Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, October 20, 2018

AURE KAN AURE COMPLETE HAUSA NOVELS ONLINE

adsense here
AURE KAN AURE COMPLETE HAUSA NOVELS ONLINE

AURE KAN AURE COMPLETE HAUSA NOVELS ONLINE



AURE KAN AURE
*Book1*
Chapter1*
Bugun qofar da ake tamkar za,a balle kyauren
shiya Tilastama Hajia nafisa tashi daga kishin
giden da take Tamkar wacce tasha wani uban aiki
ta gaji Tamkar wacce aka tunzura ta jira silifas
dinta dake gefen kujeran nata ta nufo qofar cikin
sauri Tana fadin dakata ku dakata Ta bude qofar
tana musu kallon Uku kwabo kamin taja wani
Dogon tsaki mtwwwww Kai bagidajen mutu baiba
a rayuwa inba gajidaje dan qauye ba Waye zaizo
yaita buga qofa yafi minti talatin ba,a budeba.
Kuma ya nace yaqi kama gabansa Ta kauce tace
ku shigo kar a koma qauye ace na hana yan uwa
shigowa gidan dan uwa Basuce da ita uffanba
saima da suka shige suka kama rawar jikin
gaisheta Ta daga musu hannu ku saurarar
Banason hayaniya kunji ko Kada ku cika mana
gida da warin baki tai gaba ba tare data basu
Izinin qarasowa ba Hakan bai hanasu damar
shiga falonba suna qoqarin zama kan kujera ta
daka musu tsawa Kai ku dakataa Karku sake
waye ya baku izinin zama kan kujera? Ku zube a
qasa duk wqacce ta zaunamin akan kujera wlh
sainaci mutuncinta Nina rasa irin wannan maita
sai kace ku kadai keda dan uwa Ku ala dole
dangin miji Ko wacce ta kwaso busassun
qafafuwanta babu ko wadatar basilin Dan a
ketamin yadin kujera da busassun. Fatar jikinku
ko To ku zube a qasa kuyita zama inya dawo dan
uwan naku kwa ganshi Ta balbalesu da harara
Tana fadin munafukai inda bashi Dashi babu mai
kallonsa balle ya taimaka masa da ko sisi Tai
tsaki ta juya ta haye saman benenta Tun misalin
qarfe hudu na yamma suke tule babu wanda ya
waiwayesu Saidai masi aikin gidan wata budurwa
da tsohuwa daketa kaiwa da komowa Akai sallar
magrib duk sunanan Zube soma suke a nuna
musu toilet dan su dauro alwala Suyi sallah
amman da sukaima yan aikin magana sai sukace
wai hajia bata basu iziniba Sunanan zaune har
akai sallar isha,I yar yarinyar waddah Bata wuce
shekaru27 ba ta dubi dattijuwar waddah ba zata
gaza Shekaru hamsinba Tace goggo kodai ki tashi
muje gida kawai Dubi yaddah aka watsar damu
sai kace bola anan Yar tsohuwar da ake kira da
gwaggo tace Ke tashi nan wawiya in zamu
kwanan anan munanan a zaune har sai yaxo In
har muka ganshi sakarya mun warke Ta gyada
kai to allah e kawoshi lfy Qarfe tara daidai aliyu
ya shigo gidan nasa yana shigowa yai ido hudu
da yan uwan nasa Da sauri ya qarasa yana Ah
gwaggo yaushe kukaxo? Tafiyar dare kukai? Ya
duqa gwiwa bibbiyu yana gaisheta ta amsa da
fara,arta Dajin dadi rakiya ma ta gaidashi Ya
amsa yana maimaita tambayar tashi yanxu
kukaxone Kokun biya wani kurin? Gwaggo ta tabe
baki tace ba inda muka biya ali gidanka muka
Yoma tsinke Wannan yar iskar matar taka marar
mutuncin ita ta zubar damu tun la,asar muke Nan
zube Kaidai bakai sa,ar mataba wlh Bakai sa,ar
maceba ali Cikin rashin jin dadi yace kuyi haquri
dan allah gwaggo Ya miqe da sauri sashin masu
aiki ya nufa yana kwalama ladidi Kira Tazo ta
zube a gabansa tace gani Yace anbama baqinda
sukaxo abinci kuwa? Cikin rawar murya tace ai
hajia Bataceba Ya dafe kai cike da takaici Ya
dago ya dubeta Yace jeki kai musu abinci sannan
Ki hada musu da lemukan kwali da juice kikai
musu Kuma daga yau duk wanda ya shigo cikin
gidannan kar,a sake a barshi ya fita har sai an
bashi abinci yaci ya qoshi saidai idan shine yace
bazai ciba Jiki na rawa tace an gama ranka ya
dade Sannan ya juya ya fita ya koma wajen
goggon tasa e zauna yana Fadar Amman ba
ganki da ruqayyah goggo ina mijin nata? Cike da
takaici tace ai kasan irin halin naku na maza ali,
Kishiya jibro yai mata kuma ya soma wulaqantata
dan yayi amarya Shine tayi yaji Kagantanan yau
kwananta uku Da mijin ya biyo sahu nai masa
Tatas Naja masa kunne nace Kuma gobe zan
koma da ita da kaina To kasan halin naku indai
mace Bata da wani dan sana,a bata maida taro
ya zama sisi Shikenan kun rainata kenan Shine
nazo Na rokeka ka siya mata wani dan abun da
zata dinga sana,a Dashi acan qauyen don allah
Ya gyara zama yana ai wannan Ba wani abu bane
Goggo Ya dubi rakiya yana fadar ke yanxu Me
kikeso a siyan miki Wanda kikasan yanada saurin
Kawo kudi? Tace duk abinda ka siyamin yayi
Goggo tace ni nasan abinda za,afi samun kudi
dashi Ka siya mata injin murjin taliya Da keken
dinki tunda ta iya Dinki tun tana gida Yace to
shikenan goggo allah Ya kaimu goben insha
allahu Zansa a siyo mata Nan suka shiga godia
ladidi ta shigo musu da kwandon abinci Ta jejjera
musu da flate Cokula da kayan drinks yace ladidi
Jeki kyara musu dakin baqi idan sun gama sai ki
nuna musu dan suje su huta Ta amsa da to Yace
shikenan goggo koda akwai Abinda kuke buqata?
Tace ba komai goggo allah yai Maika albarka ya
kuma sauya maka da mata ta gari Baice komaiba
murmushi kawai Yayi ya miqe ya nufi sama S
saman benen sashi biyu ne Hagu da dama.
Dauke da katafaren falo Wanda aka qawata da
manyan kujeru da kayan alatu Zamu iya kiran
wannan bangare da aljannar duniya A cikin falon
akwa bedroom biyu wanda yake dauke da
qaramin Toilet Duk abinda yake wannan sashin
akwaishi a dayan sashin Hatta capet din dake
tsakiyar dakin Sashin matarsa ya nufa ya kashe
kayan kallon daketa ruri Banza ya nufi bangaren
nata Kwance take saman katafaren gadonta dake
dauke da kayan alatu Daga ita sai wata
gajeruwar rigar bacce Iya cinya mai sulbi Gashin
kannan a barbaje saman Filo Tai rub da ciki
tanata latse latse A. Laptop dinta Yana sallama
ta tashi ta zauna Bakinta dake da murmushi
Wooo welcome my one Babu alamar zai mayar
mata da murmushin fuska ya qara daurewa Ya
jingina da bango ya harde hannayensa a jikin
kirjinsa Yana kallonta Tadai? Ta fada tana
kallonsa ba tare data qara matsawa daga inda
takeba Fuskar tashi ba walwala ya soma magana
Nafisa wulaqancin da kikemin ya soma isata cin
fuskar da kikemin ya isa haka Ki sani yanda
kikeson danginki yan uwanki da iyayenki haka
nima nakeson nawa dangin Yan uwana da
iyayena Ya taka har gabanta yana nunata da
dogon dan yatsansa Yana fadar Na rantse miki
da girman allah Ki kiyayi wulaqantamin yan uwa
ya isheki haka Wani murmushi taja hade da tabe
baki tana fadar Sannu mai iyaye dan allah kai
bakaji kunya ba? Ka dubi wadannan damejin
halittun har kake kiransu da yan uwanka.?
Kauyawa gidadawa wadanda kircin talauci ya
ishesu'' Ji yayi tamkar tana watsa mishi Garwashi
a kirjinsa Ya daga hannu zai watsa mata mari
Tunanin me yayi kuma sai ya fasa ya sake
hannun nasa Idanunsa sunyi jajir Ya juya a zafafe
yabar dakin Nata zuciyarsa na tafarfasa Kamar
garwashin wuta Shi nafisa take zagi? Yanxu ta
Zage masa tushensa asalinsa iyayensa? Ya
damqi sumar kansa yaja da qarfi Idanuwannan
suka rikice tamkar Jan gauta Shin wacce
qaddarace ta hadashi Da nafisa? Mai yasa yai
auren Kudi? Meya kaishi auren macen data
Kerema ajinsa? Kuma iyayenta suke taqama da
yayan banki? Mai yasa bai tsaya inda allah ya
ajeshiba ya auri tushensa irin asalinsa? Da yanxu
bai samu kansa a wannan baqin cikin da
takaicinba Ya ilahi Abinda ya fada kenan Ya fada
saman kujeran dake falonsa Zuciyarsa naci gaba
da tafarfasa Tamkar wanda aka tsikara ya miqe
da sauri yai hanyar fridge Ya bude ya dauko
roban ruwan faro ya murda ya dinga zazzagama
cikinsa Ya dire robar saman fridge din da qarfi Ya
koma ya kishin gida sanyin ruwan na ratsa mashi
zuciya Tunanin abinda suka faru shekarun da
suka wuce suka dinga dawo masa Shin meye ya
faru a shekarun Baya saiku biyoni danjin ko
wadanne abubuwane suka faru-------
AURE KAN AURE
CHAPTER 2
Musawa wani kauyene dake garin katsina Garine
dake dauke da jama.a da masu rifin asiri Gidan
malam shehuqaramin gidane ko a garin gidane
mai Qaramin katanga Wanda da ka hangoshi
zakasan Gidan talakane
Malam shehu mai almajirai sunan da ake kiransa
dashi kenan a garin
Ba boyeyyen mutum bane dan dan asalin garinne
Malam shehu su hudu ne wajwn mahaifinsu
Kowanne yana kasuwancinsa wato noma da kiwo
Saidai duk ba masu dashi bane saidai
Rufin asirin ubangiji
Malam shehu kuwa shi baima da gonan saidai
dan yawonsa da
Yake da koyar da almajirai a qofar gidansa
Duk Ran laraba suke harhada masa naira goma
goma
Dashi Yake samu yana rufama kansa asiri
Sunan matarsa hafsa ita kadai gareshi suna
zamansu lfy
Duk duniya da daya Allah ya basu wato aliyu tun
dagashi Allah bai qara basu
Haihuwa ba malam ya tsaya tsayin daka wajen
bashi ilmin mahammadiyyah
Dan yana dan shekara ashirin ya haddace
alqur,ani mai girma tare da sauran littafai
Aliyu yarone mai zuciyar neman na kansa hakan
yasa ya dake
Idan ya samu noma ko aikin gini kodai wani irin
aikine indai na Qarfine yake
Dan kawai yaga ya farantama iyayan nasa
Daga baya ya Bude wani dan case a bakin titi
yana siyar dasu rake biskit
Cingam tomtom dadai sauransu
A haka yake samu yana tausayama iyayensa dan
aliyu mutum ne mai Jin qai da tausayin iyayensa
Haka yasa suke matuqar sonsa fiye da komai a
rayuwa
Rannan kwasam cikin almajiran da ya koyama
karatu da yake akwai
Yan garuruwa da dama
Wani Daga ciki Wanda ake kira da muftahu
Dan asalin garin kano ne ya ziyarci malam shehu
Muftahu yayi kudi sosai dan harkar kasuwanci ya
fada tsumdum
Kuma yana samu dan yanada shaguna
Manya a kantin kwari
Bayan ya gaisheshi yai masa alkhairi
Bayan zai tafi ne ya roqi malam din Akan ya
bashi aleeyu ya
Taafi dashi dan ya saShi a daya daga cikin
shagunansa
Daa farko malam shehun yaqi yarda saida
yayansa malam sule
Yasa baaki saannan ya yarda
Sannan ya dauki aleeyu ya tafi dashi mahaifiyarsa
Kuwa har kukan rabuwa tai daashi dan tanason
dan nata kamar rai
Iyayensa sunsa masa albarka sosai
Zuwansa kano
Qaton shagone aka Bude masa muftahun ya
hadashi da wani yaro ana ce masa
Ubale
Babu laifi a shagon ana samun ciniki sosai kayan
costimetic ne ake siyarwa
Duk wata yake biyansu dan haka aleeyun ke raba
kudin biyu ya hau mota ya nufi qauyensu
Yakaima mahaifansa tare da yan siye siyen da
ba,a rasa ba
A haka alhaji muftahu ya shiga harkar siyasa
tsamo tsamo aka
Shiga damawa dashi
Mutum ne shi mai gaskia da qaunar mutane haka
Yasa bai cika samun tangarda
A Duk inda Yasa gaba
Kullun cikin kyauta yake baya gajiyawa
Takarar dan majalisa ya fito cikin ikon Allah
Kuwa Allah ya bashi sa,a ya lashe
Dan haka aka shga damawa dashi
Kasuwa ta Bude aleeyu har ya fara gyare gyare a
cikin gidansu
Ya canjama mamansa da babansa gado da ledar
qasa Yasa musu na zamani
Hatta yan uwan mahaifinsa bai barsuba yana
taimaka musu yaddah ya
Kamata
Iyayensa yanxu babu abinda sukeson gani irin
suga ya samu abokiyar rayuwa wato
Mata kenan
Shikuwa ta bangarensa babu wannan a zuciyarsa
burinsa kawai ya jiqa iyayensa
Hakan yasa ya toshe kunnuwansa game da duk
wani surutai da za,ai
Akansa
Alhaji muftahu baihau mulki ya saaukaba saida
yaimaa jama,a aiki
Naban mamaki hakan yasa jama,a suka qake
qara nunaa masa so
Aleeyu ya biyaa kudi ya zana jarabawa weaac
dan daman yaayi frimary da ya fara secoundry ne
ya watsar sbd matsalar kudi
Yayi jarabawaar a sa,a sakamako ya fito tai
masa kyau
Alhaaji muftahu ya tsaya masa shida kansa yaa
sama maasa
N,c,e yake zuwa ranar jumaa,a kaawai da asaabr
Ya maida hankalinsa a shekara uku yaa
kammaala y jona digiri dinsa
Shima a partyme yayi
Alhaaji muftahu siyasa saai abinda yai gaba dan
wannan karon kujeran sanata ya
Nema. Kuma Allah ya bashi sa,a ya samu
Wata ranar. Alhamis aleeyu na makaranTa
Alhaji mufthu ya kirasa a waya yace yai maza
maza yaje airport da mota ya dauko
Masaa yarsa nafisaa waddah zata dawo daga
qasar englaand
Da misalin qarfe uku
Ya amsa da an Gama yallabai
A take ya tau machine dinsa ya nufi
G,r,a gidan alhajin nasa daman ya saba. Zuwa
dan suna mutunci da matar
Gidan da yaransa suna girmamashi yaddah ya
kamata
Ya shige katafaren gidan Wanda za,a iya kira da
aljannar duniya
Ya samu hajia asiya a zaune kan kujera
Ya zube yana kwasar gaisuwa ta amsa cikin
sakin fuska tace kai tashi
Aliyu zauna kan kujera
Ko kuma qaraso muci abinci
Yace a,a hajia daman Alhaji ne yace naxo na
dauki mota naje na dauko
Nafisa a airport
Tai daria tace na sanka Aliyu abincin da bakason
ci yau sai naga gudun ruwan ka
Ya miqe tace ga key can Akan kujera ya dauka ya
fice
Yana daria. Har ya shga motar yana shirin tadata
ya jiyo muryar kausar
Tana kwala masa kira ya fito
Ta qaraso inda yake tare da murmushi da
muryarta mai cike da natsuwa tace
Tace yanxu ba zaka tsaya kaci abinciba
Jin shigowarkanefa yasa na shga kichin dan na
hada Maka juice
Ya sakar Mata wani murmushi Wanda ke sace
zuciyar yan mata
Yace
Amsorry kausar ba dadewa zanyiba nafisa kawai
zan dauko a
Air port just dirty minut
Lumshe kyawawan idanunta tayi tace to naxo na
rakaka?
Yace kin fasa hadamin juice din kenan?
Tai wani daria mai kama da murmushi tace
A,a zan hada Maka yaya aleeyu saika dawo
Ya juya yana fadin to kausar
Yaja motar ya fice shidai kausar tana birgeshi
Har qarqashin ranshi shidai yanason kausar
Itace irin matar daya cancanta ya aura
Kwata Kwata bata dauki duniya da zafiba yai
wani murmushi lokacin da take
Ya lumshe idonsa a daidai lokacin daya hasko
hotan fuskarta
Qarfe uku daidai ya isa airport din
SanadiYyar cinkoson ababan hawan dake kan
hanyar
Can ya hangota tana zaune a kan kujeran da aka
tanaza a wajen domin zaunawa
Da jakkunanta har guda biyu
Gabansa yai mummunan faduwa shidai duk
jarumtarsa yakan ragwance idan ya
Hadu da nafisa
Kyakkyawace ajin qarshe fara tas tanada siririn
hanci da dan qaramin baki
Idanunta basu da girma sosai sunfi kama da kalar
barci
Ta hadu anyi sa,arta saidai ba,ai sa,ar Hali ba
Macece sangartacciya an Riga an shagwabata
idanunta a tsaytsaye suke bata ganin mutuncin
kowa
Tun farkon zuwansa kano Alhaji ke aikansa gidan
amman da
Zaran yaje saita dinga kunyatashi a gaban
mutane
Taita tuntsirewa da daria tana nunama
qawayentta shi musamman idan yai
Kwalliya. Taita Kiran yan gidan tana suxo su kalli
kwalliyar dan qauye
Har akwai ran daa tacema daddyn ta daya dawo
Mata dashi gidan nasu dan kawai ta dinga
kallonsa tanacin daria
Haka kawai ta rainashi baisan me yasa ba
Gabansa ya sake faduwa a lokacinda ya hangota
tanaa duba aagogon hannuntaa
Ya qarasa da sauri tare da Jan wata doguwa
sallama
Da sauri ta dago tana kallonsa na wasu sakwanni
Tamkar mai karanta wani abu a cikin idanun nasa
Tunda take a duniya bata taba kallon idanun
namijinda suka saukar Mata da mummunan
mutuwar jiki kamar aleeyu ba
Zata iya wuni a haka tana kallon kyawawan
idanunsa
Ganin bata da niyyar amsa masa sallamar yace
kiyi haquri hajia
Goslo ne ya tsareni
Taja wata sanyayyar ajiyar zuciya
Ta lumshe idanunta ta Bude ba tare da taace
masa uffan ba
Taci gaba da kallon tsakiyar idanunsa
Ya sauke idanunsa ba tare da yayarda sun qara.
Hada idonbaa
Yace kiyi haquri bada gangan hakan ya faruba
Wani gajeran murmushi Taja tana wasa da
harshenta
Batace komaiba hakan ya qaara tilastaa masa
saake kaallonta
Tajaaa wani sakaran murmushi tana wasa da
idanunta a cikin naashi
Ji yai yanaa shirin faduwa yai saurin dafa qarfen
dake kusa dashi
Cikin kidima kuma ba tare daya kalletaba yace
zamu iya tafiya ko?
Cikin muryarta mai taushi tace zamu iya zama
anan inhar ka yarjemin naiata kallon kyawawan
idanunnan Naka da sukafi. Ko wane ido kyau a
duniya
Maganar ta dirar masa tamkar a mafarki Yama
rasa abin cewa ya kasa
Kallonta
Ta miqe taxo har gabansa dan har sunajin
numfashin juna
Tace na Fahimci kai marowacine amman muje
gida sai kai tsada na biya
Aure kan aure
Chapter 3
Tace bari muje gida sai ai tsada na biya
Bata jira amsarsa ba ta suri qatuwar jakan tata
ta hannu tai gaba shi kuma ya shuru akwatinan
ya saka a Cikin boot din motar ya shiga
mazaunin direba
Abin ya bashi mamaki ganin ta shiga Gidan gaba
ta zauna
Ita daya cancanci ta zauna Gidan baya ya bita
Yadan saci kallonta akai rashin sa,a itama kallon
nashi take
Ta kashe masa ido daya da sauri ya janye fuskar
tashi yasama motar key ya
Zungureta sukai gaba
Da hannu daya yake tukin ya daura daya hannun
nasa inda
Aka tanada dan daurawa ganin haka yasa tai
saurin riQo. Hannun nasa yai saurin
Waigowa tace
I like to se ur face please
Sauri yai ya maida kallonsa kan titin inda Allah
ya kiyayye da ya daki bayan wata
Babban mota yace ya Salam ganin haka ya
tattaro natsuwarsa ya daura Akan titin
Suna isa gida ya Bude. Qofa yana qoqarin fita ta
riqo hannunsa
Cikin bacin rai ya waigo ganinyanda taga fuskar
tashi
Ta canja yasa ta sakeshi tana wani
Ni,im taccen murmushi ba tare da ya qara
waigowa ya kalletaba yai gaba abinsa
Yan gidanne suka fito anata murna ga anty nafisa
ga anty nafisa
Kowa sai murna yake shi kuwa wani takaicine ya
isheshi yace shin daman
Haka Mata birni suke kodan baya hulda dasune
ko a qauye shi yasa
Bai fahimci hakanba
Yace kai ina Mata wasu ababene masu natsuwa
kawaici da kunya
To ya akai ita nafisa bata da ko daya to ya akai
kausar keda duk wadannan
Abubuwan amsar da e kasa ba kansa kenan
Ya shiga sashin momyn nasu ya Bama yar aikinta
makullun zai fice kenan ta fito tace ina yar
momyn takene aleeyu yai murmushi yace gasu
can a waje hajia
Sukai wajen tare tana hango momyn nata ta sasa
ihu tai kanta ta rungumeta sai murna suke shi
kuwa kai yasa ya raba. Zai wuce
Sai ji yai kausar na fadin yaya aleeyu kai yaya
aleeyu cewa fa kai na
Hada Maka zaka dawo kaci yai murmushi yana
kallon kyakkyawan
Sanyin yarinyar na tafiyar masa da hankali
Ya waigo yana mrmushi
Yace am sory kausae mancewa nai muje
Da murnanta suka jera dinning din kichiin ta
kaishi ta xuba masa komai
Sannan taja kujera ta zauna sai hira mai dadi
taake masa
Harya gamacin abincin aamman hirar bataa
qarebaa
Kamr an jefota ta fado kichin din
Da kaallo duk suka bita yaddah taai wani kichin
kichin zaakasha waani abun bacin ran ta gaani
Fuskar kausar dauke da murmushi tace me
kikesone anty ta
Qara hade rai tace me kike anan?
Tambayar bataima kausar dadiba dan haka ta
rasaa amsar da zata bata
Da hannu tai Mata nuni da tashi ki wuce kalaman
nata suka karya Mata
Zuciya idanuwanta suka ciko da hawaye muryarta
a sanyaye tace haba anty mae
Yasa........
Ta. Katseta ise get out jiki lakwas ta miqe ta kalli
yaya aleeeyum sannan ta gaba
Har Cikin ransa. Baiji dadiba takaicine fal a
zuciyarsa
Nai ankaraba saiji yai an dafa kafadara ya waigo
da sauri ransa a bace
Cikin kakkausar murya yace meye haka nafisa ya
kike abu kamar ba musulma ba?
Itama ta zaro idanunta tace yadai kake abu
kamar ba wayayyeba
Tace haba aleeyu dubekafa namiji har namiji babu
inda Allah ya tauyeka
Gaka dakyau kamar dawisu
Ga kwarjini kamar daamisa tunda nake ban tabaa
ganin namijin da zuciyata
Ta kwadaitu dashiba sai kai
Sonka nake aleeyu Wlh Sonka nake inada kishi
ban yarda ko qannena na dingaa ganin suna
kusaantarka ba ballantaana har hira ta shiga
tsakaninku
Daaan zan iyaa batawaa da Kowa akanka
Ji yai wata xufa na karyo masa Cikin hanzari ya
fice daga kichin din
Yai murmushi tace ya rage naka
Ta. Duqa ta dauki kofin da yasha juice din a ciki
ta lashe tas
Lol. Kunji mayyah
Abin duniya ya ishi kausar dan tabbas ta karanto
wani abu a idanun
Yayar tata to ya kenan?
Tace tunda take bata taba ganin Wanda lokaci
guda ta kamu da sonsa ba
Wanda ta taBbatar Shima yana son nata
Dan sau rari idan suna hira yana Mata wasu
kalamai
Dake kama Dana soyayyah tace tabbas idan
batasan abinyiba yayarta zata mataa
Shigaar saauri
Gidan Alhaji muftahu gidane dake cike da tarbiya
matarsa daya da
Yayaansa biya
Nafisa babba kausar me bi Mata
Sai ammar yusuf da kalifanafisa ta Gama digiri
dinta a wannan shekarar sai kuma kausar dake
level2. A. @B,u,k dake kano
Duk cikinsu nafisace kawai ta fita zakkah bataji
ko kadan. Dan har a dangi ana kuka da ita
Gashi ta liqema kamilin mutum irin aleeyu Wanda
kyale kyalen duniya bai
Gabansa to ya kenan?
Muje zuwa
Kwata Kwata aleeyu ya fitar harkaar Gidan sbd
shu,uma nafisaa
Dan ko Alhaji ya aikeshi Gidan sai yai saurin
kawo mishi uzuri
Abin ya fara damun kausar harta fara tunanin ko
yai fushi da abinda nafisa
Tai masa ne
Dan haka ta yanke hukuncin kiransa a waya
domin ta bashi haquri da sauri ta nufi dakintaa
ringin daya biyu ya dauka da fara,arta tace yaya
aleeyu ai mana afuwa tuba muke idan har laifi
mukai
Idan har laifi mukai da aka yanke mana wannan
hukuncin
Yai murmushi yace waneni kausar ba abinda
kukai min
Taace to shine ka yaadamu yau sati daya kenan
baka zoba dan ko daddy bai aikokoba kaana
zuwa duba momy duk ran juma,a
Yace tuba nake ranki e Dade inanan zuwa gobe
insha allahu
Tace yauwa yayana dagananma akwai Maganar
da nakeson zamuyi
Yai murmushi yace kinsanni da qaguwa Akan son
Jin zance fara labaartamin naji
Aransa addu,a kawai yake Allah yasa cewa za(ai
tana sonsa
Tace a,aa yayaa saidai kaxo yace alqawari fa
tace eh nayi
Sukai sallama ya kashe wayar
Har ranta tannason bawan allahn yanada kyau
gashi da kyawawan dabi,u
Bayan sallar isha,i duk suna zaune a falon
daddyn nasu mommy da sauran yaran
Qannenta da afisa tana kusa da mommy tace
Shinema ko kiyi cigiyata tun yammah ko?
Mommyn ta kalleta da murmushi
Tace na leqa ai naga kina Barci daxun
Tace yauwa momy daxun mukai waya da danki
yace wai yana gaisheki wai gobe zaizo
Momyn tace yai zamansama aini nai fushi dashi
Nafisa ta dubi Momyn nata kamin ta maida
kallonta kan kausar din
Ke kuma meya hadaki dashi?a ina kika samu
lambarsa?
Tace ke kinjimu da anty dan bakison mutum saiki
hana Kowa mu,amala dashi
Nafisa tace uban wa ya gaya maki bana sonsa
iye?
Kausar ta dauke kanta daka kallonta tana kallon
daddy dake fadin
Ke meye haka bana hanaki wannan dabi,ar ta
zagi ba?
Ta shagwabe tace to daddy nifa sonsa nake haka
kawai
Sai taita shishshige masa
Yace waye?
Tadanyi murmushi kamain tace aleeyu mana
daddy danka
Wani irin fara!a ce a fuskarsa yace alhamd yata
Ba qaramin farinciki wannan abun yasaniba
Da kaina zan masa magana gobe daman dazu
yake fadamin ya kammala
Karatunsa kinga sai!a tsaida rana kawai
Ko kusa mommy bataso hadinba dan haka
fuskarta ko walwala babu
Tace amman kuwa Alhaji ya kamata a tuntubi
yaronnan aji
Tabakinsa dan hadinnan Kwata Kwata baiba
Dan halinsu ko kadan baixo dayaba inama laifin a
hadashi da kausar
Dan da itace kawai zasu iya samun kwanciyar
hankali
Nafisa kuwa ta raina Kowa bata ganin jama,a da
gashin arziqi
Ga girman kai
Alhajin yace ni nasan ba zamu samu matsala da
yaronba sannan ita kausar din ba sai in
tanasonsa ba
Kinsan ni bazanma Dana auren doleba tunda dai
ita nafin na sonsa
Sai muyi fatan alkhairi
Momy taace haba Alhaji ai baabu yarinyar da
za,aa Bama aleeyu tace bai mataba
Dubi iyayi irin na nafisa amman tace tanasonsa
inaga kausar
Kawai saidai muce Allah ya zaba abinda yafi zana
alkhairi
Ya amsa da amin
Kausar ta dago da idanunta wadanda suka kada
Sukai jajir
Ta miqe jiki a sanyaye ta fice
Tuni tausayin yar tata ya kamata dan Tuni ta
Gano kausar Nason aleeeyun
Kuma Shima ta fahumci yana sonta
Saidai babu yaddah zasuyi da abinda aallah ya
hukunta
Lokacin da Alhaji muftahu ya tunkari aleeyu da
jancen
Ya rasa shi a wace duniya yake ba halin yaqi
aaamincewa dan
Bazai iya watsama uban Gidan nasa qasa a fuska
ba
Don haka ya amince
Da kansa alhajin yaaje qauyensu aleeyun ya
sanar dasu aauren ba qqaramin faarin ciki Sukai
ba aka tsaidaa ranar auren wataa mai kaamawa
Tunda akaa tsaaida maaganar auren aleeyu ya
gazaa zuwa gidaa Sbd tashin hankalin da yake
ciki
Ta yaya zai iya rayuwa babu kausar?
Alhajin daa kaansa yaima aaleeyu magaana
aakaan rashin zuwansaa zance yaji kunya sosai
dan haka ya tsaida ran Akan yau zaaije baaaayan
sallar isha,i
Yana gamaa sallr kuwaa yaaa wuce ba wata
kwallliyace a jikinsabaa
Tshirt ce kawaai baqaa da jeans
Yaasan shi mai laifine hakan yasa kai tsaye ya
nufi Cikin gidan
Yai sa,a kuwa duk suna falon gabaa daayaansu
Kai tsaye idonsaa kan kausaar yai
Zuciyaarsa ta tsinke daya lura shikenan sun
haramta ga juna kenan
Jinda yai ana fadar ah aleeyu ne yasa yai
Saurin dauke idanunsa yaa shiga yana nine momy
Suka gaisa sosai shida mommyn da daddyn
baayan sun Gama gaisawane
Daddyn yace ai saiki kaishe can falon baaqi ku
zantan ko Cikin zumudi tace taso muje tashi
kawai yai ya bita ba tare da yace komaiba
amman hankalinsa da
Tunaninsa nakan kausar Bayan sun fitane daddyn
yake cewa a wani sbn bank da za*a Bude
kwanannan na samar masa aiki. Zai zama
manajan bankin
Momyn tai murna sosai
A falon ya sameta ta saki wani irin murmushi
Tace yauwa nawan kokaifa idanunka sunfi komai
daukar hankali
Tadanyi shiru kamin tace nasan badaa son
raankaa ka kawomin wannan ziyarar ba
To amman ba yaddah zakai yaddah na ganka yau
haka nakeson ganinka gobe jibi
Kullunma ka gane ko?
Idan bakazoba to ni zanzo kuma ko gabansuwa
kake to
Saina baka kunya
Tunda na lura kai komima kunyarsa kakeji
Sannan idan daddy ya tambayeni ina zanje ko ina
naje nace masa kaika kirani kace naje na sameka
Kallonta kaawai yake dan Kwata Kwata baya
hayyacinsa
Dan haka yabarta tanata zuba kusan awa daya
sai surutu take ko qala baice mataba
Saima tashi da yai yace zai tafi ta riqeshi wai a
dole saiya qara jira
Saida yai da gaske ya samu ya zame ransa cike
da baqin ciki
Ba yaddah zaiyi dole yasama ransa sa,ida Allah
yasa hakan shiyafi zama ailkhairi
Ba yaddah ya iya haka ya dinga jera kwanaki
kullun sai yaxo
Ya samu aikinsa dan harya soma zuwa office
Sun bashi gida qato tsaraarre tare da wata mota
mai numfashi ta banki da miliyoyin kudi domin
wanke talauci
Momy tasa amarya tare da kausar Akan suje su
gaishe da iyayen aleeyun
Momy ta shirya musu tafia harda aleeyun da
tsaraba
Na kece raini
Direban Gidan ya daukesu a mota sai garin
musawa a jahar katsina unguwar saniyawa
Tunda suka hau hanyar qauyen naafisa ta dinga
waige waige
Can dai ta kasa daurewa ta dubeshi tace
Tace kai aleeyu wai yanxu mutanene ke rayuwa a
Cikin wannan dajin kauyen?
Tambayar tata ta bigi zuciyarsa tazo masa wuya
Yai wata murmushi da za* a iya kira da yaqe
yace
A wannan dajin kauyen da kika gani mahaifinki
yai rayuwa tun yana dan shekara sha biyar har
yakai ashirin
Tsit tai tankar ruwa ya cita amsar tai mataqar
yima kausar dadi
Dan ko banza yayi maganin iskancinta
Aure kan Aure
Chapter4
Tunda suka hau hanyar qauyen naafisa ta dinga
waige waige Can dai ta kasa daurewa ta dubeshi
tace Tace kai aleeyu wai yanxu mutanene ke
rayuwa a Cikin wannan dajin kauyen?
Tambayar tata ta bigi zuciyarsa tazo masa wuya
Yai wata murmushi da za* a iya kira da yaqe
yace
A wannan dajin kauyen da kika gani mahaifinki
yai rayuwa tun yana dan shekara sha biyar har
yakai ashirin
Tsit tai tankar ruwa ya cita amsar tai mataqar
yima kausar dadi
Dan ko banza yayi maganin iskancinta
A qofar Gidan nasu direba yai parkin suka sauka
nafisa sai bin lungun Gidan nasu da kallo take
Yai gaba yana kuzo mu shiga yai gaba suka
biyoshi a baya
Ba laifi Gidan shafaffene da siminti da hanzarinta
innan tasa ta taSo tana sannunku da zuwa
maraba da
Manyan baqi
Ku shiga daga ciki
Kowa ya cire takalminsa amman nafi taqi da nata
ta shiga
Dakin sai kamshi yake ga saitin kujeru
Kausar ta zauna daga qasa nafi kuwa ta dare kan
kujera ta daura qafa daya kan daya sai kadasu
take tana taunan cingam
Aleeyu bai shigoba dan yana waje suna magana
da inner tasa
Kausar ta yafitota murya qasaqasa tace dan Allah
sauke qafafunnan naki anty ki cire shoes dinnan
babu dadi wlh
Taja wani gajeran tsaki tana fadar har Wasu
tsofaffin kirkine da zan
Guji bacin ransu
A wace tashar ake nunosu ko a wace jaridar ake
bugasu?
Ta qarajan wani dogon tsaki tana
Kada ki kuma batamin rai
Bata sake magana ba Sbd tahowar innar
Baqi hansha hanya ya aka baro iyayen?
Duk kausar ne ke amsa Mata sannan direba ya
gaisheta
Saida suka Gama gaisawane sannan nafi tace ina
yini?
Lfy lau ta amsa tana tambayarta ya hanya
Inna ta dubi Direban tana wacece sirikar tamu?
Yai murmushi ya nuna Mata nafi sai taga makar
kausar ya nuna Mata dan haka fara!ar tata ya
qaru
Dan ta yaba da natsuwar kausar din
Inna ta miqe ta kawo musu burabuskon alkama
Wanda tai musu da miyar kaji
Abinci sai qamshi yake aleeeyu ya kawo musu
lemuka da robar ruwan swan
Sannan yacema Direban da ya taso suje suci
nasu a can Dakin tsohon nasa
Kausar ta dubita tace sauko mu dan taba abinnan
kar muqici ba zasuji dadiba
Da wata harara ta bita tace nice zzanci wannan
abincin?wato kwalara ta kamani ko?
To bazanciba in sunxo sun iske bamuciba haushi
e kashe su
Bata sake maganaba kausar din ta sauka ta zari
flate ta zuba burabuskon dadin abin ya ratsata
nanfa ta zauna ta cika cikinta
Da suka Gama inna ta shigo domin tattara kayan
Kausar tace barshi dan Allah mama bari zan
tattara
Inna tace kekam barshi dan Allah yarnan keda
kukaxo baqunta
Tsalam sukaji murya nafi na fadin kekam ki
barshi ta kwashe mana
Kinfa cika naci Kamar tsohuwa
Kausar taji kalaman nafin tamkar saukan ruwan
zafi tace a,a inna barshi
Barshi ai nayau ne kawai
Dan haka ta kyaketa
Ta tattara taje ta wankesu tas
Bayan ta Gama ta nufi Dakin nafi ta bita da
harara tana fadin to ayawo
Ina kikaje a wannan garin me kama da bola?
Bata tanka musu ba Sbd inna na Dakin kausar ta
qosa su
Tafi Sbd yaddah nafi keta kwabasa musu kartai
abinda zatasa a zagi iyayensu
Tai sa,a kuwa aleeyun ya shiga yace kuxo mu
gaishe da malam gashinan ya shigo saimu wuce
Kar muyi dare a hanya inna tace a,a su bari ko
sallah sayi ko?
Basuce komaiba suka wuce kausar ta duqa har
qasa tana gaida malam
Nagartaccen dattijo
Nafi ta qare masa kallo tace a xuciyarta ashe
aleeyu shi ya biyo kyakkyawan dattijo
Tamkar shi e kansa
Ya maida hankalinsa kan kausar dan yayi zaton
ko Itace sirikar tasu
Nan yai musu addu,a sannan kausar tai sallah
Bayan sun kimtsa aleeyu yasa direba ya shigo
musu da tsaraba sannan Sukai sallama
Suna kan hanyane kausar ta dubi aleeyu tace
Kai yaya aleeyu ashema garin nake ba wani
kauye bane sosai aini ina sha,awar irin wannan
garin
Da ace nan zaku zauna da babu abinda zai hana
na dinga zuwa muku hutu
Ji Sukai tace kan abinda malam ya hana ta ta
kundumo Mata wata
Ashar tana fadin kausar me kika maidanine?
Kina nufin a kawoni wannan takurarren garin
Ammman baki qaunata duk garinnan ina kika ga
yai miki kama da inda za,a sakani?
Allahi ya kyauta nai rayuwa cikin gidadawa yan
kauye jahilai
Karki sake maimaitamin wannan kalaman
Inba so kike ranki ya baciba dan nida garinnan
har abada
Shiru kausar tayi dan abin yamafi qarfin tunaninta
Shikuwa aleeyu takaicine ya Gama kumeshi ji
yake tamkar ya maqureta ya huta
Yace Aransa anya tasu zatozo daya kuwa
Ansha biki amarya ta tare a katafaren gidanta
Lokacinda iyayen aleeyu sukaji ba kausar bace
amaryar abin bai musu dadiba saidai babu
yaddah suka iya
Rainin hankalin nafi sai qara gaba yake sam bata
ganin mtuncin iyayensa
Da danginsa ko kadan shiyasa yanxu dangin nasa
baSu cika kawo masa
Ziyara ba
Tunda akai auren shekara biyu kenan bata taba
zuwa gaishe da iyayensa ba
Yayi nacin har ya gaji
Yan,uwa har an fara yi dasu jowa yasan baiyi
sa,ar mataaba
Daya samu lbrn iri wulaqancin da takema
danginsane
Yaxo yai Mata tatasa shinefa yanxu idan sunxo
take barinsu suna shiga Gidan ammanfa zasuga
wulaqanci hardana bugawa a jarida
Ya Bude idanunsa wandanda suka rine tamkar
garwashin wuta
Ina amfanin rayuwa da macen da batasan darajar
iyayen
Mijinta da danginsa ba da wadannan tunane
tunanen har Barci ya kwashesa
Saida aka kira
Sallar asuba sannan ya samu damar miqewa yai
sallah sannan ya fara shirin tafiya office a sashin
saukar baqi ya samu kwaggon nasa inda yake
musu bayanin yanxu
Zai hadasu da direba Wanda zai kaisu kasuwa ya
siyo musu duk abubuwan da suke buqata
daganan ya kaisu tasha
Su hau mota daganan ya ciro kudi masu yawa ya
miqama kwaggon yace ga wannan kui kudin mota
da tsaraba sannan ku riqe Wasu a wajenku
Godia suka dinga masa kwaggo harda kwallan
farinciki
Sannan yai musu sallamaa ya wuce office din
nasa
Misalin qarfe goma na safe nafi ta farka daga
barcin da take
Kai tsaye toilet ta nufa ta watsa ruwa sannan
tayo qasa domin yin break
Bayan ta zaunane take kwalama ladidi kira da
saurinta ta qaraso tana gani hajia
Tace
Meye da meye anan?
Ta fara lissafa Mata tadan yamutsa fuska kamin
tace zubamin dankalin
Ad sandwich a gefe
Ta amsa da to
Bayan ta Gama ta fice Kamar daga sama taji ana
knocking
Tace hu is knocking
Sorry sweety taji an fada ta miqe da sauri tana
fadar
Am coming my dear
Ta meqe da sauri ta Bude Dakin tana budewa
suka maqale juna tana fadin am
Sorry sury
Amman fa nayi matuqar farin cikin ganinki
Tana fadin sury Wlh yanxu shawarar tafiya
gidanki nnake dan
Nayi mising dinki Wlh ki yarda dani
Surayyah ta zame hannunta tana fadar ke ni rabu
dani mayaudariya kawai
Wlh afi baki sona dole na Nemo mai debemin
kewa
Mata da yawa sunamin tallar kanki ammman naqi
nace dole saike wai don kawai kar naci amanarki
Amman ke ko a jikinki
Nafi tace ba haka bae hajiya surayyah kin ganene
mijin nawane bai barina ina
Hutawa
Wata harara ta watsa Mata tace sannu mai miji
Aini kaina da nawa mijin nake wannan harkar
Bama miji dayaba
Bari na fada miki wani sirri ba miji daya gareniba
ni matar
Soja ce kuma matar chirman
Nafi tace ban ganneba sury fahimtar dani
Saida taja wani dogon murmushi kamin tace tun
daman can asalina yar qarin bauchi ce
Acan iyayena da kakan Nina suke
Ni kadai iyayena suka haifa kuma suka gani
inngattacciyar tarbiyar Arabi data boko
Bayan na Gama digirinane na hadu da wani Soja
mai suna auwal
Soyyah ta shiga tsakanina dashi har manya
sukasan da zancen aka daura mana aure
Kwatsam aka canjama auwal aiki zuwa qasar
inugu
Ni kuma na nace sai na bishi can
Shekararmu daya acam daganan aka turamu
Lagos wani qauye
Anan muka zauna na saba da mutane harkar
duniyata kawai nasa a gaba
Ke har maza nnake kawowa Gidan nawa Garine
da ba ruwan Kowa da kowa
Kwatsam rannan aka tura mai gidana wani cose a
qasar amurka
Na shekara biyu ya shirya yai tafiyarsa
Ban damuba dan inada masu debemin kewa
A haka na hadu da manyan mutane can gida
kuwa babu masu ziyartata dan nayi nisa
Saidai idan nine ke keson ganinsu naje na hada
musu sha tara na arziqi
A haka na hadu da wani dan siyasa mai rike da
muqamin charman
Na lokal government dan asalin garin kano ne
Saidai shi bada watsewa ya nemeniba dan duk a
zatonsa ni budurwace
A haka ya nuna yanasona da aure na amince na
nuna masa nida
Mahaifiyatace kawai a gidanmu
Yasa ranar da zaixo ya gaisheta
Muka hada baki nida matar da nake haya a Gidan
nata
Na tsara Mata yaddah nakeson abin ya kasance
ta amince
Kabir umar yazo shida abokansa suka gaishe da
matar a matsayinta na mahaifiyata Suka bata
maqudan kudi
Muka hada baki da wani dattijo Akan ya
tsayamin a matsayin qanin mahaifina ya amince
na biyasa aka dauramin aure da wannan charman
din aka dauko
Amarya surayyah aka kawo garin kano
Shekara uku kenan da aurena da chirman ina
zuwa akai akai ina gaida iyayena
Shima Alhaji yana zuwa gaishe da wannan matar
data tsayamin a matsayin uwata
Shi kuwa mijina auwal. Soja mijina na farko har
yau bai dawoba saidai
Duk qarshen wata ya turomin da. Rabin
albashinsa ni kuma naita wadaqata
Yaddah nakeso
Dan yanxu sai muyi wata bamuyi wayaba
Yar iskaceni?
Da yanxu inacan a jibge ina jiran gawar shanu
Dawowa ba rana ba lokaci
Nafi ta jinjina kai tace lallai surayyah kin cika
gawurtaCciyar yar duniya
Aure kan aurefa kenan kikai?''
Tace so wat inban morema duniyataba yanxu
hajiya Nafi to sai yaushe
Zan more
Gani yanxu ina hawa manyan motoci
Na mallaki manyan gidaje ina shga manyan store
na ratsa contry din danaga dama
Sannan ina tare da manyan yan gwamnati
Inda bani dasu koke ba zaki yarda na rabekiba
Cikin satinnan na lunco manya manyan jeef
baqaqe guda uku
Da wata. Shantaleleliya fara da naga akaimin
odersu gada ingland
Na zuba escot har sha shida ina tafe ana min
jiniya duk inda na shiga girmamani
Ake
Nafi tace kai dan Allah hajiya surayyah meye
sirrin fadamin naji?
Sani hanya yar uwa
Sury ta riqe baki tace waceni da daura zanin uwar
miji
Ai ina tabbatar miki da bazaki iyaba mumabar
wannan zancen kawai
Nafi tace haba hajiya Sury kinsan babu harjar
bakin ciki tsakaninmu
Fadamin ko meye Wlh zan iya
Inhar zan samu dukiya na tara na sai manyan
motocin da duk inda na gifta zan dinga jamyo
hankalin jama,a
Kowa ya rinqa girmamani
Sury ta dafa kafadarta tana kin samu yar uwa
inhar zaki iya
Ni kuma zan kaiki har bakin rigiyar da zaki dinga
zabaro kudi
Zaki zama miloniya Cikin kwana daya
Ta maqalqale surayyah tana fadar
Na gode aminiyata dan Allah fadamin ta wacce
hanyace
Sury ta girgiza kai tace kwantar da hankalinki
bazan tonama kaina
Asiriba kizo ki watsa min qasa a idoba
Kice ba zaki iyaba
Kwara na kaiki gindin abin yaddah baki isa ki
kubce ba
Wata yar dariya ta sake sakawa ta qara rungume
surayyar
Suka fara aikata masha,ar tasu
Daga qarshema miqewa Sukai suka haura sama
dan faga inda suke yan aiki na iya
Giftawa su kansu a kowane irin lokaci
Sai Bayan sallar issha,i Sannan suka rabu da
niyyar gobe zataxo ta dauketa dan kaita inda
rijiyar kudin nasu take
Cikin farin ciki Nafi take danji take tamkar tayi
kudinma tagana
Dan harta fara hangi kanta Cikin manyan motoci
Kekekekekekekekekekekekekekek duniya ina zaki
damu
Hm lol. Nafi dai toh badai zance komai ba

AURE KAN AURE Chapter 5
Aleeyu bai dawo gidansa daga gurin
aikiba Wucewa yai
can gidansu nafin acan Sukai sallar
magrib da isha,i
Anan ya samu ana Maganar auren kausar ya
samu
anayi nanda sati biyu Ita da wani
controler na
Custom ta gama digirinta kuma ta fito da
kwali mai kyau
Hira suke sosai Ita da aleeyun nata mommy kuwa
harkarta kawai take
Ta numfasa tace kasan kome zaka
siyanmin yaya
aleeyu?
Tacce yauwa kaha inason kayannan
wadanda ake tallansu na chaina
Tace dan Allah ka taimaka ka siyamin
irinsu yayana Wlh babu irinsu a. Naija
Yace lissafo inajinki
Tace akwai wata gas cooker da
vegetable marchne sai warmer
Nandai ta lissafo masa duk abubuwan da
take buqata
yace karki damu akwai wani abokina da
Aikinsa kenan shigo da kaya zan bashi.
Sai ya siyo miki Wani qara ta saka tana murna
tace na
gode yaya
Wlh naji dadi shi daddy wai komai saidai
a siyamin anan
qasa naija
Yace kema ai nasha zakiso haka yaddah kike
fadin kina
kishin qasarki ta hausa Da al,adun malam
bahaushe shiyasama kika karanta
hausan har kikai
Digiri akai
Tace baka gane bane yaya ni inada burin nai aure
na
ganni a qaton kichinne na
Hada wannan na sarrafa wancan Kullun
mijina ya dinga ganin abubuwan da
baimasan
dashiba na dinga qirqiran Abubuwa kala kala
Wanda a lokaci qanqani sai kaga na siye
hankalinsa da
tunaninsa koba hakaba
Wata irin daria ya saka shida momyn
nata Dan basu taba tunanin kunya irinta karsar
zata iya furta
hakanba
Aleeyu yace ke kausar ashe kema kin iya
haka kike
nunama mutane salihanci?
Rufe idonta tai ta tashi da gudu. Ta nufi dakinta
wai Ita ta
tunaninta bata dauka wannan Maganar
Rashin kunya bace
Aleeyu ya dubi agogon hannunsa yaga
har goma saura
hakan yasa ya miqe yaima Momy sallama ya nufi
gidansa
Nafisa kuwa duk ta shiga damuwa. Na
rashin ganin nasa
Tundaya tafi office bai kirataba inta kira
baya picking tai masa text yaqi reply Tace why
har yanxu bai huce bane
batasan aleeyu da
riqo ba saidai saurin fushi
Tun Bayan magrib take jiransa har qarfe
tara hakan
yasa ta Miqe dan gani tai kwalliyar tatama ai ya
tsufa ta cire kayan ta hade Cikin wata
hadaddiyar rigar barcinta
Wanda ake ganin komai na jikinta
Kai tsaye Dakin nasa ta nufa
Ta haye kan lumtsatstsen gadonsa ta rufe jikinta
da
bargo gamida
Rungume filo tana lallatsa waya Kamar
ta sani sashin nasa kuwa ya nufa dan
daman
kausar ta rigada ta cika masa Ciki da abinci
hakan yasa bai tsaya
neman komaiba ya
fado
Dakin nasa yana ganinta a kan gadon
nasa sai yai
Kamar bai Gantaba ya nufi. Bathroom ya watso
ruwa Bayan ya fito
ya
Saka kayan Barci ya kintsa
Tayi tunanin zai waiwayeta amman ina
saidai gani tai
Yaja filo abinsa yana qoqarin kashe wutan Dakin
a
zuciyarta tace wai mai yasa aleeyu ke
Mata hakane duk ajinta amman ace wai
itace kebin namiji
Jitai tamkar itama ta kyaleahin amman
Ina sonsa da kaunar kasancewa dashi ba zasu
bartaba
Hakan yasa ta mirgina ta daura kanta
saman kirginsa
muryarta tamsar wacce zatai kuka ta
kira sunansa
Tace yaya aleeyu dan Allah kayi haquri karka
horani ta wannan sigar na
Yarda kaimin duk wani irin horo amman
karka dinga
horar dani a irin wannan lokacin da nake
Cikin tsantsar
buqatarka Bai tanka mataba dan baima da
alamar
magana hakan
yasa ta Lumshe idanunta tana kising
dinsa ta ko ina
Aleeyu kenan jarumin maza amman bata
wannan sigar ba
Dan haka ya bada kai bari ya hau tuni
aka manta da
haushin da ake da ita
Washe gari saida yai da gaske ya kwace
daga jikinta dan Nema take yai latti Tai saurin
fadawa toilet yai wanka ya
shirya
Ya aje Mata kudinda shi kansa baisan
yawansu ba ya
fice a tsaitsaye yayi break
Yaja motarsa sai office Lokacin data saba
farkawa a daidai
lokacin ta farka ta fito ta fada toilet
Ta hade Cikin wata hadaddiyar atamfa
An Mata dinkin rapper ta saka wani
dankunnenta na
gold da yar siririyar sarkarsa Tayi kyau matuqa ta
dauko jakarta da
takalminta duk iri
daya ta saka tayo qasa Itama bata wanni
tsaya tayi break din kirkiba ta zari
makullin motarta da daddy yasai maata
Fara qal tasa akasa Mata baqin glass wato tintec
Da sauri sauri ta fita dan gani take Kamar
surayyah zata
bata Mata
Lokaci da kanta taja motar ta nufi
birgede anguwar da surayyar ke zama kenan
Hankalinsa ya tashi ganin yaddah aka
hade gidaje wajen
bakwai aka maidasu gida daya. A
wawakeken gate din
ta tsaya inda masu gadi sukazo suka Bude gate
din saida
tai tafi a ya kusa na mintuna goma
Sannan ta isa inda
aka tanazar domin aje motoci ta faka
Jeep jeep din data gani sune sukafi
komai daga Mata hankali ko waanne yafita tsawo
dan har
matakala
garesu
Tozalin da tai da farar jeef din shine yafi
komai tsnka
Mata zuciya Duk motocin sababbine qal ga Wasu
sucurities nan a tsaytsaye harsu. Takwas
Kowa duk sunsha kota da Wasu baqaqen
glas nasa kai
da niYyar tafiya daya daga cikinsu yasha
gabana yace madam lfy?
Na kureshi da kallo daan tsoroma ya
soma bani bance
masa komaiba na ciro wayata na kirata
bugu daya biyu ta dauka Nace tawaas
gani a gate securities sunqi Barina shiga kixo
kimin jagora
Kashe wayar tai Cikin hanzari ta manna
Baqin gilashintaa
Tayo waje
Ta wuce faluka sunkao goma Sannan ta
fito suka maqalqale Juna nace kai hajia surayyah
haka
gidanki ya koma
wane matsayi chirman
Ya kai da har kukaa samu wannan
daukakar?
Tace charman kodai surayyah ai rigiyar kudinane
ta
gyaramin wannan Gidan da kike gani
Rigiyar nacan Cikin wani boyayyen
falona na sirri muje
idan muka dawo zan nuna
Miki Tace da motarki kikaxo eh nace Mata tace
to muje nace
nata a,a hajia Aini qagara nai naga na
daana wadannan jbga jbgan
motacin?
Tai daria tace sha kuruminki indai wadannanne
Cikin
satinnan zaki iya aje kamarsu
A gidanki yanxu haka sirrin inda kudin
suke nakeson na
kaiki Dan ni kadai nake zuwa ko security
daya ban dauka Nafisa tace to mu qarasa ko sun
kusa isa
inda motocin
suke masu tsaronta duk suka zaburo
Ta daga musu hannu tace ku dakata ba
wani nisa zanba
babu matsala Sukace Owk hajia a dawo lfy Nafi
ta
shiga mazaunin direba Itakuma surayyar
ta
zauna a Gidan gaba
Duk tsiyarka da naci baka isa ka Gano ko
suwaye a Cikin motarba shiyasa aleeyu ya tsani
motar
Ita kuma taqi ta
cire tintec din
Tafia mai nisa surayyah ta Nina Mata
wata hanya suka karkata
Wata anguwa suka shga waddah bata da cikowar
mutane
A haka har suka. Shige Cikin wani
kuntsurmin daji
Har Nafi ta soma tsorata tace wai hajia
har yanxu bamu qaraso bane? Nafa soma tsorata
Surayyah taja wani dogon murmushi ta
zare gilashin
idonta tace amshi saka
Haska idanunki can sama zaki hango
wani katafaren gida
Aikuwa tana kallo ta hangi wani qatom
gida mai doguwar katanga
Surayyah tace to kiyi fakin a wajen ai ko
Ba musu ta bakin a daidai wajen
Suka fito Sukai Cikin gidan Gaban Nafi dai bai
daina faduwa ba tana
tsoron kar ace
Ita za,a maida Kudin
Don dukiyar surayyah ta soma tsoratata
Wani katon falo suka fada Wanda babu
komai a cikinsa a qawatashi da. Manyan
Tiyils
Tundaga qasa har bangonsa amman babu
komai a cikinsa
Surayyah ta dubi Nafi tai murmushi tace
To yanxu saimu cire kayanmu dan sai mun cire
kayanmu zamu iya shiga
Dan ba,a shiga da kaya
Nafi ta zazzaro ido tace wat kut kina
nufin tsirara ake shiga?
Bata sauraretaba ta fara cire kayan jikin nata
saidata
cire komai Sannan ta juyo ta
Kaloi nafin tana murmushi tace toya kin
shirya ko kuwa
Nafi ta duqar da kai tai shiru tana tunani...
Dan allah kuyi hakuri kwana biyu bana posting
wlh wani babban uzirine yasa dafatan kowa yana
cikin koshin lpy nagode...
Daga naku akoda yaushe...
Aure. Kan. Aure
Chapter6
Bata amsa mataba ta shga cire kayan jikin nata
saida tai tsirara sannan
Ta juyo tana murmushu tace yadai kin shirya tai
Shru tana tunani bata angaraba sai ji tai suraiyar
ta janyota jikinta
Ta bita da kis a haka har tai nasaran cire komai
na jikin nata
Ta jata suka shga wani bangare wanda
Babu komai a wajenn sai nnamun daji tuni fitsari
ya soma bin qafata
Tuni cikinta ya murda lokacinda surayyah ta juyo
ta kalleta a lokacin
Zawon datake riqewa ya kece mata
Dan gaba daya haliTtarta ya sauya jikinta yai
wani haske Kamar wutan lantarki idanunta ya
zazzaro sunyi jajir
A take ta fasa wata uban ihu ta zube a wajen cak
ta dauketa tai
Ciki da ita
Mutanene a wajen dukkansu halittarsu ta koma
irinta
Sury sun kasu gida biyu. Gabas da kudu
Sunsa wani mutm mutumi a tsakiya
Gabansa wata qatuwar tukunyace daketa hayaqi
Sai Wasu surutai suke
Surayyah ta iso ya miko Mata hannu ta mika
masa nafin Sannan ta koma gefe inda sauran
jama,ar suke ta tsaya
Mutumin ya dinga zagayawa da nafin a bakin
tukunyar har sau uku
Sannan ya ajeta a tsakiyar filin
Ya koma inda tukunyar take yana Wasu yan
surutai Bayan ya gamane ya fara
Kwara Mata kira da karfinsa wata iska na fita
daga bakinsa
Naafisa Nafisa nafisa ta meqe a gigice tana waige
waige kafin ta runtse idanunta da qarfi
Ya barke da wata mahaukaciyar dariya kafin yace
maraba da zuwa nafi
Maraba da zuwa wannan gungiya tamu
Da farko muna miki barka da isowa
Na biyu kuma sharadinmune na uku kuma albishir
Sharadi kuwa shine duk Wanda yazo wannan
gungiya tofa baya fita har sai in baya numfashi
Inkuwa yace zai bijire mana to abu mai sauqi
shine zamu yankashi aljani yasha jininsa mu
kuma mu cinye namansa
Kuma duk abinda muke buqata saian kawo mana
ba,a yin mana gaddama
Inkuwa kai to haukataka zamuyi
Na uku shine albishir kin nemi duniya kin samu
Ba abinda zaki Nema indai kudi na siyansa a
duniya ki rasa dan
Haka muna miki maraba da shigowa kungiyar
@secret society
Hankalin Nafi ya soma kwanciya taja ajiyar
zuciya qarqarfa da taji ashe ba Ita za,a
Maida kudinba
Indai har Itace zata samu to aiko ko meye zaata
iya
Dan haka ta tashi tsam
Tana fadan na amince kungiya ta shaida nima na
zama yar gungiya abin yai
Musu dadi matuqa sukasa daria
Mutumin yace Nafi aljani na buqatar jininki
Ji tai hanjin cikinta na kadawa ta dinga matsawa
baya baya tana neman hanyar guduwa
Surayyah ta fito da wata yar qaramar wuqa ido
waje Nafi ke kallonta kafin tai wata
Wata harta capki tannunta ta yanki fatarta ta
tara wata yar qaramar kwarya
Bayan ta gama tsiyayan jinin ta saki hannun nata
taje ta miqama mutumin
Tace gashi sha jini sunan data kira mutumin
dashi kenan
Ya amsa gamida sa dogon harshensa ya shanye
jinin ya fasa kwaryar gamida fasa wani uban qara
yace kinxo hannunmu Nafi duk inda zaaki shiga a
tafin hannunmu kike
Baki isa ki layance manaba dan muna ganin
abinda ke cikin
Zuciyarki
Don haka wa kikafi so a wannan duniyar nafi?
Muryarta na rawa Sbd radadin yankar da
surayyah tai mata
Tace daddy na
Ya babbake da wata iriyar dariya kamin yace
Yace to muna buqatar jininsa kungiya na buqatar
namansa
Ta miqe tsaye a gigice tana fadar waye dadin
nawa?
Wanda yafi Kowa sona a duniya. Wanda yafi
riritani a cikin yayansa
Yafi sona da Kowa? Wanda ya haifeni yaci dani
ya shayar dani
Na tsawon wani shekaru ba tare da gajiyawa ba
Wanda yaban ilmin da kansa
Bazan iyaba inndai hakane na fita.........na
fita.......,afi.....''
Dariyar da yake kyalkyata mata Ita ta hanata
qarasawa
Da hannu ya nuna mutum na farko yace
Ba bada matata
Ba biyu yace na yayata na bada
Na uku yace nahaifina na bada
Na hudu yace. Dana na cikina na bada
Na biyar yace nima mahaifiyata na bada
Akaxo kan surayyah tace mahaifina na fada da
kuma
Dana nasir Wanda shi kadai na haifa a duniya
Akaxo kanna takwas yace ni matata na bada na
tara
Tace ni mijina na bada
Akaxo kan na goma tace
Nakai shekara ashirin nida mijina ban taba
haihuwa ba Allah yaban ciki na haifi mace
kyakkyawa ran suna dodo yace yana buqata ba
yaddah
Na iya haka na miqata
Bayan sungamane akaxio kan uban gayyar sha
jini ya daka mata tsawa yace kin ganni nan
Uwata ubana matana dukkansu hudu yayyina
biyu qannena biyar yayana takwas
Uku maza biyar maza duk anan akai kwanjensu
dodo yasha jininsu gungiya taci namansu to dan
haka ko kinaso ko bakyaso ko kin shirya
Ko baki shiryaba. Tunda har kungiya ta buqaci
jinin mahaifinki tofa saikin kawoshi
Saidai zamu iya baki zabi ki zaba shin naki ran
kona mahaifinki?
Dan haka mun baki nanda kwana uku koki
kawoshi ko kuma dodo yasha jininki
Mu kuma muci namanki
Dan haka saiki zaba rayuwarki kota mahaifinki
Ya fashe da wata irin daria kafin bata ya bace
Kowa ya kama gabansa jikinta sai rawa yake sury
tai gaba har ta bita ta daga mata
Hannu ta nuna mata wata qofa tace na zatabi
Cikin tsananin tsoro tace Wlh bazan iya biba sury
Suryn ta dafata tace daurewa zakiyi ki runtse
idonki kibi inkuwa kikasa tsoro to hanyar wani
aljanin zakibi
Ya tsotse miji jini
Zakiga abubuwan ban tsoro da yawa ki nutsu in
kika tsorata to haukacewa zakiyi Ta saketa ta
nuna mata hanyar Ita kuma abi tata hanyar
Kuka nafin ta saka tace shin wane irin bala,i ne
ke tunkarota
Lol ni kaina na fara tausaya miki
Aure. Kan. Aure
Chapter7
Haka ta rintse idanunta
Tabi tata hanyar harta fito a gaban motar tata ta
hangi surayyah na jiranta cikin Shga ta alfarma
da suka taho da ita Da sauri ta dubi. Jikinta ta
tuna. Ashefa a tsirara suka shiga wajn
Abinda ya gigitata shine kayan dataxo dasu ta
gani a jikin nata
Hakan yasa ta qara firgita ainun
Sury ta Bude mata motar ta shiga ita taja motar
da kanta idon nafi a rufe har suka isa saidai ji tai
ance. Fito
Ta fito sury taja hannunta Sukai cikin gidan
Muryarta qasaqasa tace sury kin cuxeni mai yasa
kafin muje wajen baki fadamin inda zamuje da
sharadinsu ba?
Yanxu ya zanyi
Surayyah tace haquri zakiyi kibi abinda shajini ya
fadi dan ba!a masa gaddama
Nasan zakiyi farin ciki nan gaba
Nima haka nai ba gashi ina fantamawa ba
Ta kamo hannunta ta dinga zagayawa da ita ciki
da bai din
Gidan tace
Dubi gidannan duk fadinsa nafi nawa ne
Ta jata zuwa wajen gidan tace dubi ma,aikatan
gidannan. Securities duk danni suke zube anan
Ta jata wajen jeep jeep dinta ta buBbude matasu
a xuciyarta tace wannan ko fadar shugaban qasa
ai sai haka
Tace kinga motocinnan duk nawane a cikinsu
nake yawo tare da escot dina
Ta jata cikin gidan har zuwa bedroom dinta
Tajata har zuwa wajen lokarta ta janyo Wasu
manya manyan album
Tace matar gwamnace wannan qawatace dubi
waccan matar shugaban qasace inyanxu nace
inason ganinta ba bata lokaci zata baiyana
Wadannan kuma duk matan ministoci ne
Da manyan yan siyasa
Nifa a yanxu bansan me ake kira da talauciba
Yaddah naso haka nake rayuwata dan inada shi
Ta miqe tasa mukulli ta Bude wata wawakekiyar
wadroof dinta babu abinda ke ciki
Sai tsaunin yan dubu dubu abin har yaso firgita
nafi
Tace kinga duk wannan dukiyar tawace sai
yaddah naso zanyi dasu
Ta maida makullin ta ka$o hannunta juwa jikin
wani bango
Babu Wanda zai dauka akwai qofa a wajen Sbd
Wasu tsadaddun labulaye da akasa a wajen
Suna shiga fitsari ya kusa kubce ma nafi tace
duba kiga wannan mahaifinane
Wanda ya haifeni da cikinsa
Alhaji qasimu.....
Take ya dinga aman sabbbin yan dubu dubu
Tai wani murmushi ta duqa tana tsincewa
Tace kin ganshi Nina kaishe makkah da kudina
Nafi ta dinga bin dattijon da kallo Wanda ya
koma tamkar kwarangwal
Suri ta miqama nafi kudin tace ki riqesu dubu
hamsin ne
Ta janyota suka fice ta sake kukke Dakin suka
zauna saman lumtsatstsun kujeru
Ta dafa kafadarta tana fadin qawata a duniya
bakada
Masoyan da suka wuce kudi
Su kansu iyayen sai kana dasu suke sonka
Kudi suke sama mutun farinjini su sama
kyakkyawa Baqin jini
Inhar bai dasu
Nafi kiyi kudi duniya tasoki a fantama dake a
duniya
A wannan duniyar in kinyi kudi kece mutunfa
inkuwa baki dasu to dake da shara
Duk daya kuke
Dan har yayan da kika haufama qinki zasuyi
Kiyi kudi mijinki ya dawo kan tafin hannunki
Nafi tai shiru tana tunani kalaman sury tabbas
abinda ta fada
Gaskia ne
To amman ta waCce hanya zatabi ta kawo
daddyn nata itama?
Tundata dawo gida tunanin abinda take kenan
zuciyarta ta kasa natsuwa Ita kanta ta katsa
zaune ta kasa tsaye
Tabbas zataso ace itama ta zama wani abu a
duniya
Amman ta rabu da daddynta anya. Hakan zai
yiwu kuwa?
Ahaka aleeyu ya dawo ya sameta
Yai juyi« duniyarnan Akan ta fada masa abinda ke
damunta amman taqiya
Dan haka ya qyaleta ana sallar magribyabar gidan
Can gidansu ya nufa anan yaci abincin dare
Momy ke fada masa
Gobene amsar lefen kausar in yaje gida sai e
fadama nafin
Yace to ya dawo gidan nasa har ya gama shirin
barcinsa amman babu nafi
Don haka ya fita da kansa ya nufi Dakin nata
Tana kwance lamo tamkar mai Barci ya hayo kan
gadon
Ya janyota jikinsa yana fadin sunanta da
sassanyar muryarsa
Taqi Bude idonta dan a wannan lokacin bata
buqatar Kowa ya dameta
Muryarsa tai rauni yace nasan kina jina nafi
Ki taimaki zuciyata ki fadamin abinda ke damunki
Wlh in kikaqi fadamin bazan samu kwanciyar
hankaliba
Ta Bude idanunta Wanda suka kada Sukai jajir
muryarta gunin ban tausayi tace
Kayi haquri aleeeyu kainane kemin matsanancin
ciwo
Yace amman shine baki fadaminba na kaiki
Asibiti?
Laifin me nai miki da kika zabi horar dani haka?
Tace ba haka bane nasha magani nasan zai
sauka
Ya qara rungumeta yace Allah yasa yai mata
addu,a akai
Sannan ya qara kwantar da Ita a kirginsa dandai
kawai ta samu barci
Shima barcinne ya daukesa
Can cikin dare nafi tai mafarki wannan mutumin
Wanda suke kira da sha jini
Ya biyota a cikin daji sai gudu take harta gaji ta
fadi yasa dogayen hannunsa ya capkota a wuya
Yana fadar zaki kawo baban naki koko na
hallakaki yanxu kawai mu huta?
Ihu tasa dan ji tai numfashinta na fita daqar tace
zan kawo Wlh zan kawo ba
Nanda kwana uku kukaceba?
Ta dinga qaqari tana koqarin amsar kanta
Aleeyu ya farka a firgice yana fadin lafiyarki kuwa
Nafi
Ta farka a waharce tana riqe da wuyarta
Yai saurin riqo hannun nata yana duba wuyan
yaga yakuwa karce harda dan jini
Hankalinsa ya tashi saidai nata hankalin yafi na
Kowa tashi
Ya dinga tofa mata addu,o-i harya samu Barci e
dauketa
Hankalinsa ya tashi dan yanajin tsoron ace aljanu
sun fara
Taba masa mata
Barcinda bai iya komawaba kenan kai hatta office
bai iya zuwa ba
Ita kuwa sai sharar barcinta take hatta fitar
numfashinsa Akan idonsa take
Qarfe tara ta farka ya taimaka mata tai wanka
Sukai break
Ya bata magani tasha
Ta samu natsuwa sosai a jikinta Tunda ta kullla
mai fissheta
Ganin hakan ne yasashi fada mata kawo laifen
kausar cikin zumudi ta shirya ya
Dauketa a motarsa ya kaita shikuma yashiga
zaga abokansa
Lefene na nunawa a idon duniya akwatina guda
tara
Kayayyakine masu numfashi a cikin akwatinan
harda makullin mota sbw dall
Abinda ya qara tunzura nafi kenan
Tace lallai bazan zaunaba qanwata ta barni a
baya ba
Ba Ita ta baro gidanba sai qarfe tara na dare
aleeyu yaje ya daukota
Ranar data cika kwana uku ranar nafi da sury
suka gama shirya yaddah
Komai zai kasance
Tunda safe kuwa inna ta kira aleeyu take fada
masa diyar yayarta ta rasu
Maria dan haka hankalinsa ya tashi a take ya
hada tafiya
Yaje yaima daddy da Momy sallama ya tafi
Saidai ransa a bace yake yaddah yai juyin
duniyarnan Akan nafi taxo suje amman taqi
Har tana ikrarin ko iyayensane suka rasu ba zata
ba
Dan haka ransa a bace ya tafi shi daya
Tun misalin qarfe takwas na safiya ya nufi
musawa qarfe goma daidai ya isa
Surayyah ta iso nafi tasa waya ta kira daddyn
nnata
Tai sa,a kuwa shi kadaine a lokacin yaana shirin
tada mota
Ya amsa wayar yana fadin nafi yaya mai gidanki
yace bakyajin
Dadi shiyasa bai tafiyan dakeba ko jikinne ya
motsa?
Cikin muryar rashin lfy taace dan Allah daddy
kaxo gidana yanxu kaikadai amman karka fadama
kowa
Hankalinsa a tashe yace meke faruwane nafi
meke damunki?
Baibima kashe wayarba hankalinsa a tashe ya
nufi hanyar sharada
A rude ya shigo gidan a cikin falonya yana
sallama ya ganta
Yace ya haka nafi kin tasarmin da hankali daman
lfyarki qalau?
Tadanyi murmushi tace zauna daddy sai muyi
zancen
Ba musu ya zauna yana kallonta yana sauraron
abinda zatace
Surayyah dake labe a bayansu ta miqe ta hura
masa hoda a bayansa yana shaqa
Ya shiba Barci yakeba yanajin abinda ke faruwa
Saidai bai iya motsa koda dan yatsarsa
Su biyun suka kamashi suka fifta sukasa a boot
din motar tata
Sannan suka jira mai gadin gidan ya dawo daga
Aiken da Sukai masa na katin waya
Sury taja motar Sukai gaba
Basu tsaya a ko inaba sai cikin gidan na tsafin
nasu daya daga cikin gardawa
Dake aiki a gidan ya sunkuce Alhaji muftahun yai
ciki suma suka shige
Kamar farkon zuwansu yauma haka tsarin yake
Dan tana daga cikin wadanda sukabi layi
Shajini ya dinga kwala wataa irin daria mara dadi
Sannan ya dinga kiran
Suransa har sau uku firgitgit ya farka
Yana waige waige
Ya gama firgita da ganin halittunnan Shajini yace
Yace sannunka da isowa Alhaji muftahu barka da
isowa wannan
Kungiya inamaka albishir na yarka Nafisa taban
jininka
Jikinsa na rawa yace qarya kuke maqiya Allah
yata ba batacciya bace
Na tabbata ba zata iya aikata wannan
qazantaccen abinba
Kudai kuce kun daukonine Sbd wata manufarku
Shajini ya qara babbakewa da daria
Kamin ya nuna nafi ta fito jiki a sanyaye
Daddy ya kalleta cikin firgici ya fara tuno abinda
ya faru a baya
Wata gigitacciyar qara yasa
Yace ashe damann ana haka?
Ahe daman akwai danda zai iya aikatama
iyayensa irin wannan?
Lallai rayuwarsa batada wani amfani
Koda basu kasheshiba yasan Baqin cikima kawai
bazai barshi ganini
Irin wannan Baqin ranar ba
Shajini ya dafa kan nafi yace aljani lummun gyaxo
ya yarda dake kuma ya eyntaki
Ya baki duniya ki juyata son ranki
Sannan ya nufi gun daddy ya watsa masa Wasu
ruwa a take ya fad a wajen ya lullubeshi da wani
farin kyalle
Ya daukeshi ya daurashi saman wannan tukunya
dake gabansa minti talatin Sannan ya sauko
dashi
Babu abinda ya canja ajikinsa illa fatar jikinsa da
tai fari fat
Sha jini yasa wata kwarya ya kwarfo jini aa
cikinta ya dinga basu daya Bayan daya
Har yaxo kan nafi Tasha Sannan yasa ta wanke
fuskarta dashi
Ji tai tamkar ancire mata imani da tausayi a
lokavi guda
Ji take zata iya aikata komai
Saida Kowa ya gamasha Sannan sha jini yace
nasha jinin babanki nafi.
Gawarsa shine rigiyar kudinki


AURE KAN AURE 8
Yace duk lokacin da kike buqatar jini sunansa
kawai
zaki kira amman
Duk lokacin da nake buqatar jinin mutun kikaqi
kawo
Mana to jininki. Zan shanye Ta amsa da na
amince
Sury tace to amman sha jini munaso a rufe mana
bakii Jama,a kar Wanda ya tambayi ta yaya ya
mutu Sannan in an rufeshi asa mana alamar da
idan
an rufeshi zamu gane idan munje
Kwakuloshi
Sha jini yai wata irin daria
Yace yaddah bakin gawannan ya rufe haka har
abada babu wani
Mai magana Akan ta yaya ya mutu
Kuma zan sa muku Jan kyalle a bakin kabarinsa
duk kabarin da kuka gani da Jan kyalle to anan
aka
binne sa
Sukai godia Sannan akasa musu gawar a boot din
mota Kowa ya kama
Gabansa
Ihun da take kwararawane ya janyo hankalin
Kowa
a gidan
A gigice ta shiga Gidan tana kiciniya da gawar
daddyn nata
Mommy Tayo kanta itama a gigice ta kamata
suka
shga cikin gidan da gawar
Hatta ma,aikatan gidan saidai suka taru akansa
tuni
Gidan ya kaure da koke koke
Kamin kace me gidan ya cika da mutane akaima
Wasu waya
Akace Alhaji muftahu ya zama marigayi
Lallai tsafi gaskiyar maishi daidai daidai da
tambayar ya akai taga gawar babu Wanda e
mata
Musamman yaddah duk tafi Kowa shiga tashin
hankali
Kowa ita yake lallashi
Saidai kausar tafi Kowa zama abin tausayi
Yaddah daddyn nata yaci mata burin aurentshin
kenan yanxu saidai
Labarinsa
Da aka sanar da aleeyu kuwa har kusan zaucewa
yayi washe gari ya iso garin kano
Randa aka rufeshine nafi taita Suman qarya a
cikin
dare dan haka sury tace
Abarta ta kaita asibiti
Tunda duka yanxu goma na dare da wani abune
Tana daukarta a mota gidanta ta wuce Wanda
babu
Kowa a cikinsa
Tsakiyar dare misalin qarfe biyu na dare
Suka dauki mota suka nnufi maqabartan
Lokacin da suka isa dukkansu da akwai tsananin
tsoro a tattare dasu dukkansu suka fita
Nafi ta riqe hannun sury muryarta qasa qasa take
cewa
Ance babu masu gadi a maqabartannan amman
Kamar haske nake hangowa
Surayyah ta rada mata tace ki cire tsoro sury
banda
magana kinsan muna cikin
Hatsarine yanxufa
Daganan babu Wanda ya sake magana cikin
sanda
suke haska toch
Sunfi awa suna zagayea maqabartan duk sun
hada
gumi ga tsoro dake tattare dasu
Sury ta riqe kugu tace na gaji nafi gaskia mu
koma
kawai mu fadama shajini
Ya sake yin mana wata alamar dan mu gane
Da sauri ta dubeta tace haba
Sury ya duk bamuji wahalar abinda muka
aikataba
sai kawai
Wahalar tono shi a kabarin nasa
Cikin kasala tace inko baki gode abinda nai
mikiba
afi aiko ba zaki tsineminba
Duba kiga har uku da rabi tayifa
A Kowa wane irin lokaci za,a iya ganinmu kin
kuma
San tamu ta qare kenan
Nafi zatai magana sury taja hannunta Sukai gaba
Suna shirin fita daga maqabartan kenan Kamar
daga sama. Nafi ta
Hango wani kabari lullube da Jan kyalle
Tai saurin tabo sury tace ke duba min Kamar
gashi
can
Tana dubawa tai saurin janta tace xo muje shine
qawata
Suna qarasawa suka jare Jan kyallen Sannan nafi
ta zaro gatari da masassaqi
Suka fara tone kabarin
Saida suka dau lokaci kafin su Bude kabarin cikin
tsoro da fargaba suka Bude likafanin nafi tace
aikuwa daddy nane
Nan daddy ya kamata
Suka kinkimeshi sukakai cikin but
Suna niyayyar shga motar ne aka haskosu da
fitila
ana kai suwaye nan?
A firgice suka kwasa a guje har sukaso su wuce
motar sury tai saurin fadawa
Taima motar key jin haka itama nafin ta shiga
kafin
ta ida zama har anyo kansu
Sury tabama motar wuta suka kwasa a guje
Aka fara kiran jama,a ana jama,a ku taimaka ku
tare
barayin gawa
Nafi ta runtse idonta dan ta gama fiddah raai ga
nasara
Suna hawa kan titin lbr ya sauya salo dan sury
gudu take na
Fitan hankali saida ta tabbatar
Babu mai binsu Sannan ta dauki hanyar gidanta
na
sirri Sukai facking
Sufa shge ciki
Qarfe hudu da rabi daidai na asuba agogo ya
buga
Nafi ta fada kan gado tana fadin Allah ya
taimakemu
sury
Da yau asirinmu. Ya tonu
Damun tozarta mun wulaqanta a duniya
Kuma da Allah yai wadai damu
Sury tace kedai bari tawan yau ko runtsawa ban
iyayi dan haryanxu hantar cikina bata daina
kadawa
ba
Nafi tai daria tace kai sury na tsorata da tukinkifa
yaddah kikasan ina cikin jirgin sama
Hira suke sosai sai har akai sallar asuba.
Qarfe shiddah daidai suka canja mota
Sukasa gawar a cikin akwati Sukai gidan nafi mai
gadi ya Bude qofa
Ta Bayan gidan suka shiga boys quter gami da
ciccibar
Akwatin
Wani bangare suka shiga Wanda ba!ama amfani
dashi yanada babban falo da
Qaramin bed dinsa da tailet dan haka suka kutsa
ciki
Nafi taja wata ajiyar zuciya mai qarfi ta Bude
Akwatin da daddyn nata ke ciki ta gansa kwance
Tace. Muftahu
Saiga kudi na fita daga bakinsa
Lol
Ta duqa ta kwashe masu yawan gaske suka tafa
gamida sa daria
Sannan ta rufe Akwatin da Dakin da wani
shirgegen
kwado
Suka fito
Sukai gaba dan zuwa shaidama sha jini aikifa
yayi
D did is done
Bayan sun dawone
Murna ta koma ciki dan motar aleeyu ne a aje a
cikin gidan da alamar ya
Dawo kenan
Kallon kallo suke mai dauke da fargaba gamida
tsoro
Dan haka Sukai fakin din motar jiki a mace suka
Nufi cikin gidan
Yanaa tsaye riqe da maqullin mota a hannunsa
kome yake nazari
Oho masa
Suna shigowa yai juyo da hanzari yana kallonsu
kallon daya hautsuna musu yayan
Hanji yace


AURE KAN AURE Chapter 9
Yace me kukaxo dauka?
Ya akai kuka baro gidan gaisuwar? Nafi
ta shga inda
inda In....ma..... dama...'
Sury tai saurin amshewa tace bata da lfy
ne Shine na kaita asibiti tun jia ta rinqa suma
Yanxu
ta samu sauqi
sosai shine nace bari na fara kawota gida
Ta dauki abinda zata dauka saimu wuce
Ya kada kai
yace babu wani abunda zata dauka ku wuce muje
Ya tasasu gaba suka wuce Yaja motarsa
su kuma suka
shge tasu
Saida akai sadakar bakwai Sannan
aleeyu ya dauki nafi suka Koma gida
Aka qara daga bikin kausar har sai Bayan
mommyn
nasu ta gama
Takaba
Nafi kudi sun samu tarawa kawai take dan cewa
tai ai
ba zatama fara bushasha Yanxuba dan
kar duniya ta tuhumeta
Sunaji ana maganganun anshga
maqabarta an sace
gawa hardasu cikin Masu zagin masu irin wannan
halin lol
Don haka aka qara gyara maqabarta da
masu gadi
Bayan Momy ta gama Takaba ne aka Fara
shirye shiryen bikin kausar tare da rabon
gado Aka raba akabama Kowa nasa
Sun samu kudi da qasarori bata wasaba
dan Alhaji
muftahu ya tara
Dukiya da qaddarori. Bata wasaba
Hakan yasa kausar ta ciro tata aka shiga bagajajr
duniya wajen bikinta shikansa
aleeyun yayi iya bakin qoqarinsa
wajen ganin kausar din ta samu
Abimda takeso
Bangaren nafi kuwa aleyu ne matsalarta
tanason bushasha amman da zarar ta
Fara zai taka mata birki Babu kuma
yaddah ta iya
Ammanfa dukda haka saida ta sai irin
jeep jeep din da
sury ke dasu saidai Aleeyu bai barta ta saka
securties ba dan
aboyema tasai
wani katafaren
Fili ba tare da ya saninsaba Duniya kuda
ta fara tamfatsa gini
Nafi ta rinqa Jan ra,ayin aleeyu da ya shiga
harkar
siyasa
Amman sai yace mata ba yanxuba da
sauran lokaci
Shi kansa yanasan cikama daddy burinsa
Nason zama dan siyasa Qarshen wata ya shirya
ya
tafi qauye
Domin duba iyayensa
Ya gyara musu gidansu dan dama tuni
yasa aka
rusheshi akai musu na zamani Sunajin dadin
rayuwarsu a ciki dan ya
zuba musu kayan
alatu Dan har mai aiki ya aje musu yana
biyanta kasancewar
girma ya fara Jan iyayen nasa
Anan ya samu innar tasa ta dauko dandan
marigayyah
maria
Wacce ta rasu tabar yaya hudu inna ta
dauko daya
Babban cikinsu Wanda ake kira da suna
adnan Aleeyu ya taisaya masa mutuwar
mahaifiya aiba wasa
bane
Da zai tafine yacema innar tasa ta bashi
adnan din ya tafi
dashi da farko taqi dan tasan iskancin
matarsa Saida malam yasa baki Sannan tabar
masa shi suka tafi
Haka kawai aleeyu yaji Yaron ya shiga
ransa Kyakkyawane jajur dashi kaikace
balarabe
Suna tafe aleeyu ya dafa kan yaran tausayinnsa
ya
game masa jiki
Wanda a qalla bazai wuce shekara goma
a duniya ba
A haka har suka iso gidan
Nafi na kwance a falo tana game a wayarta
Aleeyu ya shgo riqe da hannun
adnan
Nafi ta bishi da kallo harya samu wuri ya
zauna
Ta wurgo ido tana kallonsa a yamutse
Kamin tace wannan Yaron kumafa mai kamada
zabiya?
Ina ka samoshi kko almajiri ka samo
mana?
Ya qarajan Yaron jikinsa kamin yace ya
miki kama da me neman taimako?
Ta tabe baki tana fadin aiko mai Maganar bai
wuce
neman taimakoba
Yace eh amman ba anan ba ko? Tace na
nawa ai saidai
kuma kar,a kuma
Yace wasa kike yarinya kinji dubeninan daga
sama har qasa na wuce na nemi
taimako a wajenki
Wannan da kike ganinsa Yaron diyar
yayar
mahaifiyatace
Dan mamansa ta rasu nakeson riqeshi na bashi
kyakkyawan kulawa
Tashi tai kamin tace Wlh baka isaba
Aikin banza gayyar arna a idi
Dole ka dauke yaronnan ka maidashi
inda ka daukoshi Aika gane ko?
Yace a,a saidai idan naji saukar bugu zan
gane kinji
uwata
Ta qara harzuqa tace kaga malam ba
neman magana nakeba umarni nake baka bawai
shawara ba
Bazan zauna da dan wai wata gawa ba
Inko kace saiya zauna Wlh to saiya
kwammace yawon
barance da zaman gidannan
Dan saina mayar dashi abin tausayi Aleeyu ya
miqe tare da Yaron ya kalleta
sama da qasa
Sannan yace
To fadama kaji dansu tattabaru tashi
suke
Bai saurari abinda zata fadaba ya wuce abinsa
yana
kwallama ladidi mai aiki
Kira Ta fito a guje yace ina binta?
Tace tana ciki yace kirata itama kuxo
tare
Batafi minti biyarba suka dawo sai kwasar
gaisuwa
suke
Ya amsa yace musu kunga yarone gashi
dan uwanane
na jini mahaifiyarsa Ta rasu nakeaon dan
Allah ku bashi kulawa yaddah ya kamata duk
wani abu da ake buqata
kumin magana
Suka amsa da to amgama ranka shi Dade
insha allahu
zamu riqeshi bisa aman da gaskia.
Gamida kulawa Binta taja hannun Yaron tana
fadin meye
sunanka yace
adnan Tace yaro mai kyau dashi kuwa
tubarkallah tamkar
balarabe
taja Yaron suka wuce ciki Shima ya wuce
bangarensa
Ba tare daya ya qara waiwayentaba abin
ya qular da ita
A zuciyata tace hum lallai aleyu. Dani
kake zaune da
kasan da wacce kake Zaune da baka isa nai
Maka umurni ka takeba
Wlh sai kayi nadamar kawo yaronnan
cikin gidannan
daan
Yanxune zaka gane cewaa nafisan daka
sani ashe kwallon shegiyace baka saniba
Sati guda da kawo adnan aleeyu ya
samar masa makarantar kudi
Da take tare da islamiyyah
Inya tafi tun bakwai bai dawowa sai 6na
yammah Makarantar tsadaddar gaskece amman
akwai karatu
Nafi ta dauki tsana ta daurama adnan
musamman
dataga ya dauki son duniya ya daurama
dan Daga office da kansa yake Wucewa ya dauko
adnan din
Kasancewar duk sai shidah suke tashi
Dasun dawo zaisa Binta ta canja masa
kaya su nufi
masallaci indan Sukai magrib da isha,i sai
su nufi cikin gari yawo
Sai misalin goma suke dawowa Hakan ba
qaramin baqantama nafi rai yakeba
ganin ta
rasa samun hanyar gallazama Yaron
Yasa ta zari wayarta ta kira sury dan ta bata
shawarar
yaddah zata raba aleeyu
Da adnan budan bakin sury sai cewa tai
kibama sha jini
shi kawai Take ke surayyah kina ganin
ba za,a iya samun matsalaba kuwa tace wannne
Matsa karki kawo wata matsala a
xuciyarki tundai dai
biyan buqatarki kike nema
Tace to ai matsalar Yaron koda yaushe
suna tare da aleeyu ne ta yaya za,ai mu iya
Bama sha
jini shi sury ta kyalkyale da raria tace
nafi kenan
Sbd ke sabon shga ce shiyasa bakisan
taqadirancin
shajini ba kedai kawai Allah e kaimu gobe kawai
A haka nafi ta koma kan gadonta cike da
murnan raba
aleeyu da adnan.........


Chapter10
Washe gari shine ranan da suka tunkari shajini da
Buqatarsu tason bashi adnan amman ina
Buqatarsu bata cimma
Ruwaba dan cewa yai ya masa qanqanta ta
barshi ya tasa
Hakan bai mata dadiba
Dan haka tasa musu ido tana kallonsa ya gama
wahalarsa a banza ba moriyarsa
Zaiciba
Kwanci tashi ba wuya adnan ya gama primary
Aleeeyu ya samar masa gurbin karatu na ajin
gaba da primary a haka nafi ta samu
Ciki
Murna wajen aleeyu ba,a magana
Don haka ya shga tattalinta da rainon cikin
Soyayyah kuwa tamkar zai hadiyeta
Hakan ba qaramin yin mata dadi yaiba dan
daman
Abinda takeso kenan
Saidai kausar ta rigata haihuwa ta haifi danta
namiji
Alokacin cikin nafi baifi wata shiddah ba
Gama Makarantar adnan ta primary taxo masa
Da sauyin yanayi
Dan nafi tamkar wata dama ta samu na shga
Rayuwar yaron
Qarfe biyu ake tashiinsu ya dawo gida sai hudu
ya wuce islamiyyah
Adnan yarone mai hazaqa ga farin jini
Kowa sonsa yake
Dalibai da malamai
Ita kuwa nafi wani tsana ta dauka ta qara Dora
masa
Shiyasa yaron babu abinda yake tsoro sama da
ita
Dan shi kansa aleeyun ya fara fahimtar hakan
Adnan tun yana yaronsa ya taso mai tsoron
Allah da yawan addu,o.i na neman kariya
Misalin qarfe hudu na yaMma nafi na kwance
saman doguwar kujera
A falo chartin kawai take da kawayenta
Adnan ya fito daga
Bangaren masu aiki sanye da kayan islamiyyah
Army Kalo sun haska fatarsa saika rantse dan
larabawane
Nafi ta yinkura da qaton cikinta dan wata tara
Ta kalleshi
Kai zonan jiki a sanyaye ya nufi inda taken
Kafinma ya qaraso wajenta din ta fincikoshi gami
da daukeshi da wani
Gigitaccen mari Wanda ya ratsa dodon kunnensa
Yasa wata qara tasa hannu ta tashe masa baki
tana
Cewa. Rufemin baki munafikin banxa wato ka
Maidani wata dodonka ko?
Inna kiraka ka hau rawar jiki dan uwarka
Ni abin tsoroce iye?
Kuka kawai yake jikinsa sai rawa yake dan ko
magana
Ya kasa
Tace eh lallai ba zakai maganaba kenan ko
Ta shaqo wuyarsa gamida zaunar dashi Wanda
har yakejin numfashinsa na fita
Daqar.
Tace to fara tsallen kwado ta lura bai iyaba dan
haka
Ta duma masa dundu ta nnuna masa yaddah
zaiyi ya fara
Ta koma ta kwanta duk ya hada gumi
Qafafunsa suka shga karkarwa tamkar mai
masassara
Masu aiki suna kalllonsa saidai babu yaddah
zasuyi
Duk Wanda ya kalli Yaron saiya tausaya masa
Har saida Yaron ya fadi Sbd Whl numfashinsa na
fita daqar
Ta miqe ta rankwasheshi akai tace
Gobema idan na kiraka kamin rawan jiki
Tai gaba abinta da sauri ladi mai aiki
Taxo ta sureshi ta nufi bangarensu dashi
Ta cire masa kayan jikinsa gami da watsa masa
ruwa a toilet
Bayan ta fito dashi ta dinga masa fifita harta
samu ya dawo hayyacinsa
Misalin magrib aleeyu ya dawo yana kiran adnan
su tafi
Masallaci
Ladidi mai aiki ta fito tace ai baida lfy
Hankalinsa tashe ya shga Dakin da sauri ya
samesa kwance
Yanacin biscuit
Ya rungumeshi jikinsa yanajin kaunar Yaron a
cikin xuciyarsa
Ya tambayesa meke masa ciwo yace ba komai
Saidai qafafuwansa da bai iya tsayawa dasu
Ya dafa kai yace bari na kira likita
Binta tace a,a yallabai ai Bama sai ankiraba mun
gasa masa nanda
Wani dan lokaci zai watstsake
Ya dafakan Yaron yace meke Maka ciwo yanxu
yace ba ko ina
Sannan yace to me kake buqata na siyo Maka
yace chocolate yace to
Shikenan bari na fito daga masallaci
Dan haka ya miqe ya fita Kowa yatafi domin yai
sallah
Daga masallaci osis ya nufa yai masa siyayyah
Ya kawo masa dan yaita murna bashi ya
baroshiba sau goma saura ya nufi nasa
Sashin
Ji yake tamkar ya kwana kusa da dan nasa
Ashe can kuma nafi nacan tana ta faman naquda
Ba sosaiba tanata faman kiransa yaqi daga
wayar
Don haka yana fitowa daga Sashin masu aiki
bangarenta ya nufa
Hankalinsa ya tashi matuqa ya gigice ya
kwashesa sai asubiti
Naqudace doguwa dan haka ya kirasu Momy cikin
daren suka iso asibitin
Kowa na mata addu,a
Saida Momy taida gaske Sannan yabar asibitin
Har washe gari nafi bata haihuba nafi ta shiga
tashin hankali
Tunda yai sallahr asuba ya iso asibitin dan haka
likitoci
Suka yanke shawarar ai mata aiki a ciro jaririn
kawai
Don haka aleeyu yasa hannu likitoci suka duqufa
aiki
Cikin ikon Allah aka ciro abinda ke cikin nata
qatuwar jaririya
Mai kyawun gaske
Tunda aka gyara mai jego da jaririya Kowa yake
rigerigen daukar yar
Harda nursisi
Don yar taxo da farin jini
Aleeyu kuwa tankar yasa rawa aka sallamosu
daga asibitin ya taci sunan
Mahaifiyar aleeyun
Wato hafsa don haka ya laqaba mata suna afnan
Sunan Kwata Kwata baima anafi dadiba dan haka
aka
Shiga rikici ita aleeyu
Wai yasama yarta tsohon suna irinna kauyawa
gidadawa jahilai
Baice mata komaiba Sbd Momy na gidan ya fice
abinsa
Washe gari akasha suna Kowa ya warwasa aka
gasa yatsu
Da da,am inji larabawa lol
Don har walima akai maai qayatarwa
Aleeyu ya daukoma mai jego da jaririya wacce
zata dingaa kula dasu
Ba wata tsohuwa bace dan ba zata wuce shekaru
arba,in ba
Aleeyu ya sallami Binta dan girma yaxo mata
sosai ya bata jarin isasshe
Daman ita Ladidi aure zatai
Dan haka gaba daya yadau dawai niyar kayan
daki da sauran abinda za,a
Buqata
Riqon adnan ya dawo hannun baba hausa ta iya
rainon yara da basu kulawa
Rikicine ya balle tsakanin aleeyu da nafi wai ita
ba zata shayar da afnan ba
Dan baa zata yarda nonota ya zube a banza a
wofi ba yaddah tanaji tana gani zai watsar da ita
yaje ya dauko yarinya mai nonuwa a tsaitsayeba
Kunji jahila lol
Ransa ya baci yai lallashin duniyarnan nafi taqi
ta watsar dashi
Ganin yar zata shga wani haline yasa ya tattara
yar yabama baba hauwa suka nufi asibiti
Aka ruButo musu madarar daya cancanta a dinga
Bama jaririyar
Tare da shawarwari
Ko wane jariri a duniya yana buqatar nonon uwa
Wanda nonon nada matuqar mahimmanci kwarai
a gurin yaro
Har shi. E sa likitoci basason anama Yaron daya
wuce wata shiddah mix da madara
Yaron daya rasa nonon uwa kan ya rasa
rayuwarsa
Sannan shayar da jinjira kansa shaquwa
Sannan ta nonone jinjirai ke daukar kyakkyawar
halayyar iyayensu ko
Mummuna
Itadai afnan ta rasa wannan gata na shayarwa
saidai tana samun kulawa yaddah ya kamata
Adnan ya samu abin wasa koda yaushe yana like
da afnan baison matsawa kusa
Da ita ko yaya
Shaquwace sosai ta shiga tsakaninsu
Kwatakwata bata da Wanda tafi sabawa dashi
irin adnan
Sai kuma babarta hausa da mahaifinta aleeyu
A haka adnan tai wayo
Saidai nafi na cikin tashin hankali
Sbd shajini yace wai jinin afnan yake buqata
A wannan karon gaskia saidai komeai zai faru ya
faru
Dan gaskia bazata iya bada yartava dan
tanasonta
Damadai ya sake dan ko waye zata iya badawa
amman
Baddah yar tilon yarta
Don haka ta kira qawarta kuma abokiyar
batancinta domin su
Tattauna Akan lamarin
Don haka cikin rudani ta kirata a waya tana
shaida mata
Abinda ke faruwa tace kyakkyawar yarta kaman
afnan bai kamata
Ace wai shajini na buqatar jininta ba. Kuma inma
hakane
Ai tayi qanqanta da yawa dan koda naje masa da
zancen
Inason na bashi adnan Cemin yaai yayi qanqanta
da yawa
Sury tai daria tace nafi kenan haryanxu bakisan
Shajiniba akwai abinda ya hango shiyasa kikaji
yace miki
Adnan ya masa qanqanta. Ai hannunka mai
sanda yai miki
Domin shajini. Indai akace miki jini ne to koda
yaushe a buqace yake
Sannan da kike Maganar afnan tayi qanqanta
Kinganni nan lokacin Dana haifi sadiya ko suna
ba,aiba shajini ya buqaci
Jininta na nuna rashin amincewata
Kuma naqi yarda yai juyin duniyarnan naqi yarda
nace saidai ya shanye nawa
Jinin ganin haka yace to saidai na zaba zai
barmin yar tawa amman duk cikin. Dana sama a
duniya nasune kuma basu yarda duk girman da
nai na
Tsaya da haihuwa ba
Shiyasa da zarar na samu ciki wata shiddah nake
juwa ya dauke jinjirin
Anyi haka yakai sau uku dan duk shekara nake
samun ciki
Da zaran an tambaya ina cikinki sai nace
Bari nai
Kema inaganin wannan hanyar kawai
Zakibi domin kubutar da yarki. Don shajini bai
mising din target Indai Akan jini
Ne
Nafi tai shiru kamin tace amman kina gani zai
amince
Sury tace. Eh to kinsan ke sabon shgace saidai
karki damu
Ina ganin gobe da yammah akwai jama a
majalisa
Zan taimaka miki wajen nemann wannan
alfarman
Ba qaramin dadi tajiba tai daria gamida rungume
qawar tata
Tace. Kemafa qawata kin kawo shawara shiyasa
nake alfahari
Dake. Kuma nake farin cikin kasancewarki
aminiyata
Itama Suryn ta rungumeta daganan zance ya
sauya salo sukaci gaba da
Aikata
Masha,ar tasu
Rayuwa taci gaba nafi tanace har saida aleeyu ya
tsunduma
Harkan siyasa kuma ya fada da hannun dama
aka shga
Fantamawa dashi. Ya samu muqamin ambasador
Dan haka arziqi yaci uban nada
An gama Maka ma nafi katafaran gidanta Wanda
keda
Part part da yawa dan wannan gidan ko gidan
shgaban qasa sai haka
Ta sake siyo Wasu Maka makan motoci
Aleeyu harya fara tsorata da ita yai fadan yai
fadan harya
Gaji dan haka yasa mata ido. Tace masa su.
Tashi su koma gidan
Data Gina yace wannanne kuma baki isaba
Nana aka shga taqaddama tace idan shi bazai
komaba to ita zata koma ita daya
Don ba zata iya rayuwar matsi da takuraba
Ta dinga zama a wani dan qaramin gida sai kace
akurki ba
Wannan ai sai qawayena su rainani abin ba
qaramin sosama aleeyu rai yaiba
Ransa ya baci yace Indai har kikaga kin zauna a
wani gida
Da ba nawaba to saidai
Idan in babu. IGIYAR AURENA. Akanki
Tace wat kut ai IGIYAR AURE sunan wani littafi
ne
Aleeyu ka sani da aurenka zanbar wannan gidan
ko kanaso
Ko bakaso koka shirya ko baka shiryaba dan haka
Kwarama ka lallashi wannan. Bagidajiyar
matsiyaciyar zuciyar taka
Wacce batason taga taci gaba a rayuwarta
Yace watttttttttttt nafi ni kike fadama wadannan
baqaqen kalaman
Tace yez an fada Maka din ko kanada abinyine
Lol. Nafi kenan. Naga alamun itamafa akwai baki
Aleeyun zai yarda kuwa koko yaya
Shin wai Shima shajinin ko zai yarda koko yaya
Amsar na cikin chapter11 in Allah ya yarda
Barka da shan ruwa.
Aure. Kan. Aure
Chapter11
Yace wattt nafi ni kike fadama wadannan
baqaqen kalaman tace anfada Maka din
Koda abinda zakaine. Harya Bude baki da niyyar
maida mata martani
Tunanin me yai kuma sai ya fasa
Baici gaba da saurarontaba kawai ya fice ya
barta anan
Abun yai mata zafi tanason ta fantama gamida
walwala duniya tasanta amman
Ina abin ya gagara
Kullun Tunanin da take kenan Kamar ba itace ta
aje miliyoyin nairoriba
Tace kodai yakice aurennan na aleeyu zatai taje
tai rayuwarta yaddah takeso?
Kiran wayar da ake ya katse mata dogon kiran da
ake mata
Ta dauki wayar sury ce tace ke qawata ina cikin
tashin hankali
Yanxu tsohon mijina auwal yaimin waya wai
gashi ya sauka a naija
Yacemin wai ina ina nadai ce masa ina kano dan
na samu aiki acan
Yanxu haka wai yana hanya ya hayo motar kano
Nafi tace abu mai ssauqi sury ki saukeshi a
gidanki na sirri
aiba Koda yaushe shi chirman din yake gariba
Tunda yanxu haka ai yana abuja ko?
Saiki komacan idan chairman din ya dawo saiki
sallami shi tsohon mijin naki ki ce
Masa zaki koma aiki dan daman a cikin wani
kauye kike aikin kuma kike zama har sai an
karbeki Sannan kike dawowa
Sury tace kina ganin zai yarda? Inajin tsoro fa
nafi tace ke haba ki cire duk wata fargaba kinji
Tace to shikenan ta kashe wayar
Aleeyu na zaune saman kujera yana harhada
Wasu takardu nafi ta
Shgo ta zauna a gefensa
Bai kulataba yaci gaba da aikinsa ta dafa
kafadunsa tace aleeyu
Dan Allah kayi haquri
Ka daina fushi dani nibawai na raina arziqinka
bane
Kawai dai ina neman mana hutu kaida yaranka ne
Amman kayi haquri idan kayi fushi
Naga ko sury da kudina ta Gina gidanta kuma
suke zaune ita da Mijinta a ciki
Shin ni nawa mijin me zaisa bazai iya zama a
gidanaba?
Ya kalleta da idanunsa kury kafin yace
Aiba lallai Mijinta da naki su zama dayaba
Mijinki mai ikone da gidansa
Bazan koma mace tai iko daniba
Kuma duniyama zata zageni ace na turaki kinata
barnatar da dukiyar gadonki
Munata bushasha alhalin kullun fada nake miki
Akan rashin dacewar
Yin hakan. Kimin addu,a duk sanda Allah ya
horemin
Zan Gina miki gidan dayafi naki
Shiru tayi kamin tace shin idan nace kasai gidan
mu
Koma ciki zaka siya?
Wani murmushi mai cikie da takaici Yaja kamin
yace
Hajia nafi kenan aiko inada kudin siyan wannan
gidan naki bazan siyaba
Dan bashine a gabanaba abinda ke gabana shine
zuwa hajjinsu inna da malam
Tadan tabe baki kamin tace
Naji yanxu ka bada miliyon hamsin na siyar Maka
da gidan
Wai wani murmushi kamin yace nida miliyon
hamsin din waya aje wani?
Tace to kawai ka bada miliyon ashirin na siyar
Maka
Ba yaddah ya iya ganin ta nace yace to shikenan
ya rubuta mata
Cheaque ya bata
Ta amsa a yamutse
Yau shine ranar da suka tunkari shajini da
Maganar. Alfarmarsu tason
Yabar mata yarta afnan amman ta masa alqawari
duk cikin data samu to nashine
Zata bada. Daqin aminncewa yai saida suka hada
da magiya harda zubar da kwalla Sannan ya
amince
Gamida kafa mata Wasu shariddan
Lokacin da aleeyu yaje ganin gidan ya tabbatar
da gidan yafi qarfin kudinsa
Dana an zubama gidan miliyoyin kudi
Haka ta matsa masa suka koma a cikin satin
hankalinsa ya kwanta
Aifa ta samu yaddah takeso sai qarya ya qaru ga
babban gida da manyan motoci
Gashi Mijinta ya shiga cikin gwamnati ana
damawa dashi
Sai harka ta balle ita da matan manya duk
qqawayenta yanxu
Daga matan kwamnoni sai matan kwamishinoni
da matan manyan yan siyasa
Aleeyu ya saka afnan a makarantarsu adnan tana
aji uku ya kammala sakandire
Dinsa aleeyu ya shiga fafutukar neman fitaar
dashi waje
Baa,a son ransaba dan shidai yafison a barshi
tare da qanwarsa
Saidai ba yaddah zaiyi haka aleeyu ya samar
masa
Gurbin karatu a jami,ar califoniya dake qasar
amurka
Afnan sarkin kwallafa da wayau saida dibara
Sannan aleeyu ya samu ya
Rabata dashi. Adnan din ya tafi
Saidai yayi nadamar yin hakan dan afnan ta
hanakanta ci dasha
Kullun kuka wai a kaita gun yayaanta adnan
Kullun sai adnan din ya kira waya yaji muryar yar
qanuwarsa
Wannan shaquwa tasu kanbama Aleeeyu
maamaki
Yacema adnan din ya dage da karatu da zarar ya
kammala ya daawo
Zai aura masa ita itama hakan ya fada mata
Sannan ya samu natsuwarsu
Adnan ya maida hakalinsa sosai wajen karatunsa
na likita
Kuma komai yaxo masa cikin sauqi Sbd hankalin
daya maida akai
Haarya samu ya kammala karatunsa cikin nasara
ya dawo
Gida
Aleeyu ya sake samun daukaka sosai a harkar
siyasarsa dan yanxu ya
Zama ministan kudi. Kudi sun zauna
Nafi ta samu yaddah takeso sai bushasha kawai
take duniya sabuwa Mijinta ya
Taka babban matsayi
Afnan tana cikin farin ciki yau yayanta adnan zai
daawo dan haka tun data tashi da
Asuba ta dinga kai kawo ta shirya masa wancan
ta hadamasa wannan
Hatta bangarensa ita da masu aiki aka taru suka
gyara masa shi
Qarfe sha daya daidai ta fada toilet ta watso
ruwa
Ta fito ta zauna gaban dressing mirro
Mai ta murzama fatarta Sannan Tabi fuskarta da
fowder
Tabi labbanta da Jan baki pinki colour
Tafi minti shabiyar tana wannan kwalliya shafa
wannan lakaca wancan fesa wannan
Sannan ta tashi ta nufi wadruf dinta inda ta
dauko Wasu kaya yan ubansu
Idan ka ganta ba qaramin kyau taiba
Dan daman kyakkyawace
Da sauri ta suri key din motarta ta nufi falon
momyn nata
Ta isketa tareda Wasu qawayenta
Ta haye saman kujeran da Momyn nata kekai
Ta dubi matan dake cikin Dakin Wanda zasuyi
sa,ar mom din nata
Tace sannunku sukace yauwa afnan kina lfy tace
lfy lau
Sannan ta dubi momyn nata tace Momy fita zanyi
Ba tare data tambayetaba tace saikin dawo afnan
dina
Harta miqe ta hango wata qaruwar roban swan
ta janyo tace nasha Momy tsumine tace eh sha
ta kafakai saida Tasha sosai Sannan ta tashi ta
fita
Hajia kubra tace ke hajia nafi yanxu tsuminne
kikebama yarinya budurwa
Itada ba mijiba?
Tai murmushi tace to yason ranki ai duk wani irin
magungunanmu na mata
Da kika sani Indai ina shanshi to itama ina bata
tun tana qaramarta dan
Inaso tun yanxu na fara hadatane kafin tabar
hannuna
Ke bafa qaramin buri na dauka Akan yarnan bafa
nanda dan
Qanqanin lokaci zata zamemin jari
Shiyasa nake tsumata tun tana qaramarta hakan
shi zaisa ta banbanta da
Sauran mata darajarta tafi ta ko wacce mace
Dan maza su dawo anan dinmu ta nuna tafin
hannunta suka kyalkyale da daria
Kubra tace ammanfa bakida dama mutuniyar
nasan afnan sai
Manyan yan boko likitoci louyoyi da bankers
Lalalala ta katseta wanne irin Wasu likitoci ko
lauyoyi wlh
Bazan amince ta auri qananun yan boko ba
Burina yata ta auri sugaban qasa ko wani
basarake ko Wanda qasa ke ji
Dashi shine kawai burina
Danni a rayuwa Indai Akan kudine banqi kowama
ya rasaba Indai ni zan samu
Hajia zeena tace koda yake ai kwamnatinma
takuce hajia nafi
Wanda keda ya Kamar afnan idan baija jari da
itaba to meye amfaninsa
Suka tafa tace kedai ganemin hanya qawata
Afnan na fita harabar gidan ta hango adnan shida
daddy suna fitowa daga
Mota adnan din yahau Wasu baqaqen suit
Kace daman danshi akayosu
Afnan ta lumshe idanunta Sannan ta budesu a
hankali
Wani abu na ratsa zuciyata tace tabbas wannan
shine yaya adnan dinta mai
Sonta daman haduwarsa takai haka?
Suka nufota tai saurin shgewa falon. Tana bata
rai aleeyu ya kamo hannunta gami da zaunar da
ita yace
Kallleninan mamana jia nace miki jirgin sha,biyu
zai biyo ashe na shadaya ya biyo yana dira
yaimin waya naje na daukoshi
Dan nasan halinki da shiririta shiyasa bance kije
ki daukoshiba ba gashi na
Kawo miki shi da hannuna ba
Yace Bude idanunki kiga yayanki yaddah ya koma
dan saurayi mijin yan mata
Ta goge hawayen nata da hannunta ta saci
kallonsa
Akai sa,a Shima kallon nata yake. Tunda suka
shigo yake mamakin yaddah
Akai cikin shekarunda basu wuce shiddah ba
afnan ta zama. Budurwa sosai
Tsaantsar kyawu da siga mai dauke hankalin
namiji
Ya bayyana a jikinta
Lallai tsarki ya tabbata ga ubangiji wannan
halittar
Wani lallausar murmushi ta sakar masa Wanda
har saida kumutaunta suka lotsa
Ta matsa kusa dashi tace ur welcome yaya
adnan ina Maka murnan kammala
Karatunka
Tanx afnan ya fada yana murmushi Wanda har
saida wutshiryarsa suka bayyana
Sannan ta juya ta kalli abban nata tace daddy an
kammala gyara masa sashinsa
Sannan na hada masa wata yar qaramar walima
ta murnan dawowansa da wanne
Zai fara?
Yace ya fara wanka ya shirya Sannan sai a
gabatar masa da komai
Tace tnx daddy
Ta juya ta kamo hannunsa tace muje na nuna
Maka sashinka
Yace to yar qanwata
Ta kaisa falon nasa ya tsaya yana kallon ko ina
yace woo duk ni daya
afnan
Tai murmushi har bedroom dinsa ta rakashi
Tace yanxu kaje kai wanka kafin ka fito zan kawo
Maka kayan da zakasa
Saika fito yace tnx yar kanwata. Binta kawai yake
da kallo harta wuce
Sannan ya zauna a bakin gado dan yadan huta
kadan
Baifi minti biyar da zamanba ya miqe da sauri ya
fada toilet domin yin wanka yana fitowa yaga an
aje masa Wasu kaya irinta yayan sarakai komai
iri daya
Hatta takalmansu
Wai wata yar murmushi ya shirya tsab kayan
sunhau jikinsa
Ya manna yar siririyar glas dinsa ba
Qaramin kyau yaiba dan haka wata qasaita taxo
masa
Ya fito tamkar yarima dan sarki
Yana fitowa yaji ana tafi raf raf ya ware ido duk
qawayen afnan dinne na
Skull dinsu
Da kanta ta qarasa taja hannunsa har kan kujerar
da aka tanada Sbd shi
Afnan ta fito filin ita tai jawabi tare da baiyana
matsayin adnan a wajenta
Walimar ta qayatar dan anci ansha an kuma
cashe
Misalin la,asar Kowa ya watse
Zuciyar afnan data adnan kuwa farincikine fal a
ciki
Baba wacce ta rainesu bata samu ganin adnan
dinba sai wajen Bayan sallar magrin ta kallesa ta
jinjina kai tace yanxu adnan kaine ka zama haka
Cikin shekarun da basu wuce shiddah ba uhm
lallai sai aure kenan
Daria yasa kamin yace yar taki ta girma kenan?
Tace wacce afnan ai Indai afnan ne daa sauranta
kam tsulum ta sako baki tace wanne da sauran
baba hauwa kina nufin nyarinyaceni har yanxu?
Daria sukasa mata yaddah tai Maganar cike da
shagwaba
Yace kai baba ashe yar taki tanasona aure
Ta xunburo baki tace niba haka nake nufiba yaya
yanxu wacce take level 3 ce za,acema yarinya
Nandai ya dinga zolayarta cikin wasa
Har lokacin sallah yayi ya tashi ya barsu ya wuce
masallaci
Dawowar adnan ya qarasa shaquwa da soyayya
mai qarfi tsakaninsa da afnan
Washe gari da wuri afnan ta farka tun takwas na
safe
Sbd yau tanada lactur qarfe goma na safe
Don haka ta farka tun takwas ta watsa ruwa ta
tsaya wajen dressing mirro ta bata lokaci wajen
kwalliya
Wasu hadaddun Riga da siket ta saka. Sun mata
kyau kuma sun
Zauna a Jikinta kai inka ganta zakasha
balarabiyace
Ta maqala Baqin gilashinta gamida daukar
qatuwar jakarta
Mai dauke da manyan littafan makaranTa ta
rataya toyo waje
Sashin baba hauwa ta fara zuwa ta gaisheta
Sannan ta wuce Sashin babanta
Ta iskeshi yana break itama ta zauna Sukai tare
Tanata zuba masa surutu daganan ta wuce wajen
momcynta
Tasan daman bata farka daga barciba dan haka
ta fito ta wuce Bangaren adnan
Saida tai knocking sau uku Sannan ya bude
Yana sanye da wando treequeter sai singileti
Wani irin kunyace ta kamata dan haka ta kasa
shiga cikin dakin
Ba tare data kallesaba tace
Barka da kwana yaya adnan ka tashi lfy?
Yace lfy lau afnan ya naki kwanan?
Tace qalau yace sai kuma ina haka?
Idanunta. A qasa tace skull dan yau inada lecture
qarfe goma
Yace shine kuma koki gaiyaceni tai murmushi
Tace in zaka ai saimuje Kaga saima ka gaisa da
qawata sady
Bata samu zuwa walimaba jia basu gari ita da
mom dinta
Yace to shigo na shirya sai muje ko? Tadanyi
wani murmushi
A,a baridai na jiraka a mota
To kawai yace mata ya juya ciki baiyi minti goma
sha biyarba ya gama shri
Yaxo ya sameta
Baqin wando yasa da Jan tshirt kayan sun masa
kyau matuqa
Shidai komai yasa kyau yake masa ya daura
siririn farin gilas dinsa Wanda ya qara
Fito da fuskar tashi
Ita kejan motar tana nuna masa gari da irin
cigaban da aka samu
Har suka isa b,u,k.
Suna shga kuwa ta hango sadiya direba ya ajeta
Ta fito da sauri ta yafitota
Tace sady zo kiga yaya adnan din gashi a mota
Cikin zumudi ta jata suka tafi tana ina yake?
Yai qasa da gilashin motar yanna kallonsu da
wadataccen murmushi
A fuskarsa
Sungaisa sosai Sannan afnan tace masa yaje da
motar Sannan dan
Allah yaxo ya dauketa zuwa qarfe uku
Yace to
Harsun juya yace bakijiba don haka ta dawo ta
duqa ta gilas din motar
Yace I frget to tell yu I luv u. Sannan ki kularmin
da kanki
Taja wani dogon murmushi kamin tace insha
allahu
Sannan ta juya inda sady ke jiranta Sukai gaba
Sadiya diyar surayyah ce qawar nafi wacce ita
kadai ta haifa tun daga kanta bata sake
haihuwaba Sbd agreement din da Sukai da shajini
Akan duk cikin data
Samu nasune to hakan take ta Bangaren nafi
itama duk kanwar jace
Dan aleeyu yayi qorafin Akan yawan jubar cikinta
in yace mata suje asibiti sai taqi yarda tace wai
daga Allah ne
Saidai ita sady ta girma afnan da kusan shekaru
uku dan ko a skull din tana gabanta
Qawancene mai qarfi a tsakaninsu kuma
halayyarsu taxo daya abu dayane
Ita afnan bata damu dason Abun duniyaba duk
kuwa da aleeyu yayi iya baki kokarinsa wajen
bata tarbiyyah
Duk kuwa da yana saqa nafi na warwarewa
A makaranTa Kwata Kwata sady ta kasa sukuni
adnan ya fizgi zuciyarta
Tunda take bata taba haduwa da namijindaya
zama ful action irinsa ba
Komai nasa yai mata maganarsa murmushinsa
darewarsa natsuwarsa kai ita komai nasa birgeta
yake
Ita kanta afnan din ta fahimci qawarta bata cikin
natsuwarsa dan haka suna fitowa
Daga lecca
Ta kirata a waya ta sameta a inda suka saba
zama
Batafi minti gomaba ta qaraso itada Wasu
abokananta maza suna isowa Sukai gaba suka
barta
Bayan sun gaisa da afnan din sady ta zauna
gamida kwanciya a kafadar afnan
Din tace na gaji gaskia. Gida kawai zan tafi
Afnan ta dubeta tace nifa na lura dake sady
bakya cikin
Natsuwarki lfy?
Tai murmushi tace lfy lau afnan kawaidai yanayin
Garinne kira yayanki ya maidamu gida
Tace ai kin hangoshima can yana tahowa
Ta miqe da sauri tana tashi muje to me zamu
tsaya jira
Bata tanka mataba suka jera dan iskeshi a inda
yake
Kafin su qarasa ya fito ya budema afnan gidan
gaba ta shga sady ta shiga Gidan baya
Ya zagaya ya shga yaima motar key afnan ta
dubeshi
Kai yaya irin wannan tuqi haka sai kace kana
rarrafe
Ya waigo ya kalleta yace idan ba,ai tuqi hakaba
ya kikeso ayi
Tace cessss ka taka mota yayana irin tuqinda zai
tada hankalin jama,a
Yace a,a niban iya wannan tuqinba ai saida raine
kuma da daukan alhakin jama,a
Bata sake tanka masaba dan haka ya canja salon
Maganar da
Ina zamu sauke qawarki ta fada masa ya dauki
hanyar
Afnan ta kwantarda kujerar motar tana kallon titi
ya riqo hannunta yana fadin
Wai qawarki bata maganane?
Ko axumin magana take?
Ta waiwayo tana wai yau yadai sady baby
Yayanama ya lura da relax dinki
Ta lankwabe kai kamin tace banida abokin hirane
shiyasa
Ta girgiza kai tace hankalinki nakan yayanki
adnan nikuma bansan inda zansa nawa hankalin
na samu sa,idaba shiyasa na maida hankalin
nawa kan titi kawai
Tunda Naga alamun Iran ta yan uwan takace
Daria Sukai Sannan adnan ya amsheta tace aimu
Bama wariyar launin fata
Asalima hirar indake xatafi armashi
Ya kalleta ta gilashin mota ya daga girarsa sama
wato ta yarda da abinda ya fada
Tai murmushi tace yayanmu kenan
lallai zaman America ta amsheka. Gabadaya
yanayinka da kalamanka irin
Nasune
Iya kwalliya magana kai Hatta halittar taka
Wai kuwa qawata ta tava fada Maka kaidin
kyakkyawane?
Daria yayi yayinda wani dadi ya ziyarci zuciyar
afnan kasancewar an yabi sahibinta
Adnan yace sady kenan gashi kin ari bakinta Kinci
mata albasa saida Allah yasa warinta bazai
damekiba
Ta kada idanu tace ko daya Tunda ba. Qarya na
fadaba
Kai kyakkyawane kyanda mata dari zasu kalla su
kyasa
Idan nai Qarya ka fadamin mata nawa ka tara
tsakanin America da nigeria
Daria ya sakeyi yace hoo sady keko wacce irin
mutunce
Tace mafadar gaskia mai yaba duk Wanda yakai
a yabeshi
Kanada kyawun dake fizgar zuciya cikin yan
sakwanni
Kasan mata akwaisu dason namiji mai kama da
zakin maza irinka
Wannan karon dariar harda kyalkyalawa dan ya
Gano zolayarsa take
Afnan kuwa kasa sa musu baki tau dan ta kasa
controll din zuciyata na kissa mata
Lallai akwai alaman tambaya a cikin kalaman
sady tome take nufi
Oho
Aure. Kan. Aure
Chapter12
Afnan ta nuna masa wani makeken gate mai
kama da qofar shiga gar
Yai horn masu gadi suka bude
Yai fakin sady tace a gaskia saika shgo ka gaishe
da hajia ta
Dan kuwa lbrnka tuni ya gama cika mata
kunnuwa wajen afnan
Yaso ya bijire saida afnan ta saka baki Sannan
suka rankaya cikin gidan
A falo na uku ta ajesu tasa mai aiki ta kawo
musu lemo da ruwa
Sannan tahau saman batafi minti gomaba sai
gata. Tare da momyn nata
Hajia surayyah
Waddat hade cikin wata qasaitacciyar shiga irinta
mata masu kudi
Ta hakince saman kujera fuskarta dauke da
murmushi
Suka gaisa da adnan tai masa sannu da zuwa
Sundan taba Hira kadan. Afnan tace zasu tafi
Hajia sury tace wannanne baku isaba dole ku
zauna a gidannan yau zakuyi
Lunch
Afnan tace kai Momy batasan zamuzo nanba
Tace ba komai zan kirata a waya na fada mata
Afnan tace a,a karki kirata mommy zataimin fada
Tace bakuyi dai niyyar zamaba kawai tace a!a ba
haka bane Momy ai
Zamu dawo wataran
Tace to Allah yasa
Suka miqe
Sady ta rakosu har bakin motarsu suka shga
Sannan sady ta dubi adnan tana wani kashe
idanu
Yanxu sai yaushe kenan yaya adnan?
Yadanja wani murmushi yace a,a wannan
tsakaninkune keda qawarki
Tadan batarai tace haba adnan yanxu dole in
zamu hadu sai qanwarka ta sani?
Shikenanan yanxu bani numberka
Amsar wayar tata yai ya saka mata Sannan
Sannan ya shga motar ta daga musu hannu
Haka kawai afnan taji ranta ya baci tsayuwar
sady da adnan
Taji tamkar ta miqe ta shaqesu wani irin kishine
Mai zafi ya tokare mata zuciya
Don haka koda ya shga motar ya tada bata
kulashiba har
Suka fara tafiya mai nisa hakan yasa ya lura
fushi take dashi
Don haka ya takalota da magana
Yace afnan yau na hadu da qawarki data fiki zafin
dumi wai!
Carkwai kenan
Ta waiga ta kallesa a hasale saidai batasan
abinda zatace masaba
Sbd takaici
Haka ya karaci surutansa har suka iso gida
Yana fakindin motar tun kafin ya kashe ta fude
motar da sauri ta fita
Don haka Shima yai hanzarin fitowa ya riqota
shidai baisan abinda yai mataba
Na fushi hakaba
Don haka yace. Haba yar qanwar laifin me nayi
ne?
Meye nai miki haka yasa kike fushi dani?
Haba matar karkimin haka fushinki zaifi komai
dagamin hankali
A duniya zan iya jure komai amman banda
fushinki
Hawayene suka cika mata ido duk qoqarinta
Nason maidasu amman
Saida suka zubo
Har lokacin zuciyata bai dena tafarfasa ba
Ita kanta batasan irin kishintaba
Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro hankachip ya
bata bata musa masaba ta amsa
Ta share hawayen suka nufi cikin gidan ba tare
daya cigaba da matsa
Mata Akan jin abindaya bata mata ranba
Tundadai ya samu ta dawo walwalarta kamr da
Sadiya na tsaye gaban mahaifiyarta ita kuwa
uwar tata na zaune tana sauraron
Abinda zai fito bakin tilon diyar tata
Saida tai taku daya zuwa biyu Sannan ta isa
gaban uwar tata sanna ta duqa tana
Kallonta tace mommy kinga adnan babban likitan
kwakwalwa ne
Na taBbata kin hango abinda na hango
Mommy adnan ya cancanci ya zamo sirikinki
Ta ko wacce fuska
Dan ya hada abubuwan da ko wacce uwa zayima
yarta sha,awar aurensa
Mommy adnan nada kyau hankali ga tunani
gamida hangen nesa
Sannan uwa uba ga wadata danna taBbata koda
baida komai nan gaba to
Zai tara dan kuwa afnan ta fadamin daddynta
nacan yana qera masa wani hadadden asibiti
Wanda za,a zuba masa qararran likitoci na nan
qasa naija
Dana qasashe waje
Mommy adnan ya shga zuciyata ki taimakamin
na sameshi a matsayin mijina
Kuma uban yayana
Ki taimakamin momy
Hajiya sury tayi wani dogon murmushi kamin tace
Tace lallai barewa ba zatai gudu danta yai
rarrafeba sady zamannan da kikaga
Nayi nima Tunanin da nake kenan
Saidai wani hanzari ba guduba adnan dinnan da
kike ganinsa ba iyayen
Afnan ne suka haifesaba babantane ya daukoshi
daga kauye lokacinda uwarsa ta rasu
Anya suma ba shirin hadashi da afnan din sukeba
dan gida bai qoshiba
Ai baza,akai wajeba
Sady tai shiru tanadan nazari danta karanci
abubuwa da dama a tsakanin
Adnan da afnan din tadanyi wani takaitaccen
murmushi tace
Tabbas na lura da wata halaqa a tsakaninsu
saidai ai Momy kwace goruba a
Hannun kuturu ai ba abune me wahala ba
Dan afnan aiba abokiyar takarata bace Sannan
kuma adnan aiba ajinta bane
Hajiya sury ta kyalkyale da daria tace wannan
abune mai sauqi Tunda
Hajia nafin ai,a hannuna take
Don haka ki kwantar da hankalinki Kamar kina
jirgin sama mai ya qare
Sady ta kyalkyale da daria ta rungume momyn
nata tana fadin ina sonki
Momy na
Adnan ya soma shirye shiryen tafiyansa zuwa
kauye
Yaje yaga sauran yan uwansa dan haka aBban
afnan aleeyu. Ya shirya masa tafiyan da
gaggarumar tsaraba
Afnan ta kafe tanason ta bishi Tunda rabonda
daddy ya kaita anfi shekara
Haka ta dinga roqon yayan nata dan tasan
abbanta mai sauqi ne
Saidai shi adnan yaqi yarda dan yasan halin hajia
nafi sarai
Dan bai manta kiyayyarsata da zaluncinta akansa
Don haka yaqi dan karta janyi masa allura ta
janyo garma
Tunda tsakanin sashinsa da nata akwai tazara
mai yawa zan saika tsallake
Faluka yakai goma
Shiyasama basa haduwa tundaya soma gaisheta
ta dakatar dashi tace karta sake ganin qafarsa a
bangarensa daganan ya daina koda bi ta hanyar
falon
Ranar asabar misalin qarfe goma na rana adnan
ya gama shiryawa tsaf
Yahau wata dakakkiyar shaddah
Afnan na gedensa tana kallonsa
Yana zuba kaya cikin jakarsa harya kammala
Ya dago yana kallonta itama shidin take kallo
Ya aje jakar ya nufo inda take
Yace yaya dai afnan Naga Kamar kina cikin
damuwa
Ta girgiza masa kai jiki a sanyaye
Yace bakiso na tafi ko afnan?
Kinason na zauna kusa dake koda yaushe ko?ta
daga masa kai alamar eh
Yace inhar kin shrya aurena yanxu in naje kauye
saina sanarma malam ya samu
Abba ai maganar
Inhar Kinason kasancewa dani
Wani gajeran murmushi taja kamin tace
Inhar hakan ta faru zanfi Kowa farinciki muyi aure
mu tare a sbn gidan
Da Abba zai Gina mana
Kullun mu kasance a tare ina kusa dakai ina
Maka Hira mai dadi
Ban yarda da yawoba balle hirar dare ka gane
Daria yai Yaja dogon hancinta yace yarinya Indai
nine har saikin gaji dani kince
Na fice na baki waje
Ta zaro ido tace injiwa?
Tace Allah a,a aini bana gajia da ganinka kusa
dani
Duk wuya mu kasance tare na maka alqawari duk
wuya duk rintsi bazan
Juya maka bayaba
Yace insha allahu nima bazan gujekiba afnan duk
runtsi
Zaki sameni mai riqon alqawari
Kedai kiyita mana addu,a kawai
Tace insha allahu ya miqe yace kinga zaki
shagaltar dani
Har inda motar da direba ke jiransa ta rakashi
Harya shga direba yatada mota suka tafi tana
daga musu hannu
Har suka fice
Afnan ta juyi ta dawo dukta damu ji take Kamar
babu sauran Wanda ya rage
Mata a gidan
Don haka motarta ta hau ta nufi gidansu sady
acan ta wuni
Saida magrib ta dawo Bayan ta canja kayan
Jikinta ta nufi falon mom dinta
Ta sameta tare da Wasu qawayenta
Wanda sukazo daga turai acan ta samosu bayann
sun gaisa ta wuce falon baba
Hauuwa ana suka kusa raba dare suna hira
Kwata Kwata babu shaquwa a tsakanin hajia nafi
da yarta dan inka gansu wuri guda to gaisheta
tajeyi inka gansu saika rantse ya da qanwane
Dan ba zakace uwace da yaba
Don babu wannan shaquwar ta ya da uwa
Da safe kafin abban nata ya fita taje ta sameshi
tana shaida masa yanxu suna level din qarshe
Watanni suka rage ta qarasa
Abban yace shikenan sai aure kenan ko tai wata
daria
Tace kai Abba kaima harda kai?
Yace to afnan idan ban miki aureba zama zamuci
gaba dayi?
Ta girgiza kai alamar a!a. Tace to amman abba
Da yaya adnan zakai mana auren ko?
Yace au ashema nidake zullumin abinda ke raina
ban saniba harkun gama
Kitsa komai tsakaninku
Yace lallai kan afnan ni kaina banga ta zamaba
cikin satinnan zanje
Musawa na sami su malam a tsaida maganar
auren Naku kawai
Banga abinda zan tsaya jiraba
Tamkar ta daka tsalle har abin ya soma Bama
abban nata kunya
Yace kai afnan wai bakijin kunyata?
Sai a lokacin wata kunya taxo mata ta miqe da
gudu tabar falon
Ya girgiza kai yana daria kamin yaci gaba da
latse latsen laptop dinsa
Satin adnan hudu da tafiya kullun suna maqale
da juna a waya
Kullun tanbayarta don Allah yaya adnan yaushe
zaka dawo
Yace mata tayi haquri a gama maganar aurensu
sai aci gaba da shirye shiryen bikin nasu
Ranar asabar itace ranar data kasance aka daura
auren yar gwamna
Ita da wani dan sarki
Don haka bikine akai irn na yayan manya
Su hajia nafi ba zama don sune qirjin biki
Qarfe takwas daidai ta turo aka dauki afnan dan
halarta wajen bikin denner din da aka shirya a
wani abban hotel
Afnan na sanye cikin dinkin ankon da akai don
diner
Tarone akai na manya. Tare da dangin amarya
Dana ango
Anasha raye raye ciye ciye da tande tande
Inda makada da mawaka suka baje kolinsu afnan
ansha r awa
Hatta momynta ta cashe yaddah ya kamata
Tun a wajen afnan ta tsargu da kallon da wani
mutun ke mata tamkar ita kadaice a
Wajen
Har aka tashi motar mom dinta tabi
Tana shirin shga taji ana kira bakijiba baiwar
allah
Tai tsaye tana kallonsa ya qaraso kamin yace
Baiwar allah sunana jibri ibra ina daya daga cikin
sojojin dake takema
General abdullahi aminu Abba baya
A yanxuma shine ya turoni zuwa wajenki
Yace na amsar masa lambar wayarki
Wani gajeran tsaki tajaa tace wannan shirmenne
yasa ka tsayar dani?
Toka koma kace masa duk randaya shirya amsa
numbert. Ya tako da qafarsa yaxo ya
Amsa. Jikinsa na rawa yace ki taimaka hajia wlh
zakisa na iya rasa aikina
Afnan tabishi da harara ta Shige motar
Momcynta dake jikin motar tanajin abindake
faruwa tace zonana malam
Shareta kawai nine mahaifiyarta ga katina kakai
masa kace zamuyi magana
Godiya ya shiga yinmata ta Shige motar Sannan
Shima ya juya
A mota kuwa sai fada takema afnan tana fadin in
bacin sakaryaba
Waya gayamiki irin wadannan manyan mutanen
akema wulaqanci
Babban mutum Kamar janar har yace yana son
lambarki ki tsaya wauta
Da sakarci. Mutuminda yadda ake tsare da
shugaban qasa Shima haka ake tsare dashi
Motocin da yaxo dasu ko gwamna bai hau
irinsuba Kowa shakkarsa yake
Yana girmamashi wofi dake Kowa na fatan
rabuwa da iyayensa lfy ammanke
Sai haukar banza kawai kike
Itadai afnan batace mata qalaba harta gaji da
bambamin fadarta tai shiru
Satin adnan shiddah da tafiya Sannan ya dawo
Afnan ta shiga murnan tamkar wacce akaima
albishir
Yana dawowa abban afnan ya damqa masa.
Asibitin daya gama Gina masa
Murna wajen adnan kamarme
Adnan ya fara zuwa aiki komai na tafiya daidai
yaddah akeso
Da dare misalin qarfe tara afnan na sashin adnan
Yana mata wani bincike cikin laoptop dinsa
wayarsa tai qara
Ya dauka ya duba yana duban number
Yai saurin kallon afnan Sannan ya katse kiran
Afnan ta kalleshi tana masa kallo irinna tuhuma
kamin tai
Magana kiran ya sake shigowa
Caraf ta kwace wayar kan yai ankara harta nufi
waje
Cikin firgici ya bita falonta ta nufa tana shirin
kullewa ya turo qofar
Don haka nu nufi bed dinta da gudu yasa kafa ya
hardota ta tafi taga taga ya fizgota
Ta dawo jikinsa
Daria take sosai tace yi haquri yaya amshi wayar
taka gashinana
Amsa yayi ya kama kunnenta yace kin rainani
afnan waini
Sa,ankine?
Tasa qara tana bashi haquri
Ya saketa yai gaba haryakai bakin qofa. Ta miqe
tana fadar
Aidai ga wayar nan tawa na baka
Yai saurin dubawa yace au hakanefa da sauri ya
bita kafin ya cimmata harta fada toilet ta rufe
Yai tsaye cike da takaici ba yaddah ya iya dole ya
tsaya yanna mata kagiya
Yace fito ki bani kinji yar matata babu abinda na
boye Wanda bakisan dashiba ta windo ta leqo
tana masa daria
Tace Allah bazan miqoba har saina karanta komai
A qufule yace waike ina wasa dakene?
Yi haquri kinji kinsan babu kyau binciki
Bata tanka masaba ta fara duba number dake
kiransa frnd kawai taga ansa
Dan haka bata gane ko waceceba
Tai saurin zuwa inbox dinsa txt taga na farko
natane na biyuma natane
Na ukune taga ansa frnd dan haka tai saurin
budewa
Dan karantawa(peace be upon u adnan
Pls adnan save my life wlh I cnt. Do without u.
Nice na dace da zama zabinka
Sbd nice ajinka am beauty edycated an rechest
Pls adnan I wnt to be ur wife
Your sady baby
Gaban afnan yai mummunan faduwa
Wacce sady din badai tata ba
Hannunta na rawa ta cire number taga aiko itace
Ji tayi wani juwa na neman kayar da ita ta dafe
kai tana kiran sunan
Allah
Ta rufe ido tana fadin wayyo Allah na shga tara
Ya Allah ka taimakeni karna rasa adnan
Jikinta ya saki ta Bude toilet din ta fita tama
rasa ina zata
Falon mom dinta ta nufa akwance ta sameta
saman kujera tana chartin da laptop
Tana ganinta hajia nafin ta tashi gamida cire
gilas din fuskarta
Afnan ta shge Jikinta tai lamo sai numfarfashi
take
Momcn nata tace Waye ya batamin ran yar
autatace iye
Idonta ya kawo kwalla murya a sanyaye tace
Momy adnan ne
Tace me yai miki dan iskan yanxu naje naci masa
mutunci?
Ta girgiza kai tace ba komai Momy wai sady
diyar gidan Momy surayyah ce take sonsa harda
aiko masa da text
Wat wata gigitacciyar tsawa ta daka mata tace
kinga dakata tare da hankadata
Gefe har kanta ya budu da bujera jini ya fara juba
ta mike tsaye Jikinta har rawa yake tace me kike
shirin fadamin?
So kike kicemin sonsa kike? Ban miki kashedi da
shga harkar matsiyacin yaronnan
Ba?dubeki mana kina nufin nasha wahalar
nakudarki abanza kenan?
To wlh karya kike in sonsa kike nida kaina zan
tsaya mata ta aureshi
Itace daidai da ajinsa ba keba
Ita yar gidan sanater ce ke kuma babanki chief
minister ne
Kinga kuwa akwai tazara sosai a tsakaninku
Tace sakarya kawai wucemin da gani tunkan
raina ya gama baci
Sannan gobe qarfe goma jirgin janar Abdallah zai
sauko
Ma,ana zaizo wajenki inkinga dama ki
wulaqantashi
Wlh da sai na miki wulaqancin da keda kanki zaki
dunga Tunanin shin wai nice
Na haifeki ko kuwa Danni Akan kudi ba abinda
bazan iyaba kinajina maza ki bacemin. Da gani
gaba daya ni bani kika biyoba wannan matsiyacin
uban naki kika biyo Wanda arayuwarsa kullun
baison ci gaba sai ci baya
Jiki a sanyaye tabar Dakin tana jinjina kalaman
uwar tata
Aure. Kan. Aure
Chapter13
Afnan ta miqe goshi na xubar da jini tabar falon
Ko kadan a haja nafi bataji tausayintava saima
wani dogon tsaki dataja
Ta koma ta kwanta tana fadar
Nonsense
Juwace ta soma kwasarta tana isowa bakin kofa
Sukai ido hudu da adnan
A gigice ya nufota yana fadin lfy afnan
Me yaji miki ciwo subhanallah
Ya zaunar da ita ya juya a guje ya kwaso kayan
aikinsa
A rude ya kamo hannunsa data dafe kanta dashi
ta fizge hannun
Ya girgiza kai yana a,a afnan kar muyi haka
Ya miqe ya zauna kan kujerar da take
Ya riqeta sosai Sannan yai mata dresing din
ciwon
Ya dubeta cikin nuna tsananin kulawarsa ya kira
sunanta
Afnan ki gafarceni. Na rantse miki da Allah ban
taba mafarki saba miki
Alqawari da mukai ba Sannan text din da kika
gani a waya wlh tundata turoshi ban mata replay
ba ban kuma sake daukar wayarta ba
Yau sati guda kenan kullun saita kirani yafi sau
ashirin
Nasan idan har kika duba wayar dakyau zaki
tabbatar ban taba kirantaba
Kuma na daina daukar wayar tata
Kimin uzuri my luve wlh bazan tava cin
amanarkiba
Na amince daki dauki layin wayar ki karya kisai
Wanda yai miki kiban naci
Gaba da amfani dashi. Kinji ya tambayeta
Wani sassaukar numfashi ta sakar ta lumtshe ido
alamar tanason yin Barci Sbd maganin daya bata
Haka ya samu ya lallabata ya kaita dakinta ya
rufeta da bargo Yaja mata qofa
Koda abbanta ya dawo yana cikiyarta adnan yace
ai taji ciwone hankalinsa ya tashi
Yaje ya dubata saidai har lokacin bata tashi daga
barcinba Sbd maganin datasha
Yanada qarfi sosai
Washe gari tundata farka kanta yai mata wani
irin nauri daqar ta iyayin sallah
Ta koma ta kwanta don haka da aleeyu yaxo
dubata bai sameta ido biyu
Ba shi kansa adnan din sau biyu yana xuwa bai
samunta
Hajia nafi ta aiko yarinyar dake mata aiki tace
taxo ta kira
Mata afnan ta samu ta farka saidai jikin nata
bakwari
Ba zata iya tashiba
Yar aikin bata Dade da tafiya ba saiga hajia nafin
ta shigo fuskarnan a turmuke
Ta taba jikin nata taji ba zafi sosai tace tashi na
taimaka miki ki shirya
Dan kuwa har baqon naki ya qaraso sunacan falo
sunacin abinci
Afnan din batace mata qalaba ita dakanta ta
tasheta ta kaita
Toilet ta hada mata ruwan wanka Sannan ta fito
ta zaba mata kayan
Da zatasa.
Bayan ta fito ita da kanta tai mata kwalliya
Adnan daya Gaza tafia aiki Sbd ciwon rabin ran
nasa ya dawo a karo na
Uku saidai a wannan karon yayi rashin sa,a
domin hajia nafi nanan
Shi kansa sai dayaji faduwar gaba
Ya zube yana gaisheta baki sake ta tsaya tana
kallonsa
Ta girgiza kai tace eh lallai akuyar daure ta samu
sake
Wato inacan mutun ya maidamin diya Kamar
matarsa
Lallai mutun mugun iccene
To bari alhajin yaxo sai inji idan shine ya baka
lasisin yin haka
Mugu kawai banza haifaffen kauyen kayau.
Qauyen da ko wutan lantarki basu dashi
Aniyarka ta bika wannan da kake gani tafi
qarfinka dan ba matar talaka bace
Dan iska a sannu sai nayi maganinka tashi ka
ficemin da gani
Ta fada da kakkausar murya
Afnan ta runtse idanunta wani irin zugi na ratsa
zuciyata tamkar ya fashe
Ta bude idanun nata lokacin data tabbatar daya
fice
Ta kafe mom din nata da idanu zuciyata na
harbawa
Ji take tamkar ta maqare mom din nata ita kanta
ta fahinci irin kallon
Da diyar tata ke mata. Tace ko zaki Rama
masane iye sai insan kinji zafi
Batace mata komaiba ta jera suka fice
Har falon da yake ta isa
Saidai zuciyata ta soma sarewa da irin rashin
mutuncin data tattaro
Dan tun daga barkon falon
Sojojine tsaytsaye ko wanne da zungureriyar
bindiga sai mazurai suke
TaBbas in banda tare da mommynta suke da
babu abinda zaisa ta arce da gudu dan ko
yanxuma dakiyar zuciyace kawai
Falo na biyu yafi na farkon yawan sojoji dan
Hatta bakin qofar shiga Sojojine
Tsaitsaye suna shga momynta ta juya kai tsaye
fuskarta ta sauka kan
Genaral farine tas tas yanada cikar halitta. Irin na
jaruman maza saidai
Bai cika wani kyauba. Saidai akwai kwarjini a
Idanunsa
Shekarunsa zasukai talatin da bakwai babu
alamun wasa a tattare dashi idanunnan nashi jajir
dasu
Yana sanye da suita baqa da jar tshirt sun zauna
a jikinsa
In bacin sallama data zama dole a addinance da
babu abinda zaisa
Tai masa sallama
Ya dago da jajayen idanunsa yana kallonta
Wanda sukaso
Tsoratata lokaci guda ta zauna kan kujerar dake
fuskantarshi
Tace sannu da zuwa ciki da qasaita yake amsawa
tamkar Wanda aka takura
Don haka bata sake maganaba cikin Wasu yan
dakiku
Kamin ya gyara zamansa kan kujeran ya soma
cewa
Malama hafsa afnan ko to ba tare da westing din
tyme ba nasan dai kinsan abinda
Ya kawoni gurin momcynki ko?
Nidai bawai buqatata Wasu dogayen
maganganuba kin gane ko
Nasan kinsan koni wanene don haka in kinji zaki
iya ina mana
Sha,awar kasancewa ma,auratane nanda Wasu
yan qanqanin lokaci ina fatan kin gane
Ta miqe ta kalleshi Bayan tayi taku daya zuwa
biyu
Sannan ta waigo tana masa wani qasaitaccen
murmushi
Tace lallai malam jenaral rashin sani yasa kai
shuka a gonar da ba takaba
Ta girgiza kai tace soyayyah kwara dayace tak
kuma na rigada na Bama wani
Don haka Kowa ye yace Maka nace ina sonka to
qazafi yaimin
Ko kuma ince yai Maka qarya ka gafarceni mai
girma janar
Banda ajiyayyen soyayyar da zan iya baka a
yanxu
Sannan ta koma ta zauna tace nasan dai wannan
bazai damekaba ko?
Yace ko daya saima ya qaraban kwarin gwiwan
Zage damtse don kwatar soyayyarki da karfin
damtse ko data aljihu na
Ko kuna na kwaceta da qarfin mulki na
Duk wannan ba abune mai Whl ba a wajen mutun
mai qarfin iko irinaba
Tai wani murmushi takaici kamin tace
Yo ashema shirme kawai kake a cikin soyayyar
Tunda bakasan meye ita sonba
To bari kaji na fadamaka shi so gamon jinine ba
gamon gambizaba
Shi so haduwar juciyane ba hasasheba
Shi so kudi ko mulki ko kyau ko iko basa samar
dashi
Duk sone ke samar dasu
Don haka Kaga kenan yanada kyau ka nemi
amincin zuciyar wacce kakeso
Shine abu mafi sauki
Genarar Kamar yaddah ta kirashi yai murmushi
Sannan ya sake kishin gida saman kujera
Yace afnan kenan ni genar banayima soyayyah
bauta. Kuma bana biyayyah
Ga mace isace ke kwatomin soyayyah a gurin ko
wacce kalar mace
Don haka a cikin uku sai anyi daya
Ko in kwaci zuciyarki dake kanki da qarfin damtse
ko in kwaceta da qarfin aljihu
Ko kuma in kwaceta da qarfin mulki
Cikin ukunnan dole sai anyi daya
Tace to lallai Indai da ukunnan kawai kake
taqama to ba zasu taba
Iya amso Maka soyayyah wajen mace ba
Balle ni afnan da xuciyata ta Dade dayin nisan da
mai rai bazai iya gano
Adadin guduntaba
Na rigada nayi nisa Akan son mutun daya dan
autan maza namijin mazaje
Wanda daddadan kalamansa ke narkarmin da
zuciya
Ta miqe tsaye tana wani murmushi sannan tace
Yaya adnan kenan idan yai murmushi yai kyau
idan ya daurema yai kyau
In yana magana har wani daddadan iskane ke
fitowa daga bakinsa mai kashe zuciya
In yana tafiya yai kyau in azaune yakema kyau
yake
Kallonsama kawai daukemin numfashi yake.
Hmmm yayana kenan
Ta ida fadar tana wani kyakkyawan murmushi
tamkar yana gabanta
Wani haushi da takaicine suka daki zuciyar genar
ji yake tamkar tana watsa
Masa garwashin wuta
Da gaskefa yanason wannan yarinyar dan
zuciyarsa ta sanar dashi
Jin yayi shiru yasa tace to yallabai ni nayi gaba
Allah raka taki gona
Dan kuwa zuciyar afnan ta Riga da tayi tauri ta
zama tamkar dutse
Dutsenma dutsen daka Wanda ko nakiya ba zata
iya fasashiba
Ya miqe da sauri zuciyarsa na radadi yace
Yarinya Indai kudi da mulki na aiki saikin dawo
saman hannuna
Yasa hannu a aljihu ya zari cheaqu ya aje kan
tebur ya zuya a zafafe ya wuce sojojinda ke tsare
lfyrsa suka rufa masa baya ba tare data qara
waiwayarsaba itama ta wuce bangarenta
Adai dai sashinta suka hadu da adnan sai safa da
marwa yake
Duk ya hada gumi yana ganinta yai saurin
qarasowa ya zaunar da ita
Itadai kallonsa kawai take
Jikinsa har rawa yake yace afnan yanxu yarda
zakiyi a rabamu
Afnan walahi ina sonki na rantse miki da Allah
bazab iya rayuwa babu keba
Afnan in kika barni bansan halinda zan shgaba
Hannu tasa ta soma share masa hawayen da
suka soma gagaro masa
Ta rasa ta yaddah zata fara lalllashinsa dan ita
kanta zuciyata ta karye
Kuka takesonyi saidai in tace zatai kukan bata da
mai lallashinta to mai lallashin nata Shima kukan
yake
Muryarta a sanyaye tace yaya adnan kasa rainka
a inuwa babu Wanda zai rabani dakai
Duk runtsi ina tare dakai
Dukda nasan kana cikin tsoro danshi so Kamar
tsuntsu yake yakan iya tashi
Daga wannan bishiyar ya koma wancan to inaso
kasa a ranka
Son da nake Maka bishiya daya gareshi a cikin
jeje
Idanma ya tashi to saidai ya fado qasa Wanda
hakan na nufin ruguwar rayuwata kenan
Nidai duk runtsi ina tare dakai saidai in har kaine
ka juyamin baya
Yace ki daina fadin haka afnan nidake saidai
mutuwa ke ko mutuwar kikai saina auri
Zuciyarki
Murmushi tayi ganin sonta na neman zarar dashi
A tare suka wuni suna Hira mai dadi
Misalin qarfe goma na dare aleeyu na zaune a
sashinsa sanye da farin gilashi yana bincike a
laptop
Hajia nafi ta shgo tana sanye cikin qasai tacciyar
shiga
Saida ya kammala abinda yake sannan ya juyo
yana kallonta
Murmushi ta sakar masa dan haka ya miqe ya
qarasa inda take
Yana fadar
Yadai hajia Naga bakinki tamkar da magana a
ciki
Tasake sakin wani murmushi kamin tace
maganganu kai
Yace to gani fesamin
Tace nida yarkace afnan daxun an kawo Maka
suriki bakanan
General Abdallah kuma mun aje magana dashi
Akan zaizo ya ganga domin turo
Magabatansa
Aleeyu ya haderai yace ban fahimcekiba nafi kina
nufin har wani qato kike kawomin cikin gida ba
tare da izninaba
Amman lallai kin cika marar hankali yasin
Ya nunata da dan yatsa yace bari kiji Yadai
tawace to narigada nai mata miji
Babu kuma Wanda ya isa ya sauyamin magana
kin gane ai ko?
Zaram ta miqe tsaye ta bigi cinya tace qarya
kake aleeyu wannan karon
Kaci qarya ka kwana da yinwa wlh
Indai ina numfashi yata ba zata auri matsiyaciba
Don haka tun wuri ka gyara bazarka inko kaqi ta
tsinke
Yaddah takeba babatun nata abin saima ya daure
masa kai
Yace lallai bakida kunya nafi harni zaki kalla
tsabar idona kice nai qarya
To kece ke qarya mu xuba nidake shge ka fasa
Tayi wani malalacin murmushi tana girgiza kai
Tace lallai aleeyu bakasan wacece nafi ba
Ganina kawai kake na rantse da Allah
hatsabibancinan ya wuce yaddah keke
Tunani
Zan iyayin komai Akan wannan lamarin
shiyasama nake shawartarka
Akan abinda nace dan kawai a zauna lfy
Ta girgiza kai tace wlh aleeyu bakasan yaro bane
kai saika tsince kanka a
Hannun manya. Zaka tabbatar
Lol
Shirmen natama ya daina bashi mamaki. Takaici
ya koma bashi
Don haka cikin tsawa yace get out
Ya fada a harzuqe yana tilasta mata ficewa
Yayinda zuciyata harta fara tausayama bala,in
data shiryama aleeyun mijin nata
Dadddah shi Wanda yake qoqarin Bama diyar tata
Da ita kanta afnan din don yanxu batajin digon
tausayi balle imani a xuciyarta
Washe gari misalin qarfe sha daya na rana
Adnan ya dauki afnan domin kaita makaranTa
don tanada lecture qarfe daya na rana
Bayan ya ajeta Yaja motar tasa sannu a hankali
yake tafiyan yana sauraron karatun alqaur,ani
Bai ankaraba saiji yai an bude motar an shigo ya
juya da sauri dan ganin abinda ke faruwa
gabansa yai mummunan faduwa
Mutanene sanye da baqaqen safa a fuskarsu baka
ganin komai na jikinsu
Daga idanunsu sai hannu
Ko wannensu rirriqe da bindiga
Tuni zufa ta soma karyo masa
Cikin murya marar dadi daya daga cikinsu yace
Zaka iya fansar ranka idan har kabi abinda muka
umurceka dayi
Don haka duk inda mukace kabi nan zakabi
Kana kuskurewa kuwa dauke kanka zanyi yasin
da wannan bindigar dan umarnin da akaban
kenan
Jikinsa yai sanyi dan ya rigada ya fiddah rai da
rayuwa
Don haka duk inda suka nuna masa nan yakebi
Har suka shiga can cikin wani daji
HmMmmm lol. Jama,a we hve done wif book1
Shin wa kuke ganin zaisa a sace adnan
@nafi ko @general shin ko sury ce uwar sady.
Sbd yaqi sauraron yarta
Kai anya ba shajini za,a kaima shiba
Guest
Kan. aure
Chapter14. Wif. Salankz
Tafia mai nisa Sukai kamin su isa wani
tangamemen gate
Daya daga cikinsu yam saurin fitowa ya zanyoshi
suka nufi ciki
Gidane qaton gaske
Ta cikin wani falo suka ratsa mai cike da daular
duniya sannan
suka isa wani daki Dakin na dauke da kujeru
tareda babban tebur a tsakiyarsa daya daga
cikinsu yace zaka zauna anan har sanda hajiya
zata qaraso. Don kuyi magana
Sukace karka damu babu mai cutar dakai Tunda
har kabi shariddanmu
Suka juya suka fice gamida kulle qofar ta baya
Adnan ya durqusa a wajen cikin tsananin tsoro
Lallai yana cikin tashin hankali marar misultuwa
shin meye dalilin kawoshi nan
Meye manufar yin haka?
Sannan suwa sukasa a kawoshi nan?
Tambayoyin da baida mai amsa masasu
Adnan har qarfe hudu na yamma tana kiran
adnan babushi babu dalilinsa
Tsawon mintina talatin kenan tana zaman jiransa
Amman da alamar bazaizoba
To wa zatace ya rage mata hanya? Daman sady
ce
Kuma ta kammala karatunta
Daman kuma sundanja baya da zumuncin nasu
Don haka ta ciro wayarta ta kira direbanta Wanda
ta hutar dashi Sbd dawowar adnan
Tace masa yai maza kome yake ya aje yaxo ya
dauketa a skull yace
Angama ranki shi Dade. Baifi minti talatinba ya
Iso ya dauketa saidai zuciyata na cike da alhinin
abinda ya hana adnan
Zuwa daukar nata
Gashi tanata kiran wayarsa saidai ta ringin harta
dauke
Ba,a dagawa to ko lfy abinda take Tambayar
kanta kenan
Zuciyata bata qara tsinkewaba saida taga har
anyi sallar isha,i bai dawoba
Har a lokacin kuma inta kira wayarsa ba!a
dagawa
Don haka ta kira abbanta ta sanar dashi don
haka yace gashinan isowa
Shima yaxu
Adnan kuwa. Tundaya durkusa a wajen yafi awa
guda Sannan ya tashi
Sbd lokacin sallah yayi dukda tsoron dake
fuskarsa hakan bai hanashi
Nufa toilet dinba domin dauro alwala
Nan ya fito Bayan yai alwalar yai sallar Sannan
ya duqufa karanto
Addu,oin neman tsari
Har akai sallar magrib da isha!i yananan
Hankalinsa ya gama tashi a wannan lokaci dan
haka hanyar tsira kawai yake nema
Gashi wayarsa na cikin mota daman a chargi
yasata
Yana cikin wannan tunane tunanenne yaji an turo
kyauren kofa
Yai saurin miqewa dan yaga mai shigowa
Hajiya surayyah ce tana cikin kyakkyawan shga
Kallon kallo suke a tsakaninsu cikin tsananin
mamaki yake
Kallonta. Ta nemi daya daga cikin kujerun Dakin
ta zauna ta daura
Qafa daya kan daya tana kadawa tana murmushi
Sannan tai masa nuni da hannu alamun ya zauna
Tace zauna mana adnan kaja ka tsaya tamkar
mai shirin kokawa
Bismillah zauna
Ba musu yaje ya zauna gami da fadin meye
dalilinki na kawoninan iye hajiya?
Murmushi ta sakeyi kamin tace kana mamaki ko
adnan
To wannan kadan daga aiki nane dan na wuce
hakama
Mai yasa nasa waya na kiraka kaqi zuwa daga
bayama saika kashe wayar?
Yace Sbd banda wata alaqar da zata kawoni
gidanki
Sannan baki da wani kyakkyawan dalili na
nemana
Tace ko daya karkace haka adnan niko keda
kyakkyawan dalili na
Nemanka
Domin kuwa yata sady tana cikin wani
matsanancin Hali duk Sbd kai
Ka taimakamin adnan banso na rasata
Don ita kadai na mallaka. Inhar kaimin haka to ka
gamamin komie a rayuwa
Kuma na maka alqawari azurtaka da dukiya mai
tarin yawa
In saka a harkar siyasa kaima a dama dakai
In tsaya maka har sai Naga ka zama wani abu a
rayuwa
Buqatata kawai ka amince da auren yata kawai
Takaicine da mamaki suka rufeshi lokaci dayaa
Yace to aini ban iya auren rashin yanciba hajia
nasan kaina da abinda
Nakeso don haka ni ban tabajin inason yarki sady
ba
Saidai koki tallata gaba don nasan akwai masu
so fiye da yaddah zuciya
Keso
Hajiya sury ta miqe tsaye cike da takaici ta
nunashi da yatsa tace
Ka taka a hankali adnan dan yanxu rayuwarka a
hannuna take
Zan iya juyata yaddah nakeso
Wannan kawai ya isheka ishara yaddah nasa aka
kawominkai haka zan iyasa a batarmin dakai
Zan iyaayin komai Sbd rayuwar yata ba baka
nanda sati biyu kaje kai
Shawara
Tana rufe bakinta tai waje Sannan qartin suka
shigo sukace
Kana iya tafiya
Abinda sukace dashi kenan cikin hanzari ya xura
takalminsa
Ya fice daga gidan jikinsa na rawa ya fada mota
ya fice daga gidana a
Guje tamkar Wanda yake tsoron a sake kamashi
Acan gidansu afnan kuwa aleeyu na dawowa kai
tsaye sashin nafi ya nufa
Hajiya nafi ya nufa yana zaune kan 2seater. Da
cup a hannunta da ala$un
Tea takesha. Wani film take kallo a tashar mbc
action ko sallama babu
Ya fada Dakin idanu waje take kallonsa bakinta
na rawa tace
Lfy dai ka shigomin ko sallama babu?
Ya nunata da dan yatsa muryarsa a kausashe
yace
Ke saurareni Nafisa kina nufin wannan hanyar da
kika bullo da ita zata
Bulle dakene?
Toki saurareni dakyau kiji na rantse da tsarkin
mulkin Allah saina
Aurar da afnan ga adnan
Inhar ina numfashi a duniya don haka duk inda
kikasa akakiai adnan kiyi
Gaggawar fitowa dashi cikin yan mintunannan
inkuma ba hakaba kuma,,,,
Ya murza yan yatsun hannunsa Sukai qara ya
juya ya fice ta bishi da
Kallo kamin taja wani dogon tsaki mtwsss
Yana fitowa ya nufi sashin afnan ya ganta a
tsaye
Zamama ya gagareta qarfe tara da wani abu
Na dare amman babu labarin adnan
Hawayene kawai ke zarya a fuskar nata tana
Tunanin shin ko a wani Hali yake yanxu oho
Aleeyu ya shgo falon ya zaunar da ita yana
lallashinta
Yace kiyi haquri yata insha allahu duk inda ya
shga za,a ganoshi na kira d,p,o
Yanxu nai masa bayani
Hawayen dake zuba daga fuskar nata bai daina
kwararaba tace
Yanxu daddy shikenan shigowar adnan din yasa
bata qarasa abinda zataceba
Ta miqe da sauri taje ta riqoshi zatai magana
kuma saita sakeshi
Tana kallonsa
Baice mata qalaba ya wuce wajen aleeyu ya
gaisheshi
Bai amsaba saidai ya jefo masa tambaya
Ina ka shga aleeyu afnan tace tun kafin sallar
azahar ka ajeta a makaranta
Tun daganan bata qarajin duriyarkaba Sannan
inta kira wayarka ba!a pickin lfy? Ina kaje?
Yace Abba wayatace ta bata a lokacin da naje
gidan abokina saddiq
Don na dubashi baida lfy
Nan na zauna ina kula dashi har saida qaninsa ya
iso daga katsina
Sbd ba Kowa a gidan
Aleeyu yace amman dai baka kyautaba aida saika
ari koda wayar abokin
Nakane ka kira kai mana bayani dan kasan dole
dai za,a nemeka
Tubi yaddah duk ka tada mana da hankali
Yace ayi haquri Abba ba za!a qaraba
Yace to shikenan gobe zan tafi musawa dan
tsaida. Ranar aurenku
Idan kanada sako saika bada yace ba komai Allah
ya kaika lfy
Kuma ba wani lokaci bikin zaijaba don haka ka
sameni a falo don baka takardun gidan Dana
kammala muku na nasarawa
Sai kaje ka duba don ganin yan gyare gyaren da
za,ai masa
Akwai Wasu motoci da za,a turomin daga
America I zuwa sbn kamfanina
Sai kuje ku duba ku zabi daya daya kaida afnan
Godiya suka zube suna masa harya fice
Da sauri adnan ya tashi ya dawo gefen afnan ya
zauna tai saurin juya masa baya alamun fushi
take dashi
Ya dafe kai yace ohh my afnan kar muyi haka
dake ki fahinceni plz
In kika juyamin baya ina kike Tunanin zanje na
samu sanyi
Yace haba afnan wuni guda nai a waje aikin tai
mako nayifa
Ba yaddah na iya amman wlh nayi mising dinki
Idanuwana sun qagu da suga kyakkyawar fuskarki
Plz matar juyo ki kalleni dan gajiyar ta tafi
Bata juyaba hakan yasa yai saurin komawa
gaban nata
Ya riqo hannunwanta yace aimin haquri my luv
Yaddah yai maganar kaman dan yaro abin ya
bata daria ta qalqale
Don haka zuciyarsa tai sanyi Tunda ya shawo
kan rabin ran nasa
Yace bari naje kiran daddy na dawo ki hadamin
abinci da tea kinji
Kai kawai ta kada masa ya fice
Washe gari Tunda safe misalin. Tara da rabi ya
nufi gidansu nafi
A falo ya samu hajia asiya zaune sanye da farin
gilashi tana karanta jarida
Ya samu kujera ya zauna. Ta dubeshi fuskarta
dauke da murmushi tace
Aleeyu mazan fama kwana biyu kai mana yaji
Yai wani guntun murmushi ya zube ya gaisheta
Ta amsa yar Hira suka Sannan ya shgar da
maganar nafi
Tunda Sukai aure yau shekara goma sha tara
kenan bai taba kawo
Qararta ba sai yaau da ya zama dole
Yace hajia daman maganar nafi ne acan gida sun
yanke shawarar hada
Afnan da adnan amman ina tunkararta da
maganar ya zama abin tashin hankali
Wai ita yarta ba zata auri talakaba wai Tunda
janar Abdallah yace yana
Sonta. Tace wai shi zata bamawa
Kuma janar ba mutumin arziqi bane dan ko
mutanen dake qarqashinsama
Kuka suke dashi
Sannan yarinyar tace batasonsa shiyasa nace
bari
Naxo na sanar dake kiyi mata makagana dan
nasan tanajin maganarki
Wlh nafi nada matsala dandai kawai zaman aure
sirrine shiyasa
Tace nasan da haka aleeyu nasan haquri kawai
kake da nafi dan bata da
Kirki
In banda Iban albarka ace a matsayinka na
mijinta har kasa
Doka ta tirge ai bai kamata ace ta Maka musuba
koda kuwa ranta bai mata ba
Ita da yar taka ai duk a qarqashin ikonka suke
ikonkane aleeyu kanada right din da zaka yanke
duk hukuncin dakaga yayi maka
Don haka ni inkama janye auren afnan da adnan
koda Bayan raina ban yafemaka ba
Namijinekai kaje ka gindaya sharadin gidanka inta
qetare ka yanke duk hukuncin
Da Kaga yafi dacewa akanta
Babu Wanda zai zargeka kuma zan kirata yanxu
ba sai anjima ba
Kaje ka qara haquri yace ba komai na gode hajia
Haka ya miqe
Ya fice tana sa masa albarka
Yana fita hajia asiya ta kira nafi a waya tana
dauka tai mata tatas
Sannan taja mata kunne sosai abin yaima nafi
ciwo matuqa
Kuma tanaji in sama da qasa zasu hadu to saita
aurar da afnan ga janer
Don haka qawarta ta kira hajia sury tai kuwa sa,a
tana zaman jiran natane don haka ko mintina
ashirin bataiba ta isa gidan nata
Cike ga qaguwa nafin ta tari qawar tata dan ko
ruwa batashaba ta fara zayyane mata
Abinda ke faruwa gameda hadin da aleeyu keson
yaima afnan da adnan
Tace na rasa mafita wlh dan iskan yaronnan so
nake Naga bayansa
Abin yaci tura nabama shajini shi yafi sau goma
yaqi karbarsa na rasa meye dalili
So nake Naga Bayan yaronnan hajiya sury duk
rintsi
Koda zan rabu da aleeyu saina aurar da afnan ga
janar
Sury tace haka nakeso qawata amman bawai ace
ki liqema wani jarababben aureba
Yanata whlr dake sai kace shine autan maza
Dubi yaddah ya maidake a cikinmu sai kace duk
kin girme mana
Kodayaushe kina kudundune cikin tafka tafkan
kyalulluwa
Sai kace wata matar malam fitama wannan sai
kiyi sati biyu baki leqa wajeba
Haka escote dinki kecin kudinki a banza duk
qarshen wata shi kuwa yana waje
Yana holewarsa
Ya zubeki a gida ke baki da wani yancin kanki sai
abinda ya tsara miki
Sai kace shine yai miki dakon cikin wata tara
kuma yai miki nakudarsa
Wlh ina baki shawara a wannan karan karki bari
aleeyu yai galaba akanki
Karki bari yaga bayanki saidai ke kiga bayansa
Nafi tace ta wace hanya sury?
Banida Wanda zai goyamin baya Hatta mommy
nan ta kirani taimin
Tatas shin ta ina zan bullo
Sury tace mai yasa ba zaki kawar da duk Wanda
zai kawo miki cikas ba
Nafi tace ta yaya sury tace saifa kin runtse idonki
kuma kin cire dan sauran raguwar imaninan dake
cikin ranki dan na tabbata in janar ya auri afnan
Saikin zama wata tauraruwa a idon duniya
Cikin yanayin tsoro nafi tace to ta wacce hanya?
Oho nima ban saniba mu hadu maybe anjima idan
na samu tyme Danjin ci gaba
Inama Kowa da Kowa barka da sallah
Sai naxo amsar barka da sallah na
Aure. Kan. Aure. Book2
Chapter 15
Nafin tace ta yaya? Sury ta qara gyara zama tace
Indai kina qarqashin ikon
Aleeyu. Baqin ciki bazai barshi ya barkiba don
haka saiki shafama idanunki
Toka tun a wannan karan ki bijirema buqatarsa
Ki tadamasa hankali ki birkita masa kwakwalwa
nina
Gaya miki da kansa zai saduda ya dawo yana
binki gwiwa biBbiyu
Kuma karki sake sauraronsa kici gaba da
harkokinki kawai
Kin manta munada iyayen qarya ne.? Don momyn
ki taqi goya miki baya
Ki sanarma janar daya turo iyayensa nida kaina
zan samarma afnan waliyyai tare da masu daura
mata auren
Qawata kibama yarki Wanda kikeso Tunda babu
Wanda yai miki
Naqudarta kekikasha wahalarta ke kadai
Ana daura auren na tabbata da kansu zasu dawo
su biki dan nasan aidai ba
Zasuyi mata aure kan aureba
Nafi tace lallai na yarda da shawararki qawata
Amman da harna fara Tunanin yaddah zan
maidama janar makudan kudin
Daya turomin tare da kyautar wani katafaren
kamfani
Da yaimin
Tace kinjifa qawata amman yarinya take neman
janyo mana tsiya
Sury tace h to inma kika tsaya sanya to ke kikaso
Tace a,a ai banga ta zamaba yanxu
Zan kirasa nace ya turo iyayensa cikin satinnan
Ki gama tsara mana komai yaddah zai kasance
tace to an gama
Yammah likis adnan ya dawo daga aiki ya duba
baiga afnan ba
Don haka ya wuce Bangaren baba hauwa
Anan ya sameta sunata Hira Shima ya zauna
yana fadan
Ya gaji da yawa baba hauwa baki rage dan
burabuskon nan da kikeba?
Tace babu saidai dambun masara da wata
qawata ta kawomin daxun
Akwai ragowansa daman afnan na rage mawa
Ya miqe yana fadan lallai kam
Baba hauwa wasama kike yar taki da ko sannu
da zuwa idan mai gidan nata ya dawo bakiyiba
Nidai ki fadamata bugu nake dan yarinyama ta
sani tun yanxu
Baba hauwa tace ba wannan maganarba yarinya
tun rana tana kichin tana Maka
Hidima shine yanxu ka dawo ko sannu da gida
babu ballentana har ta kawo Maka
Delisions din data hada maka?
Yace aina qoshi baba hauwa bari taci nata ni naci
dambun
Wani takaicine ya kule afnan din tace wato
abincin da ta bata lokaci tun rana
Take masa dan tasan shi yafi so shine zai
kwaleta a gaban baba hauwa
Tace ai nasan laggonsa don haka ta miqe
Da sauri ta warce kwanon dake niyyar surewan
cike da batsewa
Ya kalleta
To kawo ko malama tai shiru
Au ba zakiban ba? Allah na kwaso yunwa a office
dan Allah kiban
Ganin bata da niyyar bashi hakan yasa ya warce
kwanon
Saidai mezai gani wayam babu komai a ciki
Da sauri ya dubi baba hauwa tace au na
Manta ashe fa ta cinye
Yadan sosa qeya yace daman baci zanba
tsokanarki nake
Kawomin abinda kika girka min
Ta zaro ido wa? Lallaima wasa kake
Ya marairaice yana fadar haba qanwata ai nasan
ba zakibar yayanki ya wuni da
Yunwa ba
Shiyasa kike birgeni tambayima baba hauwa inba
girkinkiba babu girkin dakemin
Test a baki
Ta karkace kai tace kayi ka gama ni kagama
tafiyata
Da gudu ya bita ta shge falonta ta boye a Bayan
kyare yaita dube dube
Amman bai gantaba
Can ya hango qafarta yai saurin yaya labulen ta
daka qara ya qarasa wajenta
Yana fadin am sorry my love yunwa nakeji karna
mutu
Da sauri tace to tsaya na kawo maka
Tai saurin ficewa daidai bakin koqar taci karo da
mom din nata hajia nafi
Gabantane yai mummunan faduwa ta babbake
qofar muryarta na rawa ta
Fara fadin
Sannu momcy da qafafunki aida aikowa kikai
naxo da kaina
Tace keda baki zuwa aini nazo
Muna cikin gida guda amman saina wuni ban saki
a ido ba
Tunda kikaga ina miki fadan ki rabu da wannan
dan iskan matsiyacin yaron
Sbd baida komai ne me ya mallaka da har zai iya
riqeki?
Banson yaron nan afnan ban qaunarki
Tun yana yaronsa ba yaron kirki bane
Afnan data lura adnan na jiyo maganar nasu sai
taji wani iri ta
Riqo hannun mommyn nata tace
Muje Momy daman wajenki zani
Tace naqi tafiyar baqar munafuka yanxu haka
yana cikin Dakin naki
Fadamin abinda yake baki da kike wannan
maqalqale masan?
Ta zumburo baki tana haba mommy dan Allah ki
daina haka
Taja hannunta suka wuce zuciyata sai rawa take
Daqar ta samu ta jata sukabar wajen Bayan sun
isa Bangaren momcyn natama
Daqar ta samu ta kubce tanata hanzarin shga
kichin domin
Hado masa abincin ta dauko ta wuto falon nata
bayanan ta aje ta nufi
Nasa falon nanma bayanan
Don haka ta nufi falon baba hauwa nanma
bayanan
Jikinta a sanyaye ta dawo falonta duk duniyar tai
mata zafi
Yanxu taya zata bulloma wannan lamarin?
Ta dauko wayarta ta kirashi harya tsinke bai
dauka ba
Dole tasama zuciyata sa,ida saidai wunin wannan
ranar haka tayishi babu walwala
Bayan tayi sallar magrib da isha,i ta fito falon
dake tsakanin nata da nashi ta
Zauna. Burinta taga ta inda zai bullo amman tafi
minti talatin bashi babu dalilinsa
Ta gaji ta miqe ta nufi sashin baba hauwa
Acan sukaci gaba da Hira saidai rabin hankalinsa
nakan adnan
Tara daidai Barci ya soma cin qarfinta don haka
ta miqe ta nufi
Dakinsa har lokacin a rufe yake
Zuciyata a dagule ta nufi Dakinta ta jame kayan
Jikinta ta fada toilet
Ta watso ruwa ta rigar baccinta ta saka
Ta haye saman gadonta saidai barcin yaqi zuwa
gani take kamar
Adnan zaizo gareta har qarfe sha daya shiru
Batasan lokacinda Barci ya sureta ba
Tawon wani lokaci taji tamkar tsayuwar mutun
akanta
Ta bude idanun nata ba mafarki takeba adnan
dinne tsaye akanta
Ta yunkura da sauri tana kallonsa
Jikinsa a mace ya zauna a bakin gadon
Lallai ba mafarki takeba adnan ne dagashi sai
gajeran wando da singileti
Tai saurin maida kallonta kan agogon dake Dakin
taga biyu da Wasu yan mintina
Tace a ranta to lfy?
Ya riqo hannunta yace afnan yanxu momynki ta
kirani wai bakida lfy
Rai a hannun Allah naxo. Na kidime afnan bansan
lokacin Dana iso nanba
To amman sai na ganki kwance kina Barci afnan
nidai inada yaqinin ba mafarki
Naiba. Wai kona haukacene?
Tambayar da basu da amsarta
Kuriy kawai tai masa da idanu
Adaidai lokacinda momcy ta shigo Dakin ita da
abban nasu
Suka maida kallonsu kansu
Mumcy tace to yau ka gani da idanunka abinda
nake fada Maka kana fadin ba
Gaskia bane yanxu me idanunka suka gane
maka?
Abban nasu baice komaiba saidai wani sashin na
zuciyarsa data shiga nazari
Mumcy taikan adnan da duka tana ihu
Wayyo alllah na bani na lalace dan iska ya
batamin rayuwar yarinya
Allah ya isa tsakanina dakai
Kuma wlh sai munyi shari,a dakai
Tsabar mamaki da firgici ya hana adnan koda
lwallwaran motsi
Ballentana ya kare kansa daga dukan da take
masa da kuma
Sharrin datai masa
Afnan tai saurin saukowa daga kan gadon ta
rirriqe mom din nnata tace
Ki bari dan Allah mommy karki tara mana jama,a
Yatsu biyar ta cire cikin fushi ta dauketa da mari
Afnan ta riqe kuncin nata lokacinda Wasu hawaye
masu zafi zuka ziyarci kuncin
Nata ta koma kan adnan din da duka tako ina
Abban saif ya tako gabanta ya riqeta ta juyo tana
kallonsa
Idanunta na zubar da kwalla cikin kuka tace
Ka sakeni Abban afnan wallahi sai Naga Bayan
yaronnan
Harmu zai batama sunan gidannan ya keta mana
haddin yarinya
Har cikin gida?
Saita qara fashewa da kuka kunji munafuka lol
Aleeyu yace ya isa haka nafi shirin film din ya isa
haka ai Kinyi koqari
Ya kamo adnan dake duqe ya jashi suka barta
nan tsaye
Binsu ta dingayi da wani irin kalllo mai cike da
tsana.
Lokaci guda kuma ta dawo da kallonta kan afnan
din tace
Lallai yayi kyau afnan zaki debo ruwan dafa kanki
Dan na rantse da Allah saidai Naga bayanku
badai ku kuga bayana ba
Duk rintsi koda kuwa zanyi yawo tsirarane saina
wargaza wannan shrin naku
Da In wayi gari inga aurenki da yaronnan wallahi
gwara ace kena rasa gaba daya
Samun duniya ya fimin komai a aruwa
Daga yau zan cire tausayina akanki
Zan aiwatar miki da irin rayuwar da kika zabama
kanki
Koda hakan na nufin rasaki keda ubankine
Na rantse da Allah zanyi abinda na Dade ina
zullumin yi a baya inhar kika bijiremin
Hmmm meye wannan Abun sai mun hadu a nxt
chapter
Aure. Kan. Aure
Chapter16
Ta juya a fusace ta fice cikin kunar zuciya
Hankalin afnan yai mummunan tashi ta shga
tsoro da fargaba mai rikitarwa
Sai a yanxu take fahimtar shin wacece
mahaifiyarta data haifeta.
Lallai macace. Mai zuciyar rashin imani wacce so
ko tausayi baisa ta
Rasa duniyarta toya kenan?
Ko alama Barci ya qauracema idanunta. Fargaba
da zullumi sune
Suka jagoranci zuciyar tata
Aleeyu na zaune cikin katafaren falonsa a cikin
daya daga cikin kujerun alfarman dake dakin
Ruwan tea yake kurba ba tare da yasa madaraba
duk kuwa da kayan
Soye soyen da aka zagayshi dashi abinda ya faru
daren jiya shine kawai ya tsaya masa a rai har
ya hanashi sukuni
Shin wai shi da wacce irin makirar mace yake
rayuwa ne?
Mai kwadayi marar tawakkali?
Tamkar an hankadota ta banko falon ta shgo
Kofar ta koma da kanta ta rufe tare da wata
gaggarumar qara
Hakan ya dauki Hankalin haj aleeyu ya bita da
zara zaran idanunsa harta iso gabansa
Lafiya Tambayar da yai mata kenan cikin Ruwan
sanyi
Cike da batsewa tace lfyr ce ta kawoni
Tace aleeyu Tunda Naga alamun baka da niyyar
kwatarma yata
Yancinta Akan zaluncin da dan uwan yai mata
toni
Zan dauki irin nawa matakin
Kai har kaine jia zakafadamin shirin film din ya
isa haka
To ka sani wasanma yanxu aka fara
Yaja wani salihin murmushi yana kallonta yace
Da fatan dai kin taNaji manyan yan wasa ko dan
kinfi Kowa sanin da
Babban jarumi zaki kara
Taja tsaki tace Aikai zan fadama haka da fatan
kana cikin shirin yin yaqi da shaidan
Na rantse matuqar ina raye sai afnan ta auri
janar
Saidai in bana numfashi ta juya a fusace tabar
falon
Wani taqaitaccen murmushi Yaja yaci gaba da
kurbar Ruwan tea dinsa hankalinsa a kwance
Tunda afnan tai sallah daqar ta samu wani
gajeran Barci ya dauketa
Wanda batafi minti talatin cikinsaba ta farka
Haryanxu Jikinta a mace yake ta watso ruwa ta
sanya wata shaddah milk colour
Sashin babanta ta nufa yana kishin gide fuskarsa
sanye da farin gilashi
Yana karanta jarida
Aje jaridar yayi ya tashi zaune yace lfy lau afnan
kin tashi lfy?
Ta daga masa kai alamar eh
Ya dafa kanta yace kiyi haquri kinji yata
Ki zamo diya ta gari mai daukar qaddarar da
Allah ya daura masa
Nasan ban miki adalciba na rashin zaba miki uwa
ta gariba
Kamar yaddah manzon Allah yace ku zabama
yayanku uwa ta gari
Na rantse miki ban biyema zuciyataba wajen
zaben macen data cancanta ta zame miki uwa ba
Qaddara ce daga Allah nasan mahaifiyarki na
biybiyarki da sharri
Domin janar Kowa ya sanshi yasan wayeshi
Babu iyayen kwarai da zasu yarda su bashi aurar
yarsu
Dukkan wani laifi da kika sani janar nayinsa
sannan wannan janar din da kika
Gani yayi riddah
Yabar addinin musulunci gabadaya dan yanxu
Dukkan dabi_unsa basa kama Dana. Musulunci
Taya zan Bama wannan mutu yata
Yace ki kwantar da hankalinki afnan babu mai
miki auren dole
Kuma Dukkan mai sharrin mai sharri zai koma
kansa
Don Allah na tare damu
Ki kwantar da hankalinki kinji afnan?
Cikin sanyin jiki tace to abba
Kwance take kan makeken gadonta tana dudduba
littafanta
Na makaranTa kasancewar jarabawa ya qarato
Wayartace tai ruri tana dubawa taga momcynta
ce
Saida hantar cikinta ta kada ta dauka a tsorace
tace
Hello mommy
Kixo ki sameni a sashina abinda ta fada kenan ta
kashe wayar
Ta tashi da sauri ta dauki dan kwalin les din dake
Jikinta ta fita
Hajia nafi na ganinta taja dogon murmushi. Tace
gani mommy
Tace ba wani matsala bane kije bafon da nake
saukar baqi
Baqonki nanan yana jiranki zaku tattauna
Tace ki nutsu kije ku fahimci juna inkin samanma
kanki
Sauqi kenan in kuma kikaga dama kije kiyi masa
wulaqanci
Ki nuna masa bakisonsa
Aure dai keda shi Kamar anyi an gama ne
Don wlh ko mutuwa kikai sai nakai gawarki gidan
janar
Don banga mahalukin daya isa ya hana hauranki
da janar ba
Don harya turo da kudin aurensa da zaran kin
gama service dinki za,a
Daura auren
Ji tai tamkar ta watsa mata wuta a fuska ba
yaddah ta iya
Hajia nafi taja hannunta suka nufi sashin da take
saukar baqin
Tamkar wancan zuwan. Sojojine a gidan ta ko ina
suna tsatsetsare tako ina
Tun daga bakin gate har zuwa falukan nasu
baqiqqirin dasu sai jajayen idanu
Tana kaita bakin qofar ta juya abinta afnan tai
tsaye aranta tace shin najene kona juya
Tambayar dataima kanta kenan da batada
wannan amsar
Tamkar wacce aka hankada ta fada falon
zuciyata cike da takaici
Ya hakince kan daya daga cikin kujerun alfarman
dake falon kai kace
Wani basarakene ko jinin sarauta
Kallon tsana take masa yanxu tafijin tsanarsa
maganganun abbanta na dawo mata
Tamkar yanxu yake furta mata su
Janar Kowa ya sansa yasan wayeshi babu iyayen
kwarai da zasu yarda su aura masa yarsu
Da hannu ya nuna mata kujerar dake fuskantarsa
alamun ta zauna kafada ta fada masa. Tace ko
daya bawai zamane ya kawoni gareka ba
Illa na gargadeka a karo na karshe daka fita
harkata
Na fada Maka bana sonka da akwai Wanda
nakeso shin wai ana so dole ne?
Yaja wani katsaitaccen murmushi kafin yace yaro
yarone
Afnan zanso ki zauna ki natsu ki bude zuciyarki.
Ki karbi sakon da nazo miki
Dashi. Wanda zai zamo miki alkhairi keda
iyayenki
Ta zaro ido waje tace wane irin alkhairi ne har
kai kake dashi janar iye?
Koko zakai mana tayin kafurcin ne?
Yasa hannu ya shafi gemunsa Wanda yake a aske
ya kada kafadunsa kamin yace
A maganata dake babu batun tayin addini kuma
koda na aureki bance dole saikinbar addininki kin
dawo nawa ba Kowa da ra,ayinsa amman ta yaya
Kikasan wannan boyayyen sirrin da babu Wanda
ya sanshi illa makusantana?
Ta girgiza kai tace karkai mamakin makusancin
Naka shine ya fadamin
Amman me yasa kake tsoron kar duniya ta
fahimci addinin da kake?
Da alamun kaima kanka baka yaddah da addinin
nakaba kenan ko?
Yace ko daya illa inason inyi amfani da sunan
musuluncinne na
In bata musuluncin kuma in hallaka musulmai a
duk inda suke
Ina fatan ai kin gane. Tace tirr da wannan
mummunan Tunanin Naka
Shine a haukarka har kake Tunanin ni zan iya
auranka?
Lallai kayi wauta a duniya dan bani da abin tsana
kamarka ka fita
Harkata pasto
Don kuwa babu ni babu kai in kuwa kaqi zan
fassalawa duniya Kowa yasan
Aqidarka
Wata dariya ya shigayi harda kyalkyalawa kamin
ya nunata da hannu
Yace ashe Kinyi hauka kenan yarinya ai in zaki
rantse da abinda yafi komai daukaka babu Wanda
zai saurareki balle ya yarda dake
Duk juma,a sai naje masallaci. Idi kuwa na
qaramar sallah da babbah basa wuceni duk kuwa
da bayi nakeba
Gashi tun daga kan kakan kakana har izuwa
iyayena duk musulmai ne
Kuma babu Wanda ya taba auro wata qabilama
balle wacce ba musulma ba
Ashe kenan baki da tudun dafawa yar budurwa
Tace bandashi amman zan hadaka da Wanda
baya barci
Ballantana kyankyadi
Kuma ni hafsa afnan saidai idan gawata za,a kai
gidanka
Ya miqe tsaye yana fuskantarta yace kece ke za,a
kawo gidana afnan
Alokacinne zaki banbance kida da karatu
Nai miki rantsuwa sai na mayar dake abin tausayi
Wannan hukuncin na duk Wanda ya bijireminne
Sannan kada ki manta uwarki hajia nafi a
hannuna take
Bata da buri illa duniya ni kuma zan mallaka
mata duniya a hannunta
A yayin data faracin duniyar zan kwace komai
daga hannunta na rantse miki
Ni janar. A aminu saina mayar da mahaifiyarki
mabaraciya a cikin gari
Sannan yai mata murmushi mugunta ya juya ya
fice abinsa
Ya barta da fargaba tareda faduwar gaba
Taja qafafunta har sashin momcynta
Tana ganinta ta shigo tai saurin tarbanta
Tace yauwa yata kokefa harya tafi?
Afnan ta kalleta da jajayen idanunta muryarta na
rawa tace
Ya tafi Momy amman wlh bada alkhairi yake
binmu ba
Burinsa yai mana lalata yai mana gadar zare
Muna hawa ta rufa damu
Mommy wlh irn maganganun.....
Da wata gigitacciyar mari ta tsayar da ita har sai
dataga wuta
Dagata tace da ita munafuka kawai yanason yaga
bayanmu ko kinason kiga bayana
Waike ni zakiyima wayau to tun kafin a haifeki
nasan wannan
Afnan wlh da nasan zan rainaki ki girma daga
baya ki dinga bijirema umarnina da wlh tuni na
badake cikin firgici afnan din tace dakin badani
gawa?
Aure. Kan. Aure
Chapter17
Ita kanta momyn nata tasan taso ta kira ruwa
Cikin tsawa tace ficemin da gani tun kafin raina
ya gama baci
Kasa cewa komai tai saima juyawa da tai tabar
falon
Ga wani ciwon kai daya adddabeta Kamar kan
nata zai rabe
Adnan bai dawo gida yauba sai Bayan sallar
magrib kasancewar patient sun masa
Yawa yana dawowa sashinsa ya wuce ya watso
ruwa gamida
Canja kayan jikinsa
Sannan ya soma tattara yan tarkacensa
Tamkar yaddah abban nasa ya umarcesa
Afnan na ganin shigowarsa tai saurin qarsa
abinda take ta nufi Bangaren nasa
Yana tsugunne yana rufe jib din jakar nasa
ganinta da yai Kamar daga sama yasa
Ya miqe ya karasa gabanta. Yace afnan wlh nayi
mising dinki
Yau gaba daya ban gankiba yahan yasa wlh
nakejina tamkar wani maraya
Yini dayafa kenan afnan inaga kuma an hanani ke
gaba daya?
Wlh da bazan san halinda zan shigaba ya qara
matsawa kusa da ita
Muryarsa na rawa yace afnan babban burina a
rayuwa bai wuce ace yau mun wayi gari
amatsayin ango da amarya ba
Inhar wannan burin nawa ya cika to banida wani
sauran buri a rayuwa
Dan Allah afnan duk runtsi karki juyamin baya duk
da nasan mommy batason abin
Amman inhar taga kinasona da gaske tazata
amince ta rungumeni a
Matsayin sirikinta
Ni kuma sai nabama marada kunya sai anyi
alfahari da auren mu
Na rantse miki zaki sameni miji na gari mai
tattalin iyalansa
Wanda zai iya bada rayuwarsa dukiyarsa jikinsa
karfinsa akansu
Har abada bazanci amanarkiba duk runtsi karki
kujeni ni kuma duk tsanani ina
Tare dake
Afnan tace karka damu yaya adnan insha allahu
zaka sameni mai sadaukarwa akanka
Dan nidin da kake gani daman anyinine dominka
Mai gidana raina fansane a gareka jikina da jinina
duk nakane
Motsina da tunanina duk Nason ganin biyan
buqatunka ne
Yaya adnan I luve u
Farin cikin da yake alokacin bazai misultu ba
Ya rataya jakar tasa gamida cewa daddy tace
Na koma sbn gidan daya gida nama da zama
kafin bikinmu dan an rage bikin nanda wata daya
da zarar kin kammala service dinki
Don haka kinga ai yanada kyau naje naci gaba da
gyare gyaren gidan da amaryata zata tare ko?
Ta daga masa kai alamar eh
Saida ta liqe masa har sabon gidan nasu ta
rakashi
Gidan ba wani babba bane saidai ginin gidan da
tsarinsa ya tafi da hankalinta
Ji take tamkar a barta a ciki ta zauna ta gyara
masa ko ina na gidan sannan ya daulota ya dawo
da ita gida
Bayan ya kaitan sashin baba hauwa suka wuce
sukasha Hira sosai
Sannan ya koma sabon gidan cike da kewarta
Afnan jarabawa tadau zafi. Jarabawar kammala
Makarantar nata don
Haka ta cire tunani da zullumin komai ta maida
hankalin nata kan jarabawar
Cikin ikon Allah ta kammala jarabawar tata duk
Tabi ta rame Sbd janar ya matsa mata lamba
Duk da Shima idan tai masan ba kanwar lasa
bane
Gashi adnan Allah ya daura masa zafin kishin
tsiya duk Tabi ta damu don haka
Ta sami abbanta ta sanar dashi yai mamakin
yaddah nafi ke kawo masa
Qato cikin gida ba tare da izninsa ba
Zuciyarsa ta baci yace taje kawai zai dau mataki
Baiyi niyyar tanka ma nafinba yayi niyyar barinta
da halinta saidai hakan bai samuba don Washe
gari misalin qarfe hudu na yammah littafin babba
a hannunsa yana dubawa
Hajia nafi ta fito sanye da wata Riga da siket
damammu sun kama Jikinta har sashin pnt dinta
ana gani ta daura wani yalolon gyale
Ta daura wata qatuwar jakarta saman kafadarta
Hannunta guda kuma nna riqe da Baqin gilashinta
da. Key din mota
Wanni irin kallo mai cike da zargi aleeyu ya bita
dashi
Ganin tana niyyar ficewa yasa ya tsaidata ta
kiran sunanta da kakkausar murya
Nafi!!
Ta waigo a slow tana kallonsa kamin tace yadai?
Tambayar rainin hankali amman saiya dake ya
jefa mata tambaya
Da izininwa zaki fita?
Taja wani murmushi rainin hankali tace kamarya?
Har wani izinin wani zan Nema idan zan fita?
Ina Tunanin Kamar ka manta da yar boko ka aura
ba yar tallar furaba ko?
Yace ai gara jahilima dake dan kuwa shi ansan
rashin sanine ke kuwa fa?
Kokuwa kin manta da kedin ajeki akai ba zaman
kanki kike ba?
Tace ai duk daya wai ancema makaho ga fitila
Saidai inason sanar dakai da na gaji da zaman
rashin yanci da takurane shiyasa
Da fatan ka fahimta?
Don haka nakeso na rayu a yaddah nakeso kuma
nayi yaddah nakeso
A cikin gidana
Yace ahh wannan ne baki isaba Indai har kina
qarqashin ikon Aleeyu ne
Toki sani Kinci qarya kin kwanta da yunwa
wannan kalar iskancin ba!a gidan aleeyu ba
Taja wani tsaki tace to saika sauwaqema kanka
inhar kana nunanin kanada wani ikone
Ta juya ta fice ta barshi sake da baki
Yinin yau yaima afnan dadi musamman yaddah
suketa shirye shiryen bikinsu ita da adnan
Don sauran sati guda daurin auren
Adnan ya gama buga iv Wanda zata rarrabama
qawayenta don haka tun safe
Ya dauketa ya dinga zagayawa da ita wajan
qawayenta tana rarraba musu
Sai yamma likis suka nufo hanyar gida bawai don
sun gamaba sai don gajiyar da sukai
Gidansa suka nufa sukai sallah ya tayata suka
gyara gidan sanna suka shga kichin
Tare babu Wasu kayan abinci a kichin din daga
indomi sai kwai da conplex
Tare da kayan tea
Ta kalleshi tace kai yaya adnan wannan sune
kayan abincin?
Ya lankwabe kai yace toya na iya afnan daga
dafa indomi sai soya dankali da hada tea na iya
bandasu ban iya kirka komai ba
Yaddah yake maganar har saidaya bata tausayi
Yace amman in munyi aure zaki koyamin ko?
Yaddah in mun samu baby's *n dinga shga kichin
ina dafo muku ko?
Lumtse idanunta kawai tayi ba tare datace
komaiba da sauri yasha gabanta yace
Dubeninan afnan idan munyi aure yaya nawa zaki
haifamin?
Kinga nidai inason yaya dan Allah zaki fara da
bibbiyune ko uku uku
Wani irin kunyane suka rufeta nanta hadamasa
abinci mai raida lfy
Bayan sunci sun koshi ya dauketa ya maidata
gida ya dawo nasa gidan
Cikin dare adnan yana kwance
Bai Dade da gama waya da afnan ba Barci ya
sureshi mai nauyi
Kamar cikin mafarki adnan yaji ana tashinsa daga
nannauyan barcin daya
Sureshi
Kamar inuwar mutanene suka zagayshi yai saurin
bude idanunsa ashe kuwa ba
Mafarki yakeba
Ya tashi zaune cikin inda inda yace. La...la...fiya
malamai? Meya kawoku nan?
Kaya daga cikinsu yace kwantar da hankalinta
dan samari
Babu abinda mukaxo yin Maka saidai baka
umarni
Cikin dakiya irinta jaruman maza adnan din yace
to amman mai
Yasa bakuxo da ranaaba sai da dare?
Yace sha kuruminka dan samari. Zamu hada
makane da gargadi
Nasan kasan afnan yar gidan Alhaji aleeyu ko?
Adnan din yace eh nasanta yace yauwa dan gari
Kumaa kasan Waye ke sonta uban gidanmu genar
abdullahi aminu aabbah ko?
Yace tabbas na sanshi
Mutumin ya girgiza kai yace amman yaro kayi
ganganci wajen wasa da rayuwarka
Ai saida raine kai takara da Wanda zai iya
ajalinka ba tare da wani ya sake tuna sunankaba
Adnan din yake kai kuma ka manta da ba,a kaina
aka fara sadaukar da rai Akan soyayyah ba?
Dan maatashin mutumin yai murmushi sannan ya
kalli sauran Wanda suke tare dashi din sai kace
masu tsaron mai layar zana
Yace lallai yaronekai adnan kake ko? To inaso da
in gargadeka daka fita
Harkar oga inba hakaba to wlh lahira zatai baqo
Umarnine wannan ba shawara ba inkuwa kaqiji...
Ya zaro wata sharbebiyar wuqa daga kugunsa
Ya daura a wuyar adnan din yace Kaga wuqarnan
da umarnin mahaifiyar afnan
Zamubianbi da tuni na raba kanka da gangan
jikinka
So da yake daqiqiyace batada tunani shiyasa
oganmu yace
Mu fara Maka da gargadi inkaqiji to saimu aikata
Maka
Dan wlh saina raba kanka da gangar jikinka
Don haka shawara ya rage gareka dan samari ya
cire wuqar daga wuyar tashi yai
Gaba suka rufa masa baya
Hmmm adnan dai ya shga tsaka mai wuya
Janar da nfi sun fara tsoratashi ya abin yake
Muje zuwa Danjin shin ya abin zai kasance
Aure. Kan aure
Chapter 18
Adnan ya shga tsananin tsoro da rudani
Daidai da dan tsarsa ya kasa motsawa har aka
kira sallar asalatu
Saida ya jiyo ana kabbara a Wasu gurare sannan
ya miqe daqar yayo sallar
Bayan ya gama ya dinga rogon Allah daya cire
masa tsoro yasa masa
Dakiya Akan duk wata barazana da za,ai masa
Ya Dade yana Koro addu,o,i sannan ya shafa yaci
gaba da lazimi
Gari na gamayin haske ya miqe ya suri makullin
motarsa yabar gidan
Alhaji aleeyu na tsaye inda motocinsa suke
Anata faman gogewa masu tsaron lfyrsa wato
escote dinsa suna
Tsaytsaye da alamar wata tafiyace ta taso masa
Adnan ya faka motarsa ya fito
Da sauri ya nufi inda abban nasa yake yai saurin
duqawa yana gaidashi
Yace ina kwana daddy yace lfy lau adnan wannan
sammako haka ko duk na zumudin ganin iyali ne?
Adnan yai murmushi yana Susan keya yace
Wlh abbah jiya ban runtsaba Wasu mutanene
suka shgomin
Saidai sun sanar dani wai aikene daga janar
Sun tsoratani sosai
Abban nasa yadanyi shuru nadan wani lokaci
kamin yace kai yanxu ya kake ganin
Zamu bulloma lamarin?
Adnan din yace Abba janar nada mummunan
hatsari a garemu shiyasama na
Baro gidan
Nidai nan zan zauna
Abban nasa sai murmushi yace
Adnan ka zamo jarumi mana dakakken namiji
wannan ne zaisa janar
Ya kasa galaba akanka
Yace amman Tunda harka tsorata to zan tura
securitie uku gidan
Tunda daman babu mai gadi a gidan
Sannan ka shirya yanxu kaida afnan
Direba ya daukeku ya kaiku can kauye dan acan
za,ai sha,anin bikin naku
Da zarar an daura auren zakuwuce hajj Bayan
aikin hajj daku sai ku wuce qasashe biyar duk
Wanda kuka zaba kumin magana dan na gama
shirya komai
Ciki wata bakwai kawai zaku gama honny moon
din naku ku zdawo Sbd tafiyar afnan
Din bautar qasarta
Kaga kenan lokacin da zaku dawo komai ya wuce
farin ciki fal a fuskar adnan
Yace mun gode abbah Allah ya saka da alkhairi
kuma ya qara girma yai murmushi yace
Ka shiga ku gama shiryawa ku wuce nima abuja
zan wuce. Daganan
Insha allahu zan wuce can musawan nanda jibi
Adnan ya shga godia sai dayaga shgar abban
nasu mota sannan ya juya ya shga cikin gidan
Cikin zumudi a falonta ya sameta ttanata
harhada kayanta
Ya lallaba ya rufe mata ido daria tayi lokacin data
shaqi kamshin turarensa
Afnan din tace naso ace nine na fara Maka
wannan albishir din shiyasama na
Hana Abba ya fada Maka tun jia
Zagayowa yai gabanta ya zauna irinn zaman cin
tuwo
Ya tallabe kumatunsa da hannunsa yana
Kallonta itama kallon nasa take
Saidai ba zata jure kallon tsakiyar idanunsaba
dan kwarjinin nasa yai mata yawa
Ta saukar da kanta qasa tana wasa da yan
yatsunta
Cikin sanyayyar murya yake kiran sunanta
Afnan
Ta kasa koda kwakkwaran motsi ballet ta dago
ta kallesa
Bai tsayaba yaci gabada
Afnan I always want to be with u
Kallon fuskarki kawai kan sani cikin nishadi
inason akoda yaushe
Na dinga kallon fuskarki
Wlh afnan idan na rasaki zan iya mutu...
Tasa hannu ta rufe masa bakin nasa tace yaya
afnan
Babu abinda zaisa ka rasani
Ya girgiza kai alamun baison furta mata abinda
zai tada mata da
Hankali
Idanunta suka ciko da kwalla tace yaya adnan
kainefa kake qaramin qarfin kwiwa Akan
soyayyarmu kodai ka fara sanyine?
Da sauri ya dago yana. Kallonta cikin tashin
hankali
Yace haba afnan kinfi Kowa sanin alqawarinmu
Akan soyayyarmu wuya ko daddy bazai tabasa
daya ya rabu da daya ba
Ko kina zaton da akwai abinda zaisa mu rabune?
Da akwaishi dan kaza kaza ta bankada masa
wani bamagujen zagi
Kole ku rabu ya zame Maka wajibi ka barta Indai
har ina numfashi
Ta wargaxa musu. Iv dan dake hannunta suka
baje a gabansu
Cikin tashin hankali afnan ta dauka tana dubawa
Yayinda shi kuma adnan din bai daukaba saidai
ya karanta wadanda suka
Zubo jikinsa
Ba komai bane illah na daurin auren afnan da
janar jibi alhamis
Dukkansu sun shiga rudu dan nasu daurin auren
Asabar akasashi. Hajia nafi taja murmushi kamin
tace
Wannan kenan adnan. Ka saurari sauran
sakamakon ja dani dan tabbasa
Sai Naga bayanka kaida uban riqon naka
Cikin tashin hankali afnan din ta tashi ta rirriqe
mom din nata tana kuka tace
Kiyi haquri dan Allah momcy wlh bazamu taba iya
rayuwa idan Bama tareba
Kuma Wanda kike qoqarin hadani dashi dinfa ba
musulmi bane bafa
Da bakinsa yacemin yayi riddah momcy meye
hukuncin auratayyah
Da a matsayin na musulma?
Tas tsa ta dauketa da Marin da saidata kifa
sannan ta nunata da dan yatsa
Ki hankali dani na rantse miki domin yanxu na
janye wata alaqa ta haihuwa tsakanin nidake.
Zan iya miki duk wata azaba da zan iyama
maqiyina
Ban dauki duniya da wasaba dan wlh zan iya
badake Akan duniyar
Don haka ki guji wani yinkuri da kikasan zai iya
wargazamin shiri inkuwa kinqi
Ta murza yatsun ha Sukai qara ta juya tace
wannan kuma da yake gabanki
Ban tatasa domin nanda Wasu yan awanni an
fara wantawa da tarihinsa
Ta fice abinta
Maganar momcy ta qarshe itace tafi dagama
afnan hankali
Afnan ta dafa kai tana shirin kwalla wata kururwa
Yai saurin riqeta Yaja hannunta a hanzarce
Yace zo muje afnan wannan lokacin ba lokacin
kuka bane
Ta jari jakarta suka fice a guje
Saidai suna isowa inda motar adnan din take
suka soma kallon kallo
Dan kuwa motar sojojine sunfi kala goma
Sai jiniya suke kafin suyi wani motsi har janar ya
fito daga motar dake gaba
Sojoji sunfi talatin suka rufa masa baya
Hannu kawai ya daga musu duk suka tsaya ya
qarsa gabasu afnan da adnan din
Yana wani tafiya irinta isassun mazaje masuji da
mulki
Ya kallesu daya Bayan daya kamin yace
Two starsa ina zuwa haka?
Wai wani murmushi kamin yace badai Kuna
yaudarar kanku bane ta hanyar
Guduwa?
To kuje ina? Kun manta karan battane tsakaninku
da janar?
To kujedin amman inason ku sani duk inda
qafarku ta sauka Akan idon janar ne
Ya dubi adnan yace kyakkyawan saurayi amman
na tausaya Maka ta
Yaddah tsautsayi zaisa ka baqunci lahira da wuri
Mai yasa ka yaudari kanka samari kake qoqarin
mallakar matar datafi qarfin ajinka? Kash.... ya
girgiza kansa
Daka sauya tunanina yaro wataqila daka hango
wata wacce ta
Banbanta da afnan
Cikin kakkausar murya afnan din tace
Dan Allah malam saurara mana ai mijin dayafi
dacewa dani shine adnan
Kamilallaen mutunne kawai zai iya gane hakan
kai ba zaka iya ganewaba Sbd
Bakasan darajar soyayyah ba
To ka sani raba masoyi da masoyiyarsa tsinke
soyayyar gaskia ba abune mai
Sauqiba
Wai wata malalaciyar murmushi kamin yace ni
kuma wannan abune mai
Sauqi a wajene
In naso saina tsinke soyayyah a cikin yan
mintuna
Adnan yace wannanne kuma karyarka Tasha
qarya mai girma janar
Ada nayi Tunanin mutum irinka mai kwargiji da
isa yaro kamata
Ya girgiza Maka tunanina har karasa yaddah
zakai kake min barazana kasheni
Kai lallai na cika namijin mazaje
Shin ka mancene har abada ina manne a zuciyar
afnan wacce riba kake ganin
Zaka samu. Ga macen da kakeson aura alhalin ita
kuma bata da ajiyayyen soyayyar da zata baka?
Janar yai murmushi yace yaro kenan shin ka
mance. A wannan zamanin babu
Abinda kudi ba zasu iya siya makaba?
Koda kuwa dan Adam ne ballentana wata
qaramar alhaki wai ita soyayyah
Adnan yace aiko kudinka ba zasu iya siyan Maka
soyayyah ba dan ko da zasu iya Dasun sai maka
Kuma kudi kan iya siyan dan Adam amman ba
zasu iya siyan zuciyaba
Shiyasama ake samun mayaudara a cikin alumma
har kake yarda da mutum yaxo ya cuceka
Mai girma janar inaso kayada makamanka dan
ina guje maka ranar jin kunya
Randa zakasha kayi wurin dan cikinka
Domin kifin fadama baya gasa Dana gulbi in
bandakaima
Dattijo kamarka inakai ina yarinya kamar afnan
Aiko ba,a kwadaba limzami yafi qarfin bakin kaza
Da alamar ran janar ya fara baci da zantuttukan
adnan don haka ya nunashi dadan yatsa yana
fadar lallai yaro kayi gangancin taran aradu da
ganmo
Tabbas duk Wanda ya shga sabgata na rantse
saina kakkarya kafafunsa
Nasa ya zama mabaraci a a cikin gari
Tabbas saina nuna Maka aikin Jan biro maganin
taqadirin dalibi
Ni janar na rantse sai Naga bayanka bata dadiba.
Na rantse sai kayi
Mutuwa dubu kafin kayi ta gaskiya
Hahahaha ran maza ya baci ya abin yakene karfa
alluran
Manyan mazajen ta tashi mu hadu a nxt chapter
Danjin yaddah
Aure. Kan. Aure
Chapter19
Adnan Yaja hannunta yana ke muje kada wannan
mara aikinyin ya
Bata mana lokaci
Ai mai tsoron a mutu shi yake mata maho
Mu kuwa mun shirya mutuwa Indai Akan
soyayyarmu ne
Suka fada mota adnan Yaja suka barshi anan
zuciyarsa cike da wani irin
Gawurtaccen baqinciki
Ji yake Tunda yake ba!a taba wulaqantashi irin
na yau ba
Don haka dole raine zai zama fansar wannan
facin rain nasa
Ya juya a zafafe ya shga cikin gidan tamkar gidan
ubansa
Hajia nafi tai saurin tarar sa tace saunnu da
zuwa ranka shi dade mu shga
Hannu ya daga mata. Saurara hajia nafi
abubuwafa suna neman lalacewa
Yanxu na hadu da yarannan suna shirin guduwa
kinkuwa san abinda hakan
Ke nufi?
Hajia nafi taja wani gajeran murmushi tace na
sani janar
Afnan da adnan sun tafi qauyen musawane domin
hidiman bikinsu wanda
Za,a daura ranar asabar bazamu hanasuba Sbd
ida shirinmu
Kai ai Kaga Naka ranar alhamis za,a daura. Jibi
kenan
Ana daurawa da kaina zan tura a dauko Maka
amaryarka idan ka shirya
Sai a lokacin janar ya saki wata ajiyar zuciya
kamin yace
Na fasa kisan Yaron nan hajia tabbas Tunda ya
shgo hanyata na rantse sai yayi mutuwa kala
dubu kafin yaita gaskia
Nafin tace wannan ma daidaine ranka ya dade
komai kayi ai girmankane
Yai wani azzalumin murmushi ya jaro Wasu
takardu daga cikin yar qaramar bribcase dinsa
yace
Wannan takardan wannan campanyn da kikace
ansa akasuwa kinason ki siyane sai kuma
wannan takardar wannan sbn gidan da ake
gidamin na abuja ne
Duk na mallaka miki su
Yace kiyi haquri hajia nafi wannan qananun
kyatane duk sanda afnan
Ta shgo gidana a matsayin matata sai na miki
kyautar data birkita miki
Lissafi
Wohoho wani irin dadi daya rufeta batasan
lokacin data runngumeshi tana
Kwararo masa godia ba
Hmmm nafi kenan anyi nisa gaski muje zuwa
masu karatu
Bayan ta sakeshi yace karki damu wannan ba
komai bace ya fice abinsa
Afnana da adnan kuwa sun isa musawa cikin
qoshin lfy
Yayinda Kowa keda murnan ganinsu
Yan uwa da abokan arziqi sai murnan ganinsu
ake dan tuni ann
Zagayesu da abinnci kala kala
Yan,uwa sai nan da nan ake da afnan
gasancewar alkhairin mahaifinta garesu
Don haka ta saki Jikinta akaita harkoki da ita sai
dare suka sami kansu
Nanfa adnan da afnan suka samu kebewa da
kakanninsu
Don su tattauna matsalar kasancewar kakannin
sunsan komai
Aleeyu bai boye musu ba
Cikin takaici malam yace kai wannan yarinya
akwai matsala wajen al,amuranta
Yanxu ku dauki waya ku sanar da abban naku
abinda ke faruwa ni kuma insha
Allahu. Gobe zan tattaro dangin babanka da zarar
an gama sallar azahar a daura muku auren
Inyaso duk wani shagali da za,ai saiya biyo baya
Dukkanninsu zukatansu cikin fari ciki take shi
kansa aleeyun da suka sanar
Dashi. Zuciyarsa tai masa dadi sosai don haka
yace
Shima a goben kafin azahar din zai iso garin
musawa da a daura auren dashi
Inka kalli amarya Ada angon tamkar akansu aka
fara aure
Saidai inna ta gaji da rashin kunyar yaran don
haka ta korasu waje tai
Kwanciyarta
Tamkar yaddah malam mahaifin aleeyu ya tsara
haka kuwa abin ya faru
An daura auren afnan da adnan Bayan sallar
azahar daurin auren yasamu
Halarta mutane bakin gwargwado
Duk yaddah adnan Yaso Akan yaga amaryarsa
amman abin ya faskara Sbd
Al-adun qauye sai a hankali a dole yasama kansa
sa,ida har dare yai
Sai cikin darenema ya samu numberta ta shga
zai soma mita tace kai yaya adnan ni kainafa ba
laifina bane
Duk yaddah naso mu hadu abin ya faskara to ya
zanyi?
Kayi haquri bari na turo da madadina ta dinga
masa kissing ta wayar
Yai saurin katseta wait banaso inba so kike
yannxu ki ganni kan gadonnanba
Don banjin kunyar Kowa Indai akanki ne
Daria tai tace I miss u yayana ka kularmin da
kanka sweet dreams
Ta fada tare da kashe wayar ta kwanta abinta
cikin kwanciyar hankali har Barci
Ya sureta
Washe gari alhamis aleeyu ya shirya ya nufo
garin kano
Inda yace zaijene domin shirya musu tafiyan nasu
qasashe biyar din da yace
Su zaba. Dubai. Thailand India swetzerland
sannan kuma sai qasar da
Adnan yai karatu wato london
Don haka aleeyu ya nufi kano don samar musu
biza da kuma ticket
Ya kuma sanar ma kakannin afnan na wajen uwa
daurin auren nasu
Da akai da bazata suda shirye shirye suketayi
don tahowa musawa ran juma,a
Asabar a daura aure ayi walima lahadi litinin su
dawo
Saidai koda yaje ya sanar musu kakar afnan din
Wato mahaifiyar nafi murna tayi sosai
Kuma tace ba zata fasa zuwaba wato koda
kamune aima amarya
Domin nuna farincikinsu akansu
Don haka cikin farin ciki ya nufi gidansa. Saidai
me???????
Tuni murna ta koma ciki don tun daga qofar
gidansa yaga motoci cike har cikin
Harabar gidan nasa sojoji sun tsatstsare ko ina
Zuciyarsa cike da takaici dan Tunda ake fada
masa
Janar na zuwa gidansa bai taba arangama
dashiba sai yau
Don haka dole ya dauki kwakkwaran mataki yau
Don haka kai tsaye falon matar tasa ya nufa a
takai taccen falonta ya sameta
Saidai abin ya girgizashi
Tana sanye da Wasu matsatstsun Riga da siket
ne yan kanti wato
@engilish wear. Sun kama Jikinta ko ina na surar
Jikinta yana bayyaba
Saman kujera daya suke ita da janar din yaddah
har suna iya jin dumin juna
Tuni kishin yan maza ya motsa ya fada falon
babu ko sallama
Wanda ganinsa ya hanasu qarasa tafawan da
suke shirinyi suna daria
Da alamar tai musu dadi
Da wani irin kallon tsana ya dinga binsu jikinsa
har rawa yake Sbd
Baqin ciki
Hajia nafi. Tai saurin miqewa tace yauwa ka
kuwaxo Akan gaba
Wannan da kake gani shine janar Wanda aka
daura aurensa yau da misalin qarfe
Sha daya na safe da yarka afnan Wanda daurin
auren ya halarci manyan mutane
Ciki harda manyan abokanka ina fatan kai farin
ciki
wohoho wani irin tiririn Baqin cikine da zafin raine
suka hadu suka toshe masa zuciya
Har yaji yana shirin faduwa Sbd Baqin ciki
idanunsa tamkar garwashin wuta
Yake kallonta yace lallai nafi yau nake tabbatarda
kin zarce duk yaddah nake tunani akanki
Allah ya sani bazan iya daukan wanna tozarcinba
Don haka na yanke igiyar aurena guda aknki don
haka kije inkin
Samu miji kiyi aurenki
Yamaida kallonsa kan janar yaci gaba
Kai kuma gara zan kiraka ko baho koko salunbiyi
mai qaramin tunani
Koma da wanne ka dace inason ka sani yata
tawace
Kuma ban daga cikin mazan da matansu suke
mulka
Don haka ka ficemin daga gida tun kafin na kira
yan jarida dasu
Bata Maka suna dan ka tsallake shari,a
Sannan inason ka sani yata na aurar da ita ga
Wanda nakeso don haka
Sai kaje ka qarata da wacce take dauraka Akan
hanyar
In kuma ita tai Maka to saika haqura da yar ka
dau uwar
Don kuwa tuni yar ta zama mallakin wani
Janar yai wani lafiyayyen murmushi lokaci daya
kuma ya gimtse
Fuskarsa babu alamar wasa alokacin ya nuna
alhaji aleeyu da
Hannu yace
Lallai ka shiga hanyata qaramin dan siyasa to
inaso ka sani wlh sai naci namanka
Danye sannan Tunda naso afnan kuma harnai
nasaran aurenta to inaso ka
Sani Akan idonka za,a kawomin ita. Inyi abinda
nakeso da ita
Sannan nasa akawominkai Akan idonta naci
namanka danye
Donni janar babu Wanda ya taba shga sabgata ba
tare Dana kakkaryasaba nayi fatafata da
namansaba
Afnan dai matatace wacce aka daura aurena da
ita dunbin mutane sun halarcin taron
Yan jarida da manyan yan siyasa
Don haka kasa ido kai kallo ni janar na rantse sai
Naga bayanka
Alhaji aleeyu cikin zafin juciya yace kaje ka aikata
duk abinda zaka aikata
Ni kuma zan kwadamaka karya kake janar
Na yarda da ka saba haduwa da zakokin maza
Amman baka taba haduwa da zakin da yake
shawagi a cikin dajiba a yayin da yake farauta
Toka sani idan zaki ya afkawa maqiyinsa faduwa
yake qasa ka fita hanyata tun muna shada juna
ka ficemin daga gida
Cike da takaici janar ya nunashi da yatsa
Lallai saimun gwada gwanji a tsakaninmu wlh
saikayi danasanin cacar baki dani
Zanga yaddah tsohon minister mai neman takarar
gomna zaiyi
Nasara Akan sugaban sojoji na qasa gabaki daya
Aleeyu ya daka masa tsawa cikin tafasar zuciya
yace get out nace
Ka fita
Zuciya na tuquqi janar ya juya yabar gidan
amman zuciyarsa sai tafasa take
Lallai akwai fafatawa
Aleeyu yabi matarsa da kallo mai cike da tsana
Tunda ya furta mata saki Jikinta ya kasa
daukarta ta xube abab tana kallonsa
Batajin zata iya tankawa don haka ko ina na
Jikinta rawa yake
Aleeyu ya juya zai fice don haka ta kwala masa
kira ya waiwayo yana kallonta
Cikin tsantsar tsana
Cikin kuka na zafin saki tare da ture mata da
kyautar da janar Yaso yai mata
Tace tabbas ka zaremin mutunci da dan raguwan
imanin dake tare dani
Tabbas Tunda kasa na rasa wannan kyautar da
janar yaimin
Ka cefa zuciyata cikin kunci to wlh tallahi na
rantse da Allah
Nida kaina zan taimakama janar wajen ganin
bayanka kaida wannan tsinannan dan riqon Naka
Hmmmm jama,a shin zafin saki ne yasa nafi furta
wannan kalamai
Koko zafin rasa kyautar da janar yai niyyar yin
mata?
Aure. Kan. Aure
Chapter20
Aure kuma an daura ya dauru kuma ya samu
halartan dumbin jama,a
Sannan duk sun shaida. Don haka aurenta babu
fashi don na rantse da Allah saita tare a gidan
janar Indai har ina numfashi koda kuwa zatai.
Aure. Kan. Aure ne
Ta miqe a fusace tabar falon ba tare daya tanka
mataba Shima yai gaba
Abinsa
MUSAWA
Adnan da afnan kuwa an shirya musu lafiyayyen
kamu Wanda kausar qanuwar nafi ta shirya musu
Kowa ya halarta tun dagakan dangin uwa harnna
uba Kowa ya hallara a wajen
Afnan Tasha gyara wajen anti kausar Tunda safe
ake abu guda
Sune har mai duguri wajen gyaran jiki
Acan akai mata kwalliyar amarya sannan suka
dawo
Adnan sarkin naci a dole Yaja afnan wani
Bangare na gidan Wanda babu jama,a
A wajen
Tana shga yau saurin janyota da qarfinsa tamkar
yana tsoron kar wani ya kwace masa ita
Har dakin barcinsa yajata ya kulle qofar Jikinsa
na rawa sannan Yaja wata ajiyar zuciya
Idanuwan afnan waje tace lfynka kuwa yaya
adnan?
Bai tanka mataba ya duqa kusa da ita duk
idanunsa sun canja launi
Tamkar Wanda aka shage ya kira sunanta
Afnan ki taimakamin dan Allah wlh babu abinda
nake buqata a yanxu saike
Inaji tamkar zan mutu afnan plz
Ya fada daidai lokacin daya hade bakinsa da nata
Batada zabi danta lura mai gidan nata na cikin
tsananin buqata
Bazata iya hanashiba don kawai asu qananun
hujjoji marasa tasiri
Hadin kanta daya samu shiya taimaka masa ya
lallaba sannu a hankali
Harya samu cinma burinsa farinciki suke ciki
marar misultuwa
Samunta da yai cikakkiyar budurwa ya qara mata
qima da daraja gamida soyayyah a zuciyarsa
Ya qanqameta jikinsa yana sa mata albarka
Ji yake tamkar ya maida ita ciki Sbd so
Lallai ya gama sa,a da in,imatu baiwa daga rabbil
izzati
Yanaji a jikinsa ko mutuwa bazai iya bari ta
rabasa da matarsa ba
Saida aka soma neman amarya sannan suka saki
juna
Hartakai bakin qofa zata futa Bayan ta gama
kimtsawa ya kira sunanta ta
Waiga idanuwanta dauke da qauna take kallonsa
ya qaraso
Inda take ya riqo hannayenta ji yake tamkar ya
hadiyeta yai kising dinta
Yace afnan ji nake tamkar zan rabu da wani sashi
na jikina
Yace don Allah karki yarda a dinga min nesa dake
ni mijinkine maison kasancewa dake akoda
yaushe
Burina kullun in jini samana kafadunki in kwanta
a kirjinki ina shaqar kwamshin kyakkyawan
fatarki lol kunji marar kunya
Wani lallausar murmushi ta saki gamida kising
din goshinsa tace
I love u too my adnan
Ta jame hannayenta ta fice sunama juna
murmushi
Cike da farinciki ya koma ya kwanta saidai kewar
matarsa ne ta dinga damunsa
Burinsa kawai gobe tayu subar qasar suje inda
zai nuna mata soyayyar da bata taba ganin irinta
ba
Gaba daya gidan ya gama hadewa da jama,a
babu ko masaka tsinke
Yan kauyuka daban daban duk sun halarta
Inna ta shirya yinin biki
Inda acan Bangaren aketa shirye shiryen tafia
dinner
Anty kausar ne ke shirya afnan inda taketa mita
Akan bin adnan
Din
Tace na lura so kike kije ki miqa masa kanki ba
tare da mun gama hadakiba
Sakarya maza ba,ai masu haka da zarar kin basa
kanki kafin ki tare
Zai iya zuwa daga baya yace ya fasa
Don ya rigada ya samu abinda yakeso nan taita
mata fada
Ki nutsu ki kyara kanki ki kwatarma kanki yanci
A wajen mijinki itadai afnan jinta kawai take
amman aikin gama ai ya
Rigada ya gama
Doguwar rigace irinta India rai rawa rawa rigar
nada adon fulawowi
Baqaqe amman riqar pink ne dinkin yahau jikinta
Gashinnan yasha gyara sai kyalli yake yana
daukar ido
Wuyarta da hannayenta duk gwalagwalai ne
Duk Wanda ya kalleta zaiso ya sake kallonta ta
hadu sai kace wata
Sarauniya fatarnan tata ta qara fitowa sosai
Anty kausar ta kamo hannunta
Zuwa inda aka shirya kamun
A Bayan gidane saidai daga Bayan gidan an kafa
runfuna guda bakwai
Uku barin dama uku na hagu amman suna facing
din juna sai daya na
Amarya da ango
Inka kalli amarya da angon sun bada ma,ana
sosai
Dangin amarya da ango an cashe sosai
Domin an gayyato mawaqa da makida kalakal
Anci ansha domin anty kausa gafiya restaurant
tabama kwangilar
Shirya abinda za,a rabama mutane da abinda
za,aci kuma asha
Don haka komai na burgewa akai
Daga qarshe wani maqwani ya rufe taron da
waqarsa ta amarya da ango
Inda aka tasar da amarya da ango suka rausaya
sosai tsawon Wasu mintuna sannan aka buqaci
dasu koma su zauna
Afnan cikin daria take kallon adnan ta sigar
zolaya tace
Kai ashe yayana ya iya rawa haka
Daria yayi Shima ya lalubo hannunta ya riqe
sannan ya rada mata
Yace saima randa muka tare kullun saina miki
Rawa da waqa da zaran nai miki laifi na lallasheki
da waqa
Maganar da zai qarayi ta datse shi
SanadiYyar shigowar sojoji wurin
Qirjin adnan yai wata mummunan rugurguza
Afnan da bata lura da abinda yake kalloba ta
matse hannunta cikin nasa
Cikin shagwaba tace maganafa nake
Baimasan tanayiba don haka ta maida hankalinsa
inda yake kallo
Batasan lokacin data zaburaba ta tashi tsaye
Jikinta sai rawa yake
Kirjinta sai baraxanar fashewa yake ganin janar a
gaba sauran sojoji sunkai
Ashirin suna take masa baya afnan ta juyo da
sauri domin ganin haliin da adnan
Din yake ko motsii bai iyayi
In banda numfashi babu abinda ke motsi a jikinsa
Tamaida kallonta inda janar ke tahowa tabbas
kansu yayo
Yana qarasowa ya hada kafafuwan adnan din
duka biyun ya datsa musu ankwa
Ba tare daya cema Kowa komaiba ya cakumi
rigarsa ya miqe tsaye suna Kallon
Kallo a haka hajia nafi ta shgo cikin wata irin
shiga sai kace ba musulma ba
Ta Riga da siket damammu
Daga ita sai wani yalolon gyale gashinnan ta
bazoshi ta baya ta datse fuskarta
Da Baqin gilashi dukka kallo ya koma kansu gaba
daya jama,a Kowa
Yasha jinin jikinsa ganin bindiga tsirara
Kausar ce tai qarfin halin qarsawa wajen yar uwar
tata
Muryarta na rawa take fadar
Yadai haka anty nafi
Hannu ta daga mata tace stop yanxu ba lokacin
wasa bane ko dogon zanceba
Sannan taci gaba da fadin........
Mu hadu a next chapter yau banyi post da
yawaba kumin uzuri
Kunsan yau juma,at ne ranar ziyara amman idan
allaj ya kaimu gobe xamu daura daga inda muka
tsaya
Aure. Kan. Aure
Chapter21
Tace sojoji sun kama mijina aleeyu da hannu.
Dumu Dumu
Yana fataucin hodar iblis tare da kawalcin maza
da qananun yara
Bincike ya nuna shida adnan suke wannan
qazamar harkar
Hakanma yasa ya aiwatar da aure kan aure
Janar ya kama aleeyu da laifi Dumu dumu shine
aleeyu
Ya bashi daurin auren yarsa Akan ya zama daurin
baki
Janar ya amsa aka daura auren ba tare daya
daina binciken aleeyu ba
Hakan yasama aleeyu Bama yaronsa auren afnan
ba tare da wancan auren
Ya warwareba aure. Kan. Aure kenan yanxu haka
Aleeeyu yana hannun
Hukuma
Sunxone domin tafia da adnan inda ni kuma zan
tafi da yata
Jikin Kowa yai sanyi da zancen hajia nafi
Har Kowa nama adnan kallon azzalumin mutum
Amman banda yan tsurarun jama,a wadanda
sukasan halin
Hajia nafi farin sani
Cikin sheshsheqar kuka afnan tace na rantse
babu wani azzalumin daya
Isa ya tafimin da miji inhar ina raye
Tace momcy Nandai gidan dangin ubanane ko
Toki barni anan nai rayuwata a cikinsu bazan iya
rayuwa da waddah duniya kawai tasa a gaba ba
Ni nasan abbana mai gaskia da Amana ne
wannan kawai nasan sharri ne daga wajenku
Kuma ku zai koma mawa don inhar ina raye saina
kayar da gaskia damai
Goyon bayanta. Kuma ko Waye na rantse
Maganganun afnan sunyi tasiri a Wasu zuciyoyin
a yayin da Wasu suke ganin
Kamar tanayine kawai domin kare mahaifinta da
kuma mijinta
Sai alokacin Wasu hawaye suka ziraro a kuncin
adnan bana komai bane
Sai na ganin hawaye a fuskar matar tasa
Wanda alokacin baida hannun dazai share mata
balle lallashi
Tai saurin riqe hannayensa Wanda aka datsama
ankwa
Cikin kuka tace kayi haquri yaya adnan bazan
taba barinka ba
Ina tare dakai kuma duk runtsi insha allahu sai
munyi nasara Akan maqiya
Badai maqiya suyi nasara akanmu ba
Yana shirin magana suka tasa keyarsa a gaba
suna Harbin iska
Hajia nafi taja afnan da taimakon wata soja suka
sata a mota direba yajasu
Afnan tai kuka har saida idanunta ya qafe
Rayuwar tai mata kunci fiye da komai ji take in
akwai abinda ta tsana fiye da
Mutuwarta to momcynta ce
Don dama babu wata shaquwa ta uwa da da a
tsakaninsu
Tun tana jaririya bata shayar da itaba bata
rainetaba bata tava
Goyata da bayantaba bata taba mata kyakkywan
runguma a jikintaba da hartai Barci ta farka ba
Balle aje ga kula da lfyrta. Sunanta dai uwa
kawai
Shima ce mata akai itace ta haifeta amman
yanxu bata yardaba
Dan dole ta binciko ta Gano shin Waye
mahaifiyarta
Kuka kawai take Wanda babu hawaye a cikinsa
Idanuwanta duk sun canja launin kala har suka
isa garin abuja
Tafia mai nisa Sukai kafin su isa wani rukunin
tsadaddun gidaje
Inda zamu iya kiran. Anguwar da GRA Sbd
tsaruwarsa
Wani qaton gidane gari guda Wanda sojoji suke
gadi
Suka shga gidan ya tsaru yana dauke da bene
hawa hudu
Gidan ya gama tsaruwa dan gaba daya
ma,aikatan gidan sojojine
Hakan zai tabbatar mana da lallai ba qaramin
ma,aikacin soja bane keda gidan
Wani sashi direba ya kaisu Yadan rangwafa yace
toga sashin amarya nan
Ranki shi Dade hajia nafi tace to yayu kyau zaka
iya tafia yace na gode hajia
Haja hannun afnan din suka shga Bangaren
Wanda yake dauke da faluka
Da yawa komai ya tsaru a bangaren
Hajia nafi ta dubi afnan tana murmushi mugunta
tace wannan
Gidan shine ya dace dake. Wannan rayuwar ita na
zabar miki afnan
Ki zauna kiyi rayuwa cikin galihu yaddah duk inda
kikasa qafa akwai
Masu tsaron lfyrki
Kina tafia a mota a dinga miki jiniya tamkar wani
sarki ko
Shugaban qasa duniya tasan da zamanki
Rayuwar data dace dake kenan domin ni kaina
irinta naso amman Allah bai
Nufaba naje na auri mahaifinki koda yake mun
rabu yanxu na fara
Rayuwar galihu. Na samu yancin kaina
Duniya sabuwa domin gashi Naga bayansu
daman na furta a baya saidai ni
Naga bayansu badai su suga bayana ba
Kai Alhamdulilah ta ida maganar tana wani
murmushi mai tafe da daria
Ran afnan ya qara dagukewa ji take tamkar ta
shaqare mahaifiyar tata Sbd Baqin ciki
Ta zube saman kujera tamkar mai shirin suma
burinta a yanxu bai wuce taga halin
Da maihaifinta da mijinta suke ciki ba
Tanaji hajia nafin uwar tata ta qaraci surutun
nata harta fice
Zuciyata Kamar zata fashe tace lallai jahilcin
mahaifiyarta. Ya wuce tunanin
Mai tunani wai nan zaman aure ta daukota ta
kawotayi amatsayinta na matar wani koko ya
To meye sunan wannan AUREN? Baida wani
sunan daya wuce AURE KAN AURE
Tabbas yaqine ya tunkarota badan qaramiba
Dole ta karema mijinta haqqin aurenta koda kuwa
zata rasa ranta ne
Kuma a yanxune karatunta zai mata rana abinda
ta fada kenan
Ta miqe ta nufi wata qofar gilas ta latsa ta bude
ta shga
Kamar yaddah ta hango ta gilashin bedroom ne
ya qawatu iya qawatuwa
Da gado da shimfidu na alfarma. A gefe daya
dakin wankane Wanda za,a
Iya hango mutun ta ciki
Afnan ta zauna a bakin gadon ta rafka tagumi
tana tunanin ta yaddah za,a
Bulloma al,amarin bataga ta hanyar guduwaba
tundata shgo gidan ganin
Yaddah yake tsare da sojoji
Shin idan tace ta guduma taje ina?
Lallai yanxu batun gudu bai tasoba
Zama ya cancanta ta samu domin warqare
matsalolinta cikin sauqi
Don haka tun daga inda take ta soma shirya
komai a cikin memory dinta
Kwananta guda a gidan in banda zaman kadaici
babu abinda take
Fama dashi
Inbanda Ruwan sallah Jikinta har yau din baiga
ruwaba
Abu Kamar wasa saidata share sati babu Wanda
ya leqota
In bansa ma,aikatan gidan abinci kuwa har
turewa take domin daman bacin takeba
Daidai da wanka ya gagareta hakan yasa duk tai
duhu
Ta koma tamkar ba itace afnan ba mai tsantsar
kyau da kwalliya
A yanxu kuwa ko ma,aikatan gidan sunfita fasali
duk Tabi tai wuri wuri
Batasa aiki sai kuka kullun cikin kuka take
Babu kuma mai lallashinta Tunanin mahaifinta da
dan uwanta kuma mijinta
Shike haifar mata da matsanancin tashin hankali
marar misultuwa
Da daddare tana kudundune saman gadinta Sbd
sanyin da ake
Idanunta a rufe dan ji tayi dakin ya canja mata
daga sanyin zuwa zafi
Ta bude idanuwan nata da sauri
Tsaye yake ya zura hannuwansa cikin aljihu. Har
yanxu kwarjininnan nasa
Nanan
Cikin faduwar gaba tai saurin tashi daga kwancen
ganin yana nufota
Ta daga masa hannu cikin tsawa tace karka sake
ka kusantoni
Tamkar badashi takeba
Ya qarasa ya zauna a bakin gadon yana qare
mata kallo
Fuskarsa dauke da wani shu,umin murmushi
Jikinta sai rawa yake burinta Allah yasa ta tsira
daga sharrin wannan
Mahalukin
Yasa hannu ya riqo hannunta yana Wasu dashi
Tsoro da fargava suka hanata iya kwace hannun
Shiko a wautarsa sai yake Tunanin wai ko
lagonta ya Gano
Cikre da qasaita yake maganar
Afnan yan mata a sannu daman na fadamiki sai
wannan ranar ta kasance
Yanxu gaki a gidana kuma a dakina kuma a
matsayin matata
Yace lallai ne babba ne ta yaddah na iya tsinke
igiyar soyayyar data shga
Tsakaninmu
A wannan karon kuma a wannan gabar zanyi
abinda nakeso dake
Duk da ayanxu ban shryaba Sbd kase din dake
gabana
So nake Naga bayan maqiyana ubanki da wannan
marar kunyan Mijin naki
Sannan nazo na shimfida rayuwata dake har sai
lokacin Dana gundura
Tace amman ai kasan da auran wanni akaina ko?
Ya tabe baki yace tome ya dameni nidai burina
kawai shine na kasance dake
Na kwanta a wanna kirjin shine kawai buqatata
ba aure ko rashinsa ba
Afnan ta dake zuciyata ta kalleshi sosai kamin
tace
To inason ganin mahaifina da kuma mijina inason
ganin
Halin da suke ciki
Ya kaure da wata irin daria harda babbakawa
yana tafa hannu harda hawaye
sannan yace lallai duk Wanda ya shga sabgata
saina karya qafafunsa
Ai maadam ina tabbatarmiki da idan kikaga
mahaifinki a
Yanxu ba zaki ganeshiba
Don na maidashi mabaraci kuma kullin danai
masa duk duniya wlh babu Wanda ya isa ya iya
kwance masa shi saini Dana kulla
Yace amman Tunda kince kinason ganinsu zansa
akaiki
Domin ba kulle nake miki ba duk inda kikeso zaki
iya zuwa
Tunda duniyarki tana hannuna
Mahaifinki mijinki mahaifiyarki nasan koda Kinyi
niyyar guduwa dole zaki nemeni
Tofa gaskia ne janar kace kaima kwallon shgene
Idan Naga comment da yawa kafin safe saimuci
gaba
Misalin qarfe tara na safiyar gobe in Allah ya
kaimu
Bawai kuma nace kusa rai bane cewa nai idan
Aure. Kan. Aure
Chapter22
Ya saki hannunta ya cilla mata key din mota
Da card dinsa yace duk sanda kika shirya kixo ki
Sameni a office wannan kuma makullin motane ki
hau kije duk inda kikeso
Burina shine ki wala kiji dadin rayuwarki
Ba burina kiyi zaman kadaici ba ya miqe ya fice
abinsa ba tare
Daya sake waiwayar inda take ba
Tunda safe afnan ta tashi da zumudin son ganin
halinda
Mahaifinta da mijinta suke ciki don haka bata
tsaya sanyaba ta fada toilet
Tayo wanka t fito t murxa mai da hoda
Sannan ta nufi wadrof ta dauko Wasu kaya yan
ubansu material
Sannan ta dauki wayarta da key din motar Tayo
waje
Kasancewar abuja Kamar gida take a wajena
hakan yasa batasha
Wahalaba. Wajen gane office din janar din
Tanayin parking din motar tasa waya ta kirasa
kamain ta gama fitowa
Daga motar har yasa sojoji suxo su mata iso
zuwa office din nasa
Office din ya hadu iya haduwa. Daidai da kujeran
office din abin kallo ne
Yana zaune kan kujeran dake gaban babban tebur
din ta gilashi
Fuskansa dauke da farin gilashi ya maida
hankalinsa kan wani
File yana sanye da kayan sojoji a jikinsa. Yai
mata nuni da kujeran dake kallnsa
Ba musu kuwa ta zauna. Ta qara nutsuwa
matuqa dan office din kadai
Da yaddah sojoji keta zirga zirga a wajen ya isa
Ya tsorata dakakken namijima balle mace
Kamar afnan
Saidaya gama shan iskarsa sannan ya dago yana
kallonta
Yace lallai kin qagu da kiga wannan mai gidan
naki wannan safia haka
Nadaisan ko break bakiyiba ko?
Shiru tai Shima bai sake mata maganarba ya
latsa qararrawar dake gefensa
Ba,a jimaba saiga wani sadaukin soja ya shga ya
Sara masa ba tare daya
Kallesaba yace maza madam taxo aje a hado
mata break
Yace Owk sir ya sake sarawa sannan ya fice
Afnan ta jawo dakiyar duniyarnan ta yabama
kanta sannan tace
Ba kalaci ya kawoni office dinkaba kasan meya
kawoni
Kasa a kaini inga mahaifina da mijina kawai
Bai tanka mataba illa ci gaban da yai da rubuce
rubucensa
Yar qararrawar tai qara da alamar akwai mai
shgowa ya bada izni aka shigo
Sojan dazunne ya dawo dauke da qaton tire
Tamkar shgowarsa ta daxun yana zuwa ya Sara
masa
Sannan ya sauke tiren a gaban afnan yana fadin
gashi ranki shi dade
Bata tankaba harya fice kuma bata da niyyar
motsawa
Hakan yasa ya saci kallonta sannan ya sake
maida hankalinsa kan abinda
Yake din. Ba tare daya. Kalletaba yace duk sanda
kika shirya kikaci saina
Kaiki wajensu inkuwa kikaqici to saiki tattara ki
koma inda kika fito
Ba yaddah ta iya haka ta siyaya Ruwan zafin a
cikin cup ba tare datasa madaraba lipton kawai
tasa sai suga ta dinga kurba va wai don tanajin
dadinsaba
Saidin ba yaddah kawai zatai
Cikin dan qanqanin lokaci ta kammala ba tare
daya kalletaba ya qara latsa
Yar qararrawar Sojan ya dawo yace maja a
kwashe wadandan kayan ai gaba dasu
Cikin rawar jiki ya tattara yai waje yace sannan
kacema sajen ballo yai maza yaje
Gurdroom a dauko min wadannan yan sada
kwaurinnan a kawominsu
Yace Owk sir da sauri ya fice yayin da afnan ke
nanata sunan da
Aka kira mahaifina da mijinta dashi
Baifi minti gomaba saika sojoji hudu sun shgo
dasu a rirriqe
Tamkar sun riqo maguna
Afnan ta zabura ta miqe a daidai lokacin da
gabanta yai mummunan faduwa
Ta rirriqe mahaifin nata tare da afnan wadanda
sukasha bugu har suka fita daga hayyacinsu
fuskokinsu da jikinsu duk sun kukkunbura sunyi
Luhu Luhu tamkar an qukqulle biredi
Ko ina na jikinsu ciwukane dukda Wasu sun kame
amman har yanxu basu
Daina zubda jiniba
Dukkanninsu daqar suke gani Sbd duk
idanuwansu sunyi Luhu luhu
Afnan ta rirriqesu tana wani irin kuka tana kiran
sunansu
Abba yaya adnan Waye yai muku wannan danyen
aikin haka?
Wayyo Allah na shga uku
Kuka take sosai tamkar wacce aka kawoma
gawarwakinsu
Dukkansu babu Wanda yake iya magana Sbd
tsantsar azabar da sukasha
Janar ya miqe tsaye ya tattaka inda suke cikin
tsantsar isa
Ya zagayesu kamin ya dawo gefen afnan ya duqa
yace
Ki basu shawara tun tuni nace dasu su amince
Akan tuhumar da nakemusu susa
Hannu Akan takardar yarjejeniya su rantse kuma
su dauki alqawari bazasu qara
Safara hodar iblis ba tare da safarar qananun
yaraba
Ni kuma nai musu alqawari zan sakesu
Afnan ta miqe da sauri. Tace ba zasu aminceba
janar domin aiba wawayebane
Da zasu amince da laifin daka daura musu kuma
kake tuhumarsu dashiba
Wato kana nufin ka kashesu Akan wannan hujjar
kenan?
To baka isaba ta. Dafa kafadar mahaifina tace
kayi haquri abba
Karku sake duk runtsi kusa hannu koda kuwa zai
dau rankune
Don zaiyi amfani da wannan ne domin ya bata
muku tarihi
Insha allahu abba zanyi iya qoqarina koda zan
rasa rainane saina kwatoku daga hannun wanna
azzalumin kuma saina kwato muku haqqinku
Insha allahu
Ta sakeshi ta riqo hannun mijinta Wanda suketa
zubar da jini
Ta girgiza kai tace
Ina sonka mijina abinda ya sameka bazaisa naci
amanarka ba
Don da ace babu masifar data iya rikar dan adma
toda soyayyah batai
Ranaba
Sai masifa ta farune kadai ake iya samun alfanun
soyayyah na haqiqa
Don haka wannan lokacinne kadai yafi kowanne
lokaci dacewa
Dana kasance dakai bazan cutar da aurenkaba
bazan illata rayuwar
Masoyanaba. Janar dake tsaye zuciyarsa na wata
irin suya ya dakawa sojojin tsawa
Jikinsu na rawa suka kwashesu Sukai gaba dasu
ya koma ya zauna sai huci yake
Tamkar Wanda yasha wani uban gudu
Afnan ta share hawayen nata ta koma ta zauna
Akan kujran data zauna dazun
Cikin sarkewar murya tace
Mai yasa vaka tura wannan case din zuwa kotu
ba?
Tamkar bazai amsa mataba can kuma kome ya
tuno Oho
Ya dubeta yace. Sbd case ne da ni ya shafa ba
buqatata nace na kaisu kotuba
Buqatata su amsa laifinsu anan sannan na kaisu
da hannuna
A yanke musu hukuncin daya dace
Afnan tace to amman mai yasa kake Abun babu
yan jaridah?
Da sukasan da labarin balle yakai kan yan siyasa
har izuwa kan shgaban qasa?
Yace Sbd in hakan ta faru a yanxu da bani da
kwakkwaran hujjoji
Nine zan kwana a ciki
Shiyasa na bari har izuwa lokacin da zan
kammala harhada hujjojina da
Zasu zamemin makaman yaqin nawa
Ta kirgiza kai tace dakyau ta miqe ba tare data
mai sallamaba tabar office din
Zuciyata ta gama narkewa da lamarin don haka
tana fita kai tsaye headquetres na
Yan sanda ta nufa bata samu matsalaba wajen
sadata da. iG kasancewar sunan
Mahaifinta da kuma karatunta
Kayataccen office ne tsaruwarsa ta wuce acemai
office
Dan sandane ya shga da ita yai mata iso ta shga
tana qarema office din kallo
Zuciyata ta gama tsinkewa ganin yaddah. IG din
take zaune a saman kujera ta alfarma
Tun daga Jikinta har muryarta rawa suke wajen
fadan sady!
Fuskarta dauke da fara,a tace la,a afnan
Bismillah zauna mana
Ba musu taje ta zauna tana fadin wlh nayi
farinciki ganinki zaune Akan wannan
Muqamin matsalace tafe dani don Allah ki
taimakamin sady
Tace fadi abinda kikeso afnan fadi Indai har bai
gagareniba insha allahu zan taimaka miki
Anan ta zauna ta lbrta mata abinda ya faru tun
farko har izuwa yanxu
Da take maganar
Kwarai sady ta samu. Zuciyata kuma ta motsa.
Tunda tun a wancan lokacin tai dawainiya da
sonsa don haka zata taimakawa masoyinta
Da qarfinta basirarta da kuma aljihunta
Ta tambayi afnan din tace kice shugaban qasa
baisan da maganarba?
Tace tabbas
Ta dan jujjuya kan kujerar da take zaunen kanta
na kallon sama kamin ta tashi
Da sauri tamkar wacce aka zabura. Ta dauko biro
da takarda a take ta rubuta later
Zuwa office din sugaban qasa. A take ta tura
zuwaga office din shgaban qasan
Sannan ta dubi afnan
Tace yanxu ba zaki koma gidaba afnan domin
kuwa yin hakan zai iya
Zama mana kuskure don haka a yanxu zan
rubuta takardar shigarda qara kotu
Yanxu zan daukeki zuwa gidana
Rayuwa taxoma afnan da sauyi takoina jinta take
tamkar marainiya
Data rasa uwa da uba tare da dangi gaba daya
don haka sady ta dage wajen lallashin qawar tata
Ta dauke mata hankali da lbrun duniya wai kodan
ta saki Jikinta
Amman abin ya gagara
Damuwar da afnan ke ciki ta wuce Hira ko wani a
ta kawar da ita
Barci kansa sai yayi da gaske yake dauketa
Daga wanka ta fito daure da tawul
Daya na kanta tana tsane kan nata sai kace wata
qaramar yarinya ta fito sai
Waqa take na turanci
Tana waqar tana rawa harta iso kan kujeran dake
gaban madubi taja ta zauna
Natsuwa tayi ta zuba kwalliya fuskarnan tata tai
luqui sai kace jaririya
Bayan ta gama ta bude wadrob dinta ta dauko
kayanta na yan sanda
Ta hade cikinsu Kamar daman dan ita akayisu
Ta hau Baqin takalmi. Gamida hular yan sanda
Hmm sady kenan iyayen iya kwalliya wato kyan
da tai ya isa a bude mata duk wata qofa data
tunkara
Bata da jiki saidai ba ramammiya bace
Sady na zaune a office dinta dan yau ayyuka sun
mata sauqi don haka a
Sannu a hankali. Take nazarin files din dsake
gabanta wadanda akeso tasa
Hannu a ciki
Ji tayi an fado office din nata ba tare da an nemi
izniba
Tai saurin dago kai dan taga ko waye
Cike da mamaki taga ya tsaya suna fuskantar
juna
Cikin kakkausar murya yace ke qaramar karuwa
Harke zakisa shugaban qasa yasa na saki
mutanen da nake tuhuma
To wlh inaso ki sani inhar kikace zaki shgo
harkata
Wlh zaiyi wuya ki iya rayuwa don wlh sai nasa a
koreki a wannan dan kurkukun office din da kike
taqama dashi yanxunnan
Kin kuwa san koni waye?
Sady tai tattaki zuwa gabansa ta zura
hannayenta cikin aljihu tana kallonsa ta cikin
Baqin gilashinta
Tace nasan kokai Waye kai ba Kowa bane illa dan
ta,adda mai. Kashe alummah
Dubi yaddah ka shgomin office sai kace wani kare
Cikin kunan zuci ya daga hannu zai zuba mata
mari komai ya tuna kuma
Sai ya dungule hannun nasa ya sauke yana huci
Tai wata daria tana tafa hannayenta kamin kuma
lokaci guda ta daure
Sai kace ba itace ke daria yanxuba
Ta nunashi da dan yatsa
Tace kai kayi kadan kasa a koreni a wannan
office din sanna ni sady nayi alqawari saina kawo
qarshen ta,addancinka
Don dama qasa na sane ta qaleka kake yaddah
kaso
Ya girgixza kai yace lallai yarinya keba komai
bace wajen janar
Toki sani ko cinnaka bakikaiba Indai a wajen
janar ne
Kuma na rantse miki goshinki saiya Riga rana
fadiwa
Bai saurari abinda zataceba ya fice a zafafe ya
barta tana wani murmushi da ita
Kadai tasan fassarar sa
Bayan sady ta tura case din zuwa babbar kotun
dake qasa ta abuja
Komai ya kammala ran monnday itace ranan da
za,a zauna sauraron shari,ar
Inda sady da kanta taje ta amshi adnan da abban
afnan aka wuce dasu asibiti
Saidai Shi adnan a sume aka daukeshi aka kaishi
asibitin baisan inda kansa yakeba don haka ba,a
barin Kowa na shiga wajensa in banda likitoci
Yayinda suka duqufa wajen basu taimakon
gaggawa
Yau itace ranar Monday ranar da za,a zauna a
kotu
Don haka Tunda safe afnan da sady suka gama
kammalawa afnan
Cikin kayan lauyoyi ita kuma sady cikin kayan
yan sanda
Afnan sanye da kayan lauyoyi da hularta ta
lauyoyi gamida wani Baqin gilashi
Inda ita kuma sady ta hau wani Baqin gilshi
wuluk kalar kayan nata
Ladies din sun wanku iya wankuwa
Kamar kullun kotun dauke take da manyan
mutane inda
Yansanda da kuma sojoji suka tsatstsare ko ina
domin gudanar da tsaro
Afnan itace ta kasance lauyar dake kare
mahaifinta da kuma mijinta ita
Da wani lauya mai suna nasir adamu
Don haka Bayan mai gabatar da qara ya tashi ya
gabatar da qaran da za,a gudanar yau
Barister hafsa aliyu musawa afnan kenan ta miqe
Ta gabatar da kanta a gaban kotu
Shima lauyan da suka dauka ya tashi ya gabatar
da kansa a matsayinsa na lauyan kasuwa
Wanda ke kare tsohon minister aleeyu musawa da
kuma dan uwansa adnan muswa
Bayan ya zauna barister hilal. El.amin ya tashi ya
gabatar da kansa a
Matsayinsa na lauyan dake kare Wanda ake qara
wato janar abdullahi aminu abbah
Bayan Kowa ya zauna afnan ta miqe tace yamai
girma mai shari,a inason
Abani daman ganin janar abdullahi aminu abbah
Kotu tace an baki dama ta qarasa inda janar
yake a tsaye
Tana isa gabansa ta tsaya sunama juna kallon
kallo mai cike da ma,anoni
Shin baiyi Tunanin ganinta bane koko yana
mamakin ganinta cikin kayan lauyoyine Oho nima
bansaniba
Aure. Kan. Aure
Chapter23
Barister afnan ta kalli tsakiyar idanunsa tace mai
girma janar ana tuhumarka
Akan kulla wani abu Wanda ba gaskia bane. Akan
mai girma tsohon minister
Aleeeyu musawa shin ko meye tabbacinka Akan
yana safarar koken ta qananun yara?
Janar cikin dakewa yace hannu dumu dumu muka
kamashi
A yayin da muke cheaking din jirgin daya taso
daga amerika ya sauka
Gida najeria mun kamashi dumu dumu da jakar
koken
Inda muka daddaukeshi hotuna sannan muka
wuce dashi domin qara bincike
Afnan ta dubeshi tace shin daman Kuna cheaking
a wajen ne kokuwa a ranar kuka soma?
Tunda Naga da akwai jami,an tsaron dake kula
da filayen jiragen saman
Yadanyi Jim kadan kafin yace inada hurumin duk
sanda naso naje na tsananta bincike a duk wajen
da nake zargi
Tace to kenan ka fara zargin wasune shiyasa ka
isa filin jirgin?
Yace tabbas domin bincike ya nuna mana cewa
ana safarar koken ta jiragen sama
Tace wato kenan duk binciken da aka saka
na,urori da jami,an tsaro dominyi ya zama hotiho
kenan? Tunda har ake tafia da hodar koken daga
wata qasa zuwa wata qasa
Yadanyi Jim kafin yace kinsan mutum zai Dade
yana yana abunsa aboye inda wani zai dinga
bashi sa,a amman daga sanda dubunsa suka cika
sai kiga Allah ya toni asirinsa
Afnan tai wani murmushi ta juya ta kalli alqali.
Tace
Ya mai girma mai shari,a wannan ba hujjar da
zatasa a yarda da janar. A. Aminu bace
Domin kuwa tsananin kula da tuhumar da filin
giragen saman da America take yafi nanan
Sannan wani zargine yake da harya kaishi filing
jirgin sama bincike wannda bai taba zuwaba Indai
harba shugaban qasane zxai tafiya ba?
Sannan girman janar ya wuce da kansa yaje
bincike filin jirgin saidai yasa Wasu suje suyi
Kenan hakan na nuna akwai wata maqarqashiya
kenan da akema mai girma tsohon minister don
kawai a muzantashi a matsayinsa na dan siyasa
Sannan janar ya boye tsohon minister a wajena
ba tare da hukumar yan sanda ta kotu kota. Yan
jarida sun samu lbr ba tsawon kwana goma sha
hudu
Saida hukumar yansanda suka Gano da kansu
suka turama shugaban qasa
Leta Akan abinda ke faruwa sannan yasa aka
sakesu
A yanxu haka suna asibiti ana basu taimakon
gaggawa dayama ba tare da yansan inda jansa
yakeba a yanxu haka
Da wannan hujjoji nakeaon ita kotu data dubi
halayyar shi tsohon minister tun farkon
tasowarsa bincike ya nuna mutum ne mai gaskia
riqon Amana da kuma dattako
Tunda yake Akan muqaminsa ba!a taba samunsa
da wani laifi Wanda ya sabama dokaba
Tayi shiru. Sannan ta rankwafa tace na gode mai
shari,a ta koma ta zauna
Alqali ya ida yan rubuce rubucensa sannan ya
dago yana fadar
Ko. Lauyan Wanda ake qara yanada abinda
zaice?
Ya miqe ya gaishe da kotu sannan ya fara da
Hujjojin da barister afnan ta bayar ba abin
kamawa bane domin kuwa
Kamar wata tatsuniyace ta shirya ina roqon kotu
da tasa akawomin mutane biyun da ake zargi
domin nai musu Wasu yan tambayoyi
Alqali yace. IG. Sadiya muhammed mai nasara
muna buqatar
Akawo mana marasa lfyn da ake tuhuma koda
kuwa a cikin keken marasa lfy ne
Daganan zuwa ranar takwas ga wannan watan
Daganan kotu ta watse
Zaman kotun zamane daya halarci manyan yan
jaridu don haka koda aka
Tashi. Yan jarida sukayo kansu dan suji ta bakin
janar da kuma barister afnan
Tareda. IG don su samu abinda zasu rubuta
domin dauke Hankalin jama,a
Dashi saida Sukai da gaske sannan suka kubuta
daga tambayoyi yan jaridar suka
Fada mota direba yajasu. Sauran motocin yan
sanda suka rufo musu baya
Suna jiniya tamkar zasu tashi sama
Sady ta dubi afnan tace zaki zauna a motane
yanxu naje gida na dauko masa
Pasport dinmu dan dama na rigada na saman
mana visa zamu wuce Libya ne yanxu
Don a yanxu rayuwarmu tana cikin hatsarine
Sannan Daganan zan dauki mota na dauki marasa
lfyn na wuce dasu wani boyeyyen asibiti Wanda
ba Kowa yasan dashiba domin suma za,a iya
zuwa ai
Musu illah
Banason Kowa ya sani koda cikin jami,ainane
shiyasa zan tafi da kaina
Minti talatin yayi yawa zan dawo
Ta bude motar da sauri ta fice zuciyar afnan ta
gama tsinkewa da wannan al,amari
Satinsu guda a qasar Libya sady ta samar musu
wani namijin lauya daga can ana ce masa
barister shaldo Lauyan kasuwa ne
Ana gobe za*a koma kotu suka dira a naija
Shima basu dira a gidan sady ba wani
A wani tsadadden hotel suka sauka
Sady ta tafi a sace ta dubo marasa lfyn abban
afnan ya samu sauqi ba laifi inda duk an
daddaurashi a inda ya samu karaya
Dukda bai iyayin komai amman ya samu sauqi
sosai Tunda har yana iya magana
Kuma idan an bashi abinci yanaci
Ba laifi kamanninsa sun fara dawowa
Saida adnan ne haryanxu bai farfado daga Suman
da yaiba
Tamkar wancan lokacin Kowa ya hallara a kotun
barister ashir shehu ya miqe
Bayan ya nemi izni daga wurin alqali ya nufi inda
aleeyu yake kwance cikin keken asibiti
Yace ranka shi Dade atsohon minister aleeyu
musawa ko zaka iya fadama kotu
Shekarunka da kuma aikin da kake yanxu?
Aleeyu yace ni sunana aleeyu musawa inada
shekaru hamsin da biyu nayi karatuna na primary
da sacondry a kano
Sannan na tafi jami,ar bayero. Dake kano wato B.
U,K
Anan na kammala digirina
Maihaifin matata Alhaji muftahu babban dan
kasuwane shine ya taimakamin wajen ka$$ala
karatun nawa
Ina tare dashi a matsayin yaronsa har ya
samamin aiki a wani banki a matsayin manager
ya kuma bani auren yarsa
Daga bayane na aje aikin da kaina ba wanine
yasaniba na shiga harkar siyasa
Barister shehu yace amman meye ya baka
sha,awar shiga harkar safarar koken....?
Barister shaldo ya miqe da sauri yace ya mai
girma mai shari,a ya kamata barister shehu ya
iya bakinsa domin kuwa shi mai tuhumane Bawai
mai yanke hukunci ba
Alqali yace akiyaye baristr
Ya waigo yana na gode yamai shari,a sannan
canja tambayar da fadar
Lokacin da aka kamaka an daddauki hotunanka
da akwatun hodar koken
Kokuwa zaka iya cewa bakai bane?
Ya girgixa kai cike da takaici sannan yace
Wannan ba gaskia bane asalima naxo abuja
domin ganawa da shugaban qasane misalin qarfe
sha biyu na dare jirgin hudu nabi zuwa garin kano
Kwatsam sai Naga ana bincike ban damuba Sbd
nasan bana tare da wani mugun abu kona rashin
gaskia amman me zai faru
Kawai sai suka dosheni da wata. Qaramar jaka
wai tawace gashi tana dauke da hodar koken da
bindigu har guda biyu a ciki
Wlh bansan da watta jakaba asalima ni tawa
qaramace batakai
Wacce suka kawomin wai acewarsu tawaceba
Amman za,a iya zuwa a binciki ma,aikatan filin
jirgin da wadanda
Suka bincikeni kamin na shga jirgin
Duk Wasu shaidu da ake buqata a wajensu za,a
samu amman niba mai ha,intar qasa bane
Bana cutar qasata hasalima Bana tare da macuta
Lauyan yace gashi kuma kamanninka Kamar wani
na Allah
Amman lokaci guda an kamaka da farautar
qananun yara gashi ka
Aikata aure kan aure
Ka daurama yarka aure da amininka ka kuma
koma Kabama abokin hulderka
Yace ko kadan wannan makircin matatace
amman da bakina ban furtama
Janar cewa na bashi yataba
Asalima bansan yana zuwa wajentaba sai daga
baya take fadamin na takama abin burki
Amman da yake zuciyar matar tawa a qeqashe
take hakan yasa taqi saurarata
Barister yace kenan kana nufin bada yawunka aka
daura auren nataba kenan?
Shiyasa ka koma ka sake daurama Wanda
kakeso?
Yace ko kadan nidai nasan na tura yarana can
dangina inda suna zuwa mahaifina yace me za,a
jira Washe gari aka daura auren nasu ranar laraba
akai walima alhamis inda daganan na wuto. Kano
daga kano na wuce abuja Wanda daganan
Kuma wannan al,amarin ya rutsa dani
Lauyan yace to na gode ya koma ya zauna
daganan barister shaldo
Ya taso cikin qasaita irinta manyan lauyoyi
Yace ya mai girma mai shari,a inason a kawomin
Hajia nafi. Matar tsohon minister domin inason
yin mata Wasu yan tambayoyi
Alqali yace idan hajia nafi tana tare damu kotu
tana buqatarta yanxu yanxunnan
Nafi ta dafe girji tace yau na shga uku meye
kuma nawa a cikin wannan shari,ar
Jin shiru alqali ya qara magana yace shin hajia
nafi batananne
Ita tana cikinnan ta fito idan kuma kikaqi fitowa
to lallai fushin kotu zatau kanki
Babu inda bai rawa a Jikinta kai Hatta miyon
bakinta rawa yake
Lol shin me take nufine tsoro takejine koko yaya
Ko tana Tunanin ko asirinta zai tonune
Oho nima ban saniba mu hadu a nxt
Chapter Danjin yaddah zata kaya
Aure. Kan. Aure
Chapter24
Jikin nafi yai sanyi daqar ta iya qarasowa wajen
da ake tsayawan
Barister yace meye sunanki da kuma matsayinki a
wajen Alhaji
Aleeyu musawa?
Nafi tace ni sunana hajia Nafisa muftahu. Aleeyu
kuma yaronane Wanda yake Yaron mahaifina ta
Fannin kasuwanci
Barister yace to ko zaki iya gaya mana zaman da
kukai nadan Wasu shekaru da suka wuce?
Tace tun aurena da aleeyu na rigada na fahimci
bamai gaskia bane
Ko kusa babu tsoron Allah a idanunsa
Sauda yawa nakan kamashi da laifuka marasa
kyau
Amman saina rufe a matsayinsa na mijina
Ni kaina na lura da safaran mutanan da yake dan
da yawa yasha shigomin da
Qananun yara gida sai yacemin wai gidan marayu
zai kaisu
Daganan bana sake jin lbrnsu
Lamarin mai gidana yayi qamari harya bada
auren yata ga genar. A aminu
Akan ya rufamasa asiri a kamun da yai masa
Shi kuma ya yarda domin yar tasa burin mallakar
duk wani da namijine
Don haka saiya boye yaci gaba da nasa binciken
a boye ba tare daya bari shi Mijin nawa yasan
zagon qasan dashi janar din yake masaba
Yasa ya tura yaransa qauye aka daura musu aure
kan aure kenan
Bayan hakanne ya tafi abuja yana sauka aka
kamashi da hodar iblis koken kenan
Barister yace amman ta ina duk kikasan
wadannan bayanan
Domin Naga kina fadane Kamar a gabanki akai
Tace tabbas Wasu Akan idona akai Wasu kuma
ba,a kan idonaba
Yace yanxu zaki iya fadamin suwaye sukeda ikon
bada aure tsakanin dangin uwa Dana uba?
Tace na uba inhar suna a raye yace to yanxu zaki
iya fadamin wadanda suka zama waliyan yarki?
Tace abokon Mijin nawa sune suka zama waliyan
yar nawa
Domin kuwa mijina aleeyu bai dauki iyayensa a
bakin komai ba
Sbd su talakawane
Lauyan yace to na gode hajia tace nikeda godia
sannan ta koma mazauninta
Sannan lauyan ya juya yana kallon alqali yace ya
mai girma mai shari,a ina
Neman kotu data qara mana lokaci zajen gudanar
da bincikenmu na gode ya mai girma mai shari!a
Alqali ya gama yan rubuce rubucensa da zaiyi
sannan ya dago yana fadar
Kotu ta daga wannan zama zuwa ranan sha tara
ga wannan watan
Sannan Kowa ya miqe
Yan jarida Kamar daman jira suke a tashi suka
yayyabe afnan
Suna fadar yanxu ranki shi Dade shin meye
makomar wannan aure naki?
Tace wacce makoma Bayan an dauramin aurena?
Ina tare da mijin da aka dauramin aure dashi
Wani dan jarida ya kasheta yace
Shin ranki shi Dade kina sonsa koko Kinyi la,akari
da Wanda aka fara daura muku
Auren dashine yasa kike zaune dashin?
Tace duka biyun kuma nayi la,akari da shi aka
fara dauramin auren dashi ne shiyasa
Can wani Shima ya jefo mata Tambayar da taso
tasa mata ciwon kai
Yace hajia da alama dai zuciyarnan taki tayi zurfi
Akan son dan-uwannan nakine da har kike
Tunanin dashi aka fara daura muku aure ko?
Alhalin janar shine mutumin da aka fara daura
miki auren dashi koko
Kina nufin kice ba gaskia bane?
Ta hatsala dan haka cike da vacin rai afnan din
tace
Kayi tambaya kuma kabama kanka amsa don
haka kayi tunani Akan Tambayar taka
Ta wucesu cikin bacin rai
Daya daga cikinsu yace bai kamata ki hatsalaba
hajia Akan wadannan yan tambayiyin inhar da
kamshin gaskia a ciki
Bata saurareshiba tai gaba abinta hakan yasa
suka tare mahaifinta Wanda aka turo a cikin
keken asubiti
Sai kokawar zuwa yin masa tambaya suke
Yauwa yallabai me zakace game da zargin da ake
Maka na safarar yayan al-ummah da hodar iblis
@koken?
Alhaji aleeyu yai murmushi yana girgiza kai yace
wannan duk sharrine kawai na
Maqiya
Wani dan jarida yace to amman yallabai ta yaya
mai girma janar ya zama
Maqiynka? Cikin zafin rai afnan ta qaraso tana
fadar
Ta inda marasa tausayi suka tsare mara lfy suna
masa tambaya
Haba sai kace baku da tausayi
Ku dubi halin da bawan allahnnan ke ciki
Bai cancanci ace kun tsareshi da tambayoyi a irin
wannan halin da yake cikiba
Ta dubi malaman asibitin dake turashi tace
kukuma kuka biye musu dan Allah ku
Turashi mu tafi
Wani a cikin yan jaridar yace duk dai kauce
kaucen akuya ai akuyace uwarta lol
Maganar ta daki zuciyata amman sai bata
nunaba domin ta qagara da subar wajen
Kuma zamuga iyaka badai nanda kwanaki goma
sha bane kawai basu qara kulasuba Sukai
gabaabinsu
Da yammah afnan na cikin asibitin don sai a
yanxu take sanar da inna da malam
Halin da ake ciki
Hankalinsu ya tashi sosai don daman Tunda aka
tafi da adnan suke cikin tashin hankali su dakai
keta hidiman neman dan nasu hukumomin yan
sanda kuwa har
Head quaters saida sukaje
Amman babu lbr
Ko a yanxu da afnan din ta fada musu inda
aleeyun yake saida ba
Lfy hakan yasa suka qara shga cikin tashin
hankali marar misultuwa
Sannan suka fada mata cewa gobe sunanan
isowa asubitin
Afnan dunia tai mata kunnci ita kadai ta zauna
tai tagumi babu abinda take tunani
Sai rayuwarta ta baya
Rayuwar da tayita cikin farinciki da walwala
yanxu itace duniya ta juyama baya haka?
Yanxu haka so take taga halin da mijinta yake
ciki gashi sady tace wai an fitar dashi waje ko a
wani irin hali yake yanxu oho
Sady ta shgo asibitin tana cikin kayanta na
yansanda inda Wasu cikin yan sandan ke take
mata baya
Hannunta riqe da wata yar qaramar bindiga afnan
ta miqe cike dajin
Dadin ganinta sannan suka koma suka zauna
Afnan tace wlh Kamar kinsan cikin tunaninki
yanxu haka nake sady
Tunanin mai gidana yashamin kai burina kawai
naje na ganshi Naga halin da yake ciki
Sady tai daria gamida dafa kafadarta tace am
sorry qawata nasan yaddah kikeji yanxu dole
kadaici zai dameki
Amman insha allahu komai ya kusa zuwa qarshe
dan kuwa likitan dake dubashi
Ya sanar dani cewa ya farfado
Saidai matsala daya yayi loosing din memory
dinsa gaba daya ya rasa contact
Din dake kwakwalwarsa tace saidai ba komai
komi zai daidaita
Wani Baqin gilashine a fuskarta ta sako Wasu
matsatstsun kaya ta wani yar yalolon gyale tana
tafe tana taunan cingam ta iso asibitin escote
dinta na take mata baya sai mazurai suke
Gaban afnan ya fadi dan batasan yau ko dame
taxoba ta qaraso har gaban nata tana qare mata
kallo inka gansu ka rantse kace ba uwa da ya
bace cewa zakai
Qawayene ko kuma ya da qanwa
Don nafi Jikinta girkakken jikine ba zaka taba iya
cewa ta aje yaro dan shekara biyarba
Taja wani dogon murmushi mugunta tana qarema
afnan kallo tace lallai yarinya kin guji arxiqi kin
fadama tsiya na sakaki a cikin daula kin fito kika
fadama tsiya
Tabbas Kinyi kuskure da har kika gujemin kikabi
ubanki Wanda a yanxu yake tafin hannuna
In naso ya rayu in kuwa na juya kanbuna a yanxu
sai yabar dunia
Lallai ina tabbatar miki da Kinyi zaben tumin dare
kuma a sannu zaki tabbatar da hakan
Don dagake har mahaifin naki sai Ruwan da zaku
kurba ya gagareku badai dani zakujaba
Ai duk Wanda Yaja dani to shine zaisha wuya
kuma na rantse miki saikin dauka ba nine
mahaifiyarki
Domin kiyayyar da zan nunama babban maqiyina
irinta zan nuna miki
Kuma a bainin jama,a don nayi rantsuwa duk
Wanda ya nemi
Rushemin duniyata to tabbas saina fara rushe
tasa
Kuma na rantse miki Nida ke ta murza yan
yatsunta Sukai qara tace kukan kurciya zawabine
saimai hankali ke ganewa ta juya ta fice tana
musu dariar mugunta ita da mahaifin nata escote
dinta suka rufa mata baya
Afnan ta sulale ta zauna a qasa hawaye nabin
kuncinta tace shin anya kuwa momcy ita ta
haifeta itace mahaifiyarta wacce ta dauki cikinta
harna tsawon wata tara kuma Tasha whlr
nakudarta
Ta Dade tana zargin wannan a zuciyata amman
bata taba Tambayar waniba amman yau ta
tabbatar ma zuciyata
Aleeyu Wanda ke kwance duk abinda ke faruwa a
kunnensa ake
Ya kira sunanta cikin sassanyar murya
Afnan kiyi haquri ki daina kuka ki rungumi
qaddarar da Allah ya daura miki
Insha allahu zakici ribar rayuwa ko Bayan raina
karki taba canja halayyarki
Na sanki da haquri gaskia da wadatar zuci inhar
kika riqe wadannan sune makaman rayuwa
Afnan muna cikin jarabawan ubangiji Bawai yin
Allah na rainaba afnan
Domin shikeda komai kuma mai ikon yin komai a
duk sanda yaso
Kuma duk abinda yai ba,a tambayarsa dalili
Afnan karki zargi mutane da naimansu da laifi
afnan ki dauki Kowa mutumin
Kirki saidai Wanda ya bayyana mugun halinsa
Ki kyautata huldarki da mutane ki cika musu
alqawari inya kama tsakaninki dasu ki fada musu
gaskia koda kuwa basasone
Kiyi haquri da wautar wawaye daga cikinsu. Kiso
mutane har cikin zuciyarki
Ki jawosu jikinki ki tausaya musu ki taimaka
musu ki janyosu ga shirya da qarfinki
Da maganarki da dukiyarki
Ita duniya ba azzaluma bace duk yaddah ka zabi
rayuwa cikinta ba baki takeba
Akowane irin hali kikaga mutun a cikinta shiya
zabama kansa
Mai kyau ko marakyau
Babu wani Wanda zamani zai zalunta face shine
ya fara zalumtan kansa
Babu kuma Wanda zamani zai kyautatamawa
face shine ya fara kyautatama kan nasa
Karki yarda ki girmama son ranki sabanin gaskia
dason Binta a matakan rayuwa
Babu wani mai janyoma kansa tsiya da kansa
face son zuciyarsa
Domin shine wakilinn komi kuma karkiyi Tunanin
qoqarinki da himmarki zasu kaiki ga samawa
kanki alkhairi a,a dole saida taimakon mahaliccin
ruhi da gangan jiki
Mahaliccin sammai bakwai qagaggu da qassai
bakwai....
Ya kasa qarisawa Sbd kukan dake koqarin kubce
masa
Cikin murya sarkakkiya yace ya Allah kada ka
baini ikon saba Maka a duk
Halin Dana tsinci kaina
Dadi ko wahala afnan ki riqe maganganunnan
nawa tamkar wasiyyah nake baki
Nasan ko Bayan raina zasuyi miki amfani
Kuka afnan din take sosai
Tace Haba Abba mai yasa kakeson tasarmin da
hankali kasa na kasa runtsawa
Yanzu idan ka mutu dawa zan rayu?
Waxan riqe ya zama bangon da zan jingina
rayuwata ? Abbah
Dan Allah karka mutu ka barni please banda
Kowa sai kai ba yaya adnan
Ba momcy Abba inna rasaka nima kashe kaina
zanyi
Yace subhanallah Haba afnan kina nufin duk
nasihar da nai miki ta tashi a banza kenan?
Ai duk musulmi na gari saiya yarda da qaddara ta
alkhairi dama wacce bata alkhairi ba
Kuma ita qaddara duk Wanda ya dauketa. Bazaiyi
rashin madadiba
Sannan banda abinki ai bacemiki nai mutuwa
zanba
Sannan ki zama mai tawakkali a duk yaddah
rayuwa taxo miki
Cikin mutyar kuka tace to abbah
Yace yauwa kokefa ki saki jikinki da walwalarki
insha allahu abbanki zai taka da qafafunsa
Ta dago tana kallonsa sukaima juna murmushi
Washe gari Tunda safe su inna suka iso don haka
afnan ta nemi tranfer zuwa wani asibitin domin
kare lfyrsu don haka kai tsaye asibitin yan sanda
suka nufa Wanda ke cikin babban headquater
Inna da malam sunyi kuka sosai da rana sady
taxo din wucewa airport
Sun mata godia sosai itama
Don haka afnan har filin jirgi ta rakata taaji Inama
da ita za,ai tafiyan
Tana kuka har sady ta lallasheta da kalamai
masu kwantar da zuciya saida jirgin nasu ya tashi
Sannan ta dawo asibtin cike da kewar mijinta
Jikin aleeyu ya qara kyau don har yana dan iya
dogarawa da sanda malam ya dage wajen yin
masa addu,a ba dare ba rana
Don haka Shima aleeyun zuciyarsa ta rage zafi
ganin iyayensa kusa dashi gashi asibitin da suke
asibitin mai cike da tsaro
Wato police hospital. Ita kanta afnan yanxu tadan
rage kadaicin da take ciki
Aleeyu yasa afnan ta kira masa mahaifiyar nafi a
waya ya sanar da ita duk abinda ke faruwa itama
duniyar nemansa take don kuwa su kausar sun
fada mata duk abinda ya wakana a wajen bikin
nasu afnan din
Don haka ana gobe za,a koma zaman kotu suka
iso mahaifiyar nafin da kausar sai wani kawunsu
A hotel din garin suka sauka don asibitinma saida
dare sukaje ba Wanda yasan sunxo
Ita kanta sady data samu kwana bakwai a.
Germany
Da dare ta sauka don haka Tunda safe ta wuce
office domin rarrage Wasu yan ayyukan dake
gabanta na Wasu takardu dake gaban tebur din
nata
Tanayi tana duban agogon dake tsakiyar
hannunta
Taga ashe da sauran tyme don itakeson taje ta
dauki su afnan da iyayensu momynta da na
daddyn nata duk su rugunzuma zuwa kotun
Don haka Hatta kayan break din da aka kawo
mata ko kallon inda suke bataiba
Kamar daga sama taji an banko office din nata
don haka ta daga kai tana kallon mai shigowar
don haka cike da qasaita ya janyi kujera ya zauna
Sukai facing
Dinn juna yana mata wani irin murmushi
Yace sadiya muhammed mai nasara kina neman
zaremin mutuncina a idon jama,a to inaso ki sani
lallai sai Naga bayanki
Bata sauqiba a sannu a sannu na rantse sai Kinyi
mutuwa kala dubu kafin kiyi ta gaskia yace na
lura lallai bakisan koni wayeba
Sady ta tashi cikin zafin rai ta nunashi da yatsa
tace
Wayekai inba tsageran dan ta,addaba Wanda
rashawa ta haifoka zuwa wannan duniyar. Ka
tuna da oder da kayo ta miyagun kwayoyi
Toka tuna munada rahota Akan haka domin kuwa
mun rigada mun siye Wasu daga cikin yaranka.
Wanda kake taqama dasu sukasan sirrin ka
Tasa hannu ta kashe yar qaramar radion da take
recoding ba tare daya saniba
Ta kwalama. A,s. P. Kira ya shigo da sauri
Tace
Me zatace Oho nima ban saniba
Aure. Kan. Aure. End ov. Book2
Chapter25
Tace yi maza ka kira yan jarida. Ya sawa adnan
hodar iblis
Shikuma ai maza a loda giya da garwarwakin da
aka da Wasu daga cikin mutanensa dasu. A cikin
motarsa da zasu tashi nanda minti ashirin
In an loda sai a kira yan jarida maza nnanda
minti goma
A kama mutanen nasa
Zaiyi yinqurin tashi Wasu daga cikin yan sandan
suka maidashi
Suka zaunar tare da jona masa kan bindiga
Sady tai tattaki zuwa gabansa tana jujjuya kan
yar qaramar bindigar dake hannunta tace
Tabbas ka girgiza ranka shidade daga dan
wannan Abun harka tsorata?
Ina ikirarinka na fadin sai kasa nayi mutuwa kala
dubu kafin nai ta gaskia
Ta duqa gabansa tana murmushi tace lallai ka
tabbatarma duniya kaine kai fitsari a wando Sbd
tsoro. Dagamu saikai a office dinnan baka sanar
ma Kowa abubuwanka na sirri
Sbd baka yarda da mutane saudayawa sukanci
Amana kaikuma ka kudurcin ganin bayansu
To inaso ka sani yau asdy mai nasara zatayi
nasara akanka Kamar yaddah ta saba
Don tana tare da babban yaronka Wanda kayi
yarda dashi duk a cikin yaranka
Abro. Yanxu haka yana tare damu dakaje kotu da
karkaje ya rage naka
Cike da bacin rai da kunar zuci ya watsar da yan
sandan
Idanuwansa duk sun kada ya nunata da dan
yatsa
Karya kike sady baki isa kiga bayana saidai ni
Naga bayanki
Karki sake Abro ya isa kotu inkuwa harya isa
tona rantse sai Kowa rasa ransa
Don Dana wulaqanta a duniya gwara nabar ta
gaba daya
Ya juya a zafafe ya fice ba tare da wani yayi
yinkurin hanashiba
Sbd tsorata da Sukai da idanunsa don ita kanta
sadyn yana fita taja wata ajiyar zuciya
Ta Dora kanta saman tebur lokaci daya kuma ta
saki murmushi irin na alamar nasara
A babban kotun jami,an tsarone a tsaye suna
binciken duk Wanda zai shiga da wani abu inhar
na cutarwa ne
Janar Yaso ya hana saida sady ta kira shugaban
qasa sannan ya tsawatar masa Akan ya bari ai
duk wani bincike daya kamaata Sbd tsare
rayukan al,ummah
Hakan bai masa dadiba dukda yana zaton ba,a zo
da duk wadanda yake zaton za,a zo dasu ba
Don haka Yadan samu natsuwa kadan kotun ta
cika tayi maqil
Inda mai shari,a ya buqaci lauyoyi dasu. Gabatar
da shaidunsu
Lauyan Wanda ake qarane ya soma tashi ya
gabatar da shaidunsa marasa mafari
Sannan Lauyan dake kare. Wanda ke qara
barister nasiru adma ya miqe
Ya dubi mai shari,a yace yamai girma mai shari,a
inason na gabatar da saidata ta farko wato
kakannin afnan
Alqali yace kotu ta baka dama
Inna da malam suka fito
Yace malam so muke ka fadamana sunanka da
kuma matsayin aleeyu a wajenka
Ya fada masa ya tambayi Inna itama ta fada
masa. Sannan yace
Ko zaku iya fadama kotu yaddah aka nemi auren
afnan da adnan?
Malam yace tun yaran suna qanana aleeyu ya
sanar dani cewa yanason hadasu aure idan sun
girma Bayan sun girmane yake sanar dani cewa
matarsa naneman
Wargaza masa shirinsa. Wai yarta ba zata auri
wani matsiyaciba
Ya sanar dani Wanda ta kawo sannan yake sanar
dani cewa ba mutumin kirki bane
Don haka shi bazai bashiba nima na goyi Bayan
hakan
Don har yake sanar dani suma iyayen matar tasa
basu yarda da zabin da uwar tata Taima yar tata
ba
Don haka mukaja daurin auren zuwa wata daya
cif
Biki saura sati daya cif yaran suka iso kauyen
suke sanar dani mahaifiyar yarinyar ta samarma
yarta waliyar ranar alhamis za,a daura auren
yarinyar da Wanda takeso jin hakan yasa muka
yanke shawara gari na wayewa Bayan sallar
azahar
Na tara mutane a qofar gida aka daura auren
nasu
Ranar goma ga watan goma shekara ta dubu
biyu dasha biyu
Lauya yace mun gode suka koma mazauninsu
Yasa aka gabatar masa da mahaifiyar nafi itama
ta maimaita Kamar yaddah malam ya zayyano da
zuwar da nafin tayi Akan suk zama waliyan
afnnan sukaqi mahaifiyar tata ta koreta
Barister yace wancan zaman sunce ranar goma
sha biyu ga wata aka daura auren afnan da janar.
Amman yanxu gashi bincike ya nuna an Riga
daura auren
Afnan da adnan sannan akaxo aka daura auren
afnan da janar aure kan aure kenan
Alqaline zai fadamana a yanxu matar Waye Tunda
su duka ai musulmai ne
Sannan yace yanason akawo masa manyan
direrobin janar dayafi ji dasu
Aka kawosu jikinsu sai tsuma yake
Lauya yace kunsan dai yanxu Kuna hannu dagaku
har mai turaku zuwa aikin ashshar kuko? To
bakuda mafita yanxu munaso ku fadama kotu
sunanku da kuma aikinku
Daya yace sunanan victor dayan kuma yace
sunana emmanuel
Dukkansu direbobine kuma matuqan dake daukan
mutane a yayin da yaqi ya afkawa Wasu qasa da
sunan masu cetonsu saisu kamasu su harbe daya
Bayan
Daya.
Lauya yace dasa hannun wa duk kuke wannan
aikin?
Sukace dasa hannun general abdullahi aminu
Abba
Lauyan yace to mun sannan yan sanda suka
kamasu Sukai waje dasu
Sannan ya qara cewa inason a kawomin Abro
yanxun
Janar yai saurin miqewa idanunsa a warwaje
jikinsa sai kyarma yake
Ya zaro bindiga kamin Kowa ya ankara ya dauke
kan Abro din da ake niyyar kawowa
Abinda ya jawo Hankalin jama,ar dake kotun
kenan kamin kace me hargitsi ya kaure
Yan sanda da sojoji suka dinga yunkurin kare
rayuwakan jama,a
Daqar akayi nasan riqo janar sai rawar jiki yake
yana niyyar fixgewa
Anan alqali ya dakatar da qarar yasa aka tsare
masa janar da nafi da taci uban dress ta kame
Jikinta sai rawa yake Kamar tai fitsari a wando
lol
Aka dauki gawar Abro babban sojane nan Kowa
ya watse
Sati guda tsakani aka yankema tsohon comander
general abdullahi aminu Abba
Hukuncin kisa ta hanyar rataya Bayan an cishi
tarar kudade masu yawan gaske
Ita kuwa uwar gayyah hajia nafi hukuncin daurin
shekara ashirin da biyar aka yake
Mata a gidan yari da horo mai tsananisbd cin
mutuncin addini da tayi tare da mummunan
sharrin dake daukar hukuncin rataya ga mutanen
da basujiba basu ganiba tare dacin tarar bata
musu sunan datayi
Tayi kuka Kamar me taita rogon gafarar iyayenta
amman
Sukaqi kulata Kowa kyamarta yake
Sati guda da gama case din aka salllami a aleeyu
daga asibiti ya samu lfy masha Allah
Dukda kuwa da sanduna yake yawo
Don haka suka tattaro suka dawo garin kano
Ita kuwa sady daman tun Washe garin yanke
hukunci ta wuce. Germany wajen mara lfy inda
tace insha allahu inhar ta dawo zata dauki afnan
domin taje taga mijin nata kuma ta kula da lfyrsa
Akeeyu kuwa kai tsaye gidansa yasa aka wuce
dasu gaba daya
Iyayensama sawa yaai aka taho musu da duk
wani abu nasi da zasu buqata
Daga can qauyen nas sannan ya dauko Wasu
daga cikin yan uwan nasa yasasu a cikn gidan
kasancewarsa qaton gaske
Don haka yanxu afnan batada wani kadaici saina
mijinta
Gashi kwanannan ba abinda take fama dashi sai
yawan kasala tashin zuciya da
Yawan barci
inna na lura da yanayinta don haka tasa aleeyu
ya kira likita domin dubata
Bayan likitan ya gama yan gwaje kwajensane
yake sanar dasu cewa tanada juna biyu
Ba qaramin farinciki inna taiba dan daman tun
lokacin da adnan ya kebe da afnan ta Fahimci
wani abu ya faru a tsakaninsu dan haka ta wayar
da kowa
Babu Wanda baiyi farinciki a cikinsuba dan kuwa
harsun fara fiddah rai da
Adnan dan har yanxu babu amo ba lbr
Wayarma da ssuke da sady yanxu idan ta kira
baya zuwa saidai babu Wanda yeke nuna mata
damuwarsa ta rashin dawowar adnan din kasan
cewar kartasa ranta cikin damuwa
Itama bangarensa tana cikin damuwa saidai
ganin Kowa yayi biris da lamarin yasa itama ta
daure zuciyata. Taci gaba da rainon cikin nata
Wasa wasa har an share wata biyu duk wani
qoqari da aleeyu zaiyi Akan ganin ya samu full
information Akan sady amman ina abin yaci tura
Tun afnan na daure zuciyata harta Gaza taje ta
samu abbanta da maganan
Ya lallasheta yace
Yace insha allahu Zamuji alkhairi afnan inaji
ajikina suna lfy
Kasa daurewa tayi ta nufi gidansu sadyn har
yanxu mom dinta cin duniyarta da tsinke take
tasan komai Akan sadyn
Amman saita rufe domin cimma wata manufa
tasu
Da afnan taje ta sameta sai ce mata tayi suma
nemanta suke ruwa a jallo
Dan haka babbu yaddah ta iya dole ta koma gida
qafafu a sake
Tun a hanya take kuka harta isa gida
Duk gidan sun kasa gane kanta ta kasa cin komai
sai kuka kawai
Don ita yanxu ta Gano mijinta baya raye
Lallashinta kawai suke dan su kansu sun tausaya
mata ganin abinda ke gabanta
Cikine dan wata biyar amman saika rantse kace
dan wata tara ne
Don haka malam ya duqufa wajen yin mata
Rubutun dangana
Kuma anyi nasara don zuciyata ta rage mata
radadi da zugin da kalamanda yake mata Wanda
suke dawo mata tamkar a lokacin yake furtasu
Afnan idan na mutu Sbd ke zanbar tarihin da za,a
Dade ana tunawa dani a
Duniya
Wlh danace na barki gara raina ya zama fansar
wannan furucin
Ta runtse idanunta cikin kuka tace kayi haquri
yayana ni kainabazan iya rayuwaba idan baka ina
ka shgane kabar mai sonka?
Tambayar da bata da amsar sa sai kuka
Cikinta ya shga wata tara babu abinda aleeyu bai
siya mataba daga Wanda ta fada harda wandama
bata fadaba badon komaiba saidon kawai ya cire
mata damuwa amman ina Abun Kamar qaruwa
yake
Duk kuwa da doctor wajen scanning ya fada mata
cewa yan biyune
Amman ina tausayin yayan natane ya qara
shgarta
Don bata taba tsammanin rayuwa zatazo mata a
hakaba
Kullun tsara yaddah rayuwarta zata kasance ita
da mijinta da yayanta take amman abinda bata
saniba ashe yayan nata marayu zasu zama
Hakan kesa tayi kuka sosai har sai taji ba dadi
kuma ba mai lallashinta
Nakuda taxo mata cikin sauqi kasancewar tana
tare da inna
Don haka ta haife yan yayanta mace Dana miji
kyawawa masu kama da ubansu
Washe gari haihuwar afnan ta karade ko ina
Dan kuwa anty kausar dinta zuwa tayi ta tare a
gidan domin kula da mai jego da kuma kyawawan
baby's dinta
Taron suna na gani na fada anty kausar ta hada
an gayyaci masu hotuna da videos
Yara sunci sunan aleeyu da mahaifiyar nafi macen
ana ce mata taslim na mijin kuma aslim anci
ansha a wannan suna Kowa sai sha,awar yaran
yake daka gansu Kaga afnan da adnan Kamar har
taso ta baci
Aleeyu ya saukar mata masu raino don haka bata
da wani matsala dan ko kukan
Dare basayi inhar ba bra zata basu ba
Afnan ta soma saki da lamarin sady da adnan
don ta tabbbata basa raye
Shiyasa ta soma service dinta amman fa ba
ruwanta da
Hulda da maza harkar gabanta kawai take duk
wani abu dazai hadata danamiji
Bata kusantarsa
Yaran afnan sun fara wayo don harta fara
shawarwarin yayesu
Amman aleeyu ya hana yace ta barsu su qara
girma da kwari don duka dukafa shekarunsu daya
da wata biyu
Amman girma da wayon da Sukai saika dauka
yan shekaru biyu ko biyu da rabi ne
Harkokin aleeyu sun bude tako,ina ya gyara
al,amuransa abinda ya faru dashi
Saima ya qara masa farinjini a idon jama,a
Don sai suke ganin kaman abokan adawane Sukai
masa haka
Da sanyin safiya afnan tana saman capet dinta a
cikin falonta da abbanta ya gyara mata fiye Dana
da alokacin dama masu aslim salak take
Taji wayarta tana ruru Kamar karta dauka Sbd
abinda takema yaran
Ga gwarancin da suke mata alamun dai sun qosa
da susha salak din
Saida wayar ta kusa kashewa sannan ta dauka ta
Kara a kunne
Hello muryar wacce taji tasa takusa barar da
abinda take cikin murna tasa ihu tace sady
daman kina raye sady ina mijina dan Allah ki
fadamin inda mijina yake
Ina cikin kewarsa ina buqatarsa kusa dani please
sady
Sady tace sha kuruminki qawata ina kusa da
mijinki yau dinnan zamu dawo nanda Wasu yan
awanni
Don haka kizo ki tari mai gidanki ke kadai dan
Allah afnan kiga yaddah yake cikin qoshin lfy
Cikin zumudi tace insha allah sady yanxu zan iso
kodai baya maganata ne?
Naga baya nemana?
Sady tace kedai kin cika shegen dumi ki tashi ki
shirya ki taremu a airport dan ban fadama Kowa
dawowarmuba ke kadai na fadamawa don zuwan
bazata nakeson yinma kowa
Jiki na rawa ta miqe tace toto ganinan zuwa.
Yanxu ta nufi sashin inna tana kwala
Mata kira inna inna inna tace oh ni yasu wannan
kiran mafarauta haka afnan
Ta rungumeta tamkar ta samu adnan din tace
inna adnan yana raye nanda awa biyu
Jirginsu zai sauka
Inna tace niko kinsan banson qarya yanxu haka
wanine keson yaudararki yake tsakonarki da
adnan na rayeafnan tai wata daria harda
kyalkyalawa tace Haba inna
Waye zai jani da irin wannan zolayar inhar ba
raina yake nemaba yace anga yaya adnan tace ai
inhar naje Naga bashi bane mutuwa kawai zanyi
Inna tace. Hmm Allah dai ya kyauta ta miqe da
sauri cikin zumudi ta nufi sashinta
Domin cancaro kwalliya
Kwata Kwata ta manta da batun yaranta da take
damama salak tana shga bed dinta toilet ta fada.
Ta bata mintuna sha biyar wajen yin wanka
Bayan ta fitone taje gaban dressing mirro Bayan
ta gama kwalliyar ne
Ta nufi wadroff dinta can idanunta suka sauka
kan wata doguwar Riga irinta
Larabawa tace tabbas yaya adnan Nason kalar
kayannan
Don duk lokacin datasa inya ganta sai kaji yace
kai qanwata kinga yaddah kika hade kika zama
jinsin larabawa kuwa ?
Wlh qanwata kedin ta dabance gaki kalar
indiyawa gaki kalar larabawa sannan
In kika sauya saiki koma hausa fulani tsab lallai
ni nayi sa,ar samun mata daya
Tamkar da dubu
Na rantse ina sonki matata Bawai so na wasaba
so na gaskia Wanda bashida
Algus
Tai murmushi gamida hanzarin janyo rigar mai
kalar sararin samaniya
Wato sky blue
Wohoh wani abin sai Wanda e gani. Wato wani
madarar kyau tayi alokacinnan duk Wanda ya
ganta kai koda maqinyintane saiya yaba da
wannan kyan da tayi
Ni kaina admin na yaba dandai kawai ban fara
love bane amman da saina taya lol
Wato ita kanta data dubi madubi ta qarema kanta
kallo tasan tayi kyau iya kyau
Tace no wander shi yasa duk sanda ta fita maza
keyo mata ca ashe kyan nata na dabanne
Taja jakarta gamida makullin motarta da wayarta
tana fita Sukai karo
Da taslim da aslin
Duk sun bata jikinsu da salak din sunyi dame
dame sai yanxu ta tuna dasu ta dafe kai ta
kwalama mai kula dasu kira ta qaraso da
saurinta tace maza dauki yarannan kije ki kyarasu
dubi yaddah duk suka bata jikinsu
Tace to ranki shi Dade ta kwashe su tai hanyar
sanshinta dasu
Tana kallonsu taji tamkar ta kwashesu ta
kaimasa yaransa ya gansu
Amman ina shiryasuma yanxu bata lokacine
Abakin qofar inna ta tsaya tace ro inna na tafi
kimin addu,a don bazan shgoba ki riqeni tai
murmushi tace to afnan Allah ki bda sa,a ya
kuma kare mana ke
Tace amin inna sannan ta juya ta fice abinta
Bata dauki direbaba qatuwar jeef din abbanta ta
dauka domin taji dadin zubosu da tarkacensu
gaba daya taja motar ta nufi filin jirgin aminu
kano
Lokacin data isama jirgin bai rigada ya isoba bini
bini ta duba agogon dake
Hannunta ji take tamkar ta yayo jirgin da hannu
Cikin ikonn Allah jirgin ya sauka afnan ta dinga
ware idanu don ganin ta inda zasu
Fito Kamar daga sama ta hangosu cikin jerib
mutanen dake saukowa
Idanuwan afnan suka sauka kan fuskar data
zame mata baquwa ji take tamkar ta kwasa da
gudu ta runguMeshi
Cikin kyakkyawan girjinsa wacce ke manne da
baqar shirt
Arainta tace lallai turai ya amshesa ya qara wani
kyau da haske kwarjininsa ya qaru
Ita gani takema ya sake zama mata wani dan
gayu lallai zaman turai ya amsheshi
Batayi auneba har suka kusa qarasowa wajenta
ta. Tattaro na tsuwar duniyarnan ta daurama
kanta ta nufesu fuskarta dauke da fara,a
Saidai yanxu kallonta ya koma kan kyakkyawan
diyar da sady ta rungumo mai kama da adnan din
Don haka koda suka ida yarinyar ta karba
hannunta na rawa tace
Tace. Sannunku da zuwa sady tai murmushi tace
yauuwa afnan
Sai yanxu ta lura da wani haske da qibada sady
ta qara kyanta ya qara bayyana
Tana sanye da shga irinta mutanen turai da Baqin
gilashi a hannunta
Afnan fara,arta da mamakinta sun kasa boyuwa
tace sady a ina kika samu baby haka so beauty?
Ta qara murmusawa tana kallon adnan Wanda
yaketa yamutsa fuska da alamar duk tsayuwar ta
gunduresa
Yarkice afnan
Afnan ta zaro ido tace yata kuma ta ina?
Ta qara murmusawa kamin tace wacce na haifa
Nida adnan a zamanmu. A. Turai
Bayan an daura mana aure secretly amman ki
gafarceni afnan munyi hakanne kawai dan gudun
sabama allah
Kinsan duk inda namiji da mace suka hadu to
shaidanne a tsakaninsu
Ma,ana na ukunsu
Babu inda baya rawa a jikin afnan Hatta yatsun
qafarta hakan yasa sady tai
Saurin amsar babyn nata afnan ta Kure
Adnan da kallo kallo mai cike da mamaki tsana
da kiyayyah
Shima kallon nata yake saidai nasa kallon na
rashin sanayyah ne
Sannan ya maida kallonsa kan sady cikin
sanyayyar murya yace wai me kuke tattaunawane
hake keda wannan bagidajiyar
Woooooot kuuut yau adnan ni yake kira da
bagidajiya
Wait wait wair wait jama,a shin wai ya manta da
itane zaman da Sukai a a turai
Basu hadu bane. Koko halin da namijine
ohoooooo nima ban saniba mu hadu a
Book3. Danjin yaddah zata kaya
Zamu xan fara qila yau amman idan Naga.
Comment kenan
Naku har kullun
Abdallah s. Salankzz
Wasu na qorafin ba,ayi da wuri kuma a dingayin
musu post sau biyu a rana
Amsar buqatarku itace. I. Can't. Sbd me. Course.
Idan nai post
Aure. Kan. Aure
Chapter26. @book3rd
Muje zuwa admin
Zuciyar afnan tamkar ta tsinke qirjinta sai faman
rugurguza yake
Yaddaha adnan ke mata kallon rashin sani yasa
zuciyata qara dagulewa
Ta juya da saurinta ta fada motarta ta fizgeta da
qarfin tsiya
Tamkar mai shirin tashi sama tahau titu idonta
ya rufe
Itadai tasan tuqi take amman batai auneba saidai
ta ganta ta yanki cikin daji
Batayi yunkurin dakatar da motarba har sai
dataga tayi nisa a cikin dajin wajenda babu wani
dan Adam mai giftawa
Ta bude ta fice daga cikin motar tamkar wacce
bata cikin hayyacinta
Ta nutsa cikin dajin tamkar wacce aka datsema
kaqa ta fadi a cikin
Rairayi
Ta duqa a wajen kuka take na Fitan hankali ta
rasa lissafin kanta
Babu mai lallashin zuciyata ta qara daukar
matuqar ruri
Kuka take sosai tana kife a wajen har rana ta
gama faduwa
Duhu ya fara wani iska da sanyi ya fara saukowa
irin sanyinnan marar
Dadi mai shga qashin nan
Saidai ita ba sanyin ya dametaba zafin da
zuciyata ya dauka ya zarta duk wani
Radadi da zai ratsa jikinta
Batada mafita illa ta miqe ta kama hanyar data
biyo
Tana tafe tana tangadi tamkar wacce Tasha wani
abun maye
Tayi tafia mai nisa bata iske inda motarta takeba
don harma ta fara fiddah
Rai da ganin nata. Don lokacin data fita ko key
din jikin motar bata zareba
Ta soma gajia sosai don haka ta soma neman
agaji saidai wayar tata itama tana cikin motar
Don haka ta fiddah rai ta soma dibar sayyada
can ta hango duhun motar
Batayi tsammanin ita din bace sai data ganta a
gabannta
Ta shga ta dau hanyar gida
Zuciyata na mata lissafe lissafe harta isa gidan
nasu
Lokacin an kammala sallar isha,i. Don haka ta
fada cikin gidan
Bataso ta samu Kowa a babban falonba saidai
hakan bai samuba
Domin aleeyu inna malam da yan aiki duk suna
cikin falon
Hankalinsu a tashe
Tana shga sukayo kanta jikin aleeyu har rawa
yake. Ina kikaje afnan?
Ina kikaje kika tayar mana da hankali?
Afnan Waye yace miki kije anga adnan. Iye?
Jikin mahaifinta ta fada tana kuka sosai marar
sauti. Abban nata ya shga rudani matuqa dama
duk Wanda ke falon
Inna ta janyeta daga jikinsa ta zaunar da ita a
saman kujera
Tace ya akaine afnan kiyi magana mana kinga kin
jefa mahaifinki cikin tashin hankalifa
Dubi jikinki saceki akai?
Ganin yaddah duk suka tashi hankalinsu yasa
afnan tsagaitawa da kukan
Muryarta na rawa tace babu Wanda ya saceni
inna yaya adnan ne ya dawo
Dan har sunyi aure shida sady qawata
Wacce ta taimaki su Abba wacce ta fitar da
adnan din qasar waje sunyi aure inna harda yarsu
Inna auren sirri Sukai yaya adnan ya mance dani.
Ya zareni daga zuciyarsa baya
Buqatata a cikin rayuwarsa. Yama mance
kamannina yanxu haka nunawa tai
Wai bai sanniba har yake kirana da bagidajiya ni
inna ta qara fashewa da kuka
Duk Wanda ke wajen ya tausaya mata aleeyu
yace ban yarda adnan bane
Tabbas adnan bazaiyi miki hakaba tabbas saidai
idan maqiyane
Zasu biyo tanan su rarraba hankalinki
Amman adnan bazai taba miki hakaba
Afnan ta miqe da sauri idanunta na qara zubda
hawaye ta riqe hannun
Mahaifin nata ido waje tace. Karkace
Haka Abba ko.a cikin maza dubu zan iya tsamo
yaya adnan
Abba ka yarda dani yaya adnan na gani da idona
Abba ya riga
Ya manta dani
Cikin dakewa irinta manyan mazaje yace bani
number da aka liraki da ita
Hannunta na kyarma ta lalubo number a wayarta
tace ka kira Kaji Abba
Bazan Maka qaryaba
Ji yai tausayin yar tasa ta qara narkar masa da
zuciya. Ya lalubo dakiyar dunyarnan ya daurama
kansa bugu daya aka dauka ya fice suna
Magaba afnan ta nufi sashinta tana sharar kwalla
Kan gadonta ta fada ta bude wani babin kukan
tace yanxu shikenan soyayyar da muka Dade
muna ginawa ta zama saidai tarihi kenan
Yanxu soyayyah ta da adnan ta zama tsohon
yayi kenan
Yanxu shikenan yayana sunyi rashin uba kenan
Innalillahi wainna ilaihirrajun
Abinda take nanatawa kenan yan biyun aslim da
taslim suka shgo falon
Da gudu suka fada Jikinta suna mata yan
kwarancinsu
Afnan ta kamosu ta rungume ji take tamkar ta
tsaga kirginta ta shgar dasu Sbd wani santsar
sonsu dake fizgarta nanfa taci gaba da rera
kukan nata Kamar waqa lol
Lamarin nata ya soma tsorata Kowa a gidan dan
kuwa bata da wani aiki sai kuka
Abinci kuwa yaddaha aka kai mata na safe haka
za,a kawo mata na rana a tafi Dana safen yaddah
aka kawo mata na rana haka za,a kawo mata na
yammah a
Tafi Dana ranar gaba daya ta daina cin Abinci ta
rame
Yanxu batason magana ta zama wani slent
Duk inda inna taso wajen kwantar mata da
hankali amman ina Abun yaci tura
Dangin mahaifiyarta suna zuwa akai akai
Musamman Maman nafi da take kira da hajia
Itama tana zuwa anty kausar ma haka
Domin kuwa sun rabu ita da mijin nata babu aure
a tsakaninsu kasancewar tundaya aureta bata
haihuba hakan yasa ya qaro amarya
Zama kuma yaqiyin dadi musamman da amaryar
ta samu ciki ta dinga hada kausar din damai
gidan nasu kai taji dai ba zata iyaba nan ta nemi
saki
Dan daqar ya iya sakin nata domin kausar irin
matannanne
Wadanda da wuya namiji ya iya rabuwa dasu
Yaudai lamarin afnan ya soma isar inna dan haka
koda takai mata abincin rana ta samu bataci na
safeba saidai dan lemon datasha
Inna ta zauna tana kallonta taga duk ta fige ta
lalace tayi baqi
Inna tace lallai afnan kinsa ranki a wani irin
yanayi Indai namijine to a lbrn maza
Ba abinda kika fara gani
Ki zaunba ki kashe kanki a banza a wofi.
Wandama kike danshi baisan kinayiba
Yanacan yana shagalinsa da wata macen ya barki
anan
Kina wahalar da kanki
Nidai shawarata gareki kisama kanki dangana
inkinqi to dan Nidai bazansa a kiramin adnan na
rokeshi ya maidake dakinkiba
Dan mu kanmu ya manta damu da irin alherinmu
gareshi dan haka kisama kanki salama
Ki cire wani adnan a ranki ki samo miji kiyi
aurenki kawai
Da sauri ta dago ido tana kallon inna tace yanxu
da aurenya ake fada mata ta samo wani namijin
ta aura bacin auren dake kanta itako ai koda
cewa akai adnan ya mutu batajin zata iya sake
aure
Ballentana yanna raye ta lumshe idanuwanta
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanun
Inna ta miqe gamida Jan wani tsaki mtwss Indai
kayane ke kya kaisu yarnan
Ki zauna ciwon zuciya ya kasheki don Indai
mazane a hadisin maza yanxu
Kika soma karatu lol kunji inna mazama har wani
hadisine dasu. Hmmm
Muje zuwa
Afnan kukanta kawai take batada mai lallashinta
sai a yanxune ta somajin ciwon
Rashin uwa
Tabbas uwa maganice dan koba komai tabbas
zata saurari abinda ke cikin zuciyar
Yar tata
Amman banda irin tata uwar Wanda ita farautar
yar tata take kota wane irin hali
Wayyo umma ko a wane irin hali kike yanxu ko
kina mace ko kina raye oho
Haka kawai taji kewar momyn tata ta kamata so
kawai take ta
Ganta koda a hotone Inama ace uwar tata Kamar
sauran uwaye take
Tabbas data samu sassaucin kuncin rayuwa ta
share hawayenta ta fada toilet
Ta watso ruwa mai kawai ta murza ta dauki
makullin motarta
Gidan kakarta ta nufa mahaifiyar nafi. Dan kausar
itama yanxu acan take
Tasan idan taje can koba komai zata samu
sauqin zafin da zuciyata ke mata
Danji take tamkar ta zarota ta huta amman ba
dama yanxu hakanma dakiyar zuciyace kawai
Aleeyu na zaune a a falonsa afnan ta shgo Bayan
ta gaisheshi tace gani abba
Yadan miqe daga kishin kiden da yake Akan kapet
din yace yauwa aafnan amshi wannan ya miqa
mata wata takarda ta amsa hannunta na rawa ta
soma budewa
Yace yauwa duba da kyau offer ce kin samu aiki
a babban kotun dake. G. R. A anguwarsu hajia
wohoho dadine ya kamata tama rasa irin godiyar
da zatai masa
Har saida taji hawayen farinciki tace na gode
Abba Allah e saka da alkhairi ya qara budi cikin
jin dadi yace amin afnan Allah e maki albarka
kuma yasa miki albarka
A cikin aikin naki tace amin abba
Yace to tashi kije dan yaga alamun tanason masa
qorafi dole ta tashi ba
Tare data fadi abinda ke cikin ran nata ba
Ta soma zuwa office wato wai katon office aka
bata mai dauke da part biyu
Na ita da mataimakiyarta. Barister zainab ayuba
(zee. Zee)
Matashiyace mai kimanin shekaru ashirin da
bakwai
Da aurenta yayanta biyu salim da salima
Kyakkyawace sosai
Kallo daya zakai mata kasan boko ya ratsata don
wayayyace gata da iya dressing
Don kace don ita aka qirqiro kwalliya duniya sun
shaqu da afnan
Don haka ko a office ina aiki yai musu sauqi sai,a
hadu a office din daya aita dumin debe kewa
Yaddah afnan ta lura mustafa mijin zainab yana
matuqar ji da matar tasa don ko kadan baison
abinda zai taba masa ita ballentana har ranta e
bace
Don sauda tari idan baida aiki a office yakan
dauko yaransa biyu suxonan suyita Hira cikin so
da qaunar juna Kamar karsu rabu
Kamar idan ta tasji ba gida zata va
Wannan soyayyah ta zainab da mijinta mustafha
shuke qara tunxura afnan
Tace da yanxu itamafa irin wannan soyayyar
adnan zai dinga nuna mata ita da yaranta ko ta
rafka taguminta da hanayenta biyu Bayan ta aje
Biron dake hannunta
Zuciyata na bugawa a hankali a hankali
Shin yanxu haka zataita dawainiya da soyayyar
namijin da baisan tanayiba
Anya damuwa da take ciki bazaisa xuciyarta
fashewaba
Dole taje ta samu adnan koda hakan na nufin
rugurgujewar zumuncinsu
Dole taje ta girgiza zuciyarsa Kamar yaddah ya
hana nata sukuni
Da sauri ta miqe ba tare data nemi shawara
zuciyataba ta zari farin gilashinta dake cikin
kwabarsa ta saka ta janyo katuwar jakarta ta
rataya a kafada gamida
Suran key din motarta ta fice
A wajen falon Wanda yake tamkar qaramin falo
yana dauke da qananun kujru na siba
Kuda hudu biyu barin dama biyu barin haqu daga
can gefe kuwa wani kantace ta
Gilashi
Yau anan zainab da mustafa ke zaune shida wani
abokina Wanda afnan din batason ko Waye shiba
batama taba ganinsaba
Kallon afnan yakai kan hannun zainan Wanda ke
sagale Dana mustafan
Take zuciyata ta sartsy tace kai wannan masoyan
sudai basu iya boye soyayyarmu koda a gaban
waye
A zahiri kuwa cewa tai to romiyo da juliyet nina
fita idan masinja ya shgo da wadannan files din
ya baki saiki shiryaminsu
Kafiin zainab din tace wani abu har mustafan ya
cabe yace gaskia fa madam ki
Daina wahalarmin da babyna duk wani dan aiki
da kikasan yanada dan wlh kidan dunga taimaka
mata dan banson tana Whl sosai
Mutumin dake gefensu Wanda zazna iya sashi
cikin jerin maza masu kwarjini
Da cikan zati ya cafke da cewa kaidai malam ka
kyaleta ta aikinta kawai duk bakai ke takura
mataba ka aje aikinka a office kaxonan duk ka
cikata da zance
$afnan tace rabu dashi ai mun saba
Zainab tace Allah ibrahim karka shgarma wannan
taki bada hayar da mai tausayin
Nata zai kusantato kuma saita dinga takura
mana Nida. Gudan jinina rabin raina
Afnan tace ke nidai kinga fitata ba tare data amsa
Allah shi kiyayen da mustafan ke mataba damin
ta lura kular sa ita yakesonyi
Kai tsaye asibitin da abbanta ya ginama adnan
din ta nufa dukda batada yaqinin zata sameshi a
asibitin
Tayi mamakin yanda asibitin ya qara bunqasa ya
zama na wane da wane
Majority din likitoci duk yturawane lallai asibitin
abin tunkahone a garin kano
Idan ka shga asibitin ba zaka taba yarda da a.
Naija kakeba don komai na asibitin safarin kalar
na wajene
Azuciyarta ta yabama abbanta dayi masa addu,a
da tambaya ta samu aka sadata da office din
adnan din
Saidai masinja ya sanar da ita yana ganawa da
marar lfy don haka ta samu saman daya daga
cikin qayatattun kujerun dake wajen ta zauna
Qafarta daya kan daya tana kada key din motarta
dake hannunta
Tsawon wani lokaci Bayan ya kammala da marar
lfyr ne masinja yai mata iso
Tana bude office din kamshi da sanyin. A. C suka
dakar mata fuska ta lumshe idanun nata a hankali
ta qarasa cikin office din
Qaton office ne Wanda aka qawata da na,urori na
zamani
Komai na office din Abun kallone
Ido cikin ido suke kallon juna yasha baqar suit sai
juyi yake saman wata arniyar kujera ta gilashi
Kallo daya yai mata ta cikin farin gilashinsa yaci
gabada rubuce rubucensa hakan ya
Qara ingiza zuciyata ta qarasa gabansa
Ganin Tayo kansa gadan gadan yasa yai saurin
tsayar da ita cikin daure fuska yace ga wurin
zamanan. Sady matatace kawai keda right din
kusantata ba irin,,,,,,
Tunanin me yayi sai kuma ya kasa qarisa zancen
nasa taja wani kujera ta zauna
Tana murmushi gamida kada kai tace ba zama
naxoyiba. Doctor
Adnan aleeyu musawa
Sunan da yake amfani dashi kenan tun a skull
Tace naxone na tabbatar da abinda zuciyata ke
zargi tadan rankwafa gamida
Daura hannunta kan tebur din ta tallabe fuskarta
da tafin hannuwanta sannan taci gaba
Shin wai da gaske ka mance da wacece afnan
kokodai kana sane rabuwace da ita kayi niyyah?
Zancen yaxo masa a bazata don haka kallon
kurillah yake mata yaga ko xai
Iya tuna a inda ya Santa
Sannan yace wacece kuma afnan jinsin mazane
kona mata?meye hadin sunanta da nawa?
Inama na Santa bare nai burin rabuwa da ita?
Cike da takaici afnan ta miqe ta juya masa baya
saida tai taku daya zuwa biyu sannan ta tsaya
tace ta inda ka mance bari in tuna maka
Nice afnan aleeyu musawa kajita yaddah
sunanmu ya hadu
Ka sanni a yan uwantaka ka sanni a soyayyah
Sannan ka sanni a auratayyah
Ta waiwayo da sauri tana kallonsa idanuwanta
sun cika da kwalla
Tace mai yasa ka juyamin baya yaya adnan mai
yasa kakeson rabuwa dani
A daidai lokacin da Nida yayanka muke buqatarka
kasancewa dakai?
Ji yai tamkar tana caka masa wwuqa. A qahon
zuciyarsa ido waje yace ke mahaukaciya banza
jahika
A ina na sanki har mukai soyayyah dake dahar
zaki dubeni kice wai akwai yaya
A tsakaninmu?
Kinje kin gama gantalinki kin samo yayan titi duk
cikin garin Gano ki rasa Wanda zaki jonama
yayan saini lallai dole nadau. Babban mataki
akanki
To inaso ki sani yar matsiyata ban taba zinaba
Tunda nake
Sbd haka yanxu abinda nakeso dake shine fitamin
daga office tun kafin nasa securities suxo sumin
waje dake get out ya fada cikin daga murya
Wohohohoh wato sake baki da hanci da kunne
tayi tana masa wani irin kallo na tsana a yayin
da taji zunidar na wani. Juya mata juwa na
qoqarin kadata
Kirjinta kuwa. Wani zafi daya dauka ko giftata
kazoyi dukda sanyin. A. C. Din dake office din dai
Kaji hucin zafin qirjin nata
Ya qara maimaitawa yace ke banza karuwa nace
kibarminn ofice get out kiyi gaggawar fita tun
kafin nai loosing din temper din na
Cikin wani irin yanayi ta juyo ta kalleshi
idanuwanta sun kada sunyi jajir
Kutt ganin haka yasa nayi gefe bace bari nadan
rabe kafin su sauko don
Naga dukansu a fusace suke
Aure. Kan. Aure
Chapter27
Yace get out yaddah yai maganar har Wanda ke
waje zai iya jiyoshi
Juciyar afnan ta qara cunkushewa. Da Baqin ciki
Tace a ranta har adnan yayi girman da zai kira
iyayenta matsiyata Alhalin arziqinsu yakeci yanxu
haka?
Cidanuwanta suka firfito waje. Cikin zfin rai ta
nunashi tace kai
Dakata arziqi dan masu arziqi
Wanda baisan usilinsaba
In kana nufin kace ka manta dani ta yaya ka iya
tunawa da asibitin da mahaifina
Ya Gina maka kuma ya dauraka akai?
Hmm lallai dan Adam butulune
Adnan ka butulcema kyautatawan da mahaifina
yai maka
Yaya adnan ka butulcema kyautatawan da
mahaifina yai maka yanxu har shine
Abin zagi a wajena
Daman duk maganganun da kake fadamin a baya
duk na yaudara ne?
Ka tuna abinda kake fadamin ina sonki afnan
bazan
Iya rayuwa babu keba
Kece rayuwata kece farincikina kece jin dadin
rayuwata
Afnan karki sabamin alqawari karki bari na rasaki
don allah
Ta runtse. Idanunta hawayen dake qoqarin
zubowa suka samu hanyar kwarara
Tace shin yanxu ka juyamin baya kenan Haba
yaya adnan ban cancanci haka daga gareka ba
kuma duk zyciyar daka gani bata cutar damai
kyautata mata
Yaya adnan rayuwa tayimin qunci na tsani
duniyarma gabaki dayanta
Amman a yanxu nafi tsanarka sama da komai
kaine babban maqiyina dake kassaramin rayuwa
Ta gama kular dashi domin haqurinsa ya gama
qarewa ya nunta da dan
Ysatsa har huci yake. Sbd bacin rai yace ke
malama saurara haka
Na gaji da sauraron wadannan kalaman naki
marasa tasiri lallai da ace film ne
Da ina tabbatar miki zaiyi kasuwa
To idanma mafarki kike ya kamata ki farka kuma
wlh ba zan barki hakaba domin Naga alamun
daman can kin saba wasa da Hankalin maza
Tabbas saina nuna miki cewa ni dabanne da
sauran maza don nayi alqawari sainaga bayann
duk maison wasa da mutuncina
Tace kayi daidai ai irin wasan da nakeso mu
shirya dakai kenan
Adnan a wannan karon inhar ka shirya nima a
shirye nake dakai
A aje masa card dinta ta fice a zafafe tamkar mai
shirin tashi sama
Da ido ya bita zuciyarsa na masa kai kawo yace
tabbas dolene na dauki mummunan mataki Akan
wannan yarinyar
Dake son wasa da hankalina inba hakaba kuwa
zata zame masa qadangaren bakin tulu
Yaja wani dogon huci. Sannan ya koma ya zauna
Afnan kai tsaye office ta nufa ko sannu da zuwan
da masu gadi ke mata
Bata samu amsawaba kai tsaye office dinta ta
shge ta dare kan kujera
Gamida hada kai da tebur wani. Sabon kuka ta
bude kawai mai tsuma zuciya
Zuciyata tadau zafi matuqa
Tanaso ta daure don ta tabbatar da yaqi yanxu
aka fara
Don haka dole tana buqatar dakiyar zuciya
Tayi kukanta harta gaji ta soma ajiyan zuciya da
sauri da sauri
Zainab ce ta turo qofa ta shgo
Gamida sallama
Saidai ganin halin da afnan din ke ciki ya daga
mata hankali
Ta qarasa da sauri tana kai lfy afnan kukafa
hannunta har kyarma yake wajen dafa kafadun
afnan din tana jijjigata lfy afnan?
Wani murmushi qarfin hali afnan din tayi Wanda
zamu iya kiransa da yaqe tace
Lfy lau xainab
Damuwar data Dade tana damunace ta bijiromin
son mijina shine zai kasheni har lahira
Da ran mijina yayana sun zama maraya da
aurena na zama bazawarar qarfi da yaji
Tadan saurara tana sharce hawayen da suka
zubo mata sanna taci gaba da cewa
Baqincikina guda a rayuwa Wanda nafiso shine
babban maqiyina kuma abokin fadata
Saidai daga yau. Na gama dada yanxu na gama
hawayena sun qafe wlh saiya gwammace bai taba
sani wata ya wai ita afnan ba
Zainab tace shin wai Waye kuma kukan me kike?
Ta qarashe share kallan data dan maqale mata
tace Nida mijinane
Nasan bakisan inada aureba bakisan koni
waceceba to yau zan sanar dake
Zainab taja kujera gamida tagumi ta maida
hankalin nata kan
Afnan din
Afnan din ta qara gyara zama sannan ta
zayyanne mata tarihin rayuwarta tsaf Sbd yanxu
babu abinda take buqa irin shawara
Tana gamawa zaina cike da tausayi tace wayyo
afnan na tausaya miki
Kina cikin matsala
Kinga jarabawa amman sai nake ganin ba kince
sady ta fada miki cewa yai loosing din mewory
dinsa ba?
Tace eh hakane zainab din tace to kin gani ai
wannan damar sady ta samu harta samu damar
fadawa zuciyarsa domin ya mance da komai har
kankin kansa
Afnan tace kibar fadan haka idan har ya mance
da komai to maiya hanashi mancewa da asibitin
da mahaifina ya Gina masa
Kuma yake amsa sunan da yake amsawa tun a
wancan lokacin zainab tace eh kuma hakane
Afnan tace. Kawai halin maza ya nunamin don.
Na rantse bai rasa memoeynsaba
Kai koda kansa ya rasa gabaki daya na ranshe
sai yasan ya wulaqanta wata mai sunan afnan
Don na rantse saina Rama abinda yai min
Zainab tace a,a daba haka kikaiba
Kamata yai abi ta hanya mai sauqi wajen Ganar
dashi
Sannan kema saiki dinga cusa kanki amman bada
hayaniyab saikiga
Kin samo kansa cikin sauqi
Makar waccce aka fadama wani mugun abu iido
waje tace Haba
Zaiban ai ko sjine autan maza na gama dashi
Zaina tace a,a afnan idan rai ya baci ai zuciya
bata gushewa
Afnan tadanja wani murmushi tace zainab kenan
ai abinda zai yuwu shi ake abinda bazai yuwuba
kuwa ba,a. Cikia bata lokaci akansa
Zainab tace karekice haka afnan ai duk abinda
kikaga bai yiwuba
To saida in babu naci akai kuma da maida
hankali
Akan abun
Tace yanxu da sadyn ta maida hankali ba gashu
ta sameshiba
Haba afnan yayanki zaki taimakamawa fa
Nida kaina Zanzo miki da yan dubarun da zaki
sameshi a tafin hhannunki
Please afnan ki duba zancena
Wani murmushi takaici afnan din taja
Sannan ta miqe ta sabi jakarta don tasan inta
zaibab din zatabi saisu wuni
Anan da wannan surutan nata
Tace ni kinga tafiata kinji gaba Nidashi yanxu aka
fara
Zzainab ta miqe da sauri ta bita tana fadin Haba
afnan gaba da mijinki bata tassoba
Idanma kikace sai anyi kece da fadiwa qasa
warwars don kuwa kece mace
Ji tayi makar zainab din ta watsa mata qarwashin
wuta don haka
Ko sallama batai mataba ta fada motarta taja ta
barta a wajen
Inda zainab din ke jinjina kai da mamakin irin
kafiya na afnan da taurinkai
Kodata koma gida zuciyata bata rabu da kunciba
saima ji tayi komai ya kwance mata
Yar juriya da dakiyar da take da ita Ada ta
nemeta ta rasa
Tana kallon yan yaranta saiji tayi hawaye na
wanke mata fuskar
A ranan duk yan gidan saida suka fahimci rashin
walwalarta
A yanxu tunanina guda bai wuce ta hanyar da
zatabi ta quntatama adnan da qawarta sady ba
Shin ta wacce hanya zatabi tayi ramuwar
gayyah?
Oho muje zuwa
Kamar daga sama taji wayarta na ruri Kamar ba
zata daukaba sai kuma ta janyo number zainab
ta gani
Tai saurin dagawa dukda ba dadin yin maganar
takeba daqar take amsa mata
Zainab din tace yauwa afnan daman daxun kina
fita wani case ya shigone mana
Don haka ki bude email dinki Zakiga komai a
bayyane
Cikin qufula tace Haba zaina kinsan halinda nake
ciki taya za,ai na iya daukar wani case
Zzainab din tace kiyi haquri afnan case din mai
girmane
Don Allah ki bede don nasan ke kadaice zaki iya
warware wannan al,amarin
Ba tare da ranta yasoba tace to shikenan zan
duna
Tace yauwa afnan godia muke Maman
Adnan na tafe cikin motarsa. Tsaleliya kana ganin
motar kasan ba qaramin mutum ne a cikintaba
kalar Ruwan tokace
Sannu. A hankali yakejan motar da hannu daya
yake Jan motar daya kuma ya tallabe kansa
Kai daka gansa kasan yana cikin tsantsar
damuwa
Sannu. A hankali ya iso katafaren gidansa gari
guda horn daya yayi mai gadi ya wangame gate
din shi kuma ya tura hancin motar ciki
Da hannu kawai ya amsa ma me gadin sannu da
zuwan da yake masa
Ya gagara da motar inda aka tanaza domin aje
motoci
Ya faka tasa gefen ta matar tasa sannan ya
ratayo cot dinsa a wuya
Jikinsa a mace yake tafian
Harya isa wani qaton falo Wanda idan kana
cikinsa saika rantse kace ba,a
Naija kakeba. Komai na cikin falon na qasar waje
ne
Kamar Wanda aka tunkuda ya fada saman daya
daga cikin kujerun dakin
Ya kwanta gamida rufe idanunsa adnan ce kawai
ke masa yawo a kwakwalwarsa
Shi a duk duniya baida wacce ya tsana kamarta
Inda so na zama samu dayasa an batar masa da
ita daga doron qasa abinda yaketa saqawa kenan
daga cikin ransa
Sady ta fito daga cikin falonta ta hade cikin wani
lallausan yadi na materiyal
Ta qaraso gabansa qamshin turarenta ya daki
hancinsa
Ya bude fuskarsa a hankali yana kallonta ta shafi
fuskarsa gamida yin masa murmushi
Tace Yadai yallabai meke damunkane duk sai
Yama nemi damuwar ya rasa
Janyota yai jikinsa yace sarauniya a fadar adnan
Kinyi kyau sosai fa
Ta sakar masa wani lallausan murmushi
hannunta saman qirginsa tana masa tafiyan
tsutsa tace ranka shi Dade bakafa fadamin
abinda ya batamin rankaba
Yaja wani qaramin tsaki mtsss share kawai baby
Nida wata yarinyace dakeson dagulamin lissafi
amman barta kawai
Zan taka mata birki
Yaddah ko a sanya ta ganni sai gabanta ya fadi
Sady tace kai sweety wacece wannan Yadan
qarajan tsaki
Da alamun Abun ya bata masa rai sosai yace ina
wata yarinya da kika taba cewa
Taxo ta daukomu daga filin jirgi wacce ta ganmu
ta kwasa a guje ta barmu?
Sady tace eh Inajinka yace to itace yau ta sameni
har office taso ta cajamin brain dina
Wai take fadamin na taba aurenta harda yaya
biyu Waye ya mutu Waye ya dawo
Yace kotu kawai zansa ta shga tsakanin da ita
Cikin firgici. Sady tace a!a karkayi haka sweety ai
abinda takeso kenan domin taita yadawa a gari
kuma ta shga tsakaninmu dakai
Kawai kaja mata kunne idan ta qara tunkararka
ka nuna mata baka qaunar mai qaunarta
Idan kuma tai wasa zakasa a tozartata na
tabbatar idan har kai mata haka
Zata fita hanyarka adnan yace oh ne sweety ina
mamakin mutane
Wai yan mata Dasun qalla ido sun ganka da kudi
shikenan dawa Allah ya hadasu inba dakaiba
Yanda kikasan an watsama Kaji tsaba
Sady tace ni kaina ina qara godema Allah
dayaban jarumin namiji kamarka
Don idan ba jarumiba babu mai iya tsallakema
sharrin mata
Tasa hannu taja dogon hancinta tana dariya tace
duk wannan dogon hancin ke dibarsu
Suka miqe tare yace muje Nidai. Na watsa ruwa
Kiban abinci naci
Ranar Monday Tunda sanyin safia afnan ta shirya
cikin wata kyakkyawan shga kai
Inka ganta. Wannan danyar budurwace jagal cikin
takun qasaita Bayan ta dauki abinda zata dauka
ta nufi Bangaren abbanta
Yana kishingide saman kujera
Ta duga ta gaisheshi cikin murmushi ya amsa
yace yauwa afnan
Daman inason ganinki ya kamata kije kiga
mahaifiyarki
Don tana buqatar ganinki ta sadudu da duniya
matuqa
Kiyi mata uzuri afnan tana buqatar sake gabinki
Afnan din ta dago ta kalli abban nata ta jinjinama
tana mamakin
Haquri da tawakkali irin na abban nata
Fuskarta dauke da murmushi tace Abba kaje ka
gantane?
Cikin murmushi yace naje afnan yanxu haka tana
gidan yari Sbd ciwon daya addabeta na hawan jin
Cikin firgici tace hawan jini abban ido waje
Yace
Naku har kullun
S salankss
Yauwa masu fadin cewa basusan wane hukunci
kotu ta yankema janar da nafiba
Da kuma yaddah afnan ta samu ciki harta
haihuba inaganin da alamun Bakwa biye damune
shiyasa dan duk wani bayani da kuke buqata
yana cikin
Aure. Kan. Aure
Chapter28
Ta dafe qirji tace momyn tawa zuciyata tadan
tsarsy tace amman ne Abba mai yasa banjin son
momyn nawa a cikin zuciyata ne?
Kamar yaddah sauran mutane ke fada sai Inji
jama,a na fadin wai sunfi
Son mahaifiyarsu Akan mahaifinsu
Amman ni abbah har nafi jin son baba hauwa a
cikin raina Akan na momcyn nawa
Kodai ba itace ta haifeniba abbah?
Murmushi yai ya shafa kanta cike da tausayinta
yace
Itace mahaifiyarki afnan itace ta haifeki da cikinta
Abindayasa bakyajin son mahaifiyar taki Kamar
sauran mutane
Sbd ko wace uwa idan ta haifi danta takan
rungumeshine a Jikinta ta ciyar dashi da Jikinta
ta kuma shayar dashi da Jikinta ta raineshi da
hannayenta
itace kula dashi cinsa shansa lafiyarsa
Da komai nasa harya girma suna shaqar
numfashin juna inhar yaro ya samu wannan
rainon da kulawa ki fadamin abinda zaisa. Da
bazai qaunaci mahaifiyarsaba
Keko taki momyn ta gujeki Sbd gayu taqi
daukarki Sbd kar kiyi mata fitsari
Ki bata mata jiki batasan cinkiba batasan
shankiba
Batasan lfyarkiba don ko asubiti zan kaiki bata
yaddah taje saidai na dauki baba hauwa mu tafi
tare
Saida kika girma kikakai shekara goma sannan
tadan saki jiki dake har kuke zama kujera daya
har kidan raba Jikinta
Laifi kadan zakiyi mata ta kai miki duka
Saidai ni wannan ya zamanmin abin alfaharine
afnan don da ace ta shayar dake da Kinsha
halonta a nono
Da ace tajaki a jiki dakin tashi da irin tarbiyarta
kinga yanxu wannan ya zame mana
Abin alfahari kenan
Afnan tayi murmushi tace wai yaushe su inna
zasu dawo daga qauyene?
Yace tun jia nasa direba ya daukosu acanma ya
kwana amman inajin yau
Zasu dawo tare
Aleeyun yace amman ya za,ai da batun yarannan
don ibrahin ya matsa Akan yanatson turo
iyayensa afnan tai shiru. Ba tare data tankaba
abban nata yaci gaba dacewa
Daurewa zakiyi afnan zamanki a haka bazai
yiwuba aure shine darajar ya mace
Tunda alqali ya raba aurenki da adnan
Mai xaisa ba zakibama wani damaba
Idanunta Sukai jajir ta dago tana kallon abban
nata muryarta na rawa
Yace yanxu aurena ya mutu Abba? Wlh ni ji nake
a jikina Kamar bai mutu ba
Tunda Wanda igiyar auren nawa ke hannunsa be
warwareba baimasan an
Raba ba
Aleeyu yai murmushi yace afnan kenan na lura
har yanxu adnan nanan a
Maqale cikin zuciyarki me zaisa ba zaki cireshiba
Mai zaisa ba zaki manta dashiba Kamar yaddah
ya manta dake damu da kuma usulinsa?
Ba yaddah ta iya dole ta daurama kanta dakiyar
duniyarnan tace dole na damu Abba
Ka duba fa ka gani harsu taslim sunn fara
ganowa kaiba mahaifinsu bane yara yan shekara
hudu yanxu idan suka girma sukacemin Waye
mahaifinsu nace musu me?
Nace musu mahaifinsu ya manta dasu -ye abba?
Shi kansa abban nata ya soma tausaya mata don
haka ba yaddah ya iya
Dole ya soma lallashinta ta miqe gamida cewa
Su taslim basu fada maka a makarantarsu an
shirya musu fati na musamman ba kuma ko wane
yaro anason ganinsa da iyayensaba? Yace aiko
ban saniba basu fadaminba
Tace aiko da mamaki yaddah suketa ruruta
maganar fatin na dauka sun sannar dakai
Yace to shikenan idan har ban makaraba zan
qaraso tace to shikenan Abba ta miqe ta fice
Babbar motarta ta dauka qirar jeef ta nufi hanyar
makaranTa don dama direba ne ya dau yaran yai
gaba dasu tun da wuri
Makarantar yaran makarantace mai tsadar gaske
ta masu hannu da shuni
Don haka walimar tasu ta musamman ce kai
dakaga yanayin gurin kasan an kashe naira
Manyan mutane sun halarci wajen a cikinsu harda
mai girma mataimakin gomna da muqarrabansa
don duk da yaransu a makarantar
Doctor adnan musawa yana daga cikin wadanda
suka halarci taron shida matarsa
Sady baby
Zainab ma taxo itada mai gidana mustapha da
abokina
Don haka afnan ta saki Jikinta Kamar babu
abinda ke damunta
Yara sun cashe sosai manyan mutane sun miqa
kyaututtuka
Sannan aka fara kiran daliban daya Bayan daya
domin miqa musu kyaututtukansu
Ibrahim abokin mustapha na gefen afnan sai soki
burutsinsa yake
Wai don kawai ya samu shiga a zuciyar afnan din
amman Abun ya gagara
Zainab da mustapha suma qoqarin da suke kenan
wai ko Allah zaisa a dace
Saidai ita hankalinsa yanakan adnan da sady
taga yadda suka qara kyau fatarsu ta qara haske
Kamar basuba
Wani irn bakin kishine ya tokare afnan din a wuya
ta kuma qi dauke kanta daga kallon nasu
Don haka duk wani motsi nasu Akan idonta yake
Taslim adnan musawa abinda kunnuwan afnan
din sukaji an ambata kenan
Yayin dataga adnan yayi saurin miqewa tsaye a
cikin bainin jama,a
Yana karema yarinyar kallo kyautace ta
musamman aka bata inda sauran mutane keta
daukarta hotuna da wayoyinsu
Duk kyautarta ta dara ta sauran yaran sannan
aka kira. Aslim adnan musawa
Kamarsu daya da ta macen
Yaran sai kace yayan turawa don kyau abinda
Yaja musu farinjini kenan a. Wajen jama,a
Inka kalli bakin afnan yaqi rufuwa tana alfahari
yaddah jama,a kenan yayan nata
Shiyasa duk fitar da abbanta zaiyi saiya Tofa
musu addu,oi
Daga qarshene aka kira siyama adnan musawa
Aka kira iyayen yara Sukai jawabi sannan akai
addu,a taro ya watse
Afnan ta tasa yaranta gaba vakinta yaqi rufuwa
Sbd farinciki
Aslim yace Momy wai mai yasa kowa abbansa na
zuwa amman ke kullun ke kadai kike zuwa?
Kafin tai magana taslim$ ta amshe tace ai ance
mu bamu da abban abbanki shine abbanmu ko
momy?
Kamar ta rafka kuka murnan nata ta koma ciki ta
rasa amsar da zatabama yaran
Kamar daga sama taga qafafun mutun akanta
tana daga kai taga adnan ne
Muryarta na rawa tace Yadai malam lfy kafin ta
gama rufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen
mari ya nunata da dan yatsarsa yana cewa
Ke qaramar yar bariki ki saurareni inba hakaba
zakisha mamaki
Ki sanar dani abinda nai miki da har
Wadannan yaran
Muryarsa ba sassauci yace meye kike buqata idan
dukiya kike nukaqata ko nawane ki sanar dani
wannan ba matsalata bace
Amman sunana dakikeson batawa ya isa haka ya
isa ki ganeko? Ya qarashe maganar ccikin daga
murya
Gashi jama,a har sun fara tarata suna fadamin
wai ashe inada Wasu yaran to ya isheki haka
niba dan iska bane Kamar yaddah kike tunani
Marin ya ratsa afnan har taso rudewa daqar ta
iya shanye Marin tana masa kalln takaici
Tace lallai adnan wuyanka ta isa yanka yau nice
ka mara da yatsunnan naka
Ta girgiza kai gamida cewa lallai ka cika. Butulu
mayaudari maha,inci
Kuma na baka asignment kaje ka bincika Waye
aleeyu musawa a cikin garin kano
Koda qaramin yaro yasan wayeshi sannan ka
bincika wacece yarsa afnan
Idan ka Gano saimu gane Waye me qallen uba
Waye me taqama da uban wani ta kama yaranta
taja hannunsu tace kuxo muje
Yaja wani dogon tsaki yana fadin sakarya kije ki
kwashi ciki a titi ki haife sannan ki rasa da sunan
da zaki liqa musu sai nawa
Aslim ya bishi da kallo cikin tsawa yace daina
kallona shege marar uba
Da sauri afnan din tajasu ta turasu cikin mota ta
rufe ita kuma ta koma mazaunin direba
maimakon ta tada motar sai kwantar da kanta tai
Akan sitiyari tana kuka marar sauti yaran suka
janyo kansu suka kwanta Jikinta suma kukan
Suke babu mai lallashinsu
Saidata gaki don kanta sannan ta soma lallashin
yaran daqar ta samu Sukai shiru
Sannan ta kunna motar ta Jasu a hankali tajejan
motar harta kama hanyar gida
Kamar daga sama aslim yace wai da gaske
Momy mu shegu ne?
Ji tayi tamkar ta saki sitiyarin motar Sbd firgici
ta shafi kan yaran tace a,a kuba shegu bane
Shegu sune wadanda basu da uba kukuwa ai
kunada uba Abba aikin sanshi ko Yaron ya daga
ka
Taslim tace amman mommy....
Ta daka mata tsawa tace ya isa haka ganin
yaddah ta taso musu yasa suka tsuke bakinsu
Sukai shiru
Zuciyata sai azalzalarta take ji take Kamar tasa
hannu akai tauta ihu
Ba yaddah ta ida kodata aje yarana a gida office
dinta ta wuce. Dukda kanta na mata wani irin
azababben ciwo amman kodata isa office din nata
Ta Gaza katabus
Zainab ce ta turo office din nata ta shgo afnan ta
dago da jajayen idanuwanta
Ba tare data damu da yanayin yaddah takenba
don daman tun a Makarantar yaran ta lura da
yanayin nata
Taja kujera ta zauna gamida cewa wai meke
faruwane afnan
Afnan din tai wani murmushinda zamu iya kiransa
da yaqe
Tace damuwace kawai zaiban
Zainab din tace nasan da haka amman da Zakiji
shawarata da kin manta da batun adnan kin
Bama ibrahim dama domin bayyana miki abinda
ke cikin zuciyarsa
Tundadai yarane Allah ya rigada ya raya miki su
Afnan taja wani dan murmushi taje zaiban kenana
aini tuni nabar adnan Kamar yaddah babvar cikin
mahaifiyata
Kuma na fita harkarsa sannan abinda yaimin na
barshi da Allah saidai ban isa na hana zuciyata
takaici da kuncin rabuwa da adnan dinba
Tace dole zuciyata tai kuka amman nikam na
daina na idanu
Zainab din tace aiko dakin kyautama rayuwarki
saidai inason don Allah kibama ibrahim dama
ibrahim mai sonkine so na haqiqanin gaskia don
tun randaya fara ganinki ya damu zuciyarsa da
zancenki adnan
Ibrahim abokin mustapha ne. Tun suna. A. B. U.
Inda aka tura ibrahim bautar qasa zuwa inugu
shikuma mustapha akwaibom
Kinji Yaddaha akai suka rabu Bayan sun gamane
kowa ya dawo gida sai
Iyayen ibrahim suka hada shi aure da yar uwarsa
shi kuma mustapha ya aureni dan dama tun ina
secoundry muke tare
Don ko,a. A. B. U lokacin da suke shekara qarshe
a lokacin na shga 100level don haka na qara
saninsu da abotarsu gamida sanin halin kowa.
Wlh ibrahim mijin marainiyane don matarsa
Maryam da kike gani batada hali kona misqara
zarratan
Ni kaina shaidane ibrahim mutum ne mai haquri
don ba ko wane namiji bane zai
Iya zama da wannan annamimiyar matar tasaba
in takaice miki yanxu haka yaransu uku kuma har
yanxu yanna tare da ita
Tunda nake ban tabajin ibrahim yace zai Qaro
aureba don ko an mishi maganarma cewa yake
ba wannanne a gabansaba mace dayama na
neman gagararsa inaga ya Qaro
Na rantse miki ibrahim mutum ne na gari salihi
marar hayaniya
Dan Allah afnan ki bashi dama koda na yini
dayane na tabbatar da zaki fahinceshi please
Afnan tai. Murmushi tace zainab kenan lallai da
yar siyasaceke da jakija zama,A
Da wannan bakin naki
Zainab tace ba haka bane afnan gaskia na fada
miki ki yarda dani
Afnan tace shikenan zanyi tunani zainab tace
wane tunani kuma yanxu haka yana office dina a
zaunefa don Allah afnan ki taimaka kar yaga
gazawata
Tace kai keko zainab kin cika naci jeki shigo
dashi ai inanan
Cikin murna tace tanx afnan ta fice da saurinta
afnan din ta bita da kallo
Zuciyata na mata saqe saqe saidai jiyo
sallamarsa tayi da hannu tai masa nuni da wajen
zama ya samu waje ya zauna
Yayi kyau sosai yana sanye da qananun kaya
Yaja kujera ya zauna yace godiya ta tabbata ga
sarkin sarakuna sarki Allah
Yabo ya tabbata ga shugaban so da masoya
annabi muhammad (s. A. W)
Afnan bansan irin farinciki da godian da zan miki
kasancewar saurarata da kikaiba
Daqar ta iya qirqiro wani daria da bai kai xuci ba
Yacu gaba da cewa da alamun damuwa a tare
dake
Da zaki ban dama Dana dawo miki da farin cikin
da kika rasa
Afnan ta dubeshi tace taya baqincikina da
damuwata zasu ragu idan har na baka dama?
Yace abune mai Sauqi afnan Tunda har sonki ya
fasa qirjina ya tsaga zuciyata ya shge gamida
samama kansa mazauni
Tabbas babu abu mafi siddabaru a duniya daya
wuce kancewar so a zukata
Lallai idan ba ubangijiba babu Wanda ya isa ya
qaddara wannan
Afnan zan dawo miki da murmushinki da kika
rasa a baya zan dawo miki da fara,arki da kika
rasa a baya sannan na dawo miki da farin cikinki
a duk inda yake namiki wannan alqawarin
Afnan ta ja wani gajeranmurmushi a lokacin data
tuna da kalaman adnan din da yake ce mata.
Afnan inasonki ina qaunarki sonki zai kasjeni idan
harna rasaki mutuwa zanyi
Ta girgiza kai tace. Hmmmm maza kenan yau
kuma tanan aka bullo wato zan dawo miki da
murmushinki fara,arki da kuma farincikinki
Tace yanxu idan nace duk zancennan tsarine sai
kace bada gaske bane ba ko?
Yace karkda zuciyarki ta raya miki haka afnan
wlh sonda nake miki sone Bawai
Irin son da kike tunani bane ki yarda dani afnan
bazan taba cin amanarkiba
Ina miki sonda zan iya sadaukar da raina akanki
ki yarda dani
Tace Indai afnan ce ta baka dama ibrahim domin
taga gudun ruwan soyayyar taka
Wani murmushi Yaja sannan yace wannan ruwan
afnan bashi da qarshetashi tai tana kallonsa tace
yanxu dai gida zanje jibi ina gayyatarka gidanmu
don daman ai ka Dade da cusa kanka wajen
mahaifina
Shima miqewar yayi yana fadin irin wannan
zuqeqiyar matar idan nai sanya ai
Sai Naga sanya daria tayi dukkansu suka fice a
daidai inda masinja ke zama ya miqa mata wata
takarda yace gashi hajia akace wai na baki
Ta amsa sukaci gaba da tafia tare ba tare data
duba takardarba
Zainab yarsa ido tana maqale a ofice dinta tana
leqensu tace hofa daga farawa da iyawa afnan tai
saurin amsar ta da cewa to yarsa ido ni. Gida na
nufa
Tace to saimunyi waya kenan tare suka wuce
ibrahim ya rakata har bakin motarta yace abani
dama na kaiki har gida mana madan
Tace a,a ka barshi in Allah ya yarda zan isa gida
lfy yace to shikenan Allah e kiyaye sannan ki
gaishemin da yarana
Murmushi kawai tay sannan ta fada motar ta
figeta saidata bace da gani sannan ya juyo daga
inda yake tsayen
Tunda afnan ta dawo gida kasala da ciwon kai
suka rufeta don haka bata samu damar warware
takardar da masinja ya batabawashe gari batai
niyyar zuwa office ba don haka wata jallabiya
kawai ta saka mai dogon hannu Bayan tayi
wanka
Har zata fice ta hango takardar tasa hannu ta
janyota takardar sanmacice daga kotu idanuwa
waje tace shin masinja mantawa yai ya bata
kokuwa yaya?
Tambayar da Taima kanta kenan ta warware
takardar ta soma karantawa
Tabbas tatace sammaci ita akaima qirjinta yai
mummunan bugawa tace tabbas adnan ya debo
ruwan dafa kansa wato ita yake qara a kotu
Abinda ta fada kenan
Sannan tai saurin juyawa ta nufi saShin abban
nata da sauri hannunta
Har kyarma yake
Yana zaune a saman kafet yana break Bayan ta
nuna masa takardarne cup din dake a hannunsa
ya aje ya dago kai yana murmushi yace wato
adnan dinne ke qararki a kotu?adnan kenan
ciwone kawai ya hargitsashi kuma wannan wani
damace dazai gane koshi Waye
Gyara zamanki ki karya Allah e kaimu ranar zan
tanadar miki shaidu ki kwantar da hankalinki
Batace masa komaiba ta zauna Sukai break din
tare
Bayan sun gama break din tace amman Abba
kafin zaman kotun inason zuwa abuja
Na Gano momy kwana2 dinnan ina yawan
tunanina ga fadiwan gaba dake damuna kullun
idan na kwanta sainayi munanan mafarki akanta
Yace tashi kije sha kuruminki afnan in Allah ya
kaimi ranar asabar zamuje ki ganta Tunda zaman
kotun naku ranar Monday ne cikin jin dadi tace
yauwa daddy kaima zakaje yai murmushi yace
nima zanje. Hardasu inna da taslin da aslim cikin
jin daddy tace na gode daddy
Tana fita sashinsu. Inna ta nufa ta samu yan
tsofaffin nanfa aka bude shafin Hira
Don tana matuqar jin dadin Hira da yan tsofaffin
nata
Adnan nne zaune a falonsa Kamar mutum mutumi
yana cikin matuqar damuwa tun jia da abinnan
ya faru
Shinn wai mai yasa yarinyarnan ke masa hakane
duk mazan dake fadin duniyarnan ta rasa Wanda
zata riqama yaranta saishi
Koko don taji ya samu matsalar memory dinsa
shine zatai masa wannan
Toce mata akai hauka yake?
Yana cikin tunaninne yaji an dafa kafadarta
Bai rasazana don yasan ko Waye don haka ko
juyowa baiyiba ta zagayo ta zauna a kusa dashi
Cikin murmushi tace Yadai my love badai tun
abin jiyane ke damunkaba?
Haba adnan inhar kayi mata abinda nace kai
mata wlh ba zata sake shga harkarka ba
Adnan ya dago dara daran idanunsa wanda suka
kada Sukai jajir Sbd tunani ya cigi lebensa da
haqoransa da qarfi yana girgiza kai
Yace abin ya damenine sady fiye da yaddah
bakya tunani bafa qaramar matsala bace
matsalace babba matarnan ba qaramin abu ta
shiryama rayuwatabada alamar tanada. Babban
shiri akaina anya ba raina suke nemaba kuwa
Wlh na fahimci yarinyarnan wani abu take
shiryawa babba akaina
To nidin wani mai arziqine da suke shiryamin
wannan abun
Ady tace aiko kai mai arxiqine Tunda ka mallaki
manyan kudi gaka da asibiti da gidan mai Naka
na kankin kanka
Kana Tunanin qaramin mai arziqine zai wannan
Adnan ya girgiza kai gamida cewa dole naima
tufkar hanci
Domin harna shgar da qara kotu
Gaban sady yai mummunan fadiwa Wanda har
saidata dafe qirjinya hannunta har kyarma yake
tace kotu kuma adnan gaskia ban yardaba
Wannan ai tonon sililine ka kaisu kotu kace wai
kasan abinda suka taka
Ai ina ganin Kamar mtsalar cikin gidane wannan
Adnan ya bita da kallo yace wannanne matsala ta
cikin gida?
Baki da hankali sady
Ganin yaddah duk ya birkice mata tasan abin
nasa bamai sauqi bane
Tace to kaje ka fadamasu baba sai Kaji abinda
zasuce
Miqewa yayi yace banson na tada musu da
hankali shiyasa bannson fada musu
Nafison na magance matsalar ni daya don banson
wani ya zargeni
Da aikata fasiqanci
Sady ta fusata ta miqe tsaye tana jijjiga jiki ban
gane bakason kowa ya shga cikin lamarinba shin
babu alamun gaskia a ciki ne?kodai yayankane
adnan
Tambayr data rudar da zuciyarsa kenan ya vita
da wani irn kallo cike da takaici
Yace amman nayi mamakin wadannan kalaman
naki sady daman na tabason wata mace kafin
rashin lafiyata ko Bayan rashin lfyr tawa Bayan
ke?
Ta kifta idanu tana fadin to inba hakaba mai yasa
bakason iyayenmu su shga cikin lamarin!
Cike dajin haushinta yace haka naso kuma na
tsara kema da kikafi kowa sanin halina kin fara
zargina inaga su
Don haka duk Wanda kika kira kikaima wannan
Zancen na rantse miki a bakin aurenki cikin firgici
tace abakina aurenafa kace adnan yace abakin
aurenki so wat
Ya fada cikin daga murya sannan yabar falon
Cike da tashin hankali sady tace nashiga uku
Hmmmm lol baki shga ukuba zama ki shgane
Aimin afuwa yau banyi post da wuriba makara
Aure. Kan. Aure
Chapter29
Mun tsaya inda tsakanin adnan da sady suke
kace kace inda har adnan yaimata furucin saki.
Idan harta kuskuea ta fadama wani shirinsa nakai
afnan kotu da yayi
So muje zuwa
Nan ya barta inda sady ta tsaya cikin tashin
hankali
Tace mai yasa tun farko bata canja masa
takardunsaba ta canja masa sunansa gaba
dayaba
Ta daura hannu akai tana qoqarin rushewa da
kuka
Afnan ce zauna kan dressing mirro ta dau
kwalliya ba qaramin kyau tayiba sannan ta tashi
ta nufi falon da aka sauke ibrahim
Sannu a hankali take tafian cikin kwarkwasa tana
lallatsa wayarta
Yana zaune Akan daya daga cikin kujerun tayi
sallama idansa kur akanta.
Ta sakar masa wani lallausar murmushi idanunsa
kirr akanta ta zauna Akan kujeran dake
fuskantarsa
Shima ya qara zama yana Mata murmushi yace
Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan surar
Allah ka qaddara nine Wanda zan dinga kula da
ita don zatinka afnan tai daria tace dakata
malam duk kyanka na kaika ne
Riqe baki yayi ya zazzaro idanuwa yace waneni
afnan amman kin kashe kanki aike kyawunkine ke
fitarda adonki
Bawai adonkine ke fitar da kyawun nakiba
Sannan duk iya adon mutun idan. Idan yaxo
gabanki saiya rude
Shin wai akwai. Wanda ya tava fadamiki cewa. A
duk sanda kikai murmushi kinfi kyau?
Wlh ke kyakkyawace dubi yaddah fuskarki ke qalli
sai kallon fuskata nake a ciki
Wani qayataccen murmushi taja sannan tace
maza kenan
Tace ibrahim mai yasa kasan irin kalaman da
nakeso a fadamin magana ta gaskia da kuma mai
kama da tatsuniya?
Yace ki yarda dani afnan Wlh a rayuwa bani da
Wani buri daya wuce na mallaki zuciyarki dake
kanki gaba daya
Yace Wlh ina cikin damuwa afnan tsorona daya
karkice ba zaki amince min na zama mijinkiba
Afnan ta girgiza Kai tanajan Wani gajeran
murmushi sannan tace. Hmm
Ibrahim kenan dondai kawai inajin tsoron halinku
na mazane in banda haka danace na baka
zuciyata da komai nawa
To kudinne dai lamarinku sai allah
Amman ina mai tabbatarma da idan na shirya
aure yanxu da babu Wanda zan aura sai kai
Tuni zufa suka karyoma ibrahim ya sulale qasa
saman gwiwowinsa ya zama abin ban tausaya
Murya kamar zaiyi kuka yace
Haba afnan ki tausaya ma radadi gamida zogin
sonki dake addaban zuciyata mana
Ki tausayama lamarin dake hananin sukuni dare
da rana daman ance kama da wane ai bata wanie
a zahiri nayi kama da maza ta hanyar halitta
amman ba zai kasance ace zuciyoyinmu sun
zama iri dayaba kowa da irin tasa zuciyar
Wlh inhar kika aureni ba zakiyi nadamaba afnan
Ina mai tabbatar miki da saukin manta da duk
Wani baqin ciki dake cikin duniyarnan
Saina dawo miki da farincikinki duk inda yake
Saina Nemo miki shi
Hmmm maza kenan abinda ta furta kenan ta
miqe
Ba tare data sake kallonsaba tace
Zan sanar da Abba ka turo da iyayenka cikin
satinnnan a tsaida ranar aurenmu wohoho
Wani dadine ya rufeshi yaji kamar ya goyata don
murna yace godia marar adadi afnan don Allah
idan kika shga ki turomin da taslim da aslim
Tace to tana fita falonta ta nufa tana isa ta
iskesu suna game suka rugo da murnansu suka
rungumeta suna don Allah mommy muje ki Siya
mana ice cream
Tai murmushi ta shafi kan yayan nata tace kuyi
haquri yanxu yammah tayi ku bari sai gobe kuje
inda ake sauke baqi dadynku nacan yana jiranku
Tsalle sukasa yaran suna murna suka fice zasu
ganin abbansu Wani murmushi afnan din tayi
Wanda ya tsaya iya labba
Yaran basu suka dagowa sai bayan magrib suka
shgo da gudu suka haye jikinta tace oyoyo my
twinsss ina kuka shgane kuda daddyn naku har
hankalina ya soma tashii
Sukace bako ina momy ai munce masa ma zamu
bishi yace a,a mu bari sai an mana hutu sannan
zaizo ya daukemu afnan din tace da gaske cikin
murna Sukace da gaske momy yanxuma ya tafi
Afnan na zaune bayan taci kwalliya ta hade cikin
wata danyar shaddah. Inka ganta zaka rantse
kace wannan budurwace danya sharaf. Ita
kadaice a falon nata tai shiru ko tunanin me take
oho
Can kuma ta tashi ya nufi sashin mai kula da
yaran nata
Tana isa taga yaran suma ana shiryasu tsaf cikin
Wasu sababbin kaya kala daya na namiji Dana
mace
Don haka taja hannunsu suka fice kowa ya Gama
shiryawa don haka qatuwar jeep din daddyn nata
shga shga harda shi daddyn nata. Don haka
direba ya jasu
A. G. R. A. Suka tsaya Suka dauki kausar sannan
Suka
Kama hanyar abuja ba hira suke sosai ba don
kowa da abinda yake saqawa a cikin ransa
Ibrahim ya kira afnan suka gaisa bayan sun
Gama gaisawanne yace abama su taslim yanason
Jin muryarsu ta basu wayar inda ita kuma ta
maida kanta jikin kujeran motar
Can tajiyo ibrahin da yaran hira ta barke a
tsakaninsu tun tana sauraronsu har. Tunani ya
rinjayi zuciyar tata misalin azahar suka isa garin
abuja
Kai tsaye gidan yari suka nufa ba tare da bata
lokaciba aka sanar dasu cewa tana medical
hospital
Don haka aka rubuta musu takardar ganinta suka
nufi asibitin jikin afnan har rawa yake wurin shga
Dakin da aka kwantar da mahaifiyar tata
Ji take kamar tai Mata Wani laifi tunaninta daya
batasan sa idon da zata kalli momyn nata ba
Ji tayi an riqo hannunta abbantane she harsun
shige ita tananan a tsaye
Yana janye da hannunta har suka isa Dakin da
momyn nata ke ciki afnanan tai matuqar kidima
ganin halin da mahaifiyar tata ke ciki
Har kusan kifewa tai sbd matuqar kidima saidata
dafa qarfen gadon da maahaifiyar tata ke ciki
Idanunta suka. Ciko da kwalla duk an jirkita
halittar mahaifiyar tata ashe ciwon sashin jikine
ya kamata
Ta riqe hannunta sashi daya daya mutun tace
Momy haka rayuwa tai dake?
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta kasa boye
kukan dake fuskar tata hajia nafin dake kwance
ta daura dayan hannun nata dabe mutunba Akan
afnan din
Itama hawayen take ta soma magana amman
maganar bata fita kamar mai kwaranci
Cikin kuka afnan ta dago tana kallon mahaifin
nata idanu jage jage da hawaye
Tace abbah ban fahimtar abinda takecewa yace
cewa tai kinga yaddah Allah ya maida ita duk ta
sanadiyyyar alhakin jama,a dake kanta
Sannan tace ki roqar Mata mutane Akan su yafe
Inhar ta mutu a haka alhaki bazai bartaba. Balle
har tasa ran samun rahmar uban giji
Afnan ta kifa kanta a kan momyn nata tace momy
na yafe miki kuma nasan duk Wanda kika zalunta
zai yafe miki inhar yaga halinda kike ciki
Hakan yasa hajia nafin taci gaba da magaba
saidai a yanxu babu mai fahimta don haka itama
taci gaba da kukan don babu bakin da zata fadi
abubuwan da takeson fada musu din
Aleeyu yasa hannu ya janye afnan din daga jikin
nafin ya girgiza Mata Kai alamun kukan ya isa
haka
Hakan yasa su kausa inna da malam suka
qarasa inda take sukai Mata ya jiki basu fahimcvi
abinda take fadaba sai aleeyune ke fada musu
Wasu kalaman nata idan shima ya fahimta
Gaba daya Dakin babu Wanda baiyi kukaba sai
aleeyu da Mala wadanda keta tofa Mata addu,o,i
Su taslim ma saida sukai kuka ganin momyn
nasu na kuka nafi tai musu nuni alamun suxo
sukaqi saida aleeyu yajasu yaje ya hada
hannunsu da nata yace kin gansu jikikonkine
yayan da afnan ta haifa
Runtse idanunta tayi tana Wani irin kuka mai
ciwo da alamun abin nacin zuciyarta
Basu Wani jimaba sukai Mata sallama. Saidaya
biya da yan jikokin nasa super market yai musu
siyayyah sannan suka nufo hanyar kano
Bayan shin shga Wani restaurant mai rai da lafiya
kowa yaci ya qoshi. Sannan sukayo hanyar gida
A yanxu afnan ta daina kukan da take saidai
ajiyar zuciya akai akai don haka kausar ta
janyota ta kwantar da ita jikinta gamida
lallashinta
Dukda tana kallon wayarta dake qara ta Gaza
dauka Dukda tasa mai Kiran ibrahim ne
Basu isa kanoba sai bayan sallar magrib ta
gidansu kausar suka fara sauka sukayi sallah
sukaci abinci sannan suka wucto gida
Tun daga bakin gate afnan ta hango motar
ibrahim yana kwannce a saman boot din motar
kansa na kallon sama suna tsayawa su taslim
suka kwasa da gudu suna ga daddy ga daddy
Aleeyu yace subhanallah yaufa ashe mukai da
iyayen yaronnan zasuxo Allah dai yasa ba zuwan
yammah sukai ba
Tace ba zasuyi zuwan yammabh ba tunda aina
fada masa cewa zamuje abuja. Aleeyun yace
yauwa
Da sauri ya sauko daga motar ya rungume yan
yaran yana dagasu sama
Ganin abban afnan din ya nufo inda yake yasa ya
saukesu ya zube yana kwasar gaisuwa
Cikin nuna kulawa aleeyun ya bashi hannu sukai
musabaha yace Allah dai yasa bamuyi muku
African tyme ba yace a,a suma. Nanda minti
talatin direba zai kawosu aleeyun yace masha
Allah
Sannan ya wuce ciki afnan dake tsaye wajen tace
Kai kumai maiya kawoka?
Ya lankabe Kai muryarsa tayi laushi yace
hankalinane yaqi kwanciya afnan don na kiraki
yafi sau hamshin amman kinqi dagawa
Ta yaya hankalina zai iya kwanciya afnan?
Saidayadan bata tausayi don bataga alamun
wasa
Ko zolaya daga idanun nasaba su taslim kuwa
sai tsalle suke jikinsasuna fadin sudai ice cream
zasusha
Cikin kakkausar murya tace Kai ku shigaa gida
mana
Ibrahim din ya janyosu yace a,a afnan karki korar
minsu har Cikin jinina nakejin yarannan don Allah
ki qyaleminsu
Ki fadamin meya hanaki daga wayata alhalin
kinsan muryarkice kawai ke kwantarmin da
hankali? Ko bakyasonane
Wani qayataccen murmushi taja tace haba ibrahin
aida bana sonka da tun farko ban kulakaba don
haka bai kamata ka dingamin wannan zarginba
Dubekafa babu ta inda Allah ya rageka kanada
kyau ga zati uwa uba kwarjini
Ga haquri sanin ya kamata aikai abin alfaharine
ga duk macen data sameka a matsayin mijinta
kuma uban yayanta
Ka yarda dani Wlh ina sonka da duk zuciyata
wami sanyin dadine ya ziyarci zuciyarsa
Har yakeji tunda yake a. Duniya bai tabajin
kalaman da sukai masa zaqi kamar wadannan a
xuciyaba
Bakinsa yaqi rufuwa yace Allah sarkin dadi inji
barawontakanda abinda ya iya cewa kenan
sannan yace
Afnan Wlh bazakiyi Dana sani miqamin
saoyayyarki da kikai gareniba nai miki alqawarin
saina shayar dake gidauniyar farinciki
Afnan din ta lumshi ido tana murmushi dadin
kalaman nasa na ratsa zuciyarta
Tace na gode bari na shga gida yanxu muka
dawo so nake na watsa ruwa nadan kwanta yace
ni kaina yanxu sulalewa zanyi karsu alhaji suxo
su sameni anan suce zaqewar tawa tai yawa San
sukai sallama
Ta fada gida cike da begeb juna
Qarfe takwas daidai iyayen ibrahim suka shgo
suma attajirai ne sossai akai kudin a qasa
Don haka aka karramasu sosai
Basu rabuba saida suka aje sadaki naira dubu
dari uku da kuma naiman auren afnan ga ibrahim
don
Haka malan ya tsaida ranar daurin aure nanda
Sati biyu masu zuwa
A. Kotu
Washe garin ranar itace ranar data kama ranar
litinin tanar dasu afnan zasu zauna a kotu inda
suka Gama shirya qwararan hujjoji Akan adnan
Don haka a shirye shuke kotun
Ta cika matuqa kamar kullun
Alqali na shigowa aka tashi domin diban gaisua
bayan mai gabatar da qara ya tashi ya gabatar
da qara kowa ya koma ya zazzauna
Alqali ya buqaci lauyoyi dasu gabatar da kansu
Barister muqaddam ya gabatar da kansa a
matsayinsa na lauyan dake kare Wanda ke qara
Mutum ne mai kwaxo da sanin aiki yakai maqura
wajen sanin haqiin dan adam
Lauyan kasuwane amman kuma
Mai tsadar gaske
Yana zama zaina sufwan ilyasu zee . Zee qawar
afnan ta miqe itama ta gabatar da kanta Akan
itace
Lauyar dake kare Wanda ake qara
Bayan ta zauna ne baristar muqaddam ya miqe
ya nemi izni a wajen Alqali kamar haka
Yace ya mai girma mai shari,a inason kotu ta
bani dama Dana taso da Barister afnan aleeyu
musawa domin nai Mata Wasu yan tambayoyi
Alqali yace an baka dama
Afnan ta miqe ta nufi kan yar kantar da aka
tanada
Don tsayiwar Wanda za.aima tambaya ko tuhuma
Tana qarasawa Barister muqaddam ya qarasa
gabanta yace malama ko zaki iya fadama kotu
Sunanki da kuma asalinki?
Afnan tace nidai asalin sunana shine hafsa. Ana
kirana da afnan ne sbd sunan kakata ta wurin
ubane da naci
Kuma ni yar asalin garin kano ce don. Anan aka
haifeni
Lauyan yai saurin jefo Mata tambaya yace
Ke yar asalin garin kanoce kuma kike amfani da
musawa ko zaki iya fada mana ta inda kika samo
hakan?
Afnan tai murmushi tace musawa asalin garin
mahaifinane shi acan aka haifeshi karatune ya
kawoshi. Garin kano
Lauya yace amman gaki kamar budurwa kuma
kike iqirarin kinada aure
Afnan tace kwarai kuwa. Niba matar aure bace
kuma ba budurwa bace
Barister ya zaro ido gamida cewa woot me kike
nufi da keba budurwa bace kuma ba
bazawaraba ???
Hmmmmm jama,a ku biyoni a next chapter donjin
yaddah kamarin zai wakana
And. I will like to. Apologist again. A lot ov ppl
zasuyi tunanin kaman wulaqancine ko hakanne
kawai yasa ban muku post kwana biyu ba da
kuma. Jia da nace muku zanyi post banyiba so
dan Allah
Aimun haquri kuma aimin uzuri. Banason trust
dina dake gareku ya samu tankarda ku yarda
dani hakanan bazanqi yin muku post ba.
Jiyanma naso nai post din. Ba yadddah zanyi.
Aure. Kan. Aure
Chapter30
Barister yace kamarya keba matar aure bace
kuma ba budurwaca inda muka tsaya kenan
Good
Ta gyara tsayuwarta tace sbd bayi aure shekaru
hudu da rabi da suka uce harda yaya biyu. Aslim
da taslim
Don haka ni bazawarace
Lauyan yace ko zaki fada mana waye kika aura?
Tace dan uwana na aura adnan aleeyu musawa
da kakana da nasa uwa daya uba daya suke
Tun adnan na yaro mahaifinsa ya rasu bayan
yabar mahaifiyarsa da ciki itama wajen haihuwar
ta rasu. Hakan yasa kakata ta dauko adnan da
niyyar ta riqeshi kasancear Yanxu babu yaro a
gabanta
Don bata sake haihuwaba tun daga kan mahaifina
Alokacin da mahaifina yaje musawane duba
iyayensa yaga
Adnan ya daukoshi domin ya samu ingattaciyar
Ilmi a
Birni don shima a lokacin babu yaro a gabansa
domin bai haihuba mahaifina ya dauko wacce
zata raineshi kasancewar mahaifiyata ba iyawa
zataiba
Ya kawo baba hauwa ita ta riqeshi da aka
haifenine ta hadamu ta riqe gabaki daya
Bayan Mun girma yaya adnan har qasar London
mahaifina ya turashi karatu
Yana dawowa aka hadamu aure dashi saidai abin
yaxo da matsala. Kasancewar mahaifiyata
batason auren
Wai ita tsohon. C. G. A. Takeson na aura wato
tsohon comander genaral na sojoji ni kuma bana
sonsa
Hakan yasa mahaifina ya jajirce Akan sai an
dauramin aure da adnan Wanda aka daura a.
Musawa. Daga baya kuma akazo akai musu
sharri Akan wai suna safarar hodar koken da
qananun yara. C. G. A ya kama mahaifina da
mijina ya daure inda yaketa azabtar dasu
Ananne shi mijin nawa yai lossing din memory
dinsa shi kuma mahaifina ya kakkarye
Don haka na nemi taimakon qawata wacce
mahaifiyarta aminiyar mahaifiyatace tana a
matsayin . D. G. P. Ne a garin abuja ta
taimakamin matuqa wajen shigar da qara kotu
kuma ta tsaya tsayin daka wajen ganin gaskiya
ta tabbata
Hakan ya samu ana cikin wannan hatsaniyane
aka likitoci suka bata shawarar a. Fitar da adnan
din waje don ciwon nasa. Idan ba,ai da gaskeba
zai iya rasa rayuwarsama gaba daya
Ba damar na bishi kasancewar ga halin da
abbana ke ciki da kuma zaman da ake a kotu
Gashi mahaifiyata harda ita wajen qullama
mahaifin nawa sharri
Don haka na Bama qawata alhakin kula da mijin
nawa
Bayan an Gama shari,a ne kotu ta yankema.
Janar hukuncin rataya ita kuma mahaifiyata
shekaru 25 a. Gidan yari sai muka tattaro muka
dawo garin kano inda
Ita kuma qawar tawa sady ta wuce qasar
Germany domin kula da mijin naWa
Daman munyi da itace Akan idan taje sati daya
kawai zataiyi ta dawo mu tafi tare
Tun daga wannan tafiyar ban sake sa sady a
idonaba
Naje cigiyarta gun mahaifiyarta tace ina ai
basanma anyiba
Abbana yayi duk wani bincike ajen Gano asibitin
da suke amman ba,a samu nasaraba
Sbd haka muka haqura amman ya bada cigiya a
media da offisoshin yansanda Akan duk Wanda ya
ganshi ya sanar da hukuma
Harna haifi yayana aslim da taslim babu lbrn
adnan da sady bayan na yayesune da yan Wasu
satittika saiga sady ta kirani a waya
Wai naxo na taresu a filin jirgi na sanar da kakata
Cikin zumudi na nufi filin girgi ina zuwane na
gansu ita da shi adnan din da jaririya nake
tambayarta inda ta samo jaririya take fadamin
wai
Ai sunyi aurene acan a asirce don karsu kauce
hanya
Hankalina ya tashi matuqa don haka na barsu na
nufi gida ban sakebi ta kansuba sai sau daya
shima a asibitin da abbana ya Gina masa naje na
sameshi mukai musayar harshe
Tundana dawo ban sake damun kaina a kansaba
sai wta rana da ake children's day a makarantar
yara
Ananne na hadu da adnan da qawata sady
Bayan am kira yara an basu kyaututtkua aka kira
taslim da aslim daga baya kuma aka kira siyama
aleeyu musawa
Ganin yarana na amfani da sunansa hakan ya
fusatashi
Har saida ya mareni da sharadi da Kiran yarana
shegu wadanda basu da uba. Kuma ya gargadeni
akana na
Akann na canjama yarana suna don kalen uba
nake musu
Naji takaicin abun a raina
Sannan a wannan kotun mahaifina yaxo aka raba
aurena da adnan da irin wannan jawabin Lauya
yace na gode
Sannan ta koma mazauninta Lauya ya dubi Alqali
yace ya maigirma mai sharia wannan jawabi na
afnan ba abin dubawa bane don kuwa ka a
makaranta ana
Iya samun masu suna iri daya
Misali zainab aleeyu. A. Zainab aleeyu. B
Idan kuwa hakane don an samu suna yaxo iri
daya ba abin dubawa bane
Sannan tana iya yiwuwa kamace da kuma macin
din suna
Don haka wannan ba abin dubawa bane
Na gode mai shari,a sannan ya koma ya zauna
Alqali ya qaraci yan rubuce rubucensa sannan
yace ko lauyan wacce ke kare mai qara tanada
abin cewa?
Ta miqe tai gaisuwa sannan tace eh ya mai
giema mai
Shari,a.
Wato inason kotu ta sani anyi shari,a a baya
tsakanin adnan afnan da aleeyu musawa Akan an
Mata aure kan aure
Shi. Janar na qararsune Akan aurensa aka fara
daurawa da afnan sannana aka daura da adnan
inda sadiya muhammad mai nasara ta tsayama
afnan da mahaifinta tsayin daka har saida gaskia
ta bayyana
Ta qarasa gaban Alqali gamida miqa masa jarida
ga hoton afnan Nan da abbanta da qawarta sady
an rubuta
An rubuta gaskiya ta bayyana da manyan harufa
Sannan ta miqama Alqali hotunan afnan da adnan
tun suna a skull da kuma yar qaramar. Camara
mai hade da video rananr kamun daurin aurensu
A take aka kunna kowa ya gani lallai ko wannan
kadai sun isa shaidu
Sannan inason kotu ta bada dama domin
kawomin iyayenda suke iqirarin sune iyayen
adnan din da suxo su fadama kotu yaddah akai
suka raineshi. Makaranta da yayi dama yaddah
rayuwarsa ta kasance ni
Kuma ina tare da shgaban makarantar da adnan
yayi tundaga primary principal dinsu na sakandire
Sannan barister zainab tace da wannan shaidun
nakeson
Kotu data yankema wadannan maqaryatan
mutanen da suke iqrari sune mahaifan nasa
hukunci sannan tasa adnan ya amshi yayansa a
matsayinsa na uba kuma ya amince da
yayansane
Na gode ya mai girma mai shari,a
Sannan ta koma ta zauna saida Alqali ya Gama
yan rubuce rubucensa sannan ya dago yace
Inason sajen. Kaida jami,an yansanda kuke duk
inda adanda suke iqrarin sune mahaifan adnan
suke a tahomin dasu yanxunnan aikija duk iya
bincikensu da sukai da kwatancen da akai musu.
Abin ya faskar don daman masu iya magana na
fadin idan asubanci kayi donka Riga ani wani shi
kwana yayi. Domin rigaka sun tattara dan abinda
suka samu sun ware
Don haka suka dawo suka saNar da Alqali abinda
ke faruwa. Ba tare da bata lokaciba Alqali ya
danqama adnan yayansa sannan yaci sady tara
harna naira dubu dari uku
Da. Hukuncin wata bakwai a gidan yari gamida
horo mai tsanani
Adnan yai kuka kamar ransa zaifita yace ashe
shiyasa sady keta kakkarewa da yace zaikai kotu
daya nace shine tadau fushi dashi hardasu tafiya
gidansu
Lallai dole yaje gidan nasu tabbas yau saitaga
fushinsa
Akan wasa da hankalin da tai masa
Kowa ya watse a kotun a
Adnan yabi aleeyu yana roqonsa gafara
Aleeyu yace ka daina zubar da hawayenka adnan
ni dama ban riqeka a raiba don nasan ba acikin
hayyacinka kake abubuwan da kakeba kuma har
gobe kananan a matsayinsa na dana
Yace na gode Abba Allah ya saka da alkhairi
aleeyun yace amin
Aleeyu ya nunama adnan malam yace wannan
shine kakanka ya zube a gabansa yana neman
gafara
Ya shafi kansa yace karka damu adnan ai rashin
sanine Bawai da gangan kayiba
Karka damu kaji tashi tsaye
Yana share hawaye can ya hango afnan tare da
ibrahim da barister zee zee gefe daya kuma
mustafane ibrahim na riqe
Da hannayen taslim da aslim
Adnan din ya qarema afnan din kallo ita da yaran
nata a take yaga tsantsar kamar da suke
Axuciyarsa yace lallai wadannan yayansane kuma
jinisa so kawai yake ai masa iznin ganawa da
yayansa amman sai yaga kamar duk cikinsu baba
Wanda yai niyyar yin hakan
Yananan tsaye har malam da aleeyu suka shge
mota innda mustafa da matarsa barister zee zee
suma suka shge da alamun wucewa zasuyi
ibrahim kuwa na tare da afnan yan yaran na
maqale dashi itama afnan din tafiya zatayi tayi
tayi Akan yaran su taho su tasu amman sukaqi
waisu a dole daddynsu zasubi ba yaddah suka
iya a dole ta barshi ta nufi inda motarta take
qiqam ta ganshi a gabanta don dama guri daya
sukai fakin ita dashi
Kallon sama da qasa tai masa sannan taja wani
dogon
Murmushi tana fari da ido
Tace lallai kaci assingmenta adnan tunda harka
iya Gano tsakanin nidakai wwake taqama da
uban wani
Waye ke kalen uba ta tabe baki sannan ta fada
motarta taja
Ta barshi anan tamkar mutum mutumi
Yafi minti goma a wajen bashida mafita dayafi
shima ya shga motar tasa yabar wajen saidai
koda ya shga motar zuciyarsa bata daina mai
sake sake ba
Waye mutmin daya daukar masa yara ina zai
kaisu?
Ina kuma son da afnan din tai iqirarin tana masa
a kotu?
Wadannan tambayoyinne suka tsaya masa a
kwakwalwa harya isa gidansa
Kamar yaddah yake zato babu kowa a ciki Kai
tsaye toilet ya fada ya watso ruwa wai a ganinsa
ko zai samu sassaucin abinda ke damunsa a
zuciyarsa
Amman ina babu abinda ya ragu na damuwa
daga zuciyarsa
Kamarma qara ingiza masa damuwar ake
Ya daura kansa saman fridge so yake yaita rera
kuka kozai samu sa,ida amman ina kukan yaqi
zuwa
Robar ruwa ya janyo daga fridge din ya bulbula a
bakinsa
Can kuma ya tsaya cak ya jefar da goran ruwan
Ya durkushe anan qasan tunanine kawai ya hana
zuciyar tashi sakat yace Waye shi? Taya za,ai
yaga sauran yan-uwansa?taya matarsa zata
dawo gareshi?
Ta za,ai ya rungumi kyawawan yayansa?
Ya qara kifa kansa a qasa sosai. Shin ta yaya
memorynsa zai dawo masa
Amsar daya kasa samu kenan anan ya kusa wuni
babu mai lallashinsa yace ya zaiyi dole ya
rungumi qaddararsa hannu bibbiyu
Anya kuwa zan iya abinda zuciyarsa ta sanar
dashi kenan
To bari mugani
Muje zuwa
Babu Wanda bai tausayama adnan ba
musamman aleeyu
Da yake ganin adnan din na cikin wani irin Hali
nda yake buqatar taimako
Yake buqatar su jashi a jikinsa
Afnan kuwa duk abinda take qarfin haline tsoronta
daya karta bayyana damuwarta a kirata marar
zuciya
Mai nacin soyayyah
Don haka duk yaddah taso ta tausaya Masa. Sai
taqi ta dinga danne zuciyarta don kawai ba
yaddah ta iya
Innama da ana bata lbr har kwalla tai masa tace
mai yasa ba,a taho dashi nanba
Lol kaji mutane Wanda Ada kowa kyararsa yake
Adnan ne zaune a cikin katafaren office dinsa ya
kasa komai zuciyarsa sai tarayo masa abindaya
faru a kotu take
Kamar mai mafarki ya tashi zumbur ya lalubi key
din motarsa yace Wlh tallahi mai rabani da sady
yau sai Allah don ta Gama zubar min da mutunci
kuma. Don tunda nake ban taba samun Wanda
yai min wasa da hankali irintaba.
Lallai saina nuna Mata kuskurenta ayau kuma a
yanxu ya zari key din motarsa a zafafe yabar
offishin nasa
Aure. Kan. Aure
Chapter31
Cikin zafin rai ya isa gidan nasu Wai basanan
daga ita har uwar tata hajia sury wai sunje.
Tailand harkan kasuwanci
Baiji dadin hakanba don yayi yuyyar samun sady
a. Gidan nasu
Afnan na zaune a. Offici dinta amman ta gazayin
komai don haka ta daura idonta kan takardun
dake gabanta ba tare datasan abinda ke
damuntaba
Masinjane ya shigo cikin girmamawa yace ranki e
Dade kinada baqo a waje ba tare da tayi tunanin
ko wayeba tace ce masa ya shgo
Yace to bai jima da fitaba taji an turo qofar office
din nata ta daga Kai don ganin mai shigowan
Adnan ne kallo daya ttai masa ta fahimci yana
cikin tsanananin tashin hankali
Zai zauna tace a,a waya Baka iznin zama koka
mance a offishin Lauya kake bana likitaba
Adnan Wanda harya dosana qugunsa ya miqe
muryarsa na rawa yace tuba nake ranki ya Dade
ba tare data tanjaba ta dauke kan nata
Ba yaddah ya iya dole ya bayyana Mata abinda
ya hanashi
Barci koda bazata saurareshiba
Murya a raunane ya kira sunanta afnan
Don Allah don annabi ki tausaya ma zuciyar data
rayu da sonki kuma take dawainiya da soyayyarki
kiyima masoyinki uzuri
Ke kanki kinsani ina cikin hayyacina ba zan iya
yin miki abinda nai miki a baya ba kin soni afnan
bazan iya sanin sonda kikai minba a accen
rayuwar
Ki taimaka ki nunamin wata sbwr soyayyar a
wannan rayuwar please afnan
Ya duqa saman gwiwoWinsa idanunsa sun ciko
da qalla yace ki yarda dani afnan
Tabbas kalamanta sun ratsa zuciyarta saidai ba
zata
Yarda son nashi yai galaba akantaba
Shiyasa har a yanxu taqi yarda dasu hada ido
Yasa hannu ya share qallar dake qoqarin zubo
masa
Yaci gaba da cewa Wlh afnan tunda naji irin
soyayyar da mukai nidake a waccan rayuwar data
goge a kwakwalwata nnaji kawai inason maimaita
irinta
Afnan ta miqe cike da fusata don tanada yaqinin
idan ta biye masa to abinda take gudun aukuwa
zai auku
Ta daga masa hannu tace saurareni malam oho
Bakin daya zageni yau shine yake roqona hannun
daya mareni shine yau yake lallashina
To inason ka sani xuciyata tayi nisa batajin kira
don koda maza sun qare babu abinda zanyi dakai
Adnan meye zan qaru dashi a wannan qaramar
zuciyar taka marar alqawari?
Yana shirin magana ta nufi hanyar fita domin
tabar masa office din
Ji tayi ya riqo gefen kwat dinta ta waiwayo da
hanzari ranta ya Gama vaci
Saidai maraicin data gani a a fuskartane ya karya
lagonta amman da babu abinda zai hana bata
daukeshi da wawan mari ba
Cikin daure fuska tace meye haka doctore
Yace afnan don Allah karki guji adnan dinki
yayanki Wanda yafi kowa sonki Wlh duk duniya
dani kika dace afnan
Ta tabe baki tace a wancan tsohuwar rayuwar
kake amsa adnan amman a yanxu doctor kake
Kaje koka jira duk sanda ka tuna da wancan
tsohuwar rayuwar da kake fada kuma ka tuna da
irin soyayyar da mukai
Saika dawo na amsheka a matsayin adnan
yayana Wanda yafi kowa sona
Ta fice ta barshi anan ji yai kamar zai koma ga
mahaliccinsa
Sbd qunar da zuciyarsa take
Tana kallonsa ya fito daga office din nata sannan
ta koma da sauri ta rufo qofar kamar wacce take
tsoron kar wani dodo ya shgo ofishin
Tana zama ta hada kanta da taburin dake
tsakiyar. Ofishin ji take wani abu na yawo a cikin
zuciyarta
Zainab ce ta shgo ofishin amman bataji shigowar
nataba saidai ji tayi an dafarta ta dago da
idanuwanta da suka rine sukai jajir sbd. Tunani
Zainab tace yanxu zan shigo na hadu da wannan
dan iskan me yaxo yai miki afnan taji kamar ta
watsa Mata ruwan zafi
Sbd zafim maganar datai Mata don
Haka cikin nuna rashin fahimta tace wanene
kuma dan iska zainab?
Baki ta tabe tace adnan mana yanxu na ganshi
fitarnan da zanyi
Wani murmushi takaici afnan din taja tace yanxu
abban
Twinss din kikecema dan iska?
Zainab dan uwananefa kuma kin sani
Zainab ta riqe baki sannan tace tab lallai duk
Wanda ya shga tsakanin masoya to shine zaiji
kunya amman Nan
Wani kalar zagine baki masa ba a yana dan uwan
naki
Nidai gaskia a riqe mana amanar ibrahim don
nasan irin halinmu na Mata
Hmmm afnan din taja gajeran murmushi tace
zainab kenan amman kin ban mamaki wlh
Yaddah nake ganin taraiyyarki da mustaba sai
nake ganin idan kece abinda ya faru dani ya faru
dake kenan bazaki iyayin adalciba?
Zan iya rantsuwa da saikin aikata son ranki
Amman duk yaddah nake qoqari ina bakin yina
har an fara samun wannda yaga gazawata
Yanxuma kenan anya Nan gaba ba gani za,ai ban
tabuka komaiba?
Da alamun tayi nazarin irin abunda afnan din keji
na rabuwa
Da masoyi kuma ba irin rabuwa na cikin
hayyaciba
Anya zuciya zata iya jure zafin irin wannan
rabuwa? To idan kuma itace ya zataji?
Musamman yanxu da adnan din ya dawo yake
nuna yaji ya gani
Ta dafa kafadarta tace Kiyi haquri qawata na
fahimci abinda kikeji kuma na tabbata idanda
nice bazan iya juriyar da kikaiba
Nidai abinda nakeso dake a yanxu shine kici gaba
da juriyar da kike kodan fita daga zargi a idon
jama,a
Afnan tace Wlh zainab vazan taba cin amanar
ibrahim ba bazan taba rabuwa dashiba inhar
bashine ya rabu daniba
Ya watsamin barkono a idoba
Sannan bazan taba sauraron adnan ba koda kuwa
zai mutu a gabanane don kuwa ya rigada ya
tsinke igiyar soyayyar dake tsakaninmu
Tace badonn kuma wai sbd ibrahim ba ko wai
sbd aminda mutane zasuceba a,a saboda kankin
kainane kawai
Afnan ta miqe ta sabi jakarta tana kallon zainab
tace ke ni kinga tafiyata
Itama miqewar tayi tana Allah e huci zuciyar
manya ammanfa Nibada wata manufa nai
wannan zancenba
Tace yo da wata manufa mana ai inhar baki da
baki suna haduwa to dole watarana sai rai ua
baci
A tare suka jera suka fice daga ofice din
Afnan tana kwance Akan gadonta tana kallo a
cikin
Laptop dinta yaranta duk sun kwanta ajikinta.
Tayi rigingine laptop din na saman ruwan cikinta
Tom an jerry suke kallo ita da yaran nata
Lami mai aiki ta shigo tace ranki ya Dade inna
tace wai kixo falo kinyi baqo
Tace to kice ina zuwa tace an Gama ranki e Dade
ta juya ta fice
Aje musu laptop din tayi tace to gashinan ku kalla
kuma sauran wajen rigima kuyimin barna babu
Wanda ya tanka Mata a cikinsu don duk
hankalinsu nakan jerry yayi Satan cinyar kaza lol
Nade kanta tayi da kallabin dake hade da
jallabiyar tata
Ta nufi hanyar falon tana shga gabanta yai
mummunan fadiwa. Gani tayi ya qara Mata kyau
ga kwarjiki a take ta nemi natsuwarta ta rasa
saida tai da qar sannan ta tattaro dakewar
duniyarnan ta dorama kanta
Ta qarasa cikin falon ko kallon inda yake bataiva
tace inna
Yanxu lami taxo wai kina nemana nayi baqo
Inna tace a,a ba baqo kikai ba adnan ne yaxo
shine nace
Kixo ku gaisa
Sannan ta juyo ta kalli kujeran da yake tace ok
guud sannu da zuwa dacta ya gida
Jikinsa yai sanyi duk wani kwarin. Kwiwa dayaxo
dashi ya sulale
Muryarsa kansa tayi rauni yace Lfy lau afnan ya
aiki?
Ta tabe baki ta juya tana shrin komawa sannan
tace lfy
Ji yai tamkar yasa hannu ya janyota saidai babu
dama yana kallonta harta bace
Ji yai gaba daya zaman ya gunduresa gashi inna
sai damunsa take da hira na yan uwansa
Jinta kawai yake don ba tuna komai yakeba a
ransa yace dama kira masa afnan din tayi ta
basu wuri qila da zaifi fahimta
Tana isa falon nata taji wayarta na ruri ibrahim
ne tana dauka ta Kara a kunne. Ina waje abinda
taji ya fada kenan ya kashe wayar
Fita tai ba tare data kula yayan nataba dake
gaban laptop don batason susain yaxo suje su
dinga takura masa
A waje ya tsaya saman boot don motarsa
Yana jiran ganin ta inda zata fito ta isa inda yake
tana murmushi tace wannan wannan zuwan naka
na bazata kumafa? Lfy dai ko?
Yace duk nakine sweet heart afnan ta riqe haba
tana murmushi tace waceni da daura zanin uwar
miji na yawo tsirara ai maryam itace sweet heart
ba niba
Ya kanne ido daya yace ai kowacce da wurinta
sannan ko wacce zata iya amsa sunan daya a
cikinku
Tace hakadai ka fada yace hakanema ki shirya
gobe domin muje siyan kayan lefenki
Afnan ta zaro ido tace wani lefe kuma ibrahim
nida ba budurwa ba
Kawai za,a tsayamin dawainiya
Ya harareta da wasa yace laifine don ango ya
siyama amaryarsa kayan domin ta dinga yin
masa kwalliya?$
Tace ba laifi bane yace to ki shirya su taslim da
aslim dasu za,aje
Ta amsa masa
Sannan sukaci gaba da hirarsu
Sai misalin magrib sannan yai Mata sallama ya
tafi
Sannan itama ta shga gida a daidai hanyar falo
taci Karo da
Adnan din shima yana niyyar fita
Kallon kallo suk tsaya sunayi tsakanin shida ita
Baice Mata komaiba ya giftata ya wuce inda tabi
bayansa da kallo harya fice sannan itama ta shga
ciki
Da safe misalin qarfe sha daya ibrahim yaxo ya
dauki afnan da yaranta suka shga kasuwa
siyayyah yai musu ta gani ta fada inda har saida
afnan din tau masa magana Akan ya barshi haka
sai yamma likis suka dawo gida agajiye don
dama ba wani hira sukaiba
Akwati hudu ya cikoma afnan din harfa dan kit
duk kayan lefene a ciki sannan taslim da aslim
suma aka cicciko mutu akwatina day daya manya
aka zubo masa a cikin mota
Bayan sun isa gidan yasa masu aikin gidan suka
shga da kayan ba wata hira sukai mai tsawoba
sbd gajiyar da duk sukayi yai Mata sallama ya
tafi itama taja yaranta suka nufi ciki
Ranar lahadi da misalin qarfe biyu aka daura
auren
Afnan aleeyu musawa da ibrahim hafis mai ruwan
kudi sunan da ake Kiran mahaifinsa din dashi
kenan
Daurin auren ya hakarci manyan mutane
Awannan lokacin adnan kasa jurewa yai haka
kawai yaji ya
Jarabtu da son afnan din
So bana wasaba sonda sai data zama matar
wani yaji bazai iya rayuwa idan bata ba
Kuka yake sosai shi kadai kamar qaramin yaro
sai safa da marwa yake a falon nasa
Baida mafita illa yasama ransa salama amman
ina abun ya gagara
Shi kadai a gida haka kawai ya zama kwabron
qarfi da yaji
Tunanin me yayi oho yallabai ba wanka ba wanke
ido ya zari makullin motarsa ya fice
Kai tsaye gidansu afnan din ya nufa ya dinga
kutsawa ta cikin mutane bai damu da hayayyaqo
masan da mutane sukayo masaba
Don cikin jama,ar idan za,a daura masa wuqa
bazai iya saninn koda sunan mutum daya daga
cikinsuba
Zaune suke ita da qawayenta inda nafisa ke fada
Mata mugun Hali irinna kishiyar tata wato matar
ibrahim
Zainab sai rurrufewa take afnan din tace barta ta
fada don nasan da irin zaman da zanje Mata
munafuka ai daman na sani shiyasa tuntuni
kiketa bobboyemin
Zainab din tace,a,a afnan kinsan bazan turaki
inda zakisha whl ba
Wlh idanda ban hango zaman lfy tsakaninki da
ibrahimba da bazan tabayin ruwa da tsaki Akan
lamarinba
Batun matarsa kuwa bana tunanin akwai abinda
zai dameki sa ita gidanki daban nata daban
Afnan tace kinganni Nan tsoron kishiyace dani
don tundana taso bamuda matar uba
Harna taso
Gashi ance fitinanniyar macece kinga kuwa zama
da ita sai anyi damara
ZuwAira tace damarama kuwa don kisa a ranki
zakije fada da shaidance yasin lol. Don wannan
matar tamafi shaidan iya shaidanci Wlh
Afnan. Ta zazzaro ido gamida dafe kirgi
Saidai kafin takaida qarayin. Wata magana sai
ganin adnan tayi tsaye a cikin falon idanunsa
sunyi jajir kamar Wanda yaci babu
Gabanta yai mummunan faduwa
Bata iya maganaba ta miqe ta nufi inda yake
baicema kowa uppan ba ya juya tabi bayansa har
farfajiyan gidan ya kifa kansa kan jikin motarsa
shi kansa ya rasa gane kansa da abinda ke
damunsa
Tausayinsa ya kama afnan din taji kamar ta
kwantar da kanta Akan gadon bayan nasa itama
ta zubar da nata hawayen
Saidai babu dama hakan yasa ta kira sunansa
Yaya adnan meke damunkane?
Daqar ya iya waiwayowa yana kallonta
idanuwanta sunyi jajir yace ni kaina bansan
abinda ke damunaba afnan na samu zuciyata da
matsanancin ciwo damuwa da radadin soyayyar
dake neman illatani
Afnan na tsorata ta yaddah zuciyata ta bijire take
nunamin cewa ba zata iya rayuwaba idan babu
ke
Afnan nayi kukan fili harma Dana boye babu mai
lallashina
Daga bayansa yaji ana cewa lallai indai irin
wannan kukanne kuma Akan afnan to wlh har
duniya ta nade ba zaka taba samun mai lallashin
nakaba
A fusace adnan din ya waiwayo don ganin mai
qara tunzurashi da Wadannan. Baqaqen kalaman
Lol shin Waye wannan oho Nima ban saniba
Mu hadu a nxt 
Aure. Kan. Aure
Chapter32
Ba kowa bane illa ibrahim bai damu dashiba yaci
da cewa
Afnan sonki zai zamo ajalina bakiji yaddah
zuciyata ke bugawaba kamar ta huje bana iyacin
komai
Ki tausayamin afnan ki taimakeni idan na rasaki
mutuwa zanyi. Na rantse miki don inaji a jikina
Tabbas tausayinsa ya ratsata har cikin jininta
Saidai lokaci ya rigada ya qure don koda bai
qureba ba
Zata iya amincema soyayyar docta ba
Don gani take kamar da akwai banbanci tsakanin
wannan adnan din da wancan yayanta adnan din
data sani kafin yayi losing din memory dinsa
Ta daure zuciyata ta voye abind ke damunta tace
kayi haquri don yanxu ni matar wani ce
Ya marairaice Mata yace afnan Kiyi haquri don
Allah
Ki ceci rayuwata wlh afnan bazan iya barinkiba
Don Allah afnan ki kasance tare dani
Zuciyata zata iya karyewa matuqa Tabbas idan
taci gaba da sauraronsa
Don haka muryarta na rawa tace kaga tafiyata
malam tunda Kai bakasan dokar aureba
Ya miqa hannu kamar ya riqota saidai hakan ya
gagara gaba daya yaji duniyar na juya masa
Daqar ya miqe ya shga motar tasa ya kifa Kai
saman sitiyari
Saidau ya Gaza Jan motar
In banda sunan Allah ba abinda bakinsa ke
furtawa
Harya samu natsuwa sannan ya kunna motar
yahau hanya
Tunda afnan ta koma ta rasa natsuwarta su
kansu qawayen nata sun rasa gane kanta
Zainab cema ta dameta da tambayar abinda ke
damunta tace don akkah Zainab barni kainane ke
ciwo bari nadan samu barci karkibar koma ya
shgo Nan
Babu yaddah suka iya dole suka barta saidai
zance barci ita kanta tasan yaudarar kanta take
Don duk iya Satan barci a wannan yanayin da
take bai isa ya saceta ba
Misalin qarfe biyar a yammah motocin daukar
amarya sukazo inna taima afnan din fada da
nasiha sosai
Malam ma yai Mata nasiha mai ratsa jinin jiki
Aleeyu ma yai masa tasa nasihar sannan
Iyaye suka tasa qeyarta zuwa anguwar sharada
Duk Wanda suka kawota sun watse anty kausar
kuwa bata samu zuwaba sbd batada lfy
Saidai Wasu daga cikin danginsu wadanda suke
mutunci sosai da afnan din
Gida ya rage daga afnan sai Zainab a ciki
Bayan sunyi sallar magrib Zainab ta share Mata
ko ina na cikin gidan ta goge. Ta saki labulaye
tabi ko,ina da turarukan wuta. Gaba daya gidan
yadau kamshi lol
Ta matsama afnan din ta watsa ruwa da kanta ta
zabo Mata Wasu hadaddun kaya da zatasa Riga
da siket
Kayan sun bala,in hawa jikinta sbd dinkin yabi
surar na jikin nata ta fito shar da ita. Kamar yar
sha takwas
Misalin qarfe takwas na dare ango ya shigo
gidansa tare da abokinsa mustafha
Afnan da Zainab din na falon har suka shgo babu
Wanda ya tanka musu har sukaima kansu
masauki
Mustafa ne ya soma magana yace
Ummm amarsu ta ango dubi yaddah aka wani
hakince sai kace sarauniya
Zainab ta miqe daga inda take tana fadin toya
son ranka
Yace yafa sweety kinga yaddah Dakin ke kamshin
amarci Kai gaskia Nima dole na zama ango
kwanannan
Zainab ta bishi da wani irin kallo mai kama da
harara
Yayi yar murmushi yace au ashefa kishiya fa ba
dadi amman wata tayi ruwa tai tsaki Akan aima
wata
Ibrahim yace Kai malamai kufa nake jira please
kwa Gama captar taku a mota
Gaba dayannsu suka kwashe da daria zainab tace
eh lallai yayi kyau tunda Mun Gama gyara masa
wasan ai dole ya koremu
Mustafa yace ai malam idan Kai haquri yanxu
zamu tafi mubar Maka amaryarka
Zainab tace ammman ai Mun tsaya mu sayi baki
ko?ibrahim yace wah ai wlh ba wani siyan baki
tashi zakuyi yanxu ku kama gabanku
Mustafa ya kalleshi yana daria yace yayi ustax ka
hadu da yawa
Ya dubi zainab yace tashi muje kinji wannan
angon gab yake daya shige da amaryarsa
yabarmu anan
Zainab ta miqe ta sabi jakarta da gylenta tace
umm
Bari mu gudu tun abin bai Kai nanba
Afnan dai da ido kawai take binsu saidai
murmushi da baiki kawai
Zainab ta rankwafa tai Mata rada sukasa daria
su muStafan suka miqe ibrahim din ya tashi
domin yin musu rakiya
Ta gagara motsawa daga inda take tunani kawai
take shin yanxu ko,a wani irn Hali adnan yake.
Ciki?
Qilama matarsa ta mantar dashi komai a take taji
wani kishi ya yinkuro Mata
A haka ibrahim ya dawo ya sameta a takure waje
daya
Ya zauna gefenta yana fadin yadai madam?
Batace komaiba don haka yace taso muje ki
tAimakaminn na canja kayannan don muyi sallah
Ba musu ta bishi falonsa suka nufa Wanda ke
dauke da makekekn gado a tsakiya da duma
duman kujeru biyu
Afnan ta zauna kan gefen gadon tana kallonsa ya
zame kayan Jikinsa dagashi sai gajeran wando
Kirjinta yai mummunan bugawa tace innalillihi wa
innna ilaihir rajium
Bai kulataba dukda ya lura da tsoratar datayi ya
shga falonsa kamar jira taje yana shga ta fice da
sauri
Falonta ta nufa falone fankacece mai dauke da
bedroom niyi an qawatashi da kayan alfarma
Ta dingabin kayan Dakin da kallo. A ranta tace
lallai abbah. Ya kashe kudi Akan kayan dakinnan
nata ko
Kayan jikinta bata cireba ta haye saman gadonta
taja filo Bawai don tanajin barciba. Illa kawai don
ta rasa abinyi
Batafi minti talatin da kwanciyarba ya turo qofa
ya shgo
Har gaban gadon nata ya qaraso dagashi sai
jallabiya ta qara runtse idonta alamun tana barci
Darewa yayi kan gadon yasa hannu ya janyota
Jikinsa qara runtse idon nata tayi wai adole ita
kunyarsa takeji
Lol. Laluban kunnenta yayi yadan ciza da sauri ta
miqe ta riqe kunnen nata. Yana Mata ani siririn
murmushi
Sannan ya rada Mata tashi muje muyi sallah ko
babyna
Bata musa masaba ta yinkura da alamar. Ta
miqe ya qara janyota jikin nasa. Idanuwanta
sukai narai narai tace sallah fa kace zamuyi
Ya lumshi idanuwanta sannan ya Bude yace
banso kibar jikinane afnan zanso ace Mun kwana
a haka
Tace mubar saLlar kenan
Sakinta yayi yace no afnan muje domin mu
godema Allah daya nuna mana wannan ranar
Bata jima a toilet ba wajen dauro alwala ta fito
taga harya shimfida darduma
Bayan sun Gama ne sunyi addu,oi
Sannan ibrahin ya miqe ya nufi falo bai jimaba ya
dawo da wani qaton flask da plates
Naman kazane banqararra sai huci take sannan
ya koma ya dauko kayan sanyi. Ya aje a gaban
afnan din
Sannan ya cire Mata hannu ya cire Mata tagumin
datayi
Tana kallonsa. Yace haba afnan wannan ranar
ranacefa ta farinciki. Amman dubi yaddah duk
kikabi kika damu kanki
Haba afnan koko dai so kike ki batamin daren
angoncin nawa?
Afnan din taja wani murmushi qarfin Hali ta
girgiza Kai sannan tace masa, a!a yace to bani
abinci naci
Da sauri ta dago Kai tana kallonsa
Suka hada ido. Duqar da kanta tayi qasa sbd
wani irin knyarsa data sauko mata
Yace kinajin kunyata ko afnan bari na kashe
wutar abar marar hasken. Ya yinkura da niyyar
miqewane yaji ana bugun qofar tasu. Da sauri da
sauri kamar ana shirin balle kofar. Afnan ta miqe
da sauri don hantar cikinta harta kada
Ta zare masa idanu ya bita da kallo yace kamar
bugun qofa nakeji. Waye yanxu cikin darennan
bari na duba
Afnan tai saurin kalllon agogon Dakin qarfe sha
daya dayan mintuna tai saurin kallonsa yai
murmushi yace ina zuwa dear bari na duba
Yana shirin tashi ta rirriqo hannunsa ta rirriqe
tamkar mai shirin kuka. Tace nidai uhm /uhm.
Karkaje inajin tsoro
Yai murmushi gamida shafan gefen kuncinta yace
tsoron me kuma afnan? Babu abinda zai faru Kiyi
zamanki ina zuwa
Ta rirriqeshi jikinta har rawa yake tace a,a ba zaki
barniba saidai muje tare. Yace to muje tunda
tsoro kikeji kada wani abu ya cinye miki miji ko?
Bugun qofar ya shahara kamar za,a balle kofar
gate. Din
Cikin daga murya ibrahim din yace wai Waye
annan?
Shiru ba,ai maganaba ya sake cewa wai waye?
Nanma ba,a tankaba saima ci gaba da dukan
gate din da akeyi. Wanda idan za,a kwana ana
duka bazaiyi ko gezau ba
Ibrahim ya fusata ya nufi hanyar gate din don
yaje yaga ko waye afnan ta rigoshi jikinta na
rawa tace, a, a ibrahim ka kira yan sanda
Yaja murmushi yace karki damu babu abinda zai
faru mai dear ya shafi kanta sannan yasa hannu
ya Bude gate din
Kamar afnan din ta saki fitsari sbd Bude gate din
da yayi saidai yana budewa wata mace ta shigo
babu ko hijab a kanta ballentana gyale
Hakan yasa kirgin afnan yaci gaba da bugawa
Ibrahim din ya kalleta ido waje yace
Maryam maiya fito dake cikin darennan?
Ban saniba amsar data bashi kenan har tana
watsa masa miyon bakinta
To jama,a. Akwai rikici kenan
Don Jin kodame Maryam din taxo cikin tsohon

Aure. Kan. Aure
Chapter33. End ov. B00K3
Ta riqe kugu tana dan iska munafiki wato
amanata zakaci ko?
Kenan ni inacan ina haukata a banza kaiko
kananan ko a jikina ko? To wlh duk danda ya
hana uwarsa barci to ko rintsawa bazaiyiba
Ta juya tai cikin gidan a guje ibrahim ya bita
yana Kiranta
Maryam Maryam. Afnan ma ta rufa musu baya
Nanfa rigima ta kaure tsakanin Maryam da
ibrahim
Maryam taci damara da dankwali
Gashin kannan duk ya tattashi tsaye sbd masifa
Chaiii. Fadi take na rantse da Allah yau saina
kunnama gidannan wuta. Wlh bazan mutu ni
dayaba macuci mayaudari munafuki kawai
Kaida a mafarkinka har kana zaton zaka kwana
da wace mace bayann nine?
Ibrahim ya daka Mata tsawa yace ke Maryam
Kinada hankali kuwa? Kanki kalau kuwa wace irin
fitinace wannan kikeson kunnamin ayau daren
angoncina?
Ta tafa hannu tana fadin ohh lallai su angonci
manya
Aiko za,ai angwanci yau cikin farinciki
Ta juya zata shga bed din afnan din ibrahim ya
riqota yace babu inda zaki wlh ficewa zakiyi
kibarmin gida yanxunnan
Cikin zafin xuciya tace sakeni nace kafin ya
ankara tayi wani kukan kura ta qace hannun nata
ta fada bangaren afnan din. A guje
Afnan din dashi har rige rigen binta suke don
suga hukuncin ubangiji
Tana shga tai Karo da naman kajin da basu
somaciba da kayan sanyi tasa qafa tai fatali
dasu. Sannan ta dauki wuqar dake wajen ta nufi
kan gadon ta dinga farfarka zanin gadon da
katifar
Ibrahim na shgowa yai saurin nufarta domin
kwace wuqar tai saurin dagowa idanuwanta sunyi
jajir. Kamar wata mahaukaciya
Tace na rantse Maka da allha kana qarasowa
inda nake saina yankeka da wuqarnan
Ba yaddah ya iya haka ya tsaya yana kallonta
kaman wani dolo
Ta suri lokar dake jikin gadon da makata Akan
madubin dake tsakiyar Dakin. Madubin ya
tarwatse ibrahim yai saurin binta kanin abin nata
bana lfy bane
Ta nunoshi da wuqar hannun nata tace kana
nufoni zan Maka illa na tabbata
Cikin zafin rai yace so wat kimin din Maryam kin
Dade bakimin illar ba hakanne zai tabbatarmin da
ke cikakkiyar mahaukaciyace
Ganin yaddah yake yinkurin kamota dukda wuqar
da take kare kanta dashi. Yasa ta kwasa da gudu
ta finciko hannun afnan din suka fice falon da
gudu
Yana yinkurin biyosu Maryam din ta rufe Dakin da
key din dake jikin qofar sannan tahau afnan da
duka
Afnan ba gwanar fada bace asalima ku cacar baki
bata iyaba
Don haka ba qoqarin ramawa takeba qoqarin
Qatar kanta kawai take
Maryar ta janyo wuqar take hannun nata tana
qoqarin yankar afnan din afnan din ta dinga ja da
baya harta qureta I zuwa bakin bango
Tabi wuqar dake hannun Maryam din da kallo
tace innalillahi bata da mafita illa ta runtse
idanunta kawai
Kamar a mafarki taji tana fadin yar iska munafuka
ai tunda kikace gonata zaki shiga to wlh sai naga
bayanki
Kamar daga sama taji saukar wuqa a goshinta
afnan din ta kurma wani uban ihu takai hannu ta
shafi goshin nata
Jinine sosai kamar an watsa ruwa
Afnan Tabi hannun nata da kallo ido waje tana
qoqarin kuka
Maryam din ta sake Kai Mata wata yankar cikin
zafin nama ta kauce ta yanki bango sannan ta
rirriqeta suka kaure da kokawa
Maryam na qoqarin saita yanki afnan din kuma
na qoqarin amshe wuqar gaba daya sunjima
kansu ciwo
Hannuwansu kuwa sau zubar da jini yake
Afnan ta samu ta kwace wuqar a Lokacin data
watsar da Maryam din gefe guda ta baje ita
kuma ta kwasa a guje
Ta Bude Dakin da Maryam din ta kulle ibrahim din
Fitowa yai hankalina a tashe yaddah yaga afnan
din ke zubda jini ya riqota saidai bai samu tabuka
Mata komaiba yaddah yaji Maryam din nata ta!
adi a falon
Ta dauki dvd ta buga a jikin TV din dake manne
na bango komai ya tarwatse. Teburin dake
tsakiyar falonma ta kakkarya shogilas din dake
gefen kusurwan Dakin duk kwalaben humran dake
ciki suka watse kasa suka tarwatse
Cike da baqinciki ibrahim din ya ture afnan din ya
nufeta yana fadar Maryam ya isheki haka yar iska
marar mutunci kawai bai Gama qarasawaba
shima ya tasa kwalba cikin kwalaben da Maryam
din ta fasa ta lume cikin qafarsa
Sosai. Wata irin gigitacciyar qara ya saka ya Fadi
qasa warwas
Afnan ta kwala ihu tayi kansa ta riqe qafar jinine
sosai ke fita sosai sai kace an yanka wata
qaramar dabbar
Ta saki wani irin kuka mai hargitsa zuciya
Ibrahim ya runtse ido sbd azaba afnan takai
hannu domin zare masa kwalbar da sauri ya
janye qafar yana girgiza kai
Afnan tabi qafar da kallo harta kumbura
tausayinsa ya kamata. Don ita batama damu da
nata ciwonba
Ta miqe ta nufi bed din nata Wanda Maryam ta
Gama tarwatsa komai wayarta ta zaro ta lalubo
numbar adnan
Kota ya akai ta samu numbers oho Nima
bansaniba@admin
Ringin daya biyu ya dauka bata tsaya fada masa
komaiba tace ka taimakeni yaya adnan kada na
rasa mijina yaya........
Cikin tashi hankali yace lfy maiya faru dashine
cikin wannan daren?
Bata iya amsa masaba ta saki wayar tai waje a
guje
Sbd qarar ibrahim din data jiyo har ilokacin
Maryam bata daina Mata ta,adi da bannata Mata
kayan cikin gidan ba
Ashe garin ya dingisa ya tashine ya saje taka
wata kwalbar dalilin daya sake kurma ihun kenan
Afnan ta rude ta shga matsanancin tashin hankali
Ta riqe hannunsa tama rasa me zatai rage masa
radaDin da yakeji
Bata damu da nata ciwonba da kuma yaddah
Maryam keta
Keta rusau a cikin falon nataba
Tana riqe da hannun ibrahim din taji saukar
qarfen shogilas din akanta afnan ta dafe Kai ta
sulale qasa bata iya ko motsi
Ibrahim bai wata wataba ya yayibo qafar Maryam
din dake kanta ya watar kanta ya bigi wani dan
qaramin tebur. Saidata shede
Cikin tsananin takaici da nadamar saninta da yayi
ya nunata dadan yatsa. Yace Maryam na sakeki
saki uku ban buqatar sake hada idanuna da naki
Yar iska jaka akuya kawai Allah yai wadaran
dake tirr dame irin halinki
Gaban afnan yai mummunan faduwa dajin sakin
da yai anan take. Saidai dishi dishi take gani
Kamar Maryam din na jira ta tashi ta shaqi
wuyar. Afnan din
Tana fadin na rantse daah saidai kowa ya rasa
ibrahim din na rantse kasheki zanyi
Adaidai Nan adnan ya fado falon kafin kowa ya
ankara ya dire inda Maryam din take ya fizge
hannunta daga wuyar afnan din ya. Wanka Mata
wani irn Marin da saida tai
Sakan talatun tana ganin jajayen taurari. Lol
Bama farareba. Hmmmm
Tana qara dawowa hayyacinta ya qara dauketa
da wani wawan Marin haQu da dama har Saidata
kifa
Sannan ya nufi afnan din Jikinsa sai rawa yake
ya tallabata ya kwantar a Jikinsa
Muryarsa da Jikinsa sai rawa suke yace lfy adnan
Waye yai miki wannan danyemn aikin?
Bata iya maganaba saidai numfashinta dake fita
da sauri da sauri
Adnan ya dubi ibrahim baima lura da cikin jinin
da yakeba
Cikin takaici yace ammandai Kai kaji kunya wlh
tirr dame irin halinka yanxu me afnan tai Maka da
har zaka taimaka wajen salwantar da rayuwarta?
Ran ibrahim cinkushe da baqin ciki musamman
dayaga afnan din kwance a jikin adnan din a jikin
qirjinsa. Ta lafe tamkar wata mage saidai maida
numfashi da take sama sama lol
Cikin tsananin zafin kishi yace bansaniba Waye
Kai da har zaja fadomin cikin gida babu ko
neman izni?
Adnan yace aikai kafi kowa sanin koni Waye
sannan rashin gaskiyarkane yasa na shgo cikin
gidan naka ba tare da izniba
Ibrahim yace wacce rashin gaskiyace wacce ta
wuce shgomin da kayi cikin dare ashe kenan
bibiyata kake to lallai yau hukumace kawai zata
rabamu dakai
Afnan yace kamar yaddah na fara sanar da
hukumar kafin naxo ba
Ya kalli afnan wacce ta fara dawowa cikin
hayyacinta ya shafi ciwon dake goshin nata yace
Kiyi haquri afnan muje nai miki dressing din
ciwukan naki
Wohoho. Wato idanda zaka daura hannunka kan
kirgin ibrahim a wannan Lokacin aradu zaka iya
konewa sbd tiririn
Da yake. Tsabar kishi kawai. Ita kanta afnan din
ta lura da irin kallon da ibrahim din ke musu
ganin haka yasa ta zame jikinta tace tsaya yaya
bari nai Maka bayani
Bai tsaya saurarentava ya janyo hannunta hakan
yabama ibrahim damar. Harde qafafun adnan din
babu abindaya tareshi yai taga taga har saida yai
Karo da bangon dakin
Ji kake kuuuuuuuuuum afnan ta kwala ihu tayi
kan adnan
Din. Tana jijjiga Jikinsa tana Kiran sunansa
amman ko
Motsi bayayi. Babu alamar numfashi a Jikinsa
Afnan tasa ihun kuka tana na shiga uku na lalace
shikenan ka kasheshi. Ta kife akansa tana wani
irin kunjin kuka
Maryam ma dake tsaye ta soma tafa hannunta
tana fadin wannanma yayi min daidai ibrahim
yayi kyau daka kasheshi Akan idona wlh ka biyani
Ta nufi inda adnan din yake tasa hannu taji ko
yana Motsi ko baiyi taji shiru baya numfashi
Ta daura kanta saman ruwan cikinsa nanma
shiru tasa hannunta ta daga hannunsa nanma ya
Fadi ragwab
Maryam ta miqe tana wata irin dariyar mugunta
Tace haka nakeso don haka kaga itama yanxu
saina kasheta
Inyaso a hadamu ni dakai a kaimu. Gidan yari mu
qarasa rayuwarmu acan
Wata irin zazzafab zuface ta soma lullube ibrahim
Ya soma girgiza Mata Kai alamar kartai haka
Ko kallon inda yake bataiva ta dauki wuqar dake
qasan ta nufi kan afnan din cikin zafin rai
Afnan din cikin firgice. Da tsoro ta soma ja da
baya.
Mai zai faru mu hadu a book4
Danjin yaddah zata kaya shin adnan din ya
mutune ko kuwa? Maryam nacin nasaran kashe
afnan din?
Oho taya za,ai na sani mu hadu a book4 Danjin
yaddah wannan lamari zaai kasance
Aure. Kan. Aure. Book4
Chapter34
Cikin tsoro take ja da vayan cikin ikon allah kuwa
taci Karo da wuqar da Maryam din ta yanketa
dazun tai saurin duqawa ta dauka
Maryam na qarasowa afnan din ta runtse idonta
saiji akai Maryam ta. Kurma uban qara ashe
runtse idon da afnan tayi. Yanka takaima Maryam
din da wuqar dataci Karo da ita din cikin ikon
allah kuwa tai sa,ar yankanta a fuska
Wani irin wakakeken yankane afnan din tai
Mata tun daga gefen hanci har zuwa wajen kunne
Nanfa
Maryam ta duqa tana kururuwa adaidai Lokacin
yan sanda suka shgo suka zagaye falon afnan ta
saki uqar hannunta tana cije lebe don bataso yan
sandan sukaxiba don
A Lokacin yaddah zuciyata ta qeqashe so tayi ta.
Yayyanki Maryam din don itama taji yaddah taji
Yan sanda suka zagaye falon mai camera ya
soma daukar hoton adnan dake kwance shame
shame
Sannan aka hada hannun afnan Dana Maryam ala
datsa musu ankwa yan sanda suka tasa qeyarsu
sannan Wasu daga cikin yan sandan suka tallabi
ibrahim din shima sukai waje dashi
Dan sanda daya yasa wuqar da afnan ta saki a
cikin farin qalle sannan suka tattara harda gawar
adnan din suka fice
Aka garqamama gidan qaton kwado basu wuce
ko inaba sai police station inda aka wuceda
ibrahim da adnan asibiti
Cikin dan qanqanin lokaci akaima ibrahim din
dressing din qafar tasa aka cire masa kwalbar
sannan akai afishing yan sandan dashi inda shi
kuma adnan din suka barshi anan domin likitoci
suci gaba da bincike akansa idan zai tashi
Ibrahim ne da afnan tare da Maryam a. Ofice din.
D. P. 0
Yana zaune cikin kujeran dake gaban tebiirin
dake office din da biro a hannunsa yana jujjuyawa
yace
Yace Kai malam ibrahim kace yau aka daura
Maka aure?
Yace eh wlh. D. P. O yau aka daura mana aure
kuma yau matata ta tare wannan yar iskar matar
tazo ta haddasa mana fitina a cikin gida
Maryam ta sako baki tace ba wani Nan yallabai a
kan idona ya shaqare bawan allah ya kasheshi da
hannunsa
D. P. O ya kalleta ta cikin baqin gilashinsa yace
to yanxu kena tambaya tai shiru yace lallai zaki
fuskanci fushin
Hukuma. Inhar kika qara sako mana baki bayan
ban tambayekiba
Sannan ya maida kallonsa kan ibraheem Wanda
shi kadaine ke zaune sbd ciwukan dake qafarsa
Yace inajinka ibrahim kuma wace hujja ce zata
tabbatar mana da yau aka daura Maka aure
Yace iyayena duk zan bada number su aka kirasu
kuma matannan da kake gani anan dukansu Mata
nane
Wannan itace uwar gida dan har yaya ke garemu
waccan. Kuma amarya yau dinnan ta tare a
gidana kuma ko wacce da gidanta daban
Nanfa ya zaiyane masa abinda ya faru tun daga
A to z
Sannan. D. P. O ya koma wajen Maryam yace
wane daliline ya kaiki gidan amaryar mijinki a
ranar data tare?
Tace malam takalata akai kaga wannan mutumin
da kake gani yaudarata yayi yau kusan kwana
bakwai kenan ban sashi a ido ba babu cin yau
babu na gobe duk inda nake tunani zan ganshi
abin yaci tura don haka yau na saneshi a gidansa
D. P. O yace da musalin qarfe nawa?tace qarfe
tarane batama qarasaba
Yace dawa dawa kika samu a cikin gidan tace
shida matarsa
Sannan ya juya ya kalli ibrahim yace ibrahim
misalin qarfe tara na dare kana ina?yace ina tare
da abokina a gidansa bamu isa gidan amaryaba
sai goma na dare kuma Muna isa abokin nawa ya
dauki matarsa suka wuce
Qarfe sha daya kuma Maryam taxo
D. P. O yace to Waye mutmin da muka samu
kwance rai a hannun allaha gidan naka?
Yace saurayin amaryatane. Dr adnan aleeyu
musawa
Wanda yaxomin har cikin gidana ba tare da
izininaba ya shgo har cikin falona. Ya dinga
yinma matata rungumar da ni kaina tunda aka
daura mana auren ban mataba a cikin daren
ankwancin nawa
Ganin haka yasa nasa qafa na haurar dashi
tsautsayi yasa kansa ya bugu da bango ya Fadi
qasa warwas
D. P. O yace kace kishi ne yasa kayi kisan kai?
Ibrahim din yace a,a Bawai kasheshi naso naiba
Abinne kawai yaxo da tsautsayi amman na rantse
har yanxu banji nadamar yin hakan ba
Yace yallaba ka kwatanta abi akanka. Matarka
tsohon mijinta ya shgo Maka gida a ranar daren
angoncinku harya dinga rungumarta kuma a
gabanka kana kallo in kaine wane mataki zaka
dauka?
D. P. O yaja dogon murmushi can kuma yace
hukuma kawai zan sanar mawa domin kuwa
daukar doka a hannuna bata tasoba
Saidai kuma kasan kafin. Dr adnan ya shga
gidanka saida ya sanarma hukumar yan sanda
cewa yar uwarsa ta kirashi
Akan yaxo ya taimaka Mata gidanta babu lfy
kuma ya bamu adress din gidan ba tare daya
jiramuba yai gaba kafin mu iso
Ibrahim yace yar uwarsa kuma wacece yar
uwarsa?
Cikin kuka afnan tace gani Nina kirashi nace yaxo
gida babu lfy
D. P. O yace samun sauqinka daya shine adnan
ya farfado don kuwa inhar rai yai halinsa adnan
ya rasu to kaima kasan Tabbas. Hukuncin
ratayane zatahau kanka don kasan hukuncin
wandaya kashe shine akashe ido waje
Yace wattt ratayafa kace yallabai. D. P. O yace
yes Tabbas
Don haka yanxu haka daga Kai har matan naka
tsareka anan Zamuci gaba daya har sai result ya
fito Akan kwaje kwajen da akema. Dr. Adnan din.
Tir qashi muje zuwa
Aure. Kan. Aure
Chapter35
D. P. O yace itama wannan shu,umar matar taka
kotu zamu turata kawai a yanke Mata hukuncin
daya dace
Nan take. D. P. O ya kira iyayen afnan Dana
ibrahim ya sanar dasu duk abinda ke faruwa
Ba,a dauki tsawon lokaci ba saiga. Abban afnan
dinnan ya iso aleeyu daga bisani kuma mahaifin
ibrahim shma ya iso tare da matarsa
Bayan sun hallarane. D. P. O ya sanar dasu duk
abindaya faru. Dukkansu sunyi al,ajabin abun
Hajia iklima kuwa sallallami ta fara tana tafa
hannu tace kwarai kuwa ai duk Wanda yaqiji
bayaqi ganiba
Meye ban makaba Akan karka qara aurennan ka
zauna da matarka daya amman kaqiji wannan
tsinannan yarinyar zata sakaka cikin ba,ai daga
kawota harta fara tara Maka mazaje a gida
Da sauri suka kalleta su duka sannan alhaj ashiru
ya daka Mata tsawa
Ke ya isa haka Kinji ko ya isa haka banson
shirme
Nan taja bakinta ta tsuke sai girgije girgijen
masifa take
Ana cikin hakane sako ya shigoma. D. P. O cewa
ai
Adnan zai iya tashi akodawani lokaca. Sassanyar
ajiyar zuciya afnan ta saki. Zuciyarta shar shima
ibrahim din ba qaramin dadi yajiba don bazaiso a
ce yayi kisan kaiba kasancewar ko kaza bai taba
kashewa ba
Ananne abban afnan ya roqi alfarmar a saki
ibrahim yaje yai jinyar qafafunsa tunda komai
yaxo da sauqi
Ba musu suka sakeshi sannan sukace itama
Maryam suna neman alfarman a basu belinta
D. P. O yace! A a hakan bazai samuba koda kuwa
su mutanen sun yafe dole abar doka tai aikinta
Hajia iklima ta sako baki tace ai kuwa saidai
suma su tafi da yar tasu har sai randa aka sako
ita Maryam din
Babu Wanda ya kulata Nan sukayi sining din da
zasuyi
Sannan yan sanda Mata suka tasa qeyar Maryam
din zuwa cikin cell . Lol
Alhaj asshiru yabama Abban afnan haquri gamida
cewa insha
Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. Sannan
gaba dayansu suka wuce asibitin da aka kwantar
da adnan din
Alokacinda suka isa likitocine duqufe akansa
tsawon awanni hudu kenan. Don haka suka nemi
waje suka zauna
Wata nurse ce taima afnan dressing din ciwukan
dataji
Tsawon awanni shiddah likitoci nakan adnan
sannan suka fito da hanzari alhaj ashru da abban
afnan suka miqe
Gamida nufa inda likitan yake yace su biyoshi
office
Nanne yake fada musu sakamakon buguwar da
adnan din yayi yasa memory dinsa ya dawo
bayan sun bashi taimakon gaggawa
Don haka zai iya farfadowa daga yau zuwa gobe
Godia abban afnan din ya shga yin masa
Akayi lissafin duka abinda zasu biya sannan suka
fita suka biya abban afnan ya tilasta ma alhaj
ashiru tafia tunda sunga yaddaha lamarin ya
kasance
Abban ibrahim din da kansa y dauki su afnan din
amotarsa ya ajesu a gidan nasu inda ya dudduba
barnan da Maryam din tai musu ya girgiza Kai
gamida cewa yarinyarnan bata kullama kanta
arziqiba hajia iklima tace ai komai tayi janta akai
don haka ni banga kaifintaba wlh da subiyunsu
suke zaune tayi hakan?alhaj ashiru ya bita da
harara sannan yace wuce muje Kinji karkisa raina
ya qara baci
Yai gaba sumi sumi tabishi a baya
Afnan tai musu rakiya. Sannan yace tayi haquri
zuwa Anjima zai turi da wadanda zasu sake
shirya Mata komai na cikin gidan nata shi zai
biya
Tayi godia sannan ta dawo cikin gidan tana
kallon iri varnan da Maryam tai Mata saidai rabin
tunaninda da hankalina nakan. Da tunanin halinda
yake ciki
Sannan ta shge ciki Kai tsaye kichin ta nufa ta
bata lokaci wajen hada musu break mai rai da lfy
sannan ta dibesu ta wuce darect bangaren nasa
inda ta sameshi kwance kan doguwar gujera ya
daura qafafunsa kan tebur din dake tsakiyar falon
Ta aje komai a gabansa sannan ta dubeshi tace
bismillah
Ya kauda Kai tashi tayi ta koma wajen da yake ta
daura kanta kan kafadarshi muryarta a sanyaye
tace ka tashi muyi braek tuba nake ranka e Dade
mai gidana na kaina
Bai tanka mataba hakan yasa ta riqo hannaynsa
ya sauko ta zuzzuba masa komai ya qureta da
idanu ko kiftawa baiyi
Lol mayae kawai
Afnan ta tallabe fuska tana kallonsa tace yanxu
ya kakeso nayi da rayuwatane eye ta tashi da
kanta tana bashi abincin a baki harya qoshi shi
kansa yayi mamakin irin abincin dayaci bayan ta
Gama tasa tissue ta goge masa bakin nasa
Zata tashi kenan ya jonyota Jikinsa ya
rungumeta gamida cewa me kike nufi ke bazakici
komaina?
Tace nawa yana kichin ya qureta da idanu yace
kina nufin ba tare zamu dinga cin abinciba sbd
me?
Yaddah ya qarashe maganar har saidayaso ya
bata tausayi don haka ta zauna domin taci yace
a!a wannan aikinane da kansa ya soma bata har
saida ta ture hannunsa alamun ya isheta
Bayan ta kwahse kwanukan takai kichin ne. Takai
kicinne ta Kawo masa magungunan da aka basu
a asibiti yasha itama Tasha nata sannan ta miqe
Yace ina kuma zaki ta lumtse idanuwanta sannan
tace barci nakeji zanje nayi
Ya miqa Mata hannu itama ta miqe ya janyota
Jikinsa
Gamida qanqameta yace babu inda zakije kiji
dadin barci a yanxu sama danan. Don haka yi
kwanciyarki anan
Babu yaddah ta iya dole ta lafe a qirjin nasa tun
tana sake saqe har barci mau dadi ya sureta
Bata tashi farkawaba sai bayann sallar azahar
Tana tashi taganta manne a girjinsa shima barcin
yake sunyi filo da. Hannun kujera
Zame jikinta tai ta nufi sashinta. Ta fada toilet ta
watso ruwa duk kuwa da zafin da ciwon nata ke
Mata bayan ta Gama wankanne ta dauro alwala
tai sallah tana gamawa taji ana sallama
Ma,aikatan da daddyn ibrahim din ya turo ne don
haka tayi musu iso sannan ta koma sashin
ibrahim din shima ya farka yana sanye
treequarter da wata tshirt fara qal
Ta zaro ido tace Kai ya akai gurgunnan yai qafa
yace ej shiyasa kika sulale kika barni ko don
kinga banda qafafun binki ko?
Cikin sigar wasa tace ba haka bane kwalliya naje
nayo makaba
Yace dadin abinma aii bakiyi kyau ba
Ta zaro ido tana fadin da gaske ya daga Mata
gira ta nufi
Qofa tana fdin aiko saina sake wata yanxunnan
yasa daria
Yana ke dawo ni wasa nake miki ta waigo a
shaagwabe tana kallonsa tace. Ni allah ka barni
na sako wata
Yace zo kije dan qaraso taa zuwa ya janyota
Jikinsa yace kinyi kyau matata kyanda Mata dari
zasu kalleki su kauda kai
Kinsam Mata sunada kishi basuson ganin macer
data fisu
Kyau taja dan dogon haancinsa tace to sarkin iya
kalamai gafa masu aikin can daddy ya turosu
yace to lfy lau kice musu su soma aiki kawai
Tace angama yallabai ta fice insa tai musu izni
Akan su fara aiki kawai
Bayan ta Gama kichin ta fada domin hado musu
nagartaccen abinci bayan ta Gama ne ta jera
Akan tire ta
Nufi falon mai gidan nata suka zauna suna ci
gamida hira mai ban sha,awa kamar babu
abindaya damesu
Anan sukai sallar la,asar ibrahim ya kira musty
abokinsa yace yaje ya dauko masa yaransa a
gidan Maryam
Mustafan ya tambayeshi lfu?
Yac idan ka kawosu kaji yace to an Gama
Bayan sallar magrib aka kammala Mata komai
Dakin nata gunun ban sha!awa amman dukda
haka baikai da kyau ba kasancewar kayan da
suke nada din duka na qasar wajene
Amman wannan dinmaya bada ma,ana
Afnan na kichin tana hada musu abincin dare
musty ya shigo alokacin ibrahim na babban falo
Itama ta fito tai masa sannu da zuwa
Saidai ganinsa da yara yasa ta qaraso tana fadin
ina ka samomin yara kuma?
Musty yace dubesu dakyau kiga dawa suke
kama?
Afnan ta dafa kafadun yaran tana kallonsu kamar
ta sansu saidai ta. Rasa a inda ta sansu din
Ta dubi musty tace na Baka gari fadamin a inda
ka samosu
Daria yai yana fadin juya ki kalli mijinki
Afnan din ta juya ta kalli ibrahim Wanda ke kishin
kide yanacin ayaba tace Tabbas dashi sukai
kama
Ta kalli musty fuska dauke da fara,a tace wai
nashi ne?
Yace ba gashinan a gabankiba. Taja hannun yara
suka qarasa gabanshi take ku dubi wannan wai
abbankune da gaske?
Suka daga Kai afna tai daria tace ku zauna a jikin
abbanku kunji mai kukeso na dafa muku?
Babbar ta kalli qaramin su duka suka kalli
mahaifin nasu akai sa,a kuwa shima kallon nasu
yake sukai shiru
Tace yadai sai kallon kallo kuke
Musty dake shirin zama yace ai indai har suna
gaban. Ibrahim be basa iya magana
Babu Wanda ya motsa cikinsu sai kallon ibrahim
din suke itama shi take kallo ya wani hade rai
Yace ku tashi mana sai alokacin yaran suka tashi
Afnan ta hadiyi wani numfashi ba tar data tamka
masaba taja hannun yaran suka nufi kichin
Afnan ta dubi babbar macen wacce itace babba
tace aqallah zatakai shekara tara tace meye
sunanki
Tac sajidah ta dubi qaramin Wanda bai wuce
shekara shiddah ba tace Kai kuma fa yace salim
Ytai murmushi gamida cewa ashe dai Kuna
magana amman mai yasa bakwayi a gaban
abbanku gabadayansu
Kallonta suke ba Wanda ya bata amsa a cikinsu
Tai murmushi. Itama ba tare data takura musu
Akan hakanba tace Zaku tayani girki suka daga
Kai alamar eh tace to ku matso Nan ahaka taita
jansu da wasa da daria har suka kammmala suka
shirya komai Akan dinnif table sannan ta qarasa
wajen dasu ibrahim din suke tace yallabai ina
kayan yaran?
Ya nuna Mata trolling bags dinsu a gefe taja.
Gamida Jan hannun yaran sukai gamida fada
musu ga abinci can a dinng idan kun shirya bata
saurari amsar da zasu bataba tai ciki
Bayan yaran sun Gama cin abincin nasune ta
duba cikin kayan nasu ta dauko musu kayan
barcinsu
Bayan ta musu wanka suka saka bata Gama
shiryasuba tajiyi mustafa na fadin zai tafi don
haka
Ta Sanyo abayarta ta xo suakai sallama
Bayan sun Gama yin sallamarne ta koma wajen
yaran ibrahim na kishingide Akan kujera yaji
zaman ya isheshi
Don haka ya zaro wayarsa ya tura Mata da text
Ta soma karantawa
Wato kin samu yara kin manta dani konaci ko
karnaci ko?
Tai murmushi itama ta tura mishi da
Wanda kaci Kaida Abokinka fa?
Ya turo Mata. Waya gaya miki
Ni banciba please yunwa nakeji
Ta tura masa da ai mutum daya bazai iya cinye
abincin Dana zubo ba
Ya tura Mata da ai abincin daya naci sauran daya
Ta tura masa da ban ganeba
Ya tura Mata da Kixo inda nake zaki gane
Tai murmushi ta tura masa da anqi wayon
Yace please my wife inajin kewarki a jikina
yinwarki ta addaban
Don haka ta kashema wayar tata taci gaba da
kimtsa yaran bayan ta kammala tace to muje
kuyima abbanku saida
Safe kamar suce bazasujeba saidai ba yaddah
suka iya ita kanta ta fahimci hakan
Don haka sukaje yin masa saida safen a daqile ya
amsa musu abin baima afnan dadiba na ko in
kulan da
Ibrahim ke nunama yaran nasa
Sannan tajasu suka koma bed din nasu. Tai musu
addu,a ta fito inda ibrahim din yake ta nufa ta
nuna masa rashin Jin dadinta sosai Akan rashin
ko in kulan da yake nunama yayan nasa bai bata
amsa mai dadiba illa kaai ce Mata da yai kada ta
damu komai lokacine idan lokaci yayi ba saita ce
masa yaja yayansa a Jikinsa da nuna musu soba
akwaia abinda yasane lokaci kuda ya kasa Gano
kanta
Saidaya sanar da ita cewa in allah ya yarda zai
canja zai dinga Jan yayan nasa a Jikinsa sannan
fara,arta ta dawo
Daganan kuma zance ya sauya salo ya sureta
sukai bangarenta. Nayi qoqarin binsu amman ina
kafin na qarasa harsun datse qofar tasu hakan
yasa nayo baya nace bari na garzaya wuri adnan
naji ya abin take
A asibitin
Washe gari misalin qarfe sha biyu na rana adnan
ya farfado
Abban afnan na gefensa soma motsa yatsun
hannunsa da yai yasa alhaj aleeyun soma karanto
masa addu,oi
Harya Bude idanunsa sannan aleeyun ya kira
likita a waya yake sanar dashi abinda ke faruwa
Da hanzari suka nufo Dakin harsu uku da kayan
gwaje gwajensu
Suka Gama gwaje gwajensu sannan suka kira
sunansa in banda kallo babu abinda yake binsu
dashi
Suka sake yin masa wata allular barcin na take
barcin yai awon gaba dashi saidai barcin bamai
tsawo bane
Baifi minti talatinba ya farka a yanxu nurse suka
turo data kula dashi
Yana farkawa ya miqawa aleeyu hannu yace
Abba fadamin meke faruwane dani?
Aleeyun shima ya riqe hannunsa yana sannu
adnan sannu kaji ai daman likita yace zaka samu
sauqi
Bai kuma cewa komaiba ya lumtse idanunsa
Nurse din dake kula dashinne ta hada mishi tea
mai kauri gamida sa masa Wasu qwayoyi a ciki.
Sannan ta dauko wata yar tasa da brus ta matsa
masa maklin ta bashi yai brush sannan ya amsa
kofin shayin ya fara kurba a hankali a hankali
Can kuma saiya tsaya dashan shayin
Aleeyu yace yadaia dnan wani gurinne ke Maka
ciwo?
Ya girgiza Kai da muryarsa irin ta marasa lfy
yace ba ko ina Abba
Ina afnan?
Tambayar ta doki zuciyar aleeyu Wanda har saida
tsa ya koma kan kujerar da yake zaune. Ya fada
cikinta rakwab
Tuni zufa ta fara keto masa
Lol wacce amsa Abban afnan zai Bama adnan
Oho Nima ban saniba Mu hadu a
Aure. Kan. Aure
Chapter36
Yanayin yaddah Abban nasa ya shga yasashi
shima shiga
Cikin Yanayin tsoro har baisan sandaya saki kofin
tea din dake
Hannun nasaba ya Fadi cup din ya fashe yace
Abba lfy
Wani abune ya samu afnan din?
Don allah meya sameta? Aleeyun ya kamashi ya
kwantar yana fadin cool down adnan Baka ganin
halinda kake cikine? Koma ka kwanta babu
yaddah ya iya hakan
Ya koma ya kwanta yana fadin to fadamin abinda
ya sameta Abba ni nasan dai ba lfy donda lfy lau
da ina Bude idona da ita zanyi tozali
Aleeyu yace yanxu dai ka kwantar da hankalina
ka natsu ka samu cikakkena lfy . Afnan tana cikin
qoshin lfy don da kaina zansa tazo ta dubaka
Adnan din yace to amman abba....
Ya daga masa gamida cewa ya isa kayi abinda
na umurceka dayi kawai
Ba yaddah ya iya hakan ya koma ya kishin gida
gamida amsar wani tea din da nurse din ta hada
masa yana kurba
Dukda ba dadi yake masa ba.
Afnan taja yaran ibrahim a jikina kamar yayanta
cinsu shansu da tsaftarsu don ko mahaifiyarsu
sai haka
Burinta a kullun bai wuce taga yaran sun samu
soyayyah mai tsafta a wajen mahaifin nasu ba
Da yammacin ranar wata asabar bayan tayima
yaran wanka. Ta shiryasu cikin Wasu sababban
kayansu
Itama ta hade cikin wata Riga butic me hade da
jeans dinsa bayan anyi sallar magrib taja hannun
yaran zuwa babban
Falo inda ibrahim din ke zaune Akan kafet
dagashi sai trequater da singileti
Afnan ta qarasa wajensa ta duqa gamida kama
qafafun
Nasa tana mammatsawa
Ibrahim din ya kalleta yana murmushi yace
wannan kyau haka madam duk ni daya?
Afnan din ta ware idanu tai masa signa da
yaransa na tsaye
Yace to meye rungungumeki nayine a gabansu?
Afnan ta riqe baki wani irin kunya ya saukar Mata
dukda kuwa da turanci yai maganar
Afnan ta miqe ta kamo hannun yaran ta dinga
nuna masu yaddah zasu dinga masa tausa
sannan ta tashi ta nufi kishin dan dauko musu.
Abincin daren data shirya musu kafin ta dawo
hirace sosai ta barke a tsakanin uba da yaran
nasa
Wani dadine ya kama afnan din don har abada ba
zataso ganin yaran da iyayensu ke rayuwa dasu
kamar yaddah ta rayu da momyn taba itadai ta
rasa gatan uwa ta rasa shayarwar da iyaye kema
yayansu
Ta rasa gumin jikinta sannan ta rasa soyayyarta
Afnan ta sauke tiren dake hannunta sannan tasa
hannu ta goge yar kwallar data silalo Mata ba
tare dasun an kaarasa ta koma ta dauko sauran
kayayyakin gamida shimfida ledar xin abincin a
tsakaiyarsu
Bayan ta jejjera komai sannan ta dubi yaran
daketa daddannan jikin Abban nasu tace to ya isa
haka ku taso muci abinci
Gaba dayansu suka nufo kan ledar sunaci suna
santi daga yaran har Abban nasu afnan
itakebama salim a baki ganin bason ci takeba
ibrahim yace a,a dakata ni bari nabama salim din
a baki don na lura bason cin kikeba
Murmushi kawai tayi taci gaba dacin shima
sannan shima ya maida hankalina wajen Bama
yaron abindai. Kwanin ban sha,awa
Bayan sun kammalane afnan ta kashe kayan
abincin takai kichin sannan ta dawo ta canja
chennel. Din zee aflam fil din India ake mai kyau
don hak suka maida hankalins kan kallon sai
misalin sha daya sannan ta kashe komai ta dauki
salim ibrahim kuma ya dauki sajida suka kaisu
makwancinsu sannan suma suka wuce nasu
Dakin
Yaune ranar da ibrahim ya mallaki afnan a.
Matsayin mace don haka ranar taxo musu. Cikin
farin ciki fiye da dukkan ranakun da yai a
rayuwarsa don haka farin cikinsa a ranar yaqi
boyuwa ji yake tamkar ya daki afnan din ya goya
yaita xagaye gari da ita
Don haka koda gari ya Waye bai bari tayi
komaiba sajida da salim ya kira yace su shga
kichin don su hada ma kansu break fast a
ganinsa a zasu iya tunda duk shga kichin din da
afnan din take dasu takeyi shiyasa Baiji komai a
aransaba ya taimaka musu wajen kunna na!urar
girkin
Yana tsaye yana kallonsu suka hada ruwan shayi
da wainar kwai gamida. Soya dankali
Ibrahim ya dibarma afnan nata ya ya nufi
bangaren nasa harta tashi ta nufi toilet yanajin
saukar ruwa don haka ya aje ya fita saShinta ya
nufa ya zabo Mata kayan da zatasaka
Riga da siket ya zabo Mata inglish wear masu
kyau sannan ya fito
Sajida da salim ne Akan dinnig table ya qarasa
wajensu yana fidin yadai. In banda shayi da
biredin babu abinda suka iya ci a tsakanin wainar
kwan da dankalin
Jikin ibrahim din yai lakwas yace yadai sajida ba
zakuci bane?
Salim yace babu dadi wlh daddy bai dahuba
ibrahim din ya ture hannun yaron dake qoqarin
Kai masa wainar kwan baki. Sannan ya maida
kallonsa kan sajida yace au daman duk kaya miki
girkin da taje har yau baki iyaba?
Salim yace daddy ko shayinma baiyi dadin na
anty ba don allah daddy kace taxo ta dafa mana
Ibrahim din yaja wani gajeran tsaki ya nufi sashin
nasa ya samu harta fito daga wankan tana
kwalliya
Bayan ta gamane ya taimaka Mata tasa kayan
wohoho ba qaramin kyau tayiba Nan taje zance
ya sauya salo yaci gaba da nuna Mata wani sbn
salon soyayyar ba ita ta samu damar zare jikinta
daga nashiba sai misalin azahar don
Haka ta nufi inda kayan tea din suke shayi mai
kauri ta hada cup biyu ta miqa masa daya. Ta
amshi daya
Kurba biyu kawai tayi. Sannan ta yagi wainar
gwan takai
Bakinta saidai ta gaza taunawa don kuwa qarnin
kwan shine ya cika Mata baki kamar ba,a soyaba
hannunsa yasa ta zazzage Wanda ke cikin bakin
nata tace Waye ya soya wannan kwan kasa
magana yayi sannan ta dauko dankalin domin
taci. Shimadai Jia iyau don ko kadan bai soyuba
da gudu ta fada toilet ta wanke bakinta taxo
bakin gado sai daria take masa don duk a
zatonta shine ya hada
Ya miqa hannu zai kamota ta zille gamida fita
tana kyalkyala masa daria tana fitane taci Karo
dasu sajidah suna kallon film din India kichin ta
wuce direct ta dafo musu kuskus miyar kwai
gaba dayansu suka hadu a dinnig sunaci sai santi
suke musamman ibrahim dake fadin Ada ba
ruwana da kyau sbd duk matan dake girki dashi
saina dinga Jin qarninshi a tare dasu
Amman ke ko kadan duk yaddah kika sarrafashi
banajin qarninsa a tare dake saima wani
daddadan kamshi dake tashi shin wai nama taba
fada miki kin iya girki kuwa?
Afnan ta kyalkyale da daria tace vaka taba
fadaminba
Sajida gaskia kuyima daddyn Nan Naku waigi
Dukkansu dariar suke yace kin dauki abun santi
ne ko?
Yace na rantse ban tava tunanin kuskus nada
dadi hakaba
Afnan daria harda kyalkyalawa tace Kai ibrahim
wannan santi haka
Sajida tace wai anty mai yasa kullin kikai mana
shayi sai naji yana wani kamshin dadi amman
yau nawa baiyi hakaba
Afnan tace Kai ashe yan matane yau sukai mana
girki
Saidai ko har yanxu baki iyaba idan kuwa baki
iyaba mukai miki aure mijinnki korarki zaiyi yace
baki iya girkiba
Yar tai daria tana satar kallon abbanta anda ya
dauke kansa hankalina nakan abincin kawai
Afnan din tace karki damu sajida tunda har
kinason ki
Iya daga yau. Koda bamu shga kichin ba zan
zauna na dinga kyar dake yaddah ake girki dalla
dallah
Afnan ta miqe sbd bugun qofar da ake don taje
taga ko Waye. Hajiya iklimace ta shigo kamar an
bankadota mahaifiyar ibrahim kenan
Afnan tai saurin zubewa tana kwasar gaisuwa da
wani kallon banza ta bita ba tare data amsaba ta
shige ciki
Afnan ta miqe cikin sanyin jiki ta nufi cikin falon
Hajia iklima ta tsaya Akan ibrahim din tana
girgiza
Tace sannu shanyayye eh anyi amarya sabon jini
dole kake mannewa jikinta ka tsote man kaiga
sabon shga Wanda bai taba aureba ko
Toka saurareni duk abinda kake kaje Kai belin din
Maryam idan kuka kaqi wallahi saina tsine Maka
banza sakarai kawai
Ta kamo hannun yaran tace ku taso muje fon
neman gindin zama shine aka kwasoku aka
kawoku nan
Sajida tace mudai hajia bazamuje gidankiba ki
barmu a wajen anty kawai
Hajia ta tafa hannu tana fadin innalillahi wa
innailaihirrajiun yanxu matsiyaciyar yarinyarnan
kuma ta shanyeku ta shanye ubanku ni kadaice
na gagareta nafi qarfinta kenan?
To saikun tashi mun tafi kuma baqaqen munafuki
har kunfi son kishiya Akan uwarku
Salim ya maqale kafada yana shirin kuka ta
fizgoshi tace taso muje kona kakkaryaka
yanxunnan
Afnan dake tsaye gefe tausayin yaran ya kamata
batasan sanda tai magana ba tace don allah hajia
Kiyi haquri ki barsu anan
Kamar wacce aka sirfama zagi ta saki yaran ta
nufo wajen afnan din kamo hannunta afnan din ta
daura kan kunnenta tace . Tace kama kunnena
kiban umarni zanfiji Kinji uwata
Afnan tai saurin janye hannun nata jiki na rawa
tace Kiyi
Haquri don allah hajia wallahi niba haka ba.......
Rufamin baki munafukar banza Bude idanunki ki
kalleni
Ni nafi karfin iskancinki
Da kike ganina Nan Nima tsohuwar banzace naga
jiya naga yau kuma har gobe ma dani ake
damawa
Kai kuma saika zaba belin Maryam ko tsinuwa
don na tabbata inhar kaqi belin dinta. Saina tsine
Maka
Sannan ta juyo tanama afnan kallon uku kwabo
sannan tace ke kuma
Ta murza yatsun hannunta sukai qara sannan ta
juya ta figi jokokin nata sukai waje.
Babu inda bai rawa a jikin afnan hatta miyon
bakinta don ta fara tsorata da lamarin hajiyar
ibrahim
Chapter37
Jikin afnan yayi sanyi likis ta juya a sanyaye ta
nufi falon nata
Ibrahim ya bita da sauri yana afnan tai saurin
mayar da kwallan da suka taru a idon nata ta
qaqo murMushin qarfin Hali ta juya tana kallonsa
Ya qaraso wajenta gamida mannata a jikina yace
Kiyi haquri don allaha afnan wlh bansan......
Tasa hannu ta rufe masa baki tace meye kuma
na bani haquri ibrahim me akaimin na bacin rai da
har kakeban haquri?
Don mahaifiyarka tamin fada aiba wani abu bane
bata isa taimin fadan bane koko don ba ita ta
haifeniba?
Don haka karka kuma cewa komai Akan wannan
dan qannan abun daya faru ta sake qaqalo
murmushi qarfin Hali sannan ta nufi Dakin nata
Misalin qarfe hudu na maraice afnan na kwance a
falonta ibrahim ya fita ita kadaice a gidan zainab
ta iso
Cikin tsananin farin ciki afnan din ta tareta suka
zube Akan
Daya daga cikin tuma tuman kujerun dake falon
Zainab ta dingabin afnan da kallo tana fadin Kai
mutumiyar aurennan fa ya amsheki kinga yaddah
kikai
Wani masifar kyau?
Afnan tace dallah can gafara munafuka dubi
tabbuna a jikina ko Kixo kimin jaje
Tace aiya qawata wlh naso naxo aikine yaimin
yawa a office amman ai munje asibiti nida
mustafa da ibrahim mun duba adnan
Qirjin afnan yai mummunan faduwa cikin natsuwa
tace ashe kunje kin dubashi?
Tace eh mana bai fada mikiba tace a,a bai
fadaminba
Kuma Nima ko sau daya bai taba cemin na shirya
muje na duba mara lfy ba daman nasa masa
idone naga gudun ruwansa amman har yanxu
baicemin komaiba
Tace to kema saiki shareshi kawai wata qila
kishine ya hanashi
Kinsan mustafa ya fadamin abindaya faru wlh
hankalina
Ba qaramin tashi yaiba kinsan silar alkhairi
akeson. A samu game da mutum bana sharri ba
Afnan ta qure zainab da kallo tana mamakinta a
zuciya tace shin mai yasa mutane suka fiye son
zuciyarsune?
Zainab tace name tace na baki lbrn adnan dan
uwanane harda zuria a tsakaninmu amman
haryau qoqarin raba tsakanin dashi kike
Tace Bawai rabaki dashi nakesonyiba afnan gani
nai mijinki baison mu,amalarki dashi
Tace mijina ba zai hanani zumunciba don kuwa
fadar uban gijine duk mai yanke zumunci baxai
shga aljanna ba
Zainab din tace toki tambayesa mana idan bai
sairarekiba sai kimai wannan bayanin nasan zai
saurareki don ibrahim nada sauqin Kai
Afnan din tace bazan tambayshiba don bazan
sashin yin abinda baisoba kasancewarsa mai
haquri banason janyo abinda zai batama mijin
nawa rai
Zainab tai murmushi tace lallai afnan cikin Mata
irinku basu da yawa ke ina zaton sun qarema
Afnan din tai murmushi tace kyaji dashi da
wannan zugar
Taki ke bari na Kawo miki dan kayan motsa baki
Sai bayan magrib zainab din ta wuce don ita
taima afnan din ma girki. Don haka tana tafia
toilet ta fada ta watso ruwa ta zabo Wasu Riga
da wando masu kama jiki ta saka ba qaramin
kyau tayiba
Bata Dade da fitowa falonba ya shigo ta tashi da
fara!arta ta tarbeshi suka xube kan kujera tace na
fara Kawo Maka abincine ko sai ka farayin
wanka?
Yace a,a tashi kije ki dauko hijab dinki asibiti
zamuje an kwanta da malam baida lfy daganan
saiki duba jikin adnan
Wani dadine ya ziyarci zuciyata zataje taga adnan
dinta saidai bata nuna a fuskaba don haka ta
tashi ta nufi nata sashin ta dauko dogon hijab
dinta ta fito
A mota ta sameshi bayan ta rufe gidan Kai tsaye
asibitin suka nufa. Saidai likitoci sun hana kowa
zuwa inda malam din yake sbd Yanayin jikin
nasa. Da alamun yanadan Jin jiki
Don haka Dakin dake gefe suka nufa anan ne
suka samu Abban afnan din da inna
Afnan ta qarasa gabansu cikin tsananin
girmamawa ta duqa ta gaishesu gamida yin
musu ya mai jiki
Anan inna ke sanar da ita yaddah jikin nashi ya
tsananta don baima sanin Wanda ke kansa
Afnan tace wayyo allah malam allah e sawaqe
sannan ibrahim shima ya qarasa yai musu ya mai
jiki
Daganan kowa yaja bakinsa yai shiru ita kanta
afnan
Din jikinta yai sanyi sosai donta lura jikin malam
din yayi tsanani
Can dai ta kasa daure zuciyata ta duqar dakai
tace abbah ina aka kwantar da adnan?
Yace yana can Dakin dake kusa da wannan ai
shima ya warware gobe za,a sallameshi
Ta miqe tana bari naje na dubashi babu Wanda
yace Mata uffan harta fice
Amman zuciyata sai barazanar fashewa take sbd
tsananin bugun da qirjinta yake
Tura qofar tayi tare da sallama yana kishin kide
kan doguwar kujera mai kamar gado da alamar
dai gajia yai
Da kwanciyar yasa ya kishin gidar anan
Yana ganin afnan din ya yinkura ya miqe ido waje
yace mai ya kawoki Nan afnan iye?
Ko kinxo ki qarasanine?
Ya girgiza Kai sannan yaci gaba da cewa kin
cuceni afnan kin cucar da igiyar aurena dake
kanki
Asje kalaman da kikemin daman duk na yaudara
ne?
Daman ashe zaki iya auren wani Wanda ba niba?
Kin tarwatsa zuciyata afnan kin yaudari zuciyar
da bata taba tunanin yaudarar kiba
Ya riqe kansa kamar rikitacce sannan ya dago da
kan nasa idanuwanta sunyi jajir yace Haba afnan
Haba afnan
Ashe ashe daman kalamanki da kikaimin a baya
na alqawarin rayuwa dani wuya ko kunci duk
qarya ne?
Duk yaudarace da dadin baki?
Cikin muryar kuka tace babu yaudara ko karya a
cikin kalamaina kaine kaxo da yaudara don Baka
buqatata
Ka shirya wani tsari ka auri wacce zuciyarka ke
muradi
To don me zanci gaba da dakon soyayyar da bata
da tasiri
Ai na Maka alkawarin zan kasance dakaine idan
har kaima ka kasance dani to ka kujeni ka
juyamin baya ka Nunama duniya cewa bakayi
dani
To yaya adnan meye amfanin kasancewata da
abinda baya buqatar kasancewa dakai? Dole na
Barka ko naqi konaso
Cikin zafin rai yace qarya kike afnan na taba
fadamiki cewa zuciyar dake dauke daso to duk
runtsi bata taba juyama wannan abinda takeson
baya
Koda kuwa shine ua juya mata
Na tabbata abindaya faru dani idanda dake ya
baru bazan taba butulce miki ba duk runtsi ina
tare dake koda kuwa zaki dinga yankar naman
jikinane sbd tsabar kiyayyah
Don kuwa nasan ba,a cikin tunaninki kikeba don
kuwa duk randa kika dawo soyayyata ba zata
rasa madafa ba
Tace a yanxu kenan kake wannan tunanin
Lokacin da aka dauke alqalima takardu suka
bushe na rigada nna zama matar wani
Sa sauri sauri yake kallonta idanuwanta sunyi
jajir
Ya matsa da baya labbansa har rawa suke yace
naji ficemin daga daki
Ta Bude baki zatai magana ya daka matsa
tsawar da harta birkita Mata yayan hanji ta fice
da sauri har tanacin Karo da qofa ta firgita don
ko ina na jikinta rawa yake
Don haka ta zube a daya daga cikin jerin kujerun
dake wani daki tana mayarda numfashi da sauri
da sauri
Bata jima a wajenba ibrahim ya fito ya ganta a
zaune yana qarasowa wajen nata yace lfy dai
afnan kika zauna anan?
Ta qaqalo murmushin rashin gaskia tace na Dade
da fitowa ina fitowanne na hadu da wata qawata
muka zauna Muna hira yanxu ta shga wannan
Dakin
Yanxu dai muje muyimasu Abba sallama idan
likitoci sun bada damar shga dunashin ma dawo
A tare suka jera sukaimasu Abban nata sallama
aleeyu ya sake yin musu nasiha sannan suka
wuce abinsu
Suna isa gida afnan ta cire hijab din jikin nata
Ta nufi toilet ta dadama ibrahim din ruwan wanka
Sannan ta iso falon ta sameshi a kishin kide ta
kamo
Hannunsa gamida cewa muje my hony ka watsa
ruwa
Saida ta rakashi har bakin toilet din sannan ta
fito ta Gama shirya masa komai
Bayan ya kammala cin abincin nasa hirace ta
barke a tsakaninsu mai cike da nishadi dukda
afnan din ta maza Kai take amman ta ciki na ciki
Saidai yau nishadin nasu tafi a kullun don kuwa
wani irin nishadin da kauna kawai yake nuna
Mata mai wuyar fasaltuwa
Kullu nafsin za-katul maut. Allah sarki evry soul
shall test dead. Duk mai numfashi saiya dandana
mutuwa
A yaune aka sanarma da afnan rasuwar malam
don haka da wurwuri ta kammala ayyukanta
Ibrahim ne da kansa ya dauketa ya kaita gidan
misalin qarfe takwas na safe. Tun daga qofar
gidan kake ganin manyan motoci da dumbin
mutane
Afnan tayi kuka sosai gamida tausayama Abban
nata shikenan ya zama maraya mutum mai
haquri da tawakkali
Duk halinsa mahaifin nata aleeyu ya dauko
Misalin qarfe goma duk yan kauye Dana birni sun
hallara abokan aleeyu yan siyasa da masu fada
aji yan uwansa nako ina abokian adnan ibrahim
shima da abokansa su mustafa duk sun hallara
ba tare da bata lokaciba akayi
Gaggawar kaishi makwancinsa
Harda dangin hajia nafi tare da sauran abokan
arziqi duk an hallara gidan ba masaka tsinke
Afnan taja yayanta a jiki
Kullun ibrahim ke kawota da safe shi kuma ya
zauna gurin
Amsar gaiSuwa. Sai dare sannan ya dauketa su
koma gida a haka har akai sadakar uku
Ranar sai goma saura ibrahim yaxo daukarta
Aslim da taslim suka liqema afnan din Akan sai
sun bita
Tana. Tsaye a jikin motar ibrahim din Wanda ke
tsaye yana musu daria
Daman kullun saiya matsa Mata Akan ta kwaso
yaran su dawo kusa da ita itace rake qi don haka
yau yasa musu ido
Tace Kai ku dakata daddynku baisan zan
daukekuba don haka kuyi haquri idan na dawo
saina tambayeshi inya yarda saina tafi daku
Taslim tace momy baga daddyn nanba ai nasan
zai yarda
Suka riqe hannun ibrahim dun suna daria anan ne
adnan ya qaraso gamida cewa tadai fada muku
gaskia ko Waye daddyn ku
Amman wannan ba daddyn ku bane nine
daddynku
Gaba dayansu yaran kallon rashin sani suke
masa
Suka koma bayan afnan suka labe alamun basu
yarda da shine daddyn nasu ba
Macen tace aidai mommy ba wannan ne
daddynmuba ga daddynmu Nan ko?
Jikin afnan yai sanyi ta kamo hannun yaran
Ku juya wajensa ku dubeshi shine dadddynku
Ku gaisheshi
Gaba daya yara suka tirje suna shirin kuka. Da
sukaga ya miqo hannu yana shirin kamasu. Suka
ruga jikin ibrahim Wanda ke tsaye a jikin mota ya
harde hannuwa
Afnan ta dubi adnan din ido cikin ido duk jikinsu
ya mutu
Ta tuna maganar daya furta Mata shekarun da
suka wuce
Afnan ki amincemin mu Gina rayuwarmu cikin
soyayyah da qauna ku kasance a cikin inuwar
aure. Mu rayu cikin soyayyah. Mu raini yaranmu
cikin tattali da kulawa mu shaqu da abinmu don
bamu da kamarsu don haka dole mu basu
dukkanin lokacinmu donsu samu kulawar data
dace
Afnan ce tai wannan tunanin lokaci guda sannan
ta kamo aslim da taslim din. Ta hado kansu su
duka tai musu rada suka kyalkyale da daria
sannan suka nufi wajen adnan din
Afnan da ibrahim kuwa mota suka shge suka
wuce dan kuwa dare ya soma tsalawa
Ranar juma,a itace ranar da akai addu,ar bakwai
na malam dom kowa a ranar ya watse itama
afnan sai misalin qarfe hudu na yammah ibrahim
ya daukota
Suna dawowa ta fada kichin don hada musu
abincin dare
Shi kuma yana falo yana kallon ball bugun qofar
da ake yasa ta saki abinda take somin zuwa taga
ko waye
Tace waye?
Shiru ba,a amsa ba. Don haka ta Bude qofar ba
tare data sake maganaba don taga wane
ishashshen ne
Hajia ce ta shigo mahaifiyar ibrahim da Maryam a
bayanta
Qirjin afnan yahau wata rugurguza rugugugugu
batasan Lokacin data furta
A-uzubillahi ba
Cikin tsanananin tsorata da abinda ta furtan
kuma saita rufe bakinta da hannu
Hajian tace eh lallai Fadi kwarai ki kori shaidanu
sun shgo miki gida dole ki. Nemi tsari dasu
Maryam ma ta rankwasheta gamida cewa baqar
munafuka wlh saikin gane kuranki
Bata tanka musu ba sukai ciki itama ta koma
kichin din
Dukda zuciyata babu dadi haka ta daure ta hada
musu abinci ta shirya mus kan babban tire da
lemukan sha
Takai musu bakinta na fadin sanunku da zuwa
hajia amman babu wacce ta tanka Mata
Saima ibrahim ne dake Mata kallon tausayi
sannan ta miqe ta fice har shima ya miqen yaji
hajiyar tasa na fadin da binta zakayi. Qaramin
mara kunya to jeka munanan Muna jira idan ka
Gama ka fito sai muyi abindaya kawomu
Yai saurin komawa yana fadin a,a ba haka bane
hajia ayi haquri. Maryam taja wani dogon tsaki
tana fadin munafuka banza kawai
Da sauri ya kalleta cikin zafin rai saidai. Ba zai
iya Mata komai ba a Lokacin kasancewar
hajiyarsa na wajen
Don haka ya mayar da kansa qasa ya duqar
Afnan ce a cikin falonta ta hada Kai da kujera
kuka kawai
Take marar sauti rayuwar ta Mata kunci. Ga
damuwar da take dannewa a zuciyarsa ga kuma
wannan ta danno
Tanajin yaddah rigima ta kacame a tsakanin
ibrahim din da mahaifiyar tasa
Inda hajiyar ke fadin Kai saurarene ibrahim nidai
nice na haifeka. Ba kaine ka haifeniba.
Don haka dole nasa Maka doka ka bita ko
kannannso ko bakaso dole Maryam ta zauna a
gidannan ko kanaso ko bakaso. Ibrahim din yace
Kiyi haquri hajia don ni na rigada na saki Maryam
saki uku kinga ba damar kome kenan
Salati ta saka tana fadin kayi daidai da kake
fadamin da bakinka cewa ka saketa. To inaso ka
sani na raNnnntse ndnnann nannnnlnlanh koda
aure koba aure sai Maryam ta zauna a. Gidannan
Ballentanama da aurenta tunda Baka bata shaidar
sakiba takarda. Da baki kawai ka furta. Donka
furta Mata ka saketa ba tare da takardaba ai
wanna shirmene
Idan har Baka rubutaba to matarka bata sakuba
Yace amman hajia,.......
Ta daga masa hannu sauraramin banson Jin
komai
Maryam dai nace bata saku ba ita waccen uwar
feleqen
Nakeson karubutama takardar sakinta yanxu
kuma saki daidai har uku Cass
Da sauri ya dago Kai yana kallonta wani zufa ya
soma karyo masa muryarsa na rawa yace. A. A
hajia kar muyi haka dake allah ma ya sani duk
wata biyayyah ina miki binki sauda qafa duk
abinda kika gindayamin ina qoqarin kiyayewa
Kin sani makudan kudi na kashe wajen fito da
yarinyar Nan
Daga gidan horo na Mata
Kince saidai ta zauna a gidannan na amince don
koda babu wata alaqa a tsakanina da Maryam ni
me riqetane don yar uwatace
Amman bazan iya sakin afnan ba haka Bawai ba
tare da wata matsalaba. Don na tabbata yaddah
take miki biyayyah ko Maryam bata miki Kiyi
haquri kawai hajia
Amman idan kika matsa Abba kawai zan sanar
mawa
Hajiyar tace ka Dade Baka fada masaba dan
ubanka
To inaso ka sani ni hajia iklima nayi alqawar wlh
tallahi saika saki yarinyar Nan
Don haka na Baka sati biyu na ratse da allah
inhar Baka saki wannan yarinyarba to wlh tallahi
babu Wanda zai hanani. Tsine Maka. Tsine Maka
tsine Maka
Kalaman da suka dinga sauka a kwakwalwarsa
kenan jinsu yake kaman saukar aradu
Hmmm ya lamarin zai kasance
Anya ibrahim zai iya sakin afnan din kuwa?
Amman ya kuke ganin lamarin zai kasance sai
naji daga gareku
Aure. Kan. Aure
Chapter38
Taja tebur din gabanta tana fadin baqar daga bari
muga abinda aka kinkimo aka Kawo mana sai
kace abin kirki
Raping din datauma abincinne yaja hankalita har
tai sha!awar budewa
Tana. Budewa wani kamshi ya daki hancinta
batace qalaba ta dau cokali taci gaba daci tanaci
kuma tana mita
Anya yarinyar Nan ba!a gidan abinci ka ganta ka
auro ba don naga tayi kama da ma,aikatan
gidana abinci
Shidai baice Mata qalaba har taci iya cinta tabar
sauran
Ita da kanta taje ta zabar ma Maryam din Dakin
da zata zauna wato Dakin ibrahim din kenan
Don haka tana tafia ya shga Dakin nasa ya
tattaro duk Wasu kayansa da yasan yana aiki
dasu ya kwashe yakai Dakin afnan
Sannan ya hada dayin Mata gargadi kan wlh koda
magana marar dadice ta hadata da afnan saiyasa
an kulleta har dan makullin ya vace
Batace masa komai ba harya fice ya nufi sashin
afnan din
Wacce ya lura da akwai damuwa a cikin ranta
Don haka yaje yaci gaba da lallashina da bata
kulawa harta samu dan sassaucin zafin da ran
nata ke Mata taci gaba da harkokinta ba tare
data sake shiga sabgar Maryam ba harkar
gabanta kawai takeyi
Har huutunta ya qare ta koma wajen aiki duk
abinda tasan tanayi na game da harkar gida bata
fasaba
Tun kafin takwas na safe take kammala girkinta
ta dibarma Maryam nata takai Mata sannan ita
da mijinta suma suci kowa ya wuce wajen aikinsa
Ibrahim ya sakema afnan mota yasai Mata jeef
qirar. E. O. D motar ta hadu matuqa don haka
yanxu babu abinda ya dameta na game da
Maryam don. Tun takwas take fita office ita da
ibrahim bata dawowa sai hudu shi kuwa sai
shddah yake dawowa kafin ya dawo ta kammala
komai na game da aikin gida ta qawata jikinta da
kwalliya
Tana kichin wani lokutan da kansa yake shigowa
ya taimaka Mata su kammala aikin tare
A haka har hajia ta dawo da yaran ibrahim din
wai sbd uwarsu na gidan
Don haka afnan ta rungumi yaran hannu bibbiyu
tana basu kulawa yaddah ya kamata
Hakan yasa ibrahim ya qara shaquwa da yayan
nasa don wani lokutan idan ana hira har kashewa
yake da yayan hakan kuwa ba qaramin
farantama. Afnan din rai yakeba
Ita ko Maryam ta saki yaran ne don su dinga
dako Mata rahoto shiyasa bata damuwa da
shishigema da yaran sukema afnan
Kullun kuwa da baqin ciki take kwana don kuwa
zaunar da yaran take taita bugun ruwan cikinsu
su kuma suyita zayyane Mata komai
Abin yaxo ya dinga gagaranta barci. Sbd baqin
kishi
Shikuwa gogan gaba daya ya daina shga harkarta
Ko hanyar Dakin nata baibi idanma yana zaune a
falone yaga ta fito saiya tashi ya shge ciki
Kai ko gaiSuwa bai yarda tana tadasu da Maryam
abin ba qaramin damunta yakeba
Ita a haukarta wai zaman aure take don haka ta
fara fito da feleqenta wata kwalliya tata bata
tashi yi sai yana zaune a falon shiko baya
nunama yasan tanayi Kai ko kallon inda take
baiyi
Ko kadan bata birgeshi yana mamakin yaddah
akai jahilci yaima kanta katutu
Bayan sallar isha,i afnan ta Gama shiryawa cikin
wata ganyar green din atamfa rigar ba qaramin
kyau tai mataba kuma tahau jikinta an Mata
dinkin rapper
Tana fitowa ya jera musu abinci Akan dinnig area
Tana gamawa kuwa saiga ibrahim din sun dawo
daga masallaci shida salim riqe da hannunsa
Tai masu sannu da zuwa sannan tacema salim
ya daki abinci mamansu yakai Mata sannan ya
kira sajidah don suci abinci yace to ya dauka yaje
yakaii Mata sannan ya kira sajidan
Nan suka zauna da zubama kowa suka faraci
Ibrahim har ibrahim ya fara santin daya saba
kaman daga sama suga ganta a gabansu ibrahim
ya gimtse daga darian da yake ya hade fuska
yana kallonta sai wani girgije girgije take wai ita
a dole ta hadu
Tana tsaye da Wasu Riga da wando damammu
Ana ganin ko ina na shef din jikinta
Gaba daya kayan basu Mata kyau ba amman ita
a ganinta ta qure adaka ne ibrahim din yace
malama lfy?
Maryam din ta watsa masa wata uwar harara wai
ita adole fari take
Ta wani maqe murya tace ban ganeba ibrahim
wai meka maidanine. A cikin gidannan?
Ka juyamin baya Baka shga sashina bakacin
abincin Dana aje Maka Baka kwana dani
Tace Haba ibrahim yanxu sbd wannan karuwar
zaka juyamin baya haka?
Ibrahim yace wacece karuwa matar tawa ita kike
kira da karuwa? Lallaima Maryam baki da kunya.
Yanxu har akwai karuwar data wuce ke dubi
shigar da kikai a matsayinki na musulma bayan
kinfi lowa sanin babu wata alaqa ta aure dake
tsakanin dake
Ko kin zata Nima jahiline irinki to wlh ki shga
taitayiNki donni ba mutumin banza bane
Maryam ta hatsala tace aiko indai ni jahilace to
uwarkace babban jahila tunda. Ai tasan da sakin
ta daukoni ta dawo dani gidan naka
Nai......
Kafin ta qarasa ya dauketa da wani wawan Marin
da har saida hawayen wahala suka fito daga
idanun nata
Ta dafe wajen tana wai ni ka mara ibrahim mari?
To qarya akai ai itace babban jahil...
Kafin ta qarasa ya qara Mata wani wawan Marin
Harda tokari ta koma. Gefe a gala baice amman
dukda haka bata daina cewa to wlh inaso ka sani
ni Maryam sai naga bayanka tunda harka iyasa
hannu ka mareni wlh saikayi kuka da idanunka
Badai Akan wannan karuwar ba tai kwafa
gamoida girgiza kai
Yai yinkurin kamota ta fice a guje afnan ta rigoshi
tana bashi haquri kayi haquri kayi haquri please
adnan ban sanka da zafin raiba karka biye Mata
Baka ganin va daidai takeba zafin kishine Dana
rabuwa dake ke damunta bayin kanta bane kayi
haquri don allah kaji?
Yaja wani ajiyar zuciya sannan ya zauna
idanunsa nakan afnan din ita kuwa aikin basa
haquri kawai take
Yai wani takaitaccen murmushi yana girgiza Kai
Wasu zafafan hawaye Suka zubo masa
Yace rayuwa kenan afnan irin abindana taba guda
kenan shekarun baya da suka wuce
Nasan wata rana sai,an gorantamin ni nasan
hajia tanada ilmi daidai gwargwado saidai bata
aiki dashi
Ita kullun son ranta takebi sabanin gaskia da
matakan binta
Babu ruwanta da abinda allah da manxonsa suka
fada duk duniya babu mai iya tankwarata sai
alhaji mahaifina kenan
Shine kadai ya isa ya daura doka ta kasa
shallakewa
Bayanshi kuwa babu Wanda ya isa
Kuma na rasa Wanda zai gaya Mata gaskia a
cikin wadanda suka darata a gaban idonta ko
bayan idon nata
Nasan ganin idon mahaifin nawane da nawa
Amman yau gashi har ana fara zaginta a gaban
idon kuma cikin wadanda tafi kyautatamawa
Afnan hajia taso Maryam fiye da yaddah tasoni
Ta nuna Mata soyayyah fiye dani data haifa
Hajia babu Wanda tafiso irin marar gaskia da
marasa kunya ga irinsu Nan kin fara gani yau a
gabanki
Tabbas hajia ba zata tava Gabe cewa inada
ranaba ba zata tavajin digon sonab sai ranar da
nabar duniya kuma Tabbas wannan ranar
tananan zuwa
Afnan tace a.a dan allah ka daina fadin haka ai
komai na duniyarnan mai wucewa ne
Bai tanka mataba don haka tajashi jikinta sosai
ta share masa hawayen nasa. Sai lallashina take
tamkar dan yaro lol
Afnan ce zaune a. Office yau aiki yai Mata yawa
sbd wata rikitacciyar shari,a data kunno musu
don
Haka sau biyu ana Kiran wayar tata tana
tsinkewa ba tare data daukaba
Ana ukunne tasa hannu ta dauka don taga
alamun mai Kiran baida alamun haqura
Ba tare data duba sunan mai Kiran ba ta Kara a
kunne gamida sallama yace hello adnan ke
magana Kiyi maza maza Kixo gida keda mijinki
Abba na nemanku ba tare dajin abinda zataceba
ya kashe wayar
Afnan tabi sunnan dake jikin wayar kamar wacce
aka tsikara ta zari. Makullin motarta tai waje
Ta kira ibrahim din tana fada masa Kiran da
Abban yake musu yace to su hadu acan ba tare
datama kowa maganaba tahau motarta ta nufi
gida
Tai fakin a qofar gidan jikinta sai rawa yake.
Ganin mutane tsaitsaye daga cikin harabar gidan
Har gudu gudu take wajen shiga gidan wata
juwace ta nemi kadata a. Lokacin data hango
gawa lullube da likafani
Afnan ta zube qasa ba tare data ankaraba ta yaye
likafanin innalillihi wainna ilaihi raju,un
Kullu nafsin za,ikatul maut. Evwe soul shall test
dead
Mahaifiyartace allah e ma rasuwa wato hajia nafi
Kuka ta saka mai tsuma zuciya aleeyu ne Akan
gawar adnan da iyayen hajia nafin Harda kausar
Adnan yasa hannu ya janye afnan din gefe daya
don Bama masu daukar gawar dama domin sata
a cikin makara
Gaba daya yaji tausayinsa ya lullube zuciyarsa.
Ya rasa ta yaddah zai fara lallashina sai ce Mata
yai Kiyi haquri Kinji afnan addu,a zaki Mata shi
mamaci ba,a masa kuka sai addu,a
Daqar ya samu ta daina kukan sai hawaye kawai
Daganan shima yabi yan rakiyan gawar zuwa
kushewa
Afnan ta qule a daki wurin sauran dangi sai
sharar qallah take tace shi kenan yanzu
mommynta ta tafi
Yanxu shikenan ta zama marainiya ta rasa uwa
Nan take rayuwarta da momyn nata ya dinga
dawo mata
Har qawancen mommyn nata da mommyn sady
hajia sury surayyah kenan idan baku mantataba
Wacce tunda aka fara case din mommynta da
Abban nata ta juyama qawar tata baya ba,a
qarajin duriyartaba
Kenan a cikin dadi ake sonka babu Wanda zai
soka idan kana cikin wahala? Gaskia ne afnan
rayuwar tamu ta yanxu sai a slow allah dai isa
mu dace
A zuciyar afnan din babu abinda takema kuka illa
makomar mahaifiyar tata don tasan da wuya tai
kyau
Bata sake neman ibrahim ba har dare saidayaxo
ya dauketa
Kullun shi yake kawota ya maidata har ranar da
akai sadakar uku misalin qarfe hudu kowa ya
kama gabansa
Afnan na tare da yaranta tai mamakin yaddah
yaran suka shaqu da adnan sosai haka
Don ko wajenta basa zuwa idan suna tare dashi
adnan ne ya shigo falon afnan din ba kowa a ciki
daga ita sai yaranta saidaya qare mata kallo tsap
suka gaisa
Sannan ya miqa mata wata ambulan
Yace wannan ambulan din wasiqa ce momynki ta
rubutata a Lokacin data samu sauqi
A Lokacin da ciwon nata kuma ya tsanantane
mukaje dubata nida Abba shine masu tsaronta
suke cewa ga wasiqanan inji momynki wai don
allah abaki wasiqar hannu da hannu hakan yasa
na riqeta da hannuna
Na Kawo miki ita yanxu gatanan
Hannunta na karkarwa ta amshi wasiqar gamida
soma karantawa kamar haka ///////
Naku har kullun
My apology to. Y,ll nasan a lot ov ppl. Zasuyi
Fushi course ov ban Kawo musu ci gaba lbrn Nan
jiaya ba da kuma yau da wuri ba. Kuyi haquri
again hakan ya farune sbd. Big bro dinmu da
yake aure so serious ina busy ne. Don nasan da
yawa wadanda muke chart dasu zasuga tun day
before yesterday nake offline so sbd haka sai kuyi
haquri
Kamar yaddah bro dina yai aure allah yasa. Duk
samarin wannan page namu suma su samu suyi
auren. Yan mata kuma alllah ya kawo muku
mazajen auren Harda zawarawan page dinnan
kuma haka allah ya fito muku da mazaje. Mai
mace daya allah e Buda masa ya qara mai
biyuma haka mai ukuma haka mai hudu kuma sai
yai haquri. Shima admin ku tayashi da addu,ar
samun beb kyakkyawa. Lol
Mu tara a. Next chapter
Aure. Kan. Aure
Chapter39
Ta fara karanta wasiqar kamar haka
Salam
Zuwaga yata afnan naso ace da baki nake baki
wannan wasiyar. Amman hakan bata samuba don
nasan tawa taxo qarshe
Afnan na tabbata a rayuwata ta duniya ban
aikata komaiba
Sai son zuciya. Wanda ya kaini ga halaka Tabbas
allah kadaine yasan makomata .
Afnan ki gafarceni don na tabbata babuni babu
rahamar ubangiji
Afnan a duniya cikin manyan zunubai babu
Wanda ban taba aikatawava.
Addu,arku kawai nake bara wata qila allah yaji
qaina yaimin afuwa
Afnan ki duba cikin Dakin dake bayan
boysquaters din gidannan ai qoqarin budeshi
akwai ajiyata a ciki
Nasan duk Wanda yaga wannan ajiya zai
tsinemin yai tir da Allah wadai dani
Amman wannan tsanar ba zata dameniba burina
duk Wanda ya hada alaqa da wannan ya yafe min
wata qila kona samu wani dan sassauci daga
wurin ubangiji
Afnan koda kowa ya juyamin baya ke karki
juyamin baya duk tsanani Akan abinda kuka gani
Gudu nake kada bayan raina a zargi mahaifinki ke
kasai nakedashi a duniya addu,arki. Tafi ta kowa
Afnan wlh nayi nadamar abindana aikata kuma
na nemi gafarar ubangiji don allah karki qini
kamar yaddah kowa zai qini yata afnan please
Allah ya hada fuskokinmu a qiyama amman ni
harna fara hango kalar azabun dake jirana tun a
kabari /////
Afnan ta chukukuye takardar dake hannun nata
tana wani irin kuka mai sauti. Tana Kiran sunan
mommyn nata da qarfin gaske
Adnan dake kusa da ita ya rude gamida riqeta
yana fadin lfy?
Cikin kuka tace kiramin abbana yaya adnan
kiraminshi
Cikin rudewa baisan Lokacin daya kwasa a gujeba
baifi minti biyarba sai gashi shida Abban nasa
Jiki na rawa tace moje Dakin dake bayan
boysquaters Abba mommy tace tanada ajiya a
ciki
Ba Wanda ya tanka mata suka nufa can bayan
gidan Wanda Bama kowane ke zuwa wajenba
Adanbayan gidan Dakin yake kwata kwata babu
mai zuwa wajen
Saidai Dakin a rufe yake da wani qaton kwado
gabadayansu suka cirko cirko suna kallon qofar
Mahaifin nata aleeyu yace yanxu ya kenan Waye
zai iya yanke wannan kwadon?
Adnan yace bari na dauko zarto muga ko zan iya
yankeshi
Aleeyu yai murmushi yace adnan kenan an gaya
Maka yanke wannan kwadon qaramin aikine ai
jeka kawai ka kirawo irin masu gyaran qofar Nan
suzo su balle qofar
Afnan taji kamar ta hana saidai babu wani mafita
dole a kira mai gyara domin ya bambare qofar
Don haka adnan yasa waya ya kira engeener
mansur sale
Baifi minti ashirin ya isoba don daman shi ido a
kudi ne
Da kayan aikinsa yaxo don adnan din ya masa
bayani
Yana duba kwason yace Kai wannan kwadon
aradu bazai taba yankuwaba saidai kawai a cire
qofar
Babu musu Abban nata yace a cire gaba dayansu
suna tsaye yake aikinn cire qofar
Yafi minti talatin dukda kayan aikin nasa sannan
ya samu damar cire qofar
Kamar jira suke ya cire gaba dayansu suka nufi
cikin Dakin babu komai a ciki fayau sai wani
girkeken akwati dake tsakiyar dakin
Aleeyune yasa hannu ya daga akwatun adaidai
Lokacin daya zube qasa yana Kiran sunan allah.
Innalillahi wa inna ilaihi raji un.
Gava dayansu har rige rigen leqa akwatun suke
ita da adnan
Shima injiniya masur ya sawo Kai yana fadin lfy?
Meke faruwa?
Afnan na hada ido da abinda ke cikin akwatin ta
Fadi qasa sumammiya
Babu abinda aleeyu da adnan ke Fadi sai sunan
allah. Injiniya ya leqa akwatin yana fadin wai
meke faruwane?
Ganin abinda ke cikin akwatin shima ya rikitar
dashi bakinsa na rawa yace alhaji muftahu kafin
ya rufe bakin nasa saiga yan dubu dubu na fita
daga bakin nasa
Ai kafin kowa yai magana ya kwasa a guje. Babu
abinda ke fita daga bakin nasa sai kulya ai yuhar
kafirun har ya fice daga cikin gidan kamar
zautacce. Da alamun duk addu,ar daya ya kama
ta kubce masa ne
Gaba daya adnan ya rasa abinyi ga afnan a sume
ga abbansu ya zama kamar mutum mutumi
saidai idanuwanta kawai dake kiftawa
Ga kuma akwatin akwatin gawar alhaji muftahu
mahaifin hajia nafin toya kenan
Don haka yaita maza ya girgiza Abban nasa yana
fadin abbanh kayi haquri ka tashi don musan
abinyi
Kaga mai gyarannan dan jaridah ne karfa yaje ya
watsa wannan zancen a idon duniya
Aleeeyu ya dafe qirjinsa dake masa matsanancin
ciwo kamar zai rabe biyu
Muryarsa kamar ta Wanda ya shekara biyu a
asibiti
Yace bazan iya motsawaba adnan ka kira inna
taxo ta kama afnan sannan ka kira iyayen nafi
yanxu maza maza
Hannun adnan din na rawa ya kirasu sannan ya
taimakama
Inna suka fice da afnan daga Dakin aka shafa
mata ruwan sanyi ta farfado saidai bata cikin
hayyacinta
Ana Kiran sallar magrib iyayen nafi suka iso
adnan yai musu rakiya har izuwa Dakin da
akwatin yake
Gaba dayansu sun shiga tashin hankali sai kuka
suke mahaifiyar nafi kuwa sai tsine ma nafin take
tana fadin kada allah yai mata rahma a cikin
kabarinta
Adnan ne yasa masu daukar gawa sukaxo suka
dauki gawar alhaj muftahun aka nufi makabarta
da ita inda masu gadin gidan sukai musu rakiya
Aleeyu kuwa na bangarensa ciwon zuciya ta
tirnikeshi ganin abin na gaba yasa ya sureshi sai
asubiti
Mu hadu a next chapter
Sannan inason na sanar daku cewa banson.
Yawan complai. Da yawa daga cikinku sai Kaga
anacikin lbr sai su dinga tambayan ya akai ba,ai
guri kaza ba
Meya faru da wane kaza. Duk irin wadannan
tambayoyin ba qaramin. Cimin tuwo a qarya
yakeba. Kamata yai ku bari a Gama book din duk
inda kukaga ba!a taboba ta Zaku iya complai akai
ba,a ana cikin tsakiyar lbr ba don allah a gyara
Sannan masu qorafi Akan ba,a musu post da wuri
inason su sani
Admin nada aikinyi. Akwai week din da zakuga
gaba daya week din da safe nake post to wannan
week din ina off kenan banida aiki ina hutu
shiyasa nakeyi kullun da sassafe
Akwai kuma week din da sai yammah koda dare
nake post to wannan week din admin na cikin aiki
ne. Don bazan aje aiki naxo ina muku post din da
bakwa comment ba yess
Don. hak sai kuyima admin uzuri
Naku har kullun
Aure. Kan. Aure
Chapter40
Bayan adnan din ya tafi da Abban nasa asibiti
Ita kuma afnan ibrahim yaxo ya dauketa
Amman ya rasa kanta kuma taqi fada masa
abinda ke faruwa
Lallashi kawai yake da nasiha. Washegarima da
zazzabi ta farka mai tsanani hankalin afnan ya
Gama tashi
Dakansa ya shiga kiscin ya hada mata abinda
zataci
Don yanxu ya soma qarewa kasancear shga kicin
din da suke tare
Ta kasa Kai komai bakinta ibrahim ya rasa inda
zai saka kansa
Don haka wajen qarfe sha biyu na rana ya soma
shirye shiryen kaita asibity amman taqi don haka
yasa nurse don taxo ta dubata
Tana kwance a falo ya tasata a gaba wani
Lokacin har hawaye yake sharewa zuciyarsa ta
Gama karyewa
Don haka yaranma nasa suka sasu a gaba sukai
tsuru tsuru
Duk abinda suke idon Maryam na kansu.
Yau dai tayi kuka harta godema allah
Yaddah taga mijin nata ya lalace a gindin mace
tace tir da irin wadannan mazan
Har wuqa ta dauka zata cakama kanta sbd
tsananin kishi ta kasa ta dauko fetir domin ta
qonesu kowama ya huta nanma ta kasa.
Don haka ta zube a cikin daki tana sharbar kuka
Kamar daga sama hajia ta Sanyo Kai falon gaba
daya suka dago suna kallonta.
Ibrahim yai saurin hanyewa daga jikin afnan din
babu ko sallama ta fado falon
Yau da alamun tashin hankalin da taxo dashi ya
zarta na kullun
Afnan kuwa ko kadan bataji irin fargaban da
takejiba a duk sanda taga hajiyar don tashin
hankalin dake tare da ita yafi gaban wannan
Jaridace ta wurgama ibrahim din. Tana fadin
karanta nace
Ibrahim ya dauka yana duba muhimmun lbrn
dake shafin farko
Abinda ya gani ya rikita masa zuciya hannunsa
na rawa ya Bude pagen farko ya soma karanta
lbrn Wanda ya dauki hankalinsa
Labarine. Akan gawar da aka gani a gidansu
afnan amman babu wani cikakken rahoto bane
taqamaimaiba
Don ba,a Fadi mai akwatin gawar ba
Ibrahim ya rufe jaridar gamida maida kallonsa
kan afnan din data tashi tana gaishe da hajiyar
tasa
Tace. A,a riqe gaisuwarki yar mayu kada a lasheni
daga gaiSuwa
Nidai rokonki nake daki sakarmin kurwar da haka
don kuwa shi kadai ya ragemin
Afnan din batace mata qalaba ta koma ta kwanta
idanunta suka ciko da qallah
Ibrahim ya dubeta tausayinsa ya kamashi baisan
Lokacin da yakai hannu ya kamo nataba
muryarsa na rawa yace ashe wannan ne abinda
kike boyemin afnan?
Ashe har yanxu kina tunanin ban cancanci ace
nasan sirrinkiba ko afnan?
Idan har da rai wata rana zan cancanta kuma
bazanyi Fushi dakeba koda kuwa da wata manufa
kika aikata hakan
Nidai nayi miki alqawarin kareki na kare
mutuncinki da damuwarki.
Kamar yaddah nai alqawari koda kuwa ace Kece
maiyyar mai cinye naman mutane
Nayi miki alqawarin naman jikina ki cinye zakifi
Jin dadinsa
Fiye da ko wane irin nama
Afnan ta zame hannunta ta miqe da zummar ta
share masa hawaye
Kukan hajiyar tasace ya tsayar da ita kira take na
shga uku ni indo
Shi kenan ta Gama lashe min kurwar yaro
To inaso ka sani saika saki yarinyarnan yanxu
yanxunnan kaji na fada Maka
Wlh koka saketa kokuma na daga Maka nono kaji
na rantse don saina tsine maka
Ibrahim ya sulale qasa a gabanta cikin muryar
kuka yace
Kiyi haquri hajia ki yafemin
Bazan iya aikata abinda kike umurtata dashiba
koda kuwa naman jikina zaki dinga Yanka amman
don allah ki yafemin
Hajiyar tace na sani wlh ni nasan bayin kanka
bane
Kuma mayu ba zasu shga tsakanin da Dana ba
Ta miqe tana fadin nasan abinda zanyi
Maryam tsulum ta fito daga dakinta tana wani
irin gunjin kuka
Ta nufi inda hajiyar take. Ta tsaya tana fadin
Wlh sai yau na tabbatar dabake kika haifeniba kin
nunamin banbanci hajia. Kuma na gode
Damuwata ba wata mai yawa bace kika maida ita
gaggaruma.
To yayi daidai sai yau na amsa sunana marainiya
mara uwa da uba na rasa gata banida madafa
Don haka zanyi yaqina Ni kadai tunda ni ya shafa
ta juya ta koma falon nata hajia na Kiran sunanta
amman tai banza da ita don haka itama hajiyar
ta fice daga gidan cikin bacin rai
ZUCIYAR ibrahim gaba daya ta Gama
cunkushewa yaji a duk duniya idanda abinda ya
tsana bai wuce Maryam ba
Shidai duk yaddah hajia ke takura masa to bai
yaddah wani ya rainataba
Yaddah afnan taga ibrahim nata dawainiya da ita
yasa ta rage damun dake ranta
Don haka harta samu daman shga kichinn domin
hada masa abinci donta lura har kalacin safe bai
samu yayiba
Indomie dakwai take dafa masa tana cikin bare
kwan
Muryar ibrahim taji yana kwala mata kira da wata
irin Muryar da batasan yanada itaba
Da sauri ta waiga saidai kamin ta Gama
waigawar taji an hankadata can gefe. Faduwar
tayi daidai da kwala qarar da ibrahim din yayi
Anan afnan ta Bude idanunta domin tantance
abinda ke faruwa
Maryam ce tsaye riqe da sharbebiyar wuqa sai
digar jini take Tuni qirjin afnan yahau bugawa
Ta rarrafa inda ibrahim din ke zaune jini sai
malala yake
Kamar an yanka dabba daga gefen cikinsa
Tuni har idanuwanta sun juye wani irin numfashi
yake fitarwa Wanda ke girgiza gangar jikin nasa
Afnan ta daura hannu aka gamida Kurma wata
uban kururuwa mai rikitarwa. Mustafa dake shirin
faka motarsa ya fito a guje ba tare daya Gama
gyara fakin din motar ko kashewa ba
Maryam na ganinsa ta saki wuqar tana fadin wlh
bashi nai niyyar kashewa ba shigowa yayi ban
ankara ba
Mustafan bai tsaya Jin komaiba ya kimkimi
ibrahim din Wanda har yanxu bai daina zubda jini
dake jikin nasa ba
Yai waje dashi ibrahim tabi bayansa a hanzarce
hannunta aka sai kururwa take
Mustafa ya rude Yama rasa asibitin dazai kaishi.
Ga wai irin numfashi fitar rai ra ibrahim din keyi
Don haka Mustafan ya kira iyayen ibrahim din ya
sanar dasu bai zame ko inaba sai asibitin aminu
kano
Sbd yanada aboki likita a asibitin
Yana tsayawa motar mahaifin ibrahim din na
tsayawa
Don haka basu jira aka basu keken tura marasa
lfy ba suka sureshi sukai cikin asibitin dashi
Doctor faruk ne da ducto lawal sukai musu
Iso zuwa Dakin da za,a kwantar dashi
Basu bata mintina gomaba suka shirya wajen fara
aiki Akansa Tabbas su kansu likitoci. Sun
sadakar da rayuwar ibrahim din
Don haka likita guda ya fito daga Dakin ya sanar
dasu cewa suje su laqanta ma dansu kalmar
shahada abinda. Ya fada kenan ya wuce
Har rige rigen shiga Dakin suke Daqar alhaj ya iya
kallon halin da dan nasa ke ciki
Gefen inda Maryam din ta farka da wuqa yayan
hanjinsa sun zubo da alamun kuma Wasu yayan
hanjin nasa sun daddatse
Afnan ta kifa kanta da nasa tana wani irn kuka
mai tsama zuciya. Ta laluba hannunsa ta matse
da nasa tana Kiran sunansa
Alhaji kuma ya qarasa kansa yana Tofa masa
addu,o,i hajiyarsa kuwa ihu take kawai tana buga
kanta da bango
Don haka ma,aikata sukai waje da ita
Ibrahim baisan inda kansa yakeba
Can Jikinsa ya saki idanuwanta suka tsau kyam!
Mahaifin nasa yasa hannu ya shafi idanuwan
nasa suka
Rufe
Mustafa dake tsaye a bakin qofar Dakin yana
wani irin kuka kamar qaramin yaro. Yana ganin
mahaifin ibrahim din ya shafi idanun nasa ya fita
daga Dakin a hanzarce
Afnan bata ankaraba saidai gani tai mahaifin
nasa yaja bargon dake gadon ya lullubeshi
Idanuwanta suka tsaya kyam Akan mahaifin
ibrahim din tasa hannu tana rufe bakinta Wasu
irin hawaye masu zafi sunabin idanuwanta
Babu inda ke motsi a jikinta sai labbanta dake
rawa gaba daya ta gaza furta abinda takeson
fada
Mahaifin nasa cikin dakiyar zuciya yace ya rasu
afnan
Kullu nafsin za,ikatul maut duk mai numfashi
saiya dandan
Innalillahi wa-inna ilaihirrajiun kawai ta iya
Furtawa ta Fadi Nan a sume zuciyar mahaifin
ibrahim din ya kuma dugun Zuma cikin tashin
hankali yake Kiran
DOCTOR. DOCTOR. DOCTOR
Hmmm jama,a wai Kuna daukar darussa a cikin
wannan book din kuwa?
Karku damu baifi mu qara post biyu ko ukuba
zamu kammalashi
Naku har kullun
Aure. Kan. Aure
Chapter41
Da sauri nurses suka shigo aka taimakama afnan
din ta farfado shi kuma ibrahim din. Motar
abulanc ce taxo ta daukeshi I zuwa gidan
mahaifin nasa inda anan za,ai masa sallah.
Babu inda ke motsawa a jikin afnan din sai
labbanta
Kuma ta gaza furta abinda takeson fada
Kowa ya kalleta yasan bata cikin hankalina cikin
kuka tace yanxu ibrahim ya fanshi raina da nasa
kenan
Maganganun daya fada mata jiya sune ke mata
yawo a kwakwalwa
Afnan raina fansane a gareki abin kaunata. Jinina
da jikina duk mallakinkine. Afnan motsina da
tunanina duk Nason ganin biyan buqatunkine
Ta lumshe idanunta inda Wasu zafafan hawaye
kebin kuncin nata duk Wanda ke wajen ya
tausaya mata don haka kowa sai lallashina kawai
yake
Ta runtse idonta maganarsa ta jiya ta dawo masa
inda yake cewa. Ashe daman wannan ne abinda
kike boyemin afnan?
Ashe daman damuwarki ba zata zama tawava?
Ashe har yanxu kina ganin ban cancanci da
nasan sirrinkiba? Idan har darai wata rana xan
cancanta kuma bazanyi Fushi dakeba. Koda kuwa
da wata mafita kika aikata hakan
Nidai na miki alqawarin kareki na kare
mutuncinki. Da damuwarki. Kamar yaddah nai
alqawari koda kuwa Kece mayyar. Afnan nayi
miki alqawarin naman jikina ki cinyeshi afnan
zakifi Jin dadinsa fiye da ko wanne nama
Ba tare da bata lokaciba mustafa ya kira yan
sanda ya sanar dasu abinda ke faruwa ba tare da
bata lokaciba suka dira a gidan inda sukai sa,an
kamata a daidai Lokacin da take shirin guduwa
Bayan sati guda da rasuwan ibrahim kotu ta
yankema Maryam hukunci gisa. Ta hanyar rataya
Ita kuma hajia iklima mahaifiyar ibrahim din kasa
Gano kanta sukai a asibitin. Wani Lokacin ta zura
a guje sai an kamota Wasu lokutan kuma taita
sumbatu Kai da abu yaqici yaqi cinyewa gidan
mahaukata kawai aka kaita kasancear abun nata
qara gaba yake
Mahaifin afnan da kansa yaxo ya dauketa inda ya
maidata gida a Nan zatayi iddar ta.
Abun kamar wasa wai itace ta dawo gida take
takaba
Daga ita sai inna sai ma,aikatan gidan da yan
yaranta. Sbd adnan ya wuce qasar Egypt donyin
wani kwas harna wata biyar Akan abindaya shafi
kwakwalwa
Aleeyu kuwa siyasa ta karato don haka kamfen
kawai ake a Karo na uku kenan yana neman
kujerar na gwamna baya samu yanadai kyautata
zaton wata qila a wannan karon a dace ne.
Saidai abindaya faru yafi komai dagula masa
kwakwalwarsa don kuwa abokan hamayyarsa
amfani suke da wannan damar suna. Masa terere
Don haka shi kuma ya daura damaran gyara
lamuran nasa ya kira yan jarida. Dake zaryar Jin
gaskiyar lamarin ya dauko musu. Tarihin komai
tun daga kan janar.
Har zaman kotun da sukai zuwa ganin gawar da
akai a gidansa
Don haka yan jarida suka watsa lamarin mai
makon yai baqin jini saima sake samun daukaka
yai a wajen al,umma
Lallai ya zamo cikin mutane masu gaskiya da
taimakon
Al-ummah. Don haka ko ina ya gota sonsa ake
Wandama basu sanshi daba yanxu sun sanshi
Afnan ta kammala takabarta don haka ta koma
bakin aikinta
Saidai har I Lokacin zuciyata vata natsuba
Anyi zabe an kammal don haka aleeyu musawa
ya lashe takarar kujeran gwamna ba qaramin.
Cikin farin ciki sukeba a wannan rana
Washe gari kuma aka daura auren aleeyu musawa
da kausar muftahu. {Woooooo. Hehehe abu yayi}
Daurin auren ya samu halartar manyan masu
kudi yan siyasa da shuwagabanni
Afnan tafi kowa farin cikin auren mahaifinta da
antynta
Don daman ita burinta guda abbanta yai aure.
Gashi kuma yayi
A ranar da aka daura auren a ranan ta tare
Tana gidan aka rintsar da alhaj aleeyu a matsayin
gwamna saida akai dan gyare gyare sannan suka
tattara suka koma gidan gwamnati
Alokacinne kuma aleeyu yasa aka maida auren
afnan da adnan ba tare da dayansu ya saniba.
Sbd wasan yan burum burum da suke gaba daya
sunqi tsayawa su sake da juna ga yaransu sun
girma don yanxu haka suna promary two ne
Aleeyu baibi takansuba yasa aka Gina musu
katafaren gida aljannar duniya. Babu abinda ba,a
zuba na more rayuwaba
Komai daga qasar waje aka kawoshi
Daidai da sutura saida aka sakama kowannensu
sabbi
Gidan ya tsari matuqa fiye da tunanin mai tunani
Anty kausar ce kawai tasan abinda ke faruwa don
haka ana gobe zasu tare a gidan ta kira afnan
Falonta ta zaunnar da ita tana wani murmushi
Tace afnan inason ki nutsu ki dauki abinda zan
fada miki ki ajeshi a qarqashin zuciyarki
Ba kuma wani abu bane afnan so nake na sanar
dake matakan zama da mijine
Shi namiji da kike gani idan har kinason
mallakarsa saikin riqe abubuwa guda goma. Na
farko shine
1]haquri afnan saikin zamo mai haquri duk rintsi
karki zamo mai sa,insa da mijinki duk yaddah
takai daya bata miki rai danne zuciyarki. Kibar
abun a zuciyarki ubangiji da kansa na cewa ina
tare damai haquri
Waye mai haquri Wanda yanaji yana gani za,a
bata masa a cucesa a kuntata masa amman ya
nuna komai ba komai bane. Ba kuma don bashi
da yaddah zaiyiba
2}ki zamo maiji kiqi ji mai gani kiqi gani
Meye ji kiqi ji shine kinaji da kunnenki za,a bata
miki amman ki nuna bakimajiba
Ko ai miki abu kina gani don daman don ki ganin
akayi to saiki nuna bakima ganiba
3]saikin zamo mai ladabi da biyayyah yi nayi bari
na bari
Duk abinda mijinki ya nuna yanaso to kiyi qoqarin
yin masa.
Wanda ya nuna baiso kuwa duk yaddaj ranki.
Keso toki yi haquri ki barshi
Idan mai gidanki yace mikomin wannan karkice
masa Kai kaima akwaika dason sa aiki kafa fini
kusa dashi
A,a miqe kije ki dako masa idan kin kawo masa ki
risina sannan ki bashi
Afnan dai zaune take tana sauraronta harta Kai I
zuwa na goman na sihune mai cike da darussan.
Zama da miji
Sannan ta dinga fada mata magungunan da zata
tanada wajen gyara jikinta kala kala
Afnan tai murmushi gamida cewa aini anty
wannan nasihar taki dama bari kikai
Har sai Lokacin da zanyi aure. Don kuwa
zataimin amfani sosai amman kuwa yanxu zan
iya mantawa da Wasu abubuwan
Anty kausar din tai murmushi sannan tace
maganr da muke dakema yanxu. Haka na Gama
tanadar duk abindaya lissafa miki don yanzuma
zaki soma amfani dasu
Afnan ta zaro ido zatai magana anty kausar din
ta daga mata hannu alamun batason Jin komai
Dole taja bakin nata tai shiru ta dinga bin anty
kausar din da kallo
Tun daga abubuwan sha Dana ci hardana hayaqi
babu Wanda bataiba a gabanta
Washe garima tunda safe masu gyaran jiki
sukaxo suka fara aikin gyarat itadai in banda ido
babu abinda take binsu dashi suka gyarata tsap
masu kwalliyama sukazo suka duqufa ita kanta
tayi mamakin irin kyan datayi
Da yamma likis. Aleeyu yasa aka kira masa afnan
ta lulluba da mayafi
Adnan ta samu a zaune gefen Abban nata don
haka itama ta samu waje ta zauna. Tana
sauraron Abban nata
Aleeyu yace. Assalamu alaikum warahmatullahi
ta,ala wabarakatuhum. Ya jama,atul musulmi
Da farko inason. Nuna godiyata da allah daya
nunamin wannan ranar mai tarin albarka
Wanda zan iya cewa banida sauran wata matsala
a rayuwata burina ya Gama kammala
Makasudin taraku anan lkuwa shine son sanar
daku aurenku da aka mayar nakeson nayi. Ranar
alhamis dinnan data gabata don haka na hadaku
anan ne don nai muku nasiha
Dukda nasan Bawai rashin iya zaman aure bane
yaja muku rashin jituwankuba
Amman dukda haka inason ku zamo masu haquri
juriya da riqon amana
Wannan shine jigon zaman aure
Afnan kibi mijinki sauda qafa yi nayi bari na bari.
Komai zaki zama a rayuwa afnan a qarqashin
mijinki kike a qasa dashi kike
Dole yasaki kiyi kiyi. Kuma yace ki bari ki bari
Aljannarki tana qarqashin diddigensa
Kuma har abada baki da kamarsa domin yafi
iyayenki
Iko dake
Sannan kaima adnan kasan afnan yar uwarkace.
Har abada Baka da kamarta. Don haka ka riqeta
amana ko bayan raina adnan karkasa afnan tai
kukan maraici
Ka fito da soyayyar da kake mata a fili karka
boye koda digo wannan shinne abinda zai kawo
muku Jin dadi azaman takewar auratayyar ku
domin ita rayuwar aure rayuwace. Ta soyayyah
da kaunar juna
Don haka yanxu ku tashi ku tafi gidan da nace
kaje ka duba idan yayi Maka kace yayi
To na mallaka Maka shi duniya. Da lahira ga
takardun
Adnan din yasa hannu biyu ya karba gamida
godiya
Sannan aleeyu yasa hannu ya zaro Wasu takardu
biyu yace karbi wadannan na jikokinane. Aslim da
taslim takardun estate ne guda biyu
Sannan itama ya bata kyautar wani kamfani
dayasa aka Bude masa sabone bai Dade da zuba
ma,aikata a cikinsaba
Sukaita rafka masa godiya sannan adnan ya tashi
ya fice afnan kuwa kasa tashi tayi sbd ji tayi abin
yaxo mata banbara kyaui
Anty kausar ce ta miqe gamida kama hannunta
suka fice qatuwar jaka ta dauko ta zuba mata
magungunan data hada mata na mata sannan ta
rakota har bakin mota gamida yin mata nasiha
Yana zaune cikin motar qatuwar gaskece mai
numfashi
Securities suka Bude mata gidan baya ta shiga
inda adnan
Din ke ciki yana kwance abinsa sannan dreba
yaja motar sukabar harabar gidan
Babu Wanda ya tankama wani a cikinsu kowa da
abinda yakea saqawa a cikin ran nasa
Har suka isa katafaren gidan aljannar duniya
Yanada manyan gate har biyu da Babban qofa a
ko wanne gate da masu gadin wajen
Iya haduwa gidan ya hadu don idan mukace
zamu tsaya fasalta yaddah gidan yake sai book
din yakai na biyar Dana shiddah
A harabar gidan ga ma,aikatanan kowa nata
aikinsa
Suna fitowa daga motar dukkan ma,aikatan gidan
suka nufosu har rige rigen isowa suke
Suka zube suna kwasar gaiSuwa sannan duk
suka gabatar da kansu
Bayan sun Gama kowa ya kkoma kan aikinsa su
kuma suka nufi cikin gidan afnan ta dingabin
falukan da kallo
Komai na gidan ya qayatar kamar ba,a naijaba
Matattakalan bebe suka haye inda sukai rawun
daidai
Nan sukaci Karo da Wasu manyan qofofi daya ta
hannun dama daya ta hannun hagu. Sai kuma
daya a tsakiya
Kofar da take tsakiya nanne sashin yara wacce
take hannun haqu ita zata sadaka da Dakin uwar
gida dayan kuma wacce take dama zata sadaka
da Dakin mai gida
Nan ya nuna mata bangaren nata ta nufa shima
ya nufa nashi
Zuciyata ta Gama tsinkewa da abubuwan da aka
qawata bangaren nata dasu batasan Lokacin data
duqa tana shafar wani dan qaramin table dake
tsakiyar dakinba
Ta Dade tana santin kayan sannan ta miqe ta
nufi toilet ta watso ruwa gamida gyara Gashin
kanta ta tufkeshi gamida feshe ko,ina na jikin
nata da turare
Wasu yan ubansun kayan barci tasa. Ta koma ta
zauna saman gado tana lallatsa wayar tata
amman. Bangaren xuciyarta nakan adnan ne. Ina
yakene? Ina ya shiga?
wannan shine tunanin daya hana zuciyata sukuni
Har wajen qarfe tara babu adnan babu dalilinsa
Abu ya damu afnan arai harta kasa daurewa ta
suri hijab ta sauko qasan ko zata ganshi aiko
yananan hankalina nakan. T. V din dake manne a
jikin bango yana kallon ball
Guri ta samu ta zauna amman babu Wanda ya
tankama wani. Idanuwansu nakan allon. T. Vn
amman zuciyoyinsu na liqe da juna
Duk saima afnan din taji ta tsargu kaman
kallonta yake.
Don haka ta miqe ta haye saman ta barshi anan
zaune
Ji yayi duk kallonma ya gundureshi don haka ko
minti goma batai da hawaba shima ya haye ya
nufi bangaren nata
Harya murza qofar nata sai kuma yaji ya kasa
zuciyarsa na cike da tsoro. Gani yake afnan ta
daina sonsa yana ganin kewar mijinta a cikin
kwayar idanun nata
Don haka ya fasa ya nufi sashin nasa
Afnan kuwa tundata shga bedroom din nata ko
motsi ta kasa sai juyi kawai take. Tome adnan ke
nufi da shareta din da yai? Ko ya daina sontane
Da wannan tunane tunanen har barci ya dauketa
ba ita ta farkaba saida aka far
Kiraye kirayn sallah bayan tayi sallah Akan
sallayar tata ta zauna tanata aduun,oi har gari
yau haske
Bayan ta shiga toiket ta watsa ruwa ta hade cikin
wata danyar atamfa ta sauko qasa domin
karyawa
Kai tsaye dinning area ta nufa har ta harhada
abubuwan da zatacin taga yar gajeran takarta a
gefe ta Bude gamida fara karantawa kamar haka
Salam
Ga makullin wadruf din dakinanan ki Bude ki cire
kudin da zai isa ki Bama direba yaje yayo miki
cefane ki hadamin abincin da zanci karki ajemin
na wani can Nina wuce office
Ayimin addu,a
Tana gama karanta takardar wani haushi ya
nausar mata zuciya wato bazai ma iya zuwa ya
fada mata da bakinsaba kenan
Ta kada Kai sannan taci gaba da braek dinta tana
kammalawa itama ta samu ta karda ta rubuta
masa yar wasiqa kamar haka
Me za,a girka Maka mai gidana?
Taja wani gajeren murmushi ta aje masa sannan
ta nufi cikin gidan domin qara duddubawa
Adnan ya dawo gida a yinwace don ko karin
kumallo bai samu yayiba
Yaja kujera ya zauna kwalin lemo ya soma
budewa ya bulbulama cikin nasa yana qoqarin
dudduba abunda aka girka masanne yaga yar
takarda
Yana karantawa wani takaici ya daki qahon
zuciyarsa
A fusace ya miqe ya haye saman tana lafe saman
kujera a Dakin nata ya shigo
Afnan kin rainani ko? Ni abokin wasankin?
Afnan ta zaro ido ta tashi tsaye tana fadin me
kuma nayi yaya adnan?
Cikin zafin rai yace ban saniba meye amfanin
rubutun da kikai kika ajemin?
Taja gajeren murmushi tana girgiza Kai tace tokai
yaya adnan meye amfanin nakan?
Hannu ya daga zai dauketa da mari ta fasa wata
uwar qara ta maqalqaleshi. Wani irin yanayine ya
bijiro masa ko ina na Jikinsa yaji duk ya saki.
Kafafunsa kamar ba zasu iya daukarsaba
Muryarsa na rawa yace sakeni
Xikin muryar shagwaba tace allah bazan
sakekaba yaya adnan marinafa kace zakayi
Yace sakeni babu abinda zan miki
Ta qara maqalqaleshi tace allah nidai naqi wayon
Wata irin nannauyan kasalace ta saukar masa da
ko dan yatsunsa bai iya dagawa. Tai saurin
sakinsa ganin suna shirin faduwa. Zata ruga yai
saurin zanyota ya mannata da Jikinsa
Ya miqar da kansa yana sinsinar kamshin jikinta
har izuwa kirjinta
Ananfa zance yasha banbam don ita kanta tasan
sunyi mising din juna
Shi kansa admin da sukaga zaqewar tasa taso tai
yawa waje suka kadosa sukace idan kaji haushi
kaima kayi auren
Lol ba damuwa lokacine
Nasan da yawa zasuso Jin yaddah rayuwar hajia
sury qawar nafi ta qare da kuma yarta sady. Sai
ku biyoni gobe a
Last chapter. Mean qarshen. Book din a gobe
idan allah ya kaimu zamu kallama wannan book
din don har nasa a fara mana cigiyar Wanda
zamu fara koda zuwa Monday ne idan ina freee
Naku har kullun
Aure. Kan. Aure
Chapter42. The. End. Qarshe
Basu suka samu sakin junaba sai bayan ana
Kiran sallan magrib afnan na manne a jikin nasa
a tare sukai wanka gamida sallah
Suna gamawa ta miqe ta nufi kichin din dake
cikin falonta abinci mai rai da lfy ta hada musu
Yanaci yana santi shi kansa yasan yayi mising
din girkin afnan din bayan ya gamane ya fita
masallaci domin yin sallar isha,i itako tailet ta
fada ta dauro wani sabon wankan. Bayan ta fito
nanma ta bata kusan awa biyu a gaban miro
bashi ya shigoba sai misalin qarfe tara na
Dare. Yana shigowa bangarensa ya wuce yaje ya
watsa rua gamida canja kayan Jikinsa.
Jallabiyace fara sol ya sako sannan ya nufo nata
sashin
Tana kishin gide saman doguwar kujerarta tasa
laptop a gaba gamida rapka uban tagumi da
alamun abinda take kallo yayi mata dadi matuqa
Hannu yasa ya dauke laptop din afnan ta zabura
cikin shagwaba. Tace Kai yaya adnan don allah
ka bani
Ya harareta gamida rufe laptop din ya janyo
hannunta yace zonan na Rama Marin Dana manta
Daria tayi ta maqalqale a gefen kafadarsa ya
kamo karan hancinta yace wlh sai kika tunamin
Lokacin da kike fadin
Saiya maqe murya yace yaya....
Tai saurin zarewa daga jikin nasa tana bubbuga
qafafu cikin shagwaba take fadin nidai wlh
banaso yaya adnan ka daina
Daria ya shiga tintsirawa data gane kular da ita
yakesonyi saita tashi ta nufi inda ta qara shirya
masa abinci yace Kai afnan kasheni zakiyi ba
daxunnan naci waniba yanxu kuma kin qara dafo
wani
Bata tanka masaba ta nemi waje ta zauna shima
da saurisa ya qaraso inda take din
Ta zuzzuba masa komai gamida tura masa
gabansa
Kamshin abincinne ya daki hancinta baisan
Lokacin daya ware ciki ya nadi abincin son
ransaba
Ita kuwa tsatstsakura kawai tayi ta goge
hannunta da tissu wai ta qoshi.
Sannan ta miqe ta nufi bedroom din nata ta zame
kayan jikinta ta dauko wata yar figilar rigar barci
ta sanya. Iya cinya sake gyara Gashin kanta tayi
ta sakeshi har gadon bayanta. Sannan ta qara
gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare. Ta nufi
lokar dake jikin gadonta ta. Handa bag dinta. Ta
zuge gamida dauko kulli daya cikin magungunan
da anty kausar ta bata ta juye a cup ta dauko
peak milk shima ta juye bayan ta kadashi sosai
sannan ta farasha
Ta samu wuri a bakin gadonta ta zauna tana
cikin shanne adnan ya shigo. Yana sanye da rigar
barxcinsa mai hade da wandonsa
Kallo daya afnan din tai masa ta kauda Kai
Ya qaraso gabanta ya dauke kofin da take
qoqarin dauka domin kaiwa bakin nata
Afnan ta bishi da kallo ido waje ya daga mata
gira yace yadai?
Ta yamutsa baki tace kaban abuna mana
Ya girgiza Kai alamar a,a cikin shagwaba tace
sbd me?
Yace aike wata baiwace daga allah afnan
basaikin sha abinda zai kawo miki ni,ima ba
Damanke can duk Wanda ya kalleki yasan
ni_imatu ce
Wani irin kunyace ta saukar mata tai saurin
wayancewa
Ta miqa hannu ta wufto kofin gamida cewa niban
abuna kasan ko meye a ciki
Ya miqa hannu saiya amshe ita kuma taqi yarda
Ta miqe da sauri domin guduwa ya janyota
Jikinsa yana fadin ina zaki tofa daganan zace ya
sauya salo
Washe gari misalin qarfe sha daya na safe afnan
na kichin domin hadama mai gidan nata abinci.
Yar alamar dake nuna akwai baqo tai qara
Don haka tana daurawa ta sauko qasan don
ganin ko wacece
Zainab ta gani zaune Akan kujera. Afnan tai wata
qara ta fada jikinyta suka maqalqale juna cikin
zumudi
Afnan cikintsantsar farinciki tace taso mu shiga
ciki qawata akwai lbr
Tana qoqarin Jan natane zainab din tace ke da
baquwa nakefa
Ta kalli inda zainab din tai mata nuni. Sady ce
zaune da qafafuwanta afnan ta zaro ido waje ta
bita da kallo
Tana zaune cikin shga ta kamala hijabinta har
qasa. Sai yar yarta dake gefenta
Afnan ta juya tana kallon zainab tace ke kuma
qawata a ina kika samo wannan?
Zainab taja hannunta tace zauna kiji duk yaddah
lamarin ya kasance. Bana gaggawa bane don
zakiyi mamakin ta yaddah na kawo miki sady har
cikin gidanki
Toba wani abu bane Jia ina zaune a. Office
matarnan taxo ta sameni. Ta sanar dani cewa
afnan take nema
Na fada mata kina hutu aikine sbd baki Dade
dayin aureba
Ta rokeni konasan gidanki?
Da farko da nace mata, a a kasancear ban
santaba
Ganin haka yasa ta sanar dani ko ita wacece
kuma dalilin son ganin da takeson yin miki shine
donta rokeki gafaran
Abindatai miki
Na gasgata gaskiyarta na yarda da tayi nadama
hakan yasa na kawota gareki don allah ki yafe
mata
Afnan ta mayar da kallonta kan sady sbd shirun
da zainab din tayi.
Da sauri sadyn ta sulale daga saman kujera sukai
ido hudu
Tace ki yafemin afnan wlh nayi nadamar abinda
nai miki
Nasan alhakinkine yasa duniya ta juyamin baya
Ta share hawayenta dake zubar mata sannan taci
gaba da cewa afnan nasan. Nasan nida
mahaifiyata mun cuceku
Wlh momyna ta sanar dani ita ta sanya
mahaifiyarki a harkar shan jini.
Sannan ta dinga izata Akan taima mahaifinki
sharri
Da abun ya kwabe kuma ta guje mata taqi ta
taimaka mata
Har izuwa mutuwarta bataxo koda gaisuwaba
Amman da yake allah ba azzalumin bawansa
bane
Saidai shi bawan nasa ya zalumci kansa
Dodon dasu momy kebama jini wato sha jini yace
a dole waishi jinin dady na yakeson yasha tare da
danyen namansa
Momy tai juyin duniyarnan dodo yace saita
kawoshi tace to shikenan zata kawo
Daman Abban nawa yayi tafiya qasar london
Sai yace yau zai dawo
Sai taima dodon alqawari sai kuma akai rashin
sa,a yaqi dawowa a wannan ranar
A haka har saidaya qara wata biyu a cikin tafiyar
tasa
Dodon yai mata alqawarin idan har bata kawo
Abban nawaba to jininta zai shanye
Don haka a ranar momyna ta matsawa Abban
nawa lamba Akan ya dawo
Yace mata jirgin qarfe biyu zai biyo
A ranar batai barciba sbd jiran da take masa
Tacemai ya tsaya ita zataje ta daukoshi amman
ita da niyyar idan taje daganan kawai ta wuce
dashi gurin sha jini tayi
Don haka ta suri mota ta nufi airport amman
babu jirgin daya sauko don haka ta dauki waya ta
kirashi daria ya kamayin mata
Yace haba hajiya da kin dauka Nima haka nake
To inaso ki koma ki fadama dodon naki sha jini
jinina yayi masa daci wlh. Kurwata ba zata ciwu
a bakinsaba
Donn haka in yaso yasha naki jinin duk abinda
kika sani nawa na tattara. Ya dawo hannuna. Ke
Harda nakima na tattara na koma wata qasar a
can zanje naci gaba da sharholiyata da sauran
Wasu matan
Sadiya kuwa daman yarkice ba tawava don nasan
duk wani ahararancin da kikeyi a gari
Idan kinso kina iya daukarta kikaima dodon naki
saiya...
Kamin ya qarasa hajia sury ta zube anan
Daganan aka wuce da ita asibiti. Sannan aka
sanar dani naje ita ta sanar dani duk iya shegen
data aikata
Naji na tsaneta banason ganinta
Na juya nai tafiyata da baqincin waini ashe
shegiyace banda uba
Nai kuka harna godema allah
Ganin yaddah duniya tasamin ido har a jarida
yasa na koma wurin momyn nawa a asibiti
A Lokacin Dana sameta a jinkirta halittarta.
Qafafuwanta da hannayenta duk sun shanye.
Bakinta da idanunta sun jirkice. Bakin sai zubar
da yawu mai wari yake. Hancin na zubar da
magina
Asibitin suka dinga cajarmu kudi duk dan wani
abu dake hannuna Dana mahaifiyar tawa saidaya
qare
Daga bayama sai sukace basu Gano ainihin ciwon
dake damuntaba don kuwa idan har suka
gwadata komai lfy Suke gani
Ganin ciwo baya baya sai ci gaba yake yasa na
dinga saida qaddarar mu. Motata kawai na bari
nai mana visa muka fita qasar waje domin duba
lfyr tata
Acan allah e ma momyn tawa rasuwa na biya
kudin qasa aka binneta sannan na tattaro na
dawo gida Nigeria bayan na dawone na samu dan
qaramin gida mai dakuna biyu da kichin da bayi
na siya nake zaune a ciki
Bayan rasuwar momyn tawa duk Wasu abokan
arxiqi suka juyamin baya. Babu mai kulawa dani
duk Wanda na raba guduna yake. Nasan
alhakinkine adnan
A. Lokacin Dana ganki kinxo office dina
Badon allah na taimakekiba Donna cimma
burinane kawai
Idanda ace babu adnan a cikin case dinnan da
bazan saurarekiba. Nina fitar da adnan waje nai
sa,an yayi loosing din memory dinsa
Sai naxo masa a matsayin da kike garesa. Nace
masa nice yar uwarsa da nakeda aurensa babana
shine wandaya riqesshi da mahaifiyata
Don haka na samar masa iyayen qarya na biyasu
inason adnan fiye da tunaninki
Afnan sbd shi na aje aikina
Sbd ina ganin babu abinda na rasa a rayuwa
Ni naje nasa aka daura mana auren sirri. Da
adnan ba tare daya saniba. Mukaci gaba da
rayuwarmu a can qasar harnna haifi siyama
sannan nace masa mu tattaro mu dawo gida
naija
Na kirakine don Kixo ki ganema idonki yanxu
adnan baiyi dake don kiyi zuciya kibarmin shi
Nai sa,a kuwa don a Lokacin daya ganki yake
cemin babu macer daya tasana a duniya sama
dake
Najidadin hakan don haka nasa a raina adnan ya
zama nawa ni daya
Gidan da momy tasa aka Gina mana muka sauka
mun dawo Nigeria asibiti da komai ya dawo
hannunsa
Tunda duk abinda mahaifinki ya bashi takardun
sunanan a wajena. Kuma bai taba kulawa
takansuba har abubuwan da suka faru suka faru
Lokacin daya nace sai yaje kotu ne na soma
tattara inawa inawa don kuwa nasan zamana
dashine yaxo qarshe
Don haka a rannar daya tafi kotu Nima a ranar na
gudu
Amman saime tundana tafi adnan bai taba
nemanaba
Bai sakebi takanmuba ko a hanya bamu sake
haduwa ba
Saidai ya wuceni a mota koni na wuceshi
Har izuwa yanxu danashiga mawuyacin Hali
afnan don allah ki yafemin sannan ki roqarmin
adnan shima ya yafemin wlh na tuba inata neman
gafarar ubangiji
Afnan ta miqe ta nufi inda take suka rungume
juna sai kuka suke tace na yafe miki sady.
Duk abindaya samemu iyayenmu matane suka ja
mana
Ta saketa sannan ta balle tissu ta miqa mata
domin share hawayen nata
Adnan ne ya shigo falon da sallamarsa saidai
yana ganin sady yai kichin kichin darai
Zainab ma batai gigin zolayarsaba ganin yaddah
ya amsa gaisuwar tata a takaice
Afnan ta nufi kichin taima masu aiki magana dasu
kawoma baqinta kayan motsa baki
Har tayi hanyar saman zainab tace ki lallasheshi
don allah afnan ya yafema baiwar allahn Nan
kaddah haqqi ya tambayeta. Afnan tace insha
allahu ta nufi saman
A sashinsa ta sameshi yana zaune sai lallatsa
laptop yake ta janye laptop din tana masa tausa
Suka fara lbrnsu mai dadi sannan afnan ta sako
zancen sady wani irin kallo ya bita dashi mai
tsantsar. Jin haushinta
Yace idan naga sady sai me?
Afnan ta girgixa Kai tace ba komai yaya adnan
Amman sady tana cikin iftila,in da ko wane
musulmi ya kamata ya tausaya mata
Adnan ya aje cup din lemon dake hannunsa yace
naga alamun rainane kawai kikeson batawa afnan
Itama ta miqe da sauri tana fadin haba yaya
adnan ta yaya zan nemi bata maka rai alhalin ni
farincikinka nake nema a duk inda yake. Tace Pls
yaya adnan ka dubi maraicin da asy ke ciki da
kuma yarka dake hannunta koma dai menen sai
an kirata da yarka
Yaya adnan ka yafema sady don allah abinda
take buqata kenan daga wajenka
Adnan din yaja wata kakkausar ajiyar zuciya
sannan yace taci alnarkacinki
Na yafe mata muje na amshi yata dake hannunta
na kaima Abba ya hada da yan biyun dake
hannunsa son du tashi tare
Afnan tai daria gamida fadawa Jikinsa tace na
gode my dear my love I luv u so much.
Ina tare dakai har qarshen rayuwata
Adnan ya dago da kanta yana kallon tsakiyar
idanunta domin gasgata abindata fada
Ya saki wani lallausan murmushi gamida
sumbatan goshinta
ALHAMDULILLAH
Saimucema wadannan ma,aurata allah e basu
zaman lfy da kuma qarin qaunar juna. Da kuma.
Soyayya


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *