fice a dakin
kallo daya ta yiwa mamin gabanta ya fadi don zata iya cewa a iya saninta da ita bata taba ganin yanayin fuskarta haka ba,gefanta salma ce zaune fuskarta jazur idonta a tashe,a salube ta qaraso,qasa ta zauna daga can gefe tana fadin
''barka da safiya mami''
''matsonan''tace da ita tana nuna mata gabanta ba tare da ta amsa gaisuwar tata ba
''maryam,me ya faru jiya da misalin daya da wani abu na dare tsakaninki da abdallah?''wata mummunar faduwar gaba ta ziyarce,tsoro da fargaba suka mamayeta ,bata raba dayan biyu wani abun salman ta gayawa mami mai muni a kanta
kimanin minti uku mamin na saurarenta babu amsa,don bata da bunda zata ce din
ta fadi gaskiya?,bazata iya ba,tasan mamin mai yarda ce da gaskiyar abunda ta fada din amma bata burin shiga tsakanin soyayyar da da mahaifiyarsa don ta dan dana hakan ba lamari ne mai dadi ba kona second guda
ta musanta kuma ya zamo mata zunubin qarya,idanun mamin na kanta tana jin babu dadi cikin zuciyarta,don har ga Allah 'yar cikinta take kallib maryam,dan yanzu ba'a shaidarsa duk da ta shqida da nagartattun halayen abdallah,amma yaran zamani koda yaushe yana iya sauya halayyarsa,tsoronta daya kada ya yaudari maryam din ya bata rayuwarta,hakan idan ta tuna shike qara hasalata da sa mata suya cikin zuciya
''dake nake magana kinhi shiru''
shirunne ya sake biyo baya,tuni hawaye ya soma ambaliya cikin idanunta tana sa gefan hijabinta tana sharewa
''to tunda kinqi magana bari na kira ahi shi mai gayya mai aikin yayi bayani''
''a'ah mami,tun farki na gaya miki ba laifinshi bane''
salma ta fada da sauri har tana kamar zata dafe hannun mamin da ya dauko waya don kiran abdallah
wani kallo mamin tayi mata
''bana hukunci da ji daga bakin bangare daya ba tare da dayan ba,koma mene da nashi laifin kuma tilas ya bayyana nan,''
mami ta qare maganar tana kara wayar a kunnenta
shiru ne ya biyo baya har ahigowar abdallah,sanye yake da kayan training ajikinsgi wanda da alama yana filin motsa jiki ne,hannunahi daya handkhercief ne yana tsane gumin suma da fuskarshi,daya hannun kuma gorar ruwan swan ce dake fidda gumin sanyi bisa dukkan alamu a falon qasa ya daukota
da zolayar mamin ya shigo falon saidai yanayin fuskarta kawai ya bayyana mishi ba lafiya,shi sam bai kula da su ba cikin falon ba sai da mami ta jeho masa irib tambayar data yiwa maryam sannan ya kuka da salma
cikin ko in kula yace
''nothing happened,nasan dai sha biyu da rabi na dawo gida,so ina jin yunwa sai na bude nan na shigo naci abincina,sai waccan da na hadu da ita zaune a falo tana game''
''ita kuma maryamu a ina kuka hadu da ita?''ta fada tana nuna masa ita wadda kanta ke duqe
yatsan bata yabi da kallo har zuwa gun maryam,sai ya yamutse fuska
''wace kuma maryamu?''ya fada yana shanye ragiwar ruwanshi,sai ran mamin ya baci,ita zai bunne,tasan waskewar abdallah sarai tunda ita ta haifeahi,kadan daga aikinshi ma yace bai tabajin sunan ba sai yau
''ni zaka ninke a baibai?,ko ka manta cewa ni na haifeka na raineka?, a hannuna kayi wayo?,naci kashinka da fitsarinka?,yaushe abdallah ka sauya hali?,ita da na tambayeta ai tasan baku da gaskiya shi ya sanya tayi shiru bata ce komai ba,amma kai da yake madainiyar wayonka ta tambayeta sai ka nemi raina mata wayo ko?''
ya danyi qasa da ido dob sam kalaman mamin basu yimishi dadi ba,bazai iya yaushene na qarshe da rayi masa irin wanna fadan ba
muryarshi a sanyaye yace
''idan ita ta gayamiki ai sai ta bude baki mami ta fadi abunda na mata ko?''
''ta gaya min ne tunda tare kuka aiwatar,mai kishina binda ya faru ne ta fada salma,har yaushe ka farq neman yaran jama'a,ko kunyar ina cikib gidan bakayi ba?,kasan illar da girman zunubin abinda kuka so aikatawa badan Allah ya kawota ta hana afkuwar lamarin ba,mai makon kuma ka gode mata sai cin mutunci ya biyo baya?''
sumewa ne kadai maryam bata yi ba a zaune kukan da take aboye sai ya koma na fili,ran 'yan maza yq baci take idanunshi suka sauya kala,ya zubawa salma ido wadda runi dana sanin abinda ta aikata ya mamayeta,ita so tayi aci mutuncin maryam ita kadai a kuma koreta ta bar gidan,kasa daukar irin kallon da yake matq tqyi tqyi qasa da idanunta
muryarsa a kausaahe cike da sautin fushi yace''wanne la'a nannen Allahn ne ya mana wanna qazafin,ko da yake mami kince salma ce,amma nayi mamki mami,kin san halina ciki da bai,kinsan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba,me yasa lokaci guda wata can zato ta rushe kyakkyawar fahimtar da mukayi shekara da shekaru da gina ta,kai cina da har yau,ban kubuta daga zarin zan aikata zina ba daga gun mahaifiyata''ya fada yqnq girgiza kai jijiyoyin kansa na tashi,sai jikin mqminyayi sanyi,tabbas babu kyau gaggawar yarda da abunda baka da yaqini,balle abdallah da maryam,babu wana bata san halinsa ba,dukkansu tasan ne zasu aikata da wanda,ba zasu aikata din ba
ganin da salma tayi mami na shirin yarda da abdallan ita ta tashi a tutar kunya ya sanyata sake,zaqalqalewa
''ni ba la'a nanniyar Allah bace,kuma na gani din ne da ban gqni ba ai da bazan......''
bata qaraahe maganar ba taji quma abakinta,abdallah ya jefeta da ruwan robar dake hanjunahi wanda ko rabi bai sha ba,aka kuma yi sa'a ya sauka a bakin nata,ta dafe lebunan nata wani azabar zugi na ratsata,take lebunan suka fashe,bayan sun kumbura sunyi suntum cikin daqiqar da bata wuce talatin ba
hakan baiwa Abdalla ba ciki fushi ya yo gunta,da sauri mami ta shiga tsakaninsu tasa hannunta tana tokare qirjinsa don iya inda tsawonta yake kenan tana turashi da baya
''ki barni mami na lalata shashan bakin da bai iya komai ba face sharri da qazafi wa mutane''
''ka dakata abdallah,nutsu don Alla banason shashanci''mamin ke cewa,tasan halinshi sarai,bai fiya sairin fuahi ba amma idan ya fusata din komawa yake kamar mahaukacin zaki
kusan minti biyar mamin na artabu da shi
''na nutsu mami,amma na bata minti goma ta tattara dukkan wani abu nata tabar gidan nan,wallahi wallahi ta sake muka sake haduwa da ita sai na nakasta ta,banza shasha sha kawai,don ina rufa asirinki,sau nawa nake kamaki da syrup da capsule cikin jaka,shine har kike da bakin yiwa wani qazafin zina,to idan baki bar gidan nan ba nan da minti goma ba nine zan zamo mutum na qarahe da zaki tiwa qazafi a rayuwarki,bindigata zansa na harbeki ki mutu kowa ya huta''
cikin huci ya juya a sukwane ya fice,da sauri maryam tayi gaggawar jaye qafafunta badon tayi hakan ba kadan ya rage ya take mata dogayen yatsunta
bibbiyu ya dinga hada matattakalar har ya gama sauka daga benan,abida ce da saddiqa tsaye kowacce cikin sleeping dress tayi tsuru tana sauraron abinda ke wakana a saman,zuciyar kowaccensu tayi fari jin an kori salma suna ganin tamkar aiki aka rage musu
wani banzan kallo ya bisu da shi ba tare da ya furta komai ba ma suka watse
cikin mintina qasa da goma salma ta hada komatsanta tana kuka wiwi mami na lalkabrta ta shiga motarta ta fice agidan,ranar sai gidan ya wuni shiru kowa na dakinsa,mamin ma haqura tayi da fita asibitin ranar don tsoron kada ta tafi wata fitinar ta taso,jin shirun yayi yawa abdallah bai sake shigowa ba ya sanyata tattaki da kanta zuwa bangatenshi,don ta san cewa ba lafiya,don komqi akayi bazai iya fita bai gqyq mtq ba,to tabbas yana cikin dakinshi ne
A qurya ta sameahi kwance daidai yayi rigingine kan gadonshi,shigowartaya sanya shi miqewa ya zauna
''me kake haka har yanzu baka fito ba ko karyawa baka yi ba ga azahar ta gota biyu da rabi fa yanzu''
''bana jin yunwa mami''ya fada cikin rashin walwala,sai kuna ya dago ya dubeta
''mami ina fatan bakiyi fushi da ni ba,na kasa sukuni tun dazun''
dama ta sani a runa,yanzun haka bacin ran da ya gqni kan fuskarta ne ya sashi kasa fita,tun yana qarami haka yake,baya juriyar ganin bacin ranta
''zan iya yin fushin da kai dai na haqiqa matuqar baka gayan gaskiyar abunda ke faruwa ba''
''zan gaya miki mana mami,mami kiss ne kawai,wallahi bayan haka babu komai,kuma ko shi din ma haushi ta bani,kallon dan iska take min''ya fada bayan ya riqe hannayen ta cikin marairaicewa
dariya yaso bawa mamin amma sai ta gimtse don ba muhallinta bane
''don tana maka wanna kallon idan banda rashin dabara da wayo ta hakan zaka wanke kanka ta fahimci na gari ne kai?''
''am sorry may mami,nayi kuskure''
a nutse ta dinga masa fada sanna ta rufe da fadin
''idan irin hakan ta sake faruwa raina zai baci fiye da bacin ran daka gani yanzu,don ban yarda asabi Allah ba,duk son da nake maka zan iya ajjiyeshi gefe na hukuntaka hukunci mai tsanani,kada makamancin hakan ya sake faruwa akan ko wace ma indai ba matarka bace''sai maganarta ta qarshe ta bashi kunya ya dan sunne kai
dariya ta danyi
''da nema yau kuma nice akejin kunya''dariyar shima ya tayata
sai kuma ta hade cikin seriouse tone
''sannan abdallah,lallai lallai ya kamata kayi aure indai kana son hankali na ya kwanta yadda ya kamata,ka fidda mata cikin masu qaunarka''
qasaitaccen murmushin nan nashi ya saki
''relax mami na,insha Allahu kwanan nan zan sanyaki farincikin da kika dade kina fata,zan kawo miki mata ta har gida nan kusa,amma fa abida da saddiqa kowacce ta wuce gidansu,don wlh mami bazan iya auran kowaccansu ba''
''naji,saddiqa dama gobe tace zata tafi,abida kuwa dole ayi haquri sai an samu visa,zata sake ko sati uku ne tare da mu''
''shikenan mami,zan wa abokina magana harkarsu ce''
qememe yaqi fita yace zai je ko ina ba sai ya tabbatar ta gama hucewa haka suka wuni a gida gaba dayansu
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:53 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*



           ▶3⃣2⃣




*Allahumma ya imada man la imada lahu,ya sanada man la sanada lahu,ya giyasa man la giyasa lah,ya karimal afwu,ya hasanat tajawuz,ya khaahifal bala'a,ya azimar raja'a,ya aunaddu'afa'ah,ya munqizal garqa,ya munjiyal halka,ya muhsin,ya mujmil ya mun'im,ya mifdil,antal lazi sajada laka sawadul laili wa nurun nahaar,wa dau'ul qamar wa shu'a ushshams,wa da wiyyul ma'i wa hafifushshajar,ya Allahu la sharika lak,ya rabbi ya rabbi ya rabbi,Allah ka shiga lamarin mutanen qasar burma,Allah ka shiga lamarin jama'ar musulmin duniya baki daya don sayyadis saqalain*👏🏽👏🏽😔😔







Qarfe goma saura na dare mami ta shiga dakin nata,har ta gama shirin bacci tana kwance tana jiran wayar abdur rahim da yace ta jirashi kada tayi bacci zai kira ta,da sauri ta miqe tana maida hularta da santsin gashinta ya sa ta sabule,mamin ta dan bita da kallo qauna da tausat
yinta suka lullubeta ganin ta takure ta kasa hada ido da ita


gefan gadon ta qaraso ta zauna kusa damaryam don ta dafa gadon bayanta
'.dago ki kalleni maryamu,mamanki ce fa''sai taji qwalla na shirin zubo mata nauyi da kunyar mamin takeji,gefe daya hauhi da tsanar abdallah na takura zuciyarta
''ki kwantar da hankalinki abdallah ya yimin bayanin gaskiya,ba laifinki bane laifinsa ne,kuma nayi masa gargadi insha Allah bazai sake faruwa ba kinji,ki i gaba da kame kanki maryam kamar yadda kike,daraja mace da mutuncinta yana tqfin hannunta,ruwanta ne ta riqesu su zame mata abun alfahar ruwanta ne ta wargaza,bazan so wani abu ya shafi mutuncinki ba maryamu don tamkar amana kike a hannu na,ko bayan haka ma unajinki har cikin zuciyata,haka za bazan iya yafewa abdallah ba idan ya maki wani abu da ya sabawa shari'a da mutuncinki,duk abinda kuma nayi nayi ne saboda kare martabarki,ina fata kin fahimce ni?''
gayada kai tayi tana share hawaye 
''na gane mami,na kuma gode Allah ya qyara girma da lafiya''


wayar abdur rahim ta katse 'yar hirar da mamin ta fara janta da shi don ta saki jikinta,ganin maryam din taqi dauka yasa mamin ta dago wanda ke kiran
''bari in abku waje kinga ma shikenan ya fanshe ni sai ya qarasa lallashin,ki gaisheshi sai da safe''ta fadi tana miqewa cikin dariyar zolaya,kasa amsawa tayi ta sunne kanta saboda kunya mamin na dariya ta fice


hira suke abinsu sosai irn ta masoya kamar sun shekara da sanin juna
''maryam ya kukayi da abban,nasan dai an bani dama ko?''
ta dan zaro ido tana fadin
''wa ya gaya maka,abdul irin wannan zumudi haka''ya marairaice murya
''maryam bani so in rasaki ne inaso a bani dama koda kudine a kawo''
ajiyar zuciya ta saki
''abdul dole dai ai mu danyi haquri ko,tunda yanzun dai kaga azumi saura kwana bakwai,mu bari bayan sallah idan Allah ya kaimu sai ayi dukka abinda za'ayi''
''wa ya gaya miki azumi na hana kai kudi,akwai cousing dina safiyya hudu ga azumi aka kai kudin aurenta,so pls maryam ki barni na kawo kudin idan yaso bayan azumi asa mana ranar aure na qagu ki zama tawa,baki san ya nake ji ba duk lokacin da na kalleki ko naga kin fita a matsayin budurwa ba mata ta ba,bani da wani iko a kanki''


dariya ta saka
''yaushe ma kake ganin nawa ne abdul''
 ''ina iya ganinki mana da idon zuciya''
''shikenan yanzu mu bari zan sanar da mami na,duk yadda ta kama zaka ji''
da qyar abdur rahim ya barta bayan ya cikata da dad'ad'an kalmomin qauna

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Su hudu ne cikin lafiyayyar motar da idan ka shiga ba zakayi tsammani tafiya akeyi ba sai idan kaga kuna wulga gurare,mami ce da maryam a baya sai Abdallah da driver a gaba
mami cikin shigar leshi dinkin buba orange wanda yasha adon lemin hreen,takalmi jaka da mayafi dukka toomatch masu dan karen tsada da kyau,ba qarya mami gwanar iya ado ce,ko cikin mata masu shekarunta da wuya ka samu irinta goma,shi yasa sam sai ka rantse bata haifi abdallah ba,zakayi tsammani yayarsa ce kawai
maryam ma cikin cikin kwalliyar take amma zamu iya cea kwalliyar jiki don babu wani make up a fuskarta,material ne pich da kwalliyar sea green,tayi adon takalmi mayafi da fashion na dan kunne duka kalan sea green,ba gwanar jaka bace hakan ya sa wayarta ce kawai riqe a hannunta,abdallah dake gaban mota yake ta faman zuba mitar shi kam da an barshi bazaya je ba,ba gun zuwanshi bane idan ba kamawa tayi ba,sanye yake da shadda light blue dinkin tazarce da yaji aikin hannu na maza dan ubansu da baqar hula,takalmi sau ciki baqi da agogo,kallo daya zaka masa ka tabbatar kudin da jikin nashi ya lanqwame ya ishi mai qaramin qarfi jari


''ayita aure gab da azimi barna tayi ta afkuwa''ya fada yana yarfar da hannunshi wanda ke daure da agogon ruwan gold''nikam dai wallahi kam duk wanda yamin aure a irin wannan lokacin alhakin a kansa''


''baka da kunya ka maidani kakarka,yaro duka ka gama mitarka,dinner ce dai si kaje,minti nawa anyi an gama,hajiya mai gado idan da halacci ba zaka mata haka ba,ita tayi yayenka abdallah,ba qaramib sonka take ba''
ya dan waigo yq dubi mamin
''ayyah mami me ya kawo maganar yaye na''ta dago shi qwarai wai shi baya son raini,dariya ta saka
''to meye kowa ma an masa yaye har ni kaina''kadan kadan take bashi labarin quriciyarsa gidan hajiya mai gadon,yana son ji amma baiso wani ya ji masa ya raina shi don haka ya canza topic din


''mami,cikin kwankin nan nake son kawo miki dear ta gaidaki,so kuma bata nan sunje umarar azumi,ni kuma na qagu mami in yi wani motsi''
murmushi ne ya subucewa mami
''ummm,abdallahhh......,yaushe ka zama haka?yaushe sonta ya maka irin wannan kamun?kai har naji ina sonta data iya sato zuciyar birkitaccen yarona haka ta farat daya''
murmushi yayi hadi da lumshe idonsa,ya jinginar da kansa jikin seat din motar yana tunata yana jin wani yanayi na shigarsa,mami ta sosa masa inda yake masa qaiqayi
''dis luv inside of me is strong mami,there ar no boundaries that it can hide''


