📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶3⃣8⃣
*_JIRGINSO ZAYA TASHI KE DAI AKE JIRA ...'YAR GATA DUNIYAR SO.... KECE DA SARAUTA_*🎶🎶
*_na dawo gunki nazo baqo da sallama....kai kawo nayi qarshe...a qauna na tsunduma....kin jawo nayi roqo nazo ki ban zuma....na sawo dubi tufata mai kyau da karrama....ke naiwa kwalliyata shiga ta alfarma....._*🎶🎶
*_soyayya gaskiya ce ya zanyi in raina....wanda yake aac cikintaaa nima don na zauna.......nayi dare ban masauki gidanki in kwana....zo ka shige har abinci zan maka kwadon rama....._*🎶🎶
*_riqe sirri sai mai sirriiii....da fari a cikin taurariiiiii...._*
*wannan waqar na sadaukarwa da readers don jin dadinsu kana iya sauraronta bayan kammala karanta wagga shafi*
😜😜😂😂
Matsowa kusa da ita ya sakeyi tattausan murmu kwance bisa kyakkyawan fuskarshi,duka hannayenshi ya ware da nufin ta iso gareshi,take jikinta ya soma bari,qwaqwalwarta so take ta tsaya cik da aiki saidai ta ware qwanjinta wajen hana hakan faruwa,bata da buqatar tsayawar tunaninta a yanzu,tama fi buqatarshi fiye da ko yaushe,ya sake matsowa gareta yana nufin janyo ta jikinshi
wata hadaddiyar tsawa ta sakar masa bayan ta dira daga kan gadon jikinta na qyarma,tuni zuciyarta ta karye hawaye ya soma sintiri bisa fuskarta,dukkan tunaninta sun gama vata fyade abdallah yazo yi mata,tunda ba wannan ne karo na farko data taba ganinshi kebe da diya mace ba,amma wanne irin tsoro abdur rahim kewa abdallah da ua bashi irin wannan damar?,ko wani abu yayiwa abdur rahim din nsta har ya kai ga shigowa dakinta shi daya ba tare da wani qwaqqwaran motsi ko hayaniya ba.
Abdallan ya sake motsawa don biyota qasan,cikin daga sauti hargagi fushi bacin rai da tashin hankali ta dakatar da shi
''dakata marar tsoron Allah,me kake nema da ni?,me ya shigo da kai dakina?,kana shirin tozarta sunnar ma'aiki?,kana shirin cin mutuncin matar da bata yi maka komai ba?,to Allah ya fika''
jikinta na rawa ra fara daddan na wayar dake hannuna tun dazun da aka kawota lubabatu ta danqa mata a hannunta
Numbers din abdur rahim ne guda uku,saidai duka wadda ta kira sai taji ringin dinta cikin aljihun abdallah,cike da wani tsoron ta dago ta dubeshi,hawaye ne kawai ke kwaranya da sintiri kan fuskarta
''abdallah!,ina abdur rahim?,me kayi mishi?me ka yiwa mijina!?''ta qarasa maganar cikin qaaraaji
baisan sanda yayi alkafura ya diro daga gadon ba,gadan gadan ya nufeta don ya riqeta ganin yadda take kuka tuquru tana dafe bango,saidai kafin ya kai ga riqeta ta goce
''kada ka tabani,kaji tsoron Alkah kasan cewa ni matar wani ce''cikin cool voice dinsa mai cike da jarumta da mazantaka wadda a yau rauni ya cikata ya saje maidata sassanya yace
''pls cool down mana,ki natsu in miki bayani kinji,ki saurareni''
''bazan nutsu ba,in nutsu ka cucu ne,me kake nufi abdallah,me nayi maka,ka shigo dakin aure na,banga mijina ba,na kira wayoyinshi suna jikinka,ka gaya min me ka masa!!me kayi masa!!!''
duk yadda yaso tayi shiru ta saurareshi abun ya faskara,idanunta sun rufe bisa dukkan zatonta ko abdallah ya kashe abdur rahim ne
''ki zauna ki fahimceni...'''
''bazan fahimceka ba.....ina mijina.....ina ka kaimin mijina abdu........''
''maryam!ni ne nan mijinki,ni ne mijinki ba abdur rahim ba,ni abdallah da ni aka daura miki aure!''ya fada yana nuna kanshi shima cikin daga murya har jijiyar wuyanshi na tashi
sai kukan nata ya tsaya cak,ta tsaya tana kallonshi tamkar doluwa ko sakarya,jin maganar tayi tamkar cikin mafarki,da saufi ta kama hanunta ta mintsina sai ta tabbatar cewa gaske ne,girgizq kantq ta shiga yi tana fadin
''ba kaine mijina ba,bakai ka aureni ba ni zaka yaudara?''
''bari in baki shaida don ki tabbatar''ciro wayarsa yayi ya kira wasu nimbers,ga mamakinta sai ga muryar abdur rahim radau
''kai,bakasan ganganci bane kiran ango daidai wannan lokacin ba?,ko baka shiga dakin marya bane?''yake tambaya cikin sigar zolaya
''hmmm,abdul maryam zata amince nine mijinta kuwa?''
dariya yayi
''a'ah,mai zai hana,idan ma taqi ta amince ka dauketa kuje gidansu tunda su sun sani kaine ka aureta din,ko ni inzo gobe sai in dauko gimbiya muzo in mata bayani''
baiga qarasowarta ba sai waftar wayar da tayi,cikin rawar jiki ta kara wayar a kunnenta
''abdur rahim,ka cemin kaine mijina ba abdallah ba,ka gaya masa don Allah''
''kiyi haquri maryam bani na bada sadakinki ba bani ke neman aurenki ba,duniya bani ta shaida a matsayin mijinki ba duka wannan abdallah ne,nine *abdurrahim a fili a boye kuma abdallah,nike neman aurenki a gaban idonki a bayan idonki abdallah ne*,banyi hakan ba don komai sai don *DACE DA JUNA* da kukayi ke da shi,babu wadda ta dace ta zauna da abdallah saike......''
bata bari kunnuwanta sun qarasa ji mata kalmomin da ta yiwa laqabi da munanan kalmomi ba ta saki wayar ta tarwatse agun,taji daga baki mai tushe to shin kuma wa take jira?me take jira da zai tabbatar mata fiye da abinda taji yanzun?babu,babu shi,take taji garkuwar jikinta na raguwa,qarfinta yana yin qasa,sai ta soma sulalewa agun
da gudu abdallah ya isa gareta ya tallafota,tabbas da tana da isashen qarfi bazata yarda ta sauka ajikinshi ba,rungumeta yayi yana jijjigata,numfashinta na fita hakanan idanunta akansa suke hawaye na bin gefan kunnenta saidai numfashin na gware ne gurin fita,rungumeta yayi tsam cikin jikinsa cikin wani tashin hankalin,daukarta yayi tsam tamkqr wata 'yar tsana ya komar da ita kan gadon ya shimfideta.
mahaukacin bugu yaji ana yiwa qofar bangaren nasa ,sai ya sake diriricewa,cikin qanqanin lokaci kuma ya gayyatowa kansa dakiya da jarumta yana tafiya yana waiwayen maryam din tamkar wanda aka ce masa kafin yaje ya dawo zata bace ya sauko ziwa bakin qofar ya saka key din ya bude
jikinsa ta fado tamkar wadda aka hankado,cikin hanzari yasa hannunsa daya ya cireta daga jikinsa yayi gefe da ita saidai ita qoqarin dawowa take zuwa jikin nasa tana gunjin kuka duk ta wani burkice kamar mahaukaciya
''wai meye haka zubaidq!bana son hauka fa!''ya fada cikin hargagi
''bazan iya ba abdallah,wallahi bazan iya jure rashinka ba,ka tausaya min abdallah,ta yaya muna cikin gida daya zaka kwana da wata abdallah?''
ya tabbata idan yace ma zaya tsaya bata baki ne wahal da kansq kawai zaiyi don ba zata taba fahimtarsa ba,kai infact ma a yanzu bai da time baijin yana da time din wani a yanzu a duniya koma bayan maryam,ya tabbata idan yayi sake kwabarsa zatayi ruwa ne tsululu kuwa,a nashi zaton da hasashen abun bazai kai bacn haka ba,yayi zaton cewa duk randa maryam din ta samu labarin shine miji a gareta zatayi farin ciki ne fiye da kowa kodon,dimbin dukiya da Allah ya mallaka masa
ganin yadda take faman ahigewa jikinsa kamar hauka yasa yq cira hannu hankadata baya tayi taga taga kamar zata fadi
''ki shiga hqnkalinki zubaida,bana cike da iskanci da hauka kina jina ko,bace min da gani''
maimakon tayi kamar yadda yace din sai ta qara tasowa kansa,cikin zafin nama yaja qofqr ya rufe ya maida muqullin,ta kuwa fada jikin qofar ta saki wani kukan tana bubbugawa iya qarfinta
''ka bude min don Allah abdallah,wallahi na kasa barci,na kasa cin abinci,na gaza jurewa,ka bude min abdallah''haka ta dinga fada tqnq bubbuga qofar,yana jinta hqr ya haura sama ya barta anan
ruwan roba mai azabar sanyi yq ciro ya hado da cup ya koma dakin,yadda ya barya haka ua sameta sai qaruwa da ruwan hawayen fuskarta sukayi
ajjiye cup din yayi a side drower ya haura gadon,ya zame mayafin dake jikinta ya wulla shi gefe,ya janyo cup din ya tsiyaya ruwan yana tsoma hannunshi cikin ruwan yana shafa mata a fuskarta zuwa wuyanta,duk da yanayin da yake ciki hakan bai hanashi kin laushi da santsin fatarta ba,duk lokacin da hannunshi ya taba fuskarta ji take tamkar yana dora mata wuta ne a jikinta,zuciyarta,cike fal da tsanarshi,sannu a hankali numfashinta ya soma daidaita,qwarin jikinta ya soma dawowa,da sauri tasa hannunta tayi wurgi da hannunshi dake ci gaba da shafa mata ruwan,ta miqe dqga kan gadon tana shirin sauka,da sauri ya tareta
''ina zaki maryam?''
''ina ruwanka da inda zani?,ka rabu da ni!''tayi maganar cikin tsawa,ganin da gasken fita zatayi yasa ya tareta ya riqe dukkan kafadunta,ta soma zile zille da qoqarin qwacewa tana fadin ya rabu da ita ya saketa,ci gaba yayi da qoqarin tsaidata
''ina buqatar hankalinki maryam,ina buqatar nutsuwarki,ki zauna ki bani dama muyi magana,ki nutsu ki fahimceni,me kike so ne maryam,me kike buqata''
sak ta sakeyi tama kallonshi
''sai yanzu kake da buqatar hankali na?,sai yanzu kake d buqatar nutsuwata?me kake son gaya min,ka aureni ba da sani na ba kuma kace nutsuwata kake buqata?wacce nutsuwa kake sa ran samu daga gareni?,haka ake aure?,ok saboda kana tsammani kana da dukiyar da zata iya kawo maka duk macen da kake so kamar yadda naji kana alfahari kana gayawa abokanka?,koda dukiya zata iya kawo maka kowacce mace da kake miradi yes na yarda zata iya amma banda ni maryamu aciki,koda ina da muradin dukiyarka ina cewa saida izini na zaka aure ni?,after all ma bana aonka abdallah bana qaunarka,bani da burin auren ire irenka ma,abu guda nake da buqata daga gareka shine ka rubuta min sakina guda uku a yanzu ka bani,ni kuma na maka alqawarin bazan kwana maka cikin gida ba,ka sakeni abdallah ka sakeni!''
ta qare maganar cikin hargowa
hannayensa ya harde aqirji yana kallonta,ba qaramin duka kalamanta sukayi masa ba,tunda ya tashi mace bata taba kallon qwayar idanunshi tace bata sonshi ba,akoda yaushe kalmomin so yake samu da karba daga garesu,kalmomin da bai taba samin suna da dataja ba sai yanzun akan maryamun,ya fuskanci ba qaramin fita tayi daga controll dinta ba,kome zaya fada bai da tasiri yanzun cikin kunne da ziciyarta don hakq ya dan jada baya,ya zame rigar jikinshi ya rage daga shi sai farar vest da dogon wandon shaddarsa,ya nufo inda take gadan gadan sai ta juya zata sa gudu caraf ya kamota,duk iya yada taso qwacewa abu ya faskara,qyaleta yayi taci gaba da qoqarin qwatar kan nata har jikinta yayi tubus qarfinta ya qare
''haka kurum zaki bata mana farin darenmu kan dalilin ki wanda kika qi tsayawa kiji nawa dalilin,dare ya tsala lokqcin da ya kamata mu samu hutu amma kin hana mana''ya fada yana mirginata tare da zuge mata zif din rigarta,ganin yana qoqarin cire mata rigar jikinta ya sanya ta sake sakin wani kukan cikin dausashshiyar muryarta da kuka ya dasheta tana ci gaba da qoqarin ture hannauenshi wanda saboda tsabar rashin qwarin jikinta ko motsi hannun nashi baiyi ba
''ka qyaleni abdallah,wallahi idan ka taba mutuncina zan maka Allah ya isa kuma bazan taba yafe maka ba''
duk da yana cikin rashin nutsuwa sai da ta bashi dariya
''kome zan miki ma ai nawa ne,dukkaninki halas dina ce,so ko kin min Allah ya isan ma ba bina zata yi ba''ya qarasa sabule rigar tata,hannayenta tasa ta fara kare qirjinta tana cewa
''ka zalunci rayuwata abdallah,zamu tsaya fa hisabi gaban Allah''
hannu daya yasa ya kawar da hannayen nata wanda ita iya ganinta duka qarfinta tasa gun kare su,ya balle bra din ya zameta daga jikinta,take numfashinsa ya dauke da sauri ya lumshe idanunsa kana ya squka agadon ya isa bakin wardove dinsu ya zabo rigar bacci mai adon fari da pink mai sulbi da taushi ,saidai kafin ya qaraso har ta isa bakin qofa cak ya sake daukota kamar wani kara ya maidota kan gadon ya danneta da rabin jikinsa ya sanya mata kayan baccin
fillow guda ya ajjiye musu bayan ya duba lokaci qarfe biyu da rabi na dare,cikin jikinsa ya jata ya matseta gam suka kwanta ba tare da ya damu da sauya nasa kayan ba,yana jinta tana wutsil wutsil dinta da dan ragowar qarfinta hade da hawaye don tuni muryarta ta gama dakushewa koda tayi maganar ma ba fita take ba,gashinta mai sulbi da taushi kawai yake shafawa yana jin digar hawayen nata tamkar na dalma kan tsokar zuciyarsa.
a hankali ya zagaya da kansa kan kunnenta ya rada mata
''kiyi haquri,na yarda na cutar da ke amma relax pls mu barwa gobe,kome kikeso zan maki,kiyi bacci zuciyarki tayi sanyi''
''ka sakeni bazqn kwana daki daya da kai ba bare jikinka,ka sakeni abdallah''abinda take ta fadi kenan saidai ina muryarta bata fita bare yaji abinda take fada,gaba daya ma taga ya maia abun kamar wani wasa saboda tsabar qarfin hali irin na abdallahn.......
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶3⃣9⃣
🎶🎶🎶🎶
*_alqawari ki riqeeee..komai wuya karmu rabu kinji..._*
*m sharif song for dis page*
😜😂
A hankali ta dinga bude idonta da taji ya mata nauyi sakamakon kumburar da sukayi,tana gama budesu tarwai komai ya dawo kanta,abu na farko hawaye ne ya fara bin idanunta kamar yadda ya ta kwanta da shi,jin alamun motsi daga qasa ya sanyata wurga idanunta can,abdallah ne zaune kan sallaya,ta dubi agogon dakin qarfe bakwai saura na safe,da sauri ta miqe cikin zuciuarta tana istigfarin rashin yin sallar asubahi akan kari,jiki babu qwari ta zuro qafafunta qasa motsin wannan ne ya juyo da hankalin abdallah kanta
sai ta kasa tashi don batasan ina toilet yake ba,da suka hada idanu kuma sai ta dauke kanta gefe guda
''ga toilet din can''ya fada yana kada yatsunsa tare da yi mata nuni,ta jishi sarai saidai ba zata oya tashi ba saboda rigar baccin jikinta gajeriya ce,gashi ta wuwwurga idanunta ko ina bata hango kayanta ba,zanin gadon ta yayaye kawai gaba daya duk da girmansa ta lullube jikinta da shi kana ta samu sukunin shigewa bandakin
kuka ta zauna yi riris kan daddumar,tana ji har cikin zuciyarta abdur rahim ya zalunce ta abdallah ya cuceta,don ko kadan bata da plan din airen abdallah akundin rayiwarta,sai gashi dare daya wata qatotiwar qaddara mai wuyar afassara ta fada mata,abdallah mai girmankai,mai izgili mai taqama da dukiyarsho,mai titiya da kyawun surar da Allah ya bashi,abdallah mai tarin 'yammata,ko baya ga haka ma sama ai ta yiwa yaro nisa,ina zata kai abdallahn,batajin cikin yarin masoyansa ita din karanta ya kai tsaikon da zata daga hannu,me take da shi da zata nunawa duniya amatsayin matar abdallah abdulkarem mai nasara?,yaro dan gata gaba da baya da daya tilo tamkar taoka daya cikin miya,mai tarin kyau asali dukiya da arziqin ma baki daya,ta ina tarayyarsa da maryam diya ga malam amadu zatqyi daidai,masu nema da qyar suci da kansu da qyar,diyar da ta taso cikin qunci hantara da takurar rayuwa?,rufin asiri take nema da girma ba bankada da tonon sililin asirinta va,ta iya talaucinta haka zalika ta iya tsayawa iya matsayinta,to akan me yanzu zata yadda ta sarayar da dulka wadan nan abubuwa?,ko ta zuba ido abdallan ua sarayar mata da au lokaci guda
tasha ji daga bakunan wasu matan yadda auren mai dukiya quruciya da kyau yake zamewa mace qarfan qafa alaqaqai,don me zata zira kanta rijiya mai gaba dubu?bata taba sha'awar auren mai tarin dukiya irin abdallah ba,balle shi din da tasha jin kalmomin nuna ko ahi waye da matsayin da yake ji ua taka daga bakinsa,idanuwanta sunsha nuna mata kal kalan 'yammata dake hauka akanshi,tana cikin wanna tunanin ta tsinci tafin hannunshi dafe da saman qafafunta,da sauri ta janyesu ba tare data daga kai ta dubeshi ba
''maryam''ya kirata asanyaye
''ko baki fada ba kuka kike''
''kuka na ya zama dole,auren dole qiriqiri?,irin auren dolen da ko a fina finai ban taba cin karo da ahi ba sai gashi yau ya faru a kaina?,ka fada min wanne mataki ka dauka game da zaman mu,zaman mu ba mai yiwu bane''
''ki bani dama mafyam ni zan mai da ahi mai yiwuwa,indai matsalar taki ta zuciya ce,zuciyarki bata san abdallah,ta bawa abdallah dama na kwana talatin cif na rantse miki sai taso abdallah fiye da yadda take son kanta''
''ka taba ganin inda ruwa da wuta suka cakudu suka zauna guri guda lafiya lau?''
ya fuskanci mai take nufi da maganarta don haka bata buqatar amsa
kusan mintina goma ahiru ya ratsa tsakaninsu,ta qagauta ya janye jiminahi daga inda take,ganin babu niuya tasa ta bude bakinta murya can qasa
''ka matsa daga kusa da mi,kuma ka cika min alqawarin da ka dauka min daren jiya yanzu ba sai anjima ba''
gayara zamanshi ya kuma tamkar ma basa ahi take maganarta ba
''naji,zan sakeki.....amma bisa wani sharadi guda''
tunda suka fara maganar bata dago ta kalleshi ba sai a yanzu
''ba buqatar wani sharado daga gareka ko wanne iei ne saki nake so,kuma dole ka sakeni''
ya sanya fitinannun qwayoyin idanunshi cikin nata kana ya tabe baki
''babu dole fa maryam,abdallah ne mijin ba wai maryam ba,idan kin amince zan gaya miki sharadina daya ne zuwa biyu da zarar kin cika sharadina ba tare da bata lokaci ba agobe ma kina iya tafiya da takardarki''idanunta ta lumshe saboda yadda ya nutsa qwayoyin idanunshi cikin nata yake mata magana haka kanshi tsaye kamar ba mai laifi ba
shiru tayi,cikin dan taqaitaccen nazari zuciyarta ta bata shawarar sauraranshi kanta kawai ta gyada masa,ya sake sanyaya murya tamkar mai jin bacci tare da sake matsowa kusa da ita,tayi yinqurin matsawa da sauri yace
''babu buqatar ki kuma matsawa baya,kin manta sirri zamuyi,ko kina nayita daga sauti na bayan jiya kinsa maqogarona nata zafi har yau?''tilas ta zauna a hakan qamshin turaren da tun jiya ya fesa shi amma har yanzu yana tashi a jikinshi
''tambayoyi ne zan miki su da farlo wadanda nake buqatar amsarsu daga yau zuwa gobe da safe kafin ki bar gidan nan,kada kiyi tsammanin samun takardar sakinki daga gareni matuqar kika gaza amsa min tambayoyina cikin gamsashshiyar amsa,na farko mai yasa kika damu da abdallah da yawa,kika gaza barinshi yaci guba da aka zuba cikin abincinshi har sau biyu?''da hanzari ta dago cikin mamaki da tsoro ta dubeshi,yaushe abdallah yasan da maganar gubar data hanashi ci?
gira ya daga mata yana mata killing smile dinshi
''hey,meye na tsorata haka,bayan tambayoyin basu qare ba,daya cikin wadanda zasu biyo baya fa''
sai ta duqar da kanta zuciyarta na dukan uku uku
''me yasa kika damu da sanin irin gubar da ake ahirin kasheni da ita sai da kika dangana da asibiti a washegari aka tabbatar miki da irin qarfi da illarta ga duk mutumin da yaci?,me yasa kika gaza barin gidansu abdallah duk da irin takura raini da abdalla ke miki?,me yake saki rudewa harda kuka duk lokacin da kika ganni kebe da wata cikin tsakiyar dare?suke nan tambayoyina''
gaza daurewa tayi a wannan karon ma sai data dago ta dubeshi cikin mamaki shin abdallah yasan akwai masu farautarsa ua qyale ya zuba musu ido?,tamkar yaji abinda take zantawa cikin zuciyarta yace
''kada kiyi tsammanin abdallah wawa ne bansana ana farauar rayiwanshi cikin gidan ubanshi ba,i know kuma zuwa gobe zaki ga abinda zaya faru,naki kawai answer din question dina.....gaba ta gaba,are you ready madam?''
kai ta sake gyada masa kamar qadangaruwa
''ok,mami is unaware game da wadda na aura,nayi haka ne saboda ina son inyi suorising dinta,ta bani komai a rayuwa bansan me zan bata ba,na sani baya ga ni kece ta biyu cikin diyoyin da take so,bata san diyarta na dawo mata da ita ba,na tabbata zatayi matuqar farinciki da mamaki da ganinki...saidai kinsan me?,farincikinta da mamakinta zai dore ne matuqar taji cewa auren so da qauna ne tsakaninmu,kinsan abun duba?duk wani motion da act namu zai zama irin na masoya a gabanta daga wunin yau zuwa goben tafiyarki babu musu tsakaninmu,yi nayi bari na bari wannan shine abubuwan da zasu sana miki takardar rabuwa da ni thats all''
gaba daya ji tayi ya daurera da duka jijiyoyin jikinta,wadan nan tsauraran sharuda har ina?,har gwara ya samu bulala ya bugeta yadda yakeso kana ya sallameta yafi nata sauqi,ina zata sami tulin amsoshin tambayoyinsa wadanda bata tab tunanin ma a kansu ba?me yake nufi yace da ita?,ama ture ta wannan baki daya,ya zata iya tanqwara zuciyarta ta nuna alamu na soyayya ga mutumin da babu so ko qwauar zarra tasa cikin zuciyarta.....
''idan kuma baki iya tsallake wadan nan abubuwa.....fine....sai ki shimfida ta barma da daura damarar zama da abdallah kiga idan bazai saceki gaba dayanki ma ba zuciyarki ba cikin kwanaki talatin kacal,hakan kuwa kinga bazaya miki dadi ba tunda kince wai baki sonshi bayan tsayin daka da kikayi wajen kare mishi ranshi da lafiyarshi don kina da buqatar ra......''
''naji....naji na amince''ta fada da sauri don katse soki burutsun da tace yana shirin yi mata
''good job,shikenan Allah ya bada sa'a''ya miqe daga inda yake,har yayi taku biyu ya kalleta still tana duqe
''kada ki manta da answer din tambayoyi na,don sune bqngare na farko na yarjejiniyar mu''
Sakaliyar la'asar ce data gama hada hadari wanda ya tilastawa garin lumshewa,sannu a hankali suke taku wanda idan ka gansu sai ka rantse shaqiqan masoya ne guda biyu hannayensu sarqafe cikin na juna,sanye suke da kaya kala daya saidai bambancin sunan yadikan,nata material ne na mata yayin da nashi ya kasance na maza,dukkansu sea green colour ne,abu daya zai saka duhu yadda fuskanshi ke qunshe da wani irin haske da annuri,yayin da nata fuskar ke duqunqune cunkushe da bacin rai duk da hakan bai hanata yin kyawu ba,maryam ne da abdalla kan hanyarsu ta zuwa gaida mami bayan ya tabbata da jama'ar gidan kowa ya koma inda ya fito
sunfi minti talatin cikin bangarensa yana nuna mata salon kallo magana da ladabin da yakeso tayi masa gaban mamin wanda hakan shi ya kusan janyo rikici
ya sake waiwaya ya dubeta suna gab da ahiga bangaren mamin kana ya dakatar da tafoyar tasu,tsatstsareta yayi da kallo,ta kauda kanta tana qoqarin sabule hannayenta dddaga cikin nashi
''malam bamuyi da kai zaka dinga min akallon mayi ba ko,idan kuwa kaci gaba daidai nake da na koma inda na foto na hada ya nawa ya nawa na koma inda nafi wayo''
''kya sha tsinuwar Allah data mala'iku,runda ko banza miji nake agareki koda qarshen duniya zaki gudu,nike ma da magana dake,kinfara karya wasu dokokin tun yanzu,wanda hakan na nufin tangal tangal da muradinki ne,haka koka ga fuskar amarya na kasancewa washegarin ranar da aka kanta,look at ur self don Allah,jiya kin kwana kuka idanunki sun koma kamar kumburarren qullin qosai,an samu da qyar sun daidaita kafin yamma,sanna kina son ki sake wargaza mana shiri,to wlh u hv to make sure idan kika bari mami ta dago wani abu babu ke ba samun takardar sallama''
wani tafarfasa zuciyarya ke mata,ta debi a qalla mintina biyar kafin ta iya controlling kanta ta sauyawa fuskarta mood sabanin na dazu,cikin tafasar zuciyq ta miqa masa hannunta shkuwa yasa nashi hannu ya riqe suka ci gana da tafiyarsu daga nesa tamkar ka sacesu don kyai tsaro da marching da sukayi
A guje ta juya kamar zata ci da baka ta koma bangaren nasu tana zabgawa nene kira,saura kadan ta take zubaida dake kwance agashiyyan wanda cikin nene adnan da zahariyya an rasa wanda zai ce da ita yi haquri ba don komai ba sai don tsananin haushinta da sukeji kan wanda ta shiga halin sabo da shi
da sauri nenen itama ra iskota don dana a tsaye take cikin safa da marwa
''yaya?,ya ake ciki?''
cike da tsananin tashin hankali kamar wadda aka gaya mata uwa da uba duka sun mutu tace
''wallahi nene yana nan bai mutu ba,tas na ganshi babu abinda ya tabashi wallahi,tare suke da yarinyar nan nene bata bar gidan nan ba,hannayensu riqe da juna,mun shiga uku nene kada dai ace ita ya aura?''maganar ba qaranin sa nenen tayi a tashin hankali ba,a aukwane ta juya kan kujerar data tashi zata dauki wayarta,garin rarumar wayar ta dauki remote,sai data fara dannawa ta lura ahine,wurgar da shi tayi ta suri wayar kai tsaye ta kira malam na hayi
Mgunyar dariya ya dinga kwarawa kafin yace
''sanda muka gudanar da aikin bata cikin gidan,don haka ki kwantar da hankalinki ki zuba ido kiga abinda zai faru,saidai babu lallai abunda zai farun ya zama abunda mukai nufi da shine,kasantuwar yarinyar na tare da shi''yana gama fada ya katse wayar,nene ta dubi wayar tana jadda maganar daya gaya mata,saidai ta samu relief jin cewa wani abu na iya faruwa da abdallan,nasu kenan yanzu zuba ido suga mai zai faru kenan?
cikin falon mamin babu kowa sai yan surutai da yake iya jiyowa cikin kitchen,hanyar saman mamin yai direct da ita,bai saki hannunta ba sai da suka dangana da bedroom din mamin yace zquna ina zuwa,cikin sassarfa ya sauko qasa ya dawo kitchen din
Tun daga falon ya soma qwala mata kira,ita da wasu mata ne su uku ta hudunsu baaba uwani da alama gyara kitchen din ake sakeyi da wanke abubuwan da suka babbaci
''omg,abdallah taushe zai girma ne jama'a''ta lumshe idonta tana fada jin irin kiran da yake mata
ya qaraso kitchen din cikin hanzarinsa ya kama hannayenta
''suprise mami suprise''yake fada cike da murmushi yana dubanta,sai ta dan hade rqi
''suprise wanne iri?wai shin ma wanne abu ne ya fito da kai daga gidanka?,salon kaci gaba da takuramin ya sanya kaqi tarewa gidanka kace sai bayan sati biyu''
''mami nidai kizo muje ols mami,nasan zan sanyaki fafincikin da kika jima baki irinsa ba''
''abdallah barni in gama da aikin nan tukun kahe zan sameka ko wanne irin suprise ne sai in gani''
ya langwabe mata kamar qanqanin yaro
''mami bana ao ya huce fa don Allah kizo muje''
baaba uwani ce ta sanya baki dole ta ajjiye plates din hannunta ta bishi tana mita shikam yana qyalqyala dariyanshin nan dake fidda sigar kyawunshi
*_kuyi manage da wannan pls_*
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣0⃣
*_An karbo daga Abu Hurairah Allah ya qara yarda da shi,Manzon Allah S A W yace''ana bude qofofin aljanna duk ranar litinin da alhamis,sai Allah ya gafartawa ko wanne bawa musulmi indai ya kasance baya shirka baya hada Allah da abokin tarayya,sai dai wani mutum wanda ya kasance akwai qulli ko gaba tsakaninshi da dan uwanshi musulmi,sai ace''ku qyale wadan nan har sai sun shirya,ku qyale wadannan har sai sun shirya_*
mami na gaba yana take mata baya,sai mita take masa na ya tasota tana cikin mutane,shidai baice uffan ba in banda murmushi da yakeyi,suka ahiga falo tana qoqarin zama yace
''a'ah mami mu qarasa daki''
''kai abdallah.....abdallah trouble maker,muje dai inga suprise din nan da aka hanani sakat,amma ka tabbata indai bai kai ya kawo ba to zan ck tararka''
''na amince,amma mami idan ya kai ya kawo din fa,me ni kuma za?a bani?''
''sai abinda naga ya dace....''
''zoben daddyn dake gunki kadai nike so''
hara rarshi tayi lokacin da take tura qofan bedroom din nata
''kayi kadan yaro,gwara ka fadi amount na kudi in baka da na baka wannan zoben,bakasan tarihinshi bane har yau.....''
maganar ta maqale mata saboda ido hudu da sukayi da maryam,jikinta a sanyaye hankalinta a tashe ta nufeta ta kama kafadunta bayan ta zauna kusa da ita
''maryam,lafiya?daga ina?,ya akayi ika baro gidanki a idin wannan lokacin?,ina fata ba matsala bace ta faru?,ina maigidan naki?''
''gani...''taji ance,ta waiga da sauri don tabbatarwa,shaf ta mance ma tare da abdallan suka shigo sai da yayi magana
harararshi tayi
''kaga malam bana aon wasa,fice min a daki zamuyi magana''
idonshi ya kanne guda daya h
gami da daga girarshi
''wannu batu kam ai mu ya shafa mami,nima diyankin ne,nine kuma mijin diyar taki dai,tuwonki manki''yayi maganar yana zama kusa da mami hade da dora kanshi saman kafadarta suka sanyata a tsakiya
Ba don murmushin dolen da maryam ta qirqira ta dorawa allon fuskarta ba da babu shakka mami qaryata abdallah zata yi,duk da hakan sai da ta dubi maryam din
''bana son shashanci,maryamu gayan meke faruwa?''
da sauri ya karbi zancan
''ko zan miki wasa kan komai mami bazan miki kan wannan ba,idan maryam bani ta aura ba ina zan ganta ma a irin wannan lokacin naje na daukota''sai ya dawo gaban mamin yayi zaman dirshan harda lanqwashe qafafuwa,ganin haka yasa maryam itama zamowa tayi irkn zaman da yayi gabam mamin,saidai ita zuciyarta cike take da rauni,badon namijin qoqarin da take ba wajen danne zuciyar tata ba da tuni hawaye ya fallasa fa,cike da salo na iya sarrafa harshe cikin nutsatstsiyar muryarshi yace
''mami,zai iya yiwuwa kiga na miki qaton laifi,zai iya yiwuwa ma daga qarshe kice sai kin hukuntani kan maganar da zan gaya mikin yanzu,maryam bata da laifi ko daya don ni na nemi a boye abun,mun fara son juna har ta kaimu ga buqatar muyi aure,na boye miki ne mami saboda ina sane da dimbin so da qauna da kike wa tilon danki,farinciki bazaya bari idan na sanar miki ba ki kasa sanarwa da wasu mutanen ba musamman wadanda muke zqune gida daya da su wadanda bana buqatar kowa ya sani cewa maryam nake da muradin aura saboda tsaro,mami kinfi kowa sanin irin traps din da na shiga,an farauci dayuwata ba sau daua ba ba sau biyu ba kuma sau uku ba,wadansu trap din sun yi aiki wasu kuma Allah ya kareni basuyi tasiri ba,na tabbata da ansan maryam ce wadda zan aura ba abun mamaki bane wani mummunan abu ya faru da ita''
''mami...ga maryam nan ta sake dawo miki a karo na biyu,saidai wannan karon uasha banban da sauran lokutta,wannan karon ta dawo gareki da matsayi guda biyu,diyarki kuma aurukarki,nayi kwadayin ganin irin farincikin da zako shiga ta sanadiyyata ne mami shi yasa na sake dawowa da maryam cikin rayuwarmu,sanin maryam kikayi mami a fili amma a badini nafiki saninta kuma zuwa gobe zan warware miki ita don wace a sarari ki gani,ina fatan samu sassauci cikin hikunci boye miki wadda zan aura da nayi mami na''
ga mamakinsu saiga mamin itama ta sauko gabansu,hawaye ne bisa fuskarta wani na nin wani,a rude abdallah yasa hanninshi yana shate mata hawayen
''idan na bata miki mami kiyi haquri,hawayenki bala'i ne mami a gurina''
sai ta kasa cewa komai,jikinta ta janyosu gaba daya ta rungumesu
''barni abdallah na nayi kuka,kuka ne na tsantsar farin ciki ba baqinciki ba,tabbas addu'a bata faduwa qasa banza,na jima ina addu'ar Allah ya baka mace ta gari,lokacin da maryam ta shigo rayuwarmu na fuskanci dukkan halayenta na gari sai maji ina maka sha'awarta,domin hasken alkhairai da nake iya hangowa qunshe da ita,ganin hankulanku bai gamu guri guda ba yasa na fidda burin daga daina na dungumi yi muku addu'a gaba dayanku,kai har wayewar garin yau maryam ce a raina da ita na tashi har ka cimmani a kitchen tunanin maryam nake''
ta janye daga jikinsu bayan ta dauke qwallar idonta,kama hannun abdallah tayi da na maryam ta hade guri guda bayan ta dora nata a saman nasu
''na godewa Allah da irin wannan zabi da ya mana baki daya,naji dadi matuqa da kasancewarki maryam cikin zuri'ata,maryam,ga abdallah nan amana ce na baki ita har bayan raina,na baki amanar abdallah har abada,bani da kowa sai shi,ki zauna da abdallah cikin amana da aminci,abdallah kaima na baka amanar maryam,matuqar ka cuceta bayan zamowarka miji a gareta ban yafe maka ba,ku kula da junaku''abinda ta fada kenan tana jijjiga hannunsu
Duk yadda yaso ya daure sai da ya kasa,qaunar shi da maryam qarara yake ganowa cikin idanun mamin,baiso maryam din taga kasawarshi saboda haka ya kifa kanahi saman hannun mamin ya sumbata cikin dabara ya goge qwallar idonshi
''nikam na dauka mami,na dauka,Allah ya tayani riqo''
''kefa maryamu na?''ta fada tana kalllob maryam wanda kanta ke duqe take cure guri guda,abune goma da shirin suka cunkushe a qwaqwalwarta,zuciyarta na gaya mata wayo kawai abdallah yayi mata,mai yasa bata bar gidan salin alin ba tare da mami ma tasan wadda abdallah ya aura ba bare ta mata wanna kandagrakin mai daddaure jijiyoyin jiki?,zata iya watsawa mami mai dimbin alkhairai da karamck qasa a ido koko zata yarda ta zauna da abdallan ta sarayar da dukkan wani haqqi da 'yancinta da ya take,ya aureta ta sigar 'yar burum burum,zata barshi yaci nasara a kanta ya sameta a bulus ya sameta ta sigar qarfa qarfa da banga banga?,wani sashen na zuciyarta ke mata qarfafa ata gwiwar alqawari ya daukar mata,kuma ta riga da ta cika masa gabar farko na yarjejeniyarsu,bata jin kuma zai karya alqawarin
daga qasa kuma hannunta yaketa yamutsa mata cikin wani irib salo da yake sa taigar jikinta tashi saboda nata hannun na kife ne cikin nashi tafin hannun,dob samun hanyqr tsira do son cire hannunta daga nashi tayi saurin cewa
''na karba mami,insha Allahu''cikin zuciyarta tana sauya qudirin ma'anar na karba in don kada Allah ya tuhumeta
Mami dake sauri ta koma gun mutane sai gata ta rashe a cikinsu,hira sabuwa ta barke duk da maryam na rakube gefe guda,ga zaton mami surukuta ce da kunya irin wadda tasan maryam din ko da can baya da ita bare yanzun,saidai ga maryam kuwa takura ce data sanyawa zuciyarta na nemo amsoshin tambayoyin abdallah,sai ta hada amsar sai taji duka sun wargaje,idan ta kamo nan ta qulla da can sai ya tsinke,ita kanta ta rasa dalilin da ya sanyata kasa barin gidan a lokacin da ta fahimci abunda ke faruwa,dik da tana ta bawa kanta amsar cewa girma da darajar mami ne saidai ita a karan kanta take jin amsar ba gamsashshiya bace bare ta doshi abdallah da ita
''ina zuqa,bari naje kitchen indauko wayat na kira mr stephien,dinner nakeso a shirya mib sabuwa daga nan zuwa takwas na dare a compound din gidan nan''mamin ta fada ikin zumudi da farinciki tana fita daga dakin
bayan fitarta shiru ne ya biyo baya,abdalla nata qate mata kallo ba tare data sani ba don kanta na duqe ne
''sai faman duqar da kai kike kamar wata mai gajeran wuya,amma dai ba haka mukayi da ke ba ko?,sauran qiris ki wargaza wannan matakin da kika kusa kammalashi,ki tashi ki dauko drink cikin fridge ki zuba kin,ki kuma zauna agaba na har sai maki tazo ta ganmu a haka dn mu sake wanke zuciyarta''
batasan lokacin da ta dago ba ta kalleshi da oily eyes dinta ba ta balla masa harara,idanu ya lumshe yana jin wani abu na tsirga masa,ko banza buqatarsa ta biya,burinshin dama ya kalli oily and brown ayes nata wanda tun jiya rabonshi da su
''ka isa ma?''
''haka kika ce?''
''eh''ta bashi amsa kanta tsaye tana kawar da kanta daa kanshi,gyada kansa yayi cike da mamakin tsiwarta
''za kuwa kiga kalar tawa isad,ki bar gani na kodaki gaban mami na baki muhimmanci,ina iya qin sakin naki naga wanda ya isa ya sani in sake ki''
bata san lokacin da kuka ya qwace mata ba
''tabbas abdallah ya gama raina mata hankali,a daki mutum a hanashi kuka haka ake,ita da ya kamata a lallaba ita ake raina ma wayo
dauke kanshi yayi gefe guda tamkar bsi damu bs,saidai shi kadai yasan zugin fitar hawayenta da yakeji,hakan ya sashi gaggawar fadin
''Allah ya baki sa'a kici gaba sa kukan har mami tazo ta ruskeki a haka,idan tabi ba'asi kuma na warware mata zare da abawa kinga daga haka ta daina ganin girma da mutuncin mu baki daya,ni kuma naqi sakinki tunda igiyar na hannu na,qarshe kiyi biyu babu''
Jin hakan ya sanyata miqewa da hanzari kuma cikun nutsuwa ta durfafi fridge din,binta tayi da kallo a sace sakamakon yadda rigar tabi jikinta ta fidda surarta,ta ciro lemon ta dauki glass cup saman fridge,gabanshi tazo ta tsaya ta tsiyaya mishi ta miqa masa,qi karba yayi sai harara ma da ya gallamata
''kina tsammani idan mami ta shigo ta taddaki a haka kina bani abu ba zata zargi komai ba?kin min tsaye a ka kamar zamu shiga filin yaqi''
cikin qufula da hasala tace da shi wasu hawayen sabbi na bullowa
''ya isheni ya isheni fa,don me zaka dinga juya ni kamar wata waina,wannan wanne irin abu ne?''
sake dauke kanshi yayi
''har yanzu ke din a matsayin matata kike,ko babu yarjejiya tsakaninmu dole kiyimin dukka abinda nace tunda ban sakekin ba,ruwanki ne ki rusuna ki bani ruwanki ne ki bar leminki nima na riqe aure na''
ba maganar da taqi jinin ya fadeta kamar wannan,tilas ta rusuna ta miqa masa,sai da ya wani sha qamshi kafin ya karba,bayan zuciyarshi cike take fal da tausayi da qaunarta,daga shi sai Allah sukasan abinda yake ji cikin zuciyarsa
Ai kam a hakan mamin ta samesu
''a'ah me ya sameki maryam?''caraf ya karbe
''don nace ta miqon drink''girgiza kanta mami tayi tana miqar da ita tsaye
''a'sh banson sharri,bansan maryamu da qiwa ko ganda ba bare kan mijinta,halan bata da lafiya tafiyanne batasonyi ko?''ta fada tana kallon maryam,sam ita bata fahimci ma'anarta ba rashin sanin me zata ce yasanyata saurin gyada kai don shine kadai mafita
''ayya sannu,hau gado ki kwanta bari in lalubo miki magani,kai kuma banason takura ka qyaleta ta huta har ta warke,ko kuma na riqeta anan idan bakayi wasa tayi sati''
Wayyo Allah,ai duka sai a lokacin suka fahimci inda ta dosa,a tare suka hada ido ita da abdallah,wata iriyan kunyanshi da bata taba jin irinta ba ta saukar mata,da sauri taja idonta ta qulke gam,shi din na da sauri yaja qafafunshi ya fice a dakin don bazai iya hada ido da mamin ba tunda kallon da take masa kenan,ita kam ko a jikinta,cikin gurin da take ajiyar magungunanta ta duba ta fito da pain killer da paracetamol ta hado da ruwa ta kwowa maryam din
''tashi kisha kinjk marya,kada ki biyewa abdallah ya cutar da ke ba tare da kin warke ba,idan kinga ma da takura kimin magana zan maganinsh don nasan halinshi da rawar kai sarai,idan kinki jikin bai miki daidai ba ki sanar min sai a haqura da dinner din''ita dai kamar qasa ta tsage ta shige haka ta dinga ji,wannan abun kunya har ina,sai da taga ta sha ta kwanta taja mata bargo sannan ta fice a dakin
Tayi nisa sosai cikin saqe saqe da tunani taji dumin mutum a bayanta wanda sam bata san lokacin da ya shigo din ba,a zabure ta miqe zata sauka ya damqeta da hannu daya
''kiyi a hankali kada ki fama ciwon naki''ya fada cikin salon rainin wayo,kasa motsi tayo abdallah zai kasheta kam wallahi,sai kuma ya hade rai
''kikaci gaba da kuka zuwa anjima idanunku zasu kumbura,kinga idan anzo dinner sai ki tanadi amsar basu''ya miqe tsam daga gadon ya fice abinsa adakin bako waiwaye,ajiyar zuciya ta saki,sai da ya fita din sannan taji kamar ta bishi ta rufe da duka,gaba daya ma shi babu abunda ya shalleshi,babban isue da ya kamata ace yana cikin rashin nutsuwa amma ko a jikinshi.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Bayan ta kammala sallar magariba mami ta shigo
''yaya maryamu jikin,dinner din zai yiwu kuwa?''
kanta a duqe ta amsa mata da eh don kawar da zargin da mamin keyi na wani abu ya faru da ita,amma a zahiri ba don wannan zargin da mamin keyi ba da cewa zata yi bazata iya zuwan ba,saboda har yanzu zuciyarta cikin qunci take,nan mamin ta sakata ta shiga tayi wanka duk cikin dakin,mai makeup ta tadda na jiranta,hakanan tanaji tana gani ta zauna aka zuba mata kwalliya ta gani ta fada aka sata ta shirya cikin wedding gown irin ta larabawa fara tas mai dige digen adon zaiba kadan kadan,rolling aka mata sak irin na larabawan wanda iyakarsa saman qirjinta,hill shoes shima da earings sarqar hannu data qafa duka ruwan zaiba ne.
Kada kaso kaga kyawun da maryam din tayi,kusan duka cikin event din bikin da suka gabatar wannan itace shiga mafi kyau da tayi.
Tana zaune nan cikin bedroom din shiru kamar yadda mami ta umarceta,qofar taji an turo wanda kafin ma ta daga kanta taga waye qamshin turaren data jiyo ya sanar mata,saboda haka taci gaba da dauke ganinta daga bakin qofar,tsayawa yayi kawai ya zuba mata ido cike da sha'awa da burgewa,tayi masa kyawu fiye da tunani,bai qara amanna da kyawun da Allah ya bata ba irin yau,kasa controlling din kanshi yayi ya miqa hannunshi da nufin shafa lebenta da yaci jambaki maroon colour,har ya kusa da ita kome ya tuna kuma sai yayi saurin janye hannunsa ya daidaita nutsuwarsa hadi da cunkushe fuska
''ki tashi muje mu ake jira''
sai a sannna ta daga kai ta kalleahi cikin sakannin da basu wuce uku ba ta qare mishi kallo
eh yes ta yadda abdallah mai kyau ne,sanye yake cikin jacket mai bala'in tsada da kyau fara tas da ita komai nashi farine idan ka cire necktied dinshi takalmi da agogonshi duka ruwan zaiba kalar nata shigar sak,kau da kanta gefe tayi don bata son fiya hada inuwa da mutumin da ya yiwa rayuwarta karan tsaye
''kayi naka wuri nima nayi nawa''sunkuyowa yayi saitin fuskarta har numfashinsu na gware
''kin manta a idanun duniya mu masoya ne da mukayi auren qauna,qwarai ni airen qauna nayi amma ke da aka yiwa auren dole na fada miki dole ki ari acting na ma'abota so ki dorama kanki matuqar kina buqatar cikar burinki,wannan ne magana ta da ke na qarahe,harshe na ya gaji da yi miki tuni''
Kanta ta sake kaudawa ta yadda babu yadda zai iya ganin hawayen dake qoqarin fita a idanunta,cike da zafin rai tace
''saidai kayi dukkan abinda kaga zakayi,kaga,nifa na gaji da wanna game din naka,kawai ka sallameni a yanzu na san inda dare yayi min''
''idan anqi fa?''
ya fada bayan ya miqe tsaue ya goye hannauenshi a qirjinsa yana leqa dan qaramin bakinta dake raahin kunya
''tilas ma ka sakeni tinda nace bana so bana yi akai gaba wataqila asamu mai tayawa''
Yaji zafin maganarta amma son biye mata balle a gamu da matsalar da tafi ta baya
''lallai kam yarinya wuyanki yayi kauri,naga alama kinga makwancina da yawa,don kin samu kamar ni abdallah na nuna sonki har na aureki kikeda bakin fadin haka,kinsan kalan 'yammatan dake rububi da fatan na zame musu miji ba tare da aisin kwabo na ba ma?''
A sukwane ta juyo tamkar mai jiran ya gama fada,ido cikin ido tace masa
''ni ba irinsu bace,na sha ban ban dasu nesa ba kusa ba,baka yimin ba sam ko kusa ko alama,kuma na fada na gaya maka bana sonka bana buqatar igiyar aurenka a kaina,ka ssakeni mana dole ne,kaje ka auri masu rububin naka,idan ka taya akace ba'ayi ai sai ka matsa ga masu yi inda kake da muhalli,bawai ka tsaya ka nace a inda babu muhallinka ba''
Mamaki kam kusan kasheshi yayi a tsaye,gadan gadan ya nufota yana fadin
''ba irin mu mace ke kalla kai tsaye tace bata son mu ba duk isarta da tsadarta,bamu cewa muna so ace ba'a son mu,ni abdallah na miki alqawari sai na azabtar da zuciyarki da kalar soyayyar da baki taba yiwa wani da namiji irinta ba''bai bata damar furta komai ba ua sirute gaba daya ita da wedding gown din nata harda 'yar purse dinta marching na kayan,dike doke da zille zille ta fara tana fadin ya saketa ita ba 'yar iska bace yana sauka daga step din benen zuwa falon mami na qasa yana fain shi kuma tantirin dan iska ne sai yaya kenan?
kafin su qaraso falon tuni ta soma jiqa fuskarta da hawaye,ajjiyeta yayi saman kujera ya dora qafansji daya saman kujerar kusa da cinyarta yana huci kadan kadan,sai da ya gama qare mata kallo kana ya bude 'yar jakarta dake hannunshi yaci sa'a kuwa ya samy tissue turare da powder,cirosu yayi ua cilla mata
''ki gyara fuskanki nan da minti biyu''
cikin muryar kuka tace
''idan naqi fa?''
wani dan gajeran qayataccen murmushi irin na gefan baki yayi idanunahi sun kada sunyi ja don ta soma bashi headach bai taba fuskantar irin wanna trouble ba daga gun mace,idan suka botsare basu da dadin sha'ani saidai ka bisu ta yadda suke so ka ka musu jan ido.
''meyi baya fada,kiqi yin kiga mai zai faru a aikace kinga ai yafi dadi akan na fada miki da baki''ya sauke qafanshi ya nufi fridhe ya ciro sassanyar ruwan swan na madaidaiciyar roba ya soma daddaka,sai da ya shanye tas ya juyo inda take,tuni har ta gyara atsoronta na kada ya hanata takardarta,tamkar ya qyalqyale da dariya sai kuma ya maze yasha mur
tana shirin miqewa ya hangi igiyar takalminta ta kwance da sauri ya duqa don daure mata zata ja baya ya riqe qafan gam ya soma daure mata,lokacin mami ta ahigo tana fadin har yanzu basi fito ba me suka tsaya yi ne?,yanayin data gansu ya matuqar burgeta ta sake amanna da soyayyar dake tsakaninsu,tayi murmushi tana tunanin tana tsakiyarsu basu taba nuna mata soyayya suke ba saima fada kullum ashe ninketa suke baibai.
Compound di ya cika babu laifi da jama'a,wanda kusan rabinsu duka 'yan uwane irin mugun na jikin nan sai daidaikin maqota da abokai,tayi mamkin yadda adan taqaitaccen lokaci irin haka ma aka tara jama'a mai dan dama har haka,ko ina ka duba gurin walwali yake da decoratiom na farin yadi da wasu fararen fitilu,komai na gurin fari ne hatta da kayan mahalarta taron farine
tayi mamaki da ganin raliya da nasir lubabatu qanwarta batulu harda hindatu da jabir,to wama ya gaya musu wa ya gayyacesu?,daga sashi guda kuma nene ce da adnan sai zahariyya,idanun zahariyya da nene na kan abdallah duk wani motsi nashi suna ankare da shi,fatansu daya suga mummunan sauyi tattar da shi,yayin da adnan ya tattara nashi ma mujiyar kan maryam wanda babu abinda yake sai aukin hadiyar yawu,cikin zuciyarsa yana yiwa nene Allah ya isa da ta hanashi mallakar maryam din har abdallah ya sameta,gefe guda kuma yana tainewa abdallahn yana fadin duk taurin ranshi ne ya jawo,amma yaci alwashin da zarar burinsu ya gama cika kota tsiya kota arziqi sai ya mallaki maryam din,ko nenen na so ko bata so,kai baiqi ya kawar ma da duk wanda zaice zai kawo masa cikas ba,zubaida na gida nene ta qulleta cikin dakinsu kana ta qullen bangaren ma baki daya,ta rantse ta maya babu inda zata fito har a watse.
cikin wani irin salo mai qayatarwa dinner din ta dinga gudana,kowa ranshi fari tas cikin burgewa,tana zaune a muhallinta suka mutane suka dinga zuwa suna gaisawa da taya su murna,saidai babu daya cikin yammatan da suke son Abdallah data gani a gun,da alamu kuwa hansu zuwa gun akayi,kodai iyaye ko yan uwansu,qarfe aha daya aka taahi kai tsaye mami tace su quce bangarensu maryam taje ta kwanta ta huta.
Yana iya hangota cikin dan qaramin hasken fitilar barci takure saman gadon yayin da shi kuma ke kwance saman sofa din dake cikin bedroom din,a haka sai kayi tsammanin bacci suke saidai ko kadan kowannansu da duniyar daya shiga ita nata tunanin har yau kan amsar tambayoyinne da takeson bada su a gobe batasan ta samu failure,ya miqe ya ciro paper cikin ma'ajiyar da yake ajjiye takardu yar qarama dake can qasan gadon wanda sai ka danna wani abu take iya bullowa ya hada da biro ya dawo yayi kwanciyar rigin gine ya soma rubutu ajiki.
a qalla mintina goma ya samu kyawawa yana ruutun,a hankali yaji jikinsa ya soma masa nauyi tamkar an dora masa dutsen dala,ya sake yunqurawa da nufin daga hannun nashi a karo na biyar saidai ko alamar motsawa baiyi ba,wasa wasa sai magana ta zama babba,ya bude bakinsa da niyyar yin magan amma sai yaji kamar super glue aka saka aka manne fatar lebansa ta sama da qasa saidai.
Cikin mintina da basu gaza ashirin ba komai nasa ya daina motsi face idanunshi da kunnuwansa dake iya jin abinda ke motsi da qara baya ga haka babu wani abu dake moruwa,tuni takarda da biron hannunshi suka sulale suka fadi qasa,hannayen suka zube gefe guda,gasu a jikinsa amma ji yake kamar an cire masa su su da qafafunsa.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣1⃣
👂🏾👂🏾👂🏾👂🏾
*shin ka/kina da labarin mutune guda bakwai da zasu shiga inuwar al'arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai tasa?,ranar da rana zata matso daf da kawunun al'umma ta dinga tafasa qwaqwalwansu?,to ku matso kuji daga bakin da baya qarya*
*_An karbo hadisi daga abu hurairah R A yace:Manzan Allah S A W yace: mutane guda bakwai Allah zai saka su cikin inuwarshi,ranar da babu wata inuwa sai tasa_*
1⃣ *_shugaba adali_*
2⃣ *_da saurayi matashi ko matashiya da suka rayu cikin bautawa Allah mai girma da daukaka_*
3⃣ *_da mutumin da zuciyarsa ke rataye da masallaci,ma'ana wanda ko yaushe jira yake yaji anyi kira zuwa sallah ya tafi masallaci_*
4⃣ *_da mutane guda biyu da suka so junansu saboda Allah,don Allah suka hadu kuma suka rabu donshi ma'ana badon wani harkar banza ba ko duniya_*
5⃣ *_da mutumin da mace ma'abociyar kyawun sura tayi kiransa zuwa yin zina ko aikata wani fasiqanci yaqi yace mata ni ina tsoron Allah_*
6⃣ *_da mutumin da yayi sadaka ya boye yin sadakar da yayi har hannun hagunsa baisan me damansa ta ciyad kota bayar ba_*
7⃣ *_da mutumin da ya tunq girma Allah a kebe shi kadai idanunsa suka zubda hawaye saboda tsananin girma da tsoro Allahn_*
Duk yadda abdallah ya kai ga son motsa sassan jikin nasa bun ya faskara,ya yarda ya kima saddaqar da cewa wani mummunan abu ya gama faruwa da shi,tamkar wanda dannu ya danneshi haka yake ji
babu tsumi babu dabara sai Allah haka yake ta faman ambata
sam bata san halin da ake ciki ba,saidai gaba daya ta nemi bacci a idonta ta rasa wanda ta alaqanta hakan da damuwar dake cunkushe cikin ranta,tayi juyi kan gadon yafi a qirga,ba zata iya tantance lokacin da bacci yayi gaba da ita ba
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
qarfe biyar da rabi na asuba ta farka daidai lokacin da wasu masallatan suka kai tsakiya a sallarasu,da ddu'ar tashi a bacci ta farka a bakinta kamar yadda ta saba sannan ta lalubi wayarta don jaska dakin da babu wadatar haske a ckinsa sakamakon kashe qawayen da akayi,sai data lalubi makunnin ta kunna sanna ta sauko daga gadon,a hankali idanunta suka sauka kan abdallah wanda zuwa lokacin ya rufe idanunsa gam zuciyarshi kawai ke aiki,ya gama amanna cewa tashi ce ta zo qarshe abinda yake jira kadai shine fitar ruhinsa daga gangar jikinsa,kamar ta wuceshi sai kuma taga bai kamata ba tunda dole dai ya tashi yayi sallah.
ta tsaya saitin kanahi cikin muryar dake nuna alamun yanzu aka tashi daga barci tace
''ka tashi kayi sallah lokacin sallah yayi,anyi asuba''jin ahiru ya sanya tayi zaton ko bai farka bane,amma wannan wace idiyar kwanciya ce haka yayi ya yada hannun?,sai ta dan duqa tana bubbugar filon da ya dora kanshi tana sake fadin
''anyi sallar asuba an kusa idarwa''
jin muryarta ya sanyashi bude idabun nashi a hankali tamkar mai tsoron ganin wani abun,sai ta dan zuba masa ido ganin yadda qwayar idanun tayi jazur,a sanyaye ta juya ta ahige toilet ta daura alwala ta fito ta tada sallah,ganin har ta idar bai tashi ba ya sanyata tayi zatob ko komawa ya sakeyi ne
kanshin ta kuma komawa ga mamakinta sai taga idanuwanshi biyu
''lokacin ta zaya fita alfijir na ahirin ketowa''
''bazan iya taahi ba maryam duk yadda naso hakan,ji nake kamar an daddaureni,ki taimakamin in tashi''abinda yake aon fada kenan saidai ina bakin yayi nauyi,ci gaba kawai yayi da kallonta,saita tsinci kanta itama da kallon nashi,lokaci guda kuma taji jikinta ya mutu murus,komawa tayi bakin gadon ta zauna ta inda take iya fuskantarsa suna ci gaba da kallon juna
kusan mintina talatin suna a haka har shida da rabi
''rana fa ta fito ba zakayi sallar bane?''sai taga ya maida idanun nashi ya lumshe,hakanan gabanta taji yayi wata mummunan faduwa,sai ta kasa zaman ta qarasa inda yake,abu na farko data fara lura da shi shine hannunshi da ya zamo qasa tunda ya farka bata ga ya gyara kwanciyarshi,ta sanya hannunta tadaga hannun taga ko zai gyara saidai tan sakinshi ya biyo ta,ta sake gwadawa har sau biyu babu banbanci
batasan lokacin data furta
''abdallah lafiya kuwa kake!''cikin tsorata da rudani
idanun nasa dai taga ya kuma zuba mata tamkar zai hadiyeta,sai ta shiga kiran sunansa a jejjere saidai ko guda bai amsa mata da shi ba
Lokacin da zuciyarta tayi mata hasashen abinda ya samu abdallahn jiri ne ya debeta ta zube a nan tana fadin
''me ya sameka?,me ya sameka don Allah abdalkah,ka bude baki ka gaya min''
inda zai iya da ya mata maganar amma babu iko
sai kuma ta zabura ta miqe da gudu ta fice a sashen nasu tayi bangaren mami
da sauri nene ta toshe bakin zahariyya da ta dan saki ihun farinciki ganin shigewae maryam bangaren mamin a hargitse
''nene Allah yasa ya sambade lahira''
''ko bai mutu ba to yana kan hanyarshi ta mutuwar''ta fada tana duban zahariyya
''don da ya kammla wucewar da ihun kururuwatsu kadai ta ishemu albishir''
saman mamin ta haura kai tsaye ta fara bubbuga qofar dakin nata ba qaqqautawa,tunda taji bugun ta tabbatar ba lafiya ba,ga zatonta ma abdallah dinne,tunda ta tashi dama takejin jikinta ba normal ba yadda ta saba jinsa,da hanzarinta ta murza muqullin ta bude qofan,kama hannun maryam tayi wadda taga tsagwaron rashin hankali kwance kan fuskarta
''lafiya maryam ne ya faru?''
fara jan mamin tayi
''mami zo kiga abdalkah,zo ki ganshi mami...''ta qarashe cikin rushewa da kuka
''Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj'alil hazna iza shi'it sahla''addu'ar da mami keta maimaitawa kenan fili da zuciyarya cikin sassarfa take biye da maryam suka gifta su nene dake labe jikin window dinsu suna jiran jin abinda zai biyo baya
Yadda ta barshib hakan suka sameshi,a raunace mamin ta isa gaban kujerar ta zube,gaba daya rungumoshi tayo tana kiran sunanshi,ita din ma saidai kallo da ido daga bisani ne hawaye ya gangaro daga ianunshi saboda ganin mamin nashi na kuka haiqan babu kuma baki ko hannun lallashinta,kjran sunan Allah kawai sike daidai lokacin da nene ta shigo dakin a rude kamar gaske
kallon da abdallahn yake mata ya sata tasha jinin jikinta,saidai ta nasar kawai don babu baki ko qarfin yin wani abu a kanta,tana ma sa masa tsammanin wuta zai qara zuwa lahira,
wani kallo ta jefi maryam da shi tare da zabura ta kai mata duka''me kika yi masa muguwa azzaluma''
mami ce ta tare dukan
''haba nene''cike da haqiqancewa tace
''wlh ban yarda da yarinyar nan ba bintu,daga aure jiya jiyan nan ace mutum ya kamu da irin wanna lalurar?,anya ba mayya ya aura ba bintu?''
''me ya kawo duka wannan zancan nene,muyi ta lafiyarsa ma mana''
kuka ta dinga yi haiqan tana fadin duk daren dadewa asirinki sai ya tonu shegiya mayya daga jiya zuwa yau kin lashe kurwar yaro saboda tsabar shahara a maitadaga bisani saiga zahariya da adnan,abun nasu ma sai ya zama over acting,don mamin ce ke masu suyi shiru
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Ranar basu kwana gidan ba cikin asibitin amalam aminu kano suka kwana,cikin kwana biyar babu irin gwajin da basuyi masa ba,saidai komai ya nuna normal yake qwaqwalwarsa spinal code dinsa da zuciyarsa kai har hanta da qoda duka sai da suka duba saidai result sai yazo komai normal
A lokacin zaka tausaya wamami da maryam idan kaga yadda suka koma,duk da qoqarin boye cutan da ake saboda yanayin aikin abdallan,shi kanshi ya rame saboda tashin hankalin da yake gani cikin qwayar idanun maminshi da maryamu
cikar shi sati guda suka koma gida mami ta bada umarni ayi musu visa cikin satin zata fita da shi,kafin nan daya daga cikin manyan security dinsa mubarak wanda yake babba ne cikin masu tsaron lafiyanshi da hisham amininshi ke taimaka su mamin gun kula da abdallah,kamar daga shi zuwa toilet da sauransu,mutum ne mai matuqar kirki mubarak kamar hisham,har albashinmubarak din mami tace zata dada yace baya buqata,babu irin alkahirin da abdallah baya musu don haka bashi da abunda zai sakq masa da shi sai ta wannan hanyar,haka hisham babu komai tsakaninsa da mamin sai fatan alkhairi da sa masa albarka.
Batun fitar da abdallahn da za'ayi yayi masifar daga hankalin nene ta soma zaton kada fa a kaishi wajen ya samu sauqi haj bintu ta dawo musu da hannun agogo baya,don nene ta gama tsorata da irin kallon da abdallan ke binsu da shi duk lokacin da suka shigo duba shi
bata bata lokaci ba ta koma gun malam na hayi ta zazzage masa bakin jaka tare da qarin buqatunta
🌲🎄🌲🎄🌲🎄
Misalin qarfe sha daya ne na safiya suka gama waya da mama ta kirata don jin jikin abdallahn,tana shirin ajjiye wayar taga har sha daya da minti goma,mamaki da fatan Allah ya sa lafiya maryam din ke tayi jin shiruchar yanzu mami bata leqosu ba
mawuya cine qarfe takwas ta gita bata shigo ta dubasu ba,haka nan ba zata tafi ba sai mubarak da hisha amininshi sunzo sun gyara abdallah ita kuma maryam din ta shirya breakfasy ta gyara bangaren nasu ta miqawa mamin break din ta bawa abdallan da kanta sannan taje tayi wanka,to yau kam duka mubarak ne yayi hidimomin shi kadai ita kuma tayi saura,da taga shabiyun rana ta kusa sai ta sanya hijabinta taga gwara taje ta duba mamin,don ta tabata ko bata da lafiya ba zata iya zama ba sai tazo ta gansu
sai da ta sake leqawa bedroom din abdallah ta taddashi har yanzun baccinsa yake don ko break baiyi ba,a haka fes da shi sakamakon kyakkyawar kulawa da yake samu,sai ka rantse lafiyanshi lau,kyau dac kwarjininsa duk suna nan sai 'yar rama da yayi,tausayi yake bata sosai,ta sake girmama kadaitar zatin Allah,dan adam ba'a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,duk kuwa kyau asali dukiya da kake da shi idan yaso sai ya maidaka abun Allah sarki
ta share hawayenta sannan ta fito daga sashen,sai data tsaya ta tabbatar ta qulle ko ina don yanzun bata yadda da kowa ta barshi daga shi sai abdallah idan ba mami ko mubarak ba
Ba zato taji ansha gabanta,da sauri taci burki tana dubanshi,adnan ne ya tsaya yana qare mata kallo kamar wani tsohon maye
''babe ina zaki haka?''duk wanda ya fito daga tsatson nene yanzu haka ta tsaneshi bata qaunar ganinsa,hakanan taji bata qaunar koda hada inuwa guda da su,tsaki ta ja kana tabi ta gefansa da niyyar rabeshi ta shige,sai ya sake binta ya tare hanyar yana fadin
''haba baby ki tsaya ki saurareni mana,nifq sonki wallahi nake ki bani dama mu huta abinmu,da kyaunki da komai kin tattare kanki guri daya kin batawa kanki lokaci wajen jiyyar wancan nakasashen,kada ki cuci quruciyarki mana baby,ki bani hadin kai ni kuma na miki alqawarin biya miki kowacce iriyar buqata kike da ita''.
dan ya tsanta ta nuna shi da shi
''ka bani hanya na wuce malam ko baka ji ba''
''common baby ki.....''
batasan lokacin da ta daga hannu ta tsinka masa mari ba cikin zafi da huci tace
''ni ba irin matan da kake tnani bace,hakanqn ni ba butulu bace irinku,nakasashen mijina ya fiye min kai da yan uwanka kai da duka ma danginka,daga rana irin ta yau kada ka kuma kuskuren tarata da banzayen magnganu irin wadan nan,banza shashaaha bani hanya na wuce''
''ni kika mara,wallahi zaki san ba'a ja da ire irenmu,zaki san kin sanya hannunki kin mari adnan''
''na marekan,sai me,na mari banza na mari wofi?''ta fada bayan ta masa wani kallon banza ta kewayeshi ta shige gun mamin
Baaba uwani kawai ta taras itama tana qoqarin fitowa akitchen da alamu wanke wanke ta gama,suka gaisa a mutunce tana tambayarta mai jiki,ta amsa mata da sauqi kana ta tambayeta mamin
''hajiya tana sama,nima tun jiya da yamma rabina da ganinta,tace dqi da yammacin jiya kanra na mata ciwo zata ta kwanta,to tunda ta hau kuma har yanzu bata sauko ba''
''bari na dubata to,Allah yasa lafiya''inji maryam wadda ta fara taka benan
''ameen,kice ina mata sannu''inji baaba uwani dake ficewa daga sashen
''zata ji''
knocking tayi ya kusa goma kafin taji cikin murya kamar ta fada fada ance waye ne?''a sanyaye tace maryam ce''
ta kusa minti talatin kafin ta bude qofar bedroom din
mamin ce fes da ita ikin lace da alama bata dade da gama wanka ba saidai babu make up a fuskarta kamar yadda taje a hade kamar wadda aka aikowa da labarin mutuwa ,kusan zata iya cewa bata taba ganin kwatankwaci yanayin a gun mami ba,kullum cikin fara'a take.
fuskar maryam qunshe da murmushi ta dan rusuna tana gaida mamin,duk da adaqile take amsa mata bata kawo komai cikin ranta ba,tayi tsammanin ciwon kan ne ke damunta
Shiru ne ya ratsa tsakani bayan ta gama gaishetan
''wai lafiya malam kin min tseye a gaba na?''ta fada cikin sautin fushi
a tausashe tace
''ah.....dama ji nayi shiru baki shigo ba,shine nae bari inzo in duba ko lafiya,ga abdallah ma baici abinci ba saboda rashin shigowarkin''
''banga damar shigowar bane,ni baiwar idan ubanku ce,siyata kukayi da zanta muku bauta,ok....na ganoki ma,wato bani da lokaci sai naku ko?,to kada Allah yasa ahima yaci abincin kinibabbe,ruwansa ne daga yau kada ya kuma cin abinci a duniya,ni da zaya mutu ma da bai hutar da muta ne ba,mtswee aikin banza shine kika zo kika taahi mutane suna cikin hutawatsu,to wannna ya zame miki na qarshe da zaki sake takomin saman ma,duk abinda kuke buqata ki tsaya daga qasa har sai na sauko,kinji na gaya miki''
daga haka ta ja qofarta ta bame ta bar ta anan
tamkar gini haka maryam ta koma,mafarki ne koko gaske,almara ce ko tatsuniya ce,ji tayi wasu hawaye masu dumi na sauko mata,batasan sanda ta tsinci bakinta na furta
''ya Allah kada ka jarrabemu da wata jarabtar ta daban bayan wadda muke ciki,ubangiji idan ka saka mana wannan cikin sabuwar karrabar da zaka mana ba zamu iya jurewa ba nida abdallah,ya Allah sassaucinka muke nema''bibbiyu ta dinga gani a haka ta bar bangaren zuwa nasu,tafi qarfin minti talatin zaune afalonsu tana rasgar kuka
wanna wace iriyar jarrabar rayuwa ce da suka wayi gari da ita da safen nan,anya ma kuwa da mami tayi magana?,mamin abdallah fa,mai tattali da qaunarshi akoda yaushe,mai son ganin farinciki da walwalarsa,mamin da tasha bata amanar abdallah,tasha gaya mata bata da kowa sai shi ta kula mata da shi bata so ta rasashi yadda ta rasa mahaifinsa
cike da tantamar ba mamin bace ta dauki wayarta ta kira number dinta don ta tabbatar,saidai dagawar farko ta kuma cin karo da muryarta tana fadin
''wai nikam sa'arki ce maryam?,lallai na sakar miki da yawa kinga gadon barcina,sai na dauki tsatstsauran mataki a kanki kamar yadda nene tace''jin sunan nene kawai data ambata ya sata dauke wayar daga kunnenta tana kiran sunan Allah,tabbas akwai wani abu na daban dakeaon kunmo kai
''Allah na roqekakoma meye ka kawoshi da sauqi ya arhamar rahimeen''ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka
kiran sallar la'asar ya fargar da ita abdallah data bari,da sauri ta miqe a rude ta tura qofar dakin ta shiga,yanayin fuskarsa kawai ta kalla ya tabbatar mata ya gaji da kwanciyar,sai tausayinsa ya kamata,da sauri ta qarasa kan hadon cikin rawar murya
''kayi haquri don Allah,mun barka kai kadai wallahi ma.....''
maganr tata ta katse saboda yadda taga ya zubawa fuskarta ido,tamkar mai son tambayarta abinda ya sanyata kuka,sai a lokacin ta tuna da hawayen fuskarta,kawar da kanta tayi gefe tana qoqarin boye damuwarta,kusan minti biyar kafin ta dawo da kallonshi saiai har yanzu ita din yake kallo,data fuskanci tambaya ce yake mata sai ta girgiza kai
''ba kuka bane abu ne ya fada min io kuma daga nan sai ma dauro alwala da yaqi fita....bari na kawo maa abincinka''ta fada tana miqrwa da saudi ta fice adakin yayin da ya bita da kallo zuciyarshi cike da wani abu dake masa yawo ko ina cikin jininshi
Da qyar ta iya jingina ahi da fuskar hadon ta tattare si da filota zauna dab da shi har cinyarta na gogar tasa,ya lumshe ido cikin zuciyarshi data zame masa abokiyar tadi yake fadin
''so bala'ne,duk cikin yanayin da kake baya barinka ka huta?''
''bismillah karbi''yaji tana fada saitin kunnenshi,tsigar jikinsa ta tashi,a hankali ya bude idonshi ya sake zubasu a kanta,yana hango bacin rai da tashin hankali qarara kan fuskarta,da yana da baki zaiso ya tambayeta yaji me ya sameta?,bai taba tunanin zata ci gaba da zama da ahi a yadda yake ba,yayizaton a washegarin randa lalurar ta sameshi zata hada yanata yanata ta qara gaba ko babu takardar saki,kwatankwcin yadda yaji wasu matan nayi ga mazajensu idan lalura ta samesu,wasun su kun hayayyafa ma tare amma basu iya zama da kai da,bare su da kwana bihu kacal sukayi a matsayin ma'aurata.
kallon taga yayi yawa
''ka karbi abincin''a maimakon taga ya karba sai ya juyar da kanshi yana duban bakin qofa,hakan ya nuna mata mami yake son gani,hakan sai ya sake karyar mata da zuciya,ta sani mawuyaci ne ya karbi abinci idan bai ga mamin ba,saboda haka ta ajjiye cokali ta kuma daukar wayarta cike da fatan ta samu sauyawar yanayin mamin
''mami ya farka yaqi ya karbi abincin keyake jira''
''ke!ke fita daga idona,wai shin komayyar ce ke da gaske?,to wallahi zan ci iki mutunci fiye da zatonki,ko rayuwarku wajibi na ce,kuje kuji da kanku kada ki kuma kira na na gaya miki''daga haka ta katse wayar,hada idanu sukayi da abdallan da alamu yaji wani abu cikin abina mamin ta fada,mutum ne mai kaifin ji,hadiye kukan da yake taso mata tayi ta kuma diban abincin a cokali ta miqa masa tana fadin
''kayi haquri ka karba,anjima mamin zata zo kaji''
🎄🌲🎄🌲🎄
wasa wasa abun sai ya zama gaake,tun ranar data yi shigowar qarshe mami bata sake waiwayarsu ba,sam ta mance da su ma baki daya,gaba daya an canza mata alqiblar rayuwa,kusan gidan ma baki daya ya koma hannun nene sai abinda ta shimfida wa jama'ar gidan ciki harda mamin,a hankali a hankali suka dinga karbar takardun lamfanoni filaye gidaje da duk wata plaza na abdallahn daga hannun mamin,ba tare da musu ba haka zata dauka ta damqa musu
hisham baisan halin da ake ciki ba,bai an kara ba sai da yake duba kamfanin yin flower na abdallahn ya tadda adnan dare dare kan kujerarshi kamar wanda ya gada daga gurin ubanshi,da ya sami mamin ya mata maanar ranar ya ga bala'in da bai taba gani ba gurinta,har da ja mishi kunnen matiqar bai dauke idonhi daga lamuransu ba zata sa ahanaahi shigowa gidan kamar yadda tasa aka hana duk wani dan uwanta ko na maryam zuwa gidan,tilas ya ka bakinshi on ya san daina zuwanshi gidan ba qaramin tagayyra zai haifarwa abdallah da maryam ba,ya dai cika da mamakin canzawar mamin lokaci guda,tsana nin biyayya da bi sau da qafa da takewa nene
🎄🌲🎄🌲🎄
Sau biyu tana leqowa taga ko bacci ya daukeshi?wanka take son tayi ta sauya kayan bacci ta kwanta,a karo na uku ta tadda idanunshi ruf alamun ya samu bacci kenan,ta jima tsaye akansa tana qare masa kallo,a hankali ta sanya hannunta cikin tattausan sumarshi,yana buqatar a rage masa ita saidai bazai iya magana ba,cikin ranta ta qudirci gayawa hisham gobe ko zai iya masa yana da clipper tunda ita bata iya ba,jin ya motsa ya sanyata saurin janye hannunta tsoronta kada ya farka,sai da taga ya bar motsin kana ta tofa masa fatiha da yatul kursiyyun da take yawan tofa mishi akai akai ta juya ta isa bakin cupboard dinsu ta soma cire doguwan rigan jikinta
a hankali ya bude idanunshi ya zuba mata ido duka batasan me akeyi ba,ta janyo towel ta daura tayi banaki,ya lumshe idona wani dan murmushi ya subuce masa,maryam maryam bai san maryam ba sai yanzun,yanzun ne yasan maryam,cikin tunaninshi yaji tana qoqarin itowa ya maza ya maida idanunshi ya lumshe,yana iua hagota tana shiryawa tsigar jikinhi na tashi,ji yake ina ma yana da lafiyar da zai nuna mata irin soyayyarta dake danqare ciki zuciyarshi,har ta kammala ta zura rigar baccinta ta dora dan hijabinta a kai
Bata taba yarda ta kwanta kan gadon matuqar idonshi biyu,sai bacci ya daukeshi take lallabowa ta kwanta ga tsammaninta duk bai sani ba,saidai data kwanta din ko cikin bacci yake zai farka saboda wani dumi na musamman yake ji daga garta,yau din ma lallabowa tayi ta kwanta gefanshi bayan ta gama qare masa kllo kamar yadda ta saba,a hankali gajiya ta mamayeta,bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,a irin wannan lokacinne shima yake samun damar qare mata nashi kallon,yakan tsinci kansh ciki wani irin nishadi a lokacin
ya daga hannunshi da niyyar janyota cikin jikinshi ya kusa sau goma amma ya kasa,ya saki nannuyan ajiuyar zuciya yanajin radadin hakan cikin ranshi.
cikin sa'a tayi wani juyi tashin farko sai gata cikin jikinshi,murmushi yayi yana godewa Allah tare da dora kanshi saman kanta,duk da hijabin jikinta hakan bai hanashi jin dumi da qamshinta ba
sannu a hankali sai kuma ya dinga jin motsi kamar ana hawowa saman da suke,yaci gaba da kallon bakin qofar don ya tabbatar yau maryam tayi mantuwa bata rufe qofofin ba,idanunshi fes kan qofar yaji an turo an shigo,tashin farko aka dallare dakin da fitila mai tsananin haske kai tsaye hasken ya iso har inda suke
''wal masakinu bakayi bacci ba?''yaji an fada kana aka kunna duka qwayayen dakin,fuskar adnan ta bayyana
''gwara ma da bakayi baccin ba ai kaga ka gani da idonka tunda gani ya kori ji ko?,yau zan cika burina,zan kwanta da matarka agabanka,zan cusa maka baqinciki abdallah irin wanda na dade ina sha akanka,ka fini kyau,ka fini matsayi ka fini kudi ka fini nasaba hakanqn ka fini farinjini,yau zan kuma nakastaka kafin lokain da muka diba maka na mutuwarka ya cika,kabi bayan tsohonka ku hade acan kafin tsohuwarka ta biyoku''
gadan gadan ya hauro gadon yasa hannunshi ya janyo maryam dake jikinshi wanda hakan ya sanyata farkawa afirgice,ba qaramin kaduwa tayi da ganinshi cikin dakinsu ba cikin takiyar dare,bata ankara ba ya sabule hijabnta ya wurgar take gashinta mai tsaho da santsi ya warwatsu,runtse idonshi abdalah yayi yana jin tamkar an ciro zuciyarsa ana tststsagata,kamar an karata kusa da tukuba turiri kawai take maa,ya bude idonshi yaga yadda ake dambe tsakanin adnan da maryam,gashi kwance bashi da ikon tsinana komai,qoqari yake na daga hannunshi saidai hakan ya faskar,ihi yakeso ya kurama na baqinciki da takaici amma ko bakin ya kasa motsawa,sai ya koma kiran sunayn Allah ciin zuciyarshi tare da yunqurin motsa hannun nashi
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣2⃣
*assalamu alaikum warahmatullah,zuwa ga masoyan ABADAN,kamar yadda aka saba 😄 duk lokacin da littafi ke tafiya readers kanyi qorafi kan wani abu da ya shafi jaruman cikin littafin,wannan karon ma hakan ta faru,abinda nakeso ku sani shine bangaren rayuwar maryama true life story ne banbanci shine ita wadda abun ya faru a kanta kishiyar uwa ce ta mata hakan ba kishiyar suruka ba,hakanan na samu saqo daga gurin daya daga cikin makaranta ita kuma bangaren abdallah ne ta sani a gaske ya faru da wani da ta sani,kada ku manta babu yadda Allah baya iya jarrabtar bayinsa,gwargwadon imaninka da Allah gwargwadon girman jarrabawarka,na yarda da addu'a fiye da zaton mai zato☝🏽don ta yimin rana ta bani kariyar da har a nade duniya babu wani abu daya isa yamin kwatankwacin abinda ta yimin,na gani a zahiri na gani a mafarki,a rayuwa babu dole a lokacin da ka roqa Allah ya baka a take,yana iya jinkirta maka gwargwadon yadda yaso,kuyi haquri kuci gaba da bin littafin a duk yadda yazo muku don mu samu cimma manufofi da alfanu da gaci da nake son kaiku,idan kuma abun na damunka 😂,a shawarce ka tara littafin har sai an wuce inda baka son ji sai ka ci gaba da karatunka hankali kwance,na gode matuqa da gaske don nasan duka qauna ce,nima ina qaunarku a duk inda kuke,MRS MUHAMMAD DINKU CE*👑
Ji yake tamkar ya kashe adnan,bai kuma jin ciwon lalurar data sameshi ba irin yau,saboda ya riga da yayi amanna dukkan wani abu da zaya samu bawa da sanin ubangijinsa,hakanan bazai jarrabceka ba tare da wata manufa da take alkhairi ce a tattare da kai
bai gaza ba ci gaba yayi da ambaton sunan Allah cike da neman agaji don yana jin cikin zuciya da gangar jikinsa matuqar wani abu ya faru da maryam mutuwa zaiyi
a gigice ta sake dawowa jikin abdallan ta maqale shi tana neman agaji ta cukuikuye jikinta ta dunqule guri guda,tsabar gigita ta mance da halin da abdallan yake ciki,cikin dariyar mugunta ya biyota,ya tsaua a gabansu dukkansu ya qare musu kallo kana yace
''kin daga hannu kin mare ni ga zatonki kin ci bulus?,bakisan dama na jima ina sha'awarki ba hanyar kawar da ita kawai nake nema?,sai gashi yau Allah ya ara min dama ta yaya zan yi sake ta kufcemin''
ya kalli abdallah da idanunshi suka kada suka koma jazur,dukkan wata jijiya ta kanshi ta gama fitowa rada rada
''hmmm,sarkin zuciya,ka qaraci quncin zuciyarka amma babu abinda zaka iya yau sai na cika buri na''ya sake yin kanta gadan gadan,ya miqa hannu da niyyar damqota
cikin qaraji da kuka mai quna tace
''kaji tsoron Allah,yana kallonka,yana kallin duka abinda kake aikatawa''
ga tarin mamakinta sai taga ya qyalqyale da dariya
''ki bari idan na kammala sai ki gaya min duk abinda kike son gayamin,amma a yanzu babu abinda nake ganewa kinji ko''
ya sake yunqura zai fincikota yayib da take sake lacewa jikin abdallah kamar zata koma cikinsa
cikin hikima ta ubangiji hannun sa bai qarasa kanta ba yaji saukar wani abu mai azaba a qeyarshi,ga mamakinsa ya juya don yaga wanda ya masa wannan aika aika,abdallah ne yana daga kwance yaji tamkar an kakkatse duk wani abu daya hana hannayenshi biyun motsi,cikin hikimar Allah ya bashi sa'ar janyo plate din tangaran da maryam ta zuba abinci dazu Allah ya sa mata mantuwa bata dauke shi ba,don bata barin kwano ko daya ba'a muhallinsa ba ko ba'a wanke ba
sai kuma ya juyo yayo kan abdallah,saidai ina tuni jini ya fara dibarsa ya sona tangal tangal,ganin gaka ya sa maryan saurin maida hijabinta,qofa taje ta bude ta dakin kana ta dawo ta dinga tura adnan da ragowar qarfinta tana hankadashi yana dawowa amma da yake jini yaci qarfin sa sai ta samu nasarar tunkudashi har qasan benan yana qoqarin biyota ta dawo benan a guje ta datse qofar falon kana ta shige bedroom din ma ta saka muqulli tana maida numfashi
babu abinda qirjinta yake sai dagawa sama da qasa kamar numfashinta zai dauke,har yazu tsoron bai saketa ba,ji take kamar adnan din zai dawo,hannu ta ga abdallah na dago mata da alamun ta taho,mafaka take nema ibda zata sanya kanta taji sanyi,inda zata sanya fuskarta tayi kuka,babu musa ta isa gadon cikin sassarfa ta hada jikinsa da nata,cusa kanta tayi cikin qirjinsa wani kuka ya qwace mata
shafa kanta kawai abdallah yake yana hadiyar zuciya,godiya yake ma Allah maras adadi da ya bashi damar tserar da mutuncin iyalinshi,maryam ta riga da ta zama jinin jikinshi,sukan qirjinshi kukanta yake,saidai babu bakin hanawan babu kuma cikakkiyar lafiyar rarrashi,a hankali ta dinga jin nutsuwarta na dawowa,ta dinga sauke ajiyar zuciya kadan kadan
hannun abdallah ta tuna taga yana motsi dazun,a hankali ta zagaya hannunta ta saman cikinsa ta laluba dayan hannun abdallahn,tafin hannunta ta zura cikin nasa ga mamakinta sai taji ya sanya yatsunsa cikin nata ya hade hannayan nasu gam,wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki
''alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus saalihaat''ta fada cikin zuciyarta tare da rufe idanunta,wani farinciki taji yana ratsata,atleast tasan cewa wani ci gaba ya fara samuwa game da lafiyar abdallahn
dukkaninsu a daren babu wanda ya iya runtsawa,zuciyoyinsu tamkar anyi gobara kada ma abdallah yaji labari,ita kam takan samu sassauci kadan duk yayin data motsa yatsunta dake cikin nasa wanda yaqi sakinsu taji nashi hannun ya motsa
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
zaune yake gabanta qasan carfet din dakin kansa nannade da farin bandeji,zahariyya na agefansa saman kujera nene na kusa da ita ta zubawa danan ido
''adnan,wanne irin mahaukacin yaro ne wai akau,sau nawa ina gaya maka ka fita hanyar yarinyar akwai lokaci ka bafi idan yazo sai kayi duk abinda kake buqata?,yanzun inda ta samu dama kasheka fa zatqyi?,baka lura da irkn yadda take mana wani irin kallo ne,dukkan zarginta ina mai tabbatar maka ita da abdallan a kanmy yake don babu bakin magana ne''
cikin fushi ya dago ya dubi nene
''to wai nene ke wanne mataki kika dauka yanzu,na rantse da Allah ba za'a zubar min da jini a banza ba''wani shu'umin murmushi ta saki
''ni yanzu duk wani mataki nawa nafison abdullahi ya wuce tukun shine babbar matsalarmu,yaron ne shegen taurin ran tsiya kamar kyankyaso.....amma yanzun bamu da nutsuwar da zamu tattauna wanna batu ku tashi kuje jibi zamu zauna,na kira malam na hayi yace baya nan sai jibi zan kira shi naji mataki na gaba,zan sanar da bintu abinda yarinyar tayi don bani da burin da ya wuce ta sata ta bar gidan saidai abun mamaki duk irin aikina bata kudina da nake taqi sallamarta hakanan ko ma samu sauqin tafiyar da aikin....''
itakam zahariyya ma kasa cewa komai tayi
''amma fa nene,naga hannun abdallah ya dawo aiki''ya fada yana kallon nene,da sauri zahariyya ta tashi zaune daga kashingidar da adazu tayi tana kallon fuskar nenen tana zazzare idanu
wani murmushin ta kuma saki tana girgiza qafa
''ko duka jikin abdallah ne ya dawo aiki wanna karon naci alwashin abdallah bazai qara sati guda araye ba,don nima......''
tilas suka katse maganar kowa ya watse sakamakon shigowar zubaida dakin
nenen ta bita da kallon mamaki don tayi zaton ciwon ABDALLAH zai sata a wani hali sai ta lura ma sam tunda ya fara cutar ko hanyar part din bata yi,hankalinta kwance kamar bata da wata damuwa da shi,hakan ba qaramin dadi ya yiwa nenen ba
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Su uku ne cikin bedroom din,hisham da abdallah sai maryam dake zaune kan ressing chair data janyota bakin gadon inda abdallah da hisham ke kai hisham na bawa abdallan kunun gyada bayan masa wanka da canza kaya da aka masa ckkin baqin t shirt da trouser da suka sake haska shi
farinciki ne fal zicjyar hisham sakamakon ci gaban motsa hannun da abdallah ke iyayi yanzun,yana bashi kunun suna hirar da maryam duk da nata bai wuce eh ko a'a,ba gwanar magana bace ama sanann bugu da qari kallon da abdallan keta tsareta da shi ke dada takura ta,wani kallo ya koya daga wayewar gari zuwa yanzun,duk wani motsinta na kan idanunshi,lafiyarta yakeson ji amma babu bakin tambaya
''kai man,irin wannan kallo haka ko na baku guri ne?''inji hisham yace da abdallah cikin zolaya,kallonshi kawai abdallan yayi ya saki murmushi,duk sai suka zuba masa ido don tunda ya fara ciwon wannna ne karon farko da suka ga murmushi kan fuskarshi
cikin dariya hisham yace
''kai mutumina,anya daren jiya ba soyayya aka sha ba kuwa?''kunya ta kama maryam ta duqar da kanta ,yayin da abdallah ya sake wani murmushin yana duban fiskar hisham bisa dukkan alamu akwai abinda yake son fada wanda ya kasa fada
''Allah ya baka lafiya abdallah''inji hisham yana dafa kafadanshi,ya dubi maryam
''me kikace dazu yana buqata?''
kanta na sunkuye tace
''shaving za'a masa,naga kanshi yayi suma da yawa''
ya dan duba agogonshi ''eh gaskiya ya kamata,bari na masa na kai ke sqi kiyi masa na fuskanshi''
''ai ban iya ba''
''eh,ya kamata ki koya madam,zan nuna miki,akwai meeting da zamu shigavda ma'aikatan kamfanin suger na abdallah,don ina tsammanin gwara kawai a rufe kamfanin har zuwa lokacin da zai samu alfiya,saboda barnar da ake cikin kamfanin tayi yawa''
''Allah ya taimaka'' ta ce bayan ta miqevta dauko masa kayan askin,ya kammala kana ya nuna mata yadda zata masa na fuskar ya musu sallama ya wuce ta bishi da godiya
gefanshi ta dawo ta zauna ta fara matso cream din,a hankali take shafa masa a gefe da gefan fuskarshi,idanunahi qyar cikin nata,nauyi takeji da kunyarsa duk lokacin da ya zuba mata idanunshi,a hankali ta janye qwayar idonta tana ci gaba da shafa masa din,ta kammala ta dauko shever ta fara masa askin,ajiyar zuciyan da ya saki ya sata saurin kallonshi cikin tsoro,cikin sassanyar muryarta tace
''ko na yanke ka?''murmushi ya mata ba tare da ya nuna alamun a'a ba,kusan sakanni uku sannan taci gaba,a hankali taji ya riqe hannun nata da take shaving di dashi,ta sake waiwayo ta kalleshi shima din ita yake kallo
ta langabe kai
''da zafi ko?,dama na ce masa ban iya ba.....''bata qarasa ba taji ta kan qirjinsa sakamkon janyota da yayi ya rungumeta tsam
dukan uku uku qirjinta ya shiga yi,tayi yunqurin tashi taji ya sake maidata,idanunshi a lumshe kamar yadda nata yake,dukkansu suna jin bugun zuciyar junansu da ta qara gudu fiyeda yada take bugawa,sannu a hankali taji kasala na kashe mata duk wata gaba ta jikinta,jikinta ta saki batasan yadda akayi bacci yayi awon gaba da ita kan qirjin nasa ba,shi din ma yanayin ya masa,ji yake amar ya tsaida lokaci don su dawwama a haka,tun yana jin saukar numfashinta har shima baccin yayi gaba da shi
🍃🍂🍃🍂🍃
kusan lokaci daya suka farka,da hanzarita ta miqe daga jikinsa don tunawa da cream da ta bar masa a fuska,idanunshi a lumshe yake kallonta,sai taga ya kai hannunshi gefan kunnenta ya ciro wani abu ya nuna mata,cream dinne da sauri ta dauki madubin dake hade set da shaver din ta haska,ai kuwa gashi nan ta kwaaheshi ya bata mata fuska ta dubeshi suka hada ido sai suka saki murmushi tare,dan towel din askin a janyo ta goge fuskarta ta matsa ta dauki shaver zata ci gaba da askin,dora hannunshi yayi saman nata hannun da sauri ta janye hannun nata saboda tsigar jikinta da taji ta tashi,ya karbe abun askin ta fuskanci me yake nufi don haka ta dinga haska masa yana askin da kansa,idan ya gaji ya tsaida hannun nashi ya huta tunda har yanzun ba wani qwari ne da shi ba
towel tasa mai mai kyau ta goge masa fuskan bayan ya gama,tana shirin miqewa taji ya riqo hannun nata ya sanya tafin hannunshi cikin natan ya matsa su sannna ya gyada kai ta fuskanci godiya yake mata,murmushi kawai ta saki ta sunkuyar da kanta kana ta zame hannun nata ta sauka daga kan gadon tana tattara kayayyakin da sukayi amfanin da su har yanzu idonshi a kanta yake,yanayinta kadai burgeshi yake,kominta anutse cike da tsafta tausayi da kulawa,ya maida idonsa ya lumshe bayan yaga fitarsa yana addu'ar Allah ya bashi damar da zai nuna mata nashi kalan halaccin koda bata sonshi
da uammain mubarak ya kawo wheelchair da hisham yace ya kamata a fara dora abdalla atleast zai dinga jin dadi idan an fita dashi daga bedroom zuwa parlour zuwa balcony din saman tunda ba zata iya saukowa da shi ba falon qasa,yaji dadi kuwa don alamu sun nuna afuskarshi,yawanci idan la'asar tayi aka dorashi zata yita shawagai da ahi daga parlou zuwa kitchen zuwa balcony din wani sa'ilin ma ya mata alaman su zauna cikin kitchen musamman idan tana girki,ganin zaman shiru suke yi yasa tana girkin tana bashi labaraimasu debe kewa,hakan kuwa na matuqar sa farinciki a zuciyarshi,don zata ga fuskarsa ta fadada sosai da murmushi alamun yana jin dadi
saidai kallon qurillar da abdallah ya koya tilas yasa take zama da hijabi,don ba qaramin kunya yake bata ba,ko ina yaso kalla kallonsa yake kanshi tsaye,da sun hada ido kuma ya wani lumshe ido ya basar kamar bashi ba,wani lokacin murmushi take cikin zuciyarta tace
''hali zanen dutse,babu abinda ke saiyawa dan adam halinshi,har yau halin abdallah na basarwa da waskewa na nan cikin jininshi''
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣3⃣
*_An karbo daga nana Aisha Allah ya qara yarda a gareta tace:naji manzan Allah S A W yana cewa ''ya Ubangiji duk wanda aka dora mishi wani shugabancin na al'umata,ya tsananta musu Allah ka tsananta masa shima,wanda aka dora mishi wani shugabanci na al'ummata ya tausasa ya sassauta musu Alla ka tausasa masa ka sassauta masa shima_*
Qarfe biyar da rabi ne na yammaci mai cike da ni'ima da dadi kasancewar ko kusa garin babu rana sai lullumin hadari da ya lullube sama,su biyu ne zaune cikin falon yana kan wheel chair tana kan kan kujera saidai suna facing juna ne
novel ne a hannunta take karanta mishi sannu sannu cikin daddadar muryarta,tunda ta kifa fuskarta alittafin data kare fuskarta da shi bata dago ba saboda nauyin da kunyar kallon da abdallahn yake mata,gashi hakanan yaqi yarda yau a saka mashi kaya complete,duk wanda hisham ya ciro sai ya wurgar shi daminshi suke,wando three quater ne ajikinshi da riga armless duk wata qirar jikinsa ta bayyana
A hankali yasa hannunshi ya riqe littafin yayi qasa da shi tavdago kanta suka hada idanu,ido daya ya kashe mata yana murmushi don ya fuskanci abinda ya sata qin sakewar,littafin ta sakar mishi ta dora fuskarta saman cinyarta cike da jin kunya,taba kanta taki yayi sai taqi dagowa,ya daga littafin ya dan buga mata kadana akanta tare da cusa mata shi.
A hankali ta dago da zummar dauke littafin taci gaba da kare fuskarta,rubutu ne baro baro a bangon littafin I LOVE U,wani feeling ta dinga ji tana sake maimaita rubutun tamkar yau ta fara ganin kalmar,a dan sace ta rage tsawon littafin idanunta suka fito,karaf suka hada idanu da abdallahn daya zubawa cover littafin ido,tayi azamar maida littafin saidai tuni ha riqe da hannunshi daya yana ci gaba da kallonta,ji tayi bazata iya hada qwayar idanunsu ba saita sauke qwayar idanun nata kan cinyarta tana kallon yatsun hannayenta.
Qarar bugun da akayiwa qofar dukkansu sai data basu tsoro,kusan a tare suka kalli qofan,mami ce ke shigowa a burkice idanunta a kansu, qaraso gabansu ta ja burki
''sannunku qananun 'yan ta'adda,wato har kisa kuka so yimin cikin gida na ko?,to wallahi baku isa ba matuqar kuka ci gaba da yunqurin taba lafiyar wani cikin gidan nan zan iya tattarku kubar min gida tunda dai ba naku bane,kada ku kiskura ku sake aikata wani abu mai kama da haka don ba gidan 'yan ta'adda bane nan''duk maganar da take kan maruam na duqe a qasa,yayin da abdallah ya zuba mata ido cikin qunar zuciya da tashin hankali,me ya sami maminshi haka?me ya canza masa mami?,mamin da bata qaunar taa ko sauyawa fuskarshi tayi,mami mai tattali da qaunar farincikinsa,mami dake qauqnr maryam ta dauketa tamkar diyarta ta cikinta
ta kalli maryam''kuma ki gaggauta zuwa ki nemi yafiyar nene da danan idan ba haka ba wallahi sai na wulaqantaki,idan banda ma ke butu ce shegiya mara mutunci daga zuwa ya duba lafiyar mijinki sai ki masa irin wann mummunar sakayyar,na baki nan da minti talatin kije ki basu haquri''ta juya zata fota suka hada ido da abdallqh,hara ra ta wurga masa saboda jin wani abu na son taba zuciyarta,sai kuma wani abu daga can daban ya taso ya danneshi
shiru ne ya ratsa falon bayan fitarta,dukkansu kansu na sunkuye zuciyoyinsu na saqa musu abubuwa mabanbanta,ganin ya kusa gota mibti talatin din da mami ta bata ya sanyata miqewa da sauri,hannunta taji an damqo,ta waiwayo sai taga abdallah ne,a hankali ya dao idonsa suka hada ido,da sauri ta kawar da kanta saboda tashin hankalin da ta gani cikin qwayar idanunshi basu musaltuwa,fararen qwayar idanunshi sun juye sun koma ja baya ga jijiyar kanshi da ke tashi,kai ya girgiza mata alamar ba zata je ba,itama kan ta girgiza kana ta dawo gabanshi ta durqusa tace
''kayi haquri ka bari inje din,umarnin mami nake qoqarin cikawa ba donsu zani ba,kada ka manta har yau mami na matsayin uwa ne a garemu kaga ya zama dole mu bi umarninta don gamawa da duniya lafiya indai ba ya sabawa addini ba''
shiru yayi ma wasu 'yan daqiqu kana ya daga mata yatsunshi guda biyar alamun minti biyar ya bata,guada kanta tayi sanan ra miqe ya bita da kallo har da fice
tana gab da shiga waitin falo inda anan qofofin bangaren nau yake ta hango adnan,muta ne uku ne zabga zabga baqaqe,cikin baqin kaya masu qirar samudawa biye da shi,kallo daya zaka musu ka tabbatar cewa babu masaukin imani cikin zuciyarsu,mamaki ya cikata duk da tasan cewa lokaci lokaci zaka ganahi da ire iren mutanen a matsayin abokanshi,sai ta kasa wucewa ta rakube har suka wuce,tazarar minti biyar ta bada tasan zywa lokacin sun shiga koma ina zasu ahiga sannn tabi bayansu,a qofar waiting parlour din suka kusa karo da mami wadda ke sanye da kayan aiki da alama asibiti zata fita taja da baya ta bata hanya,harara ta watsa mata mamin kana ta fice,girgiza kanta tayi kawai tabi ta da kallo,kallo daya zaka mata ga wanda ya santa yasan cewa ta canza,tsaftarta har yanzu tana nan saidai duka gayun nan babu shi,bata mantawa shekaran kiya doctor safara'u abokiyar aikin mamin ta kira maryam take tambayarta me yake damin mamin ne,kullum tazo office bata da aiki sai kuka,tambayar duniya kuma ba zara gaya maka abinda ke damunta ba,magana daya zata gaya maka shine babu komai
Ganin babu kowa cikin falon qasan ya sanyata nufar sama,tana atep din qarahe na matattakalar ta soma jiyo maganganu,tamkar an dasata agun ta kasa gaba ta kasa baya
''yace saidai mu mu qarasa aikinmu,dalili kenan da yasa nace ka nemo min su mugu,wanna karon zamuyi aikin qarshe kan abdullahi,jibi da daddare nake so ku kashemin abdullahi,kafin ranar zansan duk abinda zanyi na kori yarinyar daga gidan nan,idan kuma tayi taurin kan qin tafiya na baku dama ku hada harda ita....''
''haba nene haba nene,ya zaki ce a kasheta bayan kinsan qudirina akanta...''adnan ya katseta
''dakata min adnan,wanna karon bana son matsala kowacce iri ce,mata gasunan bila haddin,koda an kasheta da zarar ka samu 'ya'yan banki kana iya samun dubunta ka huta da su ko ka auresu,mubar wannan maganar''
bibbiyi ta dinga hada matattakalar benan tana saukowa,badon nutsawa da sukayi kan maganr ba da babu abinda zai sanyasu jin takun saukarta,saidai ina dukkansu hankalin yayi gaba,a inda ta bar abdallah ta tarar da shi,a hankali ya dago kai yana dubanta,gqnin irin birkicewar da tay ya zuba mata ido kamar mai tambayarta,cikin rawar jiki ta tura whewl chair din suka ahige brdroom ta maida muqulli ta rufesu,jikinta na rawa ta dauki wayarta,ta fara qoqarin neman numbers dib hisham saidai bata yi sa'a ba ta samesu a kashe,bakin gadon ta koma ta dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka,tana kallon abdallah na daga mata hannu saidai ta kasa ce masaa komai,tausayinsu su duka biyin ya lullubeta
Misalin goma na dare ta samu wayar tashi ta shiga,da sauri ta fita adakin ta canza daki don bata son abdallah yaji komai,shi,kansa da baisan meke faruwa ba hankalinshi a tashe yake tun dazun fuskarsa ta nuna,bata jira jin komai daga bakinsa ta fara fada masa abinda ke faruwa
innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake furtawa,tabbas zarginsa ya zama gaskiya
''ki saka nutsuwa afuskarki maruqm,kada ki sake ki nuna musu kiji wani abu,yanzun haka ina kaduna amma gobe qarfe biyar da rabi na asuba zan taho,insha Allahu duk inda goma na safe yake ko tara na iso kano,na miki alqawarin babu abinda zai sameku,a gobe zan fiddaku daga cikin gidan insha Allahu''
Yadda ta kwana tana sallah haka ya kwana akan whellchair yana kallonta,cikin jikinshi yake jin wani mummunan abu na tunkaro su,yanayin data shiga kadai ya isheshi amsa,sam yaqi yarda ma akwantar dashi,da safe saiga nenwn zahariyya harda danna wai sunzo duba abdallahn,yanayin fuskarta idan ka kalleta dik qwaqwarka ba zaka tsammaci gana cikin mummunan tashin hankali ba,ba qaramar jarumta ta nuna ba,haka suka qaraci kallonau suka fice maryam ta bisu da ido cike da mamakin qarfin hali irin nasu
mubarak ma da yazo sam qin yadda abdallah yaui ayi masa wanka,abincin ma da qyar ta samu yaci,ya fahimci manufarsa yana son jin abinda ke faruwa ne a ganinta kuma bai kamata yaji din yanzu ba
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
yana kan wheelchair din yatsunsa soke cikin na juna yana kallon su
tsaf hisham ya gama hada duka wani atm card takardun companies filaye gidan gonaki da na duk wani estate da plaza na abdallan ya sanya cikin wata jaka baqa ua zuge zif din,maryam yasa ta ciro babban bargunan dake ninke gefe daya kan gadon,ya jera dukkan filallukan dake kan gadob ya lullubesu da bargon take suka tashi kamar mutum kana ya qarasa inda abdallah yake da niyyar sauko da shi daga kan wheel chair din
qememe abdallah yaqi yarda ya sauko da shi din,idanunahi sun kada sun koma tamkar gauta saboda tsananin fushi da masifa,jijiyoyin kanshi dana wuyanshi sin fito rada rada,ua fahimci abinda abdallan ke nufi saidai bazaiyiwu suyi masa abinda yake so ba,a tausaahe ya dubeshi
''abdallah na sani sarai tun ba yau ba kai din jarumin namiji ne ba rago ba,kaga abubuwan masu hadarin gasje ka shiga wasu da dama daga cikinsu,amma a yanzun abdallah bazai yiwu mubarka ba rayuwarka na cikin hadari,da ace yau lafiya qalau kake abdallah bazqn maka ahishshigo ba saisai na taya ka da ddu'a ko kima idan ka buqaci taimakona,nayi imanin da lafiyarka qalau ka fini experience na yadda zakqyi aolving case din,amma ayanzun haquri zakayi abdqllah dole kana buqatar taimako''
A nutse kuma ahankali ta tako gabanshi ta taugunna,hannunta ta sanya cikin tafin hannunshi ta mannesu tare hisham na gefe yana kallonsu,lumshe idonsa yayi,kimanin minti goma suna a haka sanna tace cikin tattausan muryarta
''kabi hisham mu fita daga gidan nan abdallah,ni maminka hisham dama qasarka baki daya duka muna buqatar rayuwarka,bama so mu tasa ka bamason muyi asararka abdallah don Allah''
cikin jikinshi babu inda maganarta bata shiga ta tsinka masa jijiya ba,ina ma ace zaya iya hude baki yayi magana,da banu shakka zai tambayeta ne daga zuciyarta kalaman suka fito ko ko iya labbanta ne,koma dai yaya ne ta sanya zuciyarsa cikin wani kundi mai wuyar karantawa lokaci guda,bai taba jin kalamai makamanta wadannan daga bakinta sai a wannan karon,a nutse hisham ya sauke abdallah daga kujerar ua ahimfidar da shi cikin bargon har a lokacin idanunshi na kan maryam dake tsaye tana kallonsu cikin raunin zuciya,yana shirin nanndeahi ya kanye idanunshi daga kanta ya maida kan hisham,alama yayi masa da maryam,ya fuskanci me yake nufi duk da yanayin da suke ciki sai da murmushi ya subucewa hisham din.
''ka kwantar da hankainka ba'a gidan zamu barta ba itama zata fice amma ba lokaci daya tare da mu ba don kada afuskanci me muke ciki alright?''kai ya gyada masa sanan ya lumshe idanunahi kamar mai bacci
tsaf ya gama nade abdallan kamqr kayan wanki cikin bargon,qofar shan numfaahi kawai ya bar miahi,yana nishi da qyar ya saba shi kan kafadarshi
maryam ce ta fara yin gaba,ta fita tana dube dube kamar mai neman wani abu,saida ta tabbata babu idon kowa sannata dawo ta yiwa hisham magana,ya qaraso bakin motarahi ya bude gidan baya ya shimfidar da Abdallah ya rufe cikin sassarfa ya zagayo
''mintina hamsin sun isa naje gida na dawo,kafin cikar minti hamsin din ki fita kamar zaki wani abu ne awaje ki dawo ki sameni a bakin titi sai na daukeki mu wuce''cikin gamauwa ta gyada masa kai,ta juya da sauri ta koma bqngqren naau shi kuma ya tada motar cikin sauri,mai gadi ya dage masa get ya wuce
qurar motar nene kawai ta gani ta iso gin tana tambayarsu wanda ya fita daga gidan,daya dagq cikin security din daya fusu jin hausa yace
''abokin oga ne,oga hisham''tayi qaramin mirmushi hadi da cije lebanta,cikin salon mugunta kana ta hade ranta
''dagq yau kada ku sake barinshi ya shigo cikin gidan nan,duk wanda ya kuma kuskura ya barshi ya sake shigowa to ya tabbatar ranar a bakin aikinshi''
cike da biyayya suka qameta tare da cewa''yes madam''
bedroom din nasu ta koma ta tattara 'yan qananun abubuwan da tasan zasu mata amfani ta dauki 'yar jaka qarama ta zuba aciki,ta koma kan sofa ta zauna lokaci lokaci tana duba agogo,cikar mintina arba'in da biyar da fitarsu kenan don haka ta miqe ta rurrufe duka dakunan baccin da saman ma baki daya ta fito zuwa harabar gidan
A nutse tazo fitar tata bata samu wata matsala ba don sukkansu sun ruga da sun san wace ita cikin gidan tana sake taku na fita daga gidan zuciyarta na kuma bugawa,sai data tqbbatar ya fice daga gidan baki daya kana ta qara wani irin saurin kamar zata tashi sama,ji take kamar za'ace da ita ke dawo,ajiyar zuciya ta saki da taga motar hisham na jiranta,ba bata lokaci ta hude ta fada kana ta maida murfin ta rufe,idanunta na rufe suka hau kan titi kana ta saki wata ajiyar zuciya,hawaye ne ya balle mata ta kalli hisham
''amma hisham mami fa?''
kanshi ya girgiza
''sun san sun gama da mami,bata da ikon hanasu komai sai abunda suka shomfida,babu wani abu da zasu iya yi mata,addu'a zamu bita da ahi kafin mu samu nutsuwa mu zauna mu samar da mafita,don tabbas akwai abinda ke faruwa,na tabbatar mummunan qulli ne a binne a qasa wanda bamusan inda yake ba sai Allah''
Cikin nishadi nene ta sake dawowa bakin get din zuciyarta na sake kururta mata ita mai nasarq ce,korar hisham da maryam daga rayuwar abdallah cikin lokacin da take qoqarin kau da shi ba qaramar nasara bace don a idonta maryam ta fita,sake tambayarsu tayi don tabbatarwa suka amsa musu eh itace
''goo,itama bana son ta sake shigowa cikin gidan nan ko ita ko wani nata har abada''kallon juma suka shiga yi don dukkansu sunsan wace maryam cikin gian sun san matsayinta,ganin suna son saka tantama cimin ranau yasa ta daka musu tsawa
''ko baku jina ne,wallahi zan iya yiwa mutim kowanne irin hikunci matiqar ya saba umarni na,kubar ganinku garada''ta musu wani kallo na izgili,da sauri suka amsa suna bata haquri,juya watayi tana fadin Allah yasa daya daga cikinsu ya sabawa umarnin ta
sai da ta dubi bangaren abdallah ta qyaqyace da dariya
''Allah ya jiqanka abdallah,taka kuma ta qare,wataqila kafin gove azo gamawa da kai yunwa da qiahirwa sun zama ajalinka''ta wuce sashenta tqna wani irin taku cike da nishadi da jiyo qamshin nasara
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣4⃣
*_An karbo daga abu hurairah R A yace:Manzan Allah S A W yace:babu wata rana da gari zai waye face sai mala'iku biyu sun sauko,sai daya daga cikinsu biyun yace ''YA UBANGIJI KA BAWA WANDA YAKE CIYAR DA DUKIYAR SA NINKIN ABINDA YAKE DA SHI'',dayan kuma sai yace''YA UBANGIJI KA BAWA WANDA YAKE QIN CIYAR DA DUKIYARSA ASARA A CIKIN DUKIYAR (WANDA YAKE ROWA BAYA CIYAR DA ITA GA MABUQATA DA MASU NEMAN TAIMAKO)_*
🕋🕋🕋
*ina taya daukacin al'ummar musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci,dukkan wani alkhairi na duniya da lahira dake cikin shekarar ka hadamu da shi,ka kare mu da dukkan wani musulmi da sharrin dake cikinta,ka bamu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali da yalwar arziqi ameen*
Daf da zata qarasa bangaren nasu tana ci gaba da babaka dariyarta suka ci karo da baaba uwani,wata uwar tsawa ta daka mata
''ina zaki je uwar kinibibi?''
jikin baaba uwani na rawa tace
''ah....ummm...zani mi gaisa da hajiya ne?''
tsatstsareta nene tayi da idanu
''me nace dake tsohuwar banza?''
''ahh...kince....kince ne kada ki sake ganina bangaren ku indai ba inaso ma rasa aiki na ba'' gyara tsaiwarta tayi
''kin shirya rasa aikin naki kenan?''
girgiza kai ta shiga yi
''a'ah,don Allah hajiya nene kiyimin afuwa''
''kinsan me nakeao dake?,matuqar bakison rasa aikinki cikin gidan nan kada na sake ganin qafarki a harabar gidan nan,daga yau ziwa gobe jibi ke har gata ma,kina jina ko?''
da sauri take gyada kanta ,kana ta bata umarnin ta koma inda ta fito
hawaye ne kawai ke zuba daga idon nene tana sharewa,idan banda darajar mami da take tausayawa babu abinda zai zaunar da ita a gidan,abubuwa marasa dadi da idanunta ke gane mata wanda ke faruwa shine ummul aba'isin zamanta cikin gidan badon wani abu ba
🍂🍃🍂🍃🍂
babu wanda ya sake cewa komai har suka qarasa gidan hisham din,gida ne madaidai ci mai kyau wanda ke dauke da makeken falo kitchen dining area sai dakunan bacci guda hudu
A falo suka tadda abdallah kan kujera,gwiwarta a sanyaye ta qarasa gurinshi kanshi na duqe a qasa,a gabanshi ta durqusa ta sanya hannunta cikin nashi tana kallonshi,sam yaqi daga idanunahi ya kalleta,hakan na nuna mata cikin tsananin bacin rai yake,ta leqa fuskanahi idanunahi biyu don tana iya ganin qiftawar idanunshi,sai zuciyarta ta karya ta tura kanta tsakanin cinyoyinsa da fuskarsa sai a sannan suka hada idanu,ya zuba matq idanun naahi da suke har yanzu kalar ja
shigowar hisham falon ya sata miqewa,ya taimaka suka shiga da abdallah daya cikin dakunan dake falon,dakine mayalwaci mai hade da toilet,gado madubi side bed sai cupboard da kujera doguwa qwaya daya da carfet da ya malale qasan dakin da shi a maimakon tiles
''zan fita amma bazan jima ba zan dawo''
ya qarasa gaban abdallah yace
''abokin sai na dawo mintina kadan zan dawo''kai kawai ya gyada masa ya miqa masa hannunshi sukayi musabaha
🌲🎄🌲🎄🌲🎄
Qarfe goma na daren ranar suka fito daga maboyar da nene tayi musu cikin dakunan barcinta,gaba dayansu baqaqen kaya ne ajikinsu hatta da mask din da suka sanya,kowannensu wuqa ce boye a jikinsa
taku daya biyu nene tayi ta tsaya a gabansu,dukkansu sun fita tsawo nesa ba kusa ba,ta dubesu daya bayan daya
''banason a samu kuskure ko sabani cikin aikin nan,shekaru na kwashe masu yawa ina neman wannan damar,saboda haka ku tabbatar komai ya tafi yadda ake so''
dqya daga cikinsu wanda da alama shine oga ya buda hanci ya shaqi iska
''haj,sanin kanki ne munsan aikin mu dalilin da yasa kema kika neme mu kenan''
gyada kai tayi
''haka ne kam''
da daya da daya suka dinga fita har suka isa sashen abdallah,jijjiga qofan suka yi suka jita gam hakan ne ya tabbatar musu a kulle take,don haka kansu tsaye ba tare da wani tsoro ko shayi ba tunda sun san cewa babu security ko daya cikin gidan bare su jisu duka nenen ta bawa kowa aikin da har su gama abinda zasuyin ba zasu riskesu ba,take suka hau lallauya qofan da wani shegen qarfe suka ajjiyeta saahe guda kana suka kutsa ciki
Sau uku yama luma wuqa kan tarin filallukan dake tare a kan gadon ganin qamas babu alamun jini ya sanya su yaye bargon,a mamakance suka kalli juna kana daya daga cikinsu ya ciro waya ya kira nene,da zumudinta ta daga kiran ga tsammaninta sun cika aikinsu
cikin mamaki da fushi take fadin
''wanne irin babu kowa?kada ku gauamin maganar banza mana,yaron da ko motai bai iyayi ina zaije?,kuma tun jiya babu kowa a tare da shi balle ace ya fidda shi?''
cikin ciccijewa ya maida mata amsa
''kinga hajiya duk ke kika san wannan,kizo kawai idonki ya gane miki''
da azama tq fito ita da zahariyya da danan suka bazamo bangaren abdallan,surutai take tayi kamar wadda ta samu matsala a qwaqwalwarta don bata taba sawa cikin lissafinta cewa wannan karon akwai cikas din da zasu samu ba
cirko cirko sukayi cikin dakin bayan kammala duba ko ina na cikin gidan ciki har uwar dakin mami wadda batasan me ake nema ba,ta dai ga nenwn kai tsaye ta ahige mata daki tana dube dube daga bisani ta fito
''taya ya abdallah ya fita daga cikin gidan nan''
''ke za'a tambaya hajiya''cewar ogansu yana maida locker da tasa ya balle ta dakin abdallan wadda basuyi katarin samun komai ba sai rafar din dubu hamsin
''miqo min wadan nan kudaden,yanzu hatta da takardun kadarorinsa ma ace babu su cikin dakin nan,anya wani baisan abinda muka shirya ba kuwa cikin gidan nan,anya banu mai,mana labe da leqen asiri?''ta fada tana zare ido kamar wata zautacciya
kudin ya kalla kana ya dubeta
''ban fajimci me kike fada ba,wannna kidi ai namu ne ladan zaunar damy da kika yi nuka kwana cikin gidanki,ai lissafi zamuyi kawai ki cika mana sauran miliyan dayan da mukayi da ke zaki cika mana''
''idan aiki yayi kyau ba,ana ta kai wa yake ta kaya,kwananku kuma cikin gida na ai ku kuka qaru da ni bani na qaru da ku ba asara ce ma ta hauni goma da goma,tunda har 'yata na baka ta tayaka kwana ko?baya ga haka ma ni a yanzu bani da miliyan daya bani da dalilinta,da aiki yayi kyau ne ma na tabbata cikin dukiyar da zamu samu ba komai bane cire miliyan daya daga ciki ''ta fada tana matsowa gabansa tare da zazzare idanuwa,don ji take su suka ma ja mata duk wata asara da ta fada matan
Dariya ya sheqe da ita
''haba hajiya,kinci qarya kin kwana da yunwa,muba qananan makasa bane ba irinnu akewa haka ba''ya sake matsowa inda take har tana jin warin wiwinshi na dukan hancinta,yatsunshi ya daga guda uku
''kwana uku kacal na baki ki turo mana ragowar kudinmu,wlh wlh wlh ko ke kikayo naqudata matuqar baki turo da sauran kudin nan ba ke da 'ya'yanki ki tabbatar kuna cikin masifa,domin duk ranar dana waiwayeku sai kun buraci mutuwarku akan rayuwarku,na baku dama ku gaggauta warware harqallar da kuka qulla dani''
ya juya zai wuce adnan yasha gabansa cike da taurin kai da jin shima karansa ya kai tsaiko yana ciccije lebe cikin son nuna shima jan wuya nebayan shi kansa yasan fanko ne lamba daya,kafin yace komai yasa kan wuqar hannunshi ya daki kanshi saiga adnan din a qasa,ihu nene ta saka tayo kansu,da tsinin wuqar ya juna ta ta koma baya tayi luf sai da suka kammala ficewa ta saka kururuwa ta biyo bayansu ko Allah zaisa taci sa'a wani daga cikin security din sun dawo suyi ram da su,saidai ina,babu wanda ta samu bakin get din kamar yadda ta watsa su don gabatar da aikinta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
ta kai ta kawo tayi hakan ya kusa sau goma sha biyar,ji take kamar zata hau bori ko hauka kafin ta samu guri ta iya tsugunnawa,ta dubi adnan da kanshi yasha dauri da bandeji da zaharkyya wadda ke zaune tana faman hade fuska,babu wanda take ganin laifi sama da nene,don ita kam ta gaji da wanna jeka ka dawo din,ta riga da ta yanke ma kanta hukuncin abinda zata aikata matuqar wannan karon haqarsu bata cimma ruwa ba kamar sauran lokutan baya
''babu shakka cikin hisham da maryam akwai wanda ya fidda abdallah daga cikin gidan nan,ko kuma daya daga cikinsun ya aikata hakan,kuma nafi zargin wanna shaidaniyar ce marya,tabbas kuwa''ta fada tana guada kai hadesake tabbatarwa kanta
''qwarai kuwa nene,nima na zargi haka tunda kinga fitarsu ana gobe za'a gudanar da aikin,cikinsu akwai wanda yake da hannu kan tsirar abdallah''inji zahariyya,shikam adnan ya kasa magana ta kanahi yake,tsanin ciwo yake masa kamar zai tsage gida biyu har
zumbur nene ta miqe tana fadin
''wallahi basu isa ba dukkansu,duk wanda yaci tuwo da ni miya yasha''
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Tana cikin kitchen tana qoqarin hada masu abincin rana ta jiyo hisham na qwalla mata kira,cike da mamaki ta ajjiye abinda take yi din ta fito don bata taba jin ya mata makamancin irin wanna kiran ba
tashin hankali ta gano qarara cikin idanunshi
''dauko duk abinda kika san kina da buqata ki sameni a mota na riga da na kai andallah ciki,babu lokacin bayani na miki shi a hanya''
bata tsaya tambayar ba kuwa,ta koma kitchen din a gurguje ta kashe gas din ta ahiga dakinsu da suka sauka ta dauki iya abinda take jin zata iya buqata ta fito ta taddasu cikin mota
Tafiya yayi ta kusan mintina hamsin har suka fara barin ainihin qwaryar birnin kano sanna yayi parking a nutse ya dubeta
''maryam,na samu bayanan sirri daga daya daha cikin security din gidansu abdallah wanda nake biyanshi bayan barinmu yake samin ido kan duk wani motsi da yanayi da gidan ke ciki,don na tsammaci dama lallai wani abu na iya faruwa kan barinmu gidan da abdallah da mukaui,hasashena kuwa ya tabbata ya zama gaske iya,suna na ne ma farko cikin jerin mutanen da nene ke tuhuma,don ta saka amata bincike kan inda nake,yanzu haka mutanen na kan hanyarsu ta zuwa gidana,dalilin barowarmu gidan kenan''
kuka ne ya qwacewa maruam,wannan wace iriyar mace ce nene?me ta dauki rayuwar duniya,baza'a mutu ba?dawwama kowa zaiyi yana abinda yaga dama?,me take nema ne cikin duniyar da dukkanta bata kai qima da darajar fika fikin sauro ba agun Allah,wanne jin dadi ne a ginta ta kashe ran mumini wanda qimatsa tafi ka'aba agun Allah?,tana tsammanin idan ta aikata hakan taci bulus ne ko kuwa,zata taira daga hisabi da zabar Allah ne?dukkan amsar itace a'ah,babu
''a halin da muke ciki maryam kuka babu amfanin da zai mana,ki tsaida kukan mu nemi mafita''
tabbas maganar hisham haka take,ba bata lokaci ta ciro wayarta ta sake kiran mama wadda basu yi awa biyu da yin waya ba,magan sukayi ta kimanin minti talatin da ita kana ta kashe wayar ta dubi hisham kasancewar handsfree ta saka yaji komai
kansa ya gyada
''maganar mama gaskiya ce,kuma tsarin nata yayi,nima da mun isa gobe zan wuce katsina hometown namu''ya fada yana mai gamsuwa da bayanin maman yana kuma sawa motar key,ta juya ta sake kallon abdallah har yanzu idanunshi a lumshe yake,babu baki balle ya bayyana abinda ke cin ransa,ta tabbata ba magana daya ke dawainiya da zuciyar abdallah ba,suna da dama,koda bao jude idonsa ba,koda baiyi,magana ba tana ki a jikinta zuciyar abdallan a quntace take,takan tashi kokawa afili da boye duk da shi din tsananin jarumtarsa bai taba barinta taga hawayensa ba
Da taimakon bayanin da mama ke masu a waya suka kai ga isa qauyen NI'IMA dake cikin qauyen gaya,tun daga shigowarka garin zaka bawa kanka amsa,tabbas qauyen yaci sunanshi ni'ima,qauye ne da Allah ya wadata su da yawaitar korayen shuke shuke qoramu dabbobi da lullumi ma'ana rashin haske da zafin rana
duk da haka sai da sukayi tambaya kafin su kai ga isa ainihin gidan da suke nema,gaya garin kakanninta ne tana zuwa lokaci bayan lokaci saidai qauyen ni'ima din zata iya irga iya adadin zuwanta tunda bata da wani shaqiqin da zata zo gunsa face wannan tsoho qwaya daya da yake qanin kakanta
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[6:27pm, 9/22/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣5⃣
*_Mazan Allah S A W yace:ku umarci 'ya'yanku da yin sallah suna da shekaru bakwai,sannan ku dakesu saboda ita idan suka kai shekaru goma,kuma ku rarraba musu gurin kwanciya(ma'ana ya zama gurin kwanan maza daban gurin kwanan matan daban yayin da suka cika shekaru goma)_*
Gida ne ginin qasa kamar yadda yake kasancewa ginin gidajen qauyuka,saidai wannan ya dan banbanta da nasu damin uasha shafe da ruwan makuba,hakanan ginin sumul sumul yake sakamakon fulastar kar qasa da aka yi masa da kuma makubar da akabi aka shafe ginin da ita.
Maryam ce ta fara shiga,kamar yadda muka sani yan uwanmu na karkara basa gini quntatacce hakan ce ta kasance ga wannan gida,babban tsakar gida ne mai girma wanda babu sumunti a qasan sa,turbaya ce saidai ta sha shara fes da ita,ga alamun shatin tsintsoya ne,daga can quryar katangar gidan garkene na dabbobi dake a tsaftace shima,sai rijiya daura da shi wanda lema ce duk a bakinta da tukwanen qasa da aka kikkife da alamu wanke wanke aka gama agun babu jimawa.
ta sake yin sallama kin shiru ba'a amsa ba karo na uku,cikin daya daga dakuna hudin dake jere taji muryar matashiya na amsa mata,ta fito sanye da roga da zani na atamfa wadan da suka danyi haske saboda dan jimawar da sukayi a duniya,maryam ta duba itama ta kalleta
''don Allah inna wuro fa?''maryam ta tambaha,sai ta juya ta kalli dakin kana ta kalli maryam
''tana ciki salla take amma yanzu zata....'''
''wake sallama ne mero,a shigo mana''
muryar inna wuro ta katsesu
''inna wuro baqi kikayi''
''kaddai ace su meramu ne har sun iso haka da wuri''ta fada tana yunqurin fitowa,kasancewar ta san zasu zo din mama ta kirata awaya ta mata bayanin zasu zo din ta wayar mustafa jikan gidan.
hannunta dauke da tabarmar kaba sabuwa dal ta fito,dattijuwa ce wadda aqiyasce zata doshi shekaru sittin,tsaf da ita cikin cikin atamfar itama da hijabi ruwan madara,fuskarta ta fadada da fara'ar ganin maryam din
''to kuma ya na ganki ke daya''itama murmushin ne afuskarta
''inna suna qofar gida''
''to yi maza kice musu su shigo daga ciki mana''ta fada yayin da take shimfida tabarmar.
Tare suka shigo hisham na tura abdallah kan wheelchair
''hukumullahu min zalika,Allah mai yadda yaso da bayinshi''inna wuro ta fada tama kallonsu
''sannu dam nan sannu''ta qara fada tana kuma gyarq musu gun zama
matashiyar da inna wuro ta kira da mero dazu ta qaraso dauke da kwanonsha cike da ruwan tulu mai sanyi fari tas ta ajjiye gabansu,kanq ta ja hijabinta daga kan igiya tana fadin
''inna zanje gida,idan na dawo r
yau to,idan kika ga ban dawo ba kuma sai gobe''
''to mero na gode Allah ya huta gajiya,ki gaida su azimin''
Bayan gaishe gaishe shiru,ne ya biyo baya inna tana kallon ikon Allah
''yanzu mairamu tun yaushe lalurar ta sameshi?''a nutse tayi mata bayani,kamq bqki innan tayi
''matsalar ku kenan mitanen binni,boko tasa baku da kulawa sam,ni kam ba wai zato ba amma wanna lalura ta yaron nan batayi kama da komai ba face sihiri,kuma kinsani sarai qanin kakanki masani ne kan irin wannna matsaloli baki tuntiba ba,yanzu ma zuwa kukayi kenan idan qura ta lafa ku koma ba neman magani ya kawoku ba''
hisham ya guara zqma jin hanyar waraka na shirin samuwa
''a'a inna,har maganin ma mun zo mu nemeshi''
shiru tayi ma wasu 'yan mintina kana tace
''to Allah yasa adace,insha Allahu Allah zai kawo qarshen abun nan kusa''
maryam ta dubi inna wuron
''ina tsoho alhajin ne?''
''kinsan watan tafiya gabas ne,bana Allah ya kirashi yana can qasa mai tsarki,ina tsammanin yau duka kwananahi uku da tafiya,amma muna sa ran nan da sati uku zuwa hudu zasu dawo insha Allahu''
''Allah ya dawo da ahi lafiya''suka hada baki ita da hisham wajen fada
''daya dawo insha Allahu zan masa bayanin komai,idan rabo sai kuga ya warke''
''Allah yasa''inji hisham cike da fata.
In banda sannu babu abinda inna wuro kema abdallah,gaba daya tausayinshi ke damunta,irin wanna lalura mai fama da ita kadai yasan yanayin da yake ciki,da kanta ta bude musu wani daki can bangare daya,ba laifi dakin akwai girma,malale take da leda duk da cewa ba sabuwa bace,akwai labulaye a window da qofar,sai tsohuwar katifa da kujera qwaya daya,a ahare dakin yake fes kasancewar inna wuron bata lamuntar qazanta
hisham ya qarewa dakin kallo kana ya girgiza kai
''rayuwa mai juyi kuyi,Allah mai yadda yaso''ta karanci me yake nufi,tabbas ita kanta ta sani abdallah dan gata dan gayu,young millonier yafi qarcin zama cikin qauye ma baki daya ba dakin ba.
maganar hisham ta katse mata zancan zucin da takeyi
''abdallaj bazai iya zama cikin dakin nan haka ba maryam,zan ahiga na laluba inda zan samu kayqn buqata da za'a ma dakin kwaskwarima''kai ta jonjina babu bata lokaci ya fice,ta kalli abdallah suka hada ido uana mata nacin kallon nan nashi
''bari naje nayi alwala nayi sallaar la'asar,idan na dawo sai in maka alwala kayi taka sallar''ta fada kanta aduqe sabida naugin idanunshi da take ji
kai ya jinjina mata kana itama ta fice.
Sai bayan sallar magariba sanna hisham ya dawo niqi niqi da kaya cikin akori kura,cikin mintina qalilan da taimakon yaran maqota da kuma taimakon mustafa aka gama ahigowa da komai,kayan daki ne da suka hada da katifa labulaye kujeru cusion guda biyu fanka ta tsaye carfet mai girma da zai iyacinye dakin,robobin wanka food falask har da risho dan madaidaici da set na tukwane,kayan sawa nashi da na maryam akwati wadda zata iya cinye musu kayan,duk dai wani kayan amfani da zasu iya buqata,hatta da kayan abinci ruwan roba da lemuka creet na qwai da sauransu
ba inna wuro ba hatta maryam ta jiniina siyayyar,sai da ya niqi tafiya har cikin jigawa sannan ya jado siyayyar,tunda su sinyi tsaki,yasunyo nisa da cikin birnin kano kuma basu qarasa jigawar ba.
A daren mustafa ya taimaka masa ya shimfida carfet da kujeru da katifa suka shimfida sabon zanin gadon cikin dakin hisham ya kwana tare da abdallah ita kuma ta kwana tare da inna wuro
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
zuwa goma na safe dakin ya zama gwanin sha'awa tamkar ba shi ba,sha daya na rana sai ga mutane daga company mtn sunzo hada solar,da mamaki maryam ta dubi hisham
''hidimar nan tayi yawa hisham,sai kace zamu dawwama ne a garin?''
murmushi yayi kana ya girgiza kai
''maryam kenan,baki san waye abdallah ba aguna,abdallah shine tsani na dukka wata rayuwa ko matsay da na take ko nake kan takawa a yanzun,ba don Abdallah ba ina zaton da tuni na jima gidan mahaukata,abinda abdallah ya yimin bazan iya biyanshi ba,ya taimakamin da jikinsa da aljihunsa da lokacinsa ta qwaqwalwarsa ma baki daya,Allah ne kadai zai iya biyanshi abinda yayimin a rayuwa,babu abinda bazan iya bawa abdallah ba,wannan abun da nake masa ban masa kaso daya cikin darin abinda ya yimin ba,abdallah dan halak ne dole nima na nuna masa halacci''
kallo daya ta masa ta tabbatar daga qasan zuciyarsa abinda yake fita bawai daga fatar baki ba
cikin qasa da awa uku suka kammala wearing din baki daya aka kunnata ta fara zuqar chargy,sai gidan ya zama abin kallo,al'ajabin yadda za'a samu hasken qwan lantarki daga hasken rana sukeyi har hakan yaso bawa hisham da maryam dariya,musamman yadda mero da inna wuro suka ce su kuwa zasu ga ikon Allah.
Qarfe biyar sukayi sallama da hisham ya wuce katsina,kafin nan sai da ya danqa mata duk wasu takardu na abdallah da ya debo,qememe taqi karba tace sam,shi yafi cancanta ya riqesu a hannunsa
atm,card ya bata shima da fari cewa tayi bazata karba ba don basu buqatar komai,yace a'a,kowanne lokaci buqata na iya kamasu,ta karba din don ya riga da ya kouawa mustafa yadda ake cirk kudin ta wani atm machine da suka gani cikin garin gaya,idan tana da buqata ta bashi ya ciro musu
''saidai akwai magana daya,maryam gwamnati na fara matsantawa da hutun da mukace abdallah ya dauka ne,sabida akwai cases manya da ya fara aiwatarwa kafin cutar nan ta sameshi,so na rasa me zan ce da su,don ina magana da su ne amatsayin abdallah''
shiru tayi na dan qanqanin lokaci
''yanzu idan ka nemi alfaramar qarin watanni bitu zasu qara din?''
''eh...don sunce na fadi iya kwanakin sa,zai dawo ba tare da ya sake dagawa ba,don qasa na da buqatarsa''
''to shikenan ka fada musu watannin biyun,kafin nan muga yadda Allah zaiyi''
''Allah ya iya mana,ya bashi lafiya cikin sauri''
''ameen''inji maryam,ta rakashi ya yiwa inna wuro sallama cike da kewa ya tafi don a zamansa na kwama dayan har sun soma sabo
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
firgigit ta farka daga baccin da ya dauketa kan abun sallah,da sauri ga leqa fuskan abdallah dake baccinshi ta tabbata lafiyanshi lau,komawa tayi ta jingina da bangon dakin tana share zufa tare da tuno mafarkin da tayi,tabbas Allah ne ke mata ishara,sam kamar wadda aka dakawa gudumar mantuwa ta mance da mafi yawa daga cikin addu'o'inta,ta waiwaya ahankali ta kunna wayarta ta kawo haske,qarfe uku,na dare agogon ya nuna mata,ba zata iya fita alokacin ta daura alwala ba din haka ta janyo carbinta taci gaba da ja tana ambaton Allah lokaci lokaci tana leqa abdallah
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Tana bakin murhun tana dama musu kunun duk da hanatan da inna wuron tayi qoqarin yi amma ta qiya,don tsakanin kwana ukun da sukayi cikin gidan indai ta kunna risho to abdallah zata dafawa wani abu,ta riga ta saba don rayuwar gidan sun data tashi cikinta marabarta kadan ce da wannan
Mero ce tayi sallama ta shigo gidan,ta dubi maryam tace
''takwara ina kwana''ta waiwayo fuskarta dauke da 'yar fara'a ta amsa mata
''a'ah,mero,yanzu kuma sammako zuwa min aka koya kenan,kodon,kinga kin samu abokiyar hira ne?''inji inna wuro dake fitowa daga daki
dariya tayi
''wallahi kuwa inna,na samu larabawa abokan hira''haka take kiransu maryam sabida farin da suke da shi,duk da itama din farar bafulatana ce saidai nata farin baikai nasun ba
Ta shiga dakin inna wuro da suke zaune da mero,suna hira suna cin gyada marau marau,gefansu ta samu ta zauna kana tace da inna
''inna don Allah ina zan samu ganyan magarya?''
''ganyan magarya me zakiyi da shi?''
ta danyi murmushi,a zaton innan ko maganin mu na mata takeson ta hada
''akwai cikin kayan malam,amma ina tsammanin busashshiya ce,idan danya kike so saidai ko a yago miki can qofar gidan malam haladu''
''sai nasa yara su ciro miki,yaya abdullahi zakiyiwa magani?''inji mero wadda ta cafe zancan,kallonta maryam din tayi,ta lura da yadda take yawan kulawa da duk wani lamari da ya shafesu hakan yasa ta dan saki jikinta da ita
''eh''maryam tace mata,take ta miqe tana jawo hijabinta tana yafawa
''bari na kawo miki''ta fada tana ficewa,mero sunanta maryam,tsirar gidaje biyu ne kawai tsakaninsu da gidan inna wuro,irin marasa shi din nan ne na azo a gani,hakan ya sanya hatta aurenta iyayenta suka kasa,hakan ya sanya take shigowa take taya inna wuro aikace aikacen gida,taci kuma na rana da dare wani lokaci harda na safe agidan bayan wanda tsoho malam yasa ake zubawa akai gidan naau sabida iyayenta da qannenta
zama tayi suka ci gaba da hira da inna wuron bayan ta mata tayin gyadar,cikin minti goma saiga mero da ganyan kore shar mai yawa kuwa,maryam ta miqe tana mata sannu ta saka hannu zata karba
''bari na kai miki dakin ma''kafin tace wani abu har ta fice ta nufi dakin nasu,binta tayi da kallo har ta dagaabulen dakin ta shiga,duk da ta koma ta zauna amma sai hankalinta ya kasu jiyi ganin ahiru meron bata fito ba,miqewa tayi taa cewa inna wuro
''bari na daura alwala naga an kusa azahar inna''
''to...to,nima tashin zanyi''.
sai data daura alwalar sannan ta nufi dakin,kan kujerar dakin ta tadda meron tana faman zuba surutu idonta kan abdalladake kwance,abdallah na daga kwancen yana kallonta
qarasa shigowa tayi
''kin manta bai da lafiya ne,mara lafiya baison surutu''ta fada tana qarasawa kan katifar
''amma meramu har mirmushi ya yimin fa''sai taji wani dim,ta waiga ta kalli abdallah,idanunshi na alaumshe sabanin dazun da yake tar a bude.
sauka tayi kawai ta janyo,abun salla ta shimfida sannan ta kalli mero
''ya kamata kije kiyi sallah ko,don lokaci yayi''
''shi kuma abdullahin fa?''
''zaiyi shima''ta bata amsa tana tada kanbbarar sallah,sai data kusa raka'a uku kafin meron ta tashi ta fita tana yiwa abdallah sallama
roba ta saka ta masa alwala sanna ta juyar dashi bangaren gabas,kafin ya idar ta zuba abinci cikin plate ta ajjiye,bayan ya gama ta dora mishi kan,fillow a saman cinyanshi don hisham yace a dinga barinshi wani lokaci ya dinga ci da kanshi don hannun ya dinga motsawa ya dinga jin qwarinshi sosai,ta koma saman kujera ta ta samu roba daya ta zuba ganyan magaryan tana gyarashi tare da cire qayoyin jiki
shirun da taji alamun bai fara ci ba ya sanyata dago kanta,hada idanu sukayi da sauri ta janye idonta,ta rasa dalilin da a kwanakin nan bata iya hada ido da shi na tsawon lokaci,jikinta yaci gaba da bata kallonta yake,a sace ta kuma daga kai zata saci kallonshi suka sake hada ido,ya lumshe idon nashi da sauri ya bude,sign ne da ta lura yana yawan yi mata amfani da shi idan suka hada ido,batasan me yake nufi ba saidai a duk lokacin da yayi hakan takan tsinci kanta cikin wani irin feelings,wani irin abu ne cikin qwayar idanun abdallan da bata taba ganinshi cikin idanun wani ba
ta janye idonta tana fadin
''kaci abinci kada ya huce''kai ya girgiza mata alamun a'a,babu yadda bata masa ba amma yaqi,qarahe sai daya bar abinda take yi din ta dawo kan katifar ta karbi plate din,ta debo ta miqa mishi,babu musu ya bude bakinshi ya karba yana kallon fuskarta,ganin ya karba sai ta ajjiye cokalin tana fadin ''bismillah to''tana maida fuskarta gefe
a tausashe taji an kamo habarta ana qoqarin juyo da fuskarta,qin kallonshi tayi kamar yadda shima sam ya hanata sakewa har sai da suka sake hada ido,ture plate din abincin yayi da hannunshi guda kana ya jawota ta fada jikinshi.
tayi ta qoqarin tashi,saidai ya hanata,har mamakin yadda ya iya riqeta haka tayi,kamar zata yi kuka tace
''abdallah,bafa mu kadai bane cikin gidan nan ka sani''shiru taji,alamun bazai kulata ba,tilas ta haqura da yunqurin tashin tayi luf cikin jikinshi,ya lalubi hanninta ya saka nashi ciki ya jade yatsunsu guri guda tare da sauke ajiyar zuciya wadda ta haddasa mata sauyawar yanayin jikinta gaba daya,ta runtse ido tana jin fitar numfashinshi.
*_kuyi haquri da wannan_*
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[1:55pm, 9/24/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
4⃣6⃣
*_Annabi Muhammad S A W yace:duk wanda yaje gurin boka ko dan duba haqiqa ya kafircewa abinda annabi muhammad tazo da shi,hakanan ba za'a karbi sallarsa ta kwana arba'in ba(ba yafe masa su akayi ba,kuma ko yayi Allah baya buqata baxai karba ba,babu wani abu da zaka/ki aikata ya zama kaffarar wannan zunubin da kikayi face ki tubarwar Allah tuba na haqiqa ba tuban muzuru ba,kuma kada ki yarda qafarki ta sake kusantar gurin bama zuwan ba,shin me kike tsammani idan Allah ya dauki ranki a gun ko a hanyar zuwa kota dawowa?,Allah ya kare mana imsninmu,ya,cire mana dukkan wani qulli dake zuciyoyinmu game da 'yan uwanmu musulmi)_*
*_Manzan Allah S A W yana cewa''ka tuna Allah lokacin da kake cikin jin dadi da yalwa,shi kuma sai ya tuna da kai lokacin da ka shiga qunci da matsi da wahala(ba wai ka xauna kara zube ba don kana cikin jin dadi da wadatar rayuwa,ba zaka tashi addu'a ko tuna Allah da girma yake ba sai bala'i da masifu sun maka katutu,wannan kuskure ne babba,Allah yana fushi da bawan da baya roqarsa haka annsbi S A W yace mana,Allah kasa mu dace)_*
Saukar numfashinsa ne ya alamta mata bacci ya daukeshi,ta zare jikinta cikin dabara ta maye gurin da fillow,fuskarshi tarwai,kyawunshin nan mai daukar hankali yana nan,ta zuba masa ido tana tuhumar kanta na wasu 'yan lokuta,ta janye idonta ta lumshesu hadi da sakin ajiyar zuciya,mero ta fado mata arai,sai ta ja siririn tsaki kana ta sauka daga katifar,hijabinta na kanta don haka abun sallah kawai ta gyara ta zauna akai bayan bayan ta samu roba daban ta saka ganyen magaryar qwalli bakwai aciki,a nutse tayi bismillah cikin madaidaiciyar murya ta soma karanta suratul baqara cikin robar da ta zuba ganyan magaryar da ruwa aciki,da ka take karatun cikin daddadan sauti mai cike da nutsuwa,don surar na daya daga cikin surorin data haddace saboda muhimmancin surar.
cikin barcinshi ya dinga jin tashin sautin karatun,sai ya gaza bude idonshi duk da ya farka,sosai yake jin dadin karatun,wani yanayi mai dadi na ratsashi,sannu a hankali ya dinga daga idanun nashi har ya kammala budesu gaba daya,ya zubesu fes kan fuskarta
kallonta yake da yadda bakinta ke motsawa cikin gwaninta da ita karanta alqur'ani da bawa kowanne harafi haqqinshi,ba kadan ba ta burgeshi,komai nata mai kyau ne da nutsuwa,saita tunasar da ahi ahima wani bangare mai girma daya manta ko ya saki na karatunshi ya daina tilawa.
kan idanunahi ta kammala,ko kadan batasan yana kallonta ba har ta gama ta karanta falaq da nasi da suratul ikhlas aciki ta girgiza ahi sosai har ruwan ya soma kumfa ta samu murfi ta rufe,ta zare hijabinta saboda zafin data fara ji sakamakon rashin kitso,Allah ya bata yalwar suma kamar yadda ala sana salin fulani ke da ita,ta zare ribbom dinta ta fara sake qoqarin tattara gashin guri gida donta daureshi,bin sumar tata yayi da kallo,don iya zamansu bai taba ganin gaahibta haka ba,ba qaramn hirgeahi abin yayo ba,yana son mace mai yalwar gashi sosai,shi ua sanya yawancin lokuta a zamanin quruciya shi yakewa mami tsifa,rabi wasa rabi tsifa da haka suke gamawa,ya dan lumshe idonshi kana ya bude saboda wani abi da ya soki zuciyarahi da tunawa da mamin da yayi,qaunarta da kewarta ta zamar masa sabuwa.
ci gaba yayi da kallonta ganin yadda ta daureahi ta kuma nannade jelar kamar alkaki,ta juya don sake sanya hijabinta suka hada ido,gabanta ya fadi
''shikenan ya gama qaremin kallo''ta fada cikin zuciyarta,murmushi ya sakar mata ganin yadda take faman qoqarin sala hijabinta
''dubeta,kamar ba mijinta bane ni,banga marabarki da mutanen qauyen nan ba kam,dama ina da ikon miqewa yau da sai na baki kunya fiye da haka yarinya''ya fada shima cikin zuciyarshi,fatanshi daya kada ta gudu,aikam addu'arsa bata ci ba don tana gama sanya hijabin ya gudu a dakin.
a bakin bishiyar darbejiya ta sameau zaune ita da mero
''sannu maryamu,na kiyo ki ai kina karatu,har mero zata shiga nace ta qyaleki,hala abdullahin kike wa''
''eh inna wuro''
''ai yana da kyau kam haka din,qur'ani dama ai waraka ne''
''wani baccin ya koma?''mero ta fada tana kallon qofar dakin nasu,sai data waiwaya itama ta dubi dakin kana ta dubeta ta girgiza kai
''amma aka barshi shi kadai,da fitowa akayi da shi ko inna wuro?''inji mero ta fada tana duban inna wuro
''lallai kam yasha iska shima,duk da akwai fanka,amma ta Alla tafi lafiya''
kafin maryam ta kai ga miqewa har mero ta miqe ta fara yin gaba,da sauri maryam tace
''amma inna bazan iya dorashi kan kujerar ba ni kadai,ga mustafa baya nan''itama miqewar tayo
''muje,zaki iya in sha Allahu,ai jikin ya qara qwari ba kamar da ba''
tuni har mero ta isa dakin ta bude wheel cahir din ta tsaya agaban katifar abdallahn tana kallonshi,shima idonshin na kanta,wani abu maryam taji ya taba ranta sai ta dauke kai ta qaras inda yake,gabanshi ta tsugunna
''inna wuro tace ko zaka fita waje can yafi iska mai dadi?''tana maganar ne idonta na kallon gefe ba inda yake ba,kai ya guada alamun to cikin zuciyarshi yana fadin
''Allah yama inna wuro albarka,ko banza ta samamin hanyar da yau zan wuni ina kallonki,ko ke ba zaki kalleni ba,'yar qauye kawai''.
sau uku tana qoqarin dagashi ta kasa,mero na tsaye ta dameta da maganar kaza zakiyi kinga haka zakiyi,ana hudun ne ta taho da sauri zata tayata kama shi
''me haka ne wai mero?lafiyanki?''madyam ta fada a dan zafafe,ita kanta batasan ta fada din ba sai daga bisani,sai ta waske da aon ci gaba da daga shi din,qarshe inna wuro ce ta taimaka mata suka dorashin ita ta turoshi mero da inna wuron sukayi gaba.
Da ido yake binsu hirar tasu na bashi sha'awa,zaya so ace yana da bakin da zai saka cikin hirar tasu,hakanan yaji jininshi ya hadu da inna wuro,tsohuwa ce mai karamci da dattako kamar maminshi duk da ta fita shekaru,weather din garin yaji yayi masa kamar a qasashen turai ba cikin qasar kano ba,kanon ma cikin wani qauye.
Murmushin da maryam ta ga yana tashi kadan kadan kan fuskarshi ya tabbatar mata yaji dadin zaman gun,hakan neya bawa mero damar matso da kujerarta 'yar tsuguno daura da abdallah ,ta fara bashi labaran qauyen da waqoqinsu,al'a dunsu da kuma yanayin shagulgulansu inna wuro na sa musu baki jefi jefi,yadda maryam taga ya bada hankalinshi sosai kan meron sai taji baa wai,duk da tana ta qoqarin nutsar da zuciyarta kan meye nata?,Abdallah dama temporary ne jiran samun lafiyarshi kawai take ta kaucema rayuwarsa.
Saidai duk yadda taso nutsar da kanta hakanan taji hakan ya faskara,sai tayi zaton zama shirun da tayi ne saboda gaka ta miqe tana fadin
''inna wuro bani garin tuwon nan mana na tankade miki shi''
''kwano biyar ne fa meramu?ba zaki iya ba''
''ai inna babu abinda nake Allah zan iya ki bani kawai''
hakanna inna wuro ta bata din sai ta tafi can dan nesa da au kadan bakin rijiya ta zauna ta saka kujera ta tsuguno tana son kauda hankalinta daga garesu,duk da tana iya kallosu tana kuma jin abinda suke fada.
A sace yake kallinta,qarara ya karanto damuwa cikin zuciyarta saidai miskilancinta da wani dalilinta can maras tushe ya hanata gano me take ciki?me take so?mene kuma bata so,duk sanda ya fusknci zata dago kai ta kallesu sai ya dauke kanshi ya maida kan mero,ita kam mero farinciki ya cika zuciyarta kamar ta taahi taka rawa,tqu,balaraben nan ne yake ta kallonta,kai gaskiya tafi kowacce mace dake cikin qauyen ni'ima sa'ar zuwa duniya.
har aka kira sallar la'asar yana nan zaune yana sauraron hirar tasu yana kuma tayasu da murmushi,musamman idan akayi abun dariya,tankaden da ya kamata ace ta gamashi cikin qanqanin lokaci sai gashi zuwa lokacin la'asar din ko rabi bata yi ba,hakanan ta miqe ta karkade jikinta,ta maida saura cikin buhu wani kuma cikin fanteka ta rufe ta share gun
''ayiwa bawan Allah alwala ko?''inji inna wuro,mero ce ta miqe tana fadin
''sai nayi masa inna tunda maryamu na tankade''
''a'ah,ina aka taba haka mutum da matarsa ba wai bat nan bane,haramci ne ai,ki karbi tankaden ita tayi masa alwalar....af,tama kammala kinga,to bata butar''
haka nan taji tana jin haushin meron,ko da tazo miqa mata butar karba tayi ba tare da ta kalleta ba,abdallah ma kan whell chair dinshi yana kallinsu,murmushi ya aubuce masa kana ya duqar da kanshi yana jin wani sukuni da farinciki na ratsaahi wanda tunda ya kwanta cutar nan baiji irinshi ba sai yau,ya kuma rasa na meye,a gaggauce ta daura mishi alwala ta fuskantar da shi gabas ta bar gurin taje tayi tata,da suka idar ma hirar taau suka zo suka dora,madafa tayi tafiyarta wata rumface ta bunu dake gefe daya na tsakar gidan,anan din ma tana iya hangosu amma sai ta juya musu baya.
haka ta hana kanta sakat taqi zama gu daya har sai da ta kammala tuwon masarar miyar danyar kubewa,shi kuma abdallah ta dafa miahi couse couse da miyar ganye
anan din ma dai suka zauna don cin abincin dare,qemem yaqi couse couse din,tayi mamaki matuqa da taga yana cin tuwon masarar,shi da ko na semovita bai dameshi ba
''ato,dama ai tuwo shine abinci,a tsari na abincin gidan bahaushe ma ahekari aru aru ahine abincin dare ba wadannan abinciccikan yahudawan ba da basu qara mana komai face cututtuka''inji inna wuro ta fada har sai da tasa abdallah murmushi.
ido ya zuba mata ganin kowa ya kammala cin abincin ta tattara kwanukan ta wanke ta dawo ta zauna ba tare da ta sa komai cikinta ba,ta lura sarai da yadda yake kallonta don haka ta canza ma gin zama inda ba zasu iya hada ido ba
''abdullshi me kake kallo ne?,ko wani abun kake so?''inji mero ta fada
kai ya gyada,bayqn ya kalleta,sai ta sake washe haqora tana fadin
''to me kake so?''ya tsanshi ya nuna saitin maryam,sai ta bi yatsar da kallo har kn maryam
sai ta rage farashin fara'ar fuskarta kana tace
''maryamu magana ye dake ko?''ba tare data dubesu ba tana tsincewa inna wuro qulalai daga cikin audugar da take kadi,cikin salon dakiya da shariya tace
''magana ta me kenan?''
''nima ban sani ba''meramu ta fada tana komawa inda ta taso ta zauna,qarasowar inna wuro gun yasa suka ci gaba da hirarsu,haka ya qarqci kallonta har ya haqura.
inna wuro ce ta lura da yadda ya soma lumshe ido
''bawan Allah bacci ina tsammani yake ji''inji inna wuro
''kaishi daki maza meramu,idan zaki dawo kya dawo''ta fada tana janye daeon audugar daga gabanta,yana sane ya lumahe idon yaji dadi da inna wuro ta masa hanya.
da qyar ta samu dorashi kan katifar,ta janyo masa abun rufa kan ta gama lullubeshi ta tuna da ruwan ganyan magaryarta,taso idanunshi biyu yasha,amma duka da haka ta debo cikin tafukan hannunta ta shafa mishi dukka jikinshi,kana ta masa addu'o'in kwanciya barci ta shafa masa,wani sanyi da nutsuwa yaji suna ratsashi,kamar ta shafa masa ruwan qanqara,ta juya da nufin tashi sai taji an janyota,bata zata ba sabida haka kai tsaye jikinshi ta fada
''ka sake ni''take fada tana mutsu mutsu,saidai ko ajikinshi,bata son me yasa yake yawan son rungumarta ba haka
''haba ka sakeni nace mana,kayita taba jikin mutane haka kawai''
''jiki na ne,halaliyata,lada ma Allah zaya bani''haka yakeson fada amma ya gaza.
duk yada taso zame jikin nata ta gaza,tanaji tana gani har gajiya ta sauko mata bacci ya qwace idanunta,yan jin saukar numfashinta cikin nutsuwa,shi din ma idanun nasa a rufen auke sai kayi tsammani bacci yake,saidai sam ko daya,tunanin maryam dinne cike fal da kwanyarsa,yana tausayinta,yana jin sonta har cikin jini tsoka da bargonsa fiye da da,sai yanzu yake sake tabbatarwa kanshi Alah ne kawai ya bashi maryam din ba mutum dukiya ko qarfin iko ba,maryam din kadarace mai tsada kai tama shallake kadara agunsa,samun mace mai halacci da juriya kan lalura da halayen mijinta abune mai,matuqar wuta a wananan zamanin namu,ya sani sarai bata zaman qauye iyakacinta da ahi ziyara ta kwanaki uku,sai gashi yau ta amince ta yarda ta zauna cikinsa shi da ita cikin zuriyarta har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya ba tare da damuwa raki ko qorafi ba,lokacin da dukkansu shi da ita basu san sanda zaizo ba don babu wanda ya san iya tsahonsa,baya ga dama da take da shi na tafiyarta ta barshi tunda babu zuri'a ko iddarsa akanta.
A hankali ya dinga tina yininsu shi da ita na yau,murmushi ya subuce masa,fushi da kishi daya dinga ganowa qarara cikin qwayar idanunta,saidai ita sam bata san da su ba,batasan suna bayyanar da kansu bane su duk yadda kakai ga qoqarin boyesu,murmushi ya subuce masa,ya sanya hannunshi ya cire dan hijabin dake maqale a wuyanta,ya sake zare ribbom din kanta ya sa hannunshi yana shafa gashin,santsinsa da qamshinsa na burgeta,yayi imani abinda yake ji game da maryam din wani irin jini a jiki da ba kowa Allah yake bawa ba.
Ta sake zubawa qofar dakin ido a karo na barkatai,mintina kusan goma ta sake janye tagumin da tayi ta saki ajiyar zuciya ta kalli inna wuro da ta duqufa wajen yin kadinta
''kinga inna meramu shiru bata dawo ba''
''eh.....wata qila itama baccin yayi awon gaba da ita ne,ai yau kam ta aikatu itama,meramu babu son jiki,harvta fiki son aiki''innan ta fada cikin halin ko in kula don bata kawo komai cikin ranta ba
''amma inna bacci da wuri haka,qarfe tara da rabi fa,yanzu ma wasu suke fita dandali''
''yo su mutan birni barci da wuri a gunau wani abu ne?,rayuwa suke gida a qulle,daga sallar isha idan suka shige gidajensu suka kulle sai kuma washegari''
''q'nn,bari na tashi nima na tafi''
''da wuri haka?''inna wuro ta fada tana binta da kallo
''eh''ta bata amsa gana zira sudaddun silifas dinta
''to kinga ga abincin nan kokus yake kome ne?,tafi da shi gida kwaci''duk yadda take kwadayin couse couse rin sanda ake dafashi take fata ya shigo farantinta amma a yanzu sai taji duk ya sure mata,a salube ta dauki kwanon tana fadin
''an gode sai da safe''
''Allah ya bamu alkahairi''inji inna wuron
bata haqura ba sai da ta je bakin qofar dakin tace
''abdullahi da meramu sai da safe''sau uku tana maimaitawa taji shiru,abdallah na jinta amma maryam batasan ma me ake ba don ta jima cikin daddadar duniyar barci ta musamman.
inna wuro ta dubeta
''na gaya miki sunyi bacci,kije kwa hadu da safen,ki gaida su hansai''jiki ba qwari ta fice daga gidan
ko a gida tana kallo qannanta na damben cin couse couse couse din amma ta kasa ci sai ido kawai data zuba musu tana kallonsu,sau uku babarta iya hansai na mata tayin taci bakinta cike da shi taqi cewa komai,qarshe ma tashi tayi ta shige dan takurarren dakinta wanda zakayi tsammanin duk ranar da aka samu ruwan sama mai yawa zai iya ruftowa mazauna ciki.
kasa bacci tayi,yau kam ta kai maqura,jin son Abdallan take kamar ta mutu kota haukace,ita kam ko a haka ma zata iya aurenshi,amma idan ta dubeshi ta dubi kanta sai jinta yayi sanyi qalau,tasan wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,duk da batasan waye ainihin abdallah ba,amma kallo daya da ta masa ta san cewa ba qaramin mutum bane shi da maryam din ma baki daya
tunanin da ya isheta qarshe kuka ta fashe da shi a haka bacci yayi awon gaba da ita tana Allah Allah gari ya waye ta koma gidan inna wuro.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Kamar yadda suka amida shi al'adarsu bayan sallar la'asar su zauna hira har salllar magariba wani lokaci har isha'a yanzu ma hakane.
yana zaune kan whell chair wanda yau ita da mustafa suka dorashi don ya dawo daga gona da wuri,ta karbi dan qaramin alqur'anin da ya gama karatu da ahi daga hannunshi ta ajjiyeshi a muhallinsa,ta dauko roban da take ajjiye duwan ganyan magaryar,wanda ta karanta a yoyin dake cikin surutul A'araf aya ta 117 zuwa ta 122
sai ta cikin suratul yunus aya ta 79 zuwa ta 81
sai cikin suratu Daha aya ta 65 zuwa ta 70
ayatul kursiyyu falaq da nasi da iklas duka,tana shirin tsiyayowa taji sallamar mero wadda ta fita dazun tace zata je tayi wanka,idan da savbo maryam ta saba,da safe zata zo da kwalliyarta,idan ta gama wuninta qarfe uku zata koma gida ta sake wanka da kwalliyarsu irin ta mutan qauye.
a cup ta tsiyayo ta miqo masa,sai ya dan bata rai,saboda dandanon magaryar da baiso,itama kicin kicin tayi,musamman da ta jiyo tana tambayar inna wuro ina suke basu fito ba,tasan kadan daga aikinta ta fado musu,taji dadi da inna wuron ta ce mata
''zauna anan ki tsinke zogalen nan kada meramu ta fito ta hau aikin,sonke kwana biyu naga gun hira kika fi kauri,duka kin sakar mata ragamar aikin,kullum ita ke ruwon dare ta barki da lugudar lebe''.
Dariya ta bashi cikin ranshi ganin yadda tayi wani kicin kicin
''lallai ma yarinya,wuyanki ya isa yanka,ni zaki wani budewa ido kamar qaninki,Allah ya bani lafiya zaki gane shayi ruwa ne''hakanan ya karba yayi bismillah cikin ranshi yasha donshi kansa yana jin dadin sa,wani lokacin don ya tsokaneta yake qin karba,don ya lura indai yanason ganin fushi da bacin ranta yaqi karba yasha ya kuma zauna sauraren labaran mero
ta bude wata 'yar roba mai kama data naseline,saidai ba shi bane ciki,man zaitun ne da na habbatussaudah wanda ta karantawa ayoyin da suka wuce a baya ta qara da ayatushshifa ta tofa aciki ya zama na man shafawarsa ta miqa masa don tana jin kunyar shafa masa,nan ma sai da ya gama shan qamahinsa ya amsa ya shafa ta maidashi inda yake.
komawa tayi ta zauna kamar ba fitar zasuyi ba,ya zuba mata ido yana son ganin iya gudun ruwanta saidai qememe tayi taqi kallonshi ta fara karanta azkar dinta na maraice,ta kammal ata shiga wasu sabgogin abinta,don har cikin ranta bata jin fitar,sai data qara kusan awa guda sannan ta miqe ta iso inda yake,ido suka hada sai taga ya dan harareta,dariya ma yaso bata amma sai ta dake ta tura whellchair din a tausashe suka fito.
tana kan tabarmar kabar da suka saba zama qasan bishiyar dalbejiyar,tasha daobta daidai da irin nasu baki cike da kan ta kile,koriyar atamfa ce jikinta shar wadda hatta da zanan jikinta yanzun da zaka bawa maryam ta zana maka tsab zata zanashi saboda tsabar sawar da meron keyi yau da gobe don bata da kamarta duk cikin kayanta,gaba dayanta qofar dakin take kallo,gyaran zogalen da aka batan ma ko rabi bata yi ba,inna wuro batasan me ke gudana ba don yau tayi riga malam masallaci ta shiga ta hura wutar tuwon da kanta don kada maryam ta karba yadda ta saba su ta barsu da shan inuwar qasan bishiya,sai da ta kalli gidan ko ina tsaf ya sha shara sai qamshin qasa yake kamar kullum kana ta juya abdallah can bayan mero yadda ba zata iya ganin fuskarshi ba saidai idan juyowa zatayi,ai kam kamad an tsikareta ta juyo din tana fadin
''nayi zaton yau ba zaku fito ba ai,har na fidda tsammani Allah''.
kai kawai ya girgiza yana dan qaramin murmushi wanda idan yayi meron kejin duk duniya fa ita an gama biyanta,kallon murmushin take da matuqar qima don bata taba ganin wani cikin samarin garin da idan yayi murmushi yake qawatashi ya masa kyau kwatankwacin haka ba.
yau kam innan ta zaunar da ita cikinsu babu batun zuwa kitchen wato rumfar girki,taqi kallo kosa baki ko sau daya cikin hirarsu,ranta take ji yana mata suya,kamar ta kori mero amma sai taga meye nata a cik,bata da wannan hurumin,ita kanta batasan me yake jefata damuwa mai yawa kan lamadin meron ba da abdallah,ita da ya kamata ta zama 'yar abi yarima asha kida cikin sabgar.
Dakinsu ta koma ta dora doguwar riga kan dinkin atamfa riga da skert dake jikinta,cikin kitchen ta samu inna wuro
''inna naga kuna kusa da rafo,zan qarasa da abdallah can yaga garin naku''
''to Allah ya kiyaye sai kun dawo''
bata kalli mero ba bare tace mata wani abu ta fara tura whell chair din abdallah,ya waiwayo suka hada ido sai ta dauke idonta
''ina zaki meramu?''mero ta fada tana miqewa da sauri tare da zura takalmanta ta biyo bayanta,inna dake kitchen ce ta amsa mata
''zasu rafin malam dogo na bayanmun nan''
''ai da ni za'a,dama ina son in gaya muku idan kuna son zuwa,girin na da kyau aradu''ta fada tana bin bayan maryam
''um hmmm''kawai tace da ita tana ci gaba da tura abdallah.
Tafe suke mero na nunnuna musu gurare,duk da wani gun ma maryam dauke kanta take ba kalla taake ba,saidai abdallah ya bada hankalinshi sosai bisa dukkana alamu hakan na masa dadi kuma yana fahimtar baya nanta,mero kan makar ta taka rawa don murna,yau gata ka larabawan birni,duk inda suka gifta sqi an bisu da kallo har wasu ma su tambayi meron
'''yan uwanmu ne,wannan yaya na ne''haka take fada cikin washe baki,wasu mazan har hannu suke bawa abdallah,ba qyama yake basu nashi hannun suyi musaba,kodama can shi cikin aqidunshi baya qyamar maras shi,duk wanda kuwa sukayi musabahar farinciki da murna kamar yayi me,musamman idan ya shinshina hannunahi yaji qamahin turaren abdallan,da yawa idan mero tace bashi da lafiya baya iya magana addu'a suke masa sosai Allah ya bashi lafiya.
sannu a hankali suka ci gaba da ratsa qauyen mai cike da ni'ima kamar yadda sunanshi yake,ko ina ka duba shuke shuke ne koraye shar,a yadda taji mero na gaya wa abdallah haka qauyen nasu yake ko ba cikin damina ba,cikin mintina goma suka iso bakin rafin,ruwa ne mai kyau yake guda na ciyayi baibaye da da bakinshi,wasu fararen dutsina da jajayene reras a zube a gun tamkar ana sane aka shiryasu,saidai ikon Allah yafi gaban haka ai.
Gab da bakin nan maryam ata ajjiyeshi,suna iya,hango shanu daga daya,bangaren sunata kai kawo,mafi yawancincinsu fararene qal sai kuma ruwan qasa jifa jifa,shegen surutun mero sai data gaya musu hatta da mai shanun,na wani dan garin ne saidai duk da dukiyar shanun da Alah ya bashi,matashine don bazai wuce shekara talatin ba,don ko auren fari baiyi ba,gefe ta matsa maryam ta zura qafafunta cikin ruwan tana kallon yadda yake gudana,tunanin mama da hindatunta ya fado mata,don kusan babu wanda suke waya da shi a yanzun ,hisham ne yace ta haqura din kada nene ta bayar da nim dinta ayi tracing nasu,da hakan ma saidai abinda take ji yana sukuwa azuciyarta da ranta tana jin kamar yafi haka,duk da zubar da meron keyi hankalinshi na kanta,ya fuskanci akwai abinda ya taba zuciyarta.
ji yayi kamar ya miqe da ya fuskanaci hawaye take sharewa a idanunta,mero ya yiwa nuni da 'yan qananen fararen dutsinan dake gun,ta dauko yan,madaidaita ta miqa masa ga zatonta zai dinga cillawa ne cikin ruwa har tana fadin
''ai ka danyi nesa kadan da ruwan ko na matsar dakai gaba kadan?''kai ya girgiza mata alamun a'a.
ya dauki daya ya cillashi ga maryam,ya sauka abayanta,sai tayi sauri ta waiwayo take kuwa suka hada ido,idonshi daya ya kashe mata kana ya daga mata gira alamun tambaya,sai ta kawar da kan nata ta maida kan rafin,ganin haka ya sa ya sake ciro wani ya jefeta wannan karon ta sani shine sai tayi banza taqi juyowa,da daya da daya sai da ya qarar da su duka amma taqi koda motsawa bare ta waigo gareshi,mero na tsaye a bayanshi tana kallonsu tuni tayi nisa cikin duniyar tunani har ta manta da a inda suke.
Gabanta ya yanke ya fadi,da sauri ta waiwayo,abdallah ta gani a qasa ya fado daga kan wheel chair din idonshi na kanta,a sukwane ta miqe daga inda take zaune dan tahowa inda yake,take santsin,bakin rafin ya debeta tayi baya luuuu zata koma cikin ruwan
''maryam!''
muryar abdallah da take a shaqe ta daki dodon kunnenta ba zato babu tsammani,cikin ikon Allah ta turje bata kai ga fadawar ba ta dawo gaba ta kwasa a guje ta dira a gabanshi cike da tsananin mamaki,ko ina na jikinta rawa yake,sai hawayen idonta da take ta yiwa waigi ya balle baki daya,ta rasa me ma zata yi,hawan mero tayi da bala'i ta inda take shiga bata nan take fita ba,dn me tana gani zata barshi ya fado akan me?,duk masifar da take taqi kallonshi yayin da ahi kuma ya zuba mata ido yana karanta al'amura da dama daga gurinta
''shshshhhhh''din ta taji yace yasa ta rage masifar da take, a hankali a hankali,daga qarshe taja bakinta tayi shiru
''ki taimakamin na koma kan kujerar tukunna madam''
ya gaya mata karo na farko taji,muryarsa ta fita sosai,wani abu taji yana ratsa ta tako ina.
har yanzu jikinta bai bar rawa ba don haka qarfinta ya gaza kaiwa har sai data haqura mero ta taimaka mata suka maida shi,bata sake cewa komai ba ta soma turashi suka fara barin gurin tana goge qwallarta lokaci lokaci,ta kasa tantance yanayin da take ciki,gaske ne koko mafarki,yau abdallah ke magana da bakinshi?.
Dab da zasu fara shiga cikin mutane taji yace
''bai kamata ki shiga cikin mutane kina kuka ba ko?,dakat kadan ki daidaita yanayinki''
bata qi shawararshi ba ta tsaida wheelchair din din ta ciro dankwalin atamfarta ta goge fuskarta kana ta maida dankwalinta,amma maimakon hawayen ya tsaya sai wasu sabbi,ma dake bulbulowa har mero ta iskosu
ya limshe ido ya maida bayansa sosai ya kare da kujerar yana fadin
''ya salam,to me aka yi miki?,idan don warkewar baki na ne ai godiya zaki ma Alah ko,tunda dama shine mai kowa mai komai,idan kuma don fdowar da nayi ne ai gani sumul,ba ba abinda ya gutsireni mijinki baiji ciwo ba''
batasan ta harareshi ba sai data ji yace
''maida idon kada kija min asara,don ba qaramar asara bace idan na rasa wadann nan golden oily eyes din ba''.
A nutse suka ci gaba da tafiya kamar yadda suka zo,saidai canjin yanayi da aka samu,a dazu mero keta faman zuba cike da farinciki abunta abdallah na kalle kalle babu bakin magan,wannan karon kuwa tasbihi hailala da salatin annabi ke fita a bakinshi zalla,yayin da maryam ke cikin wani irin yanayi,jin ta take kamar an rage mata wani nauyi daga cikin nauyin da aka azawa zuciyarta,mero kuwa amsa kuwwa muryar abdallah ke maya cikin kunnenta,dadin muryar ya kasa barin dodon kunnenta,tsabar kulawa da qauna da take iya hangowa daga dukkan kallo da ikin abdallah da kewa maryamu,da gaka suka qarasa gida ana qwala kiran sallar magariba.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[7:29pm, 9/25/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
4⃣7⃣
*_Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku_*
*_mala'iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur'ani a cikinsa_*
A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar
''kun dawo kenan mer.....'''sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji
''Allah qaadiran ala mai yasha'u,bawan Allah?''ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu.
murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana
''babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min''
kiran sallar magariba ya katse su
''inna muyi sallah tukun''ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci
''gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi''inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta
''haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala''
''to inna''ta fada cikin rawar murya
tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta.
Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi.
Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta
''nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai''mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa.
sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al'qur'ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur'ani ya shafa addu'anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba.
''madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana''ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar.
Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata
''ka sakemin hannu kaga duk ka.....''
''bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hira?''
ta sake kau da kanta kana tace
''to me kake so muce ko ince maka ne?''
''bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya furta kina cutar da zuciyarki hakanan babu gaira babu dalili ba tare da ta yi miki laifin komai ba''
kamar wadda ya doka sai ta soma hawaye,ita kanta batasan me yake saurin karya mata zuciya ba
''subhanallah,kuka...kuka kuma maryam me na miki''babu amsa don haka ya janyota ta fada jikinshi ragowar ruwan ya zube mata ya jiqa mata gaban dan yalolon hijabin jikinta wanda takansa duk dare idan zata kwanta,dama ba wani kauri gareahi ba,yauqi ne da shi da rashin kauri take kuwa ya manne mata a jiki.
''yi shiru ki gayan matsalarki,bazanso saki kuka ba maryam cikin irin wannan lokacin,baki cancanci haka ba''
''ka sakeni ni babu abinda ke damuna,ka qyaleni''
kai ya girgiza hakanan mutum,bazai yita kuka ba komai na da dalili''
ta tabbatar indai abdallah ne bazai saketa din ba don ya mata riqon tsauri ne don haka tace
''kayana,ka jiqamin kayana ka sakeni na canza wasu''
idanunshi ya kai kan gaban jijabin nata cikin hasken torch din wayarshin,wani abu ya tairga mishi har qasan qafarshi,ya kai,hannunshi gaban hijabin yana fadin
''bari na cire miki''
kan tayi qoqarin hanashi har yaje,gaba dayansu wuta ta dauke musu shi da itan gaba daya,sai ta sakar masa wani kikan harda dan sauti
''am so sorry my dear''kawai yake fada ya cire hijabin ya cillar gefe daya ya sake mannata kan qirjinsa,yana kin sautin kukanta bai hana ta ba don yasan koma mene idan tayi kuka sosai zuciyarta zata sassauta,tun sautin na fita kadan kadan har ta koma ajiyar zuciya kana numfashinta ya fara sauka a hankali alamun bacci yayi awon gaba da ita.
murmushi ya saka mai qayatarwa qasa qasa yace bayan ya leqa fuskarta
''rigimammiya,kin hana zuciyarki sakat''yana gyara mata kwanciya,ya fuskanci duk ranar da ta kwanta a qirjinshi bata dadewa bacci ke daukanta wani lokacin ma har taso makara gun tashi,ya saki ajiyar zuciya qasa qasa yace
''u dont know how u make me feel duk sanda kike jikina''ya dora kanshi saman habarta cike da wata iriyar nutsuwa.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
A shirye take cikin riga da wando na pakistan ruwan madara tayi rolling da mayafinsu,zaune take kan kujera ko motsi batayi kanta a duqe tana kallon yatsuntsa,ya sake dubanta tini har ta fara zub da qwallar tata abinda bai son gani
''kina son fita amma kinqi ki gyara ni,nikam yau babu wanda zaimin wanka idan bake ba,see you ko tausayina baki ji,kin gwammace mustafa yayi ta yimin bayan bako ina yake wanke min ba wani gun ni nake da kaina''
maryam cikin muryar kuka ba tare da ta dago ba
''taya zan wuce bandaki ni da kai yi maka wanka inna wuro na kallon mu,haba mana abdal....''
''fine,muyi zamanmu ko baby na ni dake yau cikin daki,babu mai cewa don me ko''qara narkewa tayi tana faman hawaye don tana jiyo muryar inna wuro na jajjabin rashin jin motsin daya daga cikinsu,duk da tasan kara da alkunya bazata bar inna wuron tayi magana ba ko zasu shekara cikin dakin.
Narkewa yayi shima cikin filallukan dake kan whellchair dinshi dariya na cinshi,ya sani cewa ba zata taba iyawa ba,ko kaya na shan iska bata yarda ta gani jikinsa kuma duka ua gama karantota,ta daukeshi kamar wani muharraminta
sallama mairo tayi tana daga labulen dakin
''yaya abdullahi muna ta cigiyarku shiru?''ta fada tana kallonashi tana kuma kallon maryam
girarshi ya dage guda daya
''eh,muma muna ta cigiyarku,daman ke nake jira ki taimaka min inyi wanka,yau meramu ta gaji''ya ambaci sunan ta irin salon da yaji suna fada
zuciyar mero qal ta rufe fuskarta da tafukan hannunta,da sauri maryam ta dago babu shiri ta dubi abdallah qirjinta ya buga kamar an dakeshi da guduma,ido daya ya kashe mata kana ya dauke kanshi ya maida kan mero wadda take fadin
''kai yaya abdullahi''cikin salon nuna jin kunya.
kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi hanyar fita da shi,sai data bude idon nata raga dakin wayam har sun fice,jiki ba qwari jtama ta fice a dakin
inna wuro bata a tsakar gidan don haka tayi maza ta tura suka shige bayan gidan
''take it easy mana madam,kada ki fadar da bawan Allah''inji abdallah cike da dariyar mugunta da yake qunsheta
tana tsaye ya soma cire kayanshi ta dauke kanta qirjinta na lugude,saura gajeran wandon daya rage wanda yake bari a jikinsa idan zaiyi wanka,gaba daya ta rude don bata yarda taga jikinshi har kamar haka,hatta da cinyoyinshi dake cike da gargasa sun fito,ganin yana niyyar fidda shi shima yasa ta qarasa rudewar gaba daya,batasan ta dafe hannunshi ba
''ayya mana abdallah ba kyau fa don Allah''ta fada cikin son fashewa da kuka
dariya sosai ta kamshi amma ya hade rai yayi kicin kicin
''to me naki,dazun fa adaki kika gayan babu ruwan wani da wani,kema me ruwanki da ni ko na cire din,ba wanka zaki tayani ba?,kimin wankanki kawai ki maida ni daki,wai haka ma ake jinyar mutum?,oh ni abdallah sam baki iya jinya ba''ba bakin maida amsa girgiza kai tayi yaci gaba da kiciniyarshi,a guje ta kwasa ta fice a bayin dariyar da yake boyewa tilas ta fito,mamaki take bashi tamkar cikin qauyen aka haifeta ko kuma shi din ba mijinta bane,kunyarta ta mata yawa ta maida shi kamar wani dodo,Allah yasa komai na wanka na gabanshi don haka ya qyaleta yayi abunshi tunda hannunshi na kaiwa.
sai da ya kammala ya bubbuga qofan bandakin tazo ta fidda shi,tana ta rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta shigo idanunta a qasa taqi yarda su hada idanu,itakam rashin kunyar shi ta fara isarta,daga warkewarsa jiya zuwa yau ya addabeta gaba daya ya hanata sukuni,ina dalili,yana abu kamar su biyu ne kadai cikin gidan.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[7:29pm, 9/25/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
4⃣8⃣
*_Manzan Allah S A W yace:shaidanu suna nisantar gidan da aka karanta suratul baqra a cikinsa har na tsawon kwana uku_*
*_mala'iku sukanyi duba izuwa sararin duniya,yayin da suka kalleta suna hangota ne baqiqqirin basa ganin komai face hasken gidaje ko guraren da ake karanta alqur'ani a cikinsa_*
A bakin murhu suka tadda inna wuro tana kwashe tuwo,sallamarasu ce ta janyo hankalinta bakin qofar shigowar
''kun dawo kenan mer.....'''sauran maganar ta maqale wa inna wuro ganin har da abdallah cikin masu sallamar,marar hannunta da take kwashe tuwon ta saki ta miqe tana fadin cikin dafe qirji
''Allah qaadiran ala mai yasha'u,bawan Allah?''ta fada tana kallonsa tare da qarasowa gabansu.
murmushi yayi yana kallon innar ganin ta kasa magana
''babu mamaki cikin ikon Allah inna,nine da bakina nake magana,yau Allah ya amince min''
kiran sallar magariba ya katse su
''inna muyi sallah tukun''ya dubi maryam dake tsaye guri daya tana faman goge qwalla lokaci zuwa lokaci
''gimbiya a dauran alwala,inna ki mata magana tun dazun nace tabar kukan nan taqi''inna wuron dake daura da maryam din ta dafa kafadarta
''haba meramu,farincikin da zaki nunawa ubangiji shine ki masa godiya ba wai kika ba,share hawayenki ki daurawa mijinki alwala''
''to inna''ta fada cikin rawar murya
tuni har mero ta debo ruwa cikin buta tazo gaban abdallan ta ajjiye ta koma bakin rijiyar ta ja wani ta fara daura tata alwala,dukkansu nan bakin qofar dakin innar suka shimfida karauni biyu sukayi sallar magaribar,shiru ya ratsa tsakar gidan kowanne na tasbihi cikin zuciyarshi banda mero da moysa bakinta kawai takeyi duk motsin abdallah ta cikin hasken qwan solar na kan idonta,har maryam ta fuskanci haka,dauke kanta tayi don ji da tayi ranta na aon baci taci gaba da tasbihi da yatsunta.
Ranar har sha daya na dare suna zaune suna hira,hiransu suke sosai shida inna wuro da yake jinta kamar maminshi.
Yana jin kewar mamin nashi sosai har bazai iya fadar adadi ba,mero ma tsakiyarsu tana sanya musu baki yayin da maryam taja bakinta ta tsuke,lokaci lokaci abdallah yana satar kallonta,ji yake tamkar ya jawota jikinshi ya rungume ko ya shiga zuciyarta ya jiyo damuwarta,shirun nata bai masa dadi sam,don haka sha daya na cika yace da inna wuro yana jin bacci zai kwanta
''nikuwa kamar mu kwana nan hirar yau tayi min dadi abdullahi,gashi yau kaima da bakinka akeyi da kai''mero ta fada yana kallonshi baki a washe,murmjshi kawai yayi ya girgiza kai,bata bar gidan ba sai da taga sun shige dakin kana ta waiwayo ta yiwa inna wuro sallama ta fice cike da jin dadin jin daddadar muryar abdallah da yau ta morewa.
sanye yake da jallabiya milk mai gajeran hannu yana zaune saman katifar tasu hannunahi dauke da qaramin al'qur'ani,daya hannun kuma riqe yake da wayarshi ya kunna torch din yana haskawa,ya sake satar kallonta sha biyu har da kwata amma bata da niyyar kwanciya,hakanan kuma ta kashe musu qwan solar dakin saboda ta lura da yadda yake ta nacin kallonta,tana zaune dirshan bisa dadduma sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja,ya saka zare kan shafin da yake na karatun qur'ani ya shafa addu'anshi,ya tabbata koya kirata kam ba zuwa zata yi ba indai ba cewa yayi yana buqatar wani abu ba.
''madam,a ataimakawa bawan Allah da ruwa mana''ya fada murya qasa qasa kamar mai rada har yasa tsigar jikinta tashi,ta ajjiye carbin kana ta miqe ta isa inda catoon na ruwan gora ke ajjiye ta ciro daya tare da cup ta hawo gadon,ta tsiyayo ta sake matsowa gabanshi ta miqo masa,jadawa yayi harda hannun nata ya riqe gam yana son saka qwayar idonshi cikin nata,ta soma qoqarin qwace hannun nata saidai ta kasa garin hakan har fiye da rabin ruwan ya zube a katifar.
Ta dago da niyyar dubanshi idanunta cike da qwalla da ya rasa ta meye,take idanunsu suka hadu,da sauri ta janye nata idanun don bata iya dauke nauyin idanunshi cikin nata
''ka sakemin hannu kaga duk ka.....''
''bazan sakeki ba,sai kin gayan meke damunki,tunda bakina ya budu baki,barni nayi magana da ke ba sai wasu ke tayani hira?''
ta sake kau da kanta kana tace
''to me kake so muce ko ince maka ne?''
''bana tunanin baki san me zaki gayan ba maryam,nasha hango maganganu da dama boye cikin idanunki,kin hana bakinki ya furta kina cutar da zuciyarki hakanan babu gaira babu dalili ba tare da ta yi miki laifin komai ba''
kamar wadda ya doka sai ta soma hawaye,ita kanta batasan me yake saurin karya mata zuciya ba
''subhanallah,kuka...kuka kuma maryam me na miki''babu amsa don haka ya janyota ta fada jikinshi ragowar ruwan ya zube mata ya jiqa mata gaban dan yalolon hijabin jikinta wanda takansa duk dare idan zata kwanta,dama ba wani kauri gareahi ba,yauqi ne da shi da rashin kauri take kuwa ya manne mata a jiki.
''yi shiru ki gayan matsalarki,bazanso saki kuka ba maryam cikin irin wannan lokacin,baki cancanci haka ba''
''ka sakeni ni babu abinda ke damuna,ka qyaleni''
kai ya girgiza hakanan mutum,bazai yita kuka ba komai na da dalili''
ta tabbatar indai abdallah ne bazai saketa din ba don ya mata riqon tsauri ne don haka tace
''kayana,ka jiqamin kayana ka sakeni na canza wasu''
idanunshi ya kai kan gaban jijabin nata cikin hasken torch din wayarshin,wani abu ya tairga mishi har qasan qafarshi,ya kai,hannunshi gaban hijabin yana fadin
''bari na cire miki''
kan tayi qoqarin hanashi har yaje,gaba dayansu wuta ta dauke musu shi da itan gaba daya,sai ta sakar masa wani kikan harda dan sauti
''am so sorry my dear''kawai yake fada ya cire hijabin ya cillar gefe daya ya sake mannata kan qirjinsa,yana kin sautin kukanta bai hana ta ba don yasan koma mene idan tayi kuka sosai zuciyarta zata sassauta,tun sautin na fita kadan kadan har ta koma ajiyar zuciya kana numfashinta ya fara sauka a hankali alamun bacci yayi awon gaba da ita.
murmushi ya saka mai qayatarwa qasa qasa yace bayan ya leqa fuskarta
''rigimammiya,kin hana zuciyarki sakat''yana gyara mata kwanciya,ya fuskanci duk ranar da ta kwanta a qirjinshi bata dadewa bacci ke daukanta wani lokacin ma har taso makara gun tashi,ya saki ajiyar zuciya qasa qasa yace
''u dont know how u make me feel duk sanda kike jikina''ya dora kanshi saman habarta cike da wata iriyar nutsuwa.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
A shirye take cikin riga da wando na pakistan ruwan madara tayi rolling da mayafinsu,zaune take kan kujera ko motsi batayi kanta a duqe tana kallon yatsuntsa,ya sake dubanta tini har ta fara zub da qwallar tata abinda bai son gani
''kina son fita amma kinqi ki gyara ni,nikam yau babu wanda zaimin wanka idan bake ba,see you ko tausayina baki ji,kin gwammace mustafa yayi ta yimin bayan bako ina yake wanke min ba wani gun ni nake da kaina''
maryam cikin muryar kuka ba tare da ta dago ba
''taya zan wuce bandaki ni da kai yi maka wanka inna wuro na kallon mu,haba mana abdal....''
''fine,muyi zamanmu ko baby na ni dake yau cikin daki,babu mai cewa don me ko''qara narkewa tayi tana faman hawaye don tana jiyo muryar inna wuro na jajjabin rashin jin motsin daya daga cikinsu,duk da tasan kara da alkunya bazata bar inna wuron tayi magana ba ko zasu shekara cikin dakin.
Narkewa yayi shima cikin filallukan dake kan whellchair dinshi dariya na cinshi,ya sani cewa ba zata taba iyawa ba,ko kaya na shan iska bata yarda ta gani jikinsa kuma duka ua gama karantota,ta daukeshi kamar wani muharraminta
sallama mairo tayi tana daga labulen dakin
''yaya abdullahi muna ta cigiyarku shiru?''ta fada tana kallonashi tana kuma kallon maryam
girarshi ya dage guda daya
''eh,muma muna ta cigiyarku,daman ke nake jira ki taimaka min inyi wanka,yau meramu ta gaji''ya ambaci sunan ta irin salon da yaji suna fada
zuciyar mero qal ta rufe fuskarta da tafukan hannunta,da sauri maryam ta dago babu shiri ta dubi abdallah qirjinta ya buga kamar an dakeshi da guduma,ido daya ya kashe mata kana ya dauke kanshi ya maida kan mero wadda take fadin
''kai yaya abdullahi''cikin salon nuna jin kunya.
kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi hanyar fita da shi,sai data bude idon nata raga dakin wayam har sun fice,jiki ba qwari jtama ta fice a dakin
inna wuro bata a tsakar gidan don haka tayi maza ta tura suka shige bayan gidan
''take it easy mana madam,kada ki fadar da bawan Allah''inji abdallah cike da dariyar mugunta da yake qunsheta
tana tsaye ya soma cire kayanshi ta dauke kanta qirjinta na lugude,saura gajeran wandon daya rage wanda yake bari a jikinsa idan zaiyi wanka,gaba daya ta rude don bata yarda taga jikinshi har kamar haka,hatta da cinyoyinshi dake cike da gargasa sun fito,ganin yana niyyar fidda shi shima yasa ta qarasa rudewar gaba daya,batasan ta dafe hannunshi ba
''ayya mana abdallah ba kyau fa don Allah''ta fada cikin son fashewa da kuka
dariya sosai ta kamshi amma ya hade rai yayi kicin kicin
''to me naki,dazun fa adaki kika gayan babu ruwan wani da wani,kema me ruwanki da ni ko na cire din,ba wanka zaki tayani ba?,kimin wankanki kawai ki maida ni daki,wai haka ma ake jinyar mutum?,oh ni abdallah sam baki iya jinya ba''ba bakin maida amsa girgiza kai tayi yaci gaba da kiciniyarshi,a guje ta kwasa ta fice a bayin dariyar da yake boyewa tilas ta fito,mamaki take bashi tamkar cikin qauyen aka haifeta ko kuma shi din ba mijinta bane,kunyarta ta mata yawa ta maida shi kamar wani dodo,Allah yasa komai na wanka na gabanshi don haka ya qyaleta yayi abunshi tunda hannunshi na kaiwa.
sai da ya kammala ya bubbuga qofan bandakin tazo ta fidda shi,tana ta rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta shigo idanunta a qasa taqi yarda su hada idanu,itakam rashin kunyar shi ta fara isarta,daga warkewarsa jiya zuwa yau ya addabeta gaba daya ya hanata sukuni,ina dalili,yana abu kamar su biyu ne kadai cikin gidan.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[2:36pm, 9/27/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶4⃣9⃣
*GA WASU FA'IDOJI*👌🏽
*_daga bakin mai gaskiya abun gasgatawa assaadiq al masduq Annabi Muhammad S A W yace''abinda yake zama hijabi tsakanin al'aurar dan adam da idon shaidanu fadin wannan addu'ar yayin da zaka cire tufarka BISMILLAHILLAZI LA ILAHA ILLA HUWA_*''
*_don samun kariya yayin yin baccinka,bayan ka kammla dukkan addu'ar baccin da annabin rahama ya koyar,ki karanta wadan nan ayoyin suma ki tofa musamman ga 'yan mata da suke fama da jinnul aashiq wato aljanin dare_*
1⃣ *_katamallahu ala qulubihim wa'ala sam'ihim wa ala absaarihim gishawah,ealahum azabun alim_*
2⃣ *_waja'alna min bani aydihim saddan wamin khalfihim saddan fa agshaynahum fahum la yubsirun_*
3⃣ *_wa'iza qara'atal qur'ana ja'alna bainaka wa bainal lazina la yu'u minuna bil aakhirati hijaban mastura,wa iza zakarta rabbuka bil qur'ani wahdahu wallau ala adbarihim nufura_*
Hira suke kamar kowanne dare zaune warqashin rumfar qofar dakin inna wuro,dukkansu sauraron inna wuron suke su ukun tana basu labarin yanayin zaman aure a shekarun baya can da suka shude
ita kam maryam fadi take taga ta kanta,ta sani sarai da biyu inna wuro ta tsiro da wannan tarihin,tana ankare da abdallah yana satar kallonta,da sun hada ido kuma ya dauke kai sai ka rantse ba kallonta yake ba.
wata yarinyarce tayi sallama ta shigo gidan,inna wuro ta kalli yarinyar lokacin da ta duqa tana gaidata
''lpy qalau indo,ya mutan gidan''
''suna nan lpy suna gaisheku''ta juya ta kalli abdallah da maryam ta gaidasu kana ta kalli mero dake qoqarin miqewa tana fadin
''amma indo yaushe kuka dawo daga kanon,gaskiya birni ta karbeki kinga yadda kika canza kika zama 'yar gayu kuwa?''.
Abdallah da maryam suka dubeta dukkansu dariya ce taso kamasu ita marysm cikin zuciyar ta ne,ina wani gayu anan,amma ita mero ganin wayewarta take a haka,abdallah kuwa sai da murmushi ya bayyana a fuskarshi yana duban yarinyar da ake batun wai ta canza din ta waye,idanun maryam yakai kansa,sai taji wani abu ya tokareta,ga zatonta su meron yakewa murmushi,ta janye idanunta a hankali tana gargadin zuciyarta.
Kama hannun indo mero tayi tana fadin ''muje waje indo''
''dan dalin fa?labaran yace tunda na tafi bai sake ganinki a dandali ba,yanzu ma shi ya aikoni na kai masa ke''bata amsa mata ba sai figar hannun indon da tayi suka fice,ci gaba sukayi da hurar wadda kusan inna wuro da abdallah ne jigon.
Kwanukan maryam ta kwashe ta kai cikin tukunyar tuwon da aka cikata da ruwa don inna wuro tuni ta hanata wanke wanken dare
ta tattare gun ta nufi soron inda suke ajjiye abun shararsu don ta zubar,soron babu haske don wearing din solar da kayi banda nan don haka bata iya ganinsu sosai,saidai tana ganin tsaiwatsu daga can qofar ficewa a gidan baki daya,muryar indo ta fara ji
''yanzu ke mero idan banda tsaurin ido inake ina wannan balaraben tsabar daukowa kai masifa da kuma jan abinda yafi qarfinka,ins laifin ma ki tsayawa labaran dinki,tunfa kina mitsitsiyarki yake sonki kuma an bashi ke,rashin kudin kayan daki ne ya hana auranku amma da tuni yanzu ai kina da yara''
''babu jan masifa,wallahi indo kada ki dauka wasa nake,da gaske sonsa nake wallahi tun ranar da na fara ganinsa,inason abdullahi sosai wallahi''
''tab,to kuwa kin debo da zafi,daidai ruwa fa daidai qurji,wai shin wannan 'yar indiyar ta gefensa ba matarsa bace,idan kuwa hakane to inake ina hada kai da ita,aradu baki fice irin aikinsu da ake kai musubirni ba,ta gurin gashi ne kawai zaku goga da ita amma ta wuceki mero,kiyi haquri kada ki wahal da kanki''.
tsaki mero ta ja
''bafulata ce kamar ni shima haka,yo to ni ina ruwana da matarsama indai shi yana sona ai shikenan,kuma ni ban taba ganin ma ta,nuna,wani abu ba sai rashin fara'a da take da ita kuma wannan halinta ne,ke koma mebe ita ta jiyo,nidai ina son abdullahi kuma bazan fasa......''
jin taku ya sanya mero yin shiru suka waiwaya da sauri,sai sukayo tairu tauru,maryam ce ke takowa inda suke ta qarasa gaban sharar tayo bismillah ta zuba kana ta juya ba tare da tace musu komai ba,zucoyarta ke mata wani irin suya,duk da qoqarin kwantarwa da kanta hankali da take kan ba son abdallah take ba don me to zata ji zafi don wata tace tana sonshi.
bin maryam suka yi da ido har ta shige cikin gidan,suka dawo da idonsu kan junansu suka kalli juna,indo yace cikin zare ido
''kinga irinta ko?yanzu gashi ta ji''cikin son nuna dakiya mero tace
''to baki ga babu abinda ta yi ba,na gaya miki ita fa babu ruwanta''harararta indo tayi
''ashe dai baki da kai mero har yanzu,wace ce zata ce bata kishin mijinta,kina kallon yadda kullum sai anje gudan mai gari rabon fadan kishiyoyi kamar zasu hallaka junansu,bakisan halin irin wadannan matan birnin bane,qila wallahi qyaleki tayi ranar da ta tashi saka ki a maqata babu mai fitar dake,ko kin manta yadda akayi da jummai ita da lantana kan mijinta?''tuno abinda ya faru din ya ruda mero tace
''wallahi hakane fa,ni ai na manta''kama hannun indon tayi qam qam tana kallon cikin gidan
''wallahi bazan koma ba ma cikin gidan,zo mu tafi''ta figeta suka fice gabanta na faduwa saboda tsoron abinda ya faru da lantana kada ya faru da ita,don a yanzun tana nan tana fama da ido daya wanda jummai ta tsiyayar mata.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Tunda nene ta yiwa malam na hayi maganar su gizago yace ta kwantar da hankalinta,ta riga ai da ta sani fada da aljani babu dadi,cikin kwana daya ya masa 'yan surkullensa ya rufe bakinsa bai kuwa sake dawo musu.
********
dukkansu suka qarewa dakin qwaya daya kallo mai azabar girma wanda aka ginashi da laka da ciyawa irin ginin qauye sosai,dukka suka dubi malam na hayi dake tsaye burgijaja cikin babbar riga da ta wadatu da maqale maqale na kayan sihiri,fuskarnam cike da suma ha hana qarya wanda yayi fiqi fiqi kamar yana barazanar tsone idon daya daga cikinsu,turo baki zahariyya tayi
''gaskiya malam nidai wanan abu yayi min tsauri,ina laifin ma asama min gida mai dan kyau ba wanann kwangon ba cikin wadancan kucakan mutanen da ake kira da mata,daga su har yaransu ni basa min,maraba da dabbobi don wallahi gwara na zauna da karnuka,da in zauna da su''ta qare maganar tana jan tsaki.
malam na hayi ya qara farashin muzuran da yake yi
''su mata na ne ke kuwa ba matata bace,matar aljani zulan anfaini ce,saboda haka babu ruwanki da wani cikin gidan nan,shi kuwa aljani ina ruwansa da wani kyawun giri,kwata kwata ke din ma ba zaki wuce wata biyu ba zakiyi naki gu,idan kuma zaman din din din kike so kuyi to sai a gaya masa,ya dauko miki gida daga dubai yazo ya ajjiye miki cikin gidan nan ki zabi wanda kike so ya maida sauran,ko kuma ya mayar da ke can bangon duniya kuyi zamanku daga ke sai shi''ido ta zaro tana ja da baya
''a'ah,ni bance ba malam kada ka jawomin salalan tsiya''
''ato,shine nima na gani ai''ya fada yana murza hana qaruarsa cikin zuciyarsa cike fal da sha'awarta,musamman idan ya dubi shigar da tayi sai yaji kamar ya janyota ya fara sha'aninsa a lokacin,zuciyarsa ke kwabarsa yabi a hankali,kada kwabarsa tayi ruwa tunda dai nan da jibi komai zai qare.
Cikin sigar lallashi nene tace
''yo banda abun zahariyya ma kwana nawa anyi an gama,ai dama bayan wuya sai dadi''
caraf adnan ya karbe zancen yana yarfa hannuwa
''ehenn,shine fa,to ni Allah na tuba ko kuttu aka ce na shiga na zauna ba shiga zanyi ba,daga fa 'ya'yan bankin sunzo fa sai yadda kaga damar yi'',hara ra zahariyya ta balla masa
''kaga idan ana zance fa ka daina sako kanka,gwara ma macen da kai''har zai hayyaqo,mata nene ta dakatar da shi don dukkansu biyayya suke mata yanzun lallaba ta suke.
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
kwana uku tsakani nenen da adnan suka rako zahariyyan gidan malam na hayi a matsayin amaryar aljani zul anfaini,babu abinda aka saka dakin face leda da katifa sai wasu qattin labulaye masu azabar nauyi da kauri wanda malam din ne ya saku su suma a dakin suka tadda shi,wai na aljani zul anfaini ne tanan zai dinga zywa gareta,buta ce kawai sai botikin wanka sai kayan sawarta akwati biyu.
sanda zasu koma ji ta dinga yi kamar ta bisu musamman da ta rakasu qofar gidan taga motarsu ta tashi bayan malam na hayi ya danqa muau 'yan dubu dubu sababbi qar na naira dubu dari uku kudin sadakin zahariyyar inji aljani zul'ainaini,ta dinga binsu da kallo suna keta duhin masara har suka bace mata,ajiyar zuciya ta saki tana jin ba dadi amma data tuna nan da wata biyi komai ya daidaita ta zama wata abar kwatance cikin alumma sai taji hankalinta ya kwanta ta juya cike da qwarin gwiwa ta koma cikin gidan.
gida ne tafkeke mai azabar girma kada ma tsakar gidan nasu yaji labari,ko ina ahimfide yake da jar qasa jazur da ita kuwa,gefe fuda bandakinsu yake mai gajeriyar katanga wadda idan kayi wani wawan tsallen ana iya hangoka,babu mamaki don ita kanta katangar gidan ma tsaf wani dogon mutum din zai kamata ya tsallaketa ba tare da ya taka komai ba,gidan tsakiyar gonaki yake,babu wani gida nan kusa da su su kadaine a gun sai dan gaba kadan bukkar da malam na hayi yake dab da wani rafi hakn ne ma yasa ake ce masa malam na hayi don sai ka hau kwale kwale sanna zaka tsallaka dan qaramin qauyen dake maqotansu inda nan din akwai mutane babu laifi.
dakuna ne rututu a jejjere kuma durqusasau kusan babu dakin,ma da ya kai nata kyua cikinsu sai qwaya daya na malam din dake can gefe guda wanda idan ka kalli dakin shi kadai sai ka dauka ba cikin gidan yake ba,gini ne sosai na zamani don hatta da bangon dakin da yar qaramar baranda da aka yi masa duka tiles ne manne da shi,alatu sosai aka zuba ciki duk da bata ganin ainijin cikin dakin amma kallo daya zaka masa daga waje ka gane hakan.
qofar bandakinsu kaca kaca da qasa da dagwalo sauran kadan ta aheqa amai tayi saurin dauke kanta,yara ne guyin guyin da mata gami da yammata gasunan ko ina tsakar gidan tamkar gidan marayu,kallo suke ta binta da shi kamar mayu manyansu da qana nanau,gefe guda kuwa yara ne zaune cincirondo guda dukakkansu babu mai tufar arziqi dan kamfai ne kawai a jikinsu daidaiku ne masu riga 'yar shar hanci kaca kaca da majina sun zuba mata idanu suna kallonta,daya daga cikin yaran ya taso daga cikin cabalbalin da suke wasa ya sheqo a guje yana mata dariya ya kama gefan rigar material din dake jikinta ruwanmadara take kuwa shatin hannunshi suka fito taya taya,batayi wata wata ba ta tsinkeshi da mari sai ga yaron a qasa warwas ya zube,da gudu wata mace cikin matan dake kallonta ta taho,hannu tasa ta dauke yaran ta janye shi gefe ba tare da tace komai ba,tayi tsammanin jin ihun kuka daga gin yaron saidai ga mamakinta ko uhm baice ba saima miqewa da yayi ya koma gun wasansa,kanta tsaye ta shige dakinta cikin bacin ran kayan da ya bata mata.
***********
tun magariba malam na hayi ya shogo ya gaya mata dokokin zaman aure da aljani zul anfaini,dole dakinta ya dinga kasancewa cikin duhu ana yin sallar magariba har garin Allah ya waye,hakanan duk abinda zata gani kada ta sake tace zatq yi magana ko tambaya a kai idan ba haka ba matsala zata biyo baya da haka ya mata sallama yace ya tafi gun iyalinshi.
wajejan sha daya na dare tana kwance cike da,azabar zafi dq sauro,ga matsanancin duhun da ya mamaye dakin,taja tsaki yafi cikin carbi,addu'a take cikin zuciyarta na bacci yazo ya dauketa kota huta,ta saba kwana cikin hasken qwai da sanyin raba kan tattausan gadonta ta lulluba cikin lafiyayuen bargo,yau sai gata cikin wani irin qadagirin daki,ko qauyensu mahaifinta basu taba marmarin zuwa ba sabida sam bata hada hanya ma da maras shi sai gata yau zata kwana cikin wani daji tsakiyar gonaki''kai neman kudi da wuya yake''ta fada cikin zuciyarta,cikin sa'a kuwa baccin yazo yayi awan gaba da ita.
Saidai ko cikakkiyar awa bata yi da fara baccin ba taji wani irin wari mai gigitarwa na ahirin tsaida fitar numfashinta,a rude ta farka daga baccin saidai nata iya ganin koda tafin hannunta saboda tsananin duhun dakin,tayi yunqurin tashi ta kasa saboda wani uban nauyi da taji samanta tare da wani irin nishi da gurnani,ta riga ta saddaqad aljani,zul anfaini ne ya iso saboda haka bata da wani saufan qarfi na qwatar kanta,haka ta koma ta kwanta daidai.
Tasha azabar da bata taba zaton shan irinta,duk da ba budurci gareta ba amma ko ranar da ta bada budurcinta wa saurayinta bata ji kalar wannnan azabar ba,tun tana ganewa har ta fita hayyacinta,bata farka ba saida hayaniya da haaken rana suka cika idonta
a hankali ta dinga bude idonta,haihuwar uwarta haka ta tsinci kanta,da qyar ta samu ta jawo rigarta ta zura,tun a yau ta fara dana sanin auren aljani zul anfaini,ta jima zaune tana tunanin me ya kamata ma tayi,idanunta suka sauka kan wata baqar leda,maiqon da taga tana yi ya sanyar janyota,kaza ce gasashahiya ciki,ture ledar tayi don bata ko burgeta ba,ganin babu sarki sai Allah donko dan tsakin gidan bata ga ya leqota ba ya sanyata miqewa din ta nemi,bandaki,don hatta da jikinta irin doyin jiya da daddare taji yana yi.
Ta fita kanta tsaye tana dingisawa,tun daga nesa ta hango dogon layi babu babba babu uaro kowa yabi,qofar bandakin suke fuskanta kowannansu da botiki wasu da qwarya wasu da kwatanniya cike da ruwa,bata damu ba ta durfafi qofar bandakin tana da niyyar shigewa,ji tayi an fincikota baya cikin wata iriyar dakakkiyar murya
''ina zakije?''waiwayowa tayi don ganin wanda ya mata wannan cin kashin,mace ce saidai idan baka lura da kyau ba zaka iya kiranta da namiji,a murde take,hakanna a tsaye take qyam,idan banda qirjinta da qudundunanniyar sumar kanta babu abinda zai nuna maka cewa ita maca ce,ba shiri ta hadiye tsiwarta da ta qunso ta sanyaya muryarta don ta fuskanci a banza matar zata dakata
''bandaki zan shiga''wata iriyar ashar da duk duniyancin zahariyya bata taba jin irinsa ba matar ta qundumo kana ta dora
''dan uwarku duka wadan nan da kika gani a gun ba mutane bane,duba har da yaran da,basu wuce shekara biyar ba kowa sai yabi layi,saike wata gundumemiyarki da ke zaki wani taho gandan gandan wai ke zaki shiga bandaki,to sai ki shiga mu gani''inji matar tana muzurai.
Ran zahariyya ya baci,tana ganin kamar ita za'a yiwa haka,tsaki ta ja kana ta juya karo na biyu da niyyar shiga bandakin,bata kai qa ida nufinta ba taji an fincikota an watsar take ta samu masauki cikin tabo da dagwalin dake kwance gaban bandakin,cikin tashin hankali ta dago don ganin wanda ya mata wanann danyan aikin
wata figigiyar matashiyace wadda gaba daya jikinta idan banda fata da jijiya babu komai,sai uban qashi a fuska,kallo daya zaka mata ka tabbatar cewa yunwa ta samu gindin zama a jikinta,tsoro da kunya suka hanata cewa komai haka ta miqe tsamo tsamo ta koma dakinta,dariya taji sun rude da ita muryoyi daban daban babu dadin ji yaransu da manyansu,wani baqinciki da bacin rai take ji ya shaqe,duk yadda takeji da rashin arziqi amma wai har yau za'a samu mai taka ta?,malam kawai take jira ta sauje masa kwanson tsiya,sam bazaiyiwu ta zauna cikin irin wannan qasqancin ba,ai neman kudi ba hauka bane,kuma ita ba matarsa bace bare ta shiga sahun irin rayuwarsu.
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Kamar kowanne maraice da suke qare shi gaban qoramar bayan gari yauma haka ne,saidai yau kam akwai banbanci domin,kwanaki uku kenan suke wasan buya da mero,koda wasa taqi haduwa da maryam saboda tsoro da kunyarta,sau daya da safe maryam ta fito ta tadda meron zaune bakin rijiya ta zubawa qofar dakin su ido suka hada udo,kallon da maryam ta yi mata yasa ta miqewa cikib hanzari da kame kame ta hau yin wanke wanken da dama shi zatayi ta zauna zaman kallon dakin,idan ta zo da safe ta yiwa inna wuro aikace aikacenta a gurguje take barin gidan duk da yadda har yanzu zuciyarta taqi yadda ta rabu da abdallah,batajin zata iya ci gaba da rashin ganinshin.
Material ne ajikinta mai santsi milk ne da adon manyan fulawoyi ash colour,dinkin bubane da ya saukar mata har qasa tayi rolling har zuwa kafadarta da mayafi cotting ruwan madara,yadine tissue a jikin abdallah light blue dinkin boda gajeriyae riga iya gwiwa,ba qaramin kyau yayi ba cikin yammacin,wani lokacin maryam kanyi mamakin yadda fatar abdallahn ke qara kyau tamkar ba cikin qauye yake ba,ta alaqanta hakan da yadda weather din garin ke da kyau da ni'imtarwa.
Kamar kowanne lokaci garin a lullume yake,a wadace da korayen tsirrai,a hankali suke tafiya,jinta take kamar wadda kasala zata lullube,shiru suke tafiya hakanan a hankali,abdallah na sake nazarin qauyan,shiru hanyar tasu take yau fiye da kullum,babu gilmawar mutane kamar ragowar kwanakin,duk dama ba hanya ce ta jama'a ba.
''haqiqa Allah mai hikima ne baiwa da kuma cikakken iko,babu shakka Allah ne kadai masanin sirruka da boyayyun al'amura,wannan garin ya amshi sunansu babu ko makawa,a koda yaushe na wayi gari,cikin qauyen nan nakanyi duba izuwa tarin ni'imomi da baiwa da Allah ya musu,hakan yake sake sakani,cikin sakankancewa da iko da isa ta ubangiji,nake sake nisa da nutsuwa gun miqa qoqon bara ta agareshi,tabbas na yadda babu makawa Allah na ji kuma akwai lokacin da zaya bude min gaba daya qofofin ni'imarshi''shiru maryam tayi na saurarensa
sassanyar ajiyar zuciya ya saki shima yana kin kasalar na saukar masa.
''maryam''ya kira sunanta cikin wani irinsalo da ya qarasa kashe mata jikinta gaba daya,hakanan taji bakinta ya mata nauyi ta gaza amsawa
''maryam.....sai yausge zaki bawa zuciyarki dama ta bayyaba abinda yake cikinta?,sai yaushe zaki bata dama yaushe zaki bata 'yancinta?''
gaba daya sai ya qarasa qulle mata duk wasu qofofin qwaqwalwarta ta shiga kai kawon nazarin maganarsa,bilhaqqi da gaskiya ya sake tubudata cikin wani duhun ne,meke cikin zuciyar tata da yake tambayarta ta bata 'yancinta a kansa?,bata kai ga warware qullin ba ya sake jefo mata wata tambayar.
''maryam,sona ne maqare cikin zuciyarki,so na ne yake hanaki sukuni duk lokacin da na kadaice da mero,so na ke saka ki cikin yanayi na kasala da mutuwar jiki,me yasa zaki takureshi a muhalli guda ki hana shi fitowa inda ya dace?''ya waiwayo yana dubanta tare da qoqarin kallon qwayar idanunta
bugun zuciyar ta ya sake yawa,tayi gaggaqar cire qwayar idonta daga cikin tasa ta maidata gefe wani abu na taba zuciyarta,me yasa abdallah ke mata haka ne,ko yaushe rauninta yake son gani kuma bata jin zata barshi ya gani din
zuciyarta ke qarfafarta ta qaryata batun abdallah,cikin muryar da ka mata dogon nazaei qwaya tal zaka gano akwai wani abu mai qarfi cikinta tace
''kada ka soma bari zuciyarka ta dora ka akan keken bera,don ko digo babu wani abu mai kama da so cikin zuciyata game da kai,ko ka manta abdur rahim ta so shi kuma ta aura a zatonta?,saboda haka babu so tsakanina da kai kaima ka sani''.
dan guntun murmushi ya saki sannan yace
''irin wanna karsashi da jurumtar na maryamu na dade ina ganinshi cikin idonta tun tana a matsayin kukun abdallah a gidan mami,saidai wani abu guda da bata sani ba,ta dade da makarowa,tun ranar farko da taga abdallah ta fada tarkon sonsa,duk da jarumtar boyewar da take amm is too late don abdallah ba a iya boyemiahi ire iren wanann abubuwan,don ya saba ganinshi cikin idanun 'yan mata daban daban,amma fa wani abu daya da maryam bata sani ba,abdallah shima ya fara sonta ne tun lokacin da ta fara sonshi,sunso juna a rana guda lokaci guda a guri guda a kuma sakanni guda''.
Gaba daya ilahirin jikinta ya kama rawa har ta gaza ci gaba da rura wheelchair din,wanne tonin silili abdallah ke son yi mata,saidai sam na zata bashi dama ya riga zare mata duk wata laka da qwarin gwiwa dake jikinta ba yadda yaga dama,don haka ta ttara sauran dukkan wani karsashi nata
''idanunka da zuciyarka sun maka qarya abdallah,ban taba sonka ban taba sha'awar na qaunaceka ba ko ka manta da bakinka kasha fadan ba kowacce mace ta dace da kaiba?bako wacce mace ta cancanci ka sota ba,nasan naso abdur rahim amma ba kai ba kuma bana sonka,bana sonka bana......''
idanunshi a rufe suke yana jin saukar maganarta,sukan zuciyarshi take da wani abu mai kaifi ba tare data sani ba,duk da zuciyarshi na qaryata duk wata magana dake fitowa daga bakinta saidai bai son jin furucin sam,sannu kuma kishin abdur rahim mai qarfi ya fara shigarsa,sanadiyyan katsewar maganarta shine fincikota da yayi ta dire a gabanshi,rashin qwarin jikinta ya sanyata zubewa a gaban nashi.
Murmushi ne kan fuskarsa wanda ko yaushe ke fidda sigar kyawunshi
''banyarda baki son abdallah ba sabida na jima da ci miki alwashin sai kin soni,alhmdlh ban zama looser ba ni nayi nasara,but now ina mai qara tabbatar miki sai son abdallah ya ninku cikin zuciyarki fiye da da,i promise''ya fada yana miqa mata qaramin yatsanshi alamar su qulla,ba tare da jinkiri ba ta miqa masa suka qulle kamar yadda yara keyi,shi ya dagata da kanshi ya kade mata jikinta kana suka ci gaba da tafiya.
suna tafe yana murmushi,raguwar kuzarin jikinta kawai ya isheshi amsar tambayarsa,sai da suka qara mintinan da suke yi akan nada kafin su isa ta ajjiyeshi inda ta saba,qur'aninsa ya ciro gaban aljihunsa don kwana biyu da suke tahowa su kadai da alqur'ani yake tahowa,yana yin tilawa kuwa mai yawa kafin su koma,wucewa tayi gurin da ta saba zama kamar ko yaushe ta zauna.
ta daga idonta take ta hango shanun su baffa da kwana biyu bata ganinsu,murmushi ta saki don sun kwana biyin basu gaisa ba,ciro qafafunta tayi ta karkade jikinta bayan ta miqe ta maida takalmanta ta fara tafiya,daga idonshi yayi a hankali ya bita da kallo,yana lura da yadda ko yaushe idan sunzo idonta na tsallaken rafin bai san meke burgeta ba a gun.
kamar ko wanne lokaci daga baya ta tsaya bata shiga cikin shanun ba sai baffa ne ya isketa,tamkar wadanda suka ahekara tare haka suka dinga hirarsu,ta tambaya kwana biyu bata ganin fitowarsu yace eh mai gida ke fidda zaka cikin dabbobin nasa to sai jiya ya kammala shi yasa sai yau suka fito
ba tare dafa tambaya ba ya ciro wani mazubi mai kyau ya fara tatsar mata madara
''mai gida yace duk sanda ka zo a baka,yana ta tambayarka ma''tayi murmushi tana fadin
''Allah sarki na gode kuwa baffa''ta miqa hannu ta karbi mazubin tayi bismillah ta fara sha
''kisha ahankali idan bai isa ba ma sai a qara miki''taji muryar daga gefanta na gada,ta daga kanta ahankali,mahmud ne yauma cikin shigar kufta,murmushi ta danyi kana ta ja baya tana fadin
''ina wuni''ya amsa mata da ''lafiya lau,tun rannan kuma sai kika bace abunki ban sake ganinki ba''
'?eh wlh ta amsa masa a taqaice tana rufe mazubin ta miqawa baffa
''baffa gashi na gode ni zan wuce''
''a'ah,jeki da shi meramu,duk lokacib da kike so kizo da shi sai a dinga zuba miki ciki''godiya ta masa don abun ya mata kyau,dan mazubi ne maikyau irin na fulani
''zaki gudu kenan kam irin na rannan?''ya tambayeta yana dan dada sauri don su jera tare
''a'ah,bani kadaice bace na fada maka,da yayana kuma mijina muke tare''ta fada cikin rashin sakin jiki
dariya ya saka
''wai ni zaki yiwa wayo,don kin fuskanci na yaba ko?''
kai ta girgiza idanunta a qasa
''da gaake ni matar aure ce''
''nima mijin aure ne''ya maida mata amsa cikin maida maganar wasa wasa,ganin da gaske yaqi yarda din ya sata tsayawa da tafiyar da takeyi don sun,kusa da inda abdallah yake bayan ta rage fara'ar fuskarta sosai
''idan baka amince ba muje ka ganshi da idonka,amma ka fara yin gaba tukun yana nan zaune akan kujera idan yaso sai na biyo bayanka''.
kafada ya daga kana yace
''is ok,bari nayi gaban,amma da sharadin idan qarya kike zaki amshi soyayyata''
kada kai tayi kawai ba tare da tace komai ba idanunta suka sauka kan abdallah zaune kan kujerarsa a gabansu,mamakin yadda ya iya kawo kanshi tayi,sai ta dubi kujerar wasu abubuwa guda biyu ta gani gefe da gefe bata taba kula da su ba wanda bisa alamu da su ya tuqa kanshi.
Kallo daya ta yiwa idonshi bata sake marmarun kuma kallonsu ba,ya kalleta ya kalki mahmud sai taga ya danna wani abu,rivearse kujerar tayi da kanta kana ta saita hanya ya soma tafiya sannu a hankali
''ko baki fada ba nasan shine mijinkin,kiyi haquri don Allah,wlh harga Allah ban dauka da gaske kike ba''mahmud ya fada cike da damuwa
a gagguce ta gyada kai bata samu cewa komai ba ta biyo bayan abdallah.
*mrs muhammd ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[2:00pm, 9/29/2017] Huguma👑: [11:46am, 9/29/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
5⃣0⃣
👁👁👁👁👁👂🏾👅
*_shin ka/kina lura kuwa 'yar uwa?,kin fuskanci kuwa yadda kwanaki keta zura gudu abinsu?,kinsan me hakan yake nufi a gareka/ki?,tamkar gaya miki suke kifa shirya kina kusantar kabari ne,ki shirya kina kisantar ajalinki,ki shirya kwanakin ki na duniya da aka diba miki na qarewa_*
*_daure ki aikata mai kyau don ki tarar da me kyau,babu yadda za'ayi ki shuka qaya kice inibi kikeson cira,duk fitar numfashinki daya daidai yake da kusantowar ajalinki,yadda idan second guda ta kubuce miki har abda bazata dawo ba haka ajalinki idan yazo daidai da qiftawar ido Allah bazai barki cikin duniya ba,to don me zaki batawa kanki lokaci kan cutar da wani?,don me zaki damu kanki da ababan duniya,duniyar da take wulaqantacciya?,duniyar da Allah yace bata kai qima da darajar da girma daidai da na fukafukin sauro a gurinsa ba,saboda me zaki shagala kin manta ki daina tuna mutuwa,bayan kina da yaqinin tabbas/lallai/babu makawa sai kin muyu kamar yadda kika ga wasu sun mace kema wataran haka ne,komai qararre ne banda zatin Allah,ya ubangijin kowa da komai ya mai rahama da tausayin bayinsa kasa muyi kyakkyawan qarshe,mu mutu muna kan tafarkinka na gaskiya_*
*ALHAMDULILLAHI ALA NI'IMATUL ISLAM*
*_kafin na fara shafin nan ya zama dole na gaisar na kuma miqa godiya ta ga masu aiko da saqonninsu gareni,saqonninku sun ishemin,ina muku fatan alkhairi naji dadi qwarai da addu'o'inku,abinda kuketa roqamin na alkhairi ina fatan Allah ya sanyaku ciki kuma_*
*ummi jos*
*mrs tafida*
*haulat m badamasi*
*Aisha kanyah*
*ummu zainab*
*sis rabi'a*
*jammy jammy zbi group*
*zahra hari zbi group*
*na gode Allah ya bar zumunci da qauna*🙏🏽
Cikin kwana goma sha hudu da zahariyya tayi cikin gidan ba qaramar dandana kudarta tayi ba,sauqinta daya malam na hayi ya tsawatarwa iyalin nasa bayan bore da tayi ta samu sauqin abubuwa,saidai babu mai kulata ci kanki babu mai ce mata,ita din ma bata damu ba domin ta dade da raina ajawalinsu,tana ganin babu wadda tayi isar da zqtq rabe ta balle mu'amala ta hadasu,banda neman biyan buqata daya tilasta ta zama cikinsu ba su isa ta zauna da su ba har wata guda,ba don suna waya da nene ba tana tausarta ta tabbatar da tuni ta jima da cika bujenta da iska,wuyar ta isheta,kullum dare kwana ake ana abu daya ita da aljani zul anfaini,ga masifaffen wari da take ji jikin aljanin wanda kullum yake sata tashi da amai da ciwon kai
Dadin bakin neme da lussafin da tayi na saura sati biyu ta bar wanann zaman shahadar,saura sati biyu ta zama mai arziqi irin aezuqin nan na kwatance na gayawa sa'a yasa ta danne taci gaba da lissafin
********
Misalin sha biyu ne na rana wanda ko ba'a fada maka ba kasan lokaci ne da rana ke kan ganiyar zafinta,bare rana irin ta qauye da take budewa sosai saboda wadatar fili da suke da shi,tana cikin dakin amma ji take kamar tayi hauka,ta riga da ta saba zama cikin a.c ko yaushe,rufin dakin na langa langa kawai ya taimaka wajan qaro dumamar zafin ranar zuwa cikin dakin
tsaki ta ja tana goge gumi
''kai,Allah ka tsinewa talauci,me za'ayi da talauci don Allah,Allah ka nuna cikar sati biyun nan nayi na gama wannan aikin na san inda dare ya yimin,ai wlh ko a hanya bazan bari mu hadu da talauci ba,zamana nan gidan kawai ya qara fito min da illarsa qarara wadda a baya ban sani ba,haba wannan azaba dole ne ma fa kasona cikin dukiyar abdallah tafi yawa idan mun karbe wallahi''ita kadai take sumbatu cikin dakin,vest,ce kawaia a jikinta doguwa har zuwa gwiwa amma ji take kamar tayi tsirara
kallo daya zaka mata kaga yadda fatarta tayo baqi ta kuma rame a hakan ma wai aljanin mujinta na dauke mata abinci irin wanda ta saba ci yake kawo mata,ta kuma jan tsaki ta gyara kwanciyarta kan katifar ta don dama ikin kenan,idan ta kwanta irin haka ko sallah saidai ta yi maja ta hadeta baki daya
Karo na farko taji ana qoqarin dago jibgegen labulen dakin da ya qara sawa dakin duhu,kanta ta dago don ganin waye,domin bata taba ganin wani ya rqbo bakin qofar dakin nata ba idan ka dauke malam na hayi
siriryar macace wadda a kallon farko zaka gane sanda duniya na damawa da ita fara ce,wuya da yunwa suka maidata baqa baqa duk da akwai sauran haskenta,tsugunnawa tayi gefan zahariyya da ta zuba mata ido tana kallonta bayab tayi kicin kicin da rai,murmushi matar ta saki wanda ya bayyana jerarrun haqoranta da suka dafe
''sannu amarya,dama zuwa nayi na gaya miki ki fito yau zaki amshi girki''
Ba shiri ta miqe zaune daga kwanciyar da take a dazu,ckkin sake hade girar dama data qasa tace
''ke malama,bana son hauka,wa ya gaya miki ni matar gidan nan ce?,akwai abunda ya kawo ni zama nan kuma nan da sati biyi zan bar muku wanann dajin naku''
murmushi ta gani matar ta yi har da dan darawa kadan
''Allah sarki,ina zaton azal din data hau kaina kema ita ta hau kanki''cikin raahin fahimta take dubanta,daga bisani ganin matar bata da niyyar cewa komai ta kafe zahariyyan da ido yasa ta tambayeta
''kamar yaya?''ajiuar numfashi tayi,wannan karon zama tayi dirshan kan ledar dakin
''malam ga aureki ba tare da sanin cewa shi kika aura ba ko''
''inji uban wa?,ni ba malam na aura ba,aljani zul'anfaini na aura,kuma ina sane,kada ki zomin da maganar banza,malam din da sai da safe yake leqoni mu gaisa ko ya kawomin saqon aljani''
dariya ta subucewa matar sai da tayi iya yinya kana ta tsagaita,zahariyya bata samu faragar tsaidata ba don kanta a qulle yake tamau
qasa qasa tayi da muryata kana tayi yan dube dube don tabbatar da babu wanda yake jinsu
''akwai wani aljani ne bayan malam na hayi?,ai malam shine aljani,zul'anfaini yana biyo dare yana turmusheki da sunan aljani,dalili,kenan da ya kafa miki sharadin zama cikin duhu daga magariba har gari ya waye''
tsawa zahariyya ta daka mata jikinta ya soma bari
''ke malama,banasom hauka don na fuskqnci duka jama'ar cikin gidan nan kamar daga gidan mahaukata aka debo ku''
murmushi fa kuma yi
''kema din kwana nawa ne kinbi sahu,badai kin gama kwana goma sha hudunki ba,ki fara duban hanya to''daga haka matar ta miqe tana niyyar ficewa,ganin indai ta fice din kuma babu lallai zahariyya ta sake samun wasu bayanai ba tunda babu da wanda take magana hakanan babu wanda ke magana da ita ya sanya ta riqo gefan daddaudan zaninta
''ya zaki sakani a duhu kuma ki tafi,don Allah zauna kimin bayani mana''sai data qarewa zahariyyan kallo na kusan minti biyar har taji ta tsargu sannan ta koma ta zauna inda ta tashin
''suna na habiba,ni nan da kika ganni ada yadda kike haka nake koma nace na fiki''cike da mamaki zahariyya ke kallin habiban wadda babu mugumin da zai kalleta baice mahaukaciya bace
''mamaki kike,to ki daina mamaki don kema lokaci kadan ya rage ki koma kamar mu,ba kanki malam ya fara haka ba,'yar gata ce ni gaba da baya,don gaba daya a buja muke zaune ni da iyaye na,haka da na tashi aure ma acan nayi aure na,na auri mijina mai kudin gaske saidai na taddashi da matarsa da yaransa uku,matarsa fatima sam bata da fitina,duk yadda taso mu zauna lafiya fur naqi,burina kawai shine na koreta daga gidan na mallake enginer abubakar,iya adalci yana nina shi tsakaninmu babu zalunci tattare da shi,wani abun ma haqqinta ne fatima amma zata ce ta barmin sabida haqurinta da kawaici,duk inda nasan zan samu malami da zai mini aiki na kutsa kai na sai dai babu nasara,sabida fatima irin matan nan ne masu yawan azumi duk litinin da alhamis bai wuceta,haka tana da yawan salla musamman ta dare,don nasha tashi aiwata da mugun nufina a kanta sai na taddata tana sallah,haka karatun alqur'ani,kafin ka samu fatima kan wata tasha ba saudi qur'an ba kai da wuya,amma hakan bai isheni iahara ba,da yake bata da haqqina Allah na tare da kta kuma yayi nufin kareta sai muka samu labarin malam na hayi
Babu bata lokaci muka shirya ni da mahaifiyata wadda ita ke taya bera bari na yiwa enginer qaryan zamu kano ziyarar yan uwan mama duk da salinmu ba kanawan bane yan katsina ne ya sani amma baice komai ba ya amince ya barni,har da bani kudi nayi tsaraba,har bakin mota fatima ta rakoni tasa yaranta na min a dawo lafiya amma ko kallo basu isheni ba muka taho,tun zuwan mu na farko yaci ace idan da ni mai rabo ce na gane inda malam na hayi ya dosa saboda kalamai da hanyoyin da riqa bi da ni neman biyab buqatarsa amma na kauce na qiya,qarshe ya harhada min duk wani abu da zan aiwatar cikin gidan muka taho bayan iyayen kudi da muka zube masa,amma wani abu da ya bani mamaki tsakanin fatima ko 'ya'yanta babu wanda yayi ciwon kai bare na sa tsammanin wani mummunan abu zai faru da su,ta tsaya tsayin daka wajen yiwa yaranta addu'ar tsari,hakanan lokuta da dama zaka ga ta cika botiki da ruwa ta musu tofin ayoyin tsari ta sa musu a frigde shine ruwan shansu duk da ruwan roba da mahaifinsu ke cika mana firizai da shi
ko cikin dare udan ta farka duk da ba dakinsu daya da yarqn ba sai ta leqa dakinsu ta tofa musu addu'o'i take komawa nata dakin nasha ganinhakan da idona,to duk abuna musulma ce ni kuma masan addu'a takobin mumini ce nice dai nasa qafa na shure,na tabbatar bazan nasar a kan fatima ba don,haka hankalina ya tashi ba bata lokaci muka sake dawowa,ashe zuwan tsautsayi da qaddara mukayi
cemin yayi kada na damu akwai wani abban aljaninsa da zai bawa kwangilar aikinsu fatima amma shifa ba biyansa ake da kudi ba,ana biyansa ne ta hanyar auransa na wasu satitika ko watanni,da fari tuburewa nayi ganin da akwai auren enginer a kaina,amma da dadin baki malam ya ciyo kaina yace sati biyu kacal zanyi zaman auren ina komawa gida na zan taras buqata ta biya,nace ta yaya za'ayi mikina ya barni nayi tafiya har ta tsawon sati uku,wani garin magani da wasu layoyi ya,bani yace na samu dutse cikin gidan mu qato na daga qasanshi na saka na danne,yadda na danne layoyin nan haka engineer zai kasa min musu duk sanda na tambayeshi,haka kuwa akayi baice komai ba face Allah ya kiyaye hanya sai na dawo
satina daya cikin gidan ina wahala don ban saba ba sam,cikin daula na tashi haka cikin gidan mijina ma,amma da yake son zuciya da son duniya ya rufemin ido na daure a haka har nayi kwana goma sha biyu,kamar irin wannan lokacin da na zo miki haka daya daga cikin matansa tazo min da irin maganar da nazo miki uadda kika yimin haka nayi mata nima,yadda na zauna na baki labarina haka ta bani labarinta ita din ma duk kusan hakane,saidai ita maganin mallaka tazo ta karba,mallakar ma ra saurayi,saidai ita tasan malam ne zai aureta don yace wani rubutu zai dinga yi a alqalaminsa yana wanke mata acikinta,ta gayan har yau ta kasa kubuta daga gunsa,na fiki shiga tashin hankali sabida tuno mijina da gidana da iyayena da nayi da yarona qwaya daya da na haifa yana gida hannun fatima tace zqta riqe minshi har na dawo
Na fita da niyyar guduwa daga gidan saidai kinsan me?,wuni nayi ina shawagi cikin duhun masada da na dawa,an qullemin kaina tamau na rasa hanya,duk inda na kewaya ina tsammanin zai fita sai inga na dawo gidan nan,daga qarshe da duhun dare yamin babu wanda ya neme ni haka na dawo,kwana na bakwai ina wannan wahalar cikin gidan babu wanda yace min ci kanki hatta da shi malam din haka zan gama walagigi na na dawo,daga qarshe na tabbatar bazan iya kubuta ba haka na dawo naci gaba da zama na fawwalawa Allah lamura na,ina zaune cikin uqubqar malam din,matansa mu goma sha hudu ne kowacce tana da rana daya a matsayin ranar girkinta,yaransa guda hamsin ne,wasu suna nan tare da mu wasu sun watsu duniya,nima haihuwata uku da shi suna mutuwa yanzu haka yaronmu daya da shi shine wanda kika mara rannan kaltime ta janyeshi,mamata kuwa ban kuma jin duriyarta ba,wani abun ya manta ta manta ni ko itama kasa gane gidan tayi Allah masani''ta qarashe maganar cike dq dacin rai da danasanin butulcewa ni'imar Allah da tayi,ta kasa zama lafiya a gidan aurenta bayan babu abinda ta rasa,dama ance idan baka godewa ni'imar Allah ba ka godewa azabarsa.
Tuni har zahariyya ta saki fitsari a zaune,gumin da take kuwa tuni ya ninka na dazu,ta tabbatar idan da za'a auna jininta banu makawa za'a ga ya hau over ma akuwa
taya za'ayi ta zauna da wulaqantaccen mutum kamar malam na hayin
Tayaya zata yarda ta zama mallakarsa,wallahi bazai yiwu ba''ta fada qarfi kuma a fili tana miqewa ta fara hada akwatunanta
kallonta habiba tayi
''wai me kike shirin aiwatarwa''a fusace kuma cikin ficewar hayyaci
''wallahi sai na bar gidan nan ko da me malam yake taqama din ni ba kalarsa bace,kudin ma raina muku wayau yayi''dariya habiba tayi
''duk yadda kike jin isa taurin kai da kafiya na fiki,malam mutum ne da baisan kalmar imani ba bare tausayi,ina mai baki shawara ki haqura ki maida lamarinki ga Allah ki roqeshi,watan wata rana idan da rabo kowa sai Allah ya kubutar da shi,amma,ina mai tabbatar miki koda kin fita ba zaki iya tsira ba,idan kuma baki yadda ba kina musu bismillah''daga haka habiba ta miqe ta gyara daurin zaninta ta fice
ko kadan zancan habiban bai shiga kunnuwanta ba don haka bata fasa shirinta ba,ta hada kayanta ysaf ta canja kayan jikinta ta jawo akwatunanta tayo tsakar gidan,da ido suka bita duuu kamar ko yaushe,wanann karon sam bata damu da kallonsu ba burinta kawai shine ta ganta ckkin gidansu
Cak ta tsaya a qofar gidan tana wara ido,ruwa ne a gabanta yake ta qugi iya ganinta,,duk hanyar da zata bi ta wuce ta zam hamshaqin kogi wanda ko da kwale kwale zaiyi wuya ka iya tsallakeshi don har wani murdawa igiyar ruwan take,duk lokacin data yi taurin rai ta tunkari kogin ta yunqura dan shigewa ruwan sai yayo ambaliya yayo,kanta tilas ta koma da bay
ta shafe fiye da awa biyu a gun tana abu daya daga qarshe ta gaji ta faahe da kuka don ta fara ganin alamun maganganun habiba
zubewa tayi a dandaganyar gun ta saki kuka tana addu'ar Allah yasa mafarki take,ya rayuwa zatq juya mata baya haka lokaci guda ba tare da ta shirya ba,dabara ta fado mata ta dauko wayarta ta soma lalubar nene don neman daukinta
Daidai lokacin da nene da adnan ke tsaye cikin daki cike da tashin hankali sakamakon waya da muugu yayi wa maman kan ta taryi zuwansa,kuma kada ta taba darsawa aranta zata gudu duk inda suka shiga sai ya bincikota kuma babu shakka kasheta zaiyi
''yanzu adnan meye abunyi?,meye abunyi?,na kikkira malam wayarsa bata samuwa,babu shakka aikin da yayiwa muugu ne ya warware''ta fada cike da tsananin tashin hankalin,shi kansa adanan din a tsorace yace don har yau bai warke ba daga bugun da suka masa,jikinsa na rawa yace
''don Allah mama ki nemo kudinsu ki basu kawai mu rabu lafiya,wlh basu da imani mutanan nan sun saba da kisa fa''
cikin jin zafi take kallinshi,saida ta zageahi sanann tace
''fashi da makami kake so na far ko karuwanci,a ina zan samu wata miliyan biyu?''
''yauwa mama''ya fada da sauri yana dubanta
''ki cewa hajiya bintu ta baki mana bana ko kokwanto akwai a hannunta''
''mtsweew,wlh bansan na haifi jaki mai toshashshiyar qwaqwalwa ba sai yau,ina cewa a gabanka malam ya gaya mana kada mu sake magana ta qara shiga tsakaninmu,ni ko kai ko zubaida idan ba haka ba asirin da yake jikinta zai karye?bacin haka ma kwananta nawa bata cikin gidan nan ni da kai duka babu wanda yasan inda ta tafi?,kuma wa'adin cikar aikin zahariyya har tau bai cika ba saura sati niyi bare mu sa ran samun wani abu''
''gashi babu company din da muka karbe qwaya daya dake aiki yanzu bare mu samu cikinshi,duk a qulle suje mun cinye duk wata dukiya nene dake ciki''ya fada yana kallon nenen da ta kasa amsawa sai ido ta take binsa da shi cikin damuwa
shiru yayi cike da tsoro
''to nene ko gwalagwalan su zubaida zaki karba ki bashi ya saida,idan yaso muji nawa zamu cika masa''
''haka za'ayi''ta fada cikin rawar jiki tana barin dakin ya rufa mata baya
ta tura qofar dakin ta shiga babu kowa ciki saidai tana iya jiyo kakarin amai cikin toilet dinsu,da sauri ta qarasa bandakin,zubaidan ce tsaye gaban sink tana ta faman kwara uban amai,cak nenen ta tsaya tana mata kallon tuhuma har ta kammala ta kuskure bakinta ta juyo
''zubaida me nake gani?''
ta tambayeta cike da tashin hankali,ko kadan zarafin da ta shiga na kwanakin nan yasa bata samu damar zama agida bare ta qarewa zubaidar kallo,ta dashe tayi fari ga cikinta da ya fara dan dagawa kadan,kallo daya tak mai hankali zai mata ya bawa kansa amsar ciki ne da ita
fuska ta yatsina tana kallonta tare da qiqarin boye cikin
''wlh nene nima bansan me yake damuna ba''hannu ya saka ta daki cikin jikinta tace
''don uwarki don ubaki tsinanniya ga abunda yake damunki nan''take zubaidan ta durqushe tana dafe da cikin hadi da cewa ''wayyo Allah na''nenen bata damu ba ta finciko ta sai ganinsu adanan yayi tana janye da ita bata saurara mata ba taci gaba da janya sai da ta kawota har falon qasa kana ta watsar da ita
''don uwarki sai kin gayan wanda ya miki cikin nan,shegiya tsinanniya mara amfani,gwara na kasheki na kashe banza bani da asara,cikin shege a jikinki zubaida''ta kai mata duka ta kuwa sameta,qara zubaidan ta saki wanda yayi daidai da shigowar kira a wayarta
a niyyarta ta cilla da wayar sabida tashin hankalin da ta fada amma ganin sunan zahariyya yasa jiki na rawa ta daga tana fadin 'yar albarka
komai sai ya tsaya mata cak jin bayanan bakin zahariyyan data yi wanda tana kuka tana zayyane mata,bata ma gama ji ba ta dakatar da ita tana fadin
''gani nan zuwa har gun malam din,shi ya isa shi din banza,a kaidina baisan komai ba yau zai sani''qita taji wayar ta katse haka zahariyyan taji,tana dubawa taga kudinta ne suka qare haka wayar ta soma warning na battery low,dama a power bank dinta da ta taho da ita take chargyn tunda ko sau daya bata taba ganinsu da wutar lantarki ba,kai ko igiyoyin wutar ma babu a ina ma zasu samu suna dajin Allah?,tana ji tana gani wayar ta mutu,hannu ta dora aka ta saki wani sabon kukan ta kife kanta tsakanin cinyoyinta
Sau uku nene na trying na kiranta sai ace mata is switched off,tilas ta haqura ta kalli adnan
''muje adnan gurin malam,wani bala'in yake son jawo mana''adnan ya zaro ido don shi,kam ya gaji da jin wannan bala'i kala kala har yau kuma babu sauqi,zaiyi magana tace
''kame bakinka muje koma mene kaji a mota''ta juya ta kalli zubaida dake durqushe
''ke kuma idan ba shirya barin duniya kika yi ba to ki nemo wanda ya miki ciki tin kafin na dawo na aikaki lahira''ta kaimata mari tana sake tsaine mata ta kuwa sameta akuncinta,dafe kuncin tayi tana fidda qwalla ba don komai ba sai don azabar zafin marin
''ga wanda yamin cikin nan''taji zubaida ta fada,ta dago kanta daga qoqarin sanya mayafin ta da take tana duban inda zubaidan ke nuna mata,saura kadan numfashinta ya dauke sakamakon ido hudun da sukayi da muuugu da yaranshi,fuskarnan yadda kasan wanda ya dauko saqon mutuwa a hade take tsaf,abu biyu zuwa uku ne suka daki zuciyar nene lokaci guda,kudinsa da yazo karba wanda a yanzu bata da shi bata da shi bata da dalilinshi,na biyu cikin da yake jikin yarta wai nasa ne?,na uku yadda taga sun cukuikuye adnan ko cikakken numfashi baya shaqa
sakin adnan din sukayi yaci qasa kana ua tako a hankali gaban nene yana jujjuya wuqar dake hannunshi,batason ta nuna masa tsoratarta don haka ta tattaro yar mitsitsiyar dauriya ta dorawa fuskarta don bata kai zuciyarta ba,hannu ya miqa mata,sai ta kalleshi sheqeqe
''me kake nufi?''dariya ya kece da ita wanda har hantar cikin nene sai data kada balle adanan da ya dade da sakin gudawa,don b qaramin tsoron mutuwa yake ba arayuwarshi
''banda ke mara mutunci ce har sai na miki bayani ma,zan mkki bayani amma ki tabbatar a bakin rayuwarki''
ta tsorata ainun amma sai ta fara masa haukan qarya
''banda kai matsiyaci ne baka da kunya ko misqalazarratin,ka dirkawa diyatq ciki sannan kuma kace na biyaka wadansu kudade,to wallahi na fika iya iskanci,baka isa ba''
Daya dagq cikin yaransa ya matso yana fadin
''ke hajiya ki iya bakinki,ai dama kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa,bamu da mutumci kamar yadda ke ma baki da shi don babu mai mutumcin dake hada sabgarsa da mu''
''kai yaro dakata a haife na haifeku gaba dayanku,to wallahi duk ba tsoronku nake ba,kudi ne bazan biya ba kuma ku saurari sammacin kotu sai nayi shari'a da kai kam cikin da ka yiwa diyata tun.......''
wani kyakkyawan duka da ya sauka tsakiyar kanta ya haddasa wa qwaqwalwarta daina aiki na wucin gadi,wasu taurari suka kewaye idanunta take ta sulale ta fadi a gun,sai da ta kusa kusan minti biyu sannan jinta ya dawo sai ta kasa bude idanunta,mugu ya tako inda take ya tsaya qerere a samanta yana dubanta
''da niyyar kasheki nazo ke da wancan wawan dan naki qauran mata,amma kunci darajar abinda yake cikin yarki wanda dana ne kuma jikanki,nasan kina jina don ban miki dukan da zaki mutu ba,amma zan baki zabi biyu,ko ki biyani kudina ko kuma na dauke yarki ta zama matarmu,na baki nan da kwana biyar kiyi shawara''
ya juya ya isa inda zubaida take ya dagata ya rungumeta yana shafa cikinta
''kada ki sake ki bari wani abu ya samu cikinan don ina buqatar wanda zai gajeni,duk dan kaza kazan(ya duro ashar) da ya kuma takuraki ki takashi kema yadda ranki keso''ya fada yana sakinta,ga mamakin adnan murmushi yaga tana yiwa mugu har suka juya suka fice daga gidan wanda shigowar mami suka yi kacibus suna ficewa a qasa ita kuma tana shigowa da motarta
bayan ta faka motar cikin mamaki ta fito ta nufi gun security guda uku da su kadai yanzu suka rage a gidan
cikin girmamawa suke gaidata don har yau suna son uwar gijiyar tasu,tambayarsu tayi
''wadan nan mutanen kuma daga ina suka fito''
daya daga cikinsu ne ya amsa mata
''daga cikin gida''fuskarta qunshe da mamaki ta sake tambayarsu
''cikin gida kuma?,gurin wa suka zo?''
wannan karon wani daban ne ya amsa mata
''gun hajiya nene,ai sun dade suna zuwa gunta,ko kin manta ne hajiya,kwanaki ke ta saka kika basu kudin mota''
cike da mamaki ta nuna kanta
''ni?ni kuma usaini?''
''eh hajiya ke''
ganin sun zuba mata ido sunata kallonta sai ta dauko wani batun
''yanzu ina su samuel da ibrahim''
''hajiya duk an dakatar da sh daga aiki,kuma da aka tambayeki kika ce kin amince,yanzu saura security biyar daga cikin goma sha biyar dake aiki cikin gidannan''
wani mamakin ya sake kamata,jinjina kai ta dinga yi don duka batasan anyi haka ba,ta yaya zata kori su ibrahim bayan sune manya manyan security na gidan tun zamanin alhj abdulkareem mai nasara na da rai,muta ne ne masu amana da cikon alqawari
''ka nemi numbers dinsu ka kira ka kirasu gaba daya kace ina son ganinsu daga yau zuwa gobe,wanda baka samu,contact dinshi ba ka dauki mota ka bishi inda kasan zaka sameshi''
cikin jin dadi yace
''yes madam'' don dukkansu suna fara ganin alamun lallai sauyi ne wata qila yake tunkaro gidan
Har tayi gaba ta dawo
''kada a sake barin wani mutum makamancin wadancan mutanen su shigo gidan nan''
cike da bin umarni suka amsa
waiwayo wa ta sakeyi
''amm...usaini,bama su ba duk baqon da za'ayi ku tabbatar da wane shi kafin shigowarsa gidan nan kamar dai yadda aka saba a daa''nan ma amsa mata sukayi a ladabce kana tayi gaba
idanunta suka kai ga hanyar sashen abdallah,can qasan zuciyarta taji tana son shiga saidai wani abu ya taso ya danneta,haka tana ji tana gani ta sauya akala ta shige bangarensu tana ambaton ya Allahu
har zata shige ta ringa jiyo ihu ihu a bangaren nene,juyawa tayi ta nufi sashen nenen don ganin meke faruwa
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
A hankali ta qarasa shigowa cikin dakin hannunta dauke da tray dake jere da kwanukan abinci a kansa,gabanshi ta qarasa ta ajjiye tray din,wanda har ta shigo ta ajjiye din yana zaune kan wheel chair dinshi kanshi a duqe a qasa,shi kadai ahi da Allahn sa yasan abinda yake ji cikin qirjinsa,wani irin zafi radadi da quna,da zai iya yana kin fiddo da zuciyarshi zaiyi waje ya huta irin azabar da yake ji,bai taba sanin so da kishi masifa bane sai yau,baiyi tsammanin son da yake mata har yayi irin wanann girman ba,ya sani cewa yana ganin qimarta fiye da duk yadda yake ganin qimar wata diya mace a duniya idan ka dauke maminsa,tana da wani girma na daban a idaniyarsa da zuciyarsa ma baki daya,wannan ne karo na farko da tunda yazo duniya kishinsa kan wata diya mace ya motsa,shi kansa baiyi zaton kishinsa ya kai haka ba,duk da agefe guda qoqarin goge firman laifin da ta yi masa yake ta faman yi saidai ina zuciyar taqi aminta,idanuwan su gaza daina hango masa maryamunsa tsaye da wani
batasan gurin da ya tsaya ba tare suka taho daga rafin malam dogo amma sai gashi har ta shigo gidan sukayi sallar magariba da isha bai shigowa ba,sai bayan isha'i ya shigo bai kuma tsaya ba kanshi tsaye ya shigo dakin dama kuma bai tadda inna wuro ba a tsakar gida ta ahiga daki dauko kayan kadinta
Jikinta gaba daya a sanyaye take,wani saahen na zuciyarta na ganin wane laifi tayi ba ita ta kira ahmad ba kuma ta riga da ta gaya masa tare suke,Allah kuma shaida ne bada wani abu ta kula shi ba,gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu
wannan tunanin ya qarfafa mata gwiwa tana tsaye a gabanshin tace
''abdallah''
''abdallah''shiru taji tamkar ba da shi take ba
''abdallah ga abincinka,ina ka tsaya na ahigo inna wuro tana tambayata inda ka tsaya sai qarya na mata,me yake damunka ne?''
shiru nan ma taji
''na zuba maka tuwo ne inna ta.....''
dagowar da yayi ya sanyata ja da baya zuciyarta na bugun uku uku,wani irin birkicewa ta ga idanunshi sunyi,wani matsanancin tashin hankali take hangowa qarar cikin idanunshi,farar fuskarshi ta hada ja kamar wanda aka mammara
Ga mamakinta sai taga ya saki murmushi yana fadin
''na gode da abinci,amma bazan iya ci ba''ya maida kansa qas kamar yadda tazo ta taras da shi,ajiyar zuciya ta sauke cikin,mutuwar jiki ta sake dawowa gabanshi ta duqa tana mai janyo kwanunkan
''dazun da rana baka ci abinci ba,bazai yiwu yanzun ma kace ba zaka ci ba''ta fara zuba masa kana ta miqa masa
Sake kallonta yayi,wannan karon raunin dake tattare da idanun abdallahn yafi na dazu,ita kanta sai da abun ya taba ta,irin raunin da ko sanda lalura ta sameshi bata gani,cikin idanunshi ba,murmushin ya kuma yi kana yace
''haqiqa Allah na iua jarabtar bawanshi ta kowanne fanni da yaga dama,ban yarda cewa ni abdallah cikakken maraya bane sai yau,na rasa mahaifina na rasa soyayyar mahaifiyata haka na rasa soyayyar macen da na riga nayi amanna cewa zata zauna da ni a duk yadda nake ko kuma nazo mata,saidai tunani na ashe kuskure ne?,duk da bai kamata naga laifinki ba maryam baki rufeni ba,kin gayamin baki sona bani kike so ba amma na gaza cika miki muradinki na rabuwa da alaqaqai abdallah,baqinciki na daya maryam igiyar aure na da aka hau kan martabarta aka tuburbudawa qasa,na yaba miki kuma ina kan yaba miki kan namijin qoqarin da kika yi kike kuma kan yi na bawa,rayuwata kariya,haqiqa bani da abunda zan iya biyanki da shi,na miki kuma alqawarin da zarar na samu lafiya zan cika miki burinki na rabuwa da ni,kici gaba da yimin alfarma zama da ni kada wasu su fuskanci wani abu,na miki alqawarin daina saki yimin duk wata wahala,kidai ci gaba da zama da ni din har na samu lpy idan da rabon haka ni kuma na baki 'yancinki da kike da muradi''
Hakanan taji maganar ta daki zuciyarta sosai,tayi yinqurin duban qwayar idanunsa saidai ta kasa tilas tayi maganar tana kallan wani gurin daban
''yanzu me nayi maka haka da kake gayamin wadan nan maganganun,duka mai ya taso da su?idan maganar ahmad kake ni babu komai tsakani na da shi hasalima zuwa yayi ku gaisa''
ambatar sunanshi shi ya dago hasalar da yaketa qoqarin dannewa,cikin tsawa yace
''ahmad yake ko watever ba ruwa na da shi,ba maganarsa muke ba anan,magan ce tsakanin na da ke,don kin kula shi kun saba har kunsan juna wannan tsakaninku ne,igiyar aure na nada qima da mutunci a wajena tunda na biya sadaki,ni ba ragon namiji bane tun fil'azar jarabtar da Allah yayimin bazata zama silar zamowa na rago ba,kin cancanci kiyi hakan don a yanzun kinfi qarfin abdallah nakasashshe,sai cikakken namiji mai lafiya ba irina ba,saidai ki sani,har yanzu igiya ta na kanki so kiyi respecting dinta,sannan a hakan na tabbata nima akwai masu sona wadanda zasu iya zama da ni duk yadda nake''
sai ta qarasa gigicewa baki daya,kamar zata shide da jin fassarar da ya mata,kanshi tayo gaba daya tuni idanunta sun fara fidda ruwan hawaye,da sauri ya dakatar da ita
''kada ki cemin komai,bana buqatar naji komai''daga haka ya danna gefan keken ya soma yunqurin ficewa daga dakin,wani irin kuka ta saki ta fada saman katifa bai dakata ba har ya fice daga dakin
tana iya jiyoshi shi da inna wuro suna hirarsu abinsu tamkar babu komai cikin zuciyarsa,yayi qoqari matuqa wajen kawar da duk wata damuwa da yake jin tana taso masa
''bawan Allah in sha Allahu jibi tsoho alhaji zai dawo daga qasa mai tsarki,da izinin Allah kasa rqn warkewarka nan kusa''a fuska ya nuna jin dadinsa sosai,amma farincikin da yake sa ran ji duk lokacin da aka gaya masa tsoho alhaji zai dawo sam baiji shi ba,bai san dalili ba,amma yana zaton hakan baya rasa nasaba da abinda zuciyarsa ke gaya masa na cewa yana warkewa rabuwarsa da maryam tazo
Shigowar musatafa kenan abdallah ya maida shi yace yake ya kira masa mairo,babu jinkiri ya fice kuwa,ya dubi inna wuro yana fadin
''sam yarinyar nan ta daina shigowa inna ko ta miki wani laifi ne?''
kai ta kada
''a'ah a'ah,ni,babu abinda ya hadamu,abinda na lura kawai tana wasan buya ne da maryamu,ban sani ba ko ita ta yiwa laifin''karon farko amsar dalilin wasan buyab ya fado zuciyarsa,tana kwancen ta jiyosu batasan dalili ba sai taji ruwan hawayenta ya dadu ta sake qunshe kanta cikin filo hawayen na sauka qamshin turaren abdallah da ya kama katifar na ratsa qofofin hancinta,cikin sakanni ya haifar mata da wani baqon yanayi cikin zuciya da gangar jikinta
duban inna wuro yayi yace
''inna''
''na'am bawan Allah''ta amsa masa bayan ta dubeshi tana ci gaba da kadin
''magana nakeson muyi da ke inna ta fahimta''sai ta ajjiye abinda takeyi din tq bashi dukkan hankalinta''uhmmm ina saurarenka''
''inna na daukeki tamkar kakata haka nake jinki had zuciyata akwai maganar da nakeson gaya miki tuntini''sai ya matsa gefan kekensa take ya qara matsawa da shi gaban innar kadan sanann cikin qasa da murya ya fara mata maganar
lokacin da taji sallamad meron sai da taji wata faduwar gaba,haka siddan ta kasa zama sai ta miqe ta yaye labulen window din dakin,shi abdallah yake fuskanta don haka ta sake lafewa sosai don kada ya hangota
Tare da mustafa suka shigo,tana ido biyu da abadallah ta fara sussunne kai cikin duqunqunan nan hijabinta,inna wuron ce ta dubeta
''au,to kuma meye hakan,wa kike kunya ne?kinga bani na kiraki ba dama tunda kin gujeni kinga mai kiran naki''
gaban abdallah tazo ta zauna kana ta gaida shi
''bani amsawa tunda bamusan laifin da muka yi miki ba kika gujemu''
qara dunqule kanta tayi guri guda wani dadi ya rikito mata kamar ta tashi tayi rawa
''ni dai babu komai''haka ta fada,abdallahn ne ke janta da hira abunka da gwanar surutu tuni ta saki jikinta suka fada hirarsu,daga bisani maryam taga inna wuro ta tattre kayanta ta shige daki ta barsu
qasa qasa suka koma magan ta yadda bzata iya jiyosu ba,sai fuskar mero da ta gani ta fadada ta fara'a tana sake boye kanta,ji tayi ta soma jin juwa juwa sabida haka ta saki labulen ta koma kan sofa tana dafe da qirjinta
''kada ki jawomina bunda bazan iya ba,kada kimin irin wannan rashin adalcin,ki rabu da abdallah bai dace da ni ba,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,abdallah ba mate dina bane''abibda ta ringa fada kenan qasa qasa wani hawaye mai zafi na bin kuncinta
tun tana duba agogo har ta haqura,sai da ya buga qarfe sha daya daidai har ya dora da mintina sannan ta sake jiyo muryarsu
''ki tabbatar gobe tare zamu fita rafi dake kinyi alqawari?''kai ta gyada kamin tace
''eh nayi alqawari''
shima kan ya jinjina
''to shikenan sai da safe goodnight sweet dream''duk da bata fuskanci mai yace ba sai ta saki dariya tana waiwayensa har ta fice
ya janye idonsa yana sauke ajiyar zuciya,har yazu nauyi da zafin da yake ji a qirjinsa yana nan babu ainda ya ragu duk da faman turereniya da yake masa amma sam ya gaza cimma nasara,cike da kasala ya danna madannin tafiya keken ya nufi dakin da shi cikin wani rin yanayi na jin kadaici da zazzafar qauna
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[8:50pm, 9/30/2017] Huguma👑: [3:02pm, 9/30/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
5⃣1⃣
*_Allah S W A yana fada cikim alqur'aninsa mai girma''haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu abubuwan tambayane (ranar alqiyama)_*
*_cikin wata surar kuma yana cewa''ku cika alqawari lallai alqawari abin tambaya ne (ranar qiyama)_*
Da sauri sauri mami ke tafiya har ta isa ga sashen nenen,nenen ta taras kwance male male tana zabga ihu saboda tashi data kasa yi,zubaida da danan na durqushe kanta suna qoqarin dagota
ta qarasa gabansu tana shirin taba nenen tana tambayarsu
''me ya sameta,lafiya?''zubaida ta bude baki dom bata amsa,da sauri nene ta sake saka wani ihun tana fadin
''wayyo Allah na,kada ku kulata,kada kuyi mata magana''
itadai zubaida da batasan me hakan yake mufi ba tayi zaton ko qwaqwalwar nenen ce ta samu matsala
''wallahi faduwa tayi ne,bamusan me ya sameta ba''ta bawa mami amsa da haka don batasan me zata ce mata ba
idanu adnan ya zq
aro don yasan babu shakka a yau dai asirin jikin mami ya gama karyewa don sun qetara sharadinsa
''Allah ya tsine miki dai albarka zubaida,haihuwarki bata qare ki da komai ba,kin sake jawo mana wata asafar,kin karya mana asiri''nenen ta fada hawaye shabe shabe,kallon rashin fahimta mami da zubaida ke mata,tuni adanna ya juya ya fice mami ta bishi da kallo
ta dawo da kallonta ga zubaida zata mata magana ifanunta ya sauka kan cikinta sai ta kasa magana ta tsaya kawai ta zuba mata idanu,udon zubaidan ya cika da qwalla don kusan duk gidan babu wanda take ganin mutumci mituncinsa kamar mamin,babu wanda yace komai nenen ta sake sakin ihu
''adnan kaje ka duba min yata zahariyya,kada su hallakamin ita''cikin tashin hankali,mami ta kalli zubaida
''kamata mu kaita sama na mata allurar barci ko zata dawo hayyacinta''
''wallahi bintu kada ki sake kice zakimin allurar bacci,lafiyatq qalau,jikina ne kawai yayi nauyin kuma zai warke,na tsaneki wallahi bintu taurin ran danki abdullahi duk shi ya jawo mana wann masifar da muke ciki''
kiran sunan abdullahi ya sanya gabanta faduwa har sai data kirq sunan Allah,haka suka kinkimeta da qyar suka iya haurawa da ita saboda azanar nauyinta,mamin ta yi mata allurar barcin,tana ta surutanta da su basu fahimvi komai ba ciki saboda basu san me ta qulla ba da haka bacci yayi awon gaba da ita
Ta fito daga sashen nene ta nufi sashenta tana dafe da kanta don tun sanda ta kira sunan abdullahi kanta yake mata ciwo,suna take ta nanatawa cikin zuciyarta
ta qarasa bedroom dinta ta shiga tayi wanka ta daura alwala ta bada faralin sallah,har yaznu ciwon kan uaqi saukar mata don haka ta balli magani ta sha ta kwanta,babu jimawa nannauyan bacci ya dauketa
Yana zaune kan kekensa yayi kyau cikin jallabiyya fara sol,fuskarshi qunshe da murmushi yana kallonta,itama shi take kallo,a hankali ya fara tahowa gabanshi tana miqa masa hamnu saidai duk sanda ta kusa zuwa dab da shi keken da yake kai sai yayo baya da shi taga ya mata nisa
Sai ta fara binsa da gudu keken na sake tafiya da shi saidai yana fuskantarta fuskarsa kuma dauke da murmushi,sai da sukayi tafiya mai nisa kana keken ya tsaya cak,sai taji an,dafa kafadarta da sauri ta waiwayo,maryam ta gani tsaye kusa da ita tana murmushi,ta nude bakinta zata kira sunanta bat taga sun bace mata gaba dayansu,dube dube ta dinga yi amma ta nemesu sama ko qasa ta rasa,wani rami ta gani a gabanta ta tafi a hankali ta keqa sai ta hangosu ciki suna zaune,ji tayi luuu ta tafi itama zata fada ciki
firgigit ta farka tana ambton sunan Allah gami da dafe kanta dake sara mata kamar zai tsage gida biyu,tafi minti talatin a haka sannan taji sannu a hankali ciwon kan yana raguwa yana raguwa har ta daina kinsa gaba daya,sai ta jita sawai kamar wadda aka kunce daga sarqa
''abdallah,maryam''ta fada a hankali
Kamar wadda aka tsikara ta dago da kanta ta miqe da sauri ta sanya hijabinta ta fito,hanyar sashen abdallahn ta nufa kanta tsaye tana tafiya wasu abubuwan da suka faru suna fado mata tamkar mutumin da yayi mafarki yake tuna abunda ya faru,kallo daya ta yiwa sashen nasa jikinta ya gaya mata ba lafiya ba,qofar na nan a lallauye yadda su muugu suka yi mata ranar da suka zo nemansa,jikinta babu qwari ta shiga ciki ta dinfa duba ko,ina da ina ta,iya qurar da bangaren yayi kawai ya isheta amsar cewa gidan ya dade babu mai rai a cikinsa,hotunan abdallahn ta dinga bi tana kalla bata ankara ba kuka ya subuce mata,zaman dirshan tayi saman carfet hawaye masu dumi suka shiga turereniyar fita daga idanunta
''ina ka shiga abdallah,ina ka tafi ka barni''abinda ta donga fada kenan a hankali cikin kukanta
mafarkin da tayi dazun ya dinga dawo mata tar kamar a lokacin takeyinsa,babu shakka ta tabbatar abdallah da maryam duk inda suke suna da buqatarta,suna da kwadayin ganinta
maganganun nene suka sako kai suma
kada kuyi mata magana,shikenan kun karya min asiri
asiri?
asiri wanne iri take nufi,wa aka yiwa asiri kuma akan ne ya karye?duka daga shigowarta gidan a tau tunaninta ke ta mata shawagi,mutanen da ta gani sun fita daga gidan kamar ta taba ganinsu cikin gidan,cikin wani dare cikin kuma wata rayuwa data yi a baya,rayuwar data dinga jinta kamar rayuwar cikin mafarki,cikin rayuwar ta dinga tsinto halin da taga abdallah,abunda ya faru da ita ranar da zata soma rayuwar mai kama da mafarki,a hankali tunaninta ya dawo zuwa yau,maganganun nene sunqi daina yi mata amsa kuwwa a kunne,a dazun sam hankalinta bai nasu muhimmanci ba sabanin yazun data dage kai da fata sai ta tuna dukkan wani abu da nenen ta fada,ficewar da adnan yayi da sauri daga gidan
''taurin ran abdallah ne duka ya jawo mana halin da muke ciki,idan da ya mutu salin alin da mun huta''
maganar nenen ta qarshe kenan sanda take surkuda mata allurar bacci
taurin ran abdallah?
ya mutu?abdallah kenan abdallah na?
tambayoyin sun mata tsauri da yawa,saidai data hada dukkan abubuwan dake wulgawa cikin idanunta sai taso sansano qamshin wani abu wanda ya sata ta qarasa shugewa rudani na haqiqa,ita kadai ke fadin duk inda abdallah yake sai ta nemoshi
ba zata iya rayuwa,cikin duniya ba cikin salama ba tare da tasan ina abdallah yake ba,wanne hali yake ciki?,a kullum addu'arta shine Allah yasa ta riga abdallahn mutuwa,zata masa addu'ar samun juriya da qarfin gwiwa kan rashinta,sabanin ita da bata da wanda zai mata wannan addu'ar,ta yaya zata jure rasa abdallah da mahaifinsa ta iya ci gaba da ingantacciyar rayuwa cikin dunuya
A hanzarce ta kima sashenta ta wuce bedroom dinta kai tsaye,kayan jikinta ta sauya ta dauki muqullin motarta,haqiqa dukkanin wani zatonta game da yadda rayuwarsu ta cukurkude lokaci guda ra dorashi ga nene,duk da ta sani wani bawa,bai isa ya dora maka wani abu ba face da izinin ubangiji amma akwai silar komai,nene ita ce sila haka zuciyarta ke gaya mata
ta bude motarta ta shige tana qoqarin tashinta usaini ya qaraso
''hajiya zaki fita gasu ibrahim kuma na zuwa''ta dubeshi kana tace
''idan sum qaraso kowa ya koma bakin aikinsa na maidashi,gobe idan Allah ya kaimu zamu tattauna da ku duka''ta samu damar fada sakamakon ambaton Allah da take yi cikin zuciyarta wanda hakan ya taimaka qwarai da gaske wajen zaunar da nutsuwarta cikin jikinta
Allah yana fada cikin alqur'aninsa mai girma
(KU SAURARA,TABBAS DA AMBATON ALLAH KADAI ZUKATA KE NUTSUWA)
Babu inda yafi dacewa ta dosa irin gidan kawunta wanda yake a yanzu tamkar mahaifi a gareta,mutum ne mai nutsuwa qwarai da fahimta babu bata lokaci ta fice a gidan kanta tsaye ta nufi can
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Ranar wunin gaba daya akanta ta qare tana zaune qofar gidan ta tasa uban ruwan dake ambaliya agabanta,tun tana zuba ido taga ta inda jirgin agajin su nene zai dira har ta sare baki daya,ta sake laluba wayarta da niyyar kunnata ko zata iya kira saidai sama ko qasa ta nemi wayar ta rasa,wasa wasa ta miqe ta hau zazzage zazzage saidai ko qyallin kalarta bata hango na,abu kamar wasa sai da ta zazzage dukkan akwatunanta amma babu ita babu alamarta,dariya taji ana qyqyata mata ta dago kanta da sauri,malam na hayi ta gano yana keta ruwan yana takashi da qafafunsa tamkar wanda yake kan tsandauri ba ruwa ba,ya qaraso gabanta ya ya daga hannunshi sai ga wayar
''duk abinda kike aiwatarwa yau na sani,kina tsammanin kubuta daha hannu na ne?,to kinzo gidan da idan aka shiga saidai a fidda gawarka,ina jinku habiba ta baki labarin abunda ya faru da ita ko?,wato wanna bai zamamiki izina ba ke yar masu taurin kai,bari na baki shawara qwaya daya a taqaice,ki fidda sa dan komawarki gida muna tare mutu ka raba,koda yan uwanki ma sunzo basu isa su gane hanya ba haka zasu qaraci walagiginsu su koma,mune maganin makwadaitan mata irinku masu butulcewa hanyar Allah,kunqi Allah muma munqi shi kinga kenan mu muka fi dacewa da ku,kin riga da kin zama matar malam na hayi na zama mijinki''
cikin zafi ta bude bakinta da niyyar yaba mishi rashin kunya,bakinta cike yake fal da maganganu masu zafi da takeson ta gaya masa,raahin mutunci ta nado mai uawa zata masa wanda tana tsammanin tunda yazo duniya ba'a taba yi masa makamancinsa ba,da saurinsa ya daga hannunshi na hagu take bakinta ya rufe qam
''daga yau ba zaki sake magana ba sai idan na baki izini ko naso,ba zaki sake min musu ba ko wani ma ba ni ba''kai kawai take gyada masa kamar bawa da ubangidansa
''wuce ki tafi dakinki,daga gobe zaki amshi girki,yau na daga miki qafa kiyi jimamin rabuwa da gida irin na amare iya na yau kawai''nan ma kai ta gyada masa ba tare da tace komai ba ta tsugunna zata kwaahe akwatunta
''shiga ciki kawai,kafin ki isa su sun riga ki isa''nan ma kai ta gyada kana ta juya sum sum sum ta shige cikin gidan,ya isa gaban kayan ya dafa su take suka bace a gun bat,wata magaukaciyar dariya ya saki yaba yiwa kansa kirari kala kala,sai kuma ya dinke fuskarsa cikin yan sakanni tamkar bai taba dariyar ba ya juya ya shige cikin gidan
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Su biyu ne ita da inna wuron zaune qarqash bishiyar lalle take kwabawa innan wanda zata saka a qafarta saboda dawiqar tsoho alhaji gobe daga qasa mai tsarki,har mamakin tsohuwar take bata ganin tsufan kanta ko na mijinta,adonta take daidai shekarubta wanda zai burge mijinta,dazu ta saka sabulu mai qamshi ta wanke kanta tas tace maryam din zata yi mata kitso
Tun kafin ta dago ta jiyo muryoyinsu,gabanta ya soma faduwa don ko kusa ko alqma bata sha'awad ta bude ido taga yarinyar,haka suka shigo cikin gidan tana tura wheelchair din suna hira abinsu,tunda ta dago kanta suka hda ido da abdallah ta dauke kai bata sake marmain kallonsu ba,miqewa tayi tsam ta isa bakin rijiya ta wanke hannunta sai tayi shigewarta daki duk da ba wani abun zatayi cikin dakin ba,tsaye tayi tana jin uadda suke hirarsu su ukun sun ma maisheta tamkar wata bare,kada ma abdallah yaji labari wanda a a yanzun ya koyi zuwa masallaci daga nan idan yaga damq yayi zamansa qofar gidan nenen suyita hira da samarin qauyen,idan kuwa ya tashi dawowa to mawuyacibe ka ganshi ya dawo shi kadai ba tare da mero ba,duk yadda taso danne zuciyarta da hanata jin kishin abdallah abun ya faskara yafi qarfinta,daga qarshe ta yiwa kanta hukunci ta yarda tana kishin abdallah saboda amanarsa da mami ta barta amma ba wai don so ba
Ko daya bata ji shigowarsa ba sai gyaran murya da ta ji a bayanta,ta dan waiwayo da sauri wanda hakan kadai ya isa ya gaya maka tunani takeyi
''excuse me madam''ya fada yana nuna mata hanyar da zai wuce din ba tare da ya kalli fuskarta ba
sai ta janye gefe ta zauna saman kujera ya qaraso ya wuce bangon dakin inda laptop dinshi ke ajjiye,tayi qasa da yawa hannunsa bazai iya kaiwa ba,tayi zaton wannan karon zai nemi taimakonta sabida gaba daya yanzun duk abinda hannunshi zai iya da kansa yake yi,ta manta yaushe rabon da ya sata wani abu,ko kwanciya ce ko dorashi saman kujerarsa mustafa ke taimaka masa
Bata ankara ba taji yana kiran mero,cikin rawar jiki ta qaraso dakin ganin maryam sai jikinta ya mutu kuma,ta soma rabe rabe
''shigo mana,wancan computer din zaki dauka min da ita zamu tafi saboda hoto ko?''sai ta washe haqoranta ta rave maryam ta wuce ta dauko conputer tana qare mata kallo din ba qaramin burgeta tayi ba ta miqa masa suka fice a dakin,wani dubqulallen abu ne ya tokare mata wuta ya hanata ta hadiyi koda yawu ne,tana jiyo su suna yiwa inna wuro sallama sun tafi rafi sai kawai ta qarasa zamewa ta kwanta gaba daya kan kujerar tana hawaye sosai
''meramu fito,ki saka min lallen nan mana,so nake na cireshi kafin mangariba ki kitse min kan nan,don malam alhaji saukar hantsi zaiyi''ta jiyo inna wuro tana fada,da zata iya da ta cewa inna wuron ba zata iya fitowa ba ta saka da kanta,tilas ta miqe ta goge fuskarta bayan ta sake saka kwalli duk don kada innar ta gane ta fito
tana kan tabarma lallen na gefanta,kallo daya ta yiwa maryamun ta maida kanta kan kwanon lallenta ba tare da tace mata komai ba,tun inna wuron na sako hira taga maryam din bata karbarta hannu biyu itama sai taja bakinta ta tsuke suka ci gaba da zaman kurame,duk yadda taso ta hana qwallar fita hakan ya faskar,haka ta dinga sulalowa tana sa gefan dankwalinta cikin dabara tana gogewa
''hmmmm,duniya kenan,Allah yana baka kana bana so,ba shikenan ba,garin kallon ruwa dama kwado kema mutum qafa,dana dam kuma dama ai butulcinsa yawa gareshi''shiru tayi gana jujjuya maganganun inna wuron cikin qwaqwalwarta masu zubi da gugar zana,sai tayi ta maza don kada ta gano kuka take ta tambayeta kanta na duqe kan qafar inna wuron da take sawa lallen
''lafiya inna,wani abu ne ya faru?''
tabe baki tayi ya kau da kanta
''a'ah a'ah,babu abinda ya faru,Allah dai ya rufa asiri,amma shi aure komai lalacewarsa ai aure ne,yafi gaban ace za'ayi shakulaton bangaro da shi''
''hakane''maryam din ta fada tana ci gaba da abunda take,wani takaici ya kama inna wuron har taja qwafa duk da yadda taso daurewa
bayan ta gama sa mata sai taja gefe,gani,zaman shirun ya,isa don innar bata sake tanka mata ba sai ta jawo kwanon lallen wanda yayi ragowa ta qunsa a yatsunta na qafa da hannu
daf da kiran sallar magariba suka cire duka ita da innar,yatsun sunyi kyau kam,lallen ya kama ram da shi gwanin sha'awa
tana gama daura alwala taji sallamarsa,wanann karon ma sai da gabanta ya fadin,idanunta ya sauka kan mero dake riqe da laptop dina abdallah taba ta shafawa bakin nan kamar gonar auduga,har uanzu jan jambakin data sanya kan ta kile yana nan radam baje baje kan bakinta,ta sake saura dankwalinta sai ta shige kawai dakinsu don ta tabbata zaman hirar,nan zasuyi,hirar da ayanzu babu abinda ta tsana kamar ta
Tana shiga ta shimfida abun salla ta tayar da sallar,ko bayan ta idar zamanta tayi kan daddumar bakinta cike da addu'o'i wadanda suk riga da sun zame mata jiki,a kunnenta abdallah ya fita sallah ya dawo,inna wuro tayi kiranta ta fito taci abinci to tace mata har suka kammala bata fito din ba saboda tana jiyo muryar mero
Awa daya tsakani ta sake jiyo innar
''ki fito ki lallabe min kan nan tunda ba zaki ci abincin ba,inaga azumin yammaci zuwa dare kika fara''
abdallah ya kalli innar qasa qasa yace
''inna dama bata ci abincin rana ba?''
baki ta tabe
''ina fa taci ta dorawa kanta nunqufurci''
ya marairaice fuska kamar yqdda yakewa mami idqn yanason wani abu
''amma inna banda zama da yunwa fa''
''qyale shu'uma,cikinta ai da kanta zata nema idan yunwar ta rarakota''
kai ya kada yana jin ba dadi cikin zuciyarsa
''a'ah inna''
''ka qyaketa nace bawan Allah,ai ba wani ya hanata ci ba''
kwanukan ya dauka ya danna kekansa ya nufi dakin,a kwance ya taddata,amsa sallamarsa tayi tana qoqarin boye hawayen fuskarta don kada ya gani,ta miqe tana gyara hijabin jikinta zata fice a dakin
''dawo ki zauna''taji ya fada,haushinsa take ji fal cikin zuciyarta don haka ta masa shiru,taku biyu ta qara ta sake jin muryarsa mai cike da dakewa da kwarjini
''zan saba miki idan kika sake koda taku guda''cak ta tsaya kana ta dawo da baya tayi zaune kan ledar dakinta bayan ta cusa fuskarta tsskiyar cinyoyinta,keanukan ya tura mata
''dauki ki cinye banason inga komai cikin kwanon''ba tare data kalli kwanon ba tace
''bana ci na qoshi''
''tunda bakici ki fadi me kike son ci?''
''na qoshi nace''
''baki isa ba''ya fada kanshi tsaye,yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata da gaske har cikin zuciyarsa bazai barta ba sai taci
''me zaki ci nace''ya kuma tambayarta cikin dakewa da ginshira
''fura mai kwakwa da shawarma''tana sane ta fadi hakan don tasan mawuyacine a nan a samu abinda ta fada din
baice komai ba ya danna keken ya fice
Awa guda ya dawo da baqar leda
''karbi kici''taji yace da ita
ta miqa hannu ta amshi ledar fuskarta a qunshe,ga mamakinta duk abinda ta lissafa din ne a ciki
babu yadda ta iya haka taja ledar ya tasata a gaba da zazzafan kallonshin nan yace a gabansa zata ci
sosai ta bata masa lokaci duk don ya gaji ya fita amma sai ta lura baiko damu ba gyara zamanshi yayi ma,tamkar ma nishadi yangarta da zaunar da shi din da tayi take sashi
duk motsin da tayi idanunshi na kanta musamman dan qaramin bakinta mai dauke da pink din lips dake motsawa yana rauna shawarmar cikin rashin son cin abincin,wani abu ya darsa cikin zuciyarshi wanda ya sashi limshe idanunsa,ji yake kamar ya kamaau ya tsotsesu tas,wani,barin na zuciyarsa ke gaya masa loka cine
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
5⃣2⃣
*_Manzan Allah S A W ya hana bacci bayan sallar magariba haka nan ya karhanta zance/hira bayan sallar isha'i_*
*_daga nana Aisha R A tace na kasance ina wanke janaba daga tufafin Ma'aiki S A W sai ya fita sallar asuba da tufafin alhalin akwai ragowar danshin ruwan a jiki_*
*_a wata ruwayar ta muslim kuma yace nana aisha tace''na kasance ina kankare janaba daga tufafin Manzan Allah S A W (kamar busashen maniyyi kenan)sai ya saka ya fita salla da tufafin_*
*_wannan shafin sadakarwa ne gareki dungurun gum baki dayansa SADNAF bama ke kadai ba har da 'ya'yana AFFAN DA IKRAM Allah ya rayasu ya yiwa rayuwarsu albarka,Allah ya bar zumunci_*
Idanunsa suka sake sauka kam yatsunta da take gutsirar shawarman da ita,yanayin yadda take ci kawai ya isa ya gaya maka kan tilas take ci din,don dama asalam ba cimarta bane da biyu tace ita don take so ga zatonta basai samo ba
ba qaramin kyau suka yi masa ba,kasancewar yana gan da ita yasanya ya kamo hannunta
''yaushe kika yi wannan abun?''
ya fada yana kallon qwayar idonta,sai ta soma qoqarin zame hannin nata ba tare da ta bashi amsa ba
''maryam''ya kira sunanta can qasan maqoshi kamar maijin barci,nan ma bata amsa masa ba ya kuma fuskanci bata da niyyar amsa masa din,sunkuyo da kanshi yayi ya tura yatsunta guda biyun cikin bakinshi ya soma tsotsa a tausashe har yana lumahe iso tamkar wanda ya samu wani abu mai dadi
wani irin abu ta dinga ji yana tsirga mata tun daga tafin qafarta har qwaqwalwarta,take jikinta ya mutu baki daya hakanan ta rasa kuzaron hana shi sai idanunta ma da taja ta rufe tana ajiyar zuciya qasa qasa
A hankali ta bude idanunta jin ya daina shan hannun,wata iriyar kunya ta kamata kamar qasa ta tsage ta shige,ashe ita ua zubawa idanu tana kallonta bata sani ba
''uhmmm,madam,zan iya ci gaba?,na kamar kema kina enjoying ko?''ya fada yana kashe mata idonsa na hagu,bata san me zqtq ce ba don ya gama kunya tata saboda hakq kawai saita fara hawaye tare da qoqarin zame hannunta saidai ko daya ya janata ya kama hannun ya riqe tsam ya kima zuba mata mayun idanunshi har tayi mutsumutsinta ta gana tq bada kai ta hanyar haqura tayi qasa da kanta kawai
Hannun ya sake mata bayan ya gama kallonta iya son ranshi,jikinsa gaba dayq ya gama yin laushi muguwar kasala ta lullubeshi
''ta yaya zan iya wanka qarfe takwas na dare,kinga ina zaman zamana kin jawo min ko?''
rasa inda zata tsoma ranta tayi,sam abdallah bai da kunya kwata kwata,lamuranshi yake gaba gadi,ko ita qaramar yarinyace ai ta gane abinda yake nufi bare da hankalinta
''ka jawowa kanka dai tunda bani na kirawoka ba''ta fada can qasan maqoshinta
''erhmmm,me kike cewa?''ya fadi yana matso da kunneshi,shaf ta mance yadda abdallan ke da shegen ji kamar maciji
''najiki sarai abinda kika fada,amma ba komai Allah zai saka min,nima na kusa aure in sha Allahu nan kusa na huta''wani abu ne ya takareta har batasan lokacin da dago kanta ba bayan ta dubeshi tace
''toni me ruwana,idan ka tashi ka aure matan duniya ma baki daya sannan ne zansan ka cika jarababben ma.......''sai ta kasa qarasa fada saboda nauyi da maganar tayi mata da kuma yadda ya tsatstsareta da mayun idanunshi wanda bai gajiya da kallonta da su
ta cukuikuye hijabinta gu daya ta miqe da sauri zata fice adakin,hannu daya yasa ya fincikota atausashe sai gata gabadaya ta fada saman cinyarshi
''babu inda zaki sai kin qarasa fadar abinda ke ranki''
kai ta girgiza gabanta na faduwa cike da danasanin fara furta maganar
''na gama magana ta ai''
''qarya kike,akwai saura''batasan sanda ta rantse ba
''wallahi babu''
''ummh,sanannan ne zaki san na cika jarababben mayen mata ko?,dama can ni mauen mata ne ai ko kin manta?idan baki sani na kuma to kibi a hankali don ta kanki zan fara maitar tawa kafin na sallameki''
tamkar tace wayyo Allah haka taji,kansu sake cewa komai an dago labulen dakin,mairo ce riqe da laptop din abdallah
''yaya abdullahi wai meramun kitson da....''sai ta kasa qarasawa sakamakon ganin maryam din kwance kan cinyar abdallahn,shi kuma ya mata rumfa da faffadan qirjinsa,hakanan sai maryam din ta samu kanta da sake narkewa kan cinyar abdallahn ta saki jikinta tare da saka idanunta cikin naahi sosai abinda bata taba yi ba,hakan yasa ya kasa daga idonshi ya kalli mero din baison yayi missing kallon kyakkyawan oily brown eyes dinta ba dake matuqar jan hankalinshi,ganin ba wanda ya dago ya kalleta yasa sakin labulen bayan ta ajjiye masa laptop din ta fice a dakin
Sai da taga alamun fitarta sanna ta janye idanunta,cikin fitar hayyaci ya kama fuskan tata don baison ta daina kallonshin sabida wasu zafafan abubuwa da yake karanta daga qwayar idanunta wanda shi kansa yasan bata san da su ba,satar amsa yake samu sosai ba tare da saninta ba,tana son qaace fuskarta yace
''ko na aure duka matan duniyan ma meye naki a ciki''
cikin fushin da batasab ya fita ba tace
''wallahi kuwa,tunda ni dama yar amshin shata ce ba,na kusa sanin inda dare ya yimun,su mero na kusa ai baka da damuwa''
Dariya taso kamashi hanin tsabar miskilanci da qarfin hali irin na mutum,ga gaskiya amma ka qita qiri qiri
''gaskiya ne''ya fada yana kamo hijabinta da take qoqarin,ficewa a dakin
''alfarma daya nakeso kiyimin don Allah,ruwa zaki dan duma ma min ki kaimin bandaki,idan inna ta tambayeki kice mata zafi nakeji duk da nasan halin innan sarai ba zata tambaya ba,amma idan da takura ki barshi sai naje nayi haka''
bata bari ta kalleshi ba don gaba daya ya gama kunyatata,har ga Allah ta dauka da wasa yake ba wankan zaiyi ba ashe shi da gaske yake gaya mata sai qeya ta turo masa
''salon ta zaci wani abun mukayi''
''to haramun ne koma me mukayi din,'yar qauye kawai,ita innan ai ba yarinya bace,tafiyarki kawai zata kalla idan ma wani abu ne ta gane,idan baki wasa ba ma sai na gaya mata munyi wani abun inga ya zakiyi''
tayi imani,kadan daga aikinshi ya kum kunyatata saboda haka kufce ta fice ta hada masa ruwan wankan
yar halak inna kam dauke kanta tayi abunta tana faman jan mero da hira,maryam din ma zama tayi can gefe tayi tsuru tsuru cike da kunya tana son ganin reacting na inna wuri saidai babu abinda ta fahimta don hirarta kawai innar take,kafin ma abdallahn ya fito ta shige daki abunta ta kama wasu sabgogin,sai gun ya rage daga ita sai sister mero(lol)
maryam ta dan dubeta
''wai nikam na tambayeki mana?''
''ina jinki''meron ta fada cikin tsoro tsoron kada ko wani abun maryam din zata yi mata
''bakisan cewa haramun bane shiga guri ba tare da kayiwa masu gurin sallama ba''shiru ta danyi don babu inda ilimin nata yakai,na salla dai ta sameshi baina baina
''ai ina yin sallama,kune bakwa ji da wuri''
''waya gaya miki idan kayi sallama cewa akayi ka cusa kanka kawai,sallama na nufin neman izini,koda kayi sallama addini cewa yayi kada ka shiga sai an baka izini,haka Allah ua fada cikin qur'aninsa mai girma''yaku wadanda kuka bada gaskiya da Allah kada kushiga wami gida da ba naku ba face sai kunyi nemi izini kuma kunyi sallama abisa ahlin gidan,wannan shine yafi alkhairi a gareku ko zaku fadaka,idan baku samu kowa a gidan ba kada ku shiga har sai an baku izinin shigar,idan kuma akace da ku koma to ku koma,wannan shine yafi tsarkakewa a gareku''kin fahimceni naga kina raba ido zancan Allah na karanto miki cikin qur'ani''kai ta gyada mata kawai
sai ta dora''kinga zancan Allah na gaya miki ko?so daga yau kada ki sake fado mana daki ba tare da na baki izini ba''sai ta dauke kanta can wani bangaren kamar bata jita ba,ran maryam ya dan sosu mai yarinyar ke nufi
''dake fa nake mero''ta fada cikin dan zafi zafi
''to ai abdullahi ne yaci na shigo ko''
''ba ruwa na na gaya mii daga yau kada ki sake sai na baki izini,ko shi ina iya hanashi shiga,idan kuma baki ji ba ni da ke ne''
sai ta danji tsoro don maryam din bata taba mata magana irin haka ba,a sanyaye tace ''to''
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
''duk abinda ta faru ko baki fada ba bintu na sani ba cikin hayyacinki kike ba,amma ki kwantar da hankakinki duk abinda yq samu bawa da sanin Allah,kuma abinda nakeso da ke,bana son ko kadan ki nunawa nene kinsan wani abu game da abinda ke faruwa din,abu na farko da zamu fara yi shine zamu raba sadaka makarantu makarantu na alarammomi a samu cikin addu'a,koda zamu nemi abdallah ba zamu nemeshi a bayyane ba saboda na tabbata babu wanda yasan halin da yake ciki koda qasa batasan wanne hali yake ciki sabida da ta sani da tuni na tabbatar an baza labarin cikin shafukan jaridu da mujallu,sabida haka yadda Allah ya rufawa al'amarin asiri muma cikin surri zamu ci gaba da bibiyarsa har Allah ya warware mana wanannan daurin gwarmai din,addu'a zaki duqufa yi masa babu dare ba rana domi, addu'ar mahaifiya karbabbiyace kan 'ya'yanta''
''na gode qwarai kawu,Allah ya qara girma ya bar zumunci''
''ameen bintu kamar diya kke a gareni,irin hiyayyar da kika yiwa iyayenki irinta kike mana,hakanan kowa naki ne babu wanda baya morar arziqinki komai dukiyarka kuwa,to don me taqi matsalar ta taso ba zamu shiga ciki ba,abinda nake dak qara jaddada miki shine ko a fuska kada ki nuna mata abinda suka miki ya sakeki,kici gaba da binta ahakan,nayi imani addu'armu Allah bazai wofantar da ita ba''
''na gode kawu''haj bintu ta fada idanunta fal da qwalla zuciyarta kuma cike da taqini da qauna cikin rahamar Allah
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Kamar wani mahaukaci haka ya fado dakin futu futu da shi,tana kwance kan gadon dakin an tallafo bayanta da filo,tun daga ranar da mugu yayi mata wannan dukan bata qara iya yin komai da kanta ba saidai a yi mata,ga baki na magana ga ido ga kunne amma dai qafafun da gangar jikin basa aiki
''yaya,adnan ka samota?''ta tambayeshi cikin zaquwa
tsaki yaja ya zauna a gefanta cike da bala'i yace
''nifa na gaji,wallahi nene na gaji babu inda zan sake komawa,zuwana biyar dajin amma na kasa gane gidan sama ko qasa na nemeshi na rasa,shikenan mu haka zamu qare cikin wahala,wallahi baqin jininki muka debo wallahi,haba da Allah malam hauka ake?''
kwantar da murya tayi tamkar ita ce uwar ma
''haba adnan,zahariyya yar uwarka ce da baka da kamarta fa,ka daure kai kuwa mana da alamu wallahi tana cikin mawuyacin hali na neman taimakonmu''
a fusace ya kalleta kamar mai shirin sharara mata mari
''jaka ce ta yimin gula a ciki?idan na koma wanann na zama alade,ke idan na koma ma Allah ya tsinemin,dazu fa ina tsammanin kurace ta tasanmin badan ina cikin mota ba da tuni yanzu na zama dan gari a lahira haka kawai akan wata banzar zahariyya da budurwata ma ta fiye min ita,nafsi nafsi fa kawai nene ehe''ya fada yana miqewa ta bishi da ido
janye janye janyen lokoki ya fara yi mata,da sauri tace da shi
''meye haka adnan,kasan fa na hanaka yimin bincike cikin daki ko?,akwai surrukana da ajjiye ajjiye na fa''wani kallon banza ya juyo yayi mata yana fadin
''dama kin kwantar da hankalinki don yau ranar diban kaso na ne,zan dibi duk abinda nakeso don ma fuskanci wannan tafiyar babu nasara,odan yaso duk ranar da kika samu nasarar kashe abdallahn ki nemo ki sai muci ganimar tare''iya bakin qoqarin hanashi da bakinta tayi amma a abanza,kallon tsiya ma bata isheshi ba balle yasa ran na arziqi,tana kallo ya dinga balle lockers dinta yana kwashe duk wata kadara tata yana hadewa cikin wata 'yar jaka,kaf ya kammala ya tako gabanta yasa hannunshi ya tsinke sarqar gwal da ke wuyanta wanda garin fincikar har biyo shi tayi sabida rashin qarfin jiki,kuka ta fashe da shi
''kada ka yimin haka adanan,nifa mahaifiyarka ce,ni nasha wuya gun haihuwarka na kawoka duniya''dariya ya sheqe da ita
''gaskiha nene kina da mantuwa,kefa kika ce farauta halak ce kuma ba'a barin ruwan gangare ace sai an dawo za'a diba,wanda ya samu dama ya dama,duk inda ka hadu da arziqi kayi qoqarin yagar rabonka don yanzu duniya sai kana da shi ake yi da kai duk fa hudubarki ce wanann,to kawai yau daya don ta dan ratsa da ke zaki hau raki,ai dama malami yanason ya koyawa dalibinsa karatu yaga yana aiki da shi pratically
''To banga abun damuwa ba don nayi aiki da hudubarki,kyan da dama.....ya gaji uwarsa,sai haduwa ta gaba nene''
ya fada yana shirin barin dakin
''wallhi adnan idan ka sake ka tafi min da dukiya sai na tsine maka albarka,butulcin da zaka yimin kenan matsouaciyacin yaro?''dariya ya sheqe da ita kana yace
''kin dade baki tsinemin ba nene,kinga idan ma kinso a sama miki lasifiqa a abaki duro ki hau kiyita gayawa duniya kin tsinewa adnan damuwarki ce,nidai na debe kasona don na gaji da gafara sa banqo qaho ba,idan na gurin abdallah ya samu kya iya kirana muci tare,byeeee''ya fada yana daga mata hannu tare da sake rungume jakar da ya lodawa duk wata kadara ta nenen yana fucewa adakin
ihun barawo take ta faman zabga masa saidai a banza don babu kowa cikin gidan idan ba security dake bakin aikinsu ba,su kuwa sunsan babu kowa cikin gidan daga ita sai danta don haka basu kulaa ba domin suna tsammanin ciwonta ne ya tashi wanda dukkansu sun dauka ciwon hauka ne ya sameta
hakanan ta qaraci ihunta ta fashe da kuka mai cin rai tana tsinewa adnan mummunan tsinuwa a haka zubaida ta tadda ra,koda ta gama mata bayani dogon numfashi ta ja tana fadin
''tabdijan,nice zan tashi a tutar babu,wannan wace iriyar magana ce ma mara dadin ji,to wallahi bazan zauna da kyau na da komai ba rayuwa ta ta qare a tantal bataiti ba,a banza wancan tsinannen mai qirar sanudawa yazo yayi awon gaba da ni ko ya kasheni,gwara tun yanzu na samawa kaina mafita,zuwa zanyi na cire cikin nan na shiga sabuwar rayuwa,ga masoya ina sa su masu yawan gaske masu kudi na gani a fada,gwara naje wlh na yagi rabona nima na kafa kaina''tana gama fadar haka ta haura gadon ta fara cire dan kunnen gwal dake kunnen nenen mai hade da banguls da zobensu wanda ta tabbata adnan bai kula da su bane,domin da ya kula da su babu abinda zai hanashi yin hauzi da su kamar yadda yayi da wadancan
''au kema zubaida haka zakiyi min,ashe dukkanku matsiyata ne,yayana na cikina babu mai tausayi na kune masu rusani?'''tsayawa tayi cak tana kallonta
''tab lallai ma nene,ke don Allah baki ji kunyar kanki ba?adnan ma yayi miki haka ballanta na ni?''
''yanzu don adnan ya yimin haka kema sai ki biye masa?''
''hmmm,sai kuma kiyi,ina ga kin dade baki bata yawun bakinki ba,ai tunda kika ahiga tsakani na da abdallah kika min asirin da aka ciren sonsa to wlh babu ni babu aure,rayuwar bariki ta fiyemin inda zan zuba jarin jikina na samu kudi''tana fadan haka tana sabule da lalube duk wani abu da yayi saura wanda adnan bai kai ga daukewa ba,cikin haka tayi katari da takardar wani gida ta dauke abinta,tana jin nenen na qwala mata kira har ta koma rsine mata itama amma kallon arziqi bata iaheta ba tayi gaba abinta,don ta riga ta sani uwar tasu ba imani gareta don me ita zataji tausayinta kuma?,ai raba arne da makami ibada ne
A ranar bata bari ta kwanan ba ta hada ya nata ya nata ta nufi gidan wata aminiyarta da ta jima tana mata hudubar shaidan kan cewa ta mori kyanta wlh ta qyale wani abdallah ta tsaya ta nace masa yana wulaqantata bayan ga samari nan da alhazawa na sonta ido rufe
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Duka hidimar ranar ita ta karbeta don inna wuro da abdallah na gurin tsoho alhaji wanda ya sauka qasa nijeria da misalin sha biyu na rana,tayi mamakin ganin hisham shima ya iso a ranar
''ina sane da ranar dawowar tsoho alhaji a lissafe nake maryam,abdallah na raina da shi nake kwana da shi nake tashi ko yaushe''qwarai ta gasgata hakan tunda gashi taga zahiri
Gidan kusan a cike yake da yan sannu da zuwa wanda basu samu sararawar mutanen ba sai bayan sallar la'asar
Tsoho alhaji wanda asalin sunanshi muhammdu dattijo ne mai cikar kamala da nutsuwa,dattijo ne da ya amsa sunan dattijo bawai muna dattijo ba,dattijo ne da kallo daya zaka masa kwarjininsa ya cika maka idanu,yadda matarsa inna wuro(fatima)ke da kirki haka shima yake
Murmushi ya saki har ya dan fidda sauti bayan ya kammal jin dukkan wasu bayanai daga bakin maryam da abdallah hisham harma da inna wuro daga dan abinda ta sani
''in sha Allahu da izinin Allah indai sammun ne bi'iznillah na bada gaskiya ga Allag nan da kwanki bakwai zaka miqe abdullahi ka taka qafafunka komai yazo qarshe,zan yabaki miki maryam kinyi namijin qoqari qwarai da gaske tunda wuro ta gayamin ba haka kuka zo ba,kamar yadda naji bayanai daga bakinki,na abubuwan da kika dinga nasa amfani da su,ayoyo yine masu kyau matuqa da gaske,gakanna masu tasiri qwarai da gaske wajen ruguza sihiri ko wanne iri ne bi'iznillahi ta'ala,yanzu akwai wasu magunguna da saiwayoyi da Allah ya horemin saninsu,yau basai gobe ba zan fara hadasu guri guda insha Allahu baka wuce kwana bakwai ka warke abdullahi kaci gaba da haquri wannan wata jarrabawa ce Allah ya maka don ya gani shin zaka gode masa ne ko zaka butulce masa?,a baya ya maka duk wata ni'ima ta dukiya kyau ilimi nasaba da gata a yanzu ya amshe abinsa yayi ne duka don ya jarabci imaninka,to alhamdulillah bisa dukkan alamu ka karbi duk wata jarrabawa daga gareshi kuma ina maka kyakkyawan fatan samun cikakken lada''
cike da girmamawa ya duqar da kansa
''na gode qwarai da gaske alhaji,Allah ya qara girma,Allah ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani''
haka hisham da maryam suka bi sahun tayashi godiya ga dattijon
Ya dubi inna wuro
''muje ki tayani duba kayan nan,don na san yanzu kin canza musu guri''bata ce komai ba ta miqe tabi bayansa
hannun hisham abdallah ya kama ya riqe
''ka taya ni murna abokina na kusa angwancewa''
dan satar kallon maryam yayi
''mtswee,har yau abdallah baka da kunya,ni kake wa irin wannan maganar?''
ya dubeshi a hagunce
''to akan me bazan maka ba?,rashin aure fa nasifa ne abokina ban sani ba sai yanzu''cikin rashin fahimta yake dubanshi
''like how,kana da mata kana kiran rashin aure a kanka?''
''neman wani auren nake cikin garin nan hisham na wata 'yar fulani''
wani irin kallo hisham din yake masa
''kanka daya kuwa abdallah?,kana da mata kake cewa wani auren kake nema?''
''tunda anqi ka meye na cusa kai hisham don Allah fa,matar tace bata yi zaka mata dole ne?''ya fada qwayar idanunshi na sauya kala,da alamu abinda yake fada din na taba zuciyarshi
''kuma a shekaru na bazan iya zama babu mace ba,kai ka sani da din ma rakawa kawai akeyi''
duk da maganar ta taba hisham yaji wani iri amma maganar abdallahn ta qarshe taso bashi dariya kafin yace komai mero ta kwada sallama bakin qofar dakin wanda duka wunin yau bata shigo gidan ba sai yanzu
''yauwa shigo ga abokina zaku gaisa''inji abdallah yana duban hisham din
jin haka yasa ta dago labulan ta shigo kanta a qas alamun kunya,gefe ta rabe ta gaidasu su duka banda maryam da da qyar ta iya amsaqa can qasab maqoshi,kasa sakewa meron tayi ta miqe zata fita abdallan ya tambayeta ina zuwa tace zata yiwa tsoho alhaji ne barka da dawowa
''idan kin masan ki dawo ina son ganinki''inji shi ta gyada kana ta fice hisham ya bita da kallo,sai da ta fice din baki daya kana ya dawo da kallonsa kan abdallah
''wannan kuma wace ce,yar fillo haka''murmushi ya saka irin mai hade nishadin nan yace
''daina saurin yabawa,itace wadda nake gaya maka ina neman aurenta a qauyen nan''
Wata guduma maryam taji ta sauka kan qirjinya,kanta da gangar jikinta sukayi mata nauyi gaba daya,a hankali ta soma fusgar numfashinya yana son qwace mata,sai ta miqe sama sama tana jiyo sa in sarsu shi da hisham,ganin tana niyyar fita ya sanya hisham kiranta,shi din ma sama sama take jin muryarshi don haka bata bi ta kansa ba ta lalubi hanya ta fice,ba kowa tsakar gidan kai tsaye dakin inna wuro ta shige,gadonta irin na qauye ne da ake kira gadon bunu mai rumfar shi ta haye,can qurya ta takure kanta tana jin wani abu na mata yawo cikin zuciyarta kuka take so tayi ko zata ji sanyi cikin zuciyarta,shin wannan shine kishin?,da gaske kishin abdallah take?sune tambayoyin data ringa jefawa kanta ta kuma takurawa kan nata sai ta fidda amsarsu
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣3⃣
*_Daga Abu hurairah Allah ya qara ya yarda shi yace:Manzan Allah S A W bai taba aibata wani abinci ba ko kadan,idan ya burgeshi(abincin)sai yaci,idan bai masa(bai kwanta masa ba ko ba cimarsa bace)sai ya barshi (ba tare da ya aibata shi ba ko ya wulaqanta shi ba)_*
*ina kuke 'yan*
*huguma conversation and novels room*
*maman aysha hausa novels group*
*haske writers asso*
*DA*
*Z.B.I*
*_bazan gaji da sadaukar muku da shafuka na ba,ina yabawa qwarai da qaunarku gareni,ina roqon Allah ya tashe mu qarqashin inuwarsa ranar gobe qiyama,ya bar mu tare bisa soyayya ta domin Allah_*🙏🏽🙏🏽
Sake lafewa tayi kan gadon inna wuron tana matse idanunta don fidda hawayen dake maqale cikinsu
tun tana jiyo maganganun mutane masu ahigowa jifa jifa yiwa tsoho alhaji barka da dawowa har jin nata ya dayke baki daya,wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita
********
Qaton fili ne dake malale da koiyar ciyawa wadda ake kira da grass carfet jifa jifa kuma jajayen furanni ne ke dashe ta tsakanin ciyawar
Iska mai dadi ke kada fingilar rigar dake jikinta wadda bata da nauyi ko kadan sai santsi,kamar yadda gashin kanta keta yawo tsakanin kafadarta da fuskarta,dauke take da faranti fari qal wanda akanshi kofuna ne fuda uku da jug tsakiyarsa wanda cike yake da madarar shanu,a hankaki take tafiya yana daga nesa cikin fararen kaya hannayensa harde a qirjinsa,dukkan wani hankali nashi da tunaninshi yana a akanta ne,kyakkyawan murmushinsa kadai ya sata mance a ina rake har ta qaraso gareshi,hannu yasa ya karbe farantin ya ajjiye a tsakiyarsu kana ya riqo hannunta
''maryama''
''na'am''ta amsa masa kanta a qasa
''maryam ki kalleni tun kafin na zauce''
ya fada qasa qasa yadda dagashi sai ita kadai zasu iya jin abinda yake fada,babu musu ta daga kanta idanunsu suka mannu da juna,kallon juna suka shiga yi babu qaqqautawa tamkar zasu hadiye junansu,kowanne na ganin zallar qauna qarar cikin idanun dan uwanshi
Shi yafara bude bakinsa
''maryam,kinsan yadda nakeji game da ke cikin zuciyata kuwa''ya fada yana tura hannunta cikin qirjinsa bayan ya balle maballan rigarsa,take tafin hannunta ya mannu da fatar qirjinsa dake cike da gashi
''kina iya jiyo bugun zuciyata a haka?''kai ta gyada masa tana murmushi don tana jin yadda zuciyar tasa kera fat fat fat da sauri
kai ya girgiza
''abinda kika ji yanzu baikai kaso daya cikin dari na yadda nakeji cikin zuciyata game da ke ba,idan da zan iya zuciyar zan ciro miki dungurun gun na ajjiye miki ita wata qila kya iya ganin kaso hamasin cikin darin abinda nake gaya miki,ragowar hamsin din sai ni da Allah''
qayataccen murmushi ta sakar masa tana sadda kanta qasa,da sauri yace
''dago ki kalleni da kyau maryamu na,kallon da kike min kawai na rage radadin da nake ji''bata musa din ba ta dago taci gaba da kallon nashi fuskarta dauke da murmushi
ya matso kusa da ita har suna gwaren numfashi
''i love d look in ur eyes maryam''murmushi ta kuma yi tana dan kawar da idanunta
''i luv ur smile,maryam ke ta musamman ce u make me feel safe nd secure,ban damu da duk wani abu da na rasa ba idan ka cire mami na matuqar ina tare da ke,i know u luv me 4 who am,pls maryam tell me kina sona...kina son abdallah''
idanunta ta lumshe kana ta bude tattausan labbanta
''abdallah''
''yes ina jinki''
''abdallah ina.....''
''umh comeon baby ina jinki''
''abdallah''
''na'ammmm''
sai taji amsawar ta qarahe tamkar ido biyu ne ba cikin mafarki ba,a hankali ta fara bude idanunta don tantance a inda take,yana zaune sosai kan kekenshi idanunsa akanta kamar wanda ya samu hoto,a firgice ta miqe ta zauna dirshan kan gadon innna wuron tana mutstsuka idanu
''me nayi miki da kika zo kina mafarki da ni?,kin daga mana hankali muna ta nemanki tun la'asar gaahi har magariba ta gota ana shirin yin isha'i ashe ke mafarkina na ma kika zo kina yi?''ya fada fuskaraa dauke da murmushi wanda sai ka kuka sosai zaka gane shi kwance kan fuskarshi
haushin kanta ya kamata,kunya da taoro suka dirar mata,kada dai ace kamata yayi tana ambatar sunansa,kai amma kam da ya gama da ita,duk da ba haske bane tarwai cikin dakin sai data harareshi
''waya damu da kai da zaiyi mafarkinka? kai kadaine mai sunan?''
hannayenshi ya ware na alamun ba ruwana
''bani na kar zomon ba,ratayar ma ba'a bani ba,kuma ni din ma na dade da sanin ba'a damu da ni ba,tsabar haushina ne yasa kike ambatar suna na cikin mafarki cikin yanayi ma shauqi ko?''ya tambaueta tana tsatstsareta da kallon nan nashi,bata san me zata ce masa ba duk da barazanar kare kanta da takeyi ba,sai kawai ya juya kekenshi zai fita yana dariya qasa qasa
''ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,na bada darasi abdallah ba rago bane,ki fadi abinda ke damunki idan ya kama taimako sai a taimaka miki''ya fice daga dakin,ba qaramin quluwa tayi ba,ya akayo ya sake ma ya kamata tana mafarkinsa,ta ciji yatsa tayi dana sanin ma yin barcin nan gaba daya,dole haka ta sauko daga gadon tazo ta wucesu suna zaune abinsu hisham tsoho alhaji inna wuro da abdallah,garwashi ne da wasu magunguna gaban tsoho alhajin wanda da alamu duka hade haden abdallah ne,taje ta dauro alwala tana jinshi yana basu labari
''gadonki taje ta naushe miki inna,taji laushin katifa tana ta mafarki barkatai,inaga alhaji sai ka bata magani ma don ina zaton akwai wani aljani abdullahi mai irin suna na da ya kamata''dariya ya basu yayin da ita kuma ta sake quluwa
ta daura alwalarta ta wuce dakin inna wuron ta tada sallarta
Cikin kwanakin gaba daya tayi qaura dakin inna wuro nan take kwana saboda hisham na gidan tare suke kwana da abdallan,iyakarta da tsakar gida ta fito ta taya inna wuro aikace aikace ta koma daki abunta,sam ta hana haduwar da abdallah duk cikin qoqarin tana hana kanta jin duk wani feelings dake barazanar kamata,kusan tayi a banza tunda ko shi bai ganta ba ita tana ganin giftawarsa ko ta jiyo muryarsa shi da su tsoho alhaji wanda ya duqufa ka'in da na'in wajen magungunan abdallah wanda alhmdlh cikin jikinsa yan jin wani irin sakewa da sukuni
Ko daya inna wuro bata ce mata uffan ba kan zaman daki data aura,sai ta tuqe kana zakaji tace
''ummm,Allah ya kyauta,kowa dai ya debo da zafi bakinsa''ta fuskanci sarai da ita take
cikon kwana na ukun tana kwance kan qaramin gadon inna wuron misalin uku na yammaci da littafin riyadul jannah a hannunta tana dubawa,yaye labulen inna wuron tayi tana fadin
''ki tashi kije ki gyara dakinsu hashimu,shida malam sun fita bayan gari debo ganye,amma fa idan zaki iya(da yake haka innan ke kiransa)''
ta fuskanci kamar da zafin ta innar ta fada,bata ce mata komai ba ta ajjiye littafin gefan gadon bayan ta saka alama,hijabinta ta,ciro ta ware ta saka kana ta fice innan ta bita da kallo tana tabe baki
''Allah dai ya sawwaqewa matan maraya wallahi''ta jita amma bata tanka ba
tsaye tayi a bakin qofar dakin zuciyarta na wani irin bugawa,kamar ta juya ta koma haka ta dinga ji,fargabar shiga takeji,jin motsin futowar inna wuro daga daki ya sanyata yin saurin daga labulen ta fada dakin tare da sallama idanunta a qasa
kan kujerar dakin wannan karon ta tadda shi zaune,yayi kyau cikin baqar rigar jallabiyya data haska fatarshi,a haka sai kayi tsammanin lafiyanshi qalau saboda kyan da yayi,ganinshin da batayi ba kwana biyu sai taga kamar an canza shi ne,wayarshi ce a hannunshi yana danne danne,da alama wani muhimmin abu yakeyi,amsa mata yayi kallon farko kadai yayi mata yaci gaba da abunda yake kamar bai santa ba
tana kallon kan katifar da kaya ke baje a aki da sauran tarkace tace
''zan danyi gayaran daki ne''
''oh,na bayar baki gidan ne har nasa a gayara din ma''
wani abu ya dan taba ranta sai tayi shiru wanda hakan yasanya ya dago kai ya saci kallonta
qasa qasa taji yace
''if u luv some one be sure to hold them close,if u don't some one else will''
''me kace?''ta fada cikin son nuna mishi bata ji abinda ya fada din ba
''no,ba dake nake ba,bismillah''ya fada yana ci gaba da abinda yake yi
katifar ta soma kintsawa,tana aikin amma jikinta na gaya mata kallonta yake,batayi qarya ba don gaba daya ya bar hankalinshi daga kan wayar ya maida kanta,duk wani motsi nata na kan idonshi,cikin zuciyarsa hakanan yaji tana burgeshi,bai taba zaton zai samu macen da zaiso ta wofantar da soyayyarshi ba,bil haqqi da gaskiya take son nuna masa iyakarsa
Wannan karon duk yadda yaso kauda idonshi kada ta kamashi yana kallonta abun ya faskara sai da suka hada ido,kamar kuma an manne idon ya kasa daukewa,ta juya ga zatonta zai daina kallonta amma sai taga yaci gaba,bata rai tayi
''gabana faduwa yake idan aka fiya samun na mujiya''murmushi ya sake yana janyo laptop dake gefansa
''ayyah am sorry''ya fada yana kunna system,bayan ta saitu ya shiga gun hotuna ya bude daya daga cikin hotunan ciki
Gefanshi taje zata dauke abun sallar dake shimfide a gun idanunta ya kai kan system din,hoton mero ne ya cika screen wanda da alama shi abdallah yake kalla
batasan ta fincike laptop din a hannunshi ba saida ya dago ya zuba mata idanunshi
''me kuma nayi?,ai na daina kallon naki ko?''ya fada a shagwabe kamar qaramin yaro
bata kula shi ba saida tayo shutting down fuska a hade cikin zuciyarta a tsinke tace
''saika tsagaita na gama gyara na tukun,baxaiyiwu ina gyaran kaya ana min janye janyen wani shirgin ba''ta fada tana canzawa computer mazauni nesa da shi
idan banda jarumtae daya aro ya tabbatar babu abinda zai hanashi fashewa da dariya
sai ya wayance da dora hannunsa guda daya kan tattausan sumarshi
''oh Allah na,mami na kin barni gashi ana nan ana gara miki ni''
shi da yayi maganar da ita kanta sai maganar ta soki zuciyarsu,tabbas ba kadan ba sukayi rashi da kewar uwa ta gari irin mamin
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Sosai ta qaranta baccinta don tayi imanin babu masifar da addu'a bata da maganinta,tana samun nutsuwa qwarai da gaske saidai gaba daya hankalinta ya karkata ga abdallah da maryam
yammacin ranar lahadi tana gida bayan ta kira baba uwaani,su biyu ne cikin parlour din,a yanzun kam da baya ga 'yan uwanta baaba uwani ce ta biyu wadda take shawara da ita
''amma hajiya tunanin da nayi,ba zamu zauna bamusan inda suke ba,mai zai hana mu nemi gidansu maryam ko suna da labarin inda suke?''
cike da gamsuwa mami ke gyada kai
''qwarai da gaske baaba,wannan shawara ce mai kyau,amma cikin ni da ke babu wanda yasan gidansu maryamu tunda a lokacin bikinta bamu samu damar zuwa ba tunda ya hade da na abdallah''
''eh hakane hajiya,amma ai da hajiya ruqayya aka kai lefan maryam dinko,ina zaton ki tambayeta zata iya tuna gidan''
''af,qwarai kuwa,bari nayi kiranta''
Cikin sa'a kuwa ta samu ruqayyan qanwarta ta tabbatar mata zata gane gidan,a nan suka shirya tafiyar nayan sallar la'asar don zata tsaya ta sallami mai gidanta zaiyi tafiya da azahar
Su uku ne cikin motar hajiya bintun ruqayya sai baaba uwani,jifa jifa suke tattaunawa kan batun har suka isa unguwarsu maryam din,sukayi parking qofar gidansu kana suka dunguma zuwa cikin gidan
Gidan yana nan yadda yake daga soro zuwa tsakar gidan suka fara sallama,inna hadiza dake kan tabarma a tsakar gidan ta amsa musu don babu kowa a tsakar gidan idan ka debe ita da huwaila dake kitchen tana fama da tuwon dare
kallo daya tayi musu ta fahimci daga irin gidan da ta fito,don haka jiki na rawa ta miqe tana fadin
''lale marabanku,sannunku da zuwa''mami batasan wace ba amma ruqayya tuni ta tunata saboda diban albarkar data yi danar kawo lefe,sake karkade musu tabarmar da take kai tayi tana fadin
''bismillanku ko zauna,ko daga ciki zamu shiga?''
ruqayya ce ta karbe cikin tabe baki tana girgiza kai
''mama muka zo nema,maman maryam''turus tayi kamar bata ji abinda suke fada din ba,don ita har yau babu abinda ta tsana irin taga wani abu na ci gaba ya samu maman,har yau bata dauki izina ba,rayuwar maman kullum sake inganta take,don hindatu kadai tafi dukkan nin yayan da ita ta haifa wadanda duk suka dawo gabanta,daya ce gidan aure saboda rashin kyakkyawan training na zaman auren,hindatun bata bar maman nasu ta nemi wani abu ta rasa ba,ta sake inganta rayuwarta fiye da da,ta sani rashin adda maryam dinta ne a akusa da ta tabbatar maman ma sai ta fi haka,duk da a yanzun ma ko hasidin iza hasada sai ya daga mata qafa
Shirun taci gaba da yi har sai da huwaila ta fito daga kitchen dinsu wanda zuwa yanzu hindatun ta gyara musu shi duk da maman ta bata girki ciki,tayi me saboda babanta da kuma huwailan wadda a yanzu ta saduda,tun ranar da aka gyara kitchen din inna hadiza tabar girki a cikinsa saidai tayi daga waje
''sannunku da zuwa''inji huwaila dake wanke hannunta bakin famfo
''yauwa,don Allah maman maryam tana nan?''
''eh tana cikin daki ina tsammanin sallah take,ga dakin nata nan ku shiga''ta fada tana musu nuni da shi suka amsa kana suka shige
''an dai ji kunya wlh,an zama 'yar kora da haka za'a qare''
''ba komai,don ma zama 'yar korar amina ai tafi minke,don qaruwar da nayi da ita banyita da ke ba''ta sa kai ta shige dakinta don tasan halinta idan ta tsaya sai su raba abun fada yanzu ba kunya take ji ba
kan abun sallar kuwa suka taddata tana raka'ar qarshe,falon nata qal da shi yanata qamshin turare,koda can ma mai tsafta ce bare yanzu da babu kowa a dakin nata sai ita kadai,suna tsaye har ta sallame,duk da batasan kosu waye ba da fara'arta ta karbesu
''ya zaku tsaya ku zauna mana''ta fada tana miqewa tare da ninke abin sallarta
sai data ajjiye musu ruwa da lemo kana ra dawo ta zauna mami nata kallon ta,take ta tuna mata da maryam dinta babu tantama ita tayo,kyau tsafta da kirki
Sun taba lemon kana suka gaisa,mami ta dubeta
''nasan baki sanni ba hajiya''murmushi tayi
''gaskiya kam,ban gane fuskar ba''
''nice mahaifiyar abdallah surukinki''
Sabuwar gaisuwa suka sake yi da mamin cikin mutunta juna kana daga bisani mamin ta gabatar mata da abinda ke tafe da su,sosai mama taji dadi don ko mamin bata fada ba takowar da tayi ta fara neman yaran ya tabbatarwa mama sihirin dake jikinta Allah ya kawo lokacin karyewarshi
a nutse mama ta gaya mata inda su maryam din suke,fadar irin dadin da mamin taji bama ita kadai ba harda baaba uwani bata baki ne
''ba shakka gobe zan je na dauko yarana,alhmdlh Allah na gode maka''
a take ta daga waya ta kira baffanta ta sanar masa,cewa yayi ta jinkirta zuwa goben,don bai kamata kai tsaye a dawo da su din ba,akwai abubuwa da ya kamata mafin dawowar tasu,baya ga haka magani yake karba,ta bari nan da wasu yan kwanaki idan ya gama tsara komai zai mata maganar
Bata musa din ba saboda tasan baffab akwai hangen nesa,cikin farinciki da zumudi suka baro gidan zuciyoyinsu fal farinciki da godiya ga Allah,ba qaramin qimar mama mami ta sake gani ba data hada diyarta da danta ta kaisu ga mafaka cikin ikon Allah,sosai ta kuma ganin qimarta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Washe gari hisham ya shirya don komawa katsina,yanason duba company din abdallah guda biyu dake can wanda abdallan yace a fidda wa ma'aikatan companies din salary dinsu tunda wata yazo qarshe
Kai tsaye ya isa dakin tsoho alhaji wanda dama abdallah na ciki suna tare bayan gama shan rubutunshi wanda ya zama shine ruwan shansa a yanzu,yana duqe gaban tsohon
''banda abunka hisham tafiyar dare ai sam bata da dadi,da ka jinkirta zuwa gobe''cewar tsoho alhaji da yaje yiwa sallama,murmushi yayi kanshi a qasa
''banso komawa ba ma malam,naso naga yadda jikin abdallah zai kaya duk da yanzun ma alhmdlh yana gayamin yana jin canji a jikinsa,tafiyar ce ta zo min haka amma insha Allahu kwana uku kawai zanyi na dawo''
''to shikenan Allah ya tsare hanya,a gaida manyan''
''ameen ameen,Allah ya qara girma''ya fada yana miqewa,ya juya ya miqawa abdallah hannu suka yi musabaha,inna wuro ta shigo da jarka biyi daya man shanu ne a ciki daya nono tace ya kaiwa gwaggonshi,godiya ya mata sosai kana suka juya dukka zasu rakashi bakin motarsa
hannunta taji an riqe da sauri ta juyo,abdallah ne,ya wani narke yana mata wani krin kallon dake sake karya duk wani makaman zuciyarta,tanajin da biyu yake mata irin wannan kallon
''baby maryam''
''abdallah mene haka''ta fada a zuciyarta
''inaji a zuciyata na kusa warkewa nan kusa,hakan na nufin mun kusa rabuwa?''
wata mummunan faduwar gaba taji,ta lumshe idonta kana race cikin muryarta nai sanyi
''sun fita fa,ka sakarmin hannu muyi sallama''
''hisham ai ba baqo bane,gwara ki zauna nayita kallonki,naga alama da gaske so kike kifi qarfina,tun jiya rabona da na ganki,jiyan ma batan kai nayi na sa kai na bandaki ashe kina ciki kina wanka''
Ba tare data shirya ba ta waiwayo tana dubanshi idanunta a waje,take kuma suka kawo qwalla,dama abinda yakeson gani kenan
''ina wanka?,ba kaya a jikina kenan''
dariyar da bai shirya ba ta subuce masa,ya dinga yi yana kallonta,sai yaga gaba daya ta kuma qaramar yarinya sosai da bazata wuce shekaru sha hudu ba
''wai ke kam shekarunki nawa,i thought ba zaki wuce twenty four ba,kamata yayi Allah a maidaki shekara goma,dubeki kamar wadda aka cewa saurayinta ne ya ganta''
ta lura ma ya maidata wata abar tsokanarshi bayan wasan kura da yake mata da zuciyarta duk lokacin da suka hadu
''Allah sai na gayawa inna wuro leqen mutane kake a bandaki...''
''a'ah,ba dai mutane ba gyara zancanki yammata,leqen mata ta nake,sai kuma mero......''
''mero?''
ta maimata sunan ba tare da tasan ta fada din ba
girarsa ya daga mata
''eh mero mana,itama matata ce baki sani ba?''ai a,hanzarce ta qwace hannunta ta fice a dakin,dariyarsa yasha sosai yana raina wayon maryam din da ta gaza gano abinda yake nufi
Ta gama shirin baccinta ciki doguwar riga mai sulbi mai hannun shimi maroon doguwa ce har qasa ta maida qaramin farin hajabinta jikinta ta haye gadon inna wuro tana karanto addu'o'in bacci,bayan ta kammala ta ja bargon inna wuron ta lulluba zuwa qugunta bayan ta lumshe idonta
Da sauri taji an yaye bargon,ta bude idanunta inna wuro ce tsaye a kanta riqe da torch light donta kashe qwan solar din dakin
''me nake shirin gani meramu?''
cikin rashin fahimta tace''me ya faru inna?''
tana nuna qofar dakin nata da yatsanta tace''ki baro dakin mijinki kizo kimin qabe qabe kan nawa gadon da yake ni ba miji gareni ba ko?''
fuska ta yamutsa
''kai inna,naga dai tsoho alhaji ai yana da turakarsa ko?''
''iyeeee''ta fada tana kama haba
''to tashi ki barmin daki,idan yaso in kinga dama kiyi shimfida a tsakar gida ki kwana can''
ta sake yamutsa fusjar tana kallon innar ba tare da ta ko motsa da niyyar tashin ba
''kai inna ni wallahi kamar ma kwanan nan kin tsaneni''
''eh koma me zaki fada ki fada amma saikin fitarmin a daki,dama kuma ni bana tarayya ai da mai kynnen qashi....zaki taahi ko sai na samo madoki?''ta fada tana dube duben abinda zata dauka na duka din,tasan kadan daga aikinta yadda take qaunar abdallah yanzun ta maketan ta sauko tana guna guni taja bargon
''ajjiye min bargona,kuma kuna da shi''ta fada tana kallonta,tilas ta ajjiye mata din ta fito
tana gab da shiga dakin taji maganar tsoho alhaji yana fitowa daga dakinsa,ta qarasa cikin girmamawa,wata 'yar farar roba ya miqo mata yana fadin
''da dakinnaki zani,tunda kuma gaki shikenan,wannan maganin banason ya wuce yau ba'a shafa shi ba,daga cinyoyin abdullahi zuwa yatsunsa na qafa,a tabbatar ko ina ya samu,kada ki barshi ya taba da hannunshi don a qa'idarsa wani ke shafa maka,sabida jikin shi har yanzu akwai ragowar abinda aka yi masa''
''to malam,Allah ya qara girma''ya amsa nata ya juya ya koma dakinsa ita ma ta shige
kan katifar ta hangoshi zqune jingine da pillow,laptop ce kan cinyoyinshi kallon wani film yake na tarihin sayyadina umar,vest ce a jikinsa da short nicker wanda iyakacinshi saman gwiwarsa,dauke kanta tayi da sauri,shima tunda ya amsa mata din ya maida kansa kan allon computer din,ta haura kan katifar ta dauki pillow qwaya daya,har zata sauka sai ta tuna da maganin
''tsoho alhaji yace a shafa a daren nan''ta fada tana miqa masa maganin
fuskarshi ba walwala yace
''wa kike son ya shafamin bayan na jishi yana gaya miki kada na taba?''shiru tayi cikin rashin sanin amsar da zata bashi,bata ankara ba taji ya damqi hannun nata bayan ya ajjiye computer din tasa can gefe ya janyota yana fadin
''malama zauna ki shafa min''take kuwa ra samu masauki kan cinyoyinshi,qoqarin miqewa tayi take amma ya danne rigarta,yasa idanunshi sosai cikin nata
''kika sake kika gudu....q'nnn,ni dake ne''ya fada cikin dakiya
''dagan rigarta to zan shafa maka''
bai amsa mata ba sai hannu da yasa yana qoqarin,zare hijabin jikinta,hannayenta ta hada ta cukuikuye hijabin saboda rigar jikinta mai fadin wuya ce bugu da qari kuma mai lafewa ce a jiki
kicin kicin yayi da fuska kamar bai taba dariya ba
''ki bar ganina a zaune bazan iya tashi ba,to kada ki kuskura na sa miki qarfina zaki sha wuya,daga ni sai ke a dakin,na bama kallonki zanyi ba,zan cire miki don kada ki shafa min ba daidai ba ko ki bata hijabin naki,ki shafa min kawai idan kinso ki koma soro ma ki kwana''
ta gama amanna da gaske yake ganin uadda yayi maganar ba wasa a fuskarshi,sakin hajibin tayi yasa hannunshi ya zare shi ya ajjiye mata shi gefe
''fatabarakallahu alhsanul khaaliqin'' ya ambata cikin ranshi saboda ba qaramin kyau night gown din tayi mata ba
''tafaddal''yace da ita bayan ya tattare short nickers dinsa can sama,kallo daya tq masa ta dauke kai,bata taba ganin wani namiji a haka ba tunda take,santalan santalan fararen cinyoyinshi masu wadatar gargasa baqa suduk suka bayyana
ta lakato maganin mak kama da man kadanya ta mutstsuka a hannunta,tamkar wadda zata taba kunama haka ta dora hannunta kan cinyoyin nasa,sai da ta runtse idonta kana ta fara shafa masa a hankali tamkar mai sanda
Shiru ya ratsa dakin dukkaninsu suna ji cikin jikinsu kada ma abdallah yaji labari,ajiyar zuciya ya dinga saki a bobboye idanunsa kan maryam wadda bata sani ba gaba daya wuyan rigarta yayo qasa,tsuntsu biyu ya dinga jifa da dutse tsaya sam ita bata sani ba,har ta gama durqusan nata ta zauna sosai
dan jan qafar tasa yayi yana fadin
''kaiiiii'' da sauri ta dubeshi tana fadin
''da zafi''kai ua girgiza murmushi ya qwace masa don dama idn nata yakeson gani ya gani din ya kuma gano abinda yakeson ganowar
''nikam gaskiya da biyu kike min irin wannan shafar mero''
baki ta muguda masa
''kada ka sake bani sunan wannan baqaiyiyar budurwa tak,ni ba suna na kenen ba''mirmushi ya kuma saki saboda tsabar iya tsokana
''ke da ita din ai duka jirgi daya ya kwasoku,gwara ma ita tunda ta iya ta sace miki miji''haushin da ya bata yasa ta kasa tanka mishi,sai qara speed din shafar da take masa da tayi
ya sake fadin
''wayyo Allah''bata ko kula shi ba har sai data gama ta rufe man tana shirin miqewa sai ya sake fincikota jikinsa baki daya ya matseta,tana sonvta qwace amma yaqi don riqon tsauri yayi mata
''ki hutar da kanki yau a jikina zaki kwana,ina zaman zamana kin jawomin,dole ki ragen zafi kafin nayi aure tunda ke kika jawo komai''
Da gasken kuwa yake don tuni har ya fara sakin layi,hannunshi ta riqe tamau tana kiran sunansa,a hankali ya janye hannunshi yana fadin
''am sorry na manta''ya fada yana kissing goshinta kana yaja musu bargo ya rufesu,tun tana a darare a jikinsa har ta saki jikinta jin shiru bai qara motsawa ba,da alama ma bacci yayi awon gaba da shi,don dole ta saki jikinta amma still tana jin yadda zuciyarta ke gudu,daga bisani ita din ma wani daddadan bacci ne ya sureta
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
5⃣4⃣
*_Allah yana cewa cikin alqur'aninsa mai girma''haqiqa ji da gani da zuciya dukkansu akwai tambaya a kansu''(ranar qiyama game da abinda suka ji ko suka gani)_*
lokacin da mami ta koma gida ita da baaba uwani bayan tayi horn an dage mata makeken get din gidan ta wuce ciki sai ta lura duka ma'aikata da security na gidan na tsaye ne cirko cirko a guri guda
kan ta fito daga cikin motar ibrahim ya qaraso cikin girmamawa
''lafiya ibrahim,me ya faru na ganku a tare guri guda?''
mamin ra fada tana kashe motar tare da qoqarin fitowa daga ciki
''wallahi mami hajiya nene ce?''
''nene?,me ya faru?''ta tambaya don wata irin tsanarta tame ji na mamaye zuciyarta,macan da ta jefa tilon danta cikin bala'i,macen da taso ganin bayan su ita da yaran da tafi qauna abdallah da maryam,ta mata alkhairi ita kuwa ta maye gurbinsa da sharri,ta zauna da ita zuciya daya yayin da ita take zaune da ita da ziciyoyo barkatai marasa kyawun manufa,ko a mafarki daidai da rana daya bata taba qullatar nenen da sharri ba sai gashi abun mamaki ita din taso abzata cikin wani rami mai tsananin hadari badan Allah ya dibi ysarkin zuciyqrta ba ya tsallakar da ita daga dukkan wasu tarakuna data dana wa rayuwarta
''ina baya ina rangadin gidan su husaini kuma suna nan zaune da sauran abokan aiki,kawai saiga husaini yazo yayi kirana waiga nene can babu ko kaan arziqi sai daurin qirji ta fito a guje daga bangarenta wai fita zatqyi nemansu adnan,kuma idan ta gansu sai ta kaagesu don sun cuceta sun ha'inceta sun gudu da dukiyarta,da farko na zata ma qarya yake saboda naga ko motsi bata iyawa komai sai an mata,amma da na bisi sai na gasgata maganarsa,to muna shawarar yadda zamu hanata fita sabida kowa yana tsoron tabata tunda ba muharramrsa bace kawai sai ta faki ido ta fice a guje,muka bita tuni har ta fita daga gidan,muna daf da zamu cimmata wata mota ta tsaya,wadan nan mutanen da kika ce kada mu sake barinsu kwanaki su shigo gian nan sune aahe a ciki suka figeta suka jefata ciki,na sa bindiga na harbi tayar har sau biyu saidai ban samesu ba''
shiru mami tayi tana jinjina kai,ibrahim ya kuma cewa
''amma mun dauki nimber din motar,gata''tsaidashi tayi
''babu bin sahunsun da zamuyi ibrahim ka qyaleta da su,qila hakan da Allah ya mata shine mafi alkhairi a gurinmu,bata dace da zama cikin mu ba shi yasa Allah ya hadata da mutanen da suka dace da ita''tana maganar ne yanayin fuskantar ya sauya saboda bacin rai da tashin hankali,ibrahim ya dubi mamin,shekara da ahekaru suna zaune tare,macace mai tausayi jin qai da taimako ga na qasa da ita,ya tabbatar ba qaramin abu bane zai sanyata tace a qyale nene ba,duk da idanuwansu sunga wasu muggan ayyukan na nene da yadda ta so maida uwar dakin tasu mamin amma ya tabbata da abinda ta aikata din yafi haka,take kuwa ya cukuikuye takardar ya yagata gutsi gutsi
''ku koma bakin aiminku ibrahim,kowa yasa cikin zuciyarsa tamkar ma baiga abinda ya faru,irin nata hukuncin da Allah zai mata kenan,don na tabbatar ba mutanem arziqi ne suka dauketa ba,kowa ya shuka na gari kai nasa''
''gaskiya ne mami,Allah ya shige gaba''
''ameen''ta fada tana juyawa cikin gidan,cikin zuciyarta tana qara jin imani kan cewa duk abinda zakayi kayishi domin Allah,matuqar kace don wani zakayi shi to kana tare da wahala,zaka kyautatawa mutum iyakar iyawarka da zuciya daya amma shi sam bai gani,qarshe ya buge da cutar da kai ko ya shiga sahin manyan maqiyanka na farko,amma idan kayi ne don Allah koda shi din wanda ka yiwan bai gani ba baka da kaico ballantana asara zaka samu ladan aikinka ne gaba ga Allah,Allah kasa mu dace,ka bamu ikhlasi
Sai data sake wanka tayi sallah tana kan abun sallar ta dau wayarta ta kira daya cikin qannenta sa'adiyya sukayi magana kan saukar qur'ani da aka raba makarantu makarantu,ko dq can lokacin marigayi alhj abdul-kareem mai nasara an musu,bayan mutuwarshi ne daga baya ta watsar,a yanzu kam ta dauki dambar ci gaba da sawa ana mata don ta fuskanci duk yadda kakai ga kirkinka kamun kai da kayuatatawa mutane wani yana nan duk duniya babu wanda yaqi jini sama da kai koda naman mahaifiyarka zaka dinga yanka kana dafawa kana bashi yana ci tsabar so,sadiyyan ta gaya mata an kammala kaso na farko gobe zasu dora kana sukayi sallama
cikin 'yan uwan nenen mami ta nemo matar babanta tace suzo su kwashe duk wani abu da ya danganci nene daga gidan don tuni kowa ya sani alfarma karamci sa darajar zaman tare yasa mami ta bar nenen a gidan,matar baban nata cewa tayi gaskiya babu abinda ya shagesu da kayan nenen,don bata manta irin cin mutuncin da tayi musu kan gadon mijinta na farko,hatta da mahaifinta ya dade da zare hannunsa cikin lamuranta
mamin tace dole kam su debe don sun gama zama tare da nene
matar baban nata ma yaba mata sukayi zaman datayi da ita don sunga namijin qoqarinta ma data zauna da ita ba dangin iya babu na baaba tsawon shekarun nan
Da qyar suka zo suka debe komai na natan suka loda a kodi kura,part din ya koma wayam babu ko tsinke nata bare na 'ya'yanta,sai a lokacin mamin ta fara jin sanyi cikin zuciyarta
''na barki da Allah nene,ko iya haka ma ya ishi yan baya ishara''abinda mamin tace kenan
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Qal gidan yake a share kamar kowanne lokaci,rairayin filin gidan tas kamar an zauna an tsince dattin cikin,banda shati shati na tsintsiya da alamun yayyafar ruwa da suka sa qasar ta danyi danshi da qamshi babu komai
gidan shiru yake kasancewar babu kowa sai ita da abdallan kawai,inna wuro ta je cikin garin gaya bikin sunan wata jikarta,tsoho alhaji kuwa kano ya tafi karbo jakarsa a hajj camp da yake kayan sun dan samu tsaiko sai ranar suka iso,ya dauki mustafa suka tafi tare don yafi jin dadin tafiyar
qasan rumfar yake a zaune kan wheelchair dinsa sanye da baqar t.shirt da red din trouser mai sulbi da kyau,yayin da maryam keta kai kawo na hada abincin dare
idan ka dubeshi a haka sai ka zaci tabbas karatunsa yake tuquru saidai ina zaman sa'ido yayi don da zarar ta kuya zqi zuba mata ido har sai ya fuskanci tana shirin sake waiwayo wa,wani kyau yaga ta yi masa cikin baqi da ja din pakistan riga da wando,duk da rigar har gwiwa take amma gefe da gefe an tsaga shi wanda hakan ya sake taimakawa wajen fidda sharp dinta,ta nanade kanta da baqin dankwali da ya sake fidda hasken fatarta muraran,sau tari yakan raya cikin zuciyarsa kodai ta hada jini da larabawa ko indiyawa
Darensu na shekaran jiya yake tunawa har yau daren yaqi fita daga tunaninsa,wani babban matsayi ya bashi don bai taba samun dama kamar ta ranar ba,har hanzu idan ya tuna yadda take shafa masa maganin sai yaji taikar jikinsa ta zuba,taushi ta laushin tafin hannunta kamar auduga,itakam ta bada hankalinta ne kan girkinta saboda haka bata lura da kallon da yake mata ba,saidai lokaci lokaci tana jin gabanta na faduwa ko taji tafiyarta na hardewa
ta fito daga kitchen zata ja ruwa a rijiya,a wannan karon kam ta kamashi dumu dumu yana kallon nata,saboda wani tsabar qarfin hali irin na abdallah tare suka hade rai hakanan kowa ya janye idonsa daga kan dan uwansa ta ita ta wuce bakin rijiya shi kuma ya bude shafin gaba na qur'anin hannunsa ya shiga sabuwar sura suratul jinni bayan ya gama suratu nuh daga sama yaje gangarowa qasa surori kadan suka rage masa ya hada saukarsa don yau yake son kammalata gobe juma'a za'ayi sadaka wa mabuqata
ta debi na farko cikin rijiyar mara katanga don kowa yasan yadda bakin rijiyar qauye yake a bude take kuma daf da qasa ta kai rumfar girki ta sake dawowa ta zuba cikin botiki duk yana satar kallonta ta gefan ido don baiso ta kuma kama shin kuma gashi bai gajiya da kallon nata,ta daga botiki kenan santsin lakar dake bakin rijiyar wadda ta jiqu da rya ya debeta,luuu gaba daya ta tafi tayi kan rijiyar
''maryam''ya fada cikin wata iriyar gigitacciyar murya idanunta a rufe tana ambaton sunan Allah,zuciyarta na bugawa kamar zata fito waje da kanta,ta gama saddaqarwa yau kam sai yanda Allah yayi da ita don ba makawa cikin rijiyar zata yiwa masauki don
qafarta ce ta fara gjrdewa wani zafi ya kuma ratsata ta saki qara,jikin mutum taji ya fada gaba dayanta kana aka janyeta gefe,a mamakance ta bude idonta saboda ta gama bayarwa zata jita tsamo tsamo cikin ruwan rijiyar ne,sai kuma ta sake haduwa da wani abun mamaki da yaso sandarar mata da jinin jikinta
Abdallah ne tsaye bisa duga dugansa kan qafafunshi kamar yadda yake a da,ta dan janye jikinta daga gareshi da fuska mai dauke fal da mamaki tabi tsawonsa da kallo,tabbas shine abdallah ne,the gentle giant man din nan,abdallah dai abdallah mami,kasa daina kallonsa tayi don har yau tana jin kodai mafarki ne daga irin mafarkan da saba yi,baya dai ta sake ja saidai wani zafi daya ratsa qafarta ya sata durqusaqa tana fadin''wash''wasu hawayen farinciki suka aulmiyo daga idanunta
Cak taji ya dauketa baki daya bai direta ko ina ba sai kan kujerarsa da ya tashi ya ajjiye ta a kai bayab ya dauke alqur'anin dake kai ya maida man window din dakin inna wuro,reshe sai ya juye sa mujiya a maimakon abdallah dake kallonta a sace dazun,yanzun ita ke binshi da kallo baki sake kuma kai tsaye
Gabanta ya dawo ya durqusa baiko damu da rairayin dake gurin kada ya bata masa kaya ba,ya kama kyakkyawar qafarta da yake tunani anan ta gurde din
matsawa wani guri yayi sannan yace
''nan ne?''bata fahimci ma da ita yake ba don ta tafi cikin duniyar mamaki,saida yasa bakinsa ya hure mata brown oily eyes dinta da suka qara sheqi sakamakon sabuwar qwallar dake ciki tana yawo,bata kai ga fitowa ba
''kada ki cinyewa mero ni mana,ina ne gun ciwon?''ya tambayeta yana sake duban qafar tata
''abdallah ka warke?ka fara tafiya fa abdallah ko baka gani ba?''kyakkyawan murmushi ya saki kana ya dago ya dubeta kana ya sake maida kansa ga qafarta
''na sani kuma na gani,tun shekaran jiya na warke maryam,ranar da kika kwana a qijina,ranar da tsoho alhaji ya baki magani kika shafan da hannayenki masu albarka''
qwallar ta subuce ta zubo ta ido daya,muryarta so cool tace
''amma abdallah kaci gaba da zama a maysayin mai lalura?me yasa ka boye samuwar....''
''shshsh!''ya fada bayan ya sa qwayar idonshi cikin nata
''akwai dalili,sannan yanzun ba muhallin nganar bane''
kai ta girgixa ya gane so take ta fake ne ta masa borin nan nata,don haka ya rigata ta hanyar matse inda ta gurde din,ai kuwa tuni ta saki abinda takeso ta fada din ta maida gurbinsa da fadin
''wayyo qafata''tare da runtse ido ta kuma damqe hannun abdallahn,sake surarta yayi daga kan kujerar ya maida ta kan rabarmar kabar dake shimfide kusa da kujerar ya ajjiyeta,zama yayi ya miqe qafafunshi ya jawo qafar tata kan cinyarsa,idanu a warwaje tace
''me zaka yimin haka abdallah,kada ka fama min ciwo''ta fada a tsorace don tasan irin wannan gurdewar ta taba irinta taja bakinta tayi shiru taqi gayawa mama,sai data yi kwana uku maman ta lura,ta takura mata sai taje an duba mata,da taje ashe targade ne,taqi yarda a gyara mata qarshe sai da maman ta kaita da kanta,ai kuwa har suma tayi kafin a gama gyaran din qafar ta gama yin tsami,shi yasa yanzun ma ta tsorata kada taje irin wancan ne
Bai tanka mata ba kamar yadda bai kalleta ba ya kama gurin,kamawar farko ra saki qara tayo jikinsa baki daya ta nanade shi saboda azaba,kasa ci gaba yayi saboda irin riqon da tayi masa ma baki daya ua zare masa lakar jikinsa,tuni ta fara hawaye tana roqonsa kada ya sake taba mata wlh zafi
shiru yayi yana kallonta yadda taje faman kuka kamar yar baby,sai kukan ya bashi sha'awa saboda duka eye lashes dinta sun jiqe sa hawaye sun sake zara zara
Tazara ya sake bata ya faki idonta ya kuma damqar ciwon,ta qara shigewa jikinsa gumi yana karyo mata tare da wani sabon kukan,har cikin xuciyarsa yake jin kukan amma yasan idan ya qyale mata gaba zafin da zatajin sai yafi haka don ya gane targade ne a qafarta,qarfinsa yasa bai qyaleta ba sai da ya gyara,tuni ta jiqe sharkaf da gumi da hawaye harda majina,ya kalli fuskarta sai yaji dariya tazo masa duk fuskar ta hada ja,miqewa yayi ya nufi daki ta bishi da kallo don har yau mamakin takawarsa bata saketa ba,ya fito da handkherchief mai kyau da kansa ya dinga goge mata fuskar har sai da tayi tsaf kana ya gyara mata zaman ya miqar mata da qafarta ya jinginata da bango
gabanta ya dawo ya zauna dirshan,ganin yadda take jefa masa harara ya sashi daukar qur'aninsa ya bude yaci gaba da tilawarsa a zuciya
sai ta tsinci kanta itama tana qare masa kallo,ko ta ina abdallah cikakken namiji da samun irinsa sai an tona,kyau zubi da tsarinsa kadai ya isheshi ya godewa ubangijin daya qerashi
Komai nashi daidai yake,babu abunda yayi kodan ko yawa a tare da shi
''ya dai yammata akwai magana ne?''taji ya fada,kunya ta kamata ta rasa na cewa sai kawai ta soma qoqarin tashi,hannunta ya riqe yana fadin
''take it easy''sannan ya maidata ya zaunar
''idan kin tashin me zakiyi,ina kuma zaki je?''
''girki na dora kuma ban kammala ba,gashi yamma na dada yi''
sai ua dinke girar sama da ta qasa kana yace
''tab,ai kuwa yai saidai kada kowa yaci abinci cikin gidan nan,babu girkin da zakiyi''baki ta saki tana kallonsa yadda yabi ua hade rai tamkar wanda ta zaga,sai taga ya ajjiye qur'anin bayan ya saka alama ta inda zai tashi ya nufi rumfar girkin,kallo ta bishi da shi,sai ta tsinci bakinta yana furta
''ahamdulillahil lazi bini'imatihi ta timmus saalihaat kana ta limshe idonta tana sake gaskgatawa da miqa dukkan imaninta ga Allah,shine mai kun fa ya kun,yadda duk yakeso haka yakeyi haka kuma za'ayin''
Tana kallonshi yana tura wutar iccen tuni hayaqi ya bulbuleshi sai gashi ya fito da sauri daga rumfar idanu jajur hawaye na diga,dariya taso kamata,dama idan banda rigimar sa ina shi ina wutar icce,wataqila ma tunda gake bai taba zuwa gaban murhu ba balle ayi batun girki,yana goge qwallan yana fadin
''kai kai kai,yanzu baby haka kike shaqar wannan abun kamar kanka zai juye,gaskiya daga yau kin gama''dauke kanta tayi kamar bata jishi ba bayan kuma ta gefab ido take satar kallonshi
Baikai ga zama ba nero tayi sallama ta shigo gidan,turus tayi ta tsaya tana kallon abdallah,gani take kamar ba shi ba,sam ta kasa dauke idonta daga kanshi
''wannan kallon fa?''yace da ita sai ta sunne kai wai ita kunya,qarasowa tayi tana fadin
''yaushe ka warka abdullahi?''
''kinga ga girki can inna ta bari jeki qarasa tukunna kya zo muyi hirar''
miqewa tayi ta isa nufi cikin rumfar tana sake mamakin warkewar tasa har ta gaza boyewa tana zaune a rumfar girkin tana waiwayensa
hakanan maryam taji wani abu ya takoreta,ta dade tana qaryata kanta akan irin abunda takeji idan mairo ta rabi kanta da sunan kishi ne saidai a yanzu a yadda abun yaqi barinta ta tabbatar cewa kishin ne
baifi saura awa daya a kira magariba ba inna wuro ta dawo gaggauce don bata kaiwa magariba a unguwa
itama dai da mamakin take kallona abdallah dake tsaye kan maryam ya harde hannayensa a qirji yana kallonta kamar wanda aka baiwa gadinta
''bawan Allah?,Allah mai iko,kaine a tsaye da qafafunka?''
kyakkyawan murmushin nan nasa ya saki kana ya qarasa ga innar yana karban daurin buhu dake hannunta ya sa mata shi daga gefe
''ni ne inna wuro''
tana kame da bakinta tace
''bari malam yazo yaga ikon Allah,Allah gwanin iyawa ya amshi addu'ar bayinsa,kai Allah mun gode maka,sannu bawan Allah,Allah ya qara lafiya''
''ameen ameen inna''
ta dubi maryam dake zaune
''ita kuma wannan fa,meron ta barwa girkin kuma?''
Ya juya ya dubi maryam da ta dan hade rai don tasan yanzun innar zata sako wani abu kuma daban,ita kam gani take sam bata sonta yanzun tafi son abdallah da mero kawai
dariya ta tasowa abdallah,bai iya hadiyeta ba sai da ya dan dara
''inna targade tayi,Allah ma ya soni ya rufan asiri saura kadan tayi iyo cikin rijiya''
cikin tsoro innar ta zaro ido
''rjiya?,garin yaya ni 'yasu mairamu?''sai ta sake yin fuskar shanu ita ala dole sai ta nuna haushi take ji,sai abdallah ne ya bata amsa
''ina tsammani santsin lakar can ne,ba shiri inna na qarasawarkewa naje na tarota''
''to Allah ya rufa asiri''ta fada tana dan masa magana da ido,shi ma ya maida nata amsa ta hanyar langabe kansa da daga hannunshi alamun ban haquri
mairo ko dake bakin wuta cikin zuciyarta take cewa
''shi kuma baya tashi warkewa sai ranar da wani abun zai sameta,haka ma fa bakinsa yayi''
(hmmm,abdallah na maryam)
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Washegari da hisham suka wayi gari cikin garin ni'ima cikin kuma gidan inna wuro,dukkansu tare suka zauna karin safe,kowanne ka dubi fuskarsa zuwa zuciyarsa cike take da farinciki mara misali,hira suke a tsakaninsu har suka kammala,maryam ta kwashe kayan ta gyara gurin
tsoho alhaji yace
''to alhmdlh abdullahi,kaga dai yadda ubangiji ya karbi addu'armu cikin lokaci qanqani''
kanshi a qasa yace
''hakane,malam naga darasi cikin rayuwa sosai,naga abunda da can bansan da shi na sai da Allah ya jarrabaceni da lalura,rayuwa abar tsoro ce haka duniya ma abar tsoro ce,darasi ne babba na koya cikin lalurar da Allah ya jarabceni da ita''
''gaskiya ne,dama wani abun baka saninsa ko gane shi sai ka shiga wata jarabtar,Allah ka bamu ikon cinye jarrabawarsa''
dukkaninsu suka amsa da ameen
tsoho alhaji ya dubeshi
''yanzu sai shirye shiryen tafiya gida kenan''
murmushi ya saki kana yace
''banjin barin garin nan da wurwuri haka,garinku ya yimin malam sosai,yaci sunanshi ni'ima,bazan taba mance wa da garin nan cikin tarihin rayuwata har abada,baya ga haka neman aure nake malam cikin garin naku''
dum kunnenta taji gaba daya yayi tamkar ba zata iya ci gaba da sauraren komai ba,sai ta rasa gane a wanne bigire take a zaune?,duk wata laka ta jikinta ta daina aiki,so take ta tashi ta bar dakin amma haka ya gagara
''a cikin karkaran nan tamu kuwa?''tsoho alhaji ua fada cikin mamaki,cike da tabbatarwa ya gyada kansa
''eh malam''
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[5:05pm, 10/4/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣5⃣
*Daga abdullahi dan mas'ud Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace ''duk wanda yayi nuni(fara aikatawa) akan wani aiki na alkhairi yana da kwatankwacin ladan wanda ya ya kwaikwayeshi(ba tare da an tauyewa kowa cikinsu daga ladansa ba''(haka yake ga wanda ya qirqiri wani aiki na sharri kuma wani koyi da shi shima yana da zunubi kan duk mutum daya daya aikata irin aikin kwatankwacin zunubin wanda ya aikata aikin)*
*An karbo daga abu ayyubal ansari Allah ya yarda da shi yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa''duk wanda ya raba tsakanin uwa da danta,Allah sai ya raba tsakaninsa da masoyansa ranar qiyama'',a wata ruwayar ta abi musa yazo da lafazin ''Allah ya la'anci wanda ya raba tsakanin uba da dansa,da dan uwa da dan uwansa''*
tuni ta miqe sabida kunnuwanta ba zasu juri jin abinda zai fada ba,saidai kafin ta kai ga ficewar har tsoho alhaji ya sake tambayarsa
''wacce yarinya ce abdullahi ka gani din,yar wajen wace?''
''ba wata bace ba malam,ta gida ce,mar........''
cike da gaggawa ra qarasa ficewa daga dakin don tuni zuciyarta ta riga ta bata sunan wadda zai kira din,dakin inna wuro ta wuce ta haye can quryar gadonta gami da cusa kanta tsakanin filalluka
''me abdallah yake so na masa ne da zai fahimceni,wacce hanya zan biyo masa da zai fahimce ni?ta yaya abdallah zai nemi auren wata?watan ma mero?eh tasan bazai wuce ita din ba don duka take takensa ya gama nuna mata haka''tambayar data ringa nanatawa kanta kenan
tana nan kwancen kimanin minti talatin da wani abu ta jiyo maganarsu,muryar inna wuro ta fara jin
''Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku,ni dama tuwo na maina ne,da kai da itan duka daya ne a guna''
wani irin abu taji ya tsirga mata da bata taba jin makamamcinsa ba,babu shakka kishi bala'i ne,bata sake gasgata kanta cewa tana kishin abdallah mai tsananin zafi ba kamar ranar,take ta yankewa kanta daga yau bata sake kwana a garin tunda ta gama iya abunda zata yi din,cikin qanqanin lokaci zazzabi mai zafi ya rufeta
Duk yadda inna wuro ta so fa fito ta qiya,gani take duka basu sonta,har,hisham wani irin haushinsa take ji,ko kowa zai goyawa abdallah baya ai bai kamata shima yabi yarima yasha kida ba,kwanciyarta tayi kan gadon tana jin yadda jikinta ke fudda hucin zazzabi ta kuma qi yarda ta gayawa kowa,sallar magariba da isha ne kawai ya tasheta daga gadon shima din sai taga innan ta fita a dakin
🍂🍂🍃🍂🍃🍂
Daga alwalar sallar asuba ta hada da wankanta baki daya ta dawo dakin inna ta canzq kayan tunda ta debo kayanta ganin hisham yazo tasan dole tare da abdallah suke kwana bazaiyiwu kuma tayi ta ziryar dauko kaya ba shi yasa ta debo duk abinda take da buqata
abin sallah ta saka tayi raka'atanil fajr wadda falalarta Manzan Allah S A W yace tafi duniya da abinda yake cikinta alkhairi,bata ko jira tayi azkar ba ta koma gadon ta sake nadewa,tanajin inna wuron na tada ta tayi banza da ita duk da idanunta biyu,ta baza kunnuwanta ne a tsakar gida ko zataji fitarsu abdallah ta shiga dakin ta dauki abinda ya mata saura
Tun tana azkar tare da tsumayin fitowarsu har wani dan qaramin bacci ya sacera sabida rashin isashshen bacci da bata samu ba jiya
Da addu'a ta tashi,ta zabura ta zauna kan gadon ganin rana ra gama fitowa sosai,ta,duba agogon dakin qarfe sha daya har da rabi na safe,takaici ya lullubeta,duka lissafinta iwar haka ta tsufa a kano,ta soma yaye bargon jikinta cike da takaici
sallama aka yo cikin tsakar gidan,kunnenta ta kasa sosai don tantance da gaske ne ko irin mafarkan da ta saba yi ne,kamar kuwa ansan tantamar da take yi aka sake rangada wata sallamar
Habawa ai duk tsawon gadon inna wuro mai rumfa batasan lokacin data dirgo daga kai ba kana ta kwasa a guje,bata dire a ko ina ba sai tsakar gidan,saura kadan suci karo da MAMI wadda ke tsaye tana son sake yin wata sallamar ga zatonta masu gidan basu jita ba
Zubewa tayi gaba daya a gaban mamin ta saki wani kuka mai cin rai,bata taba tunanin ganin mamin na a irin wannan lokaci ba dama zuciya kuma a kusa,ita ma mamin kasa daurewa tayi ta durqusawa ta dago maryam din hawaye na fita daga idanunta,rugume maryaman gaba daya tayi a jikinta cikin wani irin yanayi,daidai lokacin da inna wuro ke fitowa daga bayi dauke da buta a hannunta tana mai amsa sallamar don tana cikin bayin yake jiyo ta ya zaci maryam na bacci ne,dan tsayawa tayi tana kallonsu,take jikinta ya bata mahaifiyar abdullah ce saboda diban kama kadan da sukeyi
Dukkansu suna zaune kan tabarmar suna jimanta al'amarin,har yanzu maryam ta kasa matsawa daga kusa da mamin ganin take kamar har yanzu mafarki take,don ranaku daidai ne bata mafarki da mamin cikin baccinta
kasa daurewa mamin tayi tace
''banga Abdallah ba,ina yayi ne?''
''ya fita tattaki shi da hashimu nan bayan gari bakin rafi,kinsan an kwana biyu ba'a taka qafar ba''
cikin mamaki mamin tace
''hisham dai,dama hisham na tare da ku?''kai maryam kawai ta iya gyadawa
''Allah mai iko,shi yasa na rabu da ganinshi,babu irin cigiyar da ban ma hisham din ba ashe kuna tare''
kasa zama maryam din ma tayi ta shiga dauki ta dauki hijabinta ta sulale ta fice
tun daga nesa ta hango su zaune su biyu shida hisham da alamu magana suke mai muhimmanci sosai,a hankali ta dinga takawa tana qarasawa inda suke dukka idanunta na kan kyakkyawar fuskar abdalla
''taqi ta gane hisham taqi ta fuskanta,basan ta yadda zan fasalta mata ba,bansan hanyar da zanbi ba hisham,am doing my best hisham,ka gaya min ya zanyi?''
abinda taji yana fada kenan ba tare da ta fuskanci kan me yake maganar ba,sai ta qara sauri ta isa garesu data tuna maqaaudin zuwanta gurin,ji yayi kawai an kama hanninshi kana ta fara jansa,a mamakance ya dago yana kallonta,kasa tambayarta ma yayi sai ido da ya zuba mata,ganin yadda ta dage tana janshi ya sanya shi sauqaqa mata wahalar ta hanyar tashi ya bita tamkar raqumi da akala
bata bar jan hannunshi ba har sai da suka isa ga tsakar gidan inna wuro kana ta kauce daga gabanshi,tashin farko idanunsa suka sauka kan maminshi,runtse idonsa yayi ya sake budewa don ya tabbatar shin da gaske ne ko kuwa mafarki shina yake yi kamar yadda ya saba
''mami ce''hisham dake tsaye gefansa ya fada,ita din ma ajikinta ta ji zuwan nasa a hankali ta waiwayo suka hada ido da tilon dan nata,wani irin rauni abdallah yaji ya shigeshi,kewa qauna da soyayya irin ra da ya iyayensa ta taso masa,take jikinsa ya kama rawa yaji qafafunsa ba zasu iya daukarsa ba,yau maminsa ce a gabansa?
durqushewa yayi a gun a kan gwiwoyinsa kansa na duqe a qasa,hawaye ne ya balle masa tamkar mace,jikin mamin a mace ta miqe ta isa gabansa ta kira sunanshi
''abdallah,abdallah na ka yafewa maminka'' da sauri ya miqe ya kama hannayenra hawaye na sauka kan fuskar kowannensu,rawa bakinsa yake yama kasa magana,duk abinda yayi niyyar furtawa sai ya kasa,qaunar mahaifiyar yasa ke sake tosa masa,shaquwa da soyayya dake tsakaninsu ba qarami bane,yana jin bashi da kowa idan ba mamin ba,a lokacin data guje musu ji yayi kamar ya mutu,tawakkaki da imani da Allah ne yasa ya iya danne zuciyarsa yasa mata yadda da qaddara kafin daga bisani ta gano cewa koma meye ta aikata musu ba bisa hankalinta bane
Qarshe fadawa yayi jikinta yana jin nauyin da zuciyarsa na dada raguwa,wani sauqi ma samuwa cikin zuciyarsa daga abinda ya cunkushe mafa a da
hagu da dama suke zaune sun sanya mamin a tsakiya,ko qwaqwaqwaran motsi sunqi yi,ta dubesu cike da tausaya da qauna
''abdallah ku tafi ku kwanta hakanan,Allah ya kaimu gobe ko?''murmushi duka sukayi abdallah ya girgiza kansa
''yau mami komai iya satar baccin banjin zai iya saceni,ko na kwanta din bazan iya baccin ba,itama haka don babu ranar da bazata yi maganarki ba koda cikin zuciyarta ne,saidai idan ke kinajin sai mu qyaleki ki kwanta ko''
girgizq kantq take cikin zuciyarta tana sake jinjina qaunar dake tsakaninsu,tsanar nene ta qara cika zuciyarta,tana jin mawuyacine ta iya yafe mata haqqinsu data dauka,raba qaunar data yi dake tsakaninsu na tsawon lokaci ba tare da sunji ko sun gani ba,haqiqa Allah ne ke saka soyayyar dan adam cikin zuciya
A taqaice kwanan zaune sukayi su duka ukun don sai bayan sallar asuba kowanannsu ya kwanta
Qarfe uku na rana suna tare da ita maryam abdallah da hisham,mamin ta dubi Abdallah
''gobe nakeson mu koma gida abdallha,saboda haka ku fara hada iya abinda ke da muhimmanci,saura ku barwa mutan gidan kafin komai ya qarasa daidaita ku sake waiwayarsu''
cikin shagwabar da ya jima baiyi wa mamin ba yace
''mami a daga min qafa zuwa jibi,akwai muhimmin abinda nakeson qarasawa kafin mu wuce din''
girgiza kanta tayi
''a'ah,gobe zamu tafi''cike da ladabi yace
''shikenan mami,amma sai la'asar ko''
''Allah ya kaimu la'asar din''
wani abu ya darsu cikin zuciyar maryam,duk da zuwan mamin ya mantar da ita kaso sittin cikin dari na damuwar data shiga duk da cewa abun na manne cikin zuciyarta,ta bisu da kallo lokacin da ya miqe yana cewa hisham yazo ya raka shi,wani dan banzan kishi ua lullubeta hakanan zuciyarta ke gaya mata gurin mero zashi
''sannu maryama''maganar mami ta dawo da hankalinta,murmushi maryam din tayi ta sunkuyar da kanta,kama duka hannayenta mami tayi
''na gode na gode na gode maryam,haqiqa bani da abinda zan iya biyanki da shi,halaccinki da alkhairinki mai tarin yawa ne a garemu,haske ce hakanan alkhairi ce ke a rayuwarmu ni da dana *ABADAN* ba zamu taba mantawa da ke ba maryamu,tabbas babu wadda ta cancanci abdallah sai ke maryam,'yar halak ce kw gaba da baya,kin riqe amana da alqawarin da kika yimin tun washegarin ranar da aka kawowa abdallah ke,baka taba sanin masoyinka na asali sai wani abu ya sameka maras dadi a rayuwa,maryam ina sonki kamar yadda nake son abdallah,hakanan ina sake baki amanar abdallah,ki kasance a gefansa *ABADAN* duka tsawon rayuwarsa,na tabbatar cewa matuqar kina tare da shi koda bani duniya bazai shiga mawuyacin hali ba,don Allah maryam kici gaba da riqe abdallah kamar yadda kika yi a yanzun''
Gaba daya maryam taji mami ta rikito mata wani qaton nauyi ta dora mata ne,kamar ta daureta ne da jijiyoyin jikinta,girman mamin na da yawa a idanunta,tana daukarta ne kamar mamanta data haifeta,ta rasa mai zata ce da mamin
_kuyi haquri da wannan_
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣6⃣
*_Daga abdullahi dan umar Allah ya yarda da shi yace:Manzan Allah S A W yace''mutum bazai gushe ba yana tambayar muta ne(roqo) had sai yazo ranar qiyama fuskarsa babu tsoka daya ta nama(qwarangwal)'',ruwayar bukhari da muslim ce_*
*FANS NA ABDLLAH DA MARYAM,YA BANI SAQO YACE NA GAYA MUKU BA'A SHIGA TSAKANIN MIJI DA MATA FA😎😎,TSAKANIN MIJI DA MATA SAI ALLAH,WANDA YA SHIGAVTSAKANIN MIJI DA MATA QARSHE SHI ZAIJI..........🙈*😎😂
Itama kama hannun mamin tayi
''insha Allahu mami muna tare,babu abinda zai raba mu da ke tare zamu rayu''
giriza kanta tayi
''ko ba dade ko ba jima dole wataran na tafi na barku maryam,baya ga haka ma duk musulmi na qwarai ana son ya dinga tunawa da mutuwa ko da yaushe,haka annabi muhammad S A W ya horemu yace mu yawaita tuna mai yanke jin dadi''
''haka ne mami amma don Allah kiyi shiru,kina tare da mu insha Allahu''
mirmushi kawai mamin ta sake yi
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Kayan sawarsu kadai suka diba amma komai sun barwa inna wuro
''bawan Allah ku cire wannan abar taku mai karbar hasken rana ku tafi da ita''daroya ta basu abdallah yace
''a'a inna,ku barta ai kuma zata muku amfani,kudin shekara guda aka sanya mata kinga idan aka cire ai anyi asarar kudin ciki,tunda mu muna da inverter acan''bata fuskanci me yqce ba dai amma ta masa godiya
''mune da godiya inna,karamcin da kika mana bazai fadu ba''
Kudi mamin ta ajjiyewa tsoho alhajin amma qeme me yaqi karba,yace shi abdallah jika ko da ya daukeshi,ba don a biya shi ya masa aiki ba,ko a hanya ya ganshi yana da buqata irin wannan shi mai taimaka masa ne
mamin tace itama ba biyansa tayi ba Allah ne kadai zai iya biyansa amma sam tsoho alhaji yaqi karba bisa dole ta haqura,itama inna wuron qin amsa tayi,sai dabara mami tayi ta cusa mata qasan tabarmarta yadda bazata gani ba har sai sun tafi
Dukkaninsu suka rakosu har bakin mota cike da kewa,maryam kam harda qwallanta don tasan zatayi kewar qauyan ba kadan ba
''ka shiga motar hisham kai da hisham din idan yaso ma taho a tawa ni da maryam''
cikin shagwaba irin wadda ya sabawa mamin yace
''gaskiya mami qafata qafarki,a zamu raba mota ba''qememe yaqi yarda kuma ya kasa ya tsare maryam ba zata shiga kowacce mota ba
Dole hisham ya shige motarsa shi daya,maryam da abdallah na gaban motar mamin ita kuma mami na baya,gaba daya ta hade gabas da yamma na fuskarta don mami ce tace dole ita zata shiga gaban,shi kam dadi ya kamashi ya dinga satar kallonta yana son ta kalleshi ya tsokaneta,kamar kuwa tasan da hakan taqi uarda ta dubeshin
Yana shirin tashin motar mero ta leqo daga soron gidansu da alamu tana labe ne tun dazun a nan,idanh shabe shabe da hawaye,sai abdallahn ya kashe motar ya bude murfin ya fice yana fadin
''ina zuwa''
maryam na kallonshi ya qarasa inda meron take,sai ta rufe fuskarta da mayafi ta hau kuka sosai,tana iya hango yadda bakinsa ke motsi da alamu wani abun yake gaya mata,daga qarshe dariya ta saka,yasa hannunshi cikinaljihu ya fiddo da dubu biyar cikin kudin da jiua hisham ya rakashi cikin gaya ya ciro a ATM machine
Sai sata shige gidansu sunan ya juyo ya dawo cikin motar,yana shirin daura belt mami da hankalinta ke kan wayarta tace
''ita kuma waccan yarinyar fa wace?''
murmushi yq dan saki kana yace yana kunna motar
''zan miki bayani idan mukaje gida''
bata amsa masa ba ya tashi motar bayan yayi addu'a ta matafiyi ya soma tafiya
La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu kinaz zalimin ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta sakamkon wani irin daci da take ji,yana tuqin shima yana satar kallonta,so yake ta kalleshin kuma taqi kallonsa,ya juya ya dubi seat din baya mami ta kashingide abinta tana gyangyadi,ai dole kam sam tunda tazo garin bata yi wani barcin kirki ba tana ta 'ya'yanta
Ya cire hannunshi guda daya daga kan sitiyarin ya saka cikin tafin hannunta
''baby,me ya faru?,naga kamar baki farinciki da dawowarmu gida''
zame hannun nata tayi cikin hade rai
''ka kula fa malam da kyau,tuqi kake,kada kaje ka zubar da mu''murmushi ya kuma yi yana qoqarin sake lalubar hannunta
''mutane biyu wadamda duk duniya babu wanda ke muhimmanci a gurina sama da su fa nake tuqawa,kinga ya zamarmin dole na kula iya kulawa''
bai qyaleta ba sai da ya kuma kamo hannun nata yana murzawa a hankali kuma atausashe yana lumshe ido,ta sake zamewa wannan karon tana fadin
''ada ka jimin ciwo bana bayan kai ka adana taka amaryar''
ba don ya daure ba saura kadan ya sheqe da dariya,ya sami sarai abinda ke cin zuciyarta kenan
''anzo gurin kadan kika gani yarinya,nayi alqawari kuma sai ya cika,da bakinki zaki furtawa abdallah kina sonahi,sai kinsam ABDULLAHI ba kanwar lasa bane,a jininmu yake''ya fada cikin zuciyarsa,a fili kuwa shima sai ya janyr hannunshi ya maida kam tuqinshi yana fadin
''au haka ne fa,am sorry''sauran qiris ta fashe amma bangaren zuciyarta ya tausheta
🍃🍂🍃🍂🍂🍃🍂
Dan qaramin biki suka je suka tadda anayi a gidan duk na taryar abdallah,duka 'yan uwan mahaifi da mahaifiyarshi ne da sukasan halin da ake ciki,saidai babu wanda baiyi mamaki ba ganin abdallahn kamar ba wanda ya kwanta cuta ba,ya sani sarai hakan ya samu asali ne daga kyawun weather na garin ni'ima da kuma kyakkyawa kuma cikakkiyar kulawa da ya samu daga maryam
Cikin mahalarta taron harda SALMA da JIDDA wadanda ke ta binshi da kallon sha'awa da kishi,kishi kuma na banza,eh na banza mana don tunda ya kwanta babu wadda ta tako qafarta da niyyar gaisheshi,a zatonsu abdallan ya gama aiki ne cutar data sameshi ba qaramar mummunar cuta bace babu ranar warkewa
to ko dama can shi ba yinsu yake ba ballanta na a yanzu da yasan ajin kowa
babu batun komawa bangarensa a yanzu don mami tace bata yarda da gidan ba ma baki daya balle bangarensa don haka cikin dakunan dake corridor din nan guda hudu tasa aka gyara biyu,abdallah ya dauki daya maryam ta dauki daya,tana sane ta raba musu dakin don tuni tayi magana da hajiya laila ta sudan next weak ta zata shigo nijeria zata yiwa diyar mr presdent gyara jiki na bikinta da za'ayi so zata sauka gidan mamin don sabon gyara mamin tace tana so ayiwa maryam din,a cewarta ba zasu tare sabon gidansu da tun asali a can aka yi jeren maryam ba sai ta gama gyara diyarta,daga maryam din har abdallan ba eanda ya sani,ita dai maryam raba dakin da mamin ta yi musu da kanta ba qaramin dadi yayi mata ba don nata son ko yaya tayi wani abu da zai fallasata gurin mamin,shi kuwa abdallah ckkin tunani mamin ta sakashi da tunanin ko maryam ta gaya mata wani abu ne game da yadda aurensu ya samo asali?
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Ita kanta tayi mamakin baccin da tayi,ta jima sosai rabon da tayi bacci irin wannan,don a qauyen ni'ima yawanci daga ta idar da sallar asuba bata komawa,zama take kan abun sallah tayi addu'o'inta da karatun qur'ani sabida lokaci ne mai falala da akeson yin addu'a a cikinsa,gari na yin shaa zata jiyo kwaramniyar inna wuro take zata fito su hau aikin kintsa gidan da hada abun kari,bata farka ba tunda ta kwanta sai shida,tayi sallar asubahi ta sake komawa,sau biyu abdallah na leqota ba tare da ta sani ba tunda bata qulle dakin ba ta kwanta
sai sha daya na safe ta kuma tashi,kayan jikinta ta cire ta daura towel ta shiga wanka,bayan ta fito tayi tsaye gaban madubi tana goge ruwan jikinta kana ta ja dressing chair ya zauna akai tana qoqarin fara shafa mai
''amma fa yau garin kamar da zafi zafi,ki shafa kadan kada ya saki gumi da yawa''taji an fada,a tsorace ta waiwayo,yana kwance abinsa daidai kan gadon nata hankalinsa kwance kamar a dakinsa yake,sanye yake da t shirt fara qal mak gajeran annu sai three quater shima din fari ne tas,yayi saisaye da gyaran fuska ya sake yin kyau kmar wanda aka canza shi daren jiya
A hanzarce ta miqe da gudu ta koma cikin bandaki gqulli,tsaye tayi jikin qofar bandakin,takaici ya sake cikata data bi jikinta da kallo,yanzun qila gwanin kallon mutane ya gama qare mata kallo,ta waiwaya ga babban madubin dake maqale a bangon bandakin ta kalli kanta,daga cinyarta ne kawai zuwa qirjinta a rufe amma ko ina na jikinta awaje yake,tuni qwalla ta cika mata ido,ta koma ta sake keqashi ta jikin qofar,yana kwance bashi da niyyar tashi,danne dannensa ma yake a waya abinsa
''idan zaki fito ki fito abinki,ni zuwa nayi mu gaisa kuma na tambayeki,ba abinda kike zata bane''yq fada yana sake gyara kwanciyarshi
taja baya da sauri din gani take yana kuma hangota ne,idan banda rainin hankali irin na abdallah a haka zata sake fitowa?,kuma haka ake shiga dakin mutum ba neman izini bakasan ma ya shigo ba
tana tsakq da neman mafita taji ana knocking qofarta,kafin ta kai ga amsawa taji muryar mami na fadin
''maryam,baki tashi bane?''
gyara muryarta tayi kana tace
''na tashi mami na farka tun dazun''
''ok to bude min''
rarraba ido ta fara yikamar wadda ta yiwa sarki qarya,gaba daya ta rude,abdallah so yake ya ja mata abin kunya,haka kawaj mami ta raba musu daki ta gansu kuma tare,ita ga towel a jiki ta fito daga wanka,ta matso jikin qofar sosai yadda abdallah zai iya jinta cikin rawar murya tace
''kaga abinda ka jawo mana ko,yanzu meye haka don Allah''
tana kallo shi yana dariya
''ni ban jawo komai ba,kwato ne ni balle kice idan an ganni a dakin za'a jefeni ko ayimin bulala,ki fito kawai ki canza kayanki ki bude mata''haushi ya qara kama ta ganin yadda ya maida abun ba seriouse ba,cikin qunan rai tace
''Allah ya sawwaqe wallahi na fito ka gani a haka''
yayi wani irin juyi yai ruf da ciki saman gadon yana fadin
''mu shekara a haka mana yammata''
''maryam,me kika ce?''inji mami,sai tsoro ya sake kamata kada dai ace taji muryoyinsu,ta dan daga muryarta tace
''am...am...cewa nayi...cewa nayi dama ina bandaki ne wanka nake''ta fada cikin tsoro
''ok,to shikenan nari na shiga gun abdallah dukkanku baku karya ba shima daga cemin zaije wanka shiru,idan kin fito ki samemu a dining''ajiyar zuciya ta saki da taji alamun mamin ta tafi
Miqewa yayi ya sauka a gadon jin mamin ta soma qwaqwasa qofar dakin nashi,tana kallonshi ya murza key ya bude dakin,lallima *SAMUN WURI*(by maman farida),har ma wani key ya saka mata a daki kamar nashi dakin,bata tanka masa ba har ya fice don kada kulashi y sake dawowa ba qaramin dan neman magana bane kadan daga aikinshi
Yana fitowa suka hada ido da mami,duk sai ya dububurce,kunyarta yaji ta kamashi ganin yadda ta harde hannunta aqirji ta zuba masa ido,sai ya soma shafa qeyarsa,dariya ma ya bata ta kama hannunshi suna tafiya dining tace
''yaushe abdallah ya fara kunyar maminshi?,hala maryam ce ta koya masa?''baice komai ba sai murmushi da yayi
Cikin atamfa ta shirya super sharaton kalar lemon green da milk,ba qaramin kyau tayi mata,duk da ba wani makeup tayi ba amma hodar data shafa tabi fuskarta sosai ta qawata farar fatarta,ta sanya dan kunne sa sarqa na fashion lemon green
Tun daga nesa ya kasa kaucewa kallonta,wani kishinta da sonta na ratsashi,tayi masa kyau matuqa da gaske don bata yafa mayafi ba ma,tayi hakan ne sabida mami,tasan zata iya ganin baiken yafa mayafin da tayi bayan su biyu ne cikin gidan
Ta rusuna ta gaida mamin cikin kunya da girmamawa,ta amsa tana murmushi tare da dubansu
''nikam ai gaba dayanku kun fini kyawun gani,fatarku tayi kyau kamar ma ba'a qauye kuka zauna ba,lallai su inna wuro sun iya kiwo,dole ne kam mu nuna godiyarmu''dukkansu dariya sukayi ta ja kujera ta zauna tana gaida aliyun,ta qasan ido yake dubanta kana yayi qasa qasa da murya
''baby kinyi kyau fa ''banza tayi da shi kamar bata jishi ba,bata mantashi ba bai kunyar idon mamin yanzun sai ya jawo mata abun kunya tana zaman zamanta
Duk da haka bai qyaleta ba ganin taqi kulashi,hannu ya dinga sawa cikin kwanonta yana cinye mata chips dinta,nan ma qin biye masa tayi,saidq mami ta kula tukun
''a'ah,abdallah ya haka?,ga naka cikin olate nan kuma ma naga tare muke ci da kai ko?,don me yau zaka matsa mata''shi kansa sai ya danji kunya da ya tuna tare fa suke ci da mamin ko yaushe amma yau ya manta da ita
Ringin na wayarta ta jiyo wadda ta tabbata abdallah ne ya kunna mata don ta ajjiye ta ne kawai bata kai ga kunnawar ba,ta miqe daga cin abincin ta nufi dakin
sunan hindatu ta gani kan screen dinta,dan uwa mai dadi,wani farinciki taji ya kamata ta haye kan gado kana ta amsa
''yar uwa rabin jiki''inni hindatun,dariya maryam ta saki sannan ta qarashe mata
''banga mai kamarki ba''
''da gaske adda maryam kun dawo ya abdallah ya samu lafiya?,yanzu mukayi waya da mama ta gayamin mamin abdallah ke fada nata jiya bayan dawowarku,wallahi kinganni bani da lpy amma har naji na warke''
''eh da gaske mama take hindatu yanzu haka muna gida,ya gida ya mai gidan......''
katseta hindatun tayi cikin zumudi
''inaa,wlh adda maryam,bazan iya zama ba,ki duba hanya gani nan zuwa''tun kafin ta amsa ma ta katse wayar,ta dubi wayar tana murmushi
''hindatu uwar rawar kai da karadi,har yau ba'a canza hali ba''
Tana fitowa sukayi karo da baaba uwani na fitowa daga kitchen,cike da murna baaba uwani ta kalleta
''a'ah maryamu''
''baaba uwani''itama ta amsa mata fuskarta dauke da murmushi,sai da suka bata mintina suna hira a gun kafin ta wuce
ko da ta koma dining din tuni su mami sun kusa kammalawa,daman ita tuni taji ta qoshi zuwan hindatu kawai yasa ta qoshi,don haka jujjuya abincin kawai take
''har yanzu banga abun kirkin da kika ci ba maryam''
''na qoshi mami''ta fada tana mirmushi
''ko a ni'ima ma haka takeyi mami,batason abinci''inji abdallah cikin salon jan fada
Ya dan ja kujerarsa baya alamun ya qoshi yana hamdala abayyane
''mami,tun jiya fa aka soma turo min saqon komawa gurin aiki,don watanni da muka diba sun cika,so jiya bamu jima da dawowa ba saiga tex dinsu,zamu zauna da mr presdent gobe a abuja insha Allahu''
shiru mami tayi na dan lokaci kana tace
''anya Abdallah ba za'a haqura da aikin nan ba kuwa?''
murmushi yayi kadan bayan yayi miqa
''ba komai mami,ai duka aikin taimakon al'umma ne,idan lokacin barin yayi za'a barshi,yanzun aikin da na fara nakeso na idar da shi,alhj hamza mai qusa ina da zargi mai qarfi akansa''
''Allah ya taimaka,yanzun yaushe zaka tafi''
''da la'asar in sha Allahu,jirgin yamma ne''
''Allah ya kaimu''
satar kallon maryamun yake yaga ya yanayinta yake saidai sam taqi yarda su hada ido
*mrs muhammad*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[7:06pm, 10/6/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣7⃣
*Daga sahal dan sa'ad Allah ya yarda da shi yace''wani mutum yazo wajen manzan Allah S A W,sai yace,ya manzan Allah,nuna min wani aiki wanda idan na aikatashi Allah zai soni mutane zasu soni?,sai manzan Allah S A W yace: KA GUJI DUNIYA(dadin dake cikinta da qyale qyalenta) Allah zai soka,sannan KA GUJI ABUN HANNUN MUTANE MUTANE ZASU SOKA*
*_ruwayar ibnu maaja_*
Sam taqi dubansa,hidimad gyara gurin da suka kammala cin abinci kawai takeyi,ya san tana sanen rayi haka
''idan kinsan wata baki san wata ba yammata,duk abunki sai na dan more kan na tafi''ya fada cikin zuciyarsa yana danne danne waya,kansa ya dago kamar wanda ya tuna da wani abu da gaske ya dubeta
''af,maryam,taimakamin ki dauko mim wasu takaddu cikin cupboard please''kamar ba zata je ba haka taji saboda kunyar idon mami amma sai taga mamin ma ta sauko daga kan dining din ta koma cikin falo tayo zamanta kan kujeru,ba tare da tace komai ba ta miqe ta nufi inda ya aikata din.
Ta kusa aqalla minto goma tana dube dube cikin dakin nasa amma sam bata ga abinda yake fada din ba,dole ta juyo ta fito don ta sanar masa,a kusa da maminta tadda shi yana zaune yana nuna mata abu a waya,ta dan rusuna kadan''ban gansu ba''tace da shi,ba tare da ya dago ya dubeta ba yace
''ki sake dubawa dai da kyau,suna nan ciki ko locker din mirrow dina''a yanzu kam jikinta ya fara bata aiken bogi ne,don iya dubawa tq duba ko ina din,amma sabida bata son musu yasa ta miqe ta koma.
Ko minti biyu batayi da komawar ba ya dafe kai yana fadin
''af,na manta asge na sauya musu gu shi yasa ta kasa ganinsu,bari naje na dauka''ya fada yana satar duban mami,bata ko dubeshi ba har ya miqe yayi hanyar dakin,binsa tayi da kallo tana murmushi can qasan ranta tana fadin''dama ai bazan hanaka kebewa da matarka kuyi sallama a abdallah'',tattare itama ya nata ya nata tayi ta haye sama abinta
A hankali cikin sanda ya tura qofar dakin ya shiga,tana duqe ta duqufa neman takardu
''har yau maryam ke yarinyace na yarda da hakan ba wuya a miki wayo''ya fada cikin xuciyarsa
jingina yayi da qofar ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta son ranshi,sai datq gaji da dubawa kana ta dago,ta juyo da niyyar fita amma hankalinta na kan gado tana dubawa ko nan ya ajjiye,dalili kenan da yasa bata ganshi ba har sukayi karo,baya ta ja da sauri,tana yarfe hannunta tace
''na duba ko ina ban gansu ba nikam''.
Hannun nata ya kama yana fadin
''ba wasu takardu dama,son ganinki kawai nakeyi dama kafin nawuce,ma tabbata idan ba haka ba bazaki bari na ganki din ba sai a gaban mami''
so take ta qwace amma ya gwada mata qarfi irin na 'yan maza sai da ya kaita gefan gado ya zaunar da ita kana yayi tsalle ya fada gadon,kwanciya yayi ruf da ciki,kanshi ya dora saman cinyarta ya saka hannayenshi ya zagaye qugunta,ya gama kanainaye jikinta bata da ikon motsi
''ummm,baby,har yau bansan matsayina a gunki ba baby kin barni cikin duhu fa?''ta dan hadiye wani abu,yana nufin yace har yau bai fuskanci komai daga gareta na ko so yake sai ya qureta ya sata fadin abunda bata yi niyya ba
''ka riga da ka san matsayinka tuni a gurina ba tun yau ba''shiru ya danyi kana yace''na riga ni kuma da na manta baby,pls ki sake gayamin''.
Shiru ta sake yi don ya sakata cikin kokwanto biyu,idan ta buda baki abinda duk zata gaya masa ta tabbatarwa kanta qarya take a yanzu,idan kuma ta fadi gaskiyar wanne kallo zai mata,jin taqi cewa komai ya saka shi juyowa da sauri ya koma rigingine duka akan cinyar tata yana kallin fuskarta,sai tayi saurin runtse idonta,murmushi yayi ya saka yatsanshi ya lakace mata hanci
''yar qauye kawai,shi kenan tunda kin barni cikin duhu,idan kuma na mutu kafin na dawo burinki ya cika kenan ko?''
bata san lokacin da ta bude brown oily eyes dinta ta watsasu cikin nashi ba tana zazzaro su,shima kallon nata ya tsaya yi can qasan zuciyarsa wani sanyi na ratsashi
''mutuwa kum....''sai ta kasa idawa ganin yana sake fadada murmushinsa yana lumshe ido,idanun nata ta sake ja ta rufe ba tare da ta qarasa din ba
''a hakan ake so ace ba'a sona?,bansan lokacin da kika koyi yima kanki da kanki qarya ba''.
Bugun zuciyarta ya qara gudu jin yadda ya kama tafin hannunta yana mata tafiyar tsutsa,wani abu take ji yana bin jikinta,da hanzari ta janye hannun ba tare da ta bude idon ba,yana qoqarin sake kamowa tace
''ka bari,ba dadi''
''da dadi''ya fada cikin wara iriyar murya
cikin lokaci qanqani gaba daya yake son burkita mata tunani,hot kises ya dinga aika mata da su wadanda bata taba koda kin labarin irinsu ba,romancing dinta yake sosai kamar ba abdallah,duk da jikinta na amsar saqon amma a tsorace take matuqa hakanan bakinta bai mutu ba da fadar kalmar ''ka bari abdallah,bana so,ka bari don Allah''
ko kadan bai saurareta ba sai da ya ragewa kansa zafi,kallonta yayi idanunshi sun juye tamkar bugagge muryarshi ta koma can qasa sosai,a rufe idanunta suke gashin kanta da ribbom din ya dade ta zamewa ya warwatsu har fuskarta,wata kasala yakeji sosai a jikinsa don haka ya koma ha kwanta kamar dazu kanshi bisa cinyarta kwanciyar rigingine yana maida numfashi.
A hankali ta dinga bude idonta kamar mai tsoron cin karo da wani abun,ta dube abdallah dake kwance daidai kan cinyarta,idanunsa na a rufe numfashinsa na sauka a hankali,ta rabbatar bacci ne ya daukeshi,so take ta miqe amma ta kasa saboda gaba daya ya sakar mata nauyinsa,sai ta miqa hannunta ta dauki ribbom dinta ta hada gashinta guri guda ta dauki dankwalinta ta mayar,fuskarsa taci gaba da kallo,wani kyau baccin yayi masa sosai kamar ba mai bacci ba.
Ta riga ta yarda kyau kam Allah ya bawa abdallah shi,irin kyawun da ba kowa Allah ke azurtawa da shi ba
kusan awanni daya da rabi ya samu yana baccinshi tana zaune tamkar mai gadinsa duk motsinsa na kan idanunta,a haka taji an soma knockong qofar,ta fara qoqarin tureshi daga jikinta jin muryar mami ne amma qememe yaqi,tamkar ma yana sane sai ya sake kanannadeta abinsa yaci gaba da baccinsa,a hankali mamin ta murda qofar jinta abude yasa ta dan turo kadan tana sallama,amsa mata maryan tayi sai ta leqo da kanta,karo na biyu ta soma yunqurin maida shi gefe ta kasa cikin jin kunya,murmushi mamin ta mata kana ta mata alamar tayi shiru ta zauna kada ta tasheshi ta ja qofar ga rufe musu,ta sake kallon fuskarsa gumi taga yanayi duk da sanyin rabar dake dakin,tattausan tafin hannunta ta saka tana share masa tare da hura masa iskar bakinta,caraf taji an kama hannun naga an riqe,tsoro da kunya suka kamata sai tayi wuri wuri da ido,ya bude idonsa a hankali ya sumbaci hannun kana ya tashi zaune yana ambaton ''la'ilaha illal lah muhammadurrasululluh sallallahu alaihi wa sallam'' yana miqa
ya dubeta tana qoqarin miqewa yace mata
''sannu baby am sorry na danne miki cinya ko''bata ce komai ba tana qoqarin fita cikin zafin nama ya rigata isa bakin qofar ya saka key ya qulle,ta kalleshi cikin alamu na tambaya kafin ta furta tambayar ma ya bata amsar
''babu inda zaki je,idan kinga kin bar dakin nan nazo tafiya ne''sai ta bata fuska kana tace
''to waishin ma ni matarka ce?,bayan kace temporary ne''
girarsa ya dage kana yace''yes har yau matata ce ke,dole kici gaba da yimin abinda nakeso kafin lokacin da maryara zata iso''kasa magana tayi shi kuma ya zare key din ya jefa aljihun three quater dinsa
''daga tashina a bacci kinsani magana my mero'',jin ya ambaci sunan meron ua sake hasalata
''ai ba meron bace,sabida haka kada ka sake kira mana sunanta,kayi qoqari mu rabu lpy''shikam da yar qaramar dariyarsa ciki ciki ya zari towel dake saqale kan murfin cupboard ya shige toilet
A darare take zaune gefan gado tana bin dakin da kallo a haka ya fito ya sameta,da sauri ta dauke kanta don yaune karo na farko data taba ganinsa haka,rigar wankan jikinsa ya kunce zaren dake riqe da ita ta fadi a gun ya zama daga shi sai gajeran wando,cikin qunquni tace
''nikam naqi jinin rashin kunya''
a hankali ya tako gabanta ya durquso inda take a zaune har tana jin qamshin sabulun wankanshi da ragowar dumin dumin ruwan da yayi amfani da shi
''me kike fada?''ya tambayeta da wata iriyar murya ta daban,baya ta dan ja tana sake tsuke fuska don kusancin nasu yayi yawa
''nikam babu abinda nace''dagowa yayi yana dariya
''da kin sake kin maimaita yarinya yau da kinga yadda ake ruwan rashin kunya,yau da saidai mami tayi jinyarki ni kuwa na gudu abuja kinga ko fada ba zata samu damar yi min ba''sarai ta fuskanci me yake nufi,wai gabuntar dan fari ke damun Abdallah ko tabarar auta?,ta rasa wanne ne daga ciki,sai kuma ta tuna cewa itama 'yar farin ce take ta bawa kanta amsar saidai tabara ce kawai irin ta auta.
Babu wanda ya sake cewa dan uwansa komai har ya kammala shiryawa,itakam sai dauke kanta kawai tayi wani sashen don harkarsa yake kamar shi daya ne cikin dakin,wannan karon ma t.shirt din ya sanya saidai baqa ce long sleeve haka ma three quater dinashi baqine,wani kyau suka yiwa farar fatarsa,ya fesa turarrurrukansa,ga tunaninta ta dauka zai bude musu qofa ne su fice sai taga ya soma sauko da wasu tsadaddun akwatuna baqaqe masu kyau qana nan set ne guda uku ya ciro biyu babban da qaraminsu ya ajjiyesu
''bismillah madam,a hadamin kayan tafiya''ya fada yana dauki pillow daga saman gado ya jefar a saman rugs din dakin ya kwanta rub da ciki yana kallonta
''ammafa mami tazo nemanmu dazun kana bacci'',girarsa ya dage
''ba matsala nasqn ba wata damuwa bace indai mami ce,bamu da damuwa da ita'' qi tayi duk don ua qyaketa ta fita hakan yasa ya janyo wayarsa ya kira mamin ya tambayeta
''a'ah,ba wani abu ne,dama baqi ne suka zo matan baffa salisu ne kuma sun tadda kana bacci,har mun gaisa ma sun wuce sauri suke suna zasu''
''ok mami''ya fada ya katse wayar yana duban qwayar idonta
''sarkin kuka,komai kuka komai kuka,bayan qiri qiri baki da gaskiya''ya fada cikin zuciyarsa yana murmushi,bai ce mata komai ba har ta gaji da kallon da yake mata ta miqe ta isa ma'ajiyar kayanshin don yanzu kuma bata da wata dabarar ta kubce masa.
Tsaye tayi a gun,ta rasa ma wanne zata dauka masa,kaya ne bila'adadin iya ganinta,a sanyaye tace
''wanne da wanne zan dauka maka''
''na baki zabi,nikam,bani da ta cewa''ya fada yanajin dadin yanayin da suke,ji yake kamar ya riqe lokaci suyita zama a haka,a hankali ta dinga zaban kayan tana shiryawa cikin akwatin,tsit dakin yayi lokacin da take aikin,duk wani kotsinta yana binta da ido don,ba qaramin burgeshi take ba,komanta cikin nutsuwa,ta gama da suite suite ta saka masa yadi biyu shadda biyu tunda tasan tafiyar tasa majority sai yafi amfani da suite din,sannan ta saka masa na shan iska,ta kammala ta rufe qaramin kuma ta saka masa sauran tarkace na buqatar yau da gobe,shi kansa yanayin yadda ta tsara masa kayan ya burgeshi qwarai,komai a tsari,ta gama shima ta zuge tana fadin
''an gama'',sai da ya lumshe idonsa ya bude kana yace
''thank you verry much,shukran jazilan''
ya tashi ya zauna soasai yana fadin
''bari na qarasa daya nau'in godiyar ko''kafin tace komai ya jawota jikinsa,irin saqonnin dazu ya fara aika mata har suka so sufi na dazun zafi,nauyin da saqon nasa ya mata ya sata sakin kuka amma bai fasa ba don yana jin shine hanya daya data rage masa na samun sauqin abinda yake ji cikin zuciya da gangar jikinsa.
Kukan wayarsa ne ya ceceta,da qyar ya iya miqa hannu ya dauka,sunan mami ya gani na yawo ya daga kana yayi shiru
''abdallah,maryam tayi baquwa fa''bazai iya magana ba don yasan da yayi din tana iya harbo jirginsa don haka yace
''uhmmmmm''tuni ma ita ta kashe bata jirayi amsar sa ba,ya dubi maryam da ta dunqulr guri guda,duk da abinda yake ji sai da ta bashi dariya,sai kace wanda yake shirin yin mai gaba dayan duka ta wani tsure
''raguwa kawai,abinda baikai ya kawo ba kin gaza daukeshi''ya fada yana miqewa itakam ko daga kai ta kalleshi bata iyawa saboda azabar kunya haushi da tsoro
ya fito yana tsane jikinsa har yau tana nan inda ya barta,wayarta itama ta dauki tsuwwa da sauri ta daga hindatu ce ke kiranta
''adda maryam,jiran kusan minti arba'in''
tayi qoqarin daidaita muryarta saidai duk da haka a sanyaye take
''gani nan hindatu''ta kashe wayar ta miqe tana daidaita kanta
Sai data juya baya kana tace cikin cool voice
''bani key din zan fita ana jirana''
''dubeki,a hakan zaki fita,shiga toilet kiyi wanka''
ido ta zazzaro duk da bata kallonshi,kamar yasan zaro idon tayi kuwa yace
''eh,ko ba zakiyi ba kije ki daura alwala muyi salla azahar tayi mu samu ladan jam'i nasan yanzu masallaci sun riga da sun idar''
son fitar take don haka ta koma ta daura alwalar,kaya ta samu ya ajjiye mata da ido ta dubi kayan ya fahimci tambaya take
''ki sauya kaya na jikinki sunyi squeezing da yawa ko''ya bata masa ba tare daya dubeta ba,ba musu don itama ta yarda haka dinne ta debi kayan ta koma toilet ta canza ya jasu suka bada sallar azahar,suna idarwa ko ko addu'a bata tsaya yi ba ta dauki key din dakin da ya dora sama dressing mirrow,shima baice komai don yasan yau kam ya samu dama mai yawa,binta yayi da kallo har ta fice
A falo ta taras da hindatu da mami nata hira abinsu kamar wadanda sukayi shekara da sanin juna
''sai yanzu adda maryam har ina shirin kkmawa inda na fito''inji hindatu da sauri ta mata alamar don Allah tayi shiru don hindatu qanwar abdallah ce yanzun ta bata kunya,ashe mamin ta kula suka hada ido kunya ta kamata,sai yanzun ta gane wayo wato abdallah ya mata da ya sata canza kaya,tunda mami ai zata iya gane ba da su ta shiga ba,mamin gwanar kawaice da basarwa sai kawai ta miqe ta koma samanta ta basu gu
ajiyar zuciya ta saki tayi harr da idanunta,hindatun dai tace
''ko kunya bakwaji adda maryam,kubar mamanku zaune ita daya ku qule daki kuna cin soyayyarku''ido ta zare mana
''yi mana shiru mara kunya 'yar lukuta kawai,wai hindatu haka kika koma?,kina kallon kanki a madubi kuwa,lallai jabir shima da shi da ya barki kika yi qiba irin haka''
dariya tayi''ni da shi duka bamu ganin qibarmu,amma kowa sai ya ce mun zama 'yan lukutaye ni da shi''
''eh gaske''maryam ta fada tana kallon hindatun yadda ta koma,tayi bul bul ta sake zama fara,hira tayi hira qarshe ma dakin,maryam din suka koma,sai da suka shafe aqalla kusan awanni biyu suna hirar yaushe gamo.
Har kusan qarfe uku na rana suna hira kafin tayi haramar tafiya,a falon suka sake taras da mami hannunta dauke da poil paper ta nufi dakin abdallah hindatu tayi mata sallam,cewa tayi ta jirata ta koma sama ta dawo dauke da turaruka ta bata,hannu bibniyu hindatu ta amsa ta mata godiya kana maryam ta rakota.
Wata sabuwar matrix ash colour taga ta saka muqulli ta bude,baki maryam ta kama
''ah,lallai yarinyar nan jabir na shagwabaki,yanzu shikam ya yarda ya bawa hindatu mai shegen rawar kai mota take ja?''dariya hindatu tayi
''kai adda maryam,an girma da yanzu,idan da rabo ma nan da wata bakwai sai kizo suna''
duka ta dan kai mata
''eh lallai hindatu baki da kunya,laifin jabir ne''sai da ta shiga cikin motar ta zauna kana tace''zan biya gida fa na gaida mama,me zan ce mata?''take kewar gidan duk ta kamata,tana son taga mamanta sosai,watanni kusan nawa ta share rabonta da ita,tun ranar da aka fiddota zuwa fidan mijinta
''kice ina gaidata sosai da sosai,sannan nima ina nan zuwa''
''amma adda maryam duk ranar da zaki din zaki biyo min ko don Allah''ta fada taba yin kalar tausayi duk don tazo mata din,murmushi tayi
''kai hindatu''
''eh mana,baki fa taba zuwa min ba adda''
''to naji,zanzo insha Allahu''
''yauwa adda ta''ta fada tana dariya ta eufe murfin motar kana ta tada ta taja,bata bar gurin ba tsayawa tayi taga irin driving din hindatun,sai da ta fice a daga gidan kana ta saki yar qaramar dariya tana girgiza kai
''hindatu,hindatu''abinda ta fada kenan cikin zuciyarta ta juya ta koma cikin gidan.
Kitchen ta shiga kai tsaye da zummae dora musu girkin dare,saidai abun kunya ta tadda mami harta kammala ta adana cikin warmers baaba uwani na gyara kitchen din,cikin kunya ta fito ta koma dakinta,wanka ta shiga tayi kana ta fito ta sauya wasu kayan,doguwar riga ta sanya ta atamfa wadda ta kamata daga sama daga qasa ta bude sosai,ta mata kyau qwarai cikin ragiwar dinkunanta ne na fitar biki da bata kammala sakawa ba.
Mami na gaba abdallahn na gefanta,security din abdallah ne guda biyu riqe da akwatunansa,yayin da ita kuma ke binsu a baya a haka suka isa harabar gidan inda dalla dallan motocin da gwamnati ta sakewa abdallah guda biyar ke jiransa wadanda da su zasu rakashi airport su kuma su wuce abujan su hadu a can.
Duk suka shafa addu'an da mami ta gama jero masa kana ta dan matsa don basu damar sallama,hakan yakeso don dama tun dazun idanunshi na cikin nata,moment nasu na dazun kawai ke masa kai kawo,ji yake kamar ya dawo da hannun agogo baya,hannunshi ya miqa mata idanunshi fal so qauna da bege,a kunyace ta miqa masa nata hannun,cikin motar ya janyota a tausashe,saura kadan ta fada cinyarsa ya rungomota jikinsa kana ya miqa hannu ya rufe murfin motar driver najin haka ya kunna motar ya jata,mami na can suna magana dasu ibrahim sai gani tayi har motocin sun fice.
Gam gam ya hade hannayensu waje guda kana ya kwantar da kanshi kan kafadarta,yadda bata ce komai ba shima haka,kowannensu da abinda yake saqawa ranshi a haka har suka isa filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake nan kanon dabo
Ahankal motocin suka koma tafiya kasancewar sun fara shiga cikin airport din,sai a sannan ya fara magana
''ina fata zaki cika zuciyarki da soyayyata kamar yadda tawa take cike da taki kafin na dawo,duk da na sani cewa ko a yanzun ma nasan cike take din saidai dama da aka hanata,abu daya da zan gaya miki maryam am sorry to say bazan iya cika miki alqawarin da na daukar miki ba,bazan iya sakinki ba maryam har *ABADA* ke din tawa ce''ya qarashe maganar yana daga kansa dagq kafadarta,wata farar envalope fara qal ya ciro daga aljihun suit dinshi ya bude tafin hannunta ya saka mata,dai dai lokacin da motar tasu ta tsaya aka bude masa murfin.
''Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo dani,kimin addu'a don muhimmin aiki zan gabatar wanda koda shine aiki na qarshe da zan aiwatar insha Allahu sai na gabatar da shi,alhj hamza ya jima yana cutar da society dinmu,ya dade yana ha'intar qasarmu yana lalata rayuwar matasa maza da mata,yana shigo da mugayen makamai da qwayoyi,in sha Allahu wanann karon qarahensa yazo,ki saka ni a addu'o'inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam''
wata muguwar faduwa gabanta taji yayi,a hankali ta furta
''Allah ya tsare,Allah ya bada sa'a''saidai bata san ya ji ba ko baiji ba don ya fice da hanzarinsa ganin sun kusa makara yana baiwa driver din da ya daukosu umarnin ya fara maida masa ita gida sannan su kama hanya,binsa tayi da kallo shi da security dinsa har ta daina ganinshi,drivern ya dawo ya rufe murfin kana yaja motar
Batasan dalili ba kawai dai taji zuciyarta ta hade envalope din da ya bata tayi tsakiyar hannunta tana jin qamshi na fita daga jikinta
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣8⃣
*Daga abu hurairah R.A yace:Manzan Allah S A W yace''na haneku da yin hassada,domin hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yadda wuta take cin karmami(yayi,itace)*
Cikin motar laqwas jikinta yayi gaba daya,tana jin wani abu mai kama da kewa na shigarta kamar wadda aka cirewa wani muhimmin abu daga sassannin jikinta
Dakin ta ta wuce kai tsaye ta fada gado tayi ruf da ciki,kasala take ji da canjin yaynayi cikin jikinta,sai taji gidan ya mata fayau kamar ita daya ce a ciki,ganin matuqar taci gaba da zaman a haka kasalar zata rufeta da gasken ya sanyata miqewa ta fito kai tsaye tayi sashen baaba uwani
A tsakar gidacta tatar da ita kan tabarma tana gyara zogale,kan tabqrmar ta isa itama tasa hannu tana tayata suna hirarsu,qarar wayarta ya katse musu hiran kiran raliya ne,tana murmushi ta daga sanan ta mata sallama
''maraaba da dawowan diyana''cikin sauti mai dauke da farinciki ta maida mata amsa
''uwar gida kuma amaraya agidan muhammad nasir''
dariya itam tayi cike da nishadi
''a wannan kirarin ai sai ku,ku da ludayinku ke kan dawo''
sai da suka gama zolayar juna kamar yadda suka saba sannan suka fara gaisawa
Hira sukayi mai tsawo wadda har baaba uwani ta kammala gyaran zogalen ta kwadanta basu gama ba
Har bayan magariba tana gun baban suna hirarsu,sai sallamar mami kawai sukaji
''zuwa nayi na duba dama,nayi zaton bai dawomin da ke ba''
kunya ta kamq maryam din ta sunkuyar da kai tana murmushi,tana idar da sallar isha'i ta yiwa baba sallama ta koma bangarensu
Ta kammala shirin naccinta tsaf ta haye gadonta,saidai ko guda baccin da take da muradin yi bata ji alamunsa,wata iriyar kewa da madaici na daban take ji na damunta,juyi take tun daga farkon gadon zuwa qarshensa,tayi hakan yafi sau a qirga,tana son qaryata kanta kewar abdallah take saidai ta gaza,sai ta tsinci kanta da muradin jin muruarsa saidai ko kadan ba zata iya kiransa ba,hasalima bata tunanin akwai lambar wayarsa cikin wayarta,ta miqe a hankali ta jawo side drower ta ciro envalope din da ya bata dazun,dawowa tayi kan gadon ta kwanta ruf da ciki,a hankali ta farketa,kudi ne sababbi fil a miqe yan dubu dubu masu yawa suka fado,yar qaramar takarda ce maqale jikin bandir na kudin,ta cirota ta budeta,karo na farko da idaninta suka ci karo da kyakkyawan rubutu wanda bata yaba ganin kamarsa ba
''kiyi amfani da su idan buqata ta taso miki,love you so much my sugar''
dunqule takardan tayi ta dorata saman kudin
Ta sake bude cikin envalope din take taci karo da wata takardar fara qal mai adon furanni wadda ba shakka itake tashin qamshin nan,ajjiye envalope din tayi kana tasa hannu biyu ta ware nadin da aka yiwa takardar,sallama ce a farkon takardar cikin kyakkyawan rubutu da harshen larabci
_qoqarin mantawa da wanda kake so is like trying to remember some one you never meet,i know we feel d same baby saidai bansan me ke yawo cikin zuciya da ruhinki ba,dont let your ego stop u from doing whats right,duk abinda nayi nayi ne saboda ke,duk abinda kike gani na miki laifi a akansa saboda ke na aikata,sonki ne sanadi baby,i cant express my feelings a kanki baby,ban taba sanin haka so yake na sai a kanki,zan iya cewa kai tsaye ke kika koya min so,nasan kina tunanin na auroki ne kan tilas,ba haka bane na aureki saboda sonki da qaunarki da nake,nayi tsammani zaki qini zaki qi sona hakan ne yasa ban nemiki kai tsaye ba,but sorry for hurting u baby_
_kalmomi na sun bata ranki hakan ya sa kika riqeni,na sani na kuma san na fada,but banda ke baby baki ciki amma duk da haka am sorry again for my words and action last time,ina sonki baby ina sonki,am not with you to play games,ina fatan komai zai gyaru kafin dawowata,bazan iya jurar rasaki ba bazan iya ba,zanso ace ko yaushe kina tare da ni,baby ina da qarfin buqata tun ba yau na na sani,idan kika qi ni bazan iya sakinki ba duk tsanani matuqar ina raye amma ina fatan bani dama nayi aure,koda babu komai tsakaninmu ganinki da zamanki a matsayin matata kawai ya wadatar da ni,ke ta dabance baby ki yarda,inajin komai nawa daban duk lokacin da muke tare,am feeling safer when iam wrapped up in your arms then ever before,duk lokacin da nake kusa dake baby am overwhelmed with happiness,kin soni kin ceceni kin kubutar da ni kin kuma tserar dani,shin wannan ba so ne ba baby?bai isa a kira waannan so ba?,so mai ma kuwa mai tsada,so mai cike da sadaukarwa da fansa?,kin min abinda 'yammata da yawa suka kasa min,na haqiqance u are what i have been waiting for my whole life,so na haqiqa so na gaskiya,kina sona ba tare da kinsan ma kina sona din ba baby_
_alhamdulillah finally a found someone who loves me just for me,ba don wani abu da nake da shi ba,but ban manta ba i promise sai na ninka sona cikin zuciyarki fiye da da,nasan nayi nasara duk yadda kika kai ga boye hakan alredy na ganahi cikin idanuwanki koda zaki qaryata ni,abu na gaba shine ki fadamin shima na tabbatar miki cewa sai nayi nasara nayi alqawari,TO THE MOST BEAUTIFUL GIRL IN D WORLD,AM SORRY BABY,_
Lumshe idanunta tayi tana jin wani abu da bata taba jin irinsa ba na ratsata,gaba daya abdallah ya gama kasheta,muguwar kasala ce ta lullubeta,sai ta ninke takardar ta lalubo jakarta da take ajjiye muhimman abubuwanta zata jefa ciki idanunta suka sauka kan takardar,takarda ce data dauketa washegarin daren da abdallah ya fara cuta,sam ta mance da ita,da sauri ta daukota ta bude ninkin da tayi mata,rubutune mai kyau kamar wancan saidai bai kai yawan wancan ba
_idan da kina da masaniyar tun yaushe na fara sanki ba zaki nemi abdallah ya rabu da ke ba,na soki a lokacin da bakisan akwai mai sonki ba cikin duniya,maryam tun kina 'yar secondry school na fara sonki,cikin kulawaata da sa idona kika kammala universty dinki,can you remember sau nawa kike zuwa registration ace miki an dau nauyinki saboda hazaqarki cikin dalibai?,zaki iya tuna samari nawa kika yi suka tafi basu sake dawowa ba?,har kina tsammani ko matsala ce daga gareki,kin kusa auren jabir a lokacin bani qasar nan ban sani ba na tafi jinya na gubar da naci london,cikin qurarren lokaci na samu labarin hakan ina can,sauran qiris na rasa raina san da na samu labarin zakiyi aure amma da yake Allah na sona ya tsinke lamarin,dalili kenan da na nemi sabon mai dafa min a binci saboda na sani bangarenki ne........._
Iyakar rubutun dake ciki kenan saidai tasirin da ta yuwa zuciya da gangar jikinta mai yawa ne har ta kasa zama ta miqe tsaye,da gaske abdallah yake?shekaru nawa nufinsa yana tare da sonta,abdallah ya dade tare da ita ba tare data sani ba
A hankaki wasu abubuwan da suka dinga faruwa da ita a baya suka dinga fado mata,sautari akan tsaya da mota ta alfarma da niyyar rage mata hanya,a lokacin haushi da takaici na kamata ne don tana tsammanin 'yan kama wuri zauna ne kawai wadandq suke barewa duniya gyada taci keson hilatarta,saidai bata taba katarin ganin fuskar abdallah cikinsu ba,duk cikin nashi salon game din ne kamar yadda ya mata kan ABDUR RAHIM?.
sai kawai taji murmushi ya subuce mata
abdallah?
abdallah?,wanne irin mutum ne kai abdallah,basira da wayinka sun isa,you have play good game with me''ta samu kanta tana fada cikin zuciyarta,sai ta koma bakin gado ta zauna tana tuna abubuwa masu yawa a wancan lokacin,tasha ganin abubuwa masu yawa da suka sa ta dinga jin tsoro har take ganin ko jinnu gareta
Wayarta dake silent taga tana haske,ta miqa hannu ta daukota daga gefan pillow,baquwar number ce,sai data daga kai ta kalli agogo qarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare ,ta maida kanta kan wayar tuni har kiran ya tsinke,tana shirin maida wayar wani kiran ya sake shigowa,da tayi kamar ba zata daga ba daga qarshe ta daga din ta kara a kunnenta kana tayi shiru don tantance waye
''assalamu alaikum''muryar abdallah ta daki dodon kunnenta,kasa zama tayi sai ta sulale ta kwanta ruf da ciki saman gadon saboda wani makami da ya aikowa zuciyarta,sake maimaita sallamarsa yayi wanda wanann karon sai da ta lumshe idanunta,lebanta ne suka amsa ba tare da ko wane harafi ya fita ba
''baby nasan kina jina,zuwa yanzu na tabbatar kin karanta saqona''itama so take ta dan rama ko yaya ne kafin ya dawo kano,muryarta low sosai wanda ko kai dake dakin babu lallai kaji me take fadi
''ban duba ba,don bani da time na duba takardu''murmushi ya saka mai sauti da wata 'yar shashsheqa wanda har sai da ta jiyo shi,tsigar jikinta ta zuba
''baby,baby,baby,kullum kina yiwa kanki qarya me yasa?,i know tuni saqona ya isa,ko kice eh ko kice a'ah,na kira ne dama naji muryarki ko zan iya bacci,sai nakejin dama mu koma qauyen ni'ima muyi zamanmu,atleast acan zamu dinga kwana daki daya,idan da rabona ma sai in kwana cikin ni'imtacce jikinki,baby na kasa mance moment namu na dazun ina jin kamar ya dawo,i want feel you beside me,i want to feel your lips......on my neck and.....baby i want.... Iwant''ya fadi kamar mai tsoron magana
''i want to run my head along your chest,kiss your lips....''ai bata iya jumurin sauraronsa ba ta katse kiran nasa ta jefa wayar gefanta bayan ta tsura mata ido
Tana kallin kiran nasa amma bata jin zata iya dagawa yaci gaba da horata babu gaira babu dalili,shi dole sai ya tada zaune tsaye,sai da ya hada mata missed call kusan goma sanann ya haqura,qarfe saya da kwata ta sauka a gadon ta shiga bandaki ta daura alwala tayi nafila raka'a biyu ta kwanta,tunani ne fal kwanyarta ta kama wanann ta saki wancan,cikin haka tunanin mero ya fado mata,sai taji ranta ya baci,tana son sanin haqiqanin me tsakaninsa da ita kafin komai ya daidaita,a uziyya tayi ta kori tunanin daga ranta don haka dabi'arta take bata kwana da kowa cikin ranta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Ta makara sosai gun tashi kuma mami bata tayar da ita ba,bakinta ta wanke da fuskarta ta fito falon bata tadda mami ba sai baaba uwani tana ta gyara kitchen,nan ta tsaya sunq gaisawa har mamin ta sauko,tayi adonta cikin dogowar riga mai zubin buba saidai ready made ce wannan,bayan sun gaisa mamin ta gaya mata ta shirya hajiya laila na zuwa anjima zata fara mata gyaran jiki,ita gaba daya kunya ma kamata take duk da ta sani mami bata dauketa suruka ba amma akwai kunya tsakani,ta amsa mata da to sannan ta koma daki.
Ta daura towel tana shirin shiga wanka saqo ya shigo wayar sai ta dawo ta duba,number din dazu ce wadda ta tabbatar ta abdallah ce
''baby jiya kin kusa kasheni wlh,sauran qiris na gayawa mami yadda kike gara mata yaro,ina gaya miki damuwa ta kika gudu kika barni,me yasa baby?,i need your help baby''
bata shirya ba amma sai da murmushi ya subuce mata,ya tuna mata ma,take ta kira mamanta,hira sukayi sosai wadda ta qara mata kewar gidansu
Cikin kwanakin gyara sosai maryam kesha wanda ko bazawara aka yiwa hakan sai ta tsere ma sa'a,itadai maryam nata ido,wannan qauna da mami kewa abdallah ba kadan bace
🍃🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Zaune suke su biyu cikin fallen dakin nata wanda yafi kama da kango,idan ba kyakkyawan sani kayi mata ba zaka tsammaci mahaukaciya ce sabun kamu,tuni ta saje da su tabi sahunsu kamar yadda habiba ta shaida mata,ta tsotse ta rame kamar wadda kullum ake diba ana kada miya,ga uban ciki a gaba ya fito yayi tsororo kamar dosana shi akayi babu kyawun gani.
''yanzu habiba babu wata hanya kenan ta kubuta''ta tambayeta cikin damuwa
''bana zaton zahariyya akwai''
dariya sukaji ana babaka musu a razane suka daga kansnsu,malam na hayi ne tsaye bakin qofar dakin yana shigowa
''kuna batawa kanku lokaci ne amma babu wadda ta isa ta kubuta daga gareni,mutane ne ku masu son zuciya,kun bijerewa Allah kuna neman biyan buqatarku kan wani mummunan qudiri naku,yadda kuke da baqar zuciya nina haka nake,kunga kenan zamu je ta tadda da mujemu,a sannu sannu mata ire irenku zasu ci gaba da shiga masibu kala kala,walau a nan duniya ko a lahira,irin mu muna nan da yawa Allah ya ajjiyemu saboda ire irenku,haka gaba dayq mu da ku kuma sai munje lahira za'a hukunta mu baki daya,ni dama na riga na sani bani da rabo a lahira,kunga ai gwara naci nawa tun anan''ya juya ya fice yana sheqa dariyarsa.
Hada kai sukayi suka fashe da kuka kowacce da irin tata nadamar,sun qi Allah bayan ya musu ni'ima,idanunsu ya rufe basu ganin baiwar da yayi musu da tarin ni'imominshi a garesu sai yanzu da ya karbe abinsa,dama ya fada cikin littafinsa mai tsarki''idan kuka gode min zan qara muku,idan kuma kuka kafirce to haqiqa azabata mai tsanani ce'',sun yarda sun dauki hudubar shaidan,wanda dama bashi da burin da ya wuce batar bayan dama ya sani cewa tun can dama shi batacce ne,kuma dama yayi wa Allah alqawari sai ya batar dq bayinsa kamar yadda yazo cikin wasu surori na qur'ani lokqcin da Allah yace ya fita daga aljanna la'ananne ne shi
''kuma la'anata tana tare da kai har zuwa ranar qarshe''
sai shaidan din yace
''ya ubangiji ka jinkirta min izuwa ranar qiyama''sai Allah yace an jirka maka,har uzuwa rana da lokaci sananne,sai shqidan yqce da ubangiji
''na rantse da isarka da buwayarka sai na batar da su gaba daya,saidai bayinka daga cikinsu tsarkakakku''sai Allah yace da shi
''haqiqa bayina baka da wani iko a kansu sai wadanda suka bika dagq cikin batattu,kuma haqiqa jahannama ce makomarsu gaba dayansu,tana da qofofi guda bakwai''a wani gurin kuma shaidan din yace
''zanzo musu ta tsakaninsu data damansu data hagunsu mafi yawansu zaka samesu marasa godiya''
haka ya sake fada a wani gurin cewa
''sai na batar da su,sai na sanya musu buri sai na umarcesu su canza halittar Allah(kamar bleeching yana daya daga ciki)
shi yasa Allah da kansa yake fada mana
''haqiqa shaidan abokin gabarku ne ku ruqe shi abokin gaba'',muna mantawa ne da ranar mutuwa ranar tonon asiri ranar hisabi,ranar da duk wata rai saita bi ta saman siradi ta wuce wanda qarqashinsa wutar jahannama ce,aikinka mai kyau gaskiyarka zumunci da ruqon amana ne kawai zai qetarar da kai cikin salama
Son zuciya ya mana yawa,muna biyewa soye soyen zuciyoyinmu baka iya hana zuciyarka aikata mummuna wanda hakan ke kaimu ga halaka,Annabi muhammad S A W yana cewa''an lullube aljanna da abinda rai baya so(kamar salla azumi zakka,zumunci,da sauran ayyukan alkahairi da bamu son yi ko muke jin wuya gun aikata shi)an kuma lullube wuta da sha'awe sha'awe(kamar zina,caca,cin dukiyar marayu,annamimanci,sata da sauran abubuwa da rai kejin dadi yayin aikashi)''
Allah ya sake cewa ba don falarlarsa da rahamarsa ba da duka munbi shaidan face 'yan kadan
Allah kasa mu dace duniya da lahira
Sun jima cikin alhini da jimantawa kansu kafin habiba tace
''zahariyya nifa na gaji,anya ba kashe malam zamuyi ba?''duk da yadda taso ga neman mafita amma sai da shawara ta tsoratata,don bata manta ba irin wannan kuskuren taso aikatawa ya kawota ga wannan matsayin da take ciki yanzu
''habiba,in sake yunqurin aikata wani kuskuren kenan?''
''kashe malam,zahariyyq rage mugun iri ne cikin al'umma,bakiji abinda yace babe,malam fa bazai taba shiryuwa ba,shin kin san shi mutum nawa ya kashe cikin wannan qazamar harkar tasa?(hmmm,sai yanzu data ritsa da su suka san qazama ce)''
cikin rashin gamsuwa ta girgiza kai
''wannan shi da Allahnsa amma mu dq muke neman kubuta kuma inamu ina kisa,shawara daya ce kawai tunda mu bamu tsaya munyi karatun addini ba boko muka sa a gaba,ba wasu addu'o'i garemu ba kawai kullum mu dinga karanta masa fatiha ba adadi,ai Allah yana jinmu,kuma nasan da yardaraa wata rana zamu kubuta''
take ta yarda da shawarar zahariyyan don tafi tata fidda maslaha
*mrs muhammd ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶5⃣9⃣
*An karbo daga Abdullahi dan amru dan Aas Allah ya yarda dasu baki daya,haqiqa Manzan Allah S A W yace''yana daga cikin manya manyan zunubai mutum ya zagi iyayensa(uwa da uba)'',sai sahabbai suka ce ''shin mutum zai iya zagin iyayensa?'',sai Manzo S A W yace''eh,a zagi mahaifin mutum,mutum(wanda aka zaga) shima ya zagi mahaifinsa(mahaifin wanda ya zageshi din),ya zagi mahaifiyarsa shima(ya rama) ya zagi tasa(wanda ya zageshin)''*
_ruwayar bukhari da muslim ne_
Itakanta ko ba'a gaya mata ba tasan ta canza,wani santsi da qamahi fatarta ke fitarwa na musamman,wani lokaci har shanshana kanta takeyi kota tsaya kallon kanta a madubi,magani masu kyau mamin ke bata na ainihin 'ya'yan itatuwa ba gamje gamjen bature ba,tana jin naiyinta da kunyarta haka zata karba ta sha tana rufe ido,mamin takanyi murmushi tace
''babu kunya tsakaninmu maryam diyata ce ke kamar yadda nasha fada,namiji kuwa dan son gyara ne bashi da kunya ta wanann bangaren,balle abdallah da ina kula da rawan kanshi,idan kika zaune kara zube cikin lokaci qanqani zaki wargaje fes babu kunya zai dauko miki wata,shi yasa har yau ina alfahari da lambar yabo da na karba agun daddyn abdallah har ya mutu yana yabamin,so haka nakeso ki zama gurin abdallah koma kifi haka,koda akwai wata ma kisha gabanta''
kunya ta kuma kamata duk da maganar ta taqarshe ta dan haifar mata da fargaba
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun ranar bai kima kiranta ba,har ta dinga zaton ko fishi yayi,cikin ranta take jin ba dadi idan fushin kuwa yayi,can qasan ranta ake tsinkularta ta kirashi taji muryars amma da zarar tayi kamar ta kira din sai kunya da nauyi su hanata
Kusan tara na dare ne suna zaune ita da mami da baaba uwani,baaban ce ta musu sallama ta wuce bangarenta mami ta duba agogon kana ta miqe ta haura sama bayan ta ce da maryam tana zuwa,kallo take amma batasan ya akayi idanunta suka kai kan hotkn abdallah window size dake kafe a can kusurwar falon ba,sai ta kafe hoton da ido,a hankali wani abu ya dinga motsa zuciyarta,ta miqa hannunta ta duba call history inda num dinsa take wadda ko serving bata yi ba,ta shiga canki camkin ta kira ko a'a,kamar wadda aka tankwabi hannunta ta danna kiran gakin ya soma tafiya sai ta qyaleshi.
Daidai lokacin da yake cikin dakin hotel din da suka sauka,shi da manyan yaransa ne guda biyu,a gaggauce yake shiryawa cikin wadansu baqaqen kaya samfurin kayan jami'an tsor,duk da kqyqn qiki ne amma ba qaramin kyau suka yi masa ba,yana cikin daura belt dinsa bayan ya sanya bindigarsa a aljihun wandon na baya yaga shigowar kiran,bai lura ba sosaj ya dauke kai yaci gaba da sanya boot a qafarshi baqi don muhimmin aiki ne a gabanshi bai saba qa'idar lokaci komai nasa a tsare yake
Tana dab da tsinkewa ya kai hannu da niyyar dauke wayoyin nashi ya kashesu don bazai fita dasu ba,ba dasu zaiyi amfani ba already ya gama maqala na'urar da zasu dinga communicating da abokan aikin nasa a jikinsa,mamaki ya kamashi ganin sunan *honey sweet* bisa screen dinshi,katse kiran yayi kana ya kirata
sai da gabata ya dinga bugawa kafin ta amsa kiran,a kasalance ta kara wayar a kunnenta hade da yin sallama,duk da kuzarin da yake da shi sai da yaji an zare masa shi tas,shi da yake ta shiryawa a gaggauce yana basu order din baison bata lokaci sai gashi yana shirin kwanciya saman gado,yaran nashi suka kalli junansu da lamar tambayar ya haka?a tsakaninsu saidai babu damar furtawa oga suka ja bakinsu suka tsuke,alama ya musu da su fita su jirashi a qofar dakin yana tsoron kada ya tafka abun kunya a gabansu,don tunda yaji muryarta komai ya kwance masa.
Shima dai a kasalance ya amsa mata sallamar,daga nata bangaren ma wani dafin ya kuma zuba mata,shiru ne ya ratsa tsakaninsu tana jiyo saukar numfashinsa,ya shiryawa sata tayi magana koda bata so,ya santa da qin yarda da gaskiya ta wannnan bangaren,saida yayi dariya ciki ciki sannan yace
''Allah sarki baby,kafin kice komai nasan kewata ke damunki kika kira kiji sweet voice nawa ko?''
gabanta ya dan fadi ta zaro ido kamar tana a gabansa ne,sai data cire wayar daga kunnenta ta sake dubawa shidin ta kira sanann ta maida kunnenta
''sai kace wata kai,niba wannan yasa na kira ba,dole ce ma ta sani kiranka''
murmushi ya saki mai sauti wanda ya kusa wucewa da imaninta
''attitude naki din nan yana burgeni,kina da jarumta da yawa,aiki ne ya cushe min shi ya hanani kiranki my suger''wani sanyi taji yana ratsata har sai data cure gu daya,rake idea din yadda zata bagarar da shi yazo mata
''hmmmm,gida nakeson naje naga mama''
shiru ya danyi kana ya sake sanyaya muryarsa
''nima zanso kije ki ganta din,amma sorry baby,gaskiyq ina kishinki da yawa,na tabbatar idan zaki din saidai driver ya kaiki fa,kinga kun kadaice daga ke sai shi cikin motar....har zuciyata ta fara zafi ma wallahi da tuna hakan da nayi''
ta hade rai don gaskiya tana matuqar son ganin maman
''amma fa ka sani yaushe rabona da mama,tun ranar da kasa aka fiddani a gidan''ta fada cikin shagwabar da batasan tayi ba ma,shikam tuni taso sauya masa lissafi don sai da yayi ajiyar numfashi kana yace
''shine kuma sai kin illatani da muryarki?''
''me kuma nayi?''
''kinfi kowa sani,gaskiya my kiyi haquri idan Allah ya dawo dani na miki alqawarin kaiki da kaina ki wuni har dare sai nazo na daukeki kinji?''
hawaye taji kawai na silmiyo mata,don haskiya ta qagu taga mamanta,tayi kewarta sosai,sai kuma yqce sai ya dawo sanann zata je,bayan shi kullum sai yaga tashi maman saidai idan baya gari,kasa magana tayi shima shiru yayi yana saurarenta,can qasa ya jiyo kamar sautin kuka,da hanzari ya miqe ya zquna yana fadin
''ya salam,maryam me yasa kika maida hawayenki masu araha irin haka?,daga cewa sai na dawo zaki je?''
''eh,ai baka kyauta ba,banson rashin adalci fa abdallah ka san halina sarai''cewar mami data amshi wayar bayan ta maidata handsfree,sam maryam bata san ma ta iso ba sai da ta qaraso gabanta
kanshi ya dafe
''shikenan mami nikam abdallah bawan Allah,naga ta kaina an hade min kai''
''har hanci da goshi ma zamu hade maka indai zaka dinga matsantawa irin haka''
''mami ina da kishi sosai kin sani,dole idan zata je mami driver ne fa zai kaita,mami banason wallahi yani ya kalleta''
''oh abdallah,halin naka dai yana nan,to zuwa kam sai tajeshi haka kawai,wake raba da da uwa,yaushe rabon da tq gansu,haba abdallah''
''shikenan mami na yarda mata taje,amma ba kwana ba,yauwa......baaba sule ne zai kaita,kuma don Allah ta saka hijabi don Allah''ya fada a sanyaye,wani mugun kishinta yake ji yana yi kamar yasan gyaran jiki ake mata dan ubansu
kama bakinta mamin itama tayi kana tace
''iyeee,sannu fa ubana''marairaicewa yayi
''mami pleaseeeeee.......''
''ya isa''tayi saurin tsaida shi
''taji zata saka,ince ko shikenan?''
''i love u my mommy''ya fada cikin murmushi
''me too my son''ta fada itama,tana shirin katse wayar yace
''yauwa mami.....i need your prayer mami zami fita aiki kan mutumin nan kimin addu'a mami kamar kika saba,i know ita ke kaini ga yin kowacce iriyar nasara''maryam dake gefe duk dai taji ba dadi wani kewa da karayar zuciya na son kamata
addu'a tayi masa sosai y
hannayensa a sama kamar suna tare ta gama suka shafa su duka,sai yaji wata nutsuwa da dukka qarfinsa sun dawo.
Miqawa maryam wayar tayi dom suyi sallama
''baby....ki kulamin da kaina''
''kanka kuma?''
''eh i mean you,nine ke kamar yadda kece ni,byee love u much more''ya fada ya katse wayar sai ya barta da waya a kunne,a sanyaye ta cire wayar bayan ta sauke ajiyar zuciya
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Cikin atamfa excellent ta shirya pure cotton,duk da mai qaramin kudi ce amma ta matuqar amsarta,kalar blue black dark blue and navy blue da sea green ce,sai ta samu kanta tana aiwatar da umarnknsa duk da ba'a tuna mata ba,hijabi ta sanya blur black wanda ya rufe ilahirin jikinta,mai hannu ne hakanan yayi matching sosai da atamfar ta,ita kanta data kalli madubi sai taga tayi masifar yin kyau,hakanan tana jinta compertable sabanin mayafi,duk da cewa dama ita gwanar hijabince musamman sanda tana gida
baaba sule dinne kuwa tana fitowa suka gaisa da kanshi ya bude mata motad duk da bata so kunya ce take rufeta,don aqalla ya kusa sa'an abbanta
Ta dinga kallon unguwar tasu,babu shakka gida akwai dadi,baka gane hakan sai randa aure ya daukeki daga cikinsa ya kaiki wani gu,komai rashin sukuni na gidanku randa ka barshi sai kaji kana kewa da begensa,ta samu gidan auren da ya ninka gidansu nesa ba kusa ba amma bata daina kewar gidansun ba,may b home is nothing but two arms holding you tight when you are at your worst
Cike da zumudi ta saka kai cikin gidan da saurinta saboda yadda jama'ar unguwa keta binta da kallo,suna ganin ta sake zama ta daban,wata ma yaranta ke kai mata gulmar maryam tazo sai a hau leqe saboda ta tsaya suna magana da baaba sule ashe mami ta cika boot da kaya bata sani ba sai yanzu yace ta turo yara su kwashe
Farinciki ya cika,zuciyarta ganin gidan qal a share sabanin da da iyakacin tsaftar qofar dakinsu ne zuwa,cikin dakin nasu,lubabatu ce kan tabarma zaune da qananun qannensu wadanda suke daki daya da da qatuwar farar takarda ta shimfideta kan tabarma ta zana alifun ba'un har zuwa ya'un manya manya da alamu tana koya musu ne shi yasa ko sallamarta basu ji ba,kafin ta sake maimaita sallamar ta hango isyaku ya fito daga dakin uwarsa kanshi tsaye yabi takan takardar ya take rubutun kana yayo hanyar waje,lubabatun ce ta yunquro da sauri ta cafko wuyanshi ta baya
''wannan iskancin naka isyaku ya isheni wallahi yau sai jikinka ya gaya maka''
Da sauri maryam ta qarasa don kada abun ya kwabe tana banbare hanunta daga wuyan isyaku wanda keta kici kicin qwace kansa cike da rashin kunya
''sakeshi lubabatu kinji sakeshi''sai a lokacin taga maryam din ba musu ta sakeshin ya kuwa fice abinsa da gudu,ta saki fuskarta daga daurewar da tayi tana fadin
''sannu da zuwa adda maryam''
''yauwa lubabatu,karatu ake yi ne?''ta dubi yaran kana tace
''eh,makarantar dare suke zuwa malaminsu yace su tabbata sun iya zuwa anjima zasu je kuma naga basu iya ba''farinciki ya kama maryam ganin an fara samun ci gaba a harkar karatun yaran
''da kyau kin kyauta kuwa lubabatu''
yaran suka zuba mata ido suna shakkad zuwa gurinta,ko dama can ita ba mafadaciya bace bata dai shiga shirginsu ne saboda gudun rashin kunya irin tasu,su kuma suna ganin a yanzu ta zama yar gayu kada ta makesu idan suka matso gurinta tunda haka jamila ke musu sanda tana aure gidan jabir
sai ta bude hannayenta tana fadin
''kamar baku ga yayarku bane,ku taso mu gaisa mana asiya''
ai kuwa har rige rigen zuwa suka dinga yi,sai taji farinciki ya rufeta,zaman lafiya babu abinda ua kasihi dadi haka dan uwa,baka da kamarshi cikin duniya,hamsin hamsin ta fidda ta raba musu su biyar tace su sayi alawa
Ganin har suka gama budurinsu,aka gama shigowa da kayan da mama ta hadota da su samfurin kayan masarufi babu wanda ya leqo daga matan gidan ya sanyata tambayar lubanatu wadda gaba daya maryam ta karanci nutsuwa sosai a tattare da ita
''ina wai matan gidan ne?''
''au...''ta fada tana murmushi tare da dafe bakinta
''na manta ban gaya miki ba,sun fara zuwa makarantar matan aure qarfe tara na safe zuwa daya na rana mamata da maman hindatu(maman maryam din)ke zuwa,ya hindatu ce ta sanyasu''
cike da nuna kara tace
''inna hadiza fa?''
sai da ta kalki qofar dakin nata kana ta tabe baki
''tana ciki tana bacci,tata makarantar kenan''ta fada tana bushewa da dariya,daquwa maryam ta mata
''mamarki ce itama''daki lubabatu ta shiga ta daukowa maryam maqullin dakin maman tace
''adda ga key din ko''ta karba kana ta budr dakin maman ta shiga
ta bi dakin da kallo ya sake kyau ya canza,cike yake da tsafta da qamshi,wani kewar dakin ta kamata,sai ta cilla mayafinta da jakarta saman kujera,kai tsaye ra shige dakin maman ta fada gadonta data yi kewarsa matuqa
Tana son gadon umman nata tana jin dadin kwanciya a kai,gadon da tasha dabdalar quruciyarta a kai har yanzu katifarshi ce a kai,duk da canza kayan daki da taga umman nata tayi amma bata canza abarta ba,ta sake juyawa tana tuna rayuwarta cikin gidan quruciyarta zaqi da madaci kala kala,a haka bacci yazo ya sureta.
Can cikin barcinta taji kamar ana kiran sunanta,a hankali ta dinga bude idonta har ta budesu tarwai kan fuskar mamanta,farinciki ya kamata,yaushe rabon data ganta,tana tsaye cikin unifaorm ash colour doguwar riga da hijabi,sun mata kyau kuwa unifaorm din sosai
''ki tashi kiyi sallah kina ta bacci har anyi azahar''sai ta miqe tana mutstsuka ido
''ashe har kun dawo mama''
''eh kina ta bacci har girki akayi aka gama baki sani ba,halan bacci kika koyo''murmushi tayi ta miqe zata fice a dakin tace
''sannunku da dawowa''
''yauwa''maman ta amsa tana rataye jakar makarantar ta data daukota daga falo gami da cire hijabinta ta linke ta saka a sif
Duk inda tayi maman kallonta take,godiya take wa Allah cikin zuciyarta,farinciki fal ranta,lallai addu'a bata faduwa qasa banza,duk wanda ya kalli maryam din koda makaho ya shafata yasan ba a wahala take ba,babu shakka Allah ya share mata hawayenta na shekara da shekaru wanda ya jima yana zuba,hirarsu suke gwanin sha'awa da maman bayan baaba huwaila ta aiko mata da abincin rana don girkinta ne,bata zauna ba sai data shiga dakin baba huwailan suka gaisa,kayan dakin mama datq cire ne jere a dakin nata,ba laifi sunyi kyau kam,cike da sanyin kiki da nadama ta dubi maryam
''na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun lokaci bai qure min ba ni da yarana,maryam na cutar da ke a baya na kuma so na sake cutar da ke amma da yake ALHERI ne cikin zuciyarki sai Allah ya kareki ya kuma sanya kika mana zarrah a rayuwa,maryam don girman Allah ki yafe min ni da yara na gaba daya''
sam magiyar da take mata bata yi matq dadi ba,ko da can baya ta sani cewa shedan ke rudarsu da duhun kai,bata taba riqar baaba huwailan ba
''baaba,tamkar mahaifiya kike a gurina,nikam dama ban riqe ki ba,na yafe miki Allah ya yafemu baki daya''
Data zo cin abinci duka qannenta ne kewaye da ita suna hirarsu abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da su ba tarihin rayuwarta,nan take jin duka baaban su ya maidasu makaranta,sosqi taji dadi don babu gatan da zaka yiwa yaro da ya wuce ka bashi ilimi(har kullum haka iyayenmu ke gaya mana,burinsu kenan (rabbirham huma kama rabbayani sagirah)
maryam ta dubi mama''ni ka ban ma ga baaban ba''
kubrah tayi caraf tace''baaba yana kasuwa,sai shida zai dawo''ta juya ta kalli mama
''kasuwa kuma mama''
''eh,kin manta da shagonsa da abdallah ya bude masa cikin kwari?''
''abdallah,a cikin kwari?,yaushe abdallahn yayi haka ba ta taba sani ba,koda mami bata taba mata magana makamanciyar wannan ba''cikin zuciyarta tayi maganar amma a fili sai tace
''au na manta fa''
''ai kullum malam sai ya yiwa yaron nan addu'a,yanzu kam qlhmdlh malam ya dauje duk wani,nauyi na gidansa da a da baya iya daukeshi,abdallah kam ba baya ba wajen alkhairi,abu daya zaki mana maryam ki wanke mu kiyi zaman aure mai cike da biyayyar miji,duk yadda kika zauna da mijinki kina nuna masa irin kalar tarbiyyar da kika samu kenan,kibi mijinki maryam ki riqe abdallah hannu biyu,bawai don arziqin da yake da shi ba,a'ah ko daya,kinfi kowa sanin cewa ba wannan ne gabanmu ba,nagartattun halayen abdallah kadai sun isa su sama masa kowacce kalar mace ta gari,ina fata kin fahimceni''kanta ta gyada
''na fahimta mama''
''Allah ya albarkaceku ke da shi baki daya''
''ameen ameen mama''ta fada cike dda jin dadin addu'o'inta
kafin ta rafi sai data tambayi yan qannenta me suke so ta saya musu kowa ya fadi abinda yakeso wanda bai wuce sabon unifoarm,jakar makaranta da lunch boxs,excercise book,lubabatu ce mai registration na placemen da sauran tarkacen kayan karatu,bata bar gidan ba sai data hadasu da lubabatun da kulu sukaje aka siyo,murna da tsalle kam sun sha shi,ko idon inna hadiza bata gani ba bare jamila ko binta,tana tsammanin ma basa gidan don idan banda isyaku data gani dazun da take shigowa gidan babu wanda ta gani cikinsu
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[8:18pm, 10/9/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣0⃣
*Daga abi musa al asha'ari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni''ya Abdullahi dan qais,shin bana nuna maka wata taska daga cikin taskokin aljanna ba?LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH''a ruwayar nisa'i ya qara da ''LA MALJA'A MINALLAHI ILLA ILAIHI''*
*Daga abu hurairah R.A yace: Manzan Allah S A W yace ''duk wanda ya fadi SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI sau dari za'a kankare masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi''*
_ruwayar bukhari da muslim_
Bata bar gidan ba har baaban ya dawo,a tsaitsaye suka gaisa saboda an soma kiran sallar magariba ya daura alwala ya fice yace yana dawowa,itama alwalar tayi ta shiga dakinsu tayi sallah,tana idarwa kiran hindatu ya shigo,a dokance take cewa
''Allah yasa adda baki tafi ba,gamu nan ni da jabir''
''da daddaren nan''
''wlh,daga asibiti muke kuma akace kina gida''
''ina nan ban tafi ba baaba nake jira,sai kun iso''ta fada sanan kowacce ta kashe wayarta
Tana dakin baaban ita da shi bayan baaba huwaila ta ajjiye masa kwanukan abinci ta fice,hira suke yi abinau gwanin dadi,abin ya faranta ranta sosai,ashe akwai lokackn da zata ga rana irin wannan?,lallai komai yayk farko zaiyi qarshe,basu damu da yadda inna hadiza keta kai kawo bakin qofar dakin ba,baaban ya dubeta bayan ya ajjiye carbin hannunshi
''maryam,ina fata zaki yafemin,na dade ina daukan haqqinki,na yi watsi da duk wani haqqi naki da Allah ya doramin,tun kina mitsitsiyarki na watsar da duk wani haqqi naki da Allah ya dora min,gashi daga qarshe ta inuwarki muke samun rufin asiri,ki yafemin maryamu,haqiqa na dau darasi a rayuwata,na qiku don kuna 'ya'ya mata,ina neman dq namimi,ido rufe,sai gashi yarin yana daf da lalacewa,Allah ya sa baiyi girma mai yawa ba,duk da haka har yau na kasa saitashi kan hanya madaidaiciya saboda na riga da na batashi na nuna masa gata,duk da haka na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun da wuri,a yanzu ne nake ganin budi cikin harkokina da nake yalwatawa iyalina nake daukan duk wani nauyinsu bakin gwagwado,kimin afuwa maryam''
Itakam bata jin dadin yadda mahaifinta wanda yayi sanadiyyar zuwanta duniya ke faman roqonta haka
''nikam baaba wallahi abunda kamin bazan taba iya biyanka ba,banga wani da zaka yimin ba na riqeka,komai qaddara ne kuma nasan haka lah ya qaddara dama zanyi rayuwata''
''duk da haka,na sani maryamu ki yafe min''
''na yafe maka baaba har abada duniya da lahira''
''na gide madyamu na gode,Allah ya albarkci rayuwarki,ki sake yimin godiya gurin yaron nan abdullahi,babu shakka babu abinda zamu iya cewa da shi,tsakaninmu da shi fatan alkahairi ne''
har yanzu mamamin abdallah bai saketa ba,yaushe ya shiga jikin yan gidansu ne wai haka?,yaushe suka saba soaai har yake musu alkhairai bai taba nuna mata ba ko sau daya
Suna cikin dakin suka jiyo shigowar hindatu,shigowarta ne ya tunowa da baba sabon babur da jabir din ya siya masa ya dinga zuwa kasuw ko wata guda ba'a rufa ba yace maryam din ta tayashi godiya
Nan cikin dakin itama ta ahigo bayan sun gama gaisawa da mama suka sha hirarsu da baban,har kusan qarfe tamwas da rabi suna tare,tuni ta kira baaba sule tace ba sai yazk daukarta ba don hindatu tace su zasu maidata
har soro suka rakosu baaba huwaila da yan qannesu,a tsakar gida sukayi sallama da baaba,suna kallo su jamila da binta na leqensu ta window
cikin mota suka tadda jabir din,hannunsa ya dunqule yana mata jinjina irin ta sarakai''Allah yaja da ran antinmu,Allah ya taimakeki uwar gidan abdallah mai nasara''dariya ya bata ba kadan ba
''haba jabir,ka mance cewa ka girmeni irin wanan gaisuwa haka?''
''ai yanzu kece babba,ko kin mance kin bani 'yar qanwa,gimbiya hindatu,wadda ba qaramin yabawa da zaben da nayi nake ba har yau''dariya ya bas gaba dayansu har suka fara taciya suna hira abinsu
sai da suka fara biyawa ya yiwa hindatu siyayya ya hada harda maryam din kana suka ajjiyeta a gida sannan suka nufi nasu gidan
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
kwana bakwai mami bata bari an dakayar da gyaran da ake mata ba,tamkar ana shirin canza mata fata,ita kanta mai gyara ta yaba yadda gyaran ya karbi jikin maruym di sosai da sosai,baaba uwani kuwa zama take kawai tana kallon maryam din
''gaskiya meramu anya ba canza miki fata hajiyar nan me gyaran jiki take ba?''duk sanda ta fadi hakan dariya take basu ita da mami
Kusan tun ranar da sukayi waya da abdalla kan zuwanta gida basu sake samun kiranshi ba,ana gobe kwanaki bakwai din da ya diba zasu cika mami ta nemeshi don taji goben zai dawo,saidai ta nemi layin nasa yafi sau goma bata sameshi ba,har cikin dare tana iransa bata sameshi
da safe ma hakan ce ta faru,damuwarta ta kasa boyuwa ta tadda maryam a kitchen tana goge freezer tare da sake jera kayan ciki don mamin ta hanata yin kowanne aiki
''ni kam maryam kina samun abdallah a waya kuwa''maryam din ta waiwayo ta dubi mamin sai ta rasa amsar da zata bata,don ita kanta tasha kasa kunne cikin dare lo da rana taga ko zata samu koda texs nasa,Allah ya taimaketa tin kafin tace wani abu mamin tace
''sam ba'a samun wayanshi,na kira na kira duka akashe''
jikinta taki yayo sanyi gaba daya,gabanta ya dan fara faduwa kada kadan ta juyo gaba daya ga mamin tace
''to mami ni cewa nayi ko chargy ne babu a wayoyin nashi?''
kai ta girgiza
''bana jin haka,saboda ba cikin wani qauye bane cikin tsakiyar abuja ne fa,kusa da villa,kinga ta yaya za'a rasa chargy a wayoyi?''
sbiru ya sake ratsa tsakani,bayyanar damuwa kan fuskar maryam wadda ita kanta batasan ta bayyana bayasa mami riqe hannunta
''kada ki damu in sha Allah he is safe''
kai ta gyada asanyaye,sai ta kasa qarasa ci gaba da aikin ta biyo bayan mami ta fita a kitchen din ta koma dakinta ta kwanta
Maganganunshi na qarshe ta dinga tunawa
_''Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo da ni,kimin addu'a don muhimmin aiki zan gabatar,wanda ko shine aiki na na qarshe da zan aiwatar in sha Allahu sai na gabatar da shi,ki sakani a addu'o'inki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam''_
Wani irin juyi tayi cikin matsananciyar faduwar gaba ta tashi ta zauna sosai kan katifarta,sai taji kanta ya sara ta dafe goshinta da sauri kana ta maida jikinta fuskar gadon ta jingina
kusan wuni tayi sukuku zuciyarta ba dadi,duk motsin da tayi maganansu ya qarzhe a airport ke mata amsa kuwwa a kunnenta,ko falon bata sake fitowa ba saboda rashin kuzari,mami keta leqota don kada ta takure ranta ta sa damuwa,ta karanci wani kalarson abdallan mai qarfi cikin zuciyar maryam din,da taga ta leqo ta sai ta qirqiri murmushin dole,gaba daya walwalarta ta ragu,ta dinga kiran layin abdallah a jejjere kamar wadda aka bata aikin yi amma ko da wasa bata shiga ba is switched off computer keta faman gaya mata,
Cikin kwana biyu duk yadda taso hana kanta damuwa zuciyarta tace batasan wannan ba,bata taba jin damuwa irin ta wannan lokacin ba,bata taba jin ta damu da wani abu a rayuwarta ba kamar wannan lokacin
cikin kwana na uku ta gaza daurewa
fitowarta a wanka kenan wanda tun safe ta kasa yinsa sai kusan daya na rana ta samu tayi,mai kawai ta shafa ta fesa turare ta zira doguwar riga ta nade kanta da mayafinta,takalmanta plate ta jawo ta saka kana ta fito,babu kowa bangaren don mami ta fita asibiti don haka ta fito waiting parlour ta zauna tana kallon shigewa da ake tayi da sabbin furniture bangaren nene a da,bata cikin nutsuwarta batasan wa zai zauna anan ba bata kuma damu data sani din ba,abinda ke cunkushe kadai a ranta ya isheta jarraba
number din hisham ta laluba ta kirashi,daga yanayin yadda taji sun gaisa har yana zolayarta ta tsinke da lamarin,sai kawai ta fasa tambayarsa ta kashe kiran,lambar abdallah ta sake trying wanda ta maida kiran tamkar ibada a gareta saidai amsar daya ce kamar kullum is switched off,ita kanta ta fuskanci yanayin damuwa kan fuskar mamin duk da bata kai tata ba,jin zuciyarta take kamar ana hura mata wuta
son abdallah
kewar abdallah
duk su suka mata rubdugu,kalamansa na qarshe a gareta ke sake sanya mata karaya,kawai sai ta zame a gun ta kwanta rub da ciki,batasan ya akayi ba ta tsinci kanta ne kawai tana kuka tuquru,bakinta na fadin
''kada ka yimin haka abdallah,kada ka guje ni,kada ka tafi ka barni''take furtawa a hankali cikin kuka,Allah ya taimaka mutanen dake aikin kafa kayan furniture din sun kammala sun fice
Kuka tayi mai yawan gaske har yasa idanunta suka kumbura baya ga zafu da radadin da suke mata amm hakan baisa ta haqura ba,sai da bacci ya lallabo ta taimaketa ya saceta,bacci ne mara dadi wanda tana yinshi tana sayke ajiyar zuciya ma kukan da ta yi
Hannu taji kan wuyanta a hankali ta soma bude kumburarrun idanunta wanda hasken daya cika falon yasa ta gaza budeshi gaba daya,mami ta gani tsaye a kanta tana fadin
''bacci kuma a waiting parlour maryamu?''ta tambayeta ba tare data lura da yadda idanunta suka sauya kala ba
''tashi ki koma daki idan baki gama ba kiyi a can amma nan ai yayi waje''
sosai tayi qoqarin tashi amma ta kasa,ga zaton mamin magagin bacci ne don haka ta kama hannunta don tayata tashin,zafin da taji da hucin zazzabi ya sata furta
''subhanallahi,maryam me ya sameki haka?''sai a lokacin ta lura da yadda idonta ya suntume fuskarta tayi jawur
''ya salamu ya Allah,maryam''mamin ta fada a rude,zare wayar hannun maryam din tayi don ta miqar da ita,number din abdallah ta gani kan scrren din wayar,sai ta dubi maryam din
''abdallah dai maryam?duka a kanshi kika yiwa idanunki haka?,sai kace an ce miki ya mutu ne''kalmar mutuwa data ambata wa abdallan sai ta sake karyar mata da zuciya,take taji ko,mutuwar ma yayi ne tunda gashi mami ta fada?,sabbin hawaye suka soma tsiyayowa,sai mamin ta dafe kanta don ta fuskanci abinda ya sakata kukan
''babu abinda ya samu abdallah maryam,tashi maza mu shiga ciki ki je ki watsa ruwa ki karbi magani,zafin zazzabin nan yayi yawa kada ya zama wani abun kuma daban''
mamin ce ta taimaka mata har ta shiga toilet kana ta fita ta bar mata dakin ta haye samanta don tayi wanka,itama ta hada mata magungunan da zata sha da zai saukar mata da zazzabin,zuciyarta fal da fafinciki jinjinawa da yaba tsaftatacciya kuma ingattaciyar qauna kuma mai qarfi da ya samu daga gun matarshi,wanda tayi imanin koda bafa duniya zai samu kyakkaywan kulawa a rayuwarshi
Ta kammala watsa ruwan ta canza kaya,da qyar ta iya bada sallar azahar da la'asar da suka shigeta ta dawo ta nade a gado,har yanzu zazzabin tana jinsa cikin qashinta,a haka mami ta taras da ita
Sai data tilastata taci abincin da ta shigo da shi sannan ta bata maganin ta sha,tana nan a gurinta har bacci ya sake daukarta sanann ta fita dakin
Bata farka ba sai da wani amai mai zafi ya farkar da ita,da gudu ta miqe kanta na sarawa ta shiga bandakin ta dinga kwarashi,mami wadda ta idar da sallar magariba tana jiran isha ta dawo falin qasa ta zauna saboda maryam din ta fara jiyo kakarin amai,da hanzarinta ta shiga dakin,ita ta wanke gun data bata din ta maidata gado ta kwantar tana mata sannu,ta taba jikinta kana cikin damuwa tace
''maryam anya ba ciki gareki ba kuwa?''
duk da tana cikin ciwo sai da tambayar tq bata kunya,tayi qasa da idonta tana girgixa kai,sake matsowa mamin tayi tana lallabarta
''kada kiji kunyata idan shine ki gayan kada na yita baki magunguna muyi asararsa don Allah''
nan ma kai kadai ta iya girgiza mata ta kasa hada ido da ita
''to shikenan,allura dama zan miki naji zazzabin yaqi sauka''
sam bata qaunar allura,da kayi mata allura gwara ka zabga mata mari,ita ta sani ciwonta ba na magani ko allura bane,da sauri cikin murya ta marasa lafiya tace
''don Allah mami ba yanzu ba,a barshi sai anjima zai iya sauka''ta fahimci allurar ce bata so don haka ta qyaleta ta sake bata wasu magungunan
Ranar kam har kusan biyu na dare ana fama,qarshe dai allurar da bataso mamin ta mata,bayan tasha fama da ita kafin ta tsaya din,sai kusan uku saura na dare ta samu bacci ita kuma mamin ta koma dakinta
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
A daddafe ta tashi tayi sallar asuba sakamakon baccin daya cika mata ido,duk da zazzabin ya sauka baki daya sai ciwon kai dake son matsanta mata kuma,da qyar ta gama sallar ta kwanta saman daddumar zuciyarta babu dadi,duk wani minti idan ya wuce sai taji kamar yana sake nesantata da abdallah ne
A hankali taji an turo qofar dakin,ta daga kai tana amsa sallamar da akeyi,mami ce cikin hijabinta da carbi a hannunta da alama idar da sallarta kenan itama,tayi qoqarin tashi zaune don gaisheta mamin tace a'ah yi kwanciyarki,a haka suka gaisa ta duba jikin taji babu zazzabin,shuru tayi bata ce mata kan nata na ciwo ba din kada ta daga mata hankali
''yanzu maryamu jinkirin dawowar abdallah yasa kika matsantawa kanki da damuwa haka har da ciwo?,lallai ba shakka gaba guduwa zaki dinga yi kibi mijinki kuna barina kenan?''ta fada cikin tsokana da zolaya,kunya ta kama maryam sosai,ita kanta batasan tana misbehaving har haka ba,batasan ya akayi abun ya hudata haka ba har yake bayyana kanshi da kanshi ba tare da ta sani ba.
''a'ah daina jin kunyata,ni hakan dadi ya yimin sosai,Allah ya qara hada kanku,aikin da yayi ne ya tsaudashi jiya kafin na kwanta saiga kiranshi,amma alhamdulillahi an samu nasara ya kama dukkan jama'ar daya shirya kamawar sai mu yiwa Allah godiya''
hakanan taji wani sanyi na sauka tun daga kanta har tafin qafarta,a gida ko a waje abdallah jarumi ne tabbas babu kokwanto,a hanakali cikin zuciyarta ta dinga fadin alhamdulillah
''sai ki kwanta kiyi naccinki sosai,kiyi bacci harda minshari ko''ta sake fada cikin zolaya,murmushi tayi tana sake sunkuyar da kanta mamin ra mata sallama ta fice
Ta lumshe idonta tana jin wani shauqi na kamata,duk da ciwon da kanta yake murmushi sai daya subuce mata,ta dan dafe kanta idanu a lumshe,a hankali bacci mai dadi ya sureta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Sannu a hankali taji yanayin baccin nata na sauyawa,ta dinga bude idanunta a hankali har ta kammala budesu tas,yana zaune gefan gadon nata sanye da baqar jallabiya mai hula irin ta maza ya zuba mata idanu kamar wanda aka bashi aikin zana fuskarta,wani abu mai kama da farinciki taji ya ratsata
''welcome dear''ya fada a nutse
''an tashi lpy gimbiya?''ya tambayeta idanunsa har yanzu na kanta,kasa amsawa tayi sai cusa kanta da tayi cikin hijabinta,yayi maganar amma taqi dagiwa sabida haka ya tashi tsam ya koma gabanta yana qoqarkn dago fuskarta amma ta qiya,shima bai sakar mata qarfi ba ya qyaleta yana fadin
''kin daga min hankali da yawa baby,tun asuba na baro abuja duk sabida nazo na ganki amma kin min rowar fuskarki,shikenan na gode''ya fada yana miqewa zai fice a dakin,sai ta bude ido daya taba satar kallonshi tamkar ta tsaidashi tana kallo ya fice a dakin a hankali kamar wanda aka qididdigewa iya takun da zaiyi
Kunya da tsoro ranar suka hanata sakewa ko fitowa,sai taci gqba da kwanciyarta kan gado abinta mami na kulawa da ita a tsammaninta jikin da saura,tana son ta fito ko zata sake ganin fuskarshi amma kunya ta hanata,tana jiyo muryarshi a falo lokaci lokaci shida mami suna maganar bangaren nene da ta ga ana sawa sababbin furniture
_WASHEGARI_
Tas ta jita ta warke sosai,ko guntun ciwon kan ma babu shi,qarfe tara ta hada ruwa mai zafi tayi wanka,muradin ganin abdallah take,shi kuma kamar ya sani tun jiyan bai sake leqota ba duk da ya turo mata guntun sms
_sorry dear na zama busy kan wani abu,see u later_,iya abinda ya turo kenan
Ta shirya cikin atamfa riga normal da zani rafa,tayi lite make up kana ta feshe jikinta da turaruka masu dadi,ta daura dankwalinta bayab ta gyara gashinta kai azabar santsi ta hadeshi da ribbom madaidaici,haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar,ba qarya ta mata kyau matuqa,muryarshi da jiyo a parlour ta haifar mata da fargaba,sai ta koma bakin gado ta zauna ta fasa yunqurin fitar da takeyi,ta dauki wayarta ta fara danne danne kanta a qasa
Raliya take turawa tex don taga missed call dinta na kiran data mata tana bacci
A hankali taji ana taba qofar kana aka turota,cikin qananun sakanni tattausan qamshi ya buwayi hancinta,qamshi ne mai kwantar da rai tamkad zai saka bacci a nata bangaren wani shauqi ya qara mata,kallo daya ta masa ta sauke idanunta qasa,kunya take ji sosai,ga wani maganadisu dake fisgarta cikin idanunshi,wani kyau na musamman taga an qara masa,gani take kamar mami ta gaya masa sirrinta,nauyin hada ido take da shi,yayi kyai sosai cikin light blue din shadda,babbar riga da yar ciki da wando,fadan irin kyawun da shaddar ta masa ma bata baki ne,shadda ce yar ubansu sai maiqo take tasha bugu,a hannunshi riqe da hularse,a gogone baqi a hannunshi na fata na kamfanin armani sai takalminsa half cover irin na maza,sai ya tashi sak dan kano don ba baya bane su wajen iya wankan shadda suna sahun gaba,ba qaramin amsarsa shigar tayi ba,do da wuya ya sanya kaya komai rashin kyawunsu suqi amsarsa ,fuskarsa cike da murmushi mai bayyana sirrin kyawunshi
''amincin Allah ya tabbata a gare ki baby,ina fata kin wayi gari cikin qoshin lafiya,af kice ma anko mukayi''ya fada cikin zolaya,sai a sannann ta dubi kalar atamfar da ta saka blue ce da baqi,duk da blue din ya dan dara nashi turuwa da kadan
qarasowa yayi bakin gadon ya tsugunna kana ya dafa cinyoyinta,abinda taji a jikinta shima shi yaji,sai tayi saurin zame hannun nasa,dauke hannun yayi yayi murmushi yana yiwa hular hannunshi kari ba tare da ya dubeta ba
''am too busy jiya naso inzo in sake tozali dake,ina daya bangaren can ana jeran amaryata''
sai tayi dumm ta rasa yadda zara fassara maganarshi
Ya miqe ya isa gaban madubinta ya daidaita hular bisa kanshi kana ya sake dawowa inda take
''wanne saqo kike da shi gun imna wuro,qauyen ni'ima zamu je,yau idan Allah ya nufa zan zama angon mero''
batasan lokacin da ta daga kanta ba,ta yi masa wani birkitaccen kallo ido cikin ido,wani irin zazzafan kishi baqinciki da takaici ya lullubeta
''naga kina duba na maryam idan da magana kiyi''ya fada yana sake matsowa kusa da ita tare da riqo hannayenta ya sanyasu tsakiyar tattausan tafin hannunsa,a zafafe ta fusge hannun nata kana cikin tsananin fushi da bacin rai da kuma masifa tace...........
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[4:28pm, 10/10/2017] Huguma👑: [3:31pm, 10/10/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣1⃣
*An karbo daga Anas dan maalik R A yace: Manzan Allah S A W yace''dukkan dan adam mai kuskure ne,mafi alkhairin masu kuskure sune wadanda suke tuba(idan sun aikata kuskuren kuma bazasu sake komawa ba)''*
Tace cikin wata iriyar murya mai dauke da tashin hankali
''jeka.....jeka nace,kaje tunda ka fadi abinda kake son gaya min lallai saqonka ya isa''tayi maganar cikin zafi da juyewar kalar qwayoyin idanunta
ya sake matsota yana fadin
''to kima me nayi don Allah maryam,ina cewa ke kika bada damarcda,zan qaro auren ko?,tunda na baki dama na ganin canji kafin dawowata saidai har naje na dawo din banga wani canki ba,it means abdallah jeka auri ero ko?''
Idanunta cikin nashi tana dubanshi kuka takeson tayi saidai ta kasa
''dama kana sonta din abdallah na dade da sanin hakan,toma meye donta ka aureta,hakan na nufin yankewar numfashin maryam da qarewar rayuwarta aduniya?''ya fuskanci ta fara ficewa daga saitinta,don haka sai ya miqe yana sake saba babbar rigarsa yana shirin ficewa tare da cewa ''Allah ya kyautq,Allah ya baki haquri,sai mun dawo''
tsintarta kawai yaui a gabansa tana tura qofar hadi da jingina jikinta da qofar,hawayen da bataso su fita su suka soma turereniya kan kuncinta.
Ta jingina kanta da bango kana ta saki kuka,muryarta a shaqe cikin raahin sanin me yake fitowa daga bakinta tace
''idan kana so ka tafi kaje,amma banu inda zaka fita abdallah sai ka tsaga qirjina ka cire zuciyata ka tafi da ita,wananna wanne irin so ne?,wanne irin horo ne wanan?,na gaji.....na gaji abdallah da irin wanann horon,me yasa kake ma zuciuata irin wanann hukuncin?,me yasa ka kasa gane qirjin maryam cike yake da so da kuma qaunarka?,kasan matsayinka a cikinta kuwa?''
Kasa tsayuwa yayi har sai da ya qarasa inda take tsayen yasa hannayenahi duka biuun ya dafe shima qofar ya yiwa maryam din rumfa,numfashinsa na fita da sauri,wani irin nau'in farinciki da baiyi tsammanin akwai irinsa cikin duniya ba ya mamaye ilahirin jiki jini tsoka da zuciyarsa yace
''abdallah ya dade da sanin ya dasa qauna cikin zuciyar maryamunshi,irin qaunar da ko mutuwa kayi bata barin zuciya ta huta,abu daya abdallah yake da muradon ji daga bakin mace qwaya daya tal aduniya shine *NIMA INA SONKA ABDALLAH KWATANKWACIN YADDA KAKE SONA K......*
*NIMA INA SONKA ABDALLAH FIYE DA YADDA KAKE SONA,FIYE DA YADDA KAKE TSAMMANI KO HASAAHE CIKIN ZUCIYARKA*,ta fada cikin tare numfashinsa ba tare da ta barshi ua kammala fadar abinda zaima fada din ba,kasa daurewa yayi sai da ya ji duminta ajikinsa,sai da yaji hucin numfashinsu na gauraya guri guda,gaba daya ta narke a qirjin nasa tana sake cusa kanta cikin qirjin nasa,tsaiwa ce ta gagaresu ya jata gefan gadon suka zauna,bai janata kuka na don shi kansa badon kada ya nada yammazqn ba dira kanshi zaiyi a kafadarya ya sha kukanshi saboda tsabar farin cikin da yaji yana kewaye duniyar subhana da shi
A hankali kukan ya soma jan baya sai ta janye jikinta ta dubeshi da brown oily eyes dinta da a yau suka sauya kama
''abdallah......mero fa?''ta tambayeshi tana jan majina,dariya taso qwace masa dik da haka sai da murmushi ya wadaci fuskarsa,ta tsareshi da ido sosai da alama kishi ne ya bude fagenshi cikin zuciyarta,sai da ya lakuce mata hanci kana yace
''gaki nan,ai kece *MERO NA*kuma kece *MAIRAMU* hakanan kece *DIYANA* duka''
kunya ta kamata,wai haka abdallah ya qware wajen buga game ne?,bata tsammaci a fili tayi maganar na sai da taji yace
''yes abdallah good player ne,sanna kuma winner ne,yau nayi winning,the game is OVER today''shigewa jikinsa tayi yama boye kanta aqirjonsa murmushi kwance kan fuskarta,hannunahi duka ya sanya ya marabceta zuwa jikinsa yana fadi cikin dariya dariya
''ashe haka kike da kishi maryam?,amma fa kin danji kunya kadan,kishi da 'yar qauye?,ya akahi kika aminta abdallah zai iya duban wata mace dina ma burgewa ma balle a kai ga batun so,macen ma irin mero,kin manta da su abida salma saddiqa zubaida da sauransu,basu isheni kallo ba sai mero?''
Kuma fa haka me,but ya akayi ta kasa tunanin hakan kishi duk yabi ya rufe mata ido ,ba shakka taji kunya,sake duqunqunewa tayi a jikinsa
''amma fa ta bangare guda kin burgeni haka nan kin gama biyana''ya fada yana lalubar kunnenta son so yake maganar ta koma ta sirri tsakaninsu
''yadda kika nuna kishi na na tabbatar cewa ni din ba qaramin dan gata bane''
Tayi har da ido duk da bai ganinta,can qasa muryarta tace
''amma daurin auren wa zaku a ni'ima,kuma waye zai zauna a bangaren nene na da''
''daurin auren mero,amma fa meron qauye,kuma a ni'ima din sannan bangaren nene na da anan zata zauna nata ne''
sai ta miqe daga jikinsa,hawayen ta na som dawowa
''abdallah ya zaka yimin haka,dai da zuciyata ta gama kamuwa da qaunarka zaka qara aure,bazan iya ba....bazan iya sharing wata da kai ba Allah,ina kishinka fiye da yadda kake zato''ta fada tana girgiza kanta tare da yunqurin sauka daga gadon,wayyo farinciki ya kamashi kamar yayi adungure,tuni ya riqota yana girgiza kai shima ya birkitota ta fada jikinsa ya rungumeta tsam
''Allah na gode maka da ka bani mai kishi na,nasan ba komai ya jawo hakan ba face tsatsar qauna,calm down madam,maro zata auri labaran ne nata nacan qauye na daukota ta zauna nan ne tare da mami ta dinga tayata da aikace aikace da kula da gida,tunda mamin tace tana sonmu tana son zama da mu amma ta rantse gidan mu zamu tafi,ba zata zauna tare da mu ba gudun shiga haqqinmu,labaran kuma na bashi aiki cikin kamfanoni na na nan kano,kuma banyi qarya ba *YAU ANGON MERO NAKE AMMA MERO DIYA NA* don na tabbatar yau ba zaki tsallake tarkona ba saikin fallasa min da bakinki qaunar da kike son binneta cikin ranki bayan akwai mamallakinta,shi yasa nayi miki adon angwayen don nima ango ne,haka daga yau ba zaki sake kwana gidan mami ba sai cikin gidanmu,gidan da na fara ginashi tun daga sanda na fara tizali dake a rayuwata,don ke dama na ginashi na dana jeshi dalili kenan da yasa a china na muku shigar sauri na zabi *gadon amarcinmu* don ni kadai nasan wanda zaifi dacewa da gidan,a lokacin mami na ganin na miki shishshigi batasan tanadi na yiwa kaina ba''
''wato abdallah mugun dan duniya ne?,ya iya buga qwallo son ranshi cikin hikima kuma ya saka ta cikin raga ba tare da golan ya sani ba''maryam ke gulmarsa cikin ranta bayan tayi luf a qirjinsa,tashi yayi ua fidda babbar rigar jikinsa ya dorata saman madubi bayan ya je ya sakawa dakin key,ya cire yar cikin ma daga shi saura farar vest dinshi qal da dogon wandon shaddar,gadon ya dawo ya haye yana fadin
''yau kam nima zan more soyayya mai 'yanci''sai ya kuma bata kunya ta cusa kanta tsakani cinyoyinta,sam ta kasa hada udo da shi,kowanne sakon kunya yake sata turata ciki,anan ya lalace yana gaya mata yadda take da tasiri cikin zuciyarsairin girman matsayinta,da irin yadda yake ji game da ita,yadda sonta ya dade da illata zuciyarsa,duk inda ta duqa sai ya hanata,yace ta barshi yau ya bararraje ya fidda duk wani feelings da yake ji game da ita,daga qarshe tallafe kumatunta tayi tana kallonshi,tayi imanin ya zauce cikin so kamar yadda ita ta zauce,saidai tsakanin shi da ita batasan wanda yafi wani ba,sau biyar hisham yana kiransa yana katsewa,qarshe ma ya daga yana fadin
''kaga malam idan zaka kama hanyarka ka wakilceni shikenan,nikam a inda nake yanzu ko mami,nasan zata min uziri''da yaga yaqi daina kiran nasa sai ya kashe wayar baki daya ya jawo bedside ya wullasu ciki yana jan tsaki ya sake dawowa sukayi zaman dirshan saman gadon suna kallon junansu cike da shauqim bege da qauna
Itama mamin ba ta nemi ko daya daga cikinsu ba kamar tasan tsiyar da abdallah ya qulla,cikin dakin sukayi sallar azahar har ma da la'asar,babu wanda yayi tunanin wani abu waishi abinci a cikinsu,wani irin shauqi ke dawainiya da su wanda gaba dayansu basu taba zaton akwai irinshi ba,a haka ma maryam na doddojewa saboda tsoro da gudun kada a tafka abun kunya cikin gidan suruka,ya qaraci fitinarsa sau biyu yana wanka tana kallonsa,
Sai da suka idar da la'asar maryam tace
''ya kamata ka tafi haka,kaga kada mami taga rashin,hankalinmu''kamar ma ba da shi take ba sai ua dira kansa saman cinyarta yayi kwamciyarsa yana fadin
''babu rashin hankali,tsakanin miji da mata sai Allah ita kanta mamin ya sani,nasam ta mana uziri,uziri kam dole ne ayi mana musamman ni Allah sarki da na jima ina faman rainon soyayyarki tun kima qwaila''ya qarshe maganar cikin salon zolaya
ta fara tura bakinta tana qoqarin tureshi
''ni daga ni,nikam ba qwaila bace ko a da dinma''yadda ta turo bakin ba qaramin sha'awa ya bashi ba,bai iya haqura ba sai da tsotseshi tas,abdallah na haukata ta iya yau da salon soyayyarshi tana zaton na gaba sawa zaiyi ta manta kowa da komai
cikin haka sukaji ana knocking,aka rasa mai magana tsakaninsu,murya qasa qasa tana zare ido tace
''mami ce fa''
kafada ya daga ya ware hannunshi kana ya miqe ya nufi qofar,ido ta sake zarowa ta biyoshi da sauri tana roqonsa qasa qasa saitin kunnanshi kada ya bude sai yasa rigarsa
''sai na cire wanann ma na zauna da boxer ki da kanta ma idan mami ce anjima zata kaimu gidanmu''kunu tasha tana miqo masa rigarsa kana ta fece bandaki ta saka maqulli ta buya,bai kuwa saka rigar ba ya budewa mamin,ita kanta sai da taji kunya ta kamata,ta kautar da kanta sanan tace
''ba kai nake nema ba diyata nake nema,kasan bata gama warkewa ba akwai sauran magungunanta da zata sh''
shima sai ya hau sosa kai don ya gama fuskantar inda mamin ta dosa
''mami ki kawo sai na bata''
hararasa tayi gafara min ni na wuce,haka zaka dirka mata maganin bata ci komai ba tun safe?,baka iya kula da mutum ba sai sakarci ka iya''ba shiri ya matsa ma ta shigo,ta kalli gadon da suka yamutsashi don akai suka yini salla ke sauko da su ta dauke kanta tana kiran sunan maryam din,gyaran murya ta yiwa mamin kamar maiyin wani abu a bandakin
sai ta samu gefan kujera ta zuan bayan ta ajjiye maganin kan madubi,shima gefan madubin ya jingina yana fadin
''kinsan kuwa mami cikin wadanda na kama tare da alhj hamza da yaranshi harda adnan?,mami ashe yana daga cikin manyan yaranshi,duka poising da naci sau biyu har da hadin gwiwar alhj hamza din''salati mamin ta saka tana tafa hannayenta
''kai Allah ka tsare mana imaninmu ya Allah,wadan nan mutane wadan nan mutane sun cika butulu,amma dama hausawa sunce idan zaka gina rakin mugunta ka ginasho gajere wataqila kai zaka fada,yanzu gashi su suka fada din,nene kam ba ita ba labarinta har yau ita da zubaida,yanzu don Allah meye ranar wanann?''
kanshi a duqe yake jijjiga kai,har yau yana jin takaicin yadda mutanen suka ci amanar mahaifinaa da mahaifiyarsa,har yau yana tuna yadda babanshi da mamanshi suka hada gwiwa aka auro nene gidan cikin halin qunci da wahala ita da yayanta amma yau da ita akayi yunqurin rusa su badon Allah baya bacci ba ya basu kariya da kariyarsa,kasa cewa komai yayi don idan ya tuna su bacin ransa ne ke tashi qwarai da gaske,badon mami tace ya qyalesu ba dukkanau sai ya nemo su yayi shari'a da su har igiya tayi saura,amma gashi a yau ya samu adnan wanda ko tantama baya yi hukuncin kisa ne zai rataya awuyansa sabida irin barna da kisa da suka dinga yi
shuru shiru maryam bata sake motsawa ba,babu yadda mami batayi ta fito ba amma ta kasa,shi kuwa abdallah na gefe yana musu dariya,da mamin ta gaji tilas tace
''aishikenan gasu nan idan kin fito din kyasha,ki tabbatar da kinsha kuma sabidayau hajiya lailan tace kisha shi''ta juya ga abdallah dake masu dariya
''ka shiga tsakaninmu ko,zaka dara da kyau musamman idan na saka ranar tarewarku nan da watanni goma''
''lokacin ta haihu kenan ta gama wankan jego'' 🙄,ya fada qasa qasa yana duban sama
''me kace?''mamin ta tambaya,da sauri yana dariya yace
''babu komai mami,Allah bani na shiga tsakaninku ba,kunyarki dai kawai take ji''
''gafara min,ka maidani wata kakarka ko,tamu ce ni da kai''ta fadactana rabeshi ta fice qasan zuciyarta cike da farinciki,ta tabbatar cewa irin qaunar da take sha'awa danta ya samu ga matarsa ya gama samunta sai godiya ga Allah,abdallah kam ta sani bamai wasa bane gun kula da nunawa iyali soyayya tuntuni ta sani halinshi ne a qidarsa ce
Wanka kawai ta zarce da yi bayan ta ji fitar mamin,kayan jikinta ta maida don ta tabbatar abdalla yana dakin,towel ta rufawa kanta sabida jikqewa da sumar tata tayi,yana tsaye bakin madubin hannunshi daya ya dafe amdubin da shi dayan kuma yana ruqe da yar kwalabar maganin yana karanta rubutun lrabcin dake jiki,ta qarasa gaban madubin da sauri da niyyar tattare magungunan don batason ya gane na meye,ajjiye kwalbar yayi ya zare towel dake kanta yaci gaba da goge mata ruwan gashin nata na burgeshi tare da bata sha'awa
''baby kici abinci gaskiya kisha maganin nan''
''na ciwon kaine kuma ya riga da ya sauka''ta fada akunyace
dariya ya saka kana yace
''eh kam gaskiya ne,na gani ai''
ta tsargu don haka tace
''qarya nayi kenan?''ta fad tana hade rai din kada ya bullo da wani abun,ai kam bai fasa ba sai da ya ja habarta yana dariya yace
''gaskiya na sake tabbatar da irin son da mami na kemin,ya Alah ka sake jamin da ranta ka qara mata lafiya da tsawon rai mai amfani,kice gyarani kawai take yi ni ban ma sani ba,i luv my momma''sai kuma tayi shiru bata data cewa don ta tabbatar ya gani
sai ya leqa fuskarta bayan ya jawota ua rungumeta ta baya kana ya dora habarsa kan kafadarta yana cewa
''kina zaton Abdallah bai iya larabci ba ko yammata,zan baki mamaki kamar yadda na saba,kwanan nan zan daina magana dake da hausa''
dariya ta subuce mata
''ni din ma akace ban iya bane?''
''i know baby na,ke din gwanace ta kowanne bangarr tunda kika iya sace zuciyar abdallah tun ruwanki bai isa alwala ba shi kuma da ya tashi ramawa sai ya haukataki baki daya ko?''diddira qafarta ta shiga yi cike da shagwaba taba kukan qarya,anan ya lalace yana ta faman kallonta,don ba qaramin kyau tayi masa ba ji yaje kamar ya hadiyeta ya huta
Bai fita adakin ba kuwa sai da aka kira sallar magriba,yana fita ta rufe da key don tasan idan batayi da gaske ba ma yana iya cewa adakin zai kwana mata tundavyaga mami mai dauke kai ce wunin sur ta fita a harkarsu tana cikin mutanen dake ta aikin bangaren mero
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun kafin ta tashi abacci yake ta faman doko mata kira tazo yana son ganinta,har qaryar bashi da lpy ya mata,tana jin kiran nasa ta shareshi don haka jiya ya dinga buga mata qofa har ya bata kunya don baaba uwani ta jisu tana ji tana gaya masa qila tayi bacci ne
Takanas ya tashi ya taho dakin nata ya soma buga mata,cusa kanta tayi qarqashin fillow tana kuma qudunduna cikin bargon,qasa qasa yake kiran sunata
''wayyo abdallah wallahi kunya kawai kake bani,tun jiya kasa na kasa hada ido da mami na''haka ta dinga fada cikin zuciyarta,likimo taci gaba da yi har ta daina jin bugun nasa
Qarfe tara da rabi ta fito a wanka taba gaban madubi daure da zani ta lulluba towel a kanta ta ji ana knocking,sai da ta tambaya taji baaba uwani ce don haka kai tsaye ta bude mata ta juya tana fadin
''shigo baaba yanzu nake shirin zuwa kitchen din nasan kina can kina aiki ke daya,yau bacci ne ya danneni wlh''
''wani baccin zaki sake kuwa yanzu yanzun nan''taji muryar abdallah,kafin ta waiwayo tuni ya rungumeta ta baya hannu daya yasa ya sakawa qofar muqulli,ya sake matseta gam ajikinsa yana lalubarta
duk inda ta ruqe hannunshi sai ua zame har sai da yayi iya yinsa kana ya saketa,zatq gudu toilet yace
''wallahi kika gudu ina da spare key idan na bude ki zaki dandana aguna''tilas ta tsaya yana dubansa ya birkice gaba daya,sai ya koma gefan gadon ua zauna,ya dauki kusan minti ashirin kafin ya daidaita,ya sake kallonta tana zaune kan dressing chair ta juya masa baya
''kinsan jiya da qyar na iya bacci kuwa baby,kuma kika hanani ko duminki naji ma''
A shagwabe tace ''kayi haquri,mami sai taha rashin kunyarmu yayi yawa a matsayinmu na hausa fulani,kuma kunya kaga wani yanki ne daga cikin imani''
kai ya gyada
''alright,naga kamar tsoro na kike baby tun yanzun,idan shine ma pls ki cire shi a ranki,don ni mitum ne da keson maida matarsa ta zamar masa tamkar qawarshi,jeki saka kayankin kizo mu gaisa''ba musu ta bude kayan sawarta ta ciro atamfa,a hankali ya tashi ya isa gareta ya ruqe hannun ya maida atamfar yana fadin
''atamfa atamfa dai baby,yau kam ba atamfa nakeso ki saka min ba''yayi maganar idonshi akan kayan nata yana lalubawa,wani material ya ciro mata dinkin fitted gown,orange ne da adon baqi,ta dubeshi bayan ta marairaice
''yayi tsiraici da yawa wannan,kuma kasan bamu kadai bane cikin gidan''ya tubure mata shi au yakeso ta saka masa,da qyar ta lallabashi ya haqura ya sauya mata wani lace riga da skert tare davalqawarin koda anjima ne zata sa masa wannan din
Toilet tayi nufin shiga ta saka kayan yace sam bai yarda ba shikam,sai baya ya juya mata ta sanya underwears,bata kai ga fara sanya kayan ba ma ya juyo shi tana ji tana gani ya shiryata cikin lace din,ba qaramin kayu kuwa tayi ba,zagayata yq dingayi yana qare mata kallo kafin daga bisani ya jata cikin jikinsa yana shaqar qamshinta,sun jima a haka ba tare da ta hanashi ba kafin daga bisani ya fidda mata mayafi yace ta saka
Da qyar ta iya zuwa gun mamin ta gaidata ta kasa hada ido sam da ita,ita kuwa murmushin take,dadi take ji cikin ranta da Allah ya bata suruka mai kunya ba irin surukan zamqni ba da idanunsu ke tsakar ka,suna ganin ai an dade tare da suruka an zama daya idanunsu ya soye don haka babu wata kunya tsakaninsu,qarshe zamewa tayi kitchen gurin baaba uwani
Suna kitchen suna aikin girkin rana ita da baaba uwani,duk da yadda abdallah yaso hanata taqi,sabida ta sani sarai idan ta biye masa kadan daga aikinsa suyi wunin daki bai ko jin kunyar idin mami,ga gidan yau ba laifi akwai mutane,murya ta jiyo cikin falo tamkar ta inna wuro,da azama ta fito falon nan sukayi kacibus,ita dince kuwa,farinciki ya kama maryam din don ma kunyar mami ta hanata sakewa,ita inna wuron ta yo gaba ne sabida anjima kadan za'a taho da mero amarya,hidima sosai mami ta dinga yi da inna wuron,ina kasa ina ka ajjiye ta,jinta take kamar babbar yayarta,mutanen nada wata irin qima da matsayi mai yawa a idanunta,ba zata taba mancewa da su ba,alkhairinsu mai tarin yawa ne a gareta ita da iyalinta,daki guda aka bude nata daya daga cikin dakuna hudun dake corridor din dakinsu maryam
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[4:09pm, 10/11/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣2⃣
*Daga abdullahi dan mas'ud R.A yace:Manzan Allah S A W yace''idan kuka kasance ku uku,kada mutum biyu(su kebe)su gana (su ware cikon dayan da suke tare),har sai sun cakudu da wasu mutanen(sun fi uku kenan),saboda dalilin haka(kebewar tasu su biyu su barshi shi kadai)zai iya bata masa rai/baqinciki''*
_ruwayar bukhari da muslim_
_MASOYANA NAGA SAQONNINKU,SAIDAI,BAN KAI GA DUBAWA BA WAYAR TAYI RESTORE DI SAQONNIN,SABODA HAKA AYIMIN AFUWA NA RASHIN GANIN REPLY,INA GODIYA YABAWA TARE DA JINJINAWA QAUNAR DA KUKE GWADAMUN TA BAN MAMAKI,ALLAH YA SO KU KAMAR YADDA KUKA SONI_😍
Abdallah ya kasa ya tsare,shikam yace an takura shi saboda baqin da auka dinga yi cikin gidan sun hanashi ganin maryamansa wadda tana cikinsu ana hidima da ita,duk da mami ma ta hanata yin wani abin saboda gyaran jikinta
Gab da magariba aka iso da mero gidan,a qalla mutum ashirin 'yan rakiyarta,kai tsaye suka fara da kawota gurin mami,maryam ce ta kamata ta mata iso saman mamin
''masha Allahu,Allah ya sanya albarka,ku kaita gidanta ta hita tunda dai mina tare ai babu damuwa''cewar mamin din haka ta sauko da ita suka nufin sashen sa yake a yanzu mallakinta
Bakin yan uwan meron harda na labaran yaqi rufuwa,kowa sam barka yake yana fadin ashe wani jinkirin alkhairi ne,gashi llkaci daua ta sanadiyyar wannma nawam Allah mero kin shiga daular da duk cikin ahalinmu ko a tarihi babu wanda ya taba shigarta,ya baku mazauni ya miki kayan daki ya bawa mijinki aiki ai babu abinda yayi saura tsakaninku face biyayya da fatan alkhairi''cewarsu,kallo kam sin shashi din lungu da saqo na gidan cikindaren banu inda basu leqa shi ba,itakam maryam wami abun su bata dariya wani anun su bata mamaki
maryam ta yaye lullubin da meron ta qudundune kanta aciki tana fadin
''to ai ba kowa adakin daga ni sai ke ko,sai ki bude kan hakanan kisha iska''itakam ko kadan bata ma kin zafi sai sanyi sanyi da take ji sakamakon ac data ratsa dakin,ta yaye mayafin tana kallon maryam,ita din ma kallon meron take tana murmushi tare da fadin
''umm,su mero amarya''murmushin itana tayi tana fadin
''yauahe rabon da kimin daiya mairamu?,da kin dauka zan auri yaya abdullahi ne ko?,ai ko wani abi gaya min ba nasan yafi qarfina,a wautata dai na soshi da farko,daga baya indo ta ankarar da ni,duk abinda fa kika ga munayi tsarawa mukayi,shiri ne kawai harda hadin bakin inna wuro,amma ba gaske bane''
Dariya ta kama maryam tace
''wato harda inna wuro kuka so haukatani ko?,to shikenan nina zan rama,nan da watanni zan bawa labqran qanwata ya aura kema kiji yadda akejin kishi''dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
''kiyi haquri adda mairamu,wallahi ina sin labaran dina,musamman ma yanzu da mukayi aure''dafa ta tatyi tace
''kada ki damu nima wasa nake miki,Allah ya bar kowa da masoyinshi''
''ameen adda''
''yau kuma na zama adda kenan ko?''ta fada cikin sigar tsokana''fuskarta ta rufevtana dariya
''eh ai innata cectace duk abinda ban san ba na tambayeki kada nazo nayita yin shirme,tunda kin girmeni''
jinjina lanta tayi tana murmushi,mintuna kadan suka qara maryam din ta miqe tana fadin zata ta kwanta sai da safe din qila angon ya kusa shigowa don tana jin lokacin da ya kira meron a wayar da ya siya mata yar nokia mai torch,ta tambayeta me take da buqata ta kawo mata
girgiza kanta tayi kamar zatayi kuka,banu komai adda ni kawai tsoron kwana nake anan,murmushi tayi don ta fuskanci me take nufi
''hmmm,ni dake duka jirgi daya ya debo mu ai,ban san me ke a ciki ba balle na taimaka miki''ta fada cikin zuciyarta,amma a fili sai tace
''kada ki damu ai yanzu labaran din zai qaraso,bake daya zaki kwana ba,kiyi,haquri kinji''a sanyaye tace ''to,amma wayata ba caji ko zaki ara min igiyar cajinki''
''bara naje na dauko miki minti biyu''ta fadi tana juyawa tare da ficewa daga bangaren
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Shida mamin ne tsaye cikin falon hannunshi dauke da kayan bacci na maza,tun dazun yake mata rigima ahifa nazai koma bangarenshi ba
''hooo abdallah,to wai ya kakeso ne da ni,na gaya maka an kwashe maka kayanka dagadakin sabida duka dakin baqi ne a ciki,gobr zasu koma garinsu ko so kake na koresu daga dakin kai ka shiga ka kwanta bayan ga bangarenka can,abinda yasa dama ban barka ka koma daga dawowarka ba gyara ne akeyi kuma an riga da an kammala an maida komai muhallinsa''
cikin shagwaba kamar wani qanqanin,yaro yace
''amma mami for god sake sai kace maye za'a kaini can ni kadai na kwana''
''ohhh,da can da kake kwanar mayen ne kai,ko wani abun ya gutsiri namanka?''
kai ya mirgina
''Allah mami ki rage sona,ina ma laifin kive in kwana dakin maryam tunda ita kadai ce,kawai sai a kaini qarshen gida ni daya tal kamar maraya''
dariya taso kamata amma sai ta dake
''anzo gurin,dama abinda yake ranka kenan kakeson fada,to anqi din,ko kunyar baqi ba zaka ji ba ka tsallakesu ka tafi dakin matarka kwana?,kaga kaina ciwo yake ka wuce sashenka kaje ka kwanta har abinci nasa an kai maka,idan kaqi kuma ka kwana a parlour shikenan''daga haka ta kama step din bene ta haye tana masa dariya cikin ranta
Sai data haye baki daya sanan ha dawo da kallonsa parlour din,yaja qwafa cikin zuciyarsa yana cewa ''duk a gama boye maryam din da yi masa wasa da hankali zasu gamu ne sai ya bata punishment''haka ya juya ya fito ba haka yaso ba cikin ransa
Cikin sa'a ya hangota tana fitowa daga bangaren meron,da azama cikin qwarewa irin tasu ta SS ya labe,sam bata lura da shi ba tana gyara yafen mayafin doguwar rigar jikinta taji an kamota baki daya anrungume tsam,ta tsorata sosai ta bude bakinta da niyyar yin magana
''kina yin magana sai na cinye lips dinki''ta saki ajiyar zuciya jin muryar abdallah ne,sai ya tuna mata lokutan baya da yake tsora tata irin hakan
Luf tayi a jikinsa ta saki ajiyan zuciya ta lumshe idonta,wani yanayi take ji na daban,dumi qamshin jikinsa gami da qamshin mint mouth fresh dinsa tare da maganar da yake mata cikin kunne suka kashe mata jiki,kwanciyarta a jikinsa ya bashi daman sa hannunshi yana shafa kafadarta zuwa yatsun hannunshi
''ina zaki je?''
muryarta low tace''charger zan daukowa mero''
''kishiyarki''ya fada cikin sigar tsokana,sai ta saki murmushi tana sake narkewa a jikinsa
''yanzun ki qyale wata mero muje mu kwanta,yau sashen mami a cike yake ya mana kadan''
ta dan zaro ido
''amma babu kowa a dakina ni ai,ni kadaice''
''i know,amma duk da haka ya mana kadan tunda tare nakeso mu kwana''
''amma mami fa.......''
''shshshshsh!''ya fada yana dora yatsanshi kan lebensa bayan ya juyo da ita da sauri suka koma suna fuskantar juna,idanunsu cikin na juna ya riqe qugunta
''bana son musu,just say yes...''sai ta sauke qwayar idonta,a hankali ta furta
''to''
''good mero na,bari naje na dauko miki kayan barcinki,nasan kina da buqatarsu''ya fada da sauri yana zaunar da ita kan kujerun dake waiting parlour din ya shige bangaren mamin
white night gown ce qal da ita mai santsi da taushi armless,rigar iyakacinta cinya,sai wandonta da ya tsaya qasan gwiwa,yana fitowa daga cikin corridor din da dakunan suke yaci karo da mami na saukowa daga step din benan
''au,baki tafi ba kenan''yayi saurin boye kayan baccin a bayansa yana fadin
''no.....nazo daukan wani abu na ne da aka manta shi ba a hada min ba cikin kayana(maryam)''baki ta tabe tana fadin
''alright,sai da safe''
da sauri ya amsa mata ya fice yana dariya hannunshi a baya gudun kada ta leqa taga maryam din bata nan tabiyo sahu
Tsaf sashen yake a gyare fes komai daidai,ya zube musu kayan baccin nasu gefan gado yana dubanta
''madam muje muyi wanka ko?''
kai ta girgiza
''nikam ban jima da yin wanka ba basai na sake wani ba''
''bazaiyiwu ba,ko an gaya miki bansan yadda kike tsarin wankan ki bane,koda kinyi da magariba idan kika zo yin bacci sai kin sake hakane?''
shuru tayi,ganin haka yasa ya fara cire kayan jikinsa,tayi qasa da kanta don batason ganinshi haka,yana kallonta cikin ransa yana fadin
''zaki sani yarinya'',da kansa ya shiga ya hada musu ruwa mai dumi da turarukan wanka kala kala cikn bathtube kana ya fito,yadda ya barta haka ya taddata bata yi wani shirin yin wanka ba,saiji tayi kawai anyi sama da ita kai tsaye ya shige bandakin da ita,bai direta ba sai da suka shiga ya ajjiyeta kana ya zagaya bayanta,zif dinta ya soma ja zai zuge sai ta hade jikinta guri guda tana fadin
''zanyi wankan,amma sai ka gama,ka barni idan ka gama na shigo nayi nawa''
ya sauke hannunta yana sake zuge zif din yana fadin
''ai daga yau babu wanda zqi qara wanka ba tare da dan uwanshi ba,daya daga cikin qa'idan rayuwar aure na kenan,sabida sunna ce ta ma'aiki,na san kin sani''
Tsori duk sai ya kamata,ta yaya zata iya tsayawa haka gabanshi?
''please abdul''
ta fada cikin rawar murya don tuni har ya kai zif din qarshe
''no maryam''ya maida mata amsa yana sabule rigar anan,ta sake sunqulewa guri guda tamkar qasa ta tsage ta shige ciki haka take ji,ya zura kansa ta kafadarta ya kai bakinsa saitin kunnensa
''ci gaba da yimin musu zai jawo na miki abinda bakyaso ne,wanan abun da kike tsoro,kinga shikenan na kashe boss din mun huta ni dake baki daya''
hawaye ya soma sauka kan kuncinta bai kuka ba don yana tsaye ne a bayanta,ga qoshi ga kwanan yunwa,cikin muryar kuka tace
''naji amma pls ka barni,da underwears dina''duk da mood din da ya shiga sai da ta bashi dariya
''a garinku kika taba gani anyi wanka da underwears?....''
''please...''tayi saurin katseshi,shiru ya danyi kamar bazaice komai ba kana daga bisani ya saki ajiyar zuciya
''alright,amma fa gaskiya kin tauyeni maryam''
kusan dai abdallah rabin wanka yayi,fatar ta kadai ta tsone masa ido,sai sheqi santsi da qyalli take,ai a ranar ya bawa idonshi abinci sosai,gyaran da tasha gun haj laila ya gama rikitashi,kusan awanni hiyu suka kwashe cikin bayin yana bawa idonshi haqqinsa,duk da bai tabata ko kadan ba don ya fuskanci a tsure take sosai
Da ido tabi kayan baccin,abdallah dan garari ne qarshe,bata da daman musa masa tunda itama ya mata alfarma,kuma da sharadin zai mata abinda take gudun indai ta kuma yi masa musu,don haka ta karba ta koma toilet ta saka su,ta kalli kanta a madubi ba shakka ba qaramin kyau suka yi mata ba,saidai kunya ta lullubeta,dukka hannayenta da singalalin qafartava waje yake,haka nan ana iya hango saman qirjinta sabida net ne mai kama da code lace a gun,ba yadda ta iya haka ta fito tana rabe rabe,sai Allah ya taimaketa ya tayar da sallah lokacin da ta fito din,tayi hamdala ta haye gado taja tattausan bargon dake kai ta lulllube jikinta tana satar kallonshi,cikin nutsuwa yake sallarshi da cika qa'idoji sharudda da dokokinta,kallo daya zaka masa ka tabbatar ya samu ilimin addinin islama bada wasa ba,hakan na daya dah cikin abinda yasa take sake ganin qimar mami take sake qaunatar shi kansa abdallan,don ada ta yiwa 'ya'yan masu kidi kudin goro,saboda yawancinsu idan iyayenka nada arziqi mulki ko sarauta nasu damuwa da zuwa islamiyya,gani suke sunfi qarfinta,amma kuma ai baka fi qarfin shiga wuta ba ko?
don kaje gaban Allah kace rashin sani ne ya saka aikata ba daidai ba sam ba hujja bace a gun Allah,tunda ga makarantu na addini nan ko ina
Ganin yana niyyar sallamewa ya sata maida idonta ta gimtse don kada ya kamata tana satar kallonshi,murmushi yayi don tuni jikinsa ya bashi kallonsa takeyi,baice komai ba har ya kammala da dukka addu'o'insa kana ya miqe ya isa gadon yana jan bargon gami da cewa
''malama mai,baccin qarya a tashi a bani,abinci naci''da sauri ta damqe bargon bayan ta bude idonta,sai da ya tuntsire da dariya ganin yadda ta haqiqance wai ita bacci take amma daga jin anja bargo har ta zabure ta miqe,ya sakar mata bargon ya koma gefan madubi ya zauna bayan ya harde hannayensa ya zuba mata ido yaga ta yadda zata tashi,ai kam kasa tashin tayi qarshe sai ta yayimi bargon ta yafashi ta cukuikuye kana ta soma yunqurin tashi
''nikam a haka nakeson ki tashi''ya fadi yana boue dariyanshi,marairaice tayi
''amma fa babu mayafi kuma yakayan yan gajeru ne''
girarsa ya daga
''yes,haka nakeson in ganki,ko kinfison naje na kalli wasu?''ya fada yana dage gira.
Sai ta hade rai ta cuno baki kishin ya motsa,miqewa tayi ta sauka daga kan gadon sai ta tsinci kanta da sauya taku,binta yayi da kallo kamar ya hadiyeta haka yake ji har ta fice a dakin ya kasa dauke idonsa daga hanyar,ba kyau na fuska kawai Allah ya mata baiwa da shi ba har diri na jiki duka ta samu,shikam Allah ya zaba ya bashi bashi da abinda zaice da ya wuce alhamdulillah
Cooler ce mai dauke da friede rice da coleslow,sai farfesun hanta daban,kusan tare suka ci abincin saidai shi ya dinga bata tana karba cike da kunya
''kunyarki tayi yawa maryam,amma.....na kusa tsige miki ita''haka ya fada yana wane kashe mata idanu
cikin jikinsa ya janyota bayan ya kashe wutar dakin yana sansanar qamshin jikinta,wani qamshi yake ji na tashi a jikinta da bai taba jin irinsa ba,sai da ya gama sansana iya son ranshi kana ya hautsinota suka dawo fuskantar juna
''hira nakeso muyi irin ta ma'aurata my dear na''ya fadi bayan ya hade tafukan hannunsu cikin juna,sai ta sunne kanta a qirjinsa tana murmushi,batasan haka zama da masoyi yake da,dadi ba,sai,yanzu ta sake tabbatarwa tabbas a baya batasan farincikin zuci ba sai yanzu
''maryam''ya kira sunanta tamkar mai rada,bai jira amsarta ba ya dora
''gobe ne zamu shiga wata rayuwa,rayuwa ce da bamu taba sanin ya take ba sai a labari,rayuwa ce da bamu taba dandana irinta ba sai a mafarki,zama zamuyi na dindin din,ina son don Allah maryam ki riqe amana ta,ina sonki da yawa ina qaunarki fiye da yadda kike hasashe ko zato,zuciyata bata taba dandanar soyayya wata diya mace ba baya ga mami na sai akanki,kinsan gausawa sunce zo mu zauna zo mu saba,ni yarima ke sarauniya,inason mu gina masarauta mai cike da ni'ima nutsuwa da kwanciyar hankali,ina so matata ta kasance tamkar qawata,qanwata,yayata mahaifiyata mahaifina da kuma 'yata ta yadda ta kowanne bangare daga cikin mutanen nan da na lissafa zata iya taka rawa a gurbinsu''ya zarce da gaya mata ra'ayinsa da qa'idarsa me yakeso da abinda bayaso,ya kammala yana maida numfashi yayin da maryam tayi shiru har yanzu kanta na kwance a qirjinsa
Babu shakka abdallah mutum me mai sauqin ra'ayi da hali qwarai da gaske,tasha jin ana fadan halayen masu sunan,sai yau ta sake tabbatarwa hakan suke,yau din da Allah ya hadata zaman aure da mai irin sunan,wata qila sun samu tabarrakin sunan da ya zamto babu sunan da Allah yafi so irin abdullahi sai abdur rahman,dama ya bata ta fadi nata dukkan ra'ayin yaci mata alwashin kiyayewa shima,saboda zaman tare kowa,nada haqqin akan dan uwansa,bawai shi kadai ke da haqi ko keson kyautatawa ba,Allah ya fada cikin qur'aninsa mai girma cikin suratul baqara''walahunna mislul lazi alaihinna bilma'aruf,suna da(su mata)kwatakwamcin abinda ke kansu na kyautatawa(akan mazansu,ma'ana yadda zata kyautata maka kaima akwai kawatankwacin hakan a kanka)
itakam kasa fada tayi sai da ya matsanta mata kan haqqinta itama ta fadi din
''qaunarka kawai abdul idan ka bani ya isheni rayuwa,ka soni har mutuwarmu,ka riqe amana ta,kada ko tozarta qaunar da nake maka''
''har *ABADA* har *ABADAN* maryam banjin akwai abinda zai sa na tozarta tukuicin qaunar da kika yimin,idan dai wanan ne matsalarki ki goge shi daga babin matsala daga ciki kundin rayuwarki''ya fada yana shafa gashin kanta da ya sauka har kafadarta
wani irin bacci sukayi mai cike da qauna da tsantsar bege cike da shauqin juna
🍃🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Da safe sai guduwa tayi don ta fuskanci abdallah na son sake tsareta wai tayi wanka ta shirya anan,ita kuwa batason abinda zaisa mami ta gane bata kwana a dakinta ba,duk da tasan babu ruwan mamin ba nunawa zatayi ba ama abun da kunya tusa gaban suruki
shigarta waitin parlour din taci kark da kibrin yana fitowa daga sashen nasu,ta sake kallon agogo qarfe shida saura na safe,da,sauri ya qaraso gareta
''yauwa dama ke nake nema na rasa yadda zanyi na ganki''da mamaki kan fuskarta ta kalleshi
''lafiya?''
sai ya hau sosa kai
''ah...mero...mero ke nemanki,tana daki''
mamaki ya cikata saidai bata ce komai ba ta nufi bangaren nasu
gabanta ne ya dunga faduwa ganin meron nafa rusa uban kuka,duk da ita kanta ta tsorata amma sai ta danne ta qarasa inda take,sai kuwa ta sake qara sautin kukan nata,take ta gane abinda ya faru da ita,bata iya cewa komai ba ta taimaka mata tare da koya mata wasu dabarun data fusknaci meron bata sani ba,ta tausaya mata tsoro ya sake cikata,jikinta duk yayi sanyi saidai bata nunawa meron ba din kada ta karya mata gwiwa,haushin labaran ya kamata,me yasa sam su,basu da haquri,atleast ai ya bari yan uwanta su koma
Kukan mero yaqi qarewa,zama tayi ta dinga mata bayani sannu a hankali ta fahimceta,ta samu ta daina kukan bayan digon bayani data mata,duk da ita ma ba sanin wani abun tayi ba ga kunya na yadda zata mata bayanin,bata kai ga tafiya ba kiran abdallah ya shigo wayar ta,da sallama tare da sanyin jiki
''shine kika gudu ko?,idan kin gama da maryar labaran din kicewa mami na fita amma bazan jima ba zan dawo,shima gashi nan muna tare ki gayawa amaryar tasa''kunya ta cikata
kada dai ace ya sani abdallan,kamar kuwa ya san me take tunanin yace
''ba wani,abu yace da ni ba,nina fuskanta da kaina,naga kuma yana buqatar training,so kada kunya ta ta qaran miki akan ta da''ya qaraahe maganar yana dariya ciki ciki
A sanyaye ta sauke wayar a kunnanta,ji take ma kamar ita yakewa dariyar,ta dubi mero dake kwance hajaran majaran ta miqe
''maigidan naki sun fita da abdallah,zan je mu gaisa da su mami,amma dole ki dinga qarfafa jikinki kada ki nunawa su inna wani abu kin fahimta''kai ta gyada mata ta yi mata godiya ta fice
Tuni har sun tashi,kasancewar mutumin qauye ya saba da tashin wuri,baya malalacin baccin nan na bayan sallar asuba,Allah ya taimaketa mami bata fito ba,don haka anutse suka dinga gaisawa daga bisani ta shige dakin da inna wuro take.
*mrs muhammad [truncated by WhatsApp]
[3:19pm, 10/12/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣3⃣
*Daga jabir dan Abdullahi R A yace:naji Manzan Allah S A W yana cewa ''((idan mutum zai shiga gidansa sai ya ambaci sunan Allah yayin shigar tasa da yayin ci abincinsa,sai shaidan yace:baku da abinci baku da gurin kwana(a cikin gidan),idan kuma ya shiga ba tare da ya ambaci sunan Allah ba yayin shigar tasa sai shaidan yace:kun samu gurin kwana,idan bai ambaci sunan Allah ba yayi da zaici abinci sai yace(shi shaidan din):kun samu gurin kwana da abinci))*
Tana dakin suna ta hirarsu da inna wuro mami ya shigo dauke,da kwando wanda ta zuba kayan breakfast a ciki na inna wuron,da sauri maryam ta tashi ta amsheta kamta aduqe tana gaidata,ta amsa mata asakekamar kuma ba aurukarta ba yadda dai sjka saba,zama tayi itama aka soma hirar da ita duk da maryam taja bakinta ta tsuke,saboda kunyar mamin,sai ta tsugunna tana hadawa inna wuro tea.
''ni inna wuro dama zamanki kikahi wlh damu,da kiwa,naji dadi sosai''inji mami,kama bakinta inna wuron tayi
''rufani ki saya ni bintu,ina ni ina zaman maraya,wannan ao saiku,dubi fa don Allah wai wannan ruwan ahine karin safenku,ina kuwa zakuyi qwari''ta fada tana nuna tea din dake hannun maryam tana figita mata,dariya ta basu,baki daya,kai imna wuro nanu dama,duk yadda mami taso ta yadda tayi zamanta aje a taho mata da tsoho alhajinta sam ta qiya.
''amma dai inna ai kya zauna har a raka mairamun taki nata gidan anjima ko,ku gano nata dakin''maryam dake gefe gabanta ya fadi,sai walwalarta ta ragu,tsoro ne fal ranta
''nan fa daya,nifa yau sai qauyen ni'ima bintu''da qyar tasha kanta amma fa saidai a rakata taje ta gano don babu faahi yau zata koma,ta bar tsohonta shi kadai a gida(hmm,mata irin na da kenan masu iya tattala miji da bin umarni)
''kema sai ki zauna ki karya don hajja laila ta iso yau takeso itama ta koma audan din,tana can gun takwararki ana mata gyaran jiki da qunshi,sai kije can ki samesu don nan ba zaku sake na saboda mutane''kamar an dira mata dutse haka taji ta amsa da ''to''
''sannunki bintu,ke dai kin zama uwar kowa kenan,kin kama kowa kin riqe kamar yadda hausawa suke cewa da na kowa ne,arziqinki na kowa ne,Allah ya albarkaci rayuwarki data yaranki,da za'a samu ire irenki cikin al'umma su wadata da an bar kukan yunwa qunci da talauci,Allah ya jiqan mai gidanki''inji inna wuro
''ameen ameen inna,ai shi arziqi da Allah ya baiwa dan adam tamkar ka dauki wani abu ne mallakinka ka baiwa,wani kace ya amfana ya kuma amfanar da wasu,muma aro Allah ya bamu da rabon mu aciki da rabon wasu,ma'ana ka ci ka ciyar da wasu,ruwanka ka ci kai kadai ka tashi ran qiyama cikin wahala,don Allah na narka dukiyar ne ya dinga maka azaba da ita,abinda ka bayar shine rabonka don shi zaka taras a cikin littafinka ranar gobe qiyama,wanda kaci kuma banza ne don na wani ka yiwa ba bare a rubuta maka ladar ka ciyar da dukiyarka ga wani,kai kanka baka da tanbas din dawwama cikin dukiuar,wataran Allah na iya karbe kayansa ya baiwa wanda yaa dama,ko ka muti kabar zuriya to baka aikata alkhairi na wa kake zaton zai kula maka da su?''
''wannan haka yake binta,Allah kasa mu dace''inji inna wuro,maryam na gefe tana jinsu ita kanta addu'a takewa mamin cikin zuciyarta,ko bata taba mata komai ba ta haifa mata *GWARZON MIJI DAYA TAMKAR DA DUBU ABDULLAHI BAWAN ALLAH*,bare babu irin halaccin da bata mata ba,mami mutum ce wadda samun kamarta zaiyi wuya
ruwan shayin kawai ta sha taji cikinta gaba daya ya cushe don haka ta fice tabarsu adakin,dakinta ta koma tayi wanka ta saka baqar doguwar riga don kada kayan ta su baci garin lalle,can ta tars da haj laila tana hada lallen qunshi,tuni mero an shige cikin dilka da kurkum ga bayaga halawa da aka sha.
Ita kanta kasa gajiya tayi da sabawa fatarta sabulu saboda wani irin santsi da taji tana yi na ban mamaki,itakam dama ko ba'a gama gyaran jkkin nan ba a yau zata cewa haj laila abarta haka,tana kallon yadda mero keta fama ina ga ita,fitowarta kenan haj lailan ta miqa mata wani anu cikin cup sai qamshin citta da kanunfari yake tace
''shanye diyata''haushi ma kamata yayi bata ce komai ba tayi kurba uku ta faki idonta ta fita da shi da niyyar zubarwa
cikin garden na gidan ta shiga ta daga zqta fara zubarwa taji an riqe hannunta,a hankali ta dago kanta sai suka hada ido,sanye yake cikin suit baqi da ja saidai yar saman ya cireta tana singalalin hannunshi,da alamu har ya dawo daga fitar da yace mata zaiyi
sai da ya mashe mata ido daya sannan yace
''shigowata kenan naga wani haske ya cika gidan nan,ina waiwayawa naga ashe kece,shine na biyoki ina fata banyi laifi ba''ya fadi maganar yana qoqarin amshe cup din daga hannunta,tana qoqarin boyewa ta bashi amsa
''um um,ko daya bakayi laifi ba''
ganin yana qoqarin maida abin babba yana son ya rungumeta yasa ta sakar masa cup din a sauqaqe,sai ya leqa ciki yana fadin
''hala wanann abun dadi ne mami ta baki ko,Allah yayi da rabo na kenan nasha?''ya tambayeta yana kallonta,wani irin kyau yaga tana fitarwa,tambayar kawai yayi amma bai gane me yake fada
da sauri ta girgiza masa kai
''a'ah,kada kasha''
''why?,muba muta ne bane''yayi tambayar yana dan zaro ido gami da dage gira.
Sai kawai taga ya dangwalo ya tsotsa
''hmmmm,gaskiya da dadi''ya fada yana kaiwa bakinsa,kafin ta qwace har ya kurba,ta karbe kana ta zubar
''na gaya maka mazq baku sha,idan poising ne kuma fa?''
sai taga ya saki murmushi mai fidda sauti kana ya harde hannunsa a qirji
''sai abun ya zama abun alfahari a gareni,masoyiya ta bawa masoyinta guba sabida tsabar qauna,kuma zaqinta zanji dear na,ballantana ma na sani ke din ba zaki iya ba,saboda wasu ma da suka yi yunqurin bani naci kin kawar da hakan,ko kin manta har asibiti kika je aka tabbatar miki da irin nau'inta da kuma qarfinta?''
ido ta zaro,wai abdallah aljanine ko kuwa yana da su ne?
murmushi ya kuma yi,ta bude bakinta da niyyar yin magana,sai yayi azamar qarasowa gabanta,yasanya tafin hannunshi ya rufe labbanta yana kallon qwayar idonta tare da cewa
''yi shiru da bakinki,ki adana duk wasu tqmbayoyi da kike da,su,wannan hiran na daya dagq cikin hirarrakin da na tsara mana,cikin gidan mu na qauna,a kan gadon soyayya,a kuma qirjin masoyi''ya qaraahe maganar yana kashe mata ido.
kunya ta kamata sai ta zame bakinta tana murmushi ya sake matsowa kusa da ita yana yin qasa da murya saitin kunnenta
''ina fata kin tanadarmin salo salo na soyayya da,qauna wadda zaki shayar da ni,kinsan abdallah dan soyayya ne,yana son soyayya musamman ga matarsa''ya fada yana qoqarin janta jikinsa,gabanta ya shiga faduwa,ta faki idonsa ta zille tayi hanyar fita,baiyi yinqurin binta ba don ya tabbatqr da mutane a wajen amma sai ya matso uadda zata iya jinsa ya biyo bayanta
''ki gama zulle zullenki yarinya,awa,nawa,ne ya rage?''hakan da ya fada sai ua sata tsayawa ta juyo ta dubeshi idonta har ya cika da qwalla,dariya ya sa mata tayi hanzarin ficewa daga gun.
Zuwa la'asar gaba daya hajja laila ta gama da kyawunta,tamkar buga qunshin akayi aka dayeshi,banu kuskure ko daya aciki,ja ne amma har saman hannu da saman qafa,abinka da fara ya fito kuwa yayi marun,kyau kam basai an fadeshi ba ya gama yi,tuni yan kawo mero sun tafi don yaci ace ma zuwa la'asar din sun kai gida,saukowarta kenan daga saman mami dauke da wata leda wadda wani arnen codenet ne a ciki da aka fidda wa dinki na garari,kudadr mamin ta saka masu yawa ta siyawa maryam din sabida wannan rana,sallama akayi aka shigo falon qasan,raliya ce janye da hannun fadil(yaronta)sai hindatu da lubabatu da kulu,baaba huwaila da hajiya atika.
Cikin dakinta suka shiga ita da raaliya hindatu lubabatu da kulu,baaba hadiza da hajiya atika kuwa suna sama gun mami,mami ce tasa duka suka zo don yi mata rakiya,hira suka dinga yi wanda zuwansun ya rage mata fargaba sosai,lubabatu da kulu nata kallen kallen gidan mami don yau ne zuwansu na farko,sun tabbatar cewa Allah ya yiwa adda maryam din baiwa ba qarama ba.
Raaliya ce ta shiryata tsaf cikin codenet din orange da yellow,kana ta dora mata alkyabba da mamin ta hadota cikin kayan,yellow ce mai ratsin fari,fadar irin kyawun da tayi ma bata baki ne,su kansu tsayawa sukayi kallonta,kai tsaye gin mami suka fara zuwa kana suka fice suka barta ita da ita,kallonta mamin take cike da farinciki,burinta kam ya gama cika a yau,hannu ta miqawa maryam din ba musu ta bata,gefeanta ta zaunar da ita kana tace
''maryam,da farko abinda zan fara cewa dake shine kiyi haquri,don babu wani abu da ya wuce haquri da mace zata riqe wanda zai,zame mata jagora kuma madogarar gidan aure,haquri maryam shine komai a rayuwa,kiyi haquri a duk yanayin da zaki tsinci kanki a gidan aurenki,duk wata mace da kika gani zaune gidan aurenta wallahi ba za'a rasa wata matsala da take fuskanta ba komai qanqantarta,ta wata ne tafi ta wata,qila wadda kikewa hangen ta haye ta huta da zata buda miki cikinta wallahi saikin tayata kokawa,komai dadinki da mimi wataran sai kun samu sabani,donko tsakanin harahe da haqori ma ana sabawa,na biyu riqe sirri ki riqe sirrinki ke da maigidanki maryam,koni idan bai zama dole ba bana buqatar jin sirrinku ke da abadallah,ku riqe amanar juna,ku riqe sirrin juna,ku zauna da juna cikin amana''nasiha ta dinga mata irinta tsakanin da da uwa,kuka sosai ta dinga yi har sai da mamin tace
''a'ah,ai kuma zaki batawa abdallahn kwalliyar me akayi kenan kuma uhm.....maza share hawayenki,duk da haka kowacce mace ta saba yau hashi kowa na zaune agidanta''.
Da kanta ta kama hannun maryamun har harabar gidan ta sanyata cikin sabuwar range robber baqa wul wadda kyauta ce mamin ta yi mata,tukuici ne ta bata,kadan daga cikin irin abubuwan da take ji zata iya yiwa maryamu,yadda ta kama hannun mamin itama sai ta karya mata zuciya har sai da ta share qwalla,motocine kusan shida don akwai yayar mami da qanwarta,sai yayar marigayi alhj abdulkareem mai nasara da qanwarsa,tana nan tsaye mamin har motar ta daga suka fice daga gidan kana ta juya ta koma ciki,tun daga lokacin ta soma jin kewar maryamun,bangare daya ga abdallah dake shirin tafiya shima,babu shakka kewarsu zatayi ba kadan ba,don ma ga mero nan,amma kafin su saba su maye mata gurbin maryamunta ai ba nan kusa bane
Sai da suka fara zuwa gidansu suka kaita gun mama da malam mamuda mahaifinta kafin su wuce da ita gidanta.
Wani irin yadine ajikinsa orange colour mai bala'in kyau da taushi,dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,fuskar nan tashi tayi wani irin kyau na musamman,hisham ke riqe da wata iriyar jaka da aka qawata ta da rubutu mai kyau suna tafe yana masa tsiya har suja qarasa gun mami,tana falon nata tana sallah ya tura qofar suka shiga,kujera suka samu suka zauna suka jirayeta har ta idar,sai data shafa addu'a kana ta tashi ta dawo kan daya daga cikin kujerun itama ta zauna,hisham ne ya fara magana
''mami gashi na kawo miki shi,ayi masa nasihar zaman aure''mirmushi mamin tayi tace''ka kyauta kuwa,shi yasa nake sonka hisham badai hankali ba''
harararsa abdallah yayi''jimin dan rqimin wayo,kana nufin zan iya tafiya banzo ga mami na ba?''
dariya ya masa don ya fuskamci yanayin fuskarshi har ya canza ya kuma san ba wani abu ne ya tabashi ba sai barin mamin da zaiyi.
''abdullahi''ta kira sunanshi da salon da bata taba ba,take ya dago idonsa ya kalleta,sai ya kasa civgaba da kallon nata ya duqar da kanshi,son ya hango magana zata masa bata wasa ba
''shi aure da kake gani girma ne da shi,daraja da shi qima gareshi,sunna ce guda ta wanda akayi duniua da lahita dominsa wato annabi muhammad S A W duk wanda ya wulaqantashi baya tare da annabi na tabbatar kuma bazaka so haka ba,a duk sanda ka dauki yarinya,aka rqbata da uwa da ubanta da inda ta taso tavgirma,aka rabata da danginta aka rabata da duk wani wanda ta saba da shi aka baka to ka tabbatar da xewa amana ce aka baka mai girma,kasan sarai hikuncin wanda ya tozaratar da amana ko yaci amana ko?,ka tuna ko yauahe cewa matarka ba siyanta kayi ba,ba baiwarka bace 'yace 'yantacci ya mai yanci,kada ka dinga mu'amala da ita irin mu'amalar bawa da ubangidansa,a'ah,ka mu'amalance ta wani lokaci kamar 'yarka,ka tsawatar mata ka bata shawaea ka tausasa mata kaja girmanka,ka mu'amalanceta wani lokaci kmar mahaifiyarka,ka tausasa mata,ka kyautata mata,ka girmamata,ka mu'amalanceta wani lokaci kamar qanwarak,ka qaunaceta ka kauda duk wani abu da zai cutar da ita ko ya,bata nasabarta,ka dorata kan hanya madaidaiciya,ka mu'amalanceta kamar qawarka,ka gaya mata damuwarka,kayi shawara da ita,kuyi wasa kuyi dariya,matarka duka tana da wannan mtsayin a gareka''.
Ta dora da cewa''na tabbata har yau kana iya tuna mu'amalata tsakanina da mahaifinka wanan kawai ya isheka madubi,ya iaheka littafin da zaka dinga karantawa ko yaushe koda ban ce maka komai ba game da zamantakewa da iyali,abdallah ka guji zalunci,Allah da kansa ya fada cewa ya haramta zalunci abinsa kansa,kuma ya haramtashi a tsakaninmu,ka kyautatawa matarka,ka sauke duk wani nauyi da Allah ya dora maka,yadda kake da haqqi a kanta haka itama take da haqqi a kanka,ban yarda ka take mata haqqinta ba abdallah,iya wannan nasan ya,isheka nasanka nasan tarbiyyar da na maka,don Allah abdallah kada ka watsamin qasa a ido,kayi zama zama na haqiqa da matarka,Allah zai tsadaku ranar gibe kan yadda kuka sauke haqqin jilunanku,wallahi wannan gaskiya ne babu ko tantama aciki''
idanunshi tuni sun hama hada ja,zuciyatsji zafi take masa,karo na farko da zai rana gidan kwana shi da maminsa,a hankaki ya miqe daga mazauninsa ya isa gabanta ya durqusa kangwiwoyinshi,kana ya cire hular kansa
''mami kisa kin albarka,kici gaba da yi mana addu'a,insha Allahu zanci gaba da zama abun alfahari a gurinki''
hannunta ta dira saman kanshi kana tace
'' *BARAKALLHU LAKA,WA BARIK ALAIKA,WAJAMA'A BAINAKUMA FILKHAIR*'',ta amshi ukar da kanta ta maida masa ita saman kansa,sai ya kasa jurewa ya dora kansa saman cinyar mamin yana ajiyar zuciya,tausayinsu ya kama jisham,babu shakka ba qaramar qauna nace tsakanin wannan da da uwar ba,sai ya,kasa zama shima ya tashi a hankali ya fice,uwa ba wasa ba.
Mamin bata masa magana ba don ta saba da irin hakan,majority tun yana yaro idan zuciyarsa na quna haka yake ya dira kansa saman cinyarta har sai ya huce,don bashi da qawa a lokacin ko aboki da ya wuce maminsa(yana da kyau iyaye ku zama kune abokai ko qawa na farko wanda suka matuqar shaquwa da 'ya'yansu kafin kowa,ta hakane zaki samu damar yiwa diyanki kalar tarbiyyar da kikeso mai kyau ba tqre da wasu sin samu damar ruguje miki ba,bawa yara damar shaquwa da aboki fiyr da iyaye da rashin jansu a jiki babbar illace,da abokin nan ko qawarnan zwta dinga shawara,ita zata dinga gayawa damuwarsa bake ba,kinga kenan zai iya dorashi kan irin tasa tarbiyyar,amma idan akwai shaquwa tsakaninku kece mutum ta farko da zai fara dinga gayawa matsalolinsa da damuwarsa kafin kowa,saidai idan kuma yayi aure Allah ya bashi mace ta gari sai ki koya masa neman shawara daga matarsa,saidai idan duka su biyun tunaninsu baikai nan ba ko mas'alar tafi qarfinsu,a kuka don Allah iyaye,tarbiyya abace mai tsada da wuya,amma a qarshenta kuma ke uwa ke zaki fi kowa mora da jin dadinta koda baki duniya kuwa).
Ita ta riqo hannunshi suka sauko qasa,ya zama kamar ba abdallah ba,qwarin rai da qarfin zuciyar nan duka babu,har dariya ta dinga masa kan cewa ya girma fa,ya kamata ya koma abdallahn sa,nan da ten months yana iya zama daddy,abinda ya sashi dariya ya kuma bashi kunya kenan,bakin freezeer suka isa ta bude ta ciro wata qatuwar leda ta sake jansa har suka fito harabar gidan inda motocin security dinsa guda uku data abokansa guda uku ke jiransa,cikin motar da za'a kaishi ta bude masa da kanta ta sanyashi kana ta miqa masa ledar''Allah ya tsare hanya,a sauka lafiya''ta fada kana ta rufe musu qofar ta koma ciki,a varanda ta tsaya har sai da taga ficewar motocin duka.
Mus'ab abokinsu ke tuqa motar,usman na gefansa baya kuma hisham ne da abdallahn,cikin salonvtsokana hisham din yace
''idan bakason rabiwa da mamin kawai mu maidaka gida sai a yiwa maryam waya ta haqura kawai''harar ya galla masa bayn ya sauke ajiyar zuciya
''mami da maryam duka rayuwata ne hisham,ka sani,ba sai na maka dogon bayani ba''tsokanarsa suka ci gaba da yi tare da yi masa shaqiyanci kala kala irin na abokan ango har suka iso unguwar.
*mrs muhamma ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣4⃣
*An karbo daga Abdullahi dan salaamin Allah ya yarda da shi yace:naji manzan Allah S A W yana cewa:((ya ku mutane,ku yada sallama,ku ciyar da abinci,ku sada zumunci,kuyi salla cikin dare lokacin da mutane suke bacci zaku shiga aljanna cikin aminci))*
_imamut turmuzi yace hadisi ne ingantacce_
*gaisuwa ta musamman gareku tare da dimbin godiya da jinjina*
*mom hanee*
*fatimah zahra haske asso*
*zainab idris makawa(takari)*
*maman farida(samun wuri)*
*maman rufaida (manal)*
*hafsat mai sharif(rayuwar aure na)*
*Billy galadanchi(hanjin jimina)*
*khairat*
*mrs ibrahim*
*maman aysha(gadar zare)*
*ummu zainab*
*rabi'ah haroun*
*maryam gital(ba halul kitabi bace)*
*KAI !KAI!!, INA KUKE MASOYAN ABDAN,TO KU MATSO NA GAYA MUKU👂🏾*
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*wannan page dinfa naku ne,duk inda kuke na sadaukar muku da shi kyauta,wanda na sani da wanda ban sansu ba,na kusa da na nesa*🏆🏆🏆
*NAGA SAQONKI AISHA GARKUWA 😂😂😂,NI DAKE AI DUKA DAYA NE MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE😜😂,KICI GABA DA KARBAR SU AI DAMA NANA AISHA AI UWAR KOWA CE,UWAR MUMINAI R.A,NA GODE DA KIKA MIN KARAR KARBAR FANS DINA DA MUTUNTAWA KIKA BASU FURA DA NONO,ALLAH YAYI MANA JAGORA*😂😂🙏🏽🙏🏽
😍😍😍😍😍
Gida ne gini na alfarma,gini irin na gata,gini ne mai cike da tsari kyau da fasaha a cikinsa,kana shiga gifan kawai zaka tabbatarwa kanka cewa gida ne da ni'ima da kwanciyar hankali tayi kaka gida acikinsa,sanyi da iskarsa ma daban take albarkacin tsirrai daya wadatu da su,duk inda zai kasance ansa tiles cikin harabar gidan baki daya an maye gurbinsa ne da grass carfet mai ban sha'awa,duk cikin abokan nasa babu wanda ya iya tsuke bakinsa ba tare da ya yaba ba,a haka suka ajjiye motocinsu suka dunguma zuwa,cikin gidan
parlour na farko anan suka ci burki,ya dubesu baki daya babu ko kunya yace da su
''daga parlour na farko fa banjin zan iya barin wani ya shiga parlour na biyu bare na uku,saboda haka anan zamuyi sallama da ku''
mus'ab yace
''dan iska,zakayi abinda yafi haka ma,kamar a kanka aka saukar da wahayin kishi,mun gama maka amfani ai tunda mun rakoka''
dage gira hade da kafadusahi yayi
''eh da gaskiyata fa,haka kawai na kwasheku har bedroom din matata,ina da kishi gaskiya''
''muma bamu ce zamu shiga ba malam,tunda munyi na Allah ai shikenan''inji usman yana ajjiye ledar hannunshi,yana dariya qasa qaa ya dafa kafadarsa''yauwa mutumina,dadi na da kai sauqin kai''
Tsokana dai irin ta abokan ango haka sula yo masa yana ramawa,barkwanci sosai suka dinga yo kama suka juya suka fito ya rakasu,har sunyo gaba hisham ya dawo
''yauwa,inason ganinka fa''
''zaka batan lokaci kenan,na bar gimbiya fa batasan na shgo ba ma fa''murmushi hisham din yyi mai hade da dariya
''me kake ci na baka na zuba,kunnenka na tsaya na ja don naga yadda kamka ke rawar nan,wlh kayi a hankali kada ka cutar musu da diya,na sanka sarao idan kana som abu baka daukar lamarinsa da wasa''
kunnen abdallah ya turo masa yana fadim
''to daddy,ga kunnen,fadi da kyau,ko daki zan baka ne ma kusa da namu kayi sa idon da kyau''tare suka sheqe da dariya kana suka tafa
''Allah ai kaine da iua shege,kai wa yasan me zakayi ranar da aziza ta zama taka''har wani sosa kai hisham yayi kana yace
''wlh fa,na barku lafiya to''ya fada ya juya yabi sahun yan uwansa dake zaune cikin mota suna kiransa aballah ya bishi da kallo,yana son hisham mutum ne mai amana wanda samun kamarsa sai an tona,ba duka mutum bane a wannan zamanin zakamasa alkhairi ya saka maka da alkhairi,mafi yawancinsu da sharri suke saka maka sai yan kadan
Sai da ya tabbatar sun fice sannan ya isa ya rufe gate din gidan don bai kawo mai gadi ba tukun,bai koma ciki ba sai da ya tabbatar ya rufe ko ina
A hankali yake takawa yana nufar cikin gidan,iskar damina na kadashi,wani irin ni'ima ce yau lullube da sararin subhana,iska ake mai dadi da shiga jiki,gefe guda wani tawagar farinciki ne ke shawagi cikin zuciyarsa,jinsa yake cikin wata duniya ta musamman,yau gashi ga maryamunsa,cikar muradinsa cikar burinsa,sashensa ya bude ya ciro kayan bacci farare tas da towel dan qarami kana ya rufe ya dawo sashenta ta cikin parlour din gidan na biyu,a hankali ya,keta har falo na uku wanda daga shi sai wani dogon corridor wanda kana shiga zaka tadda dakunan bacci uku,sai matattakalar bene wadda saman shima ke dauke da dakunan bacci parlour toilets da kitchen,a hankali ya,haura saman kansa tsaye ya tura qofar daya daga cikin dakunan da ya gani a bude wanda hakan ya tabbatar masa a ciki maryam din take
''assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatu''ya shiga da sallama wanda hakan ba qaramin rage mata fargaba yayi ba,gefan kujerar dakin take zaune,kanta na duqe lullube da alkhyabbar jikinta,tsayawa yayi cak kana ya kingina da bangon dakin yana qare mata kallo duk da bai ganin fuskarta,ya kashe a qalla mintina biyar a haka zuciyarta na bugawa a hankali kanta na a qasa,ta tabbatar har yanzu yana cikin dakin saboda qamshin turaransa da ya cakude da nata ya lullube dakin,haka nan ya sake haifarwa da dakin wani irin ni'imtaccen yanayi,sannu a hankali ya dinga takowa gareta bayan ya ajjiye kayan hannunshi duka saman dan qaramin table na glass dake a gaban gadon,ya isa gabanta ya zube duka kan gwiwoyinshi,hannayenta ya kama ya sanya cikin nasa yana qarewa qunshinta kallo,tamkar yasa harshensa ya lashe haka yaji,sai da ya more kallonsa sannan ya dora kansa saman cinyanta yana leqen fuskarta,bai ga fuskar sosai ba sakamakon hular alkyabbar ta sanya ta yin duhu,a hankali ya sanya hannunshi ya janye hular take fuskarta ta bayyana saidai idon nata a rufe dai yake
Cikin wata sassanyar murya da bata zaton yana da ita ba taji yace''zan rayu dake zan mutu da ke *ABADAN* dani dake zauna''murmushi ya subuce mata don bata taba jin waqa a bakinsa ba sai a wanan karon,sai taji tafi dadi a bakinsa ma fiye da mawaqin,a hankali ta dago brown oily eyes dinta ta zuba masa,dama abinda yakeson gani kenan,shima murmushin ya sakar mata wanda saura kadan ya narka mata zuciya,ajiyar zuciya ya saki ya lumshe sexy eyes dinshi kadan sannan ya sake budesu''ya Allah ka gafartawa mami na,kayi mata albarka data sauqaqamin hanyar samunki,ta shiga lamarina'' kana ya daga girarsa
''yes....zan rayu da ke har *ABADA* maryam,haka kuma nake fatan koda mutuwa tazo min ta daukemu tare....''
Sake maida kansa yayi yi ya kwanta a cinyarta
''soyayya gaskiya ce baby,haqiqa,babu abinda ya kai so dadi,so shine abu mafi girma dake iya sarrafa zuciya kota wanene,haqiqa so ba ruwanshi da kyau nasaba ko cancanta mulki ko wata dukiya,yakan kama mutum ne kansa tsaye ba tare da qwaqwasa qofa ko neman izini ba,maryam kici gaba da zama tawa ni kadai har *abadan* don Allah''idanunta a runtse suke ya riga da ya gama kashe mata jiki baki daya a hankali ta dora hannunta saman sumarsa
''ni taka ce abdallah,takace ni,ina ji a jikina saboda kai aka halicceni,kaga kuwa har *abada* maryam ta abdallah ce,to ta yaya jiki zai iya rayuwa babu daya barin nasa?,ta yaya zuciya zata iya rayuwa da tsagi guda ba tare da daya tsagin ba?,ka zama ni na zama kai *mutu ka raba*'',qanqameta yayi kamar za'a qwace masa ita yana mata godiya tare da sheqar daddadan qamshinta dake barazanar juya akalar tunaninsa
A hankali ya dinga rage mata kayan jikinta tana zaune don ba musua tsakaninsu,a yadda taga mayen sonta cikin idanun abdallah zatayi matuqar qonashi a wanann lokaci idan tayi masa musu,da undeies kadai ya barta kana ya shige bandaki yayi nashi wankan ya fito bayan ya hada mata ruwan,kafin ta fito har ya zura kayan baccinsa ya saka 'yar hularnan tashi ka fiya naci fara ya nutsu saman abun salla,gefe taga nata kayan bacci,sai da ta qare musu kallo tanayi tana satar kallon abdallah dake salla,babu yadda zatayi haka ta juya ta sanyosu,gaba daya bata da maraba da babu dadinta daya akwai babban hijabi dogo a gun shita zura ta koma gefan gadon ta zauna,yayi sallama kana ya mata izini ta taso suyi sallah,raka'a biyu suka gabatar,addu'a mai tsaho suka yi ta neman alkhairai da samun zaman lafiya da haduwar kai a tsakaninsu sannan ya waiwayo ya kama kanta ya karanto addu'ar da annabin rahama ya koyar da mu
'' *Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi,wa a uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi*'',da salatin annabi ya rufe musu suka shafe tare
idanunsa cikin nata wanda a yanzu fargabarta ke dada yawa,girarsa ya daga yana murmushi
''wai duka tsoron nan na meye ne?''cikin nuna dakiya ta noqe kafada
''wanne tsoro?''
''gashinan ina ganinshi cikin idanunki?,kada kice a'a maryam,ina iya karanta abinda ke zuciyarki kai tsaye ta cikin idanunki,ko kin mance zuciyarmu guda ce?''
murmushi tayi cikin son nuna dakiya da jarumta amma sai ta sake ce masa
''ni tsoron me zanji''
tafa hannunshi yayi sau uku yace
''good girl,naji dadin samunki jaruma,kinsan kuwa irinki,nake so saboda irinkin ne kawai zasu iya jurata,ko da yake....nafa gasgata zancanki,kefa kince yadda kike kallon mace yar uwarki haka kike kallon *abdallah* kinga kenan ya kamata yau mu gane hakan ne ko ba hakan ba,uhmmm....are u ready?''
ta tuna sanda ta gaya mishi hakan cikin jirgi,take sai idanu suka raina fata,qwalla ta tarar mata,tana tsoron kada ya mata mugunta fa,cikin shagwababbiyar murya irinta me sonyin kuka tace
''kaima ba ka tsokane ni bane a lokacin?''dariya ya mata
''wasa nake miki matsoraciya,kwantar da hankalinki,babu abinda abdallah zai miki kinji,bacci zamuyi dukkan mu a gajiye muke,koke baki gaji ba ayi miki?''wata iriyar kunya ta dirar mata sai ta cure guru guda ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana dariya qasa qasa,waishi abdallah wanne irin dan kai tsaye ne?''na gaji,na fika ma gajiya''kai yake gyadawa yana sake gano yarinta quruciya da rashin wayonta
''to kin gani,so ki saki jikinki kinji,ni yayanki ne ko?''da sauri ta gyada kai kuma taji nutsuwa ta saukar mata,umartarta yayi ta samo musu plate da cups a kitchen
da hijabin jikinta ta miqe har ta soma tafiya ya kirata ta dawo,hannu ya miqa mata kana yace
''ciro min hijabina dama aro na baki ai''
sai ta dan zare ido
''amma fa jikina...''
ya katseta ta hanyar dora yatsanshi kan lips dinshi yace
''shshshsh,i know....haka nakeson ganinki,kin mance ba musu?,idan kika qi kuma to yau....''bata ma barshi ya qarasa ba ta zareshi ta miqa masa ya amsa idonsa akanta a haka ta fice zuwa kitchen din ya mata rakiyar idanu
wayon da ya mata yasa ta dan saki jikinta kadan taci naman da dan drinks,sai da ya tabbatar ta kwanta yaja mata bargo har zuwa kafadunta kana ya sunkuya ya sumbaci goshinta
''kiyi bacci baby,kina tare da ni''a hankali ta gyada kanta kana ta lumshe idanunta,shi ya tattara kayan da sukayi amfani da shi duka ya fidda zuwa kitchen
A qalla mintina talatin yayi kafin dawowarsa dakin,ya shigo ya rufe qofar da bismillah sannan ya isa ga makunnin qwan dakin ya maida hasken zuwa kala mai duhuwa ta bacci,tun dazun idonta biyu tadai rufe idin ne kawai amma fargaba ce fal ranta,tana jinsa ya gama tofa addu'ar bacci ya shafe jikinsa da ita,ya karanta mata itama ya soma shafa mata
zarcewan da ya soma yi shi ya sanyata bude idanunta ta riqe hannayensa duka,cikin rawar murya tace
''kayi alqawari fa....''
''baby bazan iya cikawa ba kimin afuwa''ya bata amsa
''amma....''hade bakinsa yayi da nata wanda hakan ya hana mata damar qarasa abinda take ahirin fada din
Ya kusa minti goma bakinsa kan kunnenta yana gaya mata wasu kalamai da suja kashe mata jiki gaba daya shi kuma ya samu daman aika mata da saqonni kala daban daban masu dauke duk wani tsoro da fargaba,cikin shu'umancinsa ya mantar da ita duk wani tsoro da wata fargaba,sai da ya mata jagoraxa duniya ta daban wadda ko cikin mafarki bata taba shiga makamanciyarta ba sannan ya fito mata da muradinsa muraran,sai a lokacin ta gane lallai wayo abdallah kawai ya mata,kuma a lokacin ta raina duk wani wayo nata,koma mata yayi tamkar mahaukacin zaki da yunwa ta koroshi ya fito farautar abinci,ba qaramin tsorata tayi ba,ya koma mata gaba daya kurma bebe kuma makaho,bai sauraran komai sai abinda yasa a gaba,cikin zafin nama yake fidda zazzafar soyayyarta data jima danqare cikin zuciya da gangar jikinsa
Bai ankara da barnar da ya tafka ba sai bayan shudewar awanni kusan shida,kuka take sosai idanun nata sun gama zama gauta saboda ja,sosai suka kumbura kamar an hura su,duk yadda yaso ta tsaya tsaiwar ta gagareta,dole ya maidata ya kwantar,tausayinta ya ratsashi,ta ya akayi ya yiwa maryamunsa irin wannan barnar?,shi kansa bai sani ba baisan lokacin da ya aikata ba,kawai sai ya koma saman gadon ya fara qoqarin janta jikinsa,a tsorace take da shi sosai saboda haka runtse idonta tayi sosai ta qanqame jikinta guri guda duk da ciwon da jikinta yake mata,bata so ya ko taba ta,gani take tsabar mugunta ce yana sane ya mata hakan bayan ya mata alqawarin babu abinda zai mata,wanne irin roqo da magiya ne bata masa ba amma yayi banza da ita,shi kurma ne ko makaho ne?
sarai ua fuskanci batason ya taba ta ne shi kuma kukan nata ne bayaso,cikin matuqar sanyin jiki da na murya tamkar ba abdallahn mami ba yace
''ba wani abu zan kuma miki ba maryam,kiyi haquri ki kwanta jikina,baki ganin yadda jikinki ke rawa kina buqatar taimako na''
cikin muryar kuka tace
''ko mutuwa ma nayi ba kai ka jawo min ba,ina zaman zama ne ashe baka da imani,so kake na mutu''duk da hankalinsa,a tashe yake sai da taso bashi dariya,ta yaya wannan abun zai kasheta,idan da yana kisa ai da mata da yawa sun mutu kenan,ganin ta kafe kai da fata bazai taimaka mata ba ya sanyashi shareta,ya sanyata cikin jikinsa ta dolenta,babau qarfin qwatar kai hakan ya sanyata taci gabq dq kukanta tana cewa baya sonta dama,bashi da bakin magana illa
''am sorry,am verry sorry,kiyi bacci idan yaso gobe saikimin duk hukuncin da ya dace da ni abdallah zai karba saboda laifi yayi miki,shi kansa yasan ya cancanci hukunci''
tun yana jin surutanta har yaji dif,ya keqa fuskarta data hada ja yaga bacci ne yayi awan gaba da ita,ajiyar zuciya ya kuma sake ya sake maidata jikinsa,sam bacci qauracewa idonsa yayi,tausayi qauna da soyyarta ke addabarsa,a hankali yaji jikinta ya fara daukar zafi da alamun zazzabi ne yake kamata,addu'a ya dinga yi,cikin zuciyarsa Allah ya kawar da zazzabin nan kada abun ya yiwa diya nan yawa,kafin asuba kuwa jikinta yayi rigif da zafi,har wani huci yake fitarwa
Cikin baccinta ta jita aruwan zafi yana ratsata,da azama ta bude kumburarrun idanunta ta saki qara data bashi tausayi,duk yadda yaso sata ciki ruwan dumin taqi shima kuma ya kasa saboda baison kukan da take,ahi ya gama shiryata tsaf kana ya bata guri don ta tubure masa sai wani dakin ya canza ya bar mata wannan
Qarfe bakwai ya sake leqota sai ua sameta kwance kan abun sallah bacci ya dauketa,a hankali ya lallaba ya dauketa ya maidata kan gadon ya fara qoqarin rabata da hijabin jikinta saboda zafin zazzabin dake tashi a jikinta,garin haka ta bude idonta sai ta tabe fuska zata saki wani kukan,da sauri ya kwantar da ita yana daga hannayenshi sama
''ni fa babu abinda zan miki,hijabin da kika bari a jikinki qara miki zafin zazzabin yake''
kanta ta cusa cikin filo tana fadin
''nidai ka fita wallahi''
tsam ya miqe ya fice daga dakin yana waiwayenta,ta sa gefan hijabinta tana share hawayen da yaqi tsaiwa,itakam da tasan haka ake shan wuya da ta gudu wlh,ashe duk wayo abdallahn yake mata don yaga ya girmeta
Har qarfe goma na safe yana fama da ita,taqi yarda ko dakin ya shigo bare ta sha tea din da ya dafa mata,don ba girki ya iya ba,da zarar ya shigo dakin zata fashe masa da kuka,duk yabi ya susuce,ga ciwo da alama tana jinsa sossi,ya kira raaliya bai sameta ba tilas ya kira baaba uwani,a falo ta taddashi kwance kan doguwar kujera rigingine,da sauri ya miqe yana tambayar baaba uwanin
''gaskiya ranka ya dade kuje asibiti,ta gayamin tana jin ciwo,sosai hakanan ba zata iya shiga ruwan zafin ba''shiru yayi donshi ba wani asibiti da ya sani idan ba mallakin maminshi ba,don tun yana yaro acan ake bashi duk wata kulawa saidai idan abbanshi ne yace a fiddashi waje,yana kunya kuma yajewa mami da maryam a hakan,dabara ta fado masa don haka da sauri ya yiwa baaba uwani godiya yasa driver din gidansu ya maidata
Sai da ya hada girar sama da ta qasa sannan ya shiga dakin,tana kwance don bata isa ta zauna ba,ganin fuskarsa a haka yasa bata yi masa boren ba,don ta manta rabin da ta ga fuskarsa a hakan,gaban ma'ajiyar kayanta ya isa ya ciro mata atamfa da hijabi,ganin yana niyyae sa mata su ns yasa ta saki shagwababben kukan nata sai ya kauda kai yana jin ciwon kukan har cikin ranshi ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa
''ya isa,idan zaki iya ki sauya da kanki yanzu na baku minti goma''ya fada yana ficewa a dakin
Cikar mintina goma ya dawo dakin har ta sauya din kuwa saidai zanin da bai dauru ba,ya dagata ya gayara mata daurin zanin kana ya dauketa cak ya fice da ita,Allah yasa babu kowa a gidan don har security dinshi ya basu hutun sati guda,a motar ya sakata ya dan kwantar mata da kujerar sanann ya dawo ya rufe ko ina
Sunan asibitin kawai data gani yasa ta tuna cewa asibitinsu ne,idonta cike da qwalla ta dubeshi yana gyara parking na motarsa a inda taga manyan likitoci ke parking kawai a gun
''amma ya za'ayi ka kawoni gun mami abdallah baka jin kunyarta ne?''sai da ya daidaitata ya kashe kana ya jingina jikinsa da makarin kujerar ya dubeta
''ba gun mami zan kaiki ba nima ina jin kunya ai dear,akwai doctor farida ita zara ganki kin gane?''limshe idonta kawai tayi ta kwantar da shi ba tare da ta amsa masa ba,sai taji hannunsa kan fuskarsa yana share mata hawayen
''bansan ganin hawayen nan mana maryam,ki zama jaruma kinji matata,ni da nakeson shekara iwar haka na kawoki kina naquda''ai batasan sanda ta bude idonta ta watsa masa harara ba,ana fama a yanzu ma ba'a warke ba yana mata zancan naquda,shi don ba jikinsa bane wato,dariya ua qyalqyale da ita kamar yasan me take rayawa cikin zuciyarta,bai sake cewa komai ba ya ciro wayarsa ya kira reception na asibitin yace a turo masa nurse din da take on duty
Cikin minti uku kacal ta iso sanye da fararen uniforam,matashiya ce yar kimanin shekaru talatin mai yawan fara'a,ta gaida maryam ta amsa mata cikin fara'ar yaqe tana satar kallin abdallah,ranshi a hade kamar bashi ya gama qyaqyata mata dariya ba yanxun,tambayarta yake doctor farida tazo?
''eh naga office dinta a bude duk da banga wucewarta ba amma nurse halima naga ta fara shigar da files''
''mami na fa''
''office dinta gaskiya a rufe yake''ya gyada kai kana yace
''ok,inason ki bawa nurse halima din wannan ta kaiwa doctor faridan yanzu zan shigo na gantq ni da madam''a ladabce ta amsa kana ta juya ta shige,ratar minti biyar ya bada ya fito daga mazauninsa ya rufe motar kana ya zagaya bangarenta,daukarta yayi da gaske tana masa mitar ya ajjiyeta kada ya jawo musu yan kallo
''idan daukar da na miki bata jawo mana yan kallo ba sauke kin da zanyi ya jawo mana tunda kona ajjiyekin ba iya tafiya yadda ya kamata zakiyi ba''ta yarda haka dinne don haka tayi luf ajikinsa idonta aruntse duk kunya ta gama kamata
Bai damu da jama'ar dake reception din ba kansa tsaye ya wuce office na doctor farida da ita,bayan ya sauketa a bakin qofar office din ya kama hannunta,ya tura qofar kana yayi sallama,ya juya yana maida rufin qofar ta dago kanta daga laluben takardun da takeyi,mami ce zaune kan kujerar zaman likitan,zame hannunta maryam tayi tana fatan ina ma zata iya gudu babu shakka da fellawa zatayi
fes ta gane kunya ke damunsu tunda taga highlight na problem dinsu a short note din da ya bada a kawowa doctor farida, don haka sai tayi mirsisi kamar bata sansu ba ta musu nuni da gurin zama
''bismillah''abdallah yayo gaba yayin da maryam cikin lallaba takunta ta biyo bayansa,mami ta dan bita da kallo cikin tausayawa amma afuskarta ba zaka gani ba idan baka lura ba sosai,sai da tayi yan rubuce rubucenta kana ta dago da kanta ta gyara zaman glass dinta
''uhmmm,meke damun patiente din?''sai aka rasa mai magana tsawon mintina,dariya ta dinga cin mami kamar ta fito ta dara ganin yadda sukayi tsilli tsilli maryam harta fara sharan hawaye
Abdallah ya miqe yana fadin''ummm...ina zuwa,bari naje na dawo doctor ta miki bayani''sai ta kuma hade rai
''c'mon dawo mara haquri kawai ina zaka,dora min ita saman can''ta nuna mishi wani dan gado da take duba marasa lafiya kana ta dake kamar ba ita tayi maganar ba taci gaba da rubuce rubucenta gami da dauke kanta cikin zuciyarta tana tausayin maryam tare da dariyar abdallah,tunda suke bata taba ganin bala 'yar iyar kunyarta cikin idanunshi ba irin wannan karon,sai da ya dorata kana ya taho gefanta ya tsaya
''mami,na dorata''
''doctor ce ba mami ba''ta fada cikin shan kunu,sai ya dan shafi gefan fuskarsa kana yace
''sorry......doctor''
allurai ta hada pain killer harda wadda zata sata bacci na yan lokuta kafin ta gama dubata ,don ta san da kunya musamman maryam dake da bala'in kunya,bai yiwuwa ta dubata a sake kuwa alhalin idonta biyu
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[5:58pm, 10/14/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣5⃣
*Daga abdullahi dan umar R.A.H.M yace:Manzan Allah S A W yace:((haqiqa mafi soyuwar sunaye acikin sunayenku a wajen Allah mai girma da daukaka sune ABDULLAHI DA ABDUR RAHMAN))*
✊🏽✊🏽✊🏽✊🏽✊🏽✊🏽✊🏽🙇🏽♀🙇🏽♀🙇🏽♀🙇🏽♀🙇🏽♀🙇🏽♀
💞💞💞💞💞💞💞
*cike da girmamawa mutuntawa da qauna tare da qasqantar da kai nake miqa wanna shafi a gareku*
*IBAADALLAH wato duk wani mai suna ABDALLAH*
_*musamman mahaifina,abin qaunata abin alfahari na,jigo na*_
*ALHJ ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*_haqiqa kai mahaifi ne daya tamkar da miliyan,mahaifine da samun kamarsa sai an tona,mahaifine daya da daya,mahaifi ne da babu kamarsa,Allah ya shige maka gaba,ya maka jagora cikin lamuranka,ya zama jinka ganinka,ya rabaka da sharrin mahassada magauta da maqiyanka,Allah ya cika maka burinka duniya da lahira,Allah qara maka lafiya da tsawon kwana mai amfani,ya cika rayuwarka da farinciki nutsuwa da kwanciyar hankali,yasa kayi kyakkyawan qarshe,babu shakka ka gama mana komai a rayuwa,addu'arka garemu na bin mu har kullum muna ganinta,Allah ya jiqan magabatanka ya maka jagoranci tare da dukkan nagartattun iyaye kamar KAI_*🙏🏽🙏🏽💖💘😍😘💝❣
Komawa tayi taci gaba da rubuce rubucenta kafin allurar tabi jikinta tabar abdallah nan a tsaye maryam a kwance ta nutse cikin kogin kunya,cikin mintina da basu wuce takwas zuwa goma ba baccin ya fara dibar maryam,babu bata lokaci lokaci kuwa yayi awan gaba da ita ta fara anccinta sadidan dama kuma ga baccin jiya data ci bashinsa bata yishi cikakke ba
Mami ta waiga taga ta fara nisa a baccin,sai ta ajjiye biron hannunta,ta jawo wayar girke ta tafi da gidanka ta danna wasu lambobi,bayan an daga ta lissafa kayan aikin da take da buqata,ba acika minti goma ba kuwa sai ga nurse ikilima wadda ya baiwa short note ta kaiwa doctor farida,ya faki idon mami ya watsa mata harara sai ta sadda kanta don batasan laifin me tayi ba,amsar kayan mamin tayi ta nufi drower din kusa da gadon ta ajjiye saita waiwayo ta dubi nurse iklima data ci gaba da tsaiwa
''da wani abun ne?''mamin ta tambayeta tana saka hands glove,da sauri ta girgiza kai
''a'ah,ban sani bane madam mo kina buqata ta akusa''kai ta girgizw mata tana fadin
''a'ah jeki abinki,personal issue ne''
''ok,to''ta amsa mata ta fice kamar zatayi tuntube saboda yadda abdallah ke zabga mata harara,bayanta mami tabi ta sakawa office din key kana ta dawo ta soma bincikar maryam data dade duniyar bacci
Sosai mamin ta tausaya mata don ta lura ba qaramar barna yaron nata yayi ba,har sai da ta daga kai ta dubeshi don ta sake tabbatarwa abdallahn ta ne?,suna hada ido ya sunkuyar da kanshi wata kunya na jibgarsa ta ko ina,sai ua sake miqewa zai fice don ya rasa inda zai tsoma ransa
''kada ka budewa mutane qofa malam''haka kawai tace masa cikim dakiya,dole ya dawo sum sum ya zauna,ta fidda kayan yin dinki don dama ta tsammaci haka shi yasa ta bada order din a hado mata da su,shi kansa sau dqya ya kalli yadda ake dinkin ya dauke kan ya dauke kansa taigar jikinsa na tashi cike da tausayi,sannu a hankali cike da qwarewa ta gama dinkin tsaf,ta jawo paper ta rubuta sunan magunguna kana ta zare safar hannunta ta koma kan kujerarta ta zauna tana kallon abdallahn
''duk yadda zakaji kunyar maminka dai baka da kamarta,yanzu ba don Allah ysa mun hadu da nurse halima ba na amshi takardar nayi musanyan office gun farida zaka kai case din?,kana da tabbas bakinta zaya yi ahiru kan abinda taga kayi,this is d lasr warning kada ka sake irin wanann ganganci,ni mamarku ce abokiyar sirrinku ka fahimta?''kansa a qasa ya amsa mata yana sake qaunar mamin nasa,batason kowa ya zama mai jibantar lamuransu idan ba ita ba,shikam Allah ya bashi uwa ta kere sa'a
Gyaran murya ta sake yi sai da gabansa ya fadi
''and then.....''sai kuna ta danyi jim shima yayi shiru yana jiran cewarta
''is ok''kawai tace tana maida glass din idonta,takardar hannunshi ta miqa masa
''ka fita wani clinic ka siyo wadan nan magungunan,kana ka biya reception ka biya kudin ganin likita''sai da ya dago ya dubeta,kudin ganin likita kuma,shi tunda yake bai taba jin koda wasa ance ya biya din ba,dubanshi tayi ganin yayi shiru
''yadai?,ko ka taba ganin ana aiki kyauta a sibitin private,likita doctor farida kazo gani kuma na maka aikinka kaga you must to pay''sai ya sosa kai ya matsa daga inda yake din yana cewa
''ni ban taho da kudi ba doctor,atm ne ajiki na''
gira ta daga sanann tace
''ok,ai suna da p.o.s ka basu su cira,ko da yake akwai kudi hannuna bari na ranta maka ka biyani''ta fada tana jawo hadaddiyar hand bag dinta dake saman table din too match da kayan jikinta ta zaro sabbin yan dubu dubu ta miqa masa,hannu biyu yasa ya amsa kana yace
''na gode Allah ya bani ikon biya''saura kadan ta fashe da dariya ganin yadda ya wani koma duka kalar tausayi amma sai ta dake,tana son koya masa lesson ne,haka ya juya ya fita ita kuma ta saka dan labulen nan na da ake rufe mara lafiya mai tayoyi ta kare inda maryam ke kwance taci gaba da duba patient
Har qarfe biyu maryam na baccinta shi kuma mami ta shanyashi a reception yana jira,sai da ta gama da dukkan patient din nata kana ta tura wata nurse ta kirashi,kan abun sallah ya tadda mamin zaune da alama sallar azahar ta idar
''kayi salla ne?''ta tambayeshi
''ah....ina shirin...ina shirin zuwa nayi kika kirani amma bari naje nayi sai ma dawo ko?''ya fada a daburce,tsakanin uwa da da sai Allah,ganin yadda yau ya maidata kamar ba maminsa ba yasa ta dan sassauta masa
''da toilet anan shiga kayi alwalar ga abun sallah kazo kayi''
''to''yace kana ya nufi toilet din yana satar kallon maryam dake bacci har yanzu
Satar dubanshi take yana sallar,gaskiya ne maganar hausawa dake cewa da sannu wataran yaro zai zama ango,yau abdallahn ta ne ya zama ango,turo qofar dakin akayi wani matashine baqi sanye da unifaorm mai dauke da tambarin sunan asibitin ajiki,hannunshi biyu riqe da kwanduna yayi sallama mamin ta amsa tana fadin
''bashir,har an kawo''
''eh hajiya''ya fada yana dire su a gabanta,ta jawo,kwandon tana fadin
''sannun baaba uwani kaima sannunka''ya rusuna cikin girmamawa ya amsa kana ya juya zai fice wata matashiya ta shigo itama dauke da leda baqa,ita dinma fuskarra dauke da murmushi da girmamawa ta ajjiye ledan tana fadin
''mami gashi''ta ciro canjin tana miqa mata
''a'ah zainaba riqe kyasha ruwa''murmushi tayi tace ''na gode''
''a'ah nice da godiya''ta ja musu qofar ta fice mami ta janyo ledar tana dubawa,abdallah ya dan saci kallon mamin
''wo...mami...mami,wato kudin da tasa ya kai reception na ganin likita ashe sawa tayi akaje aka siyo kayan amfani da su,irinsu tea flask,rigar sawa daya cup plate sabulun wanka turare da silifas sai abin sallah duka daidai,saidai baisan me zatayi da su ba,tunanin da ya fado masa ya sanyashi yin addu'ar Allah yasa ba kwantar da su zara ce zata yi ba
motsin maryam ya ja hankalinsu,sai tayi saurin maida idonta ra rufe tana fadin dama bata farka ba cikin zuciyarta,mamin ta qaraso tana mata sannu tare da tambayarta akwai wani pain da take ji,idanunta a rufe take fadin a'ah
''to sauko a hankali ki je toilet ki wanke bakinki kiyi alwala kizo kiyi sallah azahar tayi har taso to gota,kiyi a hankali fa banda gaggawa da dinki jikinki kada ki ja masa matsala''
''wayyo Allah na,abdallah ka gama da ni,yanzu mami ce tamin dinki ma''take fada azuciyarta,mamin ta gama karantarta don haka tace
''ki saki jikinki maryamu,ko baki yarda ni maminki bace?,tamkar nina haifeki kinji''kai ta gyada sannan mamin ta kamata ta taimaka mata ta sauka
a zaune tayi sallar gogan sai kallonta yake,mamin ta ganshi amma sai ta dauke kai ta jawo plate guda daya babba ta zuba musu abincin,shinka fa ne da miyar kifi da salad da tumatir da cocumber,saukowa tayi qasan gun bayan ta shimfida sabuwar abun sallar ta saka hannu ta fara ci bayan tace musu''bismillah''
tsuru maryam tayi abu goma da ashirin itamakam bata iya cin abinci tare da mamin abdallag kuwa tuni ya tsoma hannunshi dama shi sabonshi ne tare suke ci,ga kuma uwar yunwa dake addabarsa dama tunda baici abincin safe ba,rabonsa da abinci tun jiya da daddare,ganin har sun fara ci bata sanya hannu ba yasa mamin yi mata magana
''saka hannu mana 'yata,baki ga abdallah bane''kanta aduqe ta saka hannun suka fara cin abincin gwanin sha'awa,da wanann damar tayi amfani cikin hikima da hila take dada jan hankalinsu kan zaman aure
Sai da suka qare tas tasa abdallah ya gyara gun,nurse ta kira tace ta saka cleaners su gyara aminiyy one zata ajjiye oatient,ta juya ta fice bayan ta amsa mata,sai abdallah ya zura mata ido yana neman ba'asi
''daina kallo na haka nan,anan zan ajjiyeta sai gobe zaku koma gida''
''ni wallahi dama sati biyu kika ce mami''maryam ta fada azuciyarta,fuskarsa ta dan sauya tana kure da shi
''yes,ko kuma in dauketa mu tafi gida bayan one week ta kom''da sauri ya saki fuskarsa tare da fadin ''a'ah'' cikin zuciyarsa yace''da asara ai gwara gidadanci''tilas ya sawa zuciyarsa haquri yana ji yana gani
Sai bayan isha'i mamin ta barosu ta koma gida tace zata turo baaba uwani,bai ce wa mamin komai ba don yasan yanzun da yayi magana cibi zai zama qari,qari ya zama qaabaaba amma ya riga ya qudurce babu wani baaba uwani da zata kwana masa da mata
kiransa tayi a waya bayan ta fita din,a bakin mota ya taddata tana tsaye bayan ta bude side din da zata shiga,fuska a hade tace da shi
''abdallah....ka shiga taitayinka kana jina ko?,banason ci da zuci da rashin hankali,ba qaramin cutar musu da yarinya kayi ba,bana sin rashin haquri makamancin haka ya sake faruwa kaji na gaya maka,idan na haka ba matakin da zan dauka maka bazai ma dadi ba''shidai kansa na qasa har takammala ya shiga bata haquri,bata ce komai ba ta shige motarta ya fufe mata yana fadin''a sauka lafiya''bata tnaka masa ba ta kunna motarta tayi gaba,da sassarfa ya juya ya koma cikin dakin don ya qagu yaji dumin maryamansa,wuni guda yana ganin yayi qoqari
ya iso gareta inda take kwance kan gadon dakin,qafafunsa na qasa daga cikinsa zuwa kansa yana saman ta ya daudaitafuskarsa da tata
''kin ga abinda kika jawo mana ko?,haka kawai daga fara amarci zamu bige da jinya a asibiti?''
fuska ta bata tana zumburo baki
''na jawo mana?,bama kai ka jawo min ba,duka ka gama bami kunya gun mamin haka kurum''
Dariya ya qyalqyale mata da ita kana ya kama lebanta da ya burgeshi ya dan ciza a tausashe
''bake kika ce kamar mace yar uwarki kike kallo na ba,i hope kin banbance tsakanin aya da tsakuwa ko?,kin yarda abdallah ba rago bane,a karo na farko yasa an baki gado?''
kunya ta kamata ta tura kanta qasan kanshi,har yau tana iya tuna lokacin data fadi maganar,a lokacin faduwar gaba take ji da bugun zuciya sosai tattare da ita,amma sam taqi kawowa zuciyarta abdallah take so,yasan ya sata jin kunya don haka ya dora da fadin yana ya jujjuya kansa
''nima nasha kunya maryam na fiki shan kunya ma,gwara ke bacci kike abinki,ni fa har fada aka yimin''dariya ta kamata ya ja hancinta yana fadin
''ni kike ma dariya ko,zamu hadu ne,an shiga haqqina ma baki damu ba ko,yau fa ko dumin jikinki banji ba gaba daya dear na''ya fada ya na lalubarta
ganin abinda yake yi ne ya sanya ta cikin shagwaba tace
''dinkina fa zai farke''zaro ido yayi kana yq daga ta don yasan matuqar ya farke din shi da mami Allah ne zai rabasu,kujera ya janyo ya dawo gaban gadon kamar zai shige cikinta hannunta cikin nasa ya dora kansa saman gadon suna fuskantar juna
Sauya salon muryarshi yayi cikin rada rada yace''yanzu ya za'ayi baby,nifa gaskiya mayen abun nan ne,yanzu ma a kame nake''ya qarashe maganar yana wani kashe mata ido,sai ta bata rai cike da tsoro
''dole ki zama jaruma baby,idan kuma kinsan ba zaki iya ba ki gayan tun wuri na fara neman aure''ya fada cikin salon jan fada,ai kam sai ta fasge masa da kukan shawagwaba,shi kuma ya lalace gurin rarrashi daganan ya samu ya rage zafi abinsa,bata hanashi wannan ba kam,saboda ta fuskanci cikin sahun da yake a amzaje,idan ta hanashin ba shakka ta shiga haqqinsa sosai tunda jinya takeyi ba zata iya masa abinda ya wuce hakan ba
Allah ya rufa asiri yana shiga bayi baaba uwani ta shigo,nan ta zauna tana yiwa maryam sannu da jiki,cike da kunya take amsa mata,lokacin da ya fito sannu da zuwa kawai ya yiwa baaba uwanin ya fice bayan ya jefi sahibar tasa da wani kallo mai cike da qauna da bege,baifi minti goma da fitar tasa ba siga wata nurse ta shigo,tace baaba uwani ta taso a nuna mata dakinta inda zata kwana,nan din akwai mai kwana da madam maryam din,bata musa ba ta bita don ba sanin tsarin asibitin tayi ba batasan duk plan din abdallah bane,sai data fice kana ya dawo dakin harda maida key kana ya shigo ya fidda kayan jikinsa ya bar singlet da three quater ya qarasa gaban plasma din dake jkkin bangovya dauki remote na reciever din,kansa tsaye ya dale gadon da maryam din ke kai a kwance bayan ya bata magungunanta ta sha,jikinsa ya janyota ya rungumeta tsam bayan ya sauya musu tasha zuwa mbc bollywood cikin sa'a suna film din geet,lumshe idonta tayi ta sake narkewa cikin jikinsa,don tana bala'in son film din,hakan ya qara mata shauqi ya kuma hanata cewa abdallah komai tana jinsa yana ta rage zafinsa a zafafe kamar zai hadiyeta,saidai data fuskanci zai sauya akala zata dakatar da shi,shikam ko hakan ma ya masa,ya fi masa ace baya kusa da ita
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
qarfe goma mami ta iso ta sallamesu bayan ta sake dubawa ta tabbatar da komai normal,gargadi kam abdallah yasha shi,har ya kasa daurewa ya dafe kansa qasa qasa ''abdallah ka shiga uku,Allah ne kadai gatanka''
''baka shiga uku ba sai ka sake ganganci na dauketa gaba daya lokacin zaka tabbatar ka shiga tara ma ba uku ba''bai zaton zata ji ba din haka ya fece ya bar musu dakin
Da wannan dama abdallah yayi amfani ya shirya tafiye tafiyensa don gyara duk wata harka ta kasuwancinsa da ta samu baraka kamar kamfanoninsa da sauransu,wadda su nene da ahalinta suka so yin tsallen badake a kanta,kwana goma ya tsara zaiyi,din baijin zai iya zama guri guda da maryam bai tsallake sharadin mami ba,ya tabbata kafin dawowarsa aidai ra warke,idaan yaso yaci duniyarsa da tsinke son ranshi,don da baaba uwani ra hadosu saboda ta kula da maryam din ta warke sarai kamar wata me jego inji abdallah
Ana jibi zai tafi yayi niyyar gaya mata,ita ke kawo masa abinci har sashensa,kamar ko wanne lokaci taci kwalliyarta tsaf cikin atamfa fitted gown,babu wata sura tata da bata bayyana ba,qamshin ta kawai ya isa ya daga maka hankali,yana cin abincin ne kawai amma duka hankalinsa na gareta,daga qarshe ma fita yayi daga kansa abinci ya tureshi ya miqa mata hannu,take ta taso cikin taku na daukar hankali ta qaraso gareshi,kan cinyarsa yayi mata masauki kana ya mannata da jikinsa ya saba aikin nasa na rage zafi,luf tayi tana karbar saqonnin da duk yake aika mata,cikin salo na jan magana yace
''ke kanki kina karbar saqonni na,amma yanzu da zance zamu fara lacture saikiyi tawaye''
aikam tuni ta zaro ido don har yanzu bata manta wuyar baya ba,narkewa tayi ta marairaice masa,cikin wata shishshiqa ta kissa tace masa
''amma ka sani fa my ban warke ba''
''i know,shi yasa nace gwara na danyi nesa duk da zuciya bafa so''sai tayi hanzarin juyowa ta dubeshi
''kayi nesa kuma,kamar yaya?''
girarsa ya dage mata ya kashe mata ido daya
''zanyi tafiya inje in gyara kamfanoni na da aka so durqusarwa,kwana goma in sha Allahu na kammala,kafin na dawo nasan kin warke kinga sai shiga aji da daukar lacture ko?''
Duk da ya bata kunya amma sai da ta sa masa kukan shagwaba''amma daga yin sati daya sai kace zakayi tafiya?kasan bazan juri rashin ganinka ba har kwana gona?.....nidai gaskiya.....gaskiya.....''ido ya lumshe shagwabarta na sake rudashi ne sosai
''nima haka my dear na,nasan halina,indai naci gaba da zama din bazan iya jurewa ba,idan kuma kin amince muci gaba da darasi to''sai kuma tayi luf bayan ta noqe kafada,dariya yasa mata yana fadin
''you see''
hannunta ya kama ya dora a qirjinsa daidai zuciyarsa yace
''kada diya na ta ta damu,kin manta zuciyarmu guda daya ce,nisan dake tsakaninmu ne kadai zai raba mu amma muna tare ne,koda mutuwa dayan yayi to muna tare,after all ma gwara nayi tafiyan tun yanzu,saboda idan aka wuce yanzu gaskiya bazan iya yinta ba,kinsan ni ba ragon malami bane,dali barce dai na samu raguwa''kai abdallah na kasheta da salonsa,sai ta kasa ce masa komai,ranar bara baro bangaren ba sai kusan sha daya
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Washegari sai ganin lubabatu tayi yasa andauko mata ita,tayi murna kam qwarai duk da cike take da kewar tafiyar tasa,mami ma da ya gaya mata cewa tayi idan maryam ta yarje masa yaje shikenan,don ta riga da ta sani tafiyar tasa ce kawai zata sa yabar mata maryam din ta warke yadda ya kamata
Kuka take sosai sai taji zuciyarta tayi matuqar quntata batason tafiyar tashi,bata taba sanin rabuwa da masoyi haka yake da daci ba sai yai,ashe haka matan da mazansu ke tafiye tafiye suje ji,tun hisham na matsa masa horn har ya gaji ya daina don ya bararraje a gabanta yanata faman aikin lallashi,so yaje yaga ba hawaye ko daya cikin idanunta amma hakan ya gagara,daga qarshe ya dubeta cikin karaya
''anya dear na ba haqura zanyi da tafiyar nan ba''da sauri ta girgiza kai
''nikam gwara kaje,sai gaba kuma mun sake watanni kace zaka je?,tab,aikam,nazan yarda ba''dariya taso bashi,sai ya hade hannayensu
''is ok,indai kina son na tafi to ki share hawayen kinji''da kai ta amsa masa ta fara sharewar yana tayata,sai da yaga fuskar tata tayi fes sanann ya ciro mata hijabi ya saka mata,ya kama hannunta suka sauko,ya dubi fuskarta yadda tasha kuka sai yayi sha'awar tsokanarata
''ashe maryama ta abdallah ce,ashe maryama na mutuwar son abdallah,ashe rabuwa da masoyi da daci''yayi maganar cikin salo na waqa,sai ta fara diddira qafafunta cikin shagwaba,baya yadan ja kana ya kama baki
''iyeeee,naga fa alamar yammata kin warke,irin wannan tsalle haka,kodai na fasa tafiyar nan na zauna aci gaba da daukan darasi mu tsinki fure sosai''ba qaramar dariya ya bata ba,abdallah badai iya tsoka na ba idan yaso,sai ta fada jikinsa cikin dariya,shima baiyi qasa a gwiwa ba ya tarbeta ya rungume abarsa tsam yana jin duminta da qamshin azababben turarenta,sai da ya gama bata hot kisses sannan suka fito
Tana kan kafadarsa daya kafadar tata rataye da briefcase dinshi haka suka jero har harabar gidan,bai damu da securities dinshi ko hisham dake tsaye agun ba ya sake qwaqume abarshi,duk da kunyar da take ji amma ya hanata motsawa a haka har suka isa motar da zasu tafi din,ko kallo hisham dake waje a tsaye shida lubabatu yana zabga masa harara bai isheshi ba,sake janyita yayi ta mata kiss a kumatu da goshinta,yasa dan yatsansa yana dauke mata hawayen da ya fara silalo mata
''no baby,no,hawayenki karyamin duk wani qwarin gwiwa yake,ki bar kukan nan haka,bari na gaya miki abunda zaki min qwaya dayq da zaisa na kuma gamsuwa lallai kina sona kuma kinyi kewata bayan tafiyata''bakinsa ya sanya a kunnenta cikin kashe murya da iya salon sace zuciya da tada tsohon miki yace
''kimin wani kyakkyawan tanadi yadda zamu bargaje amarcinmu sosai bayan dawowata,idan so samu ne ma mami taga alama,ki mata guzurin jika''wayyo kunya kashe maryam,sai ta maida kanta kafadarsa tana dariya qasa qasa
''zan baka mamaki kuwa,kasha kuruminka''itama ta maida masa cikin nata salon
'ido ya dan zaro yana murmushi
''Allah tawan,kai wlh ke ta musamman ce dear na''dariya suka saki tare a hankali
''kaga malam,idan an fasa tafiyar nan ne ka gaya min,don me zaka shanya mutane kuzo ku bude wa mutane filin soyayya''kunu abdallah ya dan sha
''kaga malam,ya zaka shiga haqqin masoya,miji da mata fa sai Allah,musamman ma ni da maryam kafi kowa sanin cewa mu na musamman ne,don haka ka shafa mana lafiya tsohon gauro kawai''dariya hisham ya fashe da ita
''dududu yaushe Allah ya 'yantaka,naga tare muke fama da gaurancinmu,har gwara ni na fika qarfin zuciya ma.....''
''ko yanzu Allah ya 'yantani dai na fika''yayi sautin katseshi don kada ya masa tonon silili yana yafito lubabatu dake can gefe tana kallonsu tana murmushi
''amana zan danqa miki,ki kularmin davrayuwata,idan har kika bata kulawa yadda ya dace ni kadai nasan tukuicin da zan miki,zan baki wannan tsohon gauron ki taimaki rayuwarshi''dukkansu sai da abdallahn ya basu dariya,itakam lubabatu hannu tasa ta rufe fuskarta
Wani dogon hot kiss ya bata wanda sai da yasa hisham da lubabatu dauke kan don kunya kana ya kama hannunta yana fadin
''ki kula min da kanki,zanyi kewarki fiye da kike tsammni ko hasashe,kana ki cikamin alqawari na idan na dawo''kai take daga masa kafin daga bisani itama ta juya tafin hannunshi ta sumbata,ita da lubabatun na tsaye har motocin suka kammala ficewa daga gidan security ya maida get din ya rufe.
. By
*mrs muhammad ce*👑 BH
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣6⃣
*An karbo daga abu hurairah,R.A yace: Manzan Allah S A W yace:((MUSULMI DAN UWAN MUSULMI NE,KADA YA HA'INCESHI,KADA YA MASA QARYA,KADA YA TABAR DA SHI,KADA YA WULAQANTASHI,KADA YA ZALUNCESHI,KADA YA TOZARTASHI,KOWANNE MUSULMI A KAN DAN UWANSA HARAMUN NE(YA TABA)MUTUNCINSA,DA DUKIYARSA,DA JININSA,TSORON ALLAH ANAN YAKE,(SAI ANNABIN RAHAMA YAYI NUNI DA QIRJINSA SAU UKU)YA ISHI MUTUM SHARRI YA WULAQANTA DAN UWANSA MUSULMI*
_Allah ka tsaremu,Allah ka tsaremu,Allah ka tsaremu 🙏🏽_
_qarin haske_
_ANTY SIS ta janyo hankali na game da wani abu cikin page din baya,wato da yawa makaranta sun dauka ina nufin sixs hours abdallah yayi a first night dinsu,ba haka nake nufi ba,ina nufin after sixs hours ya fahimci barnar da yayi,abinda nake nufi kenan,don bazaiyiwu mutum yayi sixs hours din yana abu daya ba kamar yadda anty sis kika ce,hakan yake,GODIYA NAKE_
Tana zaune saman yagalalliyar daddumarta bayan ta gama karanta fatiharta da suka yi alqawarin karantawa malam na hayi duk salla ita da habiba,shiru tayi tana nazarin rayuwa,wato duk lokacin da Allah ya maka baiwa kaqi gani to idan ya tashi baka zato ba bakayi aune ba zai rabaka da ita rabuwa ta har *abada*,ba duka mutum bane yake wasa da damarsa ba karon farko bayan Allah qwace ya sake dawo masa da ita
bankado jibgegen labulen ta,da akayi ne ya sata dagowa da sauri,habiba ce tsaye tana haki tana fadin
''taso zahariyya,taso,ina zaton yau Allah ya karbi addu'armu ne,zoki ga malam''ko nauyin jikinta bata ji haka tayi wuf ta miqe suka fice a sukwane,kai tsaye dakin nan nasa mai azabar kyau da shi kadai ke shiga suka kutsa,kusan dukka mata da yaran na tsaye ne daga waje suna leqensa,gaba daya an sauya masa kammanni ya koma wani abun tsoro,kwananshi dama bakwai baida lafiya a cikin dakin,sai wani fisge fisge yake da surutai marasa kan gado da ma'ana,jini ne kawai ke fita daga bakinsa,duk shimfidar dakin ya tuttujeta saboda azabar da yake dandana,ya kusa aqalla awa guda cikin wannan halin babu wanda yayi yunqurin taimaka masa don gaba daya sun kasa motsawa kamar wadanda aka kafe a gun,abu na qarshe da yayi shine wata gigitacciyar qara da qwala wadda dukka gonakin dake maqotaka da su saida suka amsa kana kuma jikinsa ya saki baki daya bisa dukkan alamu ya wuce gidan gaskiya(haka mala'iku ke tsiga suke fisgar ran fasiqi kafiri wanda ta bijirewa umarnin Allah,haka Allah ya gaya mana cikin qur'aninsa,sabanin mumini mai biyayya wa Allah da manzansa mala'iku kan cire ransa ne cikin nishadi da tausasawa suna zara suna barinsa yana hutawa har su kammala cirewa,Allah ka sanya mu cikin muminan bayinka),mutuwa abace maisa kashe jiki da zuciya hakan ne yasa kowanne cikinsu jikinsa yayi matuqar yin sanyi suka hau kallon kallo sannan suka fara komawa tsakar gida suna shawara ya za'ayi da gawar tunda tuni suka amince cewa ya riga da ya mutu
wasu cikin yaransa masu wayon ne wadanda baiwa kafi ba suka haura can hayinsu don nemo jama'a don su kam,basu da maqota daga su sai ginakin dake kusa da su,kimanin awa guda sai gasu sun dawo jiki a sabule don ko kare bai yarda ya biyosu ba balle bil'adam,qarshe ma jama'ar qauyen hayin nasu bigewa sukayi da farinciki kowanne gida suna taya junansu sam barka na mutuwarsa,don ba qaramin tsanarsa sukayi ba,dalili kenan da yasa ya baro cikinsu ya dawo hayin ruwa
Kafin cikar awa uku da mutuwarsa saiga gawa ta fara kumbura tana fidda wari mai azabar doyi da wasu irin tsutsotsi,hakan ya sanya kowa ya fara hada karonsa dom gujewa muhallin nasa,tawagarsu guda suka yo qofar gida kowacce cike da zulumin kada fa su rasa hanya kamar kowanne lokacin,saidai cikin ikon Allah yau kowa idonsa abude yake tar,dukkan wani duhu ya yaye,hijabin da malam din ya sanya musu ya kau,kuka zahariyya ta fashe da shi zuciyarta fal da tsoron Allah tausayin kansu da kuma tausayim taragutsan yaran da malam din ya bari,yarane da basu ji ba basu gani ba,son zuciya irin na iyauensu ya jawo musu fitowa ta rubabbe kuma rusashshen taatso,kowacce iriyar rayuwa zasuyi a gaba oho?,ta dubi iyayen kana ta tsaya a gabansu tace
''ku dakata,ina da magana da ku''kowacce kuwa sai tayi tsam ruqe da hannun yaranta tana kallonta
''magana ce zan muku kan wadannann yaran wadanda son zuciya da bijeriwa Allah yasa muka sama musu uba wanda bai dace da su ba,wadan nan yaran haqiqa jarabta ce Allah ya hadamu da ita ko ince hukunci ne tun a gidan duniya da Allah yayi mana kan bijirewa umarninsa da mukayi,hanya daya ya kamata mubi wadda zamu nunawa Allah mun karbi jarrabawarsa shine mu ruqe 'ya'yan,muyi musu kyakkyawar tarbiyya,don Allah don annabi kada mu barsu su lalace su zama kamar yadda ubansu yake,kada mu bari tarbiyyarsu ta gurbace kamar yadda ta ubansu take,kada mu bari su zama guba cikin al'umma,don Allah muyi iya yinmu kan rayuwarsu,yadda malam ya mutu kawai izina ce a garemu baki daya,kada mu bari wataran su zama silar da za'a la'ancesu a la'ance mu koda ta Allah ta kasance akanmu''
babu wadda jikinta bai mutu ba,haka suka mata godiya kowacce idanunta shabe ahabe da hawaye zuciyarta cike fal da nadama da dana sani tana kada kan yayanta saboda yadda warin cikin gidan ke fitowa waje tana kama hanyarta
A haka duka suka fashe saura ita da habiba,hannunta habiba ta kama tana fadin
''mu tafi zahariyya,nikam sai yadda Allah yayi dani,bani da kudin da zasu isheni naje har abuja,amma zan fara da zuwa katsina inda dangina suke,daga can nasan zasu maida ni gida''haka suka kama hanya suna tafe suna kuka,idan ka,gansu sai ka tsammaci,mahaukatane suka gudo daga gidan gajiyayyu
Da qyar habiba ta samu mai motar daya yadda zai kaita katsina bayan ya mata tambayoyi ya tabbatar ba mahaukaciya bace sabida dauda da yadda take buga tsami,don sai sukai sati basuyi wanka ba haka gashi ba suturar arziqi garesu ba,haka al'adar gidan malam ko ince boka na hayi take,shima driver din a boot ya saka ta bayan ya lafta mata kaya don kada passingers su ganta ko suji doyi su fasa shiga
Da qyar ta qarasa jikin get din gidan ta dinga bugawa,ibrahim daya daga cikin security din shi ya fara bude yar qaramar qofar gidan yana cewa waye,turus yayi ganin mace mai siffar mahaukata tsaye a gabansa,baki ta waahe jajayen haqoranta suka bayyana tana fadin
''yauwa ibarahim,sannu ashe ka dawo aiki''kai kawai ya gyada mata
''eh na dawo''
''nene na tana ciki kuwa''rai ya hade mata kana ya girgiza kai
''bata nan''
''to mami fa,hajiya bintu''
''tana ciki''sai ta fara qoqarin shigewa tana fadin
''alhamdulillah''tsawa ya daka mata kana ya tsaidata
''hala irin mahaukatan nan ne da ke gudowa daga turu ko''
sai ta dubeshi
''haba ibrahim,na kama sunanka din,na kama na nene,na kama na mami kuma kace min mahaukaciya,zahariyya ce fa,zahariyyan nene''cike da mamaki ya zuba mata ido,yakai a qalla kusan minti goma yana qare mata kallo kafin ya ganota ta hanyar idanunta,tab aikam ko giyar wake yasha bazai barta ta shiga ba,mutanen da suka so hallaka iyayen gidansa mutane na gari,haka kawai ta dawo ta sake wargaza zaman lafiyar gidan bayan sun samu nutsuwa da kwanciyar hankali,yarinyar da bata da mutunci,bazai iya tuna sau nawa tasanya hannu ta tsinka masa mari ba a matsayinsa na soja,ko ranar da zasu sallameshi ita da uwarta bai manta irin zagin,cinmituncin da suka dinga dura masa ba,wata yazo qarshe amma da suka tashi korarsa hanashi salary din watan sukayi,wanda hakan ya zama sanadiyyar rasa danshi(hmmm,ka shuka alkhairi dai sai kaga da kyau)
murna ta fxatonta zaice ta shiga sai taga ya hado gurar sama data qasa ya hadeta gu guda
''wallahi ko cewa akayi idan baki shiga ba mutuwa zakiyi saudai ki mutu,na baki minti biyar kibar qofar gidan nan,don duka ahlin nene yanzu basa cikin gidan nan,sun shiga duniya,kema gwara kici gaba da bin sahunsu''yaja qofar ya rufe,zubewa tayi a gun tana kuka haiqan don tasan bata da wani gata kuwa
minti biyar na cika ibrahim ya sake leqowa ya sameta zaune,baice uffan ba ya fara qoqarin ciro bindigarsa yana saitata a kanta
''bari na kasheki kinga an rage iri''habawa,kamar ba mai ciki ba haka ta dinga fella gudu har ta fita babban titi,tsayawa tayi tana haki da waige waigen ko ya biyo sahunta,daidai lokacin da motar gida mahaukata ke zagaye tana kame tababbun masu rangwamen gata dake yawo kan titi suna kaisu gidan mahaukata din basu magani bisa umarnin gwamnati,cikin sa'a kuwa suka hangota,ba bata lokaci suka mata tara tara suka damqeta suka cusata cikin motar,ihu take tanason ta subuce musu fadi take
''wallahi niba mahaukaciyya bace da hankalina,gidanmu naje aka biyoni da bindiga shiyasa na gudi titi''wannan surutan nata suka qara musu amanna kan mahaukaciya ce
🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Cikin kwanakin kusan babu abinda yake damunta illa kewar abdallahn ta kawai
Kewarsa take gaba dayansa bawai wani abu daban ba,don kusan bayan kowacce awa uku zai kirata ya debe mata kewa da daddadar muryarsa,mamar kowanne lokaci yauma suna maqale a waya tana kwance ta gama shirin bacci
''baby,anya kuwa zan iya cika kwana goma nan kuwa,na hisham zan baro na taho?''a shagwabe tace masa
''sabida me?,ka barshi kawai ka qarasa din''
''baby na gaza jurewa wlh,kewarki na son kasheni,bansan kuskure na tafka da na tafi ba baqarami ba sai yanzu,kuma yadda nakeji na tabbata kema haka kike ji''
''wata qila ma na fika''ta fada a hankali,kamar ya taka rawa haka yaji saboda farinciki,son da maryam ke nuna masa irin wanda yake fatan samu ne daga macen aurensa,bashakka shikam dan gatan mami da maryamu ne
sai da suka raba dare suna musayar zafafan kalaman qauna kafin suyi sallam
Da wannan damar mami itama tayi amfani ta samo mata masu koya mota har gida matar ke zuwa tana koyawa maryamun,a haka lubabatu ta nace har itama ta fara koya,cikin sati guda sai gashi maryamun ta fara qwarewa,matar kam jinjina mata tayi don lallai kam na qaramar basira take da ita ba
🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Tun jiya abdallah ya sanar da ita suna hanya in sha Allahu,saboda tsabad murna adaren kasa komawa bacci tayi,zama tayi ta dinga lissafe lissafen abubuwan da zasuyi a gidan gobe,tunda ba zasu shigo ba sai kusan magariba,har yace da yasan haka zata masa taqi komawa bacci da bazai gaya mata ba
A parlour dinta ta samu baaba uwani da lubabatu sun gama breakfast suna zaune suna hirarsu abinsu,gu ta samu ta zauna da yawancin lokuta bata fitowa da wuri sai sun gama shan hirarsu da abdallah tayi wanka sannan ta fito ta karya,cikin girmamawa ta gaida baaba uwani suka gaisa da lubabatu sannan ta sanar musu isowar abdallan
''to alhmdlh,Allah ya iso da su lafiya''inji baaba uwani cikin farinciki,ba tare da bata lokaci ba suka soma yan sabgogin da duk ya kamata suyi din,duk da gidan amarya dama ba wani abu yaje da buqatar a sauya masa ba,amaryar ma irin maryam ami tsafata kula da tattali
lubabatu ke ce mata
''babu wani dan gyara ne haka adda da zakiyi?''batasan sanda ta harareta ba don sarai ta fuskanci me take nufi
''halan wannan karon so kuke abdallah ya kaini kushewa ba asibiti ba''ta fada a zuciyarta,a fili kuwa cewa tayi
''uhhmmm,baku fa da kunya sosai yaran yanzun''dariya lubabtu tayi tana toshe bakinta tare da cewa
''Allah ya bawa adda haquri''
Lubabatun ke mata zancan girki dane dame za'ayi?,sam ba wanda ta yadda ta bawa girkin don tace da kanta zatayi,sabida wannan ne karo na farko da zata yiwa mijinta girki cikin gidan aurensu,abinci ta tsara zata masa kala uku baya ga kala kalar farfesu shima uku,sai drinks don haka tun sha biyun ta fara ragewa don kada lokaci ya qure mata
zuwa la'asar ta kammala komai sai miya da bata qarasa ba guda biyu su din ma suna kan wuta saura kadan su kammala dahuwa,tana falo tana dan hutawa saiga baaba uwani dauke da yar jakarta,cikin mamaki maryam ta dubeta
''a'ah,baaba ne zakiyi da jaka da ranar nan?''
''gida mana meramu,zan koma gidan hajiya,tunda yau abdullahi zai dawo ko''
''haba baaba,ai kwa bari sai gobe tunda baku san zai dawo din na sai dazu da safe fa''bakinta ta kama
''rufamin asiri meramu,haba don rashin hankali sai in zqune muku gotai gotai,hajiya ma ta riga da ta aiko direba,ya iso ma yana waje yana jira na''tana mita ta miqe ta haura sama ta daukowa baban atamfa mai kyau turmi daya,sinqin sabulu da turare sai plate din takalmi guda daya,godiya sosai baaban ta dinga mata har ta sata jin kunya,hijabinta ta zura saboda umarnin abdallah na sanya hijabi ta rakata har bakin get suna yiwa juna godiya
Tana dawowa ciki saiga lubabatu itamq da nata kayan,hararata tayi tace
''wallahi baki isa ba,kada ma kice min tafiya zakiyi,ku barni ni kadai bayan sai magariba zasu shigo''dariya hindatu tayi
''wallahi ya hisham ne yace da naji zaku dawo na bar muku gidanku,idan kuma na zauna duk abinda nq gani nina jawowa kaina,kai take gyadawa
''shi hisham din ya gaya miki haka?,to babu inda zaki kuma zai shigo tamu ni da shi''haka ta tare hindatun ta hanata tafiya
qarfe shida ta fito daga wanka ana ta shiye shiryen kiran sallah magariba,duk bayan mintina sai ta duba wayarta ko zata ga kira ko saqon abdallah amma shiru,a haka ya qarasa gaban madubi ta tsara kwalliya mai cike da tsari bayan ta mulke jikinta da nau'in turaruka kala daban daban,gaban sif dinta taje ta bude cike da tnanin wacce shiga zata yi ma,ta jima tana nazari kafin daga bisani ta fidda wata gown mai bala'in kyau,ashe ce wadda aka mata ado da jajayen dutsina daga gin breast din da kuma furanni,ta gyara gashinta tayi masa kanta daurin V shafe da jan dankwali,fashion ta saka na jajayen sutsina take ta fito gaba daya kamar wadda aka sauya
Babban hijabi ta saka zata tada salla kenan taji knocking ta tambayi waye lubabatu ce tace ta jirata sallah zatayi tana fitowa,tana idarwa ta sake duba lokaci gari har ya dan fara duhu,ta cire hijabin ta sake gyara daurin nata kana ta fito falon,burner ta kunna dake lunguna na gidan duka ta sake sa turaren wuta daidai lokacin da lubabaatu ke fitowa da shirin ta na tafiya,mutuwar tsaye lubabatun tayi
''adda maryam!,kinganki kuwa,shan kyau irin wanann daukar magana haka?''dariya lubabatu ta bata ta dinga darawa,da qyar ta tsata suka fara sallama,ta tambaueta ta me takeso ta bata
''kome kika bani adda maryam yayi,ni ko zaman ma da nayi gidan nan ai ya isheni,ac din da nasha ta kwana goma bakiga har na canza ba,ga kuma babban kamu nayi ya hisham...''
''munafukai,ai dama daga yadda naga kuna wani kallin juna elh ma san da walakin kuma bari yazo sai na tsigaleshi''da sauri lubabatu ta rufe mata baki
''don Allah kada ki masa maganar,bai furta da bakinsa ba,yace kawai dai zamiyi maganar idan ya dawi zaizo gidanmu''hannunta ta cire daga bakinta
''ni kinga kada ki goge min janbakin tun kan wanda aka sa donshi ya gani''ta fada tana dariya kana ta shiga ta dauko mata itama atamfa saidai ita ta hada mata da kayan kwalliya
''inason in bada doguwar riga ki kaiwa binta amma ina tsoron halinsu,ni ko ganinsu a gida ma banayi anya ma kuwa suna nan''
dariya lubabtu ta sheqe da ita
''wallahi sunana,ai yanzu ko nawa za'a basu su miki rashin arziqi ba zasuyi ba,bakisan ya abdallah ne yasa aka debe su aka rufe ba suka kwana aka tsoratasu kan rashin mutuncin da suke miki keda mama?da suka dawo wallahi ko qofar dakin maman ma daina bi sukayi bare su kallshi,kuma da amincewata yasa akayi hakan,dama iskancinsu ya ishemu,yanzu kuwa idan kinji suna rashin mutunci a gidan uwarsu data koya musu suke saukewa''ta qarashe maganar tana cin dariya abinta
mamaki ne ya kamamaryam,a gaida abdallah,shikam halinshi ne idan dai zaiyi abun alkhairi ba wanda yakr gayawa saidai idaniyarka ta gane maka ko a baka labari,qimarsa ta sake daduwa cikin idonta,babu shakka duk wanda zaiga qimar mahaifanka ya tsare maka mutuncinsu ya girmamasu ya gama maka komai koda kuwa yankan naman juna kuke kai da shi,har harabar gidan ta rakata itama bayan ta sa driver ya dauketa zuwa gida
tsuru ta dawo tayi cikin falon tana ta duba lokaci,qarar wayarta taja hankalinta,dagawa tayi da sauri ganin sunan abdallah ne
''hello baby,kimin afuwa bazan samu danar dawowar yau ba,wani muhimmin abu ya tsaidamu,amma din Allah kada ranki ya baci,ki leqo yanzu compound na aiko wani yaro zai kawo miki saqo,idan bai iso ba ki jirashi a nan don bana so ya shigo min gida''kafin tace komai ya katse wayar,galala tayi da waya a hannunta ta rasa nayi ma,jikinta ba qwari ta zari hijabinta data tuna yace ta fito yayo aike
har tsakiyan gidan ta fito bataga kowa ba don haka ta tsaya nan wajen minti goma tana jira taga ko zai iso,ganin tsaiwar tayi yawa yasa ta yanke shawara komawa falo ta zauna bakin window ta jirashi a nan tunda tana iya ganin harabar gidan daga nan,jikinta ba qwari haka zuciyarta babu dadi tana rungume da hannayenta a qirji kanta a qasa har ta iso qofar falon
Cak taji anyi sama da ita baki dayanta,a tsorace ta soma laluben fuskar mutumin saidai tun kafin takai ga tozali dashi turatensa ya gaya mata *ABDULLAHINKI NE*,falon ya shige da ita wanda suna shigar wasu qwayaye masu launin ja da fari suka kama a take rubutun *AM BACK I LOVE YOU* ya bayyana,murmushi ya subuce mata bayan da suka hada ido,shima mayar mata da martani yayi kana suka zube kan kujera ya hau aika mata da saqonnin kewarta da yayi,da qyar ta lallabashi yayi wanka yayi sallar isha'i,kadan yaci abincin don baki daya hankalinsa na kanta,tana cikin gyaran gun da suka ci abincin taji baki daya an sungumeta bai sauketa ko ina ba sai bedroom dinshi wanda ayau suka fara amfani da shi
Rikice mata yayi kamar wancan karon sai hakan ya tsoratata,shima kuma ahankali sai ya dinga qoqarin daidaita nutsuwarshi ganin ta fara tsorata,cikin salo da qwarewa na namijin da yasan abinda yakeyi ya dinga tafi da ita,tamkar wani corse yayi a tafiyan tashi,saidai ba wani corse tsabar iya soyayya ne da tattalin mace,wata duniya ya jefasu wadda basu taba koda tunanin akwaita ba,soyayya ta gani zallah madararta daga gun abdallahn nata,soyayya ya gwada mata mai sanyi da tsayawa a rai,duk wahalar da take zaton shanta sai abun yazo mata da sauqi,duk da ba laifi ta dan jigata amma bai yi wani yawa ba
Tunda suka fito daga toilet yake zaune daure da towel,duk inda tabi idanuwansa na kanta,shi kadai yasan me yake ji game da ita cikin zuciyarsa,gaba daya ya hanata sakewa da mayen kallonshi,ga kunyarsa dake nuqurqusata,maganganun da ya dinga gaya mata kawai dazun idan ta tuna sai ta rasa inda zata saka kanta saboda kunya,sarai tasan ita yake kallo amma taqi kallonshi,sai da ta gama sharce gashinta ta saka hand drayer ta busar kana ta zo zata giftashi don ta dauki ribbom dinta dake kan gadon ta daure gashinta,baki daya ya janyota ta fada jikinsa ya dorata saman cinyarsa,cikin kunnenra yake rada mata
''baby Allah yayi miki albarka,banu shakka kin cika alqawarin,ki shayar da ni mamaki,ke din yar aljanna ce Allah baby kamar yadda kike yar baiwa''boye kanta ta dinga yi cikin gashin qirjinsa,yasa hannu ya sake maida mata gashin kanta baya
''amma baby yauma kamar nayi hurting dinki ko?''ya tambayeta a tausashe cikin tausayawa,kai ta gaya masa
''kadan ne ba yawa,kuma ba damuwa a haka ake daina jin zafin baki daya,zan dinga shiga ruwan dumi ne kawai''kissing nata yayi a goshi kana yace
''Allah ya miki albarka,ya bamu zuriyya ta gari,qarasa shiryawa ki rakani naga mami na,bazan iya kwana ban ganta ba''murna ta kamata sosai don itama tayi missing nata,duk da kunya na taba can qasan ranta
Har ta miqe ya kuma riqo hannunta
''baby kin kashe jiki da yawa,ko zaki iya taimakin na shirya?''girarta daya t dage masa kana ta kashe ido
''why not my''
kai ya girgiza fuskqrsa qunshe da murmushi
''lallai a shirye kike baby,get ready for d second round idan muka dawo,irin wannan kashe ido haka''hannu tasa ta rufe tafin fuskarta kana ta janyo wani dan towel din ta fara tsane masa jiki da shi,sai da ta gama shiryashi tsaf kana shima ya shiryata cikin wata doguwar riga mai hade da hijabi
*********
Dadi gun mami kamar ta goyesu haka ta dinga ji,cooler uku ta yiwa mamin na duk abinda ta dafa wa abdallan,kusan awa daya suna hirarau tare daga baya ta tasgi don basu guri su gana su biyu,don tsakanin da da uwa akwai sirri(qalubalenmu mata,sai kuje gaida uwar miji keda mai gida ki musu qifi qifi a tsakiya idan kika san uwar miji mai kawaici wadda ba zata iya ce miki ki matsa ki basu guri su gana ba,ke kuma ba hankali,na minti goma ba zaki iya matsawa ki basu guri ba,ta yiwuwu akwai maganar da alokacin takeso suyi da danta,don Allah mata mu gyara,koke ya yiwa haka keda mahaifiyarki ai bazakiji dadi ba)
mamin ce ta tambayeta ina zuwa
''zanje mu gaisa da mero ne''
''to...to,bata kuwa dade da barin nan din ba,sai da na korata ma tukun''tana murmushi ta sulale ta fice
Fes ta taras da meron da bangarenta,bisa dukkan alamu training na mami ne,tayi kyau da ita ta fara gogewa,haka nan fatarta ta qara kyau,kallo ta tarar da su sunayi ita da labaran din,suka gaisa sai ya miqe ya fice ya basu guri,murna mero ta dinga yi sosai ta dauko wannan ta kawowa maryam,ta rakito wancan ta bata har sai data ce ya isa,sun dan jima suna hira tana sake wayar mata da kai kan wasu abubuwan da tasan ta fita waye wa akansu,sai da ta kusa awa guda sannan labaran ya shigo yace mai gida na magana zasu wuce,kamar kada ta tafi haka mero taji tace amma zata zo itama taga gidan takwaranta,dariya tayi tace shikenan sai tazo din
A waiting parlour ta taddasu tsaye da mami,sai data rakasu har bakin mota,abdallah ya dubi mamin
''badai wata matsala ko mami zamanku da su labaran''murmushi tayi
''wallahi ko kadan,basu da matsala kam,ina jin dadin zama da alhamdulillahi''ya gyada kansa yace
''masha Allahu,mami sai da safe,muna ta missing dinki mami''murmushi tayi
''gwara ai kusan gurma ya kamaku da haka zaku saba ai''ta dube maryam da kanta ke qasa tace
''diyata ku gaida gida tinda qarfi da yaji sai kinyi surukuta da ni bayan nace ni bana surukutar,ki kula da kanki,kaima ka kulamin da ita,Allah yayi muku albarka''ameen suka amsa baki daya
Sai daya tsaya da ita a hanya ya mata siyayyar kayan maqulashe,qememe yace tayi zamanta a motar basai ta fito ba
''zan iya hadiyar zuciya fa idan kika fito wani ya kalleki,ke Allah zan iya mutuwa maryam a kanki,kishi ne da ni sosai,qaunarki ce tamin yawa,ba qaramin kamu ta yimin ba fa''dariya ta qyalqyale da ita''anya my kishin nan naka bai yawa ba''
ido ya zaro
''waya gaya miki?,bakisan yadda sahabbai keda kishi bane?,duk kishin nan nawa baikai nasu ba,kuma ma ai dole na kasance mai kishi saboda annabi muhammad S,A,W,yace maras kishin iyalinsa (addayyus)bazai shiga aljanna ba''kai ta gyada ta saka tafin hannunta a nasa tace
''gaskiya ne,sadaqa rasulul kareem,zan taya ka kaucewa duk wani abun da zai sanya kishinka motsawa RUHINA''
''na gode RAYUWATA''ya bata amsa cike da shauqinta
Sai kusan sha daya da rabi na dare suka koma gidan,da wani kasalallen tuqi ya dinga yi suka dinga hirar soyayya abinsu cikin motar kafin sukai gida
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣7⃣
*Daga abu zarril ghifari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni:((ka ka wulaqanta wani abu daga cikin kyakkyawan aiki komai qanqantarsa,koda haduwa da dan uwanka ka sakar masa fuska ne(kayi masa murmushi)*
*Daga barraa,dan Aaazib R.A yace:Manzan Allah S A W yace:((babu musulmai biyu da zasu hadu suyi MUSABAHA face sai Allah ya gafarta musu zunubansu kafin su rabu))*
Gida ne suka taru suka ginashin mai cike da ni'ima qauna soyayya da kwanciyar hankali,wanda tsabar kula da haqqin juna wanda Allah ya dorawa kowannensu shine sila,kowa na qoqarin sauke haqqin dan uwanshi a kansa ua kuma qara da kyautatawa jin qai qauna da rahama irin wadda Allah ke sanyata tsakanin ma'aurata,kamar yadda abdallah ya sake tabbatarwa kanshi yahi dace da *macen qwarai* wadda har *ABADAN* bazai iya rabuwa da ita ba haka itama maryam anata bangaren,tabbas babu shakka *abdallah kyautar Allah ne*,hikimar ubangiji mai yawace,wato alkhairi ke tafe da ita,jinkirin auren da ya mata ashe shi kadai yasan manufarsa ta yin hakan,ba shakka shine sarki gagara misali,komai da yayi kan bawansa akwai manufarsa a ciki,saidai kai ajizanci da son zuciya irin taka ya hanaka gani
*************
_BAYAN WATA SHIDDA_
Haka rayuwa taci gaba da jujjuya musu cikin hikima ta ubangiji,rayuwa ce suke yinta mai cike farinciki da qaruwar arziqi,tsantsar qauna da fahimtar juna a tsakaninsu,hakanan ci gaba kala kala suna ganinshi,albarkacin tsaftatacciyar zuciya taimako da qaunar jama'a da suke da ahi wanda raino ne irin na *MAMI* kusan a gurinta suka nashi wanann aqidar
Tuni abdallah yayi gini gini mai kyau da tsari mai dauke da part biyu,cikin tsarinsa da halinsa maryam sam batasan ginon waye,ba sai bayan da ya kammala taji ana gayyatarta tariya,gida ne da ya mallakawa mahaifin maryam wato malam ahmadu wanda aka fara kira da alhj amadu dalilin kaishi umara da yayi shida mama,godiya tazo ta masa ya rufe bakinta da zafafan kises yace bai buqatar kowacce godiya daga bakinta,shi a rayuwa sun gama masa komai mama da baaba da suka haifa masa ita
Maama da baaba huwaila ne kawai suka tare a ciki don a taohon gidan aka bar inna hadiza da jamila da bintu,don tuni malam amadu ya tsawatar wa dukka wacce take jin zata ci gaba da wasa da aurenta tana jeka ka dawo,matuqar kuwa ta kashe auren nata to saidai ta nemi gidan zama ba gidansa ba,yabi kowacce da jari daidai qarfinsa,suntsota kuwa don bai taba musu bore irin wanan ba don haka kowacce tayi luf a gidanta,abun dama akwai raahin kwaba da hantara tunda sunsan idan sun dawo din ana maraba da su,musamman yaran inna huwaila wanda itama bayan babansu yayi nashi jan kunnen itama ta dora da nata
Hisham kuwa da lubabatu tuni zance yayi nisa,don tuni ma har manya sun shiga maganar an kai kudin aurensu,hakan,na qaramin dadi ya yiwa baaba huwaila ba,girma da qimar maryam da mama suka dadu cikin idanunta,babu shakka sanin masoyi sai Allah,wanda ka tsana kake ganin bai sonka wani lokaco baka gane cewa ashe masoyinka ne sai tafiya tayi tafiya
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
kamar kowanne lokaci kafin dawowar abdallahn da awa daya ta kammala komai,haka ma yauma take ga maryam,bayan ta kammala ayyukanta ta fada wanka,lokaci ta bata mai uawa gaban madubi tana tsara kwalliya kana ta fidda wata iriyar riga mai bazar,tafe take da breast,cup daga sama hakanan hannun shimi gareta,bayan rigar kusan rabinsa a wawake yake,dududu rigar iya karta gwiwa,kusan kullum shigar maryam kenan don qa'idar abdallah ce,bata sanya manya kaya sai idan zasuyi baqi koda rana idan baya nan,amma ko dawowar rana yayi tofa sai anmasa kwalliya da shigarsa ya gani kana zai koma,saidai ko idan zasu fita unguwa,wannan kam harda hijabinta don baya taba barinta ta fita da mayafi koda wasa
Alarm da taji shi ya tabbatar mata ya dawo,ta sake duban kanta ta tabbatar komai yayi daidao,ita kanta tayaba irin kyawun da tayi,ta rasa me yasa take dada wani kyau tare da cika,har wani kumatu ta fara yi,tayi azamar sake fesa turare da gaggawa ta fito,saidai tana zuwa bakin qofar falon ta sauya taku
Zaune yake cikin motaf kamar kowanne lokaci shi daya ne,dama idan taji alarm din ta san cewa security dinsa sun tafi saura shi kadai sai ta fito,a bayan motar yake a zaune da alamu yauma driver ne ya tuqashi,sometimes idan suka taho da securityn nashi yakan karbi driving dinne ya ja suna zaune,wannan na daya daga cikin abinda ke sake burge maryam game da abdallah
Tunda ta taho din ya zuba mata idanu ko qiftawa bayayi,a kullum kwanan duniya sake linka masa qaunarta ake cikin zuciyarshi,har ta qaraso bai sani ba sai data sa bakinta ta hure masa ido,ya saki murmushi ya jawota ta fado cikin motar ya rungumeta
''hala yauma a gajiye kake *shariki hayateey*gaskiya idan basuyi wasa ba kwanan nan zan hana wa kowa ganinka,akan me za'adinga wahalmin da *zuciyata*''ta fada a shagwabe
ajiyar zuciya ya saki yana murmushi
''sosai kuwa baby,amma wai...baby ina da tambaya?''yayi maganar yana bin loko da saqo na jikinta yana shanshanawa saboda irin qamshinta dake gigita shi
''uhmmm,shariky ina jinka''tayi maganar itama tana sake qwaqumeshi
''wai don Allah ya zanyi na ragewa kaina sonki cikin zuciyata ne,yana neman fa ya hallakani''dariya ta qyalqyale da ita tana sake nadewa cikin jikinsa''saidai a qara maka wani son kan wanda kake min my''ido ya dan zaro,cikin wasa yace
''baby.....idan naci gaba da yi miki irin wanann son ai sai ki hanani qara aure''sai ta hade rai ta zame jikinta daga nashi ckkin fushi ta fara qlqarin fitowa a motar,riqeta yayi yana dariyq ciki ciki don yasan ya gama tabota
''ki jirani mana baby mu tafi tare''·
''ka bari ifan ka sake auren sai ta jiraka,tunda ni nayi maka kadan''ta zame da squri ta fice,shima da sauri ya fito yana dariya qasa qasa yadda ba zata ji shi ba,sai ya jingina da motar yana qare mata kallo yadda take tafiya da sauri sauri,abun sai ya burgeshi,'yar figigiyar rigarta ta mata kyau,hakanan yaga ta sake wani cika duk wani hips nata ya fito,sai da ta qaraci saurinta cikin takun da basu gaza biyar ba ya damqota,cak ya dagata tana eutsil wutsil dq qafa tana tureshi ya shige da ita
ya sani a bisa al'adarta kafin ya dawo ta hada masa ruwan wanka don haka ya wuce da ita kanshi tsaye toilet din,tuni ido ya soma raina fata don ta gano qarshen zancan,yau kam kwalliyarta saidai ta sake wata,da sauri tace da shi
''nifa na gane wasa kake min,pls bawan Allah ka saukeni,zan tayaka ma wankan''dariya ta bashi ya dubeta
''ai kin riga kin makara,kin manta ne babu fushi a zamanmu,you break the rule,and the rule will break you as usual''yana gama fada ya sanyata tsundum cikin bathtube kana ya fidda takalmin qafarsa da safa ya cire suit din jikinsa ya bita ciki,sai da suka gama shan qaunarsu kafin suyi wankan su fito
Yana baje saman carfet din falon maryam tana hidimar zuba masa abinci don a qasa yake cin abinci abinsa yace yaa samu ladan sunna na irin zaman da ma'aiki yakeyi idan zaici abinci(irin zaman yana taimakawa qwarai wajen hana mutum yin mugun qoshi daya sabawa addini,haka yana hana yin tumbi)bayan sun gama shiryawa sanye yake da gajeran wando shi kadai ne ajikinsa sanyin a.c na ratsashi,ta riga data saba da kallo irin ma abdallah,indai yana kusa to fa dukkan idanunsa na kanta,bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi don ya sanshi farin sani,ba macen data isa ya tsaya yana kallonta to din me ita din halaliyarsa zata hanashi more kallonta,bayan ya gaya mata ba sau daya ba basau biyu ba kallonta ba qaramin jefashi yake cikin nishadi da sabuwar duniya yake ba
Sai data lakuce masa hanci sannan tace ''mr kallo''
''na amince''ya fada yana murmushi,ta tura masa plate din abincin wanda ta cika da lafiyayyen alkubus da yayi kyau ya taahi yayi shar,da kwanon tangaran mai kyau dauke da miyar taushe wadda tasha tantaqwashi da naman kasuwa da manshanu ita kuma ta jawo wani jug na plastic tare da wani kwanon tangaran da abun zuba sugar ta bude ta fara hada garin kwaki da suger da soyayyar gyada,cak ya tsaya yana dubanta ita kam batasan yana yi ba har wani tsinkewa yawunta yake kamar wadda taga wani abin dadi,sai da ya kira sunanta sannan ta dago kai tana amsawa,ganin yadda fuskarsa tayi kicin kicin ya sanya jikinta yin sanyi,don ko kusa bata qaunar ta zama sanadin bacin ransa
''amma yaya mukayi da ke kwana ukun da suka wuce a jere.....ranar farko kika cemin sha'awarsa kike na barki kika ci kayanki,rana ta biyu kika ce min bakinki ba dadi da kika ci na jiya kinji dadi bana so amma sabida farincikinki na barki,shekaran jiya harda magiyarki da qwallarki na barki kici,jiya kuwa da kika tashi sai kika shaqeshi kika cika cikinki taf da shi kafin ma na dawo,da na dawo saboda tsabar qoshin da kikayi loma daya na abinci kika ci kika fara amai,sanann yauma dai a gain kice min shi zakici?''sai ya girgiza kai
''bazai yiwu ba maryam,sai kace wanda ake ciwon yunwa a gidansa,aiko wani ke neman taimako a guna bazan bashi garin kwaki ba bare iyalina''tuni qwalla ta cika idonta,ga qoshi ga kwanan yunwa,tana son ta kyautatawa abdallah amma wlh idan taci abincin ji take kamar numfaahinta zai dauke,ba bata lokaci hawaye suka fara silmiyo mata,idonshi ya runtse don babu abinda yaqi jinin gani irin hawayenta
''ya salamullahi,daga magana sai kuka?''
''Kinga matsonan muci abincin ko yaya ne,idan muka gama sai ki gayan meye damuwarki,idan ma duka nau'ikan abincin ne baki so ki lissafa irin wadanda kike so kona wacce qasa ne in sha Allahu ni abdallah mai nemo miki ne kinji dear,amma wanann hawayen qona min zuciya yake''ya fada yana daga mata hannu alamum ta taho,ba musu ta matso jikinsa tana goge hawayen kanta a qasa,cike da son ta faranta ransa tasa cokali ta fara ci,loma biyu kadai tayi taji wani abu ya dunqule mata sai amai tun tana yinsa tana fidda abincin da taci,da garin kwakin da tasha dazun har ya koma bata iya harar da komai,gaba daya hankalinshi a tashe yake gani yake shine sila da ya takura ta,haka ya dauketa cak yagyarata ya gyara gurin,bai samu nutsuwa ba sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita,duk son da yakewa alkubus din da qyar ya iya cin yanka uku
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
cikin baccinsa ya dinga jin qamshin girki,da sauri ya farka ya mutstsuka ido,ya duba gefansa bata nan,kenan ita ke aikin girki a kitchen qarfe tara na safe?,da azama ya diro daga gadon ya doshi kitchen din
tsayawa kawai yayi yana kallonta tamkar ba ita ta gama sheqa amai jiya ba?,tayi kwalliayarta tayi kyau kamar ka saceta ka gudu,ta matse cikin wata riga mai roba wadda iya qibarka iya yadda zata kamaka iya kacinta qauri an mata tsaga daga gabanta daga qaurin qasa zuwa gwiwa,ta gyara gashinta yayi kyau sosai,ji tayi kawai an rungumeta ta baya sai ta saki yar qaramar dariya
''kasan kuwa irin tsoron daka bani?''
''nima ai kin bani tsoro baby,ke da baki da lafiya ina ke ina kitchen fisabilillahi''waigowa tayi suna fuskantar fuskarta qunshe da murmushi juna yana zagaye da qugunta,ta shafi sajensa kana tace
''ras nake jina shariky,ina mai tabbatar maka idan za'a saka tsere sai na wuceka''dariya ya saka ya sumbaci kumatunta
''babu musu don naga alama,wai baby meye sirrin ne?''ya fada yana kashe mata ido,itama maida masa martani tayi
''name fa?''
sai da ya jujjuyata ya sake kallonta sannan yace''gani nayi sai wani kyau kike qarawa,fatankin nan har tafi tawa laushi,kumatunki kamar kin boye qwai,brown oily eyes dinki kamar an kuma diga musu zaiba da oil,ke tsaho ne kawai har yau na fiki ba.....''kasa qarasa maganar yayi saboda manna bakinta da tayi cikin nashi,sai da ta dan birkitashi sanann ta cire tana duban bakin nasa
''wannan bakin nawa kada ya cinyeni''sake janta,jikinsa yayi yana dariya
''Allah am seriouse,meye sirrin''
''matso na gaya maka''sai tayi dage don duk tsahonta abdallan ya fita ta kai bakinta kunnensa ta shiga jero masa
lumshe ido ya dinga yi yana saurarenta tare da sake shigewa jikinta,banji komai ba face kalmarta ta qarshe
''kaga kuwa kaine sirrin''dukkansu murmushi suka saki mai,hade da dariya dariya,ya kamo fuskarta ya hada goshinsa da nata shima yana mayar mata da martanin kalmomin,sun kusa kwashe a qalla minti goma a haka har ruwan shayin da ta dora ya fara qonewa sannan ta ankara ta zame jikinta da sauri tana cewa
''you see,shi yasa idan ina abu mai muhimmanci banso kazo ka riskeni,don sawa kake ina mantawa da kowa da komai ciki harda kaina''shi ya qarasa hada kayan karin tana tayashi da wasu abubuwan kana suka,yi wanka suka shirya don yaune ranar da abdallahn ke raba tallafi gidan gajiyayyu da asibitoci wanann karon kuma tare zasu shi da mami,maryam ma ta kafe itama sai taje don baza'a samu ladan babu ita ba
*********
tafe suke cikin motar gwanin sha 'awa don baka banbance waye danta,tsakanin abdallah da maryam,shike jan motar maryam na gefansa,yayin da motar security dinsa biyu ke gabansu biyu ke bayansu,yawanci indai tare da maryam ne cikin fitarsa bai yarda driver yayi tuqi wai don kada a gane masa ita,mami na baya tana duba wasu takardu jefi jefi suna hira da abdallah
''yauwa mami''
''uhmmm''taje dashi kanta na kan takardunta ,tasan tunda ya fadi haka tambaya gareshi
''dama wani lokaci mata na daina cin abinci sai wani abun daban?''bata bawa tambayar tasa muhimmanci ba,don a zatonta shirmene kawai irin na abdallah din haka tace da shi
''kamar yaya kenan?''
''mami maryam,na rasa meke damunta,safe rana dare garin kwaki mai tsamin nan,abinci saidai ta dafa min kawai ni nayita narka,jiya da na matsa mata sai taci amai tayi mami,ni tausayinta ma nake ji''
wannan karom saida ta dago ta dubeta,kunya kamar tayi me ta kama hannun abdallahn a sace ta matse cikin nata
''wayyo hannu na diyana''ya fada yana yamutsa fuska kamar qaramin yaro,da sauri ta sako hannun nasa taja hijabinta ta lullube fuskarta
''kada ka sake matsa mata kan cin abinda bataso,ka barta''cikin damuwa yace
''amma mami gari fa?,bazai mata komai ba?''
''eh yana yi ne zata daina nan kusa''ta fada zuciyarta tamkar qanqara,addu'a take cikin ranta Allah yasa hasashenta ne zai tabbata
Ya sake rausayar da kai
''amma mami ni gani nake kamar yana tsotse jinin mutum ko ruwa jikinsa''
''ba daya,nace maka zata daina ne fa''
''to Allah yasa''ya fada cike da hope,donshi har ga Allah abun na damunsa,gani yake wata cutar ce ta samu maryam dinsa,shi yasa ya sanar da mamin nufinsa idan ya gaya mata akwai wani maganin ta bata,kasa cewa komai maryam tayi,lallai ta yarda Abdallah gabuntar dan fari da tabarar auta na tabashi sosai,a hankali mamin tace
''ki kula kawai da kanki maryam,duk lokacin da kika ji wani sauyi a tattare da ke kumin magana,kada kuce zakuji kunyata,ni mamarku ce baku da kamata''kanta aqasa ta amsa da to,shi kuwa gogan cewa yayi
''ni dama maganin kawai kika rubuta mata mami Allah na tsani naga tana shan garin kwakin nan''murmushi ta dan saki
''bakasan komai nada qa'ida ba,ba'a rubutawa mutum magani kai tsaye,indai kawai kuka ga alamun canjin wani abu ko matsala to ku sanar da ni''
''to mami''ya amsa mata yana ci gaba datuqinshi
a gurin ajjiye ababen hawa suka yi oarking duka motocin nasu,mami ta riga fita saboda isowar shugaban asibitin din ya tarbeta,abdallah na qoqarin fita maryam tayi saurin riqoshi da qarfi har sai da ya dawo ya zauna don bai zata ba,ido ya kashe mata guda daya yana fadin
''ya akayi baby da magana ne?''kicin kicin tayi
''yanzu shariky don kawai ina cin garin kwaki sai ka gayama mami don Allah?''ido ya dan zaro
''to menene don mace kina shan gari dear na?,na tsammaci ciwo ne shi yasa na gaya mata ko zata rubuta miki magani''
''kada ka sake don wallahi ka bani kunya''kiss ya bata a goshi kana yace
''is ok,afuwan my sister''dariya ma ya bata tana zaune ya zagayo ya bude mata side dinta ta fito bayan ya sake gyara mata zaman hijabinta,duk yama tasa gun tsayawa don gaba daya atsarge yake,gani yake wai kallonta ake,security din ma da suka saba binsa a baya yace suyi gaba su zasu biyo bayan nasu,don kada wai su dinga kallonsu ta baya
kimanin su goma sha biyar suka kutsa kai cikin asibitin,daki daki suka dinga bi suna raba taimako,kudade ne masu tsoka suka dinga bayarwa tare da biyan kudin magunguna ga duk wanda ya kasa biya,wayyo Allah,kada kaso kaga abun tausayi kala kala,talakan qasata yana cikin wani hali,talauci yunwa fatara jahilci duka ya tattaru ya narke a kansa,wasu har kukan dadi suka dinga yi,maryam kuwa tuni zuciyarta ta karye,tunvtana share hawayenta a boye har ta saka kuka saboda azabar tausayinsu,abdallah ne ya fara jin sheshsheqarta,gefe ya janyeta hankalinsa a tashe
''sai da nace kiyi zamanki a gida dear kkka ce sai kinzo bayan ba lafiya ce da ke ba,sai na maida ke gida idan ba zaki iya jurewa ba''da sauri ta goge hawayen tana danne kukan din batason ya maida ta din,ganinsu na qara mata imani tare da godewa Allah kan matsayin da take kai,ya zabeta ya dorata ba don tafisu ba,ta yiwuwu a cikinsu ma akwai wadanda suka fita kusanci da Allah amma ya jarrabesu don ya sake tabbatar da imaninsu da shi,duk da haka fakar idinsa ta dinga yi tana goge hawayen ta handkherchief sabida abun tausayin ya isa
A haka suka gangara dakin 'yan haihuwa,tsoro ya kama maryam sosai ganin masu larura kala kala,akai kai ta dinga gigr hawayen nata wanann karon,ta tsorata sosai da haihuwar,daga bakin wani daki suka ga jama'a tsaitsaye agun anata hayaniya,mami ta tambayi jama'ar dake tare da ita,daya cikinsu ya mata bayani
''yarinya ce aka kawota daga gidan mahaukata zata haihu,ta jima agunsu ana bata magunguna ashe ba mahaukaciyar ba ce,to da suka kawota sai kuma suka yi tafiyarsu suka barta,kuma bazata iya haihuwa da kanta,ba don bata da isashiyar lafiya da zata iya jurar naquda,shine ake ta neman wanda zai sanya hannu kan fike din da za'a mata aikin an rasa mai yin signing tunda ba'asan kowa nata ba,shine aka fito da ita daga gadonta aka sanya wata akai kafin asan yadda za'ayi da ita''haushi takaici da tausayin yarinyar ya kama mami duk da batasan ko wacece ba,fada ta dinga yi sosai
''saboda tsabar rashin imani,ko cikinku ai a samu mai saka hannu dai,sanadiyyar haka fa tana iya rasa ranta,kuma idan ta mutu shikenan ta mutu a banza sabida bata da gata bata da galihu ko''da wannan fadan da takeyi suka qarasa gun da take kwance tana matagugu
Ba qaramin tsorata mami tayi ba da ganin zahariyya kwance male male cikin wani mawuyacin hali,batasan lokacin data isa gareta ba tana kiran sunanta saboda tsabar tqusayinta daya kamata,lokaci guda ta manta duk wani abu da sukayi mata ita da uwarta,kafin ta qarasa gabanta abdallah ya shiga tsakaninsu cikin tsananin nacin rai yana girgiza kai,tuni,idonsa ya sauya kala
''kada ki isa gareta mami ki barta don Allag,wannan shine sakamakon abinda ta aikata a rayuwarta,kallo daya zaki mata ki tabbatar cewa sakamako take karba''
tsawa mamin ta daka masa''matsa daga gabana kafin na tsinka maka mari abdallah,baka da hankali ne?,kasan naquda kuwa?,kasan irin azabar da take ji yanzu haka?,ciwon 'ya mace na 'ya mace ne''cewar mamin cikin fushi,ba musu ya kauce ya bata gu don baison bacin ran mahaifiyarsa
Ba qyamata ko tsangwama mami ta tattarota jikinta cike da tausayi,suna hada ido da mamin itama ta fara kiran sunanta,fadi take mami ku yafemin keda abdallah,kuyafemin mami mutuwa zanyi,tuni mamin ta bada umarni aka dauko gado don dorata a ahigar da ita tiyatar gaggawa,ana shirin daujarta tace ta saki murmushi tana kallon mamin
''mami,dama qyaleni kukayi kada ku bata lokacinku,don nasan cewa mutuwa zanyi,kuma ina farinciki da hakan,ta yiwuwu Allah ke sona yayi nufin wankeni daga zunubaina da zai dauki raina ta hanyar naquda,mutuwata a yanzu ta fiyemin rayuwata mami''
tuni hawaye ya cika idon mamin,duk da haihuwa daya tayi amma har yau bata mance zafin naquda
''ki daina fadar haka zahariyya,mata nawa ne suka haihu gasunan lafiya da su,ciwo ai baisan inda rai yake ba saidai idan kwana ne ya qare''sai taga idonta na kallon wani guri ne daban,a hankali taji ta ambaci''habiba''
duka sai suka juya,wadda aka ambata da habiban ce ke qarasowa inda take,zubewa tayi a gun tana kiran sunan zahariyya,ba wanda yasan alaqar dake tsakaninsu don haka mami ta sake bada umarni a dauki zahariyya a wuce da ita dakin tiyata,da sauri zahariyya ta tsaidasu
''mami,na fada muku wallahi a yau zan mutu bazan sake kwana ba aduniya,da tiyatar da zq'ayimin gwara ki barni nayi magana da wanann baiwar Allahn''jikinsu gaba daya yayi sanyi don haka mami ta matsawa habiba ta iso tana zubar da qwalla
''zahariyya,naga sakayya ta daidai abinda na aikata a rayuwata,aahe da gaskene son zuciya bacinta?,ashe da gaske idan baka godewa Allah ba zaka godewa azabarsa?,ashe daidai ne da ake cewa idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi gajere wataqila kai zaka iya fadawa?,tabbas Allah ba azzalumin sarki bane kuma baya zalunci saidai bawa ya zalunci kansa......''
*mrs muhammad ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
▶6⃣8⃣
*Fiyayyen halitta dan gatan Allah Annabi muhammad S A W yace:((idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa/dabi'unsa yazo muku(neman auren 'ya'yanku)ku aura masa,idan ba haka ba☝🏽(kuka hanashi),FITINA DA FASADI MAI GIRMA ZAI YADU/WANZU A BAYAN QASA))*
Juya kai kawai zahariyya take don ta qagu taji me ya faru da hqbiban duk da azabar da take ji,cikin kuka habiban ta dora
''na koma gaban mama na da baaba na,ba qaramin farinciki mahaifina yayi ba don ga zatonshi sace ni akayi tunda mamana tace masa bata nayi,haka nan itama mama tayi farinciki,tace nayi shiru da bakina kada na sanar da kowa halin da na fada da sanadin shigata wanann rayuwar da nayi,da na murmure zan koma gidan mijina,haka kuwa akayi bayan na soma murmurewa da wata biyu aka mayar da mi gidan enginer abubakar,a lokacin da aka maidani baya nan ya tafi umara,kada kiso kiga farincikin da fatima tayi,sai tausayin kaina ya kamani,naso ma cuceta amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai ya kareta daga sharrina ba tare da ita din ma ta sani ba,yarona wallahi fes da shi kamar sauran 'ya'yanta bashi da wata damuwa,sati na daya da komawa kafin enginer ya dawo na fara wani zazzabi mai zafi,wasa wasa sai tari,ba'a jima ba quraje suka feso min,idanuna suka canza kala,fatima ita ta tambayi engineer ya bata dama ta rakani asibiti''
sai habiba ta tsaya ta fashe da kuka tana tuna irin bala'i da tashin hankalin da ranar tazo mata da shi,da qyar ta saisaita nutsuwarta sannan tace
''abin takaici da baqinciki zahariyya gwajin farko aka gane ina dauke da cuta mai karya garkuwan jiki cutar sida wato HIV''kusan tare suka fashe da kukan wannan karon dom tuni zahariyya tqyi amanna itama da cutar ajikinta,tunda babu shakka habiba ta samo,cutar ta ne daga jikin malam na hayi,to kuwa dole itama ta kamu da ita babu shakka,kuka sukayi sosai kana habiban tace
''hakanan fatima babu yadda zata yi badon taso ba sai don kare lafiyarsu ta sanar da engineer ,bai bari ya dawo ba ma ya aikomin da saki uku qwarara,ban boyewa fatima komai ba kan dalilin fadawata wanan haki,wallahi baiwar Allah kuka ta dinga yi cike da tausayina ,hakanan tamin alqawarin riqe min yarona riqo irin na amana,da kanta ta daukeni ta kaini har gida,bqn boyewa mama komai ba din tana daga cikin wadanda sukaui silar fadawatq wanan mummunar rayuwar,abun mamaki qarara mama ta nuna qyamata atake agun,harda saiya mazauni sabanin wanda take a dazun da nazo gidan
Tun daga ranar na fara ganin tsantsar tsana da qyama daga gurin mama na hatta da qannena ba'a barsu a baya ba,duka babana baisan me ake ciki ba shidai ya san cewa an sakeni kuma ya nemi engineer amma yaqi sam ya sanar masa dalilin da yasa ya sakenin,yanzu nan da kika ganni na taho ne domi amsar magani da yin jinya,saboda kaucewa idon jama'a da maganganunsu yasa na baro yaho garin da babu wanda ya sanni,don nan din ya fiyemin rufin asiri''kuka sosai zahariyya takeyi nadama kam babu kalar wadda batayi ba game da bitewa son zuciya da tayi,yanzu gashi ta kaisu ta barosu,ganin haka ua sanya mami tayi aumarni a dauketa a shiga da ita don yi mata aikin,haka aka dauketa aka turata zuwa dakin
jira na kimanin awa guda sukayi wata nurse ta fito da yaron cikin zanin mamartashi saidai tuni rai yayi halinsa ya mutu sajamakon tun fari uwar bata samu kulawa mai kyau ba lokacin cikinsa da kuma wuyar da yasha lokacin haihuwa,ba qaramin haushi mami taji ba don bata iya shiru ba sai da tayi fada sosai,minti goma tsakani aka turo zahariyya iyama zuwa dakin hutu,da tambayar abinda ta haifa ra farka a bakinta mami ke gaya mata ya rasu,ajiyar zuciya ta saki
''gwara da Allah yasa ya mutu,haqiqa ya samu gata mai kyau da ya mutu din''mami ce ta tsawatar mata
''kada ki kuma fadin hak,kul''mirmushin yaqe tayi tace
''mami don bakisan dan waye ba,ta yaya aka sameshi ba,amma tunda kince haka bazan kuma fada ba,amma mami don Allah ku yafemin,ba shakka mun cika azzalumai,ba muyi muku sakayyar data dace ba,haqiqa samun mutum irinki mami sai an tona,mai saka sharri da alkhairi,mai saka mummuna da mai kyau,ke mutum ce mami,a yanzu nake kwadayin inama ace tun fari kece kika haifeni,na tabbatar da tuni yanzu ina rayuwa ingantacciya ba irin wadda nake kai ba yanzu''
''ya isa duka mun yafe miki,ko Allah muna masa laifi ya yafe mana ballanta na mu 'yan adam''
''na gode mami,ko yanzu na mutu nasan
''da ikon Allah zan samu wani sassaucin''
''ba na ce miki ki daina maganar mutuwa bane zahariyya''
''na daina mami''ta fada kana taja idanunta ta rufe ruf tana saukar da ajiyar zuciya
Maryam tasa abdallah ya dauka shi da security dinsa taje su tafi gida itakam qnan zata kwana kafin gobe ta sanar da dangin zahariyya din a samu wanda zai dinga kwana da ita,ba maryam ba har abdallah da yasan mamin farin sani mamaki take bashi,wata iriyar kubutacciyar zuciya Allah ya hadata da iya,basu ce komai ba suka juya suka tafi
************
kiran sallar asuba ya sa mami miqewa ta ajjiye wayarta dake hannunta wadda ta bude application na qur'ani tana karantawa cikin zuciyarta,kwana batayi bacci ba kusan sabonta ne saboda kowa yasan ma'aikatan lafiya da iya kwanan zaune
fara daura alwalarta kenan ta fara jiyo salatin zahariyya tana yi tana shaquwa,jade da ambaton sunan Allah,da sauri ta saki alwalar ta koma cikin dakin da gudu,shaquwa take sosai idanunta a qaqqafe suna kallon sama,da sauri,mamin ta fara bata duk wani taimako da ya kamata a matsayinta na likita,saidai duk yadda takai ga son ceton rayuwar zahariyyan wanda ya halicceta ya riga da ya wanzar mata da qaddararta,ta amsa kiran ubangijinta ta riga mu gidan gaskiya,duk dauriya irin ta mamin saida ta saki kuka,babi shakka mutuwa ishara ce izina ce hakanan abar tsori da fargaba ce ga duk wani abu ma rai,ba bil'adama kadai na hatta da sauran halittu dake numfashi a doron qasa
*************
Gidan kawunta qanin mahaifinta can suka sada gawar din su suka fi haqqi da ita,cikin qanqanin lokaci aka mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya,shikenan duniyar,zancan banza ce,idan kayi damara don ita ka kwance,don katsaham zata zo maka tace sai ka bar cikinta bata da buqatarka don wa'adinka ya cika na zama acikinta,kusan azahar mamin taga giftawar wata mace goye da yaro,tayi tsammanin daya dagq cikin dangin mahaifinau zahariyyan ne mutanen qauyensu yan gaisuwa,sai data sake ganin wulgawar matar ta saka ido sosai sai taga kamar zubaida,matar dake gefanta ta taba tana tambayarta
''waccan kamar zubaida ko?''da sauri matar ta amsa mata din cike da murna take,yau gata tana zaune daura da haj bintu
''eh,zubaidan hajiya nene ba, ita ce mana kema kin kasa shaidata ko ke da kuka zauna tare ma tun tana qaramarta,hmmm duniya ce ai budurwar wawa,wadda ta ishi kowa riga da wando,uwarsu ta gama bata su ta lalata su yanzu yau gashi yadda suka koma,dan ahege ne fa goye a bayanta,yanzu haka aikatau take wani guri tana ciyar da kanta,don babu wanda zai dauki jigilarta bayan lokacin da suke da ahi bani wanda suka morawa komai''ko kadan bayanan matar bai burge mami ba,jasalima haushi ta bata,cikin takaici tace da ita
''harshe yana iya kai mutum wuta nan da nan cikin qanqanin lokaci,anna bi yace idan kaga dan uwanka cikin wata musiba ka shiga aibata shi da yadashi,Allah yana iya yaye masa kai kuma ya jarrabceka da abinda ka aibata shi akai din,abinda aka umarcemu da cewa duk lokacin da muka ga wani da,Allah ya jarabta da wani abu ko cuta ce ko makamancinta shibe *ALHAMDULILLAHIL LAZI AAFAANI MIMMAB TALAKA BIHI,WAFADDALANI ALA KASIRIN MIMMAN KHALAQA TAFDILA*,daga haka mamin ta miqe ta bata guri
Bayan zubaidan tabi wadda ta gani riqe da robar abinci ta zagaya can baya ta kunce qarmashshan danta daga goyo ta zaunar da shi kan cinyarta ya soma bashi abincin cikin robar,don tausayi sai da qwalla ta zubo mata,ta qarasa kusa da ita tana kiran sunanta,sai kuwa tq zabura ta miqe zata gudu
''kada kije ko,ina zubaida''sai ta kira sunan mamin hawaye,na bin kuncinta,inda take ta qarasa tasa hannu ta amshi dan ta jata gefe guda
Tiryan tiryan ta debe abinda ya faru da ita bayan barinta gida,ashe gun mugu ta gudu wanda shine uban danta,ba dadeea ta ganshi ya sato,nene yazo ya hadasu,ashe abinda yasa ya nuna yana sonta,cikin jikinta yakeso ta haife ya dauke yaron ya saidawa qungiyar asiri,tun daga rqnar data fuskanci haka suka shiga tashin hankali ita da nene wadda ta dawo tamkar tababbiya,duk da haka wani lokacin idan abun ya lafa mata sai ka gantq ras kamar mai hankali,ruqon Allah suka dinga yi cikin ikomsa Allah ya kawo abokan gabarsu suka murqushesu shine su kuma sukayi amfani da wannan damar suka tsere,yanzu haka nene na gidan mahaukata ita kuma tana aikin wanke wanke fidan wani saida abinci da shi take dan taimakon kanta da nenen
kuka sosai mamin tayi kana ta amshi adress din gidan aikin nata tace zata nemeta,itakam ko wani abu ne ai zubaida bata masu komai ba face kanta data zalunta ta biyewa son zuciyarta
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Zaune suke gabanta tana saman kujeravtana rubuce rubucenta,ta sake dagiwa karo na biyu ya dubesu
''uhmmm,idan kun shirya yimin bayanin ina jinku''abdallah ne da maryam kusan awa guda an rasa mai bayani tsakaninsu,sai kallon kallon,gaba daya ta fahimci sun maidata kakarsu,akwai surukuta tsakaninta da maryam don haka ta dubi abdallah
''gayamin meke faruwa?''mutsu mutsu ua shiga yi kana cikin inda inda yace
''mami,kince ne dama idan mukaji da matsala mu miki magana wata uku da ya wuce,to maryam ce tace tana jin abu kamar dutse a mararta''sguru mamin tayi tana nazari,babu shakka zatonta ya fara zama gaskiya,ta dade tana yiwa maryam din kallon mai cikin,jin shiru babu wanda yayi maganar daga ita har shi ua sanya itama ta tsuke bakinta ta bisu da addu'a
kai tsaye dakin data ware cikin gidan ta sata ta shiga,ba tare da bata lokaci ba ta fara taba cikinta,kasa gasgata kanta tayi sai data saka na'urar scanning,hoton dan tayin jariri radam ya bayyana kan fuskar na'ura,tsura ido sukayi shida maryam din suna kallon talabijin din,tsantsar farinciki da murnar mami kasa boyuwa tayi har sai da murmushi ya qwace mata
''tabbas,gabunta da wautar dan fari bata barinsa,hakanan tabarar auta ma bata taba barinsa,Allah ya ahiryeku maryam da abdallah,ciki wata hudu amma daga ke harshi babu wanda ya fahimci hakan,wadan nan kam da aqauye kuke cewa zanyi ba mamaki,yarinya ta kusan cinye buhun kwaki amma bai isheku ku gane komai ba?''wani uban tsalle abdallah ya daka sai gashi gaban mamin saura kadan ya kada ita qarfin ba daya ba,ta dafe gadon da maryam ke kai tana fadin
''abdallah yi a hankaki mana''
''mami zan zama daddy fa kika ce,wayyo Allah na kana sina Allah''ya fada yana daga hannayenshi sama
''janye mijinki maryam kada ya targada min kafada tun kafin jikan yazo na rasa hannun daukarsa''mamin ta fada cikin tsokana,kunya ta kama maryam don ta sadda kanta qasa,tabbas cikin abinda yasa ta kasa gane cikin ko mutanen da take tare da su baya ga na fari ne tsahonta ya shanye cikin sai ya qara mata qiba kadan ta murje fatarta tayi kyau,har wani lokacin abdallah idan yana son tsokanarta zakaji yana ce mata
''diyana 'yar lukuta ta bawan Allah''sosai mamin ta zauna tana musu bayanin yadda zasu kula da cikin don ta fuskanci daga abdallan har maryam din jirgi daya ne ya kwasosu
_kuyi maneji da wannan_
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
▶6⃣9⃣
*Daga mu'az dan anas R.A yace:Manzan Allah S A W yace:((duk wanda yaci abinci sannan yace:ALHAMDU LILLAHIL LAZI AD'AMANI HAAZA WARAZAQA NIHI MIN GAIRI HAULIN MINNI WALA QUWWAH,an gafarta masa abinda ya gabata na daga zunubinsa*
*Manzan Allah S A W yace:((babu abinda yake maida qaddara sai addu'a*
*LITTAFIN NAN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA DUK WATA BUDURWA DA AURE YA MATA JINKIRI ,DA KUMA DUKKAN WANI MUTUM DAYA TSINCI KANSA KO YA TABA TSINTAR KAN NASA A HALIN SIHIRI,MU SANI CEWA SHI HAQURI WANI ABUNE DA FARKONSA MADA CINE AMMA QARAHENSA ZUMA NE,BABU WANDA YA TABA YIN HAQURI INGANTACCEN HAQURI DAGA QARSHE YA TASHI BABU RIBA,BABU SHI,SAIDAI BA HAQIQANIN HAQURIN KAYI BA*
_BAYAN SHEKARA GOMA SHA HUDU_
Abdallah ne a gaba riqe da hannun matashin yaron dan kimanin shekara goma sha hudu suna magana qasa qasa,shi da yaron dukkansu sanye suke da doguwar riga yar asalin saudiyya,kansu lullube da hirahi da kewayayyen abun nam mai siffar zero,a bayansu kuma mami ce riqe da hannun wasu kyawawan 'yammata guda biyu wadanda ba zasu wuce shekara biyar biyar ba,kallo daya zaka yiwa yaran ka bawa kanka amsa da cewa 'yan biyu ne suna tafe suna tsalle tsalle irin na yara,maryam na a gefansu riqe da wani yaron wanda shima irin shigarsu abdallah ce ajikinsa,dukkanau su kuma baqar doguwar riga ce ajikinsu kansu lullube da wadataccen mayafinta
Kana kallonsu ko ba'a fada maka ba kasan cike suke da farinciki,haka yake domin shekaran jiya aka fidda sakamakon gasar karatun qur'ani da akayi ta qasa baki daya wadda aka gabatar a qasar saudiyya,ABDUL_AHAD ABDALLAH ABDULKAREEM da ga MARYAM da ABDALLAH shi ya samu zuwa ta daya,abun ya girgiza qasashe da,dama ya kuma bada mamaki,yaro mai qarancin shekaru kamar wanan ya samu irin wanan baiwar ta haddace qur'ani kana ya zubar da duk sauran abokan takararsa da suka fishi shekaru ya daga tutar ta daya
Wannan abu ba qaramin daukaka ya sake ja musu ba,kai ba abdul_ahad kadai ba,hatta da maryam ta samu qarin soyayya da qauna daga bangaren mami harma da abdallahnta,kyaututtuka kuwa babu kalar wadda abdul_ahad bai samu ba,ko a yanzun ma sun fito ne somin amsa gayyatar da sarkin saudiyya ya musu don cin abincin dare tare da su
**********
Basu suka dawo,ba sai misalin qarfe goma na dare agogon saudiyya,a gajiye suka isa masaukinsu abdallah na sabe da yan biyu da sukayi bacci,abdul_ahad wanda shine babba kuma na riqe da hannun ABDUS SAMAD wanda keta faman gyangyadi,sai da suka isa qofan dakin mami abdul ahad suka ahige shida abdus samad kasancewar dukkansu tare da kakar tasu suke kwana,maryam ta bi bayanau abdallah shima ya bita,kan gado ya sauke yan biyun a hankali,husaina ce ta fara farkawa wadda suke kira da AMATULLAH,tuni ta riqe abdallah da suke kira da ABBU,sarai ya gane me take nufi,so take tace a gunsu zata kwana kamar jiya bayan yau ya riga da yaci burin cin amarci da mamansu
''ya akayi rigimammiya''ya tambaya
''abbu ni a gunka fa zan kwana''
''a'ah ki kwanta anan,baki gani AMATUL JABBAR anan zata kwana?''maqale kafada tayi
''nidai a gunka zan kwana abbu don Allah''duk yadda yaso lallabata ta qiya,maryam na jinau tana sauyawa abdus samad kaya zuwa na barci,dariyarta take a ciki don yasan amatullah ta gama karya masa budget a yau kam,tana lura tun rana da irin kallon da yake jifanta,har tex ya mata ya kama musu hotel tazo suje sharp sharp yanzun zasu dawo amma ta qiya,don duka wunin ranar suna tare da yaran har ma da mamin,anata ude gifts da abdul ahad ya samu
''ummi ki yiwa diyarki magana,tafa matsanta min''ya fada qasa qasa yadda abdul_ahad dake sanya socks a qafarshi yana shirin nacci da mami dake cikin toilet tana dauro alwala duka ba zasu jishi ba
baki ta tabe cikin tsokana tace
''meye nawa?,itaku,ina cewa dazu ka siya mata ice cream ka hanamu kace mamarka ce?''
kai ya dan sosa don kada ta gansu a rana su masu dariya ya sunkuya yana daukarta bisa kafadarsa yace
''haka ne fa,mama na tafi ta kowa ai''ya juya ya fita maryam na qyalqyala musu dariya,ganin yaaran na kallonta saboda dariya da suka ha tanayi da basu san dalilinta ba yasa ta daidaita natsuwarta,ta kammala shirya abdus samad ya haura gadon da abdul ahad ke kai,ta dubi abdul ahad
''idan ka kammala addu'anka ka karanta masa shima kafin ya sake komawa baccin''
''to ummi''
gadon mami ta koma ta sake gyara mata gami da shimfida mata abun sallah don ta riga ta saba bata kwanciya sai tayi sallah raka'a biyu,har ta koyawa maryam din ma,saida mamin ta fito sannan ta shiga itama ta daura alwalar
tana bisa abun sallan mami na zaune gefan gadon tana laranta azkar da bata samu damar yi ba,wayarta na hannun abdul ahad yana danne danne,bata fiye damuwa don ya dauki wayarta ba don ta san hakin yaron indai kaga wayar a hannunshi wani abu mai mihimmanci da zai qareshi yake dubawa,Allah ya zubawa yaron tsantsar basira,hankali da nutsuwa,uwa uba ya samu ingantacciyar tarbiyya ta buga misali,ba qaramar tsaiwa maryam tayi kan tarbiyyan 'ya'yanta ba musamman abdul_ahad wanda dama danka na faro kusan shine tubalin sauran 'yan uwansa,irin tarbiyyar daka nashi to sauran ma idan ka haifesu zasu taahi ne kan aninda suka ga na gaba da su nayi wato babban yayansu,saboda ko yaushe suna tare,suna ganin irin abubuwan da yakeyi suma zasuyi qoqarin yin koyi da shi,hakann idan gurbatacciyar tarbiyya ya samu,da sun fara girma zasu bi sahunsa
Ta shafa addu'o'inta kana ta miqe ta ninke abun sallar,mami ta dubeta
''ya kamata kam ki tafi haka ki kwanta maryamu,kullum ace sai kin tayamu hira zaki tafi daki ko kwanta,banda abunki ai bani,kadai ce a dakin ba balle kice kewa zata dameni,ga mai gida na ma baiyi bacci ba''
murmushi maryam din tayi cikin kunyarta din nan da har yau bata canza ba,har yau babu wani abu da ya ragu daga qaunar da mami ke mata sai ninkuwa ma da yayi
''kije ki,kwanta maryam kinji,Allah yayi miki albarka,haqiqa har *ABADAN* bazan daina alfahari da ke ba,kin cika uwa ta gari mai fidda kyakkyawar yabanya,fata na ubangiji ya cika rayuwarku da haske farinciki da kwanciyar hankali,kin haifa min jikoki maryam hudu ne amma inaji sunfi miliyan,sabida samun yara kamarsu wallahi ba don suna jikokina ba sai an tona,Allah ya miki albarka,Allah ya miki albarka''kanta na aqasa take amsawa da amin zuciyarta cike da farinciki da qaunar mami
Wayar tata dake hannun abdul ahad ta dauki tsuwwa wanda tun tana cikin yin sallah ta ji tanayi,abdul ahad ya dubi umminsa
''ummi,abba ke kira tun dazun''yana saukowa daga gadon ya miqa mata wayar,ta riga da ta horesu,sam basa daga mata kira sai sun kawo mata ko sun sanar mata,ta daga kana ta kanga wayar a kunnenta
''please dear ki taho haka don Allah,i nedd you''murmushi ya subuce mata,kunyar mami tasa ta kana magana sai kawai ta katse kiran,minti biyu tsakani saiga tex dinshi
''gaskiya fa ina alkunya da yawa,na baki minti biyar matuqar baki taho ba da kaina zanzo har,gaban mami na sungumeki,kin sani zan iya ko?''murmushi ta sake saki taci gaba da duba agogo
sai da ta minti biyar din sun cika daidai sanan ta miqe ta yiwa mami sallam,a bakin qofar dakinsu mamin taci karo da shi dauke da amatullah,dariya ta subuce mata
''gaskiya kun samu aikinyi,ta yadda kenan zata kwana cikin 'yan uwanta''
''me ruwanki da mu?,kedai ki kuka da kanki,yau sai kin biya dukka bashin da kika ci''kai ta girgiza tana murmushi ta wucesu shi kuma ya shiga dakin
Bandaki ta fada kai tsaye bata zauna ba,sai data yi wanka mai kyau kana tazo ta mulke jikinta da turaruka masu dadi wadanda ta siyosu dazu da rana da suka fita yawin miqe qafa,dukkansu na kamfanin alharamain ne masu dadi qamshi,daya daga cikin kayan baccin data siyo ta cira,doguwar riga ce har qasa mai hannun shimi mai azabar yauqi da santsi tana da dan duhun kala kadan ta sanyata,ta feshe kanta da turaren gashi kana ta rage hasken fitilar dakin ta haura gadon ta kwanta,jin shiru bai dawo,ba ya tabbatar mata yana can ana tataburza wata qila da amatullah,kiran da ya ahigo wayarta ne ya katse mata zancan zucin da take yi,lubabatu ce da hanzarinta ta daga don tana sa ran jin daddadan labari saboda sun baro nijeria hindatun nada tsohon cikin haihuwarta ta biyu ita da hisham dinta,ai kuwa abinda ta zata dinne ta sauka dazu qn samu baby girl da take ta sha'awar haifa,don haihuwar fari namiji ne ABDULKAREEM wanda yaci sunan mahaifin abdallah
''adda na haifawa abdul_ahad mata,din gaskiya tun yau na mata miji,ina son absul_ahad adda wallahi dama yaya abdallah zai barmin shi,amma na sani bazai iya ba don ya fimu qulafucinsa''dariya maryam ta saka tana cewa
''Allah ya tabbatar,zanso haka lubabatu,Allah ya raya mana baby''
''adda sunanki taci fa,nayi alqawari dama ina fatan Allah yasa ta dauko halayenki,maryam sunanta saiki zaba mata nickname''ba qaramin farinciki maryam taji ba take tace
''mu dinga kiranta AMEERA ai yayi ko?''
''yayi adda,Allah ya qara girma,kinga mama ce a gurina(maman maryam din)ga maijidda(kulu,da yake haka suka koma ce mata) ta takuramin sai na bata ta tuna kiki tsarabar da tace tana so,kuma wai abdus samad ya cika mata alqawarin da ya daukar mata''dariya ta saki kana tace
''kice mata sunfi kusa,don abdus samad yanzu,haka,ma ya jima da yin bacci amma gobe zan kira na hadasu'',ta karba suka gaisa kana ta hadata da mama ma suka gaisa sannan sukayi sallama
Bata kai ga ajjiyewa ba kiran shamsiyya (qanwarta yar inna hadiza)ya shigo,suna gama hira zara ta kira sai bintu kamar hadin baki,dukkansu taya ta murna suke kan zuwa ta daya da abdul_ahad yayi,taji dadi sosai kan yadda kullum Allah ke dada hada kansu suka fuskanci gaskiya suka zamo tsintsiya madaurinki daya,tana cikin addu'ar bacci ne jin shirun na abdallah yayi yawa kiran hindatu ya shigo,tana kaiwa kunnenta abdallah ya shigo dakin yana sakin hannun rigar baccinsa da ada ya nannade,dariya ya bata cikin zuciyarta tana cewa hala dambe akasha kafin amatallah ta yarda
''ke kam baki duba agogo?mufa anan qarfe sha biyu na dare''
''tun dazun nake kiranki naji busy wayar taki''
''eh wallahi muna ta waya da su azara''
''lubabatu ai ta haihu,shegiyar gari,dazu naje gidan na gama yi mata tsiya ai,can na samu su shamsiyyan ma....''maryam din na shirin tambayarta tsiyan me abdallah ya wafece wayar ya kara a kunnensa
''sai da safe,a barmin gimbiya ta ta huta hakanan''ya fada,dariya hindatun tayi tace
''ranka ya dade,girman kujerarka,ai kafi gaban haka ma,Allah ya bamu alkhairi''
''ameen,ki gaida min boss(haka yake kirab jabir idan yaso tsokanarsa) da duka yaran''daga haka ya katse wayar yana jifan maryam din da wani shu'umin kallo
Bayanta ya fada kana ya janyota ya rungumeta tsam a jikinsa dukkansu suna murmushi yace
''idan na barki da wannan hindatun yauma saidai na haqura''
murmushi ta saki a boye cikin son jan tsokana
''yanzun ma haqurin zakayi,tunda jibi zamu koma so nake nayi bacci sosai don gobe wuni nakeso nayi a harami ina da addu'o'i sosai''bai bi ta maganarta ba ya fara aike mata da saqonni sannan yace
''wacce buqata kike da shi haka,tunda kika sameni ai baki da sauran matsalar rat
yuwa''murmushi ta saki kaina ta juyo suka koma fuskantar juna numfasinsu na,haduwa guri guda,fuskanta qunshe da kyakkyawan murmushin daya bayyana fararen haqoranta,kasa daurewa abdallah yayi har sai da ya shafi fuskartata yana fadin
''maryam diyana''wani murmushin ta kuma yi ta kwantar da kanta cikin qirjinsa,don duk lokacin da ya mata irin haka din tssan ta taba zuciyarshi sosai,sai data saki ajiyar zuciya sannan tace
''ba shakka bawan Allah ka gama tare min komai,na tabbatar da cewa na gama samun aljannar duniya tunda Allah ya mallakamin miji kamar kai,ya bani baiwar 'ya'ya nagartattu,ya bani suruka irin mami,ya bani mahaifiya irin mama,nikam Allah ya gama min komai babu abinda ya rage gareni face inta miqa godiya ta agareshi tare da neman lahira ta kuma''kai ya jinjina yana sake jin qaunarta a ranshi,duk da ni'ima da daular da take ciki hakan bai hanata tsayawa,bautar Allah ba ka'in da na'in,hatta da abdus samad dan shekara goma sha biyu ta koya masa azumin tadawwu'i,su amatul jabbar ne kadai basa yi suma jira take sukai shekara goma goma,mace ta gari kam ya riga da ya gama mallakarta sai godiya ga madaukakin sarki
''dazun bayan fitata kai amatullah mukayi magana da abdur rahim,shikam yace mai binta mai sunan mamana yarinyar inna hadiza ta masa duk duniya so yake du Allah a bashi aurenta,adda ta taimakeshi kada ta hanashi''
''ok....abdur rahim abokin hadin bakinka ko?''dariya ya qyalqyale da ita itama ta tayashi,din duk lokacin da suka tuno da moments din a yanzu nishadi da dariya yake sasu
''kinsan kuwa sanda yana zuwa mini zance idan yazo din yadda kikasan na mutu sabida kishi,zirga zirgar da nake muku fa take hanashi sakewa maza maza yake tafiya,zaki ga yana yawan duba waya nike masa tex nace ya gaggauta tafiya hakanan fa,ke kuma kiyita jin haushi ke a lallai saurayinki abdur rahim baya dadewa yake tafiya,bakisan abdallah bane a rigar abdur rahim''
dariya ta saka ta kama dogon hancinsa tana ja
''bansan so yakan iya farawa da qi da fada ba sai a lokacin,sam bansan sonka ke yawo cikim jinina ba,a lokacim nayi zaton qinka ma nake ashe wani bala'e'en so ne ya dabaibayeni''wani dadi yakeji,har kullum yakanji sanyi na ratsa zuciyarsa idan maryam na fallasa masa sirrin zuciyarta bai gajiya da jin irin son da take masa,ya dan hade fuska kana yace
''amma fa har yau ina sha'awar in qara aure,mata biyu nakeson nayi''kicin kicin tayi ta motsa mata kishinsa da takeyi mai bala'in yawa,bai ankara ba qwalla ya gani na shirim zubowa,babu shiri ya sanya halshensa ya shanye abinsa tas kana yace yana mai girgiza kafadarta yana murmushi
''haba uwar 'ya'yana,aini tun daga kanki uwaye mata basu sake haifar mace ba,har yau ke kadai nakewa kallon mace a duniya''murmushi ya subuce mata ta boye fuskarta tana cewa
''nikam ban hanaka qara aure ba idan Allah ya riga da ya rubuta cewa qadararka ne,amma ka sani ina tsananin kishinka haka yake cikin jini da halitta ta bazan iya kankarewa ba''
''please mu bar ma wannan maganar kinji dear na''yayi magabar yana sake boyeta cikin faffadan qirjinsa tare da nuna mata zallar soyayya
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Sai kusan sha daya suka fito falon masaukin nasu,tun takwaa suke jiyo,hayaniyar yaran amma abdallah ya duqunquneta ya hanata fitowa,ko breakfast ya hanata fitowa ta hada musu yace kowa yau yaci haquri sai ya gama hutawarshi shima,haka nan ya biye masa suka sha baccinsu kafin su tashi suyi wanka su fito
Duk sun hautsine falon da kayan breakfast abdul ahad nata kai kawon gyarawa,haka yaron yake da qwazo tamkar mace ya iya aiki bakin gwargwado,don sau tari shike kamawa maryam wani abun idan aiki ya hade mata,misali idan zasu tafi makaranta da safe,ya iya hadawa kowa abincin tafiya makaranta cikin lunch boxs dinsa wanda bai wuce chips waina da indomie,hakanan shi zai hadawa kowa ruwan wankansa yaje yayi,wankan ne kawai bata barinsa ya yiwa su amatallah(hakan kuma nada kyau sabida koyawa yara kunya da sanin mutuncin tsiraici tunda akwai bambancin jinsi tsakaninsu shi namiji ne su kuma mata ne),abdus samad ke riqe da gorar ruwa ya hana amatul jabbar sha,sai binsa take suna kewaye falon,da sauri abdul ahad ya cafkoshi ya riqeshi kana ya tsugunna gabansa
''bata tasha abdys samad,bakasan cewa babu kyau ba?,akwai matar data tsare mage ta hanata ruwa da abinci har sai data mutu ta sanadin haka Allah ya sanyata a wuta,hakanan akwai karuwar da ta shayar da kare ruwa ta sanadin haka Allah ya gafarta mata ya sanyata a aljanna,ka sowa dan uwanka abinda kake sowa kanka kaji,ka hana kanka abu ka bawa dan uwanka matuqar ya fika buqata sai Allah ya saka a aljanna''jikin abdus samad yayi sanyi ya miqawa amatul,jabbar ruwan yana cewa kiyi haquri
Ba qaramin burge abdallah da maryam yaron yayi ba,abdallah ya dubi maryam
''kin gani?,rainonki,ne fa uwa ta gari abar alfaharin miji da 'ya'yanta''sai ta dora kanta bisa kafadarsa tana murmushi kana tace''harda gudunmawar jajirtaccen uba kamar kai''amatul jabbar ce ta fara ganosu da gudu ta qaraso tana abdallah yasa hannu ya dagata sama yana zagayawa da ita,abdul ahad da abdus samad suma suka qaraso suka kai har qasa suna gaidasu kamar yadda suka saba,hannu suka dira saman kansu suna amsawa kamar yadda suka saba sannan suka sumbacesu suka sa musu albarka(manzan Allah s a w yace duk wanda bai sumbatar 'ya'yansa babu mamaki Allah ya cire rahama tausayi da jin qai daga zuciyarsa,sumbatar 'ya'yanmu sunna ce mai kyau suna ce ta annabinmu bata yahudawa ba,musamman yara qana na tunda a wannin zamani da al'ummarmu bazaiyu ka sumbaci danka babba ba,fitina tayi yawa cikinmu,saidai fatan samun sauqi)
abdul ahad ke gaya musu mami da amatul lah sun tafi harami,tace sa biyosu a baya,karyawa suma kawai sukayi suka tasa yaran a gaba sai harami don babu nisa can da yawa tsakaninsu hakan yasa a qafa suka tafi
🍂🍃🍂🍃🍂🍃🍂
kwanansu biyu hudu da dawowa nijeria suna fama da 'yan taya murna,hakana suka gama yanke shawarar bayan abdul ahad din ya kammala secondry dinshi zasu barshi ya tafi madina ya qarasa karatunsa a can don hukumar qasar ta dauki nauyin karatunsa daga matakin degree har illa masha Allahu
kwana biyar suka gama watstsake gajiyarsu wanda yazo daidai da lokutan da suke warewa don ziyarar yan uwa da dangi,mami kadai aka bari a tamfatsetsen gidan da abdallah ya narka gari guda ya dauko maminsa ya dawo da ita cikinsu wancan ya barwa mero wadda tuni ta koma maryam dinta ko muce maman sayyid wadda a yanzu yaranta uku,bintu ce ta fari takwarar mami suna kiranta walida,sai hamza wato sayyid sanann zainab,mero ta zama babbar mace sosai itama,don mami bata barta da dubun jahilci ba sai data zuba kudade sosai meron tayi karatu ta koma maryam kabiru hamza sak ba mero ba
wasu lokutan da mamin ake tafiyar musamman idan bangaren yan uwan abdallah ne,wannan karon shi ya hana yace ta zauna ta huta hakanan yaushe duka duka suka dawo daga tafiya shikam ba za'a qarasa masa uwa ba,tuni dama ya sanya mamin ta ajjiue duk wani aiki,zaune take kawai aikinta dai research ne kawai kan sabbin cituttuka,tana daga zaune take,bada tata gudunmawar ta hanyar wallafa littattafai da suka shafi bangaren likitanci
kamar kowanne lokaci wannan karon ma sun zafa dangi soasai cikin yan kwanaki inda suka yada zango a gudan lubabatu don ayi bikin sunan takwarar maryam da su,suna kam yayi armashi matuqa,maryam tayi rawar gani sosai wanda komai hassadarka sai ka yaba mata,ta zama uwa yaya kuma matar aboki duka ita kadai,hakanan ta nunawa takwararta gata sabida tulin kayan barka da hidima data dinga yi,da daddare abdallah yazo ya kwashe iyalin nasa sai gida don yace ya gaji da zaman kadaici shi da mami,gidan ya musu shiru babu dadi ko kadan,a sashen mamin yaran suka kwana abinsu dom suma sunyi kewar kakarsu kamar yadda tayi kewarsu,hakan ya bawa abdallah da maryam dinshi damar cin karensu babu babbaka don kullum ganin junansu suke tamkar sabon ango da sabuwar amaryarshi
***********
Tako ina rayuwa ta musu kyau,dukkan wani abun qi Allah ya kawar musu da shi,hakanan ya shiryar musu da zuriyyarsu kan kyakkyawar turba,a yanzu maryam ta zama mudubin gidan baki daya,bama gidan ba hatta family dinsu kowa cikin inuwarta yake,tuni ta aurar da jamila da kulu yanzu a qannen nata baifi mutum hudu ya rage mata ba,kullum cikin sa albarkar iyaye take musamman babansu malam amadu da a yanzu ya samu rufin asiri fiye da zato,girman nan nata wanda ada aka take mata shi a yanzu ya dawo mata,haqiqa duk abinda yayi farko yana da qarshe banda ikon Allah,hatta da isyaku sai da ta maidashi kan kyakkyawar turba darajar addu'a da neman taimakon Allah da sanya Allah ja gaba cikin dukkan lamuranta,don a yanzu haka isyaku da ya koma ishaq ahmad na jami'ar bayero ta kano yana hada degree dinshi fannin kasuwanci wanda maryam din ke saka ran da zarar ya kammala zata dorashi kan wasu sabgogi da shima zai tsaya da qafafunshi,inna wuro ko da tsoho alhaji sunqi fafur zaman maraya don haka abdallah yasa akaje aka rushe gidansu aka tamfatsa musu gini kana aka cika gidan da kayan alatu na more rayuwa,ya ajjiyewa taoho alhaji motocin hawa har biyu baya ga kayan abinci da yake ajjiye muau duk wata da kudin kaahewa,wasu ma kayan saidai su tadda wasu su fitar da su su bayar,don yace bashi da abunda zai saka musu da shi,dukkan gonakin dake bakin rafin malam na dogo ya siyesu ya musu gini na zamani don yace bazai taba mantawa da qauyen ba hakanan bazai iya mantawa da rafin ba a tarihin rayuwarshi,lokaci lokaci idan suka samu wani hutun sukan taho qauyen cikin gidan suyi hutunsu,yaran kansu na son qauyen,wani lokaci idan sunzo abdallah kan tarasu yana basu labarin wasu abubuwa da suka faru tsakaninsa da mamansu a gurin su yita dariya suna tsokanar maryam,tun tana jin kunya har ta saba saidai ayita dariyar tare da ita,musamman idan ya tabo batun yadda tayita kishin meron take kuka aboye da yake sunsa meron momi suke kiranta a yanzu ko mama sayyid wani lokacin ma gurinta suke weekend dinsu suna jin dadin zuwa gidan suyita wasa da su hamza da zainaba
Yanayin zamansu da abdallah kawai koda bai furta mata ba ya tabbatar mata da cewa *ABADAN* da ita da shi babu rabuwa,wata zazzafar qauna mai tsayawa arai yake gwada mata kamar yau ya fara saninta,ashe samun mijin na garin shine babbar dacewa sa'a gami da farinjinin baki daya bawai gaggawar yin auren ba,tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne,hakanan wani jinkirin alkhairi ne
_TAMMAT BIHAMDILLAH_
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
_ku saurareni cikin DAURAYAR LITTAFIN ABADAN_
_tare da ni_
_safiya huguma_
_DA KUMA_
_SHARHIN LITTAFIN ABDAN_
_DAGA_
_QUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION_
*SUBHANAKALLAHUMMA WA BI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA*🙏🏽🙏🏽🙏🏽