Kasa daurewa mamin tayi har sai da ta dan daki kafadanshi ta baya dariya ta kamata,ringin din wayar maryam ya katsesu,abdur rahim ne,kamar ko yausheta kasa dagawa saboda kunyar mami shi kuma bai fasa kira
tsaki abdallah yaja yana fadin
''du Alla a kaahe wannan culculator din ya damemu haka nan''
mami ta kalli maryam
''daga kiranki maryam,ba mai jinki hirar mu muke''
tsaki ya kuma j''idan ba zata daga ba asauketa ta kammala wayar ta biyo mu daga baya kota koma gida''
''shut ur mouth,oya ina jinka,muyi maganar dake gaban mu''cewar mami


Minti ashirin tsakani suk iso gun dinner din,ita dai maryam rava idanu kawai take don bata saba zuwa ire iren guraren ba,bata da wannan rawar qafar sam,da dai su jamila ne su lubabatu tof babu na biyunsu
uwar taron dakanta ta fito ta taresu
''masha Allah hajja bintu ina kika samu kyakkyawar diya haka,ko surukar taki ce''
murmushi tayi ta wauwaya ta kalli maryam da abdallah dake bayanta,sai taga sun mata kyau din kuwa tamkar wasu couples,abinda bata taba kawowa a ranta ba ta jishi lokacin,sai taji tana fadi cikin zuciyarta ina ma da gaske ne haka dinne,ya waiwaya ya danqarawa maryam harara sai akayi sa'a suka hada ido,ya dan matso gab da ita har tana sheqar qamshinsa kana yayi qasa da murya kamar mai fada mata abun arziqi
''yi gaba mamalama,kin wani jera da muta ne kamar sa'anninki,salon 'yan jarida su ganmu tare ki samu daukaka ni kuna ki bani kunya'',itakam tsoronshi take don neman tsari take da shi hakan ya sanya batare ce masa komai ba tadan ja da baya da yake ya fita sauri tuni ya dan zar tata


mami ta kalli hajiya mai gado
''diyata ce ita din ma,amma surukar naku na zuwa insha Allahu,don shekaran jiya yaron naki ya min albishir,ya gama ruwan idon nashi da bani kunyar gun iyayen yara''
''a'ah,a qyale yaro na,ai lokacinshi ne a barshi ya zaba ya darje,ai ya cancanci yin hakan''
''um um kada ka ki fasa masa kai''
''ba zancan fasa kai sai tsabar gaskiya''da daddan hirarsu irinta qawaye suka iso gurin da ka tanada don baqi na musamman irinsu


anyi kiran iyayen amarya suzo su nuna tasu karar don haka mami ta miqe,ta dubi abdallah dake ta faman shan qamshi idanunshi na kan waya tunda sukazo
''bari muje nida martmyam liqi yanzun zamu dawo,kaima ya kamata ka qarasa ku gaisa da amaryar''
''ina zan iya tashi an cika guri da sakarkarun 'yammata marasa kamun kai,duk inda ka motsa suna kallinka kamar wasu mayu''
''kaji da shi dai,kallo kuma kayi abun kallin ne dole a kalleka,dukka abokan ango na gun stage suna liqi kaja ka zauna bayan kaima abokinka ne''mamaki ya cika maryam,yadda taji ana tababa da shi kan bazai je ba tayi zaton ma bai sanshi bane


''mami ni bazanje in kalli matar wani ba don nima babu mai kallarmin tawa''
''haka za'ayi naka bikin kenan kana nufin''
''ko za'ayi mami ba zata zo min da irin shigar da amaren yanzun suke ba,sai babballata in zubar''
hade rai mami tayi
''to ni kuwa bazaka balla 'yar muta ne ba ka barmu da jidali ba ka canza tunani''
murmushi ya subuce masa ganin yadda mamin ta hade rai kamr ma ya riga da ya aikata


miqewa yayi ya karbi jakar hannunta yana dariya
''Allah ya barmin ke mamata ni daya,muje in rakaki,Allah ya huci zuciyar hajiyata''
''hutsu ne abdallah''maryama ta fada cikin zuciyarta,suna hada ido ya daka mata harara ya kuma hade rai qyam tamkar bashi yake murmushi yanzun ba


a baya suke binta har suka isa atge din,ya miqawa mami jakar yana fadin
''gashi mami,ayi liqi a hankali''
''haba handsome,girman mami ne ai ta liqa ko nawa take so,babu ji tunda tana da kai''maryam da abdallah suka kalleta lokaci guda don mami bata ji ba tuni da kutsa ciki,wani sakaran kallo yayi mata gami da jan tsaki,ita dai maryam gaba tayi tana qoqarin bin sahun mami tana fadin cikin zuciyarta
''kin debo ruwan dafa kanki''


ji tayi an riqo tsintsiyar hannunta gam ana janta,babu shiri ta waiwayo abdallah ne tuni har ya fara tafiya,tilas ta saita wa kanta hanya ta bishi a baya tamkar raqumi da kala,don idan tayi tirjiyar bin nasa zata iya zubewa a qasa don da sauri yake jan nata
bai saketa ba sai da suka iao teburin na su kana ya sakar mata hannu hadi da yi mata nuni da kujerar data tashi dazu a kai,tsareta yayi da idanunshin nan masu kaifi
''sit,dake aka hada kutingwilar zuwa na nan,shine kuma duka zaku fashe ku barni zaune ji daya kamar yaron mayu,ki zauna ki kula da ni har mamin ta dawo ta karbeki,daga nan ma idan club zaki wuce ke ya shafa''


Tuni hawaye sun cika idanunta,bata ce masa komi ba ta zame ta zauna,shi kuma yayi tsaye hannayenshi harde bisa qirjinsa yana qarewa gun kallo tamkar mai neman wani



matashin saurayi ne yake dosowa gurin,kallo daya zaka masa ka tabbatar da cewa ya gogu cikin duniyanci,sannu a hankali yake qarasowa har inda maryam din take,shigowarsa gurin kenan idanunahi sukayi tozali da ita,totally ta gama yi masa fatanshi daya 'yar hannu ce,zai iya kashe mata ko nawa ne matuqar zai samu hadin kanta,ta bayan kujerarta ya zagayo yasa dukka hannayenshi ya dafe makarin kujerar
''hello babe...''
gabanta ne ya yanke ya fadi,har ta kasa jiyowa taga ko waye,ga zatonshi bata ji ba don haka ya ranqwafo bayan nata yana shirin sanya hannunshi ya dafa kafadunta


cafkar da yaji an yiwa hannunshi yasan bata wasa bace,tamkar tarko ya kama bera haka abdallah ya riqe hanun nashi tsam,bai gama qarewa abdallan kallo ba yaji saukar lafiyayyun mari guda biyu da suka gigita shi,
hannu abdallah yasa ya yaye dogon hannun rigar t shirt din dake jikin saurayin,take wasu yan qanan rubutu da suka fi kama da na 'yan china suka bayyana a saman tsintsiyar hannunshi,a tare suka kakki juna ahi da mataahin tashin farko tsoro qarar ya bayyana idanun matashin,motsin da matashin ya fara yi da daya hannun nasa da abdallan bai riqe ba yana qoqarin cusa hannunshi aljihun bayan wandonshi ya ankarar da abdallan,cikin hanzari ya dunqule hannunshi ya daki hannun matashin take ya sagar masa da duk wata jijiya da zata taimaka masa ya iya motsa hannun,ya zura hannunshi aljihun matashin ya ciro 'yar qaramar bindiga ya cillata cikin nashi aljihun,qarar da ya saki ita ta janyo,hankalin mutanen dake kurkusa da su,cikin zafin nama da qwarewa da hannu daya ya tsinke duk wani maballi dake jikin t shirt din matashin ya finciketa daga jikinsa hade da juyo da bayan matashin ya kalla,zane ne kala kala a jiki wanda ba lallai kai ka iya ganewa ba
''anaconda isnt it?um?yaron alhj hamza mai qusa''


Abdallah ya fada bayan ya zagayo gaban matashin sunyi face to face,hannunshi daya ya sanya a aljihub rigarshi ya ciro qaramar wayarahi keypad qirar samsung,cikin qanqanin lokaci ya bada order turo ma'aikata inda suke din kana ya maida wayar aljihunsa,idanunshi qyar cikin na matashin yake tambayarsa
''ku nawa ne agurin nan?''shiru ya masa babu alamun zai amsa masa,hakan ya bawa abdallah damar yin tsai yana karantarshi,ba tare da matashin ya masa nuni ba ya karanci tabbas akwai abokin tafiyarsa ahannun daman abdallah,sai kuwa akayi dace shima ya yunquro da niyyar kubutar da dan uwanshi,duka daya abdallah ya waiwaya ya masa a dokin wuyanahi ya zube a qasa yana malelekuwa.


minti goma kyawawa basu cika ba jami'an ss suka iso gurin ya damqa musu su yace su kira jamal hussain ya fara aiki a kansu kafin gobe ya iso office din,mutanen dake gurin kam kowa godiya yake ma Allah suna fadin Allah ne kadai yasan me zai faru badon zuwanshi ba,sai da koma cikin mota ya kira mami yace suzo su taci don baya son,jama'suci gaba da shaida fuskarshi


ko cikin motar tamkar kace ket maryam ta zura a guje take ji,tsoron abdallah ya kuma cikata,ya dubeta da madubin motar lokacin da yake goge hannunshi da handkherchief suka hada ido,hade rai yayi yaja tsaki
''mutum sai shegen tsoro,komai ma tsorataka yake''mami tayi zaton da jama'ar inda suka baro yake
''a'ah wannan lamari fa da tsoro,wannan aikin ai saiku,kawai dai Allah ya tsare mana ku daga dukkan sharri''
murmushi ya saki
''haba mami na,kema fa jaruma ce,kin manta ke ke fede mutum ki ciro abun cirowa ki,mai da na mai dawa ki hadeshi ki dinke ya tashi tsaf yaci gaba da rayuwa cikin ikon ubangiji'
''um um,wannna daban da naku abdallah,a'uzubika bi kalmaatillahit taammaat min kullu ainin lammah wamin kulli shaidanin wa hamma''ta mishi irin addu'ar neman tsari da annabi s a w kewa hassan da usaini r.a
''ameen mami''ya fada don kusan a bakinta ya haddace wanna addu'ar tsabar yi masan da take yi,kuma yasha ganin riba da fa'idar ta

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

ana jibi za'a dauki azumi ta tafi gidan raliya don su tattauna,ba qaramin dadi raliyan taji ba dq jin fitowar abdur rahim da dukkan qarfinshi neman auren aminiyar tata,ta jira har nasir ya dawo tayi mishi bayanin abdurrahim da kwantancan anguwarsu,ya dauka mata alqawarin xaiyi tattaki da kanshi har unguwar ta qoqi don ya mata bincike a kanshi,sosai taji dadin kara da karamcin da hayi mata,sun rabu kan duk yadda ake ciki nan da sati zaya sanar mata,ta mishi godiya sosai,yace babu komai ai an zama daya ya zolayeta da don ma ta qishi ne,dukkansu dariya suka saka da tuno baya da sukayi


kwanki shida kacal ba'a cika na bakwai din ba nasir ya kirata ya mata bayanin abdur rahim bashi da matsala,dukkan abunda ya fadi din haka yake,saidai abu guda bayan kasuwanci da yakeyi din yana da damara wato ma'aikacin tsaro ne,ta masa godiya mai qima sannan suka rabu,data tambayi abdur rahim din dariya kawai yayi yace yana tsammanin bata son auren mai unifoarm ne ya boye mata,bata dauki abun wani seriousd ba duk da ta nuna masa rashin jin dadinta ya kuma nemi afuwarta maganar ta wuce


azumi na da kwana goma ta sanar da abdur rahim ya shirya yazo ya gaida mami,bai musa ba ya amince,ta shirya masa girki na musamman,cikin wani dan kebantaccen gu dake harabar gidan ta ahirya komai,guri ne mai kyau davtsari cike da shuke shuke tamkar qaramin lamvu,duk da cewa daga can bayan gida akwai lambun amma wanna hakanan aka yishi darumfar bunu qwaya daya,qasanta shirye da fararen kujerun roba


mintina goma sha hudu ya rage akira magariba ta shiga wanka,ta ahirya tsaf cikin baqar doguwar riga mai sulbi data wadatu da dutsuna masu sheqi saqar qasar oman,mai kawavta shafa hoda ta zizara kwalli da man lebe,ta taje gashinta tayi acuci da shi daidai lokacin da masallatan garin kano suka  soma kwarar kiran sallar magariba dabinonta dan madina dake cikin qaramin fridge din dakin ta ciro ta ciri uku taci ta ciro ruwa tasha sanna tayi add'ar buda baki,bandakinta ta koma tayi brush hadi da alwala ta yi sallar magaribar,kusan tunda aka fara azumi tare suke yin buda baki gaba dayansu,don haka bakwai na qarasa cika ta sauko qasan


tuni har mami da abida sun hallara don haka ta gaida mamin da yi mata sannu da shan ruwa ta soma sarving dinsu,ta kammala ta ja nata ta zauan,bata kai ga fara ci ba abdallah ya shigo ya ja kujera kusa da mamin yana fadin
''mami ke daya zaki ci ki bar autan naki''
''hmmm su auta manya''abida ta cafe zancan,harararta ya danyi
''kinga bansa da ke ba,wanna magana ce tsakanin d'a da mahaifiya''
hannu yasa cikin plate din chips dinta ya soma kaiwa baki dadin na ratsashi,bai ko kalli farantinsa guda biyu da cup da maryam ta shirya masa ba


sai teburin yayi shiru kowa na harkar gabanshi,cakula kawai maryam keyi don bata qaunar zaman cin abincin nan tare,sam bata sakewa
mami ta dubeta tana goge hannunta da ya dan baci da maiqo da tissue
''amma dai maryam ba wanna ce shigar fita zancan ba ko''
tayi murmushi har dimple dinta na lobawa kanta aduqe
''itace''ta fada kanta asunkuye,kallonta abida tayi ta sheqe da dariya kana tace tab,kallonta take kwaia wadda kanta yake cikin tukunya
''ban me yasa baki wa fuskarki makeup ba ko don kinsan ke din mai kyau ce,kyanki yana qara......''
bata iya qarasa zancan ba sakamon ciko pork da abdallah yayi da chips ya cusa ma mamin a baki
tilas ta karba sai davta fara taunawa ta dubeshi
''meye haka abdallah,dure zaka min''
ya marairaice
''mami baki qoshi ba fa,kuma idan ana cin abinci ba'a magana,ki qyale koma mene sai kin qoshi''
dauke kanta tayo ta dubi maryam
''ki duba kan mirrow dina akwai makevup kit ki dauko min yau da kaina zan miki kwalliyar


raka'a shida kacal ta samuyi sallar tarawih a maimakon raka'a goma sha uku davtakeyi,cikin awa daya saiga fuskar maryam din ta canza,zama mamin tayi sosai ta mata make up,abida kanta mamaki ta dinga yi,haka mami ta iya make up mai ma'ana?haka maryam ke da kyau,tun usuli ita din ba maison cika tarkace bace ta makevup a fuska,wannan kaye kayen sai hindatu,kyan da ta yiwa mamin yasa ta ta gaza barinta sai data mata hotuna,ta yi azabqr fita kuwa ahoton


aka gama kuwa a daidai,don gamawar tasu bai wuce da minti uku ba abdur rahim ya kirata gashi a compound din gidan ya samu shigowa bayan tarin tambayoyi da waya da mami ta yiwa securities din kan su barshi ya shigo
''jeki maza diyata ki shigo da shi''mami ta fada tana maida hijabinta data idar da sallar asham
tana qoqarin fita saqo ya shigo wayarta ta zaro tana dubawa,number din abdur rahim ta gani wanda hakan ya sanyata sakin murmushi ta soma qoqarin duba abinda ya turo mata


''ya subhanallah''taji ance bayan taga inuwar mutum a gabanta,da sauri ta daga kanta kana ta duba abinda taji ta taka
qafafan abdallah ne,taja baya kadan da sauri a tsorace,dawowarshi kenan daga sallar asham,sanye da jallabiya fara sol mai gajeran hannu wadda hakan ya sanya dukka gargasar hannunshi bayyana da hular tashi ka fiya naci itama fara,sai ya koma tamkar wani balarabe,kallonta yake kawai wanda har hakan ya bata tsoro,sexy eyes dinshi ya lumshe bisa fuskarta na aecond biyu ya bude


murya qasa qasa yace
''wacce iriyar makauniya ce ke,ki hau qafafun mutum ki taka saboda rashin kunya,idan baki wasa ba zan targada qafafun''tuni idanunta suka kawo qwalla
''kayi haquri ban kula bane''
ya janye shanyayyun idanunshi ya motsa zai wuce,har ta gifta shi yace
''wannan wane irin sakarci ne kwalliya cikin ramadan a irin wannan time din''cak ta tsaya zuciyarta na bugu
''ina zaki?''
''waje zanje.....baqo......''
bai bata damar qarasawa ba ya daka mata tsawa
''oya,wuce ki koma wannan iskancin ba'a gidan nan ba,idan zaki tara mazan ki bari sai a naku gidan''
jikinta na rawa ta wuce ya take mata baya


mami data hangota tace
''a'ah,ina baqon?''kasa cewa komai tayi sai satar kallon abdallah da yayi kicin kicin da fuska ya kuma basar kamar bashi ya korota ba,ya samu gefan mamin yayi zamanshi yana shan ruwan bunun da yasha kayan qamshi wanda mamin ta zuba tana jira ya huce ta sha


''kai abdallah,kai ka dawo da ita ko?''
''eh mami dare yayi me zata fita waje tayi taje ta dauko mana magana?''
''kaga malam baqo tayi yana nan compound ba wani gu zata ba''
''ok,wannan stupid din ita yake jira?,to ki fita mu gani,mami baza a ja mana magana ba agia,ta kwatanta mishi gidansu suje can su hadu''


''kai dakata!banason iskancin banza iskancin wofi,uwarta ne kai ko ubanta da zaka hanata fita ga mutumin da zai aureta,ina cewa jiya kasa bacci kayi sai da ka tasheni ka gayamin rana ita yau akai maka kudin aure?shine zaka hana wasu saboda tsabar son kai,to wallhi ahir dinka ka fita daga sabgar maryamu indai kanason zaman lpy''
saukowa yayi qasa ya sanya gwiwoyinshi a qasa  ya kama hannayen mamin
''kiyi haquri mami,wannna ne karo na qarshe insha Allahu da zaki sake samuna da irin wannan laifin,ki yafe min banason shiga fushinki,cikin wata muke mai alfarma''


Sai da ta juya tace da maryam taje ta ahigo da baqon sannan ta kalleshi
''idan kana haka abdallah sai ta dinga jinta daban acikin mu,yin hakan tamkar takura ne agareta,ka gyra pls my son''
''insha Allahu mami''ya fada sannan yayi kissing bayan hannunta


shigowar abdur rahim ya sanya abdallah fita,a nutse suka gaisa da mamin,sosai ta yaba da hankalinshi,shi yake sanar mata maryam tace ita zata fadi ranar da za'a kai kudin aurenta gidansu,ya zabi kwana bakwai tace yayi kusa
murmushi mamin tayi
''maryam manya,kwana bakwai din yayi,Allah ya nuna mana''cikin farinciki walwala da mutuntuna juna suka rabu da mamin ya nufi inda maryam tayi masa masauki


''me yasa abdul kaqi cin komai ne''murmushi ya saki kana ya miqe tsaye yana duba agogon hannunshi,ya dauke idonshi daga agogon ya dan kalli bayanta kadan yasake dauke idonsa
''zan wuce ne maryam,lokaci yayi sai wani jiqon''ya fada agaggauce,a hankali ta waiwaya ta maida idanunta inda taga yana kalla din,abdallah ne tsaye saidai sam ba sashen da suke yake kallo,tuni har abdur rahim ya soma tattakin barin gurin,ta bishi a baya don masa rakiya,ya tsaya cak kana yace
''na gide,bana buqatar ki wahalar min da kanki ki koma ciki,sai haduwa ta gaba?''ya fada cikin sigar tambaya yana daga gira,kafadarta itama ta daga sukayi sallama ta juya don komawa mazauninsu na dazu ta kwashe kayan data shirya masa duk da bai taba komai ba face ruwan,duk da ya bata uzirin cikinshi a cushe yake baya iya cin komai sai da sahur amma bata ji dadi ba


abdallah ta taras yayi daidai yana kwasar garar abinshi,bata ce komai ba ta juya ta bar gurin ta shige bangaren mamin



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*

         ▶3⃣3⃣

💞😍💞😍💞😍

*_godiya ga masoya na_*🙏🏽👩‍❤‍👩
*_masu qaunar rubutuna_*💞✍🏽
*_qaunar da kuke min bazaiyu na manta da ku ba,na yaba qwarai da gaske_*😃😍

*_gaisuwa ban girma da jinjina mai qima ga_*

*huguma novels room and huguma conversation room*

*maman aysha novels group*

*hausa novel group by umar dalha 1&2*

*zama na amana group facebook*

*khafinga group 2012 class*

*gaisuwa kai tsaye zuwa ga GARKUWAR ABADAN SISTER RABI'ATU HARUNA*😄😄

*Allah ya barmu tare ya samu cikin masu son juna saboda shi da zuciya guda ameen*
*_rabbanag fir lana wa li ikwaninallazina sabaquna bil eman wala taj'al fi qulubina gillal lil lazina amanu rabbana innaka ra'ufur rahim_*🙏🏽





Sau biyi tana zuwa dubawa taga ko ya kammala sai tazo ta tarar bai gama ba,sai a zuwa na ukun ya sameshi ya ture kwanonin gefe alamun ya kammala kenan,bata ce da shi komai ba ta soma hada plates din guri guda tq zuba cikin kwandon
''ji mana''taji yace da ita,a hankali ta dago kai suka jada ido,ya kafeta da zaratan idanunshi sai ta kau da kanta gefe
''idan kin koma kuma ki sake hada ni da mami na kice ni naci abincin,ko da yake ko kin fada din dama ai aikina aka dauko ki yi ba wai ki dafawa wani qato ba,a qa'ida ma idan kika kuma gigin yiwa wani girki ba da izini na ba ma a albashinki''


ya ture kujerar da yake kai baya ya miqe ya kewayeta ya wuce,ta biahi da kallo tsanarsa da tsanar halyenhi na takura matsi da girman kai na addabar zuciyarta,sai da ta tabbatar ya ahige bangarenshi sannan ta shiga nasu bangaren

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

da yake azumi ne qarfe tara ta shirya taje gida,ita da hindatu suka tattauna abinda za'a shirya don 'yan kawo kudi da zasu zo jibi da safe,ruwan roba ta siya carton biyar na lemo ma haka,sai maltina itama carton uku,kujerun da aka fidda dakin mama su aka maida sitroom dinsu wanda rashin wadata yasa yake fanko babu komai a ciki,babu abinda kujerun sukayi tunda ba'a dade da yi musu kwaskwarima ba ta qarin katifa da canza yadin kujerar kuma ba yara gareta ba balke su lala ce da wuri,ko dama can ita mamsn mai tsumi tattaku da tanadi ce,ta siyi leda da labulaye duka aka sanya,sai sitroom din yayi kyau daidai talaka,tuni dama kayan gadon maman aka shiryashi bedroom din baban sun zama nashi


muqullin ta danqa hannun hindatu don tana jin su kula na rawar kan yau a ciki zasuyi zance don duka babu wanda yasan me za'ayi da dakin aka gyara shi haka,wannan rufewa fa da tayi sai taso zama dan zani sukayi dafifi a tsakar gidan suna basu amince ba ai gida dai na ubansu ne babu wanda ya isa ya musu shamakivda wani bangare na gidan,shigowar baban ya tambayi ba'asi wannan karon hindatu ce tayi uwa tayi makarbiya ta masa bayani


to shi din ma wannan karon bai basu goyon baya ba yadda suka saba samu,hakab ba qaramin qullacinsu maryam ya sake sa musu ba,da azahar sukayi sallama don tana so ta leqa raliya,mama ta dakatar da ita tana fiddo da dararen borikan fenti uku daga uwar dakanta 
''me wannan a ciki mama?''ta fada tana budewa
botikin farko alkaki ne a ciki
na biyu dubulan
na uku nakiya ce


ta dago ta dubi maman
''duka na meye wannan?''
''saboda 'yan kawo kudin nsn nasa akayi,kinga za'a kuma fita kunya ko''qauna da tausayin mamanta ya sake shigarta,Allah sarki mama,farincikin dake zuciyarta Allah kadai ne ya sani,a haka ma tana alkunya tana danne farincikin nata sabida kara irin ta dan fari


''Allah ya saka da alkhairi mama sunyi,Allah ta qara arziqi,amma mama banason ki dinga tatse kudin hannunki haka,yanzu wannan kayan ai sunci kudi da yawa''
''ai aikina ne maryamu,idan da da akwai cikakkiyar wadata ma baki cancanci ki kiyi komai ba''

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

qarfe biyu da rqbi suna falon raliyan su biyu sai fadil dake kwance kujerar geansu yana baccinshi hankali kwance,cikin farinciki raliyan take tamkar ma itace maryam din
''wani hanin ga Allah baiwa ne maryam,yau gashi Allah ya musanya miki da jabir,sun sanya bawan Allah a tsaka mai wuya har yau yana cikin damuwa,shekaran jiya yazo gidan nan yake tambayar abban fadil ke,yana son ya nemeki amma wai kunyarki yake ji,shegiyar yarinya marasa tsoron Allah itavda uwarta,duk jabir ya fita hayyacinshi kmar bashi ba,roqon Allah ne masa ya dawo cikin tuna ninshi cikin lokaci qanqani haka''


ajiyar zuciya ta saki
''duk wanda ya debo da zafi ai bakinsa raliya,nikam wanna ya riga ya wuce tamkar wani mafarki na daukeshi''
ta zura hannunta cikin jaka ta soma laluben wayarta dake ringing hade vibration ta cirota,kiran abdur rahim ne tasan shi dinne tun kafin ta ciro saboda special tune da ta sa masa
''ranki ya dade duka yau ban jiki ba ko cigiya ta baki yi anya kuwa''ya fada cikin salin zolaya bayan sun gama gaisawa
murmushi ta saki
''yau na tashi ne cikin sabgogi amin afuwa''
''ayyah,da kinyi magana ai da nazo na tayaki,ina fata basu wahalmin da ke ba''
''alhmdlh tunda tuni na kammala yanzun nake shirin in koma gida''
sai ya danyi duf kana yace 
''me yasa baki tambayeni ba da zaki fita,saiki dinga fita kanki tsaye maryam ana ganemin ke''
murmushi ta saki
''mantuwa nayi ashe fa yanzun ina da miji,baza'a sake ba''



''matsalar ban iya fushi dake maryam,yanzun dai sgikenan kimin kwatancen gidan da kike zanzo yanzun nan na maidake gida,naga hadari na haduwa kada ruwa ya dakarmin ke ya barni da zazzabi''
ba qaramin nishadi maganar ta saka ta ba ,take ta masa kwatancen inda take din sukayi sallama ta ajjiye wayar
suka hada ido da raliya tare suka saki murmushi
''gaskiya na fuskanci ba qaramin ji dake abdul din nan yake yi ba,Allah ka nuna mana wannan rana''
dariya tayi gami da dukan gefan cinyar raliyan tace
''har ya kama qafar nasir abban fadil''suka sake sa wata dariyar raliyan na fadin haba wane mutum


minti goma wayar ta sake kadawa,abdur rahim tayi tsammani shi dinne kuwa
''kiyi min afuwa maryam zuwa na bazai samu ba wani aiki ne na gaggawa yanzu aka turamu dole kuma na kasance aciki idan ba haka ba akwai matsala,amma kiyi sauri don Allah ki koma gida hadari ne sosai a garin kada ruwa ya tabaki''
macace mai sauqin kai da fahimta don haka tace masa
''babu damuwa Allah ya bada sa'a''
ya saki ajiyar zuciya
''na gode da kika fahimceni sai munyi waya''


ta dubi raliya bayan ta miqe tana hada jakarta,ta tavbata hadarin ne don tuni garin ya lumshe har ta soma jin quginsa
''wucewa zanyi raliya an samu matsala abdul bazai samu zuwa ba aikin gaggawa nebya taso muau yanzu a office''
''a'ah,yanzu da uban hadarin nan zaki tafi?ki jira abban fadil ya dawo sai ya kaiki''kama baki tayi bayan ta gama rolling mayafinta
''girkin kuma na barwa wa?,so kike kenan yau abdallah ya samu nayi ko,cikin watan nan ya tairi wani abu ko kunu ne idan bani nayiba sai ya gane,yanzun sai yace a salary dina''
ta dage girarta sama
''haka ne fa,muje in taka miki,amma jirani in shiga in fito''cewar raliyan tana shigewa bedroom dinta na qasa


kwalbar turare ta fito da shi hade da baqar leda qarama ta miqa mata
''turaren da kike ce min kina son irinsa nasa abbn fadil ya aiyo manaamma kiriqe da kyau saboda yana leeking,sai bra din nan qualitative one da mukayi maganarta jiua da muka fita na siyo mana''
''kai qawata,bani da bakin magana,Allah ya raya mana fadil ya bar mana zumuncinmu,ya tsone idon maqiya''
''ameen raliyan ta fada tana bin bayanta,haduwar jadarin ya sake rudata har ta kasa saka kayan cikin jaka,a bakin get suka rabu ta soma sauri gashi ita ba gwanar saurin bace


har ta kai bakin titin su raliyan bata ga abun hawa na haya ba,kusan dama haka yanayin unguwar tasu yake ko jama'a baka fiya gani ba,bare yanzu yanayi na azumi kowa yayi likimo cikin gida,hankalinta bai daga ba sai data tsaya atitin,taga motoci dake karakaina ma baifi ka irga au ba,adaidaita uku ne suka wuce biyu daga cikinsu duk cike take da mata dayarkuma maza ne cike har gaba kusa da mai tuqin,a hankali iska ta soma kadawa mai qura alamun dake nuna hadarin ya gama nuna a sama sauka kawai yake da buqatar yi,addu'a kawai takeyi cikin zuciyarta a haka ruwan saman ya soma sauka 


tsamo tsamo tayi don ya fara jiqata ta soma hade jikinta guri daya,motoci uku ne qirar land cruisser baqaqe wul hatta da glass dinsu suka tsaya a gabanta,gabanta yayi mummunan faduwa,tuni ta somacwaige waigen neman inda zata fake idan gudun ceton rai ya kama


glasan motar farko nagaba mazaunin mai tuqi suka sauka qasa,hassan ta gani daya daga cikin direbobin abdallah,sai a likacin taji ta samu nutsuwa,murmush yayi nata itama ta maida masa
''madam yi sauri ki shigo kina ta jiqewa''
taji dadi sosai kuwa,da saurinta ta qaraso ta bude mazaunin gaba ta shiga tana fadin
''na gode qwarai,amma ba tare kuke da og.....''
''me muka tsaya yine hassan?''
muryar data fito daga sit din baya ta katsse mata sauran magan
''nun dauko madam ne''ya fadi yana qoqarin tayar da motar
''waya baka izini ko tsabar iya sayawa mutum raini ne?''
''sorry sir,naga gida zamu ne,kuma itama gidan zata.....''
''ni na gaya maka haka?''ya tambaya murya a kaurare


''am sorry sir naga madam nada kirk.......''
abdallah ya katseshi ta hanyar fadin
''mtswee,shutup malam sauka ka barmin mota ka koma motarsu auwal''
da saur maryam ta kuma riqe jakarta wadda garin saurin ledar hannun ta har ta subuce ta fadi qasan motar bata sani ba
''kayi haquri,ni ya kamata na fita ba hassan b.....''
''hey,bana son iyayi shi nace ya fita din bake ba''


tuni hassan ya bude motar ya fice ganin hakan ya sanya itama ude na bangarenta tana qoqarin fita
''idan kija sake kika fita sai na karya sillar qafar taki inga ta rashin kunya''
tilas tana ji tana gani ta koma ta zauna
''rufemin mota malama don idan ruwa ya jiqata sai kin busar da ita tas a yanzu yanzu''taja qofar garam ta rufe cikin haushi,tana iya gano ragowar motocin suka zagayesu suka wuce


mujallar da yake research kanta tun dazun ya sake janyowa ya bude yaci gabavda karuntunshi hankalinshi kwance tamkar yana cikin dakinshi ne,sanyin a c din motar ya soma takurata gashi tayi mata kusa da yawa,tuni kanta ya fara sarawa ta qudunduna gu guda tarw da jingina jikin makarin motar ta lumshe idanunta tana ci gaba da jin yadda ciwon kan ke dada yin gaba


'yar qaramar qara taji tamkar ta waya ''siiit''a hankali sai dumi ya maye gurbin sanyin ac din,bata tantama maidashi akayi banaren dake bada dumi,duk da taji dadin hakan amma babu abinda ya rage mata daga ciwon kanta


mintina kusan arba'in basu tafi ba kamar yadda ruwan bai tsagaita ba,ta bude idanunta a hankali ta miqe ta zauna daidai,a karo na biyu ta kuma sanya hannunta kan mabudin qofar don ta qudiri aniyar ficewarta zatayi kome zaiyi mata saidai yayi,saidai taqi buduwa da alamu an saka lock,ya ajjiye mujallar hanun nashi ya jawo baqin space ya mannawa idanunshi sannan ya bude 'yar qaramar kyakkyawar baqar lemar dake kusa dasji ya fito ya dawo mazaunin driver


amadadin ysyi hanyar gida sai taga sun csnza titi,batason kulashi amma ya zama mata dole
''ina cewa gida zammu ko''
banza yayi da ita,ta qufula amma bata fasa sake fadin
''girki fa na can na jira na gashi yanzu hudu harda rabi''
''karki cika ni da hayaniya,baki da zance sai na girki kamar dinshi aka halicceki,ai bake daya kika iya girku cikin gian ba ko''
ya fada udanunshi na bisa kwalta,bata sake tofawa ba ta maida kanta gefe daya


cikin wata unguwar taga sun shiga wadda take kama da tasu mamun wajen kyau da tsari,qofar wani katafaren gida taga ya tsaya,ita kanta sai da ta bi gidan da kallo,duk kyau na gidansu mamin wanna ya dokeshi,bude motar yayi yay ficewarsa ba tare da da yace mata komai ba


zaman kusan awa guda da rabi tayi kafin ta sake ganin fitowarsa,a dan bakin qofar ya tsaya kafin ya qaraso tana iya hango jikin wanda suke magana tare,da alama macece don ga gefan mayafi nan,ba qaramar qufula tayi,ba cikin zuciyarta
''zance yazo kenan ya barni a mota ko yaya?''ranta sai ta kuma ji ya baci,ya bude motar ya shigo
''zance da ranar Allah cikin watan azimi,wanne wane irin tsari ne''ta ja tsaki,saidai cikin subutar baki tsakin ya fito


juyowa yayi kalleta
''wa kike ma tsaki?''sai ta juyo tana kallonshi itama
''idan kika sakemin tsaki sai kin fita min a mota tunda bada kudinki aka siya ba''sai idanunta suka wal 
''daina kallona''ya fada bayan ya dauke kanshi da sauri daga cikin idanunta
''kada ki cuceni''ya fadi can qasa yana lumshe idanu tarw da yiwa motar key,bata kawo komai cikin ran ta ba ta dauke idonta cike da jin haushinsa

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

Ashirin ga azumi mami ta bata kayan sallarta,a dinke suke dinki ne na gayu wadanda suka mata cif a jiki,atamfofi uku lace daya material daya,sai codelace shima daya,duka atamfofin dogayeb riguna aka mata don mamin ta fuskanci tana sonsu,jaka biyu takalmi biyu sai mayafi biyu hijabi daya,sannan tace ashirin da biyar ga azumi zasu fita sai ta zabi fashion da zatayi amfani da su,bata fasa yiwa mami gidiya ba duk da ta gaya mata diyarta ta yiwa no need tace sai ta gode mata,godiya kuwa ai tamkat wajibi ne tayi mata don ko daga gurin mahaifinta bata taba samun makamancin irin wannan gatan ba


abida kam akwati guda medium abdallan ya hada mata bayan takurawar da mami tayi masa kan ya hada matan,don shi totally baiyi niyyar mata komai ba


cikin irin kyautar da mamin ke yawan yi mata ta fidda atamfa biyu ta baiwa tela ya dinkawa mamanta,ta siya mata mayafi takalmi da jaka,albashinta na watan ciki ta cira ta baiwa hibdatu tayi siyayyar salkarta babanra ma shadda ta siya masa kala biyu ta hada mishi da kudin dinki da takalmi da hula daidai,kai kada ksso kaga baqinciki,ina wuta a saka maman da iyalsnta,godiya kam gun baban ba'a magana
''sai yanzu nasan na haifa,yanzu ne na fara cin albarkar haihuwa''baban ya fada lokacin da yake gwada hular da ta kawo masan


''oho dai,wlh malsm ka guji ranar da zaka karbi shegen jika cikin gidan nan,ka gama cin dadin dai wuyar na tafe,shi yasa gata nan har yau babu mashinshini yo kowa yasan aikin tsiyar da take aikatawa''
inji baba hadizar don daga ita har huwailsn babu wanda yasan da zancan kawo kudinta,ranar kamar Allah ya kadasu duk suka fice unguwa suda qananun 'ya'yansu,huwaila tayi gurin boksn boginta ita da uwale hadiza ma ta bazama ga nata bokan,sunacan yawon asara har yan kawowar suka tafi,'yammatan da zawarawan kuma na nade a gado suna bacci don wadan nan sukan kai sha biyu da rabi zuwa daya basu tashi ba


huwaila kuwa cewa tayi''mu namu ai shegensu mukayi muka shigo dasu gidan ko,ko ince tsinannu ne''shidai babu wadda ya kula cikinsu ya kwashe kayanshi ya shige dakinsa

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Qarfe goma suka dawo daga siyan kayan kwalliya da suka fita harda mami da abida,tayi sallama da mamin ta shige dakinta don da wuri take son yin bacci ta tashi akan lokaci sallar dare saboda yau an kai azimi ashirin da shida zuwa anjima daren ashirin da bakwai zai shi daren da akesa ran dacewa acikinsa


zuwa sha daya na dare takammala komai ta haye gado bayan ta gama addu'o'in kwanciya ta karanta saqon abdur rahim fuskarta fal da murmushi,kusan cikin watn gaba daya wayarsu bata fi aqirga ba sai tex akai akai,yace shikam bazai iya jurar jin muryarta ba,tana shirin kashe wayar kira ya shigo,ta zubawa lambobin ido tana kallonsu,tana tunanin inda ta taba saninsu


tabbas ta taba sanin numbers din,har wayar ta tsinke ta kasa dagawa,second biyar tsakani wani kiran ya kuma shigowa,jiki babu qwari ta sanya hannunta ta daga ta kara akunnenta
''assalamu alaikum wa rahmatullah''itace abinda yavdaki sodon kunnenta,mummunar faduwa gabanta yayi,babu inda zata ji muryar ta kasa ganeta,amma tan tama take kiran nata ne ko batan kaine,ta sake cire wayar akunnen ta tayi ta kuma duba screen din wayar mai kiran dai na bisa layi kuma ita din aka kirar 




*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*

          ▶3⃣4⃣

*_daga abu hurairah Allah ya qara yarda da shi yace:an tambayi  manzan Allah s a w wanne musulmi ne yafi falala?,sai yace:wanda musulmi suka kubuta daga sharrin harshensa da sharrin hannunshi(ma'ana bai cutar da kowa da harshensa ta hanyar magana,ko kuma da hannunshi ta hanyar ayyukansa,daure ka/ki zama daga cikin musulmin da suka fi falala,abun ba wuya 👌🏽matuqar ka jajirce kafi qarfin zuciyarka,Allah ta bamu iko ameen)_*

''wa alaikumus salam''ta fada asanyaye
shiru ya dan ratsa tsakani kadan
''da alamu baki ji dadin jina da kika yi ba ko maryamu?,hala ma kin manta da ni?''
''ko daya,ban kuma mance da kai ba''
''da fari kafin nace momai maryam,nasan bani da kalmomin da zasu gamsar da ke gurin ban haquri,amma duk da haka ina roqarki don Allah don annabi ki yafemin,ba da gangan abinda ya faru tsakaninmu ya faru ba,bada sani na bane maryam,ki yafewa jabir masoyinki''

tausayinshi ya kamata ta dan kumshe idonta kadan ta bude
''kada ka bata bakinka gurin bani haquri jabir,tuntuni gaskiya ta dade da yin halinta,anyi walqiya komai ya bayyana''
yaja dogin numfashi kana ya sauke ajiyar zuciya
''alhamdulillahi rabbil aalamin,dukkan godiya ta tabbata ga Allah,babu shakka ke din jaruma kuma nagartacciyar masoyiya ce,bana tantama zaki zama mace ta gari uwa ta gari gurin 'ya'yanta,bazanyi nauyin baki ba ba kuma zanyi qauro ba maryam inason ki bani damar fitowa neman aurenki karo na biyu,tare da cikakken fatsn babu wani da ya sha gabana''

sai da gabanta ya fadi,tayi shiru tana son daidaita bugun zuciyarta sannan daga bisani tace
''qaddara ta riga fata jabir,Allah ya qaddara run da dama ni ba matarka bace,hakaza matar mutum kabarinsa,bai wuce sati biyu da kawo kudin aure na da wani ba''
''la haula wala quwwata illah billah''ita ya dinga maimaitawa tsawon mintina biyar
''yanzu kina nufi maryam na rasa ki kenan,zaki auri wani na?,ki bani dama maryam mai rabo shi zaya samu tunda har yanzu ba'a daura aurenku ba balle kice kin haramta a waje na''

''kai mai sani ne jabir bakin gwargwado,ka sani cewa nema akan nema haramunne,baya ga haka ma daga ni har kai babu wanda aka bawa qudirar rubuta kundin qaddararsa da kansa,kuma buwayin sarkin dake rubuta msna din mai dumbin adalci ne,babu yadda za'ayi ya rubuta mana abinda zai zama zalunci ne a garemu''
''haka ne maryam,alhndlh Ala kulli hal,na gode maryam,na gode matuqa da gaske,bazan taba iya mantawa dake cikin kundin rayuwata ba,na barki lafiya''

tafi minti biyar riqe da wayar ra kasa ajjiyeta,tausayin jabir dinne kadai ke dawainiya da ita,babu shakka bazata iya manta dumbin alkhairansa gareta ba,koda ta tashi sallar dare bata mantashi cikin addu'o'inta ba,ta roqa masa alkhairi mai yawa kamar yadda a baya yayi nufinta da shi

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Washegari mai lalle tazo yi musu,babu yadda mami batayi da abida ba amma qememe taqiya,tabe baki tayi
''nifa mami ba za'a batan hannu ba hakakawai da wannan abun''
''banda abinki ai shi jan lalle ga mace sunna ce baya ga haka ma ado ne''inji mami
ta sake ya mutsa fuska
''um um,a muku dai,mukam a turkey bamu irin wannan abun''ba wanda ya kuma tanka mata cikinsu nanta kwanta tun tana kallin qunshin har bacci yayi awon gaba da ita

kamar ko yaushe suna table don cin abincin buda baki u ukun maryam mami da abdallah,ta zubawa mami da abida ta soma zuba na abdallah,ya dago da sauri don yaga iya wanda zata zuba din don vaiso ta cika masa plate kamar na jiya,idanunshi suka sauka kan zara zaran fararen yatsunta da qunshin yayi kwanciyarshi kai ya sake fidda kyawun hannunta,farar fatarta ta sake shar

Zanen ya burgeshi duk da ya saba gani lokaci lokaci gun maminshi,duk kuwa sanda tayi din tun yana yaro ya dinga cewa tayi kyau kenan,maryam ta janye hannunta bayan ta ajjiye nasa plate din ta koma mazauninta,sam babu wanda ta lura sai abida,kishi ya cikata har taji kamar ta guntike hannun maryam din,ya janye idanunshi daga kan lalken suka hada udanu da abidan
''ke ina naki kwalliyar?''
''abida kam ai ta manta gargajiyar al'adarta,tace bataso bata mata hannu za'ayi,bayan shi kanshi ma ganine''
caraf abidan tace
''naga kamar ya burgeka ko,ba damuwa sai amun gobe''

tabe baki yayi ta daga kafadarshi hade da ware ya tsunshi
''no,idan ta nine kada ki sauya ra'ayinki ki bata hannunki''ya qarashe zancan yana jan plate dinshi ta soma cin abincin

zahariyya ce tayi sallama hannunta duka biyun dauke da foodflask masu azabar kyau da tsada,fuskarta a washe da faea'ar data qiqirarwa kanta ta qaraso gun,ta fara da dora flask din duka saman teburin wadanda tunda aka shigo dasu maryam take jin matsananciyar faduwar gaba ta kuma kasa daina kallonsu,mami ta gaida kana abdallah,tsakanin ita da abida kuwa babu wanda ya kula wani kowa na ji da danbanzan girman kanshi rawanin tsiya

''favourite food na ya abdallah nene ra tashemu sai da mukayi masa wai yadda ta saba sanda alhj baaba(alh abdulkareem mai nasara kenan mahaifin abdallah)yana raye wai yanzun ma ba zata fasa ba''
murmushi mami tayi tana janyosu gabanta tare da fadin
''kai kice mata kam mun gode qwarai,kamar kuwa tasan yau bamuyi girki ba nace maryan ta bari sai sahur aikin yayi yawa''inji mami sanda take hude flask din,rake kuwa qamshi ya cika gurin
''ki mata godiya''inji mami sanda zahariyyan ke nufin fita
''zata ji kam''ta amsa mata lokacin da take qoqarin sanya qwayar idanunta cikin ta maryam a fakaice,cikin sa'a kuwa suka hada idon,wanu mummuna kallo mai cike da gargadi da jan kunne tayi mata kana ta fice

Gaba daya ta saki cin abincin ta zurfafa cikin tunanin yadda zata salwantar da abincin ba tare da tabar kowa ya dandana ba,tayi imani komai zasu mata ba zata iya bari tana gani gaban idonta wannan ahli su salwanta ba,qarshen butulcin da zata musu kenan wanda ba zata iya yafewa kanta ba har abada,cikin haka taga mami na kiciniyar bude food flask din zata zuba,da sauri ta miqe tana fadin
''mami barshi in zuba miki mana ''tuni har ta isa gabanta ta karba don kada ta yanke mata hanzari tace ta barshi,ta jawo flask din miyar gaban table din sosai ya zama rabi kan tebur din yake zaune rabi kuma free ba matokari,sai ta jawo na abinci ta bude,da plate a gabanta amma sau tayi dabarar miqa hannunta tavdauko na can sashen da abida ke zaune

Tana daukar plate din ta sakeshi kan flask din miyar take nautin tangaran din ya rinjayeshi sukayi qasan table din suka tarwatse kan tiles,tangaran din ya koma piece,taja baya da sauri tana salati tate da kallon gun da abincin suka kife
''subhanallahi ya haka maryam?''
''for god sake mami yanzu wannan wane irin kidahumanci,ita din qaraman yarinyace da zata kifar da abinci flask biyu,kayi magana kuma yanzun mami ta ji haushinka ta saka a black list''ya qarashe maganar cikin bacin rai yana yayyarfa hannu da jujjuyawa hagu da dama kan kujerar da yake zaune

harara ta balla masa sannan ta kalli maryam 
''ina fata baki ji ciwo ba maryamu''
kai ta gyada zuciyanta na wani irin gudu gefe daya kuma tana hamdala ga madaukakin sarki da ya bata nasara a sauqaqe ta rabasu da abinda zaya hallakasu,ita ta tsaya ta gyara gurin duk da momi tace ta bari sai ta huta tukyn amma sam ta qiya,bazata iya ba don ko quda bata fata ya dandana abincin,balle ma ta tabbata ban da awa biyu ko uku indai da gubar abincin zai fara ratattakewa

ta gyara gurin tsaf ta kwashe bayan ta rage kadan ta samu yar roba ta zuba hade da miyarshi ta shige da shi dakin gadonta ta tura ahi qasan gado,sai da ta gama komai kafin ta kwanta ta jawo robar don dubawa,cikin awa uku abincin ya fita kamanninsa kamar wancan,batasan lokacin da hawaye suka soma zuba daga idonta ba

mutum abun tsoro Allah abun tsoro
yanzu dan uwanka bil'adama kake da buri yaci wannan abun?
waishin wanne rin laifi ne abdallqh ya yiwa mutanen nan ne haka da zafi da suke da burin rabashi da soron duniya?
sai kace mudin an mana wahayin tabbata acikinta?
kwana nawa ne kaima ka hada ya naka ya naka ka qara gaba?
koda shekara miliyan zakayi wataran dai sai sun qare din ka tafi.
itakam ko kadan batq ga abun morewa ba wajen cutar da wani bayan ka san cewa Allah bazai taba qyaleka ba sai yabi kadi,duk wanda yaci nanin nanin dole ta cishi

cike da kasala da mutuwar jiki ta shige toilet dinta tayi plushing din duka abincin ta wanke robar ta wullar a dust bin

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Sallah bikin daya rana,cike da walwala farinciki bikin sallah ya soma gudana cikin duniyar musulmi baki dayanta,sai a lomacin mayama ta dinga ganin dangin su mami da na mahaifin Abdallah,don kusan kullum ne sai sunyi baqi,saboda haka bata samun zama aosai,damuwarta daya ma kada abdur rahim yace zaya zo ya samu bata da lokaci sai gashi bai ma nemi zuwanba iyakaci waya sai saqon,barka da sallah daya turo mata na credit din dubu goma yace kuma ta jirayi kayan salarta duk ranar da zaya zo

Ta fuskanci ba kadan bane maso sun abdallah cikin danginsa daga na mamin har na abbaanshi,kishi ke hana abida zama ciin gidan tayi ficewarta yawo sai dare
''rashin sani yafi dare duhu''maryam kan fadi hakan cikin zuciyarta ko kuma tace
''bonono rufin qofa da barawo''a duk sanda taga abida na wannna haukar kishin nata don bata da masaniyar kai kudi abdallah daga ita har zubaidan bare salma da saddiqa da bama ganinsu ake ba,har ga Allah tausayinta takeji kan fadawa son botsatstsen mutum irin abdallah,wanda koda yana sonki zaki sha wuya da shi bare kuma baiyi da ke a ganinta

hudu ga salla suka fara samun sararawar baqin duk da ana cikin dai hidimar sallah da shagulgulanta
da la'asar ne babu dadewa da gama salla wayarta ta fara ringing,tana kan cinyarta din haka ba jinkiri ta daga,muryar jabir ta tsinta yana mata sallama,ta amsa masa kana suka gaisa amutunce
''mai yayi zafi haka ido zaici wuta maryam,a qalla dai ai ko barka da salla a kirani ayimin''
ta dan saki murmushi
''kayi haquri,na ahiga sabgogi ne da yawa,ayyuka sun kacame min kusan yaune ma kadai na dan samu kaina''
''gaskiya ne,ai manya dama sai da uziri''dariyar zolayan da yayi mata tayi,kafin tace komai ya dora da fadin
''ko zan iya ganinki,maryam?''tavdan fiddo ido waje kamar yana ganinta
''yanzu?''
''eh idan da zan samu yau din da nace miki na gode,amma da zakimin alfarma da sai mace miki mu hadu gobe''

tunaninta daya ina zata ce mishi su hadun?,sam bata da sha'awar kawoshi nan gidan kamar yadda ko kusa ba zata yarda su hadu gidansu ba
ajiyar zuciya ta saki
''babu damuwa,muna iya haduwa gobe kamar hudu na yamma a gidan zoo ko?''
''kin ko san a itin kwanakin nan cika yake,anya zamuyi magana anutse kuwa?''
''eh nafison gurin jama'a din ai,kuma akwai bangaren da zamu iya zama da babu cikowar''
''shikenan babu damuwa na gode,amma baki tambayeni,mai yasa nake da buqatar mu hadun ba''

murmushin ta kuma yi
''a tun sani na da kai da alkhairi,na sanka,don haka yanzu bazan canza in maka zaton sharri ba,kaga kenan ina tsammatar jin alkhairi ne daga bakinka''sosai yaji dadin irin shaidar da tayi masa,har yau bai fasa yaba kyawawan halayen maryamu ba,kowa tana masa kallon mutumin krki ne kamarta,hakanan tana kowa kallin mai kyakkyawar zuciya kamar yadda ita din take

🎄🌲🎄🌲🎄🌲

Qarfe hudu suka fita daga gidan zuwa gidan zoo din ita da hindatu,dukkaninsu cikin kwalliyar atamfa suke riga da skert,sunyi kyau kam masha Allah

a can suka taddashi har yana zolayarsu sai yaci tararsu sun mishi african time,yayi kyau abinshi cikin dinkin kufta ya dswo jabir dinshi na ainihi,kyakkyawan matashin saurayin nan mai yawan ado da fara'a jabiru

gurine kebantacce dake can cikin ainihin gidan ajiyar namun dajin na garin kano,tamkar lambune ska yishi na musamman kudin shigarshi ma daban yske kusan ba kowa ne ma yasan da gurin ba,kujera ce irin ta siminti suka zauna a dayan shima ya zauna a dayan,sabuwar gaisuwa suka sake,maryam ta dubi jindatu tace dan bamu guri kadan to tace kana ta miqe,jabir din yace
''ai da kin qyaleta ma don maganan ya shafeta''ta yi gaba amma ta jiyo abinda yace din sai gabanta ya fadi hakanan

''maryam,haqiqanin gaskiya na yaba da kyakkyawar tarbiyyar da kuka samu,sannan nayi baqinciki qwarai da gaske da rasa ki da nayi duk da nasan cewa komai qaddara ce daga ubangiji,saidai ina kwadayin hada iri da ku maryam,ina neman wata alfarma guda daya,Allah yasa wannan karon bazanyi failing ba''
cikin tattara dukkan hankalinta a kanshi tace
''babu wata alfarma da bazan iya maka ba indai ina da iko kima bata keta haddin shari'a''
''be keta ba maryam''ya fada yana murmushi wanda ya qara masa kyau da kamala
''so nake ku bani hindatu''

idanu ta zazzaro tamkar taga wani abun tsoro idanunta kan jabir din
''jabir........shin ka manta alaqar dake tsakanin hindtu da jamila ne?,ya da qanwa ne fa?''
''koda na taba sanin jamila a matsayin diya mace hindatu bata haramta gareni ba tunda igiyar saki ta raba tsakaninmu balle babu abinda ya taba shiga tsakanina da ita na auratayya,yadda aka kaimin ita haka na dawo musu da ita,so kika babu maganar janamin auren hindatu kenan''

kai ta girgiza''haba jabir,yau ko maqota muke mu da su jamila ai duniya ta zagemu balle iba daya''
''ya kamata kiyi amfani da ilimin da Allah ya huwace miki,ki dinga saka addininki gaba da al'adarki,babu wani abu da ya jaramta min auren hindatu koda kuwa ke na aura matuqar mun riga da mun rabu''
cikin girgiza kai tace
''haba jabir,amma dai ai ana barin halas don kunya''

take yanayin fuskarsa ta sauya
''gwara maryamu ki fito kanki tsaye kice min ba kyason tarayyata da hindatu,gwara ki cemin jabir ba zamu baka hindatu na tafi qarfinka
wace iriyar kunya kike magan akanta ne maryam?
su waye kima wadan da za'aji kunyar?
ko kin manta jin kunyar mara kunya asara ce?
har kin manta da abunda suka miki ne,shin a lokacin da suka aikata din ba'a halicci kunya ba ne ko kiwa akwaita sune basu da ita?''ya qarashe maganar cikin bacin rai,ta bude bakinta zata yi magana ya dakatar da ita da hannunshi kana yace
''dakata maryam,bana buqatar kice komai,tun yanzun na cireki daga batun nan,ban neman kimin komai,zan yiwa kaina yaqin samun hindatu,naki kawai ido addu'a da fatan alkhairi''bai bata damar cewa komai ba ya tashi ya nar gin yabi hanyar da hindati tayi

kimanin minti talatin ta gaza tashi a gun,wani bangaren na zuciyarka na gaya mata bata kgautawa jabir ba,mai son naka ai ya gama maka komai,yayin da wani,bangaren kuma ke ganin dai dai tayi,don rigima ce zata riri ba qarama ba cikin gidan,daya barin uace mata,to sai me?,da ba naki bane jabir din suka aikata abinda suka aikata suka maidashi nasu?to ai dama idan mai guri yazo mai tabarma nade kayarshi yake

shiru shiru hindatun ma bata dawo ba,ta ciro wayarta tayi kiranta,abun mamaki sai taji jabir ne ya daga,kafin tace wani abu ya rigata
''kada ki cikata da fada gamu nan zuwa''hangame baki tayi tana kallon wayar,bata qarasa daskarewa ba sai da ta jangosu sun jero suna tafe suna qyalqyala dariya hannun jabir din riqe da fararen ledoji masu dauke da tambarin sahad store
duban hindatun tayi saivtaga yarinyar ta waske mata tamkar babu wani abu da tayi,kabir me ya katse kallon da take mata ta hanyar ajjiye mata leda daya kusa da ita
''kada ki cinye min gimbiyata ki barta hala,s
duka sauran tuhumarki ki hadiyeta na karbi tutar hindatu''
bata data cewa kallinsu kawai take,haqiqa ta san cewa indai hindatu tayo,nasarar auren jabir bata da sauran matsalar rayuwa,miji na gari kam ta gama samunshi,suka qaraci mata shaqiyancinsu suka miqe don tafiya,nan ma ya kasa ya tsare kan shi zai kaisu,hindatu ta takura tolas suka bishin ya ajjiyau har qofar gida

suna shiga soron gidan maryam tayi saurin janyo hindatu da har tayi gaba
''hindatu ashe baki da tunani?''
ta zumburo baki
''me kuma nayi adda?''
''kin manta waye jabir tsohon mijin yayarki jamila?''
sai ta kwashe da dariya har maryam na toshe mata baki kada ta dauko hankalin mutanen gidan
''nice ta biyu wajen sanin waye jabir bayan ke ta farko,to wai ma anty don autukina yaje aikin hajji sai in kasa zuwa in sauke farali nima saboda kunya?,jabir yayi min adda don na tabbatar yana da nagarta tunda har kika amince da shi a baya''
sai ta kuma yin qasa da murya
''baya ga haka adda wannan wata qatotuwar dama ce garemu ta rama duka cin kashin da aka mana,wallahi sai na dauki fansar duk baqincikin da suka cusa mana''

ta fuskanci da gaske hindatun take
''Allah ya taimaka''ta fada kana ta shigeta cikin zuciyarta tana musu addu'ar tabbatar lamarin cikin nasara da farinciki

🎄🌲🎄🌲🎄

Batasan ya akayi ba itadai taji an kawo kudin hindatun har da kudin sa rana jimillar naira dubu dubu dari uku dubu dari kudin aure dubu dari biyu kuma kudin sa rana,hakan ya sanya baba yace ta shaidawa abdur rahim ya turo a saka rana,su din ma kudin sa ranar suka bada naira dubu dari biyar,kudin sun bawa maryam din mamaki,murmushi abdur rahim din yayo yace 
''ko nawa na bada kudin aurenki yayi kadan maryam,kinfi qarfin haka,me din mai tsada ce''murmishi kawai tayi tana sake ganin qima da darajar son da yake mata

duk abin nan da ake jama'ar gidan basu da masaniya,kusan duk ranar da za'azo din basu gidan suna yawon asara yawon bidar asiri,asara goma da ashirin babu kudinsu ba imani

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*



         ▶3⃣5⃣


👇🏾 *wannan page naku ne*

👉🏾 *_haske writers asso_*
👉🏾 *huguma conversation and novels rooms_*
👇🏾 *da kuma*
👉🏾 *Zauren biebie isah*
*Allah ya bar qauna*👍🏽❤🤘🏽



*_Ankarbo daga imam bukhari r.a,manzan Allah s.a.w yace_*
*_(qarami ya yiwa babba sallama,matafiyi ya yiwa wanda ya taras,jama'a 'yan kadan su za suyi yawa masu yawa)_*

*_a wani hadisin da imamu muslim ya rawaito daga annabin rahama s a w yace(wanda a zuciyarshi akwai girman kai daidai da qwayar zarra bazai shiga aljanna ba)_*

*Allah kayi mana tsari kada ka haramta mana aljannarka,ka hanamu dukkan wata baiwa ko ni'ima taka da zata yi sanadin zamowa masu girman kai*







Fadar irin farincikin da mama da iyalinta ke ciki ma bata baki ne,sunyi amanna cewa wannan ce shekarar farincikinsu,addu'o'in da suka dade suna qwanqwasawa qofa yau kam an bude musu dukkan qofofin,duk wani tsohuwar ajiya ta mama data jibanci kadara ta daga ta saida,ta yiwa bikin shiri matuqa da gaske,ga dangi masu zuciyar yi mata da Allah ya hadata da su


takanas suka ziyarci gaya ta saida manyan gonakinta na gado guda biyu,ba qaramin kudi ta samu da su ba kasancewar yadda a yanzu kowa ya koma noma gonakin daraja suke,tuni ta fidda kudin kayan gado kayan kitchen da sauran tarkace na hindatu,maryam kam dama da yan kudadenta da take sa ka ran zasu isheta sayan kayan gado,ga mamakinsu saiga kudade baban su ya damqa masu a boye yace sukaje su zabi kayan gadon da suke so,shi din ma gonakinsa biyu ya siyar dake gayan,dama bashi yake amfana da su ba yan uwansa ne,cikin rufin aairi, Allah sai gasu sun tashi da kayan gado na kere sa'a masu kyau tsada da aminci


bata sake shiga farinciki matsananci ba sai da mami ta damqa mata passport dauke da visa ta qasashe biyu saudiyya da china
''maryam,inason inje siyayyar lefen abdallah ne,sannan ke kanki ina son in miki siyayya irin wadda uwa take wa diyarta,naso 'ya mace amma Allah bai bani ba,to a yanzun kuma sai Allah ya bani ke,naso ace lokacin bikinki da abdallah bai hade ba da ina mai tabbatar miki anan gidan zaki zauna har akammala taro a miqa ki gidanki,saidai duk da haka bikin magaji ai bazai hana na magajiya ba,zamu fara zuwa china muyi siyayya sanan mu dawo saudiyya muyi umara,kuyi addu'a kowannanku ya roqawa kanshi alkhairi kan sabuwar rayuwar da zaya shiga,ni da ke ne da abdallah''


rasa bakin da zata gode mata tayi saidai ta tsinci kanta cikin zubda qwallar farinciki,tabbas uwa ce,mami uwa ce wadda tasan ciwo da darajar 'ya'ya,babu shakka ko ita ta tsugunna ta haifeta iyakacina binda zata mata kenan,haduwars ta tabbatar daga Allah yake,bata manta yadda taqi taji batason aikin gidan mamin ashe alkhairi ne Allah yake nufinta da shi,gaskiya ne maganar Allah haka take da yake cewa cikin alqur'a ninshi mai girma
(zaku iya qin abu kuma alkhairi ne agareku,sannan zaku iya son abu kuma sharri ne a gareku,Allah shine ya sani ku baku sani ba)


mama kam rasa mai zata fada tayi,babu shakka duk yadda kaga Allah yayi da rayuwarka baiyi don zalunci a gareka ba,yayi ne saboda shi ne mafi sani ga abinda ya dace ga bawansa
raliya har da hawayen farinciki
''damuwarki tazo qarshe diyana,Allah ya yanke miki,maqiya kuma sai su kashe kansu don baqinciki''abinda ta dinga fadi kenan fuskarta qunshe da murmushi
hindatu kam buri ya cika,don tace ko iya haka Allah ya barsu sun gode masa,Allah ya nuna isa da buwayarshi,itama tata visa din umarar na nan jabir ya tanadar mata bayan sun angwance da wata daya

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

qarfe biyu na azahar jirgin ethopian airline zai debe su zuwa ethopia inda anan zasu fara yada zango kafin su isa qasar sin,cikin masu rakiyar tasu harda jabir da hindatunshi,abdulrahim sai zubaida,raliya da yaronta fadil,


ranan ne abdulrahim suka fara haduwa da jabir,tuni ya dade da sanin waye jabir din da kuma matsayin da yake kai a yanzu a gun maryam din,don haka gaisuwar mutunci sukayi tamkar sun jima da sanin juna,kusan dukkansu sama sama suka gaisa da abdallah yaja gefe yana faman cin magani tamkar wanda aka yiwa dolen tafiyar,ita kuwa zubaidan bata damu da ta qyaleshi ba ganin yadda yake faman fuskewa ba tana liqe da shi tana zuba rawar kai yayin da shi kuma yayi mata dif ko kanzil yaqi tanka mata da ita cikin hirarta
cike da bege da qaunar juna suka yi sallama lokacin da aka soma neman matafiyan


maryam ce qarshe saboda tsayawan da sukayi da abdulrahim
''abun mamaki banga irin sallmar nan da masoua kanyi ba yayin rabuwa da juna abdulrahim meke faruwa?''
murmushi ya saki yace
''me kika gani maryam?,kina tuhumata ne kan rashin damuwa da tafiyar da zakigi ki barni?''
''dole in tuhumeka mana abdulrahim,ba sau daya ba basau biyu nasha kamaka da laifin qin sakin jikinka idan muna tare matuqar abdallah na agun,wai shin tsoronshi kake ne ko meye?,aure fa zamuyi nan da sati uku kowa yasan da zamanka,ko wata barazana yake maka aboue wadda mu bamu san da ita ba''
sai taga ya tuntsire da dariyar har yana dan duqawa
''babu tsoro balle barazana tsakanina da shi,ke kika dai fuskanci hakan,hasalima abinda kike zaton ba haka bane,Allah shine mafi sani ga abinda yake cikin zukatan bayinshi,Allah ya kaimun ke lpy ya dawo min da me lpy,ki kula min da kanki matuqa,ki yiwa kanki addu'a mai yawa maryam,kada ki kashe wayarki da wuri zan kiraki kafin ku tashi''sallamar da sukayi kenan


koda ta shiga gurin tayi tsammanin ya dade da wucewa tunda sun rigata shigowa da wajen minti goma sha biyar,sai gashi tana gaba gun screening shi kuma yana tsaye a bayanta,gaba daya sai ta takura,tana ji a jikinta tamkar yana qare mata kallo ne kawai,gashi doguwar riga ta saka sai rolling da tayi wanda iyakacinsa kafada,hill shoes ta saka wanda sanadiyyar hakan yasa ta kusa kama abdallan a tsawon


ko cikin jirgi ma number din sit din nasu daga shi sai ita,mami na a sit din bayansu,tamkar ta zura a guje ta bar sit din haka ta dinga ji,tunda take basu taba zaman kusanci na tsawon lokacin da zasuyi yanzu ba,ta njtsu tsaf tamkar ace ket!ta zura aguje
wayarta tayi tsuwwa ta duba saiga kiran abdur rahim,tamkar ance mata ta kalli gefanshi sai ta tsinci idanunshi a kanta,wani irin kallo yake mata da ta kasa fassara ma'anarsa,shi ba harara ba ba kuma normal kallo ba,ya kafeta da mayun idanunshi masu cike da kwarjini,sai ta tainci kanta da kasa dagawa har wayar ta tsinke,gani tayi ya ciro tashi wayar ya fara danne danne hakan ne yasa tayi saurin jan tata wayar ta soma dubutawa abdulrahim din saqon karta kwana kan bazata iya amsa waya ba a yanzun cikin yi masa sallama da bankwana,saida kamfanin layin sadarwa suka tabbatar mata da yake sanna ta sauke idanunta daga kan wayar,ta sauke siririyar ajiyar zuciya daidai kokacin da taji shi kuma anasan bangaren yaja tsaki qasa qasa ya furta
''fool''
dayar wayarshi data fara ringin taga ya janyo ya zura earpiece
''hello baby......muna jirgi yanzu zamu tashi.....ok...ok bye take care,i will missed you too''ya kashe wayar gaba daya ya ajjiyeta guri daya


''janye cat eyes dinkin nan daga kaina,yanzun zansa a canza miki gurin zama indai kika ci gaba kallona,bansin kallo kin gane?''
ji tayi kanar ta hukunta idon nata da har yayi kuskuren kallonshi
''me zan kalla wanda babu shi jikin abdul dina?''ta fada cikin dakiya kamar ma bada shi take ba,kanta na kallon wani sashin
''there ar many,ko skin dina kawai batayi kama data baqin mijinki ba mai zubin ta 'yan garuwa,after all ma kinsan da hakan kike qarewa mijin wata kallo,kinsan kina so tun farko bakiyi magana a taimakeki ko a qwarqwara kixo,yanzun kam its too late qwalelanki''


maganan ta mata baqi da yawa,tayi qoqarin control din bacin ranta don ta samu maida masa amsa yadda ya kamata
''shi dan garuwan ai Allah ne ya halicceshi......''
''eh mana,da ke kika halicceshi''ya katsi numfashinta ba tare data idar ba
da sauri ta dora don kada yaci da rabonta ba tare data samu ta rama ba
''ba kyau ko kudi nakeso ba mutunci nake bida da daraja,kai din kuma ai inama kallon mace ne 'yar uwata kaga babu yadda za'ayi ince inason jinsina,abdul dina yafimin kowanne namiji cikin jinsin maza,ko a mai min shara bazan iya daukarka ba da dai mai wankin toile......''


''qarya kike wlh ya fada cikin fushi da dan daga sautinshi,ita kanta ta dan tsorata don qasa qasa suke maganar lokaci daya ya daga muryarshi,idanunshi data kalla kawai suka sake sata a zulumi,sai a lokacin ta tuna waye fa,abdallah ne,ta runtse ido tana jin zafin matsar da ya yiwa yatsunta kamar zai karya su ya kuma qi saki
''meye ne abdallah''mami ta fada tana dan leqo da kanta
''babu komai''yace
''ko baka jin dadi ne?''
mami ta tambayeshi cikin yar damuwa jin sautin muryarshi ya canza lokaci guda
''am fyn''ya fada a taqaice
''ok,to ku kashe wayoyinku''tace mishi bayan ta koma ta zauna daidai ksn sit dinta


sai da ya fara hucewa da kanshi sannan ya sakar mata hannu,zuwa lokacin tuni ta fara share qwalla don azaba,jin hannun take kamar ba'a jikinta ba sanadiyyar taruwar jinin da taji ya mata,tuni har jirgin ya daidata a sama,da qyar ta janye hannun tana yarfar da shi tare da fatan jin ya sake daga daurewa da zugin da yaje mata,ko da aka tamvayesu abinda zasu ci cikin jirgin kasa ma mafa na tayi,tanaji yasa aka kawo baqin coffe aka ajjiye musu,itakam ko kallo ma bai isheta ba


a hankali suke sauka daga jirgin daya bayan daya,gaba daya qafafunta sun mata tsami ga hannunta na damunta,itace a gaba abdallah a bayanta mami a bayanshi,rashin qwarin jiki ya sanya qafarta hardewa ta tafi luu zara gangara daga matattakalar
a tsorace mami tace
''subhanallahi,abdallah tarota''
tuni ya tallafota ta dawo jikinsa
''kin zame mana kaya wallahi,dama so kike a rungumeki din an miki hankalinki ya kwanta,amma net tine kika qara sai nayi maganinki''ya fadi yana tureta daga jikinsa
''sannu'' mami ke ta mata har suka sauka,duk da yanayin rashin dadin jikinta baihanata ganin qawatuwar garin ba


gida ne mai hawa ashirin cikin unguwar,gini ne qawatacce mai kyawu matuqa da gaske,cikin hawa na takwas nasu gidan yake,gida ne mallakinsu abdallan da suka siya da kudinsu,da fari falone madaidaici sai corridor daga damanka wanda idan ka shiga zaka tadda kitchen wani corridor dinne yake kallan kitchen din shi kuma dakunan bacci ne guda uku kowanne dactoilet cikinsa,sai valcony 'yar qarana mai kyau daga fuskar kowanne hawa na gidan wanda ta nan kana iya gano ainihin cikin unguwar da layinku da kuke  an qawatashi da kyawawan kujeru guda hudu da yan shuke shuke


daki daidai kowa ya dauka,tunda ta shiga dakin tayi wanka tayi akwala tayi sallah ta nade a gado sai bacci,tun la'asar dinsu sai da aka kusa idar da sallar magariba sannan mami ta tadata tayi sallah,tuni sunyi order din abinci an kawo musu har gida don haka shi kowa yaci,ba damar girki an dai siyo dan abinda zasu buqata kafin su gama kwanakinsu kamar ruwan roba qwai suger da sauran abinda zasu iya buqata,tana shirin basu guri don taji sun fara lissafe lissafen siyayyarsu mami ta tsaidata.
''maryam gaya min dame dame kike so,don gobe insha Allahu zamu fita bana son mu wuce kwana hudu,muje muyi kwana goma ko sha biyu a makka mu wuce gida lokaci na qurewa''
a kunyace tace
''bani da zabi mami,duk abinda kika zabarmin yayi''
bata ce mata komai ba ta miqa mata takarda da biro tace taje tayi mata list din duka abinda takeso nan da goma ko sha daya tazo ta kawo mata,hannu biyu tasa ta amsa ta koma daki


sai ta rasa ma me zata rubuta,bata da layin qasar balle ta kiraliya ko hindatu suyi shawara,wani tunani tayi ta koma falon,nan ta samesu yadda ta barsu,saidai wannna karo sunyi kace kace cikin takardu,rubutu kawai kowannansu ya duqufa yana yi
''hmmm,gaskiya ne,ai dole ayi bikin da babu kamarsa,da daya tilo''maryam tace cikin zuciyarta
''ya akayi maryama,har kin gama?''mami ta tambayeta bayan ta dago kanta ta maida kan rubutun da takeyi
''ummm...mami cewa nayi don Allah ko zaki aramin wayarki in dan kira gida?''
''ayya nima kuwa bani da layin qasar nan duk sanda muka zo sabo nake siya wancan faduwa yake,sai gobe idan Allah ya kaimu zan siyi wani''


har ta juya zata koma dakin mamin ta sake kiranta
''maryama zo....abdallah naga kai har ka hada naka layin ara mata tayi wayan''
yayi wani kicin kicin da rai ya saci idon mamin ya harareta kana ya ciro wayar daga aljihun trouser dinashi ya miqo mata
ta miqo hannu zata karba
''idan kinsan wannna baqin basamuden zaki kira da wayata ma gwara kiyi tafiyarki ki barmun abata,don wlh kika sake kika cinyemin credit sai na zara asalary dinki,don shi na fuskanci baya da arziqin da zai iya biya na''ya fada qasa qasa yana kallon paper din hannunshi da yayi rubutu,sai ka rantse ba da ita yake ba,murguda mishi baki tayi bayan itama ta harareshi kana ta karba duk da cewa bai ganinta,shi baisan yadda ta tsaneshi bane,idan banda lalra babu abinda zai hadata da wayarshi ma.


Ta loda numbers din raliyan ta kirata,sosai taji dadin shawarar data samu na abinda ya dace ta siya dim,ta kira hindatu ta zabi abinda itama takeso sai ta rage nata ta hada da na hindatun,kasa jurewa tayi don haka ta saka numbers din abdulrahim ta kirashi,sun taba hira sanna ta kashe,tana shirin ajjiyewa wani kiran ya shigo
*my suger* ta gani a rubuce,ta zubawa numbers din ido tana kallo,sai ta tabe baki sanna tayi rejecting.


ci gaba akayi da kira ita kam bazqta taahi ba sai ta gama rubuta duka abinda zata rubuta din ta fita gaba daya,kiran yaci gaba da shigowa ba qaqqautawa,tsaki ta ja ta janyo wayar ta daga kana ta kara akunnenta
''kada a cika mana kunne mai wayar bayi kusa''dum akayi kana taji ance
''ok''can qasa qasa


wayarta mata kyau ta dan juyata a hannunta,garin cire lock ta taba gurin pictures,daya bayan daya ta dinga bin folders din tana kalla,abinda ya daure mata kai ganin hounan abdallah da yammata kala kala,tana kalla tana tabe baki,wannnan guy din dan garari ne,waishin ma a ina yake haduwa da yammata haka zuqa zuqa yadda yake nuna he was always busy,ta shafe aqalla awa guda har taso shagala,duka hotunan babu na yarwa ya iya wanka kam babu ja a wannna tana iya bashi maki hundred parcent cif


larm din da agogon dakin yayi na qarfe goman dare ya tunasar da ita,garin sauro ta manta bata sauka daga folder din pics din ba ta kashi takardar ta fita falon,shi kadaine yanzun sai gun da mamin ta zauna,da alama yanzu ta tashi kuma ba dadewa zata yi ba,jin fitowarta bai sanyaahi daga kanshi ba,wayar ta miqa masa kana cikin cool voice dinta tace
''na gode''ya amshi wayar baiko dubeta ba,sai da ya bude screen din yaga inda ta shiga sanna yace
''awa ukun da kika kwashe wayar na gurinki hoton mitum daya dama kika tsaya kalla?''ya tambayeta idonsa cikin nata


ta dan zaro ido tana duban wayar,sai lokacin takula hotonshi ne a kai,yayi kyau cikin shigar suit yana murmushi,da alama ba'a qasar aka dauki hoton ba,bata kai ga cewa komai ba mami ta shigo falon
''kin gama maryamu''
''eh mami''ta fada tana miqa mata takardar,ta karba tana dubawa kuma tana qoqarin zama kan kujerar
''an gaisheki maryam,duk tsawon awoyin man iya ka kadai wadan nan abubuwan kika rubuta?,sunyi kadan''tace tana sake qarewa takardar kallo tana girgiza kai''
kararki tayi yawa dama nasan ba iyawa zakiyi ba,jeki kawai,zanyi amfani da wannan din da kuma wadanda na rubuta''
tana murmushi ta juya ya shige dakin ta barsu nan suna ci gaba da lissafe lissafensu

🌲🎄🌲🎄🌲🎄

ta riga su tashi kamar yadda ta rigasu kwanciya su sai yanzu suke nasu baccin gajiyar,kafin su farka harta kammala breakfast taci nata,sai tayi zaune a parlour tana kallo abinta cikin riga da wando na pakistan orange da baqi,ya mata kyau kuwa sosai


takun da taji shi ya ja hankallinta abdallah ne ke fitowa sanye da riga armless da wando three quater,fuskar an ahade kirtif ya qarasa gaban freezer ha ciro fresh milk da ta hada sanyi ya balle robar ya soma sha,baifi rabi ba ya ajiye saman freezer din ya nufi kitchen sai gashi da plate da cup,mamaki tayi yau da kanshi ya zuba baiko nemi ta zuba masa ba lallai da alamu tunwa ce ta koroshi ma,zaya zo yana wani ciccin magani kamar wanda wani ya zageshi


can gefe guda ya samu ya zauna kan ya fara break din,duk sai taji kamar ya cika falon,zaman ya daina mata dadi,neman dalilin da zaisa ta tabar falon kawai takeyi,don bata buqatar ko qanqani zama inuwa daya ya dinga hadata da shi ko naminti dayane idan ba lalura ba
''ke''taji yace sai tayi banza da shi kamar bata jishi ba,ta fuskanci wani jan bala'i gake nema da ita tunda suka taho,ita kuwa kodan daraja da kunyar mami bazata bari su raba abun fada ba


''bakiji kashein da na miki jiya ba kenan sai da kika kira wani da phone dina ko,to ki gayawa rubabben saurayinkin kada ya kuma kiran numberta don ba sa'anshi bane ni''ya miqe yana dauke cup din tea tare da bari plate din a gun,bai kai ga shiga corridor din ba sukayi kacibus da mami tana fitowa da hijabi jikinta qafarta sanye da silifas
''mami ina zaki?''
''zan sauka ne floor na qasa mu gaisa da maman farida,jiya kaga ban samu na ahiga ba saboda gajiya''
''pls mami ki taimakeni kada ki cewa zeenah tare muke,wallahi kika bari ta sani tofa na banu kafin mubar qasar nan nacinta sai yasa na rame,ango kuma da rama ami ai babu kanta kada ta koro miki ni tace na mata rama da yawa''
dariya ma ya bata gani irin marairaicewar da yayi
''ka maida ni kakarka Allah abdallah,kakannin naka ma ka shafa musu lpy a kaina abun yake qarewa,ni dai Allah ya kusa rabani da alaqaqai gwara kayi auren ko kunnuwa da idanuna  zasu huta da ganin yammata,ka shirya kafin na dawo mu fita da wuri so nake a yau a gama siyayyar baki daya''


tayi gaba suka gaisa da maryam ta fita,tayi zaton ya shige dakinsa tana zuwa sukayi kacibus bakib qofa,tana mura handle din dakin da qoqarin shigewa ciki taji yace
''kika sake mami ta miki tayin fita kika ce zaki bimu wata siyayya sai na qarasa targaden da na miki jiya''wuf ta shig dakin ta saka maqulli tadan daga murya
''to baaba na'' sanna taja tsaki,gado ta fada cikin jin haushinsa,dama ita bata sha'awar zuwan ma sam,dadai ba da si din zasu je ba shine,amma indai da shine zamanta a gida ya fiye mata dadi,qofar ya tsaya yana kallo,dan qaramin murmushi irin na gefan baki ya subuce masa ya cije lebansa na qasa kadan kana ya tura qofar nashi dakin ya shige ya cire kayan jikinshi ya fada wanka






*Mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[9/17, 12:54 PM] 80k: *ABADAN*36
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*_home of expert and perfect writers_*
*_annabi muhammad s a w ya tambayi sahabbansa_*
*_''shin ko kunsan waye matsiyaci?''_*
*_sai sahabbai suka ce''matsiyaci shine wanda bashi sa dirhami ko dirane''ma'ana bashi da cin yau bare na gobe_*
*_sai annabi yace musu''matsiyaci shine wanda zaizo ranar qiyama,yayi azumi yayi sallah yayi sadaka yayi zakka yayi hajji saidai kuma ya cuci wancan ya zalunci wancan ya zagi wancan yaci dukiyar wancan,sai Allah ya dinga dibanadan wadancan ayyuka na alkhairin da yayi ya dinga rabawa yana biyan wadanda ya zaluntar har sai ya tashi bashi da komai cikin aikin ladansa,ga ragowar wadanda ya zalunta ba'a gama biyansu ba,sai Allah ya dinga diban zunubinsu yana bashi da haka da haka har sai ya tashi bashi da komai face kayan zunubi sai Allah ya jefa shi a wuta''_*
*ya ubangiji kayi mana tsari don isarka*
Har mami ta dawo daga gidan maman farida ta shirya bai gama nashi shirin ba,sai da ta leqa ta masa magana,ta leqa dakin maryam ta taddatakwance
''ya kike a kwance mu da zamu fita?''
sai ta miqe zaune
''bana jin dadi sosai mami''
''ashsha,Allah ya sawwaqe,ki kwanta ki huta qila gajiyar tafiyar ce bata sake ki ba,Allah ya qara sauqi ma fita gobe ba damuwa,ungo wannan ajjiye min''ta miqa mata baqar leda,kayan bacci ne masu azabar kyau guda hudu
''maman farida ce ta bani su,nikam ina ni ina saka wadan nan qannnan tsirarar ai sai ku''
kunya ce ta kama maryam ta karbi kayan fana sunne kai,sanann ta tashi tayiwa mamin rakiya zuwa falo,sgi din ma ya fito sanye da qananun kaya,t shirt ce mai gajeran hannu baqa wanda a gaban rigar akayi rubutu gwara gwara kamara haka *we all have story to tell*,sai baqin trouser da ya saka,sun masa kyau aoaai kasancewarsa fari sai suka haskashi,qofan ta maida ta rufe ami tace sai sun dawo
kusan wuni sukayi ranar a waje har maryam ta qosa da zaman kadaitakar,duk da cewa ko a gida ma idan duka suka fice kusan haka ne amma acan wani okaci takan fice gidan baaba uwani susha hirarsu,da zaman shirun ya isheta sai ta fito valcony din gaban floor dinsu tayi zamanta tana qarewa unguwar tasu kallo
basu suka dawo gida ba sai da suka kammala siyayyar lefe kaf baki daya,hatta da akwatunan basu bari ba,daga can kuwa gurin da zasu dora kayansu a jirgi suka zarce basu ko dawo gidan ba,sun zabi zuwan kayan ta iska wato ta jirgin sama don shine mafi sauri,tunda kafin su koma za'a kai kayan suna sa ran kuma idan ta jirgin saman ne bazaya wuce kwana hudu zuwa biyar ba yaje sabanin ta jirgin ruwa da,zaya dauki watanni
sai da mami ta tabbatar komai ya kammala sannan ta karbi wayar abdallah ta kira qanwarta hajiya ruqayya ta mata bayanin kaya sun taho,tayi qoqari don Allah da sunzo a shirya komai yadda ya kamata aje a kai lokaci yana qurewa
a mugun gajiye suka dawo don haka suna dawowa wanka sallah da cin abinci kawai sukayi,cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zamowa shiru saboda yau babu zaman hirar daki kowa ya shiga ya kwanta
Washegari dukkansu su ukun suka fita kai tsaye kamfanin sarrafa kayan gado suka shiga,katafaren kamfani ne da suka qware wajen qera da sarrafa kayan daki da suka hada da gadaje sif madubi zuwaafiyayyun kujeru iri iri,inda suke ajjiyesun bayan sun gama sarafa su aka shiga da su,mami ta bawa maruam dama ta zabi irin wanda takeao,duk sai ta duburbuce ta kasa zabar kowanne daga ciki
sun kusa shafe awa guda saboda girman gun ba tare sa ta iya zabar koda kala daya ba daga ciki
abdallah ne ya ja tsaki
''yarinyar nan fa wahal da mu kawai take yi mqmi,kawai ki fidda mata wanda kika ga ke ya miki''
''meye naka a ciki dakina ko naka ko kuma dakinta ita zata zabi abinta''
''Allah ya baku haquri''ya fadi yana kewayesu ya barsu a gun ya nufi inda ma'aikatan ke zaune
ma'aikata biyu da leburorin gurin guda biyar suka qaraso inda suke tsaye ita da mamin,daya daa cikin su yace da mami cikin harshen nasara
''madam,ku zaku yi signing a nan za'a fitar da kayan,motocin kamfaninmu zasu kaimuku har inda kuke buqata suna wajen kamfanin suna jira''ya fada yana miqa mata wata yar matsakaiciyar takarda,ta amsa ta duba kana ta kalleshi cikin arahen nasaran itama ta maida masa
''ai bamu kai ga zabar wadanda mukeso din ba ai''
''yallabai ya riga ya zaba har ma ya biya kudaden''yayi maganar yana nuna wasu tsadaddu kuma tsararrun kayan gado dake gefan hannun damansu,kala biyu ne kujeru sif gado da madubi curtains,dressing chair da bedside sai abun maqale jakankuna dukkan kalolinsu light and dark purple ne sai wasu set din kamar haka amma su blue black ne da light blue
ba qaramin burge mami kalolin sukayi ba har ta tsaya kallinsu saboda kyawun da sukayi mata,abdallah ya iya zabe kamar mace,ta daga kai sai ta hangoshi can sama wata kujera mai siffar kwano mai azabar tsawo a zaune hannunshi riqe da cup din glass yana shan lemo,kashe mata ido yayi ya langwabar da kai alamun bada haquri tare da nuna mata agogo lokaci na tafiya kenan kana ya mata alama da hannu na kayan sunyi?,dariya ma ya bata sai ta daga masa girarta alamar eh,hannunshi ya sake dagawa ya mata alamar i love u,murmushi ta kuma yi ta girgiza kai kana ta samu gefe ta zauna tana fara signing din paper din zuciyarta cike da tunanin mahaifin abdallah,wani lokaci idan hayi wani abun sai taga ya koma mata alh abdulkareem sak,barewa batayi gusu danta ya rarrafa ba ta fada cikin zuciyarta
duka cikin kamfanin suka nufi bangaren kayan kitchen anan kam dama kawai ta basu nasu hada mata duk wani abu da yake,da amfani cikin kitchen,cikin lokaci qanqani sai gasu da,kaya bila adadin sukayi total ta biya,yawan kudin da maryam taga mamin ta kashe mata shi ya sake raunata mata zuciya sanyata kuka,kuka sosai ta saka har ta kasa magana ma,hatta da abdallahn dan garari tsayawa yayi yana kallonta,karo na farko da ta bashi tausayi,jawota mamin tayi jikinta sai ta ora kanta a kafadarta,hawaye naci gaba da zuba,itama mamin kasa magna tayi sai bayan maryam din da take dan bubbugawa a hankali cikin sigar lallashi,har cikin zuciyarta tanq jin ciwon rabuwa da maryam din,idan banda aure batq jin akwai abinda zata lamunce ya tsinke zamansu mai dadi da suka fara
washe gari ma baccinsu suka sha sai yamma sanan mamin tace su shirya su fita maryam ta danga gari,kada tazo ta kuma koma bata san ya garin yake ba
babu musu ta shirya cikin doguwar riga dark blue da adon golden din duwatsu saqar india ce,ta haskata qwarai,saidai kasala da rashin dadin zuciya da take ji ya rage walwalarta qwarai,wanna fargabar ta aure sai yqnzu taji ta fara shigarta daga lokacin da tayi tozali da kayan dakin aurenta,Allah ya sani ba zata yiwa Allah butulci ba amma tilas amatsayinta na budurwa taji fargabar aure kamar yadda kusan kowacce soya mace take ji a auren farinta a rayuwa
da qafa suka dinga tattakin suna taba hira kadan kadan cikin sassanyar la'asar din,yanayin garin ami kyau ne,babu ruwan wani da harkar wani,kusan hirar dake gudana jefi jefi tsakanin mami ne da abdallah,bata ankara ba sai da taji shirun na maryam yayi yawa,a hankali ta juyo ta dubi maryama dake hannun hagunta
''maryam''
da sauri ta juyo tamkar mutumin dake cikin tunani aka katse masa,nazarinta tayi na yan sakanni kafin tace
''lafiya kike kuwa,daga jiya zuwa yau naga duka kin canza,ko bakijin dadi ne?''kai kawai ta iya girgizawa tayi qas da kan nata tana qoqarin mayar da qwallar data cika mata idanu,hannunta mamin ta kama ta jata kan kujerar dake girke daura da su yayin da abdallah yayi tsaye hannayenshi harde a qirjinsa yana kallonsu,bai iya jin me suke fada amma yana iya ganin me ke gudana,motsawar bakin mami da gyada kan maryam,a hankali ta dinga share hawayen idanunta qarshe ta buge da murmushi kana suka taso suka iske shi
mami ta dubeshi ya wani hade rai yayi kitchen kitchen,ta dan ranqwashi qeyarsa
''kai kuma da wa mai aljanun sauyin yanayi''dariya taso qwacewa maryam har sautinta ya dan fita,tayi gaggawar gumtse bakinta ganin yadda ya zuba mata harara cikin shan mur
''nifa mami gaskiya ina da kishi,don me za'a tafi ni a barni ni kadai a tsaye kamar maye bayan da can ba haka kike min ba,kawai don an samu wasu''
''maganarmu ce ra mata bai kuma cancan ci kaji ba ehe,ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,sannan wasun ma da ka kafawa qahon zuqa suka tsole maka idanu sun kusa tafiya su baka sararin gurin kaga qarewarta sai ka koma shan nono kace ma ko yaye ka banyi ba''sosai mami ta bashi dariya har sai da ya dara yana fadin
''ni na isa,amma dai nasan tattalin da ake min irin na da zai dawo,kinga na zama dab lelen murum biyu,ga na my dear ga naki,thank god''
Da daddare suka hada dukkan wasu kayayyakinsu washegari jirgi ya debesu sai qasa mai tsarki,washegarin ranar da suka je suka sauke faralin ibadarsu ta umara,hakan bai sanyasu shiga wasu sabgogin ba sai da suka kwashe kwana biyar basu rabo da masallaci wanka ko cin abinci ke fiddasu,har gwara mami wani lokacin ta dan koma ta runtsa,maryam kuwa bata bawa kanta wannan hutun ba,tun mami na mata mita kan ta huta harta gaji ta barta,cikin kwana biyar din nan sai da tayi saukar alqur'ani biyu,dukkan alkhairi babu wanda bata roqawa mami mamanta raliya hindatu da ita kanta ba
kwana uku sukayi a madina ziyara,daga nan suka hada ya nasu ya nasu,mami tace itafa sai ta sauka a sudan tukun,cikin alamun tuburewa yace
''me zamuyi kuma a sudan mami,dear fa ta matsanta tana da buqatar gani na,i have alort to do mami a gida,inaga tafiya zanyi nikam sai kin taho''
''wa salaam wa kitabi,nima na huta da qorafi kama gabanka Allah ya miyaye hanya sai mun taho''anan suka raba jaha da shi,maryam batasan me zasuyi a sudan ba sai da suka je,unguwar tamkar tana cikin qasarta haka ta gani,sai dai 'yan bambance banbance da ba'a rasa ba na suturu abinci da al'adu.
kallo daya zaka yiwa matar ka tabbatar da 'yar sudance gabanta da bayanta,saidai mamakin da maryam tayi yadda hausa radam ta kama bakinta yanayin karyewar hatshen bw kawai zai nuba maka ba yarenta bane ara tayi ta yafa,ba abun mamaki bane jin yaren gausa bisa harsukan wasu al'umma ko qabilun da ba ahalin hausa ba,saboda yaren hausa yare ne sha kundum da ya fantsama lungu da saqo na fadin duniya,kusan a yanzu shine yare na biyu ko na uku da akafi amfani da shi,babu inda zaka tsoma qafarka a duniya ka rasa wanda ya iya ko yakejin yaren
gida ne babba mai bangare biyu bangare daya na matar ne daya bangaren kuwa harkar sana'arta kawai take gudanarwa,gyaran jiki gyaran gashi lalle ne kayan gyaran jikin na mata turaruka na ruwa dana ice da humra na tsuguno harda na wanka,kai hatta da kitso idan kana da buqata akwai mai yi maka,yadda maryam taji suna hira da matar tana tambayar mamin bayan saduwa ya fahimtar da ita lallai sun san juna dama can da mami,tunda har taji tana tambayar matar wata najwa tace taje daarfur sai gobe zata dawo,hajiya laila ita kewa mami irin wadan nan gyararrki zamanin alh abdulkareem mai nasara nada rai,gayu kam da gyaran kai mami ta yishi lokacin da mijin nata ke raye shi yasa ta zama ta gaban goshinsa,duk da a yanzun ma bata saki gayunta ba saidai ta daina wasu abubuwan tunda babu mijin
cikin kwana uku matar ta fara tsuma maryam,gyara take mata bana wasa ba tunda ta san haj bintu akwai sakin hannu idan harka ta hadaku,wani irin daddadan qamshi ta zaunar a jikinta wanda ko zama tayi a gu sai qamshin ya nasheka,farar fatarta ta canza yanayi farin nata ya saje armashi kyau gami da daukan hankali,sati guda ana mata gyararrkun taki wanne b'angare kafin suyo gida nijeria bayan haj laila ta hada muta wasu hade haden da zata ci gaba da amfani da su koda bayan bikin ne
bayan sun koma boyonta mami ta dinga yi,tuni ta daina komai a cewarta bataso nan da kwanakin da suka rage biki wani abu na gyaran da akayi mata ya samu naqasu,baaba uwani ita ta goyi bayan mami tayi uwa tayi makarbiya take komai
sunyi waya da mama da hindatu,mama cewa tayi sai tazo godiya don sam bai canci ta yiwa mami godiya iya ta waya kadai ba,amma da maryam ta sanar da mamin sai tace sam wallahi kada tazo,idan kuwa tazo din to ta nuna ba ita ta haifi,maryam ba,karamci da mutuncin mamin sunyi yawa har suka sa mama ta rasa ma me zata ce ko ta saka mata da shi?,hindatu amarya kam babu zama,ita da qawayenta ke gudanar da komai,don hatta da rabon kati su suka dinga yi,saboda mami ta riqe maryam tace babu yawon rabon iv da zata ta bata jikinta,ganin komai take tamkar a mafarki,wai tau ita maryam ce ake kira da sunan *amarya*,lallai babu wani abu da yake tabbatace sai mulkin ubangiji
bata fidda ran ganin irin wanan lokacin ba saidai koda wasa bata taba kawoshi nan kusa ba haka,dukka kayan da zata saka raliya ta fidda takai dinki,duk wata sabga da ya zamto ita zatayi raliya ta tsaya kan komai ita keyi kan jiki kan qarfi kamar a itace maryam din,kyakkyawan amincin da aka gina shi bisa turbar gaskiya da amana kenan,yakan iya kai ku zama qasan inuwar al'arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai taahi
Biki ya rage saura kwana uku da daddare tana gurin baba uwani ta kai mata wasu kaya da take son bata ita da yan jikokinta kiran hindatu ya shigo wayarta
''kinyi tsada adda maryam,mami ta tsaya miki''inji hindatu cikin salon tsokana
''kema mama ta tsaya miki ai ya akayi ya gidan''
ajiyar zuciya tayi
''lpy lau,gida alhmdlh don har wasu daga 'yan gaya sun fara sauka,saidai ta wani bangaren ba lafiya lu ake ba''sai da gaban maryam din ua tsinke ya fadi,cikin sakonni zuciyarta ta fara raya mata faruwar abubuwa marasa dadi masu yawan gaske kuma duka akanta,muryarta na rawa t tambayeta mai ya faru
dariya hindatun ta qyalqyale da ita
''kwantar da hankalinki adda mana,na gaya miki mu lpy muke alhmdlh,bangaren da babu lafiyar su inna huwaila ne da baaba hadiza,kinsan watan baqincikinsu ya kama,yanzu haka jamila na daki ita da sauran yan uwanta anata mata ruqiyyar banza da wofi ta tada aljanun qarya,wai wlh indai na auri jabir sai ta kashe kanta,ni kuwa nace shashasha ki kashe kan naki mana kanki da uwarki kika yiwa asara,ita kuwa inna huwaila sai zirga zirga take ta fita aje ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye,zuwa dare saiga aminiyarta uwani sai ji mukayi tsakiyar tsakar gida tana cewa,ke kika kawo kanki kikace na kaiki gun bokan nan bani na jawoki ba,don aiki bai ci ba kuma zak nemi tijara ni gaban kishiya?,to ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi shi yasa na biyoki ayita mai kankat kema kowa yaji,mugun qullin da kika so qullawa,ta fayyace duk abinda suka qulla din sannan ta dora da fadin,bola kuma na bogi ne kudi kuma muni babu yadda kika iya,aminad da kuke baqinciki da ita daga ke har hadizan ai ta fiku,yanzu gashi data miqawa Allah kukanta ta jadiye baqicikinta na shekara da shekaru Allah ya yaye mata damuwarta ba tare da tayi hasarar sisin kwabonta ba,ku kuwa haihuwar asara babu kudi babu biyan buqata ga asarar imani,sallolin kwana arba'in a ajejere kun rasa ta kusan kwana dari bakwai,amina Allah ya sanya alkhairi ya tsone idon maqiya,kuma wallahi ni da ku dukanku ke da hadizar shege ka fasa,naci uwar mace a iya tijara da ramuwar gayya,duk kuma wadda take jin ta haifu da jini uwarta ta haifeta ta fito ta tanka
wai in gaya miki adda saiga inna huwaila ta fito da borin kunyarta waisai sun daky wallahi bugu daya uwale rayi mata sai gata tayi plate a qasa''hindatu ta fada tana sheqa dariya
''wai kuma ta sumewa mutane jadiza tayo kanta wai huwaila kinci amanata ta hau dukanta,lubabat
u kuwa itama tayo kan,hadizar ke in taqaice miki labari kowa sai ya ahigarwa uwarsa gida ya zama na wrestling,ina ta laluben wayata in miki vedieo don,kada ayi babu ke saiga babamu nan ya shigo shi ya raba cakwakiyar,kowacce da dogon bakinta ta taho zungi zungi zata yi masa bayani don ya bata gaskiya yadda suka saba yace babu wadda zai saurara,wanna ya ishesu ishara,mama ce......''
''haba aku mai vakin magana,sai kace na kunna freedom?''inji maryam tana murmushi bayan ta katse hindatu
''kefa adda ba'a miki abun arziqi''
''to ai wanna ba baun arziqi bane''
''wallahi nikam abun arziqi ne tunda na gano tashin hankalinsu ranar kawo lefenki,da farko da suka ga anfara shigowa da qananun akwatuna har sun fara yada habaici,da suka ga dai shigowara ke sai suka fara lissafi suna tabe baki,qarshe da suka lissafi akwati ashirin da hudu cif manya da qananu sai aka nemesu aka rasa,inna hadiza na quryar daki suna safa da marwa huwaila kuwa anyi tsamo tsamo an rasa na kamawa,ana cikin haka saiga nawa lefen akwati sha uku,qarshe saiga inna hadiza na dora hannu aka tana xunduma ihu huwaila a taya ta da sharbe hawaye da fyace majina,a gaban idon mutane fa abin mamaki da dariya,ko kunya babu''ta sake qyalqyalewa da daria don tuna abun da tayi
''Allah ya rufa asiri,yanzu ya abubuwa suke tafiya?''
''komai na tafiya daidai,amma wlh adda kizo ki kalli lefanki''
''kai hindatu,me kike ci na baka na zuba,abinda za a ajjiye maka su a dakinka wataran har sai ka gaji da su''
''to ai shikenan,dazu yaya abdur rahim yazo ya kawo kudin dinkunanki,dazu naje gidan adda raliyan na kai mata,har ta fara karbo wasu ma ta bayar an goge miki,gaskiya adda raliya tayi wallahi,akwai zumunci tayi qoqari''
''gaskiya ne Allah ya bar zumunci ya saka mata alkhairi''
''ameen''
nan take aya mata kayan gadonsu da aka siya duka an hada mata sun zama biyu kenan har kayan kitchen dinsu,madyam din tace yayi babu laiciya zama dakin baqi kenan da naki dakin tunda kince shima jabir din ya zuba naahi furniture din,jibi insha Allah nima zan taho gidan gaba daya ai,ki gaida mama''
''Allah ya kaimu,zata ji insha Allah''
daga haka dukkaninsu suka katse wayar
*mrs muhammad ce*
[9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
   💖🌺💖🌺
    💖🌺💖
      🌺💖
          💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
      🌺💖🌺💖
        🌺💖🌺
          💖🌺
             💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
  *_home of expert and perfect writers_*


        ▶3⃣7⃣


*_ina so nayi amfani da wannan 'yar damar wajen miqa jinjinar ban girma tare da ddu'o'i na fatan alkahairi wajen jajirtaccen dan kishin qasa da al'ummarsa BARRISTER ABDU BULAMA BAKARTI duk da cewa ban masa sanin ido da ido ba saidai tarin gaskiya amana taimakonsa da jajircewa kan qasarshi da garinsa ya kewaye kunnuwanmu,ina tare da duk wani jajirtacce mai gaskiya da amana dan kishin qasa da al'ummarsa,ubangiji yayi maka jagora ya tsare gabanka da bayanka,ya qara yawaita mana irinku cikin wannan alumma tamu dake fagamniya cikin wani irin hali,Allah yayi ruqo da hannayenka ya dorar da kai kan gaskiya har abada ameen suma ameen_*







Kanta bisa kafadar mamin tana rabza kuka tamkar wadda zasuyi rabuwar har *ABADA*,sai yanzu take kuma jin zugin rabuwa da mamin,tabbas sabo turken wawa ne,ita kata mamin zuciyarta a karye take ta kasa cewa komai,tanajin zatayi asarar diyarta ne guda zata rabu da ita,da qyar tayi,conrtolling kanta kafin,su tsaya suyi sallama
''naso a gudanar da komai da ni maryam,saidai ga yadda lamarin Allah ya kasance,date din bikinku da abdallah yazo daya,kinga ma ko a yanzun gidan ya fara cika da mutane wasu ma rabonsu da gidan nan an jima,kinga bazan iya tsallakesu ba na fita wani guri ba,amma nayi miki alqawarin bayan komai ya lafa wuni guda zanzo nayi a gidanki,hakanan zan dinga dubaki akai akai da yardar Allah''


kafin tace komai muryar abdallah ta ratso falon yana kiran mamin
''gani nan abdallah''
da azamarsa ya shigo hannunshi daya riqe da leda baqa mai kauri mai dauke da tambarin wani gurin saida kayan maza na ado,daya hannun kuma rafar yan dubu dubu ce dauri biyu,cikin shigar qana nan kaya yake,sai ya sake wani dan banzan kyau,farar fatar nan tayi luf da ita tamkar rainon larabawa,ko dama can yafi yanayi da su din sam sai ka rantse babu abinda ya hadashi da nijeria ,sai ya danyi turus yna dubansu
''qaraso mana abdallah,ya ake ciki?''
ya qaraso ya zauna gefanta
''mami duka guest house din guda biyu sunyi kadan,yanzun dai hisham ya samar ma ragowar mutanen hotel''
''yayi kyau hakan,sai ayi total abiya kudin kwanakin da zasuyi da abincin da zasu ci basai an yi jigilar kai musu daga nan ba''
'to''yace yana dora mata daurin kudaden kan cinyarta
''wannan fa na meye?''
''wani abokin aikina ne ya bani gudun mawarshi.......''yayi maganar yana qiqarin zaro wayarshi daga aljihu wadda keta faman ringing,ya kara a kunnenshi kana ya niqe tsaye yana fadin
''gani nan zuwa''yadan dubi nami yana yin gaba
''mami ina zuwa''
''uhm,yanzu haka abincin na da nasa aka kaima baka ciba,kadai kula da cikinka abdallah''
''ok mami''ya fada yana mata murmushi gami da qarasa ficewa a gurguje


nasiha ta mata sosai irin ta 'ya da mahaifiya kafin ta saka driver ya kaita zuwa gidan cikin kuka da kewar rabuwa da juna
ita ta ruqota suka dinga tsallake mutanen da suka fara cika gidan ta rakata har bakin motar sai da suka fice kana ta juya ta koma ciki

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Tun lokacin da idanunsu sukayi tozali da katin daurin auren abdallan hankalinsu yayi qololuwar tashi
''wacce irin hasara nuke shirin tafkawa haka,me kuke tunanin zai faru matuqar muka bar abdallah yayi auren nan,cikin watanni tara ko goma da yin surensu matarshi kan iya haihuwa,zata iya kasancewa ta haifi namiji ma,wannan shike nuna munyi bankwana da cikae burinmu?''


cewar nene dake faman safa da marwa,can cikin dakinsu zahariyya da zubaida kuwa kowa da abinda ya dameshi,zahariyya irin tunanin nene take,ba qaramin tashin hankali take ciki ba,burin da take da shi ya girme mata,yau idan abdallah yayi aure daidai yake da nisanta da dukiyar da suke kwadayin zareta daga hannun mamallakanta su su amfana da roman nata.


Afusace ta kalli zubaida dake zaune a cure can quryar gadon tana ta faman surfafa kuka wanda tunda labarin auren ya isa kunnenta itama ta hana kanta sukuni,kuka take tuquru kamar ba gobe,udanunta duka akumbure suke sun ui luhu luhu sosai daga jiya zuwa yau
''dalla malama ki wa mutane shiru,banza shashasha mara kishin kanta bare yan uwanta,yasan dake din ai ya zabi ya auri wata ba'a gabanshi kike amma ke kin quntata rayuwarki saboda shi''


dama a fusace take maganar zahariyyan sai ta qara tunzurata
''anqi ayi shirun bazanyi shiru ba,kece babbar shashsha da bakison so na haqiqa ba,babu ruwanki da sha'ani na ehe''sai kuwa zahariyyan tayo kanta a zqbure tana cewa
''ni kike gayawa haka,yau zan nuna miki baya ga shekaru da na fiki na fiki iya rashin mutunci''dambe ne ya sarqe tsakaninsu har nene dak samanta ta jiyo hayaniyarsu ta sauko,da qyar ta iya rabasu tana fadin
''sai ku kashe kanku ai,yan iskan yara marasa hankali da tumani,mazq ku raba abun fada cikin taron mutane''


sai sukayi tsit suna maida numfashi kowacce zuciya iya wuya,nene ta kalli zahariyya tace ''ki sameni a sama''ta juya ta fice ita kuma ta rufa mata baya,gware suka kusa yi da adnan wanda ke qoqarin hawa saman da gaggawa
''lafiyanka kuwa?''nenen ta tambayeshi bayan ta danja baya tana qare masa kallo
''muje sama nene akwai magana''ba tare da kowa ya sake tankawa ba suka duru saman gaba daya


''barin yarinyar gidan nan babban abun farinciki ne a garemu,mun riga da mun gama magana da malam na hayi ya tabbatar min da cewa zai mana aiki ammafa matuqar tana cikin gidan nan babu lallai yayi tasiri,tana da wani irin dafa'i a jikinta tun na kakanni da iyayen kakanninta,tunanin da nake yanzu kenan ta yadda zamu gabatar da aikinmu don auren abdallah ba qaramar barazana bace da faduwa garemu sai ga kuma kyakkyawan labarin da na jima banji irinsa ba,mun gode Allah faduwa tazo mana daidai da zama,yau din nan ba sai gobe ba zamu isa vurin,malam na hayi,kwana daya zamuyi a hanya zuwa jibi zamu dawo ya kama ranar daurin aure kenan ko ana gobe daurin aure?'' 
ta tambayi,adman,sai da ya danyi tunani kadan sannan yace
''ana gobe daurin aure ne''
''to yayi,kai adnan ka zauna muje da,zahariyya,ka shiga ayi duk wata hidima da kai,banason a fahimci komai,zan sanar da haj bintu qanwar ubanku ce ba lafiya zamuje dubota''


a nan suka gama dukkan wani shiri da tsarinsu kana suka shirya ta gayawa mami abinda ta shirya gaya matan,cikin tausayawa mami tace ayi mata sannu Allah ya qara sauqi,idan sun isa zata kira su sai ta bata ta mata sannu

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

tun daga qofar gidan ta soma ganin alamun cika,mutanene maza da mata keta kai kawo,a haka ma ba'afara gudanar da bikin ba kenan ina ga kuma an fara,gefe driver din ya samu yayi parking,akwai sabo tsakaninsu da mutunci da girmama juna duk dacewa ya kusa shekaru hamsin dattijon mutum ne mai hankali da nutsuwa,malam baaba direba ya kalleta bayan ya fito 
''to malama meramu(haka yake kiranta sunan diyarahi ce ta fari data rasu),Allah ya sanya alkahairi yasa ayi a sa'a,ayita haquri da rayuwa,mu sai ranar daurin aure idan mun dawo daga na mai gida abdullahi''
kanta a sunkuye tace''na gode sosai baaba,Allah ya nuna mana''ya bude boot din motqr yana cewa
''bari in shigar miki da kayan ko''da sauri ta amshi jakar da ya fara fitowa da ita
''a'ah baaba,ka barshi ga yara zansa su shigar min da su''tayi kirqn yaran maqotan dake zaune can gefe da su wadanda da wasan qasa suke tayi da yan guje gje ganinta yasa suka bar abinda suke suka tsaya kallonta,kiransu tayi kunsan amarya da farinjini a guje suka taho dukkansu har ana rige rigen zuwa,kqn ta qarasa mqganar ma sun fara zundumar kqyqn,nata suna shige mata da su cikin gida,dubu biyar ta qirgo cikin dubu dari biyun da mami ta bata tace ta riqe a hannunta tasan amarya kudi basa zama a hannunta,da fqri qin karba malam baaba yayi


''idan da ni mai wadata ne meramu ai nine mai baki ma a matsayin gudun mawa,ke yarinya ce ta gari merama,babu komai tsakaninmu dake saidai muyi miki sai fatan alkhairi''
sai ya kuma karya maya zuciya
''indai ka daukeni 'ya baaba ka karbi kudin nan,ayi min addu'a''da qyar ta shawo kansa ya karba yana sa mata albarka,sukayi bankwana ta shige gidan ta juya don shiga gidan,tun daga qofar gidan ta fara ganin canji,yasha fenti radau ruwan madara tun daga waje har cikin gidan


mutanene da suka kusa dosan ashirin a tsakar gidan,hira ce kawai ke tashi cike da farinciki,dangin mamanta ne da na babanta na nesa,na garin gaya da sauran garuruwa,sallamarta ya sanya su saka guda atare kowa na fadin albarkacin bakinsa ganin yadda tayi kyau ta canza tamkar ba maryam din ba ,kunya ta kamata ta qarasa gurinsu suka gaggaisa,maryam mai alkahiri,ce duk da yanayin gidansun hakan bai hanata idan ta dauki albashinta ta duba mabuqata sosai cikin dangin nasu ta taimaka musu da dan abinda ba'a rasa ba iya abinda zata iya


daga nan dakin mamanta ta wuce,nan din ma da mutane dakin yayi kaca kaca da kayyaki samiru da kayan robobi wadana aketa kwashewa za'a tafi jere,suka gagggaisa ta shige dakin gadon mama,ita da hindatu ne a dakin kayan sawa ne zube saman gadon sunata aiki,gefan gadon ta samu ta zauna ta soma gaida maman,dafe bakinta hindatu tayi
''la la la adda maryam,tabdijan irin wannan canzawa haka gaskiya mami ta iya kiwo,za'a gigita ya abdur rahim kenan''alamu tayi mata da ido tayi shiru don Allah


''qaraso maryamu ki fidda kayan da kike so za'a bada na bayarwa''
''um um mama kawai a bawa wadanda za'a bawa dim babu komai''hindatu ta janyo jakar bakko gaban maryam din tana fadin
''duba kayan nan adda maryam dinkunanki ne jiya adda raliya aiko idris direba ya kawosu gobe zata amso miki sauran''
da daidaya ta dinga daga kayan,ba qaramin burgeta dinkunan sukayi ba duk ciki babu na kushewa
''Allah ya saka mata da alkhairi''ta fada bayan ta kammala dubawar


A bakin fanfo ta fito yin sallar la'asar ta tadda jamila ta fito ita kuma daga bandaki,gaba dqya ta fige ta lalace kamar mai cutar qanjamau,wani banzan kallo ta yiwa maryam din tare da jan tsaki,bata kulata ba ta bude fanfon ta kunnashi ta fara alwala,bata kai ga gamawa ba taji an bangajeta tayi taga taga kamar zata fadi sauran qiris ta qume goshinta Allah ya taqaita mata ta dafe kan fanfon,miqewa tayi tana duban bayanta,binta ce a tsaye cike da tsabar rashin kunay tana girgiza,ta arkade jikinta da ya debi qura kana ta kalleta
''baki gani ne binta kika bugeni?''
''ina gani mana sai me?,dama jiran dawowarki nake cikin gidan nan,tsofaffin munafukai maciya amana masu aure mijin yar uwarsu''
duk da kalamanta sun mata ciwo amma sai da ta bata dariya,tsayawa tayi kallonta kawai,cikin yaran gidan susu goma sha bakwai binta ita ce qanwarta ta tara,aqalla ta bata ahekaru kusan goma,sai taga ada ma ba ni ta kanta take ba sai ayanzu,ranar tqrihi a rayuwarsu,kada kai tayi tana sake yin murmushi ta juya don ci gaba da alwalarta kafin tace
''duk wadanda kika kira da wadan nan sunayen ai aun riga da sunsan kansu,kinga kenan bada ni kike ba''
''dake nake mana,kuma idan kin isa ki tanka kiga yadda ake ruwan bala'i cikin gidan nan''
ta zubar da ruwan dake bakinta ta gyara daurin dankwalinta kana ta dafa kafadar bintan
''mai abun fada baya fada,harkar girma muke da mutunci bata bala'i da masifa,ina da damar da zan miki dukan tsiya binta hakan ba gagarata zaiyi ba,amma bazanyi hakan ba abinda kuka shuka kuke girba ma kadai ya isheku duka mai taba qololuwar zuciya''ta sake mata kafada tayi dakinsu


''ki dakeni mana kinji ko karuwa kawai''
''ke kuwa tunda bata kulaki ba ai sai ki shafa mata lafiya''inji kulu dake diban ruwan wanka
''babu ruwanki munafukai,dama tun jiya naga kunatavrawar kai ke da uwarki a kansu''kulu ba haquri kamar yadda bintan keji da kanga,take suka hau dambatawa,ragowar dangin babansu da basu je jere ba ne suka rabasu


Dawowar yan jere suka hau hirar gidanjan su maryam din yadda Allah ya musu baiwar samun mazauni mai kyau da qayatarwa ta,maganar ta qara hasala hadiza da yaranta wadanda suka zame mata qawaye,suke kuma tayata haukan da take ta faman yi,don tuni jikin huwaila yayi sanyi,saidai atafau hindatu ta hanata shiga jikinsu,tace sam baza'a maimaita abinda ya faru shekarar bara ba,an dai fidda kayan sawa jakanku na da takalma cikin kayan maryam din an bawa yaranta kuku lubabatu da batulu,da murnarsu kuwa suka arba koba komai sun samu na fitar biki,wannan karbar ma da sukayi saida ya zama bala'i,hadiza da yayanta suka fito suna zubda ruwan rashin mutunci cikin dangin ubansu,hali kam sun saidashi,wanda baisan halisu ma ba ada ayanzun ya sani,kowa ya budi baki tir yake da halayensu

🎄🎍🌲🎍🎄🌲

Tara ga wata ya kama ranar talata ranar sukayi kamu,washegari laraba sukayi budan kai duk shigar da sukayi iri daya ne komai da komai ita da hindatu hatta da yari,alhamis aka musu wani wani dan reception na fulani wanda shiga ce ta fulani kowa da kowa yayi,ba qaramin qayatarwa tsarin nasu yayi ba,komai a tsare cikin nutsuwa da kwanciyar hankali


Ranar juma'a ya kama daurin aure,a gaya aka tsara za'a daura auren wannan karon,dalili da yasa kenan gidan ya zamto sai mata kawai mazan duka sun tafi gaya


Da yammacin gidan maman zahra suke zaune maqotansu,tana tsakiyar qawaye da 'yan uwa,tayi kyau cikin shadda 'yar ubansu lemon green da akayiwa adon light blue,rigace da zani dinkin ba qaramin mata kyau yayi ba,tamkar wata fure haka ta koma,raliya na gefanta tana zuba mata abinci cikin plate kana ta miqa mata
''maryam,karbi kici,tunda aka fara sabgogin nan baki ci abincin kirki ba fa''
ya mutsa fuska 
''banajin dadin bakina raliya,faduwar gaba nake fama da ita tun da safe''
murmushi tayi
''fargabar shiga sabuwar rayuwa ce,kowacce mace najin hakan har da bacin rai ranar daurin aurenta,wasu ma har kuka suke kafin suji sanyi cikin zuciyarau,kiyita ambaton Allah''


kafin tace komai waurta ta fara kuwwa,a kasalance ta ciro mami ke kiranta,mirmushi tayi sanan tace
''Allah sarki mami na''
''tun da safe naso kiranki maryam,nasan tuni an daura tun safe ko diyata girma ya hau kanta an zama manya''murmushi ta sake yi tace
''na yamma ne mami,suna can dai''
''to Allah yasa ayi a sa'a a gaida maman kice ina mata Allah ya sanya alkhairi''
''ameen mami,na gode''


batulu tayi sallama falon sanye da daya daga cikin kayan da maryam ta bata an gyara mata daidai ita,sun mata kyau kuwa don duka yaran gidan nasu babu laifi akwai kyau irin na fulanin usuli
''adda maryam kizo kinyi baqi suna falon mama''cike da mamaki ta kalleta,gau ta zama adda,sunan da koda wasa bata taba jin wani daga cikin uaran gidan ya kirata da shi ba idan ka dauke hindatu,hatta da isyaku autan gidan
''kice ina zuwa''ta bata amsa tana janyo mayafonta ta lullube jikinta,ta dubi suwaiba dake zaune gefe tace tazo ta rakata
da qyar ta samu ta kutsa ta ahiga gidan nasu saboda yawan jama'a musamman da masu kidan qwarya suka baje hajarsu cikin qwarewa don daga cikin gidan sarki aka daukosu


qannenta shamsiyya,azara,balaraba da yasira na zaune daga gu guda an samu abinci suda yaransu anata kwasa,sannu tayi,musu kafin ta shigesu,yasira da shamsiyya suka danyi qus qus kana suka tabe baki
''an samu duniya''inji azara
tayi sallama falon,maman ma zaune tayi kyau cikin dinkin atamfarya,sai ta koma kamar yarinya mai qananan shekaru,Allah ne kadai yasan farincikin da take ciki,babu shakka komai yayi farko zaiyi qarshe,aure kuwa lokaci ne idan yazo ko ba'a shirya ba sai anyi shi,fata dai kada gaggawar anason ayi auren tasa aje ayi zaben tumun dare
abokan aikinta na na gurin haj atika,taji dadin zuwansu kuwa qwarai da gaske


qarfe shida suka fita meena event center suka gabatar da wata qwarya qwaryar dinner,ta maryam ce ita da qawaye da iyayenta,su hindatu kuwa tuni jabir yazo ya dauke matarshi suka wuce dinner,fir maryam tace ma abdur rahim bata buqatar wata dinner,su din ma da zasuyi sai sun dawo,hindatu da jabir na mata dariya sukayi tafiyarsu,bashi kuwa ya dawo da ita gida ba sai daya saura na dare,maryam din zata soma mata fada tayi shigewarta bargo tayi kwanciyarta
''hindatu rawan kan amarci ya fara tabaki kenan''cewar raliya wadda ke gyara kwanciyar fadil,suna jinta tana musu dariya

🎄🎍🌲🎍🎄🎍🌲


tun qarfe biyar da rabi na yammacin ranar asabar motoci suka cika layin har suka musu kadan,tilas ya sanya wasu motocin suka dinga parking a bakin titin unguwar,moto cine na kere sa'a waccan tana wace wannan haka wannan ma haka,a nutse kowa ke zaban wadda zai shiga kasancewar tare za'a tafi,sai hindatu ta raka maryam din tukunna.


''da Allah malama kihi ki foto,kunzo kun sanya uwarku a tsakiya kuna neman sata kuka,ina cewa ba'a kanku aka fara aure ba,haba da Allah''inji yayar mama hajiya aysha,hindatu da maryam dinne duqe gaban maman,maryam ta soma qoqarin taahi amma kuka yaci qarfinta ya hanata,sanye take da atamfa riga da simple zani an lullubeta ruf da wadataccen mayafi,hajiya aushan ce ta taimaka mata ta miqe ganim da gasken ta kasa miqewar,addu'o'in fatan alkhakri ta biyo yayan nata da shi.


caraf sukaji an damqe hindatu,jamila ce a zabure kamar mahaukaciya sabon kamu surutai take zage zage da sumbatu kala kala
''shegiya tsinanniya,wallahi babu inda kika isa kije,gidan mijina nawa ne ni kadai,wallahi bazan baki damar cin irin daular da naci ba don uwar ubanki''ganin abin na gaske ne daya daga cikin qannen malam amadu sailuba ta qaraso ta daga hannu ta zabgawa jamilan mari
''saketa 'yar iskar yarinya mai kama da 'yar Allah bani,dul abinda kika aikata akayi muku shuru ba'ace muku komai ba bai isheku basai yau ranar da Allah ya tashi nina muku kuskurenku,shekara nawa kuna cutar amina baiwar Allah ta taba tadakai ta kalli waninku,tunda aka fara bikin nan baku,bar mutane an zauma lafiya ba,uwarku dai ta cuceku wallahi,kuma ki saketa tun kafin ki debi haqoranki a hannu,idan tsiyace kowa ma ya iyata''ba shiri ta saki hindatun taja da baya sai gata yaraf a qasa.


da gudu inna hadiza ta qaraso gurin,hannu ta dora a ka cikin qaraji tana fadin
''huwaila amina dake kanki sailuba,zaku kashemin 'ya,munafukai tsinannu,dama ai na dade da sanin kun fi son amina saboda 'yar garinku ce,to Allah ya fiku kina ranar daukan fansa na tafe''
babu wanda yabi ta kanta,hssalima zamewa kowa ya dinga yi ko ruwan da za'a kwarawa jamilar an rasa me miqowa,su kansu sauran 'ya'yan nata na qofar gida suna jallin yadda motocin sukayi farin dangon daukar amare,kwalliya kowaccensu taci tare da fatan daya daga cikin mamallakan motar ya taya


ta dubi sailuba sata zo wucewa tana sauri don kada ta rasa motar tafiya
''da Allah sailuba miqo min ruwa na kwarawa jamila kinga bata numfashi''kallon banza tayi mata
''kici mutuncinmu kici na uwarmu kice zaki moremu,saidai ki nemi wata ta baki wallahi badai ni ba''ta buga qafa tayi ficewarta,tilas ta saki jamilan ta debo ruwan ta sheqa mata kana ta jata zuwa cikin daki tana fyace majina.


Gwanin sha'awa motocin ke tafiya cikin tsari da nutsuwa,sam babu irin mahaukscin gudun nan da 'yan kai amarya keyi,mitoci ne kimanin guda arb'in banda na security guda goma


wani matsananciyar faduwar gaba take fama da shi idan ta tuna izuwa gidan aurenta fa take tafiya,addu'o'i ne fal cikin zuciyarta na samun sa'a da nasarar sabuwar rayuwar da zata fuskanta

🍃🍂🍃🍂🍃


sau uku tana sako qafarta waje da niyyar fita saidsi ta kasa,sakamakon mutanen dake giftawa bata da buqatar kowa ya ganta,aiki ne na sirri wanda bata da buqatar haduwarta da wani,wayarta ta fara vibration jikinta na rawa ta daga,muryar nene ta cika dodon kunnenta
''kada fa kiyi kuskuren da zaki jawo mana bacin aiki,wannan ce damarmu ta qarshe''murya can qasa take fadin
''na gama aiwatar da komai nene,fitowata ce ke neman gagara mutane na kai kawo a gun''
''kada ki kuskura ki wuce mintina talatin baki baro area din ba,wuce hakan na nufin bacin komai''din din din wayar ta katse,hankalinta ta msida sosai kan hanyar ficewarta,wuf ta faki idanu ta fice ta nufi bangaren nasu cike da farincikin nasarar aikinsu

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Qarfe goma da rabi ne na dare,gefan lallausan gadon dakin nata take a cure guri guda,tafiyar yan kawota da mintina ashirin yayyafi ya fara sauka wanda ya haddasa sanyi da garin yayi hade da qamshin qasa,bai kankama ba ruwan hakanan yayyafin bai tsaya ba,kusan tunda suka tafi suka barta anan take zaune bata ko motsa ba


hayaniyan data soma ji cikin paflour na muryoyin maza daban daban suka qara mata fatgaba,ta runtse idonta tana jin yadda zuciyarta ke dukan uku uku kamar zata yi tsalle ta fito


''ko baka fadi ba ba shiga muma za muyi ba don an dade da daina wannan''ta jiyo muyar wani daga cikinsu,tun tana jin hayaniyar tasu sama sama har taji dif alamun basu cikin sun fice kenan


da gudu gudu sauri sauri ya qaraso cikin parlojt din saboda ruwan da ya sake danyin qarfi,duk da haka ya jiqa masa fararen kayanshi,ya tsaya ya kulle ko ina ya rage yawan qwayayen dake kunne kana ya doshi dakin kai tsaye


a hankali ya tura qofar dakin kana ajjiye tarin ledojin dake hannunshi,qamshin dake dakin kawai ya isa ya tabbatar maka rana ce ta musamman,tsaye gayi hannunshi harde a bayanshi,sai ya lumshe idonshi yana zuqar qamshin qasa hade da turaren jikinsa da na dakin baki daya yadda suka hadu suka fidda wani qamshi na musamman kuma na daban,gwagwarmayar da ya fada kacin samunta ta zama mallakinsa ya dinga dan tunawa,a hankali ya bude idanun nashi ya tsaya yana qarewa shigar tata kallo


gaba daya jikinsa ya saki lokacin da wani tunani ya darsu a ransa wanda ya qada maaa qwarin gwiwa da azamar isa gareta,tamkar mai tausayin gadon haka ya hau ya dinga rarrafawa har ya isa gareta kana yayi zaman dirshan a gabanta


sannu a hankali ya dinga yaye mayafin dake kanta har ya cimma nasarar cireshi duka fuskarta ta bayyana,saidai ya cimma idanunta aruntse ne,ya karyar da kai yana ci gaba da kallon fukartata irin kallon da bai taba samun dama ya tsaya yayi mata shi ba,kyawunta yaci gaba da fito masa muraran,sosai ya shagala har baison abinda zai shiga tsakaninsa da yanayin


Qememe zuciuarta taqi amincewa da daina mugun tseran gudun da take,gashi ya sata agaba,nauyi da kunyarshi sun hanata bude ido,jin shirun yayi yawa ya sanyata yanke shawarar bude idanun nata ko yama fita adakinne ma bata sani ba


da kadan da kadan ta dinga budesu har sai da suka kammala buduwa tar,da qafafunshi ta soma tozali a hankali ta dinga daga kan nata har ya sauka bisa fuskarshi da ruwan sama ya jiqa har ruwan da ya soma taba kanshi ke diga kadan kadan,batasan lokacin data ta wuntsila gefe ba cike da *TSORO RAZANI DA FIRGITA BA* sakamakon wanda ta gani


*ABDALLAH* ne cikin daren nan cikin gidanta kan gadon aurenta?,idanunta ke mata gizo koko meye?,me yake faruwa ne?,hauka ce ta samu qwaqwalwar abdallah ko bashi bane bama gaba daya aljanu kesan mata wasa da qwaqwalwarta da tunaninta,ina abdur rahim da ya bar abdallah ya keto dakinsu na sunnah?
dimbin tambayoyin da suka nemi jirkita mata qwaqwalwa kenan tashi guda ba tare da tasan duka amsoshinsu ba





*mrs muhammad ce*👑



adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *